Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, December 29, 2015

NA DAINA SO!! 6 & 7

adsense here na-daina-so.jpg NA DAINA SO!! 6 Muhd-Abba~Gana Akwai sinadarin sonki a cikin jinin jikina to ina mai kara tabbatar miki da cewa ba zan iya rayuwa idan babu ke ba ki tuna irin halacin da ki kayi min kin so ni a lokacin da kusa kowa ya ki ni kin hasance tare dani bayan da kowa ya guje ni" idan ka tafi yaushe zaka dawo? sai da ya dan yi jim kafin ya bata amsa cikin sassanyar muryarsa kin san yanayin neman aiki akwai wahala ban san takamaimai yadda al'amura za su kasance ba amma ina sa ran yanayin yadda kike yi min addu'a ba dare ba rana Allah zai taimake ni na samu aiki da wuri da yardar Allah ka samu ka gama to Allah ya sa ameen shiru suka dan yi na tsirarin sakanni yanxu tafiya zaka yi ka barni? ta tambaye shi tana mai marairaicewa kamar zata fashe da kuka kafin yayi magana taci gaba da cewa daga yau ni kadai zan ke zuwa rafi na debo ruwa? ni kadai zan ke cin abinci? daga yau ba mai side min hannu idan na gama cin abinci? daga yau bani da abokin wasa? bani da mai yi min tatsuniya? bani da mai yin...... haba mairamu abu da ba jimawa zan yi ba na san a na dade baifi nayi wata daya ba har wata daya! yanzu zaka iya shafe tsawon wata guda ba tare da ka ganni ba? Muhd-Abba~Gana www.abbagana.pun.bz [11/15, 12:22 PM] Âbbã Gäñà: NA DAINA SO 7 Muhd-Abba~Gana ko minti daya ba zan iya yi ba tare da na sa ki a kwayar idona ba amma abin da nake son kara tunasar da ke akwai hoton fuskarki a kowanne shafi na kundin adana hotunan dake cikin tarin shafikan dake binne a kwakwalwata zazzakar muryar ki a ko da yaushe na amsa kuwwa a dodon kunnena domin jikin ki ya jima da narkewa a cikin nawa jikin don haka tafiyar da zan yi zuwa birni zan tafi da kene amma a cikin ruhina yanayin yadda mijin nata ya iya tsara kalamai masu sanyaya zuciya yasa a lokuta da dama tafi tunanin cewa zai iya zama mawaki don ta sha fada masa to amma a can cikin zuciyarta bata fatan mijin nata ya zama mawaki saboda ta san yadda ake ce yan matan birni ke rububin mawaka ina so na tuna maka wani abu tace dashi bayan sun yi sallama mene ne kada ka manta kake shan magungunan ka kamar yadda ka saba nayi miki alkawarin ba zan manta ba kuma ba zan manta da irin yadda a kowanne lokaci kike nuna kulawarki a gareni ba kafin su rabu sai da suka zubar da hawaye har bayan da mota daya shiga ta bar tasha da kusan mintina ashirin mairamu bata bar wajen ba, www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *