adsense here
[7:04PM, 5/23/2016] Mr, Smiles😃: [7:29PM, 5/7/2016] Mr, Smiles😃: [11:22AM, 3/23/2016]
💠💠 Amanar Aure 💠💠
💠💠💠💠
🔅1 and 2🔅
Via OHW📱📚
HILAL yasa hannu ya yashe mayafin dayake kan AMEELA, yana murmushi ya kura mata ido, Ameela ta mayar masa da amsar murmushinsa,
Hilal ya lumshe edo cike da godiyar yau dai Allah ya cika masa burinsa, ya mallaki Ameela a matsayin matarsa,
Bayan sun share sama ga shekara biyu suna soyayya cike da farin ciki da kuma kaunar juna,
Hilal yaja nunfashi yace "godiya ta tabbata ga Allah subahanahu wata ala, daya nuna mana wannan ranar mai cike da farin ciki a garen mu, kuma Ina kara gode masa daya mallakamun wacce a koda yaushe nake kiranta da cikar burina, hilal yayi ajiyar zuciya sannan ya kara duben Ameela yanai mata murmushi yace "bakice komaiba"
Murmushi Ameela tayi tana kallonsa tace "banda abinda zance a yanzu saidai inyiwa Allah godiya daya nunamin wannar ranar ta aurena, domin burin ko wace 'ya macce shine taga ranar aurenta, toni yau naga tawa, tayi shiru suka jima suna kallon juna cike da farin ciki da kuma nishadi,
Ameela tayi gyaran murya, hakan yasa hilal yadawo hayyacinsa,
Ameela tayi murmushi tace " yanzu nazama mallakinka, kuma nazamo matar ka, Dan Allah karikeni Amana karkaci AMANAR AURE"
Halal yaja nunfashi cike da jindadin kalaman amila yace "ki kwantar da hankalinki, Ameelata bazan taba cutar dake ba, kuma nayi miki alkawari kece kadai mata a nan duniya, kuma bana fatar wani sabani yashiga tsakaninmu" Ameela tace "nima haka, kuma Allah yabarmu tare har mutuwa"
Hilal ya amsa da ameen, sannan yatashi tsaye, yana kokarin cire babbar rigarsa ta anganci,
Ameela tabisa da kallon cike da farinciki,
Bayan hilal yakarasa cire rigarsa, sannan yacire agogon hannunsa, ya kalli amila yana murmushi," kizo muje muyui alwala muyi sallah munawa Allah godiyarmu daya nuna mana wannan ranar ta cikar burinmu"
Ameela ta janye mayafin dayake kanta tana kallon hilal cike da kunya, yaune first time dataga yanai mata wani iri mayen kallon,
Ameela tayi saurin maida mayafin ta rufe jikinta tana murmushi cike da kunya ta shagwabe fuska "too kaje ina zuwa "
Hilal yayi murmushi yace "Toh!!! yau naga sabon sanabi, amila nikike kunya yanzufa nazamo mijinki" nidai kaje zanzo nasameka" Ameela tafada cike da shagwaba,
Hilal yasaka dariya sosai sanna yanufi hanyar bandaki,
Ameela ta bishi da kallon tana lekonsa kamar marar gaskiya harya karasa bakin kofar bandakin,
Sannan yajuyo yana murmushi ya kiftawa amila edo, sannan ya murza kofar yashiga bandakin,
Shigarsa bandaki keda wuya Ameela ta janyo jakarta datake gefen gado tabude tadauko wayarta kirar Samsung galaxy s5,
Danne danne tafarayi,
Ina nesa ina rubutu amma danaga bana ganin abinda takeyi da awayarta yasa natashi nakarasa gurinta ina lekon wayar,
Janyo gurin notification tayi naga ta saka hannu ta danne gurin da ake bude data,
Zare idanu nayi ina mamakin wannan wace irin jarabar charting ce ta kamata, bazatama iya hakura da yau kadaiba, tun da yau ranar auren tace kuma first night dinta,
Bro Abdul ne ya dan dakeni a hannu nadan firgita(nadauka hilal ne yafito daga ban daki yakamani ina lekon asirin matarsa) nan nadawo daga duniyar tunanin dana shiga,
Na daidai birona na kara leka wayar Amila,
Massages naga sun fara shigowa ta ko wane App dakasan yakasance ana chart a cikisa irin su Facebook, Whtsapp, BBM, Instgrm, dadai sauransu wasuma banma san sunan suba dana fada muku sunansu,
Whtsapp Ameela tafara shiga, tana kallon wayar tana lekon kofar ban dakin a akai2,
Danna wayar take tanayin Kasa tana dunduba messages dinda suka shigo
NA:- ♥Rabi'atu sk mash Da mr, smiles😄
[11:22AM, 3/24/2016]
💠💠 Amanar Aure 💠💠
💠💠💠💠
🔅3 and 4🔅
Via OHW📱📚
Caraf edonta yafada kan wata number wadda aka rubutawa HAJNA beauty,
Danna cikin sakon tayi ya bude
Hajna " shegiya ameela bakida dama wato har first night dinki saikinhau chart, ina angon yake daya barki kina chart"
Ameela "hmm😄 yana bandaki zaiyi alwala, nima yace nazo muje amma nace masa yaje ina zuwa"
Hajna "tohh to ai saiki tashi kitafi mana, karyazo yasameki kina chart, karfa yafara gane halinki tun yanzu"
Ameela "hmm yanzu kuwa zantashi amma saina duba messages dina na Facebook domin akwai wani da wasan hausa da mukayi dashi zamu hadu 11:00pm kuma kinga yanzu 11 tayi yanzu haka nasan yana jirana"
Hajna " 😳 Ameela haryanzu baki daina kula maza a social network bah"
Ameela tana kokarin mayarwa da hajna da amsa,
Hilal ya turo kofar bandakin ya fito, da sauri ameela tamike tsaye tana sosa kanta,
Kallo daya yamata yagane batada gaskiya, lafiya kuwa " hilal yafada,
ciken da rashin gaskiya Ameela tace " bakomai ina duba wani abune a jakata "
Hilal yayi murmushi yana kara nazarin yanayin fuskarta yace, ganin waya a hannunta yasa yagane abinda takeyi "hmm kidaina karya batada kyau ameela, Annabi Muhammad s a w yana cewa alamun munafiki guda ukkune, kuma karya itace abu na farko daya fara fada, sannna kuma karya a duk yadda mutum yayita yana ganin kamar kadance yayi to karya batada kadan, yayi murmushi ganin tayi wani noke kai, yace "kije kiyi alwalar kifito inajiranki"
Bata daga kai ta kallesa ta nufi bandaki cike da kunya,
Tana karasawa bandakin tamayar da kofar ban dakin ta rufe
Takara janyo wayarta tashiga Facebook tana duna text inda akayi mata, sai reapply take musu harma ta mata da alwala tazo yi,
Hilal yana zaune gefen gado yana jiranta, kusan minti goma, shiru ko kukan ruwa bayaji,
Kina inane " hilal yafada..
Ameela ta zabura da karfi saida wayar takusan faduwa,
Sannan ta daidai kanta ta kunna fanfo tafara alwala,
Na:- ♥Rabi'atu sk mash Da Mr, smiles😄
[11:28AM, 3/24/2016]
💠💠 Amanar Aure 💠💠
💠💠💠💠
🔅5 and 6🔅
Via OHW📱📚
Koda ta gama alwalarma sai da ta tsaya ta duba wasu msgs din cikin sauri tayi reply sannan ta fito ta iskeshi yana tsaye yana jiranta saman sallaya.
Bayan sun qare sallar ya dade yana kwararo addu'a yayi mata en tambayoyi akan addini sannan ya jawo musu ledar Abnci, miqewa tayi tace "nidai a qoshe nake brci nakeji sosae, Yace "haba ameelatah, nasan bki qoshi ba ya zaki kwanta da yunwa? Tace "brci nakeji ne sosae, kuma bn iyacin abnci in inajin brci, bata jira me zaice ba ta haye gado ta jawo bargo ta lullube ta fiddo wayarta taci gaba da chat.
Harya gama dk abnda zaiyi yana kashe wutar dakin tayi sauri ta ajiye wayar don kar yaga haske ta kwanta kamar mai barci, Yaa miqa hannu yakai sau biyar da nufin tabata amma baiso ya tasheta dga qarshe dai ya haqura shima ya kwanta cike da tunane-tunane.
Saida ta tabbatar yayi brci sannan ta lallaba ta tafi falo tana sanda, saida ta tsaya ta dauki kazar da lemu don yunwar da takeji, ta zauna tana chatn tana cin abnci har dare ya fara nisa, sai murmushi take ita kadai don ba qaramin dadi chatn din ya matah ba!
Wani sabon frnd ne tayi a whatsapp yaa ita chat sosae, kota mnta da ynzu taa zama matar aurene data dage tana ta chat da maza?
1:40pm na dare hajna tafarka, jinkarar massages yamata yawa, tana chart bacci ya kwasheta ba shiru ta saki wayar akan gado, sai yanzu data farka tashiga laluben wayar, Ameela tagani online abin yayi matukar bata mamaki, Hajna ce tace "wai ke Ameelah ina kka baro Angonne daya barki kina chat first night dnki??
Ameelah tace "kinga nipa bnson iskanci in zamuyi firarmu muyi, miye a cikin chatn din??
Hajna tace "yau pa ne ranarki ta farko a gdan miji kamata yayi ku raya darenku cikin farin ciki ki bashi damar nuna miki soyayyar da yake miki,
Ameela Tace "Yayi brcinshi pa, nima jira nake 3 ta ida inje in kwanta,
hajna tace "tohm ni kinga tafiyatah don har nayi brci na farka amma kinata chat,
Ameelah tace "asha brci mai dadi mu ynxu muka fara. Lokacin hajna ta sauka
Haka taci gaba da chatn dn kusan kwana tanayi, sai da charging ta ya dauke sannan ta saka chajin ta tafi ta kwanta cike da farin ciki, don babu abnda ke saurin sanyata farin ciki kaman chat,
Na:- ♥Rabiatu sk msh da mr, smiles😃
[7:29PM, 5/7/2016] Mr, Smiles😃: [12:48AM, 3/25/2016]
💠💠 Amanar Aure 💠💠
💠💠💠💠
🔅7 and 8🔅
Via OHW📱📚
Washe gari
Tun 5:30am hilal yafarka daga bacci, (Allah sarki hilal, bai samu bacci mai dadiba, kamar irin wanda ko wane ango yakenema a daren farkonsa) haka yatashi yaje yayi alwala, sannan yadawo yatsaya yana karewa Ameela kallon, ba shakka bacci takeyi harda minshari, hilal ya girgiza kai yafita yanufi masallaci,
Bayan ankarasa sallah hilal yatsaya masallaci yayi addu'oi sosai akan aurensu, Allah ya basu zuria dayyaba,
Koda yagama addu'oin sa haske safiya yafara fito, nan yabaro masallaci yadawo gida,
Kan gadon daya barta kwance anan yasameta, ko alamun tashi batayiba,
Yadan tsaya yana kallonta kafin yasa hannu ya daki kafarta "kee...kee..Ameela, kitashi" tayi mika sannan tayi nishi mai karfi, ta bubbude hannaye kamar mai shirin tashi sai kuma ta fasa ta koma kwance,
Hilal yaja tsaki yakara dukan kafarta, takara jan nunfashi cikin muryar bacci tace "lafiya wai"
Hilal yace "ina kuwa lfy gashi har gari yawaye bakiyi sallar ba"
Ameela taja tsaki ta ya mutse fuska "haba Dee yanzu dan Allah ina amarya zaa tasheni da wannan safiya ai kamata yayi abarni natashi dakaina, dan Allah katafi kabarni" takara komawa kwance,
Ran hilal yabace jiyakeyi kamar yakai mata duka, meya shiga tsakaninsu da har zatace tana amarya za a tasheta, yace " ameela banason rainin hankali, kitashifa nace"
"To jeka naji zantashi" Ameela tafada tana kwance,
Hilal yakara jan tsaki, ya juya yakarasa bakin drower ya ajiye tazbi dinsa sannan, ya cire jallabiyar dake jikinsa ya dauko tawul nawanka yadaura sannan yanufi bandaki,
Kusan minti goma yayi acikin bandakin sannan yafito, still tana nan inda take, baccin ta takeyi,
Falo yafita yaje yadauko ruwan sanyi a firjin yazo ya auka mata su,
Da karfi tafarka "nashiga ukku na lalace" tafada cikin magagin bacci,
Yayi tsaye akanta yana jiran yashewar idanunta,
A hankali ta bude idonta suka hada ido, talura da yanayinsa ransa yabace matuka,
Sannan ta kauda kai daga kallosa tasaukar da murya "kayi hkr Dee wlh bacci ne yahau kaina"
Cikin hargowa hilal yace "wane irin bacci dazai hanaki sallah da wuri, idonsa yakai ga agogon dayake manne a ginin dakin, yace " duba agogo kigani karfe 7 harta wuce kinan nan kina bacci, yaushe kika tashi kuma yaushe kikahadamin kayan breakfast, koso kike naje waje naci, da auren nawa"
A hankali ameela ta tasauko daga kan gado tatsaya tana kallon hilal tace "ai amarya bata abinci sai tayi sati daya, haka naji ana fada"
Wani irin haushi hilal yaji kamar ya fashe da kuka yace "to shikenan tunda amarya bata abinci saitabar angonta da yunwa"
yana karasa maganar yanufi wuri shirinsa,
Ameela tayi murmushi tanufi bandaki tafara alwala,
Koda takarasa alwala tafito hilal yakammala shirinsa,
Ta tsaya abakin kofar ban dakin tana tsantsefe hannayenta, ta kalli hilal cike da mamaki "fita zakayj bazaka jira na kammala sallar na shirya maka breakfast dinba"
Yajuyo ya kalleta cike da jin haushinta, sai kuma ya danne bacin ransa, (domin bacin rai bayada wani amfani, hasali karshen bacin raima nadama yake kawowa) tana tsaye bakin kofar bandaki, baice da ita uffanba, yaje yadauko jakarsa ta zuwa aiki sannan yayi ajiyar zuciya yace "kibarshi kawai naci a waje, saboda idan natsaya jiranki zan iya yin late"
Ta shagwabe fuska "nidai Dan Allah katsaya,.karfa mutane sufara zagina suce wayewar garin daren aurenmu, an ganka kanacin abinci a waje"
murmushin karfin hali hilal ya kirkira kafin yace "bakomai matata ai kowa nada uzuri dan Haka namiki uzuri amma nayau kadai, karki kuskura kikara aikata irin hakan"
Ameela ta sunkuyar dakai cike da kunya, kalaman hilal suna matukar sanyata kunyarsa mutum baida zafin rai, dama haka takeson miji mai sanyin hali,
Na:-♥Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles😃
[12:56AM, 3/25/2016]
💠💠 Amanar Aure 💠💠
💠💠💠💠
🔅9 and 10🔅
Via OHW📱📚
Ameela tace "to shikenan mekakeso nadafa maka idan kadawo"
Hilal yace "basai kindafamin komaiba, zan siyo abinci nazo dashi idan dai ke kinada bukata kidafa kici,.na janye miki girki harzuwa nan da sati daya, ya durkusa yana kokarin saka takalmasa cover shoes, bayan yakarasa sakawa yace "to ni zan wuce, ki kularmun da kanki saina dawo" bai jira tayi maganaba yafita yabar dakin,
Bayan fitarsa ameela tayi ajiyar zuciya sannan takarsa bakin drowar tadauko hijab dinta tafara sallah,
Bayan takarasa sallah, dasauri tatashi babu ko adu' a, tafita falo (najuyo na kalli abdul nace ina kuma ameela xataje ko adu'a batayi ba, Abdul yace nima ina nasani kawai dai musa ido mugani)
Da isarta falo ta nufi gurin data saka chaji jiya wayarta tadauko, ta kunna domin akashe take,
Bayan wayar ta bude, tadan tsaya tana kallon wayar cen taji messages sun fara shigowa, daman DATA dinta a kunne take tunjiyar da wayar tadauke,
Wayar tacika full chaji, ta sance wayar a daga chaja, takoma daki, saman gado tazauna tafara bude massages dinta,
Whtsapp tafara shiga, edonta yafada kan wata number data rubutawa HMM, image taga sunshigo acikin sakon number, da sauri tafara download dinsu, pic ne guda ukku, suka bude wani hadanden guy ne yasha wanka, ga makemen gilass a fuskarsa, a hankali bakinta yabude tace "wow, guy di ba laifi"
A kasan image din anrubuta "ganawa pic nan dan Allah kituromin naki"
murmushi kawai tayi taci gaba da dundunba masseges dinta, cike da farin ciki tanai musu reapply,
Tafi kusan minti 30 tana chart sannan tatashi ta ajiye wayar tanufi bandaki tayi wanka, tafito, tanufi gaban mirror tafara chaba ado,
Abinka ga kyankyawa bawani jimawa tayi tana mek up dinba, ta kammala tayi masifar kyau tatsaya tana kallon kanta a madubi, tana murmushi, a lokacin ne kyanta yakara bayyana, (sakin baki nayi ina kallon wane irin kyaune ga ameela aiko a cikin indiyawa aka kaita tsaf zata sare dasu, gab naji a dakeni tabaya a firgice nadawo daga duniyar tunanin dana shiga nakama bakin alkalamina naci gaba da rubutu "
Na:- ♥Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles😃
[1:08AM, 3/25/2016]
💠💠 Amanar Aure 💠💠
💠💠💠💠
🔅11 and 12🔅
Via OHW📱📚
Wurin shirinta ta nufa tajanyo wasu hadandin tufafi, kananun kayane riga da wando, kayan sunyi matukar mata kyau,
Tana tsaye tana kallon kanta ta madubi tajiyo sallama a falo, da sauri takarasa bakin gado tadauko wayarta, sannan tafita falo,
Kawarta AMEERA tagani wadda suke kira da Amrah,
Suka rungume cikin jindadi da farin ciki, Amrah tafito daga jikin ameela tatsaya tana kare mata kallo tayi dariya tace " bakida dama kawata kinga wani kyau da kika kara kuwa, lallai auren nan ya karbeki, su haske manya" ameela ta yamutse fuska " ke dalla banson shashanci, wane aurene ya karbeni, nida ko morar first night dita banba" amrah ta zare ido "toh fa meya hana "
Ameela tayi murmushi tace "aikinsani mutum ne mana chart yadaukemun hankali, zoma kigani" taja hannun amrah suka zauna, ameela ta fitar da wayarta, tashiga ciki number nan HMM, tafara nunawa amrah photon guy din,
"Kinga wannan shine nake gayi miki jiya lokacin da muke cikin mota za'a kawoni gidan nan, shine guy dinda yadaukemun hankali jiya mukayita chart har kusan karfe 3 nadare, kinga pic dinsanan yacemun dan kaduna ne"
Amrah idonta nakan photon tace "aikuwa nasan za a rina wannan ai sai kaduna, ammafa ya hadu"
Ameela tayi murmushi "yace nima natura masa nawa"
Amrah tajuyo ta kalleta da mamaki "to tura masan zakiyi"
Ameela tace "eh mana to miye a ciki bafa a gari daya mukeba balle kice mijina zai iya ganin pic din, ni barima kigani, Ameela ta mike tsaye tana gyara dress dinta, tayi wata irin tsayuwa tace " yimin pic a wayata nashirya"
Amrah tace "a a ameela banbaki shawarar kitura masa photon kiba, kifa tuna akwai AMANAR AURE akan kifa"
Ameela ta tsuke fuska ta harare amrah "Amanar taci ubanta, ina ruwanki nidai kimun pic nace komai yafaru ai baruwanki, ruwanane, nidai kawai idan zakimun kimin, idan kuwa bazaki minba naji ahe"
"A a zamma yimiki, gyara tsayuwar zan dauka" amrah tafada bayan tashiga camera, tadaidaita fuskar ameela nan tafara bata flasher, ameela sai chanza style ake, wani style ko budurwa bazata yisa balle ita datakeda aure,
Bayan tayi dauka takai goma sannan ta karbi wayar tazo tazau kusa ga amrah "gyara muyi selfies" amrah ta gyara badama suka fara snapping din pics masu kyaun gaske.,
Bayan sungama selfies
Ameela tana murmushi cike da jindadi tace " yau dp zaici ubansa, domin idan nafara dura pic dinnan sai..." Amrah tana rike dawayar tace "kawata kinga wannan pic dinnan kuwa wlh yayi bala'in kyau" ta nunawa ameela daya daga cikin pic dinda taimata ne, Ameela tace "wow kamar baniba, dan Allah bani nadaurasa a dp" Amrah ta mika mata wayar, ameela takarba tadaura pic din a dp, sannan taturawa HMM sauran pics din kusan goma tatura masa, daga kasan pic din tarubuta gasunan"
Sannan ta rufe data tajuyo sukaci gaba da fira ita da amrah,
Na:-♥Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles😃
[7:29PM, 5/7/2016] Mr, Smiles😃: [9:57AM, 3/29/2016]
💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅19 and 20🔅
Afham bai jira dawowan Aneesah ba ya tashi ya tafi dakinshi cike da farin ciki, ji yake kaman damuwanshi taazo qarshe, Soyayyar Ameela ceh ke ratsa jikinshi tun daga sanda yaga hotanta Yanzunnan!
Wayarshi ya dauko ya shiga gallary, images hotan Ameelah ne farko ya tsaya yana qare matah kallo ko kadan baiso ya dauke ido daga kallonta
Tunanin kiranta yayi harya shiga contacts kuma saiya fasa ya fito ya bude datan shi ya shiga whatsapp yayi refreshing saiga numbrta ta fito, da sauri ya shiga numberta ganin wani hadadden Dp data daura yasha kyau cikin shigar atampa pink ta zubo bakin gashinta mai silbi da yasha gyara fuskarnan tata tasha makeup, naso ace kunganta, ba qaramin kyau Ameela tayi a selfie din ba!
Ya dauki mintina yana kallon pix din nata kafin ya lumshe ido ya bude yana murmushi wani irin farin ciki na ratsashi, shiga yayi zaiyi matah magana amma kuma cikin rashin sa'a bata online, tunani yayi bari yabar mata text idan tahau zata gani (brodza Abdul naga Ya dage yanaso ya hango rubutun da afham yake, daria ya bni nace let it be, mun karantah idan ya turama Ameelan)
Aneesah ce ta shigo dakin tatsaya tana kare masa kallo tana murmushi kafin tace "zan iya karantawa a fuskarka broz, lokaci daya qawatah Ameelah taa sace zuciyannka ko ba haka ba? Taku tafarayi harta karasa bakin gadon tazauna, ta kura masa tana murmushi tace "Kawai kafin in dawo harka tafi, koka mnta wurin zumudi kaa manta da keys dinka, ko duk son ameelar ne?" Daria yayi maicike da farinciki yace "kinsan yayanki sosae 6ter, da gaske ina son qawarki Ameelah!
Aneesah tace "gaskiya naji dadi sosae yayanah, daman Ameelah itace macen data dace dakai, domin nasan yayana yanason macce mai kyau da aji" takarasa maganar da zolaya
Ya shafi kyakkyawan sajenshi tare dayin murmushinshi me kayatarwa yace "shiyasa nakeji dake 6tanah! Kina saurin fahimtar abinda nakeso" murmushi aneesah tayi tamiki masa keys din sannan tatashi tafita takoma dakinta,
Na: ♥Rabiatu sk msh da Mr, Smiles😃
[10:28AM, 3/29/2016]
💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅21 and 22🔅
Ameelah qagara tayi tabar wayanta tayi charge suna cikin fira da 'Hmm' wayanta ta dauke don ita saboda tsabar son chat ko bata da charge batason ajiye wayan tayi charge.
Daqyar ta gyara dakin cikin sauri ko shara bata tsaya yiba balle aje ga batun abinci, tayi wankanta ta shirya cikin doguwan riga sky blue tayi kyau sosae sai dai shigar kamatah yayi mijinta ne ta mawa, amma ina bayada AMANAR AURE tadauki rudin shaidan,
Da sauri ta karasa inda wayanta ke charge, wayar na lake da chaja ta dauko ta zauna ta kunna data sannan ta shiga fezbuk, tafara duba text din frds dinta, kamar kullum da frdrsqt akai, nan tayi accept dinsu tun kafin massages su karasa shigo matah, bata dade a ciki ba ta koma whatsapp
Cikin nishadi take replyn har tazo kan numbrr Afham, tsayawa tayi saboda number tayi matuqar burgeta so speacil, shiga tayi ta duba text din kamar haka "Assalamu Alaiki, Sunana Afham! Ina fatan zan iya kasancewa Abokin firanki"
Murmushi tayi a ranta tace "sunan nashi ma mai dadi, ko ya kamanninshi zasu kasance?? Tunanin Amsar da xata bashi ta tsayayi, data rasa me zata ce mishi ta wuce kawai,
Taci gaba da duba text dinta, har a lokacin "Hmm" yana online, text dinsa nakarshe ta karanta kamar haka "beauty idan ina chart dake jinake gabaki daya natsuwata tadawo gareki"
Kalaman sun matukar mata dadi murmushi tayi wadda yakara bayya kyaunta sannan tafara typing
Ameela "😊hmm nima hakan nakeji aduk lokacin da muke chart, hakan yasa a duk lokacin da zamuyi chart sainaje nayi wanka na chaba ado kafin mufara"
Hmm "😀beauty kenan najidadi sosai, gaskiya inason naga irin kalliyar da kikayiwa wannan chart namu"
Ameela " To shikenan,
Daidaita zamanta tayi sanan ta kunna camera, ta dauki wani kyankyawan selfie tatura masa,
Photon yanuna alamar yashiga
Hmm "😘 wow kinyi kyau sosai, Allah ya mallakamin ke a matsayin matana,
Gaban ameela yafadi ta tsaya tana karewa text din kallo, tana tunanin wace amsa zata bashi,
Nan taji dinn, karar text yakara shigowa, text dinshine kamar haka
Hmm "Naji kinyi shiru bakice ameen ba kobakya sonane"
Ameela tayi rau rau da ido kamar mai shirin yin kuka, ta daura hannunta akan kypat tana tunani mezata rubuta masa...
Na:-♥Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
[7:29PM, 5/7/2016] Mr, Smiles😃: [9:28AM, 3/27/2016]
💠💠 Amanar Aure 💠💠
💠💠💠💠
🔅13 and 14🔅
Via OHW📱📚
Sai 12pm na rana amrah tabar gidan, haka baki suka dinga zuwan gidan zuwa ganin amarya,
Ameela tarika tarbar bakin hannu bibbiyu,
Misalin karfe biyu narana bayan ameela tagama sallar azahar sannan tadaura indomi guda biyu, bada jimawaba tadafe indomi kan danni table ta daura indomi ta cinyeta tas sanna tatashi tashiga bandaki tayi wanka, tafito tasake sabon shiri, cikin atamfa dunkin yasha aiki, kuma yakama jikinta sosai tayi kyau abinta,
Kangado ta kwanta ta janyo wayarta ta kunna DATA tana jiran shigowar messages,
Cikin seconds messages suka fara shigowa,
Bayan sun gama shigowa ameela tadanna hannunta akan Facebook,
Text tafara gani na wani frd dinta wadda yace mata shi dan fim ne kuma yana online, da sauri tashiga wurinsa bayan tagama karanta text dinda yayi mata, wadda yayi mata jiya dadare bata gansaba wayarta tadauke,
Ameela "barka da warka"
Dan fim "barka dai mai kyau meyasa jiya muna cikin chart kika fita, kina fita sainaji duk chart din badadi, gaskiya nayi miss dinki beauty"
Ameela taja nunfashi tana kallon text dinsa kafin tace "hmm sory wlh wayatace tadauke, yau baku aikine, naganka online, da rana"
Dan fim "hmm muna aiki mana yanzu haka ina gurin shooting wani fim ALLURA DA ZARE, muna tare da rahama sadau da Adam zango"
Ameela ta dafe baki cike da jindadi tana masifar son rahama sadau saboda yadda take rawa, tana burgeta,
Ameeela "woow my rahama tana tare daku yanzu, wayyo jinake kamar nabiyo iska nazo naganta, dan Allah kace mata fan dinta tana gaidata"
Dan fim "hmm zataji, karki damu mai kyau aike tamusamman ce agurina, dama ace zakiyi fim, dasai kinfi rahama fans"
Ameela "hmm inada sha'awar yin fim"
Dan fim "ayya to kizo ai zaki samu shiga indai kinaxa kyau, da ilimi, kuma ina tare dake zanmiki hanya,
Baijira tayi reapply ba yasake turamata
"Sorry director yakirani, yanzu zamu koma aiki, muhadu 12:00am zamuyi magana sai anjima beauty"
Ameela "to shikenan saimun hadu" tafito daga cikin username dinsa sannan tashiga duba notification dinta da kuma frd reqst da aka turo mata kuma duk tayi accept duka mazane babu macce ko daya, a kalla kullum zata samu frd reqst kusan mutum ashirin kuma duk maza,
Hakadai takare da Facebook, sannan tafito tashiga Whtsapp,
Badama tafara duba texts dinta bakuwar numbers tagani har guda ukku, sai sauran messages na grp dakuma kawayenta da samarinta,
Bakuwar number tafarko tafara budewa sakone kamar haka "aslm, sunana ANISA daga gombe gaskiya pic dinnan dakika saka yamun kyau shine naji ina son kizamo kawata daga Sun shine grp"
Ameela tayi murmushi kafin tafara typing na reapply, "wslm, sannunki da zuwa kuma nagode, nikuma sunana Ameela"
Bayan tagama typing din tatura mata sannan tafito tashiga bakuwar number tabiyu, sallamace kawai akayi mata tayi reapply sannan tafito ta duba ta ukkun, sakone kamar haka "wow kyankyawan surar jiki kamar na bata, ga manyan boobs, gaskiya ta ko ina kin hadu"
Tsaki taja tafara typing "kai malam dakata nifa matar aurece"
Ta sender masa daidai dayana online,
Alamu tagani na tabbas yagani kuma yakaranta, a saman number aka rubuta is typing,
Ta mannawa number ido tana jiran zuwan sakon, bada nimawaba sakon yashigo ta danna cikin number tafara karantawa "😃 wai matar aure, to ainima namijin aure ne, to koma daike mecece, nidai nagani inaso kuma, ina fatan zan more dake, sunana kamal"
Ameela jitayi kamar tayi block dinsa saikuma tafasa
Ameela "kafita harkata nagaya maka nifa matar aurece, kuma ni bayar iska bace"
Kamal "hmm kwantar da hankalinki yan mata nifa ba tabaki zanyiba kawai dai zamuna rikayin sex chart dakuma send pic din .... Kidai gane, gaskiya kinada kyau sosai domin ni harna sace pic dinki a dp dinki yanzu haka shinake kallo inasamun natsuwa"
Ameela cike dajin haushinsa tarubuta masa "dan banza, marar aikinyi tare tsaki sanann tayi block dinsa,
Sannan tafito taci gaba da sauran text dinta,
(Nace yayi kyau Yau Ameela ta hadu da gamonta, irin mazan nan masu lalata sakankun mata a chart, Allah ya shirya mu" ameen
Na:- ♥Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles😃
[9:43AM, 3/27/2016]
💠💠 Amanar Aure 💠💠
💠💠💠💠
🔅15 and 16🔅
Via OHW📱📚
Number data rubutawa HMM taduba baya online amma yabar mata sakon cewa yau su hadu karfe shabiyun dare, akwai magana, kuma yaga pic yagode"
Tagyara kwanciya tayi, tai ajiyar zuciya sannan taci gaba da chart dinta,
Tajima tanayi da samarinta, dakuma kawayenta,
Sannan taji ankira sallar la'asar, amma taki ajiye wayar haka taci gaba da chart har aka tayar da salla, aka gama kamar ba a kunnen akayiba, ko motsawa batayiba, balle tasa niyar tashi tayi sallah,
Saida tagaji sannan tatashi ta ajiye wayar akan gado tanufi bandaki tayi alwala, tun acikin bandaki takejin karar wayarta, amma taki fitowa saida tagama alwala sannan tafito,
Tataras anmata, 3miss call,
Zare ido tayi alokacin data duba number babu shakka number guy din nan ce wadda yayi mata maganar banza a Whtsapp chart tayi block dinsa, dafe baki tayi tana mamaki tace "nashiga ukku"
Dasauri tashiga blacklist tasaka number shi sanann tajiye wayar tajanyo sallaya tafara sallah,
Bayan tagama sallah, tadanyi adu oi sannan takara janyo wayarta tana kallon pic dinda sukayi dazu ita da kawarta amrah,
A hakali taji anturo kofar dakin anshigo,
Hilal ne rike da jakar aiki a hannunsa alamar gajiya ta bayya a fuskarsa karara, tashi tayi, tai masa sannu dazuwa, sannan takarbi jakarsa, cike dajindadi,
Hilal yakarasa bakin gado yazauna, bayan takai jakar a mazauninta,
Ameela tazo tazauna kusa dashi tana murmushi "Dee mezakayi wanka, ko bacci ka huta domin naga alamar kagaji."
Hilal yajuyo ya kalleta cike da kasala yaja tsaki, kamar mai rowar muryarsa yace " wanka zanyi, kuma idan nafito zanzo muyi fira kafin sallar magrib",
Ameela tace "to shikenan, bari na hada maka ruwan zafi" tana karasa maganar tatashi tanufi bandaki, bada jimawaba tafito tace "Dee evry thng is rdy"
Hilal yatashi yacire kayansa ya daura tawul yanufi bandaki,
Bayan yafito suka zauna sukayi fira irin ta mata da miji, har zuwa magriba, sannan hilal yafita yaje masallaci yayi sallah,
Bai dawo gida saida aka kira isha akayi sallar isha, bayan angama sannan yadawo gida, yatsaya yarufe kofofin gidan sannan yakaraso cikin gidan,
A kan kujera yasameta tana dannar wayarta, tanajin shigowarsa tayi sauri ta ajiye, tana murmushi,
Shima ya mayar mata da amsar murmushinta kafin yakaraso gurinta yasamu kujera yazauna, suka kara taba fira, sannan hilal yatashi yace "tashi muje mukwanta" bata musa masaba tatashi suka nufi daki,
(A lokacin harna shiga dakin nafara rubuto muku abinda zai wakana sai abdul yayi saurin janyoni baya, yace karnaje lekon asirin ma aurata bakyau, banshiga dakinba, nafito amma ina gani aka kashe wutar dakin), ... Toooh😫
Na:- ♥Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles😃
[10:20AM, 3/27/2016]
💠💠 Amanar Aure 💠💠
💠💠💠💠
🔅17 and 18🔅
Via OHW📱📚
tunda sassafe natashi, naci gaba da rubutuna,
babu abinda yachanza game da chart dinda Ameela takeyi, amma dai jiya bata samu damar chart din dareba,
Ko yau hilal bai tsaya karyawa cikin gidan ba, wanka kawai yayi yadauki jakarsa yawuce gurin aikinsa,
Bayan fitar hilal ta dauki wayarta tayita chart domin bata aikin komai, sabuwar kawarta data samu wato anisa sunyi chart yau mai dadi kuma hartayi save din number ta domin taga anisa tana da kirki sosai, duk wadan da tacewa zasu hadu shabiyun dare jiya, tabashi hakuri tace musu baccine ya dauketa, bata farkaba sai safe... Kujimun karya irin ta Ameela,
*****
A WANI GIDA
Wata wainar ake toyawa,
A Falo suke zaune sunyi jugum jugum, suna jiran amsar daga bakin AFHAM,
Afham yayi shiru ya sunkuyar da kansa kasa, yakasa magana
kawu bello yace "magana muke maka Amma kayi mana shiru, shin kanason AMAL ko kanada wadda kakesone"
Afham ya girgiza kai "aa kawu babu wadda nakeso amma kuma kawu maganar amal dince.."
Abban afham dayake zaune a gefe haushin afham yakamashi yayi saurin cewa "maganar amal dince.. To fada mana, abban afham yajuya ya kalli kawu bello yace "nifa kaine kake masa ta laluma, mumuka haifesa koshine ya haifemu, kagafa saboda gudun irin wannan matsalar yasa naki barinsa yayi karatu anan naija, nakaisa cen waje saboda karya taso ya bijirewa umarninmu, nifa nafada wannan auren shida Amal saifa anyisa domin wannan burin mune tun muna yara"
Kawu bello yace "a a yaya karka yiwa yaron nan abinda bayaso, yanzu dai abarshi yaje yayi shawara, kawu bello yajuya gurin afham yace " tashi kaje kayi shawara zamu nemeka" Afham yatashi ransa abace, shiba macceba amma ace za'ai masa auren dole, shifa baya son Amal dinnan,
Haka dai yashiga dakinsa zuciyarsa cike da wasi2 kala2,
Ya zauna gefen gado yayi jim yana tunanin wani abu saikuma yatashi yafito, yanufi dakin kanwarsa ANISA wadda akoda yaushe itace abokiyar shawararsa,
Akwance yasameta saman gado, Tana dannar waya, yayi sallama sannan yashigo dakin,
Dago kanta tayi tana murmushi ta amsa masa sannan yanemi gure a gefen gado yazauna yadan saka murmushi " chart kike koh, bakida aiki sai chart,.sai ciwon chart yakamaki"
Anisa tayi dariya sosai "la yaya harda wani ciwon chart akwai ne"
Afham yace "sosai ma idan mutum ya nace akan chart to chart zaibi jikinsa mutukar baiyi saba to bazaiji dadi ba"
Anisa tace "toh wannan likitancin kane yaya, anisa tatashi zaune tace "ai nama gama chart din daman wata sabuwar kawace nasamu wallahi yaya karka ganta ta hadu kamar ita tayi kanta,
Anisa tashiga gallery cikin Whtsapp prfil pc takai ga photon ameela tatsaya "kaganta yaya, sunanta ameela, kamar baindiya" tamikawa afham wayar, yakarba, dam yaji gabansa yafadi a lokacin dayayi tozali da kyankywar fuska ameela, sak irin yadda yake neman macce dakyau da diri da kuma kyakkawar surar jiki,
Anisa tana gefe tana dariya ganin yadda afham yakurawa photon ido,
Kamar daga sama taji muryar ummanta tana kiranta, dasauri anisa ta karasa bakin gado tasaka takalminta, tayiwa afham alama da hannu "ina zuwa yaya,.bari nazo musa labule idan yarinyar taimaka," takarasa maganar cike da zolaya dakuma dariya,
Afham gabaki daya pic din yatafi da imaninsa, lumshe ido yayi sannan yasake budewa, tabbas yasamu irin maccen daya jima yana nema, wadda tajima tana zomasa a mafarki,
baimasan da fitar anisa ba yajuyo yayi yana waige waige ganin bata cikin dakin yasa yayi saurin fitowa da wayarsa yashiga xender yatura pic din, sannan yashiga Whtsapp yaga number da aka rubutawa ameela, da sauri yadauki number yayi save a wayarsa ya ruba mata ZABINA,
Sannan yajiyewa anisa wayarta a kan gado yafita yakoma dakinsa,
Akan kado yakwanta yakamo pic din ameela yana kallo yana maimaita sunan a bakinsa, yaa lumshe ido sunan da surar jikinta duk sun masa, tabbas ya yayi gamu da katar kuma yanzunne zai samu damar tunkarar su kawu bello da abbansa yafada musu cewa yasamu wadda yakeso, matukar wadda yake gani a pic dinnan ta aminta dashi, duk azuci yake fadan wadan nan maganganun, a fili kuwa tambayar kansa yake, to ta ina zaifara....
Hmm akwai chakwakiya kenan.. muje zuwa
Na:- ♥Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles😃
[7:29PM, 5/7/2016] Mr, Smiles😃: [9:14AM, 4/2/2016]
💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅23 and 24🔅
A hankali take typing, ba 'ason rantaba harta karasa rubuta masa" ina son sosae, har cikin zuciyata"
Hmm Yace "Amma naji dadi sosae Ameelanah😃"
Suna cikin fira Afham yahau, yaga taga text dinshi harta karanta amma babu amsa,
gabanshi ya fadi a ranshi Yace "Ya Allah ka taimakeni akan soyayyatah! Ganinta online yasa ya shiga rubuta mata wani text din..
Afham "Sunana Afham, ina zaune a garin gombe, na ansa numbrki ne a wurin qanwatah Aneesha, Ameelah kinyi matuqar burgeni ne, saboda irin kyaun da Allah yamiki, lokaci daya naji zuciyatah ta kamu da sonki, ina fatan babu wanda ya rigani!"
Ameelah ta jima tana tunani akan text din kafin ta bashi amsa, kalamansa masu dadi sun ratsa zuciyarta,
Ameelah "gsky ngde sosae😃"
Afham Yace "hka kawai zakice, kinko san yadda zuciyata ta kamu da sonki, dan Allah kibani cikankiyar amsa wadda zata gamsar da zuciyata"
Ameelah taja nunfashi tana nazarin kalamansa masu sanya zuciya shaukin so da kauna, sannan tayi murmushi,
Ameelah "😊hmm tohm mezance??
Afham yace "inaso ne ki bani amsa, wlhy Ameelah daga jiya zuwa yanzu zuciyatah qara cika take da zazzafar qaunarki, idanuwana basa muradin kallon komai bayan kyankyawar fuskarki, ki aminta dani namiki Alkawarin bazan barkiba"
Murmushi take tana kara maimaita kalaman a kwakwalwarta, kanta yadau zafi, tana zaune ta kurawa text din ido,
TaRasa abinyi gashi bangare guda HMM text dinshi sai shigowa suke shima da irin nashi rigimar, ga messages na Facebook sai shigowa suke,
rufe datar kawai tayi ta zauna ta dafe kai tana tunanin Afham,
( Ameelah tabani tausayi, irin zaman danaga tayi saikace shege agurin rabon gado, saikuma wata zuciyar tace meye abin tausayi a tattare da wannan bayan nema take taci AMANAR AURE, ai Allah bazai taba barinta tasamu kwanciyar hankali ba)
*** ***
Batasan iyakar mintocin data bata tana tunani ba sai dai qarar wayarta ne daya katseta, number Aneesah ne da tayi saving da 'qawah' sai data kusan katsewa kafin ta dauka ta sanya a kunne cikin rashin kuzari.
Tun kafin tayi magana Aneesah cikin barkwanci ta fara cewa "haba qawah, gsky banji dadiba yanda kika saka yayanah cikin damuwah, Allah yana sonki da yawah ba yabon kai ba yen mata da yawa na sonshi amma ban taba ganin wadda yakeso kamanki ba! Don Allah ki amince mishi, kinji qawata"
Ajiyar zuciyah Ameelah tayi kafin tace "bazaki gane bane qawah matsalan kawai itace inada...."
katseta Aneesah tayi dacewa "kina dame nidai karkicemun kinada saurayi, kuma basaina gane ba kawai ki fitar da yayana dga cikin damuwah, kinga yadda yashigo dakina kuwa, a gigice wai ameelah taki aminta dashi"
Murmushi ameelah tayi sannan tace "shikanan zamuyi magana dashi anjima"
Dariyar jin dadi Aneesah tayi kafin tace "ngde sosae qawah bari na mishi Albishir"
Ameelah tayi saurin cewa "kenifa bacewa nayi na amint.... kafin Ameelah tayi magana aneesah ta kashe wayan, Shirun da ameela taji yasa tarinka fadan Hello, hello, a lokacin tafahimci cewa takashe wayar, tayi ajiyar zuciya, zuciyarta cike da tunani kala kala..
Na:-♥ Rabiatu sk msh da Mr, Smiles😃
[9:14AM, 4/2/2016]
💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅25 and 26🔅
Ameelah ta dafe kanta kafin ta yarfar da hannu tace "tohm miye ma A cikin Soyayyar? Soyayyah ne pa kawai shi da yake gombe ma ina xai ganni?" A zuci tayi maganar sannan ta buda datar ta taci gaba da charting dinta, amma a lokacin afham baya online, batama shiga Whtsapp ba Facebook tashiga tayi chart da dan fim..
Akayi sallar laasar duk tana zaune, charting yahau kanta,
(Wa'iyazubillah, wannan jarabar chart da masifa take, yanzu Ameelah ko tunanin mutuwa batayi, hmm Allah yakara karemu da kariyarsa, wai kaga mutum ana sallah shiyana zaune yana charting, wai bayason sauka, to idan baisauka anan duniyaba ai ya sauka kiyoma, Allah ya kyauta)
*** ***
Har lokacin dawowar hilal yayi babu Abinda tayi tana kwance falo saman kujera ya shigo da sallamarshi da sauri ta ajiye wayar tana kallonshi kamar marar gaskiya sannan ta mishi sannu da zuwa..
Ya amsa a gajiye, ganin yanayinta yasa baikara maganaba ya shige dakinsa, dasauri ta janyo wayarta ta rufe data, tayi ajiyar zuciya, tana zaune ya fito ya zauna saman kujera ya kishingida, Yace "wlhy yau na gaji da yawa, ga yunwa da nakeji"
Ameela ta dubesa tayi murmushi Tace "ayyah sannu"
Hilal yace "sannu bazata gamsar da yunwar danakejiba ki daukomin Abncinah inci"
cike da mamaki ameelah Tace "Yau kuma?
Hilal Yace "ban gane yau kuma ba?
Ameela takara yin murmushi Tace "naga ko breakfast baka tambayana ne, Yau kuma harda tambyar Abncin rana ko ka manta satin daya daka bani, baifa cikaba saura kwana biyu??
Girgiza kanshi yayi cikin takaici yaja tsaki, sannan ya daure ya danne damuwarshi ya tashi tsaye ya koma daki, ciki minti biyar ya fito ya canja shiga da mukullin motah a hannunshi, Yanufi kofar fita, tana zaune tana kallonsa,
Har yakai bakin kofa bai ce matah komi ba,
sai itace tace "ina kuma zakaje?
Hilal Yace "zan fita ne inciyo abincin waje, tunda nayi aurenma bazan huta ba"
Muryarta a shagwabe kamar zatayi kukah tace "ayni daman baka damu da cin abincinah ba"
murmushi hilal yayi yace "hmm ki fadi Abnda kike bukatah zan zo miki dashi, domin nasan kema yunwar kikeji"
Mikewah tayi tsaye sannan tace "ni sai dai ka tafi dani"
cikin mamaki yake kallonta kafin yace "ina zakije ko sati bakiyi da aure ba? Ina zanbarki ki fita wani ya kallemunke, Kiyi zamanki ki huta, kinji"
sororo tayi a tsaye don tasan maganace ya gaya matah, tana tsaye har yayi ficewarshi.
Ta tabe baki ta zauna taci gaba da chating dinta, kusan minti biyar tana jiran Afham har a lokacin bai hau ba, ta kagara suyi chart, ta rufe datar domin duk taji chart din ba dadi, ta ajiye wayar akan kujera, "Allah tadani naje nayi sallah" tafada sannan tatshi tanufi dakinta tashiga bandaki, tayi alwala sannan tafito tafara sallah, tayi raka'a biyu, tana cikin tahiya, taji karar wayarta a falo, a dai dai lokacin Hilal yashigo falo, da ledojin abinci a hannunsa, Ya dallawa Ameelah kira, saida ta zabura duk da sallah take, gabanta yayi mummunan faduwa,
Yau kam asirina ya tonu" tafada a zuci...
Na:-♥ Rabiatu sk msh da Mr, Smiles😃
[7:06PM, 5/23/2016] Mr, Smiles😃: [8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles😃: [6:16PM, 4/2/2016]
💠💠 Amanar Aure 💠💠
💠💠💠💠
🔅27 and 28🔅
Via OHW📱📚
Jitayi anturo kofar dakin da karfi, duk inda ilahirin jikinta yake yadau rawa, tayi matukar tsorata,
Hilal yashigo yatsaya yana kallonta tana sallah, ya girgiza kai ransa a bace yaja tsaki yafita ya koma falo,
Jitakeyi kamar takarawa sallar gudu, shaf2 ta gama sallar ko adu'a bata tsaya yiba tafito falo a gigice,
Wayarta tagani a hannun hilal, ta zare ido ta zabura kamar anmata sock, tayi matukar razana, taku takeyi cikin sanda ta sunkuyar da kanta kasa,
Jin tafiyarta yasa hilal yajuyo sukayi ido hudu taga yanayinsa ya chanza, ta tsaya cak guri daya tana jiran taji mezaice
A zuci take fadan nashiga ukku yau ruwa yakarewa dan kada"
Ameela ! Hilal ya kirata,
Cike da fargaba murya na rawa ta amsa,
hilal yace "karaso nan" ya nuna mata kujera da hannunsa,
Kafafuwanta har wani rawa suke dakyar takarasa bakin kujera tazauna, ta sunkuyar da kai tana wasa da dan yatsan, gabanta naduka shida shida,
Hilal yadubeta cike mamaki " ameelah kinbata wayonki a banza wlh, kin zalunci kanki, wane irin rudine shedan yamiki dahar...." Ameela ta katse masa magana da shakankiyar muryarta, kamar mai shirin yin kuka tace " dan Allah dee kayi hkr wlh..."
Hilal yadaga mata hannu, idanuwansa sunyi jajir yace "banason naji komai daga bakinki, wannan laifin da kikeyi bani kika yiwaba Allah subhanahu wata'ala kike sabawa, hilal yalura da irin tashin hankalin da ameelah take ciki, hawaye suka soma sauka kan kumatunta, yadan tsayar da maganar sa yana kallonta kafin yaci gaba dacewa "meya hanaki sallah da wuriii"
Dasauri ameelah tadago kai tallesa, zuciyarta harwani sanyi tayi, tace
Dee wlh bacci nake, koda natashi time ya wuce, amma kayi hkr bazan karaba"
Ajiyar zuciya yayi ya tashi tsaye, sukayi ido hudu yace " laifinki biyu kenan kinyi karya a yanzu kuma kinkiyin sallah da wuri, ameelah matukar kinason muzauna lfy dake a cikin gidan nan to karna kara ganin kinyi late din sallah", mika mata wayarta yayi kafin yaci gaba da cewa "karbi wayarki naxo naga ana kira, kafin nakarasa gurin wayar kiran ya tsinke, wata number mai suna Hmm"
Cike da firgita ameelah tace " ehhhm"
hilal yakara kallonta "eh amma bansamu daukaba koda na naxo ta tsinke"
ya mika mata wayar sannan yajuya yanufi dakinsa,
Wata irin babbar ajiyar zuciya tayi, ta share hawayen dake edonta, yana shigewa daki tadaga hannu sama "Allah nagodema "
Tana gama fadan hakan ta sauka daga kankujera ta zauna kasa. Ta janyo ledar abinci tafara budewa...
Na:- ❤ Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles😃
[6:31PM, 4/2/2016]
, 💠💠 Amanar Aure 💠💠
💠💠💠💠
🔅29 and 30🔅
Via OHW📱📚
Favorite food dinta yasaya mata tuwon amala da miyar yakuwa,
Zauna tayi ta gyara cikinta, taci saida ta koshi sannan tatashi, taje kichin ta wanke hannayenta tayi drooping din ledojin a dustbin,
Ta wuce dakinshi kai tsaye,
tatura kofar dakin tashiga sannan tayi sallama, a kwance tasamesa saman gado, dagashi sai singlet sai gajeren wando yayi shirin bacci,
Batare daya ko motsa daga kwanciyar dayakeba ya amsa mata sallamar.
Sum2 ameelah takarasa bakin gadon ta zauna tana facing dinshi,
Tayi gyaran murya tace " fushi kake dani mijina"
Baikulata ba hasalima juya mata baya yayi,
Sai abin yasoma bawa ameelah dariya domin tasan hilal bazai taba fushi da ita,.ba. ( a zuci nace "oooh shiyasa takecin Amanarsa. Dan taga yana sonta, da karfi naji an firgi biro daga hannuna, "idan kingaji da rubutun kibani naci gaba" Bro abdul yafada ransa a bace, na shagwabe masa fuska kamar zanyi kuka nace " haba dan Allah nina cemaka nagajine. Tunanin wani abu kawai nake" sai yace "to naji karbi amma karki sake" nayi murmushj na karbi biron naci gaba da rubutu" ...
*** ***
Ameelah takara matsawa kusa dashi, ta dora hannunta a bayansa, tasaukar da murya "Dan Allah my heart beat kayi hkr, nayi maka alkawarin baxan karaba insha Allah"
Hilal ya juyo yana murmushi suka hada ido, ameelah tamayar masa da amsar murmushinsa, sannan ta lumshe, a lokacin daya kama hannunta yana shafar tsakiyar, hilal yace "kinyimun Alkawarin baxaki karaba, to idan kika sake fah"
A hankali ameelah ta bude ido tace "kayimun duk hukunci daya dace dani"
Hilal yayi murmushi yace "to shikenan uwar yayana, Allah yakara bamu ikon hakuri dajuna"
ameelah ta amsa da murmushi "Ameen mijina"
Cikin wasa Hilal ya matse mata hannu, Ameelah ta saka ihu kadan,
dariya yayi sosai, yace "matsoraciya, sai raki"
Ameelah ta shagwabe fuska tana yarfa hannun "Allah ni saina rama, haka kawai zaka jimun ciwo dan kaga baikai karfin kaba"
Hilal yatashi zauna, ya kura mata ido yana murmushi " tohm kirama mana idan kinada karfi" ya daga mata edo,
ameelah tace " to mikon hannunka"
hilal ya mika mata hannu, ameelah ta rike hannun taje ta matse hannun yayi mata dabara yakara matse mata hannu ta kara saka ihu, dasauri ya sauko daga kan gadon yana dariya sosai, ameelah tatashi tsaye tayo kansa tana gunguni. "Allah ni bazanyi hakuriba saina rama duka biyun" tana kokarin karasawa gurinsa yana janyewa, hardai abin yazamo musu wasa...
(Toh nidai naja birona, da littafi nafita, nacewa mr smiles shima yafito mubar musu dakin domin wasar tafara karfin da dazan iya rubuta waba, wasan maaurata, dole muka fito mukabar musu daki, muka dawo falo muka zauna muna jiran sugama wasar mucigaba da rubutu, wasa2 abin har muka kusan awa daya ba labarin fitowarsu, abdul yace "ke tashi muje nina gaji da jiran wadan nan muje gidan su afham muje muga wace wainar ake toyawa, ban musa masa ba domun nima nagaji da jiran, fita mukayi muka lula garin gombe...)
*** ***
Katon hijab tasaka sannan takawo safa ta rufe kafafunta da hannayenta, kyankyawace duk da babu kwalliya a fuskarta, fuskarta mai cike da kamala, annuri, da kuma haske, ....
Wacece wannan.... (Na tambayi bro Abdul)...
Na:- ❤ Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles😃
[11:17AM, 4/3/2016]
💠💠 Amanar Aure 💠💠
💠💠💠💠
🔅31 and 32🔅
Via OHW📱📚
AMAL kenan, yarinya mai hankali da natsuwa ga son addini, ta turo kofar falon tashigo, aneesah da Ammi suna zaune a falon amal tashigo, aneesah ta tashi tana murna ta rungume amal, Ammi datake gefe tana murmushi tana kallonsu, bayan aneesah tasaki amal,
Amal ta sukuyar tagaida Ammi,
Ammi ta amsa cike da jindadi, sannan tatashi tabar musu falon, bayan sun zauna,
Aneesah tace " ya ustaxiya, ke kullum kinrufe jiki da katon hijab saikicevwata matar aure dubi dan Allah duk zafin nan kinsaka safa"
Amal tayi murmushi wadda yakara bayya dimples dinta "eh naji, komai zaki fada kifada, addinin mu yasanar damu cewa duk ilahirin jikin 'ya macce al'aurace bayan fuskarta da kuma tafin hannunta, kingakoh yazama dole narika rufe duk wata al'aura datake jikina"
Aneesah ta tabe baki "aikuwa daman nasani ana fara miki magana zaki fara yiwa mutane wa'azi "
murmushi amal tayi ta girgiza kai tace "hmm ai yanzu duk duniya tazama daya gaskiya wuyar fadane da ita, ida kuwa ka kuskura kafada to yanzu za'a rika kiranka mai waazi, karfa kimanta a cikin suratul AHZAB aya ta hamshin da tara 59 Allah subhanahu wata ala yana cewa, " يَا أَيُّهَا النَّبِيُّ قُل لِّأَزْوَاجِكَ وَبَنَاتِكَ وَنِسَاءِ الْمُؤْمِنِينَ يُدْنِينَ عَلَيْهِنَّ مِن جَلَابِيبِهِنَّ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَن يُعْرَفْنَ فَلَا يُؤْذَيْنَ وَكَانَ اللَّهُ غَفُورًا رَّحِيمًا " O Prophet! say to your wives and your daughters and the women of the believers that they let down upon them their over-garments; this will be more proper, that they may be known, and thus they will not be given trouble; and Allah is Forgiving, Merciful" " Yaa kai Annabi! Ka cewa matan aurenka da 'ya'yanka da matan muminai su kusantar da qasa daga manyan tufafin dake a kansu. Wancan yafi sauqi ga a ganesu domin kada a cucesu. Kuma Allah ya kasance mai garafa ne mai jin qai"
Aneesah taja nunfashi tace "Allahu akbar, nidai yanzu kiyi hkr zanma zo kikoyamun irin wannan shigar taki, nima naxamo ustaxiya" takarasa maganar tare da makkale murya, aneesah taci gaba da cewa " yanzu dai kitashi muje nakaiki ki gaida yaya afham yana cikin dakinsa, domin nasan wurinsa kikazo"
Amal ta sunkuyar da kanta cike da kunya, aneesah tazo ta kama hannunta suka nufi dakin Afham"
Zaune yake a kan wata kujera datake cikin dakinsa sanye yake da yadi fari, wadda yayi shara2 sosai, daga nesa zaka iya hango singlet dinda kejikinsa, yayi matukar kyau, photon ameelah yake kallon yana murmushi..
Amal ce tafara shigowa cikin dakin tare dayin sallama "Assalamu alaikum warahamatullahi ta'ala wabara katuh" complete ta cika sallamar, hakan yasa Afham ya chanza yanayin fuskarsa, domin yagane ko wace, tun a gurin sallamar,
Kamar bazai amsaba saikuma ya amsa ciki2,
Aneesah tace "to tunda munzo ni bari nakoma nashirya miki abinci kafin kifito"
Cike da kunya Amal tace toh shikenan"
Nan aneesah tafita tabar musu dakin,
Shiru amal tayi tana tunanin mezata cemasa..
Maganar sace ta katse mata tunani, cike da bacin rai yace "lafiya meya kawoki dakina"
Amal tace "gaisawa kawai naxo muyi"
Afham yace " to shikenan mungaisa, saiki tafi koh"
Amal tayi gyaran murya tadaga edo ta kallesa, a ko wane bugun zuciyarta kara son afham take, amma tarasa dalilin dazaisa ya tsaneta,
Amal tace " ya Afham meyasa kake wulakantani, nifa mutumce kamarka, kuma yar adam kamarka amma narasa dalilin dazaisa karika wulakantani, dan Adam fa abin karramawane koda kuwa baka sansaba, balleni danake yar uwar, Allah subhanahu wata'ala yana cewa nakarrama dan adam fiye da kowace halinta datake doron duniya, yaya Afham kasani cewa..."
Afham yadaga mata hannu ransa abace, "ya isa haka, naji kuma nayarda, matsalar ki kenan daga anfara magana sai kifara wa'azi, ni ko wannan wa'azin naki yana daya daga cikin abubuwan da banaso, saikace wacca aka haifa agaban littantanfan islamiya, Afham yakara kallon irin yanayin shigar Amal, yaja tsaki yace "lok amal nifa tsarinki kwata kwata baimunba, ke gabaki daya local ce baki wayeba" yatashi tsaye yana nuna mata dan yatsa kamar zaikai mata duka "dubi yadda kike shigarki saikace yar gafaka, dan Allah Amal ki hakura dani, kinji ance kwarya tabi kwarya kibarni nasamu daidaini kema kije kisamu daidai ke"
Amal hawaye take sosai, tana danasanin zuwa dakinsa datayi, daman tasan wulakancine tukwauicin dazata samu, dolece tasa tazo saboda son datake masa,
Yaja tsaki yanufi hanyar fita, a bakin kofar yaci karo ammi dasauri yaja da baya, ammi takarasa shigowa dakin ta kalli amal sannan tajuya ta kalli afham ta bata rai sosai tace "daman nasan za'a rina, hakan yasa nabiyo bayanta domin nasan halin wannan bakar zuciyar taka, inajin duk irin abubuwan dakake fada mata, ka kyauta mutumen bazan, wadda bayajin maganar iyayensa"
Afham yakara tsuke fuska yana gunguni yace " yanzu ammi saboda amal zaki cemun mutumen banza" cike da hargowa ammi tace "eh nace, maras kunya wadda baya tsoron fushin iyayensa"
"To shikenan, afham yafada cike da bacij rai yanufi hanyar fita da karfi yaja kofar kamar zai karyata, yafita yana huci yabar dakin"....
Na:- ❤ Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles😃: [4/7, 1:00 AM]
💠💠Amanar Aure
💠💠💠💠
🔅33 and 34🔅
Via OHW📱📚
kai tsaye garden ya wuce cike dajin haushin Amal, wayarshi ya fiddo yana addu'ar Allah yasa Ameelah na online ko fira suyi ya samu natsuwar zuciyarshi,
Cikin rashin sa'a kuwah bata online tsaji yaja, ya tura wayar cikin aljihu sannan ya lumshe ido, kamannun ameelah yafara bayyanowa a cikin zuciyar yana murmushi, tunanin ameelah kadai ya isa yasaka shi farin ciki,
*** ***
Sai bayan la'asar lis sannan hilal yafita, bayan duk mai wakana ta auko tsakaninsa da matarsa ameelah, sabon wanka yasake tare sukayi wanka shida ameelah, yaudaikam yasamu farin ciki sosai a gurin ameelah, basu fito daga bandakinba saida sukayi alwala, suna fitowa hilal yajasu sallah, bayan sungama yafita...
Ameelah tafita tarakashi har waje, sannan tadawo cikin Falo yanayin Falon ta kalla yadda yayi kaca kaca, tayi ajiyar zuciyah, sannan tashiga gyara, komai batayi acikin gyaranba taji wayarta tayi karar shigowar text, da sauri ta ajiye aiki tanufi wuri wayar,
Sakon afham tagani, magiya yake mata akan dan Allah ta hau online, yayi miss dinta,
Murmushi kawai ameelah tayi, ta janyo data ta bude tana jiran shigowar massages,
*** ***
Afham yana zaune yaganta online wani dadi ya kama zuciyarshi don yanason chart da Ameelah, nan take ya manta da bacin ranshi cikin nishadi yake mata typng..
Afham "Ina fatan kyakkyawar mace ma mallakiyar zuciyatah tana cikin qoshin lpy.
Murmushi Ameelah tayi cike dajindadi
Ameelah "lpylau kaipa?
Afham " ina cikin Annashuwa dajin dadi, Ameelanah yau babu wanda ya kaini farin ciki, gsky nazo duniya cikin sa'a dana hadu dake😘
Ameelah " 'nima nayi sa'a kuma ina cikin farin ciki"
Afham "kinsan me? Inanan zaune nake a garden ganyayyakin itatuwa sai kadawa suke ga daddadan iska mai dadin shaka, ji nake dama muna tare! Don Allah Ameelah yaushe zamuyi aure??
Ameelah tazare ido, kafin tayi ajiyar zuciya
Ameelah "da wuri haka? Duka yaushe na sanka? ko soyayya bmu fara bapa"
Afham yayi murmushi, yana kallon text din ameelah azuci yake fadan, da ameelah tasan yadda yadamu dasuyi aure da wuri dabata fadi hakanba, kodan yabakan tawa amal zai nemi auren ameelah da wuri, bayan yadawo duniyar tunanin daya shiga yafara typng...
Afham "miye a cikin soyayyah Ameelah? Zamu dinga chart ne ko waya, kullum tambyr bazata wuce ya kke? Kinyi mafarkina? Gsky hotannan kinyi kyau sosae! Hmm wannan bashine soyayyaba, ni Kullum burina in kasance tare dake, amma sai dai ayita musayar kalamai ana bayyana shauqi, mezai hana muyi aurenmu kawai?
Gaban Ameelah ya fadi, lallai Akwai rigima, tana cikin tunanin text dn Afham ya kara shigowa
Yace "son gaskiya nake miki Ameelah sona aure, idan kina ganin biki sanni ba ko banyi miki ba zan miki bayanin komi a kaina ga hotunanah nan, don Allah Ameelah ki zamo tawah karki gujemin!
Ajiyar zuciah tayi bayan ta gama karantawa duk ta hada zufa, hotunanshi ne take kallo ta jinjina kai a fili tace gaskia Afham kyakkyawan gaskene!
Yayi matuqar burgeta, nan tafara saqe saqe a zuci, ji take daman Afham ta fara haduwa dashi kafin ta auri hilal,
Na:- ♥Rabiatu sk mashi da Mr, Smiles😃
[4/7, 1:18 AM]
💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅35 and 36🔅
Via OHW📱📚
Ranar sunyi chatn sosae da Afham ana shirin yin sallar magrib yasauka yace itama taje tayi sallah, amma taji har akayi sallar magrib tana zaune, sai bayan angama sannan tatashi tayi sallar, bayan tagama tana tatashi tadauki wayarta tasaka chaji amma ta gagara ajiye wayar sai duban DP din frds dinta take har lokacin da hilal ya dawo babu Abnda Ameelah tayi, sai da taji tsayuwan motarshi ta ajiye wayan da sauri ta fara gyaran dakin...
Da leda ya shigo a hannushi ta amsa ta mishi sannu da zuwa ya qarema dakin kallo yanda ya barshi haka ya iskeshi, tana shafar kai tace "tunda ka tafi nake bacci ban samu nayi komai ba gidan!
Hilal yiyi murmushi
Yace "ay kara ki dinga hutawa, bari in fito in tayaki shara! Tayi murmushinta ya shge bedroom dinshi shima babu abnda ta gyara, haka ya shga toilet watsa ruwah shima ko wanki babu (sis rabi'at itama datake macce saida tace wannan wane irin jarabar chatn ne? Wasu matan zasuyi chatn bzasu gyara gdansu ba, babu ruwansu da tsaftar yaransu ko girkin mai gida! Sun gwammace su hau chatn suna cin Amanar aure, ko kuma chatn da qawayensu yaafi musu, nace "gsky ne ba duka matan ke da wannan tunanin ba)
Cikin sauri tashiga gyara gidan kafin ya fito, bayan yafito yazo yatayata suna aikin suna fira babu jimawa suka gama, ana kiran salar isha, hilal yafita yaje masallaci,
Yana fita, kamar tana jira, dasauri takoma gurin wayarta, daman datarta abude take, sakon ni taga sunshigo da yawa, harda wata bakuwar number, ta tsaya tana kallon number, number kamar bata Nigeria ba, saidai kuma hello kawai akace acikin number, saida ameelah takarewa number kallo sannan tafito, lambar hmm tagani ya auko mata sako, tayi sauri tashiga taduba, yace "beauty nayi miss din kalamanki dan Allah muhadu shabiyun dare akwai wani kyankyawan albishir dazan miki, plx kihau karki cemun kin manta saimun hadu" tayi ajiyar zuciya, kafin tafara zancen zuci "yanzu yazaayi muhadu, inason naji albishirin nan nasa" saikuma ta kada kai tace yes natuna,(na kalli rabi at nace "sis mekuma ameelah ta tuna ", tace "oho.. Musa ido mugani" nace "tomh)
Tana zaune tatuna da sallah dasauri tatashi tanufi bandaki bayan tafito tafara sallah, kamar wadda aka saka yin dole shaf shaf takarasa, tatashi ta nade sallayar sannan tafara shirin bacci kafin hilal yadawo,
Bayan ta kammala shirinta tafesa turare, sannan takoma kan gado ta kwanta, tanajiran dawowar hilal,
Kusan mintinta ashirin a kwance tana jiran dawowarsa, jitayi anturo kofar dakin, tunkafin yakarsa shigowa tayi saurin gyara kwancinta, sannan tarufe ido, tafara jan minshari.....
Na:- ❤ Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles😃
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles😃: [4/10, 11:44 AM]
💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅37 and 38🔅
Via OHW📱📚
Hilal yashigo dakin yayi tsaye yana kallonta, yanayin yadda tayi kwanciya yasa yaji aransa kamar tanada gajiya a tattare da ita hakan yasa bai tada taba,
Wurin cire kayansa yanufa ya cire tufafinsa, jallabiya ya janyo yasaka, sannan yanufi gado, har alokcin saida yayita kallon ameelah, yau cike yake da sha'awarta amma bazai takura mata ba, murmushi kawai yayi, ya kwanta ya janyo bargo, a hankali ya karanta addu oinsa na bacci sannan ya rufe idonsa,
Duk abinda ykeyi ameelah najinsa amma saita basar, kamar bacci take
Kusan awa daya tana kwance amma bacci take ba,
Sannan tatashi tayi mika tana kallon hilal, amma duk da hakn bata tashiba, sunansa tarika kira a hankali, taga ko motsawa baiba hakan ya tabbatar mata da cewa yayi bacci, sannan tatashi a hankali, tana tafiya cikin sanda harta fita daga cikin dakin,
Daman wayarta na falo tana chaji, wurin wayar tanufa ta dauko wayar tadawo saman kujera tazauna, agogon wayar ta duba 11:30, wani irin dadi taji domin bata saba alkawarin datayiwa Hmm ba,
Data ta bude cike dajindadi, massages suka fara shigowa, saida tajira suka gama shigowa kaf sannan tafara shiga whtsapp, bunbude sakonan takeyi ahankali tana yin reapply, hartakai ga number hajna beauty,
Dubawa tayi taganta tana online, ai kuwa nan suka fara chart hajna tayi mamaki sosai ta yadda taga ameelah tana matsayin matar aure amma tana chart din dare, har kusan 12..
11:56 Hmm ya shigo online, tana cikin charting da hajna taga text dinshi yashigo, da sauri tafito daga cikin hajna tadawo cikin hmm sakone yaturo
Hmm "Gaskiya beauty ina matukar jinki a raina, ta yadda kike cika mini alkawari"
Ameelah "hmm bakomai ai danna faran ta maka nake",
Hmm "😘 thnx i love yhu, ina jinsonki harcikin zuciyata, gaskiya bazan iya hakura dake ba, sonake kizamo mallakina"
Murmushi ameelah tayi kafin tafara typing
Ameelah "😀toh meyasa kakeson nazamo taka"
Hmm "hmm beauty kenan saboda ina sonki mana, wai kinkosan yadda nakesonki, bana iya minti talatin batare da ka kalli pic dinki ba"
Ameelah "🙈 toh lallai kana sona sosai to idan nazamo mallakin wani fa"
Hmm " 😡 aikuwa wlh dasai nakashesa, kuma kisa hallahira"
Ameelah "😳 kisa kuma, kana nufin zaka iya kisa akaina kenan"
Hmm "sosai ma kuwa wlh idn har akace za a rabani dake to baa nemi zaman lafiyaba"
Ameelah tayi dariya a zuce take fadan wannan baida hankali, inajin ya zauce, nadi nake matar aure taya zaiyi wannan ikirarin akaina, ni wannan soyayyar tamu a whtsapp kadai nadauketa amma banda zahiri,
Murmushi tayi sannan tafara reapply
Ameelah "😃😀 toh idan nice nace bana sonka fah, yaza kayi "
Hmm "😡😡😡 kidainamin irin wannan wasar, babu abinda natsana a duniya irin yaudara, budurwa ukku nayi kuma kowacce nina kasheta da hannuna saboda ta yaudareni, beauty idan kema kika yaudareni, kasheki zanyi sannan kuma nakashe kaina, domin nasan dacewa nazo duniya da rashin saa, bantaba jin nakamu dason macce kamar ydda nakamu dasonki ba, Dan Allah beauty karki yaudareni,.domin bana bashin yaudarah"
Tun bata gama karanta text dinba tasoma jin jiri, wani zafi taji yafara fita daga jikinta, dukda fankar datake cikin falon, amma bata hana zufa yakaryi ta jikin ameelah bah,
Wani iri tsoro taji yakamata, ayya kuwa wannan mutum ne, hannunta tadaga tana dan fifitawa jikinta,...
(A zuci nace su ameelah angamu da ...😡😡)
N:- ❤ Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles😃
[4/10, 12:03 PM]
💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅39 and 40🔅
Via OHW📱📚
Cike dajin tsoro tafara typing
Ameelah " Dan Allah da gaske kake kataba kisa akan yaudara, kodai wasa kakemun"
Hmm "😊 beauty kenan ai babu wasa a cikin maganata, ni makashi matane masu yaudara, amma idan kina tattama jirani kigani"
Gaban ameelah yafadi sosai tace nashiga ukku, motsi tajiyo a bakin kofar dakin da hilal yke kwnce,
Cike da jin tsoro ta juya gurin, bakomai bane kofar dakin ne tayi kuka, domin ta manta dazata fito bata rufe kofarba, a hankali tayi ajiyar zuciya sannan tatashi taje ta rufe kofar tadawo tazauna, tadauki wayarta..
Images tagani guda ukku sunshigo, a hankali tasaka download dinsu, nafarko wata kyankyawar maccece, a kasan pic din an rubuta "wannan itace SAJIDA itace budurwata ta farko, ta yaudareni kuma na kasheta" kuma babu abinda kayi..
Ameelah ta zare ido a zuci take fadan innalillahi wa inna ilaihi raju un",
Pic nabiyu yabude a hankali tasa hannu ta dannan cikin pic din yabude, shima photon maccece amma bata kai kyau ta farin ba, a kasan photon an rubuta "wannan sunanta FARIDA, munhadu da ita ne ta Facebook, munkusan share wata biyu muna soyayya hartakaimu gamun hadu a fili, data ganni shine tace bata sona, a take gurin zuciyata tahau na kasheta halla hira"
Cab jekaga zufa a jikin ameelah, idanuwanta sunfito bulla2, jikin ta har wani rawa yake,
( nace " ameelah tahadu da jafa i, hmm farawace idan har bata daina cin AMANAR AURE ba, )
Hannunta narawa ta danna cikin photon na ukku, tashin hankali 😳 Gawar maccece anyanka mata wuya gata akwace cikin jini, ameelah jitayi kamar ta burma ihu, (koni da nake gefe saida nakasa tsayuwa, saida bro Abdul yacemun "be a man plx" sannan na tsada hankalina naci gaba da rubutu)
Ameelah takasa tsayawa ta duba abin aka rubuta a kasan photon, domin tataba ganin photon a wani grp nata na whtsapp akace wani yakashe budurwarsa saboda ta yaudareshi,
Zuciyarta duka takeyi sama sama, a akan photo nan text ne kusan guda shida, a tsorace tafara karantasu,
1, wadan nan sune matan da suka yaudareni,
2, a yanzu haka babu ko daya a duniya
3, beauty karki yaudareni domin bazan iya hakurin rashin kiba
4, koda yake ai nasan kina sona bazaki yaudareniba
5, ina fatar kinfahimci maganata ko beauty, karfa kiji tsoron halina niba mugu bane, kuma bana cutawa kowa sai wadda ya cuceni,..
Kafin tagama karanta text 5 taji karar shigowar wani sakon a waje, bakuwar number data gani dazuce akayi mata text da ita,
A hankali ta duba agogon dayake saman screen na wayarta karfe 2:31 tagani, duk tsoro yakamata
Sannan takaranta text nashida
6, nasan yanzu kin tsorata dani. Dan haka zanbarki kije kiyi bacci kisamu natsuwa, Saida safe. Nyt swt drm my beauty😍😘 "
Saman sunansa taduba taga last seen dinsa kusan minti biyu da saukarsa, bata masa reapply ba tafito, bakuwar number data gani wadda akayi mata text kuma number bata nageriya bace sakon takai hannu ta danna sakon ya bude, sakone kamar haka " ke dan kutumar banki ya inai miki magana kin wani shareni, bana son iskanci fa" .....
(To wata sabuwa inji yan chacha)
Na:- ❤Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles😃
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles😃: 💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅41 and 42🔅
Via OHW📱📚
Ameelah tayi rau rau da ido kamar mai shirin yin kuka, ta daura hannunta akan kypat tafara typing
Ameelah "waye dan Allah, menai maka na zagi"
New no " ni bawan Allah ne kamarki amma ba irin jinsin kiba, ni aljanine, yanzu haka duk abinda kike yi ina kallonki, watar Allah ukubar Allah tana tattare da macce mai hali irin naki, yanzu haka ina kusa dake, la'ananna wacce bata san darajar Amanar aure ba"
Bashiri ameelah ta fara duba gefe gefen ta cike da tsoro tatashi tsaye, tana kallon falon,
Saida Ta tabbatar da komai aciki sannan tamayar da edonta ga wayar tana duba sakon daya turo, tsaki taja a zuci take fadan "wannan yama rainamin hankali, ni zaicewa ba mutum bane,
Cike da bacin rai da kuma raini tafara masa reapply
Ameelah "to idan kai ba mutum bane kafito naganka, ko angaya maka ni matsoraciyace "
New no " hahaha ai bazan fito kigan niba domin ku bil adam bakuda karfin halin ganin tsarin halintarmu amma zan taba kyankyawan gashin nan naki ki tabbatar da cewa ina kusa dake "
Ameelah "😡 eh nayarda kataba din...mtsw"
Taja tsaki tana kokarin rufe data taje ta kwanta domin taga karfe 3:10,
Ta rufe Datar tayi tsaye tana tunanin mutumen,
Jitayi an fizge gashinta da karfin tsiya, wata irin mahaukaciyar ihu tasaka, ko juyowoba bata yiba tafadi kasa somammiya,
( nida nake gefe saida birona yafadi, saboda tsoro, koda naduba gefen abdul shiharyakai bakin kofar fita daga falon, lolllx ...nayi kamar nabisa amma sainace to idan nabisa yazaayi nasan halin da ameelah zata shiga saina tsaya)
Kamar daga sama hilal yajiyo ihunta a cikin baccinsa, a gigice ya farka da sunan ameelah a bakinsa, yaduba bata kusa dashi, a gigice yatashi ya nufi bandaki, yaga bata ciki da gudu yafito yanufi falo,
A kwance yasame kasan cafet, da gudu yakarasa gurinta ya daga kanta yana girgizata yana kiran sunanta amma shiru, ya daura hannunsa a akan hancinta yaji bata numashi, a gigice yatashi yakoma daki yadauko makullan mota, yafito ya tallabota, ko takalmi babu a kafarsa, yafita waje a mota yasakata gidan baya, sannan yayi sauri yaje ya bude gete yadawo yashiga motar ya tada motar yafita, bai tsaya kulle gidan ba adu ar fita daga gida yayi yabarwa Allah sarkin iko... Domin yayi ikonsa akan gidan nasa,
Na:- ❤Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅43 and 44🔅
Via OHW📱📚
Wata karamar asibiti ta tabayan layinsu nan ya dosa, a manne yakarasa asibitin, ya kashe motar ko cire keys bai tsayaba yazagaya ya dauko ameelah ya tafito da ita daga cikin motar yamayar da kofar motar ya rufe, yanufi cikin asibin a gigice yake tafiya yana kiran sunanta, amma bata motsaba yana isa cikin asibin likitoci suka karbeta, suka nufi emergency room da ita, hilal yayi kokarin shiga dakin amma suka hanashi, wuri yasamu agefe yazauna ydafe kai yana hawaye tambayar kansa yake "meya faru da ameelah Allah katada kafadunta"
Zufa ya karyo masa yasa hannu ya shafe,...
(Bawan Allah hilal, abin tausayi, matarsa sai ci masa Amana take, da sannu Allah zai saka masa)...
Lalluben aljihunsa yafarayi, yafito da wayarsa ya kira iyayen ameelah,
3:40am
Suka karaso asibitin, yana ganinsu yatashi tsaye suka karaso gurinsa, a gigice momy tace "meya faru da ameelanah.. Hilal meya faru da ita"
hilal ya girgiza kai "momy wlh nima bansanibah kawai nazo naganta akwance ne a falo"
Cike da mamaki momy tace "falo kuma, tokai kana ina" hilal ya bude baki zaiyi magana abba yace "yanzu balokacin wannan tambaye2 ne ba, kuzo muje muji me likitoci zasu fada akan" abba yafice momy ta kalli hilal kallon rashin fahimta sannan tabi bayan abba, hilal ma yabi baynsu...
Sunfi minti 29 a bakin dakin da Ameelah take ciki sannan likita fito, da sauri suka taresa,
abba yace " likita meke damunta "
likita ya dube abba, momy and hilal yace " babu abinda ke damunta sock ne kawai akwai abinda ya firgitata, tasana diyarsa tasamu sock, amma batada wani matsala kowanne lokacin zata iya farkawa, idan ta farka kuma tana bukatar hutu kafin kuwuce da ita gida"
abba yace "alhamdulillah, Allah mungodema, ya juya gurin likitin "yanzu likita zamu iya shiga muganta "
likita yace " a a ba yanzuba kujira harta farka, ko kuma dayanku yashiga domin idan tafarka taga wadda tasani kusa da ita, kota samu natsuwa "
Momy tayi saurin cewa "nizan shiga likita" abba ya juyo ya kalleta, zumudin nan nata bata masa rai yake, ya harareta amma ko a jikinta, bata jira likita yayi maganaba ta tsunduma cikin dakin,
Likita yace " ita kadai ta isa ku sai kuzauna acen kafin tafarka" ya nunawa abba wuri da hannunsa sannan yafice yabar wurin,
Abba da hilal suka samu guri suka zauna suna jirar farkawar ameelah...
Na:- ❤Rabi'atu sk msh da Mr, Smiles😃
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles😃: [4/17, 12:39 AM]
💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅45and46🔅
A hankali Ameelah ta fara bude idonta, momie na zaune gefenta tayi tagumi, ta miqe da sauri ta qarasa inda take!
Qarema dakin kallo Ameelah tayi kafin abinda ya faru da ita ya fara dawo mata a qwaqwalwa! A firgice ta miqe zaune, tasa hannu ta fizge qarin ruwan da akai matah sannan ta dora hannu akai ta fasa wata razananniyar qara, jikinta sai kyarma yake nan danan taa hada xufa tana wani irin kuka marar dadin saurare!
Su abba da hilal da suke zaune a waje sukaji karar ta da sauri suka nufo dakin..
Can muka hango momie maqale jikin bango ta dafe qirji cike da tsoro, daqyar ta iya bin bango har takai qofa nan suka hado da hilal da Abbah suna shrin shgowa tare da likita!
Momie kam bata bisu ba sai dai ta tsaya riqe da qofa, su Abbah suka qarasa inda take suna tambyarta meya faru? Sai mexai faru? Muryarta ko kadan bata fita! Sai wani zazzare edo take tana kallonsu, saikace bata sansuba, edonuwanta sunyi jajir, Har lokacin jikinta bai daina 6ari ba!
A tsorace likita ke mata gwaje2..
Tashin hankali na hango muku sosae a fuskar hilal dasu Abbah, momie kam har ta fara kuka tana sambatu abinda ya qara qular da Abbah kenan!
Likita ya dade yana mata gwaje gwaje kafin ya fara musu bayani "gsky wannan aikin bana asibiti bne, rashin lafiyar Ameelah har yanzu mun kasa ganoshi, amma ina baku shawara kuje wuren malamai ku nema mata taimaka!
Momie ta dafe kirji tace "na shiga uku! Wannan wane irin ciwo ne, Allah wannan sammu ne aka mata, ture ne za'a mata, domin mu duk danginmu babu mai jinnu! Koma waye sai Allah ya saka miki!
Abbah ya watsa mata harara yace "don Allah ki shga goma ba uku ba, lafiyar 'yerki zaki nema ko kwasar ma kanki zunubi xaki tsayayi wurin zato?
Daukar Ameelah zamuyi mu koma da ita can gidanmu mu nema mata magani? Ta daga kai tana gurnanin kuka cike da tausayin 'yer tatah!
Na:- ♥Rabiatu sk msh da Mr, Smiles😃
[4/17, 12:55 AM]
💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅47and48🔅
Daga asibitin wurin wani babban malami mai bada taimako suka wuce, sun mishi bayanin abnda ke damunta malam yasa almajirinshi ya kawo mishi ruwa a kofi ya tofa mata addu'o'i a ciki sannan ya watsa mata a fuska, tai wani irin zabura ta fara ihu da kyarmar jikin, nan malam yaci gaba da mata ruqiyya!
Duk yanda yaso Ameela tayi magana ko kadan bata fita, bugu (duka) kam ameelah ta shashi duk ta qara fita hayyacinta! Gata fara fatar jikinta tayi jaa sosai da manyan borarai,
Daqyar aka samu kafaffen Aljanin ya fita, nan ta kwanta ta fara nannauyan barci!
Hilal duk da yana namiji sai da ya zubda mata hawaye, ji yake kamar ya maida ciwon jikinshi saboda tsananin tausayin matarshi, momy ma kuka take cike da tausayi, wani duka akayiwa ameelah shi saita rufe ido, saboda ihun da ameelah keyi,
Abbah ne ke qarfafa musu gwiwan basu haquri yana kwantar musu da hnkali! (Su Ameela kam anji jiki, ko wannan ya isheta darasin cin Amanar Aure??)
Tufafin dake jikin ameelah duk sun lalace,
Abbah ne yace ma hilal yaje ya dauko mata kayanta saboda daga nan idan tafarka gida zasu wuce da ita saita qara samun sauqi! Jikinshi a sanyaye ya tafi cikin tunanin halin daya bar Ameelah!
Sai da yaje gidanne ya iske a bude kamar yadda ya barshi, yananan ynda suka barshi, qafarshi yaji ya daki wani abu akasa, ya duqa wayar Ameelah ne ya dago yana dubawa kusan 9 miss calls.
Bai duba ko na waye ba yana shirin ajewa wani kiran ya qara shgowa! "HMM" yaga an rubuta, ya dauka ya kara a kunnenshi yana shirin magana.. Hmm ya rugashi!
Cikin tattausan murya yake magana "haba! Haba!! Haba!!! My Ameelah ni babu abnda zaki cemun, kinsan yanda na shaqu dake bzanso kimin nisa ba koda na qaramin lokaci ne, ya za'ay ki brni tun jiya ba chat ba waya? Yayi shru yana jiran abnda zatace.
Shikau hilal mutuwar tsaye yayi da waya a hannunshi, ko motsi yaa kasayi! HMM yaci gaba "ya zaki shru ki qyaleni masoyiyah? Kinsan irin son da nake miki ko kin daina sonah ne? Nasan hkanma bzai yiwu ba amma kimin magana ko zanji dadi a raina!
Shi kadai yake magana yana qara ma hilal quncin zuciyah! Shi da kanshi ya gaji ya kashe har lokacin hilal yaa kasa cire wayar a kunnenshi yayi tsaye kamar wanda aka dasa!
🔆kuyi haquri plz da rashin jinmu kwana biyu dabaku yiba, duk muna exam ne👏🏻 Masu neman na bayanma su mana uzuri plz🔆
Na:-♥Rabiatu sk mashi, da Mr, Smiles😃
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles😃: [9:49AM, 4/19/2016]
💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅49 and 50🔅
Via OHW📱📚
A sandare hilal yakai xaune saman kujira, "innalillahi wa inna ilaihin raju un" itace kalmar dayaketa maimaitawa a bakinsa, Ya tafe qirjinshi da hannu
yana mayar da nunfashi, gumi ya karwo masa, wani irin zafi yakeji a zuciyarsa, saboda tsananin kishi, idanuwansa sukayi jajir,
A hankali ya dora kansa a jikin kujera, ya rufe edo, kalaman dayaji a wayar sukadai ke masa yawa a kwakwalwa,
Cen bayan wasu yan mintuna ya bude idonsa, a lokacin hawaye suka sauka kan kumatunsa, yasa ya share,
Wayar ya dauko yafara duba number, number airtel ce, ya fiddo da wayarsa yayi copy na number, sannan yasaka wayoyin duka biyu aljihunsa, yatashi yanufi dakin ameelah,
wani dinkin atamfa yadauko mata tare da wani katon hijab, sannan yafito,
Saidai ya tsaya ya rufe gidan kam sannan yashiga motarsa, airtel office ya wuce direct yabasu number suduba masa, suka ce masa saiya jira nadan wani lokaci, gudun karsu abba suga yajima baidawowa yasa yabar musu number tare da cemusu zai dawo anjima,
Har a lokacin hilal yakasa dawowa hayyacinsa, jiyakeyi kamar zuciyarsa zasa fashe. Da zaiga wannan mutum da ya kira matarsa daya yayi mummunan saba masa,
Hakadai yakarasa gidan malam mai ruqiyya a bakin kofar gidan kafin yashiga yatsaya ya daidaita kansa domin ba yason su abba sugane yana cikin damuwa, sannan yashiga cikin gidan, ya mikawa momy tunfafin,
Abba da hilal suka fita momy ta chanzawa ameelah kaya, sannan suka dawo suna jiran farkawarta,
Kusan rabin wuni sukayi a gidan, tun cikin dare har safiya ta waye, sai misalin 12:00pm na rana ameelah ta farka, a hankali ta bude ido tana kallon su momy da suke gefe da ita, bakinta na rawa tace "momy ina ne nan meya kawoni nan"
murmushi momy tayi kafin takarsa gurinta tadafa kanta tace "ki kwantar da hankalinki, muna gurin nema miki lafiya ne "
Atsorace ameelah tace "lafiya kuma umma meya faru dani" momy tace " aike yakamata muyiwa wannan tambayar, meya faru dake a daren jiya ?"
Gaban ameelah yafadi domin ita harta mata da abinda yafaru da ita sai yanzu da momy tayi mata wannan maganar,
Bakinta yadau bari, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa, abba da hilal suna gefe suna kallonta, ameelah tace "nima bansaniba "
Na:-❤ Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
[9:49AM, 4/19/2016]
💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅51 and 52🔅
ViOHW📱📚
Cike da mamaki momy tace "kamarya baki saniba?" Abba yayi gyaran murya momy tajuyo gurinsa, abba yace "kedaina tambayarta kijira ta samu natsuwa daga baya maji sauran zancen a gurin mijinta"
momy taso tayi magana sai kuma tafara domin tasan tana musa masa zai hau masifa, saita kame bakinta,
Suna zaune malam yashigo, yatarar da ameelah ta farka, godiya yayiwa Allah sannan yayiwa abba bayanin zasu iya tafiya da ita, taje cen gida takara samun natsuwa, abba yaciro bandur na kudi yabawa malam sannnan yayi godiya suka dauki ameelah,
Gidan hilal suka wuce da ita, hilal yabude gidan suka shiga momy ta rikata suka karasa har cikin dakinta, saman gado ta ajiyeta sannan sukayi sallama dasu suka tafi,
A mota momy tafara masifa anhata taji matsalar yarta wlh ba ai mata adalciba, abba shiru yayi ko kulata baiba yaci gaba da tukinsa, harsuka kasa gida masifa take, suna shiga harabar gidan abba yakashe motar ya rigata fitowa zuciyarsa cike da takaici ya nufi cikin gidan,
*** **** ***
Hilal kuwa kamar jira yake su momy sufita, suna fita ya shigo dakin ameelah, tsaye yayi akanta yana kallonta, cike da bacin rai, fuskarsa a murtuke,
Yana yinsa kadai ameelah ta kalla tagane cewa akwai matsala, taja jiki takarasa bakin gado, "mijina meya matsalar"
Hilal ya tsuke fuska daman jiran yake tafar magana wayarta ya dauko yanuna mata, nan yafara fada cike da hargowa "daman abubuwan da kike aikatawa kenan a cikin wayarki, daman cin amanata kike.. Ehhh ameelah kifada mana?" yakarasa maganar cike da hargowa, da kuma zafin zuciya,
Ameelah tayi rau rau da edo, tsoro yakamata matuka, kaku yasoma kubuce mata, muryarta na rawa tace "daman .... Ehmm..ehmm... "
" daman me Kifada mana, kifada.... Ya nuna kansa da dan yatsa "me kika rasa a gurina, kulawa, soyayyah, addini , ko kuma me, menai miki kike cin amanar aure na" yayi shiru yana jiran ameelah tayi magana amma takasa kuka kawai take,
Hilal yadaga wayar cike da zafin rai "babu matakin dazan iya dauka akanki domin bazan iya sakin kiba amma nasan wannan ce koh, wannan ce matsalarmu koh, to daga yau babu ke babu kara rike waya"
Da karfi ya narka wayar a kasa, saida ta tarwatse gabaki daya,
Ko uffan bai kara cewa ba ya juya yabar dakin yana huci,
Yana fita ameelah ta share hawayenta daman na munafincine, dukawa tayi tadauko fasanshiyar wayarta, taduba sim dinta taga yana nan, ajiyar zuciya tayi, tace "alhamdulillah, daman ni saki kawai nake tsoro, amma tunda baka sake niba, da sauki" tayi murmushi takara kallon wayar kafin tace " hilal kenan kaida kanka zaka kara siyomin wata nasan yadda zanyi dakai"
Nan ta kwashe sauran fila2 wayarta ta ajiye gefe, sannan ta koma kan gado ta kwanta,
*** ***
A gefen afham kuwa, tun lokacin dayayi yiwa amal wulakanci momy tai masa magana, tun daga ranar yake gaba da momy, ya daina mata magana, koya ganta saidai ya sunkuyar dakai ya wuce, duk abinda yakeso saidai yasa aneesah ta kawo masa, (hmm kunji yayan zamani masu gaba da iyayensu, yanzu hakan wasun suke, da zaran iyayen sun sun musu fada to shikenan gaba ta shiga tsakaninsu, su ala dole ba a musu fada, hmm Allah dai ya kyauta)
Momy ce zaune a bakin gadon dakin abba tana kallonsa yana shiri, hulla yake sakawa yana duban mirror,
Damuwa ce tattare a fuskar momy tace "maganafa nake maka amma kayi banza dani, abubuwan yaron nanfa sunfara yimun yawa" tana karasa maganar tayi shiru,
Saida abba ya kammala saka hularsa sannan yajuyo gurin momy fuskarsa a daure yace " afham yana ina" momy tace "yana dakinsa mana " abba yafara taku "zomuje " yanufi hanyar fita, momy uffan baka kara cewaba tabi bayan sa,
Direct dakin afham suka shiga, abba ya turo kofar da karfi yana kiran sunansa, yanajin shigowarsu ya mike tsaye, abba yatsaya yana kallonsa, afham ya sunkuyar da kai, abba yafara masifa "ka kyauta, kuma kayi daidai, wato kai dan zamani koh, kana gaba da mahaifiyarka saboda tayi maka magana akan Amal, to shikenan nima saika shirya yin gabar dani domin wlh bazan janye maganar aurenka da amal ba, idan zaka shirya kashirya domin munsaka ranar aurenku nan da sati daya, marar mutunci kawai " abba yakarasa maganar cike da bacin rai, yajuya yabar dakin,
Kafin momy tafita saida ta dallawa afham harara, sannna tafita,
Afham ya duke kai yana kuka, sai bayan sunfita sannnan yazauna yafara masifa "Allah dai yasani nidai banason amal, auren dole saikace wata macce, wlh bazai yuyuba saidai nabar musu gidan su zauna sukadai, kuma suje su samo wani dan su aura masa amal, wlh gidan zan bari...
Na:- ❤ Rabi'atu sk mash da Mr, Similes😃
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles😃: [1:12PM, 4/24/2016] 💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅53and54🔅
Kaya afham yashiga hadawa, saida yacika akwatinsa kaf, sannan ya tsaya yana tunanin idan yafita ina zai dosa, ina zaije,
Kofar dakinsa yaji anturo, yakurawa kofar ido yana jiran yaga wazai shigo,
Aneesah ce tayi tsaye tana kallon yana yinsa, akwatin data gani a gefensa ta kurawa ido cike mamaki tace "yaya afham mekake shirin aikatawa ne, naga kahada kaya"
Afham yakauda kai daga kallon datake masa yaci gaba da rufe zip din akwatinsa, saida ya kammala rufewa yadaga kai yasake kallon aneesah "gidan nan zan bari, kuma idan natafi kigayawa su abba karsu nemeni, domin nabar gidan nan har abada, domin nayi shawara da zuciyata barin gidan nan shine kadai katangata agareni akan auren amal "
Mamaki yacika aneesah sosai, tarike kugu tana kallon afham "hmm yaya afham zuciyarka bata baka shawarar kwaraiba, domin tanema maka saukankiyar hanya wadda zata saka mahalincinka (Allah) Fushi dakai, domin yardar Allah tana tare da yardar iyaye, fushin Allah yana tare da fushin iyaye, yaya afham kayi gaggawar chanza wannan gurguwar shawarar taka, mezaka cewa Allah yanzu idan katafi kaddara takiraka kasamu matsala atafiyarka, zakacene kayi fushi da iyayenka shine kabar musu gida, mafi aka sarin irin wannan tafiyar bata zama alkhairi, yaya afham karkaje, kazauna cikin ahalinka shine mafi alkhairi agareka "
edon afham yayi jajir cike da masifa yace "yakikeson nayi kenan natsaya a auramun wacca bana so, nifa kwata2 bana son amal, wlh matukar ba'a rabani da amal ba to wallahi zanbar gidan nan"
Aneesah tayi ajiyar zuciyar, tana mamakin irin zuciyar afham shi baya daukar nasiha, a duk lokacin da kake masa nasiha shi a lokacin yake kara zafi,
Aneesah tasaukar da murya tace " Bana son katafi, kazauna ni zanyi abba da momy magana, zan fahimtar dasu cewa bakason amal, kuma insha Allah zasu saurareni, kabani nan da kwana biyar"
Afham yaja numfashi sannan ya ajiye akwatin akan gado yace "kwanar biyar kikace, nabaki, amma kisani cewa matukar ya wuce kwana biyar to tabbas zanbar gidan nan" yana karasa maganar yanufi hanyar bandaki,
Aneesah tana murmushi, takarasa kusa ga akwatin, tadauketa takaita cikin drowar tasaka, koda tajuyo yashige bandaki,
Kida kai tayi tana murmushi tabar dakin...
*** ***
Bayan hilal yabar daki ameelah cike da zafin zuciya, airtel office yakoma, koda yaje sunkarasa komai, an rubuta duk wani detail akan number, yakarba yafara karantawa, mai number bama gari daya sukeba, nisa yake dasu sosai,
Hilal yaja tsaki jiyakeyi kamar ya yaga pepar, miyakai ameelah waya da maza, meya rageta dashi meye baya mata, duk zuciyarsa yake yiwa wannan tambayoyin, saidai kuma ba amsa,
Cen kuma wata zuciya tafara kawo masa wasu wasi,
Ayya kuwa ameelah zata iya masa haka, tunawa yayi da irin soyayyar da sukayi abaya kafin aure,...
Na:- ❤Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
[1:17PM, 4/24/2016] 💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅55and56🔅
Auren soyayya sukayi, baya tunanin ameelah zata iya cin amanarsa, (hmm baisan kuwa tagama ba )... cikin motarsa yakoma, yadafe kansa, yana tunin irin fadan da yayiwa ameelah, sai yaji duk tausayinta yakamashi,
Yafi kusan minti goma cikin motar yana tunani duk jikinsa yayi sanyi,
Sannan yakunna motar yadawo gida domin jiyakeyi kansa namasa ciwo, dakinsa ya wuce baiko gayawa ameelah yadawoba,
Gado yasamu yayi kwanciyarsa,
*** ***
Sai bayan la'asar lis ameelah tafarka, jikinta duk yayi tsami saboda dukan datasha,
A kasale tatashi tanufi bandaki, tahada ruwan zafi tayi wanka,
Jikinta yadan saki, tarage jin zafin bulalar, bata fito daga toilet dinba saida tayi alwala,
Tana fitowa tayi sallah azahar da la'asar, domin bacci tayi bata samu damar yin sallar azahar ba,
(Wa'iya zu billah, yan uwa mudaina wasa da sallah, sallah itace hisabinmu nafarko a ranar gobe kiyama, Dan Allah yan uwa mukiyaye)
Bayan ameelah tagama sallah, tatashi ta nade sallaya, ta ajiyeta saman gado sannan tanufi gurin mek up dinta,
Motsi taji a falo, murmushi tayi domin tasan bakowa bane sai hilal, fushi yake da ita shine bai shigo dakintaba,
Kwalliya ta chaba, wacca bata taba yiwa hilal irintaba,
Bayan tagama ta kalli kanta ta mirror taga tayi kyau tai murmushi sannan tatashi, tanufi gurin shirinta,
Wasu kananu kaya naga tadauko, tana kokarin sakawa, ( nan mukabar dakin muka fito waje, bayan minti biyar na leka dakin, ido na kafawa ameelah, wani irin kyau datayi)
A hankali ameelah tafara zagaya dakin, kamar mai kowon tafiya,
Tabbas tasan kwalliyar datayi danta janyo ra'ayin hilal ne zuwa gareta,
Cike da kinsa da karairaya tafito waje,
A falo tasami hilal yana kallon wani indian fim, RAJKUMAR...
Tundaga nesa hilal yaji kamshin turarenta, ya juyo suka hada ido, yagagara dauke idonsa,
🔆NOTE🔆
Muna bawa Masoyan littafinnan namu AMANAR AURE, haquri zaku d'an jimu shru na kwana biyu! Da kuma masoyan HAFSATUL KIRAM, kuyimin uzuri insha Allah dana dawo zan qarasa muku! Muna godia da 'Kaunar littafanmu da kuke!😃👍🏻
Na:- ❤Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
[8:11PM, 5/3/2016] Mr, Smiles😃: [5/2, 8:57 AM]💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅63and64🔅
Momy tana zaune harya karasa sallarsa, sai da yagama adu a sannan tatashi tafita,
*** *** ***
Hilal kuwa sai bayan magriba yadawo, yayi parking na motarsa sannan yakaraso ciki falon, sallama yayita rabkawa shiru, babu amsa,
A zuciyarsa yace kodai wannan bacci take,
Dakin ameelah yanufa ya tura kofar yashiga, a kwance yasameta kasa tana kakin yawo masu kumfa,
Tadafe cikinta, tana kugi, a firgice yakarasa gurinta ya daga kanta cike da firgita yadaga murya sosai "ameelah meya faru dake, meya sameki"
Ameelah takasa magana, edanu take fitarwa bul2,
Hilal ya tsorata sosai, a gigice yadauketa yaje yasaka ta a mota ya nufi asibiti cikin gudun bala i,
Yana karasa asibin aka karbeta aka bata taimakon gaggawa,
Kusan awa Daya ameelah bata farkaba,
Hilal duk ya tsorata, yaso yakira iyayenta amma yafasa,... Yana xaune Likita yafito a firgice bai tsaya gurin sa ba yawuce office dinsa,
Hilal yatashi yabi bayanshi,
Dashigar likitan cikin office din ya dukufa gurin neman wani abu,
hilal yashigo office din, a tsorace yace "likita meya faru da matata"
likitan yadaga kai ya kallesa sai kuma ya basar yaci gaba da dubin takar dunsa, hilal yakara tambaya, sannan likitan yace " ba matarka bace a gabana yanzu, domin matarka farkawarta kawai muke jira, guba taci abinci kuma mun magance matsalar domin gubar bamai yawa bace, kuma bamai saurin illatawa bace, amma dai kukiyeye gaba,"
hilal yayi ajiyar zuciya yace "to shikenan Allah ya farkar da ita"
likitan yace amen, bai kara cewa komaiba yafita yabar office din, likitan yaci gaba da neman takardunsa,
Wata takarda yagani acikin wani file, daukota yayi, sannan yaduba yayi ajiyar zuciya, yafita,
Sai bayan isha ameelah tafarka, likita yayiwa hilal izini akan yashigo yaga matarsa,
Hilal yashiga yazauna gefen gadon da ameelah take kwance ya kalleta ta sunkuyar dakai yace "waya baki guba abinci"
Kanta a sunkuye tace "nima bansaniba"
Hilal yayi ajiyar zuciya yace "meyasa baki kiraniba lokacin da kika fara jin abin acikin ki, yanzu da Allah baisa nazo bafa yazakiyi kinga sai kawai nazo natarar da gawarki"
Ameelah tadaga kai ta kallesa cike da mamaki tace "dame zankiraka ai kasan banada waya"
Hilal yaja nunfashi "sorry kinga harnama manta, yayi shiru kamar yana nazarin wani abu, sai cen yace "to shikenan zansan mezanyi akai, yatashi yana kallonta "yanzu kijirani nakarbo takardar sallama saimu koma gida"
Ameelah ta girgiza masa kai yafita...
Na:-❤Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
[5/2, 9:00 AM]💠💠Amanar Aure💠💠
💠💠💠💠
🔅65and66🔅
Takardar sallama yakarbo yadawo suka wuce gida,
Har suka dawo gida iyayen ameelah basu san da zancen ba,
Da isarsu gidan yawuce dakinsa, ameelah ma haka dakinta ta wuce taje tasame gado tayi kwanciyarta
*** *** ***
Acikin daren afham yahada kayansa saida ya kintaci su momy sunyi bacci sannan yafito,
Tafiya yakeyi cikin sanda, harya karsa bakin kofa fita, ya bude yafita,
Motarshi yashiga, ya kunna, a lokacin mai gadi yatashi, yabude masa kofar get babba yafita,
Yakama hanyar gombe zuwa ganin ameelah ( kujimun wauta, Allah yakaremu da shairin zuciya)
Tafiya yaketa tsala sai kusashen asuba yakarasa gombe,
Wata babbar Hotel yakama yaje ya ajiye kayansa, wayarsa yadauko yayi off dinta yacire sim dinsa yadauko wani sabon sim yasaka, sannan ya kunna wayar, a cikin sabon sim din number ameelah ce kadai a ciki, kiran number yayi yajita akashe kamar yadda yasaba ji a yan kwanakinnan,
Zauna yayi a bakin gado cike da damuwa, sannan yayi ajiyar zuciya, ya wullar da wayar saman gado yatashi yanufi ban daki yayi wanka, bayan yafito yadawo ya kwanta,
Washe gari
Sai misalin 9 nasafe yatashi, a lokacin yayi sallah,
Sannan ma ai katan hotel din suka kawo masa kayan karin safe,
*** *** ***
Acen kuwa gidan su afham, momy tagama hada kayan kari, aneesah tafito tace "momy ina yaya afham duk yau bangan saba"
Momy tace "kinsan inda yake kije kisamesa "
Aneesah ta zunbure baki, ta nufi dakin afham,
Tunda ta tura kofar dakin takejin gabanta nafaduwa, a hankali takada kafarta cikin dakin, tayi sallama shiru,
Wata yar gajeruwar takarda tagani a gefen gadon sa, takarasa bakin gadon tadauko tana dubawa, karantawa takeyi a hankali, tun kafin takarasa karanta takarda hawaye suka fara zubo mata,
Juyo tayi da gudu tafita tana kiran momy,
Tana isah falo taci karo da momy da abba zaune akan danni, takarasa tana kuka tace "momy yaya afham yagudu" a gigice momy tace "innalillahi wa inna ilaihin raju un"
Abba dayake zaune agefe yakarbi takardar datake hannun aneesah, yafara karantawa, a karshen takardar aka rubuta " niban bazan iya auren amal ba natafi gurin wadda nakeso" edon abba sunyi jajir, ya dago kansa yakalli aneesah yace " wacece yakeso"
Aneesah tana kuka tace "wata yar gombe ce a chart suka hadu"
Abba ya girgiza kansan cike da takaici yace " lallai yaron nan zai hadu da fushina, wlh duniya kadai zai bari nafasa auren dazan masa shida amal, dole sai anyi wannan auren ko baya garin nan"
momy tace "aa alhaj..."
Abba yadaga mata hannu " karkice komai hajiya, wannan shine hukuncina" yana gama maganar yatashi yabar gurin , aneesah kuka take sosai momy tana lallashinta,
*** *** ****
A gidan ameelah kuwa, tunda safe hilal yafita bayan yakarya,
Ameelah takasa samun sukuni domin tunda tatashi daga bacci takejin gabanta nafaduwa, tarasa meye dalili...
Na:-❤Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
[7:10PM, 5/23/2016] Mr, Smiles😃: [11:16PM, 5/4/2016] Mr, Smiles😃: [11:06PM, 5/4/2016]
💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅67 and 68🔅
Via OHW📱📚
Ana gama azahar hilal yadawo gida, rike da jakar aikinsa a hannunsa,
Dakin ameelah yakarasa yasameta tana bacci, yaja tsaki a zuci yace "yanzu haka batayi sallar azahar ba"
Afili kuwa sunanta yafara kira yana dukan kafarta,
A hankali tafarka sukayi ido hudu ciki muryar bacci tace "harka dawo "
Hilal ya tsuke fuska yace " eh nadawo, kinyi sallar azahar"
Ameelah tadafe kai "au har lokaci yayi ne"
hilal yace "aa ki kwanta lokaci yajiraki"
Tagane bakar maganar yamata hakan yasa tayi murmushi tatashi tanufi bandaki tayi alwala,
Hilal yana tsaye tafito, saiya tashi yace "idan kingama sallar kisameni a daki"
Ameelah tace "toh"
Sallaya tadauko tafara sallah, bata jimaba tagama, tayi addu a sannan tatashi tanufi dakin hilal,
A zaune tasamesa yana kallon wata sabuwar waya datake hannunsa,
Sallama tayi yadago kai ya kalleta, takaraso kusa dashi tazauna,
Wayar ya mika mata yace "ga wayar kinan" tasa hannu takarba, iphone ce... Jita keyi kamar ta burma ihu,
Hilal yakatse mata jindadi dacewa "sim dinki na nan kona siyo miki sabo,
Cike da jindadi ameelah tace "yana nan bari nadauko "
Tatashi cike da zumudi tanufi dakinta dauko sim
Inda ta ajiyesa yana gurin, daukowa tayi tadawo dakin hilal,
Tamika masa sim din yayi off din wayar yacire murfi ya saka sim din sannan yamayar da marfin ya rufe ya kunna wayar,
Ameelah ta matsu wayar bata budeba,
Cas wayar ta bude, text massage suka fara shigowa barkatai, wadansu na mtn ne wasu kuma nawasu bakin numbers ne,
Hilal ya mika mata wayar, ganin sakonni na shigowa yace " kiduba sakon kigani mana"
Ta razana sosai tayi murmushin rashin gaskiya tace " toh jira nake sugama shigowa tukunna"
Kar kar kar sukaji wayar tadau kara,
Hilal yayi saurin duba wayar number HMM ce ,
HMM yakira, mummunan faduwar gaba ameelah taji...
Na:-❤Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
[11:07PM, 5/4/2016] 💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅69 and 70🔅
Via OHW📱📚
Hilal yagane number da sauri ya fizgi wayar, ameelah kamar tamasa kuka, ya danna yadauki kiran, ya kara a kunnen sa,
Ya gazgata muryar sosai muryar daya jice ranar nan,
HMM yace "beauty, beauty, keko acikin mayaudara bakowa bace, ni nafi karfinki, sama da sati daya ina cikin garinku kuma ke nazo nema, wlh wlh wlh duk ranar da mukayi ido hudu dake sai nayi ajalinki"
Razana na hango kaka a fuskar ameelah domin speaker hilal yasaka wayar,
Zuciyar hilal tayi matukar daukar zafi, cike da bacin rai yace "kai dan akuya ka rabu da ita matar aure ce "
Wani irin ihu da hmm yasaka kamar zai fita ta wayar, ameelah saida taja baya saboda tsoro, duk da hilal namiji amma saida yaji razana a zuciyarsa,
Cike da hargowa hmm yace "karyane wlh, beauty zaki mutu, wlh saina kasheki, ... kai kuma idan kacika kazo kasameni Honal Hotel sabon gari, sai nayi ajalinka "
Ranar hilal yayi matukar baci yatashi tsaye cike da zafin zuciya yace "gani nan zuwa "
Yana gama wayar yajefa wayar saman gado, ya juyo ya kalli ameelah wacce tuni idonta yafara fitar da hawaye,
Kauda kansa yayi yanufi hanyar fita, dasauri ameelah ta mike tashiga gabansa, tana kuka tace "karkaje hilal, dan Allah karkaje"
bangajeta gefe yayi, ya murza kofar yafita,
Dafe kai tayi tabi bayansa,
Kiran sunan sa take amma shi ko juyota baiba, motarsa yashiga, yakunna yatafi,
Saman hanya yake yana tsala uban gudu, zuciyarsa ta rufe gaggawa yake yakai unguwar sabon gari,
Gudu yakeyi a kan tati kamar zai bar duniya, mutum ya hango yana kokarin tsallake titin karrrr yayi kokarin taka birki, amma ina saida yakai garesa, kimiss ya ture mutumen dake gabansa,
Mutum ya burma ihu yafadi nan take jini yafara fita a jikinsa,
Hilal yafito daga cikin motar a gigice, tun kafin yakaraso mutane suka taru wurin,
Cikin jini aka dauki, mutumen aka sakashi cikin motar hilal, suka wuce dashi asibiti,
Da gudu yakarasa asibitin, idanuwansa sunyi jajir,
Dauko mutumen sukayi suka shiga dashi asibitin, nan take likitoci suka kawo musu taimakon gaggawa,
A emergency room aka sakashi,
Su hilal suka tsaya a waje shida mutumen daya taimakesa suka kawo wadda yakade asibiti,
Hilal duk ya fita hayyacinsa,
Kusan mintinsu talatin suna zaune suna jiran fitowar likita amma shiru,
Mutumen da sukazo tare ya mike tsaye yace "ga wannan wallet din a aljihun wadda kakade yafito, kirike nizan wuce gida" ya mikawa hilal wallet din ,
Hilal yasa hannu yakarba,
Mutumen ya wuce, cike da tsoro hilal yafara bude wallet din, sunan mutumen daya kadene yaci karo dashi dakuma photonsa a makale agefen sunan,
Sunan yafara karan tawa kamar haka "AFHAM SIDI ABUJA" Hilal yaji gabansa yafadi, sunan yakara maimaita a zuciyarsa "Afham !!!....
Na:-❤Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
[9:26AM, 5/8/2016] Mr, Smiles😃: 💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅71 and 72🔅
Via OHW📱📚
Hilal yayi Jim yana nazarin sunan, jiya keyi kamar yasan mai sunan,
hoton yatsaya yana kare kallo guy din yahadu, yafada a zuci sai yaji yanason zama da afham,
Wane gefe a cikin wallet din yakara budewa anan yaci karo da layin sim a ciki, dauko sim din yayi yana kallonsa mtn ne,
Wayarsa yaciro acikin aljihunsa, bude marfinta yayi ya cire sim dinsa yasaka wadda yagani a wallet din, a tunanin sa kozai sami number iyayen afham, domin yasanar dasu halin da yaron su yake ciki,
sannan ya kunna wayar,
Bayan wayar ta bude,
Contacts suka fara loading, a lokacin ya shiga contacts din yana bincike, 6ter aneesah itace number daya fara cin karo da ita,
A hankali yashiga kiran number , Ring wayar tasoma yi amma akaki dagawa harta tsinke, yakara kira a karo na biyu still ba a daga ba, saida yayi kusan five miss call ba a dagaba sannan yabar kiraran yashiga tura text , kamar haka "idan kinada alaka da mai wannan lambar wato afham, kuzo gombe domin yasamu hatsari yanzu haka yna asibiti" ya tura mata,
Yayi ajiyar zuciya,
yayi kamar zaicire marfin wayarsa yacire sim din saikuma yafasa, wata zuciyar take cemasa " kakara bincika contacts din ko zaka same number mahaifinsa"
Haka kuwa akayi hilal yashiga bincike cikin numbers din afham,
by mistake hannunsa yayi rolling zuwa alphabet Z numbers na kasa gabaki daya,
Tundaga Z yafara yin sama yana duba numbers , wata number yagani an rubutu mata ZABINA.
Number yashiga kamar xai kira sai kuma yatsaya yana tunanin yasoma gane number daga ina tafito,
Number yake karewa kallo, yaji gabansa yafadi, "number Ameelah" yafada bakinsa na rawa, sai kuma ya girgiza kai, yace "ina bazai samu number ameelah ba, saidai idan mtn ne sukayi mistake gurin yin number"
Zuciyar hilal cike da sake sake, "a zuci yace bari nakira naji"
A fili kuwa danna number wayayi yafara dailing nata ,
Cikin sa a kuwa wayar tashiga, saura kiris ta tsinke, aka dauka,
Ihu yaji yafara fitowa a cikin wayar hadi da kuka saida hilal yarazana, muryar ameelarsa yajiya sak,
Ameelah tana kuka tace "zai kasheni, wlh zai kasheni " sautin duka yaji yafito bayan tagama maganar, a gigice hilal ya mike yana fadan "ameelah waye zai kasheki" cike da hargowa saida hankalin mutunen da suke gurin kallonsu yadawo kansa,
Tunanin Kwakwallarsa yafara dawowa ya tuna da HMM kuma da ikirarin da yayi nacewa saiya kashe ameelah " kara manna wayar a kunnesa yace " ina zuwa ameelah" jiyakeyi kamar yabi ta wayar yakarasa gida,
A gudun tsiya yafita daga asibitin yaje ya shiga motarsa, gudu yake zabgawa akan hanya kamar zaitashi sama,
Daidai bakin layin shiga unguwarsu yataka wani irin wawan birki, saida kura tatashi, bai damuba yaci gaba da rusa gudu harya karasa bakin kofar gidansa,
A dai dai bakin kofar yaci karo da wani mutum yafito daga cikin gidansa da gudun tsiya fuskarsa rufe da mayafi, gabansa yaji yafada, dasauri yayi parking na motar, kamar zaibi mutumen saikuma yatuna da ameelah, yanufi cikin gidan, yana huci,
A kwance yasami ameelah cikin jini, a firgice yake kiran sunanta harya karasa gurinta yana magana amma bata amsa masaba,
Rungumota yayi yana laluba jikinta, yana kuka, daf yaji hannunsa yataba wani abu kamar karfe a gefen cikinta,
Cike da gigita yadaga riganta,
Wuka yagani, saura kiris takarasa shigewa cikin cikin ameelah,
Hannunsa narawa ya fizgi wukar daga gefen cikin ameelah, duk da ameelah a some take amma zafin fitar wukar yasa ta sandara wata irin wawuyar ihu,
Hannunta yasoma motsi,
Hilal duk ya fita hayyacinyasa yadago hannun yana cewa "ameelah baki mutuba"
Ameelah takasa magana tirgar nunfashi kawai take , duk jikin hilal yabace da jini,
Daukar ameelah yayi yana sambato kamar mahaukaci, yafita da ita waje,
A daidai lokacin hajan zata shigo gidan, domin ameelah takirata,
Ganin yadda hilal yadauko ameelah yasa taji gabanta yafadi,
Hilal ko kokuluta baiba yasaka ameelah a mota , ya kunna motar yakoma asibitin,
Asibitin da yakai afham acen yakai ameelah...
Na:- ❤Rabi'atu sk mash Da Mr, Smiles😃
[2:25PM, 5/9/2016] Mr, Smiles😃: 💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅73 and 74🔅
Via OHW📱📚
Yana karasawa asibitin yadaukota dukta bata masa motar da jini,
Yana shiga da ita wasu nurse suka ganshi da sauri aka janyo irin gadon nan mai taya aka azata akai, hilal yarike gefen gadon anan gudu yana kiran sunan ameelah,
Sai abakin kofar shiga emergency room sannan suka dakatar da shi,
Ba a son ransaba yatsaya, yana kuka ya jingina kansa a jikin ginin dakin da ameelah take ciki,
Kusan mintinsa goma a haka, kuka kawai yake, duk yarasa meke masa dadi, da wanne zaiji, bala in ameelah ko kade mutum dayayi,
A yanzu zuciyarsa cike take da zargin ameelah akan tana cutarsa, kuma tana cin AMANAR AUREn sa,
Cen bayan wasu yan sec yaji an tabashi ta baya, yana juyowa a kasale, suka hada edo da wadda tatabashi, ya rungume matar data tabashi yana kuka yace "umma ameelana zata mutu"
Ummansa ta taji tausayinsa sosai, tadago kansa… amma hilal yakasa bude edonsa domin idan yabude jiri yame gani, tace "garin yaya haka takasance, ina zaune gida hajna tazo tasanar dani cewa taga kadauko ameelah cikin jini"
Hilal ya bude janjayen edon dasauri yana kuka yace " ummana zuciyata tana zargin ameelah akan tana cin amanata, amma kuma saina karyata zuciyata, ummana idan kuwa hakane Ameelah tanacin amanana, umma....."
Tunkafin yakarasa maganar shock ya dibesa zube kasa a some,
Umma da hajna tare sukazo asibitin, dasauri suka kira likita shima hilal aka bashi gado acikin asibin,
*** *** ***
Acen kuwa gefen gidan su afham, tun bayan da abba yabar gidan lokacin da suka sami takardar afham ta barin gari,
Yana fita gidan mahaifin amal yanufa yasanar dashi komai dake faruwa mahaifin amal yayi jimami sosai,
Abban afham yace shifa haryanzh yananan kan bakarsa ta dauren auren amal da afham idan mahaifin amal zai amince a yanzu su daura musu aure, dan aure shedu kawai yake nema kuma gasu nan,
Abban amal bazai iya musawa abban afham ba amma baason ransa ya aminceba,
Anan abban afham yazare kudin sadaki, kamar yadda addina yatanada yabawa mahaifin amal,
Mahaifin amal yace abari yafita waje yakira koda limaman unguwane,
Abban afham ya amince da hakan,
Mahaifin amal yafita yaje yakira limaman unguwa da dattjiwan unguwa suka fita a harabar gidan su amal anan aka dauka auren AFHAM DA AMAL..
Na:-❤Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
[7:48PM, 5/12/2016] Mr, Smiles😃: [5/8, 9:30 AM] 💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅71 and 72🔅
Via OHW📱📚
Hilal yayi Jim yana nazarin sunan, jiya keyi kamar yasan mai sunan,
hoton yatsaya yana kare kallo guy din yahadu, yafada a zuci sai yaji yanason zama da afham,
Wane gefe a cikin wallet din yakara budewa anan yaci karo da layin sim a ciki, dauko sim din yayi yana kallonsa mtn ne,
Wayarsa yaciro acikin aljihunsa, bude marfinta yayi ya cire sim dinsa yasaka wadda yagani a wallet din, a tunanin sa kozai sami number iyayen afham, domin yasanar dasu halin da yaron su yake ciki,
sannan ya kunna wayar,
Bayan wayar ta bude,
Contacts suka fara loading, a lokacin ya shiga contacts din yana bincike, 6ter aneesah itace number daya fara cin karo da ita,
A hankali yashiga kiran number , Ring wayar tasoma yi amma akaki dagawa harta tsinke, yakara kira a karo na biyu still ba a daga ba, saida yayi kusan five miss call ba a dagaba sannan yabar kiraran yashiga tura text , kamar haka "idan kinada alaka da mai wannan lambar wato afham, kuzo gombe domin yasamu hatsari yanzu haka yna asibiti" ya tura mata,
Yayi ajiyar zuciya,
yayi kamar zaicire marfin wayarsa yacire sim din saikuma yafasa, wata zuciyar take cemasa " kakara bincika contacts din ko zaka same number mahaifinsa"
Haka kuwa akayi hilal yashiga bincike cikin numbers din afham,
by mistake hannunsa yayi rolling zuwa alphabet Z numbers na kasa gabaki daya,
Tundaga Z yafara yin sama yana duba numbers , wata number yagani an rubutu mata ZABINA.
Number yashiga kamar xai kira sai kuma yatsaya yana tunanin yasoma gane number daga ina tafito,
Number yake karewa kallo, yaji gabansa yafadi, "number Ameelah" yafada bakinsa na rawa, sai kuma ya girgiza kai, yace "ina bazai samu number ameelah ba, saidai idan mtn ne sukayi mistake gurin yin number"
Zuciyar hilal cike da sake sake, "a zuci yace bari nakira naji"
A fili kuwa danna number wayayi yafara dailing nata ,
Cikin sa a kuwa wayar tashiga, saura kiris ta tsinke, aka dauka,
Ihu yaji yafara fitowa a cikin wayar hadi da kuka saida hilal yarazana, muryar ameelarsa yajiya sak,
Ameelah tana kuka tace "zai kasheni, wlh zai kasheni " sautin duka yaji yafito bayan tagama maganar, a gigice hilal ya mike yana fadan "ameelah waye zai kasheki" cike da hargowa saida hankalin mutunen da suke gurin kallonsu yadawo kansa,
Tunanin Kwakwallarsa yafara dawowa ya tuna da HMM kuma da ikirarin da yayi nacewa saiya kashe ameelah " kara manna wayar a kunnesa yace " ina zuwa ameelah" jiyakeyi kamar yabi ta wayar yakarasa gida,
A gudun tsiya yafita daga asibitin yaje ya shiga motarsa, gudu yake zabgawa akan hanya kamar zaitashi sama,
Daidai bakin layin shiga unguwarsu yataka wani irin wawan birki, saida kura tatashi, bai damuba yaci gaba da rusa gudu harya karasa bakin kofar gidansa,
A dai dai bakin kofar yaci karo da wani mutum yafito daga cikin gidansa da gudun tsiya fuskarsa rufe da mayafi, gabansa yaji yafada, dasauri yayi parking na motar, kamar zaibi mutumen saikuma yatuna da ameelah, yanufi cikin gidan, yana huci,
A kwance yasami ameelah cikin jini, a firgice yake kiran sunanta harya karasa gurinta yana magana amma bata amsa masaba,
Rungumota yayi yana laluba jikinta, yana kuka, daf yaji hannunsa yataba wani abu kamar karfe a gefen cikinta,
Cike da gigita yadaga riganta,
Wuka yagani, saura kiris takarasa shigewa cikin cikin ameelah,
Hannunsa narawa ya fizgi wukar daga gefen cikin ameelah, duk da ameelah a some take amma zafin fitar wukar yasa ta sandara wata irin wawuyar ihu,
Hannunta yasoma motsi,
Hilal duk ya fita hayyacinyasa yadago hannun yana cewa "ameelah baki mutuba"
Ameelah takasa magana tirgar nunfashi kawai take , duk jikin hilal yabace da jini,
Daukar ameelah yayi yana sambato kamar mahaukaci, yafita da ita waje,
A daidai lokacin hajan zata shigo gidan, domin ameelah takirata,
Ganin yadda hilal yadauko ameelah yasa taji gabanta yafadi,
Hilal ko kokuluta baiba yasaka ameelah a mota , ya kunna motar yakoma asibitin,
Asibitin da yakai afham acen yakai ameelah...
Na:- ❤Rabi'atu sk mash Da Mr, Smiles😃
[5/9, 2:24 PM] 💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅73 and 74🔅
Via OHW📱📚
Yana karasawa asibitin yadaukota dukta bata masa motar da jini,
Yana shiga da ita wasu nurse suka ganshi da sauri aka janyo irin gadon nan mai taya aka azata akai, hilal yarike gefen gadon anan gudu yana kiran sunan ameelah,
Sai abakin kofar shiga emergency room sannan suka dakatar da shi,
Ba a son ransaba yatsaya, yana kuka ya jingina kansa a jikin ginin dakin da ameelah take ciki,
Kusan mintinsa goma a haka, kuka kawai yake, duk yarasa meke masa dadi, da wanne zaiji, bala in ameelah ko kade mutum dayayi,
A yanzu zuciyarsa cike take da zargin ameelah akan tana cutarsa, kuma tana cin AMANAR AUREn sa,
Cen bayan wasu yan sec yaji an tabashi ta baya, yana juyowa a kasale, suka hada edo da wadda tatabashi, ya rungume matar data tabashi yana kuka yace "umma ameelana zata mutu"
Ummansa ta taji tausayinsa sosai, tadago kansa… amma hilal yakasa bude edonsa domin idan yabude jiri yame gani, tace "garin yaya haka takasance, ina zaune gida hajna tazo tasanar dani cewa taga kadauko ameelah cikin jini"
Hilal ya bude janjayen edon dasauri yana kuka yace " ummana zuciyata tana zargin ameelah akan tana cin amanata, amma kuma saina karyata zuciyata, ummana idan kuwa hakane Ameelah tanacin amanana, umma....."
Tunkafin yakarasa maganar shock ya dibesa zube kasa a some,
Umma da hajna tare sukazo asibitin, dasauri suka kira likita shima hilal aka bashi gado acikin asibin,
*** *** ***
Acen kuwa gefen gidan su afham, tun bayan da abba yabar gidan lokacin da suka sami takardar afham ta barin gari,
Yana fita gidan mahaifin amal yanufa yasanar dashi komai dake faruwa mahaifin amal yayi jimami sosai,
Abban afham yace shifa haryanzh yananan kan bakarsa ta dauren auren amal da afham idan mahaifin amal zai amince a yanzu su daura musu aure, dan aure shedu kawai yake nema kuma gasu nan,
Abban amal bazai iya musawa abban afham ba amma baason ransa ya aminceba,
Anan abban afham yazare kudin sadaki, kamar yadda addina yatanada yabawa mahaifin amal,
Mahaifin amal yace abari yafita waje yakira koda limaman unguwane,
Abban afham ya amince da hakan,
Mahaifin amal yafita yaje yakira limaman unguwa da dattjiwan unguwa suka fita a harabar gidan su amal anan aka dauka auren AFHAM DA AMAL..
Na:-❤Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
[7:49PM, 5/12/2016] Mr, Smiles😃: [7:56PM, 5/10/2016]
💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅75 and 76🔅
Via OHW📱📚
Bayan angama daurin auren, abban amal yacewa abban afham to yanzu ya zaayi maganar kai amarya amal gidanta "
abban afham yace "kowane lokaci suka tashi sukaita domin yasan komai daren dadewa afham zai dawo, abban afham yaci gaba dacewa "zan dafe duk wata kafa tafitar da kudina, tayyada bazai iya fitar da koda sisi bane daga cikin kudina sobada haka idan yaji matsuwar rashin kudi zaidawo"
Abban amal yace "to shikenan ajirashin harya dawo sai a kai masa matarsa"
Abban afham yayi godiya sosai, sannan sukayi sallama ya wuce office dinsa, yau daikam yacika burinsa,
Har bayan yazauna yafara aiki, yatuna dabai gayawa umman afham batun auren ba wayarsa yadauko yakirata yasanar da ita komai dayake faruwa, saida tamsa kuka a wayar,
Ransa yasoma baci da sauri ya kashe wayar,
Aneesah tana zaune a falo tatayar da kanta sama, momy tafito daga cikin dakinta tana hawaye takaraso gurin aneesah,
Ganin da aneesah tamata yasa tatashi zaune tana tambayarta " momy lafiya kuwa "
Momy tace "an daura auren afham da amal, yanzun nan abbanki yakirani yasanar dani"
Aneesha taji gabanta yafadi, kafin tafara magana hawaye suka soma sauka kan kuma tunta tace " taya za a daurawa mutum aure baya gari, wannan wlh amal aka cuta, Allah sarki amal" takarasa maganar tana kuka,
Momy ta katse mata kuka dacewa "kitashi kije kikara afham kiji koda ke zaki samesa, domin ni tun jiya nake kiraan wayarsa a kashe,"
Aneesha ta share hawayenta tace "nima tun dazu nake neman wayata bansan inda na jefa taba"
Momy tace "tashi kishiga dakinki mana kiduba"
Aneesah ta mike tsaye tace "toh momy" tana karasa maganar tanufi dakinta,
Duk saida tayiwa dakin kaca kaca amma bataga wayarba,
Haka ta hakura tabi lafiyar gado ta kwanta domin tagaji, bacci yadauketa zuciyarta cike da tunanin dan uwanta afham
Na:-❤Rabi'atu sk mash Da Mr, Smiles😃
[7:58PM, 5/10/2016]
💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅77 and 78🔅
Via OHW📱📚
Umma da hajna suna gefen hilal, sukaji ya motsa, a hankali yake bude idonsa, har idon yayashe,
Umma ta janyo kujera tadawo kusa dashi tarike hannunsa tace " ya jikin "
hilal yayi nishi yace "yawwa naji sauki"
Hajna takaraso gurin duk ta marairaice jikinta duk yayi sanyi tace " ya hilal ya jiki "
Hilal ya girgiza mata kai,
Umma taci gaba da cewa "nakira iyayen ameelah a waya yanxu haka suna cikin asibitin nan suna dakin da ameelah take"
Hilal yamike tsaye yana tangadi kamar zai fadi, umma tayi saurin rikashi, "ina kuma zakaje kajira kakara samun sauki mana"
Hilal yajanye hannunsa daga rikon da umma tamasa yana nishi yace "ummana kibarni natafi, wani irin zafi nakeji a zuciyata, matukar bnsamu amsar abinda nake zargiba"
Umma takara kallonsa da mamaki tace "dakin ameelah zakaje"
Hilal ya girgixawa umma kai,
Umma tace " to shikenan bari na rika kah muje "
Kama hilal tayi suka fita, hajna tana biye dasu a baya, tausayin hilal takeji matuka a zuciyarta, wace macci ce zata sami irin wannan mijin mai tausayi da nutsuwa amma tabari ya kubuce mata, gaskiya ameelah tacika maciyiya amana, duk a zuci hajna take wannan zancen, jita keyi kamar tatonawa ameelah asiri,
Bbhilal yayan tane taya zata rika bari ana cutar sa, cen kuma wata zuciyar tace itamafa halira sai an tambayeta akan taki fadan gaskiya,
Duk jikin hajna yayi sanyi a lokaci data tuna da wannan zancen lahirar,
Umma ce ta katse mata tunani dacewa "budemun kofar nan" a lokacin da suka kawo bakin kofar shiga dakin da ameelah take ciki,
Hajna tasa hannu ta bude kofar dakin,
Umma na rike da hilal suka karasa cikin dakin,
Yana shiga dakin momyn ameelah datake zaune a gefe tana kuka ta mike tsaye cike da hargowa tace "meya faru da 'ya ta, wa yake wunkurin kashemun ita, hilal kafadamun" takarasa magnar tana kuka,
Hilal yasaukar da murya yace "wlh nima momy bansaniba,"
Momy ta kallesa da mamaki tace "wannan kalmar taka ta bansani ta isheni hakan, a karo na farko, lokacin data fadi cikin dare, haka muka tambayeka meya faru da ita, amma saika furta mana wannan mummunar kalmar taka ta bansaniba, yanzuma haka zaka ce mana", kuka yahana momy karasa maganar,
abban ameelah yana gefe duk ya dau zafi jiyakeyi kamar yakai wa momy duka,
Momy tana shanshekar kuka tadago kai ta kalli hilal tace " wlh zuciyata tafara zarginka akan kaine kake yunkurin kashemun 'ya, meta maka mekake nema gareta" takarsa magan da kuka,
Abba yayi sauri karasawa wurinta yace "wannan wace irin magana ce, da wanne zaiji ciwon matarsa ko masifarki"
Cike da hargowa momy tace "nafada kuma nakara fada ina zarginsa, ta nunawa abba dan yatsa kafin taci gaba dacewa " daman nalura dacewa kaima bakason yarinyar nan, tin kafin tayi aure, meyasa" kuka yakara kubuce mata tasa hannun da toshe bakinta,
Abba yaja nunfashi yace "lallai yau kin tabbatar da cewa ke butuluce, kuma wlh yau kin tabbatar da cewa haukarki maras girma mamawace "
Hilal yafita daga jikin ummansa da tangadi yakaraso gurin momy ya sunkuyar da kansa yace " momy wlh banada abinda nake nema a gurin ameelah, kuma ni meye ribata idan nakashe ameelah"
Hajna tana gefe tana kuka ganin yadda hilal ke kuka tayi saurin karbe maganar dacewa " yaya hilal bakaine kake yunkurin kashe ameelah ba
Ameelah ce take yunkurin kasheka"......
Waiii !!! 😞 kuyi hkr hannuna zafi,
Muje zuwa😛
Na:-❤Rabi 'atu sk mash Da Mr, Smiles😃
[10:43PM, 5/13/2016] Mr, Smiles😃: 💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅79 and 80🔅
Via OHW📱📚
Ameelah ce take yunkurin kasheka,
Duban kowa a dakin yadawo kan hajna,
Momy tayi saurin dago kanta tace " karki shigo cikin maganar mu keme kika sani"
Hajna tashare hawayen tayi taku takaraso kusa da momy tace " ai kuwa ninasan komai, domin kuwa ni yarki take gayawa komai kuma a yanzu zantona mata asiri, nagaji da ganin yadda take cutar dan uwana, zumuncin dake tsakanina da hilal yafi wadda yake, tsakanina da ameelah..,
Hilal yada mata hannu yace "kar inji kinfadi komai anan "
jinkalaman hilal yasa hajna tasaka kuka tana cewa " yaya hilal saidai kayi hkr amma wlh saina fada domin nagaji da daganin yadda ameelah takecin AMANAR AUREN ka, ameelah tana chart da samari a wayarta, tun kafin tayi aure, kuma datayi aure saita kasa dainawa, hatta ranar da aka kai ameelah dakinta har A ranar saida ameelah tayi chart har kusan karfe biyun dare, ta charting Suka hadu da wannan mutumen, wadda tayi save din Number shi da hmm, soyayya sukeyi, kuma ta nunan masa cewa ita ba matar aure bace, shikuwa saurayin yayi matukar kamuwa da sonta,
Wata rana naje gidan ameelah a ranar tasanar dani cewa
Mutum da take tare dashi a chart yanada hadari sosai.
Hajna Tajuya gefen da hilal yake wadda tun alokacin data fara magana ya gazgata ta,
Suka hadu edo ita da hilal taci gaba da cewa "ya hilal idan bazaka mantaba kwana ukku da suka wuce naje gidanka, to aranar ne ameelah tasanar dani komai akan saurayin, domin kuwa shi saurayin yasanar da ita cewa shifa baa yaudararsa kuma duk maccen data yaudaresa to hukuncin kisane akanta,
Aranar nabawa ameelah shawar wari dadama akan tadaina chart da maza, amma taki ji daga karshema cemun tayi, tayi wani sabon saurayi hadande wai ko sunansa AFHAM kuma dan abuja ne..
Hilal ya zare ido😳 yana kallon hajna, bakinsa na rawa yace Afham"
Momyn ameelah kuka take sosai tace "wallahi karya take, ameelah bazata iya yin wannan abunba, kazafine take mata"
Zuciyar hilal tadau zafi da karfi yadakawa momy tsawa "ya isah haka,"
Saida momy ta zabura, ganin yanayin edanunsa sunyi ja yasa takame bakinta, jikinta yadau rawa ta tazana sosai, har mamaki tarika yi a zuci "ayya kuwa wannan hilal ne, ba aljannu suka shiga jikin saba
Hawaye tab a edon hilal umma ma haka, hajna tana tsaye, tana kallon hilal habar bakinsan har wani rawa take,
Da karfi hilal yaja jikinsa, yafita waje, umma na kiran sunan sa amma yaji tsayawa,
Dataga baidawo ba, tabi bayansa ita da hajna da abban ameelah,
Dakin da Afham yake ciki ya nufa harya karasa bakin kofa, wasu likitoce da suke tsaye a bakin kofar suka hanashi shiga,
Tsawa ya daka musu saida dayan yafadi, bashiri suka bashi wuri kofar yabude ya shiga dakin...
Na:- ❤Rabi'atu sk mash Da Mr, Smiles😃
[12:23PM, 5/17/2016] Mr, Smiles😃: [12:00PM, 5/16/2016]
💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅81 and 82🔅
Via OHW📱📚
Afham yana kwance an kammala masa aiki, edonsa a bude yana kallon kafarsa, kamar zaiyi kuka,
Hilal yashigo dakin, ya isa gurinsa ya shaki wuyansa,
A daidai lokacin su umma da hajna da abban ameelah suka karaso cikin dakin, .
Afham sai kaki yake, hilal kuwa ko a jikinsa, matse wuyan yayi sosai, umma tana kuka takarasa gurinsa tana kokarin firgar hannunsa daga yuwan afham amma tagagara fitarwa,
Abban ameelah yayi saurin karasa gurin ya firge hannun hilal da sauri yasaki wuyan afham, edon afham sun fito sosai, abban ameelah yadaka hilal tsawa "meke damun kane hilal, yazakazo kasami marar lafiya kashakar masa wuya"
Hilal yana kuka yadafe kai wani irin bakin ciki yakeji da baa barshi yayi abinda yasoba,
Cikin kuka yadago kansa yace "abba shine fa "
Cike da mamaki abba yace " shine wah?"
"Shine afham wadda yake soyayyah da ameelah" hilal yafada yana kuka
Afham yana kwance yana matsar wuyansa dake masa ciwo yaji ankira ameelah, da karfi yasaki wuyan yana cewa "eh nine dan Allah ina ameelah nah, wlh danta kawai nazo garin nan, dan Allah kutaimakamun kununamin inda take" yakarasa maganar yana hawayen, zafin son Ameelah yakeji har cikin zuciyarsa,
Gaban abban Ameelah yafadi, sai yanzu ya gazgata maganar hajna " tabbas ameelah tana soyayya da wasu mazan a chart, wannan wace irin masiface take kokarin kunnu kai acikin wannan zamanin namu" duk a zuci abba yake wannan zance,
Hilal yana gefe sai kuka yake, tambayar zuciyarsa yake wane irin hukunci yakama yayanke akan ameelah,
Umma na hawaye takarasa gurin hilal tarikashi, duk zukatansu sundau zafi,
Afham yacika da mamaki, ganin kowa yana hawaye, duk ya firgita, muryarsa na rawa yace " dan Allah ina Ameelah, kodai ta mutu ne,
Hajna tayi karfin hali tana kuka tace " da ace mutuwa tayi da zai fi mata sauke fiye da wannan rayuwar datake ciki"
.
A daidai lokacin hawaye suka gangaro a kan fuskar afham yace "meya faru da ita..."
Cike da hargowa hajna taci gaba da masa magana " ameelah matar aurece, ameelah akwai hijabin aure akanta, ameelah taci AMANAR AURE, kayi gaggawar zuwa kayi istigifari tun kafin Allah ya sauko da masifarsa akanku"
Tunda hajna tafara magana afham yagaga tsayar da kukansa, kuka yajeyi sosai..
Na:-♥Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
[12:09PM, 5/16/2016]
💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅82 and 83🔅
Via OHW📱📚
Afham yana kuka yace "yanzu ameelah matar aurece amma tabarni na fara sonta"
Umma tana kuka tayi saurin katsesa dacewa " tabbas matar aurece, kaga wannan shine mijinta, ta nuna hilal"
Afham yakara fashewa da kuka, nadama ta bayyana a fuskarsa karara yana cewa " kaicona, dana kasa fahimtar iyayena, mesukamun amma nakasa bin umarninsu", jikinsa yafara ja yayi yana yunkurin tashi,
A daidai lokacin likitansa yashigo dakin, yayi sauri zuwa gurin afham ya zaunar dashi yana cewa " ina kuma zakaje, ai kafar taka bata isah takawaba"
Afham ya janye hannunsa daga rikon likitan yace " kabarni naje gurinsa yakarasa kasheni, wlh banga amfanin rayuwata ba" yana nuna hilal da dan yatsa yana kuka,
likitan ya kalli hilal cike da mamaki yana cewa "to ai wannan shine ya kadeka, kuma shiya kawoka asibitin nan a lokacin daya kawoka bakamasan inda kakeba, kakoga da ace yaso kasheka da tuni ya kasheka"
Wani irin kuka mai kara ya kubucewa afham, tabbas yasan wannan ba komai bane face iftila i, ko ince kaddara, yayi nadama sosai akan abinda ya aikatawa iyayensa,
Abban ameelah yagagara yin kuka edonsa suncika da kwallah, da sauri yafita yakoma dakin da ameelah take,
Afham yayi nadama sosai, yaso abarshi yaje gida amma likitan sa yahanashi, tare dacemasa sai yayi kwana ukku kafin yatafi,
Umma taja hilal sukabar dakin da afham yake suka dawo dakin da ameelah take,
ran umma yabace sosai dashigowar su dakin da ameelah take tafara masifa " wlh ameelah kin wahalar da hilal, kin hanashi samun natsuwa a gidan sa, takara daga murya tana cewa "Daman Allah baya hukunta Azzalumi da laifi mai sauki sai wadda yasan baxai iya dauka bah, ta juya gefen hilal, a lokacin yadaina kuka amma zuciyarsa cike da kuna, umma tace " karka kuskura kakara barin ameelah takoma Gidan ka tun kafin ta farfado ka saketah"
Hilal yadago kansa da sauri yace " a a ummana ai baa yanke hukunci cikin bacin rai kibarta tafarka, inason nasan meyasa taci amanata"
umma tayi saurin cewa " wani irin kanaso kasani ai kasani kawai bata sonka ne"
Hilal yamike tsaye yanaji ajikinsa bazai iya sakin ameelah ba, har yanzu yana sonta, "ummana kiyi hkr tafarfado duk wani hukunci daya dace a yanke sai a aiwatar"
Jin kalamansa yasa ran umma yakabace tsaki kawai taja, sannan tajuya takamo hannun hajna sukar dakin, hilal yanata kiran sunanta amma taki saurarensa,
Suna fita daga asibin suka tare napep suka koma gida..
Na:-♥Rabi'atu sk mash da Mr, Smiles😃
[7:16PM, 5/23/2016] Mr, Smiles😃: [6:43PM, 5/18/2016] Mr, Smiles😃: [9:07AM, 5/18/2016]
💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅84 and 85🔅
Via OHW📱📚
Koda hilal yafito daga asibitin su umma sunbar gurin, motarsa yashiga jinine kaca kaca, amma ahakan yashigeta yanufi gidan umma,
Koda yakarasa gidan yashiga umma da hajna suna zaune a falo, rankowa a bace yashigo falon yayi sallama, umma ta kyalesa hajna ta amsa,
Kujera mai dubin tasu yazauna yana fuskarta su ya saukar da murya yace " ummana kiyi hkr, nikaina bazan iya zama da ameelah ba amma inasone idan natashi hukuntata akan abinda tamun namata horo mai tsanani, yadanyi jim kafin yacigaba dacewa " sannan kuma cin fuskar zaiyi yawa ace agaban iyayenta zan saketa, dan Allah umma kiyi hkr"
Yana gama maganar yayi shiru,
Umna tayi shiru nakusan minti biyu kafin tajuyo gurin sa tace "shikenan naji zanbarka kazauna da ameelah amma da sharadi,
Umma tayi shiru tana kallon hilal,
Hilal yace "ummana wanne sharadi"
Umma tacigaba dacewa "sharadi na shine, inaso kakara aure, kuma bakowa nakeson ka auraba face kanwarka HAJNA, daman tun farko ita naso ka aura amma kabijiremun kaje ka aure ameeelah"
hajna datake gefen umma kunya tacikata dasauri tatashi da gudu ta wuce daki,
Hilal yace "umma hajna fa kikace, kifa tuna asanadiyarta na hadu da ameelah, kawarfa ameelah ce"
Umma tace "toh kuma aurenta haramun ne eh, ko shikenam dan tana kawarta babu aure a tsakaninku kenan, to bari kaji wannan umarni nake baka ba shawara ba dan haka tashi katafi kuma auren nan banaso ya wuce nan da sati daya,
Hilal yayi matukar girgiza shifa baitaba jin son hajna zuciyarsa ba, taya zai zauna da ita, amma bai musawa umma ba yatashi yatafi,
Hajna tana komawa dakin tadaka tsalle,
Tadanyi ihu kadan yadda umma bazata jiba, cike da jin dadi take magana tana dariya "Allah na godema daka cikamun burina, ashe mafar kina zai zamo gaske" takara daka tsalle, ta fada kan gado, wakar Adamu hassan nagudu tashiga rai raiwa inda yake cewa "Farin ciki yasameni tunda kace kayarda dani, shaukin bege yakamani acikin mata kanai dani, nazama tauraruwa acikin mata nice adon gari" ta kara tallatsa ihu, akan murna harda su hawaye, tana cikin murna kuma saita tuna da ameelah, ta murtuke fuska sai kuma tayi murmushi tace "kawata ameelah, kishiyata ameelah, hmm yanzu za a fara wasar"...
Na:-♥Rabi'atu sk mash Da Mr, Smiles😃
[9:16AM, 5/18/2016]
💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅86 and 87🔅
Via OHW📱📚
BAYAN KWANA BIYU
Ameelah ta farka, momynta tasanar da ita komai akan hukuncin da hilal yayanke, nacewa yanason yasan dalilin dayasa take cutarsa, ba wani kuka tayiba domin ita gani take bazata taba rasa hilal ba,
**** *****
Acen kuwa gidan su afham, kusan kullum sai aneesah ta nemi wayarta amma ta gagara ganinta,
Yauma tashigo dakinta tana kara dundubawa guraren dabata duba ba, cen sai tatuna da kasan gado, wadda tun ranar data fara neman wayar bata taba tunanin taduba kasan gadoba,
Bakin gadon taje tadauke katifar datake kan gadon, tana daukewa kuwa saiga wayar, cike da jin dadi tasa hannu tadauko,
Har a lokacin wayar tanada chaji, sakon da hilal yaturo taci karo dashi, tafara karantawa, tashin hankali karara ya bayyana a fuskarta,
Dasauri tafita taje tanuna momy, momy tana gani tanufi dakin abba, bayan takai masa ya karanta, cike da bacin rai yace "ba inda zamuje"
Momy tafashe da kuka tana cewa "haba alhaji ni wlh narasa gane wace irin zuciyace dakai, gabaki daya bakada tausayi, yanzu a aiko sakon yaronka yasamu hatsari amma saikace baza ajeba, toni zanje, kabani izini natafi," hawaye tap a idonta takarasa maganar,
"Ni ban baki izinin fitaba koda daga nan xuwa bakin zauren gidan nanne idan kuwa kika fita bada izinina, shikenan kuma kinsan zunubin fitar macce batare da izinin mijintaba" abba yafada yana karasa maganar yafita yabar dakin,
A hankali momy ta sulale tafadi kasan cafet tana kuka, zuciyarta cike da tunanin yaron ta afham,
Tajima tana kuka kafin tatashi tashare hawayenta, takoma dakin aneesah,.itama kuka tasameta tanayi,
Momy takarasa gurinta tace "kishirya gobe muje gombe, wurin afham" takara tambayar aneesah cewa" an rubutu sunan asibitin dayake a cikin text din,
Aneesah tace "eh anturo"
Momy tamike tsaye tace " toshikenan gobe kishirya mutafi" tohm kawai aneesah tace, momy tafita tabar dakin, ...
Na:-♥Rabi'atu sk mash Da Mr, Smiles😃
[5/18, 1:32 PM] 💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅88 and 89🔅
Via OHW📱📚
Acen kuwa bangaren Afham har kwana biyun nan suka cika kullum a matse yake yanaso yakoma gida domin yanemi gafarar iyayensa,
Tun cikin dare yakarbo takardarsa ta sallama, duk da likitansa baiso hakan bah, amma ganin ya matsu yasa yabashi, a cikin daren likitin yatai maka masa yakaisa har hotel dinda yasauka suka kwaso kayansa, sannan ya hadashi da wani driver, motar afham yajayo suka hau hanyar abuja, cikin daren,
Koda gari yawaye su afham sun isah abuja, sai cikin harabar gidan su driver yaja parking,
Yafito yazo yataimakawa afhan yafito, suka nufi cikin gidan,
A bakin kofar shiga yaci karo da abbansa zai fitowa wani irin wawan kallon yamasa, ya murtuke fuska, ya tare gaban afham "ina zakaje"
Hilal ya sunkuye kansa kasa kai tsaye hawaye suka gaggaro kan kuma tunsa"
Yabude bakin zaiyi magana sai kuma, yafasa,
Abban yaci gaba dacewa "karka shigarmun gida kajecen, kazabi wasu iyayen domin ni baka daukeni da daraja ba" nan fa abba yaci gaba da masifa yana hargowa,
Momy da aneesah suna cikin dakin momy suna hada kayan tafiya sukaji hargowar abba a waje, shi suke jira yafita saisu wuce gombe,
Momy tafito da sauri aneesah tabiyo bayan ta,
A daidai lokacin da suka karaso gurin a lokacin abba ya ture afham,
Afham ya tangada yafadi kasa, ai kuwa nan yasaka kara,
Momy tayi saurin karasawa gurinsa, a lokacin yadafe kafarsa yana kuka, momy hawaye take tana taba jikin afham taji duk ya rame ya chanza,
jini sukaga yafara fita a kafar afham, momy ta firgita sosai, dasauri ta koma cikin gida tadauko mayafinta, gurin fitowa saida ta bangeji abba,
Amma bata kulashiba,
diver daya kawo afham tace yatai maka mata, susakashi a mota akwai asibitin guragu anan kusa dasu suje sukaisa a duba kafar,
Nan suka saka afham a mota sukafitar sukabar gidan,
Abba yayi tsaye, duk yaji yanayinsa ba dadi, aneesah tana kusa dashi sai rusa masa ihu take tana kuka,
Sai kuma yafara jin tausayin afham, meye ribar zafin zuciya, babu abinda yake haifarwa face nadama da danasani,
Bashiru yafara jin saukar hawaye a kan fuskarsa, a lokacin ya juyo ya kalli aneesah yace "tashi kishiga ciki kidauko mayafinki mutafi musamesu"
Da gudu aneesah tashiga gida tadauko mayafinta koda tazo harya tada motar nan suka wuce asibinn...
Na:-♥Rabi'atu sk mash Da Mr, Smiles😃
[8:54PM, 5/20/2016] Mr, Smiles😃: 💠💠Amanar aure💠💠
💠💠💠💠
🔅 90 🔅
Via OHW📱📚
Koda su abba suka karaso asibitin har likitoci sun karbesa sunshiga bashi taimakon gaggawa,
Momy tana zaune su abba suka shigo, tana ganinsa ta mike tsaye cike da masifa tafara magana " meya kawoka, katafi kabarni dashi nizan iya kula da yarona, bazan bar ruywarsa ta lalace ba" abba ya karaso gurinta jikinsa a sanyaye, ya Bude baki zaiyi kenan likita yafito, momy tabar gurin abba tayi saurin karasawa gurin likita,
Likitan yace "hajiya saidai kuyi hkr, gaskiya daurin da aka masa a kafa yakara kwancewa, saboda haka sai aikin yadawo sabo, dan haka ba aikin gaggawa bane, a kalla zakuyi koda kwana biyarne a nan kafin mubarku kutafi dashi"
Momy tashare hawaye ta tace "likita ba matsala koda wata dayane zanyi idai har dana zai samu lafiya"
Likita yace "insha Allah zai samu lafiya, yanzu bara naje nadauko kayan aiki saimu fara" yana gama fada yawuce,
Abba yana gefe yakaraso gurin momy, momy ta dalla masa harara, abba ya soke kansa yanzu harwani kunyar momy yake, a hankali yadago kansa yace "komai yafaru kaddarace sannan kuma ..."
Momy ta daga masa hannu " banason naji komai daga bakinka yanxu, kajira sai yarona yasamu lafiya" abba yayi shiru,
Nan suka same guri suka zauna,
A ranar asibiti suka kwana, abba yayita tarairayarsu duk abinda sukeso shiyakeyi, yayi nadama sosai, ita kuwa momy tadaure masa fuska, gani take duk abinda yafaru da afham laifin abba ne,
Haka dai suka zauna asibiti suna jinyar afham,
**** ******
Ameelah kuwa tasamu sauki, aka sallameta su momy suka daukota aka dawo gida,
Basuda labarin komai akan hilal, ita dai momy tayi imani dazaizo yadauki matarsa sukoma gidan aurensu, ameelah ma haka domin tasan hilal bazai iya rabuwa da ita ba,
Abban ameelah kuwa tun suna asibiti yadaina yiwa momy da ameelah magana wani irin haushinsu yakeji,
Lokacin da suka koma gida lokacin yahada kayansa yabar kasar, saidai yabarsu komai na abinci da kuma kudin kashi,
shidai kawai bayason ganinsu yanzu,
******
Shirye2 kayan auren hilal da hajna kawai umma take,
Hilal ma haka, en kwana biyun nan dayake zuwa gurin hajna zance sai yaji duk yafara sonta,
Wani sabon gida hilal yakama, acen zai tare shida amaryarsa hajna
********
Yaune aka daura auren hajna da hilil (H + H) dangin momy ancika gida kowa yazo sai murna ake,
Magriba nayi aka dauki amarya hajna aka kai gidan angonta hilal,
*******
Ameelah tana kan sallaya tagama sallar magariba, tajiyi sallama a falo dasauri tayi adua tafito,
Amrah ce kawarta fuskarta a murtuke, ameelah tace "ah ah manya masu gari, lafiya naga kinwani murtuke fuska haka"
Amrah taja tsaki, cike da mamaki tana kallon ameelah tace "yanzu ke mijinki zai kara aure shine baki gayamunba, lallai.."
Mummunan faduwar gaba yaziyarci zuciyar ameelah, dasairi ta katsewa amrah magana dacewa " auren kuma, hilal dinne yayi aure, kodai wasa kikemun"
Amrah ta yatsine fuska tace "kamarya wasa, bari kigani, hannu amrah tasaka a jakarta tadauko invitation card ta jefawa ameelah, sannan taci gaba dacewa "kadauki wannan kiduba, wlh hilal yakara aure kuma kawarmu HAJNA ya aura"
Ameelah taja baya tasaka wata irin ihu, a hankali take fadan "innalillahi wa innan ilaihin raju un " dakyar tasamu tayi controlling din kanta,
A hankali ta zura hannu tadauki invitation card din tana karantawa ,
Tashin hankali karara ya bayyana a fuskarta, gumi yakaryo mata, harwani jiri yafara dibanta, tasa hannunta na nadama ta dafe goshinta,
Tajima a hakan sai cen kuma Ta dago kai ta kalli amrah a alokacin har kuka yasoma zomata...
TAMMAT BISSALAM
AMANAR AURE
Episode 1⃣
Anan zamu tsayar da labarin AMANAR AURE kashi na daya, banso ace mun tsayar da labarin nan anan ba naso ace munkai karshensa kafin mushiga AMANAR AURE
Episode 2⃣
Amma saka makon tarbon watan da zamu shiga wato wata mai albarka watan RAMADAN yasa muka tsayar da Labarin sai zuwa bayan sallah,
Makaranta labarin AMANAR AURE zamo kawo muku karshen wannan labarin na AMANAR AURE
Episode 1⃣
Acikin wani Labari mai suna AMEELAH wadda shine cigaban AMANAR AURE
Episode 1⃣
Kadan daga cikin labarin AMEELAH
🙆🏻AMEELAH🙆🏻
Wallahi, wallahi bazan barsu suji dadin auren nanba, saina nuna musu cewa, ni ba a cin amanata, kuma wlh saina nunawa hajna cewa tayi kuskuren auren mijina, kamar mahaukaciya taci gaba da sabbatu,
Tajuya gefe da gefe tana kallon falon, sai kuma ta tsayar da idonta akan kofar kichin, da gudu tashiga kichin din, tadan jima a ciki saicen tafito da wata sharbebiyar wuka, tana huci,
Tanufi hanyar fita, amrah datake gefe tana kallonta tace "ina kuma zakije"
Ameelah tajuyo edonta yayi ja sosai tace "zanje nasamesu wlh koni ko itah, SAI NAYI AJALINTA"
Kubiyomu domin jin yadda wannan labarin zai kasance AKWAI WATA RIGIMA
Love yhu oll masoyan labarin AMANAR AURE
Daga marubuta biyu wato ♥RABI'ATU SK MASH DA (ABDUL JEGA) MR, SIMILES😃
Next novel:-
🙆🏻AMEELAH🙆🏻
💝HAR A ZUCIYA💝
Love yhu oll Fans😘😍
adsense 2 here