Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, January 3, 2017

Waye Sanadi?? 100 (karshe)

adsense here

💘WAYE SANADI?💘 1⃣0⃣0⃣ 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘💘 💘💘 💘💘 💘 💘 💖MUH'D*ABBA*GANA💖 www.MuhdAbbagana.blogspot.com Mun sauka Kano ranar da za a yi dinner sai da na fara zuwa gidansu Momy da Sadiyya, sannan na tafi gidan Baba. Duk inda na sa kafa nan Imran zai sa tasa har muka tafi gidan Abbana. Na yi matukar farin cikin ganin Ummata. Bayan na gama cin abinci ina tare da Hassan Imran ya shigo dakin da nake Safiyya amaryar Imran kamar yau aka yi tamu dinner ana hararata tare da takan 'yanyatsu Na ce Me ye haka kai kai ka fiya tuna baya, wacce irin kulawa ce bana baka? Ya zauna kusa da ni, ki yi hakuri Safiyya Abba ya hana zuwanki dinner. Na dago da sauri kar ki damu mu yi zamanmu nima babu inda za ni, mu yi zamanmu mu yi tamu dinner mai tarin lada. Na dan yi murmushi Nima bana jin dadin jikina tunda za mu taho marata take ciwo Ya mike da sauri, 'Ban san shirme baki da lafiya tun safe baki gayan ba, ta so maza mu tafi asibiti cikin sirri kamar unguwa za mu, tunda daman da kayanmu a mota Ban yi musu ba na bi bayansa muka fita, don nima marar tawa dada takuran take. Ya yi kiran Doctor Khadijah ya tambaye ta tana asibiti ko gida? kai tsay asibitin Nassarawa muka nufa. Awa biyu da zuwanmu cikin iko na Ubangiji na haifi yarinyata mace. Imran ya rasa inda zai saka kansa saboda farin ciki. Ya shigo dakin hutun ina zaune na zubawa bayna ido cikinso da kauna. Duka awarmu biyar a asibitin muka fito tare da dankareriyar kyautar da Ubangiji ya yi mana Iokacin da muka shiga gate din gidanmu Abbana ne a zaune su da Abban Imran Lokacinda Abba ya ga na fito dauke da yarinya a hannuna bai san lokacin da ya mike tsaye ba Dadyn Imran ya ce Kai Imran yarinyar wace ce? Ya karasa yana dariya ya ce, “Dady ‘yar Safiyya ce daga asibiti muke ta haihu Duk wanda aka gayawa haihuwata ba karamin mamaki yake ba, haka ‘yan party da suka dawo. Ina gani aka tafi aka kai Momy da Sadiya gidajensu. Ba mu yi wani gagarumin taron suna ba sai walima da muka yi. Baby ta ci sunan mahaifiyar Imran Amina. bayan na yi arbain na koma gidana wanda ba mu da nisa da Rukayya illa Sadiyya da take Kano. Zaman da kauna muka shiga shimfidawa. Aminatu ta taso cikin kulawa da soyayya daga kowane bari Alhamdulillahi. Nan na kawo karshen wannan labari nawa mai suna *💖Waye Sanadi?? 💖* *SADAUKARWAR: Na sadaukar da wannan littafin ga masoyana* GAISUWA TA MUSAMMAN A GAREKU 🍄Raheem Jega 🍄Baby Afreen 🍄Hajiya Zahra B.B 🍄Abdul mr smile 🍄Abdulaziz A.A J 🍄Mrs Bilkisu 🍄Kurratulayn 🍄Herleematus Serdeeya 🍄Billy gero 🍄mrs umar 🍄Hauwa jabo 🍄Autan Hajiya 🍄jeedah aleeyu BAN MANTA DA KU BA ... . ➡ONLINE HAUSA WRITERS ➡HOME OF NOVELS ➡NOVELS ➡Hype Hausa Novels ➡ Novels Only ➡ Duniyar Marubuta ➡Home of Nobel ➡Hausa novels ayau Members na group na 📚HOUSE OF NOVELS 1-5📚 da dukkan wanda ban ambata ba nagode INA MIKA SAKON GAISUWATA GAREKU MASOYA NA ALLAH YA SADAMU DA ALKHAIRINSAH *💖Muhammad Abba Gana💖* *09039016969* adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *