Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, December 5, 2015

KAUNA CE SILA***56

adsense here kauna-ce-sila.jpg

KAUNA CE SILA56




MUHD-ABBA~GANA




WASHEGARI bayan na fito ina zaune kamar azahar sai wani ya kira ni a waya dama nasan sai yace sunana abdul nace oh ya garin yace lafiya kina da labari salisu sunyi hatsari yanzu a hanyar maiduguri nace au dama yana can ko yace ke ba ki ma san baya gari ba nace na sani na zata ya dawo yace yau da safe suna hanyar dawowa sukayi nace to Allah ya kiyaye ya basu lafiya kafin yamma zancen ya baza gari wasu sunce shi karaya biyu yayi wasu sunce uku ni dai bana iya cewa komai amma na tausaya musu har raina washegari na fito nacewa zainabb yaushe zamu tace yau mana ai ance duk suna gida nace to muje nan muka nufi unguwar sy salisu dan duba shi har a zaiciya ta naje duba salisu saboda dalilai biyu na farko don musulunci na biyu don bana so mutane su fahimci mun rabu tunda daga ni sai shi muka sani,yanayin da naga jikinshi ya bani tausayi dan ya karye a hannu da kuma kafa amma hakai bai karya min zuciyata naji kudurina ya canja ba tun daga ranar farko kusan bayan kwana biyu ko uku sai naje duba shi idan na je bayan gaisuwa bana kara komai har na tafi wannan abin ne ya bashi damar kirana a waya a tunanina yana ganin na canja niyyar ta ta rabuwa da shine ina amsa wayar shi cikin girmamawa na san bana nuna masa komai amma to bana bari yayi kokarin fadan wata kalma data danganci soyayya a inda da naga ya fara zan tsayar dashi ta hanyar jefo wani zancan mutuncin da muke yi da marwan kullum kara karfi yake kowa ya sani ni kuwa ina jin dadin zama dashi dan baya min hirar kowa sai ya ahmad abin namu kullum girma yake dan yanzu kusan kullum sai na kira marwan a waya ina kira zai fara fadamin idan ma sun hadu yau to duk abinda ya faru ranar sai naji,




MUHD-ABBA~GANA




www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *