Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, 8 December 2015

KAUNA CE SILA***2****1-2-3 & 4

adsense here kauna-ce-sila.jpg

[5:28PM, 12/6/2015] Bana: KAUNA CE SILA2**1

MUHD-ABBA~GANA
BAI ban amsa ba nima ban saka ran ganin ba da daddare marwan ya kirani ina fara masa korafi yace wallahi baya so ne mustafa yaji zancen shine hikimarsa ta karo radio ai ya fada min nace uhum kawai nan ya dinga bani labari abin da ya faru a can gidan wai bayan sun fito shi yayan ya kalli wani sabon gida yace nan za a kawo mamma ko sai salisu yace a'a sabon gidan da kake ginawa dai sai yace a'a ai ni kanwatace nan dai marwan ya dinga bani labarin sai na dinga jin haushi wato shi neman kai yake dani ina ma zan daina jin yaya a raina da naji dadi ko zuciyata ta daina fama da sonshi mai wahalarwa washegari ranar ma wata wakar biki a gurin su yaya ban gama da wuri ba ina ciki ina sallar magariba sai naji ya shigo ina zaune ina addu'a naji yana cewa wannan mama ce tayi ko aka ce masa E ina fitowa muka hada ido yayi kyau wata shadda ce a jikinshi mai kalar sararin samaniya dinki yayi mai kyau gaba naya fadi nayi kokarin dakewa nace ina wuni yace lafiya na dan zauna nesa dashi ya kalleni ya ce idan kikayi waka sai naji dadi amma idan ni kika yiwa ba kya min yanda ya kamata nayi shiru yace to me yasa tawa bata dadi nace wallahi ban sani ba ya kuma cewa shi ne ranar nan kika cewa salisu wai nina kaiki gidansu koh? na zaro ido nace kai haka yace wallahi karya yake sai naga ya bata rai yace saurayin naki ne yake karya nace to ai ni nasan ban taba fada masa haka ba ya kalli mustafa yace Dan Allah ba haka yace mana ba?MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[5:37PM, 12/6/2015] Bana: KAUNA CE SILA 2**2
MUHD-ABBA~GANA
YACE haka yace nace wallahi ba a yi haka ba watarana da daddare na kira warwan bamu kai gama gaisawa ba kawai naji muryan yaya ashe karbar wayar yayi naji yace wai meye dalilinki na kiran marwan nace masa babu komai kasan yana printing to sample zai nuna min na project din mu dana ji yayi shuru sai kuma nace da ya dinga min hirarka dariyarsa naji a kunnena sannan yace kuma shi neni baza ki kirani ba sai shi ni dai ban samu damar cewa komai ba har ya kashe wayar muna gamawa na rubuta wa marwan text kamar haka:CAN'T YOU TELL HIM AM HIS SISTER,I NEED HIS CARES AND ATTENTION ban san me suka tattauna ba bayan sun ga text dina can sai naga shigowar text da wayar yaya ME KIKE SO NAYI MIKI A DUNIYA WANDA ZAI SAKI FARIN CIKI? wani irin dadi ne ya rufe ni hade da faduwar gaba a zuciya ta nace to nime ma nakeso yayi min kawai sai naga ina rubuta masa: INA SO KA SANI INA KAUNARKA NE DAN ALLAH KUMA BA DAN KOMAI BA BAYAN NA TURA MASA BA A FI MINTI HUDU ZUWA BIYAR YA RUBUTO REPLY KAMAR HAKA: BABU DAMUWA haka dai rayuwa ta taci gaba da tafiya makaranta ma yanxu mun yi hutu wanda idan muka koma ajin karshe zamu shiga a harkar waka kuma Alhamdullilah dan na samu cigaba ba kadan ba dan yanzu duk wani mawaki mai ji da kanshi a harkar waka nayi aiki da shi ko dai wakar film ko kuma ta biki ko siyasa haka kudi ma ina samun daidai gwargwado wannan dalilin ne yasa ko iyaye na sauke musu nauyi kaina da yawa kamar kayan sawa kayan kwalliya da dai kananan bakatunmu na mata,a bangaren maza ina ta samun masoya amma bana iya daidaitawa dasu dan wasu da bukatunsu na banza suke zuwa wasu kuma su nuna maka kudi.MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[8:38PM, 12/6/2015] Bana: KAUNA CE SILA 2***3MUHD-ABBA~GANA

ALLAH ya tsare ni dan bana sha'awar kudin su har ina yiwa kaina kirari da cewa Allah ya bani sana'a mai bani rufin asiri yin hakan ai butulcewa ni'imarsa ne hakan ce ta saka bana zance idan na dawo kullum ina gida bana sake na fita sai gobe na kara zama yar gayu kuma mace mai aji bana iya saka kaya sai nayi too march wani abin birgewa bana taba saka karamin mayafi kusan duk jumm'a sai na saka sabon kaya a yanzu daka ganni zaka fahimci mace mai nutsuwa ga kwarjini muna girmama juna a tsakanunmu dan ko sauran mawakan mata ma yanzu duk akwai fahimtar juna a tsakaninmu dan ko sauran mawakan matan ma yanzu duk akwai fahimtar juna a tsakaninmu a wannan lokaci bikin maryam ya tashi akayi bikin ta lafiya ta auri wani saurayinta yusuf muka mika ta gidan ta a sultan road nayi mata wakar biki mai dadi dauke da nasiha mai ratsa jikin amarya,wata rana da misalin hudu saura na yamma na sauka kasanmu inda muke yin alwala sai nayi wayata nakara ina dubawa naga yaya ne lokacin dana daga sai naji yace marwan ya dameni wai na daina miki abin da nake miki to wai ke sona kike yi? kawai sai na fusata kamar fada nace to shi marwan din cewa yayi na aiko shi ya fada maka ina sonka? yace a'a amsa kawai nake so daga bakinki eh ko a'a sai na dan yi shiru can nace masa ni dai nasan ina maka kauna wadda ko mijin dana aura ba zai taba samun irinta ba sai nayi ya katseni shi kenan je kiyi sallah ya kashe wayar sai kawai na kasa yin alwala nayi shuru kuma wai sai na fara rabuta masa text ba kuma abinda na rage irin abinda na fada masa ta waya haka nace din bai yi reply ba nima na share zancen wajen biyar da rabi ina shirin tafiya sai ko kiran marwan sai naji yana min fada,

MUHD-ABBA~GANA
www.abbagana.pun.bz
[11:31AM, 12/8/2015] Bana: KAUNA CE SILA 2**4MUHD-ABBA~GANAHABA mamaa ga dama kin samu kina wasa da ita a gabana ya kira ki yanzu ke baki san irin san da kike masa ba meye dan kince eh bayan shima kin san yana sonki nace haba warwan yanzu ya kamata ni nace masa ina sonshi bayan shi ba sona yake yi ba ya katse ni waya fada miki baya sonki yan matan da suke son yayanki wallahi kina cikin top fives da yake ji da su nace shi kenan na gode jikina a sanyaye na fara tunanin abin yi har naje gida ba wani kizari a tare da ni a karshe dai na yanke shawarar yi masa text kawai bayan anyi sallar isha'i nayi masa text kamar haka: MAY I SAY I LOBE YOU.GUD NIT.har nayi bacci bai yi min reply ba ban kuma damu na gani ba bayan kamar kwana biyu da tura wannan sakon ranar tun tara na kwanta dan tun bayan magariba ake ta shekar auwa kuma a bani a dama na kashe wayata tuni can wajen karfe goma na farka saboda wata iska mai karfi da ta taso dama ni ba abin da nake tsoro irin iska a lokacib damuna ina bude idona na kunna wayata tana gama buduwa kawai naji shigowar sako wani abin mamaki yayane kawai sai na bude ido sosai don ganin me ya rubuta min RESEND THE TEXT YOU SEND TO ME LAST,I HAVE DELETED IT PLS a firgece na tashi na zauna na dinga maimaitawa ina kara duba sunan wayyo dadi haka nake cewa a take na duba wayata dama text din na nan na kara tura masa sai ya kara turo min haka: WHICH KNOW OF IT.gaskiya ban gane me yake nufi ba sai nace masa ban gane ba ya karanta amma bai ce komai ba nayi ta jira naji shuru sai na kara rubutw masa wani kamar haka: THE DAY IS BRIGHT AND THE NYT IS SO COOL AM SO HAPI YOU MAKE ME HAPI .TNXS GUD NIT.
MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

2 comments:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *