Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, March 22, 2017

badai kafi santa ba

adsense here [12/8, 8:51 AM] Ayusha iliasu: BADAI KAFI SONTA BA Written by:- Ayusha Iliasu. Story by hawwa saleh Dedicated to Abeeda n Baseera. A'uzu billahis samiul alim minashshaidanil la'inur rajim.Bismillahir rahmanir rahim.wassalatu wassalamu ala sayyidil kaunaini, sayyidus saqalaini(al insu wal jinnu) wa'ala alihi wa ashabihi waman tabi'ahum bi ihsanin ila yaumiddeen.Bayan hk:-Ina mai shaidawa yan uwa cewa wanna labari ba'ayishi dancin zarafin kowa b ,haka dukkan wani suna d akai amfani dashi yanayine yaxo d hakan, duk wnd yaga yai kama dashi yai hkr badan shi akaiba. Page 1 to 10 Tafiya take tana layi kmr zata fadi, kuka take wiwi kmr ranta zai fita ta nufi bakin titin unguwarsu,tafiya kawai take batare datasan inda zataba,tanabin gefen titi, wani mutum ne yai parkin gabanta ya fito dg ckn motarsa,maganar da yaimata ne ta tsaidata dg tafiyar d takeyi, baiwar Allah ina zakije ckn wannan daren haka? Kukan me kikeyi? Me yafito dake daga gida da wannan lokacin? Itadai bata amsa masaba kokarin cigaba d tafiyarta takeyi, saida y fusata y daka mata tsawa sannan tai firgigit cikin shashsheqar kuka tace 'yan gidan da nake ne suka koroni sukace nabar musu gidansu,jugum mutumin yai yace to yanzu ina zaki? ta amsa da nima bansan inda zaniba,innalillahi wa inna ilaihirraji'una shine abinda mutumin ya furta gami da cewa maza shiga mota mutafi, kin shiga tai saida yasha wahala kafin y shawo kanta saboda tsoron abinda zaije yaxo, sannan tashiga suka tafi. Wani tafkeken gida taga sun shiga,umarni yai mata dacewa tabiyoshi a baya, suna shiga palon gidan babu kowa ciki , cewa yai d yarinyar zauna anan ina zuwa, direct daya dg cikin dakunan da suka kewaye palon y shiga, shigarsa b dadewa yafito shi d wata mata abiye dashi, karasowa sukai suka xauna a kujerun da suke palon,har lkcn yarinyar bata daina kuka ba, mutumin ne yai gyaran murya sannan yace hajiya wnn yarinyar yanzu na ganta tana tafiya a bakin titi, matsanancin kukan da takene ya janyo hankalini gareta n tsaya danjin meyasameta, nan mutumin ya zayyanawa hajiya duk ydd sukai d yarinyar har ta yarda to biyoshi, hajiya ta tausayawa yarinyar, sannan yace abata makwanci kfn safiya muji me ya hadata da yan gidan datake,kasancewar hajiya mai biyayya d yarda d mijinta yasa batai masa musuba ta amasa da to alhj,yawwa hajiya yace gami d mikewa ya nufi daki. Abinci da ruwa hajiya tashiga kitchen ta kawowa yarinyar saidai takici kasamcewar bata cikin hayyacinta, hajiya tai tai d ita taci taki tace takoshi, hk hjy ta hkr ta maida abincin kitchen,umarni tai mata data biyota , wani daki takaita, wasu yarane kwance kan wani tafkeken gado,tashin daya dg cknsu hajiya tai tace g bakuwa nan, ckn bcc yarinyat tace to mama takoma bccnta,sannan hjy tace tahau gadon t kwanta ckn tsoro d firgici ta hau t kwanta. Hajiya tana shiga daki t tarar da mijinta yagama shiri harya kwanta, bakin gado t karasa ta zauna tace alhj wllh wannan yarinyar tana bani tausayi daga ganinta cikin tashin hankali take,nisawa alhjin yai yace wllh hjy ni kaina bakiji ydd takeban tausayi b yarinya yar karama batafi sa'ar sumayya bafa cikin talatainindare (11:00 na dare) batasan inda zataba wnn wace irin musiba ce?ajiyar zuciya hjy tai tace wllh fa, Allah y kaimu gobe maji meyake faruwa d ita, amin yace sannan suka gyara kwanciya. Tinda hjy t juya tabar dakin yarinyar tacigaba d rero kukan d takeyi dan bcc barawo kasa daukarta yai a wannan daren sabida tinanin halin d zata tsinci kanta aciki dan mai yiyuwa ne nan gidanma su koreta. Tashi tai ta zauna tana cigaba d tunanin ydd rayuwarta zata kare dan tasan tai kaura da farinciki d jin dadi a rayuwarta tasan cikin kunci d wahala zata kare har takoma ga ubangijinta, suko yaran hajiya bccinsu suke hankalinsu kwance sai taji dama itace a ckn wnn yanayin. Kwanciya tai tin tana kuka d hawaye harsaida hawayen suka daina fitowa sautin kukan y daina bayyana har akai kiran sallah asuba tana kwance idonta biyu bacci ya gagara ,hjy ce tashigo dakin ta tashesu dan suyi sallahr asuba aladar gidance dole suyi sallahr asubar a lkcnta,alwala suka dauro a tare suka gabatar d sallahr,alqurani suka janyo dan jajjada haddar karatunsu n islmyy. Suna gamawa suka shiga wanka kasancewar ranar juma'ace akwai skul, sun shirya tsaf ckn uniform dinsu sannan suka nufi palo dan gaida iyayen nasu da yin breakfast,sun gaida iyayen nasu sannan sukai breakfast din suka nufi harabar gidan driver ne y daukesu sai skul. Ita kuwa bakuwa tinda ta idar d sallahr bacci y dauketa ,ganin shurun d hjy taji yai yawa bata fitoba yasanyata zuwa dakin,samun ta tai tanata bacci, juyawa tai batare data tasheta ba tabar dakin. Zaune suke a dining suna breakfast Alhjin ke tmbyr hjy ina bakuwar, sanar dashi tai bacci take d alamun jiya d daddare batai bacciba,alhjin yace to inta tashi lkcn nadawo dg kasuwa ma tattauna tace to Allah y dawo dakai lpy,mikewa yai yace ni zan tafi a kula d yarinyar nanfa karta fice, to ta amsa masa gami d yimasa adduar adawo lpy. Aikace aikacen hjy tashigayi kama dg kitchen,palo,bedroom, toilet duk t kammala gyarasu, palo t dawo t zauna tana kallon wani film d akeyi a mbc action da karfe , lkcn bakuwar ta tashi dg bcc idonta duk y kumbura yai jawur dashi ta fito palon, ganinta yasanya hjy katse kallon d takeyi ta taso tace muje kiyi wanka,hjyce d kanta t hada mata ruwan wankan t bata soso d sabulu sannan t rufo mata toilet din,wata atampha yellow n red colour dinkin skirt d riga ta zabo mata dg ckn kyn sumayya tasan zasuyi mata daidai dan kusan kansu daya d sumayyan,hajiya bata baro dakin b saida t tabbatar ta shirya tsaf sannan suka nufo palo,breakfast hjy t kawo mata nanma saida tai dagaske sannan tafara ci ,tanaci tana kuka a hankali. Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 1 Hajiyace ke cewa d ita meye abin kuka kuma? Kodan na tilastaki kici abinci ne? Itadai shuru tai batace komaiba, Ki kwantar d hnklimki nanma gidanku ne lkcn take tmbyrta sunanta, ta amsa mata da sunana SARAH,sunan kuwa mai dadi, nan hjy taci gaba d lallamita har tasamu ta daina kukan da takeyi. BADAI KAFI SONTA BA Written by Ayusha Iliasu. Story by Hawwa Saleh. Dedicated to Abeeda n Baseera. Page 11 to 20 12:00am hajiya ta tashi ta shiga kitchen dan dora abincin rana tabar sarah a palo a zaune, ganin hajiyar ta shagala d aikin girki yasanya sarah cigaba da rera kuka,takurewa tai jikin kujera ta dukunkune fuskarta a tsakanin cinyoyinta, jin wani sauti me kama d sautin jiniya ne ya tabbatarwa d hjy lallai sarah cigaba tai d kukan, cikin hanzari ta baro kitchn din zuwa palo, ganin ta tai ta takure kmr kaza d sauri ta karasa gareta gami d janyota jikinta ta rumgume tana cewa haba 'yar mama kukan bai isaba ashe,nace kibar kukan nan hk kinki sai kanki yai ciwo aimiki allura ko? Cikin tsoro t dago kai ta kalli hjy kasancewar ta da tsoron allura, a'a ni banason allura, tace to kidaina kuka inba hakaba allura zanmiki ynx d sauri tace nadaina gami d share ragowar hawayen d ke fuskarta. Misalin karfe 2:00 driver yai horn get man ya bude get din gidan, direct parking space din gidan y nufa yai parking, su sumayyane suka fito dg ckn motar d sauri suka nufi ckn gida,shigarsu yai daidai d fitowar mamansu dg daki dagudu sukaje suka rungumeta suna cewa mama yau mun gaji d tsaiwa,malamin chemistry ne yasamu practical a lab km a tsaye har 1 hour, hajiyace tace kaikaikai zamuci tarar malam tinda y tsaidaku har awa daya cikin barkwanci d xolaya take mgnr kasancewarta mace mai son barkwanci,dariya su sumayya sukai gami d zaro ido d rufe bakinsu d hannunsu sukace mama malam nefa, tace malam din fa, suka kara kwashewa d dariya dukkansu. Daki suka nufa suna shiga sukaga sarah na kwance idonta biyu amma ta luluka duniyar tunani batasanma sun shigoba,kayansu suka shiga cirewa batare d sun kula sarah b, wanka sukai tare d gabatar d sallahr azahar, surayya ce kecewa d sumayya wace waccan?, tace mama tace min bakuwace,dan tabe baki surayya tai ta mike tanufi inda sarah ke kwance, xama tai kusa da ita tace ya sunanki? tace sarah itama tace kema ya sunanki?tace surayya,amma kina da kyau inaso ki zama kawata kinji sarah, mamakine y kama sarah ya akai surayya takeson kawa d ita alhali batasan ita wace ba batasan daga inda take ba "su sury anga kakkyawa xaa manne mata", jin shurun d sury tai b amsa yasanya ta taba sarah gami da cewa ko bakyaso ki zama kawatane? tabatan d taine yasa t dawo dg tunanin d takeyi,a firgice t amsa da inaso, murmushi suka yiwa junansu lkcn sumy tace sury zomoje muci abinci, to tace gami d cewa sarah kema zomuje muci, ni naci tin dazu tace to bari naje muci na dawo muyi hira. Isarsu palo suka tadda mamansu a zaune sannu d aiki sukai mata ta amsa gami d sanya musu albrk, dining suka wuce suka tarar anjera abinci take suka fara serving,sunci sun koshi sannan suka dawo gefen mamansu suka zauna,sury ce ke tmbyr hjyrsu kasancewar tafi sumy surutu tace mama ina kika samo wannan kyakkyawar matar? tace bakuwace, abbanku yakawota, to a ina ya samota?hjy tace dadina dake kincika tmby kibari y dawo ki tmbyeshi,shuru sury tai can ta kara cewa wllh mama tana da kyau inasonta nidai, dariyace ta kubucewa hajiyar batare datayi niyyar yiba tace to kinsamu ai. Tashi tai tsam d sauri tace natafi muyi hira da kawata,tsawatarwa sury hajiya tai t hanyar cewa batason surutu d yawan tmbye tmbye dan tasan halin sury kmr yar jarida take. A wannan yinin ranar sury d sarah sun saba d juna kasancewar sury tana da son mutane inda sarah km keda saurin sabo d mutum,hirar d sukai tadan debewa sarah kewa ta rage mata tinanin d takeyi n ydd rayuwarta zata kasance, hakan ya dadadawa hajiya rai ganin sarah tadan sake dasu ta daina kukan d takeyi har tana dariya. Haka sukaci gaba d hira ckn nishadi batare d kowa y tmby sarah meke damunta ba km dg ina take ba, a wannan rana sarah saida taji batason sury tai nisa d ita sbd tana debe mata kewa. Karfe 5:00 na yamma alhji y dawo dg kasuwa,cikin farin ck hajiya t tareshi tanai masa sannu d zuwa, tayashi rage kayan jikinsa tai tare d hada masa ruwan wanka a toilet yaje yai, lkcn d yafito dg wanka y tarar hajitar ta fitomasa d kayan d zai saka dariya yai y gyada kai yace yau km wnn kayan hajiya keson taga nasa, y shirya tsaf ckn kayan rigace yar shara d wando na wani yadi maikyau mara nauyi laurin ruwan madara,sbd lkcn zafine, palo y fito y zauna lkcn hjy t kawo masa juice da ruwa mai sanyi sbd baya cin abinci inya dawo dg kasu sai byn sallahr magriba,zuba masa tai a cup t mika masa y karba yana zolayar d yasaba yimata yana cewa sannu d aiki uwar gida ran gida,uwar gida sarautar mata daga ke ba kari, murmushi tai tana cewa alhji kenn banda zolaya dai, yace Allah dgske na kulle kofa dg ke, tace Allah y yarda yace to ba aminba d alamar tsokana yace dm ku mata bakwa son abokiyar zama, hmmmmm tai gami d cewa b ita muke guduba halinta muke gudu yace hakene Allah y hadani d nagari na karo uku, bata rai hjy tai tace banason irin wnn zolayarfa kar taxama gskiya, kyalkyalewa d dariya yai yace to naji sarkin tsoro tace eh naji tsoro ko gsky, to shikenan abar mgnr. Hira suke ckn nishadi yace hjya ina bakuwarmu d yaran nan suke, sbd yasaba duk lkcn d yadawo dg kasuwa tare suke irin wnn zaman a palo kfn ai kiran sallahr msgriba,ai alhj tinda ka fita take kuka dakyar nashawo kanta tai shuru dan abinci m dakyar taci saida lallami, ajiyar xuciya alhji yai yace ikon Allah ta daina kukan? eh ta amsa masa yace ynx ina take tace ai tinda su sumayya suka dawo dg mkrnta surayya tasata gaba d hira ynz bakaga ydd tafara sakewa b har ta saba da surayya kasan yar taka d surutu, dariya yai yace alhmdllh haka akeso ai. Jin kiran sallahr mgrba ne ya katse musu hirar da sukeyi suka tashi domin suje su sauke farillah. Lokacin d alhji y dawo dg masallaci zaune yatar d hjy a palo tagama jera musu dinner a kan table mat, sabon alhji ne indai zasuyi dinner a palo sukeyi shida iyalinsa, breakfast ne kawai ke kaishi dining km shima in ranar weekend ne tare d iyalin nasa sukeyi, karasowa yai kusa d hakiyar y zauna yake cemata ynx hjy yazaai d wnn bakuwar, mirmishi tai gami d gyada kai tace sarah yace au sunanta kenan tace eh baka tmbyta bane yace eh,hajiyar ce kecewa yanxu dai tmbyarta xaai maya barota da gidansu d daddare hartake kuka batasan inda zata nufaba, kwarai kwarai alhj yace d hjy kin kawo shawara, serving dinsa tafarayi saida t gama yace kinga yarannan yau sun samu bakuwa sun manta dani ko sannu d zuwa basuyimin ba yana mgnr yana er dariya, dariya itama hjyr tai tace aikuwa suna can sun tsareta d hira bari n kirawosu ta mike ta nufi dakin. Sannu d dawowa abbah, lkcn y dago kai ya wurga musu harara ckn wasa yace sai yanxu d namemeku zakumin sannu d zuwa banaso, sumy ce tace ayi hakuri abbanmu yayin d sury d sarah suke yar dariya a boye, to nahakura sumyn abbah ku zauna muci abinci Allah yai muku albrk hada baki sukai gaba daya harda hajiya sukace amin. Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 2 Sunci sun sha kowa y koshi, hjyce t umarci sury t kwashe kayan takai kitchen ckn hanzari batare d musuba ta kwashe takai sannan ta dawota zauna, alhjine yai gyaran murya yace sarah, dasauri t dago kanta dake sunkuye a kasa ta kalleshi tace naam, yace inason kifadan abinda yasa kika baro gida d daddare kina kuka? Kwallah ce tacika idon sarah takasa magana take taji kuka ya subuce mata,d mamaki hjy t kalli alhj tace ikon Allah dg tmby sai kuka,hannu y dagawa hjyn alamar tai shuru, shuru ne y ratsa palon tsawan mintuna bakomai kakeji b sai sautin kukan sarah data gagara magana,andau lokaci sannan alhj ya umarcesu sutashi su shiga daki sabida yaga sarah batada alamar yin mgn, haka suka tashi suka tafi tana kukan. Haka sarah takwashe tsawon sati a gidan alhj cikin kulawa d jin dadi batare d sunsan ko ita wace b dg ina take b me yasa tabaro gdnsu, kullin aka tmbyta bata iya magana sai kuka. *BADAI KAFI SANTA BA? *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh* *Dedicated to Abeeda n Baseera* Page 21 to 30 *WAYE ALHAJI?* Alhaji Yusuf Sulaiman haifaffen garin kano ne, a wata unguwar da ake kira hausawa cikin karamar hukumar tarauni, mahaifinsa malam sulaiman wanda akafi sani d malam sule yana d mata daya wato halimatu d yaya uku namiji daya mata biyu,yusuf shine babbansu sannan maryam da hadiza,Allah yaiwa malam sule rufin asiri daidai gwargwado yana kula d iyalinsa yadda ya dace, yabasu tarbiyya kwatankwacin yanda addinin islama y tanada , ilimin boko da arabiyya Alhj yusuf ya halarci makarantar firamare dake unguwarsu wadda akafi sani d hausawa model primary schl, dg nan ya tafi mkrntar sakandire mai suna govt senior scndry schl sabuwar kofa, ganin tafiyar d yakesha dg unguwarsu zuwa sabuwar kofa ne yasa mahaifinsa y saimasa wani dan akwalar keke,wanda kullun cikin wahalar dashi yake, yau in taya t sace koyai faci a hnyar tafiya gobe insha maka Allah a hanyar dawowa gd zaici karo d matsala har Allah y taimaka y gama mkrntar y sami sakamako mai kyau. Ganin yusuf ya kammala sakandire d sakamako maikyau ne ya zaburar d malam sule wjn ganin dan nasa ya cigaba d karatu,haka yaita fafutuka har Allah ys yasamu gurbin karatu a sa'adatu rimi college of education kano,inda y karanci history/islamic studies, akwana a tashi b wuya ya kammala karatunsa ya samu kyakkyawar shaidar karatun NCE (National certificate of education),ba karamar murna d frnciki malam sule yaiba ganin dansa y kammala krtn ba bata lkc, ganin sakamakonsa yai kyau ne yasanyashi neman aiki koyarwa,Allah baisa y samu n gwamnati ba sai a wata private schl , hk y hakura yake xuwa suna biyansa dan abinda bai taka kara balle ya karya ba. Lokanci daya yusuf y tsinci kansa d shaawar komawa karatu take ya yanke shawarar sanarwa d mahaifinsa, bai kasa a guiwaba ranar lahadi ya sami mahaifinshi Zaunee akan dakalin gidansu yana shan hantsi, sallama yai masa suka gaisa yake sanar dashi yazo d wata muhimmiyar maganace,mamakine y kama mlm sule a xuciyarsa yana cewa Allah ys yaron nan b aure y daddagoba mana ba, nisawa yai yace inajinka yusufa Allah ys alkhr ce yace insha Allah alkhrce babah yace to madallah, take yake sanar masa d bukatarsa t son zurfafa karatunshi, mlm sule yai frnck d hakan sosae amma y katseshi d cewa wani hanzari ba guduba yusuf kasan krtn digiri ba kmr wnd kai abaya bane wahalarsa tafi wancan ni bazanma alkawarin daukar nauyin krtn digiri b saidai xan taimaka ma d abinda y samu, godiya yusuf y shiga yiwa mahaifin nasa d cewa dama dan albashin d ake biyana ina cire wasu kudi dg cknsu n ajiye dasu nakeson fara krtn, mlm sule yai mirna sosae ganin dan nasa d hnkl har yana tara wasu kudade bayan hidimar gida dayake musu da kudin mkrntar kannensa, nan yasamai albrk d adduar Allah ys afara a saa. Cikin ikon Allah yusuf y samu admission a jamiar bayero ta kano inda y samu shaidar degree a history,har a lkcn bai fasa zuwa koyarwar d yakeyi a private schl dinba, lkcn d ya kaiwa shugaban makarantar result dinsa n degree yatata shi murna sanna y kara masa matsayi d albashi,mlm sule b karamin frn ck yai d hkn b har mkrntar yaje yaiwa shugaban mkrntr godiya. Haka rayuwar yusuf taci gaba d kasancewa cikin kwanciyar hankali da sanya albarkar da mahaifinsa yake masa,har zuwa wannan yanata fafutukar samun aikin gwamnati yake amma abin yaci tira, ya zauna jarrabawar daukan ma'aikata da dama amma baya ganin sunansa sabida komai yaxama na yayan masu da hanya, interview kuwa har kaduna,abuja Da sauran garuruwa yaje amma Allah baisa ya samu aikin gwamnatiba,ganin wahala tana dada yawa akansa tinda yanzu su maryam suna daf da shiga babbar makarantar sakandire ne bukatar karatunsu zaifi nada yasashi shawartar mahaifinsa kancewa yanason ya dinga zuwa kasuwar kwari a ranakun asabar da lahadi ko dako ya dingayi,mahaifinsa bai musa masa ba kasancewarsa mutum mai hangen nesa, kuma ga tsufa ya fara zuwa masa karfinsa na raguwa shiyasa ya goyi bayansa tare damai adduar Allah ya taimaka,Yusuf yaji dadin adduar da mahaifinsa yai masa. Alhamdulillahi yusuf yafara zuwa kasuwar kwari yai kamakai (kwadago) abin da yake samowa a weekend yayi rabin albashin da ake bashi,amma duk d haka bai saki aikin koyarwarba haka ya hada biyu g kasuwa ga koyarwa,akwana atashi ba wuya gurin Allah yusuf ya saba da manyan yan kasuwa, daya daga cikin mutanen da yusuf suke xama a bakin shagunansu ne mai suna alhj ya'u ya lura da nutsuwa gaskiya da amanar yusuf daga nan ya fara janshi a jiki ya zama kamar yaron shagonsa, wata ranar lahadi bayan antashi dg kasuwane alhj ya'u ya tsaida yusuf yake cewa yanason ya bude masa shago sabida ya yaba da nutsuwarsa da gaskiya d amanarsa amma sai sunje gun mahaifinsa idan ya amince sai yabude masa,farinciki gurin yusuf baya misaltuwa batare da musuba ya amince suje gun mahaifin nasa,alhj ya'u yai farinciki take ya dauki yusuf a motarsa sai gidansu. Lokacin da suka isa gidan ne yusuf ya shiga domin sallama d mahifin nasa ya tarar bayanan,fitowa yai domin fadawa alhj ya'u bayanan sai ya hangeshi ya taho. karasawa yusuf yai yacewa alhj ya'u ga baban nawa can ya taho, jira sukai ya karaso, bayan sun gaisa ne alhaji ya'u yafara sanar dashi makasudin zuwansa,cikin farin ciki yai masa iso kan dakali yana cewa ai alhj magar bata tsaye bace,zama sukai kan dakalin ya warware mishi dalilin zuwansa,nan take mlm sule ya amince da abudewa yusuf shagon, cikin murna da farinciki mlm sule ya dingayi yiwa alhjin godiya da fatan alkhairi gami da gargadi da nasiha ga yusuf ya rike gaskiya da amana,ya kara da cewa alhjin duk wani abu dakaga ba daidaiba kaxo ka sanar dani zandau duk hukunci da yadace akan yusuf, hakika alhj yai farinciki da irin gargadi da nasihat da mlm sule yaiwa dannansa, daganan alhji yaiwa mlm sule kyautar kudi sukai sallama, har gaban mota yusuf ya rakashi tare da kara yimasa godiya. Cikin ikon Allah aka budewa yusuf shago inda aka makareshi d kaya kama dg shadda, yadiddika, atampopi dadai sauransu,ciniki gadan gadan ake a shagon ,kasuwa ta bude dan har anfi ciniki a shagon akan shagon alhjin,ba karamin jin dadi alhj ya'u yayi ba da hada kasuwancinsa da yusuf dan dukiyarsa ta kara yalwata d bunkasa har gida yake zuwa yaiwa mlm sule godiya tare da yimasa alheri d hasafi n kudi,haka shima mlm sule bai gaxaba a kullin safe da dare wajen yiwa dannasa Addua da gargadinsa banda cin amana da ashararanci da dukiyar wanda y baka amana haka kuma banda hurda da abokan banxa da zasu sashi a hanyar banza,ya kara da cemasa muddin ya kiyaye wannan nasihar da gargadin zaiga cigaba a rayuwarsa, hakika yusuf ya kiyaye maganar mahaifinsa baya taba kwandala daga cikin kudin shagon sai abinda aka bashi dan haka ya bar aikin koyarwar da yakeyi batare da shugaban makarantar yasoba dan yanajin dadin aiki dashi kuma students suna gane karatunsa amma ba yadda ya iya dan yusuf kullin yana kasuwa dole sukai handing over ya daina zuwa, su kansu daliban sunyi bakin cikin hakan dan suna jin dadin koyarwarsa. *Littattafan marubuciyar:-* *AMAL* *DUNIA MAKARANTA* *RAYUWAR AYSHA* *MIJIN HAJIA* Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 3 *BADAI KAFI SONTA BA……* *A yanxu haka zaku iya samun littafin RAYUWAR AYSHA,MIJIN HAJIA d BADAI KAFI SONTA BA a blog dina kmr haka:-* *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Page 31 to 40 Yusuf ya hada hankalinsa baki daya kan kasuwanci baida lokacin kansa balle nahira da abokai, idan kagansh.i tofa da yamma ne yadawo daga kasuwa ko kuma ranar lahadi da basa bude shago, zama suke a gida su huta,Alhmdllh kuma kasuwancin ya karbeshi cafcaf komai yana tafiya daidai. Bayan shekara biyu da budewa yusuf shago ne watarana yusuf yaje gidan alhaji ya'u domin ya gaisheshi, bayan sun gaisa ne alhji ya'u yake cewa d yusuf yakamata yanxu ace ya ajiye iyali, hakika yusuf yaji dadin maganar dama yanason yai aure saidai inya jewa da mahaifinsa maganar yana katseshi da cewa ya kara hakuri dan yanzu inyace xai aure kar alhj ya'u yace kudin shagonsa ya kwasa yai aure, jin maganar da mahaifinsa ya fadane yasa yusuf ya hakura da maganr aure karshe ma ya daina zuwa gurin budurwar da yakeso, jin shurun d yusuf yai ne yasa aljhin ya kara maimaita maganar sai a lokacin yusuf ya dago yai murmushi yace ai alhji bansamu wadda nakeso ba, jin yusuf ya fadi hakane yasa alhjin yin hamdala g Allah a zuciyarsa dan dama yanada kudiri azuciyarshi nasan ya hadashi da yarsa saidai yana gudun ya tareshi d maganar ko yana d wadda yakeso amma yanxu komai zaixo d sauki,cikin hikima alhji ya'u yace kamarka yusuf kace bakada wadda kakeso? Yusuf y sosa kai tare d sunkuyar d kai yace babu , jin amsar d yusuf y bada yasa alhjn cewa to indai wannan ne ga yar wajena nan rukayya kaje ka ganta idan kana sonta na baka,amma idan kaji bata kwantama a raiba dan Allah karka boyemin sai ahakura Allah ne baiba tinda shi aure yine na Allah, godiya yusuf yaimasa sukai sallama. A daren wannan ranar yusuf ya je gurin rukayya, alhmdllh sun daidaita kansu ba bata lokaci suka amincewa juna dan rukayya yarinyace mai kamala d nutsuwa g kunya gata da kyau daidai gwargwadon yadda Allah yayita dadin dadawa kuma wankan tarwadace , a lokacin ta gama makarantar sakandire b dadewa. mlm sule yasamu labarin abin arzikin d ubangidan dannasa yayi,yayi farinciki da adduar Allah y tabbatar d alkhairi yasa ayi dasu, haka shima alhji ya'u yai murna da hakan gami da adduar sanya albarka,alhji yau dakansa yasa lokacin biki wata biyu tare da cewa zaiyi komai da yakamata su yusuf suyi hatta gidan da zasu zauna zaibasu dan yadau yusuf tamkar dan da yahaifa tinda y rikemasa amana kuma yazamo sanadin yalwatar dukiyarsa,mlm sule har gida yaje yaimsa godiya,kwanci tashi ba wuya lokacin biki yazo akasha shagalin biki aka kai amarya gidanta,zaman lafiya sosae tsakanin yusuf da rikayya har Allah ya kawo rabo,murna agun yusuf baxata misaltuba, kullin adduar Allah y sauketa lafiya yakeyi, lokacin d cikin rukayya yashiga wata n tara Allah ya karbi ran mahaifiyarsa Halimatu, tsiran sati uku d mutuwar mahaifiyarsa rukayya ta haihu tasamu 'ya mace,da kanta tabawa yusuf shawara asawa yarinyar sunan mahaifiyarsa wato halimatu, hakika yusuf yai farin ciki d hakan, ranar suna yarinya ta amsa sunan halimstus sa'aadiyya ba dangin yusuf b har dangin rukayya sunyi murna da hakan sosae. Haka rayuwa tacigaba tsakanin yusuf d rukayya cikin kulawa da kwanciyar hankali,lokacin da rulayya ta haifi yarta ta biyu ne alhaji ya'u ya mallakawa yusuf shagon daya bude masa inda akai takarda d shaidu da sahannun alhj ya'u Data mai unguwa cewa ya mallakawa sirikinsa yusuf shagonsa kyauta halak malak, ranar yusuf kasa magana yai acewarsa baida bakin godiya,har gida yusuf da iyalinsa sukaje suka sake wa alhjn godiya,haka yanuwan yusuf ma baa barsu abayaba suka dinga zuwa godiya harsaida alhjin yace ya isahaka,ana cikin wannan farin cikin aka sanya lokacin auren kannen yusuf wato maryam d hadixa,mlm sule yaci burin bikin yayan nasa saidai Allah baya barin wani dan wani yaji dadi,ana saura wata biyu bikin mlm sule y amsa kiran ubangijinsa,ba yusuf, maryam d hadixaba hatta alhj ya'u mutuwar nan tadakesu dan har lokacin bikinsu maryam basu daina jimamin mutuwar ba, alhji yau ya taka radar gani a auren su maryam yaxame musu jigo a rayiwarsu wato uba suma sun rikeshi matsayin uuba. Allah y sa albarka akasuwancin yusuf inda ya bunkasa ya zama babban dankasuwa, a shekara daya yabiya wa kanshi da rukayya kudi sukaje suka sauke farali, shekara data zagayo yabiyawa maryam da hadiza suma sukaje, bayan dawowarsu ne hadiza tasamu ciki a wajen haihuwa Allah yaimata rasuwa, haka yusuf ya dakko yaron data haifa ya kawowa rukayya ta raineshi, saboda lokacin ta yaye fatima,haka rukayya ta raineshi tamkar dan d tahaifa cikin kulawa irin ta uwa. A yanzu haka alhji yusuf yana da yaya bakwai,mata biyar maza biyu,halimatu itace babba sannan fatima sannan mariya sai abdullah sai sulaiman sai sumayya da surayya,sai kuma dan yar uwarsa d yake ruko kamal,tsarin alhji yusuf ne daga sakandire yayansa mata basa jami'a dan haka halimatu,fatima d mariya duk ya aurar dasu inada halimatu keda yara uku, fatima d mariya kuma biyu,yanzu haka abdullh yana aji 6 a sakandire sulaiman kuma aji 4, sumayya da surayya kuma aji 2, kancewar alhj yusuf mai kudi baya tsawwalawa kansa da sai yayansa sunyi makarantar kudi,abdullah d sulaiman suna boarding schl wato Govt Boys Secdry Schl Gwarzo, Sumayya kuma suna Day Science kano,shi kuma kamal yana jamiar Ahmadu Bello dake zariya,alhji yusuf ya kasance mutum mai takatsantsan d gudun duniya dan haka a gidansa ko yar aiki babu komai matarsa hajiya rukayya dakanta takeyi tare da taimakon yayanta, driver d maigadi ne kawai a agidansa sai almajirin da suke aike, shima dan drivern aikinsa kawai ya ringa kai su sumayya makaranta da yadawo dasu zai ajiye motar sai wata safiyar,hakika alhji yusuf ya tarbiyyantar d yayansa akan tarbiyyar islama ya nuna musu tausayi, hakuri da kaskantar da kai tare da nuna su ba yayan kowa bane, wani lokacin zasu tambayeshi kudi yace baidashi kuma yana dashi saidai yaki basune dan ya nuna musu in yau akwai gobe fa babu,kuma alhmdullh yaran sun taso akan irin tarbiyyar da yadorasu akai. A halin yanzu alhji yusuf yana da shaguna da dama a kasuwar kwari inda shima yaja yara ajiki ya bude musu kamar yadda mahaifin rukayya wato alhj ya'u yaimasa. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayisha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Page 41 to 50 *CIGABAN LABARI* Ranar da sarah ta cika kwana goma a gidan alhji yusuf da safe bayan sun gama breakfast suna zaune a palo da iyalinsa alhajin ya gyara zama gami dacewa sarah firgigit t dago kai takalleshi tace naam abba (kmr ydd taji su sumayya nafada masa) cigaba d magana yai yace yanzu kinga yau kwananki goma a gidannan batare da munsan daga ina kike ba dan haka nakeson yau kifadamin meye dalilin dayasa kika baro gidanku da wannan daren? Shiru ne ya ratsa gurin nawani lokaci batare da sarah tace komaiba, su sumy n sury anbaza falafalan kunne anson jin kwaf, shurun d alhj yaji yai yawane yasanyashi dakawa sarah tsawa da kakkausar murya kasancewarsa mutum da bayasan wasa yace badake nake ba, kwallace ta zararo tabiyo kunnucintalokacin da tadago, ganin hawayen yasa alhji yakara cewa duk kukan da zakiyi saikin fadamin ,dan bazai yiyu muyita zama dakeba alhalin bamusan kewaceba, jin alhj yafadi Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 4 hakane yasa sarah ta goge hawayenta gami da cewa abbah labarina mai tsahone zamudau lokaci ban gama sanar dakuba,alhaji yace komai yawansa ina sauraronki dago kanta tasakeyi sannan tafara magana cikin dakushewar murya kamar haka:- Nidai sunana sarah muhamma, mahaifina yakasance yana da matan aure guda biyu,ummana Hajara d kishiyarta bilkisu, ummana tana da yaya biyu ni d kanina khalid, itakuma kishiyarta tana da ya guda daya rufaida, babana mutumne d Allah y doramai son ummana saboda hakurinta da biyayyar da takemasa koda yaushe yana nuna mata soyayya a fili hakan nabatawa kishiyarta rai tin tanai aboye har take nuna kishin haka agabansu ,duk randa abbana yaiwa ummana wani abu najin dadi ko yayabeta agaban idanunta yana juya baya a gaban ummana zata gyada kai tace wayaga buyouts, takara d crew zata gani ne wllh,wannan kalma tanaiwa ummana ciwo amma bata taba fadawa abbana abinda d take cewa saidai tai hakuri taita addua, akwana atashi tin abin nadamun ummana har tasaba da wannan kalmar ta hassada, ganin ummana bata taba tarar abbana dan fadama sa, hakanneyasa yasa kishiyar tata ta bullo da sharri kala kala, idan abbanmu ya tafi aiki yana dawowa zata fadamasa ummana tafita batare da izininsa saba ko tace ta gayyato mutane ta dafa abinci ta juye musu tahansu ita da yarta, ko idan tai baki ummana tai girki bata basu, sharri d tuggu dai kala kala tin abbanmu yana yiwa ummata fada agabanta, har yagane sharri kawai take mata ya daina yimata fada, idan tafada masa saidai yace tayi hakuri zaiwa ummana fada, ganin yadaina yiwa ummana fada ne yasa ta bullo d wani makircin duk ranar girkin ummana saita daidaici tagama miya ko abinci saita faki idobta taje takara gishiri aciki,duk mu kasa cin abincin hakama idan abbanmu yazo zai ci yakasa ci yai taiwa ummana fada, tanaji yana fadan saita sallallabo ta zo ta cewa abbanmu yunwa sukeji sunkasa cin abinci, haka komai dare abbanmu zaicewa ummana ta tashi ta dora wani abincin, batare d musu ba ko kosawa zata sake wani girkin, akwai randa abbanmu yakawo nama a soya kuma ranar ummanace da girki saita soya naman nan takai kitchen, tana ganin ummana tashiga wanka dan lokacin abbanmu yakusa dawowa gida saitai sauri tadau galan din kalanzir ta tsiyaya acikin naman ta jujjuya tamayar tarufe, abbanmu yana dawowa aka xubo masa naman yanacin yanka daya yace da ummana ya akai kalanxir kalanzir y taba naman ,abinne ya daurewa ummana kai tace kalanzir yace eh, tace wllh ita batasan yadda akaiba, nan abbanmu yafara yiwa ummana fada yana zaginta yana cewa wace muguntace wannan tasan d yadda yai yasiyo naman zata zubamasa kalanxir aciki, budar bakin ummana tace yai hakuri kawai ya wanketa da mari,(sarah tanakaiwa nan sai naga sumy d sury harma d hajiy sun zaro ido suka hada baki mari tabdijan, nima kaina ayusha saida tausayinta y shigeni,abinda y baiwa su sury d Sumy mmki shi ne tin tasowarsu basu taba ganin abbansu y mari mamansu b, amma take cewa nata uban y mari mahaifiyarta. Jin karar saukar marin da kukan ummana ne yasa na zabura da gudu nayo waje dg cikn dakinmu dan ganin meke faruwa da ummana take kuka,ina fitowa mukai idohudu d kishiyar ummana ta watsomin hararagami dacewa indai nice zata yabawa aya zakinta tinda,aranta tace *Badai kafi sonta taba* kadanma kenan sai tagwammace kida da karatu, jin abinda da take fadene yasa jikina yai sanyi nakasa karasawa inda ummana take kukan banyi auneba sai jinai nima kukan ya subucemin. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayisha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Page 51 to 60 Sarah ta share hawayen dake gagarowa a fuskarta taci gaba da cewa ganin da ummana tayi na taho nakasa karasawa na tsaya ina kukane yasa ta karasowa inda nake tsaye ta kama hannuna muka shiga daki, bayan munshiga ne take tambayata meyasa nake kuka nace mata naji kara kamar ta duka ne sannan najiyo muryarki kamar kina kuka shine nai hanzarin fitowa naga meya sameki shine naji ammi (wato kishiyar babata dan haka muke kiranta) tana fadin wasu maganganu da ummana bata bari na fada matasuba, hakuri tashiga bani tana cewa ba abinda yasameta, taki fadamin ne dan kar kima da mutuncin abbanmu ya ragu agurina, amma tabbas ni naji komai yafaru, haka naita bawa ummana hakuri akan duk abinda ake mata a gidan nake cemata malamin islamiyyarmu yana fada mana Allah yace acikin alkurani mai tsarki *( _Hakika masu hakuri su ake cikawa ladansu batare da hisabiba_)* kuma ya kara fada mana annabi SAW acikin hadisinsa ya cewa *(Hakuri haskene)*jin haka ne yasanya ummata tai murmushi tace Allah yai miki albrk ya kara mana hakuri nace amin. Tin daga wannan ranar abbanmu yace duk sanda ya kara kawo wani abu gidansa kar ummana t kara tabawa koda ranar girkinta ne saidai ammi tinda ummana mugunta take masa a kan kayansa,dadi kuwa kamar yakashe ammi dan farin ciki, haka muka hakura intai girki tadan zuba mana baikai ya kawoba haka zamu karba muci da dadi ko badadi mun koshi ko bamu koshi bamu isa mufadawa abbanmu ba saidai muyi hakuri, ganin haka ummana ta hakura tazuba ido ba yadda ta iya saidai kullin tana kaiwa Allah kukanta yai mata magain abun, nima kullin addua nake Allah ya bayyanar d mai gaskiya. Haka rayuwar ummana taci gaba cikin kunci da takaici batada ikon tai kwakkwaran motsi acikin gidan, in kaganta a tsakar gida saidai alwala ko wata bukatar amma koyaushe tana daki tana kaiwa Allah kukanta, ita kuwa ammi gari nata kasuwa tata,gari na wayewa abbanmu y fita aiki zatai ta shewa da habaice habaice taci karenta b babbaka duk dan ummata takulata suyi tashin hankali itakuwa ummata tai banza da ita ta nuna batasan tanaiba. Tsananin adduar d ummana takeyine Allah ya fara karkato da abbanmu kan ummana,godiya ga Allah muka shigayi sanda abbanmu yace da ummana zata cigaba da girkinta tare d yimata gargadi data kula kar irin abinda ya faru a baya ya sake faruwa,wai acewarsa yagaji dacin abincin ammi baya dadi kamar na ummana baisan tsananin adduar da mukeyi bane yasashi fadar hakan,hajiya ce ta katsere sarah ta hanyar cewa ai dama addua bata faduwa kasa banxa,tabbas sarah tace takara d cewa Allah ai yafada a cikin Alkur'ani *"Duk wanda ya dogara dashi (Allah) zai isar masa".* mamakine ya kama alhj jin yarinya karama da hankali ga uwa uba ilimi ta iya zaro ayaoyi da hadisai kamar wadda ake kitsawa, take yaji kaunarta takuma shiga zuciyarsa. Ranar da ummana taci gaba da girki takaici da bakin ciki ba wanda ammi bata nunaba har tana cewa bari munafikin mijin naki y dawo yasameni, ai baifadan zaki cigaba da girkiba shine ya zage kuka kulla muna fircinku a daki wallahi indai nice bilki zamusa kafar wando daya dake tinda *Badai yafi sonki ba*,maganganun ammi sunyiwa ummana zafi saidai tadanne zuciyarta taki kulata saida taji abun ya isheta ta dago tace aimu da Allah muka dogara kuma ba haka kawai yafi sonaba hali nagari shikesa aso mutum, idan mutum yana so asoshi shima saiyai koyi da irin halin ibaiga ansoshi ba, wannan maganar da ummana t fad ita takara ruta wutar kiyayya da gaba tsakaninsu fuuuuu tashige dakinta tana cewa zaki ganine,ummana tace Allah yasa muga alkhairi, tindaga ranar ta dau gaba da ummana harma damu ta daina yimana magana hatta yarta rufaida tasa tadaina kulamu,duk ranar girkin ummana intai abinci bataci bata barin rufaida taci koda yunwa zata kasheta. Idan abbanmu yadawo taita kuka taba fada masa karya d gaskiya shikuwa bayabin takan magamarta tinda y fahimci duk karyane kawai batason zaman lafiya ne saidai yace tayi hakuri, ganin zaman lafiya yadawo kamar ada tsakaminshi da ummana ne yasa ammi kullatar saita raba tsalaninsu kotawani hali nan tafara zuwa gurin yan bori d yan tsibbu d bokaye ahada ummana d aljanun da zasu sa abbanmu ya tsaneta yaji baya son………….sai kuka ya subucewa sarahbata iya karasawa ba. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayisha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Page 61 to 70 Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 5 Duk lokacin d ammi zata gurin boka sai tabari abbanmu ya tafi aiki saita fita batare d ta tambayeshi ba,tinda ummana ta fahimci tafara zuwa gurin bokaye tasake dukufa addua da salloli ba dare ba rana tana kaiwa Allah kukanta y kareta dg sharrin da take son kulla mata,akwai ranar da tadawo dg gidan bokan tazo kofar dakin ummana ta barbada wani magani wai indai ummana ta tsallaka shikenan abbanmu xai saketa, ita ummana batasan tazuba ba data tashi zata fito dg dakin tai bismillah tafito,murna ammi tashiga yi ganin ummana tsallaka maganin tana jiran abbanmu y dawo taga yasaki ummana amma daya dawo sai taga baice yasaketa ba saidai ma cewa yai d ummana ta shirya zasuje unguwa, nan takaici y isheta, abbanmu suna fita unguwar tasa kafarta itama tafita, ashe gurin bokan takoma take fadamasa aiki baiyiyuwa, nan boka yace mata ai sharadin maganinsu ba'a ambaton Allah idanko aka sake aka ambaceshi aiki ya lalace,jin boka yafadi haka yasa abin duniya yaiwa ammi yawa ya zatai da ummana tinda bata wasa da addini, sake dabara tai takoma gurin yan tsubbu kullin d kala kalar abubuwan d zata zo dasu taita binnewa a gidanmu muna kallonta tanayi tana maganganu d habaici, ummana bata taba tanka mataba balle tafadawa abbanmu, saidai dagewa da addua da mukeyi. Haka kullin d abbanmu yana fita itama zata fita bazata dawoba sai tadaidaici yakusa dawowa sannan ta dawo dan tasan ummana baxata taba fadamasa b, ganin duk abin d takeyi baya kama ummana saidai zaman lafiya d kwanciyar hankali da yake karuwa tsakanin ta d abbanmu,nanfa ta tashi a tsaye d gagarumin asiri yau da gobe tafi karfin wasa dare daya abbanmu y juyawa ummana baya ko ta gaisheshi baya amasa dg karshe ya daina shiga dakinta ya daina cin abincinta balle yadau butar ta,kukane yaci karfin sarah cikin shashsheqa taci gaba d cewa tindaga wannan lokacin ummana ta fara mugayen mafarki tana bacci saitai ta ihu tana tsorata tana cewa zasu kasheta gasunan sun taho ku tainaka min zasu kasheni haka zatai t ihu tana zabura amma abbanmu baxaizo gurinta ba saidai y daga labule y leko yace taimusu shiru mahaukaciya kawai ta hanasu bacci, haka zan rungumeta ina karanta mata ayatul kursiyyu har tasamu bacci, farin ciki agun ammi bazaya misaltuwa, haka ummana tashafe wata uku a wannan halin kullin cikin dare bama bacci makaranta ma daina zuwa nai saboda indan natafi bansan abin d ammi zataiwa ummanaba,ganin abbanmu yaki nemawa ummana magani ne yasa naje nafadawa kawu sani wato kanin ummanmu halin da muke ciki. Zuwan kawu sani gidanmu yaga irin halin da ummana take ciki duk ta rame ta susuce kamar mahaukaciya tayi baki ba yadda yasanta ba dan duk danginsu ba wanda y kaita kyau da kwarjini gata fara mai manyan idanuwa d dogon hanci idan tai murmushi sai wushiryarta ta bayyana kyanta ya karu,kasa magana yayi kawai kuka yakeyi yana cewa yanxu haka ummana takoma,tambayata yashigayi meya sameta? Meya janyo mata fadawa wannan halin? nan na zayyana masa abinda yake faruwa da yadda ummana take tsorata cikin dare d kalmar d ammi take fadawa umman kullin ta *Badai kafi sonta ba* wallahi zata gani ne,abinne ya daurewa kawu sani kai shi kanshi kalmar tayimasa zafi a rai dan yadda fuskarsa ta nuna alama, atake ya dauke ni d ummana a motarsa bamu tsaya ko inaba sai gidan mai magani tare d cewa zai dawo y sami abban namu,sautin kukan su sumayya ne yasa sarah yin shuru. Nima danake sauraransu kukan nake shabe shabe d hawaye. ina fadin Allah y rabamu da sharrin kishiya.amin *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayisha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Page 71 to 80 Sanda kawu sani y dawo y samu abbanmu yake tambayarsa ya akai y bar ummana a wannan halin?abin d yafito dg bakin abbanmu sai yace baisan batada lafiya ba sabida kin Allah, kawu sani ya jinjina maganar d abbanmu ya fadamasa y zaai suna gida daya yace baisan batada lafiyab,kawu sani shiru kaeai yai masa batare d ya tanka masa b a matsayinsa n mijin yayarsa. Haka muka zauna a gidan magani tahom wata daya batare d inaganin sauki a tattare d ummana b saidai kullin abu karuwa yake har takai saidai a kulle ta a daki inba hakaba neman guduwa takeyiashe dg wannan somi somine, wasa farin girki wata rana muka wayi gari ummana t fara hauka tibiran duk wnd yaje kusa d ita sai duka amma abin takaici duk wannan halin d muke ciki abbanmu sau daya yazo ya ganmu sai randa muka cika kwana 35 sannan y dawo, ganin haukan d ummana takeyi ne y sanya jikinsa yai sanyi nan ya ashiga nema mata magani ka'in d na'in sbd tsananin son d yake mata. Alhamdulillah daga sanda abbanmu y fara neman maganin ne tafara samun sauki ganin haka yasa kawu sani y daukemu dg gidan mai maganin y maidamu gidanshi, har gidan abbanmu yake zuwa y kawo mana maganin batare da ammi tasan yana yiba,wasa wasa cikin ikon Allah sauki y dada samuwa satinmu biyu muna amfani d magungunan ummana ta warke, lokacin d abbanmu yazo yaga t warke yace mukoma gidanshi nanfa kawu sani yace ai baiga abinda xaisa ta koma gidan ba, saida abbanmu yaita bashi hakuri kan cewar insh Allah hakan bazata sake faruwa ba nanma dakyar kawu sani y yadda amma yace saitayi wata daya kafin t koma badan abbanmu yasoba ya hakura sai randa ta cika wata gudan sannan ta koma. Ganin ummana t dawo gidan cikin koshin lafiya ya dada tinzira ammi wjn yin asiri,shikuma abbanmu baifasa kawowa ummana maganin neman tsari b,haka kuma muma bamu fasa dagewa d addua ba, haka alamari yaci gaba d tafiya agidan ba dadi saidai zaman hakuri d mukeyi,duk sanda muke hira d ummana tana cewa yanzu sarah haka zamu kasance a gidannan b dadi sai nace tayi hakuri har ranar d Allah zai tona mata asiri,sai tace min wannan wace irin masiface, hakuri nake kara bata tare d kawo mata misali da Allah yana fada cikin littafinsa mai girma cewa *"Dasannu zamu jarrabeku da wani abu na dg tsoro d yunwa d tawaya ta dukiya d rayuka d 'yayan itacuwa, amma kuyi bishara d masu hakuri"* ko kuma *"Zakuce kunyi imani ne sannan kuce baxamu jarrabeku ba"* haka zanta bata hakuri d cewa jarrabawace dg Allah ita wannance jarrabawar d akai mata idan tai hkri zataga sakayya a gaba kamar yadda Allah yace *Yaku wadanda kukai imani kuyi hakuri kuyi juriya kuyi dako (ma'ana ku jira sakanakon d Allah zaiyi)"* dan hk kowane bawa d akwai gwargwadon ydd ake jarabtarsa a duniya, wani iya wahalar da yasha adunia zata zamemasa sauki d rangwame ranar lahira, wani a saka masa tin aduniya wani kuma a barshi sai ranar hisabi, dan annabin rahma yace *"Idan Allah y nufi bawansa d alkairi saiya gaggauta yimasa azaba a duniya idan kuma yaso saiya kyaleshi d zunibinsa har xuwa ranar alkiyana."* hakadai zanta bata hakuri d kalamai mai nutsar d zuciya nace mubarwa Allah zai saka mata,kuma kowane abu yana da iyakarsa kmr yadda annabi yace a hadisi *"……………Hakika kowane abu akwai lokacin da aka iyakance masa dan hk kuyi hakuri ku nemi lada.………"* take zanga fuskarta ta bayyanar d nishadi d annashuwa. Haka zamuci gaba d hira cikin jin dadi d nisha lokacin d nake cewa d ita insha Allah wannan jarrabawar alkairice a gareta tace kamarya wahala zata zama alkairi ga bawa nace saboda annabi saw yace *"Duk wanda Allah yake nufinsa d alkairi saiya dora masa wata larura."* ko kuma ta zama makankarin laifin d yake aikatawa kamar yadda annabi saw yace *" Duk abin d yasamu mumini na wahala kona cuta kona damuwa kona bakin ciki kona cutarwa kona bacin rai harta kayar d ya takata har sai Allah y gafarta masa zunubansa da ita."* sanda n karantaw ummana wannan hadisin sai tacemin amma wata jarrabawar d akewa bawa tana tsanani a gareshi sai nake cewa d ita babu wata jarrabawa d xata zamo mai tsanani g bawa kuma Allah baya jarabtar mutumin d bayaso kinga kuwa b kowa Allah yake gwada imaninsa b sai bawa n kwarai tinda manzon Allah saw yace *"Hakika mafi girman sakamako yana tare d girman bala'i,lallai Allah madaukakin sarki idan yana son mutanensa saiya jarabcesu, duk wnda ya yarda d wnn jarrabawar Allah y yarda dashi hk duk wnda yai fishi akan jarabawar Allah zai fishi dashi."* kawai sai naga ummana tana kuka saboda jin wannan hadisi tan rungumeni tana cewa jarrabawar d Allah yaimin kenan y hadani zama d azzalumar mata, ya Allah ka bamu ikon hakuri akan dukka musibar d zata samemu ka kuma bamu ikon cin jarrabawar d kai mana, gaba dayanmu da muke sauraron sarah muka hada baki mukace amin. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 6 *Ayushailiasu.blogspot.com* Page 81 to 85 Haka muka zauna a kurkuku tsahon wata biyar batare d ko saudaya wani yazo ya ganmu ba kamar yadda ake zuwawa sauran yan kurkukun,ummana saida tai wata cuta kamar baxa tai raiba, shugaban gidan kurkukun yasa aka fadawa abbanmu amma yaki zuwa haka takaraci ciwonta har Allah y bata lafiya. Tsananin adduar da mukeyi ne ya sa wata ranar juma'a d misalin karfe 3:00 na rana abbanmu yazo yai umarni da a sakemu, bayan munfito dg kurkukun azatanmu tare d abbanmu zamu tafi gida sai mukaji yana cewa karmu sake mu dosarmasa gidinshi duk inda zamuje mutafi amma banda gidanshi, ummana kasa magana tai saini nai karfin halin cewa yanzu abba idan ummana tana d inda zataje ta tafi gidansu aini 'yarka ce ina zanje, abinda yafito dg bakinshi sai cewa yai nashiga duniya mana, bansan lokacin dana fadi a gurinba ashe suma nayi, yana gani nasuma ya juya yai tafiyarsa ya barmu a gurin, bayan na farfado ne ummana tace mutafi gidansu,haka muka kama hanya a kafa muna ta tafiya har mukaje. Dakyar dangin ummanna suka yadda muka zauna agidan,sakakon ammi duk tayi asiri ta rabamu dasu, wani daki dake hanyar kofar gida suka bamu ko kofa babu sukace anan zamu zauna bamu d zabi illah zama a cikinsa dan idan ba hakaba bamuda inda zamu,,bayan fitowarmu dg kurkuku da kwana goma ne ummana ta kwanta ciwo ashe ciwon ajaline bazata tashiba, amma duk gidan babu wanda zai leko ya dubata ni kadai naita dawainiya d ita,idan tana ninfashi kirjinta yaita bugawa kamar zuciyarta zata fito,lokacin da sa'i yai take cemin sarah kiyi hakuri da duk halin d xaki tsinci kanki a ciki ki rike gaskiya d amana a duk inda kike karki yadda ki cutar da wani dan ni tawa takare baxan tashiba,dan haka nake miki fatan alkairi Allah yai albarka a rayuwarki, tana kaiwa nan naji tayi salati shikenan ashewai ta mutu, kuka na rusa ina ambaton Allah, jin kukan d nake yine yasanya mutan gidan zuwa inda nake suna tambayata lafiya, gawar ummana n nuna musu suka karasa inda take bayan sun tabbatar tamutune suke cewa ai gara haka sun huta d jaraba dunguremin kai sukeyi suna cewa nima dole nabar gidan dan baxan zauna ba basu barni d radadin mutuwa b suka dinga fadamin maganganun da sukaga dama. Bayan anyi sadakar uku ne yayan ummana yace nabar masa gidansa ba yadda n iya haka fito batare danasan inda zaniba tafiya kawai nake saida naga dare yayi nasamu wani kango nashiga saida nai kwana biyu acikinsa ba ci basha. A bangaren ammi kuwa batasan abbanmu yasa anfito damu dg kurkuku b saida taji labarin mutuwar ummanmu sannan tasan anfiti damu, haka da taji labarin yayan ummana ya koreni farin ciki kamar y kasheta, gida ya dawo dg ita sai yarta koshi abbanmu bashida katabus a cikin gidan sai dai ita. Tsananin yunwar da t dameni ne yasanya nafito dg cikin kangon ko Allah zaisa nasami abinda zansa a bakina,wani gida dake dan nesa d kangon nashiga danyin bara,nayi sa'a mai wanke wanken gidam t hado kayan wnke wnken zatayi rokarta nashigayi ta taimakamin d ragowar abincin d akaci aka rage a wani kwano,da tai kmr bazata baniba saidai t mikomin, sabida da ka ganni kaga siffar mahaukaciya dan nagama fita a hayyacina sbd yunwa d kishir ruwa,d hanzari n karba na koma gefe n rakube nafaraci,daidai lokacin d nakai wata loma bakina ne yai daidai d fitowar mai gidan daga ckn gidan ganin ydd nake cin abincin hannu baka hannu kwarya ne yasashi tsayawa yana kallona,niko kallanshi ban karayiba nacigaba daci saida n gama natashi n mikawa mai wnke wnken kwanon takarba, bakin famfon gurin n karasa n kafa kaina nasha ruwa sannan naimata godiya, na juya zan tafine naji wannan maigidan yana cewa ke yarinyar nan nidai banjuyaba saida yasa mai wanke wnken tabiyoni ta kirana. Karasawa mai gurin d yake tsaye n rissina na gaidashi d mamaki ya amsamin yazata ko mahaukaciya ce, tambayata yashigayi meyasa na shigo masa gida nan na zayyanamasa labarina ya tausayan sosae saida ya zuvar d hawaye,lokacin da namike zan tafi y hanani tafiya, gurin matansa y kaini suma sun tausaya min, take yaiwa mai wnke wnken umarni da muxauna tare a dakinta, ta amsa mada d to alhji batare d tamusa nasaba. *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Ayushailiasu.blogsopt.com Ayushailiasu.blogspot.com Ayushailiasu.blogspot.com Ayushailiasu.blogspot.com Ayushailiasu.blogspot.com Ayushailiasu.blogspot.com Ayushailiasu.blogspot.com Ayushailiasu.blogspot.com [12/8, 8:51 AM] Ayusha iliasu: *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *Ayushailiasu.blogspot.com* Page 86 to 90 Rayuwa mai cike d jin dadi d nusha d annashuwa n tsinci kaina a gidan wannan alhjin,duk safiya zanje n gaidashi d iyalensa sannan nadawo gurin iya ladi (mai wnke wnken gidan) na tayata aikace aikace idan tana wanke wanke zan mata sharar gidan sannan naje na tayata daurayar,sbd yawansa bata gamawa d wari,hk dai zanta taimaka mata d wasu ayyukan d tasaba yi sbd dadin zaman d nakeji d ita, bata taba yimin iyaka akan kayanta ba ko me zai tabashi kaina tsaye, suko matan gidan dg gaisuwa bana kara komawa gurinsu sai wata safiyar dan gudun fitina ko janyo magana shiyasa bana komawa. Haka yaran gidan muka saba dasu sosae dayake a gurin iya ladi suke wuni in sundawo dg makaranta inko kaga sunbar dakin iya ladi saidai malamin d yake musu lesson ko wand yake koya musu karatun addinine yazo amma haka zamuyita wasa d dariya dasu suna bani girma yadd yakamata, haka idan naji suna karatun kur'ani sun fadi wani gurin b daidaiba zan gyara musu har t Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 7 kawo suna cewa n biya musu, haka zan karanta musu har sai sun iya shi kanshi malamin mamaki yadda suke iya karatuna nan danan yake b kamat shi dazaita nanatamusu b kafin su iya,alhji d matansa b karamin jin dadi sukai d hakanba. Ranar weekend d safe naje gaidasu kamar yadda nasaba kullin, bayan mungaisa ne alhjin yake cewa na baro dakin iya ladi dawo cikin gidan d zama km lokacin yake tambayata ajina nawa km wace makaranta nakeyi dan yanaso zai kaini makaranta,na fadamasa ajin d nake d sunan makarantar yace insha Allah monday mai zuwa zanfara zuwa , godiya nashiga yimasa b kakkautawa harsaida yace ya isa haka tamkar yar d yahaifa y daukeni. Haka zamana yaci gaba d kasancewa cikin iyalin alhjin cikin jin ddi, ashe sharrin ammi bazai daina bibiyata ba katsam watarana nawayi gari yaran gidan suka fara min rashin kunya tafi tafi takai gasuna zagina batare d naimusu komaiba, tin iyayensu n tsawatar musu har suka daina tsawatar musu ya zamo suma d kansu zagina suke d hantara ta b yadda zanyi saidai nai hakuri naita kuka, itama iya ladi idan taganni nafito waje ina kuka ko kallona batayi balle ta tambayeni dalilin kukan d nake, gori d cin mutunci kuwa ba wanda matan gidan d yayansu basayimin saidai in shiga daki naita kuka, amma duk wannan abun alhajin baisani b km ban taba tararsa nafada masaba sbd nasan duk sharrin matar ubane yake bibiyata b laifinsu bane. Wata rana d daddare alhajin bayanan ina zaune a daki ina tunanin kuncin rayuwar d nake ciki ne naji an turo kofa anshigo ko sallama babu daga kai nai dan ganin waye muka hada ido d matan alhji komar d kaina nai kasa naji sun fincikoni sun rufeni d duka batarr da nasan laifin d naiba, saida suka gama dukana sannan suka koroni waje suna cewa n barmusu gidan b irin hakurin d banbasuba sukaki hakura suks dankado ni nafadi d sauri n mike nacigaba d basu hakuri amma sukaki har kofar gida suka rakoni bayan nafito inaji suna cewa mun huta d masifa suka sa sakata, kuka naci gaba dayi ganin babu mafita gashi lkcn karfe 10:30 tawuce n dare ne yasa nace innalillahi w inna ilaihir……………… wannan itace duniya dama? Haka ashe dama duniyar take? Inata tambayar kaina ina kuke, ganin dare na karayine yasanya na nifo hanya nafito titi naketa tafiya batare d nasan inda zani ba shine ka ganni ka tsaya,lokacin d kace n shigo motarka naki ne dan na gwammace n shiga duniya dan nasan kaidin kishiyar uwa bazai daina bibiyata duk inda naje zaa koreni,amma ganin k takuran ne yasa nashiga har k kawoni nan gidan naka. Sautin kukane ya cika palon baga hajiya b baga alhi baga su sumayyaba ba gani ayusha b balle uwa uba sarah d take fadin dan Allah karku koreni. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *Ayushailiasu.blogspot.com* Page 91 to 95 B wanda y kara magana tsawon wani lokaci a palon, alhji yusuf yana son yai magana saidai ko yayi b wanda zaiji sakamakon sautin kukan d ke tashi haka y hakura har tsawon wani lokaci, jin sautin kukan y sarara ne y sanya alhji yusuf yin ajiyar zuciya gami d gyaran murya yace hakika sarah kina cikin kuncin rayuwa amma nayi miki alkawarin zan taimakeki kmr yadda Allah y taimakeni kuma xan rikeki gwargwadon yadda Allah yabani iko zan rikeki duk tsanani baxan bari kibar hannuna ba dan haka kiyi hakuri ki share hawayenki zan zame miki uba ,ga hajiya nasan zata rikeki tamkar yar d ta haifa dukkan wata dawainiya d uba zaiwa yarsa nadau nauyi saidai nai fatan Allah ya dafamin kuma ya cika min burina akanki, amin hajiya tace, wani farinciki ne ya kaiwa zuciyar sarah ziyara da batasan lokacin d ta taso takaraso inda alhji yusuf yake xaune b,durkusawa tai daf dashi ta shiga kwararo masa kalmomin godiya cikin kuka wanda ita kanta baxata iya hakikance na meyeba. Duk mutanen d suke palon kasa maga sukai b abinda sukeyi illa jimamin labarin sarah, maganar d alhji yaci gaba dayi ce ta dan dawo musu d hankalinsu kanshi lokacin daya nuna hajiya d hannu yace hajiya g amanar sarah nan na dankata a hannunki daidai da rana daya kikaci amanarta amana zata ciki kuma kisani Allah bazai barkiba, hajiya tai murmushi gami dacewa insha Allah alhji zan riketa amana kamar yadda kabani kuma kamar yar da nahaifa saidai katayani da adduar Allah ya bani iko, alhjin ne yace to Allah yabaki iko gabadaya sukace amin,kauda dubansa yai kan sumayya d surayya yace kukuma g sarah nan inason ku dauketa tamkar uwa daya uba daya banda nuna banbanci banda fada kuma ban yadda wani ya tason da abu kwaya daya dg cikin labarin da tabamuba, kuma wallahi duk sanda naji wani dg cikinku yai mata rashin kyautawa zan saba masa fiye d yadda baya zato, sudai kansu na kasa sunajin duk abinda abban nasu yake fadamusu batare da sum dago kai sun kalleshiba saida ya daka musu tsawa t hanyar cewa ko badaku nake ba? a tsorace suka dago sukace munji abba km insha Allah zamu kiyaye, Allah yai muku albarka ya hade kanku yace sukace amin, tasowa sukai suka karaso inda sarah ke zaune tana sharar hawaye rungumeta sukai suna nuna mata kauna tajini a gaban iyayensu, dadi d farincikin d sarah taji yasa ta kankamesu tana kara kokawa kanta, sha'awa yaran suka baiwa mahaifin nasu y gama tabbatarwa bazasu bashi kunya b wajen kyautata mu'amalarsu d sarah nan take y kara samusu albarka. Nasiha mai ratsa jiki alhji yusuf ya kara yiwa sarah kan hakuri d duk halin d ta tsinci rayuwarta tare d yimata addua Allah y kareta daga sharrin ammi idan tana d rabo kuma Allah y shiryar da ita idan kuma bata d rabo Allah yai maganinta, hakika sarah taji dadin wannan nasihar d adduar dan kasa magana tayi saidai kuka kawai, sanna alhjin ya kara d yiwa iyalinsa nasiha d gargadi akan zamansu da sarah. Bayan yagama nasihar ne y cewa sarah,adan tsorace ta amsa masa d na'am abba yace a wace unguwa kike kuma zaki gane gidanku? gaban sarah ne ya yanke y fadi dataji haka saida tai jimmm sanna ta ce eh zangane kuma a shagari quarters ne, yace to alhmdllh bamuda nisa ma ashe soase yakamata idan ankwana biyu muje kikaimu mugani,kuka mai tsanani sarah tasaka tana cewa abba dan Allah karka maidani gidan abbanmu wallhi ammi kasheni zatai kamar yadda takashe khalid, tausayi tabashi yace ba maidake zanyiba zamuje dai mugani ne saboda gaba kuma ba shiga zamuyiba kawai nuna mana gidan zakiya dan yadace musani ko bahaka b hajiya? Eh hakane kam hajiya tace, jin alhjin yafadi haka ne d sauri sarah tace to abba zan nuna muku,yace to Allah y kaimu ranar d zamuje sukace amin. Yinin wannan ranar gidan ba wani walwala kowa tuna labarin sarah yakeyi a zuciyarsa, bangaren sarah kuwa farinciki takeji kamar ranar ta diro duniya musamman idan ta tuna d alkawarin da alhji yusuf yai mata nazai riketa d gaskiya kamar 'yar da ya haifa acikinsa, haka idan ta tuna gargadin d yaiwa iyalishi akanta na zamowa tsintsiya madauri daya da kaunar da yayansa suka nuna mata a zahiri, haka taita nishidi tana godiya g Allah da yasa zatai rayuwar gidan alhji yusuf.tamkar t taka rawa Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 8 *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *Ayushailiasu.blogspot.com* Page 96 to 100 Rayuwar d sarah bata taba tinanin zata samu a duniya b ta tsinci kanta aciki sakamakon xamanta a gidan alhji yusuf yadda take samun kulawa a gurin hajiya dasu sumayya abin baa magana saidai fatan Allah y saka mus d alkairi y tsare wata fitina d zata afku a tsakaninsu. Yau d safe ne su sumy suka shirya cikin uniform kamar ydd suka saba a rakanakun makaranta, kare musu kallo sarah tai na dg kwance akan gado tace sisters gsky uniform dinnan yai muku kyau dan hararar wasa sury t jefa mata cikin dariya tace banda tsokana fa tace Allah kedai baki ganiba dan matsa kusa d mirror ki ganki kinfi kyau dashi akan other wears sumy dake tsaye a gefe tana kallonsu tana murmushi batare da tace komaiba kasancewarta batada magana hk km yadda sury d sarah suka shaku b kamar itaba,dariya sury t saki tace gskiya sis sarah akwaiki d zolaya ina wani kyau a uniform dan bakisan yadda nagaji da sasuba ne wllh ni d abba zai yadda aimin double promotion na koma SS 2 da zanyi murna,kallanta sama d kasa sumy tai tana tabe baki tace tabb amma bakida hankali sury dallah malama zomu wuce karmuyi latti ta janyota suka fito dg dakin. Dining suka nufa danyin breakfast bayan sun kammala ne suka nufi dakin mama dan yimata sallama,suna shiga suka kara gaisheta ta amsa gami d cewa ina yar uwar taku dftn tare kukai break din? Tana daki tace sai anjima zatai tace to, sallama sukaiwa mama,tace to yayan mama adawo lafiya Allah y bada ilimi mai amfani amin sukace suka fita d hanzari. Misalin 8:30 na safe sarah t tashi tana mika alamar bataso tashi dg bccin ba saboda yai mata dadi saidan lokaci da taga yaja duk d tasan mama bazata tasheta b koda zatakai karfe daya, toilet ta fada d sauri tai wanka sannan tai brush ta fito,cikin sauri tai simple make up b wani mai yawaba dg powder, lips gloss d eyes liner tasa, wata gown yellow colour tasa ta amshi jikinta ta daura black head sbd design din jikin rigar d black stones akayishi, kallo daya zakai mata kasan ta hadu,futowa tai cikin nutsuwa tana tafiya tamkar wahainiya, straight dining t nufa ta zauna ta fara hada abin d xatai breakfast,a hankali take cin abinci har ta kammala sannan ta hada kayan d aka bata n kan dining din ta kai kitchen dan wankesu sbd ta saba tin d tasake a gidan kamar gidansu ita takeyin wanke wanke d sharar palo d moppin sannan ta koma dakinsu ta share ta gyara musu gado idan zaa canja bedsheet t canja sannan t gyara musu toilet dinsu, idan t gama wanna ayyukan km ta kamawa mama aikin girki tana wancan ita tana wannan, hk xatai ta tayata aikace aikacen gida har sai su sury sun dawo dg schl sannan su zauna hira km kfn su tafi islamiyya kasancewar ita bata zuwa makaranta. Kammala wanke wanken tai ta fito domin gyara palon sukai ido hudu d abba d sauri ta sunkuyar d kai ta rissina tace abba barka da asuba, fuskarshi dauke d faraa yace barka dai yar mama ina fata kinajin dadin zama damu? Murmushi sarah tai wanda saida dimple d wushiryarta suka bayyana tace sosaima abba yace haka akeso ai,mikewa tai tace adawo lafiya tare da karasawa inda xata dakko tsintsiyar, kallon mama dake biye da shi yai yace gaskiya uwar gida ran gida kin iya kula d yarnan taki Allah ya saka,dariya mama tayi tace zaka fara zolayarne shima dariyar yai tare d cewa zolaya ko gaskiya tace zolayar dai murmushi ya sakar mata mai dauke d sakonni daban daban yace ni natafi to,kashe masa ido tai gami d maida mishi d martani tace adawo lafiya Allah ya tsaremin kai ya bada kasuwa mai albarka yace amin amin shiyasa nake kara sonki tawan. Ni ayusha d nake gefe ina satar kallonsu nace kaga tsofaffin ma'aurata suma wai sun iya soyayya dan nasan badan sarah dake karkade kan kujerun palon xata fara shara b har kissin n huggin abba zaiwa mama yadda naga ta kasheshi d idanunwanta tai masa kallo mai cike d soyayya karara lolllllll. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *Ayushailiasu.blogspot.com* Page 111 to 115 Kullum su sury suka shirya zasu tafi makaranta sarah sai taji dama itama tana zuwa saidai baxata iya tarar abba ta fadamasa ba haka idan suna hira d su sury bata taba nuna musu tana d shaawar komawa ba, tasan indai ta bincina musu zasu fadawa abbansu km wane irin kallo zai mata n mara hakuri ko na me haka ta hakura sai wata rana d safe bayan ya shirya zai tafi kasuwa , yakirata yake tambayarta a aji nawa take yanson ya bincika mata makaranta dan bazatai ta zama haka ba yan uwanta suna tafiya ,dadi ne ya cika sarah a wannan rana jira kawai take su sury su dawo ta labarta musu, suna shigowa gida ko uniform bata bari sun cireba t baxa musu labari kmr wdd aka biyawa makka nan suka cika gida d shewa kamar zararru. Zaune suke suna hira a palo byn sallahr isha, sury d sarah na kujera daya sun hada kai suna kuskus wanda koni banace ga abinda suke fadaba,maganar d abba yaice ta dakatar dasu dg hirar da sukeyi yace yayan mama hadakan me akai ne haka baason muji abinda ake fade yar dariya sukai tare d cewa abba secret ne, jinjina kai mama tai tace kwaji da gulmarku dai abba ya ce idan tai wari maji gabadaya palon yadau sautin dariya. Abban ne yace sarah ta kalleshi kafin ta amsa ya kara d cewa end of d week xaki fara zuwa schl dan naje nayi miki registration, murna d frnciki ne suka cika sarah taimasa godiya d cewa Allah y kaimu yace amin ammafa bordin schl ce yafadi haka ne danya tsokani sury tinda y fusksnci batason suyi nesa d juna, yar halak maradinta baya kunya, kuwa a tsorace sury ta kallai abba cikin shagwaba d marairaicewa tace plxx abba karka kaita bordin schl sai kwalla shaaaa, itama sarah bataji dadin cewa bordin zaa kaita b, saidai kawai ta danne ne ba yadda zatai ina yar karere ina zabi,dafa sury tai tace sowiee swit sister don't worry ai muna tare ko kin manta abin a jini yake? dariya mama d abbah suka kwashe d ita sannan abba yace oh!!! dama n gwada Ki ne naga reaction dinku, in kunyi murna nace to ashe bakwason zama d yar tawa d sauri sury tace haba abba harnaji dadi wllh to wace schl xatafara xuwa? abba yace nan SHEIKH BASHYR EL RAYYA SCHOOL tinda naga yar tawa ta hada boko d arabic ko ina b damace a fannin km kinga schl din 2 section ce,godiya suka karayiwa abba sumy dake gefe tana kallonsu tana dan tabe baki sai lokacin tai magana, amma rashin maganarta bai batawa abba d mama raiba sbd sunsan halin yar tasu miskilace wadda tafi mahaukaci ban haushi. Sury d sarah ne suka tashi dg palon rike d hannun juna sukace abba mama Gus nyt ,iyayen suka amsa musu da Allah y tashemu lafiya amin suka ce suka wuce dakinsu batare da sunbi takan wata sumy ba tinda sarah dm ta fiskanceta miskilace bata fiya kulataba. *AFTER TWO MONTHS* Wasa-wasa sarah angama zama yar gida komai zatai a gidan kanta tsaye takeyi batare d shakkaba,yadda takewa mama d abba biyayya d girmamawa tamkar iyayenta tadau alkawarin zatai duk abinda suka umarceta komai wahalarsa muddin bai sabawa umarnin Allah d mamxonsa b. Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 9 Abba yatara dukkan yayansa da ke gidan miji ya gargadesu akan zama da sarah su dauketa tsintsiya madauri daya karya sake yaji wata magana wadda zata sosa ran sarah kuma Alhmdllh kasamcewarsu yaya masu biyayya sunji maganarsa kuma sun daukar mishi alkawarin hakan. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *Ayushailiasu.blogspot.com* Page 116 to 110 Kwanci tashi b wuya gurin Allah d fara zuwa makarantar sarah har yau zaai hutun karshen zangon karatu n biyu (2nd term),bayan driver y sauke su sury a schl ne ya zarce ya kai sarah itama tinda b schl daya sukeyiba dg nan yadau hanyar garin gwarzo dan dakko su abdullah suma. Haka shima kamal (wato dan kanwar abba d ta mutu) yau zai dawo dan sun sami hutun 2nd semester. Tinda su sumy d sury sukaji yau yaya kamal zai dawo suketa murna dan sun dade basu ganshib,sarah ma d labarinsa ya zame mata jiki son ganinsa takeyi dan kullin in suna hira d sury ta ringa bata labarinsa kenan har sai taji ya isheta. Shirye shieye mama take tayi tinda garin Allah y waye sbd ranar jumaa ce lokaci saurin yi yake,hk taita faman aikace aikace ta dafa wancan ta sauke ta dora wancan, abunci d abinsha kala kala tayi dan tarbar yayan nata musamman auta da take mutukar kewarsa,karfe 11:00 n safe ta kamma komai ta jerasu a saman dining. Wanka tashiga tayi byn tafito ta zauna tayi kwalliyar ta daidai ydd tasabayi, wata green din super Sheraton tasaka tare d fashion din sarka d dankunne d abin hannu,kai d kaganta kasan tana jin dadi yadda kalar fatarta ta nuna kasam b karamar cima takeyiva dan gaskiya tayi kyau mutuka. Palo tafito ta zauna dan jiran yayanta, bata fi minti 10 d xamaba su sury suka shigo, d gudu suka karasa inda take suna fadin wowwww mama kinyi kyau gaskiya bamu taba ganin kinyi kwalliya kamar yauba, dariya mama tayi tace kuko auta zai dawo dole nai kyau ai,kuje dining ma kuga abinda n shirya masa, sumy sarkin kishi xunguro baki tai tace gsky mama kinfison auta da mu to ai muma yau yaya kamal dinmu zai dawo kuma nice zan masa delicious dishes d ginger lemon nasan yana sonsa,yar dariya mama tayi tace Allah y taimaka, amin sukace gami d tashi su nufi dakinsu. Suna shiga a zatonsu zasuga sarah ta rigasu dawowa tinda yau b driver bane yaje y dakkosu sukaga ba ita b alamarta d sauri sury t fito tana kwallawa mama dake palo a zaune kira, mama……mama……,atsorace mama tace lafiya kike kurmamin kira haka kmr makauniya? Kara kiranta ta sakeyi mama ina sistr sarah? Dan tsaki mama tayi mtswww tace kefa dadina dake har yanzu bakida hankali baxaki karaso inda nake ki tmbyeni b saiki ringa kwalan kira haka to bansani b, marairaicewa sury tai tace plxx sorry my mum,kallonta mama tayi tace tinda ke har yanxu baxaki hankaliba shikenan tana rufe bakinta sarah tai sallama, dagudu sury t karasa tarungumeta tana tsalle gami d cewa wllh sistr sarah yanzu nake tmbyr mama kindawo shine tacemin bata saniba t karasa maganar d turo baki (kujimin yarinta d wauta irinta sury ai sai sarah tace dama mama batason t dawo ) basar da zancen sarah tai ta janyo hannun sury suka karasa inda mama take xaune tayi wiki wiki d idanuwa tana jimamin wauta da rashin hankalin sury,sarah ce tace sannu d aiki mama, akasalance ta amsa da yawwa sarah andawo lafiya tace lafiyalau,masha Allah mama tace gami d cewa maxa aje ashirya dan yau kunsan muna d manyan baki, to sukace suka kwasa d gudu sukai dakinsi. Wanka kowaccensu tasakeyi sannan suka fara kwalliya, ganin ydd sarah ke tsantsala kwalliya ne yasa sury cewa tabb wllh sistr ke zakimin kwalliya nima,kallonta sarah tai sannan ta maida dubanta kan sumy tace kalli inda ake kwalliya can gun sumy kamar meenat make over,harara sumy ta watsa wa sarahtace ni sa'arku ce karku kara sakoni a zancenku,( kaga su sumy manya harda tsare gida bayan sarah ta girme mata wai a lallai ita batason raini) murmishi sarah tai n mugunta dama tana sane tafadi haka dan kwalliyar ko alamar kyau bataiba tace Allah y baiwa manya hakuri sury batasan lokacin d dariya ta subuce mata b tace tonidai taki nakeso tare d tashi ta fada toilet ta wanko fuskarta. Shiri tsaf y kammala a bangaran su sumy inda sury tasa wata atampha dinkin skirt d riga masha Allah sunmata kyau, sumy km wani material tasa itama skirt d riga b laifi sunyi mata kyau, ita kuwa hajiyar kyau wato sarah wrapper zani d riga n atampha tasa, kallo daya batare d ka karaba zakasan ta hadu koda baa fadaba, palo suka fito suka yiwa kansu mazauni kusa d mamansu, ita kuwa hajiya miskila waro sumy kitchen aka nufa aka fara kiciniyar girkin d xaa birge yaya kamal. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *Ayushailiasu.blogspot.com* Page 121 to 125 Kallon agogon dake maqale a palon mama tayi tace ya akai har yanzu su Abdullah basu dawoba gashi har 1:00 tayi, sury tace gaskiya mama sun dade Allah yasa lafiya dai ba mota ce t lalace musuba,amin sukace gaba dayansu harda sumy da taho dg kitchen,mama tace badai har anga girkinba tace eh,sury tace no wonder shiyasa naji aroma ya cika gidan t karasa maganar tana mata gwalo alamar tsokana, tsaki sumy tayi mtswwwww aikin banza mutum sai shishshigi kawai to ko a harshenki bazaki dan danaba,dariya sury tayi tace aikuwa mutum bai isaba dole naci,sumy tace to basai kici,da gudu sury ta mike ta nufi dining tana cewa bari ma n dandana naji bayanta sumy tabi a fusace tana cewa kinganta ko mama, itadai mama batai musu magana b balle sarah da take jinsu b tace musu qala tinda dama b wani shiri sosae sukeyi d sumy ba. Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 10 Misalin karfe 1:30 driver yai parkin a farfajiyar gidan, da gudu su abdullah suka fito suka fada cikin gida, mama dake zaune batai auneba sai jitai sun fado mata a jiki sun kankameta, itama murnar ganinsu yasa t rungume yayan nata cike d farincikin ganinsu tana yimusu sannu d xuwa, bala driver ne yai sallama rike d akwatinansu a hannunsa, ajiyesu yai dg byn kujera gami d rissinawa y gaida mama,amsa masa tai tare d yimasa sannu d kokari,yawwa sannu y amasa mata tare d yimata sallama, da sauri mama ta dakatar dashi t hanyar cewa katsaya kaci abinci man,keya yadan shafa yace to hajiya,umartar sumy tayi d takawo masa abinci d ruwa.Hakika su sury sunyi murnar ganin yan uwan nasu hk sarah ita ma,ganin bakuwar fuska dasu abdullah sukai yasa su tambayar mama d cewa wace wannan? Mama tace sister din kuce tare d cewa kuje kuyi wanka maxa g delicious dishes can na shirya muku, rungume mama sukai sukace wowwww dats our momma ,mama shiyasa muke kara sonki mikewa sukai d gudu suka fada dakinsu d aka gyara musushi tas. Bayan su abdullah sunyi wanka suka nufi dining kujerar d mama take zaune akai auta mujahid yace lallai a kanta zai zauna dakyar t lallabashi t janyo masa wata kusa d ita ya zauna, bayan sunci sunsha cikin raha d barkwanci suka tashi kowa yaje y sauke farali. Dukkansu suna zaune a palo ba abinda su abdullah suke sai hirar rayuwar boardin schl dariya kawai su sarah ke kwasa , suna tsokanarsu d suna almajiran gwamnati saida mujahid yakusa kuka sannan suka daina tsokanarsu dan mama na daki balle t tsawatar musu,sukaci gaba d hirarsu cike d nishadi, sallamar d sukaji anyine ya maida hankalinsu bakin kofa dan ganin mai sallamar, ido hudu sukai d yaya kamal gaba dayansu suka tashi d gudu suka rungumeshi sunai masa sannu d xuwa, sarah kuwa kallonsu kawai takeyi tana dg zaune. Yaya kamal da aka cukuikuye anai masa oyoyoyo gaba daya hankalinsa baya kan su mujahid,abdullah, sury d sumy, ya tattare hankalinsa baki daya kan sarah d take zaune ya shagala d kallon ta, ita kuwa bama tasan yanai ba dan tinda suka hada ido dashi t kauda kallonta dg gareshi,sumy ce tace yaya kamal wai me kake kallone munata yimaka oyoyo? A dan tsorace y dawo d hankalisa garesu tare d janyosu suka karaso palon suka zauna, baibayeshi sukai suna taimasa surutu chakaiii……… chakaiiii……… chakaiiii……… Sarah dake gefece tace sannu d xuwa yaya kamal, jin zazzakar muryar yai kmr a mafarki ne yasashi jin wani zarrrrr a ckn jininsa a sanyaye y amsa mata,shafo kan mujahid yai batare d ya dauke idonsa dg kan sarah b yace autan mama ina maman taka ne? Tana daki yace,suko su sumy d suka shagala d murnar ganin yayan nasu basu lura d yanayin kallon d kamal kewa sarah b,kamo hannun mujahid kamal yai ya kalli su sumy yace bari na karasa mu gaisa d mama ko y karasa maganar yana tafiya sumy tace yawwa yaya in kun gaisa kazo kaga delicious dishes din d naimaka yace thank u my sumy shiyasa naji kamshi y cika gidan tinkan naci nasan yayi taste dariya sumy tai tace saima kaci kaji yaya,daga mata gira yayi yace ko? Yeah tace yace ok ya shige dakin mama rike d hannun mujahid. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *Ayushailiasu.blogspot.com* Page 126 to 130 Tinda yaya kamal yai tozali d sarah yakasa gane wane irin abu zuciyarsa ke saka masa gaba daya tinaninsa ya koma kanta gashi baisan ita wace ba amma zuciyarsa ta addabeshi d tinaninta ya kasa tantanceshi kuma,yana zaune a dining amma abincin d yakecima kawai ci yake yana hararo kyakkyawar surar sarar, ajiye spoon din hannunsa yayi akan plate ya dau cup y zuba juice,lokacin d yakai bakinsa y saki wani tattausan smillin shi kadai sannan y kurbi juice din. Bayan y kammala cin abincin y watsa ruwa ne yace d su mujahid su shirya zasu fita su dan zaga gari, murna gurinsu mujahida kamar me ,nan da nan suka shirya sukaiwa mama sallama,sunkai dai dai kofa sumy tace yaya kamal ina zuwa? Yace zamu dan zaga garine, cikin shagwaba tace plxx yaya nima zanje,kallonta yai yana murmishi yace srry sistr we will b back soon insha Allah yaja hannunsu mujahid suka fice suka barta saroro tsaye a gurin. Da yamma sakaliya bayan abbah y dawo dg kasuwa yana zaune a palo suna hira da mama yake cewa kinga yaran nan har yanxu basu dawo ba sun shiga gari,mama tace aikuwa kaga shuru har yanxu, yace Allah y dawo dasu lafiya dai tace amin sukaci gaba d hirarsu. Ana kiran sallahr magriba yaya kamal dasu mujahid suka shigo lokacin abba ya tafi masallaci suma alwala sukai suka nufi masallacin. Suna zaune a palo ne byn anyi sallah isha,abba cikin murna d farin cikin ganin yayan nasa yake musu barka d dawowa d tanbayar ya karatu? cikin farin cikin ganin mahaifin nasu sukace alhmdllh tare d bashi labarin wahalar boarding, kallon tausayi abbah yaimusu yace aidama karatu sai hakuri dan haka ku kara hakuri d dagewa wajen karatu Allah yai muku albarka ya bada ilimi mai amfani gaba daya suka amsa d Amin harda kamal daya budo labule yashigo palon,karasowa yai y zauna kusa d abba y gaidashi,y amsa masa tare d tambayrsa ya karatu yace alhmdllh. Cigaba d hira sukai amma kwatakwata hankalin kamal baya kan hirar, dan gyara zama yayi yace inasu sumy ne bangansu b? Mujahid ne yace wllh yaya kamal suna daki danaje m koro ni aunty surayya tayi, abba ne yace je kiramin su d sauri ya tashi yanufi dakinsu, shiko kamal azuciyarsa murna yake yana cewa dama ina sane n tambayesu dan so nake na kara ganin wannan kyakkyawar halittar d ………… bai karasa zancen zucin d yake b suka shigo palon d sallama,sallamar d sukai ne t katseshi d sauri y dago kansa tare d sauke idonsa akan sarah,bayan sun xauna ne suka gaida abba d yaya kalam,abba yace kamal kaga munyi bakuwa ko? Dasauri ya amsa da eh wllh abba dg ina take? Nan abba ya fayyace masa matsayin sarah a gurinsa take kamal yaji tausayinta y mamaye masa zuciya. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 11 Page 136 to 140 Tinda yaya kamal y koma dakinsa b abinda yake hararowa sai kyan surar sarah a yanxu xuciyarsa ta gama tabbatar masa da lallaifa inba kallon tausayi kake mataba to kallon so kake mata, tinani yashiga yi to wane bangare n xuciyarsa xai bi? Furzar d iska yai dg bakinsa ya mike yake ta zagaye tsakar dakin hannunsa n makale a bayansa ya daga kansa sama sai sintiri yake yana kaiwa d kawowa a dakin, haka y kwashe tsawon mintina ashirin yana zazzagayawa bai samo amsar b, fitowa yai dg dakin ya nufi farfajiyar gidan dan hutawa. Sannu d fitowa abbah cewar sury d sarah da suke tsaye a bakin kitchen sun gama wanke wanke,kallonsu abba yai yace sannunku d aiki Allah yai muku albrk suka amsa d amin abba, cigaba d magana yai yace sarah ki shirya d yamma idan nadawo xamuje ki nuna mana gidanku, wani zar taji a cikin jininta saida tai jimmm kafin tayi magana sannan t nisa tace to abbah Allah y dawo dakai lafiya yace amin,cikin marairaicewa sury tace abba damu za'a yace a'a yasa kai yai waje. Tinda sarah taji batun zuwa nuna gidansu gaba daya kuzari yai kaura dg gareta zazzafan zazzabi taji yana neman kawo mata farmaki sbd tsabar tsoron d takeji n matar uba, ta ke taji tunanin kuncin rayuwar da tafada abaya yana dawo mata, gado ta nema t kwanta, tinda t kwanta b abinda take sai kwaranyar d zafaffun hawaye tsoronta Allah tsoronta kar aje acewa ammi anganta taje ta sake bunko mata asirin d zai rabata da wannan gidan,haka tai ta tinane- tinane ba ita t tashiba saida akai kiran sallahr azahar,toilet t shiga t dauro alwala ta gabatar d sallahr axahar sannan t jero nafila raka'a biyu, addua ta shiga jerowa tare d ambaton sunayen Allah tsarkaka d siffofinsa madaukaka akan Allah y tseratar da ita dg sharrin ammi ya makantar d ganinta dg kanta ya toshe kunnunwanta dg jin labarinta y daure kafafunta dg zuwa gurin boka. tadau lokaci tana jero addua gami d kamun kafa d Annani muhammad SAW afadar Allah sannan ta shafa,byn ta idar d sallahr saida t jima sannan t tashi ta fito palo gurinsu sumy. Hirar makarantar islamiyya su sumy suke amma sam sarah hankalinta baya kansu dan tuni jikinta yai la'asar ta gama tsinkewa d wannan tafiyar d abba ya bijiro mata d ita,abincin rana kasa cinsa tai sbd tinani ya cushe mata cikin, haka dai tai yinin wannan ranar b dadi,byn tayi sallahr laasar ne ta sake wanka d shiri karfe 4:30 n yamma daidai abba y dawo, shima shiga yai yasake shiri sannan ya ce tafito, yaya kamal shine yai driving abba yana seat din gaba mama d sarah d kuma auta mujahid suna seat din baya,kafin yaya kamal y tada mota abba yace d sarah tai directin din shi zuwa unguwar,tsaf tai masa saida abba y tabbatar kamal y gane sannan suka dau hanya sai shagari quarters,tinda suka fara tafiya b wanda yai magana shiko yaya kamal sai satar kallon sarah yake ta mirror,sarah kuwa batasan yanayi ba dan hankalinta baya jikinta ta tafi duniyar tinani wanda ni kaina bazance g irin tinanin d takeyiba ganin sun shiga lungunsu ne yasata yin wani gwauron ninfashi d ajiyar juciya k'wallace ta gangaro dg idonta kan kuncinta daidai lokacin sukai ido hudu d umma, kallo daya za kaiwa sarah ta baka tausayi, ninfasawa umma tai tace alhji kaga kuka takeyi d sauri ya juyo yace haba sarah kukan me kikeyi?cikin shasshshekar kuka tace wllh abba idan ammi t ganni saita sake yimin asiri kun koreni, tausayinta ne y mamaye zuciyar abba cikin tattausar murya yace insha Allah baxata ganki ba kuma nace miki ai b gidan zamu shiga ba kawai nuna mana zakiyi mu juyo,handkchf din dake hannun yaya kamal abba ya karba y mika wa sarah yace t share hawayen,kanshin tiraren jikin sane y xiyarci hancinta take taji wani sanyi a ranta, shiko yaya kamal xuciyarsa cike d tausayin sarah. Haka sukaci gaba d tafiya har suka isa kofar gidan,saida suka dan gota gidan kadan sannan sarah tace g gidan can t nuna musu shi d hannunta, gidane matsakaici n bulo yasha filasta d malale a kofar gidan anmasa milk din fenti atakaice gidan masu rufin asirine baxa'a ce gdn talakawa ba,sai da abba y tabbatar d nan ne gidan sannan suka juyo d motarsu suka dau hanyar komawa gida,ganin d sarah tai sun bar lungun ne yasa taji wani nishad'i a zuciyarta rufe fuskarta tayi d handkerchief din hannunta tana murmushi. Niko d nake biye dasu nace ikon Allah ashe akwai masu gudun mahaifarsu. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 141 to 145 Isowarsu gida yaya kamal yai parkin kowa y fito,bayan sun shiga ciki ne,yaya kamal y kwallawa mujahid kira yace yaje gurin sarah y karbo masa handkerchief dinsa yace to, d sauri mujahida y nufi dakin su sarah yace aunty sarah yaya kamal yace kibashi handkerchief dinsa ido suka hada d sumy d mamaki sumy tace meyakawo handkerchief din yaya kamal gunta a zuciyarta take maganar,kauda kai sarah tai dg kallon sumy ta mikwa mujahid badan tasoba dan baxata iyacewa y bar mataba gashi tana son kamshin turaren jikinsa,karba yai d sauri ya juya y kai masa. Tinda yaya kamal y karbi handkerchief din y shige daki b abinda yake illa san sanar sa yana kissin dinsa ynx y tabba xuciyarsa ta kamu d son sarah ji yai baxai iya wanke hawayen b sbd lipstick d tasanya a lebanta ya gogu a jikinsa yai alamun kiss tamkar ita yakewa ,tinani y shigayi ya xaiyi y isarwa zuciya sakonta zuwa wata zuciyar, zancen zuciya y shigayi yana cewa gashi gobe zan koma schl gaskiya baxan iya tafiya b tare d na bayyana wa sarah ina sonta b,wata zuciyar tace haba malam kayi azarbabi kavari ka dawo wani hutun mana lokacin ta kara wayewa d girma,banyi aune ba naga yaya kamal y daki side drower din gadon sa d karfi saida n dan tsorata afili yace what? yama zaai n bari saina dawo kafin lokacin kuma wani ya ganta sun kulla soyayya tinda bata san ina sonta b kuma nasan abba aura mata shi zaiyi indai tace tana son sa, kama habarsa yayi ya karasa maganar d tirkashi wannan babban lamarine, ya zan kamo bakin zarensa gashi gobe xan koma schl?. Ilailika dai,ka nemo kai kadai bada niba dan nayi nan ni. Tinda sarah tai sallahr isha ta haye gado taja blanket t rufa ba abinda takeyi sai tinano kamshin tiraren yaya kamal, tambayar kanta tashigayi dalilin meyasa nake son kamshinsa?xuciyarta tace t bata amsa d cewa sonshi kikeyi shiyasa kike son kamshin sa kuma duk lokacin d kuka hada ido dashi gabanki yake faduwa bakya kara kallonsa,lallausan murmushi tasaki saboda t amince d abinda xuciyarta tafada mata dan ta tabajin friends dinta suna hirar alamomin soyayya a schl kuma dg cikin abinda sike fade harda wadannan d ta tsinci kanta a ciki,gyara kwanciyarta tayi tai rigingine idonta a sama tana kallon fan din dake busa mata ni'imtacciyar iska,limshe idonta tayi game d sakin murmishi taci gaba d tunani karfa na fad'a tarkon son yaya kamal naje nashiga tasku shi baya sona,daga can barin zuciyarta tace mata dalla banza ke baki lura d abinda yake mikiba ne kamar b mace ba musamman idan kuka hada ido bakiga yanayin d yake miki d giraba gami d kashe ido to ai suma alamun nuna soyayya ne,wata muguwar k'ara naji sarah t saki ta juya ta rungume pillown d ta tada kai tace Alhmdllh indai hakane kuwa na dace d masoyi,kara rumgume pillown tayi gami d kissin dinsa tace I love u yaya kamal,rufe bakinta ke dawuya tana murmushi sury t shigo, dan dukan kafarta tayi tace mutuniyar smillin din me kike ne? ko kodai kodai……………? sbd sury ta gama karantar yaya kamal tsaf ya fada tarkon son sarah, harara sarah t watsa mata tace kodai me? Dariya sury tayi tace ba komai munacan muna jiranki a palo kinanan kina smillin ke kadai har yaya kamal yashigo yana tambayarki, dad'i ne y kama sarah d taji ta ambaci sunan abin sonta saidai t basar d zancen t hanyar cewa kyaji dashi dai suka topic n hirar. *BADAI KAFI SONTA BA* Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 12 *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 146 to 150 Yaya kamal ne kwance kan gadonsa yai d'ai-d'ai tinani yake yadda ya zaiyi y tari sarah d wannan maganar? haka yaita t sakawa d kuncewa baisamo mafitaba, gashi bai kara sa sarah a idonsa b balle yai yunkurin bayyana mata manufarsa ga km sammako zaiyi ya tafi,hk dai har bacci ya daukeshi. Bangaren sarah kuwa abin sharrr yake gwanin ban sha'awa dan baccinta tasha bil hakki ba tare d tinane tunane ba dan ta gama ydd da abinda zuciyarta ta shaida mata yaya kamal sonta yake. Yaya kamal ne cikin shirin tafiya makaranta fuskarsa a daure ya karaso cikin palon inda su abba suke xaune, rissinawa yai y gaidas,yanayin d abba yaga dan nasa y shigane yasanyashi tambayarsa meya faru naganka haka? ko bakason komawane kaji dadin gida?sakin fuskarshi yai yace bakomai abba bacci ne kawai a idon nawa shiyasa,d mamaki abba y sake kallonsa gami d dafa kansa yace haba son meya hanaka bacci? Kamal dai y kara bashi amsa d bakomai,fatan alkairi abba d mama sukai masa tare d adduar Allah y kaishi lafiya,amsawa yai d amin y mike jiki sakaka b kwari ya nufi kofa,saida yakai bakin kofar ya juyo yace mama inasu sumayya bamuyi sallama b? Kaji su yaya kamal d wayo dan yaga sarah ne y tambayesu fa mikewa mama tayi tace bari nakirasu to,dad'ine y kamashi zaiga abar begensa d sauri y karasa yin waje yana cewa a ransa sa biyoni yadda zanfi karewa dear ta kallo. Yana tsaye jikin motar abba suka karaso inda yake suka tsaya, face to face sukai d sarah wani dadi ne yaji kamar me ya dinga aika mata sakonni iri-iri, sundau lokaci suna hira idan yai yunkurin kiran sarah gefe ya sanar d ita bukatarsa sai km ya kasa sbd kunyar d yake d ita hakadai y hakura har sukai sallama sukai masa Allah y tsare hanya ya tafi. Abba ne y kalli umma yace hajiya anya yaron nan k'alau yake kuwa kinga yadda y fito fuska a daure? Umma tace nagani ko bayason tafiyar ne ko?oho dai abba yace ya kara da cewa koma dai menene Allah y kyauta y kuma kaishi lafiya umma tace amin (nan kuwa basusan soyayya ce take dawainiya dashi b). Bangaren sarah kuwa bataso tafiyarsa ba dan yanzu batason yai nisa d ita burinta kawai ya bayyana mata soyayyarsa gareta tai alkawarin zata karb'eta hannu bibbiyu dan ta tabbata tayi dacen masoyi dan kamal yarone nitsattse mai hankali g biyayya, uwa uba g ilimi addini d n boko, kyau kuwa kamar shi yayi kansa,gashi dogo b gajere b km yana d dan jikin d baxa'ace masa siririba ga kunya kamar wata mace dan ita kanta sarah tayi mamakin yadda yake kallonta ido cikin ido dan yadda sury t bata labarinsa ba haka bane, niko nace soyayya ce t sanyashi canjawa , d ganinsa zai iya soyayya tinda bai cika surutu any how b,sarah nima n tayaki murna Allah y sa kamal y zamto abokin rayuwarki dan nasan zaki samu kulawa d kwanciyar hanka. Karfe 12:00 daidai mota t saukeshi a bakin gate din schl karasawa cikin hostel yai ya ajiye kayansa sannan ya nufi toilet y watsa ruwa,gado ya hau y kwanta bayan y fito dg wankan ko yayi bacci ya rage gajiya, nan bacci yace ina baiga mahalli a idon sa ba tinda soyayya ta k'ek'asar dashi,wata duniya ya tafi a takaice dai akirata d suna duniyar tunani, iya bakin k'ok'arina nayi na naga n bishi dan jiyo irin tinanin d yake amma inaaaa tuni jirginsa y daga y barni a kasa inata zare ido kamar mazarin tsirehaka dole ina gani n hakura d rahotan gurin amma f nasan b wani abu bane banda sak'onnin son sarah d zasuyi tamai zarya suna miko gaisuwa d jinjina a fadar zuciyarsa suna fadin angaida masoyin sarah………… gaisheka mai kaunar sarah …………takawarka lafiya masoyin sarah………taka asannu asannu ka isar d sakon zuciyarka a zuciyar sarah………… haka dai zasuyita kawo gaisuwa. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 151 to 155 *AFTER 4 WEEKS* Yau juma'a yaya kamal yai niyyar zuwa gida sabida y kasa samun nutsuwa, tinanin sarah ya addabeshi dan haka ya kud'iri aniyar yau zaije y bayyana mata sirrin zuciyarsa, bayan sallahr jumaa ya hau kiciniyar shiri, misalin karfe hudu n yamma ya baro cikin schl zuwa , titi yai saa yana zuwa y samu mota y hau sai birnin dabo,ana kiran sallahr magriba ya sauka gida, lokacin abba yatafi masallaci, mamakine y kama mama sabida zuwan kamal ba zato b tsammani,abinda bata tab'a ganin yai musu irin wannan zuwanba, gaisawa d mama sukayi take tambayarsa lafiya dai kamal kake tafe yanzu yace lafiyalau mama, tambayar abba yayi, tace y tafi masallaci, alwala shima yayi ya nufi masallacin. Dawowar abba dg masallaci ne mama ke sanar dashi zuwan kamal,baki bude yace kamal tace kwarai,yace inceko lafiya yake tafe yanzu? Mama tace na tambayeshi yace lafiyalau, yace to madallah abba yana rufe baki kamal ya shigo y nemi guri dan nesa d abba y zauna sannan ya gaida abban, bayan sun gaisane abba yake cewa kamal lafiya kake tafe yanxu ba notice, dan murmushi ya saki gami d shafo keyarsa yace wllh lafiya lau abba kawai dai naji inason nazo nai weekend a gidane, shima abba mamakin abin yake yace to madallah sannan y tambayeshi y karatu yace alhmdllh,tashi yai yashiga dakinsa ya watsa ruwa sannan y kara fitowa palo lokacin su sarah suma suna zaune suna kallon wani film,dagowar d sumy tai suka hada ido dashi tace laaaaaa yaya kamal yaushe ka dawo, guri y nema y xauna yace dazu nazo wallahi, sannu d xuwa sukai masa harda sarah d bakinta yaki rufuwa dan murna, cikin shagwaba sumy tace amma yaya b notice da banyima delicious ba,dariya tabashi yace ayi hakuri aunty sumayya,gaba dayansu saida sukai dariya hardasu abba dan jin yace aunty,turo baki tayi tace to yaushe zaka tafi sainayi maka snack? yace sunday zan tafi tace yawwa yayan Allah y kaimu sukace amin. Yau asabar antaso dg islamiyya su sumy d kawarsu aisha suna tafiya dan sarah bata jeba kanta na ciwo, sumy ce t kamo hannun aisha suka koma gefe sukabar sury ita kadai,sury tace gulma dai b kyau sukace eh din,sumy tace k'awata wallahi nakamu d son yaya kamal fa ya zanyi ya gane? Dariya aisha tayi tace haba qawas bakisan dabara xakiyi ki janyo hanlalinsa b? Sumy tace kedai fadamin, nan aisha ta zayyana mata yadda zatai sai d tagama sumy tace wllh aisha duk b wanda banyib amma yaki ganewa,(ashe dama duk abinda sumy keyiwa yaya kamal sonsa takeyi)kaka tsara kaka,aisha tace tabb saidai ki fadamasa to, wani mugun kallo sumy t watsawa aisha tace a matsayina n mace zance inasonsa lallai aisha soma kike y rainani, batare d taji me aisha zatace ba t janyo hannunta tace zomu tafi dalla, itakam sury d ke tsaye a gefe tana jiransu tace angama gulmar kenan sukace eh sanna suka rankaya sukaci gaba d tafiya. Weekend haka y kare yaya kamal bai samu y cimma burinsaba sbd matsanancin ciwon kai dayake damun sarah ko palo bata fitowa,haka ya shirya ya koma schl cike d tunanin sarah, d daddare ne abba yaga ciwo na k'ara gaba yace d mama tinda gobe monday d safe sai kuje asibiti tace to Allah y kaimu. Gari n wayewa suka shirya sukaje asibiti,gwaje gwaje akaiwa sarah an rasa abinda ke damunta, haka likita yayi mata yan tambayoyin d yayi mata prescribing magani suka dawo gida, bayan abba y dawo gidane dg kasuwa mama ke shaidawa abba abinda likita y fadamata cewar baiga wani ciwoba iya gwaje gwajen d yai mata,abinne y daurewa abba kai ya shiga tinani wannan to wace irin cuta ce. Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 13 *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 161 to 165 Kwana biyu a tsakanin zuwansu asibiti ciwo y canja salo,duk maganin d aka bata a asibiti kamar k'ara ciwon sukeyi,ashe dai wasa farin girki ciwo y ta'azaxxara har takai sarah tana sumbatu zantuttuka barkatai ba kan gado bare n kujera hankalin abba d mama yai matukar tashi,shawara suka yanke akan sukaita gurin mai maganin hausa,aikuwa basuyi wata wataba suka dauketa saigun mai maganin,yadda mai maganin yaga sarah nayi ne ya sanyashi karanto wasu ayoyi dg cikin alkurani mai girma, take wata murya tafara bayyana kamar muryar yan yara tana cewa aikosu akai su salwanta hankalin sarah, wata zabura d mama tayi d jin mugun nufinsu neman tsari tashigayi d ambaton Allah,mai magamin ne y tambayesu waya aikosu sukace masa bilki ce tasa aka aikomu,take mai maganin yaita karanto musu ayoyin alk'urani saida y tabbatar sunbar jikinta sannan y hado musu magunguna d zata dinga amfani dasu yace kuma azo a ringa karbar mata rubutun tsari duk sati, take abba y biyashi kudin maganin d alkawarin shine zai dainga zuwa yana karbar rubutun. Alhamdullih sati biyu d fara amfani d maganin sarh t warke kamar ba itaba amma duk d haka abba yace baxata daina amfani d maganin ba saboda kariya d neman tsari dan haka duk sati saiyaje ya karbo mata rubutun. Bangaren yaya kamal kuwa yaga b sarki sai Allah y hak'ura d tunane tunanen sarah ya mik'awa Allah yinsa indai rabansa ce Allah ya bashi idan b rabonsa bace Allah yaimasa canji d mafi alkairi dan haka yanzu y hada hankalinsa guri daya kan karatunsa tinda shekarar karshe yake ,so yake ya kawowa abba excellent grade, dan shi kadai zaiyi ya nunawa abba godiya da dawainiyar d yai dashi tin yana tsimman goyo dan hk y maida hankali kan karatunsa. Ita kuwa sumy d son yaya kamal yai mata katutu a xuciya ta rasa yadda zatai dashi kullin adduarta Allah ya karkato d hankalinsa gareta tinda duk wata hanya tabi taga bamai b'illewa bace ko daidai d rana d'aya bataga ya nuna mata wata alamar so ba dan haka t fara bayyanar da son d take matsa a tsakanin sarah da sury duk sanda suke hira zata sako maganarsa tana dan nuna alamun sonsa azatonta acikin sury d sarah wani zai tunkareshi y fadama sa,tinda sarah t fuskanci sumy son yaya kamal take ta sawa zuciyarta ruwan sanyi dan tasan b yadda zaai yar gida tana sonsa abawa yar tsintuwa aurensa dan hk ta cireshi a ranta. Haka rayuwa tacigaba d tafiya kwanci tashi b wuya gurin mai duka yanzu sarah tashiga SS3 daf suke d fara SSCE, sumy d sury kuma suna SS2 suma qualifying exam zasuyi, yaya kamal kuma yafara final paper dinsa, dan hk karatu ka'in d na'in sukasa agaba saboda su samu abinda d ake nema kuma su faranta ran iyayensu dan haka suka dukufa wajen karatu b dare b rana. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 166 to 170 Sury d sarah ne ke tafe sun dawo dg gidan aunty fateema kasancewar gidanta d gidansu b nisa Sosai, yasanya sukai strawling sukaje, sarah ce rik'e d Najma yar aunty fateema da taketa shashsheqar kuka saita biyosu suna tafe suna hira, sun kusa kaiwa gida ne wani matashi ya kunno kai a mota saura kiris y bigesu yai saurin taka birki ya tsaya cak, agigice ya fito y karaso gurinsu hakuri y shiga basu sudai kallonsa kawai sukeyi basuce qalaba saida y gama sarah tace bakomai malam amma dan Allah a ringa kula Allah y kare gaba,tinda sarah t fara magana ya saki baki y layar uban tafiya yana kallonta,ita kuwa sury t tacika tai famm dogon tsaki taja mtswwwwww wanda y dawo masa d hankalisa jikinshi, hannunta Sarah taja fuuuuu afusace tace sarah zomu tafi suka wuce sukabarshi tsaye, tinda suka tafi yake kallonsu batare d ya motsa ba, ganin sun shiga wani gida ya sanyashi juyawa y shiga motarsa ya tafi. Gobe monday su sarah xasu farah SSCE exam tin dare take ta bosho, she s ready for d exams, atakaice zamuce kawai jiran question paper takeyi ta tsarge answer,cikin dare ta tashi ta jero nafilfilu ,addua takeyi Allah yasa abinda t karanta ya fito kuma Allah y basu nasarar jarrabawar. *Bayan sati daya* Mahmoud ne xaune cikin d'akinsa b abinda y keyi sai faman tinanin wannan kyakkyawar surar d yai toxali d ita kuma yaji an kirata d suna sarah, tinda yaji muryarta mai kama d busar sarewa yaji sonta ya mamaye xuciyarsa kullin d ita yake kwana yake tashi hatta cikin baccinsa gizo take masa,yanke shawarar zuwa wannan gidan dayaga sunshiga yayi batare d bata lokaciba dan sonta d yake addabar shi, baxai yi sanya b kar wani ya rigashi,mik'ewa yai yadau key din mota da niyyar tafiya yana adduar Allah yasa nanne gidansu. Karfe 4:00 n yamma ya isa kofar gidan, maigadi ya tambaya dan Allah nanne gidansu sarah yace masa eh,ajiyar zuciya yai yace alhmdllh dan Allah zan samu wanda zaimin sallama d ita? Baba mai gadi yace to dakata dg waje n kirata tukunna yace to nagode,baba megadi d sallamarsa y iske mama a palo y rissina sika gaisa sannan y shaida mata ana sallama d sarah, cikin Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 14 mamaki tace waye yace shidai baisanshi b tace to tana zuwa,sarah kuwa dake kitchen tana girki wiki wiki tai dan taji abinda baba maigadi yace, maman ce t kwallamata kira ta amsa saida t karaso inda take tace maza kije ana sallama dake kiyi saurin ki dawo kuma banda shashanci tace to,komawar baba maigadi y sanar dashi tana zuwa b dadewa sarah tafito,ganin fuskar mahmoud ne yasa t fara tinanin inda t taba ganin fuskar amma har t karasa inda yake tsaye bata tinaba,bayan sun gaisane taimai ixini d yashigo dg farfafajiyar gidan,daya dg cikin kujerun d aka jera dan hutawa tamai umarni y zauna, bayan y zauna suka k'ara gaisawa ne yake cewa dftn kin ganeni,murmushi tayi tace gsky na taba ganin face din amma namanta inda na santa, nan mahmoud ya fada mata inda suka taba ganin juna gami d wayancewa da cewa hak'uri ya kara zuwa y bayar,yar dariya sarah tayi tace kaimadai wllh mun manta abinma,nan suka taba hira kadan sukai sallama batare d mahmoud ya fada mata abinda ke cikin ziciyarsa b. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 171 to 175 Wasa-wasa soyayya tafara k'arfi tsakanin sarah d mahmoud saidai duk wainar d suke soyawa su mama basu saniba dan sarah bata nuna alamun tana sonsa a gabansu. Hakika duk abinda akasawa rana zaizo yau ne yaya kamal y zana final paper dinsa zai dawo gida, shirye shiryen taryarsa sumy tafara tin jiya,meatpie,springrolls cake shawarma, bugga, pizza n samosa taimasa sannan tai white cuscus n vegetable soup n liver soup sai pineapple juice,karfe 2:00 n rana tagama komai ta jerasu a dining, wanka taje t sheqa tasha kwalliya tana jiran karasowarsa dan tadauki kudirin yau zata bayyana masa sirrin zuciyarta. Abin sha'awa y baiwa mama yadda taga sumy n rawar jiki akan yaya kamal tasan d walakin goro a miya, dan ruwa baya tsami banxa tini ta rafko diyar tata son kamal takeyi addua tayi Allah y tabbatar d alkairi in rabontane,saidai tayi alkawarin bazata tari abba d maganarba har sai sun daidaita kansu . Karfe 3:30am yaya kamal ya iso cikin gidansu, bayan sun gaisa d mama taimasa barka d gama karatu lafiya yanufi dakinsa toilet y fada yai wanka zaifito Kenn, yaji kiran sallahr laasar saida yai alwala sannan y fito, yagabatar d sallahr dan acewarsa baxai iya zuwa masallaciba ya gaji sosae,byn y idarne ya haye gado d niyyar baccin, jin shuru yayi yawa b alamun yaya kamal Zai fito yasa sumy tashi ta nufi dakinsa,knocking tayi lokacin ya fara bacci taji shuru saida tai knocking sau uku sannan yai magana d cewa yes, shiga tai taganshi kwance baida alamar fitowa, ta karyar d murya tace haba yaya kasan cewa nashiryama dishes fa inacan inata jiranka a dining amma saika kwanta, dan tabe baki yayi azuciyarsa yace wai yarinyar nan metake nufi dani tafa dameni idanma,take takenta sona takeyi nikuma banida raayin aurenta,jin yayi shuru baice komaiba ne yasa takara magana sannan yace Ok yanxu dai zan hutu ki kawomin abincin nan idan n tashi saina ci ko? Aa kayi baccin anjima inka tashi na kawoma saboda akwai wata magana d zamuyi yace no probs ya juya yaci gaba d baccinsa, ganin da sumy tayi baida lokacinta ne yasa tajuyo cikin fishi ta nufi dakinsu. Bayan y tashi dg baccin sumy ta kawo masa abincin dakinsa,byn tayi servin dinsa ne ta janyo stool din dake gaban dressing mirror ta zauna tana kallonsa yanaci, saida y gama tace yaya kamal yace na'am sai kuma tayi shiru bata kara maganaba, ganin tayi shuru ne yace ehim yanaji kinyi shuru kuma,cikin siririyar murya tace gaskiya yaya kamal kana birgeni zuciyata tana cike d tunaninka kullin dashi take kwana t tashi tana muradin kasancewa a cikin taka ina roka mata alfarma ko zata samu bigire? (Nikam yau naga tsantsar rashin t ido agun sumy)shiru yaya kamal yayi ganin baida niyyar bata amsa yasa tace yaya kayi shuru,dago kansa yayi y kalleta yace kije zanyi tunani,marairaicewa tayi tace tinani kuma yaya yace eh karki damu,jin yace karta damune yasa taji kwarin jikinta,mikewa tayi cike d hope taimasa sallama ta fito. Kwana biyu a tsakani sumy taji shuru yaya kaml baice mata komaiba, shiko tin randa taimasa maganr ya manta dan a gurin d taimasa nan ya barta,sake sumunsa tayi ta tareshi d mgnr ya bata amsa da cewa yana d wadda yakeso,tinda y fada mata haka farinciki ya kaurace a fuskarta b abinda zuciyarta take sai kuna da danasanin karya billenta d tayi dan vata taba tinanin zai watsa mata kasa a idoba. Iya kokarin yaya kamal yayi wajen ganin y bayyanawa sarah son d yake mata amma y kasa sabida kunyar d yakeji dan duk randa yai yunkurin fada mata sai ya kasa haka y hakura yaci gaba d addua Allah y kawo masa mafita d saukin lamarin. *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 176 to 180 *Bayan wata daya* Abbane zaune a palo bayan sallah magriba y tara iyalinsa mama na daga gefensa axaune,gyaran murya yayi yace abinda yasa na taraku wata muhimmiyar maganace zanyi dan haka kowa yabani hankalinsa nan ya saurareni,kallon kamal yayi yace kai kamal tinda Allah yasa kagama karatunka service ne ya ragemaka to zaka fara zuwa kasuwa dan akwai wani shago sabo d na bude yanxu haka anzuba komai zaka ringa zama acikinsa dan bazakaita zama a gida kamarka ba,wani dadi kamal yaji yaimasa godiya sosae mama itama tayi godiya. Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 15 Abbane y cigaba d magana yace, sannan kuma yadace ace kana d iyali dan haka idan kana d wacce kakeso ka fadamin? zarrr kamal yaji ajikinsa wata zuciya tana cewa kawai kace sarah kakeso ,candai y dake ya kalli sumy y kauda kai yace aa abba babu,wani mugun kallo sumy ta watsa masa lokacin d suka had'a ido aranta tace lallai ma yaya kamal ni zai dizga tai k'wafa,batare d abba y sake yiwa kamal magana b ya kai duban sa ga sarah yace, sarah kema tinda kingama makaranta kuma ka'idar gidana dg secondry baa cigaba d karatu dan haka kema idan kina d wanda kikeso ki fadamin,tsuru tsuru sarah tayi tana raba ido azuciyarta tace inason mahmoud amma nasan yaya kamal yana sona kin fade yayi dan haka nima cewa zanyi banida kowa Allah yasa abba y hadamu aure saida t kai karshen tunaninta kanta n sunkuye tace babu abba,hamdala g Allah abba yai ganin burin d yadade yana son ya cika zai cika, dan da ace kamal ko sarah suna da wanda suke so da baxai musu doleba dan son ya cika burin zuciyarsa,cigaba d magana abba yayi yace tinda dik cikinku babu wanda yake d masoyi kamal ga sarah nan tinda itama tagama secondary ku daidaita kanku y kare maganar yana nunashi d hannu, duk cikinsu b wanda yai magana saidai zuciyoyinsu cike suke d farinciki, mamace t nisa tace Allah y daidaita su, abba yace amin kuma sati n baku,idan daya yaga d matsala bayaso y sanar dani dan banason abinda za ayi ya janyo matsala dg baya,yana kaiwa nan yace kutashi kuje Allah yai muku albarka, kansu a kasa sum sum suka tashi kowa y nufi dakinsu,wai wazai gane min sumy d tacika kmr t fashe. Gyara zama mama tayi ta kalli abba tace alhaji gaskiya kayi dogon tinani da kai tunanin hada auren nan, dariya abba yayi sannan yace wllh hajiya a iya tunanina banga wanda zan aurawa sarah hankalina y kwanta ba sai kamal da ace abdullh shine gaba d kamal dashi zan aurawa sarah,mama tace ai da kamal d abdallh duk dayane alhji yace hakne dan nafison wanda zai kula d ita y nuna mata gata bazai wulakanta taba,yar dariya mama ta saki tace ai insha Allah kamal yaron kirkine zai riketa d amana abba yace amin Allah ya daidaita tsakaninsu karsu bamu kunya,amin mama tace saidai mu yita addua Allah y tabbatar mana d wannan abu d alkairi yace amin. Wannan rana kwanan farinciki masoya biyun sukayi, amma bangaren sumayya abin baxai faduba dan ni kaina banga fuskar rabar ta bama balle n nado rahoto sai hakura nayi. A wanna daren sarah ta yanke shawarar datse alaka d mahmoud, zata fadamasa abbanta yai mata miji kuma y zamo dole tayi mishi biyayya ,nikam nace dama kinsan kawai kina rage zafin soyayyar yaya kamal ne d shi, lolllll *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 181 to 185 Toh fa akuyoyin d'aure ansamu sake wato sarah d yaya kamal soyayya tsantsa aka finjima nunawa juna cikin kwana biyu rak soyayya tayi nisa inka gansu suna xaune suna hirar love ka rantse shekararrune a harkar. D yamma suna xaune a farfajiyar gidansu suna hira ne sumy t kawo kai zata wuce, wata dariya d taga yaya kamal ya sakarwa sarah wadda tin sanin d sumy tai masa bata taba ganin yayi irin taba sai yau,batasan duk acikin love bane, tsaki tayi, aranta tace *Badai kafi sonta ba*tare d yin k'wafaa ,ashe abinda ta fada din y futo fili ,A firgice sarah ta juya dan ganin mai fad'ar wannan muguwar kalmar d ko amafarki bata k'aunar tasake jinta,ganin sumy tayi a tsaye fuska a daure d sauri sarah tace A uxubillahi minash shaidanir rajim gami d dafe kirjinta a ranta tace me sumy take nufi? Ganin tsoratar da sarah tayi ne yasa yaya kamal cewa d ita lafiya dear naga kin tsorata ko wani abin tsoron kika gani? Itadai sarah d hankalinta rabi b ajikinta yake b tace masa ba komai gami d murmushin yake sukaci gaba d hira. Mahmoud ne ya aika aimasa sallama d sarah,bayan ta fito sun gaisa ne take sanar dashi abbanta yai mata miji dan haka yayi hakuri ta kara d cewa ina sonka saidai baxan bijirewa zabin iyayena tinda dama mahmoud baisan matsayin sarah a gidanba ya dauka yar gidance, babu irin abinda d mahmoud bai fad'awa sarah b akan son d yake mata amma tace sam bazata bar zabin iyayenta haka sukai sallama ransa a dagule. *Bayan kwana goma* Ganin shak'uwar da sarah da yaya kamal sukayi ne yasa abba bai k'ara tuntubarsu batun son jubansu b kamar ydd yace idan sati yayi zai sake tambayarsu yaji sun daidaita kansu dun, dan mama ta shaida masa suna son junansu,haka yauma y kara tarasu a palo kamar wancan lokacin ya tambayesu sun aminta d juna sudai basu bada amsaba tinda hadisin Annabi SAW yace shurun budurwa shine amincewarta,haka y kara karfafawa abba guiwa take y sanya ranar biki wata biyu. Shirye shiryen biki abba d mama suka shigayi duk abinda y shafi uba abba ya dauke nauyinsa hakama abinda uwa xataiwa yarta mama t dauki nauyinsa wannan shi ake cewa tuwona maina,abba yaje dangin baban kamal ya sanar musu d maganar aure sunyi murna sosae d adduar Allah y sanya alkairi,shawartar mama yai d cewa yadace afadawa baban sarah,tinda abba yasan shi shine dai baisan abbanba dan tinda sarah t nuna musu gidansu abba yakan dan zagaya yana tuntubar mazauna unguwar saida y tabbatar d lallai nanne gidansu kuma shine mahaifinnata, shawara mama ta bashi d karya fadamusu sabida sharrin ammi zai ta bibiyar sarah muddin taji labarin aurenta, tabbas abba y yadda d shawarar mama, bai sanar d dangin sarah b. Takowane bangare shiri yai nisa ana saura sati biyu bikine aka kawo lefen sarah dg dangin mahaifin kamal, abbane y hada lefen amma yakaiwa dangin mahaifinsa sukawo dan basu girma d daraja ,hakika suma sunyi murna d irin karamcin d abba yake musu bai wulakantasuba dan suna matsayin talakawa, lefe nagani n fade aka kawo akwati takwas kwanne cike yake d kayayyaki daban daban. Ango d amarya kowa y gama shiri rana kawai suke jira duk wanda sukasan xasu gayyata sankai masa invitation card, su sury m sun gayyaci wanda zasu gayyata.mama Kuwa tinda aka tsaida ranar bikin t fara gyara amaryarta Ana saura sati daya biki aka fara gyaran amarya, haka sumy d surym baa barsu a bayaba wajen gyara nasu jikin duk d sumy na bakin ciki d auren. Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 16 *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 186 to 190 Kasancewar ranar juma'a ake daurin auren yayan abba bayan sallahr jumaa sannan rabar asabar a kai amarya, haka wannanma aka saka batare d an canja b,tin ranar talata gidan alhji yusuf yadau haramin biki dangin kamal bus guda sukayo maxansu d matansu, dangin hajia rukayya wato mama itama sunxo kwasansu d kwarkwata , ya'ya'n abba da suke gidan miji suma baa barsu a baya b sunxo, damuwa sarah t shiga ganin b kowa nata d yaxo a bangaren amarya, ganinta b walwala yasanya mama janta daki take tambayarta lafia, sanar d ita tayi kawai tina ummanta tayi d tana d rai d da ita xaayi, dakyar mama t lallasheta tadan saki jikinta. Yau takama ranar alhamis inda amarya d k'awayenta sukai walima a farfajiyar gidan kasancewarsa mai yalwa,iya haduwa amarya tayi,tsadadden material tasa golden ammasa ado brown colour,takalmi hill tasa tarike purse duk brown colour, decoration dinma kalar kayan d tasaka akai a gurin d xata zaayi occasion din, iya hadu ta hadu,tsararriyar walima akai inda aka gayyato manyan malamai dg hukumar hisba,sun zarara hadisai d ayoyin akan hakkin miji akan matarsa d hakkin mata agun mijinta dan anan najiyo wasu hadisai dasuka raxanan duk iya biyayyar d mace takewa mijin ta sai manzon Allah SAW yace *"Da ace dg kwakwalwar mijinki zuwa kafarsa akwai wani gyambo da yake xubda ruwa mai wari d doyi d jini, sai matar tasa bakinta ta lasheshi to lallai bata biya hakkin aurba."* yakara fada *" Da mace tasan hakkin mijinta d yake kanta da tasa kuncin fuskarta ta goge kurar da take kafarsa."* y kara d cewa *"Duk matar d ta cutar d mijinta d harshenta Allah baxai karbi aikinta n farilla ko n nafilaba mai kyau harsai y yarda da ita koda ta axumci yininta ta tsayawa darenta ta 'yanta kuyangu ta bayar d zababbun dokuna saboda Allah takasance itace farkon wadda zata fara shiga wuta haka shima mijin idan y kasance azzalumine agareta."* Hakika wad'annan hadisai sun razanani kamar yadda suka razana sarah d zata taka matakin aiki dasu, dan hk mata mudage d aiki ja agabanmu sai munyi takatsantsan, Allah y datar damu amin.Haka akaita lecture mai tsuma jiki d zuciya agurin walimar,bayan angama akaci akasha b karya walimar t hadu dan t burgeni naci burin ranar bikina irinta za'ayi. Washe garin d akayi walima wato jumaa bayan an idar d sallahr jumaa aka daura auren *KAMAL DA SARAH*akan mafi karancin sadaki, inda abba yai waliccin sarah,kawun kamal kuma dg bangaren mahaifinsa yaiwa kamal walicci, an daura auren akan sadaki naira dubu hamsin lakadan b ajalanba,daurin auren y samu halartar manyan yan kasuwa d maaikatan gwamnati haka abokan kamal suma baa barsu a bayaba wjn halartar daurin auren. Bayan angama daurin auren anyi reception an ci an sha anyi hani'an sannan kowa y watse. Ranar asabar hajiya rukayya tasha kan shagalin yinin biki itama inda yan'uwa d abokan arxuki suka samu halartarsa. Misalin karfe 5:00 na yammane aunty maimuna wato babbar ya'r abba ta umarci sarah dataje tai wanka dan karfe 8:00 xaa kai amarya, sarah daketa faman kuka tinda aka daura aure ido yai jawur jiki a sanyaye ta mike t shiga toilet, bayan tafito ta shirya mama tasa aka kirawo mata ita, wani abu a kofi shi b madarab shi b kunuba b kuma nono ba,naga mama t bawa sarah tace ta shanyeshi haka t kafa kai tana sha tana yamutse fuska har tashanye. Bayan anyi sallahr magriba abba yasa aka kira sarah d kamal y tasasu a gaba yayi yana yimusu fada da jan kunnen su akan su zauna lafiya karyaji karya gani sannan suyi hakuri d juna, mama itama ta kara yimusu fada sannan y sallamesu. Karfe 8:02 n dare motocin daukar amarya suka iso, wata hadaddiyar mota naga ansa sarah aciki tanata kuka, niko nace gobe d safe rasss zamuzo musameki b alamar kukahaka akaita shiga sauran motocin sai gidan amarya. Misalin karfe 9:30 n dare ango y shigo d abokansa guda biyu bayan anyi siyan baki kamar yadda alada t tanada , nan sukai adduar zaman la [12/8, 8:51 AM] Ayusha iliasu: *BADAI KAFI SONTA BA* *Written by Ayusha Iliasu.* *Story by Hawwa Saleh.* *Dedicated to Abeeda n Baseera.* *_Ayushailiasu.blogspot.com_* Page 196 to 200 _*LAST PAGE*_ *~AFTER FIVE YEARS~* Sarah ce dauke d wani tumbulelan ciki wanda lokitoci suka tabbatar d cewa 2wins ne acikin sa maza,cikin shiga ta alfarma ta jero 'ya'yanta mata guda uku *Naufaliyya,Nabwiyya d Naubiyya* duk kusan kansu daya gwanin ban sha'awa daga gefenta kuma kamal ne shima yasha hadaddiyar shadda y sabe babbar riga a kafadarsa t hagu,jerowa naga sunyi sun nufi motarsa d kansa naga y budewa sarah front seat tashiga haka yaranma y bude musu gidan baya sannan y xagaya y shiga ya tada motar, atakaice bansan inda suka nufaba dan hk nima n tada tawa akwalar motar nace muje zuwa tinda abin ba notice balle gayyata. Binsu nake tiryantiryan banyi auneba naga kamal y karkata kan motarsa wani layi, tinani nashiga yi anya na taba shiga wannan unguwar amma a iya tinanina n kasa tina gurinwa naje,ina tsaka d tunani ban idashi b kawai naga kamal yai parkin a kofar wani gida tini kwanyata (brain )t tinamin OOOhh!!! gidan su sarah ne ashe,ganin fentin gidan y jeme ba kamar sanda mukazo dasu abba b sharrrr dashi shiyasa ban gaskata b saida n fito nai tozali d malalen sumintin kofar gidan sannan na gaskata,futowarsu kamal d yaransu yai daidai d fitowata nima, hada idon d mukai d kamal y dokon uwar harara dan b shegiyar harara bace d ubanba wnn can n tsinkayi muryarsa yana cewa d sarah maman Naufaliyya kinga waccan Ayushan mai nacin tsiya saida t biyomu y karasa mgnr yana nunani d yatsa cikin mamak sarah tace ikon Allah waya sanar mata zamuzo nan yace ohoo niko nace kwasantata kwasan zanin daura mata dan tabe baki kamal yai yace gayyar sodi saiki taho ai amma a xaure zaki tsaya nace naji dai muje d murnata n bi bayansu muka shige cikin gidan. Rakabewa nayi a saro ina leqensu suka shiga ciki,suna shiga sarah tai toxali d abbanta yashe a wata karaunin tabarma duk t gutsitstsire yai kashangararai yana wani nishi atakaice dai rai yazo gargara ko ince rai kwakwai mutu kwakwai, d hanzari tana tura ciki ta karasa gareshi ta rungumoshi,daga ido yayi yace wace? Cikin kuka tace sarah ce abba, sarah! sarah!! saida y maimaita sau uku sannan y fashe d kuka yace dama kina raye sarah? tace eh abbana ina nan d raina harma nayi aure mamakine y kamashi yace aure? tace eh ko gaisawa basuyiba ta kwashe labarin abinda y faru tindaga fitowarsu dg prison har kawo yanxu sannan tace g mijina d yayana kuma cikin kuka abban nata yaita samata albarka d neman gafararta tace ta yafe masa, tambayrshi ammi d rufaid tayi yace ai bilki taga sakamako tun a duniya dan hauka takeyi tibiran itace kan waccan bola itace cikin waccan kwalbati taxama mahaukaciya ita kuma rufaida tayi aure ashe mijin dan giyane yai mata dukan tsiya ya sakota yanxu haka ta fada yawon karuwanci, innalillahi w inna ilaihir rajiuna abinda sarah d kamal suka furta kenannan hardani d nake rakabe,cigaba Abdullahi Aliyu Alkas Facebook.com/Abokinhira WhatsApp Me 09038188199 Facebook.com/Abokinhira Page No. 17 d magana abbanta yayi gami d kamo hannunta yana shafawa yace sarah ki yafemin abinda y faru a baya ba laifina bane duk sharrin bilki ne yasanya na tozartaku gashi yau kece cikin wannan gatan, Allah abba na yafe maka Allah y yafe mana baki daya,amin yace gami d kalmar shahada yana rufe bakisa y mutu,kasancewar umman sarah a hannunta ta mutu yasa tasan mutuwa kawai ji mukai sarah tace innalillahi w inna ilaihir rajiuna kullu nafsin zai'katul maut. *ALHMDLLH!* *ALHMDLLH!!* *ALHMDLLH!!!* *KULLU BIDAYAH NIHAYA* Yan uwa anan n kawo karshen wnn littafi mai taken *BADAI KAFI SONTA BA* ina fatan zamuyi amfani d darussan d ke cikinsa, dan munji ydd karshen mai bin boka tana asiri karshe kanta y koma, km yar d akebin bokan akanta a cusa sonta a xuciyar uban g halin d tafada,wdd akeyi dan ita km ga ydd allah y daukakata. *GODIYA* _Dukkan yabo d godia sun tabbata g kwal,tal,rak,tilon sarki gwani buwayi gagara misali wanda bai haifaba km ba'a haifeshi ba tsira d aminci su tabbata g fitila mai haske mai haskakawa tsani abin takawa zuwa g mataki mai garma wato Annabi Muhammad SAW .Godiya dolece g babban sarkin da yabani ikon kammala wannan littafi_ *BADAI KAFI SONTA BA* _Ina roka Allah y shafe mana kurakuranmu ya bamu sakamako mafi cancanta g daidaidin d mukayi._ *Bani d tamkar ki Yar uwa, kanwa, qawa, abokiyar shawara, Allah y barmu tare HAWWA SALEH* *jinjina gareku marubuta* Earhart tsafe Humaira B melody Aneesa A. R Huwailart Herwwerh jidda AKA Hapsart rano sadnas fertymerh zzahra umma yahya Mmn mahbu ummi hnbali Manshat faxy Farah muku jinjina, *D sauran d ban anbaci sunayenku b, ina Mai Adduar Allah y karemu daga sharrin mahassada* *Godiya t musamman gareku* Hafsat iliasu Hajara iliasu Musa iliasu Amina iiliasu Asmau lilasu *lna tare d ku har kullum* Hawwa saleh Ummu abdulhi Qawas mmn afeefa Bestyna fatyma Aisha Iliasu bauchi Abeada n basira( kunfi kowa bibiyar littafinnan) Princess xuhra Neenerh Ummylolo Rashida Xynor *Mu hadu a littafina n gaba Mai suna Yar boko*lov u oll TAMMAT BIHAMDULILAH A adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *