Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, 3 April 2017

DASHEN ZUCIYA 1--END

adsense here [1/31, 7:51 PM] Mummy: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 *Bismillahir Rahmanir Rahim* 1⃣ *FLORIDA united kingdom* "Bisma Kullun kara kyau kike gashi ana karatu amma ke kaman bakiyi sai wani kiba kikeyi, nikam kaman ana miya da namana, kinsan yau lectures dinnan damukayi wallahi bakiji yadda nikeji ba kamar in zura takalma na in gudu kasata Nigeria Dayawa mutane suna ganin kaman cin banxane zuwa karatu kasar waje wallahi babu komai sai wahala, dadinshi dayane shekarun karatun badaya bane da gida Nigeria". Itadai bisma kallonsa kawai tak'e duk yabi ya rude saboda karatu itakoh koh a jikinta don ita tafison tayita jin chargi a brain dinta, fashewa tayi da dariya lokacin da Hamdan yayi sipping ice-cream ya juyo da sauri kedawa "Keda lafiyanki kuwa kiketa dariya kamar wata tababba?". "Hamdan na lura gaba daya kai ragone, saboda Dan wannan karatun da kak'eyi shine duk' kabi kake damuna, Allah yabani hakuri nida nake karanta (MBBS Medicine) kuma gashi am still looking more healthier than you, kasan yadda nake kashe dare nake karatu wallahi bana samun cikakken bacci". "Naji din ni ragone kek'uma ba Raguwa ba shiyasa naga Kullun tafe kike kamar wacce akayiwa sata, Kullun cikin sauri kike wai shin intambayeki mana?". Gyra zama tayi ta juyo tana kallonsa "Ina sauraren ragon namiji"? Wani littafi ya wurga mata ta tashi tana dariya, "Joke apart Bisma wai meye dalilin ki na karatun likita?". "Hamdan kenan inada dalilai masu yawa, tunda ka bukaci kaji toh yau zan warware maka komai, nak'asance Mara tausayi, sannan da wuya Abu baya sani kuka sai wata rana aka kwantar da Nabil dinmu a asibiti dake zamfara Gusau Wato federal medical centre, da shigarmu naga wata mata tanata kuka tana surutai, rungume da danta amma babu Wanda ya kulada ita bare yasan halinda take ciki, saboda talauci dayake tafe dasu Tuni na shagala da kallonsu wasu zafafan hawaye ne suka gangaro daga k'warmin idanuna". "wani wawan shaka nayima wata nurse wacce taketa surfa musu Zagi, nace ke wace irin Mara imani ce? Wace irin dabbace ke wacce batasan darajan mutane ba? Kina ganin wannan matar kika banzatar da ita bakiga halinda danta ke ciki bane? Nasha Alwashi saina zama likita don intaimakawa marasa lafya da gajiyayyu". "Tuni mutane sukayo kanmu suk'ayi mana cha sai a lokacin Ummi ta hangoni na shake Nurse cikin mutane ta kutso kai "Bisma da lafiyanki kuwa malamar asibiti kika kama ma wuya?" Ummi ki kyaleni da ita narasa meyasa wasu likitoci suke wasa da aikinsu Ummi Dan Allah dubi wannan yaron suma yakeyi amma anrasa wanda zai mishi gata? What a pity dagudu nabar asibitin, nayi waje ina kuka Bayan an gama duba Nabil ne muka koma gida". "Nanna sanarda Abbeey cewa nidai aikin likita zanyi don in taimakawa mutane musamman ma talakawa masu karamin karfi nayi alkawari koda zan mutu ta hanyan taimakone saina yi karatun likita". "Dayake shi mutunne mai son taimako haka ya goyi bayana har nazo kasar Florida USA Dan inyi karatun likita shiyasa kaga bana wasa da profession dina". Hamdan shuru yayi yana jinjina k'wazo da jarumta irinnan Bisma, "lallai kinada kyakkyawan niyya kuma insha Allah, Allah zai miki jagora Allah xai taimakeki" "Amin" Bisma tace nan suk'ayi sallama da juna kowa ya wuce hostel dinshi cikeda kewan juna, Kullun haka suke haduwa har wata halak'a mai girma tashiga tsakaninsu Wato *LOVE* lokacinda Hamdan ya sanar da Bisma bakutar sa taji wani mugun dadi da mamaki Ashe amintarsu da Hamdan zai iya zama Soyayya? [1/31, 7:51 PM] Mummy: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 2⃣ Nikam nece kwarai, alokacinda suka kusa kammala karatun su ne, suka xama hanta da jini soyayya mai karfi ta shiga tsakaninsu, Wanda tazame musu jiki kowa maganarsu yake dama suyi aure, Hamdan ne mai cewa "ai idan kukaga ban auri Bisma ba toh ajaline yaxomun baka tatan, "Banda abunka mai sanyina ai rana daya zamu mutu mubar duniya, don inhar katafi kabarni Rayuwa zata kasance mai zafi a gareni". "Haka nima Bisma bana fatan ki tafi kibarni inrayu dawa ingawa inji dadii, Dan Allah adaina maganan mutuwa saboda hankalina yana mugun tashi Gashi muna gab da mukammala karatu Mu koma gida Nigeria, Meye next target dinki?" Bisma kallon soyayya takemai "Ai banida Wani buri anan gaba saina inganni tareda dakai matsayin matarka halak malak dinka". "Gaskiya ne Bisma fatana Allah ya albarkaci soyayyar Mu, Allah yasa iyayen Mu su aminche ma bukatar mu cikin kankanin lokaci donnni ta bangarena banida wata matsala". "Nima haka *Hamdan* nasan iyayena bazasu ki abunda nake muradi ba, tun yanzu sunfara yimun maganan aure kuma nasanar dasu cewa nifa nayi gamo da katar a kasar Florida kuma insha Allah shine Wanda za'ayi dashi". "Nikam ai Tuni nayi introducing dinki a family na, yanzu haka kowa yakosa daya ganki, Kinsan farin jini gareki da banyi da gaske ba inajin da NURU yamun kafa, dayake jarumine nidin shiyasa na rike fire". Dariya Bisma tayi tace, "nikam kana bani mamaki waikai a tunaninka nuru sona yake? Toh koh kafado kawaidai mutunci mukeyi dashi saboda daga gari daya muka fito, Shikafi" "Bisma kenan kin manta aminta yanasa ayi aure koh a dasa soyayya? Lallai fatana Allah yayi mana jagora" "Amin". NIGERIA SHIKAFI Shirye shirye akeyi kwarai saboda, dawowar yar gaban goshi hatta fentin gidan sabone, an gyara ko ina donya kawata kallon yar'Gaban goshi, Inkaga mutane acikin gidan babu Wanda yake zaune kowa sabgar gabansa yakeyi, an shirya liyafa wacce babu irinta a fadin Gusau, abinchi ne kala kala sannan ga yan tarban bakuwa yan uwa sa abokan arzuka duk an halacci gidan, daga birni da kauyuk'a Ummi kuwa takasa zaune takasa tsaye tilon yarta zata dawo daga USA, Shikam Abbeey yana chan danasa mukarraban, ana hiran irin cigaba da nasaran da Bisma tasamo daga Florida. FLORIDA Acanma bikin yayesu akeyi, lokacin sunrigada sun kammala, hada kayansu dayan tsarabe tsarabe, shikam Hamdan ziri muzin shi zai koma, daman dayawa mata ke jigilan yin tsaraba koda kasa mai Girma akaje dayawa inka leka kasuwanni da dare mata ke hidima. Bayan an kammala ne, hankulansu duk yabi ya tashi saboda rabuwa da juna da zasuyi, Bisma takasa cin komai gashi garinsu guda amma kowa da shiyarshi, nikaina saida na tausayawa Bisma saboda irin shakuwar dasukayi tun haduwarsu a makaranta. [1/31, 7:51 PM] Mummy: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 3⃣ Haka suka fito kowa kagani hankalinsa a tashe yake ciki har *Nuru* daya kwallafa ransa akan Bisma amma bashida yadda zaiyi tunda *Hamdan* ya rigashi dole ya hakura saboda Bayaso su samu matsala da Hamdan, amma abun takaici Bisma takasa gane cewa *Nuru* sonta yakeyi ita a tunaninta kawai jininsu ne yazo daya shiyasa ya shaku da ita, tafe suke har filin jirgin saman dake US dayake duk gari guda suka nufa, amma Hamdan da Nuru scholarship ne gwamnatin Zamfara ta daukesu saboda kwazonsu da haxaka badon iyayensu sun gaxaba, Nuru ne zan iya cewa dan talaka ne amma kuma mai wadatar zuciya, anyi musu hakanne don kara musu karfin gwiwa, sannan suna fatan idan sukaje suka dawo zasuyiwa gwamnatin Zamfara hidima. *KASA NIGERIA* A filin jirgi suka sauka acikin garin Gusau, inda yan'uwa da abokan arziki suka cika dankam don tarban yayan gata, Nuru yashiga damuwa wacce baxai misaltu ba amma duk Wanda yaga bisma da Hamdan saiya gane cewa suna cikin farinciki, nan danan su kayiwa junansu sallama, kowa yatafi inda matsuguninsu yake, anyi murna kwarai daga Duka bangarorin, Bayan wasu yan kwanaki da dawowarsu Bisma tadamu kwarai saboda rashin ganin Hamdan, Nuru ne ya sauka daga cikin Motarsa ya k'wank'wasa kofar gidansu Bisma zaune take a tsakar gida, mai gadi ya wage kofar gidan "Dan Allah bisma nake nema ko tananan?" Mai gadi ya juya yace eh bari in sanar da ita, "Ranki ya Dade kinyi bak'o" cikin zumudi tace "Kace ya shigo" duk a tunaninta Hamdan ne amma sai taga ak'asin hakan, Nuru tagani yana shigowa da hancin Motarsa lokaci guda taji ranta yayi mugun baci amma saita boye dariya tayi tace "Manyan kasa Ashe Baka manta daniba" Lemo tasa aka kawomai da ruwa. Dariya Nuru yayi yace "Banda abunki Bisma ai zumunchin mu bamai karewa bane, fatana shine Allah yakara hada kanmu baki daya" "Tabbas wannan haka yake Nuru banida Wata kawa koh aboki Wanda ya wuce kai, ina iya gayama duk wani sirri nawa batareda naji wani dar acikin zuciyana ba, Sai kuma Hamdan Wanda yak'asance abokin rayuwana bantaba son wani da namiji yadda nakeson Hamdan ba, I really love him amma sai gashi yau Kusan satinmu uku babu Hamdan babu labarinshi koh wayarsa nakira bana samu kuma bansan yaxanyi ba, nasan ba darajata bace inje gidansu da sunan ina nemansa bansan dawani ido zasu kalleni ba". Shuru ne yadan ratsa Nuru bakaramin dadi yajiba, yadda yaji Hamdan bai damuda Bisma ba, "My friend hakuri zakiyi zuwa wani lokaci kila dakwai wani Abu so strange daya rikeshi but nasa [1/31, 7:51 PM] Mummy: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 4⃣ Nasan everything shall be well with him", kallon Nuru Bisma takeyi yadda duk ya damuda lamarinta yadda yanuna rashin jin Da dinsa akan rashin zuwan Hamdan, sun danyi hirarsu wacce batada maraba data masoya, Sallama sukayi daga bisani ta rakashi har gaban Motarsa, harya fita tana dagamai hannu cikin gida Bisma tashiga tana wasa da yan yatsunta tana wakan christ brown, cikin dakinta tashiga tafada kan gado, wayarta ta dauko ta hau kiran lambar Hamdan amma bata shiga, saidai taji the number you're trying to call is currently switch off nan ta zabga uban tagumi Wanda ya nuna tana cikin tashin hankali. Gefe na koma ina tunanin yadda Hamdan yayi barin iska da lamarin Bisma, meyake nufi da itane yana nufin duk love din da sukasha a Florida USA duk ta bogi ce? Abunda nikaina HUMAIRAH nakasa bawa kaina Amsa kenan, Chatting takeyi Wanda yaxame mata jiki, bata wannan GRP bata wancan saidai yawancin group dinta na matane sannan kuma na novel ne, wani novel ta tsinci kanta da karantawa, Wanda yayi shige da yanayin aikinta Wato NEESMA'A WAH NUSHUUF, Wannan littafin ba karamin tafiya yayi da imaninta ba, Karar bell din dakinta taji hakan yasata kashe data, ta mike ta bude kofa, Nabil tagani tsaye yanata dariya Wanda tarasa gane ma'anar hakan batayi kasa gwiwa ba Wajen cewa "Nabil lafiyanka sai wani dariya kakeyi saikace Wanda akace ga Aljanna shiga?" Nabil yace "Aunty Bisma dole inyi farin ciki tunda Allah yasa appointment dinki na aiki yafito shine nace bari inzama mutum na farko daxaiyi miki albishir" "Naji dadii kwarai nabil amma hakan baxai sani farinciki ba matukar banga Hamdan ba, shine mutum na farko daya karbi ragamar zuciyata, amma tunda muka Dawo yau kusan sati uku bashi ba labarinsa". Dukda nabil karamin yarone Wanda shakarunsa bazasu wuce Sha takwas ba, yasan cewa yar'uwarsa tana cikin halin kunci na rashin mosoyinta, Washe gari suna zaune a katuwar darduma wacce itace tazama kamar dining dinsu anan ake baje kayan abinchi kuma kowa anan yake zama doncin abinchin, Daddyn sune zaune Bayan sun kammala cin abinchi, "yabo ya tabbata ga Allah madaukakin tsarki dayasa Bisma ta karkare karatunta, nazama kwararrar likita a fannin maza da mata, har ila yau gashi tasamu aiki a Federal medical center dake garin Gusau, an dauketa a matsayin consultant, yanzu Abu daya yarage mata a Rayuwa shine tafito da mijin aure Wanda shine zaisa tacika mace". Yana zuwa nan yayi shuru, Bisma koh tashiga rudani "mai daddy yake nufi dani toh ni yanzu idan ance infito da miji yazanyi after ol Hamdan ya watsar dani dukda moment din da mukayi spending tare a USA" Muryan daddy ne yadawo da ita daga tunanin da takeyi, "Bisma yanzu Sha'awara yarage naki kiyi gaggawan fitarda miji don hadaku zanyi dasu Rumaisa da Ikram duk inyi muku aure in huta da surutun mutane". [1/31, 7:51 PM] Mummy: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 5⃣ Bata iya amsawa ba saboda, wani haushin kanta da takeji tashi tayi lokacin kowa yabita da kallo, kafin ta karasa daki taji karar wayarta dafe kai Tayi a tunaninta Hamdan ne yake kiranta amma saitaga Akasin haka Nuru ne yaketa kiranta amma takasa ta daga wayarsa saboda abubuwan dake dawainiya da zuciyanta, da shigarta daki ta taradda ikram kwance sai minshari takeyi wani wawan Duka ta daka mata a duwawu tace "Maza ki tashi ke har wani lok'acin bacci gareki toh bari kiji in gayamiki abunda baki sani ba Daddy aure zaiyi mana kuma yace kowacce cikinmu tafito da miji don yagaji da surutun mutane", Ai ikram batasan lokacin data nanawa Rumaisa dukaba, tace "maxa kitashi kiji wani sabon Al'amari daddy yace kowaccen mu tafito da miji, Zare ido rumaisa tayi tace kalu inna-nallahi wa'inna ilaihir rajiun, tashi tayi ta zauna daga ita sai half vest, Ikram tace "a gaskiya nidai a yanzu saidai Daddy ya zabamun miji Donni ubanwa nake saurara bare akaiga wani zancen aure tab wanga abun Alkhairi haka dame yayi kama?". Bisma dake zaune tace "hmm ke ikram saurayinne bakida toh ni wallahi Wallahi inada amma tunda muka zakkuwa kasar nan muka rabu airport shikenan niya babu waya babu sako, ke koda lambarsa nakira bata shiga switch off, kinga damuwata guda kenan," Rumaisa da karatun ya kare mata cikin kwakwalwa tace "Nifa bari kuji wani zancen banza zancen wofi chan kasar America saurayin nawa yake acan yake karatu muna masifan son juna amma kwana biyu nima shuru, ikram bakijin wayar damukeyi dashi, wallahi 24 waya mukeyi Donni bani sauraran kowa cikin garin ga mazan garinnan koh yan ataru a lalace". Wata safiyar Asabar gari ya daure yayi dind'um, saboda wani gagarumin hadari dake haduwa daga gabas, amma Bisma, Rumaisa da ikram shirin fita sukeyi, basu damu da yanayin garinba lace iri daya sukasa amma kowacce da kalan nata, biki akeyi na yayan Hutu yara masuji da kyau da isa basuda maraba da larabawa Wato zuri'a Wamban Gusau kenan, amma in fedewa mai karatu wani sirri Bayan fari wallahi da dukkan su bola za'ayi dasu dama dama ikram, gasu gajeru Kamar a kife da kwarya. Fitowa suk'ayi saida suka ratsa tacikin falon Ummi suka gaidata binsu kawai takeda kallo tarasa wacce zata yaba cikin su, tashi tayi ta zagayesu tace "Tabbas dawisu daban yake cikin tsuntsaye, Giwa kenan dole aganku a kyaleku, Tabbas kunyi kyau yadda ake bukata amma kun mata Abu guda" daki tashiga ta dauko Wasu warwaraye, Masu kyau da tsada tace wannan wani sirrine dake karawa mace kyau duk inda tayi sai an kalleta, Bisma tsaye tayi amma ranta yayi masifan sosuwa ganin yadda yan'uwanta sukayi mugun kyau. [1/31, 7:51 PM] Mummy: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 6⃣ Ummi kallonta kawai take tasan za'a Rina, hannun bisma ta kama tace "kema fa naki" lokaci guda Bisma taji wani mugun dadii tayi tsalle sukayima Ummi Sallama suka kama hanyan Zuwa GRA biki. Direba ne ya daukesu dayake an hanasu tuki, saboda rough driving da Bisma takeyi saboda sabo da kasar Florida, Bakin wani hall sukayi packing lokaci guda suka fito kowacce sanye da Google a idanunta, yadda kukasan makafi wakane kawai ke tashi abun sai Wanda yagani, cikin tafiyar ka saita suka isa cikin hall din daman ansan da zuwansu kowacce kodata akeyi. Guri aka sama musu a high table, inda manyan baki suke Bisma kawai ake kodawa likita likita kenan likita bokan turai, bakije Us a banza ba wallahi baba ba'ayi asaran kudin Tara ba, tashi bisma tayi ta isa wajen Mc tafara yimai barin Naira yan dubu dubu kawai take watsamai, saboda dadin washin dayayi mata. Ba'a jimaba Aka fara Event wani Abu Bisma tagani daidai da shigowan Amarya da Ango lokaci guda zuciyarta tafara bugawa, Hamdan Munnir Hameed Weds Laila Ibrahim Wambai............. Lokaci guda ta mike tace "Daman hamdan yaudarata yakeyi basona yakeyiba? Oh noo nayi regretting saninka Hamdan a rayuwana, amma yau saina bata maka ranar farin cikinka saina gayawa duniya cewa kai macuci ne maciyi amana kuma azzalumi Wanda baidau soyayya da muhimmanci ba, Hamdan menene don kace mun zakayi aure? What is dere?" Dayake bamai saurin kuka bace ta zauna ta hakimce akan kujera dayake Bisma itace babbar kawa. Itama Rumaisa abunda yake bata mamaki shine "tabbas wannan shine saurayina Wanda muka Dade munason juna har Alkawarin aure mukayi dashi shine zaiyi playing dina haka? Toh koh yadebo ruwan dafa kansa don saina canzamai halitta yadda matarsa bazata sake ganin kyawunsa ba". Bayan kowa ya zaunane aka bukaci babbar kawar Amarya Bisma Bassam Anka tafito lokacin Hamdan yaji wani tashin hankali lokaci guda ya mike zai fita Laila tace "babu inda zaka zauna tun dazu bakasan zaka fitaba saida Bisma zatayi magana kuma Sanin kankane babbar kawatace?" Ai ba shiri yakoma ya zauna zufa kawai yake zuba ajikinshi lokaci guda yayi shar kab da zufa Kamar yayi wanka da ruwa. Bisma ce tafito kan stage taga dubban mutane an taru saboda murnan bikin Hamdan da Laila, tace "ya dubban mutanen nan zasuji abunda hamdan ya tafka? Ya Laila zata daukeni? Ya makomar bikin Hamdan da Laila? I don't care wannan yarage nasu". Farawa tayi da gaisheda kawarta Laila Ibrahim da Angonta Hamdan munnir, sannan ta juyo ta gaida dubban mutane sannan tafara gabatar da kanta a matsayin aminiyar Laila tabada tarihin Laila tun daga kuruciya harya zuwa yanzu, guri tuni yadau tafi sauka tayi daga kan stage din tareda loudspeaker din.... [2/1, 5:02 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 7⃣ Zagaye kawai takeyi tace "na hutar da Abokin ango ni Bisma zan Baku takaitaccen tarihin ango dafatan zaku bani kunnen baseerah?" Tuni guri yadauka shiko gogan Hamdan yashiga rudani Wanda baitaba shiga irinshi ba, tuni idanunta sukayi jajir itako Laila abunne kawai yake bata mamaki, harde hannu wanta tayi don jin wane irin tarihi Bisma zata bada akan mijin daxa'a daura musu aure gobe?. "Hamdan munnir Hameed kasaitaccen mayaudarine, sannan kwararre maciyi Amana, maha'inci Wanda baisan darajar ya mace ba, Tabbas ban zaci haka kakeba da tun fari banyi ginin tubaliba, da ginin kasa nayi da baxan damuba, munso juna lokacin muna Florida kayimun Alkawarin zaka aureni ka yaudareni da jahilan kalamanka Ashe dakwai wacce ka ajiye agefe donka aura toh kayi kuskure Azzalumi kawai kuma Allah baxai taba barinka ba". Ajiye loudspeaker tayi tayi waje da gudu, itadai ikram abun ya daure mata kai lokaci guda na hangi Rumaisa tana taku daya Bayan daya ta haukan stage tace "Nasan koba komai Ango yasan koni wacece" Lokacin Hamdan ya zare ido yace "Nashiga uku" Rumaisa taci gaba da cewa "Nima kaci amanata ka ha'inceni bantaba Sanin cewa kai macuci bane sai yau Allah ya toni asirinka da wannan kadai nabarka sauran hukunci yana gareki amarya idan har kin zabi zama da wannan toh, kinyi zaben tumun dare". Itama ajiye loudspeaker tayi ta fice daga cikin hall din itama ikram ta mike ta bi Bayan su, tuni guri ya rude Laila kuwa suma kawai takeyi saboda tsantsar takaici, tuni taro ya tashi ran kowa babu dadii, "Gaskiya Hamdan is a player ji lokaci guda yayi playing mata biyu at the same time" wasu samarine ke magana. [2/2, 8:00 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 8⃣ Cikin mota suka shiga direba yajasu, sai gida suna shiga gida kowa ya fada bandaki donyin wanka, ran Bisma a bace na Rumaisa a bace gaba daya haushin mutum daya sukeji Wato Hamdan, Ummi ce tashigo tace "wai lafya kuwa naga kunshigo kowa tayi jugum jugum maye ke faruwa ne?" Kallon juna sukayi sukace "Ummi babu komai kawai bikinne babu wani armashi duk yadda mukadau event din ashe ba haka yakeba". Ummi tace "amma hakan ba Zaisa kushigo Baku gaidani ba, Toh kuyi maza Daddyn yadawo daga Abuja kuma nemanku yake bansan dame yadawo ba" tana gama magana ta fita tabarsu tsaye kowa hanjin cikinta ya motsa, Bisma tace "Nasan zancen Gizo baya wuce na kok'i" Rumaisa tace "Nifa gaskiya saidai adagamun kafa saboda wallahi mazan yanzu tsoro suke bani sun zama horrors abun gudu", Ikram dake tsaye ta jingina da matakalan gadonta tace "Hmm nidai daman banida zabi duk Wanda Abba yazaba mun falillahil Hamdu". Gama shirinsu keda wuya, suka kama hanya cikin Falo suka shiga suna muzurai, Daddy suka gani zaune cikin manyan kaya gyaran murya yayi yace "Nasan kunsan dalilin kiran danayi muku koh?" Suka hada baki a tare sukace "Ah Ah" Kallonsu yayi tacikin Glass yace "maganan aurene daman idan kun shirya inaso kowacce tafito da miji" dam gabansu yayi mugun fadi "Bisma kece babba kuma kece yakamata kiyi setting example akan kanninki dalili kuwa shine idan sukaga kin bada niyya toh yaxama dole suyi mubaya'a, ba burin mahaifinku bane kukai girman haka bakuyi aureba, Amma saboda Zamani shiyasa na bari kunemi ilimi Wanda za'ayi alfahari daku nan gaba Ku nake saurare". Ikram dake kusa dashi tace "A gaskiya daddy banida zabi amma duk Wanda kazab'a mun a matsayin miji zanyi Alfahari dashi" "Alhamdulillah Ikram kinyi magana mai matukar muhimmanci kuma insha Allah bazan miki zaben tumun dareba, Ku kuma fa ya muke ciki koh kuma bakuda zabi?" Rumaisa tace "Daddy inaso kadan karamun lokaci, saboda banida wani Wanda mukayi alkawarin aure dashi" daddy yace "kina nufin kice bakida tsayayye?" Rumaisa ta sunkuyar dakai tace "Eh daddy" numfasawa yayi yace "ke kumafa gadarkama?" Bisma tace "Daddy Kamar yadda ruma tace nima hakanne amma nayi maka alkawari nan bada jimawa ba". "Duk naji kuma na Aminche don haka kutashi kutafi" A tare suka mike suka rankaya sai daki nan suka dasa labarin Hamdan kowa tana faden yadda lamarinsu ya kasance. Ilai haka bikin Laila da hamdan ya fasu saboda tace bazata iya auren mayaudari maciyi Amana ba, haka komai ya watse Laila ta kama wani reshen, Hamdan yaxama abun tausayi amma gaba daya baiyi ladaman abunda ya aikata ba. Bisma ce kwance akan doguwar kujera, mai gadi yashigo da hanzarinsa yace "Ana Sallama dake hajiya" a watse Bisma tace "kaje kace waye?" Bai Dade da fitaba sai gashi ya dawo "yace ince miki hamdan ne" "What"!!!!!! Lokacin ta mike tace "lallai Hamdan yace wani Abu meyake nufidani ne?". Cikin sauri ta fita tana isa gareshi ta wankamai mari tace "Wannan shine sannu da zuwa". [2/2, 8:21 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 9⃣ Rike kuncinsa yayi yace "You have evry ryt toh waz me slapp but believe me I will always love you till death do us a part, Bisma take dis as a mistake I don't mean to hurt you, nasan nayi miki *rashin adalci na ILILEE* amma you have to forgive me dake kadai zan iya Rayuwa idan baki Bisma I will be no more" "Heyyyyyh dakata rufemun baki, suda sarkin Zak'i waxaka cuta macuci toh kasani danade da dawowa daga rakiyarka don haka kwarya tabi kwarya". "Bisma duk abunda zakicemun wallahi bazanji haushiba, Nasan cewa har gobe kinasona kuma har gobe baki yarda alkawari ba, duk abunda yafaru kidauka kaddara ce" "Meyasa kaddarar batazo da wuri ta hanani sonka ba saida tabari nayi nisa a sonka? Shine xatazo ta tarwatsa rayuwana nayi Dana Sanin barinka shiga zuciyana kasani Hamdan bana sonka bana kaunarka kaje wajen yar'uwata Ruma kila ita tanada sauran space dinka amma for me bakada shi". Da gudu ta shige gida, tabar Hamdan tsaye cikin kunar rai jingina nayi da bangon dake gefensa, yana hawayen takaici, yanzu inzai dosa Bayan yan'uwansa sun tsaneshi mahaifinsa yayi barin iska dashi, ji yayi an dafashi juyowan da zaiyi mahaifin Bisma yagani tsaye yace "yaro share hawayenka koda wasa karka sake ka zubda hawayenka gaban mace don haka shike kawo raini". Hannunsa ya rike suka shiga cikin falon baki yace "gayamun damuwarka") nikuma inyi maka maganinta" nan hamdan ya fede masa bindi har wutsiya, bai boye masa komaiba, mahaifin Bisma yace "kayi kuskure babba amma haryau har gobe kanada damar taka rawa acikin birnin zuciyoyinsu, nabaka izini kaje wajen Ruma kila Allah yasa ka dace". Godiya yayi sosai ya mike bai zarce koh inba, sai gida cikin sasansa yashiga ya kulle, abunka da uwa takasa jurewa halinda danta yake ciki, ta dauko abinci tana tafe tana waige a hankali ta kwankwasa kofar tace "Hamdan ka bude nice" jin muryan uwarsa yayi saurin tashi ya bude tace "Gashi maza kaci nizan koma". [2/2, 8:40 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 πŸ”Ÿ Ciki yakoma yana tunanin yadda zai tukari Rumaisa da wannan Al'amari shin idan taki amincewa bukatarsa ina zaisa kanshi? Ni Humairah nace kaika sani Wanda yace yaudara yasa gaba kuma ai karshensa baxai kyau ba, Koh abincin yakasa ci washe gari ranan litinin Bisma ta saba Jakarta sai wajen aiki da shiganta tafara arba da marasa lafya tuni taji wani tsusayinsu ta kamata, saida tayi reporting kannan akayi mata jagora zuwa office dinta inda zata dinga Attending patients. Zamanta keda wuya aka shigo da card din mutane haka tadinga Attending mutane, kowa sai yaba mata akeyi saboda hanzarinta wajen iya aiki, gashi turancinta daban yake hakan yanuna cewa baa gida tayi karatuba. Hamdan ne tsaye jikin Motarsa kirar BMW 4x latest version, ya juya baya inda tuni akayi mishi iso da Ruma, da zuwanta ta gane kowaye tace "Sannu tabbatacce Mara mutunci meya kawoka cikin gidanmu in short harabar gidanmu? You must be dreaming" Juyowa yayi fuskarsa babu alaman fara'a yace "idan mafarkine da baxanso in farkaba indai a harabar gidanku ne na gwam mace inta bacci har sai randa mafarkina yazama gaskiya, Ruma kidauka abunda yafaru tsakaninmu mukaddari ne daga Allah". "Allah sarki ustaz toh kasani bakada waje acikin zuciyana don haka get out of this house kafin inyi maka ihun kwarto" Hamdan yacire glass din dake idonsa yace "Go ahead kice ni kwarto ne Nasan iya kaci inyi gidan yarine koh? Toh ai mak'aranta ce kuma duk Wanda yashiga dole ya koyi darasi bakin ciki daya zanyi a gidan yari babu darasi akan SO". Rumaisa kallonsa take "Wato ya maidani wata bigi bagiro koh? Toh zanyi maganinshi, Tace "Kafin inyi irga uku kabar gidannan idan ba hakaba ba gidan yari ba duniyar zaka bari gaba daya" Maida glass dinshi yayi yace "Zan tafi nagode da kulawarki gareni amma kisani Allah da kansa yace yanason mai yafiya". Cikin Motarsa yashiga saida tayi gunji kannan yabar haraban gidan. [2/2, 11:28 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 1⃣1⃣ _*This page is dedicated to you Abdul-Aziz ILILEE Isma'il😘 Tnx for the Love and CareπŸ‘πŸ»RASHIN ADALCI yana bada magana keep it upπŸ’ƒπŸ».*_ Bisma ce tafe cikin motarta daidai roundabout din lahlah motor pack, sukayi kacibis da Nuru cikin Motarsa horn yayi mata daganan yadinga binta har saida suka shiga cikin unguwarsu, packing tayi shima yayi packing yafito yace "Beauty yakike kice harkin fara zuwa aikin waw bakiga yadda kikayi kyau acikin kayanki na likita ba, tabbas kin chanchanci yabo dole inyi miki kyauta ta musamman wacce ba kowa yake iya yiwa wata ya mace irinsa ba", kallonsa kawai Bisma takeyi waishin mafarki takeyi ko kuwa ido biyu ne Nuru ne kobashi bane, BEAUTY???? Ta tambayi kanta cikeda mamaki Tabbas dakwai magana a bakin Nuru kuma yaxama dole inbashi dama don ya furta abunda ke bakinsa. Nuru ne ya katse shurun da cewa "Inaso ki rufe idanunki, saboda inbaki gift din daya dace da kwararrar likita", ilai batareda ta wahalar da Shari'a ba ta rufe, wani katon kwaline nidai nakasa gane koh meye aciki amma, nifa Feedoh mukace sai munga abunda yake ciki laidar gaba daya zanen love ne ajiki, Yace "Gashi ya mika mata lokaci guda yace tabbas inaso alokacin dakika bude koh xaki bude kisa aranki cewa life most go on, the world most know dat a lion is a king, sannan karki bude idanunki har saina bar haraban gidannan". Haka akayi harya tada mota yafita sannan Bisma ta bude idanunta "wat a surprise, oh my God Nuru wat did I do to him to deserve such a huge amount of gift" tsintar kanta kawai tayi tana murna da kyar taja kayan cikin gida tana haki Ummi tace "Daga ina? Wannan kaya haka kasuwa kikaje ne?" Ummi ta tambaya tareda tsare bisma da ido. "Ummi NURU ne ya kawomun su nima dai cewa yayi in rufe ido kuma kar in bude har saiya tafi, Ummi bansan meye nufin Nuru ba?" Ikram dake tsaye tace "sonki yakeyi saboda naga alaman hakan a cikin kwayar idanunsa, yana cikeda shaukin ki don haka just kiyi accepting dinsa saboda daganinshi zaiyi jarumta a fagen nuna miki irin tasa salon soyayyan". Murmushi bisma tayi ta ajiye Wasu takaddu, da jakar dake hannunta ta fara bude kwalin wani kamshine ya doki hancinta nifa Feedoh kuwa ai har saida muka dunguri kwalin, saboda zumudi kati ne Wanda yake daukeda hoton zuciya, cikin zumudi Bisma ta kwashe su gefe wasu turaruka ne kayan sawa gaba daya zanen love ne ajiki lokaci guda taji wani kunya ya ziyar ceta da gudu ta haye saman bene sai Dakin. Fadawa tayi kan gado tana imagining yadda rayuwanta zata kasance da Nuru Wanda ayau ya nuna mata SO, tabbas wani hanin ga Allah Baiwa ne, Ashe Allah zai musanyamun da mafificin Alkhairi, Allah nagode maka. [2/2, 3:33 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 1⃣2⃣ _*this page goes to you ANEESA A RIMI,😘 thanks for the love and care may Allah continue to give you strength AminπŸ‘πŸ»*_ Ummi kawai dariya abun yabata tace, "maza ki k'washe kayannan kikai mata Daki, ita tasan yadda zatayi dasu wannan nakune yan'mata" dariya ikram tayi tadinga kwashe kayan tana kaiwa daki, Bisma tace "ikram am so lucky to have Nuru as my second love, he is damn kind oh ya Allah thanx be to you" ikram tace "Bisma haka daman haka Allah yake tsara abubuwansa batareda yayi sha'awara da mutum ba, Allah kadai yasan dalilin dayasa kuka rabuda Hamdan, Allah yasa yazaman miki garkuwa a rayuwanki" "Amin" Bisma tace haka ta dauki turaukan ta raba ma kanninta, Ummi kuwa tace bataso nasune na yara. Bayan Kwana biyu dazuwan, Nuru yakara dawowa amma wannan karan har office dinta ta isketa, tana ganinsa taji wani kunyansa tace "you are welcome have a sit", zama yayi yana kallonta yace "Nasan zakiyi matuk'ar mamak'in zuwana amma wannan karya daga miki hankali, nazo miki da proposal ne, dafatan zakiyi accepting dina hannu biyu, sorry fah nasan kina kan aikin ki ne na tsayar dake amma nasan bazanci lokaci mai yawa ba," Biro yaciro daga aljihunsa yace "miki hannunki". Babu musu ta mika masa ya rubuta mata kalman I LOVE YOU da manyan baki, saboda tsabar dadi Bisma kaman kanta zai fashe, itama biron ta ta dauko tace "miko hannunka amma saidai kayi hakuri ni bahaguwa ce" dariya yayi yace "shiyasa naga likitar tawa guruwace" itama I LOVE YOU ta rubutamai tana gamawa yace "nizan tafi banaso naci miki lokaci, kinsan turawa da girmama lokaci". Dariya bisma tayi tace Allah ya tsareka ya kareka, "Amin yace" a ranan da kyar bisma ta iya kammala aikinta, misalin karfe shida ta rufe office saboda abokin aikinta yazo. Waje ya fita tashiga cikin motarta tayi mata key amma taki tashi, fitowa tayi tana duba engine din motar da kyar ta tashi da isanta gida tayi wanka tayi sallah, tashiga ciki yan'uwa aka gaisa Bisma tace "Ah gaskiya umma aikin taimako da wuya yake fatana Allah yasa kada in gaxa wajen bada gudun mawata," Amin suka amsa dashi. Yaya salim ne zaune yace "a gaskiya bisma kinyi dacen masoyi Wato Nuru mutum ne Wanda baidau duniya abakin komai ba, baki gazu daya shigo gaida Ummi ba yadda kikasan yasanni" [2/3, 7:13 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 1⃣3⃣ _*This page goes to UMMI AISHA thank for the humble love and care, Am happy for you for the completion of your Novel RUWAN KASHE GOBARAπŸ”₯MAY WE SEE THE NEXT Lafya😍😍*_. Dariya Bisma tayi tace "Haka yake koh lokacin muna makaranta yakan bata lokacinsa don ganin ya farantamun rai ta Dan kaga mun rabu toh Hamdan ne yaxo saboda basa ga maciji dashi, don Hamdan yakance Nuru snatching zaiyi mishi" kowa acikin gidan yabon Nuru yakeyi ba'ayi wata gudaba Nuru ya sanarda Bisma cewa za'a turo gidansu, ranar murna a wajen Bisma dama sauran yan'uwanta ba'a magana, daddy kuwa yakasa zaune yakasa tsaye, saboda murnan tarban surukai. A Daren ranan daddy ya tarasu, acikin katon falon su, yace "Dalilin dayasa na kiraku shine, Kamar yadda ikram tace batada Zabi, toh nayimata Zabi Wanda zatayi Alfahari dashi, na zaba mata KAUSAR a matsayin miji kuma shima ya aminche dake ikram a matsayin wata bangare nashi, Kamar yadda kuka sani Kausar dandan abokina ne kuma Aminina" Ikram tunda taji ance kausar taji wani dadii acikin ranta daman ta Dade tanason Koda gaisuwa ce ta hadasu amma a yadda ta lura bai damuda magana ba, hasalima koh aboki bayidashi, Daddy yace "Ina fatan kin aminche ikram?" Saboda kunya tashi tayi da gudu tashiga cikin Daki, Rumaisa dake zaune tarasa abun cewa itama kanta daddy ya juyo yace "ke kuma Ruma tunda kin kasa fitowa da miji nazaba miki miji". Yana faden haka ya mike yafice, Ruma sarairai tayi tana tunani shin waye daddy yaza bamun a matsayin miji? Kanta take tambaya amma takasa samum amsa, Ummi ce ta dafata "Karkiji komai Ruma duk Wanda yazaba miki ki karba kiyi biyayya koba komai yaci arziki a matsayinsa na wan ubanku". Ruma mikewa tayi tace "Umma naji zanyi biyayya Allah ya kara muku Nisan kwana" "Amin" Bisma dake gefe tana duba wani katon littafi idanunta sanye da medical glass, ta juyo tace "Ninasan Wanda Daddy ya zaba miki kuma zakice na gayamiki" Ummi dake gefe tace "ke kin shiga uku ina ruwanki so kikeyi kisata cikin tunani toh inkin fasa". "Haba Ummi wasa fa nake mata Dan Allah kiyi hakuri wallahi so nake in rabu Daku lafya saboda nima gaba abani girmana a matsayin uwa, pls am sorry" Ummi dariya tayi tace "Amma keko akwaiki da abun ban dariya na hakura aini bakuyimun komaiba kuma Allah zaishi muku Albarka" Washe gari yak'asance ranar Asabar tunda sanyin safiya suka tashi, sunata aikin tarban bak'i Daddy kuwa tuni ya sanarda kawunnesa na kauye tuni suka hallaro, Ummi ta kware wajen yin kayan snacks, inda Bisma ta kware wajen iya sanwa, ikram kuwa wajen hada Lemuka nan tafi kwarewa, Ruma kuwa indai roasting ne da grilling toh nan tafi kawarewa, kuma duk sun koyi hakanne wajen Ummi saboda tun suna yara take shiga kitchen dasu shiyasa batada yar aiki ko guda daya, saboda bata yarda da masu aikiba saboda tsaro badan tsoro ba. [2/5, 7:25 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 1⃣4⃣ Alokacin da suka kammala aikine, *NURU* ya kira Bisma "My Love mun kusa isowa nanda minti goma go slow ne ya tsaidamu" dariya tadanyi mai kwantar da zuciya tace "Haba my destiny you don't have to worried we are all here for you guest" ikram ce zaune akan dressing mirror tana sheka kwalliya, itama taji wayarta tana ruri juyowa tayi taga wata bakuwar lamba jiki a sanyaye ta dauka tace "Hello" cikin sexy voice dinta, daga dayan bangaren aka amsa da "Sallama yakamata kiyi ba hello ba saikace ba yahudiya? Pls take note nasan zakiyi mamaki ganin bakuwar lamba toh inamai farincikin sanar dake cewa *KAUSAR* ne inaso in sanar dake cewa mun kusa karasowa nanda mintoci kadan ina fatan kina cikin farinciki dukda yaune zamu fara ganin juna" She's out of words tace "Allah ya kawoku lafya" ta kashe wayan saida tadau mintoci biyar tana kallon wayarta tana murmushi saboda sonda takewa Kausar dinta. Allah sarki Duk Wanda yaga Ruma abun bazai bashi sha'awa ba, saboda wani takurewa datayi saboda har yanzu tarasa waye wannan Wanda aka zaba mata a matsayin abokin rayuwanta? Kallon Bisma tayi tace "Bisma duk naga kuna cikin farinciki amma narasa meyasa Nina kasa samun farinciki, babu komai cikin raina sai tsantsar Tashin hankali, bansan dalilin dayasa tunda na wayi gari yau bana cikin walwala" Bisma tace "Ruma kenan Zabin Allah shine zabi ba zabin daddy koh mutum ba, karki sake kisawa ranki damuwa saboda wannan karamin abun, ki tashi maza kiyi wanka ki shirya cikin Expensive Cloth Wanda zaiyi suiting dinki, toh kowaye wallahi saiya yaba miki duk kasaitarsa haka duk mulkinsa" Ruma ta tabe baki tace "Nagode kwarai barina tashi, mikewa tayi zata shiga bandaki kenan wayarta tafara ruri juyowa tayi kaman bazata daukaba ikram ce ta taimaka ta mika mata wayar amsawa tayi takasa cewa komai, cikin hocky voice yace "My joy nasan kila kinata sa idon ganin call dina sorry for calling late kinsan you're the apple of my Eyes you're my nose without you baby I can't breathe for once" batasan Lokacin data fara murmushi ba dukda bata gane da Wanda take waya ba cikin muryan shagwaba tace "you don't have to worry your self sai kunzo" karaf ta kashe wayar........ Basu Dade ba saigasu cikin motoci nagani na fade, zan iya cewa iyayen NURU sune a baya wajen Arziki amma kwata kwata Bisma ba Arzik'insu takeso ba Annurin zuciyanta kawai take burin mallaka, Cikin falo aka shiga dasu Anyi musu tarban Arziki daga bisani suka fara abunda ya tarasu, anan aka tsaida watan aure wata uku, dukda halinda ake ciki na rashi Daddy yaso asa Shekara amma suka nuna su Sam basu yardaba, matan sukeso ba kayan kyalekyale na duniya ba. Haka yan'uwa suka kama hanyan komawa gidajensu, akabar Samarin da yan matansu donsu tattauna a tsak'aninsu, daga Bisma Har Ikram suna cikin walwala dajin dadii, Ranshin ganin ruma yasa Hamdan shiga wani tension, gashi yana masifar jin kunyan NURU dama BISMA. Ummi ce ta bude taga ta hangi Hamdan tsaye yana kada mukulli, ranta yayi kololuwar tashi, tace "Wato Ruma bata fita wajen Hamdan ba yau nida itane, dakinsu ta zarce tana kwala mata kira, Ruma! Ruma!! Ruma!!! [2/5, 8:04 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 1⃣5⃣ Kiranda Ummi take mata ne yasata dawowa daga tunanin data shiga Ummi ta kutsa Dakin ta wankama Rumaisa mari tace "Wato kega isassa shafaffa damai, ubanwa kika ajiye dakika wulakanta bawan Allah a waje koh bake yake jiraba ?" Rumaisa cikin muryan kuka tace "Ummi bansan me kike fadeba," "Toh maza kifita Ga Hamdan chan yana jiranki saura kiyi mai rashin kunya tabbas zaki hadu da fushina"... Tunda Ummi take bata taba daukan hannu tasa akansu Ruma da ikram ba saboda marayu ne mahaifinsu ya rasu tun suna kanana Ummi itace tazama Kamar mahaifiyarsu. Ruma tashiga tension tarasa kuka zatayi mezatayi oho, gyale ta dauka ta fita tana zuwa ta Tsaya tace "Ina saurarenka" juyowa yayi yana murmushi yace "Koda yaushe kara kyau kikeyi, sannan idan kina tsiwa gani nake Kamar in saceki, saurare kuma ai kingama tunda ga Hamdan agabanki mai shirin zama abokin rayuwanki" "Dakata ban wannan na tambayeka ba cewa nayi ina saurarenka shikenan sai ka hau bani Wasu tsoki burutsu? Look am not in the mood of talking pls you can take your leave" ta nunamai hanyan fita. Hamdan yace "koda kince kar in sake zuwa gidannan Rumaisa bazan kara zuwaba koda ranan daurin aurene baizama dole inzo ba kinga Lokacin da aka kawoki dakina kinga kinzama mallakina" cizon yatsa Ruma takeyi tace azuciyanta Wato duk abunda zanyi mai baxaiji haushiba toh ajuri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe. Mota ya bude yaciro wasu ledoji yace "gashi wannan shine tukwici na, na farincikin ansamun rana da abar kaunata Ruma" kallonsa ta tsaya yi "lallai nema hamdan ya rainani toh zanyi maganinka mik'a mata yayi yace "Gashi kidauka a matsayin wannan ce kyauta ta farko sannan ina rokonki da karki maida hannun kyauta baya". Mtwwwww wani dogon tsaki Ruma taja tace "ka maida abunka banida bukata ai ban rokaba koh nacema ina yunwansu ne?" Dukda abunda hamdan ya tsana shine tsaki amma saiya nuna bakomai, yace toh shikenan ngd kwarai da kika bani lokacinki ki gaida Ummi, da sauri tabar wajen shima yayi kaman ya shiga mota fitowa yayi ya samu mai gadi ya mika mishi kayan yace kashiga dashi ciki kacewa Ummi injini abawa Ruma babu yawa. Haka mai gadi yashiga yayi yadda akace masa, Ummi ranta yakara baci tacema ma mai gadi "kin amsa tayi? Shiko yace "Eh hajiya yanata magiya amma saita gayamai magana". Ummi tace "Nagode yi tafiyarka, kayan ta kwasa tashiga cikin Dakin ta watsa mata tace "Amma Ruma ke munafuka ce Ashe dakwai ranan da zamuyi miki Abu kice bamu iyaba? Toh kisani koh kinaso koh bakyaso aure da hamdan ba fashi sannan idan har kika kasa yimai biyayya wallahi babu yafiya tsakanin mu dake inhar kuma kinada wani zabin kiyi magana". Fuuuu Ummi ta fice Kamar zata tashi sama, tabar Ruma zaune tana kukan bakin ciki saboda bata taba tunanin Hamdan yazama mijinta ba, Ranan da akasa kowacce zataje gaida dangi Dukkansu haka sukaci kwalliya Kamar ranan aurensu, kowacce farincikinta ya dauketa, sukayi dangi Ruma dai saida tasamu yan rakiya guda biyu Abeeda da Aneesa, Haka sukabar shinkafi zuwa garin Gusau, Abeeda da Aneesa suketa magana amma ruma koh kwakkwaran motsi batayi. Bayan filin polo dake cikin Zamfara suka isa wani gidane tank'ameme mai suna ihunka banza, tuni Aneesa tace "Inane nan?" Hamdan yace "Yankaku zanyi inyi kudi daku Nasan kan wata acikinku zaiyi tsada" kutsakai yakeyi har packing loge ya tsaya yan gidansu ne suka fito suna dariya suna ma Rumaisa maraba, tuni yan gulma akafara Anya ba inyamura yaya ya Jajibo mana ba? [2/6, 7:52 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 1⃣6⃣ Saboda tsabar farin rumaisa duk Wanda yaganta zaiyi tunanin inya murace, ganin yadda kowa yake kallonsu ne yasa kowacce tashiga *frowning mood activated* Gashi sunci uban kwalliya sannan dukkansu buba mai dogon hannu suka saka shigardai Tasu kaman bata hausawa ba kowadai yasan mafi akasari yarabawa ke irin shigar koh inyamurai. Shiko Hamdan farincikine fal cikin ransa, "Tabbas na iya zabe nasan kowa zaiyayi maganan Ruma" kanwarsa ce Nabilah tace "kushigo mana saikace wasu Baki", Tafe suke zasu shiga Abeeda taji wata na cewa "yasin Kamar inyamurai tunda har yanzu sun kasa magana sai wani hada rai da sukeyi abun gwanin kyama" Aneesa data kasa hakuri tace "Abeeda nikam haushin wasu halittu nakeji saboda gaba daya idan kafisu kafisu saboda me nace haka bazasu taba taranka sugaya maka magana ba sai a bayan keyanka" Ai gaba daya sai sukayi sarere, wani palo aka kaisu yasha kayan Ado amma Dayake sun saba ganin irinshi sai bai basu sha'awa ba. Anyi musu tarba na mtunci, mahaifiyar Hamdan ce da sauran abokan zamanta, ganinsu Rumaisa yasa duka fara yar kallon kallo, yake sukayi ganin su Abeeda na kallonsu sukace "Maraba dayan shinkafi, shinkafi garin manya garin kyawawa, maraba maraba lale marhabin, zama sukayi har kasa su Ruma suka gaidasu cikin ladabi amma kwata kwata mahaifiyar Hamdan bata gamsu cewa su Ruma bahaushiya bace kuma yar Asalin garin Shinkafi ba. Kowa yan'uwa saida sukazo ganinsu kuma ba komai bane su nabila ne suka feshesu cewa suzo suga matar da Hamdan zai aura, mahaifin shi kansa saida yashiga ko kwanto, sudai su Abeeda da Aneesa saida sukaci sukasha itakoh ruma duk a takure tace, basu wani jimaba Ruma tace ma Hamdan "Mudai zamu tafi mun gaji da kallon yan kauyen da danginka suke mana sai kace yau suka fara ganin mutane" Tashi sukayi sukace a tare "Zamu wuce saboda garin namu dakwai Dan tabi" Tuni mahaifiyar Hamdan ta ta tashi ta hado musu sha Tara na Arziki sannan suka kama hanyan komawa shinkafi. Haka suma ikram da bisma tafiyar Tasu ta kasance sun tsinci Kansu cikin farinciki dajin dadii saboda samum abunda zuciyoyinsu ke muradi, bayan sati gudane wata gagarumar kura ta tashi acikin family dinsu Hamdan nacewa su Sam basu yarda hamdan ya auri Rumaisa ba saboda sunce irin dadaddun inyamuran nanne masu zuwa garin Wasu suyi kaka gida harsu hayayyafa su musulunta, Hamdan yashiga tension saida ya kusa haukace musu sannan sukayi lakwas. "Gaskiya inason Ruma Abba, saboda kawai kungasu farare shikenan saikuce musu inyamurai, su kadai aka raina ai duk farinsu basu kai yan gidansu Laila Ibrahim ba sudama suke Kamar larabawa , haka nakeso abata koda bayarabiyace zan aura tundadai musulmace yar'uwata" Abba dake zaune yace "dakata Hamdan kada so ya rudeka ka kasa tantance baki da fari, har Yanzu bakasan komaiba maza ka bacemun daga gani sainayi bincike" [2/6, 3:13 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 1⃣7⃣ Haka Hamdan ya fita, Dakin mahaifiyarsa yashiga yayi Sallama ya zauna Abunka da 'da' da mahaifiya ta matso kusadashi tace "Hamdan kayi hakuri komai mai wucewa ne, nikaina na yarda Asalin zamfarawa ne saboda naga akaman sunsha zamfaranci sun koshi, amma tunda yace saiyayi bincike kabarshi a haka kaci gaba da Adu'a kana Neman zabi," Hamdan yace "Innanmu bakisan daya Ruma ta Aminche dani ba har yanzu ba wani matsuguni nasamu acikin zuciyanta ba taji wannan abun nasan confirm cewa zatayi tafasa gaskiya Nidai abar maganar nan gaskiya inhar bahaka ba xan iya yin komai Wallahi matukar wannan maganar takoma kunnen iyayen Ruma sukace anfasa". Tashi yayi yashiga cikin Daki, Ruma yakira saida yakira sau goma kannan ta dauka, yace "My love dafatan kun huta gajiya?" Rumaisa tace "Bansani ba toh inaso kasani bani bakai tunda har yan'uwanka suka kiramu da inya murai toh ka sanar dasu nima bazan taba hada jini dakuba, jinin munana kawai Kaidinma Allah yasa ba'a gidan marayu suka tsintoka ba mtwww" taja tsaki ta kashe wayar gaba daya. Taci gaba dacewa "banda sun raina mana wayo daga sunganmu farare toh banda Ai dadinta bamu mukayi kanmu ba, tab farare sun bani Yanzu da irin wannan sharin za'a dinga aibatamu, ni humairah nace Allah yasoni wankan tarwad'a ceni😜. Hamdan tuni yaji wani jiri yana dibansa salati kawai yakeyi cikin karfin hali ya fita yana dafa bango harya isa Dakin mahafiyarshi yana shiga ya fadi yana rikeda Kokon zuciyansa, ihu nabila tayi tana kiran taimako asibiti aka wuce dashi, Ana zuwa aka kira likita, Bisma ce tsaye tace kufita kubamu waje tukunnan, itada nurses kawai aka bari abun mamaki Hamdan tagani lokaci guda taji wani mugun haushinsa inama ya mutu kowa ya wuta da wannan guban, tawani bangare saitaji tausayinsa Dana kanwar ta Ruma bazataso ta rasa shiba saboda shi aka zaba mata a matsayin miji. A iya gwaje gwajenta ta gano cewa yana dauke da ciwon zuciya sanadiyyan natsanancin damuwa daya shiga, drip aka sa mishi sannan ta fita tace "zai samu sauki amma wacece uwarshi tabiyoni," cikin rashin tarbiya Bisma ta fadi Nabila tace "Wannan likitar yar rainin wayoce gata yar k'arama Allah yasoki asibiti muke da saina lallasaki yasin" mtwwww taja tsaki ta tabe baki. Suna shiga cikin Office Bisma ta zauna ta kalli mahaifiyar Hamdan tace "Saikinyi hakuri kinsan dayake farar fatace inyamurace ni ba Hausa na fiye ganewa ba" kawai taci gaba da cewa "A gaskiya danki yana cikin matsanancin hali kuma duk ta sanadiyyan damuwa a Yanzu haka yana dauke da cutar damuwa Wato (hypertension) inji turawa idan har ba'a samu mafitaba toh sai anyi masa *DASHEN ZUCIYA*" Zare ido mahaifiyarta Hamdan tayi tace "likita menene abunyi yanzu?" Tace "Abunyi shine idan ya farka saiku tambayeshi damuwarsa idanya fadi saikuyi mishi magani damuwarsa don muna bamuda maganin rage damuwa saidai idan har Zuciyarsa ta kasa toh shine nace zamuyi mishi *DASHEN ZUCIYA* Bisma mikewa tayi tace "Muna iya fita dakwai magunguna dazaran ya Tashi kubashi Donni gida nayi tun daga shinkafi nake zuwa nan". Fita sukayi Bisma tace "Kadan ga Gani tunda kuka hada jininmu da inyamurai mun dinga kenan" mtwwww taja tsaki. [2/6, 7:36 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 1⃣8⃣ *This page goes to you Ladies name seeks AYUSHA ILIYASU, AYSHA SAYADI, AYUSHA MUHAMMAD, AYSHA GANA, AEESH CHUCHU, AYSHA WAKILI😘😘 love you all the A's Allah ya albarkaci rayuwar mu baki daya yasa kufi haka a Rayuwa.* Komawan bisma gida keda wuya, tasamu umminsu tace "Ummi kun kasa gane koh waye Hamdan Wallahi Sam ba chanchanci abashi ruma ba Allah kuwa Ummi" Ummi tace "dallah yimun shiru kotanaso kobataso aure ba fashi, saidai ta mutu irinkune masu zuga kanninku idan suna gidan mijinsu toh Wallahi kar inji kar ingani, idan tanaji zabin da mukayi mata baiyiba toh saita kawo nata zabin amma tasani duk abunda yabiyo baya ita tasani". Tashi Ummi tayi tabar Bisma Zaune ita kadai, itama tashi tayi tashiga dakinsu, ta taradda Ruma kwance tana tunani, dafata Bisma tayi tace "Ruma albishirinki" Ruma tace "Goro" "Fari koh ja?" Ruma takara cewa "Fari kal" "Toh hamdan yana asibiti rai kwakwai mutu kwakwai, ciwon zuciya". Zare ido Ruma tayi tace "Kaddai maganar Dana fadane yasahi ciwo? Take tambayan kanta, karajin Daddy sukaji daga kasan bene yana kwalawa Ruma kira, gabanta ya yanke yafadi da sauri tafita jikinta babu inda baya kyarma, tana isa ya kwasa mata mari yakara kwasa mata mari yace "Wato ke ruma kinaso kice banina haifeki ba? Kinaso ki gayawa duniya cewa niba ubanki bane rikonki nakeyi? Amma kunyi kuskure bantaba muzantaki ba acikin gidannan tun kuna kanana kawo yanzu amma shine ni kikeso kizama silar batamun rai da suna? Toh Ruma baki isaba kinyi kadan Wallahi ko Fatima bata isa inkafa doka ta taka ba ita datake mahaifiyarki". Kallonta kawai yakeyi cikeda baccin rai tuni ya fashe da kuka saboda Ruma da ikram amana suke a wajenshi ya zaiyi da rayuwansa gashi ya muzguna ma Ruma, Nidai banga laifinshi ba itadai ruma tanaso ta bijirewa umurnin wan abuntane kawai ba wani abuba, kuma batada Wanda zata tsayar idan tace batason Hamdan, kodai yaya Salim takeso? Muje zuwa mahaukaci yahau kura. Rumaisa ta durkusa har kasa tace "Daddy na hakura kuma insha Allah bazan sake bata maka raiba sannan abunda nakeso a zuciyana daddy nabarwa zuciyana, fatana daddy kashi mana albarka" tuni wani imani yazowa daddy yace "Kije na hakura amma kisani inyamura da sukace miki kidauka kuskure ne sannan ina umurtanki daki je cikin garin Gusau gobe idan bisma zata aiki don naji labarin achan aka kwantar dashi". "Toh" tace ba musu tundaga ranan ruma tasawa ranta Salama, tana rokon Allah daya sanya mata natsuwa da Hamdan, washe gari suka shirya tsaf direba yadauki mota, Bisma tanajan tata, tafe suke Bisma take labartama Ruma yadda sukayi da iyayen Hamdan da irin wulakancin data musu, da isarsu asibiti suka kutsa kai duk inda Bisma ta gifta gaidata akeyi saboda halin girman data nuna musu. [2/6, 8:09 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 1⃣9⃣ _*AUTAR HAJIYA* ban manta dakeba da kina raina *UMMI ADNAN* kema kin chanchanci in gaidaki, Ina kuma *RASHKARDAM* kema ta kwarai ce *MJAY* kema aminiyar arzikice, ina kuga ganomun *MISS XOXO* ina kaunarki my heart beat for you, Ina *MAMAM USSEEY* banida abuncewa sai godiya, Allah yabar zumunchi Amin😘_. Office Bisma tafara shiga, wayar data fara amsawa ta mai sanyinta ne, bayan sun gaisane tayiwa su Rumaisa jagora zuwa Dakin da aka kwantar da Hamdan, muryar Rumaisa kawai yaji ya bude ido lokaci guda yaji sonta yana kara shigarshi, Nabilah suka Gani ta amsa a yatsine Bisma tace "Ina Babar taku yasha magani kuwa?" Nabilah tace "Baxan iya saniba saidai kijira zuwa anjima taje gida ta dawo". Bisma tace "Kinsan cewa bacin banso inci haram koh kallon dakinnan baxanyiba, saboda your are not my type kingane, so ga kannina nan inajin kingane Wannan ta nuna ruma tace itacedai wacce kuka danganta da inyamura kuma yaxama wajibi Ku hada zuri'a damu, kallonsu Ruma tayi tace Ku zauna kujirata kila ta dawo yanzu". Nabilah irin yarannan ne marasa kunya, kuma babu Wanda ya isa yace mata bari tabari saboda taurinkai irin nata, waje ta tashi tafita tabar Ikram da Ruma acikin dakin shidai Hamdan koda kallon Rumaisa aka barshi ya warke, saboda jiyake Kamar ya rungumeta, ganin irin kallon da Hamdan yakeyi wa Rumaisa ne yasa ikram tafita batareda Ruma ta saniba, ganin ikram tafitane Hamdan yayi kokarin tashi amma kirjinsa ya sarkeshi yarasa, me yake masa dadi lokaci guda yafara kiran Ruma. Juyowa tayi bataga kowa ba, tashi tayi ta matsa kusa dashi, tana mishi sannu tace "Ka k'oma ka kwanta basai ka tashiba" Hamdan yace cikin muryan ciwo yace "Rumaisa kece annurin zuciyana kice kinasona ko sau dayane kozan samu saukin abunda yake damuna Rumaisa kece silar ciwo na, Dakin ce Wallahi zan warke" kallonta yake cikin ido gashi ya rike mata hannu kauda kanta tayi yace "Ruma juyo ki kalleni kice kina sona in warke daga wannan cutar" har hajiyarsu Hamdan tashigo basu saniba jira kawai take Rumaisa tace tanason danta amma Ruma taki magana. [2/9, 3:43 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 2⃣0⃣ Hamdan dake kwance riris yace "Pls say something pls my own" kallonsa tayi tace "I love you dearly I quest cewa zaka samu sauki yanzu?" Kallonta yakeyi cikin karfin hali ya mike da karfinsa yace "Kin yarda da cewa ciwon sonki ne ya haifarmun da ciwon zuciya?" Ruma ta gyada kai alamun eh ta yarda, Hajiyarsu Hamdan tayi Sallama lokaci guda Rumaisa taji wani irin kunya dukta lullubeta ta sinna kai cikin gyale yace "Ina kwana ya mai jiki?" a takaice Hajiya ta kalli ruma daga sana har kasa tace gaskiya Hamdan zaku haifi yara farare Ruma akwai fari Kamar tsada. Hajiya tace "Da sauki" Ruma tace "tareda direba muke yanzu zamu tafi" hajiya tace "An gode kwarai Allah ya saka da Alkhairi" Amin Rumaisa tace. Suna fita sukayi wa Bisma Sallama suka wuce Shinkafi, Kwanan Hamdan uku a asibiti aka sallameshi Rayuwa ta kasance mai dadi shida Rumaisa haka soyayyar yam mata ke bani sha'awa musamman ranan da samarin suke tsarawa don zuwa su sada zumunchin soyayya, iyayensu sai murna suke dafatan Allah yasa farincikin su ya daure har yaumuttanadi. *BAYAN WATA BIYU DA SATI DAYA* Ka mai yawan rai biki ya matso ya karato yan' uwa dangi na nesa Dana kusa sunata lisafin ranar wannan gagarumin aure, acikin haka ne Rumaisa ta kamu da wani mugun ciwo Wanda kuraje ke fito mata a fata anrasa wane irin kurajene lokaci guda tazama abun kyama, dukda ba wari takeba amma abun ba kyan gani, Nan mahaifinsu ya tuna da wani ciwo datakeyi tun tana karama ina tunanin shine ya dawo yanzu kuma babu inda za'a iya samun maganin abun sai a kaiyen Mada dake cikin jahar zamfara, zamanta achan shine kawai maganin wannan ciwon nata, ran Kowa ba dadii ciki harda na Hamdan gaba daya yaji ya karason Rumaisa, kallonta yakeyi yace "Rumaisa zan soki har karshen numfashina, indai acan garin mada zaki samu sauki zanbiki duk inda zaki" kuka kawai Rumaisa takeyi tace "My Own zuciyana Takasa samun sukuni ganin irin ciwon danakeyi nasan yan'uwanka bazasu soni ba" "Kidaina kuka Ruma digan hawayenki Kamar digon dalmane acikin zuciyana kisa aranki ni nakine kuma aure ba fashi dani dake sai an buga mana taken so". A haka mahaifin Su Ruma yakira iyayen Hamdan ya sanar dasu, a waya suka amsa da bakomai amma Bayan wayan, sukace Sam dansu bazai auri miskiniya ba kilama ciwon kuturta garesu, maganganu iri daban daban harya kaiga kunnen Hamdan yadinga bori shi gaskiya saiya auri Ruma ita yake kauna yakeso koda dukiyarsa zata kare akan Neman lafiyar Rumaisa shi yaji kuma yagani. Abun sai mamaki yakeba yan'uwa tuni mahaifin Hamdan yace anfasa auren kowa yakoma gidansa Hamdan koh ajikinsa yace "Idan kunki Tara jama'a don aurena toh tabbas zaku tara jama'a takai danku kushewa" fit ya fice gidan Aunty dinsa yaje yake sanar da ita halinda yake ciki batayi kasa a gwiwa ba suka hada wani shegen plan Wanda ni kaina saida na girgiza. Kubiyo yar MUTAN ZAZZAU donjin wani plan ne wannan? Kuyimun afuwa rashin wuta muke fama dashi shiyasa kuka jini shuru. [2/10, 7:26 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 2⃣1⃣ Hamdan yace "Aunty ya za'ayi?" Tace "duk yadda za'ayi ka dauko Rumaisa ka kawota gidannan, nasan za'a bazama nemanka babu Wanda yasan inda zakuje, sai kuzo nan dakwai wajen dazan ajiyeku sannan, duk sauran plan din saidai kayi nasaran dauko Ruma matukar tana sonka toh dole ta biyoka" hamdan yaji abun ban barakwai anya zai iya yake yambayan kansa wani tunani yashiga inda batareda bata lokaci ba, Aunty dinsa tace "Maza ka kama hanyan Shinkafi ka aiwatar da abunda nakeso". Cikin gaggawa ya kama hanyan, cikin haddadiyar Motarsa, sai shinkafi kofar gidansu Ruma ya tsaya ya aika akirata amma batareda yafadi sunaba, cikin ikon Allah kamar taji a jikinta hamdan ne, tafito sanye da doguwar Riga wacce ta lullube kafarta da hannunta daman daganan matsalar take, kallon juna sukayi suka sakarwa juna wani murmushi mai kawata zuciya, hamdan yayi saurin cewa "Nasan sak'o ya isheku daddy na yace kowa ya watse babu biki, Rumaisa inasonki zanyi duk yadda zanyi ganin kinzama mallakina don haka tafiya zamuyi karkiji komai babu abunda zai faru matukar kina sona dole kiyi abunda nakeso" tuni idanunta sukayi rau rau "yanzu My blood meye makomar guduna daga gida kana ganin haka bazai kawomun matsala ba?" Hamdan yace "babu abunda zai faru matukar su hajiya suka aminche na aureki tom zanyiwa kowa bayanin dalilina nayin haka, ruma kidubi girman Allah da son da nakemiki, kizo mutafi" batada wani choice saina tabi shi gudu yakeyi a mota cikin Awa daya da rabi suka isa cikin garin zamfara, basu zarce koh inaba sai Bayan Asibitin yariman bakura, cikin gidan suka shiga hankali kwance tuni Aunty din Hamdan ta tarbi Rumaisa ba tareda ta k'yamaceta ba. Gida tuni ya rude ba'aga Rumaisa ba, har garin Gusau suka je amma iyayen Hamdan sukace aisu sunce anfasa biki saboda bazasu hada jini da musaka ba, Yaya salim daya fusata yace "Ina danku indai muka ganshi toh sai kanwata ta fito don babu inda zamuje" Mahaifin Hamdan yace "Kuna iya zama Ku jira shi Donni kunga tafiyata". Fita zaiyi yaya salim yace "Babu inda zaka saika fitomun da kanwata inada daman kamaka saboda inada ID card, yaciro IDCard dinsa na shedar zama Police mai Anini, kana iya bina police station Tunda naga abun naka da rainin hankali" tuni gida ya rude haka yaya salim yayi matching din Mahaifin Hamdan har police station dake hanyan unguwar gwaza da kauran namoda. Ciki suka shiga da isarsu kawai suka fara sarama yaya salim, cikin kankanin lokaci yayi report din dinsa aka sakayashi, mahaifin Hamdan cewa yakeyi "Da girmana da muk'amina kusani a Bayan kanta ni Wallahi bansan inda Hamdan yakeba haka yarku," Yaya salim yace "Banyarda a bada belinsa ba harsai yafito mun da dansa tareda kanwata". Suko su hamdan tuni suka fara plan tuni suka samo wata yar kwalbar magani sukayi da sunan poison ne aciki, Cikin rudu Aunty takira wayar mahaifin hamdan tace "Yaya ba ga hamdan da Rumaisa suna shirin shan poison su kashe Kansu Dan Allah kuyi gaggawan zuwa" cikin rudu Alhaji yace "wat????? Dan Allah kutaimakeni ga Dana chan zai kashe kanshi zaisha poison shida yarinyar da ake nema banaso inrasa Dana Ku taimakeni infita daganan," cikin gaggawa wani corporal ya ruga yakira yaya Salim yasanar dashi komai, batareda bata wani lokaci ba suka isa gidan kafin suzo ai tuni Rumaisa da Hamdan sun kwankwade sai gasu a kasa suna fitarda wani kumfa a bakinsu ai Aunty ta kara rudewa tana cewa "Hamdan inace ba poison din gaskiya bane pls kar kayimun haka Alhakin duk a kaina zai kare, da jiniya suka isa gidan suka tadda hamdan da rumaisa kwance basuko motsi. [2/10, 10:13 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 2⃣2⃣ Cikin sigar rudewa sukayi kansu, da gudu tuni aka sanarda yan'uwa kowa hankalinsa ya tashi tuni mahaifin Hamdan yafara daya Sanin abunda ya aikata cewa yake "Hamdan karka mutu kabarni cikin kunci, ka kadaine Dana namiji magajina yaza'ayi kazabi mutuwa akan Rayuwa saboda mace, kadawo Dan Allah Wallahi zanyimaka abunda kakeso zan yarda ka auri Rumaisa Tunda itace zabinka" kuka yakeyi wiwi inda yaya salim yaji kamarya shake mahaifin hamdan wani kukan kura yayi yace Wallahi baxan barkaba Kaine sanadin mutuwar kanwata Kasani koda rankata kaf abunda muka Tara zai kare sainayi kararka" mahaifiyar Hamdan tace "Hamdan karka mutu kabarmu cikin kunci da fargaba da mutuwarka kwara mu aminche da auren ka da Rumaisa Dan Allah kayi magana Hamdan munyi maka Alkawarin sama maka farinciki tun ranarda kazo duniya Dan Allah ka farfado pls and pls". Shirin dibansu akeyi Tunda rai yariga da yayi halinsa hamdan ya bide ido Wanda suka kada sukayi jajir yace, "hajiya Ku aminche mun na auri Rumaisa itace muradina, karkuyi gaggawan rabamu, tuni sukaji wani irin dadi, lokaci gida Rumaisa itama ta bude fuska tana zubda hawaye da gudu ta rungume yayanta tace "Yaya Hamdan masoyina ne bayaso ya gujeni Lokacin da abu ya sameni ba laifin kowa yaya munyi hakanne don abarmu mu kasance tareda juna koda kowa zai tsaneni nasan hamdan will always be by my side we are bound to be together for life" share mata hawaye yayi tuni hamdan yaje wajen yaya salim Yana kuka yace "kayafe mun babban yaya banyi haka don muzgunama rayuwarka ba nayine don in sama ma kaina yanci sannan iyayena su aminche da aurena da Rumaisa" yaya salim yaji wani mugun tausayin Hamdan yace "karka damu aure dakai da Ruma babu fashi nanda sati biyu". Nan kowa sai murna yakeyi amma ran mahaifin Hamdan baiso ba, lokaci guda yaji ya tsani Rumaisa da haka ya cusawa kuwa kin ruma, Bisma kuwa ba karamin tashin hankali tajiba da akace musu Ruma ta rasu haka ikram nabil kuwa ai kuka saikace Wanda komai ya kwance musu haka su nuru sukaji wannan ciwon, Kausar kuwa ai yakasa koda kai ruwa bakinsa saida yaji comfirm komai yayi daidai, Nan aka cigaba da shirye shiryen biki masu gyran jiki aka kira nimadai ba'a barni a bayaba saida na tabbata nima an gyrani Kwarai saboda koh nima zanyi market, Amma Rumaisa gaba daya bata cikin hayya cinta sabanin su ikram da bisma da suketa farinciki. An kawo akwatina Wanda Yazama al'adar bahaushe Wanda inhar ba'ayi ba saiya zama abun zunde da gulma. *KAMU* Ranar juma'a ne kamu Anata shiri takota ina, ready made din kaya aka yimusu oda daga KANO harda hand fan da purse Wanda kudinsu yakai kimanin naira dubu sittin sittin, na Rumaisa yafita daban saboda arufe annoban daya sameta, mai dogon hannu akayi mata Farincikinta data daman ciwon banda fuska nan aka kira musu mai makeup HummiesTouch ce taxo ta gyra Amare Wanda yakai kimanin naira dubu hamsin hamsin saboda kwana biyu ne da ranan kamu da ranan biki. Tuni yan'uwa daga dagin Ummi Dana daddy Dana mahaifiyar su ikram, anacan ana shirya wa amare gida, Rumaisa itama anan Gusau zata zauna amma anyi hakanne don dazaran anyi auren kasar Miami xasu tafi don ganin kwararren likita akan ciwon fata, Don Hamdan bai yarda dawani zaman kauyen mada ba, haka aka fara shirin tafiya abun haushi abun farinciki, shine a dangin hamdan babu Wanda ya isa wajen reception dinnan, sai Yan tsiraru haka akayi kamu amare da angwaye abun azo a gani, haka aka yi taron aka watse cikin kwanciyan hankali. *Ranan Biki* An shirya tsaf ana hidimar biki, gida yacika misalin karfe biyu na rana ne aka daura aure. *NURU ZUNNU-RAYN da Amaryarsa BISMA IMAM HASSAN* Daganan aka dawo kan *HAMDAN MUNNIR HAMEED Da Amaryarsa RUMAISA IMAM HUSSAIN* Bayan nan aka daura auren *KAUSAR ADAM Da Amaryarsa IKRAM IMAN HUSSAIN* Dubban daruruwan mutane suka ziyarci wannan bikin har daga gidan gwamnati gwamna ya aiko Babangida Mayanan Gusau donya wakilceshi, haka akayita busa sarewa garin Shikafi ba masaka tsinke abunda zai baka sha'awa Shine yadda naga jar fata Wato turawa. Kowacce haka aka kaita gidanta babu wani bata lokaci Wasu sun kwana Wasu kuwa cikin Daren suka dawo. Saidai muce Alhamdulillah. *TARIHIN ZURI'AR IMAN* Family din iman karamin family ne Wanda zamu iya cewa gidane Wanda mata daya take zaune da mijinta da yayanta cikin rufin Asiri, Alhaji iman Dan asalin garin Shinkafi ne ya haduda Matarsa Ruma a bakin rafi inda ake kamun kifi har soyayya ta kullu a tsakaninsu harta kaiga sunyi aure cikin gidan gandu suke zaune, Ta shafi shekara goma bata haihuba har aka fara yimata gorin haihuwa takan shiga daki tayi kuka maicin rai Wanda saita baka tausayi haka iyayensa suka matsa saiya kara aure amma ya nuna bayida raayi, haka sukaci gaba da tsangwamanta bayan wata bakwai cikin dare Ruma tafara ciwon ciki adaren sukaje asibiti likitoci sukace ai haihuwane Iman yayi mamaki Kwarai yadda ruma takasa sanar dashi cewa tana da ciki hasalima ita kanta batasani ba Tunda dakwai yarinta amma Kullun taje gida sai mahaifiyarta tace Ruma anya ba ciki gareki ba tace ah ah banida komai, Haka ta ci bak'ar wuya shine Allah ya azurtata da Hassan da Hussein. [2/12, 1:18 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 2⃣3⃣ Tunda ta haifi yan biyu bata sake haihuwa ba har suka girma rana daya gobara ta tashi Lokacin duk suna makaranta haka ta lashesu suna bacci anyi bakin safiya haka suka girma har sukayi aure duk a cikin maraici gashi kwata kwata yan'uwansu basu damu da shiga harkarsu ba, haka sukayi gini a cikin garinsu don sunce babu inda zasu sunacikin mahaifarsu, haka suka haihu dayake Uwani bata haihu da wuri ba saidaga baya Allah ya azurtata da yaya mata su biyu da Ruma da ikram, shiko HASSAN yaransa biyar daya mace hudu maza, haka Hussain ya rasu Tunda kuruciya a dalilin hatsarin mota, dalilin dayasa aka kwashi yayan akaba Hassan kenan, shiya girmar dasu har aure Wannan kenan. ******* Bisma ce kwance akan kafar Nuru suna sha'aninsu suna hirar soyayya, tajamai gemu yaja mata hanci, labari suke suna dariya duk Wanda yagansu yasan cewa ma'aurata ne masu cikeda wadatar zuciya, karfe 12:00pm daidai ne Bisma ta tashi tace "my husband bari inshiga kitchen inyi mana lunch kasan anjima munada manyan baki kasan yan gidanku xasuzo yakamata mu kammala komai in time" kallon ta yayi ya sunkuceta sai kitchen, tare suka fara aikin har suka gama anan bisma tagane cewa mijin nata is a nutritionist duk wani abun Gina jiki yasanshi saboda wata makarantar cooking and pastries dasukayi attending Lokacin suna kasar America, haka yayita kai abinchin dinning wayarta ce tayi kara lokaci guda nuru ya matsa kusa Bisma dake kitchen tace "my kadauka pls am busy ryt here" Haka NURU ya amsa yace "Hello" Daga dayan bangaren yaji ance "Doctor here is an emergency and we seriously need your help" sai aka kashe wayan NURU yashiga kitchen ya kalleta yace "baby your help is needed at the hospital Call din danayi receiving kenan". Dagowa tayi ta karewa Nuru kallo taga kaman ransa baiso ba, "tsame hannunta tayi tsam daga gyran fruit din datake tace "Honey lafya naga duk ranka ya baci nasan is a mistake sunsan cewa hutun one month aka bani kuma am not the doctor on duty pls saki ranka bari na kira dean din asibitin inji daga bakinsa, falo ta wuce komai na jikinta kadawa yakeyi nuru kallonta kawai yakeyi yarasa meyasa komai na bisma yake burgeshi ta dauki wayar ta zauna ta kira number nan sukayi magana akabata hakuri akace taci gaba da Honeymoon dinta. Mikewa tayi taje ta janyo hannunsa tace, "you are a blessing to me and you are my world darling I can be a full wife without your support my dear I need you support towards my profession I need to help the needy as wel the sick people pls" tafadi suna shak'ar numfashin juna. Rungumeta yayi kwarai a kirjinsa tace "karki damu bazan barkiba my love you mean the world to me bana fatan kirigani mutuwa nafiso rana daya ta rikemu mutafi chan muzama mata da miji a aljanna, abunda banaso shine yadda kike damun kanki da karatu kinsan cewa bawa yana bukatar Hutu ina sonki bisma idan nace miki your are the breath I breathe pls kice kin yarda" yafadi tareda zura mata harshensa a kunne lokaci guda tayi wani ihu ta tashi tana yimai chakulkuli, tuni suka fara zagaye acikin wada taccen falon su. Nuru Kullun kara sonta yakeyi saboda kula datake nunamai, haka suka tashi sukayi wanka tare hatta abincin tare sukeci kwano daya chokali daya kofin shan ruwan su dayane, haka suka fito daga wanka suka fara shiri haka Nuru ya zage yana shafa mata mai itama haka tayi mai hatta kwalliya yace shizai mata haka ya chab'a mata kwalliya dukda bata mata fuska yayi amma haka tace "my Wallahi baka iya kwalliya ba amma kasan me" nuru tace "Ah saikin fadi" Tace "Am proud of my husband zan iya zuwa gaban kowa in tsaya da wannan kwalliyan saboda ba kudi na biyaba miji na yayimun". K'washewa NURU yayi da dariya tashi tayi ta fito mishi da kaya ta shirya shi tsaf, itama haka yaciro mata kaya masu kyau da tsada haka taci dauri falo suka koma suna tsumayen bakin su, da NURU ya kalli Bisma saiya kece da dariya ita kuma tawani poze, Suna cikin guje gujene sukaji ana knocking Bisma tana nizan bude nuru yana shizai bude abun mamaki suna budewa sukaga mahaifiyar Nuru itada yan'uwansa da yan'uwa tuni kunya ta lullube Bisma tayi bayan kofa tana musu sannu da zuwa. NURU yace "hajiya wai kunyarki takeji" Mahaifiyar nuru tace "meye na kunya don kina wasa da mijinki ai wannan ya nunamun cewa Nuru yana cikin kwanciyan hankali kuma Allah zaiyi miki albarka gaba daya aikace Amin suna shigowa. Bayan sun zaunane bisma tashiga kitchen takira Hamdan yazo shima ya tayata daukan kayan ciye ciye aka daura musu akan center table, kallon Bisma sukeyi irin kwalliyan datayi innar Nuru tace Bisma halan dai mai gidanne yayi miki wannan kwalliyan ai tuni suka bushe da dariya, bayan sun gamane aka yiwa su hajiya iso zuwa dining amma Sam sukace a kasa zasu Zauna haka aka shimfida musu tabarma aka kawo musu kayan abinci. Suma sukasa a kwano daya hajiya tace ma Bisma "ga chokali kici abinchin dashi," NURU yace "hajiya da chokali daya mukecin abinchi saboda karawa zuciya yadda so da zumunchi" Hajiya tace "kwarai kayi dabara harka tunamun da baya Allah yayiwa annabi daraja" akace amin Bayan sun kammlane akayimusu fada sunji dadii kwarai daga bisani sukace zasu tafi haka bisma ta kwashi Wasu a motarta NURU ya kwashi Wasu, amma saida sukayi tsiya bisma tana ita zata dauki hajiya Nuru yana shizai dauka daga karshe dai NURU yaci girma. Bisma bakaramin guri tasamu a dangin nuruba, saboda irin shedar dasuke mata, ga Albarkan iyaye gana iyayen miji gana miji sannan dadin da dawa gana jama'an gari dole Bisma tayi farin jini saboda dadi Bisma saida tayi kukan dadi. [2/12, 3:45 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 2⃣4⃣ _*This page goes to you ILILEE am sending my Condolence😭 due to the lost of our beloved and Dearing Grandpa, May Allah have mercy on him, may Allah make his final abode to be Aljanna FIRDAUSI Amin*_πŸ‘πŸ» *RIGAR GEIDE* ********* Ya k'walam ce zaune tana kullewa Baitu K'oren nono da fura tana kaiwa kasuwan datake ci duk ranan Asibi, yarinyace son kowa kin Wanda yarasa, saboda kyawunta zan iya cewa Kamar yar India amma saidai cikas guda tana dauke da lalurar ciwon zuciya, dazaran ciwon yatashin mata sai tayi kaman bazata rayuba dayawa yan garin suna masifan sonta amma Yarinya ce Mara hayaniya, wacce bata damu da rayuwan mutane ba. Baitu! Baitu!! Baitu!!! Kiyi maza kifito mana lok'aci yana k'urewa, haka tafito tana tafiya cikeda natsuwa ta dauki k'waryar nono takama hanya sai kasuwa, Jood'a yana tsaye Wato mahaifinta shida wani abokinsa dake zuwa daga birni, ta gaidasu ta wuce. Bayan wucewar Baitu ne bakonnan yace "Jood'a wai har yanzu yarinyarnan tana fama da wannan ciwon?" Jood'a yace "kwarai kuwa amma kwana biyu ciwon bai tashiba, kasan dazaran ranta ya baci shikenan zamu rasa gane kanta". Bakon ya jinjina kai yace "Toh tabbas yakamata kudinga zuwa birni ganin likita saboda wannan ciwon nata yana bukatar kulawa na musamman, sannan daganin kwararrun likitoci" "Kwarai maganarka haka take zamuje insha Allah" haka sukayi Sallama ya wuce. Kamar yadda Baitu ta saba dawowa da wuri haka ta dawo amma daganinta batada lafya sosai haka ya k'walam ta amshi Koren nonon gaba daya ta saida bamu koh barbede, haka ta nemi guri ta zauna tana numfarfashi tana cije baki, Baitu tayi karfin hali tace "Ya k'walam ina cikin wani yanayi inajin ciwona zai tashi"....... kafinta gama magana ta fadi a sume. Cikin tashin hankali ya k'walam da Jood'a suka Mike suna kuka haka, ya goyata har bakin titi gashi yakai kimanin kilometres daya daga kauyensu zuwa bakin titi, saboda kula da sukeson bawa yar Tasu k'waya daya, sun isa bakin titi duk motar dasuka tsayar sai taki tsayawa hankalinsu ya dad'a tashi, da kyar suka samu wani mai akori kura ya daukeso akan kudi naira Dari biyar zuwa garin Gusau, ya k'walam kuka kawai takeyi abun saiyaba mai karatu tausayi. GUSAU ************ Don nikaina saida nayi kuka saboda yadda idanunta suka kakkafe, cikin asibitin FMC suka shiga babu Wanda ya kallesu duk Wanda ya k'walam tagani da farin kaya saita ruga da gudu tana neman taimako amma babu Wanda yakeda tausayi cikinsu, kwatsam saiga Bisma tafe take tana amsa waya dagani da NURU take waya saboda shima ya koma bakin aikinsa, tuni ya k'walam ta ruga tace "Baiwar Allah kayimun agaji yarona ba lafya gashi chan kwance bayako motsi" Bisma ta kalleta tabata tausayi tace "Baba kidaina kuka muje" inda Bisma taga jikin yarinyar taga yadda aka barta k'wance a kasa taji ranta yayi dubu ya baci ta kwalawa nurses din kira tace "Abunda bazan lamuntaba kenan wulak'anta patient akan wannan carelessness din zan iya barin wannan asibitin akan haka, maza ku dauketa kukaita kan gado" Haka suka dauketa ranga ranga, "Bisma tace baba kiyi hakuri zaa dubata kuma duk yadda ake ciki zakuji sakamako". Haka ya k'walam ta rungume hannu shiko jood'a rikeda sandarsa, abun duniya ya isheshi, "Ya Allah Kaine gatana ka bawa yarona lafya kaba Baitu lafya" Cikin Dakin Bisma ce tsaye tana bincike akanta ansata acikin na'ura mai kwakwalwa, tuni ta nuna cewa zuciyarta ce ke cikin matsa nancin yanayi. Bisma hankalinta ya tashi ta juya tacewa nurses din "Yarinyarnan tana cikin mawuyacin hali, batasan me duniya take ciki ba, tabbas zuciyarta tana buk'atan ayimata aiki kila musamu nasara. Tashi tayi tafita tana fita ya k'walam tayi saurin cewa "likita lafya naga ka fito rai babu dadii karkace mun Baitu ta mutu" Bisma ta dago idonta jawur tace "kubiyoni Office" haka jood'a yabi Doctor Bisma aguje, har cikin office zama tayi nima nabisu hoton Bisma da NURU ne akan tebur dinta sunyi masifar kyau kaman larabawa, Doctor Bisma tace "Gaskiya sai anyi mata aiki saboda zuciyarta gab take da daina aiki saboda ciwon dayaci zuciyanta". Cikin tashin hankali Jood'a yace "likita nawa akeda bukata" Bisma taga idan tace mishi naira dubu dari da hamsin ake nema ina zasu sameshi? Tace "Malam kudinku naira dubu darine kacal". Jood'a yace "Toh likita zani gida inga yadda za'ayi Zan samo likita Baitu itace kadai yata a duniya banida kamarta baitu mai ladabi ne da biyayya Baitu bai taba batamum raiba likita karya mutu likita" haka ya k'walam itama take kuka tana ji aranta Baitu bazata Rayuba. [2/14, 7:57 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 2⃣5⃣ Haka jood'a ya kama hanyan zuwa rigar Giede don saida wasu k'adarori nasu, da isarsa rigar su ya tadda babu shanu babu kowa cikin rigar dagani barayin shanu sunyi awon gaba dasu, jood'a yashiga matsanancin hali inda ya duba gabas da yamma kudu da arewa babu dabbobinsu koh daya karshe ma an k'ona musu gari koh kukan tsuntsaye bakaji illah iyaka hucin zafi dayake tashi, ihu kawai yakeyi babu salati babu komai dayake suna cikeda tsantsar jahilci, haka jood'a ya koma cikin birni cikeda tashin hankali, yaje yake sanarda ya k'walam abunda yake faruwa gaskiya sun shiga cikin tashin hankali, "Yanzu ya zamuyi? Yanzu ina zamu sa kanmu dabbobinmu sune rayuwanmu, yanzu ina zamu samu kudin ayiwa Baitu aiki nasan cewa baitu mutuwa zatayi matukar muka kasa samun kudin da za'ayi mata aiki bara zanfita jood'a rayuwar Baitu tafi komai mahimmanci a rayuwa" Haka suka baxama cikin gari Neman taimako amma babu maison taimaka musu, kofar gidan wani Alhaji ya k'walam ta tsaya ganin zai shiga da Motarsa tace "bawon Allah taimako nake nema yata batada lafya tana kwanshe a asibiti kuma aiki za'ayi mishi a zuciya Dan Allah ka taimakeni yadda Allah ya taimakeka, Alhajin nan ya kalleta sama da kasa ya hankadata gefe yace "Aikin bazan no koh zan baki kudi bazan bayarba jiki wata bakauya dake aini yan mata Nike bawa kudi subani abun dadii" Wasu yan'matane sukazo wucewa susu shida kowacce daganinta kasan cewa tasha kudi ta koshi komawa sukayi da baya yayinda yaci gaba da cewa "maza kibarmun kofar gida kafin insa a daukeki cik" haka ya k'walam ya mike tana kuka zuciyarta cikeda tsanar wannan bawon Allah, "meyasa Wasu basuda imane maiyasa wasu sukadau talaka Mara yanci maiyasa mai kudi yakejin kyashin yiwa talaka Alkhairi nagari kadanne acikin duniyannan amma wata rana kaima saika nema wajen wani tunda ka wulantani". Yan'matan nan su shida daya tayi gaba wajenshi tana kwarkwasa tana fari da ido lokaci daya hatsabibin Mutuminnan yaji bazai bari wannan kyakkyawan yarinyar ya wuceshi ba, kallonta yayi yace "Lafya baby me kikeda bukata yanzu mushiga cikin gida inyi miki" Yumna tace "Menakeso banda kai inji kana abunda bora mata samu wajen mijinta inji ina Sosa maka tsakiyar kai" tafadi tareda Jan gaban rigarsa, tuni ta wuceda imaninsa, yayi horn mai gadi ya bude mishi kofa haka yaba sauran yan matan shigowa amma sai suka boye, mai gadi yace "wai yau Alhaji zaici banza har mata shida inama zai mikomun uku nima indan maida mugun yawu" nidai Humairah saboda dariya saida na durkusa. Suna shiga ciki da yumna sauran suka kama mai gadi suka daure shi tamau, biyu suka tsaya tsaron mai gadi sauran suka shiga ciki, Alhaji tuni yacire kayan jikinsa daga shi sai dan kamfai Wanda akafi sani da boxer, ya ajiye uban tumbi kaman mai cikin wata Tara "motso kusa mana baby yana cikin faden haka sauran ukun suka shigo daya daga cikinsu da bindiga, lokaci guda yaji mugun tsoro Kabira tace "Irinku mukeso azzalumai Wanda matan banza ne kecin kudinku matanku suna chan kun barsu da yunwa koda kanzan tuwo toh yau sai asirinka ya tonu haka Shantel ta kwabe kaya dayake cikinsu itace kabila koh ince crista. Daga ita sai bra sai pant haka Ubaida tafara daukansu hoto kuma sukasa shi dole saiyayi dariya alamun yana holewa ya ya'iya haka yadinga bashe baki bayan sun kammala ne, Aisha tace "ji yadda ka wulakanta wannan baiwar Allah Allah kadai yasan halinda yarta take ciki amma ka kasa taimaka mata toh yau kashinka ya bushe, Haka suka umurce shi daya basu kudi sannan ya rubuta musu check na naira miliyan shida haka suka daureshi suka dauki brief case dinsa suka kara gaba sannan sunyi alkawarin saisun tonamai Asiri yumna kadai zai iya ganewa acikinsu itama tasan abunda ta taka shiyasa bata rufe fuskarta. Tuni sukabar gidan tareda wayoyiinsa suna cikin tafiya suka hadu da ya k'walam a karshen layi tana kuka tana share hawaye haka sukadau kudi naira dubu Dari da hamsin suka bata suka wuce tundaga ranan sukabar garin Gusau zuwa wani garin, haka ya k'walam tadinga jin dadii tana murna taba shimusu albarka haka takoma asibiti da karfinta tuni aka fara shirin aiki nanda kwana uku, haka jood'a yadawo ransa babu dadi, saiyaga ya k'walam tanata dariya zama yayi yaga tanacin abinchi yace "Ina kika samu abinci munata lafiyan baitu?" Nanta bashi labari shima yabata labarin irin wulakancin dayasha wajen masu hannu da shuni Wasu har cewa sukai sai sunyi lalata dashi sannan zasu bashi kudi shikuma bazai iya sabawa mahaliccinshi ba. [2/14, 8:13 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 2⃣6⃣ _*Ina kiraga makaranta wannan littafin cewa DASHEN ZUCIYA littafine takaitacce baimai tsawo ba amma Inada yak'inin cewa Zamu karu daga cikin Dan abunda ya kunsa ina kaunarku masoyana na kusa Dana nese*_😻😻😻😻😻😻 Bisma ce zaune akan kujeran karatu, gaba daya tashiga tunani mai zurfi inda hasken idanunta yashigo batareda tasani ba, rungumeta yayi tabaya gamida sumbatar bakinta yace "Princess kwana biyu narasa abunda ke damunki baki cikin natsuwa kodai duk aikin ne?" Bisma ta juyo tayi mishi kallon sannu da zuwa mai gida briefcase din hannunsa ta karba ta rikemai hannu tana cewa "My king karka damu am fine sannan zan iya kulada kaina banaso damuwata ta hanaka ba aikinka concentration, kasan yadda nakesonka bansan abunda zai muzguna maka" daki suka shiga Bisma sai tsubarara takeyi shiko gaba daya yaji ransa ya baci da kalaman Bisma. Bakin gado ta zaunar dashi, tafara ciremai takalmi saida ta rabashi da komai Da gashi sai inner wears, ta haye cinyarsa tace "Yanzu ka zaba kasan dai ance ci yana gaba da sallah, idan har yunwa zatasa kadinga tunanin abinchi a sallah, wanne zamuyi?" Nuru ya kalleta a Kullun bisma burgeshi takeyi baya gajiya dajin da dadan kalaman ta, Hura masa ido tayi tace "Lafya my king kaketa kallona kodai outfit dina baiyi bane ta mike tana kallon doguwar rigar dake jikinta tafito da komai nata. "No at ol Bisma banason rabuwa dake ne nafiso idan mutuwa zatazo karta rabamu nafiso ta daukemu rana guda muna kwance akan gadonmu, na aure wallahi bana ganin wata ya mace da kima da daraja bayaga mahaifiyata saike Bisma you are my everything wallahi", rungumeta yayi suna shak'ar numfashin juna, Saida bisma ta kulada mijinta sosai sannan ta jawo hankalinsa ga abunda keci mata tuwo a kwarya Wato halinda Baitu take ciki. "My king" tafadi tareda kwanciya akan kafarsa shiko sai shafata yakeyi yace "My princess gayamun abunda ke damunki kinsan cewa I am a sycologist duk ba lurada kina cikin damuwa" Bisma taja mishi gemu tace "Wallahi wata patient aka kawo asibitin mu tana daukeda ciwon zuciya yanzu aiki zamuyi mata gobe bawai donta warke ba ah ah don rage mata radadin ciwon shine hankali yake a tashe kasan wannan shine karo nafarko daxan fede mutum" Gaba daya nuru yaji tausayin matarsa yace [2/15, 6:59 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 2⃣7⃣ "Princess meye abun damuwa aike kwararra ce, tashi zakiyi muyi sallah mu roki Allah daya baki sa'a yasa kiyi a sa'a kifito a sa'a" Taji dadi nanta tashi tayi wanka tayi shirin kwanciya misalin karfe biyu tsakiyan dare suka farka a tare abun ya basu mama, haka suka tashi sukayi sallah suka roki Allah daya basu sa'a haka NURU ya rok'awa matarsa washe gari bisma sai shirin tafiya takeyi shima NURU haka wani irin kyau tayimai wai duk baisan zaiyi harka da itaba saida ta shirya tsaf yaji wani mugun sha'awarta ya kamashi kusa da ita ya matsa. "Princess cikin rad'a yake magana pls I need your help pls" tuni idanunsa suka kad'a sukayi jawur shige mata kawai yakeyi yana shafata yana kokarin rabata da kayan jikinta Bisma mai ladabi ce wajen sauke hakkin mijinta daya rataya akanta koda girki takeyi ya buk'aceta takan sauke Girkin ta amsa kiran mijinta, abunda mata da yawa basu iyawa kenan, Wanda addinin mu ne yasanar damu kyauta ta kwanciya. Bisma takalli agogo karfe Tara zasu shiga tiyata, amma dole ta sauke wannan nauyin, haka nuru tadinga tada mata da hankali har itama ta maida martani tuni yayi nasaran rabata da duk wani kaya dake jikinta yafara shafata cikin salo da kware wa kafin kiftawan ido nayi saurin bude kofa na koma falo na zauna, Don abun bazai faduba. Saida nuru ya tabbata ya maida mugun yawunsa kannan ya dauk'eta cik zuwa toilet inda suka sarkake junansu, haka Bisma ta shirya dukda jikinta duk ya sage saboda jigata din da NURU yayi, in takaitama mai karatu Nuru dai yana daya daga cikin maxannan ne mabukata Wanda saisun samu mata mai dauriya da juriya. Kafin ta fita saida ta tabbata ta ciyar dasu sannan suka fita a tare suna kewan rabuwa da juna kowa motansa yahau sai wajen aikinsa, NURU ya wuce state House ita kuma ta wuce asibiti, da shigarta taga ya k'walam a zaune ta rafka uban tagumi koh nazarin me takeyi oho.. Sallama Bisma tayi tanabin gado zuwa gado tana tambayar masu jiki, inda dukta wuce zancenta akeyi, harta nurses din yadda take kulada mijinta duniya idan ya rasata bazai sake marnarin wata ya mace a duniya ba. Tana zuwa inda ya k'walam tace "Ina kwana yamai jiki inajin dai Baku mata wani Abu ruwa abinci taciba da safennan?" Bisma ta fadi tana gwale idon Baitu, tace "Sannu Baitu Allah ubangiji ya baki lafya dafatan kun samu kudin daza'ayi aikin?" "Eh ansamu gasu" haka ta mik'awa Bisma taje ta biya aka zo shiga da baitu Dakin operation. Kowa sai fatan Alkhairi yake musu Bisma saida tayi kuka ganin baitu da jood'a suna kuka, tajuya tace "Adu'a baitu take bukata ba kuka ba kuka ba abunda yake karawa illah bacin rai don haka kuyi kokarin furta wani Abu na Neman sauki" Haka aka wuceda Baitu tana kallon iyayenta tana musu ban kwana Don tasan mutuwa zatayi. An shafi kusan awa biyar ana aiki ansamu nasaran yin aikin amma zuciyarta tana bukatan chanji, Bisma ta kalli nurses din dake tareda ita tace "Dole sai anyiwa wannan yarinyar DASHEN ZUCIYA shine kawai Zaisa ta rayu cikin iyaye yan'uwa da Al'umma cikin koshin lafya" Gaba daya nurses din suka zare ido sukace yanzu doctor ina zamu samu Zuciya har a dasa mata? Bisma ta kare musu kallon tace "naso ace zuciya biyu mutum yake dashi kaman yadda k'oda take guda biyu da babu makawa saina bata guda daya saboda inajin baitu kamar yar'uwata ta jini, Amma zamuyita cigiya har asamu yawanci anfiyin irin aikinnan a kasar waje inda sukeda gurare na saida wasu abubuwa dasuka shafi jinkin Dan Adam, suna zuwa inda akayi mutuwar gaggawa su dauki mutum suyi mishi aiki su cire zuciyar mutum Tunda rayuwarsa ta kare" Kowa jinjina kai yayi suka fito da Baitu suka kaita wani daki daba'a shiga da takalmi, ba'a magana kuma babu wuta babu karan komai anan aka kwantar da ita Bisma tayi musu umurni dasu fita, awaje ne take sanar dasu cewa su kasance masu Adu'a ga marasa lafya don hakan shima yana daya daga cikin aikin ku" tana isa wajen ya k'walam tayi Dariya tace "Baitu tana nan lafya anyi aiki tana bacci sai nanda awa uku zata farfado amma da sauran rina akaba [2/15, 7:47 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 2⃣8⃣ Ya k'walam tace "likita meye zai faru kuma Bayan anyi aiki?" Bisma tace ki kwantar da hankalinki kici gaba da Adu'a baitu kamar ta warke da yardan Allah baitu tana bukatan wata zuciya da za'a dasa mata don rayuwarta takasance mai moriya saboda kankantar shekarunta amma Allah babu yadda baya tsara lamarinsa ran baitu baya hannuna amma zanyi iya kokarina ganin ta rayu daku ta taimakeku". Ya k'walam tace "har yanzu likita bakice komai ba? Bisma tace cikin murya k'asa kasa "Tana bukatan *DASHEN ZUCIYA* Cikin lokaci kankani". Ya k'walam ta zare ido cikin ridewa tace "likita acire zuciyana asawa baitu ta rayu dan Allah, itace kadai ta ragemun cikin yaya goma Dana Haifa yarana wabi sukeyi, mai zai hana acire nawa asamata ita Yarinya ce nikuma tsufa yazo" jood'a yakasa cewa uffan Saima jingina dayayi da bango tana salati wannan wace irin jarabawa ce Allah ya daura mana Allah kabamu ikon cin wannan jarabawan" amin ni Humairah nace. Anfito da baitu Bayan awa uku, idonta a bude tana Dariya tace cikin muryan Mara lafya, inna "Kinga naji sauki Fatana in warke inci gaba dakai miki fura kasuwa da nono inje rafi in debo miki ruwa inje daji inyo miki itace, takoma ga mahaifinta baffa kaima in ba bisashe ruwa in share maka Daki banaso Ku wahala dayawa a duniya, Bisma da sauran likitoci suka tsaya suna kallon baseerah irinta baitu, Bisma tayi Dariya tace "nikuma ne za'ayi mun?" Baitu tace "Adu'a itace a tsakanina dake Adda, Kinyi iya kokarin ganin kin ceto rayuwata lokacin danake Neman taimako, Allah ubangiji yasa kigama da duniya lafya, irinku kadanne a duniya Halinki nagari zai biki har zuwa karshen rayuwarki, Insha Allah karshenki mai kyauce likita". Tuni Bisma tafara kuka maicin rai bata taba jin wani yanayi irinna yanzun ba, Jitayi ana share mata kwallan da kyallen handkerchief kuma kamshin turaren mijinta taji, yana cewa "Ki kasance jaruma bamai saurin kukaba yin hakan zaiyi saurin k'arya zuciyar Mara lafya, Bisma kemai nasara ce sannan ki godewa Allah da ma'aikinsa, mijinki yana yabonki duniya tana yabon aiyukan Alkhairinki ai kin gama da duniya lafya saidai muce Allah ya kyauta ta karshenmu. Bisma ta juyo tana kuka tana Dariya tarasa murna takeyi koh bacin rai, Kallon Baitu tayi tace "mijina koh wace uwa tana burin Rayuwa da yayanta tabbas inajin zafin da uwa takeji Lokacin da takeyi yayanta Adu'a bayan ransu, koh a yanayin ciwo uwa tana hana kanta bacci saboda ta kulada rayuwar yayanta, uwata tana kincin abinci taba yayanta dukdan yaranta su rayu, lokacin da uwa taji kukan danta koh a ina zuciyarta kuna take, meyasa yaran baxasu rayu sujikan iyayensu ba mai yasa yaya suke fand'arewa iyayensu, meyasa yaya suke ciwa iyayensu zarafi a bainar jama'a kaico da Wanda baya tausayin iyayensa kaico ga Wanda yakasa bawa iyayensa kwanciyan hankali" Kukane yaci karfin ya taci gaba da cewa, da ace yayanmu aka daurawa nauyin iyaye Wallahi Wallahi damu iyaye mun shiga uku da yawancinmu bamu raye, don dayawa yaya bazasu Goya iyayensu ba, ba zasu kici suba iyayensu ba Allah ka bawa duk wata uwa karfin zuciya wajen hakuri damu yaya" kowa yace Amin. Nan kowa ya watse Bisma tace "kubata abumai ruwa Mara zafi zuwa gobe kila anjima abokin aikina zaizo gobe bazan zo ba, ta kalli baitu tace Allah yabaki lafya kinji, Baitu tayi saurin cewa "Likita yaushe zan bar wannan asibitin mukoma rigarmu nayi kewan gida kwarai?" Nuru ta kalli yarinyar ta burgesgi Bisma tace "My king tambaya takeyi?" Nuru yace "kece da bada amsa ai". Bisma tace "Insha Allah nan bada jimawa ba zaki bar Asibitin kije kitaya inna da baffa aiki" Murna a wajen baitu baya misaltuwa Bisma tace "Kada Ku yarda wani Abu ya bata mata rai kuyi kok''arin sata Dariya sannan ta dawwana acikin farinciki" suka amsa da toh. Rayuwa mai dadi haka nuru suka koma gida suka ajiye motarsu, waya suka samu daga wajen ruma cewa Dan Allah Bisma tazo yan uwan Hamdan zasu kasheta, bisma tace "Sunyi kadan my king muje mota tashiga shidai bita yayi suka fada cikin mota sai gidan su Hamdan da isarsu cikin zafin nama bisma ta fada falo sunyi mata ligi ligi ga ciwon ta yak'ara tsananta ga karamin ciki ai kwance suka tadda Ruma kelaye cikin jini wani kara bisma ta fasa tace "kun kasheta cikin jinin ta fada tana jigjiga Ruma amma batakoh numfashi, ka yan'uwan Hamdan tsaye suna huci tuni NURU yakira Hamdan yakira gida Shinkafi yasanar dasu. Bisma wani kukan kura tayi ta shakesu tace matukar Ruma ta mutu sainaga bayan danginku Wallahi saikun talauce don kara daganan har kotun manta Sabo saimunje saku ta watsar dasu asibiti suka kwasheta sukakai abokan aikin bisma su suka tsaya akanta saboda wani irin matsanancin ciwon kai ke damunta sai jiri take gani hamdan yashigo asibiti kaman mahaukacin zaki ana sanar dashi cewa cikin da Ruma take dauke dashi ya fita jingina yayi jikin bango yace "Haka Allah yaso sake Ruma Allah ubangiji kaba ruma lafya kabamu masu amfani" Kowa saida yaga kokarin Hamdan a yadda ya shigo cikin asibiti a hargitse lokaci daya yayi tawakkali ga Allah ya yarda shike badawa ya amsa a Lokacin dayaso. Inda nuru yake rungumeta da Bisma ne tana kuka yace "Kiyi hakuri bisma Allah shike komai a yadda yaso" "Dakata kadau mataki koh koh indauka a hannuna?" Cikin rudu hamdan yace [2/16, 2:44 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 2⃣9⃣ "Na kira su hajiya na sanar dasu amma batace dani komai ba nakira alhaji na fadamai shima shuru yayi ya kashe wayar kinsan irin zaman da akeyi na doya da manja" Bisma ta dafe kai tace "ai case bata kareba yanzu zan sanarda hukuma ayi mai tarariya" Hamdan ya rude waya kawai bisma ta dauka takira Acp Bello ta sanar dashi batareda bata lokaci ba suka isa gidan su hamdan. Hamdan ya kalli NURU yace "Dan Allah kasa baki kar a kama kannina". NURU yace "Kanaso kacemun kafison kanninka akan ran matarka? Oh Hamdan banga laifin yan'uwanka ba Dan sunzo sun Daki Ruma da goyon bayanka kuma kaima saika fuskanci hukuma" tsaki nuru yayi yaja hannun matarsa suka shiga inda Ruma take Yadda ta koma abun tausayi cikin yan lokaci ta rame takoma Kamar bulala, bacci suka tarar tanayi yan gida duksun hallaro da wayanda zasuyi jinya, bisma kuwa zuciyarta ce ke tashi bayan sun gaisa ne Ummi ta umurci bisma dataje gida don taga kaman yar tata takamu. Haka Nuru ya rike hannun bisma har gida, ya bude mata murfin mota ya dauketa cik har cikin gida sannan ya ajiyeta, kofin tea ya hado mata mai zafi tasha gaba daya ya amoyo mishi ajiki sai kakari takeyi haka, nuru dukya rude yarasa mezai fara yiwa bisma, gashi Da gashi sai ita a gida, abin ne gwanin tausayi. Tissue ya samo ya goge mata baki tareda yimata sannu koh magana bata iyawa, daukanta yayi cik zuwa toilet ya gyra mata jiki shima ya gyra nashi, suka shiga Daki ya taimaka mata tasa kaya harda sweeter saboda sanyi datakeji haka ya daura ta bisa gado ya lullubeta da bargo. Fita yayi falo ya fara kwashe aman datayi ya gyra koh ina yasa air freshener Dakin ya dau kamshi, sallama yaji yace Am coming budewan Da zaiyi yaga abokinsa Faisal yace "Abokina lafya naganka haka a hargitse?" Cewan abokin NURU. Nuru yace "dole ka ganni haka my princess ce ba lafya amai tayi shine na kwashe nake gyara wajen" "Lallai nema abokina kazama mijin tace mace kake yiwa yik'i haka ina aini baxan iyaba tab Wallahi kabi a hankali koh an jikama kasha" NURU ransa yayi mugun baci yarasa abunda ke masa dadi arai yace "Dakata Faisal banason maganar sha shanci me kake nufi toh bari kaji Wallahi akan bisma babu abunda bazanyi ba yadda kake ganina yanzu kitchen zan shiga abunda takeso shizan dafa mata". Faisal yayi sarere, daman shi halinsa kenan mazigi ne makwangari, haka yakebi yake lalata auren abokansa amma dayake nuru yasan abunda yakeyi ya sakar mai da gwiwa, "Toh mijin hajiya ni nayinan sai anjima ka gaisheta idan ta farfado, Nuru saboda haushi bai iya cewa komai ba. Nuru yashiga kitchen ya dafa musu abincin daza suci, bayan ya kammala yashiga mater bedroom dinsa ya tada bisma cikin dabara harta soma bude idanunta, murmushi tayi ta sakkoh riketa yayi saboda bayaso wani Abu ya sameta brush tayi sannan ta dauko abunyin test na ciki don duk symptoms din da takeji namai ciki ne. Ilai haka tayi test din cikin ikon Allah yanuna Jan danja, dukda NURU baisan abunda yake nufiba amma saiyaga bisma tana murmushi shima saiya fara, juyowa tayi ta rungume shi hartana jin bugawan zuciyarsa, tace "My king da a asibiti muke da wasune zasu tayamu murna amma dayake likita ce da kanta ina maka albishir da cewa ina dauke da juna biyu Wato danmu nidakai". Wani ihun dadi NURU yayi yace "Wasu sun rasa gashi mu mun samu, don haka dole muyiwa annabi salati" haka sukayi NURU yaci gaba da shafan cikin haka bisma tadinga fama yau lafya gobe ciwo dukda bawani kwantar da ita yakeba, bayan kwana biyu aka sallami ruma amma sai akai shinkafi da ita saboda sai anyiwa tufkar hanci. Baitu ce kwance bayan SATI ciwo yakici yaki cinyewa, bisma tace "Baitu dole ayimiki dashen zuciya gida" takoma da damuwan halinda Baitu take ciki NURU yace "princess gaskiya ki rage tunani akan patient dinnan wai ita kadaice kike dubawa? Haba gaskiya ki kula saboda lafiyarki data abunda ke cikinki, ko kuma ki ajiye aiki har saikin haihu". Cikin rudu da tashin hankali, Bisma tace "My king katuna Alkawarin dakayimun akan cewa zaka tsaya tsayin daka ganin na comma nasara akan aikina amma meye na canza raayi katuna rai zan ce ta" "BISMA dakata akanki da abunda ke cikinki bakida abunda zakice mini saboda dole kidaina zurfafa tunani" Bisma tace karka damu my king ana dasa mata zuciya shikenan zan dauki Hutu pls kasaki ranka. [2/18, 7:23 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 3⃣0⃣ _*This goes to basira one of our gigantic FAN Am here by saying my big condolence to you for the lost of our beloved brother may Allah forgive him may Aljanna firdausi be his final abode AMIN*_πŸ‘πŸ» Wani murmushi tasaki tareda komawa kusa dashi ta kwanta amma gaba daya zuciyarta tana wajen baitu datake fama da ciwo k'warai Wanda Bisma tarasa dalilin hakan, bayan sun kwanta bacci ne BISMA ta lallaba ta mike tafara jero salloli tana yima baitu Adu'a wacce Allah yabata iko, Shiko NURU wani Bacci yakeyi. NURU yana zaune a kujera bisma tazo ta wuceshi tana murmushi nuru tana daga mata hannu cigaba yayi da karanta jaridarsa, bayan fitarta ne yaji karar waya tuni ya dauka ganin lambar bisma hello shine abun da yafara cewa Wanda yakira yace kazo wajen DANGASKE NIG LMTD wata motace tayi hatsari kuma inajin matar dake ciki ta rasu cikin rudewa nuru yace whatt!!!!!!! W firgice ta mike yana salati juyawan daxaiyi yagansa adaki bisma kwance kusa dashi, tanata bacci cikin kwanciyan hankali. Wani numfashi yasaki ya koma ya k'wanta yana mai ajiyar zuciya, amma kuma tsoro fal da fargaba acikin zuciyarshi. Ba NURU kadai ba hatta ni humairah saida zuciyana ta karaya. Da asuban farko Bisma ta tashi taga nuru zaune ya nade hannu cikin gaggawa ta matsa kusa dashi tana "NURU lafya kake? Dan Allah lafya dagani bakayi bacci ba dubi yadda idanunka suka kumbura sannan sukayi ja pls my dear husband tell me wat is the problem?" NURU ya dago sai jitayi hawaye suna zuba kamar daman jira suke tayi magana. Bisma ta kara rudewa "Ga gayamun abunda ke damunka Dan Allah" NURU ya fashe da kuka yana cewa "Bisma karki barni bazan rayu ba kece mahadin zuciyana bisma don go and leave me I know definitely am gone too" itadai bisma a rude take tarasa dalilin dayasa NURU wayannan kalaman gamida zubda hawaye. NURU yace "Nayi mafarki Bisma mai tsantsar rikitarwa, idan kikaji tilas zakiyi kokawa amma nabarwa zuciyana banaso kiji abunda zai tada miki da hankali" bisma ta rikemai wuya tace "you most tell me wat is happening" tana jijjigashi tana kuka. NURU yace "Nayi mafarki Allah ya dauki rayuwarki shiyasa kikaga ina kuka don tabbas da ace ba mafarki bane bisma wallahi da tuni na biki na kashe kaina bisma inacikin matsanancin tashin hankali". Bisma tayi wani ajiyar zuciya tace "Amma ka tadamun da hankali Wallahi, inace mutuwa akayi ka kasa gayamun, Wato kanaso kacemun tsoron mutuwa kakeyi? Toh Kasani "Kullu nafsin za'ikatul maut" dukkan mai rai mamacine kuma idan lokaci yayi babu makawa duk soyayyar dake a tsakanina dakai Kasani Allah daya haliccemu yafika sona kuma ina maraba da mutuwa akoda yaushe". Zare ido NURU yayi yana k'ara sautin kukan sa Wanda nikaina saida nakara karaya da kalaman bakin Bisma, nikaina saida na goge wasu hawaye. "Bisma kiyi fatan mu mutu rana daya karki tafi kibarni lokacin danake matukar son mu rayu da juna Kituna kina dauke da farincikin rayuwanmu, nidake bisma rana daya zamu rasu" Bisma tayi Dariya tace "Kamanta yadda mutuwa take raba d'a da mahaifa haka take raba masoya, ma'aurata, abokai harda aminai NURU ba'a mutuwa sai lok'aci yayi idan Lok'acin ka baiyi ba zaka zauna daram a duniya Fatana Allah yasa mucika da Kalmar shahada" Amin yace yana karewa bisma kallo mikewa tayi ta dauro alwala tace "Mai tsoron mutuwa tashi maza kayi sallah kar tazo ta riskeka yanzu don arana mutuwa tana ziyartar kowani gida sau saba'in taga waye akan layi". NURU yace "pls chapter close naga kinaso kimaida abun wasa" haka sukayi sallah kowa yafara shirin tafiya wajen neman halalinsa Bayan sun gama cin abinchi ta mike tace "Nina tafi pls karufe koh ina kila bazan Dawo ba" NURU yakara kallon Bisma yace "madam zolayan ya isa haka" Haka tafita tana Dariya amma wani kallo takeyi wa NURU, fitanta keda wuya NURU yakirata yace "Amma shine kika kasa shan maganinki koh kuma kindauko gashi kan dinning" Oh barina Dawo insha haka bisma ta Dawo cikin gaggawa tasha maganin ta kalli NURU tace "Hankalinka ya kwanta barima kaga inzauna" guri ta nema tafara kiran Ummi tana sanarda ita halinda baitu take ciki sannan ta tambayi lafiyar Ruma kusan yan'uwa saida takira ta mike tace "Na wuce" NURU yace "Allah ya kaiki lafya". Fitarda keda wuya nuru yakara kiranta yana cewa ki kulamun da kanki yana mata hiran soyayya sai Dariya takeyi, wani kara yaji Wanda lokaci Guda yadaina jin maganan Bisma yayi maganan duniya amma shuru kakeji, tuni ni humairah zuciyata ta tsinke na lallaba na ajiye wayata don ingarzaya ganin abunda ke faruwa. [2/19, 3:39 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 3⃣1⃣ Cikin rud'ewa Nuru da boxer da yar vest ya fita mukullin mota kawai ya iya dauka, cikin sauri gaba daya jiri yakeji yana tunanin Tabbas Bisma ba lafya wani Abu so strange ya faru da ita daidai DAMJI yaga cin chirundon mutane saiya hango motar Bisma duk ta mokad'e ai da gudu yayi cikin mutane da mota bai saniba, fitowa yayi yaga bisma kwance shabe shabe cikin jini. Gaba daya kamanninta sun canza, numfashinta dai dai yake fita, abun gwanin ban tsoro, "Bisma Ashe yau mafarki na zai zama gaskiya Ashe wannan ranan zatazo kaico duniya ni NURU inazan dosa?" Chicciban Bisma yayi zuwa mota kafin sukai ya sullube shima yafadi asume tuni Road safety, suka iso sukayi Kansu tareda jami'an tsaro Wato yan sanda Asibiti sukayi dasu FMC inda Bisma take aiki. Cikin asibiti, emergency aka shiga da Bisma inda likitoci da dama suka shiga rudani ganin ma'aikaciyarsu cikin mawuyacin hali, NURU kuwa ruwa aka yayyafamai yana fizga abarshi yaje yaga matarsa amma likitoci rirrikeshi sukeyi. Emergency ward Da kyar numfashin Bisma yadawo gaba daya dangi duk an sanar dasu asibiti yacika damkam ba masaka tsinke Ummi kuwa Adu'a kawai takeyi amma yadda ake sanarda ita halinda Bisma ke ciki tasan cewa sai abunda Allah yayi. Nisawa bisma tayi ta bude idanunta inda sukayi jawur amma wani murmushi takeyi mai cikeda ciwo tace akira mata Ummi da hajiya da maifinta Dana NURU. Cikin kankanin lokaci aka kirasu suka shigo, halinda Sukaga Bisma aciki ya firgitasu, jini yake fita ta hanci tabaki ta kunne amma da kyar aka samu na baki ya tsaya, kanta yabugu yayi suntum kaman gungumen dutse. Kallonsu tayi tana Dariya tace "Iyayena kuyafemun iya lok'acin dazan diba kenan a duniya Ummi hajiya ngd ngd kwarai amma ayanzu inajin dani da abunda nake dauke dashi a cikina zamubar duniya, amma Inaso kuyimun alkawari guda daya" tuni iyayen suka russuna gareta suna kuka kidaina faden wannan maganan Adu'a yakamata kiyi muyi baki daya. Daddy yace "kudaina mata kuka Adu'a tafi bukata a halinda take ciki, bisma takara wani murmushi tace "daddy kuyimun alkawari zakuyi abunda nakeso, bayan raina daddy inaso ayi gaggawan cire zuciyana adasawa Baitu saboda tana matukar bukatar ta, sannan Inaso NURU ya auri baitu ya riketa amatsayin mata kuma amana ce nabashi" Cikin Rashin fahimta daddy yace "Wacece kuma baitu? Yazaayi a dasawa mutum zuciya? Kuma na matacce? Daddy ya kalli Bisma yace bazaki mutu ba insha Allah". Daddy kenan mutuwa tazama dole akan kowane bawa Fatana kuci gaba dayimun Adu'a bayan raina" tana gama magana aka umurcesu dasu fita koh minti biyar basuyi da fitaba jini yakara ballewa ta hanci ta baki, likitoci sunyi iya kokarinsu Amma fah abun yaci tura haka Bisma ta dinga salati ga ubangijinta har lokacin da rai yayi halinsa, ni Humairah nashiga tashin hankali bani kadaiba duk wani masoyin Bisma babu Wanda yafado mun arai sai NURU. Haka likitoci suka shiga tiyata aka cire zuciyar Bisma akasawa Baitu, lokacin NURU yasamu ya balle babu Wanda ya iya kamashi cikin inda bisma take yashiga yaga an lullube mata fuska da wani kyallen asibiti, wani shaka ya kaiwa likita saida mutane fin ashirin suka kwaceshi, "Likita ka kashemun mata you have made a big mistake arayuwarka wallahi Shari'a dani dakai har abada, bisma wake up pls this is not the right time to go wat abt our baby shikenan" Surutai yakeyi marasa kan gado haka kowa cikin dangi yake kuka garin shinkafi yacika damkam, ya k'walam kuwa surutai kawai takeyi har saida aka kaita inda akesa masu tabin hankali saboda mutuwar ta girgiza kowa harda ni Humairah Bashir Melody. Dakin mijinta aka maidata akayi mata duk wani abunda ya kamata ayiwa mutum musulmi mumini, Wato sutura gidajen radio haka aketa sanarda rasuwar Bisma, haka mutane daga shinkafi sukayi zuga zuwa janaza mutanen Dana gani saida kaina suka juya. Harka shirya Bisma jini yana zuba gawani murmushi afuskanta kaman tayi magana, NURU dai yana asibiti amma cewa yake abarshi yaje yaga bisma, amma ina saboda halin dayake ciki. Fitan likita keda wuya NURU ya girgide, duk wani Abu na Dakin ya fita ya tare mai mashin sai unguwarsu, yana shiga unguwar ana fito da gawar Bisma wani kukan kura yayi ya amshe makaran tuni yafara kwanceta amma akayi NAMIJIN kokarin daukeshi yana ihu abar mai bisma bata mutuba. Haka akayi mata sallah sai makabarta haka aka kaita makwancinta tareda Adu'oi daga bakunan iyaye masoya da abokan arzuka, haka aka kai NURU asibiti inda yake amsan kulawa daga kwararru, amma nuru yazama tamkar rakumi da akala ba umm ba um um, yakoma tamkar Kurma rana daya NURU yazama tamkar kara haka yaci gaba da zama a asibiti har tsawon kwana bakwai [2/20, 7:05 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 3⃣2⃣ Baitu kuma tana samun kulawa daga wajen likitoci kwararru, har daga makotan asibitoci saboda itace mace ta farko da aka taba yiwa DASHEN ZUCIYA harta samu kanta batareda wani mishkila ba, ya k'walam kuwa tafita hayyacinta saboda mutuwar Bisma ta girgizata bayan ta Dawo hayyacinta ne aka nuna mata inda Baitu take k'wance tayi murnan ganinta amma sai kuka yake Neman cin karfinta. Tuni likitoci suka fitar da ita saboda baitu bata bukatan komai a yanzu face kwanciyan hankali, haka iyayen bisma suke jigila da Baitu daga abinchi zuwa magani jood'a kuwa yanachan dashi ake amsan gaisuwa, Nuru ne zaune akan Gadon asibiti hajiya tana yimai nasiha amma kaman badashi take magana ba kallonta kawai yakeyi kaman yau yasaba ganinta. Haka likita ya sallamesu amma da sharadin kar a maidashi gidanshi saboda gudun kada ya tuna abunda ya rasa wato bisma, hakan yana iya haifar da matsalan dabaza'a iya magancewa ba, haka hajiya ta amsa dato. Direba ne yazo ya dauke su suka wuce gida inda hajiya take kokarin sashi yin sallah Adu'oi dacin abinci. Bayan kwana bakwaine gida aka watse aka koma shinkafi amma Ummi batabar Garin Gusau ba saboda baitu datake amana a wajensu, haka Ummi da hajiya Nuru suketa jigila akan baitu harta warke tasamu kanta cikin koshin lafya. Ladabin da baitu takeyi musu shine ya dasa kyakkyawan alaka acikin zuciyoyin hajiyan nuru da Ummi mahaifiyar Bisma, haka ya k'walam da jood'a sukabi Ummi bisa sharadin Alhaji, ita kuma baitu aka barta gidansu nuru, saboda hakarsu tacinma ruwa na hada NURU da baitu aure. [2/20, 7:59 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 3⃣3⃣ An shafe lokuta da dama mutuwar bisma tafara gushewa kowa yakoma walwalarsa kamar da amma kowa yasan cewa Anyi musu babban gibi Wanda suke burin samun wacce zata maye musu gurbin Bisma...... Ya k'walam dai tana gidansu Ummi inda take taimaka musu da aikace aikace haka jood'a mahaifin Baitu yakasance shikuma mai gadi Wanda kowa yake matukar alfahari dashi sau dayawa Nabil yakan kaimishi ziyara inda yake bashi labarai masu kayatarwa, haka mahaifin bisma ke kuladasu, saboda yadda bisma tabar duniya da burin faranta musu rai. Nuru ne zaune cikin Dan k'aramin garden inda baitu ke tsaye a bakin famfo tana wasa da ruwa, kallonta nuru yakeyi amma gaba daya ba ita yake tunani ba matarsa kawai yake tunawa, wani Abu tagani yana motsi cikin ruwa dagudu tayi inda NURU tana ihu yaya zo kaga maciji yana tafiya acikin ruwa, ihunta ne yadawo dashi daga kogin daya Lula. A firgice ya dago tareda wurga mata wani mugun kallo yace "Waike Baitu meyasa gaba daya rayuwarki a wasa zata kare kinsaba da zaman kauye uwa ba kwaba koh? Toh zanyi maganinki" Zare ido tayi tana "kayi hakuri yaya NURU Allah dagaske maciji nagani shiyasa nake magana" daka mata tsawa yayi yace "Keep quite Yarinya sai zuba saikace wacce komai ya kwance mata" hannunta ya rike GAM ya dinga janta da sauri har cikin Dakin Hajiya su Ashwa kanwar NURU tabisu tana Dariya tace "yau kashinki ya bushe wajen yaya" gwalo takema baitu lokaci daya baitu tace atafau saita rama gwalon da Ashwa tayi mata. Gaban hajiya ya ajiyeta ya dank'wafar da ita yana "Cewa Hajiya kinga wannan maikama dayan ruwa bataji sai tayi ta sani magana kaman ma da ganda take zuwa inda nak'e hutawa tak'e damuna". Hajiya tayi Dariya tace "Ai Baitu tayi mun daidai datak'e saka magana, tunda bakada aiki saina tunani maganinka kenan" NURU yasaki baki yana kallon hajiya itako Baitu bayan hajiya takoma tana mishi gwalo. NURU yace "Hajiya Wato kin goyi bayan taci gaba da damuna Yarinya bakifi shekara goma sha biyu ba amma ki zaman ma mutane annoba". Hajiya tayi carab tace "Banaga annoba ba" ganin ran nuru ya baci baitu ta mike tayi wajenshi tace "Yaya kayi hakuri banida burin ganin ranka a bace nasan cewa Yaya bisma tana sonka sosai batason bacin ranka kayi hakuri bazan sake ba" shuru yayi yana kallonta cikeda kaunar Baitu amma yak'asa sa wata ya mace koda jaririya ce acikin ransa. "Baitu karki damu kinji na hakura" Dariya hajiya tayi tace "Nuru yakamata ka koma bakin aiki hakan shizai sa damuwarka da tafi gaba daya" "Hajiya damuwata bazata taba gushewa ba indai akan bisma ne na dinga tunaninta kenan har duniya ta nade, hajiya Nida aure har abada saboda babu wata mace dazata mayemun gurbin matata Bisma Wallahi babu" Ashwa dake tsaye a bakin kofa tace "Yaya ga baitu wacce zuciyar bisma ke dashe acikin zuciyan ta, nasan zaka samu duk wani farincikin rayuwa a wajenta" Nuru ya kalli baitu ya kalli hajiya yace "kar kucemun zuciyar bisma ce aka dasawa wannan mai kamada yan ruwa?" Lokaci daya yafara fita hayyacinsa, tuni suka rude maganinsa aka dauko aka bashi tuni bacci yayi awon gaba dashi. Wani ajiyan zuciya Baitu tayi tacewa Ashwa "Dan Allah kicema yaya yadaina cemun yar'ruwa aljana fah kenan?" Hajiya Dan Allah. Hajiya tace "Baitu karki damu zai daina wata rana ma matata zai dinga cemiki kedai ki k'wantar da hankalinki" kada kai tayi haka aka fara shirin sata a mak'aranta tundaga aji biyar na primary tafara kamar wasa Baitu akwai k'wakwalwa ga fahimta. [2/21, 8:29 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 3⃣4⃣ Bayan shekara Biyar Rayuwa takasance mai dadii saidai tsakaninmu da wayanda suka rasu Adu'a, Nuru ne zaune cikin falon gidansu inda yan uwa daga bangaren bisma da bangaren sa suka hadu don gabatar da muhimmiyar magana ciki harda jood'a da ya k'walam iyayen baitu. Manya kowa ya hadu magana daddy yafara cikin nasiha ga Nuru na cewa yaxama dole NURU kayi hakuri kadauki komai ba komai ba ita Rayuwa dakake gani ta gaji haka kila wataran bani ba hajiya ba Ummi bokowa anan, don haka namiji majiyi karfi irinka bazai zauna zaman gauronci ba dole kanemi mata. Haka kowa ya amsa da "kwarai dagaske" NURU jinsu kawai yakeyi amma shi gaba daya babu aure a tsarin shi gani yake idan yayi aure kaman yaci amanar Bisma ne, mahaifin Nuru yace "Kuma dakwai wani Abu da muka Dade muna boyewa saboda kwanciyan hankalinka da daurewar lafiyarka, dak'wai wasiyya da bisma tabari, Wanda yin hakan shizai nunama duniya cewa kaimai tausayine da rikon amana ga wasicci". NURU dai yakasa cewa uffan illah iyaka murna dayakeyi, Allah yasa bisma cewa tayi inyi mata Alkawarin bazan sake wani aure bayan itaba dako naji dadii kwarai, Niko Humairah nace tab dakamar wuya gurguwa da auren nesa, daganin fuskan NURU a kage yake dayaji wace irin wasiyya ce. Gyran murya mahaifin shi yayi yace, "Wato wasiyya ta itace indan na rasu a cire zuciyana Adasawa Baitu, wasiyya ta biyu itace baiyan raina kurike baitu da iyayenta amana sannan Mijina NURU ya auri Baitu a matsayin mata" dam kirjin NURU ya buga inhar mafarki yake yaci ace ya farka baxai taba iya daukan baitu a matsayin makwafin matarsa ba saidai a matsayin kanwa babu wata ya mace daxata maye gurbin Bisma. Kowa NURU yake kallo an rasa me yake sakawa acikin ransa, "kai muke saurare me zaka iya cewa idan harka aminche toh baza'a jimaba zaa daura muku aure" NURU hankalinsa ya tashi yace "Abba babu abunda bisma zata nema a duniya bare wasiyya bayan ranta ink'asa amincewa, na aminche" Yana gama magana ya mike ya fita batareda ya waiga ba, kowa dake falon saida ya tausayawa NURU. Fitansa keda wuya yaci karo da Baitu tanata karatu, dagani haddarta take bita, jitayi kaman ana kalonta tayi saurin juyowa, da gudu taje ta rungume NURU tace "yaya koda yaushe Alhaji koh hajiya suka kiraka sainaga gaba daya ranka ya baci kome suke gayamaka haka na bacin rai kasanar dani inje in basu hakuri sudaina don banason bacin ranka yaya". "Baitu kenan kinada tunani da hangen nesa shiyasa kaifin baseerarki take bani Sha'awa karki damu sunayine wai don insamu kwanciyan hankali jeki cigaba da karatunki yayanki zaije ya huta". Juyawa tayi takoma taci gaba da karatunta. Haka aka watse ansa ranan biki wata biyu, lokacin baitu tasamu hutun makaranta. NURU kwance yake babu tunanin dabayayi, Baitu tayimun karama a inkirata mata SS 1 fa take bazan taba Dan ganta bisma Da wata mace ba, noo I can't dukda baitu babu inda tabaro Bisma a cikar kamala amma nooo baitu saidai kiyi hakuri bazaki taba zama mata acikin zuciyana ba saidai kizama mata a wajen zuciyata babu wani hakkinki baitu dazan iya saukarwa. Baitu ce tsaye a bakin k'ofa duk maganan da NURU yake fada akunnenta suka kare, sallama tayi tana murmushi tace "Yaya kanata magana kai kadai har na shigo bak'asan nashigo ba tunanin me kakeyi kaketa kiran Sunana?" A rude NURU yace "kawai k'yawawan dabi'unki ne suke burgeni shiyasa kikaxo acikin tunanina". Dariya baitu tayi amma tasan ba haka bane, "hajiya tana kiranka yanzu fah basai anjima ba" Tashi tayi tafita tana wasa da hannunta gaba daya maganganun NURU kawai suke Dawo mata dukda kankantar shekaru tasan abunda yake nufi dakinta ta wuce. NURU jiyayi zufa yana keto mishi, "banaso baitu tasan irin zaman dazamuyi amma sai gashi maganar danakeyi acikin zuciya harta fito, tashi yayi yashiga Dakin hajiya yayi sallama yanemi guri ya zauna hajiya dake fuskantar NURU tace "Ansa ranan aurenka wata biyu yakamata duk wani shirye shirye afara saboda baitu ta tare acikin gidanta" nuru yakalli hajiya yace "Hajiya duk haka bai tasoba ana iya daura aure ta zauna daku anan kafin zuwa wani lokaci saboda nasa gidan a kasuwa, dazaran ankawo kudin zan fara Sabo a wajen gida DARI" hajiya tace "Lallai nema NURU toh baka isaba matarka Dole koh kanaso koh bakaso ta tare acikin gidanka don haka Tun wuri ka canza Shawara" Mahaifin NURU da yake kokarin wucewa yajiyo maganganun da hajiya keyi turo kofar yayi gamida yin sallama yace "Hajiya meye na tada hankali tunda haka yazaba mubishi yadda yakeso" "Amma alhaji taya NURU zai yanke wannan Sha'awaran amma nasan maganinka tashi ka bace mum dagani kuma kayi gaggawan sanarda baitu halinda ake ciki don baxamuyi maka ciki muyi maka goyoba". [2/21, 5:19 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 3⃣5⃣ Haka NURU ya fice jiki ba kwari, ransa yake cewa ashe kam za'a mutu inhar shizai sanarda Baitu cewa zasuyi aure Allah shi kyauta, jiyayi ana gudu Ashwa ce tabiyo baitu na gudu, kawai tsayawa yayi yana kallon yadda baitu ke tsalle kaman wata biri, Ashwa ta kasa kamata yana tsaye ta shigeta OC dinshi duk yana kallon ikon Allah, da Ashwa ta gaji ta tsaya tana haki tace gaskiya ke Baitu Kamar Dan biri, dole kici inter-Sport idan mun koma school. NURU yace duk kuzo nan, haka suke tahowa kaman wayanda ruwa ya cinye a gabansa suka tsugunna, kowacce idonta yayi kwal kwal zatayi kuka, "Kuna ganin har yanzu Ku yarane koh, kuna ganin tsalennan dakukeyi baxai haifar muku da matsala ba toh Wallahi Ku kuka dakanku randa za'a kaiku Dakin aurenku mijinku ya muku wulakancimaza Ku wuce marasa abunyi" baitu ce karshen tashi tuni yasa mata kafa ta fadi rijib a kasa gashi tasamu wani Hutu tayi wata hamshakiya kibar ta saita boye nonuwan dake dafe a kirjinta hakan yasa kowa ke mata kallon kwaila. Idan kika sake guje guje saina ballaki, sakara kawai sannan idan kina yawo ba dankwali, ba gyale saina miki illah, wannan fuskar dakike takama da kinada kyau saina saba miki kamanni mai kamada yar ruwa kawai bacemun". Da gudu Baitu ta shiga Daki tana kuka, hajiya ce tazo wucewa ta jikin dakin baitu taji sautin kuka, bata tsaya ba ta fada ciki rumgumo baitu tayi taji temperature din jikinta ya hau, ga masassara datakeyi kamar bazata kai labariba a rude hajiya ya fito tana kwalawa NURU kira amma ina baimasan tanayi ba yafada kogin tunani tsundum, dadamai duka tayi tace "Saika tashi muje asibiti baitu ba lafya sai rawan Dari takeyi". Cikin sauri ya mike mukullin mota ya dauko, cik yadauki Baitu gata da shegen nauyi hajiya tashiga cikin motar itama suka wuce asibiti, private sukake nan akayi mata gwaje gwaje, aka sanar dasu cewa Tabbas tana tattare Da damuwa, acikin zuciyanta kuma ga zazzabin cizon sauro dake dumunta, hajiya ta razana k'warai don bataso taji ance wani Abu zuciya don baitu bataji da dadi ba. Baitu dai gata kwance sai bacci takeyi, baitu sai yar lukuta ce, mai fadin fuska hancin nata kamar, biro ga idanuwanta farare kal, Dan bakinta kamar an tsaga mata duk Wanda yaga Baitu Wallahi ba namijiba hatta mace saita kalleta. Haka likita ya rubuta musu magani suka koma gida, bayan baitu taji saukine hajiya ta tsareta da zafafan tambayoyi, saboda bataso NURU yayi laifi tace babu komai kila ba gaskiya Likita yafada muku ba, Ashwa dake gefe tanacin indomie tace "Hajiya Wallahi itada yayane karya take miki, duk yadda Baitu take kyaftawa Ashwa ido saida ta tona. Hajiya ta mik'e a fusace, tayi sasan NURU tace "Sannu Tabbatacce Kaji tsoron Allah ka tuna baitu amana ce ga gareka baikamata kadinga bata mata raiba kasan lalurarta ta ciwon zuciya, kuma katuna yau saura kwana ashirin da biyu bikinku dukda ba tarewa zatayi ba dole ka kula da ita a matsayin matarka, inhar na isa dakai" Shidai NURU abun yafi karfinshi, washe gari tunda sanyin safe ya fita aiki, bashi yadawo ba sai misalin karfe goma na dare dayake gwamna bayanan shiyasa komai yazo musu da sauki yau, amma NURU yazo musu da wani albishir Wanda saida kowa ya girgiza, ya siya musu gida a garin Zaria acikin KABAMA can yakeso su koma, mahaifin Nuru yaji dadii k'warai, sannan yasama ma mahaifin shi shaguna Wanda zai dinga siye da siyarwa, a FULFULDE PLAZA, abun gwanin ban sha'awa, haka suka kwana da murna. Amma abun mamaki NURU yaga Ashwa yaga kamal amma baiga Baitu ba hankalinsa ya tashi amma saiya nuna kamar bai damuba, nidai Humairah nace NURU dama kadaina na Fulani kaso Baitu tunda Wanda ya mutu baya dawowa, *Koya kuka gani masu karatu*??????πŸ˜€πŸ˜€ [2/21, 7:21 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 3⃣6⃣ Haka NURU yaci gaba da harkokinsa amma yakasa sanarda Baitu cewa aurensu ake shirin yi nan bada jimawa ba, hajiya ce zaune cikin farfajiyar gidan inda yaranta mata masu aure wani gida suka kawo mata ziyara itada hajiya wacce akafi sani da Rabi, farace amma ba Sol ba, Ta auri Alhaji Usman Wanda akafi sani da ZUNNU-RAYN, Tun tana yar shekara sha uku haka tazo gidansa tazuba yaya har shida, batasan meye kishiya ba, bare yayanta Susan yan uba ba. Baitu ce tazo wucewa ta gaidasu tana washe baki, mommy tace "Dadina da baitu ak'wai aukin dariya komai nata yana burgeni babu inda tabar Bisma, Shiyasa na labari ya iskeni cewa yaya NURU zai aureta hajiya bakiji wani irin mugun dadii danaji ba" hajiya tace "Uhumm kukenan daku kasan inda ke muku ciwo banda NURU gaba daya bayata yarinyarnan nidai fatana karya wulakanta yar mutane muji kunya". "Hajiya kenan banda abunki ai inace zata tare a gidanta ne?" Hajiya tace "Meeeeeh inji akuya ai cewa yayi tazauna damu Wato tayi mishi kan kanta toh zanyi maganinshi saiyazo dakanshi yace bani matata mutafi kannan Baitu zata koma" Ni'ima tace "Hajiya Wallahi haka za'ayi Wato yaganta Yarinya bata cika mutum ba to koh saiya yara". Kowa dai acikin k'anninsa basuji dadii ba, shiyasa kowacce ta tofa albarkacin bakinta..... Haka sukayi hira harnawani lokaci harsuka gaji da jiran nuru kowacce mijinta yazo ya dauketa, baitu tashiga damuwa k'warai saboda zancen datakeji na aurenta da NURU yaxama dole insamu hajiya insan abunda ake ciki. Washe gari Baitu ta shirya tsaf zasu wuce makaranta hajiya ta kalleta tace "ke ina zuwa?" Baitu ta kalli hajiya cikin Rashin fahimta "Hajiya mak'aranta zani mana" "kizauna yau ya k'walam zatazo saboda shirye shiryen aurenki". Baitu tasaki baki tace "hajiya wai waye zaiyi aure naji Anata zancen aure? Lallai Ashe munada shan biki baitu tafara murna duk tana sane takeyi don ya zuwa yanzu tasan komai, Hajiya ta zaunar da ita tace "Kece zakiyi aure zaki auri yaya nuru dafatan kina sonsa?" Baitu ta kwabe fuska tace "nida yaya baya sona komai nayi ban iyaba nidai gaskiya saidai a chanza mun wani bashiba" Tafara buga kafa tana kuka haka hajiya ta lallasheta ta kwantar mata da hankali harta aminche". *SAURA SATI BIYU BIKI* *********** Hajiya ta hado akwatina dagani na fade, ya k'walam kuwa tadanyi tanadi, gashi an asace musu shanaye inba hakaba sa guda ake yankawo a biki, haka iyayen bisma sunyi abun azo agani inta kama ayi gulma kayane nagani na fade saidai kash basusan cewa baitu bazata tareba amma duk bata baci ba haka aka ajiyesu inda bazasu lalace ba, Ummi tana masifan son NURU shiyasa bata mantawa dashi kusan koda yaushe saiya kai musu ziyara sannan ga kyauta dukda ba mabuk'ata bane, hajiya taji dadi tace "Haka akeson mutum yayi kyauta ta dama ba tareda Hagunsa yasani ba fatana Allah yayima wannan yaro albarka. *KWANA UKU BIKI* ********* Dayake ba wani taro za'ayi ba, Amma baitu taji gyra sai kunga kawayen baitu yan kuci kubamu wasu koh irgan dangi basu faraba, baitu tasha gyra iya gyra mommy da ni'ima sunyi kokarin yin mata komai, haka aka shirya k'asaitaccen walima acikin gida, Ango NURU in Baku labari yaki sanarda kowa sai wayanda sukeda link da gidansu, su hamdan da kausar sune kan gaba, haka aka shirya walima babu nuru, baitu bata damuba itada kawayenta sai hira suke suna dariya waaxin da akayi musu yashigesu kwarai, ba akan komai bane sai biyayyan aure Sanin kima da darajan miji yan'uwan miji, tsarekai daga fadawa halaka. [2/22, 8:19 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 3⃣7⃣ Haka aka watse kawayen amarya su Ashwa ana can ana ta hada hada, ya k'walam ce zaune tacewa hajiyan NURU "koh kunsan Baitu ba sunanta na Asali bane" hajiya tace "kai haba duk daukanmu ai sunanta kenan?" Ya k'walam tace "Ah ah sunanta *MUJEEBA JOOD'A*. Tuni hajiya tasanarma NURU cewa baitu sunanta mujeeba haka aka sanarda kowa sunan Baitu na asali. Kuma baitu tasan sunanta amma ta boye kai Fulani sai abarsu, NURU ne ke wannan maganan kuma a rayuwarsa yana masifan son sunan don har cewa tayi sunan yarsa tafari mujeeba dansa na biyu mujeebu, washe gari ajayiwa baitu kwaliya nagani na fade haka tadinga shigan kaya iri daban daban, misalin karfe biyu da rabi na rana aka saura aure *NURU DA AMARYARSA MUJEEBA*. Dayake bikin bakowa yasani ba shiyasa mutane tsiraru kake gani, mahaifin bisma shiya bada baitu ma mahaifin Nuru, akan sadaki naira dubu hamsin, aka zanyi Adu'oi aka shafa fatiha, abokan ango kausar da hamdan suke kai kawo har aka gama biki. Washe gari akayi budan kai da yamma Ummi dasu ya k'walam akayita ma baitu fada kamar zasu ari baki, koh Dan kukanda amare keyi baitu batayiba saboda baasan ciwon kaiba baasan zafin rabuwa da iyaye ba haka kowa ya watse. Gida Yaza mana shuru daga Baitu sai Ashwa sai kamal Wanda ya tasa baitu yana mata tsiya harta kulu tafara kuka, shigowan yaya NURU ne yasa kamal tashi yabar wajen, NURU ya kalli MUJEEBA yace "ke lafya kike kuka kamar wata karamar Yarinya?" Ashwa tace "Ya kamal ne yake tsokananta wai matar yaya NURU" NURU ya kulu yace "Shine yazama abun kuka? Allah wadaran naka ya lalace" mtwww tsaki yayi ya wuce Dakin hajiya ya gaidata yayi mata ban gajiya. Hajiya tace "Toh yanzu nauyi ya rataya akanka, dukda muna tare dole kasauke duk wani hakki daya rataya akanka daga sutura Rashin lafya cinta Shanta, dukda muna tare har lokacin daka mulmula ka mulmule kanemi matarka saimu baka kajini koh hantara kyara kar inji kar in gani, kanuna mata so kajata ajiki har tasan meye aure da abunda ya kunsa". Nuru shuru yayi yakasa cewa komai saida yadau minti biyar yace "Zanyi yadda kikace insha Allah" haka Alhaji yayimai fada sosai. Bayan SATI daya da biki MUJEEBA ta shirya tsaf itada Ashwa zasu makaranta dukda sunkusa komawa garin Zaria daxama, skirt ne mujeeba tasa iya gwiwa sai safa ta tuma uban gashi ta kulle tadau Beret tasa duk Wanda yaganta saita bashi sha'awa, sun kammala breakfast kenan, hajiya tace "Mujeeba yimaxa kikira yayanki yakaiku school karku makara" MUJEEBA bataso ba amma babu yadda ta iya da dariyarta ta mike tana tafe taku daidai ta isa kofar sasanshi knocking takeyi tana sallama, haka yafito dagashi sai boxer saurin kauda kanta tayi tace "Mun shirya kaxo ka kaimu school naji ance zakayi musu bayani cewa ni matar aurece" Wat!!!!!??? Zare ido NURU yayi yace "you must be out of your sences matar aure wakika aura?". MUJEEBA ta mishi wani banzan kallo ta juya zata tafi sai wata zuciya tace koma kibashi amsa, juyowa tayi saida gabansa ya fadi "Kaina aura kuma Kaine mijin look Malam idan zaka iya kaimu you better do inkoh ba hakaba munada kafa biyu don ba guragu Allah yayimu ba, banda mistake mezanci dakai look at you" haka tafadi ga turancinta dake dabo, da fillanci. Tafiyarta tayi NURU ya mutu a tsaye yace zanyi maganinki bazaki taba zama mata acin zuciyana ba saidai a waje bisma ita nakeso kuma da sonta kadai nake Rayuwa. Kafin yayi brush ya fito su mujeeba har sun tafi adaidaita suka tsare suka kama gabansu, fitowa yayi yashiga folon hajiya yace "ina suke?" Hajiya ta kallai tace "Banda labarin inda suke kai Wallahi kadaina abunda kakeyi Wallahi Wanda ya mutu ya mutu, kadaina wulakanta Mujeeba don wata rana".........sai tayi shuru arude yafita har yarigasu zuwa makarantan. Ashwa ce tacewa mujeeba "kinga kaman motar yaya?" Mujeeba ta tabe baki tace "kinga idan kallonsa zaki tsayayi ni banda lokaci mu wuceshi mununamai cewa mu fah manyan yarane" haka suka wuceshi yana mamakin yadda suka jisgashi cikin class suka shiga suka zauna suna karban darasi, aikowa akayi akira mujeeba kowa na class yace babu mujeeba, aka kara dawowa akace MUJEEBA JOOD'A akace babu mujeeba jood'a sai baitu jood'a, NURU yace "Malam itace" haka aka zakulo mujeeba sai office malam, salman yace "itace wannan? NURU ya kalleta yace "Eh Inaso pls kubarta tadinga sa hijab sannan akula banda kallo don naga kusan Duka school din Malamai mazane, haka principal yace toh takoma class saida ta harari NURU kannan ta fice. Haka NURU yakoma gida da tsananin tunanin nayi kuskure danace baxan tareda mujeeba ba Dana dinga Dana mata gyada a hannu nasan daduk wani iya shege saita rage amma zan tuntubi hajiya inji, don iche Tun yana danye ake tankwara shi don mujeeba takara shekara daya gaba nizata gasawa gyada a hannu. [2/22, 7:57 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 3⃣8⃣ Ni melody dake gefe mezanyi banda dariya nace tabbas NURU ka makara, ichen nan yarigada ya bushe, cikin gida yashiga da mota yayi packing amma kafinya shiga gida Adu'oi kawai yake rerawa acikin zuciyanshi, kitchen ya iske hajiya tana yan gyre gyre saboda hajiya bamaison yar aiki bane tafison tayi aikinta koda zai kaita dare tanayi, “hajiya sannu da aiki”kujera ya dauko ya zauna yace “hajiya gaskiya na canza sha'awara inajin nan zaku tafi kubar mujeeba saboda yan wasu dalilai”hajiya ta ballamai harara tace “kul karka sake kazomun da zancen banza don wallahi koda kukan jini zakayi mujeeba dani zata zauna sai ranan da ka bukaceta don yanzu nasan bakada wata manufa illah ka muzguna mata kar inji”ta juya taci gaba da aikinta haka NURU ya mik’e yanufi dakinsa. Misalin karfe biyu su mujeeba suka Dawo agajiye ko zama batayiba NURU yashigo yace “ke yimaza ki hadamun abinci kikaimun Daki sannan ki hadamun lemon natural ki matse ki kaimun, haka Baitu ta sakankance da kallonsa tace “wai yaya meyasa bakaso inhuta ne daga dawowa na sai aiki kabari idan cikina ya dauka nayi full charge sai ayi wacce za'ayi idan zaka iya jure yunwa toh ni bazan jureba” Daki ta wuce tabarshi tsaye yana cizon yatsa kuma abincin dabata kai maiba kenan. A kwana atashi asaran mai rai sunata shirin komawa Zaria, haka sukayita ban kwana da yan'uwa makota Baitu kam har shinkafi aka kaita tayiwa su Ummi da Abba bankwana haka suka kara yimata fada akan kama mutuncin kanta sannan tasan cewa aure ne akanki, iyayen Arziki kenan basuda wani buri illah kizauna lafya hakuri da juriya yi Nayi bari na bari, akasin iyayen banza basuda wata sha'awara saita yana miki kiyimai, daya ajiye riga ki lalube idan bai bakiba Karki dafa kaico duniya ina zaki damu iyaye mu gyara halinmu, Tabbas duk macen dakeson zama zinariya acikin gidanta awajen mijinta saita yi aiki da sha'awarar Arziki, tattausan lafaxi, iya Girki, iya kwaliya, iya kissa da kisisina, iya taku, da wannan kadai kinciri tuta bare kuma akaiga wajen kwanciya. Haka suka koma Gusau washe gari sai Zaria yaran hajiya Duka dasu aka taho rakiya kamal dashi zasu koma Ashwa itace kawai ta rage musu a gabansu saikuma baitu Wato mujeeba, dazuwansu gida suka katafaren gida nagani na fade, bangare kuda dagani ba bayani na Baitu ne sai wani achan gefe Wanda yasha kayan gabas na iyayensa ne, Hajiya da Alhaji tuni suka fara kukan dadi suna Dada shima NURU albarka suna tuna irin bakar izayan da sukasha a baya da yawon haya da dawainiya da sukayi da NURU wajen ganin Yazama wani Abu a Rayuwa, sai gashi yau sune cikin wannan daular Hajiya tace ARZIKIN YAYA kenan duk macen data haihu karta cire rai, sannan duk macen dabata haihuba ba wani rabo idan yaso zaki haihu saikin haihu saidai idan bakida kwai a duniya. Kafin abude gidan saida akayi Adu'oi sannan suka shiga ciki, aljannar duniya idan baka mutuba baka gama ganin abun duniya ba, baitu kuwa washe baki kawai takeyi sai jin dadi takeyi, Ashwa kuwa takasa zaune takasa tsaye haka sukayi settle washe gari duka suka koma saidai NURU yananan don saiyaga komai ya kan kama na gameda shagunan alhaji, harda masuyi musu hidima suka samu dayake Nuru yanada abokai a Zaria musamman a dogarawa, kayan abinci haka yasiyo musu kamar baisan zafin kudiba, hajiya tace “Kai nuru irin wannan siyayya kaman ba'a buhariyya? ” Nuru yayi dariya yace “Hajiya inda kudi suke Wallahi Sunanan talaka shike shan wuya hajiya abun sai godiyan Allah kinji” Baitu ta kalli NURU tace “Tace yaya shikenan mun daina zuwa school haddanmu shikenan ta tafi?”Nuru yayi mata wani irin kallo tuni ta natsu. Haka yakammala komai hatta makaranta saida yasasu aka sama musu direba, Alhaji Yakama Sana'a kannan yabar garin Zaria, koh waigen Baitu baiyiba ya wuce Baitu tace “Aikin banza harara aduhu Kaine da sannu baniba, kayi a banza nima na huta da kyara da zagi duk kai kadai”tsaki tayi ta shige ciki haka suke hira da Ashwa, hirarsu bata wuce na yadda ake soyayya, wata kawa sukayi ma'abociya karatun littafan Hausa, haka suke bata kudi tana siyo musu a boye tunda basuda waya, nan Baitu wadda akafi sani a yanzu da mujeeba tafara course kala kala, littafin Zainab dahiru wauwo tafara karantawa subul da baka, Wanda ya chaza mata kwa kwalwa daganan, tafara karanta littafan RAHMATU HASSAN ZARIA, Daganan baitu tafara jin shauk'in kasancewa tareda mijinta “Ashwa Ashe haka so yake Tabbas akwai dadi Zanso ace nima ina cikin wannan yanayin da yaya nuru amma taya zanyi don ganin nasamu guri acikin zuciyanshi?”Ashwa tace “kibari zan samo miki lambar Humairah wacce nasan duk Abunda zata fada miki akan yadda zaki sace zuciyarshi saikinyi mamaki”. Kubiyoni kuji yadda baitu zata sace zuciyan NURU sannan abun tambaya anan shine NURU dawuya ya aminche koh kuma ta tafi da imaninsa bayan yana soyayya da matacciyaπŸ€” [2/23, 2:20 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 3⃣9⃣ Kusan karatun littafin Hausa ya zame musu jiki, karatun bokon har nema yake ya bace musu saboda tsananin karatun Hausa, a Kullun Baitu kara koyan fasahohi takeyi naban mamaki da Al'ajabi, an shafe kwanaki babu NURU babu labarinsa k’watsam yasa ranan zuwa Zaria don gaidasu hajiya don badon mujeeba zaizo ba saboda a cewarsa bata cikin tsarin rayuwarsa, hajiya take sanarda su Ashwa da mujeeba cewa yaya NURU yana nan tafe jibi haka Ashwa da mujeeba Suka shiga Daki don shawarta yadda lamarin zai kasance. Lambar Humairah suka kira bugu daya biyu ta dauka, cikin muryan natsuwa da kamala sallama tafara daga bisani ta buk’aci jin suwaye ke magana, saboda son da takema mutane yasa duk Wanda yakirata don Neman shawara koh taimako take basu dukkan Attention dinta, Ashwa ce tace “barka dai malama Humairah nasan zakiyi matukar mamaki, sabbin kanni kikayi suna bukatar taimakonki idan har ba matsala”? Humairah ta nisa “Kufadi matsalar Ku Allah yasa inada mafita” haka suka zayyana mata komai daga farko har karshe, nan Humairah ta fara bata shawara ta farko tace “abunda zaki farayi shine kije saloon ayimiki gyran gashi, sannan kiyi kunshi nagani na fade sannan, kiyi mai special abinci sannan kisa kaya Wanda babu raini kiyi kwaliya kaman wacce zata gasar kyawawa, kifeshe jikinki da turare masu kamshi be nuru ba hatta Rossy duk girman kansa dole yaji wani Abu acikin ransa, sannan Karki sake ki nuna kina murnan zuwanshi yadda kika saba haka zakici gaba da shaaninki, ina gaya miki idan bai tafi dake acikin zuciyaba saiya Dawo dake”. Haka MUJEEBA tayi farin cikin wannan shawaran sannan sukayi mata godiya suka kashe wayan tafi sukayi sukayi shewa Ashwa tace “Yar'uwa dole mu mike saboda yanzu namiji yanasonki yakika k’are bare bayaso”Mujeeba tace ganemin hanya, wajen hajiya suka nufa suka gayamata duk bukatunsu ta aminche, kudi ta mika musu Wanda zai ishesu suka wuce SHANTEL Saloon dake tudun wada direba yakaisu yajirasu daganan suka wuce kasuwa kayan Queens cake suka siyo harda na icing, kayan hade hade na fried rice chicken soup and the rest. Gida suka wuce Ashwa tana kallon irin tsaruwan da Mujeeba tayi tace “Matar yaya kinga irin kyau da sheki dakikeyi tabbas sweet sixteen yana tasiri akanki baby kiyi komai ba komai Saima gobe”Mujeeba tayi dariya wacce take kara fito da kyawunta tace “Sweet Ashwa you will never understand yadda nakejin mijina acikin raina bantaba Sanin cewa haka aure yakeda tarin niima da ladaba saidana k'aranta *Matar So* Wallahi sainaji duniya tanamun dadii tabbas aure yayi komai kikayi lada ne acikin gidanki amma kinga bariki babu abunda mace zata tsinta sai walakanci sannan ba godi bare nagode, sannan lada saidai kiji labari a makota makotan ma Ma'auratan juna”. Shewa sukayi suka shiga gida hajiya taji dadin ganin Mujeeba yadda tayi kamar wata sarauniya, washe gari Tun Asuba suka tashi da aiki, Ashwa ranta baiso ba Amma batada yadda zatayi saboda shakuwar da sukayi da juna suyi fada su shirya, hajiya tanata mamakin Mujeeba tace “Tunda mujeeba taji mijinta zaizo naga duk ta canza Allah yasa NURU ya yaba lokacin zaiji magana”kitchen tashiga tana duba aikin da sukeyi cikin natsuwa da tsafta cikin kankanin lokaci suka kammala aka jera komai inda yakamata, Daki suka shiga suka shek’a wanka amma ita Ashwa batayi wani kwaliya ba amma duk Wanda yaga Mujeeba baxai sake cemata baitu ba wata atampha tasa mai ruwan kore, komai nata too match, turaruka ta dauko daga humra zuwa kulacca turarukan Kamshi na waje carribein shine Wanda tafi k’auna haka tasa takalmi Kore. Horn sukaji Ashwa ce tayi saurin lek’awa tace “Beb he is here waw can't you see how you're looking, hmmm Epitome of beauty kenan ”Dariya sukayi Mujeeba ce tayi sarin fita koh gyale babu sai takalmi dake sanye a kafanta. [2/23, 7:10 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 4⃣0⃣ Bada niyyan bude kofa taje ba amma jin ana kwankwasa kofa tace “Yes am coming ”bude kofan tayi lokaci guda ta juya tana tafiya cikin salo nidai anan har cewa nayi irga tafiyan takeyi NURU tsaye yayi yana kallon kirar da Allah yayiwa wannan baiwar da mamaki sai cewa yayi “koh ina hajiya tasamo wannan yarinyar datake Neman rikita mutane gosh meyasa haka wannan ai salon Asa mutum cikin halaka ne” Itadai tafiyarta tayi ganin yadade bai shigoba yasa mujeeba juyowa tace “You are welcome pls come in an have a set”tafadi tana nunamai kujera. Gabansa ne yayi mugun fadi yace “Tab Ashe yau danayi abun kunya karamar Yarinya ta rainani”sallama yayi hajiya tafito cikin zumudin ganin danta tana mishi marbabin, itako Ashwa tsale tayi ta haye kan NURU tana mishi sannu da zuwa, hajiya ta kyalla ido taga Mujeeba bata falon kwala mata kira tayi Mujeeba! Mujeeba!! Mujeeba!!!. Daga k’uryan Daki ta amsa Ashe wasu kaya aka canzo, Hajiya tace “Waw wannan kwaliya haka nasan na tarban mai gidanne Ku dauki jakkansa kushiga dashi dakinsa”. Wani irin kunya ya lullube Mujeeba amma saita basar tana murmurshi Ciki suka shiga da jaka itada Ashwa suka kece da Dariya “Yar'Uwa kinga wani irin kallo da yaya yake miki yadda kikasan yaga bak’uwar fuska tabbas shawaran Humairah ta karbu, Hajiya data gaji da jiransu ta k’wala musu kira da gudu suka fito cikin isa Mujeeba ke tafiya, “Kuyi maza Dan Allah Ku kawo mishi abinchi mutum ya shawo tafiya ace Baku bashi abinchi mujeeba aikinki ne maza ”. Mujeeba tayi far da ido tace bismillah muje dinning, tafiya take yana biye da ita saboda tsabar kallo harsaida yaci tuntube kaman zai fadi mujeeba tayi saurin tareshi tace “Kayi a hankali mijina kar jiwa kanka rauni don bansan yadda zanji in naga jini yana zuba daga jikinka ba” NURU kasa magana yayi saboda tsabar dadin murya mujeeba ga iya salon magana kaman bisma. Zama yayi tafara bude abinchi tana serving saboda kamshi saida miyansa ya tsinke don har zuba yaso yayi Niko mezanyi banda Dariya nace NURU ka kusa zuwa hannu. Bayan tagama serving dinshi ta zauna itama tasa abincin kusa dashi ta koma tace “mijina yakamata kabari inbaka abinchin a baki saboda na hutassheka kaga ka gaji, jiyayi bazai iya share mujeeba ba yace “Mujeeba Dan Allah Kidaina irin wannan magana tana rudani abinci kuma kiyi hakuri zanci da kaina” Yak’ara kai loma daya na farfesun kayan cikin rago. “Mujeeba wannan irin kwaliya haka kaman zaki gasan kyawawa, dafatan ba haka kike fitaba”? Mujeeba tace “Haka nake fita don har sabon saurayi nayi sunansa Umar Wallahi yaya baka ganshi ba son kowa kin Wanda yarasa, gashi da shegen kishin tsiya basan yadda zaiji ba Dan na sanar dashi cewa inada aure”. Abinci NURU yakeci amma gaba daya maganganun mujeeba sun ruda mishi ciki, jiyayi cikinsa ya murda inajin saida NURU yashiga toilet yafi a irga itakoh mujeeba da gangan tayi wannan maganan saboda tagane cewa yafara sonta kokuwa har yanzu? Tashi tayi tabar falon Daki ta koma ta haye gado tana tsale tana murna Ashwa ce tashigo tace “Ke gayamun yadda film din yayi ending? ” Mujeeba ta rungume Ashwa tace “Ashwa Aunty Humairah tayi a Rayuwa dole in shelantawa matan duniya cewa she is the best batada wani buri saina ganin ta gyra zaman aure da rayuwar cikin auren, Ashwa am speechless duk ranan da yaya NURU yafurta cewa yana sona Wallahi sainayiwa Humairah kyautar ban mamaki” Gaskiya ne Mujeeba tabbas Allah zai sakawa Humairah da Alkhairi. NURU kuwa Gwanin ban tausayi lokaci daya ya fige hajiya tafito tana tambayan sa lafya yake sanarda ita cewa cikinsa ne ya burge haka ta kawo mishi plygin ta hada mishi ruwan gishiri da Sugar, zama yayi yana fuskanta hajiya maganan mujeeba tana damunsa harya kasa jurewa zuciyarsa yace “Hajiya yanzu a matsayin mujeeba na matar aure bai kamata tana irin wannan k’walliyan tana fitaba, sannan hartana kula samari wayanda ba muharramanta ba kuma tasan cewa Nike aurenta amma take irin wannan? Gaskiya tare zamu koma Gusau saboda indinga samata ido sosai”. [2/24, 9:00 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: *DASHEN* πŸ’” πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 4⃣1⃣ *Ina Kara jaddada godiya na ga masoya wannan novel saboda kaunar dakuke mishi ngd kwarai Allah yabar zumunchi Adu'arku gareni Tabbas tana tasiri Allah yakaremu da karewarsa, ya Allah karka barmu da iyawan mu ya Allah*AMINπŸ‘πŸ» LYSM MY FANS😍😘 Hajiya ta wani harareshi tace “lallai wuyanka yayi kauri ka dubi tsabar idona kace zaka tafi da ita saboda kadinga sa mata ido, Toh ni me nake samata kafa ko katare? Tambaya nake kayi shuru?” NURU yayi shuru yarasa abunda zaice ga cikinshi sai kara murdawa yakeyi. “Ai mu ba tarbiya muke koya mata ba kai kadai kasan yadda zaka bata tarbiya toh koda mujeeba zata tare ba yanzu ba kuma saida aminche warta shashashan banza shashashan wofi lokacin da'akace atare me kace sai yanzu zakazo da kumfan baki wai zaku tafi Gusau kutai kebbi gaban Gusau saida kaga yarinya tayi dumimi tazama mace kayi gaggawan canza shaawara”. NURU yace “hajiya Wallahi samari take kulawa kuma kinsan bayi bane matar aure ta kula samari” “Ta kula din ai cewa kayi kaifa baka sonta toh mexakayi da ita bayan kana soyayya da matacciya Wallahi Kasani Wanda ya mutu baya dawowa, Sannan abunda babban ya hango yaro ko yahau Dutsen Mambila bazai hango ba” hajiya na gama magana saika Alhaji yadawo saga kasuwa yayi farincikin ganin dansa amma saiyaga kaman baya cikin walwala, haka suka gaida yace “Nuru lafya naganka kaman mai jinya? Koh dai...... Hajiya ta katse da cewa “Matarsa yakeso abarshi yatafi da ita shine ya tsareni yanamun wa'azi waishi kabiru Gombe na gayamai ba yanzu ba Sannan idan ka gaji da zaman kadaici kayo aure kanada daman yin mata hudu harda k’wark’wara idan kaso amma addini hudu yace namiji yayi”. Mahaifin NURU yace “Hmm yaro kenan Kanaso kace yanzu kafara son mujeeba ne? Idan harka fara sonta kamata yayi kasanar da ita hakan kila hakan yasa ta Aminche ta bika” Budan bakin NURU yace “Ni gaskiya Alhaji har yanzu banjin mujeeba araina Amma ayimun adalci mutafi tare acan kila ma saba har naji inasonta ” “Aikin banza Ashe da sauranka amma bari akira mujeeba aji idan tanason binka shikenan idan kuma tace Ah ah Wallahi kai kadai zaka koma”. Haka Hajiya ta kira mujeeba, ta zaunar da ita tace “Mijinki gashi yace zaku tafi tare” mujeeba tayi saurin dagokai tace “Hajiya babu inda zani inanan abunda basona yakeyiba salon mutafi ya dinga muzgunamun bakwa kusa ai nikam babu inda zani” tashi tayi dagudu tayi cikin daki tana shiga ta kece da dariya tace kadan kafara gani indai mujeeba ce duk ranar daka furta kanasona ranan nikuma zan tabbatar maka da irinson danake maka. Ashwa tace “kinyimun daidai Wato yaga komai yaji ya rude kuma yana fulako baxai ita cewa yanason matarsa ba lallai Girman kai rawanin tsiya ai Karki kuskura kikai kanki wata rana ayimiki gori” NURU yashiga tashin hankali kwarai iyayensa sunki bashi Goyon baya haka yakoma yana Dana Sanin zuwansa. Kusan tsawon kwanakin dayayi haka yadinga shak’an bakin cikin Mujeeba don wata rana gyale a hannu take rikewa tafita Sannan ta bazo gashi nan har Gadon baya, Sannan wasu kaya take sawa masu tada hankali ga iya kwaliya da magana fita zasuyi itada Ashwa amma itace tafara gaba, wani sak'o ya boye ganin tana tahowa ya janyota sai akan jinkinsa tuni yaji numfashinsa yana Neman daukewa saboda wani kamshi dayaji *AROOSA* marairaicewa yayi yace “Mujeeba inazaki kikayi kwaliya haka dubi irin shigar dakikayi”cikin kafin hali tace “banason wulakanci Malam meye matsalanka da inda zani Sannan meye matsalan shigan danayi? Pls kaga banason irin Wannan policy din saikace ka ajiyeni tsakarmun hannu”. Tashi tayi tana huci “Mujeeba Kituna ke matar aurece Karki manta ni mijinki ne” “Dakata malam ta ina naxama matarka? Inace kace bazaka taba kirana ba matarka ba zaifi dadi idan kama koma cemun Baitu ba Mujeeba ba koh Matarka, inace bazaka iya sauke hakkina dake kanka ba, inace soyayya kake da matarka nikuma banaso na nisantaka da ita shiyasa neke Neman Wanda bashida soyayyar matacciya acikin ransa in aura” wani wawan mari yakaiwa Mujeeba amma tuni ta chabe hannunsa tace “kul ka kuskura ka tabani ba aureba koh dadirone saika sakeni, A tarihin rayuwana babu Dan Adam din daya tabasa hannu ya mareni bare duka, idan kana ganin kanason Bisma nasan bakakai iyayenta ba haka baka kaini ba saboda sa zuciyarta nake Rayuwa”sauke hannunsa tayi ta wuce aguje sai daki, fitan data fasa kenan. [2/25, 7:57 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 4⃣2⃣ _*Ina mik'a taaziyya ta ga Mienerh Hamidan abisa rasuwar aminiyarta datayi Sadiya sani maitama Allah ubangiji yaji kanta yakai haske kabarinta yasa Yan matan Aljanna neπŸ‘πŸ»AMIN*_ Tsaye yayi yana huci takaici ya lullubeshi, ciki yakoma ya kutsa daki ya jingina da Allon gado Ga AC tana hurawa amma zufa kawai yakeyi. “Mujeeba kinsan irin sonda yaya yake miki kuwa dole ya rude yarasa kansa you are killing baby”Dariya tayi “Ashwa kenan nasan yaya yakamu dasona amma yakasa ya furtamun nasan cewa iya bakine baikai zuciyaba”. Gaba daya suka dauki littafan su suna karantawa kwankwasa kofa sukaji anayi amma babu wacce ta damu data tashi ta bude, illah iyaka gyara kwaciya dasukayi. Banko kofar akayi lokaci guda ko wacce ta boye littafin dake hannunta, yaya NURU ne tsaye yace “idan bakwa komai pls kuzo parlour” Ashwa tace “yata da kalau kuwa”? Ta tambaya wani banzan kallo yayi mata ai basusan lokacin da suka mikeba Ashwa ce ta fara fita Mujeeba ce ta karshe kayan baccine a jikinta mai shara shara amma mai wando ji yayi yaji kunya haka Mujeeba zata fita ga Alhaji a parlor a matsayinta na surika? “Malama je kisa hijabi koh bakisan kunya bane koh kin manta gidan surukai kike? Pls do as I said” gani kawai tayi ta juya ta dauki hijabi gaba tayi yana binta koh ajinkin hijabi malam abun saida yayi magana. Guri suka samu suka zauna babu mai cewa uffan nuru yace “badan komai nakiraku ba saidon in mika muku waya wacce xata zama abokiyar hira Sannan kuma don yin Assignment for Dan an baku, Sannan Inaso inja kunnenki Mujeeba idan kika sake kikaba wani lambarki Tabbas Allah shi zaiyi mana sakayya saboda auren ki nakeyi banda chatting da wayanda ba muharramanki ba Hajiya kina sheda?”. Hajiya tayi shuru daga bisani tace “kwarai maganarka gaskiya ne Mujeeba dole kiyi biyayya ga mijinki koda Baku tare hakkine akanki ki kare kanki ” Mujeeba tace “nagode Hajiya zan kiyaye”waya yamik'o musu *INFINIX HOTNOTE* kowacce da irin kalar tata kuma da layi aciki sunyi murna sukayi godiya suka koma daki washe gari suna bacci NURU ya wuce GUSAU. *TUNA BAYA ROK'O* Rayuwar gidan Ikram da Kausar abun sai godiyan Allah babu wani kwanciyan hankali tun bayan auren dukda yan'uwan taka kausar babu irin cin kashin dabaya mata, baxai Dawo gida akan lokaci ba Sannan bazai bata abinci ba, saidai ya ajiye mata naira Dari biyu, bakuma don bashidashi ba ah ah mugunta irinna namiji, cikinta yayi girma har yakaiga bata iya aiki yadda yakamata, tafe take dakyar KAUSAR ya daka mata tsawa Wanda saida taji Dan cikinta ya juya juyowa tayi ta kalleshi yace “So nake ki k’washi kayan dattin chan dake daki ki wanke daga yau nadaina kai wankau ke zaku dinga wankesu daxaran sunyi datti” jitayi jiri yana dibanta dakyar ta iya cewa wani Abu “Haba KAUSAR bakaga halinda nake cikibane amma kake Neman halakani da wanki kana gani hatta wankina yimun akeyi aikin gida sainayi dagaske ka tausaya mun KAUSAR”. “Koda nakuda kikeyi saikin wankesu ubanwa yace kiyi ciki? Dazaki gayamun halinda kike ciki bansaniba makaho ne ni idan kuma baxaki wankeba kofa abude take you are Free to go” Tashi yayi yafita ikram zubewa tayi a k’asa tana rasgan kuka Wanda babu maijinta sai Almajirinta dake zaune yanacin tuwo. Mikewa tayi tashiga Dakin kausar ta kwaso himilin wanki Wanda baita mai cikiba nida bake saket saidana razana haka tayi wankinnan tun safe har magriba kannan ta gama, Sallama taji tayi saurin amsawa Kausar ne yashigo tareda budurwarsa kallo daya yayima ikram ta kauda kai cikin falon ta suka shiga tun tanajin shewansu harta dainaji, Kara jigina tayi abango tana kuka haka ta bude kitchen anan ta kwanta ga yunwa gashi mukullin store a hannunsa yake, cikinta murdawa yakeyi “Allah Kaine gatana Kaine abun bautawa ya Allah idan Wannan aure Alkhairi ne agareni ya Allah ka sassautamun Wannan musibar danake ciki idan kuma ba Alkhairi bane ya Allah ka kawo sanadiyyan rabuwana da KAUSAR” kuka takeyi Wanda saida nima nafara kuka nace Ashe haka mata suke hakuri da mazajensu tabbas dayawa maza wuta zasu shiga. Misalin karfe hudu ikram tafarka daga nannauyan baccin daya debeta maicikeda mafarkai marasa dadi, dakyar ta mike tace “Tabbas Ana cewa dazaran namiji ya aureki yakai ki gidanshi kika dau ciki toh kin tashi daga matarso kin koma matar hakuri soyayya ta kare sai zaman hakuri Tabbas yau na gasgata maganar mutane amma wasu idan sukayi dace duniya dadi take musu” waje tafito taci karo da wata tsohuwa cikin gidanta bakaramin tsorata tayiba harta soma Jada baya tana Adu'a, tsohuwarnan tace “ke Yarinya kibarjin tsoro kuncinki yakare daga yau” yadda matar take magana gaba daya muryar saita ba mutum tsoro, nidai Humairah nace Ikram kinyi gamo da Aljanna. [2/26, 10:19 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 4⃣3⃣ Adu'a kawai takeyi cikin ikon Allah matar nan sai matsowa take tace “Ke macece mai hakuri daidai ake samu masu irin hakuri ki, nayi alwashin duk budurwar dayayi soyayya da ita sai nayi Ajalinta Sannan kedai kici gaba da hakuri wata rana Zakiga sakayya Sannan duk lokacin dakika bukaci wani Abu zan kawo miki” kiftawan ido ta nemi aljana ta rasa Ashe cikin jikinta ta kutsa ta shiga, tana bacewa ikram tafadi ak’asa war was saida gari ya waye tangaran ta mike dakyar tashiga cikin daki abun mamaki anyimata face face da daki saboda kazanta amfaniyansa a gado yake zubawa saboda gudun kar budurwar ta dauki ciki, nidai danice kwarai da wata rana nayi Ajalin kausar saboda Dan akuyane ba karshe Wanda babu tsoron Allah acikin ransa. Haka ta yaye zanin Gadon tana kuka tana kaiwa Allah kukanta, haka ta gyra Dakin cikin natsuwa da kwanciyan hankali lokaci daya ta maida komai ba komai ba, tana gama aikin tashiga mak’ota wajen wata kawarta tana kuka tana gayamata halinda take ciki matar taga kokarin Ikram dabata sabauta budurwar ba. “Ikram kenan kedai abar kaza cikin gashinta idanko ba hakaba an dinga tonon silili kenan kowacce mace dakika gani da bakincikin da da namiji yake k'unsa mata saidai hakuri kawai shine zai kaimu ga cin nasara, shiyasa bodan wak’a yace Soyayya da dadi soyayya da ciwo mai hakuri mawadaci ne wataran zai dafa dutse don haka kedai ki kalli ko wacce mace duk arzikin mijinta saukin samu Abu biyu dayake mata Wanda yake kuntata mata”. Ikram ta share hawayenta tace “Amra nagode kwarai inace duk duniya nice kadai namiji yakewa wasan kwallo Ashe mata da yawa boye sirrinsu sukeyi shiyasa bakajin damuwarsu Toh Allah yayi mana sakayya wata rana matar wani zaibi kuma ayi ajalinsa” Amra ce ta mik’e takawowa Ikram shayi mai kauri da bredi da kwai harda farfesun kifi haka Ikram ta dingaci kamar mai kwancen yunwa amra kallonta takeyi tana bata tausayi nima tabani don jinake kamar in wulla KAUSAR lahira saboda tarin haushinsa danakeji. Tana gamawa ta mik’e da sauri sai gida inda taje ta taradda Kausar ya kulle gidan da kwado sabon bakinciki yakara ziyartar zuciyarta tuni ta zube ak’asa tana kuka mai tada hankali kowa yazo wucewa saiya tsaya yayi mata magana amma bata iya koh magana bare tabada amsa, daga idon dazatayi taga kofar gida a bude tai waigen duniya amma bataga KAUSAR ba mikewa tayi tashiga cikin gidan, tana shiga taji an gark’ame kofa garam saura kadan ikram ta kifa saboda tsabar tsoro, tace “Wa'inahu sulaimana wa'innahu bismillahi innanallahi wa'inna ilaihir rajiun Allah ka mun tsari da mugunji da mugun gani nashiga tsaka mai wuya inzan dosa ni Ikram? ”. Kutsakai tayi cikin daki taga an shirya mata abinchi mai rai da motsi Wanda iya ganin kayan kyale kyale Wannan bata taba ganiba Ikram tace “Daman ance dakwai iska masu taimako dakwai kuma azzalumai wayanda burinsu su cutar da Dan Adam amma ina shakkan cin abincin nan kar yazo wata rana suce saina basu wani Abu don in biyasu” magana taji daga k’uryan daki “Kici da zuciya daya Kituna Abunda nace baki ba kunci a rayuwa ” wani hocky voice taji jiki na rawa ta juya amma bataga kowaba, tashi tayi taji ance “koma kizauna kidaina wahalar da kanki Sannan kidaina sa damuwa cikin ranki kuma Karki sake kikai kara gidanku domin babu Wanda zai aminche da Abunda zakice saboda yardan dasukayi da mijin naki Sannan yana mutuntasu fiyeda yadda kike tunani” Zufa kawai Ikram takeyi saboda wani mugun tsoro datakeji, haka ikram taci gaba da rayuwa cikin jin dadii lokaci guda ta sauya bata zubda hawaye koh kwaya duk lokacin da KAUSAR yashigo da yan mata har sannu da zuwa take musu amma saidai wani Abu guda duk yar dayayi tarayya da ita saita mutu, Abunda yakoma tadawa KAUSAR hankali kenan yafara tunanin kodai wata cuta gareshi?. Wata ranar lahadi ta tashi da nakuda, mai tsanani Wanda bata iya tashi bare ta nemi taimakon wani , KAUSAR naciki shida budurwarsa amma koh kallo bata isheshi ba haka ta haihu cikin galabaita haka Allah yabata karfi ta yankewa Dan cibiya uwa tabiyo baya haka tasamu ta gyara jikinta, tasa ruwan zafi ta yiwa danta wanka kamar wacce tayi haihuwa biyar, acikin zani ta kudundune Dan saboda koh pant KAUSAR bai siyaba haka tayi wanka kamar bata haihu ba, waya ta dauka ta aro kudi takira gida takira Ruma har Mujeeba saida takira tasanar da ita cewa ta haihu ya mace, jin tana waya ne yasa KAUSAR saurin fita ta kofar baya tunda tabar gidan koh waige sai ma aiko wani abokinsa yayi daya radawa Dan suna saboda baimasan meta haifaba. Gida tuni yafara cika da mutane amma babu kaya ajikin jaririya zuwan abokin sane yaje yasiyo gobe suna akasamata, haka ya radawa Yarinya suna *BUSHRA* Ikram tayi farin farinciki haka yadinga bata hakuri akan halin abokin nasa koh kadan bata nuna mishi bacin ranta ba. Ni Humairah nace da wuya asamu mata irin ikram azamanin nan damuke ciki, irinsu ikram basuda yawa masu shanye bakin cikin Namiji, yan uwan KAUSAR sunzo dana Ikram sunzo Amrah ma makociyarta tazo amma babu Wanda yasan halinda take ciki illah Amrah da ruma datake Yar'uwarta sune kawai sukasan dawar garin, Ummi tuni ta aiko da kayan jariri da take siya na tari itamai yaya mata. Haka Allah ya rufawa Ikram Asiri amma dayawa mutane sun gane cewa Ikram batajin dadin gidan kausar musamman yar mahaifinshi datakeyi mata wankan jego, Anyi suna anyi shagali amma babu KAUSAR babu labarinsa Ikram harta manta da KAUSAR ragon suna ma mahaifin KAUSAR ne yakawo, haka kowa ya watse sunsamu kaya Wanda sai wanda yagani bushra tayi goshi. “Abokina wallahi narasa yadda zanyi in maido da Mujeeba kusa dani wallahi Inajin sonta acikin zuciyana sosai gashi ita batada niyyan cewa zata biyoni Mujeeba tanada qualities din da kowani Namiji zai yaba gashi babu inda tabar bisma Tabbas Allah yayi gaskiya dayace Ku rok’eni zan amsa muku da gaggawa, Abokina inata rokon Allah daya musanyamun Da wacce zata mayemun gurbi toh Allah ya amsa” “Nuru kenan Tun farko Kaine kaki jin shawara kawani ce ba yanzu zaka tareda itaba kaga yanzu saika yi hakuri kaxubawa sarautar Allah ido”. NURU ta turnuke fuska yace “mafita nake nema shiyasa nagaya maka amma kana maida hannun agogo baya ” mtwww tsaki yaja ya juya fuska. [2/26, 3:19 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 4⃣4⃣ “Abokina bakasan yadda nakejin Mujeeba acikin raina da gangan jikina ba bakasan, yadda sonta ya mamaye ilahirin ruhina ba, Abokina ina ganin mutuwar Bisma kaman komai ya kwance mun amma sai naga akasin hakan pls abokina meye mafita bansan yazanyi da Rashin Mujeeba akusa daniba ka taimakeni” Mu'ammar ya karewa NURU kallo yace “Nuru waishin meyasa ka gagara gayawa Mujeeba irin wayannan kalaman ina gani da tuni ta aminche da kudirinka nasan itama a halin yanzu kai kadai zaka iya bata agaji, Nasan cewa furucin bakinka kawai takeda buk’atan ji Wato kace kana sonta face to face kaga irin murna da farincikin dazatayi banaji kace tanada wayaba? Toh tanan ai zaka dasa mata mashin sonka text safe da rana waya akai akai hakane zai nuna mata cewa itama macece mai jida kanta”. Haka suka ajiye shawara haka yafara gwada fasaharsa, waya safe rana dare yana gida yana office baya gajiya har hajiya tafara fuskantar abunda ke wakana, don daxaran tace Mujeeba dawakike waya zatace da yayane, haka sukafara son juna kamar zasu cinye juna har takaiga Mujeeba tafara dauka zafafan hotuna tana turamai Wayar Mujeeba ce keta ruri cikin sauri ta daga “Hello dear” NURU jiyayi kaman bisma ce ta amsa amma saiya basar “Mujeeba daman inaso in sanar dake wani Abu Dana Dade ina fatan Allah yakawo mun ranar dazan iya furta miki Wannan kalman” yana xuwanan ya dakata yace zai kirata anjima yanada baki. Haka Mujeeba ta k’agu dataji abunda zai sanar da ita, Wanda tayi hasashe cewa bai wuci yace yana sonta abunda ta Dade tana jira taji daga wajenshi. Ashwa itama ta kamu dason mansir Wanda gaba daya yake bata kulawa ta musamman batada wani aiki saina shigewa daki suyita zuba love, abun mamaki da baya k'arewa Wai shima mahaifin mansir son Ashwa yakeyi saboda budurwar zuciya tun ina gani yana faruwa a TV wasan kwaikwayo gashi a zahiri yana shirin faruwa, Dukda basu taba haduwa da mahaifin mansir ba amma yana kashe mata kudi na fitar hankali, itadai fatanta da Adu'arta Allah yayi mata zabin abunda yafi Alkhairi. Datake ba Mujeeba labari bakaramin razana tayiba saboda tsabar mamaki, Tabbas idan kabi ta bado saika yi nutso cikin kwaru, “Ashwa ki lazimci adu'a tsakanin ikama da kabbaran harama bakaramin amsa Adu'ar bawa Allah keyi a Wannan yan tsakanin ba, don kina bukatan adu'a” Ashwa tanisa tace “Mujeeba wazan zaba uban kodan? Tambayan danakeyiwa kaina kenan ”. Nidai anan saidai ince Allah yaraba kwarto dashan duka. Mujeeba sunata shirin xana Waec da neko harda jamb don suna ajin karshe a makarantar secondary dake therbow school dake zaria, tafe suke sun Dawo daga school direba ya daukosu wayarta tafara ruri duban screen dinta keda wuya taga Ya nuna Nurul-Qlby murmushi tayi ta gyra xama da dauka. “Hello” Daga dayan bangaren nuru yace “Kiyi hakuri jiya inata zuccin zuccin in kira ki amma nagaji da yawa Mujeeba ina daman so nake ince miki” dukta sakan kance tana jira ya gayamata abunda yake bakinsa yakara cewa “Oh Mujeeba kiyi hakuri Dan Allah Zamu shiga meeting ne” lok’aci guda taji ranta ya baci kashe wayan tayi. “Yaya Kullun burinsa yajamun rai I wonder abunda yakeso ya gayamun” Kiran ya k'walam tayi suka gaisa da jood'a mahaifinta tace “Inna ina kewanki ina Ummi intana kusa kibata mu gaisa, ummi ce ta amshi wayan suka gaisa da Mujeeba “dafatan babu wata matsala Mujeeba? ” Mujeeba tayi dariya tace “Babu Ummi kawai son ganinku nakeyi kawai Dan Allah kiyiwa yaya magana idan yazo ya taho dani shinkafi, Ikram ta haihu banzo barkaba”. Ummi tace “karki damu naji yace kinkusa tarewa a sabon gidanki dayake ginawa Dan kinzo saikiga ya k'walam dinki ” “haba Ummi har tsawon wani lokaci nidai kawai kibari inzo” harta kai gida Suna waya har hajiya taba suka gaisa daga bisani ta kastse wayar. Gaisheda hajiya sukayi suka wuce ciki suka cire kaya NURU ne yak’ara kiranta amma saida yayi kara ya katse har sau biyu kira na uku ta dauka tace “hello how may I help you? ” “Hmm Gimbiya Mujeeba idan baki ba gari nasan kindamu kwarai donjin me zan fadi miki koh”? Ya tambaya Mujeeba tace “Kodaya ban damuba hasalima na mance” NURU yace “ok daman Inaso ince................ Kubiyoni dinjin me NURU zaice da mujeeba😜 [2/27, 7:31 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 4⃣5⃣ Tadai Mujeeba dukta k’agu dayaji abunda yaya NURU zai fadin mata amma saita lura daja mata rai dayakeyi shiyasa nima nake Jan ran mai karatu “Mujeeba daman inso in fada miki cewa I LOVE YOU” Wani dadi taji Wanda saura kiris wayar ta subuce a hannunta saboda tsabar murna kasa amsashi tayi illah Dariya datakeyi cikin ranta kamar ansata a gidan Aljanna “Kinyi shuru Mujeeba baki bani amsaba” yafadi a marairaice kamar zaiyi kuka “Yaya nuru bansan dawani irin baki zan gaya maka yadda nakesonka ba you mean alot to me in this world yaya Kaine sirrina kuma Kaine gatana mijina, fadin ina sonka bata bakine, nadade ina jiran Wannan rana nadade ina Adu'a Allah ya nunamun wannan lokaci sai gashi yazo Neman guri tayi ta zauna tacigaba dacewa yaya Tabbas so gubane kuma nasha haka so Zuma ne gashi ka lasamun, so baya dubi da kyau nasaba da chanchanta gashi yau nagani, so baisan tsufa koh yarinta ba gashi na gani, inaso ina cemaka Mujeeba Jood'a tana sonka tana kaunar ka idan babu kai nasan cewa tabbas I will be no more”wani dadi shima yaji aransa a Daren ranan in takaitama mai karatu NURU dakyar ya iya runtsawa saboda zumudi da zakwadi kai so akwai dadi aure idan babu so aciki kamar miyace kanta kafura. “Mujeeba daga yau kin tashi daga Mujeeba kin koma matata ta kaina zaki sameni miji mai kula da tarairaya zaki sameni mai biyayya ga umurninki” Dariya Mujeeba tayi tace “Nidai kayi hak’uri yanzu na dawo daga school Bari na huta nayi wanka Sannan naci abinci” toh yace da Mujeeba suk'ayi sallama. *GUSAU* Ikram ce zaune akan kujera Kausar yashigo yana dariya Wanda ta manta randa taga irinta, dayake ta kare wankan jego har yar mahaifinshi ta koma gida sallama yayi Wanda mamaki yacika Ikram a cikin zuciyanta tace “Lallai ne kausar kace wani Abu Wato ka lallabo ka cuceni koh toh baka isaba kayi Dan Allah dubasshi yana tafe da doro kaman shugaban Zabbi”mtwww tsaki tayi harsaida ta fito fili. Zama yayi yana fuskantar Ikram yana lallabata cikin sigar dabara koh ince yaudara, “Uwar gida sarautar mata yau nazo miki da abun dadi Wanda baa ba yaro mai kiwya” wata ledace mak'are da kayan k'walam da mak'ulashe koh kallon Arziki Ikram batayi mishi ba dagashi har ledar, juyawa tayi tana yiwa bushra wak'a, _*wanene bayaso yaji kukanki ummanki ce bataso taji kukanki sannu yar gata yar iyaye yar dangi, Idan naji kukanki zuciyana na tashi kamar zan yi hararwa*_ Shidai kausar yasan Ikram dashi takeyi hannu yasa zai amshi bushra Ikram ta hanka d'ashi gefe tace “Duk ranar dagayi gigin tabamin ya sainaga karyar rawan gindi, sainaga Wanda yabaka odar tabamin ya, kana tunanin wannan yarinyar zata kiraka uba mahaifi har abada” daki ta shiga ta daukomai kalandan suna tace “Duba ka gani Bushra Nuhu sunanta sunan kanin ubanta daya damu da zuwanta duniya kuma banga Wanda ya isa ya sau yawa yata sunaba”. Kallonta kausar yakeyi yace “wallahi baki isaba” ikram tace “ni kuma baxan daukaba” “Me kike takama dashine wai Ikram dahar zakidinga daka mun tsawa kaman kin haifeni Sannan har kin isa kisawa yata ta cikina sunan kanina wallahi baki isaba kuma yata saina dauka kici kicin amshe Bushra yakeyi mai makwan yaga bushra sai yaga macijiya tafasa kai ai tuni ya fadi k'asa warwas don koh motsi bayayi dariya Ikram tayi tace “Hmmm kadan ka gani indai nice kuma inanan dakai hakkinmu daka danne danida yata wallahi sai Allah yamana sakayya tun a duniya” tsalakeshi tayi tashiga daki tayi kwanciyanta cikin dare haka Ikram tadinga jin ihunsa alaman yanajin jiki ita kadai tasan abunda yake faruwa. “Misalin shida na safe tafito tace “Inason zuwa shinkafi yawon arba'in kozaka kaimu ne?” da gangan Ikram tayi mishi wannan tambayan yadda taga yajigatu kwarai “baxan iya zuwaba amma idan zaki iya tuka mota ga mukullin nan kidauka” dariya Ikram tayi cikin zuciyarta tace kadan kafara gani wulakanta mace indai abunyine maza kubada himma”. K'wance tabarshi suka shirya ta dauki bushra tasata a mota da akwatin kayansu sai gida dayake ta k'ware a tuki bataji komaiba haka ta kwarari hanya batareda tunsnin halinda kausar yake cikiba. *ZARIA* “Hajiya inaso inyi miki albishir yau yaya ya furta cewa yana sona ” tafadi tarefa rufe fuska hajiya tayi dariya “Yace meye na rufe fuska aimu abunda muka Dade muna jira kenan tabbas watan tarewanki gidan NURU ya tsaya Komawa garin Gusau ya kamaki, koda yake wancan sasan har yau bamusan matsayin sa ba nakine koh Na meye Allah kadai yasani” haka hajiya takira yan'uwa tana sanar dasu cewa ankusa tarewa kowa yayi murna tareda godewa Allah haka Ummi tafara shirin gyra Mujeeba don yau Mujeeba suka shirya itada Ashwa zuwa shinkafi mansir ne zai kaisu saboda daga chan zasuje gaisuwan dangi, haka Hajiya da Alhaji suka hada musu tsaraba suka kama hanya sai Gusau, tunda suka fara tafiya Mujeeba ke waya da NURU cikin iya soyayya da Ta koya cikin littafan Hausa, harma dana online haka suka isa. *GUSAU* shinkafi suka isa Anata maraba dasu wani sanyi Mujeeba taji ganin iyayenta da gudu tafada jikin Ummi tana jin sanyi haka ta rungume ya k'walam tana dariya shiko jood'a kunya ce dukta isheshi yadda yaga baitu takeyi tawaye tazama yar burni Haka su ashwa suka gaisa harda mansir Ummi tayi murna, nan sukabar Mujeeba suka wuce cikin garin Gusau akan hanyarsu ta komawa Mansir yace “My tunda dare yayi mazai hana mushiga Aljazeera hotel mukwana inyaso gobe saimu shiga gidan Aunty mommy da Aunty Niima koh?”Ashwa ta zare ido .......... [2/27, 2:39 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 4⃣6⃣ Tace “Haba mansir gabaki ga hanci amma kawanice sai munje hotel mun kwana, muje gidan Aunty mommy harda Dakin bak'i garesu Saima kudinka su huta koh ba haka ba” ran mansir yayi masifan baci harta kaiga ya tsayar da motar yana k'arewa Ashwa kallo “What are you thinking Ashwa? Kinsan cewa ina sonki kuma ba abunda zai hanani aurenki, kiyarda dani I will not do anything stupid pls” wani irin kallo yakewa Ashwa Wanda takasa yimasa musu saboda tsabar kwarjinin dayayi mata. “Ok mansir inhar hakan zai faranta maka rai shikenan amma da sharadi saidai ka kama dakuna guda biyu naka daya nawa daya” “Asaran kudi kenan Ashwa daki biyu fah nooo noo ashwa daki daya zamu kama kinsan bafa kwana daya zamuyi ba kashe kudin will be over ai koya kikace? Ashwa dai gaba daya ta tsinke da lamarin mansir amma saboda yardar datayi dashi koh hannunta bai taba rikewa ba bare yayi tunanin yimata illah. _*Ni Humairah Bashir nace hmmm ba'a ba namiji yadda saboda namiji kunama ne mai d'anin bazata, kayarda dashi Dari bisa Dari ya watsar dakai batareda ya waiwayeka ba, burin wasu mazan da mace a waje su lalata mata rayuwa kuma ya tozartata, yayi mata wulak'anci dacin mutumci har idan wani zai aureki shine gaba gaban cewa wannan zaka aura tab zaka kwashi ragowan maza ai taxi ce no carriage mata mazaisa bazamu nisanta kanmu da namiji ba matuk'ar ba aure akayi muku ba? Allah yasa mudace.*_ Haka suka kutsa cikin farfajiyan hotel din, abunda magani saida yayi mutukar tadamun da hankali yan'matane suke bushaharsu da samari kaico duniya Ashwa jitayi jiri yana Neman dibanta kafarta takasa daukan jikinta wani kara ta saki Wanda saida kowa ya waigo Mansir kuwa tuni yashiga rudanin abunda ke damun Ashwa kodai zazzabi ne? Haka Yakama daki naira dubu hamsin kwana daya. Ciki suka shiga kan gado ya ajiyeta yana kallonta lokaci guda yana lashe baki wanka yashiga, lokacin Ashwa ta mik'e tana kiran mansir fitowa yayi daga toilet dagashi sai Dan kanfai. “Darling lafya kika fadi kodai yunwa kikeji ga abinci nan nayi Mana oda” wani hararsa takeyi “Amma yau ka nunamun cewa bakada kunya yau shine rana na farko da naci karo da ashararanci irin wannan haba yanzu dayawansu dauka zasuyi nima irinsu ce Dan Allah bakaga yadda suke kallona ba lallai *Ummu sabreena tayi gaskiya datace MACE KADARACE MAI TSADA* Amma just look abunda wasu matan sukeyi dole a aunashi a *MIZANIN TUNANI littafina mai fitowa nan gaba, Nasan da yawansu iyayensu basusan ina suka dosaba wasu karya sukayi zasu wani guri sukazo nan Allah ka karemu da karewarka”. Kallonta mansir yagama yi acikin zuciyanshi yace “Hmmm Ashwa kenan yau zan rusa duk wata tarbiya da iyayenki suka dade suna baki kuma daga yau zan jiyar dake dadin namiji, hmm Karki damu Ashwa kici abinci ki kwanta kiyi bacci kinji zandan fita indawo” toh Ashwa tace tafara jin fried rice da naman kaxa da drink din hollandia saida taci tayi tatil amma har yanzu zuciyanta bai kwanta ba, waya ta dauka takira aminiyarta kuma matar yayanta Wato Mujeeba budu daya tasamu “Hello mujee hmmm ina cikin wani hali Mansir ya kawoni hotel wai anan zamu kwana kuma daki daya Dan Allah Karki gayawa kowa kitayani da adu'a pls” dagajin yadda Ashwa ke magana mujeeba tasan cewa bada son ranta mansir yakaita hotel ba “Ashwa zan tayaki da Adu'a insha Allah kema kiyi tayi don kubuta daga sharrin namiji don zuciyana bata yarda da mansir ba tunda kika sanar dani wannan maganan”. Haka sukayi sallama Ashwa ta nemi guri ta kwanta tayi lankwas kaman tana bacci, *Allahumma ajirni fi musibati wa Akhlifli khairan minha* kawai take maimaitawa acikin zuciyanta tana *Innanallahi wa'inna ilaihir rajiun* Allah gani gareka ya Allah, abunda taketa fade kenan cikin zuciyanta, k'aran muk'ulli taji ta kara likimo yana shigowa yasaki wani dariyar mugun ta hahahaha “Ashwa kenan har kin kwanta, Kusa da ita ya matsa yana shafata you are looking beautiful baby amma daga yau kyawunki yak'are duk wata daraja kima saidai kigani a wajen wasu amma badai a wajenki ba” Cire kayansa yafarayi yashiga toilet donyin fitsari wata kwalban fitila ta saita, yana zuwa yafada mata sai romancing dinta yakeyi ta koh ina yana lasar bakinta sai wani nishi yakeyi kamar numfashinsa zai fita, sai surutai yakeyi saida Ashwa Tabari jinkinsa ya mace daman bai cire mata kayan jinkinba wannan abun ta wawuro ta kwadamai tuni ya gigice ta dauki akwatinta da wayarta harda gyale ta fita a guje tana isa wajen mutane saita sassauta gudunta tana zuwa gate aka bude mata tafita Dan adaidaita tasamu ya ajiye wasu bata zarce koh inaba sai layin kotu dake Hanyan kauran na moda kofar gidan mommy yayarta ta tsaya ta sallami mai keke, gari yayi tsit koh mota baka gani, haka mijin mommy yafito yana waye? “Nice Ashwa brother ka bude” jin muryan ashwa ne ya bude tashiga ciki ya taho mata da kayanta kan jikin mommy ta fad'a tana kuka tace [2/28, 7:55 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 4⃣7⃣ _*This humble page goes to All online Hausa writers da wayanda nasani da wayanda zan sani nan gaba Allah yakara daukaka, baseerah da hazak'a Hakuri da juriya LYSMπŸ˜˜πŸ˜πŸ‘πŸ»*_ “Aunty yau nashiga wani hali Wanda bana fata wata ya mace ta shiga Aunty Ashe mansir mayaudari ne tabbas yau Da burinsa yacika akaina Dana kashe kaina nabari duniya saboda baxan iya cigaba da rayuwa ba don nasan babu wani Namiji daxai zo gurina da sunan zai aureni saboda narigada na zubda mutunci na da kimana harma da darajata” Itadai Mommy kallon kanwar tata takeyi tace “Wai meya faru Ashwa gayamun bansan inda maganarki ta dosa ta kalli mijin tace koh ka fahimta?” Yace “Ah Ah gaskiya kibita a sannu zaki gane abunda take nufi don nasan yanzu a rude take” “Aunty fyade mansir yaso yimun shine Allah ya kubutar dani don banace dabarata ba sannan da karfin Adu'a ” zare ido sukayi “lallai yace wani abu tabbas daya cimiki mutunci wallahi dasai nayi karansa koh Dan gidan uban waye” cewar mijin yarta haka akasa mata ruwa tayi wanka taci abinci ta kwanta zuciyarta cike fal da tunani tace “Tabbas da naga takaina ni Ashwa _*ni humairah nace Amma haka Wasu har suke iya zubda mutuncinsu a waje toh Wallahi duk macen data rasa BUDURCINTA bazata taba kima da daraja a idon mijinta ba inhar yasani toh koh Gindin gwal gareki wata rana saiya miki gori koh ba jima koba dade”*_ _*An aureki an sameki virgin yakika k'are da wulakancin namiji bare kuma kinyi bariki? Ai sai cin mutunci dacin kashi”*_ Allah ya karemu damu Da yayanmu. Wayarta ce kirar iPhone 7 take ruri number mujeeba tagani tayi saurin dauka haka ta labarta mata komai budan bakin mujeeba tace “Tab amma mansir yayi kuskure dole ki auri aubansa kodan ki juyashi yadda kikeso dole kiyi kishi da uwarsa Dan ubansa, dole yaje miki aiki koh dolensa yakiraki da matar babanshi me kikeci na baka na zuba kyaleshi ai bariki bata kareba sa saura” Ashwa tayi dariya tace “Matsala na daya yamun tsufa ne mujeeba kuma kingafa nice ta uku yazanyi? ” mujeeba tace “Aikin banza ai Wallahi koh a k'wark'warane bare ta uku Wallahi saina aureshi don wulakanta mansir kedai Allah ya tsareki dakin bani wallahi mijinka na sunnah bai ji dadinka ba wani tinkis yaji Allah yadada karewa yazama ishara ma yan baya” . Mujeeba kam gyara takesha na ban mamaki, ranan da NURU zai fantama inajin yini zaiyi yana k'walk'wala, don saboda gyara kamar atabata jini ya fito haka Ikram take gurje mata jiki da turaruka Wanda saitayi wata shida kamshin bai fitaba, ga tsumi hadin gida ga kaza yan shila nidai gefe na koma nace gwarama kenan yarinya sai kinji kamar bindinki zai fita. NURU ne tafe shida abokinsa sun dauki hanya zuwa shinkafi don sanar dasu cewa Zaria zaa kai kayan mujeeba cikin gidansu. Da isarsu don tsabar murna mujeeba ta k'osa a gama koga mata turare a falo suka zauna inda aka tarbesu cikin girma Nabil kuwa sai dariya yake basu saboda akwai shi da barkwanci, Abdul yace “Ah gaskiya abokina idan kayi dace da manyan mutane Wallahi ba iyayenba hatta yaransu bazaka taba samun problem dasuba amma idan akacema, kananan mutane kasamu marasa mutunci har zuri'arsu haka suke kuma yawanci a tsiya suke karewa mutumina da'ace da sauran yanmata a gidannan yasin saina auri daya, saboda kwata kwata abokina bana jin dadin zama Da muneeba Kullun iyayenta cikin kirana suke cin mutuncin yau daban na gobe daban”. NURU yayi dariya zaiyi magana kenan yayi ido biyu da MUJEEBA ai tuni ya shagala, shidai Abdul shuru ne yayi yawa ya waigo yaga wata tsaleliyar yarinya danya jagal, taba NURU yayi yace “Mutumina irin wannan kallo ai saita tsufa kafin ranan kai abokina kana wuta ina binka fetur”dariya sukayi guri tanema ta zauna ta gaidasu daga bisani ta tashi zata fita NURU koh kunya ya janyo mujeeba ba shiri Abdul yafita yadan basu waje, “Mujeeba kinga wani irin sheki dakikeyi Wallahi saikisa in gudu da ace bansan ke matata bace I love you baby kissing dinta yakeyi itako saida tabari ya nutse kannan ta zame tana dariya tace “Kamanta cewa gidan surukai kake, wai yaushene tarewan Ummi tayi magana wai in tambayeka anan ne koh a Zaria? ” “Mujeeba naso ace anan ne amma idan nayi haka nasan zanbar Hajiya da kewa idan akace Ashwa tayi aure ba zasuji dadi ba kuma ganina zaiyi musu wuya, Amma indake acan nasan time to time zan dinga dawowa” magana yake cikeda lalaci saboda jikinsa ya mutu “Hakane kuma toh zan sanar dasu amma ai bakasa ranaba?”nuru yace “nanda ranan juma'a kinga zamu tafi amma gobe zamu dawo dakwai surprise din da zanyi miki” tashi yayi yayi hugging dinta yaji wani irin kamshi ai lokaci guda sha'awarsa ta motsa tuni yace “kiyi musu sannu ga wannan kibasu” MUJEEBA ta bishi da kallo tace hmmm salo yanzu kafara gani don nida kishiya nesa nesa. [2/28, 9:37 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 4⃣8⃣ Ni humairah nace badaganan takeba. Ruma ce zaune duk tsawon lokacin da aka diba tun zubewan cikinta bata kara koda bariba bare batan wata ba, illah yawon kasashe dasukayita yi har Allah yasa aka dace ruma hamshakiya ce maiji da kanta don mai aiki gareta wacce take mata duk Wata hidima, amma kuma wani hanzari ba gudu ba ta mance Wanda ta aura Wato Hamdan ido a mata, budurwace dankwaleliya kirjinta tumbul da nonuwa, maxaunai kuwa ai tace ruma batayi komai ba, Ruma tazama masifaffiyan karfi dayaji saboda dangin Hamdan sun sata gaba, yanzu kuwa duk shegiyar data daga bata yatsa ita walki take daga mata, mai aikince tashigo aguje kamar an sako awaki ba sallama ba komai, Ruma tace “Wat!!!! Meye haka kinwani shigomun daki a guje? Sannu isassa mai walkin SA sau nawa zance miki kidaina shigomun daki haka kamar wata tinkis, sau nawa zan gayamiki cewa tsakanin mace da namiji tafiya, babu wata natsuwa bare kamun kai ina gargadinki Karki sake shigomun haraban falo bale ki wuce daki Wannan ai raini ne mtwww” Hindatu tayi kwalkwal da ido aranta tace “Inda kinsan abunda nake gudu dabaki fadi haka ba wannan mijin naki dayakejin kansa kaman bunsuru hmmmm kiyi hakuri Hajiya bazan sakeba” “Dafatan kin kammala aikin Dana saki koh kina tsalle tsalle kamar tinkiya na dara?” tace “Nagama duka gida nakeso in tafi” Ruma tace toh “Sai anjima kigaida gida”. Tana fita dayake gidan katone Hamdan yana labe ya rarumo Hindatu yace idan kikayi ihu kema kinsan sauran hajiya saita kusa yankaki, haka tayi shuru jikinta sai rawa yakeyi shiko Hamdan shafata kawai yakeyi ta koh ina itama dayake yarinyar yar tasha ce daman nema takeyi sai tayi lankwas, tuni ya tube mata Riga yafara shan breast dinta yana lagudasu itakoh sai wani narkewa takeyi saida yagama lallatsata kannan yabata Dari biyar yace ta tafi gida. Ciki yakoma yasamu Ruma a zaune kusa dashi ta matsa tace “nifa gaskiya haihuwa nakeso inyi inason yara sosai Wallahi” “kiyi hakuri Ruma Allah zai azurtamu da yaya masu jin kanmu Allah shiyasa San tanadin dayake mana a gaba ” “Nifa bawani hakuri duk yadda zakayi nidai kayi don baxan yarda ba kanninka su sukayi sanadiyyan kashemun da ysnzu ka bani hakuri, toh Wallahi hakuri yayi kankanta yabani hakuri idan ma dakwai wani problem ne is better muje asibiti don inhar nikeda problem toh baka ba kara aure saboda kanninka ne sanadi” Hamdan yashiga rudani saboda rigimar Ruma yawa gareta idan bai bata hakuri ba tuni zata je gidansu tayi musu tijara mai isarta idan ma bai kaiga an zubda jini ba Alhamdulillah. “kiyi hakuri kinji ruma zanyi komai ganin kin samu baby yi dariya ingani” haka tayi murmushi ta kwanta jikinsa. Washe gari tun safe ta fita aiki, dayake tana aiki a magistrate court na zamfara state. Tun kafin Hamdan ya tashi ta fita, itako Hindatu harta iso gidan, saboda tsabar yardan da Ruma tayi da hamdan shiyasa take tafiya tabarshi da mai aiki ita zatayi mishi komai hatta ruwan wanka, aiko dole bad'ala ya wanzu, kuma dayawan mu mata haka mukeyi tun baran ma idan mace tana aiki toh muje zuwa wai hakaukaci ya hau kura, Hindatu ce cikin kitchen tana hada breakfast gashi bawani tsafta gareta ba kayan jikinta ma kamar ba nataba duk sun matseta shape dinta komai ana gani, kunsan dai daga namiji har mace ba katako dole sai an samu sha'awa aciki, Hamdan ne yatashi dayake ya saba da fitan da Ruma takeyi kitchen ya nufa batareda Hindatu ta sani ba ya taba mata duwawu tayi zullo tuni dukiyar fulaninta suka fito yaji wani Abu ya so keshi kusa da ita yake matsawa haka itama take matsawa har saida takai bango ya matseta “Hindatu ki saki jikinki Dan Allah Wallahi ina masifar sonki ki kwantar da hankalinki babu abunda zai faru kibani hadin kai Wallahi bake ba talauci gidankuma rusashi zanyi agina muku na bulo kinji”. Yana magana yana huci daukanta yayi cik sai daki fita yayi ya kulle koh ina har gate, ni humairah nace banda talauci mezaisa kidau yarki zuwa gidan aiki Allah yayi mana tsari da talauci don talauci musiba ne, haka ya koma ciki tuni ya rudi Hindatu saboda batada wani buri illah iyayenta su fita daga k'angin talauci, gashi tanason aure amma babu Wanda yake kulata saboda kazanta, shiko hamdan bai damuba Da isarsa yadinga shafata takoh ina sumbatu kawai yakeyi “Hindatu Dan Allah kibari in shiga saida yayi mata tsirara haihuwar uwarta sannan yadinga kokarin shiga abun bakin cikin Hindatu virgin ce haka yayita kokarin shiga har yayi nasara, abun gwanin ban tak'aici Tun Hindatu da ihu yana toshe mata baki har ta daina Saima gurnani datakeyi, shiko dadin duniya kamarya kasheshi, ihu kawai yakeyi yanayi kaman zai suma abun haushi abun kazanta. Yana gamawa mai makwan ya hakura ah ah Hamdan yaci gaba da matsa dukiyar fulaninta kamar zai fara tana sha itako Hindatu koh motsawa takasa yi, haka ta dauketa cik sai toilet ya hada ruwan zafi ya gasa mata jiki sosai shima yayi wanka yashirya tafiya aiki kudi yabata dubu goma yace kuma karta fadawa kowa, inta kaitama mai karatu haka Hamdan ya maida Hindatu kamar matarsa ta sunnah hidima kuwa tanasha, harta kaiga idan Ruma tayiwa Hindatu tsawa koh zagi kawai Hindatu saita rama, haka Hindatu take shiga Dakin Hamdan ta gyra koda yana cikin Ruma tashiga rudani, Rumace zaune tace “Hindatu tashi ki daura mana abinci”budar bakin hamdan yace “Ruma yarinyarnan tana aiki Dan Allah kidinga saurara mata” baki bude ruma tace “Da sake anjefi biri da rani baa gidana ba nikam dole Hindatu kibar gidannan don naga dakwai zare cikin nad'i”, zuciya take magana. [2/28, 10:39 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 4⃣9⃣ Da safiyar lahadi Ruma takira Ummi tasanar da ita halin da take ciki, gameda Hamdan damai aikinta Ummi tace “Allah shi kara Wato ke ga mai walkin sa koh? Toh kisani mijinki yaka mu da soyayyar Hindatu ne tunda kikaga haka, saunawa ina gargadinki akan mai aiki keba daba keba tsohuwa ba mexai kaiki dauko kiyashi dazai dinga bi miki jiki koda nake da kuruciya banida yar aiki bare tsufana kinga sharrin ta ai sai kisan yadda zakiyi da ita tun wuri inba haka ba sanadiyyanta yan yan takalmanki sa katse a hanya” Ruma shuru tayi tana nazari Ummi koh don haushi katse wayar tayi don bazata iya bariki ba, Haka ruma ta shirya dayake ranan asabar ne gidan Hajiya rukayya taje wata kawarta ce dukda ta girme mata nanta labarta mata abunda ke faruwa Tas hajiya Rukayya tace “Ruma kenan kinga dalilin dayasa ban yarda da yar aikiba saboda bansha da dadi ba don Har aurota akayi aka kawota cikin gidannan ba tsoron Allah ba tsoron sarkin gari, daga karshe tuni kasuwa ta watse dayake abun munfunci ne nan suka fita suna yiwa junansu tijara, harda danta tabarmin, kije kidage da Adu'a Sannsn kiyi gaggawan sallaman shegiya tun kafin ta aure miki miji, ai idan kikaji mai aiki tana daka miki tsawa toh abunda kike gwali dashi na miji itama yana soka mata kingani ai dole ta nuna miki ta isa”Ruma huci kawai takeyi kamar wata zakanya. “Ina baki shawara Karki sake wannan yafaru don idan tafiki iyawa zata fiki kwashewa, ai ni koh tsohuwa ban yarda da itaba don idan batada ya zata bashi jika” Ruma tace “Kwarai kam Hajiya nima saboda Dan aikin nan ne yasa na daukota, don a gidanmu Wallahi bamuda yan aiki har yau kuma har gobe ” . Haka suka gama hiransu ta wuce gida abun Al'ajabi tun kafinta isa gida gabanta ke fadi Hamdan kuwa ya sakankance Ruma sai dare zata Dawo Dan haka yadinga lagudan Hindatu dayake ta saba har cewa takeyi bataso ya daina shiko gani yake babu mai rabashi da Hindatu saboda tana sarrafa shi yadda takeso don harijace ko goma ne zata dauka, bude idonsu Ruma suka gani tsaye tarasa abunda ma zatayi sai hawaye dake zuba a kwarmin idanunta, Tsirara tasamesu babu koh sutura Hindatu kuwa tashiga rudani don tasan ajalinta tazo. “Hamdan Nagode Kwarai wannan shine sakayyan dazakamun koh Allah yasani ban Gaza a kowani fanni ba da wannan shirmen Wallahi da auro Hindatu kayi insan cewa aurenta kayi amma meye ribar Zina banda bala'i da masifa sannan baxai tseratar dakai daga shiga wutaba ke kuma tsohuwar muna fuka yau sanayi ajalinki yar iska kawai Mara mutunci, shake Hindatu tayi tadinga dukanta saida taga bata motsi sannan tabarta takoma kan Hamdan tace zamana dakai yakare saidai ka auri yar aiki kuxauna tare amma Kasani Rashin haihuwana saina shigar da kara kotu don abimun hakkina, idan kaki sakina anan Kasani nice kotu zaka bani a bainar duniya inda zakaji kunya Alhamdulillah bani da yaya a tsakanin mu damunsha kunya amma dayake kai dayane sai kasha kunyarka. “Ruma Wallahi bazan taba rabuwa dake ba zama daram kidauka kaddara ne Ruma sharrin shaidanne, kuma kisani kinada laifi kin fifita aikinki akan sauke hakkina daya rataya akanki, bakida lokacin dafamun abinci da kanki sannan, awajen auratayya kinada rauni ki gafar ceni Ruma”. “Dakata shine ka zab'i ka cimun mutunci saboda wayannan abubuwan karasa wacce zaka nema sai yar aikina? Hamdan kayi kuskure kuma aure dani dakai babu saida wata Ruman amma baniba” fuuuuuu ta fice daki tashiga tana kuka tace nashiga uku Hamdan meyasa kaci amanata? Meyasa ni humairah nace ihu kikeyi Bayan hari keda kanki kika debo kaimami kuma yazo yaji miki rauni, _*Da yawa mata suke jefa maxajensu ga halaka, suke kashe aurensu da Kansu nasan cewa zamani yanzu ya canza mata suna fita neman halaliya suna karatu amma Meyasa bazaki sauke hakkin daya rataya akanki ba kina ganin Allah baxai tambayeki ba? Hmm mata iyayen shagali sai Abu yafaru ace haka Allah yaso bacin ke kika sowa kanki*_ Haka hamdan yayita kokarin shawo kan Ruma harta sakko ta hakura amma fa da sharadi saiya auro Hindatu yakawota cikin gidan don shine kawai kwanciyan hankali, haka Rayuwa taci gaba da tafiya a gidan Hamdan harya auro Hindatu Bayan tayi *ISTIBRA'I* wata uku wato jini uku, inda Ruma take gasa mata gyada a hannu lokaci daya suka dauki ciki murna wajen Hamdan baa magana saidai mujira haihuwa. [2/28, 12:03 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 5⃣0⃣ Anata shirin tarewa MUJEEBA tana ta kaiwa da komowa haka yan'uwa suka baxama zuwa Zaria achan akayi Jere aka shirya komai Hajiya tayi musu tarba na mutunci ranan Alhamis aka shirya liyafar ban girma a garin Gusau, Duk Wanda yaga MUJEEBA saiya tofa kowa ya halarta bikin harda Ruma dake laulayin ciki harda Hindatu abun tausayi batako iya shiga mutane saboda kyrar da Ruma take mata, har saida Ummi tayi mata magana tace “Amma Ruma kina ganin Allah baxai sakawa yarinyarnan ba jitafa yadda ta rakube toh wallahi ki daina wannan zalunci ne kiriketa Wallahi wata rana zakiyi alfahari da ita, kisani Ruma zakaran da Allah yanufa da chara koh ana muzuru ana shawo sai yayi ki rike girman ki kishinki azamanin nan aljihunki maza ki kirata ta zauna kusa dake an riga an daina irin wannan kishin” haka Ruma takira Hindatu suka zauna tare har hira sukeyi dayake katon gidane shiyasa aka kira masu decoration suka k'awata wajen. Kayanda MUJEEBA tasa abun azo a ganine Ashwa kuwa tamance da wani mansir tacigaba da harko kinta, itama tadau kyau Kwarai saboda tsabar fari Wasu cewa sukeyi MUJEEBA tanada jibi sa yan India shiko NURU banda huta dayadan ratsashi bakine Kwarai, sai idanu ka tsawo abun sai Wanda yagani, baba lanti kuwa gaba daya hashin NURU takeji saboda taso ace yarta Labiba ya aura amma iyayensa suka zabamai MUJEEBA amma fah taci alwashin sai yarta tashiga gidan koda boka koda Malam, Baba lanti yar Alhaji Usman ce itake binsa haka hajiya taci bak'ar a zabanta don har saki Alhajin yataba yiwa Hajiya saboda ita. Haka akayita shagali saboda tsabar haushi labiba tashi tayi tafice sai gida saboda arayuwanta tana masifar son NURU shiko koh gidansu baya zuwa, bare ya kare mata kallo. Haka aka watse abokan NURU sunata yaba kyawun mujeeba yace “Ku dakata matata ce meyasa kuke irin haka ba kusan cewa haramun bane yaba matar daba takaba?”. Dariya sukayi washe gari aka kawo motoci kusan goma haka akayi sakko sai Zaria, inda akakai mujeeba dakinta, gida ya tsaru iya tsaruwa haka suka Kwana aka watse, Kanwar Ummi ce takira Mujee tace “Wannan ya k'walam tace in baki kidinga sha saboda akwai yan bakin ciki tsarine sosai kuma tace zakuyi waya” Karba tayi ta boye haka washe gari akayi mata fada aka watse shiko ango NURU yana garin Zaria don an bashi hutun wata guda, kunga amarci sai anci anji ba dadi, “Misalin shida na yamma NURU tashigo Ashwa ya tarar suna hira tana ganin yashigo tace “Allah ya bamu Alkhairi”Nuru yace “Amshi ki kaiwa hajiya” haka tafita tabar Mujeeba a zaune ta kudundune fuska, tana wani irin shu'umin dariya tuni NURU ya matsa kusada ita yace yau dai gaki ga yaya Nuru, lokaci guda yafara tuno wani Abu tuni yaji hankalinsa ya tashi ji yayi bazai iya kwanciyan aure da Mujeeba ba don gani yake Tabbas yaci amanan BISMA, ganin Nuru ya sauya ne yasa Mujeeba zare ido tace “My soul and heart lafya naga dukka canza koh nabata maka Raine? Girgiza kai kawai yakeyi saboda wannan tsakaninsa da zuciyansa ne. Haka ya daidaita kanshi ya rungume Mujeeba yace “hmmm kiyi hakuri Mujeeba wata sa'in nakan rasa tunanina ta kowani fanni sai inji duniya inama banzo ba, narasa meyasa Wasu abubuwa suka kasa bacewa daga kwakwalwa na,” Dayake Mujeeba yarinyace mai fasaha tuni tagane abunda yake nufi itama saita nuna bakomai “Damuwa dolene musamman idan karasa muhimman abubuwa, a duniya nima idan na tuna yan'uwana dangina da dukiyar mu Wato shanu hankalina yana tashi” lokaci daya tafara kuka lallai damuwar mujeeba tafi nashi tunda shi Alhamdulillah yanada dangi harma da dukiya. Lallashinta yakeyi har suka fara dariya har bacci ya dauke Mujeeba a kan kafarsa nidai nace waiyo Mujeeba kinsamu soyayya wajen NURU amma har yanzu da sauran Rina a kaba, dakyar nuru sai iya saduwar aure da ita, gashi Mujeeba ta jik'u iya jukuwa Tabbas dakwai matsala Ku biyo ni yar MUTAN ZAZZAU kuji yadda zata kaya don nasan dole asamu mafita. *kuyi mun afuwa banso littafinnsn yayi tsawo ba amma babu yadda na iya saboda labarin bai karaba*πŸ€₯πŸ˜ŠπŸ˜„❤ [3/1, 3:33 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 5⃣1⃣ _*Washe gari tun da sanyin safe Mujeeba ta tashi Bayan baccin Bayan Asuba data koma, kitchen tashiga yaba kallon tsaruwan kitchen din babu wani colour rayot komai kala daya sai abunda baa rasa ba, dube dube takeyi har idanunta suka hango wani lungu ba tantama store ne wajen ajiye kayan abinci, gurin ta nufa tafara kici kicin daura abinci tuni tayi Abu Mara nauyi ta jera akan dinning table daki ta koma ta fetsa wanka tasa atampha super Exclusive tayi dauri mai Wanda ake kira da network sannan ta fesa turare kusan kala biyar, takalmi ta dauka plat Tafara tafiya cikin natsuwa cikin dakinsa ta kutsa ta zauna kusa dashi Tana hura mishi fuska yana bude idonsa yayi tozali da Mujeeba, tace “Good morning my prince ka tashi lafya? Yakamata ka tashi kayi brush muyi breakfast ”*_ _*Murmushi nuru yayi yanajin tsananin son mujeeba acikin ransa yace“Hmmm Mujeeba kenan har kin tashi lallai bakison ki kwanta ki huta koh” cikin shagwaba tace*_ “My nidai ka mik'e Muje inyima brush pls wani fari tayimai Wanda yaji jikinsa ya mutu, Tashi yayi suka shiga toilet din ta taimakamai sannan sukaci abinci, Rayuwa suke kaman ba ma'aurata ba kamar wa da kanwa abunda yake munana zuciyan Mujeeba kenan. Tashi tayi zatayi Alwala Ta rik'e maranta wani kara ta saki Wanda yajawo hankalin NURU, tuni ya ajiye jaridar hannunsa Da gudu yashiga toilet yaganta kwance sai juyi takeyi, baiyi wata wata ba yafara salati daukanta yayi cik, yana zuwa falo yadauki mukulli yana fitowa yadinga kwad'awa Ashwa kira Hajiya ce tafito a gigice hankalinta yayi kololuwan tashi hijabi ta dauko sai *SALAMA MATERNITY HOSPITAL LTD* dake cikin unguwan kwangila, dake Zaria daura da flyover cikin gaggawa aka karbeta batareda bata lokaci ba, likitoci ne suke dubata tuni akayi gwaje gwaje aka gane cewa maniyyinta ne ya taru a mararta shiyasa ta matsanancin ciwon Mara. Cikin tashin hankali Hajiya ta juya ta kalli NURU tace “kaji abunda Likita yace koh bakaji ba Wato yarinyarnan haka kake azabtar da ita toh Wallahi Kasani Allah baxai barka ba matsawar kace abunda zakayi kenan”Likita yace “Inason magana dakai”nuru ya sadda kai yabi bayan likita, suna shiga Likita yafara wayar mishi dakai sannan ya sanar dashi illolin dake tattare da barin mace da sha'awa nanya bashi shawarwari ingantattu Wanda NURU yayi alkawarin gujewa afkuwan hakan. Fita yayi duk yaji kunyan Hajiya takama shi haka Mujeeba ta farfado suka wuce gida, haka NURU yake tarairayanta kamar kwai, yana lallabata hajiya ta leko tace “nuru Inaso kasan wani Abu hannu mai miya shi akebi da lasa ” tana gama magana ta wuce adaren ranan Mujeeba tasan inda yake mata ciwo duk wani rawan kai taji babu shi taji maza, NURU yayi ihun dadi yayi godiya ga Allah sannan yayiwa Mujeeba godiya ji yake duniya ina Zaisa kanshi idan yarasa Mujeeba?. Haka ya taimaka mata ta gyra jikinta sukayi sallah suka koma bacci abun mamaki nuru ya biyayi Mujeeba saboda jinta yakeyi on top the town. Ashwa kuwa love akeyi sosai da mahaifin mansir inta kaita ma mai karatu har ansa rana, kishi da uwar mansir dole Ashwa tace “waiyo Allah sarki inji barawon takanda duniya sabuwa ango da daurin zani,” mansir duk yabi ya damu yana Neman yarinyar da ubansa zai auro kwatsam yaji ai Ashwa ce kofar gidansu yaje ya aika a kira mishi Ashwa tace aje ace waya mansir ya takarkare yakira sunan ubansa, cikin takama tafito lokaci guda gabanta ya yanke ya fadi ras, amma saita dake ta karasa tace “Barka da zuwa Dana dafatan kaxo lafya kodai ya aikokane? naga kazone kamar saukan mankade” “Kwarai kuwa zuwa nayi insanar dake ki nisanci auren ubana idanko kikaki duniya tayi miki gwatson mage in kunne yaji gangan jiki ya tsira” buda Ashwa tayi tace “Aure ba fashi nanda watan gobe kasan cewa duk rikan kadangare bazai zama kada ba don haka yaro bar kofar gidannan kafin in Tara maka mutane suyi mun butu butu dakai” [3/2, 7:52 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 5⃣2⃣ Ba shiri mansir ya wuce sum sum amma hankalinsa baya tareda dashi yaza'ayi budurwarsa ta auri ubansa ai wannan abun kunya ne bagashi kadaiba har a wajen abokansa itako koh a jikinta Tashige gida, mahaifiyar mansir kuwa kamar tayi hauka har gidansu ashwa tazo tana mata barazana, “Ke malama kiyi hakuri ki dauka kaddara ne don aure da mijinki ba fashi inda nice ke wallahi baxan tada hankalina ba koh kadan zanjene inta adu'a Allah yabada zaman lafya” Shigewa tayi tabarta tsaye tanata haushi Mujeeba ta lek'o tace “Ashwa memuke jira da ita tunda bakowa suka kulle gida sukaci wando sukayi mata dukan kawo wuk'a Ashwa tace “Sharia muzuba nidake kinsan duk inda mukaje kece Mara gaskiya ke kika biyoni don haka kinyi a banza” Haka mahaifiyar mansir ta mik'e tana dinkishi sai gida, hankalin yayanta ya tashi baran ma yar budurwa saboda tana masifan kishin mahaifiyarta, “Maman Mu kema banda abunki maiya kaiki kinsan cewa ko kotu akaje kece bakida gaskiya kiyi hakuri mama tunda aski yariga yazo gaban goshi.... Bata gama rufe bakiba saiji tayi ance “Banji dadi da basu kassara kiba wallahi tunda ke bakida mutunci, da izinin wa kika fita gidan toh kisani aure sai nayi saidai ki mutu, ina mansir shima ina gargadinsa matsawar bai shiga taitayinsa ba” “baban mansir menene banayi maka dazaka yimun kishiya? ” mtww “Rashin mutunci dacin zarafin yan'uwana sannan ribar wulakantamun uwa da kikayi harta koma ga ubangiji shine wannan auren dazanyi wallahi kin cutar dani saidai Allah yayi mana sakayya” “Sa'ar Mimi zaka auro yaza'ayi inyi kishi da yata yar cikina naji ance budurwar danka cema” “Look indo wannan duk surutan banza kikeyi ba gida daya zaku zauna ba zancen mansir kuma wannan kedashi ne tunda dai ba abun kunya bane ya aureta Na aureta saikiyi hakuri” fuuuu yafice yana surutai, biki sai matsowa yakeyi lokacin indo take nan nan da yan'uwansa sai binsu takeyi suko tuni suka Riga suka gano inda ta dosa. Shirye shirye akeyi sosai amma babu wani reception kowa daga zamfara gida yacika Ummi ce tazo ya k'walam gema dagas taki zuwa saboda kunya, ita aka bari sai jooda da girma yafara zuwamai, gidanta a hanwa Lowcost yake yaji komai da komai babu abunda baasa ba Andaura aure nisalin karfe shida aka kawo motar daukan amarya tasha fada sosai Wanda saida taci kuka kaman ranta zai fita ankai amarya kowa ya watse sai Mujeeba datake jira axo a dauketa, gida ya tsaru baran ma kitchen, duk basu gama secondary ba akayi musu aure amma anbada makudan kudi ayi mu komai, Misalin Tara nuru yakira Mujeeba tafito su wuce nanma Ashwa tayi kuka amma yata iya sai hakuri, fitansu keda wuya mansir yayo zuga mai uban yawa hayaniya kawai Ashwa taji tana lekawa taga matasa da adda wuk'ak'e ai tuni taci hanjin cikinta sun kad'a sanda kawai takeyi har saidai takai gun wata kofa ta bude a hankali, tana bi a hankali Ashe gidan kofa biyo ce dakwai barauniyar hanya, cikin ikon Allah ta sameta a bude tuni ta bude kafa mai naci ban bakaba, wajen tsallaka titi ne wani mai mota ya banketa fitowan daxaiyi ashe mijin natane tuni akayo kansa, Ihu kawai takeyi yana kiran sunan Ashwa amma ina jiki Na bari ya sunkuceta sai asibiti, bakaramin rauni tajiba har ake sanar dashi cewa tana bukatan Dashen zuciya tuni hankalinsa yasake tashi yarasa wazai kira ya fadama halinda amaryar dako kwana daya batayi acikin dakinta ba, tabbas idan yagano musabbabin fitowanta kowaye sai hukunci yahau kansa. Haka yakira gidansu Ashwa yasanar dasu ai Mujeeba tuni ta sulale tafadi asume tuni aka yayyafa mata ruwa tayi firgigit ta bude ido tace “Kar kucemun Ashwa tashiga halinda nataba tsintar kaina aciki waiyo ni duniya inaxaki damu, zabura tayi aka riketa tuni ragowan yan'uwa suka bazama Salama hospital, dayake babu nisa tsakaninsu haka suka taradda Mijin nata dukunnar dakai yana kuka maicin rai haka aka bige da bashi hakuri shiyasa sanar dasu komai, haka likita yafito yace Ku kwantar da hankalinku munasa ran matsalar mai saukice inajin batama bukatan dashen zuciyan, murna wajen kowa saida tayi wata daya cir a Asibiti aka salla mesu, gidanta aka kara maidata sai masuyi mata hidima shiko mijin nata tuni yasa aka kama mansir da duk wasu abokansa sai gidan yari daurin shekara goma ne duk Wanda aka kama da makami, kuma ba beli indo tayi kuka shiko koh a jikinsa. Tuni sauki yasamu Ashwa aka dinga cin amarci duk Wanda yaga kulan da Dan tsohonnan yakeba Ashwa ai koh Mujeeba albarka, saboda yasan darajar mace shiyasa soyayya da tsoho ka aureshi ba aibu mutukar babu talauci aciki. [3/2, 8:59 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 5⃣3⃣ Akwana a tashi babu wuya wajen Allah Kamar, haka Mujeeba tasamu juna biyu murna wajen nuru baa magana bashida wani buri a rayuwa illah ya farantama Mujeeba karshe Zaria yadawo da aiki, ABU suke zuwa direba garesu Wanda mijin Ashwa Alhaji bala mai vespa yasama musu, karatu suke babu kama hannun yaro, hajiya tana iya kokari wajen kulada Mujeeba haka Mujeeba take mutunta hajiya dama sauran dangi, Mujeeba tasamu kyakkyawan shedan mutanen gari harda makota, karatun likita takeyi saboda tacika gaba daga inda bisma ta tsaya, amma wani hanxari ba gudu ba labiba tuni ta tattaro kayanta ta dawo Zaria inda ta hana Mujeeba rawar gaban hantsi duk abunda tayi saita kushe ita kuma intayi ya kwabe, Mujeeba tashiga damuwa har takaiga tambayan nuru waishin wacece labiba, tuni yasanar da ita koh ita wacece sannan ya sanar da ita kudirinsu na ya auri labiba shikuma bata acikin tsarin matan dayakeso shiyasa baya sakar mata fuska. Da sanyin safe ne Mujeeba ta shirya tsaf zata school fitowan da zatayi ta dauki lab coat dinta, taga anyi mata butu butu dashi tace “inda jakku baba bankumajo wane Dan tsiyanne yamun haka toh koh yau da ruwan masifa acikin gidannan ba kwammace in fadi jarabawan akan wannan danyen aikin, wallahi duk ma Wanda yayi yafito imba hakaba yasin sai anyi k'aramin yak'i acikin gidannan, Nuru dake shirin fita office ne yaji hayaniyan Mujeeba abunda bai tabaji ba ko ada bare kuma yanzu, “Wai Sweet kedawa kike hayaniya?" muje tace “nidawa banda akuya meeeeeeeeh kawai har wata halitta ta isa ta shigo gidan mijina tace zata fini fada toh wallahi wallahi ba'ayita ba” Nuru yace “wai me aka miki Kituna abunda ke jikinki baya bukatar tashin hankali pls sweet kiyi hakuri muje school din in siya miki sabuwa idan har kikayi missing Exam dinnan wallahi baki ba zuwa horsemanship”. Gsjiya dake tsaye ta harde hannu tace “Mujeeba kiyi hakuri kinji nasan cewa kemai rama sharri da khairan ne, Duk abunda mutum yayi don kansa” Mujeeba tace toh amma kasan Fulani da ruko haka ta wuce makaranta ranta babu dadi saida nuru ya siya mata sabuwar riga saura minti UKU a rufe hall Mujeeba tashiga nuru yaji dadi sosai. Wayarsa ce keta ruri bak'uwar lambace Etisalat, saida tayi ringing biyu ana UKU yadauka “Hello yaya labiba ce ina kwana?” Keeee yadaka mata tsawa“Ki kiyayeni wallahi meye dadi acikin kwanan daxaki tambayeni ina take pls look labiba wa'adin zamanki a Zaria ya kare gobe zaki wuce gusau don bazaki rudamun gidaba mtweee”ya kashe wayan yasata a blacklist, sakato tayi tace “naga takaina duniya tabbas yaya Nuru ba ajina bane yayi nisa bayajin kira an gama dashi anjikamai ya dinkirama cikinsa amma inyasan wata toh baisan wataba”. _*Waiyo Shikenan idan anga miji yana haba haba dakai shikenan anyimai asiri wallahi yan'uwa muji tsoron sarkin Mu, musamman yan'uwan miji wallahi kuna daukan babban zunubi, kyautatawa yanasa miji ya kaunaci matarsa, iya girki, kwalliya, tsafta, tattausan lafazi, hakuri juriya, da kai zuciya nesa, lallami, iya kwanciya, gyran Jiki wallahi dole namiji yayi zakwadin matarsa babu boka ba Malam abunda wasu matan basu ganeba kenan shiyasa karuwa take saurin am she miki miji saboda tsabar makaman tsaro da take dashi*_ Allah yasa mudace Amin. Dawowar Mujeeba gidane taci karo da labiba tana waya tana kwarkwasa “Yaya nuru wallahi nak'osa ka dawo gida I miss you” wai ita bariki Mujeeba tayi dariya tayi shewa tace “Amma anyi asaran kudin tara indai Mujeeba ce nan gani nan bari Nuru kuwa, saidai jifa nidashi mutu karaba takalmin kaza, duk wani karatunki na iya saidai ki kara wani nasan koda second my belove husband will never give you a tiny space in his heart bare har kiyi waya da my humble love. [3/4, 4:38 AM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 5⃣4⃣ _*Ina mika cikakken ta'aziya zuwa ga ILILEE a bisa rashi Aunty dinshi dayayi Allah yaji kanta yasa ta huta ya yafe kura kurenta ya raya abunda tabari Amin ya AllahπŸ‘πŸ»*_ Banda ke gara aiba haka akeyi don kwatan abunda kakeso ba kinga tafiyata” tsaki Mujeeba tayi ta wuce kafin takai bakin kofar Hajiya tuni labiba ta dauketa da wani wawan mari Wanda saida Mujeeba taga wuta, daga bayanta Nuru ta dauketa da mari yace “Babu wani nahaluki daya isa ya tabamun mata banyi fito nafito dashiba, kisani har abada bazaki taba zama matata ba inshort gwara ma kin kwashe tsumman kayanki ki wuce inda kikafi wayo banza karya Mara zuciya” Juyowa yayi yana kallon Mujeeba da fuskarta tayi jajir abunka da farar fata rike take da kuncinta takasa cirewa, babu abunda ke kona mata rai irin ramawar dabata samu tayiba, ni HUMAIRAH nace banda abunki ai taji hannun maza, “Kiyi hakuri pls precious queen ki yarda dani babu wata mace bayanke, wannan itace mace tafarko data mareki kuma ki tuna na nuna mata kuskurenta kiyi hakuri” turbune fuska tayi tace “tabbas zan iya barin gidannan matsawar an kasa daukan mataki akanta don zan iya kassara mutum in watsar banda rainin wayo azo a isheka har gida” haka nuru yajata sai daki, washe gari labiba ta kwashe komai nata sai Gusau ranta cikeda Dana Sanin zuwa gidan kuma duk inna ta matsamun gashi taja an cimun mutumci dawannan ta is a gida. 3years later Mujeeba ta haihu da namiji, mai suna Usman Wato sunan surukinta akasa, Ashwa kuwa gwarne takeyi yayanta biyu duka maza, Nuru yana matukar son Mujeeba saboda hakurinta da hangen nesa batada wata damuwa bare matsala, hajiya ba karamin dadinta takejiba, saboda ba a gidaba hatta a waje shedar arziki ake mata wajen taimakon na k'asa da ita batada kyashin yimaka hidima kota nawane, bata damuwa da abunda tabaka, shedar duniya itace ta lahira toh Mujeeba tasamu kamar yadda Bisma tabar duniya, mutanen cikinta na yaba mata, Mujeeba batada rowa shiyasa yan'uwa suke cewa Itace Bisma ta biyu rayuwarsu sukeyi mai tsafta, haka ta kammala karatunta tazama babbar likita a Asibitin jami'an Ahmadu bello dake Zaria, karatun da kowa yake alfahari dashi. Ikram ce zaune cikin gidanta aka doka sallama jiki ba kwari ta mike ta ajiye bushra, fitowanta keda wuya taga yan sanda har UKU tuni ta zare ido tace “Lafya bayin Allah wa kuke nema?” “Mijinki muke nema mai gidannan, ana zarginsa da kisan wata yarinya yar kimanin shekara 20 wacce report ya nuna cewa saurayinta ne shi kuma a yadda zancen ya nuna sun kama hotel ne wajen hutawa, haka bayan yayi amfani da ita Allah yayi mata rasuwa, har yanzu likitoci basu fadi mak'a sudin rasuwar nataba” abun ya dameta amma kwata kwata Kausar bai bata tausayiba saboda ya cutar da ita kuma tabbas Tasan karshen alewa k'asa, “Kuyi hakuri kusan sati daya kenan bansashi a ido ba amma Duk sanda yashigo nayi muku Alkawarin damkashi a hannunku koda duniya zata zageni, bakincikina daya Bushra wacce batasan me duniya take cikiba” Godiya sukayi suka wuce suna xancen cewa itakanta matar tasa batajin dadi. Bayan k'wana biyu da zuwan yan sanda sai gashi tuni ikram ta sanarda su sukaxo sukasa masa handcuff sai station, tuni ikram ta koma gida, haka akayita tafka shari'a kamar ba gobe karshe dai an gano cewa bashida hannu amma kotu tabada ixinin a kaishi gidan yari na shekara ashirin da biyar saboda case din kaman na fyade ne. Haka akayita yadawa kafin a tafi dashine Ikram ta bukaci Alkali daya amsar mata takaddarta saboda batada raayin rayuwa dashi koh bayan ya fito, haka aka umurceshi yabata saki UKU reras babu jeka kadawo. Haka kowa yake jinjina mata saboda babu Wanda yasan halinda take ciki sai makociyarta Amrah sai ruma, haka duniya ta dauka gidan redio harda jaridar Aminiya Dana daily trust, wannan shine kaddarar data fadawa Kausar saboda rashin kare hakkin iyalinsa bakasan cinsuba bare shansu yaushe zaka gama da duniya lafya mace ita yar Hutu ce, kuma ranar gobe sai an tsaida iyaye akan tarbiyan dasukaba yayansu, miji da mata wane irin kyauta tawa ne sukayiwa juna idan wani ya xalunci wani toh tabbas Dole akwai hisabi mai girma, haka Ikram taci gaba da training yarta amma tana tunanin anya Bushra zata auro saboda abun kunyan dayabar mata a idon duniya Niko humaira da Aysha sayedi mukace mace bata kwantai duk muninta aka auri shegiya yar gaba da fatiha bare gori akan abun duniya fatana anan shine Allah yasa mudace mufi karfin zuciyanmu Ikram taga ta kanta kuma komai yayi farko zaiyi karshe hakuri ribane gamaiyi yakamata yagani. [3/4, 7:48 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 5⃣5⃣ Dole in gayawa duniya irin k'aunar da kukemun tabbas kun chanchanci in karramaku *MAMAN MUJEEBA* *MAMAN KHALEEL* *AISHA* *HUSSNAT* *ABEEDA* *ZARAH ABDULLAHI* *UMMEE GEE* _*Da sauran masoyana masu kirana da turomun sako masu yimun fatan Alkhairi Allah yabar zumunchi ysbar kauna ya raya mana zuri'aπŸ‘πŸ»πŸ˜˜πŸ˜*_ Ruma da hindatu kuwa zama yayi dadi amma hindatu babu abunda take tsinta sai bakinciki daman duk Wanda yazubda tsakinsa a cikin yashi yasan abunda zai tsinta............... Ruma ce ta kasance mai tausasa zuciyanta gashi koh primary batayiba bare azo zancen secondary yaxuwa jami'a, haka ruma tasamu tasata a makarantar yaki da jahilci dukda kudinta, don hamdan yace babu ruwansa, har takaita kawo yace shifa banda kaddara data fadamai babu abinda zaici da hindatu, Ruma tashiga daki tayi dariya ta daga hannu sama tace “Allah Kaine abun godiya nasan cewa baka bacci, baka haifaba baa haifeka ba hmmm yau naga karyan rawan kan Hamdan yau gasu a rana fatse fatse Allah baya bacci kuma mai hakuri mawadaci ne wataran zai dafa dutse yasha romonsa ya more abunda hakuri bai bakiba wallahi uwar gida rashin hakuri bazai taba bakiba”wannan kenan. Labiba ce xaune akan tabarma tana gayawa inna abunda ya faru budar bakinta tace “Dolensa ya aureki dole muci arziki mubarshi inda yake auta guda ai kamar anyi” nidai HUMAIRAH nace tabbas duk abunda baasa Allah aciki ba duk shirmene, kuma dayawanmu haka muke magana kamar zarar bunu babu insha Allah aciki Takanas ta kano inna tayi tattaki zuwa Zaria da isarta Hajiya tace “Sannu da zuwa yaya anzo lafya? “Dakata bana bukatar wata kalma daga bakinki aure dole a hada da nuru da labiba dan'uwanta ne jini yafi ruwa kauri king dole yar uwarsa tafi bare” Nuru dake tsaye a bakin kofa yaji cin mutuncin da takeyima Hajiya tuni yasa baki yace “Inna ruwannan dabaikai jini ba ita nakeso nake kauna saidai labiba tabi wani sarkin amma baniba da ake zancen auren dole ba yanzu ba, maimakon kiyi mata fatan Alkhairi na samun miji nagari kin bige da Hadata da jininta Toh badai wannan jinin ba saidai kamal don inajin shine Wanda ya dace da ita bani ba” Yana gama magana yayi waje Hajiya tayi zugudi tunda kuruciya Hajiya ke fama da yaya amma har zuwa yanzu bata hutaba, cikin dare ne da Alhaji ya dawo Baysn sun gaisa take gayamai bukatunta budar bakinsa yace “Idan har nuru yanason labiba babu Matsala idan koh yace bayaso ba zanyi mai dole ba saboda rayuwa babu dole musamman Wanda ya mallaki hankalin kashi” tayi matuk'ar mamaki tayi tunanin cewa zai goyi bayanta amma saitaga akasin hakan, a daddafe ta kwana washe gari sai tashi sukayi sukaga bata, Hajiya tace “Agayas mun yarda kwalon mangoro mun huta da K'uda” Mujeeba taba Hajiya hak'uri sosai tayita bata labari har zuciyanta tayi fari kal, koda yaushe hajiya tana alfahari da Mujeeba, Usman sai girma yake dadayi haka kowa ke rubibinsa, inna kuwa sun bazama basu boka basu malam amma an gayamusu cewa auren bazai taba yuwuwa ba haka suka fawwalawa Allah suka hakura harta samu wani yataya akayi shagalin aure amma abunka da barbada kwana daya yasakota batareda yagadi dalili ba haka suka rungumi kaddara. Mujeeba ta natsu sai haihuwa takeyi tana kara zama hamshakiya itakadai cikin gidanta tana wandaka hajiya koh ansamu mutuwar gefe daya, haka Mujeeba ta ajiye aikinta ta koma jinyar hajiyar Nuru, kusann Kullun saita shimata albarka, taci kashinta taci fitsarinta, Ashwa Kullun saitaxo duba hajiyar ranar wata laraba Allah ya amshi abunsa harta komaga Allah tana yiwa Mujeeba kyakkaywan fata, haka mutuwar Hajiya ta girgiza kowa ciki hard a Mujeeba datayi mugun Sabo da ita, amma babu yadda suka iya saidai fatan muyi kyakkywan karshe. [3/5, 5:32 PM] Melody🀸🏻‍♀🀣: πŸ’” *DASHEN* πŸ’” *ZUCIYA* _Written by_ _*HUMAIRAH Bashir Melody*_πŸ‘„ *Dedicated to Abeeda(Tautah)*😘 *LAST PAGE* 5⃣6⃣ Bayan wasu shekaru da damane, Su Mujeeba ana cikin kwanciyan hankali da miji, Alhaji Wato mahaifin Nuru yana gadon asibiti jikoki da yaya sun zagayeshi, da surukai Ya kalli Nuru yace “Inaso ka auri labiba saboda banaso zumunchi ya lalace, Ya kalli jikokinsa yace kuma Allah yayi muku albarka kuda iyayenku, Yana juyowa wajen Mujeeba yace Allah ubangiji yasa kikagama da duniya lafya, tabbas ke yar halak ce yadda Hajiya ta rasu tana mai yabon halinki haka nima zan cika yimiki adua, tuni suka fara kuka Mujeeba kuwa jingina tayi da jikin Nuru, yaci gaba da magana kizauna da abokiyar zamanki lafya insha Allah babu abunda zai faru sai Alkhairi sannan Ku kasance masu farantawa juna rai, shakuwace ta sarke shi aka bashi ruwa amma yace ah ah haka likita yace kowa ya fita daga Mujeeba sai Nuru, Alhaji dai da kalman shahada yacika haka akayita koke koke Wanda yaxaman ma mutane al'ada...... Bayan anyi kwana arba'in ne aka daura auren nuru da labiba amma badason ran Nuru ba biyayya yayiwa mahaifinshi kamar yadda ya umurta. Nuru yasamu aiki a United kingdom, a state din Kasar Wato Florida inda sukayi karatu an daukeshi a matsayin lecturer haka ya kwashi iyalansa sai Chan harda Labiba, ya kwalam an tsufa Ummi kam kwance take saboda ciwon sugar dake damunta, Mujeeba batasamu zuwa yi musu sallama ba amma dai sunyi waya sannan ta turawa iyayenta makudan kudi, Jood'a kuwa shanu yasiya dukda tsufa dayayi jiyake tamkar matashi gidan gona aka budemai achan yake wuni wataran har kwana................ Yara kowa yayi aure daga gidansu Bisma kowa saida yasa sunan bisma saboda kaunar da suke mata, Haka mutuwa ta dinga dauki daidai saida tadau Ummi kannan ta zagaya tadau jooda mahaifin Mujeeba, haka su Mujeeba aka rankaya sai Nigeria inda tabar yaran wajen labiba. Mujeeba tayi kuka rashin mahaifinta saida kowa yakoma bata hakuri saboda yitake kamar ranta zai fita, idan ta kalli hoton Ummi saitaji duniyar tamata fadi. Alhaji kuwa shi akayiwa mutuwa babu Ummi babu jood'a banda imani da tuni yafadi shima yabisu, saboda shakuwar dayayi da jood'a tayi yawa harta kaiga bayacin abinchi sai dashi, sunkulla alaka wacce duniya take alfahari dashi. Haka aka gama zaman makoki su Mujeeba aka koma taso tafiya da ya k'walam amma babu hali tana cikin takaba, haka su ikram suka rik'e ya k'walam kamar Ummi tana fita takaba su yaya salim da babban wansu hadi da nabil suka sa aka daurawa ya k'walam aureda mahaifinsu, su Mujeeba labari kawai sukaji abunda ya dadada musu rai kenan zumunchi yakara karfi zuria sai bunk'asa takeyi, tako ina Alkhairai budi ta koh ina saboda sun gama da iyayensu lafya. Mujeeba ce zaune a falo bayan shekara labiba ta haihu Nuru yasawa yarinya Bisma atafau tace bataso sunan matacciya Allah shi kyauta, haka Nuru ransa ya baci tuni ya karbe yar tasa yayi mata bisa yace ta wuce Nigeria saiya nemeta nikam nace mai hali baya chanza halinsa, Dan talaka bai iya samun wajeba Mujeeba tayi juyin duniya yabata yarta yace ina har abun yadawo kanta nikam HUMAIRAH nace ina dalili ina Dan mafari ai ki kyaleshi kawai, Mujeeba ta hada da tata yar macen mai sunan Hajiya taci gaba da rainonsu haka rayuwa takasance mai dadi, haka Mujeeba tadinga haihuwa harta koma tsarin iyali, tafara kwalliya kamar wata budurwa abun sai Wanda yagani anan sai ince Allah yabamu rayuwa da zuria mai amfani. Alhamdulillah...... Godiya ga Allah mai kowa mai komai daya kawoni karshen wannan littafi abunda nayi kuskure Allah ya yafemun Wanda nayi daidai Allah yasa mishi Albarka ya sadamu da Annabin rahma. *Godiya ta musamman ga masoyana na nesa Dana kusa wayanda suke bibiysr novel dina tundaga farawa harya zuwa yanzu bazan iya faden sunanku ba Amma zan fadi sunan garuruwanku* Kaduna\zaria Kano Jigawa Katsina zamfara Saudi Nijar Abuja Kwantagora Gusau Jo's Bauchi Maiduguri Lagas Sokoto Kebbi Gombe Dadai sauransu masoyana na wannan gari ina godiya Allah ysbar zumunchi😘❤😘. Ina kaunarku Abeeda Mardia Rookie Kax Umme gee Sarah Mjay Miss XOXO Da wayanda ban ambataba. Allah yabar zumunchi ANEESA A RIMI FIDDY SODANGI AUNTY SIS UMMU SABREENA AUNTY LUBBIE LYSM GAISUWA GA YAN UWANA Maryam shehu Muhammad Abdool shehu Muhammad Sani shehu Muhammad Dauda shehu Muhammad Ahmad shehu Muhammad Musty shehu Muhammad Bashir shehu Muhammad Habib isyaku wada abokin wasa😜. Godiya ta musamman ga duk group din novels danake ina godiya da hadin kanku musammam group dina Melody novels group da jamaar ciki. Saimun hadu a littafi ba gaba MULKI KO SARAUTAπŸ€” Ga kadan daga ciki _*bana bukatar a akara haihuwa gashi Maimuna tana daukeda ciki dole saina fitar da abunda zaa Haifa saboda banaso a hada soyayyan DANISH danata dole ta fita daga gidan SARAUTA Maryam ce ke wannan maganar wacce takasance yar MULKI ce yar shugaban k'asa ne, ana haihuwa aka dauke ya wacce akasawa suna tunkafin taxo duniya Wato RAINA(kyakkyawan Gimbiya)😜😜😜*_ adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *