Wednesday, January 6, 2016
NA DAINA SO!! 25
NA DAINA SO 25
Muh'd-Abba~Gana
"eh"ta ba shi amsa tana mai sunkuyar da kai aina san shi..... ya fada min tare kukayi makaranta a birni tabbas haka ne amma a zuciyarsa sai yace na san bai fada miki bin kunya daya taba yi ba wanda ta dalilin haka aka kore shi daga jami'a yaya kabir! ta tari hanzarinsa na'am mai yasa a gida baka fadi gaskiya ba? gaskiya game dame? sai da ta dan kawar da kanta ba cewa matsalar daga.......daga ......ni ai wannan ba matsala ba ce mairamu ni mai son abin da kike sone kuma ba naso aga laifinki duk da cewar don baki amince kin aure ni ba ba wani laifi kikayi a addinance da al'adance ba to amma kin san yadda mutane suke yanzu nan sai wasu su fara yin wata irin fassara amma yanzu kin ga cikin hikima da azanci na janye maganar ba tare da anyi ta gutsuri-tsoma ba to shin da gaske akwai wacce kayi alkawarin aure kamar yadda ka fada? bbbu to amma dai ai kana da budurwa ko? naso nayi budurwar amma na kasa yi ( ashe muna daya dan uwa) saboda me? saboda ke nake so ya fadi a zuciyarsa amma a fili sai yace saboda ba yanzu zan yi aure ba sai na samu wacce take sona sosai.......ai zaka samu,, hmmmm! a matan yanzu kam zayyi wuya
Muh'd-Abba~Gana
www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Burodin ayaba
Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.
Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.
MAJNOON hausa love novels
Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more