Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Sunday, March 6, 2016

BANA KAUNARKA!!! 33

adsense here bana-kaunarkajpg.jpg BANA KAUNAR KA!!! 33 muhd abba gana 09039016969 -------------------------------------------- ya amin yace mata meya hada ku ta ce zagi wahida fito na fito nace ya zanyi ta dinga raina min hankali wai acikinku waccece babba? da sauri wani abokin yaya saifu yaya amin yace ke wahida bata hakuri yaya itace fa ta fara tsokanata ni dai nace ki bata hakuri kiyi hakuri mun juya zamu tafi yace kuzo nan baku iya gaisuwa ba ko ba kuga baki nai ba na kalleshi kunya ta kama ni da gudu na fita dakin mom na shiga na kwanta jikinta mahida ta shigo nace mahida don Allah kama min kaina ai kuwa sai dai ki mutu.....please anty wahida, ina kwance ina yiwa mom hira har bacci ya soma daukata,mahida ce tace daga ganin yadda wahida take lumshe ido bacci zatayi mom tace ai gwanda tai bacci muma mu huta da rigima,mahida tace mom in tambaye ki ina jin ki kar fa kiji haushi mom tai dariya wanne irin haushi wai mom ina iyayenki? ban taba ganinsu ba ko sun mutu in sun mutu ina ne garinku sannan ina yan uwanki? hawaye mom suka digo min a kumatu,zumbur na mike ke mahida dan me zakiyi wa mom irin wanan tambayar me daga hankali,wai ma ina ruwanki gashi nan ai gashi kin sata kuka ya amin ne ya shigo ganin mom tana hawaye duk sai ya rude ya tsunguna gabanta yana fadin lafiya nace ba mahida bace ta saka ta kuka meye tayi mata? wai cewa tayi mom ina iyayanki ban taba ganinsu ba ko sun mutu in sun mutu ina yan uwanki,ina ne garinku kuma kina da yan uwa koke kadai ce? ya amin yace kiyi hakuri kin ji mominmu ke kuma mahida kar ki kara yi mata irin wannan tambayar mai tada hankali mom tace ba komai ku kira faruq sai in baku labarina ya amin ya kira faruq suka nutsu kamar masu cin dan wake don jin labarin mom. Da farko dai ni sunana maryam mahaifina mallam abdulkadir haifaffen gyambu ne auran zumunci akai musu shi da mahaifiyata fulani ne sosai mahaifiyata ta kasance tana tallan nono kasancewar mahaifina ba shi da hali koda ta haife ni sai ya kasance muna tallan nonon tare ko dana girma sai nace inna ta zauna ni zan ci gaba da yin tallan,mahida tace Allah ya kiyaye in yi tallan nono yaya yasa kafa ya doke ta mikewa tayi ni bazan ji labarin mom din ba nina dauka iyayen mom masu kudine kamar abbanmu,ya faruq yace in baki zauna ba sai na duke ki da sauri tace na zauna yi hakuri yaya nace sannu yar masu kudi waya sani ma koda abban dako yake yi sai lokacin ya amin yai magana yace ku tashi ku fita yaya yi hakuri ni dai ba zan kuma magana ba mom cigaba. a wanan lokacin na hadu da wani saurayi wai shi jauro ya nuna yana sona domin kullum naje kasuwa sai ya goyo ni a mashin dinsa ya kawo ni gida abu kamar wasa har aka sa ranar bikinmu da jauro,amma har lokacin ina tallan nono mahida tai tsaki domin bbu abinda ta tsana irin tallah bbu wanda ya kulata koda lokacin biki ya zagayo akayi biki irin na al'adarmu an daura aure anzo an min jere iya bakin kokarin iyayena sunyi kokari. Abbagana hausa novels@ faceebook. www.abbagana.pun.bz adsense 2 here
Share:

3 comments:

please after reading drop down your comment here!...

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *