Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 22 March 2017

CIWON IDANUNA

adsense here ***CIWON IDANUNA 1 *** NA Benazir umar (BASED ON A TRUE LIFE STORY) . (wannan labarin gaskiya ne, yafaru, sai dai nacanja gari, suna dakuma wasu abubuwan, I just hope it should be useful) . Wawan birki naja, gabana ya tsinke ya fad'i, numfashina na kokarin daukewa, tunanina ya tsaya cak, na sa hannu na murza idanuna don tabbatar da cewa ba bacci nakeyi ba, bakuma mafarki nakeyi ba, na kuma tabbata ba gamo nayi ba, toh ko dai gamon ne? . A tarihin rayuwata nasan India da kyau, nasan larabawa da kyau nakuma san jinsin Fulani da shuwa harma hausawan kasanmu da kyau, sai dai a film ko labari, tadi ko wasa, bantaba ganin halittar 'Da namijin dake gabana ba, nayi ayatul qursiyu natofa ajikina, gashi dai bai matsamin akan hanyan ba balle nasa ran wucewa, da alamu ya bugu iya buguwa, ya sha wani Abu. "innalilahi wainnailaihi rajiun" na ambata wa kaina a lokacin Dana kara hada ido na danashi, dogo ne , fari ne ,saidai ba fari can ba akwai alamun dishewa a alamarinsa, yana da dogon hanci, gashin kansa ta kwanta luf tamkar na bahaushen balarabe, idanunsa manya ne,, saidai Wanda bature kekira da sexy eyes, a lumshe suke tamkar yanajin bacci gasu farare sol, innalilahi wainna ilaihi rajiun shinaci gaba da ambata dasauri najuya akalar motar dan barin gurin, zuciyata takasa amincemin cewa mutum ne ba aljanniba, ina tafiya ina waigawa don tabbatar dacewa baya biyoni Nashiga uku ni Nadra nayi gamo da katar!!!!! . Dasauri na nufi gida, maigadi yabude min gate nashige, tsantsan rikidewa mantawa nayi ban rufe kofar ba balle nacire key din, dakina na nufa kai tsaye, Allah ya taimakeni mammy( mahaifiyata) batanan narufo kofan nafada kan gadon, na lumshe ido ina tunanin halittan da nayi, nidai banyi gamo ba, mutum ne zahirin gaskiya, ahaka bacci ta kwasheni ban farka ba sai magrib, na dauro alwala nayi sallah,na mike na fito falo inda naga mammy na shirya dinning abinci abamama (mahaifina, yadda natashi naga yayuna nakiranshi), "ke kuma wani sabon salo kika samu na bacci dayamma!, ko dai jikinne?" " a'a mammy, wlh nadawo gun tela ne, daga kwanciya ashe bacci ya kwashen," "toh ai saiki zo ki nutsu kisha ruwa, kullum ke zakiyi azumi amma kina mantawa , bayan nace miki manzon Allah SAW ya umurcemu da mu gaggauta shan ruwa, mu jinkirta suhur, amma banda ke, ki kiyayeni fa" "oops, mammy naci dabino a daki AI" na nufi hanyar kitchen don maganan gaskiya na manta azumi nakeyi, tsantsan damuwan Dana Shiga yau, kuma kasanchewar yau baayi rana ba, nidai na nufi talatu ta hada mini kayan shan ruwa nazauna zanci, ikon Allah saikuma nagagara CI, tunanin bawan Allah yadamen, yakamata na koma gun ko zansameshi, toh amma ko ma shi giyan wake baza'a barni nafita ba, tuni dabara yafado min, namike na leka falo abamama nacin abinci, na zauna gefensa ina murmushi, shima murmushin yakeyi "lafiya auta?, ko jikin ne? " "ae daddy ciwon kai ne shine nakeso ko zanfita na leka chemist" "subhanallah, ya za'ayi kije ke kadai?, ina kamal ? kirashi yazo yakaiki, shi ko wani dai a samarin gidan nan!" nayi murmushi nace "toh" jikina na bari naleka daki nadauko mayafi na da mukullin mota na, Nazo nawuce, fannin samarin gidanmu na nufa, su rai shida narinka buga musu dakuna, Wanda dama dakuna shida ne a bq din, kowa da nasa, yaya kamal bayanan donhaka na buga na ya amir, yana shirin fita asham , "ya amir abamama yace ka rakani asibiti" ya kallen ta gefen ido batare da yayi magana ba yana kokarin rufe dakin nasa , na maraice kaman zanyi kuka, bai amsa ba nabi sawunsa, daman ban sa araina zai kulani ba, miskilancinshi daban ne, nidai inzai fita dani shikenan, motar sa yanufa nabi bayansa kaman agwagwa da yayanta, "wani asibiti?" "reemee" dama a gida nayi analysing cewa daga gidanmu wani asibiti zanbi Wanda dole nabi wannan hanyar naganshi? . Nagano remee ne kawai, aikuwa muna yanko kwanar fita daga layin , hasken wutan titin ta haskoshi yana zaune sanye da jallabiya, gabana ta tsinke ta fadi, ba shiri nace "yaa amir ka tsaya" yaja birki tare da juyowa alamun tambaya, ban kulashi ba nabude kofan motan, dasauri na nufeshi, bashiri ya amir yabiyoni kaman na zauce, ina zuwa nasa hannu nataba shi, ya Allahu, mutum ne, ba aljanni ba, dagowa yayi yakallen idonsa tayi jaa hasken wutan ya haskashi sosai, gabana bata bar fadiba, cikin sassanyar murya mai zaki wanda kunnena yajiyomin yace "lafiya?"jinayi an janyoni da karfi aka wurgani mota "ya amir ka tsaya mudaukeshi, ba mahaukaci bane , wallahi mutum ne, ba aljanni bane" Ba tare da ya saurari kalamuna ba ya jefani motar, wani bakin ciki naji ya gulleni a rai hawaye ya soma ruwa a idanuwata ina kallonsa har muka wuce, yaa Amir in banda jan tsaki babu abinda yakeyi nasan ranshi ya baci anma nashi kadan ne akan nawa, da zai auna bakin ciki na da nashi da zai san cewa shi wasan yara yakeyi, rai a bace nace kaina ke ciwo akaban magani muka biya kudi muka fito, a hanyan komawa haka nayita lekawa ki zan ganshi, aikuwa yana kwance akan wata kujera kamar wani sarki muna shiga gida mammy tana falo zaune dasu yaa kamal duk sunyi jigum suna jiranmu ganina yasa tamike da hanzarinta "zo auta na, meya faru? sun baki magani? kan yadena ciwo?" na lumshe ido jim yadda ta kamo kaina " toh mammy kin rike kan" dasauri ta sake tana tofa min addua, mikewa nayi na nufi daki ba tare da na kula yayuna dake cikin falon ba, tabbas sunsan ina cikin damuwa don a yanda nake da gagara da kansu suke korata daga falon amma yau ni ce a nutse hakan ya daga hankalin mammy batasan ciwon so bane ya damen Allah sarki ni, sallahn ishai nayi nayi nafila sannan nabi lafiyan gado sai dai bacci ya kaurace wa idona, tunani da fargaba ya damen , dafarkon ina tunanin waye bawan Allahn nan nabiyu ina tunanin ya akayi yake sheme a wajen? ko dai maraya ne? bai da yan uwa ne? meya sameshi? oh ni Nadra a kunnena aka kira asuba, dakyar na mike nayi nakoma kan gadon nan bacci barawo ya saceni. Ban farka ba sai karfe sha biyu na rana, mummy na zaune a gefeta ta tsura min ido dasauri na mike nace " mummy nace miki kidena bude ni da extra key, narufe kofan fa" " ke yar nan, saboda tsautsayi ne kinsa hankalina yatashi daga kwanciya kin kwanta kaman gawa dole na saki a gaba ina gadi" dariya tabani sai dai na daure nace " wanka zanyi natafi lalle da saloon kinga jibi sallah" " tashi to! ko kefa yanzu nasan auta ta tawarke anma kwanciyan ki bana son shi ko kadan" tana fada ta mike tanufi toilet ta kunna min heater sannan tafara ciro towel nayi murmushi sannan nace " ayya mammy dai, banma gaysheki ba, ina kwana? ina abamama?" "lafiya lao, ya jikin naki? yaje aiki anma zai dawo dawuri yasan baki da lafiya ai" "da yayi zamansa na warke nikam" na nufi toilet na rufo kofan, ruwan da ya danyi zafi nashiga na kunna ina wanka a hankali ina tunani har na fito mammy tafice dasauri na shafa mai dama nayi alwala na , nayi sallah nasaka abaya baki da bakar jaka sai snickers baki kasancewar inada haske sosai yasa nayi kyau fuska na farau farau na fice mukullin motata na dauka nayiwa mammy sallama sannan na fice, yau banci saa ba domin kuwa banga bawan Allahn nan ba nadamu matuka sai dai naji dadin rashin ganinsa a wajen, toh ko dai sai dare yake zuwa? . anma ranan da yamma na ganshi, tunani dai barkatai araina nawuce saloon sannan naje gidan lalle ban gama lalle ba sai karfe shida na yamma dasauri nafito don tafiya gida, dai dai gun na tsaya banganshi ba , toh ai yana azumi, anma ranan a buge yake kuma ana azumi, Allah ya kyauta, da tunani na nufi gida har ankira sallah domin masallacin gidanmu har an idar nasamu nashige ciki, naci karo da rikakkun samarin gidanmu wai sun shigo shan ruwa, bakinciki kaman ya kasheni ganin dukkansu sunkai aure anma sunbar mammy da musu abun shan ruwa, ganin sun baje a falon abamama na kan dinning yasa na murtuke fuska sannan nace " mu dai mungaji da ciyar da manya, kowa ya fito da mata ayi aure abar min uwa ta huta" yaa usman ne yasamin kafa sai gani Dim akasa, " wayyo Allah mammy zasu kasheni" dasauri ta nufi kaina " Usman ka kiyayeni, bana son bakin mugunta, karya tayi? yara kunanan dirka dirka kunki aure, duk mata zan nema muku" bai ce komi ba sai harara dana ke kwasa, yaa amir kam daman ba mai magana bane, su yaa kamal kuma yunwa ta debe shi baya magana sai yayi nak, mikewa nayi na dauki tray dina da aka zuba min nawa kason na nufi kan dinning gun abamama , muna ci muna tadi har muka gama, nan muka dawo falo ana tadin sallah, yaa kamal yace " zanyi hawan daushe fa, tunda abamama bai son hawa zan shiga ayari kawai , tawagan sarki kawai zamu duru mu shiga, da fatan zaki zo kallon hawa? don naga bakya son zuwa?" " me zanje yi in banda shan rana inyi baki kirin nasamu ruwan gida ya karben nayi haske" " aikuwa sai kinje" haka dai muka yita tadi da yayuna har goma tayi kowannensu yamike ya nufi fanninsa, ina dokin sallah gashi saura kwana biyu ne! . *** CIWON IDANUNA 2 *** . Yau take washegarin sallah, sannan kuma hawan daushe a garin bauchi, tun karfe tara na safe dana mike na fada bandaki wanka nayi nazo gaban madubi nafara kwaliyya, sai dana tabbatar nayi kyau na kalli kaina sosai ajikin madubin sannan na yi murmushi na bude wardrobe dina nadauko kayan da zansa, super wax ce peach nd green colour yasha lafiyayyen dinki dana saka aka yimin a abuja, na saka sannann na kara dauko gyaleta na yafa ta agefe, na jefa wayata da powder cikin jaka da turare kwaya daya sannan na fito ina murmushi, yaa Amir na jirana mutafi kallon hawan daushe dama su yaa kamal sun dade da tafiya kasancewar shi zaiyi hawa, mammy na falon abamama nafito muka wuce, yaa amir ke jan motar har muka isa state low cost inda zanhadu da yan ajinmu domin dadin kallon, duk da cewa ni yaa kamal nafito kalla. Anfara kallo rimi rimi abu yayi kyau ayi dariya ayi kallo nida kawata amma ty munata dariyan wani daya ke rawan shoki na ga tawagan gaba sunzo wucewa, ban lura da sunan tawagan ba , sai dai na hangoshi gabana ya tsinke ya fadi, na kara zura ido tabbas shine! rabon da na ganshi tun ran jajibar dana ganshi a hanyan komawa gida daga kasuwa , innalilahi wainna ilaihi rajiun gabana sai bugawa takeyi, yasha farin rawani da farin kaya duk da fuskansa arufe take bai hanani ganesa ba, dasauri rike da coke din hannuna na isa gabansa na mika masa, duk da yana kallon sama bai hanashi sauko da fuskarsa muka hada ido ya lumshe idonsa sannan ya karba, "nagode" cikin sassanyar muryarsa ya fada agefeta wata sai daga masa hannu takeyi " . Yaa Aliyuu! Yaa Aliyuu!! Yaa Aliyu!!!" na kalleta ina murmushi ko ba komi nasan sunansa , drinks din hannunta takoma dasu don ya riga yakarba na hannuna, ko yayi tunanin muna tare ne oho 'ALIYU HAIDAR' nafada acikin raina, sannan naja numfashi na juya na koma na ci gaba da daga masa hannu, zuciyata tayi wani sanyi, naji sanyi araina, haka na rinka fara'a har su yaa kamal suka wuce, cikin jin dadi nazauna inajiran yaa amir saiga wannan yarinyan dasauri na rike gyalenta tajuyo tana murmushi nace mata " inbazaki damu ba don Allah tambaya nakeyi?" ta gyra tsayuwarta tana kurban ruwa daga goran hannunta sannan ta gyada kai alamun tana jina "Yaa Aliyu danaji kince yayanki ne?" "ohh!! hamma Aliyu? yes, same mum same dad" naja numfashi sannan nace " don Allah numbanshi zaki bani " batare data ce komi ba ta kirgo min numban nikuwa na saka awayata, numban ba wahala sauki gareshi don harna rike, special number ne, sannan tace Aliyu hameed sunan,godiya na mata sannan na wuce, kuma sai data sanar min cewa yayanta ne na lura cewa suna kama asalin kama sukeyi , murna kaman me ahaka muka isa gida da gudu naje na rungumi mammy, ina dariya ita kanta tasha mamaki domin tayi sati bata ga farin cikina irinna lokacin ba , . daki na nufa nayi adding numban a whatsapp, dpnshi hotonshi ne dasauri naje nayi saving nasa a wallpaper na, sai juyi na keyi, yau zanyi baccin dadi,Allah na gode maka Allah. na saka hannu na danna layin yayi ringing har ya gama baa dauka ba, dasauri na kara dannawa wannan karon ya dauka cikin sassanyar murya yace "hello" jikina yana bari nace "hy ina wuni" sai kuma yayi shiru zan kara magana ya kashe wayan, nakara kira kawai naji switch off, innalilahi wainna ilaihi rajiun . . Nakara kira naji akashe, sai kawai hawaye yabi idanuna nayi ragon azanci dana karbi numbern kanwar, oh Allah ni ga samu ga rashi, haka na zauna inata kiran numban bai shiga ba, akalla nakai awa biyar ranan walwala ta kadan ne na tsaya tunanin rayuwata ma tukunna, nasan mai karatu ya matsu yaji wacece ni!, ga tarihina kadan kuji, Sunana Nadrah Ahmed ni ce ya mace agun iyayena, inada yayu maza kwaya shida, yaa kamal first born, sai yaa Amir, yaa Usman, yaa Anas, Yaa faisal, sai yaa ahmed kafin ni, ni kadai ce mace kuma yar gata, a gidanmu anhada manyan maaikata domin kuwa yaa kamal lawyer ne, yaa Amir banker, yaa usman quantity surveyor, yaa Ahmed da yaa faisal na medical school suna medicine, yaa anas kuma yatafi maritime sai ni danake karanta architecture a atbu, Abamama yana bala'in son yaransa, duk abunda muke bukata yana mana, tunda natashi izuwa yau bantaba rashin wani abu ba ko acikin kawayena nafita zarra, nadawo abun kwatance, shekaruna ashirin cif a duniya sannan kuma ni banda tarukucen kawaye kawata kwaya daya ce Ammaty, itama don iyayenmu abokai ne munsan juna, inada gagara da neman tsokana fara'a dakuma son mutane, sai dai bana shiga mutane, Allah yaban ilmi da wayo sosai, inada farin jini sosai agun samari tun daga yara zuwa magidanta sai dai duk cikinsu babu wanda raina ke biyawa, asalima ni bantaba soyayya ba bansan so ba bankuma san dadin so ba sai yanzu danake shan azabanta, nake son hauka domin kuwa so ne yafita acikin addini, ni kaina nasan yayi yawa anma yazanyi da raina? . iyayena basa kaunar fushi ta domin anhaifeni da ciwon zuciya lallabina sukeyi duk abunda nakeso anamin haka zalika yayuna, acikin yayuna nafi shakuwa da yaa kamal nakan manta inada mahaifi domin duk wani nauyi yadaukemin, ba yabon kai ba samarin gidanmu duk flowers ne maana sunada kyau domin gidanmu duk farare ne babu baki a gidanmu gamu da manyan idanuwa da gashi basai nakara bayani ba mai karatu zaigane cewa yan mata ba karamin safa da marwa sukeyi a gidanmu ba anma samarin gidanmu sun rufe ido babu niyyar aure akansu, tunda babu wanda bai kai aure acikinsu ba, ya Ahmed ma da nake binsa ma shekaranshi ashirin da shida. Iyayena asalinsu yan gombe ne Abamama kuma shuwa ne , mammy yar gombe sai su Abamama suka koma zama a gombe sanadin zamansu kenan. . #ays adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *