Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, 5 December 2015

KAUNA CE SILA***51__55

adsense here kauna-ce-sila.jpg

[12/1, 8:55 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 51
MUHD-ABBA~GANA
Sai tace ya kuma ce min yaji wata wakar da kuka yi tare da ahmad din kuma soyayya take nunawa nace ni ban sani ba idan haka ya dauka kyaleshi kawai tace min ai ni ce masa nayi ahmad ba saurayin mamaa bane dan bata taba fadamin haka bana dan sanshi a matsayin yayanta sannan karba mata waya ba zai hana mu'amalarsu ba idan tana so dan da ni da ita duk mutumin da muke bashi muhimmanci to number sa ta na haddace a kanmu saboda haka kayi kakuri ka bar maganar ta wuce don Allah nace mata ko shi yasa ya baki wayar ne? tace a'a dama yace yau yake da niyyar baki abarki har muka bar makaranta zancan abin muke a inda idan na tuno raina yake baci dana je gurin aiki ma ban bi ta kansa ba na shiga yin abin da yake gabana har lokacin tashi yayi na tafi gida yanzu kuma warwan ne ya tsarkafe gurin mu kusan kullum sai yazo mun yi ta hira wadda kusan duka hirar ya ahmad ce ni kuma ina jin dadin haka dan ko bai zo ba sai na kira shi a hira da muke da marwan ina jin abubuwan da dama a kan ya ahmad wani abin mamaki jita jita na fara ji wai ya ahmad zai kara aure abin ya bani mamaki ni kuma na kasa tambayar shi kuma ban tambayi marwan ba a zuciya ta kuwa cewa nake haba shi kuwa meye haka ko shekara bai yi da yin auren ba wata rana ina tsaye sai ga marwan bayan mun gaisa mun dan taba hira sai yace ga sabon layin yayanki sai na karba ina dubawa na haddace number amma sai nace masa to me zan da shi yace wai kiyi saving a wayarki nace a'a ai ni bana haka kawai bashi ya bani ba sai na hau ajiyewa duk randa ya bani na karba tunda dai ai ba daina amfani yayi da wanda nake da shi ba.MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
[12/1, 9:10 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 52
MUHD-ABBA~GANA
Yace shi kenan to wata rana na zo studio sai na shiga kusa da gurin muna saita caji naje naci gaba da harkokin gabana wajen uku da yan mintuna naxo duba wayata sai na ga missed calls har biyu dana duba layin da kyau sai naga kamar layin da marwan yace min yaya na ya sake ne gashi waya ta ba kudi sai na ajiye wayar na sauka kasa dan nemo kati ina sauka na siyo na dawo sai naga ya kirani da layin shi nada shima har ya zama miss call ganin haka ina saka katin sai na fara neman layin nashi wanda na sani din yana dagawa sai yace ke bakya daga layin da baki sani ba ko? nace a'a caji take yi bana kusa da wayar ne yace dama ina sonki zo ki yi min aiki ne kuma yanxu haka na fito zanje gida na dawo sai dai an jima zan fito yaushe zaki tafi gida? nace kamar biyar yace to idan zaki tafi ki kirani idan ban dawo ba nace masa to har biyar ta dan gota banji kiranshi ba kawai sai na fara neman layinshi yana dagawa yace zaki tafine nace eh sai yace to kawai je ki gurin gani nan zuwa nace to kawai kuma sai na kara ganin ya kirani ina sakawa a kunne naji muryar mace gabana yayi wata muguwar faduwa rtun kafin tace komai sai naji tace min mamaa ke wace yare ce? sai kawai naji raina ya baci nace ban gane ba tace ina nufin bahaushiya ko bafulatana,koh bayerabiya ban san lokacin da baki na ya furta mata cewa bamagujiya ce ni kawai sai tace yi hakuri ba wani abu nake nufi ba sai naji ya karbi wayar yace kin san wace?MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
[12/3, 9:50 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 53

MUHD-ABBA~GANA
Nace a'a yace matata ce nace au ban sani ba aii sai ya kara bata wayar nace kiyi hakuri ai ban san ke bace tace aui baga kin dau zafine nace a'a ba haka bane nan dai muka kara gaisawa bayan mun gama wayar naji raina ya baci to meye nayi min irin wannan tambayar kawai dai na share a inda yake mu hadu a nan yazo ya same ni bayan ya zauna har ya fara aiki sai ya kalleni yace dazu kin dauka wace nace na zata wata ce yace shi yasa zaki fadi bakar magana? nayi masa shiru yace to matata ce nace en na zata ta biyun ce ai yace to matata ce ce min tayi wai ta taba jin hirarki a radio ne nace masa to aini ko a radio ban taba zancan yare ba ai shuru nima kawai nayi shuru muka fara aikin daya kawo ni
wani abunda na fuskanta shine duk lokacin daya ce min nazo nayi aiki cikin nishadi nake jina gashi dai ba wani aiki bane yawanci wakokin biki ne amma dadi nake ji matsala daya na fara fuskanta bana iya yi masa aiki me kyau sai dai idan baya gurin ko kuma ya sauka wani yayi recording dina a yanzu kuma marwan ne ya takuramin duk lokacin da muke zaune sai ya yi ta min maganar cewa shifa ya sani ina ta yaudarar kaina ne amma ba wani namiji da zuciyata take so sai ya ahmad sai nace masa ai ni yaya nane sai yayi dariya yace wallahi mamaa ki nutsu ki bi abin da zuciyarki take so ko kya samu kwanciyar hankali sai kawai nayi dariya na kau da kaina wata rana yafara min nasiha yace ina ji miki tsoron rayuwa da idan baki samu ahmad ba rayuwarki ba zata yi dadi ba ko wa kika aura baza ki daina jin shi a ranki ba"by muhd abba gana{sharifin-zamani}MUHD-ABBA~GANAwww.abbagana.pun.bz
[12/3, 10:00 PM] Ábbä~Gåñā: KAUNA CE SILA 54
MUHD-ABBA~GANAHar ya fara ba ni misali da wani mutum da sun so juna basu yi aure ba har sai ada ko wanne su yayi aure har da manyan yaya sai da mijin nata ys mutu ta nemo tsohon saurayin nata suka yi aure da ya gama nace masa to ai shi ba sona yake yi ba yace waye yw fada miki baya sonki sai kawai nayi murmushi to a ko da yaushe idan ka ganmu da marwan irin hirar kenan a in da mafiya yawan lokuta nake nuna masa nifa ba son soyyaya nake masa ba inajin ya ahmad a cikin jikina saboda haka yayanane kawai dai yana jina yana kuma kallona wata rana munje gurin wani biki mu hadu ne dukanmu mawaka ne kuma kewaye amma kowa gurin da take zama daban asma'u tana zaune ne gurin su ya ahmad sai sadiya ita kuma a gaba da gurin mu take kadan sai zainab ita kuwa da ma gurin mu daya muna hanyar komawa gidan mu kamar ance karbi wayar sadiya sai kawai nace muga ta miko min ni kuma kawai sai na tafi gurin kira wai naga wa ta kira ba tare da tunanin komai a raina ba ina dubawa naga number salisu abin ya daure min kai nan da nan na shiga call history dan naga sau nawa suka yi waya ina farawa ta fizge wayar ko tunawa tayi ko kuma jikinta ne ya bata bincike nake mata oho nan da nan raina ya baci na taba asma'u nace dama salisu soyayya suke yi da sadiya sai tace min dama wallahi ina da niyar na fada miki nafi so sai bayan an gama bikin nan ki bari mu sauka dan Allah karki bari masu gane nace mata shikenan da muka sauka sai nace asma'u ina son ganinki tace to sai ta taso ta bar sadiya da zainab suna hira nace asma'u naga fa wajen sau nawa ta kirashi mintina daban daban tace ki nutsu kiji ni kin san dai halin sadiya da kwace samari mutane to gaskiya ba zan ce miki ga yanda suka hadu ba to shekaranjiya muna zaune a studio sai sadiya tace min taje wajen ku zata siyo CD a lokacin ma na san kun tafi dan magariba ta yi,


MUHD-ABBA~GANA


www.abbagana.pun.bzKAUNA CE SILA 55MUHD-ABBA~GANA
INA zaune sai ga ibrahim na gurin mu ya shigo yace min ga saurayin kawarki can da dayar kawarki taku suna zaune yana fada min haka sai na mikei ina zuwa naga sadiya da salisu a tsaye suna ganina suka fara kame kame nace musu wallahi sai na fadawa kawata sai duk suka sa dariya ai ba komai ta sani to kinji kuma da gaske nake ina sone sai mun hadu na fada miki to na san idan na fada miki ba zaki iya yin komai gurin bikin nan ba nace mata asma'u kin san me? tace a'a nace in Allah ya yarda yau bani ba salisu na tsani namijin da zai iya soyayya da kawata wataran nasan zai iya neman kawata tace karki yanke wanan hukunci nace mata Allah na gama mun tashi sai ga sadiya duk ta hana kanta sukuni tace min tafiya zakiyi nace mata eh tace tsaya kiji na san abin da kike tunani salisu ba wani abu ne ya hadamu ba yace min dai yana sona da nace masa ai nasan yana sonki sai ya ce ai ke dabance a ransa kawai na kyale ki dashi nace mata sadiya ai ba wani abu nace ba kawai dai ki bar zancen nan kawai tun ina hanya na yanke shawarar abin da zanyi ina zuwa gida na kira shi yana dagawa nace masa ashe sadiya budurwarka ce to Allah ya barku tare ni dai daga yau bani ba kai in Allah ya yarda ba zan iya irin rayuwar nan ba ba zan ce ga abin da ya hana salisu cewa komai ba dan bai yi koakarin kare kanshi ba bai kuma nuna min ya amincewa hukunci na ba ban damu ba ni dai na yanke hukunci kuma ina ganin shi ne daidai duk da banji dadin abin da yayi min ba dan taba zato ba.MUHD-ABBA~GANA adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *