Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 22 March 2017

CAPTAIN RASHEED

adsense here [4/9, 8:37 AM] Jeeddah ja’o🏵: 💕☄CAPTAIN RASHEED☄💕 1⃣〰5⃣ Na 🏵 Jeeddah ja’o🏵 Tsaye yake ,tsayuwa irin na jaruman sojoji ,ya hard’e hannayen shi ta bayanshi ,kai a k’asa yana sauraron mutumin. Wanda ya cigaba da cewa ” Ashe in bana nan bazaku iya kula da komai ba ? Am very disappointed in you !! Wannan ai zancen banza ne!!!! A lokaci guda yayi wurgi da jaridar da ke hannun shi a fuskar jarumin gami da cewa ” take a look at these!!! Jaridar ta bugi fuskar shi sannan ta fad’i k’asa amma abunka da namiji ko motsawa bai yi ba!!! Dattijon da ke maganar yace ” na baka nan da sati daya a san yadda akayi aka nemo min kayayyakin nan in kuma ba haka ba I will held you responsible!!! Kaji na gaya maka! Yana kai wannan ya kwashi wayoyin sa ya fice wasu sojoji suka bi bayan shi , aka bud’e masa k’ofar mota ya shiga suka bar gidan.. Mutumin da ke tsaye kuwa wanda da ka ganshi kaga mai yi masa fadan ya tab’e baki ya nemi kujera ya zauna zuciyan shi na tafarfasa gaba d’aya tunanin shi ya dagule ,ya maida duban shi ga jaridar da ke jefe a k’asa ya sake kauda kai. Wata mata ce sanye da bak’in leshi yasha silver stones idonta da farin gilashi ke sauk’owa daga bene ,har ta zauna kusa dashi bai ma sani ba ,ta d’aura hannun ta akan nashi ta rike ,ya juyo ya dubeta ,tare da k’arfin halin yin murmushi ,itama murmushin tayi sannan tace” My son! Kayi hakuri ,Abban ka fa ya rasa a kan waye zai yi quenching fushin shi ne ,nima saida yayi min saikace ni din ma soja ce ,balle kai kuma da jiya ma sai bayan abun ya faru ka iso garin🙂 ranshi ne kawai a 6ace. Dan nata ya dubeta yace ” but mom ai……,.” Kafin ya k’arasa tace ” shhhhh!!! ” don’t stress your self !!, breakfast is ready! Naji kace kana da meeting ko? Ka tashi Kaje ka ci abinci ka shirya ka fita, bana kuma so in sake gani kana had’e rai!! Babu musu ya tashi ya nufi dining section don yin breakfast yayin da ita kuwa Hajiyar ta koma stairs abunta……. ☄☄ asalin labarin☄☄ Major General Abubakar Rasheed babba ne a Cikin Nigerian Military kuma wanda aka dama aka shanye dasu a Army!! Matarshi Fad’imatu bafulatana ce daga Gombe state fara kyakkyawa doguwa amma kasantuwar sunan kakarta aka sa mata kuma suna k’iran kakar da inna sai ita ma suke kiranta da INNA FETEL (INNA K’ARAMA), Dansu guda d’aya tilo mai suna RASHEED sunan baban mahaifin shi aka sa mishi , suna zaune a Abuja army barracks ,Rasheed har ya girma burinshi ya zama soja irin baban shi ,sun bashi ilimin addini da na boko ,karfi kuwa ba’a magana domin tare yake workout da mahaifin shi ,balle ma Yaron da ya tashi cikin sojoji sannan kuma ya kasance mai himma haka kuma suke tafiyar da rayuwar su cikin jin dadi ,family ne mai cike da soyayya, duk da kankancin familyn akwai abokanan Rasheed da suke tare da shi a gidan su biyu Muhammed wanda suke ce mishi Al’amin da kuma Abubakar Sadiq wanda zaman su a gidan ya maida familyn tamkar babba ne domin Inna da Abba sun d’auke su tamkar yayan cikin su ne , Al’amin air force ne while Sadiq ma captain ne a takaice dai familyn duk taron military ranks akayi😜. Wannan kenan. ☄ Rasheed na gama breakfast ya nufi side nashi don shiryawa ,already ya kusa yin latti ma haka ya shirya cikin gaggawa ya fito ,direct sai d’akin Inna. Tana zaune sai faman rubuce rubuce takeyi yayi sallama, ta amsa fuska cike da fara’a tace ” har ka shirya kenan!” Murmushi shima yayi yace ” yes mom” tayi masa adduoi da ta saba in zai fita, ya amsa da Ameen sannan ya fice ya nufi motarshi💕 ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/9, 11:32 AM] Jeeddah ja’o🏵: 💕☄CAPTAIN RASHEED☄💕 6⃣〰1⃣0⃣ Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Ya d’auki hanya bai zame ko ina ba sai No 7 Garki road ,inda military defence headquarters yake ,isarsa gate din aka bude mar ya shige ya yi parking, yana fitowa wayar sa tayi kara saida ya gama kwashe files din da ke motan sannan ya d’aga wayar ,daga d’ayan 6angaren wanda ya kirashi yace ” ina hanya fa dude !! Na jika shiru tun jiya baka min emailing wannan article d’in ba” Rasheed ya d’an shafa kanshi yace ” Oooh !! Am sorry I was totally carried away by circumstances around here wallahy ni na k’osa ma ka dawo ko zan huta ” daga d’aya ‘bangaren yace babu wani nan !! Wato so kake in dawo a had’a dani a fad’an ko?” Rasheed yace hmm kana jin dad’i fa lallai mom tana yi da kai!! Wato har ta fad’a maka abunda ya faru ? ” yana maganan ne a lokaci guda yana kallon agogon hannun shi ,ya zaro ido waje:oops: sannan yace ” look dude!! We’ll talk later am already late for the meeting !! Dad is going to finish me up today,” Sadiq ya bushe da dariya yace ” OK ltr :D:D” Sauri yake ta zubawa a hallway din nan yana wuce offices na manyan soji har ya kai meeting room sannan ya tsaya ya gama kimtsawa ya bud’e k’ofar a hankali yana shiga sukayi ido hud’u da Abba ,ya kafse kamar bai ma san da shi ba ,ya nemi guri zama ,bai zauna ba saida yayi apologising for lattin da ya maka ,don ya lura wasu har sun k’osa ma. Ba tare da ya kalle she ba Abba yace ” you may start presenting how the operation is going to be ” ya kwashi files din aka kashe wuta sannan aka kunna projector wato majigi sannan ya fara presentation din nashi hankali Kwance ya kammala duk Kowa kuma ya yaba da hakan. Minti talatin ne kachal dama meeting d’in Kowa ya fice banda Rasheed da Abban shi ,shi Abba kawai bai ga daman tashi bane amma Rasheed files d’in yake tattare wa , har ya gama zai fita Abba yace ” a office d’ina akwai wasu files guda biyu red colour an rubuta operation red I want you to go through them ,Kaje ka d’auka yanzu!!” Rasheed yace “SIR!!!👮🏾👋🏾 ya fice ya barshi cikin room d’in….,……. K’arfe biyar na yamma Sadiq ya k’ira Rasheed ,yana dagawa yace ” dude na iso fa amma kuma I can’t drive anymore jikina ba k’arfi sosai wlhy ,Kazo ka d’auke ni plssss!! ” Rasheed yace OK kana ina yanzu?Suleja road ! OK ganinan zuwa” ya kashe wayar ya tashi ya saka wata Yar shirt nashi blue armless gashi button din a bud’e hakan yayi displaying twelve packs nashi ,bai saka buttons din ba har saida ya iso inda Sadiq yake ,shima yayi hakan ne saboda tarin y’an mata da ya gani a chan gefe ,saboda mutum ne mai kunya when it comes to issue na mata saboda haka ne ko a barrack bai cika shiga sabgarsu ba sai na mutum d’aya ,wato childhood friend nashi wanda ban ambace ta tun farko ba ,sunan ta Imtihaal ya fita da wajen shekara biyar amma sun shaqu sosai, saidai yanzu bata k’asar ,taje karatu a Malaysia… Sadiq ya d’an lallaba ya k’araso inda motar yake ,shi kuma Rasheed ya bud’e masa ya shiga sannan ya zagayo shima ya shigo gami da rufe k’ofar, har zai sa key ya kunna ya juya ya dubi Sadiq da sai yamutsa fuska yake yi yace ” ya dai dude! Me ke damunka ne? ” wlhy ina fada maka na tsaya ne na ci fast food a wani restaurant cikina ya birkice sau wajen bakwai ina tsayawa a hanya sai na nemi gurin juyewa💩 lol. Rasheed ya bushe da wata irin dariya ta mugunta wanda har saida yasa Sadiq razana 😂😂😂 ” yanzu kai dan Allah meye abin dariya 😠 ni shiyasa bana son fad’a maka wallahy nasan dama abunda zaka min kenan🙄 ” Rasheed ya ci gaba da dariyarsa haka suka isa gida tun Sadiq na fushi har shima ya biye masa suka ci gaba da dariyar😀. Rasheed na parking motar kafin kace me har Sadiq yayi wuf ya fice daga motar a guje yayi cikin gida ,mom na parlour ya wuceta ko gaisuwa babu ,ya barta da sake baki 😧, Rasheed na fitowa daga motan ,dariya ta ci shi sosai yace ” nifa bani naje na ciyo mama abinci ba don haka bazaka barni da d’aukan wannan k’aton jakar taka ba!!” Shima ya bi bayanshi yana wasa da makullin motar tasa:mrgreen: ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/9, 4:55 PM] Jeeddah ja’o🏵: 💕☄CAPTAIN RASHEED☄💕1⃣1⃣〰1⃣5⃣ Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Yana shiga Falo ya hangi mom zaune ,kafin ya ce komai ta riga shi da cewa ” yaya naga mai gidan nawa haka? Sunan da take k’iran Sadiq kenan dayake sunan su d’aya da Abba ,abunka da bafulatana 😜 ganin Rasheed bai amsa mata ba ,ta zare glashin idon ta ,ta sake maimaita abunda ta fad’a, Rasheed da ya kusa kecewa da dariya yace babu komai mom ,daman yana fama da intestinal disorder ne , yanzu ma motarshi na chan bakin hanya ya kasa driving, yana magana yana Sosa ‘keya ,mom tayi murmushi irin nasu na manya tace its alright bari zan duba shi ” kai kawai ya girgiza mata shima ya haye sama yana dariya ,shi ba komai ke bashi dariya ba sai ,juyewa da Sadiq ya ambata😅. Oh ni hauwa’u!!! da ganin Rasheed kasan rigimamme ne musamman in yana tare da friends 👨‍👨‍👦‍👦.wannan kenan!!! ☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄ GOMBE STATE💕 Rana ake yi kamar me ☀ta fito daga wata silver coloured mota kirar Nissan maxima takalmin k’afarta black stilettos masu uban tsayi ta fara sauk’ar wa ta jima a haka kafin daga bisani ta fito ,wata yellow jallabiya ne a jikinta mai adon duwatsu black and white tayi rolling kanta da multicoloured gyale wanda yayi matching da kayan nata ,sai simple beaded bracelet da ta saka bak’i shima ,ba fara sosai bace amma baza’a sakaya ta a jerin bak’ak’en mata ba ,siririyar fuska gareta daga ka ganta kasan ta tashi cikin gata ,sannan kuma siririya ce ba wata k’ibar a zo a gani gareta ba sai wani shan kamshi take tana yamutsa fuska. Abuja quarters ne inda ta tsaya d’in d’aya daga cikin unguwannin da ake ji dasu a garin Gombe kenan. Juye juye take tayi kamar me neman wani abu ,chan kuma ta d’auko wayarta daga purse din dake hannun ta ta kira wata number ” hello !! Ke nifa na rasa gidan gaba d’aya na kasa gane wanne ne a ciki kawai ki fito ki kai ni!! OK toh ina jira kiyi sauri pls its sunny out here!” Abunda ta fad’a kenan ta katse wayar. Bata dad’e ba kuwa wata y’ar budurwar chocolate brown amma kyakkyawa ta fito sai washe 32 take yi:D suka dunguma suka shiga gidan tare……… ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/10, 7:53 AM] Jeeddah ja’o🏵: 💕☄CAPTAIN RASHEED☄💕 1⃣1⃣〰1⃣5⃣ Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Sadiq na zaune saman mota a parking lot na gidan nasu ,Rasheed ya fito d’auke da traveling bag nashi ya kafa waya a kunne sai faman zuba yake, sai da ya iso gurin motar yace ” imtihaal zan k’ira ki anjima ,pls I’ll be on my way to Gombe state ,gobe bikin cousin d’ina ,I missed you soooo much !😘 take care !” Sai ya katse wayar ,Sadiq yayi dariya yace sarkin surutun naka Mukam ta yaye mu gaba d’aya ,by the way how is she doing there in Malaysia? ” Rasheed yayi murmushi yace ” lapyarta k’alau ” nan suka shiga mota don tun safe su Inna suka tafi ,su sun tsaya sabga, yanzu karfe biyu ga uban rana amma haka suka d’auki hanya suna tafe Rasheed na zolayan shi ” Kar fa kace mu tsaya ka juye don bazan iya ba:roll:”……… Basu suka sauk’a a garin Gombawa ba sai wajen to nine, a gajiye ko kayan su basu d’auka a mota ba suka wuce side d’in da suka saba zama in sun zo ,akayi sa’a kuwa tun isowar su Inna ta sa an share an gyara don tasan halinsu da iya tafiyan dare, daga sukayi wanka da sallar maghrib da esha ai nan suka zube sai bacci ,gwara ma Rasheed cikin dare ya koma saman gado ya kwanta amma sarkin barcin kam ko juyi bai yi ba sai da aka k’ira sallar asubah🕌. Sukayi alwala , da yake akwai wasu kayan nasu a dakin suka saka ,sai masallaci basu ma dawo cikin gidan ba sai wajen seven thirty (7:30)am, ko da suka shigo main house suka shiga don gaida y’an uwa, kakar shi Maryama wato maman Inna ita ta fara hango shi, tace toh sai kuyi ta yi nima ga jika na ta zo “:D da dariya ya karaso domin ita Inna ba k’arami aikin ta bane ta maida namiji zuwa mace and vice versa, ya zauna gefen ta yace ” me sukayi miki ne kakcy?” Abunda yake kiranta da shi kenan, ta had’e rai tace kagan su nan basa sona 6ingel am!! Tun jiya sun samu yan uwansu sun ya dani ,toh nima ga jika na ya zo ” Rasheed ya sake kwanta wa jikinta yace kwarai ma kuwa !!” Mommy Yayar Inna ne sunanta na asali zubainatu amma auna kiranta da Adda jube, akwai mutum biyu maza tsakanin ta da Inna wato maman Rasheed ,uncle Hasheem, da Hamman last born nasu kuma Goggo Aisatu. A takaice mata uku kenan maza biyu a gun mahaifiyar su. Mahaifin su ya rasu ba da dad’e wa ba. Mommy wato Adda jube ta mik’a mishi food flask dauke da p. Soup na cow tail tace ga breakfast naku sai kuje ku karya an kai muku sauran ya karb’a rai a dagule yace ” ni fa mommy madara kawai zan sha” nan mommy ta had’e rai tace ” yanzu da sassafen nan so kake inje in tatso madarar saniya ,in tafasa maka ko kuma a ina zan samu madara !! Kai dai wallahy fulatancin nan bazai kaika ko ina ba fa ,kai Sadiq tashi Kaje ka karya ka barshi in ya ji yunwa zai je ya ci ai!” Su kakcy an tab’o d’an jikalle nan tafara azalzalar mommy da masifa don kaf jikanun ta babu wanda take ji dashi kamar Rasheed. Tashi tayi da kanta ta ce ” muje ni ina da madara tun jiya yana furji yayi sanyi muje ko kindirmo kake buk’ata akwai sai wanda kayi niyya ” ya mike ya bita yana danna wayarshi ko kallon su Inna bai yi ba balle Sadiq da suka zo tare. Karfe goma aka d’aura auren Mujaheed cousin din Rasheed da Nusaiba Daneji. Taro akayi ba kad’an ba amma Rasheed bai ma san wainar da ake toya wa ba don tun da ya shiga gurin kakarshi bai fitoba suna chan yana ta mata hira yadda ya saba ,don shi yafi sabawa da ita akan kowa. Sadiq se k’iran wayar Rasheed yake bai san cewa mutumin ya bar wayar a cikin d’aki ba wanda yake amfani da shi kuma ko sim card babu a ciki ,don game kawai yake tayi da wayar. Wajen 10:30 tukunna ya fito yaga gida cike mak’il da jama’a da ‘kyar ya wuce ,filin gidan ma duka an d’aura canopies ana reception da sauri ya wuce ya bud’e side nasu ,yayi wanka ya kimtsa cikin farar shadda tayi mugun yi masa kyau ,ya kafa hula bak’a abunka da d’an fari ya fitar da shi sosai ,ya fito sai dube dube yake ,karaf ya had’a ido da Abba:oops: wani kallo ya watsa mar ,ya nuna masa ranshi a 6ace yake, Rasheed ya sunkuyar da kai ya nemi gurin zama bai ma san inda ya zauna ba sai da ya yi adjusting ya ga ashe ,Sadiq ne da Al’amin. Al’amin ya 6alla masa harara yace fi sabillilah har na iso ace kana chan kana shirme kamar ba bikin Mujaheed d’in ka ba ,ina ka shiga ne haka? ” Sadiq de bai ma ko kalle shi ba ,shima bai ku lashi ba don baya so ya takalo wa kanshi rigima…….. ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/10, 3:43 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED☄💕 1⃣6⃣〰2⃣0⃣ Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Ana gama reception Rasheed ya mik’e don ya nemo ango ,Sadiq yace ” toh masu kaka!! Saura in Kaje hiran ka manta akwai dinner da dare kayi zamanka :roll:” Al’amin de dariya kawai yake yi don yasan hakan zata iya faruwa. Rasheed ya daka musu harara yace ” Baku ma tsaya kunga inda zani ba kun fara surutan naku ,toh Mujaheed zan nemo ,kuma I need a quite place nayi magana da Imtihaal naga missed calls nata har hud’u. Sadiq yace ” Hmmmm daga nan kuma sai gun kakcy ko?!” Bai tanka masa ba ya wuce ,su kuwa suka bushe da dariya….. ☄💕☄💕 Bayan sallar isha aka fara programs ,amarya da ango ansha kyau , k’awayen amarya ma haka , amaryar sai juye juye take yi da alama wata take nema ,chan wata daga k’awayen nata ta gano hakan ta zo tambayar ta ko me take buk’ata? ” Babu komai Hanan kawai banga Ilham bane ,ko ba tare muka fito bane ?” Hanan tace ” Haba amarsu ! Saikace ba kisan halin mutumiyar taki ba? Ai tana chan waje tak’i shigowa ,wata’kila in ruwan saman ya sauk’o zata shigo” kafin ta gama rufe baki kuwa aka fara ruwa… Daidai bakin k’ofar shiga ta d’auki glass na cherry drink tana shigowa tana taku tabbas tayi stealing show d’in kam ba kad’an ba ,ankon bikin ne a jikinta kamar yadda sauran k’awayen suka sanya fushia pink da silver goggoro yau kam dai simple makeup tayi amma tayi kyau ,tahowa kawai take yi tana danna wayarta ,hannu daya ta rik’e glass cup ,suka ci karo da Rasheed da ke neman hanyar fita yana waya, duk wannan drink din ya zube a kayan shi ,gashi shadda ce fara da ita ,duk kallo ya koma kan su. ” Kai Malam baka gani ne ko kuma makaho ne kai da zaka na tafiya ba tare da ka duba inda kake tafiya ba? How arrogant!! Mtsew!!!!” Abunda ya ziyarci kunnen Rasheed kenan ,Sadiq sarkin zuciya har ya mik’e Al’amin ya hana shi , shima Rasheed din murmushi kawai yayi yana rike da inda drink d’in ya zuba ,ya fice ya barta tsaye a gurin sai tauna takeyi ,ta sake yin wata tsakin da ta ga su Sadiq sun bi bayanshi, duk da Sadiq baya son raini haka ya hak’ura ya wuce bai kulata ba ……. Haka dai aka gama dinner kowa ya watse. Karfe shida na safe suka yi sallama da family su kakcy har mota ta rako jikallen ta 😜. Abunda yarinyar nan ta mishi yayi matuk’ar 6ata mishi rai ,shi kanshi ya rasa dalilin da yasa ya kasa tanka mata…… Two weeks later:: Tafe yake yana waya da mutumiyar tashi ,wato Imtihaal ,wani ‘kara da yaji wata mota tayi yasa ya katse wayar da sauri ya juya. Hayak’i duk ya karad’e gurin , saida ya washe tukunna ta fito sanye da kayan sojoji saman shi ta d’aura lab coat ta kama gashin kanta kamar doughnut ta kasa sannan ta d’aura hular soji ,Barrett a kan ,tana tafe tana waina key d’in motar da ke hannun ta. Kai tsaye ta nufi office na lieutenant….. Tabbas Rasheed ya gane fuskar ta duk da ma yau shigarta daban da na ranar dinner d’in…… Toh fa !! Masu karatu d saga begins here!! Ni kaina bansan iyakar tsanar da Rasheed ke mata ba amma muje zuwa ……. ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/11, 9:21 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED☄💕 2⃣1⃣〰2⃣5⃣ Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Wata muguwar dariya yayi ya wuce yana wayarsa ko gurin bai sake waiga wa ba. Ya shiga gida kenan bai jima ba ,wayarshi tayi ringing ya duba yaga Abba ne ,” ka shirya Kazo yanzu da sauri zamu shiga emergency meeting ,ina fatan Sadiq na tare da kai ,your presence is needed ” yes sir” !! Kawai shine amsar da ya bayar ,ya shige bathroom…… Suna shiga defence headquarters , ya ga motar Ilham ne a gaban nasu ,kawai ya kara gudun motar da gangan ,ya buga mata bayan mota har danger motan ya fashe ,yayi wata muguwar dariya ya kau da kan motar shi ya wuce parking lot yayi parking motar shi ya barta a gurin tana ta surutai kamar mahaukaciya😂 ,da gudu tabi bayan shi ta sha gaban su gashi ta tsuke cikin khaki. ” suna had’a ido ta sunkuyar da kai ,ta gane shi sosai ,gashi kuma ko a matsayi ya fita (rank). ” lapiyar ki kuwa? Kika tare min hanya ,ko dai kin tab’u ne? Sadiq kuwa bashi da aiki sai hararar ta don tun farko ya tsani yarinya , ganin bata da abun cewa yasa ta matsa suka wuce ,cikin ranta kuwa tace ” Oooo I see !! Wato rama abun da na maka kayi ko,in dai wannan ne kuwa ka d’ebo ruwan dafa kanka zan hadu da kai ne ,gani na kake yi baka san hali na ba:roll:. Fitowan su daga meeting ta ci karo da shi da General ma’ana Abba ,abunda ya ziyarci kunnenta shine Kalmar DAD da ya ce wa General d’in. Ta wani juya idanuwa tace ” lallai wannan yana da k’arfi ta ko wanne fanni ,wato don shi d’an General ne sai ya wulak’anta ni ko?zan yi maganin ka! ” suka wuceta suna discussion nasu ta bishi da kallo ,yayinda shima ya tsareta da ido, duk abunda ta fada kuwa Sadiq ya ji ta ,don bata san yana bayanta ba , tana juyawa ta ci karo dashi,gata da tsoro tuni ta rikice ta rasa yanda zata yi ta bud’e wata k’ofa ta shiga ta rufe k’ofa, daga waje Sadiq ya bushe da dariya yace ” tabdi yarinya kin yi gudun gara ne kuma kin tadda zago😂 Office din Rasheed ta shige bata sani ba ,yana zaune yana fama da computer yaji an bud’e k’ofa a zaton shi ma Sadiq ne kawai ,sukayi ido hud’u ,idanuwan shi kadai kan bata tsoro in ya zaro su ,ta d’an daure ta juya zata fita ,yace ” come here!!! Ta juyo gami da watsa masa harara yace ” excuse me!!! Wannan kallon fa? Ta kauda kai gefe ,yayi dariya irin na mugunta ya watsa mata wasu files yace ” ki kai wad’annan wa captain Sadiq and pls hurry baby !!” Baby da ya k’irata yayi mugun bata haushi ,ganin hakan shi kuwa ya samu abin yi:D. Ta juya ta fice rik’e da files d’in. A kofar fita ta hango Sadiq yana faman bud’e k’ofar mota ga dukkan alamu fita zai yi ,da sauri ta nufi inda yake ,tana isa ya tada motarshi ,ya sauk’e glass d’in motar yace ” ya dai?” Ta mik’a masa files d’in ” gashi captain yace in kawo maka ” Sadiq yayi wata y’ar dariya yace ,sorry ki rik’e yanzu Ina sauri pls Kar ki 6ata min lokaci ,in na dawo sai ki bani in kuma ban dawo ba mu had’u a barracks🙂 ya daga glashin motar ya yi tafiyarsa ya barta anan baki a sake. Bak’in cikinta ,tun da take ba’a tab’a cin mutuncin ta haka ba. Ta juya jiki a sanyaye ,tace ,zan rama ne!!” ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/11, 4:46 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED☄💕 2⃣6⃣〰3⃣0⃣ Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Saman motar ta take a kan hanya metres kad’an daga headquarters d’in tana hango motar captain Rasheed ya danno kai kawai sai ta watsa wasu k’ananan k’usoshi a kan kwaltan ,ta ci kunu tana danna wayarta ta toshe da bak’in gilashi saboda rana da ake yi, duk da Rasheed ya ga abun da ta aikata kafin ya iso hakan bai hana shi bin hanyar ba ,kamar yadda take tsammanin gani ,tayun motar duk sun sace ,yayi parking a gefe ya jingina da motar ya fiddo wayar shi daga aljihu ya kara a kunne ya k’ira daga chan wani ya taho mishi da mota ,ya karb’a makullin sukayi wasu yan maganganu mutumin ya koma da baya ,ita kuwa tana zaune cikin mota ta shagala sai shek’a dariya take yi bata san wainar da ake toya mata ba , duk tayun motar ta Rasheed yasa Wannan sergeant d’in ya sace ,sai ji tayi tana yin k’asa, ba shiri ta fito tana ta dube dube a rikice ta rasa yadda zatayi ,ga zafin rana , ta fito ta banke k’ofar motan tana hararan Rasheed shi kuwa murmushi kawai yayi ya ja motar sa yayi gaba:D. Yana tafe yana cewa lallai ma yarinyar nan ain in tana cin k’asa kamata yayi ta kiyayi na shuri!! Ya sake AC yaci gaba da tuk’in shi, sai da ya isa gida ya yi wanka ,har yaci abinci ,suna hira da Inna a palour Sadiq ya kirashi yana d’agawa yaji sai dariya yake ta yi kamar mahaukaci ” kai meye haka ka k’ira mutum kuma sai dariya kake kamar sintacce? Sadiq yace yanzu naga mutumiyar taka ,tana ta faman tafiya ga rana ,kaga ni ba gida zan dawo ba da na taimaka mata” jin haka ta bawa Rasheed tausayi yace ” bari na koma na d’auko ta ,haushi take bani yarinyar ta maida ni kamar wawa ,sa’an ta. Tafiya take tana ta faman share gumi , duk wuyanta ya bushe gashi ba kowa ta sani a garin ba ma balle ta k’ira, motar Rasheed ce ta bullo ta tsaya a gabanta ,tana k’arasawa gurin ya bud’e k’ofar motar ba tare da ya fito ba ,ta tsaya tana ta shan kamshi, ganin ya saka hannu zai rufe yasa ta shigo ba shiri ,abun ya bashi dariya matuk’a ya girgiza kai ya tada motar. Tafiya suke babu wanda ya yi ko tari ,yasan zata ji kishirwa ,ya d’auko ruwa chilled a cooler ya bata ,kamar bazata karb’a ba kuma naga ta mik’a hannu,ta kafa kai bata sauk’e ba saida ta gama shanye ruwan😂 sannan tayi relax a jikin kujerar sanyin AC na ratsa ta ta koina. ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/12, 8:33 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED☄💕 3⃣1⃣〰3⃣5⃣ Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 K’ofar gidan su ya dire ta ,bud’e k’ofar motan tayi ta fice ba tare da yi masa godiya ba,shikam ya ma kasa sa key a motar balle yayi tunanin tafiya ya bita da kallo don yaga iya gudun ruwanta, har tayi nisa ta dawo kai a ‘kasa tace ” nnn… Aa gode !” Ta fad’a ne kamar wanda aka tilastawa sai ta fad’a. A fusace ya fito a motan ,ya shak’e ta ya manneta da motan yace ” ke wace irin jahilar mace ce? I have been doing you Favour’s amma bari kiji in fad’a miki ,yau kin kaini mak’ura , a girme na fiki, amma bakisan ki girmama na gaba da ke ba ,who the hell do you think you are!!! Since from d first day I saw you naji na tsane ki !! I will give you this as a warning!! ,ki fita daga harka ta ,kar ki sake wani abu ya had’a ki dani ko da wasa don sai na miki wulak’ancin da bazaki tab’a manta shi ba har ki gama rayuwar ki!! Mark my word!!!!” Yana kai wannan ya juya ya barta a gurin ido cike da hawaye wad’anda suka kasa gangarowa har saida ya ja motarshi ya bar gurin. Daren ranar Ilham ko runtsawa bata yi ba ,gaba d’aya abin duniya ya dameta ,daga ta rufe ido shi take gani ,” lallai nasan ban kyauta ba , kuma gashi na kasa samun nutsuwa! 🤔 tabbas dole in bashi hak’uri but how? Gaskiya bazan iya giving up so easily haka ba !!!! Ilham kenan !! Ni kaina Jeeddah ja’o na ce tana da ji da kai !!! Karfe sha d’aya na safe Rasheed ya shigo office d’in lieutenant kawai sukayi ido hud’u da ita ,ya kauda kansa gamida mik’a wasu file’s ma lieutenant d’in yace ” ina buk’atar reports within the next five hours ,ni zanje d’auko Imtihaal daga airport, kuma pls in har akwai wani sudden abu ka sanar da ni🙂 lieutenant ya Sara mishi yace ” yes sir!!” Rasheed ya juya ya fice ,bai ko sake kallon inda take ba. ☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄☄ Tafe take tana dariya rigar jikinta mai dogon hannu ne fari sai ta d’aura jacket na khaki a saman tasa wani skirt flattered bak’i ,Kyakkyawar gaske amma babu gyara ,don ita Sam a birkice take ,gashin kanta bak’i ta saka wata hula hat👒 itama bak’a😂 shirin de na hauka tana goye da jaka k’atuwa ,ga kuma trolley tana ja,tana hango Rasheed tsaye yana jiranta ,ta fara d’aga masa hannu tun daga nesa ta rugo da gudu ta k’araso inda yake ,ya ja hancin ta yace ” welcome home my precious!! ” abunda yake kiranta da shi kenan ya kama mata kayan suka fice daga airport sai barracks!! Imtihaal akwai kyau ba na wasa ba a haske kuwa ta fi Ilham sosai ,saidai babu tsari a mode of dressing, yadda taga dama haka take shirinta kuma ga zafin zuciya musamman in aka mata dariya akan shigarta , kaf barrack babu wanda ya yi mata farin sani sai Rasheed don duk kusan d’abiun su d’aya ne, duk da ya fita nesa ba kusa ba. Saidai mace ce mai son murmushi ,da kuma bada dariya ,in har kana cikin 6acin rai tazo gunka toh har mantawa zakayi ma, sojojin nan babu wanda kuma baya shakkar ta da kuma 6acin ranta don baza su ga da kyau ba in har hakan ta kasance, in kuma tana tare da Rasheed shi kanshi rigimamme yake zama 😂 don tun asali dama rigimammun ne cliq nasu su hud’u ita da Rasheed sai Sadiq sarkin zuciya sai kuma Air force officer wato Al’amin, shi da yake ba a nan yake ba zuwa yake yi in ya samu tym……. ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/12, 12:29 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED☄💕 3⃣6⃣〰4⃣0⃣ Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Hirar su suke ta shek’a wa har suka iso gida ,ita y’ar gidan major ne kuma abokanai ne da Abba wato General, itama soja ce amma ta fannin bincike,Babu kuma wani wanda ya kaita k’warewa a Wannan fannin ,saboda haka ne ma ta fita Malaysia don karanta psychology and was successful! Babu abunda ya fi soyuwa a zuciyar ta irin Rasheed duk da shi kawai ya d’auke tane a matsayin best friend nashi wanda babu wanda ya kaita kusanci da shi ,ko su Sadiq ma basu san wani halin Rasheed yadda ta sani ba. Bayan ta huta, karfe hud’u na yamma ta fito zata gurin Rasheed ,ta saka wani over size Jean’s trouser blue, da wata rigarta shirt light blue takalmin k’afarta sneekers ne blue da fari, ta kafa irin hular nan me kama da na sanyi💂🏽, hannun ta rik’e da wayarta ta saka dayan kuma a aljihun ta babu abunda ya dameta tafiyarta kawai take yi, horn d’in motar da taji a bayanta yasa ta juya ,Rasheed ne cikin motar Army ,ya ja birki ya tsaya kusa da ita yana murmushi ,yace ” hop in!! ” ma’ana ta shigo motar , shiganta ke da wuya ,sai ga Ilham ta iso ,ta d’an Kwankwasa glass d’in motar ,bai wani damu ba ya sauk’ar don jin da wacce ta zo yau kuma. “Nazo ne in baka hakuri captain, I know I was wrong since from d very beginning, pls accept my apology” murmushi kawai Rasheed yayi ya d’aga glass d’in motar shi yayi gaba ya barta nan tsaye jiki a sanyaye. “Bro Wai waye wancan d’in” tambayar da Imtihaal ta fara jefan shi da shi kenan, yace ” don’t mind her precious! Bata da tarbiyya ne kwata kwata ,I want her to learn some morales☺ suna tafiya yana bata labarin abunda ya faru tsakanin shi da Ilham. Ta d’an yi murmushi tace ” forget that nutty girl and let’s have some ice cream🍦 yayi parking suka tsaya shan ice cream har kusan magariba sannan suka dawo,ya ajiye Imtihaal a k’ofar su sannan ya koma gida ,yana zuwa bakin gate nasu abun da ya gani ya bashi mamaki 🙄 da kuma haushi…… ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/13, 9:50 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED☄💕4⃣1⃣〰4⃣5⃣ Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Wai ke wace irin jarababbiyar mace ce? Abunda Rasheed ya fara furtawa kenan ,Ilham tayi murmushi tace ” captain nifa bazan bar gurin nan ba in har am not convinced kayi accepting apology na ba! I told you am d one who made d mistake,kuma na gyara kum………. Kafin ta k’arasa yayi murmushi yace “Fine!! Apology accepted little miss you may now take your leave(zaki iya tafiya) tayi murmushi tace ” thanks for that,ta juya ta nufi hanyar gida ,yana tsaye yana kallonta ,yadda take tafiya ma kad’ai abun kallo ne ,ya rasa gane yadda akayi tsanarta tabar zuciyar shi, yayi giving up so easily,yarinyar tana neman shiga zuciyar shi ne tabbas kuma duk yadda yayi ya kawar da tunanin ta a wannan dare sai ya kasa. Bangaren Ilham ma dai hakan take domin kuwa ya dad’e da samun mafaka a zuciyarta ,wannan kuma shine karo na farko da hakan ta faru da ita. A kwana a tashi yau kwanan su biyar da zama friends ,tunanin Rasheed duk ya gushe gaba d’aya tym d’in da ya saba bawa Imtihaal ya koma kan Ilham, shi a iya sanin shi Imtihaal friend nashi ce bai san ita a zuciyarta ya fi hakan ba ,Sadiq da Al’amin kad’ai suka san hakan ,suma ba don ta sanar da su ba sai don wani takardanta da suka gani ta manta a motan su ,duk wani feelings nata akan Rasheed ta rubuta. Sadiq tun da yaga yanda suka fara shakuwa da Ilham yasan akwai matsala babba ba kad’an ba. Rasheed na zaune a office nashi shi da Ilham suna hirarsu Imtihaal ta shigo da murmushin ta ,amma tana ganin Ilham ta turnuk’e fuska ta k’arasa ciki rai a dagule duk ta rasa abun da ke mata dad’i. ” precious! Tun d’azu nake so in k’ira ki muka tsaya hira!” Cewar Rasheed kenan. Ba tare da ta saurare shi ba ta d’auki wasu files da ta ke saman table nashi ta fice, ya bita da kallo cike da mamaki, bud’ar bakin Ilham tace ” k’anwar ka kamar bata sona! Yayi murmushi yace ” she’s my best friend” Ilham ta d’an juya ido tace ” oh I see, am sorry! ” ya ce no it’s ok she’s more like a sister to me,kuma ba bata sonki bane ,hala an 6ata mata rai ne, kinga its almost lunch time ,muje mu ci abinci mana” Ilham tayi murmushi ta mik’e suka fita tare. Tun fitar Imtihaal ta ke kuka har takai office nata ,Sadiq yaga wucewar ta har zai tsokane ta yaga halin da take ciki sai ya fasa ya nufi office din Rasheed ,ganin shi da Ilham ya bashi haushi ,ya juya ya tafi ,Rasheed zai k’ira shi yaga ya juya shiyasa ya kyale shi. Imtihaal ta gama aikace aikacen da zata yi a office ta fice,tana fita a motarta su kuma suna dawowa suka yi ido hud’u da Rasheed amma ta d’auke kai ,abunda bata saba ba. Though abun ya d’aure mashi kai amma ya wuce itama ta wuce. Daidai inda zaiyi parking Sadiq kuma yana mota shima zai fita ,duk da sun had’a ido ,ya ja motarshi ya fice da ya lura cewa Rasheed gurin shi zai zo…………… ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/13, 3:01 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED☄💕 4⃣6⃣〰5⃣0⃣ Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Wutar d’akin dim light ne kalar blue hakan ya k’ara kyau a d’akin ,Kwance take tana danna laptop nata ,ta kifa ciki a kan pillow ta rungume teddy bear da hannun ta na hagu ,gashin kanta kuwa a kitse yake ya biyo ta wuyanta ,duk da ma ba wani tsayi ne da shi na sosai ba ,saidai ya kusa kirjin ta, hawayen idonta ne ya gangaro ya d’iga a kan wata takarda da ke gaban ta kusa da system din. Tana cikin wannan halin wayarta tayi k’ara, sunan Rasheed da ta gani ne yasa ta ajiye wayar ya kira har kusan sau shida yaji shiru ,kuma tabbas ya san ba bacci take yi ba sai ya hak’ura. Kira na bakwai ta d’aga wayar zata wurga gefe sai ta lura ba Rasheed bane ,K’awarta ne Rukayyah kaxs tana zama Kaduna ,ita kuma ta karanci cosmetology (karatun duk wani abun da ya shafi kwalliya)a London bata ma dad’e da dawowa ba. Imtihaal ta share hawayen fuskarta sannan ta d’aga wayar ,suka sha hirar su Ruky tace mata zata zo Abuja next week, Imtihaal cikin murna sukayi sallama da Ruky kaxs sannan ta kwanta. Rasheed kuwa bayan nan ma yayi ta trying number busy har ya gaji ya bari ,shi Sam ya kasa gane matsalar Imtihaal dat day……. K’arfe takwas na safe ta fito daga chan nesa ta hango Rasheed da murnan ta ta nufi wajen shi don ta fara surprising nashi saboda yau ne birthday nashi da gudun ta takarasa tana d’aga masa hannu. Rasheed ma ya mik’e yana murmushi ,ya daga hannu yana waving sai da ta k’arasa gurin da yake tsaye kawai taga ashe ba ma ita yake gani ba ,da Ilham yake jiki a sanyaye ta juya da gift din hannun ta ta nufi hanyar gida ,sai Lokacin da ta juya kawai ya ganta ,kafin ya tsayar da ita Ilham ta shiga gaban shi tace ” Happy birthday captain!!! Gami da mik’a masa wani box an yi wrapping. Yayi murmushi yace ” thank you ” Ilham ta kauda kai tana wata murmushi wanda na kasa ganewa munafurci ne ko kuma me????……… ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/13, 9:23 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED☄💕 5⃣1⃣〰5⃣5⃣ Na 🏵Jeedah ja’o🏵 Har aka kusa gama celebration na birthday party nashi Imtihaal bata zo ba ,yayi k’iran har ya gaji, tun da Imtihaal ta taso bata tab’a fashin zuwa wani occasion da ya shafe shi ba tun ma bata san ciwon kanta ba ,amma yau kad’ai tayi breaking record. A gajiye suka koma gida shi da Sadiq da Al’amin don shi ma ya zo , Rasheed ya zauna bakin gado yana Kallonsu suna ta hidimomin gaban su, guys ko wani zai fad’a min abun da ke damun My precious!!!? Sai da yayi tambayar har kusan sau uku sannan suka dubi inda yake ma ,Sadiq yayi k’arfin hali yace ” banda abunka Rasheed ina zamu sani tunda duk a tare muke da kai? Al’amin yayi murmushi yace ai se Kaje ka tambayeta lover boy !! Ko ba haka bane??” Duk suka yi kwanciyar su suka kyaleshi a gurin. Yaji zuciyar shi ta kasa danne wa kawai ya sa riganshi ya fice yasan inda zai sameta a wannan lokacin saboda haka ya wuce kai tsaye zuwa wajen da suka saba shan iska ta bayan wani lalataccen motar yak’i ,tun suna yara a nan suka saba zama lokacin zafi ko lokacin wasannin su ,gurin ya zame musu tamkar gida don wataran Imtihaal har bacci take yi a gurin. Zama Yayi a gefen ta yace” Haba my precious!! Can’t you tell me what wrong I have done to you da zan yi deserving such a punishment? ” wani mahaukacin kallo ta watsa masa ta mike tsaye,ba shiri shima ta mik’e.” Haba don Allah! Yanzu saboda Allah ni nake punishing naka ko kuma kai kake azabtar da zuciya ta ? Tun da ka samu Ilham na zama kamar kashi a gurin ka ,ka yada friendship namu, ka manta da ni , you don’t even come over to say sorry !! Now tell me ,ka fad’a min tsakanina da kai wa yake wahalar da wani ? In da kasan akwai wata wanda matsayin ta zai fi nawa da baka sa ni a ranka yadda zan kasa daurewa ba!!!” Rasheed cikin mamaki ya ce ” Ban fahimce ki ba Imtihaal, what are you trying to say?!!me kuma ya kawo wannan maganar? Imtihaal na zaci mu best friends ne kawai?!!” Cikin hawaye Imtihaal tace ” Best friends kawai!!? Did you know how much I go tru when I see you roaming about with that bloody bitch you call Ilham??!! Did you know how much pain it got me into ??” Rasheed ya daka mata tsawa yace WHY!!WHY DID YOU FEEL THIS WAY IF I ONLY SEE YOU AS MY BEST FRIEND??!!!! cikin razana da k’arfin hali tace “Because I LUV YOU RASHEED!! DATS WHY!!!” Rasheed yayi k’asa ‘kasa da murya ya ce ” am sorry Imtihaal ,ban san yaushe hakan ta faru da ke ba ,koma yaushe ne I can’t lie to you ban d’auke ki a matsayin wata abar ba sai a matsayin abokiya ta wanda muka taso tun yarinta , I am in luv with Ilham na zaci kece ta farko da zaki nuna farin cikin ki akan hakan but sai na samu akasin haka, am sorry Imtihaal bana ganin hakan zai d’aure a tsakanin mu ,pls ki tsaya a limit naki as my best friend. Ko kin manta cewa kikayi kin min alk’awari in dai abu zai sa ni farin ciki toh kece kan gaba a nema min shi? My precious Ilham na d’aya daga cikin su ,I loved her so much am sorry my precious. Yana kai Wannan bata saurari me zai fad’a a gaba ba ta ruga a guje ta yi cikin gida yayinda shi kuma ya bi bayanta da kallo har ta 6ace ,ya juya shima zai koma gida ya ci karo da su Al’amin suma cikin k’walla. Ya wuce su ba tare da ya furta ko kalma d’aya ba ya shige gida. Hannun Sadiq rik’e da wannan takardan da Imtihaal ta dad’e tana bayyana soyayyar ta ga Rasheed a ciki… ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/14, 6:25 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED☄💕 5⃣6⃣〰6⃣0⃣ Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Daren nan babu wanda ya runtsa a cikin su, ba ita Imtihaal ba har Rasheed, Sadiq, da kuma Al’amin! Da sassafe Imtihaal ta fita aiki yau, shirin ta de yadda ta saba ne yau kam ko d’an kwallin ma da ta saba sawa bata saka ba ,idon a kod’e ta fito. Ya kai kusan minti talatin yana tsaye a bakin office nata yana ganin halin da ta ke ciki ,jiya kad’ai amma yau bazaka d’auketa a sisi ba ,k’arasawa ya kasa yi don ya fi so tayi kukan ko zata d’an samu relief, a hankali Sadiq ya fice ya rufo mata k’ofar,shi kanshi ya mugun tausaya wa baiwar Allah, kuma da yana da hali ko ikon sa Rasheed yayi da ya saka ya aureta ko baya so. Tun daga wannan ranar Rasheed ya daina sa Imtihaal a ido ,duk guraren da yasan zai ganta ma baya samun ta, ta 6angarenshi komai yana tafiya yadda yake so soyayyar su sai ‘kara girma take shida Ilham. Sadiq kuwa baya wani shiga harkarshi sosai balle kuma Al’amin da baya ma gida ya koma aiki…… Tana Kwance a Falo ta k’urawa TV ido duk da ma bata san me suke yi ba don hankalin ta baya jikinta Sam,ta shiga wata duniyar tunanin ta daban, knocking d’in k’ofa da akayi ne ya sa ta dawo hayyacin ta wannan ma har me bugawan ya gaji da bugun, da sauri ta tashi ta bud’e k’ofar tana share d’an hawayen da ke fuskar ta. Rukey kaxs ce tsaye da y’ar jakar ta a hannu an sha kyau, abunka cosmetologist😜 ta shigo sai azalzalar Imtihaal take yi da masifa Wai ta barta tana ta knocking sai yatsun ta sunyi ciwo. Imtihaal tayi murmushin dole tace my ‘kawas kenan yi hak’uri ban ji ki bane shiyasa ” a take Ruky ta gane Imtihaal is off mood ,Tace “k’awata me ke damun ki ne haka gaba d’aya kin rame kin chanza ,ke matsalata da ke ko dan powder baki san ki shafa ba🙄 , bama wannan ba pls tell me me ke damun ki ne?? Imtihaal ta rungume Ruky tana ta kuka sai da tayi mai isarta sannan ta kwashe labarin komai ta fad’a mata ,Ruky ta tausaya mata sosai domin itama shaida ce yadda Imtihaal ke matuk’ar k’aunar Rasheed ,a iya sanin ta kusan shekaru goma yanzu kenan. Ruky tayi murmushi na takaici tace kar ki damu k’awata!! If it is your destiny to Marry Rasheed ko ta wane hali ne zai aureki in kuma ba haka bane babu yadda zakuyi ko da kuwa yana son ki ,amma kafin nan ,ina so ki nuna min wannan Ilham d’in in gani ,zan ga me ya gani tattare da ita da har zai ‘ki ki duk yadda kukai matuk’ar shak’uwa!! Imtihaal ta share hawayen fuskar ta tace yanzu dai my dear tashi Kije kiyi freshening up ,gacan abinci a dining sai kici ki huta kafin magariba tayi. Ruky ta mik’e ta shiga ciki itama duk ranta a dagule don haka kawai jinin su ya had’u da Imtihaal jin ta takeyi kamar yar uwarta na Jini……. ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/18, 6:05 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED☄💕 6⃣1⃣〰6⃣5⃣ Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Tafiya suke suna shek’a hirarsu irin ta yaushe gamo ita da Ruky kaxs, suka hango Rasheed tsaye yana waya da ta fuskanci ya hango su har ma ya fara tahowa kawai suka koma suka shige mota, duk ranshi a dagule ya bi motar tasu da kallo cike da mamakin precious d’in shi ,bai yi zaton akwai abunda zai rabasu cikin sauk’i haka ba ,saidai kash!!! Bai san halin da zuciyar ta ta shiga ba dalilin shi ,shi a ganin shi zata yi supporting soyayyar shi da Ilham ta mance da soyayyar ta a gareshi wanda hakan ba mai yiwu wa bane Sam, Rasheed bai san me so yake nufi ba bai kuma iya babanta tsakanin so da kuma k’auna ba!!” Rukey kaxs tace , Haba ‘kawas ban ga abunda wannan Ilham din ta fiki da shi ba, kyau? Matsayi? Ko kuma me? In ma akwai bai wuce na wanka da take d’auka ba kuma nasan hakan ne zai ja hankalinshi zuwa gareta in ba haka ba menene? Gaskiya dole ki bar irin wannan shigar hauka da kike yi ,ki duba fa ki gani kwata kwata ko d’an gyaran gashin nan ma bakya yi kema ki fita a matsayin ki na mace me class! Ni na tabbata Rasheed na k’aunar ki ,bai iya banbance tsakanin kauna da kuma so ba , da wani ne bazai ma damu ya dinga kiranki duk da bakya d’aga wa kuma in ya ganki ya nufi inda kike ba! Ina tabbatar miki kawai saita mishi zama zamuyi sai ya dawo hankalin shi. Imtihaal tayi murmushi kawai ta shiga d’aki. Satin Imtihaal d’aya tare da Ruky suka yi shirin tafiya India don attending auren wata friend nasu RASIKA CHANDRA wanda sukayi schl tare a Malaysia da imtihaal duk da ma Ruky bata Santa ba don a London tayi nata karatun amma zata rakata. Suka yi sallama da mutanen gida driver ya kaisu har airport basu wani dad’e ba jirgin Yayi take off 🛫sai 🇮🇳 Rasheed ya gaji da trying numbern Imtihaal shiru tun yana zaune ya mik’e tsaye daga bisani ya wurgar da wayar ya dafe kanshi, hakan yayi daidai da shigowar Ilham yau itace d’auke da files din da Imtihaal ta saba kawowa,ya dubeta sama da kasa yace ” ina my precious na ganki da files haka?” Tayi murmushi tace En… Bata nan ne ,sun jj eee India dazu suka shine Major yayi assigning d’ina kafin ta dawo don zata kai at least three weeks a can. Rasheed ya mik’e a fusace yace why won’t my precious even inform me about that?? ” yayi maganar cikin 6acin rai ya karb’i files d’in daga hannun Ilham yace ” pls zaki iya tafiyah gami da nuna mata k’ofa ” cike da mamaki da takaici ta juya ta fita ba musu ta rufo mishi k’ofa . a cikin ranta tace “wato har yanzu bai cire ranshi a kan yarinyan nan ba ko? Amma ba komai na lashi takobi bazan sake na koma ruwa ba har da me tafini da zai wani damu da ita haka ? Kazama da ita!!!:roll:” ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/19, 8:39 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED☄💕 6⃣6⃣〰7⃣0⃣ Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Satin su uku a India su Imtihaal suka yi haramar dawowa Nigeria , cikin wadannan satikai kuwa haukacewa ne kad’ai Rasheed bai yi ba ya rasa gane meyasa ya kasa fitar da Imtihaal a zuciyar shi, duk da dai yana son Ilham ne kad’ai,Sadiq de ya zuba mishi ido ne don ya tabbata Rasheed bai san me ake nufi da asalin k’auna ba!! Taku take irin na k’asaita d’aya bayan d’aya take sauk’owa daga benen takalmin k’afarta blue mai tsini (high heels) designer na Manolo, doguwar rigarta fitted ce na wani hadadden material shima turquoise blue designed by Jimmy choo ,sai purse nata shima design na Manolo, sark’a dankunne, bangles kuma design na Megna ne (wata indian designer) sannan tayi rolling da gyale kalan stones d’in rigar wato dark blue, tana tafe tana y’ar hirarta ita da Kawarta….. Wani kyakkyawan mutum sanye da suite bak’i da rigar ciki kuma fara ce ya d’aura black and white polka dot necktie, hannun shi rik’e da briefcase ya fito daga cikin jirgin shima sai uban sauri yake dokawa ya kara wayar shi a kunne , daidai exit na airport d’in ya ci karo da ita wayar hannun nashi ta fad’i, IMTIHAAL ta juyo da sauri tana cewa “oops!!! Am very sorry sir! Actually I didn’t notice you coming this way ” ta durkusa ta d’auko mishi wayar ta mik’a masa. Ya karb’a cike da murmushi yace ” it’s alright thanks ” Muryar shi ma kad’ai abun sauraro ne. Suka fice daga airport kowa yayi nasa waje. Abun mamaki shine waje d’aya suka nufa, Ruky kaxs tace “My Frnd kiga wancan mutumin kamar fa biyo mu yayi ,Imtihaal tayi dariya tace ba biyomu yayi ba ga dukkan alamu wani babba ne a nan don naga tag d’in a jikin suit nashi” Ruky tace *Better!!!. K’afarta ta fara jefowa daga motar, fuskarta ta saka sunglasses saboda rana da ake yi saidai brown colour ne ba bak’i ba, tana fitowa duk kallo ya koma kansu basuyi tsammanin an taru haka ba is like General yana expecting bak’i, kowa neat cikin uniforms tsaro ta ko ina an sa tsaro shi yasa ma bata wani damu ta k’arasa ciki da motan ba suka sauk’a don k’arasawa ciki. Kaf cikin wad’anda suka Santa babu wanda ya gane cewa Imtihaal ne duk kowa ya sake baki don basu tab’a ganin kyau irin Wannan ba. Babban abun mamakin shine even Captain Rasheed doesn’t seem to recognize Imtihaal!!!:oops:. Ana wata ga wata!!!! Shin waye mutumin da suka yi clash a airport? Is captain Rasheed really captain Rasheed?? And if he is me yasa ya kasa nuna k’auna ga Imtihaal?? This really change the story my dear readers coz this is where the truth unveils!!!!! Masu karatu ayi min afuwa kun Jini shiru kwana biyu I was very busy dis day’s, but I’ll try and make it up to u. L💗v you all!!! ☄🏵Jeeddah ja’o🏵☄ [4/20, 9:42 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 💗7⃣1⃣〰7⃣5⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Mutumin da suka ci karo a airport da shi bai zame ko ina ba sai inda General (Abbah )yake tsaye suka yi wata maganar su k’asa k’asa sannan mutumin ya yi cikin gidan General d’in wato gidan su Rasheed, yayin da captain Rasheed ma ya bi bayanshi. Major Ahmad Suraj (baban Imtihaal)ya hau stage ga press a gaba ya gama speech nashi ,haka dai suka gama aka watse daga taron kowa yayi nasa guri. Band’aki ya shiga ya tsaya gaban mirror yana kallon fuskar shi,a hankali yake shafa fuskar yana murmushi domin ya tuna da abun da yafi mishi sauyuwa a zuciyar shi wato Imtihaal, ya gama kallon fuskar shi sannan ya fara yage mask din dake fuskar abun mamaki fuskar babu wanda wanda zai gani yace ba nashi bane ashe na roba ne!!! Dagowan da zaiyi nima Hauwa’u saida na tsorata😳 domin kuwa babu abunda ya raba shi da captain Rasheed !!! Ya sani cikin zullumi domin masu karatu in baku manta ba captain Rasheed ba yan biyu bane ,sannan bashi da wa balle kani !!!muje zuwa!!……… Imtihaal na zaune a palour tana ganin video na auren da sukaje a India d’in sai dariya take yi,taji an buga k’ofa ,tana lek’a wa taga Captain ne sai ta k’i bud’ewa ta koma tayi zamanta, ya gaji da tsayuwa ya jiya ya tafi duk ranshi a dagule domin kuwa bai san me ya faru ba. Yana tafiya hannun shi rik’e da wani Jan jewelry box mai kyau kawai yaji an ja riganshi ta baya a fusace ya juya yace ” and who the hell are you?!! Cike da mamaki Ilham ta ce “Haba captain!! Yau kuma baka ganeni ba ko? Toh Sannu sarkin zolaya gaskiya Muryar ka ta chanza!!” Rai a 6ace ya daka mata tsawa yace ” look I don’t know who the hell you are ! Just get out of my way!! A firgice ta matsa gefe idanuwan ta suka kad’a sukayi jaa ta bi bayanshi da kallo. Dakin shi ya shiga ya zauna shiru sai ga Sadiq ya shigo d’akin ba tare da ya kulashi ba ya hau cire kayan jikin shi, Rasheed ya dubeshi yace ” dude Wai nikam my precious bata nan ne? Ko bata dawo daga Malaysia bane?? Sadiq ya juyo cikin sauri ya rungume shi yace ” its you dude!! Ashe kai ne ,yaushe ka dawo ko kira bakayi ba? Duk a lokaci guda yayi maganganun nan. Rasheed yayi wani latest murmushi wanda ya kara fitar masa da kyau yace ” ai numbern ne yak’i shiga kasan Pakistan sai a hankali !! Especially chan Kashmir d’in. Sadiq Yayi darya yace ” abokina am glad you are back don wallahy abubuwa sun kusa dagule wa a nan fa , Duplicate Rasheed din nan yaso ya 6ata rawar shi da tsalle!!!:oops::oops: Rasheed ya mik’e da sauri yace ” me yayi? Imtihaal ta dawo ne?? Ina shi duplicate Rasheed din yake?? Duk a lokaci guda Rasheed yayi tambayoyin. Sadiq ya sauk’e Ajiyar zuciya ya kwashe labarin abunda ya faru tun daga farko har zuwa dawowan Imtihaal da had’uwa duplicate Rasheed da Ilham………….. 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [4/20, 10:45 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗7⃣6⃣〰8⃣0⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Rasheed ya mike a fusace as well very heart broken saboda bai yi tsammanin har duplicate Rasheed din nan zai yi affecting love life nashi ba ,tabbas zuciyarshi tayi bak’i!! Suna cikin haka sai ga duplicate Rasheed ya shigo ,yana faman cire mask na fuskan shi wanda akayi shi mai kama da Rasheed Sak!! Fari ne kam kuma shape na fuskarshi irin na Rasheed ne abunda yasa ma aka za6eshi kenan duk cikin sauran captains domin har tsayin su d’aya ne!! Yana gama cire mask din captain Rasheed ya zuba masa wani uban mari wanda saida yaga wuta💥 a take ya rik’e kuncin shi yana kallon Rasheed. “Am very disappointed in you khaleel!!! Sunan da RASHEED din ainihi ya K’ira duplicate Rasheed da shi kenan. Amana fa na baka ! Just because I trusted you I left you amanar abunda yafi soyuwa a zuciyata ,na zaci zaka nuna mata gata har in dawo sai ka chusa mata tsananin tsanata a zuciyarta! Ka lalata min rayuwa ta!!! Rasheed ya sake chukume kwalar rigar khaleel yace ” kasan Allah in har Imtihaal is not able to forgive the mistakes you have made in my position I am going to teach you a lesson that you will never forget in a hurry!! Ya fadi hakan ne cikin rawar murya idanuwan shi sun ciciko da k’walla jikinshi har rawa yake yi. Hayaniyar da Inna ta jiyo ne yasa ta hauro sama domin ta duba ko me yake faruwa, a gigice ta k’arasa inda suke ta kama hannun Rasheed wanda da kyar ta iya janye shi daga jikin khaleel tayi waje da shi ,yayin da khaleel ya nemi bakin gado ya zauna sai maida numfashi yake duk jikinshi na rawa ,cikin zuciyar shi yace ” kai Wannan mutumin akwai k’arfin bala’i” yana yi yana shafa gurin da aka shak’e shi…….. “My son! Lafiyar ka kuwa? Yau khaleel d’in kake shak’e wa kamar zaka kashe? Ko kayi hauka ne, mutumin da ya karb’i matsayin ka ya goge duk wani personality nashi don kawai ka je ka gama assignment d’in da ke gaban ka har ma ya kula maka da duk wasu business naka bai yi wa iyayen shi ba shine zaka yi wa haka?? Rasheed bai yi wata wata ba ya kwashe labarin duk abubuwan da khaleel (Duplicate Rasheed)ya aikata ya fad’a mata ,Inna tayi mamaki matuk’a kuma ta san yadda d’anta ya ke k’aunar Imtihaal duk hankalin ta ya tashi domin kuwa tasan akwai matsala babba idan har ya rasa abun da yake k’auna. Tayi shiru jiki a sanyaye shima ya tashi ya mik’e ya fice daga d’akin daidai ana shiga sallar maghrib,tare suka yi sallan da Sadiq suna idarwa bayan sun yi adduoi basu zame ko ina ba sai k’ofar su Imtihaal akayi sa’a house maid d’in ce ta bud’e musu k’ofar ,suka gaisa sannan tace su zauna zata yi magana da Imtihaal d’in. Suna zaune suna jira wajen minti talatin har sun fara cire rai zata ma fito sai gata,saukowa take daga stairs tana danna wayarta, hannun ta yasha henna tattoo (lalle) riga na atamfa dinkin high waist da skirt ne a jikinta tayi dauri irin me step step din nan ,k’afarta slippers ne baki me kyau tabbas sai lokacin yayi recalling cewa da Imtihaal d’in shi suka yi clashing a airport ! Lallai precious d’in shi ta chanja Sam !! She’s so beautiful but yayi missing crazy looks nata:D. Guri ta nema ta zauna tana k’are musu kallo d’aya bayan d’aya sannan suka gaisa ,ta amsa musu babu yabo ba fallasa. Abun takaici shine duk yadda Rasheed yaso yayi explaining abubuwan da suka faru ,Imtihaal ko sauraron shi bata yi hasalima cewa tayi dama ba son tsakani da Allah yake mata ba ,ta gane kawai yanzun ma don yaga tayi kyau ne shiyasa ya biyota kamar yadda yake bibiyan Ilham!! Ta mik’e ta fice abunta ta barshi a gurin baki a sake. Jikin a sanyaye ya ajiye wannan jewelry box d’in da ya kawo mata da yamma ta ‘ki bud’e kofar a kan center table suka fice house maid d’in ta rufo k’ofar……. 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [4/20, 1:34 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗8⃣1⃣〰8⃣5⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Yana Kwance kan gadon shi daga shi sai 3quater trouser sai faman kirga ceiling yake yi ya yi zurfi sosai a cikin tunanin da yake yi ,har Abbah ya shigo ya zauna kusa da shi bai sani ba ,ya ajiye files din hannun shi sannan ya had’a hannun shi da na d’an nasa duk da haka Rasheed bai ko kifta ido ba ya dauko wani glass cup da ruwa a ciki ya zuba mar a fuska. A d’an firgice Rasheed ya tashi ya zauna sannan ya jingina da gadon yana ajiye numfashi sama sama. Abbah ya fara da cewa ” my dear I know you are having hard times tun da ka iso garinnan d’azu ,kuma nasan game da Imtihaal ne coz Sadiq ya fad’amin komai in fact I have spoken with the Major about issue naka da Imtihaal,soon zamu je nema maka auren ta ” Rasheed na jin haka ya zaro ido ya gyara zama. Kafin yace wani abu Abbah ya ce yanzu dai ga wad’annan files din ka duba su don gobe akwai possibility za’a buk’acesu during the meeting kuma akwai issue na wad’annan Sargent guda biyu Ezekiel da simon make sure an gano wanda yayi laifin!!” Abbah yana kai wannan ya nufi kofar fita ,gami da turo masa k’ofar d’akin ,shi dai Rasheed murna fal ransa Imtihaal ta kusa zama mallakin shi. Yau da ruwan sama mai k’arfin gaske aka tashi tun bayan sallar asubah ,babu wanda ya shirya fita aiki kowa yana Kwance ,Imtihaal na tsaye a saman balcony tana ta mik’a hannu tana wasa da ruwan sama ,sai dariya take yi a haka har kusan k’arfe tara na safe ruwan ya d’auke, garin yayi matuk’ar sanyi ba kamar jiya ba! Bai ma gama d’auke wa ba ta hango Rasheed ya fito da motarshi yayinda mai gadi ya mayar da gate ya rufe shi kuma ya yi parking motar ya fito waje yana waya ,hannun shi guda kuwa yana buga key d’in motar da ke hannun shi. Duk abun da yake yi tana tsaye tana gani, ta tuna da gift d’in da ya ajiye mata jiya a Falo ta ruga ta nufi gurin ta k’urawa box din kallo kafin ta sa hannu ta bud’e. Wani hadadden silver ring ne me dutsen diamond a saman shi da kuma necklace nashi💍 mai matuk’ar kyau ,designed by Michael korrs. A k’asan zoben akwai wani card mai kyaun gaske an rubuta, ” will you marry me? ” 🙄 ta dad’e a gurin tana kallon card d’in ashe Ruky kaxs na bayan ta. Ruky ta wafce card d’in ta gudu tana dariya Imtihaal ta bita da gudu itama suka fara zagaye falon tana cewa ” Oooh my Frnd pls ki bani mana !! Ai kuwa bata bata ba sai da ta gama karantawa duk suka zube a kasa tsabar gajiya suna maida numfashi kamar wanda aka sasu gudun dole. Ruky ta mik’e da wuri tace ” k’awata duk da wannan fa ba cewa nayi kiyi giving up so easily ba!! Ki nuna masa baki ma san da zancen ba kuma by the way plan d’in mu zai fara aiki yau, kin san na yarda da Ahmad sosai ,saurayina ne zai iya yin komai for my sake saboda haka zai zama acting boyfriend naki ,har sai Mun tunzira Rasheed dinki ya gane kuskuren shi !! Duk suka bushe da dariya sannan suka cigaba da hirarsu……… Rasheed na zaune a office nashi sai fama yake da computer yana duba files d’in da Abbah ya bashi,jin karar bud’e k’ofar shi da akayi ne yasa ya d’aga kai don ya gane ma idon shi wanda ta shigo…….,…………. 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [4/21, 6:38 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗8⃣6⃣〰9⃣0⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Kallon kallo kawai suke ta yi kafin daga bisani ya mik’e tsaye cikin 6acin rai yace ” what the hell did you think you have done!!? Yaya zaki shigo min office ko sallama babu ? Ko kin dauka nan wajene wanda zaki shiga sakaka haka?” Ilham ta gyara murya tana juya manyan idanuwanta ta k’araso gaban table d’in tace ” seriously ka cika zak’ewa d’azu fa muka sha hirarmu da kai a parking lot ,yanzu kuma Kazo kana chanja salo anan nifa gaskiya banason irin Wannan ” Rasheed ya daka mata wani uban tsawa mai tsoratarwa ni kaina saida na girgiza balla ita da take kusa da shi yace ” don’t you dare lie at me!! Yaushe muka hadu da ke?? Kije chan ki nemi sa’an ki kar ki sake sa kafarki a office d’ina in kuma ba haka ba I will definitely ruin your career!! ” Ilham ta bushe da dariya tace ” lallai kuwa zamu ga waye zai yi ruining career na wani a tsakanin ni da kai ta buga table din da hannun ta a fusace ta fice ya bita da kallo yadda take rangwada ya k’ara tabbatar masa cewa y’ar bariki ce wannan ta asali ,shi gashi ko sunanta bai sani ba. Ya doki table din gabanshi da hannun shi hakan yasa har wasu takardu suka zube, yace ” what kind of life is this!! Shekaran jiya kawai na shigo k’asar amma komai ya cunkushe min, khaleel ya bi son ransa ya rabani da my precious and now all of a sudden ga wata jaka tana son shiga rayuwa ta babu dalili….. ” Duk abunda ya faru a kunnen Imtihaal ne don ta d’auko files zata kawo mishi ne ta hangi Ilham a cikin office din ,taji duk maganganun da yayi, tabbas hakan yayi tallying da maganar da suka so su sanar da ita shida Sadiq!!. Nan ta daskare ta kasa ko motsawa domin yanzu itama tayi believing cewa ba Rasheed bane na farkon ,because of the way he acted towards her!! A ranta tace but wannan ba shi bane zaisa nayi giving up so easily!!! Tayi wata yar murmushi. Tana cikin wannan yanayi captain ya fito daga office bata ma sani ba saida yayi banging k’ofa sannan ta tsorata ta dawo hayyacin ta ,kamar mai kinkina take magana a lokaci guda tana mik’a masa files din hannun ta, ” gashi wannan shi za’a turawa lieutenant colonel” tana kai wannan ta juya ta barshi a gurin shima da sauri ya bi bayanta ,ta shiga motar ta bai wani damu ba shima ya bud’e ya shiga. Motar ta d’auki silence na wajen mintina biyar ,Rasheed kuwa kawai k’aremata kallo yake yi yadda tayi matuk’ar kyau lallai uniform d’in ya karbeta sosai,ita ma kallon nashi take yi duk sun shagala. Khaleel ya fito kenan yana ta kad’a key d’in motar shi ya hango su ,ranshi a 6ace zuciyan shi na tafarfasa yace ” Oohh!! So this is it !! Ai bana so game din yayi over a nan kusa!! Rasheed ban yi expecting haka da wuri ba amma all the same tunda plan A bai zama accomplished ba lallai plan B zan sako a gaba believe me sai na tarwatsa maka duk wani farin ciki kamar yadda nima na rasa nawa farin cikin!!!! Ya ci gaba da tafiyar shi yana lalumar wayar shi a aljihu……….. WAYE KHALEEL?? 💗🏵 Jeeddah ja’o🏵💗 [4/23, 12:13 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗 9⃣1⃣〰9⃣5⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Khaleel yana d’aya daga cikin soji masu bincike, aikin shi d’aya da Imtihaal saidai itace babba a gurin sun kuma san amfanin ko wanne irin makami daga k’arfin shi har zuwa weakness nashi da kuma yadda za’a sarrafa shi ,in fact duk wani file na abubuwan gurin yana hannun su ne…… Khaleel yana da k’anwar shi mai suna Husnah ,kuma asalin haifaffun garin Kaduna ne ,transfer akayi mishi aka dawo da shi Abuja saboda kwazon shi kuma da kaifin basira ya karb’i lambobin yabo da dama, shi da imtihaal. A dalilin Imtihaal suka shaqu da Rasheed har suka zama friends. Husnah k’anwar khaleel tana matuk’ar k’aunar Rasheed yayinda shi kuwa Rasheed bai d’auketa a karan komai ba face k’anwa ,khaleel kad’ai ya san haka… Wani lokaci kimanin shekaru uku da suka wuce khaleel ya umarci Husnah da ta bayyana sonta ga Rasheed kuma ta yarda, ta samesu zaune shida Al’amin suna hirar Imtihaal sai ta ‘boye a bayan wani pillar tana jin su. A nan ne hankalin ta ya tashi domin kuwa Rasheed ya bayyana irin son da yake wa Imtihaal kuma yanda ya bayyana ta tabbatar babu abunda zai iya shiga tsakanin soyayyar shi da ita bai kar shi ba!:oops:ko Al’amin ma kasa cewa komai yayi don yasan yadda zuciyar Rasheed take in har aka tab’a abun da ya riga da ya shiga ranshi!! Husnah ta ruga a guje ta nufi gida ,khaleel na zaune ta wuce shi da gudu tana kuka bata zame ko ina ba sai cikin d’akin ta ,ta rufe , khaleel yayi yayi ta bud’e tak’i bud’ewa hankalin shi ya tashi. A bakin k’ofar ya kwana har gari ya waye yana tashi kamar zai bud’e kofan kuma sai ya fasa yayi tunanin bacci take yi ma ,sai ya wuce masallaci ,kusan k’arfe bakwai ya shirya zai fita sai ya gwada murd’a door handle din kawai kofar ta bud’e……… Tunda yake bai tab’a shiga tashin hankali irin na ranan ba , a gurin ya durk’usa jikinshi na rawa kamar mazari ,yana hawaye da kuka mai sauti na ban tausayi ,ya d’aga kanshi yana kallon ta Kwance bakinta duk Jini har ta hanci ga kumfa ,wasu kananan magunguna a zube a k’asa hannunta guda ta damk’e wata paper ,ya d’aura kanta a cin yarshi yana hawaye yana karanta abunda ta rubuta. Mikewa yayi tsaye idanuwan shi duk sun kad’a sun yi jajir ya damk’e paper d’in yana ambaton sunan Rasheed har wajen sau uku sannan ya fice daga d’akin ,dama basuda kowa sai k’anwar baban su itama tana cikin gari don tayi aure ,anan akayi janaiza ,khaleel tun daga wannan ranar ya dauki alkawarin sai ya zubar wa Rasheed hawaye domin dalilin shi kanwarshi ta hallaka kanta kuma ita ce Hasken idanuwan shi a rayuwa bashida abunda ke saka shi farin ciki irin Husnah.. Amma kuma cikin ruwan sanyi ya yi niyyar yi. Wannan yasa lokacin da Rasheed zai yi tafiya zuwa Pakistan General Abubakar Rasheed ya zabi khaleel yayi shige irin na Rasheed domin kar a yi suspecting wani abu a base ,saboda shima Rasheed da wata fuska zai shiga Pakistan din ,mission din ba karami bane , khaleel ya ji dadi da jin haka yana ga kamar wannan shine step na farko da zai fara amfani da shi don rusa farin cikin Rasheed, kafin ya tafi kuma babu wani day to day activity na Rasheed da khaleel bai sani ba ,domin dole ne yayi acting as Rasheed, harta lokacin da Rasheed ke waya da Imtihaal an sanar da shi ,da duk wasu abubuwan da ya kamata ya sani tunda shi basajan Rasheed ne!!….. Zuwan Ilham ya ‘kara masa k’arfin guwiwa na tarwatsa soyayyar Rasheed da Imtihaal!! Wannan kenan 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [4/24, 9:05 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗9⃣6⃣〰1⃣0⃣0⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Imtihaal ta murd’a key d’in motar ta fice a d’ari ,shi kuwa Rasheed na zaune yanda yake yana kallonta bata fasa gudun ba kuma ba hanyar da ya kamata subi ta bi da su ba , da yaga abun natan na yi ne sai ya ce ” park d damn car Imtihaal ko so kike ki hallaka mu ne?bata bi ta kanshi ba ,direct wani city Hall ta wuce da shi shi de bai yi magana ba tun daga wancan maganar ta bud’e kofa ta fice shima hakan yayi ya bi bayanta though bata umarce shi da ya yi hakan ba….. Hall d’in cike yake da sojoji wad’anda ake damawa da su a Army wasu ma bak’i ne daga Niger ,totally Rasheed ya manta da za’a yi taron tuni ya fara Sosa ‘keya Imtihaal ta juyo sai dariya take masa ,da iPad d’in hannun ta ta bugi kafad’ar shi sannan ta wuce ciki ta barshi nan a tsaye ranshi fal farin ciki yau abunda yafi soyuwa a zuciyar shi ta yi managing to forgive him🙂 sannan ya wuce ciki. Major Ali wato mahaifin Imtihaal ya ji dad’in ganin reunion d’in y’arsa da Rasheed domin kuwa babu abunda ke burgeshi irin yaga y’ar shi cikin farin ciki kasancewar ta marainiya , bata samu motherly love ba sai daga gurin mahaifiyar Rasheed abunda ya sake ‘kara musu shakuwa kenan, ta kula da ita ta kuma tarbiyyantar da ita bisa tafarki na addini ,ita dai matsalar Imtihaal dama chan a fannin dressing ne da makeup shine kad’ai Inna ta kasa gyara mata don in tayi kokarin yi to bazasu wanye lafiya ba. General ma ya ji dad’in ganin hakan ba kad’an ba. Kowa ya ci yasha ana ta murna amma banda khaleel da ke zaune yana kallon su ,yayinda ganin shima yana cikin damuwa kamar yadda take ciki yasa Ilham itama ta yi joining nashi, suka d’an fara hira. “Amma Muryar ka seems familiar ! Kamar na tab’a jin Muryar ka at several occasions gashi kuma sai yau na tab’a ganin ka” abunda Ilham ta Fadawa khaleel kenan. Murmushi kawai yayi ba tare da ya amsa ba ya d’auki glass cup yayi sipping sannan ya maida kallon shi ga su Imtihaal. Cikin ranshi yace ” Celebrate all you want !! Day will come that your laughter will turn to streams of hot tears!!!! 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [4/25, 6:23 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗1⃣0⃣1⃣〰1⃣0⃣5⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Alhamdulillah komai ya dawo kamar yadda yake tsakanin Rasheed da precious nashi kamar basu taba samun sabani ba, suna tafe a hallway din headquarters na defence sai zuba Imtihaal take yi kamar aku ,in da sabo ya saba da irin surutai na Imtihaal saboda haka baya damun shi Sam!! Uncle Hashim da uncle Hamman da kuma wasu guda biyu su ma dattijawa ne zaune a falon sun Imtihaal an tarbesu sosai cikin karamawa ,daya daga cikin dattijawan wanda da ka ganshi kaga General don suna kama ya fara magana bayan ya gode ma ubangijin sammai da kassai, ” Major Ali , wato abunda ke tafe damu ba wani bak’on abu bane face maganar nan ta nemawa d’an mu Rasheed auren d’iyar ka Imtihaal…. Kafin ya k’arasa Major yace ” Haba !! Toh yanzu banda General da abunshi ai Imtihaal y’arsa ce ,yana da iko akanta yana da ikon bayar da ita ga duk wanda ya chanchanta, kar fa a manta Imtihaal ta samu kyakkyawan tarbiyya ne daga gurin su ,sune komai nata domin ni nayi imani sunan uba kawai naci ,Nikam a gurina wannan ba matsala bane , with all my heart na amince hundred percent. Duk suka fara hamdala ana godewa Allah ,sai a lokacin kawu Hamman yace ” toh muna dad’a godewa Allah ,Allah kuma ya yi mana jagora yasa ayi a sa’a🙂 ya karashe maganar da wani murmushi Marar adadi, nan bayan sun d’an yi hira suka kama hanyar tafiya ,Saidai basu tafi ba har saida suka tabbatar an sa ranar auren nan da wata d’aya!! Farin ciki fal ran General Abubakar da Inna domin sun fi kowa sanin yadda d’ansu da Imtihaal ke kaunar junansu , Sadiq da Al’amin kuwa suna samun news din suka k’udiri niyyar yi masa albishir saboda haka Inna ta fasa k’iran sa ta sanar da shi ,ita ma dai Imtihaal bata san wainar da ake toyawa suna chan suna harkokin su. Ilham na tafe tana ta rangaji kamar bazata taka k’asa ba ,a cikin wannan yanayin kamar ance ta d’ago kanta sai tayi ido hud’u da Khaleel yana zaune sai kalle kalle yake yi yadda kowa yake safa da Marwa kullum nan ne wajen zaman shi dama , k’arasa wa tayi inda yake ta zauna a gefen shi tana k’are masa kallo kafin daga bisani ta ce ” Jiya da dare a gurin partyn nan you luk some how disturbed da ka ga Rasheed tare da Imtihaal !! What is the problem ? Khaleel yayi wani mahaukacin dariya ,ya zari karan sigari guda daga aljihun rigar shi ya kyasta ashana ya d’an zuk’a kafin ya ci gaba da cewa ” kina so kisan ma’anar wannan kallon da nayi musu ne?? Sai ya mik’a mata card nashi ,yace meet me tomorrow by 8:00 pm a arena zan fayyace miki komai ” yana kai Wannan yayi murmushi ya tashi yana gyara rigar shi kafin ya take sauran sigarin ya yi tafiyar shi ,yayinda ita kuwa ya barta nan ta sak’a Wannan ta kunce wancan……. 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [4/26, 4:00 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕 CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗1⃣0⃣6⃣〰1⃣1⃣0⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Imtihaal na isowa gida ta iske Dad a Falo yana kallon news, cike da fara’a ta yi sallama tak’arasa cikin falon shima fuskar shi cike da annashuwa ya d’auki remote ya rage muryan TV sannan yace ” my little darling! Welcome back home” cikin langwami ta k’arasa kusa dashi ta zauna k’asa yayinda shi kuma yana sama tace “Sannu da hutawa Dad! Naje dubaka a office baka nan Wai baka fita ba ,I hope komai lafiya?” Major yayi murmushi yace ” ah lafya lau my princess , bak’i nayi ne kuma they are very important persons ,in fact they are here for you!” Imtihaal ta zaro idanuwa waje tace ” Ni kuma Dad?? I just hope ba wani matsala, dad in ma maganar files din ne na riga na gama aikin su, mutumin baya Nigeria yanzu haka yana south Africa shi da wasu yaransa guda uku ,komai na gama bincikowa Dad bayar da su ne ban yi ba.” Tana kai wannan Dad ya katse ta kafin ta sake fad’ar wata Kalmar ” Ba wannan zancen bane my daughter! This one is different, daga gidan su Rasheed ne aka turo don nema mishi auren princess d’ina ,you see now my little princess is all grown up gashi zata yi aure tabar Daddy;) ya yi winking mata ido. Cikin jin kunya ta rufe fuskar ta da hannayenta tana dariya ta mik’e da sauri tayi upstairs shi kuwa Major dariya ma ta bashi, ya girgiza kai yace ” Bafulatana kawai sarkin kunya😀..,……. Karfe takwas daidai ta iso Arena (Eagle square stadium) tana shigowa taga gurin wayam kamar ba kowa, sai cikin field d’in wasu matasa suna training duk da wannan daren , stadium d’in koda alluran ka ne ya fad’i zaka iya samu, guri kawai ta nema ta zauna sannan ta fiddo da wayarta don ta k’ira shi amma kafin tayi dialling k’iran shi ya shigo ,kai tsaye ta d’auka ta kara a kunne ” ki duba left side ta inda kike zaki ga wani a zaune kanshi rufe da hood ki karaso inda yake ki zauna.” Abunda khaleel ya fad’a mata kenan gami da katse wayar. Ta tashi ta nufi inda ya sanar da ita ta kuma zauna kusa da mutumin, bai wani 6ata lokaci ba ya yaye hood din daya rufe fuskar shi ya juyo sukayi ido hud’u:oops: Gabanta ya fad’i ta mik’e tsaye tace ” Raaash….ed!!! What are you doing here captain?!!! ” khaleel da ya saka fuskar roba irin na Rasheed yayi wata muguwar dariya yace” come on take your sit ! Meye kin wani firgita kamar wanda kika ga dodo??” Saida Ilham ta samu natsuwa tukunna don tun lokacin da Rasheed ya mareta take tsoron sa. Khaleel ya yaye mask d’in da ke fuskar tashi, a nan ya kwashe labarin duk abunda ke faruwa tun daga mutuwar k’anwar shi har tafiyar Rasheed da kuma dawowan shi ,har ma da fansa da yayi niyyar d’auka akan Rasheed!……….. Ilham ta mik’e tsaye ta kama kunkumi tana karewa Stadium d’in kallo kafin ta ce ” Lallai wannan wasan zai yi kyau !!! Kai zaka rama abunda Rasheed yay ma k’anwar ka ne ,ni kuma zan d’auki fansa ne akan Imtihaal ,she is my target kaga kenan duk tafiyar d’aya ne. Rasheed ya sa hannu ya mari fuskata amma ba laifin shi bane laifin wannan gud for nothing d’in ne ,da nayi zaton samun shi is easy but tunda har maganan auren su ake yi this means ya min nisa saboda haka in jifa ta tsallake kai na ta fada kan koma waye!!” Duk suka bushe da dariya khaleel ya matso kusa da ita yace ” Yauwa y’ar gari!!!!”…………. 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [4/27, 10:11 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗1⃣1⃣1⃣〰1⃣1⃣5⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 TWO WEEKS LATER…….. Yau saura sati biyu kachal auren Rasheed da Imtihaal, su Ruky kam tun daga yau ma tana hanya abunka da kirjin biki😜. Rasheed na zaune a office yana waya, jin ‘karar bud’e k’ofa yasa yayi saurin d’agowa a zatonshi Precious d’in shi ne ,amma sai yaga akasin hakan domin kuwa Mujaheed ne tare da Al’amin da Sadiq suka shigo, yayi murna sosai ba kad’an ba ganin mutane masu muhimmanci a rayuwar shi irin su ne suka shigo ya zagaya suka yi hugging juna cike da shauqi yace ” Guys wallahy kun zo at the right time coz am very confused!!” A tare suka kwashe da dariya Mujaheed yace ” Kad’an ma ka gani within these weeks sai ka ma fi haka ramewa! Al’amin yace ” bama wannan ba tukunna akwai fa sauran abubuwa a gaban mu ,come on take the whole day off! Muje mu k’arasa sauran shopping da zamuyi” Rasheed ya had’e rai yace ” Gaskiya ni bazan fita haka in uniform ba ,akwai zafi zan nemi kayan da zan sha iska. Mujaheed ya katse shi da wuri yace ” tab!! Ai kana shiga gida nasan bazaka fito ba saboda zaka had’e da kakcy kuyi ta hirar ku da bata k’arewa. A haka suka jashi ya fita shopping din ba tare da ya koma gida ya chanza ba. Suna gamawa about k’arfe takwas na dare kawai suka nufi silver bird chilling a movie theatre📽 ba su suka bar silver bird ba sai kusan sha d’aya saura. Suna shigowa ko kula su bai yi ba suka jidi kayayyakin ya na ta musu dariya suna shigewa ya juya ya nufi side d’in kakcy nan ya zauna suka bud’e sabon shafin hira in takaice muku sai kusan karfe biyu ya samu ya kwanta don saida ya tabbatar ta samu bacci ko da suka gama hirar ma………. 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [4/29, 9:58 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CIGABAN CAPTAIN RASHEED💕☄ Episode 💗1⃣1⃣1⃣〰1⃣1⃣5⃣💗 Safiya mai cike da Ni’ima, ruwan sama suka tashi da shi marka-marka garin shiru alamun kowa yana indoors. Rasheed yayi juyi a hankali yake bud’e idanuwa har ya tashi ya zauna kuma ,ya sake dukunkunewa a bargo. Duk abunda yake yi Sadiq na zaune a kan reading chair rik’e da jarida yana kallon shi bai sake motsawa ba har Sadiq ya kammala abunda yake yi yayi wanka ya shirya tsaf still mutumin bai tashi ba ,a hankali ya d’ebo ruwa mai sanyi a fridge ya watsa masa. A firgice Rasheed ya Mik’e ya bi bayan Sadiq da gudu har downstairs k’arar wayar Sadiq ne yasa suka tsaya Rasheed ya bugi kafad’ar shi sannan ya wuce ya nufi d’akin su Inna don su gaisa daga nesa Sadiq yace ” bro Karfa ka manta karfe sha d’aya zamu fita , look at the time yanzu its almost 10:20am ka shirya da wuri pls:roll:. Ko kulashi Rasheed bai yi ba ya d’auki glass na fresh fruit drink ya wuce side na mom yana dariya. Imtihaal da k’awayen ta Ruky kaxs , Mrs Zainab Ahmad and Zeetu ne zaune suna shaqatawa a Grand palace anyi serving nasu spring rolls da banana milk shake suna ta chilling da ka gansu kasan daga shopping suke suka d’an tsaya su yi chilling don ga dukkan alamu basu ma gama ba.” Yan mata kuyi sauri mu tafi mana nifa Wollah na fara jin bacci” Zeetu ne ke maganan lokaci guda kuma tana wasa da bakin glass na milk shake nata. Imtihaal ta hararota ta ce “toh Sannu kasa sarkin bacci kin fi waye jin barci ki duba fa kiga tun nine muke yawo yanzu wajen sha biyu ai in baccin ne ma duk zamu fara complain ba ke kad’ai ba🙄 Ruky kaxs ta kwashe da dariya tace ” Nidai yanzu ku tashi mu karasa gurin kayan nan muga ko an gama dinka wa. Zainab Ahmad dai bata ce ‘kala ba ta mik’e tsaye duk suka fice bayan sun yi settling bill 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [4/29, 11:38 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗1⃣1⃣6⃣〰1⃣2⃣0⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Suna fita har zasu shiga mota kamar anche “kalli chan ” Ruky kaxs ta hango motar su Rasheed sun yi parking ,Rasheed yana jingine a jikin motar yayin da Sadiq da Mujaheed suka shiga wani shop. Ruky ta d’an buji hannun Mrs Zainab Ahmad tace ” kinga chan mutumin fa” ta nuna Direction d’in da yake,Zainab tace ” heee!! What a coincidence gashi kuma fa Chan muka nufa! Imtihaal ta kauda kai ta tsare ,Wai sai sun bar gurin zata je. Zeetu tace ” toh Sannu!! Mukam kinga tafiyar mu in kinga dama ki biyo mu tunda ai kayan naki ne. Duk suka wuce suna zolayarta suka barta a gurin kamar gunki…. Rasheed na kallon duk abunda suke yi kawai ya basar ne kamar bai gansu ba. Ganin sun tsallaka sun barta yasa ta yi sauri itama don ta tarosu tana isa tsakiyar kwaltan kawai wata bak’ar mota Jeep Prada mai tinted glass ta yi wuf ta gabanta ,ko da motar ta wuce duk suka nemi Imtihaal suka rasa.:oops: Rasheed ya yi wurgi da papers na hannunshi ya shige motar kamar zai tashi sama ,yana wani mahaukacin tuk’i ba tare da ya saurari traffic light ya bashi right na movement ba ya kutsa kai da gudu mai tsanani, yana bin bayan wannan motar wanda itama gudun take yi kamar zata tashi sama. Cikin y’an mintina motar ta 6ace masa dalilin Wutar da ta kama daga bonnet na motar duk da ya samu ya tsaya amma k’ofar motar tak’i bud’ewa gashi kuma hanyar kamar babu kowa sai buga k’ofar yake yi amma ta kame. Haka hayak’i yayi masa over ya kasa yin komai gashi kuma Wutar bata daina ci ba….. Motocin fire fighters ne da su Sadiq ga kuma Ambulance da kuma y’an K’ungiyar Red Cross suka iso da kyar aka samu aka cire k’ofar motan aka fiddo da shi Sadiq cikin matsanancin kuka yace wa su Ruky su wuce gida kawai shi zai tafi asibitin a ambulance da Rasheed, Ya kuma umarci Mujaheed da ya sanar da General abun da ake ciki…… 💗🏵 Jeeddah ja’o🏵💗 [4/30, 6:49 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗1⃣2⃣1⃣〰1⃣2⃣5⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 “What!!?” Innalillahi wa inna-ilaihirrajiun!! Wane asibitin?? Ok I’ll be on my way” Abunda General ya iya cewa kenan da Mujaheed ya sanar da shi abunda ake ciki a waya, Hankalin kowa ya tashi saboda haka Inna ma tace bata ga ta zama ba,tare suka nufi asibitin da Dad d’in Imtihaal mutumin da ba’a ma sanar da shi halin da y’ar shi ta shiga ba…. “Doctor pls do your best to save him!! Pls I beg of you! Plssss!!” Cikin rudani da tashin hankali Sadiq yake maganar, Dr ya sa aka dakatar dashi daidai kofar emergency room. “You have to stay here sir ,wait outside pls” Abunda d’aya daga cikin nurses d’in ya fad’a kenan yayinda suka k’arasa tura Rasheed dake Kwance rai a hannun Allah a kan stretcher……. Inna ta kasa zama sai kai kawo suke daga ita har Sadiq. Abbah ya k’araso kusa da Sadiq gami da dafa kafad’ar shi yace ” Be a man my son in shaa Allah He’ll be alright I know he’ll fight through it instead of being worried why not pray for his wellbeing! Nasan yadda kake ji a ranka yanzu coz baka da wani wanda ya wuce Rasheed but I want you to be strong my son” Sadiq ya sake fashewa da kuka, cikin kuka yace “Abbah in da nasan haka zai faru bazan tilastawa Rasheed sai Mun fita ba a wannan lokacin, kuma sannan da bamu je wajen ba da motar su kawai zasu shiga su koma gida, amma saboda sun ga Rasheed a tsaye ne suka taho, and now my friend is hospitalized because of me and his fiancé Imtihaal is being kidnapped !! Dum!!!! Kirjin Inna ya buga ta juyo cikin rudani tace ” Imtihaal!! Ta rik’e hannun Sadiq iya k’arfin ta ” Yaya akayi haka ? Ina aka kaita? Su waye suka d’auke ta?? Ka sanar da ni mana Sadiq ba magana nake maka bane ??!!” Tana magana tana jijjiga shi. Da kyar ya bud’e baki yace “Inna nima ban sani ba, hankali na baya tare da ni ,am very confused! Bansan ta ina zan fara ba ya sulale ya zauna kan wani waiting chair yayinda Major Ali (Dad d’in Imtihaal) tuni ya riga ya saddaqar, suna cikin wannan yanayin likita ya fito daga emergency room, da sauri suka ruga domin suji lafiyar Rasheed. Doctor !!yaya jikin nashi ? How is he?!! I hope he’s alright ? Likitan yayi murmushi gami da dafa kafad’ar Sadiq yace ” yes !! D’an uwanka yana nan lafiya ,he just suffer some cases of suffocation ,kasan hayak’i ne yayi masa yawa hakan ya sa duk wani air pass way nashi suka kusa daina function ,its good kun kawoshi Twenty minutes earlier da ina tabbatar muku da cewa we couldn’t have save him ,kuma ku godewa Allah (S.W.T) Domin shine me yin yanda yaso kuma a lokacin da yaga dama, ya kaddara cewa d’anku yana da sauran kwana a nan gaba. In kun gama ina son ganin mahaifin patient din a office nawa pls akwai wasu papers da zai yi signing a kai da kuma wani muhimmiyar magana da zamuyi…….. 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [5/1, 8:18 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗1⃣2⃣6⃣〰1⃣3⃣0⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Sadiq ya d’an nisa sannan yace ” doctor, zamu iya ganawa da patient d’in kuwa?” Likitan ya juyo da murmushin shi yace ” No my son! Yanzu bazai yiwu ba har sai Mun yi transferring patient din zuwa VIP room tukunna sai ku duba shi but for now yana buk’atar Hutu saboda, ka ‘kara hak’uri…… K’arfe takwas na dare Inna tana zaune kan kujera as a gefen gadon Rasheed tayi jigum ta k’ura masa ido Sadiq ya jingina da bango ya nad’e hannuwan shi a kirji idonshi a kan Rasheed baka jin k’arar komai a d’akin sai na na’urar da take aiki. Bud’e kofar da likita yayi ne ya dawo da su daga tunanin da suka shiga duk suka maida duban su ga likitan. ” Har yanzu soja bai tashi bane? Inna ta d’an yi murmushin dole tace Eh bai tashi ba. Likita ya gama dube duben da zai yi sannan yace” zai iya farkawa a ko wanne lokaci daga yanzu you need to stay closer to him because zai iya tashi cikin ko wanne yanayi depending on abunda ya faru da shi, don’t worry we’ll also stay alert:) Inna kai kawai ta girgiza ba tare da ta tanka ba…… 🏵🏵🏵 🏵🏵🏵 Gudu motar take yi kamar zasu tashi sama tun da Imtihaal ta hango yadda motar Rasheed ke cin wuta yayin da yake bin bayansu ta saddaqar babu wani mai cetonta sai mahaliccin ta saboda haka ta yanke shawarar amfani da k’arfin da Allah yay mata, mutanen da suka sa ta a tsakiya sukayi mata alluran bacci ganin tana neman zubar da su gaba d’aya da motar a take ta sulale ta zube k’asa sannan suka samu natsuwa suka nufi hanyar zuwa Lagos..,…….. A hankali yake motsa hannun shi ,idanuwan shi suna bud’ewa kafin su ankara yayi wuf ya mik’e yana faman fizge cannular dake hannun shi Sadiq yayi kokarin rik’e shi ya fizge kamar mahaukaci da kyar ya iya furta sunan Imtihaal. Sun ga hauka iya hauka kam a wannan daren don saida akai mishi alluran bacci tukunna hankalin kowa ya kwanta ,shi dai buk’atar shi ya fita neman masoyiyarshi bai kuma damu da halin da yake ciki ba……. My dear readers!!:) kar ku ga kamar ana ja muku rai ne dalilin rashin turo muku da wuri ,Aa Sam ba haka bane ,kwata kwata I am busy this days ,but I’ll continue squeezing tyms at least to make ur day!! Luv you all!! 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [5/3, 11:01 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗1⃣3⃣1⃣〰1⃣3⃣5⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 A hankali ta bud’e idanuwan ta tana bin d’akin da kallo ba tare da ta motsa jikin ta ba, d’akin babba ne sosai babu komai cikin shi sai wani yamutsatsen katifa wanda take Kwance a kai daga nan kuma sai band’aki wanda ko marufi bashi da, window’n d’akin nada matuk’ar tsayi yadda duk kokarin mutum bazai iya kaiwa ba batare da ya nemi wani abu da zai taka ba. A nutse ta tashi ta zauna tana sake kare wa d’akin kallo ,wanda duk farin fentin ya k’ok’e ya zama brown don datti ga kuma Cobwebs ta ko ina musamman ma k’ofar band’akin a takaice dai d’akin ya yi shekara da shekaru bai samu tsafta ba. Gaba d’aya abun duniya ya dameta ta rasa ta ina zata fara , tana cikin wannan yanayin ne aka bud’e kofa, cikin sauri ta Mik’e tsaye gami da k’ura masa ido 👀 gaba daya ta kasa tunanin abu daya, gani take kamar mafarki take yi. “Khaleel!! Me kake yi anan kuma? Ina nufin daman kai ne ka sa aka d’auko ni??” Khaleel yayi wata muguwar dariya yace ” Baby!! I hope you are not surprised coz bana expecting haka daga gareki , wannan ai irin aikin mu ne ko ba haka bane? By the way naga kamar yunwa na damunki ko? Bari yanzu a kawo miki abinci, in yaso sai na dawo anjima muyi magana ko?”. Imtihaal tace ” bana buk’atar sauraron ka ,koma me zaka ce ina so ka mayar da ni inda ka d’auko ni sannan ka sanar da ni ,a yanzu bazan saurareka ba !!!” Dariya kawai khaleel yayi ya juya saida ya isa bakin k’ofa ya tsaya chak ba tare da ya juyo ba yace ” Hmmmm Baby kenan babu matsala ai ,kiyi ta zaman har sai lokacin da kika yi ra’ayin sauraran abunda zan fad’a miki sai ki sanar da ni ,ni yanzu na tafi……. “Haba Sadiq!!! In su sun hanani tafiya ai kai bazaka min haka ba ,bazan iya barin Imtihaal all alone haka ba I have to go and rescue her , nasan zata tsammace ni this is the best time for me to show her how much I loved her ,pls brother I need to get out of this hospital!!!” Sadiq yayi shiru na d’an wani lokaci sannan yace ” ok amma saidai mu tafi tare coz I can’t leave you go out there alone!!” Ba tare da Rasheed ya amsa masa ba ya mik’e tsaye gami da zare drip d’in da ke hannun shi ya soka alluran a jikin katifan ya sakala takalman shi suka fice daga wurin cikin sirri. Suna fita basu zame ko ina ba sai defence headquarters duk abubuwan da Rasheed ke buk’ata ya d’eba sannan suka kama hanyar barrack. Rasheed na zaune a mota Sadiq ya shiga cikin gidan ya d’ebo musu abubuwan da zasu buk’ata ya fito babu kowa a falon duk suna side d’in kakcy…….. Hanyar da accident din ya afku suka nufa ba tare da sun san ina ne ainihin inda kidnappers d’in suka nufa baa……….. 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [5/3, 11:39 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗1⃣3⃣6⃣〰1⃣4⃣0⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 “I told you Ilham cikin sauk’i zamu cimma burin mu ,yanzu nasan babu d’aya daga cikin iyalan biyu da hankalin su ke Kwance cikin nutsuwa, musamman shi lover boy din Looser Rasheed” khaleel kenan yayi maganar hannun shi rik’e da glass na ruwa. Ilham tayi wani murmushi tace ” ban san me ya rasa ba a jiki na da har zai so wancan kazamar, lallai sai na 6ata mata fuska sai muga wanda zai biyota da sunan wani abu Wai so!!! ” ta mik’e tsaye tace yanzu zan bata zab’i ta rabu da shi ko kuma in kashe ta kowa ya huta!! Khaleel ya mik’e tsaye yana faman kunna sigari yace ” Oh come on! Kema kin san da kamar wuya ace ta janye, kuma in kin kasheta ai baki rama ba bazai tab’a jin ciwon sosai ba kamar yadda zata gama numfashinta nan k’arshe a gaban shi, nifa babu komai a raina da ya wuce fansa!! Kamar yadda na rasa farin ciki haka shima sai na dandana masa bak’in ciki Mara misaltuwa!!! Sai yayi bak’in cikin da yafi wanda nayi!!! Ina tabbatar miki da cewa in kinga ban tarwatsa rayuwar Rasheed. Ni k’anwa ya kashe min amma kuma itace farin ciki na ,tunda shi bashi da wani farin cikin da ya wuce Imtihaal sai na tarwatsa mishi farin ciki ,the game has just begun !! Wannan somin tab’i kenan!!!” Yana kai wannan ya bushe da wata muguwar dariya. Ilham kuwa cikin zuciyarta cewa tayi ” Amma fa wannan mutumin da gaske yake!!” Ita kanta tasan nata wasa ne a kan nashi domin Kishi kawai ne ke damun ta… Inna tana ta kai kawo a cikin VIP room d’in asibitin (d’akin da Rasheed ke jinya) hankalin ta a tashe , sauran ma sun yi jigum musamman Al’amin da Mujaheed. “Wannan wane irin yaro ne Rasheed!? Pls ka sake trying numbern Sadiq ko za’a same shi. Al’amin ya sake dialling numbern wannan karon ya shiga amma ba’a d’auka ba. Haka suka tattara suka koma gida, Isarsu Falo Inna ta yanki jiki ta fad’i cikin sauri aka kaita d’aki ,Abbah ya kira Dr Mufeen domin ta duba lafiyarta……….. Jikin ta na rawa saboda wani mugun zazzabi da ke neman rufeta, a hankali ya bud’e k’ofar gamida wurga mata leda d’auke da take away da kuma robar ruwa guda d’aya , haka ya saba yi mata cikin kwanaki hud’u da tayi kamar wata dabba ,ya juya zai fita tace ” Kai!!! Wai ni me nai maka ne a rayuwa!!! Me na tare maka !? Kazo ka ajiye ni kamar wata dabba ka kulle a keji ,sai wulak’anci daban daban ,ni gaskiya na gaji ka fitar dani daga nan gurin in ba haka ba…….!! ” In ba haka ba me!!!!??? ” ya katseta da sauri sannan ya dawo ya tsugunna a gabanta ,karan sigarin da yake sha kawai ya manna mata a kafad’a tayi wani ihu ,shi kuwa dariya kawai yake yi irin na k’eta. Ilham na jin ihun ta rugo gami da banko k’ofar d’akin ,jin hakan yasa ya d’auke karan sigarin yana kallon Ilham yayinda take ta Ajiyar numfashi kamar ita aka sawa Wutar ……….. Shin Ilham tana tausayin Imtihaal ne ko kuwa har yanzu tana kan bakan ta?!! Ku biyo ni a next episode domin jin yadda zasu k’are!! 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [5/3, 12:13 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗1⃣4⃣1⃣〰1⃣4⃣5⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 ” Kinga !!! Wannan shine babban dalilin da yasa bana aiki da mata!! Tausayi baya d’aya daga cikin akida na ,tausayi ya dad’e da barin zuciyata bashi da gurbi ko na misqala zarratin!! Saboda haka in har Kinsan you cannot control your patience with abunda nake aikata wa sai ki daina sauraron abubuwan da zanyi domin sanin kanki ne ban kawo Imtihaal nan gurin don taji dad’i ba ,ba kuma don a bani kud’i ba! She is here because ina so in d’au fansa!! Ilham ta mik’e tsaye ta fice ba tare da ta ce k’ala ba kai tsaye ta shige mota ta zauna , sai da ya gama guntun juice nashi dake glass cup sannan ya mike yana gyara kwalar riganshi shima ya fice ya isketa a motar ,ba tare da ya tanka mata ba ya tada motar suka bar gurin,……….. Imtihaal har ta saba domin muddin suka sa kafa suka fita wannan lokacin toh baza su dawo ba sai washegari k’arfe takwas ,dan fursuna ma ya fita jin dad’i da walwala… ” Rasheed Lagos kuma? Kana tunanin zasu tsallake duk garurruwan da ke kan hanya kuwa? Rasheed yayi murmushi yace ” ga Abun da yasa nace maka Lagos suka nufa, ya nuna masa wani numberplate na mota da ke jefe a ‘kasa kusan kilometres uku daga inda accident d’in ya faru da kuma wani ID card jefe a gefen plate din wanda yayi indicating wanda ya jefar a Lagos yake , Rasheed ya cigaba da cewa ” mistakenly aka jefar da wannan kuma basu damu su d’auke plate d’in ba saboda suna tunanin still ana biyo su ne ,a garin shiga motar ne ID d’in ya fad’i ‘kasa ,saboda haka Sadiq Lagos muka nufa!!” Sadiq cike da mamaki yace ” you are right bro!! Come on!!! Suka shiga mota a take suka d’au hanyar Lagos……….. “Al’amin Rasheed bai dawo ba ko? ” Inna da ke Kwance ne keyin wannan tambayar kafin ya bata amsa wayar shi tayi ringing ,yana d’agawa yaga Numbern Rasheed jiki na rawa ya d’auka ” Hello Rasheed ina ka shiga ne haka? Ga Inna ta damu sosai tana son ganin ka ,pls tell me ina kuke ne ?? Daga dayan ‘bangaren Rasheed yace ” lafiya nake Bro! Ina hanyan Lagos state pls I ka bawa umma wayan! ” babu musu ya mik’a mata cikin sauri ta mik’e zaune ta kara a kunne ” My son !! Yaya zaka tafi haka! At least sai ka sanar da mu inda kake baza mu hana ka ba , amma ka tashi ka tafi cikin dare duk hankalin kowa ya tashi kum….. Ya yi saurin katseta da ” Mom don Allah kiyi hakuri kawai na kasa daurewa ne ,wannan shine lokacin da zan nunawa Imtihaal that she’s adored by me ,iyaka kaunar da zan nuna mata kenan in je in yi rescuing nata daga hannun mutanen da suka d’auke ta. Kuma na tabbatar Mun kusa cimmusu domin kuwa Mun samu clue wanda zai iya taimaka mana mu sameta, albarkar ki kawai muke buk’ata da kuma addua👏🏽. Inna ta yi ta musu addua tana sa musu albarka kafin daga bisani ta mik’a wayar ga Al’amin… Inna ta samu relief da taji Muryar d’anta. 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [5/4, 1:16 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗1⃣4⃣6⃣〰1⃣5⃣0⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 ” Victoria island ne address d’in jikin katin, me zai hana mu tafi a matsayin bak’i a gareshi ,in har mutanen area d’in suka sanar damu inda zamu iya samun shi sai mu far masa cikin sauk’i amma yanzu in mukaje kai tsaye ,akwai possibility zai iya sanin ko ni waye ,I definitely have this feeling saboda haka Sadiq inaga dole mu nemi Al’amin domin nasan he will play it well , amma kafin nan yanzu mu fara bincike ko waye wannan Yusouf Adewonmi d’in !!” Duk Rasheed ne ke wannan maganar yayin da suke tsaye a bakin bar beach na Victoria Island🏖… A gurguje ta shigo hannunta d’auke da sachet na anti_malaria da kuma bottle na ruwa ta mik’a mata, sai da ta kusan mintina biyar sannan ta karb’a ta sha ,itade Ilham batace ‘kala ba ta juya zata fice ,Imtihaal da bata da wani ishashen k’arfi ta kamo k’asar rigarta tace ” yanzu ke da kece a position d’ina ya zakiji! Tell me the truth from d bottom of your hrt !!! Wanne irin reaction zaki bayar?? Kar fa ki manta ke mace ce , kawai saboda son zuciyar ki zaki kai kanki ga halaka,a yanda mata ke da raunin nan kina tsammanin khaleel ko da ya kashe ni zaki zama free ne?? Dole kema zai dinga bibiyar ki domin zai yi tunanin zaki fallasa duk wani sirri nasa da kika sani ki je kiyi tunin irin hadarin da ya jefa ki a ciki babu ghaira babu dalili kun sato ni, kina tunanin haka zan dawwama cikin wannan kurkukun naku ne? Ko da ba raina nasan dole sai kun fitar dani waje me kike tunani ne Ilham?? Nasan yanzu kina tunani ko abunda nake fad’i gaskiya ne ko?? This is not the right time to think ,Kije ki samu nutsuwa ,yanzu abunda ya fiye miki shine ki fice daga nan tun kafin ya shigo ya ga cewar yau har kin rigashi shigowa daga nan kuma sai ya fara doubting abilities naki as a villain!! ” Da sauri Ilham ta fice ba tare da ta juyo ba ta danna key din ta rufe yadda yake sannan ta tafi fitanta kenan ta hango motar shi yana shigowa gidan tuni ta lab’e bayan wata k’ofa har saida ya wuce ciki sannan ta fice ta bar gidan. Tafiya yake yana murmushi irin na k’eta har yakai bakin k’ofar d’akin ya saka key ba bud’e, yana shiga kamshin turaren Ilham ne ya fara bugan hancin shi yayi wata muguwar dariya irin na k’eta sannan ya k’araso cikin d’akin kai tsaye yaja kujerar sa da ya saba zama ya ya zauna ” tun yaushe ta shigo d’akin nan??? Me kuma kuka tattauna? Imtihaal tayi banza da shi ta kauda kanta gefe. Ranshi a bace ya zabura ya shak’e ta kana ya had’a ta da bango ya kaura mata mari. ” ba magana nake miki bane !! Tell me when exactly did she come in ,and what did she told you what are her plans!! ” Imtihaal ta hankad’a shi gefe guda duk gashin kanta ya barbaje tana ta huci a lokaci guda tace ” OVER MY DEAD BODY!! Ta tofa masa miyau a fuska , kusan minti biyu bai d’ago ba ya zaro tissue a aljihun shi ya goge fuskar tashi yana wata muguwar dariya sannan ya d’ago gami da doketa ta bayan hannu ta zube a k’asa warwas bakinta ya fashe ,cike da nuna jarumtar ta ta sa hannu ta goge jinin tana masa wani mugun kallo ,ji yake kamar ya shaketa,ta sheqa lahira amma tukunna so yake ya gama sanin take taken Ilham!!! Yayi wata yar karamar tsaki sannan ya juya zai fice ,karaf idonsa ya kai kan maganin da Ilham ta kawo mata ya durk’usa zai d’auka ko me ya tuna ,kuma sai ya fasa ya juya ya fice daga d’akin kamar kullum ya rufe k’ofar yayi waje…… A hankali take sulale wa a jikin bango har ta kai ‘kasa duk tayi gumi gashin ta ya mammanne a fuskarta ,doguwar rigar jikinta kuwa tayi duku’n-duku’n dalilin fad’uwar da tayi, domin d’akin kura ne kawai da datti . zazzafan kuka me sauti irin na ban tausayi take yi na takaicin irin mugun yanayin da suka saka ta take yi, bakinta addua kawai ya iya furtawa a wannan lokacin ,domin tasan Allah ba azzalumin kowa bane sai wanda ya zalunci kansa………….. 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [5/4, 2:35 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 2 Episode 💗1⃣5⃣1⃣〰1⃣5⃣5⃣💗 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Zaune yake cikin wata mota yana danna wayarsa,ya toshe da bak’in gilashi hannun sa guda yana buga jikin stirring motar, ” hey Wai ya haka ne??? Tun d’azu nake jiranka shiru pls let’s settle this once and for all!!” Yana kai wannan ya katse wayar gami da yin tsaki. Sanye yake da bak’ar vest da wando 3quater yana wasa da key d’in motar shi da yayi parking a chan gefe yana tafiya irin na bosawa💪. Kai tsaye motar da khaleel ke jiranshi ya shiga ya zauna gami da rufe k’ofar ba tare da ya furta magana ba. Khaleel yayi wannan shu’umin murmushin da ya saba sannan ya zare glashin fuskar shi yace ” Yousuf!! Nasan by now you are fed up by yanda nake treating naku for not paying you guys properly amma ba haka bane ,I have double your money but sai ka min wannan last aikin da zan saka ,duk da ma dai nasan this is not the right time but ina so ka zama ready domin ina suspecting wani abu ne , for now kayi manage da wannan kafin in waiwaye ka ” ya mik’a masa bunch ba dubu d’ari d’ari guda uku (dubu d’ari uku) da kyar Yousuf ya karb’a sannan yayi masa sallama ya fice daga motar rik’e da ledar kudin…….. motace k’arar Mercedes Benz a chan gefe suka yi parking suna kallon isowar Yousuf domin gaba da baya suka tafi ,basu gaza ba bayan ya fita suka bi bayan shi har ya isa k’ofar wani Bar a nan duk y’an iskan abokanan shi suke chilling. Rasheed ya juya yana kallon Al’amin yace ” yanzu ne ya kamata kayi making first step naka, ka tabbatar lallai lallai ka samu connection da shi , kayi acting wise har ya yarda ya biyoka make sure you work this step with charisma da kuma brain naka ,coz nasan gayen mugun d’an air ne!! In har ya biyoka shikenan zamu yi duk yadda zamuyi mu samu information daga gareshi” Al’amin yayi murmushi gami da dafa kafad’ar Rasheed yace ” You can count on me bro!!” Ya fice daga motar shigar da yayi ma da ka ganshi kaga shigar y’an air:D. Mata da maza kowa kawai sai sha’anin gaban shi yake da masu rawa da masu shan giya babu ruwansu , Al’amin na d’aga kai ya ya hango Yousuf d’in tare da abokan sa guda biyu suna zaune kan kujeru table d’in gaban su kuwa babu kwalbar da babu sai fama suke. Da gangan Al’amin ya zo wucewa ya banke wani daga cikin waiters d’in gidan duk na cikin glasses din da ya d’auko suka kware a jikin Yousuf, kafin su ankara Al’amin ya chukume waitern.” Kai wane irin kidahumi ne ! Gara dalla chan baka gani ne ,kana tafiya kai a sama kamar mai tallen hayak’i!!! Baka ga oga Yousuf bane a nan ,dubi fa yadda ka zuba masa giyar nan a jiki eh? Wai kai tukunna ma me kake ji da shi ne ??! ” yana magana ne irin na y’an iskan y’an daba d’in nan ,Hakan yayi impressing d’in Yousuf ya wani baje yana murmushi yaran shi ma haka, da gangan ya d’aga hannu zai kai punch a wannan waitern sai Yousuf ya hana shi” dakata!! Kyaleshi ya tafi !! ” Al’amin ya sake yin fuskar y’an duniya yace ” hey oga ai da da ka barni na gyara mar zama ai!! Ni ba’a yi wa oga na wulak’anci in kyale ehe!!” Yusouf yayi wata muguwar dariya yace ” I like that charisma and courage in you!! Kai d’in namu ne! Pls join us kai a kawo masa kwalba d’aya!!!” Sadiq sanye da kayan waiters d’in gurin ya tunkaro gurin d’auke da kwalba guda amma saidai ba giya bane a ciki ,sannan Yousuf bai san Sadiq ba shiyasa ya shigo freely. Al’amin ya d’aga kwalbar a take ya kafa kai bai sauk’e ba saida ya shanye tas, hakan yaja hankalin jama’a sai tafa mishi ake shi basu san ba giya yake sha ba ,su kuwa sai dirkar giya suke yi duk sun bugu ,shima yana ta biye musu sai Marisa suke yi. Da wayo ya jawo su duka hud’un suka kai cikin motar su sannan Al’amin ya k’ira Sadiq shima ya fito gami da wurgar da kayan aikin gurin da ya saka a cikin shara🗑…….. 💗🏵Jeeddah ja’o🏵💗 [5/5, 9:04 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 3 Episode 💕1⃣5⃣6⃣〰1⃣6⃣0⃣💕 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 “Sweetheart Ilham I didn’t expect pity from you to that bloody bitch!! Amma kin bata rawar ki da tsalle, kar ki manta ni fa ba yaro bane !! Kin barni babu wani zab’i da ya wuce in aikata hakan!!” “Khaleel pls!! Wallahy ni bazan iya bane ,I promise you bazan tab’a fallasa ka ba ,amma ni na ajiye makaman yak’i na!! I realize I have no reason to be jealous of Imtihaal, Allah ne bai yi ba cewa Rasheed nawane saboda haka I quit!! ” Ilham ta katse wayar ta yayinda shi kuwa khaleel yayi wurgi da tashi wayar a fusace duk ta tarwatse a k’asa ya dauki glass d’in giya ya kurba sannan ya dauko wata wayar daga aljihun shi ya yi dialling numbern Yousuf don suyi magana amma kwata kwata a kashe take, haka ma na sauran yaran nashi, ya buga tsaki tare da buge glass cup din da ke gefen shi ya tashi ya nufi d’akin da Imtihaal ke kulle. Mik’ewa tayi cikin sauri ganin yadda ya shigo yana Marisa da ka ganshi kasan ya bugu, Gadan-gadan ya nufota tare da wanketa da wani mari ya mak’ure ta a bango ” ke!!! In the first place Kinsan dalilin da yasa na kawo ki nan?? Toh in baki sani ba kisani!! Na kawoki nan don in razanar da ke daga k’arshe kuma in kashe ki kuma babu wanda zai ceceki!!!” Murya k’asa ‘kasa tace ” toh me nai maka kake son ka kashe ni?” Ya yi wurgi da ita gefe guda sannan yace ” baki yi min komai ba Imtihaal!! Hasalima baki san komai da yake faruwa ba ko da abun ya faru baki nan a k’asar!! Ya juyo a fusace ya nufi inda take gami da durkusawa gabanta yana waina y’ar k’aramar wuk’ar hannunshi yace ” baby bakida laifi , kuskuren ki d’aya ne da kika kasance kece farin cikin me laifin! Rasheed !!” A fusace ta mik’e zuciyarta na dukan uku uku tana girgiza kai tana ja da baya” A’a…… A’a!!! Wannan ba mai yiwu wa bane! Rasheed ba mai fitina bane Kaje chan ka nemi wanda yay maka laifi ba shiba kuma in ma shine yay maka laifin wannan wane irin laifi ne da zai sa ka d’auki mataki da kanka ina kabar hukuma?? “Hahahahahahhh!!!! Hukuma!! Hukuma ai bazata yi min adalci ba iri wanda na buk’ata!! Wannan alamarin ni ne hukumar kaina!!Husnah ta kasance komai na rayuwata bamuda kowa ita kad’ai ne family na!! Ta nuna min tana k’aunar Rasheed na umarceta da ta sanar da shi amma kafin tayi hakan taji cewar wata ta riga da ta maye wannan gurbin da take nema, hakan yasa ta kashe kanta don taga its the best solution ,again kuma don ta samu relief amma ni har yanzu na kasa samun relief mutumin da dalilin shi na rasa k’anwa shine zai samu farin ciki mai daurewa? NO!! Bazai tab’a faruwa ba!! Na sha alwashin rabashi da duk wani farin ciki na rayuwa!! Sai ya d’and’ana bak’in ciki a rayuwar sa !!!” Imtihaal na jin wannan tace “Amma lallai ka cika Mara imani da tunani, duk wannan abubuwan da suke faruwa shi wanda kake yi a kansa bai san cewa kana yi ba! Hasalima bai san wata ta soshi irin haka ba bai kuma san dalilin mutuwar ta ba!! Kai kuma kana wahalar da zuciyar ka ne domin da Husnah tana son Rasheed zata zauna ne tayi winning love dinshi ko ta yaya , ba Wai ta gaza ta kashe kanta ba!! Wannan ya nuna gudun halin da zaka shiga ciki idan har ta rasa abunda take so tayi ta kashe kanta ba Wai gudun halin da zata shiga ba!!” Tass!! Saukar mari ne har guda hud’u Imtihaal taji a fuskar ta wanda yasa ta gigice ta d’auke wuta :idea:bai tsaya bata lokaci ba ya luma mata y’ar wuk’ar nan a ciki ya sake zarewa ya mayar yana gamawa ya zare wuk’ar ya fice ba tare da ya rufe k’ofar ba. Abunda Imtihaal da ni kaina Jeeddah bamu sani ba shine ashe tun tuni ya kunna gas a kitchen d’in wannan tsohon gidan ya mamaye ko ina ,yana ficewa ya wurga ashana ciki kafin kace wani abu har gidan yayi exploding:oops:………….. 💕🏵Jeeddah ja’o🏵💕 [5/5, 9:43 AM] Jeeddah ja’o🏵: 💕☄CAPTAIN RASHEED☄💕 Season 3 Episode 💕1⃣6⃣1⃣〰1⃣6⃣5⃣💕 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 “What!! You mean an biya ku million d’aya domin ku kamo ta ?? Meaning mutumin da ya baku aikin nan ba kud’i yake nema ba daga gurin mu, yana da nashi dalilin na daban !!? Al’amin ne yayi wannan tambayar hannun shi rik’e da pliers babba yayinda su Yousuf suke d’aure a jikin kujerun katako salim na zaune shima a gefe yayinda Rasheed yake zaune a gaban Yousuf sun yi facing juna. Rasheed yace ” now tell me ! Waye ya aiko Ku ku aikata hakan ga yarinyar da bata da wani aibu me tayi muku? Yousuf yayi wata muguwar dariya yace ” kiss my ass!!! ” Rasheed ya kaure shi da mari yace ” How dare you, now you tell me who assigned you to do such thing or I cut out your finger!! 🙄 Yousuf ya tofa ma Rasheed miyau a fuska ,a take fuskar Rasheed tayi ja tsabar wani tafarfasa da yaji zuciyar shi na yi ya kama yatsar Yousuf ya fincike 😩 cikin tsawa yace “NOW TELL ME !! INA KUKA KAI MIN ITA!!!?” Cikin yanayin firgici da tashin hankali d’aya daga cikin abokan Yousuf yace ” nikam zan fad’a pls kar ku cire min yatsa, ni wannan ba hali na bane dole ce tasa nayi domin ina buk’atar kud’i don kammala karatu na!! Wallahy zan fada amma don Allah ku kyale ni in tafiyata pls !!! Rasheed yayi murmushi yace “Good!! Fad’amin abun da ka sani duk ! Ni kuma na maka alk’awari in har na tabbatar gaskiya ka fad’a toh lallai I will file for your freedom amma in kuwa k’arya kayi toh ka tabbatar zan sheqe ka!!” Mutumin yace “Wani ne mai suna captain khaleel shi ya bamu wannan aikin amma kuma bamu san manufar shi ba akan ta mudai ya bamu hoton ta da kuma duk wani shige da ficen ta ya kuma umarce mu kar mu tunkari inda take sai Mun tabbata babu kowa tattare da ita.” “CAPTAIN KHALEEL!!! CAPTAIN KHALEEL!!! Rasheed ya maimaita sunan har sau uku sannan yace Sadiq kunce shi” Sadiq ya kunce mutumin Rasheed ya dubeshi yace ” Muje ka kaimu inda yake Ajiyar yarinyar first!! ” suna fita kenan a bakin hotel d’in da suke suka ci karo da Ilham anan ne ta zayyano musu komai da ya faru sannan ta nuna musu cewa ita ta riga ta yi giving up, ta kuma nemi gafara a gurin Rasheed bawan Allah cikin ruwan sanyi ya yafe mata. Suna isowa gidan babu abunda yake fita sai hayak’i ko ina ya k’one. Ilham ta sa ihu ta fice da gudu ta nufi k’ofar suma duk suka dunguma suka yi gurin, wutan kam ya mutu don kanshi amma akwai guraren da basu daina ci da Wutar ba , a rud’e duk suka shiga ciki hayak’i sai tari yake saka su basu zame ko ina ba sai hanyar d’akin da Imtihaal ke amma kuma abunda ya d’aure musu kai shine babu ita babu labarin ta jikin Ilham ya dau rawa ta zube a k’asa tana kuka Rasheed ya tsaya kamar an dasa shi . Ilham ta mik’e tsaye da sauri tace ” kuga !! Tayi nuni da hannun ta zuwa floor d’in d’akin duk suka maida dubansu gurin , Jini ne yayi layi har ya isa bakin k’ofa daga nan kuma basu sake ganin inda jinin yayi ba sanadiyyar toka da ya zuba a floor d’in. Rasheed yace ” She’s alive !! Tayi escaping ne ya ruga ya fita suma suka bi bayan su daga k’afar fita kuwa suka fara ganin d’igon jinin yabi wata hanya ta daban haka suka dinga bin hanyar da k’afar su har ta fitar da su bakin titi…. Daga nan basu san kuma inda tayi ba ,cikin sauri suka koma suka d’auki motar su basu zame ko ina ba sai General hospital domin shine asibitin farko da yake wannan hanyar a tunanin su nan ne first place da duk wanda ya taimake ta zai je amma ina babu ita babu labarin ta………….. 💕🏵Jeeddah ja’o🏵💕 [5/5, 10:37 AM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED 💕☄season 3 Episode 💕1⃣6⃣6⃣〰1⃣7⃣0⃣💕 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 ” Sannu ko? Ni sunana Dr Mufeen daga specialist Hospital a Abuja nazo nan ne don attending wani conference da Association of Nigerian medical doctors ta had’a ,kuma accidentally na sameki helpless a bakin titi ,nasan akwai mysteries a tattare da ke but ina so ki nutsu tukunna ki trying ki matar da kanki komai for now and relax don kina buk’atar Hutu for a while , akwai dinki a jikin ki yanzu haka so pls bakya bukatar kwakwaran motsi. Tana magana ne kawai amma Imtihaal ba sauraron ta take ba ,tunanin ta Halin da Rasheed yake ciki da kuma mahaifin ta, a haka har bacci ya saceta……. Rasheed na zaune kan kujera Sadiq ya mik’a masa take away na abinci , ba tare da ya kalli ma meye ba ya sa hannu ya ture yayi wani ajiyan numfashi gami da duba tym yace Wai me Al’amin ya tsaya yi ne a waje har yanzu ?? Sadiq yace ” wa ya sani ne kasan shi da son kallon stars maybe yana chan yana fama. Rasheed ya ce ” k bari in dubo shi tun dazu ya kawo min recharge card d’in ya kasa kuma network din is somehow not clear today , na kasa recharging through mobile phone 🤕. Sadiq de bai ce qala ba Rasheed ya fice abunshi.. Daidai third to the last step na stairs d’in suka ci karo duk magungunan da ta siyo suka fashe, Dr Mufeen ta ce ” Subhanallah!! Malam ya haka? Ina kake kallo ne ?? I really need this medicines now ,gashi kuma duk sun fashe I have a patient kuma na barta ita kad’ai tun d’azu sannan I have to check on her , yanzu ya zanyi!?? ” Rasheed yace am sorry ,don Allah kiyi hak’uri its just that I was desperate ,ki bani list na magungunan ko a ina ne zan nemo in kawo ,am sorry once again!” Mufeen ta d’an yi Jim sannan tace gashi nan ta mik’a masa list d’in har ya fara tafiya tace ” room number 102″ ya juyo gami da girgiza mata kai ya fice. Kafin kace wani abu masu aikin hotel din har sun gyara gurin da magungunan suka fashe………. K’arfe tara dai dai ya dawo d’auke da maganin kai tsaye ya wuce room 102 kamar yadda ta sanar da shi ya Kwankwasa k’ofar in no time ta bud’e k’ofar ,ya mik’a mata tayi murmushi ta karb’a yace ” I just hope ban yi latti ba?” Maganar nan da ya furta ya doki kunnen Imtihaal da ke Kwance ta firgita ta fad’o daga kan gadon tana neman hanyar k’ofa, Mufeen tayi murmushi tace you are just in tym ,suka yi sallama ya juya kafin ta rufe k’ofar Imtihaal tace Ccc.. Aaaa… Ptain.. Wannan Kalmar captain d’in ta doki kunnen shi amma sai bai kawo wani abu a ranshi ba ya wuce abunsa amma tun da ya dawo d’aki ya kasa samun sukuni gaba d’aya. Sati biyu kenan cir Rasheed bai ji wani improvement ba ,yau kamar kullum sun fito zasu fita neman ta kamar yadda suka saba ,chan ma Abuja an samu labarin khaleel sun kuma yi nasarar chafke shi amma yana nan a rufe ne , domin ya ki confessing komai kuma ya nuna bai san komai ba. Tana tafe tana Jan k’afa a hankali hannunta kuma guda d’aya na cikinta d’ayan kuma Dr Mufeen ta rik’e ta ” kar ki damu Imtihaal ai if am not mistaken yanda kika bani labarin ki ,na tabbatar it was your captains that I treated a asibiti , kwanan shi d’aya ya tafi neman ki ,look nasan duk yadda akayi yana nan yana ta neman ki kum……. Kafin ta k’arasa Ilham tace ” Imtihaal!! Imtihaal stop !!! A rikice ta juyo tana kallon Ilham wanda tun tuni ta riga ta k’araso inda suke tsaye.. Tun yaushe muke neman ki da captain munje har haunted house din nan bamu same ki ba ina kika shiga ne pls😭 Imtihaal pls forgive Me I was so selfish that I couldn’t even think about others!! Amma na gane kuskure na ! Don Allah ki yafe min pls 👏🏽 Imtihaal cikin kuka tace ” babu komai ai ya wuce ,its good kin yi realising mistakes naki before its too late babu komai na yafe miki:'( Mufeen tayi murmushi tace ” yanzu ina su captain d’in suke? Ilham cikin sauri ta mik’e tace ,sun fita neman ta ne bari nayi musu waya kuzo muje d’akin da suke, a d’an tsorace Imtihaal tace ” Me zai hana mu jira su a nan kawai?” Ilham ta juyo da d’an guntun murmushi tace “I know baza ki tab’a trusting d’ina ba right?” Imtihaal tayi murmushi jiki a sanyaye suka bi bayanta har d’akin da su Rasheed suka kama……. 💕🏵Jeeddah ja’o🏵💕 [5/5, 5:56 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 3 Episode 💕1⃣7⃣1⃣〰1⃣7⃣5⃣💕 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Kusan mintina talatin sannan suka k’araso hotel d’in kai tsaye suka shigo d’akin ba tare da wata wata ba. MY PRECIOUS!!! Ya fad’a yayinda ya k’arasa jikin gadon da take jingine ya zauna gabanta cikin kuka tace ” Hanny !! I’ve missed you a lot!! I have been tortured by him so much that I can never ever forget!! ” ta rik’e kwalar rigarshi tace ” where have you been?? Na jira zuwanka, da yanzu bani da sauran numfashi a doron k’asa Hanny !! Ya cutar da ni sosai ba a kan laifi na ba! Kuma ya zarge ka da cewar Kaine silar mutuwar k’anwar shi Husnah ,saboda Wannan ya k’udiri niyyar raba ka da farin ciki! Hanny I tried to convince him that baka da masaniya akan soyayyar Husnah but he couldn’t believe me! Ya sokeni da wuk’a sannan ya yi setting house din on fire, saboda rashin tausayi ,yayi tafiyarsa ya kyale ni, da Jan ciki na samu na fito ,ga k’unar wuta ga ciwo , Captain ina kuka tsaya ne 😭!!! Rasheed cikin hawaye yace ” relax my precious am here now ! Ya gyara mata pillown ta koma ta jingina sannan ya kwashe labarin komai ya sanar da ita. Da kyar ta runtsa a daren ranan domin ji take yi kamar zaa zo a sake d’auke ta duk da ma bayan Ilham tana tare da Dr Mufeen. Karfe takwas na safe jirgin su ya tashi daga Lagos zuwa Abuja ,tafiyar da bata wuce 45 minutes ba by air. Kowa da kowa an hallara domin tarbar su kama daga iyayen da y’an uwa har ma da wasu tight friends na Rasheed da Imtihaal , hand bag dake hannun ta ta wurgar kamar ance dole sai tayi gudu ta ruga , Dr Mufeen tace ,kar kiyi gudu mana !! Ko a jikinta domin a lokacin bata jin komai a tare da ita ,Inna ta rungume tana kuka itama Innar haka , ranar de Mufeen taga reunion mai ban tausayi 😍. Tana cikin haka ta hango nata ogan 😜 tare da wata nanny ta rik’e wani handsome baby boy da bai wuce two years ba , da fara’ar ta tanufi gurin su ta karb’i Yaron yayinda Nanny ta karb’i luggage d’in nata.” Oh I missed you my Little Areef! Mummy loves you much more!!😘 tayi kissing kumatun shi yayinda shi kuwa yake ta kyalkyata dariya , Oga na daga gefe yayi folding hannayen shi yace ,hala baby Areef kad’ai kika gani Abban Areef kuma ko oho!😎 da sauri ta juyo tace ” Oh look at you !! Ai ka girma da oyoyo😂 but don’t worry I’ve something special for you !! Yanzu de mu tafi Wollah ni a gajiye nake sosai!! Murmushi yayi ya mata nuni da hanya yayinda ta shige yana biye da su a baya. A wajen airport d’in ne ,su Imtihaal suka gabatar da Dr Mufeen and her family yayinda Areef ya mak’ale ma Inna da kyar ya koma gun momyn shi a nan suka yi sallama ,motar su Mufeen na tafiya suma suka shige tasu suka bar gurin basu zame ko ina ba sai main house d’in su Rasheed wanda yake Asokoro domin nan ne zai iya d’aukan guests d’in su gaba d’aya Abba ya umarci Dad d’in Imtihaal da ya zauna a other side na gidan kawai domin it will be more safe than ayi bikin a chan main House na su Imtihaal da ke Maitama haka ya hak’ura aka ci gaba da shiri ,nan da sati ,yayin da aka saka ranar da za’a gurfanar da khaleel Ranar Monday wato bayan sati da auren su Imtihaal. Su Yousuf kuwa suma an dawo dasu nan Abuja ,anan za’a ci gaba da tsaron su har ranar da za’a yanke musu hukunci daidai da abun da suka aikata!! Domin Rasheed ya ce is better kar suyi ido hud’u da khaleel kafin a yanke mishi hukunci don za’a iya kifar da shi…………. ✍🏽🏵Jeeddah ja’o🏵✍🏽 [5/5, 7:25 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 3 Episode 💕1⃣7⃣6⃣〰1⃣8⃣0⃣💕 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Kwance take a kan darduma ta yi rigingine da 3quater a jikinta da kuma wata bak’ar top ,da alama ta saka ne don kar lallen ta ya tab’u, sai hira suke da k’awayen ta Serdy Maskara ne da Hersna suka shigo da shopping bags nik’i nik’i suka zuba a gurin ba tare da kowannen su ya tanka ba , Zeetu ta bisu da kallo tace ” hehehe an yo halin kenan tun daga hanya:D ! Serdy Maskara ta watso mata wani kallo tace ,kin jita fa !! Se kace kema bakisan halin Hersna ba🙄 she always take the first step Wai kinji daga cewa takalmin yayi min kyau tay karaf ta d’auke kuma shine last piece a mall din Wollah ko ki bani ko in hana ki sawa a bikin ehe:roll:. Ruky kaxs da ke gefe ta ce wallahy kun ban wata yar bakauyiyar dariya 😂 ni na zaci ma har kun yi settling issue d’in takalmin ,toh yanzu dai ba wannan ba kuzo muje karb’o sauran dinkin amaryar haute couture tukunna! Hersna ta zaro idanuwa waje tace ” Ku tausaya min in k’ara hutawa Wollah a gajiye nake dazu tafiya nake amma kamar yar giya 😫 duk suka bushe da dariya Ruky tace Haba mana pls kunsan fa gobe ba tym zamu samu ba , nan ma de da rikicin suka tashi Ruky na musu dariya ,Imtihaal kam in da sabo ta saba da halin su tun suna boarding school lokacin a Queen Amina college. “Sadiq I told you am tired pls ku bari na huta mana!!!” Al’amin da ke gefe yace ” ka huta a ina?? Ai kai da Hutu sai nan da bayan two weeks lokacin am sure daga kai se sister in-law 😜! Rasheed ya jefa masa pillow yayinda Al’amin ya kauce yana dariya Rasheed ya mik’e gamida zira rigar shi half jumper ya kafa hula sannan ya kwashi wayoyin shi suka fita. Yau take jumma’a !! An d’aura auren Imtihaal Major Ali da Rasheed Abubakar Rasheed (General). Taro yayi taro kowa ya shaida jama’a an yi murna babu abunda ke bakin yan uwa da abokan arziki sai fatan alkhairi. Bangaren angwaye kuwa ba’a misalta farin cikin da suke ciki a wannan lokacin haka ma 6angaren amaren💃🏻. Dr Mufeen na zaune bakin gado tana gyara wa amarya zaman dankunnen ta wanda da ka ganshi kasan asalin silver ne K’arar dubai pink lace ne gown a jikinta dankwalin kuwa launin satin ne ash colour kamar takalman k’afarta ,tasha kyau iya kyau ba’a magana domin idan guri akwai Ruky babu bukatar wata professional makeup artist!! Biki yayi biki ,daga kamu da akayi ran Alhamis, walima da dai sauransu komai ya tafi yadda ake so Alhamdulillah. Ana shirin kai amarya abokan ango wad’anda ya had’a harda soji suka yi escorting bride yayinda Rasheed na chan side nashi tare da Al’amin, Sadiq, da Mujaheed, sai faman zolayan shi suke yi, k’arfe takwas na dare Abban Areef yazo d’aukan Dr Mufeen , tayi sallama da k’awayen amarya kan cewa gobe zata yi attending Honouring ceremony da Yan uwan Rasheed wato military personnel suka shirya musu don nuna murnan auren nasu ☺ Gidan me kyau ne 3 bedroom ga babban palour da kuma kitchen wannan ba wani gida bane illa gidan da Rasheed ya taso a ciki kuma yayi wayo ,wannan ya tabbatar ma Imtihaal cewa rumours da taji cewa Abban Rasheed zai yi resigning gaskiya ne ,renovation kawai aka yi a gidan amma kamar ba a Nigeria ba don in ka shiga kamar kar ka fita ko nan da kofa! Ceremony yayi ba k’arya ,anyi parading ba kad’an ba ,a gurguje har Mr President yayi attending , a nan ne General yayi announcing resignation date nashi wato ranar Monday bayan an saurari karar su khaleel wanda a yanzu haka an yi striping nashi off his ranks! Stadium d’in ya cika iya ba k’arya kuma bikin ya kawayar! K’arfe hud’u na yamma kowa ya watse an gama komai abubuwa sun tafi yadda ya kamata sai godiyar Allah! “Ilham baki bani amsa ta ba har yanzu, kar fa ki manta da Rasheed da kuma Sadiq duk tafiyar d’aya ne ” Rasheed kenan yayi wannan maganar idon sa cikin na Ilham…….. Nawaooooo readers kunji fa !! Nima dai JEEDDAH nayi mamaki ,ashe Sadiq ma yana ciki kawai de ya basar ne , hehehe!!am surprised!! ✍🏽🏵Jeeddah ja’o🏵✍🏽 [5/6, 12:12 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ Season 3 Episode 💕1⃣8⃣1⃣〰1⃣8⃣5⃣💕 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 Dariya kawai tayi ta dukad da kai ‘kasa ,shikuwa Sadiq na zaune cikin mota gurin driver ya kallesu yace ” a tsaya dai b’ata lokaci mu makara kaga dai gwara mu kai mata abunta ko ya kuka ce frndz? “Duk cikin raha suka ce dats right! Gwara kam a rakashi kar mu yi latti amarya tayi maganin mu 😝.. Rasheed dai kawai kai ya girgiza musu ya shiga motar Sadiq na tafiya yana tuk’i a hankali kamar ba tafiya suke ba duk don neman tsokana.” Oooooohhh!!! Dude in ka kasa driving d’in ne sai kabawa wani ko ni ka bani in yi kayana🙄 ni har na gaji da zaman motar!!” A tare suka bushe da dariya Sadiq ya juyo ya kalleshi ta gefen ido yace ” Haba bro !! Me kake ji na baka na zuba !! After all gidan ka zamu kai ka fa ba wani waje ba ,have patience naga ma wataran sai ka gaji da gidan ;)!” What !! In gaji da gidan bayan my precious na cikin gidan? Kaima kasan its way too impossible!! ” haka dai sukayi ta yi har aka kai gidan………. Yau lahadi ne ,kuma gobe Monday shine ranar da za’a gurfanar da su khaleel a gaban kuliya, kasantuwar weekend ne Rasheed na gida yana shanawa da amarsu. “My precious tashi ki bani rigana mana pls 👏🏽 Imtihaal da ke Kwance sanye da rigar khaki d’in shi ta d’ago manyan idanuwan ta tana kallon shi, take ya durk’uso jikin gadon yace pls pls☹. Ta tashi zaune hannunta rungume da pillow tace ” shikenan weekend d’in ma sai a saka wani meeting me yasa baza a bari Monday ba , ni bazan bada rigar nan ba saidai Kaje a haka” Rasheed yayi murmushi yace ” Oooo Hanny !! You are acting as if bakisan fitinan mutanen nan ba! I really have to be there ,kuma d’aya uniform din na kai laundromat da safe, pls ki bani wannan d’in na saka. Da ‘kyar ya karb’i rigar don gudun rigimar ta ma a palour ya saka rigar don yasan in yayi sake zata wafce ya gano so take ta b’ata masa lokaci yayi latti ,dama tun asalin shi ma babu aure ma ya saba latti balle kuma yanzu:D Cikin sati d’ayan nan Sadiq da Ilham sun daidaita kansu sosai kamar wanda sun dade suna tare abun dai se godiyar Allah……… ✍🏽🏵Jeeddah ja’o🏵✍🏽 [5/6, 3:26 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 3 Episode 💕1⃣8⃣6⃣〰1⃣9⃣0⃣💕 Na 🏵Jeeddah ja’o🏵 “Bayan kotu ta saurari shaidu da kotu ta gabatar ,da kuma amsa laifi da shi wanda ake tuhuma da laifin sace Mrs Imtihaal A. Rasheed da sace ta tare da tsananta mata horo da kuma niyyar kisan kai da ya yi ,ga Imtihaal , kotu ta yanke wa Mr Khaleel hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso tare da mukarraban as wato Yousuf Adewonmi, Zak ,Bolaji. Captain Ilham kuma dalilin had’a kai da tayi aka yi wannan aika aikan da ita kotu ta yanke mata hukuncin daurin wata uku a gidan kaso!! ” Ilham ta d’aga ido ta dubi Sadiq yayinda ya sakar mata murmushi sannan yayi Mata nuni da hannu cewa ta kwantar da hankalin ta yana tare da ita ,anan ta samu relief Alhamdulillah komai ya tafi daidai yadda ya kamata ,khaleel ya yi getting even better than abunda yayi deserving amma duk da haka sun tausaya mishi domin ba laifin shi bane amma kuma ba laifin kowa bane, kuma its good that ya amsa laifin shi da kanshi ba tareda an jaa abun da nisa ba. Rasheed da su Imtihaal suna fita kenan shima aka fito da shi ya nemi a bashi yan mintina yayi magana da Rasheed aka kuwa bashi…….. “Nasan ban kyauta maka ba ,amma ko kad’an bana nadamar abunda na aikata , sai guda d’aya ,kuma shine har yanzu kana cikin farin ciki tare da abunda ya fi soyuwa a ranka ,nayi accepting defeat ne don already the game is over , Babu irin muguntar da ban kitsa a kan Imtihaal ba ,but abun ya ki ci, shi yasa na saduda na tabbatar gaskiya ta fad’a cewa Husnah ta raguwa ce !!! I even wonder why she has to commit suicide, but then I realized nine k’arfin ta!!! Rasheed I gave up because I have to not because you win!!” Khaleel na kai wannan bai saurari me Rasheed zai ce ba ya fara tafiya yayinda Jami’an da ke rik’e da handcuffs nashi suma suka taka masa baya ,Rasheed kam ko motsawa bai yi ba daga inda yake har saida motar su khaleel ta tashi. “Sadiq am very scared !! ” Ilham kenan tayi wannan maganar cikin firgici da hawaye kasantuwar bata tab’a tsintar kanta a cikin irin wannan hali ba sai yau duk ta nemi dauriyar ta,ta rasa sai zufa take yi. “No sweety! Kar ki damu ,I’ll visit you everyday, I promise babu kuma wanda zai takura miki inn shaa Allah! Just calm down ! Babu abunda zai faru ,besides its just 3 months so pls don’t worry your self.” Yana kai wannan ,suka wuce da ita Sadiq ya bisu da kallo har saida motar ta tashi. Hmmmm Ilham kenan ,a wata uku tayi kuka na ban tausayi ,ina kuma ga shi khaleel da zai kasance ya gama duk rayuwar sa ne a gidan kaso?? “DAN ADAM ME WUYAN GANE HALI!!” ✍🏽🏵Jeeddah ja’o🏵✍🏽 [5/6, 4:01 PM] Jeeddah ja’o🏵: ☄💕CAPTAIN RASHEED💕☄ season 3 Episode 💕1⃣9⃣1⃣〰1⃣9⃣5⃣💕 A yammacin ranar kuwa Abbah Yayi resigning, washegari kuwa suka d’auki flight zuwa Germany don hutawar su. “Hey Hanny!! Ina da wata shawara ! Naga kamar kin kasa mantawa da abubuwan da suka faru , since we both are on leave me zai hana mu tafi abroad mu shaqata? You know!! I really want you to forget all that happened.” Tana Kwance kan cinyar shi tana jin duk abin da ya fad’a ta rufe bakinta da remote bata ce komai ba kusan minti biyu sai kuma ta mik’e da wuri ta zauna tana kallon shi ido cikin ido tace ” nasan inda zamu je Hanny !!” Ta mik’e da saurin ta tahaye upstairs yayinda ya bita da kallo har ta k’ure☺. Bata jima wani sosai ba ta fito dauke da wani d’an leaflet a hannu an rubuta EXPLORE DUBAI!!* tana zama ta mik’a masa ,yana gani ya saki wani d’an murmushi ba tare da yace komai ba sai subatar ta da Yayi a goshi ya mik’e ya nufi k’ofar fita, kafin kace me har ta iso inda yake tsabar tsoro 😂 cike da mamaki ya juyo yace ” what!! My precious pls a rage tsoro mana wayata na zo d’auka ba barin ki zan yi ba fa..a. Dariya kawai tayi ya sureta suka yi cikin gida yana ta zolayarta Wai matsoraciyar soja” ……… DUBAI🌃 Dare ne mai Ni’imar gaske, kowa yana ta harkokin gaban sa ga kuma Hasken wuta na lantarki wanda ya maida gurin kamar wani gold , tsaye take a d’aya daga cikin tagogin glass da ke hawa na kusan tara na hotel d’in duk abunda ke faruwa kuwa tana gani mutane se shawagi sukeyi. A iya sanin Imtihaal de Rasheed wanka ya shiga ,da ta shagala da kallon windown bata san har ya fito ya sa kayanshi da ke kan gadon ya fice ba . “Hanny! Hanny !! Ka fito mana mu tafi nifa yunwa nake ji pls 👏🏽 ko da ta bud’e bata ganshi cikin band’akin ba ta rikice sosai harda hawayenta sai zubowa yake yi ,tana ta faman danna waya ta bawa k’ofar baya ,ko da ya shigo kuwa a tsorace ta juya fuska duk hawaye ,da kyar ya samu ya rarrashe ta , Wai yana so ya gudu ya barta😀 yayi murmushi yace. ” My precious na yarda har yanzu ke yarinya ce Wollah:D:D” ta d’an langabe kai tace ” Who said soooo” yace “gani nan;)” haka suka ci love din su a Dubai in ka gansu kamar wasu tattabaru🕊🕊……… Haka ma Sadiq da Ilham ,bayan ta fito aka d’aura auren su kuma suka zauna cikin so da k’aunar juna ba’a magana , Ruky kaxs kuwa ana chan England tare da husbyn ta Heesham and were blessed with a cute looking baby boy Ahmad😘 💘 THEY LIVE HAPPILY EVER AFTER!!!💞 ✍🏽🏵Jeeddah ja’o🏵✍🏽 [5/6, 4:18 PM] Jeeddah ja’o🏵: 💞☄CAPTAIN RASHEED💞☄ Na HAUWA ESAH JA’O🏵 (Jeeddah ja’o) Wannan sadaukar wa ne ga Besty RUKAYYA ABDULLAHI KAKUMI (Rukey kaxs)😘 Da kuma daukacin fans d’ina gaba d’aya wadanda na waye su da kuma wad’anda ban waye su ba, Allah ubangiji ya had’a fuskokin mu a Aljannatul Firdausi👏🏽 Godiya mara adadi ga dukanin members na ROOKIE SADAU GRP OF WRITERS JA’O AND KAKUMI NOVELS RASH KARDAM NOVELS KHADIJA CANDY NOVELS ZANGON LABARAI HAUSA NOVELS AJAJIGEEE GROUP ZEENARE BOOKS AND others that play significant roles in world of online Hausa writing😘 thank you!! For without each and every one of you I wouldn’t be able to reach such a destination☺ GAISUWA ME TARIN YAWA ZUWA GA UNFORGETTABLE SISTERS AISHAT MUHAMMED (Maman Shakur😘) SUFY ABDOUL NANCY TROUBLE 💃🏻 MEENAH ISMAEEL ROOKIE SADAU MY BESTY ZAINAB A. ZEETU HERSNA AND SERDY MASKARA😎 @UT@R H@JIY@ P@CKS AND GROUP MEMBERS😘 SPECIAL THANKS TO MUFEEN (Maman Areef) thank you for the supports ALHAMDULILLAH FOR COMMENTS AND CORRECTIONS CONTACT 08160354469 💞 ✍🏽🏵 Jeeddah ja’o🏵✍🏽 MAY 22, 2016 JEEDDAHJAO LEAVE A COMMENT DOCUMENT MADE BY °°°°°°°°••••SALMA°°•••√°°°° adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *