Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Sunday, 19 July 2015

WACE CE*****ITA? 50

adsense here computerimages1.jpg

.: WACE CE ITA..?? 50
Na muhammad Abba Gana
Suna zaune gindin bishiya sun fito break aka
fara kora ko ajikinsu tadinsu suke yi suna baiwa
iffaat shawara kada ta yarda ta nuna tanason
farhaan harma yanda suke gida daya da wacce
zai aura, daga sama suka ji bulala akansu
Malam tunde ne zibraheem ta tashi ta riqe
bulalarshi, haba sir miyasa kullum sai ka riqa
dukanmu Dan muna kunyar Kane kawai muka
sharewa but gaskiya ya isa haka.!
Ta fuske, ki sakarmin bulala Mara kunya, sai
nayi maganinku a skull dinnan, duk da English
suke zancen nan.
Da hausa zumar tace saidai muyi maganin juna
bayajin hausa so baiji mi sukace ba, yadai
qyalesu ya wuce gaba abinsa, iffaat tace
malamin nan Dan rainin wayo ne, suka kama
hanya ko wacce ta kama hanyar clss dinsu da
yake duk yara sun shiga clss sai su gagararru.
Koda iffaat taje clss malami ya shiga kuma
Malam jocob ne baya wasa ko kadan,economic
master, ta fuske yace from ware? Tace daga
gidanku da hausa ta fada duk clss suka saka
dariya, Habawa yaji haushi ya gane zagin sa
tayi ya fara zuba mata bulala taji zafi tuni tayi
cikin sa tana duka ta kamashi da kokowa clss
ya dau ihu ana buga table, saida sukaci uban
juna kawai ta saki jiki ta fadi wai ita mai aljannu
so aljanun sun tashi, dama su ZZ sun gaya mata
cewa tayi iskancinta idan ta qare ta fadi kawai
ita batasan tayiba,
Kaji iskanci...
Haka dai akasha oga jocob a banxa gashi ta
wawwaskamai mari ta karyamai glass..
Tofa iffaat hatsabibanci ya dawo.
Akaje gun principal tace ita sam batasan tayiba
sharri ake mata, haka a ka rufe case akasha oga
jecon a banxa.
Wata rana suna zaune suna tadinsu kowa ya tafi
class saisu kawai saiga principal ta biyo hanyar
duk yara suna clss amma su suna nan zaune
kamin ta qaraso iffatu tuni ta haye bishiya,
principal taga hawanta amma bata San
kowayeba, iffaat kuwa tayi tsanda a hankali ta
hau rufin classes din kamar mage taje qarshen
rufin ta diro qasa, koda taje class ta tarar
malimi ya shiga yana note ta lallaba ta shiga ba
tare da ya gantaba tayi sauri ta dauko note book
ta fara rubutu.
Tana fara rubutu saiga principal tare da ZZ
akaxo nemanta, malamin mu yace lallai koda ya
shigo ina clss din, students dinda suka ganni
sukace yanxu Na shigo malamin yaji haushi kuna
nufin kunfini ganine ko qarya nakeyi? ya za'ayi
mutum ya shigo clss banganshiba.....MUHADU A LITTAFI NA 3 by Abba~Gana adsense 2 here
Share:

1 comment:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *