Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, April 3, 2017

DAN ADAM complete

adsense here     Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Novels villa Duniyan novels Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: +2347039625239                 D'AN ADAM        @Rufaida Omar Sadaukarwa....ga....          Jiki na rawa take kwankwasa k'ofar d'akin da k'arfi tana fad'in.   "Habiba! Ke Habiba!" "Na'am." Ta furta cikin magagin bacci kafin ta mik'e ta bud'e d'akin. Ganin aminiyarta Saude ne ya sanyata wartsakewa babu shiri. Ta waro ido. "Lafiya dai Saude?"   Saude ta rage murya. "Ina fa lafiya? Ga waccan shegiyar tana nak'uda. Ai idan ta haihu na kad'e."   Habiba ta dafa kafadarta. "Karki damu, ai idan har ni ce unguwar zoma ba zata haife d'anta da rai ba. Itama muje sai ta bar duniya."   Wani sanyi ya mamaye zuciyarta. Habiba ta dauko kayan amfani ta yi gaba Saude na biye da ita. Lokacin karfe shida na safe.   Acan suka iske Malam Balarabe yanata faman zirga-zirga a tsakar gidan. Shigowarsu ne ya sanyashi nufarsu da saurinsa.    "Yauwa, Habiba don Allah taimaka mata."   "Ka kwantar da hankalinka Malam Balarabe, in sha Allahu lafiya kalau zata sauka. Ka sama mana itatuwa dai na dora ruwan zafi.   Daga haka ta shiga ciki, Saude na gefe tana matsar kwallar munafunci ita a lallai tausayin abokiyar zamanta takeyi. Da ire-iren kissar da take cin galabar Malam Balarabe kenan. Da sauri shi kuma Malam ya fice.     Saude dake tsaye sai jin kukan jariri tayi. Gabanta ya bada ras ras! A gigice ta fad'a d'akin. Bakinta na rawa ta tambaya. "Ta..ta.." Ina maganar gaba daya ta mak'ale a saman le66anta.  Habiba ta dubeta tayi mata alama da tayi shiru. Dole ta rufe bakinta ba don ta so ba.    Habiba ta kammala yanke cibi ta mik'awa Saude d'iyar. Saude cikin kukan bakin ciki marar sauti ta kar6eta tana ji kamar ta shak'eta ta mutu.     Ga mamakin Saude, Habiba filo ta dauko ta danne fuskarta da shi, tun Hasiya na shure-shure har tayi lakwas. Saida ta tabbatar da cewar ta cika sannan ta yi jifa da filon ta mik'e tana sharce gumi.     Saude jikinta babu inda baya rawa. "Ta mutu." Ta fad'a a gigice.  Habiba ta gyada mata kai sannan ta dubeta.   "Eh na cika burinki. Yanzu Malam na dawowa mu nuna mutuwa tayi bayan ta haife d'iyarta. Ko kusa kada ki nuna wata alama ta rashin gaskiya Habiba. Ita kuma wannan k'aramar alhaki ce, ni nasan yanda zamuyi da ita nan gaba kadan."    Saude ta amince da batun aminiyarta.  "Shikenan."   Ai kuwa sunajin sallamar Malam suka hau salati da koke-koke. Malam baisan sadda ya yarr da itatuwan da ya riko ba. Jiki na rawa a gigice ya fada dakin yana tambayar ko lafiya.   Ya dubi Saude hannunta rike da jaririya tana ta canyara ihun kuka kafin ya kai dubansa ga Habiba. Bai yi wata-wata ba ya yi kan Hasiya yana kiranta a rud'e. "Hasiya! Hasiya!!"   Ina! Ya fahimci abinda ake nufi, Hasiya ta rasu. Ya hau salati yana zubda  ruwan hawaye. Baice uffan garesu ba ya fita zuwa tsakar gida ya zauna.                      *    *     *    Haka yana ji yana gani aka wanke Hasiya aka kaita gidanta na gaskiya batare da 'yan uwanta sun sani ba saboda nisan dake tsakanin garuruwansu.      Malam Balarabe ya shiga tashin hankali matsananci, ya rame yayi bak'i kamar ba farin mutum ba. Ga duk wanda ya ganshi dole ya tausaya mishi musamman abokansa wadanda suka riga sukasan irin kaunar da yake yiwa matarsa Hasiya don kuwa baya 6oyemusu irin yanda take kyautata mishi a rayuwa ta hanyar yin biyayya ga dukkanin umarninsa.       Sai ranar bakwai sannan babban yayan Hasiya da kuma mahaifiyarta da sauran yayyunta uku mata suka iso. Sun koka kwarai da rashin yar uwarsu. Saidai babu yanda suka iya, su mutane ne wadanda sukasan ya kamata, sam basu zargi komai ba. Toh me zasu zarga? Bayan sun san irin kaunar da Saude ke nunawa Hasiya a gabansu tamkar ba kishiyarta ba. Wannan ne yasa koda Saude tace zata rik'e yarinya, babu wanda baiyi na'am ba. Haka suka tattara suka koma garinsu batare da shakkar komai ba.                         *   *   *   Wahala, tsangwama da kyara, babu irin wacce d'iyar Hasiya, wacce ta ci sunan mahaifiyarta Hasiya suke kiranta da Ummi, bata gani ba wajen Saude. Saidai a gaban idon Malam Balarabe, babu abinda Saude bata yiwa Ummi na nuna kulawa da kauna. Yarinya ce mai hakuri, haka take hakura da komai ta shanyeshi, anan ma Mahaifiyarta ta dauko.   Saida ta kai shekaru goma sha uku a duniya sannan Saude ta samu ciki. Zo kaga murna wajen Saude da mijinta. Sai ya zamana bayan Saude ta haifi diyarta Mariya. Ta chanja kwarai a gidan. Ta hanyar asiri da tsafi, ta siye zuciyar Malam Balarabe ya zamana ko kallon Ummi baya kaunar yi. Komai ya samo, daga Saude sai Mariya. A wannan lokacin ne, Habiba ta zo da shawarar tura Ummi aikatau. Ba musu ba jayayya, Malam Balarabe ya amince da a turata ko bangon duniya ne. Duk acewarsa, bashi da matsala ko wata damuwa...!      DAN ADAM @Rufaida Omar   (02) "Wai kina ina ne? Baki kammala shirya tsummokaran naki ba?"   Ummi dake d'aki tana kuka, ta tsinci muryar Baba Saude wacce ta sanyata rud'ewa babu shiri. Cikin rawar murya ta amsa a tsorace.   "Na gama Baba, ganinan." Daga haka ta mik'e da saurinta ta dauki ledarta ta fito har lokacin kuka takeyi sosai.    Baba Saude na zaune tare da Habiba sai wata mata wacce ita ke dillancin mata zuwa gidajen aikatau, a gefe kuwa, Mariya ce ke faman cin masara hankalinta kwance, ta yi filo da cinyar uwarta.    Wata harara Baba Saude ta watsawa Ummi.   "Shegen bakin hali, kukan me kikeyi na kinibibi toh? Gwara ki share hawayenki ma, don babu abinda zai hana yau ki bar gidan nan."    Ummi ta durkushe a gefe tana share hawaye yayinda wasu ke k'ara kwaranyowa har da majina tana gogewa da hijabinta.    Baba Saude ta juya ga dillaliya. "Ina jinki Yaha, yanzu dai duk wata zaki dunga aiko da albashin nata?"   Wacce aka kira da Yaha ya gyara zaman mayafinta lokacin da ta mike tsaye.   "Karki damu, duk wani abin arziki da ta samu ma, naki ne Saude. Komai zan tattaro na kawomaki. Kedai ki kwantar da hankalinki kamar kin kashe d'an maigari."   Sukayi dariya sannan Yahanasu ta dubi Ummi tana yamutse fuska.   "Wannan dogon gashin idan bakiyi wasa ba sai na yankeshi kafin mu k'arasa, yarinya sai shegen munafunci. Zaki maidashi cikin hijabin ko kuwa?"    Jiki na rawa Ummi ta ja jelar kitson kalbar da ta jagwalgwala a kanta ta maidashi cikin hijabi. Don kuwa bata isa ta je gidan kitso ba har ya saka ran samun mai kyau. Ta mike ta bi bayan Yaha wacce tuni tayi sallama da su ta bata umarnin ta taso.     Suna ficewa Habiba da Saude suka tafa suna shewar jin dadi.   "Ina sonki wallahi aminiya, bani da tamkar ki." Cewar Saude wacce ke jin ranta yayi wani mugun sanyi.    Habiba ta gwaguyi masarar hannunta tana wani rausaya kai.   "Ni ce fa, sai ma idan kudi sun soma shigomaki a hannu zakisan cewa ba k'aramin gata nayi miki ba. Ai ba'a saurin illata d'iya mace haka, ita tamkar jari ce, ko zata bi duniya in dai zata nemo ta kawomaki to kada ki damu kanki, ke dai ki more rayuwarki ta jikinta. Amma fa 'yar kishiya nake nufi."     Sukayi shewa da dariyar farin ciki. Koda Malam Balarabe ya iso suka sanar mishi cewar Ummi ta tafi, ko a jikinsa, karshe ma watsar da zancen yayi ya bi Mariya da tsarabar 'yar tsanar da ya siyomata.                       *   *   *     Tun Ummi na kuka a motar kasuwa, har ta gaji tayi shiru tana kallon hanya kafin bacci kuma mai nauyi yayi awon gaba da ita.  Cikin baccin kuma ta ji Yaha na tashinta.   "Ke! Ke!" Firgigit ta farka tana dubanta. "Na'am." Ta amsa a tsorace don kuwa kusan zuwa yanzu Ummi ta saba da hakan, da wuya tayi bacci a tasheta batare da ta firgita ba. Don sau da yawa ruwan sanyi ake kwara mata ko kuma a sanya k'afa a haureta, wani sa'in kuwa da bulala ake tashinta. Yaha ta watsa mata mugun kallo.   "Sai ki sauko tunda motar bata ubanki bace ko? Shashashar yarinya."   Ummi ta lura su kadai ya rage a motar, cikin rawar jiki ta bi bayan Yaha suka fito. Sai lokacin ta lura cewar cikin wani babban gari suke lura da yawan mutanen da ta ga suna faman zirga-zirga. Haka tayi ta bin bayan Yaha har suka fito daga tashar zuwa bakin titi. Saida gabanta ya fad'i ganin ababen hawa da yawa saman kwalta. Ta tsorata sosao da yawan mutanen da ke zirga-zirga awajen. A kauyensu na Ringim babu motoci har haka. Yaha ta tsayar da d'an sahu. Nan Ummi ta ji tace ya kaisu Gadon K'aya.    A hanya Ummi tayi ta rarraba ido tana duban tituna. Abin bai gama bata mamaki ba, saida ta ga sun hau wani dogon kwalta ta sama.    Ta kankame ledar kayanta, basuyi aune ba sai ji sukayi ta fashe da kuka.   "Wayyo Allah zan mutu!" Ta fad'a iyakar k'arfinta. D'an sahun harda kokarin juyowa.   "Lafiya?!" Yaha ta rankwashi kanta. "Ka bar 'yar iskar yarinya mana, "yar kauye. Ta ji ta a titin 'yan birni zata kawomin iskanci. Yanzun nan zan bubbugeki idan baki rufemin wannan  karamin bakin naki ba mai kama da na tsutsa."     Dariya d'an sahun ya kwashe da shi. Ita kuwa Ummi da sauri ta rufe bakinta, tana kuka a ciki-ciki har suka sauka idanunta a runtse yayinda jikinta ke kad'awa.     D'an sahun kuwa har da labarin tsohuwar da tayi makamancin hakan ya shiga bawa Yaha. Kasancewar Yahar itama ba baya ba wajen surutu, nan ta biyemishi suna tayi tana 6a6aka dariya. Ummi dai tana jinsu, alokacin ta bar kukan.     Sunyi kusan rabin awa suna tafiya sannan suka iso unguwar da ta ji Yaha tayi kira da Gadon K'aya. Haka ta ji Yaha nayita zuba mishi kwatance har suka iso wani gida d'an flat da shi. Ta biyashi kudinsa sannan ta dubi Ummi. "Sauka muje."   Ba musu Ummi ta sauka da saurinta. Yaha tayi gaba ta bi bayanta tana wulk'a idanu tana duban layin. Yaha ta shiga kwankwasa k'ofar tana sallama. Can ta tsinci muryar maigadin na cewa.  "Ana zuwa."         Yaha ta rik'e k'ugu tana taunar cingam ta dubi Ummi. Ganin haka yasa Ummi kauda nata idanun cikin sauri.     "Don ubanki saura kiyi min halin kauyenci sai na shak'e ki kin mutu har lahira. Banason yawan kalle-kalle. Kiyi ladabi so..."   Sauran maganar ya mak'ale a fatar bakinta ganin an soma k'ok'arin bud'e k'ofar.    Maigadin ya d'an lek'o da kansa. Farin buzu ne. Ganin Yaha ya sanyashi sakin fuska.    "A'a mai yara, kaine?"   Hakanan yake kiranta. Tayi dariya. "Ni ce dai Baba. Hajiyar na ciki ko?"   Ya bata hanya ta shigo yana amsa mata.   "Eh yana nan. Ina ka samo d'an garinmu?"    Ya fad'a yana duban Ummi wacce ta durkusa da rawar jiki ta gaisheshi.    Yaha ta dubeta tayi mata alamun ta mik'e.    "Wannan ba 'yar garinku bace. 'Yar Maiduguri ce."    "Anya? Yana kama da mu." Yaha dariya kawai ta d'anyi batace uffan ba.    Daga haka sukayi ciki.  Ummi na bin farfajiyar da kallo a sace don bataso Yaha ta kamata tana kallon bayan ta ja mata kunne. Babban gida ne sosai, an k'awatashi da shuke-shuke. Daga wajen ka rantse ba shi da wani kyau ko girma don kuwa ko fenti ba'ayi ba daga wajen.     Haka suka isa har bakin wata k'ofa. Yaha ta murd'a ta shiga. Suka cigaba da tafiya a doguwar barandar dake wajen har suka iso tsakar gidan. Acan bakin rariya, wata babbar mace dattijuwa ce ke zaune saman kujera irin ta tsakar gida tana wanke-wanke.   Ganin Yaha ta washe baki.   "A'a, lale marhabin da Hajiya Yaha. Yau kuma zuwan rana ce?"   Yaha ta numfasa fuskarta na nuna gajiya.    "Bari kawai Ramma, duk a gajiye nake. Hajiyar na ciki mu k'arasa?"    Ramma fuska a sake ta amsa tana duban Ummi wacce ke takure jikin bango.    "Eh tana ciki." Ummi da sauri ta gaisheta. Ramma ta amsa. Har suka kama hanya Ramma na binta da kallo, yarinyar da alamu zasu d'asa da Hajiya Madina, don kuwa da alama nutsastsiya ce DAN ADAM @Rufaida Omar           04       "Sannu Ummi." Muryar Amina ta katsemata tunani, ta dubeta, sukayi murmushi a tare.   "Yauwa."   Amina ta ninke abin sallar ta ajiye a gefe. Zama tayi a gefen katifa kusa da Ummi tana dubanta.    "Daga wane gari kuke?" "Ringim." Ta amsa a takaice.  "Lallai, baku da nisa sosai." Ummi zuwa yanzu ta dan saki jiki da Amina ganin irin yanda take janta a jiki.  Wannan yasa itama bata ji nauyin tambayarta ba.   "Ke ba anan kusa kike ba?" Ta gyada kai. "Anan dai nayi rayuwata, amma mahaifina d'an Maradi ne can cikin jamhuriyar Nijar. Zama da neman abinci ne ya kawoshi Nijeriya sukayi aure da Innata, amma yanzu ya rasu, ya barmu mu hudu yaransa. Ni ce 'ya ta uku a cikinsu."   Ummi ta d'an tallafi kumatunta. "Kema aiki kike yiwa Hajiya?" Amina ta murmusa. "Ni ina yiwa Hajiya Mama aiki ne, kanwar Hajiyarnan ce, abinda yasa kika ganni a gidannan, sunyi tafiya ne da mijinta da yaransu, shine dalilin da yasa na dawo nan da zama kafin su dawo."     Ummi ta jinjina kai cike da gamsuwa. A ranta ta ji babu dad'i, kenan itama wataran zata bar gidan ta barta?     "Ya dai Ummi? Kinyi shiru ina magana."   Ummi a sanyaye ta girgiza kai. "Bakomai."   Jin haka yasa Amina yin murmushi. "Shikenan, tashi muje mu tattara falo da kicin kafin Hajiya tayi magana, ki dunga lura da dukkan abinda nakeyi, nasan karshe ke zaki maye gurbina."    Ummi bata ko damu ba, idan ana sabo da aikin wahala, ai yaci kuwa ace ta saba, ina take samun damar yin cikakken awa sadda tana gidan babanta batare da an had'ata da wani nannauyan aikin ba? Gashi anan har gatan da za'a gyara mata kai a bata wajen kwana tsaftatacce da abinci mai kyau ta samu. Ai babu abinda zata ce ga Ubangiji sai godiya.    Haka ta bi bayanta zugui-zugui suka fita. A falon suka iske Adnan da kannensa su biyu, wadanda ta ji Ramma ta ambacesu da Ihsan, Hanifa da Fahad wanda shi ne auta a d'akin nasu.      Adnan hankalinsa kacokam yana kan wayar hannunsa yana faman latse-latse, yayinda Ihsan ta dukufa wajen koyawa kannenta aikin gida da aka basu a makaranta. Shekarun Ihsan goma sha uku a duniya zata shiga na hud'u, sa'ar Ummi ce. Hanifa kuwa, tana da shekaru goma sha biyu bata da tazara tsakaninta da Ihsan, Fahad ne mai shekaru takwas a duniya. Daga kansa kuma, Hajiya Madina bata k'ara haihuwa ba.     Yaranta gaba daya su takwas ne cif, mata uku ne kafin zuwan Adnan duniya, Rahila, Na'ima, Aisha, gaba dayansu ukun suna gidajen aure.       Shigowarsu falon ne yasa su d'ago kai su dubesu. Adnan ya k'urawa Ummi ido fuskarsa a sake sannan ya maida dubansa ga Amina.   "Ummi sunanta ko?" Amina ta gyada kai tana murmushi wanda ya riga ya zamto jikinta, ko kusa bata rabo da shi.    "Itace." Ummi ta durkusa ta gaisheshi da saurinta sannan ta gaida su Ihsan. Ai kuwa  su Ihsan suka tuntsire da dariya. Adnan ya dauki filon kujera yana dariya ya jefi Ihsan da shi.   "(See you), mene abin dariyar?  Ai na isa a gaisheni, kune dai daga yau kada ki k'ara gaishesu, na tabbatar kin girme musu." Ya karashe yana maida dubansa ga Ummin.    Ihsan ta jinjina kai. "Tab, wallahi saidai mu tafa, na tabbatar bazata girmeni ba. Kuma idan ma aka ajiye wannan a gefe ai 'yar aikinmu ce dole ta girmama mu."    Ta karashe tana jifan Ummi da kallon eh sun isa. Ummi dai ta kara sunkuyar da kanta. Amina batace komai ba don kuwa bata fiye shiga harkar Ihsan ba, sanin da tayi mata na cewa ta tsani wasa da duk wani wanda yake karkashinsu. A ganinta, bai kai har a zauna a sakar mishi fuska ba.    Abin yakan bawa Amina mamaki, yarinya tun bata tafasa ba tana neman k'onewa? Ta tabbata nan gaba idan Ihsan tafi haka za'a ga abu.    "Zaki fara ko?" Cewar Adnan lokacin da ya mike tsaye.   Ihsan ta dara a karo na biyu sannan ta dubi su Hanifa.   "Malamai ku maido hankalinku mu cigaba. Nasoma jin bacci wallahi."   Wannan yasa su Hanifa nutsuwa don suna d'an shakkarta kasancewarta itama wani sa'in akwai masifa. Hakanan ta iya kaiwa mutum bugu, kodan ita din tana da jiki kamar kazar gona.     "Muje Ummi."   Sai lokacin Ummi ta mike, Amina daman tana tsaye bata russuna ba. Tasan Ummin itama don yau ta zo ne, amma ita kam tuni an wuce wajen, don wani lokacin bata daukar rainin Ihsan, saidai duk randa ta biyemata suka yi cacar baki ko yaya ne, toh fa tana shan zagi da gori wajen Hajiya Madina. Sam, bata daukar cin mutunci akan yaranta, komin girmanka, muddin ka ta6a mata yara toh fa zatasan yanda tayi ta rama. Idan kuwa daga matan gidan ne, acan fadar maigidan ake k'ulla musu k'ullalliya. Shi kuwa ya hau ya zauna.       Haka Ummi ta taimaka suka kammala gyara komai na kicin sukayi wanke-wanke. Lokacin ana gabatar da sallar isha'i a masallacin unguwa.    A gurguje suka fito suka tattara falon, Ummi na lura da komai, a karshe bayan sun kammala, Amina ta fiddo dukkan abinda tasan zasu bukata wajen cin abinci ta jera bayan ta shimfid'a babbar ledar cin abinci a tsakar falon. Daga nan ta dubi Ummi.   "Jeki kiyi sallah, zan sanarwa Hajiya mun kammala." "Toh."   Daga haka Amina ta mik'a wani d'an (Corridor) ita kuwa ta nufi dakinsu.    Har ta idar da sallar Amina bata dawo ba, nan kuma ta zauna ta soma gyangyadi don kuwa ba karamin gajiya tayi ba. Ta kwanta saman katifar dake shimfide ta mutum d'aya, wani dadi taji ya ratsata, yayinda iskar fanka ke kad'ata.   "Ashe nima zan kwana saman katifa wataran?"   Ta fad"a a fili. Tana nan kwance ta ji shigowar Amina. Da sauri kuma ta mik'e zaune tana mutsistsika ido.   "Har kin soma bacci wai? Taso mu ci abinci."   Ta mike ta bi bayanta, falon wayam, kadan-kadan ta dunga jiyo sautin dariya da hirarrakinsu daga can cikin da batasan iyaka zurfi da yanayinsa ba.    Amina ta kammala kwashe komai ta wanke na wankewa, tayi mamakin yanda bata nemi tayinta ba. Suka zauna suka ci tuwo da miya sukayi nak, a karshe suka sha ragowar romon kifi wanda duk an jagwalgwalashi da k'ayoyi, haka suka dan tsinci na tsinta suka zubda sauran.    Bayan sun kammala, Amina ta rufe kicin din bayan ta kashe fitila, ta rage fitilun falon sannan suka shige dakinsu suma.   "Bazasu dawo falon ba?" Cewar Ummi. Ta gyada mata kai. "Ai kuma shikenan, acan babban falon Hajiya suka fi zama, matukar kinga sun shige, toh sai kuma wata safiyar, don daga nan kowa makwancinsa yake nufa."    Ummi ta jinjina kai kawai.  DAN ADAM      @Rufaida Omar             05   Bayan shigarsu Amina ta dubeta. "Idan kika bi shawarwarin da zan baki, toh lallai zaki zauna da kowa lafiya a gidannan. Yanzu na lura kina tattare da gajiya, ki kwanta ki huta, gobe ma yi maganar idan Allah Ya kaimu da rai da lafiya. Kinji ko?"   Ta gyada kanta tana murmushi, haka kawai ta ji tana kaunar Amina.   "Toh Anti." Antin da ta kirata da shi ya sanyaya ranta sosai, itama ta ji tana kaunarta kamar yar uwarta ta jini. Tana mamakin uwar da ta haifi yarinya kyakkyawa har haka, ta juma iya barinta ta fito aikatau. Kodayake, rayuwa ce ke sanyawa wani lokacin, ba don rai yana so ba. Ita ta ta6a zaton zatayi wani aikatau? Ko a mafarki a'a.     Ta barwa Ummi katifa; ita kuwa tayi amfani da bargo ta shimfida a gefenta ta kwanta. Ummi na jin sadda take zuba ruwan addu'o'i, abin ya bata sha'awa. Daga nan bacci ya kwasheta batare da ta shirya ba.         ■●♣♣♣♣♣▪▲♥♥♥★★★★★        Washegari dakyar ta iya mik'ewa saboda dad'in baccin da ta ji. Amina ta jima tana tashinta, har daga karshe ta hakura tayi sallah sannan ta k'ara dawowa ta tasheta. Sai lokacin ne kuma ta farka. Ummi harda su miyan bacci.    Bayan ta idar da sallah tana shirin komawa ta kwanta Amina ta dubeta tayi dariya kad'an.   "Lallai Ummi kinaso Hajiya ta bud'emiki wuta. Ai muddin yaranta zasu makaranta to bacci fa ya k'are mana. Sai an had'a musu shayi an dafawa Fahad indomi don kuwa kullum da shi yake tafiya. Sauran kuma wani sa'in shayin ma ba shansa sukeyi ba haka suke tafiya basu damu ba. Sannan akwai gyaran dakunan yara da Hajiya. Sauran ayyukan da ya shafi kicin da falo da tsakar gida, duk ba namu bane, yana cikin aikin Ramma, sai da daddare ne ma tattara falo da kicin yake dole a kanmu. A yanda nasani kenan yanzu, bansani ba ko kema haka zata d'oraki akai ko kuma zata chanja tsari."   Ummi dai tayi shiru kawai tana sauraronta. Suka fita falon. Amina ta kunna fitilu wanda ta tabbatar ita da ta kashe d'in, ita ta kunna don babu wanda zai fito. Adnan ko zai tafi masallaci, zagaye yakeyi ta k'ofar waje ta d'akinsa. Ummi 'yar mik'omin wannan da wancan ce, tana lura da abinda Amina keyi. Haka kuma tana biye da ita da fahimta.     Komai suka hada, Amina ta zuba Indomin a filas din Fahad na makaranta, ta had'a shayin sannan suka fito. A falon suka iskesu, kowannensu na shiri. Ihsan ta shirya Fahad tsaf cikin riga ruwan goro da bulun wando na makaranta. Itama ta shirya cikin riga fara da siket ruwan toka, sai farin hijabi da safa fara, ta saka bak'in takalmi. Shima Adnan irin kayan Ihsan ne saidai wando ne nashi dogo, da farar hula (Face cap) wanda aka buga tambarin makarantar daga gaba. Shima bak'in takalmin ne sai farar safa, wanda hakan ya kasance tsarin makarantar.    Ba karamin kyau da burge Ummi sukayi ba, gaba d'aya sai ta shagaltu a kallonsu tana murmushin inama itace ta samu wannan gatan na zuwa makaranta. Tana son karatu sosai saidai bata da mai mata gatan nan.    Adnan na kokarin zura (belt) na wando ya ankara da ita. Ya dubeta batare da ya cigaba da abinda yakeyi ba, bai kai ga magana ba, tayi sauri ta durkusa ta gaisheshi, ya amsa sannan ta juya ga Ihsan wacce take zura littafi cikin jakarta ta makaranta, itama gaisheta tayi. Ihsan ta amsa tana hura hanci cike da jin ita d'in ta isa ta kai. Adnan ya girgiza kai ya ja karamin tsaki. "Na gayamaki ki daina gaisheta ko? Kodayake don kanki zaki bari ai."    Ihsan ta turo baki. "Nidai wallahi broda kana ban kunya a gaban 'yan aiki. Kaga banason irin haka, wannan jawomin raini ne fa."   Harararta kawai yayi baice uffan ba. Ta dubi Amina. "Ki zubomin shayi."   Amina ta juya bayan ta ajiye na Fahad a gabansa da biredi da bota. Can sai gata ta fito da kofuna biyu a hannunta. Ta ajiyewa Ihsan d'aya, sai Adnan wanda take yace bazai sha ba. Ta ajiyewa Fahad filas d'in abincinsa sannan ta ja Ummi suka fad'a d'akin da  Ihsan da Fahad ke kwana. Karamin daki ne sai gado mai hawa biyu na yara. Saman an saka zanin gado kalar ruwan hoda mai zanen (Barbie), na k'asan kuwa an saka bulun zanin gado mai zanen (spider-man). A gefe kuwa, kwabar kaya ne guda biyu, shima d'aya ruwan hoda da fari, dayan kuma bulu da fari. Sai kafet mai duka kaloli ukun da aka kawata tsakar dakin da shi, da kuma k'arami na takawa a daidai hanyar bandaki. Daga can kuwa, karamin madubi ne, sai kwaba da abu mafi yawa akansa, kayan kwalliyar Ihsan ne. Fanka ce kawai a d'akin, sai bada wadataccen iska take. Ba k'aramin burge Ummi dakin yayi ba. Ta saki baki tana kallo.     "Ummi ki dunga lura kina rike abubuwan da nakeyi fa, don kuwa gobe zai iya kasancewa ke d'aya zakiyi. Da zarar Hajiya Mama ta dawo zan tafi."   A sanyaye Ummi tayi magana. "Yaushe zasu dawo?"    Tana murmushinta na sabo ta amsa. "Hausa nayi miki, ni kaina bansan sadda zasu dawo ba amma na tabbatar ba zata kaisu da nisa ba tunda an koma makaranta, yara zasu je. Nufina yau idan ina nan gobe bana nan, kece zakiyi."   Ta jinjina kai. Tare sukayi aikin, har inda ake daukar sabon zanin gado idan na kai sunyi datti saida Amina ta nunamata. Suka fito, tuni yan makarantar sun tafi lokacin takwas ma ta wuce, saidai sam Hajiya bata lek'o ba. Saida suka shiga dakin Adnan nan ma suka gyarashi tas, shima madaidaicin daki ne, da katifa babba wacce bata da bukatar katakon gado. Komai na dakin adon fari da bulu ne, babu wani tarkace a dakin sosai. Amina ta barta da gyaran gado don taga yanda zatayi, sai kuma ta bata mamaki don tayi kokari ba laifi. Ta dan gyaggyara inda baiyi ba sannan Ummi ta share dakin, anan kam ko Amina ba zata nunamata iyawa ba. Bayan sun fito, shayin suka zuba suka sha da sauran biredin sannan suka maida komai kicin suka koma dakinsu. Suna daga kwance Amina ta soma magana.   "Zanso kafin na fad'amaki halayen mutanen da zakiyi zama tare dasu, na soma gayamaki tsarin gidansu don ya dace kisan da wadanda zaki zauna."   Ummi ta muskuta tana dubanta gaba daya ta tattara hankali da nutsuwarta ga Aminan. Ganin haka Amina ta soma. DAN ADAM @Rufaida Omar (03) "Assalamu Alaikum." Cewar Yaha alokacin da ta murd'a k'ofar falon ta sanya k'afa. Wata dattijuwa wacce ke zaune, wata budurwa mai kimanin shekaru sha shida. Tana zaune a k'asan lallausan kafet tana daddanna mata k'afa. Ta nutsu sosai, kamar kace arr! Ta arce. Ummi dai kallonsu take, daga yanayin yanda ta ga Hajiyar na dubanta, ta sha jinin jikinta, da alama dai matar ba ta da mutunci don kuwa fuskarnan nata babu ko alamun fara'a. "Ranki ya dad'e baya goya marayu, barkanki da hutawa." Hajiya tayi wani murmushi, da alama ta ji dadin wannan kirari na Yaha. Ummi dai kallon ikon Allah take, yanayin shigarta da komai ma, sun isa shaidar tana cikin rayuwar daula. Wani kallo da Yaha ta watsa mata ne ya sanya ta ba shiri russunawa sosai gami da rankwafar da kanta ta gaisheta. Hajiyar bata ko amsa ba, saidai ta k'ura mata ido tana k'are mata kallo. Can kuma ta yamutse fuska ta rausaya kai gami da maida dubanta ga Yaha. "Wannan ce?" Yaha ta washe baki tana jinjina kai. "Kwarai kuwa ranki ya dad'e uwar gida ran gida, itace, sunanta Hasiya amma Ummi ake kiranta." Ummi dai sai zazzare ido take kamar shege a rabon gado, Hajiya Madina tayi murmushi, ko babu komai takan ji dadin wannan kirari da Yaha ke mata. "Tayi sosai, na tabbatar, zata iya dukkan ayyukan da na na bata. Ince dai bata da son jiki?" Yaha har lokacin bakinta ya k'i rufuwa don ji take kamar ta shid'e don dad'i domin kuwa ta sha kawowa Hajiya Madina yara, basu yi mata ba. Ta janye k'afafunta, gami da kallon budurwar batare da tace uffan ba, ta mik'e ta wuce don ko Hajiya batayi magana ba, ta karanceta, wato dai ta basu guri. Bayan komawarta ciki ne, Hajiya Madina ta dubi Yaha. "Yahanasu, ina fatan kin shaida mata cewar banason wasa, ba kuma na son son jiki. Dukkan wasu ayyuka da na sanyata, inaso ta kammala su alokacin da ya kamata. Ba kuma na son k'azanta, ta kula sosai don kuwa naga yanayinta, da alama k'azamar ce." Ummi ta sunkuyar da kai tana sosa gashin kanta wanda amosani ya bi ya takura mata, idan ma ance da kwarkwata lallai babu musu don bata da gatan da Saude zata wanke mata kai. "Kiyi hakuri, na tabbatar ba zaki samu wannan matsalar ba. Sau daya aka gwada mata yanda zata gyara jikinta, na tabbatar babu wata matsala da zata biyo baya." Hajiya Madina ta jinjina kai alokaci guda ta yamutse. "Yauwa, don kinsan banason abinda wadancan shirmammun zasu samu damar zagina. Ko kusa banason wani mishkila ya fito daga d'akina." Dariya Yaha tayi, ta gane Hajiya Madina tana nufin kishiyoyinta, Hajiya Rakiya da Hajiya Munira. "Ai kin wuce nan Hajiyata, baya goya marayu. Kar kiji komai, yarinya ce mai kaifin basira. Zata bi dukkan umarninki batare da kin 6ata rai ba. Kwarai, ta ji dadin kalaman Yaha. Daga nan ta mike da nufin zuwa gabatar da sallar la'asar, bayan ta umarci budurwar nan da ta ambata da Amina, da ta nunawa Ummi wajen kwanansu. Amina a gaggauce ta bi umarnin Hajiya. Suka wuce tarr har Yaha wacce zata d'auro alwalar sallah itama. Ummi ta dubi d'akin, katifa d'aya ce sai filo, a gefe kuma jakar kaya ne. Sai kofa daya wacce ta ga Yaha ta shiga ciki, wannan ya tabbatarwa Ummi, bandaki ne. An malale dakin da ledar tsakar daki. Fentin dakin mai wani kyalkyali ne, fari da ruwan hoda, saidai babu komai na more rayuwa ciki. Acan kusa da jakar kayanta, ta ajiyewa Ummi nata da murmushi saman fuskarta ta dubi Ummi, haka kawai ta tsinci kanta da murna sosai, ko babu komai ta samu abokiyar hira. "Nan zaki dunga kwana." Ummi ta mayarmata da martanin murmushin, saidai har lokacin bata saki jiki ba don kuwa ko k'arar k'ofa ta ji sai ta firgita. Ta riga da ta saba da hakan. Yaba ta fito ta shimfida dardumar dakin ta tayar da sallah. Itama Ummi ta shiga, saidai tayi turus don kuwa bata saba da bandakin yan gayu har haka ba. "Bari na nuna maki yanda zakiyi." Cewar Amina daga bayanta, wannan yasa Ummi matsawa, ta shigo. Nan ta gwada mata komai, Ummi tayi godiya cikin muryarta sassanya sannan ta shiga ta d'an kara k'ofar don ta tsorata, bata so ta rufe ta kasa bud'e kanta. Bayan tayi alwala, irin yanda ta saba ganin mutane nayi don kuwa ko alfarmar zuwa makarantar islamiyya, Ummi bata samu ba. Tayi yanda ta iya sannan ta fito ta tayar da sallar. Tasan ana yin sallah raka'a hud'u a lokacin nan hakan yasa ta soma babu wani karatun kirki don babu abinda ta iya. Ta idar ta zauna tana motsa baki sannan ta yi jugum tana kalle-kalle. Bayan Yaha ta kammala suka fita, Ramma ta basu abinci, nan suka ci sannan Hajiya ta sallami Yaha ta tafi da abin arziki       DAN ADAM            06 Maigidan, sunansa Alhaji Muhammad Modibbo. Shi d'an asalin garin Adamawa ne, bafulatani ne. Hajiya Madina 'yar uwarsa ce, saidai ita mahaifinta anan Kano ya rayu, anan ya tara zuri"arsa. Soyayya ta kullu tsakaninsu har ta kaisu ga aure lokacin shi Alhaji Muhammaf ya dawo Kano da karatu ya kuma kama aiki anan.  Yana da mata biyu bayan ita, Hajiya Binta itace wacce kika gani rannan, sannan amaryarsa Hajiya Lubna, ita 'yar Maiduguri ce, yanzun ma da baki ganta ba, taje biki can Maiduguri da yaranta su hud'u gaba d'aya.     Hajiya Madina tana da yara takwas kamar yanda na fadamaki, ita kuwa Hajiya Binta yaranta shida. Iklima itace babbar budurwar 'yarta sannan Hanif, Sadiya, Nafisa, Usman da Jabir.   Ita kuwa Hajiya Lubna, yaranta biyun farko 'yan biyu ne mace da namiji. Hassan da Hussaina, sai Adam da Hajara.     Bar ganin gidannan kamar ba shi da girma Ummi, sai kin shiga can 6angaren zaki k'ara tabbatar da girmansa. Sashe hud'u ne har na Alhajin.     Saidai duk haduwar sashen matan bai kai na maigidan ba, da girma da komai.     Hajiya Madina duk ta fisu fada a wajensa, ko don tana ganin ita din 'yar uwarsa ce kuma tana da daurin gindi wajen mahaifiyarsa Gwaggo ne? Bani dai da masaniya. Amma tabbas Gwaggo bataso ko kusa Hajiya ta kai k'ararsa wai ya 6ata ranta, yanzun nan zata bud'emishi wuta. Shiyasa daga Hajiya Binta har Hajiya Lubna, basu kaunar zuwan Gwaggo Kano, kawai saboda bambancin da take nunawa tsakaninsu da Hajiya Madina. Hakanan tafi zuzuta kaunar 'ya'yan Hajiya Madina har yakai ma bata iya 6oyewa.     Bada son ranta akayiwa Hajiya Madina kishiyoyi ba, saidai kawai don Hajiya Madina ta nunamata tafison kwanciyar hankalin mijinta akan tashin hankali da damuwarsa.    Gaskiya Ummi a wani 6angaren, Hajiya Madina tana da mutunci duk kuwa da cewar bata kama k'afar Hajiya Mama ba. Hajiya Mama ciki d'aya suka fito, saidai ita bata da raina 'yan aiki kuma yaranta sunsan girman ★DAN ADAM★ basu rainashi ko yaya ne. Toh yanda Hajiya Mama take, hakanan itama babbar yayarsu, Hajiya Fatima take. Su uku daman cif a wajen babansu, daga su bai kara haihuwar wasu ba kuma matarsa daya, Baba Ummahani.   Ita a Abuja take zaune. Tana da yaranta hudu samari manya, sai yan mata biyu. Ta aurar da yaranta maxa biyu na farko, matan da ragowar mazan biyu sune dai basuyi aure ba. Mijinta tsohon soja ne kafin daga baya yayi ritaya.       Amina ta d'an tsagaita sannan ta d'ora tana duban Ummi wacce gaba daya kacokam ta maida hankali gareta tana sauraro.   "Hajiya tana da saukin hali idan kika zama mai bin umarninta kan lokaci, sannan tafiso kafin tayi korafi akan bakiyi aikin da kika san kina yi ba toh ki kammala shi. Ko kusa bata son kazanta, hakanan bataso kice zaki wulakanta abinda ta haifa. Batason kuma shigen d'akunan abokan zamanta, idan kika kiyaye bakinki daga daukar magana ki kai wani dakin toh fa zaku d'asa da ita. Ba ruwanki da shishshigi a lamuranta matukar ba ita ta so ki tanka ba. Ki kiyaye kawo mata gulma, nan ma zaku 6ata da ita. Sannan ko wani abu marar dacewa kikaga ta yi, bataso ki tanka mata, nan kuwa zaku 6ata. Batason ta kamaki da cin amanarta.  Yaranta suna da saukin hali Ummi, matukar kika kama kanki ba zasu rainaki ba. Ihsan ce ma mai matsalar, ita kuma kiyi kokarin fita harkarta. Idan dai ta sanyaki aiki kada ki k'i, kiyi hakuri kiyishi hakan saboda itace ma musabbabin da yan aiki basujin dadin zaman gidan.       A duniyar nan, kawai dai ki tsare abinda za'a ci mutuncinki ko yayane, kedai ki tsaya matsayinki baruwanki da cusa kai kinji ko?"     Ummi ta danyi murmushi alokaci guda hawaye suka zubomata ta sharesu, wai yau itace da samun mai bata shawara a lamarin rayuwa? Itace ta samu wannan gatan har haka? Wani irin kaunar Amina ya k'aru a zuciyarta.    Amina da mamaki ta mike zaune. "Ummi kukan kuma na menene?" Ummi ta girgiza kai. "Bakomai." Amina ta ji wani tausayi ya dabaibayeta. Tasan akwai wata matsala a rayuwar Ummi, tafi kuma tunanin bata da iyaye. Ta numfasa, batason ta matsa mata da tambaya, ta tabbatar wataran don kanta zata gayamata tarihinta.     "Komai yayi zafi maganinsa Allah Ummi. Ki bar damun kanki da lamuran rayuwa har haka kinji ko? Ki rik'i addu'a da karatun Alkur'ani da sallar dare. In sha Allah komai zakiga ya wuce."    Ummi da fuskar tausayi ta dubeta. "Nifa bansan komai na Addini ba wallahi. Kawai dai ina yin sallah idan naga lokaci yayi mutane sunayi."   Mamaki karara ya bayyana saman fuskar Amina, batasan ya akayi ta jefomata tambaya ba. "Wai Ummi, iyayenki basu raye ne? Shekarunki nawa yanzu?"   Ummi tayi k'as da kanta ta soma hawaye.  "Mahaifiyata ta rasu tun ina jaririya, babana yana raye. A hannun matarsa na taso."   Kwallah ta cika idanun Amina, ta gano bakin zaren.    "Idan ba damuwa ki sanarmin tarihinki mana."   Tiryan-tiryan ta sanarmata da irin rayuwar kuncin da ta rayu ciki. Cikin muryar kuka tace.   "Kalmar da ta kasa ficemin a rai bai wuce da babana yace wai ko birnin sin ne na tafi ba shi ba damuwarsa bace. Babana baya sona yanda yakeson kanwata Mariya."   Kuka sosai takeyi, itama Amina tana tayata. Wani kaunar Ummi ya k'aru a ranta, ji takeyi tamkar kanwarta ce ta jini. Dakyar Amina ta rarrasheta tayi shiru sannan ta dubeta da kulawa.                  "Karki damu Ummi, ki cigaba da hakuri sa mik'awa Allah lamuranki. Komai kika gani, daga gareshi ne. Watarana zaki ga komai kamar ba'ayi ba, nan gaba zakiji dadi a rayuwa in sha Allah. Kada kiyi bakinciki da zuwanki gidan Hajiya, na tabbatar ko a kwana d'ayan nan da kikayi, kinga chanjin rayuwa ballantana kuma idan ya zamana kin shure satittika anan. Nasan dai duk wani wuya da zaki ci anan bazai kai rabin wanda  kika labartamin ba. Hajiya bata duka, bata zagi haka kawai, saidai idan ka ta6a jininta, zata budemiki wuta tayi fada sosai harma idan baki taki sa'a ba ta goranta miki. Duk kuma wani abu na rayuwa ki daukeshi mukaddari ne daga Allah, ba wanda zai tsallakewa kaddararsa kinji ko?"   Cikin jin wani sanyi ta gyad'a kanta.  "Toh Anti nagode." Amina tayi murmushi. Baccin safen da basu samu komawa kenan ba, sukayi ta hira a karshe Amina ta mike ta shiga wanka. Bayan ta fito Ummi itama ta fad'a.    Ta kammala ta fito, Amina tuni ta shirya cikin doguwar riga ta yadi, daga gaban rigar, anyi adon duwatsu, ire-iren dai wanda take samu daga Hajiya Mama ko yaranta. Ummi ta dubeta, tayi mata kyau, zata soma duba jakar kayanta ta ji muryar Amina.   "A'a Ummi, ga kaya ki saka." Ta juyo don ganin ko ta ciro mata ne, saidai ta ga wasu da ba nata na asali ba, riga doguwa ce ta abaya. Ta dubi Amina ido a waje.   "Lah, anya kayanki zasu yimin Anti?" Amina ta murmusa. "Wannan na jima bana sakashi, na kuma tabbatar ba zai k'i yi miki ba. Kedai gwada mugani. Idan kin kammala ki fito ki gaida Hajiya, nasan yanzu ta farka."   Ummi ta amsa da toh, Amina ta fice. Rigar ta kar6eta kwarai tayi mata kyau kasancewarta farar yarinya. Ta dauki dankwalin ta d'aure gashinta wanda idan mutum yaga yanda yayi mata, zai iya cewa tayi d'aurin acuci.     Saida ta dauke shimfid'a ta d'an gyara d'akinnasu duk da ba daud'ar azo a gani don Amina akwai tsafta, sannan ta bi bayanta. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 07   A falon ta tarar da Hajiya Madina zaune cikin kwalliya tana karyawa, Amina bata nan, ta karasa ta durkusa ta gaisheta a ladabce. Hajiya Madina ta amsa fuskarta a sake, bai wuce ganin yanda Ummin tayi fes ba don ita ba mace ce mai son zama cikin k'azanta ba.     Ummi ta zauna, idanunta akan talabijin, saida Hajiya ta kammala sannan ta umarceta  da d'auke kayan, ta d'aukesu ta kai kicin. Acan ta had'u da Ramma tana faman gyare-gyare. Ta gaisheta a mutunce, Ramma ta amsa har tana zolayarta wai har ruwan birni ya soma kar6arta ta chanja saidai k'ashin wuya. Ita dai murmushi tayi kawai.     Tana shirin fitowa sukayi kici6us da Amina, hannunta rik'e da tsintsiya da kwandon shara.    "Kinga yayi miki kyau ko? Nima na gyaro d'akin Hajiya ne, kije tana kiranki ma."   Ai da sauri Ummi ta fita don amsa kiran.    Wannan karon a kan kujera ta sameta tana amsa waya. Zama tayi har ta kammala sannan tayi magana. "Gani Hajiya." Ta dubeta a nutse sannan ta soma magana.   "Yauwa Ummi, dafatan dai Amina ta nunamaki dukkan ayyukan da takeyi? Toh inaso ki zamo mai rike amana, muddin kika ci amanata, bazan kyaleki ba. Yanda zan rik'i amanarki da gaskiya a matsayinki na Amanar a hannuna, haka kema nakeso ki rike, ki kula da dukkan ayyukan da zaki dunga yi."  Ta k'ara karanto mata ayyukan harma da na gyaran sashenta ciki da falonta na biyu, banda wannan da suke ciki don duk cikin aikin Ramma ne. Ta k'ara jaddamata cewar batason k'azanta, hakanan ta kiyaye tsaftar suturunta, duk sadda zatayi wanki, ta tambayi omo zata samu. A dai maganganun Hajiya, Ummi ta fahimci cewa dagaske batason k'azanta kuma tana da kyankyami.     Ta rausaya kai. "In sha Allahu Hajiya zan zama mai kula da dukkan abinda kukace, nagode Allah Ya k'ara girma da arziki." Har a ranta ta ji dad'in maganganun Ummi.   "Shikenan kina iya tafiya."                        ☆☆☆    Tun daga wannan ranar, Ummi ta kama aikinta sosai, Amina na taimakonta. Har ya kasance wani sa'in kafin Amina ta tashi, ta rigata tashi. Tana jin dad'in zama da Amina saboda shawarwarin da take bata, har karatu tana koyamata. Duk da cewar Amina na cin wuya don Ummi ko bak'i bata iya ba. Duk sai ta bata tausayi, haka take lalla6awa ta biyamata, amma ta tabbatar muddin tana wajen Hajiya Madina, bazata ta6a bari ta zauna mata da jahilci ba, duk wadanda suka ta6a zama sukayi aiki awajenta, ba wacce bata sanya a islamiyya ba, boko ne dai ba lallai ka samu ba.       Saida Ummi tayi sati da zuwa, sannan Amina ta soma shirin tafiya don Hajiya Mama sun dawo. Gaba daya ta ji babu dadi, tana zaune gefe tana duban yanda take ninke kayanta tana sanyawa ciki jaka. Amina ta ankara da duban da takeyi mata, itama sai taji batason rabuwa da ita.   "Haba Ummi, menene abin damuwa har haka alhalin muna gari d'aya? Karki damu, na tabbata zamu dunga ganin juna. Kedai ki cigaba da hakuri da zama da su tsakaninki da Allah."    Ummi ta gyad'a kai. "Toh Anti." Sai yamma suka tafi har Hajiya da su Adnan, gidan ya rage Ummi kad'ai da Ramma. Bayan ta kammala ayyukanta ta fito farfajiyar gidan tayi zamanta. Bata kai mintuna biyar a zaune, budurwar da bazata ta6a mance fuskarta ba wacce suka samu sa6ani da Adnan a farkon ganinta da su, ta fito daga sashensu tare da k'awayenta har su biyu suna dariya.     Hararar da ta sakarmata ne yasa ta dauke kanta babu shiri ta saddar a k'asa, ta gabanta sukazo wucewa, ai kuwa ta sanya takalminta mai tsini ta take yatsun k'afarta har saida tayi k'ara. Ta juyo ta rankwasheta. "Munafuka, sharri zakiyimin kina gidan ubana kina cin arziki? Shegiya kawai."   K'awayen dariya kawai sukayi, d'aya tana fad'in "Kai Iklima baki da kirki." Iklima ta ta6e baki.   "Na kaiku?" Suka fice Ummi ta mike da sauri tabar wajen, saida ta tsaya a lungun ta share kwallah sannan ta k'arasa ciki. Ta zauna a kicin tana kallon yanda Ramma ke faman had'a miya, tana dan jan Ummin da hira har ta share batun Iklima ta saki jikinta.                       ☆☆☆ DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 08 Bayan tafiyar Amina, Ummi dole ta sabarwa kanta hira da Ramma, don Ramma mace ce mai abin dariya. Ayyuka ko kusa basu bata wuya sosai don a ganinta ta saba da fin haka acan gidansu. Sau da yawa takan tuna Mahaifinta, tana tunanin ko wane hali yake ciki yanzu, saidai daga zuciyarta ta tunano mata irin tsana da tsangwanar da take sha a wajen shi kansa, sai ta ji tunanin ya kau. A d'an zaman da sukayi da Hajiya Madina ta fahimci Ummi lallai bata da wani ilimi da addini, ta lura ko sallolinta akwai gyara ciki, wannan dalilin ne yasa ta sanya Ramma kaita makarantar da yaranta(ita Rammar) ke zuwa, karfe biyu suke zuwa su taso k'arfe biyar na yamma. Babu ruwanta da shiga sashen kowace matar gidan don sosai ta dauki gargadin Hajiya Madina, hakanan tana rike da nasihar Antinta. Alokacin Hajiya Lubna amaryar gidan sun dawo daga Maiduguri, ta lura yaranta suna da kirki basu da hali irin na yaran Hajiya Binta. Saidai uwarsu ce sai a hankali, mace ce mai shan k'amshi, saika gaisheta sai ta ga dama take amsawa. Maigidan ma bai rufe sati biyu ba ya dawo. Ranar da ya kasance Hajiya Madina ce da aiki, sun ci aiki sosai, har da Hajiya Madinar. Ummi banda wanke wannan mik'o wancan babu abinda takeyi. Abinci kusan kala uku ta ga anyi ciki harda suyar kaza bayan an tafasa an tura shinkafa da kayan hadi a k'asanta an toshe bakin da dankali babba guda d'aya. Sai lemun zo6o da taga sun had'a sai kamshin abarba yakeyi. Aka kammala aka zuzzuba, suka ajiye a saman tebur. Ummi da Ramma suka tattara kicin din, can bayan magriba, lokacin Ramma ta tafi, sai ga Hajiya Madina ta fito daga dakinta ta ci ado cikin wani (yellow lace) wanda ya sha adon duwatsu, tayi kyai sai k'amshi kawai ke tashi a jikinta. Ummi na rak'u6e a can gefen kofar kicin tana kallon wani fim na yak'i da su Adnan suka nutsu suna kallo. "Wow! Wallahi Mom kinyi kyau." Cewar Ihsan tana mikewa tsaye, daga ita sai riga iyaka gwuiwa da riga tshirt kanta hula ce ta sanya. Ta isa ga Mamin tana mai sanya hannu ta k'ara gyara mata zaman d'aurin. Murmushi kawai Hajiya Madina tayi. "Naji, taho ki kaimin kayannan sashen Abbanku." Ihsan tayi dariya. Tare suke fice ta dauki wasu Ihsan ta dauki sauran. Ummi ta bi Hajiya Madina da kallo cike da sha'awa don kwalliyar ta burgeta. Idan kana da kudi babu abinda ba zakayi ba. Har ta gaji da kallon, ta koma daki ta hau duba karatunta, a karshe da ta gaji, kwanciya tayi abinta wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita don bata ta6a aikatuwa irin na yau ba saboda girkin dawowar Alhaji da ta taimaka da shi. Bayan kwanaki biyu da dawowar Alhajin, ranar juma'a bayan ta je ta gaida Hajiya. Hajiya ta dubeta a nutse. Doguwar bakar abaya ce jikinta na wajen Amina. "Wai ke baki da kaya ne sai wadannan guda ukun? Yau idan kin saka doguwar riga bak'a, gobe sai jan atamfa kodadde, jibi ma haka? Bakizo da kaya bane ba?" Ummi ta sunkuyar da kai gaba daya jikinta yayi sanyi, cikin rawar murya tace. "Eh su kadai ne masu d'an dama-dama Hajiya." Hajiya tayi shiru da mamaki, kafin tace. "Daukomin duka kayanki nagani." Ta mik'e da sauri ta cika umarninta, Hajiya ta sanyata ta zazzagesu. Kayan duk ba wani na kirki kam da gaskiyar Ummin. "Kwashesu ki maida ledar, kada su koma wannan d'akin. Fita kimin kiran Ramma." Ta amsa da toh, ta mayarda kayan jaka sannan ta fita ta kira Ramma. Tana ji Hajiya tace idan ta kammala tayi magana zata bata kudade gobe ta shiga kasuwa ta siyo mata kananun atamfofi guda hud'u sai dogayen riguna yan kanti su kuma guda uku sai wanduna da vest guda shida-shida. Ramma ta amsa da toh, zata mike Hajiya ta dakatar da ita. "Tafi da wannan ledar a zubar don Allah." Ramma na dariya ta dauka tayi gaba tana fadin toh. A washegarin kuwa Ramma bata zo da wuri ba sai wajen sha d'aya na safe. Sai gata da kayan da Hajiya ta umarceta. Hajiya ta duba sannan ta bata atamfofin ta kai dinki, tayi kiran Ummi ta mik'a mata ledar kayan ta kara jaddada mata cewa ta kula da tsaftar jiki da dakin da take kwana. Ummi ta amsa tayi godiya ranta fari k'al ta zubawa Hajiya ruwan addua wanda hakan ba k'aramin faranta Hajiya Madina yakeyi ba. Saida ta shiga ta zazzage kayan tana duba, ai kuwa dai abinda Hajiya ta karanto shi d'in aka sissiyo harma da k'arin man shafawa da turare (Lovilla) na roba. Har wani tsalle tayi na murna, ko babu komai a makaranta yan ajinsu zasu dinga jin tana k'amshi kamar yanda ta ga yan babban aji a makarantar suna yi idan sunzo giftasu ko kuma monitoci. ☆☆☆ DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 10  Wani ajiyar zuciya Ummi ta saki ganin yanda aka k'awata farfajiyar gidan da shukoki, wurin motocin da ta hango acan wata 'yar rumfa ta ga sun nufa suma, saidai bai karasa ba ya faka.  Duk suka fito, sannan ya karasa ciki.   Suna gaba tana binsu a baya hannunta rike da Fahad wanda zuwa yanzu ta saba da shi ba kad'an ba kasancewarshi yaro mai son mutane. Banda kalle-kalle babu abinda takeyi har suka iso wata kofa da kai tsaye ta sadasu da wani dan karamin tsakar gida wanda aka dan yi gewaye a tsakiyarsa aka dasa shukoki. Ihun da ta ji ne ya katseta, wasu yan mata ta gani sun rungume Ihsan yayinda shima Adnan ya hau cafkewa da wasu maza a karshe suka hau rungumar juna ana dariya.     'Wadannan kuma su wanene?' Ta wurgawa zuciyarta tambayar, bata kai ga gama tantancewa ba ta k'ara ganin wasu yanmata biyar suma sun fito  suna fadin oyoyo Anti Mami. Ukun dai ta sansu, da Intisar ne da Rukayya da kuma Maryam yaran Hajiya Mama, biyun ne dai bata sansu ba duk kuwa da cewar sun had'u a sunan Aisha.    Bayan sun kammala rungume-rungumensu ne suka dunguma zuwa ciki gaba daya. Ihsan ta juyo da sauri ta matso daidai gefen Ummi. Tana dubanta duba na raini tace.   "Saura kiyi karambanin biyomu, ki nemi wuri ki zauna anan."   Ta amsa da toh sannan ta ja baya ta fasa niyyarta na binsu. Bayan shigewarsu ta koma can gefe ta ja kujerar roba daya cikin hudun da ke zagaye da tebur ta zauna ta zabga uban tagumi. Ko kusa bata ganin laifin Ihsan, daman ai ita ba wata bace a wajensu face  yar aiki, dole ne kuma ta cigaba da amfani da nasihun Antinta gudun abinda zai jawo a dizgata gaban mutane.    'Dizgi?' Ta  tambayi zuciyarta, toh kuma dizgi ya wuce wanda ta gama sha awajen shakikanta wadanda su kadai ne zata iya bugun kirji ta kira a matsayin nata? Sun gujeta sun manta da ita, tunda suka kawota har gashinan ta kusa yin wata a garin da babu iya babu baba, a wajen mutanen da bata da had'i da su sai na Allah. Bata kara sanin tayi rashin uwa ba sai bayan ta soma zuwa makarantar islamiyya, yanda ake kara koyar dasu gami da nuna musu muhimmancin biyayya ga iyaye. Ita kam bata da wannan gatan, har fargabar ranar da Hajiya zata gaji da ita ta koreta daga gidanta takeyi, tana rantsuwa da Allah batasan hanyar da zata bi ta koma garinsu ba a karan kanta matukar ba Yaha ce zata zo ta maidata ba.    Daddad'an kamshi da kuma zazzakar muryar da ta tsinta awajen ne ya katse mata tunani, ta d'ago kanta tana duban mai ita.     Tsaye yake ya zura hannunsa na hagu acikin aljihun wandonsa, hannun damansa kuwa, waya ce wacce ya kafa a kunne. Farin bafulatani ne, kansa cike da suma, saje a kwance saman fuskarsa yayi luf-luf. Yana da matsakaicin tsawo,hakanan yana da fadin fuska kadan, idanuwansa daidai misali hakanan siririn karan hancinsa da tsukakken le66ansa ruwan hoda, ya kara taimakawa wajen fiddo da tsantsar kyawun halittar da Allah Ubangiji Ya mishi. Sanye yake cikin shadda ruwan k'asa, kansa babu hula, agogon daya d'ora a hannun hagunsa ya kara fiddo da kyawun hannunnsa wanda ke cike da gargasa.   A tsanake yake fidda kalmomi, hausa da turanci kawai yake gwamutsawa, idan yayi hausa, can gaba kuma ya jefa turanci, abin sai ya burge Ummi. Tayi shiru ta zubamasa ido tana sauraron yanda yake hada yare biyu lokaci guda duk da cewa ta sha jin hakan daga Ihsan, saidai ko rabin kwarewarsa Ihsan batayi ba. Daidai lokacin da yayi sallama da wanda suke wayar da shi, suka had'a ido, babu shiri tayi gaggawar janye nata idanun daga gareshi. Koda ta k'ara d'agowa, bata ganshi a wajen ba don tuni ya koma ciki.     Ta sauke ajiyar zuciya, ta tuno da 'yar ajinsu wata Khadija, wacce bata da aiki sai hirar samari a aji, burinta bai wuce ta samu namiji kyakkyawa kuma mai kudi ta aura ba. Har mamaki suke bata, duka-duka tasan da wuya idan suma zasu fi shekara goma sha biyar kamar ita(GYARA) amma har ace sun waye da batun samari har haka, sai kuma ta tuna da cewar da ace a kauyensu ne da tuni watakila itama an aurar da ita. Abin kuma sai ya sanyata murmushi, wa zai aurar da ita? Ai kenan ma  Saude ta nunamata gata, akan kunnenta ta sha jin tana fadin saidai ta karar da rayuwarta a bauta mata, aure ne saida ta ga ana yi ba dai ita tayi ba. Hawaye ta ji suna kokarin taho mata da takaici, gaskiyar Saude tunda yanzun ma gatanan acikin hali na aikatau wanda duk a sanadinta ne, kudin da ta riga tasan na amfaninsu ne banda ita. An barta dai da wahalar.   "Kamota nan!" DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 11 Firgigit ta dubi wanda ya tsoratatan don gaba daya ta zurfafa cikin tunani. Ganin Amina yasa ta mikewa tsaye da mamaki, sai kuma suka hau dariya. "Kai Ummi, tunanin me kikeyi haka wai?" Ummi wacce ta kasa rufe bakinta don tsabar murnar ganin Amina ta amsa da fad'in. "Bakomai, kikacemin ba zaki zo ba?" Amina dauke da murmushinta na sabo tace. "Wallahi ban saka ran zanzo ba, Hajiya Mama ta matsamin akan na biyosu kawai." Abin ya bawa Ummi mamaki, ta kara gaskata cewa Hajiya Mama ba ruwanta. Amina ta dubi ledar hannunta. "Ina zuwa bari na mikawa Anti Rahila famfas nazo." Daga haka ta shiga ciki da sauri ta nufi ciki. Ummi ta koma ta zauna ranta yayi fes cike da murnar sake haduwa da Amina wacce ta dauki matsayin Anti kacokam ta bata ba don komai ba sai don yanda ta nuna kauna gareta a farkon haduwarsu da kuma yanda take da kokarin yi mata gyara aduk lamuranta na rayuwa. Bata jima da shiga ba sai gata kuma ta fito, tana kokarin jan kujera ta zauna ne ta dubeta. "Meyasa baki shiga ciki ba?" Ummi ta zaro ido kadan. "Ciki kuma? Um um, Ihsan tace kada na sake na shigo." Amina ta ja guntun tsaki. "Bansan sadda yarinyar nan zata dawo saiti ta gane cewa shima dan aiki mutum ne ba. Ki dai kara hakuri." Murmushi kawai Ummi tayi. "Anti 'yan Abuja ma sunzo ne?" "Su ai tun jiya suna garinnan, basu je gidan Mami ba kenan? " Ta girgiza kai. "A'a." "Sunzo, Ikram, Baraka, Yaya Usman, Yaya Ridwan, Yaya Haidar da kuma Yaya Faruk." Jinjina kai kawai Ummi tayi batare da tace uffan ba. Sai kuma suka fad'a hirar da ta shafesu, sun jima sosai anan kafin kuma wata dattijuwar mace ta leko. "Ke Amina, kuzo ku taimaka mu kaiwa bak'i abinci." "Toh Larai." Ta dubi Ummi. "Muje." Ummi ta mike gaba daya sai ta ji wani nauyi, kamar kada ta je haka take ji, fatanta kada Ihsan ta ci zarafinta a bainar jama'a. Takalma baja-baja a dan koridon shiga falon, suka shiga da sallama. Saidai abin mamaki bata ga kowa anan ba sai ta dunga jiyo muryoyi da dariyarsu daga can sama, hakan ya tabbatar mata suna can. Zugui-zugui tayita bin Amina har zuwa wani kicin mai girma. Nan taga kuloli manya guda hudu sai tarkacen filettoci da cokula da kofina a saman teburin dake tsakiyar kicin din. "Yauwa ku soma kaiwa, Amina ga ledar nan ki soma da shinfid'ata." "Toh" kawai Amina tace sannan ta ja linkakkiyar ledar ta hada da filas guda d'aya, itama Ummi ta dauki filas d'aya don girma ne da su, ta bi bayanta suka soma taka bene. ★★★★★ Wani sanyi da daddadan kamshin (roomfreshner) ne ya soma yi musu marhabin kafin dariya da hirar jama'ar falon ta doki kunnawansu. Suka shiga da sallama, Ummi gabanta banda bugu babu abinda yakeyi. Ga wadanda kunnensu ya ji suka amsa musu sallamar, wadanda basu ji ba kuwa, sai hira suke. Babban falo ne wanda ba'a cikashi da kayan ado sosai ba, saidai iyakar wadanda aka dan kawatashi da su masu kyau da tsada ne. Kujeru masu jikin leda farare tas ne zagaye a tsakiyar falon, iyayen na zaune saman kujera harda dattijon kwarai, wato maigidan Alhaji Atiku Modibbo, tare da uwargida ran gidansa, mahaifiya ga Hajiya Fatima, Hajiya Madina da karamarsu gaba daya wato Hajiya Sadiya(Hajiya Mama). Sune a zaune saman kujera, su kuwa jikokin suna a kasan tattausan kafet din dake shimfid'e a tsakar falon. Kallo d'aya Ummi tayiwa 6angaren da suke tayi gaba ta bi bayan Amina zuwa inda ta nufa. Tsakiyarsu ne Amina ta shimfid'a katuwar leda ta cin abinci, suka ajiye komai anan. Anan ne ta ji Amina ta shiga gaishesu, itama ba shiri ta gaishesu. Ba zata iya tantance wadanda suka amsa ba da kuma wadanda basu amsa ba don kuwa sauri takeyi su bar wajen, haka kawai ta kara jin ta raina kanta, ji take kamar wari takeyi ma tsabar kamshin wajen. Cikin yaren fulatanci ta ji wata cikin yanmatan tayi magana da bata fahimci ko menene ba. Gaba daya matasan suka dara, tana ganin sadda wani a samarin ya jefamata filo. "Baki da kirki." DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 10 Wani ajiyar zuciya Ummi ta saki ganin yanda aka k'awata farfajiyar gidan da shukoki, wurin motocin da ta hango acan wata 'yar rumfa ta ga sun nufa suma, saidai bai karasa ba ya faka. Duk suka fito, sannan ya karasa ciki. Suna gaba tana binsu a baya hannunta rike da Fahad wanda zuwa yanzu ta saba da shi ba kad'an ba kasancewarshi yaro mai son mutane. Banda kalle-kalle babu abinda takeyi har suka iso wata kofa da kai tsaye ta sadasu da wani dan karamin tsakar gida wanda aka dan yi gewaye a tsakiyarsa aka dasa shukoki. Ihun da ta ji ne ya katseta, wasu yan mata ta gani sun rungume Ihsan yayinda shima Adnan ya hau cafkewa da wasu maza a karshe suka hau rungumar juna ana dariya. 'Wadannan kuma su wanene?' Ta wurgawa zuciyarta tambayar, bata kai ga gama tantancewa ba ta k'ara ganin wasu yanmata biyar suma sun fito suna fadin oyoyo Anti Mami. Ukun dai ta sansu, da Intisar ne da Rukayya da kuma Maryam yaran Hajiya Mama, biyun ne dai bata sansu ba duk kuwa da cewar sun had'u a sunan Aisha. Bayan sun kammala rungume-rungumensu ne suka dunguma zuwa ciki gaba daya. Ihsan ta juyo da sauri ta matso daidai gefen Ummi. Tana dubanta duba na raini tace. "Saura kiyi karambanin biyomu, ki nemi wuri ki zauna anan." Ta amsa da toh sannan ta ja baya ta fasa niyyarta na binsu. Bayan shigewarsu ta koma can gefe ta ja kujerar roba daya cikin hudun da ke zagaye da tebur ta zauna ta zabga uban tagumi. Ko kusa bata ganin laifin Ihsan, daman ai ita ba wata bace a wajensu face yar aiki, dole ne kuma ta cigaba da amfani da nasihun Antinta gudun abinda zai jawo a dizgata gaban mutane. 'Dizgi?' Ta tambayi zuciyarta, toh kuma dizgi ya wuce wanda ta gama sha awajen shakikanta wadanda su kadai ne zata iya bugun kirji ta kira a matsayin nata? Sun gujeta sun manta da ita, tunda suka kawota har gashinan ta kusa yin wata a garin da babu iya babu baba, a wajen mutanen da bata da had'i da su sai na Allah. Bata kara sanin tayi rashin uwa ba sai bayan ta soma zuwa makarantar islamiyya, yanda ake kara koyar dasu gami da nuna musu muhimmancin biyayya ga iyaye. Ita kam bata da wannan gatan, har fargabar ranar da Hajiya zata gaji da ita ta koreta daga gidanta takeyi, tana rantsuwa da Allah batasan hanyar da zata bi ta koma garinsu ba a karan kanta matukar ba Yaha ce zata zo ta maidata ba. Daddad'an kamshi da kuma zazzakar muryar da ta tsinta awajen ne ya katse mata tunani, ta d'ago kanta tana duban mai ita. Tsaye yake ya zura hannunsa na hagu acikin aljihun wandonsa, hannun damansa kuwa, waya ce wacce ya kafa a kunne. Farin bafulatani ne, kansa cike da suma, saje a kwance saman fuskarsa yayi luf-luf. Yana da matsakaicin tsawo,hakanan yana da fadin fuska kadan, idanuwansa daidai misali hakanan siririn karan hancinsa da tsukakken le66ansa ruwan hoda, ya kara taimakawa wajen fiddo da tsantsar kyawun halittar da Allah Ubangiji Ya mishi. Sanye yake cikin shadda ruwan k'asa, kansa babu hula, agogon daya d'ora a hannun hagunsa ya kara fiddo da kyawun hannunnsa wanda ke cike da gargasa. A tsanake yake fidda kalmomi, hausa da turanci kawai yake gwamutsawa, idan yayi hausa, can gaba kuma ya jefa turanci, abin sai ya burge Ummi. Tayi shiru ta zubamasa ido tana sauraron yanda yake hada yare biyu lokaci guda duk da cewa ta sha jin hakan daga Ihsan, saidai ko rabin kwarewarsa Ihsan batayi ba. Daidai lokacin da yayi sallama da wanda suke wayar da shi, suka had'a ido, babu shiri tayi gaggawar janye nata idanun daga gareshi. Koda ta k'ara d'agowa, bata ganshi a wajen ba don tuni ya koma ciki. Ta sauke ajiyar zuciya, ta tuno da 'yar ajinsu wata Khadija, wacce bata da aiki sai hirar samari a aji, burinta bai wuce ta samu namiji kyakkyawa kuma mai kudi ta aura ba. Har mamaki suke bata, duka-duka tasan da wuya idan suma zasu fi shekara goma sha biyar kamar ita(GYARA) amma har ace sun waye da batun samari har haka, sai kuma ta tuna da cewar da ace a kauyensu ne da tuni watakila itama an aurar da ita. Abin kuma sai ya sanyata murmushi, wa zai aurar da ita? Ai kenan ma Saude ta nunamata gata, akan kunnenta ta sha jin tana fadin saidai ta karar da rayuwarta a bauta mata, aure ne saida ta ga ana yi ba dai ita tayi ba. Hawaye ta ji suna kokarin taho mata da takaici, gaskiyar Saude tunda yanzun ma gatanan acikin hali na aikatau wanda duk a sanadinta ne, kudin da ta riga tasan na amfaninsu ne banda ita. An barta dai da wahalar. "Kamota nan!" [8:55am, 12/4/2016] Sister ruffy: DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 14  Anan falon farko ta iske yanmatan suna ta hirarsu. Gaba d'aya suka zubomata ido. Ta gaishesu suka amsa suna binta da kallon tara saura. Bata kara cewa uffan ba ta yi hanyar falon Mami.    "Wannan 'yar aikin taku ai har ta so ta k'ere ki a kyau."    Abinda ya daki kunnuwanta kenan har saida ta ji faduwar gaba. Ta tabbatar da Ihsan sai ta fusata.    Da sallama ta isa falon, Hajiya Babba (Hajiya Fatima) na zaune  saman darduma tana addu'a yayinda Mami ke zaune saman kujera tana danna waya. Ganinta baisa ta d'ago kanta ba. Ta durkusa ta gaisheta. Mami ta amsa har lokacin idanunta na kan wayarta.   "Ya akayi ba ki wankemin bandaki ba?"   Sai lokacin ta tuna, shaf ta mance sakamakon sadda zata wuce makaranta, Mamin na wanka, hakan yasa ta fice da zummar idan ta dawo sai tayi. Cikin tausassan muryar Ummi, ta amsa.   "Kiyi hakuri don Allah Mami, dazun kina wanka shiyasa ban samu yi ba."   Kafin Mami tayi magana Hajiya Fatima ta rigata.   "Wannan 'yar fulanin fa Madina?" Mami ta dubeta.   "Ummi ce, ita ku ka gani ranar (meeting) dinnan ai. Aiki takemin."   Hajiya Fatima ta sauke mayafinta har lokacin tana duban Ummi wacce ta gaisheta, ta amsa mata.     "Shikenan ai, shiga kiyi yanzu."   "Toh."   Ta mike ta shiga d'akin Mamin. Kai tsaye band'aki ta nufa. Cikin mintuna baifi goma sha biyar ba ta kammala wanke band'akin ta fito.   Acan kuwa bayan shigewar Ummi, Hajiya Babba ta dubi kanwarta.   "Ga dukkan alamu kinyi sa'ar mai aiki wannan karon Madina, na lura yarinyar tana da nutsuwa kamar ba zata bada matsala ba."   Mami ta jinjina kai da murmushi dauke saman fuskarta, ko babu komai tana jin dadi idan wanda ya fita ya dame ta a kudi da komai na rayuwa ya yabi wani abu nata. Tabbas Mijin Hajiya Babba ya fi nata kudi da komai, da shi ake damawa a k'asar gaba d'ayanta kasancewarshi tsohin soja wanda a shekarun baya ake matukar ji da shi. Bayan wannan ma, ita kanta Hajiya Babba tana kasuwanci sosai, takan fita zuwa Dubai ta saro kayayyaki, a yanzun da yaranta suka tasa, sai ta hutarwa kanta don kuwa Yaya Usman shi ya cigaba da fita yana saro mata, a karshe sai ta bud'e shago babba na suturun mata.  Shiyasa babban burinta bai wuce Faruk ya nuna yana son Ihsan ba, koda ita Ihsan din ta nuna, to babu abinda zai hana auren.     Ta gyara zamanta ta numfasa.    "Haka Ummi take, a farko ma nayi zaton rashin sabo ne, sai bayan ta kwana biyu na gane haka halittarta take, bata da rawar kai sannan ba laifi tana da kamun kai."    Hajiya Babba ta girgiza kai. "Kai ai kuwa kinyi sa'a, ni kinga da na dauki mai shekarunta bamu wanye lafiya ba, don saida ta dankaramin sata na kudi da sutura sannan ta gudu."   Mami ta mike sosai ta zauna tana dubanta.   "Yaushe akayi wannan banda labari?"   Nan akalar labarin ta chanja. Acikin wannan hirartasu ne, Ummi ta fad'o falon bayan ta kammala, a ladabce ta sanarwa Mami ta kammala. Mami ta amsa da toh shikenan, daga nan ta mike ta fice.       A falon farko ta tarar da 'yan matan da mazan sai hira da dariya sukeyi. Kallo d'aya ta yiwa 6angaren da suke ta kauda kai, ta so ta wuce batare da ta gaishesu ba gudun kada Ihsan ta k'aramata wani sharrin, saidai ta ji ba zata iya aikata hakan ba, ta durkusa daga nan bayan kujera ta gaidasu. Hankalinsu sam baya kanta don ya tafi a hira hakan yasa basu ko lura da ita ba. Tana kokarin mikewa suka had'a ido da Faruk, kai ya gyad'a mata alamun amsawa, sai ta dan ji sanyi, ko babu komai an amsa mata, ta bar wajen a nutse. Saida ta isa kofar dakinta ta juyo kadan, ga mamakinta idanun Faruk a kanta har lokacin, saidai suna hada ido ya kauda kansa ita dinma da sauri ta fad'a d'akin ta rufe da mamaki dauke saman fuskarta wanda ko kadan ya gaza 6uya. Toh shi kuma wannan haka yake da kallo? Ta tambayi kanta, sai kuma ta girgiza kai had'i da ta6e baki. Yunwa ta ji ya addabeta, rabonta da abinci tun wajen sha biyu na rana, ga shi batason fitowa ba don komai ba sai don nauyin mutanen falon da take ji. Hakanan ta hakura ta yi sallar isha'i sannan ta zauna tana jiran tafiyarsu. Babu jimawa sosai ta tsinci muryar Mami tana kiranta. Da sauri ta fito falon, Hajiya Babba tare da ita suna tsaye, Hajiya Babba ta sha mayafi ta zura takalmanta.   "Dauki ledar can ki bi bayan su Ihsan a sanya a mota."   "Toh Mami." Ta fad'a a ladabce sannan ta bi umarninta. [8:56am, 12/4/2016] Sister ruffy:   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR         15                        Anan ta iskesu tsaitsaye ana hira banda babban yaya wato Yaya Usman da ke zaune cikin mota tare da Faruk wanda gaba d'aya ya matsu su koma gida don jinsa yake a gajiye.     Ihsan ta bita da kallon harara, hakan yasa ta kauda kanta.   "Kanki ake ji." Ta fad'a a ranta. Ta dubi wata doguwar budurwa siririya bak'a, bata san itace Ikram ba ko kuma Baraka, don sunayensu kawai Amina ta sanarmata ba ta nunamata su ba a fuska.     "Ga wannan a ina zan ajiye?"   Ta dubeta, sannan ta nunamata motar da yatsa batare da dogon bayani ba.     "Kinga, saka anan." Ta dubi Yaya Haidar dake nunamata boot wanda yasa hannu ya bud'e. Ta karasa ta ajiye gami da fad'in.   "Allah Ya tsare hanya." Daga haka ta juya ta bar wajen.            "Adnan ina mutuniyata ne? Ban ganta ba."   Adnan ya yamutse fuska yana duban farar budurwar siririya da tayi mishi magana, wato Baraka.    "Wa kenan?" Ya tambaya cikin basarwa kamar bai fahimci ko wa ta ke nufi ba da gaske.     "Abokiyar fad'arka mana, your lil sis."   Ya harareta, ya gane Iklima take magana akai.     "Ai kinsan hanyar gidansu ko? Sai kije." Baraka tayi dariya.   "Kwarai ma kuwa wallahi, idan ma kana ganin kamar bazan iya zuwa ba zaka sha mamaki. Kada fa ka manta k'awata ce, mun riga mun saba da uta adalilin (whatsapp group) da muke ciki tare. Zo muje Ihsan ki rakani."        Ba musu ta ja Ihsan suka tafi. Hajiya Binta suka soma gani a falo tare da Usman, Jabir da Hanif, gaba daya kallo ya daukemusu hankali. Sallamarsu ce ta sanyasu maido hankali garesu. Ta soma shan kamshi yayinda ta amsa ciki-ciki.   Suka karasa suka gaisheta. Saida ta k'arewa suturar dake jikin Baraka kallo sannan ta numfasa, ta riga tasani iyalan Hajiya Fatima ba su ta6a zama a baya wajen suturu da sauran kayan more rayuwar duniya.     "Baraka ko?" Baraka fuska a sake ta amsa. "Eh ni ce Umma."    "Sannu, yanzu kuka zo?" "Za mu tafi ne dai, ina Iklima?"   Hajiya Binta ta nunamusu hanya. "Ku shiga tana d'akinta."   Suka shige ta bi bayansu da kallo cike da jin wani tuk'uk'i a ranta, dole Madina ta dunga yi musu wani gani-gani kasancewar daga ita har Lubna, ba wasu 'ya'yan masu kudin azo a gani bane, a komai dangin Hajiya Madina sun k'ere musu, yana daga dalilin da yasa suke matukar kishinta. A gefe kuma tana tak'ama da cewar ita din fa jinin Alhajinsu ce, shi kansa Alhajin koda hira akeyi da ya shafi danginsu, sau da yawa yakan yabawa bajintar mahaifin Madina, da irin yanda ya iya rik'e iyali da sauransu. Wannan yasa ko kad'an acikinsu babu mai kaunar suyi wata doguwar hirar da ta shafi dangin Alhaji Modibbo. Babban burinta yanzu, bai wuce yaranta su kasance wasu shahararru ba a fannin kudi, ta ci buri akan Iklima wannan yasa ta haneta abota da dukkan wani jinin talaka, dukkan abokan Iklima 'ya'yan wasu ne. Koyaushe tana hanyar biki da party. Babu laifi takan samu samarin masu ji da kudi saidai da yawansu ba da aure suke sonta ba, saidai wata manufarsu ta daban. Idanunta sunyi masifar budewa wanda hakan nai ta6a damun Hajiya Binta ba, acewarta, idan bata kasance wayayyiyar ba, a ina har zata samarwa kanta miji dan zamani.        Acan kuwa su Baraka suna shiga Iklima ta rungume Baraka tana ihun murna don sosai kawarta ce, kusan halinsu yazo d'aya na son gayu da samari.    "Shegiyar gari, daman kinzo shine ko ki nemeni?"   Baraka tana dariya tace "Afuwan tawan, kinsan tun dazu na so shigowa Allah baiyiba, ina su Yaks?"   Fad'in haka yasa ita da Ikliman suka tuntsire da dariya ita dai Ihsan ta zama 'yar kallo, ko ita da suke tare da Ikliman basu hira mai tsayi har haka, lallai ba karamin sabo Baraka da Iklima sukayi ba.    "Yana inda yake, kwana biyu munyi fad'a ma, zan baki labari kedai. Ina mijina?"   Cewar Iklima tana mai kashe mata ido d'aya, Baraka ta ja guntun tsaki tana dariya. Ta fahimci Faruk take nufi, tun daga sau daya da ta ga ta dora hotonsa a dp lokacin shi kuwa yana gani ya shigo har dakinsu ya hauta da fad'a har yakai ga mangarinta, yace tayi gaggawar goge dukkan hotunansa a wayarta. Daga ranar bata kara dora hotonsa. Daga ranar Iklima ta makale akan lallai ita fa sai ta hadata da shi, hakuri kawai ta bata ta gwadamata Faruk sam ba irin nasu bane don ba shi da wannan rawar kan akan mata.    "Kedai ki kama kanki baruwana na gayamaki."   Cewar Baraka. Iklima tayi dariya.   "Ina ruwanki? Bazan kama ba sai randa kika bani lambarsa."   Ihsan duk bata fahimci komai ba saida ta ji Baraka na fadin.   "Kizo muje da kanki ki tambayeshi, ga shi can a waje." Ai sai Iklima ta zaro ido.   "Dagaske?" "Wallahi." Cewar Baraka cikin dariya, tuni ta ja dankwalinta ta rufe kanta, daman riga 'yar kanti ce a jikinta sai siket ruwan madara na leshi da dankwalinsa.   "Muje wallahi na gaisheshi na tambaya."   Suka kamo hanya Baraka cikin dariya ta na fad'in. "Kamar gaske, bakisan wanene Yaya Faruk ba wallahi."   Gaban Ihsan ya fad'i, me Baraka ke nufi? Wato Iklima batun Faruk take? Aikuwa ba zata sa6u ba, saidai su yi BIYU BABU. Muddin ita bata samu soyayyarsa ba, to babu wata ta jininta da zata samu, ta gwammace ya je ya auri bare akan tana ji tana gani ya auri wata jininsu. A ganinta, itama fa tana da aji, ba zai yiwu ta zauna wani namiji na sha mata kamshi ba, ta tsani dukkan wani namiji mai ji da kansa, baruwanta da kyansa, idan kyau ne, akwai wadanda suka fishi da suka nuna suna sonta tana sha musu kamshi.       Anan kofar shiga sashen Alhaji Modibbo suka ga takalman Mami da Hajiya Babba, wannan ya tabbatar musu suna ciki. Da rawar jiki Iklima take tafiya, Allah-Allah takeyi ta had'u da Faruk ko don shima yasan da zamanta. Ta tabbatar ba kowane namiji ne zai iya dauke idanu daga kanta ba. Haka suka karasa bakin motar, alokacin Haidar da Adnan ne kawai tsaye sai Ikram wacce ta jingina jikin mota tana danne-dannen waya. Iklima suka gaisa da Haidar, Adnan sai dauke kai yakeyi. Itama bata bi ta kansa ba ta dan lek'a motar, kasancewar akwai wadatar haske a farfajiyar gidan hakan yasa ta hangi Faruk dake zaune a mazaunin direba ya d'ora tafin kafarsa akan kujera, kansa jingine jikin kujerar yayinda kunnensa ya sanya (Earpiece) yana shan sauti. Idanunsa a lumshe. Wani wawan ajiyar zuciyar Iklima ta saki, ta ko'ina Faruk ya had'u. Ta gaida su Yaya Usman suka amsa mata fuska a sake kafin tayi ta wajen Faruk tana gaisheshi. Ko kusa baisan ma tana yi ba saida Usman ya cire mishi kunne d'aya na (Earpiece) sannan ya juyo da rinannun idanunsa, da alamu ma bacci ya soma.    "Au bacci kakeyi ma? Ana gaisheka."  "Ina wuni." Ta k'ara fad'a. Ya juyo ya zubamata idanu, ai ji tayi kamar ta saki fitsari tsabar yanda kallon ya kad'ata, duk inda take zaton Faruk a kyau da komai, ya wuce nan. Kansa kawai ya gyad'a mata sannan ya dauke kai. Ji tayi ta kasa koda kwakkwarar magana, to ta ina ma zata iya furta mishi wani abun har ya kai ga tambayar lambarsa? Ba zata iya ba, hakan yasa ta koma ga su Baraka wadanda ke yi mata dariya har Ihsan wacce ba karamin dadi abin ya yi mata ba.       "Wace ne?"   Faruk ya tambaya ba tare da ya bud'e idanunsa ba.    "Iklima, step-sister dinmu." Cewar Adnan. Ya yamutse fuska.   "Har yanzu Hajiya bata fito ba? Wallahi na soma bacci."   Kafin waninsu yayi magana, sai ga Mami da Hajiya tafe suna hira, Yaya Ridwan ne yayi magana.   "Ai idan iyayenmu mata suka had'u wallahi har mamaki suke ban, ko kusa basu kaunar rabuwa da juna."   Faruk da Usman suka d'an dara, kamar ba zasu karaso ba haka suke tafe suna hira. Ganin dai da gaske basu da niyyar tahowa ya sanya Faruk dannan hon, wannan ya maido hankalinsu wajensu. Ya koma can gefen mazaunin direba yana fad'in.   "I can't drive wallahi, bacci ya soma kama idona."   Haidar ya bude mazaunin direba ya shiga yana fad'in.   "Ai nayi mamaki ma da ka iya kaiwa war haka, kodayake na dole ne. Mutumin da wani sa'in takwas ma yayi bacci."   Murmushi kawai Faruk yayi ya kara lumshe idanunsa sannan ya budesu. Hajiya Babba ta karaso ta shiga, ganin haka yasa yanmatan sallama da juna, bayan shigarsu Iklima ta zubawa Faruk ido kamar ta had'iyeshi, tsaf ya lura da kallon da take jifansa da shi, wannan yasa a sannu ya zuge gilas wanda ya kasance mai duhu, shi ya yi mata katanga daga dubansa. Ta sauke ajiyar zuciya, ta juya ta kama hanyar ciki bayan ta gaishe da Hajiya Babba, sun kara sallama da Baraka.                                                 "Maganar banza ce kikeyi, wacce ba zata ta6a kasantuwa ba matukar Binta na raye wallahi. Da kinsan yanda nake kishin Madina da danginta, da baki soma tunanin son Faruk ba Iklima."    Cewar Hajiya Binta tana faman hura hanci fuska a murtuke kamar bata ta6a bud'a hakoranta ba don dariya. Iklima ta tur6une fuska tana kunkuni ta mik'e ta barta tana faman bud'e wuta.     "Eh lallai, gwara tun wuri na tashi tsaye kafin kema ki rikita lamurana, shawarar Hadiza zan bi."   Ta karashe tana daukar wayarta, Hadiza ta dannawa kira sannan ta mike ta fad'a d'aki. Suka gama kulla-kullarsu akan yanda Alhaji zai shigo hannunta sai yanda tayi da shi, da kuma irin nau'ikan muguntar da za'a yiwa Madina a lalata rayuwar 'ya'yanta, itama a dusasar da tauraronta dake haskawa a idanun Maigidan da surukarsu. Haka suka ajiye wayar cike da jin wani nishad'i ko babu komai itama tana dab da samun matsayi babba.                             ☆☆☆  Haka rayuwa tayita tafiyarwa Ummi, yau dadi gobe babu dadi. Yawanci matsalarta bai wuce Ihsan ba don Mami matukar zata yi abinda ta sanyata to fa babu ruwanta da harkarta. A wannan halin ne wata ranar Asabar ta tashi da ciwon mara marar misali, tun tana dauriya har ta kasa, ko tashi ta kasa yi balle ta kai ga aikace-aikacenta. A wannan hali Ramma tayi sallama ta shigo bisa umarnin Mami da  ta dubo ko lafiya bata fito ba har ga Ramma ta rigata zuwa.     Ganinta ba lafiya yasa ta fita ta sanarwa Mami. Kafin su dawo ta soma jin ta da lema, saida Ramma ta d'agata ne suka fahimci abinda ke faruwa. Ramma ta taimaka mata bayan ta kar6o (Always) wajen Mami, ta gwada mata yanda zatayi, saida ta kimtsa sannan suka rankaya kemis da Ramma.     Tun daga wannan ranar Ummi ta fahimci girma ya hau ta, Ramma ta k'ara jaddada mata hakkokin da suke akanta yanzun wadanda ta riga ta sani don a makaranta duk ana koyardasu.    Mami bata yarda da kazantar kunzugu ba, hakan yasa ta bata (pads) cikin na Ihsan wacce ta rigata somawa tuni. Saida tayi kwanaki hud'u sannan tayi wankan tsarki. Daga wannan lokacin ta k'ara kame kanta ta zama mai kula sosai da takatsantsan musamman ma ga sallolinta.                     ☆☆☆           A KWANA A TASHI...! DAN ADAM   @RUFAIDA OMAR   12   Daga haka bata da masaniyar abinda ya karu don kuwa tuni sun bar wajen sun sauka da niyyar dauko sauran kayan. Larai ta taimaka musu itama. Haka sukayita zirga-zirga, bayan sun kammala kawowa, suna shirin tafiya, Hajiya Mama tayi musu magana.   "Yauwa Amina sauranku lemu da ruwa ko?" "Toh." Amina ta amsa.    "Muje." Cewar Amina tana duban Ummi wacce ke tsaye. Suka nufi falon kasa, suna jin sadda Hajiya Fatima ke tambayar Inna ko Ummi sabuwar yar aikinta ce. Inna ta amsa da aa, Hajiya Mama ta sanarmata a wajen Mami take. Nan fa Alhaji ya hau fadan yawan chanje-chanjen masu aiki da takeyi. Daga haka basu kara jin tattaunawar ba suka yo k'asa suna dariya don abin ma dariya ya basu. Amina ta dubeta.   "Kinsan wani abu kuwa? Duk fa abin su Mami, suna gudun abinda zai 6ata ran iyayensu, duk abinda suka ce suyi basa musawa shikenan ta zauna. Wallahi suna burgeni yanda suke kaunar iyayensu." Ta karashe lokacin da take kokarin bude firij.   Ummi tana murmushi tace "Toh Anti ai sune abin alfaharin, idan baka da mai maka fad'a ina wani jin dadi a rayuwa?"    Amina ta jinjina kai sadda ta soma ciro lemuka tana dorawa a saman firjin.     "Gaskiyane kam, mik'o tire a kicin mu dora."   Larai ta tambaya ta mikamata, ta goge sannan ta koma suka dora akai, wannan karon Ummi ce a gaba tana biye da ita, saida suka zo daidai dan korido wanda daga shi sai kofar shiga, ta ja baya ta marairaice.   "Don Allah Anti shiga gaba." Abin sai ma ya bawa Amina dariya, babu musu ta shiga gaba da sallama sannan itama Ummin ta bi bayanta. Ido hud'u tayi da wannan matashin na dazu, ya tamke fuska ya kauda kai, hakan da ta gani yasa itama dauke nata idanun da sauri ta cigaba da tafiya a tsanake, tuni sun soma zubawa, har Hajiya Fatima na yiwa wani cikin matasan fada akan bayason cin abinci alokacin da kowa yake ci, wanda akeyi domin shi murmushi kawai yakeyi.  "Shiyasa fa bana sonshi, wannan idan mukayi aure mai yiwuwa nima haka zai dunga hora ni da yunwa, barni dai na lalla6a da Gadanga." Cewar Inna kenan, aka sanya dariya gaba d'aya.    "Kai tsohuwa, dad'ina dake kenan. Ai Faruk banda harkar neman kudi bana jin akwai abinda yasa a gaba, yanzu sai ya juya miki biyar zuwa dubu." Cewar wani wanda ga dukkan alamu shine babbansu, don fuskarsa kadai ya nuna akwai shekaru.    "Yauwa Usmanu, ashe ka fahimta."   Ummi da Amina tuni suka bar wajen, Amina na rike da Samir d'a awajen Rahila babbar d'iya ga Hajiya Madina.        Haka sukayita zolayarsa ko kusa bai mayar da martani ba, asalima banda murmushi babu abinda yakeyi, idan kuma abin ya wuce murmushi, sai ya dara.       Acan k'asa suma abinci suka ci sukayi nak, bayan sun kammala kuma sukayi zaman hira har zuwa sadda akayi kiran sallar La'asar. Sai lokacin samarin suka sauko, Ummi ta bisu da kallo kamar yanda Amina ta umarceta. Ta kara jaddada mata cikin rad'a-rad'a. "Kinga na farkon nan mai dan jiki shine babban d'an Hajiya Babba ta Abuja, Yaya Usman yana da matarsa d'aya da yaransu uku, na biyun shine Yaya Faruk, shine autansu baiyi aure  ba, na ukun mai farar shadda shine Yaya Ridwan, shima yana da matarsa daya 'yar Ghana ce, yaransu biyu. Na karshen shine Yaya Haidar, shi ake shirye-shiryen bikinsa yanzu tare da Yaya Intisar babbar d'iya ga Hajiya Mama, bikin baifi ragowar sati uku ba."   Wannan dogon bayanin da Amina takeyi, tuni wadanda akeyi don su sun fice saidai Ummi ta fahimta kuma ta gane, kenan dai Yaya Faruk shine wanda ta gani dazu a tsakar gidan yana waya? Ta tambayi kanta kuma ta bawa kanta amsa. Ba karshen dai Adnan ne wanda ba sai an mata bayaninsa ba.   Koda suka idar da sallah, anan suka zauna tsakar gidan suna ta hirarsu har zuwa lokacin da samarin suka dawo suka shiga ciki banda Faruk wanda ya tsaya amsa waya acan farfajiyar gidan.    Kiran da Larai ta kwalawa Amina yasa ta mikewa tana amsawa. Nan ta bar Ummi da Samir yaro mai shiga rai. Wasa ta shiga yi mishi, babu ruwansa sai 6angale dariya yake. Ya shiga jan dankwalin abayarta yana dariya, ta rike hannun. "A'a Samir, daina."   Maimakon ya daina, saima ya karasa janyewa gaba daya yana ihu da dariya, ta mike da zummar kamoshi, saidai da gudu ya shiga zagaye a wajen. Abin ya bata mamaki da dariya, a garin ta cafkoshi ganin yayi hanyar kofa, ba tsammani tayi karo da mutum har ya kai ga faduwar abin hannunsa.    "Bismillah." Ta fad'a batare da ta shirya ba.  Ta dago kai sukayi ido hud'u da Yaya Faruk, fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bakinta ya soma rawa saidai ta kasa fidda ko kalma d'aya, tana so ta bashi hakuri amma batasan ya akayi hakan ya kasa fitowa ba, wani kwarjini kawai ta ga yayi mata. Ta durkusa da sauri ta dauki wayarsa da ta tarwatse ta hado mahadinta wato batir da murfi ta mik'a mishi batare da ta mike ba. Sai lokacin ta samu yin magana. "Don Allah kayi hakuri."   Ta fada cikin sanyin murya. Yasa hannu ya kar6a.   "Is ok." Ok din karshe kawai ta fahimta, ya kad'a kai ya barta anan, ganin haka da sauri ta mike ta bi Samir wanda  maigadi ya cicci6o a hanya ganin zai fice, ta kar6eshi ta kuma kar6i dankwalinta ta rufe gashinta.    Ba su suka tashi tafiya ba sai bayan Magriba, anan dinma kamar baza'a tafi ba, don ta jima a tsaye a farfajiyar gidan bayan ta kammala sanyamusu kayayyakinsu a mota tana jiransu. Su dinma ji sukeyi  kamar kada su rabu don dadin da gidan yayi musu ganin kowa an had'u. Haka dai suka fito suka fice. Tana jin sadda Ihsan ke rok'on 'yan Abuja akan su kawo musu ziyara kafin su tafi.   "Haba Lil, ai ba saikin rok'a ba." Cewar Yaya Haidar cikin sakin fuska. Daga haka suka rabu, Ummi ta saki ajiyar zuciya ganin sun hau titi don daman gaba daya ta gaji likis har ta ji inama a gidan suka barta bata biyosu ba.                   ☆★☆★☆★ DAN ADAM @RUFAIDA OMAR     13  A gajiye likis Ummi take, suna zuwa sallolin dake kanta kawai tayi ta kwanta. Bata kara sanin abinda ke faruwa ba a duniyar sai bayan farkawarta da Asuba. Bayan ta idar da sallah ta zauna anan addu'o'i har garin Allah Ya waye, kasancewar babu makarantar boko ballantana ta tashi had'e-had'en karin yaran yasa ta komawa tayi kwanciyarta, baccin da tayi har ya fiye mata na farko dadi, ta jima tana bacci kafin kuma ta soma jin ana bubbuga kafarta ana kiran sunanta. Farkawa tayi a firgice tana salati, ganin Fahad yasa ta sauke ajiyar zuciya. Kira ne daga Maminsa akan ta soya mishi kwai ta had'a da biredi da shayi. Dole ta mike ba don baccin ya isheta ba ta fad'a bandaki ta wanko bakinta da fuska sannan ta bi bayansa.    Saida ta kammala komai sannan ta fad'a d'akinsu, ganin Ihsan bata farka ba yasa ta fitowa batare da tayi abinda ya kaita ba(wato gyaran daki). Tana gudun ta shiga bandakin don wankewa Ihsan ta yi mata rashin mutunci tace ta hanata bacci.     Misalin karfe biyun rana, kowannensu yayi shirin Islamiyya, kai tsaye yaran wajen mahaifinsu suka nufa sanin da sukayi cewar yana garin suka kwashi gaisuwa ya sallamesu da abin kashewa bayan makaranta sannan suka d'uru cikin mota, suka tafi. Sai lokacin ne Ummi ta samu sararin yin nata shirin na makaranta tana ta zabga uban sauri adalilin lattin da ta so yi, haka ta fito cikin shiri ta yiwa Mami sallama. Mami ta amsa gami da yi mata fatan alheri, har ranta ta ji dadi don abu ne da sam Mamin bata saba ba, alamun Mami gaba daya a yau sun nuna tana cike da nishadi wanda babu damar tambayar dalilinsa. Ta sanya kai ta fice daga gidan.    A makaranta nan dinma ta ji dadi sosai don kuwa ta kai haddarta saidai ta sha gyara duk da baikai yawan yanda a baya Malamin nasu ke cin gyaranta ba, ta lura yana yi mata uzuri ganin ko bak'i bata iya had'awa ba, wannan dalilin yasa ya ware mata lokacinta daban yake koyar da ita wasula da bak'ak'e.     Koda suka tashi, cike da nishadi ta dawo haka kawai a yau batasan farincikin ko menene takeyi ba, ta godewa Allah yafi sau biyar a zuciyarta. A farfajiyar gidan ta iske motar Danliti, hakan ya bata tabbacin cewar Ihsan sun dawo. Hajiya Binta ta gani tare da wata wacce ba yau ta soma ganinta ba ga dukkan alamu kuma kawarta ce. Ta gaishesu a ladabce, suka amsa ciki-ciki suna karemata kallo. Bata kai ga karasawa ba ta ji suna maganarta, inda matar ke cewa.  "Ina mamakin Hajiya Madina, ko a ina ta kwaso wannan mai ruwan buzayen? Wannan ko Alhajinku ya gani mai yiwuwa yayi ta hud'u da ita."   Ta karashe tana dariyar zolaya. Hajiya Binta ta ja tsaki. "Ai kuwa da anyi girman kwabo, ballantana kuma sanin kanki ne Alhaji banda waccan shegiyar babu mai fad'amasa ya ji acikinmu, abin na kona raina."   "Ai ku kukayi sake, ki bada hadin kai kika yanda komai zai chanja mana."      Iyakar abinda Ummi ta tsinkaya kenan cikin zantukansu kafin kuma ta ta6e baki kawai, a kasan ranta kuwa tana tsoron ranar da Mami zata gaji ta korata daga gidan, watakil shikenan kuma dukkan gatan da ta soma samu na ilimi ya rushe. Saidai kuma tayi mamakin yanda Hajiya Binta take kula kawaye irin haka, da ace sun saba kwarai, da babu abinda zai hanata yin shishshigi wajen bata shawarar watsi da zantukan wannan mata. Da sallama ta nufi shiga falon, saidai kuma tayi turus ganin takalman maza har sawu hud'u da kuma na mata a bakin kofar, haka kawai ta ji gabanta ya fad'i, koda ta shiga bata ga kowa ba a wannan falon, ta numfasa ta karasa ciki, har ta chanja sutura tana cike da tunanin wadanda suka zo, sai kuma ta tunano da su Yaya Haidar, watakila su d'inne suka zo. Ta shirya cikin atamfa riga da zani da dankwali bayan tayi wanka sannan ta d'auro alwala ganin Magriba na dab da yi, fitowa tayi falo, tana son zuwa sanarwa Mami cewa ta dawo saidai kuma batason iske bak'in gaba d'aya nauyinsu take ji.   A kicin ta had'u da Ramma, ta gaisheta. Ramma ta amsa tana fad'in.   "Yanzu kuwa Hajiyar ke tambayarki, ta ji shiru nace kin dawo kina ciki. Kije tana nemanki."   Gaba daya ta ji tsoro ya kamata har yanayin fuskarta ya nunawa Ramma.   "To ai naga tana tare da bak'i yanzu." Ramma ta kama baki. "Su waye bak'in? Ai 'yan gida ne, Hajiya Babba ce fa da yaranta."   Ta gyada kai sannan ta juya ta nufi hanyar falon Mami gabanta na dukan tara-tara, ita da ba don ance Mami ke nemanta ba da babu inda zata. Har ta kai kofar shiga sai kuma ta juya da sauri don ji tayi ba zata iya ba. Muryoyin da ta jiyo daga bayanta na matasan yasa dole ta juyo. Gaba daya mazan ne suka fito da alamu dai masallaci suka nufa sakamakon kiraye-kirayen sallar da aka soma. Kallo d'aya tayi musu ta durkusa da sauri ta gaishesu. Suka amsa sannan ta basu wuri don su wuce. D'ago idon da zata yi sukayi ido hud'u da Faruk wanda dagaske kallonta yakeyi, ta gwammace ace bai kalleta din ba domin kuwa kallo ne ba na arziki ba face kallon raini, fuskarsa babu wata alamar fara'a; ta sadda kanta da sauri.    "Ai kuwa Mami na ta cigiyarki da alama kin mata wani gagarumin laifi Ummi." Cewar Adnan ya karashe da dariyar zolaya.    "Um." Shine abinda ta furta kawai da murmushi dauke saman fuskarta. Bayan sun wuceta ta bi bayansu da kallo. Wannan karon, Yaya Usman ne kadai ya sanya manyan kaya, gaba daya su ukun k'ananun kaya ne jikinsu. Hajiya Babba Allah Ya bata arziki na zaratan maza wadanda dukkansu basuyi kama da ragwaye ba a komai da ya shafi gwagwarmayar rayuwa da sauransu. Saidai da ace za'a bata za6in wanda yafi kyau da burgewa a fuska acikinsu, toh fa babu abinda zai hanata nuna Yaya Haidar bisa hujjarta na ganin duk ya fisu fara'a. Koda kuwa tasan da yawa cikin wasu matasan yanmata irinta, zasu iya bugun kirji su za6i Yaya Faruk, ita kam banda ita. Tsakani da Allah ta ji haushin kallon da ya bita da shi tamkar wanda ya ci karo da kashi, ta numfasa don tuni sun jima da kauracewa ganinta ta juya, gabanta ya fad'i ganin Ihsan tsaye ta harde hannuwa a kirji ta zubamata na mujiya fuskarta dauke da wani mugun murmushi. Ummi ta kauda kai ta bi ta gefenta zata wuce saidai maganganun da ya soma fitowa daga bakin Ihsan ya tsayar da ita cak!    "Mutum dai ya tsaya iyakar matsayinsa, ko kusa kada yayi tunanin zai iya da Babban Goro, duk cikinsu babu sa'an aurenki, don haka ki maida maitarki, kurwar kaf dinsu, ta fi karfinki."    Daga wannan ta sanya kai ta fita tana kwalawa Ramma kira. Iyakar radadi da bacin rai, Ummi ta ji shi a ranta, batasan sadda idanunta suka ciko da kwalla ba, wannan cin zarafi har ina? Kai tsaye an yankemata mummunan hukuncin da ko a mafarki bata yi zaton koda mak'iyinta zai shaideta da aikatawa ba, toh daman ina ita ina ire-iren wadannan mazan? Yaudarar kai ne, koda ta auna cewa Ihsan batasan irin zargin da ya kamata tayi mata  ba, yasa ta yin murmushi mai ciwo, da alama Ihsan bata gama sanin bambancin matsayinta da su ba, tabbas ta cucesu tunda har ta had'asu da ita, watakil da zasu ji da sai sun had'a da kai mata bugu don haushin abinda tayi musu. Ta share batun gami da goge fuskarta sannan ta juya ta koma don ta tabbatar a yanzun Mami ta shiga sallah. Dakinta ta koma itama ta tayar da nata sallar, saida ta idar ta kaiwa Allah kukanta akan Ya ji6anci lamuranta. Bata da kowa sai Shi, Shi ne gatanta. Yayi rahma ga Mahaifiyarta. Haka tayita kwararo addu'o'i har tana fidda ruwan hawaye kafin kuma ta shafa. Bata kai ga mikewa daga wurin ba ta ji Fahad na kwala mata kira adaidai sadda ya murd'a kofar dakin nata.   "Ummi! Kizo inji Mami."   Ta mike batare da ta cire hijabin ba ta bi bayansa.      DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 15 Anan ta iskesu tsaitsaye ana hira banda babban yaya wato Yaya Usman da ke zaune cikin mota tare da Faruk wanda gaba d'aya ya matsu su koma gida don jinsa yake a gajiye. Ihsan ta bita da kallon harara, hakan yasa ta kauda kanta. "Kanki ake ji." Ta fad'a a ranta. Ta dubi wata doguwar budurwa siririya bak'a, bata san itace Ikram ba ko kuma Baraka, don sunayensu kawai Amina ta sanarmata ba ta nunamata su ba a fuska. "Ga wannan a ina zan ajiye?" Ta dubeta, sannan ta nunamata motar da yatsa batare da dogon bayani ba. "Kinga, saka anan." Ta dubi Yaya Haidar dake nunamata boot wanda yasa hannu ya bud'e. Ta karasa ta ajiye gami da fad'in. "Allah Ya tsare hanya." Daga haka ta juya ta bar wajen. "Adnan ina mutuniyata ne? Ban ganta ba." Adnan ya yamutse fuska yana duban farar budurwar siririya da tayi mishi magana, wato Baraka. "Wa kenan?" Ya tambaya cikin basarwa kamar bai fahimci ko wa ta ke nufi ba da gaske. "Abokiyar fad'arka mana, your lil sis." Ya harareta, ya gane Iklima take magana akai. "Ai kinsan hanyar gidansu ko? Sai kije." Baraka tayi dariya. "Kwarai ma kuwa wallahi, idan ma kana ganin kamar bazan iya zuwa ba zaka sha mamaki. Kada fa ka manta k'awata ce, mun riga mun saba da uta adalilin (whatsapp group) da muke ciki tare. Zo muje Ihsan ki rakani." Ba musu ta ja Ihsan suka tafi. Hajiya Binta suka soma gani a falo tare da Usman, Jabir da Hanif, gaba daya kallo ya daukemusu hankali. Sallamarsu ce ta sanyasu maido hankali garesu. Ta soma shan kamshi yayinda ta amsa ciki-ciki. Suka karasa suka gaisheta. Saida ta k'arewa suturar dake jikin Baraka kallo sannan ta numfasa, ta riga tasani iyalan Hajiya Fatima ba su ta6a zama a baya wajen suturu da sauran kayan more rayuwar duniya. "Baraka ko?" Baraka fuska a sake ta amsa. "Eh ni ce Umma." "Sannu, yanzu kuka zo?" "Za mu tafi ne dai, ina Iklima?" Hajiya Binta ta nunamusu hanya. "Ku shiga tana d'akinta." Suka shige ta bi bayansu da kallo cike da jin wani tuk'uk'i a ranta, dole Madina ta dunga yi musu wani gani-gani kasancewar daga ita har Lubna, ba wasu 'ya'yan masu kudin azo a gani bane, a komai dangin Hajiya Madina sun k'ere musu, yana daga dalilin da yasa suke matukar kishinta. A gefe kuma tana tak'ama da cewar ita din fa jinin Alhajinsu ce, shi kansa Alhajin koda hira akeyi da ya shafi danginsu, sau da yawa yakan yabawa bajintar mahaifin Madina, da irin yanda ya iya rik'e iyali da sauransu. Wannan yasa ko kad'an acikinsu babu mai kaunar suyi wata doguwar hirar da ta shafi dangin Alhaji Modibbo. Babban burinta yanzu, bai wuce yaranta su kasance wasu shahararru ba a fannin kudi, ta ci buri akan Iklima wannan yasa ta haneta abota da dukkan wani jinin talaka, dukkan abokan Iklima 'ya'yan wasu ne. Koyaushe tana hanyar biki da party. Babu laifi takan samu samarin masu ji da kudi saidai da yawansu ba da aure suke sonta ba, saidai wata manufarsu ta daban. Idanunta sunyi masifar budewa wanda hakan nai ta6a damun Hajiya Binta ba, acewarta, idan bata kasance wayayyiyar ba, a ina har zata samarwa kanta miji dan zamani. Acan kuwa su Baraka suna shiga Iklima ta rungume Baraka tana ihun murna don sosai kawarta ce, kusan halinsu yazo d'aya na son gayu da samari. "Shegiyar gari, daman kinzo shine ko ki nemeni?" Baraka tana dariya tace "Afuwan tawan, kinsan tun dazu na so shigowa Allah baiyiba, ina su Yaks?" Fad'in haka yasa ita da Ikliman suka tuntsire da dariya ita dai Ihsan ta zama 'yar kallo, ko ita da suke tare da Ikliman basu hira mai tsayi har haka, lallai ba karamin sabo Baraka da Iklima sukayi ba. "Yana inda yake, kwana biyu munyi fad'a ma, zan baki labari kedai. Ina mijina?" Cewar Iklima tana mai kashe mata ido d'aya, Baraka ta ja guntun tsaki tana dariya. Ta fahimci Faruk take nufi, tun daga sau daya da ta ga ta dora hotonsa a dp lokacin shi kuwa yana gani ya shigo har dakinsu ya hauta da fad'a har yakai ga mangarinta, yace tayi gaggawar goge dukkan hotunansa a wayarta. Daga ranar bata kara dora hotonsa. Daga ranar Iklima ta makale akan lallai ita fa sai ta hadata da shi, hakuri kawai ta bata ta gwadamata Faruk sam ba irin nasu bane don ba shi da wannan rawar kan akan mata. "Kedai ki kama kanki baruwana na gayamaki." Cewar Baraka. Iklima tayi dariya. "Ina ruwanki? Bazan kama ba sai randa kika bani lambarsa." Ihsan duk bata fahimci komai ba saida ta ji Baraka na fadin. "Kizo muje da kanki ki tambayeshi, ga shi can a waje." Ai sai Iklima ta zaro ido. "Dagaske?" "Wallahi." Cewar Baraka cikin dariya, tuni ta ja dankwalinta ta rufe kanta, daman riga 'yar kanti ce a jikinta sai siket ruwan madara na leshi da dankwalinsa. "Muje wallahi na gaisheshi na tambaya." Suka kamo hanya Baraka cikin dariya ta na fad'in. "Kamar gaske, bakisan wanene Yaya Faruk ba wallahi." Gaban Ihsan ya fad'i, me Baraka ke nufi? Wato Iklima batun Faruk take? Aikuwa ba zata sa6u ba, saidai su yi BIYU BABU. Muddin ita bata samu soyayyarsa ba, to babu wata ta jininta da zata samu, ta gwammace ya je ya auri bare akan tana ji tana gani ya auri wata jininsu. A ganinta, itama fa tana da aji, ba zai yiwu ta zauna wani namiji na sha mata kamshi ba, ta tsani dukkan wani namiji mai ji da kansa, baruwanta da kyansa, idan kyau ne, akwai wadanda suka fishi da suka nuna suna sonta tana sha musu kamshi. Anan kofar shiga sashen Alhaji Modibbo suka ga takalman Mami da Hajiya Babba, wannan ya tabbatar musu suna ciki. Da rawar jiki Iklima take tafiya, Allah-Allah takeyi ta had'u da Faruk ko don shima yasan da zamanta. Ta tabbatar ba kowane namiji ne zai iya dauke idanu daga kanta ba. Haka suka karasa bakin motar, alokacin Haidar da Adnan ne kawai tsaye sai Ikram wacce ta jingina jikin mota tana danne-dannen waya. Iklima suka gaisa da Haidar, Adnan sai dauke kai yakeyi. Itama bata bi ta kansa ba ta dan lek'a motar, kasancewar akwai wadatar haske a farfajiyar gidan hakan yasa ta hangi Faruk dake zaune a mazaunin direba ya d'ora tafin kafarsa akan kujera, kansa jingine jikin kujerar yayinda kunnensa ya sanya (Earpiece) yana shan sauti. Idanunsa a lumshe. Wani wawan ajiyar zuciyar Iklima ta saki, ta ko'ina Faruk ya had'u. Ta gaida su Yaya Usman suka amsa mata fuska a sake kafin tayi ta wajen Faruk tana gaisheshi. Ko kusa baisan ma tana yi ba saida Usman ya cire mishi kunne d'aya na (Earpiece) sannan ya juyo da rinannun idanunsa, da alamu ma bacci ya soma. "Au bacci kakeyi ma? Ana gaisheka." "Ina wuni." Ta k'ara fad'a. Ya juyo ya zubamata idanu, ai ji tayi kamar ta saki fitsari tsabar yanda kallon ya kad'ata, duk inda take zaton Faruk a kyau da komai, ya wuce nan. Kansa kawai ya gyad'a mata sannan ya dauke kai. Ji tayi ta kasa koda kwakkwarar magana, to ta ina ma zata iya furta mishi wani abun har ya kai ga tambayar lambarsa? Ba zata iya ba, hakan yasa ta koma ga su Baraka wadanda ke yi mata dariya har Ihsan wacce ba karamin dadi abin ya yi mata ba. "Wace ne?" Faruk ya tambaya ba tare da ya bud'e idanunsa ba. "Iklima, step-sister dinmu." Cewar Adnan. Ya yamutse fuska. "Har yanzu Hajiya bata fito ba? Wallahi na soma bacci." DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 16 Kafin waninsu yayi magana, sai ga Mami da Hajiya tafe suna hira, Yaya Ridwan ne yayi magana. "Ai idan iyayenmu mata suka had'u wallahi har mamaki suke ban, ko kusa basu kaunar rabuwa da juna." Faruk da Usman suka d'an dara, kamar ba zasu karaso ba haka suke tafe suna hira. Ganin dai da gaske basu da niyyar tahowa ya sanya Faruk dannan hon, wannan ya maido hankalinsu wajensu. Ya koma can gefen mazaunin direba yana fad'in. "I can't drive wallahi, bacci ya soma kama idona." Haidar ya bude mazaunin direba ya shiga yana fad'in. "Ai nayi mamaki ma da ka iya kaiwa war haka, kodayake na dole ne. Mutumin da wani sa'in takwas ma yayi bacci." Murmushi kawai Faruk yayi ya kara lumshe idanunsa sannan ya budesu. Hajiya Babba ta karaso ta shiga, ganin haka yasa yanmatan sallama da juna, bayan shigarsu Iklima ta zubawa Faruk ido kamar ta had'iyeshi, tsaf ya lura da kallon da take jifansa da shi, wannan yasa a sannu ya zuge gilas wanda ya kasance mai duhu, shi ya yi mata katanga daga dubansa. Ta sauke ajiyar zuciya, ta juya ta kama hanyar ciki bayan ta gaishe da Hajiya Babba, sun kara sallama da Baraka. "Maganar banza ce kikeyi, wacce ba zata ta6a kasantuwa ba matukar Binta na raye wallahi. Da kinsan yanda nake kishin Madina da danginta, da baki soma tunanin son Faruk ba Iklima." Cewar Hajiya Binta tana faman hura hanci fuska a murtuke kamar bata ta6a bud'a hakoranta ba don dariya. Iklima ta tur6une fuska tana kunkuni ta mik'e ta barta tana faman bud'e wuta. "Eh lallai, gwara tun wuri na tashi tsaye kafin kema ki rikita lamurana, shawarar Luba zan bi." Ta karashe tana daukar wayarta, H Luba ta dannawa kira sannan ta mike ta fad'a d'aki. Suka gama kulla-kullarsu akan yanda Alhaji zai shigo hannunta sai yanda tayi da shi, da kuma irin nau'ikan muguntar da za'a yiwa Madina a lalata rayuwar 'ya'yanta, itama a dusasar da tauraronta dake haskawa a idanun Maigidan da surukarsu. Haka suka ajiye wayar cike da jin wani nishad'i ko babu komai itama tana dab da samun matsayi babba. ☆☆☆ Haka rayuwa tayita tafiyarwa Ummi, yau dadi gobe babu dadi. Yawanci matsalarta bai wuce Ihsan ba don Mami matukar zata yi abinda ta sanyata to fa babu ruwanta da harkarta. A wannan halin ne wata ranar Asabar ta tashi da ciwon mara marar misali, tun tana dauriya har ta kasa, ko tashi ta kasa yi balle ta kai ga aikace-aikacenta. A wannan hali Ramma tayi sallama ta shigo bisa umarnin Mami da ta dubo ko lafiya bata fito ba har ga Ramma ta rigata zuwa. Ganinta ba lafiya yasa ta fita ta sanarwa Mami. Kafin su dawo ta soma jin ta da lema, saida Ramma ta d'agata ne suka fahimci abinda ke faruwa. Ramma ta taimaka mata bayan ta kar6o (Always) wajen Mami, ta gwada mata yanda zatayi, saida ta kimtsa sannan suka rankaya kemis da Ramma. Tun daga wannan ranar Ummi ta fahimci girma ya hau ta, Ramma ta k'ara jaddada mata hakkokin da suke akanta yanzun wadanda ta riga ta sani don a makaranta duk ana koyardasu. Mami bata yarda da kazantar kunzugu ba, hakan yasa ta bata (pads) cikin na Ihsan wacce ta rigata somawa tuni. Saida tayi kwanaki hud'u sannan tayi wankan tsarki. Daga wannan lokacin ta k'ara kame kanta ta zama mai kula sosai da takatsantsan musamman ma ga sallolinta. ☆☆☆ A KWANA A TASHI...! DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 17 A kwana a tashi ba wuya a wajen Ubangiji, har ga shi ana sauran kwanaki hud'u bikin Haidar da Intisar. Wannan ya janyo Ihsan komawa gidan Hajiya Mama don taya 'yar uwarta shirye-shirye. Alokacin tuni su Hajiya Babba sun iso Kano don anan za'a yi sha'anin bikin kasancewar mijinta, Gen. Ahmad Danzaki, uba ga su Usman, shima dan asalin Kano ne. Mami ta yiwa Ramma da Ummi kyautar atamfa turmi d'aya na anko. Ramma ta had'a ta kai musu dinki wanda ya zauna d'as a jikinsu. Ana washegari za'a soma biki, suka ziyarci Hajiya Mama wacce ke fama da shirye-shirye. Amina ta ji dadi kwarai na ganin Ummi. Anan gidan Mami ta barta tare da Fahad suka fita zuwa babban shagon siyar da kayayyakin kicin, hakanan su Ihsan suma sun fita wajen gyaran Amarya. Ummi ta dubi hannun Amina da suka sha kunshi. "Anti na kasa dauke ido daga kunshin nan naki wallahi, yayimin kyau sosai." Amina fuska a sake ta amsa mata sadda take gyara zaman tsintsiyar hannunta wanda take shirin yin shara. "Idan kina so muje na rakaki sai na dawo, wallahi yarinyar ta iya kunshi, baki ganta ba kuma ba wata babba ba." Ummi ta zaro ido, ga koshi ga kwanan yunwa. "A'a, banason fad'an Mami, idan suka dawo basu tarar da ni ba ai nasan ba zata kyaleni ba." Amina ta dara kadan. "Kedai akwai matsoraciya, ni na fadamaki har babban gida sai sun shiga tunda Gwaggo ta zo (surukar Mami kuma yar uwar mahaifinta). Na tabbatar su da mu gansu a gidan nan sai Magriba. Bari nayi shara na rakaki, keda kike fara tas ma ai sai ya fi yi miki kyau a kaina." Ummi tayi tsuru da ido bata kara cewa komai ba, tana kallo Amina ta kammala share tsakar falon, ta wanko hannunta sannan ta yafa gyale. "Muje." Ummi ta girgiza kai. "Ai baki isa ba, tunda har kina so wallahi sai kinyi, saidai wani ikon Allahn ya hana. Idan kudin kike ji, kada wannan ya dameki, zan biya." Dakyar ta shawo kanta ta amince suka tafi. Babu nisa sosai, saida Amina ta ga an soma yi sannan ta taho bayan ta rok'i alfarmar mai kunshin akan ta sanya a raka ta gida. Ba wani mai yawa akayi mata ba, saidai duk kushen mai kushe bazai kalli hannu da kafafun Ummi ba ya ce baiyi kyau ba. Bak'in lalle ne, hakan yasa babu jimawa sosai ya bushe adalilin iskar dake kad'awa. Ta wanke a gurguje, alokacin anyi sallar la'asar, gaba daya fargabanta bai wuce na kada ya zamana su Mami sun dawo ba. Saidai cikin ikon Allah daga su Mamin har su Intisar babu wanda ya dawo. Amina ta rude ganin yanda Ummi tayi kyau. "Kai amman lallen nan yayi miki kyau sosai masha Allah, sauranki kitso." Ummi ta murmusa. "Anti nikam banason kitso wallahi bansan dalili ba." Amina ta harareta kad'an. "Eh mana, don kinga kina da gashin ne ai, amma idan kana da kyau saika k'ara da wanka. Gashinan yanzu kunshi yasa kin fito a Mace." Sukayi dariya. Koda Ummi ta idar da sallah, tare suka shiga kicin tana kallon yanda Amina ke had'a girke-girke. Abin sai ya bata sha'awa matuka, don duk iyakar girkinta a gidan Mami, bai wuce dahuwar kwai da indomi ba. Amina ta bata shawara akan ta k'ara zage damtse wajen lura da yanda su Mami da Ramma ke girke-girke. Anan suka shantake wajen hira, har Amina na labarta mata batun wani saurayinta wanda shi kadai take saurara, har a yanzu haka ya soma matsawa da batun turo magabatansa. "Allah Sarki, toh Anti ki ba shi dama mana." Amina ta murmusa. "Ba anan matsalar take ba, dangin mahaifina ne abun ji, kina ganin yanda suka wancakalar da lamuranmu, ina gudun kada azo a samu matsala ne." Ummi ta gyada kai. "In sha Allah babu abinda zai faru, ki gwada ba shi dama." "Ai ko na k'i ko na so babu yanda na iya, tunda dai ina kaunarsa haka kuma Innarmu ta ba shi wannan damar har ta sanar da ni muddin ya kara tuntu6arta da maganar zata kwatanta mishi gidan su Mahaifina, kinga kuwa ai bani da ta cewa sai addu'a." "Gaskiya kam, Allah Ya yi miki za6i." "Amin, bari mugani, idan banyi lattin gama dahuwa ba, zan kaiki ki gaida Inna." Wani sanyi ya mamaye kirjinta. "Toh Anti." Ba haka suka so ba, don lokaci k'urarre suka kammala, alokacin kuma Mami suka dawo, duk da haka ba su bar gidan nan ba sai bayan Isha'i, wannan yasa Amina yi mata alkawarin duk randa suka k'ara zuwa zata yi kai ta. Koda Mami ta ganta da kunshi babu abinda tace, illa iyaka ta tambayi yanda ta samu kudin, ta shaidamata Amina ce ta biyamata, daga wannan bata k'ara uffan ba. Washegari ya kama ranar Kamu wanda za'a gabatar a wani tsadadden dakin taro wanda ake ji da shi sosai a birnin Kano, wajen da sai wane da wance. Tun misalin karfe uku na rana, dakin Mami kaf suka shirya, a ranar ma Ummi ta kara fashin makaranta wanda ko kadan ba haka ta so ba, saidai tasan Mami ba barinta zatayi ita d'aya. Daya cikin kayan da aka dinkamata tun farkon zuwanta ta sanya don kuwa Ramma ta sanar da ita cewa sai ranar yini za'a sanya anko. Tsari da kwalliyar wajen ya burgeta kwarai, banda wak'a babu abinda kakeji yana tashi a filin taron, waka marar sauti sosai, acikin nutsuwa akeyinta. Har shagala tayi wajen kallon gogaggun yan boko mata wadanda suka ci ado har suka gaji, sai faman fara'a suke kowacce na harkar gabanta. Tana nan zaune tana rarraba idanu, ta ji an dafa kafadarta. Amina ta gani, suka washewa juna hakora, haka kawai itama Ummi ta tsinci kanta da tsantsar farinciki kai kace bikin wani nata akeyi. Amina ta ci kwalliya kamar ba ita ba duk ta chanja. "Kedai Ummi kina da ban haushi, bansan meyasa bakyason gyara fuskarki ba wallahi, kalli dai yanda yanmata suke cakarewa, amma ke inaga ko hoda bakya shafawa, kodai baki da ita ne?" Ummi tayi dariya har hakoranta suka bayyana a fili. "Anti nida ban iya kwalliyar ba?" "Ai ba lallai sai kinyi mai zafi ba, ko hoda kadai kika shafa kika saka jan baki mai kala a le66anki ya wadatar, ji yanda kika hadu, wallahi da ace kina kwalliya na tabbata sai kin fi haka." Ummi ta rausaya ido tana dariya. "Ko?" Suka dara gaba d'aya. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR       19   "Ki sanar da ita cewar tana iya tafiya, don banason had'a tafiyata da shirgi."   Ummi dai toh kawai ta furta sannan ta mike.   "Tsaya Ummi." Cewar Iklima wacce ta fito daga d'aki cikin shirin shadda ruwan k'asa mai turuwa, dankwalinta a hannu da ribuna. Gaba daya suka dubeta. Ta dubi Hajiyarta.   "Ni zan bisu yanzu mu tafi."   Hajiya Binta ta bita da mugun kallo, ta tabbatar wannan rawar kafar da takeyi bai wuce na son ganin Faruk ba, ita kuwa ta ci alwashin koda Iklima zata mutu, ba zata ta6a bari ta auri jinin Mami na kut da kut ba.    "Banyi miki iznin binsu ba, ke wuce ki isar da sak'ona. Tana iya tafiya."   Ummi jin haka yasa ta juya gami da dan ta6e baki, da sauri ta kara gaba batare da ta jira jin yanda zata kaya tsakanin 'ya da uwarta ba.       Kai tsaye dakin Anti Amarya wato Hajiya Lubna, ta nufa. Ita kam babu laifi tana da tsafta itama duk da cewa ko rabi-rabin kafar Mami bata kama ba, bata falon sai yaranta. Babu wanda ya yiwa Ummi kallon banza, saidai kuma basu bada muhimmanci akanta ba don hankalinsu ya tafi ga kallon wani film na yak'i da ake haskowa a (Mbc Max). Ganin haka yasa ta kara magana.     "Don Allah ina Anti Amarya? Mami ce ta aikoni wajenta."    Hassana ce ta dubeta. "Me za'a ce mata?"   Ummi ta sanarmata, Hassana ta shiga dakin mahaifiyarsu. Ummi ta cigaba da nazarin falon, ta lura dai kusan duk girmansu daya da na Hajiya Binta, Mami ne komai nata ya fita daban mai yiwuwa kuma don itace farkon zama a gidan kafin zuwansu. Hakanan ta kasa bambance falon wanda yafi shan kaya acikinsu, don kowanne falo akwai nasa kyawun na musamman. Tunaninta ya katse bayan fitowar Hassana.   "Tace sai zuwa anjima yanzu kanta yana sarawa ta sha magani ne."   "To, Allah Ya bata lafiya." Daga haka ta mike ta fita.    Mami tuni sun shiga mota, itama shiga tayi sannan ta sanarwa Mami sakon data samu wajen kowannensu bayan ta yiwa sakon Hajiya Binta kwaskwarima inda tace kawai sai zuwa anjima zata taho. Danliti yasa hancin mota ya fita daga harabar gidan.      Sunci sa'a don kuwa ba'a kai ga daura aure ba an dai tafi. Motoci cike makil ne a kofar gidan har babu wajen fakin, dole daga nan waje Danliti ya saukesu sannan yayi gaba don neman wajen ajiye mota.     Gidan a cike yake da yan uwa da abokan arziki na jiki sosai, Ummi banda rarraba ido yanda zata ga Amina babu abinda takeyi, saidai ko kusa bata hangota ba. Ga waje da mutane ba kadan ba ballantana tace zata nemeta. Haka ta hakura ta nemi gefe guda saman tabarma anan tsakar gidan ta zauna tana kalle-kalle. Kwalliya iri-iri, da wadanda suka burgeta da wadanda ko kusa basu burgeta ba take gani, a haka Ihsan ta zo ta wuce, har ta gaji da haduwa sai daukar ido takeyi. Ummi ta bi takalminta da kallo wanda yake da tsini sosai, jinjina kai kawai tayi tunanowa da Tasleem ta 'Yar Bariki wacce ta tsinci Ihsan kwanaki tana labartawa Adnan yanda labarin yake, har take mishi batun takalman da Tasleem ke sanyawa. Toh ita kam bata ga marabar takalmin da Ihsan ta kwatanta  da wannan dake kafarta ba. Da ace itace ai babu abinda zai hanata karyewa a kaita d'ori, sai ikon Allah.     Ta jima sosai anan zaune, kafin ta soma jiyo gud'a sosai yana tashi daga hancin tsoffin dake a wajen.   "An d'aura." Shins furucin da ta ji a bakunansu. Nan kuma ta ga tawagar kawayen Amarya dake a tsakar gidan sun karasa falo suna faman ihu da gud'a. Haka aka cika mak'il a falon Innar su Mami. Ganin da tayi ba zata iya lek'e ba yasa dole ta hakura ta koma da baya ta raku6e jikin bango ta zubamusu ido. A haka tawagar angwaye kuma kusan yan uwan juna gaba dayansu, don da yawansu daga Adamawa suke, yan uwansu ne sai kuma Abokai suma babu laifi.     Bata ci wuyar hangen Ango Haidar ba, ya cakare cikin farar shadda wacce ta sha aiki mai tsada. Sai wani shek'i yakeyi. Hakanan kusan gaba daya tawagarsa fararen kaya ne jikknsu idan ka cire yayyun Ango da kaninsu Faruk, wadanda sukayi ankon shadda ruwan madara. Sunyi kyau har sun gaji da haduwa, Ummi ta karemusu kallo, tabbas 'ya'yan Hajiya Babba abin so ne ga dukkan wata diya macen da take ji da kanta ita din mai aji ce. Idanunta suka fi karkata ga Faruk wanda ta ga kamar an kara matso kyawunshi, a yau yafi koyaushe haduwa domin kuwa fuskarsa yau a sake take hakanan hakoransa a bayyane har gefen kuncinsa na dama ya lotsa. Ya sanya farin tabarau a idonsa, ta sauke ajiyar zuciya, koda ace batasan me ake kira da hadadden namiji ba, to shakka babu akan Faruk ta sani. Cikin sa'a kuwa shima idanunsa suka sauka akanta daidai lokacin da yake gyara zaman agogonsa. Haka kawai ta tsinci yanayinta ya sauya adalilin kallon da yayi mata wanda ta tabbatar haka kwayar idanunsa suke, ba wai da gayya ya yi ba. Ga mamakinta fuskarsa bata sauya  daga murmushin da yakeyi ba duk kuwa da cewar sun hada ido da shi, ta numfasa ta kauda kanta har suka shige zuwa Falo wajen iyayensu.     DAN ADAM   @RUFAIDA OMAR       18    Babu jimawa sosai Amarya ta iso filin da Angonta. Baki bud'e Ummi ta dubi Amina, alokacin wuri ya hargitse, k'arar kid'a ya yawaita da ihun mutane da masu daukar hoto. Ta so ta tambayi Amina daman namijin na zuwa kamu? Saidai babu damar hakan sakamakon hayaniyar da tayi yawa awajen, sunyi kyau matuk'a. Gaba dayansu fararen kaya suka sanya, Haidar cikin farar shadda, yayinda itama Intisar ta had'e cikin shadda dinkin doguwar rigar da ta sha aiki. Su Ihsan da sauran kawayen Intisar suna take musu baya, hakanan shima ango, abokansa na Abuja da na nan Kano kalilan cikinsu sun samu halara, yayinda wasu suka barwa gobe daurin aure. Ba anko sukayi ba, saidai shadda brown kowannensu ya saka, na wani yafi na wani turuwa.     Sunyi kyau kwarai, sai kirari ake yiwa Ango da Amaryarsa har suka isa mazauninsu. Duk raba idanun Ummi bata ga yayyun Haidar ba da kuma Faruk. Har akayi nisa da sha'anin, mata ne kawai da daidaikun matasan wajen wadanda dukkansu yan uwansu ne na Adamawa sai kuma yan uwan mahaifin Haidar Danzaki da ma'aikata.     Sun jima sosai a wajen, an ci an sha, har saida aka kusan tashi sannan ta hangi mota ta faka daga can gefen na amarya da ango. Su biyar ne suka fito daga motar, Yaya Ridwan ne sai wasu wadanda suka fi kama da abokansa, a hannunsa kuwa, wata kyakkyawar yarinya ce wacce bata fi shekaru uku ba tana bacci saman kafad'arsa. Har aka tashi daga wajen babu Faruk da Babban Yaya.       Duk da irin gajiyar da Ummi ta kwaso, wannan bai hanata watsawa jikinta ruwa ba kafin ta chanja sutura ta kwanta.                       ☆☆☆   Washegari ya kama ranar da za'a daura aure da kuma yini. Tun safe da mutanen dakin Mami suka farka, babu wanda ya koma bacci. Daga Maigidan har sauran yaransa maza, shirye-shiryen karyawa sukeyi su wuce d'aurin aure, yayinda Mami itama ke shirin tafiya gidan biki. Ummi kuwa, ayyukanta ta shiga yi cikin sauri-sauri bisa umarnin Mami, don kuwa a son Mami, tafiso tana can a daura aure maimakon ace bata isa ba. Itama Ramma sanin da tayi na cewar Mami da wuri zata fita ne, yasa ta shiryawa da wuri, bata da wani aiki a kanta mai yawa kasancewar yaranta sun je k'auye. Wannan karon dai Ummi ta ji maganar Amina, don kuwa ta shafe fuskarta da hoda sannan ta sanya jan baki kalar ja sai kwalli data zizara a idonta. Ita kanta tasan tayi kyau, irin kyawun da bata ta6a ganin ta yishi ba, ko don ba kwalliyar takeyi ba?    Ankon bikin da Mami tayi musu ne a jikinta, ya zauna d'abas kamar a jikinta aka d'inkashi, ya fito da kyakkyawar surarta wanda ita kanta batasan tana da diri mai kyau ba kamar haka. Har ta dauki mayafi ta yafa sai kuma ta ga sam ba zata iya ba, hakan yasa ta janyo farin hijabinta wanda ya hau sosai da atamfarta mai adon fari da koren fulawoyi. Kiran da Mami ta kwalamata ne yasa ta amsawa da sauri don bata da masaniyar cewa Mamin ta shigo falon domin itace a fadar Alhajinsu.    "Masha Allah." Shine furucin da Ummi tayi a ranta, duk iyakar yanda take ganin ta fito tayi kyau, sai ta raina shigarta ganin shigar Mami, ba irin ankonta bane a jikinta. Wani tsadadden  leshi ne ruwan madara mai duwatsu dinkin doguwar riga da zani ta sanya, anyi aiki a gaban rigar leshin wajen kirji, banda kamshi babu abinda kakeji yana tashi a falon. Hannunta rike da jaka da mayafinta. Ta dubi Ummi duban tsaf kafin cikin sakin fuska tace. "Ashe dai kin iya kwalliya." Abin  ya bawa Ummi mamaki, kodayake dai tasan yau Mami cikin farinciki take. Ramma dariya tayi kawai, itama tayi tsaf da ita tana rike da karamar jaka na kaya wacce ta tabbatar na Mami ne.    "Shiga ki cewa su Hajiya Binta idan sun shirya su fito mu wuce."   "Toh." Sannan ta kama hanya da mamakin wannan irin iko na iyayen gida irin Mami, wato bata damu da ta sanarmusu su shirya ba tun farko saida ta tashi tafiya. Sashen Hajiya Binta ta soma zuwa, a zaune ta sameta tana latse-latsen waya ko wanka batayi ba. Ciki-ciki ta amsa sallamar Ummi, gabanta na dukan tara-tara, ta durkusa ta shaida mata sak'on Mami. Kamar ba zata ce komai ba saidai ta dubeta a wulakance har saida ta ji ta muzanta.      DAN ADAM @RUFAIDA OMAR            20      Ta sauke ajiyar zuciya, gami da zame jiki ta durkusa a wajen. Yau Faruk ne yayi mata murmushi? Sai tace tun zuwansu bata ta6a ganinsa cikin fara'a haka ba. Mai yiwuwa saboda farincikin bikin dan uwansa ne. Jin da tayi ana ihu da shewa daga falon ne yasa ta saurin mikewa itama ta samu dama dakyar tana lek'e. Turare ta gani wata tsohuwa cikin wadanda suka zo daga Adamawa tana ta fesawa Ango da Amarya. Masu hoto suna faman yi, Faruk na daga hannun kujera zaune agefen wata mace da bata fi shekaru ashirin da bakwai ba, wacce itama cikin bak'in Adamawa take. Sai hira sukeyi suna dariya. Sunyi kama kwarai, kana gani ko ba'a fada ba kasan jini d'aya suke. Haka dai aka gama hotuna, Ango Haidar da tawagarsa suka fita. Wannan karon banda yayyun Haidar da Faruk, su kam zama sukayi ana gaisawa da hira da 'yan uwa. Tana ji anata yiwa Faruk tsiya akan shima ya dace yayi aure, abin banda dariya babu abinda yake ba shi, domin shi dai har kawowa wannan lokacin bai ga matar da ta kwanta mishi a rai ba har yakejin cewar zai iya aurenta. Duk cikin masu nuna masa kauna da so, duk cikin masu yi kishi tallar jikkunansu batare da sun buk'aci ko sisinsa ba, babu wacce ya ta6a yiwa kallon rahma. Asalima wannan d'abi'ar gaba daya haushi take ba shi wai ace mace ke tallatawa namiji kanta, yana daukar hakan a matsayin rashin aji da sanin darajar kai.     Dakyar ya samu ya silale ya fito daga falon, Ummi ta bi bayansa da kallo sannan ta maida hankali ga tsoffin dake faman shige da fice suna rabon abinci.    "Ummi." Ta ji muryar Amina a kanta. Wani sanyi ya mamayeta, ko babu komai zata samu abokiyar hira. Ta zaro ido tana murmushi.   "Anti, kinga kuwa yanda kikayi kyau? Masha Allah." Ta harareta kadan   "Lallai ma Ummin nan, wallahi ban kaiki ba, kinga yanda kikayi kyau kuwa yau?"    Ummi ta girgiza kai.    "Ban kaiki ba Anti." Amina ta dara gami da jan hannunta.   "Taso mu zagaya baya, tun dazu ai ina can."    Ummi ta mike suka zagaya. Babban fili ne mai shuke-shuke, nan dinma akwai mutane saidai ba kamar cikin gidan ba, kusan ma yanmata sunfi yawa anan. K'asan wata bishiya suka zauna asaman kujeru inda wasu yara biyu da Mace rike da yarinya wacce bata fi watanni uku ba suke zaune. Ummi ta hango kamannin matar sosai da Amina, hakan yasa ta gaisheta, cikin sakin fuska itama ta amsa. Amina ta dubi yaran.     "Ahmad, ja  Kulsum ku tafi wasa Antinku ta zauna."   Ba musu yaron ya amsa sannan ya mike suka bar wurin, daman sun k'agu su tafi wasansu amma ta hanasu da cewar sai sun ci abinci.     Bayan sun zauna Amina ta kalli 'yar uwarta wacce daga ita sai ita a haihuwa.    "Anti Hauwa, wannan itace Ummi da nake baki labarinta. Ummi wannan itace yayata Anti Hauwa, daga ita sai ni a wajen Innarmu. Babbar yayarmu Anti Fiddausi tana Katsina, acan take aure. Yaranta biyu, da Kulsum da kuma wannan bebin, Anisa. Ahmad shine auta wajen Innarmu."   Bayan ta kai aya, Anti Hauwa ta sanya dariya.   "Toh 'yar jarida, oh Amina." Ta karashe tana kama ha6a, abin sai ya bawa Ummi da Amina dariya.    Anti Hauwa ta dubi Ummi fara'arta ta k'aru don kuwa babu abinda Amina ta 6oyemata dangane da Ummi.   "Sannu Ummi, fatan kina lafiya?" Ummi ta gyada kai gami da sakin kyakkyawan murmushinta.    "Lafiya kalau Anti. Ya wajen su Inna?"   Abin ya yiwa Anti Hauwa da Amina dadi.   "Inna tana lafiya, taso ta zo amma matar kaninta bata ji dadi ba, ta je dubota. Watakil daga can tayo nan."   Ta gyada kai gami da yi mata fatan samun lafiya.  Nan kuma hira sosai ta 6arke tsakaninsu. Anti Hauwa da Amina suka gangaro kan batun Saurayin Aminan, Bello wanda ya matsa akan shi zai turo magabatansa. Anti Hauwa ta bata shawara akan ta sanarwa Inna idan yaso sai a had'ashi da wani ya rakashi har can Nijar su gaisa da yan uwan mahaifinsu.    Haka suka tsayar da shawara.   Sun wuni tare, Anti Hauwa sai bayan la'asar ta bar gidan, Hajiya Mama harda bata kudi tayi na mota. Dakyar ta kar6a don mutunci da karamci irin na Hajiya Mama har yana so yayi yawa, mace ce da babu ruwanta. Harda kayan rabo ta had'a ta bata, ta sanya aka yiwa Inna (takeaway) na abincin biki tace ta kai mata domin ba wani nisa ne tsakanin gidansu Inna da gidan Anti Hauwa ba. Ta kar6a da godiya.    Tafe suke gaba dayansu da Anti Hauwa da Ummi da Amina, wadanda suka yo mata rakiya don ta samu abin hawa, kasancewar babu laifi akwai 'yar tazara tsakanin gidan da babban titi. Ummi na rike da Anisa wacce ke faman kalle-kalle idanunta tarr a bud'e. Yarinyar ta shiga ranta, haka kawai ta ji tana kaunarta ko don bata ta6a ganinta rik'e da yarinya k'arama haka bane? Oho.     A farfajiyar gidan, samari ne da d'aid'aikun yanmata suna hira, daga ganinsu kaga yan uwan juna. Suka wucesu suka fita.     Suna tafe suna hira a haka har suka iso titi, bayan sun samarmata d'an sahu, ta shiga sukayi sallama. Ta dubi Ummi da murmushi mai bayyana hakora a saman fuskarta.   "Toh Ummi, sai na ganki a gidana wataran ko?"   Ummi ta amsa da toh tana maida martanin murmushin. Suka juya tare da Amina suka kama hanyar komawa. A hanyar ma hira sukeyi, Amina na yi mata korafi akan ita ko dan fita unguwa bata tambayar Mami ne? Ummi ta ta6a baki kadan.   "To Anti wa nake da shi a garinnan?"   "Kina da mu, wataran ki tambayeta kizo na kaiki wajen Innarmu ku gaisa."   Murmushi Ummi tayi wanda yayi daidai da giftawar wata farar honda mai bakin gilasai ta gabansu.   "Wannan kamar motar gidan su Alhaji." Cewar Amina kenan. Ummi da batasani ba ta bi motar da kallo kawai wacce ta koma tafiya sannu-sannu tamkar matuk'in baya so. Kafin daga bisani ya fisgi motar ya k'ara gudu.    Ai kuwa kamar yanda Amina ta fad'a haka dinne, don suna isa kofar gidan suka iske motar a fake, na cikin motar baikai ga fitowa ba saidai kafarsa d'aya da ya fiddo waje. Ta madubin hannun kofar, Ummi ta hangeshi. Kansa a jingine jikin kujera yana amsa waya. Akayi katari suka had'a ido, gani tayi ya yafito ta da hannu. Abin ya bata tsoro, gabanta ya hau dukan tara-tara. Tayi saurin dauke idanunta don bata gaskata hakan ba.  Har zasu shige ciki ya danna hon.  Wannan ya sanyasu dakatawa.    "Da ku ake." Cewar Maigadi. Amina ta dubi motar, saidai bata hangi ko wanene ba sakamakon duhun gilashin. Suka zagaya suka isa ta mazaunin direba, idanunsa akansu, suka durkusa a ladabce suka gaisheshi. Yaya Faruk ya dago kanshi ya dubesu da idanunsa masu tafiya da dukkan wata diya mace mai lafiya da zata kalleshi. Ya gyad'a kai kafin ya maida dubansa cikin motar, hannu yasa ya janyo leda bak'a babba ya mik'awa Ummi.   "Ki mik'awa Hajiyata." Ta sanya hannunta dake faman rawa don gaba daya wani kwarjini yayi gareta, ta kar6i ledar wanda bisa kuskure hannayensu suka gogi juna har ta gogi tattausan gashin dake kwance a hannunsa, a gigice ta dauke hannunta had'i da kar6ar ledar tana mai amsawa da toh wanda bai fito sarari ba saidai kawai le66anta da ya nuna alamun hakan. Baice uffan ba har suka fice ya bisu da kallo, ya lura yarinyar kamar a tsorace take da shi. Ya dan ta6e baki cike da mamaki, mamakin bai wuce na ganin yara kyawawa haka ba ace wai suna aikatau ba karatu ba, tabbas ya tausayamusu. Ya kuma raina iyayensu wadanda tunaninsa yafi ba shi cewar kwadayin abin duniya ne kawai yasa suke sakin yaransu sakaka suna yawon gidajen mutane don bauta da neman kudi wanda duk yawan abinda zasu samu bazai haura dubu goma ba, aganinsa wannan cutar da rayuwarsu ce kawai. Ya lumshe ido, ya jima a haka kafin ya maida kafafunsa ciki ya rufe kofar gami da yin ribas yabar unguwar.                DAN ADAM   @RUFAIDA OMAR   21    Acan kuwa Ummi kasa shiga ciki tayi haka kawai bata son shiga cikin mutanen gidan, tana jin nauyinsu. Amina ce ta kar6a ta mik'awa Hajiya Babba sannan suka koma inda suke. Sai misalin karfe bakwai kowa ya soma shirin tafiya wajen (Party) wanda Ango ya shirya na musamman da iyayensu da yanmata da samari. Abin har ya bawa  Ummi mamaki, aganinta wannan kawai rashin sanin abinda za'ayi da kudin ne, ko kuma dai kudin ne suka yawaita garesu. Tana gani Amina tayi mata sallama suka wuce sakamakon yara da zata kula dasu a gida kafin dawowar Hajiya Maman. Ummi ta dubeta.   "Nima na tabbatar yanzu zamu wuce ko don Ramma."   "Wace Ramma? Ramma ai ta tafi gida tun dazu tare da su Hajiyar Iklima. Baki ga su Iklima sunzo dazu ba?"   Ummi ta zaro ido. "Aa banma gansu ba wallahi, na tabbatar Mami ta manta ne da ta had'a tafiyata da su. Toh yanzu wa zan bi?" Amina ta jinjina kai. "Mamin ce zata barki ki tafi da kishiyoyinta? Wasa kike ma. Na..."   "Ummi, kizo inji Mami." Suka tsinci muryar Fahad wanda yayi sanadin katse Amina daga maganarta. Ta dubeta. "To saida safe, nasan kuma mu da kara haduwa ba yanzu ba." Sukayi sallama Amina ta wuce.    Ummi tana d'ari-d'ari haka ta daure ta shiga falon, Mami na daga zaune wata tana d'aura mata d'ankwali. Ta gaida mutanen falon sannan ta koma gefen Mami.    "Gani Mami." Mami ta dan dubeta. "Ramma ta riga ta tafi, nikuma da wuya idan zan dawo ta nan gaskiya don gaba d'aya zamu tafi can wajen party, ki zauna a inda zan ganki idan mu  fito."   "Toh Mami."   Daga haka tayi gaba, tana ji wata tana zolayar Mami wai da alama ita bata iya rayuwa saida 'yar aiki, har sauran suna dariya. Suna tsokanarta wai sai kace itace autar innartasu.     Ummi ba haka taso ba, don alal hakika ita zuwa wajen wani party ko waje mai hayaniya baya burgeta, da ace Mami zata barta anan da ta zauna har zuwa lokacin da zasu ci su cinye su dawo su tafi. Ta dubi jikjnta bayan wucewar wasu yanmata da suka dauki ado cikin wani leshi yellow da nadin kai ja, ta yaya ma zata shiga taron jama'a da kayan nan? Ta tabbatar ita kadai zata bambanta acikinsu. Ta langa6ar da kanta, kodayake daman ita din ba kowa bace face 'yar aiki. Bata da wani daraja, babu wani wanda zai ra6eta da sunan kauna ta jini ta yan uwantaka, shiyasa take matukar kaunar Amina, ta tabbatar su Amina  suna kaunarta saidai bata da sa'ar 'yan uwa. Batasan halin da suke ciki ba a yanzu, da ace ma zatasan dangin mahaifiyarta, lallai da ta kai kanta garesu komin nisan dake tsakaninsu. Ta sauke ajiyar zuciya kafin kuma da saurinta ta share hawayen da suka zubomata.   Ko mintuna biyar batayi ba awajen, Mami ta aiko kiranta, kaya ta dunga kwasa tana kaiwa boot din motarsu, sannan ta zauna a motar tare da Fahad da wasu iyaye matan, Mami na fitowa suka wuce wajen party.       Tun a farfajiyar otel din Ummi tayi bala'in raina kanta. Ta sauke ajiyar zuciya gami da sakin baki galala tana kallon yanda wajen ya k'ayatu, anyiwa wajen adon fulawoyi wadanda sai buso sanyi sukeyi, hakanan kuma wajen sai kamshi yakeyi. Daga can ciki kana jiyo tashin kid'a. Wadanda basu shiga ba suna tsaitsaye a farfajiyar wajen. Haka suka dunguma zuwa ciki. Sanyi ba bak'on Ummi bane don tun bata saba shan sa ba a falon Mami, har ya zamana yanzu ta saba. Wajen kowa ya dauki kwalliya. Matasa masu ji da ilimi da gayu sai kuma iyaye wadanda kallo daya zakayi musu ka tabbatar cewa kud'i sun riga sun gama jik'asu. Zugwui-zugwui take bin bayansu Mami, gaba dayanta a d'arare take, gani takeyi kamar kowa awajen ita ya zubawa ido. Idanunta suka cika da kwalla, bata saba da irin haka ba. Tunaninta ya katse sadda ta ji an damki hannunta. Ta juya da sauri, Ihsan ta gani ta ci ado har ta gaji da haduwa, saidai fuskarta a murtuke. Bata ce mata uffan ba ta soma janta, gaban Ummi na faduwa haka ta bi bayanta har zuwa d'an (Corridor) na shiga dakin taron.    "Uban wa yace ki shigo? Kalleki kiganki, typical 'yar kauye, wallahi kika yi kuskuren shigowa wajennan sai na miki wulakancin da baki ta6a zato da tsammani ba. Shegiya kawai marar galihu!" Daga haka ta ja tsaki tayi gaba ganin mutane sun nufo hanyar shigowa. Ummi kuka ya taho mata, da saurinta ta juya zata fita, ta bawa mutanen hanya suka wuce ta bi ta gefe ta fita da gudu-gudu. Kai tsaye ta wuce bayan motoci inda babu  mai ganinta ta durkushe ta soma kuka mai shiga rai. Kuka sosai takeyi, lallai ta k'ara gaskata cewar halayen DAN ADAM sun bambanta. Ta gaskata cewar ita din ba wata bace face marar galihun kamar yanda Ihsan ta jaddada mata. Kaiconta! Kaicon rayuwarta! Ace mahaifinka ya bude baki yayi furucin cewa ko bangon duniya za'a kaika, ba matsalarsa bace, baka da wani makusanci mai kaunarka, daga dangin mahaifin harma da shi kansa mahaifin. Takan rasa abinda ta yiwa mutane, wai meyasa dangin mahaifiyarta bazasu nemeta ba? Ta tabbatar koda duniya ta k'i ta, su bazasu ta6a gudunta ba, ta tabbatar zasu bambanta da sauran 'yan adam din da ta sani kuma ta rayu da su. Tana fatan su zamto irin Amina da su Anti Hauwa, tana fatan su zamto masu nunamata so da kauna ta gaskiya.     DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 22    K'arar rufe motar da ta ji ne yasa ta saurin mik'ewa a firgice. Ido hud'u sukayi, kallonta yake cike da tsantsar mamaki, yayinda ita kuwa take mishi kallo tamkar wacce ta ga wani dodo. Gaba d'aya tsoro takeji kada ya bud'emata wuta akan me takeyi anan. Ta sunkuyar da kanta tana duban motar, sai lokacin ta lura cewa motar da suka ganshi dazu a ciki ce.    Kamar yayi mata magana, saidai ya fasa ya juya ya soma tafiya. Ta mike ta bar wajen ta soma tafiya kai tsaye ta nufi k'ofar fita daga Otel din. Kamar ance ya juyo, ya ganta.     "Ke!" Ya fad'a a sannu yanda yasan zata ji don ba wani nisa tayi ba. Ta juya gabanta na fad'uwa. Sai lokacin ta lura da shigarsa, ya had'u karshen haduwa, a yanzun yana sanye da shadda ruwan kasa mai duhu wacce aka yiwa dinkin da ya zauna daidai a jikinsa. Takalmi da hular da ya dora ma su kansu abin a kalla a k'ara kalla ne. A haka har ta karasa wajensa ta durkusa. Ya bata umarnin ta mik'e. Bayan ta mike ya kare mata kallo sannan ya jefota da tambaya.   "Ina zaki?"   Ta soma rawar murya.   "Gi..da." Ya yamutse fuska.   "Ke kika kawo kanki?"   Ta girgiza kai.   "To shiga ciki."   Tunanowa da maganar Ihsan yasa ta soma zubar hawaye ta dubeshi da jajayen idanunta wadanda kuka ya maidasu hakan, sai lokacin shima ya lura da su.     "Kayi hakuri Yalla6ai, bazan iya shiga ba."   Shiru ya biyo baya ayayinda ya kafeta da ido yana kallon fuskarta. Haka kawai sai ya ja guntun tsaki.   "Akan wane dalili?" "Ih..ih.san tace kada na shiga zata wulakantani."    Ya ji wani abu a ransa, sai kuma ya cije le66ansa na kasa.   "Ko menene ku kuke jawowa rayuwarku, da ace kun hakura da yanayin rayuwa, kun godewa kad'an din da kuke samu a gidajenku, da babu abinda zaisa kuzo ana wulakantaku ana baku tamkar wasu karnuka."   Batasan sadda ta cigaba da 6ul6ulo da ruwan hawaye ba. Ta so tayi shiru ta barwa zuciyarta amsa, saidsi ta tsinci kanta da kasa aikata hakan.    "Ka gafarceni Yalla6ai, saidai akwai lokutan da ba'ason ran mutum yajr aikata abinda ya aikata ba. Akwai tilastawar rayuwa, wani ba shi da yanda zaiyi ne, sai yaga da yaje ya aikata abin turr gwara ya gwammace ya rufawa iyayensa da kansa asiri ta hanyar nema ta halal. Wani kuwa, rashin gata da rashin samun kulawar yan uwa ke sanyashi tsintar kai a halin da yake ciki. Kowane bawa da yanda Allah Ya tsaro rayuwarsa, ba mu muka za6awa kanmu wannan rayuwar ba. Akwai KADDARA."   Daga haka ta juya da sauri-sauri ta bar wajen gami da nufar get, batayi wata-wata ba ta fice daga wajen batare da tasan inda ta nufa ba, burinta kawai tabar wajen ko ranta zaiyi sanyi....!           Ta dubi sararin samaniya, hasken farin wata ya taimaka kwarai wajen k'ara haskaka unguwar, hakanan kuma akwai hasken fitili domkn unguwa ce ta manya. Ta numfasa ta soma bin hanyar da taga Danliti ya biyo da su dazun. Tafiya kawai takeyi batare da tasan takamaiman inda zata nufa ba bayan nan, hakazalika batajin ko son ta koma wajen walimar. Ta gwammace idan ma saceta ayi muddin za'ayi nasarar rabata da wajen nan. Ita kam ta tsani cin zarfi da disgi. Tayi nisa amma ba sosai ba, ta ga mota a gefenta tana tafiya sannu-sannu, wannan baisa ta tsaya ba ballantana kuma ta waigo. Ta ji k'arar hon da k'arfi, ta runtse ido tana mai cigaba da tafiya kai ka rantse Ummi tsabar yanga ce takeyi, ga wanda ya santa kuwa yasan tafiyarta ce hakan, saidai duk da hakan na yau yafi na kullum don tana taku ne jikinta babu laka, gaba daya a sanyaye yake, zuciyarta banda bugu da sauri-sauri babu aikin da takeyi.     "Ummi." Taji faduwar gaba jin muryar Yaya Faruk. Ta waigo da sauri ta dubi motar, kasa jure kallon kwayar idanunsa tayi masu kyau da fisgar hankali tayi gefe da idanunta batare da ta cigaba da tafiya ba.     "Shigo."   Ta daure ta kara dubansa tana mai share hawayen da suka zubomata, girgiza kai tayi.   "Kayi hakuri Yaya Faruk, bazan iya komawa..."   "Gida zan kaiki." Ya katseta da fad'in hakan. Ta danyi jim, tana tsoron kada Hajiya tayi fad'a saidai kuma ta gwammace fad'an Hajiya da dai ta k'ara komawa wajen da ba'a dauketa a bakin komai ba face wulakantacciya. Jiki babu kwari ta sanya hannu zata bud'e gidan baya, ya rigata bud'e na mazaunin gefensa.    "Nan za ki shigo." Gabanta ya fad'i. Ta kasa cewa komai duk kuwa da cewar ta raina aji, matsayi da kuma girmanta ace wai itace zaune agefen matashin da ya had'a dukkan wadannan abinda takejin ita din bata da shi, abin kamar dai a mafarki. Da bismillah a bakinta ta shiga ta rufe a sannu, ajiyar zuciya ta saki jin wani azababben kamshi ga kuma sanyin Ac da ya ratsa jikinta. Ya soma tuk'i cikin gwanancewa bayan ya maida gilas ya rufe, ya k'ara k'arfin Ac kad'an. Saida suka bar layin gaba daya sannan ya rage gudun da yakeyi ya soma magana tamkar baya so, magana mai cike da nutsuwa da kasaita. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   23    "Bansan da haka ba, idan ma nasani toh watakila zuciyata ce wacce ke jin tsananin tausayi yaran da kuma jin haushin iyaye masu barin yaransu yawan aikatau, ya sanyani kasa nutsuwa nayi tunani mai kyau akan haka. Akan abinda na fad'a, ina neman afuwa, kiyi hakuri kinji?"    Ya karshe yana k'ara k'ank'an da muryarsa tamkar mai rad'a. Wannan yasa zuciyar Ummi cigaba da harbawa da sauri-sauri. 'Nayi hakuri fa yace?' Ta tambayi zuciyarta, ta lumshe ido ta bud'esu, ashe daman masu kudi sukan yi laifi kuma su bawa 'yan aikinsu hakuri? Ikon Allah.     "Kinji?" Ya k'ara furtawa cikin kara kankanta murya, sai kuma alokacin ya dubeta. Gani yayi fuskarta ta yi fayau, hakanan idanunta sun d'an kumbura adalilin kukan da ta ci. Haka kawai ta ga ya gangara gefen titi ya tsaya. Tayi duba da wajen, wajejan gidan gwamna ne na garin Kano, abinda yasa ta rike hakan ma bai wuce adalilin Fahad da ta ta6a ji ya fad'a ba.      Ta dubeshi kad'an, shima ita ya fuskanto. Ta kauda kai tayi narai-narai da fuska tamkar mai shirin yin wani kukan.   "Na hakura, ni daman banyi fushi ba. Ni wace da zanyi fushi da.."   "Ni d'in wanene da na fi karfin ayi fushi da shi?"   Ya katseta ta hanyar jefomata tambayarnan. Tayi kasa da kanta batare da tace uffan ba.     "Ni ba kowa bane face DAN ADAM, kuma duk dan Adam ajizi ne, yakan kuskuro, wani da saninsa wani kuma baisan ma kuskuren bane. A rayuwa, bani da raayin shiga lamuran da bai kasance matsalata ba, ban fiye damuwa da shiga rayuwar mutane  har ma na takura musu ba ok? Abinda ya kaini har nayi miki batun bai wuce na fusata..."   Sai kuma yayi shiru bai k'arasa ba.   "Kiyi hakuri." Shine abinda ya k'ara furtawa. Cikin rawar murya Ummi ta share fuskarta wanda zuwa yanzun batasan dalilin kukannata ba, ta dangana da tuna mahaifiyarta da tayi wacce kokusa bata ta6a jin dumin jikinta ba.    "Ya wuce Yalla6ai, don Allah ka daina bani hakuri."   Ya zubawa fuskarta ido kafin ya saki murmushi mai 6oyayyar fassara.    "Thank you." Daga haka ya soma tafiya, tana jin wayarsa na faman ruri. Duk bai dauka ba, sai ana uku ta ga ya dauka. Haidar ne, hakuri ya shiga ba shi ya sanarmishi wani uzuri ne ya hanashi karasowa da wuri amma yana nan tafe. Daga haka sukayi sallama.    Ummi tayi lamo tana tunane-tunanenta, ko a mafarki idan akace mata  Faruk nada mutunci har haka, toh zata iya musawa idan tayi la'akari da yanayinsa koyaushe cikin daure fuska, sa'a ce ke sanyawa kaga fuskarsa a sake kamar yanda sa'ar ce ta ci ta ganta dazun dauke da murmushi.    "Mene sunanki na ainahi?"   Ya watsomata tambayar batare da ya maida hankali ga dubanta ba.   "Hasiya." Ta fad'a a tsanake kamar ta karawa sunan dadi domin kuwa babu wacce ta fad'omata a rai alokacin sai mahaifiyarta wacce sunanta ne ta ci.   "Nice name, suna kika ci ne?"   Ta gyada kai. "Sunan mamana ce."   Da mamaki ya dubeta. "Mamanki tana nan?" Ummi idanunta suka k'ara ciko da ruwan hawaye, ta k'ara narkar da murya tana son yin kuka. "A'a ta rasu wajen haihuwata." Maganar ta dakeshi, ya daure ya hadiye abinda ya ji na tausayinta, saidai duk da hakan saida muryarsa ta kasa 6oyewa.   "Allah Yayi rahma agareta." Ta amsa da amin cikin zuciyarta. Duk da wani 6angare na zuciyarsa tana so tasan fin haka game da ita, saidai bai ga wata hujja da zai kare kansa ba idan ta nemi sanin dalilin tambayar duk da baya zaton haka din.     Har suka isa babu wanda ya k'ara cewa uffan, hakazalika, kowanne da irin tunanin da yake. A zahiri Ummi ta fi karkata ne ga tuna rayuwarta, babban abin tambayar da bata da amsa shine inda zata ga dangin mahaifiyarta, a 6angare guda kuwa, tana mamakin Faruk da halinsa wanda batasani ba. Bata manta gargadin Ihsan gareta a kwanakin baya.   'Mutum dai ya tsaya iyakar matsayinsa, ko kusa kada yayi tunanin zai iya da Babban Goro, duk cikinsu babu sa'an aurenki, don haka ki maida maitarki, kurwar kaf dinsu, ta fi karfinki.'   Wani murmushi mai ciwo ya su6uce mata daidai kuma lokacin da Faruk ya kallota, kawai sai ya tsinci zuciyarsa cikin jin sanyi, ko babu komai bazata fita motarsa da fushinsa ba.    Tsayuwar da ta ji yayi ne yasa ta fahimtar sun iso don gaba daya ta luluk'a tunanin dabi'un Ihsan wanda ya sha bamban da na sauran yaran Mami.  Suka dubi juna ido cikin ido, gaba daya sun ji wani iri wanda tsakaninsu babu wanda ya bada tunani na daban.    "Saida safe."  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    24   Ya sanya hannu ta 6angarensa ya ciremata (lock). Batare da ta amince sun kara hada idanu ba ta amsa.   "Nagode, Allah Ya tsare hanya. Don Allah ka sanarwa da Mami na taho gida kada ranta ya 6aci, idan da hali kada ka nuna kai ka kawoni don Allah."   Yayi shiru yana mamakin dalilinta na fadin hakan,  sai kuma ya ta6e baki ya daga kafada kadan.   "Nifa ban iya karya ba, ba kuma zan fara saboda ke ba ok? Idan ta tambaya zan fadamata."   Ya karashe da murmushi yana dubanta, ta kauda kanta. Banda toh babu abinda tace ta sauka. Ta rufe kofar batare da ta kara kalla ba sakamakon duhun gilashin.   Ya bita da kallo har ta shige ciki, ya numfasa. Mace kam har mace Ummi ta kai. Shine kawai abinda ya ayyana a ransa daga haka ya ja motarsa yabar wajen a miliyan. Mintuna goma bai cika ba ya isa ga wajen party. Ya kuwa iske Mami na nemanta, nan ya sanarmata yanda akayi, yayi kokarin cewa a hanya ya ganta tana kuka tana tafiya ya taimakamata baisan abinda ya faru gareta ba. Mami tayi mamaki, karshe ta yanke da zarar sun koma zata ji ko menene.   "Mutuminki gashican ya iso."   Da sauri Iklima ta kai dubanta ga inda kawarta Hassana take mata nuni, wani wawan ajiyar zuciya ta sauke har tana hamdala a fili. Abin ya bawa Hassana dariya, kawai gani tayi Iklima ta ja hannunta.   "Muje ki rakani na gaisheshi."   Hassana ta so k'in zuwa don gudun kada ya disgata, saidai dole hakanan ta bi bayanta suka nufi inda yake a tsaye bayan amarya da ango suna  Haidar ya dubeshi yana mai kai bakinsa saitin kunnensa.   "Tsaya muyi hoto mana." Yana murmushi yayi kokarin zillewa, abin saima ya bawa Haidar domin kuwa yafi kowa sanin Faruk bai fiyeson hoto ba. Ya dank'eshi, a hakan ma sunsha hotuna wajen jama'a masu wayoyi, dakyar ya tsaya yana duban Haidar fuskarsa dauke da wani hadadden murmushi, a haka aka daukesu.    Cikin masu daukar hoton, har da Iklima wacce gaba daya ta gama narkewa cikin so da kaunar Faruk wanda ya gama tafiya da ruhinta.  Bata bi ta kan Hassana ba ta mara mishi baya da sauri tun baikai ga k'arasawa wajen yan uwansa ba wadanda su yake yiwa kallon abokai domin Faruk ba shi da babban amini ke6antacce da za'a kira nasa akoyaushe. Bazai rasa abokan ba, duk wata shawara acewarsa yayyunsa sun isheshi.   "Ina wuni Yaya Faruk." Muryar da ya tsinkaya kenan daga gefensa. Ya kai dubansa gareta, take kuma sai ya tsuke fuska tamkar ba shine ke murmushi ba yanzun. Kansa kawai ya gyada sannan yayi gaba. Da sauri ta juya itama tun baikai ga bata kunya ba. Tun kafin ta kai ga Hassana, take watsa mata harara har ta dangana da mazauninta. Alokacin ne ta samu damar yi mata magana.   "Ai ga irinta, saida nace kada kije amma kika k'i saurarona, yanzun da ya jefeki da kallon banza ai kinji dadi."   Tana maganar a fusace. Iklima idanunta akan Faruk wanda ke hira abinsa hankali kwance, ta murmusa.   "Yasan ya had'u ne shiyasa yake shan kamshi ga yanmata. Wallahi ina sonsa fa."   Hassana ta ta6e baki. "Shi kuma baisan da zamanki ba."   Sai alokacin ta dubeta tana harara. "Wai me kikeson ki cemin? Kin manta  alak'armu da shi ne?"   "Naga Ihsan ma k'arewar alak'a da shi ai." Hassana ta fada gami da jan dogon tsaki sannan ta cigaba da maganarta.   "Shi namiji idan yaga kin fiye zakemishi rainaki zaiyi wallahi, ki kula dakyau leema, kisan dai dabarar da zakiyi ki shawo kansa, amma idan har zaki cigaba da yi mishi irin wannan shishshigin agaban jama'a, toh fa zaki raina kanki."   Iklima tayi shiru tana sauraronta, ga dukkan alamu dai maganganun Hassana yana shigarta. Tayi na'am da shawararta na cewa ta dinga yi mishi ladabi a fili da kuma online.(chatting), a sannu idan suka saba sai tayi kokarin shawo kansa.   Haka aka tashi taron kowa cike da farinciki idan an cire Iklima wacce bataji dadi ko kadan ba na yanda Faruk ya gwatsaleta ba. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR        25      Koda su Mami suka koma gida, ta tuntu6i Ummi akan dalilinta na barin wajen (party), bata 6oyemata yanda sukayi da Ihsan ba, da kukan da Faruk ya ga tana yi ya taimaka ya kawota gida. A take Mami ta nemi Ihsan a waya amma fir ta karyata tace batasan ma da zaman wata Ummi awajen ba. Ranar duka ne kawai Ummi bata ci ba, amman ta sha fad'an Mami sosai, acewarta bazata lamunci a dinga yiwa yaranta karya ba akan abinda bai zama halinsu ba.    Haka Ummi tana ji tana gani aka k'aryatata aka bata laifi, dole ta bawa Mami hakuri sannan ta bi umarninta ta chanjawa Fahad kayan bacci ta nemi makwancinta. Bacci gaba daya gagararta yayi don ta kasa tsaida hawayenta, sai wajen asuba ta samu ya dauketa.         Washegari suka shirya tafiya Abuja kai amarya. Da yawansu ta mota zasu tafi, ciki harda Mami. Hakan yasa da sassafe ta kammala komai, kasancewar kwana daya zasuyi ta amince Ummi ta zauna agidan tare da su Adnan. Ta mascara mata cewa ta rik'e amanarta. Daga haka sukayi sallama, ita da Ramma na binsu da adduar sauka lafiya.     Misalin karfe biyar na yamma, babu kowa a sashen Mami sai Ummi dake kwance a tsakar gida. Fahad da Adnan sun fice yawo, Ihsan kuwa har lokacin bata dawo ba, da alama da ita aka nufi Abuja, Ramma kuwa daman tun tafiyar Mami tana kammala ayyukanta ta bar gidan.    Muryar da ta ji tayi sallama ne yasa babu shiri ta mike zaune a matukar razane. 'Hajiya Binta?' Ta fad'a a ranta cike da mamaki. To mene ya kawota sashen Mami alhalin a baya ba shigowa takeyi ba?    Fuskar Hajiya Binta a sake  ta k'arasa shigowa ciki tana d'an waige-waige.     "A'a Ummi, ba kowa ne sai ke kadai?" Ummi ta russuna cikin ladabi ta amsa mata.   "Eh Hajiya. Ina wuni." Hajiya ta zauna a saman wata kujerar roba cikin karamar murya kamar mai rad'a ta amsa. "Lafiya lau Ummin Hajiya. Sai kyau kike k'arawa Masha Allah."   Murmushi ta dan yi mai kama da yak'e domin ba wani sabo tayi da ita ba, banda munanan kalamai da take watsamata aduk haduwarsu, babu abinda ke shiga tsakaninsu. Maganar Hajiya Binta wacce ta k'ara matsowa dab da ita ya katse tunaninta.   "Ummi ina neman wata alfarma daga gareki, matuk'ar kika amince kika yi yanda na sanyaki, toh ina miki rantsuwa da Allah zakiji dadin rayuwarki. Ina tabbatar miki sai kin samu 'yanci agidannan kamar kowace 'ya matukar kikayi yanda nace."   Ummi ta ji kanta yayi dumm. Ta rasa gane alkiblar da maganganun Hajiya Binta suka dosa. Ta dubeta duba na neman karin bayani. Hajiya Binta ta kara lek'en bayanta, bata ga wani ko wata dake tahowa ba. Ta fiddo wata bak'ar leda daga zaninta ta bud'eshi gami da nunawa Ummi. Ummi ta zaro ido cikin matukar kad'uwa ganin wani abu wanda aka duk'unkule da farin zare mai yawa wanda har ya zamana baka ganin komenene aciki sai zaren da yayi kamar bal.    Ji tayi ta soma gumi cikinta kuwa wani hautsinewa ya yi na ban mamaki.     Hajiya Binta wacce gaba daya ta gama kwadaituwa da samun cikar burinta ta cigaba da magana.   "Wannan kadai zaki ajiye a k'ark'ashin gadon uwardakinki, daga tsakiyar gadon, shikenan kin kammala mini komai. Wallahi Ummi zakiji dadin rayuwa fiye da zatonki. Zaki samu duniya yanda baki ta6a kawowa ba. Za kuma ki jera da yaran gidannan a zuwa makaranta mai tsada, a fannin ci da sha da kuma sutura. Rik'e kiyimin yanda nace."   Ummi na k'ok 'arin magana ta tsaidata ta hanyar damk'a mata abin a hannunta. Ta jefeta da murmushi.   "Zan nemeki gobe." Daga haka ta mik'e sai kuma ta dawo baya. Fuskarta a murtuke ta dubeta, duban da ya k'ara hautsinata.   "Karki soma yunk'urin tonamin asiri, muddin kika soma sai na lahira ya fiki jin dadi. Ki kula." Daga haka ta fice da sauri. A nan kofar shiga ta tarar da aminiyarta ta, Hajiya Luba wacce ke tsayuwar gadi kada wani ya taho ya iskesu.  Tana ganinta cikin rad'a tace. "Angama?" Hajiya Binta tayi dariya. "Ta isa daman ta k'i?"   Sukayi dariya k'asa-k'asa gami da cafkewa sannan suka bar wajen da sauri.   Ummi ta shiga tsaka mai wuyaaa....!         DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    26    Gaba d'aya gigicewa tayi, tayi sauri yarr da kullin a kasa kafin ta cigaba da ambaton Allah a fili. Ita kuwa Hajiya Binta me take nema haka a duniya da har zata iya yiwa wani asiri? Ummi a iyakar tsawon rayuwarta ta tsani mugunta ta tsani mai yinsa.     Ta k'ara kallon kullin cikin zubar hawaye, tunanin kada Adnan ya dawo ya isketa da shi yasa ta mike a gaggauce gami da daukarsa da hannun hagu don kuwa tsoro da kyankyaminsa take. Allah Yayi mata tsari da aikata mummunan aiki irin wannan. Shine addu'ar da take ta nanatawa a ranta.  Kai tsaye ta nufi dakinta da shi ta kulle cikin bak'ar leda da zummar washegari idan zata makaranta ta yarr koda acikin kwata ne.     Bayan ta adana shi inda babu mai gani tunda ba mai shigowa dakinta, ta fito ta zauna jigum, gaba daya a tsorace take. Kuka kam ta sha, a karshe dai tayita addua akan Allah Ya ku6utar da ita daga sharrin Hajiya Binta.    Bayan dawowar su Adnan dole ta saki ranta kada su gane. Ya damkamata karamar robar (ice-cream) da suka siyo, suma suka zauna a falon suna kallo suna shan abinsu hankali kwance. Ita dai sha takeyi amma kokusa kallon baya gabanta, koda ta soma jin dadinsa da zarar ta tuna da Hajiya Binta sai jikinta yayi lakwas. Karshe rufe robar (ice cream) din tayi gami da shigewa daki bayan ta nemi zubomusu abinci sun tabbatar mata sun k'oshi. Daman ta ga alama, kawai dai gudun kada ace tayi laifi ya sanya ta tambaya.    A ranar Ummi dai bata runtsa ba, gani takeyi kamar wani abin zai sameta asanadin kullin da ke a dakinnata. Bata ta6a fatan ace tana da wayar hannu ba sai a wannan dare, da babu abinda zai hana ta sanarwa Antinta ko don ta bata shawarar yanda zatayi.             Washegari Adnan suka fice makaranta, ya tabbatarmata su Mami sai wajen yamma zasu dawo. Hakan yasa suna tafiya ta bude dakin Mami don daman mukullin yana hannun Adnan sai a yanzun ya damk'amata. Ta tsaya cak a tsakar dakin tana tuno da mugun aikin da Hajiya Binta ta sanyata. Tausayin Mami ya mamayeta.   "Baiwar Allah kenan, tana zama da ita da zuciya d'aya, ashe tana da wani mugun kulli dangane da ita." Cewar Ummi a fili don bil hakki tausayin Mami ya gama mamayeta. Haka ta gyaramata ko'ina tsaf ta wanko bandaki ta goge duk inda ya dace sannan ta feshe dakin da turare ta kulle.     Tana shirin soma gyaran falon Mamin ne. Ta tsinci sallamar Hajiya Binta. Gaba daya saida ta ji tsayuwa na neman gagararta. Dakyar ta samu nutsuwa bayan karanta addu'o'i. Ta nufi falon tana mai amsawa cikin dakiya. Wani zun6ulelan hijabi ne ajikinta, fuskarta ya nuna bata jima da tashi daga bacci ba. Ta sanya hannunta a k'ugu, fuskarta a murtuke wanda ya rud'a Ummi saidai tayi iyakar kokari bata bari ta fahimta ba. Da sauri ta durkusa.   "Ina kwana Umma." Batare da ta amsa ba, ta zarce ga abinda ya kawota.   "Kinyi aikin da na sakaki?"   Ummi ta k'ak'alo murmushi. "Fitowata kenan ma daga aikin Umma, nayi yanda kika umarceni."   Wani sanyi ya ratsa zuciyar Hajiya Binta don har ga Allah bata yiwa Ummi kallon mak'aryaciya, dari bisa dari ta yarda da cewar ta aikata.    "Tabbas kin biyani Ummi, kuma muddin Hak'ata ta cimma ruwa, bazan watsamaki k'asa a ido ba. Abu d'aya nake gargadinki akai, ki kiyaye bakinki. Wallahi Ummi kikayi kuskuren tonan asiri saina k'ullamiki mummunan sharri."   Daga haka ta fice da sauri. A can kofar da ta raba sashensu da na Hajiya Madina, sukayi kick6us da Ramma. Ta gaisheta tana cike da mamakin ganinta. Hajiya Binta ta amsa cikin basarwa gami da fad'in.   "Ashe kuma Hajiyar bata dawo ba? Na dauka tana nan na aikomata tallar dogayen riguna."    Ramma ba don ta gamsu da wannan shirgaggiyar ba, ta amsa da.   "Ai Hajiya munyi waya sai zuwa yamma tacemin zasu iso."   "Allah Ya kawosu lafiya."   Daga haka ta wuce da sauri don ta tabbatar da wuya idan karyarta ta samu shiga. Ummi wacce tub jiyo muryar Ramma ta biyo bayanta a guje cikin kad'uwa, ta ji tattaunawarsu. Tayi saurin komawa. Bayan shigowar Ramma ta hau kwalamata kira da k'arfi, a rud'e ta k'araso.     "Baba Ramma ashe kin zo, ina kwana." Cewar Ummi ba a nutse ba. Ramma ta zubamata ido, gaba daya zargi ya d'arsu a ranta.    "Lafiya naga Hajiya Binta anan? Ki fadamin gaskiyar abinda ya kawota."   Ummi wacce ta soma had'a zufa ta bata amsa batare da ta kalleta ba.   "Um..nima nayi mamaki,  tambayata tayi ko Mami sun dawo nace aa shine ta tafi."   Ramma ta gama hango rashin gaskiya k'arara a fuskar Ummi, saidai kasancewar tasan k'arya baya daga cikin d'abi'arta yasa nan take ta amince.   "Toh Allah Ya kyauta, wannan dai salon munafuncine, tana nan ba'a shigo ba sai bayan da ta k'aura. Mutane dai ba tsoron Allah, Allah Yasa ba wani mugun abin ta..."   Sai kuma ta datse maganar da fad'in.   "Um, Allah na tuba. Bari na kama abinda zai fishsheni."   Daga haka ta fice daga falon, Ummi Ta sauke ajiyar zuciya don gaba daya ta gama tsorata. Ita kanta jinta takeyi wata marar gaskiya.       Koda ta fita bata k'arasa makaranta ba har saida ta raba kanta da k'ullinnan ta hanyar wurgashi cikin wani k'aton kwata nesa da gida.   Ummi na zaune acikin ajinsu da misalin karfe hud'u kowa ya fito don yin alwala da sallah kamar yanda aka saba a makarantar, ajin babu kowa sai ita da wasu yanmata kusan sa'annin juna su uku wadanda suma da alama suna fashin sallar ne.    Abin duniya gaba d'aya ya tarar mata, babu abinda take tunani sai Hajiya Binta, mamaki da tsoro lamarin mutane ke k'ara bata, idan mutum yana son kansa da yawa babu abinda ba zai iya aikatawa don samun cikar burikansa ba ashe? Ta tsunduma tsundum cikin wannan tunanin ta tsinkayi muryar d'aya cikin yanmatan nan mai suna, Maijidda tana magana wanda yayi sanadin maida hankalinta garesu.   "Wallahi ban ga wawuya irin Anti ba a duniya, shiyasa da zarar ta fita nake yanda na so a gidannan, ko jiya da ta ficewarta wurin aikin dare a asibiti, kar kuga tsaleliyar budurwar da Abba ya kawo gidannan, agaban idona suka shiga d'akinsa da ita."   Ido waje suka dubeta, wata fara mai bille, 'yar siririya, Amina ta soma magana.   "Ke Jidda! Maimakon ki gayamata?" Wata uwar harara ta watsamata kafin tace.   "Wa kike tunanin zai gayamata? Amma wallahi ba ki da wayo, bakisan irin kud'aden da nake samu ta hanyar yin shiru da bakina ba? Ai wallahi da dai nabar samun wadannan kud'ad'en na gwammace nayita rufawa Abba asiri. Ko iyayenmu ban sanarmusu ba ballantana wata suruka. Ke Surayya ai kin ta6a ganin Antin, kinga dai bata rageni da komai ba amma wallahi akan kud'i banga wani abu da zai gagareni aikatawa ba. Wai ma da kikemin wani ihu, ba gwara ni ba akan ke da kike dauka ba'a sani ba?"   Fad'in haka yasa cikin sauri Amina ta kai dubanta ga Ummi wacce saika rantse hankalinta baya kansu yana ga wani dan littafin addu'o'in dake hannunta. Tana jin sadda Amina ke fad'in.   "Ummi na jinmu fa." Surayya da Maijidda suka dara. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   27    Surayya tace.   "Itama ai rik'onta akeyi, na tabbatar nata idan an bincika yafi namu bak'i."   Wannan maganar ya shiga kunnuwanta saidai bata nuna ta ji ba. Suka cigaba da magana. Surayya na fad'in abinda tayi ayau.   "Ai wallahi kunganni, ko gobe na ziyarci Katsina, sai na k'ara ziyartar Malamin nan, yanzu bakiga yanda nayi mugun raina Saddik'a ba, dad'in zama 'yar aikin budurwa kenan wallahi, agaban mijin saiki rantse ba ni bace mai zugata, idan kin ganmu saikiyi zaton k'awayennan ne, shegiya kuw a duk abinda nace shikenan yayi zaman dirshan a kwakwalwarta. Ko yau da safe saida nabata shawarar ta rage shayar da Khalifa idan ta k'i nononta ya zube."   Suka tuntsire da dariya. "Ke Sury, shakka babu kin fimu shu'umanci." Cewar Amina kenan.    Hirarsu ta katse sa'ilin da d'alibai suka soma dawowa aji, banda 'Innalillahi' babu abinda Ummi ke ayyanawa a ranta, hawaye suka cika idanunta, bata samu nutsuwa ba har saida ta nemi izni wajen Malamarsu da zummar zagayawa ta sha kukanta sannan ta goge fuskarta. Tabbas DAN ADAM nada halaye mabanbanta, yana da wuyar gane hali. Wa zai ga Maijidda, Amina da Surayya ace zasu iya mugun abu kamar haka? Tun zuwanta Kano, jiya da yau ne kad'ai ta fi girgizuwa. Batun Hajiya Binta, da kuma na wadannan bayin Allahn uku.    Haka ta koma gida sukuku, ta sha tambaya wajen Ahmad wanda ya kasance babban d'a awajen Ramma kuma mai wayo sosai akan dalilin yin sanyinta saidai babu kwakkwarar amsar da ta iya bashi har suka rabu ta iso gidan.     Ta tarar da su Mami sun dawo, ta ji dad'i ainun. Bayan tayi mata sannu ta shige d'aki ta chanja sutura sai bayan isha'i sannan ta fito falon lokacin Mami ta fita gaida Alhaji. Ta wuce zuwa kicin ta dauki abincinta ta zauna agefe tana ci. Daga can saman tebur, Ihsan ce tare da su Adnan, tana ji tana labartawa Adnan had'uwar gidan Intisar da Yaya Haidar, akarshe hotuna ta shiga nunamishi. Zuwa yanzu babu ruwanta da shirgin Ihsan domin ta tsani halayenta, ita kad'ai ta fita zakkah a yaran Mami.                                              ***  ***  ***          Buguzum-buguzum take tafiya tamkar zata tashi sama, babu ko sallama ta shiga gidan ta hau kwalamata kira.   "Dije! Dije!!" Wacce aka kira da Dije ta fito da sauri daga d'aki hannunta rik'e da waya.   "Zan makivfulashin anjima." Daga haka ta kashe wayar tana mai watsawa uwarta ta wani kallo kamar mai shirin dukanta.     "Menene wai haka Baba?"   Habiba ta ja hannun 'yarta suka koma d'aka. Cikin sauri ta fiddo da k'ullin magani ta dubeta idanu a waje.   "Kinga Dije wannan, shine warwarar dukkanin matsalolinki, daga gidan Mai Bori nake, ta tabbatar muddin kikayi sha da wankan turaren nan, to fa kin gama samun miji tsayayye a duniya."    Dija ta yamutsa fuska. "Karki k'ara kirana da Dije nasha gayamaki nafison Dija, idan bazaki iya fad'a ba ki cemin Khadija."   Habiba ta washe baki.   "Allah Ya huci zuciyarki to, don Allah kiyi." Dija ta kalli k'ullin ta ta6e baki. "Yanzu idan baki manta ba shekaruna fa ashirin da takwas yanzu, tun inada ashirin kike faman takuramin da shaye-shayen magungunan da basu amfanata da komai, nafi zargin babu abinda suke k'aramin sai bak'in jinin samari. Nidai gaskiya..."   Tayi saurin toshewa 'yarta ta baki. "Kul! Kada na k'ara jin kin yiwa kanki mugun fata, wannan bana tantama za'a dace. Ke kad'ai gareni Dije, kinga dole na damu da rashin aurennan naki."   Dija ta tur6une fuska, ita a yanzu auren ma ya daina damunta tunda tana samun abinda take so hankali kwance.     Haka uwar tayita lalla6ata har a k'arshe ta amince zata yi, jin haka ta numfasa gami da washe baki.   "Yauwa kokefa, tace har ki bushe kada wani ko wata ya ganki, bari na shiga gidan Saude ki rufe k'ofar kada Malam ya dawo."   Ta amsa sannan uwar ta juya ta shuri takalmanta ta fita, kai tsaye gidan aminiyarta kuma makwafciyarta ta fad'a, gidan da idan baka san shi ba, to fa bazaka ce shine ba saboda gyararrakin da ya samu.    A zaune ta isketa a falo tana kallo. Wani gud'a ta saki.   "Ayyiruri nanaye! Dakyau uwargidan Balarabe, uwa ga Mariya da Atika. Kina sha'aninki fa."   Suka tuntsire da dariya cike da nishad'i.   Saude ta bata hannu suka cafke kafin ta k'ara gyara zamanta akan kujerarta wadanda ta siya a sakan tana musu kallon masu kyau adalilin a baya bata mallakesu ba.     Habiba ta zauna sharab akan kujera tana k'ara washe hak'ora.     "Wallahi duk sadda na ganki kina watayawa bakiji yanda nakejin dad'i a raina ba, kai duniya."   Wata dariya Saude ta saki. "Bari kawai Habiba, a duniya banajin inada aminiyar da ta kaiki, karki tona zuciyata kiga tarin kaunar da ke dank'are aciki tamkar wata yar uwata ta jini, ke kin fiyemin dayawa cikin 'yan uwannawa ma wallahi."   Habiba har lokacin bakinta ya gaza rufuwa.    "Burinmu kenan, yanzu don Allah ya kikaga ranar wannan shegiyar? Ai matukar za ki cigaba da bin shawarata za kiyita ganin aiki da cikawa."   Saude ta lumshe ido ta budesu tsabar dad'in da zantukan Habiba sukayi mata.   "Tabbas nagani, yanzu fa Balarabe ba shi da kata6us a rayuwa, komai nashi nike iko da shi, hatta da kadarorin da ya gada na iyayensa, yanzu sun dawo mallakina. Bakiga yanda k'aramin albashin wannan Shegiyar na farko ya juyemin zuwa babban jari na siye da siyarwa ba? Ai har abada ke mai kaunata ce Habiba, shiyasa na damu da damuwarki."       "Ga kuma k'iyayyar da kika jazamata a dangin Mahaifiyartata." Cewar Habiba kenan suka feshe da dariya har suna fidda ruwan hawaye. Saude ta nunata da yatsa.   "Maakira." "Ban kaiki ba." Habiba ta amsa mata.   Sai kuma Saude ta koma kalar damuwa.   "Yanzu Habiba babbar damuwata bai wuce na ranar da Boka yace mu kiyayi zuwansa ba, ranar da Balarabe zaiyi tozali da Ummi."   Habiba ta harareta. "Wa zai bar wannan ranar ta zo aka gayamaki? Har abada bazamu kyale ba, wannan bari sai Yaha ta dawo daga Kaduna, ita zatasan tuggun da zata shirya duk lokacin da bukatar zuwa ganin gidan Ummin ya taso."   Saude ta jinjina kai cike da gamsuwa daga haka suka rufe babin Ummi suka koma na Dija inda take bata labarin maganin da ta samo mata.   "Hakan ma yayi, Allah dai Yasa a dace. Ni kaina rashin namiji tsayayye ga Dije yana ta6an zuciya. Allah Ya had'ata da mai mota."   Habiba ta dara cike da jin dadin wannan kyakkyawar addu'ar da ya fito daga  bakin aminiyar kwarai.    "Amin." Nan suka shantake suna hira, can sai ga Mariya d'iyarta mai shekaru bakwai ta shigo hannunta rik'e da kud'i. Da gudu ta k'arasa ga Habiba tana dariya.   "Lah, Baba yaushe kika zo?" Habiba ta rungumeta tana dariya. "Yar Baba, ban dad'e ba. Mene wannan a hannunki kamar d'ari biyar?"   Mariya ta kwakume kudinta tana dariya. Ganin haka yasa Saude rik'ota.   "Waye ya baki kud'i auta?" Ta mik'awa uwarta. "Usi mai kanti ne fa ya bani, wai na kawomiki ki sakamin a bankin gwangwani."   Ta kar6a tana washe baki. "Kai madallah, Usman ba dai kyauta ba, ince dai kin mishi godiya?"    Habiba ta gutsiri goro ta soma tauna.   "Haka yaronnan ya ke ai, ba dai kyauta ba."   Daga nan suka cigaba da hira kafin daga bisani suyi sallama.                    ***  ***  ***            BAYAN SATI BIYU   Rai a matukar'ar 6ace ta ke dubanta, duban da ba k'aramin kad'a 'yan hanjinta ya yi ba. Ta daure ta numfasa, cikin dakiya ta russuna.   "Ina wuni Umma." Maimakon ta amsa, sai ta nunata da yatsa, da kakkausar murya ta soma magana.   "Kar ki ce za ki ci amanata har haka! Kinyi kad'an ba ki isa ba wallahi!"   Cikin rawar murya ta soma magana. "Me..me..nayi Umm.." Bata kai ga k'arasawa ba, ta sanya hannu ta d'auketa da mari wanda har ta daina ji na wasu 'yan dak'i k'u. Maganarta ce ta maidota hayyacinta babu shiri.    "Ya kikayimin aikin da na sanyaki?".  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 28 Gaban Ummi ya fad'i. Ta had'iyi wani miyau dakyar tana duban ofishin mai kula da makarantartasu inda anan ne Hajiya Binta ta zo ta sameta har Malamin ya basu wuri suyi magana bayan an jik'ashi da kud'i. Babu dai alamar akwai wanda zai kawomata d'auki, dole ta maido dubanta gareta idanuwanta na zubda ruwan hawaye, dakyar ta iya magana. "Nayi yanda kikace bayan nayi bismillah." Hannu Hajiya Binta ta d'ora a ka tana buga salati. "Kin kasheni Ummi! Uban wa yace kiyi bismillah? Akan wane dalili zaki karyamin dokar..." Sai kuma tayi shiru don tsabar takaici da tsananin 6acin rai har idanunta sun ciko da ruwan hawaye, ita kad'ai tasan irin wuyar da ta ci kafin samun magani garanti wanda aka tabbatar zaiyi aiki sosai akan Hajiya Madina, har bokan ya tabbatar mata cewar matukar'ar bata ga aiki da cikawa ba, toh ta dawo ta kar6i kud'inta. A dokokin saida ya tabbatar cewar a kiyaye ambaton Allah. (Wa'iyazubillah). Mik'ewa tayi jiki babu kwari ta watsawa Ummi wani mugun kallo tayi kwafa sannan ta fice a zuciye. Bayan tafiyarta Malamin makarantar ya dawo, da sauri Ummi ta mik'e ta fice, saida ta zagaya bakin famfo ta ci kukanta ta kuma godewa Allah da Ya kimtsa mata wannan dabarar sannan ta wanke fuskarta ta bar wajen zuwa aji. Salma wacce ta kasance k'awarta kuma abokiyar shawararta ta dubeta. "Lafiya dai Ummi?" Ummi ta k'ak'alo murmushi. "Bakomai." Salma ta girgiza kai. "Ina mamakin wannan amincin namu, sai nake ganin tamkar ba ki daukeni komai ba." Ummi ta girgiza kai. "Kiyi hakuri Salma, wani abin ba ya bukatar magana. Kedai ki tayani addu'a. Kada kiyi kokwanto akan yacce nake ganinki, Allah ne Ya had'a zumuntarmu." Salma ta murmusa. "Shikenan, Allah Ya yayemana dukkan matsalolinmu." "Amin." Ummi ta fad'a sannan suka bar magana sakamakon karatun da aka soma. Tun zuwan Ummi makarantar bata shiga harkar kowa, daga baya ne suka saba da Salma d'iya ga d'aya daga cikin malaman makarantar, Malama Zainab. Tun bata bayarda fuska, har dai ta dan sakarmata suka saba ganin da ta yi nutsastsiya ce. Haka ranar suka tashi jikinta duk babu kwari. Tana zuwa gida ta soma kici6us da Ramma a tsakar gida. "Au, kinga 'yar halak d'inma, to ki shiga ku gaisa da Yaha." Gabanta ya fad'i. "Yaha?" "Eh, wacce dai kikasani." Ramma ta bata amsa wanda ya sa ta fahimci maganarta ta fito fili. Ta saki murmushin yak'e, ta tabbatar zuwan na kar6ar kud'in watanta ne ba wai na bincikar lafiyarta ba. Allah Sarki, shiyasa ta ke tausayin kanta, tana tsoron ranar da Mami zata soma gajiyawa da ita ta korata, ita kam wa zata runguma? Ta ja kafafunta wadanda suka k'ara yin sanyi ta k'arasa cikin falon da sallamarta. Yaha ta amsa tana daga zaune saman kafet yayinda Ihsan ke zaune ko kayan makarantar islamiyya bata cire ba tana danne-dannen waya. Fahad kuwa ya cire daga shi sai singilet da short yana kallon (cartoon). Ta washewa Ummi hak'ora cike da mamakin yanda ta chanja. 'Shegiya, birnin ya kar6eta.' Ta fad'a a ranta. Ummi ta k'arasa ta gaisheta tana mai k'ok'arin sakin fuskarta bayan ta kauda kanta daga duban Ihsan wacce ke jifanta da murmushin rainin hankali da k'ara kallonta a ba komai ba. "Ashe kinzo, sannu, ina wuni." "Yauwa Ummi, lafiya lau. Oh! Haka kika bi kika chanja? Eh lallai." Ta karashe tana k'aremata kallo gami da d'an ta6e baki. Murmushi kawai Ummi tayi. "Ai dole ta chanja, cimar ai ba d'aya ba. Anan ai akuyar d'aure ta samu sake." Muryar Ihsan suka tsinta ta tsomo musu baki. "What the hell is this?" Daga baya aka bata amsa. Suka dubi mai shi, Adnan ne wanda ya fito daga d'akinsa daga shi sai dogon wandon makaranta da singilet. Yana watsawa Ihsan wani kallo mai nuni da lallai bai ji dadin maganarta ba. Ihsan ta had'e gira gami da d'aga kafad'a mai nuni da ko ajikinta ta cigaba da danne-dannenta tana dariyar rainin hankali. Yaha kuwa ta bata amsa. "Ai fa, da gaskiyarki 'yar Mami." Ummi ta mik'e. "Bari na chanja kaya." "Muje toh." Suka d'unguma da Yaha zuwa ciki, duk kokarinta saita hawaye ya zubomata ta daukesu da hannunta, wannan cin zarafi ya soma yawa, amma bakomai, tana ji a jikinta komai zaizo k'arshe in sha Allah. Tana chanja kaya, Yaha kuwa na tsaye tana k'arewa d'akin da ita kanta kallo. Dakin yana ayanda ta ta6a ganinsa saidai suturar Ummi take kallo duk ta chanja. Baki ta ta6e. "Oh'oh, hum, da gaskiyar Ihsan. Wannan irin samun sake? Yaushe aka sanyaki a makarantar?" Ummi cikin dakiya ta amsa. "An kwan biyu." "Lallai, amma bakomai tunda kina abinda ya dace, har kud'i Hajiya ta k'ara na aikinki. Kinga nan dubu shida, ta bani dubu uku. Idan naje zan damk'awa uwarki." Ummi ta amsa da to kawai, daman batasa ran za'a bata komai ba. "Ina su Baba?" Yaha ta harareta. "Kalau suke, da dai kin bar saka kanki a layin 'yan gidan Balarabe, bana tunanin ma wani cikinsu yana tunaki." Ummi ta jinjina kai tayi 'yar dariya na dole. "Bazan bar tuna shi ba, ko ba komai shi ne ya haifeni." "To 'yar makaranta. Bari na rage mara dai." Bayan shigarta bandaki, kuka sosai Ummi ta yi, dakyar ta rarrashi kanta. Saida akayi Magriba sannan Yaha ta shirya tafiya, har titi ta rakata, tafiyar bata dad'i ba don kuwa magana take gaggasamata wai ita ko 'yar satar nan ma batayi don a samu a tara na aurenta cikin sauri, har suka rabu batayi mata hud'ubar arziki ba. Ummi dai ta gama tabbatarwa a duk duniya babu wani dan uwanta na jini mai kaunarta. Ko a hanyarta ta komawa gida tana tafe ne tana hawaye saids ta iso daf da gidan sannan ta gyara fuskarta. A farfajiyar gidan suka had'u da Adnan, ta dauke kai zata shige yayi azamar shan gabanta. Ta dubeshi tana dan murmushi. "Lafiya?" "Sorry." Ya fada cikin sassanyar murya harda rik'e kunne. Abin sai ya bata dariya, ta dara. "Me kayimin?" Ya gyara tsayuwa. "Banyimiki ba amma Ihsan ta miki." Ta girgiza kai. "Ayya, ni ya wuce. Kuma ai gaskiya ta fad'a." Ya daure fuska. "Ba gaskiya bace. Karki k'ara daukar hakan amatsayin gaskiya. Ga idanunki sun nuna alamun ma kin koka. Kiyi hakuri Ummi." Ya burgeta, yasan darajar DAN ADAM. Ta numfasa hakoranta a bayyane tana murmushi har zuciyarta. "Ya wuce." Ya dara. "Yauwa kokefa, keep smiling always." Daga haka ya juya ya tafi, me yake nufi? Oho, bata da masaniyar fassarar turancinsa, amma duk da haka ya burgeta. Ta girgiza kai ta shige ciki itama. *** *** *** UMARUL FARUK DANZAKI DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 29       UMARUL FARUK DANZAKI Kwance yake saman doguwar kujera dake a tsararren falon mahaifiyarsu. Idanunsa a lumshe kai ka rantse bacci ya ke, a can d'aya 6angaren na falon kuwa wanda nan ma komai ya ji, Hajiya Babba ce da bak'uwarta suna lissafin kayayyaki. Rabin hankalinsa na garesu, rabin kuwa kan jefashi duniyar tunani wanda kokusa baya kaunar hakan. Ya ja guntun tsaki gami da mik'ewa zaune, wayarsa ya d'auka ya bud'e (data), nan take sak'onni suka shiga tururuwar shigowa wayarsa, duk daga (Whatsapp). Ba sabon abu ne awajensa ba, yana da tabbacin kusan maza abokan aikinsa da yan uwansa sunfi yawa, mata masu turomasa sak'o k'alilan ne don bai basu damar mallakar lambarsa ba, saidai har mamaki yakeyi na yacce mafi yawa na 'yanmatan suka samu. Babban dalilin kenan da ya yiwa kannensa gargad'i akan kada su yarda su k'ara bawa kowace yarinya lambarsa. Sun ji gargad'in kuwa don sun kiyaye.    Kai tsaye ya soma bud'e sak'onnin yana karantawa. Ga mamakinsa ya tsinceshi a wani group na Zumunta. Koda ya shiga yan uwansu ne burtik, mata da matasan. A sunayen (Admins) ya hangi wacce ta tsundumoshi ciki.   "Iklima?" Ya fad'a a fili fuskarsa cike da mamaki, ya koma cikin group inda ya ji tana mishi marhabin da shigowa. Ayayinda wani dan baffansu dake Adamawa ya sanyo alamun dariya. Guntun tsaki ya ja gami da ficewa batare da yace uffan ba.   Yana fita kuwa suka hau kyakyata mata dariya harda masu turo sak'on murya wanda hakan ba k'aramin k'ular da ita ya yi ba. Daman sun san halinsa, ba yau ya soma arcewa daga groups ba, da dai zaka mishi magana ta akwatin sirri, anan kam zai iya baka amsa, harma idan ka ci sa'arsa kuyi hira mai tsayi da dariya.       "To sai anjimanku." Muryar Bak'uwar Hajiyarsa ce ya katseshi daga danne-dannen da ya ke a waya. Ya dubeta ya gyad'a kai cikin dan murmushi ya amsa    "Allah Ya kiyaye hanya." Daga haka ta yi gaba tana mai amsawa da Amin. Mik'ewa ya yi ya koma wajen da Hajiyarsa ke zaune. Ta maida lesussukan gabanta gefe ta dubeshi fuskarta dauke da murmushi.   "Miskili kafi mahaukaci ban haushi, Sadauki nawa ya akayi ne?"   Ya d'an turo baki kamar mace, abin ya bawa Hajiya dariya ta girgiza kai. "To shagwa6arce ta motsa?" Ya shafi sumarsa yana 'yar dariya, itama tana tayashi, aduk yaranta tafi so da tausayinsa kasancewarshi mutum marar son hayaniya ga kuma hak'uri da rauni. Kullum addu'arta bai wuce na Allah Ya had'ashi da mace ta gari ba, ba wacce zatayi amfani da rauninsa da hakurinsa ta cuceshi ba. Ya katse tunaninta ta hanyar sanarmata batun group da aka sanyashi ya fice. Da murmushi dauke saman fuskarta tace.   "Toh banda abinka Sadaukina, ai k'ara dank'on zumunta ne, ina zaka so ku had'u da d'an uwanka a hanya ayi abin kunya ba ka san da zamansa ba? Kaga mu ma duk muna da group na zumunci, na yan Adamawa daban, namu na dangin mahaifinku daban."   Ya dauki filo ya sanya agefenta ya kwanta yana mai juya mata baya. Ya lumshe ido.   "Hajiya duk wannan takura rayuwa ce, nafi ganewa mu gaisa ta private ko kuma na kira mutum ko ya kirani. Surutu ne zalla sukeyi."   Ta dafa kansa. "Zumuncin kenan Sadauki, wani ma hakan ya nema ya rasa. Wasu na can basu da dangin ma da zasuyi musu hakan."   Bud'e idanu ya yi, tabbas Hajiya ta fad'i gaskiya, babu wacce ya tuna sai Ummi. Yana ji ajikinsa, akwai wani babban lamari a rayuwarta, har yau ya kasa cire kwad'ayi akan sanin tak'amaiman tarihinta.    "Hakane Hajiya." Daga haka ya basar da zancen. "Wai yaushe yarannan zasu dawo?"   "Af, su Baraka ai ansamu gidan zuwa, suna can nasan suna zuba da Intisar."   Ya girgiza kai gami da ta6e baki. "Ai Yaya Haidar shi ya barsu." Hajiya ta rik'e ha6a. "Au kai kace babu mai zuwa gidanka?"   Ya mik'e zaune ya rungume filon yana dariya kad'an-kad'an.    "Bance ba, amma kada a yawaita." "Eh lallai Sadaukina, ga shi har yau ni banga surukar tawa ba, Alhajinku ma na fama."    Ya yamutsa fuska. "Ni wai..." Sai kuma ya yi shiru gami da mik'ewa da daukar wayarsa.   "Aifa, daga ansoma maganar gaskiya saika gudu."   Ya yi murmushi mai bayyana hak'ora.    "Kai Hajiyata, ya dace dai ku d'an huta, ga na Baraka nan fa tafe, abin sai ya yi muku yawa."   Hajiya ta harareshi. "Wane irin yawa? Ai hutunmu yana bayan aurar da ku lafiya."   Ya gyada kai.   "Hakane, bari na d'an fita."   Ya fice da sauri kada ta cigaba da magana d'aya wanda shi amsarsa har zuwa lokacin bai wuce A'a ba, don kuwa ba zaice ya ta6a soyayya ba balle  har ya ji yana son auren wata mace.                         ***  ***  ***         Ahmad Bashir Danzaki, haifaffen garin Kano. Ya kwashi tsawon shekaru sittin a rundunar sojoji yana aiki kafin ya yi ritaya. Matarsa d'aya tun lalle, Hajiya Fatima wacce suke kira da Hajiya Babba.    Yaransu shida cif, Usman shine wanda ya yi karatunsa kacokam akan kasuwanci. Ridwan ke bi mishi, shi din ya kasance kwararren likita a fannin mata, sai Haidar wanda ya ke lauya, sannan Faruk wanda yake ma'aikacin banki.  Baraka wacce suke sa'anni da Adnan da Iklima, tana aji na karshe a sakandare wanda tare suke tafiya. Sai auta Ikram, wacce sa'ar Ihsan ce, itama tare suke tafiya da ihsan, suna aji na biyu a babbar sakandire.             Umarul Faruk ya kasance ma'abocin son zane, daidai da dakinsa idan ka shiga haka zakayita cin karo da takardu masu dauke da zane kala-kala. Sau da yawa haka mai gyara sashensa, Bala, zaiyita kwasarsu yana zubarwa. Son zanensa bai ragu ba saida ya soma aiki ka'in da na'in, alokacin ya zamana babu kwakkwarar lokacin zane, wani sa'in kuwa sai ranar da babu aiki yakan ta6a.  Idan kuwa ka ganshi a falo, to fa hira ce ta motsa. Kokuma yan uwansa sunzo nan zasu had'u suyita kwasar hira suna dariya har mahaifinsu.     Rayuwarsu tana tafiya cike da sha'awa, ga ilimin addinin da na boko. Babu mai takurawa wani, hakan bai hanasu kiyaye dokokin Ubangiji ba.              WANNAN KENAN.. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   30    Alhaji  Muhammad zaune a k'ayataccen falonsa bayan ya kammala cin abinci. Ya kai duba ga sanyin idaniyarsa da ta fito daga d'akinnasa bayan kammala feshe d'akin da maganin sauro, murmushi suka sakarwa juna, ya rik'o hannunta ya zaunar da ita a gefensa.    "Bakya tsufa Madina, menene sirrin?"   Mami tayi dariya gami da yin farr da ido.    "Oh Abban Ihsan, kai dai kullu yaumin baka rabo da zolaya."   Ya yi dariya. "Ina zolaya anan? Babu sai tsagwaron gaskiya."   Sukayi dariya. Ya rik'o yatsunta yana murzawa.   "Kiramin d'ana."   Ta cire yatsunta, zata mik'e ya dakatar da ita.   "Ina wayarki? Kiyi amfani da ita mana."   Ta sa hannu ta dauki wayar a saman tebur kafin ta hau laluben lambar Adnan.    Lokacin yana zaune a falo suna kallon Dadin Kowa suna kyakyata dariya har Ummi dake gefe zaune.    Bayan ya d'aga ta sanarmishi kiran Abba, a take ya mik'e ya fita.     Da sallama ya shiga falon bayan sun amsa. Ya k'arasa ga Abbansa ya zauna agefen kafafunsa.    "Abba gani."   Da murmushi saman fuskarsa ya dubi d'annasa.   "D'an Abba, ya makaranta? Naji kun soma jarabawar karshe ko?"   Adnan ya sosa kai yana murmushi. "Eh Abba, komai yazo karshe in sha Allah."   Abba ya jinjina kai.  "To haka akeso, Allah Ya taimaka."   Mami da Adnan suka amsa. Ya cigaba da magana.   "Kaje kayi nazari dakyau, saika zo ka sanarmin makarantar da kakeson zuwa k'aro karatu a k'asar waje. Kada kayi gaggawa ka bi sannu, idan ka sanarmin sai mu bincika mu ga yanayin ingancinsa. Allah Ya yi maka za6i na alheri."   Wani dad'i ya daki zuciyar Adnan, ya yita nanata ambaton Allah a zuci, a k'arshe cikin tsananin murna da d'oki ya hau yin godiya ga mahaifinsa. Haka ya tashi ya koma falon Mami cikin tsananin murna.    Yana shiga ya saki k'ara don tsabar farinciki har yana doka tsalle. Tunda suke basu ta6a tsallaka Nijeriya ba, sai a wannan karon da yake fatan burinsa ya cika.   Gaba daya suka zubamishi ido. Ihsan a guje ta taso.   "Yadai broda?" Nan ya sanarmata, ai don dadi itama ihun ta sanya gami da rungumeshi, shima Fahad agefe yana tsalle. Ummi kanta itama saita tsinci kanta cikin farinciki matuk'a, domin burinta ta ga duk wani masoyinta cikin farinciki.     Ya yi dakinsa a guje, Ihsan ta mara mishi baya tana mai cewa.   "Yi browsing mu dudduba makarantun."    Bayan shigewarsu ta numfasa, babu jimawa da shigarsu wayar Adnan ta dauki k'ara. Da sauri Ummi ta mik'e ta dauka da zummar kai mishi.    Hoton Faruk ta ci karo da shi 6aro-6aro akan screen din wanda Haidar ke  rik'e da hannunsa shi kuma yana dubansa da murmushi mai bayyana hak'ora. Gaba d'aya sai ta tsinci kirjinta na bugu.   "BRO FARUK." Sunan dake saman screen din kenan, ta ajiye wayar da sauri, ta kama hanyar d'aki har lokacin wayar na k'ara, haka ta juya ta koma ta dauka. Haka kawai ta tsinci kanta da d'agawa batare da tasan dalili ba. Ta gwada (sliding) wajen koren kamar yanda ta sha ganin Adnan ya yi idan zai d'aga waya. Cikin sa'a kuwa ta soma jin maganarsa yana sallama.     Ta kasa magana don gaba daya ta tsorata, jin maganar Adnan kawai ta yi a kanta.   "An kirani ko?" A razane ta juyo ta mik'amai. Kasa magana tayi sai kai data gyad'a. Allah Ya taimaketa batare da Ihsan suka fito ba.    Ta juya da sauri ta nufi dakinta. Tana ji sadda yake fad'in. "Afuwan dan uwa wallahi Ummi ta d'aga, fitowata kenan daga d'aki."   Daga haka ta shige ciki da sauri.   Shigarta d'akin ba wuya ta ji an kwankwasa k'ofar, a gigice ta dubi bakin k'ofar. Adnan ne tsaye yana murmushi. Ya mik'omata waya.   "Kar6i, za ku gaisa da Yayana. He's my best." Ya k'arashe cikin muryar rad'a yana mai kanne mata ido d'aya, ta yi mamakin rashin ganin kowace alama a fuskarsa kamar yanda nata fuskar ya nuna tashin hankali tsantsa. Ta kasa kar6ar wayar har saida ya yi mata magana karo na biyu, alokacin tasa hannu ta kar6a, kasancewar har lokacin cikin zumudin daddadan albishir na mahaifinsa yake, yasa yana mik'amata ya juya zuwa dakinsa on don ganin abinda Ihsan ta binciko da (Laptop) dinsa. Ta tsaya cak tana duban wayar har lokacin a matukar tsoro take. Kawai sai ta ji idanunta sun cika da kwalla, to wai me zata ce? Inama tun farko bata d'aga wayar ba? Batasan cewa ya katse ba saida ta ji sabon ringing wanda ya kad'a har cikin ranta. Hotonsa ne dai 6aro 6aro wanda idan kiran ya katse bata gani, hakan ya tabbatarmata cewa a sunansa kawai ya sanya.    Tana hawaye ta danna ta kara a kunnenta, ji takeyi inama kada ta d'aga, ita kam ta shiga tara...!       "Assalamu alaikum." Ta fad'a cikin rarrauniyar muryarta wanda sautin kuka ya ta6a.   Faruk dake tsaye a barandar dake a sama wajen dakinsa yana duban  farfajiyar gidannasu, ya numfasa jin muryarta.   "Waalaikumussalam, Ummi kina lafiya?"   "Umm, ina wuni Yaya Faruk." Ta fad'a gami da kai gwuiwoyinta k'asa kamar yana ganinta.     Murmushi ya yi lura da ya yi na cewar ta tsorata da shi. "Lafiya lau." "Wai Ummi dodo na zame miki? Gaisuwa kad'ai na buk'ata fa..." Sai kuma ya yi shiru kafin ya d'ora maganarsa. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    32 Ranar juma'a da misalin karfe bakwai, gaba daya yaran Hajiya Babba sun had'u suna hira kamar dai yanda suka saba, duk juma'a anan suke wuni matuk'ar ba wani aikin ne ya tasowa dayansu ba ko duka. Wannan lokacin ma Faruk baya tare da su, a haka ya dawo daga aiki ya samesu suna ta zuba hira suna dariya ga kayan marmari agabansu a babban faranti an yayyanka suna sha.     Yana sanye cikin riga kalar sararin samaniya, ya d'ora kwat dinsa bak'i akan hannunsa na dama, d'ayan hannun kuwa (briefcase) ne, gaba d'aya fuskarsa ta tona gajiyarsa. Suka amsa sallamar da ya yi ciki-ciki. Cikin dariya Ridwan ya dubeshi.    "Kaga manyan ma'aikatan banki."   Gaba daya suka dara, shi kuwa gogan sai ya k'ara marairaice fuska ya karaso ciki ya zube a saman kujera gami da fad'in. "Wash!"   Haidar ya birkita sumarsa. "Sannu lil, haka muke fama." Faruk ya murmusa. "Kai, anya kana aikin da mukeyi?" Cewar Likita (Ridwan) kenan.    Usman ya cafe. "Mu da ke wuni a shago sai mu ce me?"   Nan da nan kuma sai hira ta koma musu tamkar wasu abokai kowanne yana k'ok'arin nunawa sauran zafin aikinsa musamman  Babban Yaya da Likita wanda idan da sabo sun saba. Ikram na goyon bayan likita ayayinda Baraka ke bayan Barista Haidar kasancewar itama fannin da ta ke son karanta kenan.       Faruk dai sulalewa ya yi zuwa dakinsa don watsa ruwa.     Bai fito ba saida ya yi wankansa tsaf ya sanya riga t-shirt bak'a da farin wando wanda da kadan ya wuce gwuiwa, kasancewarsa farin mutum, ba karamin kyau da haske ya yi ba, ya jona wayoyinsa a chaji ya fito.     Alokacin sun nufi masallaci, shima ya bi bayansu.   Tare suka shigo gaba daya har Daddy dinsu. Bayan an kammala cin abinci ne, kowanne Daddy ya tambaya ko da wani matsalar. Duk suka tabbatar mishi babu, Babban Yaya ke sanarmishi zai je Kano ganin wani babban dan kasuwa da ya buk'aci ya shigo mishi da kaya suyi lissafi.  Daddy ya gyada kai.   "Allah Ya bada sa'a." Suka amsa da amin. Faruk wani abu ya tuno hakan yasa ya dubeshi.    "Ko nayi maka rakiya?"   Babban Yaya ya washe baki. "Wallahi da ka kyauta, daman banson bin hanya ni d'aya babu abokin hira."   "Toh kai baka da wani uzurin ne goben?" Cewar Daddy yana duban Faruk. Faruk ya daga kafada kadan yana girgiza kai.   "Babu."   "Ai kuwa da kun biyamin gidan Alhaji Labaran, akwai saurin auren 'dansa ran lahadi, bazan samu zuwa ba. Kuje a madadina."   Sukayi na'am har Haidar na fadin ba don yana da abin sabgogi ba a goben da ya bisu.   Faruk ba murmushi ya karkata wuya zuwa saitin kunnen Haidar.   "Kaidai fad'i gaskiya, Intee ce zata hanaka zuwa."   Haidar ya dubeshi ya harara da wasa, hakan ya bawa Faruk dariya, ya saki murmushi mai bayyana hak'ora.    Basu jima ba anan, duk matasan suka mik'e. Haidar saida ya tsaya a falon Faruk sukayi kallon ball kafin ya wuce gidansa bayan waya da Intisar ta dameshi da shi.     Faruk haka kawai yakejin nishad'i game da zuwansu Kano. Yana matukar kaunar k'ara sanyata a idanu.                    ***   ***   ***    Washegari kuwa misalin tara suka bar Abuja da Babban Yaya, koda suka isa saida sukayi  La'asar a gidan kakansu Modibbo suka ci abinci sannan Babban Yaya ya k'arasa ga abinda ya kawoshi, shi kuwa Faruk waya ya yiwa Adnan ya sanarmasa yana Kano, ba jimawa kuwa sai ga Adnan suka fice yawo. Idan ka gansu kamar abokai don babu laifi shima Adnan ba dai tsawon k'afa ba.      Saida suka gama zagayansu sannan suka nufi gidansu Adnan domin ya gaisa da Mami.       Ummi na zaune a inda ta saba, wato can hanyar kicin tana kallon tashar cartoon wanda Fahad ya sanya, ko kadan kallon ba dadi ya ke mata ba, asalima ba ba fahimtar komai take ba, wannan dalilin ne yasa ta mik'e gami da nufar hanyar d'akinta. Ya yi daidai da sallamarsu. Adnan na gaba, yana biye da shi. Ta amsa tana dubansu. Yana sanye da riga T-shirt ja da dogon wando bak'i. Shima idanunsa cikin nata, ta tsinci kirjinta da bugawa da sauri-sauri. Da sauri ta zube tana gaisheshi cikin rawar murya. Ya sauke ajiyar zuciya kafin kuma ya amsa. Daga haka ya bi bayan Adnan, ta mik'e jiki a sanyaye ta karasa dakinta da sauri. Juyowa ta yi a sadda ta kai kofar shiga, suka had'a ido sa'ilin da yake cire takalmi shima din ita ya waigo. Alokaci guda suka janye idanunsu bayan da suka ji wani sauyin yanayi na daban a jinin jikinsu. Ta yi wuf ta fad'a d'aki, tana jin ihun Fahad yana ambaton sunansa.     Ihun ne ya janyo hankalin Ihsan da Mami wadanda suke dakin daga cikin falon Mami suna magana akan dinkin da za'a yiwa Mamin na ankon bikin Baraka. Da sauri Ihsan ta fito, ganin Faruk ta hau dariya, cikin daga murya tace. "Mami dagaske ya ke, Yaya Faruk ne."   Jin haka yasa Faruk suka k'arasa ciki, daga lokacin kunnuwanta suka daina jiyo sautikansu.   Ta zauna a kasan kafet tana mai jingina kanta jikin bango. Haka kawai ta tsinci kanta da murmusawa. Wani sanyi ya doki zuciyarta. Ta tabbatarwa kanta akwai wani abu a ranta game da Faruk, tafi danganta abin da kauna ta don Allah irin wacce ta ke yiwa Antinta Amina, haka kawai Faruk ke burgeta.     'Kodai kina sonshi?' Gabanta ya fadi jin tambayar da ya darsu a zuciyarta. Ta zaro ido kamar wani na ganinta.   'Ina ni ina Yaya Faruk? Ai ko zan so wani na gwammace ya kasance cikib samari masu takuramin a hanyar makaranta da dai son abinda bazan ta6a samu ba.'   Ta ayyana a ranta, tunaninta ya katse sa'ilin da ta ji Fahad ya kwalamata kira. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR     31   "Ok, daman naji ance ke kika d 'aga waya ne, shiyasa na buk'aci k'anina da ya ba ki mu gaisa. Fatan komai lafiya?"   Ta ja ajiyar zuciya wanda ya jishi har cikin ransa, ya tsinci kansa da lumshe idanu.   "Lafiya lau, ya su Hajiya? Agaishesu don Allah."   Ta burgeshi, hakan da ta yi ya nuna tana da hankali. Murmushi ya yi mai ban mamaki wanda da wani cikin yan uwansa zai ganshi da ya zargi koda wata budurwarsa ya ke wayar.   "Zasu ji, thank you." "Um." Shiru ya biyo baya ta cire wayar a kunnenta ta ajiye gefe gami da zuba tagumi.   "Na shiga uku, meya kaini d'aga wayar Yaya Adnan tun farko? Yanzu wace masifar zan jawowa kaina?" Tayi maganar a fili wanda tsaf ya shiga kunnen Faruk kasancewar bai riga ya katse kiran ba, sai lokacin ya kashe ya sake kira. Har razana ta yi gami da ja baya. Ido waje ta duba ta ga shine har lokacin, ta d'aga ta kara a kunnenta.   "Ba..bari na mik'aaa mishi, ya fita."   Ya girgiza kai tamkar tana ganinsa alokacin da ya koma d'aki ya zauna saman kujera.   "No, ke nake nema ai. So nake nasan masifar da na jawo miki?"   Muryarta na rawa yayinda hawayenta suka zubo ta girgiza kai. "Wal..walla..." "Ki zama jaruma a komai na rayuwa Ummi, matsoraci bai zama gwani. Duk abinda zakiyi a rayuwa kiyishi da zuciya d'aya, ki zauna da kowa zaman gaskiya. Komai da zakiyi kiyi don Allah ba don wani halitta ba ok?" Ta gyada kai gami da numfasawa, sosai nasihar ya shigeta, haka kawai ta tsinci kanta da jin wani sanyi a zuciyarta.   "Nagode Yaya Faruk."   Ya yi murmushi mai sauti kafin ya amsa.   "Mu'assalam." Daga haka ya katse wayar, batayi gangancin k'ara wani tad'in a fili ba sai a ranta. Gaba daya batasan cewar kiran bai katse ba. Lamarin ganinsa takeyi tamkar a mafarki, wai itace ke waya da Yaya Faruk? Ikon Allah! Yau kuma meke a kansa?    Haka tayi lamo a saman katifa cike da fargaba, sallamar Adnan ta sanya ta mikewa zaune tana mishi murmushi na yak'e. Fuska a sake ya kar6i wayarsa da take mik'o mishi gami da fadin.   "Har an gaisa? Wai daman kun ta6a gaisawa da shi?"   Ta gyada kai. "Eh, shi ya taimaka ya kawoni gida ran fatin Yaya Haidar ai."   Ya dan daga kai alamar tunani kafin kuma ya dan daga gira.   "Oh, na tuna anyi haka fa. Kinsan Yayannawa ba dai kirki ba."   Murmushin dai ta k'ara yi sannan ya juya ya fice.  Ta zauna ta yi tsuru cike da tunanin wannan lamari. A karshe dai da ta ga babu wani abu da ta tsinkayo ta share batun.                                 ***  ***  ***    'Me nayi?' Ya jefawa zuciyarsa tambayar da baisan amsarta ba. Ya jingina kansa jikin kujera gami da k'urawa talabijin ido. Babu abinda ya yi banda sada zumunci.     'Kar ka d'arsawa zuciyarka wani abin daban, kana tausayinta ne kawai.'   Cewar wani sashe na zuciyarsa. Ya kauda maganar gaba d'aya ta hanyar kunna talabijin.                      ***  ***  ***   Sallamar da aka doka ne ya katse hirar da Habiba ke kwasa da mijinta. Ganin mai sallamar yasa duk suka washe baki, mijinta Yahuza ya mik'e.   "Kai lale da mutan Kaduna."   Fad'in Habiba kenan tana kokarin gyara tabarma.      Bayan sun zauna aka shiga gaisawa, Habiba ta zari gyale ta fita siyo ruwa.     Hajiya Munira kenan, 'yar kanwar Yahuza mijin Habiba, wacce ke auran babban ma'aikacin gwamnati a Kaduna. Ta zauna suka soma gaisawa da kawunta yana tambayar sadda ta iso.    "Kwanana biyu kenan ai Kawu."   Ya jinjina kai kafin su cigaba da hira a haka har Habiba ta dawo dauke da leda mai ruwan sanyi da lemu tana fad'in.   "Um, kaga fa tsabar zumud'i ko kudi ban dauka ba, bari yarinyarnan su zo su mik'a mishi."     Suka dara sannan aka hau hira. A haka Dija ta dawo ta samesu. Ta ji dadin ganin Munira, suka shiga hira harma a karshe Munira ta nuna tana gayyatarta Kaduna koda na sati ne. Babu musu Dija ta nuna zata.     Kawu Yahuza da Habiba sunyi murna kwarai, ko ba komai sa dan huta da surutun mutane na cewar anbar yarinya ba aure sai gantali. Man aka tsaida idan Munira zata wuce, tare zasu tafi.        Koda ta gama kwanakinta a kauyen, suka shirya tare da Dija da yaranta biyu, direbanta ya kwashesu zuwa Kaduna.                    ***  ***  ***                        ABUJA DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   33 A kofar dakin sukayi kici6us, ya  sanarmata wai ta zo ta k'aro faranti su Yaya Faruk zasu ci abinci. Ta amsa da to, a sanyaye ta gyara daurin dankwalin atamfarta sannan ta bi bayansa. A zaune ta gansu a saman tebur gaba daya, ta dauke kanta ganin shi dinma gogan idanunsa akanta suke, kicin din ta fad'a ta bi umarnin Mami. Ta dauraye ta goge sannan ta karasa garesu cikin sassanyar tafiyarta, sam bata da kwaramniya...      Ta kawo falon, tana kokarin ajiye suka had'a ido da ihsan ta samu tsarabar harara kuwa. Ta ajiye a gaban Faruk, wani daddad'an kamshi na turare ya bugi hancinta.   "Thank you."  Daga haka ta juya ta bar wajen, ya bi bayanta da kallo kafin ya numfasa muryar Ihsan ta doki kunnuwansa. "Let me serve you."   Ya dubeta ya dan murmusa gami da gyada kai, cikin siririyar muryarsa ya amsa.   "Kar ki cika, ban tare da yunwa."    Suna ci suna hira, jefi-jefi yakan dubi hanyar da ta bi, Mami ke faman jan shi da hira yana bata amsa. Ihsan gaba d'aya ta gama tafiya a kallonsa, sai yanzu take tabbatar da hakikanin gaskiyar abinda take ji game da yayannata.        Ummi a d'aki zaune ta yi zugum tana tunani. A karshe ta d'aga rigarta ta shinshina gami da lumshe ido. Ita kam tana son kamshi a rayuwarta don dai babu yanda zatayi ne ta samu. Musamman wannan turaren da ta ji awajen Faruk, sai ta ji ya doke duk wadanda ta saba shak'a wajen masu gidan.     'Komai na Yaya Faruk ba irin na kowa bane, komai nasa daban. Ya ji dad'in rayuwa.' Cewar wani sashe na zuciyarta.     'Kada ki kai kanki inda Allah bai kaiki ba Hasiya, babban goro fa sai magogin karfe, a komai na rayuwa Faruk ya d'ara ki, babu gatan da Allah bai ba shi ba. Yafi karfinki nesa ba kusa ba.'   Wannan tunanin yasa ta numfasawa, wani hawaye ya taho mata wanda bata iya hanashi kwaranyowa ba, shikenan su yan aiki basu da gata?    A daren dakyar ta iya kokawa da zuciyarta har ta samu ta runtsa domin kuwa bata k'ara fita falon ba, asalima batasan sadda Faruk ya bar gidan ba, ta dai ji maganar Ihsan na fad'in  Babban Yaya wanda ya nuna shima yazo daga baya.      Tunanin duniya ya ishi Ihsan, ta gama tabbatarwa lallai tana kaunar Yaya Faruk, a wannan daren yini ta yi kallon hotonsa wani dad'add'e da sukayi da Adnan da Haidar. Karshe dai ta kirashi a waya, bayan sun gaisa ya nemi sanin wace don bil hakki ba shi da lambarta.    "Ihsan ce."    Ya yamutsa fuska cike da mamaki sa'ilin da yake goge fuskarsa da tawul daga shi sai gajeran wando ya fito wanka.   "Oh, kanwar Adnan?" Ta ji haushin kanta, wato ko lambarta babu a wayarsa? Da tasan da haka da bata bayar da kai wajen kiransa ba. Kamar zata yi kuka ta amsa da eh.   "Ok, fatan lafiya?" Ta daure ta had'iye 6acin ranta. "Daman na kira na ji ya kuka isa gida?"   Ya dan saki fuska. "Alhamdulillah. Nagode."   "You are welcome." Ya dan murmusa gami da jinjina kai. "Good night.". Daga haka ya ajiye wayar batare da ya katse kiran ba ya cigaba da abinda yake yi. Babban Yaya na gefen gado zaune yana tura sak'o email a laptop dinsa.   Takaici da bakin ciki suka tararwa Ihsan, ta katse kiran don kanta. Duk da ta ji haushinsa, hakan baisa ta ji zuciyarta ta bar magagin kaunarsa ba. Inama zai aureta? Ta ayyana a ranta, wani tsalle tayi a saman gadonta gami da kwakwume filo tana murmushi, a haka har bacci ya soma fisgarta ta yi addu'a ta kwanta.                          Faruk yana kwance, ya zurfafa cikin tunani, a gefe yana dan tsintar hirar Babban Yaya da matarsa tamkar wasu sababbin aure, ya lumshe ido yana mai fatan bacci ya yi awon gaba da shi ko don ya daina ganin abinda ya ke gani a kwayar idanunsa, hakanan yabar jin sautin muryar da ta k'i gushewa a dodon kunnensa ba don komai ba sai don tsoron kada tunaninsa ya tabbatar da hakan, bayaso yanayin ya sauya zuwa ga abinda ya ke tsananin gudu.    Haka bacci ya sureshi cike da tunani da mafarkai masu dadi da ban mamaki.    Washegari da wuri suka tashi, bayan sun kammala shiri suka dunguma zuwa daurin auren da Daddy ya turasu, sosai kuwa Alhaji Labaran ya ji dadin zuwansu, a karshe sukayi sallama suka nufi gidan Hajiya Mama. Basu jima ba suka wuce don a ranar zasu juya zuwa Abuja.     Suna komawa gida kuwa suka tattara suka bar garin Kano...!        [truncated by WhatsApp] DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 35                   KADUNA   Mutan Kaduna sun isa lafiya lau, Dija cikin garin ya zamemata bak'o don bata ta6a zuwa ko'ina ba banda Katsina kauyen k'urfi inda nan ne asalin mahaifinta Yahuza. Ta yi mamakin ganin k'erarren gidan da Munira ke rayuwa cikinsa a unguwar Malali, ta sauke ajiyar zuciya har ta kasa 6oye mamakinta ta fito da shi fili.   "Gidanki mai kyau." Munira ta murmusa. "Nagode 'yar uwa."      Bayan shigarsu ciki ne ta gane wajen ba komai bane, domin sakin baki tayi tana karewa falon kallo wanda ya yi bala'in had'uwa. Zata iya cewa tunda take bata ta6a zuwa gida makamancin wannan ba. Haka Munira ta rakata har dakin bak'i a sannan ta koma ga yaranta Tasleem da Haris.    Ita dai Dija k'arewa komai kallo takeyi, tsaf, kamar ansan da zuwanta. Gado ne sai aka shimfida kafet a k'asa, a gefe sif ne maidaidaici na kaya, sai bandaki. Ina zata samu wannan a kauyensu kuma gidansu? Tunda dai akwai masu ginin zamanin, amma bata ta6a kwana ba. Tayi tsalle saman gado don dadi saikace wata 'yar shekara goma.      Munira ta dawo ta ajiyemata sabulu da soso a bandaki, ta umarceta da tayi wanka. Bayan ta kammala ta shirya tsaf sannan ta fito suka ci abinci saman tebur abin sai ya yiwa Dija banbarakwai, hatta yaran and saida sukayi mata dariyar yanda ta dunga nuna kauyenci saman tebur. A karshe suka tashi sukayi magriba mai aiki ta kwashe komai.  Suna zaune a falon ita da yaran suna kallo, Munira kuwa na kicin tana shiryawa maigidanta abinci, suka ji sallamar maigidan.     Gaba daya yaran suka mike suna ihun murna, hakan yasa Dina kallonsa. Sakin baki ta yi yayinda gabanta ya hau dukan tara-tara, haka mijin Munira ya had'u?          Sanye yake cikin farar shadda, bak'i ne kuma dogo, yana da kyau babu laifi.    Ya rungume yaransa yana mai farincikin ganinsu, zuwan Munira da sauri ne yasa shi bud'emata hannu ta karaso ta shiga ya hadasu ya rungume gami da lumshe ido, a hankali ya yiwa matarsa rad'a ta dubeshi tana murmushi ta sakarmishi hararar wasa shima ya kashemata ido yana murmushin.    "Sannu da zuwa." Maganar Dija ta maidosu hayyacinsu, sukayi saurin sakin juna, ita kuwa tuni ta tafi a kaunar mijin Munira. Munira ta matsa da sauri shi kuwa ya dake ya amsa yana mai tambayarta mutanen kauye.   "Duk suna lafiya, sunce a gaisheku."   Ya amsa fuska a sake sannan ya maida hankalinsa ga Tasleem da Haris.   "To, a jira nayi wanka na fiddo muku tsaraba ko?"   Suka hau tsalle da ihun murna. Ya jinjina kai. "Kuma ku nemomin tsarabar da ku ka kawomin idan ba haka ba nima zan fasa baku."   Nan ya yi gaba yana dariya Munira da Dija na tayashi. Yaran kuwa kansu ya dauki chaji don basu yowa babannasu tsarabar komai ba. Haka sukayita tunani lokacin har Munira ta bi bayan mijinta, hakan yasa suka koma ga Dija don ta nemomusu mafita.    Munira na shiga mijinta Deen (Zahraddeen) ya d'agata cak yana juyi da ita gami da fadin.   "Oyoyo sweetna." Sukayi dariya, dakyar ta zame daga rik'on da ya yi mata ta dan daki kirjinsa. Cikin muryar shagwa6a tace. "Kaidai wallahi ba ka rabo da abin dariya." Ya k'ara janyota yana murmushi da nok'e kai.   "Eh mana, musamman ma idan agaban sweetna nake."   Tayi dariya ta kwace jikinta gami da fad'awa bandaki don had'amishi ruwan wanka.    Acan kuwa Dija ta kasa sukuni, hankalinta gaba daya baya wajen Tasleem da Haris masu tambayarta tsarabar da zasu bawa babansu. Mik'ewa ta yi.   "Kuje kicin ku nemi wani abun da mamanku ta kawo.".  Da gudu suka wuce, dakinta ta koma ta zauna tana tunani, tunda take bata ta6a susucewa akan kowane d'a namiji ba kamar wannan, ta yi murmushi gami da k'udurta mugun abu a ranta.                     ***  ***  ***      Da sallama ta shiga turakar mijinta, ya amsa yana mai dubanta fuska a sake, ta ci ado har ta gaji sai kamshi ke tashi ajikinta. Ya yi ta dubanta itama idanunta akansa ta karaso ta zauna.   "Barka da..." Maganarta ta katse ganin irin razanar da Alhajinnata ya yi gami da mik'ewa yana mai saurin toshe hanci. A tsorace Mami ke dubansa da mamaki.   "Lafiya Abban Adnan?"   Ya girgiza kai. "Wane irin turare ne kika fesa haka Madina?"   Mami ta dubi jikinta kafin ta dubeshi cikin rashin fahimta.    "Bangane ba?" Ya kauda kai gami da k'ara ja baya.   "Don Allah ki shinshina jikinki, wallahi turaren naki sam babu dadin shak'a, ki tashi don Allah ki je kiyi wanka kinji?". Ya karashe da muryar rarrashi da kwantar da kai.     Mami ta jinjina kai ranta na soyuwa, ba don Muhammad bane ayau da ta gasa mishi magana, saidai girma da darajarsa a idanunta yafi gaban haka, ga kuma soyayya tsantsa a gefe.     Mik'ewa ta yi bayan shigewarsa daki da sauri da sauri, ta fice ta koma zuwa sashenta.          Ummi dake zaune su kadai a falon ita da Fahad suna kallon (Harry porter) sai ji sukayi ana kwankwasawa, Ummi ta bude, kallo daya ta yiwa Mamin ta fahimci akwai damuwa shimfide saman fuskarta, itama Mamin zubamata ido ta yi domin ta ga ko zata nuna wata alama na cewa ta ji wari ajikinta, sai ma ta ga duk hakan bata kasance ba. Wannan yasa ta sauke ajiyar zuciya ta giftata, ga mamakin Ummi, Mami har waiwayenta ta yi, ko me take son hangowa? Oho.    Fahad ya mike zaune. "Lah Mami, ya kika dawo?" Ta yi yak'e. "Mantuwa nayi ne."   Daga haka ta shige zuwa dakinta da sauri-sauri.    Suka cigaba da kallonsu, can kuma da jimawa, har Fahad bacci ya daukeshi saman kujera, Ummi kuwa na jiran Mami ta fita ta k'ulle k'ofar, sai ga Mamin ta fito tana zuba wani tsadaddan k'amshi na ban mamaki. Ummi dai tun kafin Mamin ta karasa fitowa kamshin ya ratsa kofofin hancinta. Tana mamaki kodai Mami 6arin turaren ta yi. Ta fito sanye cikin doguwar rigar abaya wanda daga k'asa kayan bacci ne,ta dora hijabi saman doguwar rigar.     "A'a, bacci ya yi?" Ummi ta amsa a ladabce. "Eh." Ta jinjina kai fuskarta na nuna alamun bata so hakan ba. Ta dubi Ummi jiki a sanyaye. "Ki kaishi makwancinsa."   "Toh."    "Saida safe." "Allah Ya tashemu lafiya." Cewar Ummi tana kokarin cika umarnint.  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 34   Ya gama buge-bugensa akan k'asa kafin ya yi wata arniyar dariya ya dubesu.   "Shakka babu kun hadu da yarinya mai basira da har ta yi muku dabara batare da ta shiga matsalarku ba."   Hajiya Binta ta dubi kawarta Luba sannan suka maida hankalinsu ga bokansu.   "Kamar ya ranka shi dad'e?" Cewar Hajiya Binta kenan cikin rawar murya. Ya girgiza kai. "Babu wani k'ulli da ta sanya a k'asan gadon abokiyar zamanki, asalima acan kwatami ta yarr."   Wani bakin ciki ya turnuk'e zuciyar Hajiya Binta, ta ji wata muguwar tsanar Ummi ya turnuk'eta, maganar Luba ta katse tunaninta. "Yanzu ranka shi dad'e ya za'ayi? Tabbas munyi kuskuren saka wata, kada dai ta tona asirinmu?"   Ya girgiza kai yana dariya. "A'a, yarinyar ba haka ta ke ba, kada ku ji ko d'arr, yanzu me kukeso ayi?"   "A maimaita mana irin wancan." Fad'in Hajiya Binta kenan tana dubansa da jajayen idanunta wadanda 6acin rai ya kad'a. Nan take bokan ya turnuk'e fuska yana watsamata kallon banza na baki isa ba. Hakan ya kad'amusu 'yan hanji. Ya cigaba da magana da kakkausar murya....!         "Kafin na baku na gayamaku wuyar k'ara samun aiki irinsa, domin a shekara, sau daya Aljani Tsingil ya bani damar tambayarsa buk'ata, saidai ko kuyi hakuri har wata shekarar."   Hajiya Binta ta narke tana rok'onsa ko akwai wani abu da za'a iya yi? Ya jinjina kai. "Tabbas, abu mai sauki, zamu sanyamata warin ja6a, ta yacce ko ta ra6i mijin zai ji gaba d'aya ya tsaneta, amma hakan bazai sa soyayyarta ta fice a ransa ba, za dai ya kaurace mata kamar yanda kukeso, itama zata shiga tashin hankali. Ke kuma ga wannan (ya mik'a mata wani k'ulli) Ki dunga shafa kwallinnan aduk sadda za ki turaka, hakanan ki dunga shafe fuskarki da turaren nan, ina mai tabbatar miki za ki samu kulawar da ya saba bata, hakanan kuma ba dai kije da buk'ata ba, ya k'i aminta. Idan hakan ya yi muku..."    Hajiya Binta da Luba suka amsa da eh har suna rige-rige. Yayi murmushi mai k'ara fiddo muninsa.    "Ku tafi, ku saurareni nan da kwana uku, zakuga aiki da cikawa."    Suka mik'e suka bar wajen da sauri gaba daya a tsorace.          A mota suna tafe Hajiya Binta na faman surfawa Ummi ashar tamkar tana gabanta.    Luba ta dakatar da ita. "Laifin fa duk namu ne Binta, munyi wawancin sanya wata ta yi alhalin bamu gama fahintar halayenta ba. Wannan bata da son abin duniya kamar Zinaru tsohuwar 'yar aikin Hajiya Madina. Ya dace ko nan gaba mu kiyaye."    Ta saki huci. "Naji, yanzu me kike ganin zamuyi mata?"   Luba ta murmusa. "Me kike ci na baka na zuba ne? Wannan k'aramar alhaki ce muddin kika zama uwargidan Alhaji Muhammad Modibbo."     Jin haka yasa Hajiya Binta kyalkyalewa da dariya itama aminiyar shaid'ancin nata na tayata. Ta jinjina kai.   "Tabbas zasu san basu da wayo."      Alokacin da suka iso kofar gidan, Ummi na kokarin shigewa ciki, dawowarta kenan daga islamiyya, gabanta ya fad'i ganinsu, suka bita da mugun kallo har ta shige lokacin da maigadi ke wangale musu k'ofa.     Ummi wani zargi ya d'arsu a ranta, ta tabbata mutanennan da wuya idan sun kyaleta, tana kuma jiyewa uwar dakinta tsoronsu, ta tabbatar basu hakura ba, dole akwai abinda suke shirin k'ullawa. Ta sauke ajiyar zuciya sadda isa kofar sashensu. Da ace ita din tana da dama, da ta shawarci Hajiya akan ta dage da addu'a don ta fuskanci Umma akwai mugun abun da ta taka.                            ***  ***  ***                       ABUJA     Zaune yake saman kujera (resting chair) a 'yar barandarsa, ya sanya (sketch board) a gaba wanda aka kafa ajikin katako ya tsaya kyam, hannunsa alkalamin zane ne, daga shi sai singilet da gajeran wando, dawowarsa kenan daga aiki ya yi wanka, hannunsa na hagu rik'e da kofin (coffee) yana sha, ya dukufa sosai wajen kokarin zana abinda ke ransa, yana yi yana shan(coffee), saida ya kammala ya dubi zanensa yaga babu abinda ya manta sannan ya saki murmushi mai burgewa.  Komawa yayi ya kwanta jikin kujerar bayan ya tara kansa da hannunsa na hagu yana mai cigaba da shan (coffee) dinsa da dama, ido ya zuba k'irr yana k'arewa zanen kallo alokaci guda kuma zanen na k'ara shiga ransa.   "So beautiful." Ya fad'a a bayyane, ya jima sosai yana kallon zanen kafin daga bisani ya mik'e ya dauko laptop dinsa ya yi aikin gabansa. A karshe ya nemi makwancinsa cike da dumbin tunani, abinda bai taba yi ba kenan duk tsawon rayuwarsa, kwana da tunanin abinda ya ke yiwa kallon 6ata lokaci a baya.                 ***   ***   *** DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   36 Har Mami ta kusa k'ofa sai kuma ta juyo alokacin Ummi na susar hancinta dake k'aik'ayi. Gaban Ummi ya fad'i ganin ta dawo. Mami ta dubeta lokacin da take matsowa gabanta.   "Kinji wari ajikina Ummi?"   Da sauri Ummi ta girgiza kai a tsorace.   "Wallahi a'a, asalima kamshi kikeyi sosai Mami."   Mami ta dubeta na dan lokaci kafin ta saki ajiyar zuciya. "Amma naga kin toshe hanci."   Ummi mai saurin kuka tuni murya ta raunana.   "Aa wallahi k'aik'ayi yakemin shine na sosa."    Mami ta numfasa. "Saida safe." Ta furta a hankali sannan ta yi gaba tabar Ummi na binta da kallon mamaki. Ga dukkan alamu dai akwai abinda ke damun uwar dakinnata. Ta yi shiru, duk tunaninta bata gano komai ba hakan yasa ta basar da zancen ta tashi Fahad ta kaishi makwancinsa sannan ta rufe k'ofar.      A hankali bacci ya soma fisgarta ta ji ana kwankwasa k'ofa sannu-sannu. Mik'ewa ta yi a tsorace ta fito falo, agogo ya nunamata sha biyu harda mintuna. Ta karasa ta bud'e ta fita don bude kofar sashen. Shima Adnan lokacin ya mike ya fito don jin k'arar bugun don bai riga ya yi bacci ba yana karatun jarabawa. Ya dubi Ummi da mamaki. "Waye haka?"   "Adnan ku bud'e ni ce."   Suka firgita jin muryar Mami, da sauri Adnan ya bud'e k'ofar. Ta shigo,ta dubesu da jajayen idanunta kafin ta wuce a sanyaye bayan ta umarci Adnan da rufe kofar.      Ummi ta tsaya a falo cikin tsananin firgici, Adnan ya bi bayan mahaifiyarsa, can ba jimawa ya fito rai babu dad'i. "Rufe kofar Ummi." Ya fada batare da ya kalleta ba hankalinsa na kan hanya da alama Mamin bata ba shi fuskar sanin damuwarta ba. Itama ta rufe jiki babu kwari ta koma dakinta.       Daren daga Adnan har Ummi babu wanda ya yi bacci isashshe, gaba daya hankalinsu ya tafi ga Mami wacce basusan dalilin damuwarta ba. Hakanan ta yi abinda shi Adnan tun tasowarsa bai ta6a gani ba, wato ta baro sashen Abba aranar (duty) dinta, abu ne da bai ta6a faruwa ba saifa a yau. Itama Ummi abinda ya dauremata kai kenan, domin tunda take agidan tsawon wata daya da kwanaki bata ta6a ganin Mami ta kwana a sashenta ba alhalin Abba na garin kuma itace da aiki.      Inaga mai gayya mai aikin, wato Mami, wacce kwana ta yi tana kuka tana kai kukanta ga Mahaliccinta. Ta kasa zaune ta kasa tsaye, idan ta runtse ido babu abinda ke fad'omata a rai sai tsawan da Mijinnata ya dakamata a sadda ya nufeta da niyyar runguma ya rarrasheta ya nunamata dazun da gaske ya ji wari da baisan dalilin wanzuwarsa ba a tattare da ita. Yana jin warin kuwa ya tureta da k'arfi gami da jan tsaki. Ta matso da nufin tambayar ko lafiya, ya yi azamar matsawa gefe gami da dakamata uban tsawa akan kada ta kuskura ta k'araso inda ya ke. Haka ya kyaleta ya fice daga dakin, ta jima anan tana kuka, har ta ji maganarsa inda ya ke bata umarni kan ta fita zai kwanta. Haka ta tashi ta fito nan ma hancinsa a toshe har wani runtse ido.   Haka ta k'araci zamanta a falo, ganin babu Sarki sai Allah yasa ta mik'e ta bar masa sashennasa.    Mami ta numfasa ta kwanta lamo saman filo, a iyakar rayuwarta da Muhammad, matsala makamancin haka bai ta6a shiga tsakaninsu ba. Kullum cikin yabonta yakeyi musamman a 6angaren kwalliya da tsafta. Ayau ga wani sabon lamari ya 6ullomata.         Washegari da safe Ihsan ta yi mamakin ganin Maminta a d'aki, koda ta gayamata, bata 6oyemata cewar ga abinda Abban yace tana yi ba. Ihsan har kuka ta yi ganin yanda Mamin ke hawaye. Ta girgiza kai. "Allah kuwa Mami kawai wani abin ne na daman Abba ya 6ullo da shi, amma babu wani abu da na ji ajikinki, asalima wani bala'in kamshi kikeyi."   Murmushi kawai Mamin ta yi, cikin dauriya ta dubi 'yarta.   "Nagode, ki tashi ku je kada kuyi latti."    Haka dai Ihsan suka fice duk jiki babu kwari. Daidai da yan uwansu sun lura yau yaran dakin Mami basu da walwala. Hassana d'iyar Anti Amarya, wacce basu fiye daukar kishi zazzafa ba akan yan uwansu, ta tambayi Ihsan ko lafiya. Ihsan ta nunamata babu komai hakan yasa dole suka dan saki jiki gudun wata tuhumar.      Acan gidan kuwa, Ummi ta kammala komai na gyaranta a sashen yara sannan ta fad'a sashen Mami da sallama. Bata falon, ta hau gyara saida ta gama sannan ta lek'a d'akin. Duk a zatonta Mami na bandaki wannan yasa ta juya da zummar sai ta kammala zata dawo. Ji ta yi an kira sunanta, ta juya da sauri ta dubi gadon tana mai amsawa. Can ta hangeta ta dukunkune cikin bargo tana faman rawar d'ari. Ta karasa ta russuna ta gaisheta. Kai kawai ta gyada. Murya na rawa tace     "Kashemin fanka." 'To." Ta amsa gami da mik'ewa da sauri ta aiwatar, ta dawo ta durkusa.   "Sannu, a kawomiki kari nan?" DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 37   Dan yamutsa fuska ta yi ta cire yatsa ta yi mata nuni da dirowar gefen gadon. Cikin rawar muryar dai ta ce. "Duba ki daukomin Paracetamol."    Koda batasan (spelling) din ba, tasan maganin, ta bude ta hau bincike cikin sa'a kuwa ta samu ta ciro. Ta taimakawa Mamin kamar yanda ta buk'ata ta mik'e zaune. Saida ta sha maganin sannan ta koma ta kwanta.       "Ki yi aikinki." Cewar Mami a sanyaye.      Ummi ta mik'e ta hau aikinta, tana yi tana kallon  Mami wacce itama tun tana dubanta m, jefi-jefi tana goge kwalla har bacci ya dauketa.    Kamar wasa, karamar magana ta zama babba. Tun Mami na ganin lamarin a kanta ita d'aya, har ya soma shafar yaranta. Abba ya chanja musu, ko gaisheshi suka je to ba fa kamar da ba, a yanzun ko yana cikin fara'a suka shiga to fa zai tamkemusu fuska, ya zamana Hajiya Madina bata da girki, abin kuma mamakin bai wuce ganin matan sun had'emata kai ba kamar ma sunyi farinciki da hakan. Idan yaran suka tafi makaranta, Mami haka zata zauna da Ramma da Ummi tana nuna damuwarta a fili don tun tana 6oyuwa har zuciyar ta kasa d'auka.                  BAYAN WATA D'AYA   Rayuwa ta yi musu kunci, ayau Ummi suna zaune da Mami a falo suna sauraron rediyo, Adnan ya shigo rai babu dad'i ya zauna d'abas saman kujera yana kunkuni. Mami bata saurareshi ba sai bayan da ta kammala sauraro, ganin an kammala Ummi ta kyalesu su zanta. Ta dubeshi, gaba daya ya bata tausayi ganin yanda ya rame, wannan wasa da dariyar tasa duk ta ragu.   "Ya akayi d'an Abba?" Ji ya yi kamar ta watsamasa garwashi a zuciyarsa, a yanzu babu wanda ya ke tsananin jin haushi kamar mahaifinsa, ko hanya ya k'i jinin su had'u.  Ya k'ara tamke fuska.   "Please Mami ki bari."   Mami ta yi murmushi, ita kanta ta rame matuk'a, a baya Mami ba dai ta zauna ta yi hira da su Ummi ba, halin rayuwa yasa duk ta yi sanyi don har Ummi tana bawa ta yi mata sadaka a kofar gida. Hakanan gaba daya sun dage da addu'a, ko ta ji kamar ta sanarwa iyayenta sai wata zuciyar ta hanata, gani takeyi kamar ba jimawa komai zai yanke.     "Shikenan, gayamin, meyafaru na ga ranka a 6ace?"   Ya numfasa gami da cizan le66ansa na k'asa. Dakyar ya k'ok'arta ya yi magana.   "Zan bar gidannan Mami." Gabanta ya fad'i ta zaro ido tana ambaton Innalillahi a ranta.   "Kamar ya za ka bar gidannan Adnan? Meya faru kuma?"   Ga mamakinta, hawaye kawai ta ga ya soma. Hankalin Mami ya tashi yaronnata akwai hakuri da dakiya, sai ta iya k'irga sau nawa ta ga kukan Adnan tun tasowarsa. Ta yi shiru lokacin da ya katse tunaninta inda ya soma magana.   "Wai yau ni Abba ya kira da zargin nayi mishi sata, wai jiya da dare bayan na fito ya yimin fad'an ya fasa turani k'asar waje karatu shine da safe ya laluba bai ga wasu kudadensa da ya bari a falonsa ba, shine yau ya kirani akan wallahi sai na fito mai da kudinsa har Umma na fadin tabbas ta ga sadda na fita wai ina gyaran aljihu. Ni bazan iya rayuwa a gidannan ana tafiya haka ba, na gaji Mami, zan yi nesa da ku."    Yana kaiwa nan kawai sai ya cigaba zubar kwalla har yana sheshshek'a. Idan hankalin uwar ya yi dubu to ya tashi, duk a lamarinnan, bata ta6a kuka gabansu ba sai a yanzun. Kuka sosai ta shiga yi, yau Mijinta Modibbo ne ke kiran d'anta da sunan 6arawo, wane irin tashin hankali kenan ya ke faruwa dasu?    Jin kukanta ne yasa Ramma da sauri ta fito daga kicin harma da Ummi wacce itama ta ji hankalinta ya yi tsananin tashi.   "Hajiya lafiya?" Cewar Ramma. Adnan ma kukan yakeyi babu mai bawa wani hakuri, karshe a fusace ya mik'e ya fita daga falon.    Ummi tuni ta soma kukan itama, Ramma da jiki ya gama sanyi ta karasa ga abinda uwardakinta ta russuna.   "Haba Hajiya, haba, idan kina haka agaban yarannan sai ki karyamusu zuciya, komai na rayuwa idan ya samu bawa hakanan ya ke hakuri ya dangana. Addu'a kadai ce mafita, duk wannan fa bazai sanya abubuwa su chanja ba sai addu'a."   Mami ta jinjina kai idanu a kod'e ta dubi Ramma. "Yanzu har yakai Alhaji da soma zargin d'ansa da sata?"   Abinda ta fad'a ya yi mugun kad'a hanjinsu. Ramma ta hau salati, ita kuwa Ummi daskarewa ta yi kukanma ya kasa fitowa. Basu kai ga samun abin fad'a ba suka ga Adnan ya shigo goye da k'atuwar jaka fuskarsa duk ta kumbura.    "Zan wuce Mami."   Daga haka ya yi gaba, Mami ta mik'e tsaye da azama gami da dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa.   "Adnan."  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 38 Ya tsaya gami da juyowa, ta tako har wajensa tana dubansa cike da tsananin tausayi.   "Ka yi hakuri, bari naje ga mahaifinnaku."   Ya girgiza mata kai da sauri, cikin tsananin fushi da daga murya ya soma magana.   "Sai kiyita zuwa yana wulakanta mana ke Mami? For what reason?!! Idan har don ni za ki ki barshi, kudi da yace na dauka, ga wayata can da Laptop zan aiko a kar6a a siyar..."   "Kasan abinda ka ke fad'a kuwa? To kada ka soma, na gayamaka ka tsaya bari na je ga Abbannaka."   Mami ke maganar a fusace kafin a karshe ta sassauta, daga haka ta giftashi ta zura silifas dinta ta yi gaba, daman da mayafi jikinta, idar da sallar walha kenan ta zauna jin rediyo. Mami ta isa har k'ofar sashen Abba cike da jin kwarin gwuiwa, hakanan ranta a tsananin 6ace, ayau ta gaji, saidai ayi wacce za'ayi kawai.    Ta murd'a k'ofar da sallama ta tura kai ciki. Rabonta da turakar maigidan nata wata daya da satittuka kenan, dariyar Abba da Umma ta katse sa'ilin da sallamar Mami ya ratsa dodon kunnuwansu.     Abba nan take ya daure fuska, ita kuwa Umma ta k'ara muskutawa jikinsa kai kace wata yarinya. A hankali ta tako, da sauri ya toshe hanci gami da dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu.   "Tsaya anan don Allah!" Ya yi maganar cikin tsananin fusata, ya d'ora da cewa. "Wai Madina meyasa bakya ji ne? Inace na yi miki iyaka da sashena?!"   Yana maganar ne kamar zai taso ya daketa ga hancinsa dake a toshe, itama Umman hancinta tosheshin ta yi.    "Alhaji agaskiya bazan iya zama ba, ku kammala maganarku tukunna." Umma ta mik'e tana yamutsa fuska kamar gaske, ta shige d'aka, tana shiga ta la6e bayan ta gama kyakyata dariya tana sauraronsu.    Mami ta sauke kanta k'asa tana mai fidda gwauron numfashi, DAN ADAM kenan mai saurin manta halacci, tamkar wani abu na kyautatawa a rayuwa bai ta6a wanzuwa tsakaninta da Mijinta ba.    Ba tare da ta dubeshi ba ta soma magana, domin kallonsa ma ayanzun kunci ya ke k'ara mata. "Kayi hakuri, na sa6awa umarninka na shigo inda kayimin hani, saidai wannan karon ba zuwan kaina bane, zuwan 'ya'yana ne."   Ga mamakinsa sai ya ga ta russuna k'asa. "Domin Allah Abban Adnan, komai da zaka yimin kabar sanya yaranmu ciki, ka cigaba da kyautatamusu kamar yanda kakeyi a baya. Ni..."   "Ke sauraramin don Allah!" Ya yi maganar cikin tsawa.   Yana zaro ido ya jefamata tambaya. "Wane abu makiran yaran naki suka ce miki nayi musu na wariyar launin fata?" Ta daure ta ciji le66anta, dakyar ta cigaba da magana. "Wani mugun zance naji, wai kana zargin Adnan da yi maka sata. A sanina kafi kowa sanin halayyar danka, bazai ta6a aikata hakan ba."   "Toh, kenan kina nufin kice k'arya nayi mishi? Madina ba fa ko isa ki dunga koyawa yarana mugun hali har haka ba. Ki kiyayeni wallahil azim idan ba haka ba zan miki abinda ba ki ta6a zato ba ko a mafarki. Iskancin banza! Don kaza kazansa ni ban isa na hukuntashi ba? Da wannan mugun halin da ya koyo ne ya ke tsammanin zan turashi waje karatu ya lalata yaran mutane? To bazai ta6a yiwuwa ba wallahi, kuma ki amsomin dubu ashirin d'ina idan kuwa ba haka ba, karatun ma kwata-kwata ya jawa kansa bazai yishi ba."    Daga haka ya mike yana cigaba da masifa kamar zai ari baki, a haka ya shige daki ya barta durkushe.   Mami wacce tun ashar din da ya yi ta girgiza bata iya cewa uffan ba, ta jima anan ta kasa tashi don tsananin tashin hankali, dakyar ta iya mik'ewa ta zura silifas d'inta ta fita. Tana tafe zuwa sashenta tana juya maganganun mijinnata, zuwa yanzun ta k'ara tabbatarwa lallai akwai wani babban lamari. Watakil ko mijin ya soma hauka ne shiyasa abin ya kai har da zagi.  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    39   A falo ta tarar da Ummi da Ramma sunyi jugum, ta dubesu ta dauke kai tana waige. "Ina Adnan?"  Ramma suka dubeta. "Ai kina fita ya wuce, inaga dakinsa ya shiga."   Da sauri ta juya zuwa dakinnasa, babu kowa, ta lek'a bandaki nan ba bayanan, akan gadon ta ga takarda ta dauka ta warware ta soma karantawa.      "KIYI HAKURI MAMINA, WALLAHI BAZAN IYA ZAMA BA. KADA KI DAMU WAJEN YAYA FARUK NA NUFA WATO ABUJA, MAMI DON ALLAH AYI YANDA NACE, GA WAYOYINA DA LAPTOP A SIYAR A BAWA ABBA KUDINSA KADA KI BADA KWANDALARKI. IDAN NA ISA ZANYI KIRANKI."   Jin haka yasa ta zauna d'abas saman gadon tana numfarfashi kafin ta soma hawaye. Shikenan farin cikin gidanta ya rushe, ta dauki wannan matsayin jarrabawa daga Allah, ta kuma tabbatar komai yana nan zuwa k'arshe. Hankalinta ya kwanta da jin inda Adnan ya nufa, ko babu komai zai samu kulawa hakanan tasan inda ya ke.    Bikin Baraka duka-duka sati d'aya ya rage, itama tana tunanin tattarawa zatayi ta tafi ko zuciyarta ta dan samu nutsuwa idan ta shiga cikin 'yan uwanta.     Ta linke takardar ta ajiye gami da kashe komai da ya danganci kayan wuta ta rufe dakin da mukulli ta fito.         Ta sanarwa su Ramma cewar Abuja ya wuce su kwantar da hankalinsu. Daga haka ta wucesu zuwa daki. Ramma ta girgiza kai. "Oh, akace zato zunubi amma ina tunanin anya matannan na Alhaji babu sa hannunsu?"   Ummi ta yi shiru cike da tunani, kuma mai yiwuwa ne saidai kamar dai yanda Ramman ta fad'a ne, wato zato zunubi ne, hakan yasa ta ja bakinta ta yi shiru batare da ta tofa nata ba.   Koda su Ihsan suka dawo sunyi mamakin jin wai Adnan ya wuce Kaduna, saidai Mami ta nunamusu akan abinda ya shafi karatunsa ne. Hakan yasa suka hau murna da tunanin ko Abba ya sakko.     A ranar Mami ta saka Ihsan zuwa Atm ta ciro mata dubu ashirin ta kaiwa Abba. Ihsan dai bata da masaniyar ko ta menene, ta ji dai Abba na kiran 6arayin banza da wofi har yana dokamata harara. Sai bayan ta zo da korafin gaban Mami sannan Mami ta rarrasheta gami da nunamata kawai fad'ansa yakeji.                       ***  ***  ***    Hajiya Binta zaune a falon Hajiya Lubna (Anti Amarya) wacce ita kanta ta dan ji mamakin shigowarta don a yan kwanakin nan ta dauke k'afarta da shigowar, a cewar Anti Amarya ba don komai ta yi hakan ba sai don ganin ta samu kan Alhajin yanamata yanda ta ke so.     "Bakya ji dadi ba, na yanda Alhaji ya juyawa 'yar gwal dinsa baya?"   Cewar Hajiya Binta kenan tana mai duban Anti Amarya wacce ke danna wayarta. Mace ce gwanin shan kamshi da yanga, shiyasa sau da yawa ta ke k'ular da Hajiya Binta, har a ranta tana yawan fad'in 'Da ace Hajiya Lubna ce ta samu kan Alhajin ba Mami ba, to da gaba daya sun kad'e, domin ta iya daukewa mutum kai ga wulakanci.' "Ke kike ganin haka Hajiya Binta, saidai ni ban gano komai ba."   Hajiya Binta ta yi mata wani kallo. "Bangane nufinki ba?"   Sai lokacin ta ajiye wayar ta dubeta da murmushi saman fuskarta.    "Ba nasara a gaba Hajiya Binta, duk abinda za'ayi idan ba na Allah ba, babu inda ya ke zuwa, da dai anyi hakuri an cigaba da yarda da kaddara tunda shi wanda ya ajiyemun yana nunamana kulawa tsantsa da kauna. Amma ina tabbatar miki wannan ba abun murna bane, abu ne na lokaci k'ank'ani."   Ta danyi shiru ta dora bayan ta gama lura da irin k'uluwar da Hajiya Bintar ta yi da maganganunta.     "Ina jiyemana ganin abinda yafi na baya tsakanin Muhammad da Madina anan gaba."   A fusace Hajiya Binta ta mik'e. "Ya isheni Malama, na lura ke kin daina damuwa da kayan takaicin da muke kuntsa. Shikenan ai, fatan da kikeyi ba dai ni na ganshi ba, saidai ko ke din. Idan kin k'ara ganina a sashenki ki gasamin wanda yafi wannan." Fuu! Ta fice tamkar akan iska, dariya Anti Amarya ta yi gami da girgiza kai.   "Za ki gani ganin idanunki Binta." Ta fad'a a bayyane.        Inda Hajiya Lubna ta fi Hajiya Binta kenan, tana da kokarin 6oye sirrinta hakanan bata kauna bin malamai tafi yarda da shaye-shayen magungunan mata, a wannan 6angaren kuwa saidai su tafa da Mami don bazata gwada mata ba. Saidai tasan kaunar dake tsakanin Muhammad da Madina, dad'add'iya ce wacce ko mutum ya yi yunkurin rabasu, to fa a karshe zai ji kunya matuk'a. Ta numfasa, tana da tabbacin uwarmijinsu bata da masaniya akan wannan sauyin lamarin, da tasan yanda d'an nata ya maida 'yar gaban goshinta, da tuni ta yiwa abin tufka.                        ***   ***   ***                      ABUJA   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   40    Yana tsaye a wajen ajiye motoci a Bankinnasu, lokacin misalin biyar na yamma, dawowarsa kenan daga wani aike da manajansu ya yi mishi, yana kokarin barin wajen wayarsa ta dauki k'ara. Ya yi mamakin ganib lambar dw bai sani ba a kuma layin da mutane d'aid'aiku ya ta6a kira da shi. Jikinsa ya ba shi cewar kowanene wannan, wani na jikinsa ne, hakan yasa ya d'aga da sallama.    Daga can Adnan ya amsa, Faruk ya saki fuska. "A'a, k'anina ashe kai ne."   Adnan ya gyara zaman jakarsa yana duban cikin tashar gami da yin yak'e. "Ni ne my best, ina Abuja." Faruk ya ji wani dadi har cikin ransa domin yana kaunar yaron, duk kuwa da tazarar dake tsakaninsu na shekaru, yana daukarsa tamkar wani sa'ansa.     "A ina kake yanzu?" Ya sanarmishi yana tasha, ya umarceshi da daukar taxi yazo banki ya sameshi. Ya mik'awa mai wayar wayarsa gami da godiya sannan ya kama hanya. Bayan zuwansa saida ya jira Faruk ya kammala sannan suka fito. Faruk ya lura da yanayin Adnan ba mai dad'i bane, ga wata rama da ya yi kamar ba ya cin abinci, har ya kasa hakuri bayan sun hau titi ya tambayeshi ko lafiya.   Adnan daman kiris yake jira, kawai sai ya hau kuka, daman tun dazun ya ke cike da tunanin halin da Maminsu ke ciki ga wani dumbin tausayinta. Faruk na ganin haka ya cigaba da tafiya har ya samu wurin fakin ya tsaya.     "Ka tayarmin da hankali fa k'anina, meke faruwa ne?"   Adnan ya yi shiru, to me kuma ya rage? Dole daman wataran yan uwan su ji abinda ke faruwa muddin Mami ta zo biki ko don yanda gaba daya suka fita hayyacinsu, ya 6oyemasa komai sai abinda Abba ya yi mishi a yau kawai ya sanarmishi.   Faruk bai ji dadi ba sam, ya sauke ajiyar zuciya, baiyi zaton Abba zaiyi haka din ba koda a mafarki.  Ya dubi Adnan cikin muryarsa sassanya yace "Mami tasan ka taho?"         "No, na barmata takarda dai."   Faruk ya girgiza kai gami da daukar waya ya dannamata kira.    Mami na zaune saman darduma, idar da sallar magriba da gabatar da nafilarta kenan ko mik'ewa batayi ba ta ji wayarta na k'ara. Ta janyo da sauri, Faruk ta gani ta numfasa, daman tun dazun take jiran kira daga wani na Abujan don jin ko Adnan ya isa batason tayarmusu da hankali.     Bayan sun gaisa yake sanarmata da isowar Adnan. Farin ciki ya lullu6e zuciyarta. Fuska a sake ta yi hamdala a fili, ta cigaba da magana.   "Don Allah Faruk kada ka barshi cikin damuwa, kayi iyakar kokarin ganin ya samu walwala. Nima ina nan zuwa nan da kwana uku da zarar yarannan sunyi hutu."   Ya murmusa cikin ransa yana mai tausayinsu, ya gama fahimtar akwai wasu al'amura dake faruwa tare da su duk da suna 6oyewa.  "Karki damu Mami, in sha Allah zan yi yanda kikace."   Ta yi murna da jin hakan har ta sauke ajiyar zuciyar da hatta Faruk saida ya ji.   "Nagode d'ana, Allah Ya k'ara muku albarka."   "Amin." Ya mik'awa Adnan. Adnan murya a raunane yace. "Maminaa."   Mami ta lumshe ido hawayenta sukq zubo ta bud'e tana murmushin k'arfin hali. "Na'am d'an Maminsa, ka gujemu ko?"   Adnan ya yi shiru baice komai ba sai  huci yake.  "Karka damu, Allah Yana tare da mu. Kayi kokarin 6oyemin sirrin gida, idan ma ka gayamishi wani abu, to don Allah karka k'ara daga abinda ka fad'a. Kayi kokarin sakin jikinka kada tambaya ta yi maka yawa."   Adnan ya gyada kai. Haka sukayi sallama bayan tace ya gaishemata da Hajiya Babba.    Faruk ya dubeshi da murmushi.    "To ya? Domino's Pizza ko kuma Jabi Lake Mall?"   Adnan ya dubeshi sukayi dariya, ya kanne mishi ido. "Kaima kasan inda nafi kauri."   Faruk ma dariyar ya yi kafin ya tashi motar ya harba titi. Bai zarce ko'ina ba sai da suka samu masallaci sukayi sallah sannan suka karasa ya siyamusu Pizza da ice cream sukayi gida. A hanya Hajiya Babba ta kira Faruk a waya jin ya dad'e, ya tabbatar mata suna tafe da Adnan shima yazo. Ta ji dadi kwarai don Adnan yaro ne dan shafta, yanzun sai ya k'ullar da cikinta, sam baya mata bak'unta.    Saida suka isa dakin Faruk, Adnan ya yi wanka shima Faruk ya yi suka chanja kaya daga nan suka nufi cikin gidan. Hajiya na falon tare da Ikram da Baraka suna hira. Ganin Adnan yasa yaran soma ihun murna. Shima a take ya ji ya mance da komai ya washe hakora. Ya karasa ya gaida Hajiya har tana mishi fadan dalilin da bai zarto gidan ba ya soma zuwa ga Faruk. Ya daga ledojin hannunsa yana dariya. "Saboda wannan ne."   Sukayi dariya gaba daya.  "An kammala karatu kuma sai tafiya ko?" Ya dan yi murmushi bai ce uffan ba.  "Ai nima ji nake kamar na bishi wallahi."   Cewar Baraka. Ya harareta. "Ki barwa mijinnaki wa?" Ta yi dariya. Nan suka shiga hira, Hajiya ta tambayi dalilin ramarsa ya sanarmata ya danyi rashin lafiya ne. Tare suka ci suka sha kayan makulashen sannan Faruk da Adnan suka shiga wajen Daddy suka gaisheshi ya tambayi yaushe ya iso ya ke sanarmishi daga karshe suka koma sashen Faruk.    Faruk kwance saman gado yana danne-dannen waya, yayinda Adnan ke sarrafa Laptop din Faruk yana duba shafin sada zumuntarsa na Facebook, hankalinsa ya kai ga zanen da Faruk ya yi a jikin sketch board. Ya k'urawa hoton ido yana son tuno inda yasan yarinyar. Zaro ido ya yi gami da ajiye Laptop din da sauri ya nufi wajen. Wannan ya ja hankalin Faruk ga dubansa, gabansa ya fad'i. Shaf ya mance bai cire takardar zanen daga jiki ba. Ya kauda kai sa'ilin da Adnan ya dubeshi. "My best, wannan ta yimin kama da Ummi sosai. Ya akayi ka zanata?"   Faruk ya daure ya k'ak'alo murmushin yak'e. "Hobby na kenan, kasan zane babu inda baya zuwa, haka kawai na tsinci kaina da zanata."   Adnan ya yi shiru, zarginsa yana bashi kamar akwai wani abu game da Ummin a zuciyar Faruk. Ya numfasa, idan ta yi wari watakil shine wanda zai soma ji. A fili kuwa murmusawa ya yi.   "Wallahi ta yi kyau, kamar wacce aka dauka a hoto. Gaskiya Allah Ya baka."   Faruk ya share maganar ta hanyar jefomishi tambaya.   "Wace k'asa ka za6i zuwa ne?" Adnan ya baro wajen zanen ya dawo, ransa ya sosu don ya tuno abin haushi. Ya dan daga kafada. "Bar wannan zancen my best, ni nafasa anan zanyi."   Faruk ya lura da wani abu, kawai sai ya share.                    ***   ***   ***                      KADUNA DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    41                      KADUNA    Dija gaba daya ta sauya, daga mai surutu da zafi zuwa marar son hayaniya da kuma sanyi. Komai takeyi muddin Deen zai shigo, to fa zata mance komai ta shagaltu a kallon dukkan wani motsinsa. Tun Deen bai lura ba har dai ya soma tsarguwa da yawan bibiyarsa da takeyi da kallo.      A yau juma'a, Munira batanan ta wuce gidan wata aminiyarta da ta haihu, saida ta dauko yaranta daga makaranta suka wuce tare, gidan babu kowa sai Dija wacce ganin Denn a gida yasa fir ta k'i binsu ta fake da ciwon jiki. Misalin karfe uku da mintuna, Deen yana kwance a falonsa yana duban talabijin, ya ji sallamar Dija. Da mamaki ya dubi hanyar falon, yana mai amsawa. Ganin da ya yi mata cikin shigar mutunci marar mishkila sosai yasa ya dan ji nutsuwa a ransa. Ya mike zaune yana murmushin yak'e.   "A'a Dija, k'araso mana." Ta dubeshi ta sauke ajiyar zuciya, komai nashi burgeta yakeyi. Ita kuwa ko zata mutu sai ta sace zuciyarsa, shekarunta sun kai munzalin da ya dace ace tana gidan miji ba yawon gidajen yan uwa ba. Itama fa mutum ce ba dutse ba, tana da sha'awa, koda dai takan biyewa k'awarta wacce waya ta hadasu, mai yawan yi mata hudubar banza akan ta amince ta je Kano su had'u don d'ebewa juna kewa, ta k'i yarda amman takan ta6a hirar banza da ita a waya(Wa'iyazubillah).       Ta samu wuri ta durkusa gami da gaisheshi. Ya amsa batare da ya kalleta ba yana mai wayancewa da chanja tasha.   "Ashe sai kai kad'ai, ga abinci can an jera tun dazu."   Ya dan dara. "Eh yanzu zan taso na ci." Ta narkar da fuska. "Haba Deen, don Allah ka zo muje, ni kaina sai yanzu zan ci. Na riga na saba da ci da ku ana yi ana hira, yanzu da basunan bazan ji dadi ba."   Ya jefeta da wani irin kallo har saida ta ji gabanta ya fad'i, tsoro ya cikata, sai kuma ya numfasa gami da maida dubansa ga talabijin.   "Jeki ina zuwa." Ya bata amsa a gajarce ta mike jiki babu kwari ta fita. Har ta cire ran zai zo sai kuma gashinan, wani sanyi ta ji a ranta ta mike zata zubamishi. Ya dakatar da ita. "No barshi, zan yi da kaina." Ta girgiza kai. "Ban ta6a ganin kunyi haka da Munira ba, nima bazan bari ka zuba da kanka ba kada nayi laifi awajenta." Jin haka ya kauda kai, ta zuba tana murmushi ta tura gabansa sannan ta zauna saitinsa tana cin nata. Idanunta a kansa, da zarar ta ga zai kallota sai ta yi sauri dauke idanun.    A ransa ya ji yana mai jin haushinta, da ace yar uwarsa ce da tuni ya korata gidansu, saidai ba yanda ya iya, baya son ran Munira ya 6aci ya lura sosai take kaunar Dija hakanan tana tausayinta wai adalilin har yau bata samu mashinshini ba.   Ya rigata mik'ewa ya bar wajen, ta bishi da zazzafan kallo gami da k'ara cin alwashin ba fa zata barshi ba sai ta cika burinta na aurensa. Babu wacce ta fad'omata a rai sai Baba Habiba, ta tabbatar ita daya ce zata iya yi mata kokarin shawo kan Deen ko ta wane hali. Idan ma da hali ya saki Munira ya aureta. (Kun ji butulcin DAN ADAM)                   ***   ***   ***    Bikin Baraka ya iso, komai na shirye-shiryen Mami, ita da kanta ta yi bata saurari Abba ba balle ta tambayi wani abu a aljihunsa har ya samu damar cin zarafinta. Ta yiwa Ihsan anko, hakan ta siyawa Fahad shadda tare da Adnan aka dinka musu. Ummi kuwa ta yi mamaki da Mamin ta bata kudi suka je da Amina bayan isarsu gidan Hajiya Mama ta siyo 'yar kanti da kuma wani abin idan tana so. Ta yi murna matuka duk da tasan ba da ita zasu je ba.    Hajiya Mama ta jajantawa yar uwarta kwarai na abinda ke faruwa da ita. Ta kuma yi mata fada sosai akan dalilinta na rashin sanar da ita tun wuri. A karshe tace zata sanya ayi rokon Allah, suma kuma ba kwanciya zasuyi ba, su dage sosai da addua da sadaka har Allah Ya kawo makarin koma menene.      Bayan Amina da Ummi sun dawo daga shago suka biya gidan Innar Aminar. Mace mai mutunci kwarai, ta yi murna da ganin Ummin da duk sadda Amina ta zo saitq bata labarinta. Sun jima anan sannan suka lek'a gidan Anti Hauwa yayar Amina daga nan suka kamo hanyar gida. A hanyar ne ma Ummi ke labartawa Amina yanda suka ta6a yi da Hajiya Binta. Amina sosai ta tsorata, hankalinta ya dan kwanta jin Ummi bata bi turbar shaidan ba ta aikata. Ta k'ara fahimtar da ita lallai mai yiwuwa yanzun ma da sa hannunsu cikin lamarin Abba da Mami. A karshe ta kara shawartarta akan ta dage da addu'a akan Allah Ya kareta daga sharrinsu.      Ashe kuwa dai sharrin na tafe, domin a daren da suka koma gida daga gidan Hajiya Mama, Abba ya kira Mami ya ke fadamata ta gaggauta korar Ummi daga gidansa don labari ya iso mishi cewar tana biye-biyen maza tana fakewa da zuwa makaranta. Acewarsa, yaransa basu jawomasa abin kunya ba, to babu 'yar wata can da zata janyomasa. Mami ranta ya 6aci, cike da mugun 6acin rai ta dubeshi. "Wannan kuma ba halin Ummi bane, da ace Ummi na yi kasan kafin ka gane ka koreta, da tuni na yi hakan don bana zama da maci amana. To Ummi babu inda zata je, zamanta daram a gidan nan!"   Ta yi maganar cikin daga murya har kirjinta na bugu da sauri-sauri saboda tsananin 6acin rai, ba wai don kwatarwa Ummi yanci kadai bane, aa, har ma da gajiyawa da jin zafin yanda ya ke bayar da ita gaban kishiyoyinta, don a wannan karon ma har hadasu ya yi gaba daya a falon yana mata korafi akan Ummin. Abin ya soma isarta.   A fusace ya ce. "Sai mu gani idan gidan ke kika ginashi Madina! Amma wallahi kinji rantsuwa ta musulunci babu yar iskar da zata zauna a gidana, saidai ko ki bita."   Hankalin Mami ya tashi, su kansu matan sun razana da furucin Abba, Anti Amarya wacce bil hakki ta tausayawa Mamin, ta saka baki. "Haba Alhaji, ya kake..." "Kiyimin shiru Malama, bansaka dake ba, daman na taraku ne don na gargadeku da ku jawa yan aikinku kunne, banaso and iskancin banza da wofi. Ke kuma ki tattara taki ki maida inda kika amso ta, bazan lamunci iskanci ba."   Takaici ya sa Mami jan tsaki batare da tasan sadda ya fito ba. "Sai kayi, na gayamaka babu inda Ummi zata je, sa'arka d'aya zan je Abuja da na soma gwadamaka gaskiyar abinda nake fad'a tun yanzun. Naga ai wasu ma nasu cikin suka ta6a yo wa aka zubar aka cigaba da zama da su a gidan."   Hajiya Binta ta fahimci da yar aikinta Sa'ade take wacce ta ta6a yo ciki suka zubarmata. Ta fusata ta yi kwafa batace uffan ba.    Kafin Abba yace wani abu, Mami ta zura silifas dinta ta fice cikin kunar rai.   "Ummi! Ummi!!" Ummi dake daki ta ji Mami na kwalamata kira cikin daga murya. Ta fito a kidime ta russuna. "Naam."   Ta tamke fuska. "Ki shirya kayanki, dake zan tafi."   Ummi gabanta ya fadi don bata ta6a zato ba,  ta mike ta wuce bayan ta amsa da toh kawai.     Shigarta da mintuna biyar Fahad yazo ya kara kiranta wai inji Mami. Ta mike ta isa gareta a can daki. Mamin na zaune gefen gado ta yi jugum tana tunani, bayan Ummi ta durkusa ta dubeta fuska daure.   "Ki gayamin tsakani da Allah akqn dukkan abinda zan tambayeki Ummi."   Ummi a tsorace ta ce. "Toh." Mami ta zubamata ido, ita tasan sharri aka yiwa Ummi, saidai dole ne ta tambayeta don amana ce ita a hannunta.  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 42 "Dagaske ne kina...." Sai kuma ta yi shiru, haka kawai ta tsinci kanta da jin nauyin maganar, ta daure ta karasa.   "Labari ya iso ga Abba na kina bibiyar maza, ki gayamin gaskiya Ummi."   "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!"   Abinda Ummi ta furta kenan a fili kafin wani kuka ya tahomata, kuka sosai harda sheshshek'a. Mami na kallonta bata katseta ba, bata ta6a jin tausayin Ummi ba aduk zaman da suke sai a yau, k'azafi abu ne mai matukar cin rai, tasan yanda Ummi ke ji irinsa Adnan ya ji a sadda aka mishi sharrin sata, hakanan itama irinsa ta ji alokacin. Maganar Ummi ta katse tunaninta.   "Wallahil Azim ban aikata abinda ake zargina akai ba Mami, ban ta6a koda tsayuwa na saurari wani d'a namiji  ballantana har ya kai da ta6a jikina ba, ki yarda da ni wallahi Allah ban aikata komai ba. Na shiga uku." Ta k'ara fashewa da wani kuka wanda ke k'arawa Mami jin wani mugun tausayinta. Ta numfasa muryarta a sanyaye.   "Ya isa, nasan ba ki aikata ba daman, kawai don kiyaye amanar da aka ban naki ne yasa ni tambayar. Na riga nasan kazafi ne na mahassada amma babu komai wataran sai labari. Kiyi hakuri, kina iya tafiya ki soma shiri, dole dake zamu wuce."   Ummi ta mik'e ta fita, a hanya suka ci karo da Ihsan ta bita da kallon mamaki ganin ta fito daga dakin mahaifiyarsu kuma tana kuka, da sauri ta karasa dakin don duba Mami. Sai ta tarar ta yi shiru ta zuba tagumi. Ta karasa gareta. "Mami lafiya? Naga fitar Ummi daga nan ta na kuka."   Mami ta murmusa. "Bakomai, kin gama shirye kayanki?" Fuskarta cike da damuwa ta amsa da eh. Bata kaunar ganin Maminsu a wannan yanayin, Allah-Allah takeyi su bar garin su shiga cikin yan uwansu ko zuciyarsu zata sanyaya. Ta kasa hakuri saida ta k'ara tambayar Mamin dalilin da yasa Ummi ke kuka. Haka dai ta sanarmata don ta k'i jinin 6acin ran yarannata. Ihsan duk da tana k'in Ummin itama ta ji babu dadi musamman jin cewa a gaban kishiyoyin Maminnata Abba ya gasawa Mamin magana. Ta yi kwafa. "Ai Allah Ya fisu, munanan mugun abinsu zai juye kansu." Mami ta jinjina kai. Tabbas ayanzun ta soma zarginsu duk da zato zunubi, tana yi musu kallon munafukai masu fuska biyu.      Ummi ji ta yi duniya ta mata zafi sosai, ta riga tasan makircin Umma ne, ita kadai ce matar da ta ci alwashi akan lalata rayuwarta, ta barta da Allah domin bata da karfin yin fad'a da ita, koda tana da shi, bata jin zata iya ramuwar gayya. Allah zai mata sakayya, saukinta ma Mami bata gaskata hakan ba.                   ***   ***   *** Ta dubi 'yarta tana mai zaro ido. "Me kike nufi ne? To wallahi babu inda zakije. Na rabaki da wannan shegen yaron ba kiji, idan ba kiyi a sannu ba zan mugun sa6amaki."    Iklima ta turo baki ta mike daga saman kujera. "Wai don Allah inace ni zan zauna da shi? To ni gaskiya ina sonshi kada ki yi yunkurin rabani da shi. Kuma meye idan naje Abujan? Baraka fa k'awata ce, ana bikinta don kawai wani kishi naki kice..."   Bugun le66anta da ta yi ne yasa ta yin shirun dole tana sosawa don zafi.  A fusace Umma ke magana. "Kinyi kadan! Wallahi iklima kinyi kadan, ban haifi 'yar  da zata fi k'arfina ba nan duniya. Biki ne kuma babu inda za ki taka kije, mu zuba ko ni ko ke a gidannan."   Daga haka Umma ta nufi dakinta a fusace kasancewar ranar ba aikinta bane. Kai tsaye layin bokonsu ta nema ta sanarmishi akan tana so ya raba zuciyar 'yarta da soyayyar Faruk. Ya sanarmata abu ne mai sauki amman sai ta zo ta amshi wasu magunguna. Ranta ya yi sanyi ta bishi da godiya gami da tabbatar mishi da zuwanta a goben da kuma kudin aikinsa. Daga haka suka rabu.    Washegari Iklima tana ji tana gani su Mami nata shiryen-shiryen tafiya. Rahila da Aisha suma nan suka zo, dan Aisha, Tahir ya yi wayo sosai. Rahila da yaranta biyu itama, Bintu da Samir wanda shine karami yana da wayo sosai, cikin ikon Allah bai mance fuskar Ummi ba, hakanan ya yarda ya je hannunta. Ko kusa Ummi bata da matsala da Rahila da Aisha, babu ruwansa, sannan basu fiye zuwa gidan ba face da babban dalili. Wannan ne dalilin da yasa basu san wainar da ake toyawa ba, a wannan zuwannasu ne ma ta tsincesu a dakin Ihsan tana faman labartamusu komai harda tafiyar Adnan Abuja. Aisha da mamaki tace "Haba, shiyasa kwana biyu banga keyarsa a gidana ba, ashe baya garin. Bakomai, komai zai wuce."   Abinda ta tsinkaya kenan ta dauki kayan Fahad da Mami ta aiko ta dauka ta fice daga dakin.    Nan su kuma sukayita jajantawa har saida Mami ta gaji ta soma fadan zata tafi ta barsu sannan suka fito.     Kai tsaye gidan kakansu suka nufa wato Alhaji Atiku Modibbo inda anan zasu hadu har Hajiya Mama da iyalanta su wuce Abujan. Tafiyar har da Innarsu. Suka yi sallama suka bar dan tsoho daga shi sai yan aiki da wani dan uwansa na Adamawa suka kama hanya. Ummi na rike da Samir a gefen Antinta Amina suna shan hira, kowa a Bus din abinda ya shafeshi yakeyi, Mami kuwa su uku ne a mazauninsu, ita da Hajiya Mama da Innarsu sai hira sukeyi. Nan ma Ummin ke labartawa Amina kazafin da akayimata, Amina abin ya yi mata ciwo saidai fadan da yafi karfinka...  Har dai suka isa kowa da abinda yasa gaba kafin a karshe a gaji ayi shiru.    Amina da Ummi wadanda basu ta6a takowa Abuja ba, suka saki baki suna kalle-kalle. Har suka isa gidan Gen. Ahmad Danzaki inda anan kallo ya koma sabo dal. Suka saki baki suna k'arewa haduwar gidan kallo. Wannan ko a Turai ne sai hakan. "Aljannar Duniya." Abinda Amina ta fada kenan cikin rada yanda Ummi kadai ce zata ji. Sukayi 'yar dariya. "Bari Anti, basu da matsala a fannin kudi."   Amina ta jinjina kai. "Tabbas." Direban ya hau hon, maigadin da sauri ya budemusu kofa yana washe baki gami da dago hannu yana musu lale marhabin.  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 43    Yana daga samansa yana dubansu da murmushi, ya karasa ga Adnan wanda bayan karin safe ya yi wanka ya cigaba da bacci ya kai mishi duka. "Tashi kaga wani abu." Adnan ya mike da sauri yana dubansa ido waje. "Sun iso?"   Faruk na murmushi ya ja hannunsa zuwa barandar. Ihu ya saki wandq har saida su Mami da suka riga suka fito suka kallo shi, dariya suka sanya. Da gudu ya fira ya sauka garesu. Shima Faruk ba shi da za6in da ya wuce na bin bayansa.  Adnan ya kama hannun Maminsa tamkar ya rungumeta don murna.     Baraka da Ikram a guje suma suka fito har Hajiya Babba wacce ta kasa hakurin k'arasowar yan uwannata ciki. Ta rungume Innarta, su Amina da Ummi suka zagaya domin kwasar kaya.    Tana janye da katuwar jaka, idanunta ya sauka akan Faruk, yana gefe ya hard'e hannuwansa yana zabga murmushinsa mai burgewa. Sanye ya ke cikin kananun kaya, riga bak'a anyi rubutu da farin abu, wandonsa ma bak'in ne, ya yi kyau har ya gaji da had'uwa. Cikin sa'a idanunsa ya kai kanta sa'ilin tuni sauran sun kama hanyar cikin gidan. Murmushi ya sakarmata, itama ta tsinci kanta da mayarmasa da martani har(dimple) dinta na dama  na bayyana. Ya ji wani abu da bai ta6a ji ba na tsirgashi, ya kauda kansa gami da soma tafiya zuwa ciki. Tana jan akwatin tamkar bata so sanadin kallonsa da take yi, namiji mai aji kenan, ina ita ina shi? Ta sauke ajiyar zuciya ta dubi gefenta jin alamun mutum. Amina ce itama rik'e da katuwar jakar Hajiya Mama tana dubanta cikin nazari, sai kuma bayan sun hada ido ta sakarmata murmushin yak'e. "Muje mana naga bakya daga kafa ne." Ummi ta gyada kai ta k'ara sauri. Amina mamaki kwarai takeyi na irin kallo da murmushin da ta ga Faruk na jifan Ummi da shi, da kuma kallon da Ummi ke bin bayan Faruk din da shi har ya illata tafiyarta. Ta numfasa, 'Idan ma akwai wani abun ya zama dole nasa ido na gano, bazan bari Ummi ta jefa kanta cikin matsala babba ba, ina mata kallon kanwata kamar ta jini.' Ta ayyana a ranta. Da taimakon yan aikin Hajiya Babba aka shishshigar da kayan gaba daya ciki.    Tsarin gidan Hajiya Babba wane sauran gidajen yan uwanta, iyakar haduwa ya had'u. Kayan duk ansaka a inda ya dace, Ummi da Amina daki guda aka hadasu wanda duk na yan aiki ne, yana daga can bayan(garden) din gidan.      Hira ta k'i ci ta k'i cinyewa tsakanin yan uwan, dakyar sukayi wanka suka chanja kaya sannan aka gabatar da sallar la'asar akayi zaman cin abinci. Alokacin kuma Haidar da Intisar suka shigo. Da gudu suka rungume juna ita da Ihsan sannan ta koma ga iyayen kowanne ta hau rungumarsa don dadi.    "Wai ke bakya girma ne?" Cewar Hajiya Mama kenan alokacin da ta rungumota.    "Kema dai kya fad'a Sadiya, yau kam dole kiban mijina tunda na iso." Cewar Inna kenan.   "Ahaf, mai zuwa gidanmu sai ya shirya fa." Fadin Haidar kenan, akayi dariya gaba daya. Su Faruk na daga falo suna jiyo caftarsu, shima Haidar bayan gama gaisuwa ya komo wajensu ana hira. Faruk kusan hankalinsa ya kasu biyu, hakanan ya ji yana d'okin ganin daga inda Ummi zata 6ullo, fatansa ya k'ara cin karo da kyakkyawar fuskarta. Da zarar ya soma tunaninta, sai ya yu saurin kwa6ar zuciyarsa, aganinsa babu wani dalili da ya ke da shi da zai dunga tunanin wata can. Abu ne da tun da ya ke a rayuwa bai ta6a faruwa gareshi ba.      Ita kuwa baiwar Allah, suna can tare da Amina suna cin abinci, saida suka kammala suka kai komai kicin. Alokacin ta fita wanka, bayan dawowarta itama Amina ta tafi wanko jikinta. Doyuwar riga ta sanya na kanti marar nauyi na yawon gida, itama Amina doguwar rigar ce jallabiya. Ummi ta dubeta taba daga rigingine saman katifa  "Anti ashe duk tsaruwar gidajen su Mami bai kama rabin k'afar na Hajiya Babba ba?"   Amina ta murmusa yayinda ta zauna gefenta. "Haduwa ma ba daya ba kedai, na ji ance fa har wajen wanka akwai(swimming pool)."   Ummi ta zaro ido. "Haba?" "Wallahi a bakin su Anti Intisar na ta6a ji, ba don ma kada muyi laifi ba da mun zagaya gidan." Ummi ta amsa. "Wallahi kam, zanso ganin wajen wankan kuwa."   Haka sukayita hirarrakinsu, Amina na son yi mata magana akan abinda ke gudana tsakaninta da Faruk, tana kuma tsoron kada ya kasance zarginta ne kawai, wannan yasa ta barwa zuciyarta.      Sun sakankance suna hira har Ummi ta soma lumshe ido na jin bacci, ganin haka Amina ta kyaleta. Cikin baccin kuma ta ji ana tashinta, ta mike zaune tana murza idanu. Ta yi mamakin ganin lokacin Magriba ya taho. "Ki tashi magriba fa ta yi, an turo a kiramu ma sai ni na je nayi aikin." Cewar Amina wacce ke kokarin gyara hijabinta bayan dauro alwala da ta yi. Da sauri ta mik'e ta fita zuwa bandaki domin dai bandakin yan aiki mata guda daya ne kuma ba cikin dakuna ya ke ba, yana daga dan lungun dakunan. Ta iske yan aiki biyu na alwala, ta gaishesu. "Kece Ummi?" "Eh." Ta amsa da murmushi. Suka saki baki. "Kema kuma yar aiki ce?" Ta gyada kai don ta soma mamakin tambayar.    Daga haka ta wucesu ta shiga bandaki. Tana jiyo hirarsu, daya na fadin. "Kinsan Allah Binta, da ace ni na samu kyawun wannan ba zan bautawa wasu a aikatau ba, na gwammace na ci duniyata da tsinke."   Bintar ta ja tsaki. "Kedai matsalarki Sa'a kina da son maza kamar wata karya wallahi. Nayi zaton ma batun aure zakiyi."   Sa'a ta ta6e baki. "Aurena biyu ban ji da dadi ba, don haka ko marmarin k'ara yi bana yi."   Lokacin Ummi ta fito sukayi shiru, ta isa ga famfon dake a gefen garden din inda suke tsaye ta soma alwala suna kallonta, suka saki baki ganin har wata suma take da a goshinta ga gashi daidai misali, ita dai ta samu ta kammala a gaggauce, ta yi musu sallama ta tafi da tunani hali irin na wasu mutanen da suke da karancin godiya ga Allah, wasu suna can ma basu samu koda rabin yanda su suka samu ba.   A haka ta shiga ta tarar har Amina ta idar da sallar tana addu'o'in da ta saba. Itama ta zura hijab ta tayar, bayan idarwarsu suka yi zaman hira anan take ji daga bakin Amina cewa su Haidar ma sunzo. "Mai yiwuwa suma sauran ki gansu." Amina ta karasa.   Ummi ta bata labarin hirarsu Sa'a akanta, Amina ta dara. "Mata kenan, muna da matsala wallahi. Mudai mu kama kanmu babu ruwanmu da harkarsu idan ba gaisuwa ba da hirar da bata shafi kowa ba.      Suna nan Sa'a ta lek'o. "Ummi, Anti Aisha na kira." "Toh." Ta mike cikin sauri ta gyara zaman hular kanta.     Ta fito tana waige-waige don har ga Allah ta mance yanda tsarin gidan yake. Ta karasa wajen doguwar baranda wacce akwai bene daga wani loko, ta yi shiru, ta cigaba da tafiya, wata kofa ta gani makamanciyar wacce suka shigo, hakan yasa ta bude kofar, kawai sai ganinta ta yi a wajen (pool). Daga tsakiya ya ke, a gefensa rumfa ce aka sanya kujerun zama, wani murmushi ta yi don sosai wajen ya burgeta. Ta rufe jin kamar motsi ana saukowa daga bene. Tana shirin barin wajen suka yi kici6us da Adnan. Kowannensu ya saki fuska.    "Lah, daman dake aka zo?" Ta yi dariya. "Eh, kana murnar ganin Mami baka lura ba."   Ya dara shima. "Bari kawai, ai nayi kewarku wallahi. Ina za ki ne?"    "Kaga hanyar na rasa, Anti Aisha ce ke nemana."   Yana dariya ya soma tafiya. "Ke kam ba dai saurin mantuwa ba, biyoni ki gani."  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    44   Ta bi bayansa kuwa, ta yi mamakin ganin ashe ba wata doguwar tafiya bace, ya bude kofa suka shiga babban falon Hajiya Babba. Wani kamshi sassanya ya bugi hancinta har tana sauke numfashi, kunya da nauyi suka cikata domin falon babu kowa sai samarin da su Baraka da matan yayyun ana hira da dariya. Tun shigowarta ya jefeta da kallo daya ya kauda kansa duk a kokarinsa na yak'i da zuciyarsa game da ita. Ya maida hankali ga Ihsan wacce ke faman yi mishi surutu ko kusa bai fahimtar inda ta dosa ma. Ta russuna ta gaishesu da tattausar murya, suka amsa. Anti Aisha bata falon, hakan yasa ta yi karfin halin tambayar Ihsan. "Ihsan, ina Anti Aisha?" Ihsan ta yi tamkar bata ji ba don haka kawai ta tsani ganin Ummi awajen yaran Hajiya Babba, ta rasa dalili don ko Amina bata jin hakan akanta sai ita Ummin.    Faruk ya zubawa Ummi fararen idanunsa, ta kauda kai. Alokacin ne Adnan ya bata amsa. "Tana sama ina ji, jeki ki duba." Ta dubi hanyar saman, to wane dakin zata dosa ne?   "Tashi ki rakata." Ta tsinci muryar Faruk sadda ta ke kokarin mik'ewa, sauran yayyun hankulansu naga hirar da sukeyi suna tuntsirar dariya.    Ta soma tafiya ta ji Ihsan ta bangajeta ta yi gaba da fadin. "Ki biyoni."   Ta jinjina kai ranta na suya saidai babu halin tankawa, haka tayita binta tamkar rak'uma. Ya kasa kauda kai daga gareta har saida ta 6acewa ganinsa kafin ya juyo kansa sukayi ido hud'u da Jidda matar Dr Ridwan. Ta daga mishi gira kadan  "Ya akayi? Akwai fa wani abu." Faruk ya yamutse fuska. "Kefa matarnan kin samin ido wallahi."   Yan uwan sukayi dariya. Jidda ta dubesu. "Na gayamaku ai akwai wani abu tsakanin wannan kanin naku da Ihsan kun k'i aminta, bakuga irin kallon da ya bita da shi ba yanzu." Faruk ya dubeta duban rashin fahimta.   "Ihsan kuma? Please karki jawomin raini mana."   "Wane raini anan? Kaidai fadi gaskiya Malam, irin wannan kallon ba'a yinsa sai ga wanda ake tsananin so. Da idona fa na kamashi."   Haidar ya kai mishi naushi a kafad'a yana dariya. "Kyalemin kanina Maman Ma'aruf, idan ma hakan ne da bakinsa zai fad'a ai."  Takaici ya ishi Faruk, ga shi a gaban kannensa ne kada su rainashi, ya watsawa su Baraka wani kallo, ba shiri suka mike har Intisar sukayi sama. Ai kuwa yayyun suka kwashe da dariya.    "Aa, ya zaka korarmin matata?" Faruk ya shagwa6e murya. "Wai ni menene haka don Allah? Kun ta6a ganina da wata nace ina so ne da za a takuramin?"   "Munfi kaunar ka ce din ai k'anina, akan ka zauna kana kallonsu tamkar wani dutse."   Cewar Haidar cikin rad'a. Faruk ya lumshe ido ya bude alamar gajiyawa da jin zantukansu, mikewa ya yi tsaye.   "Please stop this, ku rufamin asiri ma kada ta ji  raini ya biyo baya."   Daga haka ya bar wajen. Suna kiransa amma ko waige. Adnan dake kallonsu ya riga ya gano wacce bestinnasa ke kallo ya kuma fahimci lallai akwai abinda Faruk ke 6oyewa a ransa, watakil ma bai fahimci komai ba har zuwa yanzun.            Acan kuwa Ummi goyon Tahir aka bata, daga nan aka hadata da kayan wankinsa ta sauko.     Babu wanda ya damu da kallonta haka ta wucesu zuwa sashensu goye da Tahir a bayanta wanda baikai ga yin bacci ba. Tazo wucewa ta hanyar da ta biyo ne ta hangi kofar nan ta wajen pool a bude. "Ya akayi na manta ban rufe ba?" Fadin haka yasa ta nufar wajen don rufewa. Ta hangi Faruk zaune saman kujerar wajen ya jingina kansa jikin kujera, jin alamun mutum yazo wucewa ne yasa shi waigowa batare da ya raba kansa da jikin kujerar ba. Ya dubeta, da sauri ta saki kofar ta juya don barin wajen. "Kina neman wani abu ne?" Ya kira sunanta a hankali, gabanta ya hau dukan tara-tara ta juyo a gigice ta amsa da "A'a, kayi hakuri na dauka dazu ban rufe ba shine nayi niyyar rufewa yanzun."   Ya tsaya kawai yana k'are mata kallo, itama kuma ta juya har lokacin bata da nutsuwa ta fice da sauri. Ya numfasa gami da shafar sumar kansa. "Ya Allah, wannan wane irin yanayi ne? What's about to happen?"   Ya fada a fili.... Duk iyaka tunaninsa bai fahimci komai ba hakanan ya share zancen, bai mik'e daga wajen ba sai da ya ji ansoma kiraye-kirayen sallar isha'i.   Bayan an idar suka ci abinci da yan uwansa sannan kowannensu ya kama hanyar gidansa bayan an gaisa da Daddy.    Washegari 'yan Adamawa da wasu da yawa daga dangin Daddy na Kano suka iso. Gidan ya cika kwarai kasancewar wannan ne bikin 'ya mace na fari a gidan, sauran duk maza ne. Su Ummi kam babu ta hutu, sune wancan sune wannan, haka suke wuni aiki. Daga rainon yaran su Rahila sai taimakawa wajen wanke-wanke.    Ranar Asabar aka soma biki inda aka sanya Baraka a lalle. A ranar dai kuma za'ayi kamu, a katon filin farfajiyar gidan akayi, wajen ya tsaru matuk'a sai ka rantse cewar ba a gidan bane. Kwalliyar fari da golden aka yiwa wajen, Amarya Baraka ita kuwa ta fito cikin farin leshi, nad'in kanta kuma kalar golden. Yanmatan kaf din su doguwar riga sukayi (golden), iyaye ne kowa yasa ra'ayinsa. Ummi ta had'e itama cikin wani jan leshi da Mami ta yi mata kyautarsa acikin kayan Ihsan, ta yi kwalliyarta daidai misali har da kwalli a idanunta, duk da hakan ba k'aramin kyau ta yi ba. Amina ita kuwa yadi kore ta saka mai adon fulawoyi. Suna daga can kujerun baya, Ummi na rungume da Tahir tana aikin raino. A haka suke kallon komai. Babu abinda ya burgeta kamar(step-dance) wanda Ihsan, Maryam (mai bi wa Intisar 'ya ga Hajiya Mama), Rukayya (mai bi wa Maryam) da kuma Ikram sukayi na wata wak'ar turanci (Looku-looku) sukayi. Sunyi shigar riga da wando, Ihsan da Maryam kuwa a maza suka fito. Abin ya yi kyau matuka kuma ya burge har ihu da tafi ya cika wajen, ga baibayesu da akayi ana daukar hotuna da bidiyo.     Ifice-ificen ne ya hana Tahir nutsuwa, ya hau canyara ihun kuka. Duk iyakar rarrashin da sukayi mishi ita da Amina ya k'i nutsuwa. Amina ta dubeta. "Ko za ki kaishi wajen Mamanshi?" Ummi ta hangeta can sai harkar gabanta ta ke yi, ta girgiza kai. "Bari na dauko zani na goyashi mugani."   Amina ta harareta. "Haba dai goyo, kinga kyan da riga da siket din ya yi miki kuwa? Don Allah kar ki soma goyon nan za ki 6ata kwalliyarki." Ummi ta yi dariya, ita bata ga wani kyau da ta yi ba da suke faman zuzutuwa. Yanda Tahir ke zillewa yasa ta maida hankali gareshi.   "Oh  Allah, Anti bari mu dan bar wajennan ko zai nutsu."   Amina ta maida dubanta ga abinda akeyi. "Jeki ina nan kallo bazai wuceni ba tunda ke kam bakya jin shawara."   Da murmushi saman fuskar Ummi, ta yi gaba ta kyaleta.     Can wajen(garden) ta nufa tana faman jijjigashi, har lokacin bai gama rufe baki ba, zama ta yi a daya daga cikin kujerun dake a lambun.  "Oh Tahir, don Allah ka yi shiru kaga kallo ya barni saboda kai ko?"    Kamar ya ji abinda ta ce, ya hau kallonta yana faman sheshsheka irin na wanda yaci kuka, ganin haka yasa ta nufi hanyar dakunansu don 6ulla zuwa kicin ba shi ruwa.  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 43    Yana daga samansa yana dubansu da murmushi, ya karasa ga Adnan wanda bayan karin safe ya yi wanka ya cigaba da bacci ya kai mishi duka. "Tashi kaga wani abu." Adnan ya mike da sauri yana dubansa ido waje. "Sun iso?"   Faruk na murmushi ya ja hannunsa zuwa barandar. Ihu ya saki wandq har saida su Mami da suka riga suka fito suka kallo shi, dariya suka sanya. Da gudu ya fira ya sauka garesu. Shima Faruk ba shi da za6in da ya wuce na bin bayansa.  Adnan ya kama hannun Maminsa tamkar ya rungumeta don murna.     Baraka da Ikram a guje suma suka fito har Hajiya Babba wacce ta kasa hakurin k'arasowar yan uwannata ciki. Ta rungume Innarta, su Amina da Ummi suka zagaya domin kwasar kaya.    Tana janye da katuwar jaka, idanunta ya sauka akan Faruk, yana gefe ya hard'e hannuwansa yana zabga murmushinsa mai burgewa. Sanye ya ke cikin kananun kaya, riga bak'a anyi rubutu da farin abu, wandonsa ma bak'in ne, ya yi kyau har ya gaji da had'uwa. Cikin sa'a idanunsa ya kai kanta sa'ilin tuni sauran sun kama hanyar cikin gidan. Murmushi ya sakarmata, itama ta tsinci kanta da mayarmasa da martani har(dimple) dinta na dama  na bayyana. Ya ji wani abu da bai ta6a ji ba na tsirgashi, ya kauda kansa gami da soma tafiya zuwa ciki. Tana jan akwatin tamkar bata so sanadin kallonsa da take yi, namiji mai aji kenan, ina ita ina shi? Ta sauke ajiyar zuciya ta dubi gefenta jin alamun mutum. Amina ce itama rik'e da katuwar jakar Hajiya Mama tana dubanta cikin nazari, sai kuma bayan sun hada ido ta sakarmata murmushin yak'e. "Muje mana naga bakya daga kafa ne." Ummi ta gyada kai ta k'ara sauri. Amina mamaki kwarai takeyi na irin kallo da murmushin da ta ga Faruk na jifan Ummi da shi, da kuma kallon da Ummi ke bin bayan Faruk din da shi har ya illata tafiyarta. Ta numfasa, 'Idan ma akwai wani abun ya zama dole nasa ido na gano, bazan bari Ummi ta jefa kanta cikin matsala babba ba, ina mata kallon kanwata kamar ta jini.' Ta ayyana a ranta. Da taimakon yan aikin Hajiya Babba aka shishshigar da kayan gaba daya ciki.    Tsarin gidan Hajiya Babba wane sauran gidajen yan uwanta, iyakar haduwa ya had'u. Kayan duk ansaka a inda ya dace, Ummi da Amina daki guda aka hadasu wanda duk na yan aiki ne, yana daga can bayan(garden) din gidan.      Hira ta k'i ci ta k'i cinyewa tsakanin yan uwan, dakyar sukayi wanka suka chanja kaya sannan aka gabatar da sallar la'asar akayi zaman cin abinci. Alokacin kuma Haidar da Intisar suka shigo. Da gudu suka rungume juna ita da Ihsan sannan ta koma ga iyayen kowanne ta hau rungumarsa don dadi.    "Wai ke bakya girma ne?" Cewar Hajiya Mama kenan alokacin da ta rungumota.    "Kema dai kya fad'a Sadiya, yau kam dole kiban mijina tunda na iso." Cewar Inna kenan.   "Ahaf, mai zuwa gidanmu sai ya shirya fa." Fadin Haidar kenan, akayi dariya gaba daya. Su Faruk na daga falo suna jiyo caftarsu, shima Haidar bayan gama gaisuwa ya komo wajensu ana hira. Faruk kusan hankalinsa ya kasu biyu, hakanan ya ji yana d'okin ganin daga inda Ummi zata 6ullo, fatansa ya k'ara cin karo da kyakkyawar fuskarta. Da zarar ya soma tunaninta, sai ya yu saurin kwa6ar zuciyarsa, aganinsa babu wani dalili da ya ke da shi da zai dunga tunanin wata can. Abu ne da tun da ya ke a rayuwa bai ta6a faruwa gareshi ba.      Ita kuwa baiwar Allah, suna can tare da Amina suna cin abinci, saida suka kammala suka kai komai kicin. Alokacin ta fita wanka, bayan dawowarta itama Amina ta tafi wanko jikinta. Doyuwar riga ta sanya na kanti marar nauyi na yawon gida, itama Amina doguwar rigar ce jallabiya. Ummi ta dubeta taba daga rigingine saman katifa  "Anti ashe duk tsaruwar gidajen su Mami bai kama rabin k'afar na Hajiya Babba ba?"   Amina ta murmusa yayinda ta zauna gefenta. "Haduwa ma ba daya ba kedai, na ji ance fa har wajen wanka akwai(swimming pool)."   Ummi ta zaro ido. "Haba?" "Wallahi a bakin su Anti Intisar na ta6a ji, ba don ma kada muyi laifi ba da mun zagaya gidan." Ummi ta amsa. "Wallahi kam, zanso ganin wajen wankan kuwa."   Haka sukayita hirarrakinsu, Amina na son yi mata magana akan abinda ke gudana tsakaninta da Faruk, tana kuma tsoron kada ya kasance zarginta ne kawai, wannan yasa ta barwa zuciyarta.      Sun sakankance suna hira har Ummi ta soma lumshe ido na jin bacci, ganin haka Amina ta kyaleta. Cikin baccin kuma ta ji ana tashinta, ta mike zaune tana murza idanu. Ta yi mamakin ganin lokacin Magriba ya taho. "Ki tashi magriba fa ta yi, an turo a kiramu ma sai ni na je nayi aikin." Cewar Amina wacce ke kokarin gyara hijabinta bayan dauro alwala da ta yi. Da sauri ta mik'e ta fita zuwa bandaki domin dai bandakin yan aiki mata guda daya ne kuma ba cikin dakuna ya ke ba, yana daga dan lungun dakunan. Ta iske yan aiki biyu na alwala, ta gaishesu. "Kece Ummi?" "Eh." Ta amsa da murmushi. Suka saki baki. "Kema kuma yar aiki ce?" Ta gyada kai don ta soma mamakin tambayar.    Daga haka ta wucesu ta shiga bandaki. Tana jiyo hirarsu, daya na fadin. "Kinsan Allah Binta, da ace ni na samu kyawun wannan ba zan bautawa wasu a aikatau ba, na gwammace na ci duniyata da tsinke."   Bintar ta ja tsaki. "Kedai matsalarki Sa'a kina da son maza kamar wata karya wallahi. Nayi zaton ma batun aure zakiyi."   Sa'a ta ta6e baki. "Aurena biyu ban ji da dadi ba, don haka ko marmarin k'ara yi bana yi."   Lokacin Ummi ta fito sukayi shiru, ta isa ga famfon dake a gefen garden din inda suke tsaye ta soma alwala suna kallonta, suka saki baki ganin har wata suma take da a goshinta ga gashi daidai misali, ita dai ta samu ta kammala a gaggauce, ta yi musu sallama ta tafi da tunani hali irin na wasu mutanen da suke da karancin godiya ga Allah, wasu suna can ma basu samu koda rabin yanda su suka samu ba.   A haka ta shiga ta tarar har Amina ta idar da sallar tana addu'o'in da ta saba. Itama ta zura hijab ta tayar, bayan idarwarsu suka yi zaman hira anan take ji daga bakin Amina cewa su Haidar ma sunzo. "Mai yiwuwa suma sauran ki gansu." Amina ta karasa.   Ummi ta bata labarin hirarsu Sa'a akanta, Amina ta dara. "Mata kenan, muna da matsala wallahi. Mudai mu kama kanmu babu ruwanmu da harkarsu idan ba gaisuwa ba da hirar da bata shafi kowa ba.      Suna nan Sa'a ta lek'o. "Ummi, Anti Aisha na kira." "Toh." Ta mike cikin sauri ta gyara zaman hular kanta.     Ta fito tana waige-waige don har ga Allah ta mance yanda tsarin gidan yake. Ta karasa wajen doguwar baranda wacce akwai bene daga wani loko, ta yi shiru, ta cigaba da tafiya, wata kofa ta gani makamanciyar wacce suka shigo, hakan yasa ta bude kofar, kawai sai ganinta ta yi a wajen (pool). Daga tsakiya ya ke, a gefensa rumfa ce aka sanya kujerun zama, wani murmushi ta yi don sosai wajen ya burgeta. Ta rufe jin kamar motsi ana saukowa daga bene. Tana shirin barin wajen suka yi kici6us da Adnan. Kowannensu ya saki fuska.    "Lah, daman dake aka zo?" Ta yi dariya. "Eh, kana murnar ganin Mami baka lura ba."   Ya dara shima. "Bari kawai, ai nayi kewarku wallahi. Ina za ki ne?"    "Kaga hanyar na rasa, Anti Aisha ce ke nemana."   Yana dariya ya soma tafiya. "Ke kam ba dai saurin mantuwa ba, biyoni ki gani." DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 45   Yana saukowa daga bene, tana tahowa, ta ji numfashinta na barazanar daukewa tsabar had'uwar da ya yi. Ya gama hadewa cikin kufta bak'i wanda ya sha aiki dinkin riga da wando, ya sanya hula, sanyawa na musamman don kuwa ya zauna dabas a kansa. Takalminsa bak'i sai shek'i yakeyi. Bak'in gilas ne a idanunsa bazaka iya tantance inda ya ke kallo ba, saidai jikinta ya bata ita din ya ke kallo shima.    Kamar kuwa tasan hakan, domin babu abinda Faruk ke kallo irin tsarin halittarta. Yarinya cikakkiya, da ace ta samu jin dadi fiye da wanda ta ke ciki da babu abinda zai hana tsantsar zubin halittarta fitowa fili. Ya kai kallonsa ga le66anta masu surkin bak'i da ja wanda hakan ba karamin k'awata siririyar fuskarta ya yi ba, ya lashi nasa le66an gami da kauda kai daga kallonta. Itama ta yi niyyar wuceshi sai kuma ta hango rashin dacewar hakan, wannan yasa ta tsayawa har ya karasa saukowa sannan ta durkusa ta gaisheshi.    Ya amsa yana mai kai hannu da niyyar kar6ar Tahir. Ba musu ta sakarmishi shi. Cillashi sama ya hau yi yana mishi wasa, nan yaro ya hau dariya. Ita kuwa batasan ya akayi ta tsinci kanta da sakin baki tana mai dubansa ba. Wani irin kyau ta ga ya yi mata musamman yanda fararen hakoransa suka fito yana dariya.    Ganin zai kallota ne yasa ta saurin sunkuyar da kanta. Babu kowa awajen domin gaba daya suna can wajen taro, ya durkusa kamar yanda itama ta ke a durkushen. Gabanta ya cigaba da lugude har da surfe(lol), wani kamshi na turaruka ke bugun hancinta wadanda suka kashemata jiki.    "Kinyi kyau." Kasa gaskata abinda kunnuwanta suka ji ta yi, hakan yasa ta dago ta dubeshi, ya cire gilas din idanunsa, ya zubamata ido da murmushi a saman fuskarsa. A rud'e ta ke waige-waige babu wanda ta gani domin dai ba'a fiye zuwa wajejan ba matukar ba wani abu babba ne ya taso ba, sai ko su din dake kwana a dakunan wuraren. Mikewa ta yi niyyar yi ba zato ta ji ya rik'e hannunta ya maidata durkuson sannan ya saki hannun yana jifanta da kallo fuskarsa dauke da mamaki. "Wai ban hanaki wannan tsoron ba? Na lura ni kadai kike tsoron ma, ko bakyaso ina shiga harkarki? If yes ki sanarmin sai na daina."   Ummi fa kiris ya yi saura ta saki fitsari, ta dubeshi da idanunta wadanda suka kawo ruwan kwalla amma basu kai ga zuba saman fuskarta ba, sai kuma ta kasa jure kallon kwayar idanunsa mai k'ara jefeta cikin tsaka mai wuya.   Ya mike tsaye. "Rik'eshi." Da sauri ta kar6i Tahir a hannunsa domin dai Allah-Allah ta ke kira a ranta don ya kyaleta ta wuce. Ta rasa sabon lamarin da ke shirin 6ullowa tsakaninsu. Ya maida gilashinsa, ya dubeta da murmushi saman fuskarsa. "Ke kam ko ni saurayinki ne sai haka. Bansan sadda tsoro da kunya ya shiga tsakaninmu ba alhalin ba shiga harkarki nake yi ba. Yanzun ma dalili ne ya yi dalili." Ta dubeshi cikin neman karin bayani, ya daga mata gira yana murmushi da gefen kumatu. Kamar mai rad'a, ya furta "Bye." Daga haka ya k'ara gaba.    'Meyasa ya na jin kansa mai aji idan yana gabanta ne wai?' Wannan ne tambayar da ya cillawa zuciyarsa alokacin da ya ke nufar can bayan inda ake taron domin shiga motarsa ya bar gidan, duk iyakar tunaninsa, ya kasa tunano komai, sai lokacin ya ke jin haushin abinda ya ke yi, ya ja guntun tsaki ya bude motar ya shiga gami da barin gidan.     Acan kuwa Ummi ta shiga yanayi mai wuyar fassaruwa, wai yau itace Faruk ke yiwa haka? Kodai yana jin yanda ta ke ji ne? Tasan ba wani so bane, kawai dai jikkunansu da zuciyoyinsu na chanja yanayi duk sadda suka ga juna ba don wani abun ba, hakanan kawai dai. Shine abinda ta ayyana a ranta.      Koda ta koma Amina ta nemi sanin dalilin jimawarta, fakewa ta yi da fadin dakyar ya yi shiru. Har taron nan ya watse, babu wani chanji daga yanayinta na sanyin jiki da yawan tunanin abinda ya kere ta, yafi karfinta gaba daya ma.                      ***   ***   ***                      KADUNA   Zaune suke tare da Munira suna faman hira, a haka Deen ya sanyo kai ya iskesu, kamar yanda Munira ta saba, mik'ewa ta yi ta isa gareshi ta taroshi, ya bata kyakkyawar runguma da sumba a kunci. Wani abu ya tokarewa Dija wuya, abin kuma kamar da gayya Deen keyi don ta tabbatar koda bata furta ba, to fa ya fahimci manufarta akansa. Ganin basu ko kula da ita ba, yasa ta amfani da hannu ta tunkude kofin tangaran din dake saman tebur, ji kake taratsatsa. Hankalinsu ya yi saurin zuwa gareta, ita kuwa ta hau salati tana fadin "Wayyo, ina shirin mik'ewa ne bansan na ta6ashi ba." Munira da sauri ta karasa gareta. "Sannu yar uwa, ba ki ji ciwo ba? Lanto! Lanto!" Ta juya ta soma kiran yar aikinta domin ta tattara wajen, Deen kuwa wani kallo na kina sani ya hau watsawa Dija, wani murmushi ta sakarmishi, ya hade girar sama da ta k'asa ya bar wajen zuwa dakinsa.    Tun daga wannan ranar ta ke faman tsiro da sirfa kala-kala musamman ma idan dare ya yi ta ce bata da lafiya Munira ta yita zirga-zirga kenan zuwa wajenta itama da bata gajiya.     A gefe kuwa, ga Raihana wacce ta matsamata da waya da kuma ta whatsapp akan zata iya rasa rayuwarta muddin bata amince da bukatarta ba. Akwai sadda ta budemata wuta ta nunamata ita yanzu haka akwai namijin da take mutuwar so amma ta kasa shawo kansa ya kaunaceta. Raihana ta aikomata audio tana dariya. Ta tabatar mata ko waye shi muddin ta amince da ita to ita mai yi mata komai ce don ta mallakeshi kuma ya aureta a sauk'ak'e.    Jin haka yasa Dija kiranta kai tsaye bayan ta rufe dakin gam. "Me kike nufi?" Acan Raihana dariya ta yi. "Wallahi muryarki dadi."   Banzan tsaki Dija ta ja, batasan ya akayi ta bawa yar uwarta mace wannan damar ba, fatanta dai a yanzu ta samu Deen don gaba daya idanunta a rufe suke. "Kinga don Allah ki sanarmin idan da gaske kike." Ganin haka yasa itama ta nutsu. "Wallahi muddin za ki amincemin babu abinda za ki rasa a duniya Dijat. Kedai ki yarda na zo inda kike kigani." Dija ta girgiza kai. "Ki soma yimin aiki akan Deen idan na aureshi na rantse miki da Allah komai kikeso kin samu." Ta karashe a tsorace.     Wani ihun dadi Raihana ta saki gami da mannawa kan wayar kiss. "Angama wallahi, Zahraddeen sunansa ko? Karki damu, yau dinnan zan kira Malamina na ji yanda za'ayi." "Dakata (please), ki san sunan da za ki kai, kada ki cutar da ni ta hanyar asiri."   Raihana ta marairaice murya tamkar da wani saurayi ta ke maganar. "Ba cuta tsakanina da ke don ina sonki. Ki rike wannan." (Wa'iyazubillah)       Dija ta murmusa ji ta ke yi inama Deen ke gayamata hakan ba jinsinta ba.    "Nagode sai na ji ki." Daga haka suka rabu.      A sati daya kuwa komai ya kammala, Raihana ta aikomata sak'o ta hanyar wata abokiyar ashararancinta da ke a Kadunan. Itama ta so ta latsa Dija ta ga ba fuska sannan Raihana ta gargadeta akanta kafin ta zo. Koda Munira ta tambayi Dija wacece, cewa ta yi kawarta a yanar gizo. Munira sam hankalinta bai kwanta ba da budurwar don da gani kasan yar duniya ce, haka ta yita yiwa Dija nasiha akan ta kula da wadanda zata dunga kulawa a yanar gizo, wasu da yawa 6ata gari ne. Ta amsa da to kawai. Ta kudurta a ranta sai ranar weekend zata soma amfani da turaren, na wanka kuwa a daren ta yisu. Na zubawa a abinci shima sai ranar da ba aiki.                        ***   ***   ***                       ABUJA Ranar da ya kama na yini da(mother's day) ranar akayi sanya ankon atamfa mai fari da bulu. Sunyi kyau matuk'a. Gaba daya abin ya burge, sai bayan magriba kowa ya soma shirin tafiya wajen fatin. Abin nasu ya yi kyau matuka, su Ummi a gida aka barsu rainon yara, har saida suka yi hira suka gaji suka soma gyangyadawa sannan suka soma dawowa. Alokacin suka koma dakinsu suka kwanta.     Washegari kuwa tun asuba basu koma bacci ba, suna kicin suna dirkar aiki na hada karin kumallo. Sai wajejan tara suka kammala komai suka mik'amusu.    Wajejan sha daya na safe sunyi wankansu tsaf, Aisha ta hada Ummi da wankin Tahir. Haka ta kar6a don ba ma su yawa bane sosai.  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   46    (Sadaukar ga shafin nan gareki sisna...forgive me... Meena Yoruba) Wajen garden inda ta ga anan suke wanki da shanya ta zagaya ta soma yi. Tare suke da Amina suna hira inda Amina ke labartamata batun aurenta da ya taho, Sa'a ta zo ta sanarwa Amina kiran Hajiya Mama. Wajen ya rage Ummi kadai cike da tunanin duniya.  To ita meyasa bata ta6a jin son wani ba ne? Ga dai maneman suna tururun zuwa har da yaran manyan dake layin makarantarsu masu son ta kulasu saidai ko kad'an babu wanda ta ta6a saurara, maganar Antinta ta fad'omata a rai. "Kema auren nan ya dace kiyi Ummi, shi kadai ne jin dadinki, ki tara zuri'ar kanki."    Abinda tace mata kenan a wannan hirar da sukayi. Ta girgiza kai tana duban wani dan lilo dake a wurin.   'Babu wanda nake so a raina yanzu Anti.' Ta ayyana a ranta. Haka ta k'arasa wankin ta mik'e ta nufi wajen shanya, tana cikin shanyar ne ta ji sallamar mutum agefenta. Da sauri ta dubi wajen jin muryar namiji. Ta gane ko wanene duk da batasan sunansa ba, amman cikin bak'in Adamawa ya ke. Kana ganinsa shima kaga bafulatanin usuli, ta gaisheshi ya amsa da harshensa mai sirkin yare biyu(Hausa fulani).   "Sannu, ina daga can ina ganinki tun dazu ai, ya sunanki ne?"   Mamaki karara ya bayyana saman fuskarta, baiyi kama da saurayin arziki ba, yafi yin kalar 'yan duniya. Ta k'ara kare kirjinta da ya zubawa ido don kuwa doguwar rigar jallabiya ce jikinta kusan duk ta jik'e agarin wanki.  Murya na rawa batare da ta k'ara kallonsa ba ta amsa. "Ummi." Ya lura da abinda ta yi din sai kawai ya yi murmushin duniyanci ya shafi ha6ansa. "Wow, kina da suna mai dadi fa. Ni sunana Kabir but you can call me KB. Ke 'yar uwar su Daddy na Baraka ce?"   Ta girgiza kai don ta k'osa ya bar wajen. "Aa, ni 'yar aiki ce." Ya zaro ido da mamaki. "Yar aiki? Kike da wannan kyan?" Ya ta6e baki    "Gaskiyar magana bebi kin fi karfin zama yar aiki. Idan za ki ban had'in kai to zakiji dadin rayuwa son ranki."   "Innalillahi..." Ta karashe a fili. Zaiyi magana, Amina ta katse hirar ta hanyar gaisheshi. Suka dubeta don basusan ta iso ba, ya amsa ba don yaso zuwannata ba, ya wani tamke fuska gami da fadin. "Sai wani time din bebi, zan nemeki." Daga haka ya fice, da sauri Amina ta nufota gami da rike kafadarta a tsorace.   "Mene hadinki da Kb? Kinsan kuwa ko wanene?"   Itama Ummi duk sai ta k'ara rud'ewa. "Wallahi shi yazo nan yanamin magana." Ta zayyanemata yanda sukayi. Amina ta numfasa. "Nagode Allah da ba ki ce komai bayan wannan ba, ki yi kokarin nisantarsa, yaron dan iska ne fiye da tsammaninki. Akwai sadda ya ta6a zuwa gida Hajiya Mama basunan sai ni kadai, wallahi Allah ne kawai ya kwaceni daga hannunsa, ya so 6atamin rayuwa. Ki kiyaye Ummi, nasan halinki, ki k'ara akan wanda nasanki na tsare mutunci."   Ummi ta dubeta. "In sha Allah Anti zan kiyaye." Ta taimakamata wajen k'arasa shanyar sannan suka nufi ciki. Da gudu Sa'a dake la6e ta koma ciki. Kai tsaye dakinsu ta nufa kicin ta nufa inda Binta ke goge-goge ta fesamata yanda Kb da Ummi sukayi harma da nasihar Amina gareta. Binta ta ja tsaki. "Banza da ita, ta samu damar da muke nema ta yi watsi da shi, ji dai yanda ya nemeki sau d'aya kuma ya dawo ya juyamaki baya sai zagi idan ya zo kamar gidan ubansa."   Sa'a ta yi kwafa cike da jin takaici. "Bari kawai, ni su Ummin ma sunfi ban takaici su basu yarda ba masu tsoron Allah. Gulma ce dai, ta ciki na ciki."   Binta ta ajiye tsumman hannunta. "Ke, ga hanyar samun kudi wajen Kb. Mezai hana tunda ya ganta ya kyasa, mu kai mishi ita kinga kuwa ba karamin kud'i zai bamu ba." Sa'a ta yi shiru tana nazari, tasan Kb akwai sakin aljihu musamman akan mace. Ta dubi Binta suka kyalkyale da dariya sannan suka cafke. "Shegiya, kina ja wallahi. Bari zan sameshi a 6oye mu ji yanda zaayi."   Cewar Sa'a, Binta ta jinjina kai cikin gamsuwa.       Da yamma kuwa duk ana ciki ana shan kid'a da rawa kasancewar an daura aure kuma ba wani(event) da suka shirya zasuyi sai dinner wanda Ango ya shirya kayansa. Sa'a ta yi nasarar ganin Kb a farfajiyar gidan yana amsa waya can gefe, da sauri ta karasa wajensa tana fadin. "Yalla6ai." Ganinta yasa ya ja guntun tsaki ya daure fuska, saida ya kammala waya ita kuwa na waige-waige bata hangi wani mai ganinsu ba.  "Lafiya?" Ta dubeshi tanq murmushi. "Lafiya kalau, daman wata magana na zo maka da ita."   Ya daga kafada. "Ta mecece?"  "Dazu na ganka kana magana da Ummi, nasan kuma ka kyasa dw ita ne. Idan babu damuwa ni zan kawomaka Ummi, idan har ka yarda za ka biyani."   Wani sanyi ya ji a ransa, sai lokacin ya sakarmata wani shu'umin murmushi ya sosa kai yana duban farfajiyar gidan, babu wani mai kallonsu sai tsirarun ma'ikatan gidan dake harkokin gabansu.   "Idan kudi ne, kinsan bani da matsala da su. Kedai ki cika alkawari."   Ya kara dubanta fuska babu wasa. "Kada kuma ki kawomin rainin hankali idan ba haka ba kinsan sauran. Ki zauna cikin shiri, yau da zarar kowa ya tafi wajen(party) ki yi yanda zakiyi ki kawomin ita sashenmu, zan iya biyanki ko nawa ne."    Daga haka ya fiddo dubu biyu ya damk'a a hannunta.    "Ga wannan ki sanyawa wayarki kati, ai kina da lambata ko?" Ta gyada kai farinciki ya cikata ganin dubu biyu, wanda idan ta yi wayasan ko nawa zai bata.     "Eh akwai." Daga haka suka yi sallama fuskar kowanne a sake.       Faruk dake daga sama yana dubansu ta windo, mamaki ya cikashi, shi yasan wanene Kb, yasan kuma illarsa ga diya mace. Babban abin daure kan menene hadinsa da Sa'a? Ko har ita din ma akwai abu tsakaninsu? Ya girgiza kai cike da jin tsanar Sa'ar domin ita ta bada fuska. Ya juya ya koma falo cikin yan uwansa kusan sa'anninsa kuma bak'in Adamawa aka cigaba da hira kafin duk su fito waje don shan iska.       Misalin takwas duk an soma tafiya wajen party da zaayi a Nicon, su Ummi dai na tsaye a farfajiyar wajen sai kallon kwalliya sukeyi. Kowacce ka gani ji takeyi da kanta, duban kanta takeyi a had'add'iya. Wajen sai kamshi kakeji, matasan ma kuwa da alama har da samarin wasu cikin yanmatan. Duk wadannan ba su suka damu Ummi ba face ta inda zata ga 6ullowar Faruk. Shi kadai zuciyarta ta kwadaitu da gani batare da tasan tak'amaiman dalili ba.   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   47   Daga gefensu ta ji Ikram na balbale  Ihsan da fad'a. "Wallahi zakiyi asarar fatin yau matukar kika kafe sai tare da Yaya Faruk za ki je, idan ma kin shirya tafiya gwara tun wuri ki taho mu tafi don wallahi a yanda nasa halin Yaya Faruk zai iya cewa ya fasa. Mun tafi na daukarmaki komai a waya." Daga haka ta yi gaba. Ihsan ta yi saroro, ganin dai dagaske Ikram take yasa ta bin bayanta da gudu-gudu, abin sai ma ya bawa Amina da Ummi dariya.  "Wallahi yanzu lamuran Ihsan dariya sukeban." Cewar Amina. Ummi ta ta6e baki. "Ato, tunda ta maida kanta wata tsiya ba."     Saida suka ga tafiyar kowa amma basu ga na Faruk ba. Hankalin Ummi ya tashi, ranta ya sosu, ta so kwarai ta ga tafiyarsa, ta kwadaitu matuka da ganin kalar wankansa. Haka suka koma falon, iyayen daga Hajiya Babba sai Inna da wasu dattijai mata yan Adamawa ya rage, suna sama, suka tattara komai sannan suka wuce 6angarensu.   Suna zaune anan sai ga Sa'a ta shigo.   "Ummi, ki zo Adnan na nemanki."   Da mamaki ta dubi Amina. "Na dauka Adnan ya wuce." "Tabbas nima naga shigarsu mota."   Sa'a ta yi yak'e. "Dawowa ya yi, wai ki zo sak'o zai ba ki daga Mami."   Basuyi tunanin komai ba don babu wanda ya kawo Sa'a zatayi hakan cikinsu, Ummi ta mike da sauri yana gyara zaman daurin dankwalinta na atamfa, don sauri ko hijab bata tsaya sanyawa ba ta zura takalmi tana fadin. "Bari naje." Amina ta kishingida tana fadin. "Wash!" Gami da lumshe ido, Sa'a ta kunce gefen zaninta ta yi amfani da hodar da Kb ya bata ta wuce sadaf-sadaf ga Amina ta shek'a mata a hanci, Amina kafin ta yi wani yunkuri bacci ya sureta. Da sauri Sa'a ta bi bayan Ummi.    Ita kuwa Ummi kai tsaye waje ta nufa saidai bata ga mota ba, hakan yasa ta zuwa wajen fakin motoci nan ma bata ga mota ba sai guda daya, da alama da mutum ciki sakamakon kidan da ke dan tashi amma zuwanta aka kashe. Zata nufi wajen Sa'a ta karaso tana kiranta. Ta tsaya gami da juyowa. 'Yauwa ina Adnan din?"   Sa'a ta dubeta. "Yanzu na ganshi ya nufi sashensu, shima nemanki yakeyi." Ummi ta jinjina kai. "Munyi sa6ani kenan, bari na je." Da sauri ta nufi hanyar sashensu Adnan, Sa'a ta saki dariya yanda ba zata ji ba, ta bi bayanta.         "Adnan?" Ya furta a hankali, a iyakar saninsa Adnan baya nan sai Kb wanda ya bari yana shiryawa amma don tabbatarwa ya dauki waya ya dannawa Adnan kira, koda ya dauka ya tabbatar mishi yana farfajiyar wajen taron. Ya tsaya yana tunani, kada dai cutar Ummi zasuyi?   "Oh No!" Ya fad'a da karfi sannan ya fito daga motar cikin zafin nama.        Ita kuwa Ummi kai tsaye saman ta nufa ta hau kwankwasawa, aka budemata, ana budeww daga bayanta ta ji an hankadata cikin dakin sai jikin KB. Kafin ta kai ga duban wanda ya hankad'atan ta ji an rufe k'ofar har da sanya muk'ulli.    A gigice ta d'ago tana fadin. "Adn..." Maganar ta makale a fatar bakinta ganin Kb daga shi sai gajeran wando. Fisge jikinta ta yi da karfi jikinta ya soma rawa.   Ya soma nufota da murmushi yana shafar gefen fuskarsa.   "Helloo bebi."   Ta nufi kofa da sauri zata bude, saidai ga mamakinta ta ji kofar gam! Ya kamo k'ugunta yana dariya.   "O'o, guduna kikeyi?"    Ta fisge jikinta, tuni ta soma kuka tana ja baya.   "Don Allah ka yi hakuri ka kyaleni."   Ya jinjina kai. "Ki yarda da ni zan kyaleki." Ya cigaba da nufota tana ja baya. "Don ke na k'i tafiya wajen party fa Bebi."        Faruk na hayowa sukayi kici6us da Sa'a tana saukowa tana dariya, ganinsa yasa ta sakin ihu don tsoro, jikinta ya dauki rawa, tunda ta ke bata ta6a ganin Faruk a yanayin da ta ganshi yanzun ba, gaba daya idanunsa sun kad'a, fuskarsa tamkar bai ta6a dariya ba. Ya shak'o wuyanta, cikin kakkausar murya yace. "Ina Ummi?" Muguwar shak'ar da ya yi mata ne yasa muk'ullin dake rik'e a hannunta ya fadi don sunyi da Kb da zarar ya kammala zai nemeta a waya ta bud'esu, jin faduwar abu yasa shi kai dubansa k'asa. Da sauri ya dauka ya dago ya dauke fuskarta da lafiyayyun mari har biyu sannan ya nufi saman da gudu, tuni Sa'a ta gudu ta bar wajen.        Daidai lokacin da Kb ya rungumo Ummi da karfinsa na da namiji yana sumbatar wuyanta duk kuwa da irin turjiya da duka da cizo da ya ke sha, bai fasa abinda yakeyi ba, alokacin Faruk ya bude kofar ya hankadata ya shigo. Baiyi wata wata ba ya janyoshi ya wanke mishi fuska da mari. "Are you out of your senses?!!" Ya k'ara janyo ya kai mishi naushi a baki.    "Baka da hankali KB?!! Kazamin jikinka kake hadawa da na Ummina?!! Kayi kadan wallahi!!!"   Ya cigaba da bugunshi, Kb babu karfin haka ya yi ta jibguwa. Da dai Ummi ta ga yana shirin kisa a guje ta yi kansa ta shiga tsakani gami da rike kafadarsa a gigice tana kuka.   "Don Allah Yaya Faruk ka yi hakuri, ya isa ka rabu da shi."   Ya watsamata kallon da ya kad'a hanjin cikinta. Ya fisgi hannunta suka fita, bai tsaya ko'ina dq ita ba sai wajen(swimming pool) dinsu, wajen babu kowa. Ya saki hannunta ta fada gefe tana kuka sosai.   "Ga irinta! Ga irinta nan!! Yau da kina gaban iyayenki, wane shege ne zai shigo ya nemi 6ata rayuwarki..." Sai kuma ya yi shiru har lokacin cikin zafi ya ke, ya dauki kujera daya ya yi jifa da ita da karfi har ta 6alle. Ummi ta fahimci ya fusata, ko me za ta ce bazai ta6a fahimta ba, mutane nawa ne a gaban iyayennasu ake lalatasu, wasu ma ubannasu ne da kanshi? Ya zauna saman kujera ya dunk'ule hannu wuri daya gami da dafe goshinsa har lokacin bai huce ba, babu abinda ya ke hangowa sai Ummi a jikin KB. Maganarta ta katse tunaninsa.   "Wallahi bani da laifi, yaudarata sukayi." Daga nan ta labartamishi dukkan abinda ya faru, sai kuma lokacin ya dan samu nutsuwa duk da daman ya zargi hakan. Ta cigaba da kuka mai shiga zuciya. Ya kasa daurewa ya mik'e ya isa gareta gami da yin zaman durshen agabanta yana lankwashe kafafuwa. Ta dago idanunta jajaye ta zubamishi, shi dinma ita ya ke duba.     Sakonni kala-kala ta ke amsa daga gareshi duk da yanda idanunsa suka kad'a don 6acin rai, hakan bai hana ta ganin wasu abubuwa masu wuyar fassaruwa ba, masu kashe jiki ba. Shima awajensa ji yakeyi yau bazata wuce ba sai ya sanarwa Ummi abinda ya ke ji gami da ita, idan ta san amsoshin ta k'aramishi ilimi a kai.    Ta sauke idanunta tana tuna furucinsa na dazun. "Ummina."   Hannunsa ta ji a saman ha6anta ta razana don har lokacin fargaba bai barta ba na abinda Kb ya yi mata. Ya cire hannunsa da sauri don ya gani hakan. Ya fiddo hankicif ya mik'a mata.   "Share fuskarki, yau zan gayamaki abinda ban ta6a fad'awa wata diya mace a doron k'asa ba Ummi."   Ya yi magana tamkar mai rad'a, ta dubeshi, shima ya zubawa gashinta ido wanda ya tabbatar garin kwatar kai ta baroshi a can, ya maida kansa gareta yayinda ta ke bin umarninsa. Gabanta sai lugude ya ke yi, shiyasq bataso ta ra6eshi, don duk sadda suka hadu suka rabu, dakyar tunaninsa ke barinta ta sake.  Ya soma magana.....!    DAN ADAM @RUFAIDA OMAR     48   "Ummi shekaruna ashirin da tara a duniya, amma bazan ce miki yau ga wata mace da nakejin irin abinda nake ji ba akanki ga ita ba."   Ta dubeshi a matukar kaduwa. Ji ta yi kamar ta shid'e don tsoro. Idanunsa sam babu wasa sai ma wani kankancewa da suka k'ara yi yana mai dubanta duba na saurayi a gaban budurwar da ya ke mutuwar so tamkar numfashi.     "Yes, ki kalleni sosai Ummi, ina a cikin hayyacina ba wani abu na sha. Amsa za ki bani please, idan har kin sani, idan ma ba ki sani ba ki tayani nemowa." Hawayenta suka zubo tuni ta sunkuyar da kanta k'asa. "Ban ta6a runtsuwa batare da na tunaki ba tun farkon ganin da nayi miki a gidan Grandpa (Alhaji Atiku Modibbo), ban kuma ta6a jin faduwar gaba aduk sadda na tuna wata diya mace ba sai a kanki, ban kuma ta6a gajiya da kallonki ba Ummi. Kin ga nan." Ya yi nuni da kirjinsa, ta d'ago ido ta bi hannunsa wanda ya d'aurawa agogo na bak'in fata da zobunansa na azurfa biyu. Ta maida kanta ta sunkuyar har lokacin tsoro da firgici bai saketa ba. Faruk ya cigaba da magana tamkar ba muryarsa ba.   "Koyaushe kina cikinsa, bansan kuma dalilin da yasa har abada bana fatan fitarki a ciki ba. Na rasa amsar abinda nakeji akanki, na baki yau zuwa gobe, ki taimaka ki nemomin amsa, zan nemeki."   Ya yi shiru yana cigaba da kallonta ita kuwa ta kasa koda kallonshi. Har ta gaji da shirun ta dago ta dubeshi. Murmushi tattausa ya sakarmata wanda saida ta ambaci 'Subhanallah' a ranta adalilin kyawun da ya yi, bata ta6a ganin murmushi irin haka a wajensa ba, kallon ma na musamman ne Faruk ke jifanta da shi. Ta maida kanta kasa, ya daure fuska shima. "Ki k'ara kula sosai Ummi, KB dan uwana ne don d'a ne ga cousin din Hajiyata amma ban aminta da ki kara shiga huldarsa ba duk da nasan cewa wannan karon tilasta ki aka so yi, ita kuma Sa'a barin gidan nan ya zamto mata wajibi, yanzun ma ba don dare ya yi ba, da a yau sai ta bar gidannan."   Daga haka ya yi shiru, can kuma ya mik'e tsaye yana kakka6e jiki.   "Kinga kin janyomin chanja kaya, fatin ma ba zan iya zuwa ba zan yi tsaronki." Ita dai mamaki ya hanata cewa uffan duk da kalamansa sunyi mata dadi matuka saidai iyakar tunaninta ta kasa gano amsoshin tambayoyinsa. Hannun da ta ga ya mik'o mata ne yasa ta dubansa da sauri, murmushi ya sakarmata, wani yadi bak'i sidik yasa mai ratsin yellow, sai hula. Farar fatarsa ta fito ainun, ta mik'e batare da ta kama hannunnasa ba.   "Saida safe. Ki kara kula please." Bai kara sauraranta ba don yasan ba abinda zata ce ya juya ya fice domin zuwa kashe mota da kwaso wayoyinsa don dagaske ya ke jin tafiyar ta fice aransa. Ta bishi da kallo har ya 6acewa ganinta. Ta numfasa, sai kuma ta tuno abinda ya faru da ita yanzu, kai tabbas koda ta ji hirar su Sa'a bata ta6a tsammanin zata ci amanarta har haka ba ta yaudareta. Sai kuma ta tuno Antinta, ko me zata zarga akan dadewarta? Da gudu-gudu ta fito ta nufi dakinsu. Murdawa ta yi ta shiga, saidai kuma ta yi mamakin ganin Aminar na kwasar bacci, ta sauke ajiyar zuciya, watakil ta yi jiranta bata zo ba. Ta shigo gami da sanyawa kofar mukulli don gudun abinda zai kara faruwa da ita. Saida ta dauro alwala sannan ta rufe kanta ta kwanta lamo tana tunane-tunane.  A hankali kuma ta cigaba da kuka, ba don Allah Ya jefomata Faruk ba, da a yau kashinta ya bushe, da ta rasa mutuncinta na 'ya mace. Ji ta yi nan duniya ta tsani Kabir tsana tsantsa, shi kadai ne ya ta6a yin wannan yunk'urin a kanta, ta tuna sadda ya tsotsi wuyanta da sauri ta mike ta cire kaya ta je ta wanke jikinta don bai bar kamshin turarensa ba. Saida ta tabbatar kamshin ya bar jikinta sannan ta k'ara dauro alwala ta fito, saida ta yi nafila ta nunawa Allah godiyarta da Ya tserar da ita sannan ta yi addu'o'inta ta kwanta. Sai kuma sabon tunanin Faruk ya namayeta. Gani takeyi kamar a mafarki ba gaske ba, kamar kuma tana karanta litattafan hausa na soyayya da ake yawan yi na yan aiki da soyayya da dan masu gida. Ta runtse ido ta budesu, tabbas komai a zahiri ne, ya faru kuma a yau din, ga Faruk wai yana gayamata kalamai dad'ad''a har ya ke sanarmata yanda ya ke ji akanta bai ta6a ji akan kowace mace a doron k'asa ba.      Ta lumshe ido ta budesu don dadi, ya tabbata dai abu daya su ke ji.  A haka har bacci ya dauketa bata ankara ba.      Washegari har ta farka ta yi sallah Amina bata motsa ba, abin har ya soma bata tsoro, karshe dai itama baccin ta koma. Amina dai bata farka ba har sai da gari ya yi haske, kanta ya yi nauyi, lokacin Ummi tana bandaki tana wanka, a ranar ne zaa kai Amarya gidanta misalin karfe hud'u.    Ta yi shiru da son tuna abinda ya faru can kuma ta tuno yanda Sa'a ta shigo kiran Ummi, da kuma hodar da ta shak'a mata bacci ya yi awon gaba da ita. Ai da sauri ta mike ta fita kan babu ko kallabi.   "Ummi! Ummi!" Yan aikin basu nan sun tafi ciki don kama ayyukansu, Ummi na jin muryar Amina ta fito tana gyara mazaunin daura kirjinta don ta kammala dama.    "Anti kin tashi?" Amina ta waigo, ganinta yasa ta karasa a guje cikin tsoro tsantsa. "Ummi, na farka, gayamin ina Sa'a ta kaiki jiya?"   Ummi ta dubi hanya sannan ta kama hannun Amina. "Ki kwantar da hankalinki, ki yi sallah zan ba ki labari."   Ta tuna ko sallar asubahi bata samu damar yi ba, ta matsa Ummi ta wuce, sannan ta fada zuciyarta ta dan sanyaya ganin Ummin lafiya, amma tana son tarar Sa'a don ta ji nufinta.     Bayan ta idar ta dubi Ummi wacce ta ke sanya riga doguwa'yar kanti sabuwar da suka sayo, baki da orange ne adonta, ta yi kyau daidai gwargwado duk da ba wani kwalliya ta yi ba. Ta cigaba da addu'ointa sai bayan ta kammala ta shafa sannan ta juya ga Ummin.   "Ki sanarmin, meyafaru jiya?" Ummi ta soma bata labarin har tana zubda hawaye, itama Amina har hawayen saida ta zubar tana mai yin salati.    "Innalillahi... Wannan masifa da me ya yi kama? Ashe ba'a banza ba ta shak'amin hodar da ta fiddani a hayyacina." Ummi ta zaro ido. "Hoda kuma?" Amina ta ja majina ta share hawayenta. "Tabbas, hoda ta shak'amin duk don kada na yi wani yunk'urin, saidai batasan cewa ba Amina ke karewa ba, Allah Shi ke kare bayinSa kodayaushe. Wallahi tun farkon ganina da Yaya Faruk ya ke burgeni don alamu sun nuna yasan mutuncin DAN ADAM. Ba shi kadai ba, dukkan yaran Hajiya Babba haka suke. Ki k'ara yi mishi godiya Ummi don ba karamin taimako ya yi miki ba. Ita kuma Sa'a na tabbatar tunda har Yaya Faruk yace zai hukuntata, to babu makawa. Kb kuma ki k'ara nisantarshi, biki kuma ai ya k'are, nasan ba za mu k'ara kwana biyu ba za mu tattara mu tafi."   Ummi ta jinjina kai, tana son gayawa Amina yanda sukayi da Faruk saidai tana tsoron abinda zata ce, a karshe dai bayan fitowar Amina daga wanka ta daure ta soma labartamata abinda Faruk yace. Amina na shafar mai bata ko katseta ba, haka kuma fuskarta bata nuna wata alama ta razana ba. Bayan kammala bayanin Ummi ta saki murmushi.   "Ai daman nasan za'a rina!"   Shine abinda ta fada wanda ya yi matukar razana Ummi har ta kasa daurewa ta kalleta, Amina ta jinjina mata kai alamar tabbas dagaske ta ke.   "Eh, nasan ke da Faruk kuna SON JUNA, ganewa ne kawai bakuyi ba."   Ummi ta dafe kirji ta zaro ido. "So kuma?" DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 49 Amina bata k'ara kulata ba saida ta sanya kaya, ita kuwa ta yi mutuwar zaune kawai tana bin ta da kallo duk inda tasa k'afa. Sai lokacin ta dubeta. "Muje mu gaida su."   Ummi ta girgiza kai ta rik'o hannunta. "Wallahi ba inda za muje sai kin amsamin, me kike nufi da muna son juna?"   Amina ta dara ta koma ta zauna gami da cire wasa a maganganunta. "Ummi kina jin Faruk a ranki, daidai da kallon da ku ke jifan juna da shi abin a tambaya ne. Karki 6oyemin abinda na sani, kina son Faruk so na AURE. Hakazalika shima yana sonki, kuma ya sani nafi zaton gwadaki kawai yakeso ya yi ya ji ko ke din kina sonsa. Bar wannan batun, Faruk ya fi karfinki Ummi, ina gujemiki matsala. Wallahi na daukeki tamkar ciki daya muka fito, bana son abinda zai sa a ci mutuncinki. Karki manta matsayinmu awajen mutanen nan, mu 'yan aiki ne, ba su daukemu komai ba face wannan Ummi. Bar ganin suna mana dariya, duk sadda muka bari wasu lamura suka afku ranar zasu tunamana cewar mu kaskantu ne awajensu, ranar zasu tunamana matsayinmu na marasa galihu. Ki cire Faruk a zuciyarki Ummi, babban goro sai magogin k'arfe, ina gujemiki shiga matsala. Abinda ya shafeki ya shafeni. Sannan ina so duk juyin duniya idan Faruk ya nemi amsa ki tabbatar mishi cewar babu wani abi da kika fahimta game da hakan haka kuma ke babu abinda kikeji game da shi. Kinji?"   Ummi ta yi iyakar kokari wajen maida kwallar da ya tahomata, ta aminta hakan ne tana son abinda ya yi mata nisa. Ta yi murmushin yak'e. "Naji Anti kuma in sha Allah zan dau abinda kika shawarceni akai."   Ta murmusa. "Nasan da ciwo Ummi, amman gwara kiyi jinya daya da k janyowa kanki jinya na har abada....."    Ta gyada kai tana murmushi. Daga haka suka fita, kai tsaye wajen iyayen suka shiga suka gaishesu sannan suka fito. A hanyarsu ta zuwa taimakawa su Binta da aiki ne suka hadu da Faruk ya shirya zai wuce aiki. Ummi ta dan saci kallonsa, shi dinma idanunsa akanta. Suka gaisheshi, ya amsa.   "Fatan babu wani matsala?" Ya cewa Ummi, ta girgiza kai a tsorace.    "Kinji?" Ta yi shiru, ya k'ara maimaitawa. Hakan yasa ta dubeshi da mamaki.    Ya kashemata ido daya daman fuskar ya ke son k'ara kallo daga haka ya wuce. Amina ta kama baki. "Mun shiga uku, Yaya Faruk da gaske ya ke fa."   Ummi dai ba bakin magana don gaba daya ya kashemata jiki. Suka karasa ciki, sunyi mamaki na rashin ganin Sa'a, sai Binta ke basu labari ai tun daren jiya ta harhada kayanta ta bar gidan ba anan ta kwana ba. Suka ta6e baki, anan Amina da karfin hali ta yi ta yiwa Binta nasiha har tana nunamata ba yi bane abinda sukeyi don abokin 6arawo 6arawo ne. Sai kuma Binta ta hau borin kunya da fad'an wai kazafi akayimata batasan komai ba.                    ***  ***  ***                    KADUNA   Dija tuni ta kammala dukkan abinda aka sanyata, zaman jiran sakamakon kawai takeyi wanda hakan ya soma faruwa domin a yanzun koda bata fito ta karya ba, Deen da kansa ya ke aika su Tasleem kiranta.     Yau ta kama ranar talata, misalin daya Munira ta fice domin daukosu. Tana zaune tana karanta sakonnin Raihana wanda ya kasance naci ne ta ke mata tana rok'on ta rik'e alk'awarinta. Banda tsaki babu abinda ta ke ja duk da cewar zuwa yanzun Raihana ta dan burgeta bisa taimakon da ta yi mata akan Masoyinta.      Tsayuwar motar da ta ji ne yasa ta saurin mik'ewa, jikinta ya gama bata Deen ne ya dawo cin abincin rana don Munira sau da yawa sai wajejan uku ta ke shigowa gidan.  Tana lek'awa kuwa ta hangeshi, da sauri ta saki labule. Ta k'ara gyara zaman rigarta k'arama wacce ta tabbatar ta fiddo komai na jikinta. Babu laifi Dija na da kyau daidai gwargwado, bata da k'iba sosai, ba kuma ta kasance cikin masu rama ba, bak'a ce, dogon hancinta da fararen idanunta ne suka taimaka matuka wajen k'awata fuskarta. Tana da dirin jiki daidai.    Da kanta ta isa ta bud'e mishi k'ofa. Idanunsu suka tsarku cikin juna, ya ji wani abu ya dakeshi. Kwanaki biyu kenan yana fama da tunaninta da kuma wani shauki na soyayyarta wanda ya ke jin zai iya mutuwa idan har bai sameta ba.      Ta kasheshi da murmushi wanda ya kara rud'ar da shi. Ya bi jikinta da kallo sannan ya sauke ajiyar zuciya.     "Sannu da zuwa Deen."   Ya amsa da sauri yana kallonta. Ta ba shi hanya ya wuce, ta rufe kofar ta koma ta zauna a falon. Babu jimawa da shigarsa daki ya fito.     "Sannu Dija, kin ci abincin ne?" Ta yi dariya a ranta, shakka babu aiki ya soma ci. A fili ta danyi kasa da kanta.    "A'a, bana iya ci ni kadai ina jiran su dawo ne." Ya zaro ido. "Haba Dija, sai ki zauna da yunwa? Wannan bai yi ba, yaushe za ki tsaya jiransu alhalin daga nan zata biya kasuwa? Taso maza ki ci abinci please."   Ta girgiza kai tana jin dadi a zuciyarta kamar zai kasheta, yau Deen ne ke rarrashinta haka? Ai ji ta yi wani kaunar Raihana na kwararuwa cikin zuciyarta. Gudun kada ta yi saurin bayar da kai ne yasa ta ce "A'a, zan bar..."   "Ki bar me? Lallai nima kinaso na juya da yunwata kenan."   Ta zaro ido tana dubansa fuskarta dauke da murmushi.   "Ina zan so haka? Muje." Ya bita da murmushi sannan suka dunguma zuwa tebur.     Da kansa ya ja mata kujera ta zauna tana jin dadi a ranta tamkar ta mike ta daka tsalle.      Ya zauna ya yi (serving) dinta shima ya zauna ya zuba nasa sannan ya dubeta da murmushi har lokacin dauke saman fuskarsa yana kasheta da wani irin kallon da tun da suke bata ta6a ganinsa a tare da shi ba sai idan yana tare da Munira.     "Bismillah."   Itama ta kasheshi da nata salon kallon sannan ta murmusa ta soma ci, tana ci amma ta lura shi sam hankalinsa baya kan abincin. Ta dubeshi cikin alamun tambaya, ya sauke ajiyar zuciya.   "Kinga nakasa cin abincin ko? Naga kinmin kyau ne."    Ta yi dariya. "Kai Deen, ba fa wani kwalliya nayi ba."    Ya kashemata ido d'aya. "Anya? Kamar kin yi kurkur kin shafa jan baki da kwalli, haka nake ganinki a idona." Suka tuntsire da dariya lokaci guda. Ta shagwa6e fuska.   "Abin har da tsokana?" Ya yi dariya gami da lakuce hancinta.   "Ba zancen tsokana." Ta yi soror tana dubansa, tamkar fa a mafarki ta ke gani, anya kuwa ba mafarkin bane? Cikin dabara ta kai hannu ta mintsili fatar hannunta.   "Wash!" Ta fad'a a fili, a rikice ya dubeta. "Meyafaru?" Ta dan dara. "A'a bakomai, gaskiya ka ci abinci idan ba haka ba nima zan daina ci."   Ta karashe gami da ture farantin, ya maida mata filet din gabanta. "Na tuba, zan ci. Don Allah karki fasa ci."   Sukayi dariya suka hau cin abinci. A ran Dija murna fal ya cikata, ashe akwai sauk'aki'yar hanya da zata samu zuciyar Deen amma ta tsaya shirme da wahala?   Deen ji yakeyi kamar ya rungumeta don tsabar so da kauna, bayan sun kammala ta rigashi mikewa ta koma falon, ya bita da kallo cikin shaukin so.     Da biyu ta koma falon tasan dole ya bita da kallon. Wayarta ta janyo ta tarar da missedcalls har goma, kasancewar a (Vibration) ta sanyata ne yasa basu ji k'arar ba. Ta dauka ta duba, duk daga Raihana ne, dogon tsaki ta ja, tabbas Raihana dagaske ta ke. Kafin ta yi yunkurin ajiye wayar kiran ya k'ara shigowa. Saida ta waiga bata hangi Deen ya taho ba sannan ta d'aga.   "Ina jinki."   Raihana ta marairaice murya ta hau yi mata magiya akan ta sanarmata dalilin da yasa ta k'i d'aga wayarta da wuri. Wani bakinciki ya tokare zuciyar Dija, sa'ar da Raihana ke ci awajenta bai wuce na ita din itace silar taimakonta wajen samun Deen ba. Ta daure ta 6oye 6acin ranta.   "Kiyi hakuri, ina tare da Deen ne." Wani bakinciki da kishi ya turnik'e zuciyar Raihana, ta daure ne kawai don tana taya masoyiyarta son abinda take so. Ta daure ta ce. "Allah Sarki, ya ji dadinsa tunda yana samun kulawar da bansamu ba."   Dija ta ji kamar ta shak'eta. Motsin da ta ji na Deen ne yasa ta fadin. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   50   "Zan kiraki karki k'ara kirana." A hankali yanda bazai ji ba, wannan muryar ta k'ara kashe Raihana da dadi. (Wa'iyazubillah) ji ta yi kamar ta shiga wayar ta rukunkumeta, dole ta yi mata sallama ba don taso hakan ba.      Deen ya karaso, ya kammala shirinsa zai koma ofis, ya dubeta lokacin da ta ke k'ok'arin ajiye wayar. Suka yiwa juna murmushi.   "Har zaka koma?"   Ta tambaya cikin kankan da murya. Ya gyada kai. "Zan koma, ga shi basu dawo ba kamar kada na tafi nayi zaman tayaki hira."    Ta kasa jurewa ta dubeshi fuskarta na nuni da tsantsan farin ciki.   "Wai don Allah kaine kuwa? Ashe akwai ranar da za ka nuna kulawarka a kaina har haka?" Sai kuma ta yi shiru a tunaninta ta yi azar6a6i, amma sai bai bata kunya ba ya amsa.    "Idan ban kula da ke ba ai bazan iya kula da kaina ba kenan Dija, bakisan yanda nake jinki a zuciyata ba wallahi."   Ta lumshe ido don jin dadin maganarsa gami da murmusawa.    "Nagode Deen, yanzu kayi hakuri ka tafi ofis, ai idan ka dawo ina gidan."    Ya nok'e kafad'a kamar wani k'aramin yaro.    "Aa." Sukayi dariya. Ya kar6i lambar wayarta don a baya ba shi da, sannan sukayi sallama. Ai yana fita ta hau doka tsallen murna, daga wancan kujerar sai wannan tana yi tana dariya.     Ba ita ta nutsu ba saida su Munira suka dawo bayan la'asar alokacin har kiranta saida ya yi suka sha hira. A gefe Raihana na faman jaddadamata cewa ta rik'e amana ta cika alk'awari ta yanar gizo. Banda toh babu abinda ta ke cewa a fili kuwa ta ja tsaki don haushi.                     ***   ***   ***                        ABUJA       KB ya ji haushi matuk'a akan abinda Faruk ya yi mishi, kuma ya tabbatar muddin ya ce zaiyi wani yunkurin na daukar fansa, to fa Faruk ba karamin aikinsa bane ya tona mishi asiri. A karshe ma sai ya ga menene abin tayar da jijiyoyin wuya akan wacce yasan ya ketare a komai, saidai ya fahimci tabbas akwai wani abun a zuciyar Faruk akan Ummi. Ya yi murmushi a yayinda ya ke kwance saman kujera da misalin karfe uku na rana.   'Baka san wacce ta dace da wacce bata dace ba Faruk, duk abina bazan ta6a ajiye 'yar aiki a matsayin matata ba. Zubda aji kawai.'   Ya ayyana a ransa sannan ya ja tsaki a karshe ya shafi goshinsa wanda ya kumbura ya yi dariyar da shi kadai yasan manufarsa. Misalin takwas na dare, gidan babu kowa sai kalilan cikin iyaye da kuma yan aiki, sauran duk an tafi raka Amarya Baraka gidan mijinta. Amina na hanyarta ta komawa sashensu bayan ta yi aikin da Hajiya Babba ta sanyata na watsawa gaba daya jikokin nasu ruwa da sanyamusu kayan bacci, ta gyaresu tsaf ta shafa musu hoda sannan ta barsu anan falon k'asa suna kallon(Cartoon), alokacin Faruk ya sauko da zummar neman mai kira mishi Ummi, cikin sa'a ya had'u da ita, ita kanta Amina saida gabanta ya fad'i.   'Ina Ummi ina wannan babban goron? Tab!' Ta ayyana a ranta, a fili kuwa durkusawa ta yi ta kwashi gaisuwa ya amsa yana mai dubanta.   "Lafiya, idan kin shiga ki cewa Ummi ta sameni a inda muka had'u jiya."    Ta amsa da to sannan ta bar wajen, tana shiga ta tarar da ita sai faman danne-danne takeyi a wayar ita Aminan, Amina ta kwace tana jan tsaki.   "Kefa yanzu sai ki hargitsamin ita, ya kamata ki koyi sarrafa waya sai bala'in son wayar amma babu abinda kika iya ciki."   Sukayi dariya, Amina ta bar dariya, fuskarta ya nuna alamun damuwa da kulawa.    "Ummi ke din kina da babban matsayi gareni wallahi, ina son don Allah ki kula ki kuma dauki dukkan abinda na gayamaki. Nasan tabbas kina son Faruk shima kuma yana sonki , saidai ki dunga tunanin ke wacece ki kama kanki. Yanzu ki tashi ki je yana kiranki, yace ki sameshi a inda ku ka had'u jiya."    Ummi ta yi dumm ta tabbatar dukkan abinda Amina ta fad'i gaskiya ce, hakazalika kauna ce ta sanya ta kwa6arta. Ta jinjina kai tare da yin murmushi.   "In sha Allah Anti zan yi aiki da shawararki. Daman nima ina tsoron shiga kowace matsala adalilin Yaya Faruk."   Amina ta yi murmushin jin dadin irin wannan matsayin da ta samu wajen Ummi wacce a shekaru bai fi biyu ko daya ta bata ba.    "Nagode Kanwata, sai kin dawo." Daga haka Ummi ta zura hijabinta ta fita bayan ta duba babu wanda ya ganta. Kai tsaye wajen (swimming pool) na gidan ta nufa ta murda kofar ta shiga.     Zaune ta sameshi yana waya, ya juyo yana dubanta yana cigaba da wayar, alama ya yi mata ds ta rufe kofar, hakan yasa ta juyawa gami da rufewa, itama zata fi son hakan kada wani ya iskesu tare.     Tana kokarin durkusawa ya ja hijabinta hakan yasa ta dubansa.   Da ido ya yi mata alama da ta zauna gefensa akan daya kujerar. Ta numfasa gabanta na dukan tara-tara ta zauna. Ko kamshin turaren Faruk ta ji, takan ji sauyi a jini da tsokarta, ballantana akai ga jin muryarsa da kuma kallonsa.       Tunda ta zauna bata dubeshi ba, shine ma ya karkato yana amsa waya yana karewa fuskarta kallo. Ga dukkan alamu da ogansa awajen aiki ya ke magana, ganin yanda ya ke bawa mutumin girma hakazalika batu ne na kudade da wasu takardu sukeyi. Maganarsa tafi yawa da harshen turanci.  A jikinta ta ji yana kallonta, ta dan juyo ta saci kallonsa, ya kuwa kafeta da ido kafafunsa saman kujerar ya tankwashesu. Ta kauda kanta ta yi shiru, ji ta ke tamkar ba zata iya rabuwa da Faruk ba, saidai hakan dole ne agareta, ko ta karfi ko kuma ta lumana. Ta karfin kuwa, daga yan uwa da danginsa ne, wadanda a karshe zasu ci zarafinta su korata kauyensu, ta lumanar kuwa shine ta bi shawarar Antinta wanda idan har ta kiyaye to fa baza'a kai ga sauran matakan ba masu ciwo. Saida ya kammala wayar sannan ya ce.   "Bari kiga na kashe wayoyinnan, ko waye zai k'ara nemana saidai ya hakura na kammala da iyalina ko?"   Kanta ya yi dumm, jin kowanne kalamansa ta ke yi tamkar sun fi gwal da daham tsada a wajenta. Da a bata komai na jin dadin rayuwa ta gwammace a mallakamata Faruk a matsayin mijinta, saidai me? Wutsiyar rak'umi ta yi nesa da k'asa. Tunaninta ya katse sa'ilin da ya dora wayoyinsa a saman cinyarta. Ta dago ta dan dubeshi fuskarsa babu alamun wasa hakan yasa ta maida kanta ga duban wayoyinsa biyu manya wadanda ta tabbatar masu tsada ne saidai hankalinta yafi karkata ga son son jin abinda zai fito daga bakinshi.    DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   53    Washegari kuwa tun safe mutane suka soma tafiya, yan Adamawa kaf dinsu suka fice, Gwaggo surukar Mami bata zo wannan karon ba saidai ta aikowa Mami tsaraba hakanan ta aikowa Hajiya Babba g2udunmuwa.       Sai bayan Azahar su Mami suka soma shirin tafiya. Ummi suma sun kammala hada komai nasu ta tsinci sak'on kira daga Mami. Mamin na daki daga ita sai Ihsan wacce jin cewar zata karasa hutunta a gidan su Faruk ya sanyata kasa rufe baki don tsabar farinciki. A haka Ummi ta shiga ta riskesu, Mamin na faman kimtsawa don tafiya.     Bayan an gaisa ta ce. "Gani Mami." Mami ta dubeta.    "Yauwa Ummi, anan za ki zauna har muga abinda hali ya yi, saidai bayan komawata tukunna."   'Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!' Shine abinda Ummi ke ambata a can kasan ranta, ta ya ya zaayi a barta a gidan su Faruk, ina laifin ma idan sun je Kano ta je koda gidan su Hajiya Mama ne ko gidan su Inna?   'Ai ba danginki bane.' Cewar wani sashen zuciyarta. Ta ji babu yanda ta iya don yan uwannata basu ma damu da sha'aninta ba.     "Wai bakya ji ne wani sabon wulakanci ana ta yi ma ki magana kin yiwa mutane banza kamar tsararki?"   Maganar Ihsan kenan wacce ta maidota hayyacinta batare da shiri ba.  Ta dubi Ihsan din wacce a take ta watso mata harara kamar idanunta zasu zazzago, gaba daya bakin cikin jin cewa har Ummi itama anan zata zauna ta ke, kamar ta shak'eta haka ta ke ji, tsaki ta ja ma a karshe ta fice daga dakin cikin kunar rai.      Ummi ta maida hankalinta ga Mami. "Toh Mami. Allah Ya kaiku lafiya, Ya gyara lamura."     Har cikin ran Mami ta ji dadin addu'ar.    "Amin. Kina iya tafiya."   Ta mike jikinta babu kwari ta fita, tana zuwa dakinsu ta fad'a saman katifa ta yi tagumi. Haka Amina wacce ta fita kai kaya mota ta shigo ta risketa.   "Aa ya ki ka zauna, yanzu fa zasu fito."   A sanyaye ta dubeta ta sanarmata yanda Mamin ta ce. Amina ta numfasa.   "Allah Ya sa alheri ne ya tsayar da ke Ummi. Nidai fatana ki kiyaye dukkan nasihuna gareki, ban zama mai cutarwa gareki ba."    Ummi ta yi yak'e tana duban Amina. "Wallahi Anti babban ma fargabata bai wuce Ihsan ba, na tabbatar zan sha wulakanci daga gareta."   Amina ta girgiza kai da dan murmushi saman fuskarta wanda na yak'e ne.   "Karki damu Ummi, Allah Yana tare da ke. Kedai kiyi takatsantsan da lamura, bari naje kada su Hajiya Mama su rigani fitowa."      Ummi ta mike sanye gami da zura hijabinta a saman riga da siket na koriyar atamfa ta bi bayanta.       A fusace ta shiga dakin babu ko sallama, hakan yasa su Ikram, Intisar harma Anti Aisha da Rahila dubanta.   "Ke lafiyarki kuwa? Ku ganemin yarinya kamar mai iskokai yanzu kika fita kina murnar za'a barki garin masoyinki, kin shigo kuma kina fushi, meyafaru?" Cewar Rahila kenan.    Ihsan ta zauna gefen gado inda Aisha ke sanyawa Tahir famfas ta ja tsaki. "Wai don Allah meyasa Mami ta ke yin haka ne? Ya zaayi don nima zan zauna anan ace itama Ummi nan zata zauna? Wannan abun ya isheni, Mami bata da masaniyar yanda na tsani yarinyarnan wallahi da bata soma cewa ta zauna inda nake ba."    Mamaki ya bayyana a fuskokinsu. "Sannu sarauniyar wauta, sai akace zamanku a rumfa daya yana nufin matsayinku daya? Kai wallahi har gobe banga randa kuruciya zata fita kanki ba Ihsan."   Fadin Rahila kenan kafin ta fice daga dakin rataye da jakar kayanta.    Dariya sauran suka sanya, Intisar ta ja rigar Ihsan kadan.   "Kina bani mamaki, kodai kishi kikeyi don Ummi ta fiki kyau ne? Wannan tsana haka?"   Ihsan ta yamutsa fuska, kusan ma har da hakan saidai ita kanta tasan da abu k'alilan zata fi Ummi, shi dinma wuyarta Ummin ta samu hutu kamar yanda ta ke samu. Saidai kuma ta fusata sosai da zancen Intisar. Ta mike a fusace ta fita suna mata dariya wanda hakan ba karamin k'ara rura wutar kiyayyar Ummi ya yi a ranta ba.     Amina da Ummi sune suka taimaka wajen fidda jakunkuna, Ummi a sace sai sharar hawaye take yi don har cikin zuciyarta bata so zaman garin Abuja, ga kuma fargabar kada Faruk ya yi wani abun da zai janyo mutan gidan su fahimci manufarsa a kanta.     Haka suka tafi banda Adnan wanda ya ce ko zai koma ba yanzu ba. Mami dai ganin bai gama hucewa ba ne yasa ta kyaleshi.      Ummi ta juya jikinta a sanyaye zata koma ciki, Ihsan da suka hada ido harara da dallara mata, Adnan kuws murmushi ya sakarmata.   "'Yar Abuja." Ya fada cikin tsokana, murmushin yak'e ta yi mishi. Tana shirin barin wajen ta tsinci muryar Ihsan bayan Hajiya Babba ta riga ta koma ciki tana fadin.   "Rashin dangi ne yasa ta ke yawo daga nan zuwa can, duk dai abin mutum bazai chanja iyaye ba. Kauyen dai da ake gudu nan ne asali."    Daga haka ta tsinci muryar Adnan yana mata sababi bayan ya kai mata bugu ta kauce. Daidai da su Intisar basu ji dadin abinda ta aikata ba.   "Bansan halin wa kika biyo ba, don danginmu ba ma wulakanta mutum, muna girmama DAN ADAM daidai gwargwado." Cewar Intisar kenan sannan ta juya ciki ranta babu dadi.   Haka suka watse suka bar Ihsan cike da k'ara jin haushi da tsanar Ummi a nata ganin duk a kanta akeyi mata hakan.      Ita kuwa Ummi duk yanda ta so shigewa daki kai tsaye don kanta da ta ke ji yana sarawa ga kuma wani kuka da ya ke tahomata hakan bai samu ba sakamakon kiran da Hajiya Babba ta yi mata. Ta karasa ta durkusa cikin ladabi.   "Gani Hajiya." Hajiya ta dubeta fuska a sake. "Yauwa Ummi, sai kuma kika ga an barki a wajena ko? To ina so muyi zama na tsakani da Allah da ke, daman na riga nasan da kyawawan halayenki daga bakin Madina, ki k'ara a kan hakan. Gyaranki na dakina ne sai falon sama da kuma wannan na k'asan. Sauran dakunan kuwa suna karkashin kulawar Binta. Girki daman ba aikinku bane da wanke-wanke, kinji ko? Akwai mai yi na kwanaki ma ganin bak'i da yawa yasa nake cewa ku shiga, fatan kin fahimceni?"   Ummi ta jinjina kai, ranta ko digon farinciki babu sakamakon har lokacin ranta a tsananin 6ace ya ke.       "Na fahimta Hajiya kuma in sha Allah zan kiyaye zan kula."     Hajiya Babba ta ji dadin furucinta ta sakarmata murmushi.   "Na lura dai ranki bai miki dadi ba akan zaman da za ki yi anan, karki damu, na dan lokaci ne, da zarar na sanya an samomin wata za ko tafo, mai yiwuwa ma tare da su Ihsan."    Jin an k'ara ambaton Ihsan sai ta ji duk zancen ya gundureta, ta daure ta k'akalo murmushi.   "Lah bakomai Hajiya, ai can da nan din duk daya ne."    Daga haka Hajiya ta sallameta. Tana shiga daki ta zube saman katifa, a hankali maganganun Ihsan suka dawo mata kawai sai ta fashe da kuka sosai har tana sheshshek'a. Wannan rayuwa ta soma isarta, Ihsan ta soma kaita bango, abin nata yana neman wuce gona da iri, ko don tana ganin ita din bata da wani karfin ikon da zata kwaci 'yancinta ne? To wane 'yanci ma ta ke da shi a yanzun tunda ba wani babban jigo abin tunk'ahonta wanda zai iya yin wani kata6us akan lamuranta? Kewar mahaifiyarta yafi komai damunta, ko babu komai ta tabbatar ba zata watsar da ita kamar yanda Mahaifinta ya yi ga rayuwarta ba.     A karshe dai wani sashe na zuciyarta ya yi ta nusar da ita da muhimmancin Yarda da Kaddara, haka har dai zuciyarta ta danyi sanyi ta mike don d'auro alwalar La'asar.              Yana zaune saman kujera a ofis cike da dumbin tunani da damuwa, ya daga kai ya dubi agogon bangon dake a ofishin nasu, agogon ya nuna karfe hudu saura mintuna uku, ya ja guntun tsaki gami da dafe goshinsa. Ya san zuwa wannan lokacin sun wuce, tabbacin farin cikinsa ta tafi saidai hausawa sun ce garin masoyi baya nisa, yasan ko yaushe ya yi niyya muddin ranar babu aiki zai iya kai mata ziyara. Saidai zai so matuk'a tafiyar ta kasance babu ita.   'Akan wane dalili?' Cewar sashe na zuciyarsa, ya runtse ido gami da jingina kansa jikin kujera.                       DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 51    "Ummi, ina muka kwana a zancenmu na jiya? Abin nufi me kika fahimta da yanayin da muke ji game da juna a zukatanmu?"   Ta girgiza kai ta daure ta ce. "Babu." Ya yi wani murmushi. "Ai nasan zaayi haka." Ba ta ce komai ba, shi kuwa saida ya ja fasali sannan ya cigaba da magana.     "Kin sani kamar yanda na sani Ummi, amma mu ajiye wannan a gefe." Shiru ya dan biyo baya kafin ya dora. "Bani tarihin rayuwarki idan da hali."    'Rayuwata?' Ta yi tambayar a ranta. Ganin ta yi shiru ya k'ara magana. "Look Ummi, ki saki jikinki da ni please, ba ma ke ba, ni kaina ban yi sabo da hakan ba, sai kin zauna da Faruk za ki fahimci ko waye shi. Ban fiye sakin jiki da mutane na yi hira har haka ba, da dai cikin brothers na ne ko Hajiyata. So please Ummi ki min alfarmar nan, ki saki jiki da ni, ina so nan gaba ma mufi haka kusanci kinji ko?"  Ya k'arashe cikin rad'a gami da yin murmushi mai sauti, baiwar Allah idanunta suka cika da kwalla, ga samu ga rashi. Tana son abinda ba za ta ta6a samunsa ba don a yanzun da ya ke magana ji ta ke yi tamkar ana k'ara rura mata wutar kaunarsa. Bata ba shi amsa ba face ta shiga labartamasa labarinta iyakar wanda ta sani banda wanda batasani ba kuma bata ta6a samun labari ba, wato na zamantakewar mahaifinta da mahaifiyarta. To mai labarta matan ma ba shiga sabgarta ya ke yi, bai dauketa matsayin 'ya ba.    Tiryan-tiryan ta ke bashi labari tana yi tana zubda ruwan hawaye har ta kai yanda aka kawota aikatau.     Tana kaiwa karshe ta cigaba da kuka mai kona zuciya, ba don komai ba sai tunanin rashin gatanta da kuma na son abinda ba zata ta6a samu ba.    Tattausan hannunsa ta ji a saman kumatunta yana share mata fuska, baki ta saki tana kallonsa, ba kwayar idanunta ya ke kallo ba, kyakkyawan farar fatarta ta ke kallo yayinda ya cigaba da magana yana murmushi mai kama da yak'e, fuskarsa dauke da damuwa da tausayi.        "Kinzo inda za'a share miki hawaye da taimakon Allah, idan har Faruk na numfashi, in sha Allah zai zame miki haske a rayuwarki. A yanzu ta bakinki nake son ji."   Sai lokacin ya dubeta, ita kuwa idanunta a lumshe suke sakamakon yatsunsa da ke akai yana sharemata kwalla. Daidai lokacin kuma ya dauke hannunsa daga kanta. Ummi bugun kirjinta k'aruwa kawai ya ke yi, ita dai bata ta6a jin yanayin nan kan kowa ba sai shi, ta kasa dubansa, anya kuwa zata iya daukar shawarar Antinta Amina? Kai, dole ta dauka don Antinta ba zata cuceta ba.     "Kin yarda kin amince mu k'ulla alak'ar da zata kai mu ga AURE? Ta wannan hanyar kadai zan iya taimakon rayuwarki Ummina."     Kamar ta tashi ta ruga a guje ta ke jinta, Faruk dama ya muryarsa ta ke wajen sanyi kamar mace ballantana kuma yana cikin yanayi na shaukin so da kauna. Ta dan matsa don rage kusancin da ya yi mata.      "Kayi hakuri, ni babu wani abu da nake ji game da kai, ban dauke ka komai ba sai dan uwan Yaya Adnan kuma iyayen gidana, ka yi hakuri, bazan iya jefa zuciyata cikin abinda zan wahala ba."    Daga haka ta kwashi wayoyinsa ta mik'a mishi, saidai ba shi da niyyar kar6a, asalima idanu ya zubamata yana murmushi. Ganin haka yasa ta ajiyewa a kujerar da ta mik'e zata tafi.   "Ji mana."   Ta tsaya cak gami da juyowa. Ya dauke wayoyinsa ya dubeta. "Dawo ki zauna."    Ba musu ta dawo ta zauna tana share hawayen saman fuskarta.   Ya dawo ta gabanta ya durkusa.  "Hey, kalli tsakar idanuna ki ce ba ki amince ba."   Ta kauda kanta tana jin tamkar ta fashe da kuka gaba daya ita ta gama tsorata ganin Faruk dagaske ya ke babu wani sassaunci.      "Ummi say something please, ki ce wani abu mana."    Ya fada cikin shagwa6a66iyar muryar da bai fiye amfani da ita ba sai ko a gaban Hajiyarsa. Ta girgiza kai.   "Ni ban amince ba."   Ya dubeta na sakanni ya na murmushi.   "Dagaske ba ki amince ba?" Ya fad'a yana mai kwaikwayon muryarta, abin ya so bata dariya ta kuwa saki murmushi.   "Masha Allah, ko kefe. Naji wannan kuma nagode, amsa tuni na sameshi, hirar ce nakeson muyi don bakisan yanda nakejin dadin ganinki bane."   Shiru babu wanda ya k'ara magana, can kuma ya sauke ajiyar zuciya ya kunna wayoyinsa.    "Goma har ta kusa."   Ya fad'a yana duban wayar, can kuma ya mik'e ya sanya wayoyin a aljihun wandonsa, ya yi amfani da tafukan hannayensa ya dafa gwuiwarsa gami da sunkuyowa yana dubanta.   "Saida safe." Ta gyada kai sannan ta gifta ta mike tsaye da sauri don daman tun dazu ta soma jin tsayuwar motoci a harabar gidan ta tabbatar yanzun su Mami sun iso.     "Allah Ya tashemu lafiya."   Daga haka ta yi gaba da sauri, koda ta isa ga kofar saida ta kasa jurewa ta juyo kanta ta dubeshi, shi ba shi ma da niyyar barin wajen don komawa ya yi ya zauna. Su ka yi ido hud'u da shi, ta dauke kanta da sauri-sauri ta bar wajen tana ji yana fad'in.   "Ko na zo ne?" Bata ko juyo ba balle ta tanka mishi. Ya yi murmushi karo na ba adadi sannan ya kwantar da kansa jikin kujera, kai tsaye hotonta ya lalubo wanda ya yi mata a wata rana da ta ke zaune tana wanki a (garden) da kuma na zanen da ya yi mata.   "Ke tawa ce in sha Allah." DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 55                       KANO Mami ta yi mamakin chanje-chanjen da ta gani wajen Mijinnata. Abin mamakin bai wuce yanda ya dage akan lallai su bata girkinta ba. A ranar kuwa suna isa ita ce ta shiga fadarsa. Saboda Fahad, Ramma ta kwana a gidan kasancewar yaranta suna kauye ziyarar dangin ubansu.      Ta sha rok'o a wajensa akan ta yafemishi har ta gaji domin duk da nunamishin da ta yi komai ya wuce, bai iya sakin jiki ba. Ranar kam komai ya yi lafiya, ya sanarmata haka kawai ya soma tsintar kansa cikin halin tunani da kuma tsananin kewarta.   Tsakanin mata da miji dai sai Allah, a wannan daren suka dinke har ma ya nemi kiran d'ansa don ya dawo ya soma shirin tafiya karatunsa.      'Babu abinda ya fi karfin Allah.' Shine abinda Mami ta fad'a a zuciyarta cikin murmushi lokacin da ta saci kallon fuskar mijinta ta ga annurinsa ya dawo ba kamar da ba.                      ***  ***  ***                         ABUJA     Misalin karfe shida a gaggauce ya kammala shirinsa ya fice zuwa aiki ko karyawa bai tsaya yi ba.    Ummi tun misalin takwas suka soma ayyukansu, ta yi gyararrakinta tsaf, Binta itama ta kama nata. Hajiya Babba ta yaba kwarai da gyaran Ummi. Koda ta shigo ta iske falon kyal-kyal tana(mopping) ta kalli wajen kafin ta amsa gaisuwarta da murmushi dauke saman fuskarta.   "Eh lallai, dole Madina ta so zamanki wajenta, ashe haka kika iya gyara? Lallai kam na yaba miki Ummi." Wani murmushi ta yi har kumatunta saida suka lotsa, kwarai ta ji dadin wannan yabo da ta samu. Hajiya Babba ta yi dakinta, nan ma an kyalkyaleshi tamkar ba'a ta6a kwana cikinsa ba. Komai tsaf, hakanan ta ga bambancin aikinta da na Sa'a kwarai.    Ummi duk jikinta babu dadi, duk da cewar tana son gujewa Adnan, rashin had'uwarsu a kwana biyunnan yana damunta, batasan dalilin son sanyashi a kwayar idanunta da ta ke yi ba. Hankalinta ya kai ga tafkekan hoton matasan yaran Hajiya Babba. Dukkansu sanye suke da shadda ruwan k'asa tazarce, ta sha surfani mai tsada. Hularsu mai surkin ruwan k'asa mai duhu da marar duhu, a tsaye sukayi hoton a farfajiyar wani  (hall), daga hotunan bayansu za ka tabbatar cewar a wajen wata walima ne.   Ta kauda idanunta gami da sauke ajiyar zuciya, duk cikinsu babu wanda yafi haskakawa a idanunta kamar Faruk, ko don shi zuciyarta ke so ne? DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   54 A wannan ranar dakyar ya jure suka kammala suka tashi, a hanya Magriba ta riskeshi haka ya karasa gidan ya yi fakin duk jiki a sanyaye. Bai zarce ko'ina ba sai sashensa. Saida ya yi sallah ya watsa ruwa ya sanya bak'ar jallabiya a saman gajeran wandonsa sannan ya yi niyyar shiga cikin gidan.  Hankalinsa ya kai ga Adnan wanda ke kwance saman gado yana danne-dannen waya. Yatsun k'afarsa na hagu ya ja wanda ya tilastawa Adnan yin gefe da wayar yana mai sakin k'ara lokaci guda kuma da dariya.     "Kai my best."   Faruk ya murmusa kadan. "Baka da aiki sai(chatting) kwanakin nan,  ya dace na soma haramar kora ka makaranta naga ta (chatting)."   Dariya Adnan ya cigaba da yi. Faruk ya zura silifas dinsa ya fice zuwa sashen Hajiyarsa.      Bayan saukowarsa daga bene saida ya tsaya cak yana k'arewa hanyar dakunan yan aikin kallo, yasan Ummi zuwa yanzu ta yi mishi nisa. Ya sauke ajiyar zuciya gami da juyawa ya cigaba da tafiyarsa.    A falo ya iske Ikram da Ihsan suna cin abinci suna hira. Ganinsa yasa duk suka dubeshi suna mai amsa sallamarshi. Yana duban Ihsan da mamaki ya jefamata tambaya.   "A'a, baku wuce ba?"   Ihsan cikin kashe murya ta ce "No sun wuce, ina nan sai bayan sati biyu zan koma."     Bai wani ji dadi sosai ba, zaman Ihsan takura rayuwarsa kawai ne, ba yau ba ya soma lura da take-takenta, shi din ya kasance mai saurin fahimtar masu nunamasa so haka. Yana sane da Iklima ma, sai yanzu ne ma ya fahimci ta dan kwana biyu bata mishi koda sallama ba a whatsapp ballantana kuma akai ga kira.     "Ok." Shine kawai abinda ya ce sannan ya k'ara gaba. Ihsan ta bi bayanshi da kallo har saida Ikram ta zungureta.   "Kin shiga uku wallahi kedai, nikam har na daina mamaki." Ihsan ta yi murmushi. "Me kike nufi?" "Ina nufin ki sanarmasa kina sonsa."   Ihsan ta zaro ido. "Zubda aji."    Ikram ta yi kwafa. "Tsaya kallon ruwa kwado ya yi miki k'afa."   "Wai kina nufin akwai wacce ya ke so?"   Ikram ta yi dariya. "Bani da tabbacin hakan. Amma kada ki sake ki tsaya wani jan aji wallahi. Yayanki ne, koda zai wulakanta kowa banda ke."   Ihsan dai ta yi shiru ta cigaba da kai loma, maganar Maminta kawai ta ke tunanowa inda ta yita bata shawara akan ta yi kokarin jawo hankalinsa ta kissa.               Ya dan jima wajen Hajiyarsa har akayi kiran salla tukunna ya fito. Daga masallaci dakinsu.     Ya dan jima wajen Hajiyarsa har akayi kiran salla tukunna ya fito. Daga masallaci dakinsu ya wuce, can su Ikram suka kai musu abincinsu, har lokacin sam ba shi da masaniya akan Ummi na Abuja. Koda ya shiga wajen Hajiyarsa, bata sanarmishi ba.                    *** *** ***                    KADUNA   Wasa-wasa karamar magana ta zama babba, domin kuwa Deen da Dija soyewarsu sukeyi son ransu, saidai hirarsu ta fi a waya ko kuma idan sun yi sa'ar rana Munira bata gida. Tun ita Munira bata ganewa har ta soma zargin akwai wani abun. Kamar yanda Deen ke damuwa da harkar Dija sosai, abin mamaki har zuwa ta ke ta zauna a hau wasa da dariya da ita har ma su dinga wareta cikin hirartasu saidai ta yi shiru tana sauraronsu.      Dija da kanta ta bawa Deen shawara akan lokacin komawarta gida ya yi idan har da gaske ya ke sai ya turo magabatansa. Alokacin ne kuma ya yi dumm, ya dubeta. "Kina ganin hakan bazai janyomin matsala da Munira ba?"   Ta ji haushin furucinsa, ta fahimci koda asiri ya ci shi akanta, tofa baisa ya mance da matarsa ba. Ta nunamishi idan ba zai iya aurenta saboda matarsa ba, shikenan. Anan kuma ya hau bata hakuri suka ajiye maganar yanda za'a 6ullowa lamarin.    Kwanaki biyu da yin maganarsu ta tattara ta koma Ringim, Munira ta ji dadin tafiyarta don Allah shaida ta soma tunanin akwai wata alak'a tsakaninta da maigidanta wanda bata fatan zatonta ya kasance gaskiya.  Ta rik'i Dija yar uwa haka kuma da zuciya daya ta ke zaune da ita. Koda zasu rabu, tayi mata kyauta ta sutura da abin hannu, idan kuma zaa hada da wanda Deen ya yi mata, to fa ba komai bane.                    ***   ***  ***                      RINGIM       "Lale da 'yan Kaduna. To, saukar yamma ce?" Baba Habiba ta fada tana mai dan tafa hannuwa kamar kawata Bingel a fagen nanaye (LOL). Dija ta sakarmata jakar kayanta ta kar6a da gaggawa tana mai k'arewa diyartata kallo da dumbin mamakin yanda akayi ta chanja, wani k'iba ta k'ara da kyau.    Sai da dare bayan sun zauna ne suna 'yar hirarrakinsu, wayar Dija ta k'ara daukar k'ara a karo na biyar tun shigowarta gidan. Baba baki bude ta ke dubanta, ta rasa inda zata tsoma ranta don tsananin murna, ga dukkan alamu dai diyarta ta samu saurayi dan birni, lallai ba zasu yi sake ba.      Bayan Dija ta ajiye wayar ne ta dubeta.   "Ya sunansa?" Dariya ma tambayar ta bawa Dija, bayan ta gama kyakyatawa ta ce "Wa kenan?"   Baba ta girgiza kai. "Ke bafa za muyi sake ba, fadamin sunansa mu k'ara kamashi a hannu yanda bazai ta6a iya su6uce mana ba kafin zuwa lokacin da za'a tashi aurenku muyi shiri na musamman."   Wani murmushi Dija ta saki. "Zahraddeen sunansa."   Baba ta zaro ido waje. "Wanne kenan?"   Babu ko d'arr ta amsa. "Zahraddeen dai da kika sani, mijin Munira, shi nake so kuma ya ke sona."    Baba ta yi tsit, Dija tiryan-tiryan ta labartamata ire-iren hidimar da yake mata har da kyautar kudi dubu talatin da ya yi mata da za ta taho ya kuma siyamata sabuwar waya tana nan cikin kayanta. Har ma da yanda suka ajiye magana da shi akan zai zo neman aure. Bayan ta kammala bayanin ta fiddo kudaden ta damk'a a hannun Babarta, ta zaro kwalin wayar shima daga jakarta tana mai nunamata. Baba Habiba ta zurawa kudin ido da wayar kafin ta washe baki. "Ke Dije! Wadannan yanzu duk mallakinki ne? Shakka babu daman bokanya ta tabbatar min idan mijin aurenki ya zo za muyi mamaki gashinan tun ma ba'a je ko'ina ba na soma. Abun yi yanzu, gobe zan koma gidan bori na ji yanda zamuyi ayi komai cikin salama batare da ansamu matsala ba, don ta ubanki mai sauki ne, sai yanda nace."   Wani ihun dadi Dija ta saki gami da rungume mahaifiyarta. "Shiyasa nake bala'in sonki wallahi Baba."   Suka yi dariya, nan suka soma shawara kan irin k'ulle-k'ullen da zasu sanya ayi bayan auren. Ko kusa Dija bata sanarmata komai akan Raihana ba gudun yanda zata yiwa kallon abin.                   ***   ***   ***                       KANO DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 56        Har Ummi ta yi kwana biyu a gidan, Faruk ba shi da masaniya don gaba daya aiyuka sun mishi ca a ofis. Ba shi ya samu kansa ba sai ranar Asabar. Ranar kam ya sha bacci, bai farka ba sai sha daya. Kai tsaye wanka ya fad'a, bayan fitowarsa ya shirya cikin t-shirt fara tas da wando na (Adidas), bak'i mai surkin fari kadan sannan ya zura silifas ya nufi sashen mahaifiyarsa.         Tafe take a hanyarta ta zuwa wajen(garden) don dauraye tsummokaran da ta kammala gyaran dakunan Hajiya da su. Kallon benen da zata yi ta ganshi yana saukowa shima a daidai lokacin ya bar duban wayarsa ya maida ga hanya alokaci daya kuma yana kokarin sanya wayar aljihun wando. Karaf idanunsa cikin nata, yanda ta tsaya bata motsa ba, shima ya tsinci kansa da mutuwar tsaye. Abu biyu ke yawo a kwakwalwarsa. Buri na son kasantuwar abinda ya ke gani yanzu tamkar mafarki da kuma tambayar daman tana gidan?    Dakyar ya yi jarumtar k'arasawa har gabanta, alokacin ita kuwa ta sunkuyar da kanta cike da matsanancin fargabar abinda zai k'ara ce mata.    Saida ya kai dab da ita har suna jin numfashin juna sannan ya sauke ajiyar zuciya ya matsa, ya tabbata ita din ce ba gizo ta ke mishi ba. A hankali ya matsa baya, cikin rawar murya ta gaisheshi bayan ta durkusa. Ya amsa cikin jin wani irin nishadi a ransa, ta mik'e tsaye, tana shirin barin wajen maganarsa ta dakatar da ita.   "Daman ba ki tafi ba?"   Ta dan saci kallonsa, murmushi ta gani dauke saman fuskarsa wanda ya kara fiddo kyawunsa.   "Eh."   "Saboda ni?" Ya fada a tausashe bayan ya dan rankwafo da kansa yana kallon fuskarta.    Ta k'ara satar kallonsa, shi dinma bai kauda nasa idanun daga kanta ba. Ta ji wani iri a jikinta, wai saboda shi. Maganar ma nauyi ta yi mata, ta kauda idanunta.    "Mami ta ce na zauna zuwa wani lokaci."    Ya ji dadin maganar, ba zai iya misalta farin cikin da ya shiga sanadin hakan ba. Ya dubi hanya babu wani ko wata da ke tahowa sannan ya dubeta.   "Ummi, yau kenan za ki tayani hira?" Ta zaro ido batare da ta dubeshi ba, cikin sauri ta girgiza kai.   "Kayi haku..." "Shiit." Ya dakatar da ita ta hanyar dora yatsansa a saman le66ansa.   "No please, karki hana zuciyarki abinda ta ke so mana Ummi. Ko kina so wani abu ya faru da mu sanadin hana zukatanmu farin cikinsu?"   Ba amsa sai idanunta da suka kawo ruwa, ya mik'e da rankwafawar da ya yi.     "Shikenan, ki tafi, mu had'u wajen pool."    Daga haka shiru ya biyo baya, karshe ma ya juya ya cigaba da tafiya. Da ido ta bishi, ta tabbatar shi babu abinda ya ke tsoratashi, kamar yanda babu matsalolin da ya ke hangomusu, ita kadai ta damu da duk wadannan.    Koda zai shige saida ya juyo domin ganin yanayin da ta shiga, suna hada ido ta juya da sauri ta soma tafiya. Murmushi ya saki kafin ya karasa cike zuciyarsa cike da tsantsar farinciki. Daidai da Ikram da Ihsan sun ga chanji yau wajen yayannasu, don kuwa biyemusu ya yi akayita hira da dariya. Ihsan ji ta ke tamkar ta buga tsalle don murna da farinciki, yau ita Faruk ya dage hira da ita? Tabbas shawo kansa zai zo mata da sauki muddin ya d'ore a haka.     A yan kwanakin da ta yi tsaf Hajiya Babba ta fahimci inda ta dosa, a farko bata gaskata Ikram ba da ta sanarmata cewar Ihsan na son Faruk ba, saida ta lura da kanta. Abin ya yi mata dadi, zata so hakan ta kasance, saidai d'annata ne batasan abinda ke ransa ba. A ganinta da wuya ya kaunaci yarinya mai rawar kai irinta, hakanan Ihsan sam bata da hakuri, ga saurin fushi. A raayin Hajiya Babba, bata kaunar abinda zai damu 'ya'yanta, kusan halinsu daya da Mami na son 'ya'ya.    Acan kuwa Ummi tana isa ta zauna saman kujera gami da zubawa famfo ido, hankalinta gaba daya ba a wajen ya ke ba, ya tafi gaba daya ga tunanin Faruk. 'Dagaske fa ya ke.' Shine abinda ta fad'a a ranta, tabbas Faruk dagaske ya ke, asalima babu wani alama na tsoro ko fargaban abinda zai biyo baya. Yanzu ya zata yi? Bai bata damar cewa ba zata zo ba, ya riga ya yanke cewa lallai kawai ta zo ta sameshi. Ta riga tasan duk ranar da wani a gidan ya gano to fa tashin hankalin da zata shiga ba k'adan bane. Tagumi ta zuba tana tunano da Antinta, yau ne rana ta farko da ta soma jin bukatar waya a rayuwarta, ayau inda ace tana da  waya, tuni zata yi kiranta ta bata shawarar da ta dace. Ta ja guntun tsaki sannan dakyar ta mike ta soma aikin da ya kawota, saida ta kammala ta shanya sannan ta koma ciki.     Misalin biyar na yamma tana zaune a k'asan bishiyar mangwaro tana wasa da ganyen, hankalinta gaba daya ya tafi ga tunanin Faruk, banda murmushi da wani annuri, baka ganin komai saman fuskarta. Ita tasan tana sonsa, bata ta6a son wani d'a namiji ba sai shi, saidai kawai bambancin dake tsakaninsu, shi kadai zai hanasu aure.     Ta jima kafin ta sauke ajiyar zuciya ta maida dubanta ga inda ta ji sautin dariyarsu. Ihsan ce da Ikram dukkansu sanye da kananun kaya, riga da siket, sun nad'e kansu da karamin dankwali. Hira sukeyi abinsu da dariya har suka iso wajen motar da tun zuwansu Abuja, Faruk tasan yana hawanta. Suna hada ido da Ihsan ta maka mata harara, Ummi ta kauda fuskarta. 'Kanki ake ji.' Shine abinda ta fad'i a ranta.    "Har kun fito?" Tattausar muryarsa ta ratsa dodon kunnenta. Ta so ta jure kada ta kalleshi, saidai hakan ya k"i yiwuwa, ji ta yi tamkar bazata nutsu ba idan bata ga tasa shigar ba. 'SubhanAllah!' Shine abinda ta fad'i a ranta. Riga tshirt ce yasa kalar(golden, long sleev) mai mannuwa a jiki, sai (blue jeans) ya sanya gilas dark brown, agogonsa na k'a'ida yana daure a hannunsa sai zobunansa da baya rabo da su. Ji ta yi tamkar numfashinta zai dauke tsabar kyawun da ta ga ya yi mata a idanu.    To ba Ummi kadai ba, Ihsan kanta baki ta bud'e tana kallonsa, ji takeyi tamkar ta dora hannu a ka ta ce wayyo Allah, kamar ta matsa bakin Faruk ya furta yana sonta.     "Wow Yaya Faruk, kayi kyau wallahi." Muryar Ikram ya katse Ummi da Ihsan daga tunanin da zukatansu suka lula. Ya dan rankwashi kanta yana dan murmushi.    "Ko?" Ta yi dariya. "Allah kuwa."   Ya jinjina kai sannan ya zagaya zuwa mazaunin direba ya bude motar, Ihsan da sauri ta bude gidan gaba ta shiga, hakan bai wani dameshi ba, don shi bai dauketa wata aba ba face k'anwa.     Ya bud'e motar kenan yana shirin shiga idanunsa ya kai gareta.  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 57 Ita dinma har lokacin shi ta ke kallo, batasan tana da kishi ba sai a yanzun, Faruk ne da Ihsan wacce ta riga tasan tana tsananin sonshi, babu walwala a fuskarta hakanan bata daureshi ba, ta mik'e da sauri ta bar wajen ta nufi ciki. Ya  dan dubesu.   "Ina zuwa. Zo ki tayar da motar kafin na zo." Ya karashe zancensa da duban Ikram. Ba musu ta kar6i muk'ullin, basu kawo komai ba don babu wands zai yi tunanin wai Faruk zai dauki Ummi wata aba.     Shi kuwa da sauri ya nufi hanyar da ta yi da zummar komawa sashensa saidai ya zarce kai tsaye wajen dakunansu da zummar kwankwasa mata.  Hawaye ta ke fitarwa da batasan dalilinsa ba, tasan dai tana jin zafi ne cikin zuciyarta na ganin Ihsan a gaban motar Faruk. (Ji karfin hali!) Tana shirin lek'ensu ta windo, ta ji bugun kofarsa yana kiran sunanta. A rude ta saurara ta ji, tabbas shi dinne, ta share fuskarta da sauri sannan ta bud'e k'ofar. Ya fidda gilashinsa yana dubanta, bata yarda ta kalleshi ba.   "Kar kiji shiru Ummina, zan kai yaran nan siyayya amma bazan jima ba kinji?"   Kai kawai ta gyada cike da jin haushi, da tana da iko da ta ce ya fadawa Ihsan ta koma baya saidai yin hakan wani nuna karfin hali ne wai 6arawo da sallama. Ita da ke cin arziki?   "Ko za kije?"   Ta girgiza kai a tsorace. "Sai kun dawo."   Ya daga kafada yana mai wani shagwa6e fuska kamar wani yaro. "Allah kuwa idan kina so ki zo muje."   "Don Allah kayi hakuri." Itama tayi maganar cikin marairaice murya don gaba daya tsoro ya cikamata ciki, bata so wani ya zo ya gansu tare.    "Shikenan, me kikeso na siyomiki?"   Hankalinta ya tashi ga shi ya tsare bakin hanya babu damar ta duba hanyar ta gani ko wani ya taho. Ta dubeshi gaba daya a rude ta ke. "Ko menene."   Ya fahimci duk a rude ta ke, murmushi ya saki yana mai juyawa.   "Bari na tayaki duban hanyar."   Ya dan kalla sannan ya dubeta har lokacin bai bar murmushin ba, kafada ya daga gami da daga gira kadan.    "Karki damu, idan don Binta ce, tana tare da Hajiya, can na barota. Bazan tafi ba sai kin gayamin abinda kike so na kawo miki."    "Na shiga uku." Ta yi furucin da bata shirya fitowarsa fili ba, ga mamakinta sai ta ga yana dariya har yana dan jijjiga kafada. Ta yi sakato tana kallonshi, bai ta6a yi mata dariya har haka ba, sai taga ya k'ara yi mata kyau matuk'a. Hon din da suka ji ya katse su, tasan su Ihsan ne. Ta dubi windo kafin ta juyo ta dubeshi. Ya dan daga gira.     "Kina 6atamusu lokaci."   Ta rasa ya zatayi. "Ka siyomin alawa." Ta fada kamar zata fashe da kuka. Ya kwaikwayi muryarta.   "Guda nawa?"   Ta yi mishi nunin biyu da yatsa. Ya murmusa.   "Bye, sai na dawo."   Kanta kawai ta gyada, ya juya ya tafi. Ta lek'o ta na kallonsa har ya maida gilashinsa, murmushi ta saki gami da juyawa ciki ta rufe kofar. Wajen windo ta k'arasa da saurinta tana lek'ensa, tana ganin yanda ya had'e musu gira tamkar ba shine ya gama yi mata murmushi harda dariya ba yanzun. Akan idanunta ya bude motar ya shiga, daga haka ta daina ganinsu sakamakon gilashin motarsa mai duhu ne. Sauke ajiyar zuciya ta yi gami da rike kirji tana dariya marar sauti idanunta a lumshe, dariyar Faruk kawai ta ke gani ta ke jin sanyi, yanda ya nunamata tsantsar kulawa har mamaki abin ya bata, ashe ire-irensu sukan ji dadin duniya? Da ace wannan farincikin zai dore da ta fi kowa sa'a a rayuwa. Ta numfasa gami da bin lafiyar kafet ta kwanta. Sauranta jiran dawowarsa da ganin da wacce ya zo, duk kuwa da tsantsar fargaba da ke cin kasan ranta. Bata so wani ya san alaka'ar da ke tsakaninsu...   Ba su suka dawo gidan ba sai bayan Magriba. Yana fakawa suka fito kowacce hannunta rik'e da leda wanda kayan mak'ulashe ne zalla. Ihsan bayan sun danyi gaba ta dubi Ikram.   "Wai duk wancan kayan zak'in da Yaya Faruk ya loda na shi ne sho d'aya?"   Ikram ta harareta. "Meya hanaki tambayarsa?"   Ta yi dariya. "Mezai kaini gangancin nan?"   "Wai ma, kina ganin dai ya mik'o mana na Hajiya, kinsan dai nasa ne ko? Amma dai bansani ba ko anjima zai je hira." Ta k'arashe cikin zolaya. Ihsan ta buga tsaki gami da k'ara d'aga kafa. "Ke dama ai ba'a hirar arziki dake sai kin kwafsa a wani 6angaren."   Ita dai Ikram da dariya kawai ta bita.           Shi kuwa gogan kai tsaye sashensa ya nufa, saida ya yi sallah ya fito ya lek'a su Hajiya kafin ya koma sashensa ya fito rike da ledar Ummi wacce ya yo mata siyayya.     Daidai lokacin da ya kwankwasa mata, Binta ta fito daga bandaki, zaro ido ta yi domin mamaki da ya cikata. Me Yalla6ai ke yi a bakin k'ofar dakin Ummi har yana kwankwasawa? Ta so ta yi magana saidai ta kuma la6ewa don ganin wannan abin Al'ajabin.     Ummi ta shafa adduarta, idar da sallar isha'in ta kenan, mik'ewa ta yi ta nufi k'ofar gami da bud'ewa. Suka dubi juna ta gaisheshi, ya amsa fuskarsa dauke da murmushi. Ledar ya mik'amata.   "Ajiye wannan sannan ki zo ki sameni."   Gabanta ya fad'i, ta dubi ledar sannan ta dubeshi.  "Kar6i mana." Jiki a sanyaye ta kar6a.   "Nagode." Ya yi gaba gami da fadin. "Ina jiranki."    Ta juya ta koma ciki har lokacin jikinta babu kwari.   "Anya batayi wauta ba? Meyasa ta kar6a batare da tunanin kada wani abin ya biyo baya ba?"    Ganin dai babu wanda ya ganta, yasa hankalinta ya dan kwanta. "Anyi na farko, in sha Allah shine na karshe." Ta fada a fili, sanin da ta yi babu wani aikin da bata yi ba ne ballantana wani ya nemeta yasa ta saurin mik'ewa bayan ta daga hannu sama.   "Ya Allah ka taimakeni yau wannan bawa naKa ya fahimceni."   Daga haka ta shafa sannan ta fice.      Akan idon Binta, Ummi ta fito ta wuce, ganin Ummin na shirin waigowa ne yasa ta saurin komawa baya yanda bazata ganta ba, saida ta tabbatar ta bar wajen sannan ta shiga tafa hannuwa tana salati.   "Tabdijam! Ashe dai duk jirgi daya ya kwasosu da Kb? Duk wannan shiru-shirun na wofi ne? Kuma wai Ummi?!" Tayi maganar a fili cikin nuna tsananin mamakinta. Lallai DAN ADAM mai wuyar gane hali ne. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   58   Ba su suka dawo gidan ba sai bayan Magriba. Yana fakawa suka fito kowacce hannunta rik'e da leda wanda kayan mak'ulashe ne zalla. Ihsan bayan sun danyi gaba ta dubi Ikram.   "Wai duk wancan kayan zak'in da Yaya Faruk ya loda na shi ne sho d'aya?"   Ikram ta harareta. "Meya hanaki tambayarsa?"   Ta yi dariya. "Mezai kaini gangancin nan?"   "Wai ma, kina ganin dai ya mik'o mana na Hajiya, kinsan dai nasa ne ko? Amma dai bansani ba ko anjima zai je hira." Ta k'arashe cikin zolaya. Ihsan ta buga tsaki gami da k'ara d'aga kafa. "Ke dama ai ba'a hirar arziki dake sai kin kwafsa a wani 6angaren."   Ita dai Ikram da dariya kawai ta bita.           Shi kuwa gogan kai tsaye sashensa ya nufa, saida ya yi sallah ya fito ya lek'a su Hajiya kafin ya koma sashensa ya fito rike da ledar Ummi wacce ya yo mata siyayya.     Daidai lokacin da ya kwankwasa mata, Binta ta fito daga bandaki, zaro ido ta yi domin mamaki da ya cikata. Me Yalla6ai ke yi a bakin k'ofar dakin Ummi har yana kwankwasawa? Ta so ta yi magana saidai ta kuma la6ewa don ganin wannan abin Al'ajabin.     Ummi ta shafa adduarta, idar da sallar isha'in ta kenan, mik'ewa ta yi ta nufi k'ofar gami da bud'ewa. Suka dubi juna ta gaisheshi, ya amsa fuskarsa dauke da murmushi. Ledar ya mik'amata.   "Ajiye wannan sannan ki zo ki sameni."   Gabanta ya fad'i, ta dubi ledar sannan ta dubeshi.  "Kar6i mana." Jiki a sanyaye ta kar6a.   "Nagode." Ya yi gaba gami da fadin. "Ina jiranki."    Ta juya ta koma ciki har lokacin jikinta babu kwari.   "Anya batayi wauta ba? Meyasa ta kar6a batare da tunanin kada wani abin ya biyo baya ba?"    Ganin dai babu wanda ya ganta, yasa hankalinta ya dan kwanta. "Anyi na farko, in sha Allah shine na karshe." Ta fada a fili, sanin da ta yi babu wani aikin da bata yi ba ne ballantana wani ya nemeta yasa ta saurin mik'ewa bayan ta daga hannu sama.   "Ya Allah ka taimakeni yau wannan bawa naKa ya fahimceni."   Daga haka ta shafa sannan ta fice.      Akan idon Binta, Ummi ta fito ta wuce, ganin Ummin na shirin waigowa ne yasa ta saurin komawa baya yanda bazata ganta ba, saida ta tabbatar ta bar wajen sannan ta shiga tafa hannuwa tana salati.   "Tabdijam! Ashe dai duk jirgi daya ya kwasosu da Kb? Duk wannan shiru-shirun na wofi ne? Kuma wai Ummi?!" Tayi maganar a fili cikin nuna tsananin mamakinta. Lallai DAN ADAM mai wuyar gane hali ne.   Saida ta lek'a dakin ta gama bud'e ledar ta ga kayan mak'ulashen da ke ciki sannan ta fita tana had'iyar yawu.   "Ina yarinya, wannan kam dole nima ki bani rabona."        Acan kuwa Ummi ta iske Faruk durkushe gaban ruwa yana sanya tafin hannunsa na dama yana wasa da shi, fuskarsa a sake. Jin shigowarta yasa shi kallonta, ta kauda idanunta ta karasa bayan ta rufe k'ofar.     Mikewa ya yi ya koma ya zauna, itama ganin haka ne yasa ta zama a dayan kujerar kamar yanda sukayi wancan karon saidai a wannan karon ya sanya kujerun suna kallon juna, hakan yasa shi bawa k'ofa baya ita kuwa tana fuskanta.     "Na yi zaton bazaki zo ba ai." Babu abinda ta ce sai wasa da gefen hijabinta da ta ke.     "Ummina."   Ba ta amsa ba sai kirjinta da ke lugude.    "Wai meyasa ne kike kasa sakin jiki da ni? Idan da magana a bakinki ko fad'a."    Ta ga dama ta samu, hakan yasa ta daurewa ta dubeshi. "Don Allah Yaya Faruk ka yi hakuri ka kyaleni." Ta sauke idanunta daga kansa kafin ta cigaba da magana a raunane. "Wannan abu ne da ko a mafarki ban ta6a ganin ya faru ba, 'yar aiki da auren d'an masu gida, kayi hakuri domin Allah, komai dake a ranka game da ni ka ajiyeshi gefe. Ni bazan iya abinda ka ke so ba, banason saka kaina cikin kowace matsala. Ka gafarceni amman idan akwai inda na kuskuro a maganata."     Tun soma maganarta ya zubamata ido hannayensa biyu dunk'ule wuri guda. Ya lura iyakar gaskiyarta ta ke fad'a ba kuma don bata sonshi ba. Ya girgiza kai.   "Meyasa ni ban ta6a hangen matsalar da kike yawan ikrari bane Ummi? Kina da tsoro, nasan kuma abinda ke tsorata ki wanda sam bai dace ba. Na farko dai nasan iyayena ba zasu hanani aurenki ba matukar na nuna musu ke ce za6ina, su din sun kasance maso abinda nake so, haka kuma yan uwana na tabbatar ba zasu hanani rayuwa da ke ba Ummi, koda ace kuma basu yi na'am da ke ba, to fa hakan ba zaisa na k'i aurenki ba muddin iyayena sun yarjemin. Batu na gaba, ni ban daukeki daban da ni ba, Allah ne Ya haliccemu duka, ina yi miki kallo daidai da matsayina, ki ture dukkan wadannan kananun matsalolin Ummi, ki sauk'ak'awa zuk'atanmu, nasan kina jin abinda nake ji duk da cewar ba ki kama koda rabin k'afata ba."   Shiru ya dan biyu baya, ya rankwafo kadan ya soma magana cikin rad'a.   "Kin yarda kin amince na sanarwa Hajiya..."   Bai kai ga karasawa ba ta hau girgiza kai tana dubansa da idanunta wadanda suka ciko da kwalla. "A'a, a'a, don Allah kada ka fadawa kowa idan ba haka ba zan gudu."   Ya dan hade gira jin kalmarta na karshe.     "Saboda kada ki aureni ne za ki gudu?"   Ganin yanda muryarsa ta chanja da kuma yanayinsa yasa ta yin shiru gami da duk'ar da kai. Ya lumshe ido.   "Shikenan, tashi ki tafi."   Ta kasa motsawa, sai ta ji bata kyauta mishi ba, shi kuwa har lokacin bai bude idanunsa ba, dagaske bai ji dadin furucinta ba, kenan akan ta aureshi, ta za6i guduwa?      "Ka yi hakuri don Allah."   Ya tsinci muryarta, da sauri ya bude ido don kuwa muryar ta nuna alamun kuka takeyi.  Kukan kuwa takeyi, ya girgiza mata kai. "No Ummi please, banson hawayenki fa. Ni na hakura."   Faruk ya cigaba da kasheta da dad'ad'an kalamai wadanda nan take suka kashemata jiki suka sukurkuta ta. Allah Ya mishi baiwar iya lafuzza masu dadi da saurin sace zuciya wanda shi kansa bai sani ba sai a yanzun da ya fad'a cikin soyayyar Umminsa. A wannan zaman da sukayi saida Faruk ya ci galaba don kuwa Ummi ta dan saki jikinta sun yi hira mai dadi har da dariya. Kowannensu yana jin zuciyarsa sakayau, gaba daya ji sukeyi tamkar a duniyar babu sauran bil adama sai su biyu tallin tal! A karshe ya duba wayarsa da ta soma k'ara, yayansa Likita ne(Ridwan). Ya dauka. Bayan sallama ya tambayeshi inda ya shiga, ga shi kuma a falon Hajiyarsu bai ganshi ba.   Ya dubi fuskar Ummi wacce ke dan satar kallonsa, murmushi ylm    a yi ganin ta kauda kanta. "Hira nake yi da surukarku amma ina nan zuwa."    Daga haka ya katse kiran ya bar Ummi da sakin baki. "To sarkin tsoro, rufe bakin." Yana fadin haka ya mik'e tsaye. "Bari na wuce Dakta ya zo. Sai mun hadu gobe kuma in sha Allahu ko?"   Ta girgiza kai alamar aa. Ya ja dan guntun tsaki. "Kinga dadin waya kenan, da sai mu sha hira, amma dai ba wani abu."   Daga haka ya yi mata sallama ya wuce, itama barin wajen ta yi da saurinta. Tana shiga dakin ta fidda hijabinta ta zauna, a yau ji take dukkan shawararwarin Antinta babu daya da ta iya dauka, ji take kamar ana k'ara rura mata wutar kaunar Faruk. Ta matso da ledar ta bude, ta yi mamakin ganin kayan kwalam har da su meatpie nad'e a jikin tissue guda uku, ga wani kullin leda karami wanda tana budewa ta ci karo da alawoyi kala-kala. Harda su cake da robar ice-cream manya biyu.     "Assalamu alaikum." Da bude kofar da sallamar nata duk lokaci guda ne DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   60 "Ya Salam, haba Ihsan, meyasa haka?"   Ihsan ta mike zaune idanunta jage-jage da ruwan hawaye. Ta ja majina. "Kinga lokaci ya k'uremin ko Ikram? Da ace na bi shawararki da banga wannan rana ba."   Ikram tausayinta ya mamayeta, ta dafa kafadarta gami da girgiza mata kai. "Aa, lokaci har yanzu da sauransa Ihsan. Na fadamiki ki cire kunya ki sanarwa Faruk abindq kike ji game da shi koda ta hanyar  kafar sadarwa (whatsapp)ne. Kada ki karaya da wuri."    Haka ta yita lallashinta sannan ta fita wajen yan uwanta. Tana fita Ihsan ta dauki waya ta kira Maminta. Ko sallama bata iya yi ba ta fashe mata da kuka gami da labartamata abinda ake ciki. Mami ta shiga damuwa ainun.   "Ihsan kina kyautatamasa kuwa kamar yanda nace?"    "Babu abinda bana yi Mami, har gyaran dakinsa hana Ikram nayi na ke yi, amma wannan duk ba ya gani, ni yanzu na yanke shawarar sanarmishi irin illar da sonshi ya yiwa zuciyata."   Mami ta karya murya. "Kina ganin hakan zai fi?" "Eh Mami."   Mami ta jinjina kai, kwarai kuma tasan Faruk yana da mutunci, bazai so damuwar 'yar uwarsa ba.     "Shikenan, ayi hakan. Amma ki san abinda za kice dai."    Haka ta yita lalla6a diyarta, bata son abinda zai ta6a farincikin 'yar tata ko kadan. A karshe ta sanarmata cewa an soma shirye-shiryen tafiyar Adnan Dubai inda ya za6a. Maganar ta yi mata dadi, hakan ya rage zafin da zuciyarta ke yi ta dan samu nutsuwa. Falon da bata koma kenan ba!                   ***   ***   ***                       RINGIM       TSAFI GASKIYAR MAI SHI... Kwarai wannan zance haka yake, don a kwana uku kacal! Dija da uwarta sun yi dukkanin k'ulla-k'ullarsu sun dauke hankalin Deen tsaf daga kan matarsa, kacokam zuciyarsa ta koma ga Dija. A yau lahadi ya yi shirin zuwa Ringim, don tun cikin ranakun aiki ya ke son kawomata ziyara tana hanashi. Yau kam ko sanarmata baiyi ba sai ganinsa sukayi. A kofar gidan ya faka motarsa, ya kirata a waya ya sanarmata yana kofa. Ta yi mamaki har da tsalle da ihunta na murna, Baba Habiba itama ranta sakayau. Ta taimakamata ta shirya sannan ta mik'amata turare da kwallin da suka kar6o.   "Saka 'yar albarka."   Tana dariya ta soma da kwallin sannan ta feshe jikinta da turaren mai kamshin 'yan bori, wanda aka tabbatarmusu cewar Deen zai ji ba kamshin da ya fi so anan duniya sai shi.    Daga haka ta fita ta sameshi, ai kuwa yana ganinta ya budemata kofa ta shiga. Nan take ya ji wutar kaunarta na k'ara ruruwa cikin ransa, sun sha hira inda ya matso dab da ita yana jin kamar ya sanyata jikinsa saidai ganin idanin mutane dake kansu yasa ta tsawatarmishi. Ya sanarmata cewa da zarar ya koma zai turo magabatansa, wannan yafi komai yi mata dadi don ta lura ya shiga hannu ta yanda shi kansa kwata-kwata ya bar shakkar dangin Munira su ji labari.      Ya sha hira sannan ya tafi, a daren ya k'ara dawowa, har suka gaisa da Malam Yahuza wanda ya yita mamakin ganinsa kuma da sunan ya zo wurin diyarsa. Koda ya shiga ciki ya tambayi Habiba, ta sanarmishi ai da aure ya ke sonta. Hankalinsa ya tashi da wannan amsa da ya samu, ya so nuna rashin goyon bayansa saidai ba shi da wannan isar a gidansa, sai ma ya tsinci bakinsa da furta kalaman nuna jin dadin al'amarin ba don har cikin zuciyarsa hakan bane.    Ita kuwa Dija da Deen murzar juna sukayi son ransu, dakyar suka rabu.    Washegari Baba Habiba ta nufi wajen aminiyarta ta sanarmata komai, shewa Saude ta yi don abin ba k'aramin dadi ya yi mata ba.    "Kice lokaci ya yi? Ai karku damu da abinda mutane zasu ce matar mutum fa kabarinsa, atoh."   Dariya Habiba ta yi tana dan waige-waige.   "Wai ina Mariya ne ban ganta ba tun zuwana?"   Saude ta murmusa. "Mariya kuma da farin jini, tana nan zaune Dauda dan gidan Zinaru ya aiko kiranta."   Habiba ta dan yi jim. "Anya Saude? Dauda fa kamar na ta6a ji ya yiwa wata budurwa ciki?"    Saude ta girgiza kai. "Bar mutane da shegen karya Habiba, yaron nan har nan ya ke zuwa mu gaisa, kar kiso kiga irin kyautatawar da ya ke yiwa Mariya. Kuma banda abinki, yarinya da bata fi shekara tara ba?"   Habiba ta jinjina kai. "Shikenan, amma gaskiya ki saka idanu." Saude ta gamsu da zancenta.                  ***   ***  ***                      ABUJA      Washegari Faruk da wuri ya tashi kawai don ya ga Umminsa. Ai kuwa yana sanya kai a falon Hajiyarsa na sama ya yi tozali da ita tana aikin shara.      Ta dago kanta jin sallamarsa, ta amsa a hankali sannan ta russuna ta gaisheshi.   "Lafiya, kin tashi lafiya?" Ta amsa da murmushi dauke saman fuskarta. "Alhamdulillah."   Ya dubi falon sannan ya dubeta. "Kai Ummi, duk girman falon nan haka kike share shi? Sannu kinji? Karki damu na wani dan lokaci ne."   Ta dubi hanyar dakunan mutanen gidan, (Hajiya  tana sashen mijinta)sannan ta dubeshi cikin murya k'arama ta ce.   "Ka yi hakuri ka kyaleni don Allah kaga a falon Hajiya ne, komai zai iya faruwa."    Ya ta6e baki yana mai gyara tsayuwarsa.   "Ke ni na soma gajiya da wannan tsoron naki, me kike tsoro ne alhalin wataran gidana zasu daukoki su kawo? Kalli,(ya dubi jikinsa sannan ya maida dubansa gareta, ko wanka banyi ba na zo kawai domin na ganki ki ji dadi shi ne kike korata, why?"   Maganar ma ta so bata dariya saidai kasancewar ba a nutse ta ke ba yasa bata dara ba, wato don ta ganshi ta ji dadi?   "Na ganka amma don Allah ka bar..." Jin motsin murda kofar dakin kwanan su Ikram ne yasa ta saurin juyawa ta cigaba da shara. Ihsan din ce ta fito daga ita sai riga iyaka gwuiwa da dogon wando (cotton) na bacci. Kanta ko hula babu, Faruk ya juyo yana dubanta. Ta karemishi kallo daga shi sai dogon wando na bacci da singilet, yana tsaye hannuwansa cikin aljihun wandon, ya kauda kansa daga gareta, ta fito cike da mamakin abinda ya kawoshi da safe bayan ta riga tasan baya fitowa sai ya yi wanka ya shirya, ta kai dubanta ga Ummi, shara take yi abinta, babu wani abu da ta gani wanda zai sa ta tsargu cewar akwai wata a k'asa, saidai zuciyarta ta kasa nutsuwa akan ganin da ta yi mishi tsaye kuma shi kadai tare da Ummi.   A sanyaye ta gaisheshi, ya gyada kai, daga haka ya juya ya fice. Ta bishi da kallo kafin ta dubi Ummi wacce ta yi kamar batasan wainar da suke toyawa ba.  Karasawa ta yi ta tsaya a gabanta tana mai take tsintsiyar, Ummi abin ya bata haushi, ji ta ke kamar ta tureta ta fadi k'as. Saidai a fili bata nuna komai ba, ta dago ta dubeta fuskarta ba walwala babu kuma fushi. Ihsan ta watsamata kallon tsana don ta lura yarinyar kamar ta k'ara gogewa a yan kwanakin da ta yi a Abuja.    "Tun yaushe Yaya Faruk ya shigo?"   Abin ya so bawa Ummi dariya, ta barwa cikinta. "Yana zuwa kika fito falon." Ihsan ta dan yi sakato tana dubanta kamar dai bata yarda ba don jikinta ya bata akwai wani abun, sai kuma ta ja tsaki.   "Koma dai menene, mutum ya kiyaye yasan matsayinsa."   Ummi ta dan rausaya kai. "To me ya kawo wannan maganar kuma?" Cike da mamaki Ihsan ta dubeta. "Eh lallai, har anzo ga6ar da zan fadi magana ki tuhumeni akanta? Lallai wuyanki ya soma kauri." 'Tukunna ma dai Ihsan, matukar zaki cigaba da gasamin magana za kico karo da fin haka.'   A fili kuwa ta ce. "Allah Ya baki hakuri."   Wawan tsaki ta ja ta yi gaba ta zauna saman kujera gami da kunna talabijin, daman abinda ya fito da ita kenan, kallon wani(series)na 'yan Philippines wanda bata samun kallo da dare sai karfe takwas na safe suke maimaicin sati duk ranar lahadi.     Ummi murmushi kawai ta yi sannan ta cigaba da shararta zuciyarta wasai.       DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    59 Ta daure ta 6oye razanar da ta yi, ta amsa mata. Karasowa ta yi tana mai zaro ido.   "Ke Ummi yau asirinki dai ya tonu, ashe kema 'yar hannu ce, naga ma kusan kin fi Sa'ade sa'a don kuwa ke kamun babban goro kikayi."    Ummi da ta rasa meke mata dadi a duniya ta cigaba da kallonta tana ji kamar ta saki fitsari.   "Me..me..kike so ki ce?"   Binta ta yi dariya kadan lokacin da ta zauna tana mai sa hannu ta janyo ledar. "Eh lallai dole ki rude, ki kwantar da hankalinki ki ci arziki, ai ni idan har za ki dunga yagamin abinda kika samo to fa kar kiji komai don ba ko da matsala da ni. Ki bi sannu dai da mutan gidan da su Bala(mai kula da shukoki), su ne abin ji."   Ta fiddo meatpie ta gutsira. Ummi dai banda innalillahi babu abinda take fada a ranta, Binta ta ganota saidai ta to musu mugun fassara, to daman ina zata aminta cewar soyayya na tafi tsakani da Allah, namiji kamar Faruk zaiyi mata?    "Wallahi babu makamanciyar abinda ki ke zargi tsakanina da Yaya Faruk."   Binta tana taunar meatpie ta watsamata harara.   "Wai kina zaton ban ganku sadda ku ka shiga wajen wanka ba? Haba Ummi, wannan ba abin rufemin bane, nifa makwafciyarki ce, idan ban rufamiki asiri ba wa zai rufa? Tun yaushe ya soma nemanki?"   Ran Ummi idan ya yi dubu to ya 6aci don jin wannan mummunan zaton da Binta ta yi mata.   "Ina miki rantsuwa da Allah abinda kike tsammani tsakanina da Yaya Faruk ba haka bane."    Binta ta yi sakato. "To menene? A banza zai kawowa 'yar aiki kayayyaki har haka batare da cewa yana da buk'ata akanki ba? Haba Ummi, ko kunnuwana sun kai dubu bafa zan yarda da abinda ki ke fad'a ba. Kedai ki saki jiki kawai arziki ne ya zo miki, idan ma kin ci sa'a nan gaba ya daga darajarki a gidannan."    Ummi ta runtse ido, ta fahimci Binta ta yi nisa cikin zargin abinda ba haka ba. Bai kuma kamata ta barta da wannan bahagon tunanin ba.   "Tsaya ki ji gaskiyar magana, amma don Allah ki rufamin sirrina."   Binta ta tsaya tana dubanta. "Karki damu, ki saki jiki ki sanarmin, wallahi zan bar zancen a tsakaninmu."   Ummi ta kwashe abinda ke faruwa ta sanarmata. Binta wacce ta daskare awajen ta kasa ko kwakkwarar magana, mamaki ne ya cikata kwarai dagaske, ba don ya ganewa idanunta ba da sai ta iya karyata Ummi nan take, saidai kuma har zuciyarta ta aminta da hakan. Ta cigaba da karewa Ummi kallo, ba k'arya tana da kyawun gani a yaba kuma a so, amma abin mamakin, akwai fiye da ita masu son Faruk saidai wai ace basu isheshi kallo ba sai ita?   Ummi duk ta k'ara tsorata ganin irin kallon da Binta ke bin ta da shi, ga dukkan alamu bata yarda da zancenta ba ne. Wannan yasa ta kara riko hannunta.   "Wallahi iyakar gaskiyar kenan, na gayamaki banda wannan babu abinda ke tsakaninmu, na rasa kuma yanda zanyi ya bar shiga harkata."    Binta ta jinjina kai gami da sauke ajiyar zuciya. "Tab! Babbar magana. Amma kin kusa kiyi wauta wallahi Ummi, da ace ni na samu wannan damar da babu ta yanda zanyi watsi da ita. Aure fa Ummi? Auren ma da matashi irin Yalla6ai Faruk? Gaskiya ki sake tunani, ki cire tsoro kamar yanda yace din ki tabbatar kin ba shi goyon baya. Karki damu ni don na rufamiki wannan asirin to ba komai ba ne wallahi. Idan ma na ce zan tona ai na shiga uku don nasan nima korata zaayi."   Ta karashe da dariya, Ummi kuwa ta murmusa, hankalinta ya kwanta kadan.    Ta dibarmata kusan rabin kayan sannan Binta ta fice zuwa dakinta bayan ta kara jaddada mata akan kada ta sake ta bari wannan dama ta kufcemata. Ummi da to kawai ta bita.                  Ihsan tunda ta ji abinda Faruk ya ce wa Dakta hankalinta ya tashi, ji ta ke kamar ta yi tsuntsuwa ta je sashensa ta ganewa idonta ko dagaske ne. Wai ashe dai yana da budurwa wacce ya ke so ta ke zaman jiran gawon shanu? Sam bazai yiwu ba! Sai a yau ta ji tana son bin shawarar Ikram, wato ta sanarwa Faruk yanda ta ke jinsa a ranta. Ta numfasa. 'Shi kadai ne mafita.' Ta ayyana hakan a zuciyarta.    Mintuna biyar da haka, sai ga shi ya shigo falon. Suka dubeshi. Haidar ya ce. "Ina shirin bin sahu na ga 'yar gidan taka sai kuma gakanan."   Faruk wanda tun shigowarsa ya ke murmushi ya zauna a saman kafet kusa da kafafun Babban Yaya, hannu yasa ya dauki ayaba guda cikin wanda suke ci.    "Yanzu Dakta saida ka tonamin?"   "Ana 6oye abin farinciki ne?" Cewar Dakta. Ya girgiza kai yana 'yar dariya.   "Yanzu fa na soma yak'in, ban kai ga cin nasara ba."   Sukayi dariya gaba daya har Ikram, Ihsan ji ta ke yi tamkar ta fashe. Gaba dayansu sun yarda don tunda suke da kaninnasu basu ta6a jin ya yi musu zancen kowace mace ba sai a yau din.    "Dariyar me akeyi?" Fadin Daddy wanda shigowarsa gidan kenan daga waje, ya yi bak'o. Bayan ya karaso ya zauna suka dubeshi. Babban Yaya ne ya soma magana.   "Daddy kaninmu ya samo maka suruka fa."   Da mamaki ya dubi Faruk wanda banda murmushi da taunar ayaba babu abinda ya ke yi.   "Dagaske?" Faruk bai amsa ba. Daddy ya ji dadi a ransa. "Kai Masha Allah, na ji dadin wannan lamari. Ai gwara ka soma shirin auren kafin na yi maka na dole." Aka dara, Daddy ba ruwansa matukar yana da lokaci yakan zauna da iyalinsa suyi hira da dariya. Hajiya Babba ta sauko itama tare da wata budurwa da uwarta ta aiko daukar mata mayafai, bayan ta sallameta ta dawo wajensu, alokacin Ihsan ta sulale ta bar falon don tsabar takaici. Nan itama aka fesamata, murmushi kawai ta yi tare da addu'ar nemawa danta za6in Allah. Daga nan kuma hira ta 6arke, Ikram tuni ta ankara babu Ihsan a falon hakan yasa ta bi bayanta.     A can karshen gadonsu ta risketa ta sanya kanta cikin filo tana kuka har da sheshshek'a. Ta karasa ta zauna a gefenta. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 61   Zaune ta ke a (Garden) tana wanke kayanta kala daya, tana yi tana dan wak'e-wak'enta. Bata da masaniyar cewa Faruk na daga barandarsa yana kallonta, a gabansa abin zane ne. Ya jima yana dubanta da murmushi dauke a saman fuskarsa kafin daga bisani ya hau zanata. Iyakar fuskar kawai ya zana, bayan kammalawarsa ya mike ya sauka.   Ba zato ta ji shi zaune a gefenta saman kujera. Ta dubeshi gabanta na dukan uku-uku sannan ta dubi hanya.    "Kar6i wannan kiga, hoton matar da zan aura ce."    Gabanta ya fadi, ta dubi takardar da ya kanannad'e sannan ta dubeshi, shi dinma ita ya ke kallo da son lura da yanayinta. Murmushin yak'e ta yi. "Hannuna da ruwa, kada na jik'a maka."    "Kar6i ba komai." Ta sa hannunta wanda ya soma rawa ta kar6a. Koda ta bude, kallon tsoro ta yiwa zanen don kuwa wani kishi ta ke ji yana sukar zuciyarta.     "Ta yi kyau, Allah Yasa alheri." "Ameen, nagode." Ya fada yana dubanta, ya tabbatar bata kalli zanen sosai ba, wannan alamu ne na tana sonshi kuma tana kishinsa hakan kuma ya mishi dadi.     Ya dan lek'a fuskarta. "Za ki halarci bikin?" Ji ta yi kamar ta kai mishi bugu, ashe komai da ya ke fadamata a baki ya tsaya? Daman itama ta yi wautar daukar zantukansa ta saka a rai. Yaudarar kai kenan. Ta kauda fuskarta gefe. "Um." Ya yi wani murmushi. "Mungode." Daga haka ya bar wajen, ta bi bayansa da kallo, daidai da fatarsa fara k'al kalar 'ya'yan hutu ne, ina ita ina shi ne? Bata kyautawa kanta da rayuwarta ba da har ta bari kaunarsa ta shiga ranta.    Ta k'ara duban takardar cike ba tayi wata-wata ba ta d'aga da zummar yagawa saidai me? Karo ta ci da wata mai kama da ita, ta zaro ido tana k'ara duba sosai, shakka babu ita ce, har  dan lotsawar kumatunta. Kunya ta kamata, shikenan Faruk ya gane tana kishinsa tunda har ta kasa 6oyewa. Kamar ance ta daga kanta, sukayi ido hudu da shi daga barandarsa. Ya kashemata ido daya, ta yi saurin mikewa ta bar wajen tana murmushi tare da mamakin yanda akayi har ya isa ga dakinsa, kodayake ba wani nisa ne daga nan ba.  Ta adana takardar cikin kayanta, saida ta tabbatar ya bar wajen sannan ta koma ga aikinta.                Ihsan ta dubi Ihsan fuska a washe. "Kina ganin hakan yafi?"   Ikram tana murmushi ta gyada kai. "Kwarai kuwa, ke kanki kusan komai zai fi zuwar miki da sauki, kinga cikin kyautar da za ki ba shi sai ki isar da sak'onki ta nan." Ihsan harda tsalle ta yi ta rungume Ikram. "Yaushe ya kama ranar haihuwar tasa?"   Ikram na dariya ta amsa. "Jibi ne, sha shida ga watan (March), kada mu sanarmishi batun fatin, ya kasance mun bashi mamaki, saidai ya dawo gida ya tarar da komai."   Sukayi dariya. "Daidai kenan." Cewar Ihsan. "Naji, taso muje mu yi shawara da Hajiya."   Koda suka je, batun fatin kawai suka sanarmata, nan kuwa ta basu goyon baya dari bisa dari don Faruk tun yana da shekaru ashirin rabon da ayimishi wani birthday party. Ta taimaka musu da kudade suka soma shiri da sanin Daddy da yayyunsa maza har ma da matansu. Duk uban gayyar ma baida labari, asalima ya mance da wani batun ranar haihuwarsa da ta kusan zagayowa.                     ***   ***   ***                         RINGIM     Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba don kuwa a ranar litinin Deen ya iso da wani baffansa wanda shi kadai ya samu dakyar ya lalla6a akan zai nema mishi auren Dija, iyayensa dai sunce babu hannunsu hakanan basu yarje mishi ba don wannan cin amana ne, saidai adalilin makancewa da ya riga ya yi a son Dija ko kusa bai dauki maganarsu da girma ba, haka ya samu wani kanin mahaifinsa ya shige mishi gaba. Koda suka zo ga Malam Yahuza, ba yanda ya iya hakanan ya kar6i kudin auren shi da wani makwafcinsa, a karshe aka tsaida maganar aure nan da wata daya kamar yanda Deen ya nema, Malam Yahuza ya zo mishi da korafin cewar sai ya shirya amma Deen ya tabbatar mishi matukar saboda kayan d'aki ne, to fa ya dauke mishi komai. Sun cika da mamaki kwarai, shi kuwa Deen ji ya ke yi idan har baayi auren nan ba, to kuwa so da shaawar Dija zasu iya mishi lahani.    Kafin kace me, gari ya dauka cewar Malam Yahuza ya kar6i kudin auren Dija daga Zahraddeen miji ga'yar uwarta. Ai kuwa magana har gidan iyayen Munira. Sai ga mahaifiyar Munira da kanta, Bilkisu ta zo har gidan.    A tsakar gidan ta iske Malam Yahuza da Habiba, da sallama ta shiga suka amsa. Habiba ta saki fuska. "Aa, Bilkisu kece tafe? Karaso mana."   Bilkisu ta zauna saman kujera yar tsugunno sannan ta dubi dan uwanta dake cin magani kamar ya ga kashi.   "Yaya ina wuni." "Lafiya." Ya amsa dakyar, ta gyada kai, bata wani damu sosai ba tunda daman haka ya saba amsa gaisuwarsu a wasu lokutan idan Habiba ta murda kambunta.   "Wani labari na ji a gari shine na zo don tabbatar da gaskiyarsa."   Habiba murmushi kawai ta ke, Malam Yahuza ya kara tamke fuska, acan kasan zuciyarsa ko kadan bai jin dadin abinda ke faruwa saidai ba halin nunawa tunda yana gaban sarauniyartasa.    "Wane magana kuma?" "Wai Zahraddeen zai auri Khadija?" Kafin ya yi magana Habiba ta amshe. "Gaskiyar maganar kenan Bilkisu, yanzu nake shirin aikamuku cewar ku zo amsar kayan saka rana da lefe jibi, sai kuma ga ki da kanki don Allah ki aika a gayawa sauran dangi na kusa da ke."     Bilkisu ta rasa me za ta ce, tsananin mamaki da tsoron hali na DAN ADAM su ne suka fi cikata. Ganin abin ta ke yi kamar almara, kamar dai a ire-iren litattafan da ta ke sauraro a shirin Rai Dangin Goro, ashe da gaske yana zama gaske?    Ta mik'e tsaye sakamakon ruwan hawaye da ya soma kwaranyo mata a saman fuska. Ta dubi dan uwanta. "To madallah, nagode kwarai da wannan cin amanar zamantakewar, babu abinda zance muku saidai duk wanda ya yi mai kyau kansa, akwai ranar k'in dillanci. Tabbas kun nuna hali irin na DAN ADAM na butulci, amma bakomai, Allah Yana nan."   Daga haka ta sanya kai ta fice tana share fuskarta da mayafi. Tana jin sababin da Habiba ta ke yiwa yayanta akan yana ji ta ci zarafinsu bai dauki wani kwakkwarar mataki ba.     Koda Bilki ta isa gida saida ta sha fadan mijinta Malam Amadu akan dalilin da yasa bata bi maganarsa ba ta je gidan, ya kuma gargadeta akan kada ta sanarwa diyartasu tukunna har sai anga abinda hali ya yi. Daga wannan suka rufe maganar sai jimami da tunane-tunane.                    ***   ***   ***                       ABUJA DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   61                       ABUJA   Tun wajejan uku na rana ta lura gidan kamar akwai wani shagalin da zaayi a dalilin gyara(decoration) da ta ga Ihsan, Ikram harma da Intisar (wacce ke fama da ciki wata uku) suke yi a (Garden). Abin kyalkyali suke sanyawa mai ban shaawa, ita tana gefe saidai a bata umarnin mik'o ruwan sha, mik'o balan-balan(balloon). Hada ido goma idan zasuyi da Ihsan, to fa saita watsa mata mugun kallo har dai a karshe ta raba kanta da kallonta. Hajiya Babba na zaune saman daya daga cikin kujerun da suka jera sai waya ta ke yi da surukarta(Jiddar Dakta Ridwan) akan batun (Cake) da(snacks) da suka bayar da oda. Abinci kuwa, Fadila matar Babban Yaya ce ta dauki nauyin girkawa a gidanta sannan ta zo.      Suka dauko wani tangameman hoton Faruk wanda ya ya juya fuskarsa yana dan murmushi, kamar dai wanda bai so akayi hoton ba saidai hakan da ya yi ba karamin kyau ya yi ba, yana sanye da riga mai hula sai dogon wando a farfajiyar gidan, ya yiwa Ummi kyau sosai. Hoton an kafeshi a daidai inda suka sanya teburin ajiye (cake). Bayan komai ya kammalasannan Ummi da Binta suka tattare ledojin da sauran takardun da aka zubar a k'asa.      Haidar shine ya yi musu taimakon sanar da dukkan wasu abokan karatun Faruk da suke a garin, hakanan a 6angaren Ihsan ta gayyaci wasu kawayenta biyu mazauna Abuja domin su zo ta nunamusu mutumin da ta ke fatan ya zama mijinta. Ikram itama kusan dukkan kawayenta ta gayyata, bayan Magriba suka sanya fatin.      Duk wannan abu da sukeyi, Faruk ba shi da masaniya, zuwa dai lokacin yasan da cewa ranar ce ta(birthday) dinsa don tun sha biyun dare ya soma tsintar sak'onnin tayashi murnar cika shekaru talatin cif a duniya. Wasu ya basu amsa, wasu kuwa bai saman dama saidai ya aikamusu da alamar jinjina(like).     Tun karfe shida, mutane suka soma zuwa, kowannensu ya ci ado kamar wani gagarumin biki akeyi musamman ma matan da suke zuci-zucin haduwa da Matasan yaran Gen Ahmad Danzaki ko wani cikinsu zai kyasa koda kuwa ace basu samu shiga wajen Faruk Danzaki ba.     Binta ta dubi Ummi. "Oh ni Binta, ji yanda ake daukar kwalliya kamar baza"a mutu ba, ji sutura?"   Ummi wacce har lokacin bata bar lek'en windo ba ta murmusa. "Masu abu da abinsu?" Ta6e baki Binta ta yi. "Lallai kam, nasan dai duk don ya kyasa ne suke hakan, wasu ma ga dukkan alamu gayyar sod'i ne. To kwalelansu, Yalla6ai sai ke."   Abin ya bawa Ummi dariya ta dara tana mai girgiza kai. "Kai Binta, wai wa ya gayamaki hakan mai yiwuwa ne?"    Binta ta yi kwafa. "Ke kike ganin wuyarsa, amma na tabbatar karamin abu ne saidai kuma kin toshe kunnuwanki, ko kina da labarin Ihsan ma tana mutuwar son Yalla6ai?" Ta yi kamar bata sani ba. "Haba?"   "Wallahi, jiya ina jinsu ita da Ikram tana zugata akan ta za6i kayan da zata sanya masu kyau sosai don ta burgeshi."    Murmushi Ummi ta yi. "Allah Ya tabbatar." "Ba amin ba." Cewar Binta cikin sauri tana harararta, dariya kawai Ummi ta yi. Ta maida kanta ga duban windon inda ta nan suke lek'e, a ranta tana zuci-zucin ganin shigar da Ihsan din zata yi na sace zuciyar wanda ya riga ya fada tarkon kaunarta(ita Ummin).    Misalin bakwai da mintuna kowa ya gama halartar wajen, ya yi daidai da dawowar Faruk gidan, ya yi hon yana duban kofar gidansu ganin motoci fin takwas a fake, mamaki karara ya bayyana saman fuskarsa, to me akeyi hakan?  Maigadi ya budemishi kofa ya shigo, a lokacin, kai tsaye wajen fakin ya isa, nan ma cike da mamaki ya ke duban(garden) din wanda a kusa da wajen ake fakin, duhu ne a wajen babu haske, haushi ya kamashi ganin ga shi akwai wuta, to meyasa Bala bai kunna fitilun wajen ba? Idan ma mutuwa kwayayen sukayi ai da sai ya sanarmasa tunda shi keda alhakin kula da komai na gidan, shi ya ke sanyawa a gyara, tun soma aikinsa ya daukewa mahaifinsa wannan nauyin.        Ya fito kai tsaye yazo giftawa zai shiga sashensa, hasken fitilu suka dallare shi sakamakon kunnawa da akayi, ya dubi wajen da sauri. Mamaki tsantsa ya bayyana saman fuskarsa na ganin yanda wajen ya dauki ado ga wani tangameman hotonsa a wajen har da cake babba. Bai gama shanye mamakin ganin hakan ba, ya tsinci muryar su Ma'aruf dan Dakta Ridwan da sauran yaran Babban Yaya sun fito, dukkansu yaran  maza da mata cikin riga mai (coat) da wando, suna fadin. "Happy birthday to you!"    Fuska a sake ya ke dubansu, bai kai ga gama shanye mamakinsa ba ya tsinci tafi da sowar tsoffin yan makarantarsu maza da mata wadanda basu kai ga yin aure ba da kannensa da kawayensu harma da yayyunsa maza suma suna masa wakar taya murna. Baisan lokacin da ya saki 'yar dariya ba.    "What a surprise!" Shine furucin da ya yi a fili na bayyana tsananin mamaki. Ko babu komai wannan abu ya burgeshi matuk'a, ya kuma ji dadinsa. Haidar ya dafa kafadarsa. "Tafi ka chanja kaya, yau ranar murna ce."   Ya yi murmushi sannan aka bashi hanya ya wuce. Ihsan wacce ta ci ado cikin doguwar riga(gown) kalar fari da ruwan hoda, gashinta mai tsawo an tufkeshi ko dankwali babu akanta ta yi kyau matuk'a, ta rungume Ikram tana ihun murna.   "Kinga ni ko? Yaya Faruk ya ji dadin abinda mukayi."   Ikram ta dara. "Sai ma idan ya ji wacce ta kawo shawarar hakan." Ta lumshe ido don dadi, suka sanya dariya.     Acan kuwa saida ya watsa ruwa, daman ya yi sallar Magrib dinsa, wasu sabbin kaya ya gani ajiye a saman gado,  coat ne fari k'al mai bulun 'yar ciki masu dankaren kyau. Sun kar6eshi matuk'a, daidai da turare sabo fil aka ajiye mishi a saman gado, ya feshe jikinsa da shi. Shi kansa yasan ya kai a kirashi da Namiji.     Tun da ya fito yanmatan suke binshi da kallo, ya karasa kai tsaye da Hajiyarsa ta rungumi kafadarsa tana jin kamar ta hadiyeshi don kauna. "Kayi kyau Sadaukina." Ya yi murmushi. "Thank you Hajiyata." Daga nan ya karasa ga inda aka tanadar mishi don zama, nan kuma shagalin ya soma. Aka kirashi ya yi jawabi na nuna tsansar farin cikinsa, sannan ya yi godiya ya koma mazauninsa yana k'arewa wajen kallo.   'Ina Ummi?' Shine tambayar da ya jefawa zuciyarsa. Baiwar Allah tana daga can wajen hanyar shiga dakunansu a tsaye tana kallo, tana gani Binta da karambani har da chanja sutura gami da karasawa wajen sosai amma ita ta ce sam bada ita ba, tana tsoron cin zarafin da Ihsan kan iya yi mata a cikin taron jama'a, tasan ba k'aramin aikinta bane ba. A can kasan ranta kuwa, tsananin kishi ne ta ke jinsa kamar ya kasheta na yanmatannan ta tabbatar kowaccensu shi ta ke hari, tana tsoron kadan ya zamana wata acikinsu ta burgeshi har ya ji yana kaunarta. Ganin da ta yi bazata jure ba ne yasa ta juyawa gami da komawa ciki.       Shi kuwa daga nan inda ya ke zaune ya kasa nutsuwa haka nan ya ke daurewa kawai, ya yanke kek ya soma da sanyawa Babban Yaya a baki don tuni Hajiya ta koma ciki wajen mijinta, a ganinta taron na yara ne. Saida ya bawa yayyunsa kaf sannan suma suka bashi har suna 6ata mishi baki.  Daga nan kuma aka tafi sallah, bayan an dawo aka saka (cool music) inda kowa ya zauna aka hau ciye-ciye, Faruk dai ba magana ya kasa cin komai, burinsa kawai ya sanya Umminsa a ido, yana so ta tayashi murnar wannan rana itama.    Tunaninsa ya katse sa'ilin da aka tsayar da wak'a, Haidar ne ya yi magana inda ya ce kafin a kammala ciye-ciye, za'a bawa Faruk dama ya zana musu macen da ya ke burin ace ta zama mallakinsa a rayuwa. Habawa, zo kaga ihu da sowa, kowa fadi ya ke hakan ya yi. Faruk ya yi wani murmushi kafin ya kai duba ga yanmatan da su ke zaune a wajen, kowaccensu da salon kallon da ta ke jifansa da  shi, har da masu chanja wajen zama yanda zai gansu sosai. Ya kai dubansa ga Ihsan wacce ta ke dubansa itama gaba daya kasan a tsorace ta ke. Duk waigensa bai ci karo da Sanyin Idaniyarsa ba, tunaninsa ya katse sa'ilin da aka janye teburin kek dake gabansa aka ajiyemishi karamin tebur mai dauke da alk'aluman zane da fente-fente. Sai(sketchboard) wacce aka sanya farar takarda a jiki. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR         63     Ya dubi Haidar, duk wannan aikinsa ne, Haidar ya sakarmishi dariyar mugunta, sannan ya juya ga jama'ar ya bada umarnin kowa zai iya cigaba da ciye-ciyensa. Daga nan aka maida(cool music) din mai tashi a sannu-sannu.     A hankali ya zare(coat) dinsa ya dora a saman cinyarsa ta hagu sannan ya dubi jama'ar wadanda suna ci suna dubansa.   Ummi wacce tun sanarwar da Haidar ya yi ta tsinci kanta cikin mugun tashin hankali da fargabar abinda zai faru, tana tsaye ta kasa zama a dakinta karshe ta bude labule kadan tana lek'ensa.     Cikin sa'a idanunsa ya sauka akanta, da sauri ta saki labulen gami da zamewa ta zauna kirjinta na luguden tara-tara na fargabar abinda ke shirin faruwa.      Ya lumshe ido yana murmushi kafin ya dauki fek'akk'an fensir ya soma zanensa.    "Wa Faruk Danzaki zai zana?" Shine tambayar da kowannensu ke yi a junansu saidai babu tak'amaiman mutum daya da ya sani. Daidai da yayyunsa sun k'agu su ga fuskar masoyiyar dan uwannasu wacce basu ta6a sanin koda sunanta ba...!    Toh fa!!!!          Ummi a rud'e ta k'ara d'agowa gami da lek'awa. Hankali kwance ya ke zanensa banda murmushi babu abinda kake gani a saman fuskarsa. Wasu ruwan hawaye ne suka zubomata, shikenan yau babu ita ba k'ara kwana a gidannan. Da sauri ta juya ta soma harhad'a kayanta don bil hakki ita kadai tasan iyakar rudanin da ta shiga.     Gogan kuwa, ya kwashi tsawon minti goma sha biyar kafin ya kammala ya mik'e tsaye, ganin haka yasa kowannensu mik'ewa, kowace budurwa awajen babu wacce kirjinta bai bugu da sauri-sauri don fargabar fuskar da zasu gani. Haidar ya k'ara tasowa ya iso gareshi, ya kai dubansa ga takardar zanen, ya k'urawa zanen ido, babu abinda kake gani sai manyan idanunta, ya yi alamun nikaf wanda ya rufe gaba daya fuskarta,  sai kadan daga siririn hancinta da ya dan fiddo mai dauke da karamin bak'in tabo daga sama. Ya kauda lasufika sannan ya harareshi.   Haka mukayi da kai?" Faruk da ke kokarin saka kwat dinsa ya daga mishi gira kadan. "Ina kishin a ganta."   Haidar ya jinjina kai yana dariya sannan ya kara duban hoton sosai. "Kamar na ta6a ganin mai irin tabon nan, saidai bazan iya tuna a ina ba."    Faruk ya murmusa kafin ya k'ara daukar alk'alami, daga k'asa ya rubuta farkon sunanta. "H" Haidar duk iyakar tunaninsa bai ganeta ba, a karshe ya daga kafada kadan gami da maida dubansa ga jama'a wadanda ke jin kamar su tashi su warci hoton su sha kallo. Baice komai ba ya juya zanen ya nuna musu.   "Ga wacce Kanina ya zana, sunanta da harafin H ya soma, ya dai yi mana kwalelan fuskarta inda ya ce yana kishin a ganemishi kyakkyawar fuskarta."    Dariya matasan suka sanya, ita kuwa Ihsan ido ta k'urawa zanen, ta kasa gane ko wacece ita.   "Wace kenan?" Shine tambayar da da yawa daga yanmatan. Ihsan ta dubi Ikram cikin rawar murya don har ta soma kwalla.   "Wa ki ka sani mai farkon suna H?" Ikram wacce tausayin Ihsan ya mamayeta ta daga kafada kadan.   "Bani da masaniya akan kowacece, Hafsa kadai na sani sai Hadiyya, yanzu duk sunyi aure ma."    Ita kuwa Ummi jin maganar Haidar ne yasa ta tsayawa daga abinda ta soma na watsa kayanta cikin yar jakarta. Ta mike da sauri ta lek'a, saidai bata ganin zanen yanda ya kamata, hakan yasa ta fitowa wajen, a daidai bayan bishiyar dogon yaro ta dan la6e tana hangen zanen. Ta dan sauke ajiyar zuciya duk kuwa da cewar akwai sauran rina a kaba, ta shafi karan hancinta, tabbas bakin a tabon nan yana nan inda ya ke wanda ta samu asanadin wani ciwo da ta ji awajen tun tana yarinya. Gabanta na dukan tara-tara ta zaro ido. 'Yanzu idan aka gane ni da wannan tabon ya zanyi ni Hasiya?' Ta tambayi zuciyarta, tambayar da tasan amsar bai wuce na ta shiga uku ba.     Lokacin da Haidar ya kammala addu'oin fatan alheri shi da budurwar da ya ke so, aka soma mikewa da kadan kadan ana mik'a mishi kyautuka. Ihsan ta so barin wajen don ita kadai tasan yanda ta ke ji, saidai Ikram ta lalla6ata gami da nunamata kada ta sake ta yi wasa da wannan damar, shi kadai ya yi mata saura, haka ta daure ta karasa gami da mik'a mishi kyautar da ta tanada domin shi wanda a ciki sak'on da ta ke son isar mishi ya ke. Ya kar6a yana mai dubanta, ko baa fada ba, idan ka kalli idanunta kasan ta yi kuka. Bai nuna ya gane komai ba, godiya ya yi mata sannan ta bar wajen da saurinta.     Haka kawai sai Ummi ta ji tausayinta, tana son maso wani, son wanda ta ke yi don shi baisan tana yi ba. A sanyaye ta juya ta bar wajen ta koma daki. Bata yi mintuna uku da shiga ba ta ji an murda kofar da sallama an shigo. Ai batasan sadda ta mik'e tsaye ba tsabar kidimewa. Murmushi ya sakarmata sannan ya tura kofar ya rufe. Karasowa ya yi yana dubanta.   "Matsoraciya Ummina."   Ta yi raurau da ido, ya girgiza mata kai. "Kar fa kice kuka zakimin."    Ta yi k'asa da kanta. Yasa hannu a ha6anta ya dago fuskarta suka dubi juna ido cikin ido. Ta lumshe idonta don ba zata jure kallon kwayar idanunsa ba. Ya saukr hannunsa gami da sakin ajiyar zuciya. Allah kadai yasan irin wutar kaunarta da ke ruruwa a zuciyarta a kowane dak'ik'a. Hankalinsa ya kai ga kayanta da rabinsu ta sanya a jaka ga wasu a k'asa.   "Menene wannan?" Ta dubi kayan sannan ta tuna ashe fa guduwa ta yi shirin yi.    "Bakomai, linkesu nake yi." Ya durkusa gaban kayan ya soma dagasu, duk ba wasu kayan kirki gareta sosai ba, ya girgiza kai kawai ya mike tsaye. Ta dubeshi kadan. "Domin Allah ka tafi Yaya Faruk, kada a je nemanka."    Ya rungume hannunsa a kirji. "Wai kuwa Ummi kina kallon kanki a madubi kuwa?"   Bai bari ta yi magana ba yasa hannu ya dauki hodarta dake gefe ya bude gami da juyamata, ta dubi dan madubin na hodar, kafin ta sauke idanunta kasa. Ya numfasa da murmushi saman fuskarsa.   "Shikenan dai."   Shiru ya biyo baya, tana ji Haidar na cigiyarsa ta lasufika akan ya zo sallamar bak'insa. Ta daure ta yi magana. "Ina tayaka murnar wannan rana, Allah Ya k'aro shekaru masu albarka, Ya taimaki rayuwarka."   "Amin. Allah Ya nunamana na aurenmu haka. Thanks my Ummi, zo muje ki rakani mu sallami bak'inmu."    Ya kai hannu da zummar riko nata, ta ja baya da sauri tana girgiza kai. "Ke na soma gajiya da 6oyon da muke yi, aurenki fa nakeson yi. Amma dai..."   Ya jinjina kai kawai sannan ya juya ya fita, a kofar sukayi kici6us da Binta ta gaisheshi, fuska a daure ya amsa gami da fadin.   "Ki kiyaye bakinki." Shi ne abinda yace, ta amsa da to cikin sauri, daga nan ya yi gaba. Da sauri ta fad'a dakin wajen Ummi. Ummi na ganin itace ta sauke numfashi don a farko da ta ji maganar da Faruk ya yi duk ta dauka ko da Ikram ya ke. Binta ta kama ha6a bakinta a washe.     "Ke Ummi, abu fa ya soma zafi, anya kuwa nan gaba Yalla6ai bazai daukeki daga sashen yan aiki ya maida cikin gidansu ba, kafin daga baya ya daukeki cancak zuwa gidan aurenku?"    Ummi ta yi dariya, maganar Binta ta karshe ta yi mata dadi. Ita kuwa Binta k'irr ta tsayar da ido tana duban fuskar Ummi kafin ta doka tsalle ta rungumeta tana ihun murna. "Kece, daman nasan ke ce wallahi." Ummi ta kwaci kanta tana kokarin rufewa Binta baki. "Ki rufamin asiri kiyi shiru kada wani ya ji."   Binta tana dariya ta yi mata nuni da tabon dake a saman hancinta.    "Wannan tabon nayi mamakin yanda Yalla6ai ya ganoshi, naga sai an k'ura miki ido ake ganeshi."    "Shiyasa nake gudun ranar da asirina zai tonu."   Guntun tsaki Binta ta ja. "To menene? Ke saifa kin zama jaruma wallahi. Ni kizo muje kaya aka bani na kai dakin Yalla6ai, ki zo ki tayani kwashe kyaututtukansa."   Girgiza kai ta yi. "Ki taimakeni ki je ke kadai babu inda zan je." Dariya Binta ta saka. "Kekam ban ga irinki a fagen tsoro ba." Ummi ta bi ta da kallo kawai har ta fice.    Haka shagalin ya k'are kowacce budurwa jiki a sanyaye don ba'a samu shiga ba ta ko'ina. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR       63      Misalin tara na daren, falon Hajiya Babba babu kowa sai matasan yaranta da matansu, sai kuma su Ikram.   Fadila ta kar6i hoton zanen daga hannun Jidda tana mai kuramishi ido itama. Jidda ta dubesu. "Nikam kaina ya k'ulle ai, nayi iyakar yi na na kasa gane wacece wannan wallahi. Kai na karfen baka kyauta mana ba, yanda muka ci burin yau mu ga hoton matarka?"   Ta karashe tana duban Faruk wanda abincinsa ya ke ci babu ko alamun damuwa a fuskarsa.   "Ke dai bari kawai Jidda, ni kaina ya soma sarawa ma don kallon zanen." Cewar Fadila. Sukayi dariya, Hajiya Babba ta mike tana fadin. "Um, idan dai Sadauki ne kadan daga aikinsa, a komai sai ya bada mamaki." Daga haka ta barsu suka bita da kallo. Faruk ya dubi Haidar. "Broda, ina fa da magana da kai."   "Bakasan hanyar gidana ba?"   Ya yi murmushi. "Sau daya fa na ta6a zuwa gidanka tun kafin tariyarka, kaga kuwa na mance."   "Aa Lil, baka kyauta ba kam." Cewar Dakta.     Babban Yaya na murmushi ya cafe. "Kuyi mishi uzuri, aikinsa babu hutu sosai."     Haka sukayita hirarsu, a karshe bayan duk sun tafi, Ikram ta mike rike da takardar zanen zuwa dakinsu.    Ihsan na kwance har kanta ya soma sarawa sanadin kukan da ta ci. Ta mike zaune gami da kar6ar takardar.   "Duk iyakar tunani ban gane wacece wannan ba Ikram, saidai na rasa dalilin da yasa jikina ke bani kamar na santa, kuma na ta6a ganin kwayar idanun nan."   Ikram ta jinjina kai. "Ni kaina nakasa hakura da kallon zanen wallahi, gani nakeyi kamar nasanta." Ihsan ta ja tsaki gami da wurgi da takardar. "Me zan amfana da shi a saninta ma? Ni yanzu gaba daya na gaji da zaman Abija, gida zan koma."   Ikram ta dubeta. "Kada kiyi saurin karaya ina kara baki shawara, ni nasan taimakon da zan miki."   Ihsan ta dubeta cikin rashin fahimta. "Ban fahimceki ba." Murmushi Ikram ta yi. "Kedai ki bani lokaci."   Jin hakan yasa Ihsan ta dan samu nutsuwa.                      A daidai gaban motar Haidar suka tsaya, Intisar na ciki tana jira su kammala. Haidar ya dubeshi.   "Ina jinka." Faruk ya gyara tsayuwa. "I am serious fa, wacce na zana dagaske ita nake son aure, saidai ni a wajena ban dauki hakan matsala ba kamar yanda ku ma bana tunani za ku k'i farincikina."    Haidar ya daga kafada kadan cikin rashin fahimta. "Me ya kawo duk wadannan? Yarinyar musulma ce?" "Eh." "Tana da asali?" "Kwarai kuwa." Murmushi ya yi gami da dafa kafadarsa.   "Idan akwai hakan, a ganina babu wata matsala, gayamin a ina ta ke?"   Faruk na murmushin shima ya shafi sumarsa. "Zan zo gidanka gobe daga ofis." "Dayake taka ce zata kawoka ko? Ai yanzun na ga kafarka."   Sukayi dariya sannan sukayi sallama ya shiga motar suka wuce.                      ***   ***   ***                         KADUNA                         Munira tana zaune ta kurawa talabijin ido, saidai gaba daya hankalinta baya tare da kallon, Tasleem da Haris sai wasa da keke sukeyi ko kusa basu da wata matsala. Babban damuwarta bai wuce na auren da Deen ya sanarmata zaiyi ba da macen da sai su share awanni uku cikin dare suna waya, har yau batasan wacece ba saidai babu irin cin kashin da bata gani daga gurinsa tun soma soyayyarsa da yarinyar. Tunaninta ya katse sa'ilin da wayarta ta dauki k'ara. Ganin lambar yar uwarta Atika mai aure a Ringim yasa ta rage k'arar talabijin gami da dauka. Bayan sallama ko gaisawa Atika bata bari sunyi ba ta soma magana.   "Wai kuwa Munira kinsan abinda ke shirin samunki kuwa?"   Munira ta kara gyara zamanta kafin ta saki murmushi mai ciwo.   "Na sani Yaya, to ya zanyi? Aure kaddara ce ai, shi ya sani."   Atika ta saka salati. "Ikon Allah, oh ni Fatima, ba dai kema sun shanyeki kamar yanda suka shanye Deenin ba? Wallahi na tausayawa rayuwarki Munira, cab!" Munira ta ji gabanta na dukan tara-tara. Daman ya lafiyar giwa....   "Yaya wai me kikeson cewa? Ko kina da labarin wacce zai aura ne? Ni wallahi nan da kike gani ko sunanta bazan iya kawomiki ba don a Yanzu bai daukeni wata abar ba yanzu ballantana ya sanarmin."    "To wallahi Munira bacci bai ganmu ba, tashi tsaye ya dace muyi da addu'a, Deeni ba kowace zai aura ba face Dijar Baba Yahuza."   Jin zancen ta yi tamkar saukar aradu, wani salati ta saka da karfi kafin kuma ta yi wurgi da wayar ta zube anan ta hau kuka.   A guje yaranta suka yo kanta tare da Asiya mai tayata aiki.    "Lafiya Hajiya?" Ta kasa barwa cikinta, ta sanarwa Asiya matsalar da ta ke ciki yanzun. Asiya ita kanta hankalinta ya tashi ainun, daman ta zargi hakan tsakanin Dija da Oga, ita take ganin yanayin muamalarsu a gidan. Ta yi ta bawa Munira hakuri, karshe dai ganin yaranta sun shiga damuwa ta mike ta dauki wayarta da ke faman ruri ta yi daki. Atika ce, nan ta shiga bata baki da nunamata addua kadai ce mafita   "Yaya ai ni na hakura da zama da Deen ma."   "Me kenan kikayi idan kinyi hakan Munira? Ashe ma ta ci galaba kenan, kada ki soma wannan bahagon tunanin."   Daga haka sukayi sallama. Munira ta cigaba da kuka har ta gode Allah, lallai DAN ADAM butulu ne, kayi mishi alheri ya sakamaka da sharri, ko a mafarki bata ta6a hangen haka ga Dija ba, bata ta6a kawowa zata ci amanarta har haka ba. Wannan rayuwa da me ta yi kama?    Ta jima cikin wannan hali har dawowar Deen daga wurin aiki bata iya komai ba. Daman ba wani nemanta ya ke yi ba yanzun, taso zuwa ta sameshi saidai kuma ta ga rashin alfanun hakan. Wannan yasa ta zuba ido ganin yanda lamuran zasu cigaba da kasancewa, mik'awa Allah lamarin shi yafi kamar dai yanda Yayarta ta ce.                 ***   ***   ***                     ABUJA DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 64 ABUJA Intisar sanye cikin riga doguwa 'yar kanti, ta ci kwalliyarta daidai misali ta fito daga kicin dauke da kwanukan abinci ta jera saman tebur inda Haidar da Faruk ke zaune. Ta gaida Faruk ya amsa shima ya gaisheta. Abin ma ya basu dariya. "Ba dariya, matar yaya ta ke ai." Haidar ya harareshi da wasa. "Sai yanzu ka sani?" Dariya kawai ya yi, Intisar dai bata saba irin wasan da Faruk ba don bai fiye sakarmusu ba, murmushi kawai ta danyi. Bayan ta gama(serving) dinsu ta bar wajen. Saida suka kammala ci sannan suka wuce masallaci bayan dawowarsu ne suka zauna a falon Haidar. Haidar ya dora kafa daya kan daya. "Ina sauraronka." Faruk ya mik'a mishi waya. Haidar ya kar6a yana kallo, ido waje kuma ya ke kallonsa. "Wannan kamar Ummi yar aikin Mami." Faruk cikin jin zafin yar aikin da ya kirata ya jinjina kai. "Yes itace, a wurina ba 'yar aiki bace, budurwar da nake shirin aure ce, ita kuma nake son ta zama surukarku." "Kasan abinda ka ke cewa kuwa?" "Kwarai kuwa, Ummi nake so da aure." Haidar ya dan yi jim kafin ya girgiza kai cikin sauyin yanayi, "Bazai yiwu ba." "Saboda ita ba mutum ba ce?" Faruk ya jefamishi tambayar rai a 6ace. Haidar ya dafa kafadarsa. "Cool down mana, ba nufina wai wani abin daban ba, saidai matsayinku ya bambanta, wannan abu ba mai yiwuwa bane, ka chanja tunani Faruk, da kamar wuya su Daddy su yarjemaka." Faruk ya murtuk'e fuska. "Haka kake gani?" Haidar da mamaki ya ke kallonsa. "Kai baka gani?" Ya girgiza kai gami da kwantar da kai jikin kujera. "Ban ta6a hangen hakan ba, ban kuma sani ba ko don na riga na yi nisa a kaunarta ne yasa ban gano ba? Ni yanzu kai na zo ka ban shawarar wanda ya dace na soma tunkara tsakanin Hajiyarmu da Daddy?" Haidar ya shafi goshinsa yana kara duban hoton Ummi sannan ya dubi Faruk. "Ka sanarwa dukkansu alokaci guda. Ni a raayina, banga aibu a auren Ummi ba, na lura yarinya ce nutsastsiya sannan tana da kyawun hali da na fuska. Matsalar dai iyayenmu, idan sun amince shikenan, bansan raayin Babban Yaya da Dakta ba." Faruk ya dan ta6e baki. "Nifa zan zauna da ita. Shawara kawai daman na zo nema awajenka, ka kuma tayani adduar samun nasara akansu." Haidar ya gyada kai yana dan murmushi. "In sha Allahu, mai Ummi, zan tayaka. Amma wacece H din da ka zana?" Faruk ya dan dara gami da kashe ido daya. "Hasiya, real name dinta ne. Sunan mum dinta ta ci, amman ta rasu yanzu." "Kai Nawan." Cewar Haidar gami da ba shi hannu suka cafke kamar wasu abokai. "Wato komai nata ka sani? Duk ta yaya?" Faruk ya gutsira mishi labarin Ummi, ya dora da fadin. "Tausayinta ne ya soma rinjayar zuciyata har na soma jin sonta a raina." Shi kansa Haidar ya tausayamata. "Allah Sarki, rayuwa kenan, kowa da inda Allah Ya ajiyeshi, babu wanda yafi wani a wajenSa sai wanda yafi tsoronShi. Allah dai Ya datar da mu." "Ameen broda. Ni bari na k'arasa, waya nakeson zuwa na siyo." "Na wa kenan?" Murmushi Faruk ya yi, Haidar ya dafa kafadarsa yana tayashi murmushin. "Lallai na yarda da Dakta ke cewa irinku da bakwa soyayya idan kun tashi yi to zakuyi mai ban mamaki." Abin ma sai ya bawa Faruk dariya, har wajen mota ya rakashi sannan sukayi sallama da zummar duk yanda Faruk sukayi da iyayen zai sanarmishi. Hajiya Babba ta ajiye wayarta a gefe bayan ta gama amsawa ta dubi Ikram wacce ke zaman jiranta ta kammala. "Ina jinki." Ikram ta yi gyaran murya ta soma magana. "Hajiya daman akan Ihsan ne." Cike da mamaki ta dubeta. "Meyafaru da Ihsan din? Ko ta gaji da mu ne?" "A'a, daman..." (Ta kwashe tun farkon sadda Ihsan ta soma son Faruk har zuwa jiya da ta shiryamishi party na taya murnar ranar haihuwa. Hajiya Babba bayan gama sauraronta ta numfasa fuskarta dauke da damuwa. "Tun ba yau ba nasan yarinyarnan tana son Sadauki, saidai banga alamun Sadauki yana sonta ba." Ikram itama ta jinjina kai, tasan gaskiya ne. "Amma Hajiya bakya ganin a haka ya aureta idan yaso son ya shiga a hankali?" "Kina ganin zai yarda? Banason abinda za'a zo zumunci ya lalace, matukar akayi aure ba da son ran daya ba to shakka babu zai shafi zumuncinmu abinda bazan ta6a fatan naga ranarsa ba kenan." Ikram ta yi mamakin abinda Hajiyarsu ta ce, duk da tasan gaskiya ne, amma ai ya dace ta duba alak'a. Ita shaida ce akan yanda Hajiya ke tsananin kaunar dannata, batasan 6acin ransa tun yana karami kamar yanda ta samu labari daga yayyunsu. Ta bude baki zatayi magana Hajiya ta dagamata hannu. "Ya isa hakanan, sai naji ta bakinsa, banason yi mishi katsalanda a lamari irin haka. Musamman lamari irin wannan na aure." Jiki a sanyaye Ikram ta mike zata fita daga dakin, ta dakatar da ita. "Maganar ta tsaya iyaka nan, ban yarje miki sanarwa Ihsan ba." Ikram da ta rasa bakin magana, kai kawai ta gyada sannan ta fice har lokacin mamakin Hajiyarsu bai saketa ba, ko babu komai naka ai naka ne, saidai batasan hukuncin da zata yanke ba. Mintuna k'alilan da yin hakan, Faruk ya dawo gidan a gajiye, kai tsaye sashensa ya nufa ya yi wanka ya sanya doguwar jallabiya ruwan madara da wando kafin ya dauki wayar da ya siyowa Ummi na kamfanin HTC ya sanyata a chaji. A karshe ya nufi sashen Daddy. Acan ya iske Hajiya, suka gaisa kafin su shiga hira da iyayennasa. Can Daddy ya dubeshi. "Son shekarunka talatin a duniya, ya ci ace zuwa yanzu ka soma tunanin aure." "Ai ina jin ya samu matar aure, bai kai da fad'amana wacece ba ko Sadaukina?" Murmushi ya yi yana mai shafar sumar kansa. "A ina take?" Fadin Daddy kenan yana mai gyara zamansa don yasan dagasken ne don dannasu koda wasa bai ta6a zancen kowace mace ba. "Ba ta yi nisa da mu ba sosai Daddy." Hajiya da Daddy suka dubi juna, kafin su dubeshi. "Ko 'yar gidan Alhaji Hamza? (Makwafcinsu)" Ya yamutsa fuska. "A'a, asalima ita ba 'yar garin nan bace." "Wacece kenan?" Hajiya ta tambaya. Ya yi shiru can kuma ya sunkuyar da kai. "Zan kawomuku ita ku ganta cikin satinnan In sha Allah." Suka gyada kai lokaci guda. "Allah Ya kaimu." Fadin Daddy. Faruk da Hajiya suka amsa da amin, ita kuwa Hajiya ta soma tunanin kodai Ihsan ce? DAN ADAM    @RUFAIDA OMAR 64 Washegari Ummi ta kammala aikinta, tana shirin barin wajen Hajiya ta shigo, bayan ta gaisheta ta dakatar da ita da fad'in.   "Ina jin zuwa Asabar zaki koma fa, ba don naso hakan ba sai don Madina da ta takura da zama ba mai tayata wasu hidindimun, ta ce yanzu ba wata matsala. Zuwa gobe za'a kawomin wata."    Gaban Ummi ya fad'i, jikinta ya yi sanyi matuk'a. Shikenan ta kusa rabuwa da ganin sanyin idanunta. A fili ta k'irk'iro murmushi wanda ya yi kama da na yak'e.    "To Hajiya, Allah Ya kaimu." "Amin."   Daga haka ta bar wajen da saurinta, tana zuwa (garden) ta zauna a kujerar da ta saba zaman wanki, ta ajiye bokitin mai dauke da tsummokarai, shiru ta yi tana tunani kafin ta daga kanta tana duban barandar dakin Faruk, shikenan ta kusa daina sakashi a ido koyaushe? Hawaye suka zubomata, ta jima tana shararsu kafin ta daurewa zuciyarta ta cigaba da aikinta. A ranar haka ta wuni jiki babu kwari, daidai da Binta ta lura da hakan, tambayar duniya ta yi mata saidai amsar daya ce. "Babu komai." Koda dare ya yi, ta taimakawa Binta da shirya tebur har lokacin bata da wani kuzari, abincin ma kasa ci ta yi sosai. Binta sai kai loma take yi, can ta dubeta. "Wai menene matsalarki ne?" Ta numfasa. "Na fadamaki babu komai, kaina ke ciwo."   Daga haka ta dan ja guntun tsaki ta mike.   "Ni na k'oshi ma." . Binta na kallonta ta wanke hannu ta bar kicin din zuwa daki.  "Um, ai shikenan idan ta yi wari ma ji."   Daga haka ta cigaba da cin tuwonta. Ummi na tafe a sanyaye, wasa takeyi da jelar dankwalinta, yayinda ta fad'a duniyar tunani, ko kadan bata san inda take jefa kafarta ba, tasan dai hanyar dakinsu ta nufa. Babban damuwarta bai wuce Faruk ba, da kuma irin yanda take tunanin ko aurensu mai yiwuwa ne ko kuwa dai kawai iyakar soyayyar ce?     Bata ankara ba ta ji ta yi karo da mutum har goshinta na ta6a kirjinsa, ta yi saurin ja baya a tsorace, sai kuma ta yi ido hud'u da hasken rayuwarta. Wani hadadden murmushi na gefen kumatu ya sakarmata. Sanye yake da riga marar hannu mai hula da wando(3quarter).     Ta sauke idanunta kasa sannan ta russuna cikin rawar murya ta gaisheshi ya amsa sannan ya dubeta. "Zo, ke na fito nema daman, na lek'a daki ban ganki ba."   'Gwara da Allah Yasa ka ganni a hanya.' Ta ayyana a zuciyarta. Ya soma tafiya zuwa samansa. "Biyoni." Ta yi sakato tana dubansa. Har ya taka matattakala uku, ya juyo yana dubanta. Tana tsaye cak, ya dan yi jim yana karemata kallo, ita dinma shi ta ke kallo a sace, can kuma sai ta daga kafafunta da sukayi mata nauyi ta soma bin bayansa. Ganin haka ya murmusa ya cigaba da tafiya tana biye da shi tana waige, cikin sa'a Binta ta zo wucewa da sauri ta sauka ta nufeta.   "Ina zuwa don Allah, Yaya Faruk ke kirana, ki rufamin asiri." Ta yi maganar cikin rad'a, Binta ta gyada kai tana dariya ciki-ciki don wannan soyayya tasu burgeta take yi, daga haka Ummi ta juya. Tuni gogan ya shige, a falo ta iske baya nan, tun da take bata ta6a yiwa sashensa kallon tsanaki ba, ko sadda Sa'a ta yaudareta ta kawota wajen KB, sam ba'a cikin nutsuwa ta ke ba. Falon adon fari da bulu ne, ya tsaru iya tsaruwa. Anan kasan (tiles) ta durk'ushe kamar yanda kowace yar aiki ta saba a gaban masu gida. A haka ya fito rike da kan waya da kwalinsa ya iso ya zauna saman kujera. Da hannu ya yi mata nuni da gefensa. "Dawo nan Malama, saikace ba dakinki ba?"     Ta saci kallonsa kawai ta dan yi murmushi kafin ta mike cikin tausayawa rayuwarsu, shikenan sun kusa yin nisa da juna duk da hausawa kance garin masoyi ba ya nisa. A kasa ta zauna saman kafet, shima ya zamo ya zauna a k'asan ta dubeshi saidai babu abinda ta ce.   "Kamar kina cikin damuwa Ummina, sanardani abinda ya faru."   Mamaki ya kamata yanda har ya fahimci yanayinta. Ta girgiza kai.   "Bakomai." Ba don ya yarda ba ya gyada kai sannan ya mik'amata wayar.     "Rik'e." Ta bude tafin hannu ya dora mata a kai.    "Naki ne."   Ga mamaki ta dubeshi.  "Ai..ai ni ban iya amfani da waya ba."   Ya gyada kai da murmushi saman fuskarsa.   "Nasan da hakan shiyasa na kiraki don koyamiki."     Ji ta yi ranta ya yi wani mugun sanyi, saidai fa haduwar wayar ya tsoratata, bata ta6a ganin irinta ba.     Jin kamshin turarensa ta yi daf da ita, hakan yasa ta dagowa a razane ta dubeshi, ya matso gefenta hankalinsa naga wayar, ya kar6a daga hannunta ya soma nunamata da yacce zata cire (pattern) wanda ya sakamata saboda tsaro. Sannan ya shiga ya soma da gwada mata budo sak'onni, da amsa waya, har gwada kiranta ya yi ta ga sunan "Hubbyna." Ya fito, bata san dai yanda zata fadi sunan a baki ba. Amma tasan wani abun ya ke nufi na soyayya.     Sun dauki kusan mintuna fiye da talatin a haka har saida ya tabbatar ta iya yanda yake so, har (whatsapp) saida ya nunamata yanda zata amsa sak'onshi da mayarmishi da amsa, lambarsa kadai ce a wayar na gaba daya layukansu hudu masu tsada da ba wata diya mace da ta ta6a mallakarsu haka.      Bayan ya kammala ya mik'amata kwalin.   "Mun gama da wannan Ummina, yanzu maganar aurenmu ce ya ragemana." Ta lumshe ido tana mai jin kamar ta saki ihun kuka, ya matsa yana fuskantarta.     "Gobe juma'a nakeson bayyana ki ga su Hajiya matsayin wacce nakeso da aure."      Ido waje ta ke dubanshi, hawayen da ta ke dannewa tuni ya fito ya soma sauka saman fuskarta.     Ji ya yi wata iriyar kasala ta saukar masa, ya runtse ido cikin kasalalliyar murya ya ce. "Please stop it mana, na tsani ganin hawayenki ya zuba Ummi akan kuma dalilin da bai taka kara ya karya ba. Idan ke kin kasa jarumtar jure koma menene zai zo wanda bana fatansa ma, ni ya kikeson nayi ne? A'a Ummi, wallahi Faruk bazai iya daukar wani tsawon lokaci batare da Hasiya ba. Na soma gajiya, ni ban iya wannan rayuwar ta 6oye abinda zuciya da gangar jikina ke muradi ba. Bazan iya ba, gobe ki shirya, ina zuwa." DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 66 A fili kuwa don ta kwantar mata da hankali. Ta nunamata bawani abu bane, ya dace ta koyi jarumta tun daga yanzu. Ta k'ara bata shawarar tashi tsaye da addua, inda ta tabbatar mata itama zata tayata. Ummi ta yi godiya sannan ta jawo ledar suka bude. Wani hadadden Atamfa (pink) ne mai turuwa, a wani 6angaren mai dan haske-haske, anyi dinkin riga da zani, koda Ummi ta daga rigar ta girgiza kai. "Anya rigar nan zata yimin?" "Tsaf ma kuwa, tashi ki gwada kedai." Ba musu ta gwada, ai kam ba karamin kyau ya yi mata ba. Ta cire suka cigaba da duba ledar, harda dan kunne da sark'a fashion mai kyau da agogo, harda turare kala uku da kayan kwalliya, abin bai tsaya anan ba har dasu takalmi fari kalar mayafin da ya sanyomata. Binta banda washe baki babu abinda takeyi, ita kuwa mai abin jikinta sanyi ya k'ara yi. Wayar ta k'ara dagawa tana juyawa. "Kai Ummi ki godewa Allah, kin samu mijin da ya iya kula da matarsa wallahi."   Murmushi Ummi ta yi. "Kai Binta, har ya zama mijina?"   "Haka nake miki fata 'yar kanwata, nidai nasan gudunmuwar da zan baki a wannan lokacin idan ya zo."   Dariya kawai Ummi ta yi gami da girgiza kai, a ranta fatan hakan ya ksance takeyi. Sun dan jima tare da Binta kafin ta mik'e ta yi mata sallama don ta soma hamma na jin bacci. Bayan fitarta ta maida kayan cikin ledar ta yi gefe da su.     Alwala ta d'auro ta gabatar da nafila, ta jima tana addu'o'i kafin ta shafa ta koma makwancinta. Wayar ta k'urawa ido tana jujjuyawa, ta yi nisa cikin tunani wayar ta dauki k'ara.  'Hubbyna.' Shine sunan da ya fito, wani ajiyar zuciya ta saki gami da yin murmushi. Kafin ta dauka kamar yanda ya koyamata yacce zata yi.    Sallama ta soma yi mishi ya amsa. "Ba ki yi bacci ba, meyasa?" Ta ji daddadan muryarsa har cikin jini da bargonta.   "Bakomai." Shiru ya dan biyo baya can kuma ya yi magana. "Ina fatan ba kuka kikayi ba?" Da mamaki karara akan fuskarta ta girgiza kai. "Ni..ni banyi kuka ba." Ya yi murmushi mai sauti. "Ni kuma jikina ya bani kinyi kuka Ummina, amman dai shikenan. Ya kika ga kayan, sunyi miki ko a chanja?"   'Ni na isa nace basuyi ba?' Ta fada a zuciyarta batare da sanin ya fito fili ba. "Har kin yi yawa indai awajen Umar Faruk ne. Ni ban ajiyeki nan kusa ba fa. Amma yanzu duk bazaki gane hakan ba sai bayan aurenmu."   Ta lumshe ido tana mai jin wani kaunarsa sabuwa fil a cikin ranta. "Inama hakan zata faru Yaya Faruk." Furucin ya yi mishi dadi, ya fahimci ta soma sakin jiki da shi. "Zai faru in sha Allahu Ummina, ki kwantar da hankalinki har zuwa ranar da Umarul Faruk zai mantar da ke dukkan bakkan ciki da iznin Allah, ranar da zamu kasance mata da miji abin so da alfahari. Matukar ni ne mijinki, bazan k'ara barin ki cikin hali na damuwa ba. Watakil sai kin gaji da ni, don daga ranar da na aureki, na daina zuwa aiki."   Dariya sosai ya bata, sai gashi ta shiga yinta kwarai. Ya lumshe ido gami da k'ara rungume daya daga cikin kananun filon dake saman gadonsa. Shi kadai yasan yanda ya ke jin dariyarta. Ta tsaida dariyar cike da jin kunya. Murya kamar na wanda baya son magana ya ce. "Naso ace kina gabana kike dariyar nan Ummi, yana daga cikin abinda ban ta6a gani ba daga gareki, kuma zanso na ganin."    Ta sunkuyar da kanta tamkar yana ganinta ta hau wasa da igiyar hular t-shirt din dake jikinta.    "Saida safe Yaya Faruk, bacci nake ji."   "Ko na zo?" Ta zaro ido kamar yanda ganinta, ya yi 'yar dariya. "Matsoraciyata, na tabbatar kin tsorata. Shikenan saida safe, kiyi mana adduar fa."   "To." Daga haka sukayi sallama. Ta bi wayar da kallo tana murmushi. A karshe ta ajiyeta gefe, mikewa ta yi ta yi nafila sannan ta karanta istihara tana kallo a takarda kafin ta shafa ta kwanta.                  WASHEGARI....!!!!   Cikin ikon Allah ta tashi da jin kwarin gwuiwa a zuciya da gangar jiki, kaso sitti na damuwarta ya ragu.    Bayan Magriba ya shigo gidan, kai tsaye sashensa ya soma nufa. Bayan ya yi wanka ya nemi Ummi a waya, tana zaune tana harhad'a kayanta sanin da ta yi cewar gobe Asabar kuma a ranar Hajiya ta sanarmata shine na komawarta Kano, wayar ta katseta. Hannu tasa ta dauka, tasan ko waye mai kiran, gabanta na dukan tara-tara ta dauka da sallama. Ya amsa sannan ta gaisheshi.   "Ki shirya Ummi, na dawo ina sama, da zarar na kammala abinda nakeyi zan sauko mu je."   Ji ta yi kamar ta saki fitsari, ta daure ta gyada kai don bakinta ya yi mata nauyi. Shaf ta mance ma waya ce suke yi.   "Ummi, meyafaru kuma?" Ya tambaya a sanyaye. Sai lokacin ta dan samu ta yi magana. "Bakomai, zan shirya." Ya yi murmushi mai sauti. "Ko kefa."   Daga nan sukayi sallama. Ta yi k'uri tana duban wayar kafin kuma ta ajiyeta. "Allah ka saukaka mana." Ta fada a fili, tana mai amsawa kanta.       Shigowar Binta ya katseta, ta amsa sallamarta. Binta ta k'araso. "Naga fa Yalla6ai ya dawo." Ummi ta yi murmushin karfin hali.  "Munyi waya yanzu, yana nan kan bakansa, yanzun ma cewa ya yi na shirya."   Binta ta jinjina kai. "Sai ki tashi, hakanan za ki je kedai kiyita addua a ranki."   Ta saka kayan, Binta ta gyaramata fuskarta, ta yi mata daurin dankwali mai hawa-hawa irin na zamani. Ta taimaka mata da sanya dan kunne da sark'an. Sai kuma ta saki baki tana kallonta.   "Masha Allah, wallahi Ummi na k'ara ganin abinda Yalla6ai ya hango wajenki, Ummi bakiyi kalar 'yan aiki ba."   Ummi ta girgiza kai bata iya cewa komai ba don a yanzun ita kadai tasan yanayin da ta ke ciki.  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   65   Mik'ewa ya yi ya koma daki ta bishi da kallo cikin jin wani shauki na kaunarsa.   'Kaico, Yaya Faruk an kusa rabamu.' Ta fad'a a ranta, jikinta yana bata cewa komai ya zo karshe, watakil harda zamanta cikin zuri'ar tasu gaba d'aya, tasan maganar Antinta ya kusa tabbata wanda ta ce. 'Karki manta matsayinmu awajen mutanen nan, mu 'yan aiki ne, ba su daukemu komai ba face wannan Ummi. Bar ganin suna mana dariya, duk sadda muka bari wasu lamura suka afku ranar zasu tunamana cewar mu kaskantu ne awajensu, ranar zasu tunamana matsayinmu na marasa galihu.'    Hannunsa ta ji saman fatar fuskarta yana sharemata ruwan hawaye. Ta dubeshi, fuskarsa kai ka rantse bai ta6a dariya ba.    "Kinaso muyi fad'a kenan, na tsani nayita nanata magana d'aya. Karki so ki ji yanda nakejin zuciyata idan kina kuka, amma ke naga kamar kin fison damuwata."   Karo na biyu da ta ji tana son fadamishi damuwarta. "Kayi hakuri Yaya Faruk, saidai gani nakeyi kamar an kusa yimin katanga da kai."    Ya zubamata ido baice uffan ba, hannunsa tuni ya sauke daga saman fuskarta. Can kuma ya soma magana. "Fata nagari lamiri, ki saka a ranki in sha Allah babu wani abu da zai yanke alak'armu har ya zuwa aurenmu da rayuwar auren. Banaso kina kawo komai a ranki. Yau idan da dama, kada ki rage bacci ki tashi mu yiwa junanmu addua akan Allah Ya za6amana abinda yafi alheri. Kin iya karanta istihara?"   Ta girgiza kai. "Ban iyaba, saidai ina da Hisnul muslim."    Ya gyada kai. "Ki yi adduar istihara a yau Ummi, in sha Allah zamu ga daidai a lamuranmu. Ga wannan."   Ya mik'amata wata leda, ta sa hannu ta kar6a.     "Shi nakeso ki saka gobe idan na kiraki a waya, kinji?" Ta gyada kai. "Yauwa." Daga nan ya sallameta ya yi mata rakiya har suka sauka daga matattakala sannan ya tsaya ta wuce. "Zan kiraki." Ya fada da muryar rad'a. Ta dubeshi ta murmusa ya yi mata alamun (kiss) da baki, a kunyace ta wuce da sauri. Daga haka ya koma sama.    Bayan ya kammala dukkan wasu ayyuka, ya soma duba kyaututtukan da yan uwa da abokan arziki suka ba shi, sai a yau ya samu wannan damar. Turaruka sunfi komai yawa, agogo kuwa kusan biyar ya samu, wasu kuwa kayan kwalam ne har da katina kala-kala. Hankalinsa ya kai ga na Ihsan, yasa hannu ya dauka ya bude. Kamshi ya soma ziyartar hancinsa....!   Wani hadadden agogo ne sai kuma zobe na azurfa. Murmushi ya yi sadda ta ci karo da kati mai dauke da kalaman so. Ya bude ya karanta.       "My friends told me that falling in love would be the most beautiful feeling in the world. After I fell in love with you, I realized that even the most beautiful feeling in the world would look ugly against your love. Frm Ihsan Modibbo."    Ya ta6e baki kadan, ya cigaba da daga sauran katinan, duk kalamai ne na nuna soyayya.     'Ya tabbata tana sona din kenan?' Ya ayyana a ransa kafin ya lumshe ido. Baya fatan shiga matsala saboda ita, a rayuwarsa bai ta6a shaawar kasancewa da kowace mace ba face Umminsa, ta makaro, bayajin zata samu wani gurbi a zuciyarsa, saidai kuma ta dan ba shi tausayi. Ya dan ja guntun tsaki sannan ya mik'e ya tsallake kayan ya shiga harkar gabansa.       Ummi kuwa tana shiga daki ta tarar Binta na zaman jira. Binta na ganinta ta mike ganin yanda jikinta ya ke duk a sanyaye.   "Lafiya?" Ba ta ce uffan ba, sai kayan da ta ajiye saman katifa ta zauna, batasan lokacin da kuka ya kufcemata ba. Binta wacce ta sandare tana kallon waya hankalinta ya komo ga Ummi. "Me ya faru wai? Ki gayamin don Allah mana."    Ita dai Ummi kukanta ta ke, ji takeyi inama yau ace mahaifiyarta na raye, ta rungumeta ta rarrasheta ta kuma bata shawarar da zai taimaki rayuwarta.    "Allah Ya ji k'an ki Ummana, Allah Ya yi rahma agareki,  na taso ban ta6a jin dumin uwa ba, na taso cikin wahala da tsanani na rayuwa har zuwa sadda aka maidani 'yar aiki. Babu wani mahalukin da ya ta6a rungumeni ya ji matsalata ya rarrasheni ya min addua acikin shak'ik'aina, Babana bai ta6a tarana ya yimin fad'a akan rayuwa ba, ko sau daya bai ta6a sakarmin fuska ba, asalima kyamata yakeyi, bai ta6a tambayar Ummi ko kin ci abinci ba, Ummi zan saki makaranta, Ummi ki kula da kanki, Ummi ki tsare mutuncinki, ko sau daya babu wani cikin yan uwana da suka ta6a nunamin kulawa ko k'auna. Babu, babu su Ummana, Ummana nasan da kina raye da wasu lamuran zasuyi sauk'i agareni, ayau ga wata rana babba da nake bukatarki Ummana, saidai kinmin nisan da bazan iya kamoki ba, kin koma ga Ubangijinmu da ya fini kaunarki, babu wani da ya ta6a ban cikakken tarihinki da kyawawan dabi'unki, asalima saidai ayita aibatamin ke, ana miki kazafi. Nayi rashinki Ummana, Allah Ya yi rahma agareki."   Daga haka ta k'ara sautin kuka mai tsanani, ta cukuikuiye jikinta wuri guda, a rayuwa koda a gaba wata sila tasa Antinta Amina da yar uwansu juyamata baya, koda shima Faruk zai juyamata, bazata ta6a mance da tarin kaunar da suka nunamata ba. Sun nunamata itama DAN ADAM ce. Faruk ya gwada mata cewar itama ta cancanci komai a rayuwa, ya dauketa a mutum, haka nan danginsu gaba daya, banda matsala ta Ihsan da kishiyar Mami, babu wani abu da ta ta6a fuskanta na cin zarafi cikin zuri'arsu. Watakil a gobe zama da su zai k'are. Ta daga kai tana mai duban dakin, sheshshekar kukan da ta ji ne ya tunasar da ita cewar bafa ita daya bace a dakin. Ta kai duba ga Binta, kuka takeyi kwarai. Ta share hawayenta tana mai dukar da kanta k'as.   "Meyafaru Binta?"   Binta wacce zuciyarta ta cika da dumbin tausayinta ta dago kai tana dubanta. "Shakka babu ke abar a tausayawa ce Ummi, saidai ki yi hakuri, komai na rayuwa mai wucewa ne, babu abinda ya ke dauwamamme a duniya. Wataran sai labari, Ummi akwai wadanda idan kika ji matsalarsu sai ki gane naki ba komai bane, za ki gane ke lallai kina cikin rufin asiri, ina wadanda suke kare rayuwarsu a wahala babu ko digon jin dadin rayuwa? Ummi akwai matsalolin da suka sha gabannaki, wata ma iyayenta na raye uwa da uba, amma bata ji dadinsu ba ko kusa, kuma tana gabannasu. Ina ji a jikina za ki auri Yalla6ai in sha Allahu, kuma za ki ji dadi a rayuwa. Ki cigaba da mik'a lamuranki ga Allah, in sha Allahu zai magance miki. Nima ina so ki sanyani cikin layin masu kaunarki, har abada bazan cutar dake ba, wanda mukayi a baya ma, ina neman afuwarki, ajizanci ne na DAN ADAM."    Ranta ya dan yi sanyi da jin zantukan Binta masu dadi. Haka ta cigaba da yi mata 'yan nasihu da misalai da wandanda suka fita shiga matsala kuma cikin ikon Allah ya wuce kamar baayiba. A karshe Ummi ta labartamata yanda Faruk ya ce na ta shirya gobe zai kaita gaban iyayensa matsayin wacce zai aura.   'Tirk'ashi!' Shine abinda Binta ta fad'i a ranta DAN ADAM @RUFAIDA OMAR     67 Ji takeyi kamar ta gudu tsabar rud'ani. Binta na sambatu tana feshe mata jiki dq turare, hakanan mayafinta shima ta bi ta fesheshi sannan ta yafamata akanta. Takalmin ta mik'omata ta sanya, banda Masha Allah babu abinda Binta ke kira don iyakar haduwa ta hadu, kai ka rantse dinkin aunata akayi.    "Ni ganinki nakeyi kin saje da mutan gidan, babu wani bambanci."   Anan ne Ummi ta murmusa don gani takeyi kawai zolaya ce don Binta ba laifi akwai barkwanci. Suna nan zaune Binta ta bata baki wayarta ta dauki k'ara. Ta yi sakato tana dubanta, ganin zata katse yasa Binta mik'amata.   "Ki d'aga mana." Ta kar6a hannunta har rawa yakeyi ta d'auka. A kunnenta ta kara, bai bari ta ce komai ba sai cewa da ya yi.   "Fito." Ji ta yi cikinta ya bada wani sautin k'ululu. Tuni ya katse kiran, ta mik'awa Binta wayar sannan ta dubeta idanunta har sun ciko da kwalla. "Don Allah ki tayani addu'a." Tausayinta ya kama Binta, Binta ta rik'e hannunta. "Allah Yana tare da ke, na tabbatar zai taimakeki, ki saki ranki. Komai na Allah ne."   Ummi ta mike jikinta a sanyaye ta fita. Ido hud'u sukayi da shi yana tsaye a bakin matattakala ya sanya kafarsa daya jikin bango yana danne-dannensa a waya. Ya yi mata kyau kwarai dagaske haka kuma ya bata mamaki, sai kace wasu Amarya da Ango duk yasa su yin shigar kaya masu kyau, shi dinma wani boyel fari k'al yaa sanya da hula wacce ta dace da kayan.  Tunda idanunsa suka sauka akanta, ya kasa daukesu, daskarewa ya yi a wajen kawai don  ya yi kamar zuciyartasa ma tsayuwar ta yi. Haka har ta k'araso wajenshi ta tsaya gefe tana wasa da jelar mayafin. Yasa hannu ya dago ha6anta, idanunsu cikin juna sannan ya kauda hannunsa.   "Kinyi kyau matuk'a."   Ta lumshe ido gami da kauda kanta cikin bugun zuciya mai sauri. To Faruk ina wani kyau a wajenta idan aka had'asu? Gaba daya ganinta ta keyi wani tsami akansa, ta k'ara raina ajinta kwata-kwata, har ta hangowa kanta irin kyamar da za'a nunamata yau. Watakil ma su Ihsan su yi mata dariya. Idanunta ya yi kwal-kwal. Hannu ta ji yasa ya janyo mayafinta ya dan rufe kusan rabin fuskarta da shi.   "Muje." Ya yi maganar cikin dusashshiyar murya. A hankali suka soma takawa, Faruk shi kansa dakewa yakeyi don ba shi da yak'inin samun goyon baya, yana dai ji a jikinsa kawai zai yi nasara idan Allah Ya so.   Haka har suka shigo falon Hajiya, babu kowa, daman hakan yafi buk'ata, yasan a wannan lokacin Hajiya na sashen Daddy, kai tsaye kofar zuwa sashen Daddy ya shige. Anan kofar falon ya dakata gami da umartar Ummi da tsayawa anan. Ba musu ta tsaya, ta bishi da kallo har ya shiga da sallamarsa, kirjinta ta dafe jin irin yanda ya ke bugu fiye da baya, addu'o'i kawai ta ke karantowa.    Daddy da Hajija suka amsa sallamar dan nasu fuska a sake.      Ya karasa yana taku a kasaitance ya zauna a gefen kafafun Daddy ya gaishesu. Suka amsa suna k'are mishi kallo. Daddy ya kasa hak'uri ya tofa.   "Wai ni kodai wajen surukartawa za ka tafi ne? Wannan ado haka?"   Ya shafi k'eyarsa da murmushi saman fuskarsa, Hajiya na dariya.   "Daddy na je na dawo, kuma tare muke da ita ma yau za ku ganta."   Sai Hajiya ta hau salati. "Kai Sadaukina, haka kuma akeyi babu sanarwa? Maimakon ka fad'amin a shirya?"   "To yanzu dai ai magana ta k'are tunda daman ya sanarmana a satinnan zai kawota, kinsan halin d'annaki komai nashi daban ne."   Cewar Daddy yana duban matarsa kafin ya maida dubansa ga Faruk.   "Tana ina ne?" Faruk ya dubesu, su dinma shi suke kallo fuskokinsu a sake. Hakan ya k'ara mishi wani k'arfin gwuiwa, ya mik'e tsaye ya nufi hanyar waje.    Ya dubi Ummi wacce ya tabbata a rud'e ta ke.    "Addu'a zakiyi, Allah na tare da mu." Ya fada cikin muryar rad'a. Ta gyada mishi kyau kafin ya bata hanya. "Bismillah."   Dagowa ta yi ta dan bude fuskarta ta dubeshi kamar zata yi kuka, ya jefeta da kallo mai sanyaya jiki, dole ta maida ta rufe fuskarta sannan ta saka k'afa da sallama, shima ya biyo bayanta. Iyayen suka amsa fuskarnan a sake, suka zuba mata ido har ta k'araso ta zauna, Hajiya dai gani ta ke kamar muryar da kuma tafiyar ba yau ta soma ganin irinta ba. Ta dai danne, ta amsa gaisuwar surukarta ta wacce ke ta bad'ad'a k'amshi. Kafin su kai ga tambayar wani abu, Dakta Ridwan ya yi sallama ya zo gaida iyayensa.    Ya dubi Ummi sannan ya dubi Faruk yana 'yar dariya.   "Ikon Allah, ashe na zo a daidai, da rabon ayi da ni." Sukayi dariya iyayen, shi kuwa gogan murmushi kawai ya yi.     Dakta ya gaisar da su Daddy sannan aka zauna yana fadin shi fa sai ya ga fuskar surukarsu.    Ikram ce ta shigo rik'e da hannun yaron Dakta, Ma'aruf, wanda ke faman rigimar zuwa wajen ubansa. Nan itama ta yi sararo tana duban Ummi.   "K'araso mana, yau fa babbar bak'uwa mukayi, matar Sadaukin Hajiya."   Ikram ta dubi Hajiya, Hajiya ta kauda kanta, to me za ta ce? Idan Faruk ya ce ga wacce ya ke so ya zata yi? Batun Ihsan ne sai yanda sukayi da shi.    "Mene sunanta ne?" Daddy ya tambaya. "Hasiya." Cewar Faruk, Ummi ta lumshe ido jikinta na rawa, tana gudun ace za'a bud'e fuskarta.    Ikram ta saki hannun Ma'aruf sannan ta karaso tana yar dariya na dole. "Nidai sai naga fuskar Antina."   Kafin Ummi ta yi wani yunk'uri, ta d'an bud'e mayafin ta lek'a. Zaro ido ta yi gami da bud'e mayafin gaba daya tana salati.    "Me..." Kowannensu ya mak'ale tambayar da ya yi niyya sakamakon fuskar Ummi da ta bayyana agaresu. Daddy yana mata kallon sani don tabbas yana ganinta jefi-jefi a gidan, saidai baisanta a suna ba ko matsayi.    Hajiya ta ji jikinta ya yi mata nauyi ta dubi Faruk, shi dinma ita ya ke kallo, gaba daya alamun tausayi, tsoro da kuma firgici sun bayyana saman fuskarsa. Ta maida kallonta ga Ummi wacce ta ke kuka sosai ga jikinta da ke kad'awa kamar mazari.    "Meke faruwa ne?" Fadin Daddy yana dubansu. Hajiya ta kasa kwakkwarar magana, karshe ma ta mik'e ta nufi dakin Daddy. Ikram da ta ke duban Ummi duba na tsana ta nunata da yatsa.   "Daddy wannan ba kowa bace face 'yar aiki, a gidan Mami ta ke a Kano shi ne ta dan zo nan, ita Yaya Faruk ke son kawomuku matsayin suruka alhalin ita din ba..." Wani kyakkyawan mari ne ta ziyarci kuncinta daga uban gayya, ta rike kuncinta wanda ba karya ta ji marin matuk'a. Ya nunata da yatsansa mai rawa, idanunsa sun kad'a ainun.   "Koda wasa, koda wasa ki ka k'ara wannan kuskuren sai kin raina kanki! Yaushe raini ya shiga tsakanina da ke?!"   Dakta cikin 6acin rai ya ke dubansa. "Ba ka da hankali Faruk! Akwai wani abu a kwakwalwarka, ina kai ina wannan? Akanta har ka d'aga hannu ka mari k'anwarka?!! Haba Faruk!! Wannan zubda k'ima har ina?!!!"          Faruk ransa ya yi mugun 6aci, ya girgiza kai yana duban Dakta.   "Na yarda k'ima da komai nawa su zube, sannan don Allah ba kai na kawowa Ummi ba, da ta yi maka da bata yi maka ba, wannan ruwanka."  Tsananin mamakinsa ne ya kama su, tunda suke da shi basu ta6a ganin kalar tashin hankali har haka akan fuskarsa ba sai a yau d'in, haka koda wasa bai ta6a yiwa wani cikin yayyunsa rashin kunya ba ko dai mayar musu da magana.  Daddy kallonshi ya ke yi yana nazari, shi yasan waye Faruk, mutum ne mai tsananin hakuri, kusan duk a yaransa daga Usman(Babban Yaya) sai shi a fannin hakuri, yakan hakura da abu duk son da ya ke mishi matukar wani cikin yayyunsa ya nuna baiyi ba saboda tsantsar kauna ta jini d'aya da ke gudana tsakaninsu.    Ya maida dubansa ga Ummi yana nazari, can kuma ya dubi Ridwan.   "Wuce gidanka." DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    69Ya bud'e dakinta, saidai Binta ya gani wacce ke yawo a tsakar dakin tana jiran dawowarta, ganin Yalla6ai da kansa yasa ta russunawa ta gaisheshi, batare da ya amsa ba ya jefomata tambaya. "Ina Ummi?" Ta girgiza kai. "Bata shigo ba tun bayan fitarta." Ya juya kai tsaye wajen garden ya nufa, acan kuwa ya ganota durkushe k'asan bishiyar mangwaro tana faman kuka sosai. A gigice ya isa gareta ya durkusa kusa da ita. Jin motsi ne yasa ta dago kanta da sauri, ganin shine yasa ta numfasawa. "Kaga abinda muka janyo ko? Ni nasan wannan lamari ba mai yiwuwa bane." Baisan sadda ya rik'o hannunta ba. "Wa ya gayamaki bazai yiwu ba? Kada ki damu da abinda ya faru domin na zo miki da kyakkyawan albishir, iyayena sun amince da aurenmu." Ta yi sakato tana kallonsa, babu alamun wasa ya ke yi, ganin ta yi shiru ya girgiza hannunta. "Ba mafarki ki ke ba fa Ummi, dagaske sun amince da zancen aurenmu. Godiya ya kamata muyi ga Ubangiji." Ta lumshe ido, ta rasa irin yanayin da ta ke ji a jikinta, ji ta yi yana kokarin mik'ar da ita, a kunyace ta zare hannunta daga nasa ta mik'e, jerawa sukayi suka soma tafiya tamkar basu so, kallo daya idan kayi musu, zaka so kayita kallonsu tsabar dacewa da sukayi da juna. Ya dubeta. "Ummina shiru fa, kiyi magana please." Ta share ruwan hawayen da suka k'i tsayuwa. "Yaya Faruk." Ya tsaya a gefen kujera mai lilo ya zauna, sannan ya yi mata nuni da gefensa. "Zauna nan." Ba musu ta zauna jikinta a sanyaye. Ya juyo yana fuskantarta yana ji tamkar ya had'iyeta don so da tsantsar kauna. "Ina sauraronki." Ya fada cikin kankan da murya tamkar wanda baya son magana. "Kamar fa 'yan uwanka ba..." "Shiii.." Yasa yatsa a saman le66anta, ta kauda kai tana mai takaicin yanda bayason ta kawomishi zancen abinda ya kasance gaskiya kuma shima ya sani. "Ya dace ka bani dama ka ji abinda zan fada Yaya Faruk, akwai babbar matsala da kai ka ke mata kallon sassauk'a. Yaya Faruk kana da labarin Ihsan na sonka?" Ta karashe tana kallonsa, shima ita ya ke kallo, kenan dai shi 6oyon ma da ya ke mata ta sani? Abu daya ne bazai iya sanarmata ba, batun auren da Hajiya ta ce zaiyi da Ihsan don bai dauki hakan mai yiwuwa ba, kuma ba wai don Hajiyartasa bata isa ba, aa, sai don kokusa ba shi da tsarin had'a mata biyu a gidansa. Saidai abinda ya ba shi mamaki, bai wuce ta yacce akayi tasan da cewa Ihsan na kaunarsa ba. Ya kauda fuskarsa yana mai dan hade gira. "Ya akayi kika sani?" Ta yi murmushi mai ciwo itama ta maida dubanta ga wata shuka a wajen. "Shi so ba'a 6oyonsa, itama nata ya fito fili, k'alilan ne basu san tana sonka ba a gidan..." "Kinga ya isa haka please, ya isa. Ke bakya kishina ne? Bakya jin wani abu a ranki idan kina had'ani da wata bayan ke? Bazan iya rayuwa da kowace mace ba bayan ke. Ummi wai kinsan waye Umar Faruk kuwa?" Ya k'arashe yana mai tsuramata ido da wani murmushi. Daman ba kallonshi ta ke yi ba, wasa kawai ta ke yi da yatsunta. Ya girgiza kai. "Shikenan dai. Ban labari game da farin cikin da zaki yi ranar da aka shafa fatiha?" Maganar ma sai ta bata dariya, ta rufe fuskarta tana murmusawa. Karaf akan idanun Ihsan wacce ta fito don bawa wani mai wankin gidan ya siyo mata kati don kiran Maminta, ta jima tsaye tana kallonsu basu sani ba, hawaye kawai ke zuba daga idanunta. Ta k'arewa Ummi kallo, ta yi wani kyau a suturar dake jikinta, sannan ta dubi Faruk wanda ya bawa inda ta ke baya, ya wani duk'ar da kai a gaban Ummi yana lek'en fuskarta kamar mai shirin kai mata sumba. Nan duniya ta ji ta k'ara tsanar Ummi, ta k'ara tsanar Faruk da wai suke takara a sonsa da ita. Ina ita ina had'a masoyi da wacce tasan ta fi? Faruk ya cuceta, inama bai soma son Ummi ba ita ya so? Katin da bata bada an siyomata kenan ba, da gudu ta koam ciki tana rusa kuka, a kicin ta yada zango ta yi mai isarta sannan ta fito ta fada bandakin dake falon ta wanke fuskarta ta koma sama zuciyarta na wani irin zafi. Daddy ya cigaba da yiwa Hajiya nasiha mai ratsa jiki gami da nunamata shi fa lamari na aure ba'a dole, ya amince da bukatarta na aurawa Faruk duk su biyun saidai su dage da mik'a lamarin ga Allah kafin komai, a karshe ya ce su bar maganar nan zuwa kwanaki uku. Hajiya ta aminta da hakan, ta kuma sanarmishi cewar a gobe Ummi zata koma Kano. "Badai don maganarnan ba?" Ta girgiza kai tana dan murmushi duk don ta kwantarwa da mijinya hankali. "Ko kusa, saidai Madina ta buk'aci hakan tun ba yau ba, daman ina shirin sanarmaka sai wannan al'amari ya 6ullo." Ya jinjina kai alamun gamsuwa. "Shikenan ai, Allah Ya nunamana. Shima Ridwan zan ganshi gobe, banason abinda zai kawo rikici tsakaninsu." "Hakane." Hajiya ta amsa kafin ta mike don kawomishi ruwan lipton wanda ya saba sha duk dare. *** *** *** RINGIM Abu kamar wasa, k'aramar magana ta zama babba, don kuwa tuni Deen ya damk'awa Dija mak'udan kudi ta had'o lefenta. Tare da Saude da Baba Habiba suka shigo kasuwar Kano, nan suka shek'o kayayyaki masu dan karen kyau da tsada don har saida Deen ya k'aramusu kud'i. Yan uwa daidaiku ne kawai suka halarci ganin lefen don kuwa acewarsu abin kunya ne da abin tirr irin wannan cin amana da suka yi ga Munira. Kuma tabbas Allah bazai barsu ba, to ance wanda ya yi nisa ba ya jin kira, ko a jikinsu wai an tsikari kakkausa, Malam Yahuza abin na damunsa a kasan zuciya saidai babu abinda zai iya cewa, haka zai zauna tare da Balarabe mahaifi ga Ummi ya yi ta gayamishi bayason auren, shima kasancewar ba wani kata6us ne da shi a gidansa ba, saidai ya ce "To ya zaayi banda hakuri da addua? Matar mutum babu makawa sai ya aureta indai Allah Ya kaddaro tasa din ce." Haka suna gani matansu suka shiga shirye- shirye, an kai Dija wajen bokanya yafi sau biyar ana mata tsafe-tsafe don ta mallaki zuciyar Deen. Aikam sai haukacewa ya ke k'ara yi akanta, Munira dai yanzu abin ma ya ca6emata don hatta Yaransu ba shiga harkarsu ya ke ba, idan ka gansu kasan suna cikin tashin hankali marar misaltuwa. Har ana washegari Asabar daurin aure, Deen bai samu wata fuska daga yan uwansa ba, Munira kuwa a ranar ta juma'a ta iso Ringim din suna k'ara jajanta lamarin da yan uwanta, iyayenta kuwa nasiha kawai sukai ta binta da shi akan ta yi hakuri ta rungumi kaddara. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    68 Dakta daman a fusacen yake, hannun dansa ya rik'e ya bar falon bayan ya jefi Ummi da mugun kallo wanda batasan ma yana yi ba don kanta a sunkuye ya ke tana faman kuka da sheshshek'a. Itama Ikram mara mishi baya ta yi a guje tana kukan marin da ta sha. Daddy ya dubi Ummi. "Tashi ki je Hasiya." Ummi ta mik'e tana had'a hanya ta fita, tasan daman lamarin ba mai yiwuwa ba ne sam, tun yanzu ta soma fuskantar tashin hankali ina kuma ga idan ta koma Kano? Daddy ya zauna sannan ya dubi Faruk wanda ke tsaye yana duban hanyar da Ummi ta bi cike da matsanacin 6acin rai, har lokacin bai daina jin dacin maganganun yan uwansa ba ga matar da yafi so duk duniya. "Zo ka zauna." Cewar Daddy cikin kwantar da murya yana mai mishi nuni da gefensa. A hankali ya taka ya zauna a k'asa rai a jagule. Shiru na yan mintuna ya biyo baya kafin Daddy ya soma magana....Ihsan tsaye a falon Hajiya Babba ta yi tana jin yanda 'yar hatsaniya ke tashi a sashen Daddy, ji takeyi kamar ta je ta ga abinda ke faruwa. Tana nan tsaye Dakta ya fito a fusace, ko lura da ita baiyi ba haka ya fice, bata kai ga cewa komai ba Ikram ma ta sanyo kai, hawaye sha6e-sha6e saman fuskarta, a guje ta yi saman Hajiya, baki sake ta dubi saman, tana shirin maramata baya Ummi ta fito itama cikin shigar da ta mugun kad'a hanjin cikin Ihsan, gabanta ya hau duka da sauri-sauri. Suka dubi juna ido cikin ido kafin kuma a sanyaye Ummi ta soma tafiya, har ta bar wajen bata iya ce mata uffan ba, ta dafe kirji wanda ta ke ji kamar zai fad'o. "Me Ummi kuma ta ke yi a sashen Daddy, da kuma shiga irin haka?" Ganin babu mai amsamata ne yasa a karshe ta yanke shawarar bin bayan 'yar uwata tasan ko menene zata ji. Daddy ya dubi Faruk cikin kwantar da murya ya soma magana. "Tun tashinka ban ta6a kamaka da laifi na k'arya ko yaudara da makamancinsa ba Faruk, hakazalika ka kasance mutum wanda bai 6oye abinda zuciyarsa ke so." Daddy ya danyi shiru sannan ya cigaba da magana. "Ni ba k'aramin mutum bane, ba alfahari ba, Allah Ya azurtani da yara masu d'abi'u kyawawa hakazalika masu iyakar kokari wajen kiyaye dukkan wasu dokoki na Ubangijinsu, wannan karon sai aka samu akasi, zuciyata ta kasa nutsuwa da za6inka na matar aure, ina ganin kamar da wata manufa ta daban ka ke son auren wannan baiwar Allah da idan a batu na dukiya ne da jin dadin rayuwa, to kai din kana sama da ita, ina so ka gayamin tsakani da Allah, wane irin so ka ke ji ga yarinyar nan? Bazan lamunci tozarta DAN ADAM ba, don kowanne akwai darajarsa ta musamman, bazan lamunci ka aureta daga baya azo a samu matsala ba. Ka fadamin gaskiyar abinda ka ke ji game da ita." Faruk ji ya yi kamar ya d'aga Daddy ya cillashi sama yana ca6e don dad'i. Ya dan saki fuska. "Tsakani da Allah nake sonta Daddy, asalima kaunarta ta samo asali ne daga tausayinta da nake ji, wallahi ba ni da haramtacciyar nufi akanta." Daddy ya yi murmushi gami da dafa kan Faruk. "Tun da kake a rayuwa, ka ta6a zuwar min da wata buk'ata na k'i?" Hakoransa a bayyane yana murmushi ya girgiza kai. "Aa Daddy." "To wannan ma bazan k'i ba, matuk'ar na yi bincike akan yarinyar na samu kyakkyawan magana, baka da matsala. Ni mai aura maka Hasiya ne." "Da SHARADI.!" Suka tsinci muryar Hajiya daga bayansu, Faruk a rud'e ya ke dubanta, ta karaso idanunta na zubda ruwan hawaye ta zauna saman kujera. "Ki ka ce me?" Daddy ya fada da mamaki yana kallonta. Ihsan ta iske Ikram a daki tana kuka da sheshshek'a, wai yau Yayansu Faruk mai hakuri shine ya mareta akan wata banza yar aiki Ummi? Wannan abu da cin rai ya ke. "Ke wai meke faruwa? Tashi ko sanardani don Allah, ni gaba daya na shiga rud'ani wallahi, naga Ummi da wani shiga mai ban mamaki." Ikram ta mik'e zaune tana dubanta cikin dacin rai. "Za ki ganta da fin wannan ma wallahi muddin ba ki bud'e baki kin fayyacewa iyayenmu yanda ki ke ji game da Yaya Faruk ba, a yau Yaya Faruk ya kawo Ummi gaban su Daddy matsayin wacce ya ke so da aure. Har akanta ya mareni." Ihsan daskarewa ta yi tana duban Ikram, ji take kamar jinin jikinta baya gudana yanda ya dace, kamar wata sokuwa ta bude baki ta na kallonta. Ikram ta fayyacemata duk yanda akayi tun daga farko har zuwa marin da akayimata da rikicin Dakta da Faruk. Hawaye ne kawai ke kwararowa daga saman fuskar Ihsan ta kasa kata6us. Abin ne ta ke masa kallon mafarki. Ummi dai 'yar aiki, Ummin da ta ke ganin ta fita a komai na rayuwa, ta fita kudi da ilimi kai harma da yawan dangi kuma wadatattu da sauransu. Faruk matashi abin so da shaawa ga duk wata mace mai lafiya, matashi irinsa da ko 'yar shugaban k'asa ko wani basaraken, bata isa ta yi mishi kallo daya ta kauda kai batare da ta yabawa tsarin halittarsa ba, mata nawa ne ke son dace da samunsa? Su nawa ke rububi da fatan inama ace suna da damar da zaisa ya kasance a matsayin mijin aurensu? Ta girgiza kai tana sheshshek'a tana mai cigaba da sak'e- sak'en zuci. Abin kaico, ya buge a auren 'yar aikin gidansu, wacce zai iya samun dubu da suka fita komai ya aura. Abin kunya ne da takaici ace wai suna takara akan namiji daya tilo ita da'yar aikin gidansu, wannan kam raini ne da kaskanci agareta, wannan zubewar k'ima da ajinta ne a idanun kawayenta da duk wanda yasan irin mutuwar son da ta ke yiwa Faruk. Ikram kasa zaman dakin ta yi ta fito falo don ta ji da nata zuciyar dake mata wani irin daci, ga kuma tausayin Ihsan din da ta ke ji. Wasu lokutan so baima san kan wanda ya dace ya fad'a ba, ba don zargi babu kyau ba da sai ta ce anya kuwa ba wani siddabarun Ummi ta yi ga yayannata ba? Idan ba haka ba, ina shi ina wata Ummi? Ko diri da kyawun fuskarta ne ya d'ebeshi? Ta jefawa zuciyarta tambayar, sai kuma ta girgiza kai. Kayya da kamar wuya, idan don hakan ne kadai akwai wadanda suka ketare Ummin masu kaunarsa amman bai za6esu ba. Hajiya ta share hawayenta don daga daki ta ji dukka abinda ke gudana, hankalinta ya tashi jin wai yau yaranta sun samu sa6ani akan zancen auren Faruk. Ga kuma a gefe da ta ke tsoron abinda zai rushen k'akk'arfan zumuncinsu da kanwarta Madina. Ba zata ta6a amincewa hakan ya afku ba, don Ummi kuwa, kwarai yarinya ce mai hankali, ta cancanci zama matar d'anta don a halayya bata ta6a kamata da wani dabi'a mai muni ba, hakanan bata ta6a cin amanarta ba, daidai da Madina ta sha yaba hankalin yarinyar. Ta dubi mijinta kafin ta maida dubanta ga Faruk wanda ya sunkuyar da kansa cike da jin wani mugun tashin hankali. Yana fargabar abinda zai fito daga bakin Mahaifiyartasa. Baya fatan ace itama bata goyi baya ba, to amma a maganarta, ta nuna goyon bayanta saidai ta ce da sharad'i. "Kwarai kuwa Abban Ridwan, akwai sharad'i. Na amince ya auri Ummi, amma ina so itama Ihsan ya aureta!" Gaban Faruk ya bada sauti mai k'arfi, ya juyo a razane yana duban Hajiya, fuskarta a daure wanda hakan ya nuna babu alamun wasa a zancenta. "Ita Ihsan din ce ta ce tana sona?" "Na tabbatar kasan tana sonka Sadauki." Daddy ya yi shiru. Faruk ya girgiza kai a gigice. "Ni bana son..." "Kaga, tashi ka tafi zan nemeka." Cewar Daddy, Faruk ya mik'e ransa babu dadi ya fita, bai ta6a sha'awar zama da mata biyu ba, ta ya ya Hajiya za ta k'ak'aba mishi Ihsan alhalin tasan bai ta6a sonta ba? Asalima bai ta6a soyayya da wata diya mace ba sai Ummi. Hankalinsa ya koma ga Ummi, a wane ta ke ciki ne? Kai tsaye ya nufi wajenta don bincikawa.   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 71       "Ummi " Ya kira sunanta wanda ya yi sanadin katsewar aikinta da baya sauri don kusan rabinsa tunani ne ja gaba da zubda hawaye. Ta d'ago a sanyaye ta dubeshi, ya zauna gefenta duk jikinsa a sanyaye, ganin haka yasa ta yi kokarin maida kanta ga aikinta, saidai bai bata dama ba don kuwa da sauri yasa hannu ya taro ha6anta. Gefen fuskarta na hagu ya zubawa ido ganin yanda shatin yatsu ya fito 6aro-6aro, hakazalika wajen ya yi jawur, ya dubi tsakar idaninta da nasa idanun wadanda har sun soma kad'awa don 6acin rai.   "Wa ya mareki?" Shi ne tambayar da ya jefamata cikin kakkausar murya. Ta girgiza kai tana sheshshek'a.   "I'm asking you, who slap you?!!" Ya yi maganar cikin tsawa batare da ya ko tuna cewar wacce ya ke yiwa bata jin yaren ba.  Ta runtse ido don a zatonta ma duka zai kawomata.   "Ka yi hakuri don Allah." Ta yi maganar cikin muryar kuka, ya sauke hannunsa gami da yamutsa sumar kansa idanunsa a runtse, baya son jin kukanta ko kadan. A tausashe ya kara fadin.    "Naji, gayamin wa ya mareki?" Ina, ba fa zata fad'a ba, batason tashin hankali ya k'aru a gidan sanadiyyarta.     "Idan kana kaunar Allah da Manzonsa (S.a.w) abar maganar, ni ba wanda ya mareni ma." Yanda ta ke maganar gwanin ban tausayi yasa shi saukowa. "Shikenan tunda kin 6oyemin, share hawayen fuskarki."   Ba musu ta sa hannu ta sharesu. "Meyasa ba ki sanardani yau ake shirin tura ki Kano ba?"   Ta sunkuyar da kanta, dagaske ba kaunar Kanon nan take ba don ta tsorata da kalaman Ihsan.  "Kin dauka bazan sani ba? To babu inda za ki k'ara takawa da sunan aikatau in sha Allah, idan kinga kin bar nan to fa sai da niyyar tafiya gidanku." Jin haka yasa ta dubansa, ya gyada mata kai. "Dagaske." Kawai sai ta tsinci kanta da murmusawa, ta tuna Ihsan da alwashin da ta ci akanta, kenan dai Allah Ya yi nufin ku6utar da ita?   "Tunanin me kike? Kin ma karya kuwa?"   Kai ta gyada.  "To yanzu wannan ruwan da ki ke faman tsoma yatsunki ciki, zai iya sanyaki mura, kinga tashi mu shiga ciki. Bala!" Ya juya ya soma kwalawa mai kula da shukoki kira, mintuna k'alilan sai ga Bala ya iso, ya russina a ladabce. "Ranka ya dad'e." "Matse ka shanya wadannan." "To." Ya dubi Ummi da wani kallo wanda ta kasa jurewa. "Muje ko?" Ta kauda kanta ta soma tafiya. Bala ya soma wanki yana binsu da kallo cike da tunane-tunane a ransa da kuma mamaki, to me ya had'a kashi da fura?   "Ikon Allah." Ya fad'a a fili sannan ya cigaba da abinda ke gabansa.                       ***  ***  ***                         KANO       Ta kama baki cike da mamaki sadda ta ke fitowa daga d'aki sai kuma ta saki fuska tana 'yar dariya-dariya.   "Ikon Allah, ashe dai yaronnan da gaske ya ke, to, halan dai yau 6atan kai kikayi?"   Hajiya Mama ta ja guntun tsaki tana dariya alokacin da ta cire takalmanta ta k'arasa har falon Mami na biyu tana fadin. "Jimin ke da wata magana? Sai kace wacce ta kwashi shekaru bata lek'o ba."   "Aa, ba zancen shekaru, saidai idan ban manta ba rabon da ki zo gidannan tun kafin bikin Baraka, saidai fa a waya ko kuma idan na je."   Ta dan dara. "To naji marar mantuwa, ai gani yau na lek'o."    Mami ta zauna tana dariya. "Na ganki kam."   Hajiya Mama ta bi Mami da kallo cikin shak'iyanci ta ce. "To wannan k'ibar kuma fa? Anya Fahad bai kusa samun k'anwa ko k'ani ba?"   "Um, haka fa shima Abbannasu ke fad'i, wai duk na chanja kodai juna biyu gareni."   Hajiya Mama ta gyada kai. "Da alamu dai wallahi, amman ki je asibiti ki ji tunda ba kiyi girman da za ki tantance ko kina da ciki ko babu ba." Ta k'arashe tana 'yar harararta, sai ma ta bawa Mamin dariya, suka dara. Sun dan ta6a hira sai kuma Mamin ke sanarmata cewar yau Ihsan zata dawo tare da Ummi. Alokacin ne Hajiya Mama ta taso da maganar da ya kawota.    "Ke, ni wata magana ma na zo miki da shi, aikoni Hajiya Babba ta yi wajenki."   Cikin rashin fahimta Mami ta ce. "Toooh, meyafaru? Ba dai wani abun na rashin d'a'a Ihsan ta yi musu acan ba."   Hajiya Mama ta ja tsaki tana mai kokarin cire mayafi.   "Kinji wata maganar kuma, to idan hakanne ai bata wuce Hajiyar da kanta ta lallasata ba, wa zai tsaya wani kawo miki k'ara?"   Murmushi Mamin ta yi, tasan hakanne don ko kusa Hajiya Babba bata fiye daukar raini ba ba dai kamar Hajiya Mamar, wacce ita sha yanzu magani yanzu ce duk kuwa da cewar tana da mutunci kwarai.    "Abinda ya ke faruwa shine..." Ta kwashe bayanin cikin hikima ta gayamata. Mami tunda aka ambaci Ummi aka jogana da Faruk ta daure fuskarta tamau, duk da Hajiya Mama ta lura da hakan, bata fasa cigaba da bayaninta ba saima kauda fuska da ta yi daga dubanta har ta kawo karshe da fadin.   "Kinsan dai Yaya Fatima awajenmu da kuma yanda muka dauketa, ba zata so abinda zai ta6amu ba, nikam ban ga wani aibu a yin haka ba, duk da kema nasan babu wani abu da..."   "A ina? Bazai yiwu ba wallahi. Haba Hajiya Mama, ban ta6a zaton zakuyimin haka ba, da ace ba ciki daya muka fito ba zan iya kiran haka da 'YAN UBANCI! Abin kunya abin turr ace keda Hajiya Babba jinina, ku ne kuka amincewa Faruk had'a Ihsan kishi da 'YAR AIKI? Ko don Ihsan ba ku ku ka haifeta ba? Wannan wane irin magana ce haka kika zo da ita?"   Maganar ta ke yi a matukar fusata, idanunta ya rufe akan makahon son da ta ke yiwa d'iyartata wacce ita ta kasance mace d'aya tilo awajenta, wacce ta ci burika akanta da kuma ranar aurenta, ta ya ya tashi guda zaayi tunanin had'ata kishi da wacce bata isa ba? Lallai acewarta wannan tsagwaron cin amana ne da yan uwanta sukayi gareta.     "Kina da hankali kuwa Madina? Yau ni Sadiya ki ke yiwa haka? Anya kina cikin hankalinki?"   Ta dubi Hajiya Mama da idanunta wadanda suka cika da 6acin rai.    "Ina cikin hayyacina wallahi, amman tabbas idan magana ce ta gaskiya wannan rashin kyautawa ne, Hajiya Babba ta nuna kaunar nata a fili."   "Wallahi Madina kin ban mamaki, ashe haka kike?!! Ashe son diyarki zai iya chanjaki bansani ba? Aure ba kaddara bace? To wallahi bar ganin ana lalla6aki, ba fa tsoronki mukeji ba don ba kece sama da mu ba, aurene kuma yanda Hajiya ta fada hakan zaayi idan Allah Yaso, idan kin isa saiki hana!"    "Ayi, amman ba dai da diyata ba, har abada ba zata yi zaman kishi da Ummi ba, abu ne da Ihsan ba zata ta6a aminta ba, ni na haifeta kuma nasan halinta, bazata ta6a son haka ba. Idan dagaske kaddarar ne, meyasa bai fad'o kan diyarki ba..."    Bata kai ga karasawa ba adalilin marin da ta dauketa da shi.   "Bansan ba ki da kunya ba sai yau, kuma wallahil azim muddin ina raye idan Allah Ya kaddaro babu mahalukin da zai hana auran Ummi da Faruk. Kina nan kuma itama 'yar taki tana nan tana gani za'ayi, ta je kada ki barta ta yi kishi da 'yar aikin da kike ikrari, akwai mazajen 'ya'yan masu kudi da mulki, kina iya had'ata kishi da su. Sannan ina mai tabbatar miki Madina, akwai ranar k'in dillanci, sai kinyi dana sanin wannan abu da kikayi, sai kinji kunyar kanki Madina."   Daga haka Hajiya Mama ta dauki jakarta da mayafi ta kama hanya tana zubda hawaye, a haka ta shuri takalmanta har tana had'a hanya.  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    70                   ABUJA     Misalin takwas na safe, Ummi ta kammala gyara sashen Hajiya duk jikinta a dar-dar, burinta ta yi ta kammala ta bar wajen kafin wani ya risk'eta, saidai cikin rashin sa'a tana murnar har ta kammala za ta tafi ba wanda ya fito, Ihsan ta fito falon tare da Ikram. Daman tun jiya suke dakonta. Tsayawa ta yi kyam tana kallonsu, fuskarta alamu na rashin gaskiya ya bayyana, ta numfasa dakyar tana mai hadiyar yawu, suka k'araso har inda ta ke, idanunsu k'arara ya nuna alamun 6acin rai, babu ma kamar Ihsan wacce bacci 6arawo ne kadai ya saceta shima cike da mafarke-mafarke.    "Ina kwana..." Bata kai ga k'arasawa ba ta ji an dauketa da wani zazzafan mari, ta rik'e kuncinta lokaci guda kuma ta saki bokitin hannunta tana duban Ikram fuskarta cike da tsananin damuwa, tuni hawaye sun soma sauka a fuskarta.    "Kinyi kad'an a mareni saboda ke ba kasa tararki na rama wallahi! Ke din banza! Sa'arki daya ma jiya a gaban wadanda suke da daraja aka mareni, da tun jiya na huce. To saidai mu din an koyamana tsayawa iyakar matsayinmu bamu saba ketarewa ba, ke kuwa da alama ba ki samu wannan tarbiyyar ba tunda har ya kasance kinyi tsaurin idon kai kanki inda aka fi karfinki. Banza mai kwadayi."    Ikram ce ke wadannan kalaman tana mai jifanta da wani banzan kallo, ba ta ce uffan ba, ta sa hannu zata dauki bokitin Ihsan ta buge hannun da k'afarta.   "Aiki kuma a gidannan ya k'are miki, sannan ki sa a ranki muddin yau muka isa Kano zamanki a gidanmu ya k'are, sai naga ta inda zaki auri Yaya Faruk din. Banza kawai!"   Ummi da ta kasa dagowa daga durkushen da ta yi, ta runtse idonta cikin jin zafin wannan abu.   "Meke faruwa ne?" Suka tsinci muryar Hajiya, da sauri suka nutsu kamar ba su ba.   "Bakomai Hajiya, k'arewa Matar Yaya kallo mukeyi." Cewar Ikram tana dariya ta raini. Hajiya ta daure fuska.   "Ku bar wajen nan tun ban sa6amuku ba." Suka juya suna gunguni suka koma daki. Hajiya ta zauna saman kujera ta yi shiru tana kallon Ummi dake faman goge ruwan da suka zubar suka 6ata mata guganta, tana yi tana hawaye. Murya na rawa ta gaida Hajiya, Hajiya ta amsa mata.  Saida ta kammala sannan ta mik'e da zummar barin wajen, ta dakatar da ita ta hanyar kiranta, jin yanda Hajiya ta kira sunanta da sanyin murya, yasa ta dan ji sauki na rad'ad'i da kuma fargabar da ta cikata. Ta amsa a ladabce tana mai zama a gefe kanta a k'asa.     "Kiyi hakuri Ummi, nasan daman tunda Sadauki ya 6ullo da maganar aurenki, dole irin haka ta faru koma fiye da hakan kafin a samu fahimtar juna. Ni ban ta6a k'in ki a zuciyata ba, haka kuma ina miki kallon mutum kamar kowa mai nata darajar ta daban. Ko yanzu hakurinki yasa kin k'ara samun wani gurbi a zuciyata. Ki sani, ni mai son abinda Sadaukina ke so ne matukar ba abin assha bane don haka kema na yarda da lamarinki da shi. Kar kice kuma zakiyi amfani da wannan damar ki cutar da d'ana, bazan ta6a lamunta ba. Idan kin d'ore a yanda kike yanzun to fa zamu shirya da ke. Sannan Ihsan..."   Sallamar Gogan ya katse Hajiya daga maganarta, suka amsa suna dubansa. Idanunsa shima a kansu da mamaki, musamman ma na ganin yanda abar kaunarsa ke fidda ruwan hawaye saidai bayason cewa wani abu don gaban Hajiya ne, fatansa dai kada Hajiya ce ta sanyata kuka.    Ya karaso cikin shigar kananun kaya wanda ya nuna shaidar ya yi wanka, ya zauna gefen Hajiya yana mai gaisheta, ta amsa fuskarta a dan sake ba kamar jiya ba da ta daure mishi, hakan ya dan sanyamishi nutsuwa. Ummi ta gaisheshi batare da ta dubeshi ba, ya amsa yana bin fuskarta da kallo, yana son ya tambayi dalilin kukanta saidai babu dama.     "Je ki sai na nemeki, kin shirya kayanki?" Ta gyada kai, Faruk ya yamutsa fuska yana duban Hajiyarsa cikin rashin fahimta, bayan fitar Ummi dauke da bokiti da tsummokarai, ya dubi Hajiya.   "Ina zata?"   "Kano zata koma mana, ko ka manta daga can ta fito?" Ya daure fuska yana mai kauda kai. "Idan har a matsayin yar aiki zata je don Allah ayi hakuri Hajiya." Ya karashe fuskarsa cike da damuwa kwarai. Ta yi shiru tana dubansa, ta gama karantar ba karamin so ya ke yiwa Ummi ba, tasan halin d'anta, wannan magana har cikin zuciyarsa ya ke yinta.    "To yanzu Sadauki za'ayita rike musu ita ne? Karka manta fa kawota akayi Kano aikatau asalinta ba ma'yar garin bace."   Ya lumshe ido kafin ya bude. "'Yar Ringim ce. Kuyi hakuri har ta cika watanta, idan wacce ta kawota ta zo Kanon, sai aje har Ummin ayiwa mahaifinta bayani don Allah Hajiya. Amma yanzu ba girma kuma ta cigaba da aikatau, a duba wannan lamarin Hajiyata."   Hajiya ta gyada kai cike da gamsuwa. "Shikenan, na ji zanyi tunani." Bayan fitarsa daga falon ta rasa ma abin yi, mikewa ta yi ta nufi dakinta. Karshe dai ta yanke hukuncin kiran kanwarta Hajiya Mama, don ita har nauyin Hajiya Madina ta ke d'an ji a yanzu.   Hajiya Mama ta dauka, bayan sun gaisa ta ce. "Sadiya kina jina?" "Ina jinki Hajiya." Ta koramata dukkan yanda ake ciki tun daga jiya da Faruk ya zo musu da maganar Ummi har zuwa yanzun da ya ce shi bayason komawarta aikatau Kano. Ta k'ara da fad'in. "Ki ban shawara Sadiya, kwakwalwata ta cushe, na rasa abinda zanyi, ina kuma jin tsoron Madina ta ji maganarnan daga bakin 'yarta."   Hajiya Mama da ta sandare don mamakin wannan al'mari ta numfasa. "Allah Mai Iko, wannan shine ana zaton wuta a makera. Karki damu Hajiya, ni banga aibu a aurensa da Ummi ba matukar zai had'a har ita Ihsan din kamar yanda ku ka ce, don bazamu so wannan abu ya kawo matsala a zuri'armu ba. Amma don Allah kamar yanda Genaral ya ce, ku daure kuyi bincike sosai akan Asalin yarinyar nan, Ummi dai a halayya bata da aibu daidai gwargwado yarinyar akwai hakuri da sanin yakamata sannan har gwaje-gwaje ayi ko don gujewa wani abu da zai je ya dawo. Ki kwantar da hankalinki, daman yau zanje saloon, zan fasa idan yaso na sanarwa Alhaji na je gidan Madinan. Allah Ya za6a abinda yafi alheri."    Cike da jin dadin kalamanta Hajiya Babba ta ce.   "Kai da kuwa kinyimin babban taimako wallahi, nagode sosai."   "Haba Hajiya, kina gaba da ni ai kin wuce haka, na tabbatar Madina ba zata kawo matsala ba in sha Allah."   Ta jinjina kai. "Ina fatan hakan." A karshe sukayi sallama da zummar duk yanda akayi zata sanarmata. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 73 Ko wanka baiyi ba, hankalinsa na ga abar kaunartasa. Zai so jin amsar da zata bawa Binta. Hakan yasa shi yin cak yana mai zubamata ido don sun ba shi baya.        Ummi ta yi murmushi wanda har gefen  kumatunta ya lotsa. Batasan sadda ta soma magana ba.    "Ni nasan yanda nake jin Yaya Faruk a raina Binta, akwai da yawa daga abubuwa wanda ba sai ka 6ata lokaci wajen bayyanashi ba, watakil ya nuna kansa wataran. Ina son Yaya Faruk fiye da kaina, zan iya sadaukar da nawa farincikin don kawai ya samu nasa. Binta me zance ga mutumin da ya daraja ni ya nunawa duniya ni din mutum ce mai daraja? Ke kuwa idan ban kaunaceshi ba me zan mishi?"   Binta ta yi dariya. "Tabbas kinyi gaskiya, kin kuma burgeni matuk'a. Allah Yasa wannan kauna taku ta d'ore har ku haayyafa ku tara zuri'a guda taku."   Kunya ta hanata amsawa face murmushi da tayi.   "Ameen." Jin muryarsa yasa duk suka juyo a razane, ta zaro ido duk ta bi ta diririce, shikenan ya ji abinda ta ce kenan? Ji ta yi kamar ta nutse a k'asa don kunya. Ita kuwa Binta tana yar dariya ta russuna ta gaisheshi, ya amsa fuska a sake yana duban Ummi. Ita dinma gaisheshi ta yi dakyar sakamakon harshenta da ta ji ya yi nauyi duk don tsabar kunya.   Ya amsa yana ji kamar ya nufeta ya rukunkume don dadin da kalamanta sukayi masa.      "Zo nan Ummi." Ya fad'a gami da juyawa ya fita. Ta bi bayanshi da kallo, daga shi sai dogon wando da singilet bak'a.     Ta dubi Binta wacce ke zungurar kafadarta tana mata nuni da ta je. Ta yi murmushi mai bayyana hak'ora cikin muryar rad'a ta ce. "Anya bai ji maganarmu ba?" "Lallai ke dinnan, to meye idan ya ji? Daman kinason fadamishi kin kasa kinga ya hutar da ke." Ta girgiza kai gami da wanke hannunta da handwash sannan ta mara mishi baya.    A tsaye ta tarar da shi wajen hanyar da zata sada ka da sashensa. Ya kura mata ido kamar ya hadiyeta. Ta kauda fuskarta ta karasa gareshi. "Meyasa kike barin wayarki a daki sai nayita kira bakya d'agawa?' Yana maganar cikin muryar shagwa6a kamar wani k'aramin yaro, abin ma sai ya bata dariya, idan yana wannan shagwa6ar wani kyau ya ke yi mata, ita dake mace ma bazata iya yinta ba.   "Ka yi hakuri, aiki ne mukeyi." "Naji, maimaita abinda kika fad'awa Binta yanzu a kicin." Ta zaro ido tana kallonsa fuskarta dauke da murmushi, shima murmushin ya yi ya daga mata gira. "Kinyi zaton ban ji ba ko? Na ji dukkab tattaunawarku, oya idan dagaske ki ke maganarki ki cemin 'Ina sonka Faruk' na ji." 'Innalillahi...' Ta karantota har karshe a ranta, gaba daya ta diririce. Shi kuwa dagaske ya ke, don tsayuwarsa ya gyara yana jiranta. "Kinyi shiru." Ta hau wasa da yatsunta, murya a raunane ta ce. "Ni..ni ban ta6a fad'a ba fa." "Shiyasa nakeso ki fad'amin, ya zama ni ne farko nine kuma karshen wanda za ki fad'awa hakan ok?"   Ta runtse ido, yau ta shiga uku, ji ta ke yi kalaman sun yi mata nauyi da tsauri, bazata iya fad'a ba. Ya dan saka saman yatsansa manuniya ya zunguri hannunta.   "Kin yi shiru Ummina." Ta ja baya kadan ta hadiyi miyau.  "Ka yi hakuri don Allah." Ya lura a tsorace ta ke ma, sai kawai ya yi murmushi. "Ki ka ce ba ki da abinda za ki biyani? Ke kuwa ki ke da shi, kawo kunnenki ki ji."   Bata motsa ba, tuni shi kuwa ya matso da bakinsa dab da kunnenta. Maganar da ya fad'i ce ta rud'ar da ita, da gudu ta juya ta koma kicin. Ya bita da kallo yana dariya kafin ya juya ya soma tafiya. Wayarsa ta dauki k'ara, ganin Haidar ne yasa shi dauka da sallama. Bayan sun gaisa Haidar ya ce.  "Ya Man, na ji ka shiru, ka kuwa fad'awa su Daddy?"   Faruk yana taka matattakala yana murmushi ya shafi sumar kansa. Kafin ya soma kora mishi duk yanda akayi harma da rikicinsu da Dakta Ridwan da kuma cewar Hajiya na sai ya auri Ihsan ma.    "I just don't know what to do brother, ban ta6a son Ihsan ba, ban kuma ta6a yi mata kallon budurwa ba, ina mata kallon kanwata wacce ban bambanta ta da Baraka da Ikram ba."    Haidar wanda ya yi shiru ya soma magana. "Duk wannan bai dameni ba, kamar yanda ku ka samu sa6ani da dan uwanka ba Faruk, zan so ka je ka sameshi har gida ku fahimci juna. Banason akan lamarin aurenka a samu rarrabuwar kai a family, it's something that never happen, so please don't let it now."   Ya gamsu matuka da zancen yayannasa. Daman shima ya sauko daga fushin da ya yi da Dakta saidai kunya ce ta hanashi zuwa gidansa ya ba shi hakuri, wai shine ya nemi yi mishi rashin kunya akan ya ta6a matar da ya ke ji cikin zuciya da gangar jikinsa. Maganar Haidar ta katseshi. "Batu kuma na Ihsan, wannan ba yanda ka iya, ka zamo mai biyayya ga umarnin iyaye ko don ka cika d'a nagari. Ka yawaita addua akan neman za6in Allah ka ji?"   Ya zauna a karshen matattakala batare da ya bude kofa ya shiga ba falonnasa ba, murmushi dauke saman fuskarsa na jin dadin maganganun dan uwansa ya ce. "Na ji Brother, zan yi yanda ka ce, bari na yi wanka nayi breakfast, zan je gidan Dakta idan ma ban sameshi ba zan shiga asibitin."    Ya ji dadin maganarsa. "Yauwa that's my lovely brother, haka nake son ji. Nasan anjima zai shigo, gwara ka je kafin shigowarsa, nima ina nan tafe bayan Magriba idan Allah Ya yarda, don na k'ara ganin surukartamu da akai mana 6oyon fuskarta."     Dariya Faruk ya yi kafin suyi sallama ya mik'e ya fad'a d'akinsa.                     ***   ***   ***                        RINGIM DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 72 A farfajiyar gidan suka hadu da Anti Amarya wacce ta dawo daga gidan wata kawarta, ta lura da yanayinta saidai baki kawai ta saki tana kallonta, Hajiya Mama itama ganinta ne yasa ta dan saita kanta duk da kuwa bai hana komai 6oyuwa ba. Anan kofar gidan ma Adnan ya dawo daga yiwa wasu abokansa sallama sakamakon tafiyarsa da ta k'arato nan zuwa kwana biyu ya ci karo da ita, daga yanda ta amsa sallamarsa ma yasan ba lafiya ba, ta shiga mota direba ya ja suka bar wajen. Hawayenta ya kasa tsayuwa, wannan wane irin rana ce ta zo musu? Kamar yanzu ne suke wasa da dariya da kanwartasu, ace har lamari na aure ya had'asu rikici na ban mamaki. Wai yau Madina ce ke kiran sun ci amanarta, ta nuna suna mata son kai, wannan abu da me ya yi kama? Har take nuna basu suka haifi Ihsan ba ga da ga. Ran Hajiya Mama ya k'ara jagulewa, ta kasa hadiye kukanta, haka hawayenta ya yi ta zubowa tana daukesu da mayafinta. Babu abinda ta fi tunowa sai yanayin shakuwarsu tun suna k'anana har zuwa girmansu, yau sa6ani ya shiga tsakaninsu akan auren Ummi da Faruk. Ta runtse ido. 'Madina ina kika mance tarbiyyar da iyayenmu suka bamu? Yaushe kika chanja daga kyawawan d'abi'unki? Ya akayi kika bari son 'yarki ya rufemiki ido har haka? Wannan abu abin kunya ne ya shiga kunnen iyayenmu. Abin kunya ne gareki idan Hajiya Babba ta ji wannan lamari.' Tana dukkan wadannan maganganun ne cikin zuciyarta. Akan hanya wayarta ta yi k'ara fiye da sau biyu amman ta kasa d'auka, tsoron dagawar ma takeyi, me zata iya cewa Hajiya Babba? Sam bazata iya da wannan abin kunyar ba wanda ta ke ganinsa tamkar a mafarki. Adnan cikin sauri ya shiga wajen Maminsa, saidai bata falo hakan yasa ya nufi dayan falonnata, nan ma batanan, a karshe ya yanke hukunci shiga dakinta. Gefen gado ya sameta zaune tana kuka. Hankalinsa idan ya yi dubu to yau ya tashi, ya isa gabanta ya durkusa. "Mami meke faruwa ne? Ga Hajiya Mama ta fita hankalinta a tashe tana hawaye, kema ga ki na tarar dake kina kuka, rasuwa akayi ne?" Ta share hawayenta. "Da rasuwa ce to da sauki don ansan tana kan kowa, wannan yafi mutuwa k'ona zuciya Adnan. Yau akan Ummi har Hajiya Mama ta mareni, sai nace tun tasowarmu da ita sa6ani irin haka bai ta6a shiga tsakaninmu ba." Kansa ya danyi dum, ya kasa tantance tak'amaiman yanayin da ya shiga. "Ummi kuma?" Ya furta yana dubanta. "Kwarai kuwa." Ta kwashe maganat ta gayamishi, ya dan ji hankalinsa ya kwanta, daman ba yau ya fahimci akwai wani abu a zuciyar Faruk game da Ummi ba, shi yasan daman irin haka zata faru wataran, Faruk ya ce zai auri Ummi. Saidai Ihsan fa? Bai ta6a kawowa tana son Faruk ba. Tabbas shi bai ga aibu a had'asu ya auresu ba. "Kayi shiru?" Ya dago ya dubi mahaifiyarsa. "Mami shi fa lamari na aure Allah ne Ya tsara abinsa, babu wanda zai chanja kaddararsa. Kuma..." "Tashi ka ficemin! Shashasha kawai da baisan kishin nasa ba." Sum-sum ya fice don ya lura ta shiga cikin zafi, da alama babu abinda zai iya fadamata a yanzun ta fahimta. Har ace ta manta irin gwagwarmayar da ta sha a baya wajen Abbansu, har ace zata mance komai na duniya rubutaccen al'amari ne, idan Allah Ya yi za'ayi, za'ayin? Ya waigo yana mai dubanta, waya ya ga ta dauka ta na kokarin kira. Gabansa ya fad'i kada fa ta ce zata kira Hajiya Babba. Da sauri ya isa gareta ya rike hannunta. "Don Allah Mami karkiyi haka, ki duba zumuncinku, kada a sanadin abinda bai kai ya kawo ba ki 6ata kyakkyawar alak'arku da yan uwanki wadanda kowa ya gani sai ya yi sha'awarta." Sai kuma jikinta ya danyi sanyi, ta dubeshi fuskarta har lokacin a daure. "Tashi ka ficemin Adnan tun ban kai ga ta6a lafiyarka ba." Ya tashi jiki a sanyaye ya fice, bata fasa kiran ba saidai jin da ya yi Ihsan ta kira ta ke tambayar ko ta taho, hankalinsa ya dan kwanta. *** *** *** ABUJA Hajiya Babba duk ta bi ta damu akan rashin amsa kiranta da Kanwarta Sadiya bata yi ba, batason kiran Mami tukunna. Ihsan ta shigo da sallamarta ta yi shirin tafiya don tuni an fita da kayanta, sam lokacin ma batasan anfasa tafiyar da Ummi ba. Ganinta yasa Hajiya sakin fuska tana dubanta. "A'a, d'iyata har an fito?" Fuskar Ihsan ba walwala sosai ta amsa. "Eh Hajiya, an fita da kaya ma." Hajiya ta gyada kai. "Zo ki zauna mu danyi wata magana." Ta zauna a gefen Hajiyar kamar yanda ta umarceta. "Ihsan inaso kiyimin kyakkyawar fahimta akan maganar da nakeson yi dake. Zamanki anan tare da mu yasa na fahimci kamar kina son Sadauki, ban tabbatar da hakan bane saida naji daga bakin Ikram. To sai kuma Sadauki ya zo mana da zancen Ummi tashi guda da sunan ita ya ke so da aure. Saidai ya amince zai hadaku tare ya aura. Ina fatan baki da matsala akan hakan?" Takaici ya hana Ihsan magana, lallai ma ta yaya ake zaton za ta yi zaman kishi da 'yar aikin gidansu? Wannan ma jawowa kai raini ne wallahi. Haushin Hajiya ma ya hanata cewa uffan har lokacin kanta yana k'asa. Hajiya ta yi shiru tana karantarta, sai kuma ta numfasa. "Ki je Ihsan ki yi tunani, bazan matsamaki ba. Ke tawa ce, bazan k'i farincikinki ba kema, bazan kuma so k'untata miki akan wata ba. Dake da Sadauki abu daya na daukeku, babu wanda zanso shiga hakkinsa." Ihsan ta sauke ajiyar zuciya. 'Kedai kome za ki ce daga baya ne kin riga kin nuna son danki fiye da kowa." Cewar Ihsan a zuciya. Shigowar Binta ce ya katse maganar. Suka amsa sallamarta. "Ya ce ta fito." Ta mike Hajiya na mata adduar komawa lafiya itama tana godiyar abubuwan alherin da suka bata. Saida zata shiga motar ne ta dubi Ikram. "Wai bada Ummi za mu tafi ba?" Kafin Ikram ta amsa Hajiya ta amsa. "Ki je zata zo." Ran Ihsan ya k'ara yin bak'i, kenan plan dinsu da Ikram ya tashi a banza? Niyyarsu da zarar ta koma Kano a koreta sai aga ta aurenta da Faruk, ranta ya yi wani irin daci, a fusace ta shiga motar ta banko murfin. Mamaki ya kama Hajiya, anya babu wata a k'asa? Daman ta lura kamar bata yi na'am da maganganunta ba. Haka ta bi bayan motar da kallo, tuni haushi da 6acin rai yasa Ikram juyawa ciki. Watakil nan gaba ma Ummi ta zama mai mulkar kowa a gidan, don taga alama ta samun kar6uwarta wajen Hajiya da Daddy. Acewarta DAN ADAM tara ya ke bai cika goma ba, zasu ga hali na butulci da Ummi za ta yi musu nan gaba indai akayi auren. Don ta sha jin labaru na irin hakan. Ummi duk tana kallon abinda ke faruwa, daman tun jiya da dare Hajiya ta sanarmata an fasa tafiyar da ita, sannan Faruk ya kira ya bata tabbacin kada ta sake ta shirya da zummar komawa Kano, ta daina aikatau daga ranar. Ta saki labulen kicin din gami da sauke ajiyar zuciya ranta ya danyi haske, ko babu komai alwashin da Ihsan ta ci akanta bazai tabbatu ba. Yanzu ita ina tasan zata ta samu motar garinsu idan suka korata? Saidai da tambaya kam. Ita har fargabar komawarta Ringim take, ko wane k'alubalen zata fuskanta a wajen Saude da Babanta? "Ke!" Ta firgita matuk'a ta juyo idanunta a zare kirjinta a sama don ji tayi har numfashinta ma kamar yana barazanar daukewa. Ganin Binta yasa ta dafe kirjinta gami da rufe ido tana sauke ajiyar zuciya. Dariya sosai Binta ta sanya, Ummi ta girgiza kai. "Wallahi ba ki ji yanda na tsorata ba, kai Binta saiki kashe mutum." Binta cikin dariya ta daga mata hannu. "Yi hakuri, daman cewa nayi bari nagani ko za ki tsoratan, na manta yanzu ke fa a tsorace kike da kowa ma." Ta yi murmushi tana tattare tafarnuwar da ta zubar a k'asa don kid'ima. "Na yi zaton Ikram ce ko Ihsan din ce ta dawo." Sukayi dariya. Kafin kuma Ummi ta cigaba da 6arar tafarnuwa. Binta ta dubeta sa'ilin da ta janyo robar kifin da ta saka a ruwa don ya yi kankara ta soma kokarin gyarawa. "Wai ni don Allah meyasa ban ta6a jin kin fad'i wani daddad'an kalami na soyayya ba game da Yalla6ai? Sai nake ganin kamar ya fi sonki fiye da yanda ke kika daukeshi." Wannan tambaya ta Binta, yasa Faruk cin burki daga kofar kicin don ya zo ne daman da niyyar tuhumar Ummi dalilinta na barin waya a daki ga shi yana ta kira. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   74                        RINGIM Bud'a ne ya cika gidan Baba Habiba sakamakon auren da aka daura na Zahraddeen da Khadija. Yawanci gaba daya danginta ne suak halarci bikin, daidaiku ne cikin dangin Malam Yahuza suka zo, wadanda zuwansu ma ba amfani awajen Baba Habiba don acewarta sun zo kwasar rahoto da gulma.     Ita da aminiyarta Saude sun yi shiga ta sutura har kala uku ana yi ana chanjawa, Amarya kuwa kusan kala biyar ta yi domin wannan ranar. Da yamma Amarya na cikin taron jama'a suna gaisawa, wata yar uwarsu ta zo kiranta. "Kizo kinyi bak'i fa daga Kano." Ta bi bayanta da mamaki don iyakar saninta bata da kowa a Kano. Gabanta ya bada wani bugu mai karfi ganin Raihana cikin shiga ta wata shegiyar shadda mai tsadar gaske, daidai da sark'ar da dan kunnenta abin kallo ne, ballantana kuma idan ka dubi agogo da awarwaronta kasan na gwal ne. Tana da 'yar k'iba hakanan doguwa ce, ba laifi tana da kyau daidai gwargwado, wacce suke taren itama ta ci nata adon har ta gaji da haduwa. Murmushi Raihana ke jifanta da shi da wani dan iskan kallo wanda bai kyautu a matsayinta na yar uwarta mace ta yi mata ba. Ta daure ta k'ak'alo murmushin yak'e ganin cewa cikin mutane ne.    "A'a, Raihana kece a garinnamu? Sannunki da zuwa."   Raihana da har lokacin bata bar murmushi ba ta amsa. "Yauwa Dijat , ke kuma haka akeyi?" Dija ta rude gudun kada ta ce wani abu da mutane zasu dagosu, tana shirin kwa6arta Baba Habiba ta karaso wajen duk ta had'a zufa saboda shiga da fita. Ganinsu yasa ta washe baki kamar gonar auduga, ta bisu da kallo daga sama zuwa k'asa sannan ta dubi Dija.   "Wadannan fa?" 'K'awayena ne na yanar gizo, sun zo tayani murna ne."   "A'a sannunku kun ji ko? Ina wuninki?"   Ba kunya ta gaishesu, kasancewar suma yan duniya ne sai suka amsa.  "A'a baza'a barsu anan ba kinga nan a cike yake, kaisu gidan Saude su zauna. Bari na kar6o muku muk'ulli."   Daga haka ta karasa ga Saude ta Kar6o ta damk'awa Dija. "Jeki can na kawomiki kazar ma ki ci acan kinga asiri a rufe." Ta fada cikin k'ank'an da murya. Dija ta murtuke fuska.   "Aa, ki barshi sai dare.". "To shikenan."   Ta ja su Raihana zuwa gidan Saude. Bayan sun zauna Raihana ta rik'o hannunta idanunta sun kada tsabar kishi.   "Ba ki kyautamin ba Dijat, yanzu wannan kwalliyar duk don Deen kikayi ba don ni na ganki na ji dadi ba? Haba Dijat, ba ki ta6a yimin kwalliya irin haka kin aikomin na gani ba." (Wa'iyazubillah)   Dija ta daure fuska gami da zame hannunta. "Ki bar wannan magana mana Raihana, ke meyasa kike da sa6a alk'awari? Ban gargadeki kada ki zo gidanmu bane?"   Raihana ta yi raurau da fuska. "To ya na iya tunda dai kin kashe wayarki kwana biyu bana samunki, ni kuma hankalina duk ya tashi na ji tsoron kada ki juyamin baya shine na zo."   Dija ta ja tsaki sannan ta mik'e. "Ina zuwa." Daga haka ta fice, Raihana da abokiyar tafiyarta, Saima, suka bita da kallo cike da shaawa. Saima ta maido dubanta ga Raihana. "Ashe dai a kauye ana samun mata har haka? Ke kam kinyi dace." Ta daure fuska. "To meye naki ciki?" "Aa, bakomai ranki ya dade, ni mamakin ma da nakeyi ya zaayi kamarki ki zauna wai wannan ta gagareki juyawa? Haba Hanah, dubun da suka fi ta ma kin shawo kansu ta hanyar malamai balle kuma ita?"   Raihana ta numfasa. "Ni wannan so nakeyi mata na gaske, ba don ta kafe akan wannan shegen Deen din ba da har aurenta zan so yi. (Waiyazubillah) saidai ya zo yana son yimin shigar sauri."   Saima ta jinjina kai, lallai ba karamin so take yiwa Dija ba, banda haka, manyan mata nawa ne suka so samun wannan damar amman ta k'i basu sai ita?      Duk yanda taso ta shawo kan Dija abu ya ci tura don kwata-kwata bata bada fuska ba, ta ce ko menene sai ta je Kaduna, haka gwuiwa a sake Raihana ta juya bayan ta bata makudan kudade da suka girgizata.      Washegari aka tattarata aka mik'a Kaduna gidan Deen, har lokacin Munira bata dawo ba tana Ringim don ta ce bazata iya ganin rawar kan da mijinta zaiyi akan yar uwarta ba da ta ci amanar yan uwantaka.    Gudu ta ke yi itama tana binta a guje suna k'ara runtumawa cikin dajin da babu gida gaba babu a baya, har ya kai ta taka k'aya, ta zube a wajen tana numfarfashi, takobi ne shar6e6iya sai kyalli ta ke, doguwar mace kyakkyawa ce rik'e da wuk'ar kafin akan idanunta ta fuskarta ta rikid'e zuwa kalar kore.   "Saina kasheki! Saina kasheki ke Makira!!"    Tana ihun kuka tana fadin kiyi hakuri na tuba Hasiya karkimin haka don Allah. Amma ina bata ko saurareta ba ta daga takobin nan, ai kuwa ta fasa k'ara.   Yi ta ke babu kakkautawa duk ta hargitsa mutanen dakin, suka rirrik'eta, fadi take. "Zata kasheni! Wayyo zata kasheni wallahi! Ku taimakeni!" Cikin gigita Saude ta kai hannu ta toshemata baki.    "Ke Habiba shiga taitayinki, mafarki kikayi?"   Sai lokacin Habiba ta gane ta farka, ta dubi jama'ar dakin 'yan rakiyar amarya Kaduna ta sauke ajiyar zuciya gumi yana ta tsastsafowa daga goshinta, ita kuwa Habiba idanunta a zazzare, rashin gaskiya ya bayyana k'arara akan fuskarta. Tana jin matan na fadin addua ya dace ta dungayi idan ta yi mafarki. Har dai kowa ya koma makwancinsa. Dabara ta fadowa Saude. "Tashi muje ki sha ruwa." Suka mike suka fita zuwa kicin, ta dakata gami da rike kafadar Habiba.    "Gayamin wane irin mafarki kika yi?" Habiba wacce har lokacin jiki ke rawa ta zayyanemata komai, hankalin Habiba ya tashi, ji ta yi hanjin cikinta sun kad'a.  "To, meke shirin faruwa haka? Mun shiga uku."   "Ba ke kika shiga uku ba Saude, ni da na ganta ganin idona ai ni ce da shiga uku."   Saude ta dubeta da idanunta da sukayi kwalkwal. "Kada fa allura ta tono garma?" "Kar ki damu, da zarar mun koma zanje wajen bokanya, ko menene zata sanarmana sai a dauki mataki." Saude ta jinjina kai cike da gamsuwa. A karshe suka koma makwancinsu batare da ko ruwan Habiba ta iya sha ba.                   ***   ***   *** DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 75                        KANO   Da yamma suka isa, direba na fakin, ta sauko daga motar a hargitse, tana rataye da jakarta ta hannu. Sukayi kici6us da Iklima wacce ke shirin fita zuwa makwafta, daga ita sai doguwar riga(fitet gown) da mayafi karami kalar kayan. Ta watsamata kallon tara saura. "Akwadaita an dawo?" Ihsan ko kallonta bata yi ba ta gifta ta wuce. Iklima ta bita da kallo gami da sakin dariya, batasan meyasa yanzu gaba daya ta tsani Faruk ba, wani mugun so ta ke yiwa dan wata k'awar Hajiya Binta, Mu'azzam, shima sonta ya ke yi tamkar ya mutu. Ihsan bata zarce ko'ina sai sashensu, tuni Fahad ya isar da zuwanta ga Mami wacce ke kicin tare da Ramma suna aiki, saidai duk fuskarta babu digon walwala. Jin zuwa Ihsan yasa ta fito, Ihsan na shiga itama uwar ta hau kwalawa kira. Suna yin kici6us ta fad'a jikinta gami da ruk'unk'umeta ta soma hawaye. Mami ta lumshe ido tana mai rungumeta, ta riga tasan meke damunta.    "Aa lale da manyan gari." Maganar Ramma ya katse tunaninsu, jin hakan Mami sakinta.   "Shiga ciki ina zuwa." Bata ko amsa sannu da zuwan Ramma ba, ta yi gaba abinta, wannan ya bawa Ramma tabbacin akwai matsala kenan. Mamin tasa Ramma mik'amata kayan sama. Tana jin Ramma na fadin. "To ita kuma Ummin tana ina?" Saidai babu mai amsamata, koda ta shiga dakin Ihsan harara ta samu da ta kulata. Ramma ta kama baki. 'O'o, ko ta yi gamo ne a hanya?' Ta tambayi zuciyarta don tasan ba mai amsamata. Ta fice tana jimamin wannan lamari na sauyin da aka samu daga uwar har d'iyar, tana nan Hajiya Mama tazo saidai kafin ta je gida ta dawo ta tarar batanan.       Sai bayan Magriba, Mami ta yi wanka ta shirya tsaf da nufin zuwa turaka, alokacin ne ta shiga dakin diyarta ta inda ta tarar da ita tana goge jikinta alamun wanka ta yi.  Ganin Mami yasa ta zama gefen gado, itama zaman ta yi. "Mami kin ji..." "Kar ki ma 6ata bakinki, nasan komai." Cike da mamaki ta ce. "Au Mami har daman zasuyi mana wannan cin fuskar su iya kiranki su sanarmiki?"   Ranta ya dan sosu da jin kalma ta cin fuska da 'yarta ta jefi Hajiya Babba da shi, zata so ita ta kirata da komai amma bataso yaranta su rainasu. "Kar ki k'ara fad'ar haka tunda ba ke ta ciwa fuska ba, ni ta yiwa. Kuma idan har muna raye zasu ga sakayya." Ihsan ta yi kwafa tana mai jin zafi a zuciyarta. "Wallahi Mami ni na hakura da Yaya Faruk, na ji na tsaneshi ma. Wai akansa aka ci zarafina, banda cin zarafi ta ya ya za'a had'ani kishi da 'yar aiki, wallahi nafi karfinnan." Ta ji dadin kalaman Ihsan din, daman ita ta ke ganin zata bata matsala sai kuma ta bata mamaki. Cikin murmushi ta dafa kanta.  "Kin burgeni matuk'a, barni da su suna gani sai kin auri mijin da yafi Faruk komai da komai, sai sunyi mamakin mijinki Ihsan. In sha Allah kuma sai kin riga d'anta aure. Ita kuwa Ummi su jik'ata su shanye, mu ba'a koyamana yawan malamai ba, idan ita ta bisu don kawo mana rashin jituwa a zuri'armu to ta cigaba idan zaiyi tasiri."   Ihsan ta dan ji wani iri, so daban ya ke, anya zata so wani nan gaba irin son da ta yiwa Faruk?  Tana ji Mami ta gama maganganunta kafin ta mike bayan ta ce idan ta kammala ta zo ta gaida Abbanta, daga nan ta fice, Ihsan ta bita da kallo. Sai kuma ta dan ja guntun tsaki gami da cije le6e. Ummi kadai ce matsalarta fa, da babu ita, babu abinda zai hanata auren Faruk. Amma kuma Mami na da gaskiya, watakil fa ba banza ta bar su ba, ta yi kwafa. "Babu abinda yafi karfin addua, za ki gane kurenki." Ta yi furucin a fili. Saida ta kammala shiri cikin doguwar jallabiya ta fito, bayan kammala cin abinci da Fahad ta ja hannunsa zuwa ga Abbansu, Adnan tun maganar da sukayi da Mami ya bar gidan.      Abba ya yi farinciki da zuwanta, ita kuwa dadin sake ganin dariyar Abbanta ne ya cika zuciyarta, gani ta ke yi kamar a mafarki.      Sun jima suna hira kafin Mami ta umarceta da shiga sashen matan gidan a gaisa. Haka ta soma da zuwa sashen Hajiya Binta, babu kyakkyawar tarba daga gareta harma yaranta, itama ganin haka ta nuna yar zamani ce ta fito batare da ta k'ara kallonta daga gaisuwa daya.     Kai tsaye wajen Anti Amarya ta nufa, ta sakarmata fuska fiye da baya don ita bata da matsala a hakan, hakanan su hussaina yaranta, har Anti Amarya tayita janta da hira tana fadamata ta yi k'iba. Ihsan ta ji dadin zuwa sashenta kafin su yi sallama.   Haka halayen Anti Amarya ya ke saika rantse dagaske so na tsakani da Allah ta ke maka, takan yi iyakar kokarin boye ainahin sirrin zuciyarta agabanka. (DAN ADAM MAI WUYAR GANE HALI KENAN...!)                     Hajiya Mama ranta duk a 6ace, Amina da yaran Hajiya Maman, Rukayya, Maryam, Na'im da autarsu mai shekaru goma, Mufida. Intisar ce babbat diyarta don Hajiya Mama bata samu haihuwa da wuri ba.   "Lafiya kuwa yau?" Cewar Rukayya tana duban yan uwanta. Amina wacce suka zama kamar yan uwa ta jinjina kai.   "Nifa na lura tun dawowar Hajiya Mama daga gidan Mami bata cikin hayyacinta, Allah Yasa ba wani abun ne ya faru ba."     "Amin, ni duk jikina ya yi sanyi ma wallahi, bakuga wainar fulawar nan ta dazu ba gaba daya fita daga raina ta yi wallahi."   Rukayya ke maganar tana yamutse fuska cike da damuwa, duk da ita ce ma karfin cewa suyi wainar fulawa har ana rabon aiki, wannan ce zatayi suya a farko idan ta gaji waccan ta yi, wancan mai daka yaji.   "Allah Ya jishshemu alheri." Fadin Amina kenan. Suka amsa da amin, ita kam Amina ko aka bata ta6a kawowa wani batun Ummi ne ya tashi da Faruk ba? To wa zai kawo hakan ma?     Suna nan zaune Adnan ya shigo da sallamarsa. Suka amsa, Maryam ta saki baki tana dariya. "Ikon Allah, kodai mafarki nakeyi, ku mintsileni mugani."   Ai kuwa Amina da Rukayya harma da Mufida suka hau rige-rige, ganin dagaske suke ta yi tsalle ta ja baya suka sanya dariya gaba daya. Adnan ma cikin dariyar ya zauna, hankalinsa ya dan kwanta da yanda suka tarbeshi, ko babu komai ya ji dadin ganin Hajiya Mama bata sanarwa yaranta ba. Bayan an gaisa yake sanarmusu batun tafiyarsa gobe, Rukayya harda ihun murna, Maryam ta zaro ido.   "Dagaske?" Adnan ya jefeta da kallon kauna don kuwa sun had'a kansu saidai a 6oye suke soyewa ta kafar sadarwa harda yiwa juna alkwarin rikon amana. "Kamar baki sani ba?" Sai kuma ta yi murmushi. Maryam ta ta6e baki.   "Ato, ai munsan komai saidai mu yi shiru." Ya yi dariya da mamaki kafin ya dubeta. "Ke kika sani malama, ina uwata?" "Au, daman baku hadu ba? Daga gidanku fa take."   "Eh, ni na dan fita ne."   "Ayya, bari ayi mata magana." "Kamar ba gidanmu ba?" Ya fad'a yana hararar Rukayyar, sukayi dariya kafin ya wuce.   Sallama ya yi, Hajiya Mama ta amsa don ta ji maganarsu da yaranta. Fuska a sake tana mai kokarin danne damuwarta ta ce. "Aa Adnan? Karaso mana." Ya karasa jiki a sanyaye ga kuma kunyar abinda Maminsa ta aikata gareta ya russuna ya gaisheta. Ta amsa. Shiru ya biyo baya kafin ya soma bata hakuri kan abinda ya faru. "Kayya, dama baka shiga ciki ba don kuwa wannan tsakaninmu ne. Karka damu, ka yiwa mahaifiyarka uzuri kasan ance mai d'a wawa, watakil son nata ne ya rufemata ido har haka. Amma nasan Madina ba lallai har zuciyarta hakan bane." Ta fad'a ne kawai ba don har zuciyarta tana ganin hakan bane, saidai bata kaunar yaransu su shigo cikin maganar wanda dai da kamar wuya. Bazata so ya shafi zumunci yaransu ba da mazajensu.     Adnan shi kansa yasan Hajiya Mama ta fad'a ne kawai.   Ta share maganar. "Ashe kuma gobe zaka wuce ko?" "Eh." Ya fada yana mai shafar sumarsa.   Ta shiga yi mishi nasiha tamkar dan cikinta, da nunamishi sanya Allah a rai da kuma gujewa mugayen dabi'u da abokan huld'a. Adnan ya ji dadi matuk'a na shawarwarinta, ya ji dukkan damuwarsa ta warware daman ya dauka shikenan Hajiya Mama ta barsu kenan, sai ya ga ba haka ba. Koda ya ce zai wuce, dakatar da shi ta yi don saida ya ci abincin dare sannan ta kaishi har wajen Alhaji Haruna mahaifin su Intisar suka gaisa shima ya bishi da kyawawan nasihu da kuma addu'o'i kafin suyi sallama ya tafi bayan su Maryam sun tabbatar mishi zasu zo rakiyarsa zuwa(Airport) goben.                     ***  ***  *** DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   77                       RINGIM     Habiba da Saude suna komowa Ringim kai tsaye wajen bokanyarsu suka zarce. Suna isa bayan anmusu iso suka shiga gami da zubewa agaban Uwar Biyu mai bori. Habiba ta zayyanemata dukkan yanda ya faru a mafarki.    Ta mike ta soma jijjige jiggigenta da kad'e-kad'e kafin ta zauna fuska a murtuke sai kuma ta kyakyace da dariya wanda ya razanasu ya kada yan hanjin cikinsu. Maganarta ta katse tunaninsu.    "Karki damu kanki! Wannan ba komai bane sai shaida na cewar diyarta na nan tafe da wata gagarumar nasara a rayuwa wanda zai iya janyo tonon silili kala-kala ciki harda mutuwar auren daya a cikinku! Abubuwa da yawa a rufe su ke nakasa fahimta amman ina mai tabbatarmuku ba mai kyau bane gareku! Wannan duk ba damuwa bane idan ni Ade Mai Bori na raye to ba bazai afku ba ko kadan!"    Cikinsu ya k'ulle tsabar rud'u, Saude har fitsari ta soma a wando, Habiba da ta soma had'a gumi ga jiki da ya dauki rawa ta daure ta soma magana cike da dauriya.   "Mudai yanzu bokanya da ke muka dogara, ki taimakemu ki fiddamu wannan hatsari."  (Waiyazubillah)       Dariya na hauka Ade Mai Bori ta yi kafin ta yiwa kanta kirari cikin karaji sannan ta dubesu fuska murtuke. "Zan yi muku aiki fiye da yanda na rufemuku bakin shegu a baya! Me ku ke bukata?"   Saude ta riga Habiba magana. "Idan da hali a kashe Ummi!" Ta tsaya ta gama tsaface-tsafacenta kafin ta dubesu idanuwa a zazzare. "A'a! Na duba wannan bazai yiwu ba!" Saude da hawaye ya tahomata ta kasa magana sai rawar jiki, Habiba ta cafe.   "Bokanya nidai a haukatar da ita yanda bazata yi amfani ba koda ta zo."   Ta gama tabbatarwa da ba mai yiwuwa bane ba a hanyar tsafinta, saidai bata son ko kusa ta nuna gazawarta har karo na biyu hakan yasa ta kyakyacewa da dariya. "Angama!!! Ko garinnan ba zata ta6a waiwaye ba!!!"   Ransu ya danyi sanyi, suka had'a duk kudaden dake jikinsu wanda ya kai dubu ashirin suka ajiyemata. Haka suka baro wajen hankali tashi, Saude suna fita ta ke6e bayan gini ta rage mararta, tana ji cikinta na kad'a saidai ta danne har su isa gida ta kasaye. A hanya babu wanda ya iya magana kowanne tunaninsa ya ke yi, duk tunaninsu ya basu cewar karshensu fa ya kusanto. Babu babban abinda ya k'ara hargitsasu sai mutuwar auren dayansu da Bokanya ta ambata.      Ko kan wa zai fad'a???           Koda suka isa a gidan Saude suka yada zango, saida Saude ta rage cikinta sannan ta samu zama don su tattauna, alokacin kuma Mariya ta shigo gidan daga gidan makwafciyarsu acan ta kwana.    "Habiba, kinji kuma sabuwar masifa ko?" Habiba ta numfasa. "Hum, bari kawai Saude, wallahi don ba ki ji yanda kwakwalwata ta dauki chaji ba, kai wannan jarabar da me ta yi kama? Da nasan akwai wannan ranar tafe wallahi da sadda na gama da shegiya lokacin zan gama da ita itama. Ni na yi zaton shikenan ta zama hanyar arziki ashe akwai sauran rina a kaba?"   Saude ta share gumi da mayafinta.   "Wallahi dadin da naji daya ne, na cewa da Bokanya ta yi zata haukata mana ita, kinga shikenan sai daga nan ta k'ara gaba, idan ma ta samu motar da ta kad'eta, mun huta."   Habiba ta saki fuska. "Allah Yasa hakan." "Ameen dai."   Nan suka cigaba da maganar, hankalin Saude ya kai ga diyarta Mariya da ta zura hannu a wando ta yi shiru tana kallonsu. Cikin tsawa ta ce. "Ke ciremin hannu daga nan tun ban bubbugeki ba!"   Habiba ta mik'e gwuiwa a sake. "Atoh, ki ka sani ko k'aik'ayi ne?" "Ai ina zaton haka, mantawa na yi ma ina son kar6omata maganin sanyi wajen Bokanya, wannan yawan soshe-soshen ya isheni."   "Yafi dai kam idan ba so ki ke ta diyarki ta 6aci tun yanzu ba. Bari na je na huta gajiyar bikinnan tunda hankali ya kwanta." Saude ta taka mata har kofar gida kafin su yi sallama itama ta koma ga harkokin gabanta batare da ta k'ara maida hankali ga yarinyar ba....!                     ***  ***  *** DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 76                        ABUJA   Faruk kuwa yanda sukayi da Haidar ya yi, ya shirya ya wuce gidan Dakta.  Bai iskeshi ba sai Jidda da ta hau shi da tsiya akan ta ji da auren wacce kuma ya 6ige. "Amman wallahi ka bamu kunya." Ya watsamata wani kallo yaso ya tanka sai kuma ya tuna maganganun Haidar, bazai so kam zumunci ya 6aci ba. Ya yi kwafa. "Kin fa ci darajar yarana, da a yau za ki koma Ghana." Ta yi dariyar k'ular da shi. "Dad'in abun ba kauye na tashi ba ballantana na tsoraci komawa."   Bai ko k'ara kallonta ba ya fice yana murmushin kinyi kad'an.    Kai tsaye asibitin da Dakta Ridwan ya ke ya isa. Duk da ba ranar aiki ba ya shiga don duba wata mai nak'uda da ta samu 'yar tangard'a, ya yi nasarar ciro bebin lafiya yana cikin dinketa ne, ya hango kaninnasa daga jikin windo kasancewar windon gilas ne, ya dubi nos dake gefensa cikin fad'a. "Ba ki da hankali ne? Ta ya ya za'a barmin windo bud'e ina aiki?"   "I'm sorry Sir." Daga haka ta karasa cikin sauri ta saki labulen, murmushi Faruk ya yi ya zura hannuwa a aljihu kafin ya wuce kai tsaye ofishin Dakta. Zama ya yi akan kujerarsa yana kalle-kalle kafin ya ta6e baki. "Wani aikin sai likita, duk wani jagwal suna gani." Ya k'arashe kafin idanunsa ya kai ga dan karamin frame din dake saman teburin, su hud'u ne a hoton wanda akayi musu ran bikin Ridwan din.  Idanun Faruk a rufe don lokacin ma bai zama cikakken matashi ba, su kuwa sun dubeshi suna dariya aka yi hoton. Murmushi ya yi, shi kam haka Allah Ya yishi bai fiyeson hoto ba. Duk da dai yayyunnasa sun ce bikinsa ne da baizo ba, muddin ya tashi aure watakil ma da kansa zai dunga kiran mai hoton ya dauka. Yakan yi dariya don yana ganin lamarin wasa kawai.    Baifi mintuna goma ba sai ga Dakta ya shigo. Yana ganinsa ya tsaya ya daure fuska.   "Get out of my office." Ya fada yana mishi nuni da k'ofa. Faruk ya mike tsaye ya na dubansa fuskarsa dauke da damuwa. Ganin ba shi da niyya yasa Dakta soma tattara abin amfaninsa zai wuce gida don daman abinda ya shigo da shi kenan, da sauri ya sha gabansa ya rungumeshi. "Please forgive me brother, kayimin dukkan hukuncin da kaga ya dace da ni." Ya dago jikinsa yana dubansa da idanunsa wadanda suke nuni da gaskiyar abinda ya ke fad'a.    "Amma kada ka hukuntani ta hanyar dauke fara'arka daga gareni da kuma fita harkata."   Jikin Ridwan ya yi sanyi, daman dauriya kawai ya ke yi don tun bayan barinsa gidan Daddy, ya ji babu dadi, yasan kaninnasu mai son farincikinsu ne, ta ya ya shi ya kasa kar6ar abinda yazo musu da shi da hannu bibbiyu ko don faranta ransa?   Ya dafa kafadarsa. "Kamin laifi Lil, saidai na yi maka uzuri tunda baka ta6a yimin makamancinsa ba. Karka damu ya wuce."   Ran Faruk ya yi sanyi, tare suka jera suna tafiya, Ridwan na k'ara nunamishi dalilin da yasa ya nuna rashin goyon bayansa. "Gani nake kamar ka wuce ajin yarinyar ne, na kuma yi tunanin kodai wani asirin ta yi maka? Amman ka yo hakuri." Faruk ya yi murmushi. "Babu abinda ta yimin, ka manta muna dagewa awajen adduar neman tsari? Duk da dai akwai kaddara, amma bama fatanta. Wannan kauna ce daga Allah nake jinta game da ita." Suka dubi juna sukayi dariya, ya bugi kafadarsa. "Lil ne da soyayya? Kamar ranar nan ba zata zo ba."   Faruk ya shafi sumarsa yana shagwa6e fuska. Hanashi wucewa ya yi suka nufi gidan Ridwan din da niyyar zuwa yamma su wuce gidan gaba daya. Ta (whatsapp) ya sanarwa da Haidar cewar sun shirya. Ya aikomishi da rawa na mace har abin ya sanyashi dariya.   Jidda ganinsu yasa ta hau cakar Faruk akan batun Ummi, shi kuma ya ce ta yi ta gama aure ne babu fashi sai idan Allah baiyiba. Shi kam Dakta na jinsu saidai baisa baki ba, saida ya kula da Jiddar na neman korar mishi k'ani yasa shi tsawatarmata dole ta saki hirar ta yi shigewarta daki da alama dai 'yar bayan Ihsan ce.                      ***   ***   ***               .       ABUJA    Hajiya Babba ce zaune a falonta tare da yaranta maza ana 'yar hira. Ta dubesu cike da farincikin ganin yanda Ridwan ya sakarwa Faruk fuska kamar yanda suka saba, fatanta Allah Ya cigaba da had'a kan yarannata haka. Suna zaune a saman kafet ga katuwar leda agabansu an shimfid'a sai kulolin abinci duk Ikram ta zuzzubamusu.  Haidar ya sanyo batun auren Faruk da irin kyauta ta musamman da ya tanadar mishi.   "Mata biyu lokaci guda? Ai wannan ni kadai nasan tanadin da na yi ma." Ya fada saitin kunnen Faruk , ya yi kamar bai ji ba ya cigaba da cin abincinsa. Babban Yaya na jin haka ya ajiye cokali gami da dan kora ruwa sakamakon kwarewar da ya so yi babu shiri.   "Wai wa zai auri mata biyu?"   "Oh, baka da labari fa ashe Dan uwa." Cewar Dakta.    "Abincin za ku ci ne ko hira zaayi?" Suka tsinci muryar Daddy wanda ya katse hanzarin Haidar da Dakta masu zuci-zucin bawa Babban Yaya labari kamar wasu yara.     Ya karaso fuska a sake ya zauna. "Ke kuma na lura duk ranar da 'ya'yanki ke gidannan kina mantawa da lamurana, ina ga dai na kusa hanaku irin wannan zuwan." Ya karashe yana kallonsu, suka yi dariya har Faruk. "Kai amma da na ji dadi Daddy." Ya fad'a yana kanne ido daya. Suka watsamishi hararar wasa banda Babban Yaya da ya ke dariya. "Kwana nawa ne kaima?" Fadin Haidar kenan.   Daddy ya dakatar da su da hannu. "Ya isa hakanan, a ci abinci a nutse. Idan kun kammala ina nemanku." Daga haka ya tashi Hajiya ta bi bayansa.    Bayan sun kammala suka hadu sashen Daddy har Ikram. Ya soma da fadin. "Ku amanar Allah ce awajena, ya kuma zama dole na dunga nusar da ku akan lamura na rayuwa." Ya cigaba da yi musu nasiha mai ratsa jiki kafin ya sanyo batun auren Faruk da Ummi.   "Idan Allah Ya shiryo hakan babu wanda zai hana, hakazalika kowa da kaddararsa a rayuwa." A karshe dai ya kara nusar da su batu na hadin kai, akan ko bayan ransa yana fatan su rike zumunci.     Sun jima anan, Babban Yaya bai nuna wata alama ta k'in sha'anin ba, Ikram dai har lokacin zuciyar bata lafa ba, koda ta yi yunkurin hakan da zarar ta tuno da wacce zaa aurar sai ranta ya yi bak'i. Ko yar uwarta Baraka lamarin baiyi mata dadi ba, Intisar ma ta nuna rashin yardarta ga Hajiya Mama nan ta ci karo da fushinta, dole ta ja bakinta ta yi shiru ba don ranta naso ba, ga mijinta shima da ya goyi bayan dan uwansa.      Haka taro ya tashi zuciyar kowa a sake har Ikram don ta samu dama Faruk ya sakarmata fuska.      Bayan fitarsu Daddy ya sanarwa Hajiya cewar lokaci ya yi na dauke Ummi daga sashen yan aiki, itama daman ta yi tunanin hakan saidai tunanin da ya yi mata yawa akan k'in daga wayarta da Madina ta k'i yi duk kuwa da cewar ta samu magana da Hajiya Mama ta nunamata komai lafiya amma sam hankalinta bai kwanta ba. Sunyi waya da Adnan ya sanarmata gobe zai wuce, ta bishi da kyakkyawar addua da kuma nasiha.      DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 78                       KADUNA Amarya Dija an dirji amarci, Deen kamar ya haukacemata tsabar rud'ashin da ta yi, ita kanta tasan ta yi aure ta samu miji na nunawa sa'a.    Munira baiwar Allah, a wannan daren ta ci kuka har ta gode Allah, tana yiwa ranar kallon bak'ar rana agareta, wai mijinta da yar uwarta da ta dauketa tamkar wadda suka fito ciki daya, sune tare a makwanci guda. Dakyar ta iya saita kanta don a daren ba wani bacci da ta yi. Da safiyar litinin ta daure ta rigasu fitowa ta hada karin kumallo na gaba dayansu. Kamar ta je ta kwankwasa musu sai kuma ta tuno cewar ko sallama a daren jiya Deen fa baizo ya mata ba, koda a waya bai nemeta ba sai ita da ta mishi sakon taya murnar aure nan ma bai amsa ba. Anya yanzu ba bada kai bane ta je kwankwasa musu? Ai ta daure ma da ta yi girkin. Juyawa ta yi ta koma suka karya da yaranta ta shiryasu ta fice kaisu makaranta.     Su kuwa masoyan basu tashi ba sai bayan takwas, suka shiga wanka bayan sun gama suka shirya. Dija ta hade cikin wani leshi kore dinkin da ya kama jikinta, shi kuwa kananun kaya ya ci don ya samu hutu wajen aikinsu na amarci.   Koda Munira ta shigo, dariyarsu ce ta bata shaidar sun tashi, ta daure ta hadiye abinda ta ke jin ya tasomata a zuciya ta shige dakinta.   Su kuwa karya kumallo sukeyi hankali kwance, Deen na so ya je ganin Munira saidai yana gudun 6acin ran Dija. Bayan sun kammala suka koma daki, wayarta ta dauki k'ara, ganin mai kiran yasa duk ta dan diririce ta wayance da katsewa gami da saurin sanya wayar a(silent), ta jefa wayar k'asan filo tana murmshin yak'e. "Mutane ayita takura mutum." Ya yi murmushi yana mai janyota jikinsa. "Madam ko za kimin rakiya mu gaisa da yarana?"   Ta daure fuska. "Kodai kace za ka ga matarka?"  Ya ja karan hancinta. "Ta ci albarkacin yaranki mana." Zata k'i sai kuma ta tunano da kiran da Raihana ke mata, ta yamutse fuska. "Jeka kai daya, ni babu inda zanje." Ya yi murmushi. "Shikenan." Ya mike ya fita saida ta tabbatar ya tafi din sannan ta ciro wayarta a k'asan filo. Mayyar lokacin m wayar kiranta ne ke kara shigowa. Takaici ya isheta, ita fa yanzu duk ta ficemata aka, idan ma abinda ya shafi bukatarta ne to yanzun ta samu mai daukemata, duk wannan haukan ya fice daga kwanyarta daman ba ta6a aikatawar ta yi ba a fili. Ta daure ta kai zuciyarta nesa ta daga wayar. Daga can kuwa Raihana har wani gwauron numfashi ta saki wanda Dija ta ji shi har ta ji kamar ta shiga wayar ta mak"urota. Ta daure "Kin kira ban kusa."   "Eh kina can kina amarci ai, ni na dauka ma ko wani laifin nayi miki."   Ta cije le66anta. 'Laifin uwaki.' Ta fad'a a ranta, a fili kuwa ta dan yi murmushi mai sauti. "Haba ni ina na yi wannan isar da za ta ce haka gareki? Ko kusa." "To ya ango? Dijat kada fa ki k'i cika alkawarin da ki ka dauka, ki yi hankali, idan har ki ka ce za ki juyamin baya zan iya daukar kowane mataki."   Hankalin Dija ya tashi, yau ta shiga uku, hankalinta ina ya tafi da ta mance da batun bokanyar uwarta har ta amince da Raihana akan ta sama mata mafita? Kodayake lokacin ji ta ke ko menene ma zata iya aikatawa matukar zata samu ta auri Deen.   "Kinyi shiru." Ta dan gyara murya. "Ina na isa na mance da hakan? Karki damu ina sane." Raihana ta yi dariya. "Ina Kaduna, da zarar kin gama satin amarci, zamu soma namu."   Ai saita mike tsaye tsabar kaduwa. Kasa magana ta yi ta kashe wayar gaba daya, ta koma ta zauna gefen gado. Babu wata mafita face na kiran Babarta, dole ta bar yin rufa-rufa gareta yanzu, idan yaso ta je mata wajen Bokanya ta gayamata duk halin da ake ciki.        Acan kuwa, Deen ya shiga dakin Munira, tana zaune gaban madubi daga ita sau daurin kirji ta yi wanka. Ganinsa ba sai ta juyo ba, sallamar ma a ciki ta amsa.     Zama ya yi gefen gadon yana dan satar kallonta tana shiryawa, tunaninsa bai wuce tsakanin matannasa biyu ba wace ta fi k'ira? Yana lura da abubuwa da dama wanda Munira ta mallaka, Dija bata mallakesu ba saidai ya dan lura da ramarta, ya kasa jurewa ya mike ya isa gareta gami da rungumota ta baya.   "Wai ba gaisuwa?" Ta tureshi kadan sannan ta gaisheshi, ya amsa. Cikin gatse ta tambayi amarya, ya shafi kansa ya amsa a dan kunyace. "Idan na kammala abinda nake na je mu gaisa."   "Am ina yaran nan?" Ya fada cikin basar da wancan maganar, ta watsamishi wani kallon da bata shirya ba. "Ka manta yau litinin?" Ya jinjina kai yana dan kame-kame. "Oh hakane fa." Daga haka bata k'ara ce mishi uffan ba, har ta kammala shirinta ta hau gyara, ganin haka yasa shi ficewa sum-sum. Ta bishi da kallon tausayawa kanta. Kamar ba Deen din da ta sani ba, gabadaya ya chanja, ta soma tunano kyakkyawar rayuwar da suke gudanarwa kafin zuwan Dija, yanzu kam babu shi. Hawaye ya zubomata, ta kasa cigaba da aikin don daman kanta ciwo ya ke, kwanciya kawai ta yi bayan ta sha magani, cikin taimakon Ubangiji kuwa bacci ya yi awon gaba da ita.                     ***   ***   ***                           ABUJA   Ta rude iyakar rudewa jin da ta yi wai yau zata koma gefen dakin da Ikram ta ke wato dakin Baraka harma da batun da Binta ta zo mata da shi na cewar ayau dinne sabbin yan aiki biyu zasu zo.     Binta ta zunguri kafadarta. "Wai kina daukar hakan wasa? Wallahi dagaske nake, Hajiya na ji tana sanarwa Ikram kar kiso kiga yanda yarinyar nan ta hada fuska, karshe ta kwalamin kira ina daga kicin akan na zo na kiraki."    Ummi ta jinjina kai, wato shikenan ta tashi daga matsayin 'yar aiki? Allah kenan mai yanda ya so.    Jiki a sa6ule ta bi bayan Binta, ai kuwa kamar yanda Binta ta fad'i haka dinne ya tabbata wato dai za'a chanja mata muhalli, ita kuwa Binta ta samu k'arin albashi wanda yafi ba baya tsoka. Wannan abu ba karamin dadi ya yi mata ba.     Ita ta taimakawa Ummi suka gyare dakin tsaf, dakin sak irin na Ikram ne, saidai bambanci and kala, na Baraka komai adon ruwan hoda akayi, ita kuwa Ikram (sky blue)da fari.     Binta cewa ta ke.. "Ki godewa Allah Ummi, Allah Ya daukaka ki lokaci guda ke kam alherin Allah ne ya kiraki Kano ki ka hadu da Yalla6ai har ga shi sanadinsa kin samu matsayin dab an ta6a ganin wata 'yar aiki ta samu ba.    Ummi kam murmushi kawai ta ke, gaskiyar maganar kenan da Binta ta fad'a. A ranta godiya kawai ta ke ga Allah, saidai a gefe guda tana jimamin haduwarsu da Antinta Amina, anya lamarinnan zaiyimata dadi?     Bayan sun kammala ta zauna bakin gado ta zuba tagumi tana kallon Binta wacce ta dage sai an jera kaya a sif, ita kuwa sam bata so hakan ba, gani ta ke kamar za'a maidata sashenta. Ta daga kai ta dubi(Ac) da Binta ta kunna sai aiki ya ke yi, acewarta gwara ta dinga shan ra6a itama ta murje.     Aka banko kofar aka shigo babu ko sallama Ikram ce, ta rike k"ugu tana bin dakin da kallo kafin ta yi musu duba na raini. Sai kuma ta kyalkyale da dariya. "Abinka da wanda bai saba ba kenan."    Ta dauki(remote) ta kashe Ac, sannan ta dubi Ummi tana yamutsa fuska. "To sarauniya dangin matsafa ki zo Hajiya na kiranki."    Daga haka ta fice bayan ta yi wurgi da remote din har yana dukan k'afar Ummi. Ummi murmushi kawai ta yi ba tare da nuna damuwa ba ta dubi Binta. "Ina zuwa." Binta ta yi kwafa. "Wallahi da ni ce ke Ummi sai na gayawa yar banza bak'ar magana, bansan sadda Ikram ta 6aci haka ba. Wallahi ki daina ragamata, ya dace ki dunga kwatarwa kanki 'yanci, ko babu komai yayanta za ki aura." DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 79   Ummi da har lokacin bata bar murmushi ba ta ce. "Meye duniya? Wataran don kanta za ta gaji ta bari."   Binta ta ja tsaki. "Ai ke daman hakurinki kusan ma ince ya yi yawa, ba fa komai za ki zuba ido ayimiki ba wannan raini ne."   Ummi ta yi hanyar fita tana fadin. "Gwara dai na tafi kada na yi laifi." "Je ki dawo ranki ya dade!" Ta karashe cikin zolaya, itama Ummin tana jinta bata tanka ba bayan dariya da ta danyi.   A falon sama ta tarar da Hajiya, agefenta wasu atamfofi ne da leshi. Sai wata mace wacce daga gani ba bahaushiya bace zaune a can gefe. Bayan ta gaishesu ne, Hajiya ta bata umarnin zuwa ga matarnan.   "Hafsa aunata." Wacce aka kira Hafsa ta amsa da gur6atacciyar hausarta sannan ta shiga auna Ummi bayan tasa ta cire hijabin jikinta.     Saida ta gama sannan Hajiya ta bata umarnin tafiya, haka ta koma daki jiki duk a sanyaye, wato har dinkuna zaayi mata.    A kwanaki uku kuwa sai ga Hafsa da dinkuna kala goma kala-kala. Atanfa biyar leshi biyu sai wasu yadi guda biyu. Ta rasa bakin godiya tsabar murna, Hajiya kam ta sha addua har saida ta dakatar da ita da fadin"Yiwa Kai ne." A ranar kuma ta hadata da Ikram don ta zuwa siyo kayan undies da na shafa. Jin da Ikram ne Faruk ya kira wayar Ikram ya yi mata gargadi da babbar murya don tun a daren da Hajiya ta sanarmata ta ke faman cika da batsewa, ya tabbatar mata ya lura da hakan. Hakan da ya yi sai ya samawa Ummi lafiya, Ikram na dawowa daga makaranta suka wuce. Har gaba ta ke yi wai don kada su jera da Ummin don ta lura sai wani d'ar-d'ar Ummin ta ke na rashin sabo da shiga ire-iren wajen da sai dan wane ko wance. Don mugunta babu abinda ta za6ar mata saita barta da za6in wannan yasa Ummi ta d'ibi undies kala bibbiyu, a 6angaren shafa ma ta rasa kalar da ya dace kawai sai ta dauki wani(Cream) da batasan ko na menene ba, hoda ma ta dauki daya sai janbaki da jagira, daganan Ikram ta fiddo kudi masu yawa ta ciri adadin abinda Ummin ta dauka ta biya suka tafi babu mai yiwa wani magana. Ummi gaba daya sai ta ji tausayin kanta, wane irin rayuwa ne haka za ta yi cikin mutanen da suka fi ta?  'Allah Ka dafamini." Ta fad'i a ranta. Yana kwance yasa filo tsakaninsa da mahaifiyartasa sannan ya dora kansa saman filon suna 'yar hira akan ginin gidansa wanda ya yanzun ya yi nisa sosai. A haka suka yi sallama suka shigo, ya lumshe ido jin muryar abar kaunarsa kafin ya bude ya kai idanunsa gareta. Bata ko kalleshi ba saboda idon Hajiya dake kansu, ya mike zaune gami da rungume filon kujerar a kirji.     "Wash! Sannunku da gida." Cewar Ikram, itama Ummi ta gaishesu. Sannan ta mike don zuwa gabatar da Magriba don a hanya ta yi musu. Kasancewar Ikram na fashin sallah, ta dakata gami da budewa Hajiya ledar kayayyakin kamar yanda ta buk'ata.    Tun ganin kayan Faruk ya daure fuska, ya yi shiru yana jiran abinda zai fito daga bakin Hajiya. Ita dinma fuska ba walwala ta dubi Ikram. "Menene wannan ki ka kwaso kuma? Wannan cream din nasa haske fa?"   Ta girgiza kai. "Ita fa ta za6i abinta wallahi, bari na yi ta za6i abinda ranta ke so."   Suna hada ido da Faruk ya watsamata wani mugun kallo da ya yi sanadin kadawar yan hanjin cikinta, ta daure ta kauda kai. Baice komai ba, yana ji Hajiya ta hauta da fad'a sosai akan wannan ba daidan ba da ta yi mata.  "Haka na sanyaki? Bance ki za6omata ba? Ko don kinsani ita din bawani za6e zata yi ba?"    Gogan waya ya hau dannawa abinsa yana mai nazari, amma kwarai Ikram ta rainashi, wannan ba Ummi ta raina ba, shi ta raina.    "Ai dole sai kin koma gobe..." "Is ok Hajiyata, ki yi hakuri." Ya katse Hajiya da ke faman sababi, ta mike ta wuce sashen Daddy daman yana nafilfilu shiyasa ta zauna nan.    Bayan fitarta ya dubi Ikram. "Tashi muje." Ta kasa motsi ta hau ba shi hakuri, ya dakamata tsawa. "Na ce ki tashi!" Ba shiri ta mike shima ya mike tsaye ya nufi dakin Ummi, tana zaune saman darduma mai taushi ta idar da salla tana addua, saida ya jira ta kammala sannan ya bata umarnin ta taso. Ba tambaya ta bi bayansa sanye da hijab ajikinta.    Tare suka fice bayan ya sanarwa Hajiya ta waya, gudu kawai ya ke shararawa a saman kwalta, har suka isa wani katafaren boutique wanda duk Abuja babu irinsa indai a fannin saida kayan amfanin mace ne. Haka ya shiga ya lodowa Ummi kayayyaki masu matukar kyau da tsada wanda Ikram zata iya rantsewa ita kam bata ta6a amfani da irinsu ba, saidai ta yi ta burin ta siya. Jikinta ya yi sanyi tana kallo takalma kala-kala da kananun kaya masu kyau da tsada amma babu halin ta ce ya siyamata. Ta k'ulu matuka, wato don ya ramawa Ummi ya yi mata haka kamar ba kanwarsa ba, saida ya gama jidar son ransa har da abaya kala uku da kayan shafe-shafe masu kyau da gyara fata sannan ya biya ta hanyar Atmcard dinsa. Haka aka loda kayan a boot wasu a gefen Ikram da ke zaune bayan mota sannan suka tafi, a hanya ma sai jan Ummi da hirar soyayya ya ke tana kakkaucewa, wani abin kuma ya sanyata dariya. Wannan ya k'ular da ikram matuka.    Hajiya ita kanta ta yi mamakin yawan kayan da Faruk ya siyo saidai tasan don an 6ata mishi ne, yasa Ikram ta shigar mata da su daki, kamar ta yi kukan wannan abu haka ta yita kwasa tana shigarwa. Ya shigo har dakin ya tsaya bayan komawar Hajiya sashen Daddy, ya umarceta da ta jeramata na shafar a gaban madubi, tana hawaye tana yi, Ummi na zaune bata so hakan ba saidai ya hanata motsi, asalima zama ya yi gefenta ya soma nunamata wasu hotunanta a wayarsa da ya dauka batare da saninta ba, soyayya dadi, nan ta mance da wata Ikram, saida ta juyo ta ganta ne yasa ta dan janye daga hirar. Bayan ta kammala yasa ta jera takalman harda su abayoyin da sauran kananun kayan na shigar mutunci a kwaba. Faruk bai bar dakinnan ba saida ta shirya komai tsaf sannan ya dubeta. "Get out now."    Ya fada gami da maida dubansa ga abar kaunarsa, ta dubesu suna hada ido da Ummi ta watsamata harara sannan ta fice tana goge fuskarta.    "Da ka barshi wallahi zanyi Yaya Faruk, ba ka gudun janyomin bak'in jini?"   Ya daga kafada. "Sun jima basu yi ba, karki damu kanki ai kin wuce haka a wajensu, kannenmu ne fa." Ta yi murmushi kawai can kasan ranta damuwa ce fal, ta lura shi ko a jikinsa, dakyar ta korashi kada Hajiya ta ganshi. Ya fice yana dariya ta bishi da kallo tamkar ta hadiyeshi don so.                     ***   ***   ***                          KANO DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 80                          KANO Ranar litinin ya kama na tafiyar Adnan, ranar ne su Rahila da Aisha suka zo gidan.    Suna zaune a dakin Mami su duka banda Adnan sai kuma Mamin dake labartamusu batun auren Ummi da Faruk. Salati su Rahila suka shiga yi. "Tabdi! Ni narasa ma yanda zan fassara wannan lamarin? Wallahi karki sake ki yarda a had'a darajarki da wata can wacce ba komai ba. Anya haka Ummi ta barsu?" Rahila ke maganar cikin 6acin rai. "Wallahi nima ina tunanin da walakin, goro a miya. Amma don Allah ku yi tunani, ta ya ya Yaya Faruk zai so Ummi har ma wai ace son aure ya ke mata? Na yarda yarinya ba laifi ta hadu saidai anya kuwa ba zaa bawa Hajiya Babba shawara akan dagewa da rok'on Allah ba? Nikam wallahi ina tantama idan bawan Allahn nan cikin hayyacinshi ya ke." Ta k'arashe cikin jimami, Ihsan na jinsu saidai takaici ma ya sa ta kasa cewa komai. Mami ta ta6e baki. "Su suka sani, idan aure ne suyi ta yi, munanan sai ta auri wanda yafi Faruk din kud'i in sha Allah."   Haka sukayita tofa na bakinsu, ko kusa Mami bata sanarmusu da sa'insar da ta shiga tsakaninta da Hajiya Mama ba. Sai a ranar ma ta daure ta amsa wayar Hajiya Babba, ta kuma fadamata cewar Ihsan kam ta hakura da Faruk akwai wanda ke sonta.   Hajiya Babba gaba daya ta fahimci Madina fushi ta yi, ta nunamata hakan ma karin dankon zumunci ne idan akayi.   "Kenan za'a fasa da Ummi ya aureta ita kadai?" Hajiya Babba daga can ta dan yi shiru, ina ita ina yiwa Sadaukinta wannan gangancin? "A'a Madina, menene idan ya auresu duka? Ina ce shi ya ga zai iya?" Mami ta yamutse fuska ta ji haushin maganar sosai.    "To Ihsan dai ta dawo kuma ta tabbatar min matukar ba ita kadai zai aura ba to bata son auren."    Hajiya Babba ranta ya 6aci, wannan son kai ne kawai. "Amma Madina kin ban mamaki, menene ciki..." "Don Allah Hajiya ke babba ce, ina ganinki da girma, na gayamaki raayin 'yata tunda bazai samu ba hakan to don Allah ki samamin lafiya, aure kuma idan ana daurawa sau dari a daura na Faruk da Ummi." Daga wannan ta kashemata waya.      A daren Adnan ya tafi, koda suka hadu da su Rukayya a(airport) hankali kwance suka gaisa yanda suka saba don babu wanda yasan wani abun, sun yi hotuna har Adnan na hawaye suna tayashi, haka suka yi bankwana cike da jin kewar juna.                   Hajiya Mama na zaune a falonta tana kallo, yayinda Amina ke gefe daga kicin tana 6arar tafarnuwar girkin rana, yaran gaba daya sun wuce makaranta. Lokacin karfe sha daya na rana. Wayarta ta dauki kara, Hajiya Babba ce, gabanta ya fadi, to har yaushe ne za ta yi ta 6oyon wannan lamari ga yayartasu? Ta rage k'arar talabijin ta dauka. Bayan sun gaisa Hajiya Babba ta jefomata tambaya. "Sadiya ya za ki 6oyen gaskiyar yanda ku ka yi da Madina?"   Hajiya Mama ta gyara zama, shikenan fa ranar da ta ke gudu ya zo don jin muryar Hajiya Babba ta yi duk a sanyaye. Kafin ta nemo abin fadi Hajiya Babba ta zayyane mata yanda suka yi da Madina ta waya. Ran Hajiya Mama ya 6aci. "Bata isa ba wallahi ta yi kadan, auren Faruk da Ummi saidai ikon Allah ne kadai zai sa a fasa shi, Madina ta raina mutane. Hajiya kada ki soma yarda da wannan banzan maganarnata, itace sama da mu ne?"   Cikin damuwa Hajiya Babba ta ce. "Sadiya zumunci nake dubawa, da dai Madina za ta yarda da tsarina da nafi kowa jin dadi."   "To Hajiya tunda ta nuna mana iyakarmu ba sai mu fita hanyarta ba? Ko ita ce ta haifemu?"   "Hannunka bai ru6ewa ka yanke ka yarr Sadiya. Bari dai zan duba na gani, idan na samu zuwa Kano a satinnan zan zo mu hadu a tattauna."   Hajiya Mama bata so hakan ba sai don dai Hajiya Babbar ta dage akan hakan ne, dole ta amince suka yi sallama akan hakan.       Amina dake kicin mutuwar tsaye ta yi jin an ambaci wata kamar Ummi kuam wai da Yaya Faruk aure. Anya kumnuwanta sun jiyemata daidai? Sai kuma ta ji Hajiya Mama na faman surutai tana fadin.   "Ai ba ita ta haifemu ba, a da Ummi ke yar aiki amma yanzu yarinya ta tashi anan, sai ta hada diyartata kishi da yayan masu da shi, shegantaka kawai."  Batasan lokacin da ta bar abinda ta ke ba tana salati, ta dafe kai don tsananin kaduwa, ji ta ke kamar ta saki fitsari anan, haka Ummi ta yi? Ina shawarar da ta bata? Shikenan ta kawo rarrabuwar kai acikin zuri'ar nan. Hawaye ta ji ya soma zubomata, inama tana da hanyar da zata bi ta samu Ummi koda ta waya ne su yi magana, anan kam babu abinda za ta ji sosai.  'Ba ki yiwa kanki dabara ba Ummi, ba ki kyautawa rayuwarki ba.' Ta fad'a a ranta cike da tausayin Ummin, kokisa bata son abinda zai ta6ata, ita mamakin ma karfin halinta ta ke yi na yanda ta iya bari suka kai ga haka da Faruk wai magana har kunnen iyaye? Sai kuma ta tuna abin na Allah ne, idan Ya yi babu mai iya hanawa. Ta sauke ajiyar zuciya. 'Allah Ya kauda dukkan fitinu. Ya yi miki za6i na alheri a rayuwa.' Daga nan ta cigaba da aikinta bayan ta je ta rage marar, yinin ranar cikin sanyin jiki ta yishi, tunaninta ko wane yanayi Ummin ke ciki a Abuja? Tasan dai ba kowa ne zai so aurennan ba.                    ***   ***    ***               BAYAN SATI DAYA                                  ABUJA DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    81               BAYAN SATI DAYA                                  ABUJA   Ummi an soma gogewa, fatarta fara ta kara haskawa sai sheki da wani sul6i da jikinta ke k'arawa, hakanan har wata 'yar k'iba ta yi, Ikram kadai ce matsalarta sai kuwa Baraka da matar Babban Yaya(Fadila) da Jidda idan sun zo. Su dinma a fili suke nuna rashin goyon bayansu. Wannan abu na yi mata zafi saidai fad'an da ya fi karfinka....!    Hajiya Babba ta bi jirgi zuwa Kano ita kadai tun ran alhamis, gidan ya rage daga Ikram sai kuwa su din.   Ranar Asabar misalin biyar na yamma Ummi zaune acikin (garden) tana sauraron wakokin hausa a waya wadanda Binta ta aikamata su da yawa, sanye take cikin wata atamfa ruwan madara mai adon fulawoyi, fuskarta fayau sai hoda da kwalli da ta sanya, kadan-kadan ta ke motsa lilon ta kwantar da kanta saman lilon idanunta a lumshe tana mai jin dadin wakar da ta ke bi na Alan waka na (Ummina). A hankali kuma hawaye suka soma zuba saman fuskarta, ta k'ara gyara zaman (earpiece) din kunnenta. Daidai lokacin da Faruk ya shigo gidan, dawowarsa kenan daga nan makwaftansu wajen wani dan makocinnasu mai mutunci da bai ji dadin jikinsa ba, kasancewar sun saba haduwa duk weekend yawanci anan kofar gidan su gaisa yasa koda ya ji ba shi da lafiya ya yi yunkurin zuwa dubashi. Yana sanye da riga koriya da wandon jeans bak'i, kai tsaye hanyar cikin gidan ya yi saidai idanunsa ya hangomasa sanyin idaniyartasa zaune saman lilo, ya dan kuramata ido duk a zatonsa ma bacci ta ke yi a hakan ganin yanda ta lumshe ido, ya taka a sannu ya karasa gareta, sai lokacin ya lura da(earpiece) dake a kunnenta ga kuma hawaye da ta ke zubarwa. Zama ya yi gefenta kamshi na turarensa ya ankarar da ita zuwansa. Da sauri ta bude idanunta gami da sa hannu ta share hawayenta, duk yana kallo saidai baice komai ba hannu yasa ya ciro kunne daya yasa a kunnensa, ya yi shiru yana nazarin wak'ar kafin kuma ya cire daga kunnensa yana mai dubanta, ta maida hankali ga wayar don kashe wakar.    "Kina tunawa da Ummarmu ne?" Ta kasa magana sai gyada kai. Ya sauke numfashi. "Hakan yana da kyau, saidai ba kukanki ne abin so awajenta ba, addua ya kamata ki yi mata idan har kina son ta yi farinciki da ke. Duk wanda ya mutu yafi bukatar adduarmu sama da komai."    Ta gyada kai. "Hakane." "Allah Ya jikanta." "Amin." Shiru ya dan biyo baya. "Ni kuwa Ummi kin ta6a ganin hoton Ummanki?"   Ta girgiza kai, wannan ma na daya daga cikin abinda ke sosa ranta muddin ta tuno.   "Ko a hoto bansanta ba, nasan dai muna kama ta bakin matar babana shima sai tana zagina ta dunga hada yanayina da ita sai ko makwafta da zan ji suna fadin kamarmu da ita."   Ya jinjina kai. "Allah Sarki. Kenan babu wani nata da ki ka ta6a gani?" Ta amsa da eh.    Shiru ya biyo baya kafin kuma ya ce. "Bayan wuya sai dadi in sha Allah, wataran za ki zama abin so da alfahari wajensu."   Ta yi murmushi don har cikin ranta ta ji dadin maganar. "Allah Yasa." "Amin." Sun jima suna yar hira tana amsawa a kunyace kafin su mike su shiga ciki.                      ***   ***   ***                            KANO     Hajja ta dubi Fatima babbar diyartata da kulawa. "Ke kam menene haka mai muhimmanci da ya taso ki daga Abuja zuwa Kano, maimakon ki bari tunda sati na sama ne zaayi taron zuri'a (family meeting) ku taho gaba daya da yara?" Hajiya Babba ta murmusa, kwananta biyu kenan da zuwa amman kullum sai Hajja ta yi mata korafin zuwannata don gani ta ke yi kamar wata matsalar diyartata ta samu da maigidannata.    "Ke kam Hajja ba wani abin bane ba fa, daga zuwa ganinku duk kin bi kin damu kanki da tunani." "A'a to, gani na yi ba ki saba wannan zuwan haka ba."   "To ke tunda kinsan bata saba ba, ai kinsan banza bazai kawota ba, akwai wani abun, bari yan uwannata su zo ko menene sai mu ji."    Cewar Dattijo Modibbo mahaifinsu. Jin haka Hajja ta rausaya kai. "Ai shikenan na bari." A karshe ma suka shiga wata maganar inda Modibbo ke fadin ya dace ma su kai ziyara Adamawa don sun jima basu je ba, ya ce idan anyi zaman taro zai fad'a.  Sai bayan Azhar Hajiya Mama ta iso ita daya sai autarta Mufida. Bayan an gaggaisa suka zauna hira da zaman jiran Mami, ba ita ta zo gidan ba sai yamma. Nan din ma ta zo ne tana daure-dauren fuska, ko kallon inda ta ke Hajiya Mama bata yi ballantana wata gaisuwa ta shiga tsakaninsu. Sai lokacin Hajja ta fahimci akwai matsala.  Bayan sun zauna har mahaifinnasu, Hajiya Babba ta zayyane batun auren Faruk da Ummi da kuma maganar Ihsan kaf ta fadawa iyayen, sai kuma Hajiya Mama ta dora da yanda suka yi da Madina a gidanta.    Shiru ya biyo bayan gama saurare, can kuma Modibbo ya yi maimaita Innalillahi wa inna ilaihir raajiun har sau uku.   "Hakika shaidan ya so shiga tsakaninku, ina nema muku tsarin Allah daga sharrinsa." Ya dan yi shiru kafin ya dora. "Kin bani mamaki Auta, kinyi abinda ban ta6a zatonki da aikatawa ba, da ace wani bare ne ke sanarmin kin yi wannan gagarumin laifin da babu ta yadda zan amince da hakan. Karki manta cewar Aure shi kaddarar Ubangiji ne, idan Allah Ya kaddarowa shi Farukun da ita Ummi aure, to babu mahalukin da zai chanja yin Allah, hakazalika idan kaddararsa ce aurensu su biyu duka, nan ma duk wani tashin hankula da zaayi zai je ya dawo ne ba fa zaa fasa abinda Allah Ya shirya ba."   Shiru ya dan biyo baya, Mami ji ta ke yi ranta na zafi, wato iyayensu ba su ga hadin da ake so ayi na diyarta da yar aiki ba? To wai ma Faruk kadai ne namiji da har zaayita takurawa akansa?    Modibbo ya cigaba da yi mata nasiha don ba shi da zafi sosai, ita kuwa Hajja shiru ta yi, wannan fadan da ake yiwa Madina yafi komai yi mata zafi, tana ji da yar autarta ta. Bayan Modibbo ya kai aya ta soma magana a fusace. "Nifa banga laifin Madina ba yarinyar nan da gaskiyarta. Ke banda rashin wayo da girman kwabo ki rasa da wacce za ki had'a dangantaka saida yarinyar da bakisan komai game da ita ba, 'yar asali ce, shegiya ce, oho! Duk ba daya da ki ka sani,duka-duka ko wata uku bata cika ba inace tare da mu, kece kuma har da marin kanwarki saboda..."   Tsawar da Modibbo ya dakamata ne yasa ta yin shiru tana kwafa, zuciyarta na tafarfasa kamar ta rufe Fatima da Sadiya da duka haka ta ke ji. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   82 "Ke meyasa baki da tunani ne? To ko fita idona tun ban sa6amiki ba wallahi! Kina ganin ana kokarin gyara lamari ke kuwa kina neman ki k'ara dagula shi? Ko an gayamaki shi Amadun ba shi da hankali da ba zai yi bincike ba kafin hada zuria da su? Haba!"   Ya juya ga yarannasa kafin ya kai ga magana Mami ta soma. "Ka yi hakuri Baffa, amma don Ihsan ita ta hakura, mahaifinta ma ya yi mata miji bata sani ba."    Ta fadi hakan don ma kada ya ce lallai hakan zaayi, Modibbo ya so fahimtar kawai ta fada ne saidai ya yi tunanin barin mutum da halinsa, ya jinjina kai ransa baiyi mishi dadi game da wannan sa6ani da aka samu ba tsakanin yaransa wadanda ya ke alfahari da su wajen kokarin zumunci da hadin kai.      Haka dai aka rabu ran kowa babu dadi.      Hajiya Babba kuwa ji ta yi kamar ran lahadi ta bi mota ta bar garin Kano sakamakon Hajja da ke ta jifanta da bakaken maganganu marasa dadi, daman Hajja ta na da fada idan an ta6ota musamman idan aka ta6a autarta. Ranar litinin kuwa jirgin safe Hajiya Babba ta bi zuwa Abuja zuciyarta a cunkushe, saukinta ma ta samu goyon baya wajen mahaifinnasu inda ya ce kuma ta dage nemawa dannata za6in Allah, Allah ba Ya bacci, Shi Mai amsawa ne.    Da wannan hankalinta ya dan kwanta, itama Hajiya Mama ta jaddadamata ta kwantar da hankalinta, karon kanta Mamin zata zo ta gano kuskurenta, wannan zamanin namiji mai rikon aure sai an auna, tana kyautata zato akan Faruk. Madina zata yi da na sani acewarta.                      ***  ***  ***                        RINGIM   Salati Habiba ta shiga yi tana kallon Saude wacce ta shigo a rude ta zubar da Mariya akan kujera tana rusa ihun kuka sakamakon maganar da wata makwafciyarsu ta kawomata akan ta sanya ido akan yarinyarta don ta ganta sun shiga wani lungu da Dauda fitinannen d'a ga Zinaru itama makwafciyarsu, wannan dalilin yasa ta duba diyar ta tabbatar ana amfani da ita.   "Kingani ko? Daman na sha kwa6arki akan sakacin da ki ke na barin yarinyar nan tare da wannan yaron, itace har shagon Usi mai kanti, yanzu ga irin ABIN DA AKE GUDU!"    Ita dai Saude ba bakin magana, don cuta an gama cutarta diyarta kenan daya a duniya, tana ji da ita ta kuma ci buri akan aurenta idan ta girma don yanzu duka-duka shekarunta bakwai a duniya.     "Ba kuka ya kamace ki ba, mu lalla6a mu kaita asibiti a aunata ko tana da cutar kanjamau, idan babu duk sauran mai sauki ne."    Suka dunguma zuwa asibiti, anci sa'a bata da cutar saidai ciwon sanyi da ya yi mata yawa a jiki, likitan ya tabbata musu ana amfani da yarinyar, abu ne da suka riga suka sani, ya nemi yardarsu a yi mata dinki suka k'i acewarsu sunsan yanda zasuyi.    Daga asibiti suka wuce wajen bokanya nan ta hadamusu magunguna, anan kuma Habiba ta je da batun matsalar Dija da Raihana, Bokanya ta ce zata yi aiki akai.   Haka suka wuce ran kowannensu ba dadi, Saude ta so zuwa gidan Zinaru ta zagesu tas saidai Habiba ta kwa6eta gami da nunamata wannan tonon silili ne don wanda bai sani ba ma zai iya sani. Basusan cewa ba, mutanen gari sunsha tarar Malam Balarabe akan ya saka ido akan diyarsa, anan kuma Saude idan ta ga ya hana diyar fita ta nunamishi bai isa ba.  Daman yasan shi din ba shi da wani kata6us a gidan, yan uwansa ma an rabashi da su, ba wanda ke takowa Ringim da zummar ganinsa tun bayan rasuwar Yayar Malam Balaraben da ta rik'eshi, itama har ta mutu bata ta6a haihuwa ba. Daman iyayen na Malam Balarabe sun rasu da jimawa.                   ***   ***   ***                      KADUNA... Lamura sun ca6ewa Dija tun ranar da Raihana ta yi mata waya akan tana nan zuwa, ta fahimci dukkan wani abu da su ke yi don a rabasu ya ci tura hakan bai samu ba, ranar da Deen ya koma dakin Munira a ranar Raihana ta zo. Da shirinta ta zo wajenta don kuwa wani shegen kwalli ta sanya a idanunta da yasa Dija kasa yi mata musu a dukkan abinda ta ce, ga wani dan iskan turare mai saukar da shaawa. A wannan ranar Raihana bata bar gidan Dija ba sai dare, Dija kuwa saidai ace Allah Ya kwatota don kuwa tuni ta fada tarkon shaidaniya Raihana. Tun daga ranar suka kara shak'uwa ta waya, har Raihana ta yi zuwa biyu gida, mutan gidan ba wanda ya ta6a kawo munin abu irin wannan a kansu saidai sun shaida Raihana ba ta yi kalar nutsastsun mata ba.                    ***   ***   ***                         KANO   Ihsan ta yi tsai tana duban hoton saurayin da Maminta ta bata, babu laifi kyakkyawa ne kuma bak'i, yana da 'yar kiba. Ta numfasa, ba wai ta ji sonsa a ranta ba, kawai dai ya kai yanda zaa iya auren huce haushi da shi.   "Dan wani babban abokin Abbanku ne dake Adamawa, mahaifinsa babban Injiniya ne, Alhaji Kabir Jimeta."   Ihsan ta ajiye hoton a gefe. "Yana da d'a Abubakar?" Cikin dariyar mamaki Mami ta ce.    "Ashe kin sanshi ma, ai shine wannan din."   Ta dan ta6e baki. "Yana da kirki, muna chatting da shi ai saidai ban sanshi a hoto ba, ya sha gwada yana sona saidai ni ce ban ba shi fuska ba."      "Ai kuwa ya zama dole ki so shi, kin kuwa san matakin arzikinsa yanzu a Adamawa? To ana sanyashi cikin goman farko na yara matasa masu kudin garin sannan kalleshi da kyau ba shi da makusa a halitta."   Ihsan ta danyi jim, kafin ta ce. "Yana da mata fa Mami." Tsaki Mamin ta ja, ta soma fusata da lamari na diyartata kuma. "Shikenan sai ki zauna jiran aurenki da Faruk ki yi kishi da wacce bata kai ba, ni wallahi bansan irinki ba, ina ruwanki da matarsa? Matarsa gogaggiyar yar boko ce kuma bata ta6a haihuwa ba da shi, shi kuwa ba shi da burin da ya wuce na ganin ya haihu a duniya. Idan ki ka haihu da shi tabbas mun warke, kada ki bar wannan dama ta wuce mu. A zamanin nan samun matashin da ba shi da aure kuma mai rikon aure sai an tona, gwara ki auri wannan da kowa ya shaida kyawawan dabi'unsa."    Haka Mamin ta yi ta kod'a Abubakar a wajen 'yarta, ita Ihsan har mamaki ta ke yanda uwar ta sanshi haka, sai kuma ta tuna sunan mahaifiyarsa da ta ambata, wato Hajiya Salma kusan tare suka tashi da Mamin a Kano, aure ya rabasu. Dole Ihsan ta amince da hakan, saidai abinda ta kasa sanar da Mamin shine, Abubakar ya sha janta da hirar da bata dace ba tana k'in ba shi fuska, hakan yasa ma dangantakarsu ta yi tsawo.  Ai kuwa kamar jira Mamin ta ke, Abba na dawowa ta tare shi da zancen, ya ji dadi matuka don kuwa acewarsa daman Alhaji Kabirun ya ta6a neman tayin hakan tun akan Aisha saidai Allah baiyi rabon dannasa bace, yanzu kuwa yasan zai ji dadi idan ya kasance da Ihsan, daman burinsu a k'ulla zumunci.     Kwana biyu da yin hakan Alhaji Muhammad ya yi magana da abokinnasa. "Kamar kuwa kasan ina kan ga6ar nemarwa dan nawa aure, ina burin ganin jikokina, fatana Allah Yasa idan anyi hakan mafarkina ya tabbata."   Nan suka sasanta magana inda Alhaji Kabiru ya tabbatar mishi cewar cikin(weekend) zai zo tare da dan nasa don su ga juna. Da wannan suka ajiye wayar ran kowa ya yi dadi.  Bayan Abba ya ajiye ne ya dubi Mami. "Kinga cikin ikon Allah sai a had'a auren harda na Iklima, itama ta tsaida yaron nan dan gidan tsohon kansila, Mu'azzam. Itama Hussainar ba barinta zan yi ba, lokaci guda zan aurar da su idan Allah Ya yarda, da zarar sun kammala wannan ajin, ba don ma yaron ya ce sai ya gama gini ba, da sai a soma na Iklimar."   Mami ta gyada kai, ranta baiso ba, ta so ya zamana ba za'a hada auren diyarta ta da na kowa ba, ko don a fi ganin kalar bajintar da zata yi. Amman ta riga ta saba da binshi yanda yaso. "Hakan ma ya yi, Allah Yasa ayi muna raye." Ya amsa da amin cikin jin dadin sha'ani na uwargidan tasa wanda ya sha bamban da Hajiya Binta, da ita ce sai sun kai ruwa rana, gwara-gwara Hajiya Luba, itama akan yi abin arziki da ita idan kishinta bai motsa ba.                    ***   ***   *** DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 83                        ABUJA    "Allah Mai Iko." Shine abinda Gen. Ahmad ya fad'a sa'ilin da ya ajiye waya da Alhaji Atiku inda suka tattauna a mutunce.    Hajiya Babba da ke kokarin zuba mishi abinci babi abinda ta ce, tamkar duk bata ji abinda suke tattaunawa akai ba. Shima Daddy ita ya yi shiru yana duba.   "Meyasa ki ka 6oyemin wannan batu? Na yi tsammanin don shi ki ka je Kanon?" Hajiya ta ajiye (serving spoon) tana mai duban mijinnata cike da kulawa.     "Me fa?" "Ai shi Alhaji Muhammad ya riga da ya yiwa diyartasa miji, d'an abokinsa, Alhaji Kabir Jimeta."   Hajiya Babba ta yi wani murmushi. 'Madina kenan.' Ta fada a zuci, a fili kuwa ta nuna rashin damuwarta. "Allah Yasa alheri, ni sai yanzu da ka fada na sani daman iyakar tattaunawarmu da ni da Madinar ce, watakil sai bayan ta sanarmishi itama ta ji hakan don da ace ta san da haka ba zata 6oyemin ba."    Ta fad'i hakan ne don batason ta nunawa mijinta basu dadi da yar uwarta. Ganin fuskarsa ta cika da damuwa ta ce. "Ba wani abu fa, kasan babu mai aurar matar wani, watakil ba rabo tsakaninsu, idan akwai sai kaga lamarin ya juye."    Ya jinjina kai cike da gamsuwa da maganganunta. "Hakane kuma, to Allah Ya za6amusu abinda yafi alheri. Ita wannan ya ake ciki?"    "Ga dukkan alamu lokacin zuwan matar da ta kawota ya k'arato inaga tunda ga watan saura kwana biyu ya mutu, ( family meeting) din namu shima ina tunanin jibi ne zaayi." Cewar Hajiya kafin kuma ta cigaba da zubamishi abinci.                   Kwance a saman lallausan katifa a saman gado, Ummi ce tana faman duba wasu litattafan addini da Hajiya ta had'ata da su, ta ji dadin hakan kwarai, Hajiya ta k'ara da batun sanyata Islamiyyar da Ikram ke zuwa don zuwa lokacin hatta form an kar6omata, hakanan an bada a dinka mata (Uniform). Ga shi kuma gogan ya nuna yana mata sha'awar karatun boko, acewarsa neman ilimi ko gemunka na ja a k'as ba ka yi latti ba. Wannan shine kyakkyawan albishir gareta.      Wayarta ta yi k'ara alokacin da ta tsunduma cikin karatu, ta sanya hannu ta janyota. Tsai ta yi da ido tana duban lambar wacce ta ta ganta banbarakwai, har ta katse bata iya ta d'aga ba, sai a karo na biyu ne ta d'aga da sallama.    Daga can Adnan ya amsa yana dariya. "Kaga sabon shiga kin tsoraci kada a gudu da ke ne?"   Ta so gane muryar saidai bata da tabbacin shi dinne ko aa, ta dan saki fuska. "Ba haka bane." "To ina My Best?" Kalmarnan babu a bakin wanda ta santa sai Adnan, ta washe hakora gami da mikewa zaune. "Lah, Yaya Adnan?" Sai kuma ta yi dariya shima darawar ya yi.  "Ni ne nan kanin Angonki." "Kai Yaya Adnan." "Ai gaskiya ne, yanzu ko kin yi tsada karki so ki ji kashedun da aka yimin kafin a bani lambarki." Ta yi murmushi. "Ina wuni." Ta fada cikin basar da wancan maganar.    "Ba zan amsa ba tunda kin yi waya amma ba ki nemi a ba ki lambata ba."   "Ka yi hakuri to, ya su Mami?"   "Suna k'asarku, ni ina nan Dubai." Ta dan bude ido kadan. "Au na manta, Yaya Faruk ya gayamin kwanaki wai za ka karatu ko?"    "Inye! Abu ya yi nisa haka ashe?" Ya karashe yana dariya, ita kuwa murmushi kawai ta yi, ita sai lokacin ta tuna da ashe fa da yaya Ihsan ta ke magana, sam halinsu ya bambanta.   Adnan ya sake da ita suka shiga kwasar hira sosai yana bata labarin Dubai tamkar wata abokiyarsa,  duk da tana jin wani dan kara(din-din) ta cikin wayar bata fahimci ko na menene ba. Bayan sun kammala wayar ne ta ajiye, nan ta fahimci Faruk ke kira. Kafin ta kai ga yunkurin kiransa sai ga shi ya kara kira.   Bai ko amsa sallamarta ba. "Da wa ki ke waya?" "Yaya Adnan ne." Ya sauke ajiyar zuciyar da har ta ji. "Ok, amman kun jima kuna waya, me ya ke fadamiki haka?"    Ta yi murmushi kadan. "Hira ce ta makarantarsu ya ke min." "Ok, kina da labarin tafiyarmu Kano gobe?" Gabanta ya fadi. "Har da ni?" "Au, Hajiya bata sanarmiki kenan? Watakil sai zuwa anjima, family meeting zaayi, kusan wannan karon ni da ke ne masu muhimmanci a gurin, akwai wani ma albishir din amman ba yanzu zan yi miki shi ba."   Ita kam duk ta tsorata, ta lura shi gogan ma bai gane hakan ba.   Suka dan ta6a hira kafin su yi sallama.    Ai kuwa a daren Hajiya ke sanarmata cewa ta shirya kaya ko kala uku ne.        Washegari gaba daya da misalin biyu na rana suka kama hanya har yayyun Faruk da matansu, a motar can lungu ta zauna don gujewa wani abin da zai je ya zo, tana ji Intisar, Baraka da Ikram suka juye harshe zuwa fulatanci suna hirarsu, duk ta bi ta tsargu duk da basu ko kallon inda ta ke.                      ***   ***   ***                          KANO      Acan kuwa gidan Mami, da misalin karfe uku Yaha ta diro. Mami ta dubeta bayan ta zauna. "Aa Yaha sai yau ki ke tafe?" "Wallahi kuwa Hajiya, Minna na je shiyasa na kwan biyu ba ki ganni ba, su ma can gidan su Ummin suna min waya wai sun ji shiru."    Murmushi Mami ta yi na takaici.  "Ai kuwa Ummi bata gidannan yanzu." Yaha ta karkato gami da yin sakato da baki. Mami ta koramata bayani.   "Jar Uba!" Shine kawai abinda Yaha ta ambata....!   Don gyara ko shawara a tuntu6en... [email protected] or through facebook acc. Rufaida Omar   "Jar Uba!" Shine kawai abinda Yaha ta ambata....!   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 84     Yaha ta yi furucin cike da tsananin mamaki, ba don Mami da kanta ke sanarmata ba da kai tsaye zata kira hakan da shaci fad'i. Mami ta cigaba da magana. "Ba abin mamaki bane, shi DAN ADAM idan ya samu guri fin haka zai iya aikatawa, banda haka ki duba irin yanda na dauki yarinyarnan, tunda nake yin yan aiki ban ta6a yin wacce na kyautatawa ba kamar ita, har wai yar aiki ta samu matsayin da zan zauna na dan yi hira da ita. Anan menene bai faru ba.." Sai kuma ta yi shiru tana mai jin zafi a ranta.   Yaha ta yi shiru cikin nazari, to ita fa Saude kudi ta ke nema, ita dai acewarta ko karuwanci yarinyar zata fad'a to ta fad'a matukar zata samu abin duniya sanadin haka, ga kuma yanzu a karshe da suka yi waya ta sanarmata kada ta kuskura yarinyar ta k'ara koda kallon hanyar garinsu ne ballantana wai ta kawota ganin gida. Yanzu ya za ta yi?    "Ki ka yi shiru? Idan za ki iya komawa gobe ki dawo to, idan kuwa za ki yi zaman jiran zuwansu daga Abuja yau din to babu laifi."(Ta sani ne ta hanyar Ihsan wacce su ka yi maganar da Ikram.)     Sai lokacin Yaha ta dawo cikin hayyacinta, lallai kam tana bukatar nazarin. "Bakomai ranki ya dad'e, zan iya tafiya na dawo goben." Mami bata ko kara kallonta ba, daga haka itama ta mike ta bar gidan ba tare da ta samu ko na mota daga Hajiyar ba kamar yanda ta saba yi mata duk zuwanta.    Bata zarce ko'ina ba sai gidan 'yar yayarta Abida wanda anan ne ta saba sauka duk sadda ta shigo garin Kano. Abida ta yi mata kyakkyawar tarba yanda ta saba. Yaha ta sauke mayafinta. "Su Abu sun wuce makaranta ne?"   "Eh sun dan jima." Sai bayan ta ci abinci ta yi sakato tana tunani, Abida da ke gefe tana kokaarin zuba kananzir cikin risho tana mata hira amman shiru hakan yasa ta dubanta. "To Inna meke faruwa ne haka?" Yaha ta hau lashe kwana kafin ta tureshi gefe ta dubeta.  "Bani shawara Abida, kaina ya cushe na rasa ma menene abin yi."   Abida ta maida risho ta gyara sannan ta karkato tana dubanta. "Ina jinki Inna." Ta karanto mata tun kai Ummi aikatau da kuma ire-iren abinda Saude ke sanarmata akan yanda ta ke son ganin Ummi har ma da yanda suka yi da Mami. Ta karashe da fadin. "Yanzu wallahi gaba daya jikina jinsa nake a sanyaye, ni tunda nake kai yan aiki ban ta6a haduwa da mai hakuri irin Ummin nan ba wallahi, zan iya ce miki tun tashinta a hannun Saude bata huta ba, ga kuma tsangwama da tsanar da ubanta ke nunamata tamkar ba jininsa ba."   Abida ita kam mamakin Innarta ne ya cikata, ashe daman zata iya mugun abu har irin haka? A haka idan ka ganta tamkar ba zata aikata ba.    "Allah Mai Iko!" Ta fada a fili kafin ta cigaba da magana. "Inna a farko ina mai baki shawara kan ki ji tsoran Allah, ki kuma sani cewar dukkan wani abu da muke aikatawa za'a tashemu gobe kiyama a kuma tambayemu. Wannan sam ba daidai bane a hada baki dake wajen cutar da rayuwar baiwar Allah wacce bata ji ba, kuma bata gani ba, ki sanya Rahma (diyar Yahan) a matsayinta ki auna ki gani, za ki ji dadi ace yau babu ranki Kulu(kishiyarta tun mijinsu na raye) ta aikata hakan agareta? Kada hakkin Ummi ya kamaki anan gaba Inna, don Allah ki yi tunani wannan ba daidai bane ko kadan."   Daga haka Abida ta juya ta cigaba da aikinta zuciyarta cike da dumbin tausayin Ummi duk kuwa da cewa labarinta kadai ta ji. Yaha wacce ta yo shiru tana nazarin maganganun Abida ne, jikinta ya yi sanyi, babu abinda ke yawo a kwakwalwarta face irin zagi da hantara da ta dunga yiwa Ummi a hanya da kuma zuwansu Kano, harma da zaginta da suka yi zaman yi da su Saude duk akan abim duniya wanda ba wani mai yawan azo a gani bane.    Ta sauke ajiyar zuciya kawai.                     Mutanen Abuja sai Magriba suka shigo garin Kano, Ummi sai rarraba idani ta ke har suka shiga gidan Modibbo. Sai lokacin ta soma jin kamar ta saki fitsari a wando tsabar rud'ewa. Adduo'i kawai ta soma karantowa.      Bayan sun isa ne aka soma fitowa, kusan itace karshen fitowa daga motar, tana saukowa suka hada ido da Faruk wanda ke sanye da yadi fari k'al da aka yiwa aiki da bak'in zare, murmushi ya sakarmata ta kauda kanta ganin ba su kadai bane.  Bayan shigarsu ne aka hau gaggaisawa, Ummi ta tsorata da kallon banzan da ta samu daga Hajja wanda a baya ba haka ta ke amsa mata ba. Haka har dai aka basu wajen kwana, abinda ta tsorata ne ya faru don kuwa daki daya aka basu su uku, wato ita, Ikram da kuma Baraka, Intisar na tare da su Jidda.     Baiwar Allah duk da a matse ta ke da shiga bandaki saida ta tsaya suka gama uzurirrikansu sannan ta shiga, lokacin an yi sallar isha'i. Wanka ta yi ta chanja auduga sannan ta fito sanye da mayafi saman daura kirjinta, basu dakin duk sun fita, ta karasa ga yar jakar kayanta ta ciro doguwar riga ta jallabiya ta sanya sakamakon zafin da ake yi sosai. Ta tsaya shafa mai tana kallon fuskarta a madubi yanda duk ta chanja ta yi wani haske mai kyau hakanan fatarta ta murzu. K'arar da ta ji wayarta ta yi ne yasa ta mikewa ta dauka. Da sallama ta amsa wayar.   "Dear ya gajiyarki? Kin yi sallah?" Kunya ta kamata, wato bai lura koda aka tsaya sallah ba ita bata yi ba?  "Gajiya ta bi lafiya, ya naka gajiyar?" "Ta ya zan gaji alhalin ina ganinki?" Murmushi kawai ta yi tana duban madubi jin an murda kofar,  mikewa ta daga wajen gami da komawa gefen gado ta zauna. Ikram ta ta6e baki kafin ta dauki wayarta (don daman abinda ya shigo da ita kenan) ta fice.    "Ba za ki fito cin abinci bane?" Ta girgiza kai. Gaba daya bata saba da shiga cikinsu ba, ta saba rayywa da su matsayin yar aiki mai kai musu su ci sannan a kwashe, anya zata iya ci tare da su? "Kinyi shiru? Ki fito ga shi fa duk an hadu."   "Toh." Shine kawai abinda ta ce sannan suka yi sallama.    Faruk kuwa yana ajiye wayar suka hada ido da Haidar, dariya ya yi. "Wannan kashem muryar fa?" Cewar Haidar.  Murmushi kawai ya yi. "Ya wuce ace yana waya da Juliet dinsa." Cewar Fadila cikin gatse. Ya dubeta kamar ya tanka sai kuma ya share kawai.     Hajja ta so tofa nata saidai kuma tana gudun idanun Modibbo wanda ba karamin gargadi ta sha daga wajensa ba tun kafin zuwansu.      Har zaa soma cin abinci babu ita ba dalilinta, ya dan rausaya kai suka yi ido hudu da Hajiyarsa. Murmushi ta yi mishi, ta riga tasan damuwar dannata, ta kai dubanta ga Ikram.   "Ikram maza tashi ki je ki kiramin Ummi ta zo ta ci abinci."   Ba'a son ranta ba ta mike ta nufi dakin nasu. Ummi na zaune har lokacin ta zubawa wayarta idanu tana tunani ta ji an kara shigowa dakin ba sallama. Ikram ta watsamata harara. "Ki zo." Daga haka ta fice abinta, gaban Ummi na faduwa ta mike ta dauki mayafi ta yafa a saman jallabiyar dake jikinta sannan ta mara mata baya.     A falon dai da ta sani na Modibbo anan suke, ta dan dubi hanyar kofar, kamar ba'ayi sadda ta kasa shiga ba don kunya ta ce Amina ta taimaka ta soma shiga su kai musu abinci, wai yau itace zata shiga cikinsu su ci su sha tare? Idanunta ya ciko da kwalla, ta daure cikin rawar murya ta yi sallama, suka amsa mata, kamshin turaruka da na abinci ne ya soma dukan hancinta ga kuma sanyi na (Ac) mai ratsa jiki, tana tafe kanta a kasa tamkar zata fad'i haka ta ke ji x durkusawa ta yi a gefe yanda yan aiki suka saba.    Ya lumshe ido gami da yin k'asa da kansa, ji ya ke kamar ya tashi ya rungumeta cikin jikinsa, ya fahimtar da ita cewa yanzun matsayinta ya wuce zatonta, ya nunamata itama mai daraja ce da k'ima, saidai doka ta addininsa bata ba shi wannan damar ba. Ya tsinkayi muryar Hajiyarsa na fadin. "Dawo nan mana Ummi, ke kadai ake jira aci abinci."   Ta mike jiki a sanyaye Modibbo na kallonta cikin yaba nutsuwa da hankalinta, ya ji yarinyar ta burgeshi, haka ta karasa ta zauna a gefen Jidda can bakin kujera. Hajiya ta umarci Jidda da ta zubamata, shinkafa ce da miya sai farfesun kifi ta nuna shinkafar ma ta isa.     Nan ta yi bismillah ta dan soma ci, idanu ta dan dago kadan, karaf a cikin na gogannata wanda ke shirin kai loma, ya yi wanka yana sanye da wando (3 quarter) sai riga marar hannu don shi din bai fiye son yanayin zafi ba.      Ta yi saurin kauda kanta, duk bata saki jiki ta ci sosai ba har aka soma kammalawa, kusan ta riga dukkansu ja baya. Hajiya ta dubeta "Kada dai kin k'oshi? Haba, me ki ka ci?" "Na koshi ne." Ta fada a hankali, Modibbo ne ya yi magana cikin harshen fulatanci sannan Hajiya ta dubeta. "Tashi dauki filet din ki wuce daki ki ci."   Ta nuna ta koshi, karshe dai ganin Hajiya ta dage yasa dole ta mike ta dauka tana jin Modibbo na fadin. "Lallai Amaryar tawa mai kunya ce kamar bafulatanar itama."   Kalilan ne suka dara banda masu jin haushin lamarin.    Kai tsaye k'asa ta sauka zuwa kicin, Larai mai aikin na ganinta ta saki baki. "Ummi, ashe idanuna ba gizo sukamin ba dazu ke dince ki ka koma haka?" Ummi ta dan yi murmushi cikin jin nauyi tana mai fatan kada a yi mata wani mugun zargin ganin irin kallon da wata dake tare da Laran ke mata, da alama sabuwar yar aiki ce. "Ni ce Larai, ina wuni." "Allah kenan, Mai maida talaka sarki, Mai maida sarki kuma talaka. Ashe kuma autan hajiya za ki aura?" Shine abinda kawai Larai ta ce batare da ta amsa gaisuwarta ba. Ta ajiye farantin tana murmushin dai saidai ta kasa amsawa. Zata fice ta ji Larai na fadawa dayar. "Allah dai Ya kwato musu dansu, wasu mutanen ba tsoron Allah, daga sun samu wuri sai kuma a asirce dan masu gida." Ta yi maganar a hankali wanda karaf a kunnen Ummi, ta fice da sauri..... DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   85   Kasa komawa saman ta yi ta fita nan wajen barandar tsakar gidan ta tsaya cike da tunani. Tasan ba Larai kadai ce mai irin wannan tunanin a kanta ba, ba'a rasa mutane da dama da zasu kawo hakan a ransu game da ita ba. Ta yi shiru tana nazarin wajen alokacin da ta tunano ranar daurin auren Haidar inda anan ne ta soma ganin murmushin Faruk agareta, sai ta ji rabin damuwarta ta kau, ta shagala a tunani ne ta soma jin hirarrakin mazan suna fitowa. Da sauri ta yi baya, Babban Yaya ne ya soma ankara da ita. "A'a, Ummi me ki ke yi anan? Ko duk zafin ne?"   Ta girgiza kai saidai ta kasa magana.    "Ka sani ko plan din da suka shirya kenan da mutumin nata? Su hadu a nan?"   Abin ya basu dariya, ita kuwa kunya duk ta bi ta isheta ga babu bakin magana. Jin sun cigaba da tafiya ne yasa ta saurin juyawa zata koma ciki. "Tsaya mana." Ta tsinci muryar Faruk, dole ta dago kanta ta ganshi tsaye bai tafi ba, hakan yasa ta kalli yayyunnasa, ko waige basu yi suna nufar kofar gidan suna hirarrakinsu.  Ya tako har gefenta ya tsaya.     "Ummi." Jin yanda ya kira sunanta a sanyaye ne yasa ta amsawa a hankali tamkar bata so.    "Ki yi hakuri." Ta dubeshi, fuskarsa cike da damuwa.   "Hakurin me kuma?" Ya dan jinjina kai. "Nasan zamanki cikin yarannan ba zai miki dadi ba, saidai idan ki ka k'ara hakuri kan wanda na sanki da shi, na dan lokaci ne zai wuce kinji?"   Ta yi dan murmushi, tana son Faruk kusan fiye da yanda ya ke sonta. (A ganinta) don acewarta ya cancanci komai daga gareta, matashi irinsa da ya ketare ta amman bai ko damu da wadannan bambance-bambancen da jama'a ke gani ba ya aminta da ita har ya furta yana sonta da aure, ita kuwa me za ta ce ga Allah banda godiya?    "Na ta6a fad'amiki kina da kyau?" Ya yi furucin a hankali cikin murya mai kama da ta rad'a bayan ya soke hannuwa cikin aljihun wando gami da kwantar da kansa jikin bango. Ta dan dago idanunta a hankali tana dubansa, saida ta ji cikinta ya kad'a hakanan gabanta ya cigaba da dukan tara-tara, ba ta k'ara marmarin kallon idanunsa ba, kusan tunda ta ke da Faruk bata ta6a ganin irin wannan kallon daga gareshi ba. Shi dinma ya fahimci razanar da ta yi, ya runtse ido kafin ya budesu.    'Ya Salam' Ya yi furucin a ransa kafin ya tsaya sosai. "Sai munyi waya, ki koma ciki." Bai jira cewarta ba ya juya da sauri, maimakon ya bi bayan yan uwansa sai ya wuce dakin da aka saukesu.      Ita dinma da sauri ta yi ciki, yau wani Faruk din ta gani ba wanda ta sani ba, wannan Faruk din ya tsorata ta.       Koda ta koma sama, a falon daga Hajja sai Hajiya Babba zaune suna hira sai kuwa Modibbo dake gefe yana jan carbi. Ta wuce a sannu ta yi dakin da aka basu don kwana. Gaba daya masu kwana tare da ita basu nan sai Baba karami(mai sunan daddy), Amal da Yasmeen. (Yaran Babban Yaya) da kuma Ma'aruf da Ahmad (Yaran Dakta) suna wasansu saman gado.  A dakin kusa masaukin su Jidda ne ta jiyo shewa da hirarrakinsu.    Zata zauna saman gadon ne ta ji Ma'aruf na fadin. "Ke! Karki zauna a gadon nan, wari ki ke yi."   Ta yi shiru tana kallonsa, ba laifi bane don ya yi mata, ya danganta da abinda aka fadamasa a kanta. "Lala lala, sai na fadawa Grandma, ka manta abinda ta ce mana? Ita fa Uncle Faruk zai aura." Cewar Baba Karami kenan.    Ta dubi fuskar Ma'aruf ganin yanda ya ke yamutsa fuska. "Ai Momi ta ce mana 'yar aiki ce, ko boko ba ta yi ba ko?"   Ya fada yana duban kaninsa Ahmad wanda ke yin doki da filo, Ahmad ya gyada kai. "Eh, Momi ta ce kuma kada mu dunga kulata."    Amal a guje ta yi hanyar waje tana fadin. "Sai naje na gayawa Grandma." Da sauri Ummi ta rikota tana murmushin yak'e.   "Dawo kinji, rabu da su." Amal cikin kalar tausayi ta ce. "Gashinan sun sanyaki kuka." Ummi a wayance ta share fuskarta. "Ba kuka nake ba abu ne ya shiga idona." "Lah Uncle fa ya ce mu daina k'arya kuma kin yi."   Cewar Amal, yarinyar ta burgeta, ta yi murmishi har cikin ranta. "To na daina, jeki ku yi wasanku bazan zauna saman gadon ba."   Gefe ta zauna tana danna waya saidai zuciyarta cike fal da damuwa, Amal ta matso. "Lah Anti kina da game?" Ta yi murmushi kadan. "Akwai, za kiyi ne?" "Eh." Nan ta kunna mata, suma yaran duk suka matso zasu yi, Ma"aruf yana gefe yana kallo, yana son ya ce zaiyi saidai ba dama, sai kuma ya mike ya nufi waje yana fadin. "Ai nima Momina tana da game bari na amso wayarta." Murmushi kawai ta bishi da shi har ya fice.      Haka sukayita jagwalgwala wayar tana kallonsu har chaji ya kusan k'arewa sannan ta kar6a ta jona ta. Tana jin bacci saidai batason hawa gadon ace ta yi laifi, haka ta kwanta nan saman darduma. Har ta soma bacci ta ji wayarta ta dauki k'ara, mikewa ta yi tana salati, har lokacin basu shigo ba, yaran ma sun gaji da wasa sun kwanta. Ganin Faruk yasa ta yin murmushi kafin ta dauka duk a gajiye don muryarta ma ta nuna.    "Bacci ki ke yi wai?" "Eh." "Shikenan bari na kyaleki saida safe." Ya fada cikin dauriya don shi kam tunaninta ya so ta6a nasa baccin, suka yi sallama daidai lokacin su Ikram suka shigo.    "Wai yarannan bacci suka yi anan? Lallai ma, ke kuma kina kallonsu idan suka yi mana fitsari fa?" Fadin Ikram kenan. Baraka ta dubi Ummi don ita sam bata ko lura da ita ba ma. "Tashesu su wuce dakinsu."   Bata ji ko darr a ranta ba, don ita bata jin kanta a wata har yanzu ballantana ta musa musu, haka ta tashesu ta mik'asu wajen iyayensu inda akayi musu shimfida a k'asa, saidai ta sanyasu fitsari kafin ta kwantar da su, tuni Intisar ta yi baccin don ga gajiya ga kuma ciki.    "Saida safenku." Ta fada bata ko saka ran zasu amsa ba sai kuma ta ji sun amsa din sannan ta rufemusu kofa ta koma dakinnasu.     Nan ta kwanta k'asa gami da yin filo da hannunta, babu wanda ya ce mata uffan, tana ji suna yara fulatancinsu suna dariya, sai ta juyamusu baya don duk ta tsargu.   Basu jima da hakan ba sai ga Hajiya Babba ta shigo. Suka amsa sallamarta, ta shigo ciki sosai. Daman tasan hakan zai iya faruwa, ta daure fuska. "Ke kuma mene na kwanciya a k'asa? Tashi ki hau gado. Ku kuma kuna ganinta ku ka kyale?" "Ita ta za6i nan fa." Cewar Baraka.     Harara kawai ta samu daga Hajiya Babba wanda yasa ta jan baki ta yi shirun dole. Ba ita ta bar dakin ba saida ta tabbatar Ummi ta hau gadon, kafin ta juya harshe ta gargadesu sosai sannan ta fice.    Ummi dai tun tana jin hirarsu har mijin Baraka, Sa'ad ya kirata suka hau hira, sama-sama ta ke jinsu har bacci ya yi awon gaba da ita.      Washegari.... DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   86 Washegari da misalin karfe sha biyu na rana, Hajiya Mama da iyalanta suka dira a gidan Modibbo. Ummi tun gaishesu da ta yi ta sauko. Ido hudu sukayi da Antinta Amina dake tsaye a kofar kicin suna gaisawa da Larai. Da sauri Amina ta juya ta fita, itama Ummi cikin saurin ta karasa sauka daga bene ta fita, tsaye ta ganta a baranda ta sunkuyar da kai. Cikin sanyin jiki ta karasa gareta ta dafa kafadarta fuskarta dauke da matsanancin farinciki. "Anti." Koda Amina ta dubeta ta razana da ganin hawayen dake saman fuskarta.    Hankalinta ya tashi. "Anti ki yi hakuri don Allah, ban.."   "Meyasa haka Ummi? Meyasa bakya tausayawa kanki da rayuwarki? Anya kuwa kinsan hatsarin da ki ka jefa kanki? Kina sane cewar a sanadinki zumuncin dake tsakanin Mami, Hajiya Babba da Hajiya Mama ya raunana?"   Gabanta ya fadi, Amina ta koramata bayanin duk abinda ke faruwa ta dora da fadin. "Ina jiyemiki tsoron abinda zai je ya zo. Karki dauki maganganu a baibai, ni mai kaunarki ce, ba kuma zan so wani abu ya sameki ba sanadin auren Yaya Faruk, saidai kishi tsakaninki da Ihsan?" Ta yi shiru tana mai girgiza kai kafin ta share fuskarta. Bata kara komai akai ba ta yi gaba, Ummi hankalinta ya yi mugun tashi, duk wannan abun ya faru ne sanadinta? Ya akayi bata da masaniya? To wa zai fadamata, bata ji daga bakin kowa ba, ta tuno dai sadda Hajiya Babba ke kokarin yi mata magnar Faruk ya shigo wanda hakan yasa Hajiya katse maganar da ta yi niyya alokacin.     Durkushewa ta yi awajen sai kuma ta ji kuka mai karfi ya tahomata, da sauri ta zagaya dan lungun gidan ta durkushe ta soma shek'asa, duk a sanadinta hakan ya faru, anya bata zama mai son kai ba? Tana ina akayi hakan? Meyasa babu wanda ya sanarmata? Sai gaba daya ta ji kunyar kanta ya mamayeta, ya za ta yi da wannan abu? Da wane ido zata kalli Mami a yanzu?  Don ita sam Ihsan bata gabanta kamar Mami, Mami ta fi ji. Acan kasan zuciyarta kuwa tana ji kamar ba zata iya rabuwa da Faruk ba.     Ta jima anan har saida ta ji Amina na cigiyarta sannan ta taso ta zo tana mai amsawa. Ganin yanayinta ne yasa Amina jin wani mugun tausayinta, ta janyo hannunta suka zauna a baranda.   "Anti wallahi ba ni da wannan labarin, bansan da shi ba da babu abinda zai kaini ga amincewa hakan."   Amina ta yi murmushi cike da tausayawa Ummi, tana kaunar yarinyar ko don hakurinta. Ita kanta ta yi mamakin yanda aka ce Ummi ta yarda da batun auren Faruk batare da wani tunani ba.    "Karki damu kanki Ummi, Ubangiji Ya fi kowa sanin dalilin hakan, idan kuma Ya kaddaro aurenki da Yaya Faruk to babu makawa sai an yishi. Kawai dai ni na yi mamaki ne daman yanda akayi ki ka amince har haka."   Ummi ta dubeta sai kuma ta shiga bata labarin dukkan abubuwan da suka faru bayan tafiyarta, Amina tana murmushi ta tsaida idanunta kawai tana duban Ummin. Har saida Ummin ta shiga damuwa, ga wani gumi da ta ke yi sakamakon iska mai zafin dake kadawa haka kuma garin hadari ne kwance.    "Ki godewa Allah da Ya hadaki da mutum mai matukar kaunarki irin Yaya Faruk, lallai kin yi sa'a."   Kunya ta kama Ummi, ta sunkuyar da kanta don har lokacin hankalinta bai kwanta ba.    Kiran da Larai ta yi musu ne ya katse hirarsu, abinci ne. Ta dubi Ummi sadda ta mik'awa Amina filet din abinci. "Sama za ki hau ai, kya ci a anan?" Cewar Larai.   Ta ji babu dadi. "Kai Larai, to ni wacece da ba zan ci da yar uwata ba?    Larai zata yi magana Amina ta rigata. "Ai nasan halin kanwata ko wane matsayi ta taka ba zata wulakanta DAN ADAM ba."   Larai ta jinjina kai tana mai kya6e baki. 'Inama ni na samu damarki.' Ta yi furucin a ranta, a fili kuwa hannu ta mik'awa Amina. "To kawo na k'ara muku." Bayan ta k'ara Ummi ta kar6a suka koma falon dake k'asa suna ci suna 'yar hira anan ne Ummi ke jin batun saka ranar Amina wanda aka daga sai bayan azumi don lokacin watanni biyu ya rage azumin.                Misalin karfe uku kusan kowa ya iso har Mami. Ummi kasa zuwa ta yi gaida Mami, wajen Amina ta wuce har lokacin da aka bude taro da addua suka soma abinsu.   Ummi da Amina na nan zaune suka ji sallama, suka dubi kofar suna mai amsawa. Wani saurayi ne dan dogo bak'i saidai kana kallon sumarsa Kaga bafulatanin mutum(lol) yana sanye da shadda fara k'al sai hula da ya dora a kansa. Shima idanunsa a kansu musamman ma Ummi wacce ya k'urawa ido har ta tsargu da hakan ta sunkuyar da kanta. Suka shiga gaisheshi, ya amsa, kafin su yi wani yunkurin Abba da amininsa Alhaji Kabir Jimeta sun shigo, kai a kasa Ummi ta gaishesu don kuwa tana tsoron kallon da zata samu daga Abban wanda bata mance irin rabuwar da ta yi da gidansa ba duk kuwa da ance komai ya wuce. Kafin su kai ga cewa komai sai ga Babban Yaya da Dakta sun sauko daga sama, su suka jagorancesu zuwa saman. Abubakar Kabir Jimeta har ya soma taka benen bai bar waigen Ummi ba shi fa kallon sani ya ke yiwa fuskarta saidai ya kasa tuna ko a ina yasan fuskar! Zai so Baffansa ya gani saidai kuma sam bata k'ara dago kanta ba.     Acan sama kuwa bayan an zauna aka gaggaisa, Modibbo cikin harshen fulatanci ya ke tambayar Alhaji Kabir Jimeta mutan gida. Bayan gama gaisuwa Abba ya gabatar da Abubakar matsayin wanda ke son Ihsan da aure.    Banda Hajiya Babba da ta riga tasan zancen da kuma Faruk da shima ya riga da ya sani a bakin Hajiyarsa, babu wanda bai girgiza da jin wannan batu ba sai ko Hajiya Mama dake murmushi kawai.    ((Ku yi hakuri da wannan, kaina ne ciwo...))              ***   ***   ***   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   88    Misalin karfe goma na dare, Ummi kwance saman gado tana tunane-tunane, ta ji shigowar su Ikram, wannan dalilin ne yasa ta rufe idanu tamkar mai bacci. Tana ji suna faman hirarsu kafin Ikram ta ce. "Wai wannan isashshiyar har ta yi bacci? Lallai yau ko ta jira a yi mata iso kan gadon? Um, kan mage ya waye."   Baraka ta dara. "Ai ko bata hau ba dole ma ta komo, ni banason abinda zai ta had'amu da Hajiyarmu muna 6ata ranta kan abinda mukasan mun fishi."     Ikram ta ta6e baki gami da mikewa. Cikin muryar rad'a ta ce. "Bari yau dai na bincika wayar nan nata." Ta mike tsaye tana mai zagayawa 6angaren da Ummi ta ke, Ummi na jinta ta dauki wayar a hankali, can kuma ta ja tsaki. "Wallahi nasan aikin Yaya Faruk ne don wannan illiterate din ba zata iya ba."   "Me kenan?" "Wai pattern lock yasa mata." Baraka ta yi dariya, za ta ajiye wayar ne hankalinta yakai ga zoben dake yatsar Ummi, ta zaro ido tana karemishi kallo kafin ta dubi yar uwarta da muryar rada ta ce. "Kinsan zoben gwal ne a hannunta." Baraka ta mike tana mai soma takowa wajen hadi da fadin. "Wasa ki ke." Sai kuma ta kama yatsan a hankali ta kurawa zoben ido itama, kafin kuma ta saki yatsan. "Lallai abin babba ne, a ina ta samu?" Yar harararta Ikram ta yi suna kokarin barin wajen. "Wa ki ka san zai bata bayan Yaya Faruk? Ai inaga nan gaba ma (salary) dinsa gaba daya akanta zai k'are. Har tausayi ya ke ban, Allah dai Ya karya wannan sihirin tun ba'a kai ga aurennan ba, idan kuwa aka yishi ba karamin mijin tace zaayi ba."    Haka sukayita hira akanta tana jinsu hakanan tana ji kamar ta yi kuka har suka gaji suka gangaro kan Ihsan. Inda Baraka ke fadin tasan mijinnata, don kuwa saurayin wata kawarta ce a baya, ta tabbatar shi din yana da yanmata kala-kala acewarta saidai Ihsan ta yi hakuri ta kauda idanu akan wannan tunda har ta nuna ta ji ta gani.        Tun tana jinsu har bacci ya yi awon gaba da ita.    Cikin dare aka yi ruwa sosai wanda bata da masaniya sai washegari bayan tashinta daga bacci. Ruwa duk ya shigo ya jik'a labulen dakin, ta dubi inda su Baraka ke kwance, har lokacin (karfe shida da mintuna) basu tashi ba, murmushi ta dan yi, tasan jiya sun jima basu kwanta ba.     Kai tsaye wanka ta fad'a sanin cewa da wuri zasu wuce don Hajiya Babba ta ce kafin takwas zasu tafi. Tana fitowa ta iske Baraka zaune bakin gado, itama bandakin ta shiga tana mitar Ummi bata ko tashesu sun yi sallah ba, ita dai hakuri kawai ta bata daman ita fashi ta ke.     Garin ya yi sanyi-sanyi hakanan har lokacin akwai hadari bai gama yayewa ba duk kuwa da cewar duhu bai gama fita ba. Ta shirya cikin wani bulun Swiss Atamfa mai haske, tana da adon manyan fulawoyi wanda acikinsu aka yi kwalliya da kalar bulu mai turuwa. (Lol..ku nemi Aysha ku siya). Dinkin riga da siket ne, rigar simple akayi mata mai hannu (3 quarter) ta zauna das a jikinta, hoda da kwalli kawai ta shafa, lokacin har Baraka ta fito ta yi sallah ta shiga wanka, ita kuwa Ikram na saman darduma tana addua saidai idanunta na satar kallon Ummi don duk hassadar mai hassada bazai k'i aminta da kyawun da ta yi ba. Ko ita kanta shigarta ta burgeta saidai ba fa zata nuna ba.     Ummi ta tattara kayanta a jaka sannan ta soma gyara saman gadon bayan ta dauke musu wayoyinsu, tana kokarin share dakin ne Intisar ta shigo da sallama. Bayan sun amsa ta zaro ido tana duban Ikram don ita tuni ta yi wanka ta saka doguwar riga 'yar kanti mai mayafi.    "Ke Ikram, ko wanka ba ki yi ba?" Ikram ta mike tana cire kayan jikinta. "Wallahi yanzu zan shiga yau sanyin da gari ya yi yasa mun makara sallar Asuba ma."   "Kedai fadi gaskiya tun daga can dakin muke jin hirarku fa har muka yi bacci." Intisar ta amsa lokacin da ta shigo dakin sosai.     Ummi ta gaisheta, ta amsa fuska a sake tana kallonta, kwarai shigar Ummi ta burgeta don ta yi kyau ainun, ga dirin jiki da Allah Ya bata.      Fitowar Baraka ce ta katse tunaninta, Ummi ta fice don dauko tsintsiya da tsumman tsane ruwan da ya shigo ta windo.       Babu kowa a falon sama, kai tsaye ta sauka k'asa, nan dinma ko fitila ba'a kunna ba, ta karasa hanyar kicin inda anan ne ta gano haske, Larai ce ke faman soye-soye tare da Hafsatu sabuwar mai aikin Hajja, ta gaishesu Larai ta kama baki. "Oh ni, Ummi kinga yanda ki ka haska kuwa?" Ta basar da zancen tana  dan murmushi lokacin da ta ke kokarin daukar tsintsiya da abin kwasar shara. "Larai tsumman guganku yana ina?" "Me zaki yi 'yar nan? Ke ai kin wuce aiki yanzu." Ummi ta dan daure fuska. "Ni wallahi bana son hakan da ki ke yimin." "Jimin 'ya, Hafsatu ko karya nayi ne? Ina Ummi ina aiki?" Hafsatu dake mikawa Ummi tsumma ta yi dariya kawai, ai kuwa Ummin na kar6a ta fice da sauri don dagaske Larai ta bata haushi.  Tana jin dariyarsu. Ta soma taka matattakala ta ga an kunna fitilun falon, hakan yasa ta kai dubanta ga mai shi. Ido hudu sukayi da shi yana sanye da riga da wando yan kanti sai jacket da ya dora bak'a a saman rigar wacce kana hangota fara k'al, hakanan farin wando ne dogo na jeans a jikinsa.      Idanunsu suka sark'e cikin juna, wani kyau ta ga ya yi mata na daban duk da ta lura da jan da saman hancinsa ya yi can kuma ya saki atishawa, ya rufe bakin ta hanyar amfani da dan hankicif din dake a hannunsa. Kafin ya kai ga cewa wani abu, Haidar ya shigo shima sanye cikin kananun kayan, da sauri ta haye sama bata bari ko gaisuwa ta shiga tsakaninsu ba. Ya numfasa yana duban Haidar wanda ke kokarin zama.    "Wai murar ce haka? Ai saida nayi-nayi akan ka kashe fanka ka nuna kai zafi ka ke ji."    Shima zaman ya yi yana mai dan ta6a karan hancinsa da ya ke ji yana mishi zafi.    "Daban da murata na zo saidai ba ta yi karfi haka ba sai yanzun." "Ya dace ka nemi magani ka sha." Haidar ya amsa yana kallon hanyar sama. "Wai kada dai basu tashi ba? Muna da ayyukan yi fa."   Ya tuna hasken idaniyartasa wacce shigarta ta yau ta daukemasa hankali, murmushi ya danyi. "Sun tashi mana."    Acan kuwa Ummi ta tarar har Baraka ta shirya sun fice daga dakin ita da Intisar, ta goge inda ruwa ya 6ata kafin ta hau shara. Tana cikin yi itama Ikram ta fito, bayan ta kammala ta fito. Anan falon ta iske Hajiya da su Hajja sai kuwa Larai da Hafsatu dake jera kayan karin kumallo.   Ta ajiye ta karasa ta gaishesu kanta a kasa, suka amsa, Hajja ko ciki-ciki ta amsa tana karewa yanda yarinyar ta chanja ta wani murje.    Har Ummi ta bar wajen da kallo ta ke binta. Kafin ta kya6e baki.   "Wannan yarinya nan gaba sai ta ce bata sanmu ba.". Ta yi maganar ne da harshen fillanci ganin su Larai dake wajen ga kuma su Amal dake dudubniyarsu. Hajiya Babba 'yar dariya kawai ta yi na wayancewa don ita har ga Allah tana jin kaunar Ummi a ranta.      Ummi kasa sauka kasan ta yi jin muryoyin yan samarin Hajiyar tare da su Intisar ana hira, jin suna kokarin hayowa ne yasa ta juyawa da sauri har suna karo da Hafsatu. Ta numfasa. "Don Allah Hafsatu taimaka ki karasamin da wannan."   Ba musu ta kar6a, ita kuwa da sauri ta koma ciki, zata shiga daki ne Hajiya Babba ta dubeta.   "Ummi kirawo yan uwannaki mu karya." Dole ta nufi dakin su Jidda, ta tarar duk sun shirya, Jidda na sanyawa Ahmad wandon jeans. Ta gaishesu sannan ta isar da sak'on Hajiya Babba.    Wannan karon ma a darare ta ci abincin, idanun Faruk kacokam yana kanta ko kunyar su Hajiya ba ya ji. Yana kammalawa Modibbo ya ba shi maganin mura ya sha.    Karfe takwas saura suka kama haramar tafiya. Modibbo ya yi ta jan Ummi da wasa yana kiranta da amaryarsa. Ita kam kanta na kasa kawai tana dan murmushi har suka gama shiga mota. A mota wannan karon ita da su Amal suka zauna don har rige-rigen zama kusa da ita suke, shi kam Ma'aruf har lokacin bai sake da ita ba ya rike abinda Mominsa ta ce masa akanta.      Itama ta maida hankalinta ga yaran, duk a takure ta ke don duk dagowar da zata yi sukan hada ido da Faruk wanda ya saita madubi yanda zai dunga ganinta har Haidar na mishi dariya.      Ita kuwa damuwa ta yi jin yanda ya ke atishawa, tabbas mura ta kamashi. Garin ya danyi duhu, sunyi nisa aka soma yayyafi kafin kuma a soma ruwan ba mai karfi sosai ba, duk aka daga gilasai, abokan hirar nata duk sunyi bacci, wayarta ta yi karar shigowar sako, ta duba duk a nata zaton kamfani ne saidai Faruk dinne.    "Ko na dawo nan?" Ta dan dago suka hada ido cikin madubi, ya narkar da ido, da hanzari ta kauda kanta. Shi Faruk bai kunyar ma a dagosu?      Bata kara kallon madubin ba, shi dinma murmushi ya yi kafin ya soma lumshe ido maganin mura na son sakashi bacci, can kuwa ya shimfida hankicif saman fuskarsa bacci ya yi awon gaba da shi. Itama tun tana kalle-kalle har nata baccin ya iso.    Haka dai har suka isa garin Abuja inda suka tarar ana ruwa kamar da bakin kwarya. Koda suka isa gidan Dakta ne ya yi amfani da lemar bayan motar ta kai yaran ciki, su Ikram kuwa iyayen son ruwa haka aka shiga a guje.     Ummi duk hankalinta na ga Faruk wanda ta ga yana shirin shiga ruwan shima, tana son ta haneshi saidai da kunya ainun, to ta ce masa me? Wata lemar Ikram ta daukomusu a ciki Binta na bin bayanta da guda uku, Hajiya ta shige tare da su Jidda, itama Binta ta mikamata tana dariyar murnar ganinta.     Ta kar6a gami da fitowa.   "Ni fa?" Ya fada yana dubanta da dan daga murya don karar ruwa.    Binta ta dubeshi, Haidar ne kadai ke wajen yana bada umarni ga maaikatan masu shirin kwasar kaya cewa abar kayan har ruwa ya tsagaita. Sai kawai ta mikawa Binta lemar da sauri gudu-gudu ta yi ciki rike da takalman su Amal wanda suka cire a mota.    Faruk ya na murmushi ya kar6i lemar daga hannun Binta, itama ciki ta yi cike da shaawar yanda suke tafiyar da soyayyarsu.      Kai tsaye itama falon ta shiga. "Aa, garin yaya kika shige? Kema biyewa Ikram ki ka yi kenan, maza tafi ki chanja kayannan." Fadin Hajiya Babba kenan, ta ajiye takalman kafin ta nufi sama.      Babu k'ura ko kadan a gidan don su Binta sun gyara tsaf, Binta ce ta gyara kuryar Hajiya. Ita dai ta yi mamakin ganin dakinta tas, ta jinjina kai, tasan aikin su Binta ne, wai kenan har ita keda wannan matsayin.                                                      DAN ADAM @RUFAIDA OMAR       87 "Allah Mai Iko, abu ya yi kyau." Cewar Modibbo a sanyaye yana dan murmushi, tabbas yaso kwarai Faruk da Ihsan su yi aure, saidai kuma ba yanda zaiyi tunda Muhammad Modibbo ya daureshi da jijiyon jikinsa, ba zai kira Alhaji Kabir da bare ba don kuwa zumunta mai karfi ta auratayya ta shiga tsakani. (Za ku ji idan an shiga tuna baya)     Saidai a ganinsa wata kusan ai tafi wata, haka dai ya sanya alheri a lamarin. Alhaji Kabir ya dubi matasan yaran Hajiya Babba yana mai fad'ad'a fara'arsa. "Yanzu Hajiya Fatima wadannan duk iyalinki ne? Masha Allah duk sun girma."   Hajiya Babba ta yi murmushi, zai iya mantasu kuwa a fuska don rabonta da shi tun tana goyon Faruk da ta je Adamawa, ko su Ikram bai sani ba. Hajiya Mama ce ta soma nunamishi yarannata.   "Wannan shi ne Usman, ga Ridwan nan babban likita, sai Haidar da karaminsu a maza Faruk."      Yana mamaki yana binsu da kallo da murmushi, idan kaga Alhaji Kabir ba za ka ce shi ya haifo Abubakar ba don kuwa shi farin bafulatani ne tas, dogo ne kuma siriri.     "Ai na dan gane Usman da Ridwan tun shigowata, wadannan ne dai bansani ba." Ya nuna Haidar da Faruk. Akayi dariya, gaba dayansu yaran saida Modibbo ya yi mishi bayani akansu.    "Kenan dai Faruk kai ba ka yi aure ba? Me ka ke jira?"    "Ai shima yana niyyar yin, akwai wacce zai aura. Ina ta ke ne ma?" Cewar Modibbo yana waige-waige. Ihsan ta ja tsaki a ranta. Haka kawai za'a dunga tsoma wata can cikin abin zuri'arsu, daidai da Faruk din haushinsa ta ke ji yanda duk ya gama lalacewa akan wacce bata ketare ta a komai ba.   Wata hirar da aka sanyo ce yasa Ikram wacce aka tura kiran Ummi ta yi mursusi ta gyara zama bata tafi ba, anan kuma Modibbo ya sanarmusu da batun zuwa Adamawa, aka bari sai idan anyi hutun makaranta.      Daga nan aka yi zaman cin abinci, Abubakar hankalinsa ya kasu biyu, ga tunanin yarinyar da ya gani mai kama da Inno, sannan ga kallon Ihsan wacce ya ke jin kamar ya sanyata a aljihu ya fice da ita ko babu komai irin kalarsa ce.      Mami na tare da yan uwanta wadanda Modibbo ya hadasu ya musu nasiha sosai, duk da har lokacin takan ji zafinsu saidai ganin irin mijin da diyarta ta samu na nunawa duniya kadai yasa ta sassauto aganinta ko babu komai ta burge. Wayarta ce ta yi kara wanda ya yi sanadin katsewar lomar da ta ke shirin kaiwa bakinta. Ta duba ta ga Yaha ce, ta dauka, bayan sun gaisa ne Yaha ke sanarmata cewar ta iso gidanta bata sameta ba. Mami ta yi murmushi. "Kinsan gidanmu na Sharada ko?" "Kayya Hajiya, na kwan biyu banje ba koda na shiga layin ba lallai na gane gidan ba."   "Karki damu ki taho sai ki kirani idan kin shigo."   Daga haka ta ajiye wayar, Hajiya Babba wacce sam bata da fushi sosai ta dubeta fuska a sake. "Wacece zata zo?" Mami ta amsa. "Yaha ce wacce ta kawo Ummi, ta bukaci ganinta ne da kar6ar kudin wata na sanarmata bata wajena yanzu."   "Don bata wajenki idan kin fidda kudinki kin bayar sai cibi ya zama k'ari?"   Cewar Hajiya Mama a kufule don daman har lokacin bata gama hucewa ba. Mami ko kallonta bata yi ba, Hajiya Babba ce ta danyi dariya. "Ke kuma menene abin daukar zafi to? Kefa haka ki ke ba dai zuciya ba Sadiya." Ta maida abin wasa hakan yasa Hajiya Mama ta dan sake itama. "Ai Madinar ce sai a hankali." Mami itama dan murmushin ta yi kada ta bada su agaban surukai (Jidda da Fadila).         Ummi tana tare da Amina suna hira anan kicin tare da su Larai har sadda Larai suka tafi kai abinci. Alokacin Amina ta dubeta. "Wallahi kar ki so kiga yanda fatarki ta kara kyau saidai kin rame don har gwara kafin zuwanki Abuja."   Ummi ta ta6a wuyanta tana murmushi. "To Anti ba dole ba, nifa koyaushe cikin tunani na ke na wannan abu wallahi."   "Ya za ki yi to?" Alokacin da Larai suka dawo ne ta dubesu. "Wai kuwa kunsan cewa wannan saurayin da ya zo shi zai auri Ihsan?" Amina da Ummi suka dubi juna ido waje kafin su dubeta. "Anya kuwa?" Cewar Amina. "Wallahi kuwa, sunansa Abubakar nima zan fito na ji su Rahila na zancen wai sun dace kuwa."     Ummi ta yi shiru kawai batare da ta tantance yanayin da ta ke ciki ba, Amina zuciyarta fal murna, hankalinta ya kwanta Ummi ba zata hada kishi da Ihsan ba kenan.   "Lallai, Allah Ya tabbatar da alheri." "Ameen dai, ai daga gani dan hutu ne, wannan baisan talauci ba."   Suka danyi dariya. "Kai Larai." Fad'in Amina kenan.     Nan suka shantake don gaba daya Ummi nauyin fita ta ke ji, ko kusa batason wani ya ganta, tana ganin Faruk na faman dokomata kira saidai ta kasa dagawa har ya gaji ya daina. Har lokacin bata bar tuna kallon da wanda aka kira da Abubakar ke jifanta da shi ba, ta rasa ko na menene.      Sai bayan sallar Magriba su Abba suka tafi banda Abubakar da ya tsaya hira da Ihsan ya ce zai taho, gaba daya suka yo musu rakiya.   Shigowar Mami kicin dinne yasa Ummi kallonta cikin rudewa. Ta durkusa ta gaisheta murya na rawa. Daga kallo daya bata k'ara duban inda ta ke ba ta soma magana. "Amina ki je ki taho da Yaha tana nan bakin titi wajen kantin Nura."   "Toh." Amina ta amsa, daga haka Mamin ta fice. Ita kuwa Ummi ta shiga tashin hankali matsananci, Yaha kuma? Shikenan yau zata koma garinsu, tasan abinda Mami ke shirin aikatawa kenan.    "Muje ki rakani." Ta bi bayanta jiki a matukar sanyaye, a falon kasa, su Rahila ne da su Jidda gaba daya sun hadu hankalinsu ya tafi a kallon (Swaragini) a tashar Bollywood, sam hankalinsu ya tafi a kallo.     Suka fito, a farfajiyar gidan su Faruk ne tsaye, lokacin walkiya ake yi da cida na alamun saukar ruwa duk sadda Allah Yaso.     Idanunsa ya kai kanta, ya yi tsai yana dubanta da tunanin inda za ta je a daren nan, kasa jurewa ya yi ya kira sunanta. Ta juyo tana mai amsawa.  Ya karaso. "Ina za ku je?" Amina ta sanarmishi aiken da Mami ta yi musu. Ya gyada kai kafin ya dubi Ummi. "Ina wayarki?" Ta dago mishi ita ta mik'a batare da ta yarda da kallonsa ba. Ya kar6a duk da ya so kallon kwayar idanunta ko zata fahimci 6ata mishi ran da ta yi na k'in daukar wayarsa saidai hakan ya gagara.  Suka wuce wayar na hannunsa.    Abubakar dake can gefe saman kujera tare da Ihsan suna hira ya yi tsai yana k'ara duban Ummi.   'Kamar ta yi yawa.' Ya fad'a a ransa. Ya kai duba ga Ihsan wacce gaba daya ta gama k'uluwa da wannan kallon da Abubakar ke yiwa Ummi, kada ace shi dinma ya fad'a tarkonta ne?     "Honey, wacece wannan please?" Ranta ya 6aci.   "Bansanta ba nima." Ganin yanda ta yi maganar a fusace ya sanyaya mishi jiki, ya sassauta murya yana mai dan dafa cinyarta. "Sorry i don't mean to hurt you." Ta dan janye cinyarta gami da jan guntun tsaki. "Please Abbakar babu kyau fa abinda ka ke yi, kada ka k'ara ta6ani."    Ya numfasa. "Ki yi hakuri zan kiyaye, ke dince kin hadu ne Ihsan samun irinki sai an tona." Ta dan ji sanyin abinda ya ce har cikin ranta, wannan yasa ta dan sassauto, shima ya ajiye maganar Ummi gefe ya cigaba da shigar da kansa wajen mutuniyartasa.                    ***   ***   ***    Ummi sun danyi tafiya kafin su ga Yaha. Koda suka isa gareta, baki bude kawai ta ke kallon Ummi, wani arnen material ne a jikinta dinkin riga da siket, ta kara wani kyau sosai, duk da ramar da ta yi, dirin jikinta yana yanda ya ke bai girgiza ba.    "Ummi ke ce?" Ummi da har lokacin bata bar shakka-shakkar Yahar ba ta yi dan murmushin yak'e. Gaisuwar da Amina ta yi mata ne ya katse tunaninta tana mai amsawa sannan suka soma tafiya. Yaha ta dubi Ummi. "Na ji abin arzikin da ya sameki ai jiya a bakin Hajiya." Furucin da ta yi yasa suja dubi juna ita da Amina fargabarsu ta dan kau jin ta kira hakan da abin arziki.   "Um." Shine kawai abinda ya fito daga bakin Ummi.   "Allah Mai Iko kenan, in sha Allahu babu abinda zai hana wannan aure naki sai ikonSa, yarinya kin yi goshi. Na gano kuskurena Ummi, ki gafarceni kinji 'yarnan, bana so hakkinki ya kamani alhalin ba kiyi min laifin komai ba haka siddan na biyewa makiran nan(Saude da Habiba) na tsaneki." Ta k'arashe kamar zata yi kuka, wanda hakan ya basu tabbacin da zuciya daya ta ke maganar.    Farin ciki yasa Ummi soma zubar da ruwan hawaye ba tare da ta ankara ba, tana kuka tana dariya don murna, ta daga kai ta dubi sararin samaniya yanda ake faman walkiya. Yau ta kira wata babbar rana da ba zata ta6a mancewa ba. (Wani abun na gaba Ummi), Yau ita Yaha ke yiwa magana cike da nuna kulawa da nadama? Amina ta dafa kafadarta. "To sarkin kuka, akan hanya ki ke fa, kada a dauka sato ki mukayi." Suka yi dariya har Yaha, ta yi kasa da kanta tana share fuskarta da mayafin jikinta kalar yadin. Banda hamdala babu abinda ta ke yi har suka karasa Yaha na basu labarin auren cin amanar da Dije diyar Habiba ta yi da mijin yar uwarta. Tabbas Ummi tasan wacece Dija don kuwa kusan bata da iyaka da gidansu, duk sadda ta so shiga ta ke yi, itama ba dai mugunta ba kodayake ba a k'asa ta dauka ba.  "Ina Babana?" Yanda ta yi tambayar cikin sanyin jiki ne yasa suka ji tausayinta musamman Yaha wacce tasan ko sau daya bai ta6a tambayarta ba, saidai batason ta karyamata zuciya ta yi dan yak'e. "Babanki yana nan cikin koshin lafiya."   Har suka k'arasa hirar Ringim sukeyi, Yaha na bata labarin irin abubuwan da suka faru.     Koda suka isa gidan Amina ce ta karasa da ita wajen Mami don kuwa ita Faruk ne ya tsaidata, duk yanda ta so k'i hakan bai samu ba don Yaha sun ce ta dakata. Sai anan ma Yaha ta ganshi, shakka babu Ummi ta yi katari da babban goro.       Can gefe suka tsaya k'asan bishiyar dogon yaro. Haidar da Dakta sun fita kai Abubakar masaukinsu. Ya dubeta fuska ba walwala. "Shi ne ki ka k'i daukar wayata ko?" Tana wasa da gyalenta ta ce. "Ka yi hakuri ina cikin mutane ne." Ya dan ta6e baki. "Don kina cikin mutane kuma shikenan sai ki kasa amsa wayata Ummi? Kinsan yanda na ji kuwa?"   Shiru ya biyo baya kafin ta furta kalmar hakuri. "Da abinda ki ke kwarata kenan, kinsan duk girman laifin mutum matukar zai ban hakuri to nakan hakura, amma idan ya k'ureni za'a ji kanmu fa."   Murmushi kawai ta yi. Iskar da aka soma mai zafi yasa suka dan rufe idanu.   "Kwanakin nan ana zafi Alhamdulillah, gwara ruwan ya sauka ko an dan ji sanyi." Fadin Faruk kenan. Ita dai 'Um' kawai tace.   Saida iskar ya lafa ya dubeta. "Ko ki tambayi albishir da nace zan miki ko?" "Ina shirin tambaya ne." "Aa Ummina banda karya fa, shikenan ma na fasa sai aurenmu ya tashi. Ga wannan." Ya mik'omata wani k'aramin gida na zobe, ta dubeshi ya dan daga mata gira. "Kar6i mana, ko na sakamaki?" Ta girgiza kai sannan ta kar6a. "Oya bude ki saka na gani." Ta bude a hankali, wani kyakkyawan zobe ta gani mai kyau ruwan gwal, watakil ma na gwal dinne bata sani ba. Ta sanya a yatsanta na kusa da karamin, ya zauna das sai daukar ido ya ke. Ya zubawa yatsun idanu tamkar ya sumbata ya ke ji, sauke ajiyar zuciya ya yi yana mai dubanta. "Ya miki kyau sosai." Ta dan russuna kadan. "Nagode Yaya Faruk, Allah Ya k'ara arziki." Har cikin ransa ya ji dadin adduarta. Ya amsa da murmushi. Ganin an soma yayyafi ne yasa dole suka yi sallama ta nufi ciki rike da gidan zoben.                    ***   ***   ***   Acan kuwa Yaha na tare da su Hajiya Babba suna magana akan Ummi, Hajja da Mami suna zaune babu damar aibata abin don kuwa Modibbo na zaune a gefe don kusan anan falon ya ke wuni. Hajiya Mama ce ta sanarwa Yaha dukkan abinda ake ciki, Hajja sai kallon banza take watsawa Yaha ganin yanda ta wani washe baki kamar gonar auduga.   "Daman dole ta yi murna tunda an gama tsafe miki d'a kin kasa ganewa." Ta yi furucin a hankali cikin harshen fulatanci, babu wanda ya tanka saidai Yaha ta tsargu don ta lura kamar tsohuwar bata farinciki da hakan.    Nan dai aka gama tattaunawa Yaha ta tabbatarmusu ba'a yiwa Ummi miji ba, karshe aka tsaida magana inda bayan shawara da Modibbo da kuma Gen. Ahmad (ta waya) cewar Asabar mai zuwa za'a je can Ringim bisa jagorancin Yaha a tsaida magana da mahaifin Ummin sannan a saka rana. Da haka aka rufe tattaunawar, Yaha ta so tafiya anin an soma ruwa suka tsaidata sai ta ci abinci, idan yaso sai su fita tare da su Hajiya Mama.      A dakin su Larai Ummi ta zauna tare da Yaha. Yaha na cin abinci ta dubeta. "Amma sai naga kamar mutanen nan ba suyi marhaba dake ba Ummi, kinga yanda tsohuwar nan ke dubana kuwa?"   Ta dan yi yak'e ba tace komai ba. Yaha ta kai loma. "Um, Allah dai Ya fiddamu daga zargin mutane, kada a dauka wani mugun abin muka k'ullo." Fadin hakan yasa idanun Ummi cika da kwalla, ai hakan ma ake zargi. Ta yi nasarar sharesu bata ko bari Yaha ta lura ba.    Saida wajen takwas suka yi shirin tafiya, suma su Ummin gobe da safe zasu wuce Abuja. Ta kar6i lambar Antinta Amina da Yaha don a dazun Faruk ya bata wayarta. Da hawaye ta rabu da Antinnata. "Ki gaishemin da su Anti Hauwa da Inna."  Amina ta amsa itama idanunta cike da ruwan kwalla. "Za su ji Ummi, nasan har ku wuce Ringim ba lallai mu hadu ba, saidai ko waya, ki dage sosai da addua karki gaji, in sha Allahu Allah zai taimakemu."   Da wannan suka rabu zuciyar kowannensu babu dadi. Itama Mami alokacin suka fice.                     ***   ***   ***        DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 89   Yana zaune yana shan(coffee) alokaci guda kuma ya lula duniyar tunani har Alhaji Kabir na mishi magana sam bai ji ba. Ya dan ta6o shi.   "Abubakar." Ya dan dubeshi sannan ya sauke ajiyar zuciya. "Naam Baffa." "Tunanin me ka ke yi ne har ina magana ba ka ji ba? Me kuma ya faru? Ko akwai wata matsala?"   Ya girgiza kai. "Aa, saidai Baffa jiya naga wata yarinya mai kama da Inno sak, na yi mamaki."     Alhaji Kabir ya dan yi shiru kafin kuma cikin rashin fahimta ya ce.   "Ikon Allah, watakil kawai kamanni ne. Kasan ana samun haka sosai." Abubakar ya girgiza kai. "Wannan kamar har ta so ta 6aci, ba don sanin da na yi cewar Inno bata raye ba da sai na ce itace, anya wannan itama ba daga Gombe ta fito ba?"   Shi dai Alhaji Kabir abin mamaki kawai ya ke ba shi, wacece wannan da har ya ke had'ata da danginsu na Gombe? Har suka bar Kano Abubakar bai kara sanyata a idanu ba wanda ba haka yaso ba. Yaso ko hotonta ne ya daukarwa mahaifinnasa ya ganta.                     ***   ***   *** A satin Ummi ta soma zuwa islamiyya yare da Ikram duk kuwa da cewar Ikram din bata so hakan ba, saidai dadinta daya, ita tana aji na karshe na yan hadda ita kuwa Ummi aji biyu aka sanyata. Ta hadu da wata daliba mai kokari, Husna, wacce a kwana biyu kacal jininsu ya hadu da ita. Ita din diyar wani mai kudi ce don kuwa makarantar ta masu da shi ce, wayayyiya ce amma ba irin wayewar nan ta banza ba. Har musayar lambar waya sukayi.      Ranar juma'a Yaha ta dira a Abuja, Hajiya Babba har tasha ta sanya direba ya daukota.     Wannan ne zuwanta na farko gidan Hajiya Babba, lallai Mami ba cikin gida take ba, ga inda gida ya ke. Bayan gama cin abincinta ta shiga dakin Ummi inda anan ne zata kwana. Yaha baki ta saki tana mai karewa ko'ina kallo har sadda Ummi ta shigo dakin ta ajiye mata robar ruwa a gefen gado.     Ta bi Ummin da kallo. "Ummi, wannan dukiya har haka?" Ummi murmushi kawai ta yi ba tare da ta san abin cewa ba.     "Kinsan fa ban sanar da Saude batun zuwanki ba don kuwa sam bata kaunar ki je."   Tasan hakan daman ba wani sabon abu bane, matar da ta yi mata mummunan rik'o ina za ta amince da k'ara sanyata a ido?    "Ina Minna ta kirani ta jaddada min cewar kada na yarda ki je Ringim, acewarta ko nawa nake so zata dunga bani cikin albashinki, ita dai fatanta kada ta budi ido ta ganki a Ringim, ta ce na yi mata wannan taimakon har zuwa sadda wani buri nata a kanki zai cika."   Gaban Ummi ya fad'i, wannan tsana har haka? Yanzu ko me zuwan nata zai haifar? Ta sauke ajiyar zuciya cike da damuwa.     "Idan ma wani mugun abun ne ki kwantar da hankalinki, Allah zai kareki."                 ***   ***   ***                   RINGIM ((Pls kuui manage))   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 91 Abubuwa da yawa suka shiga dawo mishi tamkar a mafarki, shi dai yasan sadda aka haifi Ummi da irin kauna da so da ya nunamata har izuwa sadda ya soma tsanarta, karshe kuma yana ji yana gani aka turata aiki ba tare da ya ji ko digon damuwa ba. Daga nan kuwa komai da ya shafi Ummi ya mance, Mariya kadai ya ke yiwa kallon diyarsa. Me zai cewa Allah ranar da Ya tsaidashi da tambayar amanar da Ya ba shi? Sai kawai ya soma kuka gami da jawo Ummi jikinsa. "Ummi ki gafartamin, na yi babban kuskure a rayuwa, na tabbata idan ba ki yafemin ba Allah bazai yafemin ba, na yi watsi da lamuran rayuwarki." Yana kaiwa nan Yaha kamar jira ta ke ta cafe, tiryan-tiryan ta bada labarin yanda sukayi da Saude akan Ummi na cewar bata kaunar ko kusa ta k'ara takowa Ringim har su hadu da shi. Ya dago ya dubi Saude da babu inda ba ya kadawa a jikinta tsabar tsoro, cikin alamu na rashin gaskiya ta hau fadan borin kunya. "Ke Yaha ashe bakar munafuka ce mai shirin kashe auren sunna? Yaushe mukayi haka dake? Inace Malam da kansa ya ce a kaita aikatau?" Malam Balarabe da har lokacin ita ya ke kallo ya mike yana tunano yanda ta dunga iko da shi har ta rabashi da diyarsa, baisan lokacin da ya cira hannu ya kwasheta da mari ba wanda ya sanyata soma fitsari a wando, kafin ta yi wani yunkurin ya k'ara marinta a daya gefen kuncin. Babu wanda cikinsu ya yi yunkurin hanashi sai Babban Yaya da Ridwan, Faruk kuwa ko gezau baiyiba sai ma wani murmushi da ya ke yi, acikin ransa kuwa godiya kawai ya ke yi ga Ubangiji Ma ji rokon bawa. Ummi kuwa kuka ta ke yi don ganin lamuran ta ke tamkar a mafarki, tana kukan tana hadawa da dariya. Bata gama mamaki ba sai sadda ta ji marin da Malam ya kwashe Saude da shi. "Allah Ya isa tsakanina da ke makira! Azzaluma!! Mai fuska biyu!!! Kin cuceni Saude na yi da na sanin aurenki, bana fatan k'ara koda kwakkwaran awa ne tare da ke! Ki ficemin na sakeki! Na sakeki!! Yanda ki ka cuceni ki ka cutarmin da d'iya kema in sha Allah zaayi miki fin haka, duniya ce cikinta muke!!" Ya dan numfasa kafin ya dora, daidai lokacin wayar Hajiya Babba ta yi kara ganin lambar mijinta ne yasa ta fita wajen cike da tsantsar mamaki da wani mugun tausayin Ummi da mahaifinta. Malam Balarabe ya nuna Saude da yatsa. "Hasiya ta daukeki abokiyar zama ba kishiya ba, Hasiya ta bauta miki tamkar kanwarki, abinda Hasiya ta yi miki ko kanwarki da ku ka fito ciki daya ba za ta yi miki ba, yan uwan Hasiya suna miki kallon mutuniyar arziki, ko alheri ne zasu yi, basa ta6a bambantaki da jininsu, ashe ke din da zuciya biyu ki ke tare da su? Da har ki ka kasa rike Ummi riko na gaskiya da amana? Kin cutar da ni! Ni bani da tabbacin ko kina wani abin, amma ina rantsuwa da Allah bansan yanda akayi na kuntata rayuwar diyata ba." Sai kuma ya sunkuya cikin zubar hawaye wata razananniyar k'ara Saude ta sanya, ta nufi hanyar waje tana fadin. "Daman Bokanya ta fad'a! Wayyo na shiga uku na lalace!! Allah Ya tsinemaka Balarabe, Allah Ya sa ka gamu da nau'ikan azabobi kala-kala, wayyo ni Saude!!" Haka ta ke tafe tana surutai kamar wata sabuwar kamu, burinta ta isa ga Bokanya. Mariya zata bi bayan uwarta, Malam ya janyoya a fusace, ta isa ga Yaha tana ajiyar zuciya don ta tsorata yau da babannata. Hajiya Babba da mijinta suka bi Saude da kallo, ta dubi mijinnata. "Wannan itace kishiyar uwar Ummin. Bari na shiga na gani." Gen. Ahmad ya jinjina kai yana mai bin Saude da kallo cike da jimami. "Baba ni ban ta6a rik'onka a zuciyata ba, duk wani abu da ka yimin na yafemaka, nima ina rokon gafararka har..." "Kul Hasiya, kar ki ce komai, ni nan ba ki ta6a yimin laifin komai ba, ni ne mai laifin daman. Yanzu kuma tunda gaskiya ta fito, in sha Allahu bazan k'ara aikata makamancin hakan ba." Dariya kawai ta ke yi tana hawaye, suka hada ido da Faruk ya mikomata hankicif ta kar6a. "Alhamdulillah, yau ranar sa'a ce. Allah Ya k'ara kauda shaidan." Cewar Yaha kenan, sai lokacin hankalin Malam ya dawo jikinsa, ya dubi su Hajiya Babba da su Faruk. "Sannunku, ina wuni." Nan matasan wadanda mamaki da farinciki ya cika, suka gaisheshi sannan ya juya suka gaisa da Hajiya. "Saidai ban gane fuskokin ba?" Ya karashe da duban Ummi fuskarsa cike da fara'a. Itama yau bakinnata ya k'i rufuwa, kafin ta ce komai Yaha ta koro mishi bayanin ko su su waye da kuma abinda ke tafe da su, ta k'ara da fad'in. "Maigidan ma yana k'ofa tsaye." Jin haka yasa Malam Balarabe mikewa da sauri yana fadin. "Ya Salam." Daga haka ya fita ya shigo da Daddy soron gidan, bayan sun gaisa. Tabarma Ummi suka shimfida musu, matasan suka fita waje sai Yaha da su Hajiya a tsakar gidan suna magana kan lamarin Ummi, Mariya kuwa ta yi gum sai kallonsu da ido. Bayan Daddy ya zauna, suka k'ara gaisawa. Malam Balarabe ya hau mishi godiya sosai da addu'o'i game da taimakonsu ga diyarsa wacce aka so wulakanta rayuwarta. "Ba komai, wannan yiwa kaine ai." Cewar Daddy. A karshe ya koro mishi bayanin dake tafe da su. Malam ya yi shiru yana nazari, can kuma ya soma magana. "Hakika na yi farinciki matukar gaske da wannan magana, sannan na yabawa karamci irinnaku da har ku ka taso daga Abuja zuwa nan don Ummi, tabbas kun kasance cikin mutane masu daraja DAN ADAM, ko don wannan bazan hana Umar auren Hasiya ba. Saidai ina neman wata alfarma daga wajenka Yalla6ai." Daddy ya gyara zama kadan. "Ina sauraronka Baba." "Na yi kuskuren da zan so gyarashi kafin komai ya faru. Ummi da ka ke gani, babu wanda ta sani cikin dangin uwa da na ubanta. Hakazalika ni kaina na manta rabona da zuwa wajen yan uwana. Ina neman alfarmar soma zagayawa da ita muje ta ga dangi idan yaso daga baya sai ayi zancen aurensu. Ina fatan hakan ba zai zamto matsala..." Cikin 'yar dariya Daddy ya ce. "Haba Baba, wannan ba matsala bace. Tabbas gaskiya ka fad'i, saidai me zai hana a tsaida lokaci idan yaso kafin zuwan lokacin an zaga dangin?" Malam Balarabe ya yi shiru, idan ya aminta da hakan tabbas ya kwasowa kanshi aiki babba, yanzu me ya mallaka na aurar da Ummi cikin wadannan mutanen 'yan babban gidan? Ya dan girgiza kai yana duban Daddy. "Ka yi hakuri Yalla6ai, ni mutum ne da yasan girman alk'awari! In sha Allahu Hasiya bata da miji sai Umar matukar tana sonsa. Ku kwantar da hankalinku, a satinnan in sha Allahu zan wuce da Hasiya." Cikin gamsuwa Daddy ya jinjina kai. "Bakomai Baba, hakan ma ya yi, Allah Ya k'ara dankon zumunci." Cike da jindadi Malam Balarabe ya amsa kafin kuma Daddy ya mik'e. "Bari mu wuce dare yana yi mana." Sukayi musayar lambar waya sannan Malam Balarabe ya shiga ciki ya yi kiran Hajiya akan zasu wuce. Ummi ta yi musu rakiya don kuwa ita kanta yanzu zumudin kwana ta ke yi wajen mahaifinta ko ta dandani gatan da ta ke burinsa a rayuwa wanda ta rasa zamanin kuruciya. Faruk ji ya ke tamkar kada ya tafi, shikenan kuma za suyi nesa da juna? Ya kafamata ido, itama a sace take kallonsa. Gaba daya sai ya bata tausayi ganin yanda jikinsa ya yi sanyi, shi fa gani ya ke tamkar za'a rabasu ne. Hajiya ta yiwa Yaha kyauta mai tsoka hakanan Ummi itama, suka rabu zuciyoyinsu cike da kewar juna musamman ga masoyan da basu ji tattaunarwar iyayennasu maza ba. Bayan tafiyarsu suka koma ciki, yaran makwafta sai bin Ummi suke da kallo tamkar tauraruwa. Matan makwafta kuwa wadanda suke jin komai har da dan lekensu don kawai su ga bak'in birni da kuma Ummi. Ai kuwa yara aka yita cika gidan ganin Ummi, da yawansu ma basu santa ba, wadanda suka santa duk sunyi aure a yanzun. Ummi sai hawaye ta ke yi, ta dubi kanwarta Mariya wacce har lokacin ta ke dan kuka-kuka hankalinta na ga mahaifiyarta. Ta jawota jikinta ta rungume. "Mariya ko?" Mariya ta gyada kai. Murmushi Ummi ta yi cikin hawaye ta shafi kanta. "Ni yayarki ce, sunana Ummi." Jin haka Mariya ta yi kuri da ido tana dubanta, Malam Balarabe dake alwalar sallar Magriba yana duban Ummi diyarsa tamkar ya maidata ciki tsabar so da kauna ta uba da da. Komai na Ummi da murmushinta, sanyin maganarta duk irin na Hasiya mahaifiyarta ne, take ya tsinci zuciyarsa ta cika da kewar Hasiya, matar da aka yi musu auren zumunci kenan don kuwa iyayensu aminan juna ne. "Tashi ki dora alwala kinji Hasiya. Bari naje masallaci." Ya fada yana dubanta bayan ya idar da alwala, ta amsa da to tana mai jin ranta tas, bayan fitarsa ta cika ruwa a butan ta soma alwala tana duban Mariya wacce ta makure a lungu, daga sun hada ido sai Mariyan ta dauke kai. Murmushi kawai ta yi don ta tausayamata, rashin uwa ai ba dadi. Yanzun ko ina uwar ta tafi? *** *** *** Saude da Habiba gaban Bokanya.... DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   90                     RINGIM   "Wayyo Allah!!" Ta yi furucin da karfi tana mai mikewa zaune a firgice. Malam Balarabe ya tashi a tsorace yana duban Saude. Sai uban gumi ta ke had'awa duk kuwa da cewar garin ya danyi sanyi.   "Lafiya Saude?" Ya tambaya cike da fargaba. Saude dake dafe da kirjinta tana numfarfashi, ta dubeshi, sai lokacin ta dawo hayyacinta. Ta yi tsai da ido tana dubansa domin kuwa tsoro ya ke bata, gani ta ke yi kamar mafarkinta gaskiya ne, wai Malam Balarabe ne da daukarta ya jefa a rijiya bayan ya bata kyakkyawan mari har biyu a gefensa kuwa Hasiya kishiyarta ce tsaye tana faman kyakyatar dariya.    "Addua ya kamata ki dunga yi idan kinyi mafarki ba wai ihu ba. Duk kin tsorata ni." Daga haka ya ja guntun tsaki ya juyamata baya, ta bishi da kallo cikin zubda ruwan hawaye sannan itama ta kwanta rigingine tana goge fuska.  'Meke shirin faruwa? Kada fa asirinmu ya tonu.'   Ta ke maganar a zuciyarta, ta kudurta komawa wajen Bokanya gobe don ta k'ara bincika mata lamarin.  Dakyar ta samu ta koma bacci a wannan daren.                      ***  ***  ***                       ABUJA Mutan Abuja da karfe biyu suka kama hanyar Ringim, wannan zuwa na musamman ne, Hajiya da Gen. Ahmad ne sai ko Babban Yaya da Ridwan sai kuma uban gayyar Faruk da Ummi da Yaha wacce suna shigowa Ringim ta soma rarraba ido na son nuna inda za su sha kwana. Haidar kadai ne bai samu zuwa ba. Ummi gabanta sai bugu ya ke da sauri-sauri, ga mararta da ta k'ulle, tana cike da tsoron irin cin kashin da za'a yiwa bayin Allahn da suka san daraja ta dan Adam. Wane irin tarba zata samu daga mahaifinnata? Sam, bata da masaniya. Hajiya Babba ta lura da yanayin da ta shiga, ta ji ta bata tausayi don kuwa ta ji daga bakin Yaha irin wahalar da ta sha a hannun ubannata da matarsa, ta dan dafa hannunta, wannan yasa Ummin dubanta. Murmushi na karfafa gwuiwa ta sakarmata. "Ki kwantar da hankalinki Ummi, ki yi ta addu'a, babu abinda yafi karfin Ubangijinmu."    Ta jinjina kai tana dan murmushi. Daga haka ta cigaba da addu'o'inta har Yaha ta nuna layin da zasu shiga.   Saude ce tsaye rik'e da k'ugu tana faman jan tsaki, a zaune saman kujerar falon, Habiba ce tana faman kai lomar dan wake. Mariya na waje suna wasa da yara.    "Ki yiwa Allah ki taso mu wuce, wai menene haka?"   Habiba ta dauki dunkulen dan wake guda ta jefa a bakinta tana mai dubanta cikin yanayi na santi.   "Ai kwarankwatsa sai na gama, wa ya ce ki yi dan wake alhalin kinsan bana ganinsa na kyale balle kuma da yanzun ma babu abinda na saka a cikina, na fadamiki fa daga kasuwa na fito."    Ta k'ara sud'e man wanda ya hade da yaji sannan ta cigaba da magana. "Na fadamiki ki saka ranki a inuwa, ko makamancin tunaninki bazai afku ba, idan yar banza ta takura mana sai ma mu saka Yaha ta maido diyarta ta mu kasheta mu kashe banza."    Saude wacce ta gaji da tsayuwa ta zauna sai lokacin ta dan numfasa. "Anya hakan ma bai fi ba?"   Kafin Habiba ta samu abin cewa, sallamar Malam Balarabe ta karad'e kunnuwansu. Suka dubi juna da mamaki kafin kuma Saude ta yi wuf ta fito.    Ya ajiye ledar hannunsa a gefe. "Malam lafiya yau ka dawo da wuri?" Ya dauki buta jikinsa duk a sanyaye ya nufi hanyar bandaki yana fadin. "Ina zuwa." Ganin yanda ya ke magana a sanyaye ya kad'a yan hanjin cikinta duk kuwa da cewa tasan halittarsa can daman ba mai zafi bane, idan har kaga bacin ransa to ba karamin kai shi bango ka yi ba. Habiba ta fito rike da kwanon dan wake a hannunta, cikin muryar rad'a ta ce.  "To bari na koma na cigaba da bawa cikina hakkinsa kafin nan kun kammala." Ta karashe da dariyar shakiyanci Saude na harararta. "Malama yanzu zan shigo." Ita dai Habiba ta sa kai ta fice.    Bayan fitowar Malam Balarabe ya ja kujera yar tsugunno ya zauna gami da zabga uban tagumi. Cikin fargaba ta ce. "Wai menene? Ko babu kasuwar balangun ne yau naga ko rana bata ida faduwa ba ka taho."   Ya numfasa. "Haruna(yaronsa) na bari a can na taho, jikin nawa duk babu dadi, haka kawai na tsinci kaina da jin wani sanyin jiki, fatana Allah Yasa alheri ne."   Saude ta yi tsuru da idanu, yau kuma meke shirin faruwa?    Shigowar Mariya a guje ne ya katse tunanin kowannensu.   "Umma! Umma!!" Suka maida hankali gareta jin yanda ta ke ihun kira, babu wanda gabansa bai fad'i ba acikinsu. Malam Balarabe ne ya riko hannunta. "Menene 'yar Baba?" Tana haki tana nuna kofar waje da yatsa, bakinta a washe ta ke fadin. "Wasu ne suka zo da katuwar mota suna..." Kafin ta karasa magana suka tsinci sallama mutane, Yaha ce a gaba Hajiya Babba na biye da ita.    Saude ta zaro ido. "Yaha?" Malam Balarabe ya mike yana mai amsa sallamarsu yana dubansu duban rashin sani don daidai da Yahar bai rike kamanninta ba. Kafin kuma wani cikinsu ya kara cewa komai, Ummi itama ta sanyo kai da sallamarta wanda dakyar ta iya daurewa ta yi shi don a matukar tsorace take.     Ganinta yasa Malam Balarabe zaro ido ya nunota da yatsa. "Ha...ha..si..daman ba ki mutu ba?!" Kawai sai ya zube anan, ihu da salatin Ummi ne ya ankarar da Saude cewa lallai yau ABINDA AKE GUDU ya afku!     Ta kasa koda kwakkwarar motsi tana ganin Ummi ta yi kanshi tana jijjigawa.  Faruk da suke waje, yana jin ihun Ummi baisan sadda ya sanya kai cikin gidan ba su Babban Yaya na biye da shi. Hajiya Babba ta hangi buta, da sauri ta nufi butar ta dauko, Faruk ne cikin zafin nama ya kar6a ya soma yayyafa mishi, aka ci sa'a ya farfado. Saude jikinta sai kadawa ya ke yi tamkar mazari, ana haka itama Habiba ta shigo don kuwa ta ji hayaniya saidai bata gask'ata ba hakan yasa ta zo ganewa idanunta. Wata budurwa ta gani sanye da tsadaddun kaya durkushe tana kuka sai mazan dake tsaye a wajen. Malam Balarabe aka kamashi ya zauna gami da jingina da bango. "Sannu Baba." Cewar su Babban Yaya, bai amsa ba sai binsu da ya ke yi da kallo kafin ya sauke idanunsa akan Ummi, da sauri ya runtse ido ya soma salati. Duk sai ya basu mamaki, babu kamar Ummi, mamakinta bai wuce na ganin wai mahaifinta ke tsoranta ba. "Wai Malam lafiya?" Saude ta yi maganar cikin rawar murya tana mai fatan ace Malam Balarabe ya koresu daga gidan matsayin ya ga fatalwa matarsa. Ya nuna Ummi. "Wai Hasiya ce dai ta dawo? Daman ba ta mutu ba?" Tambayar da ya yi ne yasa hankalin su ya dan kwanta banda na Saude da Habiba wacce jin hakan yasa ta sulale ta koma gidanta, bata yi wata-wata ba ta dauki mayafi sai gidan Bokanya har jikinta na rawa tsabar firgici. Acan kuwa, Yaha ta amsawa Malam. "Aa Malam, wannan Hasiyar Ummi ce diyarka diyar marigayiya." Ya kurawa Ummi idanu kamar yau ya soma ganinta, Ummi! Ummi!! Shi kuwa ina ta shiga kwana biyu ba ya ganinta?   ((Ku yi hakuri, rashin chaji ke sa ku ji ni shiruuu..)) DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   92            Saude tana shiga gidan Bokanya ta yi turus sakamakom ganin Habiba da ta yi zaune itama tana faman kuka. Habiba na ganin Saude ta mike da sauri ta nufi wajenta.    "Yanzu Mai Bori ta ke gayamin kin tafe daman, munyi sake Habiba, lamura sun yi 6acin da gyarasu sai Bokanya. (Wa'iyazubillah)" Saude ta wuce zuwa gaban Bokanya ta zauna. Bokanya tana dubansu tun soma maganganinsu tana dariyar k'eta. Kafin Saude ta ce komai ta rigata.   "An sakeki Saude, Balarabe ya miki saki biyu ko? Hahaha." Ta kyalkyale da dariya, Habiba ta razana da jin wannan, ta zaro ido ta dubi Saude ta koma duban Bokanya. "Kunyi kuskure babba! Kun kasa kiyaye dokokina, yanzu ku ka soma fuskantar kalubalen rayuwa! Babu wani abu da zan iya, lokacin afkuwar ABINDA AKE GUDU ya iso!"   "Karya ki ke wallahi! Ke din banza, idan ba ki yi mana aikin ba kin dauka babu dubunki?" Cewar Saude kenan wacce sam ba cikin and hayyacinta ta ke ba. Ita kuwa Bokanya dariyar keta kawai ta ke yi babu kakkautawa.   "Allah Ya isa tsakaninmu da ke, ashe bokancin naki ya k'are tunda ki ka kasa gyara abinda ki ka san zai 6aci." Cewar Habiba itama cikin kuka. Sai lokacin Bokanya ta dan tsagaita dariyarta tana mai duban Habiba. "Kun yi kuskuren zagina! Sakamakonku zai biyo baya! Ke Habiba! Ke ki ka kashe Hasiya! Tare da taimakon Saude! Diyarki tana can ta fad'a harkar madigo! Aurenta zai mutu! Sai na karya duk aikin da na yi mata! Sai kun koma abin tausayi. Asirinku sai ya tonu! Ku tashi ku bar nan azzalumai!!"   Ta karashe fuska a daure, suka mike don ko damar bata hakuri basu samu ba, Bokanya ta karanto musu laifinsu wanda duk a zatonsu asirinsu ya rufu ruf babu ta inda zai fito don kuwa su biyun cewarsu sun aminta da juna.    Suna tafe ga duhun Magriba, Saude fadi ta ke. "Allah Ya isa tsakanina da ke, duk kece ki ka soma kaini wajen bokanyar nan yau ga shi nan abinda ya afku. Ga shi yau aurena ya mutu." Habiba da ke kuka da tunanin tashin hankalin da ke gabanta na mutuwar auren diyarta ta dubeta. "Au, haka ma za ki ce?  Kin mance dadin da ki ka ji a baya ta sila ta shine yau da akayi miki ba dadi za ki zageni? Lallai DAN ADAM mai mance halacci, DAN ADAM butulu, ban ta6a kashe rai ba sai akan kishiyarki, shi ne tsabar son ki nunamin ke kina cikin masu mance halacci za ki ce na cutar da rayuwarki? Ai babu wacce aka cuta sama da ni."   Wannan kalamin na Habiba ya tunzura Saude, nan suka hau cacar baki suna tafiya, wannan ta fad'a, wannan ma ta maida martani, karshe haka suka rabu baram-baram, Saude kai tsaye ta kama hanyar gidan kawunta wanda shi da banza duk daya ta daukesu, sai kuwa a yau din da ta ke neman agajinsu kan su rok'i mijinta akan ya maidata dakinta.     Habiba hankalinta idan ya yi dubu to fa ya tashi, babu abinda yanzu ke damunta kamar batun diyarta Dija, yanzu idan auren ya mutu ta yi ya ya? Ta dauki waya da zummar kiranta saidai ko kusa batasan yanda ake sarrafa wayar ba, sau da yawa idan za ta yi kira saidai ta shiga makwafta budurwar gidan ta danna mata. Tana nan zaune duk tunaninta ya jagule, Malam Yahuza ya shigo gidan da sallamarsa saidai bata ko amsa ba. "Habiba, lafiyarki kuwa ina sallama ba ki ko kalleni ba balle ki amsa?"   Sai lokacin ta dubeshi gami da jan tsaki.   "To menene kuma? Za ka cikani da hayaniya, mtsw." Ta karashe gami da jan tsaki. "Habiba ni ki ke yiwa tsaki kuma? Toh bazan dauki wannan rashin kunyar banzar ba, ki kiyaye!"   Sakato ta yi tana duban mijinnata, yau Yahuza ne ya samu 'yancin d'aga murya sama da nata? Tabbas Bokanya dagaske ta soma karya dukkan ayyukan da ta yi musu, ta yi tsuru don tsoro ma ya bata, ya kammala komai ya dubeta. "Ina abincina?" A sanyaye ta amsa. "Ai ba ka bada kudin cefane ba." Ya yi kwafa kafin ya mike ya fice zuwa masallaci. Ta bishi da kallo kafin ta dora hannu a ka ta hau kuka. "Oh ni Habiba wannan wace irin bak'ar rana ce gareni?" Ta fad'a a fili babu mai amsa mata.                     Ummi farincikinta ba ya misaltuwa a wannan rana, ta yi sallar Magriba anan tsakar gidan, saida aka yi sallar Isha'i sannan Malam Balarabe ya shigo rike da leda, da sauri ta mike ta kar6a suna duban juna da murmushi saman fuskar kowannensu. Kauna ta da da mahaifi shi ke yawo a jinin jikinsu. Tarr ya ke ganin diyartasa sakamakon wutar lantarki da suke da shi don a baya sosai suna samun wuta a kauyen, sai ayi kwana biyu ba'a dauke ba, koda kuwa an dauke, to fa babu jimawa za'a maido musu, yanzun kuwa da aka shiga yanayi an dan rage samu kamar da.     "Sannu da zuwa Babana." Ta karashe cikin jin wani irin sanyin dadi a zuciyarta, yau ga ta ga mahaifinta kamar yanda ta ke yawan mafarkin ta gani har ya damu da ita ya sakarmata fuska. Kwalla ta cika idanunta sa'ilin da ta ke kokarin ajiye ledar ya dakatar da ita da fadin. "Sannu 'yar Baba, dauko faranti a ciki nama ne da gurasa ku ci." Ta bi umarninsa, ta kawo ta juye, ta dubeshi. "Baba mu ci." Yana murmushi lokacin da ya ke share hawayen da suka zubomishi ya soma ci shima. Mariya itama ci ta ke sosai don daman da yunwarta.    Bayan sun kammala ta debomusu ruwan randa mai sanyi suka sha kafin su yi zaman hira. Malam Balarabe ya dubi Ummi. "Kamanninki da mahaifiyarki har ya 6aci, tamkar an tsaga kara an karya, hatta sanyin muryarta." Ya danyi shiru kafin ya numfasa. "Allah Ya jik'anta." "Amin." Ummi ta amsa jikinta a sanyaye tana dubansa kafin ta ce. "Baba kana da hoton Ummana?" Ya gyada kai yana murmushi. "Bazan rasa ba saidai yanzu nasan yana cikin kaya, sai zuwa gobe zan dubo miki. Bani labarin zamanki a hannun bayin Allahn nan." Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta soma labartamishi tun farkon zuwanta har kawowa yau da suka taho nemawa dansu aurenta.    Malam Balarabe dake ta faman jinjina kai, wani abin ya yi murmushi ya ce"Allahu Akbar" wani abin kuwa ya yi hamdala idan ya ji. Bayan ya kammala ya dubeta. "Babu abinda zanyi na biya mutanen nan da shi sai addu'a. Hakika sunyi abinda Allah baiyi ni zan miki shi ba. Babu abinda yafi faranta raina kamar sanyaki a makaranta da suka yi basu barki kin zauna da jahilci ba.  Haka kuma rayuwarki bata lalace ba, har kuma suka tako daga Abuja zuwa kauyenmu don kawai su nemawa dansu aurenki, tsakanina da su sai addua, Allah Yasa aljanna ce makomarsu, in sha Allahu ba ki da miji sama da Umar. Zuwa yanzu na dakatar da maganar don nafison ki soma sanin dangina da na mahaifiyarki, ayi aurenki kina cikin dangi. Itama Amina Allah Ya yi mata albarka, Ya bata mijin da zai rik'eta rik'on Amana." "Amin Baba." Ummi ta amsa da murmushi mayalwaci saman fuskarta, ai ko don zagin da su Ihsan ke mata, zata so ta hadu da dangin iyayenta, ta ga gatanta. Sai kuma ta dubi mahaifinnata, lokacin Mariya ta soma bacci saman tabarmar. "Baba inason jin tarihinku da Ummana, ku din 'yan ina ne?" Malam Balarabe ya murmusa kafin ya ja baya ya jingina da bango ya soma magana. "Yanzu za ki ji takaitaccen tarihinmu da Ummanki, sauran idan munje kya ganewa idanunki." Suka yi murmushi tare kafin ya cigaba da magana....!        DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 93   ((Wannan shafin naku ne yan uwa sis Aisha Samarou & Maman Adil))   "Da ni da mahaifiyarki duk yan gari daya ne, wato Gombe. Saidai ita din  ta yi rayuwa ne a kauyen Jar Kwami dake Gombe. Da mahaifinta, Malam Manu(Usman) da kuma mahaifina Malam Buba(Abubakar) aminan juna ne wanda amintarsu ta samo asali tun kan iyayensu wanda tarihi ya nuna suma haka suka taso kansu a hade.     Malam Buba  bayan aure ya koma cikin birnin Gombe da zama Unguwar Tudun wada tare da mahaifiyata Fatima wacce muke kiranta Dada. Yaransu bakwai, uku sun rasu, ya yi saura daga  Haruna, Baffa(wanda ya ci sunan Usman baban Hasiya) sannan ni Abdullah wanda hasken fatata yasa suke kirana da Balarabe sannan kuma kanwarmu Aisha.      Gaba daya danginmu bamu da yawa sosai don bamu kai yawan dangin mahaifiyarki. Mahaifinta d'a ne ga Muhammadu Lamido, tsohon Sarkinmu na kauyen Jar Kwami, kafin ya mutu yana da mata har hudu banda uku da suka ta6a rabuwa duk kuma sun ajiye mishi yara, mata sunfi yawa cikin yaransa, bayan mutuwarsa aka dora wani kan karagar mulkin don alokacin yaransa maza su uku duk basu kai minzalin rike mulki ba.     Koda lokacin ya yi, babban yayansa ne kawai  ke shaawar mulkin sam kakanki Malam Manu(dansa na biyu) ba ya so.       Gaba daya a gidan sarautar su ke zaune, manyansu da yaransu. Sai kuwa matan da aure ke rabasu da gidan, wasu cikinsu ma auren gida ake musu da yaran yan uwa.     Duk cikin yaran Malam Manu, mahaifiyarki ce k'aramarsu, babban dansa namiji ne, Ado sai Bilkisu, Safiya, Asma'u sannan Mahaifiyarki Hasiya saidai Boddo suke kiranta, wato mai kyau. Don Masha Allah duk cikin yaran Malam Manu babu mai kyawunta.  Innarsu Aisha da suke kira da Inna tun bayan haihuwar Hasiya suka koma kiranta da Inna Boddo.       Tun farko anso yi mana auren zumunci da mahaifiyarki tun ma bata isa aure ba, amma fir na k'i sakamakon soyayyar da muke yi da Saude diya a wajen wata mai siyar da abinci a tsohuwar kasuwa inda nan nake zuwa siye da siyarwa. Asalinsu yan Kano ne can kauyen Ringim, saidai aure ne yasa Atine uwa ga Saude  baro garinsu zuwa nan Gomben, bayan rasuwar mijinta ne ta fad'a harkar siyarda abinci. Saude kadai ce diyarta, nakan yawaita zuwa shagonnasu daga shagon yayana dake zuwa Kano saro yadikan maza,  haka har muka saba da Saude kafin kuma soyayya mai karfi ta shiga tsakaninmu. Kullum kwanon abincina na rana anan ya ke.     Ranar da na zo wa mahaifinmu da maganar auren Saude, sam bai aminta ba don kuwa ya ce shi fa ba ni da mata sai Hasiya, lokacin idanuna sun rufe na ce bana sonta, nan duniya  Saude kadai ce abar sona.     Akan wannan saida ran Malam ya 6aci ainun, ya budemin wuta sosai. Har ya yanke shawarar zuwa Jar Kwami don ayi wacce zaayi, hankalina ya tashi, ina gani babu wanda ya goyi bayan na auri Saude. Karshe kuwa da ni aka je Jar Kwami, koda Malam ya gama magana akan aurena da Hasiya, Malam Manu ya aminta kuma ya ji dadi sosai, saidai ya bawa Mahaifina hakuri inda ya nunamishi har lokacin Hasiya bata kai munzalin aure ba saidai ko ta zo a ta biyu. Malam fir ya k'i amincewa, ya jajirce akan lallai a daura aurenmu da Hasiya.    Koda na sanarwa Saude halin da ake ciki, ta shiga tashin hankali matsananci ga shi a wannan lokacin mahaifiyarta na shirin zuwa ganin gida can Ringim.  Ana gobe za'a daura aurena da Hasiya na bi Saude da babarta zuwa Ringim don kuwa a wannan lokacin ji mu ke yi idan ba mu auri juna ba to fa za mu iya rasa ranmu. A hanyarmu muka yi hatsari mahaifiyar Saude ta rasa ranta, har suma saida Saude ta yi don tashin hankali, inda ma aka ci sa'a Sauden tasan garin tana zuwa. Da taimakon jamaar gari da kuma kwatancen Saude, Allah Ya yi isarmu gidan Kawunta Isah, anan aka yiwa mahaifiyarta jana'iza bayan nan Saude ta gabatar da ni matsayin wanda za'a auramata, ta sanarmusu wannan ne musabbabin zuwanmu garin. Koda aka nemi sanin tarihina, muka rufe komai muka nuna cewar ni din maraya ne, dangi kuwa sun sakoni gaba, babu mai kaunar ya ra6eni. Kawu Isah bai so aurennan ba don yana ganin kamar mun 6oye wani abu bayan wannan, saidai ganin yanda Saude ta tada hankali ga kuma maraicinta da ya duba hakanan itama bata samu wani sukuni daga dangin ubanta ba, ya amince ya daura aurenmu, gidannan da ki ke gani nawa ne, a farkon zuwanmu gidan Kawu Isah muka zauna har na tsawon shekaru biyu kafin na samu abin hannuna ta hanyar sana'o'i daban-daban na gina wannan gidan ginin k'asa. Wannan na sumuntin duk na yanzu ne. (Ya yi nuni da bangon gidan sannan ya dora). Tun zamanmu tsawon shekarun nan Yahuza mijin Habiba makwatanmu ne, yanda na saba da Yahuza haka Saude ta saba da unguwar zoma Habiba kusan ma da ya ke su mata ne shakuwarsu ta fi namu.    Ashe su kuwa acan da na tafi sun daura aurena da Hasiya, saida watarana tunanin gida ya addabeni tashi guda na ji inason komawa Gombe. Zuwana na ji labarin rasuwar mahaifiyarmu da kuma auren kanwata Aisha. Na yi kuka kwarai, Malam kuwa ko kallon inda nake baiyi ba. Gwara ma yayyuna sun saurareni, Haruna da kansa ya bani shawarar zuwa ga Malam Manu don shi kadai ne zai iya shawomin kan mahaifina ya yafemin. Banyi kasa a gwuiwa ba washegari na wuce Jar Kwami. Malam Manu kusan ya yi murna kwarai da ganina, yanda ya kar6eni har kunya na ji don ban ta6a daukar an daura aurena da diyarsa Boddo ba. Ya bini doguwar nasiha, karshe washegari muka wuce cikin Gombe.  Malam ya tabbatar ya hakura muddin zan ba shi takardar Hasiya, ashe ma tun bayan auren aka kawota gidanmu saboda gudun maganar mutan gari.   Malam Manu kuwa ya ce bai isa ba, babu mai kunce aurennan, ni kaina ba zanso hakan ba. Dakyar da sidin goshi Malam ya hakura saidai ya ce nan zan zauna da Hasiya. Nan ma ansha artabu kan ya amince da tafiyarmu Ringim da ita. Saida na yi sati uku kafin na taho da Hasiya da yayyunta da wasu cikin dangi duk don a ga waje.    Ina cike da tsoron irin kallon da Saude za ta yiwa lamarin, saidai ga mamakina ta nuna ta fini farin ciki, har da durkusawa ta yi ta nemi gafarar yan uwana acewarta itama ta yi musu laifi na rabasu da ni. Wannan abu ya k'aramata k'ima a wajena, haka suma yan uwana suka cika da farinciki fad'i su ke, "Balarabe ka yi dacen mace ta gari." Har suna kwatantawa Hasiya da ta yi koyi da Saude. Ko bayan tafiyarsu na barwa Hasiya dakina, daman dakuna uku ne a baya, daya a zaure sai biyun nan kafin yanzu da aka yi ciki da falo.     Zaman lafiya suka gudanar, hakurin Hasiya da kyawawan dabi'unta su suka sanya ni cikin shaukin so da kaunarta ainun, abin Allah sai Ya doromin so da kaunarta fiye da irin wanda na yiwa Saude. Dakyar nake kokarin kwatanta adalci atsakaninsu.    Alokacin ne kuma Saude ta soma nunamin damuwarta kwarai akan rashin samun ciki. Kullum cikin yi mata nasiha nake, saidai takan yawaita tambayata kudi na zuwa wajen wata mai maganin gargajiya da aminiyarta Habiba ta bata labari na wai tana bada maganin samun ciki. Duk yanda na so fahimtar da ita cewar haihuwa lokaci gareshi, bata fahimta ba.     Haka har Hasiya ta samu ciki, kusan Saude ta fimu nuna murnarta, har kuma ta raineshi Saude har ayyuka ta ke kar6amata, magungunan gargajiya duk da tasan zai amfaneta takan kawo, haka itama Habiba ta kyautatawa Mahafiyarki, Allah kadai yasan zuciyoyinsu, ko tun wancan lokacin da gaske suke nunawa Hasiya kauna, ko kuwa dai da biyu su ke yi? Ba zan ce komai akai ba don bani da tabbas.    Cikin ikon Allah cikin Hasiya ya kai wata tara, tana haihuwarki kuma sai Allah Ya dauki ranta."    Malam Balarabe yana kaiwa nan ya dubi Ummi ya na mai haska wayarsa sakamakon wutar da tuni aka dauketa. Ummi hawaye ta ke yi don ita tasan duk ba don Allah suka yi ba, ta sha ji suna hirar, Allah ne kadai ya yi itama za'a haifeta don tun tana ciki aka so cikin ya zube, cewar Saude kenan duk sadda ta ke goranta mata da zaginta a baya.   "Hasiya ki gafarceni, bansan dukkan abinda ya biyo baya ba bayan mutuwar mahaifiyarki, don lokacin gaba daya tsanarki ce ta dirar min, su kansu yan uwana sai suka fita hanyata haka kema daga dangin mahaifiyarki babu mai zuwa su ganki. Sun aminta da Saude fiye da zatonki, kamar yanda nima na aminta da ita ta yimin halin DAN ADAM na butulci." Ya karashe yana mai share hawaye. Murmushi Ummi ta yi gami da kamo hannun mahaifinta....   ((Inda gyara kofa a bude ta ke [email protected] ko fcbk.. Rufaida Omar)) DAN ADAM @RUFAIDA OMAR     94 "Idan kana bani hakuri bana jin dadi wallahi Baba, ni na hakura komai ya wuce awajena. Abinda ya faru kaddara ce, kuma Allah Ya yi ba makawa sai ya faru. Ka daina damuwa kada wani ciwon ya kamaka."   Ya jinjina kai yana murmushi can kasan ransa kuwa, yabawa ya ke da kaifin basira irin na 'yartasa. Damuwa dole ce a wajensa, ko don ma rashin sanin irin kallon da danginnasu zasu yi gareshi. A fili kuwa ya nunamata komai ya wuce. Wayarta da ke(ringing) ne ya katsesu, ta sa hannu ta janyo jakarta ta ciro don ita ta mance da ita ma, ganin mai kiran yasa ta ajiye wayar don kunyar dauka ta ke ji gaban Babannata, lura da hakan yasa shi yin murmushi sannan ya mike. "Bari dai na lek'a wajen abokan hirata yau sun ji shiru, daga nan na saka kati na kira su Yalla6ai na ji yanda suka isa. Wannan ki kaita ga daki nan akwai katifa ku kwanta anan." Ya karashe yana nuni da Mariya.     Ta amsa da to, bayan fitarsa ta janyo wayar da sauri saidai kafin ta kai ga amsawa har ta yanke, ta bi wayar da kallo cike da shauki anan take ta kira ya kuma shigowa. Ta d'aga da sallama.     Faruk da ke kwance saman gadonsa rungume da filo ya lumshe ido jin muryarta ya amsa sallamar ciki-ciki.    Jin yanayin muryarsa ne yasa ta fadin. "Kun isa lafiya? Ya mura?" "Alhamdulillah, kin samu Baba kin mance da mijinki ko?"   Ta ji kunyar maganar, har lokacin bata gamsu da yanayinsa ba, kamar dai akwai damuwar da ya ke 6oyemata.   "Ummina." Ta kasa amsawa sakamakon jin kiran sunannata da ya yi yana zaga dukkan ga66an jikinta, ta lumshe ido gami da jingina kai da bango tana kallon sararin samaniya wanda ke cike da taurari.      "Ba za ki amsa ba?" Ta daure ta amsa. "Um." Murmushi ya yi mai sauti kafin ya ce. "Ina kewarki. Ina matukar kewarki Ummina, ban gane hakan ba saida muka dawo gida, duk sai ya yimin fad'i."    Murmushi ta ke yi saidai ta kasa cewa komai don ita kunya ma ya bata, ga kaunarsa da ke k'aruwa sosai a ranta. Ita kanta ta yi kewarsa fiye da tsammaninta.   "Ba magana ko? Wannan kunyar fa ta gulma ce akwai ranar da zan kaudata don na gaji da ita tana cutata."    Ta rufe idanunta da hannu tamkar yana ganinta, banda "Um" ba abinda ta ce.     "Banso aka k'i tsayar da maganarmu ba yanzu ba, saidai Baba yana da gaskiya, ni kaina zanfi so kiga danginki ko burinki zai cika tukunna. Ina kara tayaki murnar sasantawa da mahaifinki, Allah Ya k'ara kauna tsakaninku."   "Amin Yaya Faruk, nagode." "Na gaji fa da Yaya yayannan, ki chanjamin suna."    Ta danyi dariya kawai.  "Dagaske nake, ana muku ruwa?" Ta girgiza kai. "A'a."   "Ayya, mukam ruwa sosai ake yi." Murmushi ta yi. "Alhamdulillah, kun ji dadi." "Ina wani dadi, babu Ummina a gida?" Kamar ta nutse don kunya ta kasa magana can kuma ta ce. "Saida safe."   Ga mamakinta ta ji ya saka dariya sosai, sai itama yasa ta murmushi. Bayan ya tsagaita ya ce. "Allah Sarki Ummina, ina son wannan kunyartaki saidai please ta kasance iyakar yanzu kafin mu kai ga aure kin ji ko?"    Murmushin dai ta ke yi ba ta ce komai ba. Atishawa ya saki har uku a jere, ya karashe da fadin Alhamdulillah, ta amsa da YarhamukAllah sannan ya amsa mata da  "Yahdikumullahuwa wa yuslihu balakum."    Shiru ya biyo baya kafin kuma ta daure ta ce. "Don Allah ka sha maganin mura." Ya ji dadi ainun na kulawar da ta nuna gareshi.     "Banason magani, sau daya na sha ya sanyani bacci ban k'ara sha ba."   "Haka za ka daure ka..." Sai kuma ta ji nauyi ta yi shiru. "Kin damu da ni har haka Ummina?" Wasa ta hau yi kawai da jelar dankwalinta batare da ta ce uffan ba. Ya sauke ajiyar zuciya. "Zan sha tunda ba kya sona da mura."   Ta murmusa. "Ka turomin lambar Hajiya don Allah."    "Me za ki ce mata?" "Gaisawa za mu yi." "Shikenan zan aikomiki." Daga haka suka yi sallama, ta mike ta shiga dakin da Baba ya yi mata nuni da makwancinsu, ta gyara shimfidar, dakin katifa ce kawai sai shirgin kaya a gefe. Da taimakon wayarta ta haska ta dauko Mariya bayan ta kai ta ta yi fitsari ta shimfideta. Ita kuwa kayan jikinta ta rage ta d'ebi ruwa ta zagaya kewaye don garin akwai zafi, bayan ta yi wanka ta fito ta shirya cikin doguwar riga na bacci cikin wadanda Faruk ya siyamata. Ta feshe jikinta da turare mai sanyin kamshi sannan ta zauna gefen katifar tana tunanin ko ina mahaifinta ya wuce? Sallamar Saude ta ji wanda ya sanyata jin wani mugun faduwar gaba, kafin ta amsa, ta tsinci muryar Babanta wanda daman ba nisa ya yi ba yana zaune kofa.    "Me ki ka zo yi a gidana?" Saude ta dubeshi, daman a k'ule ta ke don acan Kawunta Isah ci mata mutunci ya yi ya nuna babu inda zaije daman tuni ta bar ganinsa da daraja. Da ta gaji da zama ta ga dai babu wanda ya kulata an barta a tsakar gida yashe yasa ta taho ko tayin abincin da akayimata bata ci ba don ta rantse gidanta za ta kwan.     "Ka manta inada 'ya? To babu inda zanje sai na yi idda." "Idda a gidan wa? Wallahi ba ki isa ba Saude, ke ba irin matar da zan yi marmarin na komawa aurenta bace, tun muna mu kadai ki tattara ki barmin gida kafin na jibgeki na tara miki jama'a!"   Ummi dai tana daga daki tana lek'ensu don tsakani da Allah har yanzu tana jin tsoronta sosai.     Saude ta yi shewa. "Ahayye! Lallai Abdullahi wuyanka ya isa yanka! Har ni Saude ka ke gayawa haka? To ni kuwa yau babu inda zanje, anan gidan zan kwana don uban mutum!"    Tana maganar kamar ta6a66iya, daidai da su Habiba da sauran makwafta mafi kusa suna ji, ko daga majalisar su Malam Balarabe suma suna jiyo ihunta da maganarta. Zagin da ta yi ya firgita dukkan masu sauraro, ai Malam Balarabe baisan lokacin da ya janyo igiyarsu ta shanya ba nan take ta tsinke, ya soma tsulamata yana fadin. "Kinyi kadan, karyarki ta yi karya ki zagi ubana! Kin yi kadan Saude." Ihunta yasa mutane suka shigo, itama Ummi fitowa ta yi tana rokon mahaifinta da ya kyaleta.  "Haba Malam Balarabe da girmanka? Wannan ba girma bane, dukan mace don Allah ka yi hakuri." Cewar Malam Yahuza kenan, Saude wacce ta ci duka ta hayayyako mishi. "Kai dalla can rufewa mutane baki, solo6iyon banza da wofi, duka-duka yaushe ka samu kwato kanka a hannun Habiba?"   Hakan ya harzuka Malam Balarabe ganin bakar maganar da ta ke fadawa abokinsa, ya k'ara tunzura zai kai mata duka, gam! Ummi ta rike igiyar gami da durkusawa tana fadin. "Don Allah Baba ka yi hakuri, ka kyaleta." Saude ta mike tana gyara zaninta tana ihun kuka, Malam Yahuza da sauran mazan suka rasa bakin magana, suna shirin fita ai kuwa ta cakumo wuyan Ummi ta baya tana fadin. "Kema sai kin bar duniya yadda Hasiya ta barshi, sai na kasheki!"   Ummi da ta ji shak'a ta soma kwatar kanta saidai ta kasa, cikin zafin nama mutanen suka yo kanta, dakyar aka yi nasarar kwatar Ummi daga hannunta, kuka sosai Ummi ke yi tana shafa wuya tana tari don ba kadan ba, ta ji shak'ar. Mari lafiyayye Malam Balarabe ya wanke fuskar Saude da shi, ai kuwa ta hau tsalle tana zage-zage, ya finciki hannunta tana tsalle tana ihu tana zagin iyayensa da Ummi har tana fadin "Da nasan haka za ki zama da tun kina jaririyar kema mun kasheki!!" Haka har ya watsar da ita a kofar gidan ya kulle ta waje.  Mutane sai hakuri suke bata daidai da mata fitowa sukayi kallon wannan abin al'ajabin. Bata jira komai ba ta nufi kofar gidan Malam Yahuza. Hannuwanta a k'ugu tana karkad'a jiki. "Ina ki ke shegiya bak'ar munafuka? Ki fito! Ki fito nace!!!" Tana shirin shiga gidan Malam Yahuza ya tureta daman cike ya ke da haushinta. "Karki sake ki shiga gidana, kada na k'ara ganin kafarki wallahi."   Dariya ta shiga kyakyatawa ga hawaye jage-jage saman fuskarta kamar mahaukaciya sabuwar kamu tana nunashi daga sama har k'asa kafin ta rangad'a bud'a.    "Ayyiririii! Eh babu shakka akuyar daure ta samu sake! Yahuza kai ne ka samu iko haka? To wallahil azim yanda aurena ya mutu kema Habiba yau naki zai mutu!"     "Idan ke ce da shikan a hannu sai ki zo ki rabamu!"   Cewar Habiba sa'ilin da ta leko kanta, Malam Yahuza na kokarin tsawatarmata akan ta koma ciki saidai maganar Saude ya dakatar da shi, duk jama'a na kallo, Malam Balarabe kuwa jira ya ke yi ta gama haukanta ta bar wajen ba zata shigar mishi gida ba.     "Keda ki ka kashe rai! Wallahi jama'ar gari ku shaida Habiba da hannunta ta kashe Hasiya!!!"         Can na hango Bokanya tana faman kyakyata dariya tana kara jijjiga abin tsafinta a hannu, cikin ihu da kururuwa ta dauki wata kwarya ta fasa tana fadin.   "Kadan ku ka gani shegu! Kadan ku ka gani!! Na soma karya dukkan mugun aikin da na k'ullamuku!  Daman kwa yarda da wani bayan Allah? Hahaha! Mu daman ta6a66u ne mun yarda!!! Hahahaha!!!" Wannan furucin Bokanya kenan sa'ilin da ta ke kallon dukkan abinda ke faruwa ta cikin wata k'atuwar kwaryar sihiri. (Wa'iyazubillah). Mutanen wajen suka yi sak, Ummi a guje ta fito daga gidansu kanta babu ko kallabi ta zubawa Saude ido jin abinda ta fad'a. Habiba fitsari ta soma saki a wando don kuwa bata ta6a tsammanin akwai ranar da Saude za ta yi mata haka ba!     Gaba daya waje ya dauki salati. Wuf Habiba ta fito bayan ta ture hannun Malam Yahuza wanda ya tokare kada Saude ta shigar mishi gida. "K'arya ta ke yi! Ta haukace! Kada ku yarda karya ta ke min!!"   Saude wacce bata bar kyakyata dariya ba ta ce. "Ina rantsuwa da Allah ita ta kasheta amman da sa hannuna!"   Ta karashe tana soshe-soshen jiki don haka kawai ta soma jin wani k'aik'ayi a fatar jikinta. Kafin wani ya yi yunkurin karasawa gareta Ummi cikin zafin nama ta k'arasa, ta rik'e kafadunta tana kuka cikin daga murya ta ce. "Ki gayamin, dagaske kune ku ka kashe Ummana?" Dariyar dai ta ke yi itama cikin kwaikwayon daga murya ta Ummi ta amsa. "Eh! Ni da Habiba muka kasheta! Kema na so a kasheki saidai Habiba ta bada shawara a kyaleki nan gaba jari za ki zamarmana! Kuma kin zama." Ta karashe cikin dariya. Sai kuma tiryan-tiryan ta shiga bada labarin yanda komai ya faru.  Ummi batasan sadda ta fidda hannu a zafafe ta dauketa da mari hagu da dama ba, tana yi tana kuka da fadin. "Ban yafemiki ba Saude(ta fada gatsal don girman ya fadi)! Ban yafemiki ba!!" Sai kuma ta durkushe tana kuka sosai, nan aka ankara Habiba ta gudu. Ai kuwa wasu matasa suka rufamata baya.    Ita kuwa Saude wacce bata ji marin Ummi ba asalima dariya kawai ta ke yi, ta karasa ga Malam Balarabe wanda ke kuka har da sheshsheka saidai ya kasa samun karfin zuwa ya rarrashi Ummi sai wasu matan makwafta ne suka zo suka dagata.    "Abdullahi kai mutumin kirki ne, ka so ni sosai, saidai ni tun daga ranar da ka yimin kishiya na tsaneka." Ta cigaba da dariya sannan ta dora. "Habiba kawata ta ban shawarar 6oye kishina kuma na bi, babu irin maganin da ban barbada muku ba a abinci kai da ita, sai kuma duk da haka ka fifita ta a kaina!" Ta karashe ciki daga murya a fusace sannan ta dara. "Kuma ta zo ta samu ciki." Fadin haka yasa Saude soma kuka duk mutane na kallonta cike da takaici har lokacin wadanda suka bi bayan Habiba basu dawo ba, Malam Balarabe da ya rasa ta cewa tagumi kawai ya yi yana hawaye yana dubanta, can kuma ta dora tana soshe-soshenta.   "Na sha gwada kashe Hasiya da dan cikinta ta hanyar duramata magunguna ina fakewa da fadin na gargajiya ne na kara lafiya, saidai banga wata illa da ya yi mata ba har zuwa sadda cikinta ya shiga wata tara ta soma nakuda muka kasheta muka bar jaririyar. A karshe na asirceka ka daina kaunarta, na saka dangin uwarta da danginka suka daina zuwa inda ku ke, amma Abdullahi duk wannan kaunar da na nunamaka bai hana ka sakeni ba?!!!" Ta karashe tana mai dibar k'asa ta watsamishi ya rufe fuskarsa. Nan kuma ta hau tsalle da soshe-soshe, baiyi wata-wata ba ya soma yunkurin dukanta dattijan suka hana. Malam Sule makwafcinsa ya ce. "Ai dukanta yanzu kuma 6ata lokaci ne Malam Balarabe, ba ka ganin ma bata cikin hayyacinta?"   Malam Balarabe kawai sai ya juya ya shiga gidansa yana kuka, Ummi ta bi bayansa da sauri itama.    Habiba cikin sa'a aka cafkota, ana zuwa Malam Yahuza ya tsinke igiyar aurensa da ita, nan ta hau kuka da neman gafara, Malam Balarabe ya fito aka hada kansu sai ofishin yan sanda. Habiba da kanta ta yi bayani don Saude hauka ta ke yi tuburan tana faman kyakyata dariya.      Aka gark'amesu da zummar sai washegari a k'arasa maganar.      Ummi da mahaifinta wannan ranar kasa bacci suka yi ga ciwon kai mai tsanani da Malam Balarabe ya kwana da shi, ita kanta Ummin da shi ta kwana sakamakon kuka da ta sha. Nafila kuwa a wannan daren ta yi shi hakanan addu'o'i. Babu wanda cikinsu ya ta6a kawo hakan, kowannensu tunaninsa bai wuce mutuwa Hasiya ta yi ba kawai ashe azzaluman ne suka kasheta.   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   96     "Ina a Tudun Wada?" Cewar matuk'in. "Bayan gidan Sarki."   Suna tafe Malam Balarabe na nunawa Ummi wurare gaba daya ya kasa ma rufe bakinsa, itama saita tsinci kanta da farinciki, Mariya ma kalle-kallen ta ke yi bakinta washe har suka iso unguwar. Wayar Ummi ta yi k'ara ta amsa. Hajiya Babba ce don kuwa ta yi kiranta kwanakin, suka gaisa kafin ta tambayi ko sun isa, ta amsa mata da eh. Ta ce ta gaishe da mutanen gidan. Daga haka suka yi sallama alokacin da kuma ta ga sun tsaya daidai wani gida karami ya sha fenti ruwan madara, wanda a kusa da shi wani gidan ne shima shigensa don hatta da fentin iri guda ne. Zaune a kofar gidan, wani dattijo ne kishingide saman tabarma, a gefensa kuwa wani ne da bai wuce shekaru hamsin ba suna hira da dariya saidai tsayuwar tasi din a kofar gidannasu yasa hankalinsu ya dan koma gareta.  Jikin Malam Balarabe har rawa ya ke don ko shekaru nawa ya yi ba fa zai mance wadannan fuskokin ba, Haruna yayansa ne sai kuwa Mahaifinsa.     Shima Harunan mik'ewa ya yi da sauri. "Abdullah!" Jin sunan da ya ambata yasa Dattijo Malam Buba mikewa zaune daga kishingidar da ya yi yana mai gyara zaman gilas dinsa na masu ciwon ido gami da k'urawa wanda aka kira da sunan Abdullah dansa idanu.    Tuni Malam Balarabe ya karaso da sauri suka rungume juna shi da yayannasa. Kawai sai suka fashe da kuka, Ummi ganin haka itama ta soma hawayen tausayamusu. Duk a silar kaddara sun rabu da juna. Ganin mai tasi ya gama sauko kayansu daga boot, ta tambayeshi ko nawa ne kudin sannan ta zaro a jakarta ta biyashi ya wuce.  "Abdullah ashe za mu k'ara sanyaka a idanunmu?" Cewar Harunan kenan cikin zubar hawaye.    Malam Balarabe ya na sharar hawaye ya karasa ga mahaifinsa wanda ya yi shiru yana ta faman jera hamdala a zuciyarsa ganin addu'arsa ta shekara da shekaru ta kar6u a yau.        Ya riko hannuwan mahaifinsa shi kuwa Haruna ya nufi wajen su Ummi wadanda ke gaisheshi.    "Malam gani gabanka, ka yankemin dukkan hukuncin da kaga ya dace, na yi babban laifi, na manta da dukkan hakkinku da ya wajaba a kaina na kula da shi, ka gafartamin Malam, na tabbatar har da k'in jin maganarku da na yi na auri son raina."   Malam ya damk'i hannunsa cikin rawar murya ya ke fadin. "Ba ka da laifi Abdullah, na jima da fahimtar hakan, shiyasa ban ta6a rik'eka ba a raina. Gareni, na yafemaka, tashi mu shiga ciki Abdullah mahaifiyarka ta sanyaka a ido ka nemi gafararta." Da taimakon Malam Balaraben Mahaifinnasa ya mike, suka yi ciki, yana dogara sandarsa.    Ummi wacce Haruna ya gama ja da hira yana fadamata irin matukar kamar da sukayi da mahaifiyarta, itama tasan hakan sakamakon hotonta da mahaifinnata ya bata. Suka mara musu baya suna mai daukar jakankunan wadanda uku ne kacal.     Saida suka shiga ta fahimci ashe dai ginin nada dan girma, irin ginin nan na gidan yawa, yara suka yita binsu da kallo, Abida mata ga Usman wato Baffa ta dubi Haruna bayan shigewar su Malam Balarabe da Malam.    "Waye wannan?"   Yana murmushi mai bayyana hakora ya amsa. "Har kin mance da Balarabe? Ai shine da iyalinsa." Ta zaro ido tana mai dafe kirji, yayinda ta ke bin su Ummi da kallo, Ummi ta gaisheta sannan itama Mariya ganin haka ta gaidata.  Dada na zaune a rumfarta tana gyaran wake, tsohuwa mai ran karfe, idan ka ganta ba ka ce yara bakwai sun fito daga jikinta ba don kuwa da kuzarinta.     Ta ajiye waken gefe ta yi sakato tana duban wanda ke rike da mijinta. Ko shekara nawa Malam Balarabe zai yi ita din mahaifiyarsa ce da ba zata ta6a mance fuskarsa ba. Kafin su kai ga karasawa gareta ta mike da sauri ta shige dakinta. Suka karasa suka isketa zaune saman gadonta na karfe tana faman sauke ajiyar zuciya. .  Bayan zamansu ne ta dubeshi kamar ta tashi ta makureshi. "Me ka zo yi mana?! Ka zo ka ga ko mutuwa muka yi ka ci gado ne?!!!" Tana maganar a zuciye, hakan ya karyawa Malam Balarabe zuciya ya hau zubda ruwan hawaye.     "Haba Fatima, ban sanki da zuciya ba, kada fushi yasa ki aikata abinda za ki nadamarsa nan gaba."   Cewar Malam cikin harshen fulatanci.    "Nadamar..." Sai kuma ta kasa magana sai kawai ta fashe da kuka sosai don kuwa ita bata ta6a takawa ta je inda suke ba, hakazalika tun zuwan da ya yi sau daya bayan aurensa ya wuce da Hasiya bai k'ara takowa garesu ba don ko mutuwar Hasiya sai Jar Kwami ta je musu gaisuwa.  Har da wannan zafin ta ke ji na dumbin shekaru har goma sha takwas da aka kwashe ba tare da ta sanya dannata a ido ba.      Duk iyakar lalla6awa da ban hakuri da Malam da Malam Balarabe suka bata, babu alamar saukowarta haka suka tattara suka fita inda Malam ya ba wa dansa shawara akan ya yi hakuri har ta huce don a yanzun tana cikin zafi ne.     Ko bayan fitarsu, dakin Malam din suka nufa har Haruna don Baffa yaba can kasuwa har lokacin bai dawo ba, nan Malam Balarabe ya yi sallar la'asar sannan ya yi zaman hira da mahaifinsa. Acan suma su Ummi sun samu tarba kwarai daga matan gidan da yan uwansu, daidai da Dada ta ja su jiki musamman Ummi wacce ke tunano mata Hasiya yarinya mai shiga rai da sanin ya kamata don shekaru biyun da ta yi a nan wajensu kafin zuwan mijinta sun saba kwarai da ita.     Haruna ya hau ba shi labarin bayan rabuwa, Malam na sauraronsu, anan ne Malam Balarabe ya dubeshi. "Ni kuwa Malam ya labarin Kanwata Aisha? Har yanzu suna can Adamawan? Yaranta nawa da Yakubun?"   Shiru ya biyo baya kafin Malam ya yi dauriyar ba shi amsa. "Sai hakuri Abdullah, Allahn da Ya fimu son Aisha ya kar6i abarsa, yanzun ta shekara da rasuwa." "Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun!" Cewar Malam Balarabe kafin ya soma kuka har da sheshsheka, kanwarsa ma ciki daya ta rasu ba tare da ya sanyata a idanu ba? Rabonsa da ita tun kafin tafiyarsa Ringim.     "Addu'a za mu yi mata, ciwon koda ta ke fama da shi har da abin ya gagara Yakubun suka dawo nan tare da ita don ta yi jinya, saidai takan yawaita tambayarka, har Yakubun yaso zuwa wajenka ya kira mata kai amman Allah baiyi ba, har ta rasu. Yaransu uku, babbar wacce ta ci sunan Hasiya, shekarunta sha shida, tana can Jar Kwami hannun Lamido kakanta, Yusuf da Aminatu kuwa suna can Adamawa hannun mahaifiyar ubannasu.     Malam Balarabe ya jima kwarai cikin jimami don kuwa bayan mutuwar Hasiya, wannan ce mutuwa ta biyu da ta girgizashi. Rayuwa kenan.     "Allah Ya ji kan Aishatu, Yasa ta huta. Zuwa jibi sai naje Jar Kwami mu gaisa da su." "Ku tafi gobe, Manu ya jima yana son ganin jikarsa." Cewar Malam kenan, ya amsa da toh.     Garin ya yiwa Ummi dadi matuka, har hawaye ta yi ganin irin gatanta, ashe daman tana da gata har haka? Kwanon abinci kuwa sai wanda ta za6a ta ke ci, don daga matar Baffa har Halima matar Haruna kowacce saida ta aiko, aka yanka kaji aka soyamusu. Dada sai nan nan take yi da su, acewarta su basu da laifin komai awajenta.......      DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   Wannan naku ne..  SallyMoh Sadia maman ashraf   AB Kura   95 Malam Balarabe da Ummi saida suka yi kwanaki uku kafin su bar Ringim zuwa Gombe don kuwa saida aka yi shari'a a babban kotun jaha dake birnin Jigawa a karshe aka yankewa Habiba hukuncin daurin rai da rai. Ita kuwa Saude bayan an tabbatar dagaske ta haukace kai tsaye aka mik'ata asibiti, cikin danginsu babu daya da ya zo banda Malam Yahuza.     A motar suna tafe har Mariya saidai ran kowannensu babu dadi suna cike da tunani, shi Malam Balarabe tunaninsa bai wuce na irin kar6ar da danginsa za su yi gareshi ba sakamakon watsi da su da ya yi, yayinda a 6angaren Ummi ta ke tunanin rayuwa ta DAN ADAM mai cike da kalabule, ga jarabta kala-kala. Shi dan Adam kwata-kwata a rayuwa ba shi da wani jin dadi da hutu face na idan ya kyautata mu'amalarsa da Mahaliccinsa, wannan kadai zai tsira da shi har mutuwarsa. Abin sai godiyar Allah, kaga dai duk mutum mutum ne amman a halayya da dabi'u an bambanta, wani sai ka rikeshi da gaskiya ya ci amanarka, wani sai ka dunga yi mishi kallon mak'iyinka, batare da sanin shi din mai sonka domin Allah bane, DAN ADAM ne zai fidda makudan kudade, ya aikata dukkan wani nau'i na sa6on Allah don kawai ya k'untatawa dan uwansa DAN ADAM rayuwa, haka kawai sai ya tsaneshi, ya hana kansa sukuni idan ya ganshi cikin jin dadin rayuwa batare da shi din ya yi mishi laifin komai ba, dan uwa sai ya cuci dan uwansa, ya kasheshi.   Ta sanya hannu ta share hawayen da suka zubomata tana mai k'ara rungume Mariya wacce ta yi filo da cinyarta tana bacci.    'Ya Allah, mu bayinKa ne masu yawan zunubai, Ya Allah ka gafartamana, Ka barmu kan tafarki na gaskiya. Ya Allah ka sa mufi karfin zuk'atanmu. Mun shaida babu abinda bautawa sai Kai, mun yi imani Annabi Muhammad(s.a.w) ManzonKa ne. Allah Ka jik'an wadanda suka rigamu gidan gaskiya.' Tana maganar a zuciyarta, sannan ta k'ara goge hawayenta, kwantar da kanta ta yi saman kujera ta lumshe idanu tana tunanin rayuwarta har zuwa yau, tamkar rana makamanciyar yau ba zata zo ba, ranar da komai zai zo karshe.   Haka ta yi ta tunane-tunane har suka iso cikin Gombe bayan sun ci awa kusan biyar akan hanya. Kai tsaye Gombe Motor Park suka shiga sannan kowa ya soma saukowa.    Malam Balarabe ya tarar musu taxi. "Tudun Wada zaka kaimu." ((Pls manage...dare ya yi sai da safe zan dora in sha Allah)) DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   Kin cancanta.... Sis Aisha Kalli...Allah Ya bar zumunci duniya da lahira...ameen. 97      Washegari Dada da kanta ta yafa mayafi ta shigar da Ummi makwafta suka yita ganinta tana nunamusu jikarta diyar Hasiya. Ummi har ta rasa inda za ta saka kanta don murna, fararen hakorannan nata sun kasa rufuwa, a karshe suka dawo gida.  Batun Mariya kuwa, Dada har mancewa ta ke yi da ita don dagaske jininta yafi haduwa da diyar Hasiyarta.    Koda suka dawo anan waje suka tarar da Malam Balarabe da mahaifinsa suna hira. Ta daure fuska tamau kamar bata ta6a dariya ba, ko sannu da zuwan Malam Balarabe bata amsa ba. Ta gaida mijinta ta yi gaba. Haka ya sauke ajiyar zuciya ransa duk ba dadi. Malam ya girgiza kai.  "Kar ka gajiya, ka cigaba da rok'onta gafara, Fatima mace ce mai hakuri saidai tana da zafi idan an ta6ota, ni nasan tana kaunarka matuka, na sha kamata tana kuka duk akanka, yanzun kuma da ka zo sai ta yi fushi? Karka damu zata sauko."   Wannan magana ta karfafawa Malam Balarabe gwuiwa, ya saki fuskarsa sosai. "Ai ni na yi mata laifi, dole na bita a sannu."   Murmushi kawai Malam ya yi.  "Ina matarka ne?" Gaban Malam Balarabe saida ya fadi, cike da damuwa ya labartamishi dukkan abinda ya faru tun bayan mutuwar Hasiya kawowa yanzu da Saude ta haukace da irin tone-tonen da ta yiwa kanta.   Malam banda ambaton Innalillahi babu abinda ya ke yi, tausayi matuka na Ummi da dannasa ya mamayeshi. "Yanzu Hasiya saida ta yi aikatau? Allah Mai Yanda Ya so da bayinSa."   Shima Malam Balarabe da jikinsa ya yi sanyi ya amsa da eh. Kafin ya sanyomishi batun maneman auren Ummin. Da kuma irin taimako da suka yiwa Ummin a rayuwa.   Malam ya danyi jim sannan ya numfasa. "To, shi lamari na aure ai na Allah ne, kwarai sunyi mana halaccin da suka cancanci mu dauki diyarmu mu basu. Allah Ya za6amata abinda ya fi alheri." Malam Balarabe ya amsa da amin.  Haka sukayita hirarsu abin sha'awa.    Bayan Magriba suna zaune suna hira a tsakar gida har Dada, Ummi na kwance ta yi matashi da cinyarta ita kuwa tana aikin tsefemata kai tana fadan tabar kai kitso ya tsufa.    Ita dai banda murmushi babu abinda ta ke yi, ta lumshe idanunta, gatan kawai ta ke gani tamkar a mafarki. Wayarta ta dauki k'ara, ta bude idanunta da sauri, tun dazu ya ke kiranta a hanya saidai ganin tana cikin mutane ne yasa ta jin kunyar dagawa, ta janyo wayar a sanyaye ta ce. "Dada tsaya na amsa waya." Dada ta saki kannata, ta dan dubi Dada, ita din kuwa ta zubawa ido, kawai sai ta mike a guje ta fada daki tana murmushi daidai lokacin da ta ke amsawa da sallama.    Wata nannauyar ajiyar zuciya ta ji ya saki wanda ta ji shi har cikin ranta. A sanyaye ya amsa sallamar gami da fad'in.   "Ki yi hakuri kin ji don Allah." Ta kasa gane inda maganarsa ta dosa, ta yi hakuri fa? Yaya Faruk ke bata hakuri? "Hakuri kuma? Akan me?" "Ba ki ji yanda hankalina ya tashi jin shiru ba ki amsa wayata ba Ummi, har ina niyyar biyo bayanki Gombe." Ta numfasa sannan ta murmusa, duk a zatonta wani abin ne daban ko kuma cewa zai yi ya fasa aurenta.   "Kai zan bawa hakuri Yaya Faruk, wallahi muna tare da su Dada ne ni kuma kunyar daukar wayar na ke yi."   Ya yi murmushi mai sauti. "Karki damu, ya wuce, saidai dagaske ina jin zan shigo Gombe karshen satinnan, nisan ya na takurani, na soma gajiya da rashin ganinki." Ta kasa cewa komai sai murmushi, a haka Dada ta shigo daukar damammiyar furarta a kwanon sha ta ganta, duk sai ta diririce, Dada murmushi kawai ta yi ta fice. "Kin yi shiru, dagaske za ki iya ganina."   "Ba ka kunyar su Daddy?" Ta fada cikin sanyin muryarta. Ya dan yi dariya.     "Haba Ummi, Daddy fa ki ka ce? Kar ki damu, sunsan irin kaunar da nake miki wacce sai na daure matuka na ke iya 6oyonsa, bansan wace irin addua ki ke min na har kullum kaunarki ke k'aruwa cikin raina." Ta girgiza kai tana dan dariya kawai.  Sun dan jima suna hira sannan suka yi sallama.   Koda suka kammala sai ta kasa fita ta yi zamanta a dakin ta kwanta saman gadon karfen Dada tana game. Can jimawa kadan Dada ta shigo tana fadin. "Wai 'yarnan ba ki gama wa..." Ganin da ta yi mata kwance tana wasa da waya yasa ta rike ha6a. "Au, tsifar kenan? Shi ne ki ka yi kwanciyarki anan? To kin kyauta ai daman dare ya yi nima hannuna ya gaji, taso ki sha fura ga farfesu can Abida ta aikomiki."    Ta mike tana mai kokarin rufe kanta da dankwali don sam bata mance tsifar ake mata ba, kawai nauyinsu ne ya hanata fita.     "Allah Yasa ba sukari sosai a ciki irin na dazu."    Dada ta murmusa. "Kema bakya son sukari sosai? Allah Ya jik'an Boddo, itama haka ta ke ko kadan bata son sukari. Komai naku dai daya."   Jin haka yasa Ummi zamowa daga gadon bayan ta amsa da amin. "Ni kuwa Dada wai da wa Ummana ta yi kama tsakanin kakana da kakata."    Jin haka yasa Dada zama gefenta gami da dubanta fuska a sake.   "Mahaifiyarki ta dauko kamannin Kakanki Usmanu Lamido, wanda suke kama sosai shi da yan uwansa, musamman babbar yayarsu Bintu dake aure garin Adamawa da yaranta uku, danta namiji guda ne Allah Ya azurta mata shi, a hannunta Karamar uwarki (Zahra) wacce suke kira da Inno ta girma, ana shirin aurenta ta rasu.  Idan da zaki ganta itama marigayiya Zahra, sai ki rantse mahaifiyarki ce don kamannin da kuma jini.   Ta jinjina kai kafin ta k'ara da fadin. "Wai akwai yan uwanmu ne a Adamawan nan sosai? Naga har kanwar Baba itama can aka ce ta yi aure har ta rasu." "Dangantaka mai karfi kuwa da Adamawa, duk kuwa da asalinmu Kwami da Jar Kwami, saidai mazajenmu da iyayenmu sun yi tafiye-tafiye, wasu suka yada zango Adamawa har suka tara iyali. Ba acan ne shi Lamido Shuaibun ya auro mahaifiyar Yakubu mijin marigayiya Aishatu kafin kuma su rabu ta koma can, a hannunta Yakubun ya girma ai wani zuwansa nan ya ga Inna Boddo a Jar Kwami ya nuna yana so, sai mutuwa ta rabasu." Ummi zata k'ara magana saidai bata samu dama ba, don Dada mikewa ta yi.   "Kinga, tashi mu je ki sha fura sai mu zo ki ban mijinnawa a waya mu gaisa don na lura sai kumbiya-kumbiya ki ke kada ya ji muryata ya fasa da ke." Jin haka Ummi ta yi dariya tana rufe fuskarta, Dada ta fice itama tana yar dariyar.    Washegari.... Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Novels villa Duniyan novels Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: +2347039625239        DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 98 Washegari misalin takwas bayan sun gama karyawa suka yi shirin tafiya, kamar kullum, yau ma  Malam Balarabe ya shigo har dakin Dada don gaisheta, saidai ko kallo bai isheta ba, Ummi tana duban mahaifinta cike da tausayi har ya gaji ya kara da fadin. "Za mu wuce." Uffan ba ta ce ba sai ma mikewa da ta yi ta fita, ya dan bita da kallo jiki a sanyaye kafin ya dubi Ummi. "Idan kun gama sai ku fito, bari na je nan makwafta wata gaisuwa na dawo." Ta amsa da to, bayan fitarsa ta ja bakin mayafinta mai adon jajayen fulawa ta rufa akan riga da siket din dake jikinta na wani fari da jan yadi, ta ci kwalliya don ta fi so suna ganinta cikin lumana koda suna fushi da mahaifinta su huce. Idan ka ga Ummi ba zaka ce itace ba, ta yi kyau kwarai hakanan ta ciko a kwana ukun da sukayi kacal, babu damuwa babu mai tsangwamarta ko kuma jifanta da kallon banza balle uwa uba gorin gida. Shigowar Dada ne ya katse tunaninta, ta rataye bakar jakarta. "Kaga 'yata ta fito." Ta dan tamke fuska don har zuciyarta bata jin dadin abinda Dada ke yiwa mahaifinta. Ganin haka yasa Dada ta rude. "Ke meyafaru? Ko wani abin ya ce miki?"  Ummi ta dan karyar da wuya sa'ilin da ta ke zura takalmi kamar bata so ta ce. "Don Allah Dada ki daina yiwa Babana haka ba dadi, don girman Allah ki yafemishi. Ya yi muku laifi saidai shima ba laifinsa ba ne, da kanta Saude ta tona dukkan mugun ayyukan da ta yi ciki har da.." Zata fadi na kashe Ummanta da ta yi sai kuma ta yi shiru don batasan zafin da zata kara dauka ba.   "Bari ki ji kadan daga abinda ya faru." Ta soma koro mata bayani a gajarce, da kadan cikin zaman da suka yi da Saude bayan mutuwar Hasiya da aikatau da ta yi da irin karamcin mutanen da suka dauketa aikin har zuwa komawarta Ringim da yanda abubuwa suka kasance har da haukacewar Saude da kai Habiba gidan yari. Ta dubeta. "Naso 6oyemiki cewa kashe Ummana sukayi saidai naga kamar ba amfani. Komai da ya faru babu laifin Baba, idan hakane nima zan iya yin fushi ai tunda babu wani cikin yan uwan Ummana da ya nemeni, amma na yi hakuri da na fahimci ba ku da laifi kusan laifin na Saude ne tunda Baba ba cikin hayyacinsa ya ke ba. Ko don wannan don Allah ki yafemasa."   Dada ta dan daure fuska. "Jeki suna jiranki, Allah Ya saukeku lafiya, ki gaidamin Inna Boddo."   Ummi ta dan yi murmushi a sanyaye kafin ta amsa da toh sannan ta juya ta fita. Dada ta bita da kallo, kafin bayan fitarta ta zauna da6as a saman gado. Kawai sai ta soma shar6ar kuka tana ambaton Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun! Ashe haka lamuran suka afku? Ko jiya Malam ya yi niyyar fadamata saidai bata ba shi dama ba asalima tashi ta yi ta bar wajen. Ta tausayawa dannata ainun amman daman wanda bai ji bari ba zai ji hoho, illar rashin jin maganar iyaye kenan, sai gashinan ya janyowa kansa bala'i.    "Allah Ya jikanki Boddona, Allah Ya yi miki rahma." Ta fada a hankali.      Acan kuwa su Ummi suka gama sallama da kowa suka kama hanyar Jar Kwami har Haruna wanda shi ya yi musu rakiya.     Bayan sun isa kai tsaye gidan Lamido Shu'aibu yaya awajen Manu kakan Ummi.    Ummi ta dubi gidan, gidan gargajiya, saidai babba ne, suka shiga ciki. Anan kofar gidan k'asan 'yar rumfa, Lamido Shu'aibu ne kishingide saman wata darduma akan tabarma, ga wasu dattijai su biyar zaune gefensa ana hira, saidai ganinsu ne yasa su maida hankali garesu. Ummi ta lura da mutum uku masu kamanni farare ne saidai tsufa ya dakusar da haskensu. Malam Balarabe da Haruna ne suka karasa suka durkusa wajensu, yayinda Ummi da Mariya suka durkusawa a gefe suma. Bayan an gaisa, Lamido Shuaibu  cikin harshen fulatanci ya ke tambayar ko su waye.    Shima ya ba shi amsa da fillancin ai tuni waje ya karade da murna, Malam Balarabe ya karasa suna dafashi baki a washe, wani har da goge kwallar farin ciki. Tsoho Mai ran karfe Usmanu Lamido ya dubi Malam Balarabe da harshen fulatanci ya ce. "Ashe da rabon na kara sanyaka a ido kafin na mutu Abdullahi?"   Kunya ta bi ta cika Malam Balarabe ya hau bada hakuri yana nuna ba laifinsa bane. Ya waiwaya ga su Ummi.  "Ku karaso nan." Suka taho, Ummi ta durkusa ta gaishesu, suka zubamata idanu.  "Wannan itace diyar wajen Hasiya, itama Hasiyar sunanta, Ummi."    Suka yi kabbara. "Ai ko baka fada ba na ga kamanni, matso gareni Boddo." Cewar Dattijo Usmanu. Ummi ta matsa gareshi tana jin hawayen farin ciki na kokarin zubomata. Ya rungumeta ya fashe da kuka, itama kasa jurewa ta yi ta sanya kukan, bawan Allah jikinsa har rawa ya ke yi. Saida aka basu baki sannan ya yi shiru. Ya dagota yana shafa fuskarta kamar Boddonsa.     Ta karasa ga Lamido Shuaibu shima ya dafa kanta yana murmushi mai bayyana hakora, duk girma ya kamashi dakyar ya ke gane mutane.  "Allah Ya yi miki albarka. Ya ji kan Mammarki."   Ta amsa da amin. Bayan duk an gama gaisawa sukayi cikin gidan inda tuni labari ya je musu ga diyar Hasina ta zo daga burrni. (Lol).    Nan aka zubawa Ummi ido ana kallonta baki sake, wasu dakyar suke samun karfin gwuiwar gaishe da su sakamakon ganin tsantsar kamanninta da mutan gidan. Kai tsaye Haruna ya nufi da su 6angaren Inna Boddo wacce tuni labari ya iso gareta saidai babu mai kaita ta ganota. Inna Boddo wacce ko tashi bata iya yi saida wanda sakamakon ciwon kafa da ta ke fama da shi, tana zaune a tsakar gida cikin rumfa saman gadonta na karfe don koyaushe nan ne wajen zamanta saidai yaran gidan su zo nan tayata hira.    Shigowarsu ce ta katse tunaninta, ta zubamusu ido, tana hada ido da Ummi ta zaro ido. "Boddona!" Sai kuma ta soma kuka tana mikamata hannu, a guje Ummi ta karasa ga kakarta don ta gane wacece daga sunan da ta ambata, suka rungume juna. Fuskar kowannensu cike da farinciki.    Bayan an gaggaisa, ta ke tambayar Malam Balarabe sadda ya dawo, a kunyace ya bata amsa ya kara da neman gafara. Ta yi kamar bata ji ba don kuwa kokusa bata da rikeshi ba. Mariya dai an zama yan kallo sai rarraba idanu kamar shege a rabon gado.     Ranar Ummi dai ra rasa inda zata sanya kanta don dadi, haka ta wuni cikin yan uwa, dangi sai zuwa akeyi rututu ganinta. Wasu sunfi danganta kamanni da yanayinta da Inno Zahra data rasu saidai ita tana da yawan barkwanci da dariya, wasu kuwa sun fi karkata ga Hasiya.    Ranar fura da nono har saida ta ture, ga cima kala-kala da aka kawo musu. Mariya tana samun yaran abokan wasa shikenan kuma ta saki jiki har ta fice tare da su.    Ranar Ummi ta mance dukkan wasu bakkan cikinta. Kwanan Malam Balarabe biyu suka juya tare da Dan uwansa da kuma Mariya wacce itama ya ke son kaita ganin dangin mahaifinta wadanda bata sani ba, ba kuma yaso nan gaba azo baya raye ta tambaya ba wanda ya sani.     Ummi ta zama 'yar lele, kullum cikin hira, idan ta jima wajen Inna Boddo, nan kakanta zai nemeta, nan ma ba jimawa sauran matan musamman uwa ga Inno da Binta, Danejo itama zata shiga nemanta, don tunda ta ga Ummi ta ji kamar Innonta ce ta dawo. Rayuwa kenan, bayan wuya sai dadi idan har mutum zai jure ya yi hakuri da dukkan lamura, Allahu Ya bamu ikon juriya da hakuri ba don isarmu ba, Amin.     Ranar talata da misalin biyar na yamma, Ummi da wata yar uwarta Abu wacce itama jika ce a gidan suna tafe a hanyarsu ta zuwa gona kaiwa baban Abun abinci. Ummi na sanye da doguwar riga bulu mai adon fulawoyi bakake, ta tufke gashinta wanda tun tsifar da Dada ta yi mata bata yi kitso ba, fuskarta fayau, ta yafa mayafi akanta bata ko daura dankwali aciki ba, sai gashin ya yi tudu a tsakiya kadan, tana wasa da karar dake a hannunta. Suka tsinci muryar yayan Abu, Gidado yana kwalamusu kira ta bayansu. Tsayawa sukayi gami da juyawa, gaban Ummi ya yi wani mugun faduwa ganin wanda ke tare da Gidado. Murmushi tattausa ya ke jifanta da shi da kallon dama na fadamiki... DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   99 Kasa kwakkwarar motsi Ummi ta yi, ya hade cikin farin yadi wanda ake ganin farar singiletinsa ya dora bak'ar hula hakanan takalminsa bak'i ne. Ya yi kyau kwarai duk ya chanjamata. Abu  ke tambayar Gidado abinda ya faru. Daidai lokacin da suka karaso wajensu ya kasa dauke idanunsa daga Ummi.    "Bak'o ki ka yi, tare da Mai sunan Baffa(Usman kanin Malam Balarabe) ya zo, bayan an gaisa kuma ya ce bazai jira ku dawo ba na yi mishi rakiya." Duk wannan dogon bayanin da Gidado ke yi gareta ita gaba daya jikinta ya yi sanyi, Yaya Faruk? Ina ya baro aikinnasa? Yanzu babu kunya ya cewa su Daddy zai zo wajenta? Wayyo, wannan abu akwai kunya. Saida ta ji Abu ta gaisheshi da hausa ne ya amsamata da fulatanci har Abu na dariyar mamaki, itama ta dawo hankalinta, ta tuna ashe fa shima bafulatanin ne.    Ta durkusa ta gaisheshi da girmamawa kamar yanda ta saba. Ya amsa, Gidado ya dubesu. "To, za ku juya ne ko mu wuce tare?" Faruk ya dubeshi har lokacin fuskarsa da walwala. "No ku karasa, ta nan za ku biyo ko?" "Eh." Abu ta amsa. "Idan kun zo nan sai mu koma tare." Suka amsa da to kafin su soma tafiya, shi kuwa baice uffan ba ya soma tafiya ya nufi wajen wani dutse ya sanya hankicif gami da zama. Garin babu rana sai ma hadari da ke haduwa. Ya dubeta, ta sunkuyar da kanta ta soma takowa don ta fahimci manufar kallon, gefe ta dan zauna.    "Sai ki ka ga Faruk ko?" Ta murmusa. "Ai na yi mamaki, naga kuma yau ranar aiki." Yana binta da kallo ya amsa. "Kar ki yi mamaki, kina da daraja da matsayi babba awajena wannan yasa ni daukar hutun sati kawai don na zo na ganki. Na horu da yawa fa Ummina, ji yanda na ajiye k'ashin wuya sadda ke ki ke mulmula k'iba har wani tumbi ki ka ajiye." Ya karashe a shagwa6ance kamar yana gaban Hajiyarsa. Kunya da dariya ta kamata lokaci guda. Ta dan ja mayafinta da ya zamo har ana ganin kwantaccen gashin goshinta wanda ya kusan haduwa da gira. Tabbas tasan ta yi k'iba saidai bata hango tumbin da ya hanga ba. Ya dan daga gira. "Dagaske nake." "Um, ya akayi ka zo nan?" "Garin masoyi yana nisa ne?" Bai saurari amsarta ba ya cigaba. "Zuciyata ce ta kasa samun nutsuwa, rashin ganin mahadinta kwana biyunnan ya jefata cikin tarin damuwar da ba za ki gane ba. Da naga ina neman mutuwa kawai na yanke shawarar biyo jirgi na taho Gombe. Ina isa kai tsaye na kira Babana, shi kansa ya yi mamakin jin wai ina Gombe, ya fadamin sunan unguwar ya ce idan na shiga tasi na hadashi da direban. Ya mishi kwatance, Alhamdulillah, don kuwa Ummina yan uwanmu sun min kyakkyawan tarba sannan sun ji daga bakin Baba cewa ni ke son aurenki. Jiya na iso Gombe, sai yau na taho nan. Kin gane dagaske Faruk bai iyawa babu Hasiya?"   Ta rufe idanunta tana murmushi, har cikin ranta wani wutar kaunarsa ke kara ruruwa. Bata ji tashinsa ba sai bude ido da ta yi ta ganshi durkushe gabanta ya kuramata idanu yana murmushi, yayinda ya tokare hannun damansa saman dutsen. Sunkuyar da kanta ta yi.       "Mu godewa Allah da Ya amsa mana addu'armu ya sadaki da farincikinki, na tayaki murna ainun Ummina. Abu daya ya rage mana."   Ta ji sarai abinda ya ce sai ta basar. "Nagode Yaya Faruk."   "Dayan fa? Ba za ki yi tambaya akansa ba?"   Ta dan saci kallonsa yanda ya ke maganar cikin rad'a-rad'a. Ya kashemata ido daya, ta yi kasa da kanta da  sauri.   "Ko bakyaso ki ganki a gidana matsayin matata?"   Da sauri ta karkata  ta kauce daga saitinsa tana mai ambaton Innalillahi a fili don ji ta ke kamar ta dora hannu a kanta don kunya. Dariya sosai Faruk ya shiga yi adaidai lokacin da iska ta yi awon gaba da mayafinta, ta rike kannata tana mai da na sanin fitowa ba dankwali, tunda suke da Faruk bai ta6a ganin gashinta tsirara har haka ba, ya yi mata kallo daya yana mai kauda kansa da sauri alokaci guda ya na mai tsintar yanayinsa da chanjawa, ita kuwa da sauri ta janyo mayafin ta rufe gashinta sannan ta mike tsaye, muryarta ba rawa ta ce. "Yaya Faruk mu tafi kada ruwa ya riskemu anan kaga har yanzu ba su tahowa." Ya sanya hannuwansa cikin aljihun wando, yana mai shakar daddad'ar iskar da ke kadawa, kafin ya juyo ya dubeta sannan ya yi kasa da kansa. "Muje." Ya fada cikin yanayi na mutuwar jiki. Ta fahimci kamar yana niyyar barin hankicif dinnasa anan, shi kuwa yana sane ya yi hakan, ta dan saci kallonsa, ganin ba ya kallonta yasa ta dauka da sauri ta cusa a riga, ya yi kamar bai gani ba sai ma juyar da kan da ya yi yana murmushi ya soma tafiya. Suna cikin tafiya suka ji yo muryar su Abu da Gidado, hakan yasa suka tsaya suka jera tare suna tafiya da dan sauri-sauri ganin yanda ake iskar sosai, don ma a dazun ba wani nisa Ummi da Abu su ka yi ba ya taddosu.     Suna dab da karasawa aka soma yayyafi, cikin taimakon Ubangiji ruwa bai tsuge ba sai bayan isarsu gidan. Suka yita godiya ga Allah.     Faruk bisa jagorancin Gidado ya koma dakin Dattijo Manu, wanda a yan kwana biyunnan ne ya dan ji saukin jikinsa don yana fama da hawan jini.      Bayan sunyi sallar Magriba, Faruk ya sanya (jacket) sakamakon sanyin da garin ya yi, sannan suka shiga hira da harshen fulatanci, Faruk ya daukeshi tamkar Modibbo, Dattijo Manu na watso mishi tambaya game da ko su fulanin ina ne yana amsawa dalla-dalla. Kafin shima ya labartamishi nasu, ya ji dadin hira sosai da Faruk din, shima Faruk din ya sake da shi ainun don bai ji nauyin sanarmishi yanda ya ke kaunar Ummi ba wanda hakan ba karamin dadi ya yi masa ba. Cikin tsokana ya ce. "Saidai fa banason kara yin nisa da amaryata." Dariya Faruk ya yi. "Karka damu, akai-akai za ka dunga ganinta, idan ta kama ma ai sai mu daukeka mu maidaka Abuja." "Kayya, barni inda nafi wayo, nan Buba ma ya yi da ni akan na koma can birni Gombe wajensa na k'i." Duk suna maganar da fulatanci suna dariya.    "Nima inaga mun kusa zuwa Adamawa, amma fa da Amaryata."   Cewar Faruk cikin wasa da dariya har ya bawa Dattijon dariya. Saida ruwa ya tsagaita sannan Inna Boddo ta umarci Ummi da kai musu abinci, ta yi tsuru da ido saidai ganin ba yanda ta iya ta ja Abu suka wuce tarr kowanne dauke da kwano bibbiyu don har kaza aka soyawa Faruk, gaba daya dattijan ke haduwa su ci abinci tare saidai ruwa yanzu ya hana hakan ita kuwa tunani ta ke yi Faruk dan gayu dan hutu da shi anya zai iya cin cimarsu? Haka dai suka karasa da sallama, bata kallesu ba, kai a kasa ta gaida Dattijo Manu, ya amsa yana fadin. "Amaryata ki yi zamanki anan kinji? Sai kin iya fillanci." Murmushi kawai ta yi, duk yanda Faruk ya so su hada ido ta k'i, saida suka kawo musu komai har ruwan wanke hannu da na sha na randa mai sanyi sannan suka fita.      Ummi kuwa kowa a gidan cewa ya ke ta yi sa'a ga shi mutumin kirki ga shi kuma bafulatani shima, murmushi kawai ta ke yi ba ta cewa komai.    Tana kwance a dakin Inna Boddo, Innar na cikin sange(mosquito net) an lullu6eta da bargo mai kauri sosai saboda sanyi. Bayan ta tabbatar Innar ta yi nisa a bacci ta fiddo hankicif din ta rufa a fuskarta tana mai shak'ar kamshin idanunta a lumshe, murmushi saman fuskarta. Wayarta ta soma k'ara da sauri ta zarota daga k'asan filo ta danna kada Inna ta farka, Faruk dinne kuwa. Ta dafe kirji kadan, a hankali ta sauka daga gadon ta fito waje ta zauna.    "Ummina." "Um." "Na yi mantuwa fa a wajen dazu." Ta zaro ido gami da hadiye miyau na fargaba. "Mantuwar me?" Ya danne dariyarsa yana duban Dattijo wanda munsharinsa ya hanashi runtsawa kwata-kwata.  "Hankicif dina, ko kin ganshi?" Idanunta ya yi kwal-kwal, to ta ce me? Ta ganshi yana wurinta? Me zata yi da shi da bata mayarmishi ba? "Kinyi shiru." ((Afuwan..ni kaina na qagara na kammala muku saidai haka Allah Ya nufa labarin zai fi yanda na zata a tsawo...not much..lol)) DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 100 Ta runtse ido gami da dan mak'e wuya kamar wacce ake shirin kaiwa mari, ba ta ce komai ba.   Ya kasa rike dariyarsa saida ya dara kadan. "Ummina kenan, ki rikeshi na bar miki."   Ta zaro ido kawai saita kashe wayar don kunya, ashe daman ya ganta? Ya k'ara kira bata daga ba, karshe ma ta kashe wayar.     Washegari misalin takwas na safe, tana zaune tana shirin karyawa suna waya da Amina wacce ke labartamata cewar itama za su je Nijar dangin mahaifinsu su dawo, ta tayata murna a karshe ta sanarmata Faruk yana nan. Amina ta yi dariya kwarai. "Oh wannan soyayya ta ku? Kedai ki yi ta godiya ga Allah da wannan babbar kyautar." Murmushi kawai Ummi ta yi mai bayyana hakora.     Sun sha hira sannan su ka yi sallama.     Kwanan Faruk biyu ya soma shirin komawa bayan zuwan Malam Balarabe garin an zauna an tattauna inda ya yi musu bayanin karatun da Ummin ta soma a Abuja, sun ji dadi matuka saidai basu aminta da komawarta gidan surukai ba, haka dai ba don ya so ba ya hakura da raayinsa, yasan idan ya turo su Daddy to watakil su amince ta koma can.    A zaure suka tsaya suna sallama, Faruk ya dubi Ummi gaba daya ji ya ke kamar ya zubda hawaye, ita kuwa kanta a k'asa, ya fiddo wayarsa ya kara daukarta hoto, sautin camera yasa ta fahimci abinda ya ke. Ta ja hijabinta tana fadin. "Kai Yaya Faruk na kusan goma kenan fa."   "Ke an fadamiki ina gajiya da kallon hotunanki?"    Murmushi kawai ta yi mai bayyana hakora kafin su yi sallama, a sanyaye ta mishi adduar isa lafiya suka yi sallama ran kowannensu cike da jin kewa.     Saida Ummi ta yi sati biyu a Jar Kwami, kawarta ta islamiyya, Husna A Rashid har ta gaji da tambayar ranar dawowarta makaranta ganin lokaci ya ja bata dawo ba. A wannan sati biyun har Kwami ta je ta ga dangin kakarta wadanda wasu da yawa sun rasu, kwananta biyu ta dawo sannan ta wuce birnin Gombe gidan su mahaifinta.      Kwanakinta uku da zuwa ta lura da sauyin da aka samu tsakanin mahaifinta da Dada don zuwa yanzun ta sake da shi ta nunamishi komai ya wuce abin ya bata mamaki ya kuma yi mata dadi don har hira sosai suna yi.    Kamar yau juma'a da yamma, sun hadu gaba daya tsakar gida ana hira, wayar Malam ta yi kara. Ya saki fuska sosai ganin Malam Yahuza ne. Fadi ya ke. "Yau Yahuza ne ya tuna da ni?"   Ya dauka da sallama, bayan gaishe-gaishe Malam Yahuza ya soma ba shi labarin bayan rabuwa, ya sanarmishi ya samu ya shirya da yan uwansa ya nemi gafararsu, ya gangara kan labarin da ya ba shi mamaki da al'ajabi har saida ya tashi ya bar wajen yana fadin. "Innalillahi." Suka bishi da kallo musamman Ummi da ta ji wata irin faduwar gaba don tsoronta ya kasance ko Habiba ce ta gudu daga gidan yari.     Bayan ya gama wayar ne ya dawo, anan Haruna ke tambayarshi ko lafiya. Ya dubesu. "Diyar Malam Yahuza, Dije, 'yar Baba kin santa ko?" Ta gyada kai don hankalinta ya dan kwanta. "To itace mijin ya turowa mahaifinta takardar sakinta, aciki ya ke shaidawa mahaifin ya kamata tana mu'amala da yar uwarta mace, ya yi mata duka ya korota tun washegarin faruwar lamarin saidai an tabbatar mishi bata zo wannan yasa yanke turomishi takarda. Bayan haka kuma da kwana biyu labari ya riskeshi cewar an ganta can gidan wata Bokanya ta je tare da abokiyar shaidancinnata har an samu wasu sun k'ona gidan kurmus. Dakyar ita Dijen ta samu arcewa, fitarta kuma ta hau titi da zummar tsallakawa mota ta bi ta kanta."   Kowa a wajen ya dauki salati. "Duniya abar tsoro, wannan masifa da me ta yi kama?" Cewar Baffa kenan, Dada ta ca6e. "Karshen duk wani mai aikata mummunan aiki kenan matukar bai tuba ba, Allah Ya karemu da al'ummar musulmi ga fadawa halaka irin wannan." Ummi girgiza kai kawai ta ke yi tana salati, lamarin mutane abin tsoro, wani abin kamar a mafarki, ba don na kusa da kai bane idan ka ji a wani wajen kana iya cewa ba gaskiya bane.  "Allah Ka sa mu cika da imani." Cewar Malam Balarabe, suka amsa da amin.       Washegari misalin karfe uku na rana, Ummi kwance a dakin Antinta Abida matar Baffa tana karanta wani littafi na Ahlari da ta taho da shi, ta tsinci muryar Baffa na tambayar Abida ta ba shi tabarma anyi bak'i daga Abuja. Batasan sadda ta mike tsaye ba tana lek'ensu ta windo.    "Su waye?" Cewar Abida tana mai mik'amishi tabarmar. "Maneman auren Ummi." Ai batasan sadda ta dafe kirji ba gami da komawa saman kujera ta zauna.  "Su Daddy ne?" Shine tambayar da ta jefi kanta da shi a fili. "Ina ki ke 'yar nema? Fito nan ki ji labari mai dadi." Cewar Abida tana kokarin shigowa dakin, a guje Ummi ta mike ta 6uya bayan labule tana dariya ciki-ciki.     "Au 6uya ki ka yi? Kya ma fito, ai ni tun ganin da na yi wannan saurayin ya kasa hakuri ya biyoki har nan, nasan ba lallai ya iya hakurin barinki ba."    Ta daga labulen da Ummi ke 6oye, ganin haka ta durkusa tana mai rufe fuskarta da hannu tana dariya. "Kai don Allah Anti." Abida ta dara. "Za ki san Anti, bari mu zo mu soma gyaraki yarinya." Daga haka ta saki labulen ta koma duba sanwarta.    Ummi ta fito ta zauna da saman kujera tana dariya, karatun dai bai samu shiga ba.             Gen. Ahmad Danzaki ne, sai kaninsa Alhaji Aminu Danzaki da babban Abokin Gen. Ahmad Danzaki, wato Major Yusuf Bashir mahaifi ga Sa'ad miji ga Baraka. Sai ko Babban Yaya wanda shi ne ya tuk'osu daga Abuja, bayan shigowarsu da tambaya suka iso unguwar sannan suka yi kiran Malam Balarabe kamar yanda suka tsara ya tura aka taho da su.    ((Thanks for your votes on wattpad.... Love you all..))  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR      101 Har la'asar, Ummi na mak'ale wajen Abida ta kasa fitowa. Tana cikin sallah   ya shigo, tana ji suna magana k'asa-k'asa da Abida, sai kuma ta ji Abida ta soma bud'a wanda ya sa Ummi gabanta ya fadi adaidai lokacin da ta sallame. Furucin da Abida ta yi ne yasa ta durkuso a wajen tana salati....!    "Alhamdulillah, Allah Shi ne abin godiya, amma ya akayi haka ta kasance?" Cewar Abida kenan. "Wallahi abu na Alllah, da kansu suka buk'aci hakan sai kuma Malam bai musa ba don a farko sun bukaci komawarta Abujan saboda karatun da ta soma amman bamu amince ba, sai suka yanke shawarar kan a daure auren kawai, to shine fa aka daura, tarewa kuma aka barshi nan da wata daya."    Duk wannan bayanin da Baffa ke yi a kunnen Ummi, ta ji jikinta ya yi mugun sanyi, take ta ji ruwan hawaye na kwaranyo mata, wai shikenan ta zama MATAR AURE? Ta zama mata wajen Umarul-Faruk Danzaki? Allah mai Iko, yanzu komai za ta yi saida izninsa?    Tana nan durkushe saman darduma tana hawaye, Abida ta shigo bayan fitar maigidanta.     Ta rik'ota. "Haba Ummi, kukan menene? Godiya za ki yiwa Allah, wannan ikon naSa ne anzo da zummar a sanya rana aka daura aure gaba daya kinga kuwa babu mai yin hakan sai Allah."   Haka ta ja ta har suka isa dakin Dada, nan sauran jama'ar gidan suka yi mata caa, ita kuwa jikin Dada ta shige tana kuka, kukan da batasan dalilinsa ba. Hakanan ba zata iya tantance yanayin da ta ke ciki ba, farin ciki ko akasinsa.     Kiran da Malam ya aiko ayimata ne yasa ta dan nutsu.     Har lokacin daman hijab dinne jikinta, tana tafe kanta a k'asa har ta shiga rumfar Malam inda anan su Daddy ke zaune, sun yi sallah sun ci abinci.    Bata iya kallon kowa ba ta durkusa ta gaishesu, suka amsa. Daddy ya ce. "Ke kuma daga mun bawa Balarabe aronki shikenan sai ki mak'ale ki gujemana?" Ya karashe da dariya, su dinma dariyar su ka yi ita dai murmushin yak'e ta yi don har lokacin jikin ba dadi.     Ta mike ta tafi bayan sun sallameta, a ranar su Daddy suka koma. Bayan tafiyarsu Malam ya kara kiranta. Zaune ta samesu su uku, da Baffanta Haruna sai Babanta da kuma Malam din.    Malam ne ya soma magana. "To Hasiya, kinga dai yanda Allah Ya yi lamarinsa ko? To inaso ki yarda da hakan a matsayin kaddararSa, Allah Ya yi yau din ita ta kama ranar daurin aurenki ba baiko ba. Sadakinki dubu hamsin muka kar6a don neman albarka cikin aure. Yanda su ka ce, gobe litinin zasu turo direbansu idan yaso a wuce da ke can, sun buk'aci komawarki zuwa zuwa lokacin bikin ba don komai ba sai domin karatun da ki ka soma kada ayi miki nisa. Ina fatan ba za ki bamu kunua ba Hasiya?"   Shiru ta yi cike da jin nauyi yayinda hawaye ya zubomata don babu abinda ya fado ranta sai matan su Babban Yaya da kuma Ikram da abokiyarta Ihsan wadanda a rayuwa basu kaunarta, a gefe kuma wane irin kallo Mami za ta yi gareta? Malam ya cigaba da nasiharsa, a karshe shima Baffa Haruna ya tofa nasa sannan ta suka sallameta ta koma ciki.    Da Magriba tana kwance saman gadon Dada duk jiki babu kwari ta luluk'a cikin duniyar tunani wayarta ta yi k'ara wanda har saida ta firgita, salati ta yi sanya a hankali sannan ta janyo wayar, gabanta daman tuni ya ke bugu da sauri-sauri, ta sauke ajiyar zuciya ganin ba wanda ta zata bane. Ganin sunan Antinta Amina yasa ta dagawa da sallama. Dariya Amina ta yi bayan ta amsa tana mai rangad'a bud'a. Ummi ta runtse ido tana murmushi kawai.  "Kai Ummi, wato maimakon ma ya kasance ni ce farkon ji shikenan saidai na ji a wajen su Hajiya Mama? Ba ki bugomin waya ba?" Ita dai Ummi shiru kawai ta yi mata, dariya Amina ta yi, ai nasan daman babu abinda za ki ce. To Ummi, Allah Ya sanya alheri, hakika na tayaki farinciki sosai. Nima gobe za mu wuce Nijar yanzu haka ma ina tare da Inna. Sai lokacin ta yi magana. "Allah Ya kaiku lafiya Anti, ban ita mu gaisa." Amina ta mik'awa Inna. Bayan sun gaisa Inna ta yi mata fatan alheri, murmushi kawai ta yi a kunyace ba tare da ta amsa ba, Inna ta dan yi mata nasiha kadan sannan ta mik'awa Amina wayar suka yi sallama.     Ta ajiye wayar tana shirin komawa ta kwanta Dada ta shigo. "Wai ke ba zaki tashi haka ba ki sanya wani abu a cikinki?" Ta dan tur6une fuska. "Dada bana jin yunwa fa." Dada ta zauna gefenta tana murmushi. "Ina fa za ki ji? Farinciki ya cika miki ciki kinmin kwacen miji kin ji dadi ko?" Batasan sadda ta 6oye kanta a saman cinyar Dadan ba, kamar za ta yi kuka ta ce. "Kai don Allah Dada." Murmushi Dada ta yi gami da dafa kanta. "Allah Ya yi miki albarka Hasiya, Yasa ki gado mahaifiyarki wajen hakuri a zamantakewar aure duk kuwa a hakan ma na fahimci kema mao hakurin ce. Wannan aure, auren gata ne, bazan 6oyemiki ba, a dan zaman da yaronnan ya yi tare da mu na fahimci da yawa cikin kyawawan halayensa, kwarai yana sonki don banajin ko Abdullahi mahaifinki yana miki son da Umar ke yi miki. Ki yi biyayya ga dukkanin umarninsa, ki dage ainun ki bawa marar d'a kunya wajen neman ilimi Hasiya, wannan shine babban gatan da ki ka rasa a baya, kada ki sake ki yi wasa da ita. A kulkum ina k'ara ganin daraja da k'imar Hajiya Madina, wacce a labarin da ki ka bani itace farkon wacce ta soma yi miki gatan sanyaki neman ilimin addininki. Allah Ya sakamata da alheri, Ya jik'an Hasiya." Kuka ciki-ciki Ummi ke yi, da gaskiyar Dada, Mami ta taimaketa a rayuwa, babu abinda za ta iya yi ta biyata ita da Abba face addua.     Haka Dada ta yi ta rarrashinta sannan ta mike ta shiga hadamata kaya bayan ta lalla6ata ta zubamata abinci. Anan Ummin ke jin ashe ba ita kadai za ta wuce ba, har da rakiyar Abida da mijinta Baffa wadanda zasu kawai don ganin waje bisa umarnin Malam. Ta ji dadin hakan.   Karfe tara na dare, Anti Halima da Anti Abida suka sanyata tsakiya sunata yi mata nasiha. Ita dai ta kumbura ta yi fum don bata ga amfanin nasihar ba tunda ba tarewa za ta yi ba. "Yauwa, kuma karki sake ki zubda ajinki, karki ba shi fuskar da wani abu zai shiga tsakaninku, zai fi d'okin ki, wallahi ki kiyaye. Duk abinda zai je ya zo karki bari wannan kunuar taki ta yi saurin tafiya kinji ko? Idan ku ka yi hakuri wata daya kamar yau ne." Cewar Anti Halima kenan. 'Wayyo Allah.' Cewar Ummi a zuciyarta kafin ta yi soma kwalla, wadannan me su ka maidata ne? Ganin hakan yasa suka yi dariya don su ganin Ummi suke yi kamar kanwarsu ba diyarsu ba. Ta mike a guje ta bar musu saman tabarmar ta koma cikin daki wajen Dada. "Au ki ka gudu ko? Ai yanzu aka soma." Cewar Abida kenan cikin daga murya. Dada wacce har ta kwanta ta dubeta saidai ba ta ce komai ba.   Kamar jira akeyi ta shigo dakin, wayarta ta soma k'ara, ita kam yanzu duk sadda ta ji k'arar wayar ma sai gabanta ya fadi. Adnan ne, ta ji kamar kada ta daga, shikenan fa labari ya zagaya ga kowa. Ta dan dubi Dada wacce idanunta ke rufe kafin ta d'aga da sallama. Bud'ar da ta ji ya yi ne, yasa ta dariyar da bata shiryamata ba ga kuma kunya da ta ji, yau kuma namiji ne da bud'a? Wannan abu lallai ya bata dariya.   "Kai Yaya Adnan." Ta fada tana dan marairaice murya. Ya yi dariya. "Da girman kujerarki Antina Matar Best, tuba nake ranki ya dade nasan na yi lattin tayaki murna, abubuwan ne sai a hankali, sannan don Allah ki daina kirana da Yayan nan, yanzun ma kina fad'a kamar na nutse don kunya." Dariya ta k'ara yi tana mai sa hannu ta rufe fuskarta, ba zata iya rike dariyar ba, shi dai Adnan ba dai iya tsokana ba. Shima cikin dariyar ya ce. "Atoh, ai gaskiyane, yanzu idan My Best ya ji ai sai ya dauki fushi da ni. To Allah Ya sanya alheri, Ya nunamana ranar aurenku, abin dai zai min takaici don inaga watan zamu soma jarrabawa kinga ba lallai na zo ba." Ta gyada kai tamkar yana ganinta. "Allah Ya baku sa'a." "Amin, ina Amarena? Kakanninmu." Ba ta yi mamakin Adnan ba, daman ai Shi Allah babu ruwansa, idan Yaso sai ya yi daya mai kyakkyawan zuciya acikin dubu, to ballantana kuma suma su Ihsan din rashin fahimta ne yasa suke mata hakan.   Tana dariya ta amsa da duk lafiya. Sun dan ta6a hira yana jifanta da tambayoyi akan Gombe tana amsawa a karshe suka yi sallama.   Babu jimawa kuma ta ji wani kiran alokacin da ta ke kokarin kwanciya, shi ne dai wanda ta ke gujewa kirannasa. BABBAN GORO, UBAN GAYYA...!!!    Ta zubawa wayar ido kamar ba zata amsa ba, sai faman safa da marwa numfashinta ke yi, har dai ta kusa yankewa sannan ta yi bismillah ta amsa. Shiru ba ta ce komai ba shima baice ba, can kuma ta ji ya sauke ajiyar zuciya ya yi sallama cikin sanyin murya.    Ta amsa itama kamar wacce aka shak'ewa wuya don dakyar muryar ta fita.    "Kema hawayen ki ke yi kamar ni?" Ya fada a shagwa6ance, ta rufe bakinta da hannu don dariyar da ta so su6uce mata. Ya cigaba da magana. "Dagaske nake fa, wannan idan zan rabu da Hajiyata sai yaya? Kawai kina shirin rabani da gidanmu ko? Dazunnan Haidar ya gama yimin dariyar mugunta ya tafi."   Ta hadiye dariyarta ta maidashi murmushi mai bayyana hakora. "Um." Shine kawai abinda ta ce sa'ilin da ta saci kallon Dada, minsharin da ta ji ne ya tabbatar mata cewar yanzun ta yi nisa da bacci.   "Tashi Ummi, tashi mu yi salla mu mik'a godiyarmu ga Allah, zan k'ara kira karki kashe wayar kinji?"   Ta gyada kai kawai, saida ya kara maimatawa. "Kinji?" Alokacin ta amsa da to, bai jira cewarta ba ya katse kiran. Ta bi wayar da kallo tana murmushi, soyayarsa na k'ara ratsa dukkan sassan jikinta, fita ta yi, babu kowa a tsakar gidan duk an shiga makwanci, alwala ta dora bayan ta kama ruwa sannan ta koma dakin ta tada sallah, ta jima tana adduo'i har da hawayenta kafin ta shafa ta mike. Mintuna biyar bayan haka, har ta fidda ran zai kira don lokacin sha daya ta kusa sai ga kirannasa. Ta daga da sallama, ya amsa kafin ya tambaya ko ta yi? Ta amsa da eh. "Alhamdulillah." Ya maimaita sau uku sannan ya cigaba da fadin. "Matata." Ta ji sunan har cikin jini da jikinta, ta lumshe ido tana murmushi ga kirjintata dake lugude da sauri-sauri, saidai ta kasa amsawa, ganin abin ta ke yi tamkar a mafarki.   "Matata Hasiya, ko ba ita bace? Kina jin mijinki na kira ki ka yi shiru ko?" Ya karashe a shagwa6ance, ai daman tasan ko wata macen ba fa zata nunawa Faruk shagwa6a ba, don ko ita ba zata iya yanda ya ke yi ba.   "Um." Ta fada kanta na k'asa tana wasa da kasan t-shirt din dake jikinta na bacci.   "Kin zama matata yau, shikenan na girma, haka Hajiya ta ce." Har lokacin murmushin ne dai ta yi. "Gobe za ki zo gareni Hasiya, ina fatan kin shirya tarbata?" Ta zaro ido a tsorace. "Kamar ya?" "Au ba ki sani ba? Shikenan sai kinzo din." Ta tsorata, ta tunano maganganun su Anti Halima, ya zama dole ta yi takatsantsan don kuwa dagaske ba fa za ta bari ajinnata ya zube ba.    Ya cigaba da janta da hira, hirar da ba zata iya dauka ba, ganin dai dagaske ba zata bude baki ta ce wani abin ba yasa shi yi mata sallamar dole ba don yaso ba. Daga nan suka kwanta kowanne zuciyarsa cike da begen dan uwansa....!   Washegari...!!!       DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   102 Bayan Ummi ta kammala karyawa, ko mikewa daga wajen ba ta yi ba, Dada ta mik'omata wani abu a kofi, ta dubi kofin, tasan daman tun zuwanta tana bata nonon saniya tana sha, saidai wannan karon wani abu ta gani cikinsa mai kama da lalle, ta dago kai tana dan yamutse fuska ta dubeta. "Menene wannan Dada?" "Kar6i ki shanye sai na gayamaki." Ba musu ta kar6a ta shanye tas gami da saurin korawa da ruwa don dacin bakinta ya kau. Murmushi Dada ta yi sannan ta mik'amata wani kullin itatuwa a farar leda. Ummi ta kar6a tana dubanta. "Maganin sanyi ne, da zarar kin dawo kafin biki, za ki dunga sha kina tsarki da shi, mahadinshi jar kanwa, wannan da ki ke gani ba'a wasa da shi, sakacin iyayenku kenan, sai a yita dabkawa mata kayan gyara amma ba a basu maganin sanyi. Sai ki ga bayan aure anzo anata faman zaryar zuwa asibiti."     Ita dai Ummi a kunyace ta ajiye ledar a gefe, Dada ta dauka tana cigaba da fadin. "Ki dage wajen kula da jikinki, ko yanzu ai ke kanki kin ji chanji ba kamar yanda ki ka zo garinnan ba." Ummi ta yi shiru, kwarai kuwa da gaskiyar Dada, don kuwa tun zuwanta kullum da abinda za ta bata ta sha, daga ta ce maganin basir sai kuwa na ciwon jiki. Ita dai hakanan ta ke sha batare da tasan wani abu na maganin ba.      Misalin bakwai na safe, Faruk ya yi mata text ya shaidamata tahowar direban tun biyar na Asuba, alokacin tana zaune Dada ta kira wata makwafciyarsu tana tsantsara mata kananun kitso, ga kunshi ana yi mata. Sun kwashi awanni uku suna yi kafin a kammala kitson, sannan ta wanke lallen, kowa ya ga kitson da kafarta sai ya tanka, wannan yasa ta rufe gashinta mai laushi da bak'i. Kafar kuwa ta makamishi safa. Ta yi wanka ta hade cikin wata doguwar rigar abaya mai ru6i biyu, bak'i da ruwan k'asa, wanda ya fiddo (shape) dinta, daga gefen hannuwan kuma sai aka yi shi mai fadi kamar buba. Ta yane kanta da mayafinsa.   Wajen karfe goma sha biyu da mintuna, Babanta ya kirawota, ya yi mata nasiha sosai akan ta kula ta kuma bi mijinta sau da k'afa a karshe ya sallameta bayan ya sanarmata cewa an damk'awa Dada sadakinta zata bata, nauyi ya hana Ummi cewa komai ta tashi ta wuce.     Shigarta ciki babu jimawa ta ji yaran gidan na ihun mota ta zo. Gabanta ta ji ya soma bugu, haka kawai ta ji kamar za ta kara yin nesa da yan uwanta.     "To Hasiya, tashi ki yi sallah za ku kama hanya. Shiru ta yi domin yau da asuba jini yazo mata. Shirunta ya fahimtar da Dada, kawai sai wuce ta dauki jakar kayanta ta mikawa Aliyu d'a na biyu wajen Baffa Haruna wanda baifi sa'an Adnan ba.    Ummi ta soma sharar hawaye, tana nan zaune har zuwa lokacin da aka ce ta fito su wuce. Nan ta rike Dada tana hawaye, Dada dakyar ta iya daurewa ta cireta daga jikinta. "To mene na kukan kuma? Kiyi hakuri kinji, ai ba'a rabu ba. Rike wannan, sadakinki ne." Ta girgiza kai. "Ki yimin abinda ki ka ga ya dace." Daga haka ta zira takalminta mai tudu ta janyo jakarta bak'a wacce da ita ta zo sannan ta fito Dada na rike da ita.    Haka dai da kuka Ummi ta rabu da gidannan, mahaifinta shi kansa saida ya ji kamar ya yi kukan, Baffa na gaba ita da Abida suna baya.     Wayar direban ta yi kara, nan ya ke sanarwa da mai kiran cewa sun taho, ya yi musu adduar isowa lafiya sannan sukayi sallama. Ya dubi Baffa yana dan dariya. "Yalla6ai ne." Baffa ya yi murmushi kawai. Direban kuwa dan surutu, sai ya hadu da Baffa shima ba kanwar lasa ba, tun Ummi na jinsu har ta yi matashi da cinyar Abida bacci mai nauyi ya dauketa.    Basu suka isa Abuja ba sai karfe bakwai da wasu mintuna, shima don sun yi tsaye-tsaye ne yin sallah da sauransu.     Tunda aka shigi garin Abuja Ummi ta ji kamar ta ruga aguje ta koma Gombe, da wane ido zata kalli Hajiya? Wai shikenan fa itama ta zama suruka a gidan.    Bayan isarsu kofar gidan, ya yi hon, da sauri Maigadi ya budemusu suka shiga yana dagamusu hannu. Ta rike hannun Abida. Abida wacce ta suma a kallon gida, ta dubeta, ganin yanda duk ta firgice yasa ta fadin. "Ki yi ta addua." Sai lokacin ta tuna ta shiga yi, a harabar gidan babu kowa har zuwa lokacin da suka fito sai lokacin kuma suka Gen. Ahmad ya shigo dawowarsa kenan daga masallaci, a bayansa kuwa Haidar Danzaki ne sai ko Faruk Danzaki.    Ummi sai sunne kanta ta ke yi, Baffa ya karasa ya mikawa Daddy hannu suka yi musabaha, yana tambayar yanda suka iso. Su Ummi suka russuna suka gaishesu, sannan suka shiga ciki. Faruk ya tsunduma a kallonta baya ko kifta idanu, saida Haidar ya dan mintsileshi a kafada sannan ya dafa wajen yana 'yar kara kadan. Dariya suka yi. "Control yourself mana." Murmushi kawai ya yi kafin ya russuna yana gaida Baffa, sannan sukayi ciki.   Da Binta Ummi ta soma karo, suka rungume juna suna murna, harda hawayenta don Ummi kam akwai arhar kuka.     Binta ta dubeta. "Kinga yanda ki ka koma kuwa? Ranki ya dade." Dariya sukayi, lokacin da ta share hawayenta. Saukowar Hajiya daga sama ne yasa ta sunkuyar da kai a kunyace. Hajiya wacce ta kasa 6oye farincikinta ta karaso tana duban Abida. "Sannunku da zuwa, diyata kunya ta shiga tsakaninmu kuma?" Ta karashe tana mai rikota, dariya Abida da Binta sukayi.    Ta ja su zuwa sama, dakin Ummi suka sauka, saida sukayi wanka suka chanja kaya sannan Abida dake zaune saman darduma ta idar da sallah ta dubeta. "Kai Ummi ki godewa Allah, na tayaki murna wallahi. Irin wannan karramakin da su ke yi? Ga uwa uba kuma suna da arziki? Kinyi sa'a sosai, sai naga ma haduwar gidan ta zarce yanda nake kissimawa."    Murmushi kawai Ummi ke yi lokacin da ta ke kokarin jona matacciyar wayarta a chaji. Tana sanye da doguwar riga(cotton) wacce da kadan ta wuce gwuiwa tana da botila a gaban rigar mai dogon hannu sai ta dora zani akai. Kanta rufe da hula, aka kwankwasa kofar da sallama, suka amsa sannan Binta ta shigo. Suka kara gaisawa da Abida kafin ta fadi sakon Hajiya na su fito su ci abinci.  Kamar ta tambayi Binta ina Ikram, sai kawai ta share.    Ta yafa mayafi suka fita itama Abida da lullu6inta.      A saman katuwar ledar cin abinci aka jera komai, Hajiya Babba ta yi musu bismillah, Ummi da kanta ta zuzzubamusu a ranta ta ji sanyin rashin ganin Faruk awajen don kunya ta ke ji.     Bayan sun kammala ta tattara, Hajiya na fadin ta barshi saidai bata saurara ba, ta yi k'asa, Abida ke fadin. "To Hajiya ai an zama daya."  Saukarta yasa ta gwammace bata sauko din ba don kuwa Haidar ne da gogan zaune suna cin abinci. Dole ba yanda ta iya ta karasa saukowa, ta dan durkusa ta gaida Haidar, ya amsa fuska a sake. "Sannu Amarya ya hanya?" Ta kasa dubansu, ciki-ciki ta amsa da Alhamdulillah.    Faruk ya bi le66anta da kallo don kuwa maganar bata fito sosai ba, murmushi ya yi sannan ya kauda kansa ya cigaba da cin abincinsa hankali kwance.     Ta mike ta karasa kicin, suka fito tare da Binta suka koma sama, nan suka iske Hajiya Babba da Abida suna ta hira, suka tattara suka koma kasa.    A kicin dinne Ummi ta samu danar tambayar Binta dake faman binta da kallo. "Wai ina Ikram?" Dariya Binta ta yi. "Wallahi tana dawowa daga makaranta ta hada jaka ta gudu gidan Yaya Haidar, saidai fakewa ta yi da cewa zata taimakawa Intisar da ayyuka tunda cikinta ya soma tsufa, har shi Yaya Haidar din ke cewa ta barshi tunda ba tun yau ba yaso zuwannata ta k'i. Yanzu dai ta tafi can, nasan kuma karya ta ke yi wallahi saboda bakin cikin za ki zo matsayin matar Yalla6ai ne."   Murmushi mai ciwo Ummi ta yi, tasan daman da wuya Ikram ta chanja.    Saida ta lek'a ta ga sun bar falon sannan ta fito daga kicin ta haye sama. Babu kowa a falon wannan karon, Hajiya Babba ta yi wurin mijinta, Abida kuwa ta shiga daki, tana shirin murda kofa ta shige daki ta ji sallamar Faruk a bayanta. A rude ta juyo ta tabbatar shi dinne. Ya zubamata idanu yana sanye da riga da wando fari da ja.    "Waalaikumussalam." Ta amsa a hankali.  Ya karaso daf da ita gami da sanya hannu ya dago ha6anta.  "Ki sameni wajen pool...please." Ya karashe a tausashe. Ta gyada kai cikin rawar jiki, ya saketa sannan ya juya ya fice, ta bishi da kallo. Bata koma ciki ba sai kawai ta bi bayansa jiki ba kwari. Haidar ya wuce, ta gama waige-waigenta kamar mara gaskiya kafin ta murda kofar ta shiga. Kofar na waje baya ganin na ciki saidai na ciki ya ga na waje. Yana zaune yana duban ruwan, shigowarta yasa shi dago kai yana dubanta. Ta yi kasa da kanta tana mai kara gyara zaman mayafinta. Tana kokarin zama a kujerar gefensa ya janyota ta fada saman kafafunsa ba da niyya ba. Ji ta yi gaba daya ta rude, ta shiga kokarin mikewa saidai ya tare dukkan hanya. Take kuka ya tahomata. "Don Allah ka yi hakuri." Ya lumshe ido yana shak'ar kamshin turarenta. Ganin haka ta fisge da karfi ta mike gami da ja baya. Jingina kansa ya yi jikin kujera yana dubanta fuska dauke da murmushi.    "Come to me please Ummi." Ko gezau ba ta yi, come dai ai ko dan kauyen yau da gobe zai san me kalmar ke nufi. "Ka yi hakuri ka kyaleni na tafi."  Har lokacin bai motsa ba, saida ya kusan mintuna biyu yana dubanta sannan ya janyo kujera ya nunamata. "Zo ki zauna." Saida ta tabbatar dagaske ya ke sannan ta karasa ta zauna.   "Kun iso lafiya?" Kai ta gyada don har lokacin cike ta ke da fargaba.   "Idan ba ki yi magana ba zan sanyaki yin ta dole fa."   "Alhamdulillah." Ta fada da sauri har muryar na hardewa, abin yaso ba shi dariya.     "Na so mu yi hira saidai na lura kamar kina tare da gajiya ko? Tafi ki kwanta, saidai Antinmu na tafiya za ki had'a kayanki ki komo dakina." Ta zaro ido tana dubansa, shi kuwa ya hade fuska kamar gaske.    Kawai sai ta sunkuyar da kanta ta soma hawaye.    Karamin tsaki ya ja ya durkusa gabanta. "Why? Komai kuka awajenki ko Ummina?" Ya fada a sanyaye, bata ankara ba ta ji ya soma lashe hawayen, ta soma girgiza kai kafin ta yi yunkurin tureshi tana fadin. "Don Allah Yaya Faruk..." Yasa hannu akan le66anta kafin ya girgiza mata kai. "Karki hanani please. Idan bakyaso ki daina kuka. Bakisan suna da tsada wurina ba?" Ya karashe da murmushi saman fuskarsa. Sannan ya mike yana dubanta. "Tashi na rakaki." Ta mike da sauri don daman abinda ta ke zuci-zucin ta ji kenan.     Saida suka kai kofa ya riko kugunta ya kai bakinsa daf da kunnenta. "I LOVE YOU." Ta lumshe ido, abinda tunda suke bai ta6a furtamata kenan ba, jikinta ya dauki rawa, zata murda kofar, ya kai hannunsa kan nata suka murda tare. Da sauri ta fice. "Hey!" Ya fada yanda yasan za ta ji, ta tsaya cak batare da ta juyo ba.  "Ba ki ban amsa ba." Da sauri ta cigaba da tafiya har da gudu-gudunta. Ya bita da kallo yana murmushi sannan ya juya ya nufi samansa yana dan rera waka cike da nishadi.       DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 103 Koda ta koma daki, kwance ta iske Abida saidai bata kai ga baccin ba. A kunyace da alamun rashin gaskiya. Abida bata ce mata uffan ba, itama ta cire mayafin jikinta sannan ta hau ta kwanta bayan ta yi alwala ta kashe musu fitila.     Ta lullu6e jikinta da bargo tana tunano abinda ya faru yanzun. Runtse ido ta yi ta bude, ganin abin tamkar mafarki ta ke, ta dan saka hannu ta mintsili kugunta, nan take ta yamutse fuska irin na jin zafi. Sai kuma ta rufe kanta da bargo tana murmushi, shakka babu dagaske ne, amma kuma abin ya bata tsoro.     Har Baffa da Abida suka yi kwana biyu bisa umarnin Gen. Ahmad don su  niyyarsu washegari su juya. Ummi wasan 6oyo ta ke yi da Faruk, don daga ta ji Magriba ta yi zata shige daki suyita hira da Abida. Hakanan idan ya bugo waya bata dagawa.  Washegari kuwa yana tafiya ofis, suma su Abida suka tattara suka wuce, har hawaye ta yi haka suka rabu zukatansu cike da kewa. Tare sukayi komai da Binta na abincin rana, har lokacin Ikram bata dawo ba. Acewar Binta, ba zata dauwama acan ba, koda ta yi an dai riga da anyi abinda bata so, Ummin ta zama matar yayanta.    Hajiya Babba zaune a falonta tare da Ummi da har lokacin bata saki jikinta ba, waya Hajiyar ke yi da Hajiya Mama. A karshe ta dubi Ummi dake zaune a kasa tana mai mik'amata wayar. "Amsa ku gaisa da Sadiya." Kunya ta cikata sanin kowacece Sadiyar, Hajiya Mama. Ta kar6a a kunya ta yi sallama. Daga can Hajiya Mama ta amsa mata murya a sake.  Ummi ta gaisheta, ta amsa. "Sannu surukarmu, kinga yanda Allah ke ikonSa ko?"   Kanta kawai ta dukar tana murmushi. "Um." Ta fad'a a kunyace.  "Allah Yasa alheri, Ya baku zaman lafiya, sai a dage a nemi ilimi banda wasa kinji ko?" Ta gyada kai." "To Hajiya." Daga haka ta mik'awa Hajiya Babba wayar, itama sallamar suka yi.   Bayan sallar isha'i tana kwance saman gadonta, ta juyawa kofa baya, ba bacci ta ke yi ba saidai ta yi shiru tana tunane-tunane, ga ruwan sama da ake kwarawa kamar da bakin kwarya, sam ba ta ji sadda ya murda kofar ba sai jin mutum ta yi a bayanta ya rungumota. A firgice ta mike zaune za ta yi ihu ya yi saurin rufe mata bakin. "Shii..." Ta tsaya tana mai dubansa daga shi sai riga marar hannu sai dogon wando na Adidas, ta sauke ajiyar zuciya, ta ja baya, ya saketa, ta sauke kafafunta daga saman gadon shima ya yi yanda ta yi yana mai dubanta fuskarsa a daure. Sai wani jan riga ta ke yi don sanye ta ke da t-shirt mai karamin hannu sai zani da dankwali, gaba daya t-shirt din ta matseta don kuwa ba Ummin da ya sani a baya bace, wannan ta yi k'iba ta k'ara haske.     Ya kauda kansa yana ta6e baki kadan, tana gaisheshi saidai bai amsa ba. Ya zarce da maganarsa. "Laifin me na yi ki ka k'i amsa wayata sannan bakya tunanin zuwa gaisheni kafin na fita ko kuma idan na dawo, kin manta yanzu duk wadannan hakkine a wuyanki?"   Ganin ba alamar wasa a fuskarsa ta kara sunne kanta. "Ka yi hakuri don Allah." Shikenan ta gama da shi, wuyarta ka ba shi hakuri, yana iya yafemaka.   Ya dubeta yana murmushi. "Ya wuce." Da dabara ta janyo hijabinta zata sanya caraf ya rike hannun. Ta dubeshi kamar za ta yi kuka shima ya narkar da nashi idanun cikin nata.   "Wai Ummina yaushe ne za ki bar wannan halin? Har yanzu kunyar..." Sai kuma ya yi murmushi sadda ya je janye hijabin. "Kodayake, laifina ne." Ta ja baya a tsorace tana mai turo baki kadan don ita gani ta ke yi ya takura rayuwarta.    "Nidai don Allah ka fita kada Hajiya ta leko ta ganka." Ya dan daga gira yana gyada kai. "Oh, gani na nawa kuma? Da nasan ita ki ke tsoro ai da ban shigo ba, yanzu tashi ina bukatar shan ruwan lipton, saidai nafison ki cire wannan ledar ta jikinsa ki zazzage garin ki zuba sugar idan ya dahu ki tacemin, ok? Idan kin kammala ki kawomin." Ya mike ya yi gaba batare da jiran amsarta ba. Ranta a dan 6ace ba ta bishi da kallo ba don komai ba tasan wayo zaiyi mata dole ta shiga sashensa. Yanzu idan ya ce zaiyi mata abinda aka ce kada ta yarda sai an kaita gidansa fa? Ta kauda wannan tunanin ta mike ta chanja kaya zuwa doguwar rigar jallabiya ta sanya hijabi sannan ta fito. A falon ta tarar da Hajiya na shirin ratsawa sashen mijinta, ta dubeta. "Ya akayi Ummi?" A kunyace Ummi ta bata amsa. "Shayi ya ce na hadamishi." Hajiya ta gyada kai ta yi shiru, kamar ta ce wani abu sai kuma ta chanja tunani da fadin. "To idan kinje ki dawo." Daga haka ta shige abinta, Ummi ta gane hausar. Ta mike ta sauka. Kicin din har an kashe fitilu, sai walkiya da ke haskoshi ga kuma karar ruwan sama wanda ake makashi sosai. Ta kunna fitila a ranta tana mai godiya ga Allah da wannan yanayin na damuna mai dadi.     Saida ta kammala kamar yanda ya ce sannan ta juye a flask ta sanya karamin kofin tangaran a filet dinsa sannan ta nufi saman.    A bude ta tarar da shi don haka ta shiga da sallama, fitilun a kashe suke sai ko hasken talabijin da ke aiki, yana zaune a falon da laptop saman cinyarsa yana dannawa. Shigowarta ne yasa shi maida dubansa gareta. Ya sauke kafafunsa saman tebur ta ajiye kafin ta zubamishi.    "Gashinan." "Thank you." Ya fada cikin kankan da murya, ta juya ga kallon barandarsa wacce ke a bud'e ga kuma labulen dakin dake kadawa har ruwa na fallatsowa, ta ga alamun baya jin sanyin.    "Saida safe." Zata mike ya fisgota. Cikin kankan da murya ya ce. "Na sallameki ne?" Ummi wacce yanayinta ya sauya ta kasa magana sai girgiza kai. Ya gyara mata zama sannan ya sa hannu ya soma kokarin ciremata hijabin. "Ke bakya jin zafin gari ko? Cire ki shak'i iska mai rahma." Bata da kata6us har ya cire ya yi saura daga ita sai hular kanta da doguwar rigar. Ta hade hannuwanta wuri guda gami da dan muskutawa ta ja baya da shi. Idanunsa akan laptop saida ya murmusa, wai shi yarinyarnan ke kakkaucewa? Ya share batunta ya soma shan ruwan shayinsa yana danne-dannensa cikin email account dinsa.    Ita kam Hajiya kawai ta ke tsoro, yanzu don Allah idan ta ji ta shiru me za ta ce?    Faruk bai k'ara duban inda ta ke ba sai bayan ya kammala sannan ya kashe laptop dinsa ya dubeta. Duk ta 6ata fuska kiris ya rage ta soma kuka.     Yasa hannu ya janyota jikinsa. "Zo ki fadamin me ya 6ata ranki?" Babu amsa, ya shafi gefen fuskarta har zuwa wuyanta nan ma ba ta ce komai ba, ganin yana kokarin yin son ransa ne yasa ta saurin rike hannunsa gami da ja baya.   "Don Allah zan tafi kada Hajiya..." "Tell me, Hajiya ki ke aure ko Faruk wai? Tsoron me ki ke yi mata haka alhalin tasan kina wajen mijinki? A baya ina miki haka ne?"   Ya na magana a hankali saidai muryar na nuni da 6acin rai. Ta girgiza kai sai kuma ga hawaye, runtse ido ya yi gami da kwantar da kansa jikin kujera, ba kuma yaso ta zargi ko abinda ya ke so daga gareta kenan, baya son 6acin ran Ummi. Saidai shi kunyar ce baya so, yanzun kuma ya lura harda tsoro ma. Tunda ya ke a rayuwarsa bai ta6a ko rungume wata diya mace ba balle ya aikata wani abin. Ya ja guntun tsaki.   "Tashi ki tafi. Saida safe." Ya yi maganar a sanyaye.   Ta dubeshi sai ta ji soyayyarsa na karuwa ga kuma tausayi, tasan bata kyauta ba. Murya na rawa ta ce. "Don Allah ka yi hakuri Yaya Faruk." Ya dubeta yana murmushin karfin hali da kokarin hadiye abinda ke taso mishi.   "Karki damu ba fushi na yi ba, muje na raka ki."    Suka mike yana rike da hannunta, ya janyo hijabinta ya sanya mata, ta zura takalminta, suna isa kofa baisan sadda ya fisgota ba har ta firgita, ya hada bakunansu wuri guda, saida ya gaji don kansa ya saketa ya ja baya kadan yana dubanta.   "Goodnight." Itama da sauri ta fita, ya rufe kofar.    Ta juya ta dubi kofar sannan da sauri-sauri ta fice tana numfarfashi.        Wannan daren daga ita har shi sun jima kafin bacci ya kwashesu...                     ***  ***  *** Abu kamar wasa, Ummi ta shiga yi mishi 6oyo, duk wata hanya da zasu ke6ance ta tosheta, shi kuma idan ya ganta tare da Hajiya ba ya iya cewa uffan don mikewa ta ke yi ta bar falon. Zuwa yanzu ta dan soma sabo da Hajiya don Hajiya Babba ta sakarmata sosai ta yi ta janta da hirar Gombe, itama har ta sake ta yi ta bata labari.  Bai kara sanyata a ido sosai ba sai ranar Asabar, shima ta fito cikin shirin Islamiyya ne. Gabanta ya fadi, ta durkusa ta gaida Hajiya sannan ta gaisheshi. Ya tamke fuska kwarai har Hajiya saida ta yi mamaki.    ((Manage pls...jiki da jini....))    DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 104 "Ba kai ake gaisarwa ba?" Cewar Hajiya. Ya yamutse fuska kadan. "Lafiya."   Ya mike. "Hajiya bari na je na dawo." "Aa, to ka tafi da ita mana kawai. Tunda duk hanya ne." Ya runtse ido kadan sannan ya yi gaba, Hajiya ta dubeta. "Tashi ku je." Ummi wacce duk jikinta ya yi sanyi, ina laifin mai sonka? Ta ji haushin kanta na 6atawa Faruk rai, mutumin da ya so ta tun kafin ta zama 'yar gayu haka, tun tana matsayin 'yar aiki.  Sam bata kyauta ba, Faruk bai cancanta ta dunga 6atamishi rai haka ba.     Ta iske tuni ya fiddo motar yana jiranta, ta karasa kanta a k'asa, ta bude gaban mota ta shiga, sanyi da kamshi ya doketa, garin ya yi sanyi hakanan babu rana kamar zaayi wani ruwan. Ta rufe kofar gami da satar kallonsa saidai ko inda take ba ya kallo, fuskarsa babu digon walwala, gaba daya haushin kanta ya kamata, suka soma tafiya nan ma babu alamun zai shiga harkarta, wannan ne dalilin da yasa ta daure ta soma magana dakyar. "Yaya Faruk." Bai amsa ba hakanan bai kalleta ba. Ta sunkuyar da kanta idanunta suka ciko da ruwan hawaye, ta dubeshi cikin rawar murya. "Yaya Faruk don Allah ka yafemin." Ya lumshe ido ya budesu yana mai duban gefen da zai yanka kwana, can cikin zuciyarsa babu dadi, ji ya ke tamkar ya janyota ya rarrasheta, ko kusa ya tsani kukanta.    Ita kuwa ganin ya yi shiru yasa ta kauda kanta ta maida dubanta ga gefenta tana sharar hawaye. Shiru ya biyo baya har dai suka isa.  Daidai Islamiyyar ya tsaya, dalibai har sun shiga wasu kusa na tsaitsaye a k'ofa, gaba daya suka zubawa motar ido don ganin wanda zai  fito. Ya cire (Lock), bata dubeshi ba ta bude kofar ta fita bayan ta share fuskarta.    Haka ta shiga ciki, mintuna uku da shigarta suna tsaye wata Malama na tambayarta ko ita sabuwar daliba ce, ya shigo. Gaisawa ya yi da wani Malami sannan ya yi ciki zuwa ofishin headmaster bayan ya yi mata umarnin ta biyoshi. Nan ya bada hakurin rashin zuwanta na tsawon lokaci, ya nuna babu komai. Aka sallameta ta fito, da isarta kofar ajinsu suka hadu da Husna da wasu.    "Lah, ashe dagaske ki ke Fati, Hasiya ce." Cewar Husna kenan, Ummi cikin rashin fahimta ta dubesu, saidai kafin ta ce wani abu, ta ji suna duban bayanta wata na fadin. "Gashinan wallahi, wayyo Allah, very handsome, please Hasiya ki hadani da shi, wallahi yayanki ya min, kalar mijin da nake fata kenan." Cewar wata Shukra Aminu. Wani mugun kishi ya turnuk'e Ummi, ta juya ta dubi Faruk sa'ilin da ya ke kokarin sanya kansa a waje ya fice. Sanye ya ke da bak'ar t-shirt bodyhug wanda ya taimaka wajen fiddo da kyakkawar halittar da Allah Ya yiwa jikinsa na kirar karfi, sai farin wandon jeans da ya sanya, sumarsa kwance luf, bak'ak'irin kamar mai sanya (hair dye). Ta juyo ba ta ce uffan ba ta nufi ciki, tana jinsu suna kod'a mijinta saidai bata da bakin magana.    Gaba daya suka biyota ajin. Husna ke tambayarta game da Gombe, su kuwa tambaya suke akan Faruk, duk sun isheta, Allah Ya taimaketa Malam ya shigo ajin, wannan yasa duk aka nutsu.    Ranta a matukar 6ace ya ke, har aka fito sallah basu bar bibiyatar da son jin ko wanene ba, tana tsaye bakin famfo tana daure dankwalinta, jiran Husna ta ke yi ta idar su bar wajen, idanunta ya kai ga Ikram suna nufo famfon ita da tawagarta. Ba shiri ta ja hijabinta ta rufe fuskar gami da basu baya, saidai duk da hakan bata tsira ba Ikram ta ganta, saidai bata ko nuna tasan da itan ba bisa gargadin Haidar wanda ya gargadeta sosai akanta. Dogon tsaki ta ja kawai wanda Ummin ta ji, daidai lokacin ne kuma Husna ta kammala ta dubeta. "Mu tafi." Suka bar wajen zuwa masallaci. Zuciyar Ummi ko kadan babu dadi har aka tashesu, direba ya dauketa.     A farfajiyar gidan suan fakawa ta fito, idanunta ya kai ga baranda Gogannata. Yana makale da earpiece a kunne, hannunsa na hagu lemun gwangwani ne da ya ke kur6a, sai sketct-board a gabansa yana zane. Ta dubeshi sosai, ganin zai kallota ne yasa ta saurin k'asa da kanta gami da soma tafiya zuwa ciki, ta goge kwallar da ta tahomata.  Wannan cutarwa ne, ba zata jure wannan fad'an nasu ba. Ba haka ya sabarmata ba a mu'amalarsu.      Bayan sun gaisa da Hajiya, ta shiga ciki ta watsa ruwa ta sauya kaya zuwa riga da siket na Atamfa mai fari da (orange), bata daure dankwalin ba saidai kawai rufashi da ta yi. Fita ta yi zuwa kicin wajen Binta. Anan ta zauna, Binta ta yi akan ta ci abinci saidai ta ce ita sam bata jin yunwa duk kuwa da irin yanda ta ke jin yunwa na addabarta saidai damuwarta na rashin ganin fuskar Faruk yafi komai damunta.  Tana daga kujera yar tsugunno suna hira da Binta. Anan ta ke bata labarin yanda suka yi da Ikram. Dariya sosai Binta ta yi. "Duk yanda akayi ba banza ta kyaleki bata tofa ba." Murmushi kawai Ummi ta yi wanda bai kai zuci ba, da ta ji hirar babu abinda ta ragemata sai ma k'ara hargitsata da ta yi don kuwa Binta ta sanarmata da zuwan matasan gidan da iyalinsu gobe, anan zasu wuni, duk sai ta ji hankalinta ya k'ara tashi, hakan yasa ta mikewa.   "Bari dai na dan zagaya." Kai tsaye (Garden) ta nufa, zama ta yi saman lilo ta kwantar da kanta jikin igiyar, a sannu ta ke lulata tana tunani, rayuwarta na tafiya daki-daki, daga matsayin yar aiki zuwa ta surukar gida, har ta gangaro ga irin kyautatawar da Faruk ya yi mata zuwa ga yanzu da ta 6ata mishi rai.     Bata ji motsin zuwansa ba, saidai ji ta yi yana share mata hawaye.    "Yaya Faruk!" Ta fada da sauri tana dubansa, sai kuma kunya ta kamata ganin dagaske ba mafarki ta ke ba shi dinne zaune durkushe gabanta yana dubanta.     "I'm sorry. Ki yi hakuri kinji?" Ya fada cike da damuwa a fuskarsa, ta girgiza kai. "Ni zan baka hakuri, don Allah ka gafartamin kada Allah Ya yi fushi da ni." Ta burgeshi har baisan sadda ya dora gwuiwoyin hannunsa ba akan kafafunta yana mai dubanta. "Sai kin chanjamin suna."   Ta rufe fuska tana dariya.   Ya riko hannunta gami da mik'ar da ita. "Oya, muje mu ci abinci." Ta mike ba musu suka shiga ciki yana rike da hannunta.    Kusan tare suka ci abincin a falon Hajiya, Hajiyar na sama ta yi bak'uwa mai zuwa sarar kaya.     Suna ci daga zai bata a baki sai ta yi saurin kaucewa, har ya gaji ya bari, abin kan ta6a zuciyarsa, shi sam ba ya kaunar rayuwa haka, Yana yawan hangowa kansa rayuwa ta wayewa, baya kaunar kunyar Ummi ta cucesu a zamantakewa, idan har hakane, zata tauye musu jin dadi.... '((Nagode da adduoinku.. Allah Yabar zumunci..ameen)) DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 105 Ya ji abincin ya fita ransa dole ya ja baya gami da zuba ruwa ya sha.     Ta dubeshi, tana son tambaya ko ya k'oshi saidai ta kasa, ita batasan meyasa duk kunyarsa yanzu ta ke ji ba, ta fahimci kuma ba haka ya ke so ba. Yana kallonta tana faman juya cokali, kawai ta mike ta dauke zuwa kicin. Koda ta fito bata ganshi a falon ba, itama sama ta nufa don jin an soma kiraye-kirayen sallah.     Saida ta idar sannan ta ciro Al-kur'ani ta dan karanta inda aka biyamusu sannan ta rufe. Wayarta ta dauko, tana son kiran Antinta Amina don neman shawara saidai babu kudi cikinsa, tunawa ta yi da kudin da babanta ya bata cikin wanda ta ba shi da ta taho da shi, ya ragomata koda za ta siya wani abun, hamdala ta yi kafin ta mike ta nufi jakarta ta rataye, dubu daya ta ciro sannan ta fita, daman da hijab a jikinta.     Allah Ya taimaketa Hajiya bata falon hakan yasa ta zarcewa kasa.  Kai tsaye farfajiyar gidan ta nufa, saida gabanta ya fadi ganin Faruk ya shigo, da alamu dai daga masallaci ya ke, shi dinma ita ya zubawa ido da mamaki, ta ja ta tsaya har ya karaso. "Ina za ki?"  Ta nunamishi kudin hannunta. "Kati nake so shine zan bayar a siyomin." Jin haka ya tamke fuska. "Meyasa ba ki sanarmin ba? Hakkina ne fa nasan dukkam abinda ki ke so, ya kamata ki chanja Ummina, banason wannan kunyar taki a yanzu, bani da bukatarta, please ki saki jikinki da ni. I'm now your husband." Ya karashe da murya mai kamar rada sannan ya gifta ta ya yi gaba, gaba daya jikinta ya yi sanyi dole ta bi bayanshi. Sashensa ya nufa, itama ta yi nata dakin. Kwanciya ta yi saman gado ta yi shiru kawai, haka har aka soma kiraye-kirayen sallar Isha'i, ta gabatar, jimawa kadan ta fito falon bayan ta cire hijabin ta linke. Hajiya ta tarar zaune tana waya da Hajiya Mama inda suke tattaunawa akan bikin dangatan nata har ta ke sanarmata da batun zuwan su Babban Yaya gobe don tattaunawa. Ummi daman bata zauna falon ba, kai tsaye k'asa ta sauka don kuwa saida ta yi da na sanin fitowa don tuni ta fahimci maganar me sukeyi.    A kasa ta samu su Binta sina kallon wani series da akeyi da harshen larabci, zama ta yi saman kujera kafin ta dubesu sannan ta maida dubanta ga talabijin din kawai kuma sai ta kwashe da dariya sosai, dariya wacce rabonta da irinta tun dawowarta daga Gombe da suna hira da Binta a kicin. Suka dubeta. "Lafiya Ranki ya dade?" Ta dan harareta da wasa don ita ta nuna sam batason sunan saidai kamar da gayya ma Bintar ke yi. Dariya itama Bintar ta yi.   "Ku ku ka sanyani dariya, kun nutsu kun zubawa talabijin idanu kai kace kunsan abinda su ke cewa." Suka dara, Samira wacce ta zo bayan tafiyar Ummi Gombe ta dubeta. "Ai soyayyar kadai idan ki ka kalla wallahi ranki fari zaiyi, kinga nan." Duk suka maida hankalinsu kan talabijin, abinci zata ba shi da cokali  yayinda ya ke jingine da filo a gadon asibiti, ya tarr ya hanata ba shi da cokalin, dole tasa hannu har wani take aka sakomusu, har idan ya 6ata bakin ta gogeshi mishi, karshe ma ya hada da yatsunta ya tsotsa. Ummi ta saci kallon su Binta suka kwashe da dariya, sai kuma suka nutsu. Shiru ta yi har da taguminta tana kallo da murmushi.  Basu ji zuwansa ba, hakanan bata ko lura da sadda ya yiwa su Binta alama da su bar wajen ba, balle kuma zamansa gefenta. Hankalinta ya lula wata duniya, tunaninta bai wuce inama itama za ta iya hakan gareshi ba, sumbatar da ta ji a wuyanta ne yasa ta juyawa a firgice tana salati a fili, murmushi ya ke jifanta da shi, idanunsa sun kankance yana dubanta. Gabanta ya hau bugu, ta waiga babu su Binta ko dalilinsu, ta dubi talabijin, tuni ashe an wuce wajen sai ma likita da ta ga ya shigo dakinnasu(a film din), ta dan ja baya gami da shafa goshinta. Duk ta rasa me zata yi don kunya ta hau wasa da zoben gwal din dake hannunta wanda ya bata. Ya matso daf da ita. "Kina so kina kaiwa kasuwa kenan?" Ya watsamata tambayar cikin narkakkiyar muryarsa wacce soyayya ta cika. Ta hau girgiza kai batare da ta ce komai ba. Bai saurareta ba ya ja hannunta sadda ya mike tsaye. "Oya, taso ki ga wani abu." Ta mike ta zare hannunta da dabara kafin ta bi bayanshi a sanyaye. Ganin hanyar da ya nufa na samansa yasa ta tsaya cak duk a firgice. Ya juyo ya dubeta idanunta ya yi rau-rau, tsoronta lokacin cin abinci ne kada Hajiya ta nemesu, kada ma Hajiyar ta dauka ita ke zuwa wajensa tunda ta ga sadda ta sauko.  Hannunta ya kama ya soma taka matattakalar, tana zamewa kadan-kadan saidai bai saketa ba har suka isa. Tsoro ta ji ganin sun wuce falo har ya sada ta da k'uryarsa.     Dakin yana nan yanda ta sanshi, bai jira cewarta ba ya sanyata jikinsa. Tun tana a'a, da kuma rokonsa akan ya kyaleta, kamar baisan ta na yi ba. Ganin yana kokarin zuge mata zif yasa ta yin baya da sauri ta fito falo, tsaki ya ja, abin kuma ya soma ba shi haushi, wannan sam ba zai lamunta ba, tana abu kamar wacce batasan menene aure ba, ya dauki dankwalinta ya biyota da shi, tana tsaye hanyar matattakala, mik'amata ya yi fuskarsa a murtuke. Yana dubanta da jajayen idanunsa wanda har da 6acin rai cikinsu ga kuma fitina. Wannan abun ya zama sakarci kuma, ina laifin ma da ya iya jurewa har aka daura auren? Da ace tasan yanda ya ke mutuwar so da sha'awarta da bata soma tunanin yi mishi gardama a dan abinda zai yi na rage zafi ba, sam ba shi da nufin wani abu bayan kalilan din da ya ke kwadayi a yanzun. Anan zasu samu matsala.   "Kina iya tafiya." Ta yi narai-narai da fuska. "Ki tafi nace!" Ya fada da dan daga murya, ta soma hawaye sai kuma ta juya da sauri-sauri ta bar wajen.      Ta ci saa Hajiya ta yi sashen Daddy, ta wuce dakinta ta kwanta ta soma kuka. Saida ta yi mai isarta sannan ta share fuskarta, wayarta ta ji ta yi karar shigowar text, ta janyota, shi dinne ya turomata kudi daga acc na banki. Ya saba yi mata hakan shiyasa tun bata gane ba ta fahimta, bata yi wata-wata ba ta dannawa Amina kira, saidai bata sameta ba, shaf ta mance cewar sun je Nijar. Ta ciji le66anta, shigowar Hajiya Babba ne ya sa ta gyara fuskarta da sauri, ta amsa sallamarta. Hajiya ta lura akwai wani abun, ta karasa rike da wata roba a hannunta ta zauna gefen gadon. "Lafiyarki kuwa?" Ummi ta yi murmushin yak'e. "Bakomai Hajiya." "Ya za ki cemin bakomai alhalin ga idanunki a kode?" "Kaina ke ciwo." Ta samu bakinta da shararo karya. Hajiya ta numfasa. "Allah Ya sauwake." "Amin." "Rike wannan." Ta mikamata robar, ta dubeta. "Da safe da dare ki dinga sha da madara kinji? Akwai wasu ma da na sanya akawomin, Ummi ina miki kallon diyata, abinda zan yiwa Ikram zan miki shi, wannan kunyar tawa nakeso ki daina jinta kinji ko? Ki daukeni kamar uwa agareki." Kanta a kasa ta gyada kai. "In sha Allahu Hajiya." Murmushi Hajiya ta yi sannan ta dafe kanta. "Allah Ya yi miki albarka, ki tashi ki je ki ci abinci." Da murmushin itama ta amsa da toh.  Ta bi bayan Hajiya da kallo, ji dai yanda mutanen nan suka dauketa da girma, ta tuna yanda ta ke 6atawa dansu a rai akan hakkinsa, dagaske batasan rayuwar aure sosai ba, duk wani kissa ko kisisina bata ta6a hirarsa da wani ko wata ba, to waye mai koyamata ma? Duka-duka idan a makaranta ake koya, yaushe ta soma zuwa makarantar? Ko wata biyar cikakkiya bata yi ba a makarantar Kano, sannan ita din ba karatun litattafai ba, hakan kuma bai hadasu da Amina, ta dai soma jin kadan daga bakin su Abida, kamar biyayya da bin umarni da sauransu. Dole ta zage damtse ta koya, kamar dai yanzu da ta ga kulawar matar nan ga mijinta duk da cewar a fim ne, amma kwarai sun burgeta.     'Mijinki dan boko ne wayayye, sai kin zage damtse kin kula da shi.' Cewar wani sashe na zuciyarta.       A ranar basu kara haduwa ba, ta kira wayarsa yafi sau biyu bai daga ba, hakanan ta hakura, ranar bata iya baccin kirki ba.   Washegari....   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 106 Suna zaune a falo da Hajiya dake lissafe-lissafenta na kaya hannunta rike da biro da dan(Memo) na lissafi, yayinda Ummi ke gefe tana karyawa, zuwa yanzu ta soma sakin jiki da Hajiyar. Sallama ya yi ciki-ciki, suka amsa, Hajiya bata dubeshi ba dalilin batason 6ata a k'irgenta. Ummi ta saci kallonsa, fuskar babu digon walwala, ta daure ta gaisheshi, ya amsa ganin Hajiya na wurin. Ta mike ta janyo tebur gabansa da niyyar hadamishi kari. "No barshi, sai anjima zan karya." Ta kada kai kawai ta koma mazauninta, Hajiya ba tare da ta dubeshi ba ta ce. "A'a, kodai ba ka tare da yunwa ne? Wannan lokacin nasan kana karyawa Sadaukina, maza Ummi gama ki hadomishi."   Ta amsa da toh. Ya yamutse fuska yana duban Hajiya. "Wai kwanab biyun nan wa ke gyaramin daki ne? Toilet dina k'arni. Ko kusa gyaran bai yi." "Samira ce." Cewar Hajiya tana dubanshi. Ya dan muskuta.  "Daga yau ta daina bana bukata, sam bata iya aiki yanda ya kamata ba." Hajiya ta dubi Ummi, kamar ta ce wani abu sai kawai ta share da fadin "Allah Ya kyauta." Daga haka ta bi bayan wayar da aka kirata har ta yanke bata daga ba. Shi kuwa kwantar da kanshi ya yi jikin kujera ya lumshe idanunsa, shi kadai yasan me ya ke ji a zuciyarsa. Har Ummi ta gama ta hadamishi abin kari bai dago ba balle ya kalleta, itama dauriya kawai ta ke yi hakanan tana jin kunyar kanta bata son Hajiya ta fahimci akwai abinda ya hadasu, saidai tuni ta dagosu shiru kawai ta yi ta zubamusu ido.      Kai tsaye kicin ta sauka ta maida kofi da filet sannan ta yi hanyar sashensa, gyara ta hau yi, saida ta kammala ta tabbatar komai ya yi kyau sannan ta koma ga bandaki ta hau wankewa, saida ta kammala ta goge sannan ta fito rike da tsummokaran a bokiti, ta dubi ko'ina ta ga ya yi kyau sannan ta rufe kofar. Allah Ya taimaketa har ta zagaya wajen garden basu hadu ba, zama ta yi da niyyar wanke tsummokaran, sai kuma ta dakata cikin tunani, Allah Sarkin bayinSa kenan, kamar bata taka matsayin 'yar aiki ba kafin zuwan wannan lokaci da ta ke matsayi na Matar Dan Gida.     Acan kuwa Faruk koda ya hau samansa ya tarar da komai tsaf ya yi mamaki sosai da sosai, kamshi daddad'a kawai ke tashi, da sauri ya karasa ga dakinsa, nan ma an gyare tas hakanan bandaki wanda ke kamshi babu wannan k'arnin.  "To wa ya gyara?" Ya tambayi kansa, ya fito ya nufi barandarsa don ganin nan dinma ko an gyara, shima(tiles) din kamar ba'a ta6a takawa ba. Kamar ance ya dubi ciki garden, ya hangota tana faman wanke tsummokarai, ya kasa gaskata idanunsa, sai kuma ya ga ta mike tana matsewa gami da shanyawa. Ji ya yi kamar ana k'ara kwararo mishi sonta, ga wani tausayinta da ya ji ya dirar masa, ina laifin ma ta yi gyaran kawai banda wannan wanke-wanken? Ya soma ja baya yana girgiza kai. "No Ummina, matsayinki ya zarce haka gareni."    Kawai sai ya juya ya fita zuciyarsa na yi mishi babu dadi, ganinta ya ke yi kamar Ummin baya, wacce ta ke yiwa kanta kallon wata marar gata.      Ita kuwa tana tunane-tunanenta akan rayuwa har ta gama shanya, ta sanya hannu da zummar zubar da ruwan, sai ganin mutum ta yi tsaye, ta dubeshi shima din ita ya ke duba, ya kar6e bokitin ya ajiye, a kunyace ta sunkuyar da kanta. Ta kasa cewa uffan.   "Kinyi min gyara, na gani kuma na ji dadi, Allah Ya yi miki albarka." "Amin, nagode." Ta amsa jiki a sanyaye ganin ba digon walwala a fuskarsa har lokacin.   "Don Allah Yaya Faruk ka yafemin na..."   "Ki dunga barwa ita Samirar ta dunga wanke wadannan." Ya yi nuni da tsummokaran, fuskarsa a daure ya juya ya tafi. Ta bishi da kallo idanunta cike da kwalla, wannan fushinnasa yana cin ranta kwarai, saidai me za ta yi mishi ya huce?   Misalin karfe sha daya Dakta da iyalinsa suka diro gidan, Jidda har daki ta biyota lokacin tana goge kayan Islamiyyarta, ta dan yi yak'e sadda gabanta ke bugu da sauri-sauri, tasan yau kam zaman gidan zai mata zafi saboda su da basu kaunar su bud'i ido su ganta.    "Anti Jidda sannu da zuwa, ina kwana." Jidda wacce ta yi sakato tana dubanta da mamakin chanjawarta ta hau jinjina kai. "Lallai kan mage ya waye, Ummin ce kuwa?" Ba kunya ba tsoron Allah ta furta a fili.  Ummi ta na murmushi ta maida kanta ga gugarta batare da ta ce komai ba.  Jidda ta ta6e baki sannan ta karewa dakin kallo kafin ta fice. Rufe kofarta ne yasa ta duban kofar, ga mamaki sai ta ji ta daure don ko kwallar bata yi ba, inda sabo kuma ai ta soma sabawa da wannan cin fuskar nasu. Fatanta lokacin makaranta ya yi ta wuce tun kafin su taru gaba dayansu abin ya zame mata da yawa, ga fushin Faruk gareta, sannan ga cin fuska daga su Jidda.      Faruk ya dubi Jidda, kwarai ya ji furucinta saidai ya basar ya cigaba da hirarsa da Dakta.     Ta iso garesu ta zauna gefen mijinta. "Matarka ta yi k'iba ta kara kyau." Ta fada tana duban Faruk, idan dutse zaiyi magana to ya yi gareta, ya cigaba da jan Dakta da hira. Jidda ta yi dariya kawai don tasan halin Faruk, koda zata wuni tana magana tunda kamar ransa a 6ace ya ke to fa bazai amsa mata ba.     Wajen karfe biyu saura sai ga Haidar da Intisar banda Ikram wacce daga can zata wuce makaranta, kamar hadin baki shima Babban Yaya ya iso alokacin da Fadila, Ummi na jin hayaniyarsu saidai bata ko lek'o falon ba, asalima alwala ta yi sannan ta shiga shirin tafiya makaranta. Turo kofar da akayi ne yasa ta waigowa, Intisar ce, ta shigo da murmushi saman fuskarta. "Aa, Amarya Ummi sannu." Ta gaisheta itama fuska a dan sake ganin ita dinma ba wani sabo suka yi ba amman bata bita da kallon banza ba irin na wadancan.     Ta karasa shigowa ciki tana fama da cikinta wanda ya doshi wata biyar saidai yana da girma.    "Makaranta za ki kenan? Ikram ma can muka barota a gida zata wuce, tare za ku yo nan." "Toh." Ta fada cikin rashin sabo.  Daga haka ta fita itama ta cigaba da shirinta, saida ta yi sallar Azhar sannan ta dauki jakarta ta fito. Duk suna falon, yaransu suna gida saboda Islamiyya sai an tashi zasu yo nan.     Duk suka dubeta, ta yi kasa da kanta tana karanto adduoi cikin ranta, haka ta karasa ta durkusa ta gaishesu, duk suka amsa. "Amaryar Lil, Allah Yasa alheri." Cewar Dakta, bata amsa ba banda kasa da ta yi da kanta tana murmushi kadan. Hajiya ta dubeta. "Ki tsaya fa ki ci abinci kan ki wuce." "Toh." Sannan ta mike daga durkuson da ta yi ta nufi kasa, Jidda kallon kafafunta ta ke yi da suka sha kunshi wanda ya kara haskakata, ta ta6e baki gami da yin kus-kus da Fadila suka dara gami da tafawa.   Mazan suka dubesu kawai suka kauda kai. Faruk kuwa tsam ya mike. Ya dubi yayyunsa. "Ina zuwa." Daga haka ya sanya takalmi ya bi bayan Ummi, dariya sukayi, Hajiya kuwa murmushi kawai ta yi. Ta gama gaskatawa Ummi ce farincikin dan nata.     Ita kuwa baiwar Allah, a tsaitsaye ta ci fried rice din loma uku kawai ta yi, Binta na cewa ta k'ara, fadi ta ke a'a saita dawo. Ruwa ta sha sannan ta fito, har zata fita ta ji maganarsa. "Ki jira na kaiki." Ta tsaya cak batare da ta waiga ba, ya yi hanyar dakinsa, mukulli ya dauko, tana tsaye sai jin hon dinsa ta yi hakan ya fahimtar da ita cewar ta kofar baya ya zagaya. Ko a motar baice mata uffan ba, suna isa bayan ya tsaya ya dubeta. "Yau me ya hanaki sanya safa?" Cikin soma gajiya da wannan fushin na Faruk ta amsa cikin rawar murya. "Na manta ne wallahi." Ya sa hannu gefensa ya bata wacce ya fito da shi ta sanya sannan ya cire lock ta fita.  "Nagode." Shine abinda ta ce cikin rawar murya sannan ta rufe kofar ta fice.     Tana shiga su Shukra suka tareta. "Anti Hasiya yau ma Yayanmu ne ya kawoki?" Tsaki ta ja wanda batasan sadda ya fita ba, ta giftasu ta wuce, suka bita da kallo kawai.  Husna ta lura kamar tana cikin damuwa, ta bi bayanta har kusa da kujerarta ta zauna gami da dafata. "Lafiya kuwa Hasiya?" Kamar jira ta ke yi kawai sai ta soma kuka, Husna ta rike kafadarta, ta duba ta ga ana kallonsu. "Ki yi hakurin danne damuwarki, kinga idanuwa duk a kanki fa." Jin haka yasa ta share idanunnata, ta daure ta nutsu, ayau ta ji kewar Antinta Amina kwarai, saidai itama Husna ta yarda da ita, tana da hankali, watakil ta samu shawarar da zata iya bata. .....   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 107 Saida aka tashi ne suka samu damar ke6ewa. Anan Husna ta yi shiru tana kallon Ummi, ganin haka yasa Ummi soma magana.   "Wata shawara nake nema agareki." Husna ta gyada kai cike da k'osawa don sau wajen biyar kenan tana furta hakan amman ta kasa magana.  "Ina jinki."   Dakyar ta samu ta labarta mata kadan cikin labarinta wasu abubuwan kuwa ta sakayasu, ta nuna mata kawai dai tana fuskantar matsala yanzu da saurayinnata da aka daura aurensu aka bar biki daga baya. Ta karanto mata matsalar a sakaye sannan ta k'ara da fadin.   "Husna kin ganni ko? Ban budi ido naga mahaifiyata ba, sannan ban samu wata kulawa daga kishiyarta ba, har zuwa yanzu da aka zo batun aurennan, sannan ni duka-duka ma a Islamiyyar Kano da na ke fadamiki ban jima ina zuwa ba, wani sa'in idan wata fita ta zo shikenan bana zuwa.  Ina cikin tsaka mai wuya Husna, ina 6atawa mijin aurena rai, ki taimakamin da iya abinda ki ka sani, yarda dake ne yasa na sanarmiki abinda ban ta6a fadawa kowa ba a makarantar nan." Husna wacce ta cika da mamakin wai Hasiya yanzu matar aure ce, ta numfasa bayan kalamanta na karshe wanda yasa ta jin tausayinta.Murmushi ta sakarmata. "Ki sha kuruminki k'awata, in sha Allah daga gobe zamu soma. Saidai abinda nakeson ki sanyawa ranki, shi fa mijinnan wajibi ne gareki ki bishi sau da k'afa, karki bari damarki ta wuce, idan ance biyayya ciki har da ba shi hakkinsa na aure idan ya nema tunda dai ansan da igiyarsa akanki, wannan zamanin ba'a sakaci Hasiya,  mata da yawa neman mai aurensu su ke yi, wasu kuwa kamar su jawo namijin ya kwanta da su su ke ji, ballantana kuma idan mijinki wani hadadden ne, tuni za ki yi sake. A baya ne za ki ji duk iyayenmu na irin wannan kunya-kunyar, ansan tana da kyau saidai bisa shawara ki rageta, ki rungumi mijinki hannu bibbiyu. Karki damu, yanzu kinga dai anzo daukata, bari zuwa gobe zan taho miki da wani littafi SIRRINMU na wata tsohuwar marubuciya sai kuma wani  Sinadarin Rayuwa shima marubuciyar ta yi kokari matuka wajen koyawa mata salon kula da miji da gida, zan kuma k'ara miki a kai. Duk fa litattafan Antina ne matar Yayana da nake hannunta, zan rufa miki sirrinki Hasiya koda baki nemi hakan ba." Ummi ta dan ji sanyi, ta yi mata godiya sannan suka zagayo farfajiyar makarantar, anan suka yi kici6us da Fati.  "Yauwa, anzo daukarki fa tun dazu Anti Hasiya." Ummi na jin haka ta daure fuska. "Nikam karki kara kirana Anti banaso wallahi." Fati ta rike ha6a. "Ah, ai sai na kiraki da fin haka, kin kai wallahi. Sai ma idan kin hadani da yayannaki." Dariya Husna ke yi ita kuwa Ummi tsaki ta ja kafin a fusace kuma ta bar wajen. Ganin haka Husna ta sha jinin jikinta, ta biyota da sauri gami da dafe kafadarta.   "Wai Hasiya kodai shine mijinnaki?" Ummi ta juya, ganin Fati bata biyosu ba sai ma dagomata hannu da ta yi alamun (bye-bye) ta juyo ga Husna, kai kawai ta gyada mata a sanyaye. "Innalillahi! Kai Hasiya wallahi ban ta6a ganin irinki ba, kina da kamar wannan me zai hanani zage damtse wajen ba shi kulawa ta musamman? Kodayake..." Sai kuma ta yi shiru don ta tuna kalaman Hasiyar a dazu ta kuma fahimci cewa ko karatun litattafai ba ta yi, ita kuwa har na yanar gizo yi ta ke yi, tana kuma cin karo da abubuwan karuwa na Matan Aure, wasu kuma idan sunfi karfinta bata karantawa kasancewar yayanta kusan kullum sai ya bincika wayarta yasa ta ke takatsantsan.      Ummi babu abinda ta ce saima haushin kanta da ta k'ara ji, lallai kam ta yi babban kuskure a rayuwarta.    Suka rabu Ummi ta nufi motar, direban gidansu Haidar ne, Ikram na zaune ciki sai faman cika ta ke yi da batsewa.  Ummi ta shigo sannan ta gaida Direban, ta kara da fadin. "Ku yi hakuri don Allah, bansan ya zo ba."    Tsaki kawai Ikram ta ja sai direban ke amsawa da babu komai.   Earpiece Ikram ta sanya a kunnenta tana jin wak'a , ita kuwa sai ta maida hankalinta ga kallon hanya cike da tunanin maganganun Husna, kwarai ta yi ganganci, tasan har da hudubar su Anti Abida da Halima ya taimaka wajen k'in sakarwa Faruk. Wanda sam bai cancanci haka ba, sai ta ji tana zuci-zucin gobe ta yi ko don Husna ta damk'a mata litattafan. Har suka isa ba wanda ya cewa wani uffan, koda suka shiga kai tsaye sama kowannensu ya nufa. Nan suka iske daga Babban Yaya sai ko Faruk da Hajiya sai su Jidda kowanne na kawo raayinsa, lefe Babban Yaya da Hajiya ne zasu hada, na Faruk bai wuce kawai gani ba, kudin ma sunce ya barshi, sai batun dinner party da suke yi da kuma fiddo anko wanda Babban Yaya ya ce su fadi irin wanda zasu yi zai kawo musu su za6a. Duk wannan za su yi shi ne a cikin sati biyu, saboda zuwa Adamawa da zasu yi su kwana uku su dawo don Modibbo ya matsa akan lallai sai an tafi saboda wadanda tsoffinsu basu sani ba.      Shigowar su Ikram dinne ya katse su, Faruk idanunsa akan Ummi ya kasa daukesu, haka kawai ya ke jin kewarta ainun, wannan karon fuskarsa a dan sake,  suka gaishesu sannan Ummi ta yi ciki ta bar Ikram anan, itama tana jin batun da akeyi ta mike zuwa nata dakin inda ciki ta riski Intisar kwance saman darduma ta idar da sallah.     Wajejan biyar na yamma, Haidar da Ridwan wadanda suka je daukar yara daga makaranta suka shigo ciki, don daman direban suka hutar da sanyashi dauko su Ummi kawai. Nan gidan ya k'are kacamewa, Ummi duk ta takura har saida suka wuce, koda aka kirata cin abinci ta ce ta ci, akan haka har fad'a Hajiya ta yi mata  gami da nunamata kada ta sake irin hakan ta dunga ci tare da su. Daddy yana dawowa daga Kano inda ya je ta'aziyya matasan suka koma wajensa har Hajiya, nan ya ke jin dukkan shirye-shiryensu, ya yi na'am da hakan, ya kuma ji dadin yanda kansu ke a hade har kowanne ya dauki nauyin abinda zai yi. Haidar na buga I.v da rabo ya dauka, shi kuwa Ridwan na dinner party, yayinda Babban Yaya da Hajiya zasu yi lefe, karshe Daddy ya dauki alkawarin yiwa Ummi kayan daki da komai na mata, acewarsa ko don zaman da ta yi da su ta cancanta, bai dace su bar iyayenta da nauyi ba, ta zama tamkar jininsu. Faruk ya ji dadi matuka, bakinsa ya kasa rufuwa, bawai don wani abin ba sai don ganin kowannensu ke nuna kaunarsa da wannan auren, hakazalika hadin kansu ya fi komai faranta ransa, fatansa har mutuwa su kasance tare haka.        Washegari sam basu hadu da Ummi ba, sai ta waya ta kirashi, wannan karon bai gwanyata ba don ya amsa, ta gaisheshi ya amsa ba kamar jiya ba, a karshe ta rasa abin cewa kawai ta yi mishi adduar sa'a sannan suka yi sallama. Daga lokacin kullum sai ta gyara mishi daki tas.      Koda ta je makaranta Husna ta damk'a mata litattafan, shikenan kuwa ta samu abin karatu, koyaushe cikin karatu ta ke yi har ta soma gano kuskurenta kwarai, har sai gashi tun tana kunyar wanke mishi undies har ta gwada yi na rana daya sai ta kasa shanyawa kawai ta matsar da labulen dake wajen kwamin wanka ta shanyasu a karfensa.    Ranar Alhamis ta yi wannan aikin, yana dawowa ya ganewa idanunsa, ido ya fiddo yana kallo da mamaki, sun wanku tas, saidai anya Umminsa ce za ta yi? Ya kasa gaskatawa har ya gama wanka ya shirya cikin doguwar jallabiya fara ya nufo cikin gidan.      Hajiya na sashen mijinta, Ikram kuwa wacce ta dawo kenan, tana dakinta tana aikin makaranta. Wannan ya ba shi damar shigewa dakin Ummin. Sallamarsa ce ta sanya ta mikewa zaune da sauri gami da tura littafin kasan filo ta riko wayarta kamar ita take dannawa, ya dubeta sannan ya dubi hannunnata, ta yi kasa da kanta. 'Ya Allah, Ka bani ikon dauriya ga dukkan abinda Yaya Faruk zai zo min da shi.' Ta yi furucin a zuciyarta, a fili kuwa dan zamowa ta yi gami da mishi barka da zuwa, ya amsa sannan ya zauna gefenta, hannu yasa ya kar6i wayarta, ya gama bincikensa har open apps ya duba saidai ba abinda ta bude, ya ajiye wayar saman kafafunta yana dubanta fuskarsa cike da damuwa.   "Ki yi hakuri Ummina." Ta dubeshi ido waje. "Hakurin me?" Ya lumshe ido ya bude. "Na 6ata miki rai kwana biyunnan, na yi miki laifi, ki gafarceni." Ta girgiza kai da sauri. "Wallahi ni ce mai laifi Yaya Faruk, don Allah ka yi hakuri, in sha Allah na daina yi maki abinda ba ka so..." Ta karashe a dan kunyace, ya yi murmushi wanda ya jima baiyi gareta ba gami da riko hannunta ya dan murza.   "Is ok, share wannan, ni yanzu dai ki gayamin, daman an iya wankin undies aka bar Faruk nata wahala?" Ya fada a shagwa6ance, ji ta yi kamar ta nutse a wajen, ai fa kunyarnan sai a sannu zai saketa gaba daya. Ta hau sussunne kai tana murmushi, ya yi dariya yasa hannu ya karkato fuskarta gareshi, ganin haka ta lumshe idanunta batason su hada ido. Ya yi mata k'uru da nasa idanuwan. Can kuma ya numfasa ya sanyata jikinsa ya matse.   "Ummina idan addua ki ke min ki rage yinta, don idan Faruk ne kin gama mamaye zuciyarsa, please ki ragwanta kinji? Ina jin kamar zuciyata zata fashe da sonki." Ta bude idanunta tana numfarfashi, tausayinsa ta ji, ta yi amannar cewa son da Faruk ke yi mata bai kai wanda ta ke mishi ba, kuma ba hakan na nufin ita din bata son nashi bane. Tana ji bata iya hanawa ba, tana gani bata iya ta kwa6a ba, haka sakonnin suka yita shigarta, duk inda ya biyo bata ko tureshi, har abin ya kai ga fin karfin tunaninsu, sai kuma don kansa ya kyaleta yana dubanta.    "Za ki tayani kwana yau? Tsoro nake ji."  Batasan sadda ta dan harareshi ba sannan ta kauda kai gami da dan turo baki, ji ta ke kamar ta nutse saidai batason 6ata ranshi, batason ya k'ara nisantarta. A kwana biyun nan ta wahala da shariyar da ya ke mata.     Ya hau gyara mata sutura yana fadin. "Kinji? Please." Shiru ta yi, kamar ta ture hannunshi don tasan ba a iya gyaran zai tsaya ba,  ai kuwa ta ji ya sumbaci hannunta. "Lallen nan naki ya burgeni Ummina, ki dunga yimin please." Ta gyada kai kawai, sallamar Hajiya yasa ta ja baya da sauri gami da rufe kanta, shi kuwa baya ya ja kadan ya gyara zamansa sannan ya amsa. Hajiya jin muryarsa ta yi mamaki, hakan yasa ta fasa shigowa don kuwa wani hadin ne ta kawowa Ummin na mayuka masu gyara jiki don ance in kana da kyau ka k'ara da wanka.     Ganin ta maida kofar ta rufe bata ko shigo ba yasa Faruk duban Ummi yana murmushi mai bayyana hakora. "Kinji Hajiyata fa?" A rude ta ke kallonsa. Ta karya wuya. "Don Allah Yaya Faruk ka tafi kada ta dauka wani..." Sai kuma ta yi shiru don gudun 6ata ransa, ya dan ja jelar gashinta da ya lek'o. "Kada ta dauka me? To naji zan fita, amma kirani da wani suna banason wannan." "To Sadauki." Ta fada da sauri. Ya yi 'yar dariya. "Aa, wannan Hajiyata kadai ke fada." Ta marairaice fuska can kuma ta ce. "Yalla6ai." Ya ta6e baki ya girgiza kai. "Chanja." Kamar zata yi kuka ta yi shiru can kuma ta dubeshi, ko ajikinsa asalima dariya ya ke mata.   "Um..um...toh Yaya Umar." Dariya kawai ya yi ya mike gami da sumbatar le66anta sannan ya ce cikin rada. "Ina sonki kamar na mutu." Daga haka ya juya ya fita, ta bishi da kallo tana murmushi har ya fice.     Daga ranar masoyan suka shirya....!!!          [truncated by WhatsApp]   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 109    Zirga-zirga ta ke yi a dakinta ko kayan makarantar ta kasa fiddawa, can dai ta k'arasa fisge dankwalinta ta ajiye gefe, har da ribbon din da ta ke tufke yalwataccen gashinta na fulanin usul, ta zaune gefen gado.    'Kai anya kina da hankali Ikram? Me za ki yi da DAN KAUYE?'   Shine tambayar da wani sashe na zuciyarta ta jefomata.    Ta runtse ido sannan ta ja tsaki gami da mikewa tsaye.   "Craziness!" Ta fada a fili sannan ta rage kayan jikinta ta fada wanka.       Bayan fitowarta ne daga ita sai tawul ta tarar da kira har sau uku a wayarta, ta yi saurin dubawa, biyu daga wani saurayinta ne Khalid wanda kawai ta ji ba ta yi murna da kirannasa ba, ba kamar a baya da ya ke dan burgeta ba, ta shareshi ta bi bayan kiran 'yar uwarta Ihsan wacce itace ta kira sau daya.    "Ke ina ki ka shige ne ina nemanki?" Cewar Ihsan. Ta dan dara, "Yi hakuri baiwar Allah, wanka na shiga fa. Ya akayi, ya su Mami?"   "Mami ta fita siyayyar tsaraba na mutan Adamawa, ke ni bugowa na yi na ji ko da waccan munafukar za'a je?"    Murmushi Ikram ta yi. "Babu inda za ta je, gobe ma zata koma kauyensu. Ina Man dinki?"   Ta ja guntun tsaki. "Yana can inda ya ke, na ji yana batun shima ba a soma bikin Yayannaki yana nan ba don zasu je dangin Abbansa." Dariya Ikram ta yi karo na biyu. "Me ye na tsakin wai? Kefa ki ka cemin kin soma sonshi." "Bazaki gane ba, ya iya tsara kalamai wallahi, matsalar daya yana son sanyomin batun zai min kaza da kaza bayan aure. Haka fa zuwan da ya yi satin da ya wuce, wallahi har rungumeni yaso yi na kauce. Amma hakan bai hana ni sonsa ba, saidai banason hakan ne kawai."   Baki Ikram ta ta6e, "Sai hakuri da neman tsari daga sharrin shaidan, mai yiwuwa saboda shi kadai ya tashi gaban iyayensa shiyasa, kinga kuma yanda suke ji da shi."    Tsakin dai Ihsan ta k'ara yi. "Za ki yi ankon Yaya Faruk? An fiddo." Cewar Ikram. "Allah Ya sauwake!" Cewar Ihsan cikin daga murya.  Ikram ta ja tsaki sadda ta isa ga sif din kayanta da zummar fiddo na sanyawa.  "Kefa wani zubin banza ce, rashin yinki bakisan kamar kin nunawa mutane har yanzu kina sonshi ne ba, ai wallahi gwara ki yi ki cekare abinki, ga Abubakar dinki a gefenki. Ke kanki kinsan hakan ma abin alfaharinki ne tunda gayen karshe ne shima a haduwa."   Ihsan ta yi shiru sai kuma ta amsa. "Barni tukun, sai na yi tunani. Bari na barki kada na cinye miki dan katin." Daga haka suka ajiye wayar.   Ummi kuwa tun a daren ta karasa shirin kayanta, sun yi waya da mutan Gombe ya fi sau uku a ranar duk su dinma d'okin zuwanta suke yi. Yau ko ta kan abincin dare bata bi ba don ta dage wajen shirye-shiryenta, daga ta rufa akwati sai ta tuna da wani abin ta bude ta sanya, kamar yanzu da ta ke kokarin sanya wasu kayanta da zata bayar, tana cikin jerasu ciki ne, Faruk ya yi sallama ya shigo.  Ta amsa tana mai duban kofar, fuskarsa cike da damuwa, kananun kayan da suka zame mishi jiki yau dinma su ya sanya. Cikin dauriya ta sakar mishi murmushi don kuwa ta fahimci sam tafiyar ce baya so saidai don babu yanda ya iya ne. Kafin ta yi wani yunkuri ya karaso ya kwantar da kai a kafadarta gami da rikota jikinsa ta gefe, ta lumshe ido batare da ta yi yunkurin hanashi ba don tuni ta daina wannan sai idan ta ga abin zai fi karfinta tukunna.     "Tafiya za ki yi ki bari mijinki?" Ta sunkuyar da kanta tana duban hannuwansa dake cike da gargasa. Har lokacin murmushi ta ke.   "Kaima ai tafiyar za ka yi." Ya dago gami da sanya bakinsa saitin kunnenta.    "Ba zan samu rakiyarki ba kuma ko?"   Ya fada a shagwa6ance, numfashinta sai safa da marwa ya ke yi, ta kasa cewa uffan kasancewar ya cigaba da sarrafata son ransa, haka har tsayuwa ta nemi gagararsu.      Can kuma ya dago kai yana dubanta da idanunsa da suka yi k'ank'an.    "Na yi? Kin amince?" Ta zaro ido tana dubansa. Abin ya ba shi dariya, ya ja kumatunta.    "Matsoraciya, kodayake na ga kin rage tsoron, oya tell me, ya akayi ya ragu?"   Ya karashe yana mai zama gefen gado ita kuwa na saman kafafunsa. Shiru ta yi kawai tana murmushi, ya ja karan hancinta har saida ta yi 'yar k'ara.     "Wani 6angaren kunyarki na burgeni, yana k'aramin sonki sosai, ina son mace mai kunya, shine babban ado ga diya mace, yanmatan yanzu basusan wannan ba, za ki yi mamaki idan ki ka ga yanda mata ke tallata kansu ga maza, za ki yi mamaki idan ki ka hau yanar gizo yanda mata ke aika hotunansu babu ko rufin kallabi da sunan neman mijin aure alhalin basusan cewar sam mazan da suka san abinda sukeyi bazasu kallesu da daraja ba, ke har fa wajen biki kawo tallar kawunansu suke yi ga maza har kuwa inda suke, za kuma ki yi mamakin ganin mahaukatan da ke tallatawa mijinki surarsu." Ta hade fuska kadan. Ya kara matsarta a jikinsa yana dan murmushi. "Saidai sun yi kadan, tsarin Allah muke nema koyaushe daga sharrinsu, in sha Allah zai karemu. Kinsan a inda na tsani kunyarki?"   Shiru ta yi ganin ya maimaita yasa ta girgiza kai. Saitin kunnenta ya yi mata rad'a.    Ai batasan sadda ta runtse ido gami da kokarin zamewa ba, saidai ba rikom ragon namiji ta samu ba. Dariya kawai ya yi mata.    Ya fi awa daya a dakin, daga an soma hirar arziki zai hau lalubenta, sannan a cigaba har dai a karshe ya fita sakamakon Daddy da ya yi kiransa ta waya yana nemansa, wannan ya sanyashi tafiyar dole. Kwance ta ke tana faman juyi, can kuma idan ta gaji ta ja tsaki, wai meyasa haka ne? Ina ita kamarta ina kuma wani dan kauye? Meyasa ta kasa daina ganin hotonsa a kwayar idanunta, ta mike zaune gami da jingina da katakon gadon, batasan sadda hawaye ya zubomata ba, ba don komai ba sai don takaicin wannan lamari, abin kunya ne babba agareta, ta ja wawan tsaki cike da jin haushin kanta, wannan kuwa abu ne da bazata ta6a bari ya yiwu ba, wai ta ce KO A MAFARKI....! Ta yi adduoi ta shafa sannan ta kwanta, har dai bacci ya yi awon gaba da ita. Washegari tun Asuba da Ummi ta farka bata koma ba, karfe bakwai zasu wuce, kai tsaye wanka ta fad'a ta sanya leshinta ruwan hoda marar nauyi. Karfe bakwai kuwa aka fidda akwatinta, bayan sun kammala karyawa, Faruk har dakinta ya zo kafin ya wuce ofis suka yi sallama, haka ta wuce cikin kewarsu da kuma d'okin zuwa ga mahaifinta da kakanninta...!!!           DAN ADAM @RUFAIDA OMAR     110 Sai wuraren karfe daya suka isa Gombe, kai tsaye Tudun Wada suka nufa, da yaran gidan ta soma tozali a kofar gidan, da gudu suka shiga ciki domin sanarwa jama'ar gidan, dariya kawai ta yi sannan ta ja jakarta ta hannu ta yi ciki, a zaure suka yi kici6us da Anti Halima wacce ta taho ganin ko dagaske suke, ai kuwa ta rungumeta suna murna gami da lale marhabin da Amarya. Suka karasa ciki, ganin Dada tsaye tana rarraba idanu na son ganin ta inda zata 6ullo yasa ta k'arasawa a guje gami da rungumeta, Dada ta dan tureta cike da farinciki. Kafadarta ta dafa. "Use Hasiya, kun sha hanya." Dariya ta yi. Haka suka yi ta nan da nan da ita kamar wannan ne ganinsu na farko da ita.     Saida ta gabatar da sallah sannan ta isa dakin Malam, yana kishingide yana gyangyadi saman darduma, sallamarta ce ta sanyashi wartsakewa yana mai amsawa fuska a sake. Bayan sun gaisa ne ya ke tambayar mutan Abuja. Bata jima sosai ba ta koma ciki. Sai yamma iyayensu maza suka dawo daga kasuwa, alokacin har direban da ya kawo Ummi ya juya bayan ya gabatar da sallah ya ci abinci. Malam Balarabe ya yi farinciki da ganin diyartasa.  Sai bayan Magriba suka samu ke6ewa da Malam Balarabe, anan ta ke jin labarin zuwansa Ringim bayan tafiyarta, inda ya sanya gidansa a kasuwa, ya hada kan kudadensa ya sallami Haruna yaronsa mai tayashi aikin balangu a kasuwa sannan ya taho da zummar idan an siyar Malam Yahuza zai aikomishi da kudaden. Hakan ya yi mata dadi, shikenan sun rabu da Ringim kenan. Ya shiga bata labarin kiran da ya samu ta waya daga Daddy cewar kada ya yi komai na kayan daki shi zai yi don shima diyarsa ce, ya sanarmata koda ya ji hakan, ya ji abin banbarakwai, ya so tambayarta ta waya saidai yasan ba lallai ta samu labarin, koda ya sanarwa yan uwansa, su kansu sunyi mamaki, Malam da kansa ya sanya suka kira Daddy. Bayan an gaisa ya ce.     "To kai Alhaji ayi haka? Kwa daukarwa kanku nauyi har haka?" Dariya Daddy ya yi ya nuna zai iya yiwa Ummin haka koda ace ba dansa za ta aura ba, acewarsa itama diyarsa ce." Jin haka har Malam saida ya yi kukan farinciki, ya yi mishi godiya da binsa da kyawawan addu'o'i, Daddy ya nuna bakomai, tunda har suka bawa dansa aurenta sun mishi komai a rayuwa.    Ummi jin dukkan lamarin ta ke yi wani iri, jikinta ya yi sanyi, ko kusa bata da masaniya kan abinda ake ciki a Abuja.    "Kada ki bani kunya Hasiya, ki yi kokarin bin mijinki tsakani da Allah, tabbas Umar yaro ne nutsastse, ki godewa Allah don kuwa kin yi babban sa'a, yana sonki kuma iyayensa suma suna sonki, ki zauna da su da zuciya daya, wanda zai yi maka haka a rayuwa lallai bai kamata ka yar da shi ba." Har da hawayensa alokacin da ya ke fadin haka gareta, ita kanta saida ta share ruwan hawayen, acan kasan ranta kuwa, adduo'i ta ke ta jerowa ga Daddy da iyalinsa.      Kwanan Ummi biyu a Gombe, su Hajiya sun wuce Adamawa gaba dayansu har Modibbo. Saidai banda su Ihsan da sauran yaran masu zuwa makaranta da kuma surukansu.     Ita kuwa sosai su Abida suka shiga gyarata, duka-duka bikin a wannan lokacin bai fi saura kwanaki goma sha biyar ba, a bakin Dada ta ke jin cewa har mutanen Adamawa suma zasu zo. Dattijuwa Binta, tsohuwa mai ran karfe kenan Yaya ga Dattijo Manu(kakan Ummi) da zuri'arta wadanda rabonsu da Gomben tun rasuwar Inno.     Gaba daya sai ta k'ara ji ta d'okantu da son ganinsu.      Duka-duka su Hajiya kwanansu biyar a Adamawa suka dawo har da wasu cikin yan uwansu wadanda sai bayan biki zasu koma, wasu kuwa sai dab da biki sannan zasu iso.    Shirye-shirye sosai akeyi, ba ga nan Abuja da mutan Kano ba, ba kuma ga can Gomben ba.      Amarya Ummi ta murzu iya murzuwa, idan ka ganta sai kace bata ta6a shiga rana ba tunda ta zo duniua tsabar kyau da murjewa da fatarta ta yi, ga shi kuma daman lokaci ne na damuna ba ranar ake yi sosai ba. Kayan gyara mace kuwa, har gajiya ta ke yi da sha, don Dada bata barta ba, haka suma surukan Dadan, (Anti Halima da Abida), daga sun ke6e da ita suke duramata. Kusan kullum sai sun kai ukun dare suna waya da ango wanda ya nuna gaba daya kewarta ya isheshi, har rantsuwa ya yi mata akan wani lokacin ji ya ke kamar ya yi tsuntsuwa ya biyota Gombe. Dariya kawai ta ke yi wani lokacin, wani lokacin kuwa tausayi ya ke bata.    Amina kuwa, tun kafin tafiyarsu Hajiya Adamawa ta kirata akan ta dawo.  Ana sauran kwana biyar biki da yamma tana zaune ta gama yin sirace na gyaran fata, hannunta rike da kofi wanda aka kad'a madara da wani gumba, su Abida sun sanyata gaba har da wasu yayyunta daga Jar Kwami akan sai ta shanye, kiran Amina ya shigo wayarta, dakyar suka bata wayar don da fari sun k'i wai sai ta shanye, wayar duk ta koma yaluwa, aun gaisa ta ke sanarmata cewar ta iso Gombe tana tasha wai ta yi mata kwatancen unguwarsu, ai Ummi daskarewa ta yi a zaune don mamaki, gani ta ke wasa kawai ta ke yi, saida ta rantse sannan ta saki dariyar murna.   "Bari na bada a yi miki kwatance." Ta mikawa Abida wayar, nan ta kwatantawa direban Adaidaitan.    Ummi kasa zama ta yi, zata mike suka dakatar da ita, batasan sadda ta kwankwade maganin ba don hankalinta ya tafi ga Antinta. Dariya suke mata saidai bata ko sauraresu ba ta sanya dogon hijabi ta yi sashen Dada cike da mamakin yanda akayi Hajiya Mama ta barta ta zo.   "Dada! Dada!!" Suka yi kici6us a kofa. "Lafiya Boddo?"   Ta rungumeta. "Ga Anti Amina nan zuwa, ta Kano wacce na baki labarinta." Itama Dadan ta hau farinciki. "Kai Alhamdulillah, shiga ki yi wanka kafin ta karaso, bari na hadamiki ruwan dumin." Ai da gudu ta shige ciki ta dauki roban sabulunta, sosanta shanye a saman igiya ta ja, Dada da kanta ta hadamata ruwan wanka ta fad'a.  Tana daga bandaki ta ji muryar Amina na gaggaisawa da mutanen gidan dake mata lale. Ai sauri-sauri ta shiga yi, tana fitowa ta ajiye bokitin sabulun anan kofar dakin Dada, hannunta rike da soson ta fada ciki sai jikin Amina, suka hau dariya. Dada ta kai mata dundu a baya. "Ke kam Allah Ya sauwaka miki, kai Boddo, a jik'e fa ki ke." Ummi na dariya ta mike zaune, "Wallahi murnar ganinta ne, ta yimin bazata." Dada ta kar6i sosannata ta fita tana dariya.     Amina wacce ke dubanta fuska a washe ta kamo hannunta ta zauna gefenta. "Wai kece kodai mafarki nake yi?" Cewar Amina. "Ai Anti ni zan ce ina mafarki ma wallahi, ban ta6a zaton za ki zo Gombe [truncated by WhatsApp] DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 111   "Asiri ya tonu, bayan dawowar su Mami daga Adamawa da kwana biyu Abban Adnan cikin dare idanunsa ya gane mishi Hajiya Binta na tone-tone bayan windon dakinsa, bai ma gane kowacece ba, Mami ce a dakinnasa ita dinma idanunta biyu, ganin ya fita da sauri ta mara mishi baya, saida suka zagaya suka isketa tana kokarin binne wasu layu, ke wallahi idan karshen mugunta ya zo babu mai iya tserar da mutum idan ba Allah ba, kuma daman shi Allah ba Ya zalunci, mata ta rude, har kusan sakinta ya yi, itace har da durkusawa neman alfarma wajen Mami akan ta taimaka ta tayata rokar gafararsa. A daren bai sauraresu ba, kiris ya rage a saketa saidai ta ci darajar 'ya'yanta, dakyar da sudin goshi ta samu ya yafemata, saida Mami ta sanya baki sosai. Amma fa nima ina daga kicin ina aiki na ji Mamin suna hira da Hajiya Mama don gida ta zo ta sameta. Tun daga lokacin kuwa jikin Hajiya Bintar ya yi sanyi, har sashen Mami ta je ta fayyacemata mugun kullin da ta yi mata Abba ya juyamata baya da kuma yanda ta so had'e baki da ke amma ba ki bata goyon baya ba, tana kuka ta nemi gafarar Mamin, yanzu ba ki ga idan kin je gidan ki ka shiga sashenta yanda zata kar6eki ba, wallahi sai kinyi mamaki, duk ta yi sanyi har sashen Mami ta biyo Hajiya Mama suka gaisa, Iklima itama yanzu duk ta chanja kodayake ance ita wani saurayi ne ya yaudareta ya kaita gidan masu zaman kansu zai yi mata fyade, kinsan Iklima yar son zuwa party, dakyar Allah Ya kwaceta a hannunsa sakamakon zuwan yan sanda kame, aka hada har ita, saida ta kwana biyu a kaso Abba ya ce babu inda zai taka ya je belinta, sai fa can cikin yan uwan Ummanta ne suka je suka yo, ranar kuwa ta ci duka wajensa don har  makaranta ya hanata zuwa yanzu ya ce aure zaiyi mata." DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 112 Sanye ya ke da shadda kalar sararin samaniya sai hula shima bulu, sai murmushi ya ke bugawa yana gaisawa da yan uwa har da mikawa Dada hannu suna gaisawa gami da dariya. Ummi bata iya motsi ba hakanan ta kasa cewa uffan saida ta tsinci muryar Amina na fadin. "Wai daman *ABUBAKAR* dan uwa ne gareku?"   Ta girgiza kai sannan ta maida dubanta ga Amina kamar wata doluwa.    "Wallahi bani da masaniya nima." Basu kai ga tsinkewa da lamarin ba saida suka ga shigowar Alhaji Kabiru Jimeta da sallamarsa. Mamaki, rud'ani da tsananin faduwar gaba duk suka tararwa Ummi da Amina, aka rasa mai magana cikinsu har wasu cikin mutanen Jar Kwami suka shigo wasu rirrike da jakunkunan kaya.    "Wai ina Amaryar?" Cewar wata mace da zata kai shekaru arba'in a duniya.     Da sauri ta ja baya daga jikin windon tana sussunne kai, wata gwaggonta ta riko hannunta tana dariya.   "Oh 6uya ki ke? To fito nan ga uwarki da ba ki sani ba, Safina, sannan kuma (ta nuna wata doguwa mai rike da bebi a hannunta, bazata wuce talatin da tara ba) itama uwarki ce Nafisa sunanta, duk yaran gwaggonki ce Binta." Sukayi dariya, wacce aka kira da Nafisa ta ce. "Maza fito na kaiki ku gaisa da Innarmu ta ga Innonta ta dawo." Amina ta hau janyo musu ita don ta mak'ale a bayanta, ita kanta dauriya kawai ta ke yi saidai jikinta ya yi mugun sanyi, tambayar da kowannensu ke yiwa zuciyarsa bai wuce na son sanin dangantakar Alhaji Kabiru da mutanen gidan ba.    Ummi na kallo suka ja ta har rumfar Dada inda ake zazzaune ana gaisawa, kan Ummi a k'asa yayinda aka zaunar da ita gefen wata dattijuwa wacce shekaru suka ja saidai garas tana gane mutane sannan tana fahimta. Da harshen fulatanci ta ji wacce ta zaunar da ita ta yi magana. Abinda ta fada ne ya janyo hankalin sauran bak'in duk suka dubeta, Abubakar da hankalinsa ke kan wayarsa yana kokarin turawa uwargidansa sak'on isowarsu lafiya, shima ya dago kai yana duban wacce aka kira da Amarya kuma jininsa mai kama da Innonsa.    Mamaki k'arara ya bayyana saman fuskarsa, a yayinda shi kuwa Alhaji Kabiru ke kallon Ummi cike da al'ajabi na kamanninta da Antinsa Inno wacce a girme ma ya girmeta saidai duk da hakan kanwa ce ga mahaifiyarsa GWAGGO BINTA babbar Yaya ga Manu Lamido uba ga marigayiya Hasiya...!     Hannun Gwaggo Binta na rawa ta kamo na Ummi tana mai rike kafadarta da hannun damanta.   "Sannu Hasiya, shakka babu wannan jininmu ce diya ga diyata Hasiya, ashe da rabon mu k'ara sanyaki a idanunmu?" Sai ta janyota jiki tana hawayen farinciki ga kuma bakinta da ya k'i rufuwa don murna.      "Ke ce?" Cewar Abubakar da mamaki yana nunota da yatsa, hakan yasa duk wanda ke fahimtar hausa sosai ya kalloshi don ba kowa cikinsu ne ke jin hausa ba, Malam Balarabe da Alhaji Kabiru har suna hada baki wajen fadin.   "Ka ta6a ganinta ne?" Ya jinjina kai yana murmushi mai bayyana hakora. "Tabbas Dad ita nace maka na gani fa a gidansu Abban Kano mai kama da Inno. Saidai..." Sai kuma ya yi shiru, har lokacin bai bar mamaki ba. Kallon Ummi kawai ya ke yi kamar Innonsa, Innonsa Zahra mai matukar kaunarsa, sun shaku sosai, ayi wasa ayi dariya, yana mata kallo kamar wata sa'arsa kuma kanwa gareshi don koda zata girmeshi ba da wasu shekaru na azo a gani bane sannan gajeriya ce bata da jikin girma. Sune har guje-guje, komai na shawararsa idan ya dauko to fa da Inno zasuyi ta, sau da yawa kafin iyayensa su san wani abu nashi, Inno ta sani don gaba daya tare suke zaune har Gwaggo Binta a gidan Baffansa Kabiru.    Bai mantawa ana shirin bikinta ta yi bankwana da duniya, mutuwar da sosai sun ji ta a zukatansu don har kwantar da shi ta yi, hakanan mahaifiyarsa Hajiya Salma ita kanta saida ta yi kamar ba zata rayu ba tsabar razanar da ta shiga sanadin mutuwarta. To me ya kaita Kano? Me kuma ta ke yi gidan su Ihsan? A ina Faruk ya ganta ya ce yana so?    Wannan shine tambayoyin dake  yawo a kwanyarsa da ba shi da mai amsa mishi.    Kowa a wajen ya cika da mamaki banda wadanda sukasan silar zaman Ummi a Kano da Abuja.     Bayan gama gaggaisawa mazan suka fita, itama Gwaggo daki ta koma.  Ummi ta ja Amina suka koma sashen Anti Halima.   "Kinga ikon Allah ko Anti?" "Allah kenan, ashe duk firiritar Ihsan kuma danginku za ta shigo? Wannan lamari saidai Allah, ya dangantakar ta ke?"   "Gwaggo Binta kakarsa uwa ce ga Ummana. Nima tana matsayin kakata."   Amina ta hau gyada kai sai kuma ta soma dariya Ummi na tayata tana tambayar ko lafiya. Girgiza kai ta yi. "Wallahi Ihsan gwanar wulakanci ce ta ban tausayi kawai, yanzun ko da wane idon zata kalleki? Shiyasa a duniya ba'ason ka dunga wulakanta DAN ADAM don bakasan mai yi maka rana ba gobe."    Murmushi Ummi ta yi kawai tana kokarin goge wayarta wacce ta koma yaluwa saboda kurkum.     Sai dare Abubakar ya samu damar ke6ewa da Ummi sadda ita da Amina suka je kai mishi damammiyar fura inda ya je zaune tare da Gidado (wanda shima bai jima da zuwa ba daga Jar Kwami) suna hira. Kusan ma a kyau har Gidado ya tsere Abubakar saidai shi zai nunamishi wayewa da hutu sosai da kuma zurfi a ilimin boko don kuwa shi Gidado iyakarsa sakandire ya watsar ya fada kasuwanci, Kano ya ke zuwa saro kayan sawa na mata ya ke siyarwa, sosai yana samu don asirinsa a rufe. Matarsa daya Aisha wacce sukayi auren soyayya sai dansu da baifi shekara daya ba don duka-duka aurensa ko shekara biyu baiyi ba saidai idan Gidado ya sanya sutura sai ka rantse ba mazaunin Jar Kwami bane musamman idan Abubakar ya mishi aiken suturu daga Adamawa.      Da sallama suka shiga suka ajiye furar kafin su gaishesu, suka amsa. Ummi ta dubi Gidado da murmushi saman fuskarta.    "Yaushe ka zo?" Shima murmushin ya mayarmata. "Ko awa biyu cikakku banyi ba." Ta gyada kai sannan ta mike zata bi bayan Amina wacce daman suna ajiyewa ta fito, Abubakar ya dakatar da ita. "Ummi." "Naam." Ta amsa tana dubansa gabanta na dukan tara-tara. "Please ke ce dai wacce na sani a Kano gidansu Ihsan?"   Ta gyada kai a sanyaye.  "To meya kaiki can?" Gidado ya cafe. "Au ka ta6a ganinta acan kenan? Ai ta zauna can." Jin haka Ummi ta mike da sauri, tana jin Gidado ya soma labartamishi yanda lamura suka kasance ita kuwa tuni ta soma zura takalminta, suka kama hanya da Amina tana sanarmata yanda akayi, Amina murmushi ta yi. "Allah Sarki." Shine abinda ta ce kawai.                    ***   ***   ***                      ABUJA  Tun bayan sati da kwanaki da tafiyar Ummi, Ikram bata cikin nutsuwarta, gaba daya ta rame ta koma wata shiru-shiru, koyaushe bata da aiki sai na kuka ga wani ciwon so da ya addabi zuciyarta har tana ji idan bata samu cikar burinta ba zata iya rasa rayuwarta. Har mutanen Kano suka iso Abuja bata da walwala sosai, kowa sai ya tanbayeta damuwarta amman ta nuna ba komai kawai bata jin dadi ne, Ridwan har dubata ya yi ya kuma gano damuwa ce kawai ta sanyawa kanta, tanbayar duniya ya yi mata amman babu amsa. Daidai da dinkin ankon da sukayi kala biyu ya yi mata yawa sakamakon ramar da ta yi.    Yau ma babu kowa a gidan, Hajiya sun fita tare da su Mami ganin gida, ita kuwa Ihsan da su Maryam sun tafi gidan Baraka can zasu wuni har da wasu cikin bak'in Adamawa, manyan kuwa suna can kwatas suna hira da Hajjah wacce ta zo ko don jikanta. Tana kwance daga ita sai shimi da dogon wando wanda da kadan ya wuce gwuiwa, wuf ta mike tsaye, kai tsaye kofa ta nufa, babu kowa a falon, hakan ya bata damar zarar mukullin kofarta wanda ana iya amfani da shi wajen bude kofar dakin Baraka inda ya zama na Ummi a yanzun. Ta bude dakin ta shiga gami da sakayawa yanda ba za'a gane ba, dakin a gyare tsaf don duk bayan kwana uku sai Binta ta gyarashi, ta hau rarraba idanu har Allah Ya taimaketa ta hango jakar Islamiyyar Ummi rataye a jikin wani dogon karfe na rataye kaya. Da sauri-sauri ta isa wajen ta janyo jakar ta soma bincikawa, ba ta ci wuyar ganin hoton da ta ke nema ba, ta kurawa hoton Gidado ido hawaye suka zubo a kuncinta, shine saurayin da a iyakar tsawon rayuwarta bata ta6a ganinsa ba sai a hoto, ba kuma ta ta6a son wani ba kamar yanda ta ke sonshi, da sauri ta dubi kofa sannan ta shiga maida litattafan Ummin cikin jaka gudun kada wani ya zo ya isketa, ta sanya hoton cikin rigarta ta fito ta maida kofar ta rufe.    Shigarta dakinta nan ma hoton ta yi ta kallo tana murmushi, bata ta6a zaton zata so wani namiji haka ba, kuma wai dan kauye.  "Ba kauye ba, ko cikin daji ka ke rayuwa zan iya binka Hubbyna, bansan sunanka ba na kamu da sonka, ban ta6a ganinka ba ido da ido, amman na ganka a mafarki fin sau uku har dariya ka yimin. I so much love you." Ta rungume hoton, ranar kam kowa ya ga chanji a tattare da ita don ta yi wuni na dadin rai, babban burinta yanzu bai wuce na son ganin zuwan su Ummi Abuja ba ko Allah zai taimaketa da ganin sanyin idaniyarta.    Mami na dakin Hajiya zaune suna hira da yan uwanta, wayarta ta yi k'ara, kai tsaye ta daga da sauri ganin Hajiya Binta abokiyar zamanta. Suka gaisa a mutunce suka sha hira tana tambayar mutanen Abuja sannan sukayi sallama, sai kuma ga kiran mijinta. Labarin da ya zo mata da shi yasa jikinta wani mugun sanyi, banda ikon Allah kenan babu abinda ta ke ambata a fili hakan yasa su Hajiya Mama da Hajiya Babba harma da Hajiya Karima (cousin) dinsu ta Adamawa suka zubomata idanu. Bayan ajiye wayar ta dubesu. "Kun ji ikon Allah ko?" "Meyafaru?" Cewarsu har suna hada baki. Mami ta numfasa. "Ashe Alhaji Kabiru Jimeta uba ne wajen Ummi? Dan uwan mahaifiyar Ummin ce."   Mamaki ya cika kowannensu banda Hajiya Karima da batasan kan zancen ba saidai tasan Alhaji Kabirun.     "Lallai fa ikon Allah!" Cewar Hajiya Mama.   "Yanzu suka yi waya da Alhaji Kabirun ya ke sanarmishi, don su suna ma Gomben."   Murmushi Hajiya Babba da Hajiya Mama sukayi wannan karon, banda hamdala babu abinda kowannensu ke yi a zuci musamman Hajiya Mama da ke jin kamar ta yi ta kyakyata dariya ga yar uwarta. Ai kuwa ta kasa hadiyewa ta hau yinsa, Mami duk kunya ta isheta ta yi shiru kawai tana Umm. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 113 "Allah Sarki rayuwa." Shine kawai furucin da Hajiya Mama ta yi bayan kammala dariyarta.    "Wai duk meyafaru ne?" Cewar Hajiya Karima. Hajiya Mama ta dubeta. "Ba zaki gane ba Karima, bari har mu je Gombe gobe za ki gane komai." "Toh ganar dani mana."   Mami ta ta6e baki gami da mikewa. "Ina zuwa." Ficewa ta yi tsabar ta rasa abin cewa, suka bita da kallo kawai. Hajiya Babba ta ce. "Ki share batun Sadiya, kinsan ita fa abin dariya ba ya mata kadan."   Hajiya Mama ta k'arawa darawa kawai.     Hajiya Babba ta share maganar gami da sanyo maganar yanda zasu yi tsare-tsarensu.                     ***    ***    ***                        GOMBE Misalin bakwai na safe matan gidan suka tashi da aiki tuk'uru sakamakon bak'in da zasu yi daga Abuja masu kawo lefe da sauran kaya na al'ada.  Wajen karfe goma sha daya ita kuwa Ummi tana dakin Abida tana gwada kayanta kaloli biyar da Mahaifinta ya dinkamata na fitar biki anan, kaya masu tsada wanda acewarsa tunda bai yi na daki ba to wannan bazai gagareshi ba. Dinki na zamani akayi mata wanda ya zauna d'abas a jikinya, daidai da Amina saida ya siyamata ankon da yan uwan Ummi mata na Gombe suka yi, abinka da aikin kudi telar washegari sukayi zata je kar6a don a ranar sauran kwana daya bikin.                        ABUJA     Su kuwa mutanen Abuja mutane shida kawai suka tafi kai lefe, Hajiya Mama da Hajiya Karima suna ciki, sai kuwa Hajiya Hadiza da Hajiya Bahijja, kanne ga Gen. Ahmad Danzaki sai kuwa wata Yayarsu da cikon mutum daya daga Adamawa. Sauran jama'a kuwa da zasu halarci yini da budar kai sai washegari zasu iso cikinsu kuwa harda su Mami da su Jidda.  Ikram ji ta yi kamar ta zuab ruwa a k'asa ta sha jin cewar zaaje Gombe daga can a taho da Amarya ayi na nan. Murnarta har mamaki ya bawa su Jidda balle kuma Ihsan wacce bata ta6a zaton hakan ba. Koda ta ga yanda Ikram ke rawar jikin hada kaya tun ma lokacin tafiyar baiyi ba ta gyada kai.  "DAN ADAM kenan, yanzu ke ba abun ki tayani bakin ciki bane Ikram, ba abun ki tayani zubar da hawaye bane, ko labarin matsayin Ummi ga Abubakar mai iso ga kunnuwanki ba?" Ikram ta dubeta jiki a sanyaye. "To ya zamu yi Ihsan banda mu yi hakuri, komai fa na Allah ne, ba yanda zamu yi tunda haka Ya tsaro za ki auri dan uwan Ummi, ni ai ba zuwan farinciki zanyi ba, ba kyaso ki ga yanda zasuyi shagalinsu ba?" Ihsan ta ja tsaki yayinda idanunta suka cika da ruwan hawaye, shikenan fa k'aryarta ta k'are, wani aji da jijji da kai yanzu saidai ta yiwa wata ba Ummi ba tunda dan uwanta zata aura, ita kam tasan ko giyar wake ta sha, ba zata tunkari Abbanta ta ce ta fasa auren Abubakar ba, sannan bayan wannan ma ga sonsa da ta ke ji a ranta. Sam, ba zata iya hakura da shi ba a yanzun, da ya ya ma ta soma sonsa da har za ta soma tunanin guje mishi? Ita kuwa babu Gomben da kafafunta zasu taka. 'Ko ba ki je yanzu ba dole ki je a gaba tunda za ki auri dan Gomben.' Cewar wani sashe na zuciyarta.                     ***   ***    ***   Bayan Azhar su Hajiya Mama suka isa, alokacin Ummi suna dakin Abida suna faman kwasar hira, Mariya wacce itama Malam Balarabe bai jima da daukota daga gidan kakanninta ba saboda bikin ta shigo a guje da yaran gidan.   "Adda Ummi, Adda Ummi!" Haka ta ke fad'a kamar yanda ta ji sauran yaran gidan na fadawa Ummin. Ta zube gabanta tana numfarfashi, yarinyar gaba daya ta chanja ta yi ki6a kamanninta da Saude na nan kamar an tsaga kara an karyashi.  "Meyafaru?" Cewar Ummi wacce duk kiran ya rudar da ita.    "An kawo lefenki." Ta ja guntun tsaki tana tureta, su kuwa su Amina suka dara, nan suka ja mayafi suka nufi hanyar fita Amina na fadin. "Ah, bari muje na gaisa da mutan Abuja."   Gaba daya kowa ya tafi aka bar Ummi nan zaune ta yi shiru don gani ta ke kamar mafarki ta ke yi, wai lefenta? Ta yi tsuru tana rarraba ido.     Hajiya Mama ta kama baki ganin Amina lokacin da ta ke gaisheta. "Ke kam ai kin zama 'yar gida shiyasa tunda ki ka kira ki ka ce kunzo lafiya ban k'ara ganin kiranki ba." Akayi dariya, Amina ta hau sunkuyar da kai itama tana darawar.  Masaukin da aka tanadarmusu(wato gidan da ke makwaftaka da wannan, wanda ya kasance na Aminin Malam, Manu kakan Ummi saidai ba wanda ke ciki sai kuwa bak'i da ake saukewa) nan aka kai kayansu, saida suka yi sallah sannan aka hau gaggaisawa daga nan suka ci abinci, nan kuma aka hau buda lefe, ita dai Ummi banda sautin bud'a babu abinda ta ke ji, kaya ne masu tsada aka sanyamata, akwatinta saiti cif, harma da wani daban na kayan lalle da na budar kai da sauransu, cikin suturu kuwa har da dinkakku.    Ummi na faman zirga-zirga ta yi can ta koma nan ba zato ta ji Amina ta d'ane bayanta tana tsalle da dariya. A farko ta tsorata don har gabanta ya fadi saidai jin muryar yasa ta numfasawa.   "Kai don Allah Anti." Kafin ta kai ga juyowa ta ji Amina na kuka har da sheshsheka, da sauri ta juyo daman itama karfin hali ta ke yi kawai, nan suka hau kuka babu mai rarrashin wani. Kusan duk abu guda suke tunawa. Amina ta dubeta.   "Ki godewa Allah Ummi, ki godemiShi, Ya so ki da rahmarSa, Ya baki matsayin da kudi ko karfinki bazai ba ki ba har abada. Na ta6a ce miki Yaya Faruk ya fi karfinki, matsayinki da na shi ya sha bamban, a wancan lokacin ina jiyemiki tsoron shiga wahalar rayuwa ne, shiga cikin wadanda suka fiki da komai. Ga shi da Allah Ya yi ke din matarsa ce, sai Ya maida komai ba komai ba, ma'ana tulin matsalolin da muke hange ba wasu matsaloli ba, shakka babu ayau na k'ara godewa Allah da naga lefenki, na kalli dama da haguna naga dangin Ummina cike a daki, Ummina 'yar dangi ce! Allah Ya baku zaman lafiya da Yaya Faruk, Ya baku ikon rike juna bisa amana har abada."   Ummi ta kasa komai sai murmushi ga hawaye na zuba, Amina ta ja ta suka zauna ta hau share mata hawayen, kafin waninsu ya ce komai, wayar Ummi ta hau ringing, suka kai dubansu ga wayar sannan Amina ta dara. "Bari na koma wajensu Hajiya Mama, ki gyara fuskarki fa don nasan zasu buk'aci ganinki." Daga haka ta fice, haka ya bata damar janyo wayar, gogannata ne kuwa. Dakyar ta iya dagawa, tana dagawa kuwa ta ji ya sakarmata gud'a a kunne, batasan sadda ta tuntsire da dariya ba sosai, shima yana tayata, saida suka yi mai isarsu sannan suka tsagaita.    "Kai don Allah." Ta fada a shagwa6ance, yanzu kam ta saba da Faruk ta saki jiki da shi.    "Kai don Allah me? Ko ba Amaryar Faruk din bace?"    Murmushi kawai ta yi.  "Ina zuwa, kiran Daddy na shigowa, zan k'ara nemanki."   "Toh." Ta fada sannan sukayi sallama, kafin ya k'ara kira su Abu da sauransu suka shigo tafiya da ita gaisawa da surukai.    Haka suka sanya ta lullu6e fuskarta da mayafi sannan suka fita. Ba yanda ta iya dole saida sukaa budemata fuskarta, kowannensu ya yaba, to idan ma basu yaba din ba ya zasuyi tunda an riga da an daura?  Hajiya Mama ita mamakin kyawun da Ummi ta k'ara kawai ta ke yi, ashe rashin samun hutu da gyara ne ya sanya ta koma gatanan? Bayan fitar su Ummi, matasan gidan suma suka shigo aka gaggaisa, Hajiya Mama bata yi mamakin ganin Abubakar ba tunda labari ya iso gareta, acewarta ma sai ko baa fada ba za'a ga kamannin Alhaji Kabiru da wasu cikin yan uwan Ummin.     Anan ne kuma sauran abokaan tafiyarta suka ga mijin da Ihsan zata aura, sun yaba kwarai.     Dangin Ummi suka hada su da(snacks) da kwalayen lemuka da suka yi musu aka kai masaukinsu aka ajiye. Washegari wajen daya da mintuna su Ikram su Mami aka iso, Mami ta dake matuk'a don yanzu jikinta ba karamin la'asar ya yi ba musamman ma ganin kawarta mahaifiya ga Abubakar, Hajiya Salma.  A ranar ne kuma ake lalle.Tun zuwansu basu sanya Amaryar a idanu ba sai da aka soma biki. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 114 Ummi ta shirya cikin wata koriyar atamfa mai adon kaloli jiki, ta yi kyau matuk'a a wannan rana, filin taro sosai Abubakar ya kama, shi ya biya komai, abinka da aikin kudi, nan aka gyare wajen aka yi kwalliyar kumbo a gefe da gefe inda amarya zata zauna sai kuwa tuntun da aka aka sanya, da katon darduma inda akai kawayen amarya zasu zauna sai kujeru.    Sai awajen taron Mami suka hadu da Amarya Ummi, Ikram tun zuwanta ta ke rarraba idanu na son ganin inda zata ga rabin rannata saidai bata ganshi ba.    Wajen ya burgesu ainun, da ka gansu kaga  zuri'ar Modibbo da ta Danzaki, sunyi kyau har sun gaji, suma dangin Ummi, sun cekare abinsu. Kowannensu da baiwar kyan da Allah Ya yi mishi bakake da fararensu.     Amarya ta sha lik'i a wajen dangin mijinta hakanan suma danginta ba'a barsu a baya ba. Mami koda ta je lik'amata har saida ta rungumeta, wannan abu da ta yi yasa Hajiya Mama jin dadi matuka har batasan sadda ta hau lik'a musu kudi ba. Ummi har hawaye ta yi don dadi, shakka babu wannan ya nuna Mami ta sauko.  Jidda kam su dai yan bin yarima asha kida ne, to me zasu ce tunda wacce suke ganin kusan ba'a kyauta mata ba itama ta sauko? Ina ga su 'yan karan kada miya?    Sai wajen Magriba suka tashi. Misalin karfe takwas da dare, Amarya ta kammala waya da Angonnata wanda sai gobe zasu iso da tawagarsa don budar kai, tana tare da yan uwanta ana hira da dariya, Ikram ta shigo da sallama. Duk suka dubeta suna masu amsawa, Ummi ta saki fuska saidai can kasan ranta gabanta ne ke dukan tara-tara to da me kuma ta zo mata?    "Amaryata ki zo mijinki na kira." Fuskar kowannensu da mamaki, sauran mamakinsu na zuwan ango, Amina da Ummi kuwa bayan haka harma da na sabuwar fuska da suka ga Ikram da shi wanda basu saba ganinta da shi ba akan lamura na Ummin, wato fuskarta a sake saidai idan ka nutsu za ka fahimci a kunyace ta ke dakewa kawai ta ke yi. To ya zata yi? Tunda tana son dan uwan Ummi ai dolenta ta sauko.  "Wai Angon ne ya zo?" Cewar wata budurwa.     Ikram ta dubeta tana 'yar dariya. "Gani nan, ai nima miji ce tunda kanwar mijin ce." Sukayi dariya gaba daya har Ummi, ta saci kallon Amina, Amina ta yi mata alama da ta je. Ta mike ta bi bayanta, anan kofar dakin suka tsaya. Ikram ta ga shirun ba zai amfaneta ba ta yi magana cikin sanyin murya. "Don Allah Ummi ki yafemin abubuwan da na yi..." Sai kuma ta ji kunya, hakan yasa ta yin shiru. 'Rayuwa kenan." Cewar Ummi a zuciyarta. A fili fad'ad'a fara'arta ta yi don dagaske ta ji dadi kamar ta shid'e. Hannunta ta riko. "Kai haba, ni ban rike ki da komai ba, daman nafi daukar hakan a rashin fahimta, na yafemiki duniya da lahira nima don Allah ki yafemin."   Dariya ta yi ta dafa kafadarta. "Nagode Ummi." Ummi ta ja hannunta. "Zo muje kiga yan uwana." Daman haka ta ke so, ta bi bayanta suka koma ciki. Zama sukayi ana hirar tare, yawanci duk Ummi suke koyawa yanda ake kula da miji ita kam shiru ta yi don ta ga su babu ruwansu, Ikram dinma da ta ke kunyar ita dinma ta biyemusu. Sallamar Gidado ce ta katsesu, suka amsa, yana daga kofa yana dubansu, sanye ya ke da shadda ruwan toka babu hula akansa, gashinsa ya yi luf-luf.     "Me ake tattaunawa ne aka manta da kawomin furata?" Cewarsa yana duban Matarsa Hafsa dake aikin dama mishi fura, ita kuwa baiwar Allah Ikram tun shigowarsa ta daskare a wajen gami da k'ura mishi idanu.    Shi kam sau daya ya kalleta kallo na ganin bak'uwar fuska daga nan bai k'ara dubanta ba.    Hafsa ta bishi da murmushi. "Na gama yanzu zan kawo." "To saiki hanzarta, kinzo kin biyemusu kun samin kanwa a gaba kuna cikata da surutu ko?" Aka dara, Ikram murmushin yak'e ta yi gabanta na bugu da sauri-sauri jin wai Gidado na da mata, ta dubi matarsa, babu laifi bata daga sahun munana amma a diri na halittar jiki ba zata nunamata ba, babu gaba balle baya. Ta kara satar kallonsa. Ta ko'ina ya kere matarsa saidai ta kula kallon ma da ya ke jifar matartasa da shi wacce ta ji a dazun sun ambata da Hafsa, kallo ne na musamman mai  nuni da tsantsar so da kauna. Ta sauke ajiyar zuciya yayinda ta ke ji kamar ta dora hannu aka ta hau rusa ihun kuka.   "Kai Yaya Gidado, ba kunyar idanu irin wannan kallon?" Cewar wata Maimuna abokiyar wasansa, ya kai mata duka ta kauce. "Kefa kin raina ni yarinyarnan, kinga taso ki ji zan dan fita ne da Abubakar."    Ba musu Hafsa ta mike ta bi bayan mijinta, su kuwa yan dakin aka sanya dariya banda Ikram. Duk zaman ya gundureta, ji ta ke kamar ta bar wajen, ai kuwa da sauri ta mike. "Bari na tafi na kwanta na gaji." Ta yi maganar a sanyaye tana duban Ummi, Ummi bata kawo komai ba bayan rashin sabo don kuwa ita kanta bata sake da ita ba ganin abin ta ke banbarakwai wai namiji da suna HAJARA.       A nan soron gidan ta yi kici6us da Gidado da Hafsa, ya wani kankance murya yana magana kamar saurayi gaban budurwa, suka dubi juna ya jefeta da murmushi. "Sannu da bakunta." Ya bata haushi saidai ta danne. "Yauwa." Ta amsa a dakile kafin ta wuce da saurinta zuwa wajen yan uwanta.    Koda ta shiga su Jidda ke kwasar hira akan yan uwan Ummi kowacce na tofa albarkacin bakinta,  sam basu dauka zasu gansu kai a waye ba, sun yi zaton kauyen da zasu je yafi haka muni sai kuma abin ya basu mamaki ganin komai tsaf.     "Ke kuma daga ina?" Cewar Baraka.  Ta yamutse fuska. "Wajen matar Yaya mana." Mamaki yasa su sakin baki kafin su hau dariya. "Shishshigi ko?" Cewar Fadila. Ta daure fuska gami da kwanciya saman katifa ta basu baya. "Ba ruwan mutum." Suka shareta. Wannan daren har hawaye ta zubar na tausayawa kanta haka kuma bata ji komai na digon son Gidado ya ragu a zuciyarta ba...!                 WASHEGARI BUDAR KAI....! Karfe biyu Ango ya iso da tawagarsa saidai a Otal suka sauka....!                  DAN ADAM @RUFAIDA OMAR Wannan naki ne yar uwata... Sis Aisha Samarou... 115 Ranar ko waya bai samu damar yi da amaryartasa ba. Dukkan wani masoyi ga Ummi zai so ganinta a wannan rana don kuwa ta yi kyau ainun, har wani kumatu ta ajiye, kasancewarta fara k'al, sai kunshinta ya yi kyau ainun, hakanan siraran kitson da akayi mata shima ya taimaka kwarai wajen fiddo da zahirin Hasiya Abdullahi. Karfe hudu aka sanya na yin Budar Kai saidai ba'a soma ba sai karfe biyar harda mintuna, anan kofar gidan zaayi. Ummi ta hade cikin wata hadaddiyar shadda kalar sararin samaniya wacce ta sha aiki, suka sanyamata Alkyabba, duk a cewarsu itama jinin sarauta ce don kuwa jika ce gidan Lamidon Jar Kwami. Shima angonnata ya sanya riga da wando sai kuwa babban riga ta shadda kalar na Amaryartasa. Hular nan ta zauna d'abas a kansa, shi kansa Angon wani kamshi da annuri kawai ka ke gani saman fuskarsa. Fuskar Amarya a rufe ruf, haka aka riketa har mazaunin da aka tanada mata, Ango na zaune tare da su Haidar sai kuwa abokan karatu da na aikinsu, sannan danginsa mata a baya suna fuskantar Amarya Ummi da nata dangin itama daga bayanta. Algaita kawai ka ke ji ana busawa awajen, nan aka soma inda Ango Faruk ya mike, Haidar da Jafar wano abokin aikinsa sune a gefensa, haka ya nufi wajen Amaryarsa mata na faman gud'a da hanci ya bud'e fuskar Amaryarsa kuma matarsa, idanunta a k'asa tana faman doka murmushi yayinda ta ke kokarin danne kukan da ke son kwace mata. Nan ya soma zuba ruwan kudi waje ya cika da sowa da gud'ar mata, bayan ya gama nasa suma abokansa suka soma kafin daga bisani bayan komawarsu danginsa su tashi suma su yiwa Amarya nasu lik'in. Bayan sun kammala ne, itama Amarya ta mike da Amina da Abu kanwar gidado suka isa ga Angon wanda ya kasa dauke idanu daga kan Amaryarsa yana ji kamar ya dauke abarsa su gudu. Durkusawa ta yi suka mik'a mata turare na maza mai tsada da dadin kamshi ta hau fesa mishi, ya lumshe idanu ya bude yana dubanta, hawayen da ta ke kokarin dannewa saida suka zubo, ta daure ta daukesu da sauri, sannan ta amshi hankicif a kunyace ta hau goge mishi gumi kamar yanda aka koyamata, habawa zo kaga sowa da gud'a, su kuwa su Mami, al'adar Gombe ta tafi da su matuka don abin ya burgesu musamman ganin ba kure kamar yanda Abubakar ya koyawa Faruk haka din ya yi shima. Daga haka Amina ta mik'amata bandir na dari-dari, nan ta shiga lik'amishi itama, abin ya burge matuk'a, bayan ta kammala suma danginta suka dan yi nasu lik'in sannan aka dau hotuna wannan karon Ango Faruk babu wani batun iyayi na rashin son hoto har yayyunsa na zolayarsa yana dariya, daga nan kuma aka tashi taro....! ((Ku yi hakuri da wannan ba chaji ne...)) [2/5, 6:52 AM] ‪+234 703 962 5239‬: DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 116 Ikram zaune ta yi shiru yayinda yan uwanta ke faman danne-dannensu a waya, babu kunya Jidda da Fadila harma Baraka na aikin sanya hoton Amarya da Ango a dp, harma da aikawa group na zuri'a Baraka ta yi. Intisar na kwance saman katifa tana shan iskar fanka ga tulelan cikinta wata shida tana kallonsu da sauraron hirarsu tana dariya jin Aisha na fadin. "Um su Yaya Faruk ashe shi yasan me ya hango da ya mak'alewa 'yar aikin Mami." Suka kara darawa.     Hankalin Intisar ya kai ga Ikram, ta zunguri bayanta da kafarta. Ikram ta dubeta, da hannu ta yi mata alamar tambaya na meke faruwa?    Ta yi murmushin yak'e sannan ta girgiza kai a nufinta babu komai. Intisar itama murmushin kawai ta yi duk da ta fahimci lallai akwai abinda ke damun Ikram din, tun zuwansu ta yi sanyi kamar wata miskila yanzun.    Ita kuwa Ikram ganin haka yasa ta wayancewa ta hanyar mikewa ta dubesu.   "Bari naga Hajiya Mama." Daga haka ta mike ta fito tsakar gidan, saidai kai tsaye waje ta fito inda matasa da wasu cikin matan gidan ke tsaitsaye, wata hira ta ke yi wasu kuwa kawai gaisawa da yan uwa. Ta yi ta faman wulk'a idanu tana mai fatan ganin Gidado, cikin sa'a ta hangoshi saidai hangen nasa baiyi mata dadi ba don kuwa tsaye ya ke da Hafsa sai wata mace wacce ta kasance Yaya awajen Gidadon suna hira da dariya, ta kasa dauke idanu daga kan Gidado wanda ayau shigar fararen kaya ya yi ya dora bak'ar hula akansa. Babu zato ya kallo gefenta, murmushi ne saman fuskarsa, murmushi ta sakarmishi ba tare da ta san lokacin da ya su6uto mata ba sannan ta yi saurin kauda kai ta juya ta koma ciki. Ya soma fahimto wani abun a irin kallon da Ikram ke yi mishi, ya sha kamata tana satar kallonsa daga sun hada ido sai ta kauda kanta, a farko ya dauka kuskuren fahimta ne saidai zuwa yanzun ya soma saka alamar tambaya ga hakan. Ya basar da tarin tambayoyin da ke yawo a kwanyarsa ya cigaba da maganar da sukeyi akan  zuwan Hafsa Abuja inda ya ce babu inda zata je ita kuwa ta kawomishi abokiyar shawararsa kuma yayarsa Sumayya akan ta lalla6ashi saidai firr ya k'i aminta acewarsa ta ji da karamin cikinta tunda tana fama da laulayi, dole ta hakura don daman karambani ya kaita matsawa kanta akan zuwan saninta da Gidado, shi din kaifi daya ne.      Misalin takwas da rabi na dare Ummi ta samu waya daga Mijinta akan ta fito yana kofar gida. Ta nunamishi akan ya yi hakuri akwai mutane ya nuna baisan zance ba.  "Na baki mintuna biyar karki wuce Malama, gani kofar gida. Mutanen ai sun san mijinki ne." Ta ajiye wayar a sanyaye ganin ya katse ba tare da ya ko saurareta ba.  Dada ta dubeta, don ta shigo wajen Dada daukar chajar wayarta. "Idan kiranki ya ke karki k'i zuwa Boddo, mijinki ne."   Daga haka Dada ta fice, a kunyace ta mike rike da chajar ta fito, saida ta wuce wajen Amina ta bata har wayar sannan ta yafa mayafi akan doguwar rigar jallabiya da ta sanya don bacci daga haka ta fita tana ra6e-ra6e. Ta ci sa'a mutanen kofar gidan sun ragu sosai, ta hau lek'e-lek'e saidai ko mai kama da shi bata gani ba, sai hon da ta ji wanda ya sanyata duban motar, jeep bak'a wuluk sai shek'i ta ke, ba ka ganin na cikinta.   "Bismillah Amarya, angon na ciki." Cewar Jafar kenan abokin aikin Faruk wanda bata sanshi ba sai a yau ta soma ganinsa.  Ta gaisheshi tana sunkwui da kai, ya amsa, kafin ta isa ya budemata kofar baya, ba musu ta shiga ta zauna sannan ta rufe kofar. Sanyin Ac da na tsadadden turaren Faruk Danzaki shi ya soma bugar gangar jiki da kofofin hancinta.  Ta dan d'ago ta dubeshi, wannan katon sanye ya ke da riga fara k'al da dogon wando bak'i, ganin sun hada idanu yasa ta saurin sauke kanta.   "Ina wuni." "Bazan amsa ba, keda ki ka so ki k'i fitowa wani wai mutane."   Ta yi shiru tana wasa da zoben hannunta. Ganin shima bai ce uffan ba yasa ta fadin. "Ka yi hakuri don Allah." Ya lumshe ido yana murmushi alokaci guda kuma ya tura yatsunsa na dama cikin sumar kansa.     Ba zato kuma ta ji kansa saman kafafunta yana duban fuskarta, yanayin jikinta ya sauya, ta na mai jin wani iri tun daga tsakiyar kanta har kafafunta. Bata kuma ankara ba, ya kunna wayarsa hakan ya taimaka wajen ganin fuskarta sosai, ta runtse idanu zata kauda kai saidai bata samu damar hakan ba don tuni ya ajiye wayar ya janyo fuskarta zuwa tasa. Nan kuma lamura suka chanja daga gareshi zuwa gareta. Don kansa ya saketa ya na dubanta, ita kuwa mayafinta ta sha zata rufe fuskarta yayinda ta ke faman sauke ajiyar zuciya.     "Kimin alfarma daya, kinji?" Ya yi maganar cikin rad'a, a hankali ta daga kwayar idanunta ta dubeshi, idanunsa a rufe sai ta ganshi kamar mai shafa mai na k'ara hasken fata sakamakon hasken da ta ga ya yi mata. Bai saurari amsarta ba ya bude idanu cikin nata ta yi saurin wayancewa da kallon kasa. Murmushi ya yi.   "Abinda ki kemin a waya shi na ke fatan samu yanzu." Gabanta ya buga, ta dubeshi kadan ya shagwa6e fuska. "Please." "Ka yi.."  "Ba za ki bar motarnan ba sai kinyi ko kuma na wuce dake Otal." Ya fada babu alamun wasa, tasan sarai zai iya aikatawa. Ta runtse ido tana ji kamar ta yi me, ta daure ta kai hannu ta ja wayarsa ta danne hasken da hannunta, da sauri ta aikata abinda ya umarceta, dariya ya yi gami da mikewa zaune.   "Matsoraciyata." Ta hau murza idanu da hannu tana murmushi.    "Na yi masifar kewarki Ummina, ina kara sonki a kowane rana."    Shiru ta yi tana mai jin wani dadi a kasan ranta.    "Inama zan iya bayyanamaka irin son da nake maka Yaya Faruk?" Ji ta yi ya dora kansa a kafadarta ya sanyata jikinsa da hannu daya.   "Mezai hana Ummina, please sanarmin, na jima ina son jin kin furta kina sona da bakinki ba don bansani ba, saidai ina son ji."    Ta hau rarraba idanu, ya akayi maganar zuci ya fito fili har ya shiga kunnensa? Ta hadiyi miyau, anya zata iya?  'Ki ka yi wancan ma bare wannan?' Cewar wani 6angare na zuciyarta. Ta ji ya kara matsar hannunta. "Please Ummi, taimaki Faruk dinki kinji? Ji yanda kirjina ke bugu don kaunarki." Ya kai hannunta saitin kirjinsa, aikuwa bugun ya ke da sauri-sauri. Ya kai bakinsa saitin kunnenta. "Zuciyata zata fashe da sonki." Ta lumshe ido tana jinta kamar a Aljannah, murmushi saman fuskarta ta yi kasa da kanta. Dakyar ta bude baki ta yi magana.   "Ina...ina..." Sai kuma ta yi shiru. "Say it please." Ya yi maganar da siririyar murya, ta kasa jure sakonnin da ya ke aikamata, ta kara runtse idanunta. "Ina sonka." "Irin wanda na ke miki?" Ya yi tambayar ba cikin nutsuwa ba, ta rasa bakin amsawa, shi dinma bai saurari amsar ba ya cigaba da jero tambayoyin kamar a dakin jarabawa. Ita dai Um kawai ta ke binshi da shi, yanda ya ke mata yasa har hawaye ta ji sun zubomata na tausayi da kuma tsananin kaunar Faruk, ta ji ko k'uda bata kaunar ya shiga tsakaninsu, ta ji ta kara sallama mishi zuciya da gangar jikinta, ta ji nan duniya babu abin so da kauna gareta sai Faruk. Shi kadai tallin tal ta ke so ta ke kauna koda kuwa za'a kawomata wanda yafi Faruk komai da komai, ita sai Umar-Faruk Danzaki, babu gudu babu ja baya....! So kenan...!!!    K'arar wayar ce ta firgitasu, ya ja tsaki gami da dauka. Jafar ne, ya soma mishi magana akan dare ya yi haka kuma ga hadari a garin. Dole ya amsa da toh sannan ya ajiye wayar ya kwantar da kai saman kujera yana duban Ummi da murmushi saman fuskarsa. Ta kauda kai tana gyara zaman mayafinta.   "Saida safe." Cewarsa, ta amsa, "Allah Ya tashemu lafiya." Daga haka ta soma kokarin bude kofar. "Ummina." Ta juyo tana dubansa.  "Ina sonki dagaske fa." Murmushi ta yi wanda yasa ta k'ara burgeshi. "Nima haka." Daga haka ta yi saurin bude kofar ta fice. Jafar ya shiga shi kuwa ya tsallako gaba suka bar unguwar.      Ta yi mamakin ganin har wasu sunyi bacci, saida Amina ke sanarmata cewa goma ta wuce sannan ta yi guum kawai da bakinta duk kunya ta isheta sai kuma ta hau fadin.   "Lokaci yanzu ba dai gudu ba, Allah Yasa mu cika da imani." "Amin dai." Cewar Amina da sauran wadanda basu kai ga bacci ba suna masu danne dariyar da ta tahomusu.     Washegari aka rankaya Jar Kwami inda aka ga tsoffi aka gaggaisa shima Ango ya je suka ganshi sannan ya wuce da tawagarsa a ranar, su kuwa su Ummi ba su suka baro Gombe ba sai washegari bayan ta sha nasihu daga iyayenta da kakanninta, Malam Balarabe har kuka ya yi na ganin zai kara nesa da diyartasa saidai wannan karon hankalinsa kwance tunda yasan gidan aure ta nufa. Mutan Jar Kwami kowa aka nuna mishi Mami da su Hajiya Mama matsayin surukan matar da Abubakar zai aura wato Ihsan sai su hau cigiyarta saidai ace musu bata zo ba, koda Ihsan ta ji baki kawai ta ta6e don har kuka ta yi sakamakon ganin hoton Ummi da Faruk saidai ko zata mutu ta barshi kenan, amma har lokacin akwai ragowar tabon sonsa cikin zuciyarta.                   ***     ***     ***      [truncated by WhatsApp] [2/5, 6:53 AM] ‪+234 703 962 5239‬: DAN ADAM @RUFAIDA OMAR Sadaukarwa ga dukkan masoyan FAR HAS....! 117 ABUJA Amarya da danginta har ma da dangin miji suka iso gaba daya, Hajiya Babba da su Hajja wacce ta sauko ta dangana, suka tarbesu hannu bibbiyu. Har da kishiyoyin Mami, wato Hajiya Binya da Lubna da yaransu, su Iklima yanzu gaba daya ta chanja kamar ba ita ba don har rungume Ummi ta yi. Ummi a dakinta ta sauka da kawayenta wannan karon ko Amina ba'a ware ba. Saida sukayi sallah sannan aka ci abinci, a ranar ne zaayi Dinner, ango ya wuce da amaryarsa. Gidan a cike suka iskeshi sakamakon ranar ne Hajiya Babba ke yininta. Wanka suka sanya Ummi ta yi ta hade cikin wani tsadadden leshi ja mai adon duwatsu, dinkin ya zauna d'abas a jikinta, haka aka rufemata kai aka kaita wajen su Hajja, nan suka rufarmata da nasihu, bayan kammalawa aka wuce da ita wajen Hajiya Babba da kawayenta har su Hajiya Mama gaba daya, suma suka tofa nasu albarkacin bakin har Hajiya Babba na fadin. "Ummi diyata ce daman." Wannan furucin ya yiwa Ummi dadi matuka, abin mamaki wajen la'asar sai ga Husna da abokan karatunsu na Islamiyya, ashe Faruk din da kansa ya kaiwa Husna kati na dinner party ta bawa abokan karatunsu harma da na yinin Hajiya Babba inda duk suka sanya ankon da suka yi, har kunya ta ji don tasan ta fadawa Husna bikin kuma suna waya saidai bata samu damar bata kati ba. Su Fati burinsu bai wuce na son sanin waye mijin ba don har lokacin Husna bata sanarmusu komai ba hakanan ko hotonsa basu gani ba. "Ni dai Anti Ummi sai rarraba idanu nake naga ta inda zan ga Yayanmu." Ummi murmushi ta yi kawai. "Za ki ganshi." Husna ta dara. Nan kuwa Ummi ta shiga nunamata yan uwanta suna gaisawa. Ihsan kwance saman gadon Ikram tana waya da Abubakar, Ikram na gefe tana duba mahadin kayan da zasu sanya na dinner party wani leshi ne ruwan hoda saik uwa sauran yan mata sa'anninsu, Intisar ta shigo, ta dubesu kaf sannan ta tsaida idanunta kan Ikram. "Kanwata zo." Ta dubeta kafin ta mike ta maida kayanta sif ta bi bayanta. Kai tsaye yar barandar Hajiya Babba suka isa wacce kana iya hangen harabar gidan ta nan. Ta dubeta da kulawa. "Ki fadamin damuwarki don Allah Ikram, ke ba ki lura da sauyin da ki ka yi ba tun kafin soma bikin Yaya Faruk? Menene ya ke damunki haka da har ki ke ramewa? Kin koma wata shiru-shiru kamar ba Ikram din da na sani ba mai yawan hira da dariya." Ikram ta ji gabanta ya fad'i, wato har an fahimci damuwarta? Ta k'ak'alo murmushi. "Kai in-law, nifa babu abinda ke damuna..." "Karya ki ke wallahi, ko yanzu kin fuskarki ta kara tona miki asiri, lallai kina cikin damuwa saidai kuma idan ba ki yarda da ni ba ne shiyasa bakyason sanarmin. Barin kashi a ciki fa ba ya maganin yunwa. Yanzu gayamin, me ya hadaki da hoton wannan Gidadon a jakarki, dan uwan Ummi?" Idanuwa a waje ta ke duban Intisar, ga wasu ruwan hawaye da suka ciko mata. Daidai lokacin Gidado da Abubakar da kuma Haidar suka shigo harabar gidan suna hira da dariya kamar dama can sun saba, daman suna kofar gidan, hankalinsu ya kai garesu, suka dubesu, Gidado ya saje da yan birni, sanye ya ke cikin farar shadda marar nauyi mai tsada cikin wanda Abubakar ya dinka mishi don Abubakar mutum ne mai yiwa yan uwa sosai, sam abin hannunsa bai rufemishi idanu ba, barshi dai da son ta6a mace idan yana sonta wanda ya ke fatan ya daina. Su kuwa basu ko lura da su ba har suka wuce, Ikram hawayenta ya zubo wani irin wutar so tana kara ruruwa cikin zuciyarta har batasan lokacin da ta dubi Intisar ba ta soma magana bayan ta rike hannunta. "Ina sonshi tun sadda na soma ganinsa a hoto." Ta kwashe labarin komai ta sanarmata har zuwa sadda ta fahimci yana da mata. Ta karashe tana kuka, kasancewar wajen gilas ne yasa na falo ma yana kallonsu, Hajiya Mama ta kwala kiran sunan Intisar. Ikram ta juya baya da sauri tana share fuska, Hajiya Mama ta karaso. "Ku kuma lafiya? Me ya sami Ikram din?" Ta fada tana duban Ikram mai share fuska, Intisar ta wayance. "Um wai kanta ke ciwo shine abu bai kai ya kawo ba ya bata haushi wai ana damunta da hayaninya a daki." Hajiya Mama ta hau ta da fada. "To shine za ki zauna kina faman kuka, jimin aikin banza, ke kuma ki ka biyemata? Zo ki je ki bata magani mana, kuma ku soma shiri ga Magriba ta yi yanzu za'a wuce." Suka amsa da toh. Intisar ta dubi Ikram cike da tausayi. "Shakka babu wannan lamari ya bani mamaki matuka wallahi, amman ki bari za mu yi maganar daga baya, mubar nan kafin Hajiya Mama ta dawo." Suka fice. Wajen biyar da rabi Ummi ta amsa kiran Daddy don yi mata nashi nasihar. Kanta a rufe da mayafi, ga mamaki nan ta tarar da Faruk, ta zauna ta gaisheshi ya amsa fuska a sake. Nan ya shiga yi musu nasiha mai ratsa jiki da jini har ta kai Ummi ita mace mai rauni soma hawaye, shi kuwa gogan gaba daya jikinsa ya yi sanyi matuk'a, can kuma ya sallami Ummi, ta yi mishi godiya bisa karamcin da ya yi mata, ta nuna ta daukeshi matsayin uba gareta, ya ji dadin kalamanta da addu'o'inta gareshi. Ya yi mata fatan alheri gami da sanyamata albarka. Haka ta koma dakinta jiki babu kwari, yan uwanta yan Gombe da yawansu sun wuce ganin gidanta da kuma kai ragowar kayan da suka zo da shi da na gudunmuwa da ta samu. Karfe bakwai na dare aka soma shirin tafiya Party, alokacin sun dawo gida kowannensu na yaba tsarin gidan Faruk da Ummi. Har hotunan suka nunamata banda murmushi ba abinda ta yi, kwarai ya tsaru duk da cewa flathouse ne. Ana wannan shirye-shiryen ne wata arniyar mota jeep ta shigo harabar gidan, inda wasu mata su bakwai suka sauko. Da gudu Husna ta isa garesu ta rungume, Fati ta nemi sanin ko su waye musamman ganinsu da anko wanda yafi na mutan gidan kyau da tsada, kafin ta amsa mata wata motar bus ta k'ara shigowa, nan kuwa ta ga matan rututu duk cikin ankon suma, wani arnen leshi suka sanya saidai suma kalar ruwan hodar ne, sun yi kyau har sun gaji da haduwa. Dariya Jidda ta yi tana duban Fadila. "Wannan (ta nuna wata 'yar fara-fara doguwa cikinsu) Farha sunanta, schoolmate dita ce, ina yawan basu labarin kawata Ummi shine fa suka ce sai sun zo bikinta, kinga ango saida ya bani katin kowaccensu ya ce na bawa duk wasu masoyansu, nan da ki ke gani har da yan groups dinmu na whatsapp. Su Sally, Bingel, sophie, Fatima Aminiya, Ummu abdool, shamsiyar katsina, Ab kura, shukra, Dg da sauransu wallahi suna da yawa ne." Fati ta dubesu, tabbas kuwa harda wadanda suka girmewa Ummi. Suka shiga ciki don gaisawa da mutanen gidan kafin su wuce wajen fatin. Husna zata bisu Fati ta janyota ta dawo baya. "Wai wane group da wanne ki ke fad'a?" Dariya Husna ta yi, akwai yar Taskira, su Neena su sholingaye su Aisha da Sadiya, akwai yan Rof gaba dayansu wasu ta gidajensu zasu je, da yan Classic Ladies ga Matan Aljanna da Matan Aure Only, da Matan Aure na antinmu Amina Mamser, ban rageki ba, kaf yan Dm masoya labarun soyayya mazansu da matansu kalilan ne bazasu ba wato tsoffin haka ma yan group din khalisat da..." "Ke ya isa, wallahi kinsa na kara jin son halartar fatin nan, Angon ma nafi dokin gani, kai Ummi ta godewa Allah wallahi, mutane ai rahma ne." Dariya Husna ta yi. "Muje mu karasa shirinmu Madam." Suka rankaya ciki. Wajen takwas aka soma tafiya, saida aka ragu sosai Ango ya iso daukar Amaryarsa....! [2/5, 3:45 PM] ‪+234 703 962 5239‬:    DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 118 Idan kaga Ango Faruk da Ummi sai ka ji tamkar ka sacesu tsabar kyan da suka yi. Gaba daya shigar fari sukayi, shi shadda ita kuwa wani arnen leshi ta sanya, akayi mata nadi da silver, ta yi kyau har ta gaji da yinsa, gaba Angon kusan susucewa ya yi da ya ga Amaryarsa, dauriya ce kawai ya yi gudun 6atamata kwalliya.    Wajen ya hadu, har iyaye suma sun je har kuwa Ihsan wacce ke faman dagawa.     Shigowar Ango da Amaryarsa yasa su Fati zaro ido suna dubansu, Husna ta hau dariyar mugunta. "Ya akayi ne Fati? Ga Yayanmu nan fa da matarsa."  Ta rad'amata saitin kunnenta alokacin da ta ke daukar bidiyon Amarya da Angonta. Fati banda Umm babu abinda ya fito daga bakinta don ita har kunyar Ummin ta ji, ashe shine wanda zata aura amman basu sani ba ta kyalesu suke faman zuzutashi?    Sai bayan an zazzauna ne Husna ke labartamusu cewa tun alokacin ma mijinta ne kawai dai ta 6oye ne. Suka yi ta mamaki, can kuma suka hau yiwa kansu dariya na rashin hankalin da suka yi.       Ummi ta maida hankali ga duban dubban mutanen da suka taru dominsu, ta sauke kanta tana mai jin nauyi, tasan fa dakyar idan rabin wadannan mutanen basu san tarihinta ba, don da yawansu matan sukan zo siyayya ko zumunci wajen Hajiya Babba, wasu suna ganinta matsayin yar aiki wasu kuwa basu san ta ba saidai jikinta na bata cewar zasu ji labarinta. Jin hannun Faruk cikin nata  ne yasa ta dago kai gami da dubansa. Kallo ya ke mata, ba irin kallon da zata iya watsarwa ba ne, kallo ne mai nuni da tsantsar soyayya. Ya dan rankwafo saitin kunnenta.    "Tunanin daren ki ke? Gidana fa za mu wuce daga nan."    Ta turo baki tana ji kamar ta saki kuka don haushi da kunyar da ya bata, ta lura yau tsokana ya ke ji da shi don tun a mota ya ke faman tsokanarta. Dariya ya yi wacce ta bawa dumbin yan uwansa mamaki musamman yan Adamawa da basu saba ganin miskili Faruk na dariya haka ba. "Lallai yau ango ya ke." Acewarsu.      Taro ya yi kyau, Ango da Amarya sun sha lik'i da hotuna, hakanan sun yanka kek (cake) har sun ciyar da juna, abinda ya burge mutane bai wuce dan russunawar da Ummi ta yi ba, da kuma shi din da ya bata cike da kulawa.      Ikram ta yi ta cilla idanunta, ta kasa daukesu daga kan Gidado wanda a yau ya yi shigar kufta bak'i wacce ta haskaka shi ta kara fiddo tsantsar kyawunsa. A sace ta ke daukarsa a hoto duk Intisar na lura da ita, ita a nata ganin me zai hana ta nemi Ummi ta sanarmata cewar tana son dan uwanta ko da taimakon da zata iya yi gareta? A ganinta wannan ce damar da zata iya cin galaba ta samu ya saurareta. Amma abun ne da daure kai ace mace har mace kamar Ikram ta 6uge a soyayyar wanda ke zaune a kauyen Jar Kwami, anya wannan zata haifar mata da d'a mai ido?     Hankalin Intisar ya dauke sa'ilin da mijinta ya kirata a waya akan ta je gareshi.       Bayan an tashi da taro kalilan cikin iyaye suka raka Amarya gidanta, sai kuwa kawayen Amarya wadanda suka ce sukam komin dare sai sun tsaya siyan baki, nan iyayen suka tafi suka barsu ganin sha biyu ta wuce, suna fita Angwayen suka shigo, nan fa suka ce sai an basu kudin siyan baki, abin sai ma ya bawa su Haidar dariya, basu tsaya ja in ja ba Ango ya ajiyemusu bandir na d'ari-d'ari guda biyu, suka ce sam basu amince ba tunda sun san Angon ma'aikacin Banki ne to kudin su fi haka.   "Wai kuwa ba ku ganin hadarin da ke a garinnan?" Cewar wani cikin tawagar da dariya. Murmushi Faruk ya yi, Haidar yasa hannu ya ciro yan dubu-dubu saidai ba rafa ba, ya mik'awa Husna wacce ta fi kowa daga murya. Nan suka sanya shewa gami da basu hanya su shiga, wani cikin abokan ya yi takaitacciyar nasiha sannan suka yi addua aka shafa, daga nan suka titsa keyar yan matan suka fice, Abubakar na fadin.   "A kularmin da Innota, ko k'uda banaso ya takura rayuwarta fa."   Dariya kawai Faruk ya yi sadda ya yi musu rakiya.     Ya daga kai ya dubi sararin samaniya ganin yanda ake walkiya akai-akai da kuma cida ga kuma iska mai dadi da karfi, ya juya ya koma ciki bayan ya rufe kofar gam!     Kai tsaye dakin Amaryarsa abar so da kaunarsa ya nufa, a zaune ta ke kamar yanda suka barta, wannan karon kukanta ya yi karfi fiye da baya, ya karasa ya hau saman gadon ya cire lullu6in fuskarta gami da d'ago ha6anta.    "Ummin." Wannan murya ba ta koyaushe bace, ita kadai tasan zak'in da muryar ke yi mata, ita kadai kuma tasan yanda ta ke ji a jiki da zuciyarta aduk sadda ta ji.      Kasa amsawa ta yi, saidai kuma dif kukanta ya tsaya sai hawayen.    "Kukan ya isa haka, ko kina so na kasa cika alkawarin da na daukarmiki cewar ni Faruk bazan bari Ummina ta shiga kuncin rayuwa ba da iznin Allah? In sha Allah Ummina kuka ya k'are miki saidai ko na dadi muddin kina tare da Sadaukin Hajiya." Ta lumshe idanu kawai sa'ilin da labulen dakin da ke kadawa da karfi ya soma feso musu ruwa da aka soma sakamakon windon dakin dake a bude. Ya runtse ido yana murmushi yayinda ya dan ja yatsun kafarta har ta danyi k'ara kadan.   "Na ta6a sanarmiki cewa inason lokacin ruwa?"   Ta girgiza kai a hankali tana mai lumshe ido sakamakon ruwan dake dan fesowa fuskarta. Ya dora yatsansa saman  idonta na hagu yana wasa da shi.   "Kinsan dalili?" Yana maganar tamkar ba ya so. Zuciyarta na bugu da karfi-karfi ta k'ara girgiza kai. Ya dan bugi bakin kadan. "Magana fa za ki yi, yau hira zamu yi." Ta dan turo bakin kadan batare da ta ce uffan ba. Saitin kunnenta ya matsa ya yi mata rad'a.     "Zuciyata na nishadantuwa aduk sadda ake ruwa, ina jin wani farin ciki." Ta hade jikinta wuri daya. "Um." Shine abinda ta iya furtawa adalilin sanyin da ta soma ji sakamakon ruwan da ke dan shigowa.  Ganin haka ya mike ya rufe windon ya koma gareta. "Tashi ki watsa ruwa ko kya ji dadin jikinki, daga nan ki yi alwala, ko kina bukatar taimakona?"   Ta girgiza kai cikin sauri, ya shafi fuskarta yana 'yar dariya daga haka ya fice daga dakin, ta mike tana mai bin bayan mijinta da kallo, ta daga hannu sama gami da yiwa Allah godiya da Ya bata miji har miji irin Umarul-Faruk, fatanta zamantakewarsu ta yi kyau su shimfida rayuwa tsabtatacciya.     Kafin yazo ta hau k'arewa dakin kallo wanda yasha adon fari da ruwan hoda, har ya gaji da haduwa. Nan ma bandakin ya yi mata kyau don gaba dayansa farin tiles aka shimfida har jikin bango. Da ruwan dumi ta yi wanka sannan ta dora alwala, bayan fitowarta ta sanya doguwar riga fari k'al mai ru6i biyu ta bacci sabuwa dal wacce aka sanyamata a akwati,  Abida ta jaddadamata ta sanyashi yafi sau uku, ya hadu iya haduwa, na k'asan iyakarsa gwuiwa, sai kuwa na saman wanda ya ke dogo. Ta dora zani a sama sai hula mai taushi da suka sanyamata mahad'in kayan. 'Ina zan iya yawo haka gaban Yaya Faruk banda abin Anti Abida?' Ta yi maganar a zuci. Tana cikin ninke wadanda ta cire ne wayarta ta shiga k'ara. Ta yi saurin cirota daga yar fos din da ta halarci Dinner party. Gogannata ne, saida gabanta ya fadi, ta yi addua kafin ta amsa.    "Ummina zo gareni." Ta hau dube-duben hanyar shigowa da dakin. "Kana ina?" Ta fada a sanyaye. Murmushi ya yi mai sauti kafin ya amsa. "D'akina." Shiru ya biyo baya, kamar ta ce ina ne dakinnaka saidai ta fasa. "Toh." Ta furta a hankali kafin kuma ya ajiye wayar. Hijabinta fari k'al ta ciro cikin karamar akwatin da Anti Abida ta had'amata sai kamshin turare ya ke yi ta zura ajikinta. Silifas ta sanya ta fito falon, saida numfashinta ya kusa dauke don kyau da tsaruwar falon, ba tarkacen kaya saidai komai mai tsada ne acan gefe kuma wajen dinning ne. Labulenta lemon green ne mai surkin bak'i haka suma kujerunta. Ta numfasa tana mai kara yiwa Daddy adduar fatan alheri a zuciyarta. Kai tsaye ta nufi wata kofa ta bude, nan ma daki ne amman gado ne kawai madaidaici sai bandaki. Ta rufe ta bi dan corridor da ke a gefe, nan kofa daya ce ke fuskantarka. Ta murda ta shiga, wani sanyi ya ratsata yayinda kafafunta suka nutsa cikin wani lallausan kafet na bakin kofar, fitilu a kashe hakazalika an bude baranda sai iska kawai ka ke ji ta ko'ina, ba ka ganin komai sai hasken katuwar talabijin dake jikin bango, sallama ta yi saidai babu alamun yana falon. Sai kuma ta ji ya amsa yana fitowa daga dakinsa rike da darduma. Sanye ya ke cikin doguwar jallabiya shima, ya kunna fitila yana fadin. "K'araso mana." Ta karaso gabanta na dukan tara-tara ta kasa kallonsa.    Bayan ya shimfida ya ja su sallah raka'a biyu bisa sunnah, sannan ya yi musu adduoi daga haka kuma ya janyo ledar gefensa, da kansa ya fita ya dauko filet ya dawo.      Da kansa ya ciyar da Umminsa tana taunawa kamar bata so, bayan sun kammala ta taimaka mishi da kwashewa ta kai kicin, a karshe ta zarce dakinta ta wanko baki.      Gaba daya ta kasa komawa sashensa, to ta koma ta ce mishi me? Kawai sai ta kashe fitila ta haye gado saidai kafin ta kai ga runtsawa wayarta ta dauki k'ara. Ta daga don tasan shi ne.   "Ummina zo ki amshi wani abu." Ta danyi shiru sai kuma ta bishi da toh. Dole ta mike ta maida hijabinta ta fito.     Koda ta shiga wannan karon ya kashe komai sai hasken walkiya da ke dan haska dakin. Kafin ta kai ga wani yunkurin ta ji mutum ta bayanta har saida ta firgita.  "Haka akeyi kuma daga kai kaya kicin sai ki gudu ko?" Ya yi maganar k'asa-k'asa, a hankali ya kunce daurinta kafin ya cire hijabin. "Wannan duk sanyin ne? Zo mu je ki ji." Ita dai ba bakin magana sai uban tsoro da ya mamaye zuciyarta. Tana a jikinsa har suka shiga dakinsa wanda ya fi nata girma da haduwa, can wata kurya ta hango gadon nashi wanda baifi na kwanciyar mutum biyu kacal ba an sanya labule an rufeshi ruf ta yacce ba ka hango cikinsa.  'Shi kuwa yana son kalar blue a rayuwarsa.' Ta fad'i a zuciyarta ganin nan din ma fari da bulu ne kalar dakinsa. Dif ta ji ya kashe fitila sadda ya karasa da ita ga makwancinsa.    Kamar ta tambayeshi ko baya jin sanyin gari ganin yanda ya bude winduna yabar net ga iska na kadawa sai kuwa hasken walkiya da ake yi akai-akai saidai ko me zaayi yau kam bazata iya magana ba, to ina bakin maganar? Ko daga rikon da Faruk ya yi gareta tasan yau sai a hankali, gabanta sai safa da marwa ya ke yi saidai ta yi alkawarin faranta ranshi a wannan rana...!   "Welcome to your love Asiya... I love you and i will show you...!!! ( Barka da zuwa ga masoyin ki Asiya. Ina sonki kuma zan muna maki...!)"   Bai damu da ko ta fahimci yaren nasa ba ko a'a, saidai wannan Faruk sak ne haihuwar Ahmadu da Fatima, ba wani can da boko da gayu ya ratsashi ba. Daga wannan babu wanda ya kara doguwar maganar da hankali zai dauka acikinsu...!!!         ASUBA TA GARI FAR HAS....!!! [2/5, 11:52 PM] ‪+234 703 962 5239‬: DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   119 Murmushi ta yi ta k'ara muskutawa gami da k'ara k'ank'ame lallausan bargo wanda ya hade da tsadadden kamshin turarenta da na Faruk, saidai kasancewar nashi yafi nata karfi yasa ya rinjayi nata, mafarki ta ke yi mai dadi wanda gaba daya cikin baccin ta ke yinsa har tana murmusawa gami da k'ara rukunkume bargon, wai ga ta ga Faruk yana kara jadaddamata irin mugun son da ya ke yi gareta. Ta yi nisa a mafarkinta ta ji ana zagaye kunnenta da yatsa, firgigit ta farka, Faruk ta gani zaune sanye da jallabiya wacce ta manne jikinsa kasancewar daga wanka ya fito sai kuwa fuskarsa da ta nuna hakan don jik'e ta ke da ruwa har kuwa sumar kansa.  Ai da gudu ta tura kanta cikin bargon tana jin kamar ta nutse awajen ga wani radadi da ta ke d'an ji a jikinta.      "Morning Ummina, tashi ki yi wanka kada lokacin sallah ya wuce ko na yi miki?" Da sauri ta girgiza kai, murmushi ya yi kafin yasa hannu ya lalubo nata, wani sanyi ya ratsata. Ya soma kokarin taimakamata ta mike saidai ita gaba daya nauyi ta ke ji ya ganta a yanayin da ta ke duk kuwa da cewar a daren ya fadamata kunya tsakaninsu yanzu ta kau.     Mikewa ya yi ya bar mata dakin ganin yanda ta ke d'ari-d'ari da shi. Yana fita ta yi wuf ta dauki abinda zata dauka ta fad'a bandaki. Saidata yi wanka da ruwan dumin da ya tara mata kafin ta fito.     Nan kuma ta maida hijabinta ta d'ora zani a samansa, zata tayar da sallah ya shigo dakin.  "Zo mu yi jam'i mana." Ba musu ta bi bayansa ya tada kabbara ya ja su sallah, bayan sun idar ya yi musu addua suka shafa. Ta karasa ta durkusa gabansa kanta a k'asa. "Barka da Asuba." Ya sumbaci goshinta. "Kin tashi lafiya? Ya gajiyarki?" Murmushi ta yi a kunyace saidai bata iya amsawa ba.    Ta mike zata fita ya dakatar da ita. "Ina za ki kuma?" Ta dubeshi a sanyaye. "Shida naga ta kusa kada ka makara a ofis zan dora maka kari ne." Ya taso ya zagayeta da hannuwansa. "Kar ki takura kanki, yau babu inda zanje ina nan tare da ke koyaushe."   Ta lumshe ido tana murmushi ya ja ta suka koma daki nan ya kwantar da ita bayan ya rage mata kayan jiki ya barta daga ita sai fingilar rigar baccinta, hakan shima ya rage sannan ya hau suna fuskantar juna, ya kuramata idanu ya matse hannuwanta cikin nasa. "Allah Ya albarkaci rayuwarki Ummina, Allah Ubangiji Ya bani ikon kyautatamiki har abada, Allah kada Ya kawo kaddarar da zata gifta tsakaninmu har ta rabamu. Ina sonki ina kaunarki, bayan Hajiyata da Daddy, bani da wacce nakeso nan duniya kamarki, bazan gaji da gayamiki kin mamaye ko wane sak'o na zuciyata ba Ummina, bazan gaji da gayamaki yanda nake sonki ba, da ace akwai kalmar da ta fi I love you nuna tsantsar so da kulawa da na fadamiki, saidai fatana bai wuce na Allah Ya bani ikon nunamiki a zahiri ba a kuma kowace rana. Matso nan." Ya karashe gami da janyota ta kwanta saman lallausan kirjinsa, ta lumshe idanunta tana jin so da tsananin kaunarsa na k'ara zagaye jini da jikinta.  "Kinji yanda bugun da zuciyata ya k'aru?" A hankali ta gyada kanta. Ya shafi kanta.   "Haka ya ke yi tun farkon ganin da na yi miki a gidan Modibbo (Ranar meeting), haka ya cigaba da yi har zuwa ranar daurin auren Haidar, bai tsananta ba sai a daren da na daukoki daga wajen party zuwa gidan Mami, kinga kuwa Faruk ya jima cikin mayen son Asiya. Ki rike Faruk da amana, ki guji yi mishi hali irin na DAN ADAM na butulci, in sha Allah za ki ji dadin zama da shi." So kenan, don kuwa Ummi batasan sadda ta matse Mijinta a jikinta ba.   "Ina sonka Yaya Faruk, kai ne hasken rayuwata, da kai nake tunk'aho, kai ne ka soma nunawa duniya nima mutum ce kamar kowa, ina da tawa darajar, zan iya mallaka maka dukkan abinda na mallaka ba ma jikina kawai ba, ina sonka ina kaunarka, bana fatan Allah Ya nunamin ranar da zan yi butulci agareka."    Baisan lokacin da ya dagota ba, ruf ta rufe idanunta yayinda kirjinta ki matsanancin bugu, ya zubamata idanunsa masu nuni da tsantsar kauna kafin yasa hannu ya ja abin rufa....!      Sai wajen takwas na safe suka farka daga baccin da ya kwashesu, ta rigashi farkawa hakan yasa ta zare jikinta a hankali daga nasa, ta zubamishi ido tana murmushi, komai na shi abin sha'awa ne, a sannu ta dauki abinda zata dauka ta fice zuwa dakinta.    Kai tsaye wanka ta yi ta shirya cikin wani jan yadi ta yi kwalliya. Har wani ajiyar zuciya ta saki ganin yanda ta fito ta yi kyal da ita. Murmushi ta yi ta murza daurin dankwali kamar yanda Husna ta koyar da ita bayan bidiyo kala-kala da ta aikomata na daurin dankwali.      Saida ta kammala ta feshe jikinta da turaruka masu dadin kamshi kafin ta fita zuwa kicin ta soma kiciniyar hada musu karin kumallo, tana cikin yi ta ji mutum a bayanta. Har saida ta firgita ta juyo, ganinsa yasa ta sunkuyar da kai tana murmushi.  "Bana ce karki wahalar da kanki ba?" Ya fada a shagwabance. Ita kam batasan ita da shi wa zai rarrashi wani ba...!   ((Sorry yau na fita ne...manage)) [2/6, 1:41 PM] ‪+234 703 962 5239‬:        DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    120 "Ka yi hakuri gani na yi..." Sai kuma ta yi shiru. Murmushi ya yi ya ja hannunta zuwa dinning table ya zaunar, ta dubeshi ya sanya yatsansa a baki alamu na ta yi shiru.    "Shii! Yau aikina ne ba na ki ba." Daga haka ya yi hanyar kicin yana murza hannuwansa. Ta bishi da kallo kamar ta yi dariya, yana sanye da riga tshirt marar nauyi sai kuwa wandonsa 3 quarter. Tunaninta ko zai iya tace ruwan shayin, sam batasan ma akwai kayan abinci ba da ta soyamusu kwai.     Shi kuwa sanin akwai din yasa shi tsayawa gami da rike k'ugu bayan ya ciro kwai guda bakwai a firij. Toh ya zaiyi? Me da me ake sanyawa acikin kwai idan za'a soya? Ya ta6e baki don yasan bai wuce maggi kawai ba sai a yanka albasa. Nan ya tace ruwan shayin ya sanya a filas kafin ya koma ya dauko (bowl) ya soma fasa kwan, ya bi wata kofa dake cikin kicin din  wanda ya kasance store, ya dauko albasa guda daya. Haka ya na gyarata yana hawaye, idanunsa a rufe  ruf, ji ya yi an rike hannuwansa. Ya bude idanun dakyar ya na duban Ummi wacce jin shiru ta biyo baya, ta hadiye dariyarta. "Kawo zan karasa don..." Ai bata karasa maganar ba ya sakarmata albasa da wukar ya fita da sauri-sauri yana fadin. "Ina sonki fa."   Saida ta tabbatar ya yi nisa kafin ta tuntsire da dariya ta yi mai isarta sannan ta soma aikin.   Shi kuwa gogan yana bandaki ya na fama da wanke idanunsa, saida ya wanke hannunsa tas da handwash kafin ya soma da fuskarsa, bayan ya kammala ya goge da karamin tawul, sai kuma ya tunano da Umminsa wacce ya ce ba zata shiga kicin ba, ya dan daga gira. Toh ya zai yi? Daman fa ba ta6a shiga kicin din ya yi ba, shawarar Haidar ya bi wanda ya ce a ranar farko ya yi mata karin kumallo da kansa. Alokacin dubansa ya yi ya yamutse fuska. "Kasan dai ba shiga kicin na ta6a yi ba ko?"  Haidar ya yi dariya ya daki kafadarsa. "Koya za ka yi for the sake of love."   Alokacin murmushi kawai ya yi. Sauke ajiyar zuciya ya yi gami da ajiye tawul din a ma'ajiyarsa, kai tsaye ya fito falon, kamshin suyar kwai ya cika falon, k'arar kwankwasa kofar da akayi ne yasa shi fasa shiga kicin din ya nufi wajen kofar. Malam Ado direban Hajiya Babba ne rike da kwando. Ya gaisheshi da girmanawa, Faruk ya amsa kafin yasa hannu ya kar6i kwandon da ya ke mik'o mishi. "Gashinan, Hajiya ta aikoni na kawo." Murmushi Faruk ya yi, da yasan zata aiko ai da bai wahalar da Umminsa ba, ya mishi godiya sannan ya sallameshi.    Ummi da ta ke jera kayan kari a saman tebur ta soma bin hannun Faruk da kallo ganinsa rike da kwando. Ta karasa bayan ta ajiye tiren hannunta, ta kar6i kwandon alokacin da ya ke fad'in.   "Kinga Hajiya ta aikomana da abin kari kuma."   Murmushi kawai ta yi.     Farfesun kaza ne sai kuwa ruwan shayi a filas, farfesun ta zubamusu, suka yi zaman sha. Yanda ya ke tarairayarta tamkar wata bebi abin har ya soma daina bata kunya don ta lura kamar halinsa kenan idan zata tsaya kunyarnan sai ta cuceshi kamar yanda ya sha fadamata kenan, ba ya son kunyarnan idan sun yi aure.     Karfe sha daya da mintuna suna zaune a falo ya sanyata jikinsa suna hira inda ya ke k'ara yi mata albishir da zai nemamata Malamar da zata dunga zuwa har gida domin koyar da ita, wannan albishir da ya ke yawan yi gareta yafi komai sanyata cikin farinciki. Hon da aka yi ne yasa hankalinsu ya koma ga waje, maigadin ya bude aka shigo, hakan yasa shi mikewa gami da lek'e ta windo. Murmushi ya yi sannan ya dubi Ummi. "Yan uwanmu ne fa 'yan Gombe." Jin haka batasan sadda ta mike tsaye ba tsabar d'oki ta nufi hanya don budemusu.    "Tsaya mana." Muryarsa ta katseta. Dankwalinta ya mik'omata ta yafa a kanta suka sakarwa juna tattausan murmushi kafin ta nufi kofar da ake kwankwasawa don ta bude shi kuwa ya koma sashensa.     Anti Halima ce ta soma shigowa sai kuwa Hajiya Salma a bayanta da sauransu. Ta rasa ina zata sa kanta don farinciki, wannan ya rungumeta wannan ya shafa kanta, duk sai ta ji kunya ta cikata. Abu ta yi mata rada a kunne. "Har kin chanja." Ta harareta, ta tuntsire da dariya.     Haka suka shiga suka zauna. Nan wadanda basu samu zuwa ganin gida ba suka hau zagaye, Faruk ya fito wannan karon sanye da dogon wando maimakon gajere ya durkusa yana gaidasu. Ummi ta dan dubeshi. 'Ashe yasan kunya.' Ta fada a ranta. Bayan gaishe-gaishe ne ya fita jin cewar da Gidado suke. Hajiya Salma ta ja Ummi har d'aka, wasu kayayyakin ta kara damk'amata sannan ta bita da nasihu masu ratsa jiki da jini. Karshe ta rungumo kafadarta yayinda kwalla suka cicciko mata har saida suka zubo. "Ina ganinki tamkar Zahra Innon Abubakar, ina kaunarki har cikin zuciyata Ummi. Ki rikeni matsayin uwa kamar yanda na rikeki nake miki kallon diyata kinji?" Ummi dake hawayen farinciki itama ta gyada kai tana murmushi mai bayyana hakora.   "In sha Allahu Mama (Kamar yanda ta ji Abubakar da kowa ma suna fad'a) za ki sameni mai yin biyayya gareki irinta d'a da uwa."   Hajiya Salma ta share fuskarta yayinda ta ke ji kamar da Zahra ta ke magana, ta rike hannun Ummi. "Allah Ya albarkaci rayuwarki Ummi. Tashi ki adana wadannan kafin wani ya shigo."   Ta amsa da to sannan ta mike ta bude sif ta bude dirowar dake cikinta daga tsakiya ta zubasu.      Sun jima suna hira da mutan Gombe sannan sukayi shirin tafiya.                    ***   ***   ***    Ikram kwance saman gado bayan dawowarta daga makaranta ta yi shiru tana jin takaicin rashin sallamar da basu yi ba da Gidado hakanan bata samu ta kar6i lambarsa ba har ya tafi. A haka Ihsan ta shigo tana sanye da riga da siket yan kanti, su sai gobe zasu wuce. Ta dubeta duban kurilla kafin ta zaune gefen gadon cike da damuwa. "Na tsani na ganki cikin wannan yanayin wallahi 'yar uwa, ji na nake yi kamar zazza6i. Ke kuma ga shi nayi-nayi ki fad'amin damuwarki kin k'i, karki manta a baya kece mai bani shawara kan na cire damuwar komai cikin raina game da Yaya Faruk, yanzu kuma da Allah Ya yayemin sai ke ki ke neman jefa kanki cikin damuwa wacce jikina ke bani kamar damuwar irin tawa ce."      Ikram ta dubeta da mamakin yanda akayi ta d'agota da sauri haka. Ta numfasa kafin ta mike zaune ta matso gareta jiki a sanyaye.    "Ki yi hakuri Ihsan, banaso sanyaki damuwa shiyasa ban fadamiki ba, wallahi son..." Sai kuma ta yi shiru tana mai jin nauyin furucin. Ihsan ta dubeta cikin zak'uwa.   "Inajinki ki yi magana."    Ikram ta sadda kanta. "Wallahi Soyayyar Gidado yayan Ummi ne ya maidani haka, bansan..." "What?!" Cewar Ihsan hankali a tashe cikin daga murya, wannan yasa Ikram kasa cewa komai ta yi shiru kawai. Ko me Ihsan ta tuna sai kuma jikinta ya yi sanyi ta buga tagumi ta yi shiru. Batasan sadda ta soma hawayen bakin ciki ba. "Mun shiga uku Ikram, mun shiga uku, ya akayi muka k'are a fadawa tarkon jinin Ummi? Kin kamu da son Gidado wanda bai fiki da komai ba, asalima kin ketareshi a aji, ga shi ina shirin auren Abubakar wanda a baya nake hura hanci nake tunk'aho nake kuma gani kamar na yi miji na nunawa sa'a wanda yafi Yaya Faruk komai na jin dadin rayuwa, ashe tunk'aho nake yi da dangin Ummi, yarinyar da tun farkon ganina da ita ban ta6a jin digon kaunarta ba, yarinyar da nake kishi a kanta. Saidai zuwa wannan lokacin na makaro don ban isa na tunkari Abba nace bana son Abubakar ba, ban kuma isa na ce hakan ba koda a karon kaina ne don yanzu inason Abubakar Ikram, ina jinsa a raina sai nake ganin abin tamkar a mafarki duk da cewar jinin Ummi ne, kinsan kuwa Abubakar koyaushe mukayi waya ba shi da hira sai ta Ummi? Sai ince miki wallahi ko matarsa Badiyya, ba ya yimin maganarta kamar yanda ya ke min ta Ummi a yanzun, koyaushe cikin kwatantamin yanayinta da Innonsa ya ke yi, ya na yawan cemin ya na jinta kamar Innonsa, sai ince miki tun jiya da na 6ata ransa a wajen fatin Yaya Faruk akan Ummi har yanzu ya k'i kiran wayata balle na samu damar ba shi hakuri, ni kuma gani nakeyi zubda aji ne na dauki waya na kirashi akan wata Ummi. Don Allah Ikram kada ki sa mu ji kunya, ki barmu ma da wannan da muke sha sanadiyyata, kuma naga kin soma shigewa Ummi, don Allah ki fita hanyarta."    "Kuskure babba da ku ka tafka a rayuwarku." Suka tsinci murya daga bakin kofa, gaba daya suka juya ga kallonta. Intisar ta karasa shigowa ta rufe kofar don kuwa a dazun Ihsan bata karasa rufeta ba. Ta tako a sannu sakamakon kumburin da kafafunta sukayi ta isa garesu ta janyo kujerar gaban madubi ta zauna kafin ta dubesu a tsanake fuskarta a daure sannan ta soma magana....    [2/8, 12:30 PM] ‪+234 703 962 5239‬: [2/7, 10:35 PM] ‪+234 703 663 6364‬:    DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   121 "Kin 6ata wayonki Ihsan, kin kuma bani mamaki sosai wallahi, ban yi zaton a duniya za ki iya zurfafa kiyayya ga DAN ADAM ba. Wannan jahilci zan kirashi ko kuwa dai hauka? Tabbas akwai ban mamaki, na daya, idan a baya hujjarki Ummi 'yar aikin gidanku ce, to yanzun ta tashi daga wannan matakin. Na biyu Ihsan, idan rashin dangi yasa ki ke uzzura rayuwar baiwar Allahn nan, toh fa wallahi a yanzun idan bata nunamiki yawan dangi ba, ba za ki fita ba. Ki ji tsoron Allah Ihsan, yarinyarnan Allah Ya kaddara dole zata shiga cikin zuri'armu, kar kuma ki manta Kawunta (Alhaji Kabiru) aminin kut da kut ne da mahaifinki, kinga kuwa babu, babu ta yanda zaayi ki gujewa auren dan uwanta Abubakar saidai idan Allah Ya kaddara ke da shi ba za ku kasance ma'aurata ba. Ihsan ko Annabinmu sallallahu alaihi wasallam ya hanemu da zurfafa kiyayya har haka, akan wane dalili za ki dasawa zuciyarki muguwar tsanar Ummi? Toh wallahi Ummi 'yar halak ce, ta kuma wuce a kirata da Butulu mai mance halacci, Allah Ya bata baiwa ta hakuri, haba jama'a, ki tuna irin wulakancin da ki ka sha yi mata tun zuwanta gidanku har kawo lokacin da akace ta zama matar Yaya Faruk, ki kuma tuna irin yanda hakan baisa ta rik'emu ba a zuciyarta, asalima har yau bata bar bamu girman da ta ke bamu ba, shi DAN ADAM yana da matsala, ya na manta cewar shima halitta ce mai daraja har kiga wasu lokutan yana wulakanta kansa ta hanyar biyewa sharrin zuciyarsa ya yi ta aikata 6arna alhalin a karon kansa yasan cewa lallai 6arnar ce. Ba ku kadai ba, daidai da su Anti Jidda basu kyautawa kansu ba da a baya suka zagi baiwar Allahn nan suka tsangwameta, Yaya Faruk ya burgeni burgewa da bai fasa ja baya ba har ya kai ga cimma burinsa da taimakon Allah, ya auri Ummi. Idan wannan bai isheki ishara na ai ya kamata ace gujewa Yaya Faruk da ki ka yi ki ka za6i Abubakar kuma ya zo ya kasance jinin wacce ki ke ikrarin kin tsana, ya isheki ishara. Saidai na yi mamaki yau da na saurari maganganun da ke fitowa daga bakinki, anya Ihsan kina da imani kuwa? Toh ko kina da shi ba ya tasiri akan Ummi, ina fatan shiriya gareki, Allah Ya ganardake. Ke kuma." Ta juya ga Ikram wacce ke faman hawaye ga gumi da ta had'a sakamakon da na sani marar misaltuwa da ya k'ara shigarta gami da kunyar Ummi da ta ke gani kamar tana gabanta, bata mance marin da ta yi mata akan an mareta da tozarcin da ta yi mata cikin shago.   "Ki zauna nan ta zugaki ta baro ki, kuma kinsan Allah? Inaji a jikina soyayyar Gidado sai ya wahalar da ke kamar..."   Da sauri Ikram ta toshemata baki da hannu, ta soma girgiza mata kai tana kuka sosai.  "Don Allah karki yimin baki, ki dubi daraja ta zumuntakarmu Sis."   Ta sauke hannunta gami da rike kanta tana kuka.   "Na jima da gane laifina, na jima da neman gafarar Ummi, bana fatan soyayyar da nake ji game da Gidado ta fi yanda nake ji a yanzu, na tabbatar zan iya mutuwa aduk sadda ya k'i aminta da soyayyata, in sha Allah shi ba MIJIN MACE DAYA bane, ku tayani addua."   Ta kara fashewa da kuka, dan uwa rabin jiki, duk sai ta karyamusu zuciya, Ihsan ji ta ke da ace tana da iko da ta raba Ikram da wannan makahon son, da ta raba zuciyarta da son Abubakar. Hawaye kawai suke yi, Intisar ta daure ta hadiye nata kukan don batason kara karya zuciyarta. Ta dafa kafadarta.   "Allah Yana tare da ke, mu cigaba da mika kokenmu gareShi, zanyi miki taimako daya, zan samu Ummi da kaina na sanarmata na tabbata ba zata bamu kunya ba, ita zuciyarta ba irin tamu bace, ta fimu hakuri."   Tana kaiwa nan ta mike jiki ba kwari. "To tsaida hawayen mana Matar Gidado."  Cewar Intisar tana riko ha6anta, dariya sukayi banda Ihsan wacce ta kasa gane hakikanin abinda maganganun Intisar suka sanya ta ji.                    ***   ***   ***  A gidan Ango da Amaryarsa kuwa, babu abinda sukeyi sai dirzar amarci hankalinsu kwance, kwanaki biyun da suka yi sai bak'i suke samu, a rana ta uku ne suma 'yan Adamawa suka je gidanta, Hajiya Salma tuni ta bi yan Gombe har Abubakar sun koma don shi Alhaji Kabiru kwana biyar ya yi ya juya Adamawa. Basu jima gidanta ba suka wuce su dinma a ranar suka tafi. Gidan ya rage su kadai a koyaushe, babu ranar da basa waya da mahaifinta da su Dada, hakanan Hajiya Babba kullum saita kirata sun gaisa. Hatta su Hajiya Mama da Mami Ummi kiransu ta ke yi hakan ba karamin dadi ya ke musu ba. Tsakaninta da mijinta sai sam barka don kuwa kullum soyayyar junansu k'aruwa ta ke a zukatansu.     Haka har suka yi kwanaki shida suna tare, ita kadai ce zaune wajejan karfe uku, Faruk bai jima da cin abincin rana ba ya fita zuwa gaida su Hajiya Babba. Zuwansa na uku kenan tun bayan auren, ta ji ana kwankwasa kofar falon, koda ta bude ta yi mamaki na ganin Husna da kanwarta karama Siyama. Batasan sadda ta daka tsalle ta rungumeta suna dariya ba. Sai bayan sun shiga ciki hira kuma ta 6arke, Husna sai kod'a irin chanjin da ta ga ta yi ta ke, Ummi banda murmushi babu abinda ta ke. Sun jima, ta taimakamata hada abincin dare kafin ta dubeta.  "To sai wanka ko?"  Ummi dariya ta yi, ba musu ta fafa wanka, bayan ta fito ta soma shiri suna hira da Husna wacce ke zaune saman gadonta tana kallon hotunan biki gami da yaba irin wankuwar da sukayi harda daukar wanda akayi musu su biyu, can ta dago ganin Ummi na kokarin sanya wata atamfa dinkin riga da zani rafa ta dan harareta.    "Kar ki cemin tun zuwanki kwalliyar atamfa da lesuna ki ke yi? Gaskiya yau ki sanya kananun kaya."   Ummi ta murmusa. "Ke wallahi don ba ki ga kananun kayan ba ne duk kama jiki sukeyi, kusan iyakar tsawon rayuwata ban ta6a sanya kananun kaya ba banda riga da siket su kuma ba matsastsu ba."   Husna ta  mike tsaye. "Shiyasa fa na cewa Amina sai mun dunga sanyaki a aji don duk abin Amina wallahi ta fiki wayewar kai, matsa kiga ina suke na za6o miki? Ai nan gidan mijinki ne ba haramun ki ka aikata ba, ko ba ki ji yanda Anti Jamila Bappa ta group ke yawan magana akai bane? Duk kuma litattafan da na ba ki ai anyi bayaninsu."   Daga haka ta shiga duba kalolin kayan, kananun kaya ne masu kyau matuka da tsada, wata abokiyar kasuwancin Hajiya Babba ta aikomata na Amarya da kuma kudade wanda ta ce na Ango ne.     Wata riga (purple) mai hannun shimi ta dauko da wando bak'i dogo mai kama jiki ta dubi Ummi tana mai mik'amata.   "Kar6i ki saka wadannan." Ummi ta zaro ido saidai hararar da ta samu daga wajen Husna yasa ta darawa. "Wannan kallo sai kace na ce bazan saka ba?"   "Ki ce din ma mana mugani." Suka dara kafin ta fita ta bata wuri don ta shirya, tana zaune falo Ummin ta fito. "Masha Allah!" Shine furucin da ya fito daga bakin Husna ganin irin kyan da Ummi ta yi. Batasan sadda ta mike tsaye ba, rigar har taso matseta hakanan ta fiddo da halittarta sosai kamar yanda shima wandon ya zauna d'abas a jikinta. Fuskar ta sha kwalliya, ta tufke kitsonta da ribbon sai kuwa dan mayafi na pashmina da ta dan daura akanta da kuma dan kunne fashion mai kyau.     "Kai Ummi, kin fito wallahi kamar ba ke ba."    "Anti Ummi kinyi kyau." Cewar Siyama.   Ummi ta murmusa kadan tana jan riga. "Nagode, saidai anya zan iya bari ya ganni haka?"   Tsaki Husna ta ja don haushi ta dauki mayafinta don daman ita ta ke jira ta fito su yi sallama. "Matsalarki, wallahi da kinsan waye mijinki da ba ki tsaya wannan kauyencin ba, tuni wata a waje ta yi miki sakiyar da ba ruwa, koda su Fati na kafa miki misali ya isheki, ga ki da dan karen kishi kuma kina ja baya wajen gyara, don Allah Ummi ki k'ara sakin jikinki, wallahi duk abinda ki ka yi ga mijinki ba ki fadi ba. Wallahi mata suna nan suna harin miji irin naki basu samu ba, amman Allah Ya damk'a maki ba don wayonki ba, ki watsar da kunyar komai ki rungumeshi hannu bibbiyu. Shikenan dai ni zan wuce sai munyi magana ta whatsapp." Ummi cike da jin kwarin gwuiwa ta yi mata rakiya iyakar kofa, daman yanzun kusan ma ta rage kunya-kunyar don salo-salon Faruk kadai ya isa sanyata dainawa domin kuwa shi babu ruwanshi koyaushe janta ya ke yi.     Ba shi ya shigo gidan ba sai bayan sallar isha'i adalilin rakiya da ya yiwa Daddy wani wuri.      Tana jin tsayuwar motarsa, ta ruga daki a guje ta kara gyara fuskarta ta fesa turare sannan ta fito ta budemishi kofa, sak ya yi yana dubanta, ta yi kasa da kanta gami da sa hannu ta kar6i ledar hannunsa. "Sannu da zuwa." Ta fada gami da ba shi hanya. Ya shigo ya tura kofar ya rufe har da mukulli, har lokacin dubanta ya ke yi don ya kasa cewa uffan, ya ja hannunta zuwa falon ta ajiye ledar saman tebur, ya riko kafadunta.    "Mamaki fa ya k'i saki na, Ummin Faruk ce kuwa?"   Ta na murmushi amman ta kasa magana saima ta sa tafin hannu ta rufe fuskarta. Ya janyota jikinsa. "Kinyi kyau fiye da zatonki, ina kara sonki Ummina, ki dunga yimin irin shigarnan ina so."   Ta gyada kai kawai don ta tsorata da ganin yanda ya susuce tasan babu sauki.    Ai kuwa janta ya yi sai sashensa.              Washegari suka samu bakuncin Haidar da Intisar, Haidar nan ya bar Intisar suka wuce masallaci tare da Faruk kasancewar juma'a ce, Ummi ta saki jiki da Intisar ganin yanda itama ta saki jiki da ita, daman ta riga da ta kusan kammala girkinta, ta taimaka mata suka karasa tana labartamata yanda rainon ciki ya ke da kuma sanadin kumburin kafafunta.  "Kai, mata na fama wallahi, Allah dai Ya rabaku lafiya." . Cewar Ummi jiki a sanyaye dalilin tunanowa da Ummanta, yanzun ko awane hali Saude suke ciki? Allah Masani.    "Amin kedai, fatanmu Allah Ya bamu mai sauki." "Amin." Bayan sun kammala suka dawo falo, suma sallah sukayi sannan suka yi zaman hira, kusan ma Intisar ce mai yin rabin hirar. A haka kuma ta gangaro zuwa ga maganar dake sosa ranta inda ta soma magana.   "Ummi ina neman wata alfarma gareki akan kanwata Ikram." Saida ta ji gabanta ya fadi batare da tasan dalili ba, ta dafe kirji.   "Gareni kuma Anti?" Ta gyada kai. "Kwarai kuwa." Ta girgiza kai. "Ai a duniya babu abinda za ku nema na kasa yi gareku matukar baifi karfina ba idan har Allah Ya bani ikon yin."   Murmushi Intisar ta yi. Ta soma labartamata yanda akayi tun farko tasan Ummi na son Gidado har zuwa kadan daga hirarsu kwanaki ta dora da fadin. "Don Allah Ummi ki taimakawa kanwata, na gaskata tana son Gidado da gaske ba wai iyaka baki ya tsaya ba, nasan kuma wannan jarrabawa ce babba ta iso gareta."    'Anya ba mafarki nake ba?' Ummi ta jefawa zuciyarta wannan tambayar....!!        [2/8, 10:05 AM] ‪+234 803 862 6581‬: DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 122 Ta kasa gaskata lamarin, gani ta ke yi kamar ba idanunta biyu ba, dafa hannunta da Intisar ta yi ne yasa ta dago kai tana dubanta kamar wata wawuya. "Kar ki yi wani zargi akan haka, nasan wacece Ikram, wallahi da ace karya ta ke yi da maganar kafin ta iso kunnenki ta ruguje don bazan amince mata ba saidai iyakar gaskiyarta ta nuna kuma ta furtamin na ji." Ummi ta numfasa kafin ta dora daya hannunta saman na Intisar tana murmushi. "Anti da ki ke kiran Ikram da kanwarki, nima 'yar uwa na dauketa, ina mata kallon jinina, wallahi ko kusa ba wani zargin nake ba, kawai dai abin ne na ji shi banbarakwai saidai tunawa da na yi Allah Shi ke da wannan ikon, yasa na ji zuciyata ta wanku kuma na kara gaskata faruwar hakan. Na tausayawa Ikram matuka kuma in sha Allahu zan taimakamata, saidai ta saka a ranta shi aure nufin Allah ne, idan Allah Ya yi matarsa ce ita to ba makawa zata zama idan kuwa ba matarsa bace..." Sai ta yi shiru, Intisar dake kallonta kallo na burgewa tana mai kara jin kaunar halayya irinta Ummi wanda ya sha bamban da mafi yawa cikin mutane ta fadada murmushin. "Karki damu, munsan komai kaddara ne, in sha Allahu na tabbatar ba za mu ji kunya ba." Ummi ta murmusa. A kasan ranta ta shiga damuwa, ta ina zata faro? Tasan sanarwa Gidado abu ne mai sauki saidai kuma da wane ido zata dubi Hafsa matarsa? Batasan kalar nata kishin ba, kada fa ta rik'eta a zuciya? 'Komai na Allah ne, zai taimakemu.' Cewar wani 6angare na zuciyarta. Shigowar mazan ne ya katse tunanin kowaccensu, dukkansu cikin fararen kaya, sunyi kyau hakanan kamanninsu ya kara bayyana sai hira suke yi har suka karaso falon. Suka yi musu sannu da zuwa, nan suka zauna, ba kunya Faruk ya zauna kusa da matarsa gami da riko hannunta. "Ummina na dawo, kinsan addu'ar da na yi mana?" Kunya ta kamata, Haidar ya ja guntun tsaki yana dariya. "Daman haka ka ke? Ina maka kallon wani mutum da baisan komai ba, ashe-ashe?" Faruk ya shafi sumarsa yana taya Intisar dariyar da ta ke yi. Ummi kuwa kanta na kasa tana murmushi gami da kokarin zare hannunta cikin na Faruk saidai hakan ya gagara. Baice mishi komai ba saima ya sanya bakinsa saitin kunnen Ummi. "Addua na yi akan Allah Ya bamu twins." Ai da sauri ta mike ta na fadin. "Nan za'a kawo muku abinci ko acan za ku ci?" Su Haidar da ke dariya suka mike yana taimakawa matarsa. "Ina zamu wahalar da ke? Wannan Angon naki ba shi da ta ido gwara muyi-muyi mu tattara mubar gidannan." Faruk ya shagwa6e fuska. "Kai brother." Cikin dariya Intisar ta dubi mijinta. "Don Allah ka kyaleshi hakanan." Ta yi maganar cikin kasa da murya don har lokacin ba wani sabo ta yi da Faruk ba, ya ja karan hancinta yana dariya. "Ke bakisan waye wannan ba da ba zaki tausayamishi ba." Murmushi ta yi kawai suka rankaya gaba daya wajen tebur. Bayan gama ci da sha kuma suka dawo falon inda Haidar da Faruk suka wuce sashen Faruk din suka barsu, nan kuma hira sosai suka shiga yi, Ummi ta sake sosai da Intisar wannan karon har suna kyakyata dariya. Sai kara yabawa da halin Ummi ta ke yi, ashe haka ta ke da dadin sha'ani? Ba su suka bar gidan ba sai yamma, tana zaune itama Faruk ya ce ta shirya su fita. Har tsalle ta yi don murna ta fada daki, mayafi kawai ta dora saman maroon lace din dake jikinta ta sanya takalmi mai tudu mai kalar bak'i da maroon. A kofa sukayi kici6us da gogannata, bai chanja kaya ba, ya karemata kallo, ta yi mishi kyau ta kara haske. Ya shafi gefen fuskarta. "Bazan gaji da fadamaki ina sonki ba." Murmushi ta yi cikin jin wani sanyi a ranta. "Nima haka." Ya dago ha6anta. "Kema me?" Ta lumshe ido tana murmushi. "Ina sonka." Ya ji dadi gami da sumbatar le66anta. "Nagode Ummina, muje ko?" Yana rike da hannunta suka fita, kai tsaye wajen ice-cream suka nufa, nan suka siya suka yi zaman sha, saidai ko mintuna uku basu yi ba ya kasa jurewa ya ce ta taso su sha a mota, gani ya ke yi kowa a wajen ita ya ke kallo, kusan ma baisan ta fishi murna da hakan ba don kuwa gani ta ke yi yan matan gaba daya na wajen idanunsu akan mijinta suke. Bayan mota suka zauna kamar zai shige jikinta, yana bata tana ba shi, ba zato aka kwankwasa musu gilashi, suka dubi wajen kadan daman suka bude, ya karasa sauke gilas din batare da ya matsa daga jikin matarsa ba, wata budurwa ce sanye cikin kananun kaya kanta ko kallabi babu. Ta daga mishi yatsu tana mishi wani kallo bayan ta dubi Ummi dake gefensa. Irin zaman da sukayi ya nunamata alakar dake tsakaninsu, wato dai matarsa ce. Sai ta ji ta kasa maganar da ke bakinta. Fuskarsa kamar bai ta6a dariya a duniya ba, ita kanta Ummin fuskarta daure tamau tana jin zuciyarta na wani zafi, ashe haka kishi ya ke? "Lafiya dai?" Cewar Faruk cikin kakkausar murya. Duk saita daburce, ganinsa dazun yana murmushi ta dauka bazai yi wuyar aminta da ita ba, yanzun kuwa sai ta raina kanta. "Sorry, na dauka wani face da na sani ne, ashe ba shi bane." Ya dan daga gira kadan bai kara kallonta ba ya daga gilas ya rufe! Sum-sum tabar wurin gayu na mata dariya. Ya ja tsaki. "Mata kenan, sun maida kansu tamkar karnuka." Ummi dai ba ta ce komai ba, jin shirun ne yasa shi dubanta, ta miko mishi ice-cream dinta. Ya hada har hannun ya rike ba tare da ya saki ba ya ce. "Lafiya dai?" Ta girgiza kai tana murmushin yak'e. "Bakomai ya isheni ne." Ta fada tana kokarin danne hawayen da ke son zubomata, duk da ranta ya yi sanyi da irin yanda ya yiwa budurwar nan saidai ta kasa fidda kishin a ranta. Ya gane hakan, ta kuma kara burgeshi, ya juya ya cigaba da shan ice-cream din, cikin kara son zolayarta ya ce. "Haka fa yan matannan suke tsareni ko a ofis, saidai ni ba ruwana da kowaccensu. Bakiga ma wata ba kyakkyawa da ita.." Bude kofar da ya ga ta yi ne yasa shi yin shiru, fita ta yi ta dawo gaba ta zauna. Ba tare da ta dubeshi ba ta soma magana cikin rawar murya. "Don Allah mu tafi kaga Magriba ta kusa." Baice uffan ba har ya kammala shan ice-cream dinsa, ya goge bakinsa da tissue kafin ya tsallako gaba ya zauna mazaunin direba. Ya dubeta bayan ya sanya bak'in gilashinsa wanda ke kara mishi kyau. "Wai ni fushin nan na menene?" Ta girgiza kai. "Bakomai." Ya rausaya kai kawai ya tada motar ya ja, har suka isa gida rediyo ne kawai ke aiki. Suna shiga ta fada dakinta ta ajiye mayafi sannan ta shiga bandaki ta dauro alwala ganin an soma kiraye-kirayen sallah, shima ganin haka yasa bai bi ta kanta ba saida ya je ya yi alwala ya fice masallaci. Bayan ta idar ta yi ta rokon Allah akan ya sauwaka mata zafin kishin da ta ke ji a ranta game da Faruk. Babu abinda ke tayar da hankalinta face furucinsa na a ofis dinsa ma ana mata na takura mishi. Kenan ma abin dadi ya ke mishi ko? Ai kawai sai ta sanya kuka. Jin motsin mutum ta yi a kofar dakin, hakan yasa ta saurin goge fuskarta. Ya karaso ciki ya zauna a kasa gefen dardumar da ta ke zaune. "Ni ne ko?" Ta kauda kai gami da kokarin mikewa, ya ja hannunta ta koma ta zauna suna fuskantar juna. "Ki yi hakuri, Ummina da ace zasu burgeni da tun kafin na ganki na soki su zan fara so saboda nasha ganin ire-irensu, amman babu daya da ta ta6a kwantamin cikinsu, sam ba su daga cikin kalar matar da nakeson aure infact ma ni ban ta6a son wata ba bayan ke, bana fatan kuma Allah Ya jarabceni da son wata din bayan ke." Ta ji ranta ya yi sanyi, tasan banda ma abin kishi ina ita ina wani kishi da wasu bayan tasan matsayinta wajen mijinnata? Ta sauke kanta kasa tana murmushi, abin ya ba shi dariya. Ranar kam sai a hankali....!!! "Allah Sarki." Shine furucin da Amina ta yi bayan gama sauraron jawabin Ummi game da Ikram. Amina ta cigaba da magana....!   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   123 "Kinga yanda Allah ke jarraba bayinSa ko Ummi? Kiga dai yanzun kin zame musu wata abar, kinga ikon Allah wannan karon wajenki Ikram ke neman alfarma ko? To don Allah kar ki rikesu da komai duk kuwa na tabbatar ba ki rikesu a rai ba. Yanzu ni bansan me zan ce miki ba akan wannan abu, saidai gaskiya inajin tausayin Ikram kamar yanda rayuwar Gidado da Hafsa ta burgeni, anya kuwa ba za mu yi musu shishshigi ba?" Ummi ta dan cize le6anta na k'asa gami da mikewa tsaye daga zaman da ta yi a gefen gado.     "Shine nima wallahi Anti, wannan ne matsalar, da ma ace Yaya Gidado ba shi da mata ne, da babu abinda zai hanani sanarmishi, kawai..."   "Ko za ki jarraba fadawa Yaya Abubakar? Watakil shi yasan shawarar da zai bada."    Ta gyada kai jin abinda Amina ta ce. "Kuma fa hakane." Suka tsaida wannan shawarar kafin kuma suyi sallama ta yi kiran Abubakar. Bai daga ba sai ya yi saurin yankewa ya kirata.  "Innota ya akayi?" Murmushi ta yi sannan ta gaisheshi ya amsa gami da tambayar lafiyarta da ta maigidan.  Bayan gama gaishe-gaishe ne ta fadamishi maganar Ikram, ta kara da fadin. "Ni kuma wallahi ina kunyar Anti Hafsa, banaso wani abu..."   "Kar ki damu, shi aure ai nufin Allah ne, idan Allah Ya yi sai ta zama matarsa to zata zama din. Yanzu dai abin yi bai wuce na a sanarmishi ba, ai ko don halaccin da mutanen nan suka yi mana na rikemana ke amana ba tare da sunsan komai naki ba ya kyautu mu yi musu abinda yafi haka muddin bai fi karfinmu ba, zan nemi shi Gidadon, batun kuma wai Hafsa karki damu kanki, Allah ne Ya bamu damar yin fiye da daya matukar zamu yi adalci tsakani."     Ita dai ta yi tsuru da idanu ta rasa abin cewa banda um don kuwa tsoronta bai wuce daukar da Hafsa zata yi mata ba. Abubakar ya ce kada ta damu daga haka ya tambayeta ko akwai wata matsalar ta amsa da babu sannan suka yi sallama. Koda ta shaidawa Amina yanda sukayi Amina ta amsa da cewa. "To, sai mu tayasu da addu'a, idan akwai kaddarar aure tsakaninsu, Allah Ya hadamishi kansu, Allah Ya kawo lamarin da sauki." "Ameen." Daga haka sukayi sallama.   A washegari kuwa Abubakar ya kira Gidado ya sanarmishi, dariya Gidado ya yi don zatonsa wasa kawai Abubakar ke yi. "Banda abinka, ina diyar birni wacce ta tashi cikin daula ina ni dan kauyen Jar Kwami? Haba dan uwa, gyara zancenka."    "Kada ka dauka wasa na ke yi Gidado, I'm serious. Ka yi tunani akai please." Gidado ya yi shiru, daman fa ya tsargu da irin yawan kallon da ta ke mishi hakanan kuma da yawan murmushinta gareshi saidai ba shi da kakkarfar hujja, to shi me zai iya yi mata? Alal hakika babu wacce ya ke so kamar Hafsa, kuma ace ko yanzu ko shekara basu yi ba ya tashi neman aure? Auren ma wacce yasan zai sosa zuciyarta fiye da auren wata a kauyennasu? Ya girgiza kai tamkar Abubakar na gabansa.   "I'm sorry Abubakar, gaskiya..." "Karka yanke hukunci da gaggawa mana, ka yi tunani don Allah, ko don irin rikon da suka yiwa Ummi ai..." "Ya isa, karka sanyo batun wannan don Allah, ana magana ne fa ta aure wanda ya kasance raayin mace da namiji." "Idan Allah Ya kaddaro fa?" Abubakar ya tari numfashinsa.    Ya sauke ajiyar zuciya wanda har kunnen Abubakar. "Wannan kuma kaddara ce, sai ayi." "To haka nake so ka saka a ranka, idan Allah Ya kaddara aurenka da Ikram sai fa anyishi koda ace babu son ranka ciki. Ka barwa Allah za6i sannan don Allah zan aikomaka lambarta ka dunga kiranta, mai sonka ai yafi makiyi, don Allah dan uwa ko gaisuwa ce ka daure ku dunga yi, yarinyar na wahala ne akanka." Dariya Gidado ya yi don abin mamaki ma ya ke ba shi, to me ta gani a jikinsa da har ta ji ya burgeta?   Haka Abubakar ya cigaba da yi mishi magiya har saida ya aminta da hakan sannan suka rabu. Ko mintuna uku baayi ba ya aikomishi lambar ta whatsapp. Koda ya adana ta cikin wayarsa, ya bude hoton da ta dora, hotonta ne na bikin Haidar da Intisar, da k'ibarta a hoton, tana dariya ta rungume Amarya da Ango aka dauka, ya kuramata idanu, bata da makusa saidai bai ji wani sonta a ransa ba illa tausayi da ta bashi na kamuwa da son wanda ba ya sonta. Ya yi mata sallama gami da cewa. "Kina magana da Gidado, ina fatan mutanen Abuja lafiya?"   Daga haka ya rufe wayar ya maida aljihu inda ya cigaba da sauraron (customers) dinsa da ya bari suna cinikayya da yaron shagonsa.     Sak'on bai iso ga Ikram ba sai Magriba bayan ta dawo daga islamiyya, ta zauna da zummar duba litattafan makaranta sakamakon jarabawarsu ta karshe da ke k'aratowa, ta janyo wayar ta bude.     Ta yi mamakin ganin bak'uwar lamba ta whatsapp dinta, saidai me? Tun bata bude gaba daya ba idanunta ya hango mata sunan da ya ambata nasa, wato Gidado sai kuwa hotonsa da ya dora, hannu na rawa yayinda gabanta ke bugu da sauri-sauri ta soma da budo hoton don gaskatawa, ai batasan lokacin da ta diro daga saman gado ba tana buga tsalle hakanan hakoranta a waje ta kasa rufe bakin tsabar murna har da hawaye farinciki, ta dafe kirji. Oh yanzu ya zata ji idan ya furta yana sonta tunda ganin ya kulata kadai ma ya sanyata farinciki, to wai ma a ina ya samu lambarta?  'Ummi.' Cewar wani 6angaren zuciyarta.    Ta k'ara tsalle tana ihun farinciki wanda batasan da karfi ta ke yi ba saida aka murda kofar aka shigo. "Lafiya?" Jin muryar Hajiya yasa ta nufarta gami da rungumeta tana murna.  Hajiya cike da mamakin na abinda yasa Ikram wannan farincikin ta dagota daga jikinta tana dubanta, can kasan zuciyarta hamdala ta yi domin kuwa ta mance rabonta da ganin irin wannan fuskar fara'ar ta Ikram, to amma hawayen na menene?   "Meyafaru ki ke mana ihu?" Cikin zak'uwa ta ce. "Yau Yaya Gidado ya yimin magana, ki tayani addua Allah Ya..."   Dif ta yi don gaba daya ta mance gaban wacce ta ke, idanunta sun riga sun rufe. Ita kuwa Hajiya ta tsareta da kallo, duk duniya Gidado biyu ta sani. Da wani kawunsu na Adamawa wanda tsoho ne, sai kuwa Gidadon wajen su Ummi.    "Wane Gidadon ki ke magana akai?" Ta hau kame-kame, bata yi zato ba ta ji Hajiya ta zare wayar daga hannunta, kafin ta yi wani yunk'urin ta budo. Ta yi shiru tana duban hoton kafin ta dubi Ikram cikin sanyin murya mai nuni da karaya ta ce.  "Shi Gidadon ne ke sanyaki rama da tunani dama? Kinsan waye Gidado wajen Ummi kuwa?"   Shiru Ikram ta yi babu amsa ga kunya da ta cikata, wani murmushi na manya Hajiya ta yi.    "Saidai kuma na ji ance yana da mata, kina da tabbacin za ki iya aurensa ki zauna a Jar Kwami? Sannan za ki iya hakurin zama da matarsa?"   Sai lokacin  ta iya dago kanta ta dubi mahaifiyarta idanunta na zubda ruwan hawaye.    "Duk abinda ki ka lissafo Hajiyarmu, babu daya da ba zan iya jurewa ba, ni nasan harda hakkin Ummi ya kamani, saidai wallahi a yanda nake ji a zuciyata, kamar ba zan iya auren wani ba bayan Yaya Gidado."   Ta karashe cikin kuka, zuciya irin ta *MAHAIFIYA* nan take ta ji tausayin diyarta ya mamayeta, ta share mata hawayen gami da mikawa mata wayarta tana murmushi.    "Allah Ya za6a abinda yafi alheri gareku."   Daga haka ta juya ta fice, Ikram murmushin jin dadin ta saki, ko babu komai ta ji dadin kyakkyawar adduar da ta fito daga bakin Mahaifiyarta. Ta karasa saman gadon ta zauna sannan ta bud'o sak'on. Sallama ce da gaisuwa, nan take ta ba shi amsa, ai ko babu komai samun lambarsa da ta yi cikin wayarta, abin alfahari ne, zata cigaba da janyo hankalinsa da dabara hakanan zata cigaba da tsananta addu'ar neman za6in Allah.          Tun daga wannan ranar sai ta ja shi da hira, abinda ya burge Gidado bai wuce ganin yanda koda wasa bata sanarmishi cewar tana sonsa ba, hakazalika babu ranar da bata tambayar Hafsa, har Anti ta lak'aba a farkon sunanta. Ya yi mamaki matuk'a don ya yi zaton zata dunga kishinta ko don ma yanda ya ke yawan yi mata zancenta, abin daure kan ma ita da kanta ta nemi ya bata tarihin farkon haduwarsa da Hafsa inda ya kirata suka dan ta6a hira kafin ya bata.   Kishi fal ya cika kirjinta jin yanda ya ke kod'a Hafsa a zuciyarsa, saidai ya zata yi tunda ita ta nemi da ya bata labarin.   "Ya ki ka yi shiru?" Ta yi murmushin yak'e. "Bakomai, kwarai soyayyarku ta burgeni, ina fatan nima Allah Ya bani miji wanda zai yimin irin wannan son da ka ke yiwa Anti Hafsa, ko fiye da hakan ma." Ransa ya sosu, ta kuma ba shi tausayi, anya yana kyautawa yarinyarnan? Ya tuna ya cewa Abubakar suna hira sosai da ita, saidai ya 6oyemishi cewar bai yi mata wata magana da ta danganci soyayya ba.      "Hello." Ta fada muryarta a sanyaye. Sai lokacin ya tuna ashe waya ya ke yi.  Ya numfasa.    "Allah Sarki, Allah Ya ba ki fiye da ni."    Ta gyada kai idanunta cike taf da kwalla, shakka babu Gidado fa ba sonta ya ke yi ba.    "Um, da wuya na samu hakan, koda zan samun ma bana bukata, nafison daidai kai din a komai da komai."   "Kamar ya?" Sai alokacin ta fahimci lallai su6utar baki ta yi. Ta yi saurin gyara furucinta. "Eh idan na samu fiye da kai ai inajin mata ba zasu barni na huta ba, inada kishi kuma, banajin zan iya jure waccan ta kiraka waccan ta zo."   Cikin dariya da muryar zolaya ya ce. "Kuma gashinan kina shiga lokacin wata ko?"   Itama dariyar ta yi. "To ai ni kanwa nake wajenka." Ya yi murmushi mai sauti. "Hakane."   Suka kara ta6a hira kafin su yi sallama.     Ta k'urawa wayar idanu kafin ta hau ambaton 'Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun', wannan ba karaalmar musiba bace ace kana son wanda ba ya sonka.     Ta k'ara daukar alkawarin zage damtsenta wajen kyautata mishi da yawan hira da shi da kuma danne soyayyarta, watakil a haka Allah Ya taimaketa ta ci galaba ya soma sonta.           ***    BAYAN SATI UKU   ***                 GIDAN FAR HAS Faruk ya jima da komawa bakin aikinsa, yayinda ya cikawa Ummi alkawari inda ya daukomata matar da zata koyar da ita karatu kafin zuwan lokacin da zata soma shiga aji.     Koyaushe soyayya suke zubawa, a wannan lokacin har Hajiya sun kaiwa ziyara, hakanan ya dauketa zuwa gidan yayyunsa, nan ma ta yi mamakin ganin chanji daga su Jidda duk kuwa da cewar bata iya ta saki jiki da su ba tunda basu saba da hakan ba.      A ranar wata laraba Faruk na tsaka da aiki ya tsinci kiran Ummi, a take ya ajiye biron hannunsa ya daga.   "Assalamu alaikum Ummina." Ta amsa da fara'arta kafin ta tambayi lafiyarsa. Ya yi murmushi.  "Ganinan sai afkin tunaninki kuma ga ayyuka sunmin ca." Ta yi murmushi mai sauti kan ta dora da fadin. "Allah Sarki, Ummi ma ta kasa rabuwa da tunanin Faruk dinta." Ya lumshe ido gami da jinginar da kansa jikin kujera yana murmushi. "Kasan meyasa na kiraka?" "Saikin fad'a tawan."   Cikin shagwa6e murya ta ce. "Fura nakeson sha."   Ya yi dariya. "Yau kuma gida ki ka tuno?"  Itama ta dara. "Dagaske wallahi, na kasa cin komai, shi kawai nakeson sha."   Ya mike zaune. "Ya Salam, meyasa tun dazu ba ki gayamin ba kuma ki ka zauna da yunwa? Bari nasa a kawomiki."    "Yauwa FAR HAS."   Tunda ya ke bai ta6a jin ta ce hakan ba, ya yi saurin jefamata tambaya. "Me kenan?"   Dariya ta yi ta katse kiran ta barshi sakato da waya a hannunsa ba tare da yasan tak'amaiman manufarta ba. Tunawa da ya yi da furucinta na bata ci komai ba yasa shi saurin katse wannan gami da kiran Ado direban gidansu da zummar ya bashi aike.    Cikin mintuna da basu gaza ashirin ba ya je ya siyo damammiyar fura mai dadi ta cikin roba har guda biyar bayan ya kar6i kudin a hannun Hajiya daga nan bisa umarnin Faruk ya zarce ya kaiwa Ummi. Ai kuwa shi ta wuni a wannan ranar tana sha.  Koda ya dawo suna zaune, yayinda ya ke cin abinci ita kuwa tana faman sha fura tana kallon talabijin, ya k'uramata idanu yana k'aremata kallo cikin lura. Ta tsargu, hakan yasa ta dubansa.....!    DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 124 "Meyafaru?" Ta fada cikin sanyin muryarta, ya dagamata gira yana mata murmushi.  "Zo nan." Ba musu ta ajiye robar furarta ta mike ta nufi inda ya ke gami da zama a gefensa, sanye take cikin riga iyaka gwuiwa da dogon wando(tight).  Ya janyota jikinsa.  "Gaba daya kin chanja, anya babu ajiyata anan?" Ya karashe yana mai kai hannu cikinta gami da shafa.    Ta yi shiru, ita daman wata nada sati daya ta tare a gidan yanzu gashinan har watan ya cinye bata ga komai ba.  Ya zungureta. "Answer me." Ta shagwa6e fuska. "Nidai bani da komai." Ya yi murmushi. "Anya kuwa? Ji fa yanda ki ka k'ara girma a komai."  Ta lumshe idanu jin yanda ya kasa tsayar da hannunsa wuri guda, da sauri ta zame ta koma gefe tana fadin. "Kai FAR HAS abinci fa ka ke ci." Ya yi mata duban rashin fahimta. "Af, kinga na manta ko? Inason tambayarki ma'anar wannan FAR HAS din na manta."   Dariya ta yi wacce ke burgeshi, bai iya 6oyewa ba saida ya furta, don Faruk sam bai iya 6oye abinda ya yi mishi, ko girki ta yi sai ya yaba balle idan idan ta ci ado, hakazalika duk sadda ya shigo gidan sai ya yaba da gyaranta, wannan ba karamin kara mata sonsa ya ke ba, babu macen da batason a yabawa kokarinta, wasu mazan nasu tunanin su kadai zasuyi ana yabawa, su ba zasu yaba naka ba, basusan cewa yabo na kara soyayya tsakanin maaurata ba,  koda ta yi ba daidai ba idan ka fada bazata ji haushinka ba saboda tasan ka yabawa kokarinta kafin haka.    "Har kullum bana gajiya da ganin dariyarki." Ta rage dariyar tana murmushin jin dadin kalamansa.   "Nagode FAR HAS." Ta fada cike da zolaya, ya basar gami da maida kansa ga faranti yana murmushi.     Bai kara magana ba hakanan itama kowanne na bawa cikinsa, ita kuwa saida ta shanye robar fura tas. Lokacin shima ya kammala cin abincin ta dauke kwanukan sannan ta dawo ta zauna kusa da shi kamar yanda ya nunamata yafi bukata idan suna zaune.     Ya ja yatsun hannunta. "Fadamin ma'anar FAR HAS." Ta saki k'ara kad'an kafin ta turo baki. "A kyauta?" Ya na murmushi ya girgiza kai. "Fad'i bukatarki."   Ta kanne ido daya. "Gobe a karomin fura." Ya janyota ta yi filo da cinyarsa. "Mai sauki kenan daga abinda za ki samu, just tell me."    Ta lumshe ido tana murmushi. "Faruk da Hasiya nake nufi." Sai lokacin ya dan tsaya nazari kafin ya dubeta da mamaki ya na murmushi. "Sunan ya burgeni ya kuma ban mamaki ta yanda har ki ka yi tunanin hadawa."   Ta rufe ido da hannu tana murmushi. Ya sunkuyo da fuskarsa zuwa nata....!                                ***    ***     ***                       KANO   Kwance ta ke tana duban hotunan da suka shigo wayarta ta (whatsapp) don bisa al'adarta duk dare idan ta gama komai sai ta bibiya ta ga ko akwai wadanda basu dace ba ta goge, kamar abinda ya shafi gawarwaki da hatsari. Karaf, idanunta suka kai ga wani hoto wanda yasa ta mikewa zaune babu shiri.    Hoton Abubakar ne tare da wata 'yar ajinsu Rukayya Tsigai, ai ba shiri ta hau online ganin wacce ta aiko,  Zahida Taskira ce daya daga cikin yan ajinsu wacce suka sanyamata sunan sanadin surutunta da tone-tone don ba a sirri da ita. Inda ta yi mata bayani kamar haka.   "Aslm, Ihsan please ba batun gulma ko hada husuma ba, inace wannan shi ki ka ta6a nunamin matsayin wanda zai aureki? Magana ta gaskiya guy dinnan na sanshi tare da Tsigai, saidai ban gayamaki ba time din kada ki ji haushi, idan har dagaske shi ki ka za6a matsayin mijin aure zan baki shawara ki chanja tunani saboda wallahi guy din yana da son mata, Rukayya ba wajen Partyn wata cousin dinta sukayi hoton nan kuma na tabbatar suna chatting."   Kan Ihsan ya yi dum, ta rasa meke mata dadi a duniya, batasan lokacin da ta soma hawaye ba tana ambaton Allah, saidai me? Ko kankani bata ji soyayyar Abubakar ta ragu ba sai kishi mai zafi da ya turnuketa, ba don tana sonshi ba babu abinda zai hana a yau ta rabu da shi.    Bata maidawa Zahida amsa ba don tasan zai iya komawa kunnen Rukayya Tsigai, kawai sai ta kira Abubakar ta ce ya hau online zata mishi magana.    Badiyya na kallonsa yana waya yana tambayar ko lafiya duk ya rikice saidai bata ce uffan ba, banda murmushi, idan da sabo ai ta saba da halin Abubakar na hira da yanmata balle kuma ta tabbatar cewa wannan Ihsan ce don duk cikin yanmatansa tana da yakinin ita ya ke yiwa so na aure tunda har ankai da sanya rana. Mikewa ta yi ta bar falonnasa shi dinma bai tsaidata ba don hankalinsa ya tashi jin muryar Ihsan din ba'a hayyaci ba.     Nan ta aikamishi hoton, duk sai ya ji jikinsa ya yi sanyi, shakka babu wannan hoton ya jima, yanzun ma ba ya tare da Rukayya sun rabu akan zafin kishin Rukayyar kan yanmatansa, shi kam kullum adduarsa bai wuce na Allah Ya yaye mishi wannan mugun hali ba.    Ranar kam Ihsan ta yi kwanan bakin ciki, dakyar bacci ya saceta don idanunta saida suka kumbura.  Washegari da ciwon kai ta tashi, koda Mami ta tambayeta sai ta ji bakinta ya yi nauyi ta kasa fadamata, tsoronta kada a fasa auramata Abubakar don Allah shaida tana sonsa yanzun musamman yanda ya ke kasheta da soyayyarsa mai tsayawa a rai wanda ta tabbatar da shi ya ke yaudarar yanmata sai kuwa kudi.    Ikram kadai ta sanarwa, Ikram da ranar ta tashi da farincikin jin Hafsa matar Gidado ta haihu da kuma dan kishinta a kasan rai duk sai ta ji nata 6acin ran ba komai bane idan an hada da na Ihsan. Ta hau salati, tasan tabbas Abubakar yana da kula yanmata don tasan wata kawarta wacce tasan shi saidai batasan har zuwa wannan lokacin ba, nan ta shiga bata baki da nunamata ta cigaba da adduar neman za6in Allah, katse wayar kawai ta yi. Abubakar ranar ya kira yafi sau biyar saidai ta k'i dagawa, ya bita whatsapp hakanan ya yi mata text saidai ko kusa bata maida amsa ba.       A ranar dai suka shirya don kuwa bata iya dogon fushi da shi, abin mamaki Zahida ba ta daddara ba ta turo wani, ai kuwa ta sha zagi kafin a karshe ta rufeta yanda babu damar da zata k'ara shiga sabgarta.                   ***    ***    ***         A KWANA A TASHI....! DAN ADAM @RUFAIDA OMAR    125 Tun Ummi na zuba idon ganin 6atan watanta, har dai ta ji shiru, wannan ya daga hankalinta, ga wani haske da ta kara hakanan komai nata ya k'aru, watarana suna kwance da Faruk ya dubeta.    "Ummina ban yarda ba, anya babu ajiyata a wannan cikin naki? Kwadayinki ya yi yawa, yau kice magwaro, gobe ki ce bakyason kamshin turarukana."   Ta kwanta jikinsa tana mai turo baki. "Nifa bani da komai." Ya ja karan hancinta. "Zamu tantance yanzu. Taso muje." Ta mike zaune idanu a waje ta ke dubansa. "Ina?" "Asibiti mana." Ta yi narai-narai da fuska. Ya yi saurin toshe bakinta da hannu. "Shii..karki soma rok'ona don kuwa sai munje." Ta langa6ar da kai tana sosa idanu. "To ai..ai yau babu aiki." Cikin muryar rarrashi ya ce. "Wajen Dakta zamu je, bamu jima da waya ba ya cemin yana asibiti."  Ta turo baki. "Please FAR HAS, allura fa zasu yi min."   Ya matso da ita yana ji kamar ya hadiyeta. Saitin kunnenta ya yi magana. "Ba wanda zan bari ya soka maki karfe a jiki, tashi ki chanja kaya kinji?"   Ba musu ta mike, daman sanye ta ke da riga wacce ko k'ugu bata karasa ba sai kuwa wando shima da bai kai gwuiwa ba, ta kai kofa ya kira sunanta. Ta juyo fuska a turnu6e. "I love you." Furucinsa yasa ta murmusawa gami da lumshe ido ta budesu akansa.  "Love you too." Ta furta a hankali ya sanya yatsunsa cikin sumar kansa yana murmushi gami da sauke ajiyar zuciya, wasu kance soyayya na raguwa bayan aure, shi kam ya rasa dalilin da yasa koyaushe soyayyarta gaba ta ke k'ara yi a zuciyarsa, Allah Ya sani kauna fisabilillahi ya ke yi gareta, tun dora idanunsa da ya yi akanta, bai ta6a hutawa daga tunaninta ba har saida ya mallaketa. Mikewa ya yi shima ya fad'a bandaki don kimtsawa.     Lokacin karfe hudu ta kusa, Ummi ta kammala shirinta cikin wani koren leshi dinkin riga da siket, ta yafa farin mayafi ta sanya takalmi flat mai kalar fari da baki.     Saida sukayi sallar la'asar kafin su fito kasancewar ranar bata da lesson don daga litinin zuwa juma'a sukeyi, kwarai Malamar na yabawa da kokarin Ummi don har mamakin kaifin basirarta ta ke, ko wata basuyi da somawa ba, ta iya abubuwa da dama.    Gogan kananun kaya ya sanya, wandon 3quarter ne fari k'al, sai kuwa t-shirt dinta mai layi-layi fari da bak'i.    Idan ka gansu dole ka k'ara daga ido ka kallesu don kuwa sunyi matukar dacewa da juna. Saida ya budemata 6angarenta ta shiga ta zauna kafin shima ya shiga, maigadi ya budemusu gate suka fita.     A asibitin suka iske Dakta Ridwan, yana duba wasu kasancewar yawanci ranakun hutu, manya yafi gani, saida ya sallami wasu kafin suka shiga.   "Ango na Amaryarsa." Ya fada yana dubansu fuska dauke da murmushi.  Suma murmushin sukayi Ummi na sunne kanta, Faruk ya kara matse hannunta cikin nasa. "Ya son ranka?" Sukayi dariya don tsakaninsu babu wani zancen raini, sun dauki junansu tamkar abokai musamman su ukun nan idan an cire Babban Yaya wanda ba koyaushe ya ke biyewa shiriritarsu ba.     Ummi ta gaisheshi ya amsa tana tambayar su Muhsin.  "Suna nan lafiya." "Ai ba'a kyauta ba, ya dace a kawo mana su koda ran Friday ne." Cewar Faruk.    Dakta ya yi dariya. "Karku damu, duka yaranku zasu zo hutu, ai (second term) din ya kusa k'arewa."   "Wai me? Noo, kar a kawosu duka, ba zasu takura min Bebina ba." Dariya Dakta ya yi. "Oh, har ka tabbatar da ka samu bebin? Toh ai sai ku tashi ku je Allah Ya raba lafiya." Ya karashe yana mai daure fuska da wasa. Faruk na murmushi yana mai dafe goshi. "Please ka yi hakuri, dubamin ita yau wata biyu kenan bata ga period dinta ba." Saida gaban Ummi ya fadi ta dan dubeshi, ya dagamata gira yana murmushi. "Eh ko?" Ta kauda kanta a kunyace. Dakta murmushi ya yi ya ce. "Lil kenan." Daga haka ya janyo takarda ya yi rubuce-rubuce bayan gama yiwa Ummi tambayoyi daga haka ya mikawa Faruk takardar. "Sai ka je a auna fitsarinta." Ba musu ya kar6a suka fita, bayan fitarsu ta dubeshi. "Kai FAR HAS, ko kunyar Dakta ba ka ji ba ka ke magana haka?" Ya daga kafada kadan yana yamutse fuska. "Don bakisan ma waye Dakta ba shiyasa ki ke fadin haka, sa'ar da na ci yana jin kunyar idanunki da sai na koma ni ke jin kunyarsa." Dariya kadan ta yi kawai batare da ta ce uffan ba. Bayan angama auna fitsari an basu sakamako suka koma ga Dakta. Ya bude takarda ya karanta yana murmushi kafin ya dubesu kadan, Faruk ji ya ke kamar ya warce takardar, cikin zakuwa da son sanin meke faruwa ya ce. "Wai don Allah ka yi magana mana." Dariya Ridwan ya yi.  "Bani goron albishir." Ya fada yana mai mikamasa hannu. Faruk ya wawuro na'urar auna jini (Sphygmometer) ya dora saman hannunsa. Har Ummi saida ya bata dariya, shi kansa dariyar ya yi.    "Toh nagode dai na tausayamaka tunda naga ka damu." Ya dubi Ummi fuskarsa a sake. "Congratulations, you are two months pregnant." Sunkuyar da kanta ta yi, ta fahimci me ya ke nufi, wato dai tana da ciki wata biyu. Faruk mikewa ya yi ya karasa ya rungume Yayansa suna dariya.    "Congratulations my lil, Hajiyarmu zata yi farinciki da jin hakan." Sukayi dariya. Tunda Ummi ta sauke kanta bata k'ara dagoshi ba har zuwa sadda Faruk ya dawo ya zauna gami da lalubo hannunta yasa cikin nasa, idanu ta lumshe ta saci dubansa, shima ita ya ke kallo. A hankali bakinsa ya motsa.  "I love you." Ta fahimci hakan ya fada, ta kauda kanta tana murmushi gami da damke hannunsa alamun ta amsa. Hankalin Ridwan ba ya kansu, ya gama rubuta magunguna kafin ya mikowa Faruk.    "Sai a kula banda yawan aikace-aikace. Yau za ka shiga Gida ne?"   "Ai can na nufa ma." Sukayi dariya, Ummi hankalinta ya tashi, kamar ta ce mishi kar su je, tasan kawai kunya zai sanyata gaban su Hajiya.  Ai kuwa suna fita ta hau rok'onsa akan kada su je, baice uffan ba banda murmushi. Saida suka je din, Ikram ta tarbesu kamar ta hadiyesu don yanzu bil hakki tana kaunar Ummi, soyayyar Gidado ya shafeta.    Hajiya ta yi murnar jin cewar Ummi na dauke da juna biyu, don Faruk da bakinsa ya fadamata, ta hau yi mata gargadi akan ta kula za'a samo mata mai tayata hidima, ta nuna a barshi saidai Hajiya ta dage sai anyi hakan. Faruk bai ce uffan ba don da ta raayinsa shi kansa bazai so ba saidai yana tuna maganar Dakta da ya ce ta dunga hutawa ya amince. Da Magriba tana dakin Ikram sunyi sallah suka yi zaman hira, anan Ikram ke labartamata yanda sosai yanzu Gidado ke damuwa da ita har idan ya ji shiru bata hau online ba zai damu ya kirata a waya.  "Ikon Allah." Shine kawai abinda Ummi ta ce, duk kuwa da cewar ta yi mata murnar hakan saidai kasan ranta tana tsoron abinda zai je ya dawo idan Hafsa ta samu labari. Ko da wane ido za ta dubeta?      A hakikanin gaskiya ko a baya idan Gidado bai jin wani abu game da Ikram to a yanzun yana ji, don ita kanta Ummin ta fahimta ta yanda duk sadda sukayi waya sai ya yi maganar Ikram, wataran ya ce suna hira wataran ya dunga yabon halin kirkinta . A bakinsa ne ma ta ji cewar suna chatting Abubakar ne ya bashi lambarta. Ko Abubakar din da kullum suke waya bai sanarmata ba.    "Ya karatun? Kina ganewa sosai ko?" Ikram ta fada gami da katse shirun. Murmushi Ummi ta yi. "Ina fahimta." "Allah Ya taimaka, ga Azumi ma ance nan da sati biyu ko?" Ta gyada kai. "Hakane, abin ba wuya, kamar yau ne muke lissafi da Anti Amina ta ke cemin bayan Azumi bikinta, yanzu har ga azumin ya zo."   Dariya Ikram ta yi. "Kina ban dariya idan kina ce mata Anti, sa"arki ce fa."   Dariya itama Ummin ta yi kadan.  "Ta cancanta, ita ta mayemin gurbin uwa kuma Yaya a gurina alokacin da bani da kowa cikin DAN ADAM dake son ya ra6eni, alokacin da kowa ya gujeni. Ita ke cemin na yi wancan mai kyau ne, kada na yi wannan babu kyau, ta zama Malama agareni tun ban kai ga soma zama a aji ba. Kinga kuwa ta cancanta na kirata da Antina."   Ikram ta gyada kai, ita kam yanzu Ummi na burgeta, mutum ba zai san tana da shiga rai ba sai ya zauna da ita, daman bata tsaneta ba tun a baya sai sadda Faruk ya ce zai aureta har ya mareta akanta ga kuma taya Ihsan kishi.     "Lallai ta cancanta har ta wuce cancantar ma. Ni kuma nan gaba ina fatan zama yayarki." Ta karashe da gwalo, Ummi ta gane, wato ta zama matar Gidado.  Sukayi dariya lokaci guda.    "Dagaske nake, kinsan kuwa Hajiya da Daddy sunce saidai nima na karasa jami'a a gidan mijina, da zarar mun gama jarabawarnan ta karshe sai aure."    Ta jinjina maganar. "Kice tare za mu sha bikinku da su Ihsan."   Dariya Ikram ta yi sai kuma ta maida fuskarta kalar damuwa. "Allah Yasa mu auri wanda yafi alheri garemu." "Amin."    Sai bayan isha'i sannan suka bar gidan zuwa gidansu. Nan kuwa aka shiga rainon ciki babu wasa, yarinya karama aka kawomata, batafi shekaru goma sha hudu ba. Farkon kawota Ummi idanu ta zubamata tana kallonta cike da tausayawa sannan ta dubi wacce ke tare da ita wacce aka kira da mahaifiyarta da ko kusa bata ga kama ba.    "Yanzu Baba wannan aiki zata dunga yi?"   "Eh, aiki kowanne da ki ke so ki sanyata, babu wanda ba zata iya yi gareki ba."   Ta k'ara duban yarinyar wacce ta yi wani firi-firi da idanu. Tausayinta ya kamata.    "Shikenan." Jin haka matar ta hau washe baki tana gyara mayafi zata mike. "To bari na koma tunda naga gidan, ke kuma Batula ki kula, kada inji kar in soma gani kin sa6awa uwar dakinki kinji ko? Hajiya don Allah ki dunga kula yarinyar akwai shegen munafunci."   Ummi da ke jin kamar ta makureta ta ce. "Wane irin munafunci kuma?"   "Um, kada ta dunga yi miki la6e wai, to shikenan ai, sai anjima, Allah Ya kara arziki." Ta karashe cikin basar da wancan maganar. Ummi ta bata dubu biyu ta hau mota. Nan ta hau zuba godiya ta fice.    Ta maida hankali ga yarinyar da aka kira da Batula.   "Sannu Batula, inaso ki saki jiki da ni, ki rikeni tamkar yayarki, ni bazan cutar da ke ba, zan kuma rikeki bisa amana kinji ko?" Cikin mamaki mai tsanani da rashin gaskatawa ta gyada kai don gani ta ke kamar wani salo ne na cutarwa, gida na uku kenan da aka kawota, wadancan biyun duk guduwa ta yi saboda matsi da takura.    "Fadamin gaskiya Batul, mene alak'arki da wannan matar? Dagaske itace ta haifeki?" Ta girgiza kai cikin raunin zuciya kiris take jira ta fashe da kuka. "A'a, kanwar mamana ce uwa daya uba daya da ta rasu."   Runtse idanu Ummi ta yi ranta na suya.   "Meyasa ta ke kawo ki aikatau?" "Babana ne ya aureta bayan rasuwar Mamana, ba da son ransa ta ke kawoni gidan aiki ba, ko yau da zamu taho da kuka muka rabu da shi. Kullum saita dakeni, komai ni nake yi mata."   Hawaye Ummi ta shiga fitarwa, DAN ADAM kenan, ace 'yar yayarki ki ke yiwa rikon sakainar kashi? Duniya abin tsoro.    Ummi ta tabbatar mata zata riketa bisa amana, ta bata kyakkyawan muhalli ta sanyata a makaranta. Ita da kanta ta wankemata kanta bayan ta tsefemata kitso, suna yi suna hira Batul na kara bata labarin kauyensu Maraba.     Cikin kayanta ta dauko wanda ya yi mata kadan ta bata ta sanya kasancewar yarinyar akwai tsawo nan suka zauna das a jikinta.     Koda Faruk ya dawo, ya yi mamaki, bai gane ko wacece ba ganin tana zaune a kasa suna hira da Ummi suna dariya. Batul ta gaisheshi ta yi ciki, ya zauna yana duban Ummi wacce ta tashi ta tarbeshi. "Ummina wacece wannan?" Da murmushi ta amsa. "Itace wacce Hajiya ta turo zata tayani aikace-aikace." Ya jinjina kai. "Naga kamar wata kanwarki kunata hira ai." Murmushin ta kara yi. "Kanwartawa ce ma. Tausayi take ban." Nan ta labarta mishi labarinta, shi kansa ya yi mamaki. "Allah kenan, DAN ADAM babu mai iya masa sai Allahn da Ya halicceshi, Allah Ya datar da mu." "Amin." Tun daga wannan ranar Ummi ta riki Batul bisa amana, har makaranta an sanyata na Arabi.     Haka har azumi ya zo, nan ma komai tare sukeyi, cikin azumin ne kuma Intisar ta haihu diyarta mace. Kowa ya yi murna da hakan, ranar suna aka sanya sunan Hajiya Mama, wato Sadiya. Hajiya Mama ta ji dadin wannan karar da sukayi gareta.     Anci suna an kare lafiya kowa na yaba yanda Faruk ke nan nan da Ummi ko gaban mutane ne ba ya iya 6oye son da ya ke mata.    A ranar sunan ma ganin yanda Ummi ke yiwa Batul saida su Jidda suka tofa. "Wai wannan inace 'yar aikinki ce ki ke mata haka?"   Murmushi ta yi. "Ni ina mata kallon mutum mai daraja." "Don kema a baya yar aikin ce ko?" Cewar Fadila. Abin ya ta6a zuciyar Intisar da su Ikram, Ummi kuwa ko a jikinta ta soma bata amsa.     DAN ADAM @RUFAIDA OMAR   126 "Ko bayan wannan, yan aiki mutane ne kamar kowa, hakazalika suma suna da nasu daraja da k'imar, da yawa cikinsu kan fito aiki bisa kaddara ba da son zukatansu ba, wasu anfi karfinsu ne wasu kuwa halin rayuwa ce. Ni Ummi bana fatan ranar da zata zo na wulakanta wani DAN ADAM a duniya, da yawa suna kuskure, sukan dauki kansu wasu har su dunga wulakanta masu tayasu hidima don kawai tak'amarsu biyansu su ke yi, sai yaronki karami ya budi baki ya zagi dattijuwar da ko ke ta haifa amman ba zaki kwa6eshi ba kasancewar kina mata kallon yar aikinki, sai ya zagi direba ko maigadinki duk ba za ki ji ko darr ba, asalima har ya kai ga kin shigarwa danki don kawai kina yi musu kallon kaskantu, watakil kuma sun fiki matsayi a wajen Allah. Ba ma akan masu aiki ba, kowaye kada ka wulakantashi don shakka babu bakasan mai yi maka rana ba, ko ya ya, bana mance halacci."     Fadila da Jidda suka k'ulu da maganganun Ummi, musamman Jidda wacce ke ji kamar da ita ta ke, basu kadai ba har da wasu cikin gayyar sunan wadanda sun kasance suma sukan dauki yan aiki ba komai ba face kaskantu maganar Ummi ta shigesu, nan kuma wasu suka hau fadin ai yan aikin ma suna suka tara akwai mugaye. Ita kuwa Fadila bata kara cewa uffan ba don ta cika da mamakin yanda har Ummi ta yi kaurin wuyar mayarmata da martani.   "Ku bar ganinta haka, yar aiki ce a baya shiyasa ta fiye wannan zakalkalewar, ai duk inda mutum wanda bai saba da arziki ba ya ke to fa sai kun gani ko a jikinsa ko furucinsa." Cewar Jidda a fusace. Ummi ta dubeta, kamar ta ce wani abu sai kuma ta hadiye kawai tana murmushi. "Kai don Allah Anti Jidda." Cewar Intisar kenan, Jidda ta watsamata mugun kallo. "Na ambaci sunanki?"   Ta rausaya kai. "Ko ba don wani abu, ku yi duba fa da cewar cikin azumi ake..."   "Please ya isheni, wani abin nace?" Jin haka Intisar ta ja bakinta kawai. Wata hamshakiyar mace da ta hade cikin wani tsadadden leshi ta tofa. "Kwarai Jidda suna haka, don wallahi wata yar aiki da kawata Mariya Sadik ta ta6a yi, ai kinsanta, yarinyar a dakin mijin ta kamata. Ai babu butulu kamar dan aiki saidai mata mu kiyaye." Nan kuma babin ya koma hirar yan aiki, Ummi ganin abin nasu kamar da biyu ne, yasa ta mikewa ta bar dakin zuwa falo, Intisar da Baraka suka biyo bayanta har Ikram don abin ya 6ata ransu suma. Ta nunamusu ba komai ganin yanda suka damu. Ita kuwa damuwarsu akai ma kadai ta sanya komai gogewa a zuciyarta.    Sai Magriba Faruk ya zo daukarta, anan ya sha ruwa da su Haidar hakanan suma nan ciki suka sha ruwa sannan  ya shigo ya ga bebi, anan ne Fadila da Jidda suka kai mishi k'arar Ummi akan ya ja mata kunne. Ya cigaba da danne wayarsa yana yiwa yarinya hoto, gefensa Haidar ne zaune sai Ridwan wanda shima bai jima da zuwa ba.    "Wai muna magana ka maidamu wasu shashashai." Cewar Jidda mai saurin fusata.  "Wai meyafaru? Me Ummin ta yi muku?" Cewar Dakta yana duban Jidda. Jidda ta yi kwafa.    "Mene idan ba rashin kunya ba har tana kiranmu masu raina mutane. Yaushe kan mage ya waye da har raini zai shiga tsakaninmu?"   Faruk ya bar abinda ya ke ya dubi Jidda ransa a 6ace kamar ya yi magana saidai shigowar Ummi da Intisar falon Haidar ya katseshi, sanye ta ke cikin wani leshi bak'i mai adon orange flowers, sai mayafinta (orange) da ta yafa, hakanan jakarta da takalminta marar tudu. Idanunta akansa suka soma sauka.    Wani sassanyar murmushi suka sakarwa juna kafin ta karaso ciki ta gaida Angon karni da Dakta.     Faruk ya mik'awa Dakta bebin. "Bari mu wuce."   "Ai daman fuskar da ta samu wajenka ne yasa ta ke..."   "Ya isa! Haba!" Cewar Ridwan ga Jidda wacce ke zak'alk'alewa.  "A'a Dakta, babu batun ya isa fa, magana ta gaskiya."  Cewar Fadila tana taunar cingam da kallon banza.    "Ummi me ya hadaki da yan uwanki?" Cewar Dakta kenan, Faruk na tsaye hannuwa ciki aljihu kawai yana kallonsu.     Ta dan murmusa don ita bata ga abin daukar zafi ba. "Ba abinda ya hadamu."   "Karya ki ke yi uwar kissa." Cewar Fadila.    "Ya isa, Intisar me ya hadasu ne?" Cewar Dakta.  Tiryan-tiryan ta fadi duk yanda aka yi, Faruk ransa ya yi mugun 6aci ya soma magana. "Ku rike girmanku, ina girmamaku, kada ku janyo abinda zaisa nabar ganin girmanku. Duk wacce ta kara cin zarafin matata bazan lamunta ba, ko wacece cikinku komin girma da kimarta da nake gani zan yi watsi da shi wallahi!"    Jidda da Fadila ba bakin magana, shiru sukayi sai faman harararsa sukeyi amma ba bakin magana, ko babu komai yana da kwarjini.    Haidar ya dubeshi. "Ka yi hakuri mana. Gaskiya ba ku kyauta ba Maman Ma'aruf,  kune masu laifi ba Ummi ba, sai ku duba matsayinta a yanzu a Family namu, ku dunga sakaya bakinku."   Shima Dakta cikin tsananin 6acin rai ya hau zazzagawa matarsa fad'a, Ummi dai ganin mijinta ya nufi hanyar fita, itama ta yi musu sallama ta bi bayansa.     A mota ta sameshi zaune yana jiranta, ta shiga gami da dubansa, idanunsa sun kada bai ko dubeta ba ya figi motar a guje, ganin Batul yasa ta yin shiru ba don taso ba, duk da haka saida ta mishi magana. "Don Allah ka rage gudu." Ta fada gami da dafa hannunsa dake rike da sitiyari. Ya lumshe idanu yana mai jin zafin abinda ya faru, ganin ta damu yasa shi sassauta gudu har dai suka isa gida, Batul ta yi shiru tana mai tausayawa uwar dakinta don kuwa ta ji kadan cikin abinda ya faru.     Koda suka isa, dakinta ta nufa. Ta cire mayafi kenan ta isa gaban madubi da zummar cire dan kunne da sark'a ya shigo, ta dubeshi ta madubi suka hada ido.  Murmushi ta sakarmishi a kokarinta na 6oye damuwarta. Karasowa ya yi da sassarfa ya rungumeta ta baya yana sauke ajiyar zuciya idanunsa a runtse.    "I'm sorry." Ya fada a hankali, ta lumshe idanu, sai lokacin zuciyarta ta raunana, ta ji kamar ta zubar da hawaye saboda tsananin farinciki na samun miji kamar Faruk mai so da kaunarta.     Ta juyo ta dago fuskarsa gami da girgiza kai yayinda hawayen da ta danne suka shatato.     "Haba FAR HAS, don Allah ka daina  inajin wani iri wallahi." Ta rungumeshi tana hawaye yayinda lokaci guda ta ke murmushi mai bayyana hakora na farinciki.    "Ko babu komai wannan kaunar da ka ke yimin ta zarce komai a wurina, ta isa wankemin dukkan wani 6acin rai dake zuciyata. Wallahi na yafemusu bazan kuma rikesu da hakan ba, DAN ADAM ajizi ne."   Ya dago kanta yana murmushi gami da share mata fuska.  "Shiyasa nake kara sonki Ummina, halayenki sunfi komai burgeni. Na damu ne don nasan koda ya miki ciwo ba za ki bari na fahimta ba, cin zarafi ne abinda suka yi gareki wanda wallahi Allah idan suka ce haka za su dunga yi gareki bazan lamunta ba, zan jure komai idan ni ka yiwa amman banda abinda ya shafi lamuranki. Kema kin sani ko?"    Tun soma maganarsa ta zubamishi idanu tana murmushi gami da jin tamkar ta hadiyeshi don so, ya hure mata idanu hakan ya basu dariya. "Eh mana naga kamar mai shirin hadiyeni, wannan kallo haka?" Ta bugi kirjinsa tana kukan shagwa6a. "Kai don Allah." Ya ja karan hancinta yana dariya kafin ya taimakamata da abinda ta soma kokarin yi.         Su Jidda daidai ga Hajiya saida ta nunamusu rashin dacewar abinda su ka yi, hakuri suka bawa Hajiyar kasancewa suna ganin girmanta ainun don bata kasance cikin surukai masu sanya idanu kan abinda ya shafi zamantakewar yaransu ba, ta kama girmanta hakanan bata daure musu fuska.     Bayan wucewar watan azumi aka gabatar da karamar sallah. Ko ranar da suka hadu da sallah a gidan Hajiya banda gaisuwa babu abinda ya hadasu duk kuwa da cewa basu bita da kallon banza ba.      Nan kuma ta soma shirin zuwa Kano halartar bikin Amina wanda dakyar Faruk ya aminta ganin tana fama da jikinta itama. Ko su Ikram sun zo zuwa saidai makaranta, itama Baraka na fama da ciki dan wata biyar babu damar zuwa. Da kansa ya kaita, kai tsaye gidan Mami ta soma zuwa inda zata yi kwanaki uku sannan ta wuce gidan Hajiya Mama har zuwa gama biki. Babu tarbar arziki daga Ihsan sai dai ta samu sosai daga Mami da sauran mutan gidan wanda yanzu suke zaman aminci.      Mami sai nan nan ta ke yi da ita, abin ya sanyata farinciki sosai. Ihsan kuwa kallo bata isheta ba, sai idan ita ta gaisheta ko ta yi mata magana sannan zata tankamata a dakile kamar bata so. Ga shi kuma daki daya suke kwana, wannan abin na bawa Ihsan haushi don dai ba yanda ta iya ne.   Yau Ummi na kwance saman gadon Fahad wanda yanzun ya ke kwana dakin Adnan, tana tunanin yanda ita ke gyarashi a baya, lokacin sha dayan dare bata jima da gama waya da rabin ranta ba inda ya ke fadamata tsananin kewarta da ya yi. Ihsan ta shigo dakin daga falo, jin haka yasa ta yin makwas tamkar mai bacci. Itama duk a zatonta bacci ta ke yi, hakan yasa ta saka waya a handsfree tana amsawa.  Ita da Abubakar ne wanda rikici ne zalla.   "Kasan ina sonka shiyasa, kuma kasan bazan iya rabuwa da kaunarka ba amma a yanda na ke jin labarin irin yanmatanka da tuni na yi watsi da lamuranka."   Ummi ta yi shiru jin amsar Abubakar wanda ta ke mamakin inda ya bar matarsa a wannan lokaci. "Ki kara hakuri da halina, ni nasan ina da son mata, ki yarda kawai wannan kaddar..." "Kada ka karasa, wannan son zuciyarka ne. Daga waccan yarinyar ta sanka, sai waccan ta dora hotanka a dp dinta, na soma gajiya Abubakar, kishi na neman fasamin zuciyata." Kawai sai ta sanya kuka, ya rude yana faman kiran sunanta da magiya kan ta yi hakuri, saidai ina, tuni ta katse kiran da ta ga bai bar kira ba, kawai sai ta kashe wayar gaba daya.  Ta jima tana kuka kafin ta kwanta cike da tausayawa rayuwarta, yanzu idan suka yi auren haka zata dunga fama da shi?    Ummi ta ji babu dadi kwarai, tana ganin Abubakar kamar bazai aikata irin haka ba, ashe kusan jirgi daya ya kwasosu da Kb dan uwan su Faruk, koda bikinsu bata ganshi ba ta ji ance yana Ghana karo karatu. Ta tausayawa Ihsan ainun, ta dan juya ta dubi gadonta, ta bata baya saidai ta tabbatar bacci ya kwasheta, juyar da kanta ta yi gami da numfasawa. 'Rayuwa kenan, kowa da kalar jarabtar da Ubangiji zai mishi, Allah Yasa mu dace, amin.' Ta fadi a zuciyarta kafin ta yi adduoi ta kwanta itama. DAN ADAM @RUFAIDA OMAR      127 Kwananta uku gidan Mami har ankon bikin Amina, Mami ce ta bada a dinkamata. Har ta cika kwanakinta babu wata jituwa tsakaninta da Ihsan duk da ita Ummin bata dauki gaba da ita ba don duk wayewar gari sai ta gaisheta matsayin yar uwarta musulma, a dakile Ihsan ke amsawa.    Saida Mami ta soma biyawa da ita wajensu Hajja suka gaisa, har Hajja ta matsa akan sai ta kwana, dole ta barta anan ta yi musu kwana daya daman acewar Mamin, ya dace ta kwanarmusu, a wannan kwanan saida Hajja ta kara neman afuwar Ummi don shakka babu ta ji kunya musamman jin cewa Ummin na dauke da juna biyu, tabbas idan Rabo Ya Rantse to duk kiyayyarka da auren sai an yishi.      Ummi ta ji dadi ta nunamata babu komai, sun sha hira kwarai har da dariya da su Modibbo wanda ke jikinsa ya matsa mishi a yan kwanakin, washegari ta wuce gidan Hajiya Mama.     Nan ma ta ga kulawa da tarba mai kyau daga iyalan Hajiya Mama har ita kanta. Su Maryam kamar su hadiyeta.   Amina Amarya ta yi kyau ta gyaru tsaf, anan gidan zaayi yinin biki, kwarai Hajiya Mama ta yi musu kara. Acan gidan Innar Amina, yan uwan babansu ne na Nijar da na Innarsu anan Kano suka cika gidan. Amina ta sha mamaki jin cewa Malam Balarabe da kaninsa Baffa zasu zo daurin aurenta, ta hadata da Dada ta waya inda ta bata hakuri gami da nunamata ta so zuwa saidai bata samu dama ba, Amina ta nuna babu komai.      Da dare suna zaune a dakin su Maryam gaba daya suna hira da dariya, wayar Maryam ta yi k'ara, ta mike da sauri ta fita.    "Mene na gudun? Ai munsan mai kiran, Adnan ne."    Cewar Rukayya cikin daga murya. Amina da Ummi suka dara. Amina ta cafe. "Kai ke kuma ba'a sirri dake."    Dariya Rukayya ta yi. "Ai naga sai wani 6oye-6oye sukeyi kamar bamusan komai ba, gwara mu nunamusu mun d'agosu."   Ummi da mamaki ta ce. "Wai don Allah soyayya su ke yi?" "Ba ki da labari? Gaskiya Amina kinci amanar kauna da ba ki fesamata ba, ai kullum suna mak'ale da juna ta waya duk da wani 6oye-6oyen da sukeyi munsan komai, daidai da Hajiya Mama ta sani."   Ummi fara'arta ta karu. "Kai na ji dadi wallahi, Yaya Adnan ya yi dace kam, Maryam ba ruwanta halayenta na burgeni. Sun dace wallahi." "Karshe ma." Cewar Rukayya daidai lokacin da Maryam ta shigo ta mikawa Ummi wayar. "Ga Yaya Adnan ku gaisa." Ta kar6a tana tsuke baki. Ta yi sallama ya amsa gami da fadin. "Allah Ya kiyayemana ke ranki ya dad'e."    Ta hadiye dariyarta. "Ai ni na yi fushi Yaya Adnan, ka daina nemana kuma ko na kira layinka yanzu ba ya shiga." "Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun! Na ji kunya biyu. Na farko kirana da Yaya Adnan da ki ka yi, na biyun kuma, kiran da ban yi miki da sabon layina ba kasancewar wancan ya fad'i sai na barshi. Ki yi hakuri Ranki ya dade matar bestie."   Sukayi dariya a tare, ta girgiza kai. "Har abada, Yayana ne kai wallahi. To na hakura, ya fama da biro da takarda?"   "Gashinan sai kuyita tayamu da addua. Kinga surukarki ko? Ta yi ko akwai gyara?" Ta daga idanu ta dubi Maryam da su Rukayya ke tsokana ta yi dariya. "Ta yi 100%." Ya yi dariya cike da mamakin yanda tasan wani 100% domin ko kusa ba shi da labarin ana mata darussa. Saidai kuma bazai iya tambayarta ba.    "Yauwa Ranki ya dade, ai da kince akwai matsala tuni zan dakata." "Wace ni da fadin haka?" Suka dara kafin su yi sallama.   An soma bikin Amina lafiya, ana gobe daurin aure Malam Balarabe suka zo, sun sha hira da diyarsa har ya rasa inda zai sakata don tsabar farinciki. Ita ta yi musu jagora har wajen Inna don yi mata fatan alheri, wani abu ya darsu a zukatan tsoffin sadda suka yi arba da juna. Bayan an daura auren ne Malam Balarabe ya kasa jurewa har saida ya sanarwa Baffa kaninsa don daman ya samun labarin cewa yanzu Inna bata da aure, hakanan yana iya cewa tun bayan Hasiya babu wacce ya kara gani ya ji yana so ya karashe rayuwarsa da ita matsayin mata kamar Inna Bilkisu. Baffa ya ji dadi kwarai kuma zai so hakan. Abinka da batun manya nan suka tuntu6i babban Yayan Bilkisu, Mahmuda, nan ya nunamusu jin dadinsa a fili don kwarai ba ya son zaman kanwartasa haka babu aure duk da cewa ta aurar da yara biyu Fiddausi da Hauwa, sai Amina ta uku, ga kuma autanta Ahmad mai shekaru goma sha daya a yanzu, ya yi musu alk'awarin tuntu6ar Inna Bilkisu. A karshe sukayi musayar lambobin waya sannan a karshe sukayi sallama da kowa suka tafi, Ummi har hawaye ta yi don kewa, shi kuwa babanta dadin yanayin da ya ganta ya ji don ta yi k'iba ta kara kyau.     Inna ta ji lamarin banbarakwai duk kuwa da cewa a ganin farko da ta yiwa Malam Balarabe ya kwantamata, ba musu ta amince da hakan. Nan ya kira ya shaidamusu, basu yi wata wata ba suka sanarwa iyayensu, Malam ya ji dadi haka ma Dada wacce ke tausayawa dan nata. Aka tsaida magana nan da sati biyu za'a je a daura aure.    Su Anti Hauwa sun ji abin banbarakwai, wai Innarsu aure. Tun basu ji ko waye mijin ba suka nuna rashin goyon bayansu, acewarsu da shekarunta na arba'in da takwas me ya ragemata banda ibada? A bakin matar Kawunnasu suka ji waye manemin auren, hankalinsu ya kwanta suka ji dadi, kusan Amina ta fisu jin dadin lamarin don a take ta bugawa Ummi wacce ke shirin komawa Abuja.     "Albishirinki." Ummi ta ware ido. "Goro fari k'al Antina."   "Inna zata zama matar Babanmu." Cikin rashin fahimta ta ce. "Anti inace kin cemin Baba ya rasu." Ta ja tsaki. "Dallah can, babanmu fa na Gombe." Daskarewa ta yi a tsaye ta bar ninke kayan. Ita abin kamar mafarki haka ta jishi.  "Ke ya ki ka yi shiru, wallahi dagaske ne." Tiryan-tiryan ta labartamata abinda ta ji. Hawaye kawai Ummi ta shiga fitarwa tana kara jin kaunar Amina da yan uwanta. Banda hamdala babu abinda ta dunga nanatawa a fili.     Bayan komawarta Abuja ta sanarwa Faruk wanda shima ya ji dadi ainun, ya sanyawa lamarin albarka. Kowa ya ji sai ya sanya albarka ciki. Koda ta kira mahaifinta, dariya kawai ya yi ya ce. "Lamarin Allah kenan Hasiya, a tayamu addua." Farinciki fal cikin ranta haka suka sha hira suka yi sallama.                 ***    ***    ***         BAYAN WATANNI BIYAR Ayau ake bikin yaye su Ikram daga sakandire, acan Kano ma su Ihsan na nasu shagalin don lokaci guda aka yi bikin yayesu.     Duk yayyun Ikram sun je mata banda Baraka dake wankan jego ta haifi danta namiji wanda ya ci sunan mahaifin Mijinta suke kiransa da Abulkhair. Ummi ma da cikinta dan wata bakwai katon gaske haka ta zo. Fuskarta duk ta chanja, tana sanye da wata tsadaddiyar abaya Faruk na rike da hannunta.      Ikram duk bata tare da walwala sai lek'e-lek'en wuya ta ke faman yi.  "Wai me ki ke nema haka?" Cewar Fadila wacce ta kasa shiru. Ikram ta dubeta, kafin ta yi magana suka ji sallama a gefensu duk suka waiga, mamaki karara ya bayyana a fuskokinsu.    Yana sanye da doguwar riga da wando na shadda dark green wacce ta sha aiki, ya dora hula mai fari da koren din sak'a, ya yi kyau kuma ta haskakashi ainun. Sai murmushi ya ke faman dokawa.   "Yaya Gidado?" Ummi ta furta da tsantsar mamaki kafin kuma ta saki fara'a sosai.  Ya bita da murmushi kafin ya karasa ya soma mikawa Mazajen Hajiya Babba hannu suna gaisawa. Suma sun saki fuskokinsu, Fadila da Jidda suka yi turus suna kallon ikon Allah, sun kuwa gane waye shi amman idan ka ganshi saika rantse ba daga kauyen Jar Kwami ya fito ba tsabar iya daukar wanka.    Ikram ta kasa rufe baki, zuciyarta na kara nutsawa cikin kogin so da kaunarsa, babban abinda yasa ta ke kwadayi da mafarkin zuwan wannan ranar kenan don kuwa ya bata tabbacin zai zo mata da kyakkyawan albishir duk ranar da ta yi Candy. Toh yau ga ranar ta zo.      "Ashe kana tafe ba ka sanarmana ba mu yi maka kyakkawan tarba?"   Cewar Faruk cikin sakin fuska. Gidado ya danyi dariya. "A yi hakuri surukina, ai gani yanzu ma bata 6aci ba."   "Lallai kam, saidai kamar zuwan ba namu bane na kanwarmu ne ko?." Cewar Haidar wanda ya riga yasan dawan garin daga Intisar., ya fada yana duban Ikram.    Suka yi dariya, kunya ta kama Ikram. "Eh to, kusan hakan."   Cewar Gidado, shi kuwa babban Yaya da Ridwan mamaki sukayi don basu zata ba , hakanan Faruk shi kansa bai ji daga matarsa ba. Ya dan matse hannunta ta yi karamin kara.    "Shine ko ki gayamin?" Ta waro ido. "Babu wani abu fa tsakaninsu." Murmushi kawai ya yi.   Har aka tashi taron Gidado bai samu ke6ewa da Ikram ba sai bayan sun koma gida, bayan ya gaisa da su Hajiya suka ke6e da ita a dakin bak'i.  Ya fiddo wani akwati daga aljihunsa ya mik'amata. "Ga kyautar da na zo miki da ita, ki yi hakuri babu yawa.". Ta kar6a tana washe baki. "A wajenka ne babu yawa." Sukayi dariya.    "Ba za ki bini bashin zance ba Ikram, yau zan sanarmiki abinda ban ta6a sanarmiki ba. Haka kuma zan cika alkawarin da na daukar miki."   Ta lumshe idanu ta budesu. "Ina jinka Yayana."   Shiru ya dan biyo baya kafin ya cigaba da magana. "Karambanin so ke neman kaini inda aka fi karfina, duk iya kokarin da na yi na dannewa da kaucewa faruwar hakan, saidai ya gagara, bazan iya hana Allah zartar da hukuncinSa, ban isa ba ban kuma kai ba. Wallahi na kamu da sonki Ikram, so na gaskiya, a rayuwa ban ta6a zaton zan kara son wata diya nace ba bayan Hafsa, amma cikin ikon Allah da sannu-sannu kyawawan d'abi'unki da kuma hakurinki suka rinjayi zuciyata na afka cikin kogin son wacce ta fi karfin dan kauyen Jar Kwami."   Ta kasa motsi, ta kasa gaskatawa, ta kuma kasa tantance hakikanin yanayin da zuciyarta ta fada. Kallonsa kawai ta ke tamkar wata doluwa. Ya kai yatsa kamar zai tsone idonnata ta yi saurin lumshewa, sai kuma ta yi kasa da kai tana murmushi.    "Wannan kallon fa ya tsoratani, ko ba'a sona?" Ya fada don jin ta bakinta kawai bawai don baisan cewar tana sonsa ba.     "Bance ba, saidai na yi mamaki ne kawai ace kamar ka kana sona?"   "Kina neman ki ce kinfi karfina ko?" Ya fada a raunane. Ta yi saurin girgiza kai kamar mai shirin kuka ta ce. "Wallahi aa, ni don Allah ka daina bambanta kanka da ni, kaima cikakken DAN ADAM ne mai daraja, ina girmamaka hakanan ina sonka tsakani da Allah."     Ya murmusa gami da sunkuyowa saitin fuskarta cikin muryar rada.   "Za ki iya zaman aure da ni a Jar Kwami?"    Ta lumshe idanu gabanta na bugu da sauri-sauri.   "Yayana ba Jar Kwami ba, koda cikin daji ka ke rayuwa wallahi zan iya binka muyi zaman aure, ina sonka fa." Ta karashe kamar za ta yi kuka, ai kuwa hawayen da ta ke makalewa suka kwaranyo.    "Komai na Allah ne." Ta tuna furucin Ummi gareta a watarana da ta je gidanta da korafin yanda ta ke kara jin son Gidado a ranta kamar ta mutu.     "Idan Allah Ya kaddaro mijinki ne, za ku yi aure." Fadin Intisar a watarana suna hira ta ke kokawa bisa yanda Gidado kan share kwanaki ba ya nemanta koda ta waya sai idan ta nemeshi.   "Na gaji da jin maganar Gidadon nan, don Allah ki hakura ki fiddashi cikin ranki, idan mijinki ne fa sai kunyi aurennan ko ba ya so." Cewar Hajiya a wataran da ta risketa tana kukan yanda ya ke yawan yi mata hirar matarsa wanda batasani ba wani zubin da gayya ya ke yi don kawai ya gwada ko tana kishinsa.   Ta share hawayenta. Gidado zaune ya cigaba da fayyacemata irin son da ya ke mata ya kuma tabbatarmata ba da wasa ya zo ba, sonta ya ke yi tsakaninsa da Allah. Koda ta yi mishi batun Hafsa, ya nunamata wannan ba matsala bace, matarsa nada saukin kai tana son abinda ya ke so.  Ranar saida ta yi nafilfilu don nuna godiyarta ga Ubangiji. Daidai da Hajiya ta taya diyarta murna hakanan duk wani masoyinta da yasan tana son Gidado, ko Ihsan ma ta dan ji sanyi ganewar ba yar uwarta kadai ke wahala ba, ashe shima yana so.    "Allah Ya ba ki sa'a." Shine kawai abinda Jidda ta fadi.     Ita kuwa bata biyemusu ba don ta gane yan adawa ne.                 Kamar wasa, aka tsayar da maganar auren Ikram da Gidado wanda takanas iyayensa suka zo Abuja nema mishi bayan an samu an shawo kan Hafsa dakyar wacce ta dage akan saita bar gidan Gidado ta ya ya zai hadata kishi da wayayyiya kamar Ikram? Acewarta wannan cutarwa ce, da dai ya auri Ikram gwara ya auromata yar kauyen Jar Kwami irinta sun zauna.     Wasu cikin yan uwa suka goyi bayanta wasu kuwa ba su goya ba, hakanan a cikin dangin Gen. Ahmad Danzaki, wasu da yawa basu amince ba, acewarsu Ikram ba zata iya rayuwa a kauye ba da kuma dan kauye, ita kuwa ta dage lallai sai Gidado, to Daddy shima ya goyamaya baya ko babu komai autarsa ce yana ji da ita. Haka aka tsaida auren Ikram da Gidado wata uku ba da son ran wasu ba.       Aka shiga shirye-shiryen bikin Abubakar da Ihsan, sai Iklima da Musaddik, mijin da Abba ya za6ar mata akayi sa'a sun hada kansu, da kuma kanwarsu Hassana da Abdullatif.     Biki ya yi biki, dukkan yan uwa sun iso Kano, ciki harda KB wanda ya zo hutu daga Ghana, gaba daya ya chanja ya zamo na kirki kamar ba shi ba. Ummi ce ta samu dakyar Faruk ya amince da zuwanta, acewarsa cikinta ya tsufa babu yawo....!     Ansha shagalin biki su Abida da sauran yan uwan Gombe na Jar Kwami duk sun hallara. Sai nan nan Hajiya Salma ke yi da Ummi, hakanan duk motsi da zata yi sai an tambayi ko akwai wata matsala.     Tana zaune ta sanya kayan ankon Party a gaba tana kumbure-kumburen fuska, Ikram ta dubeta. "Allah Sarki Antina, yanzu shikenan ba za ki je ba?"   Dariya su ka sanya gaba daya wanda ya kara k'ular da ita.    "Tana gani zamu wuce amma ba inda za ta je tunda Oga ya hana." Cewar Baraka kenan.  "Ke banda abinki, kina fama da wannan katon ciki haihuwar yau ko gobe ina ke ina wani dinner party?"   Ta yi narai-narai da fuska. "Nasan da wanda zan hadashi ai, bari na kira Yayana." Sukayi dariya, ta kira Abubakar. "Innota ya akayi na ji muryarki na rawa?"   Daman kiris ta ke jira kawai ta soma kuka.  "Innalillahi wa Inna ilaihirraajiun, me akayi? Kinga kina ina yanzu?" "Dakin Ihsan." "Ok ina zuwa." Ya katse kiran Faruk dake zaune gefensa a benci ya dubeshi. "Me ya samu Innontaka?" "Bari na je na gani." Ya bi bayansa da kallo kafin ya ta6e baki don yasan zancen bai wuce na party ba.   DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 128 Suna daga dakin suka ji falon ya dauka ga Ango ga Ango, da mamaki Baraka ta ce. "Eh lallai yar gatan yayanta, kiga har ya shigo."    Ihsan wacce bata jima da shigowa dakin ba batasan me akeyi ba, sai ganin Abubakar ta yi ya shigo. Tana zaune saidai ban ma lura da ita ba ya yi wajen kanwarsa. Itama tana ganinsa ta kara turo baki tana murmurza idanuwa.    "Ya Salam, meyafaru ne wai kanwata? Hankalina ya tashi wallahi."   Ganin yanda duk ya rude yasa ta dan sassauta fuskarta, fuska ba walwala ta ce.   "Ba shine ya ce wai bazan je dinner party ba."   Ya dan runtse ido gami da numfasawa, hankalinsa ya dan kwanta.   "Inji wa? Ai ya zama dole ku je don kafarki kafata. Barni da shi, kedai ki tabbatar kin shirya kinji ko?"   "Yanzu bayanta za ka goya? Da wannan tulelan cikin ina ita ina wata dinner?" Cewar Rahila yayar Ihsan.   Ya dan harareta don sun saba wasa da dariya.   "Ina ruwanki to? Zuwa kuma ai ta yishi ta gama, atoh."   Dariya sukayi banda Ihsan da ta k'ulu ganin kamar baisan da ita wajen ba.   "Idan kaine mijinta ma ji ma gani." Ta kara fadi cikin dariya.    "Shima a tafin hannuna ya ke, surukai muke."   Daga haka ya fice suna mishi tsiya. Ihsan jikinta ya yi sanyi, wane irin Ango ne mai fifita wata akan matarsa? Haushi ya cika zuciyarta saidai dole ta danne ta mike bisa umarnin Aisha wacce ta shigo kiranta zuwa kwalliya don Magriba ta gabato kuma ana sallar Isha zaa wuce.      Ya murza karan hancinsa gami da dora kafa daya kan daya kamar wani basarake yana dubansa. "Ka ce me?" Abubakar ya harareshi. "Na ce idan Inno ba zata je ba to fa nima babu inda zanje, kafarta k'afata." Wani murmushi mai burgewa Faruk ya yi kafin ya dubeshi. "Shikenan, ai ba kai kadai ne Angon ba, sai muje mu sha shagalinmu." Dariya su Haidar da Kb su ka yi don duk gaba daya suna zaune a babban falon na bak'i.    Abubakar cikin dariyar ya amsa. "Kafata kafarta fa Malam, ai ba yawo za ta yi ba, wuri daya zata zauna."   Baki Faruk ya ta6e baice uffan ba, yana ji Abubakar ya dauki waya ya kira Ummi gami da kara jaddadamata cewa ta shirya zuwa babu fashi don ya amince.     Ya kalleshi kawai ya kauda kai kawai.      Haka har aka tashi tafiya, idan kaga Amarennan saika k'ara kallonsu tsabar haduwar da sukayi domin kuwa wani arnen leshi suka sanya fari da silver ya zauna das a jikinsu., su kuwa Angwayen farin shadda k'al mai surfani ruwan toka suka sanya. Saura kuwa suka yi ankon bulun french lace mai ratsin ruwan toka sai silver head, yayinda tawagar samarin suka hade cikin (Sky blue)shadda, sunyi kyau har sun gaji da haduwa.  Kowa ya shirya tsaf harda Ummi, ita buba ta yi na zani sannan ta dora mayafi ruwan toka-toka, ta yi kyau duk da cewa ta ajiye kumatu ga chanjin fuska da jiki sakamakon ciki.     Aka soma fita itama ta fito, Mami ta kama ha6a. "Harda ke Ummi?" Hakan yasa sauran iyayen suka dubeta. Ta yi murmushi. "Eh Mami."   "To ki bi a hankali banda tsalle-tsalle don Allah ki zauna wuri daya."   Fadin Hajiya Mama kenan don wannan karon banda manyan iyaye a zuwa. Da haka Ummi ta fita ta na cigaba da gwada kiran Faruk wanda ya kashe wayoyinsa kaf. Takaici ya isheta, a waje ta tsaya tana waige-waige, motoci masu tsada sun cika farfajiyar gidan wasu kuwa da basu samu shigowa ba suna daga waje, to biki ne bana mutum daya ba, Hajiya Lubna itama yan uwanta na Maiduguri sunzo da yawa don bata ta6a aurar da diya ba, hakanan Hajiya Binta wacce rabin yan uwanta a Kano suke, su dinma duk hallara.    Tana nan tsaye anata tafiya ta hango Gidado na kokarin shiga mota da sauri ta karasa gareshi. "Yaya Gidado." Ya waigi, yana ganinta ya karaso ya cimmata ganin yanda ta ke tafiya da sauri.   "Yi a hankali mana Ummi, za ki je dinne?"   Ta gyada kai gami da yin narai-narai da fuska.    "Eh, ina Yaya Faruk?"   Ya yi murmushi.  "Yana kofar gida amma nasan yanzu sun wuce, taho mu tafi kawai."    Ba musu ta bi bayansa, kafin ta kai ga shiga wayarta ta dauki k'ara, Abubakar ne. Ya tambayeta ko tana ina, ta sanarmishi gatanan za ta bi Gidado, ya ce ta jira tare zasu wuce. Ta amsa da toh gabanta na faduwa, kada fa ya zamana Faruk bai yi na'am da zuwannata bane, to amman ai Abubakar bazai mata karya ba tunda ya ce ya amince ta je.    Aikuwa motar Ango da Amarya ta hau, gidan gaba ta zauna, Kb ne matuk'in Abubakar da Ihsan. Ihsan ta ci magani ganin Ummi k'ame a gaban mota, har akaje ba ta ce uffan ba sai kuwa Abubakar da Kb ke kwasar hirarsu, jefi-jefi sukan sanyo Ummi da Ihsan, motocin Amare a jere haja suka isa.     Gaban Ummi ya fadi ganin Faruk zaune saman mota a farfajiyar wajen tare da Jafar abokin aikinsa suna hira. Ya yi kyau har ya gaji da haduwa. Tun shigowar motocin idanunsa suka hangomishi matarsa a gefen mutumin da har gobe bai mance abinda ya so aikatawa ga iyalinsa ba, wato Kb. Wani abu ya soki kirjinsa, kishi mai tsanani ya turnuk'eshi x ya dauke kai fuskarsa kamar an aikomishi sak'on mutuwa, wannan ba karamin firgita yan hanjin cikin Ummi ya yi ba, ta hau karanto adduo'i cikin ranta har motar ta daidaita fakin, har Amarya da Ango saida suka rigata fita, sannan a karshe ta daure ta bude mota ta fito, nan masu hoto suka yi musu ca, da sauri ta samu ta bar wajen ta nufi wajen mijinta, saidai babu shi babu dalilinsa, can ta hangeshi wajen Angwaye suna gaisawa da Abokai, jiki a sanyaye ta koma ta shiga ciki, saidai me? Zaman namiji da mace ne, ga mai aure da matarsa, marar aure kuwa budurwarsa. Intisar ana k'ame gefen Haidar, hakanan su Jidda, ta yi shiru ta kasa karasawa ciki dole ta juya da zummar fita saidai ta ji an riko hannunta. Da sauri ta dago kanta, Faruk ne saidai fuskarnan tasa babu digon walwala ya ja hannunta zuwa ciki, ta kasa cewa uffan ga uban tsoro da ya cikata kamar ta saki fitsari a wando, ya dan saki fuska gudun kada a dagosu, itama ganin haka ta saki nata. Haka suka karasa mazauninsu kusa da su Ridwan.    "Madam daga nan sai Asibiti ko?" Cewar Ridwan cikin zolaya. Murmushi kawai ta yi.  "Kema dai Ummi, ai da kin hakura kin zauna gida." Fadila wacce ta sauko yanzu ta fada da murmushi saman fuskarta.     "Ina zata zauna wata ta yi mata kwace? Da gaskiyarta ai."   Haidar ya fada yana yar dariya, hakan yasa Ummi fadada fara'arta wanda duk yak'e ne ganin gogannata bai wani sakarmata ba, sai murmushi da ya ke wanda ya zamto yak'e.     "Au Madam ashe kinga ogannaki ina can ina nemanki naga kamar ba ki shigo ba." Suka tsinci muryar Kb daga gefe, ta yi yar dariyar yak'e tana fargabar abinda zai biyo bayan amsawarta.     "Um, na shigo yanzu." "Yauwa." Daga haka ya maida akalar hirar da Haidar dake tambayarsa ko da wa zai zauna.  Ya nunamishi wata cikin kawayen Ihsan wacce a ganin farko ta kwantamishi.      Can kuwa Gidado na tare da Ikram kamar su hadiye juna don so. Party ne na yan boko, komai bisa tsari aka yishi, ba'ayi wani raye-raye sosai ba, sai ko (step-dance) da dangin Ango Abdullatif suka shirya suka yi wanda ya k'ayatar sosai.       Anci an sha, an kuma yiwa Angwaye da Amare lik'i kwarai.     Kafin akai ga tashi ta soma buga uban hamma don ta gaji ga bacci dake cinta, ta dubi Faruk da hankali kwance ya ke kur6ar lemu abinsa, lokacin su kadai ne saman tebur su Babban Yaya da sauransu an tafi daukar hoto.    "FAR HAS na gaji wallahi bacci nake ji." Ko kallo bata isheshi ba, kamar ba da shi ta ke magana ba haka ya nuna. Jikinta ya kara sanyi, ta lalubo hannunsa na dama ta matse cikin nata.    "Don Allah ka yi hakuri na yi maka lai..." Kallon da ya watsamata ne yasa ta hadiye maganarta babu shiri, har lokacin hangota ya ke zaune kusa da Kb a mota.  Ya zare hannunsa cikin nata.    "Ai ba ni na kawoki ba, ki nemi wanda ya yi miki iznin zuwa da wanda ya kwasoki a motarsa har ku ke hira da dariya su yafi dacewa ki je su maidaki."    Hawayen da ta ke rikewa suka zubo. "Amma Yaya Abubakar cemin ya yi ka amince."   "Tunda shi ki ke aure ai ya miki izni kin zo, shikenan kuma, komawa kuma ni ba yanzu zan tafi ba sai na gama abinda ya kawoni." Daga haka ya mike ya soma tafiya a kasaitance, tafiya mai cike da aji, babu budurwa da bata kyasa ba, ya wuce gurin Angwaye, yana zuwa ya fiddo rafar yan dubu-dubu ya hau lik'i. Nan wuri ya chanja, kida ya chanja, Mai wak'a ya tambayi sunansa aka sanarmishi habawa tuni ya hau wak'eshi yana mishi kirari da yayan Amare kuma Abokin Angwaye.     Ummi hawaye ta ke na bakinciki da tsananin kishin yanda yan mata ke faman zubamishi lik'i shima, ji ta ke kamar ta dora hannu akai ta kwara ihu, ga bakincikin fushin da ya ke da ita, ga kuma na kishin mijinta. Mamaki ta ke na yanda yau bai damu da zubar hawayenta ba. Mikewa ta yi jiki a sanyaye, ji ta yi fatin ya fice a ranta, ita kuwa ko tasi ne zata hau ya maidata gida da dai ta zauna ta shak'i wannan kayan takaici. Tana jinta wani iri, Faruk bai kamata ace ta bak'anta mishi rai haka ba, idan da alk'awari sam Faruk bai kyautu ta musgunawa zuciyarsa ba, ya cancanci komai daga gareta. Haka ta ke faman tunani har ta fito farfajiyar dakin taron. Nan kuma ta shiga rarraba idanu, to ina zata nufa? Waya ta ciro da zummar kiran Abubakar sai ta tuna abinda Faruk ya ce kawai ta fasa, ta maida wayar jaka ta soma tafiya tana fatan ganin direban gidan su Mami ko Hajiya Mama don ya maidata gida, saidai akwai mutane da motoci sosai babu damar gane hakan. Takalmin yana da tudu, ya isheta, hakan yasa ta zuwa daidai motar Haidar ta tsaya gamicireshi sannan ta soma kokarin dauka, saidai durkuso ya yi wuya agareta, ta kara kokarin durkusawa ta ji an rike kafadarta, a razane ta dubeshi, Faruk ne, ya durkusa ya dauki takalmin ya rike mata, kai tsaye ya wuce ya bude motarsa ya tayar, ya yo ribas ya saita kafin ya budemata gidan gaba. Sauke gilashin motar ya yi yana dubanta batare da ya ce uffan ba. Hawayenta suka zubo ta soma tafiya, ya kuramata idanu cike da tausayi, tabbas ya kula a gajiye ta ke, abinda ya gujemata kenan shine babban dalilinsa na dagewa kan ba zata zo ganin anyi kamu anyi yini duk tana faman zirga-zirga. Ta shigo ta zauna ta rufe kofar, ya soma ja a sannu-sannu har suka fita, saida ya hau titi kafin ya dan k'ara gudu. Ta dubeshi saidai ta kasa magana, a hankali ta soma kuka sosai harda sheshsheka, duk yanda yaso ya basar, ya kasa, dole ya sauka daga saman titi ya yi fakin a gefe. Dubanta ya yi na yan mintoci kafin ya soma magana cikin sanyin murya. "Meyafaru kuma?" Ta dan matso kadan ta dora kanta saman kafadarsa gami da rungume hannun gam.    "Don Allah FAR HAS ka yafemin, na fito bada izninka ba kuma na yi abinda kishinka ya motsa, don Allah ka yi hakuri."   Wani so da tsantsar tausayinta ya cikashi, shima yana cikin dakin taron ya dawo daga lik'i ya ga batanan hakan yasa shi fitowa a rude, karshe ya hangeta jikin mota. Ta ya ya zai iya fushi mai tsawo da Umminsa? Ya sanya hannunsa na hagu ya dafa kanta.  "Kinmin laifi Ummina, saidai duk iyakar laifin da za kimin bazan iya rabuwa da ke ba saidai wata kaddarar da bana fatan ta rabamu idan har ba mutuwa dayanmu ya yi ba, ina kishinki Ummi musamman da Kb wanda ya kusan cin rabona."   Ta dago kanta cikin marairaicewa ta ce. "To ka yi hakuri bazan k'ara ba." Murmushi ya yi ya ka karan hancinta. "Haka ake bada hakuri?"  Ta yi murmushi. "A hanya muke fa." Ya share mata fuskar. "Muje ki huta, daman nasan bebina bazai jure wannan Dinner ba shiyasa na hana ki zo amman Abubakar ya nunamin ke yar uwarsa ce." Ya karashe da dariya, ta tayashi kawai. Haka ya cigaba da tafiya, ta koma kujerarta ya kwantar mata da kujerar kadan ta yi filo da hannunta tana dubansa yana tuk'i, a haka bacci ya yi awon gaba da ita don sosai ta ke jinsa.    A waya Faruk ya sanarwa Abubakar sun taho Ummi ta gaji don ba wanda ya sani. Koda ya yi fakin, saida ya karemata kallo don ba don baccin ta ke ji ba da bai ci ace ta yi ba don tafiyar ba wata tafiya ce sosai ba. Ya shafi gefen fuskarta, hakan ya sanyata bude idanunta. Kyakkyawan murmushi ya jefeta da shi. "Mun iso."   Ta mike, ya zagayo ya budemata, da taimakonsa ta zura takalmi ya rike fos dinta suka shiga ciki. A falon Mami duk an ragu babu kowa, wasu sun yi bacci, har daki ya kaita, nan ma yaran su Jidda ne duk sun yi bacci, ya dubeta. "Ko za ki dakin Fahad? Kinga nan ma a cike."   Ta dubeshi ta girgiza kai. "Aa zan kwanta gefensu karka damu." Bai bar dakin ba saida ya tabbatar ta rage kayan jikinta ta chanja zuwa na bacci ta kwanta, ya sumbaci goshinta. "Goodnight." Ta lumshe idanu tana murmushi. "Kaima ka kwanta fa." "Aa, zan koma wajen budurwata." Ya fada a wasance, ta kai mishi bugu a kirji sukayi dariya.  "Bakasan na ji haushin yanmatan nan masu yi maka lik'i ba ko?" Ya ja karan hancinta. "Na fiki kishi Madam, karki damu ke kadai zuciyata ke so da kauna. Oya kwanta." Ta muskutawa ya rufeta, sannan ya kashe musu fitila ya fice, Allah Ya taimakeshi babu wanda ya ganshi balle tsoffin su ce ya yi rashin ta ido....!   Washegari da safe ya koma bakin aikinsa Abuja, a ranar aka kai Amaren biyu, Iklima da Hassana, ita kuwa Ihsan Adamawa zasu wuce washegari.    Bayan Magriba Mami ta yi kiran Ihsan da Ummi zuwa sashen Abba ta rufe don samun damar yin maganar da ta ke so....! DAN ADAM @RUFAIDA OMAR 129-130 Kowaccensu ta yi shiru tana mamakin wannan kiran, Ummi zata zauna k'asa Mami ta nunamata kujera. "Zauna nan Ummi kada ki takura." Ba musu ta zauna kujerar da ke fuskantar Mamin hakanab Ihsan ta zauna gefenta saidai nesa da ita. Tsaf Mami na lura da yanda Ihsan ke faman cin magani, ta numfasa ranta babu dadi kafin ta soma magana.     "Abinda yasa na nemi da na ganku bai wuce fahimtar irin rashin jituwar da ke tsakaninku ba har zuwa wannan lokacin da ya ci ace komai da ku ka sanyawa zuciyoyinku ya kau. Matsalar ba daga Ummu ta ke ba sai daga ke." Ta nuna Ihsan wacce ta kara tamke fuska.     "Na lura kin sanyawa ranki kiyayya, muguwar kiyayya ta Ummi alhalin banga wani mugun abu da ta ta6a yi miki ba har ta cancanci hakan. Ihsan kina wasa da addininki, wannan ba d'abi'ar musulmin kwarai bane, ina mamakinki, ba ki da rik'o akan kowa sai akan Ummi, yarinyar da gatanan zan shaidi cewa takan yi kokari matuk'a wajen kulaki saidai ba za ki amsamata ba, ko sau daya ban ta6a ganin kin bita da kallon arziki ba. Anya kina son gamawa da duniya lafiya?"   A razane Ihsan ta dubi mahaifiyarta har idanunta sun ciko da ruwan hawaye saidai ta kasa cewa uffan. Mami ta jinjina kai cikin tabbatarwa. "Hakika wannan hali ba inda zai kai ki a rayuwa, ke duk abinda ya faru bai zame miki ishara ba? Ni na haifeki, ni nasan halinki saidai ban ta6a saninki da nunawa mutum kiyayya ba sai akan Ummi."   "Ni Mami me ta yimin da zan k'i ta?" Ta fada cikin rawar murya idanunta cike da ruwan hawaye. A fusace Mami ta ke dubanta, Ummi ta dubi Ihsan kadan saidai ba ta ce uffan ba ta maida kanta k'asa.     "Shi nakeson a yau ki bude zuciyarki ki sanarmin, me Ummi ta yi miki ki ke k'in sakin jiki da ita kamar yanda sauran yan uwanki ke yi? Ko kinsan cewa nasha kamaki kin harararta? Fuskarki na nuni da tsantsar kiyayya gareta koyaushe. Annabinmu s.a.w ya hanemu da zurfafa kiyayya ga dan uwa musulmi.    Abu hurayrah ya ruwaito Annabi SAW ya ce "Na rantse da wanda raina ke hannunsa mutum ba zai shiga aljanna ba har sai ya mika wuya,  sannan ba zaka mika wuya ba har sai kunso junanku. Ku yaɗa alkhairi zaku so junanku. Sannan ku guji kiyayya don kaifi gare ta,  bance yana aske gashi ba amma yana aske addini." Wannan kadai bai isheki hujjar da za ki yi watsi da makamanki ki rik'i Ummi yar uwa ba?       Mami ta cigaba da magana, ta inda ta shiga ba tanan ta ke fita ba har yanda ta fusata ya tayarwa Ihsan da Ummi hankali, musamman ma Ihsan wacce ke son mahaifiyarta ta sosai, kokadan batason abinda zai 6ata ranta, kuka sosai ta ke yi, ta mike ta nufi wajenta ta durkusa gami da riko hannunta. "Ki gafartamin Mami, wallahi na daina, zan riki Ummi duk yanda ki ke so, Ummi don Allah ki yafemin abubuwan da na aikata gareki, bazan k'ara ba in sha Allah." Ummi ta share hawayenta tana murmushi a hankali ta mike ta tako har wajen da suke, zama ta yi gami da riko hannayen Ihsan. "Ban ta6a rikeki a raina ba daidai da rana daya, na yafemiki tun kafin ki rok'a, karki damu, nima ki gafartamin idan akwai abinda na yi miki da bansani ba."   Kunya ta rufe Ihsan, ta sauke kanta jiki a sanyaye. "Ba abinda kikamin, idan ma kin yi to na yafemiki duniya da lahira." Mami murmushi kawai ta ke yi, ko babu komai tana alfahari da Ihsan a fagen jin maganarta, da wuya ta sa6a umarninta.    Ta riko hannuwansu ta sanya cikin na juna. "Allah Ya muku albarka, Ya kara hada kanku."   Ummi da Ihsan suka dubi juna suka yi murmushi alokacin da suka amsa da amin.     Tun daga wannan lokacin, suka dinke, idan ana zaune ana hira, Ihsan ta daina barin wajen idan ta ga Ummi, har takan tsokani Ummi cewa ita fa yayarta ce yanzu. Ummi dariya ta yi saboda rashin sabo da hakan daga gareta.     Su Intisar gaba daya sunyi mamaki. "Ko kefa." Cewar Aisha yayar Ihsan a saitin kunnenta, ta dubeta kawai suka yi murmushi. Hatta Amina, saida Ummi ta kira a wayar ta sanarmata batun shirinsu don ranar yini kawai ta zo wanda shima Bellon dakyar ya amince don acewarsa bai isa ace ta soma fita ba.      Babu wanda bai yi murna da shirin Ihsan da Ummi ba.    "Wallahi kinsan me Ikram? Yanzu jin zuciyata nake wasai babu ko digon damuwa, ashe kiyayya babu dadi? Ni sai yanzu ma na ke kara fahimtar Ummi mutum ce, halayenta abin so da sha'awa." Abinda Ihsan ta fadawa Ikram kenan sadda suka shigo falon Mami bayan ta raka Ihsan din wajen mijinta da ya bukaci ganinta. Ikram murmushi ta yi. "Kwata-kwata gaba bata yi ba ai, Allah Ya k'ara nisantamu daga shaidan."   "Amin."   Washegari aka yi shirin tafiya Adamawa tun karfe takwas na safiya, Ihsan nan ta shiga kuka sosai dakyar aka 6an6areta daga jikin Maminta, nan kuma ta kama hannun Fahad gam ta rike, shi kansa kuka ya ke kasancewar sun shaku da ita.     "Ya kamata ki samarwa Fahad k'ani." Mami ta tuno furucin Mijinta a daren jiya, kwarai da zata kara haihuwa tasan ba karamin dadi zaiji ba, saidai kuma likita ya tabbatar mata cewa tsarin iyali na shan magunguna da ta yi ya janyomata matsala a mahaifa, abu ne mai wuya ta kara haihuwa sai ikon Allah, ya yi mata wannan bayanin ne sadda ta ga 6atan watanta kwanakin baya da har Hajiya Mama ta shawarceta da zuwa ganin likita ko ciki ne da ita.    Kwarai ta yi da na sanin yin tsarin iyali musamman ma da ya kasance ba da iznin mijinta ba.      Haka kukanta ya kasance biyu, da jimamin rabuwa da diyarta wacce kusan tafi kaunarta duk a yarannata idan an cire Adnan wanda Abban ke so sosai, sun shaku da ita yau ga aure ya raba.    Aka wuce gaba daya har su Hajiya Babba, Ummi kuwa a ranar suka wuce da su Jidda zuwa Abuja.                   ***    ***    ***   A farkon zamantakewar Ihsan da Badiyya, sun sami matsala na kishi, saidai da ikon Allah komai ya zo ya wuce suke zamansu lafiya, ga Abubakar ya na takatsantsan sosai don ya rage kula yanmata musamman da ya ke 6arje Angoncinsa, hakanan ya rage hira a waya a gaban matansa gudun 6atawa wata cikinsu, yanmatan ma duk sai ya ke ji suna ba shi haushi, watan Ihsan biyu a gidan, ta samu ciki, murna wajen iyayen Abubakar ba a magana, shi kansa har kuka ya yi don tsananin farinciki. Ya zamana hankalinsa kacokam ya koma ga kula da Ihsan, Badiyya ta shiga tashin hankali matuka saidai ta yi jarumtar 6oyewa bata nuna ba. Da ita aka hadu aka yi ta kula da Ihsan.                     Ummi cikinta ya shiga tara cif, a wannan lokacin sosai an soma shirye-shiryen bikin Ikram da Gidado, bata fita ko'ina banda asibiti, wataran kuwa ya kwasheta ya kaita gidan Hajiya ta wuni, komai ba bukatar mace da danta na haihuwa Faruk ya siya ya ajiye, haka itama kamar yanda aka Jidda ta yi mata bayani, ta sanya dukkan abin bukata na ranar farko ga macen da ta haihu cikin karamin akwati. Bata da aiki sai adduoi, da kallon kayan bebi, yau ma tana zaune saman gado ta bararraje tana kallon kayan jariran da Faruk ya siyo duk kuwa da cewar dauriya ce ta ke yi sakamakon mararta dake dan murdawa, Batula na aikin jera wasu cikin 'yar kwaba na saka kayan yara da Faruk ya siyo. Ta juyo gami da sakin murmushi  "Kai Anti, kullum idan Yaya ya siyo kaya sai kinyi zaman kallonsu." Ummi ta numfasa tana dariya. "Bari kawai Batula, wallahi idan ina kallon kayan sai na ji son bebi na k'ara shiga raina ne, yanzun ma ba ki ji yanda na ke ji ba, Allah dai Ya rabamu lafiya."    "Amin Anti." Fadin Batula cikin dariya.    Suka kammala hada komai suka maida duk Batula ce karfin aikin, ta mike saman gadon.   "Bari na kwanta ko ciwon marar nan zai yi sauki, inajinsa kadan-kadan." "Sannu Anti, ko za ki sanarwa Yaya?" Ummi ta girgiza kai tana dan yamutse fuska. "Kayya, barshi, nasan yanzu yana tare da su Hajiya, in sha Allah idan na samu  na dan runtsa zai bari."   Ta gyada kai. "Allah Ya baki lafiya." Ta lumshe idanu tana mai amsawa, bayan fitar Batula daga bacci ya dan fisgeta sai ciwo ya motsa ta farka, lokacin karfe biyar na yamma, can dai ta ji ciwo ya motsa babu kakkautawa, firgigit ta mike zaune tana ambaton sunan Allah gami da rike cikin.     Ta kasa jurewa ta sauko kasa bayan ta dafe gadon da hannunta na dama.    "Wayyo Allah."   Ya yi daidai da shigowar kiran Faruk wanda ta sanyawa sauti na daban, ta daure ta kai hannu saman dirowarta ta dauka gami da sanyawa a kunnenta.     "Ummina kina lafiya?" "FAR HAS zan mutu..." Ta fada cikin rawar murya wacce ke nuni da jigata.    "What?! Nakudar ce?!!!" Ina! Tuni ta ajiye wayar sakamakon murdawar da cikinta ya k'ara yi.     A wannan yanayin Batula ta iso domin ta lek'ata ko ta samu baccin, gaba daya ta diririce ta hau salati, ganin yanda Ummin ta ke ba'a hayyaci ba kawai sai ta soma kuka don ta rasa taimakon da zata bata. Dabarar kiran direba ne ya fadomata, a guje ta fita tana kiransa.    "Malam Musa! Malam Musa!!" Da sauri suka shigo gidan har maigadi kasancewar suna waje saman benci suna hira. "Lafiya?" Suka fada har suna rige-rige.    Ta nuna hanyar gidan dakyar ta iya magana.   "Anti..Anti zata mutu." Ai da gudu suka nufi ciki, saidai kafin su karasa ciki suka ji ana doka mahaukacin hon, da gudu kuma suka fito, har suka ci karo da Faruk wanda ya bar motar waje ya shigo Hajiya Babba da Dakta na mara mishi baya.    Suna shiga suka tarar tana ta fama, da sauri ya riketa. "Sannu Ummina." Ya dauketa cak ya nufi waje, lokacin har maigadi ya bude kofar. Suka sanyata a mota sai asibiti.    Shima Haidar wanda isowarsa kenan tare da Intisar suma har da su a gidan sadda Ummi suka yi waya da Faruk, suka bi bayansu zuwa asibitin.     Dakta Ridwan wanda tun a mota ya yi kiran wayar abokiyar aikinsa Dakta Farha, ita ta kar6i Ummi suka shiga dakin haihuwa.     Suna nan tsaye suna faman adduoi, Faruk ya kasa mance furucinta na ambaton mutuwa da ta yi gareshi, ya runtse idanu ya budesu, tuni suka kada zuwa ja. Hajiya ta umarci Intisar da ta koma ta dauko akwatin Ummi na kayan haihuwa, Haidar ne ya jata suka koma.     Mintuna talatin da shigar da Ummi, lokacin an soma kiraye-kirayen sallar Magriba har Intisar sun dawo, kukan jariri ya cika kunnuwansu, suna cikin wannan farin cikin, suka kara jin wani kukan. Fitowar Dakta Farha ne yasa su maida hankali gareta.     "Alhamdulillah, ta sauka lafiya ta haifi...." Sai kuma ta sanya dariya lokacin da ta kar6i akwatin kaya tana mai mikawa nos din gefenta dake dariya, nos din ta yi ciki. Su kuwa duk sun k'agu da son jin abinda zai fito bakinta.    "Me ta haifa?" Cewar Haidar.  Dakta Ridwan wanda ya riga yasan manufarta ya sanya hannu cikin aljihu ya fiddo dari biyar ya mik'amata yana dariya.    "Ga abinda ki ke jira." Ta kar6a suka yi dariya, Faruk ji ya ke kamar ya tura kansa dakin.     "Na kar6a amman ya yi kadan kaima ka sani, ta samu twins mace da namiji."   Ai Haidar da Faruk tuni suka rungume juna suna dariya, Hajiya murmushi kawai ta ke yi tsabar farinciki ta rasa inda zata saka ranta, wai Sadaukinta ne da d'a, har biyu ma, kyautar Allah. Hawayen farinciki ya tahomata ta yi saurin daukewa da hannu.   "Dakta jikin Ummi fa?" Cewar Faruk. "Alhamdulillah, babu wata matsala."   Ta koma ciki, nan fa suka shiga kiran abokan arziki suna sanarmusu. Ihsan saida ta ji kamar ta budi ido ta ganta a Abuja tsabar murna don yanzu sosai su ke dasawa da Ummi saika rantse wani abu  bai ta6a giftawa tsakaninsu ba.     Bayan an gama gyara yaran wadanda sak kamannin mahaifinsu suka dauko, aka miko musu.     "Masha Allah." Cewar Dakta Ridwan wanda ke rike da macen yayinda Haidar ya matsa ga Hajiya yana kallon namijin. Faruk ya kuramusu idanu yana kallo cike da sha'awa da tsananin so da kauna, burinsa ya yi tozali da Umminsa wacce ta haifa mishi wadannan kyawawan halittar abin so da kauna.      Koda suka shiga, kasa daga idanu ta yi ta dubesu haka kawai ta ji tana kunya musamman ma ganin har Hajiya Babba aka zo.     "Madam sannu, kin kawowa Hajiya miji, Daddy kuma mata ko?" Cewar Haidar, akayi dariya. Faruk dake rungume da macen ya saci kallon Ummi saidai bata ko kallo inda ya ke ba, murmushi ya yi yana ji kamar ya hadasu duka ya rungumesu.    Ko awa uku ba'a cika ba, su Baraka da Jidda duk aka iso har babban Yaya.     Haka suka cika daki mai lamba hudu wanda aka bawa Ummi don ta huta. Faruk da kansa ya kira Gombe ya sanarwa Malam Balarabe da Gidado,  wannan abu ba karamin dadi ya yi musu ba. Dada ta hau shirin tahowa Abuja don daman ta ce ita da zuwa Abuja sai idan Ummi ta haihu.    Ana gobe suna yan uwa duk suka zo har mutan Kano da Gombe, Amina ta so zuwa saidai babu dama don ita kanta tana fama da jikinta, Binta itama ta yi farinciki sosai don itama ga kusa aure lokacin.      Yara suka ci suna Afra da Afreen, da yawa tsoffin suka kasa maimaitawa.    "Dan nema, za ka zo ka sameni, idan ba mugunta ba mene na saka sunan da bamu iya fad'i ba sai kace sunan aljanu?" Cewar Hajja kenan lokacin da sukayi waya da Faruk, banda dariya, babu abinda Faruk ya yi. A karshe suka gaisa da Modibbo wanda ke kwance ba lafiya har lokacin. Dakyar ya amsa wayar kafin su yi sallama.     Sati biyu da haihuwar Ummi, Dada ce awajenta tana kula da ita, alokacin ne kuma aka soma bikin Ikram da Gidado wanda babu abinda Ummi ta halarta a ciki bisa umarnin Faruk, acewarsa yaushe ma ta haihu da zata soma fita?     Haka aka yi biki aka k'are, Ihsan itama ta zo daga Adamawa anan gidan Ummi ta yada zango, sosai Ummi ta ji dadi, tsakanin Ihsan da Faruk zumunci na yan uwantaka ke wanzuwa ba kamar a baya ba da ya ke daddauremata, hatta Badiyya kishiyarta ta zo wannan karon.    Haka aka kammala bikin Ikram aka mik'ata Jar Kwami, gidan da Gidado ya gyarashi kaika rantse cikin birnin Gombe ne don daman ko kadan basu da matsalar wutar nema. To me zai dameta tana tare da masoyinta?   Bayan Ummi ta yi arba'in babu inda kafarta bai taka ba itace har Gombe, a wannan lokacin ne kuma Faruk ya biyamusu Umarah, har hawaye ta yi don tsabar farinciki.                   ***    ***    ***            BAYAN SHEKARU UKU                      DAN ADAM Mace mai shekaru ashirin da daya mai tsohon ciki na hango sanye cikin kananun kaya riga iyakar gwuiwa da dogon wando,  kanta nade da mayafi tana bin wani kyakkyawan yaro wanda ya ci riga marar hannu da wando karami na shan iska, yana gudu yana dariya rike da 'yartsana tana binsa da tsinken tsintsiyar kwakwa. Wata kyakkyawar yarinya da aka nade gashinta da ribbon tana biye da ita tana murza idanu baki a ta6e lamun kuka ta yi.     "Afreen! Afreen! Ba zaka tsaya ba wai?"    Saidai kamar k'ara tunzurashi ta ke ya hau zagaye falon, a haka Uban ya fito daga sashensa yana dubansu, ganinsa yasa Afreen rugawa gareshi ya rungume kafafunsa.   "Papa kaga Maama pho?" Ya fada cikin gur6atacciyar hausarsa.    Daidai lokacin da ta karaso a fusace ta daga zata kai mishi bugu, Faruk ya rike hannunta. Ta dubeshi tana huci. "Allah kuwa FAR HAS karka hanani, tun dazu ya ke ta sanya yarinyarnan kuka don ya ga bata da hayaniya duk ya bi ya takura rayuwarta. Bata yartsanarta tun kan na 6ata ranka."   Murmushi Faruk ya yi ya daga Afreen cak ya sanya a kafadarsa suna dariya. Ganin haka yasa Ummi ta k'ulu, ta yi kwafa gami da jan hannun Afra su wuce. Faruk ya riko kunnen Afreen har saida ya saki yar kara da dariya. Yaron ba dai wayo ba.    "Bigboy meyasa ka ke takurawa Bebina ne? Duk maganar da zanyi ba ka ji ko? Zamu 6ata fa." "Na daina Papa, ka yi hakuli."   Ya ja kumatunsa kasancewar Afreen tubarkallah akwai k'iba don har yafi Afra jiki.   "Oya muje ka bata hakuri." Suka nufi wajen Ummi wacce ta dannowa Afra game a wayarta ta mik'amata. Ko kallonsu bata yi ba, Faruk ya sauke Afreen, ai kuwa daman jira ya ke a guje ya je ya mikawa Afra 'yartsanarta kafin ya soma raba idanu yana kallon wayar Ummin don a rayuwarsa yana son ya ganshi yana danne-dannen waya duk kuwa da cewar ba iyawa ya yi ba. Abin yaso bawa Ummi dariya sanin halin dannata saidai ta danne. Ya dubeta kamar wanda ya yiwa Sarki k'arya.  Faruk ya na dariya ya dan sanya yatsa cikin kunnen Ummi ta yi saurin tarewa tana dariya. Bayan sun tsagaita ya ce. "Kinsan fa abinda dannaki ke so ki ke mishi yanga ko?"   Ta dan tsuke baki. "Allah kuwa shine abin ban haushi." "Na daina Maama, ki yi hakuri." Ya fada yana mai dafa kafafunta.  "Please Ummina ki yi hakuri bazai k'ara ba ko?"    Ta yi murmushi kafin ta rungume dannata ta sumbaci goshinsa.    "Is ok my son, Maama ta hakura."   Ya hau tsalle sannan ya dane cinyarta har ta danyi k'ara sakamakon dan bugun cikinta da ya yi, da sauri Faruk ya dagashi cak. "Afra, tashi ku je dakin Maama ku yi game din amma banda danne-danne kunji?"  "Toh." A guje suka mike suka yi dakin, ya janyota jikinsa ta kwanta saman kafadarsa.    "Ina sonki Ummina." Ta lumshe idanu tana murmushi, shekarunsu uku da aure amman har gobe tana jin kalmar nan tamkar sabuwa fil a kunne da gangar jikinta.    "Kasan me FAR HAS?" Shima idanunsa lumshe ya amsa. "Sai kin fada Ummina."   Ta kara rungume hannunsa. "Inajin dadi aduk sadda ka cemin I love you." Ya yi yar dariya. "Zanyita ce miki har sai zuwa komawarmu ga Allah, ki tayani addua, Allah Ya bani ikon farantamiki har karshen rayuwata." Ta dago ta dubeshi shima ita ya ke kallo har suna shakar numfashin juna, kai ta girgiza gami da shafar gefen fuskarsa.     "Ni kuwa menene ba ka yimin ba ma a yanzun FAR HAS, ka nunawa duniya cewa nima ina cikin yan Adam masu girma da daraja, ka yimin dukkan wani abu na rayuwa, ka barni na samu karatu har gashinan zan zana jarabawar wucewa jami'a, me zanyi gareka banda addua da kyautatamaka. Ni nake ganin ma kamar banyi maka wani abu ba..."   Ya girgizamata kai cike da jin shaukin sonta da kauna. "Ke ki ka yimin kuwa Ummina, tunda har ki ka amince da aurena ki ka zauna da ni bisa amana har kika haifamin Afreen da Afra kin biyani Ummina, ga kuma bebina mai zuwa nan gaba,( ya shafi cikinta), kinmin komai kina bin umarnina kina nunamin kauna ta hakika, ai kuwa kin biyani."   Ta yi murmushi, wayar Faruk ta yi kara ya daga, Abubakar ke sanarmishi haihuwar Ihsan haihuwa ta biyu, farinciki ya cikashi don daman yaronta na fari  Badiyya abokiyar zamanta ta barwa wacce itama cikin ikon Allah yanzun ta ke dauke da juna biyu.     Ummi kanta ta yi farinciki don takanas ta kira Ihsan suka shiga hira kafin Abubakar ya kar6e wai ta takurawa matarsa daga haihuwa, don yanzu Abubakar ya nutsu sosai ya bar dukkan mugun dabi'u cikin nufin Allah.     Faruk ya mike gami da miko mata hannunsa, ta dubeshi ya kashemata ido daya. Ta bishi da murmushin da ya fi so daga gareta, kafin ta sanya hannunta cikinnasa suka nufi sashensa....!!!!           Tammat Bi Hamdullah...!!!      Godiya da Yabo sun tabbata ga Ubangijina da Yaban ikon rubuto muku labarin DAN ADAM, tsira da amincinSa su tabbata ga Annabi sallalahu alaihi wasallam.     Godiya gareku fans masu karfafamin gwuiwa, duk inda kuke koda ban sanku ba, wallahi ina kaunarku, Allah Ya hada fuskokinmu duniya da kuma lahira (aljannarSa)..ameen.    Godiya ta musamman ga yar uwata kuma mai kaunata koyaushe...   Safiyya Ummu Abdoul..Allah Yabar kaunata...kwarai kin taimaka sosai wajen ganin DAN ADAM ya tafi bisa tsari... Allah Ya barmu tare..ameen...    Ina mika godiya ga mutan DM, Hdy, rof facebook & whatsapp, khalisat group fb, Matan aure, matan aljanna, meema's novels, classic ladies, taskira da sauransu.    Don Allah duk wanda na mance ya yi hakuri..kuna da yawa ne...inda muka kuskuro muna fatan zaayi mana uzuri sannan zaa yi mana...  DAN ADAM AJIZI NE, DAN ADAM NADA DARAJA, DAN ADAM BA ABIN WULAKANTAWA BANE...Bakasan mai yi maka rana ba cikin DAN ADAM...    Allah Yasa mu dace..ameen...!!!    adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *