Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 22 March 2017

DAN IZALAH

adsense here [11:52AM, 10/20/2016] Malam Jameel A Kabo: *DAN IZALA!!!!????* . . *DAGA ZAUREN* . *KITABU WAS SUNNAH* . . *ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ* 📓📔 Watsaps 08036222795 08136182627 . . Yau 18-01-1438 20-11-2016, Itace ranarda muke gabatarda wannan lekca me taken *DAN IZALA!!!???* . _Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode mishi kuma muna neman taimakonshi da agajinshi, wanda Allah ya shiryar shine cikakken shiryayye***_ ... _bayan haka wannan lekcace wacce muka shiryata musamman domin mubayyana wasu kanun bayanai, amma bawai tsawaitawa zamuyiba kawai takaitawa zamuyi dan mu bayyana hakikanin manufarmu****_ ... _kalmar izala kalmace ta larabci wacce ma,anarta shine gusarwa, wato akawarda wani abu****_ . _toh amma anan arewacin najeriya inkace izala, toh suna daukartane kawai cewa ahlu sunnah, sune yan izala, koda kuwa baka taba shiga kungiyar izalaba***_ . _Dalili kuwa shine wani bawan Allah ne mutumin jihar bauchi kokuma ince mutumin garin jos, inda ananne yafi shahara dan anan aka sanshi sosai***_ . _Sunanshi Isma,il Idris Zakariyya, wanda dalubine almajiri wanda baya shakka ko tsoro akan fadin gaskiya koda kuwa akan waye takama***_ . _Isma,il idris yayi karatu bakin gwargwado awajen malamai dadama, acikinsu harda Malam Abubakar Mahmud Gummi, toh wannan isma,il din yana xaune agarin kaduna yana koyon ilimi dakuma karantar dashi,****_ . _yana nan zaune sai sojoji sukayi juyin mulki kuma suka dinga banbarma acikin gari har suka rushe wani masallaci suka maidashi gidan giya sukaita aikata masha,a***_ . _Awannan lokacin kakaf najeriya aka rasa malaminda zaije yayiwa sojoji wa,azi, aikuwa Isma,il yace shikam seyaje yayima sojoji wa,azi****_ . _awannan dalilin nashi na son yima sojoji wa,azi shine kawai beyi shawara da malaminshiba malam Abubakae gummi kawai seyaje yashiga soja, kuma yacigaba dayin wa,azi yana bada fatwa abarikin sojoji****_ . _Toh da,awarda malam isma,il yakeyi da kakin soja batayiwa manyan sojoji dayawa dadi, wanda hakan yasa sukaita yimishi makar kashiya da sharri, gakuma yan dariku suma suna cewa Isma,il yana yin abinda yaga damane dan yaga shi soja ne, wanda akan wayannan maganganun yasa Isma,il yabar aikin soja yakoma yacigaba da wa,azi****_ . _yana cikin wannan wa,azine toh seyaga abubuwa sunmishi yawa, saboda awannan lokacin yana gwagwarmaya sosai yana caccakar bokaye da matsafa da 'yan dariku****_ . _yana cikin wannan da,awane sai wararana gidan tv na jihar kano suka gayyaceshi yaje yayi karatu, wanda yana cikin wannan karatune 'yan sanda sukazo suka kamashi suka tafi dashi gidan yari a garin kalaba suka tsareshi****_ . _da tafiya tayi tafiya bayan Isma,il yafito daga gidan yari sekawai yakara zage damtse da,awa tazama sabuwa, saboda ada yana maganane akan dariku kawai, amma yana fitowa sai yafadada da,awarshi akan bokaye da matsafa da mayu da sauran dukkan wata bidi,a***_ . _toh ashekarar 1977 shine sai yaga yakamata yakafa kungiyane saboda abun babu sauki yazama yana dawainiya da wannan akin shi kadai***_ .. _bayan yagama shawara seya kafa kungiya kuma yasaka mata suna *JAMA'ATU IZALATUL BIDI'A* wato *RUNDUNAR KAWARDA BIDI'A*awannan lokacin sai yaje wajen sarkin Musulmi Abubakar na uku, dake sokoto yai masa bayani gameda wannan kungiya***_ . _jin wannan batu sai sarkin musulmi yace bazaka iyaba yaro, sha,anin kasarnan yafi karfinka, kabari kawai wanda Allah ya shiryar shikenan, amma idan kace sudena bidi'a toh zasu kasheka***_ . _isma,il yacewa sarki insha Allahu zan iya kudai samana Albarka, ananne sai sarki yace toh shikenan Allah ya taimaka, har isma,il yatashi yakama hanya sekuma sarki yasake kiranshi yace: Abinda za,ayi shine tunda kamatsa kuma kace zaka iya kawarda bidi,a toh lallai kuwa kayi kokarin tsayarda sunnah, dan haka sai ka karada wa'ikamatis sunnah, wato tazama sunan kungiyar *JAMA'ATU IZALATUL BIDI'A WA IKAMATUS SUNNAH****_ . _Toh anan wajen kuma tarihin yarabu biyu, awata kissar kuma cewa akayi, ranarda akazo kaddamarda kungiyar agarin jos, sai malam Abubakar gumi baisamu zuwaba wanda kuma shine mataimakin uban kungiya, uban kungiyar kuma shine Sarkin bauchi Malam Adamu gimba, wanda shima baisamu zuwa wajen kaddamarda kungiyarba, amma dukansu suntura wakilai, wanda ya wakilci Abubakar gumi shine Malam Lawal Abubakar, wanda alokacin yace malam yabani sakon cewa inbaka shawara kakarada Wa'ikamatu Assunnah,***_ . _idan kuka lura zakuga cewa wannan karin yanada ruwaya guda biyu kenan****_ . _yanzu dai atakaice kunji makasudin kafuwar kungiyar izala wacce dama nace ba tarihi mukazoyiba, Aa bayani kawai zamuyi atakaice gameda shin wanene dan izala, toh yanzu dai kunji kungiyar izala atakaice, amma sekun biyomu fitowa tagaba zakuji ko wanene dan izala***_ . . Allah yasa mudace . . Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/ [1:52PM, 10/20/2016] Malam Jameel A Kabo: *DAN IZALA2!!!!????* . . *DAGA ZAUREN* . *KITABU WAS SUNNAH* . . *ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ* 📓📔 Watsaps 08036222795 08136182627 . . Cigaban lekca me taken *DAN IZALA!!!???* . Wannan shine bayani nabiyu**** . . _Kar ku manta jama,a nafada abaya bawai tarihin kungiyar izala mukeba, Aa somuke mugayamaka wanene dan Izala sekuma mugaya maka bambancin dan izala da dan kungiyar izala kawai****_ . _Toh bayan malam Isma'il yagama tabbatarda kafuwar qungiyar izala shine sai aka fitoda manufofinta, wanda Babbar manufar kungiyar shine dawoda hankulan jama,a zuwaga Qur,ani da sunnah***_ . _kungiyar tarika kiran mutane zuwaga akida, ana karantarda jama,a ana koya musu addini ana rabosu da gargajiya dakuma maguzanci****_ . _Alherin kungiyar izala aka fara gabatarda wa,azozin jiha dana kasa da wa,azin mako, harma ake sanya karatun fiqhu da hadisi amasallatai aka kuma bude islamiyoyi****_ . _izala takoyarda mata su saka hijabi, sudena bayyana tsaraici, kuma adena zuwa ana baita a kaburburan shehunnai, sannan taraba jama,a da laya tabasu La,ilaha illallahu, kuma take koyawa mutane karatun tajwidi da usulul fiqhu****_ . _jama,a sukaita shiga wannan kungiya, yayinda yan dariku sukuma suka rika zuga jahilai sukaita tura musu shubiha suna yiwa yan izala karya suna cewa wai 'yan izala suna raba 'ya'ya da iyayensu suna kafirta iyayensu, suna cewa kaza kasa hakadai sukaita yiwa yan izala karya, wanda ana cikin hakane sai yan darika suka hada kai, da 'yan shi,a suka kama yaki da kungiyar izala****_ . _yan dariku sun shiga tashin hankali sosai lokacinda izala tafara wa,azinta, wanda sukasa akaita tsangwamar duk wanda yashiga kungiyar izala, wanda abin yafi tsanani a yankin arewa maso gabas, musamman jihohin bauchi da gombe wanda seda takai kamar za,ayi yaki kafin izala tasamu tafara gabatarda sallar juma,a ababban masallacin juma,a na gwallaga dake jihar bauchi****_ . _hakadai akaita kuntatama yan ixala wanda ayankin adamawa seda takaiga har kasuwanni ake rabawa tsakanin kasuwar yan darika da kasuwar yan izala, yan darika sunata bin jahilai suna hure musu kunni, yayinda yan izala sukuma suka cigaba da wa,azi suna koyaww mutane akida da tauhidi****_ . _tafiya tafara nisa cikin ikon Allah kungiyar izala tazauna sun kuma fara samun 'yanci, ba,a jifansu zagima ba,a ko ina akemusu ba***_ . _kungiyar izala bata sanya wani sharadiba ga wanda yakeson zama dan kungiyar, wato ba,a bukatar rubuta sunanka kuma ba sai kacika wani forma ba, kawai dazarar kayarda zakabi qur,ani da hadisi kuma zakabi sunnah babu bidi,a toh shikenan kazama dan izala****_ . _kawai ana cikin tafiya sewasu yan kananan matsaloli suka shigo cikin wannan kungiya, wanda ba matsala bace ta akida matsalar tiqhu ce, kamar maganar sakin hannu asallah dakuma matsalar daga sauti abayan liman****_ . _Toh izala tasamu kanta acikin matsalar farko ajihar bauchi, wacce abauchine inda izala tafara rabuwa biyu, wacce Izalar bauchi ta rabune ashekarar 1987 lokacinda akazoda magana akan christocin najeriya shin ahlil kitabine su, kokuwa ba ahlil kitabi bane shin kuma za,a iya cin yankansu??***_ . _'yan masallacin Bakin kura wanda sune su Malam Isma'il Idris shi kam yace sam babu ahlul kitabi anajeriya kuma bai halasta aci yankansu ba, wanda sukuwa yan masallacin gwallaga sukace sam ai christocin najeriya ahlil kitabine kuma lallai ya halasta aci yankansu****_ . _hakadai izala taraba kanta biyu a jihar bauchi har suka fara adawa da junansu suna yadama juna magana, wanda tundaga wannan rikici na bauchine sauran jihohi suka fara dauka, ammadai su basu rabeba****_ . _Tunda wannan fitina tafara kutso kai, toh saishi malam Abubakar Gumi yazama shine alkalinsu, duk sanda mutanen wasu jiha suka samu rikici sekawai sukwaso gayya sutaho kaduna susamu malam Abubakar gumi yashiga tsakani, hakadai sukaita fama har zuwa shekarata 1990 inda akazo akayi zama harda malaman saudiyya akan sasanta kungiyar izala, amma abun beyiba saboda wasu sunce sudai bazasu kara zama karkashin Isma'ila idris ba, yayinda wasu kuma sukace yanzu kamar malam isma'il ace baza,aji maganarsaba??***_ . _toh wannan shine babban rikicinda yabarke acikin kungiyar izala, wanda zamuce abinda yahadasu bashine abinda ya rabasu ba****_ . . Zamu tsaya anan sekuma fitowa tagaba zami shiga cikin hakikanin bayaninda mukeso muyi kaitsaye amma wannan sharar fagene muka gama yanzu . . . Allah yasa mudace . . Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/ [7:31AM, 10/21/2016] Malam Jameel A Kabo: *DAN IZALA4!!!!????* . . *DAGA ZAUREN* . *KITABU WAS SUNNAH* . . *ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ* 📓📔 Watsaps 08036222795 08136182627 . . Cigaban lekca me taken *DAN IZALA!!!???* . Wannan shine bayani na hudu**** . . _Abinda ban gaya mukuna gameda rabuwar kan kungiyar izala shine, can baya idan baku mantaba nagaya muku Abubakar Gumi shine mataimakin uban kungiyar na kasa baki daya, kenan shi ba dan kungiyar izala bane, uban kungiyane shi***_ . _Toh bayan an bangare yan izalu sun raba kansu kashi biyu sai kuma aka samu wasu bangare na yan baruwana, wayanda su sam basa goyon bayan kowanne bangare kuma sunabin kowanne bangare kuma basu kafirta kowanne bangareba, toh wayannan seyazama su basuda aiki face karantarwa kamar yanda sukaga babban malaminsu Abubakar gumi yanayi***_ . _Toh wayannan mutanen 'yan tsaka tsakiya wayanda basu tareda kowanne bangare toh sesuka kafu akan asalin tushe da ginshikinda yasa aka kafa kungiyar izala, wato karantarda mutane, seya zama su baka ganinsu akan mumbarin wa,azin kasa ko wa,azin mako, ammadai suna tattara dalubai a zauruka suna koya musu ilimin qur,ani da hadisi da nahwu da sarfu da sauran fannonin addini***_ . _Toh sukuma wayancan bangarori guda biyu seya zama sanda tafiya tayi tafiya sai aka samu dayawansu sunbar kan tafarkinda yakafasu, wato karantarwa, seya zama sun koma suna kokarin kamfe da neman kare kungiyarsu, yazama su babu ruwansu da duk wata bidi,a dakake aikatawa inhar zaka shiga kungiyarsu katayasu yakida wayancan abokan adawar tasu****_ . _wayannan bangarori guda biyu sesuka rika kokarin zawarcin wayancan mutanen yan ba ruwana suna kiransu da suzo suhade dasu sugoyi bayansu, amma wayannan mutanen suka kafe sukace sam, sufa abarsu akan abinda yakawosu, wato qur,ani da sunnah, toh wayannan mutanen sune daga baya suka koma suna kiran kansu salafiyya, ammafa ko sunki ko sunso sumafa yan izalane, saboda a najeriya duk wanda zebi tafarkin sunnah toh yazama dan izala koda kuwa baitaba shiga cikin kungiyarba, inhar yayarda zebi sunnah toh zakaji duk yan bidi,a suna kiranshi da sunan dan izala kuma suna zaginshi*****_ . _Toh lokacinda wayancan kungiyoyi biyu na izala masu gaba da juna yayinda sukaji wayancan yan baruwana sun fara kiran kansu dasunan salafiyya, toh shikenanfa se dukan kungiyoyin suma suka fara kokarin fada da jin haushin wayannan yan izala salafiyyar, saboda wai aisuma kungiyace suka bude***_ . _Toh amma wannan zantuttukan nasu be girgiza wayannan yan salafiyyaba sema suka kara fitowa karara suka bayyana manufofinsu, wanda manufar tasu kuma saita daceda asalin manufarda tasanya Malam Isma,il yakafa kungiyar izala****_ . _kungiyar izala ba,a kafata dan ta kare mazahabanciba, ba,a kafata dan takare kungiyanciba, kuma ba,a kafata dan ta zagi wani ko tozarta waniba, sannan ba,a kafata dan tayarda hankalin waniba, amma kawai an kafatane dan karantarda qur,ani da hadisi, ta kawarda bidi,a ta tsaida sunnah***_ . _Bayan yan salafiyya sun bayyana kansune se suka tsayu wajen kiran mutane zuwaga qur,ani da hadisin amma suna cewa abisa fahimtar magabatan kwarai, toh se wannan karin yakara tunzura wasu bangare na wayancan kungiyoyi biyu na izala masu gaba da juna, har takaisu ga suna bayyana adawarsu karara da wayannan yan salafiyyar wayanda sune suke kan asalin izala basu karkaceba****_ . _Awannan lokacin sai aka raba aikin biyu, wayannan yan salafiyyar suna kokarin kare qur,ani da hadisi, yayinda sukuma wayansu daga cikin wayancan kungiyoyi biyu suke kokarin kare kungiyarsu, yazama suna bayyana adawa karara ga duk wanda baizo yashiga kungiyarsuba koda kuwa yana karantarda qur,ani da hadisi kuma yana kokarin kamanta riko da sunnah, su babu ruwansu da riko da sunnarka sudai kawai kazo kashiga kungiyarsu***_ . _wannan tasa zakaga mutum yana bayyana bidi,a afili amma an nadashi shugabancin izala na wata gunduma ko unguwa, saikaga mutum yana take wando, ya aske gemu, baya rungume hannu asallah, baya aswaki, amma dukda haka saikaji ance waikuma shine shugaban izala na wata gunduma*****_ . . Zamu dakata anan saikuma fitowa tagaba zamu dora . . . Allah yasa mudace . . Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/ [8:15AM, 10/21/2016] Malam Jameel A Kabo: *DAN IZALA5!!!????* . . *DAGA ZAUREN* . *KITABU WAS SUNNAH* . . *ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ* 📓📔 Watsaps 08036222795 08136182627 . . Cigaban lekca me taken *DAN IZALA!!!???* . Wannan shine bayani na biyar**** . . _Siffofi da kamannin dan izala shine, mutum ne meson gaskiya kuma mai naci da kafuwan akan ayi gaskya, kuma bayajin tsoron bayyana gaskiya, wanda inbaku manaba abaya nagaya muku yanda akayi Isma'il Idris yashiga aikin soja badan komaiba sedon yayima sojoji wa,azi kuma yagaya musu gaskiya, bawai dan yasamu wani abuba na duniyarshi acikin aikin kuma yashiga aikinne bama tareda neman izinin malaminshiba wato Abubakar gumi, Aa kawai tunda yaga akwai bukatar agayama sojoji gaskiya kai tsaye kawai seyaje yashiga aikin soja, kuma kunji yanda yaita gwagwarmaya aciki yaita samun matsala da manyanshi saboda yana gaya musu gaskya, toh wani abunda bangaya mukuba shine, wata rana Isma'il yayi wani wa,azi irin wanda ake kira free huduba, toh seyafadi abinda beyiwa manyansa dadiba, sai kawai suka chanja mishi wajen aiki suka maidashi kwantagoro, cikin jihar sokoto awancan lokacin, amma yanzu takoma jihar Naija, toh acan garin na kwanta gora koda yaje baifa chanzaba sema yakara daukar zafi yana fitada sojoji suna zuwa wa,azi cikin gari bayan yagama wa,azi acikin bariki, toh acanne rikici yai rikici akayi kararshi wajen Kungiyar Jama,atu nasril islam, cewa gafa wani matashin soja yanaso yakawo rikicin addini, sai su yan jama,atu suka tura Abubakar Gumi yaje can garin kwanta goran dan yagana da wannan fitinannen matashin soja, aikuwa malam Abubakar gumu yana zuwa sai yaga ashema almajirinsane ai kawai seyace: Isma'il yaushe kazo garinnan?? Yaushe kashiga aikin soja??? Anan dai aka tattauna sosai akarshe aka tabbatarda isma'il akan abinda yakeyi kuma aka tabbatarda cewa dariku dukansu ba musulinci bane, toh wannan shine dan izala jama,a mutuminda bayajin tsoron fadin gaskiya akan ko wanene kuma ako ina takama***_ . _sannan dan izala baya jayayya kuma baya raina nagaba dashi, jayayya shine kuhadu kawai kuyita gaddama da muhawara akan wani abu bawai dan neman maslaha ba, kawai dan ace na kure wane, toh dan izala baya irin wannan, shi dan izala duk abinda zeyi toh dagaske yakeyi***_ . _Dan izala bayajin kunyar aikata sunnah, kamar dage wando ko cika gemu, ko makamancin wannan, kamar yanda zakuga malam Abubakar gumi inkuna ganin hotonshi zakuga gemu sosai, toh wannan shine kamannin dan izala jama,a****_ . _Dan Izala baya boye gskya saboda neman yardan wani ko dan abashi girma, kamar yanda kukaji isma'il Idriss sanda yashiga aikin soja girman manyanshi da mulkin mallama irinna soja baisa yayi shiruba kuna baici amanar Allah ba bai boye gaskiya, toh duk dan izala nagari haka yake***_ . _Son girma ko mulki bayasa dan izala ya boye gaskiya kamar yanda kukaji, sanda yan dariku suke cewa ai Isma'il yana yin abinda yakeyine saboda yaga shi sojane, kuma babba yana tareda kananan sojoji wayanda suke bashi kariya, wanda jin wannan maganar tasa anan take Isma'il yarubuta takarda yace yabar aikin, kuma yasake dawowa yaciga da wa,azinshi***_ . _sannan dan izala baya fushi kk fada saboda anki shiga kungiyarshi, wannan yasa sanda Isma'il yakafa kungiyar izala baya kiran mutane yace suzo sushiga kungiyarshi, Aa kiranshi kawai shine jama,a suzo subi Qur,ani da sunnah, toh haka dan izala yake***_ . _kuma baku tabaji ance Isma'il idriss yayi fada dawaniba wai saboda yaki shiga kungiyarshi, Aa shifa ba yakafa kungiya bane saboda yanason kungiyanci, kuma baikafa kungiya dan akirashi dan kungiyaba, Aa yakafatane kawai saboda ta taimakeshi wajen yada sunnah, kuma baice dole sai kowa yazo yashiga wannan kungiyaba, Aa inhar kayarda da qur,ani da sunnah, toh shikenan kazama nashi koda baka shiga kungiyarshiba, toh wannan shine asalin sifar dan izala duk garinda yaje yaga ana karantarda qur,ani da sunnah toh shikam murna yakeyi yaga yan uwa, amma babu ruwanshi da jin wai wacce kungiya suke?? Sudai badai yagansu suna karanta qur,ani da hadisi ba?? Toh shikenan sunzama yan uwanshi kuma zai iya bada jininshi akan kare hakkin wayannan mutane, dukda cewa baisan kungiyarda sukeba tunda dai qur,ani da sunnah sun hadasu***_ . _Dan izala yana fifita dan uwanshi wanda qur,ani da sunnah suka hadashi dasu toh yaba basu fifiko fiyema da yan uwansa na jini, toh wannan shine cikakken dan izala***_ . _Dan izala baya fada saboda sabanin mazhaba, ko wani karamin sabaninda bekai na aqida ba, dan kawai kazo wani gari kaga limamin garin dan malikiyyane misali kaikuma dan hanafiyyane toh wannan bambancin baya hana kabishi sallah, kuma baya hanaka kaci yankanshi***_ . _sannan kuma dan izala fada saboda wani aiki ya bambantaku, misali ace wani limami baya rungume hannu asallah kokuma yanayin sallama daya, toh dan izala saboda wannan dalilin baya cewa kada abishi sallah***_ . _sannan kuma dan izala baya yima shugaba tawaye, kuma baya harzuka mutane suyi ta,addanci, sannan dan izala baya tashin hankali inhar za,a barshi ya karantarda qur,ani da hadisi****_ . _Dan izala baya tsokanar fada, kuma baya zage zage, wai saboda wani ya zageshi kokuma ya zagi malaminshi toh wannan bayasa dan izala shima yafita yana maida martani da zagi ko zambo***_ . _Dan izala baya husuma baya ta,addanci kuma dan izala baya zama da jahilci, sannan kuma dan izala baya dogewa akan wata bidi,a matukar yasan wannan abin bidi,ane****_ . _kai dan izala yanzu zakaganshi yana aikata wani abu sekawai kacemai yabari babu kyau, akwai hadisi toh nan take zebar wannan abin kuma koda baka gayamai hadisinba indai yayarda dakai da akidarka, toh dazarar kacemai akwai hadisi zakaga yakame saboda dan izala baya shishshigi acikin lamarin Allah da manzonshi****_ . . Zamu dakata anan saikuma fitowa tagaba zamu dora . . Allah yasa mudace . . Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/ [11:12AM, 10/21/2016] Malam Jameel A Kabo: *DAN IZALA6!!!????* . . *DAGA ZAUREN* . *KITABU WAS SUNNAH* . . *ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ* 📓📔 Watsaps 08036222795 08136182627 . . Cigaban lekca me taken *DAN IZALA!!!???* . Wannan shine bayani na shida**** . . _Dan Izala baya gaba jama,a kuma dan izala baya hassada sannan kuma dan izala baya kyamar gaskiya koda kuwa ba daga bakinshi tafitoba, kawai atakaice in dunkule maka ma,anar dan izala shine mai neman gaskiya kuma me aiki da gaskiya***_ . _Dan izala baya fifita maganar wani akan ta manzon Allah koda kuwa wannan wanin wanene kuma koda malamine****_ . _Toh bayan kungiyar izalar tarabune sai kamar yanda nagaya muku aka samu wasu bara gurbi suka shiga cikinta, wayanda sayansu dama larurace tasa suka shiga dan babu yanda zasuyi almajiransu sunriga sunkoma can, toh sesukaga idan basu shiga almajiran zasu rabu dasu***_ . _wasu kuma sunshigane saboda neman duniya, wasu kuma sunshiga saboda neman suna sunaso duniya tasansu ace suma malamaine***_ . _wayansu kuma sun shigane saboda sukara ruruta wutar waccan fitinar***_ . _wasu kuma sun shigane da jahilci, sudama can zunzurutun jahilaine dan haka su basuma san hakikanin manufarda tasa aka kafa kungiyarba, sesuka dauka kawai dazarar kashiga izala shikenan Allah ya gafarta maka shikenan kazama dan aljannah, baka bukatar neman ilimi sedai kawai karika halartan wa,azin kasa ko mako mako, kuma in aka zagi malamanku kuma kurama zagin kuje aita hayaniya daku sesuka dauka wannan shine manufar kafa izala***_ . _toh alokacinda aka samu wayannan jahilan suka shigo ciki seya zama kowanne bangare daga cikin wayancan bangarorin biyu masu gaba da juna, kowannensu yana amfanida mabiyanshi musamman wayannan jahilan yana amfani dasu wajen suka da aibanta wanda baya tare dasu, atakaice dai yazama ansamu wasu daga cikin malaman izala wayanda sukawai manufarsu ba shine su karantarda mutane ba, sudai kawai sosuke sukare kungiyarsu****_ . _Toh wannan kokarin nasu nakare bangarorinsu shine yasasu suke gabada duk wani wanda baizo yashiga cikin kungiyarsuba, koda kuwa shima ahli sunnah ne, koda ace kira yakeyi zuwa abi qur,ani da sunnah, wanda shine asalin makasudinda yasa aka kafa kungiyar izala, shine dan takira jama,a zuwa qur,ani da sunnah, toh amma da,aka fara kishin kare kungiya sekaga malami da sunan izala yana gaba da wasu mutane kawai dan basuzo sun shiga kungiyarshiba***_ . _wannan kishin kungiyar shine yasa malamancan bangare na uku wayanda suke tsaye akan turba ta asalin izala wato masu kira azo abi qur,ani da sunnah abisa fahimtar salaf, toh masu irin wannan da,awar sun kara shiga kunci kwarai, saboda yan shi,a suna fada dasu, yan dariku suna fada dasu yan siyasa da sarakunan gargajiya sunata fada dasu, yayinda ahannu guda kuma ga wayancan masu kokarin kare kungiya suma sunata fada dasu, wanda wannan abin kuma yafi zafi ayankunan jihohin kano da zariya, dayake suna ko kalmar salafiyya kusan zance tafaro tashene a jihar kano, ammadai tafi shahara a zariya***_ . _toh suko wayannan malaman yan salafiyya wato izalawan gaske se basu damuba kuma basa matsama kansu sesunyima wani raddi, sudai kawai karatunsu sukeyi, basu taba dena karantarda jama,aba saboda suje suna raddi ma wani, toh wannan kafewar da sukayi tabada gudunmuwa kwarai wajen samun tatattu kuma ingantattu ahli sunnah awannan kasar ta najeriya, sannan kuma ko yanzu idan kabibiya zakaga dalubannan wayanda aketa karantarwa zakaga sune sukafi samun cikakkiyar kamala da siffa da dabi,un dan izala***_ . _ammafa har yanzu acan cikin wayancan kungiyoyi guda biyun masu gaba da juna akan samu wayanda suna cikin kungiyar amma su basa kungiyanci kiran jama,a kawai suke zuwaga qur,ani da hadisai ingantattu***_ . _Toh sukuma wayancan yan izalun masu gaba dajuna wayanda suke kokarin kare kungiya ba kare sunnah ba, sesukaita kokarin rufe wayansu masallatai wayanda ake karantarda Alqur,ani da sunnah, sekawai awayi gari kaji ance kungiyar izala ta rufe masallaci kaza, toh kai idan kasan masallacin sekaji mamaki yakamaka, yaya za,ace izala kuma tarufe masallacinda kai kasan qur,ani da sunnah ake karantarwa???***_ . _jeka kasar kano ko zariya ko abuja ko kaduna kabincika kaji shin kungiyar izala bata taba rufe masallaciba kokuma basu taba hana karantarda qur,ani da sunnah ba, saboda wayanda suke jagorantar karatun ba yan kungiyarsu bane????***_ . . Zamu dakata anan sekuma darasi nagaba idan Allah yakaimu . . . Allah yasa mudace . . Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/ [12:44PM, 10/21/2016] Malam Jameel A Kabo: *DAN IZALA7!!!????* . . *DAGA ZAUREN* . *KITABU WAS SUNNAH* . . *ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ* 📓📔 Watsaps 08036222795 08136182627 . . Cigaban lekca me taken *DAN IZALA!!!???* . Wannan shine bayani na bakwai**** . . _Dan izala baya bin yan siyasa dan sugina mishi masallaci, Aa shi dan izala nagaske baya gasar gina masallaci, shi kokarinsa kawai shine yaga ya gina dalubai, kuma dan izala baya damuwa koda ace acikin daki yake sha,aninsa, wannan dakin shine makaranta kuma shine masallaci, amma dan izala baya zuwa yana roko ko maula dan wani yagina mishi masallaci, sedai shida wayannan daluban nashi sune zasurika tatsar kansu suna taimakawa da,awarsu har sugina masallaci ko babban makaranta****_ . _Dan izala baya gasar hawa mota ko sanya manyan riguna, amma yana daga cikin rudaninda kungiyancin can yakawo sai kaga mutane suna da,awar izala kuma suna gasar gina masallaci harkaji dalibansu suna cewa malaminmu aiyafi naku daukan wanka, masallacinmu yafi naku, toh wannan jama,a ba aikin dan izala nagari bane, domin shi dan izalan asali bashida wani aikinda yafi karantarda al,uma da samarda hadin kansu****_ .. _Dan izala baya gaba kuma baya fada dakai dan baka cikin kungiyarshi, matukar kana kira zuwaga sunnah toh shi dan izala gani yakeyi kaima nashine dukda cewa baka cikin kungiyarshi, saboda dan izala nagari baya damuwa da kungiya ko kungiyanci shidai kawai damuwarsa shine azo abi sunnah****_ . _Izala tariga tazama uwa a najeriya ga duk wani me da,awar sunnah koda bezo yashiga cikin kungiyarba, saboda dole seya fa,idantu da fa,idar kungiyar izala, ko saiya amfanu da amfanin kungiyar izala, wannan yasa dan izala nagari baya fada da duk wani mekira zuwaga sunnah, waboda yasani cewa dakai dashi duk manufarku dayane, kawai hanyar isa zuwaga manufar itace kawai tarabaku****_ . _Amma bama shakkar cewa malaman izala suna kuskure saboda ba ma,asumai bane, kuma duk dan izala nagari bayaso yaji an ambaci waccan rabuwar seyaji abin yana yimasa ciwo, duk dan izala nagari yana bakin cikida wannan rabuwar****_ . _Dan izala nagari duk inya tunada wannan rabuwar kuka yakeyi kuma yana addu,ar Allah ya gafartama wayancan malaman wayanda suka gabata musamman wayanda suka mutu acikin wannan sabanin, sannan kuma dan izala nagari kullun addu,a yakeyi akan Allah yahada kan kungiyar izala ayanzu takoma tahade akan bin qur,ani da sunnah abisa fahimtar magabata***_ . _ammafa wannan addu,ar babu wanda zakaji yanayinta sedai wanda yafito takarkashin wayancan yan izalar wayanda basa cikin kungiyar kowa wato wayanda suke cewa asaita tafiyar takoma kan manhajin salaf****_ . _Duk dan izala nagaske baya zama sai yanada sana'a, wacce da wannan sana,ar ne yake samun abinda yake taimakama kanshi harma ya taimakawa kungiyar tashi, amma cikakken dan izala baya zuwa neman taimako wajen wani dan yagina mishi makaranta ko masallaci kokuma yabiya mishi kujerar hajji, sedai acikin dalubanshi shidasu suke haduwa suna taimakon junansu kuma su taimakawa kungiyar tasu, amma yan izala nagari basa maula kuma basa cin mutuncin kowa****_ . _Amma waccan maganarda mukayi abaya na cewa masu rajin kare kungiyar izala wayanda suke rufe masallaci saboda ba,azo anhade dasu acikin kungiyaba, toh wannan duk mutuminda yake jihohin kano da kaduna yasan ana haka, wanda yanzu danake wannan rubutun jiya nagani da idanuna inda kungiyar izala ta wata gunduma acikin jihar kaduna tahana karantarda qur,ani da hadisan manzon Allah awani masallaci, kuma badan komaiba sai dan wayanda suke karantarwan basuzo sunce sunshiga kungiyaba, toh yanzu mutanen wannan unguwa sunanan sun zur ido sugani shin choci za,a maida masallacin ko mene?? Toh kaga irin wayannan sune yan kungiyar izala, wayanda sukawai kungiyarsu suke karewa bawai qur,ani da sunnah ba, toh amma kubiyoni zuwa anjima idan har ta tabbata sun rufe wannan masallaci kokuma sunhana wannan karatu wanda ni nasani qur,ani da sunnah ake karantarwa dare da rana, amma kungiyar izalar wannan gundumar tace tarufe wannan masallaci, amma kubiyomu zuwa anjima inhar suka tabbatarda rufewan toh zamu baku addreshin masallacin da unguwarda yake wanda yanzu haka izalar yankin yake kokarin rufewa***_ . _toh irin wayannan mutanen ba yan izala nagari bane, sune ake kira yan kungiyar izala, amma wayancan wayanda ake cewa an dakatar toh sune cikakkun yan izala na asali wayanda suke koyarda jama,a***_ . _Dan izala nagaske kuma baya fada saboda anhanashi karatu kokuma an kwace mishi masallaci kuma baya tarzoma dan anhanashi karatu, ansan dan izala da hakuri da maida hankali wajen koyon karatu dakuma karantar dashi ***_ . . Zamu dakata anan sekuma fitowa tagaba . . Allah yasa mudace . . Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/ [3:27PM, 10/21/2016] Malam Jameel A Kabo: *DAN IZALA8!!!????* . . *DAGA ZAUREN* . *KITABU WAS SUNNAH* . . *ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ* 📓📔 Watsaps 08036222795 08136182627 . . Cigaban lekca me taken *DAN IZALA!!!???* . Wannan shine bayani na takwas**** . . _Bayan Allah yataimaki Al,umma ansamu wayannan tsayayyun yan izalar wayanda su basa kira akan azo ashiga kungiyar izala, Aa su kawai karantarwa sukeyi suna wayarda kawunan jama,a suna kafa majalisan koyarda ilimi akan fahimtar malaman farko***_ . _toh wannan al,amari beyiwa sauran wayancan wayanda suke kokarin kare kungiya dadiba kamar yanda nagaya muku, sai kawai wayancan masu kokarin kare kungiya saisuka rika kama sunayen wasu bayin Allah suna zaginsu, suna cin mutuncin manyan malaman duniya musamman malaman hadisi kaji suna kama sunayensu suna cewa yahudawane kokuma kaji sunce yan bidi,ane***_ . _toh duk dan izala nagari baya irin wannan, duk wanda kaji yana zagin malamai toh babu shakka wannan ba dan izala bane dan kungiyar izala ne***_ . _ammafa alura jama,a bama kushe yan izala kuma bama aibantasu, hakika munsani cewa mutanen kirkine kuma muna kyautata musu zato, sannan muna Addu,ar Allah yakara hada kansu yakauda shaidan a tsakaninsu, yasa sudawo sukoma karkashin tutar kitabu was sunnah, sudena zagi da aibanta junansu kuma sudena fada da wayanda suke kira zuwaga sunnah dan basu shiga cikin kungiyarsuba****_ . _duk wanda kaji yana tada jijiyar wuya akan dole dole sai anzo anshiga izala toh wannan ba hakikanin dan izala bane dan kungiyar izala ne****_ . _duk wanda kaji yana maida martani da zagi dan anzageshi kokuma anzagi malaminshi toh shima wannan ba hakikanin dan izala bane****_ . _wanda duk kaji yana raina malamai yana kushe wayanda ba yan kungiyarshiba koda sun fadi gaskiya toh wannan shima jabun dan izalane wato dan kungiyar izala****_ . _wanda zakaga baka ganinshi awajen karatu baya halartan majalisan ilimi kuma zakaji yana tsoma baki cikin sha,anin addini yana cece kuce, toh shima wannan dan kungiyane ba hakikanin dan izala bane****_ . _amma dan izala na gaske sune wayanda zagi ko cin mutunci baya hanasu karantarda mutane, kuma inkaga suna tada jijiyar wuya toh sunnah aka taba bawai su aka taba ba***_ . _Dan izala na gaskiya baya neman taimakon duk wani dan bidi,a gameda da,awarshi, kuma inyana yaki da wata shirka ko bidi,a toh baya neman taimakon wasu yan bidi,ar daban***_ . _dan izala na gaskiya baya murna dan kan wasu jama,a yarabu matukar dai yasan wannan jama,a akan sunnah suke tafiya, koda ba yan kungiyarshi bane****_ .. _kuskurene mutum yazauna baya neman ilimi sedai yaita zuwa wa,azin kasa ko wa,azin mako amma baya zuwa wajenda ake koyarda karatu na sosai, kawai shi seya zauna tunda shi dan izalane shikenan basai yaje yayi karatuba***_ . _Aa dan izala zagewa yakeyi sosai ya maida hankalinshi akan karatu kuma zargin me zargi ko zagi baya damunshi***_ . _zakaji ana sharri ana cewa yan izala suna zagin malamai, ko ace yan izala sun zagi Annabi ko ace yan izala sune suka raba kan musulmin najeriya toh wannan duk karyane jama,a, kamar yanda nafada jiya shehu kaulaha shine wanda yafara sawa aka raba masallaci a najeriya, kuma shine yafara kafirta yan kadiriyya sannan kuma ya kafirta sardauna***_ . _Ana cewa wai munce iyayen Annabi suna wuta ko muna kafirta iyayenmu toh wannan kuma hauma haumace ta yan bidi,a sanda sukaga izala tanata kwashe mutanensu sai suka dinga kirkirar karya suna danganta musu***_ . _Dan izala baya aske gemu kuma dan izala baya take wando sannan kuma dan izala baya sakin hannu asallah***_ . _dan haka jama,a duk inda kaga jama,a suna karantarda qur,ani da sunnah toh wayannan sune hakikanin yan izala koda kuwa baka taba ganinsu akan mumbarin izala suna wa,azi ba, kuma koda kaji sunce maka su ba yan izala bane, toh suna nufin su ba yan kungiyar izala bane, ammadai su azuciyarsu sunsan su yan izala ne***_ . _ko wayanda zaka gani suna shiga facebook da sauransu suna maida martani marakyau dan an zagesu kokuma anzagi malamansu sekaji sun shiga grp sunata zage zage da cin mutunci toh suma wayanna duk yan kungiyane, bawai cikakkun yan izala bane na gasken gaske, saboda haka jama,a yanada kyau mugane aqidarmu kuma musan mu,amalarmu da mutane***_ . _amma mu dakake gani Alhamdulillahi mune hakikanin yan izala wayanda muke tsaka tsakiya, bama kafirta wayanda basa cikinmu matukar basu aikata kafircin kararaba, kuma bama zagin wani saboda ya zagemu, bama kushe wani dan ya kushemu, sannan kuma bama jayayya dan neman kure, sedai mukanyi muhawara dan neman gskyiya dakuma karama juna ilimi, bama kin bin mutum sallah matukar bai kafirtaba, bama zagin shugabanni kuma bama cewa aimusu tawaye****_ . _bama cewa arufe masallaci saboda kare ra,ayinmu, bama hana abi mutum sallah saboda yana aikata sabo matukar bai halastaba, bama cewa ayiwa gwamnati tawaye koda kuwa takama malamanmu,***_ . _mu aikinmu kawai shine abar malamanmu sukarantar damu, kuma bama boye gaskiya saboda neman biyan bukatarmu, bama kira ko rokon wasu mutane muce wai suzo sutaimaka su gina mana masallaci kokuma suzo sudauki nauyin da,awarmu ko sukaimu hajji ko sugina mana gidaje ko siya mana motoci, Aa mukam komai sedai muyishi muda dalubanmu da malamanmu bama shigo da kowa kuma bana shiga shirgin kowa***_ . _wannan bawai ina yabon kanmu bane, kuma bawai cewa nayi bama kuskureba, Aa muna kuskure kuma muna aikata ba daidaiba, amma in akai mana tambihi muna kokarin gyarawa, amma tabbas muna kuskure kuma bama cewa munsan komai, Aa munadai kokarin kamantawa kuma muna karawa da addu,ar neman taimakon Allah****_ . . . Wannan shine karshen wannan lekcar da yardan Allah . . Allah yasa mudace . . Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/ [5:04PM, 10/21/2016] Malam Jameel A Kabo: *DAN IZALA9!!!????* . . *DAGA ZAUREN* . *KITABU WAS SUNNAH* . . *ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ* 📓📔 Watsaps 08036222795 08136182627 . . Cigaban lekca me taken *DAN IZALA!!!???* . Wannan shine bayani na tara*** . . _muna fatar masu karatu zasuyi mana afuwa, saboda abaya munce mungama wannan lekcar, toh daga bisani kuma sai muka tuna cewa ai kamar munyi tuya mun manta da albasane, toh ga albasar zakuji yanzu***_ . _Kungiyar izala babu shakka mutanen alherine kuma kungiyar alherice, sannan kuma muna musu kyakkyawan fatan alheri***_ . _kungiyar izala sunyiwa bokaye wa,azi kuma bokaye dayawa sun tuba sunbar bokanci karkashi alherin da,awar izala***_ . _kungiyar izala tayima christoci da fastoci wa,azi kuma ansamu christoci da fastoci dayawa sun musulinta akarkashin alherin da,awar kungiyar izala***_ . _zan ita cewa tun wucewar Shehu dan podiyo ba,a sake samun wasu mutaneba wayanda suka tsaya sukaiwa sunnah aiki sedai zuwan kungiyar izala***_ . _yan izala sun zagaye kauyuka da biranen najeriya harma makofta duk izala tazagaya taje tayi wa,azi kuma ta musulintarda mutane masu yawan gaske***_ . _Duk wata mace wacce kaganta sanye da hijabi akasar najeriya birninta da kauyenta toh tasamu wannan hijabine sakamakon hasken da,awar ixala koda kuwa wannan matar yar shi,ace ko yar darika***_ . _Inbanda kungiyar izala babu wata kungiyarda za,ace ta zagaye kasar najeriya kakaf da wa,azi, amma sharrin wannan rabuwar yasa suka dena wannan kokarin na musulintarda kafirai suka koma suna rubdugun wayannan ayoyin akan junansu***_ . _Sharrin wannan rabuwar tasa zakaga hatta yan agajin izala ayau zakuga wasu igiyarsu ahannun dama take wasu ahagu, wanda wannan shima ba alheri bane***_ . _sharrin rabuwar kungiyar izala babu shakka yakawowa musulinci tasgaro akasar najeriya da makoftanta, kuma hakan yasa yan bidi,a suka samu bakinda har suke iya raina malaman izala***_ . _muna rokon Allah yaji tausayinmu ya hade kan wannan kungiya yasa sukoma tsintsiya madaurinki daya, suzo suyi abinda zai amfani jama,a suden shagaltuwa da sukar junansu***_ . _amma ina kiraga matasan kungiyar atashi ayi karatu dan Allah, kuma ayi karatun sosai kuma ayishi agaban malamai, amma zuwa wa,azin kasa kadai bazaisa kasamu cikakken iliminda zaka zama malamiba dan uwa***_ . _kuma babbar hanyarda za,abi asamu hadin kan kungiyar shine atashi ayi karatu musamman matasa, kuma mucire hassada da kyamatar juna atsakaninmu, murika duba girman abinda ya hadamu, karmu duba abinda yazo ya rabamu****_ . _Kuma dan Allah mudena zaman gulamace gulmace, muden sukar malamanmu, addu,a zamucigaba dayi akan Allah yahada kawunansu bawai murika shiga cikin rigimarba****_ . _Dan Allah murika kauda kanmu daga duk wani kuskurenda mukaga malamanmu sunayi mubi hanya ta hikima muyi musu nasiha bawai murika zaginsuba, kuma karmu rika zagin wayansu mutane saboda basu shigo cikin kungiyarmuba***_ . _Kuma idan aka zagemu ko aka zagi malamanmu toh dan Allah mudena maida martani da zagi, kokuma arika cin mutunci, Aa murika maida martani cikin natsuwa kuma da dalilai na sharia ba wai murika kafa hujjah da kwatanceba***_ . _Allah yajikanmu yajikan malamanmu yajikan iyayenmu, yasa muyi karshe mai kyau, kuma Allah ya tabbatarda diga digau akan sunnar Annabi muhammad (s.a.w)***_ . . . Wannan shine karshen wannan lekcar da yardan Allah . . Allah yasa mudace . . Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like https://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/ adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *