Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, March 22, 2017

BABBAN KUSKURE

adsense here BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Bismillahi rahmanu raheem, dukkan godiya, da yabo, tsarki da mulki sun tabbata ga Ubangijin sammai da kassai. Na fara rubuta wannan littafin cikin iko Allah, ya Allah ka bani ikon isar da sak’o mai amfani aciki, san nan ka sanya, mutane zasu, nishad’an tu dashi, ta hanya mai kyau ameen. Pg-1~5 Wani kyakyawan Matashi, mai jini ajika, sanye yake cikin, kakin sa na Police, kalan blue da bak’in wando. Kayan sunyi matuk’ar amsan jikinsa, tamkar dashi aka tsara kayan, ko da na kali wannan guy d’in. Dogon ne fari sol, yana da faffad’an k’irji, sannan ga shi da dogon hanci tamkar pencil, yana da k’aramin baki, ga kuma wasu sexy eyes, d’insa da suka rikitani, shekarunsa bazai wuce 37 ba. A hankali yake tafiya, falo ya nufo, dai-dai nan, naji muryan mata tana kiran Indo! Indo! Indo!. Wacce a ke kira da indo ta fito da sauri, sam bata lura da Yallab’oi ba, tana yankowa sai jin, garam sunyi karo, take jikinta ya d’au rawa ta fara dan Allah kayi… Bata k’arasa ba yasakar mata, wani lafiyayan mari a fiska. Da gudu tayi ciki don tana matuk’ar tsoron Haiydar. Shi ko gogan kar-kad’e inda ta tab’a ya fara, cikin zuciyarshi kuwa, cewa yake”mtss na tsane ki bana son ganinki, don ba yanda na iya ne. Indo tana shiga, sai da ta share hawayenta,ta k’arasa cikin d’akin, taje ta rusuna agaban wata mata, wanda da’alama itace matar gidan, cikin sanyi muryanta mai dad’in sairaro tace”gani Hajiya”. Wacce aka kira da Hajiya sai wani yatsina take, tace”ga hulan Haiydar nan ki kaimasa, ya fita ni bazan iya tashi ba, cikin tsoro Indo ta bud’i baki tace”Aunty wal…. “Kee yi min shiru umurni na baki, tashi ki kai masa, kina yar aiki, har zanyi magana kema kiyi. Jikin Indo ba k’wari ta k’arba ta fito falo, dai-dai koma ciki ya d’auko hulan, wani kalo ya watsa mata, take yan hanjin cikinta suka soma rawa, sam bata son had’uwar su, da Haiydar, don ya matuk’ar tsanata, sam baya son ganinta, Indo kuwa ta mak’ure ajikin garu kamar munafuka, duk tayi kalan tausayi. cikin fushi yayi kanta. DEDICATED TO AISHA MUH’D (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/26/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-6~10. Cikin fushi Haiydar yayi kanta, hularsa ya fin cike tare da tofa mata yawu, ya wuce abunsa, cikin zuciyarsa na masa suya, “mtss ace wai matar ka ta sunna, batasan kula da hakkin miji ba. “Bata damu da duk wani abun da nake bukata ba, wai sai yar aiki. “Yar aikin ma wanda bata min ba, sam na tsani ganinta mtss. Yayi tsaki, dai-dai lokacin ya shiga motar sa, mai gadi da sauri ya bud’e masa yafita. Tafe yake cikin nutsuwa har ya isa area Commander, yana shigowa aka fara sara masa, da han zari ya nufi office d’insa dake sama. Yana shiga na biyo sa, nima da sauri don na fara aikina, d’an madai- daicin office ne, d’auke yake da tebur sai kujeran zama, gefe ga k’araman fridge, da nesa na hango yar k’aramar TV bango da ke mak’ale, office d’in yayi dai- dai misali. File d’in da ke kan tebur ya duba, nan ya fara yan rubuce-rubuce, nan ya d’aga waya yace”hello Sargent Nasir, kazo ina nemanka a office d’ina yanzu. Wayar ya ajiye ya cigaba da rubutu, ba’a d’au lokaciba wani d’an matashi, ya turo qofar office d’in, yana shigowa ya kame kamar katako tare da buga k’afansa a kasa, hannusa ya sanya shi a gefen damansa tare da waresu. Cikin girmamawa yace” Morning sir”. Naji an kira da sir, bai s’ago kansa ba, yana rubutunsa yace” Morning how is your work?. Sergent Nasir yace”fine too. Haiday ya ci gaba da cewa” na duba file d’in case din mutanen nan, kun kaisu CID ne?. “Eh Sir tun jiya ma aka kaisu. “Ok daman abun da nake son ji kena. “Zaka ita tafiya. Sergent Nasir ya sake sara masa tukunan ya juya ya tafi. Haiydar ko aikin da ke gabansa yayi, bai fito ba sai lokacin Sallah, k’arfe uku da rabi na yamma, ya kamala duk aikin da zaiyi ya fito ya shiga motarsa ya nufo gida. Tun a hanya da yayi tunanin abunda zaije ya tarar tsaki ya farayi, duk sai yaji baya son komawa gidan. DEDICATED TO AISHA MUH’D (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/26/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-11~15. Indo ko tun lokacin da Haiydar ya tofa mata miyau, da gudu tashiga d’akinta, kan gado ta fad’a tasoma rusa kuka kamar ranta zai fita, a fili take cewa”wannan wani irin rayuwa ne?. “Mai na tsare masa ya tsaneni?. “Ina da iyayena suna nan nasan duk rashinsu ba ran zauna cikin wanna k’uncin ba. “Wayyo Ummi na! Allah ya jikanki, tabbas nayi rashi. “Ina zansan inda dangina suke na nemesu, nasan su bazasu tsaneni ba. A hankali ta tashi ta d’auko wasu fotuna, da wani awarwaro masu kyau, sai d’aukar ido sukeyi, rungumesu tayi tana kuka mai tsuma zuciya, a haka har baci ya d’auketa. Kamar ama mafarki takejin ana kiran sunanta, firgigit tanfarka, aiko taji an sake kiranta, da sauri ta mike ta b’oye war-waronta da hotunanta, ta fito cikin hanzari. Cikin isa Falmi tace”kee mai kikeyi da baki min aiki na ba?. “Kin san Darling d’ina ya kusa dawowa. “Ke harkina da wani saken da zakiyi bacci a gidan nan?. “Ko kin manta matsayinki na baiwa ne?. “Mtss na baki nan da 30 minutes ki gyara gidan nan, kuna in kin gama kije ki gyara ma only d’akinsa. “Zakiga kayan daya ciresu ki wanke su tass, kuma karkisasu a engine kinsan bai cika son wankin…. Sallamansu Xahra da Meesha luv ne yahanata k’arasa magana. “Oyoyo sis kune haka?. Cikin sakin fuska sukace”eh mune da mayya. Falmi tace”ni fushi nake daku ma rabon ku da gidan nan yau kunsan wata 2 fa. Meesha tace”kawas tuba muke amana hak’uri. “Sadeey tace” kyaleta kamar ita ta a zuwa mana a kai-akai. Falmi tace”kudai ku k’araso tukun sannuku da zuwa. Juyaa tayi ta kali Indo tace”keee mai kikeyi anan har yanzu baki mik’e kinyi aikin gaban ki ba?. “Ko sai na b’ata miki rai ne?. Sum-sum Indo ta wuce cikin gida. Xahrah BB tace”Falmi wacece wannan?. Cikin ko in kula Falmi tace”house girl d’ina ne. Meesha tace”kee baki da hankali zaki d’auko wannan zankad’ed’iyar budurwa, wanda duk na miji mai lafiya sai ya yaba da ita. Sadeey tace”tayani gani fa, amma kinyi gan-ganci. Falmi tace”kai banza haka zan barta, yanda nake da kishi ae ba zan so wani ya rab’i Haiydar d’ina ba. “Muna tare daku bari ku ga yanda zasu k’are in yadawo. “Kuma bana barinta tayi kwaliya. “Kai gasalima ya tsaneta tsana mai muni. Xahrah tace”kee baki san wani lokacin tsana yana dawo soyayya ba. Falmi tace”kee zan bar Haiydar hakane, san a haka ma baya son ganinta. DEDICATED TO AISHA MUH’D (MAMAN ABDUL-SHAKUR) RASH LUV [2:30PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [26/5/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-16~20. Shewa sukayi, hiransu ta yaushe gamo sukeyi. Indo ko kitchen tashiga, ta d’aura girki, tukun tayi side d’in Falmi, sai da ta gyara ko ina, sannan ta je bedroom d’in Haiydar ta gyara, ta d’ebo kayansa da sukayi datti, ta wankesu, tana duba abinci. K’arfe uku da ta gama komai, ta jera a dining. Falmi tace”ki kawo mana abincin mu falo”. Sai da da d’an rusuna tukun tace”to Aunty”. Taje ta zubu musu a cooler da plate takawo, Falmi cikin isa tace”kee wazai kawo miki ruwan ko ni zanje ba d’auko?. Indo ta rusuna tace”ayi hak’uri zanje na sauke abune akan wuta. “Mtss wuce ki d’auko kafin kiyi abunda zakiyi. Indo ta jera musu komai agun gar zata tashi Falmi tace”ni zanyi serving d’in ko sai na fad’a miki?. Indo ta tsuguna ta jera musu komai, tasaka ta mik’a musu, tukun ta mike ta nufi kitchen, don k’arasa sauran aikin da takeyi. Sadeey tace”Falmi baki da k’yau, gaskiya kina juya yarinyan nan. “Irin tsawan da kike mata ni har ta ban tausayi wallahi. Meesha tace”niko yarinya k’yau ta min gata black beauty. Falmi ta b’ata rai tace”mtss dad’ina da ke rashin ganewa, mai maza zasuyi da bak’ar mace. “Bakijin yanzu cewa suke su Fara ko da mayya ce, suna sonta. Xahrah tace”Falmi ae bazaki gane ba, sirrin k’yau yana tattare da bak’ar mace, don fara inda za’a kwashe farin ba komai zaki gani ba zai tsaban muni. “Amma magaanan gaskiya Indo ta had’u ba k’arya. “Sai dai rashin gyara da wayewa ne ya mata cikas. “Ki kali tsarin jikinta mana, irin shape d’in da maza keso ne. Take Falmi ta b’ata rai jin an kushe farare, don bak’aramin ji take da haskenta ba, gani take tafi kowace mace kyau. A haka har suka cinye abinci su, Indo ta fito ta tattara kwanuka ta kai kitchen, tana ajiyewa ta k’oma d’aki, ko zama batayi ba taji k’aran shigowar motar Haiydar. Sai da gabanta ya fad’i, addu’a tafara yi, sabida duk lokacin da suka had’u, bata kwashewa ta dad’i. Haiydar cikin takun isa ya shigo ckin gidan da Sallamansa, su Sadeey suka amsa, ganinsu yasa ya d’an saki fuska don yasan k’awayen Falmi ne sosai. Gaisawa suka kafin ya wuce d’akinsa, yana shiga wani sassayan, k’amshi ya bugi hancinsa. Ajiyar zuciyzuciya ya sauke, kayansa ya cire ya nufi toilet, yayi wanka ya fito, k’ananan kaya yasaka, sabida ga bak’i, da na shan iska zai saka. A hankali ya tako zuwa falo, Falmi tun da taga ya fito tasan in ba’a yi serving d’insa ba, zata sha surutu, cikin muryan isa ta fara kiran, Indo! Indo! Indo dake d’aki jiki sai b’ari yake ta fito da sauri, ta rusuna a gaban Falmi. DEDICATED TO AISHA MUH’D (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/26/2016] RashKardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-21~25. Notice Masu karatu, na cire Sadiya a k’awar Falmi, zan maidata k’awar Indo, sabida wani dalili, ku kasance da YAR’GIDAN JARAWA. Falmi tace”ke kwai bakinsan aikinki bane?. “Bakiga Haiydar ya dawo bane?. “Kije ki zuba masa abinci. Indo ta mik’e jikinta ba k’wari, sai bari yake, ta nufi dinning area, Haiydar ko tun da ya hango ta, yayi yar karamar tsaki, cikin zuciyarsa ko cea yake”wato falmin bata ji, nace mata bana son aikina tana saka wannan wariyan taki ji. “Dun taga ina qaunarta da yawa bana son abunda zai bata min rai. Indo tana zuwa dining ta fara serving d’insa, sai da ta zuba maza jelop d’in shinkafa yaji Salad, sai k’amshi yake tash, gaskiya Indo ba ya bace gurin girki, don ta taso cikin horon aiki, shiyasa bata samun matsala game da iya girki, gyaran guri. Wani lokacin in tayi decoration ta gyara ka d’auka, ba ita bace tayi, wasu daban akayi hayansu sukayi. Sai da ta zuba masa shinkafan ta tura masa gabansa, hannuta sai rawa yakeyi, a haka ta d’auko kofin glass ta zuba masa zob’o drink da tayi, ta d’auko zata ajiyea gabansa, hannuta sai b’ari yakeyi, bisa tsautsayi ya sub’uce ya fad’i aiko sai jikin, Haiydar, take rigansa tarine. Nan ganjin cikin Indo suka soma shooky, hawaye ta fara yi. Haiydar cikin b’acin rai yaga yanda ta b’ata masa jiki, ransa ya b’aci ya rasa mai zai mata, mikewa yayi har yazo zai tafi, sai ya fasa, d’auko juke d’in zobon yayi, ya shek’a mata a fuska. Ae ko sai cikin idonta take tafara mutsu-mutsu, tana niman hanyan saukowa, ganin abunda ya mata bai sheshi ba, sai da ya bari tana lalub’en hanya, ya saka k’afarsa ta fad’i timm! A k’asa, aiko ba shiri ta saki k’ara shiko ya mik’e abincin da bai ciba ya kima d’akinsa. Duk abunda ya faru a idon su Falmi, cikin jin dad’i tace”kun gani ko ita kanta yariyan tsoronsa take, bare shi uban gayya da baya son ganinta. Xahrah tace”to ki dai bi a hankali, don in wahala yayi wahala karta gudu. Falmi tace”ina zata je wa take dashi a Bauchi. “Ina ga ma la Uwarta cikinta tayi tazo ta haife ta. “Don tun zuwanta sai tana cemana ubanta Indo na raye, kulum maganan d’ayq kenan. Meesha tace”Xahra ya kamata mu wuce fa yamma tayi. Falmi tace”kai Messha wato ke kike zugawa ku tafi ko?. Duka sukace yau ai mun dad’e, mu zamu wuce sai gani na biyu. Falmi tarako su har gate kafin ta koma ciki. Haiydar ya fito zai wuce Falmi tace”darling bazaka ci abincin bane?. Ko kalonta baiyi ba yace”nagode fita zanyi. Ya na fita motarsa ya shiga bai zarce ko ina ba, sai k’aton katafaren gida, na alfarma, tun daga kan gate d’in, gidan abun kalo ne, horn yayi mai gadi ya bud’e masa, ya danna hancin motarsa, cikin gidan, gurin da’aka tanada don ajiye motoci, nan ya nufa, sai da ya ajiye motar ya fito. Gidan yana da girma sosai ko da na kali harabar gidan, zagaye yake da fulawas ja da yelo, sun matuk’ar k’awata gurin, a hankali yake takawa har yashiga cikin gidan, falo ya fara tararwa, ko da na kali falon, gaskiya ya tsaru komai na ciki Silver colour ne da baki, abun gwanin burgewa. Daga nesa na hango wata yarinya wacce bazata gaza 17yrs ba, tana danna waya, farace sol kamar Haiydar, kuma suna d’an kama amma shi yafita kyau sosai, da sallama ya k’arasa shiga ciki, Hasna ta mik’e tace” Yaya Haiydar sannu da zuwa. Cikin fara’a ya amsa mata, zama yayi a d’aya daga cikin kujerun dasuke falon. Yace”Hasna kawo min abinci naci”. Cikin tausaya ma Yayanta, mik’e wa tayi ta nufi kitchen, abinci ta kawo masa, sai da tayi serving d’insa, tukun koma gefe ta zauna. DEDICATED TO AISHA MUH’D ( MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/26/2016]RashKardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-26~30. Cikin zuciyarta ko tana tausaya ma yayanta, wanan wani irin aurene ace mutum sam bai isa da matarsa ba, ko yasata abu batayi, ga rashin kunya, ga kin jama’a, Hmm Allah ya kyauta. Sai da ya gama cin abinci, Hasna ta kale Yayanta tace” Yaya Ya Indo?. “Ina son yarinyan tana da hankali, ga kirki wallahi, Hajiya ma tana yawan tambayanta. Wani harara ya sakar mata, wanda yasata jan bakinta tayi shiru, a zuciyarta ko cewa take”wai me Indo tayi ma Yaya ya tsaneta, ko sunata bai son a kira, kuma ni tafin Falminsa sau dubu wallahi. “Mtss ina ma da itace matar yayan. Maganan Haiydar ne ya dawo da ita daga duniyar tunani, da ta luka. “Hasna ina Hajiya fa? “Tana d’akinta. Mik’ewa yayi ya haura sama. Haiydar na fita Falmi ko kafad’a ta d’aga, alar ko in kula ta d’aki ta koma, WhatsApp ta hau taci gaba da chatting da friends d’inta. TUSHEN LABARI Alhaji Hashim Marad’i, Haifafen d’an Niger ne, ya kasance mutum ne mai neman na kansa, Allah yana bud’a masa, a haka har ya auri matansa Firdausi, bayan aurensu da kwanki ya tattara, yan dukiyarsa ya baro gari, ya dawo Bauchi da zama, shago ya bud’e, cikin ikon Allah, kasuwansa ta bun k’asa, Allah ya sanya ma dukiyar Albarka, nan da nan ya shahara ta ko ina a garin Bauchi. Ana haka Matarsa ta samu cikin karkuso kuga kulawa da tattali, har cikinta ya kai wata tara, ana haka nakuda ya tashi, baiyi wata-wata ba sukaje Asibiti, nan aka karb’e su, sai d’akin haihuwa. Bata dad’e sodai ba ta sankato, yarta fara sol, Nurse suka gyarata, suka dawo gida, ranan suna Yarinya taci sunan Fatima, Alhaji Hashim ya d’au son duniya ya d’aura ma fatima, baya son abunda zai tab’ata, Firdausi ma duk d’ayane, kula ta musamman suke bata, har yarinya tayi wayo ta girma sosai. Fatima tana da shrkara biyar, tayi wayo ko ina tana zuwa har sun sata a makaranta. Wani safiya ranar asabar, anyi ruwa sosai wata mata tana d’auke da k’aramin ciki, tazo qofar gidan Alhaji Hashim ta zauna, sai b’ari takeyi, ana haka Alhaji ya fito, ko da ya ganta, sai yaji ta bashi tausayi sosai. Mai gadi ya kira yace”kaje ka shigo da ita, gida ya koma ya samu Hajiya Firdausi, yace”ga wata mata tana buk’atar tai mako, ki bata duk abunda ya dace. Tukun ya fita. Firdausi tasaka a ka shigo da matar sai yatdina take, ganin kayan jikinta yasa tace”ke biyo ni boys quater ta kaita, nan ta ce bara na kawo miki abinci. Cikin gida takoma ta d’ebo abinci ta kawo mata, nan matan taci sosai, tayi godiya ma Allah. Ko da Firdausi ta dawo, tace” ina zaki kuma daga ina kike?. “Matar tace”ni bakuwace banda kowa na fito garin Yola ne. Firdausi tana wani isa tana yatsina tace”ok kya iya zama anan kafin mai gidan ya dawo. Bata jira amsanta ba ta fita a d’akin, Alhaji Hashim bai dawo ba, sai yamma sai da yaci abinci, tukun yana hutawa, Firdausi tace”matar nan fa tana na. “Oh! Na manta mai ta sanar dake gameda ita, don naga kamar ba’a cikin nutsuwarta take ba. Firdausi ta mayar masa yanda matar ta fad’a mata. Yace”kira min ita. DEDICATED TO AISHA MUH’D (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:31PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-31~35. Firdausi ta kirata, suka taho tare, can gefe ta zauna, sai da ta gaidasu. Alhaji Hashim yace”baiwar Allah ya sunanki?. Matar nan tabashi amsa da”sunana Safinatu”. Alhaji Hashim yace”matana tamin bayani yanda kika fad’a mata. ” ko zan iya sanin mai ya kawoki Bauchi?. ” nan take matar ta fara kuka, tace”Ni sunana Safinatu, ni haifafiyar garin Yola ce. “Ina gaban k’anin mahaifina, na taso cikin kulawa, har na girma, duk ran laraba, ake cin kasuwar garin mu, kuma duk ranan laraba, na ke kai tallen nono, cikin garin mu na Girei, a haka har Allah, ya had’ani da Muhammadu, shikuma yana kawo shanu, duk ran kasuwa, yana da zama’a Rugan Ribad’o. Ko da muka dai-daita kamu, nan iyayena suka mana aure. mijin dana aura ya kasance yanada garken shanu sosai, hakan yasaka wasu ke jin haushinsa. Har suna masa gorin zuwa yayi, duk da shima bafulatanine, kwanaki suka tafi, kulum garken shanunsa sai hab’aka yakeyi, hakan yasa mak’iya suka fara kawo masa hari. Tundaga likacin ya fara sanar dani, duk da banjin dad’i, ina fama da laulayin ciki. Bayan wasu watani, lokacin cikina ya fito, dadadare muna kwance, wasu yan rugan mu suka zo donsu kashe, Muhammadu su kwashi dukiyarsa, ganin hakan ya d’ebi, kud’i yaban da wasu hotuna, tare da awarwaro, yace na rike wannan. Ya kad’a shanunsa muka d’au hanya muna tafiya, su Sale suka biyo mu, sunyi artabu da Muhammadu, da kyar Allah ya basu ikon kwad’a masa sanda’a kafad’a, ganin bazai iya kare kansaba, yace”Safinatu ki gudu ki tafi garin Gombe ki nimi yan’uwana, suna Gombe. Kafin yayi wani magana sun kwad’a masa sanda take jini yasoma zuba, a gun ya fad’i ko motsi bayayi. Ganin ina kuka Sale yace”ku kamata don zata iya tona mana asiri, jin haka nasa gudu. Haka har Allah ya taimakeni na fito bakin titi, saiga mai mota na shiga ya kaini, cikin gari nasamu motar Gombe ta tashi, sai na Bauchi, nan wasu sukace, idan ina sauri na shiga na Bauchi, haka nashiga motar Bauchi, ko da na iso yan kud’i na sun k’are, hakan yasa nayita yawon bara, gashi bansan ta inda zan fara niman dangin Muhammadu ba. Alhaji Hashim ya nisa, Yace”naji labarinki, kuma a yanzu niman mutum batare da wani Address ba, ba k’aramin tashin hankali bane. Awarwaro ba zai zama abun shaidan da har za’a gano suba. Firdausi tace”Alhaji mai zai hana tana mana aiki sai ana biyanta, tunda Lami tayi aure wancan Satin. Alhaji yace”haka za’ayi. Ya kali Safinatu yace”Safinatu sunanki ko?. Tace”masa eh! hakane. Yaci gaba da cewa”zaki iya yin mana aikatau, ana biyanki duk wata?. “Kuma zamu baki d’akin da zaki zauna har sai lokacin da kika buk’aci tafiya?. Cikin girmamawa tace”eh zan iya. Alhaji yace”Alhamdulilah! Firdausi zata gwada miki komai. “Sanna salary ki a wata dubu shabiyar. “Tace”nagode Allah ya ban ikon kiyaye komai. Haka tamik’e ta koma d’akin, tundaga wannan rana tadawo itace wankin kayan Fatima da wanke-wanke, ga shara, abunci sai da Firdausi ta koya mata. Duk wani abu ita takeyi. Ana haka har ta haihu, cikin ikon Allah a gida bataje Asibiti ba. Ranan suna yarunya taci Sunan Aisha, amma tana kiranta da Indo, haka rayuwansu ta kasance. DEDICATED TO AISHA MUHAMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RAS LUV 5/27/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-36~40. Aishatu Indo ta girma sosai,, gata da wayo, Indo tana d’ibi dani amma wasu abubuwanta na haifinta ne, hatta muryanta irin nasane, kwayar idonta, yatsun k’afarta duk nasane, bak’in fata na ta d’auko. Gata da gashi kamar me, ganin Indo tayi wayo ga Fatima tana zuwa makaranta, ko d’an abu ya had’asu, karara Fatima ke mata gori, Aisha tayita kuka. Hakan yasa na duba wani private school d’in da ke nesa da gidan mu nasata, 30k ne kud’in makarantan, amma duk term zan bada 10k hakan yasa na sakata a Sky criest, kulum da sassafe zan shiryata, na d’aukota a kafad’ana da kafa zan kaita. Ina dawo gida nayi aikina da wuri inje na d’aukota. Da kud’in aikina nake biya mata, dubu shabiyar, duk wata ake bani kud’in aiki. Kuma ba abinda nake da kud’in kasancewan su suke ciyar damu. Sai in Sallah yazo nayi mana kayan Sallah. Ahaka har Aisha tashiga Junior school, ina biyan mata, na sata a Islamiya, sam Aisha bata isa tayi k’awance da kowa ba Fatima wanda a tana Senior Secondary school, ta sata a gaba, yanzu Aisha itama tana tayani aiki, sosai mukeyi tare. Fatima tana SSS3, a Doll pine Maria, ta canza sunanta daga Fatima ta dawo Falmi, hatta Baban da Falmi yake kiranta, tana harka da kwaye wayayu, masu nutsuwan kenan Meesha da Xahra BB. Sune masu hankali. A haka ta kamala secondary school d’inta. Ko da result yafito sam baiyi kyau ba. Hakan yasa ta fara diploma, tana karanta estet management. Tana final semester, ranan ta fito a motarta, dai-dai Bauchi club, motarta ta tsaya. Ga dare ya farayi, tun daga nesa ta hango wani mota Range Rover baka, bakowa bane aciki face Aliyu Haiydar. Da kamar zai wuce ganin macece tana buk’atar taimako hakan yasa ya, ko da yazo da sallamansa ya mata, ta amsa. Yace”lafiya mai ya samu motarkin?. “Wlh ina tafiya naji k’aranta ya canza, kafin nayi wata-wata ta tsaya. Bud’e motar yayi, yayi nasa iyawar taki tashi, hakan yasa yace”in bazaki damuba in taimaka miki. Tace”ba matsala. Wayarsa ya kira mai masa gyara yazo ya d’au motarta, tare ma da bata address d’insa, abunda yasa bata damu ba, taga Haiydar cikin kayan Police, shiyasa tasan ba zai cutarta ba. Motar suka shiga ya kaita har qofar gidansu, zata fita tace”nagode da taimako gashi zamu rabu bamu san juna ba. Murmushi yay8 yace”Sunana Aliyu Khaleeb Baba, ama ana kirana da Haiydar wasu kuma sukan ce min AK Baba. Cikin yanga tace”wooow nice name!”. “Ni kuma sunana Fatima Hashim Marad’i, amma ana kirana da Falmi. Cikin fara’a yace”suna mai dadi. “Ku ya Niger ne?. Tace”masa eh zamane ya kawo mu Bauchi. Nan sukayi exchange d’in phone number, tamasa godiya tashiga gida. Kwanki sun tafi, yanzu Aisha tana Jss3 suna third term, ranan jumma’a ranar da Aisha bazata manta ba a rayuwanta, shine randa ta wayi gari mahaifiyarta ta rasu, ranan tayi kuka, ta dawo bata kowa bata da gata sai Allah. Bayan kwana bakwai Hajiya Firdausi tace”yanzu sai ki maye gurbi Uwarki da aikin da kike ko kuma kisan inda dare ya miki. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/27/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-41~45. Aisha Indo ba yanda ta iya, haka taci gaba da aiki a gidan, Hajiya da kanta ta rage mata Salary zuwa 7k, hakan yasa bazata iya d’aukan nauyin, karatunta ba ta hak’ura. Aliyi Khaleed Baba, tun randa yaga Falmi ya rasa nutsuwarsa, kasancewan ya ganta irin matar da yakeso, gata fara sol, don shi tsarinsa bai son bak’ar mace. Masu karatu zamuso sanin, WAYE ALIYU KHALEED BABA(AK BABA). Alhaji Khaleed Baba asalin d’an Bauchi ne shi, cikin k’aramar hukuman Sakuwa, dake garin Misau. Yata so cikin garun Bauchi yana aiki a kar-kashin Treasuring a yawon aikisa yaje garin Gombe suka had’u da Hajiya Khairat wanda take da zama a garin Gombe. A haka akayi auresu da Alhaji Khaleed ya d’aukota suka dawo cikin garin Bauchi, Suna da zama a State Low cost, bayan aurensu Allah ya azurta su da d’a Aliyu, sai da Aliyi ya girma sosai kusan shekara 12 kafin aka Haifi k’anwarsa Hasna. Wanda yanzu itace auta. Wanan kenan bari mu dawo labari. Haiydar yakasa hak’uri takanas yazo gidan su Falmi, tun daga ranar suka sasanta kansu. Soyayya mai k’arfi tashiga tsakaninsu. Kusan kulum suna tare da juna, wata rana yazo gun Falmi tun daga nesa yaga, Aisha zata shiga gidan sam bata lura dashiba, horn ya mata sosai don tayi nisa cikin tunani. Sai da ya taka burki ya fito ya fara zazaga mata masifa. Ko da Falmi tadawo ta ga sai huci yakeyi, tace”My Haiydar mai ya faru haka?. Nan ya fad’a mata laifin da yarinya tamasa. “Mtsss miye na d’aga hankalunka, akan wannan yar shegen, da ba’a san ubanta ba. “Uwarta tazo tayar mana ita. Nan taba ma Haiydar kabarin komai harda k’arya aciki. Madadin Haiydar ya tausaya mata sai yaji haushinta. Kwanaki sun tafi, magabatan Haiydar sun zo ansaka ranar Aure wata d’aya, sai shiri sukeyi, Falmi tasha gyara sosai, Falmi kasancewar yar casu ne, event tashirya bana wasa ba, tun daga rantalata suka fara event, har Friday idan nace zan tsaya baku labari, events d’in bikin nan da yanda komai ya kasance, charged d’in wayata zai d’auke, ban gama shiba. Ranar Friday aka d’aura aure. Duk wani abun al’ada anyishi, ranar yini da daddare abokai suka raka ango, sai da sukayi yan barkwanci, kafin suka musu sallama suka tafi. Haiydar ya rakasu ya dawo, Falmi tana ganin ya dawo, tazo cikin shagwab’a tafad’a jikinsa, azuciyar Haiydar kuwa cewa yake”wanna wata irin Amarya ce ba kunya, amma sai ya share wata zuciya tace”Son da take maka ne yasaka haka. Falmi bata bari sukayi Sallah farinci da godiya ma Allah ba, ta fara aikin sha- shafa Haiydar tare da masa wasu salo, Haiydar kasa jurewa yayi ya d’auketa sai kan bed. Salon da ya mata, ya rikitata ranar Falmi taji jiki, kasancewa ta kawo budurcinta, Haiydar irin Mazan nane wanda zamu iya cewa shi Hariji ne, a ranan sai da ya gurjeta sau uku. Da safe sai da yayi wanka yayi Sallah kafin, yazo ya mata wanka ya gama shiryata kena, wayarsa tayi k’ara ya d’aga, ganin daga office ne, ya kara a kunnesa tare da fad’in “Hello” daga d’aya b’an gare akace”Sir kazo Commissioner ne yazo yana son ganika yanzu, akan wani case d’in da’aka kawo. Ba yanda ya iya dole ya fita, Falmi ko tunda taga 8:00 bai dawi ba, ga bedsheet d’in da suka kwanta ya b’aci, ko yaye wa batayi ba. Waya ta d’auko ta kira, Mum bayan sun gaisa tace”Mum ki turo min da Indo zata min aiki. Mum tace”ke kina da glhankali kuwa?. “Kice na turo miki Indo gidanki. Falmi tace”Mum Haiydar bayanan ankirashi a gentle a gun aiki, gashi bana iya tashi ne fa, kuma ban karya ba. Mum tana jin haka ta gane sunyi abun garin, sai da tayi murmushi tace” gata zuwa yanzu. Mum ta bama Indo kud’in mashine ta hau tazo. Sai da ta mata girki ta jera mata, Falmi tace”kee jeki d’akina ki yayi bed sheet d’in ki wanke. (Mata kira gareku, ku kasance masu kiyaye duk wani abun da ya shafi Sirrin Auratayyan ku, bakomai ake fad’a ba ko anuna, wanna Sirri ne tsakaninku). Indo tunda ta gani, sai taji ba dad’i, amma ba yanda ta iya dole sai ta wanke. Ta d’ebo ruwa kenan ta fara wanki, sai ga Haiydar yashigo, tunda ya hango ta, yaji ransa ya b’aci. Ko da ya ajiye mota ya fito, dole sai yabi gefenta ya shiga gidan kasancewar qofar main falo yana rufe, yana isowa kusa da ita, karaf idonsa ya sauka kan bedsheet cikin kuna rai da zafin zuciya gami da wani kara yayi kamta da gudu. Ni ko Rash ina ganin haka na tattaro yan komatsena, nasa ka gudu dan kar Haiydar ya had’a dani. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD ( MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:31PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-46~50. Da sauri yayi kanta, ganin haka, tasoma ja da baya, jikinta sai bari yakeyi. Haiydar yana zuwa kutu ball yayi da boket d’in. Yana huci tamkar wani namijin zaki, yana jin yuwa yafito farauta. Indo ko ta mak’ure a jikin gini, sai b’ari take, don tunda take a rayuwanta, bata tab’a ganin fushi irin na Haiydar ba. Don in ta kali fuskansa, sai taga kamar na zakine yazo gabanta yana huci. Kanta ya nufo yana cewa”waya kawo ki gida na?. “Meye had’in ki da wanke bedsheet d’in da na kwanta da matata. Indo ko gani tsanani fushi ya had’u da tsoro, bata san lokacin da ta sulale, kasa sumamiya ba. Haiydar ganin idonta sun kafe, hakan ya tabbatar masa da suma tayi, wuceta yayi ya nufi cikin gida, da fushinsa. Falmi ko tana zaune a kan gado, takecin indimiee, wani gululun bak’in ciki ya k’ara tokaraansa, wannan wani irin iskanci ne?. A kan gado take cin abinci. “Mtsss yayi tsaki”. Cikin muryan shagwab’a tace”My Haiydar ka dawo?. “Bayan tafiyanka yunwa ta dame ni da… “Keee wa ya kawo min wannan bak’ar mai ido kamar na mage, gida na kuma don iskaci da rainin hankali, zanin dana kwanta da ke take wankewa. “Mtss shikenan nikam nagama yawo, yarinyanan zata rainani. “Ta gama sanin sirina. “Shikenan nikam kin gama dani mtsssss. Falmi tace”to ya kakeso nayi, ni kasan ko a gida ita, take min wanki. Hatta under wears d’ina ita take wankewa. “Mtsss sai kiyi tayi ae. Falo ya fito tare da bata guri, ganin zaman gun bazai masa ba, ya nufi d’akinsa cike da kunan zuciya. Falmiko tana gama cin abinci a gun ta bar kwanon, ta sake kwanciyarta. Indo ko ta dad’e a sume a gun, sai da ruwan da ya zuba ya iso jikinta, hakan yata daman farkawa. Hasken ranane ya haska mata ido, da sauri ta mik’e, cike da tsoro, tace”yanzu ta koma gidane ko ta shiga gidan?. Wata zuciya tace”in kika tafi baki gama aiki ba, wani tashin hankaline. A hankali tashiga gidan d’akin da Falmi take ta nufa, poss d’inta ta d’auka, tafito falo da shirin ko ta kwana. Haiydar ne ya fito, nan rake ta soma b’ari. Cikin fushi da muryan hargowa yace”ke mai kikeyi a cikin gidan nan da baki tafi ba?. Kasa bashi amsa tayi masifa ya cigaba dayi, wanda hakan ya tashi Falmi ta fito. Haiydar janyo Indo yayi yace”ki fita min a gida kar na k’ara ganin k’afarki a gidan nan sai na karya ki. Falmi tace”miye haka wacce zata min aiki zaka kora?. “Kasan dai ni ban iya aiki ba ko?. “Ita zata na mana girki da sairan aiki. Haiydar ya kulu iya kuluwa, yace”kee miye aikin ki da baza kina aiki ba?. “Ni fa ka ganni ko agida ruwan Lipton sai an dafa min. Cike da ta kaici yace”baki isa ba to ni bana son girkin yar aiki. Ya wuceta fuuuu yayai d’akinsa qofar ya bako ya kwanta yana mai takaicin abunda ya faru, “daman haka halin Falmi yake?. Falmi tana zuwa d’aki Mum d’inta takira, sai da ta sanar mata da komai. Mum tace”yayi kad’an daga zuwanki zai fara fida halinsa to bai isaba wallahi. “Yar’aiki kuma kamar ta zauna daram, dole Indo ta dawo cikin satin da zamu shiga, tunda baki saba aiki da kanki ba. “Ki bar min komai a hannuna dole yayi biyayya. Falmi cike da jin dad’i ta mata sallama, ta kashe wayar. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/28/2016] Rash Karda BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-51~55. Indo tana fita, kuka take maras sauti, tana rokon Allah ya fitarta ya bayyana mata da danginta. Haka har ta iso gida, tana zuwa bata huta ba ta kama wasu ayyukam, da zatayi ma Hajiya, gashi sun k’aru sabida yan biki. Falmi kuwa bata sake leko falo ba sai dare, da yunwa ya dameta, wasu matsatsun kaya tasaka. Haiydar na falo yana kalon tashar BBC WORLD ta shigo sai karairaya rakeyi, kalo d’aya ya mata ya kasa d’auke kansa, kasancewan bai da hak’uri. Take ma manta fushin da yakeyi da ita, ganin taki zuwa kusa dashi, tashi yayi a hankali yaje ya rikota, cikin rad’a yace”haba baby na fushin ne har yanzu?. Sai da ta d’anyi farrr kafin tace”ni yunwa nakeji fa. Hannu ta ya kamo sukaje dinning, asai yamusu take away. Nan yaringa bata a baki tana ci sai da ta k’oshi, ya sun kuceta sai d’akinsa, nan labarin ya canza. Hajiya Fiddausi, sai datayi shige da fice, tasamo kan Haiydar, ya yarda Indo ta dawo gidan da zama tana musu aiki. Hajiya tace”ma Falmi ta bari sucika wara sai Indo tazo, a kwai abunda takeyi ne. Falmi badan taso ba ta amsa ma Mum d’inta. Kwanaki sun tafi yau 3weeks da bikin Falmi, tasoma caza ma Haiydar kai, Haiydar duk lokacin da yazo da buk’atarsa Falmi tayi burus dashi, ko kuma in tabashi had’in kai sau d’aya, to ba zai k’ara ba. Haiydar har ya d’an rame. Mum takira Falmi tace”to ba zama zakiyi ki zuba masa ido ba. “Zaki fara tatsansa ne mu had’a jari. Falmi tace”Mum to taya zan tatse sa da yawa bacin akwai komai a gida?. “Mtss kee sai kace ba mace ba, bakisan tanda zakiyi ki samu kud’iba. “Kina tambayansa mana. “Ko kuma in yazo kwaciyan aure dake, kice sai yazuba kud’i ke bazaki iya ba. Falmi tace”to Mumcyna hakan zanyi ma kawai. Mum tace”yauwa yar albarka. (Kira gareku mata masu irin wannan galin, idan mazajenku sun zo muku da buk’ata, kuce sai sun baku kud’i, wannan BABBAN KUSKURE NE, aikata hakan haramci ne dan Allah akiyaye). Da yamma Falmi tayi wanka tayi kyau sosai, kasancewan bata girki Haiydar ke sayo musu tayi zaman jiransa. Haiydar ko da sallamansa ya shigo gida, tunda ya kyalo Falmi, ya had’iye wani yawu. Take yaji jikinsa ya mutu, dining ya wuce ya ajiye abinci da ya sayo musu, Falmi ko bata iya cemasa sannu da dawowa ba. Sai shine yace”ya gida fatan kin na lafiya?. Sai da ta d’au lokaci, kafin tace”lafiya lau nake. ‘Dakinsa yaje ya watsa ruwa ya saka 3quater da singlet ya fito, a dining ya ganta. Shima can yaje ya zauna, ya kaleta yace”ki d’auko plate da spoon kiyi serving d’in mu. Sai da ta ya tsina fuska taje ta d’auko ta dawo, har ta zauna yace”ruwa fa ko sai mun gama ci za’a d’auko?. “Mtssss ta yi tsaki ni na gaji da yawan tashi. Sai da suka gama ci, Falmi ta zo jikinsa ta zauna, don yau tanason ta fara wankansa, tunda tagane shi mai yawan bukatane, wasani tafara masa, wanda yasaka hankalinsa tashi, gashi kwana biyu Falmi ta hanasa kanta. Shima biye mata yayi suka dulmuya, sai da taji zai wuce ta mike zubur, cikin dashashiyar murya yace”Falmi karki ki amincewa dani. “pls ki taimaken una cikin yanayin bukata. Kafad’a ta ya tsina tace”ni bazan iya ba. Cikin yanayi tausayi tafara”pls My Falmi ki taimaken dan Allah ina buk’atarki sosai. “Duk abunda kike buk’ata zan miki matsawan zaki bani had’in kai. Sai da tayi wani murmushin mugunta tace”kayi alkawari ina fad’i abunda nakeso zaka bani? Da sauri ya amsa mata”da eh! Zan baki koma miy ne. Falmi tace”kud’i nakeso masu yawa. “Haiydar jikinsa na b’ari ya tashi ya duba Aljihun wandinsa ba wani kud’i masu yawa, sai 10k ne kawai don d’azu a gun aiki, yayi sadaka da kud’ade’en da ke jikinsa, ma masu bara, duka dubu goma ta d’ebo yace”ga abinda suka rage min nan. Falmi tace”nawane wannan don naga da alama basa da yawa?. Haiydar yace”10k ne kawai bana da kud’i a jikina suna banki. “Mtss mai dubu goma zasu min, asai baka shirya jin dad’i ba. Haiydar kamar zaiyi kuka yace”haba Falmi ki taimaka ma halin dana ke. Zugunawa yayi akan gwiwansa, don bayason abunda zai b’ata mata rai. “Mtsss to mai kake so na maka ne?. Da rauri yace”ki taimaka min. Ummmm”zan iya barinka kayi kiss a 10k amma fa da sharad’in bazaka wuce haka ba?. “Eh na yarda in har zaki bari namiki d’an kiss d’in. Okay!. Da sauri Haiydar ya taso yazo zai rungumeta, Falmi ta ja da baya, tana masa kalon raini wayo. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:31PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-56~60. Haiydar ya rairaice mata, yana had’a ta da Allah, bata yarda dashi ba sai da ta yamata Alkawarin 100k tukun ta yarda tabashi kanta. Tun daga wannan rana Falmi tadawo galfa Haiydar son ranta, tana sati na hud’u, Indo ta dawo gidan da zama, duk wani aiki Indo keyi hatta gyaran d’akin Haiydar, abincinsa da wankin kayansa duk itatakeyi. Bayan kwana biyu, Hasna ta shirya tace”hajiya zanje gidan Yaya indaidasu”. Hajiya tace”ki gaidasu sai kin dawo. Mota ta d’akua sai New GRA, tana zuwa horn tayi ma gadi ya bud’e mata. Sai da ta ajiye motarta, a ma’ajiyin mota, tafito cikin nutsuwa tashiga cikin gidan. “Assalamu’alaikum” Falmi da ke zaune taji sallama, amma tsaban iskanci taki amsawa, Hasna tasake mai-maitawa, Indo da tafito daga kitchen ta amsa, Hasna tashigo cikin falon. Falmi tana ganin Hasna ta ganeta don tun kafin biki sunjemata, amma dan iskanci tawani yatsina fuska, cikin zuciyarta ko cewa take”mtss wannan dangin miji daga gani zanyi fama daku?. “Wata d’aya da sati biyu da biki, amma ace har sun fara sintiri wa mutu. Hasna da murna ta k’araso gun Falmi, tace”Aunty na sannu da gi…. Wani kalon da Falmi ta aika mata dashi, yasata kasa k’arasa maganta. Falmi bata tanka mata ba, sai da ta mik’e tsaban iskanci tace”daga ina haka?. “Wacece ke naji har kina cemin Aunty. Husna ta danne zuciyarta tace”lah! Baki ganeni bane ai k’anwar Haiydar ne Husna. “Oh! Haka fa yana da kwanwa ko?. “Sanuki da zuwa, Indo! Indo!”. Da sauri Indo tazo ta rusuna, tace”gani Aunty”. Falmi tace”ga wannan yarinya, ki bata ruwa tasha, in kin gama girki, sai ki samata”. Falmi ta juya ta kali Hasna tace”kya iya zama anan kafin Yayanki ya dawi. Ta wuce d’aki tana wani karairaya, Hasna baki tasaki tana kalon ikon Allah. Indo tace”Hasna sunaki ko, sannu da zuwa ya gida?. Hasna cikin raha ta amsa, nan suka fara hira tana taya Indo aiki har suka gama. Hasna taji dad’i zamansu da Indo, haka kurum takejin ta kamar yar’uwata, duk da Indo zata ba ma hassna kamar shekara d’aya haka. Da yamma Haiydar ya dawo, ganin Hasna ya saki fara’a, a falo ya zauna suna hira, tukun ya mik’e yaje yayi wanka, yafito zaici abinci, yaga Hasna da Indo suna hira, wani mugun kalo ya sakar ma, Indo sum-sum tamik’e tayi d’akinta. Duk abunda yakeyi Hasna tana lura dashi, abinci yasa Hasna tayi serving d’insa yaci. Sai can Falmi tafito cike da isa tace”kadawo shine bazaka zo ka fad’an ka dawo ba. Haiydar yace”tayi hak’uri. Hasna da yamma tayi musu sallama ta tafi. Ko da takoma gida, tabama Hajiya labarin Indo da kirkinta. Ta kuma yaba da hankalinta, Hajiya hartaji tana son ganin Indon nan. Bayan kwanaki Haiydar yace”Falmi ki shirya zamuje gaida Hajiya na. Da farko Falmi taki ganin Haiydar ya dawo Aliyu na da dole ta shirya sukaje, ranan kam Hajiya taga rashin kunya ayinin da sukayi, nan Hasna ta bata labarin abunda ya faru, nan Hajiya tagane anyi ma Aliyi asiri don ba haka yake ba, sam bayason raini. Hajiya tace “Don haka dole na mik’e da addu’a. Haka su Falmi suka dawo gida. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/28/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-61~65. Falmi kulum da kalan tsiyar da take tsula ma Haiydar, Haiydar sam baida hak’uri, wani sa’in da dambe yake kusantanta. Kuma dole sai ya biya Haiydar ya rame sosai, har d’an bak’i yayi. Hajiya ko ta dage da Addu’a, har masallatai ta aika ana tayata da addu’a, Allah maji rokon bawansa. Haiydar ne zaune a office d’insa, ga tarin takardu, amma ya kasa tab’uka komai, a hankali yake tariyo komai na rayuwansa, duk lokacin da yatuno Falmi, sai ya rintse ido don wani matsanacin sha’awan dayakeji, ajiyar zuciya yayi. Surar Falmi ne ke yawo a Indonsa, a hankali ya mik’e ya d’au key d’in motarsa. Gida ya nufa don ji yake in bai samu biyan buk’ata ba, komai ma zau iya faruwa. A gida ko Falmi tayi wanka, bata aikin komai sai chatt, ga iya taunan chewing gum kamar tsohuwar karuwa. Ita kad’ai tana murmushi, ga k’aran shigiwan massage na Whatsapp kamar me, duk ta cika mana kunne. Indo ko tanata aiki, don karta makara in Haiydar, ya dawo bata gama ba tasan sauran. Haiydar ko gudu yake sosai, don yanda yake jinsa ba k’alau ba. Yana zuwa gida horn ya dinga yi, kamar zai tashi sama, mai gadi ya bud’e masa gate ya shigo, da gudu yaje yayi parking, ya fito cikin sauri ya nufi cikin gidan, yana shiga falo ya hangota, da sauri ya nufi inda take. Yana zuwa ya janyota jikinsa, ya fara shin-shinata, cikin tsawa tace”Malam lafiyarka kuwa?. “Wani irin iskanci ne haka?. “Mutum na zamansa zaka zo kawani damesa. “Ko kamanta da dokanda na kafa maka ne?. Sake matsowa yayi kusa da ita, ta matsa ya biyota, nan suka fara kokawa, ganin yafi k’arfinta tasoma dukansa, d’aukarta yayi kamar yarinya, yanufi bedroom d’insa da ita, yana ajiye ta ta mike tace”Makam anawa zan baka kaina?. Cike da mamaki yace”kamar yaya?. “Bayan kud’in sadakin dana akwai wani kud’in da zan sake biya ne?. “Oh kamanta ko?. Hanyar fita tayi, kafa ya samata ta fad’i ya mayar da qofar ya rufe. Hmmm ranan Falmi taji jiki dan sai da kusan magriba Haiydar ya kyaleta, yace”kuma kisa ma ranki kulum da dadre sau uku ko hud’u, da safe biyu kafin na fita, in nadawo uku in ba ida zanje. “Kinga ina kyaleki ko to daga yau ba sasauci, in kuma kinki to nasan matakin da zan d’auka. “Don bazan saka miki ido nayita kalonki ba. Ya shiga wanka ya fita masallaci abunsa. Ranan Falmi tayi kuka sosai, don taji jiki, kuma ta gane maganin da suka masa yanzu baya aiki Haiydar tun daga wannan ranan ya mayar da Falmi kamar engine sa. Tunda tagane suka shiga wasan b’uya, gashi ya hanata zuwa gidansu. Falmi ko tayi planning, na 5yrs, bazata haihu ba. Haiydar abun duniya ya ishesa, yanzu kusan shekara 3yrs da aurensu, ba abunda ya canza, a halin Falmi, ga shi ba tatab’a koda b’atan wata ba, kuma shi ya kasance mai son yara. Ganin ba zai juri iskancin Falmi ba ya yanke hukuncin k’ara aure. Amma sai ya fuba mai hankali da nutsuwa tukun, ana haka aka kawo wani case, wani mutumi sunyi fad’a da barayi har sunjimasa ciwo, ga jini na zuna asibiti suki k’arbansa, key motarsa ya d’auka yanufi asibiti, duk wani abunda za’ayi yayi aka k’arb’i mutumin. Nan ya had’u da wata nurse sunanta Amrah tana da hankali, hakan yasa ya k’arbi number ta. Tundaga ranna soyya tashiga tsakaninsu mai k’arfi. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/28/2016] Rash Karda BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-66~70. Haiydar ya samu Hajiya ya mata bayani, yace”ta fad’a ma Dad, Hasna kam tafi kowa murna. Falmi tun dataga take-taken Haiydar tasaka, aka fara bibiyarsa nan tasamu labarin, yana neman Aure nan hankalinta ya tashi, baran da taji ma’aikaciyar asibiti, take ta kira Mum, tana kuka ta sanar mata. Hajiya Fiddausi tace”karyane dole yau naje gun Malam kiyi shiru. “Ki bar komai a hannuna. Hajiya Fiddaisi tana tashi sai gun malamin dake mata duba, ko da ya buga k’asa yayi wasu surkulensa. Yayi shiru can ya d’ago yace”Hajiya sai dai hak’uri fa, dole mijin yarki zai k’ara aure, sai dai shawaran da zan baku shine. “Zamuyi aiki a kai ku sai ku zab’a masa mata. “Don Mahaifiyar yaron ta dage masa da addu’a. “Aikin mu bazaiyi wani tasiri akansa ba. Hajiya jiki ba kwari ta dawo gida nan ta sanar da Falmi kimai. Hankalin Falmi ya tashi ta rasa mai ke mata dad’i, don hatta indo bata barta ba bare Haiydar, kulum cikin fad’a suke. Haiydar ya tsayar da ranan jumma’a magabatansa zasuje, gidansu Amrah. Falmi ta fito zatayi d’akinsa taji yana waya da Amrah ya na sai damata ran Friday, magabatansa zasuzo, Falmi tayi kukan kura tace”kwace wayar nan ta kamashi da fad’a, farko Haiydar ya kyaleta, ya dawo falo tafiyosa. Nan tasha kwalansa, suna kokuwa saiga Hasna ta iso, ganin halin da ake ciki, yasa takiya Hajiya ta fad’a mata. Hajiya ta sanar da Abbansu Haiydar, ta sa driver ya kawota. Zuwan Hajiya tasa Haiydar ya bar dukan Falmi, Hajiya ta musu nasiha sosai, bud’an bakin Falmi tace”Hajiya nifa aure ne bana so ya k’ara. “Yin hak’uri da k’ara aure shine zaman lafiya a gidan nan. Nan tafara rashin kunya son ranta, Haiydar ya taso zai daketa Hajiya ta hanasa. Hajiya tace”kee Fatima aure kam ba fashi sai anyi dole. Falmi tace”to ya auri wata ba wannan ma’aikaciyar ba. “Ai da ya aureta gwara ya aura min Indo a matsayin kishiya. Hasna da ke gefe tace”Hajiya ae gwara Indo sau dubu tana da hankali. Hajiya tace”kee wayasa ka bakinki a ciki. Hasna tace”yi hak’uri Hajiya. Hajiya tace”ke da bakinki kikace haka ko?. “To zan gwada miki na isa da d’ana. “Kuma ina Indon mutum ce?. “Kuma macece?. “To zai aureta in Allah ya yarda. Cikin sauri Haiydar yace”Hajiya ina bana son Indo gwanda ke kini momin wata daban na tsani Indi. Hajiya tace”hukuncin dana yanke kenan. “Fatima ta raina Indo ne tace haka ko?. “Watarana d’an hakin da ka raina shi zai tsole maka ido. “Aliyu! Haiydar da sauri ya d’ago don tunda suke da Hajiya bata tab’a kiran suma ba. Hajiya tace”in nina haifeka to ina si kamin biyya. “Indo ita na zab’amaka kuma wataran zakayi alfahari da ita, amatsayin mata. Hajiya tace”Fatima ina Indon take?. Falmi cikin muryan kuka duk ra rud’e tace”bata nan na aiketa gidan mu. “Ok! In ta dawo Hasna zata zauna sutaho tare. Hajiya ta mik’e tace”ni na tafi kaiku ma kazo dadaddare ina son ganinka. Hajiya tana fita Haiydar ya mik’e sai jiri yakeji ya nufi d’aki, wannan wani irin al’amarine?. “Naike shirin faruwa dani. Hasna abun ya mata dad’i hawan kan kujera ta mik’e, tana jiran dawowan Indo du tafi. Falmi ko ta d’aura hannu aka tana cewa”shikenan naja ma kaina tabbas NA TAFKA BABBAN KUSKURE. “Mai ya kaini furta haka ya akayi na ambaci sunan Indo?. “Wannan shine BABBAN KUSKUREN DANA TAFKA. “YAR AIKINA ZATA DAWO KISHIYATA. “KUMA YAR CIKIN SHEGE. Nima Rash daga gefe nace Falmi gaskiya kinyi KUSKURE BABBA. Bari dai muga ya wannan gurmin zai k’are don nikam banso abarni a baya. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:31PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-71~75. Indo bata dawo ba sai daf magriba tashigo, da sallamata, Hasna dake falo tana kalo tace”oyoyo Aunty Indo sanu da dawowa, tun d’azu nake jiranki. Cikin sassayan murmushi Indo tace”sannu Hasna ya kk?. Yasu Hajiya?. Hasna tace”lafiya lau”. Indo tace”kin dad’e da zuwa ne Hasna. Hasna tace”eh! Hajiyar ma tazo, bata dad’e da tafiya ba. “Tace muje tare dake yanzu nan. Indo ta zaro ido tace”lafiya dai ko Hasna?. Hasna tayi murmushi tace”lafiya lau mudaije zakiji. Indo tace”bara na fad’a ma Aunty aika. Hasna tace”kyaleta ki zo muje kinga Hajiya ke kiranki. Indo tarasa mai zatace ma Hasna, can tace”karfa ta zage ko ta maren ina tsoro. Hasna tace”Itama tasan da Hajiya tana kiranki itama. “Karki damu yanzu zo mu tafi. Ba musu Indi ta bita suka fito, motan Hasna suka shiga ta su zuwa State Low cost. Cikin nutsuwa suke tafiyar har suka iso katon katafaren gidansu, horn tayi mai gadi ya bud’e mata, ta danna hancin motarta cikin gidan. Gurin ajiye motoci taje ta ajiye motar suka fito tare, sannu a hankali sushiga cikin gidan, Indo tun zuwarsu taji gabanta na fad’uwa, addu’a tasomayi. Da sallama suka shiga falon ba kowa, Hasna ta nuna mata kujera tace”zauna Aunty na” Hasna taje fridge ta d’auko mata lemu da cup ta kawo mata, saida ta siyaya sannan tace”Aunty na barinje na kira Hajiyan. Indo murmushi tayi wanda ya k’ara fitar mata da kyauta. Hasna ta hausa sama zuwa d’akin Hajiya, ta tura da sallama tashiga. Hajiya tace”Hasna kun zo tare da ita ne?. “Eh! Hajiya gata a falo tana zaune. “To kije gunta ina zuwa yanzu. Hassana ta sauk’o a hankali zuwa falo, kalo ta kunna musu, sai ta mik’e ta koma d’akinta ta d’ebo ma Indo, hotunansu na school ta kawo mata. Kusa da ita ta zauna Indo ta fara ganin photo, Hasna tana fad’a mata sunan kwayenta. Tun Indo na d’ari-d’ari, har ta saki jiki da Hasna, suka fara hira sosai, a tsakaninsu nan Indo kece ma Hasna itama tayi karatu, amma a Jss3 ta tsaya bata ci gababa. Hasna tace”maiya hana ki ci gana Aunty n?. Nan take idon Indo yaciko da kwalla, ta fara sharewa tace”Mamana ke biyan min kud’in makaranta, ta rasu kuma ba mai d’aukan nauyina. “Hakan yasa na hak’ura da karatu. “Amma ina son nayi karatu wallahi. Hasna tace”Allah sarki Allah ya jikanta da rahma. Indo ta amsa da amin. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/28/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-76~80. Hasna hira sosai sukeyi da Indo, abun gwanin burgewa in ka gansu ka d’auka sun dad’e da sabawa da juna. Haiydar da kyar yashifa d’aki wani irin jiri yakeji, cikin zuciyanshi ko cewa yake” amma Fatima ta cuceni gaskiya. “Mai ta kawo bakinta na cewa na Auri Indo. “Ina zan kai b’akar mace?. “Sam ni tsarina bana son b’aka. “Kuma a b’akar ma yar aiki, wanda bata wayeba. “Mtssss halama ko secondary school batayi ba?. “Gashi hajiya fiskanta ba alamar wasa aciki. “Dole nasan matakin da zan d’auka. “Don Indo da k’afarta zataje tace ma Hajiya bata son auren. Wani lallausan murmushi ya saki. Falmi ko tana shiga d’aki ta kira wayar Mum d’inta yakinshiga, ganin wannan kukan bazai fiddata ba, tafito d’akin Haiydar ta nufa tana kuka wi-wi da hawaye. Qofar ta tura tashiga tana zuwa ta fad’a jikin Haiydar, kuka mai tsuma zuciya ta saki. Haiydar jin Falmi ajikinsa duk ya rikece, bare yana hannu, take yasa hannusa ya fara share mata hawaye. A hankali yace”Falmi duk ke kika jawo mana. Cikin muryan kukan tace”pls kaje kace ma Hajiya ta hak’ura ni bada nufin ayi auren na fad’a ba. Na fad’a ne irin nagana rainamata, ko kamarta gwara kanemo a waje. Ajiyar zuciya ya sauke yace”karki damu zanbi duk hanyan da ya dace. Haiydar ya lalub’o bakin Falmi ya had’a danasa, a hankali yake mata masu salo mai rikitarwa, duk wani gab’ar cikinta yana bi yana aika musu da sak’o mai sanyi. Cikin nuysuwa ya soma cire mata kayan jikinta Falmi ta rike hannusa, cikin da shashiyar murya yace”kinga irin abun ko mai yasa kike hanani kanki. “Why! Why! Why! Falmi”. Ganin da gaske wai ita fushi take hakan yasa shikuma bazai iya hak’ura ba, ta k’arfi yasoma cire mata kaya. Hajiyansu Haiydar wanka zata shiga, cikim gaggawa ta yi wanka tasaka kayanta, da fara’a ta soma sauk’owa k’asa, tana mai farinciki yau zata yi surka ta gari mai nutsuwa. Don yanda takeyi Husna na yabonta, gakan yasa da Falmi tayi gatse, itakuma ta mayar da gaske, don rasan watarana Falmi zatayi danasani. A hankali take tafiya ta kusa sauk’owa daga step, ta soma jin muryan da ko a mafarki bazata manta shi ba. Ko a wani yanayi take bazata manta da muryanan ba. Duk da shekara ishirin da d’oriya. Cikin hanzari tasoma sauk’owa step d’in don gani take, tankar mai muryan zai gudu. Nima Rash ganin haka yasa nace barana biyo Hajiya. To madu karatu wani murya ne Hajiya ta tsinkayo a falo?. Shin Hajiya tana gane mai muryan nan kuwa?. Donjin wannan amsar ku biyo YAR KARDAMAWA. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:31PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-81~85. Cikin hanzari ta soma sauk’owa daga step d’in, don ko makawa babu, wannan muryan Lamid’o ne. Jikinta har b’ari yakeyi, da sauri ta isa falon, sam su Indo basu san, hajiya ta isoba. Sabida karatun da ke tashi a falon, gashi hankalinsu gaba d’aya, yana kan hotuna. Hajiya ta dad’e tana kalon Indo, cikin zuciyarta ko cewa take, “tabbas wannan jinin Lamid’o ne. “In kuma ba haka ba to kaman yayi kama. “To tayama za’ayi ace jinin Lamid’o ne, bayan Lamid’o da’akace ya mutu, har anga tokan gawansa. Jikinta duk ya mutu, da kyar ta iya jan kafarta, zuwa cikin falon tare da yin sallama. Indo a hankali ta d’ago kanta karaf suka had’a ido, take k’irjin Indo ya bada rass! Rass!, kasa d’auke fuskanta daga kan hajiya tayi. Cikin zuciyarta ko cewa take”wannan kamar matan, dana ke gani a photo da Umma tace na Baba nane. “Sai dai wannan ta tsufa wancan kum yarinya ne. “Hmm to nida bayida yan uwa ma. “Kai inaga kama ne, kawai sukayi da matar. Ajiyar zuciya ta sauk’e a hankali, ta sunkuyar da kanta, cikin girmamawa tace”sannu Mama anyini lafiya?. Hajiya da takasa b’oye mamakinta a fili, sai da Hasna tace”Hajiya ana gaidaki ne fa. Firgit ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula, cikin fara’a tace”lafiya Aishatu”. “Ya aikin dai? Indo kanta a k’asa tace”Alhamdulilah!. Can sukayi shiru, don Hajiya tana jin wani abu gameda Indo, ta dawo mata da abunda ya wuce, shekara ishirin da d’oriya. Cikin dauriya hajiya tace”Hasna taci abincin kuwa?. Cike da girmamawa Hasna tace”eh hajiya. Hajiya ta kali Indo tace”Aishatu nina aika ki zo keda Husna. Kan Indo a k’asa tana wasa da yan yatsun hannuta, masu kyau gasu dogaye gwanin burgewa. Hajiya taci gaba da cewa”Aisha ina son ki d’auken a matsayin Mahaifiyarki, kuma wacce zata baki umarni ki bi. “Aishatu! Ta kira Indo, cikin girmamawa Indo ta d’ago, karaf suka gad’a ido, take taji wani qaunar Hajiya ya shiga jikinta, kuma ta hango tsananin soyayyan uwa da d’a acikin kwayar idon Hajiya. Indo ta amsa da”Na’am Mama!. Hajiya tace”Aisha ina rok’on wani alfarma a gunki, kuma ina so kimin alkawari. Zaki amince da duk abunda na fad’a miki. Indo cikin sanyin murya tace”Mama ae ke uwace. “Duk umurnin da kika ban zan kasance mai biyayya a gareki, matsawan bai sab’ama addini ba. Hajiya tace”Alhamdulilah! Nagode Allah ya maki Abarka Aisha. Indo ta amsa da”Ameen ya Allah. Hajiya tacigaba da cewa”Aisha inason na had’a ki aure da d’ana Haiydar. Cikin rud’ewa ta d’ago fiskanta, don ta gaskata mai kunneta ke jiyomata. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/30/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-86~90. Cikin rud’ewa ta d’ago fuskanta, tabbas Hajiya da gaske take maganan, hmm cikin zuciuarta kam cewa take”anya Hajiya tasan mugun tsanar da Haiydar yamin?. “Taya ma zanyi na auri mijin Aunty Falmi. “Ina bazan iya ba Hajiya ki canza. Tana wannan tunanine ta ji muryan Hajiya tana cewa”karki damu nasan tunaniki Fatima ce ko?. “To ita da kanta ta zabi hakan. “Kuma shi Haiydar d’in ma ya amince. Indo sam gani take kamar ma farki abunke faruwa. Hajiya tace” ina fatan bazakiyi min jayayaba. Indo haka kurum ta tsinci kanta da d’aga ma Hajiya kai ta amince. Hajiya albarka tayi ta sa mata, tukun ta mik’e tace”barin hau sama zan yi wani abu. Hasna ne ta amsa da”to Hajiya. Hajiya na tafiya Indo ta fashe da kuka sosai, Hasna ta dawo kusa da ita tace”Aunty Aisha kiyi hak’uri nasan Hajiya bazata tab’a cutarki ba. “Kuma wataran zakiyi alfahari da aurenku. Indo cikin kuka tace”Hasna kin san yanda Yayanki ya tsaneni kuwa?. “Sam baya k’aunar ganina ina numfashi. “Bazan iya kishi da Auntyn Falmi ba Hasna. Hasna tace”hak’uri zakiyi komai zai yi dai-dai. “Kuma batun Ya Haiydar ke zaki ja ra’ayinsa da naki salon. “Amma sai kin dage kin kuma daure. “Tashi muje d’akina in miki make-up, don tare zaku koma in yazo. “Zan kuma baki wasu kaya kina kwaliya sosai. “Ki bar zama ba gayu pls. Hannu ta takama suka haura sama, Hasna ta wanke ma Indo kanta ta gyara ta sosai kamar ba ita ba. Wasu sababin kayanta, da bata saba ta bama Indo, tare da had’a mata kayan kwaliya mai yawa. Falmi ko ita da Haiydar kokuwa suka sha, da k’yar ya rabata da kayan jikinta, sarrafata yasomayi son ransa. Falmi ihu take masa tana cewa”tunda ka amince ma Hajiya sai kaje gun Indo ta baka kanta, banda ni Falmi, tana kuka tana dukansa. Shiko gogan bai masan tanayi ba, sha’aninsa kawai yakeyi. Falmi ta wahala kam, don taki tsayawa, sai da ya d’ibi 2 hours masu kyau, kafin ya koma gefe yana maida numfashi, a hankali ya matso kusa da ita, ya rungumota yace”Falmi ina matuk’ar sinki, amma ke kike jawomana duk abunda suke faruwa. “Mai yasa kike guje ma shimfid’ata?. “Ina kiraki bak’ya amsa min why Falmi?. “Kuma kinsan ni na kasance mai yawan bukata Fatima. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKIR) RASH LUV [5/30/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-91~95. “Mtsss Falmi ta saki wani tsaki tare da mik’ewa tashiga wanka, sai da tayi wanka tana fitowa, kalo d’aya Haiydar ya mata, ya mik’e ya nufi bayi wanka yayi ya fito, yazo gunta yanyota jikinsa yayi, cikin salonsa na rikitarwa yake shafa bayanta, yace”haba my Falmi kinsan ba wata macen da zata tab’a sayen zuciyata. “Ni nakine ke kad’ai kuma ina qaunarki. Kalon banza ta masa cike da masifa tace’ kai Haiydar kasani nayi danasanim aurenka ni Fatima. “Gashi yanzu ka jamin kayan raini. “Wacce nake gani a k’ark’ashina, wai ita zata dawo kishiyata. “In sam ba zai yiwu ba ina. Haiyadr cikin muryan lalashi yace”kinsan bazan tab’a had’aki da wata ba. “Aure ai kamar an fasa tunda baki so. Hararansa tayi tare da d’iban kayanta ta fita. Haiydar ko mai ya sha, tare da saka kayansa, ya d’auki key d’in motarsa, don zuwa amsa kiran Hajiya da bata hak’uri ta janye k’udirinta na batun auren Indo. A gidan su Hajiya kuwa, Hasna ta wanke ma Indo kai, ta gyaramata tare da busar mata shi da dryer, alwala sukayi suka gabayar da Sallah magriba, suka jira sai da akayi Isha’i nan ma sukayi, Hasna tace”Aunty na zo ki zauna gaban madubi kiga wani abu. Ba musu Indo tazo ta zauna, Hasna ta gyara mata fuska, ta gyara giranta, ta fara mata kwaliya, ni dai Rash ina gefe ina kalon ikon Allah, don naga shafe- shafen da goga wancan yayi yawa. Indo tace”kai Hasna nikam abun ae zai min yawa. Hasna ta k’yalk’yale da dariya, tace”Aunty na ki tsaya ke dai kiyi kalo kawai. Murmushi Indo tayi. Hasna tayi kealiya ma Indo, tare da d’auko mata, wani atamfanta riga da skirt, mai kalan ja da bak’i. Indo ta karb’a ta shiga bayi ta saka, tana fitowa Hasna sai murmudhi take, Hasna tace”zauna ki gani. Indo tace” oh ni kam Hasna har yanzu duk a make-up d’inne haka?. “Ina zani da kwaliya bacin yanzu bacci zanje nayi. Hasna tace”Aunty bazaki gane bane. Hasna ta d’aura mata d’an kwali, ta mik’o mata flat shoe, shima kalan ja da bak’i, sai gyale shima ja da bak’in, yana da stone farare, sai haskawa sukeyi, ne sa kad’an Hasna takoma, tana kalon indo, cikin muryan farin ciki tace”wooow My Aunty na you look so beautiful. Muryan Hasna danaji yasa ni Rash na d’ago da sauri, bansan lokacin da wayata ta sub’uce ta fad’i ba. Ba abinda na furta sai kalman”tsarki ya tabbata ga Ubangiji daya k’agi wannan k’yak’yawan suran. “Hmm masu karatu kuyi Imagine d’in Indo a cikin wannan shigan, ya kuke gani zata haska?. Hasna ta fara yabon Indo, tare da d’auko wayarta tashiga d’aukarta photo. Haiydar yana shigowa gidan su Hajiya, d’akinta ya nufa, da sallama ya shiga, ta amsa masa, bayan ya gaidata, Hajiya ta fara masa nasiha mai ratsa jiki, sanan tace”kar kuma naji kasake cewa kalman da za’a fasa aurenka da Indo. “Wataran in Allah ya yarda zakayi alfahari da hakan. Ta dad’e tana masa kalamai masu tsuma jiki, wanda dole yafasa abunda yaso fad’a mata. Hajiya tace”katashi muje ku tafi, in Abba ka ya dawo duk yanda muka tsayar dashi zakaji. “In zata dawo gidan nane kafin ayi aure to ko kuma ta zauna acan, duk sai in ya dawo zamu tattauna. Jiki bak’wari Haiydar ya mik’e suka fito falo, Hajiya ta kira wayan Hasna tace”ku sauk’o k’asa ke da Aisha. Bata jira amsansu ba ta kashe wayar, Hasna ta kama hannu Indo suka fito, suna saukowa kenan Haiydar ya d’aga kansa, dake yana kalon saitin step d’in. Daram! K’irjinsa ya buga, kasa d’auke fuskansa daga kalon Indo yayi, tun dayake da ita yaune rana ta farko da ya fara ganinta da kwaliya, kuma ta saka gyale, gashi shara-shara. Sai da suka iso falon, suka zauna Hasna ta gaida shi, haka Indoma. Hajiya nasiha ta musu sosai tukun tace”ku tashi muje ku tafi kar dare yayi, duka suka mik’e Hajiya ta kama hannu Indo, da kanta tasakata a gaban motar, ta lek’o tace” Aunty na sai kin jini. Wani mugun kalo Haiydar ya sakarmata, bashiri ta jabakinta ta bar gun, ta damotan dukayi yabar haraban gidan, sai da sukayi tafiya mai d’an nisa, kafin suka iso qofar gidansa, horn yayi mai gadi ya bud’e masa suka shiga. Indo ta bud’e qofar mota tafita, hartayi nisa Haiydar cikin tsawa yace” kee tsayawa tayi bata juyo ba, cikin zafin nama ya nufota yana huci kamar zaki, da k’arfi ya k’ara cewa”Kee bakiranki nakeyi ba. Cikin razana Indo ta juyo sam batasan Haiydar ya tahoba, aeko jiyowanda zatayi, sai a k’irjinshi tasamu mzauni, Falmi ko jin muryan Haiydar yasa tafito, hmm dai-dai lokacin kuma Indo ta fad’a jikin Gaiydar bisa tsautsayi, Falmi wani razananen k’ara tasaki, tare da yi kukan kura tayi kansu. Ni ko Rash jin irin gurnanin da Falmi tayi yasa na arci na kare. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-96~100. Indo na fad’awa jikin Haiydar, wani sanyi da ni’ima yaji ga wani lafiyayen k’amshin dake tashi daga jijinta. Bai san lokacinda ya mayar da hannusa, yazamana ya mata rumfa, sosai ya matseta a jikinsa, take ya sake wani sassayan ajiyan zuciya. Indo ko jikinta ya fara b’ari, hawayene ya soma zubo mata, don tunda take a rayuwanta, namiji baligi bai tab’a ko da rike tafin hannuta ba. Haiydar ko sai wani shashafa bayanta yakeyi da d’aya hannusa, d’ayan kuma ya sauko dashi kan wuyanta, take yaji wani laushin da bai tab’a ji ba, duk farin da Falmi ke dashi da laushin jikinta, bai kai na Aisha Indo ba. Indo tana kiciniyar kwacewa sai dad’a kamata yakeyi, don Haiydar ya manta wani duniya yake ne d’aya, ko ni Rash dana leka fuskansa, ya wani lumshe ido, tankar mai bacci. Falmi ganin haka tayi wani kukan kura tayi kansu, Indo ta ta tsin kayo muryan Falmi, tak’ara kaimi gun tureshi. Amma shiko sai k’ara rungumeta yakeyi, Falmi da ta saki wani ihu ta k’araso gurin, wani naushi ta kai ma Indo, amma kash!! Cikin rashin sa’a Indo tasamu ta kwace, sai ta samu Haiydar a k’afa, Indo na kwacewa tayi cikin gida da gudu, d’akinta tashiga tasaka key a qofar. Falmi ko shan kwalan, Haiydar tayi tana ihu tana cewa” munafuki ae daman kana Sonta kake b’oyewa, maci a mana kawai, MAYAUDARI, butulu mai sakayan Quna da kiyayya, waya sani hala kulum d’akinta kake zuwa kuna iskancin ku. Kafin ta k’ara yin wani magana, Haiydar ya sauke mata wasu lafiyayun mari, tass! Tass! Tsss! Kakeji, cikin zafin rai yace”asai bakida hankali?. “Ni Haiydar kike ma cewa d’an iska?. “Innalilahi wa inna ilaihi raji’un, tunda nake bantab’a lalata yar wani ba. “Har zaki ambaceni da wannan mumuna kalma. Take idonsa ya canza kala tsanani bak’inciki nake hangowa a kwayar idonsa. Cikin kausashiyar murya yace”duk wani abunda ke faruwa ke kika haddasa. Falmi cikin mafifa tasake yo kansa da niyar kamasa da fad’a, yace” kik kuskura kika tab’anini hmm sai na lahira ya fiki jin dad’i. “Mtsss ya wuce yayi cikin gida zuciyarsa na masa rad’ad’i. Wannan wani irin masifa ne, d’akinsa ya tura ya shiga, kayan jikinsa yasoma cirewa yaji kashin jikin Indo ke tashi, har zai ajiye sai yabsamu kansa, da sanya rigan a hanncinsa, yana shakan daddad’an kamshinta, harda lumshe idanu, take abunda yafaru d’azu yasoma dawo masa. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [5/30/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-101~105. Manna rigan yayi a sai tin hancisa yana shak’an k’amshi, sai ya tsinci kansa cikin nishad’i. Hasna da Hajiya suka koma cikin gida cike da farin ciki, Hasna tace”Hajiya gaskiya naji dad’i wannan al’amarin. Hajiya tace”hmm ae ni nafi kowa farin ciki wallahi. “Sabida Aisha tana da nutsuwa a kalon dana mata. “Kuma haka kurum kalonta danayi sai ta tuno min da Lamid’o na. “Muryansu na tsananin kama, kai hatta murmushinsu iri d’aya ne. “Ko d’azu dana ganta shi kawai nake tunawa. Hasna tace” Allah ya shigan sa. “Hajiya dan Allah in Abba ya dawo in za’asa bikin nan kar asa da nisa. “Inason ayi a kare don gudun makircin matansan nan. Hajiya tace”makircinsu ya kare musu su kad’ai. “Yanzu na gane komai addu’a kam yanzu na fara masa da ikon allah. Haka har suka iso falo hiransu ta yai duk akan Indo da Haiydar ne. Falmi kuka taci agun da k’yar ta iya jan k’afarta zuwa d’akinta, wayarta ta d’auko ta kira Mum d’inta cikin kuka take fad’a wa Mum. Mum tace”jakar uba tun ba’aje ko ina ba?. “Ina fatan kin mata duka kin nakasata?. Falmi tace”tagun cikin d’aki ae. “To ki tabbatar kin bata najaki sosai. “Yanda ko gobe ance ta kali Haiydar bazata kaleshi ba. “Kiyi shiru gobe zanje gun Malam ya duba mana abunda zai biyo baya. Haka sukayi sallama, Falmi ranan ko wanka ba tayi ba ta kwanta bacci. Jikinta duk ba k’wari tafito falo, tun daga nesa takejin nishi, da sairi ta k’araso, turus tayi don abunda ta gani ya matuk’ar razanata, Indo ne sanye cikin wani mini skirts, ya matuk’ar kamata sosai, k’afanta d’aya na kan kujera, d’aya kuma Haiydar ya d’aura akan cinyansa, rabin jikinta yana nata, hannusa yana kan k’irjinta, sai sarrafa na fulaninta yakeyi, a hankali ya kai bakinsa kan nata, tsotsansu yakeyi kamar ya samu lollipop, yana wani nishi. Indo ko sai wani smiling takeyi, tana k’ara rungumosa, Haiydar cikinsanti yake cemata”Ina matuk’ar qaunaki, ke dabance acikin mata. “Tundanake kiss bantab’a jin dad’i irin yanda nake ji dak…….. Cikin k’araji ko salati babu Falmi ta…….lol…. Masu k’aratu sai gobe, maji yanda za’a kaya. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-106~110. Cikin k’araji ko salati babu ta farka, daga mumunan mafarkin datayi cikin baccinta, duk sassan jikinta rawa yakeyi, kasa hak’ura tayi, tana ga kamar abun da ta gani a mafarki, shi zasu aikata a zahiri. Da sauri ta duro daga kan gado tayi hanyar qofar falo, tsit kakeji ba kowa sai k’aran fanka. Wani ajiyan zuciya ta saki, tare da zuwa window d’akin Indo ta leka, Indo na kwance tana baccinta hankali kwance. ‘Dakinta ta koma ta kwanta itama. Haiydar ko da ya rungume rigan can kuma yayi tsaki”mtsss wai me hakan ke nufi?. “Ni bana son raini kar yarinyan nan tazo ta rainani. “Amma fa gaskiya yau tayimin kyau. “Kamar ba itaba wallahi. “Mtss to ina ruwana ma da kyanta?. A haka yayi wanka ya kwanta bacci. Hajiya Fiddausi taje gun boka, a duban da yamata, ha hango zallan koyayar da Haiydar ke ma Indo, don haka yace mata karta damu, su hak’ura ayi auren, don in basu bari anyi da Indo ba, to fa ba makawa sai yayi aure. Hajiya tana dawowa ta sanar da Falmi duk abunda ake ciki, amma tace”karta ragarmata, ta yanka mata kazan wahalan da bazata iya figewa ba. Indo ko wasan b’uya suka shiga yi da mutanen gidan, dan tabbasa tasan abunda ya faru, Falmi bazata kyaleta ba. A gidan Hajiya kuwa Abba ya dawo ta sanar masa da komai. Yace”zaiyi bincike akan yarinyan, bayan kwana biyu da yayi bincike, duk wani labari ya samu gameda zaman gidan su Falmi, ta hankalin Aisha ila dai rashin mahaifinta da basu saniba. Hakan bai damesa ba yana dawowa gida ya mayar ma Hajiya, yace”inaga bikin nan da wata guda kawai, inyaso komai da uba ke ma yarsa, ni na d’au nauyi zanmata. Hajiya cike da murna ta masa godiya, Haiyadar suka kira sukace”yazo yasamu Abban sa, zasuyi magana da shi. Haiydar da yazo Abba yace”mun tsayar da biki nan da wata d’aya dan haka kaje ka fara shiri. “Sannan zansa a gyara maka gidana da ke bayan Airport nan zaku zauna tunda part biyu ne a gidan, kuma tsarin gidan yayi kyau. Haiydar godiya yayi ya tashi ya fita. Hajiya ta mik’e tabi bayansa, a falo ta samesa, ta zauna ya kara gaidata ta amsa, tace”kaji yanda al’amarin ya kasance ko?. “Dan Allah inaso ka d’au komai da sanyi wataran zakayi alfahari da auren nan. “Sannan ina son ka kawo kud’i zamuje mu had’a kayan lefe dana fad’an kishiya. Haiydar cikin girmamawa yace”to zan ciro kud’i zan kawo muku. Hajiya ta sanya masa albarka ya mata sallama.ya tafi. Bayan kwana biyu, Hajiya ta aika Hasna ta je ta d’auko Indo, da duk abunda take da buk’ata, don in ta bar gidan Falmi, ta tafi kenan sai in sun had’u a gidansu. Hasna jiki na b’ari tayi wanka ta d’au hanya, tafiya mai d’an nisa tayi kafin ta isa gidan, horn tayi mai gadi ya bud’e mata, tashiga da murnanta tayi sallama. Turus ta tsaya sakamakon ganin Falmi da tab’arya a hannuta, tana tsaye a qofar d’akin Indo tana son ta shiga ta kwad’a mata. Hasna tace”Aunty Falmi lafiya kuwa?. Cikin fushi ta huyo tace”to bak’ar munafuka algun-guma. “Har wani tambayan lafiya kikeyi? “Bacin duk wani muna furcin da ake had’awa dake ne, da tdohuwar uwar ta…. Bata k’arasa ba taji saukan, lafiyayyen mari a fuskanta. Cikin zafin rai ta d’ago da niyar kwad’a ma Hasna tab’arya don a zatanta Hasna ce ta mareta, amma me cikin mamaki take kalon wanda…… DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH KARDAM [5/31/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-111~115. Cikin mamaki take kalon Haiydar yau ita zai mara a gaban Hasna ga Indo, shikenan ai raini kam yagama jan mata yau, cikin muryan kuka tace”Haiydar ni ka mara?. “Kamaren? “Lallae yau zakasan ka maren?. Haiydar yace”na lura bakida kunya wato?. “Duk iskancinki ya tashi a kaina harda uwata ko?. “Don akan auren da ba so nake ba?. “Mtss ki sani ni uwata ta isa dani dole ta ban umarni nabi. “Kuma duk randa kika k’ara zaginta sai kinga abunda zan miki wallahi. Kalon Hasna yayi yace”kekuma mai kika zo yi ne?. Hasna tace”Hajiyace tace nazo in tafi da Indo. Kafin Haiydar yayi magana Falmi tace”ai daman na fad’a bakinku d’aya gashi nan. “Yauko ba wanda ya isa ya fita da Indo a gidan nan. “Tunda ni na kawota a k’ark’ashina take. “Kuma dalilina kuka santa, dan haka ba wanda ya isa ya fita da ita. Haiydar yace”kinyi k’arya mahaifiya ta ke son ganinta dole taje ta. “Don na san darajanta. “Hasna zo ki mata magana ku fita ina nan gurin. Falmi ta gyara d’amaran skit d’inta, tace”inga mai fitan da ita yau?. “Shege ka fasa, yau ko ni ko Indo. “Wai dad’in abun ma shegiyace, a titi akayi cikinta yar kwararao ne. Ran Haiydar sai tafasa yakeyi, don yatsani kalman cikin shrge ko yar shege. Hasna tasaka Indo ta b’ud’e qofar d’akin, sai kuka takeyi sosai. Hasna tace”Aunty ki tattara duk wani abunda kike buk’ata, don in kin tafi bazaki dawoba. Indo bata iya tanka mata ba sai kukan da takeyi, Hasna ce ta taimaka mata suka had’a kayanta, a yar madai- daiciyar trolley d’inta suka jawo zuwa falo. Indo ko sai kuka takeyi, kalo d’aya Haiydar ya mata yaji ta bashi tausayi, yaune rana ta farko da Haiydar ya fara tausaya mata, Falmi tana ganin sun fito tayi kansu, cikin zafin nama Haiydar ya samata k’afa ta fad’i, kanta yayi ya mata kyakyawan runguma, yanda bazata iya kwaceba. Hasna su ganin haka suka fita. Haiydar sunsha rigima da Falmi sosai, don daga k’arshe kuleta yayi a d’aki ya fita abunsa. Hajiya kaya na dai-dai misali suka had’ama Indo na lefe, a kwati hud’u da kit, sai kuma Falmi sun mata biyu da kit itama. Hajiya damtse ta zage gurin gyara Indo, Haiydar ko abun duniya ya ishesa, don sam bai son wannan aure. Shiyasa ma ko ya fad’a ma wani yayi shiru, Hajiya ko ganin haka tasaka a ka kira mata abokinsa, Sadiq ta sanar masa, tace”ya kuma shirya duk wani abumda ake buk’ata, zata bada kud’in. Yau ya kai kayan fad’an kishiya suka nufi gidan Falmi, da Sallamansu suka shiga. Hajiya Firdausi da ke kitsa ma Falmi makirci, ta amsa musu, cike da mamaki suke kalonsu, Aunty Rahma ce tace”daman kayan fad’an kishiya muka kawo muku. Falmi ta zabura ta mike tace”kayan fad’an me?. Aunty Rahma tace”kayan fadar kishiya ko bakiji bane?. Hajiya ta mik’e tace”ke kale mu daga sama har k’asa waye matsiyaci. “Mai zamuyi da wannan d’an tsiyakon kayanku?. Falmi ta mik’e tare da d’eban kayan ta fara watsa ma su Aunty Rahma. Masu karatu kumin afuwa na rashin jina yau, ina busy ne amma in Allah ya yarda, zan tak’aita labarin nan mugama kafin azumi. Sabida wasu na min message, da qorafin a gama kafin azumi, zanyi iya yina inga na k’arasa, In Allah ya so hakan. Khaleesat Haiydar Novel facebook, ina mik’a godiyata mai tarin yawa, comments d’inku, shi yake k’ara bani k’arfin gwiwa. Whatsapp members kuma ban manta kuba nagode dayawa, Allah ya bar zumunci Ameen. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH KARDAM [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-116~120. Falmi ba kalan rashin mutuncin da basuyi masu Aunty Rahma ba, amma suka kyalesu suka fita a gidan, batare da sun d’au kayan fad’ar kishiyan ba. Indo ko tun tana d’ari-d’ari da Hajiya har tazo ta sake da ita, sam Hajiya bata d’auketa matsayin surkaba, sai dai matsayin d’iyarta. Hasna ko sai rawan kai aketayi, duk wani d’inkunan da Indo zata saka, ita ta kaita gun telan ta, ya ciremata mayun d’inkuna, masu kyau sosai. Hasna ta gayyato k’wayenta Pinky lady da Cutie, sabida Indo bata da k’awa ko d’aya. Hasna ta samu Sadiq shiya basu kud’in events d’in da zasuyi. Walima suka shirya sai kamu, da fulani day. Sadiq kuma dinner da kuma bikin paret d’in police. Tun daga ran laraba aka fara Fulani Day sun tsara gurin yanda ya kamata, su Hasna da Cutie tare da Amarya sun sanya kayan Fulani, sunsha kyau ba kad’an ba, bare daman fulanin asali ka., ae ba’a cewa komai sai wanda ya gani. Duk wanda ke gurin ya girgije, an raba k’warya masu kyau da ado, sai ludaya da bulogari, da nono kindirmo mai kyau yaji fura, hmm masu karatu ko ni Rash danaje gurin sai dana shaida hakan, ga rawan fulani da yan sandunan su kaika d’auka wani k’aramin rugan Fulani ne. Haka taro ya watse kowa cike yake da murna, bayan sun dawo gida Hasna ke kalon photo da ta d’aukesu a waya, tana yaba kyan da sukayi. Yan’uwan Hajiya na Gombe sunzo duk wanda yaga Indo to sai ya tuna da Lamid’o, dan tabbas baza su mantashi ba sunyi rashi a family d’insu, don duk irin dukiyar da Sarkin Fulani ya tara ace baya da magajinsa namiji, sai Hajiyar su Haiydar kad’ai ta rage masa, wannan abun yasa baya yawan magana da mutane, sabida rashin Lamid’o don duk cikkin ‘ya’yansa yafi sonsa fiye da kowa. Falmi ta kaici ya isheta, da k’yar ta kira su Meesha ta sanar musu halin da take ciki, Meesha ta jin-jina al’amarin nan tace”zanzo sai ran yini don yanzu bana gari na tafi Kaduna. Haka sukayi sallama, Falmi duk ta rame sosai, abunci ma bata iya cinsa mai kyau sosai, baran in ta tuna cewa Yar’aikinta ne zata zama kishiyanta, nan take zuciyanta ya d’au suya da k’una. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR). RASH KARDAM [6/2/2016] Rash Karda BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-121~125. Nan take Falmi zataji zuciyarta ya d’au k’una yana mata rad’ad’i. Gashi Hajiya Firdausi tace”ta hak’ura boka yace, suna da nasara tunda yar aiki ce. “Kuma Haiydar ya tsaneta Falmi yake matuk’ar qauna, a zuciyansa. “Kuma bazai tab’a sin Indo ba. A gidan Hajiya kuwa yau akaje akayi jere ma Indo, d’an kayan rufin asiri suka mata bak’arya, side d’inta ita d’aya da d’aki biyu, sai kitchen da store. Komai yaji dai-dai, gidam kam ya tsaru ba laifi, don a tsakar gidan ga swimming pool, ga garden, da wajan wasani abun gwanin nurgewa. Yautake Alhamis duk inda ka leka a gidan su Haiydar, anata kamu ne, kawayen amarya sunsha kyau, suna sanye cikin wani material baki da ash colour, sunyi kyau sosai, sai da aka debi mutane tukun aka kawo wata k’atuwar Jeep ciki za’a d’au amarya. Niko Rash zuba ido nake inga fitowar wannan amarya mai ji da kyau. Mutane naga suna ta d’aukar hoto, da sauri na mik’e, ina zuwa kuwa na hango amarya cikin kayanta, less ne dark ash da silver colour, ohohoho masu k’aratu, gaskiya in baku ga Indo a wannan rana ba, to kalo ya wuceku, don da kyar na iya gane cewa Indo ne, yar wanke- wanke da shara, don yau inda Falmi zata ganta, inaga sai zuciyarta ya buga. Cikin takun nutsuwa su Hasna da Pinky suka rike hannuta, yayin da Cutie ke gabansu, har suka isa mota. Larema hotel sukaje, gurin ya tsaru sai wanda ya gani, a cikin kwanciyan hankali aka gudanar da komai, Sadiq wasu abikan ango suka kirasa suna yabamasa irin tsabin da su Hajiya suka masa, gaskiya tayi bana wasa bace. Shiko haushi suka basa ma, ana haka har aka kammala kamu, suka dawo gida cike da murna, kasancewan gidansu Haiydar na da girma side guda aka bama yan biki, basa ta cikin gidan side d’insu daban. Hajiya ce ta kira Haiydar, bayan yazo ta masa nasiha sosai, gameda rike mata biyu, Hajiya tace”Haiydar na sanka da zafin zuciya ka k’ara hak’uri da halin Fatima. “Don rashin kunya da kishi suna damunta, amma dan Allah kayi hak’uri. Sai da sukayi hira sosai yace”zai tafi a kwai wanda suke jiransa, ya mik’e ya fito. Hasna ko sun dawo sallah sukayi nan suka soma hiran yanda biki ya kasance, Hasna ta mik’e barinje na karbo mana sakon da Aunty Rahma ta bari. Shiru- shiru Hasna bata dawo ba, hakan ya sa Falmi ta mik’e don taje gun Hajiya taji ko tananan, kanta ko d’an kwali babu, gashi yasha gyara, gashinan yazubo har gadon bayanta, cikin karai-raiya take tafiya mai d’aukan hankali. Tazo dai-dai corridor d’akin Hajiya aka d’auke wuta, laluben hanya ta fara tana kiran sunan Hasna, sam bata lura da mutum yana tahowa ba, sai ji tayi ta rungumi mutum, cikin tsoro da ta gudu, Haiydar dake ya ganeta, sai ya tsinci kansa da kara rungumeta, harda sakin ahiyan zuciya. Duk jikin Indo ya d’au bari, ga k’amshin turarensa ta cikata, da sauri da sauri k’irjin Haiydar ke bugawa, hannusa d’aya, ya sanya cikin gashinta yana wasa dashi, cikin zuciyarsa ko cewa yake”duk da gashin Falmi amma Indo ta fita sosai. Sunkuyo da kansa yayi dai-dai hab’arta, ya tallabo, yana mai kalon fiskanta duk da duhun da ke gun, d’an k’aramin bakinta nan ne ya burgesa, bakinsa ya kai kusa danata kenan, Nepa ne suka kawo wuta dai-dai lokacin take wajan ya gauraye da haske, ni Rash ina d’aga kaina wa zan gani…….. Sai kunji ni gobe in dama tasamu, in kuma bansamu yin typing ba, sai bayan Sallah in Allah ya kaimu. Taku a kulum mai qaunarku Rasheedah Abdullahi Kardam DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH KARDAM [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-126~130. Haskene ya mamaye ko ina nacikin corridor d’in, da sauri ya kali fuskan Indo hawaye ke sauka, yana d’aga kai yaga Husna tsaye zata fito daga d’akin Hajiya. Take ya ji haushin kanshi, cikin zuciyarsa ko cewa yake”wai me ke shirin faruwa dani ne?. Hannusa da ke rike da Indo yayi saurin tunkud’ata, sai data kai har kasa ya tsata mata yawu, Hasna kuwa wani mugun harara ya wurga mata, wanda yasata komawa d’aki bashiri jikinta harna b’ari, don ta san halin Haiydar in ransa ya b’aci bayida sauki. Sai da taji ya banko qofa alamun ya fita, kafin ta fito da sauri tayi gun Indo, ta kamata ta d’agota tace”Aunty na dan Allah kiyi hak’uri da halin Ya Haiydar. “Watarana sai labari kinji. “Kuma ga dukkan alamu ya Haiydar na sonki amma shi kansa bai san haka ba. Indo kam in banda hawaye ba abunda takeyi, haka har suka koma cikin d’akin, Indo kaya ta cire tasaka na bacci ta kwanta, amma sam ba bacin take ba, sai tunanin irin wulakancin da Haiydar ya mata. Wata zuciya tace”Indo ina ke ina Haiydar. “Inake ina iya kishi da Falmi ko kin manta suwaye Falmi?. “Ke fa ba kowa bace face yar aikin gidansu. “Marar asali bakida gatan ki sai Allah. “Bakisan kowa ba. Wani zuciya kuma yace”a kul d’inki Indo, guduwa ba naki bane. “Kina d’iya mace kinsan inda zakije ne?. “Ta iya yuwa kije gunda za’a b’ata miki rayuwanki. “Kawai dai ki hak’ura har Haiydar ya gaji ya sakeki. Ajiyar zuciya ta sauke tare da k’ara lumshe idonta, tare da tuna abunda ya faru dazu. Washe gari da safe, aka tashi da aiki sosai, don ranane ran d’aurin aure. Abba saida ya yanka saniya, Hajiya ko baki har kuni, don murna. K’arfe d’aya da rabi bayan Sallah jumma’a dubban mutane suka sai da d’aurin auren Aisha Muhammad da agonta Aliyu Khaleed Baba(AK Baba) da Amaryansa Aisha Muhammad(Indo). Akan sadaki naira dubu sitin 60k. Bayan d’aurin aure ne, jama’a suka wuce Sogiji Hotel don gudanar da Waliha, duk wanda yaje gun yaci ya sha, sai fatan Allah ya basu zaman lafiya, tare da k’azantan d’aki. Haiydar tun daga nesa na hango shi, cikin fararen shadda da gare, ya matuk’ar yin kyau tamkar bashi ba, fiskan nan tashi ba yabo ba fallasa, duk yanda naso in gane wani abu, amma dul yanda naso na kasa tan-tace, yau farin ciki yakeyi ko bakin ciki. Haka suka kammala kowa ya kama gabansa. Ango ko ya nufi sabon gidansa, inda Falmi da kyar ta koma, don cewarta ita sai dai ya barta ita kad’ai, da kyar ya lallab’a ta takoma, sai da ya zuba mata kud’i masu yawa kafin ta yarda ta koma. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH LUV 6/3/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-131~135. Haiydar sai bayan la’asar ya nufi gida, tun a falon Falmi yaji muryan yan’uwanta, sai ya fasa shiga d’akinsa ya nufa ya cire manyan kayan, ya shiga bayi ya watsa ruwa, yana fitowa ya tsane jikinsa ya saka kaya maras nauyi don ba inda zai je. Kwanciya yayi ya d’auko wayarsa Falmi ya kira, wayar sai ringing takeyi amma taki dagawa, don wani masifan haushinsa takeji kamar tayi hauka. Nasiba tace”Falmi ki d’auka kiji mai ze ce miki, ai yanzu ne lokacin da zaki zuba mulkinki son ranki a gidan nan. Kowa da kalan nata munanan shawaran, Falmi ta d’aga wayar tace”hello ina jinka. Cikin isa take maganar, Haiydar yace”My Luv bazakizo ki ga lafiyata ba?. “Gani sai tunaninki nakeyi nakasa samun sukuni. “Mtssss to mai zan maka bacin ga amaryanka ba sai kaje gunta ba. “Ai tana da abunda kake buk’ata sai ta baka. Kawshe wayar tayi suka tafa tare da shewa, Nasiba tace”shawaran da zan baki duk yanda zakisan yanda zakiyi kar ki bari yaje gun dinner nan. Falmi tace”Nasy taya zan hana shi zuwa gun dinner?. “Mtsss haba Falmi sai kace ke ba mace ba. “Kisan duk wani hanyan danzakibi ki hana sa zuwa. Nuwairay tace”kin san mai zakiyi Falmi. Cike da k’osawa tace a’a. Nuwairat tace” yanzu in ya sake kiranki ki d’auka ki gwada masa kin sauko, amma kice kina tare da baki, ya d’an jiraki. “Sai ki bari dab da magriba kiyi kwaliya ki tafi d’akinsa, kar ki bari ko sallah isha’i ya fita waje. “Ki nuna masa salonki ki kuma nuna masa kina da buk’atarsa yanzu, ko da kunyi ki nuna bai ishe kiba, kin ga ai dole bai son bacin ranki dole ya hak’ura. Shewa sukayi da tafawa Nasy tace”shegiyar kin kawo idea fa. Ana haka ko sai ga kiran Haiydar haka Falmi ta d’auka ta rinka fad’amasa kalamai masu dad’i, tace”Honey ina tare da baki barin sallamesu zanzo mu gaisa. Ko da ankira magriba karka fita kayi a gida, ko in kaje ka dawo ka jiran zamuyi magana. Haiydar cike da murna ya amsa mata da”ba komai ni yau ji nake kamar nafi kowa farin cikin, tunda kin bar fushi dani. Haka sukayita hira daga k’arshe sukayi sallama. A gidan Hajiya ko bayan d’aurin aure, da yamma walima suka shirya na gani na fad’a, komai cas-cas, akayi walima aka tashi, da daddare kuma zasuyi dinner. Tun bayan sallah magriba suka soma shirin dinner, amarya na hango cikin fafaren net yayi matuk’ar yi mata kyau. Abun gwanin burgewa, ana kiran Sallah isha’i sukayi sallah suna jiran zuwan angwaye. Falmi bayan sallah magriba wanka tayi na musamman ta sanya wani riga iya gwiwa, daga gefen cinyan a tsage yake, bata sanya bra ba, duk wani sassan jikinta kana gani. Kayan sun haska jikinta dake fara ne, dai-dai lokacin Haiydar ya fito daga wanka d’aure yake da towel, ganin falmi da sauri ya k’araso gunta, janta jikinsa yayi, yace”Honey nayi misin d’inki kwana biyu. Hannuta tasa tafara wasa da sajensa da ya kwanta luf-luf gwanin burgewa, cakul-kuli tasoma masa, dariya yayi yace”wato yau tsokana kikeji ko?. Hannu ta kai tasoma ware towel d’in da ke jikintsa, wasa yasoma yi da gashin kanta, ganin tsayuwa ba zai d’aukesuba ya d’auketa cak sai kan gado, yasoma mata wasani sai da abu yayi nisa Falmi tasoma jan jikinta, komai ta tuna ta tashi zata mik’e, ya kamo hannuta cikin dashashiyar murya yace”Honey miye haka? “Kinsan ina tsananin buk’atarki a wannan lokacin. Wani banzan kalo ta wurga masa da niyar mikewa ta fita, cikin azama ya diro tare da kaimata wani kyakyawan cafka. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR). RASH KARDAM [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-136~140. Cikin hanzari ya kaimata cafka, yayi sa’an riketa, Falmi tayi ta kwace takasa, kuka tasoma masa duk ya rikice, sakowa yayi ya mata nil down ya riko hannuta yace”haba Falmi na mai na miki kike hukuntani ta wannan hanyan?. “Shin kaki tsoron kamun Allah Falmi?. “Kisani ko dai-dai da seconds daya kika tutarni a wannan harka Allah zai saka min. “Kulum cikin azarbtar dani kikeyi Falmi. “Ko so kike in fara bin matan banza. Wani kalon ko oho ta aika masa cikin muryan kuka tace”Aliyu in ka ga dama ka kama d’aki a bayan gari ba ruwana. “Kasani da *KISHIYAR GIDA GWARA TA WAJE* na tsani in gani da wata matsayin matarka. cikin kuka tace” ni daka auro min Indo gwara ka ringa bin mata a wa…. Bata k’arasa ba taji saukar lafiyayen mari a fuskanta, cikin huci yace”Falmi asai baki da hankali?. “Asai bakisan mai kikeyi ba?. “Tabbas na yarda bakisan ciwon kanki ba. “Kinga ina lallab’aki ko don kibani hakkina. “To wallahi ta karfi zan ringa karb’a yanzu, banza kawai. Falmi ba k’aramin tsorata tayi da yanayin Haiydar ba, qofar d’akin yaje ya zate key d’in ta sanya a saman Waldrop d’insa, ya suma bin Falmi tana hawaye suka soma kokawa da kyar Haiydar ya samu ya wurgata kan gado, Falmi ta fara ihu, kamar k’araman yarinya, cikin b’acin rai yace”keee baki da hankali ko? “Yau ko a gaban wakike sai na karb’i hakkina, Haiydar da iya karfin sa ya zage yake abunda yakeso. Niko Rash ina ganin haka na tattaro yan matan kafata na fito. Su Indo sun gama shiryawa shiru ba labarin ango, har an kai wasu a mare cikin *LAREMA HOTEL* anan za’ayi dinner, ya rage daga cutie sai Hasna da pinky suma yanzu saurayin Pinky Nura yazo d’aukarta, sai Hasna da Cutie Sadiq zai tafi dasu. Ana haka saiga Haugal ta iso ita da Ghalinta,(masu karatu ina fatan baku manta da Haughal ba ko?. Nacikin litafin *BAZATA*). Ghali yaje gunsu Sadiq yace”wai ina Man d’in ya shiga ne?. “Tun zamu taho nake ta kiran wayansa bai d’aga ba. Sadiq yace”wallahi muma hakane amma bari zamuje gidansa muduba shi, daga nan sai mu wuce. Jiddah da sallama ta shiga gidan, da su Hasna ta gamu da su, cikin girmamawa Hasna tace”lah! Aunty Jiddah kin isone? “Jiddah tace”eh yanzu muka zo. “Hasna tace”ina Uncle Ghalin”yana waje yanzu zanje muwuce kenan. Jiddah tazo kusa da Indo tace”amaryan mu kinsha kyau bari mu fara gaba sai kun iso. Indo murmushi ta iya mata don tana gabda yin hawaye, sabida tasan daman Haiydar ya tsaneta wahala zatasha ba kad’anba. Haughal ta fita zuwa gun Ghali don su wuce gun dinner. Sadiq yace”Ghali bari muje gidansa kawai mu duba sai muga ko lafiya ne. Ghali yace”ok hakan za’ayi. Sadiq ya kira Hasna yace”ku fito da amaryan kawai mu wuce. Da kyar Indo ta fito don hawaye take amma sai kalura ka gane hakan, suka sakata a motar da za’a kaita Cutie a da Hasna motar Sadiq Hasna ce a gaba sai cutie a baya. Pinky kuma Ya Nuranta. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR) RASH KARDAM [6/3/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-141~145. Suka d’au hanyan gidan sa, Indo ko in banda hawayen takaici babu abunda takeyi, tana rokon Allah ya kawo mata d’auki a rayuwanta. Haiydar ko bai kyale Falmi sai da ya tabbatar ya gamsu sosai, ya mike ya shiga wanka. Bayan ya fito yayi Sallah isha’i kenan ya d’auko wayarsa, mai zai gani 60miss call na Hajiya 20 na Sadiq 46, sai na Ghali da wasu abokansa, sam ya manta da zasuje dinner sai a lokacin ya tuna, cikin hanzari yasa d’anyar boyal d’insa mai ji da shek’i, ya kawo agogon hannu ya d’aura ya sanya takalminsa, ya d’auko hularsa itama fara yazo gaban miro ya na d’aurawa, Falmi dake kwace jiki ba k’arfi ta mike cikin zuciyarta ko cewa take”nayi ma kaina gashi ban hanasa zuwa dinner ba, gashi ya gurjeni son ransa amma dole na b’ata kwaliyan nan kuma bazaije ba. Tana d’ingisawa tazo ta tare qofan fita Haiydar ya gama shiryawa yazo zai wuce tace”baka isa ba yau kaje dinner auren wata marar asali. “Yar titi kuma tsintaciyar mage bazai yuwu ba. Haiydar yace”kiyi hak’uri ana jira na kuma kinga mutane sunzo doni ne. “Ni badan Yar aiki zanije ba. “Sabida mutanen da suka taru domin ni zanje in fita kunya. “Falmi kinsan ina matuk’ar qaunanki. Falmi tace”k’arya ne *MAYAUDARI* maha inci kawai. “Da kana sona bazaka yarda ka auri Indo Yar aiki na ba. “Haydar yau ko ni ko kai don ba inda zakaje maci *AMANA* kawai. “Ka kasa rike *AMANA TA* da iyayena suka baka. Ganin zata b’ata mishi lokakaci ya d’auko key zai bud’e qofa tazo ta rike hannu qofar. Ganin bata da nutsuwa a tare da ita, kuma ya mata magana duk taki fahimta. Wata zuciya tace”bata k’yak’yawan mari zata fi fahimtan wannan yaren. Sai da ya gyara hannusa ya bata lafiyayen mari, take Falmi takoma gefe don sai dataga wasu Stars suna mata shining. Haiydar ya bud’e qofa har yafito harabar gidan yana shirin sanya k’afarsa waje kenan, Sai ga su Sadiq nan suka fara tambayamsa lafiya?. Sadiq ya fara masa surutu Haiydar yace”mutafi lokaci ya kure. Yazo sai shiga mota kenan, Falmi ta fito da gudu ta rik’e murfin motan tana cewa”yau ba inda zakuje indai inanan. “Alo tsiya alo danja ba mai fita da kai. Cikin takaici ya tureta ya rufe motar. Falmi batayi k’asa a gwiwa ba ta je ta tatare gaban motar tabaje tana cewa”yau sai dai in ta kaina zakubi ku fita ehe. “Sai ku kasheni in huta. Haiydar bai ma lura da Indo da take gefe tana hawaye ba. Takaici duk ya ishesa da kunya, gashi a gaban abokansa. Sadiq ya mata Horn amma taki matsawa sai ihun da take kurma musu kamar masu satan mutane. Cikin zafin rai Haiydar ya bud’e qofar mota. Ga d’an wannan ina samu lokaci zakujini da daddare in nasamu lokaci, in bansamu ba kuwa sai bayan *SALLAH* In Allah ya kaimu da rai da lafiya. DEDICATED TO AISHA MUHAMMAD (MAMAN ABDUL SHAKUR). RASH KARDAM [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-146~150. Sam Haiydar bai ma lura da Indo, da take gefe tana sharan k’wala ba. Sadiq ya mata horn amma Falmi taki matsawa, sai ihu take musu kamar wacce tayi hauka. Cikin zafin rai da qunar zuciya Haiydar ya bud’e murfin motan ya nufota, kasancewan gidan da hasken k’oyayen wuta, yasa ta ga Haiydar ya nufota. Sai data ga ya kusa da ita da sauri ta mik’e taje jikin motar ta bud’e side din da Indo take, ta soma shiga duk ta buge indo ta ture ta, tana shirin haye kanta ta zauna ne Haiydar ya finciko ta, cak ya d’agata tana turjewa sai da ya kaita dakinta, yasaka key ya fito. Duk ta ya mutsa masa kayan jikinsa. Takaici goma da ishirin ya had’u masa, zuciyar sa sai rad’ad’i take masa tamkar zata fito waje. Ji yake ina ma da zai iya kuka, tabbas da yaji sassaucin zafin da zuciyar sa ke masa. Da k’yar ya janyo k’afarsa ya shiga mota, sai a lokacin ya lura da Indo da ta had’a kai da gwiwa tana rusan kuka. Nan yaji wani sabon bak’in ciki ya tur nukesa. Shi kenan shikan yazu ya rasa farin cikinsa, ga auren yar aiki, ga Falmi ta rikice masa. Bai san lokacin da yasaki wani tsaki mai k’arfi ba. Haka aka ja motar duk da sun makara, suka nufi gun dinner, mutane har sun soma tafiya, MC ya fara magana da ayi a hakuri, a zauna ga ango sun iso. Sai da abokai suka shiga, ya rage daga Ghali sai Jiddah da Sadiq da Hasna, Su zasu shigo da Amarya da Ango. Amarya da Ango a gaba, sai abokai a bayansu, bayanda Ghali baiyi ba akan Haiydar ya rike hannuta fir yaki. Harda d’an matsawa gefe, ya bar tazara a tsakaninsu. Jidda ta jawo Ghali tace maasa” kasan me kai ka dawo gefen Ango, ni zan dawo gefen Amarya, in munzo dai-dai qofar shiga ka d’an ta kurasa. In hanyar yaji ya takura, dole zai matsa ya mannu da Amaryan. Hasna kuma saita san yanda zatayi, ta manna hannusu guri guda, nasan ba haufi zai rike hannuta. Aiko haka akayi Jiddah ta cike gu, wanda yasaka Indo matsawa kusa da Ango, shi ma haka Ghali ya masa, dai-dai lokacin DJ ya sake musu kidan Loakcin kine yayi Amarya yar *AMANA*. Kasancewar Haiydar na son wak’ar, bai san lokacin da ya saki lallausar murmushi, wani farin ciki ya ratsa zuciyarsa, yasoma bin wak’ar a hankali. Hasna ko hannu Indo ta kama ta d’aura kanna Haiydar. Take yaji wani sanyin dadi ya ratsa zuciyarsa, sai ya samu kansa da k’ara rik’e hannun. Ya d’an janyota jikinsa, sabida laushin fatarta da kanshim da ke tashi a jikinta, ya mantar da shi da wa ma yake tare. Indo ko sai niman zillewa take, don tun da take in banda ranar da suka dawo daga gidansu Haiydar yayi hug d’inta sai ranar walima, namiji bai taba mata irin wanann rikon ba, sai yau. Shiko sai janyota yakeyi cikin jikinsa. Masu k’aratu karkuga yanda suka burge, suna sanya k’a farsu cikin Hall d’in, masu d’aukar photo suka fara, Jiddah tace”ma Hasna bari kuga next target d’in mu. Hasna yi sauri ki d’an zo kusa da Aisha, kin ga ta kalminta na da tsayi, ki d’an samata k’afa kamar zata fad’in, zai taro ta tunda kinga rabin jikinta ansa yake, ba zai bari ta fad’i ba. Ina son ayi shooting d’insu a haka don ya isa gun Falmi, ni kuma zan d’aukesu da IPhone d’ina. Sai ki tutura masa a wayansa. Hasna ta d’aga ma Jiddah hannu, ta sara mata alamar target d’in yayi. Hasna ta yi saurin sanya ma Aisha Indo k’afa sai gata zata fad’i, da sauri Haiydar ya tarota, ya rik’ota duk gaba d’aya ajikinsa take, ita kuma ta rufe ido ta sadak’ar fad’uwa zatayi, shiko kallonta yakeyi, da d’an k’aramin bakinta nan, mai d’aukar hankali. Sam ya manta ida suke, sai ji yayi ya samu kansa da yi mata kiss a lab’en bakinta. Haiydar sai da ya wani lumshe ido, azuciyar shi ko cewa yake”tabbas mata suna suka tara. Don kiss d’in da yayi ma Indo, wani laushi yaji a leb’en bakinta, ga k’amshi gamida zaki. Jama’an da suke hall d’in, abun ba k’aramin burgesu yayi ba, take suka saka sowa da ihu. Masu camera kuwa suna kan aikinsu, haka Jiddah ma ta d’aukomai harda yin editing. Abun sai wanda ya gani, Don ko ni Rash sun burgeni, amma ina tunani photo nan in ya isa gun Falmi da k’aramar yaki. Haiydar cak ya d’aga Indo, bai ajiyeta ko ina ba, sai kan kujeran da aka musu mazauni, ya sak’aka hannusa cikin nata. Hasna da Jiddah ko sai murna suke, don ba wanda zai gane cewa Haiydar ba son Indo yake ba, niko Rash na tab’a k’awata Lovely Aisha Mazoji nace”Lovely kin ga kirsan mata ko, da kirsa da dabara Jiddah tasa Haiydar ya manta k’iyaya, ya shagala da soyayya. Aisha Mazoji tace”taya ni gani kam, kuma in an tab’ashi, ya iya kurin baya son bak’ar mace, sai gulmar tsiya. “Kiga yanzu a gaban mu harda mata kiss fa. Nace”hmm kedai bari kawai zamuga yanda wannan drama zai k’are. *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [7/4/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-151~155. Haka aka gudanar da dinner kowa cike da farin ciki, Haiydar kam tun da ya rike hannu Indo ya kasa saki. Sai da aka gama taro suna sauk’owa Sadiq ya kasa hakuri yazo kusa dashi, yace”ASP Aliyu Khaleed Baba. Sai da Haiydar yayi murmushi yace”Haka sunan yake A.K Baba. Sadiq ya cigaba da cewa “gaskiya yau naga lurv, wato wannan kiss d’in ma duk acikin kiyayyar ne ko?. “Da tsanar bak’ar mace. Sadiq yana wani shu’umin dariya Hasna da ke gefe itama dariyan tafara, sai alokacin Haiydar ya dawo hayyacinsa, ko kalon gunda Indo take baiyiba, ya tureta wanda k’ad’an ya rage ta fad’i, Hasna ta taro ta. Ghali yace”kaga Man d’in nan kora kunya da hauka zaka mana. Ko sauraronsu baiyi ba ya nufi mota. Indo ko daman atakure take don tayi hawayen har ta gaji, ba wanda ta bari ya gane kuka take, ta b’oye har aka gama taro. Hasna ta rikota, tazo zata sata motar da suka zo, Haiydar ya daka mata tsawa”kee ina wasa dake ne?. “Ni sa’anki ne?. Sadiq ya iso gunsu yace”mai kake nufi ne?. “Da wani mota kakeso tashiga?. Cikin harzuk’a Haiydar yace”in dai zata shiga motar nan sai dai in koma a qafa. Gannin yanda ya yake masifa, yasa Sadiq ko magana bai k’aramasa ba, Yace”Hasna kushiga mota in mai daku gida. Hasna ta rik’o hannu Indo suka shiga mota sai gida. Haiydar ko kansa ya jawo ya dawo gida. Ransu Ghali ya baci sun bar masa motan suka tafi. Ko da ya dawo gida dakinsa ya nufa ya kwanta, baibi ta kan Falmi ba, bare yaja ma kansa magana. Washe gari a harabar gidansu aka shirya crossing sword, police ne suka sha kakinsu da mopol, sai wasu friends d’insa yan *WAI BURGET* su kuma sun sanya kaya Green white green. Abun dai sai wanda ya gani. Police sun cire yan Colour paty da yan Sub gard n gard Commander. Haka yan WAI ma. Ba abunda ke tashi a filim sai kid’an Band, har wata yar waka suke musu, da busa mai dad’in sauraro. Amarya na hango cikin shigar cut less mai kalar blue da baki, sai handbag da takalmi blue da baki. Ta sha gwagwaro tayi kyau sosai da sosai. B’ab garen Falmi ko dak’yar su Meesha lurv da Xhara BB, su tursasata tasaka less light pink, gata fara bai mata wani kyauba. Fir taki tsayawa tayi make-up, duk kishi ya dameta. Ta dauro d’an kwali suka fito, gun Haiydar suka nufa, sai wani harara take aika masa, in ta ga Hasna ko ji take kamar ta shak’eta. Ana ahaka akace Amarya da Ango da Uwargida su fito za’ayi Inspection kafin a fara gabatarda bikin. Haiydar ne yazo dai- dai inda Falmi take yariko hannuta. Sai k’ok’arin fisgewa take, yace”kinga mutane a nan gwamma ki tsaya. Tsaki tayi masa ta kauda kanta gefe. Ana haka sai ga Jiddah da Hasna sun riko hannu Indo, ae take kalo ya koma kanta, don hatta mazan da ke gun sun yaba da tsarin kwaliyarta. Cikin nutsuwa take takawa, Haiydar tun da ya d’aga ido ya kalleta, ya kasa d’auke kai yarasa mai yasa duk lokacin da ya kalleta, sai yaji wani abu gameda ita. Sam ya shagala da kallonta, sai da Falmi ta mutsunesa ya dawo hayyacinsa. Hasna ta saka Indo a gefen damansa, yayin da Falmi ke hagunsa. Wasu police ne biyu da wuk’a a hannusu sai shek’i take suka mik’e, tare da sarawa da buga k’afarsu a k’asa. Ba tare da b’ata lokaciba masu band suka saki kid’an taken k’asarmu *NIGERIA*. Duk wanda suke gurin saida suka mik’e tsaye, tare da kame domin girmama qasarmu. Cikin busa mai dadi, akayi kidan National anthem, yayi da mutane ke bin sautin kidan har aka gama. Mutanen dake gun suka saka tafi raf-raf. Aka zauna nan masu band suka cigabada bugawa, ni da lovely na munsaki baki sai kalo muke, nan wayan nan police biyun nan suka soma paret, suka iso har gabansu Haiydar suka sara masa, tukunan su juya tare da buga kafa, sukayi masauni a gabansu. Anan masu kaya kalan green white green suma suka fito, bayansu Haiydar suka tsaya . Karan kidan ya fara tashi da k’arfi. Take suka soma zaga filin da paret, in gun manyan Haiydar suka je, sai ya sara musu in k’ananan sane, su sara masa. Masu camera sai d’aukarsu sukeyi. Sai da suka zaga ko ina, kafin suka zo suka zaun. Gard d’in police suka fara wucewa, suna parret suna zuwa gun Haiydar da iyalansa, sai su sara masa. Sai da police suka gama nasu kafin yan *WAI BURGET* suka faso karkuso kuga ihu da sowa, don yanda suke gudanar da parret d’indu, da tsarin komai abun burgewa ne. Fatyma S.Y itace parret commoder, yayi da Farida Jigides take yan colour patty. Gaskiya abun ya k’awatu sai wanda suka gani. Sai da aka gama parret tukun masu mik’a musu gifts suka taso. *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH LUV * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-156~160. Ba yan gama wanan shagalin, Falmi ita da tawaganta suka koma gidanta. Yayin da Hajiyansu Haiydar ta kira Amarya d’akinta, ta bata wani abu a cofi tasha. Hajiya tace”ki k’wanta ki huta sosai. Sai da a kayi sallan magriba Hajiya tasa ta gaba taci abinci mai yawa. Hajiya ta saka ruwa a murhu, tare da lalle da magarya ya dahu sosai, sanna tasaka ruwa daban wanda ba komai aciki, ta juye farin ruwan a bokiti ta surka ta kai bayi. Kafin ta d’au wani bokitin ta tace ruwan lallen nan, da rariyan ta, sannan ta d’auko madaran turaruka kala-kala tasaka mata madaran turaren wanka acikin ruwan lallen. (Shi ruwan lallen ba’a cika ruwa da yawa sosai, d’an dai- dai za’a saka). Ta kai bayi tace”Aisha tashi kiyi wanka zaki ga ruwan biyu ne, kiyi wankan sabulu da farin, ki tabbatar ki dirje ko ina. Bayan kingama wankan sabulu, sai ki d’auki ruwan lallen nan zakiga ba yawa, ki tabbatar kin game jikinki dashi ta ko’ian. Aisha Indo ta amsa da”to Hajiya nagode. Saukowa tayi tashiga bayi, wanka sosai tayi kafin ta yiwankan lallennan. Tun daga bayi k’amshi ke tashi har falo. Hajiya ta taho da kasko k’arami, Indo na fitowa tace”zo nan. Fallen zani ta bata, ta lulub’u dashi kafin ta samata kasko tare da zuba turarukan wuta aciki masu kamshi.(masu k’aratu amfanin wannan wankan lallen, da turare yana saka jikin mutun yayi k’amshi, sannan k’amshin yana kama jiki, yana sa mutum kara haske da kyau. Sannan a zuba turare aciki zaki ringa kamshi ne sosai. Idan mutum ya fito daga wanka, bazai bari jikinsa ya tsan- tsame ba. Da ruwan zaki saka turaren wuta a kasko ki luluba jikinki, sannan ki tabbatar kamshin turaren na bin jikinki, in turaren ya k’are ki k’ara sakawa har sai kin tsan-tsame.zakiji k’amshin ya kama jikinki). Hajiya ta d’auko atamfa riga da zani, acikin a kayan Indo ta d’auko kwalban turare yar mai duguri, ta juje akan kayan, hatta ina wears d’inta saida suka sha turare masu sanyin kamshi, wanda duk namiji lafiyaye in ya shaki kamshi, sai ya yaba. Hasna ne ta turo qofa tashigo, ita ta tsara ma Indo kwaliya, kafin tasaka kayan. Masu k’aratu tundaga haraban gidan zaku iya jiyo kamshin da indo takeyi. Waya hajiya ta d’auko lokacin tara da rabi, Haiydar takira tace”kazo yanzu ina son ganinka. Cikin girmamawa yace”to Hajiya gani zuwa. Bai dad’e ba ko sai gashi, cikin shaddarsa ja sai maik’o takeyi. Ko da yazo Main falo, bak’ine aciki sai tsokanarsa sukeyi, murmushi ya musu ya nufi cikin d’akin Hajiya. Qofar tura tare da yin sallama. Tsayawa yayi cak dan ganin Indo a bakin madubi tana saka sarka. Sam ya kasa d’auke kansa daga gareta, ji yake kamar yaje ya rungumeta, amma jinkai da girman kai bazai barshi ba. Wata zuciya tace”to mai zakayi da bak’ar mace ma. Wata zuciyar ko cewa take”ai kuma duk randa tayi gayu sai ta fi falmi kyau. “Mtss kai k’aryane, yama za’ayi tafi Falmi kyau. Yana wannan tunani Hajiya tashigo da sallama tace”yauwa Babana ka iso. Sosa keya ya fara tare da rusunawa ya gaidata, Hajiya ta zauna abakin gado, Haiydar ya zauna akan dadduman dake kasan d’akin. Hajiya tace”Aisha zo nan. Cikin nutsuwa Indo ta tako zuwa kusa da k’afar Hajiya ta zauna. Hajiya tayi gyaran murya, tare da fara musu nasiha mai shiga jiki. Harda yan ayoyinta takawo musu, wanda yake nuni hakkin miji akan matarsa, tare da hakkin mata akan miji. Bayan ta gama tace”Aliyu!”. Kansa asunkuye yace”na’am Hajiya. Taci gaba da cewa”ga *AMANA* Aisha na baka, ban yarda matarka ta takura mata ba. “Itama matarka ce kamar yarda Fatima take matsayin matarka. Ko da tagama musu nasiha ta sanya musu Albarka tare da cewa Indo d’auko gyalenki. Hajiya ta d’auko Hijab tace”tashi muje da kaina zan kaiki d’akinki. Hannuta hajiya ta riko suka fito falo, sai tsokanar su akeyi. Haiydar shi ya jasu har zuwa gidansa, ko da suka shiga duk yan biki sun watse sai Falmi da taci riga da wando, tayi shirin ko ta kwana, don yau a shirye take da in dakuwa ne ma suyi a gidan. Ganim Hajiya yasa ta rusuna,, bata ko gaida ta ba sai wani hararan da ta aika musu. Hajiya ta shigar da Indo d’akinta kafin ta fito Haiydar yazo ya rakata yace”zai maidata gida. Hajiya tace”a’a na yafe driver ya maida ni. Sai da suka bar gidan, sannan ya nufi gida. Yana shiga Falmi ta ja ta tsaya a dai-dai qofar shiga side d’in Indo. Dake shi ba ma niyayar sa shiga gun bane ko kalonta baiyiba yanufi side d’insa. A dai-dai bakin qofarsa ta kwanta, wai dan karyazo ya wuce d’akin Indo bata sani ba, a haka har bacci ya d’auketa. Haiydar ko yana shiga d’aki kayansa ya cire ya watsa ruwa, ya sanya kayan bacci ya kwanta. Ko da ya rufe idonsa photon suran Indo ke masa yawo a idonsa. Da duk al’amuran dasuka faru a tsakaninsu. Sai juyi yakeyi gashi duk yana hannu, amma yasan in ya tink’ari Falmi, bala’i zai ne mo ma kansa haka yayita juyi har bacci b’arawo ya d’aukesa. *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [7/5/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-161~163. Gari na wayewa Falmi ta tura d’akin tasamu Indo tana bacci. A fili tace”eyeh lalle fa kin samu kanki acikin bak’ak’en labarawa. “Har wani lokacin bacci kika samu. “Lalle ko zanyi maganinki yanzunan. Cikin hanzari ta juya zuwa kitchen d’inta, ruwa mai sanyi ta d’auko a fridge, in kunga ruwan har wani tururi yakeyi na sanyi. Tana zuwa tasamu har yanzu Indo bata farka ba, cikin zafin nama cike da masifa Falmi ta shek’a mata ruwan sanyi a jiki. Cikin razana indo ta farka, sai wuk’i-wuk’i take da ido. Falmi tace”ke waya baki damar yin bacci a gidan nan ko kin manta matsayinki ne. “Na yar shege kuma yar aiki maras amfani ke da babu duk d’aya kuke a gidan nan. “Maza sauk’o ki had’a mana breakfast. Indo ji take kamar ta kurma ihu, ba wai watsa mata ruwa, da masifan da Falmi ke ta mata bane ya dameta ba, ila cemata da tayi yar shege, wannan maganan ya na k’ona mata zuciya. In dai zagi ne kam inda sabo ya kamata tasaba. Tsawa Falmi ta sake mata wanda yasata dirk’owa daga kan gado, da sauri ta nufi hanyan falo. Kitchen d’in dake baban falo ta shiga ta had’a musu breakfast, sai da ta jera komai kafin ta d’ibi na ta, cikin d’akinta ta koma, tayi wanka tare da yin brush kafin ta karya. Hajiya sai da tabari Indo tayi 3 days tasaka driver ya kaimata ak’watunanta. Rayuwan Indo ya canza a gidan ba’abinda ta ke fuskanta ila tsangwama da tsana daga gun Falmi da Haiydar. Tun da ta fahimci duk ranar da sukayi karo da Haiydar sai ta gane kurenta. Hakan yasa indai taji yana falo to bata fitowa sai ya fita. Kwanaki sun tafi yau ki manin 2 month da yin bikinsu. Hajiya ce ta had’a goma na arziki tasaka Hasna ta zo duba lafiyar d’iyarta Indo. Hasna tana zuwa ta wuce d’akin Indo tasamu tayi tagumi. Ta rame ga wani bak’in da ta k’ara, cikin hanzari hasna ta yar da jakanta, taje tace”Aunty na mai ya sameki haka?. “Kinyi rashin lafiya ne?. Cikin dauriya Indo ta k’ak’alo murmushi tace”lau na d’anyi zazab’ine amma na warke yanzu. Sam Hasna bata gamsu da maganarta ba, suna cikin haka, sai ga Falmi ta shigo tana kiran Indo harda ashar d’inta. Sam bata san da zuwan Hasna ba kasancewar daga yawonta ta fito. Hasna ne tace”kar ki amsa wannan kiran yan tashan. Falmi jin Indo bata amsa ba tasan kuma tana jinta, abun sai ya kular da ita. Har zata tura qofar ta fasa ta koma d’akinta, zuk’ek’iyar bulala ta d’auko, ganin jikin bulalan yasata sakin wani murmushi, don tasan wannan bulalan in har yashiga jikin Indo zata gane shayi ruwa ne. Cike da isa da gadara, tana wani wawwaina bulalan a hannuta. Ta iso falon Indo, Kiran yantasha ta sakeyi. Hasna kuwa ta hanna Indo amsawa harda tushe ma Indo baki. Falmi a harzuke tashigo falon, sam bata lura da Hasna ba tayi kan Indo da bulala. Cikin sa’a ta tsula mata na d’aya, ta kai na biyu kenan Hasna tayi saurin shiga tsakaninsu. Falmi ganin Hasna ta razana amma sai ta dake tace”kee bani guri inyi abunda nayi niya. Hasna tace”ke Fatima kike kowa, kar ki kuskura tsautsayi ya gifta miki kice zaki sake dukan Indo. Falmi cikin fushi tace”ke ce mai tare mata ko. Cike da gadara Hasna tace”eh da abunda zakiyi ne.. Tsautsayi yasa Falmi ta d’aga bulala wai zata zuba ma Hasna. Amma kash ina ae ta makara Hasna tayi saurin k’wace bulalan tashiga tsula ma Falmi, iya karfinta, Kan kuce mai ta cika gida da ihu. Sai da Hasna ta mata lilis sai ihu take, karar motan Haiydar ne ya dawo gida, hakan baisa Hasna ta daina ba, Haiydar jin ihun Falmi ko mota bai rufe ba ya shigo gidan da gudunsa. Falon Indo yaji muryanta cike da mamaki yayi side d’in da gudu. Masu karatu bari mu huta a nan, ina muku murna da zagowan k’aramar sallah. Allah ya amsa mana ibadun mu ya kumasa muna daga cikin wa’yanda aka ‘yanta daga wuta zuwa aljannah ameen. *HAPPY SALLAH IN ADVANCE* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-164~166. Cikin hanzari Haiydar ya tura qofar d’akin. Cike da mamaki ga takaicin abunda ya gani, wai Hasna ke dukan Falmi. Kanta yayi ya bata lafiyayen mari, tukun Hasna ta koma gefe. Falmi ko ganinsa ta k’ara sautin kukanta. Cikin b’acin rai Haiydar yace”ke husna mai ya kawo ki gidan nan?. “Wa ya baki daman dukan matata?. Hasna tace” Yaya baka abu….. “Ke ni sa’anki ne ina magana kina magana. Ganin yanda ke huci, ya nufo kanta zai daketa, ta d’au wayarta da gudu, tayi bayi tasaka key. Ganin ta gudu Haiydar ya dawo kan Indo yace” wato kece munafukar gidanan nan ko?. Belt d’insa yasoma zarewa, nan Indo tasoma kuka tana basa hak’uri. Hasna jin Haiydar zai daki Indo, da sauri ta kira Hajiya ta saida mata ga Haiydar zai daki Indo. Hajiya ta kira wayan Haiydar dai-dai lokacin da ya d’aga belt, zai zuba ma Indo wayarsa tayi k’ara, yana cirowa sunan Hajiya ya gani. Ya d’aga tare da fad’in “Assalamu’alaiku. Hajiya ta amsa masa da”Ameen Wa’alaikumusalamu. “Ali wallahi karka kuskura ka daka min ‘ya’ya, mai suka maka ne haka?. “Ka jirani ina zuwa yanzu, tunda Abba ku baya gari, bare yazo da kansa. Bata jira amsan shi ba ta kashe wayar, Hijab ta zara da waya ta fito driver ta kira, suka d’au hanyan gidan. Haiydar ko wani takaici ne ya tokaresa, tabbas Hasna ne ta fad’a ma Hajiya, cikin zuciyarsa ko cewa yake”lalle duk randa na rike yarinyan nan, bansan wani irin duka zan mata ba. Falmi ya d’auketa, tare da kaita falo. Itako ta wani sakan jiki, da baki tana kuka kamar yarinya. Hajiya ne ya shigo da sallaman ta, Haiydar ya amsa mata, kalon tambaya ta tsaya masa, kai ya sunkuyar k’asa. Hajiya tace”ina yarana?. “Wallahi in ka duki d’aya a cikinsu, ranka sai yayi mumunan b’aci. Bata jira amsansa ba ta nufi side d’in Indo, tana shiga taganta, ta had’a kai da gwiwa, tana kuka mai ban tausayi. Hajiya da sauri ta yi gunta tana cewa”Indo ya dakeki ko?. Hasna jin muryan Hajiya yasa ta bud’e qofa ta fito. Hajiya tace”mai ya kaiki bayi?. Hasna tace” Ya Haiydar ne ya tashi zai buge mu. “Na gudu toilet. Hajiyan tace” muje falo tukun inji komai. Hasna ta kama hannu Indo suka nufi falo, Haiydar na ganin su Hajiya sun fito, ya sauka kasa ya zauna, Hajiya ta zauna a kujera, su Indo suka zauna a kasa suma, Falmi ko tana zaune a kujera taki saukowa. *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [7/6/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-167~169. Hajiya ta kalli Haiydar tace”mai ke faruwa?. Cikin in ina Haiydar yace”Hajiya na dai dawo ne, naji muryan Falmi na ihu, ko dana shigo gida da gudu, sai naji sautin kukanta a side d’in Indo. “Ina zuwa sai na samu Hasna tana dukanta. Hajiya tace”shine ka tashi zaka da kamin yara?. “Shin kayi bincike akan mai ya had’asu?. Kai ya gir-giza alamar a’a, Hajiya taci gaba da cewa”haka babba ya kamata ya yanke hukunci, ba tare da binkiken mai ya faru ba. “Haiydar bana son ka da hakan ba adalci bane. “Yanke hukunci batare da bincike ba. Ta juya ta kalli Hasna tace”ke Hasna mai ya faru har kika daki matar wanki?. Hasna ta fara basu bayani tundaga shigowarta, harda kiran da Falmi tayi ma Indo, bata rage ko wasali ba. Hajiya ta saki salati tace”daman kuntata ma yar mutane kukeyi?. “Matarka har tasamu daman dukan yata?. “To bazaiyiwu ba. Hasna tayi sauri cewa”Hajiya ina rokon alfarma da amayar da Indo makarantar boko da islamiya. ” Tayi karatunta taga ma, kuma hakan zai bata daman samun sakewa, da samun ‘yancinta, da wayewa, batare da wata ta takura mata ba. Hajiya tace”rufe mana baki manya na magana kina saka baki. Hajiya ta musu fad’a tace”duk randa wani ya sake ya daki Indo a gidan. “Tabbas zakuga bacin raina. “Kuma daga yin aure, bazan so yata tafara yaji ba. “Amma komawa makaranta yazama dole ta koma. “Haiydar yanzu zan tafi da matarka, za’amata registration sai angama komai ta dawo. “Inaso gobe kazo ka kaita, amma sai mun zab’i makarantar da zatayi karatu. Kafin Hajiya tak’ara magana Falmi tasaki ihu, tana fad’in Hajiya ki taimakeni karta koma makaranta. Nayi alkawarin bazan daketa ba, gwara ta zauna a gida, In Har Indo ta koma makaranta to nakad’e nikam. Magana Falmi takeyi ba uwa k’wab’a. Hajiya ta mata kalon bakida kunya. Hajiya tace”Hasna kuje da Indo ta d’au hijab d’inta, da kayanta kala biyu, kuzo mu tafi. Hasna kamar jira take, da sauri ta kama hannu Indo suka nufi d’aki. Basu dad’e ba suka fito, Hajiya tace”mun tafi. Haiydar ya rako su, har gun mota suka tafi. Haiydar yana dawowa ko kalon Falmi baiyi ba, ya wuce d’akinsa. Hajiya suna zuwa tasaka Indo tayi wanka, ta bata abinci taci, sai da suka huta Hajiya tace”Hasna yanzu wani makaranta ne yakamata a yi registration ma Indo?. Hasna tace”inaga *SABIL SUNLIGHT* za’a mata. “Don makaratan yana da kyau ana karatu sosai. “Kuma sabon skul ne. Hajiya tace”to ba matsala gobe zamuje tare kawai. “Tunda Haiydar na fita aiki. Hasna suka shiga d’akin da Indo, suna hira, Hasna tace”kin san me aunty na? Indo tace” a’a sai kin fad’a. Hasna tace” ina rokon Allah yasa in anje registration d’in nan su baki science class. “Kinsan sabida mai yasa nake son abaki science class. Indo tace” a’a sai kin fad’a. Hasna tace”sabida ina so Falmi tayi regret cos taki ya auro mai aikin asibiti. “Ni kuma tun randa aka yi bikinku, na d’au alwashin da ikon Allah sai nayi hanyan da kika koma school. “Sannan inaso ki waye ki zama kikakiyar likita ba nurse ba. Indo tace”nima ina da burin karatu da, sai dai rashin mai taimaka min. “Gaskiya nagode Allah ya barmu tare. Hasna tace”Aunty Jiddah tana kirana a waya tana tambayarki. “Wai tanaso inta dawo zatazo ta koya miki abubuwa dayawa. “Basa k’asan ne ita da Yaya Ghali sun fita yin wani course a waje. Indo tace”ayya ni ae suna burgeni da Ghalinta dukansu Doctors. Hasna tace”wallahi kam ae sai kinji labarin soyayyan su gwanin burgewa wanda aurensu, yazo musu a *BAZATA*. Haka sukayita hira a tsakaninsu. Washe gari Hasna ta jasu a mota suka nufi *SABIL SUNLIGHT*. duk wani abunda ya dace suyi anyishi. Anyi interview ma Indo ganin k’ok’arinta, yasaba suka bata Science class. SSS1 daman tayi JSCE ta. SSS1A aka bata, nan suka bata uniform da komai hatta books, da text book suke bayarwa. Malamin da kansa ya kaita ajin, ya kira wata Sadiya S Adam, bayan da Sadiya tazo yace”Sadeey ina k’awarki?. Wacce aka kira da Sadeey tace”yau batazo ba, bata jin dad’i. Uncle d’in yace”ga frd nan na muku. “New comer ce gobe zata fara zuwa, inaso ku zauna tare da ita. Sadeey tace”okay sir!. Malamin yace”sunanta Aisha Muhammad. Nan suka gaisa Sadeey ta koma aji. Su Hajiya kuma suka dawo gida, Indo in banda murna ba’abinda takeyi, wai yau itace ta koma makaranta. Masu karatu ku shirya yazu ne gurmin zai fara, don Indo zata shigo gari, zata kile. Masu karatu ya kuke ganin Haiydar zai yi akan Indo nan gaba, k’iyayar zata ci gaba ko zai k’are?. Shin Indo zata ci gaba da d’aukan rainin da suke mata?. Shin ya rayuwan Falmi yake kasancewa nan gaba?. Ku biyo yar *JARAWA* don ji yanda zata kaya. *HAPPY SALLAH IN ADVANCE* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [7/6/2016 Rash Kardam] BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-170~173. Ko da suka dawo gida, Hajiya ta zaunar da Indo tayi mata nasiha, game da aurenta, sanan ta k’ara da cewa”Aisha kiyi hak’uri ina sane, da duk irin abunda Aliyu yake miki. “Abunda yasa ba zan takurasa ba a kwai lokacin dana ke jira, zan ramamiki duk abunda ya ke miki, inaso ki nutsu kiyi karatu nan gaba sai Haiydar yazo da kansa yana baki hakuri. “Alokacin ne zamu rama duk abunda ke mana, Hajiya wani murmushin mugunta tayi, kafin taci gaba da cewa”zan saki a makaranta islamiya, don ki rage yawan zaman gida. “Sannan ki k’ara hak’uri da duk abunda zasu miki, wataran zakici riban hak’urin ki, har sai ni da kaina nazo, ina cewa Aisha ki d’an ji tausayin Yayanki, ki sassauta ma Haiydar. Hasna ne tayi murmushi don itama tanason ta ga wannan ranan. Hajiya tace” a kwai motar da Abban na, Sarkin Fulani(Gakansu Haiydar ) ya ban range rover zan baki ita, tadawo naki halal malak. “Zansa Hasna ta koya miki mota amma sai naga kunyi jarabawa, da irin sakamakon da kika fito da shi kafin na damk’a miki motarki a hannuki. “Sai gobe zaki fara zuwa school, in kin dawo da kaina zan maidaki gida, kuma zansa driver yana kaiki makaranta. “Ku tashi kuje ku huta Allah ya muku Albarka. Suka amsa da”ameen. Gidan Haiydar ko yau ya dawo da niyar ko ta kwana, don yau yayi niyar karb’a hakkinsa a gun Falmi. Don yayi hak’uri har ya gaji, rabonsa da ya kusanceta har ya manta. Wanka yayi ya nufi d’akinta, yana zuwa ya tarar ta baje a gado, tana sharan baccin ta. Hawa gadon yayi, yazo kusa da ita ya kwanta. Salon sa da yake rikitar da mace, ya fara aika mata sak’onsa. Cikin bacci Falmi taji ana shafata, farat ta farka ganin Haiydar yasa ta rik’e hannusa, tace”mai kake shirin yine?. “Ko ka manta dokata ne?. “Matsawan kana son biyan buk’atarka sai ka ajiye min kud’i. Cikin da shashiyar murya Haiydar yace”haba Falmi anya kina tsoron Allah kuwa?. “Matar aure na na sunnah, don zan kusanceki sai na biya kud’i. “Kisani fa hakan haramun ne. “Kisani mala’iku su tsine miki fa?. Falmi tace”ai yau in har kaga ka samu abunda kakeso to kasaka min kud’i har 200k. Haiydar yace”Falmi bayan kud’in sadakin dana biya?. “Ki sani bana son miki ta k’arfi. “Ina rok’onki da kiji tausayina, ba wai don bana da kud’in da zan baki ba, a’a saidan hakan baida kyau. “Kuma duk irin k’yautata miki danakeyi ba k’ya gani?. “Yaushe na baki 300k fa falmi?. Tsaki ta ja ta mik’e, za ta sauk’a daga kan gadon, ya fincikota, sak’onni yasoma aika mata dashi. Duk iya k’arfinta ta kasa kwacewa sai tasoma masa ihu. ( kira gareku mata masu irin wannan halin, kusani baida kyau, Allah da mala’ikunsa, suna tsine wa duk matar da mijinta ya nimeta, ta juya masa baya. Ko kuma ta nimi sai ya bata kud’i kafin ya kusance, ta kamar yanda Falmi takeyi. Dan Allah ku kiyaye inda maiyin haka ku daina. Kisani duk randa kika faranta wa mijinki rai shi da kanshi zakiga canji a gunsa kuma komai kika roka matsawan na dashi zai baki, amma ba kice sai ya baki kafin ki basa hakkinsa ba, hakan haramu ne. Allah ya tsaremu da aikata hakan ameen). Bai k’yaleta ba sai kusan asuba, wanka yaje yayi ya kwanta, yana tunani irin halin Falmi sam baida k’yau. Gidan Hajiya kuwa, da safe Indo tayi wanka tasaka Uniform d’inta purple da light purple, riga da skirt sai barret. Hijab ta d’auko ta d’aura akan kayan, Indo tayi kyau sosai, Hasna ne ta kaita school d’in. Suna zuwa school d’in registration office suka nufa. Bayan sun gaisa da uncle d’in jiya, Hasna tace”gata nan mun kawota. Uncle d’in yace”ok wata yarinya ya kira, yace”ta je SSS1A ta kira masa Sadeey S Adam da Sanah S Matazu. Ko da yarinyan ta tafi, bata dad’e ba saiga su sunzo. Nan ya had’a su yace”su je su zauna tare. Sanah da Sadeey suka kama hannu Indo suka nufi class. Hasna kuma ta wuce school d’inta itama. *MASU NIMAN WANNA BOOK ‘DIN DA WA’YAN DA SUKE MIN MAGANA TA PRVT, PLS KUYI HAK’URI SAK’ONNI YANA YAWA, BA WULA’KANCI BA. KUNA TAMBAYA A GROUP DAN ALLAH. KUMA ‘YAN GROUP MAI SHI KUNA BAYARWA COS MUTANE SUNA YAWA, KUMA GA MESSAGES ‘DIN MASU YIN COMMENTS, SUMA ZAN MUSU REPLY, INA HÀU DA NIYAR INA GA SAK’O IN CIGABA DA TYPING, AMMA SAI NA TSAYA TURAWA MUNAE, WASU IN BAN TURA MUSU AKAN LOKACIBA SUNA FA’DAN BAK’AR MAGANA DUK IYA K’OKARIN DANAKE AMMA BASA GANI, DAN ALLAH FANZ A TAIMAKA ANA TURAWA A GROUPS IN AN TAMBAYA PLS N PLS* GA WANNAN KUYI HAK’URI BAYAWA KAINA YA DAMEN DA CIWONE NASO NAYI YA FI HAKA . *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [7/7/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-174~176. Sanah da Sadeey suka nufi class da Indo, ni ko Rash ina biye da su. Tun shigarsu class, yan aji suka fara tambayan Sanah da Sadeey wacece?. Sanah suka sharesu ganin sunyi hanyar sit d’in da ke k’usa dana su, wani yaro yace”kai new comer ce fa. “Jiya ina gani aka kawo ta. Wasu sukafara cewa ke kizo nan ki zauna, wani yaro yace”kai gaskiya tana da kyau. “Zamu zama frds ko?. Wani kalo Sanah ta musu, wanda yasaka shi yin shiru yana dariya. Sit d’aya aka bata kasancewa kowa da sit d’insa, had’e da kuma lokansa na ajiye wasu littafa. Sanah ce a farko sai sit d’in Indo a tsakiya sai Sadeey a baya. Ana haka Uncle d’in Biology yazo, darasin da yamusu shine. *CELL* sai da ya gama darasi yayi bayani sosai, ko da yazo yin Evaluation, ya tambayesu kamar haka, “class what is cell?. Shiru ba wanda ya d’aga hannu, sai Indo ta d’aga hannu, ya nuna ta, Indo ta mik’e tafara cewa”Cell is the fundamental total unit of life. Cikin salon da take karatun, abun burgewa ne, bare muryanta tamkar mai yin busa. Tana gamawa tun kafin malamin ya bada umurni a tafa mata, ‘yan class suka d’au sowa da tafi. Jikake raf raf raf, sannan malamin yace”well done good girl clapp for her once again. A haka har aka tashi. School bus ne ya maidata gidan Hajiya. Washe gari ta koma gidanta, Haka rayuwa taci gaba da tafiya, kulum school bus ke zuwa d’aukan Indo ya dawo da ita. Sannu a hankali sun shaku dasu Sanah da Sadeey, anan ne ma take sani asai Sanah yar gidan bababn Malaman nan ne mai wa’azin biki da gyaran Amare. Sai Sadeey kuma gurin gayu ba’a barta a baya ba. Niko Rash nace”lalle abun yayi wato kaya, ya tsinke a gaban mai kaba. Aisha ta soma kilewa, duk da haka ita take aiki a gidan Falmi, ko kad’an bata nuna gajiyawarta, Haiydar ko ya saba da girkinta duk randa bata gida, ko ya je Hotel baya iya cin abincin su. Indo ko mungun kama kanta take bata bari ma ya ganta bare ya nimi takura mata. Falmi ko bala’in yau da ban nagobe da ban, Meesha lurv da Zarah BB sun bata shawaran ta kama kanta, ta fita hark’ar Indo tak’i, sabida duk randa Indo ta waye sai ta gane KUSKURENTA amma fir taki, tana bin shawaran mugayen k’awayenta, hakan yasaka suka zuba mata ido. *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [7/7/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-177~179. Rayuwan Indo haka yaci gaba da tafiya, tana zuwa makaranta. Sun had’a kai da su Sanah da Sadeey, da zamansu ta ga na da kyau, bata b’oye musu komai na rayuwanta ba, ta fad’amusu. Sanah tace” mukuma zamu bada tamu gudumawar gurin ganin kin gyaru. Sadeey ita ta dage gun koya mata k’waliayar zamani, Sanah kuma gyaran jiki, hatta yanda Indo zatayi tafiya saida suka koya mata. Bayan kwana biyu suka zo mata da form d’in makarantar kwaliya ta cika, da kanta ta biya kud’in kasancewar tana samu ‘yan kud’i, a haka ta fara zuwa. Hajiya ganin jarabawan Indo yayi kyau hakan yasaka ta bata motarta, ranar da Falmi tasamu labari kamar zatayi hauka a gidan, don saida Hajiya ta tsayar mata ita da Aliyu, don motar Falmi bai kai na Indo ba. Sanah suna hira da Sadeey da Indo, Sadeey tace”Indo gaskiya ni bana son ana kiranki, da Indo nan sai kace yar kauye. Sanah tace”kamar kina raina. “Shawara daga yau duk wanda yace miki Indo, in ba wanda kike jin kunyarsa bane karki amsa. Tun daga ranar sunan Indo ya b’ata yakoma Aisha, nima Rash nace” daga yau na daina cewa Indo sai Aishat.********* 2yrs later Wata k’yak’yawan budurwa na hango, tana fitowa da ga cikin gida ta na k’ok’arin bud’e motar ta, mai k’irar RANGE ROVER, sanye take cikin wani doguwar riga ya d’an kamata daga sama, sai d’an k’aramin cikinta dake a shafe ya fito. Hakan shi zai baka daman gane irin halittan da ubangiji ya mata, harta shiga mota ko mai ta tuna cikin damuwa tace”oh shirt! Da sauri ta fito ta nufi hanyan cikin gidan, gudu-gudu sauri sauri, sam bata ankara da wanda ke fitowa ba, sai jin garam sunyi karo da mutum. Ko ta nuna alamar damuw ta d’ago kai tare da d’an zaro gilashin dake idota, sai da ta d’an rausaya ido, ta wani kashe murya tace”oh i’m sorry! you guy. Bata jira amsan shi ba ta sakai ta wuce abunta, Haiydar da tsananin mamaki kasa motsi yayi, shafa ida ta buge sa yayi, haryanzu dadda d’an k’amshin ta yana tashi. Wani yawu ya had’iye da ya tuna yanda take sarrafa mazaunanta, da k’irjinta. Tabbas Allah yayi halita a gun, cikin zuciayrsa ko cewa yake”wannan taci a kirata da zallaziya ko zank’aziya hmm wannan tamk’ar ita tayi kanta. “Gaskiya ta had’u ba k’arya. “Gashi ta had’a duk wani abunda nake so ajikin mace amma taya zan tink’areta?. “Hmm ni shakkanta na ke ji ma yanzu. Wata zuciya tace”to ko kana jin shakkanta sai ka tin k’areta, ai girmanka zai zube. Yana tsaye tazo ta wuce sa, motarta tashiga sai da ta yi ribas, kafinta ta da kura ta bule Haiydar ta wuce da gudu. Haiydar ko gizau baiyi ba ila bin motarta da kallo. Zuciayrsa tana masa wani irin abubuwa nai wuyan fasaruwa, kasa motsi yayi don duk jikinsa ba k’wari. Masu karatu wai shin wata yarinyace wanna, da har zata iya taka Haiydar, ta masa wannan wargin batare da ya d’au mataki ba?. Don son jin wannan amsar ku biyo ni. *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH LUV * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [7/8/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION. Pg-180~183. Da k’yar Haiydar ya iya jan k’afarsa, zuwa gun motarsa ya shiga. Yana shiga motar sai da ya d’an zauna, don gabad’aya ganin Aisha, ya haddasar masa da kasala a jikinsa. Kansa ya d’an jingina a steering motar, ya lumshe idanunsa, ba abun da ke gani illa fuskan Aisha, da suran jikinta, suna masa gizo a idonsa. Imagine ya farayi, wai ga Aisha tazo, cikin tafiyarta mai burgewa, kusa da shi tazo, tana masa k’wark’wasa, sai da ta matso kusa dashi, kiss ta manna masa a baki. Shiko sai wani murmushi ya saki, tare da k’ara lumshe ido, wayarsa ce tayi k’ara, sai da yaja karamin tsaki, don bai so ya katse tunanin da yakeyi ba. Ni ko Rash nace”da ka tafi sabgar gaban ka ne, da zaifi maka wanna kayan jaki da karan. “Don yanzu Indo ta maka nisa, yanzu Indo matar manya ce. Wayarsa ya zaro, sunan Falmi ya gani akan scream d’in wayan, tsaki yayi kafin ya d’aga wayar. Cikin muryansa da ba yabo ba fallasa yace”hello ya akayine?. Daga b’an garen Falmi tace”Haiydar pls ka turan kud’i a cikin account d’ina, ina….. Bai bari ta k’arasa ba ya katse kiran. Ransa duk ya gama b’aci, sai huci yakeyi, cikin zuciyarsa ko cewa yake”wai ya rinyan nan tana da hankali kuwa?. “Bata san hakki na da ke kanta, ta sauke ba amma ta iya tambayan kud’i?. “Rabon da Falmi ta zo d’akina na manta, wai sai kasuwanci ta saka a gaba. “Dole in d’au mataki akan ta. Motarsa ya ja ya fice abunsa, zuciyarsa ko sai zafi take masa, don shi yanzu ya gaji da halin Falmi, ta soma hawan masa kai sosai. Aisha ko tana fita daga gidan, gidan Hajiya ta wuce, tana shiga ta perker motar ta fito. Masu aikin gidan sai sannu suke mata, cikin girmamawa ta amsa musu. Cikin falon ta nufa, da sallamarta ta shiga falon, Hasna da ke goge TV da gudu tazo ta rungumeta, tace”haba Aunty eeshat kinanan kwana biyu?. Aisha tace”washhh nikam sakeni karki karyani, gwamma ke. Hasna ta saki dariya. Aisha tace”Hasna ina Hajiyata ban ganta ba?. Hasna tace”ta tafi dubiyar maralafiy. Aishat tace”Allah ya dawo da ita lafiya. Hasna ta kalli Aisha sama da k’asa tace”Baby Eeshat irin wannan wanka haka?. “Gaskiya zaki rikita Yayana. “Hmm Aishat duk gayuna yanzu kin d’aramin sosai, sai dai mu biyo bayanku. Wani lalalusar mirmushi Aishat ta saki tace”ke ban son iskanci fa. Hasna tace”gaskiya ne ae, ko da yake hausawa sunyi gaskiya da sukace, bakauye bai iya wayewa ba. Cikin zolaya tayi maganan, dariya suka saka dukkansu. Aishat tace”barin je gidansu Sanah suna jirana zamuje saloon ne. Hasna tace”okay! To sai kin dawo. Har jikin motarta Hasna ta rakata, tashiga ta ja motar ta bar gidan. Hmm masu karatu kenan Indo mu na da ne tawaye. Gidansu Sanah ta shiga, tana ajiye motar tashiga gidan, Sadeey tace”ae na d’auka bazakizo ba. Rausayar da kai Aishat tayi, tare da had’a hannu alamar ban hakuri, tace”tuba nake amin afuwa. Sanah ne tafito da gyale suka wuce, sai yamma suka dawo, sai da ta ajiyesu a gida ta nufi gidanta. Tun a harabar gidan, taga motar Haiydar yadawo, cikin zuciyarta ta fara tsara irin rikitasa da zatayi yau. Tana shiga gidan bakowa a falo, side d’inta ta nufa, kaya ta cire tukun tayi wanka, saida ta tsane jikinta, tukun ta zauna a gaban madubi, ta kusa d’aukan awa d’aya tana k’waliya. Three quarter ta d’auko tare da wani riga marar hannu, irin wanda ake d’auresa a wuya, rigan kalar ja, sai ta d’auko ribom ja ta d’aure kanta, bak’aramin k’yau tayi ba. Main falo ta fito, sai da ta kunna CD, ta d’auko kaset d’in waka tasaka, don niman magana ta k’ure speaker, don ta san Haiydar baya son hayaniya sosai. Kitchen ta shiga ta had’a zob’o, daman tayi girki kafin ta fita, a plate tasako a binci ta fito falo, ta zauna abinci taci ta k’oshi, ta tattara plate da cups d’in ta mayar kitchen. Falo ta dawo sai da ta huta, ta je gun speaker ta k’ara volume a hankali tafara rawanta, cikin salon k’warewa take gir- giza jinkita. Haiydar ko na bacci ya ji kid’a na tashi, har sai da ya toshe kunnesa, cikin masifa ya nufo falon, ko da ya iso falon kasa motsi yayi, don gani irin rawan da Aishat takeyi. Aishat kuwa ganin Haiydar da gan-gan tasoma matsowa kusa da shi tana rawa. ®NWA. *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [7/8/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. ®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION. Pg-184~186. A hankalin take rawa, mai d’aukan hankali, harta iso gun Haiydar, hannusa ta kamo tana rausayawa tamkar yanda turawa suke in suna rawa. Kwanto da fuskanta tayi akan k’irjinsa tare da lakace hancisa, ta d’ago da kanta tazo dai-dai kumatun Haiydar, ta sakar masa lafiyayan kiss, wanda sai da numfashin sa ya kusa d’aukewa. Salon rawan ta canza zuwa na India, da gudu tayi side d’inta, don tasan in ta k’ara minti biyar agun, zata gane kurenta, don yanayin Haiydar ya canza. Haiydar gani ta yi side d’inta gashi duk ta gama rikitasa, da gudu yaje don ya tura qofar, amma kash! Saijin qofar yayi ansa key. Cikin dashashiyar murya ya fara k’iran”Aishat! Aishat! Aishat! Please ki taimaka min ki bud’e qofar nan, inason inga rawanki yamin kyau kuma ya burgeni, nayi miki alkawarin zan miki kyautar da baki tab’a tsamani ba. Ko mai kikeso nayi alkawarin zan bakishi dan Allah”. Aishat na jinsa ta shek’e da dariya, tazo jikin qofar tace”Ya Haiydar naki d’in ko ka manta bak’ar macece kuma ‘yar aiki ke rawa a gabanka, mai zata burge ka dashi a jikinta?”. Haiydar ya marairaice fuska tamkar mai shirin yin kuka Yace”komai zakice na yarda, ko wani irin horo zakimin, bazan damu ba, amma rawan ki ya burgeni”. Aishat na jinsa tayi banza dashi, ta hau kan gado ta kwanta tana murmushin mugunta. Haiydar ya jima ajikin qofar, kafin ya ja tsumar k’afarsa, ya bar qofar d’akin, don Aishat tak’i bud’e qofar, gashi duk ta d’aga masa hankali”mtss”. Ya ja tsaki, cikin zuciyar shi cewa yake”to mai yasa na fito ne ma?”. “Gashi na ja ma kaina ae, ita kuma ko tausayina ba zata jiba?”. Da wannan tunanin ya koma d’aki ya kwanta, duk abun duniya ya ishesa, don yanzu baida burin ganin kowa a gaban sa, sai Aishat dake rikitasa. Haka ya k’araci zamansa har lokacin sallah magriba yayi, sai da ya jira akayi isha’i kafin ya dawo gida, yau sam yaki shiga d’aki, jira yake ko zaiga Aishat ta fito, sai da ya kusan kwashe awa d’aya, a gun bata fito ba, har yana shirin tashi yaji alamar tana bud’e qofa, da sauri yaje ya b’uya yanda bazata ganshi ba. Aishat ko yunwa ne ya dameta, shiyasa ta fito ta had’a tea, mini skirt ne ajikinta, wanda dashi da babu duk d’aya ne(wai an karya matacce). Bata sa riga ba, sai yar bra top tasa, wanda ko cibiyarta bai rufe ba, duk k’irjinta na waje. Tafiya take duk ilahirin jikinta motsawa yakeyi, ta shiga kitchen ta had’o tea, falo ta dawo ta zauna, kafa ta d’aura d’aya a kan d’aya. Wanda hakan yasaka duk wanda ke saitinta zai iya hango kalar pant d’inta. Ganin irin zaman da tayi, saida Haiydar ya had’iye miyau, ji yake tamkar ya rugo da gudu, ya rik’eta, amma yana tsoron masifarta. Aishat ta gama shan tea ta d’ibi kayan taje kaiwa kitchen, Haiydar na ganin tashiga kitchen, sauri yayi yashiga d’akin ta ya kwanta akan gadonta. Aishat tana yar wakanta ta shigo d’aki, sam bata lura da mutum ba, harta tura qofar amma bata rufe ba, ta juya zata hau gado kenan, taga Haiydar a kan gadonta, ba k’aramin razana tayi ba, ta juya da niyar zata gudu kenan ya diro daga kan gado ya biyo ta. ®NWA. *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [7/9/2016] Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*. Pg-187~189. K’ofa ta ru fe, ta ju ya za ta hau kan gado ke nan, ta ga mutum a kwan ce, ba k’aramin razana ta yi ba, ci kin sauri ta ju ya za ta fita, Haiydar ya yi saurin dirowa da ga kan gado, ya kai ma ta cafka, amma kash! Ka fin ya iso, cikin za fin na ma ta fita. ‘Dakin da ke kusa da na ta, ta shi ga, key da ke ji kin k’ofar ta murd’e, cikin sa’a ya kullu. Haiydar ya na zu wa, ya sa mu har ta sa key, ya tsa ya ci za, sam bai so ha ka ba, d’akin ta ya ko ma ya kwan ta. Rigan baccin ta ya ga ni, hannu ya sa ka ya d’auko, kan hancin sa ya kai, ya na shin-shinan dadda d’an kamshin da ke jikin rigan. A haka har bacci b’arawo ya d’au ke sa. Aishat ko duk illahirin jikinta rawa ya ke yi, sai da ta kusa awa d’aya, ta zauna a bakin gadon, sai da ta yi addu’a kafin ta kwanta. Asuban fari ta mik’e tayi sallah, sai da ta ji Haiydar ya fita, kafin ta lallab’a ta koma d’akinta ta kulle. Wanka ta shi ga sai da ta ga ma ta fito, sama-sama ta shirya, uniform ta sa ka, ta d’au bag d’in ta, ko karyawa ba ta tsaya yi ba, ta fito bakin gate, Napep ta tare sai gidan Hajiya, da sallama ta tura k’ofar falon ta shi ga, da Hasna su ka fara karo, ci ke da mamaki Hasna ta ce”lafiya dai na gan ki da sassafe nan?. Murmushi Aishat ta yi ta ce”lafiya lau wallahi, yau sauri na ke yi shi ya sa ko ka yan breakfast, ban tsaya had’a wa ba”. Hasna ta ce” ina Bros d’ina fa?”. Aishat ta ce”ke barni yau ina sauri ne, yi ki had’a ma na breakfast ka wai, Hasna Hajiya fa? Tana ciki ne?”. Hasna ta ce”eh! Ta na d’aki”. “Okay! Barin shi ga gun ta, na gaida ta”. Da d’an gudunta ta haura step d’in, da sallama ta shiga d’akin Hajiya, ta samu tana karatu, a gefenta ta zauna, sai da Hajiya ta idar da karatun, Aishat ta ce”Hajiya an ta shi lafiya?”. Hajiya ta ce”lafiya lau, ya karatu?”. Aishat ta ce”Alhamdulilah! Mu na kai”. Hajiya ta ce” ya Haiydar d’in? Ina fatan ba ku na zaman lafiya, bai ta ku ra mi ki?”. Aishat ta ce”lafiya mu ke zaune ba wata matsala”. Hajiya ta ce”Alhamdulilah!”. Aishat ta ce” barinje na karya don zan wuce school daga nan”. Hajiya ta ce”to in kin gama karyawan ki min magana”. Aishat ta amsa mata tare da fita falo. Ita da Hasna su ka karasa aikin, su na hira har Aishat ta karya, lokacin Hajiya ta sauko, kud’i ta mika ma Aishat ta ce”ga shi ki rik’e ki na b’atarwa”. Aishat ta yi godiya ta fita. Driver ne ya kaita makaranta. Haiydar na dawowa da ga masallaci, ya ko ma side d’in Aishat ya na tura k’ofan d’akin da tashiga, sai ganin k’ofar ya bud’u, sa kai ya yi cikin d’akin amma me?. Sai ganin d’akin empty bakowa, d’akinta ya sa ke zu wa shi ma k’ofar a bud’e, sai ya d’auka ko wanka tashiga, kan gadon ta ya sa ke kwanciya, ya na za man jiran fitowarta. Shiru-shiru ba bai ji Aishat ta fito ba, bare ya ji karan ruwan wanka, tashi ya yi ya nufi bayin, k’ofar bayin ya tura, nan ma ya ga empty bakowa a ciki, tsoro ne ya kama Haiydar to ina Aishat ta je?. Ko dai ta na kitchen ne?. Da sauri ya yi hanyar kitchen, ko da ya je nan ma ba kowa. Ba karamin razana ya yi ba, ga shi time d’in fitar sa aiki ya yi, da sauri ya koma d’akinsa ko wanka bai tsaya yi ba, ya saka kaya, ya fito mota ya d’auka ya nufi gidan Hajiya, Ko da ya shiga a falo ya sa me su a falo, ya rusuna ya gaida Hajiya, Hasna ma ta gaida shi, Hasna ta sa ma sa abinci, sam kasa cin abincin ya yi, hankalinsa ya tashi, tunani ya ke, kardai ace Aishat ta gudu ne?. Tabbas da ya yi hauka, don yanda ya ke jin sonta a cikin zuciyarsa ba zai iya hakuri da rashinta ba, mikewa ya yi, ya mu su sallama ya nufi gun aiki. Ko da ya shiga office, bai iya tab’uka komai ba, key d’in motarsa ya dauka, ya nufi hanyan makarantarsu Aishat, ya na zuwa, bai wani samu matsala da mai gadi ba, don kakin police ne ajinsa. Ya na shiga harabar makarantar, ya ga mu da abokinsa Malami ne a makarantar, suna zuwa office ya masa bayanin Aishat Malamin ya ce”oh! Head girl ka ke fad’a?”. Haiydar ya ce” eh ita ce”. Malamin ya aika aka kirata, bata dad’e ba ta zo. Malamin ya basu guri a office d’in, Aishat wani mugun kalo ta masa, ta ce”lafiya Malam mai ya kawoka makarantar mu?. Miye alakarka da ‘Yar aiki, kuma ‘Yar shege?. Haiydar ba na son ganinka, i hate you”. Nan ta ke ya ji zuciyarsa na tafarfasa, don jin kalamanta ya ke, har cikin kwakwalwan kansa, cikin tsawa ya ce”ya isa haka!, Aishat mai ya sa bakya tausayina ne?. Aishat in kinji yanda zuciyata ke bugawa a kan k’aunarki. Please ki taimaka ma rayuwata, ki yi kahuri da abunda ya faru, ki manta komai dan Allah!”. Wani kalon banza ta sama nai nuna alamar baka da wayo, juyawa tayi za ta fita, cikin hanzari ya sha gabanta, matsawa ta soma yi, shima ya na binta, cikin dakiyar zuciya tace”wai lafiyanka kuwa? Wannan wani irin iskanci ne haka?”. Haiydar ya yi wa ni murmushi, ya ce”Aishat ko kin manta matsayina a gunki? Ni fa mijinki ne na sunnah, kuma ina son inji d’umin jikin matana a tare da ni”. Cikin tsiwa Aishat ta ce”Allah ya sauwake wa ye za ta had’a jiki da kai? Wai ko ka manta Aishat ‘yar aiki ce? Cikin zafin na ma Haiydar ya matso kusa da ita, hab’arta ya kamo. Kuyi hakuri da wanna ba yawa, yau ina bussy ne. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [7/10/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* Pg-190~193. Cikin tsiwa Aishat ta ce”Allah ya sauwake, wace zata had’a jiki da kai?. Wai ko ka manta Aishat ‘Yar aiki ne? Kuma ba’kar mace, wanda bata waye ba, marar ilimi. Mai zakayi da ni Indo?”. Cikin zafin nama Haiydar ya riko hab’arta, ya ce”mai ki ka ce?”. Aishat ko alamar tsoro babu a tare da ita, ta sake mai-maita abunda ta fad’a. Haiydar ya sassauta murya ya ce”Aishat always be the first to forgive the other person”. Wani mugun kalo ta masa ta ce”oh! Yanzu ne kasan da haka? Ko ka manta irin tsa….. Bai bari ta k’arasa ba, ya toshe mata baki da hannusa. Aishat hannu tasa tare da zage iya k’arfinta ta turesa, sai da Haiydar ya d’anyi tangal- tangal kamar zai fad’i. Aishat tana kaiwa bakin k’ofar office d’in, ta juyo tare da rike k’ugu, ta ce”Haiydar ni Aishat ba tsaranka ba ce, a yanzu ne na dawo mutum? Kasani kwarya ta bi kwarya, kuma *DAI-DAI RUWA DAI-DAI GARI*. Ni Aishat Yar shege ce kuma bakace ni, sai kuma nayi sa’a baka son ba’kar mace, to mai za kayi dani?. Haiydar duk ya rasa inda zai sa kansa, hannusa ya had’a biyu alamar hakuri. Aishat ta aika masa da harara ta ce” Aliyu kake da suna ko? To ka sani wutsiyar rakumi tai nesa da kasa, da ga yau sai yau, karka kara shiga sabgata, kayi hanyarka nayi tawa mtsss”. Ta saki tsaki ta fita abunta ko ta wai-wayesa. Haiydar dafe k’irjinsa yayi, don zuciyarsa wani irin zogi take masa, kujera ya nima ya zauna, ya lumshe ido, a haka Abokinsa yazo ya samesa, fuska yayi ya b’oye damuwarsa, sallama yayi ma Abokinsa tare da masa godiya ya fito ya bar makarantan. Aishat ta na shiga class da Sadeey suka fara karo, Sadeey ta ce”ya dai lafiya? Mai ya sameki?”. Aishat batace komai ba, Sanah ce ta shigo class d’in, da sauri ta k’araso gurinsu ta ce”Aishat lafiya kuwa yanzu naga Haiydar zai shiga motarsa a school d’in nan? Ko dai shi ya aika a kiraki?”. Aishat taso ta b’oye musu amma jin Sanah taga Haiydar, kawai ta sanar musu komai. Sanah ta ce”Aishat ba wai ina had’a ki da mijinki ba, gaskiya karki kuskura ki basa fuska, yanda ya wulakanta ki, ya kamata ki rama kema, ki basa wahala har sai ya gane kurensa, don baiyi nadama ba tukun da sauransa”. Sadeey ta ce”gaskiya kam”. Haka sukayita hira har lokacin tashi yayi suka fito. Haiydar ko da kyar ya iya jan motar ya koma gida, don ko ya koma office ba zai iya aikata komai ba. ‘Daki yaje ya kwanta tunani yake kala-kala, cikin zuciyarsa ko cewa ya ke”ya zanyi da k’aunar Aishat da ke baraza ga rayuwa ta? Duk wanda yayi yunkurin rabani da Aishat, to tabbas na san baya k’aunata, barema in Allah ya yarda ba abunda zai sa na saketa, ko da zatayi ta gallaza min a haka”. Aishat ko tana tashi daga makaranta gidan Hajiya ta wuce, a gun ta yini, sai yamma ta koma gidanta, ta na zuwa d’akinta ta shiga, wanka tayi kafin ta fito, kitchen tashiga ta girka kuskus da miyan stew, falo ta fito ta zauna tana cin abinci, Haiydar ya d’an kwaso yun warsa ya ga Aishat tana cin abinci, cike da isa ya ce”ke tashi ki zubo min nawa”. Banza tayi dashi kamar bata jishi ba, ganin bata da niyar tashi, ya ce”in fa bazaki zubo min ba, to zan kwace naki”. Nan ma bata ce masa ba, ganin haka yayi kanta zai kwace abinci da gudu ta mike ya bi bayanta. Dai-dai lokacin Falmi ta sanyo k’afarta cikin falon, dai-dai lokacin kuma Aishat ta iso gabanta, turus suka tsaya dukkansu a gabanta cike da tsoro a fuskansu, jakan da ke hannuta ne ya fad’i a kasa, ba k’arami gir-giza tayi da ganin su haka ba. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH LUV * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [7/11/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-194~196* Ba k’aramin razana tayi da ganinsu cikin wannan yanayi, Aishat ta razana amma shirin ko ta kwana da tayi, hakan yasa ta shanye damuwarta, ta juya sai murgud’a jiki takeyi, ta kama hanyan komawa falo, Haiydar ko yanuna damuwarsa, shima ya juya da niyar komawa cikin falon. Falmi da sauri tasha gabansa, cike da masifa ta fara ce wa”Haiydar asai baka da mutunci? A sai kai d’an iska ne? Maciyi *AMANA*. To asirinka ya tonu, karasa wacce zakana bi sai Yar aiki na?”. Wani mugun kalo ya sakarmata, bai tanka mata ba yabi gefe zai wuce, da sauri ta sha gabansa tare da shan kwalar rigansa. Hannunsa yasa ya b’amb’are hannuta daga jikin rigarsa, da sauri tasake tare gabansa, Haiydar ya ce” Falmi ki bini a hankali duk wani rashin kunyar da kike take, tsaf zanyi maganinsa, karkiga na kyaleki kina yanda kikeso, kice zaki takani son ranki, a k’ark’ashina kike”. Wuceta yayi ya nufi d’akinsa, sam shi baya son hayaniya. Falmi ganin ya tafi, ta juya gun Aishat daniyar mata rashin mutunci. Aishat ko ta d’aura kafa d’aya akan d’aya, Falmi ganin irin zaman da tayi gashi k’ananan kaya ne ajikinta, don duk suran jikinta ya bayyana, hakan ya k’ara b’ata mata rai, ta iso gaban Aishat ta ce”ke Yar aiki kuma Yar shege wa ya baki daman saka wa ‘yannan kayan?”. Aishat tayi banza da ita bata amsa mata ba, hakan yak’ara kub’ular da ita. Ta sa ke ce wa”ke k’aramar ‘Yar iska da e fa nake magana”. Aishat ta saki lallausar murmushi, ta mik’e tare da gir-giza jikinta ta tak’o har gaban Falmi, sai da tamata kalon ido cikin ido, ta sake k’ara taku biyu zuwa uku, kafin ta juyo ta ce”Fatima kike ko Falmi? Ko ma dai wa kike duk ba damuwa ta insan sunan bane”. Falmi kasake tayi don tsananin mamaki, ko motsi ta kasa, sai bakin da ta sake tana kallon Aishat. Aishat ta ci gaba da cewa” ina sane da duk wani wulakancin da kika min tun daga tasowa ta, harda cin mutuncin da kukayi ma uwata, kin wulak’anta ni wulak’ancin da ko kare baza’a masa ba. Falmi ki sani da da yanzu ba d’aya yake ba, ki sani biyu yafi d’aya, kamar yanda uku tafi biyu. Ki sani wutsiyar rak’umi tai nesa da k’asa, kamar yanda na tsere miki yanzu. Ki sani a da kin taka Indo ta kyaleki, a yanzu na canza daga Indo zuwa Aishat, kuma Aishat bata juran wani raini da wargi. Samun kwanciyar hankaliki da zaman lafiyanki a gidan nan, shine kiyi sabgarki, banda shiga hark’an Ashanty baby, domin bana juran wani wargi. A hankali tasoma takawa tana sarrafa mazaunanta da k’irjinta, taku uku ta k’ara ta juyo ta ce”oh! Na manta ban sanar da ke, ko da gigin wasa karki ce zaki ne mi Aishat da fad’a, don bana had’a k’irji da kishiya kuma banga wannan kishiyarba, kuma ina fatan kinji duk abunda na fad’a miki?. Ta juya idonta ta ce” na manta ban miki godiya da karamcin da kika min, gaskiya kin can-canci in gode miki, kin had’a ni aure da gwarzon Mijiki Haiydar kuma kin iya had’i sosai, don ni kaina na san, nasamu mijin nuna wa sa’a gashi kyakyawa, jarumi a kowanne fage nagode”. Hannu Aishat tasaka akan bakinta tare da yin kiss ta hura ma Falmi, ta saki wani murmushin mugunta, don yanda taga Falmi ta dawo, juyawa tayi ta nufi d’akinta tana rangwad’a. Falmi batan lokacin da ta d’aura hannu aka ta fara ihu tana cewa”lalle yau nasan na *TAFKA BABBAN KUSKURE* wato d’an hakin da na raina…… Na raina Indo sai ita ce zata gasa min aya a hannu”. Ni ko Rash ina gefe na ce”gaskiya wannan show d’in yayi Aishat ta burgeni. Lalle wannan shi ake kira da *BABBAN KUSKUREN DA KI KA TAFKA* Falmi”. Gyara zama nayi don inci gaba da kalon wannan gurmi mai k’ayatarwa, kashh! Sai ga wayata tana nuna battery low. *®NWA.* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [7/12/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-197~199.* Ta juya idonta ta ce” na manta ban miki godiya da karamcin da kika min, gaskiya kin can-canci in gode miki, kin had’a ni aure da gwarzon Mijiki Haiydar kuma kin iya had’i sosai, don ni kaina na san, nasamu mijin nuna wa sa’a gashi kyakyawa, jarumi a kowanne fage nagode”. Hannu Aishat tasaka akan bakinta tare da yin kiss ta hura ma Falmi, ta saki wani murmushin mugunta, don yanda taga Falmi ta dawo, juyawa tayi ta nufi d’akinta tana rangwad’a. Falmi batan lokacin da ta d’aura hannu aka ta fara ihu tana cewa”lalle yau nasan na *TAFKA BABBAN KUSKURE* wato d’an hakin da na raina…… Na raina Indo sai ita ce zata gasa min aya a hannu”. Falmi ta fara Safa-da-marwa a falon bakinta ta ciza tare da dunkule hannu, tana tunanin mafita yanzu wani mataki zata d’auka gashi taga Aishat da zafin ta take can komai ta tuna tasaki lallausa murmushi ta nufi dakinta wanka tashiga don tasamo ma kanta matakin da zata d’auka. Aishat ko tana barin falo da gudu tayi d’akinta key(mabud’i) tasa ma d’akin ta rufe tare da jin gina a jikin k’ofar dakin tana maida numfashi. Wani sassanyan ajiyar zuciya ta saki a fili ta furta” lalle na iya cika baki duk wannan kurarin kamar zan iya dukan Falmi ai ko yau da ta shakeni sai dai wata Aishat bani ba”. Jin kamar motsi yasa ta zabura jikinta sai b’ari yake ta ce”wayyo yau na janyo ma kaina tabbas yau inta rikeni nikam sunana gawa”. Wani dabara ne ya fad’o mata doguwar kujeran hutuwa dake cikin d’akinta ta janyo zuwa bakin k’ofar ta tokare k’ofar dashi, wai ko da Falmi ta biyo ta bazata iya b’alle k’ofar ba. Sai zufa takeyi ga tsoro da take ji duk a razane take sai zare idanu takeyi tamkar wacce tayi ma sarki lafi. Haiydar ko d’aki ya koma yana tunanin irin rayuwan da zaiyi da matansa biyu, gashi yanzu ba abunda yake da k’auna da muradi kamar Aishat amma sam bai ganin fuska ajiyar zuciya ya sauke a fili ya furta”Allah ka sanya Aishat sona”. Mik’ewa yayi tare da d’aukar key (mabud’i) d’in motarsa ya fita waje don ya samu abunda zai ci. Falmi ko tana fitowa cikin hanzari tasoma shiri make-up (kwaliya) tayi ta d’auko kaya tasaka tare da d’iban kud’i tana wani murmushin mugunta ta fita. Wayarta ta d’auka ta kira wata magana sukeyi kasa-kasa wanda nikai na Rash duk son d’ibo rahoto na bansamu damar naji mai take ce wa ba, dole na hak’ura injira ta gama na bita naga mai take shiri aikatawa. Haiydar yana fita gurin cin abinci yanufa ya sayo guda uku, gida ya dawo ko da yazo falo yaga ba kowa, d’akin Falmi ya nufa yaga batanan da alamar ta fita ledar da yaso nata ya ajiye mata. Ya nufi b’an garen Aishat ko da ya tura k’ofar yaji a kulle sai ya kwan-kwasa k’ofar. Aishat da take ciki jin an kwan-kwasa k’ofa take cikinta ya bada sautin kululuuu! Wani fitsari ne ya taho mata bashiri ta sa hannu tana matse k’asan k’afarta duk a tunaninta Falmi ne, bata san lokacin da yanka bayi da mugun gudu ta kulle bayi sai ga fisari na gan- garowa ta k’asan k’afarta. Niko Rash mai zanyi in banda dariya nace”haba Indo karki bada ni mana duk kurarinki nan ace kina wannan tsoro haka?”. *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-200~203.* Aishat da take ciki d’aki jin an kwan- kwasa k’ofa take cikinta ya bada sautin kululuuu! Wani fitsari ne ya taho mata bashiri ta sa hannu tana matse k’asan k’afarta duk a tunaninta Falmi ne, bata san lokacin da yanka bayi da mugun gudu ta kulle bayi sai ga fisari na gan- garowa ta k’asan k’afarta. Sai rarraba ido takeyi jin an kara buga k’ofar ae sai ga fitsari na zuba take idanunta suka soma ciko da kwalla addu’a ta fara karantowa duk wanda yaxo bakinta kawai yi takeyi. Falmi ko duk wani tugu da zata had’a ta had’a, bata soma shirin dawowa gida ba sai k’arfe tara da mintuna. Haiydar jin shiru yayi yawa ba a bud’e ba da har zai tafi sai ya fasa, sunan Aishat ya kira sai da yayi baki uku. Aishat daga bayi taji muryan Haiydar da kamar bazata fito ba, amma sai ta daure tana d’an sand’a ta fito falo muryan shi taji, sai da ta tattara nutsuwarta ta amsa ta ce”gani ina zuwa”. Bayi ta koma ta d’auraye jikinta ta fito zani ta d’aura kafin ta bud’e k’ofar. Haiydar ya ce”beauty ina kika shiga?”. Sai da ta d’anyi jim kafin ta ce”na d’an shiga wanka ne shiyasa”. Haiydar yayi murmushinsa mai k’ayatarwa ya ce”beauty shine bazaki kirani inzo na miki ba, bai kamata kina wahala da kanki alhalin gani a cikin gidan miye amfanina? Kin san bana so ki wahala da yawa”. Haiydar ya karashe maganan tare da d’aga ma Aishat gira tare da kashe mata ido d’aya. Aishat ta kauda kanta gefe ta ce”bana bukatar hakan kuma da wake min wanka? Ko kaine kake min? Don haka bana bukatar hakan”. Zai sake magana ta ce”wai lafiya kuwa? Ni fa zan rufe k’ofa don ina da abunyi”. Haiydar ya san halinta da sauri ya mik’a mata ledar bata bari yayi magana ba ta ce”thanks you”. (Nagode maka). K’ofar ta mayar ta rufe tare da sakin sassayan ajiyar zuciya ledar ta ajiye taje tayi wanka kafin tazo ta bud’e ledar sai da taci abinci dake ciki tayi hamdalah ta tattara kayan zata fitar waje nan fa ta tuna da abunda ya faru kamar zata koma ta ce”ai Haiydar yana gida ba zai bari ta bugen ba”. A hankali ta bud’e k’ofar d’akin da sand’a ta ke tafiya, sai da tazo dai-dai falo ta d’an leka taga ba koma sai da ta leka hanyar d’akin Falmi taga ba kowa kafin ta fito sad’af-sad’af take tafiya har ta kai komai kitchen (madafi) tukun ta dawo nan ma sai da ta leka har tazo tsakiyar falo taji ance kee ba karanin razana tayi ba take kayan cikinta suka soma bada sauti shooky. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [7/14/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-204~206.* Kee taji ance bak’aramin razana tayi ba sai da kayan cikinta suka fara shooky. Duk ta gama d’auka Falmi ce harta had’a hannayenta biyu alamar zata bada hak’uri, a hankali ta juyo sai ganin Haiydar ne ke waya da alamar ransa na b’ace gashi kuma ya ganta ta rasa ya zatayi sai kawai ta wayance taci gaba da sand’ar sai ta d’an jiyo kamar mai wasa abinko sai ya mata kyau. Haiydar kasa d’auke idonsa yayi daga gareta harta shiga side d’inta. Aishat tana shiga ta sauk’e ajiyar zuciya bayi taje tayi brush tazo ta kashe wuta tayi addu’a ta kwanta. Haiydr kasa tashi yayi a falon yana jiran yaga dawowar Falmi ransa ya gama b’aci sosai. Falmi ne tashigo da sallamarta ganin Haiydar ta b’ata rai itama tare da k’arasowa cikin falon, Haiydar cikin b’acin rai ya ce” kee daga ina kike?”. Falmi bata tanka masa ba sai wani harare-harare takeyo, Haiydar ya ce”Falmi kinason ki b’atamin gidana don Aishat duk abunda taga kinayi shi zata koya wanda ni kuma bana so ko kad’an ta koyi munanan d’abi’unki”. Wani harara Falmi ta b’alla masa tare da jan tsaki tayi d’akinta, da sauri ya bita ama kash! Ta sanya ma d’akin key (mabud’i). Ransa ya gama b’aci bai san lokacin da ya fara safa-da-marwa a falo tare da dunkule hannusa ya bugi iska, da kyar yasamu ya koma d’aki ya kwanta zuciyarsa na masa suya. Da safe da wuri Haiydàr ya fita Aishat ma ta shirya school bus yazo d’aukarta, ko da taje school da suka zauna da su Sanah ta basu labari abunda ya faru dariya sukayi sosai kafin suka bata shawarwari. Sai da aka tashi ta bi gidan Hajiya sai da tayi la’asar kafin ta d’au motar ta nufi gida daman a gidan ta bar motar. Tafe take tana tuk’i cikin nutsuwa tun daga unguwansu Haiydar taga kanar wata mota kirar jeep bak’a da glass bak’ak’e tana binta, sam bata kawo komai ba tayi ta tafiyanta sai da tazo hanyar shiga unguwansu bayan Airport taga wannan motar tazo da gudu tasha gabanta, gashi gurin bakowa shiru gurin wasu bak’ak’en mutane ne suka fito daga bak’ar jeep d’in nan tare da zuwa dai-dai jikin motarta suka bud’e, cike da tsoro ta ce”lafiya mai na muku? Dan Allah kuyi hak’uri in motar kukeso in fita na baku amma kar kuyi min komai”. Wani daga cikinsu ya wanka mata lafiyayen mari ya ce”zaki rufa min baki ko-ko sai kinji maza?”. Take jikinta ya soma b’ari idonta sai ruwan hawaye ke zuba, d’aya daga cikin mutanen ya ce”yah! Oga zamu gama da ita a nanne?”. Wani murmushi Ogan yayi ya ce” no zamu tafi da ita don naga ta min zata yi test(d’an-d’ano)dole sai na huta da ita kafin mu gama da ita. Aishat najin haka ta fara zatayi ihu d’ayan ya zaga ta bayanta ya mata kyakkyawan riko wani yazo manna mata salatab a baki, k’okarin janta suka somayi amma tana turjewa abunka da fatar mace mai samu hutu, garin janta taji ciwo a hannu sai ga jini yana zuba har saida ya d’idd’iga a gun. Ogan gani tana da taurin kai kuma zata b’ata musu lokaci yazo dai-dai ita cikin muryan ‘Yan iska ya ce”tun da ki kayi taurin kaikuma ki ka b’ata mana lokaci kafin mu aiwatar da aikin da’aka samu sai nida Yarana mun biya buk’ata dake, bakinsa ya lashe tare da kawo hannusa ya shafi k’irjinta ya saki mayen murmushi haka suka jata zuwa motarsu suka tayar su ka bar gurin. Ni Rash bansan lokaci da nasaki k’ara ina binsu ina kiran Haiydar amma ina sunyi nisa ba taimakon da zan iya bata a lokacin sai addu’a. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH LUV * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [7/16/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-207~209.* Ogan gani tana da taurin kai kuma zata b’ata musu lokaci yazo dai-dai ita cikin muryan ‘Yan iska ya ce”tun da ki kayi taurin kaikuma ki ka b’ata mana lokaci kafin mu aiwatar da aikin da’aka samu sai nida Yarana mun biya buk’ata dake, bakinsa ya lashe tare da kawo hannusa ya shafi k’irjinta ya saki mayen murmushi haka suka jata zuwa motarsu suka tayar su ka bar gurin. Gudu suke sharara wa Aishat ko sai hawaye takeyi tanaso ta basu hak’uri amma ina ba hali bakinta yana rufe gam da salatab Ogansu ko tasata yayi a gaba yana kalonta don ya rinyar ta matuk’ar masa kyau ji yake koma dai ya fasa aiwatar da abunda aka sasune kawai ya b’oyeta ya mayar da ita Matar sa kuma inda zai na hutawansa. Fatan bakinsa ya lashe tare da yin wani murmushin mugunta. Falmi ko tana cikin wasu kawayenta wanda kalo d’aya zaka musu ka gane tattatun ‘Yan bariki ne masu ji da bariki, wata kawar Falmi ta kaleta ta ce”Falmi gaskiya baki da kyau yanzu abunda ki ka sa ayi kenan niko kishiyarki kyau ta ke min”. Wani mugun harara Falmi ta sakar mata ta ce”yanzu zamu b’ata da ke don duk wanda zai bi bayan Indi ko ya sota to tabbas makiyina ne ina adawa da shi”. Gwantsi da ke gefe jin kalaman Falmi ta shek’e da dariya ta ce”har uwar Haiydar d’in kenan kina adawa da ita”. Falmi ta ja tsaki”mtsss ita a su wa yanzu next harina ita ce daga nan ina fita gidan mu zaje gun Mummy na ne, dole mu koma gun Malamin nan inaga asirin nan ya karye ne”. Gwantsi ta ce”ni ko in da ni ne ke Falmi bazan tayar da hankalina ba tunda gaki kintara kud’i kin dawo babbar mace, gaki da naira kuma ai Haiydar yana sonki da yawa tunda ke kikace da hannusa ke baki kud’in nan”. Falmi ta ce”ke fa zabaki gane bane Haiydar nawa ne ni kadai da kinga abunda Indo ta min jiya sai kin bani goyan baya dari-bisa-dari”. Wata Mama Zeey da ta ke gefe ta ce” ina bayanki karki ragar musu ko d’aya ai kishiya ba abin so bace kishiya! Kishiya!! Kishiya!!! ina bayanki a gama da ita kawai ki huta”. Haka suka ci gaba da hiransu kowace da gur-guwan shawaran da take bata a gun. Haiydar yana office duk ya ji hankalinsa ya tashi ya kasa zaune ya kasa tsaye zuciyarshi ba abunda take tunaso masa sai Aishat, haka kurun ya tsinci kansa da son ganin Aishat a wannan lokacin cikin hanzari ya tattara komai daman time d’in tashi ya kusa. Da sauri ya fito ya nufi motarsa ya shiga cikin sauri ya ke tuk’in sai da ya kusa shiga unguwamsu gabansa ya soma fad’uwa sai gumi ke ketomasa, k’ara gudun motarsa yayi ga gumi sai k’ara keto masa yakeyi duk da sanyin A.C da ke motar amma bai hana sa yin gumi ba. Tun daga nesa ya ke hango wani mota sak irin na Aishat amma sai wata zuciya ta ce masa” mai zai kawo Aishat nan kawai dai kalar motar ce d’aya, ko da ya iso gun k’ofofin motar a bud’e ya ke, ganin school bag d’in Aishat bai san lokacin da yatak wawan burki ba ya fito daga motarsa. Da gudu yayi gum motar baiga kowa ba sai ya lek’a ciki ba ta nan ga hijab d’in mak’arabtarta a gun da hularta, sai takalminta kafa d’aya ko da ya kali kasa nan yaga jinin da ya d’id’iga a hankali ya soma bin jinin har ya kaisa gun da ‘Yan iskannan suka aje motarsu, nan ma yaga alamar kafa inda kayi kokawa da kuma alamar ta k’arfi aka d’auketa, ga tayar motarsu da yayi ribas da kuma yanda ya tashi. Haiydar baisan lokacin da yasaki k’ara ba ya na kiran”Aishat! Aishat!! Aishat! Kina inane? Mai ya same ki? Wa ya tab’a min ke?”. Fad’uwa yayi a kan gwiwarsa kamar mai (nil down) yana k’araji yana ihu ga hijab d’in Aishat a hannusa ya na kuka wi-wi kamar yaro. Da gudu ya tashi yayi gabar yana kiran Aishat! Da gudu ya dawo yayi yamma yana kiran Aishat!! Ya sake dawowa yayi Arewa yana kiran Aishat!!! Yazo ya sake yin kudu yana kiran sunanta, ya dawo kaman zarare. Masu karatu sai kun gansa abun gwanin ban tausayi ni kaina Rash bansan lokacin da hawaye yasoma gan-garo min ba. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-210~213.* Fad’uwa Haiydar yayi a kan gwiwarsa kamar mai (nil down) yana k’araji yana ihu ga hijab d’in Aishat a hannusa ya na kuka wi-wi kamar yaro. Da gudu ya tashi yayi gabar yana kiran Aishat! Da gudu ya dawo yayi yamma yana kiran Aishat!! Ya sake dawowa yayi Arewa yana kiran Aishat!!! Yazo ya sake yin kudu yana kiran sunanta, ya dawo kaman zarare. Ya dad’e a haka ya kasa tab’uka komai sai kuka tamkar mace kamar ba jarumin d’an sanda ba mai hazak’a da kwazo wayarsa ne tayi k’ara yana kuka ya ciro daga aljihunsa ya ga sunan Hajiya kafin ya d’auka harta tsinke. B’an garen Hajiya ko ta ce”yau lafiya banga Aliyu ya d’au wayata ba?”. Kamar ta ajiye wayan sai wani zuciya ya ce”kawai ki sake kira kiji lafiyarsa dana d’iyarki”. Cikin hanzari ta danna kira. Haiydar jin waya na ringing ga jikinsa sai b’ari yakeyi (daman wannan yanayinsa ne in ransa ya b’aci jikinsa b’ari zainayi). Da kyar ya iya danna gun amsa kira yasa a kunnensa kuka yakeyi yana kiran Aishat! Ciki razana Hajiya ta ce”Aliyu lafiya mai yasamu Aishat?”. Bai iya amsa mata tambaya ba sai ce mata” Hanyan gida b’ata Aishat”. Sam kwakwalwarsa ta kasa tuno masa ma ya zai had’a kalman a dai-dai ya fad’a Hajiya cikin kid’ima tun da taji yananyi Haiydar tasan abun ba k’arami bane, ta d’auko hijab d’inta ko Abban su Haiydar dake hanyan dawowa yau bata sanar masa ba ta fito a gi-gice, bata tsaya kiran driver ba(mai tuk’a mota) kasancewar daman ta iya mota da sauri ta figi mota tun daga nesa take horn ma mai gadi, shi kansa mai gadi sai da ya rud’e da horn d’in da takeyi ai ya na wangale gate(gareji) da mugun gudu ta fita. Gudu take shararawa cikin min tunan da baifi hud’u ba ta soma hango Haiydar ga kuma motar Aishat! Gudu ta k’ara tana isowa ta gansa a durk’ushe a kan gwiwansa zuwa tayi da sauri ta rugumesa tana jijiga sa ta ce”Aliyu lafiya? Ina Aishat d’in?”. Jinsa a jikin Hajiya ya saki sassayan ajiyar zuciya sai a lokacin nutsuwa ta zomasa, cikin kuka ya sanar da Hajiya abinda ya tarar Hajiya ta ce”innalilahi wa inna ilaihi raji’u ai ba zama zakayi kana kuka ba, kaman ba jarumin police ba?” Abunda ya da ce zamuyi yanzu tashi kabi sawun motar sannan ka kira duk wata ma’aikatar police da ke kusa a sane dasu don a baza matakan tsaro. Haiydar ya shiga motarsa zuciyansa na suya gun aikinsu ya kira yasanar musu ya ce”susanar da sauran ma’aikatar hukumar ‘Yan Sanda a bazama wasu su biyo sa, hayar da mota tayi yafara bi har ya fitar dashi bakim ti-ti, daga nan kuma hanya ta kasu kashi uku ya tsaya yana tunani sai ga wasu motocin police(‘Yan sanda) sun iso mota uku nan suka kasu kashi uku d’aya yabi Haiydar biyu suka bi sauran hanyoyin. Abu wasa-wasa suna neman Aishat ba labarinta gashi har anyi sallah isha’i. Aishat tare da ‘Yan iska tafiya sukeyi sai shiga cikin daji sukeyi yayinda jinin jikinta sai zuba yakeyi kasancewar ta mai yawan cin abinci mai kyau tanada wadattace jini amma sanadin zuban da yayi da yawa ya haddasa mata jin jiri, idanunta suna wani iri, hakan baisa Ogan ‘Yan iskan nan yayi niyan saurara mata ba sai aika mata da mayen kalo yakeyi. Su Haiydar ko sunyi nima harsun gaji amma shi baijin gajiya a tare da shi zuciyarsa suya yake masa yama rasa wani irin kalan hukunci zai yanke ma wanda ya d’au Aishat d’insa tabbas ba zai iya saurara masa ba baran yanda yanzu yake jin tsananin k’aunar Aishat na yawo a jinin jikinsa da jijiyoyinsa tafiya suke ga dare yayi ko da ya kali agogon da ke hannusa 11:49 wani kwana ya gani wanda ya lula cikin deji kuma hanyar k’aramace mota bazata sake acikin hanyan ba wasu suna cewa kar abi hanyan halane ko sunbi ta gun gashi yayi daji ko da Haiydar batunsu ransa da ya b’aci ya finciki motar ya shiga cikin dajin, sauran suna ganin ya shiga suka bisa a baya sai yayi tafiya sosai sai yaga wani abu a gefe kamar mutum ne ko tudu, da sauri ya tsaya ya fito da wani touch light d’insu mai haske yana haskawa ya hango Aishat kwance bata motsi da gudu yayi gunta yana haskawa yaga jini na fitowa daga k’asan skirt d’in makarantarta wani razazane k’ara ya saki ya soma jijigata ganin bata motsaba, dai-dai lokacin sauran police d’in suka iso, bai bi ta kansu ba da gudu yayi mota da ita ya sanya ta a mota ya juyo ya ce”ku tabbatar da kunbi mutanenan kuma kun kamosu zan turo wasu motocin su biku”. Bai jira amsansu ba ya juya ya shiga mota ya figeta da gudu ya nufi cikin gari. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMA ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [8:05PM, 7/16/2016 BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-214~216.* Dai-dai lokacin sauran police d’in suka iso, bai bi ta kansu ba da gudu yayi mota da ita ya sanya ta a mota ya juyo ya ce”ku tabbatar da kunbi mutanenan kuma kun kamosu zan turo wasu motocin su biku”. Bai jira amsansu ba ya juya ya shiga mota ya figeta da gudu ya nufi cikin gari. Gudu yakeyi sam ba nutsuwa a jikinsa wani wawan duka ya kaima sitiyari motar tare da furzar da wani isaka mai zafi zuciyarsa na masa rad’ad’i wai ace abunda yagama tanadi wani ya rigasa wasu zafafan hawayene suka zubo masa wata b’an gare na zuciyarsa ya ce”haba Haiydar duk da abin da ciwo kardai kace zaka guje ma Aishat don son da ka ke mata na gaskiya ne bawai jikinta kake so ba. A fili ya furta” Aishat a kowani hali ki ke ina k’aunarki ke ce SIRRI NA bazan gujeki ba”. Wasu hawaye ne suka sake zubo masa, wayarsa ce tayi k’ara sunan Hajiya ya gano ya d’aga cikin muryan kuka ya ce”Hajiya an sameta amma sun mata fyad’e gata ko motsi batayi”. Hannu a ka Hajiya ta d’aura ta saki salati ta ce”yanzu kuna ina ne Aliyu?”. Ya ce”gani a hanya da ita zan wuce T.H”. Hajiya ta ce”okay gamu zuwa da Abban ka yanzu shima ya dawo”. Kashe wayar yayi ya k’ara gudu wanda kiris ya rage motar ta kwace a hannusa Allah ne ya kare. Bai dad’e ba ya isa Asibiti take a ka shiga da ita Emergency Haiydar ya gagara tsaye ya gagara zaune sai safa-da-marwa ya keyi a k’ofar idonsa na zubar da hawaye, Hajiya ne da Abba suka iso kalonsu kawai yayi ya fashe da kuka mai cin rai, Hajiya ma hawaye tafara don abun ya mata ciwo bana wasa ba. Falmi ko gidansu ta nufa ita da Mum d’inta suka tafi gun boka ita duk a zatonta an gama da Indo dan haka ta ce”boka kaban maginda sai abunda na fad’a ma Haiydar zai yi ba kuma zai ki bin umarni na ba”. Bokan ya bushe da wata mahaukaciyar dariya ya ce”anyi angama yarinya kinzo inda za’a share miki kukan ki hahahah”. Kwarya ya d’aga sama saiga wasu magun-guna sun zuba a ciki nan ya mik’a mata ya ce”ga wannan turaren ki tabbatar kulum kinshafa a jikinki, sannan wannan maganin ki kuskure bakinki da shi kulum”. Falmi cikin zud’i ta ce”anyi an gama boka”. Bokan ya kara wata dariya kafin ya ce”maganin mu da doka kisani duk randa kika tsallake d’aya aciki asiri zai karye kuma zai miki wulakanci mummuna”. Ta ce”zan kiyaye boka”. Kud’i ta zuba masa suka tafi. A can asibiti kuwa Dr ya bata taimakon gaggawa saida numfashinta ya dai-daita kafin suka duba kasanta asai ba fyad’e a ka mata ba kukkurjewa tayi acinya wanda ya janyo mata zuban jini. To ni Rash abun ya d’auremin kai bare masu karatu, amma bari mu wai-wayi baya, in baku manta ba na ce muku”ciwon da Aishat taji ya haddasa mata zuban jini sosai wanda haryasa idonta yin wani iri”. Bayan da ‘Yan iskan nan suka cigaba da tafiya da ita jininta ya zuba ga razana da tayi hakan ya sanya ta yanki jiki ta fad’i tayi dogon suma idanunta sun kafe, ‘Yan iskan nan da suka ga haka sun d’auka mutuwa tayi, shiyasa Ogansu ya ce”kawai su yarda ita anan tunda ta mutu ba amfanin su fita da gawa karma a kamasu”. Tundaga bakin hanyar da zai shigarda mutum dajin da aka sameta suke janta a kasa wanda yasa skirt d’inta kwayewa jikinta ya jijiciwo kunji dalilin zuban jinin bari mu koma labari. Ko da Dr ya gama dubata ya gito cikin hanzari Haiydar da Hajiya sukayi gunya a tare suka jefo masa tambaya “Dr ya jikinta?” Dr ya ce”da sauki Alhamdulilah kuma ba fyad’e aka mata ba kurjewa tayi, ga jini ya zuba da yawa don haka muna buk’atar jini cikin sauri Haiydar ya ce” Dr muje a d’ibi nawa a samata”. Cikin ikon Allah jininsu yayi dai-dai aka samata Dr ya ce”ya kamata a canza mata kayan jikinta sun b’aci”. Haiydar ya amsa da “to”. Ya kalisu Hajiya ya ce”barinje gida na d’auko mata wasu kayan”. Hajiya ta kalli agogo wayanta karfe biyu da rabi ta ce”to kaje Allah ya kareka”. Ya amsa da “Ameen”. Ya fita gudu yaringa shararawa har ya iso gida horn ya ringa yi Falmi cikin bacci taji horn d’in kafin da sauri ta leka taga Haiydar ne ke shigowa cikin sauri ta shafa turaren nan ta kuma shiga bayi ta kuskure bakinta da ruwan maganin ta nufi k’ofar falo. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [7/17/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-217~218.* Dr ya ce”ya kamata a canza mata kayan jikinta sun b’aci”. Haiydar ya amsa da “to”. Ya kalisu Hajiya ya ce”barinje gida na d’auko mata wasu kayan”. Hajiya ta kalli agogo wayan ta karfe biyu da rabi ta ce”to kaje Allah ya kareka”. Ya amsa da “Ameen”. Ya fita gudu yaringa shararawa har ya iso gida horn ya ringa yi Falmi cikin bacci taji horn d’in kafin da sauri ta leka taga Haiydar ne ke shigowa cikin sauri ta shafa turaren nan ta kuma shiga bayi ta kuskure bakinta da ruwan maganin ta nufi k’ofar falo. Cikin rashin sa’a kafin ta riskeshi har ya shiga d’akin Aishat ya d’ibi mata kaya kala biyu marasa nauyi ya fito kenan sukayi two eyes(ido biyu) da Falmi hannuta a kan k’ugunta cikin isa da gadara ta ce”kai daga ina kake a cikin wannan dare?”. Haiydar duk sai ya ji komai ya kwance masa ya tsinci kansa da ba zai iya yi mata musu ko gardama bare yaki bin umurnin ta, sai da ya yayi jim kafin ya ce”daga Asibiti nake”. Cikin hanzari ta ce”waye a Asibiti?” Haiydar ya kalleta ya ce”Aishat ce”. Dammmm! k’irjin falmi ya bada sauti bata san lokacin da ta sanya hannu a k’irjinta ta dafe ba ta ce”mai ka ce?”. Haiydar yasake mai-maita abunda ya fad’a nan take zuciyar Falmi yafara azal-zala ta ciji bakinta hannuta ta had’a ta buga tare da fara safa-da-marwa tana zagaya guri idonta ya kad’a yayi jajazur ta d’ago ta ce”yanzu a wani hali take?”. Haiydar ya ce” jikin da sauki sosai”. Ran Falmi in yayi dubu ya b’aci ta kalli Haiydar ta ce”maza kaje ka ajiye kayan nan ka wuce d’akinka”. Da sauri ya amsa mata da “to”. Amma wani bangare na zuciyarshi bataji dad’in haka ba yana so yaje amma ba halin yi mata musu. Haka Falmi ta tasashi gaba sai da yaje d’akinsa ya kwanta ta nufi d’akinta. Acan Asibiti kuwa shiru-shiru hajiya suka ga bai dawo ba hankalinsu ya tashi sosai, da sassafe hasnat tazo musu da kayan tea da ruwan zafi har wajan bakwai Haiydar bai zoba, hakan yasa Abban da kansa ya ce”Hasna muje gidan Aliyu muga ko lafiya”. Hasnat da sauri ta amsa suka nufi gidan a motan Abba suna zuwa mai gadi ya wan gale musu gate(gareji) suka shiga, Mai gadi yana ganin Abba ne ya gaidasu cikin mutunci da girmamawa, Hasnat ta bud’e falo taga bakowa ganin haka tayi magana ma Abba ya shigo kasancewar tsakanin Main falonsu da side d’in kowaccen su da taraza Abba na zama Hasna ta nufi k’ofar d’akin Haiydar ta kwan-kwasa kamar a kunne Falmi sai gata ta fito tana karairaya ganin Hasna ta ja tsaki ta ce”ke lafiya zaki zo kina tashin mutane da safen nan?”. Hasna ta kalleta a wulakance ta ce” gun d’an uwana nazo ni da Mahaifinsa ke son ganinsa”. Falmi tayi dariya kice min ke da tsoho kuka zo”. Ran Hasna ya baci ta juya ta koma falo Falmi ta biyo bayanta ta ce”aa Tsoho ne haka a gidan mu”. Abba yana jin ana bada labarin rashin kunyan Falmi bai tab’a gani ba sai yau ransa ya b’aci sai karairaya take tana fad’an banzan magana Haana cikin fushi ta kaiwa bakin duka wanda saida jini ya zuba, Abba kasa cewa komai yayi ila fitowa daga gidan Hasna ta kalleta ta ce” ki iya da bakin ki don bazaki tab’amin iyaye na kyaleki ba banza shasha”. Fuuuu Hasna ta bi bayan Abba sai a lokacin suka ga motan Haiydar kenan yana gida. Ran Abba ya gama b’aci amma ya daure ya boye ya ce”Hasna muje gida ki d’auko ma Aishat wasu kaya acikin kayanki”. Haka ko akayi suka dawo Asibiti da kayan Hasnat. Satin Aishat d’aya a Asibiti aka sallameta jiki yayi sauki, wanda duk kwanakin nan Haiydar bai tab’a tako k’afarsa ba abun yayi ma umma ciwo amma taki nunawa a b’an garen Aishat ma haka. Falmi ko ta samu yanda takeso don juya Haiydar takeyi son ranta shiko duk da wani b’an gare na zuciyarsa baya kin dad’in abunda yakeyi amma ba yanda ya iya. *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDIL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [7/17/2016]Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-219~220.* Hajiya tasa ka Hasna taje ta d’iba ma Aishat duk wasu abunda zata buk’ata ta koma gidan su da zama kulum tana cikin sanyaya mata zuciya akan halin Haiydar. Falmi ko ta samu yanda takeso don juya Haiydar takeyi son ranta shiko duk da wani b’an gare na zuciyarsa baya jin dad’in abunda yakeyi amma ba yanda ya iya sai dai abun na damunsa a cikin zuciyarsa kulum yana cikin tagumi da damuwa.******************** 8months latter. Cikin wa’yan nan watannin abubuwa da dama sun faru harda fara jaraban Aishat sunyi WAEC yanzu suna NECO har sun kusa gamawa, yanzu driver Hajiya ta samar mata shi ya ke kai ta ko ina, Hajiya kuma ta dage da addu’a akan halin da Haiydar ke ciki tanayi kullum bata daina ba. Rayuwan Falmi da Haiydar ko abin tausayi don tana gasa masa aya a hannu bana wasa ba duk ya rame yayi baki kamar ba ASP A.K BABA ba. Kuma duk da tsareshi da Falmi keyi bata bashi hakkinsa wataran sai ya mata kuka kafin tasa ya ajiye mata kud’i tukun ta kulashi, a hakama sai ya sha masifa kafin ya samu. Tabbas Allah baya bacci kuma shine maji rokon bawansa don shi ya ce mu rokesa zai amsa mana sai dai ya jinkirta don ya ga imanin bawansa. Haka abun ya faru a gun Hajiya don yau Haiydar yana office yaji kaman an tsikaresa take ya tuna abunda ya faru da irin rashin zuwa gun iyayensa har kuka sai da yayi, cikin hanzari ya mik’e ya nufi gida wanka yayi yasaka kaya mai kyau ya fesa turare yayi kyau amma ya rame yayi duhu amma kyansa nanan hancinsa ne yakara fitowa. Ya fito falo sai zuba k’amshi yakeyi dai-dai lokacin Falmi ta fito ganin wanka da yayi ranta ya b’aci da sauri ta nufosa sam yau ta manta bata shafa turare bare ta kuskure bakinta da magani ta ce”kai Haiydar ina zakaje harda yin wanka haka? Ko kamanta kana k’ark’ashin izini nane?”. Bai tanka mata ba don zuciyarshi na azal-zala ganin zai fita tazo tasha gaban sa daman yana cike da ita yanda da safe tayi ta masa tsawa kamar shi d’anta ne, kwalan rigan sa ta sha cikin hanzari ya bata kyawawan mari ya fara ball(kwallo) da ita saida ya jibgeta son ransa ya fita, motarsa ya shiga sai gidan Hajiya masu gadi na ganinsa sai da sukayi mamaki da sauri ya ajiye motarsa ya nufi cikin gidan da sallamansa ya shiga, Aishat ya fara hangota tana jikin Hajiya Hasnat ma ta hango shi kasa d’auke idonsa yayi akan Aishat Hajiya na ganin sa tayi hamdalah amma ta d’aure fuska dole ta gwada masa kurensa duk da ba da sonsa bane. Hajita ta ce”Hasna Aisha maza tashi ku shiga d’aki da sauri suka mik’e Aishat duk da taji dad’in ganinsa amma zuciyarta na suya da abunda ya mata da sauri tayi d’akinsu da gudu ta fad’a kan gado ta fara kuka mik’ewa tayi ta d’au hoton Abban ta da Ummanta da na iyayen Abban ta tare da awarwaron zinari mai tsada da kyalli nan tasa a gaba tana kalon su tana kuka. Hajiya ta ce”lafiya dai ko? Amma b’atan kai kayi yau ko?” Ya russuna ya gaida ta ta amsa cikin sakin fuska san nan ta ce”yauwa da man kai nake jira tunda yau Allah ya kawo ka inaso ka ba ma ‘Yata takardan sakinta don bazata koma gidan ka ba wannan shine hukunci dana yanke kuma umurni nake baka ba wai shawara ba”. Haiydar ya durk’usa akan k’afarsa ya soma kuka yana bata hakuri. Hajiya ganin ita tsaya kallonsa zai sa ta kayara ta mik’e ta bashi guri d’akinta tashiga taga Hasna ita kad’ai ta ce” Hasna ina Aishat d’in?” Hasna ta ce” tana d’akin mu ina ga”. Hajiya ta mik’e ta nufi d’akin su sam Aishat tayi nisa cikin tunanin iyayenta bata san da shigowar Hajiya ba. Hajiya kuma ganin Aishat na kuka ga hoto a hannuta yasa ta k’arso da sauri don ganin hoto hannuta wannan Awarwaron gwal d’in tafara karo dashi tabbas ko a mafarki bazata manta da wannan a warwaron ba, tana duba ga hoto hannu Aishat damm! Gaban k’irjinta ya bada sauti take numfashinta yasoma d’aukewa hannun take nuna hoton dashi tana fad’in La….mi…..d bata k’arasa ba ta yanki jiki ta fad’i kasa sumamiya dai-dai da shigowar Hasna d’akin ta saki razananne k’ara tayi kanta. Ni Rash danake gefe na ce” to mai ke shirin faruwa kar dai ace……… Bari dai zamuji koma miye. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [6:58PM, 7/18/2016] Kardawiya : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-221~222.* Hajiya kuma ganin Aishat na kuka ga hoto a hannuta yasa ta k’arso da sauri don ganin hoto hannuta wannan Awarwaron gwal d’in tafara karo dashi tabbas ko a mafarki bazata manta da wannan a warwaron ba, tana duba ga hoto hannu Aishat damm! Gaban k’irjinta ya bada sauti take numfashinta yasoma d’aukewa hannun take nuna hoton dashi tana fad’in La….mi…..d bata k’arasa ba ta yanki jiki ta fad’i kasa sumamiya dai-dai da shigowar Hasna d’akin ta saki razananne k’ara tayi kanta. Hasna ta fara jijiga Hajiya amma ina ta sume Aishat ma da sauri ta sauko tazo ta k’ank’ame Hajiya tana kuka, Haiydar da ke falo jin k’aran Hasnat yasa ya hauro sama da gudu ya nazuwa yaga Hajiya a k’asa duk ya rud’e sai da ya jijigata da sauri ya mik’e yayi cikin bayin d’akin ya d’ibo ruwa yana zuwa ya watsa mata, ya k’ara watsa mata take ta saki sassanyan ajiyar zuciya gefen idonta hawaye ne ke zuba. Ta ja jikinta ta jin gina da jikin gado Haiydar da su Aishat sai sannu suke mata Haiydar ne ya bata ruwa mai sanyi tasha ta sauk’e ajiyar zuciya ta ce”Aishat ina son ki fad’amin gaskiya dan Allah ina kika samu wannan awarwaron da hoton d’an uwana k’anina Lamid’o wanda shekara da shekaru ya rasu?”. Haiydar da Hasna sun zuba ma Hajiya da Aishat ido suna masu mamaki da rud’u a cikin al’amarin Aishat jiki a sanyaye ta ce”Hajiya wannan hoton Mama na ne da Baba na sai d’ayan kuma Mama na ta ce Baba na ya ce mata Kakan ni na ne suke d’ayan”. Cikin hanzari Hajiya ta mik’a hannu zuwa inda hoton ya ke ta d’auko tabbas ko makawa babu Lamid’o ne d’aya hoton kuma ita ce a ciki tana budurwa sai Lamid’o yana k’arami ya dai girma ba sosai ba sai Iyayensu dukkansu sanye suke da alkyabba wanda taji ado da k’ayatarwa cikin rashin fahimta ta ce”Aishat ban fahimce ki ba kina so ki ce min Lamid’o shine Mahaifin kuma kenan bai mutuba?”. A fili ta ce”Aliyu to kodai in mutum ya mutu yana dawowa ne?”. Aliyu ya kalli Hajiya tabbas bata hankalinta don a rud’e take. Aliyu cikin sassanyar murya ya ce”ai duk wanda ya mutu baya dawowa sai dai in daman bai mutum ba”. A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya ta ce”Aishat ina so ki bani labarin ki iya yanda Mahaifiyarki ta sanar dake”. Ba tare da b’ata lokaci ba Aishat ta basu labari ta harzuwan Mamanta garin Bauchi, idon Hajiya cike da kwalla ta ce”tabbas ke ‘Yar Lamid’o ne ga saida nan wannan awarwaron da kuma cewa Mahaifiyarki ta je Gombe ta nimi ‘Yan uwansa da hoton nan ya isa sai da bare wasu sassan jikinki duk irin na Mahaifinki ne shiyasa ko da yaushe nake jinki a jikina tamkar ‘Yar dana Haifa, a sai da ‘Yata nake tare nan Hajiya ta fashe da kuka wanda itama Aishat kukan farin ciki takeyi Hajiya ce ta mata alamar tazo kusa da ita tana zuwa suka rungumi juna suna kuka zuwa wani lokaci suka tsagaita Hajiya ta kali Aishat ta ce”ke ba ‘Yar shege bane da ake fad’a miki haka ke ‘Yar gatace kuma ‘Yar dangi kafin muje gimbe ya kamata ki san ko ke wacece kuma waye shi Muhammad Lamid’o”. Haiydar ko yafi kowa farin ciki da bayyanan iyayen Aishat asai ‘Yar uwansa ce kanwan sa tabbas sai yanzu yake jin kunyan zagin shegen da yamata tabbas yasan dole yanzu Hajiya ta k’ara hura masa wuta a kan Aishat don yasan yanda Hajiya take tsananin son d’an uwata Lamid’o bare ace yarsa dole ya k’ara kwantar da kai. Hajiya ta ce”Kamar yanda ki ka gani a hoton nan Mahaifin mu Sarkin Fulani ya kasance shahararen mai kud’i a cikin garin Gombe tun asalin Kakan mu shine sarkin Gombe kinga kenan wannan Sarautan tana k’ofar gidan mu ne lokacin da Kakan mu ya rasu sai ya zamana Mahaifin mu Sarkin Fulani bazaiyu a bashi Sarauta ba, sai aka d’auka aka bama Wazirinsa kinga daganan Sarauta ta bar gidan mu kenan ko da Mahaifin mu ya girma ba halin k’arban Sarauta sai aka bashi Sarkin Fulanin Gombe wanda alokacin matan sa biyu ne sai nice ‘Yarsa ta farko kuma bai kara haihuwa daga kaina ba sai bayan shekara biyar aka Haifi Muhammad wanda ake kira da Lamid’o kasancewan shine d’a namiji d’aya ma Sarkin Fulani ya d’auki son duniya ya d’aura masa wanda hakan ya ke kona ran Kishiyar Hajiyan mu tun yana k’arami take kai masa hari da niyar kasheshi Allah bai bata sa’a ba har yasoma tashi, ana haka akayi aurena da Baban su Aliyu muna zama a cikin garin Gombe lokacin a gun yake aiki kafin mu dawo Bauchi da zama kasancewar shi d’an k’aramar hukuman Katagun ne da ke Bauchi, bazan manta da ranar da Abban mu ya dawo daga saudi ba rannan nazo gida masa murna da dangi duk mun had’u a gida”. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [10:16PM, 7/18/2016] Kardawiya : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-223~224.* Abban mu ya dawo daga Saudi na zo gida masa sannu da dawowa da wasu dangi bayan ya huta ya ciro tsara ba ya bai ma ‘Yan uwa da abokan arziki ya raba musu su Hajiyar mu ko wanna awarwaron ya sayo musu wanda kud’insa bana wasa bane anan yaraba musu ana bama Hajiyar mu nata Lamid’o yasa kuka shidai sai dai abasa wannan awarwaron ne na zinari ya masa kyau ba irin rarrashin da ba’a masa ba yaki nan Hajiya ta d’auka ta bashi kyauta. Haka rayuwa yaci gaba da tafiya Sarkin Fulani na gwada mana gata kasancewar mukad’ai ya haifa ‘Ya’ya biyu bayan wasu shekaru Lamid’o ya girma a kwai ranar da bazan manta ba ranar da muka masa ganin k’arshe ranarda kishiyar Hajiyar mu ta aiki driver (mai tuk’a mota) garinsu Lamid’o naji zasu tafi ya ce shi sai ya je Alkaleri kasancewar ita ‘Yar garin ne nan Lamid’o ya d’au yar jakarsa yasa kaya kala 2 kasancewarsa mai tsafta ne kuma sai washe gari zasu dawo, kuma duk inda ya ke baya rabuwa da hoton iyayen mu wanda mukayi tare don shima ya shaku da baban mu sosai, suka tafi da driver(mai tuk’a mota) can kusan yamma sai ga wasu mutane da kukan su wai Lamid’o sunyi hatsari harshi kamma ya kone k’urmus sai tokan sa akà gani to kinji labarin rabuwan mu da Lamid’o wanda sanadin rasuwarsa yasa hawan jini ya kama Hajiyar mu itama bata dad’e ba Allah ya mata rasuwa. Aishat wacce take hawaye ta sauke ajiyar zuciya Hajiya ko ta ce”Hasnat je d’aki ki d’auko waya na kira Abba na in sanar masa don na san zaifi kowa farin cikin ganin ‘Yar Lamid’on sa” Hasna ta d’auko waya Hajiya ta kira Sarkin Fulani ta koro masa bayani cike da murna wanda sai da yayi kwalla harda sujudu shukur yayi nan take yasa aka bama Aishat suka gai sa. Hajiya ta karb’i wayar Sarkin Fulani ya ce” Gobe ku biyo jirgi da wuri kuzo naga jikata don bana jin dad’i ne ni da yau nazo”. Hajiya ta saida masa suna zuwa, take Hajiya ta sanar ma Babansu Haiydar shima yayi murna ya ce”in Allah ya yarda cikin satin nan shima zai dawo”. Haiydar shi ya je ya musu komai harda shi a tafiyan, ranan Aishat kasa bacci tayi dan farin ciki da murna harda yi nafiloli ta gode ma Allah tare da addu’a Allah ya jikan mamanta. Washe gari da safe suka shirya sai gombe, tun daga Airport suka ga jerin dogaraye suna jiransu ga wata rantsaysiyar lemozine k’atuwa da akaje d’aukarsu a cikin ta. Aishat kam in banda kalo ta dawo kamar ‘Yar k’auye sai kale-kale takeyi har suka zo wani k’aton katafaren gida wanda in aka bar Aishat sai ta ce wannan shine white house da ake fad’a na Abuja. Suna sauka nan dogaraye suka fara gaishesu har suka shiga falo, Sarkin Fulani dake Falon idonsa nakan Aishat tabbas wanan jinin sa ne take idonsa ya kawo kwalla duk da yana daurewa hannu yamata alamar tazo ya rike hannuta tare da dafa kanta yana hawaye ji yake kamar Lamid’o ya rike sai da suka zauna kowa ka gani fuskan sa d’auke da fara’a da farin ciki in ka d’auke Hajiya k’arama da ko dariya batayi nan Sarkin Fulani ya sake niman jin k’arin bayani Hajiya ta basa labari Aishat ma ta d’aura da iya sanin ta nan ya rungumi jikarsa yana kuka itama tanayi. Ana haka sukaji an turo k’ofa tare da sallama dukkansu suka d’ago kai tare da kallon k’ofar ko ni ma Rash dana kalli k’ofar wani farin bafulatani dogo mai karan hacci kyakyawane wanda za’a kwatanta a gurin kyau amma ya d’an girma amma kuma girman ta had’u da wahala fuskan sa ta cika da k’asun ba da alamar dai yana cikin wahala cikin sauri Hajiya ta mik’e a razane Sarkin Fulani da k’afarsa ke ciwo bai san lokacin da ya mik’e ba murtsuk’e idonsa yasoma yi don yaga ko mafarki ne yakeyi amma ina ba mafarki bane wannan zahiri ne tabbas wanna ko ba makawa babu tam-tama……… *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHAT MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: Rash Kardam BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-225~226.* Ba kowa bane ya turo k’ofar illa Muhammad Lamid’o d’a d’aya tilo Namiji kuma magaji ga Sarkin Fulani Gombe cikin razana da firgici Hajiya k’arama ta mik’e don ba k’aramin kid’ima tayi da ganin sa ba nan take taji wani fitsari na shirin zubo mata sai zazzare ido takeyi jikinta sai b’ari ya farayi Sarkin Fulani da kansa ya taka ya je ya rik’o hannu Lamid’o yana hawaye bai san lokacin da ya rungume sa ba farin ciki ba’a cewa komai baran Aishat da ganin fuskan sa ba tam-tama ta gane Mahaifinta ne don yawan kalon sa da takeyi a hoto, Sarkin Fulani ya kamo hannu sa ya zaunar da shi Hajiya ma kukan murna takeyi ikon Allah kenan, sai da suka zauna Sarkin Fulani ya ce”Lamid’o kaine?”. Lamid’o ya ce”eh nine Abba”. Sarkin Fulani ya furta ikon Allah kenan ya wuci wasa”. Ya kalli Hajiyan su Haiydar ya ce”kije d’akina ki had’a masa ruwan wanka tukun ya ci abinci don naga da gajiya a tattare da shi ga alamar yunwa”. Haka ko akayi nan take ta kaisa d’akin Babansu ta dawo kitchen da ita da su Aishat suka had’a masa girki mai k’ayatarwa, yana fitowa a wanka ya tarar da sabbin kayan da aka ajiye masa ya sanya ya gyara jikinsa, falo ya fito ya tarar da su, sai a lokacin idonsa ya kai kan Aishat da ta k’ura masa ido shima kallonta ya farayi cikin zuciyar sa ya ce” wannan tamkar Safinatun sa, ayya ko dai ita ce yar cikin Safinatu da taho da shi?”. Hannusa yaji an rike ko da ya duba Sarkin Fulani ne ya kama hannusa duka suka nufi dining, Hajiya da kanta ta sanya ma kowa abinci ta zauna Sarkin Fulani yana mak’ale da Lamid’on sa sai Hajiya da ke kusa dashi sai Aishat a kusa da Hajiya yayin da Haiydar ke kusada Lamid’o sai Hasna a kusa dashi. Haiydar yana kallon Aishat yana aika mata da wasu sak’on ninsa, gun shiru kowa yana fama da abinci fiskan kowanne su yana d’auke da murmushi don suna cikin farin ciki bana wasa ba. Haiydar ne ya mik’ar da k’afan sa ta k’asan dining table d’in yanda zai na tab’a k’afar Aishat babban yatsan k’afarsa ya sanya a tafin k’afar Aishat ya fara mata tafiyan tsutsa a take taji wani yarrr! saurin d’ago fiskan ta tayi karaf su ka had’a ido wani lalalusar murmushi ya sakar mata ya kashe mata ido d’aya. Sai da ta d’an saci kalon su Hajiya taga kowa na ta kai da abincin sa ta murgud’a masa baki, Haiydar yayi murmushi ya sake sosa mata k’afa harda wuce wansa zuwa sawun k’afar ta da sauri ta kau da k’afar asai Hajiya tana lura dasu ta share ne kuma taji dad’in hakan suna kammala cin abinci suka koma babban falo suka zazzauna. Sarkin Fulani ya kalli Hajiya ya ce”wai ina Hajiya k’arama ne banganta ba har a gurin cin abinci kuma yanzu ma bata fito ba ko lafiya?”. Hajiya ta ce”ina ga lafiya zata fito”. Sarkin Fulani ya kalli Lamid’o ya ce” zaka iya gane wannan fuska kuma da wa ta ke maka kama?”. Lamid’o ya kalli Aisha sosai ya ce”tun shogowata fuskanta ke min kama da fiskan Matata Safinatu”. Sarkin Fulani ya murmusa ya ce”tabbas wannan d’iyarka ce da Safinatu”. nan suka kwashe labarin komai suka fad’a masa sosai Lamid’o yayi kuka ya tausaya wa Matarsa da ‘Yar sa tare da mik’o hannu ma Aishat tazo yana kuka ya rungumi d’iyarsa take Aisha taji sanyi dad’i na ratsa ta wai yau ita ce take tare da Mahaifin ta daman ita ba ‘Yar shege bane da ake kiranta, zanso Falmi taga gatana taga Mahaifina asai mu ‘Yan uwa ne da Haiydar nan tasaki sassanyan Ajiyar zuciya, Sarkin Fulani ya ce”zan so kabamu labarin bayan barin ka Gombe yanda al’amura suka kasance”. Lami’o ya nisa tare da gyara zama ya ce”bayan da muka shiga mota munyi nisa sai da muk’a k’usa shiga Alkaleri Idi driver ya tsaya”, ya ce” Lamid’o bazanso na kashe ka da hannuna ba don an bani kwangilan kasheka ne Hajiya k’arama amma sabida kirkin Hajiya babba bazan ci *AMANAN* ta ba ta rik’e mu da gaskiya” Lamid’o ya ci gaba da cebwa”kafin nayi wani magana kawai ya shafamin wani abu a hanci na tun daga lokacin ban san inda kaina yake ba sai a cikin wasu kauyukan Yola na samu kai na tare da wani mutumi wanda aka had’a ni dashi dan ya baro bauchi dani gudun kar Hajiya k’arama ta ganni, mutumin nan sai da ya tabbatar da na dawo cikin hayyacina shima ya zame ya barni, a tasha kauyen ribad’o na zauna nan yunwa ya fara damuna daga nan na fara aikin k’arfi ina kula da kaina kuma na samu wani Bafulatani mukayi dashi zanna tayasa kiyo yana biya na haka muka fara randa ba kiwo inje niman kud’ina da haka har na tara kud’ad’e na sai na sayi saniya ta mace nan muka fara kiwo cikin ikon Allah ya sanya ma saniyar nan albarka tayi ta haihuwa kuma inayi niman kud’ina na sai na sai wasu da haka Allah ya azurtani da garken shanu na kuma yi suna a cikin kauyukan da ke yanki don ba mai shanuna a haka har Allah yayi na auri Matana Safinatu muna zaman lafiyan mu wasu daga cikun yan kauyen suka fara adawa da dukiyata hakan yasa suke min barazanan kisa, a haka wasu daga cikin ranar laraba da bazan manta ba suka fara bina suna neman kashe ni cikin hanzari na taho gida na umurci matata da tazo mu gudu. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-227~228.* Na tattara dukkan shanuna da ‘yar sanda na muka d’au hanya sai da mukanshiga cikin daji kawai mutanen nan suka b’ullo mana ba k’aramin razana mukayi ba amma duk da haka nayi iya k’ok’arina akan su amma Allah baiyi ina da nasara ba haka suka kwad’a min sanda a kafad’a ganin bazan iya kare kaina ba shine na wurgo ma Safinatu jakata da kud’i a ciki da awarwaron da Hajiya ta ban sannan da hoton mu da ku da nawa ni da ita wanda mukayi a auren mu”. Ya nisa tare da gyara zama ya d’an kurb’i ruwan Faron da ke gefensa ya ce”kunji yanda muka rabu da Safinatu”. Duk fiskan su d’auke da hawayen tausayi Sarkin Fulani ya share kwala ya ce”muna jinka yanda ku ka k’are da mutanen”. Lamid’o ya ci gaba da ce wa”bayan tafiyar Safinatu tana kuka tana waige na haka mutanen nan suka kwada min sanda na suma a gun, sukuma suka kad’a shanuna suka tafi, ana haka sai ga wani Maharbi ya zo ganin halin da nake ciki ya d’aukeni yaje ya ta min magani, da ikon Allah ciwukan dana ji duk sun warke amma me sai na samu tab’in hankali haka Maharbin nan yayi ta jinyana tsawan shekara goma sha bakwai kafin da ikon Allah ya samomin magani shekara guda da rabi yayi yana min jinya da maganin cikin ikon Allah na samu lafiya, daga nan ya tambayeni labari na na basa labarina tun daga kawo ni da akayi Yola har zuwa lokacin. Maharbin nan shi ya tara ‘Yan uwansa da mai gari aka karb’a min shanuna ko da suka dawo hannuna sai na saida guda uku a cikin garin yola na dawo kauyen fofure na sai babban fili a jeji wanda filin ba k’arami bane (kunsan filin kauye ba zada sosai). Nan na sake biyan kud’i aka kewaye min da wayoyi nazuba shanuna aciki sannan nasaka su kaji da raguna da akuyoyi da talotalo da agwagi ruwa, bayan dana gama aikin sai na damk’a wa Maharbin nan gonan a hannusa zai na kula dasu don ana saran koyayen zabbi da sayan madaran shanu a gun na masa sallama na sanar da shi zanzo Mahaifata na ga iyayena da Matata da na turota tare da cikin da ke jikinta nan na kamo hanya zuwa Gombe, to kunji labarina”. Wannan karon harda Haiydar a ‘Yan yin kwalla labarin gwanin ban tausayi. Sarkin Fulani cikin fushi ya ce”yanzu abinda Hajiya k’arama zata min kena batare da b’ata lokaci ba ya kira police ya ce su zo gidan sa yanzu-yanzu”. Hajiya k’arama da ta lab’e tana jin duk abunda ya faru cikin sauri ta koma d’akin ta tafara shirya kayanta a k’aramin jaka sai ta nufi d’akin Sarkin Fulani ta d’ibi kud’i da dollars cikin jaka, nan ta fara dariyan mugunta tasan wa’yan na kud’in sun isheta rayuwa a ko ina take ga kuma wanda ta tarasu a account d’inta K’ofar baya tabi tayanda sarki bazai ga fitarta ba cikin hanzari take tafiya dan kar a ganta. A falo kuwa police sunzo d’akinta aka nufa kai tsaye amma me sai wayam suka gani ba kowa nan suka bazama aiko suna zuwa k’ofar baya suka ga ta k’ofar a bud’e cikin hanzari suka bazama bakin titi suka hango ta tana shirin shiga napep ganin haka wasu suka tsari mashin aka bita wasu a mota [10:29PM, basuyi nisa ba aka kamata aka sa mata ankwaf aka nufi C.I.D da ita ana kamata aka sanar ma Sarkin Fulani nan ya ce”Lamid’o muje C I D tare suka fita a jikin mota ko da suka je nan ma aka basa duk abunda aka kama a hannuta, ransa ya k’ara b’aci sai da yabata kyawawan mari masu lafiya ya kuma ce” wallahi kin cucen na yarda da ke sakayyar da ki ka min ke nan ki sani ba amfanin zamana da ke na datse igiyar aurena uku da ke kanki”. Nan ya ba da umurnin abata wahala sosai tukun a turata kutu. Haiydar ko Hajiya na mik’ewa ya nufo gun Aishat Hasna na ganin haka ta ja ‘yan matan k’afar ta ta bar falon, Aisha cikin hanzari itama ta mik’e har ta fita a falon taku k’alilan yayi ya fisgota sai a k’irjinshi ta fad’o nan wani kamshi mai tattare da sanyi ya daki hancinta Haiydar cikin kwayan idonta ya fara kallo ganin haka ta lumshe ido dul jikinta b’ari yakeyi, hancinsa ya d’aura akan nata ya fara gogawa tare da sanya bakinsa cikin nata nan yaji wani laushi a labb’an ta, tun da yake da Aishat sai yau yasamu wannan damar Aisha ko k’ok’arin ta gudu take amma me hannuta ya manna da garu tare da d’aura hannusa akan nata yasona kiss d’inta kamar wani mayunwaci, duk yanda taso ta kauce ba hali gashi jikin ta na b’ari sosai hawaye ke zuba harshensa yasaka yana lasar hawayen sai da ya lashe tass, Aisha gashi ba halin tayi magana ya had’a bakinsa danata dai da ya jagwa-gwata son ransa ya saketa da gudu tayi hanyan cikin d’akinsu sai hakki takeyi cikin sa’a ba Hasna a d’akin kan gado ta fad’a tana maida numfashi sama-sama tare da lumshe ido cikin zuciyarta ko cewa take” a sai haka kiss d’innan ke da… *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [3:18PM, 7/22/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-231~232.* Tuni ya fara rikita ta da salon soyayyan sa wanda ganin yafi k’arfin idona yasa na tattara ‘yan matan k’afana nayi gaba, ina daga k’ofar d’aki ina jiyo kukan Aisha wanda ba halin na kai mata taimako haka na zauna jigum, sai kusan k’arfe uku Haiydar ya saurara mata, Aisha in banda hawaye ba abunda takeyi ni ko Rash ina gefe na ce”yau Ashanty anji maza bakin tsiwa ya mutu…..lol..”. Haiydar ruwan zafi ya had’amata sai da yayi wanka kafin yazo ya taimaka mata sam tak’i yarda su had’a ido da kanshi ya mata wanka tukun ya barta tayi wankan tsarki, sai da tafito ya mik’a mata wasu kaya kafin ta sanya harda hijab a ciki tayi sallah kafin ya kawo musu abinci suka ci. Haiydar ya kalli Aisha ita duk kunyansa takeji sabida in ta tuna irin sambatun da yayi jiya sam bata son su had’a ido, hab’arta ya kama ya d’ago fiskanta ido ta lumshe cikin sanyin murya Haiydar ya ce”Aisha Allah yayi miki albarka na rasa kalman da zan gode miki ila wannan yukurci”. wani d’an k’aramin a kwati yaciro mai kyalli ya bud’e tare da zaro wani zobe white gold mai kyalli da haske wanda ni kaina Rash sai dana kare fuskata da tafin hannuna sabida hasken yana kashe min ido, ko da na duba da kyau jikin zoben naga ansa A&A forever, yana sanya mata yayi kiss d’in zoben don bak’aramin kyau yayi mata ba hannu ya rike yana murzasu tare da janyota jikinsa yana mata wasu kalamu masu dad’i acikin kunnenta wanda duk sonjin gulmata ban jiyo mai ya ce ba. Hajiya ko ganin sak’on sai da hankalinta ya tashi tabbas tasan Haiydar yayi hak’uri sosai, dole ta bashi matarsa don taga ya nitsu sosai kuma ya damu da Aisha, ganin matarsa ce bata kawo komai ba amma zuciyarta na d’ar-d’ar. Basu bar gidan ba sai bayan magriba suka d’au hanya sai da yabiya da ita super market ya mata sayya masu yawa suna isa harabar gidan sai da yaga tashiga falo ya juya ya tafi sabida yasan bai da gaskiya shiyasa bai shiga ba. Aisha tana shiga sai da ta d’an lek’a bata ga kowa ba hakan yasa ta fara tafiya a hankali, Hajiya da tafito daga kitchen ta hangota ganin tafiyar da takeyi tuni ta d’ago abunda ya faru a zuciyar ta ta ce”lalle Haiydar ya gwada min shi d’an yau ne ai ban isa ba tun kafin ya sanya na fara jin kunya gwara ya d’au matarsa su k’ara gaba”. Tana fitowa dai-dai Aisha na hawa matakala Hajiya ta ce”ah! Aisha har kun dawo”, cikin jin kunya ta sun kuryar da kanta ta amsa da “eh mun dawo”. Hajiya ta ce”to yayi kyau kije d’aki Hasna zata kawo”. Miki abinci, Aisha ta ce”Hajiya a k’oshe nake naci abinci a can” Hajiya ta ce” to shikenan”. Aisha ta wuce d’akinta sai da tasha maganin Haiydar ya bata kafin ta kwanta sai ido ta lumshe tana mai tuna abunda ya faru tsakanin su da nan wani tunani ya fad’o mata yanzu fa in da rabo hala ciki ya shigeki, murmushi tayi kafin ta shafa cikinta haka har bacci ya d’auketa. Yau Aisha ta kammala jarabarwata wanda aka shirya musu liyafa nagani na fad’a Sarkin Fulani da shi da Lamid’o sun halarci bikin walimar abun dai sai wanda ya gani walima akayi na gani na fad’a, bayan walima da kwana biyu Hajiya ta shirya ‘Yarta da kanta ta mayar ta gidan Haiydar tare da mata nasihu masu sayaya jiki. Da dadare Haiydar da wuri ya dawo Falmi ya samu a falo tayi d’aurin rashin mutunci sai kad’a k’afa takeyi. Ganin ko kallonta bai yi ba zai shiga d’akin sa tazo tasha gabansa ta ce”to muna fuki wai mai kake nufi ne kasani lokaci yayi da zaka saki Indo, ko ka manta kai da bakin ka kace baka sonta sai yanzu kuna neman ku kareta wai tasamu ubanta mtss zaku raina min Hankali ai ‘Yar shehe ‘Yar she……”. Wani kyawawan mari Haiydar ya bata nan tafara shirin kama sa da kokuwa shi kuma bai son yawan dukar mace kawai ya jata zuwa d’akinta ya kulleta ta baya, d’akin sa yaje yayi wanka kafin yasaka kayan bacci d’akin Aisha ya shiga ya ganta cikin wasu mayun kayan bacci wanda dashi da babu duk d’aya. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [10:50PM, 7/21/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-229~230.* Da daddare haka suka sha hiransu cike da k’aunan juna sai kusan goma Sarkin Fulani ya musu sallama shima Lamid’o d’akinsa ya tafi da ya kwanta yau jinsa yake cikin farin ciki, Hajiya ta kalli su Aisha ta ce”kuma ku tashi ku tafi d’aki ku kwanta dare ya soma yi”. Duka suka mik’e tare da mata sallama, Haiydar ko ya marai-raice fuska Hajiya duk ta d’ago nufinsa ta ce”kai kuma mai ka tsaya yi da bazaka tafi masaukinka ba ne?”. Jiki ba kwari Haiydar ya mik’e ya nufi d’akin sa shima tukun Hajiya ta tafi nata. Aisha tana shiga d’aki wanka ta fad’a Hasna kuwa kitchen taje had’a ruwan zafi take so tasha kafin ta kwanta, Haiydar ganin Hajiya ta tafi d’akin ta ya dawo cikin sand’a ya tura d’akin su Aisha nan ya ga ba kowa sai da ya rufe k’ofar tukun ya k’arasa ciki k’aran ruwa yaji a bayi gefen gadon kusa da bayi ya zauna don kar ma tana fitowa ta gansa, Hasna da take shirin fitowa ganin Haiydar ya shiga d’akin su tayi murmushi sai ta nufi dining kawai don ta sha ruwan zafinta a can. Aisha da ‘yar wakanta fito d’aure da tawul iya cinya sam bata lura da mutum ba dake ta na goge kanta zagawa yayi ta bayanta ya rungumeta tare da zare d’an k’aramin tawul d’in, cikin razana tayi tana shirin sakin ihu ya toshe mata baki da hannusa a kunne ta ya rad’a mata” nine mijiki Haiydar kuma d’an uwanki”, dumm! Taji gabanta ya fad’i juyo da ita yayi duk kunya ya ishe ta, hannu tasa tana kare k’irjinta, ya saki murmushi ya ce”mai yasa kike rufe min abunda yake halal a gareni kuma nake marari ganinsu tare da begen…”. Magana kunya ta bata sai ta rufe ido hannuta ya kama ya kawar daga k’irjinta tare da janta zuwa gado cikin muryan kuka ta ce”Ya Haiydar miye haka? Dan Allah ka bari mai kazo yi a nan?”. Murmushi yayi ya ce”yau nazo karb’an hakkina da ya dad’e shekara da shekaru ana min rowa kai ta gir-giza masa tare da k’ok’arin turjewa sai da ya kaita kan gado ya kwantar da ita, salon k’auna iri-da-kala yasoma nuna mata wanda ya fi k’arfin in tsaya zayya ne mu ku acin nan. Hasna ko ganin haka da man akwai d’aki wanda da komai a ciki d’akin hajiya ta koma ta dauko kayan bacci, tazo tayi wanka ta kwanta a nan. Haiydar ko sai da yayi wasa da Aisha son ransa ya kuma tabbatar da ya gamsu kafin ya mik’e cike da nishad’i ya fito cikin sand’a ya koma d’akinsa wanka yayi ya kwanta yau yana mai jinsa cikin farin ciki kasa bacci yayi can iya tuna mai ya faru sai ya saki lallausar murmushi tare da buga hannusa a katifa alamar jin dad’i. Aisha ma wanka ta sakeyi kafin tazo ta kwanta tana mai tunano abunda ya faru haka har bacci ya d’auketa. Da safe bayan sun karya sun dawo falo an gaggaisa yau Aisha sai wani sunne kai takeyi Haiydar ko idonsa akan ta yake suna had’a ido zai kashe mata ido d’aya, Sarkin Fulani ne yayi gyan murya sai da yayi addu’a kafin ya fara da cewa”hukuncin dana yanke shine da zaran Aisha ta kammala jarabawan ta zamu tafi Yola a kaita taga dangin Mahaifiyar ta sanna gonar Lamid’o inaso zamu mayar dashi kamfanin yin su Madara da yogurts san nan gefe d’aya kuma a mayar dashi gidan gona gefe d’aya kuwa zamu k’awata shi ya dawo gun tutawa zamu zuba k’ananun namun daji don su kawata gun da d’akunan hutawa da gun abinci mai kyau, hakan zai kawo kud’i kuma wasu manya zasuna zuwa gun kasancewar yayi wajen gari kuma ba hayaniya a gun”. Ya d’ago ya kallesu ya ce”kunaga hakan yayi ko da wani tsarin da yafi hakan?”. Hajiya da Lamid’o suka amsa da yayi nan ya ce”to na nasa an muku komai sabida komawarku Bauchi don gobe Aisha tana da jarabawa”. Daga nan kuma suka ci gaba da hiransu. Da yamma kuwa sarkin Fulani har dashi da Lamid’o aka musu rakiya zusa filin jirgi suka dawo Bauchi. Washe gari Aisha ta nufi makaranta nan taba masu Sadeey da Sanah labari ba k’aramin murna suka mata ba da samun Mahaifinta. Haiydar ko yana komawa gida ya samu Falmi amma sai me fiskanta yaga kamar alamun nadama da murna ta tarbesa don ita damuwarta taji ina yaje sai da ya huta cikin kissa take tambayarsa ko da yabata labari nan fa ta dira tsalle ta mik’e ta ce”ina wannan k’arya ne kawai baki kuka had’a don ku rufa mata asiri” nan fa rikici ya kaure a tsakanin su daga k’arshe falon ya barmata ya koma d’akinsa. Bayan kwana biyu duk damuwar sa ya ga Aisha gashi yanzu saura mata jarabawa d’aya ta gama, zuwa makarantar yayi yasamu suna jarabawa ya tsaya ya jirata sai da suka fito yasa aka kirata tana zuwa ya ce”ki shiga mota”, sam fiskan sa ba alamar dariya hakan yasa ta shiga da sauri ya ja motar ya bar harabar makarantar gudu yakeyi sosai hanyar UNGUWAN SARAKUNA ya nufa, cikin razana Aisha ta ce”lafiya yanaga ba hanyan gida ka nufa ba?”. Wani kallon da ya aika mata dashi yasa tayi shiru har suka isa wani k’ofar madai-daicin gida mai kyau horn yayi mai gadi ya bud’e masa yana shiga ya ajiye motarsa ya zago ta gun Aisha fiska a d’aure ya ce”matsawan in kika min gardama to kinsan sauran”. Yau kam ya dawo mata Haiydar d’insa na da tuni wani tsoro ya shige ta hannun ta ya kama tare da mannata da jikinsa suka nufi cikin gidan suna shiga ya kulle k’ofar tare da zare makullin yasa a aljihun sa, wani d’aki ya nufa da ita, suna shiga ta ja ta tsaya a k’ofar d’akin cikin dauriya ta ce”wai lafiya yau kuwa mai yasa ka kawo ni nan gidan?”. Wani mayen kallo ya bita da shi tare da matsowa kusa da ita ya ce”yau hakkina nake buk’ata a gunki nagaji da jamin rai da kikeyi”. Janyota yayi ta fad’a jikinsa tare da rufe k’ofar d’akin tafara k’ok’arin kwace kanta wani tsawa ya daka mata ai ba shiri tayi shiru sai hawaye ke sauka, wayarsa ya ciro ya tura ma Hajiya message kamar haka. *_Assalamu’alaikum_* _Hajiya barka da rana kar a tura d’auko Aisha naje d’auko ta muna tare yanzu haka da ita, zamuje unguwa karkuga shiru sai mun dawo_. Yana tura ma Hajiya yana ganin ta bud’e sak’on ya kashe wayarsa ya sa a gen gado, hannunsa yasa ya janye karamin hijab d’in Aisha tare da sanya hannusa a gashin kanta ya fara shafawa Aisha ko sai hawaye takeyi, hannusa ya zura ta cikin riganta ya balle bra d’in ya fara….. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *_RASH LUV_ * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [4:09PM, 7/22/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-233~234.* Zuwa yayi ya rungumeta ya ce”baby na kinyi kyau sosai”, murmushi tayi ya lakaci hancinta ya ce”kullum kyau kike k’arayi ina rok’on Allah banu baby mai kama da ke”. Da irin wannan kalaman ya lallab’a Aisha suka lula duniyar masoya. Washe gari Haiydar ya fita zuwa aiki Falmi ta tattari kawayen ta ‘Yan bariki suka zo da niyar dukan Aisha kowacce da bulalarta a hannu ana haka sai ga Haiydar ya dawo ganin su yasa ya kira jami’an tsaro aka tattaresu ko wacce taji a jikinta suna kulle a gurin jami’an tsaro, cikin Falmi ya faro ciwo kafin me sai ga jini wanda hakan yasa aka kira Haiydar da gaggawa aka kaita asibiti suna zuwa ana dubata cikin inkon Allah suka zai da jinin suka shaida ma Haiydar cewa magani Hana Haihuwa ta sha wanda yayi wa haifarta illa, nan ran Haiydar ya k’ara b’aci sosai, sai da aka taimaka mata jini ya tsaya, tana farfad’owa ya ce”Fatima naga abu abunki yayi yawa don haka in kin samu sauki ki wuce gidan ku”. Ya juya ya fita hawaye ke zuba afiskansa tabbas Haiydar na son Falmi amma ita tana bin zugar kawayen banza shi yasa da kishin hauka dake damunta. Bayan kwana biyu Haiydar, da Sarkin Fulani dasu Lamid’o da Hajiya suka tafi Yola tabbas Aisha taga ga tanta da dangin ta ko ina sai murnan ta akeyi. Batun gona ko Sarkin Fulani ba k’aramin kud’i ya kashe a gun ba an k’awata gun sosai gwanin burgewa wanda aka sanya masa suna *AISHA VILLA GARDEN* sai da akayi bikin bud’e gurin Lamid’o ya damk’a amanar gurin wa Maharbin nan daga nan kuma aka d’ibi ma’aikata a kauye da birnin Yola, kafin suka dawo lokacin Aisha ta k’ara kyau tayi haske ga wani kwad’ayin da takeyi kulum sai tasha ice cream rigimar yau daban na gobe daban. Yau ma kamar kulum Haiydar ya dawo Aisha ta tasashi gaba da shagwab’a dole sai sunje shan ice cream ba yanda ya iya dole ya fita su tafi, bayan sun saya ice cream dai-dai zasu shiga mota Aisha ta hango wasu mutane take ta rud’e tafara kuka ta mak’ale Haiydar yayi ta tambayan ta duk ta rud’e sai da Haiydar ya sanya bakinsa cikin nata ya bata wani sassayan kisses kafin ta dawo hayyacinta rungeta yayi ya ce”mai ya faru wa ya tab’a ki mai ya tsorata ki”. Cikin kuka ta ce”sune sune”. Haiydar ya ce”waye su d’in?”. Aisha ta ce”sune suka d’aukeni lokacin dana b’ata”. Haiydar ya ce”what!!” Gwada min su nan ta nuna masa su suna shiga gun shan ice cream d’in Haiydar yasa ta a mota ya ce”ki zauna anan karki fito”, rikesa tayi ta fara kuka dan Allah ka kyalesu kar su cutar da kai”. Murmushi yayi ya ce”karki damu kimin addu’a Allah zai kareni”. Kai ta gir-giza masa wayansa ya d’aga ya kira ‘Yan sanda da suke kusa ya na zuwa ya bada umurni aka rufe gun aiko saiga police nan suka shiga aka kamasu duka, nan yasa aka tafi dasu ya ce”bari ya mayar da matar sa gida”. Gidan Hajiya ya kaita ya koma gun aiki. Azaba akayi ta gana wa mutane nan da kyar suka fad’i wacce ta sa su ran Haiydar ya k’ara b’aci da kansa yaje har gidansu Falmi yasa aka kamota sai da ta daku a gunsa sosai kafin ya ce”ki sani na sakeki saki d’aya tunda har haukan ki ya kai kiyi tunanin kisa”. Falmi taji wahala har tayi nadama abunda ta aika, ga wahala ga auren ta ya mutu,.*************** Bayan wata takwas Aisha na hango da zungureren ciki tana tafiya tana ciza baki ta dafe cikin ta Haiydar ne ya fito daga d’aki da sauri ya riketa ganin kamar nak’uda ne da gudu yayi d’aki ya d’auko akwatin kayan haihuwar ta ya fitar ya dawo ya sun kuceta sai asibiti cikin ikon Allah bata dad’e tana nak’uda ba ta haifo baby boy d’inta, nan fa Haiydar yayi ta kiran ‘Yan uwa yana fad’a musu kasancewan lafiyarta lau ta haihu hutawa tayi aka sallame su kafin kace me gida ya cika da ‘Yan uwa da abokan arziki. Bayan kwana bakwai ranan suna yaro yaci sunan *_ABDUL SHAKUR_* Yaro kyakyawa gwanin burgewa bikin suna yayi kyau ida muka samu kyatuttuk’an zannuwa ne mai hoton yaro da Al- qur’ani mai girma abun sai wanda ya gani haka aka watse. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [4:42PM, 7/22/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-235~236.* 4yrs latter Wani kyakyawan Yaro na hango rik’e da teddy a hannusa yana gudu yana dariya ko dana kalli wanda yake bi wani kyakyawa ne fari sol tamkar shi yayi kansa ko dana kalleshi da kyau sai naga kaman Haiydar wata kyakkyawar mace ce ta fito ta ce”Abban Abdul in kun fara wasa kai ma sai kadawo kamar wani k’aramin yaro ya tsaya jin maganar ta Abdul~shakur ne yazo ya kama Abban sa ya dariya ya ce”na kama na kama”. Haiydar yayi dariya ya d’agashi ya cilla shi sama duka suna dariya, Assalamu’alaikum jin sallama duka suka juya sai da suka kalli mai sallaman sosai suka gane Falmi ce da sauri tazo ta durk’usa tana basu hak’uri Haiydar ya kau da fuska ya tashi zai tafi Aisha ce tazo ta rungume Falmi ta ce”Aunty na ni bakimin komai ba na yafe miki Aunty na”, Falmi ta share hawaye ta ce”nagode ina rokinki dan Allah ki rok’ar min Haiydar da ya mayarni d’akina wallahi nayi nadama”. Ta karashe maganan tana kuka Aisha ta rungume ta tace”Aunty kar ki damu Haiydar zai mai daki kuma Haiydar na sonki kawai zugan kawaye ne daman”. Falmi tayi godiya ta tafi, Aisha da daddare tasamu Haiydar da maganan dawo da Falmi ya nuna bazai dawo da ita ba, ganin tayi yaki hakan yasa tayi fushi ta juya masa baya kusan kwanan su uku basa magana kafin Haiydar yaga bazai iya jure rashinta ba da kansa yazo ya bata hak’uri ta ce”in ka ga na hak’ura ka mayar da Aunty na”. Haiydar da kyar ya yarda sai da suka sanar da su Hajiya tayi murna don ita ma Falmi har gida taje ta bata hakuri. Aisha ita da Hasna sukayi ta jagale Haiydar shi ya basu kud’i suka had’a kayan akwati aka biya sadaki ranar jumma’a aka d’aura aure, dadadare amarya ta tare a gidan ta Haiydar bayan ya shigo sai da ya tarasu ya musu nasiha tare da kashedi banda fad’a bare hayaniya suka amsa, Aisha ita taje ta taya Haiydar shiryawa ta basa jallabiya mai kyau sabo ta fesheshi da turare ta kama Hannusa kafin ta rakosa Har d’akin Falmi bayan sun shiga da sallama Aisha tana ta addu’a a zuciyar ta don wani irin kishi takeji amma tana ta addu’a ta kori shaid’an cikin sanyi murya ta ce”Aunty ga Ango ki na kawo miki ina muku fatan alkairi sai da safe”. Tana fita da gudu tayi d’aki tanahawaye niko Rash na ce”hmm kishi kumallon mata”, Falmi ita ta matso kusa dashi ta fara shafa sa daga haka na fito, washe gari Aisha ta shirya musu karin kumalo mai lafiya. Bayan kwana biyu zaman lafiya a gidan Haiydar ba’a magana dukkansu suna girmama junasu, yau k’awar Falmi ne Gwantsi ta kawo mata ziyara ganin irin zaman da sukeyi nan ta fara hure mata kunne tun kafin tayi nisa Falmi ta ce”kee tsaya da fa da yanzu ba d’aya band in ada kin zugani na d’auka yanzu na nutsu nasan mai nakeyi, dakam nasan *NA TAFKA BABBAN KUSKURE* amma yanzu ina cikin hankali na kinaso in fito muna yawon kan titi tare tare”. *®NWA* *DEDICATED TO* *AISHA MUHAMMAD* *(MAMAN ABDUL SHAKUR)* *RASH KARDAM * [2:32PM, 9/14/2016] Rash Kardam: [4:50PM, 7/22/2016] Rash Kardam : BABBAN KUSKEREN DANA TAFKA NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. *®NWA.* *Pg-237~238.* Falmi ta ci gaba da ce wa”a yanzu kam na gane hanya kuma na rungumi kawaye na na kirki sune Mesha luv da Zahra BB sune masu sona da gaskiya, kamar yanda naga ‘Yar uwata Aisha bata da kawayen da suka fi mata Sanah da Sadeey don haka tashi ki fita bana son ganinki”. Gwantsi ta tsaya tana mata kallon mamaki ganin bazata fita ba Falmi ta d’auko waya ta ce”ko ki fita ko na kira Haiydar”, jin haka yasa Gwantsi fita ba shiri tana zuwa k’ofa taga Haiydar wanda duk abunda sukeyi yaji, Falmi da sauri taje ta rungumesa ta masa sannu da dawo hannusa ta kama ta kaishi d’aki tare da rugemasa kayan jikinsa sai da yayi wanka ta kawo masa abinci a baki take basa, Haiydar ya kalleta ya ce”Alhamdulilah! Tabbas yau ina farin ciki kuma na yarda matata Fatima ta nutsu kuma ina gode ma Allah da ya kawo Aisha cikin rayuwan mu don yanda nake samun kulawa da k’auna daga Falmi ba tare da na biya kud’i ba”. Ya karashe maganar cikin zolaya dukan wasa ta kai masa tare da rungumesa ta na sha fa kansa, suna haka aka kwan- kwasa k’ofat suka bada izini a shigo Aisha ce tashi go rik’e da hannu Abdul~shakur yaro mai kyau da gudu yazo ya haye Baban sa yana masa oyoyo Aisha da Falmi sai dariya suke masa nan ya biye masa sukayita wasa. *ALHAMDULILAH!* Dukkan yabo ya tabbata ga ubangiji sammai da kassai , nan na kawo k’arshen wannan labari na *BABABN KUSKUREN DANA TAFKA* kuskuren dana yi aciki ya Allah ka yafe min ka bani ikon gyarawa Ameen. *KIRA GARE KU MAKARANTA* Ina fatan kun gane sak’on da na isar a ciki kusani ba wai ina nufin d’aukar ‘Yar aiki da matsala ba a’a sai dai kamar yanda Falmi ta sake ma ‘Yar aiki komai na Mijinta hakan ba dai-dai bane, sannan kuma da masu halayyan hana mijinsu hakkinsu sukuma nuna cewa sai aun basu kud’i kafin su biya musu buk’atarsu na Auratayya wannan ba dai- dai bane haramun ne ke/ni dukkan kowace ta san kanta inda mai yi sai ku gyara Allah ya bamu ikon bin dai-dai Ameen. *SADAUKARWA* Na d’auki wannan *LITTAFIN* mai suna *BABAN KUSKUREN DANA TAFKA*na sadaukar wa *AISHA MUHAMMAD (MAMAN ADUL~SHAKUR)* Allah ya bar k’auna. adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *