Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, 5 January 2016

NA DAINA SO!! 15-16-17-18-19 &20

adsense here na-daina-so.jpg [11/19/2015, 5:01 PM] Äbbä Gãñā: NA DAINA SO 15 Muh'd-ABBA~GANA SHIN mene ne dalilinsa na kin sanar da ni kafin furta maganar a gida? tambaya da ta yi ta munta don a kwanaki biyun nan ko isasshen bacci ba ta samu to amma ko ba komai tana ganin yanxu ne lokacin da zata samu amsar tambayar da ke addabar kwakwalwarta mairamu ya kira sunanta a tausashe na'am ta amsa a sanyaye kin yi mamaki samun labarin? eh mai ya sa ki ka yi mamaki? batace bamai ba nayi mamakin abin da zai saki yin mamakin jin cewa ina sonki a gaskiya mairamu tun kafin na mallaki hankali sosai ina nufin tun iya yaro lokacin dana fara ganin ki naji a jikina cewa ko ba dade ko ba jima wani al'amari zai faru a tsakaninmu na tsinci kaina cikin wani yanayin na son kasancewa tare da ke so ganin fara'a a fuskarki son ganin samun dimbin nasarori a rayuwarki daga bisani na fahimci sunan yanayin da nake ciki so kuma ba son kowa ba face ke na jima ina tunanin ta hanyar da zan bi don ganin na bayyana miki sirrin dake zuciyata na jima ina hasashen ranar daza ta zo na nemi alfarmar samun wani matsayyi na musamman a zuciyarki na kwashe shekara da shekaru ina laluben kalmomin da zan yi amfani da su wadanda za su iya gamsar da ke irin gagarinmin matsayi da martabar da kike da ita a rayuwa ta na so ace akwai yadda zanyi na bude miki ki ga irin yadda kika yi sansani a harabar xuciyata. Muhd-Abba~Gana www.abbagana.pun.bz [11/19/2015, 5:37 PM] Äbbä Gãñā: NA DAINA SO 16 Muhd-Abba~Gana shiru ya dan yi yana mai ci gaba da kallon daguwar kyakkyawar fuskarta mairamu a takaice dai ina mai farin cikin bayyana miki cewa ina so ki so ns hakika son da ban taba yiwa wata ba kuma koda wasa ba zan yi wa wata irinsa ba ina so ki amimci ki zama abokiyar rayuwata ki zama matata nayi alkawarin zaki same ni miji na gari mijin da zai ke kula da hakkin matarsa nayi alkawarin faranta miki rai zan kasance mai nisantar duk wani abi da zai kai ga bata miki rai zan ke tausaya kasance mai nisantar duk wani abin da zai kai ga bata miki rai zan ke tausaya miki zan kasance mai..... yaya kabir karo na farko data kira hanzarinsa tun sa'ilin da ya soma bayani duk da cewar cikin sassanyar murya ta kira shi amma akwai wani abu a muryarta daya nemi dakatar da bugun zuciyarsa na"am ya amsa na tambayeka ? mai zai hana kaba ni izini? nabaki izinin jan ragamar rayuwata don haka zaki iya tambayata komai don Allah mene ne dalilin da yasa tuntuni ba ka taba fada min wannan bayayyan sirrin da ke zuciyarka ba? ga mamakin kabir sai ya ji tambayar kamar ta dan yi masa tsauri sai daya dan yi jim kafin ya gano cewa wannan ita ce tambaya mafi sauki da aka taba yi masa a rayuwarsa saboda babu kalamomin da a hakikanin gaskiya zasu iya bayyana irin matsayin da kike da shi a rayuwata saboda ina ji a jikina cewa ke ma kina jin abin da nakeji saboda in da tabbacin cewa ko yaushe na nemi alfarma a wajen janwata ba zan rasa ba saboda yanzu ne lokaci saboda...saboda...saboda...saboda mairamu dalilan na da yawa daya daga ciki muhimman dalilan da sukasa a yanzu na bayyana maganar saboda la'akari da nayi cewar idan na tsaya kallon ruwa babu abinda zai kana kwado yayi min kafa kuma bazan yarda bishiya ta fito a gidanmu ba amma kuma wani a can gefe yafi ni shan inuwarta dadin dadawa ina tsoron ka da wankin hula ya kai dare mairamu da fatan zan samu masauki sauran furucin ya makale a fatar bakinsa sannan a lokaci guda murmushi murmushin da yake yi ya rikide zuwa wani irin yanayin da aka fi gani a fuskar mutumin dake fama da ciwon hakori hakan kuwa ya faru ne sakamakon alamar daya gani a fuskar mairamu babu fara'a fuskarta....baya ga haka kuma akwai daya fi tsorata shi tagwayen hawaye ne ke zuba daga idanunta kafin ya samu damar cewa wani abu tuni har ta juya a guje ta bar wajen MAIRAMU!!! MAIRAMU!!! MAIRAMU!!!! Muh'd-Abba~Gana www.abbagana.pun.bz [11/21/2015, 9:02 AM] Äbbä Gãñā: NA DAINA SO 17 Muhd-Abb~Gana kwalla mata kira yayi ta yi bata tsaya ba batw waiwayo ba bata amsa ba karo na farko data taba yi masa irin wannan tun a lokacin ya gane cewa akwai matsala karo na farko da wani tsohon ciwon kansa ya dawo masa tun bayan shekaru biyu da warkewa al'amura sun rikicewa mairamu mai yasa tuntuni yaki sanar da ita? sai yanzu bayan ta riga ta kamu da son wani daban hakika duk abinda yaya kabir ya fada na game da irin son da yake yi mata ta amince dari bisa dari musamman datayi ta tunawa da wasu al'amura da suka yi ta faruwa tun a shekarun baya,ta tuna irin yadda tun suna yara yake fifita ta a kan sauran kannensa to mai yasa tun a lokacin bai fada mata ba? mai yasa tun a lokacin ita bata gane ba? rashin sanar da ita laifinsa ne rashin daukan haske laifinta ne kasa bacci tayi a daren ranar cikin talatainin dare ta farka a gefen katifa ta zauna gami da rafka tagumi yaya kabir duk wata budurwa zata so ace ta samu miji kamar kabir saboda kyawawan halayensa ita kanta mairamu zata so yaya kabir ya aure ta da ba don wani kwakkwaran dalili ba ita tana daukansa ne a matsayin wanta dan'uwanta............amma wannan ba dalili bane. www.abbagana.pun.bz [11/21/2015, 9:10 AM] Äbbä Gãñā: NA DAINA SO 18 Muhd-Abba~Gana akwai dalili akwai wanda take so kuma sun yi alkawarin aure kawai dai basu bayyana a fili ba to shin zatace da yaya kabir yayi hakuri? ya nemi wata? mene ne dalili? saboda ni bana sonka......a'a ba haka zata ce ba ya nemi wata,saboda ita tana da wanda take so...an ya zata iya fadar haka kuwa? idan ta fada mai zai faru? idan bata fada ba mai zai faru? ta tuna da irin yadda kabir yake kaunarta ta tuna da irin yadda iyayensa suka rike ta tun tana karama kuma suke ci gaba da rike ta ba tare da sun taba nuna wani bambanci s tsakaninta da yayan da suka haifa ba to ta wacce hanya zata ce bata son dan da suka haifa? ina mafita? kifa kanta tayi a kan katifa tana kuka kafin wani tattausan hannu ya dafa kafadarta da farko tayi tsammanin ko rukayya ce ta farka a sanadiyyar jin gunjin kukan da take yi to amma sa'ilin data dago kai ga mamakinta sai taga kabir ne. www.abbagana.pun.bz [11/21/2015, 9:23 AM] Äbbä Gãñā: NA DAINA SO 19 Muhd-Abba~Gana yaya.....yaya ka...birrr! karkarwa baya ga in'inna a tare da muryarta "mairamu" ya kira sunanta cikin sassanyar murya tabbas shine! ta fadi a zuciyarta toya aka yi har ya turo kofa ya shigo ba tare da taji motsin shigowarsa ba? dadin dadawa a wanne dalili zai shigo musu daki cikin talatainin dare? kasa cewa komai tayi face kura masa ido kamar tana sa ran daga sama ya fado a hankali ya zauna a gabanta fuskantar juna sukayi ki kwantar da hankalinki ba aljani bane don naga irin kallon da kike yi min amma duk da haka kin cancanci a baki lambar yabo saboda jarumtar dakika nuna bakiyi ihu ba kuma baki ji yunkurin gudu ba kasa-kasa yake yin magana saboda yanayin dare nima kasa bacci nayi kuma naji a jikina cewa kema kin kasa yin bacci wannan ne dalilin daya sa na zagayo sai dai bambanci na da ke shine ni bs kuka da hawaye nake yi ba kukan zuci nake yi kuma ina da dalilina nayi hakan.by muhd abba gana ban yi niyyar shigowa cikin dakinku ba to amma kukan da naji kina yi ne yasa ni sauya shawara shiru ne ya dan biyo baya a dan wannan tsakaninne ta sharce hawayen dake fuskarta ""mairamu"" 'na'am ina sonki ki bani amsar wasu yan tambayoyi da zan miki kuma gaskiya na ke son kifada min ba tare da kin boye min komai ba shiru ne ya kuma biyo baya na tsawon wasu tsiraran sakanni. www.abbagana.pun.bz [11/21/2015, 9:35 AM] Äbbä Gãñā: NA DAINA SO 20 Muhd-Abba~Gana mairamu "na'am" a wanne matsayi kike daukata? yaya na kuma dan uwana to ina so ki ci gaba da daukata a wannan matsayin a matsayina na dan uwanki mai kaunarki zan so ace na gan ki cikin farin ciki da walwala duk wanda zai takura miki a duniyar nan to ni abokin adawarsa ne don haka na gano rashin adalci na hukuncin dana zartar dana fada a gida cewa ina sonki ba tare dana tuntube kina ji ra'ayinki game da lamarin ba hakika ban kyauta ba nice ban kyauta ba' ta wacce hanya? da tuntuni na kasa fahimtar cewa kana so na har sai yanzu da......shiru tayi ta kasa karasa maganar "ki karasa maganar mana a maimakon haka kwalla ne suka cika idanunta mairamu nasan cewa ba so na ne ba kya yi ba kawai dai an riga nine shirun dana yine ya jawo min ba komai mairamu ki kwantar da hankalinki ni mutum ne mai saurin fahimta na janye wannan maganar amma har yanxu dan'uwanki ne ni wanda ko yaushe a shirye yake ya tallafi rayuwarki. www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *