Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, 20 July 2015

WACE CE*******ITA? 63

adsense here computerimages1.jpg

WACE CE ITA..??

63

na ABBA-GANA
Tun daga ranar ta kamawa su mama mutunci ta
daina musu magana tadaina chin abinci ba
ruwanta dasu ita dole fushi, anyi sati biyu da
maganar sai ranar taji su yy da mama suna
maganar, ana maganar daurin aure kuuut saidai
wata ba itaba, ta miqe tsaye ta riqe kunkumi ta
fara shawara da zuciyarta yanxu ita iffaat har
sun isa su mata auren dole? Waima...! Idan ta
saka musu ido zasu aurar da itane, su Basu
damu da damuwartaba, abinda ya fado mata
kawai ta gudu, kai guduwa ba jarumta bace, duk
macen da za'ayiwa auren dole ta gudu ba
jaruma bace,so bataso ta gudu a ganinta ba
jaruma bace duk wani tunani sai taga bai dace
da itaba, nidai Abba gana zaune nayi ina kallonta ina
jiran muga abinda zata aikata, amma ga dukkan
alamu ba wani Abu da ya rage gwagwalwarta
bata aiki, sai fashewa tayi da kuka..
Yanda ta tsani halin Yy farhaan ko sonsa zai
kasheta bazata aureshiba, tanada mahaukacin
kishi
Tayita tuna yan matan farhaan din da yanda
yake musu ta runtse ido da qarfi ta daki madubi
tace Nooooooooooo, ta na kuka tana dukan
madubin duk ya yayyanke mata hannu, ashe su
mama sun jiyo mama ko a jikinta, Yy amin ne
yaxo gunta da sauri ya riqe hannunta duk ya
yayyanke, ya yiqeta ya kalleta yaga yanda ta
rame tana juyowa ta fada jikinsa tana kuka, tana
cewa Yaya ka taimakeni wallahi banason sa Yy
Ku aura min wani not Yy farhaan, yace to
shikenan kiyi shiru zamuyi magana da mama,
dagyar ya samu tayi shiru ya dauko first aid
yadan gyara mata hannun ta ta ta yayyanke, ya
jata da hira har tadan saki jiki, qarshe yace tazo
su fita yawoooooo...
muhd-Abba~Gana
www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *