Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 30 December 2015

NA DAINA SO!!***8 & 9

adsense here na-daina-so.jpg NA DAINA SO 8 muhd-Abba~Gana wata kakkafar ajiyar zuciya ta kuma yi bayan da ta kammala tunanin abun da ya faru tun shekaru da dama da suka shude mairamu ta tuna da irin halin kadaici data tsinci rayuwarta a ciki tun bayan da mijinta ya tafi birni ta tuna da irin zulumin da ta shiga bayan da aka shafe tsawon kwanaki siitin bai dawo ba babban abin daya fi tayar mata da hankali tunani data yi na cewar ko mijin nata ya hadu da wani mugun bala'ine toh amma surukarta ce ta yi ta kwamtar mata da hankali bayan shekara guda mahaifiyar mijin nata ta kira ta mairamu wata magana nake si muyi dake kin ga tun bayan tafiyar dan nan yau tsawon shekara guda kenan bai dawo ba bai kuma yi wani aike ba kin ga har wasu abokansa sai da suka je birni nemansa amma ba suji duniyarsa ba kin ga kuma ke yarinya ce bai dace rayuwarki ta ci gaba da da kasancewa cikin wannan yanayin ba kuma kina sane da surutan da jama a ke ta faman yi don haka ina ganin mai zai hana ki mika wuya bori ya hau? mai zai hana ki amincewa a raba auren ki samu wani mijin" bata tanka mata ba kuma bata amince da shawarar ba tsinin kibiyar sabon bakin ciki yayi dirar mikiya a zuciyar mairamu bayan da ta kuma tunawa da wani abu. Muhd-Abba~Gana www.abbagana.pun.bz NA DAINA SO 9 Muhd-Abba~Gana abin da ya fi tsaya mata a rai fiye da komai mijinta na sane da cewar lokacin da zai bar ta tana dauke da juna biyu har ta haifi da namiji bai zoba har dan ya kai shekara guda bai taba ganin mahaifinsa ba har yaron ya rasu mahaifinsa bai taba yin ko da aike ba shin mene ne dalilinsa daya sa mijinta zai yi mata haka? shin da gaske ya manta da ratuwarta kamar yadda aka sha fada mata tsanin so da take yi masa ne ya sa ba ta iya ganin laifin mijin natan ba bakon abu bane a kauye miji ya gudu birni ya bar iyalinsa cikin kunci da talauci,don ita kanta mairamu ta sha ganin haka to amma a iya saninta mazajen kan dawo bayan shekara daya ko biyu don haka ita mene ne dalilin da yasa mijinta ba zai dawo ba har sai bayan kusan shekara shida mai ya sa zai yi mata haka? da fada ya dace ta tareshi wata zuciyar ta bata shawarar idan yazo kada ki sakar masa fuska toh shin da wacce irin fuska zai dubeni,wadannan kalamai zai fada min daza su iya sa na manta da halin zulumi na rashin tabbas daya jefa ratuwata na tsawon shekaru wanne irin uzuri zai kawo min da zai gamsar dani? ban samu aiki da wuri ba aiki ne yayi min yawa,kauyen ne yayi min nisa nasan nayi laifi ki yafe min. www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

1 comment:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *