Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, January 5, 2016

NA DAINA SO!! 21 & 22

adsense here na-daina-so.jpgna-daina-so.jpg NA DAINA SO 21 Muh'd-Abba~Gana 09039016969 NASAN kina tunanin kamar zan ga kina yi min rashin mutunci to ina mai tabbatar miki da cewa bana daga cikin samari masu karamar kwakwalwa na dauki alkawarin zan ke yi miki addu'a a kan Allah ya tabbatar da alkhairi tsakaninki da wanda kikeso yasa ya zama miji na gari wanda zai ke kula da hakkokikin ki ki cire damuwa daga zuciyarki ki kwanta kiyi bacci sai da safe har ya isa wajen kofa da zummar ficewa daga dakin ya tsaya sakamakon kiran sunansa da tayi yaya kabir na'am to...ka kana da wata budurwar ne? murmushi yayi ba tare da ya bata amsa ba ya fice daga dakin sai dai kafin ya fita sai da mairamu taci nasarar ganin hawaye a fuskarsa. kwanaki biyu da faruwar al'amarin kabir ya bayyana wani labari a gida labarin da ya girgiza kusan kowa domin mahaifiyarsa ya fada wa cewa ya janye maganar son mairamu a yayin data nemi dalilinsa na daukar wannan matakin kawai ji nayi na fasa.....kuma na tuna akwai wata da muka taba yin alkawarin aure a birni ya kawo wannan uzirin ne don gannin bai dorawa mairamu laifin komai ba itama ta fuskanci haka a zahiri ya hakura amma a badini ba zai iya ba babu irin kokarin da kabir bai yi ba don ganni ya cire son mairamu daga zuciyarsa amma abu ya faskara kusan ko yaushe kuma a duk inda yake akwai tunanin mairamu a tare dashi har kokarin yin wata budurwar yayi don ganin ya shafe babin rayuwar mairamu daga zuciyarsa da rayuwarsa gaba daya to amma daga bisani ya gano cewa babu gurbin da wata zata iya samun mafaka ko da ta siyasa ce a zuciyarsa saboda yadda mairamu ta yi mamaya yana ji a jikinsa idan har ba mairamu ba to ba zai iya yin aure a rayuwarsa ba zai mutu tuzuru NA DAINA SO 22 Muhd-Abba~Gana har bayyan sallar magariba ba wani labari shin ko fitowar yamma yayi? mairamu ta tambayi kanta bayan da ta idar da sallar magariba tun la'asar cikita ke gugi saboda azababbiyar tunwar dake addabarta amma ta ki yarda taci komai don ta tsara cewar da mijinta zasu ci tare duk da cewar tana sa ran murnar ganinsa ma kadai zai iya hana ta cin abinci mai yasa har yanzu bai iso ba? karfe takwas na dare agogon dake manne a jikin bangon dakin ya nuna mijinta bai dawo ba to ko fitowar dare yayi? ko motace ta lalace musu a hanya? ko hatsari suka yi? ko yan fashine suka tsare su? bata yi aune ba sai taji hawaye na barazanar fitowa daga idanunta sannan al'amari ne cewar hanyar shigowa kauyen bata da kyau ana yawan yin hadarirrika baya ga yan fashi dake tare mutane daga lokaci zuwa lokaci hadari? yan fashi? tana faran ba daya daga cikin wadannan al'amuran ne......rashin fitowa da wuri? amma mai yasa bai fito da wuri ba? kuma ma...........tunanin dake kwakwalwarta ya datse kusan a lokaci guda numfashinta ya nemi daukewa sakamakon kwankwasa da taji an soma yi. www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *