
[10:55PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨:
★ALKAWARI★
.
Part 1.
Yunkuri nayi domin intashi amman naji gaba
daya nakasa yin komai sakamakon rashin karfin
jikina, wani zafi naji a hannuna kamar
antsiramin wani abu cikin hanzari nayi sauri na
dagashi, sai lokachin nalura da wata allura soke
ga hannu na dawata roba doguwa, nanne nabi
robar dakallo har inda tushenta yake, abinda
idanuwa na suka gani shine yadauremin kai tare
da bani mamaki. Ledar jini che nagani arataye,
yana biyowa tachikin wannan roba mai allura
yana shiga achikin jikina. A chikin zuchiyata
nake tambayar kaina, mike faruwa ne har ake
karamin jini? Nanne nakali kane na wanda
yaketa murna yana faman danna wayarsa
domin yakira umma na yafada mata na farka
amman ntwrk ya hanashi, kunsan network din
9ja da matsala... nache ahmad meyafaru dani
ne akemin karin jini, budar bakinshi sai yache
"yaya yusuf awarka ashirin da hudu kwanche
anan, wannan itache leda ta ukku da akasanya
maka" rufe bakinshi ne yayi dai dai da turo kofa
da akayi,.... wani mutum ne mai matsaikachin
tsayi da alama shine likitan dayake kula dani
saboda ganin yadda yayi shiga ta fararen kaya
kamar wata sabuwar gawa. ba tareda wani
bata lokachi ba ya karaso a'inda nake kwanche,
tare da tambayar kanena chewa, tunyaushe
yafarka? sai yachemai "yanxu yafarka bada
dadewa ba", a nanne naga yabuda wani file
dake hannunsa yana karantawa tachikin siririn
farin gilashin dake sargafe a idanuwansa,
batare da ya sakeyin magana ba yabude kofa
yafiche abinsa. Jim kadan sai gashi yadawo da
magunguna achikin leda, yaba kanena tare da
umurtarshi yadda zaya bani maganin. Ananne
ya yafiddo yabuda yabani wasu kwayoyi tareda
ruwa achikin cup domin insha, amman achikin
raina inata kokonto wane asibiti ne wannan
masu bada magani kyauta batare da masu
jinya sunbiya kudi ba? Ina gama shan maganin,
najuya domin ajiye kofin akan wani dan teburi
dake gefen gadon da nike kwanche, ananne
naga wata yar dunkulalliyar takarda wadda ake
kimlache sako mai mahimmanchi achikinta,
wadda ake kira da "envelop", nadauka tareda
kokarin duba ko minene achiki. sunan yasmeen
ne nagani abayan takardai wannan ne yasa na
kagu da inbude domin ganin abinda ke kunshe
achiki, ina budawa sai naga wata yar takarda
mai dan tsawo ta fado daga chikin envelop din,
chikin hanzari nasanya hannu nadauka tareda
duba abinda ke achiki, wanda idanuwa na suka
bani tabbachin chek ne nabanki, mai dauke da
kudi naira naira dubu dari biyar, 500,000naira a
rubuche, tare da sa hannun yasmeen,... Nanne
naji wani irin faduwar gaba, kasanchewar ni
bako ne awurin kama kudi masu wannan irin
yawa haka, lokachi guda kuma xuchiya ta
tambayeni me yasmeen take nufi da wa'annan
kudin masu yawa? Idan kyautache tayiman, to
miye silar yiman wannan kyautar haka? Ananne
namaida hankali na akan envelop sakamakon
akwai wata takarda wadda banfiddo ba, hannu
na nasanya achikin emvelop din tare da zaro
wata takarda wadda take chike makil da rubutu,
kamar haka....
[10:56PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: Alkawari
Part2
Nafara karantawa kamar haka.... "amincin Allah
ya
tabbata agareka masoyina tauraro acikin taurari,
nasan zakayi mamakin abnda nake kokarin sanar
dakai sakamakon alkawarin damukayi na zama
dajuna har abada, yusuf kasan inasonka kuma na
tsani dukwani abnda yake kokarin shiga a
tsakaninmu, shiyasa xuchiyata take takaichi tare
da
tsoron sanar dakai saura kwana biyu jirginmu zai
tashi ranar asabar, sbd abbana ya matsa akan
dole
sai nafita waje nayi karatu, nayi iya kokarina
domin
inkauda wannan maganar amman abin yachi tura,
shiyasa ma haryaje yachi gaba da shirye shirye
batareda ya sanar dani komai ba, saida lokachi
yakure sannan yafadamin ya samarmin
admission,
inshirya domin tafiya "massachusett (code fish)
university" dake london... yusuf dan Allah
karikemin
soyayyata amana zandawo bayan nagama
karatuna kuma kai kadaine namijinda xuchiyata
takeso amatsayin abokin zaman rayuwa, kuma ga
kudinan kaje bank ka amsa domin duba
lafiyarka...
Daga mai kaunarka "yasmeen jafar muhammad"...
Bayan nagama karanta takardai wasu hawaye
sukarinka yin ambaliya suna sulalowa ahankali
sunabi tabisa kumatuna, wani sashen xuchiyata
kuma yana fadamin "wannan ba abin tada hankali
bane, abinda zakuji dadi ne saboda neman ilmi
tatafi kuma zata dawo" wani bangaren nadaga
xuchiyata kuma yanata tinanin yadda rayuwata
zata kasanche batareda yasmeen ba"... Karar
bude
kofa naji wanda shine yayi silar fiddoni daga
tekun
tinaninda na afka, tunkafin sushigo naji sunyi
sallama, muryar mahaifiyata che naji tareda
kanwa
ta suna shigowa, Karasowa tayi agabana tareda
yin magana dawani irin launi mai nuna alamar
tausayi karara "yaya yusuf ya jiki" na amsa jiki
dasauki kanwata, sai alokachin mahaifiyata ta ida
karasowa a'inda nake tareda fadar "sannu dannan
kaji ya jikin naka"?? Nikuma sai nafada "da sauki
umma" a takaiche... Lokachinne takalli ahmad
dake
tsaye abakin gadon ya sanyamu agaba da alama
tinanin wani abu yakeyi, umma che takatse shi
daga tinanin dayakeyi, "ahmad me likitan yafada
ne
akansa?"ahmad yadago kansa tareda ba umma
amsar tambayar datayimasa "yaji sauki sosai
umma, kuma doctor yace idan wannan ledar jinin
takare za'a iya sallamarshi gobe in Allah ya
yadda"
bakaramin dadi naji ba danaji ahmad yafada gobe
za'a sallameni "nasan zankara ganin yasmeen"
abnda nafada kenan achikin xuciyata batareda
kowa yajiba... Shiru kowa yayi wurin seconds
talatin sannan najuya nakalli kanwata tana tayin
wasa da yan yatsun hannunta, sannan nakatse
shirun da tambayarta, kanwata yau wace rana? "
yaya yusuf yau juma'ah (friday)" atakaiche
tafadaman tana kallona da alamar mamaki karara
a
fuskarta na ganin yanda namanta lissafin
kwanaki,
nikam bandamu da abnda take nufiba saima wani
dadi danakeji achikin raina ina fada gobe asabar
in
Allah ya yadda kafin su yasmeen su tafi za'a
sallameni.... Haka nawuni tunani tareda kosawa
gobe tazo, ji nake kamar injuya agogo kawai
kowa
yaga lokachi yakoma karfe 6 nasafe, wanda
danasan abinda zai biyo baya, da banyi zumudin
zuwa filin jirgi ba da niyar yima yasmeen
bankwana......
[10:59PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: Alkawari
Part3
A daren ranar juma'ah bawani bacci
nayiba sosai wanda zai ishi idanuwana saboda
rigimar danarinka yi da bacci akan bazanyiba
shikuma yazo yayiman kane-kane a idanuwa,
nikuma gani nake idan nakwanta lokaci bazaiyi
gudu ba sosai, nafiso inayi ina duba agogo,
shiyasa
duk bayan dakika daya ko biyu sai nadaga kaina
naduba agogon dake makale ajikin bangon
asibitin,
haka nakasance bankwanta ba sai wurin karfe
02:30am na dare sakamakon karfina da bacci
yaci,
shima hakan yanada nasaba ne da ruwan da aka
tafka jiya da daddare achikin garin namu na
katsina wani sanyi yarinka shigowa tako ina har
saida nasanya mayafi na lullube, ina lullubewa
shikuma bacci sai yasamu wurin zama a idanuwa
na....... Cikin ikon Allah batare da wani bata
lokaci
ba, gari na wayewa saiga likita yazo yaduba
lafiyata tareda bada iznin zamu iya tafiya gida
yanxu saboda ansamu abinda akeso, dadi da
murna aguna abin ba'a magana, tamkar wanda
akaba kyautar kujerar makka domin sauke farali.
Bayan fitar likita sai kuma ga mahaifiyata tazo
itada hadiza domin kawomana karin kumallo,
ananne ahmad yashaida masu ansallamemu.
Shiryawa mukayi muka tattara komai namu
domin
tafiya gda, fitowa mukayi daga asibitin muka
doshi
tudun wada..... bayan munxo gda ne nashirya
domin infita batareda kowa yasani ba, sbd idan
umma tasan zanfita, bazata barni ba... Tsohon
mashin dina najawo wanda idan ina tafiya
kararshi
tamkar ana bakacen tsakuwa acikinsa, ina sauri
intafi saboda lokacin tashin jirgin yakusa saura
30
minute, bantsaya ko inaba sai filin jirgi, na'aje
mashin dina inda aka tanada domin ajiyar ababen
hawa.... Wani irin faduwar gaba naji saboda
abinda
idanuwa na suka hango... Wata mace ce, wadda
nikeda tabbacin aunty bilki ce...... Aunty bilki
mace
ce mai matukar masifa kuma ta tsani talaka
batason talaka ko kadan, kanwa ce ga alhaji jafar
muhammad mahaifin yasmeen, wanda babban
dan
siyasa ne wanda yarike mukamai daban daban
acikin mulkin nigeria, matarsa guda daya kuma
yanada 'ya 'ya guda ukku, biyu maza sai daya
mace, usman, aliyu sai yasmeen yar autarsu....
Aunty bilki ta taba yin aure wanda ta auri
"ibrahim
sabo", abokine ga alhaji jafar, amman saboda
tsabar masifar aunty bilki, dole tasa suka rabu da
mijin nata tadawo gidan yayanta da zama tareda
da danta guda daya wanda take masifar so kuma
take nuna masa gata, wanda suke kira da
"Abba".........Bayan natsaya ina tinanin tayadda
zantunkari aunty bilki, nasan idan taganni bazata
barni inshiga agun yasmeen ba, wani bangaren na
zuciyata kuma yache "kaje kawai babu abinda
zaifaru" cikin karfin hali naci gaba da tafiya, ina
karasawa agunsu, sai naduka nagaida ta, wani
irin
kallo tayiman tareda yatsine fuska kamar taga
wani
mummunan abu, cikin bacin rai take magana "kai
maye har anan saida kabiyota? Wai kai wane irin
dabba ne? Yasmeen tayi kama da kalarka ne?
banza matsiyaci talaka wanda rayuwarsa batada
wani amfani", nidai bance komaiba, kawai na
sunkuyar dakaina ina sauraren ikon Allah...
Abayan
aunty bilki kuwa wasu bakaken mutane ne katti
guda biyu masu jajayen idanuwa, tsaye suke
kikam
ko motsawa basuyi kamar gumaka, batareda
tayimasu wata magana ba, kawai tadan juya
kanta
kadan, kamar tana kallon kafafuwan mutanenda
dake bayanta, cikin kwarewa da sanin aiki
irinnasu,
har suka gane abinda take nufi, cikin zafin nama
sukayo kaina suka sungume ni inata billayi,
sukanufi wani dan jeji dani sukayiman bugun tsiya
kamar zasu fiddamin rai, saida sukaga nadaina
motsi sannan suka kyaleni, daman ba cikakkar
lafiya gareni ba, anan nasuma sukuma suka kama
hanya sukayi tafiyarsu.... Bayan wani dogon
lokaci
sai nafarka, ganin yanda yanayin garin yachanza
nayi zaton yamma ce tayi, amman azahari dana
duba agogo sai naga karfe 01:30pm ananne sai
nagane hadari ne yamaida garin haka kamar
za'ayi
ruwa..... Dakyar nasamu nafiddo kaina bakin titi
inazuwa nan naji kamar ana juya duniyar gaba
daya komai yakoma upside down anan nakara
faduwa, daganan bansan abinda yakara faruwaba
saidai kawai nabude idona naganni acikin asibiti,
daga gefena kuma wata kyakkyawar yarinyace
nagani matashiya da gashinta dogo har gadon
baya, "achikin raina nace ita tahuta basai tayi
acuci maza ba" ina dago kaina nahada ido da ita,
kyakkyawa ce ta bugawa a jarida, ga idanuwanta
dara-dara, fuskarta tana dauke da wani dan siririn
hanci kamar biro, wani irin murmushi tayi wanda
yabayyana fararen hakoranta tareda fadar "sannu"
acikin wata siririyar murya mai zaki kamar ana
busa sarewa..
[11:00PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: Alkawari
Part4
Cikin tsoro nake tambayarta "a'ina ne kuka
kawoni?" "ku suwaye" cikin sanyayyar murya naji
tana fadar " kwantar da hankalinka bamuda niyar
zaluntarka" wata ajiyar zuciya nayi wadda take
nuna alamar hankalina ya sauka daga kololuwar
tashinda yayi, sannan ta tashi tafice abinta
batareda takara yin wata magana ba... Wani
mutun
ne yashigo dakinda nike dawasu karikitai a
hannunsa irin wa'anda likitoci sukeyin gwaje
gwaje , tareda ledar magunguna, turo kofarda yayi
ne yabani damar ganin abinda ke wajen dakin, sai
alokacin nagane ashe ba'acikin asibiti nake ba...
Karasowa yayi agabana yaci gaba da sanyaman
magani a wurarenda naji raunika ajikina, bayan
yagama, sannan yabi jikina yanade da bandeji,
lokacinda yagama aikinsa shine yayi dai dai da
dawowar wannan matashiyar yarinyar wadda
bansan ko wacece ba. Zama tayi akan wata
kujera
wadda take a gefen gadon danake kwance sannan
tafara magana dacewa "bawan Allah inaso
kafadamin ko kai waye kuma suwanene
sukayimaka wannan aikin? wani dogon lumfashi
naja sannan nabata labarin abnda yafaru dani a
filin jirgi tundaga farko har karshe.... Bayan
nagama ne sannan nakara da tambayarta, ita
wacece kuma a'ina kuka kawoni?... Sunana
haleematu "Badole bane kasan ko ni wacece"
tafada ayayinda take girgiza kanta, "amman inaso
kayadda dani, kuma kasanya aranka na
taimakeka
ne kawai kuma banida wata manufa bayan hakan,
kuma nan dakake gani gidan gona ne. "nakawoka
nanne, sbd bansan ko suwaye sukayimaka
wannan
abinba shiyasa naji tsoron shiga dakai cikin
gari.......
Yau kwana biyu kenan rabona da gida, hankalin
kowa ya tashi bama yan gidanmu ba kadai, hatta
mutanen unguwarmu suna chikin damuwa, anyi
sanarwar gidajen radio da t.v amman babu wata
magana mai dadi... Tafiya muke achikin mota
bamutsaya ko inaba sai acikin garin daura......
Zaune suke acikin wani makeken fallow tsararre
wanda yake daukeda abubuwan kayatarwa
dayawa,
Alhaji usman ne zaune shida matarsa hajiya
binta,
sun maida hankalinsu akan makekeyar t.v din
dake
makale ajikin bango. "alhaji kaidai bakada wani
channel din kallo sai kttv" matarsa ce tafada ta
fuskar tsokana, "hajiya kenan ai kallon kttv
yanada
amfani saboda kana gida zakasan halinda garinku
yake chiki dama kasarku baki daya... Shigowarmu
a falon ne yayi silar tsaidasu daga firar dasukeyi
tareda maido kallonsu akan kofa domin ganin
wa'anda ke sallama. Barka daxuwa diyata yar
auta
daga ke babu wata duk mai sonki shine nawa
makiyinki ko kallo bai isheni ba" hajiya binta che
takeyiwa diyarta wannan kirarin. Alhaji yadubeni
tareda bani umarnin inzauna, bayan nagama
gaishesu ne sannan alhaji yake tambayarta
wanene
wannan ko abokin karatunki ne? Wani murmushi
tayima mahaifin nata tareda fadar "a'a dady",
sannan ta sunkuyar dakanta tagayamasu duk
abnda yafaru, alhaji usman yanuna tausayi karara
a
fuskarsa..... Alhaji usman salisu zango mahaifin
haleematu ne, kuma haifaffen garin daura ne dan
asalin garin zango, babban dankasuwa ne wanda
yayi suna acikin garin katsina, matarshi daya
Itace
hajiya binta da diyarsu guda daya
haleematu......Muna nan zaune sai mukaji ana
sanarwa a cikin t.v... Kowa tsuru-tsuru yayi babu
wanda yayi wata magana saidai kallonda Alhaji
yakeyiman kamar mai niyar gano wani abu acikin
fuskata. Nikau hankalina yayi matukar tashi
domin
jin yanda ake nemana kamar kudi, sai alokacin
tunani na gaba daya yakoma akan gida, cikin
kaguwa da rawar jiki namike tareda yimasu
sallama
daniyar tafiya gidanmu saboda nasan hankalin
kowa a tashe yake yanzu sakamakon rashin
ganina... Cikin sauri nanufi hanyar fita waje,
muryar Alhaji usman ce ta ratsa kunnena "yaza'ai
katafi kai kadai batare da wani ba? Kaduba fa
kaga
yadda jikinka yake, yakamata ko wanka kayi kafin
katafi ko, yakarasa maganarsa da yanayin tausayi
karara a fuskarsa. A ranar nagane gidan "Alhaji
usman salisu zango" gida ne na mutunci kuma
sunsan darajar mutane. Bayan nagama komai
nayi
shirin tafiya, kamar wani dansu wanda suka haifa
ne zaya tafi, haka sukazo mukayi bankwana,
nayimasu godiya sosai akan taimakonda
dasukayiman...
Haleematu ce nagani tsaye a gaban mota
tanajiran
inxo mutafi, har ta tada mota sai ga hajiya tafito
dasauri tana kiran sunanta, chikin sauri
haleematu
tafito daga mota tanufi wurin mahaifiyarta domin
taji kiran me takeyimata, bayan sundan tsaya
suna
magana wurin minti daya, nidai bansan abinda
sukeyi ba, saida suka gama sannan hajiya tashige
gida haleematu kuma tayo guna fuskarta da
alamar
damuwa, tace " kayi hakuri yanxu dreba zaizo
yakaika gida, ni bazansamu damar kaika ba sbd
wasu dalilai" nidai ban nuna mata naji komaiba,
amman acikin zuciyata ina tambayar kaina
"meyasa tafasa kaini dakanta"... Tsayawa nayi
agabanta inayimata godiya akan abin alkhairinda
tayiman, murmushi kawai tayi tareda cewa " babu
komai na taimake kane saboda Allah bani bukatar
wata godiya daga gareka, nima wata rana zan iya
zuwa agunka domin neman taimako" haba
haleematu ni ai banida wani abu wanda zaki
nema
aguna. "hmm hausawa fa sunce ba'a san inda
rana
ke faduwa ba" tafada lokacinda daidai lokacinda
idanuwa na suka shiga acikin nata......
[11:02PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: Alkawari
5Part5....
babu komai na taimake kane saboda Allah bani
bukatar wata godiya daga gareka, nima wata rana
zan iya zuwa agunka domin neman taimako".
haba
haleematu ni ai banida wani abu wanda zaki
nema
aguna. Na kare maganta tareda yimata kallo
wanda yake nuna alamar mamaki "hmm hausawa
fa sunce ba'a san inda rana ke faduwa ba"
haleematu tafada tana kallona... inkau har akwai
abinda zaki nema aguna to na tabbata dakin
nema
nikuma zanyimaki koma minene.... Ahaka dai
mukayi bankwana, sannan tajuya fuskarta ixuwa
inda wasu mutane da suke zaune, da alama yan
aikin gidan ne, sannan takira " sadam! Sadam!!"
har sau biyu, sannan naji wani ya amsa "na am
hajiya" tache kakai wannan mutumen a katsina
"angama hajiya" yafada atakaiche... Daganan
muka
dauki hanya muka doshi garin katsina... Bamu
zame ko inaba sai unguwar tudun wada, sadam
dreba ya saukeni adai dai kofar gidanmu sannan
yakada motarsa tareda kugamata wuta.... Ina
shiga gida khadija ce nagani aduke tana hura
wuta,
sallamar danayi ne yasanya ta dago kanta. Da
gudu ta nufoni tayi tsalle tafada ajikina tareda
fadar yaya yaya, hawayenda suka zubo daga
idanuwanta ne suka hanata fadar wata magana,
saidai murmushi kawai takeyi wanda bayada
maraba da dariya, sai alokacin nagane hawayen
murna ne takeyi.. Khadija kanwata ce itace yar
auta a gidanmu, mu ukku ne mahaifinmu ya rasu
yabari, ni sai ahmad sannan khadija. Jin muryata
ne yasanya mahaifiyata fitowa daga daki cikin
murna muna hada ido da ita, kawai sai naga ta
duka ta daga hannuwa sama tanayima Allah
godiya
da yamaido mata danta. Bayan nazauna ne
umma
tanemi tasan abinda yafaru dani, nikuma
nakwashe
komai nafada mata tundaga farko har karshe...
Bayan nagama ne nake tambayarsu ina ahmad??
Sallamar da akayi itace ta hana su umma bani
amsar tambayar danayimasu... Wani dan saurayi
ne yashigo tareda tambayar "anan ne gidan su
ahmad bashir muhammad? Nace eh nanne, kafin
inkara wata magana, sai naji yakuma cewa "ana
bukatar ganinku da gaggawa saboda yanxu haka
yana emergency a general hospital sakamakon
mota data kadeshi" nan take muka dunguma
xuwa
asibiti. Dukda bawani nisa kedakwai ba daga
unguwar tamu xuwa asibitin ba amman saida
mukahau mota kirar (keke napep), wadda kanawa
suke kira da (adaidaita sahu). Shigarmu keda
wuya
muka dauki hanyar da zata sadamu da
emergency,
muna shiga muka nufi dakinda ake kai yan
accident, wani likita yataso yatarbi gabanmu
tareda
fadar muyi hakuri yanxu ana chikin dubashi idan
angama za'a yimaku magana, yanuna mana wasu
kujeru dake jere ajikin bango, muka zauna... Jim
kadan saiga wani dan tsamurmurin likita yafito
mai
wani katon kai, fuskarshi da alamar damuwa
karara kamar wanda yake shirin yin kuka, cikin
hanzari natashi nakarasa agunshi tareda
tambayarshi likita ya jikin nashi?? Sunkuyar dakai
yayi daga bisani kuma sai yadago kansa tareda
fadar.....
[11:04PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: Alkawari
6-7Part6......
Dago fuskarsa yayi, wadda tuni hawaye
sunyimata
kawanya sannan yakara dacewa, "munyi iyakacin
kokarinmu naganin mun ceci rayuwar wannan
bawan Allah, amman babu yadda zamuyi Allah
yariga ya yanke hukunci, saidai kawai aci gaba
dayimasa addu'a Allah yajikansa kuma ya
gafartamai!!!" yana gama fadin maganarsa kawai
yawuce gaba batareda yatsaya yin wani abuba,
Umma dake tsaye a gefenmu babu abinda ke fita
daga bakinta sai "Inna lillahi wa'inna
ilaihirraji'un"yayinda khadija kau kuka kawai take
rusawa abinta batama ko tinanin acikin mutane
take..... Koda yaushe umma acikin tinanin rashin
ahmad take, munyimata magana wannan tinanin
zai iya haifar mata da matsala, amman taki
saurarenmu sai abinda yayi gaba. Bayan rasuwar
ahmad da sati daya, inacikin daki sai naji karar
khadija, cikin sauri nafito domin inga abnda ke
faruwa. Umma ce nagani kwance abakin kofa
dasauri nakarasa na tambayi khadija lfy miya
faru?
Bantsaya jin amsa daga garetaba kawai nafita
waje
dasauri nasamo mota bamu zame ko inaba sai
asibiti... Batare da bata lokaci ba akashiga da ita
domin duba lfyarta.... Mundauki kamar awa guda
(1hour) zaune sai wata likita mace tafito, cikin
hanzari natashi na tarbeta tunkafin takaraso nake
tambayarta doctor tana ina? Dagamin hannu tayi
tana magana ahankali, "ku kwantar da hankalinku
munyi iya gwaje gwajenda zamuyi mungano cewa
jininta ne ya hau, saidai kuma faduwar datayi
tasamu matsala a kashin bayanta..." tanagama
magana sai na tambayeta, likita yanxu miye abin
yi? Batareda tabani amsa ba, sai dai ta nunamin
wani office tace inshiga likitan da zaiyimata aiki
yana nan ciki, Shiga nayi da sallama sannan
nazauna akan daya daga cikin kujerun da aka
tanada domin masu ganin likita... Zaune yake
hankalinshi kwance, ya dukar da kanshi a kasa
yanata wasu yan rubuce rubuce, daga bisani
kuma
yadago kanshi "kune wa anda kukawo wannan
matar?" yakarasa tambayarsa yana kallona ta
cikin
siririn farin gilashin dake sanye a fuskarsa. Gyada
kai nayi kamar kadangare cikin wata sarkakkar
murya nabashi amsa "eh nine" atakaice... Sannan
yace marar lafiyar tana bukatar aiki sakamakon
faduwa datayi akan wani abu wanda yayi silar
fitar
wani kashi daga cikin kasusuwan bayanta, kuma
kashin da yafita bai tsaya a'inda yakeba, ya bar
wurinsa yafada akan (spinal code) wanda
hakanne
yasanya bata iya yin komai dakanta, tundaga
kugunta har zuwa kafafuwanta sundaina aiki,
bazata iya yin komaiba, kuma kome zakayimata
bazatasan kanayi ba, daga kugunta xuwa abinda
yayi samnta har kanta nanne kawai zaka taba
taasan kataba. kuma bakomai bane yasanya
haka
sai wannan kashin daya je agun (spinal code) din
yayi kane kane. Yanxu dole sai anyimata aiki,
kuma ana bukatar kudi (naira dubu dari da
ashirin)
kuma tana bukatar aiki da gaggawa sbd kashin
yanada tsini, idan ba'ayi aiki da gaggawa ba zai
iya yin silar datsewar (spinal code) din, kuma
idan
tadatse babu maganar gyarawa saidai hukuncin
Allah. Nan take zufa tayoman lale marhaban, duk
ta mamaye jikina kamar wanda aka tsamo daga
cikin teku, tinani na kawai ina zansamo wa'annan
kudin, nan take natuna da chek dinda yasmeen
tabani lokacinda zata tafi makaranta, cikin azama
da kwarin guiwa na nufi gida, ina shiga na nufi
dakina, wanda yakoma kamar dakinda mahaukata
ke kwana, kana shiga wasu ledoji ne bakake da
farare, zasu rinka yimaka barka daxuwa, daga
gefen hannun dama kuma wasu kujeru ne
murgudaddu wa'anda suke shirin burmawa da
duk
wanda yazaunasu batareda ixni ba, gefen haggu
kuma wani teburi ne wanda yake kama da teburin
masu shayi, a samanshi wata tsohuwar t.v ce
black and white wadda nima bansan shekarunta
ba,
daga kasa kuma wata shekararriyar radio ce
wadda marhin gidan kaset dinta ya dade da tafiya
yawon duniya, daga ganin radion zaka fahimci ita
kanta ganimarta aka ciwo, daga sama kuwa wata
fanka ce take juyawa wadda take barazanar
fadoma dukwanda ya isheta da kallo..... Tsalle
nayi
nafada akan katifata wadda batada maraba da
kasa sbd tsabar tauri, wata kura ta tashi tareda
wasu kwari, suka tashi suna kuka da alama Allah
ya'isa sukeyimin saboda nazo na takuramasu...
Dan danan nadaga fillow na inda na ajiye chek
din,
amman abinda nagani shine yayi matukar
tadamin
hankali, nakara murje idanuwa, a tinani na wai
idanuwa nane basu ganemin dai dai ba, nasanya
hannu na laluba amman shiru babu chek babu
alamarsa.... Nan take maganganun likita suka
rinka
ziyarar kwakwalwata, "dole sai anyi sauri
anyimata
aikinnan nanda kwana ukku, idan har aka dauki
lokaci ba'ayiba, to zaku iya rasa mahaifiyarku"
cikin sauri namike tsaye nasanya takalma na,
nafice daga gidan......
7Part7...
Bayan nafice daga gidan ina cikin tafiya nafara
tinani " to waye zai dauki wannan chek dinda na
aje, bayan babu wanda yasan nayi ajiya agun?"
wani bangaren na xuciyata kuma ya shaidamin
"kadai koma kakara dubawa" banyi kasa a guiwa
ba wurin juyawa, nadauki hanyarda zata kaini
gida
a saukake... ina shiga nafara bincika ko ina acikin
dakin, ina cikin dubawa ne naga wasu takaddu
ajikin bango, dasauri nakarasa, abinda nagani
shine yayi silar zubar hawayena batareda nasani
ba, chek dinda yasmeen tabani ne amman saidai
duk an ciccireshi da alama bera ne yaci rabonsa
yabar sauran... Fitowa nayi daga gida nakoma
bin
gidajen mtane wa anda nasani ina fadamasu
matsalata domin su taimakamin, atinanina zan
iya
hada kudin ta wannan hanyar, amman duk wanda
natunkara da wannan maganar sai shima
yanufoni
da matsalar iyalinsa, haka nayini yawo acikin gari
amman ba'asamu abinda ake nema ba...
magriba nayi nanufi asibiti bantsaya ko inaba sai
wurin likita. Shiga nayi office din natarar akwai
wasu mutane wa anda suke magana dashi. Wuri
nasamu nazauna domin jiransu, jikina duk yayi
sanyi hankalina atashe na hada kaina da guiwa
inata tinani, muryar likitance ta doki dodon kunne
na wanda hakan yayi silar maidoni daga duniyar
tinanin da na afka. "inafatan dai ka hado kudinda
za'ayi aikin gaba daya?" likita ne yake tambaya
ta,
nidai bance komai ba, saidai mikewa nayi tareda
sanya hannu na acikin aljihu. Kudinda na fiddo
shine yayi matukar ba likita mamaki wanda
yasanyashi bude hangamemen bakinshi tareda
fadar "kanada hankali kuwa?, amfada maka ana
bukatar kudi naira dubu dari da ashirin, amman
ka
kawoman dubu biyu, me za'ayi da dubu biyu?"
yakarasa maganarsa wadda take kama da fada.
Cikin wata sarkakkar murya nake fada, dan Allah
kutaimaka kuyimata aikinnan wlh wa'annan kudin
sune kadai ke garemu kuma bamuda kowa
agarinnan dan Allah kutaimaka wlh zanbiya kudin
koda bayan... Tsaidani yayi da hannunsa, sannan
yaci gaba da magana "wannan ka'idace ba'ayin
aiki sai anbiya kudi duk irin tsananin ciwonda
mutun ke fama dashi" ya ida maganarsa yana
kallon fankar da keta faman juyawa makale
saman
office din domin bayarda iska. Ahaka natashi cikin
kyarma nanufi hanyar fita waje, inazuwa bakin
kofa
naji muryar likitan yana fadar "daga gobe duk
abinda yafaru da mahaifiyarka kada kazargi kowa
kazargi kanka", kawai ficewa nayi ko juyowa
banyiba, haka nanufi dakinda aka kwantarda
umma,
natarar da ita kwance duk an daureta da wasu
karafa wanda suka tokare ko ina daga jikinta,
batada damar da zata juya kanta balle tayi wani
motsi, koda yaushe idanuwanta suna kallon
sama,
abinci kam saidai abata mai ruwa ruwa wanda
zaya wuce batareda da taba hakoranta wahala
ba.
Inanan nida khadija har akayi kiran sallar isha'i,
natashi nayi alwala nanufi masallaci nayi sallah
sannan naroki Allah yafiddamu daga halinda
muka
tsinci kanmu...
Tafiya nike batareda nasan inda zanje ba, duk
inda
naga taron jama'a sai inje wurin infadamasu
matsala ta domin sutaimakamin, cikin dan lokaci
kankane nakoma kamar mahaukaci, hatta
takalman
dake sanye akafata sunyi spanner saboda tsabar
tafiya kasa,
[11:06PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: 7Part...
Hatta takalma na sunyi spanner saboda tsabar
tafiya kasa. ina tafiya ina tsayawa aduk inda
naga
mutane, har Allah yakawoni awurin wani shago,
nazo agaban shagon natsaya ina duba jikina
yadda
nakoma kamar mahaukaci, wata murya naji daga
cikin shagon tana fadar kai me kakeyi anan? Ina
dubawa sai naga wasu yan samari ne su biyu,
karasawa nayi abakin kofar shagon natsaya ina
fadamasu matsala ta domin sutaimakamin, sai
daya daga cikin samarin yacemin
"kai malan dallah wuce katafi inda zaka, wa
zakazo kayima karya anan?"
sai dan uwan nasa yake cewa, "haba farouq miye
haka, idan bazaka iya taimaka maiba ai
baikamata
kacimar mutunci ba, ko yadda kaganshi haka ai
kasan yana bukatar taimako"
acikin raina nace lallai wannan bai biyo halin
masu
irin sunansa ba, duk farouq dinda nasani yanada
tausayi tareda son jama'a... Turani naji anyi
wanda
hakan yasanya faruwar faduwata kasa warwas
kaina yakalli sama, daga saman shagon naga
anrubuta BIN YUSUF TEXTILE.. Farouq ne ya
tureni
yana fada cewa muhammad irin wa annan
mutanen ba abin tausayi bane yawancinsu duk
makarya tane...
"meyafaru ne?"
wata murya ce mai zaki naji tayi wannan
tambayar... Sunkuyar dakaina nayi kasa sannan
nafada mata duk abinda ke faruwa, cikin yanayin
tausayi take magana
"wayyo bawan Allah danyi hakuri bara insayi
wasu
kaya anan sai mutafi asibitin ko"
cikin mamaki nadago kaina naiduba ixuwa gareta,
kyakkyawar macece budurwa kuma bawani tsayi
garetaba sosai amman bazaka cemata gajera
ba...
Juyawa tayi tashiga shagon. cikin mamaki naga
farouq yanayi mata ladabi kamar uwarda
tahaifeshi, "hajiya barka daxuwa me ake so ne,
ankawo sababbin kaya daga dubai" cikin raina
nace, duniya kenan idan bakada kudi kazama abin
wulakantawa agun kowa, bayan tagama sayayyar
da zatayi ne tasanya farouq yadaukarmata kayan
xuwa cikin mota, sannan tabani umarnin inshigo
daga ciki, dukawa nayi na tattara takalmana na
matsesu a hammata ta sannan nashiga motar,
Dubana tayi kamar zatayi dariya sannan takara
dacewa "miye haka? Sanya takalmanka mana"
nace hajiya ai kar inbatamaki mota, murmushi
tayi
tareda fadar " haba kai kamardai wani bakauye
sanya takalminka mana, kuma ba sunana hajiya
ba, sunana sa'adiya amman zaka iya kirana da
(sady)" cikin kwarewa tafizgi mota muka nufi
asibiti... Muna zuwa muka kutsa cikin asibiti,
sady
ta tsaida motarta aguraben da aka tanada domin
ajiye motoci, cikin hanzari muka fito daga cikin
motar muna takawa akasa domin karasawa a
office din likita, ina gaba itakuma tana bina a baya
har mukaje batareda wani bata lokaciba akayi
magana, nan take tarubuta chek dauke da tsabar
kudi naira dubu dari da ashirin arubuce taba likita
tareda bashi umarnin agaggauta yima umma aiki,
batareda bata lokaciba akashiga da ita domin yin
aikin...
Part8...
Bayan anyima umma aiki da sati guda, tana
kwanche akan gado, daga gefenta khadija ce
zaune, a gudan gefen kuma nine zaune akan wata
kujera dukkanmu babu wanda yayima wani
magana
saidai kallon dakin mukeyi da mutanenda ke
shiga
suna fita, sallamar da akayimamu itace tajanyo
hankalinmu zuwa inda muryar tafito, inajuyawa
muka hada ido da ita! Sady ce take tahowa inda
muke ahankali take tafiya kamar tana jin tausayin
taka kasa, mikewa nayi tareda yimata sannu
daxuwa sannan nabata wuri ta zauna, cikin wata
siririyar murya take magana
"sannunku ya maijikin"
khadija ce tayi carab ta'amsa mata "mai jiki
dasauki sosai harma tafara zama dakanta"
"Alhamdulillahiai daman haka ake bukata" sady
tafada yayinda takeyin wani murmushi wanda
yayi
matukar fiddo kyawon fuskarta, sannan taduka
tayima umma sannu nandai suka gaisa, umma
tayimata godiya sosai akan abin alkhairin da
tayimana, bayan sady tadauki kamar minti 30
sunata firarsu ita da khadija, sannan tamike
sukayi
bankwana daniyar zata tafi gida. Tana tafiya
nima
sai nabi bayanta daniyar inyimata rakiya, ina fita
bakin kofa sai nahadu dawani abokina anan
natsaya muka gaisa itakuma tawuce gaba...
Bayan mungama gaisawa ne muka rabu nikuma
nakarasa agun sady, tajingina ajikin bakar
motarta
kirar 406 prestige, bakaramin kyau sady tayiba
alokacin, saboda wasu bakaken kaya ne tasanya
irin wanda ake cema after dress, sannan tadaura
wani jan kyalle akanta wanda nakasa ganewa
shin
kallabi ne ko mayafi, ga wasu takalma tasanya
daga ganinsu kasan badaga nigeria sukeba,
kwalliyar sady tayi dai dai da yanayin da akeyi a
garin namu, saboda wani yanayi ne kamar
lokacin
sanyi kuma kamar za'ayi ruwa, babu rana saidai
wani iska iska da akeyi garin yayi lullumi kamar
da
yamma, amman idan kaduba agogo alokacin
zakaga karfe goma na safiya... Bari
intakaicemaku
anan saboda idan natsaya bayyanamaku komai
sai
mucinye dan lokacin batareda munyi komai ba.
Karasowa nayi agabanta tareda fadar hajiya ranki
ya dade,
wata harara ta wurgamin tareda fadar "banace
kadaina kirana hajia ba?"
sannan nadan duka nace ayi hakuri sady baza'a
karaba...
Dauke kanta kawai tayi tareda fadar "daman
nazone infadamaka gobe zantafi abuja kuma ba
lallai bane indawo saboda acan zanci gaba da
zama gidan kanen mahaifina".
Hankalina yayi matukar tashi saboda sady itace
tadauki nauyin komai a asibitinnan hatta kudin
magani itace take bayarwa, lokaci guda kuma
tunanina yajuya acikin duniya, natambayi kaina,
ina
zansamu kudinda zanci gaba da tafiyar da umma
har a sallameta, maganar sady ce tamaidoni
daga
duniyar tinaninda na afka
"amsa wannan chek ne kaje banki kafidda sai
kuyi
amfani dasu, idan kuma basu isa ba ga number
wayata zaka iya kirana"
tamikomin wani dan kati mai rubuce da lambarta
har adress dinta.... Bansan lokacinda naduka
agaban sady ba inayimata godiya,
dasauri taja baya tareda fadar "subhanallah Miye
haka? tashi tsaye mana" da alamar mamaki
karara
a fuskarta.
Mikewa nayi tareda fadar bansan da irin kalmar
da
zangodemaki ba sady Hakika samun.... Dagomin
hannu tayi alamar inyi shiru hakanan sannan taci
gabada magana
"kar kadamu na taimakekane saboda Allah bawai
saboda wani abuba, kuma taimako yazama dole
akanmu saboda manxon Allah yayimana umurni
da
musulmi yasoma dan uwansa musulmi abinda
yake
soma kansa, nima wata rana zan iya xuwa
wurinka
naiman taimako" tana xuwa nan da zancenta naji
wani irin faduwar gaba, lokaci guda kuma natina
da
haleematu wadda itama tafadamin irin wannan
kalmar "zan iya zuwa agunka neman taimako"
kwalwata taci gaba da maimaita kalamin... Wani
bangaren na xuciyata kuma sai yatunomin da
abinda yasmeen tafadamin "karikemin soyayyata
amana har lokacinda zandawo daga
makaranta"...
Hannun sady ne naga yagifta akan idanuwa na
hakanne yasanya nadawo daga tinaninda nakeyi,
"tinanin me kakeyi" tafada tana kallona, babu
komai nafada alokacinda najuyo duba agunta...
Shigewa mota kawai tayi tareda dagomin hannu
lokaci guda kuma takuga ma motar wuta tafice
daga asibitin.....
A bangaren gidan alhaji jafar muhammad kuwa,
Saura wata daya yasmeen tadawo daga
makaranta, hakanne yasanya aunty ta tunkari
alhaji
jafar da maganar tanaso a hada auren yasmeen
da
danta abba! Tabbas alhaji jafar yaji dadin
shawarar
da aunty bilky tabayar saboda shi maison
xumuncine kuma yanason yan uwansa sosai.
Acikin
xuciyar aunty bilki kau bahaka abin yakeba,
tanada
wata manufa can tata daban ta kashin kanta.......
[11:08PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: Alkawari
9Part9...
Bayan anyima umma aiki da sati guda, tana
kwanche akan gado, daga gefenta khadija ce
zaune, a gudan gefen kuma nine zaune akan wata
kujera dukkanmu babu wanda yayima wani
magana
saidai kallon dakin mukeyi da mutanenda ke shiga
suna fita, sallamar da akayimamu itace tajanyo
hankalinmu zuwa inda muryar tafito, inajuyawa
muka hada ido da ita! Sady ce take tahowa inda
muke ahankali take tafiya kamar tana jin tausayin
taka kasa, mikewa nayi tareda yimata sannu
daxuwa sannan nabata wuri ta zauna, cikin wata
siririyar murya take magana
"sannunku ya maijikin"
khadija ce tayi carab ta'amsa mata "mai jiki
dasauki sosai harma tafara zama dakanta"
"Alhamdulillahiai daman haka ake bukata" sady
tafada yayinda takeyin wani murmushi wanda
yayi
matukar fiddo kyawon fuskarta, sannan taduka
tayima umma sannu nandai suka gaisa, umma
tayimata godiya sosai akan abin alkhairin da
tayimana, bayan sady tadauki kamar minti 30
sunata firarsu ita da khadija, sannan tamike
sukayi
bankwana daniyar zata tafi gida. Tana tafiya
nima
sai nabi bayanta daniyar inyimata rakiya, ina fita
bakin kofa sai nahadu dawani abokina anan
natsaya muka gaisa itakuma tawuce gaba...
Bayan mungama gaisawa ne muka rabu nikuma
nakarasa agun sady, tajingina ajikin bakar
motarta
kirar 406 prestige, bakaramin kyau sady tayiba
alokacin, saboda wasu bakaken kaya ne tasanya
irin wanda ake cema after dress, sannan tadaura
wani jan kyalle akanta wanda nakasa ganewa
shin
kallabi ne ko mayafi, ga wasu takalma tasanya
daga ganinsu kasan badaga nigeria sukeba,
kwalliyar sady tayi dai dai da yanayin da akeyi a
garin namu, saboda wani yanayi ne kamar lokacin
sanyi kuma kamar za'ayi ruwa, babu rana saidai
wani iska iska da akeyi garin yayi lullumi kamar
da
yamma, amman idan kaduba agogo alokacin
zakaga karfe goma na safiya... Bari
intakaicemaku
anan saboda idan natsaya bayyanamaku komai
sai
mucinye dan lokacin batareda munyi komai ba.
Karasowa nayi agabanta tareda fadar hajiya ranki
ya dade,
wata harara ta wurgamin tareda fadar "banace
kadaina kirana hajia ba?"
sannan nadan duka nace ayi hakuri sady baza'a
karaba...
Dauke kanta kawai tayi tareda fadar "daman
nazone infadamaka gobe zantafi abuja kuma ba
lallai bane indawo saboda acan zanci gaba da
zama gidan kanen mahaifina".
Hankalina yayi matukar tashi saboda sady itace
tadauki nauyin komai a asibitinnan hatta kudin
magani itace take bayarwa, lokaci guda kuma
tunanina yajuya acikin duniya, natambayi kaina,
ina
zansamu kudinda zanci gaba da tafiyar da umma
har a sallameta, maganar sady ce tamaidoni daga
duniyar tinaninda na afka
"amsa wannan chek ne kaje banki kafidda sai kuyi
amfani dasu, idan kuma basu isa ba ga number
wayata zaka iya kirana"
tamikomin wani dan kati mai rubuce da lambarta
har adress dinta.... Bansan lokacinda naduka
agaban sady ba inayimata godiya,
dasauri taja baya tareda fadar "subhanallah Miye
haka? tashi tsaye mana" da alamar mamaki
karara
a fuskarta.
Mikewa nayi tareda fadar bansan da irin kalmar
da
zangodemaki ba sady Hakika samun.... Dagomin
hannu tayi alamar inyi shiru hakanan sannan taci
gabada magana
"kar kadamu na taimakekane saboda Allah bawai
saboda wani abuba, kuma taimako yazama dole
akanmu saboda manxon Allah yayimana umurni
da
musulmi yasoma dan uwansa musulmi abinda
yake
soma kansa, nima wata rana zan iya xuwa
wurinka
naiman taimako" tana xuwa nan da zancenta naji
wani irin faduwar gaba, lokaci guda kuma natina
da
haleematu wadda itama tafadamin irin wannan
kalmar "zan iya zuwa agunka neman taimako"
kwalwata taci gaba da maimaita kalamin... Wani
bangaren na xuciyata kuma sai yatunomin da
abinda yasmeen tafadamin "karikemin soyayyata
amana har lokacinda zandawo daga
makaranta"...
Hannun sady ne naga yagifta akan idanuwa na
hakanne yasanya nadawo daga tinaninda nakeyi,
"tinanin me kakeyi" tafada tana kallona, babu
komai nafada alokacinda najuyo duba agunta...
Shigewa mota kawai tayi tareda dagomin hannu
lokaci guda kuma takuga ma motar wuta tafice
daga asibitin.....
A bangaren gidan alhaji jafar muhammad kuwa,
Saura wata daya yasmeen tadawo daga
makaranta, hakanne yasanya aunty ta tunkari
alhaji
jafar da maganar tanaso a hada auren yasmeen
da
danta abba! Tabbas alhaji jafar yaji dadin
shawarar
da aunty bilky tabayar saboda shi maison
xumuncine kuma yanason yan uwansa sosai.
Acikin
xuciyar aunty bilki kau bahaka abin yakeba,
tanada
wata manufa can tata daban ta kashin kanta.......
[11:10PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: Alkawari
Part10...
Zaune suke su biyu akan maka makan kujerun
dasuke zagaye da falon, aunty bilky ce tareda
danta abba tsawon mintuna biyu babu wanda
yayi
magana a tsakaninsu, kwalbar mentos ce a
hannunsa yana kurba lokaci zuwa lokaci yana
kallon umman tasa wadda take zaune kamar tana
tinanin wani abu...
Abba ne yakatse shirun da cewa, umman gani
nazo wani abu yafaru ne? yatambayi ummansa
lokacinda yake daga kwalbar lemu yana tararawa
acikin bakinsa,
aunty bilky tayi ajiyar zuciya sannan tafara
magana ahankali kamar wadda take magana da
mahaifinta, "abba wata magana ce zanfada maka
kuma inaso kanatsu saboda baniso asamu
matsala
acikin wannan aikin",
sannan ya gyara zamansa ya ajiye kwalbar lemun
dake hannunsa "to umma inajinki"
"kasandai yasmeen takusa kammala karatunta,
baifi wata daya ba tadawo gida"
"eh umma haka naji su yaya usman suna fada"
yafada tareda daura kafarsa daya akan daya,
"to narigaya nayima alhaji maganar aurenka kaida
yasmeen"
dasauri ya tube bakin gilashin dake sanye a
fuskarksa yafara magana cikin yanayi wanda yake
nuna alamar mamaki "umma aurefa kikace"
tace eh aure kuma ba yardarka nazo nemaba,
nafadamaka ne kawai saboda yakamata kasani,
ko
kanasonta ko bakasonta ita zaka aura saboda
bazaka lalatamana aikinda nadade inayi ba
shekara da shekaru"
"to umma...."
Katseshi tayi da magana "banason jin wata
magana taka kaji abnda nafada maka" ta tashi
tafice daga falon tabarshi nan zaune yanata
karanta wasikar jakki......
Abba mutun ne wanda yataso cikin gata
mahaifiyarshi tanasonshi matuka haka ma
mahaifinshi, amman abba baidamu da addininsa
ba, hatta sallah bazai iya fadamaka yadda
akeyintaba, bayada aiki sai bin abokanan banza
duk yan tsotse tsotsen nan nazamani babu wanda
abba bayayi, saidai kuma duk irin rashin jinsa
baya
neman mata, hakanne yasa yasmeen tatsani abba
jininsu baizo daya ba.........
Zaune muke akan tabarma mahaifiyarmu tana a
tsakiya daga gefenta kuma khadija ce, dayan
gefen
kuma nine nake zaune munata fira kamar yanda
muka saba, munacikin fira khadija tayima umma
wata tambaya
"umma wai bamuda wasu yan'uwa acikin
garinnan?"
tambayarce tasanya dukanmu mukayi tsit umma
kuwa sunkuyar dakanta kawai tayi tana kallon
kasa batareda tayi wata magana ba, saida khadija
takara magana akaro nabiyu
"kinji umma bamuda yan'uwa anan garin??"
wani nishi tayi wanda bayada maraba da ajiyar
zuciya sannan tafara magana "khadija mahaifinku
malan bashir badan asalin kasar nigeria bane,
kamar yadda yafadamin. Dan wata kasace wadda
ake cema (seraliyon) su ukku ne agun mahaifinsu
(kakanku) subiyu maza sai mace guda daya. Tun
suna yan yara wani fadane ya barke acikin kasar
wanda bansan abinda yatada fadanba, lokacin
mahaifinku shekararshi biyar, sai yayanshi yanada
shekara bakwai, sai yar kanwarsu tanada shekara
ukku. Sannan umma tagyara zama tachi gaba da
bamu labari.... Ankashe kowa acikin danginsu
sukadai ne sukarage sai yawo acikin gari, duk
inda
zasuje yayan mahaifinku shine yake goya yar
karamar yarinyar shikuma mahaifinku yana binsu
a
baya. Suna cikin wannan halin na uquba, sai Allah
yakawo sojojin nigeria daniyar taimakawa, anan
aka hada dasu aka kwashe. Daga seraliyon zuwa
nigeria sai antsallaka ruwa, lokacinda akaxo
wurin
kwale kwale za'a hau domin tsallakowa zuwa
nigeria, to ananne suka rabu, basu samu damar
hawan kwale kwale guda daya ba su ukkun,
saidai
yayansu yahau shi da yar kanwarsu macen,
daman
goye take abayansa, sai shikuma mahaifinku aka
daurashi akan wani kwale kwalen, tundaga
lokacin
suka rabu basukara haduwa ba.....
Mahaifinku malan bashir awurin mahaifina yayi
karatu saboda mahaifina babban malami ne
akasar
maiduguri, shine yarike mahaifinku yadaukeshi
tamkar danda yahaifa saboda yasan bashida
iyaye... Nida mahaifinkiu munshaku dajuna tun
muna kanana saboda ko makaranta zanje idan
batare dashiba to bana zuwa, duk abinda zamuyi
tare mukeyi bacci ne kadai yake rabamu, ganin
hakane yasanya mahaifina yahadani aure da
mahaifinku... Munanan zaune a maiduguri wani
fada yatashi, rikichin yan boko haram, wannan
fadan ne yayi silar rasa yan uwana hadda
mahaifana gaba daya, kuma shine yayi silar
dawowarmu anan garin katsina, bamu dade da
dawowa ba mahaifinku yarasu yabarmin ku."
umma tana zuwa adai dai nan da zancenta sai
tamike tashiga daki, bayan wani dan lokaci sai
tadawo dawani dan akwati ahannunta, tabude
tafiddo wani zobe ta mikomin sannan tacemin
"wannan zoben mahaifinka ne yace inbaka a duk
lokacinda ka mallaki hankalinka, kuma wannan
zoben yanada matukar tarihi a rayuwarka, saboda
shikadaine mahaifinku yatsira dashi lokcinda
rikicin
seralion yabarke, daman al'adar gidansu ce,
dukwanda aka haifa sai anbashi irin wannan
zoben" tana mikomin nikuwa na kargamashi a
hannuna......
Part11...
Tana mikomin nikuwa nakargamashi ga hannuna
ina dubar zoben, fari ne kirar azurfa, bawata
kwalliya ke gareshi ba saidai zanen wani tambari
dake a saman zoben, tabbas naji dadin wannan
kyauta saboda ko babu komai zanrika tunawa da
mahaifina aduk lokacinda nadubi wanga zobe...
Ranar alhamis ina tafiya akan hanya da misalin
karfe 03:00pm na agogo inata sauri zannufi gida
ga rana sai kwalarmin tsakiyar kai takeyi, wata
mota ce naga taci birki a gabana, ina karasawa
sai
naga dreban gidansu yasmeen ne wanda naji
suna
kira da (dan balya), bude marfin motar yayi
tareda
fitowa waje muka gaisa, bayan mungaisa ne yake
fadamin yasmeen ta kammala karatunta kuma
gobe ma zata dawo gida nigeria insha Allahu. Ba
karamin dadi najiba maganar da dan balya dreba
yafadamin, bayan mungama magana ne yace
inhau
yaragemin hanya zuwa gida, haka kuwa akayi
nashiga muka lula zuwa gida...
Zaune suke acikin falo suna shawarwarin yadda
bikin yaran guda biyu zaya kasance, Alhaji jafar
ne
shida uwar gidansa tareda aunty bilky... "Sannan
alhaji yadubi aunty bilky yace kinyima abba
maganar damukayi dake?" tadan sunkuyar
dakanta
tareda fadar "eh Alhaji nafadamai, kuma ya
amince
tareda yimaka godiya akan abin alkhairin da
kayimasa" sannan alhaji yayimata nuni da kofar
fita daga falon yana fadar "kirawomin abba",
mikewa tayi tareda niyar fita takirawoshi, turo
kofar da akayi itace ta tsaidata. Abbane yakunno
kai batareda yayi sallama ba, dago kanshi dayayi
yaga su alhaji shine yasanyashi yin sauri yabude
baki yayi sallama, yazo gaban alhaji ya duka
yagaishe shi sannan yatashi yanufi hanyar
dakinsa, Alhaji ne yakira sunansa tareda bashi
umarnin yadawo yazauna yanada maganar da zai
fadamai, cikin ladabi kamar mutumin kirki yazo
yazauna akan kafet din dake malale a tsakiyar
falon, "mahaifiyarka tagayamaka maganar
damukayi da ita ko" alhaji yake tambayar abba,
alokacinda abba shikuma yake duke yana wasa
da
gashin kafet din tsakar dakin, sannan yace "eh
alhaji tafadamin" to "Alhamdulillahi" alhaji yafada
daga bisani kuma yafidda wani iska daga bakinsa
yadubi abba yace "idan babu wata matsala ka
tashi kawai katafi", sannan abba yamike yanufi
hanyar dakinsa, koda yashiga daki sai aunty bilky
tabishi, tana shiga batareda yabarta tayi magana
ba, yafara tambayarta " haba momy meyasa
kukeson hadani da yasmeen ne?" karasowa tayi
agabanshi ta dafa kafadarshi, sannan tace zauna
dana zanyimaka bayanin komai, sannan tadago
kanta tafara magana ahankali yadda na waje
bazai
iya jin abnda take fada ba "abba kasan Alhaji
yanada dukiya sosai, kuma yanada kadarori
dayawa a fadin kasarnan" girgiza kai abba yayi
alamar "eh hakane" sannan aunty bilky taci gaba
da koramai bayani "kaga ni kanwar alhaji ce
kaikuma danane nacikina, alhaji kawunka ne,
yanxu idan alhaji yakwanta yarasu kana tinanin
zamu samu wani kaso daga cikin dukiyarsa?
Daga
ranarda yarasu babu sauran wani jin dadi
dayaragemana duka dukiyarshi za'a tattara aba
wannan matar tashi da 'ya'yanta" Nanfa abba
yafara murmushi alamar yagane inda mahaifiyar
tashi tanufa, daman halin nasu duk daya ne,
sannan yadubi ummansa yace "to momy idan na
auri yasmeen sai ayi yaya kenan" wata dariyar
keta tayi sannan tace "yauwa dana kagane inda
nanufa kenan" yadubeta yace "eh mana momy
mu
duniya ai gaba muka bata ba baya ba, amman
wani hanzari ba gudu ba, koda na auri yasmeen
alhaji yarasu bawani kason kirki zamu samuba
saboda yanada yara maza har guda biyu kuma
kinga yasmeen mace ce kasonta dan kadan ne"
sannan aunty bilky ta dubeshi tace "to kana
tinanin idan ya mutu zamu barsune suma suci
gaba dashan iskan duniya?" sannan abba yadan
gyara zama yakurama ummansa ido kamar yana
neman wani abu akan fuskarta daga bisani kuma
yace umma kina nufin... Yayi mata nuni da
yatsanshi akan jijiyar dake gefen wuyansa yaja
layi
zuwa jijiyar dake gudan gefen wuyanshi" sannan
ta
gyadamashi kai alamar "eh" daga bisani kuma
tace, basu kadai bama, duk wanda yatsaremana
hanya shima zai bakunci lahira.....
[11:11PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: Alkawari
Part12...
kayana nadauko wa anda nafi jidasu nasanya,
nanufi gdansu yasmeen ina tafiya ina sake sake
acikin zuciyata, wani sashen nazuciyata kau cike
yake taf da farin ciki... Batareda bata wani lokaci
ba na isa bakin kofar gdan, nayima malan
zayyana
mai gadi sallama kamar yadda nasaba, aduk
lokacinda nazo gun yasmeen, wurin mai gadi nake
tsayawa inyimata waya sannan tafito ta iskeni...
Dasauri tafito tanufo inda nike, ni kaina bansan
lokacinda namike tsaye ba, amman abin mamaki
babu wanda ya iya bude baki yayima wani
magana
saidai kallon kallo kawai mukeyiwa juna har
kimanin tsawon mintuna biyu. Sai alokacin
nakauda idanuwana daga cikin idonta, tareda
sunkuyar dakaina, nace mata barka da dawowa,
sannan tayi wani kayataccen murmushi wanda
yakusa fiddani daga cikin hayyacina tareda fadar
"yusuf kaine yau agabana?" sannan nima narama
murmushinda tayiman, tareda binta muka nufi
inda
muka saba zama domin fira... Duk wanda
yaganmu alokacin yasan muna cikin farin ciki
marar misaltuwa, muna cikin firarmu irinta
masoya, nacemata darling wlh cikin yan
kwanakinnan ina cikin damuwa, tace me yafaru
dakai ne? nadubeta nace gaskiya darling wani
mafarki na tabayi wai ansaceki...Takuramin ido
da
alamar mamaki "ansaceni?"... Haba sweety
wannan mafarkin shaidan ne kawai ka kwantarda
hankalinka.. Sannan nagyara zama tareda fadar
shikenan abar wannan maganar... Bara
intambayeki mana darling don karwai kiga kinje
kasar turawa kindawo nikau haryanxu ko kano
banwuce ba, kinsanni malaminkine ko kinaso ko
bakiso, nakarasa maganata ina murmushi da
alamar wasa a fuskata... Ta kalleni tareda rama
murmushinda nayimata, tace "dama ai banyima
gardamaba ina saurarenka". Nadan gyara zama
nace, minene yafi komi kwarjini a duniya?.
Murmushi tayi mai kama da dariya, alamar ta
harbo jirgina "haba waye baisan wannan amsarba,
ai tun acikin wani film din hausa, na san wannan
amsar"... Tana zuwa nan nakatseta ta magana,
kenake saurare ki bani amsar kawai ba sai
kintsaya yin wani dogon sharhiba... amsarka
itace
"wata daren 14" ko bahaka bane ". kwarai kuwa
wannan haka yake, ashe dai tawan da sauranta...
Wani farr tayiman da idanuwa tareda fadar
"mikake
nufi da saurana?" ina nufin kina da sauran ilimin
gargajiya. Nafada tareda nunata da dan yatsa
na...
ashema! To ni bari inyi maka tawa tambayar...
Nakalleta da alamar mamaki nace, harkinada
abinda zaki tambayeni wanda bansaniba?.. bari
cikamani baki, abinda nakeso intambayeka shine,
minene yafi komidadi a duniya?, lokacin nacire
hulata nace tabdi! Amma wannan ke kika kirkiro
abinki ko... Ta kalleni tace "ko kadan, nima acikin
film din hausa najita"... Sannan nadan nisa nace,
to indai hakane bari inkokarta ingani, wannan
inaganin shine soyayyen naman kaza da
yanshila... Kawai tawani bushe da dariya tana
tafa
hannuwa, "wane irin naman kaza kuma, idan
awajenka tanada dadi ai awajen wani batada dadi
ko... Sannan nakara cewa, ina ganin amsar shine
mutum ya gama da iyayensa lafiya ko?, tayiman
wani irin kallo alamar tayi kamu tareda fadar
"gaskiya bahaka bane"... Nakara gyara zama
nace,
to inaganin aurene... ko kadan ba aureneba, wani
auren ai bana dadi baneba na wahalane, takarasa
maganarta tana wasa da hannunta... Dadai
narasa
amsarda zanbata sai nace, to ni nabaki gari!, tayi
wata dariyar keta tareda fadar "yauwa nima
zanrama, kaga nima yanzu nazama malamarka
tunda nayimaka tambaya ka gaza amsawa...
Natabe baki nace, eh! Kedai nake saurare, kilan
ma
ko ke bakisan amsar ba... "wannan bakomai bane
illa rashin sanin ranar da zaka mutum" takarasa
maganarta tanayiman gwalo (tongue)... Nakalleta
daga bisani kuma nace, rashin sanin ranar da
zanmutu?... "ko kana tababane"... Nadan karkace
nace, kumafa gaskiya inajin hakane, domin idan
mutum yasan ranarda zai mutu tokullum
hankalinsa atashe yake kuma zaita kidayar
ranakunsa, kullum yace saura kwana kaza kinga
saboda zullumi duk yabi yarame... Tadanyi dariya
"to kagani ko"... Muna cikin fira sai ga usman
yayan yasmeen yazo zai shiga gda.. Usman
yayan
yasmeen ne yana bala'in son kanwarsa kuma
yana
son duk abnda takeso, shiyasa jininmu yahadu
dashi cikin dan kankanen lokaci.......
[11:13PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: Alkawari
Part13.....
Usman yayan yasmeen ne yana matukar son
kanwarsa kuma yana son duk abnda takeso, haka
zalika ya tsani duk abinda zai bakanta mata rai,
shiyasa jininmu yahadu dashi cikin dan kankanen
lokaci... Bayan mungama gaisawa yashige gd
abnsa, nikuma adai dai lokacin nayima yasmeen
sallama zantafi gida domin dare yayi, nakarkata
kafafuwa na nanufi hanyar fita waje, "my D"
yasmeen tafada, wanda hakanne yasa natsaya
tareda juyowa alokaci guda na amsa mata da "na
am darling", bani numberka, sai inkiraka da
anjima,
kasan tunda naje makaranta acan nacanza sim,
kuma yanzu banmasan inda yakeba, amman
nacanza wani sim din... Shiru kawai nayi ina
kallonta, daga bisani kuma nace, jiya wayata
tafada aruwa kuma nakai agun mai gyara yace
bazata gyaru ba.. "Sai tace ok danyi hakuri bara
inshiga gida infito". Bayan tatafi ne, narinka
tinanin karyar danayi, bayan nasan rabonda inrike
waya tun ranarda yasmeen tatafi makaranta,
lokacinda nasha bugu awurin yaran aunty bilki,
bansaniba ko sune suka dauki wayar ko anan
nabarta, oho! Ina cikin wannan tinanin ne nadago
kaine dai dai loakcin aunty bilki takaryo kwana,
ba
karamin faduwa gabana yayiba ganin tanufoni
gadan gadan, fitowar yasmeen daga gida shine
yayi silar karkata kafafuwan aunty bilki tacanza
hanya.... "Ya akayi naga duk kawani canza daga
inshiga gda infito" tafada da alamar mamaki
karara a fuskarta.. Hannu nasanya namurje
idanuwa na daga bisani kuma nace babu komai,
kawai nafara jin bacci ne. Sannan tamikomin
kwalin waya tace gashinan akwai sim aciki, idan
kaje gda kasanyata charge zankiraka da anjima.
Nayimata godiya sosai sannan najuya nayi
tafiyata..... Aunty bilky kuwa daga nan bata zame
ko ina ba sai wurin Alhaji jafar, mahaifin yasmeen,
tasanar dashi cewa yakamata afadama yasmeen
zabinda akayimata tunda dai yanzu hankalinta ya
kwanta, Alhaji baiyi wata gardama ba sbd ya
yadda da aunty bilki sosai, kuma ko babu komai,
yar uwarshi ce ita kadai taragemai duk cikin
danginsu... Batareda bata lokaci ba Alhaji yasa
aka
kiramai yasmeen yazaunar da ita agabanshi,
yafara yimata magana "auta kinga dai babu
abnda
kika rasa a gidannan kuma babu abnda kika taba
nema baki samu ba" ta girgizamai kai tareda
fadar
"eh dady"... Sannan yaci gaba da magana, "inaso
kimani wata alfarma guda, dukda nasan bakitaba
yiman gardama ba kuma bazakiso abnda zai
janyo
gardama tsakanina dake ba" sunkuyar dakai
yasmeen tayi tareda fadar "dady naji dadin
wannan
magana taka tun kafin kafadi abnda kakeso in
aikata maka, sbd na dade inaneman abnda
zanyimaka wanda zai farantamaka rai sakamakon
dawainiyata dakayi tun ina yarinya gashi yau har
nakai matsayin da zaka nemi inyimaka wani abu,
nagode ma Allah daya zabamin kai amatsayin
mahaifi, tabbas nayi dacen iyaye" murmushi alhaji
yayi sannan yace "nagodemaki diyata tabbas ina
alfahari dake kuma naji dadin wa annan
maganganun naki..." Sai alokacin alhaji jafar
yazauna akan kujerar dayaketa kai da kawo
agabanta yana magana...Bayan yazauna ne
yakurawa yasmeen ido daga bisani kuma yayi
ajiyar zuciya tareda fadar "auta inaso ne
zanhadaki
aure da Abba, dan wajen bilkisu"... Hankalin
yasmeen ba karamin tashi yayi ba nan take taji
komai najikinta yadaina aiki, takoma tamkar
gawa,
sai idanuwanta dasuka fito waje kuru kuru kamar
zasu fado, tana kallon mahaifinta dasu, sannan
alhaji yaci gaba da magana "kuma bazamu
tsawaita aurenba sbd baza awuce sati biyu ba,
hatta gdan da zaku zauna, na tanadarmaku"
yakarasa maganarsa yana duban yasmeen, sai
alokacin ya fuskanci canji daga fuskarta, "lafiya
naga kincanja ko bakisonsa ne?" sannan tayi
firgigit tafarfado tareda fadar "dady nayi mamakin
maganar ne, aure fa kace". "eh aure mana ai kin
isa ko" bai bari takara yin wata magana ba, yace
kitashi kitafi kikwanta kinga dare yayi sosai".
"Tace
to dady" tafada acikin wata murya kamar mai
shirin yin yin kuka. alhaji yace "lafiya naji kamar
kina kuka?". "a'a dady bacci ne yakeson yaci karfi
na". "to kiyi sauri kije ki kwanta" yafada batareda
yakalli inda take ba.... Tana zuwa tafada akan
gado tana kuka mai kona zuciya wanda ko
kararsa
ba'aji....... Nikau koda naje gida na tarar da
hadiza
kanwata ta ajiyemin abincina adaki, banyi wata
wata ba nazauna nacika cikina... Bayan nakimtsa
ne nakwanta sai naji wayar da yasmeen tabani
tanata kara, inadubawa naga anrubuta, "darling"
akan secreen din, murmushi kawai nayi nadauka
tareda kangawa a kunne na "salamu alaikuma"
nafara fada, amman maimakon inji an amsamin
sallama sai naji ana sheshshekar kuka....
[11:14PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: Alkawari
Part14.... Hanakalina ba karamin tashi yayiba
sakamakon kukan danaji yasmeen tanayi, nasan
bakaramin abune yafaru ba, dakyar nasamu
nashawo kanta tadaina kukan, sannan tafadamin
anbnda yafaru. Bansan lokacinda nasaki wayar
dake hannu naba. Bayan yan kwanaki kalilan
yanayina yacanza gaba daya duk nabi narame na
kode, dukwanda yaganni yasan akwai damuwa
atare dani. Bangaren yasmeen kuwa itama haka
abin yake idan kaganta kamar kabusa mata iska
tafadi sbd tsabar rama ko abnci bataci, kuma anyi
anyi da ita tafadi abnda ke damunta amman taki
fada, saidai duk lokacinda alhaji yatambayeta sai
tacemai babu komai. Haka suka kasance har
tsawon sati daya... Zaune take acikin falo itada
yayanta usman, sunmaida hankalinsu akan
makekiyar tv din dake manne ajikin bango, duk
wanda yaga yasmeen alokacin zaice kallo takeyi
amman azahiri hankalinta baya akan tv din
tanacan tana tinanin matsalarda tayankemata
walwala da jin dadi. Usman ne yadubeta yana
magana ahankali acikin yanayi na tausayi
"yasmeen meyasa bazaki fadama dady kinada
wanda kikeso ba?" ajiyar zuciya yasmeen tayi,
daga bisani kuma taba usman amsa "yaya bazan
iya tunkarar dady dawannan maganar ba, kuma
kai
kanka kasan dady yanada tsaurin ra'ayi, ko na
fadamasa bazai canja maganarsa ba" takarasa
maganarta tana duban yayan nata tareda wasu
yan matan hawaye daketa yar rige rigen fitowa
daga cikin idanuwanta... Kauda kanshi yayi sbd
bayason ganin ambaliyar hawayenta sannan yaci
gaba da magana batareda yadubi inda takeba
"yasmeen karki damu, kuma kidaina kuka insha
Allahu sai kin auri wanda kikeso "dasauri tazo
agabanshi tazauna tana magana acikin yanayi na
ban tausayi ga hawaye sai wanke kyakkyawar
fuskarta yakeyi "yaya usman dan Allah kataimake
ni wlh bazan iya auren kowa ba inba yusuf ba,
wlh
shi nakeso dan Allah yaya...." Bata karasa
maganartaba tadaura kanta akan kafafuwan
yayan
nata tana zubarda hawaye. Mikewa yayi tareda
fadar karki damu nasan abnda zanyi... Daga
bayansu kuma aunty bilki ce boye a bayan labile
tanajin duk abnda suke fada, saf saf tayi takoma
dakinta batareda sunjita ba, tana shiga tadauki
wayarta takira danta abba, yayi sauri yazo da
gaugawa... Bayan yazo ne take fadamai abnda
yafaru tsakanin yasmeen da usman, sannan
takara
dacewa "yazama dole sai munyi maganin wannan
yaron domin zai iya zuwa yakai maganar agun
alhaji, dukda nasan babu wanda ya'isa
yacanzama
alhaji ra'ayi, amman ina tsoron usman sbd shine
babban dan alhaji kuma alhaji zai iya sauraren
maganarsa, dole sai munyi wani abu acikin
gaggawa" bayan ta idarda maganarta ne tazauna
akan gadonta, shikau abba yana tsaye agabanta,
sai alokacin yacire makeken gillashin dake
sargafe
akan fuskarsa, yace "umma inaganin da yaya
usman zamu fara", mikewa tayi tsaye tana
tambayarsa cikin mamaki, "kana nufin mufara
aikashi?"."Eh ina ganin wannan itace hanya mafi
sauki". "nabar komai ahannunka kuma katabbata
kar asamu wata matsala", "angama umma danki
bazaibaki kunya ba", yafada yana murmushin
mugunta...
Wanshekare tunda safe Usman yashirya yanufi
gidanmu sbd yanason mutattauna yanda za a
bullowa lamarin, baiyi wata wataba kawai
yakutsa
kai cikin gidan, sbd daman ko baninan yakanzo
lokaci zuwa lokaci yagaida umma, hakanne yasa
har yasaba da hadiza kanwata, sukan dade suna
fira aduk lokacinda yaya usman yazo gidanmu...
Yana shiga yatadda hadiza, yatambayeta "ina
yusuf?" tace "bayanan" cikin hanzari yabata sako
tafadamin "idan yadawo kicemai muhadu a
katsina
club da karfe hudu na yamma, yanzu sauri nakeyi
zantafi office" cikin hanzari yashiga yagaida
umma
sannan yawuce wurin aiki... Karfe hudu tanayi, na
isa katsina club amman banga usman ba, bayan
nakirashi awayane, sai yake ceman yanzu yana
office kuma ayyuka ne dayawa agabansa, amman
injira zai turo kanensa (aliyu) sai yazo yakaini
office din, inanan zaune sai ga aliyu yazo, bayan
mungama gaisawa ne har zamu tafi sai mukaga
wasu mutane sun zagayemu duk sun rufe
fuskokinsu dawani bakin abu yadda bazaka iya
ganesu ba. Cikin wata kakkausar murya babban
cikinsu yake magana "takwalale" me kake jira
dashi ne, cikin zafin nama naga daya daga cikinsu
ya nufi aliyu, alokacinne nikuma nayi yunkuri
domin inshiga gabanshi, amman sai naji wasu
bakaken katti su biyu sunyi carab dani, basusha
wata wahala ba wurin rikeni sbd daman bawani
afki gareniba... Inaji ina gani suka sanyamai wuka
aciki. Sannan suka sakeni, suna juya baya sai
suka
bude fuskokinsu, dai dai lokacin kuma idi mai gadi
yafito daga dan dakinsa, suka hada ido biyu
dashi... Dasukaga haka sai suka kamashi sukaita
bugunsa harsaida yadaina motsi sannan
sungumeshi sukayi gaba dashi.. Inanan duke
agaban gawar aliyu ga wuka acikinsa narasa
yadda zanyi... Hannu nasanya dakyar nazare
wukar daga cikinsa, wadda tuni tayi jage jage da
jini, adai dai lokacin yan sanda suka shigo... Basu
tsaya saurarena ba kawai suka sanyamin ankwa
kamar sunkama wani gagarumin dan fashi....
[11:15PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: 15ALKAWARI
Part15......
Hannu nasanya dakyar nazare wukar wadda tuni
tayi jage jage da jini, inata zare idanu, hankalina
atashe sai kiran sunan aliyu nakeyi, ga wukar
ahannuna amman nakasa yaddawa kamar
ansanya
wani abu anmanne hannu na da wukar, adai dai
lokacin wasu yan sanda su hudu suka kunno kai,
abin kamar hadin baki, da bindiga ahannunsu
suna
nuna ni da ita suna fadar "you are under arrest".
Na daga kafata daya zan mike sai daya daga
cikin
police din yace "kar kasake katashi daga inda
kake,
idan har kasaba hakan, bindiga ta bazatai jinkirin
shiga cikin naman jikinka ba" yakarasa
maganarsa
yana matsowa akusa dani. Sai alokacin natina da
akwai wuka ahannu na, dasauri nayadda wukar
inata zare idanu, nasan babu wanda zai iya
fiddani
sai Allah... Bayan dan sandan ya ida isowa aguna
sai yasanya wani farin kyalle yaduka yadauki
wukar tareda fadar "sajen lawal gwanda,
sanyamai
ankwa" dasauri wanda aka kira da sajen lawal
gwanda yakaraso aguna tareda fiddo ankwa daga
gefen wandonsa ya kargama man ahannu,
dasauri
namike ina magana cikin kyarma ina fadar,
wallahi
bani nakashe shiba, tsawa sajen lawal gwanda
yayiman tareda fadar, "banan yadace kafadi haka
ba, idan munje can zakayi bayani" basu tsaya
saurarena ba, suka tasa keyata gaba izuwa cikin
mota bamu zame ko inaba sai sabon gari
station...
Dukwanda yaji abnda yafaru dani saida
hankalinshi
yatashi daga abokaina har yan gidanmu..... Alhaji
jafar muhammad shine yafara cin karo da labarin,
yana zaune a falo yana sauraren radio fm katsina,
yaji labarin kamar haka: "dazu dayamma muka
samu labarin rasuwar wani yaro matashi mai
suna
(aliyu jafar muhd) a katsina club, saidai kuma
abnda yabaiwa mutane mamaki shine, ankama
wanda yayi kisan batareda yaruga ba kuma baiba
jami'an tsaro wahala ba wurin kamashi. ga
cikakken bayani daga bakin kwamishina of police
na jahar" muryar dan jaridar tadauke sannan
muryar kwamishina taci gaba da tashi "adazu ne
yaranmu suna cikin aiki sai sukaga wata mota
kirar golf ta wuce aguje wanda gudun yawuce
ka'ida, wannan ne yaba yansanda damar bin
wannan mota amman suka kasa cimmata
sakamakon wata danja data tsaidasu adai dai
round about din kofar kaura, bayan sunsamu
sunwuce ne sukabi sawun motar har a katsina
club, amman basuga motar ba, ananne suka
samu
wanisaurayi mai suna yusuf da laifin kisankai
dumu dumu... Innalillahi wa inna ilaihirraji'iun
alhaji jafar yake fada, sbd baya bukatar wani
bayani tunda aka bayyana sunan dansa, kuma
aka
fadi sunan yusuf amatsayin wanda yakashe shi,
sbd yasan yusuf yakangansu tareda usman ko
aliyu amman baisan abnda yake kawoshi gidansa
ba.. Dasauri alhaji ya yadda radion dake
hannunsa
yana fadar "me dana yayimaka zaka kashe shi?
Wlh kaima sai ankasheka ko dan gidan uban
wanene kai" ya ida maganarsa kamar mai
sabbatu.
Dan lokaci kankane gidan alhaji ya hargitse...
Dasauri yasmeen tadauki waya takira yayanta
usman tashaidamai abnda ke faruwa, tana gama
fadamai yace "ina wannan ba gaskiya bane, yusuf
bazai iya kashemin kane ba" daga dayan
bangaren
kuma Yasmeen tafada "wlh yusuf bazai iya yin
kisan kai ba, kuma ko halinsa ne nasan bazai iya
kashe dan uwana ba" ta idarda maganarta tareda
sanya hannu ta share hawayen dake gangarowa
akan fuskarta... Suna gama waya itada yayan
nata, shikuma yanufi gidanmu ko sallama baiyiba
ya kutsa kai aciki, yana shiga yatararda hadiza
kanwata tagama sallar isha'i, cikin rudu yaci
gaba
dajero mata tambayoyi, "hadiza kinji abnda
yafaru?
Ina umma? Hadiza idan dagaske ne ya..."
tsaidashi tayi bata bari yaci gaba da magana ba,
itama ta watsomai tata tambayar "meyafaru ne
yaya usman lfy?" jin tambayar datayimai shine
yabashi tabbacin batasan abnda yafaru ba,
dasauri
yamike yanufi dakin umma, hadiza ma mikewa
tayi
tabiyoshi tana tambayarsa amman ko kadanma
baisan abnda takeyiba, yanata Alla Alla Allah
yasa
umman yusuf bataji ba, sbd yasanta ma abociyar
jin radio ce... Yana shiga dakin yatarar da umma
yashe akan gado ga radion ta nan tayi dai daya a
tsakar daki duk ta watse, battery daban marfi
daban hatta area din radion ta karye... Hankalin
hadiza ba karamin tashi yayiba da taga umma
acikin wannan halin, dandanan tafice waje dagudu
ta debo ruwa ta watsama umma a fuska, wanda
hakan yabata damar farfadowa daga suman
datayi, sannan takamata tazaunar da ita, hawaye
na kwarara a idanuwanta, hadiza takalli usman
tace "dan Allah kufadaman abinda ke faruwa"
amman babu wanda yabata amsa, sai kuka kawai
sukeyi usman da umma, sai akaro nabiyu datayi
magana hade da kara tareda kuka cikin wata
murya mai gunza "dan Allah ku fadaman" sannan
ta sauko da muryarta tana magana ahankali "ko
yaya yusuf ne yarasu" ta idar da maganarta
acikin
wani yanayi wanda idan kaganta dole tabaka
tausayi......
[11:16PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: ALKAWARI
Part16....
Sai akaro nabiyu datayi magana hade da kara
tareda kuka cikin wata murya mai gunza "dan
Allah ku fadaman" sannan ta sauko da muryarta
tana magana ahankali "ko yaya yusuf ne yarasu"
hadiza ta idar da maganarta acikin wani yanayi
wanda idan kaganta dole tabaka tausayi, amman
still su umma basu bata amsa ba, ganin haka ne
yasa hadiza zubarda hawaye masu radadi a
fuskarta, takuma tambayarsu a karo na ukku "ina
yaya yusuf din yake?". Sai alokacin umma tayi
ajiyar zuciya tareda fadar "(Allahumma la sahla
illa
ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alul hazna iza
shi'ita sahlan). Yanzu ina yusuf din yake?" umma
tafada tana kallon usman, "yanzu yana hannun
hukuma domin sai anyi bincike akan lamarin"
usman yafada... Sannan umma tajuya agun
hadiza
tana zubarda hawaye tana magana kamar wadda
ta tashi daga bacci "hadiza yayanki ya jamana
bakin duniya yayimana tabon da bazai taba
bacewa ba aduniya, ankama yayanki da laifin kisa
yanzuma yana hannun hukuma.." dasauri hadiza
tamike tsaye kamar a tsikareta ta daura hannuwa
abisa kai tana fadar "inna lillahi wa inna ilaihi
raji'un, Allahumma ajurni fi musibati wakhlifli
khairan minha" dasauri kuma tadurkusa agaban
usman tana fadar " wlh usman ba yaya yusuf
bane,
yaya bazai iya kashe maka dan uwa ba, wlh ko
kare bazai iya kashewa ba, dan Allah ka yadda"
takarasa maganarta tana wani irin kuka kamar
wadda aka aiko mata da rasuwar uwarta da
ubanta, sannan usman yamike tsaye yana fadar
"nima nasan yusuf bazai iya aikata hakan ba,
amman kuyi hakuri yanzu yana hannun hukuma
ana gudanar da bincike akan lamarin" a hakadai
usman yasamu yashawo kan hadiza da umma,
tareda fadar yanzu zaije police station din domin
jin abnda ke tafiya... yana fita bai zame ko inaba
sai police station inda yanemi a fiddomai yusuf,
baisha wata wahala ba wurin ganina sbd yasan
mutanen wurin, "yusuf ya akai haka tafaru miye
gaskiyar lamarin?" yakarasa maganarsa yana
kallona da alamar mamaki a fuskarsa. Wasu
hawaye ne masu zafi suka gangaro akan fuskata,
ina magana cikin sarkakkar murya, wlh usman
banine nakashe aliyu ba, bani nakashe shi ba
wlh.
Lokacin usman yadafa kafadata shima da alamar
kuka a idonsa, yana fadar "karka damu yusuf
nasan bazaka iya aikata hakan ba, kuma ko zaka
iya nasan bazaka iya kashemin dan uwaba, in
Allah ya yadda sai kafita daga wannan kangin"
sannan yagyara zama yaci gaba da magana yana
tambayata "fadamin yadda abin yafaru", dai dai
lokacin ne mukaji muryar wani police a bayanmu
yana magana "lokacinda oga yadibar maku yayi,
harma kunkara minti biyar". Mikewa kawai usman
yayi yana fadar kar kadamu bara intafi, insha
Allahu komai zaitafi lfy lau kuma sai angano
dukwanda yakeda sa hannu aciki" yajuya yatafi,
nikuwa akayi ciki dani..... Daga nan usman ya
falli
mota yanufi gidanmu, yana shiga yatadda su
umma sunyi jugum jugum kowa yayi tagumi
kamar
masu zaman gaisuwa, yana shiga umma tayo
kansa tana tambayarsa "ina yusuf din? Dagaske
shi yayi kisan?" "a'a umma bashine yayi ba",
"yanzu ansakoshi ko?" takuma tambayar
usman ,Jingina yayi ga bango daga bisani kuma
yace "babu wata hujja wadda zata bayyana hakan
awurin hukuma dole sai anyi bincike akai"
zaunawa umma tayi kamar wadda aka yadda
akasa bakinta yanata mai maita "qadaru lillahi
wama sha a fa'al"..... Bangaren su aunty bilki kau
suna can suna murna domin hakarsu ta cimma
ruwa, wannan karen ma zaune take acikin daki
itada danta, "nayi mamaki da har yau kwana biyu
amman alhaji bai shigarda kara kotu ba" abba ne
yake magana yana kallon mahaifiyarsa, "haba
yaufa kwana biyu ko sadakar rasuwar aliyu ba
ayiba yaza ai yashigar da kara, ai sai anyi kwana
ukku sannan" ta idar da maganart lokacin da take
ajiye kofin dake hannunta, daga bisani kuma tace
"amman fa wannan game din yanada dadin kallo
saboda gidannan rabuwa zayayi kishi biyu, alhaji
da matarsa daban, usman da yasmeen suma jam
iyarsu daban, shi Alhaji zai hakikance ne sai
ankashe wanda yakashemai yaro, usman kuma
zaiyi kokarin kare abokinsa yusuf saurayin
yasmeen, sbd ya yadda dashi yasan bashine yayi
wannan aikin ba, amman kuma haryanzu alhaji
baisan abnda usman da yasmeen suke shukawa
ba", aunty bilki ce take magana tana wani
murmushin mugunta, sanna abba yayi magana
"momy amman ni ina gani yakamata alhaji yasan
usman da yasmeen suna kokarin kange yusuf,
kinga sai yasan matakin da zai dauka akansu,
sbd
munaso ayi shari ar nan cikin gaggawa batareda
bata lokaci ba, ayankemai hukunci shima yabi
aliyu, kinga idan akai haka dole yasmeen zata
amince da aurena batareda wata matsala ba sbd
ankashe wanda take so", dasauri aunty bilky
tagyara zama tace "eh gaskiya haka yakamata
muyi amman bai kamata mufada ma alhaji
wannan
maganarba, shi yakamata yagani da idonsa"
takarasa maganarta lokacinda take jingina akan
kujerar datake zaune, "ta yaya zamu bullo ma
abin" abba yatanbayi aunty bilky, "wannan karen,
kabar komai a ahnnu na, nasan yanda zanyi"
tafada !tareda mikewa tsaye tanufi hanyar fita
waje........
[11:19PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: 17ALKAWARI
Part17.....
Yau kwana hudu kenan da faruwar
wannan al'amari... Zaune nike nasanya kaina
acikin kafafuwana inata tinanin duniya dakuma
tinanin wannan al'amari wanda ya yankemin
jindadi da kwanciyar hankali tareda na dangina...
"taso kabiyoni muje ga yan uwanka nan sunzo
ganinka" muryar wani gandroba ce ta doki dodon
kunnena, faruwar hakan ne yayi silar tsinkewar
tinani na, banyi gardama ba nayi kamar yanda ya
umurta natashi nabiyoshi, zuciyata tana tinanin
suwanene kuma sukazo gurina, wani bangaren na
zuciyata kuma yana rayamin usman ne yazo
aguna
sbd nasan shine yake zuwa adai dai irin wannan
lokacin akowace rana. Kai tsaye nawuce inda aka
tanada domin ziyartar masu laifi, ina shiga
yasmeen idona yafara hangowa wadda ta kode ta
rame kamar wadda ta shekara tana ciwo
batareda
ankulata ba, duk wanda yaganta yasan tana cikin
tashin hankali, idan kuwa mutun yadubi
idanuwanta sai ya fahimci ta kulla abota da kuka,
saboda ilahirin idanuwanta duk sun rikida sunyi
jajur sbd zirga-zirgar da hawaye keyi acikinsu,
daga gefenta kuma mahaifiyata ce zaune idan
kaganta sai karantse bata taba sanin wani abuba
waishi kwanciyar hankali, hatta farar fatar jikinta
tayi jajur kamar wadda ta shekara acikin rana,
dayan gefen kuma hadiza ce nagani a tsaye itada
usman, ina ganin hadiza nafahimci tana cikin
mawuyacin hali, fuskarta da idanuwanta duk sun
kumbura. Tunkafin inkarasa agunsu naji wasu
hawaye suna gangarowa akan fuskata batareda
izni na ba, dakyal nakarasa agaban umma
nadurkusa nagaisheta... Bayan mungama
gaisawa
ne usman yadubeni cikin damuwa yana fadar
"Alhaji ya shigar da kara a kotu nan bada dadewa
ba" sannan yayi wani nishi mai kama da ajiyar
zuciya daga bisani kuma yace "karka damu yusuf
zansamar maka lauya wanda zai kareka kuma za
asamu nasara insha Allahu" rufe bakinsa shine
yayi dai dai da shigowar alhaji jafar tareda aunty
bilki, ba karamin tashi hankulanmu sukayiba
zuwan alhaji jafar da aunty bilky, musamman ma
usman da yasmeen yadda suka kidime lokaci
guda
zufa tayomasu lale marhabin. Usman ne yayi
karfin
hali yakarasa agaban Alhaji tareda rusunar
dakanshi kasa yaci gaba da magana muryarshi
tana sarkewa "Alhaji barka da yini", (fassssss)
karar mari ce tagarwaye wurin, maimakon amsa
gaisuwa daga bakin alhaji, tabbas usman yaji
zafin
marin sbd har tangadawa yayi kamar zaifadi kafin
yabude baki yace wani abu, Alhaji yaci gaba da
magana yana nunashi da dan yatsa cikin zafin rai
"kai usman ashe kai shasha sha ne bansani ba,
me
kakeyi awurin wanda yakashe maka dan uwa, me
kake nufi ne" shirun da Alhaji yadanyi shine yaba
usman damar yin magana, "wlh dady bashine
yakashe aliyu ba wlh ba...." saukar hannun alhaji
akan fuskar usman shine yayi silar hana usman
ida
maganar, sannan alhaji yaci gaba da magana "to
wlh baka isaba, kuma babu wanda ya isa yahana
akashe wannan yaron ko dan wanene" yakarasa
maganarsa yana nuno ni da danyatsa. Wannan
maganar da alhaji yafada ba karamin tada
hankalin
mahaifiyata yayiba sbd tasan babu wanda ya isa
yashiga gaban Alhaji Jafar saidai ikon Allah,
dasauri umma tazo ta durkusa agaban Alhaji jafar
tana magana hade da kuka "dan Allah alhaji
kataimakeni kayimana rai wlh shikadai ne
yaragemin a duniya sai kanwarsa bamuda ko..."
dagama umma hannu yayi tareda fadar "kinfini
sanin dadin haihuwar ne kika bari danki ya
hallaka
nawa? Ke wlh ko dan dan shugaban kasa ne
yakashemin yaro shima sai ankashe shi" dasauri
kuma yajuya yafice, su aunty bilki suka rufamai
baya, suna fita sai wasu bakaken mutane suka
shigo su biyu katti sukayo kan usman tareda
rikemai hannuwa daniyar tafiya dashi ko yaki ko
yaso, cikin mamaki yake tambayarsu "me kuke
nufi
ne? Kunsan koni waye?" yana rufe bakinsa sai ga
alhaji yadawo, "ni nasanyasu kuma bazaka kara
fitowa koda kofar gida ba harsai angama shari'a,
ko asiri wa annan mutanen sukayimaka saidai
yatsaya akanka amman nafi karfinsu" alhaji
yafada
cikin fushi, nan take bakaken mutanen nan sukayi
waje da usman, yana kallona yana zubarda
hawaye... Hadiza ce takaraso aguna tana kuka
tana fadar yaya yusuf munshiga ukku yazamuyi
kenan" sunkuyar da kaina kawai nayi ina zubar
da
hawaye sbd banida amsar da zanbawa hadiza.
Maganar umma ce tayi silar dago kaine "ku
kwantar da hankalinku babu abnda zai faru insha
Allahu, kudauka wannan jarrabawa ce Allah
yakeyimana, yakamata mudaure muci wannan
jarrabawar kota halin kaka" umma ce take
magana
daniyar kwantarmana da hankali, amman
zuciyarta
cike take fal da damuwa tareda tashin hankali
wanda gayanan karara a fuskarta, sannan tadafa
kaina tace "yanzu babu abnda yaragemana sai
addu'a" sannan nadago kaina nace "umma
yaushe
za'ashiga kotun ne?" ajiyar zuciya tayi sannan
tace "ranar litinin 16 ga wannan watan"
[11:21PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: ALKAWARI
Part18....
Ranar litanin 16-6-2014, kotun tacika makil da
mutane maza da mata. bayana wasu police ne
guda biyu wa'anda suka sanyani gaba duk idan
nadaga kafata suma sai su daga tasu, haka muke
tafiya, hannuwana daure suke da ankwa ina
tafiya
amman kaina a duke inata zubar da hawaye,
nakasa dago kaine inkalli mutanen dake wurin
sbd
tsabar kunya da bakin ciki, "wai yau nine a kotu
da
laifin kisa" nafada acikin zuciyata tareda takaici
acikin raina, rakani sukayi har acikin wani dan
akurki wanda yaboye duk ilahirin jikina amman
daga kirji na zuwa kaina duk awaje suke. Bayan
kowa ya maido hankalinshi akanmu sannan alkali
yadubi wani mutun wanda yake zaune akan wani
teburi, daga mai kai kawai alkali yayi, naga
mutumen nan yamike alamun ya fahimci abnda
alkali yake nufi, sannan yadukar dakansa yaci
gaba
da karanto wata takarda dake hannunsa "zamu
shiga shari'a ta biyu awannan rana, akan kisan
da
akayiwa aliyu jafar muhammad, wanda ake zargin
yusuf ahmad muhammad da aikatawa" sannan
yakoma akan teburinsa yazauna. Alkali yadukar
dakansa yayi wasu yan rubuce-rubuce da
alkalaminsa sannan yadago kansan yadubi
sashen
wasu mutane wa'anda daganinsu kasan
lauyoyine.
Daya daga cikinsu yatashi dawasu bakaken kaya
na lauyoyi, yamike yaci gaba da magana "sunana
barista Auwal mu'azu rimaye, lauya mai zaman
kansa daga chamber din M.A Bello & co. Kano.
Nine lauya wanda yake kare hakkin wanda aka
kashe" sannan yakoma yazauna. Nikam a lokacin
zuciyata sai dukan tara tara takeyi saboda a'iya
sanina banida wani lauyan dazai kareni, kamar
ance indago kaina, ina dagowa nahada ido da
umma tana zaune ita da hadiza sai faman zubar
da hawaye sukeyi, mantawa nayi da halin danake
ciki sakamakon tinani da tausayin su umma daya
kamani, tabbas suna cikin damuwa wadda tafi
tawa, da alama sunfini shan azabar faruwar
wannan lamari. Alkali daya gama rubuce
rubucensa
yadago kansa a zatonsa zaiji lauya wanda ke
kare
wanda ake kara yagabatar dakanshi, amman yaji
shiru. Hakan shine yabashi damar buda baki yayi
magana a karo na farko tunda muka shigo, "lauya
wanda yake kare wanda ake kara" haka kawai
yafada yana kallon bangaren da lauyoyin suke
zaune, kafin ya rufe bakinsa aka turo kofa dakarfi
kamar za'a balle ta, hakane yayi sanadiyar
karkata
idanuwan alkali tareda hankalin duk mutanen
dake
cikin kotun domin ganin wanda yake shigowa, ba
karamin mamaki nayiba danaganta acikin kayan
lauyoyi wa'anda sukayi mata kyau matuka kamar
daman dan ita akayisu Karasowa tayi gaban
alkali
batareda bata lokaci ba muryarta taci gaba da
tashi, "sunana barista sady al-mustapha, lauya
mai zaman kanta, nice wadda take kare wanda
ake
tuhuma" alkali yakalleta kamar zai fadamata
wata
magana amman sai yayi shiru yadukar dakansa
yaci gaba da yan rubuce-rubucensa ganin haka
ne
yasa barista sady tanufi wurin zama tazauna,
daga
bisani kuma alkali yadago kansa "idan akwai
wanda yake bukatar tambayar wanda ake
tuhuma,
zai iya farawa ayanzu" yafada yana mai duban
lauyoyin. Barista auwal ne yamike "idan kotu
tabani dama inaso inyima wannan mutum wasu
tambayoyi". "Anbaka dama" alkali yafada
atakaice.
Sannan barrister yakaraso agabana "malan zaka
iya bayyana ma kotu sunanka" sunana yusuf
ahmad muhammad, nabashi amsa atakaice, "ina
fatandai kasan abnda yasa aka shigo dakai anan"
yakuma tambayata, dagamai kai nayi alamar
"eh",
"naji sunan naku daga karshe kamar iri daya dana
marigayi, ko zaka iya fadama kotu dangantakarka
dashi marigayi aliyu?" barista auwal yafada,
"babu
wata dangantaka ta jini tsakanina dashi" nafada
muryata na sarkewa, sannan barista yagyara
tsayuwarsa "sbd babu wata dangantaka
tsakaninka dashi shiyasa ka kashe shi kenan..".
"Objection ya mai girma mai shari'ah! Yakamata
mai tambaya yakiyaye kalamansa sbd haryanzu
bincike akeyi ba'a tabbatarda wanda yayi kisan
ba". "mai tambaya sai yakiyaye" alkali yafada
atakaice. Barista yakuma tambayata "yusuf
lokacinda aka kashe aliyu, ku nawa ne awurin?"
babu kowa mukadai ne, nabashi amsa atakaice,
sannan yaci gaba da magana "babu kowa! Kana
nufin shi yakashe kanshi kenan koko wukar ce ta
taso dakanta takashe shi?" sady tamike
"objection
ya mai shari'ah! yakamata mai tambaya ya
sassauta kalamansa na tsoratarwa akan wanda
ake tuhuma sbd bako ne a shiga kotu...", barista
yayi sauri yatarbi hanzarinta da fadar "yakamata
kotu tayi watsi da korafin abokiyar aikina, sbd
bankauce hanya ba, ina akan hanya tane ta
kokarin gano gaskiyar wannan lamari", "mai
tambaya bai kauce hanya ba, zai iya cigaba da
tambayoyinsa" alkali yafada, sannan sady
tazauna
fuskarta da alamar damuwa.. Barista na gama
tambayarsa yayi godia ga alkali yazauna. Alkali
yadukar dakai yayi yan rubuce-rubuce sannan
yadago kansa, "akwai wanda keda wata
tambaya"
alkali yafada, shirunda akayi ne yasa alkali ya
disa
aya akan takardarsa, "Sakamon rashin isasshen
lokaci kotu ta daga wannan kara zuwa daya ga
watan janairu shekara ta dubu biyu da shahudu"
sannan yabuga wata guduma akan tebur tareda
mikewa tsaye. kooootu!!.....
[11:36PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: 19ALKAWARI
Part19....
Barista yace "babu kowa! Kana nufin shi
yakashe kanshi kenan koko wukar ce ta taso
dakanta takashe shi?" sady tamike "objection ya
mai shari'ah! yakamata mai tambaya ya sassauta
kalamansa na tsoratarwa akan wanda ake
tuhuma
sbd bako ne a shiga kotu...", barista yayi sauri
yatarbi hanzarinta da fadar "yakamata kotu tayi
watsi da korafin abokiyar aikina, sbd bankauce
hanya ba, ina akan hanya tane ta kokarin gano
gaskiyar wannan lamari", "mai tambaya bai kauce
hanya ba, zai iya cigaba da tambayoyinsa" alkali
yafada, sannan sady tazauna fuskarta da alamar
damuwa... Barista yakuma dubana yasake
maimaita tambayar dayayiman akaro nabiyu,
"yusuf kana nufin shi yakashe kanshi koko wukar
ce ta taso dakanta takashe shi?". Wasu hawaye
ne
suka gangaro afuskata kyarma takamani, naci
gaba da magana kamar dan koyo, wlh wasu
mutane ne nima ban sansuba kawai ganinsu nayi
sun zagayemu. nakarasa maganata ina kallon
barista auwal a tsorace. Wani dan gajeren
murmushi yayi sannan yajuya agun alkali yaci
gaba da magana "yakamata kotu tayi duba izuwa
maganganun wanda ake zargi, saboda bayaninsa
nabiyu ya karyata bayaninda yayi abaya, dafarko
cewa yayi babu kowa subiyu ne kadai lokacinda
wannan abu yafaru, yanzu kuma yace wasu
mutanene sukayi abin, wannan yana nunamana
babu gaskiya acikin zancensa, dawannan kadai
ya
isa kotu tayima wannan mai laifi hukunci na
daidai
da laifin da ya aikata". Barista auwal yana zuwa
nan dazancensa sai yayima alkali godiya sannan
yakoma mazauninsa yazauna. Bayan barista
auwal
yazauna sai barista sady ta mike tareda fadar
"ina
neman izni da kotu tabani damar yin magana da
wanda ake tuhuma" "anbaki dama" alkali yafada
yana dubanta. Tasowa tayi tayo tattaki izuwa
gurina sannan tace, "sannu malan kaji, da alama
kana cikin damuwa sosai, kuma ko shakka babu
ka taka sawun barawo wanda hakan ne yayi silar
shigar dakai cikin mawuyacin hali, amman inaso
ka
kwantar dahankalinka kuma kasani nan kotu ce
mai adalci baza'a taba yankema mutun hukunci
ba
matukar bashine ya aikata laifinda ake zarginsa
dashi ba, inaso kafidda duk wata damuwa aranka,
ka kaddara wannan nadan wani kankanen lokaci
ne kafin agano wanda yayi wannan aikin" sady
tafada tana kallona, sannan na girgiza kai alamar
na gamsu, cikin dan kankanen lokaci sady
tashigar
da kalaman dasukayi silar kwanciyar hankalina
acikin maganganunta, sannan takalleni atsanake
taci gaba da magana "malan yusuf ko zaka iya
fadamana wannan ko zuwanka na nawa ne
akotu?" a'a bantaba zuwa kotuba, nabata amsa
atakaice, "shiyasa naga duk katada hankalinka
hatta sunanka ma kakasa fada dai dai sbd
fargaba" tafada fuskarta asake kamar wadda take
shirin yin murmushi, sai alokacin natina da
kwamacalar danayi, sunan danabawa kotu
lokacinda barista auwal yatambayeni. Maganar
barista sady ce takatseni daga tinaninda nakeyi
"yanzu naga hankalinka akwance, zaka iya
fadama
kotu sunanka?" ta tambayeni. Sunana yusuf
bashir
muhammad, nafada da kwarin guiwa. Cikin
hanzari
barista auwal yamike tareda fadar "Objection Ya
mai girma mai shari'ah yakamata kotu taduba
tagani kuma tayi gaggawar yanke hukunci, sbd
tundaga maganar farko har karshe babu zancen
gaskiya acikin lamarinsa, shiyasa har sunansa
yakasa fada dai dai..." yana zuwa daidai nan
dazancensa, abin kamar hadin baki sai muryar
barista sady taci gaba da tashi "yakamata kotu
tayi duba izuwa maganganun abokin aikina wato
barista auwal, idan kotu taduba zata fahimci
wannan ba korafi bane yayi, saidai yanabada
umurni ne ga kotu domin tayi gaggawar yanke
hukunci batareda wani kwakwkwaran bincike ba,
idan kuma korafi ne to yakamata kotu tayi watsi
da korafinsa, sbd wannan kuskurenda wanda ake
tuhuma yayi afarko yanada nasaba da kalamanda
aka rinka furtamai na tsoratarwa tun afarko,
shiyasa duk hankalinshi yatashi kuma gashi
baisaba shiga irin wannan yanayinba" tana zuwa
nan da zancenta sai tajuyo akaina tareda
tambayata, "malan yusuf ko kataba tsintar kanka
acikin irin wannan halin a baya?" girgiza mata kai
nayi tareda fadar a'a, sannan tajuya agun alkali
taci gaba da magana "ya mai girma mai shari'ah
yakamata kotu tayi duba kuma tayi adalci akan
wannan bawan Allah wanda baitaba aikata wani
mummunan laifiba, ko hukuma tasan da haka,
tayaya zai iya kashe mutun, yakamata kotu
taduba
tagani ayayinda zata zartar da wannan
shari'ah"...
bayan tagama maganarta ne sannan tayi ma
alkali
godia, takoma wurin zamanta tazauna, yayinda
alkali shikuma yadukufa yanata rubuce
rubucensa,
bayan yakammala ne sannan yadago kansa
tareda
fadar"Sakamon rashin isasshen lokaci kotu ta
daga
wannan kara zuwa daya ga watan yuli shekara ta
dubu biyu da shahudu, kuma kotu tana bukatar
lauyoyin kowane bangare suzo mata da kwararan
hujjoji a zama na gaba" sannan yabuga wata
guduma akan tebur tareda mikewa tsaye.
kooootu!!.....
[11:36PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: 0ALKAWARI
Part20
Gaba daya naga kowa nacikin kotun yamike yana
niyar fita waje idan kacire umma da hadiza sai
barista sady, sune kadai azaune suna kallona
cikin
damuwa, police dinda suka kawoni sune suka
kuma tasa keyata gaba domin fita daga kotun,
cikin zuciyata nike tinani wai yanzu komawa
za'ayi
dani gidan maza yayinda kowa zaya nufi gidansa,
ashe zamana bai kareba acikin wannan kazamin
wuri... Ta gabansu umma muka wuce muna
kallon
juna, da alama kowa yanada maganarda yakeso
yafurta amman taki fitowa, saidai motsi kawai da
bakinmu yakeyi idanuwanmu kuwa sai zubarda
hawaye suke, Hadiza ce tabiyo bayanmu dagudu
tana kwalamin kira cikin shakakkar murya amman
ina, kafin takaraso agunmu har anjefani mota anyi
gaba, tsayawa tayi tadafe kai tana kallon motar
harsaida taga tadaina ganinmu, sannan barista
sady tazo ta lallasheta tareda bata hakuri sannan
suka tafi, tattaki sukayi zuwa inda umma take
daga bisani kuma sady tagaida ta, sai alokacin
umma tagane ko wacece agabanta "sa'adiya
daman kece" umma ta tambayi sady da fuskar
mamaki, girgiza kai barista sady tayi tareda fadar
"eh nice umma" "kiyi hakuri banganeki ba naga
kinsha bakaken kaya, daman aikinki ne wannan"
umma takuma tambayar sady tana kallonta, eh
umma yanzu kushiga inkaiku gida sannan" sady
tafada lokacinda take nuna wata farar mota dake
gefensu, tattaki sukayi zuwa wurin motar sannan
sady tabude ma umma kofar baya hadiza kuwa
tazagaya tashiga gaba, batareda bata lokaci ba
ta
fizgi motar suka hau hanya... Tafiya suke
ahankali
cikin kwarewa, babu wanda yakema wani magana
acikinsu, dukansu sun dunguma zuwa duniyar
tinani... "Umma ya akai har haka tafaru tunfarko
ba'asanar dani ba" sady ce tayi magana
lokacinda
tamaida dubanta zuwa ga umma, daga bisani
kuma tamaida hankalinta akan tukin datakeyi.
"Wlh
kaddara ce idan Allah ya tsara ma bawa abu,
babu
yadda za'ayi ya tsallake" umma tafada daga
bisani kuma tace "kuma keda kika tafi abuja, ta
yaya zamu ganki". "Hakane! nima nasamu lbrn
faruwar lamarinne lokacinda nashigo garin a
daren
jiya" sady tafada... Haka dai sukaci gaba da
magana akan lamarin har suka isa gida, bayan ta
kaisu gida itama tawuche nasu gidan domin
tinanin ta yadda zata bulloma lamarin... Zaune
nike jingine ga bango nikadai acikin dakinda aka
kulleni sai tinani nakeyi, "kafito ana son ganinka"
muryar wani bakin gandroba ce tadoki dodon
kunnena itace tayi sanadiyar dawo dani cikin
hayyaci na.. Tasowa nayi nabiyoshi tinkis tinkis,
har wurinda nasaba zuwa idan akazo gani na.
Barista sady ce nagani zaune akan wani tan
benci.
tabbas nayi mamaki sosai yadda naga sady ta
bayyana amatsayin lauya, alokacinda nike neman
taimako takowane hali "Yusuf ya akai wannan
abin
yafaru kuma miye gaskiyar lamarin" sady ta
tambayeni lokacinda tasanya hannu acikin jikka
tadauko biro dawani dan littafi, wlh sady bani
bane, nafada ina kallonta, "tabbas nasan
bakaibane, amman zaka iya tuna yadda abin
yafaru?", sannan nagyara zama nafada mata
abnda yafaru tundaga lokacinda usman yace yana
nemana har lokacin afkuwar wannan abu, bayan
nagama koramata bayani sannan takalleni tareda
fadar "kuma cikin mutanenda sukayi kisan bazaka
iya gane koda mutun dayaba?", gaskiya bazan iya
ganesuba sbd duk sunrufe fuskokinsu. "shikenan
inaso ka kwantar da hankalinka kuma insha
Allahu
zaka fita daga zarginda akeyima... Zaune suke su
biyu akan wasu yan fararen kujerun roba, sai
table
a tsakiyarsu daga samansa kuma drinks ne da
wasu yayan itatuwa, "momy banyi zaton za'ayi
zama biyu ba ashari'ar nan" abba yafada
lokacinda yake bulbular wani lemu cikin cup, "ko
zama goma za'ayi ai doledai sai anyankemai
hukunci sbd baza ataba gano wa anda sukayi
aikinba" aunty bilky tafada tareda jingina akan
kujerar datake zaune, sannan takara dacewa "ina
fatandai lokacinda wannan abu yafaru ko tsuntsu
baya gurin" tafada tareda yin kasake tana kallon
dan nata, "haba umma ai babu kowa awurin sai
wani mai gadi, shima ba agabanshi akayi aikinba
amman yaga fitowarmu" dasauri tamike a fusace
"kai bakada hankali, me kake fadamun?" aunty
bilki
tafada acikin tsawa, "haba momy kwantar da
hankalinki ai, bamubar wurinba saida muka rufe
bakinshi bazai kara magana ba har abada, sbd
saida mukaimai bugunda bazai iya wuce hour
guda
yana lumfashi ba, sannan muka jefashi ruwa"
abba
yafada lokacinda yake ajiye cup din dake
hannunsa, zaunawa tayi tareda yin wata
gawurtattar ajiyar zuciya sannan takara dacewa
"amman dukda haka kunyi kuskure sbd kamata
yayi ku kasheshi dakanku bawai yamutu dakanshi
ba, idan yanada sauran kwana agaba ai kaga zai
iya tashi, kuma daya tashi kaima kasan sauran
basai nafadamaka ba" takarasa maganarta tana
kallon abba afusace, murmushi yayi sannan yaci
gaba da magana "momy kwananshi ne yakare
shiyasa har yahadu damu kuma ina tabbacin
mutuwarsa tun kafin mujefashi a teku"
[11:36PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: 21ALKAWARI
Part21...
Ranar talata 01-07-2014, kamar kullun
yauma mutane ne cike makil acikin babbar kotun
dake garin katsina, mutane dayawa sun hallara
domin son jin yadda wannan shari'ah zata
kasance, sbd shari'ar ta zagaya nigeria yadda
mai
karantawa baya tinani sbd alhaji jafar muhammad
yana daya daga cikin manyan kasar nan, shiyasa
wasu mutane dayawa ma ba yan garin katsina
bane amman sun hallara, domin sunsan ba
karamin abu bane zaisanya alhaji jafar kai kara a
kotu, wasu mutanen kuma sunzo ne sbd yadda
mutane ke zuzuta abin, wasu suna cewa "ankama
dan mafia ya yanka dan gidan alhaji jafar zai
fiddamai yan hanji sai police suka kamashi".
Wasu
kuma cewa sukeyi "wani dan siyasa ne abokin
gaba yasa akashe dangidan alhaji jafar sbd anaso
adagulamai lissafi a wannan zaben na 2014", kai
maganganu dai da dama kowa da yadda yake
tsara abinsa, shiyasa kotun ta dauki mutane
dayawa kowa yazo domin yakashe kwalkwatar
idonsa. Tacikin mutane aka ratso dani, muna
shigowa kowa yamaida dubansa akaina wasu
suna
tabe baki, wasu kau hararata sukeyi, wasu kuma
yadda naga yanayinsu da ba cikin kotu bane da
har buguna sai sunyi, wasu kau fuskarsu asake
hankalinsu kwance. Hakan tasa dole nasunkuyar
dakaina ina tafiya ahankali har zuwa cikin wani
dan akurki inda masu laifi suke tsayawa, dago
kaina nayi naga dandazon mutanenda suka
hallara
a kotun domin ni... Cikin zuciyata nace tabbas
tunda nike a duniya tsawon rayuwata bantaba
ganin shekarar da tazoma mutane da rikici ba
kamar 2014, itace shekarar da aka zubar da jinin
miliyoyin mutane acikinta, wasu kuma suka rasa
rayukansu, itace shekarar da rayuwar dan adam
takoma kamar rayuwar sauro, idan ankashe
mutun
ankashe banza sbd babu wani matakin da ake
dauka indai talaka ne, itace shekarar da aka rinka
satar mutane kamar yadda mahaukaci yake
tsintar
leda akan titi, ni kaina nashaida 2014 sbd acikine
nafada sharrin da babu wanda zai iya fiddani sai
Allah, yakamata mugyara zuciyoyinmu mukoma
ga
Allah domin kubuta daga wannan yanayi....
Muryar
maga takarda ce tayi silar dawo dani daga
tinaninda nakeyi, "Yau kotu zatayi zama nabiyu
acikin karar da alhaji jafar yakawo akan kisan
dansa wanda ake zargin yusuf bashir da
aikatawa,
dafatan lauyoyin ko wane bangare sunzo da
shaidun da kotu take bukata" yafada tareda
zaunawa akan kujerarsa, sannan alkali yaduka
yadanyi rubuce rubucensa wanda yasaba sannan
yadago kansa, "idan akwai wanda yakeda
magana
zai iya farawa" alkali yafada yana kallon
bangaren
lauyoyin... Barista auwal ne yamike yazo
agabana
"yusuf kana yawan zuwa gidan alhaji jafar ako
wane lokaci kaga dama hakane ko bahaka
bane?",
hakane, nabashi amsa atakaice, "inaso kotu
tabani
dama domin gabatar da mai gadin gidan Alhaji
jafar anan" barista yafada tareda rusuna kai
agaban alkali, "kotu tabaka dama" alkali yafada.
Hankalinshi kwance yaratso mutane tareda zuwa
yatsaya inda masu bada shaida ke tsayawa,
sannan barista auwal yayi tattaki izuwa gabanshi,
"malan kotu tanaso tasan ko kai waye" barista
yafada yana kallon mai gadi, Sannan mai gadi
yagyara tsayuwa tareda gyara zaman hularsa
abisa kansa, "sunana auwalu amman ana kirana
da kalafta" yafada yana duban barista, "malan
kalafta ko kasan wannan?" barista auwal yafada
tareda nunoni da dan yatsa, "eh nasanshi sbd
yana
yawan zuwa gdan alhaji, kuma ko daren ranarda
za akashe aliyu, yazo gdan" kalafta mai gadi
yafada yana kallona. Ji nayi gabana yafadi dass
sbd akalla nakai sati guda banje gdanba, tun
lokacinda yasmeen tasanarmin da zabinda
mahaifinta yayimata. Barista yaci gaba da
magana
"malan kalafta, yusuf yaje gdan alhaji awannan
ranar wane yanayi kaganshi, ina nufin daren
ranarda abn yafaru?". "Tabbas ranar wurin karfe
9
na dare ina zaune a bakin kofa sai naga yusuf
yashigo ranshi abace, har inamai magana amman
yayi shiru bai tankamani ba, saidai yawuche yana
huci kamar tukunyar dambu" kalafta yakarasa
maganarsa yana kallona da wutsiyar ido. Cikin
zuciyata nace lallai kalafta mai gadi kacika
makiri... Bayan barista yagama yima kalafta mai
gadi tambayoyi sai yajuya yayima alkali godia,
sannan alkali yace "ko lauya wanda yake kare
wanda ake tuhuma yanada tambaya akan mai
gadi?", sai alokacin barista sady tamike akaro
nafarko tayi magana "eh ya mai girma mai
shari'ah" karasawa tayi a'inda kalafta yake tsaye
tafara tambayarshi "malan kalafta zaka iya
fadama kotu ko miye aikinka a gdn alhaji?", "eh ni
mai gadi ne" yafada, "shekararka nawa kana aiki
a
gdn alhaji" takuma tambayarshi, "akalla nakai
shekara 8" yabata amsa atakaice, sannan sady
tadanyi murmushi tareda fadar "shekara takwas
kana gadi alamar ka kware kenan acikin aikinka",
"tabbas alhaji ma yana alfahari dani" kalafta mai
gadi yafada. Sannan sady tadan karkace kai
tareda
fadar "a matsayinka na kwararren mai gadi
wanda
yadade yana aiki, ya akai lokacinda yusuf yashiga
gdn alhaji cikin fushi, kakasa fadama masu gdn,
ko
kafadama alhaji abnda ke faruwa" sady tafada
tana kallon kalafta mai gadi......
[11:36PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: ALKAWARI
Part22...
Barista sady taci gaba da magana "a matsayinka
na kwararren mai gadi wanda yadade yana aiki,
ya
akai lokacinda yusuf yashiga gdn alhaji cikin
fushi,
kakasa fadama masu gdn ko kafadama alhaji
abnda ke faruwa". Wani dan gajeren murmushi
yayi kamar daman yashirya amsar tambayar da
za'ayimashi, daga bisani kuma yace "Nifa aikina
gadi, babu ruwana da matsalar cikin gida saidai
inhana matsala shiga cikin gda, kuma nasaba
ganinshi tareda marigayi aliyu" kalafta mai gadi
yafada, sannan sady tajuya agun alkali tayima
kotu godiya tareda komawa mazauninta. Barista
auwal ne yazo wurin kalafta mai gadi yaci gaba
da
magana "mungode malan auwalu kalafta zaka iya
komawa mazauninka", sannan barista yajuyo
aguna tareda fadar "yusuf anshaida mana kaje
gdn
alhaji daren ranarda wannan abu zai faru acikin
wani yanayi, kotu tanaso kafadamana abnda
yakaika gdn a irin wannan lokacin" barista auwal
yatambayeni. Hawayene kawai ke zuba a
idanuwana nakasa buda baki inyi magana sbd
bansan abnda zanafada ba, shirunda nayi nadan
seconds 30 shine yasanya barista auwal yaci
gaba
da magana "idan bazaka iya bada amsa ba ni
bara
inbada amsar" sannan yagyara tsayuwa yaci
gaba
da magana "kaje gdn Alhaji da niyar aikata abnda
zuciyarka tabaka amman sai kayi rashin sa'a
baka
samu damar aikatawa ba sbd kasamu akwai
mutane acikin gidan, kaikuma baka bukatar
asirinka yatonu shiyasa ka yanke shawarar tadda
shi har katsina club domin cimma burinka" yana
zuwa anan sai yajuyo gaban alkali yana magana
"idan kotu tabani dama zangabatar da shaidata
ta
gaba" barista auwal yafada. Wani kasurgumin
kato
ne yaratso jama'a yana tafiya kamar agwa-gwa
sbd kafafuwanshi kamar duk bai-bai suke, daya ta
kalli gabas daya kuma ta kalli yamma, yakaraso
inda akatanada domin masu shaida, bayan
yatsaya
sai barista yaje akusa dashi yafara magana
"malan
ko zaka iya sanarwa kotu ko kai waye?" barista
yafada yana wani karkace kai, "sunana (Isah
bare),
kuma nine shugaban masu kare lafiyar mutanen
gidan alhaji, (body guard)" yafada acikin wata
katuwar murya. "malan isah bare ko kasan
wannan?" barista auwal yafada yayinda yake
nunoni da dan yatsa, "eh nataba ganinshi sau
daya
a airport" isah bare yafada yana girgiza kai. "a
airport kuma me yahadaku ne a airport?", barista
auwal yafada, saida isah bare yayi wani nishi
sannan yaci gaba da magana "wata rana munje
airport domin raka yasmeen diyar Alhaji zata tafi
makaranta, lokacin ina tare da hajiya bilkisu
wadda
duk inda zataje dani take tafiya amatsayin body
guard, bamukai ga shiga cikin airport dinba sai
gashi yazo yana sauri zai shiga, ananne muka
kamashi da makami (wuka) ajikinsa, munyi
kokarin
mukwace makamin kuma muji dalilin zuwansa
amman yaki yadda, har yasamu hanya yagudu
muma muka rufamai baya daniyar kamashi, muna
cikin gudu ne wayarshi ta fadi, damukaga
yayimana nisa sai muka kyaleshi muka dauki
wayar (phone),Muka dawo filin jirgin domin gudun
faruwar wani abu idan bamu nan" isah bare
yakarasa maganarsa yana kallon barista,
mungode
(isah bare body guard), barista yafada, daga
bisani
kuma yajuyo aguna "malan yusuf inafatan kaji
abnda isah bare yafada" barista yafada. Dagamai
kai nayi alamar "eh", "kayarda abnda yafada
gaskiya ne kenan"barista yafada. Wlh ba gaskiya
bane, nakarasa magana cikin kuka. murmushi
kawai barista yayi sannan yafiddo wata waya
daga
aljihunsa "kasan wannan wayar?" barista
yatambayeni. Tabbas nayi mamaki matuka, sbd
wayata ce nagani wadda tabace tun lokacinda
aunty bilki tasa akaman bugun tsiya a airport.
Dakyar na iya bude baki nabashi amsa, eh
wayata
ce. Sannan barista yamikama maga takarda
shikuma maga takarda yamika ma alkali, alkali
yana dubawa. Sannan muryar barista auwal taci
gaba da tashi "ina fatan kotu zata fahimci rashin
gaskiya atareda wanda ake tuhuma sbd yakaryata
gaskiya domin neman kubutar dakanshi, wannan
itace wayarshi wadda tafadi lokacinda yake
neman
kubutar dakanshi ahannun su Isah bare body
guard. Kuma inaso kotu tasan yusuf ya dade da
alwashin kashe wasu daga cikin iyalan alhaji sai
yanzu Allah yabashi sa'a"... "Idan dayan
bangaren
sunada magana akan maganar da akayi yanzu
zasu iya gabatarwa" alkali yafada, sannan barista
sady tazo agaban isah bare, tafara magana "isah
bodyguard kotu tanaso ka maimaita maganarda
kafada yanzu, abnd yafaru a airport...", shiru isa
body guard yayi har tsawon second biyar, daga
can gefe naji muryar barista auwal tana tashi
"Objection ya mai girma mai shari'a yakamata
kotu
tasanarda mai tambaya nan ba wurin wasa bane
da har za arinka magana ana maimaitawa"
barista
auwal na rufe baki sai sady tadauka, "yakamata
kotu tayi watsi da wannan korafi sbd anaso
wannan kotu mai adalci tagano gaskiyar abnda
ke
faruwa, idan abnda yafada gaskiya ne, to zai iya
maimaitawa batareda kuskure ba", "korafi bai
karbuba" alkali yafada... Sannan sady tayi godia,
isah bare yafara magana kamar zai iya
maimaitawa dai dai, kuma kamar bazai iyaba....
[11:57PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: 23ALKAWARI
Part23...
"yakamata kotu tayi watsi da wannan korafi sbd
anaso wannan kotu mai adalci tagano gaskiyar
abnda ke faruwa, idan abnda yafada gaskiya ne,
to
zai iya maimaitawa batareda kuskure ba", "korafi
bai karbuba" alkali yafada... Sannan sady tayi
godiya ga alkali tajuya wurin isah bare tareda
bashi iznin yamai maita maganar daya fada, kallo
daya zakamai kasan yana cikin fargaba, sunkuyar
dakai yayi yafara magana kamar zai iya
maimaitawa dai dai, kuma kamar bazai iyaba.
Nayi
mamaki matuka ganin yadda yasaki jikinshi yaci
gaba da magana hankalinshi kwance kamar
wanda
yabuda littafi yana karantawa, saida yamai maita
kalamansa kaf batareda yayi kuskure ba, sannan
yadaga kanshi suka hada ido da barista auwal
naga sunyi wani murmushi gaba dayansu, cikin
raina nace, lallai wannan al'amari akwai lauje
acikin nadi, barista sady kau dake tsaye agaban
isah bare kasa motsawa tayi tana kallonsa kamar
tana shirin yimai wata tambayar amman sai naga
tajuya cikin damuwa tayima alkali godiya takoma
wurin zamanta. Tasowa barista auwal yayi
agaban
kotu tareda fadar "idan wannan kotu mai adalci
ta
bani dama zan gabatar da wani jami'in tsaro
wanda yasan wani abu daga cikin wannan case
din", "kotu tabaka dama", alkali yafada yana daga
kansa. barista yakarasa maganarsa yana kallon
inda mutane suke zaune burjat suna kallon
wannan
birkitacciyar shari'ah. Ratsowa yayi cikin mutane
sanye da bakaken kayanshi na ma'aikata bai
zame
ko ina ba sai agaban barista auwal, sannan
barista
yayimai nuni da wurinda masu bada sheda ke
tsayawa tareda fadar "bismillah sajen", kallo daya
nayimai naganeshi, shine mutun nafarko da yayi
silar shigowata nan wurin, sbd shine mutun
nafarko dayafara rikeni dasunan mai laifi hadda
sanyaman ankwa... Tsaye yake yamaida
hannuwansa abaya ko motsawa bayayi saidai
kallon mutane dayakeyi daya bayan daya, sannan
barista yazo gabanshi yatsaya "kotu tanaso
tasan
ko kai waye" barista yakarasa maganarshi yana
duban sajen, "suna na sajen lawal gwanda kuma
ni
jami'in tsarone ina aiki a karkashin sabon gari
station" lawal gwanda yafada, sannan barista
yagyara tsayuwarsa yaci gaba da magana "sajen
lawal gwanda ko kasan wani abu dangane da
kisan da akayiwa dan gidan Alhaji jafar
muhammad?" barista yakarasa maganarsa tareda
dan kannare idonsa guda da alamar tambaya
karara a fuskarsa, gyaran murya sajen lawal
gwanda yayi sannan yafara magana "tabbas ina
daya daga cikin jami'an tsaronda suka kama
wannan mai laifin. Ranar talata 3-6-2014 Muna
cikin aiki sai mukaga wata mota tawuce a cikin
gudu wanda yawuce ka'ida, munyi kokarin
mutsaida mai tukin amma yaki tsayawa, dole
saida
muka bishi amman yasamu sa'a yabace mana
tundaga roundabout din kofar kaura, dukda haka
bamuyi kasa a gwuiwa ba mukabi hanya ko
munganshi, harsaida mukaje katsina club inda
ananne muna dai-dai zuwa muka taradda
wannan
bawan Allah yadurkusa da mutun agabansa sai
dakamai wuka yakeyi aciki, munyi iya kokarinmu
wurin ganin munyi sauri mun isa a'inda suke
amman kafin mukarasa har yagama aikinsa"
Sajen
lawal gwanda na zuwa nan da zanjensa sai
yafashe dawani irin kuka wanda yakarya zuciyar
musu saurarenshi, daga bisani kuma yaci gaba da
magana "na dade ina aikin dan sanda, kuma na
kama masu laifi dayawa, amman bantaba ganin
case dinda yatadaman hankali ba kamar wannan,
yadda naga yaduka yana dakama dan tahalikin
Allannan wuka aciki babu alamar imani atare
dashi
balle ayi maganar tausayi, bai daina dakamai
wukaba har saida muka...." yana zuwa nan sai
yayi shiru alamar kuka ne yaci karfinsa har
yakasa
ida maganarsa. Nan take wasu gunguni kasa
kasa
suka rinka tashi acikin kotun, masu sallallami
nayi
masu tsinuwa nayi, hadda masu yin Allah ya isa.
Nikau wani abune naji yataso ya tokareman
makoshi shi baikoma ciki ba shikuma bai fito ba,
sai alokacin na hango umma zaune takuraman
ido
sai faman zubarda hawaye take kusa da ita
hadiza
ce ta hada kai da kujera, ko baka tambaya ba
kasan kuka takeyi... Saida alkali yabuga wata
guduma akan teburinsa sannan kotun tayi tsit
kamar babu kowa aciki. Barista auwal yadafa
kafadar sajen tareda6 fadar "kayi hakuri sajen
kunyi
iya aikinku kuma, za'ayi ma wannan mai laifi
hukunci dai dai da laifin daya aikata, mungode
sajen zaka iya tafiya" yana gama magana da
sajen
kuma sai yajuya agun alkali "ina fatan kotu zatayi
duba zuwa ga wa'annan kwararan hujjojin dasuka
gabata domin yin amfani dasu wurin zartar da
hukunci akan wanda ya aikata wannan laifin
yadda
masu hali irin nasa zasu gani suma sudaina"
sannan yayi godiya ga alkali yakoma yazauna
kusa
da barista sady wadda fuskarta tacanza kamar
wadda aka aikomawa da rasuwar iyayenta. "ayau
1-7-2014 ne kotu takawo karshen wannan
shari'ah
bayan sauraren kwararan hujjoji da kotu tayi....."
turo kofa da akayi dakarfi, shine yayi silar tsaida
alkali daga maganar dayakeyi... "ku dakata" naji
amfada da karfi. cikin hanzari tanufo alkali da
wani
mutun a bayanta da alama da gudu suka karaso
kotun yadda naga su dukansu sunata faman
sheshsheka......
[11:57PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: ALKAWARI
Part24.....
"ayau 1-7-2014 ne kotu takawo karshen wannan
shari'ah bayan sauraren kwararan hujjoji da kotu
tayi da....." turo kofa da akayi dakarfi, shine yayi
silar tsaida alkali daga maganar dayakeyi... "ku
dakata" naji amfada da karfi. cikin hanzari tanufo
alkali da wani mutun a bayanta da alama da
gudu
suka karaso kotun yadda naga su dukansu
sunata
faman sheshsheka... Nayi mamakin ganin
haleematu cikin kotu a irin wannan lokacin, wasu
tambayoyi ne suka rinka ziyarta kwakwalwata,
me
yakawota? Ya akai tasanda wannan al'amarin?
Saidai bansan amsar tambaya ko daya daga
cikiba. "wlh bashi yakashe shi ba" takuma fada a
karo na biyu, wasu yan sanda ne guda biyu
sukayo
kansu da niyar fiddasu daga cikin kotun, ga
mamakina sai naga alkali ya daga masu hannu
alamar su tsaya, yan sandan nan basuyi gardama
ba wurin bin umarnin alkali ta hanyar komawa
inda
suka fito. Kotun tayi tsit kowa hankalinshi
yakoma
agaban alkali domin ganin abnda ke faruwa
"maimaita abinda kika fada" alkali yafada yana
kallonta "wallahi wanda ake zargi bashi ya aikata
wannan laifinba" cikin wata murya kamar wadda
take shirin yin kuka. alkali yakuma dubanda
tareda
tambayarta "ke wacece?", "suna na haleematu
usman zango" tabashi amsa atakaice, alokacin
alkali ya ajiye alkalamin dake hannunsa ya harde
hannuwanshi guda biyu yakara jefomata wata
tambayar, idanuwanshi akanta ko kiftawa bayayi,
"Haleematu kinada shaida akan abnda kika fada?"
tunkafin yarufe bakinshi ta dagamai kai alamar
"eh" sannan kuma tafada a bayyane "eh" tareda
juyowa bayanta tanuna wannan mutumen wanda
suka shigo tare kansa a duke. Alkali yadubesu
sannan yadauki alkalamin dake a gabansa yayi
rubuce-rubucen da yasaba, sannan yadago kansa
yaba mutumen umarnin yashiga inda aka tanada
domin bayarda shaida, batareda bata lokaciba
yakarkata akalarshi yashige cikin dan akurkin da
masu shaida ke tsayawa... Cikin hanzari barista
sady tamike tayi tattaki zuwa inda yake tsaye,
"bawan Allah kotu tana bukatar sanin ko kai
waye"
barista ta tambaya, "sunana idi mai gadi" yabata
amsa atakaice, sady ta daga kanta tadubeshi
tace
"idi mai gadi, kamar yadda kotu take zato kasan
wanda yayi wannan kisan, ya abin yake?" sady
tafada da alamar tambaya a fuskarta, sannan idi
mai gadi ya girgiza kai kamar kadangare tareda
cewa "eh tabbas naga wa'anda sukayi wannan
kisan", "kotu tanason taji gaskiyar abnda kasani"
barista sady tafada tareda kurawa idi ido, "ranar
wata talata ina cikin dan dakina wanda aka
tanada
domin masu gadi, ina zaune ina sauraren radio
sai
naji kamar ana kokowa, sai banmaida hankali
akai
ba saboda nasan wurine na mutane, jim kadan
kuma naji ankwalla wata irin kara wadda
dukwanda yaji karar yasan bata lafiya bace,
hakan
yasa nafito domin inga abinda ke faruwa, ina
fitowa nagansu tsaitsaye sun rufe fuskarsu da
wani bakin abu, ga wani dan saurayi wani dan
saurayi kwance a gabansu da wuka soke a
cikinsa
sai jini ke bin jikinsa, nayi yunkurin inruga domin
neman ceto agun mutane amman nakasa ko
juyawa Nakasa motsawa daga inda nike, nan take
nayi mutuwar tsaye, na kasa buda baki inyi
magana balle mutane suji, har sukagama abnda
sukeyi suka juyo domin tafiya sai suka hada ido
biyu dani, nayi zaton zasu tafi su kyaleni amman
naga sunyo kaina sun sungume ni suka sanya
acikin mota suka kaini bayan gari, daya daga
cikinsu yace akasheni kawai saboda kar asirinsu
yatonu, sai wani yace a'a kar sukasheni da
hannunsu amman suyiman abinda zanmutu
dakaina bayan nasha wahala, nanfa suka hau
duka
na saida sukaga ko dan yatsa bani iya motsawa
sannan suka daukeni zasu jefa acikin ruwa, sai
daya daga cikinsu ya daureman ido dawani kyalle
daganan bansan abnda yakara faruwa ba saidai
nabude ido naganni cikin asibiti wannan baiwar
Allah tana dubani, wadda itace ta ceci rayuwata"
yakarasa maganarsa yana nuna haleematu,
sannan
barista sady tace "lallai idi mai gadi kasha
wahala"
lokacin tayi wani nishi mai kama da ajiyar zuciya,
daga bisani kuma taci gaba da magana "yanzu
idan kaga wa anda sukayimaka wannan
ta'annadin
zaka iya ganesu?", "eh zangane su indai naga
fuskar daya daga cikinsu" inji idi mai gadi, "idi
mai
gadi akwai daya daga cikin mutanen dake zaune
anan?" takarasa maganarta tana nuni da mutanen
dake zazzaune suna kallon wannan shari'ah
marar
kan gado. Nanfa idi mai gadi yafara duban
mutanen dake zazzaune a kotun kowa yasha jinin
jikinshi... Cikin hanzari barista auwal yamike
tareda fadar "Objection ya mai...." tunkafin
yakarasa maganarsa Alkali yatarbi hanzarinshi da
cewa "korafi bai karbu ba".............
[11:57PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: 25ALKAWARI
Part25....
Cikin hanzari barista auwal yamike tareda fadar
"Objection ya mai..." tunkafin yakarasa
maganarsa
Alkali yatarbi hanzarinshi da cewa "korafi bai
karbu
ba", barista auwal yakoma yazauna a sanyaye,
barista sady kau wani dan gajeran murmushi
kawai tayi tareda ba idi mai gadi umarnin yaduba
acikin mutanen ko za'aga daya daga cikin
wa'anda ake nema. Cikin lokaci dan kankane
kotun tayi tsit ko kwakwkwaran motsi babu
maiyi,
saidai wannan yakalli wannan, wannan yakalli
wancan, nan take wani zafi yayoma kotun lale
marhabin dukwanda kagani sai zufa (jibi) yakeyi
kamar wa anda aka watsama ruwa. Cikin raina
nace wai abinda nake ganin yana faruwa acikin
wasu fina finai da littattafan marubuta, shine yau
yake faruwa agabana kuma akaina... "Ga daya
chan!!!" kalmar datayi silar maidoni daga tinanin
danakeyi, itace kalmar data tada hankalin
dukwanda yake acikin kotun, ni kaina saida
gabana
yafadi sanadiyar jin wannan kalma, "ga daya can
zaune" idi mai gadi yakuma fada a karo nabiyu
yana nuna gungun wasu mutane dake zaune acan
baya. Tunda nike tsaye a kotun bantaba sanin
suna nanba sai yanzu... Abba ne zaune akan
kujera daga gefenshi kuma mahaifiyarshi ce aunty
bilki, daga bayansu kuma wasu bakaken mutane
ne tsai tsaiye kamar gumaka. mikewa yayi kamar
wanda aka tsira ma allura "karya yakeyi kada ku
saurareshi" abba yafada a rikice bakinsa har wani
kumfa kumfa yakeyi, kafin yakara motsawa yaji
wasu police guda biyu sunyi carab da kugunshi
suka jawoshi har agaban kotu. Barista sady
takalli
idi mai gadi tareda cewa "ka tabbata yana daga
cikinsu?" ta idar da maganarta tana nuna abba
amman idanuwanta suna akan idi mai gadi. "eh
shine, bazantaba manta wannan fukar ba" idi
yafada yana nuna Abba. "mungode idi zaka iya
zuwa kazauna, mai yiyuwa zamu bukaci wani abu
agareka nan gaba kadan" barista sady ta fadama
idi.. "Ya mai shari'a inaso abani dama domin
zantawa da abokiyar tafiyar idi mai gadi" sady
tafada tana duban alkali, "kotu ta amince" alkali
yabata amsa atakaice, batareda bata lokaciba
haleematu ta hallara agaban kotu, "malama
kibayyana ma kotu ko ke wacece", "sunana
haleematu usman zango, kuma ni likita ce mai
zaman kanta a asibitin a Alheri clinic a garin
zangon daura", barista sady tadan nisa sannan
takuma tambayar haleema, "malama haleematu,
ko
ince doctor haleemah, tabbas aikinki yayi rana
kuma yayi amfani ta hanyar ceton rai biyu lokaci
guda, amman kotu tanaso kifadi abnda kika sani,
dakuma yadda har kukasan da wannan shari'ah?"
sady takarasa maganarta tana duban haleemah,
"ranar wata talata da misalin karfe 8:30pm, wasu
makiyaya suka kawomana marar lafiya
magashiyan, bamuyi niyar amsarsaba saboda
9:00pm muke tashi, amman ganin yadda marar
lafiyar yake yasa dole muka amsa saboda zai iya
rasa ransa akowane lokaci. Hannunsa daure
fuskarsa ma daure dawani hankici, haka suka
kawoshi kuma suka shaida mana cewa abakin
ruwa suka sameshi, suma basusan abnda yafaru
dashiba, anan asibitin muka dauki dawainiyarshi
tundaga aikinda akayimai, har kudaden magani
hartsawon wata guda sannan muka samu yaji
sauki sosai har yake iya takawa yana tafiya
dakanshi, sannan yabamu labarinshi da abnda
yafaru dashi, kamar yadda yafadamaku abaya"
haleematu tana zuwa nan da zancenta sai tayi
shiru, itakuma barista sady dataga haka sai
takara
jefomata wata tambayar "ya akai kukasan
wannan
shari'ar ta shafi abnda akayima idi mai gadi?"
sady tafada fuskarta cike da mamaki, haleematu
kau gyara tsayuwa tayi taci gaba da koro bayani
"wannan shari'ar tayi suna sosai acikin jahar nan
harda ma kewaye, shari'ar ta zagaya ko ina ta
hanyar kafafen yada labarai, kusan ko wane
media
sun sanarda faruwar wannan abu.. Jiya da
misalin
karfe 8:00pm muna zaune hadda idi mai gadi
muna kallon kttv, anan mukaji sanarwar wannan
shari'ah, idi mai gadi ya tabbatar mana akan
wannan abn ne akayi niyar halakashi sbd dan
jaridar dayayi sanarwar, saida yafadi ranar da
akayi kisan kuma da wurin da abn yafaru, hakan
yasa muka tabbatar da labarin da idi mai gadi
yafadamamu, shiyasa muka garzayo domin fadar
gaskiyar abnda yafaru", barista sady tayi ajiyar
zuciya tareda girgiza kai "idan hankicin da aka
daurema idi mai gadi fuska dashi yana kusa, kotu
tana bukatar ganinshi", nandanan tafiddo hankicin
tareda mikawa barista sady kamar daman jira
take
atamabayeta, barista sady taduba sannan tajuya
agun alkali, "ya mai shari'ah wannan shaidar
kadai
ta isa ta wanke wannan bawan Allah da ake
zargi,
kuma wannan shaidar ta isa takama wanda ya
aikata wannan laifin yakoma gefe yazauna cikin
yan baruwana, yanayima mutane kallon tom and
jerry, saboda ajikin hankicin harda sunanshi kuma
sunan ba irin wanda ake rubutawa ba da biro ko
makker, wannan daga company ne kamar yadda
wasu mutanen suke zuwa anayomasu abu da
sunansu ajiki", barista sady tamikama maga
takarda hankici, shikuma maga takarda
yamikama
alkali, alkali yayi yan dube dubenshi tareda
rubutun
da yasaba........
[11:57PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: 26ALKAWARI
Part26...
Barista sady tamikama maga takarda hankici,
shikuma maga takarda yamikama alkali, alkali
yayi
yan dube dubenshi tareda rubutun da yasaba
daga
bisani kuma yadago kansa yaci gaba da magana
"anan kotu zata diga aya tahanyar yin amfani da
kwararan hujjojin da suka gabata domin yanke
hukunci, kotu ta wanke wanda ake zargi da
aikata
laifin kisa, kuma kotu ta yankema wanda yayi
wannan aikin hukuncin zama a gdan kaso tsawon
shekara 25 tareda aiki mai tsanani" Alkali yana
rufe bakinshi yabuga gudumar dake ajiye
agefensa
tareda mikewa tsaye. Batareda bata lokaci ba
wasu police suka sanyama abba ankwa suka fice
daga kotun... Nan danan naga mutane sunyo
kaina
sai mikoman hannu sukeyi daniyar mugaisa,
wasu
nayiman barka wasuma bansan abnda suke cewa
ba sbd hankalina yana agun umma na wadda take
tsaye ta daga hannayenta sama tanayima Allah
godiya... daganan bamutsaya wani abuba muka
dunguma muduka zuwa gida....... Nida umma
mun
nuna farin cikinmu sosai tareda nuna jin dadinmu
akan namijin kokarin da haleematu da barista
sady
sukayi mana. Bayan sati daya dagama wannan
shari'ah muna zaune nida umma da hadiza muna
fira, kamar yadda muka saba sai mukaji anyi
sallama, dukda banjuya ba amman nagane
muryar
wanda yayi sallamar, usman ne yashigo har
gaban
umma yazauna yagaisheta fuskarshi da alamar
damuwa "umma kiyi hakuri da duk abnda yafaru
kuma ina rokonki gafara kiyafema mahaifinmu
akan
abinda yafaru tabbas yayine akan rashin sani..."
kafin yakarasa maganarsa umma tadagamai
hannu
"ya isa haka, babu abnda kukamana kuma, kuje
Allah yasanyamaku Albarka, idan kuma
mahaifinnaka ne ya aiko ka, kacemai babu
komai"
umma tafada cikin wani yanayi fuskarta babu
yabo
kuma babu fallasa, nayi zaton usman zaiji dadin
maganarda umma tafada amman sai naga
fuskarshi bata canja ba daga alamar damuwar
dake damunshi, "ai yanzuma tareda alhaji mukazo
shi yace inkawoshi" usman yafada lokacinda
yasunkuyar dakanshi kasa yana wasa da
makullan
dake hannunshi, "da ba kai kadai kazo ba,
amman
kabaroshi waje yanata jiranka kamar wani
abokinka" cikin sigar fada take maganar, "tashi
mana, yusuf kuje kushigo dashi" takarasa
maganarta tana kallona... Tunkafin mushigo
hadizah ta shimfida tabarma yadda kowane bako
yagani yasan shi akayima wannan shimfidar,
shiyasa alhaji baiyi wata wata ba kawai yazauna
akan tabarmai, bayan sungama gaisawa ne alhaji
yake fadama umma "nazo dakaina ne domin
abnda
yafaru lokacin baya, tabbas kuskure ne anriga
anyi
kuma ina rokonku kuyafemana, bawai dan
matsayina ba ko dukiyata ba, shiyasa nataso
dakaina batareda na aiko wani ba", "a'a babu
komai alhaji wannan abu matsayin kaddara ne ko
ince kaddara ce daga Allah, shikadai yasan
dalilinda yasa haka tafaru atsakaninmu, bakada
laifi alhaji ai danda mutum yahaifa kuma aka
kaudashi alokaci guda ai dole mutun yadau
mataki
tare da bin diddikin abnda yafaru, wannan shine
halin iyaye nagari masu kula da yaransu, babu
komai wlh komai yawuce" umma takarasa
maganarta tana girgiza kai amman idanuwanta
suna kallon kasa "Nagode sosai" alhaji yafada
atakaice, sannan kuma yaci gaba da magana
"kuma naji duk abnda ke tsakanin yaron wajenki
da
diyata... Kinsan aure wani nauyi ne wanda mutun
zai dauka kuma aure bazaitaba yiyuwa ba idan
babu sana'a, hakan dana fada bawai yana nufin
na
hanashi auren diyata bane, amman gaskiya bazan
bayarda itaba a'inda zatasha wahala, kuma
bazan
iya sakin akuya ba daga baya tadawo tana ciman
danga, su yara ne bazasu iya fahimta taba,
amman ke amatsayinki na babba kuma
mahaifiyarshi kinsan abnda nike nufi". "haka Allah
yaso alhaji ai duk abnda Allah yaso to babu
yadda
bawa zayayi, talauci da dukiya dai duka na Allah
ne, Allah yasa hakan shi yafi alkhairi" umma
tafada. Ba karamin faduwa naji gabana yayi ba
sanadiyar jin wa'annan maganganun da alhaji ke
fada, ina dago kaina sai nahangi usman hawaye
sai tsiyaya suke daga fuskarshi, cikin raina nace
daman yasan za'a hanani auren yasmeen ne
shiyasa yazo ranshi abace, a gurguje alhaji ya ida
maganarsa wanda ni banma san abnda yake fada
ba sbd hankalina gaba daya yabar jikina, "to sai
anjima Allah yakiyaye" naji umma tafada sai
lokacin nalura alhaji da usman har sun miike
tsaye
suna niyar tafiya, nikuma danaga haka sai nayi
sauri namike tareda mikama usman hannu
daniyar
mugaisa tunda zasu tafi, ga mamaki na sai naga
Alhaji yamikoman hannu shima muka gaisa,
mungaisa lafiya lau amman abnda yabani mamaki
shine, alhaji yakurama hannu na ido, kuma
nakasa
gane abnda yake kallo, nayi kokarin fidda
hannuna
daga cikin nashi hannun amman naji yakara
rikewa
gam, kamar anyimai umarni da yarikeni kar
ingudu,
nakara duba hannu na naga babu komai ajiki inba
zoben dake acikin danyatsa na ba......
[11:57PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: 27ALKAWARI
Part27....
Zaune suke acikin falo babu maiyima wani
magana
acikinsu, kowa hankalinshi a tashe kamar yan
zaman gaisuwa... Usman da yasmeen ne suke
zaune akan carpet dinda ya mamaye falon sun
sunkuyar dakansu kasa, daga chan gefensu kuma
aunty bilky ce zaune. Akan kujera kuwa
mahaifiyar
su yasmeen ce tare da mijinta alhaji jafar, wanda
yahada hannayenshi guda biyu yadora abisa
kanshi yana kallon kasa kamar mai shirin kwalla
ihu, sunkai wurin dakika 2 babu wanda yayi
magana acikinsu, alhaji ne yadago kansa
fuskarshi
cike da damuwa, yakalli yaranshi guda biyu dake
zaune usman da yasmeen sannan yamaida
dubanshi ga kanwarsa aunty bilky mahaifiyar
abba,
sai alokacin alhaji yakatse shirunda yamaida
dakin
kamar makabarta "na kulle ku har tsawon wani
lokaci sbd ina tinanin zaku kawoman matsala
acikin wannan shar'iah wadda aka kashe dan
uwanku" alhaji yafada yana kallon usman da
yasmeen dake zaune babu wanda yadago kansa
acikinsu balle yafadi wata magana, "kuyi hakuri
'ya'ya na nayi hakane sbd naga kuna neman
kukawo man matsala kuma sanin kanku ne,
yazamar mani dole inga bayan dukwanda
yakasheman dan danahaifa da cikina, shiyasa
nadamka wannan case din a hannun kotu dan
abimamu hakkinmu, matsalar dake dakwai yanzu
akalar shari'ar tacanza alkibla tana neman
tadawo
cikin gidannan gaba dayanta, sbd abba ne mutun
nabiyu wanda ake zargi kuma binciken da kotu
tayi
kamar yana nuna cewa yusuf da ake zargi
bashine
yayi kisanba" yana zuwa nan da zancensa aunty
bilky tamike cikin bacin rai "haba alhaji wace
magana kake son kafada ne, dukda bakai ka haifi
abba ba ai abba danka ne, saboda ni nahaifeshi
da
cikina, kuma 'ya'yana naka ne saboda kana
uwana, ta yaya kake tinanin abba zai kashe aliyu
haba alhaji" takarasa maganarta tareda mikewa
tsaye kamar wadda take shirin yin dambe, ganin
haka ne yasa usman mikewa tsaye daniyar fita
daga falon sbd bayason jin maganganun dake
shiga tsakanin mahaifinshi da aunty bilky, muryar
alhaji ce tasaidashi daga niyar ficewa dayake "ina
zakaje?", shiru usman yayi tsawon daqiqa 5
sannan yace "dady zanje kitchen insamu abnci
yunwa nakeji", "dawo kazauna, kayi waya yanzu
akawo maka anan kaci" badan usman yanaso ba
dole tasa yazauna, yakira kuku yafada masa
uzurinsa. "ke samu wuri kizauna", alhaji
yafadama
bilki cikin tsawatarwa, "zama?! A ina zan zauna
ana neman sanyamana kisa..." "ke ni kike fadama
wannan maganar?, matsala ce wannan tataso
kuma mu zamu maganceta amman kina nunaman
ke dabba ce", "ni kake cewa dabba alhaji?, ni
kake
wulakantawa acikin 'ya'yanka gaban matarka!"
bata jira komaiba ta fizgi dan kwalinta tayi waje
tana sabbatu wanda babu mai iya gane abnda
take
fada, afusace tafita tana zuwa dai dai kan kwana
indo tafadi agabanta da kwanonin abnci
ahannunta, "ke mahaukaciyar inace tsohuwar
banza, ni zaki fadomawa?" aunty bilki tafada tana
dafe kirji, "yi hakuri hajiya wallahi tuntube nayi
kuma bansan zaki karyo kwana ba kingani abincin
dazankaima usmanu ne nadauko cikin hanzari ki
gafarceni" indo tafada cikin sanyin murya, ko
saurarenta bata tsaya yiba, tawuce fuuu.......
Saura kwana biyu akoma kotu wanda ake tinanin
shine zama na karshe a cikin wannan shari'a
wadda tashare watanni ana gabatarwa... Umma
ce
zaune tareda hadizah kanwata, dakuma
haleematu
(doctor). Zaune suke suna tattaunawa akan
wannan shari'ah su dukansu suna jimamin
sakamakon dazai wakana bayan angama wannan
shari'ah. "umma zantafi gida kafin yamma tayi
zanbiya wani wuri ne" haleematu tafada tareda
sanya hannu daniyar daukar jakarta, "to
tunyanzu,
bakibari ko rana tayi sanyi", "aa umma kinsan
hanyar tamu batada kyau, kuma inaso zanbiya
gdan wani kanin baba na shiyasa", "to diyarnan
mungode Allah yakaiki gda lafia, kigaidaman
mahaifan naki" "ameen umma zasuji", hadizah
tarakata har bakin motar ta... bayan tafiyar
haleematu baifi 30mnt ba sai ga barista sady
tashigo, ba karamin dadi umma tajiba data ganta
sbd itace lauyar datake kare ni batareda ankirata
ba kuma batareda anbiyata ba.. Agajiye tashigo
tanemi wuri tazauna. Hadizah ta tashi ta
debomata ruwa... "umma mun gama duk
bincikenda yakamata muyi yanzu rana kawai
muke
jira tazo, kuma kitayamu da addu'a Allah yabamu
sa'a" sady tafada lokacinda take ajiye cup dinda
ke hannunta, "addu'a itace muketayi koda yaushe
barista, mungode da irin wannan halacci dakike
nuna mana", "a'a umma babu komai wannan
kamar nayima kaina ne" sady tafada, "samun irin
haka yanzu yanada wahala, musamman ma ace
mutun bai sankaba kuma bakasanshi hakanan
yashigo rayuwarka yataimaka maka ai ya
cancanci
yabo..." Umma kibar wannan maganai, yanzu
zanje gdan alhaji jafar wurin usman abokin yusuf,
akwai wasu bayanai danike bukata agunshi, gashi
kuma lokaci yakure, saura kwana biyu akoma
kotu", sannan tamike tsaye tana magana "daman
zuwa kawai nayi ingaidaku kuma insanar daku
cewa mungama komai" barista sady tafada,
"mungode sosai Allah yashigarmana gaba, kuma
Allah yabada sa'a" inji umma........
[11:57PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: 28ALKAWARI
Part28....
kamar kullun yauma kotun tacika makil da
mutane
amman da alama yau mutanen sunfi yawa
saboda
har ta window kawunan mutane ne suke lekowa,
wa anda basu samu wurin zama acikin kotun
ba...
"ayau kotu zataci gaba da sauraren kara wadda
Alhaji jafar muhammad yashigar akan kisan gillar
da akayima dansa Aliyu, wanda ake zargin mutun
biyu wa anda ke tsare da aikata laifin, yusuf da
Abba kuma wannan itace shari a tafarko daza
afara gabatarwa a safiyar yau litanin wadda tayi
dai dai da 11-8-2014" maga takarda yana
kammala bayaninsa yasamu wuri yazauna, adai
dai
lokacin aka shigo damu kowannenmu daddaure
kamar awaki. Wuri daya aka hadamu nida abba
acikin wani dan akurki muna fuskantar
mutanenda
sukayima kotun cikar kwari.... Alkali yakalli
bangaren da lauyoyin suke zaune barista sady ce
tafara mikewa, cikin kayan aikinta "kamar yadda
kuka sani nice barista sady kuma nice lauya
wadda take kare wanda ake zargi na farko
(yusuf)"
tana gama fadar haka tayima alkali godia tareda
zama wurinta.... "sunana barista auwal kamar
yadda akasani, kuma nine nadawo amatsayin
lauya wanda yake kare mutun na biyu wanda ake
zargi (abba)" sannan shima yakoma wurin
zamansa tareda yima alkali godia, bayan alkali
yagama yan rubutunsa yakuma dago kai akaro
nabiyu, "kamar yadda yagabata muna bukatar
lauyoyin kowane bangare sukawomana shaidu da
hujjojin da zasu gamsar da kotu akan wannan
zargi da akeyima wa annan mutane guda biyu,
kotu tabada dama wanda yakeda magana zai iya
farawa" alkali yakammala maganarsa yana kallon
inda lauyoyin suke azaune, barista auwal ne
yafara
mikewa "kamar yadda nafadama kotu abaya
cewar
yusuf shine yayi wannan kisan hakan yasa
nadawoma kotu da hujjoji kwarara wa anda suke
bayyana hakan, inaso kotu tabani dama domin
zantawa da wa anda ake zargi" barista auwal
yafada yana kallon alkali "anbaka dama" alkali
yafada atakaice, barista yafara da abba "malan
abba inaso kasanarma da kotu ko kai waye
dakuma yadda kuke da alhaji da yan gdansa",
"sunana abba ibrahim sabo, alhaji kawuna ne,
kuma shine matsayin ubana, sbd tunda nabude
ido
a gdanshi na tsinci kaina kuma yanamin duk
abnda
uba yadace yayima dansa ci da sha sutura harda
karatuna", "mungode malan abba" barista auwal
yafada, sannan yajuya agun alkali "ya mai
shari'ah
inaso kotu taduba tagani tsakanin alhaji jafar
dakuma abba. Ai ko kare idan akayimai wannan
halaccin bazaiyi abnda ake neman cewa abba
yayi
ba, wannan sharri ne kawai aka lakafa masa"
barista auwal yafada yana nuna abba da
hannunsa
amman idanuwansa suna akan alkali, "ya mai
shari'ah inaso kotu tabani dama domin zantawa
da wanda ake zargi na farko" barista auwal
yakuma fada, "kotu tabaka dama" alkali yafada
lokacinda yake rubutu akan takardar dake
agabansa...Barista auwal yakaraso agabana
yatsaya yana kallona daga bisani kuma yace,
"basai na tambayeka kokai waye ba sbd kotu
tasanka sanadiyar laifinda ka aikatane yataramu
anan...". "Objection ya mai shari'ah!" sady tafada
dakarfi tareda mikewa tsaye sannan taci gaba da
magana, "yakamata mai magana yasan irin
kalaman da zai rinka amfani dasu wurin tuhumar
mutun, kuma yadaina alakantashi da laifinda ake
zargi, sbd haryanzu ba'a tabbatar da wanda yayi
laifinba cikin bincike ake", sady tafada tana kallon
alkali, "mai magana yagyara harshensa" alkali
yafada. Sannan barista sady tadan sunkuyar
dakanta tayi godiya tareda komawa mazauninta...
"yusuf inaso kasanar da kotu hakikanin gaskiyar
yadda akayi har kasamu hanyar yin mu'amala da
iyalan gidan alhaji jafar" barista auwal yafada
yana
kallona "mutunci ne kawai yahadani dasu"
nabashi
amsa, "mutunci kamar ya kenan, wa kasani acikin
gidan?" yakuma tambayata akaro nabiyu, "inada
aboki a gdan sunanshi usman" nafada batareda
wani fargaba ba, sannan barista yagyara
tsayuwarshi "minene tsakaninka da yasmeen yar
gdan alhaji jafar?" nayi mamakin jin wannan
tambayar hakan yayi silar daureman kai narasa
abnda zancemasa, ganin haka shikuma yaci gaba
da magana "idan ka kasa fada, ni bara
infadamaka" barista yafada yana kallona tareda
wani murmushi "yusuf kundade tareda yasmeen
yanayin shakuwarku ne yasanya har soyayya
tashiga tsakaninku. hakane ko bahaka bane?",
kawai dagamai kai nayi alamar "eh hakane",
"bayan tadawo daga makaranta kaji labarin
anyimata miji, ma'ana anzabamata wanda zata
aura. na fada dai dai?" barista auwal yakuma
tambayata a karo nabiyu, wannan lokacinma kai
kawai nadagamai kamar kadangare tareda fadar
"eh hakane", sannan barista auwal yajuya agun
alkali yaci gaba da magana, "ina fatan kotu zatayi
duba kuma tayi la'akari da irin abnda yashiga
tsakanin iyalan gidan alhaji jafar da yusuf, kowa
yasan zafi dakuma radadin da masoya keji idan
aka rabasu da junansu, wannan kadai ya isa gaba
tashiga zuciyar yusuf shida yan gidan su
yasmeen,
har zuciyarshi tasa ya aikata mummunan aiki
akansu da niyar daukar fansar abnda akayimai.
sai
tsautsayi ya afka akan marigayi aliyu...
[11:57PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: ALKAWARI
Part29....
Barista auwal yajuya agun alkali yaci
gaba da magana, "ina fatan kotu zatayi duba
kuma
tayi la'akari da irin abnda yashiga tsakanin iyalan
gidan alhaji jafar da yusuf, kowa yasan zafi
dakuma radadin da masoya keji idan aka rabasu
da junansu, wannan kadai ya isa gaba tashiga
zuciyar yusuf shida yan gidan su yasmeen, har
zuciyarshi tasa ya aikata mummunan aiki akansu
da niyar daukar fansar abnda akayimai. Kuma ya
mai shari'a na tanadi shaidu wa anda suke nuna
cewa ba abba bane yayi wannan kinsanba, inaso
kotu tabani dama domin gabatar da wa'annan
shaidu nawa", "kotu tana jiran shaidunka" alkali
yafada yana kallon barista auwal... Barista
yamaida dubansa ga zuwa mutanen da ke zaune
a
kotun tareda fadar "kotu tana bukatar ganin dan
tashe", batareda bata lokaci ba wanda ake nema
yabayyana agaban kotu, "bawan Allah kotu
tanaso
kabaiyana mata ko kai waye" barista yafada,
"suna
na S.D dan tashe" mai bada sheda yaba barista
amsa atakaice, "s.d dan tashe ya kake da abba
kokuma ince me kasani akan abba" barista
yafada
yana kallon dan tashe, "nasan abba sosai, sbd
abokina ne na kusa da kusa kuma tunda nike
dashi
bantaba ganin yayi wani mugun hali ba dahar
za'a
iya kwatantawa da kisan kai, abba ko dan tsako
bazai iya kashewa ba balle mutun", "mungode sd
dan tashe" barista yafada tareda komawa
mazauninsa. Alkali yadukar dakansa yayi rubutu
akan takardar dake gabansa sannan yadago
kansa
tareda cewa "idan mai kare wanda ake zargi
nafarko (yusuf) tanada magana da shaidar da aka
gabatar, zata iya mikewa", sady tamike tareda
gyara zaman rigarta tadubi dan tashe tace "sd
dan
tashe kace kasan abba sosai harma kafadi wasu
daga cikin halayensa", "eh hakane nasanshi farin
sani" dan tashe yafada, "shekarunku nawa tareda
abba", "akalla munkai shekara biyar zuwa shida"
dan tashe ya amsama barista tambayarta, "kuna
tareda abba ne alokacinda akace wannan abu
yafaru?", sady takuma tambayar dan tashe, "aa
gaskiya bamu tare kuma bansan inda yatafi ba
sbd
nima na nemeshi a lokacin banganshiba kuma
nakira wayarshi bansamu ba", dan tashe yafada
"to dakanemi wayarshi baka samuba ko kaje
gdansu nemansa?" sady takara tambayar dan
tashe, "a'a bantaba shiga gdansuba balle inje
daniyar nemansa, duk idan ina nemansa muna
haduwa ne a majalisa".... "Ya mai shari'a
yakamata kotu tayi duba izuwa zancen wannan
mutum wanda yake ikrarin yasan abba farin sani
amman baitaba shiga gidansu ba to tayaya
zaisan
halayensa, inaso kotu tayi watsi da wannan
shaida
sbd babu makama acikinta" sannan tadan rusuna
kanta tareda fadar "nagode ya mai sharia" tana
gama magana takoma tazauna... Bayan alkali
yayi
yan rubuce rubucensa dayasaba sannan yadago
kansa, "idan akwai mai wata magana, kotu tana
saurare", barista sady ce takara mikewa tsaye
"inaso kotu tabani umarni domin zantawa da
abba", "anbaki dama" alkali yabata amsa,.. "abba
kamar yadda ka tabbatarma kotu dacewa anbaka
yasmeen amatsayin wadda zaka aura, shin ku
kuka hada kanku kokuwa iyayenku ne suka
hadaku?", "Iyayenmu ne sukayi wannan
shawarar",
"Objection ya mai shari'a, banyadda da
maganganun da ake tuhumar abba dasuba sbd
basu shafi wannan shari'ar ba" barista auwal
yafada tareda mikewa tsaye, yana karasawa
kuma
yakoma yazauna, bayan yazauna ne sai barista
sady tamike "ya mai shari'a inaso kotu tayi watsi
da wannan korafi saboda babu wanda yasan
dalilin
faruwar wannan abin, kuma wannan ba karamin
case bane zai iya shafar duk inda ba azato",
"korafi bai karbu ba" cewar alkali, "nagode ya mai
shari'a" sady tafada tareda juya agun abba "abba
lokacinda aka shaida maka za ahadaku kaida
yasmeen, kasan abinda ke tsakaninta da yusuf?"
sady tatambayi abba, "eh nasan abnda ke
tsakaninsu", "meyasa kakeson aurenta dukda
kasan tanada wanda takeso?", "saboda bazan iya
juya hannun kyautarda alhaji yayimanba, idan
naki
amincewa kamar na nuna rashin godia ne kuma
nima inasonta", abba yafada, "itama ta amince
kamar yadda ka aminche da zabin iyayenku,
kokuwa ta kawo gardama acikin maganar?", "a'a
batayi gardama ba amman har bayan anhadamu
bata fidda son yusuf a zuciyarta ba" abba yabata
amsa... Ya mai shari'ah ina fatan kotu ta fahimci
acikin zancendanayi da abba ya tabbatar mana
dacewa yasanda yusuf amatsayin saurayi ko ince
masoyin yasmeen ne. Idan kotu tayi duba da
abinda ke tsakanin yusuf da abba dakuma
yasmeen, shi zai nuna mana cewa abba ne yayi
laifin, sbd hakane ma yasa lokacinda suka kashe
aliyu suka kyale yusuf batareda sunyimai ko
kwarzane ba amman akayi yunkurin kashe idi mai
gadi, dan agoga ma yusuf wannan laifin tareda
chusa kiyayya tsakanin yusuf da yasmeen,
saboda
zatarinka yimai kallon wanda yakashe mata dan
uwa, shikuma abba yasamu abnda yakeso kenan,
sai ya aureta batareda wata fargaba ba sbd
shima
yana sonta kamar yadda yafada ma kotu abaya"
barista takara gyara tsayuwa sannan tace
"wannan
shine mabudin dumbin hujjoji da shaidun da nike
tafe dasu agaban kotu kuma zan gabatar idan
kotu
tabani umurni".....
[11:57PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: Part31...
"barista auwal ko kanada wata magana
ko tambayoyinda zaka iya yima wannan shaida",
barista auwal yamike tsaye yadubi indo yace
"malama indo shekararki nawa kina aiki a gdan
alhaji?", "shekarata 8 gidan alhaji", "tsawon
shekarunda kikayi kina aiki a gidan, shin kintaba
jin wata yar hatsaniya ta tashi a gidan", "gaskiya
zaman lafiya akeyi a gidan alhaji rigima bata taba
kaurewa a tsakaninsu ba" indo tafada tana girgiza
kai, barista auwal yayi wani gajeren murmushi
sannan yajuya agun alkali "ya mai shari'a abisa
tambayoyin danayimata sun nuna cewa shedar da
wannan baiwar Allah tabayar karyane kawai
takeyi,
kirkirarren labarine sbd ita dakanta tashaida ma
kotu cewa gidan alhaji zaman lafiya akeyi
sashensu yanason sashe shiyasa babu wanda
yataba jin kansu, to tayaya wa'anda sukeyin irin
wannan zaman zasuyi yunkurin kashe junansu,
yakamata kotu tayi watsi da wannan shaida"
yana
gama surutunshi yayi godiya yasamu wuri
yazauna, alkali yakuma yin rubutunshi na al'ada
daga bisani kuma yadago kansa "barista sady
kinada wata tambaya dazakiyi?", barista tamike
tareda fadar "a'a ya mai shari'ah iyakar
tambayoyin dazanyimata kenan", sannan tamaida
dubanta akan indo tace "mungode malama indo
zaki iya komawa mazauninki kizauna idanma
kinada uziri a gida zaki iya tafiya" tana gama
magana kuma takara juyowa agun alkali "ya mai
shari'a inaso kotu tabani izni domin gabatar da
shaidata ta gaba", "kotu tana saurare" alkali
yafada, "kotu tana bukatar ganin inspector jabir",
cikin bakaken kayan police ya ratso kotun tareda
wasu mutane guda ukku wa anda suke a daure,
bansan ko suwaye ba amman nayi mamakin
yadda
naga abba ya gigice dalilin bayyanar wa'annan
mutane, bansan abinda yabashi tsoro ba, police
din
koko mutanenda ke adaure, bankarasa tunaninda
nakeyiba natsinto muryar barista sady tana
magana "inspector dukda dai gaka acikin kayanka
amman kotu tana bukatar saninka da aikinka",
"sunana inspector jabir aliyu dodo ina aiki ne a
state c.i.d dake modoji a garin katsina" inspector
yagyara zaman hularsa lokacinda yake karasa
maganarsa, "inspector jabir wa'annan mutanen
fa?" sady tafada tareda nuna mutane guda ukku
wa anda suke adaure "mun kamasu ne a ranar
asabar 09-8-2014 muna cikin aiki a dadai round
about din dake g.r.a, muka tsaida wata mota
domin yin aikinmu kamar yadda muka saba,
bayan
mungama bincikar motar sai wadda take acikin
motar tashaida mana, itafa tunda ta taho talura
dawata mota tana binta a baya kuma batasan ko
suwanene ba, ta fadamana number motar muka
shiga muna dubawa daga cikin motocin dasukayi
layi suna jiran mu tantance su domin susamu
wucewa, cikin ikon Allah muka samu motar da
wannan mata tafada mana, bamuyi kasa a guiwa
ba muka damkesu muka nufi station dasu domin
sanin dalilinda yasa suke binta, munsamu
makami
acikin motarsu wa anda suka hada da bindiga
pistol 9.9m dakuma wuka, saida muka tsananta
bincike sannan suka fadamana anturosu ne
domin
su kasheta kokuma su nakasata yadda bazata
kara yima kanta amfani ba balle tayima wani,
saboda basu so taziyarci shari'ar da ake
gudanarwa azama nagaba a matsayinta na
lauya",
"mungode inspector jabir da wannan kokari naku,
tunda ka kawomana su zaka iya komawa
kazauna
idan muna bukatar wani bayani zamu kira ka"
sady tafada sannan tajuya agun mutanen guda
ukku wa anda suke daure da ankwa, tadubi
nafarko tace "bawan Allah minene sunanka",
"sunana takwalale", nabiyun kuma yace "sunana
turwa", sannan tamatsa agun na ukkun kaifa ya
sunanka "sunana mun lume", barista sady takara
dacewa "minene hadinku da wannan shari'a har
kukayi kudirin tsaida ita tahanyar kashe daya
daga
cikin wakilan wa anda ake zargi?", "bamune muka
sanya kanmu ba sanyamu akayi ta hanyar
biyanmu kudade masu yawa" barista sady takara
gyara tsayuwarta tareda fadar "wanene yasanya
ku wannan aikin?", "hajiya bilki" yafada cikin
wata
kakkausar murya. Sannan barista tajuyo agun
alkali tace "ya mai shari'a inaso kotu tabani
dama
ta karshe", "kotu tabada dama", "kotu tana son
ganin malan idi" barista tafada tana kallon idi
mai
gadi, ba tareda bata lokaci ba idi ya hallara,
"malan idi ko kasan wa'annan" barista tafada
tana
kallon idi, idi yadubesu daya bayan daya sannan
yace "tayaya zan manta da wa'annan fuskokin,
sune wa'anda sukayi yunkurin kasheni",
"tambayar
dazanyimai kenan ya mai shari'a" barista tafada
sannan tajuya agun alkali tayi godiya, "barista
auwal kanada wata magana?" alkali yafada yana
kallon inda lauyoyin guda biyu suke azaune, "a'a
ya mai shari'a duk hujjojin data kawo sunyi daidai
da shaidun ta suka gabata" barista auwal yafada
kanshi yana kallon kasa, "abisa hujjoji dakuma
shaidu dasuka gabata agaban kotu, kotu ta gano
cewa yusuf bayada laifi sbd haka kotu ta
wankeshi,
kuma kotu ta yankema abba hukuncin kisa ta
hanyar rataya kasancewar shine wanda yakashe
aliyu da hannunshi, wa'annan mutane guda ukku
tareda hajia bilki za'a zaunar dasu a gidan kaso
har tsawon shekaru 25. Idan kuma akwai wanda
yakeda bukatar daga kara zuwa kotun gaba,
yanada dama kafin kwana30. Kooootu!!!...
[11:57PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: ALKAWARI
Part30.....
Tana zuwa nan dazancenta sai tayima alkali
godiya tasamu wuri tazauna, "barista auwal
kanada wata shaida wadda zaka sake
gabatarwa?"
alkali yafada yana kallon inda lauyoyin suke
azaune, "eh ya mai girma mai shari'ah" barista
auwal yafada lokacinda yake mike tsayewa,
sannan yayi gyaran murya tareda fadar "inaso
ingabatar da shaidata kwakwkwara wadda take
nuna wanda yayi wannan aikin baro baro, wadda
itace wukar da akayi amfani da ita wurin kashe
aliyu, kuma anyi bincike angano zanen hannun
yusuf ne kadai yayi amfani da wannan wuka"
yana
gama fada sai yamikoma maga takarda wukar,
maga takarda kuma yamika ma alkali, bayan
alkali
yagama dubawa sai yabuda baki yace "barista
sady ko kinada ja dangane da wannan shaida da
dayan bangaren suka gabatar?", "a'a ya mai
shari'ah" sady tamayarwa alkali da amsa, sannan
alkali yadubi barista auwal yace "kotu tana
sauraren hujjarka ko shadarka ta gaba", "iyakacin
shaidata ta kenan ya mai girma mai shari'ah"
barista auwal yafada tareda yin godiya gami
dazaunawa a mazauninsa. Alokacin alkali yakuma
gyada kanshi a rukuninda lauyoyin suke azaune
"barista sady kotu tashirya sauraren hujjoji
dakuma shaidunki", yana gama magana barista
sady tamike "kotu tana bukatar ganin karime"
batare da bata lokaciba karime ta bayyana
agaban
kotu, "karime kotu tana bukatar sunin ko ke
wacece" sady tafada "suna na karimatu salisu
kuma ni yar asalin garin agadaz ce" karime
tafada
tana kallon sady, "ke yar agadaz ce to me
yakawoki agarin katsina" sady tafada da alamar
tambaya karara a fuskarta, "nabaro garinmu
nashigo nigeria ne kasancewar rashin karfi
damuke
dashi gdanmu shiyasa nabaro gida dan nema
mana abnda zamu rike kanmu da yan gidanmu",
"kinaso kice neman kudi ne yakaiki har gidan
alhaji
jafar kenan" sady tafada, "eh hakane sbd ina
daga
cikin yan aikin gidan wa anda ake biya duk
karshen wata" karime tabada amsa tana gyada
kai,
"malama karime ance tunda kika tafi ganin gida
baki kara dawowa ba, kinsamu kudinda zasu
isheku keda sauran yan gidanku ne koko?", "a'a
gaskiya nabar gidan Alhaji ne batareda niyar
dawowa ba sbd wata matsala dana lura tana
niyar
samun gidan, kuma nasan idan matsalar tafaru
harmu yan aiki bazamu tsira ba" sadda tazo nan
da zancenta sai tayi ajiyar zuciya sannan kuma
taci gaba da magana "ranar wata laraba ina
zaune
sai mai dafa abnchi(kuku) ya umurceni da
inkaima
abba abnchi a dakinsa kamar yadda yabukata,
bayan na hada komai nanufi dakinsa ina zuwa
daidai kofa sai najiyo muryar aunty bilki tana
magana daga cikin dakin "kana tunanin zamu
barsu ne suma suci gaba da rayuwa? kai basu
kadai bama, dukwanda yatsaremana hanya shima
sai ya bakunci lahira......" karime na gama
zancenta sai barista sady tadubi alkali tace
"iyakar
tambayar dazanyimata kenan ya mai shari'ah",
"barista auwal ko kanada tambayar dazakayima
shaidar da aka gabatar?" alkali yafada, "eh ya
mai
shari'ah", "karime shekararki nawa kina aiki a
gidan alhaji jafar?" barista auwal yatambayi
karime, "cikin shekara ta ukku ce wannan",
"lokacinda kikaji abnda su abba suke fada a daki
meyasa baki fadama alhaji abnda ke faruwa ba,
kokuma kisanarda hukuma hakan?", "gaskiya
bazan iya tunkarar alhaji infadamashi wannan
maganarba sbd banida wata hujja mai kwari, idan
nayi haka nice zanshiga cikin matsala, shiyasa
ma
nayanke shawarar barin gidan domin gudun
abnda
zaije yadawo, amman lokacinda zantafi na
fadama
abokiyar aikina indo duk abnda ke faruwa tareda
alkawarin bazata fadama kowa ba", "zaki iya
fadamana inda abokiyar aikin taki take?" barista
yafada yana kallon karime, "eh nama ganta acikin
kotunnan" karime na bayarda wannan amsar sai
barista auwal yacema alkali "iyakar tambayoyin
dazanyimata kenan ya mai shari'ah".... Barista
sady tamike tace "nagode karime zaki iya
komawa
kizauna", sannan tajuya agun alkali "ya mai
shari'ah ina neman iznin gabatar da shaidata ta
gaba", "anbaki izni", alkali yafada, "kotu tana
bukatar ganin indo", batareda bata lokaciba indo
tahallara agaban kotu, "malama indo kotu tanaso
tasan ko ke wacece dakuma aikinki" barista
tafadama indo, "sunana a'isha amman anfi
sanina
da indo, ina daga cikin masuyin hidima agidan
alhaji kamar yadda karime ta gabatar, nima ina
daya daga cikinsu", "malama indo kinji abnda
karime tafada shin dagaske ne abnda tafada
koko?" barista ta tambayi indo, "eh tabbas yadda
tafadamun haka ta fadama kotu kuma ta
gargadeni
dakar infadama kowa, kuma nima na gasgata
maganarta saboda akwai wata rana da daddare
aka umurceni da inkaima usman abnci yana falo,
akan hanyar kai abncin ne nahadu da aunty bilki
tana tafiya tana surutu amman nadanji kadan
daga
cikin abnda take fada, "(eh mu muka kasheshi din
kuma saima munga bayan dukwanda ke
gidannan)", tabbas naji wannan kalami daga
bakinta har saida nazubar da kwanonin abncin
dake ahannuna sbd tsabar storota danayi, amman
nafake da tuntube nayi" indo takarasa maganarta
lokacinda take gyara zaman wuyan hijab
dinta....
[11:57PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: ALKAWARI
Part32...
"hujjoji dakuma shaidu dasuka gabata
agaban kotu, sun tabbatarda cewa yusuf bayada
laifi sbd haka kotu ta wankeshi daga wannan
zargi,
kuma kotu ta yankema abba hukuncin kisa ta
hanyar rataya kasancewar shine wanda yakashe
aliyu da hannunshi, wa'annan mutane guda ukku
tareda hajia bilki za'a zaunar dasu a gidan kaso
har tsawon shekaru 25 tareda tarar kudi naira
dubu dari, akan kazafin da akayima yusuf. Idan
kuma akwai wanda yakeda bukatar daga kara
zuwa kotun gaba, yanada dama kafin kwana30.
Kooootu!!!...
Haka kowa yawatse tareda mamakin yadda
wannan shari'ah takasance mai kama da wasan
kwaikwayo, muma muka dunguma muka nufi gida
cikin murna, bawani dadewa nayiba a kurkuku sbd
ban kwashe wata ukku ba amman naga garin ya
canza man hatta iskar danike shaka tasha
banban
da iskar gidan maza... Ba karamin farin ciki
mukayiba awannan rana wanda idan natsaya
fadamaku sai munbata lokaci dayawa....
Bayan wani dan lokaci da faruwar wannan lamari
tun ba ayi nisa ba soyayyata da yasmeen
tadauko
wani sabon salo wanda aduk rana idan daya
baisanya daya acikin idonshi ba to ranar babu
kwanciyar hankali, hatta wayoyinmu sunshaida
hakan sbd muna wahalar dasu, wurin kiraye
kiraye... Kwance nake a daki da misalin karfe 11
na dare, har bacci yafara dauka ta naji wayata
tana ta faman ruri, ko dubawa banyiba kawai
nadauka tareda kangawa a kunne na, salamu
Alaikum nafada,
"wa alaikassalam" aka fada daga dayan bngaren
tareda wata yar gajeriyar daria, hakan yasa
nagane ko dawa nike magana sbd nasan muryar
kamar yadda nasan kofar baki na,
mutum yana baccinshi mai dadi anwani tadashi,
"hmm hakama zakace ko to shikenan sai dasafe"
aka fada daga dayan bngaren.
laaaaa dan Allah yi hakuri bafa dake nike ba, ai
kema kinsan duk dadin bacci baikai dadin
muryarki
ba, nafada tareda mikewa zaune,
"to idan badani kakeba dawa kake?"
nifa da saurayen(mosquetoe) gidanmu nike
magana, sune sukazo saman kaina sunata yiman
waka har suka tadani,
"bawani nan! Saurayen ne zasuyimaka waka?",
eh mana ko in reramaki kiji,
"eh yiman inji idan gaskiya ne",
buuuuuuuu! Tunkafin inrufe bakina naji sautin
dariyarta yadaki dadon kunne na, nima sai
natayata muka idarda dariyar tare.
"oh kai Allah yashiryeka" tafada tana murmushi,
sannan takara dacewa, "daman dady ne yace
inyimaka magana kazo gobe yanason ganinka",
na
nunamata jin dadina sosai daganan kuma mukaci
gaba da firarmu irinta masoya.....
Wan shekare da misalin karfe 9am natashi
nasanya ruwan zafi kasancewar safiyar ranar ana
wani irin sanyi mai tattare da iska sakamakon
ruwan saman da aka malala cikin dare, bayan
nayi
wanka nashirya tsaf wurin 10am natafi domin
amsa kiran mahaifin yasmeen..... Ina shiga
natarar
dashi zaune akan kujera ya daura kafa daya akan
daya yana kallon jarida tacikin siririn farin
gilashin
dake sanye a fuskarsa. Bayan nagaidashi
gaisuwa
kamar yadda yadace na saurara inajiran dalilin
kirana. Wani dogon numfashi yayi tareda linke
jaridar dake hannunsa
"yusuf nasa ankiraka ne sbd wata magana
danikeso inyi dakai" yakarasa maganarshi yana
kallona, sannan yaci gaba da magana "na fahimci
abnda ke tsakaninka kaida diyar wajena, nayi
bincike akanka yadda yakamata, daga ciki har
nagano ku ba yan asalin garinnan bane daga
maiduguri kukazo, kuma mahaifinka ya dade da
rasuwa, hakane?" yakarasa maganarshi da alamar
tambaya,
eh hakane alhaji, nafada batareda nadago kai na
kalleshi ba,
"yusuf aikin me kakeyi yanzu?"
lokaci guda jikina yadau kyarma sbd bnyi
tsammanin wannan tambayar ba saboda nidai
nasan banida wani aiki amman dakyar natsinci
kaina ina fadar, banida wani aiki alhaji,
"to wane mataki kake acikin karatunka?",
na gama secondry amman karatun yatsaya
sakamakon rashin karfi kuma...
"what!" muryarshi naji tayi tsalle ta daki dodon
kunne na, hakan yasa nayi shiru batareda
nakarasa maganar danakeyi ba. "kana nufin
ahaka
kake neman diyar tawa batareda kanada wata
madafa ba" yana magana ne cikin mamaki, "to
bari
kaji infada maka ni bahaka nikeba, saboda bazan
iya sayar da akuya ba kuma tadawo tana ciman
danga" yafada lokacinda yake zare gilashin dake
sargafe a fuskarsa "daga yau na rabaka da diyata
babu kai babu ita, kaje kasamu daidai dakai
amman ba a gidana ba" yafada tareda mikewa
tsaye yanufi hanyar fita waje, har yakai bakin
kofa
sai yatsaya, "kuma idan baka rabu da itaba
zandauki mataki mai tsanani akanka" yafada
batareda yajuyo yakalleni ba, nikau tuni na dade
da
mutuwa daga zaune narasa minene kemun dadi,
wani sabon gumi yarinka fita daga jikina zufa
tayiman kawanya, tareda wasu zafafan hawayene
dasuka rinka ambaliya akan fuskata, hatta
lumfashinda nakeyi zafinshi ya tsananta acikin
kofofin hancina... Dakyar nasamu nafiddo kaina
daga cikin dakin, ina fitowa nahadu da yasmeen,
hankalinta yatashi ganin yadda nafito a kidime
shiyasa tayi gaugawar jifata da tambaya
"me yafaru naganka haka?"
shiru nayi ina kallonta nakai dakika biyar ina
neman sulhu acikin zuciyata, akan infada mata
gaskiya wani bangaren nadaga zuciyata kuma
yana cewa a'a......
[11:57PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: 33/34ALKAWARI
Part33......
Ina fitowa nahadu da yasmeen, hankalinta
yatashi
ganin yadda nafito a kidime shiyasa tayi
gaugawar
jifata da tambaya "me yafaru naganka haka",
shiru
nayi ina kallonta nakai dakika biyar ina neman
sulhu acikin zuciyata, akan infada mata gaskiya
wani bangaren nadaga zuciyata kuma yana cewa
a'a, bansan lokacinda zuciyata tagama wannan
tattaunawar ba saidai kawai naji har anyanke
hukunci natsinci bakina yana fadar. kaina ne
yakemun ciwo, dukda dai nasan badole bane ta
yadda da abinda nafada ba. "haba yusuf me
kadaukeni ne, kaima kasan babu abnda bansani
ba
dangane dakai" sannan tayi ajiyar zuciya daga
bisani kuma taci gaba da magana "ko acikin duhu
bazaka iya boyemun damuwarka ba, me yasa
kakeson boyemun abnda ke damunka ne", dady
ne
yace dole sai na rabu dake, maganar tafito daga
bakina tareda wani kululu wanda baisamu damar
fitowa ba saidai yatsaya acikin makoshi na, "ka
kau san abinda kake fada?", na sani nima ganin
abin nakeyi kamar a mafarki, daidai lokacin
hawaye
suka samu damar gangarowa akan fuskata,
itakau
tsaye take tabude baki kamar zatayi magana
amman ta kasa, sai hawayen da keta zirga zirga
daga idanuwanta zuwa fuskarta, juyawa nayi da
zummar ficewa sai naji ta riko hannu na, "haba
yusuf kayi tinanin da gaske ne?, wlh dawasa
dady
yake yimaka, yaza ai arabani dakai bayan bazan
iya wata rayuwa idan batare dakai ba, dan Allah
kada katafi" cikin kuka take zayyano kalamanta
cikin wata irin murya kalar tausayi, dole tasa
najuyo nakalleta fuskokinmu duk sunyi share
share
da hawaye, kiyi hakuri yasmeen babu maganar
wasa aciki, wannan kaddara ce Allah ya dora
mana
babu yadda zamuyi kuma yazama dole mubi
maganar iyayenmu, "haba yusuf ya kake zaton
rayuwata zata kasance idan babu kai? Zuciyata
fa
kamar shukar ayaba(banana) ce, sau daya
takeyin
'ya'ya, idan tayi sau daya to tagama amfani
saidai
a sareta kokuma abarta domin kwalliya. Nima
haka
nike zuciyata zabi daya takeyi kuma soyayyata
guda daya ce" , to yanzu yakike so muyi? Na
tambayeta tareda kuramata ido, "sai mugudu
mubarmasu garin mutafi can wani wuri inda babu
wanda yasanmu muyi rayuwarmu acan" takarasa
maganarta tareda kara matse hannu na dan
karma
inkubce mata. Haba baikamata kifurta wannan
maganarba ko dawasa kada kikara tunanin fita
daga gidan mahaifanki batare da izninsu ba, "aan
ya kake kokarin juyamin baya dan Allah kayarda
mutafi, idan duniya tajuyamun baya kaine kadai
zaka karkato agareni insamu sassauci, amman
idan kajuyamun baya ko duniya damutanen
cikinta
suka karkato zuwa gareni bazasu amfaneni
dakomai ba. Dan Allah kada kabarni". Haba
yasmeen duk irin so da kaunar danikeyi maki
batakai irin sonda iyayenki sukeyi makiba, kada fa
kimanta ta hanyarsu kikashigo duniya, sukayi
renonki tun bakisan ko ke wacece ba harkika san
kanki, ci da sha sutura, babu irin kulawar da
basuyi maki, yasmeen ta yaya zaki hada soyayyar
wa'annan da soyayyar wani, ko kin manta azabar
da Allah ya tanadar ma wanda ya bijirema
iyayensa, "ya kake magana da wadda tinaninta
yakoma bin zuciyarta Ya kake kokarin fahimtar da
wadda kwakwalwarta ta toshe da soyayyar zabin
zuciyarta, yanzu bazan iya hakuri ayi kokarin
rabani dakai ba" takarasa maganarta tana girgiza
kai, ko kadan bazan iya rabuwa da iyayena ba
kuma bazan sanya kirabu da naki iyayenba,
saboda nasan dole muyi nadama a lokacinda
baza8
taimana amfani ba, har na juya natafi sai naji
tana
rera wani irin kuka cikin wani kalar sauti mai
matukar karya zuciyar dukwanda yayi tozali dashi
acikin dodon kunnenshi, bansan lokacinda najuyo
nadawo a gareta ba, "kiyi hakuri yasmeen Allah8
yana tare damu kidauka wannan jarabawa ce
agaremu. Adai dai lokacin nafiddo zoben dake
sanye a danyatsana, nasanya mata ga hannunta
najuya natafi, inaji tana kiran suna na amman
bazan iya amsa kirantaba a wannan
lokacin......Tu
nda nashiga gida banyima kowa magana ba
nawuce dakina nakwanta cikin wani irin yanayi
wanda bazan iya misaltamaku ba amman
dukwanda yaganni yasan ba cikin hayyacina nike
ba, duk yinin ranar haka na kasance banida aiki
sai
tinane tinane wani lokacin kuma zuciyata tarinka
yiman tambayoyinda bansan amsarsu ba, "wai
meyasa rayuwata take cike da wahala da kunci?
me nayima Allah ne yake jarabani da hali mafi
wuyar jurewa? Wani bangaren nadaga zuciyata
kuma yana shaidamun cewa "kadaina irin wannan
tinanin domin gujema fushin uban giji. Basai na
fadamaku halinda yasmeen tashiga ba sbd zamu8
bata lokaci sosai, amman damuwarta tafi tawa....
Sati daya da aukuwar wannan kaddara a garemu
tunda safe na nufi dakin umma da niyar ingaidata
kamar yadda nasaba a kowace rana... "haba
yusuf
meyasa kakeda rikon abu a zuciyarka ne, ko so
kake kadorama kanka hawan jini tun kana dan
kankane duba kaga yadda ka rame, duk kabi ka
kanjame kamar wani mai ciwo" umma ce take
magana cikin sigar fada, muna cikin wannan
yanayin ne sai mukaji anyi sallama, Salamu
alaikum!!!.........
[11:57PM, 23/09/2016] ✨@lh@ji✨: ALKAWARI
Part34....
"haba yusuf meyasa kakeda rikon abu a zuciyarka
ne, ko so kake kadorama
kanka hawan jini tun kana dan kankane duba
kaga yadda ka rame, duk kabi ka
kanjame kamar wani mai ciwo" umma ce take
magana cikin sigar fada, muna cikin
wannan yanayin ne sai mukaji anyi sallama,
Salamu alaikum!!!... Gaba daya muka
amsa tare da juyawa domin ganin wanda yake
shigowa, "sannu dazuwa halimatu"
umma ce take magana acikin fara'a. Banyi
mamakin ganin haleematu ba sbd tunda
muka fito kotu tana dan zuwa jefi jefi tana gaida
umma. Bayan sungama gaisawa ne
tabukaci komawa gida, sukayi bankwana takama
hanyar fita nikuma nabita abaya
nadan ta ka mata har zuwa inda tayi packing din
motar ta "yusuf wurinka nazo sbd
wata guguwa datake neman tasowa ta tarwatsa
duk abnda nake kokarin tanadarwa",
halimatu ce take magana cikin damuwa. kamar
yah kenan halimatu bangane inda kika
nufa ba, nafada tareda zakuwa domin jin bayanin
daza tayiman in fahimta, "wai aure
za ayiman" tafada tareda jinjina maganar, iyyeh!
kice munkusa shan shagali kenan,
nan gaba kadan zandaina kiranki da halimatu
saidai ince amarya, "haba yusuf kana
tinanin zan auri wanda bana so ne?". Kina nufin
bakison wanda mahaifanki suka zaba
maki kenan, "gaskiya ni bana sonsa" takarasa
maganarta tareda girgiza kai. Halimatu
kada soyayyar wani tarufe maki ido har tasa
kiwuce zabin da iyayenki sukayi maki
kuma ki ketare umurnin da addini ya tsara mana,
"kaima ka goyi bayan a auraman
wanda bana so kenan" tafada kamar mai shirin
yin kuka, ba haka bane kinsan
yazama dole mutun yabi iyayensa indai har yana
son yasamu tsira. Ko kinmanta da
hadisin da Umaimata (R.T.A) ya ruwaito wanda
yake cewa: Hakika wani mutum ya
tambayi manzon Allah: "Ya Manzon Allah,
menene HAKKIN IYAYE
AKAN DANSU??? Sai Manzon
Allah (S.A.W) yace Sune "ALJANNARKA DA
WUTAR
KA.... Kuma awani hadisin manzon Allah yana
cewa: "kubauta ma Allah shikadai kada
kuhadashi dawani abu awurin bauta, kuma ku
kyautata ma iyayenku". "tabbas hakane
kuma nasani aljannar 'ya'ya tana karkashin
iyayen su" sannan tayi ajiyar zuciya daga
bisani kuma taci gaba da magana "amman kasani
zanbi iyayena ne idan har basu
sabama addini ba, idan kuma suka kauce to
bazantaba binsuba. bazanyadda in auri
wanda baniso ba, dan kowa yasan acikin addini
babu auren dole sbd A lokacin
Manzon Allah anyi wani mutun da ake kira da
suna Mughir wanda Allah ya jarrabe shi
da tsananin son wata mata da ake kira da suna
Barira, amma kuma cikin ikon Allah
ita kuma duk duniya babu wanda bataso irinsa
(Mugheer), har saida takai yana bin ta
a hanya, yana kuka, yana rokonta da ta soshi,
amma ita kuma ta kekasa kasa.
Watarana sahabbai suka ga irin halin da mughir
ke ciki, suka cewa manzon Allah shin
baza kashiga cikin al’amarin Mughir da Barira ba,
Manzon Allah Salallahu Alaihi
Wasallam, da kansa yace hakika anjarrabi Mughir
da soyayyar Barira. Manzon Allah
ya taka da kafarsa mai daraja, yaje wajen barira
da kansa, ya ce yanzu barira baza
kiso Mughir ba! Ta ce ya Manzon Allah! kana
bani umarni ne, ko kuma kana bani
shawara, yace ina baki shawara ne, ta ce ya
Manzon Allah bana sonsa, haka Manzon
Allah ya taso yana mamakin irin yadda zuciyar
Barira bata nutsu da Mughir ba duk
kuwa da irin yadda yake nuna soyayya a gareta.
Kaga kenan da auren dole yana da
muhalli a musulunci da Manzon Allah ya umarci
Barira ta auri Mughir sai dai baiyi
hakan ba. Wannan shi ya nuna mana cewa
addinin Musulunci bai yarda da auren dole
ba, domin da ana yi, da saboda yadda Manzon
Allah ya tausayawa Mughir da ya
umarce ta da ta aureshi". Tana zuwa nan da
zacenta sai tayi shiru. To yanzu me kika
fadama mahaifanki?, "kwana biyar 5 suka bani
domin infitar da wanda nike so, idan
lokaci yayi ban fitar ba, zasu auramin wanda
ransu yake so", sai ki gaggauta fitar da
zabinki kafin suzabar maki, "saidai wanda nike so
haryanzu baisan abnda nikeyi ba,
na budamai zuciyata amman ya kasa fahimta ta,
na nuna mai amman yaki ganewa"
alokacin wasu yan hawaye suka samu damar
gangarowa akan fuskarta, nakalleta
cikin tausayi tareda fadar, ya kamata ki gaggauta
fadamai kafin lokaci yakure maki.
Rufe bakina yayi dai dai da saukowar ruwan
sama, cikin sauri nayimata bankwana
tashige mota ta tafi nikuma na karkata kafafuwa
na zuwa gida... Zaune take akan
gado tana kallon kyakykyawan zoben azurfar
dake sargafe a dan yatsanta, tahada kai
da guiwa tanata rera abinta kamar yadda tasaba,
da ace bangon dakinta zaiyi
magana to da zai iya rera irin kukan bakin cikin
data dade tana rerewa ba dare ba
rana, turo kofar da akayine yasanyata dago
fuskarta dasauri. "wai me kike so kizama
ne yasmeen, ko kinaso kinuna mana kinfimu
sanin abnda yadace" yana maganarsa ne
acikin fada, "a'a dady bahaka nike nufi ba" tafada
cikin wata dakusasshiyar murya
tana sarkewa, "nasan yadda kikeji amman kisani
nayi hakane domin.........
[12:02AM, 24/09/2016] ✨@lh@ji✨: Part35.......
Zaune take akan gado tana kallon
kyakykyawan zoben azurfar dake sargafe a dan
yatsanta, tahada kai da guiwa tanata rera abinta
kamar yadda tasaba, da ace bangon dakinta zaiyi
magana to da zai iya rera irin kukan bakin cikin
data dade tana rerewa ba dare ba rana, turo kofar
da akayine yasanyata dago fuskarta dasauri. "wai
me kike so kizama ne yasmeen, ko kinaso kinuna
mana kinfimu sanin abnda yadace" yana
maganarsa ne acikin fada, "a'a dady bahaka nike
nufi ba" tafada cikin wata dakusasshiyar murya
tana sarkewa, "nasan yadda kikeji amman kisani
nayi hakane domin nema maki mazauni wanda
yadace dake, ko kadan bazanyadda inkaiki inda
zakisha wahala ba, sanin kanki ne wannan yaron
bayada sana'a kuma karatunma bayi yake ba
tayaya zai rike kanshi balle har yakula dake, ko
kintaba ganin inda akaci soyayya a zaman aure?"
shiru kawai tayi tana sharbar kukanta, bai tsaya
jin
amsartaba yamike daniyar tafiya, "wlh ina sonshi
dady inasonshi ko ya yake kuma zan iya zama
dashi a haka, dan Allah kutaimaki rayuwa ta"
siririyar muryar matashiyar taci gaba da fitowa
tareda kuka, ko saurarenta baiyiba yaja
kafafuwansa yanufi hanyar ficewa daga dakin,
"ina
sonshi! Wlh ina sonshi" dakarfi tayi magana
yadda
har nawaje zai iya jin abnda take cewa, yana fita
daga dakin yajingina da kyauren dakin diyar tashi
cikin nadama dakuma tausayin halinda yasanya
diyarshi dakanshi, wani sashen na zuciyarshi
yana
bashi shawarar yazama dole yanemamata farin
cikinta idan ba haka ba zai iya rasata, baisan
lokacinda yatura kofar dakinba tareda kutsa kai
cikin dakin yaci gaba da magana ahankali cikin
sanyin rai "kiyi hakuri yasmeen bawai ina nufin
rabaki da wanda kike so bane, nayi hakane domin
daukar mataki akanshi indai yana sonki da
gaskiya
to hakan danayimai shi zaisanyashi jajircewa
tareda neman abin kansa, amman ko kusa banyi
hakaba domin rabaku kokuma sanyaku acikin
wani
hali ba" ya karasa maganarsa yana jira yaga
hankalin diyar tashi ya kwanta amman ga
mamakinsa sai yaga kwance take ko alamar
lumfashi babu atare da ita, cikin sauri yakarasa
agunta tareda yimata wani irin kira guda ukku a
jere, yasmeen! yasmeen!! yasmeen!!! Cikin hanzari
ya kwasheta zuwa asibiti.... Tsawon lokacinda
likitoci suka kwashe sunata fafutukar ceto
rayuwarta yasanya alhaji da sauran iyalansa
kaguwa domin jin halinda yarsu take ciki, zaune
suke akan kujerunda aka tanada cikin asibiti
musamman domin irin haka... Wani dan siririn
likita yafito tareda nufowa inda suke, tunkafin
yakaraso alhaji jafar ya tarbeshi "doctor ya jikin
nata? Ta tashi?", "munyi iya kokarinmu domin
ganin munceto rayuwarta sbd zuciyarta ce tabuga
sakamakon wani mawuyacin hali data shiga,
la'alla
wurin wani dogon tinani kokuma sanadiyar rasa
wani abu datayi, wanda hakanne yayi tasiri wurin
samun matsala a wani sashe na zuciyarta" likitan
yafada a tsanake cikin kwanciyar hankali, "to
doctor yanzu ya ake ciki kenan" alhaji yayi
magana
tareda cire hular dake saman kansa, "munyi iya
kokarinmu yanzu haka ma tananan kwance Kuma
idonta biyu, tanajin magana tana ganin abnda
yake
wakana, saidai bazata iya komai dakanta ba, ko
magana bazata iya yiba, kuma idan tayi 3hours
acikin wannan yanayin batareda ta farfado ba, to
gaskiya saidai ayi hakuri da ita", "innalillahi wa
inna ilaihirraji'un doctor yanzu minene abin yi?"
usman yafada tareda mika hannuwa guda biyu
biyu agaban doctor kamar wanda zai amshi wani
abu, "gaskiya yazama dole asamu abnda zai
maye
gurbin abnda yasanyata cikin wannan halin, idan
wani abu tarasa, yakamata ayi gaugawa a
musanyamata dawani abin kamarshi, idan kuma
tinanin wani abune takeyi to dole sai annemi
hanyarda zata fidda wannan tinanin a ranta koda
dai dai na second daya ne, idan kuma wani abune
yasanyata cikin bakin ciki to sai ansamu
hanyarda
za asanyata farin ciki. Wannan ce kawai mafita
kuma itakadaice hanyar data rage domin ceto
rayuwarta." yana gama fada yakama hanya
yawuce, sukuma sukayima dakinda aka kwantar
da
ita tsinke....
[12:02AM, 24/09/2016] ✨@lh@ji✨: ALKAWARI
Part36......
idan tinanin wani abune takeyi to dole sai annemi
hanyarda zata fidda wannan tinanin a ranta koda
dai dai na second daya ne, idan kuma wani abune
yasanyata cikin bakin ciki to sai ansamu
hanyarda
za asanyata farin ciki. Wannan ce kawai mafita
kuma itakadaice hanyar data rage domin ceto
rayuwarta." yana gama fada yakama hanya
yawuce, sukuma sukayima dakin da aka kwantar
da ita tsinke... Sunkwashe tsawon awa guda
kowa
yana nuna gwanintarsa da fasahar da Allah
yayimasu wurin ganin sun ceto rayuwarta amman
basuyi nasara ba, saima dai lokaci dayake cin
nasara akansu yanata tafiya abnsa. "Alhaji
yakamata akirawo yaronnan kilan Allah yasa a
dace" mahaifiyar yasmeen tafada tana kallon mai
gidan nata kamar zatayimai kuka, baiyi
gardamaba
wurin amince warsa akirawo yusuf sbd kowa
yasan
shine ummul aba'isin faruwar wannan
al'amari.....
Arikice nashigo asibitin ina wata irin tafiya sauri
sauri gudu gudu baccinma bansan dakin da aka
kwantar da itaba, yazama dole inbi usman abaya
saboda shine yasan wurin, da zan iya fallawa da
gudu sbd na kagu inje inda take. Ko sallama
bamuyiba muka banka kyauren dakin. Suntaru
sun
zagayeta masu kuka sunayi masu hawaye sunayi,
abinda ya bakantaman rai shine, wai harda kayan
wasan yara aka kawomata burjat acikin dakin
kamar wata jinjira. Alhaji da mamar yasmeen ne
tsaye sun daddafe gadon datake kwance, na
bubesu daniyar ingaidasu tun kafin inbude bakina
naji muryar mahaifiyar yasmeen nashiga cikin
kunne na, "dan Allah dannan kataimaka mana
kayi
iya kokarinka domin ceto rayuwarta, awa ukku
likitoci suka bata tun karfe 12 har 2:30 tayi
amman shiru bata tashiba", tana magana kamar
tana bada umarni tawani bangaren kuma kamar
kamar tana neman taimako awurina ganin yadda
take miko hannuwa biyu biyu tana langabe kai,
lokaci guda tausayinta yakamani ba ita kadaiba,
dukma wanda yake acikin dakin sbd hankalin
kowa
yagama birkicewa. Cikin kyarma nike magana
bakina yana rawa, Umma ki kwantar da
hankalinki
bazata mutu ba, babu yadda za ayi yasmeen
tamutu lokacinta baiyiba. "kai kada kamaidamu
kana nan yara mana" murya alhaji taci gaba
dafita
cikin bacin rai, "kaduba kagani likita ya tabbatar
mana da wannan abin yakai kasa to shikenan ta
mutu" yakarasa maganarsa yana nuni da wata na
ura akan wani teburi kusa da gadon, haba alhaji
kada damuwarku tasa kumanta da wanda ya
halicceku mana, kada wannan yasa ku sabama
uban gijinku, kadafa kumanta babu wanda ya isa
yadauki ranta sai Allah sbd shine ya halitta
abinsa,
kuma shine kadai wanda yakeda ikon yin komai,
shine yake bayarda arziki ga wanda yaso, shine
yake rayawa kuma shine mai kashewa babu
abnda
likita zai iya yi anan, nafada ta sigar kwantar
masu da hankali, amman ina alhaji yayi nisa
lokaci
guda kuma naji hajiya ta rusa kuka, wasu hawaye
suka zuboman, kaiya kaiya dan Allah kitashi
domin
susan abnda nike fada gaskiya ne. Nafada tareda
durkusawa adai dai inda fuskar yasmeen take dan
Allah kiyimasu magana domin sudaina yimaki
kuka, kingani fa cewa sukeyi mutuwa zakiyi,
kitashi
domin ki tabbatar masu da ba mutuwa zakiyiba.
Nakarasa maganata cikin kuka, lokaci guda dakin
yayi tsit kamar babu halittar data taba shigowa.
Yasmeen! Yasmeen!! Ki amsa mana ninefa yusuf
dinki, ko nima bazakiyiman magana ba? Ko
dagaske ne mutuwa zakiyi?. Dai dai lokacin
natsinci kaina ina wani irin kuka ciki ciki. Dan
Allah
kada kitafi kibarni, kada kisa inzama maraya
acikin
masoya ko kinmanta kece gata na? Kinmanta
kece
abumai mahimmanci acikin rayuwata? Kinfi kowa
sanin bazan iya yin komaiba idan babu ke,
murmushina karewa zayayi sbd babu wanda
zanyimawa, na tabbata bazan taba samun kaina
cikin farin ciki ba sbd kece farin cikina, wace irin
rayuwa kikeso inshiga ne? Dan Allah kiyi magana,
ki amsaman tambayata mana... Ni ba shirunne
yake tadaman hankali ba sbd nasan zan iya zama
dake ahaka har tsawon rayuwata, burina kawai
kifadamun damuwarki masoyiyata, minene
yasanyaki cikin damuwa, gani agabanki na
mallaka
maki kaine yasmeen wlh bazantaba barinki cikin
kadaici ba, kifadaman ko me kikeso ni zanyimaki
shi koda kuwa hakan zaiyi silar rasa rayuwata,
dan
Allah kitashi kada kisa mafarkinmu yazama karya
mana, ko kinmanta da yadda muka tsara rayuwar
aurenmu? kinmanta burin zuciyarmu na musamu
yara kyawawa masu kama dake, haba yasmeen
kinmanta da alkawarin dakikayiman cewa zaki
tarbiyyantar da yaranda zamu haifa, dan Allah
kitashi muci gaba da rayuwarmu. Adai dai lokacin
nakamo hannunta ina kuka. Mantawa kikayi da
ajiyar zoben danabaki akan zaki maidoman abuna
a acikin daren farkon amarcinmu, idan kika tafi
kika barni wazai maidoman kenan, wanene zai
cika
maki wannan alkawarin. Ina magana ina murza
zoben dake acikin dan yatsanta tareda wani irin
kuka mai shiga zuciya. Su alhaji kau dasauran wa
anda ke acikin dakin sunyi tsit suna saurarena
kamar masu sauraren wa'azi... "Inna lillahi wa
inna ilaihir raji'un!!" doctor yafada lokaci guda
kuma yadora hanuwa bisa kai.......... hahaha
sorry nandai anyi over act
[12:02AM, 24/09/2016] ✨@lh@ji✨: ALKAWARI
part37
...Su alhaji kau da sauran wa anda ke acikin
dakin
sunyi tsit suna saurarena kamar masu sauraren
wa'azi... "Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un!!"
doctor yafada lokaci guda yadora hanuwa bisa
kai,
"kuyi sauri ku fiddashi", bangama fahimtar abnda
yake nufi ba naji ankama hannuwa na daniyar
fiddani waje, lokacin na tsinto maganar alhaji "ya
ida kasheta ko??". Dago hannun datayi ne yasa
kowa yayi cirko cirko "yusuf kada katafi kabarni"
tafada kasa kasa tareda miko hannu tana
kallona... Ba karamar murna muka shiga ba ganin
ta dawo hayyacinta lokacinda kowa yagama fidda
rai da ita, basai na fadamaku irin farin ciki
dakuma
murna damuka shigaba... Ranar laraba da safe
misalin karfe 10am na safe suka kammala
breakfast amman dukansu babu wanda yabar
dining area din, suna zaune sunata hirarsu irin ta
iyaye da 'ya'ya, alhaji jafar ne zaune kusa da
matarsa hajia binta, suna fuskantar yaran nasu
guda biyu usman da yasmeen, kasancewar ranar
antashi dawani irin ruwan sama mai karfi shiyasa
alhaji baifita aikiba. "dukanku babu wanda
yafadamun abnda yakeso a wannan sallar, ko
baku
bukatar komai ne a wannan lokacin?", usman yayi
carab yace "haba dady aini wannan sallar a
saudiya naso inyita, kawai dai...", yajuya agun
yasmeen "kefa me kike so?", "ni bani bukatar
komai dady" yasmeen tafada tareda maida
dubanta ga mahaifin nata. Murmushi kawai yayi
sannan yace, "kifadama yusuf din na bashi umarni
yaci gaba dazuwa nemanki", a razane tadubi
mahaifin nata tana tinanin kodai kunnenta ne
yajiyo mata ba dai daiba, bata tabbatar ba saida
taji yakara dacewa "kuma kicemai yakawo man
credentials dinshi zanduba mai aikinda zaici gaba
dayi tareda ci gaba da karatunshi", tayi kokarin
saita kanta akan murnar datashiga amman
takasa,
harsaida bakinta yatonama fararen hakoranta
asiri,
usman da hajiya kau murmushi suka cigaba dayi
da alama dama sunsan da maganar, lokaci guda
taji kunya ta rufeta, tasanya hannuwanta tarufe
fuskarta. Alokacin alhaji ya kyalla ido ya hango
zoben dake makale a hannunta cikin hanzari ya
cakumo hannunta kamar zai ballashi yakama dan
yatsan da zoben yake yana kallo lokaci guda
kuma
yasaketa tareda shiga dakinsa cikin sauri.
Wannan
ba karamin tadama yasmeen hankali yayiba
dukda
dai batasan abnda mahaifin nata yake nufi ba,
nandanan sai gashi ya dawo a firgice yakuma
fizgo
hannunta yakalli zoben kuma yadubi gudan zobe
dake hannunsa babu wani banbanci danashi "ke
kifadaman ina kika sameshi", yakara tambayarta
acikin tsawa, "haba alhaji kayimata ahankali
mana
sai tafada maka" hajia binta tafada, yasmeen
takwashe komai tafadamai... Daganan suka
dunguma su duka suka nufi gidan su yusuf...
Muna
cikin daki nida umma da hadiza kasancewar
tsakar
gidan namu duk ya jike da ruwan sama, a lokacin
sukayi sallama su duka suka shigo, nayi mamakin
ganin wannan bakuntar dukda dai awurina babu
bako acikinsu. Muka tarbesu yadda yadace.
Bayan
mungama gaisawa alhaji yafadi abnda yake tafe
dasu, munyi mamakin wannan ikon Allah, ananne
alhaji ya labarta mamu kamar yadda umma ta
labartamamu a baya... Munyi farin ciki marar
misaltuwa a wannan lokacin, idan natsaya fadar
komai zamu bata lokaci. Hawayen dasuka rinka
zubowa daga idanun alhaji yasa hajia bnta
tambayarshi dalili bayan abnda yaketa mafarki
yafaru, ya samu abnda yafidda rai dashi a duniya
('yan'uwa), "ba komai nake tunawa ba sai
bilkisu"
alhaji yafada yana kuka, "dukda dai ba ciki daya
muka fito da itaba ai mahaifinmu daya baikamata
tayi hakaba, bilki ta cuci kanta, yanzu ni kadai..."
Kuka yaci karfinshi batareda ya ida maganarsa
ba.
nanfa aka shiga bashi hakuri dole yatausasa
zuciyarsa. Aranar alhaji ya mallakaman yasmeen,
kuma yanemi alfarmar a aurama usman hadiza
kanwata, umma batayi musu ba, saimadai tace
"ai
'ya'yanka ne gasunan duk yadda kayi shine dai
dai". Can na hangosu sunayima junansu wani irin
kallo suna murmushi, basusan na dade da gano
abnda ke tsakaninsu ba tunda dadewa... Ranar
kau murna har ta bayan kunne, muna cikin wann
halin sai haleematu takirani, ina dagawa
tafadamun gatanan kofar gida, cikin murna nafita
domin inyimata albishir, kuma inji ita wane mijin
ta
samo.. Su biyu nagani a kofar gidanmu ko wacce
tana tsaye agabn motarta, kowace taci kwalliya
tayi kyau sosai idan natsaya fada zamu cinye
lokacin anan. Barista sady ce da haleematu
usman
zango... Ananfa suka daureman kai akan abnda
sukazo man dashi sbd dukkansu sunzoman da
maganar aure ne kuma babu wadda zata zauna
da
kishiya, barista ta gama komai har gidan dazamu
zauna ta shirya kuma ta shaidama iyayenta,
haleematu kuma nine ta fiddo a matsayin wanda
take so sabanin zabin iyayenta kuma yauce rana
takarshe dasuka bata cikin kwanaki biyar. Lokaci
guda nafara tinanin halaccin dakowannensu
tayiman a rayuwa, nanda nan wasu kalmomi suka
rinka yawo acikin kaina "kada kadamu nima wata
rana zan iya zuwa agurinka neman taimako!!!"
Wata hajijiya tafara daukata ina juyawa sai naga
yasmeen tsaye abayana tanata zubarda
hawaye....
[12:02AM, 24/09/2016] ✨@lh@ji✨: 38ALKAWARI
Part 38(Karshe)
Su biyu nagani a kofar gidanmu ko wacce tana
tsaye agabn motarta, kowace taci kwalliya tayi
kyau sosai idan natsaya fada zamu cinye lokacin
anan. Barista sady ce da haleematu usman
zango... Ananfa suka daureman kai akan abnda
sukazo man dashi, sbd bantaba tunanin dayansu
zata fuskanceni da maganar soyayya ba, sai
gashi
lokaci guda dukkansu sun bijiroman da maganar
aure kuma babu wadda zata zauna da kishiya
acikinsu... barista sady ta gama komai na
aurenmu har gidan dazamu zauna ta shirya kuma
ta shaidama iyayenta... Haleematu kuma nine ta
fiddo a matsayin wanda take so sabanin zabin
iyayenta kuma yauce rana takarshe dasuka bata
cikin kwanaki biyar tafiddo wanda takeso kokuma
su bata wanda ransu yakeso. Lokaci guda nafara
tinanin halaccin da kowannensu tayiman a
rayuwa,
nanda nan wasu kalmomi suka rinka yawo acikin
kaina "kada kadamu nima wata rana zan iya
zuwa
agurinka neman taimako!!!", tabbas komai ba mai
wahala bane awurin Allah (S.W.A). Wata hajijiya
tafara daukata ina juyawa sai naga yasmeen
tsaye
abayana, ina hada ido biyu da ita natuna da
maganar da doctor yafada: "dole asama mata
farin
ciki arayuwa kuma aguji sanyamata bakin ciki ko
bacin rai indai anason lafiyarta"... Gaskiya inason
yasmeen sosai kuma bazanso inyi silar raunana
wani bangare na rayuwarta ba, nafada acikin
zuciyata, ko bakina baisan da maganarba balle
mutanen dake kallona... Lokaci guda kuma
namaida dubana akan yan matan guda biyu
kowacce ta hade fuska kamar basusan ko minene
fara'a ba balle ayi maganar murmushi. Cikin
kasala da rashin kwarin gwuiwa na nufesu
kafafuwana na kyarma ina tafiya kamar dan koyo
mai tafiyar ta ta ta, dakyar na iya tsayawa
agabansu nayimasu bayanin duk abinda ke
faruwa
kuma na shaida masu har anmallaka min
yasmeen
wadda take masoyiya kuma yar'uwa tajini aguri
na
sbd haka aurena da ita yana nan tafe batareda
jimawa ba. Rufe bakina keda wuya haleematu
tajuya a fusace tanufi motarta, bayanta nabi
dasauri ina kiran sunanta Haleematu! Haleematu!!
Amman ko kallona batayiba balle ta amsa kiran
danakeyi mata, afusace tabude motarta tareda
kargama mata key "haba haleematu dan Allah
kisaurareni, yaya zamuyi irin wannan rabuwar",
ko
kallona batayiba, ta fizgi motarta tayi gaba. Nayi
bakin cikin irin wannan rabuwa damukayi. Ahaka
najuyo agun inda nabar barista tsaye domin ganin
ita ya tamu zata kare, amman naduba sama ko
kasa babu barista sady saidai sawun tayar
motarta, alamar itama tabar wurin... "me yasa
zakabarsu su tafi, na yadda ka auresu", sama
sama naji maganar tana shiga kunne na shiyasa
nayi saurin juyowa domin tabbatar da abnda
kunne na yakeji, "na yadda ka auremu mu duka",
haba yasmeen kinsan zuciyata dake kadai
takudurci zama har karshen rayuwa ta, bazan
taba
yimaki kishiya ba ta yaya kike kokarin sanyani
abnda bazai yiwuba, ina gama magana nawuce
zan koma cikin gida, ita kau ko motsawa batayi
ba, "kitaho mushiga ciki mana" nafada tareda
juyowa agareta, "bazan taba barin wurinnan ba
harsai ka nemosu" tafada tareda dauke fuskarta
daga gareni, dakyar nasamu na shawo kanta
muka
koma cikin gida tareda alkawarin na yadda zan
auresu gaba daya. Bayan munshiga gida sai ga
haleematu ta dawo, har cikin gida ta fadamun ta
yadda zata aureni ahaka zata zauna da kishiya.
Bamu dauki wani lokaci ba sai ga barista sady
itama ta shigo tareda fadar itama ta yadda in
auresu gaba daya. Murna kau awannan ranar
abin
ba acewa komai. Nan muka daidaita kanmu iyaye
suka shiga ciki akayi duk abinda yadace. Aka
tsaida ranar aurenmu tareda na su usman lokaci
guda akayi komai. alhaji jafar ne yadauki nauyin
komai kuma ya hana iyayen kowane bangare yin
wani abinda yashafi bikin, hatta kayan daki shi
yayima kowace amarya kuma ya mallaka mana
gidan dazamu zauna. Lokaci yazo akayi biki cikin
farin ciki akasha shagali.
ALHAMDULLAH
Anan labarinmu ya kare,
sai kuma wani lokaci in Allah ya sake hadamu
Shin Ana Bukatan Blog ko website Kamar wannan kodai kamar Shafin
Duniyan Fasaha, za'a iya samu a kan farashi mai rahusa daga Babban kanfanin
Be With Me Technology Yola, Wayanda suka kware wajen
Website Design da kuma hada Mahajar Waya. Za'a iya tuntubansu
anan ko a wannan layin +2349039016969
Get Professional
Website Design For your business Today
Here. You can also visit our
Tech Blog for more awesome Information.