Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, December 5, 2015

KAUNA CE SILA***58

adsense here kauna-ce-sila.jpg

KAUNA CE SILA58




MUHD-ABBA~GANA




SAI kawai naji na fara shirya karya nace e zuwa na daya tun lokacin da abin ya faru sai yace to Allah ya saiwake nace ameen kaima baka je ba ko yace E ban samu lokaci ba amma zanje nace toh bayan kamar awa daya na sauka kasa ina dawowa sai na ganshi a zaune a gurin mu suna zaune shi da su manajan mu bayan na yi sallama sun amsa bance komai ba naje na tsaya na fahimci kamar hirar saudiya suke yi ina nan din dai sai naji yace wa manajanmu yanzu shi ne kuka kyale yarinyar nan bata je ta duba salisu ba ko manaja yace waye ya fada maka bata je ba to zuwan ta tara kuma yau ma zata je kawai sunkuyar da kai nayi ta juyo ya kalleni yace meye ribar karyar da kikayi min? wata irin kunya ce ta rufeni kamar na nitse kawai sai nayi ciki ban san lokacin da ya bar gurin mu ba dan sai lokacin tafiya ta na fito na nufi gida bayan kamar kwana biyu ya kira ni nayi masa amshi ina zuwa na samu anayi masa kida ban dade ba sai ya kalleni yace ashe wai an kara karya hannun salisu ko wai gyaran farko baiyi ba nace E ciwo ne ya fito masa a hannunu kawai sai naji tace wa wanda yake masa kida yarinyar nan kawai ka kalleta kawai munafuntar kanta takeyi ni ban gane me yake nufi ba sai nace to ai ni a waya ya fada min bai kara cemin komai ba anyi kamar sati daya ban ganshi ba amma ina jin labarin duk halin da yake ciki gurin marwan ranar da wuri na tafi gida dan zan wanke kaina ina cikin drier sai naji wayata na ringin ina dubawa sai naga marwan na daga cikin doki dan nasan akwai labari ina sakawa a kunne yace daga dubo saurayinki muke ni da yayanki da mustafa.




MUHD-ABBA~GANA



www.abbagana.pun.bz
  1. Item 1
  2. Item 2
adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *