Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, 24 April 2017

DODON JATAU 1-END.

adsense here

[12/5/2016, 8:16 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 1⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Duk kan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mad'aukakin sarki, tsira da aminci su k'ara tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (swa) tare da alayen sa. Kamar yanda muka fara wannan rubutu a cikin yarda da amincewar Allah, muna fatan mu kammala wannan labarin acikin amincewar sa. Wannan labari ne daga marubuta uku:- Rabiatu sk msh, Amrah A msh da Zarah bb (RAZ), labari ne k'irk'irarre ba da gaske bane, bamu yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba, haka kuma bamu yarda wani ko wata ya mana satar fasaha ba, duk wanda ya aikata hakan mun barshi da Allah mai kowa da kuma komai. Muna fatan sak'on da muke son isarwa zai isa kuma zai amfanar da al'ummar musulmai baki d'aya, labari ne mai k'unshe da tsantsar hausa da kuma al'adar bahaushe, idan har mai karatu yaci karo da kalma d'aya ta turanci a ciki to akasi aka samu, asha karatu lafiya. **** Zaune yake a 'yar rumfar sa sai had'a zufa yake kasantuwar yanayin zafi ake ciki, daga gefen rumfar sa kuma wata babbar rumfa ce wadda take cike da mutane sunyi dafifi kowa na jiran kayan sa. Hawaye sukaci gaba da kwaranya daga idon Mati saboda babu kowa a tashi rumfar ga tarin dukiya daya kashe wurin siyayyar kayan sak'i amma kwata kwata baya ciniki, sosai ya zurfafa a tunani yana yi yana kallon tarin dukiyar daya kashe wurin siyan aiki, daga can gefe tarin auduga ce, a d'ayan gefen kuma karare ne wanda aka jera su saboda sak'a. Bai ankara ba yaji muryar mutane suna fad'in "jama'a ku kawo taimako gobara!", Firgigit ya dawo hayyacin sa yana waigen ta ina gobarar take, Hankalin shi bai tashi ba sai da yaga gobarar a cikin rumfar sa, Da gudu ya fita hankalin shi a tashe yana waiwayen rumfar sa, a ransa yake tunanin "me ya jawo wannan gobarar?" ji yake ina ma ace da yanda zayyi ya fitar da kayakin sa daga cikin rumfar, amma ina, babu hali dan dama da karare akayi rumfar saisa nan da nan ta kama taci gaba da ci da wuta. Banda kuka babu abunda yake, mutane suna ta bashi hak'uri amma ina, ko sauraren su baya yi, Babban abun mamaki bai wuce yanda wutar ta gama ci tas amma ko kad'an bata shafi rumfar kusa data Mati ba duk da tare suke jingine kuma itama kara aka rufe ta dashi. Sai da wutar ta cinye komai tsaf sannan ta daina ci, Kaf mutanen wurin babu wanda bayyi mamaki ba, amma suka kawar da mamakin saboda sun san halin *JATAU MAI SA'A,* duk wanda yayi sana'a iri d'aya da tashi to tabbas zayyi nasarah ya barshi. Da wannan tunanin kowa ya kama gaban sa, Jatau kuwa yaci gaba da bama Mati hak'uri har da taya shi hawaye yayi yana fad'in "kayi hak'uri mati ka barma Allah, Allah'n daya baka wannan sana'ar shi zai sake baka wata, ka daina kuka kaji?", Shiru mati yayi yana sauraren Jatau kafin yace "tabbas Jatau nasan kai aboki ne na gari mai so na, na daina kukan, nagode sosai da kulawar ka". "Yauwa mati aboki na, abunda nake so da kai yanzu ka tafi gida ka sanar da iyalin ka, zan sa a gyara gurin kawai, nima naji wannan sana'ar ta fita min a rai saboda asarar da kayi, na hak'ura da ita kawai", "Anyi haka Jatau? Da kaci gaba da sana'ar ka kawai, nasan idan naje wurin yaya Na'Allah zai bani wata" Mati ya miyar masa da amsa. "Kar ka damu aboki na, hausawa sunce _"Idan kaga gemun d'an uwan ka yana ci da wuta, yayyafa ma naka ruwa"_ kaga kenan ya zama min dole na hak'ura da wannan sana'ar, sai mu kama wata, zan jira ka har sanda zaka samu wani jarin". Da haka suka rabu Mati ya nufi gida kamar yanda Jatau mai sa'a yace masa, shi kuma Jatau cike da farin cikin samun nasarah yasa yara suka gyaggyyara rumfar mati data k'one ya biya su kud'i, kayakin sa yasa suka kwashe suna kaiwa gidan sa. Cike da damuwa Mati ya isa gidan sa, da shigar shi yaci karo da matar shi Larai ta fito daga ban d'aki da buta a hannun ta, ganin mai gidan ta da tayi cikin damuwa yasa tayi saurin ajiye butar tana mai isa inda yayi dirshan ya zauna, "Lafiya malam? Me ya faru na ganka haka? Mesa ka baro wurin sana'ar tun da wuri haka?" Duka a tare Larai ta jero masa wannan tambayoyin. Shiru ya mata bai bata amsa ba, Cike da damuwa ta shiga d'aki ta d'auko tabarmar kaba ta shimfid'a tace "malam ka zauna anan, kaga akwai k'ura da k'asa a k'asan", Da k'yar ta samu ya murgina ya zauna, ganin har yanzu bai da niyyar bata amsa yasa ta sake tambayar sa "malam lafiya? Ko wani ya b'ata maka rai ne?", Sai a lokacin yace mata "Larai rumfa ta ta k'one k'urmus babu abun da aka fitar a ciki, na shiga uku Larai yanzu ya zanyi? Ki fad'a min ya zanyi Larai? Shin a haka rayuwa zataci gaba da tafiya mana ne? Duk abun da na tab'a sai ya lalace?" Ya k'ara fashewa da kuka kamar k'aramin yaro. Itama hawayen taci gaba dayi sosai amma bata fasa kukan ba, Sun jima a haka kafin ta kuma bud'e baki tace "baka da abunda zakayi daya wuce hak'uri malam, Allah'n daya baka wancan jarin shi zai baka wannan ma, shawara ta itace; kawai kaci gaba da mik'a al'amurran ka ga Allah, shi yasan halin da kake ciki kuma shi zai maka magani". Da haka Larai ta shiga 'yar k'aramar madafar su da aka zagaye da karare ta kawo masa abinci a cikin 'yar tasar data saba zuba masa abinci, Haka ya k'urawa abincin ido duk da yana matukar son tuwon dawa da miyar karkashi amma ya kasa ci sai zubar da hawaye kawai yake. Rabee'art sk❤ AmrahπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/6/2016, 9:23 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 2⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Suna cikin haka ne Talle ya shigo a rikice har yana cin tuntub'e, Da hanzari Larai tace "wannan yaron! Me ya faru na ganka haka?", "innah wani labari ne na jiyo a waje, ban san ko gaskiya bane", "Wane labari ne ka jiyo?" Larai tayi caraf ta tambaye shi duk da tasan ko menene. "Innah wai rumfar baba ta k'one na jiyo a gari", Sai a lokacin Mati ya tanka dan wasu sabbin hawaye ya fara ji suna fito masa, "ta k'one Talle, rumfa ta ta k'one ko kara d'aya ban fitar a ciki ba". Salati Talle ya d'auka had'e da kuka yana fad'in "mun shiga uku baba! Yanzu shikenan ta k'one da gaske? Dama fa dabbobin mu ne ka siyar ka kama wannan sana'ar ta sak'a tunda aka sace kayakin mutane na rini ka samu ka biya su, Allah gamu gare ka, ka kawo mana d'auki". Larai cikin tausayi tace "haka ya kamata ka fad'a tun farko ba kace ka shiga uku ba, ku shirya anjima idan Audu ya dawo gidan sai muje gidan kaka ta tare, akwai dabbobi na na gado dana fad'a maku Baaba Haja tana kiwata min su, zan siyar dasu sai ka kama wani jarin, ku cire duk wata damuwa a ranku dan Allah". Nannauyar ajiyar zuciya Mati ya sauke kafin yace "amma Larai kina tunanin Baaba Haja zata yarda ki siyar da dabbobin ki na gado? Ki tuna fa dama tana d'aya daga cikin wanda basa son auren mu", "Kar ka damu malam, da yarda da amincewar Allah zata yarda, idan ma bata yarda ba ai nawa ne ba nata ba, sai in mata ta zafi tunda ita bata san arzik'i ba, abu ya wuce tun tuni har da yara hud'u amma ita ta kasa hak'uri". "Idan ma ta hana Innah ni ki barni da ita, idan tasan wata ai bata san wata ba" Talle ya fad'a a k'ufule. "A'a Talle, kar na sake jin irin wannan daga bakin ka, ku bita a hankali idan bata bayar ba sai mu hak'ura har lokacin da yaya Na'Allah zai dawo" Mati ya fad'a yana kallon Innah da itama shi take kallo. "To idan haka ne ku barni zanje ni kad'ai ko kuma nida Kande, bari ta dawo daga makarantar allo sai mu tafi, dake ita sunan ta ne aka saka mata nasan ko saboda ita zata iya bayar wa". Da wannan shawarar suka gama magana, kai tsaye Talle ya wuce madafa ya zuba wa kansa abinci sannan shi shiga ban d'aki ya fito ya d'auki abincin sa daya ajiye a bakin madafa, koda ya dawo tsakar gida Larai da Mati sun koma ciki, saboda wani irin zazzab'i had'e da amai da Mati yake ji yana sauko masa, D'akin ya shiga ya tayar Larai ta rufe shi da zani sai kyarmar d'ari yake, hankali tashe yace "sannu baba! Me ya same ka yanzu yanzun nan? Allah ya baka lafiya" Larai tace "tafiyar ka zuba abinci kenan sai ya kama kwara amai, take zazzab'i kuma ya taso masa" "Allah sarki baba! Sannu Allah ya baka lafiya" Abincin da baici ba kenan ya zauna jinyar mahaifin sa da har hawaye yake tsabar zafi da jikin sa ya d'auka. Basiru ne ya kamo hannun Kande suka shigo cikin gida, jin kamar babu kowa a gidan gashi sai sallama suke rafkawa ba'a amsa ba yasa Kande ta k'ara yi da k'arfi, "Salamma alekum" suna k'ara kutsa kai a cikin gidan. Wannan karan kam Talle yaji ya amsa sallamar, Sai yanzu hankalin su ya d'an k'ara kwanciya ita da Baseerun, kai tsaye suka shiga d'akin da yafi kusa dasu kasantuwar shine na baban nasu, Ganin Mati lullub'e da k'aton zani yasa Kande saurin rik'e baki, "Baba me ya same ka? Lafiya?" Talle yayi saurin katse ta da cewa "kar ki damu Kande, masassara ce yake yi kuma yasha sassak'e yanzu zai samu lafiya" Shiru tayi ba wai dan ta gaskata abun da ya fad'a ba, a daidai inda yake kwance itama ta kwanta har gumin jikin shi yana shafar ta, tana jin yanda numfashin sa yake fita da zafi sosai. Cike da fargaba ta tashi zaune tace "shikenan Innah! Shima baban mu mutuwa zayyi, kin manta irin wannan ciwon ne Ta'ishalle tayi bayan baba yaje da ita gidan Jatau mai sa'a? Kuma daga shine ta mutu, Innah ina tsoro kar shima Baba ya mutu" hankalin ta a tashe take wannan maganar wanda tayi daidai da shigowar Jatau mai sa'a kuma yaji duk abunda ta fad'a. A dabarce ya tsaya bai k'arisa ciki ba, a ranshi yace "ya akayi wannan yarinyar k'arama tayi wannan tunanin? Kenan tana nema ta ruguza min duka wasu tsare tsare dana tsara? Hhhhhhhh!! Dole ne na canza salo ko dan kar asiri na ya tonu!!!" ya d'aure fuskar shi kuma kamar bashi ne ya gama dariya ba, komawa baya yayi bai ma k'arisa shiga gidan ba. Saurin katse ta Innah tayi tace "kar in kuma jin irin wannan maganar a bakin ki Kande, idan kika bari na sake ji kuma sai na baki kashin gaske, waye ya fad'a miki baban ki zai mutu? Waya fad'a miki saboda anje da k'anwar ki Ta'ishalle gidan shi ne ta mutu? Ki daina irin maganar nan kinji Kande ta?". Kai ta gyad'a ba tare da tace komai ba, Innah tace "ki tashi kiyi wanka mu tafi gidan Baaba Haja" Take kuma ta washe sai farin ciki, dan inda abun da take so to bai wuce Innah taje da ita gidan Baba Haja ba, saboda tana son ta sosai sunan ta ne aka saka ma Kanden. Wanka tayi jik'a jik'a ta fito ta saka sabbin kayan ta da Baban ta ya sak'a mata jiya, Fitowa tayi ta samu Innah na jiran ta a waje, "Innah gani na fito" ta fad'a da k'arfi. Kama hanyar gidan Baba Haja sukayi a hanya Innah sai faman addu'ah take ko Baabah Haja zata amince mata. Rabee'art sk❤ Amrah πŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/7/2016, 9:32 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 3⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Da sa'a kuwa suka samu Baaba Haja ta zagayo daga baya inda turken dabbobi yake, baki ta washe ganin su Innah tana "lale maraba da takwara ta Meramu", Fuska Kande ta b'ata tace "wai ke Innah sai kita b'atawa mutum suna, wai Meramu, ana Mairamu ke kina Meramu, idan bazaki iya gyara sunan ba sai ki kira ni da Kande na". Dariya Baaba Haja tayi ta rik'e baki tana fad'in "oh! Wannan 'ya, ke har nice zaki koyawa magana? Duka yaushe kema d'in kika iya da har kike koyawa wani?", Baki Kande ta murgud'a kafin tace "nidai mu shiga d'aki ki bani tab'en k'uli k'uli, nasan kina dashi tunda ga k'amshin mai nan ina ji alamar baki dad'e da gamawa ba", "Nak'i in baki d'in, bani ce kike koyawa magana ba? Bazan bayar ba sai kin koya min yanda ake yin k'uli k'ulin" Baabah Haja ta fad'a cike da zaulaya. Ita kam Innah aikin ta kallo ne, ga gajiya da tayi da tsayuwa ga kuma dariyar lamarin Baabah Haja da Kande, Ganin bata iya jurewa tsayuwar yasa tace "Baabah nidai na shiga d'aki sai kun shigo, naga alamar baku gaji da tsayuwar ba ku kam". Baabah Haja tace "wannan 'yar taki ce ke neman fad'a min magana, uhm! Nima fa na gaji da tsayuwar nan mu shiga ciki inyaso ita kuma sai ta tabbata anan" tana gama fad'in haka tabi bayan Innah da tayi nisa da inda suke tsaye, Ba shiri itama Kanden tabi bayan Baabah Haja. Bayan sun zauna Innah ta duk'a har k'asa ta gaishe da Baabah Haja, Kande ma ta gaishe ta sannan kuma suka hau fira, Sai da sukayi nisa a firar sannan Innah tace "Baabah wai kuwa kin samu labarin cewa malam yayi gobara a sabuwar rumfar daya bud'e? Har komai na rumfar ma ya k'one ba'a fitar da komai ba", "Wane malam d'in kike magana Larai?", "Baban Kande nake nufi Baabah, d'azun nan rumfar sa ta kama da wuta babu dalili kuma babu abunda aka fitar daga ciki, gashi kuma kaf jarin sa ne a ya k'one, yanzu haka yana gida kwance ba lafiya". Kamar Baabah tana jiran Innah tayi caraf tace "to sai akayi me kuma? Ni ina ruwa na da gobarar sa? Wannan ku ta dama ba ni ba, yanzu da kika kwaso k'afa kika zo har kike fad'a min me kike so na miki?", Innah tace "Baabah nazo ne akan ki taimaka cikin dabbobin nan ki bani koda guda biyar ne, rago uku sai tunkiya biyu, nasan da yardar Allah zasu ishe shi yaja koda k'aramin jari n..." "Yimin shiru wawuya kawai, kin girma amma har yanzu zuciyar k'ananan yara gareki, in banda hauka me zaisa ki siyar da dabbobin ki na gado saboda namiji? Ki kiyaye ni Larai kinji na fad'a miki". Hawaye Innah ta farayi tana fad'in "yanzu shikenan dan na taimaki miji na sai ace bani da hankali? Ashe taimakon miji rashin hankali ne" taci gaba da kukan ta kamar wadda akaima dukan tsiya. Cike da tsiwa Kande ta tashi tace "kuma wallahi tunda kika saka min Innata kuka bazan k'ara zuwa gidan ki ba, ke babu ni babu ke ko a hanya kika ganni kar ki kuma nuna kin sanni tunda ke baki da imani, mutum ya nuna miki yana buk'atar abu amma ba zaki iya taimakon sa ba, Innah tashi mu tafi tunda abun haka ne, dan an ganki ke 'yar baiwar Allah ce baki da Innah da Baba saisa ake miki haka". Hatta da Innah sai da tayi mamakin kalaman da suka fito daga bakin Kande 'yar shekara goma sha d'aya, wani zai iya rantsuwa da Allah cewa koya mata su akayi. Ganin kamar Innah bata da niyyar mik'ewa yasa tasa hannu taja ta ta mik'ar tsaye, bata sakar mata hannu ba taja ta suka fita bakin k'ofa ta gyara mata takalman ta ta saka sannan suka nufi hanyar fita, Baabah Haja data gama sandarewa tsabar mamaki tayi saurin dakatar dasu, "Ku dakata Kande! Indai dan na hana mahaifiyar ki abunda take so ne yasa kike fad'a min magana haka to kiyi hak'uri ki dawo da ita, indan tani ne ma ta kwashe duka dabbobin ta siyar ta farantawa mai gidan ta inga wa gari zai waya?". Cike da farin ciki Innah ta juyo duk da hawayen da har yanzu basu daina fita daga idon ta ba, Dawowa sukayi suka zauna Innah ta hau yima Baabah Haja godiya kamar kyauta ta bata su, Baabah tace "ki fita k'ofar gida idan su Ilu na nan kice suzo su kwance miki su su kama miki ku tafi dasu", Da gudun Kande ta fita ta kira Ilu da Habu da wasu abokanan su guda uku, Koda suka shigo kowanen su yaja d'aya suka fita Innah da Kande na bayan su. Fitar su waje ne sukayi kicib'us da *JATAU MAI SA'A* akan jakin sa zai tafi gida, Kallon mamaki yabi dabbobin dasu kafin a ranshi yace "me zasuyi da dabbobi? Hmmm! Ina fatan abunda ke raina ya kasnace da nafi kowa farin ciki" yaja jakin sa ya k'ara gaba. Rerbee'art sk❤ AmrahπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/8/2016, 10:16 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 4⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Basu zarce ko ina ba sai kara (kasuwar dabbobi), Cikin sa'a kuwa aka siya dabbobin da daraja saboda lokacin darajar su ne, Cike da farin ciki Innah da Kande suka koma gida, abun mamaki suka tayar Baba ya warke tas kamar bai tab'a yin ciwo ba, Bayan Innah ta zauna tace "malam ya jiki?", "Angode Allah Larai, jiki yayi sauk'i sosai, kuna tafiya naji kamar an zare min wani nannuyan abu daga k'irji na, tun daga nan naji ban k'ara jin ko alamar ciwon wani abu ba", "Abu yayi kyau malam, ina tunanin ko suracin ganyen sabara da kayi ne, kasan yana maganin ko wace irin masassarah da amai", "To gani nan dai Larai, ya maganar Baabah Haja? Ince dai anyi nasarah?", Murmushi Innah tayi bata ce masa komai ba sai zaro kud'in da tayi daga aljihun k'aramin bujen ta na ciki, kallon mamaki Mati ya ringa yi ma kud'in saboda yawan su, cike da farin ciki Innah ta mik'awa Mati kud'in tace "ungo malam, duka naka ne, kaje kayi duk kalar sana'ar da kake so indai zasu ishe ka, na baka su duniya da lahira". Wani irin dad'i Mati yaji yana ziyartar sa, bai ko ji kunyar yaran sa maza uku da Kande ba a gaban su ya rungume Innah yana kukan farin ciki, Bayan ya sake ta ya share hawayen sa yace "ni a iya sani na Larai ba'a tab'a mace ta gari a duk fad'in duniyar nan ba kamar ki, Allah ya baki abunda kike so, Allah ya barmu tare ya kawar da tashin hankali a tsakanin mu, Allah ya kawo ranar da zamu daidaita da Baabah Haja", "Ameen" Innah tace sannan taci gaba da "kaji malam, wai ba'a tab'a mace ta gari kamar ni ba, ni d'in dai ka sani", Murmushi Mati yayi yace "to ai dama saisa nace miki ni a gani na, tunda dai iya kyautatawa daya kamata mata tayi wa mijin ta dai kina yi min, ni kuwa dole na nuna godiya ta tunda dai kina yi min d'in, ina fatan Kande zata d'auki irin kyawawan halayen ki", Murmushi Innah ta kuma yi a karo na biyu tare da mik'ewa tace "malam barin nufi d'aura girki, ina da sauran garin dawar nan, tunda kafi son shi jiya kasa na maka shi dan ka samu cin d'umamen safe amma tashin hankali ya hana ka ci, yanzu zan maka shi kaci cikin natsuwa", "To shikenan Larai, idan mun gama ci kuma sai muyi shawarar sana'ar daya kamata nayi". *** Zazzaune suke Baba, Innah, Talle, Audu, Baseeru da kuma Kande suna cin abinci cike da walwala da farin ciki, sunyi nisa a ci ne yaro ya shigo yace "wai ana sallamah da Baban Kande", "Waye?" Baba ya fad'a ya d'aga asaberin d'akin yana kallon yaron, "Jatau mai sa'a ne" (haka Jatau yake a cikin k'auyen, kowa ya san shi tun daga yara har manya babu wanda bai san shi ba), "Kaje ka fad'a masa ina fitowa yanzu", Innah ta haska shi sosai ta gane yaron d'an mak'otan su ne tace "D'an Lami zo kaci tuwo kaji?", "Na k'oshi Innah, Lami ce ta aike ni gidan su Ladidi kuma tace inyi sauri" yaron ya fad'a da ganin shi yana son cin tuwon. "To shikenan, ka gaishe da mamar taka", "To zataji Innah, sai da safe" ya fita ya samu Jatau ya sanar dashi ga Baba nan zuwa. Cikin sauri Baba ya gama cin abincin ya fita wurin Jatau mai sa'a, Hannu ya bashi su gaisa amma Jatau yayi saurin janye hannun sa saboda wani mummunan kud'urin sa da shi kad'ai ya barwa kansa sani, k'ok'ari yayi ya k'ak'alo murmushi yana kallon Baba dake mamakin k'in bashi hannu da yayi su gaisa, "Mati nazo ne dan na k'ara maka jaje akan abunda ya faru d'azu, ina so ka kwantar da hankalin ka, gobe ko jibi zan sayar da tumakai na sai na baka jari rance, inyaso daga baya idan kayi naka sai ka miyar min dashi", Murmushin jindad'i Baba yayi yace "Allah sarki Jatau aboki na! Saisa a koda yaushe nake alfahari da kai a matsayin ka na babban amini na, hak'ik'anin gaskiya duk abunda ya kamata ace aboki yana yiwa abokin sa to kana yi min, sai dai na maka godiya saboda har ma na samu kud'in da zan ja jarin dasu, nasan kuma da yardar Allah zasu ishe ni", "To yayi daidai Mati, yanzu wace sana'a ya kamata muyi?", Shiru Baba yayi na wani lokaci kafin yace "tun d'azu nayi tunanin kawai mu fara rini, saboda na koya a wurin abokin kaka na tun ina yaro, kuma na iya sosai, ina ganin kawai sai mu fara ta, zuwa gobe da safe sai mu tafi garin Shuni, an fi samun kayan rini da sauk'in kud'i kuma a wadace acan d'in", "Abu yayi kyau Mati, gobe zanzo da sassafe, sai in taho da jaki biyu saboda kaima ka hau ba sai mun hau amalanken shanu mun biya kud'in mu ba, ka shiga kawai Mati ka gaishe da iyalin, da 'yata Kande" Jatau ya fad'a had'e da kanne ido d'aya bayan ya fad'i sunan Kande, ko me yake nufi oho, RAZ kansu basu san manufar Jatau ba, sai dai suna biye dashi zasu ganowa Fans d'in su duk abubuwan da yake aikatawa wanda har yanzu babu wanda yasan yana aikata su. Shigar Baba gida ya labartawa su Innah shawarar da suka yanke da Jatau mai sa'a, ya kuma fad'awa Kande cewa "yace a gaisar masa ke", Bud'ar bakin Kande tace "bana amsawa ni dai, nikam Baba ban san had'in ka da wannan mutumin ba, kana son shi yana son ka amma ni ko labarin sa bana son ji, haka kawai naji na tsane shi", Cike da mamaki suke kallon Kande, lallai ma yarinyar nan, ita har tasan ta fad'i wannan maganganun, Cikin tsawa Baba yace "ke baki da hankali ne!? Ki shiga taitayin ki Kande, ina k'yale ki ne saboda ke auta ce, ba yau kika fara fad'in munanan kalamai game da aboki na Jatau ba, duk ranar da na kuma jin haka daga gare ki sai na sassab'a miki!", kuka Kande ta fashe dashi da k'arfi kamar wadda akama dukan tsiya, Innah ta fara rarrashin ta duk kan su babu wanda yace komai, Baba kuwa sai ajiyar zuciya yake a dole yaji haushi, abun kunya wai da 'yar sa k'arama yake kawai dan ta fad'i ra'ayin ta. Wannan kukan shi ya zama silar baccin Kande, haka tayi bacci da busasshen hawaye a fuskar ta, Audu yaji haushin fad'an da Baba yayi ma Kande sosai, ba wai Kande kad'ai ba, duka mazan ma sun fara jin haushin Jatau mai sa'a, saboda a kanshi ne baban su yake yawan masu fad'a, daren ranar dai haka kowa yayi bacci yaran cike da jin haushin Jatau, Innah kuwa tama rasa abunda yake b'ata mata rai, ita dai har ga Allah tasan Jatau bai mata komai ba, kuma babu wani abu da zata fad'a tace yau gashi Jatau yayi mata shi, tsakanin su dashi a koda yaushe bai wuce kyautatawa ba. A b'angaren Baba kuwa maimaita kalaman Kande kawai yake, ji yake in dama yayi mata duka ko zai huce abunda Kande ta fad'a game da aminin shi, sauk'in shi d'aya ma ba a gaban Jatau d'in ne tayi maganar ba. Rerbee'art sk❤ AmrahπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/12/2016, 10:45 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 5⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 *kuyi hak'uri na rashin jin mu kwana biyu, wani dalili ne ya tsayar damu, amma yanzu da izinin Allah komai zai ci gaba da zuwa kamar baya, muna k'aunar ku masoyan mu* Washe gari Tunda Mati ya dawo sallah'n asuba ya hau shiri saboda sunyi da Jatau tunda sassafe zasu tafi siyo kayan rini, da wannan tunanin ya kwana a ransa dan har k'agara yayi gari ya waye, Kande tayi sallama d'akin shi da kwanon koko a hannunta, ta duk'a har k'asa tana gaida mahaifin nata, sallamar kawai ya amsa ya juyar da kanshi gefe don har yanzu haushin ta yakeji kan maganganun data fad'a game da aminin shi Jatau mai sa'a, donshi a ganin shi baida babban masoyi sama dashi a duniya wanda kuma Kande ta dad'e da fahimtar cewa Jatau ba masoyin baban su bane. Kwanon kawai ta ajiye, ta juya zata fito a 'kofa suka had'u da innah da kwanon d'umame a hannun ta, ta ra'ba gefe ta wuce sannan ta fita. Innah tace "malam badai harka shirya ba da sassafennan ko karin kumallo bakayi ba?" Yace "Ai kinsan da zafi-zafi ake dukan 'karfe don munyi da Jatau da sassafe zamuje mu siyo kayan rinin nan, idan ma hali ya samu yau zamu harhad'a kayakin da komai don mu fara aiki". Tace "Tohh malam Allah ya taimaka, ya kuma saka a fara aikin nan a sa'a, Allahu ya shige mana gaba ya raba ka da sharrin mahassada" Yace "Ameen 'Yar Aljannah zan tafi saina dawo" tace "d'umamen ma bazakaci ba?" Yace "zanci saina dawo insha Allah" Addu'ah ta 'kara mishi, dai dai da shigowar d'an aiken Jatau. Malam ya fita ya iske Jatau da jakunan shi biyu kamar yanda ya fad'a, cikin fara'a suka gaisa sannan ya umurci Mati da shima ya hau saman nashi jakin, hawa yayi sannan suka nufi garin shuni suna tafiya suna 'kara labarta sana'ar tasu. Sai la'asar lik'is suka dawo daga garin shuni da kaya ni'ki-nik'i, har 'kofar gida Jatau ya raka mati Abokinshi, ya sauka daga kan jakin shi ya kama mishi suka sauke kayan. Dai dai lokacin Kande ta fito innah ta aiketa, ta taho da murnarta zata tari mahaifinta, ganin tare yake da Jatau ta juya kawai kamar bata gansu ba. Cikin d'aga Murya mati yace "ke kande ki kiyaye ni kinji na fad'a miki, baki ganni da ba'ko ba zaki wuce baki gaisheshi ba? wallahi zan miki tsinannen duka ko ki kiyaye ni" kasancewar ita yarinya ce mai tarbiya ta dawo inda suke ko kallon shi batayi ba tace "ina yini", Murmushi yayi mai d'auke da ma'anoni kala kala sannan ya amsa da "lafiya lau Kande, sannu ya gida?" "Lafiya ya hanya?" Ta fad'a har yanzu bata ko d'aga kai ta kalle shi ba, ya wani washe ha'kora sannan ya amsa yana 'kara 'kare mata kallo, ko tsayawa batayi ya ida amsawa ba tayi tafiyar ta aiken innah. Yaci gaba da cewa "Ai mati lamarin yarannan ne sai ha'kuri, anma kande ai daman ba cika magana tayi ba" yana 'kara washe baki har lokacin yana kallon hanyar da kande tabi, mati Yace "Hakane Amininah, haka Kande take da miskilanci dama, sam bata d'auki hali na dana mahaifiyar ta ba, kayi hak'uri" "Uhmm! Babu komai aboki na, ai yarinya ce har yanzu bata gama mallakar hankalin kanta ba" Malam Mati yayi murmushi tare da fad'in "nagode sosai bari in shiga gida" Yace "to a gaida mutanen gidan saimun had'u gobe wurin sana'ar" yace "tohh zasuji. Tun a hanya Jatau keta sak'e sak'e a ran shi, yana tunanin tabbas yau ne ya kamata yayi duk abunda ya dace, murmushin mugunta yayi a daidai isar shi cikin gidan shi. Da shigar shi yaci karo da mata wasu na shiga wasu kuma suna fita, ya fara tunanin to me ya faru da har gidan shi yayi wannan cikar bayan tafiyar shi? Lallai akwai magana. Bayan ya shiga a daidai tsakar gida yaci karo da Malka unguwar zoma, gud'a ta rangad'a lokacin da taga Jatau ya shigo tare da matsowa inda yake tace "d'aga hannu ka godewa Allah, domin kuwa ya albarkace ka da jinjiri namiji bayan tafiyar ka", Da mamaki Jatau yace "wacece ta haihu? Dije ko Gaje?", "Dije ce ta haihu, itama Gajen nasan tana bisa hanya, kuma cikin iko da hikimar Allah yaron na nan lafiyayye ba kamar yanda ta saba haihuwar su kafin su rasu ba", Wani mayen murmushi yayi sannan ya shige d'akin sa, sosai yayi mamakin yanda akayi Dije ta haihu bai sani ba, gashi kuma ance yaron lafiyayye kuma namiji, Wani irin ihu yayi kafin ya saita kanshi kuma, a zahiri yace "na samu jinin da DODO na zaimin aiki yanzu kenan" fita yayi daga d'akin ya nufi k'aton rumbun shi wanda babu wanda ya tab'a ko lek'en sa, baya bari kowa ya shiga barin har asan abunda yake ciki, ko abinci ya k'are matsan shi babu wacce ta isa ta bud'e wannan rumbun da nufin ta shiga sai dai su jira har sai lokacin daya dawo sannan ya basu da kanshi. Shiga rumbun yayi ya d'ad'd'aga buhunnan hatsin dake ciki, da mamaki sai ga wani irin k'atuwar halitta abun tsoro a wurin, Take ya fara wasu saddabaru yana wani irin yare wanda shi kad'ai yasan abunda yake nufi, d'aga kanshi yayi ya saita idon shi akan 'yar k'aramar k'ofar rumbun, kurwar jinjirin da aka haifa masa ce ta ringa yawo a sama har ta shigo cikin rumbun, wata irin dariya yayi da k'arfin gaske tare da d'aga hannu ya cafko jinjirin ya rik'e shi, A daidai inda wannan halittar take ya jefa yaron da 'karfin gaske kamar ba mutum ba, aikuwa wannan halittar ta rik'e shi tam ta saka bakin ta a daidai inda kunnen yaron yake ta tsotse duk jinin shi har sai da ya k'are sannan ta barshi, Dariya Jatau yayi a karo na biyu tare da jefar da kurwar jinjirin shi. Jaririn yana hannun unguwar zoma ya ringa fizge fizge, sosai ta tsorata ta kira Dije ta gwada mata abunda yaron ta yake yi, suna cikin haka ne ran yaron ya fita, inda sabo Dije ta saba da mutuwar yaranta a duk lokacin data haihu, wannan ma yayi tsawon rai da har ya yini yana raye, amma da yake mutuwa bata da sabo wani irin kuka ya kufce mata ta rungume yaron tana kallon shi hawayen ta suna sauka akan jikin shi. *** Lokacin da kande ta dawo ta iske har Jatau mai sa'a ya tafi, taja tsoki tana k'ara jin haushin shi a ranta, tana shiga gida taji kanta ya wani irin sara mata, da sauri ta dafe kanta da yake barazanar fashewa, nan da nan jikin ta ya fara rawar sanyi bayan ya Ι—auki zafi, zazzab'i ya sauko mata da 'kyar take iya d'aga 'kafafunta jikinta yayi mata nauyi. Gidan da bata iya shiga ba kenan anan cikin soron gidan ta kwanta jikin ta na kwankwatsa wani irin zazzab'i takeji ga amai dake tuk'ar ta, nan da nan ta fara kwara amai har da gullamar jini ke fita daga bakin ta, take Kande ta fad'i sumammiya. Rerbee'art sk❤ AmrahπŸ’“ Zahra bbπŸ’• NAGARTA WRITERS ASSOCIATION [12/13/2016, 9:18 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 6⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Tun daga nan Kande bata k'ara ko motsi ba, sai faman ajiyar zuciya take ga idon ta a rufe tamkar bata numfashi ba. A hankali kurwar Kande ta fita daga jikin ta tayi sama ta ringa yawo sai dai babu mai ganin ta, bata zarce ko ina ba sai cikin rumbun Jatau mai sa'a ta same shi sai ambatan sunan ta yake yana fad'in "Kande! Ki iso gare ni!! Ki iso yanzu nace!!!" Koda ta iso kuwa wata irin dariya ya b'arke da ita yana kallon kurwar Kande har ta sauka k'asa da k'afafuwan ta, wasu tsubbace tsubbace ya ringa yi yana sujjada ga wannan k'atuwar halittar wadda ha ringa ambata da *DODO,* Saurin d'ago kanshi yayi tare da fad'in "a d'auko gangar jikin ta ya ke *MAI SA'A,* Cikin k'ank'anin lokaci gangar jikin Kande ta iso har cikin rumbun ya zamanto ga gangar jikin ta ga kurwar ta amma kurwar bata shiga jikin ta ba, K'ara duk'ar da kanshi yayi sannan yace "kar asha jinin ta *YA MAI SA'A,* zan gama koyar da ita hankali ne kafin ayi mata aiki, aci gaba da tsaron ta har sai lokacin da nace ayi mata aiki", Da k'arfi *DODON* ya saki wata irin gumza tare da sakin wani irin haske a daidai fuskar Kande, take kurwar ta ta koma jikin ta, A hankali ta fara tuno abubuwan da suka faru da ita har aman data ringa shek'awa, Bata gama mamaki ba sai da ta d'aura idon ta akan fuskar k'aton *DODON JATAU* wanda tunda uwar ta ta haife ta bata tab'a ganin abu koda mai kama dashi ba, Da k'arfi ta bud'e baki zata saki ihu amma *DODON JATAU* ya aika mata da wani iska wanda ya tsayar da bakin ta a bud'e, tayi k'ok'arin rufe shi amma ta kasa, Addu'a take neman ta karanto amma ina, ta nemi kanta da manta duk wani karatun Qur'ani a bakin ta, gashi kuma tama kasa rufe shi barin har tayi k'ok'arin tunowa. Kallon ta Jatau yayi sosai sannan ya fashe da dariya da k'arfi yace "Duk wanda yaci tuwo dani miya yasha Kande! Na kula da cewa ke kad'ai ce kika fara fahimtar abunda ke tsakani na da mahaifin ki saisa na miki haka, Zakici gaba da zama anan har k'arshen rayuwar ki, babu ke babu iyayen ki, keda farin ciki kunyi hannun riga ma'ana kowa da hanyar daya kalla, ke 'yar k'arama dake har kinsan cewa wai ba tsakani da Allah nake son baban ki ba? Yanzu ai sai inga ta inda zakici gaba da fad'in ra'ayin ki game dani barin har mahaifiyar ki ta fara yarda da maganar ki, nasan dai har abada mahaifin ki na gama dashi, bai isa yaja dani ba, duk abunda na fad'a masa shi zai ji" ya k'ara fashewa da dariyar cuta. Har yanzu k'ok'arin magana Kande take yi amma ta kasa sai hawaye dake fita a idon ta, ga wani irin tsoro da take ji, "yanzu kenan da gaske na rabu da Innah da Baba? Na rabu da Talle, Baseeru da Audu? 'Yan uwana masu k'auna ta, masu son ganin farin cikina, kenan da gaske Jatau mai sa'a shi ya kashe min 'yar uwata Aisha?" A zuci tayi maganar amma bata san ta fito bayyane ba. "Hahahahahaha! Ni na kashe miki 'yar uwar ki, mahaifin ki yazo da ita har nan gidan kuma *DODO* na ya nunar min da yana sha'awar shan jinin ta, kin san irin nasarar dana samu da jinin Aisha kuwa? Na samu dukiya mai yawa, na samu d'aukaka sosai, na k'ara kashe bakin baban ki da jinin 'yar sa, har yau har gobe babu wanda zai san ni na kashe Aisha, kuma ina mai tabbatar miki cewa na kashe bakin kowa naki, babu wanda zai k'ara tunanin ki a doron k'asa barin har ayi tunanin inda kike, k'wara ma tun wuri ki cire duk wani tunanin gida da 'yan gida a ranki dan kin rabu dasu kenan har abada" ya k'arisa maganar fuskar sa d'aure kamar ba shine ya gama kwasar dariya ba. Wasu abubuwa ya k'uk'k'ulle a k'ananan ledoji har guda biyar, D'aya bayan d'aya ya ringa jefa su waje har sai da ya gama duka, Ta farkon daya jefa ta sauka akan k'irjin malam Mati, ta biyun kuma ta sauka a k'irjin Larai, ta uku a k'irjin Talle, ta hud'u a k'irjin Baseeru, da k'arshen kuma ta sauka a gefen k'irjin Audu, bata sauka a daidai bisa k'irjin ba, Sam Jatau bai kula da cewa k'ullin bai sauka a daidai k'irjin Audu ba. Bayan ya gama duka ya kwashe da dariya sannan ya duk'a yayi wa DODON shi sujjada ya miyar da buhunnan komai sannan ya fita (wal-iyadhu billahi). TUSHEN LABARI. Rerbee'art sk❤ AmrahπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/14/2016, 10:36 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 7⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Zuri'ar malam Na Sidi zuri'ah ce albarkatacciya kuma sananniya a cikin k'auyen Bagu dake k'ark'ashin garin Illaila cikin jihar Sokoto, Malam Na Sidi mutum ne na gari kuma sananne a halaye na gari, Yana da mata biyu Wasilah da Laritu, sun kasance masu had'in kai a tsakanin su, babu wanda zaice ga ranar da aka gansu suna fad'a, Wasila itace babba tana da yaro d'aya mai suna Muhammadu suna kiran shi da Na Allah, Tunda ta haife shi sai haihuwar ta d'auke mata bata sake haihuwa ba, tun abun yana damun ta har ya daina damun ta saboda mijin ta yana kwantar mata da hankali a koda yaushe, haka Laritu ma kullum tana k'ok'arin kwantar wa kishiyar ta da hankali. Laritu itace k'arama kuma ita keda yara da yawa, Ta fara haihuwar Saratu, sai Hansai, sai Talatu sannan ta haifi Sani suna kiran sa da Mati saboda ya fito a cikin mata sannan ta sake haihuwar 'yan biyu suma duka mata, Zaune suke zama mai cike da ban sha'awa da walwala, Mati ya taso cikin so da k'aunar iyayen shi, Mahaifin su Malam Na Sidi yana sana'ar sayar da fata, ya taso da ita tun iyaye da kakanni, Haka kuma Na'Allah ya taso da sana'ar mahaifin shi ta sayar da fata tun yana k'arami har ya girma, Shi kuwa Mati sam baya sha'awar wannan sana'ar, babban burin shi a rayuwa bai wuce ya ganshi ya zama mai sana'ar jima ba, Tun lokacin daya tashi ya nunar da sana'ar da yake so baban shi bai hana shi ba saboda shi ya kasance mai son farantawa yaran sa, Haka rayuwar su taci gaba da tafiya har lokacin da Malam Na Sidi ya kwanta damar sa, Kasantuwar ya had'a kawunan iyalin shi yasa suka ci gaba da tafiya a haka, kaf mutanen gari suna sha'awar yanda rayuwar su take kamar ba kishiyoyi ba, Bayan rasuwar baban su da shekara biyar ne Mati ya fara neman aure a lokacin yaya Na'Allah yayi aure har ya haifi yara biyu, Ya fara neman auren Larai take ta aminta da soyayyar shi, sai dai kuma kash! Baabah Haja ta tsane shi bata k'aunar shi, ba dan komai ba sai dan wata muguwar gaba da kakannin su sukayi a shekarun baya, Baabah Haja kakar Larai ce ita ta rik'e ta bayan rasuwar iyayen ta, Bata tashi tasan kowa ba sai Baabah Haja hakan yasa take matuk'ar k'aunar ta, A lokacin da Larai ta bijiro da tana son ta auri Mati sosai Baabah Haja ranta ya b'aci, Tace sam bata aminta da wannan auren ba, hakan yasa Larai ta miyar da kuka abincin ta, Kullum ta zauna sai kuka saboda Baabah Haja ta dage akan Mati ba zai auri Larai ba, Shi kanshi kullum ya zaune bashi da walwala sai kuka ya rasa yanda zayyi, Ganin kuka bazai zamar masu mafita ba yasa Larai ta yanke hukuncin zuwa wurin yayan kakar ta Malam Sa'idu, koda takai masa kukan ta ya ajiye hankali ya fahimce ta, Da farko shima bai amince ba saboda yasan muguwar gabar dake tsakanin kakannin su, amma daga baya ya goyi bayan ta saboda komai ya riga da ya wuce, Da k'yar malam Sa'idu ya shawo kan Baabah Haja ta amince da auren Mati da Larai amma da sharad'in kar Larai ta kuskura ta kawo mata koken ta game da mijin ta Mati, Larai taji dad'i sosai ta kuma amince da wannan sharad'in, Cikin kwanaki kad'an akayi auren Mati da Larai. Bayan shekara d'aya da auren su Larai ta haifi d'anta namiji mai suna Na Sidi (baban Mati) suke kiran sa da Talle, Talle yana samun soyayya sosai daga wurin kakkannin shi na wurin uba, dan kuwa Wasila yanda take kula dashi tamkar itace ta haifi Mati d'in, Baabah Haja kuwa ko kallon inda Talle yake bata yi, koda Larai taje gida sai dai ta gaji tayi tafiyar ta dan ko kallon su Baabah Haja bata yi. Mati nada shekara d'aya ciwon ajaliyya ya kama Laritu, kwana biyu da fara ciwon Allah ya d'auki rayuwar ta, Tsabar shak'uwar dake tsakanin Laritu da wasila yasa itama wasilar ta kama ciwon zuciya, watan ta uku tana jinya itama rai yayi halin sa. Iyalan Na Sidi sun shiga tsantsar tashin hankali, sai a lokacin suke jin mutuwar iyayen su d'anya shakaf kamar a lokacin ne Malam Na Sidi da Laritu suma suka rasu, Sun jima suna jimamin rashin iyayen su kafin daga baya suka dayaye sukaci gaba da yiwa iyayen su addu'ah. Haka Larai taci gaba da zubawa Mati zuri'ah har sai da ta haifi yara biyar sannan haihuwar ta tsaya, a lokacin Yaya Na'Allah yana da yara goma a duniya, Har yanzu dai zumuncin su yana nan bai yanke ba, sai yanzu da yaya Na'Allah ya auro wata muguwar mata mai suna Juma, Tun shigowar Juma zuri'ar yaya Na'Allah ta kashe masu duk wata walwala, ta tsani ganin Mati yazo wurin d'an uwan shi, a duk lokacin da Mati yazo gidan sai Juma ta tsira wani munafurcin da Yaya Na'Allah zaiji haushin Mati. Muje zuwa dai, Gobe insha Allahu zakuji asalin *DODON JATAU* da kuma mugayen abubuwan daya aikata tun baya har zuwa wannan lokacin. Rerbee'art sk❤ AmrahπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/16/2016, 10:30 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 8⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Sunan shi na yanka kenan JATAU, sunan mahaifin shi Mani, mahaifiyar shi kuma Salamatu, Mani da Salamatu auren had'i akayi masu ba tare da sun san junan su ba, Hakan ya samo asali ne a al'adar k'auyen su, uba ne kawai yake nema ma d'an sa aure a wurin abokin shi ko wani makusancin shi, wato auren ladar noma, Yaro baya sanin matar da zai aura har sai lokacin da aka d'aura auren su, Haka itama macen bata sanin mijin da zata aura har sai taje gidan shi, Hakan ne ya kasance tsakanin Mani da Salamatu, duk da had'in da aka masu bai sa sun k'i al'adar garin su tun iyaye da kakanni ba, Bayan an kai amarya ne Mani ya ga Salamatu itama ta ganshi, take suka aminta da junan su duk da basu tab'a sanin juna ba, Haka rayuwar auren su taci gaba da tafiya cike da soyayya da k'aunar juna, Shekarar su biyu da aure amma har yanzu Salamatu bata samu haihuwa ba, hakan kuma bai sa Mani yaji raguwa ko kad'an a soyayyar da yakewa matar sa ba, A cikin shekara ta uku ne Allah ya albarkaci Salamatu da juna biyu, sunyi farin ciki sosai da wannan al'amarin, daren ranar basu samu bacci ba sai farin ciki da suke yi, Salamatu tayita Sallah tana godiya ga Allah, inda Mani kuma ya ringa washe hak'ora yana kallon ta tana sallah, Tayi k'ok'arin saka shi yayi sallar shima dan ya godewa Allah amma yak'i, kasantuwar tasan halin mijin ta dama can ibada bata dame shi ba yasa ta hak'ura ta k'yale shi, Ko sallar farillah ma sai yaga dama yake yin ta barin yayi ta nafilah, Washe gari ya ringa sanar wa mutane kyautar da Allah ya masu, kowa na taya shi farin ciki. Wata tara cif da samun cikin ta ta fara nak'uda, Cike da tashin hankali Mani yaje ya kira Timba unguwar zoma tazo, Ganin an d'auki tsawon lokaci Salamatu bata haihu ba yasa hankalin Timba ya tashi sosai, Fita tayi ta kira k'awayen ungozomancin ta domin su taimaka mata, dan wannan al'amarin yafi k'arfin ta, tana ganin yanda Salamatu ke wahala amma har yanzu ko kan yaro yak'i fita. Taimakon ta sauran matan suka fara amma duk da haka babu wani ci gaba, Wata tsohuwa mai suna Laraba tace "kiyi yunk'uri 'yar nan, ga alamar kai nan zai fito" Yunk'uri Salamatu tayi da k'arfi sai ga kan yaro ya fito, hannu Laraba tasa ta k'arisa jawo jinjirin. Sannu kawai suke mata ita kuwa iya galabaita ta galabaita, Wata sabuwar nak'udar Salamatu taci gaba dayi ashe akwai sauran jinjirin a ciki, hakan yasa Laraba ta k'ara cewa "Daure ki k'ara yunk'uri da k'arfi Salamatu, sannu kinji?", Kasantuwar babu sauran k'arfi a tare da Salamatu yasa har yunk'urin ta kasa yi, Ga d'ayan jinjiri a hannun Timba sai tsala kuka yake yana wawurar hannun Timba alamar ya fito da yunwa ne. "Har yanzu Salamatu yarinya ce Laraba, duka fa bana zata cike shekara sha hud'u a duniya, kinga kenan komai a hankali zai ringa fitowa, kuma sai gashi 'yan biyu ta fara dasu, naji tausayin ta sosai Allah dai ya sauke ta lafiya" wata unguwar zoma mai suna Asabe ta fad'a cike da tausayi. _(wannan bayanin dana kawo gaskiya ne, domin kuwa aurar da yaro da wuri babu abunda baya haifarwa, shine yake saka ciwon yoyon fitsari a k'arshe azo ayita fama da ciwo, wasu ma har su mutu da cutar basu warke ba musamman ma mutanen mu na k'auye, auren wuri baya k'aruwar mu da komai face cutar da iyalan mu, ya kamata mu sani cewa mutanen da dana yanzu ba d'aya bane, mutanen da suna bin mata a hankali ne yayin saduwa dasu, wasu ma basa kusantar matan su a lokacin har sai sun k'ara mallakar hankalin su, sab'anin mutanen yanzu da kema matan su ta k'arfi da yaji har su illata su, karshe azo wurin haihuwa ayita fama, ba kuma ina nufin ak'i aurar da yara cikin lokaci bane, ina nufin a bar su har sai lokacin da suka kai shekara sha shida zuwa sha bakwai sannan a aurar dasu. Ga masu k'in zuwa asibiti kuma ya kamata mu kiyaye, yanzu muna kan wani zamani da sai da taimakon malamin asibiti a kowane lokaci, ya kamata a duk lokacin da mai ciki taji alamar nak'uda tayi k'ok'arin garzayawa zuwa asibiti domin karb'ar haihuwar ta, haihuwa a gida babbar matsala ce a wannan lokacin, saboda su kansu unguwar zoman na yanzu wasu basu k'ware da karb'ar haihuwar ba, mu kuma mata sai mu dage da cewa lallai mu bazamu tafi asibiti ba. Allah yasa mu d'auki wannan shawarar, Allah kuma ya had'a mu da mazaje masu tausayin mu). Haka Salamatu ta gama galabaita amma d'ayan jinjiri yak'i fitowa, in banda hawaye babu abunda take yi, Tun suna shiru har takai ga su dukan su kuka suke yi, Ganin haka bazai masu ba ga Salamatu sai sabbatu take tana fad'in "ku kira min Mani in rok'i gafarar shi, nasan tawa ta k'are mutuwa zanyi, ku kira min shi". Cike da tashin hankali Timba ta fita, ta samu Mani a k'ofar gida zaune shi da abokin shi Sani, Saurin mik'ewa yayi lokacin da yaga Timba ta fito, Ganin Timba na kuka yasa hankali tashe yace "Baba Timba me ya faru? Lafiya na ganki kina kuka? Salamatun ta haihu ne? Ki fad'a min me ya faru?", Kasa fad'a mishi komai tayi face komawa baya da tayi ta shiga gida, ganin haka yasa shima yabi bayan ta cikin razana har suka isa bakin d'akin, Sosia hankalin shi ya tashi jin sabbatun da take yi, Saurin shiga yayi ya rungume ta duk da jinin dake malala daga jikin ta, "Ka...kakkk...ka yafe min Mani, nasan tawa ta k'are, ga amanar yaro na nan, ina so ka saka masa sunan baba na Jatau, ka rik'e shi da amana, ka kasance mai faranta masa rai, kar ka zalunce shi saboda amana ce a gare ka, ka kasance mai yi masa duk abunda yake so" tana gama fad'in haka tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya. Da k'yar ta samu taci gaba da fad'in "Mani dan Allah kar ka auri wadda zata cutar da Jatau, Mani wani irin abu nake ji wanda ban tab'a jin sa ba tunda nake a duniya, Mani..." bata k'arisa maganar ba mala'ikan zarar rai ya ziyarce ta, take kuwa aka zare rayuwar Salamatu. Wani irin kuka Mani ya fashe dashi da k'arfi kamar k'aramin yaro "Kar ki mutu ki barni Salamatu, bazan iya rayuwa babu ke ba, na miki alk'awarin zan kula da Jatau, zan masa duk abunda yake so, ko ta wace hanya ce zanbi dan ganin na cika miki alk'awari na kula da Jatau" ya k'ara fashewa da kuka, Da k'yar su Timba suka rarrashe shi ya fita ya fad'awa mutane, babu b'ata lokaci aka sallaci Salamatu aka kaita tabbataccen gidan ta. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/17/2016, 10:17 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 9⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Tun bayan rasuwar Salamatu Mani bai sake samun farin ciki ba, Kullum ya zauna sai faman kuka da tunane tunanen yanda sukayi rayuwa tun farkon auren su har izuwa samun cikin ta, Ga kuma amanar d'an su Jatau data damk'a masa, a duk duniya burin sa bai wuce yaga ya farantawa tilon d'an sa Jatau rai ba, Burin shi yaga ya kyautata masa, kwata kwata ya cire aure a ran sa, ya riya ma ranshi cewa ya gama aure har abada sai a lahira idan anayi, a lahirar ma yana fatan a had'a shi da matar shi Salamatu. Zaune yake kamar kullum yana shayar da Jatau koko a hankali yana sha yana dariya dan yanzu har ya fara dariya da k'arfi, Shima Manin biye masa yayi sukaci gaba da dariyar suna wasa shima ya zama kamar k'aramin yaron, yanzu Jatau yana da wata hud'u kenan kuma yayi b'ul b'ul abun shi kamar d'an shekara d'aya, duk wanda ya ganshi zayyi tunanin mahaifiyar shi tana raye, babu wanda zaice baisha nonon mahaifiyar shi ba. Kwanaki na tafiya lokaci na gudu yau gashi har Jatau ya cika shekara biyar a duniya, Yaro yayi mul mul abunshi sai dai bak'i ne sosai mummuna kamar baban shi, sam bayyi fuskar mahaifiyar shi ba da yayi kyau. Jatau ya zama sangartaccen yaro sam Mani baya masa fad'a koda abunda ba daidai bane yayi, babban burin shi bai wuce yaga ya farantawa Jatau rai ba, Duk abunda Jatau keso komai munin shi sai ya masa shi, Gashi da rashin kunya da d'aukar magana, idan wani wuri sukaje yaga yara ya ringa cizon su kenan yana fasa masu fata, koda iyayen yaran sun fad'awa Mani baya d'aukar wani mataki sai hak'uri da yake bayarwa. Komai talaucin da Mani yake yi idan Jatau ya nunar masa da yana son wani abu dole sai ya nemi kud'i ya siya masa shi, Jatau har baban nashi ma bai k'yale ba rashin kunya yake masa, zagi kuwa ta uwa ta uba yake bin Mani dashi, Sam Mani bai nunar ma Jatau da ilimin addini ba, ko kalma d'aya data shafi addini Jatau bai sani ba barin ace ya koya masa sallah, Duk dangin shi ya guje su kawai dan suna fad'a masa gaskiya game da Jatau, ce masu yake suna masa bak'in ciki da tilon d'an sa ne. Yau ta kasance Laraba ranar kasuwar k'auyen su, Mani ne tafe ya goya Jatau a bayan shi suna tafiya suna fira Jatau na kawo masa gulmammkin mak'otan su shi kuwa fad'in yake "ka barni dasu duk sai na zane su tunda su basu da tausayi", Wani irin dad'i Jatau yaji saboda idan ya kai k'arar wasu wurin baban shi yaji zai d'auki mataki wani irin dad'i yake ji. Cikin kasuwar suka shiga Mani ya fara da rumfar abokin shi Shamsu mai gyad'a, Bayan sun gaisa ne Mani yace "yau kawai yawon zumunci muka fito nida d'ana Jatau, shine nace bari mu fara da rumfar ka", Sosai Shamsu yaji dad'i, Mani ya zauna sukaci gaba da fira sosai kafin ya tashi yace "to zamu tafi aboki na sai wata rana kuma", Leda Shamsu ya d'auka ya zuba gyad'a soyayya mai yawa ya mik'awa Jatau a hannu yace "ga wannan Jatau, aje aci" Da yake Jatau baida tarbiyya bai iya godiya ba kawai karb'a yayi sannan suka k'arisa shiga cikin kasuwar. Haka suka ringa zuwa rumfa rumfa ana ma Jatau kyauta har da cefane, Daga k'arshe suka tafi rumfar Sada mai nama, Bayan sun gaisa ne Mani yace kawai sunzo zumunci ne, Cikin farin ciki Sada ya d'auko kan akuya wanda aka babbake yace "Mani ga wannan aje a dafa ma Jatau yasha da romo", Murmushi Mani yayi yace "aikuwa Jatau ya gode aboki na, Allah yabar zumunci" suka kama hanyar gida saboda har yamma tayi. Da komawar su gida Mani ya wanke naman kan sosai sannan ya jajjaga cefanen da Garba mai cefane ya bashi, d'ora naman yayi a tukunya ya saka d'and'anon gishiri ya hau dafa shi. Wuraren k'arfe tara na dare naman ya dahu sosai, a lokacin har Jatau yayi bacci, sauke naman Mani yayi ya rufe saboda baya son ya tashi Jatau daga baccin da yake wanda da alama yana matuk'ar jin dad'in shi. Washe gari da wuri Jatau ya tashi, babu sallah babu wanke ido Mani ya d'umama naman suka fara ci, Sai da sukaci sosai sannan Mani yace "mu ajiye wannan sai anjima ko gobe mu k'arisa cinye shi dan da alama ka k'oshi, kuma yau kasuwar Shuni akwai wanda zan gani k'ila ma acan zamu kwana". Cike da farin ciki Jatau ya tashi yace "yauwa baba, dama ina shon juwa galin nan, wannan abokin naka yana bani kayan dati", Dariya Mani yayi yace "to bari in maka wanka sai mu tafi". Wanka yayi masa cikin lokaci kad'an ya shirya shi, sauran naman ya juye a wani kwano mai marfi ya tura shi k'ark'ashin gado sannan suka kama hanyar Shuni. Kwanan su biyu a garin Shuni basu dawo ba, a hanyar dawowar ma basu zarce gida ba wani k'auye suka tafi sai da sukayi kwana biyar sannan suka dawo gida. Naman da Mani da Jatau suka manta dashi a k'ark'ashin gado kenan har yau shekara biyu da watanni da ajiyar naman kan. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/18/2016, 9:37 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 1⃣0⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 *AYI HAK'URI DUK JIYA BAMUYI POSTING BA, WANI DALILI NE BABBA YA HANA, AMMA YAU INSHA ALLAHU ZAKU SAMU DA YAWA* ************ A yanzu Jatau nada shekara bakwai da watanni kenan a duniya, a lokacin kuma Jatau nada buk'atar taimakon mace, hakan yasa Mani ya fara tunanin neman aure domin neman wadda zata taimakawa d'ansa Jatau. Wurin abokin shi Sani yaje ya fad'a masa cewa shi fa yana son zayyi aure, ba kuma auren soyayya yake so yayi ba, kawai dai zayyi ne saboda ya samu mai taimakon d'ansa Jatau, Sani yace "indan wannan ne me sauk'i kenan, akwai wata 'yar uwata bazawara, mijinta rasuwa yayi yana tafiya akan jaki aka soke shi da kibiya, ta gama takaba tuntuni kuma har yanzu babu manemi, idan har kana da sha'awarta zanje mata da maganar anjima idan Allah ya nuna mana". "Ehh to, duk yanda take bazan k'i ta ba, saboda nasan bazaka tab'a yi min zab'en banza ba, nidai buri na ta zama ta gari wacce zata rik'e min amanar d'ana Jatau, shi kad'ai gare ni saisa ma kaga tuntuni ban nemi aure ba dan bana son na auri wadda sata takura masa", "Kar ka damu Mani aboki na, Talatu nada kirki da tausayi, ina da yak'inin zata rik'e Jatau tamkar d'anta na cikin ta, zata rik'e maka amana sosai", "Yauwa aboki na, haka nake son ji, anjima sai kaje mata da maganar, duk yanda kukayi sai mu had'u bakin majalissar mu, amma fa aboki na kar ka manta kayi mata bayanin Jatau, dan wallahi duk yanda nake da mutum komai son da nake masa kar yayi kuskuren tab'a Jatau, kaga da dama na b'ata da 'yan uwana saboda Jatau, ko fad'a bana masa dan kar ranshi ya b'aci", "Duk nasan da wannan Mani, yanda ka fad'a d'in duk haka za'ayi". Da haka suka rabu Mani ya koma gida ya tayar Jatau ya tashi daga bacci sai kuka yake wai baban shi ya tafi ya barshi shi kad'ai. Da k'yar ya samu ya rarrashe shi yayi shiru da sharad'in bazai sake tafiya wani wuri ya barshi ba. Mani da Talatu sun daidaita kansu, ta kuma yarda da duk wasu sharud'd'an shi, An tsayar da ranar aure nan da sati biyu masu zuwa, Hakan yasa Mani ya fara 'yan gyare gyaren tarbar amarya, Kayan d'akin shi ya fara fiddowa dan yau za'a fara shafen d'akin a shafa farar k'asa, yana so amaryar shi tazo taga gidan shi da kyau. Ya fitar da komai daga d'akin gado ne kawai ya rage, Jatau kam tsaye yake yana kallon shi dan bai iya aikin komai ba, Langa langar katifar kan gadon ya fara saukewa ya fita waje sannan ya fara raba gadon, Kayakin k'ark'ashin gadon ya fara fitarwa a hankali yaci karo da murfin kwano k'asa, Janyo shi yayi sannan ya fara k'ok'arin fiddo kwanon ma, Da mamaki yaji kwanon yak'i tafiya, yayi yayi amma yak'i tafiya, Hankalin shi tashe ya janye gadon ya zamanto fili ne kawai yanzu, Da mamaki sai ga wata irin k'atuwar halitta a cikin kwanon ta kunno kai, Bak'ik'irin da ita da ido d'aya amma k'atuwar gaske ce dan har kwanon ma ya mata kad'an, daga k'ugunta ne kawai ke cikin kwanon sauran ta duk waje take. Cike da fargaba Mani yake kallon wannan al'amarin, shi bai gudu ba bai kuma tab'a ta ba, Ga halittar ta tsura mashi ido sai kallo take tana fiddo harshe waje. Tsoro fal a ranshi ya fita, dauk'ar Jatau yayi yana gudu gudu sauri sauri, basu zarce ko ina ba sai wurin boka Zul-za'u (boka Zul-za'u wani mashahurin boka ne wanda 'yan k'auyen suka yarda dashi, duk wata matsala da zata tasowa 'yan garin wurin shi suke zuwa, sun yarda dashi sosai domin yana biya masu buk'atun su, boka Zul-za'u baya k'arya a cewar su, shahararre ne saboda har k'auyukan dake mak'waftaka dasu suna kai masa ziyara, hakan yasa Mani ma ya yanke hukuncin tafiya wurin boka Zul-za'u dan yana da tabbacin shi kad'ai yasan ko menene a ka'rk'ashin gadon shi). Da zuwan shi ya samu akwai layi sosai, haka ya daure duk da cike yake da tsoro har layi yazo kanshi, Tare ya shiga da Jatau d'auke a kafad'ar shi yana k'ok'arin yin bacci, Bai zauna ba har saida bokan ya bashi izinin zama, A tsawace yace mashi "waya fad'a maka ana zo mana da yara? Ka fita dashi sannan aljannu zasu saurare ka", Kallon shi Jatau yayi cike da tsoro yace "baba waye wannan muka zo wurin shi?", "Abokina ne Jatau d'ana, ka kwantar da hankalin ka, zan kaika waje ka zauna kafin in fito". Dad'i sosai Jatau yaji saboda shikam tsoron wannan bokan yake, Wajen kuwa ya kaishi ya ajiye sannan ya dawo ciki ya zauna kusa da boka. "Nasan abunda yake tafe da kai, wata bak'ar halitta ce ka gani a d'akin ka, baka san asalinta ba shine kazo na maka bayanin ta idan na sani, koba haka bane?!" Jiki na rawa Mani yace "hakane boka". Dariya ya fasa da k'arfi yace "arzik'in ka ne! Arzik'in ka ne idan kaso Mani!!", Cikin mamaki Mani yace "arzik'i na kuma boka? Ban santa bafa, ban san daga ina take ba, haka kawai na ganta k'ark'ashin gado na". "Kai ka kawo ta da kanka ba wani ya kawo ta ba, ba kuma ita ta kawo kanta ba". Wata k'warya dake gefen shi ya jawo ta dawo gaban shi, yayi wasu tofe tofe a ciki tare da wasu saddabaru ya murza wani gari a cikin k'waryar sai ga wannan halittar da Mani ya gani a d'akin shi ta b'ullo. Wani irin tsoro ne ya ziyarci Mani, kallon boka yayi sannan ya sake miyar da kallon shi ga k'waryar. "Ka ajiye hankalin ka zata maka bayani da kanta yanzu" bokan ya fad'a yana k'ara kallon k'waryar yana saddabarun shi da shi kad'ai yasan abunda yake fad'a yana tottofawa ciki. Cikin wata irin k'ara da k'arfi halittar ta fara magana "kimanin shekara biyu da suka wuce kayi ajiyar naman kai a cikin wani kwano ka rufe ka tura shi k'ark'ashin gado, tun daga ranar kayi tafiya ta kwanaki da yawa, bayan ka dawo kuma ka manta da kayi ajiyar naman kai, A hankali naman ya fara rub'ewa har ya zama tsutsotsi, d'aya bayan d'aya suka fara cin junan su suna cin junan su da haka har suka zama k'atuwa guda d'aya, Wannan k'atuwar d'aya itace ta zama *DODO* wato ni, Idan ka miyar da hankalin ka gare ni zan maka duk abunda kake so na rayuwa, Zan baka arzik'i koma wane iri kake so, zaka zama mai sa'a a rayuwar ka, saboda duk wani abu daka tab'a sai ya zama naka, Amma akwai sharud'd'an hakan, Zaka ringa bani jini ina sha, ina nufin jini koma wane iri ne, na kaza, akuya har izuwa shanuwa, Amma ka sani, akwai minzalin da za'a kai wanda jinin dabbobi bazai ishe ni ba sai an k'ara min dana mutum, inhar ka amince da wannan sharud'd'a to na zama taka, sannan kar ka fitar da wannan sirrin ya zama tsakani na da kai ne kawai sai kuma d'anka Jatau dan kune kad'ai kuka ganni" ta k'arisa maganar da wata irin kuwwa wadda har Mani d'in saida ya tsorata. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/18/2016, 3:00 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 1⃣1⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Izini boka Zul-za'u ya masu dasu tafi ya gama dasu, "To boka ya zanyi da DODO na? A haka zan tafi dashi cikin k'waryar ko kuwa?", "Kai kazo da ita ne dama?" Bokan ya fad'a cike da tsawa, "A'a bani nazo da ita ba ya boka, kai ka kira ta", "To ka tafi ka barta, da kanta zata koma gida, kuma ina mai shawartar ka da karka fad'awa kowa d'in kamar yanda ta maka gargad'i, duk ranar da asirin ka ya tonu to fa komai zai iya faruwa, ka koyar da yaron ka yanda zai mata ladabi, yanda zai kula da ita yanda ko bayan ranka zataci gaba da bashi duk abunda yake so", "To boka, yanda kace d'in haka za'ayi, nawane kud'in duba?", "Ka tafi kawai anbar maka, kai abokin kasuwanci ne ai", "Godiya nake boka Zul-za'u, sai anjima". Mik'ewa yayi ya fita waje, ya samu Jatau sai sharar baccin shi yake a k'asa, Tausayin shi ne ya kama shi sosai ya d'auke shi ya goya a bayan shi. A hanya yake ta sak'e sak'e a ranshi, "Lallai ya kamata in janye maganar auren nan, saboda matuk'ar nayi aure to asiri na zai iya tonuwa, gashi kuma ance kar mu bari kowa ya sani, Yanzu ne lokacin da zan b'arje gumi na, Zan kyautatawa d'ana Jatau, zan cika alk'awarin dana d'aukar ma Matata Salamatu cewa zan farantawa Jatau, Jatau d'ana sai abunda kake so, zan maka komai domin ganin ranka yayi fari, Zan iya kashe mutum saboda in faranta maka rai" da wannan zancen zucin ya isa gida. Yanda yabar gidan haka ya same shi, Sai dai DODON shi ya miyar da kanshi ya dunk'ule cikin kwanon dan kar wani ya shigo. Kayakin shi ya hau miyarwa yanda komai yake a baya, Ya d'auki kwanon DODON shi ya tura k'ark'ashin gado sannan ya kwanta shima domin ya huta, Cike da farin ciki bacci ya d'auke shi, yau kam burin shi zai cika, Gashi zayyi kud'i har zai iya zarce kowa dake k'auyen dukiya, in kau haka ta kasance da yafi kowa farin ciki. *BAYAN SHEKARA GOMA.* Abubuwa da dama sun faru a cikin wannan shekarun, ciki kuwa har da bunk'asar da Mani yayi a bautar DODON shi, Babu ruwan shi da ibada kwata kwata, kullum sai bautar DODO, Tun mutane na tuhumar shi inda ya samu dukiya har sun gaji sun daina, domin kuwa Mani ya zama shahararren mai dukiya, duk k'auyen su babu mai dukiyar shi, Kullum sai yayi ma DODON shi yanka ya bashi jinin sannan ya tona rami ya bunne naman, Jatau kuwa ya k'ara girma sosai ya zama saurayi cikakke, Babu ruwan Jatau da ibada ko d'aya, Sai rainin wayo daya d'aukarwa kanshi, musamman ma yanzu da yake ganin babanshi ya zama mai kud'i a cikin k'auyen. Jatau kad'ai yasan sirrin mahaifin shi, wani lokacin ma tare suke shiga cikin d'akin da Mani ya gina musamman saboda DODON shi. Yau ta kasance ranar talata ce, tun da safe Mani ya farka daga bacci saboda mafarkin da yayi wanda kuma bayyi mamakin shi ba dan dama Dodon shi ya fad'a masa hakan, Da tashin shi yaga Jatau na shirin shiga wanka har ya cire kayan shi ya zama daga shi sai gajeren wando, Cikin damuwa Mani yace "Jatau, zo ka zauna anan", "Nifa Baba gaskiya wanka zanyi sai na fito" Jatau ya fad'a cikin rashin ladabi. "Na rok'e ka Jatau kazo ka zauna anan, akwai matsala ne", Ba dan yana so ba ya zauna amma fuskar nan tashi d'aure tamau ya duk'ar da kanshi k'asa. "Jatau akwai babbar matsala ne, jiya da dare Dodo ya sanar dani cewa na kusa mutuwa, amma ganin na shiga kokonto yasa ya bani wani gari na shafe jiki na dashi, yace inhar nayi mafarkin mutuwa to tabbas na kusa mutuwa, na tambaya yaushe ne zan mutu amma tace itama kanta bata san tak'amaimai ranar ba, ta dai san kawai na kusa mutuwa, Saisa na kira ka domin muyi wannan maganar, Tabbas Jatau mutuwa zanyi, ina so ko bayan rai na *KA D'AUKI DODONA YA ZAMA NAKA,* ya zama sirri daga kai sai zuciyar ka, Akwai had'arin gaske idan ka bari wani yasan wannan maganar, Duk yanda kake da mutum kar ka fad'a masa sirrin ka, Sannan kuma bazan hana ka aure ba, kayi aure idan kana da ra'ayi amma fa ka kula Jatau, Ko matar ka kar ka bari tasan da ajiyar Dodon nan, Zai baka duk abunda kake so na rayuwa, Zaka zama abun alfahari a cikin k'auyen nan kai har ma da wasu k'auyukan, Zaka samu sa'a a rayuwar ka duk inda ka shiga kaji ana fad'in *"GA JATAU MAI SA'A",* Ka kula da kyau Jatau, daga yau Dodo ya tashi daga nawa ya koma *DODON JATAU,* Ka ringa shayar dashi da jini, kaga dai yanda nake masa bana barin shi da yunwa, Kai idan ma ka samu jinin mutum ka bashi kaga kud'in da zakayi, Zaka kashe bakin kowa dake garin nan, kowa zaina jin tsoron ka, Duk maganar daka fad'i ita za'aji komai girman mutum". Duk da rashin tausayin Jatau sai da yayi kuka, dan ganin yake idan ya rasa baban shi tamkar ya rasa komai ne na rayuwa, dama dashi kad'ai ya tashi, bai san kowa ba bayan shi, sai ko babban abokin shi Mati, Yana ji da Mati sosai yana kyautata mashi, Duk da banbancin halayya a tsakanin su amma Jatau yana k'aunar Mati, wani lokacin Baban Mati har korar Jatau yake idan yazo wurin Mati d'in amma hakan bai sa shi yayi zuciya ya daina zuwa, da haka har ya gaji ya k'yale shi dan ya kula had'uwar jini ce kawai tsakanin su. Bayan sati biyu kuwa Mani ya mutu kamar yanda yasan dama ya kusa mutuwar, Jatau yasha kuka sosai na rasuwar baban shi, Mati ne kawai ke rarrashin shi amma hakan bai sa yayi shiru ba, Sai da Mani yayi sati d'aya da mutuwa sannan JATAU ya samu ya dayaye har yama samu damar tunawa da Dodon shi, Suna zaune da Mati yace "Mati ka tafi gida kawai dare yayi, bana so baban ka yayi maka fad'a kayi dare", "Hmm! Aboki na Jatau kenan, babana ya hak'ura ya barni dakai, yace tunda yanzu kai kad'ai ne in ringa zama ina d'ebe maka kewa sai dare sannan in koma gida, kar ka damu aboki na", Wani iri Jatau yaji saboda yana so Mati ya tafi dan ya ziyarci Dodon shi, amma haka ya hak'ura har Mati d'in ya tafi sannan yaje d'akin DODO. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/18/2016, 7:06 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 1⃣2⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Da shigar Jatau d'akin kuwa yaci karo da Dodon shi kwance ya galabaita, Cikin tsananin tausayin dodon nashi yace "Ka gafarce ni ya Dodo na, ina cike da kewar rashin baba na ne, tsananin damuwa tasa na manta da kai har sai yanzu da ka fad'o min a rai, ina mai neman afuwar ka". Jinjina kai kawai dodon yake yi, sai dai kallo d'aya za'a mashi a tabbatar da yana cike da buk'atar abinci, Ba kowane abinci yake so ba kuwa face jini, jinin ma ba kad'an yake so ba, a yanda ya dad'e baisha jini ba yanzu mai yawa zaisha sannan zai samu kanshi. Shiru ce ta biyo baya Jatau bai k'ara yin magana ba, Dodon ma ya sunkuyar da kanshi k'asa jikin shi sai rawa yake, Da tausayi Jatau yace "zan biya maka buk'atar ka yanzu DODONA, Zan baka jini wadatacce wanda na tabbatar da zakaji dad'in shi. Yana kaiwa nan ya fice daga d'akin, d'akin shi ya shiga ya d'auko kibiyar shi da sauran makamai wanda babanshi Mani ya koya mashi amfani dasu idan zasuje farauta, fita yayi daga gidan ma ya bari baki d'aya ya nufi bayan gari, A lokacin dare bayyi nisa ba sosai, da damar mutane basu koma gidajen su ba, Masu zama a majalisu suna zaune basu tashi ba, Yara da dama suna k'ofar gidajen su suna wasanni, 'Yan mata da samari ana ta fira wasu kuma a dandali ana wasanni, Sosai Jatau yaji dad'in hakan, da sauri ya tafi inda wasu yara su biyu suke suna wasa. Da sand'a Jatau ya isa inda yaran suke duk basu kula dashi ba, saurin jan yaro d'aya yayi ya soka masa kibiya a zuciya, Wata irin k'ara yaron ya saki tare da furzar da iska ranshi ya fita, D'ayan yaron ma yaji tsoro sosai ya bud'e baki zai fasa ihu Jatau ya soka masa kibiyar shima, take ya rasu. Wani irin dad'i Jatau yaji ya tallabe su su duka biyun, duk da nauyin su da yake ji bai hana shi d'aukar su ba, a b'ob'b'oye ya ringa tafiya har ya isa gida cikin sa'a babu wanda ya ganshi, Da sauri ya shiga d'akin da Dodon shi yake, Ya same shi yanda ya barshi yanzu ma haka yake alamar yunwa taci k'arfin shi, Murna fal a fuskar shi yace "ga abinci nan na kawo maka ya Dodo na, ina fatan hakan zaisa ka daina fushi dani" ya jefa masa gawar yaran a kusa dashi. Cikin hanzari Dodon ya kafa bakin shi a kunnuwan yaran, bai d'aga kanshi ba har saida ya shanye kaf jinin su, Daya tabbatar daya gama ne ya fita tsakar gida ya tona rami kamar yanda baban shi yakeyi da naman dabbobi ya binne su a ciki sannan ya koma d'akin, Ya samu Dodon yana tayi mashi ambaliyar kud'i, kamar yanda mutum yake yin amai to haka Dodon ya ringa yima Jatau aman kud'i, Kallon shi yayi fuskar shi d'auke da alamar tambaya, shima dodon ya kalle shi yana jinjina kai alamar yaji dad'in jinin da yasha. Hakan yasa tun daga lokacin Jatau ya ringa kawo ma Dodon shi jinin mutane shi kuma yana mashi aman kud'i, ya kuma bashi wata hanya mafi sauk'i wadda zai ringa kawo mashi mutane ba lallai sai ya kashe su ba, ta hanyar ce kuma yake bi a sauk'ak'e yana satar yara. Abu wasa ba wasa ba Jatau ya giga a wannan hanyar, duk wannan abun da yake faruwa bai sa ko kad'an mutanen garin sun fara zargin Jatau ba, gashi kuma kullum b'atar yaran su k'ara yawaita yake, ta kaiga iyayen basa barin yaran su fita ko kad'an saboda idan sun fita basa dawowa, Hatta da aike sai dai uwa ko uba su fita da kansu suyi abunda suke so, Hakan yasa Jatau ya yanke shawarar ya fara bama Dodon shi jinin manyan mutanen wata k'ila ma zaifi jind'ad'in shi, Hakance kuwa ta kasance, har manyan mutane suka dawo b'ata, amma da mamaki sam Dodon baya jindad'in jinin manyan mutane mace ko namiji, shidai yafi jindad'in jinin k'ananan yara kuma yafi kawo kud'i idan yasha jinin su, Gashi kuma yara sun daina fita daga gidajen su. Wata rana Jatau na zaune tare da dodon shi ne ya bashi shawara akan yayi aure, ya auri mata hud'u ta yanda duk wacce ta haihu zai bada jinin 'yar ta wa dodo, wannan shawarar ita Jatau ya d'auka, Neman auren kuwa ya fara yi, nan da nan mata suka fara rububin shi saboda dukiyar shi, kowane uba yana burin Jatau ya auri 'yar sa koba komai mutane zasuce 'yar wane tana auren Jatau mai sa'a. Dama tuni Mati yayi aure har matar shi ta haifi Talle, Cikin lokaci kad'an aka gama maganar aure, A rana d'aya aka d'aura mashi aure da matan shi hud'u. Wata rana Jatau ya samu Mati da shawara "Mati me zai hana mu fara sana'a tare? A yanda muka tashi tare ni da kai zanso ace mun k'ulla kasuwanci tare, hakan zai zame mana abun alfahari", Sosai Jatau yaji dad'in hakan, take kuma ya amince da wannan shawarar, A ranar suka fara sana'ar k'ira tare, sun samu mutane sosai duk da ranar farko ce saboda Mati ya k'ware a fannin k'ira da duk sana'ar hannu ma. Sai dai kuma kash! Baki d'aya dukiyar Mati ta lalace, duk wani samun shi ya tsaya cak! Dan dole ya ajiye wannan sana'ar. Haka rayuwar su taci gaba da tafiya sana'a tare amma na Mati na lalacewa, kuma hakan baisa ko kad'an Mati yayi zargin abokin shi Jatau ba, saboda ya kashe ma mutane baki babu mai zargin shi ta kowace hanya. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/19/2016, 11:38 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 1⃣3⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Haka Jatau ya ringa hayayyafa matanshi na zuba masa yara amma basa rayuwa, Wani lokacin ma tun suna da ciki kafin su haihu yake bama dodon shi jinin su yana shanyewa, daga k'arshe sai cikin ya zube, Ya bada kimanin yaran shi goma zuwa sha biyar a wannan lokacin, Da zarar sun haihu ko wanke yaran ba'ayi suke mutuwa, Su dai matanshi aikin su kawai kuka ne, kuma har yanzu babu wanda ya fara zargin shi tun daga matan nashi har mutanen gari, Dodon shi kuma ya dauka ya saka shi a wani babban rumbun shi (rumbu wani abu ne wanda mutanen k'auye suke ajiyar hatsi a ciki, yakan zama sirri gare su ko iyalan su basu cika sanin sirrin cikin rumbunan su ba, wani suna yin babba ne wasu kuma makimanta, ya danganta da yanayin arzik'in mutum, hakan yasa Jatau ya gina k'aton rumbu ya saka dodon shi ciki, sannan ya zuba kayan abinci yanda babu wanda zayyi zargin shi da komai barin har a kama tuhumar shi akan abunda ke cikin rumbunshi). Mati ma ya hayayyafa sosai yanzu yana da yara biyar har ma da cikin na shida, 'Yar autar shi a yanzu itace Aisha suna kiranta da Ta'ishalle, Sosai Mati yake ji da 'yar sa hakan yasa wani lokacin yake fita da ita duk inda zaije sai dai idan tana makaranta, Wata rana da safe Mati yace ma matar shi Larai "ki shirya Amadu zanje gidan Jatau mai sa'a yau, matar shi d'aya bata da lafiya, kema gobe sai kije ki duba ta", Babu gardama Larai ta shirya Amadu duk da tsohon cikin da gareta, Nan fa Ta'ishalle ta hau kuka wai dole sai an tafi da ita, Da k'yar Mati yayi mata wayo akan tayi hak'uri itama gobe zai fita da ita. Jatau na cikin Rumbun shi tare da dodo, dodo yayi mashi alama da yana da bak'i kuma akwai yaro a ciki, shi har ma yaji yana sha'awar shan jinin yaron, Murmushi kawai Jatau yayi yace "zaka sha jinin shi kuwa yanzu ya dodo na" yayi saurin fita daga rumbun ya koma d'akin shi. Da komawar shi kuwa Jatau ya iso, cikin farin ciki suka gaisa da baki kasantuwar Jatau baya gaisawa da mutane da hannu, duk wanda ya yarda ya gaisa dashi to ranar tsafin dake tsakanin su zai kare, rufe mashi bakin da yayi ma duk karewa zayyi. Kai tsaye d'akin Ladi ya kai Mati, ya gaishe ta yayi mata ya jiki sannan sukayi bankwana ya tafi shida Amadu ya rik'e hannun shi, Da tafiyar su kuwa Jatau ya koma rumbun shi, Saddabarun shi yayi sannan ya mik'a hannun shi a daidai saitin 'yar k'aramar k'ofar rumbun, Take idon shi yayi jajur kamar garwashi, Hannun shi ya ringa rawa da k'arfi, ya mik'ar da yatsar shi ta kusa da babba, wata irin akaifa doguwa mai tsini sosai ta fito, Sakin akaifar yayi ta fita ita kad'ai tabi iska, Bata tsaya ko ina ba sai kan hanyar da Mati yake shida Amadu, A daidai cikin Amadu akaifar ta caka. Wata irin k'ara ya saki tare da duk'ewa k'asa yana daddafe da cikin shi, Da k'arfi ya ringa kwara amai take jikin shi yayi zafi rau, Sosai hankalin Mati ya tashi hakan yasa ya d'auki Amadu jiki na rawa ya nufi gida dashi har da gudu yake had'awa, Da komawar shi gida ko zama bayyi ba Amadu ya mutu. Shi kuwa Jatau tunda wannan akaifar ta caki Amadu tare ta tafi da kurwar shi, Wata irin dariya ya fashe da ita kafin ya mik'a ta ga Dodon shi, Kanshi ya kafa a kunnen Amadu har saida ya tsotse jinin shi tsaf sannan ya k'yale shi. Matuk'ar tashin hankali Mati da iyalin shi sun shiga, in banda kuka babu abunda sukeyi, Haka aka sallaci gawar Amadu aka kaishi tabbataccen gidan shi, Jatau munafuki harda kuka yayi yana fad'in "Allah sarki! Tare fa dashi akazo gida na suka duba matata da jiki, da yake Allah babu ruwan shi da mai lafiya ko marar lafiya sai gashi ita matar tawa bata mutu ba shi kuma mai lafiyar ya mutu, wayyo Amadu! A duk cikin yaran Mati munfi shak'uwa da Amadu, ina son yaron saboda yana da hankali da tunani" ya k'ara fashewa da kukan munafurcin. Ba k'aramin dukiya Jatau ya samu da jinin Amadu ba, dodo yaji dad'in jinin shi sosai hakan yasa Jatau ya k'ara samun d'aukaka sosai a garin, Mati kuwa tunda d'anshi ya rasu duk ya susuce, ya koma kamar bashi ba, duk da yana da yara da yawa amma shak'uwar shi da Amadu tamkar shi kad'ai gare shi, dama daga shi sai Ta'ishalle ko gurin haihuwa, kuma su biyun ne yakema son da ba kowa yake ma irinshi ba a cikin yaran shi. Bayan rasuwar Amadu da sati biyu ne jikin Ladi ya k'ara rikicewa, hakan yasa Mati yacema Larai ta shirya domin ta gano Ladi da jiki, "Malam kafa san ciki na ya tsufa bana son fita, haihuwa ko yau ko gobe ai babu amfanin fitar", "Larai indai kina son ki faranta min rai to kije ki duba Ladi da jiki, Jatau jikin shi har rawa yake idan wani abu ya faru damu yazo ko ya turo iyalinshi, don me ke ba zakije ba?", Ba dan taso ba ta tashi a daddafe ta saka hijabin ta, "Malam gashi kuma yara duk sun tafi islamiyya babu wanda zai raka ni", "Ki tafi ke kad'ai mana, ai kinsan hanya ba dole sai an raka ki ba, nima gidan yaya Na'Allah zanje ai da sai mu tafi tare, ki daure kije ai bazaki dad'e ba". Haka Larai ta kama hanyar gidan Jatau mai sa'a tana tafiya tana zama ta huta, tafiyar da ba wata mai yawa ba amma sai da ta dad'e bata isa ba, Lokacin da ta isa ta samu Jatau k'ofar gida tsaye da wani abokin shi, Gaishe shi tayi amma shiru saboda baki d'ayan hankalin shi ya kad'u ga k'aton cikin dake gaban Larai, Sai data gaishe shi sau uku amma bai san tayi ba, D'ayan abokin nashi ne yace "Jatau ana gaishe ka fa" Saurin zabura yayi yace "au...ai banji ba, lafiya, Larai ce da yammacin nan?", "Ehh nice kuwa, ya mai jiki? Malam yace min jikin Ladin har yanzu", "Ehh wallahi Larai, ki shiga daga ciki ki duba ta" har yanzu idon shi na kan cikin Larai. Duk da ta kula da irin kallon da Jatau kema cikinta amma bata kawo komai a ranta ba, shiga gidan tayi kai tsaye ta nufi d'akin Ladi, Shi kuwa baki d'aya ya rikice yana son ziyartar d'akin dodon shi, "Wai Jatau lafiya dai naga lokaci d'aya duk ka canza yanayi?". Jin maganar da abokin shi yayi yasa ya rufe idon shi d'aya ya fara saddabarun shi sannan ya bud'e idon, Yayi ja sosai tamkar garwashi ya ringa fitar da wasu irin abu daga idon suna isa cikin idon abokin nashi, Sun d'auki tsawon lokaci a haka kafin ya koma daidai, shima abokin nashi ya koma daidai sannan yace "aboki na ni zan koma gida, sai ka fito anjiman", "To aboki na, zanzo maka da wancan sak'on anjiman" Cikin gida Jatau ya koma dan ya matsu yaje ya shiga rumbun shi, baya son Larai ta fito bai gama abunda yake so yayi ba. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/19/2016, 9:36 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 1⃣4⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Da shigar shi kuwa ya samu har yanzu Larai bata fito ba, Cikin hanzari ya shiga rumbun shi ya fara sassauke buhunnan da dodon shi yake k'ark'ashin su, Fahimtar abunda ya kawo shi yasa dodon ya fad'a masa cewa "nasan kudurin ka kuma hakan ba mai yiwuwa bace, abunda yake cikin Larai yafi k'arfin musha jinin shi, Akwai abunda Larai takeyi a kowace safiya wanda yasa cikin ta yafi k'arfin mu, ka cire wannan a ranka ka tashi ka tafi, Nacewa akan sai munsha jinin yarinyar dake cikin ta zai iya sakawa daga ni har kai mu halaka, Ka bari har sai ta haihu ta daina karanta mata abunda take karantawa a yanzu, kaga daga nan sai mu mata duk abunda zamuyi". Cikin gamsuwa da maganar *dodon Jatau* yace "yanda kace ayi haka za'ayi ya dodo na, Bani da damar yin musu ko kuma ja da maganar ka, naji kuma na gamsu da bayanan ka" Yana gama fad'in haka ya tashi ya fita daga rumbun. Fitar shi tayi daidai da fitowar Larai daga d'akin Ladi, Cikin sakin fuska Jatau yace "ahh Larai ba dai har tafiya ba", "Wallahi kuwa sai tafiya Jatau, jikin ne babu dad'i da k'yar na kawo gidan ma sai da na ringa yi ina hutawa", "Ayyah! Allah dai ya raba lafiya Larai, sai anjima a gaishe da yaran". Bayan zuwan Larai gidan Jatau mai sa'a da kwana uku kuwa ta haifi kyakkyawar yarinyar ta mai kama da ita, Yarinya taci sunan kakar Larai wato Haajarah, hakan yasa tayi mata lak'ani da Kande, Kande tazo da goshi sosai saboda kyaututtuka da Larai ta ringa samu bayan ta haife ta. Da garin habbatussaudah aka ringa yima Kande gashin cibiya dashi, idan aka rura garwashi sai a zuba garin a ciki, shi Larai ke gasa mata cibiyar dashi har ta warke sarai. (Bayan ta haihu ne RAZ suka isa wurin Larai domin yi mata wasu tambayoyi, Bayan mun gaisa ne ni Amrah na fara da; "Mama wata 'yar tambaya ce ta kawo mu wurin ki", Murmushi tayi tace "to ina sauraren ku", Rabi'atu tace "wai Mama menene kike karantawa a lokacin da kike da ciki?", "Lafiya dai? Mesa kuka min wannan tambayar?", Zarah tayi caraf tace "saboda mu isar da ita ga masu bibiyar labarin mu, nasan zasu k'aru da ita", Shiru tayi kafin tace "tun lokacin dana fahimci ina d'auke da juna biyu duk safiya kafin inci komai ina karanta suratul-nas, falaq da Ahad k'afa uku uku, idan na gama sai in karanta ayatul-kursiyyu k'afa d'aya, sai in dafa ciki na in karanta "U'idhuka au ki bi kalimatullahi taammaat, wa min kullu shaid'anin wa haammaat, wa min kullu ainillaammaat" k'afa d'aya, idan na gama kuma sai in sake dafe cikin ince "La haula wala k'uwwata illa billah" sau uku, Daga nan sai inci dabino k'wara bakwai, wani lokacin idan ban samu bakwai ba sai inci uku, ko kuma biyar, maaraa dai ake so ayi, iyakacin abunda nake yi kenan", 'Yar takarda ta dana kwafo wa masoyan mu wannan addu'ar na soka cikin k'aramar jaka ta, bankwana mukayi mata tare da godiya sannan muka tafi. K'arin bayani:- wannan addu'o'in dana kawo maku suna da matuka'r tasiri ga mai juna biyu, yaron cikin ta zayyi lafiya sannan kuma zai samu tsarki sosai da kariya daga Allah, ina fatan zamu d'auka kuma zamuyi amfani dasu). Da kud'in da Larai ta samu na suna ne Mati ya sake jan wani jarin, Kafin ya fara sai da ya shawarci Jatau abokin shi cewa "Aboki na Larai ta bani kaf kud'ad'en data samu na haihuwa, shine nace zan fara wani kasuwancin ko za'a dace, amma ya ka gani kai?", Jatau yayi shiru kafin yace "kawai mu fara sana'ar dabbobi, mu ringa zuwa Shuni muna sarowa sai mu ringa kiwata su bayan sun girma mu siyar, Wannan kasuwancin yana jawo kud'i sosai", Cike da jin dad'i Mati yace "wannan shawara ce mai kyau aboki na, yaushe zamu fara kenan?", "Ni ko yaushe ma a shirye nake, kai ko yanzu ma zamu iya tafiya", "Shikenan ma, sai mu tafi nima a shiryen nake". Daga nan sukaci gaba da sana'ar dabbobi, wannan karen kam ya jima bai samu tangard'ar sana'ar ba, Har sai da Kande ta fara girma sosai yanzu ta kai kimanin shekara bakwai a duniya. Mati ne tafe shi da Ta'ishalle suna tafiya suna fira, Ta'ishalle na kwaikwayon yanda Kande ke kuka wai ita ank'i tafiya da ita, Dariya sosai Mati keyi har suka iso gidan Jatau mai sa'a. A tak'aice dai wannan zuwan da sukayi ne Jatau ya bada jinin Ta'ishalle ga Dodo, a ranar daya bada jinin ta ranar ta rasu, Sosai Kande taji mutuwar 'yar uwarta duk da ba wani sanin mutuwa tayi ba amma tana zuwa islamiyya kuma an sanar dasu cewa idan mutum ya mutu ya tafi kenan bazai sake dawowa ba kuma rami za'a tona a binne shi. Kande ta d'auki tsawon lokaci tana kuka, ta saka 'yar uwarta a ranta sosai hakan yasa kullum ta kwanta sai tayi mafarkin ta, Yau ma kwance take tana bacci Ta'ishalle tazo mata cikin fararen kaya, Idon ta fayau ta k'ara kyau sosai, bubbuga Kande tayi ta tashi daga bacci tana kallon ta, "Haajara ki tashi in fad'a miki wata magana" Sosai Kande tayi mamaki saboda tunda take zo mata a mafarki bata tab'a yi mata magana ba, wani lokacin ma data had'a ido da ita take b'acewa. "A duk cikin 'yan gidan mu kece kad'ai basu kashe ma baki ba saboda mutuwa ta, A tunanin su saboda ke yarinya ce bazaki fahimci komai ba, Haajarah ki kula da *DODON JATAU,* akwai matsala Haajarah, ya zama sirri a tsakani na dake, Jatau nada wani dodo wanda yake bashi jinin yara k'anana, shine ya shanye jinin d'an uwan mu Amadu, duk yaran da muke wasa dasu ana sace su duk Jatau ne, kar ki yarda ko da wasa kije wurin shi ba tare da kinyi addu'ah ba, amma karki fad'awa kowa saboda ko kin fad'a ma wani babu wanda zai yarda dake, hasali ma Baba zai iya yi miki komai saboda kin soki abokin shi wanda yake ganin tamkar tsakani da Allah yake son shi, Hatta da rashin sa'ar baba na kasuwanci duk Jatau ne, saisa ya zama MAI SA'A" Tana gama fad'in maganar ta b'ace b'at, Sosai hankalin Kande ya tashi, duk da take yarinya amma maganganun Ta'ishalle sun zauna mata a rai. Wannan shine tushiyar tsanar da Kande tayi ma JATAU MAI SA'A, TASAN CEWA YANA DA DODO, KUMA TASAN SHINE YA KASHE MATA 'YAR UWARTA WADDA TAFI K'AUNA FIYE DA KOWA A DUNIYA. CIGABAN KABARI. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/20/2016, 9:05 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 1⃣5⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Har a lokacin shiru Kande tayi bata kuma cewa komai ba, Ga wani irin sauyi da jikinta ya samu, baki d'aya ji take kamar ba ita ba, A wani b'angaren na zuciyar ta tunanin yanda rayuwar ta zata kasance a cikin wannan rumbun take kuma ma kusa da wannan k'azamiyar halittar maras ko kyawun gani, Wasu sabbin hawayen ne taji sunci gaba dayi mata kwarara. A b'angaren su Mama kuwa zaune take tana jiran dawowar Kande daga inda ta aike ta, Jinta shiru yasa ta d'aura ruwan tuwonta da kanta, saboda yanzu Kande take k'ok'arin koyama girki yasa ita ta daina yi da kanta. Bayan ta d'aura ruwan tuwon ne da k'arfi taji wani abu ya soki zuciyar ta tamkar mashi, Rufe idon ta tayi tana jin ciwon abun amma ta samu kanta da kasa fad'in sunan Allah barin ta karanto ayar Al-Qur'ani, Take taji ta manta komai daya shafi Kande, ta rufe ta daga baki d'aya shafin rayuwar ta, Ta d'auki tsawon minti goma a haka kafin ta dawo hayyacin ya, take kuma taci gaba da aikin ta daga inda ta tsaya. A b'angaren Baba ma haka ne, yanda Mama taji shima haka yaji, abokin shi Sani dake tare dashi yace "lafiya dai Mati? Me sameka?", Shiru Mati yayi har saida yaji ya dawo daidai sannan yace "babu komai Sani, wani abu ne naji ya soki zuciyata, amma kuma yanzu lafiya lau nake ji", "Allah sarki! Allah kawo sauk'i to, wata k'ila ko masokiya ce ta soke ka", "Ehh haka nake tunani Sani, bara in tafi gida yamma tayi" ya tashi ya tafi gida amma ranshi cike da kokonton abunda ya same shi, wannan wane irin ciwo ne na lokaci d'aya? Tunanin daya tafi yana yi kenan har ya shiga gidan shi. A b'angaren Talle da Baseeru ma hakane, suna zaune su biyun sukaji wannan abu, cikin mamaki take suka manta da akwai wata Kande a rayuwar su, sun manta da sun tab'a yin wata 'yar uwa mai suna Kande. Audu kuwa yana makarantar allo yaji wani abu ya soki kafad'ar shi, hakan yasa yayi shiru da karatun da yake yi yana sauraren ikon Allah, A cikin kunnen shi yaji tamkar ana fad'in "ka manta da ita, ka manta da ita a shafin rayuwar ka, ka d'auka a ranka baka tab'a yin wata 'yar uwa mai suna Kande ba, ka rabu da ita ta rabu da kai kenan har abada, kar ka kuma tada maganar ta a gurin kowa saboda kowa zai manta da ita", Kyakkyawar bulala malamin su ya wanka masa, "Tunanin me kakeyi da ina maka magana ka k'yale ni? Ana karatu kai kuma kayi shiru ko? Nace tunanin me kake iye?", Har malamin ya gama maganar da yakeyi Audu baisan yayi ba, duk da bulalar daya masa bata sa ya dawo hayyacin shi ba, Zuciyar shi cike da mamakin abunda kunnuwan shi suka jiye masa, "to wannan wane irin abu ne? Wake min wannan maganar? Dama Kande batazo Makaranta ba yau kenan? Ai na tuna kafin in baro gida Innah tace ta aike ta, ina ta tsaya ne?" Duk wannan tambayoyin da yakema kanshi bashi da amsoshin su, Hakan yasa ya zabura ya dawo daga tunanin da yake, "Audul-majidu lafiya dai? Tunanin me kake da har na wanka maka bulalar da kafi komai tsoro amma baka dawo hayyacin ka ba?", Shiru Audu yayi a ranshi yana tunanin "in fad'a ko kar in fad'a?", Wata b'angaren zuciyar shi ce tace masa "kar ka fad'awa kowa", "Babu komai malam, kawai dai bana jin dad'in jiki na ne", Cikin tausayi malamin yace "ayyah! To ka tashi ka tafi gida duk da dai dama lokacin tashi ya kusa, ka biya ta gidan Indo ka karb'i sassak'e a dafa maka kasha sau uku, da yardar Allah zaka samu sauki", "Nagode malam" Audu ya fad'a tare da mik'ewa jiki babu k'wari ya nufi gida. A hanyar ma tunanin Kande kawai yake, shidai yasan yana da 'yar uwa Kande amma wani b'angaren na zuciyar shi fad'a mashi take "ka cire tunanin ta kamar yanda aka fad'a maka, Audu baka da wata 'yar uwa Kande a yanzu, ka manta ta mutu tunda dad'ewa?" Da wannan tunanin ya isa gida jikin shi duk ya mutu, ji yake tamkar mafarkin duk wannan abubuwan yakeyi. Shigar shi gida yayi daidai da kiran sallar magrib, hakan yasa kai tsaye ya nufi band'aki, bayan ya fito yayi alwala sannan ya tafi masallaci, duk wanda yaga yanayin Audu zai san lallai yana da matsala, hakan yasa ko a masallaci kowa ke tambayar lafiyar shi amma yace lafiya babu abunda ya same shi. A tak'aice dai daren ranar haka Audu ya kwana, wani b'angaren zuciyar shi na fad'a mashi cewa yana da 'yar uwa Kande amma ta mutu da dad'ewa, wata zuciyar kuma na fad'a mashi cewa bai tab'a sanin wata Kande a doron k'asa ba, Wadda ta bashi sahwarar bai tab'a sanin Kanden ba ya d'auka, yayi k'ok'arin cire komai a ranshi babu b'ata lokaci kuwa bacci yayi awon gaba dashi. *Ayi hak'uri da wannan wallahi bamu da wuta ne* Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/21/2016, 4:17 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 1⃣6⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Tun daga wannan lokacin kowa ya manta da rayuwar Kande, babu mai tunawa da ita ko kad'an in banda Audu, Shikam wani lokacin tana d'an fad'o masa a rai amma take zai kawar da tunanin ta daga ranshi, ya d'auka tamkar ma mafarki yake daya tab'a yin wata 'yar uwa mai irin sunan. Ita kuwa Kande tana can duk wani jini da Jatau zai bama dodon shi a gabanta akeyi, Sun sank'arar da ita wuri d'aya kamar gunki, Idonta ya kafe wuri d'aya ko k'yafta shi bata iyayi, Baki a hangame bata iya rufe shi, tana numfashi amma tamkar batayi, Halittar dai mutum da sunan mutum amma bata komai da mutane keyi, gata dai tana cikin hayyacin ta amma tamkar bata ciki ne, duk abubuwan da su Jatau keyi tana sane dasu amma bazata iya yin komai ba. An d'auki kimanin wata biyu da farauwar haka Baabah Haja taji Kande shiru batazo wurin ta ba, Tayi matuk'ar mamaki saboda ko cikakken sati Kande bata tab'a yi ba tare da tazl inda take ba, amma sai gashi yanzu har wata biyu har da kwanaki babu Kande babu Larai, "To kodai dama maganar da Kande tayi min da gaske take? Idan bazan manta ba ai dama tace babu ita babu ni har abada, amma kuma daga baya na masu abunda suke so d'in, wata k'ila dai har yanzu fushin ake dani, Hmm! Kande kenan, barin baki lokaci idan har bakizo ba zan karya rantsuwa ta inyo bikon ki, dan bazan tab'a iya rayuwa ba tare da ina ganin ki ba, Amma kuma ai akwai mummunar gaba tsakanin mu da iyayen Mati na d'aukarwa kaina alk'awarin har abada bazan tab'a zuwa gidan Mati ba sai dai Larai d'in da kanta ke zuwa inda nake" Wata zuciyar ta kuma tace mata "haba Haajarah! Wannan wace irin muguwar gaba ce kuke wadda bazaki iya janye ta ba? Gaba sai kace *Haydar da Haybar* (Zarah bb) ? Kosu dai da sukayi *Haramtaccen zama* (Rabi'atu sk) ai daga baya sun daidaita kansu *Har a zuciya* (Fido Sodangi), ya kamata in sakawa zuciya ta ruwan sanyi kamar yanda Usman ya sakawa tashi zuciyar a cikin labarin *Ummu Haydar* (Princess Amrah), domin kuwa inhar na kud'uri mugun abu a cikin raina zan tsinci kaina da kasancewa tamkar Farouk a cikin *D'an bautar k'asa* (Princess Amrah), naga dai irin hak'uri da *Hafsatul kiram* (Rerbee'art sk) tayi kuma daga k'arshe ta samu sakayya mafi alkhairi daga Allah, Ramuwar gayya (Princess Amrah) bata da amfani ko kad'an, na hak'ura na janye komai da duk wani mugun k'uduri daga raina" Da wannan tunanin ta tashi ta nufi turken dabbobin ta domin basu abincin su. Mati da Jatau kuwa tuni suka kama sana'ar rini kamar yanda suka tsara zasuyi, Rumfa kusa da juna suka kama yanda kowa zai iya jin abunda kowa yake ciki, 'Yar rijiyar ruwan rinin Mati ta cika taf da kala, ga sauran kayakin aiki barkatai cike da rumfa, duk abunda ya kalla a rumfar wani irin dad'i yake ji tamkar yanzu ne ya fara sana'a, shidai fatan shi Allah ya tsayar masa da wannan sana'ar, saboda yanda yasan duk sana'ar daya fara bata d'aurewa. **** Jatau ne zaune a gaban dodon shi ga Kande can daga gefe kuma tana kallon duk abunda sukeyi, Dodon nashi ne ya fara magana "ya zama dole ka saki Ladi, bata da sauran wani amfani a gareka, dama duka dalilin auren da kayi saboda suna haihuwar maka yara kana bani jinin su, to ita kuma gashi al'adar ka ta d'auke kenan bazata sake haihuwa ba, Dole zaka sake ta ka nemi wata yarinya ka aura, yarinya shakaf wadda bata dad'e da fara al'ada ba, ita zata hayayyafa maka yara, idan anyi sa'a ma sai ta haifar maka magaji, saboda kaima d'in ba mai dawwama bane, dole zaka mutu barin yanda shekaru suka fara yawaita, saisa nima nake son in samu abokiyar huld'a dan in haifi koda Dodo d'aya ko biyu, kaga daga haka sai Dodon yaci gaba da bunk'asa a wannan garin koda bayan babu ni da kai". Shiru Jatau yayi hawaye na ziyartar kumatun shi, babu abunda yafi tsana irin yaji an ambato mashi mutuwa, ya tsani mutuwa baya sonta, dama shi baya ciwo, yana da wuya ace gashi Jatau yayi koda ciwon kai ne, idan ma yayi d'in to take dodon shi zai bashi waraka. Da k'yar *DODON JATAU* ya samu ya rarrashe shi yayi shiru tare da fad'a masa cewa akwai sauran lokaci kafin ya mutu, hakan yasa yaji kwanciyar hankali tare da tashi ya fita domin sakin matar shi Ladi. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/22/2016, 10:27 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 1⃣7⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 *K'AUYEN GARU* Garu wata K'aramar rugar fulani ce dake k'ark'ashin jihar Yola, Zallah fulani ne a cikin garin masu tsauri da ak'ida irin wanda ake kira da *fulanin daji* (asea b aleeyu), A duk fad'in kauyen Garu bazai wuce gida biyar ba, sai dai a duk cikin gida d'aya za'a iya samun iyalin mutum uku zuwa hud'u. Wata kyakkyawar bafulatana ce tafe ita kad'ai kanta d'auke da k'waryar nono wadda aka k'awata da zane mai kyawun gani, Wuyanta sanye da sark'a irin ta fulanin nan, kunnen ta sanye da dogon d'ankunne, kunnen dama nashi kalar daban haka na hagu ma tashi kalar daban take. Kayan fulani ne sanye a jikin ta sai wata 'yar doguwar igiya wadda ta rataye goshin ta da ita bayan ta d'aura madaidaicin d'an kwali, K'afar ta sanye da takalman roba rufaffu irin wanda fulani ke kiwo dasu. Ita kad'ai ce ke tafiyar ta cikin natsuwa kanta sadde a k'asa da d'agaggen zanin ta kamar dai yanda fulani ke d'aurin zani. "Hassu! Hassu!! Ke Hassu wuya ta dake k'yaliya, kina ji ana miki magana sai kina share mutane kamar ba dake ake ba" wasu 'yan mata ne su biyu wanda dai da gani ta girme su tafe a bayan ta, d'aya daga cikin su ce ta fad'i haka. "Ina jinki ai haka nan na k'yale ki, kin san ni gulmammakin nan naki ne bana so, kuma da zarar mutum yaji kina masa irin wannan kiran to tabbas gulma ce, yau kuma gulmar wa kika kawo min?" Wannan kyakkyawar bafulatanar da suka kira da Hassu ce ta fad'i haka. D'ayar da bata tanka masu ba tace "ke Bod'ejo matsala gareki wallahi, kina son yima Hassu magana tana wulak'anta ki, ai wallai inda ace nice da yanzu nayi zuciya na k'yale ta dan ni bana son wulak'anci". "To sai me? Tayi zuciyar mana kiga wa zai dama? Ke nifa kun dame ni a cikin rugar nan, ku k'yale ni in sarara mana" Hassu ta fad'a tare da cigaba da tafiyar ta. "Hinye! Lallai ma Hassu, wato ni kullum ina nace miki har kina ja min gori a cikin k'awayen ke kuma kina min haka ko? To wallai ni kam bazan k'yale ki ba, ya zama dole kiyi k'awancen dani ko bakya so" Bod'ejo ta fad'a tare da bin bayan Hassu duk da tayi mata nisa. A wani makimancin gida Hassu ta shiga, Cikin natsuwa ta duk'a har k'asa ta gaishe da maman ta da baban ta, Baban nata ne yace "ba dai har kin siyar da nonon tunda wuri haka ba?", Cikin farin ciki Hassu tace "aikuwa duk na siyar dashi Baffa, da shike yau kasuwar cikin Yola naje, suna siyan nono sosai nan da nan yake k'arewa", "To Allah ya miki albarka 'yar baffa, anjima sai Iro ya dawo ke kuma ki amshe shi kenan tunda dai yau gashi kin dawo da wuri", Caraf matar zaunen tace "gaskiya Baffan su kar kayi haka, mesa yarinya tasha wahala ta dawo daga Yola kace kuma ta tafi kiwo? Nikam aradu ban yarda ba, ka manta nisan dake tsakanin garin nan zuwa Yola? Kuma duk a k'afarta fa taje, gaskiya nasan Hassu a gajiye take a halin yanzu, ka bari dai shi Iron yaci gaba da abunshi tunda dama aikin shi ne, ita kuma dama aikin ta tatsar nono ta siyar ne kawai", "A'a Amina, ki bari yarinya tayi kiwo nafi so ta horu sosai da kiwo yanda zatayi gado na game da komai, kinga dai itace babba, ina so har sauran ayyuka na ta gaje ni", "Baffan su naji na gamsu da wannan, amma yau dai ka barta kaga alamar a gajiye take, gobe sai tayi sammako shi kuma Iron sai ya tafi da nonon", "In banda haukan ki Amina a ina kika tab'a ganin an siyi nonon hannun namiji? Ki barta dai kullum idan ta dawo daga tallar nonon sai ta tafi kiwo, da dare kuma idan ta dawo sai in fara koya mata wancan aikin, na san k'walwar Hassu babu wuya zata hardace komai". Shiru matar tayi bata da yanda zatayi taci gaba da damun furar ta, Bayan ta gama ne tace "Hassu kizo ki kisha fura nasan kin kwaso yunwa". Bata bata amsa ba wani yaro ya shigo, har k'asa ya gaishe da su Baffa sannan yace "wai Sade yace a mishi sallama da Hassu, kuma wai sauri yake kiwo zai tafi", Yaron na gama fad'in haka Hassu tayi saurin mik'ewa tsaye tace "ba zanje ba, kaje kace masa nace wai bazan fito ba, wai nikam a duk rugar nan ni kad'ai ce budurwa da maza ke damu na? Ga su Bod'ejo nan, dasu Saude nan amma dole sai ni? Nikam su shafa min lafiya ba wannan ke gaba na ba", "Sai uban me ke gaban ki? Nikam Hassu na matsu ki fitar da miji kiyi aure ko zan huta da surutai da tsaigunan mutanen rugar nan, duk tsarakin ki sunyi aure fa yanzu, duka 'yan matan dake rugar nan kin girme su, shekarar ki fa sha biyu kenan har da watanni amma kink'i ki fiddo miji kiyi aure, duk tarihin rugar nan wa kika tab'a ganin ya kai tsawon wannan lokacin bai aurar da 'yar shi ba? gaskiya Baffan su da sakel, dole ka fitar mata da miji idan ita bata shirya fitarwa ba" Goggon Hassu ce ke wannan maganar cike da jin haushi, shi kuwa d'an aiken tuni ya fice abunsa ya fad'awa wanda ya aikoshi cewa Hassun tace wai ba zatazo ba. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/22/2016, 12:12 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 1⃣8⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Da yamma lik'is Iro ya dawo daga kiwo a gajiye, kallo d'aya za'a masa asan ya kwaso gajiya, Baffa ne yayi saurin ce masa "Hannu Iro, ka kwaso rana ko?", "Aradu kuwa Baffa na kwashi rana kam" Iro ya fad'a cike da gajiya. "Hassu! Ho Hassu" Baffa ya k'walawa Hassu kira, "Na'am Baffa, gani nan zuwa" Hassun ta fad'a tare da fitowa daga d'aki. "Ki tuttulowa Iro ruwa a tulu, sannan ki kawo masa fura, ki fito da shirin ki ki tafi kiwo", Rai b'ace Hassu ta tafi, ruwan ta d'ibo masa daga tulu sannan ta kawo masa fura, ba dan taso ba ta had'a kayan kiwon ta ta kora shanu ta tafi. Tun fitar ta samarin k'auye ke tayi mata magana tana k'yale su, itakam har bata son fita waje saboda samarin k'auyen su, kamar ita kad'ai ce mace a duk garin da suke takura mata. Tayi nisa sosai har ta fita daga rugar su ta kusa shiga wata rugar ta had'u da Hard'o, Cikin tand'ar leb'o Hard'o ya k'ariso inda Hassu ta zauna take hutawa, "Hannu Hassu, duk gajiyan ne ya zaunar dake kika saki dabbobin ki?", Banza ta masa tamkar ba da ita yake ba. "Haba Hassu ki kula dani mana, kin san ina son ki bazan iya rayuwa ba tare dake ba, dan Allah ki kula ni" Hard'o ya fad'i a karo na biyu amma har yanzu Hassu bata ko kalle shi ba. A hankali ya tako inda take ya zauna, saurin matsawa tayi daga kusa dashi saboda Goggon ta ta fad'a mata inhar ta sake ko tab'a ta namiji yayi to zata d'auki ciki, Bayan ta matsa shima Hard'o ya sake matsowa, Haka ta ringa matsawa Hard'o yana binta har suka matse ma icce, Mik'ewa tsaye tayi tace "kaga Hard'o ka kiyaye ni, wannan wane irin iskanci ne ina matsawa kana bina? Ka kama kanka kaji na fad'a maka" taci gaba da tafiya tare da kora shanun ta. Ci gaba da binta Hard'o yayi har ya shiga gaban ta, Saurin tad'e ta yayi ta fad'i k'asa da k'arfi har saida ta fasa wata irin k'ara alamar ta bugu, Da wata irin shu'umar dariya Hard'o ya fara cire wandon shi, Sosai hankalin ta ya tashi ta ringa kuka tana fad'in "dan Allah Hard'o kayi hak'uri karka min komai, wallahi bazan sake yi maka rashin kunya ba", "Ai idan kika ga na k'yale ki to tabbas na biya buk'ata ta ne Hassu, na dad'e ina sha'awar ki kuma ni bazan iya aurenki ba saboda babanki matsiyaci ne, iyakacin abunda zan miki kenan in samu sassauci". Wani kukan Hassu ta sake fashewa dashi tana ja da baya da kwance tana kad'a kanta alamar kar yayi, amma ina, Hard'o baya ko sauraren ta, Haka ya afka mata babu sassauci babu imani har ya biya buk'atar shi duk da yarintar Hassu, 'Yar shekara sha biyu ko al'ada bata fara ba har yanzu amma Hard'o ya lalata mata rayuwa, Sai da yayi lalata da ita so uku sannan ya k'yale ta, ya kuma kore baki d'ayan shanun ta yabar wurin dasu, bai koma k'auyen su ba sai Yola ya nufa dasu a lokacin ita kuma Hassu ta suma ga jini sai malala yake daga jikinta kamar famfo. Shiru shiru Hassu bata dawo ba har magrib tayi, Cike da tashin hankali Goggo ta samu Baffa yana alwala tace "Baffan su kaga fa har yanzu Hassu bata dawo ba, kuma bata tab'a kai haka a wurin kiwo ba", "Ki kwantar da hankalin ki Amina, nasan yanzu Hassu tana bisa hanya, kinga yau bata fita da wuri ba saisa bata kamo hanya da wuri ba". Shiru kawai Goggo tayi ba wai dan ta gamsu da abunda Baffan su ya fad'a ba, itama alwalar tayi ta nufi sallah a tunanin ta ko kafin ta gama sallar Hassu ta dawo, rabi da rabi ma tayi sallar rabin hankalin ta duk yana ga waje ko zataji muryar 'yarta. Har lokacin sallar isha yayi babu Hassu, hakan yasa shima Baffan su nashi hankalin ya tashi, tun yana iya bama Goggo hak'uri har ya kasa, ga kuka da takeyi daga ita har Iro d'in, "Ku tashi mubi hanya ko lafiya, hankali na ya fara tashi yanzu kam" Baffan ya fad'a cikin yanayin tashin hankali. Saurin tashi kuwa Goggo tayi, gyalen ta ta yafa ta zura takalmi tace "mu tafi" cikin muryar kuka. Haka suka bi hanya Iro na gwada masu ta inda Hassu ke zuwa kiwo amma babu ko alamar Hassu, hankalin su in yayi dubu ya tashi, Haka sukaci gaba da tafiya babu mai cewa kowa komai, tun Goggo na iya tafiyar har ta gaji ta zauna tana kuka sosai tace "saida na fad'a maka Baffan su cewa kar Hassu ta tafi kiwon nan, kace dole sai taje, ni yanzu ina tsoron Allah yasa ba b'arayi suka sace min ita ba", Kasa ce mata komai Baffa yayi shima wasu hawaye yaji suna masa ambaliya a fuska, dan yasan kome ya samu Hassu to shine sila, fatan shi dai Allah yasa lafiya take. Sunyi tafiya mai nisa gashi babu ko hasken farin wata sai na 'yar fitilar dake hannun Iro, Dalle ta yayi sosai ta inda ya hango wani tuli guda kamar kayan wanki, Da sauri Baffa ya k'arisa inda tulin abun yake, Nan yaci karo da d'an k'ullin kayan Hassu wanda ta saka gorar ruwan ta da sauran abubuwan buk'atar ta na kiwo, Sai anan hankalin Goggo ya k'ara tashi "shikenan sun kashe min 'ya, sun sace ta sun kashe ta na shiga uku!" Ta k'ara fashewa da wani kukan. Wata murya suka jiyo daga can nesa dasu "su waye nan kuma wa kuke nema?", Da sauri Baffa yace "mutane ne kamar kai, 'yar mu ce ta fito kiwo tun yamma har yanzu bata koma gida ba, kuma ga kayakin ta nan mun gani a zube", Cikin tausayi mutumin ya k'ariso inda suke yace "'yar ku tana cikin bukka ta na ajiye ta, nan wurin na tsince ta jini sai malala yake a gabanta kamar bata numfashi, na jira ko zanga wanda suke tare amma babu, shine na kaita na ajiye yanzu ma fitowa nayi ko zan samu magani in tsinkar mata". Salati suka d'auka su duka ukun, Goggo taji sanyi a ranta tunda dai an samu 'yar ta, da hanzari suka bi bayan mutumin har 'yar k'aramar bukkar shi da ita kad'ai ce a duk fad'in dajin. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/22/2016, 11:20 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 1⃣9⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Da shigar su suka samu Hassu kwance har yanzu bata farfad'o ba, ga sawun jini kwance malale malale tundaga kan cinyarta har izuwa tafin k'afarta, "Innalillahi wa inna ilaihu raji'un!" Shine abunda Baffa da Goggo suke ta maimaitawa a ransu, Iro kuka ne yaci k'arfin sa sosai, Itakam Goggo ta samu kanta da rasa kukan ma, ta neme shi baki d'aya ta rasa, taji ta dake sosai sai addu'a da take maimaitawa a ranta. Cike da dana sani Baffa yace "duk abunda ya sameki ni naja miki Hassu, sai da keda mahaifiyar ki kuka nunar da bakwa son tafiyar amma na tilasta maku akan lallai sai kinje, ashe rabon wannan mummunan al'amarin zai same ki ne" ya fashe da kuka sosai yana shafar kyakkyawar fuskar Hassu da hawaye suka gama bushewa a kanta. "Koda baka tilasta min zuwa nan ba Baffa dole hakan zata kasance, ko ka manta cewa kai kake koyar damu cewa 'imani da k'addara mai kyau da maras kyau' yana d'aya daga cikin rukunnan imani? Duk abunda ya same ni na d'auka a raina cewa daga Allah ne, na bar Hard'o ga Allah shine kawai zaimin sakayya" Hassu ta fad'a a hankali saboda muryarta har ta dishe tsabar kukan da tasha a lokacin da Hard'o yake mata fyad'e. Cike da mamaki Baffa da Goggo suka mik'e tsaye "Hassu kar dai ki fad'a min cewa Hard'o ne ya aikata miki haka?" Baffa ya jeho mata wannan tambayar, "Hard'o ne Baffa, shine ya...." ta kasa k'arisa maganar. "Ya salaam! Shikenan aikin gama ya gama, Hard'o shine d'an shugaban rugar mu, shikenan baza'a d'aukar masa hukunci ba, indama ace wani ne da munkai k'arar sa, amma tunda Hard'o ne bamu da yanda zamuyi, dama ba yanzu ya fara aikata haka ba, ya gallabi duk mutanen rugar mu, hatta da matan aure Hard'o bai k'yale ba, saisa ma yak'i yayi aure tsabar iskanci" Baffa ya k'ara fashewa da kuka. "Hak'uri zakuyi komai yayi zafi maganin shi Allah, ku d'auke ta ku tafi ku nema mata d'anyen ganyen lalle, ku shanya shi a cikin d'aki yayi bushewar inuwa bata rana ba, idan ya bushe sai ku daka a ringa jik'a mata shi cikin ruwa mai d'umi tana zaman shi, karku gaji da aikata hakan kuyi tayi har kusan wata biyu ko uku, da yardar Allah zata samu sauk'i duk wani raunin daya mata zai sauk'ak'a" mutumin daya tsince tan ne ya masu wannan bayanin cikin sigar tausayi. (Duk bayanin da mutumin ya masu gaskiya ne, ko cutar toilet infection mace ke fama dashi idan tayi amfani da bayanin dana kawo da yarfmdar Allah zata samu sauk'in shi). Godiya sukama mutumin tare da sungumar Hassu suka kama hanyar rugar su. A gajiye suka koma duk da sun saba tafiyar k'afa amma kam wannan mai yawa ce, ruwan zafi Goggo ta dafa ma Hassu ta mata wanka sannan ta sirka shi ta mata gashi, Ihu kawai Hassu keyi saboda azabar ciwon da takeji ga raunuka marasa adadi da Hard'o yayi mata, Goggo bata tsaya ba har saida ta gama gasata sannan ta sake yi mata wani wankan. A daren ranar dai babu wanda ya rintsa a cikin su, fatan su dai kar wannan maganar ta fita dan idan har suka bari akaji maganar tsaf za'a iya korar su a garin dan dama duk macen da aka bari tasan namiji tana budurwa to tabbas korar ta akeyi, kuma baban Hard'o shine yakeyin korar duk da yasan mafi yawancin wannan ta'asar d'anshi Hard'o ne yakeyin ta. Washe gari. Da sassafe aka aiko shugaban rugar su yana kiran Baffa, sosai hankalin shi ya tashi amma Goggo tayi k'ok'arin kwantar masa da hankalin shi ta hanyar cewa "ka kwantar da hankalin ka Baffan su, wannan maganar babu inda zataje tunda babu wanda ya sani in banda wannan mutumin daya tsince ta, kuma wannan mutumin kirki ne bana tunanin zai iya zuwa dan ya tona mana asiri, wata k'ila dai wani dalilin ne yasa ya kira ka" Ba wai dan hankalin nashi ya kwanta bane ya tafi. Sallamah yayi a 'yar k'aramar fada, kanshi sunkuye yace "yallab'ai ka aika a kira ni shine nazo", Shiru shugaban yayi bai kula shi ba, sai can da yaga dama yace "an kama ka da laifin da babu wanda yayi tsammanin haka daga gareka", Damm! Gaban Baffa ya fad'i. "Kaba yarinyar ka tarbiyyar banza, tana so ta b'ata mana sauran yaran rugar mu, to baku isa ba! Ashe saisa kak'i aurar da ita bayan kuma ta isa auren? Wato kuna neman kud'i da 'yarku ko? Tsawon lokacin nan ashe abunda take aikatawa kenan? To labari ya riske mu kan duk halayen ta, mun yanke hukuncin korar ku daga rugar nan, kai bama daga rugar nan kad'ai ba, zanu aika da sak'o a sauran rugage dan kar ma kuyi kuskuren zuwa, a duk kusa kusan nan bamu buk'atar sake gani ko jin labarin ku da kai da iyalanka, bamu buk'atar ko kwana d'aya ku k'ara a garin nan, an sallame ka tashi ka tafi". Wani irin kuka Baffa ya fasa da k'arfin gaske, "nikam dame zanji? Da cin zalun d'in da akama 'yata ko kuwa da korar mu daga haifaffen garin mu? Ya Allah gamu gare ka, kai kad'ai kasan yanda zakayi damu, Allah kayi mana sakayya" duk a zuciyar shi yake wannan maganganun. "Ance an sallameka ka tashi ka tafi ko bakaji bane?" Wani d'an kazal yayi caraf ya fad'a. Jiki suku suku Baffa ya tashi, tafiyar da ba wata mai nisa ba amma ya dad'e a hanya kafin ya isa gida, shikam baisan inda zasu nufa ba idan suka tafi. Da tunani kala kala ya isa gidan shi, koda ganin yanayin shi duk suka san akwai matsala, saurin taryar shi Goggo tayi tace "sun kore mu ko Baffan su?", Shiru yayi ya kasa bata amsa sai wasu hawayen dake fita a idon shi. "Ku kwantar da hankalin ku baki d'aya, sun kore mu kuma zamu tafi yanzu, ku harhad'a duk abubuwan da akeso mu tafi, Allah'n daya halicce mu shi yasan yanda zayyi damu, ki had'a min kayan aiki na a cikin babbar jaka guda d'aya" Baffa ya fad'a tare da kallon Goggo. Haka ta hau harhad'a kayakin su baki d'aya cikin buhuhuna, kayan aikin Baffa ta samu wata babbar leda ta saka su. Suna shirin fitowa ne Hard'o ya shigo gidan ba ko sallamah ya k'yalk'yale da dariya, Ku daina mamakin wanda yayi maku had'i da shugaba, nine nan ba wani ba, Nasan idan ban fad'a ba ku zakuyi saurin fad'a masa abunda nayi, shine nayi sauri ni na riga ku fad'a masa d'in, Hahahhahaha! Kun san inda zakuje yanzu? Hahaha kuyi sauri ku tafi tun kafin in turo wanda zasu raka ku da k'asa da duwatsu" ya k'ara fashewa da muguwar dariya. Ko kallon shi babu wanda yayi cikin su, haka suka fita kowanen su na kuka su duka hud'un, Tafiya suke sosai ba tare da sun san inda zasu dosa ba. Sun yini suna abu d'aya har yamma ta fara, Hakan yasa Baffa ya yanke hukuncin kawai su zauna a inda suke d'in, sai suyi bukka da kansu su zauna a ciki kafin wani lokacin su san yanda zasuyi. Akan wannan hukuncin suka tsaya, kwantar da Hassu sukayi akan kayan su har da Goggo suka ringa kwaso kara da itatuwa suna tirkawa har suka gama bukkar su makimanciya a lokacin har dare ya soma yi. *masu cewa mun bar chapter'n DODON JATAU mun shiga wata ku kwantar da hankalin ku, mu munsan yanda muka tsara labarin mu da kuma yanda zai tafi daidai, kudai kuci gaba da karantawa komai zai tafi kamar yanda kuke so. Mu masu son garin mun farantawa fans d'in mu rai ne, ku bimu dai da sannu za'a kai ga inda kuke so.* Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/24/2016, 10:35 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 2⃣0⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Da dare duk suka kwanta baccin gajiya ya kwashe su, banda Baffa daya fara zazzage babbar ledar kayan aikin sa da yake magana akan su, yake fad'in cewa zai koyawa Hassu saboda shekarun Iro basu kai na ya koya masa ba, kuma yana fatan koda d'aya daga cikin yaransa ne su koyi wannan aikin. A cikin ledar ya bud'e sai ga wani babban buzu anyi rubutun larabci a jiki, Daga sama an zana ka'abah sai sunan Allah daga can sama k'arshe k'arshen, Wasu manyan litattafai ne da alama Qur'anai ne masu tarin yawa da wasu litattafan suma na addini, Sai cazbaha irin doguwar nan me duwatsuna mai nauyi sosai, dutsi dubu ne a jikin ta, Sai wata 'yar gora madaidaiciya da ruwa a cikin ta. Alwala ya d'auro sannan ya zauna yaita lazimi har saida dare ya raba tsakiya (k'arfe ukun dare) sannan ya tashi yayi nafila raka'a biyu, Lazimi da manya manyan sunayen Allah ya ringayi yana amfani da cazbahar shi, idan ya ritse wani sai ya sake dasa wani, Ya d'aga gorar ruwan shi yasha kafin yaci gaba (ruwan saman farko na sabuwar shekara ne yake addu'ah a ciki). bayan ya gama duka ya d'aga hannun shi biyu sama yayi addu'ah sosai a sirrince sannan yaci gaba da salati, Sai da alfijir ya keto sannan ya tashi iyalin sa yaja su jam'i sukayi raka'atainin fajr sannan sukayi sallar subahi duk da har yanzu Hassu bata iya ko tsayuwar kirki. Washe gari da sassafe suka k'ara had'a wata bukkar, ya zamto bukka biyu ce yanzu, Baffa ya tsinko ganyen lalle domin a fara yima Hassu magani kamar yanda mutumin daya tsince ta ya basu shawara. *** Rugar Garu Hard'o ne kwance hannun shi daddafe da cikin shi sai matsar hawaye yake, Magana ma kanta ya kasa yi banda rawar lab'b'a da yakeyi, Jin shi shiru har rana ta fara fitowa bai fito ba yasa mahaifin shi aikawa domin a kira shi, A yanayin da d'an aiken ya same shi ya bashi tsoro sosai, hakan yasa ya koma d'akin shugaba da gudu ya same shi har yana k'ok'arin fitowa fada, Shessheka d'an aiken ya ringa yi yama kasa fad'in komai sai sauke ajiyar zuciya yake, "Halle lafiya dai? Mefaru? Ina Hard'on yake?" Duk a jere shugaban ya jero masa wannan tambayoyin. "Yallab'ai akwai matsala, ga Hard'o shan konshe hannun shi daddafe da shikin shi sai hawaye yake", Cikin tashin hankali shugaba yace "Hard'on nawa? Kai da sakel aradu k'arya kake, lafiya lau fa muka rabu dashi jiya da dare ya kwanta, dan me zakace min wai yana kwance ba lafiya?", "Yallab'ai ba k'arya nake ba, muje ka ganshi da kanka" d'an aiken ya fad'a tare da mik'ewa da nufar hanyar d'akin Hard'o shugaba na biye dashi. Hankalin shi tashe ya sunkuya inda Hard'on yake kwance ya dafa shi yace "Hard'o da gaske bakka da lafiya? Me same ka?", Kai kawai Hard'o yake kad'awa alamar ciwo ya kasa magana, Cike da tashin hankali ya sungumi Hard'o ya nufi waje dashi, Kai tsaye hanyar gidan Malam Nafi ya nufa, Mahaifiyar Hard'o na fad'in "malam lafiya? Ina zaka kaishi?" Ko sauraren ta bayyi ba ya tafiyar sa. A bakin gidan malam Nafi ya kwantar da Hard'o tare da yin sallamah, Bayan an amsa sallamar ne yace "malam Nafi na nan kuwa?", "Ayyah! Baya nan yayi tafiya tsawon kwana bakwai kenan, kuma ba zai dawo yanzu ba sai bayan sati biyu ko uku dan ya tafi neman magunguna ne kudu" matar shi tayi magana daga cikin gida. Dafe kanshi yayi ya sake sungumar Hard'o suka koma gida, har yanzu Hard'o bai saki cikin shi ba dan tsananin azabar da yake masa ga wani irin ciwon mara da yake ji wanda tunda yake bai tab'a ciwo ko mai kama dashi ba sai yanzu. Haka Shugaba ya koma gumida da Hard'o ba tare da samun mafita ba, dan dama duk a garin mai bada magani d'aya ne wato malam Nafi, kuma gashi bai same shi ba babu ma ranar dawowar shi, su kuma rugar dama basu san asibiti ba barin su kaishi Yola a duba lafiyar shi. Bayan wata d'aya. A cikin wata d'ayan nan ne ciwo ya miyar da Hard'o tamkar wani zautacce, baya bacci ko kad'an, da zarar ya rufe idon shi sai ya ringa ganin jerin 'yan matan da yayiwa fyad'e tsaye kowace rik'e da makami tana tinkarar shi, sai wata guda d'aya wadda ita kad'ai ce babu makami a hannun ta, sai dai tayi tagumi tana ta rusar kuka kanta duk'e bisa cinyoyin ta, hakan yasa baya ganin fuskar ta, A duk lokacin da yayi wannan mafarkin sai ya zabura ya tashi daga baccin, Haka yake a kowane lokaci sam baya samun isasshen barci, ga azabar ciwo ya dame shi, abun fitsarin shi ta kumbura sosai tayi jajur tsabar ciwo, wani lokacin ma idan ciwon ya taso mashi har suma yakeyi saboda rad'ad'in da gurin ke masa, Sai a yanzu yake danasanin abubuwan daya aikata a baya, fyad'en daya ringa yima matan rugar su har da sawar da yake ana korar su, "Lallai wannan shine *babban kuskuren dana tafka* (Rash Kardam) a rayuwa ta wanda wanke wannan kuskuren ba abu ne mai sauk'i ba" magnar da yayi da zuciyar shi kenan. Saurin tashi zaune yayi saboda yanda ciwon ya tsakure shi, wani lokacin har gudu yake dakawa dashi idan yaji ciwon, baki d'aya ya koma tamkar mahaukaci, rashin bacci ma kanshi wata babbar matsala ce barin wannan mugun ciwon da ko a tarihi bai tab'a jin wani yayi shi ba. *** Hassu kuwa ta warke sarai har tafiyar ta ta gyaru kamar dama babu abunda ya tab'a samun ta, Dajin da suke kuwa har sun saba da zaman shi, basu da matsala ko d'aya a halin yanzu. (Da gudu RAZ suka iske Baffa domin yi mashi wasu tambayoyi, Zarah ta fara da; "nikam Baffa idan ba zaka damu ba akwai wata 'yar tambaya da zamuso muyi maka ita", Murmushi Baffa yayi yace "babu damuwa 'ya'ya na kuyi ina jinku", Rabi'atu tace "Baffa maganar wannan aikin ne wanda kake yawan fad'in kana son ka samu wanda zai gaje ka, ka fara koya ma Hassu shi kuma naga alama har ma ta koya d'in da dawowar ku dajin nan, shine nace ko zaka fad'a mana ko wane irin aiki ne dan bama son mu ragewa masu karatun wannan labarin ko 'A' dake cikin sa", Shiru Baffa yayi kafin yace "wannan aikin ba wani aiki bane face aikin addinin musulunci, Na taso a hannun kakana saboda baba na ya rasu tun ina k'arami, Kakan nawa kuma malami ne sosai ta fannin addini, hakan yasa ya koya min abubuwa da dama kuma ya bani sirrin abubuwa, Lokacin daya rasu saida ya koya min komai game da kayan aikin sa, Ya sanar dani asirtattun addu'o'i wanda take Allah yake karb'ar addu'ar bawan shi idan yayi su, Hakan yasa duk lokacin da wani ya cuce ni nakan zauna in hana ma idona bacci in rok'i Allah, indai bani da hakki akan abun kuma sai Allah ya min sakayya, Wannan addu'o'in sune nayi a farkon dawowar mu wannan dajin akan abunda aka mana nida iyali na, kuma nasan indai har Allah bai mana sakayya ba to tazara ce ya basu dan shi ba azzalumin bawan sa bane, Sune na koya ma Hassu su dan nasan ni rayuwa ta bai mai dad'ewa bace, a kowane lokaci mutuwa zata iya riskata koda yake ba'a san gawar fari ba". Shiru mukayi mu duka ukun har Baffa, saboda jikin mu yayi sanyi sosai, Lallai kuwa wannan addu'o'in sun karb'u, saboda munga halin da Hard'o yake ciki a halin yanzu", "To shikenan Baffah mungode da amsa mana tambayar mu da kayi" ni Amrah na fad'a tare da goge d'an guntun hawayen dake kan kumci na). Daga nan kuma sai muka bar su Hassu a cikin dajin su, muka koma K'auyen Bagu domin gano halin da *DODON JATAU* yake ciki, saboda hausawa sunce *waiwaye adon tafiya* (pherty). *Bamu samu yin typing ba jiya ayi hak'uri.* Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/25/2016, 5:08 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 2⃣1⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Malam Mati ne zaune ya buga tagumi siraran hawaye sai fita suke daga idon shi, Saurin goge hawayen yayi a lokacin da yaji muryar Jatau Mai Sa'a yana sallamah a cikin gidan shi, Amsa sallamar yayi ya fita tare da yin murmushin k'arfin hali, "Aboki na Jatau barka da zuwa" Mati ya fad'a yana murmushi, "Barka dai Mati, nazo ne na k'ara yi maka jaje akan abunda ya faru, ashe asara kayi sosai dai ban sani ba" Jatau ya fad'a cikin muryar damuwa. "Wallahi kuwa aboki na, cikin lokaci d'aya baki d'ayan dabbobi na sukayi mushe, kuma babban abun haushin bai wuce sai da na gama kiwon su ba, sun girma sosai sun hayayyafa, jiya jiyan nan fa muke maganar da kai cewa zamu tafi kasuwar Shuni mu siyar da wanda suka girman, amma wai dawowar da zanyi da dare na tarar baki d'ayan su sun mutu, babu ko d'aya data rayu" yana hawaye ya gama fad'in haka. "Ka kwantar da hankalinka aboki na, na samar mana mafita kuma nasan hakan zayyi mana amfani" Jatau ya fad'a yana kallon Mati, "To Jatau ina jinka, Allah yasa hanyar b'ullewa ce", "Tabbas kuwa hanyar b'ullewa ce aboki na, kasan kafin Baba na ya rasu muna fita farauta tare dashi, muna yin nisa sosai wani lokacin ma har fita munayi daga wannan jihar, na iya sosai kuma ina da kayan aiki, indai zaka iya bina sai muje zuwan farko tare da kai, idan kaga yanda akeyi shikenan kaga daga nan sai kaci gaba da zuwa kai kad'ai, ana samu sosai da wannan hanyar". Cikin jin dad'in wannan kalaman Mati yace "tabbas samun aboki na gari irinka a wannan zamanin abu ne mai wahala, ni da kai mun zama *Aminnan juna* (Zarah bb) babu wanda zai iya shiga tsakanin mu, mun zama tamkar *tagwayen maza* (pherty) duk wanda ya shiga tsakanin mu kuwa yana tattare da jin kunya". Wata irin shu'umar dariya Jatau yayi yace "maganar ka dutse ce Mati aboki na, ni da kai mutu ka raba takalmin kaza", Dariya sukayi su duka sannan Jatau yayi ma Mati sallamah ya tafi, Cike da nishad'i Mati ya shiga gida, Kallo d'aya Innah tayi mashi ta gane lallai yana cikin farin ciki, duk da tasan halin bak'in cikin da ya shiga tun jiya har wayewar garin yau. "Sannu malam! Me faru ne na ganka cikin farin ciki? Ko dai mun samu kyautar kujerar aikin makka ne ban sani ba?" Innah ta fad'i maganar ne cikin zaulaya dan tayi matuk'ar jin dad'in yanda taga Mati ya warware harda dariya, tun jiya take k'ok'arin bashi baki akan yayi hak'uri amma ya kasa sai gashi yanzu cikin lokaci kad'an ya saki jikin shi ya saki fuska tamkar bai tab'a shiga damuwa ba. Da tafiyar Jatau kuwa kai tsaye rumbun shi ya shige, Idon Kande a kanshi shima yana kallon ta, "Shegiyar yarinya, sati biyu kenan muna k'ok'arin salwantar da rayuwar ki amma abu yayi wahala, na kula dai jinin ki ba mai shayuwa bane tunda tun kina cikin cikin uwarki muka kasa shan jinin ki, tunda abun haka ne zaki dawwama a haka har lokacin da zaki mutu tunda mu mun kasa gamawa dake". Dammmm! Gaban Kande ya fad'i, ita ta k'wammaci susha jinin nata ma akan wannan halin da take ciki, a gaban ta suke kashe mutane suna shan jinin su, a gaban ta Jatau ke tsafin shi shida dodon shi, a gaban ta Jatau ya sarrafa naman kai yayi mashi tsafi ya zama dodo ta mace, a gaban ta Dodon Jatau ke saduwa da sabuwar dodo ta macen da Jatau ya had'a, ta zamanto ita ba rayayya ba ita kuma ba matacciya ba, Wannan rayuwa har ina? Dame zataji? Da halin da Jatau ya saka mahaifinta yake ciki ko kuwa da halin da take ciki? Ta d'aukarwa kanta alwashi insha Allahu da hannun ta zata kashe *DODON JATAU,* fatan ta dai Allah ya kub'utar da ita daga hannun wannan azzaluman wato Jatau da dodon shi. Jatau ya kalli Dodon shi yace "na aikata duk yanda kace d'in kuma ya amince cewa zai tafi farautar tare dani, Yanzu daga gareka kawai nake jira, ka saka mana ranar tafiya". "Ku tafi gobe, kuyi nisa sosai daga wannan garin, Ku tafi garin da keda fulani sosai, acan zaku fi samun sa'ar farauta, shima d'in kuma zaiji dad'in hakan, duk da kai bata da wani amfani gareka, kaga sai ka kawo min ko jinin su insha saboda ina matuk'ar jin dad'in jinin dabbobin daji, ga kuma matata har yanzu bata saba da shan jinin mutane ba, zata fi jin dad'in shan na dabbobin har lokacin da zata saba da na mutanen", Murmushi Jatau yayi yace "naji ya dodo na, yanda kace ayi d'in haka za'ayi, akwai maganar da nake so muyi da kai kafin mu tafi", "Ina jinka, ka fad'i kome ke ranka Jatau" dodon shi ya fad'a bayan ya ajiye matar shi k'asa yana sumbatar goshin ta. "Maganar Ladi ne dama, kasa na sake ta kuma har yanzu baka min maganar yanda zan cike gurbin ta ba", "Ku tafi kawai Jatau, duk 'yar fulanin daka fara had'uwa da ita a garin da kaje kawai ka aure ta itace matar ka, zaka ji dad'in ta sosai, kuma kasan *fulanin daji* (Asea b aleeu) akwai su da saurin haihuwa, nan da nan suke haihuwa kamar karya". "Naji ya dodo na, hakan zan aikata, zan auri 'yar fillon kamar yanda kace, dan nasan ba zaka tab'a sani a bak'ar hanya ba, duk abunda ka umurce ni in aikata ina ganin ribar abun daga baya, saisa a kowane lokaci nake sonka, nake kuma alfahari da kasnacewar ka a cikin rayuwa ta, da ace babu kai a rayuwa ta da bansan ya zanyi ba, tabbas ka zame min wani jigo na rayuwa" Dariya dodon ya fashe da ita alamar yaji dad'in kalaman Jatau. Da wanaan maganar Jatau ya fito daga rumbun shi cike da farin cikin dodo yace mashi ya auri 'yar fillo, dama yana da sha'awar auren 'yan fulani sosai. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/26/2016, 10:46 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 2⃣2⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Washe gari. Tun bayan da Mati ya dawo daga sallar asubah ya fara haramar shiri, Ita dai Larai iyakacin ta kallo ne, saboda ita dai sam hankalin ta bai kwanta da tafiyar nan ba, barin ma da koshi kanshi Mati d'in bai san ta ina zasu fara ba, Tun gari da duhu duhu ya fito hannun shi rik'e da buhun bako da 'yan kayakin sakawar shi kala biyu a ciki, Talle, Baseeru da Audu sunyi tsaitsaye suna kallon yanda mahaifin su ke zakwad'in wannan tafiyar, Talle ne yayi k'arfin halin cewa "Baba inda ace ka nemi shawarar mu da sai ince maka ka tafi da wani cikin mu, saboda ko ba komai zamu taimaka maka, duk da dai nasan Kawu Jatau shima zayyi bakin k'ok'arin shi, amma dai zakafi buk'atar naka a tare da kai", "Kai rufa min baki shashasha kawai! Kana nufin shi Jatau d'in ba nawa bane ba kenan? To ka shiga taitayin ka, idan ma baka sani ba yanzu ka sani, Jatau yayi min abunda ko 'yan uwana na jini basuyi min shi ba, Jatau ya taimake ni a lokacin da nake da tsananin buk'atar taimako, Dan haka kar in kuma jin ka fad'i ko makamanciyar wannan maganar, idan ba haka ba kuma zaka yabawa aya zak'i". Shiru Talle yayi yana kallon mahaifin shi yanda ya zabure da fad'a daga wannan 'yar maganar, Larai ce tayi k'arfin halin cewa "wai nikam dan Allah malam yaushe zaka daina yiwa yaron nan fad'a a gaban k'annen shi ne? Ya kamata ace idan ma wani laifi ya maka sai ka kira shi gefe ka tsawatar masa akan abunda ya maka duk dai dai wannan ni banga abun laifin a ciki ba, ba wai ka ringa tsinka shi a gaban k'annen shi ba, wannan kamar cin fuska ne dan Allah ka daina, koni kaga idan ma wani abu yamin bana masa fad'a a gaban k'annen shi barin ma wannan yaron baya min laifin komai ni, ko Baseeru fa bana ma fad'a a gaban Audu dan kar ma raini ya shiga takanin su", "Ke kikaga cin fuska ni ban gani ba, kuma ko gobe Talle ya kuma shigar mana harka nida aboki na Jatau sai na masa abunda yafi haka, idan kinga dama sai kisaka shi ya dake ni, mtsw! Kunga tafiya ta" ya d'auki bakon shi ya fita, Larai na fad'in "Allah tsare hanya" amma ko saurarenta bayyi ba har ya fita daga gidan dan yanda kanshi ya d'auki zafi ji yake idan bai fita ba zai iya marin wani daga cikin su. A k'ofar gidan Jatau mai sa'a sukayi kicib'us dashi shima ya fito, hannun shi rik'e da k'aton buhu cike da abubuwa, Cikin tsoro da ladabi Mati yace "kawo in rik'e maka kayan aboki na", Mik'a masa kayan yayi suka d'auki hanya da k'afa suka ringa tafiya. Kasantuwar a duk fad'in k'auyen da kewayen shi basu da abun hawa yasa suka ringa tafiyar k'asa har saida duhu ya fara yi masu sannan suka yada zango a k'auyen Dangi, Zaune sukayi a bakin wata itaciya suna neman inda zasuje su kwana, saboda dai basu san kowa a garin ba, Suna cikin tunanin ne wani mutumin yazo gittawa, ganin su zaune wurin yasa shi matsowa inda suke ya masu salllamah tare da mik'awa Mati dake kusa dashi hannu suka gaisa, Ya mik'o wa Jatau ma hannun su gaisa amma sam Jatau ya d'auke kanshi kamar bai ganshi ba saboda maganar da dodon shi yake yawan yi masa akan kar ya yarda koda wasa ya had'a hannun shi da wani da sunan zasuyi musabaha, da zarar yayi haka d'aya daga cikin manya asirran shi zai kare, wannan dalilin ne yasa yake taka tsantsan akoda yaushe, duk yanda mutum yaso ya gaisa da Jatau da hannu baya yarda sai yayi yanda yayi ba'a gaisa dashi d'in ba. "Malam mu bak'i ne a garin nan, hanya ce ta biyo damu shine muke neman masauki" Jatau ya fad'a dan yayi k'ok'arin kawar da maganar gaisawar da mutumin yake son suyi, Ba tare da tunanin komai ba mutumin ya ajiye hannun shi sannan yace "Allah sarki ashe ku bak'i ne, nifa naga duk bak'in fuska ne ku, me zai hana kuje masallaci gashi can sai ku kwana a ciki? Nasan dai ana sanyi sai inje gida na in kawo muku abun rufa yanzu" "Aikuwa malam da mun gode sosai, bari muje can d'in" Mati yayi caraf ya fad'a tare da mik'ewa ya rarumi buhun kayakin su. Shima Jatau d'in mik'ewa yayi ya nufi hanyar da Mati yayi dan tacan ne masallacin yake, Tsaye cak yayi a lokacin da yaji wata murya kamar ta dodon shi tana mashi magana, "Jatau karkaje! Kar ka yarda ka shiga masallacin nan, komai zai iya faruwa idan ka shiga ciki, baka san da irin abunda zaka had'u a ciki ba, zaka iya had'uwa da wanda zai karya mana duk wani tsafin mu". "Me kake jira ne Jatau aboki na? Kazo mu shiga ciki mana" Mati ya fad'a bayan shima d'in ya tsaya nesa da inda Jatau ya tsaya. "Babu komai Mati, kawai kajeka kai ka kwana a ciki ni zan kwana anan babu damuwa" Jatau ya fad'a tare da komawa k'ark'ashin itaciyar da suka fara zama ya zauna. "Mesa ba zaka je masallacin ba?", "Haka kawai naga muda zamuje farauta ai bai kamata mu nemi wurin fakewa ba, kamata yayi ace mu zama jarumai masu kare wasu, saisa na sake shawara kawai anan zan kwana", "To in kuwa hakane ai nima d'in nan ya kamata in kwana tunda dai kaine zaka koya min, kaga dole abunda kayi nima shi zanyi, amma dai ana bina sallar magrib data isha, zan shiga inyi sai in fito", "To babu damuwa, nima zanyi tawa a nan" Jatau ya fad'a bayan ya karb'i buhun kayan su a hannun Mati. (Haka Jatau yakeyi idan baya so a gane baya sallah, a gaban mutane yanayi saidai kuma ba ta kirki ba, zayyi k'ok'ari ya b'ata alwalar shine ta hanyar kin wanke fuska ko kuma hannu kodai wani abu da yasan farillah ne daga cikin alwala duk da dai dama ba wani iya alwalar yayi ba dan sam Jatau bai san komai akan addini ba, zaman shi da Mati ne ma yake dan d'aukar wani abun idan yayi, a sanadiyyar tarayyar shi dashi ne ma har ya iya alwalar, Sai ya jera yabi sahun mutane, amma fa duk rintsi baya shiga masallaci kamar yanda dodon shi ya bashi umurni tun bayan rasuwar baban shi Mani). Koda mutumin ya fito masu da abun rufa ya same su a inda ya barsu, yayi mamaki sosai duu sanyin nan da ake amma su a k'ark'ashin itaciya suke, Koda ya tambaye su Jatau ya bashi amsa da cewa su mafarauta ne dan haka dole su zama jarumai, bayyi mamaki ba kawai ya basu abun rufar sannan ya masu saida safe ya tafi gidan shi, Su kuwa anan suka kwantar har asubah tayi aka fara kiran sallah a wannan masallacin na kusa dasu, Tsaki kawai Jatau yayi ya sake juyawa ya koma baccin shi, Shi kuwa Mati tashi yayi ya nufi masallacin yayi alwala sannan ya zauna yana lazumi kafin a tayar da sallah. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/27/2016, 12:10 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 2⃣3⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Tun gari bai k'arisa wayewa ba Jatau ya mik'e yayi mik'a bakin shi duk yawun bacci abun k'yama, Hannun shi yasa ya goge bakin yawun ya k'ara b'ata fuskar shi, "Sannu aboki na, ka tashi kenan" Mati ya fad'a bayan ya ajiye casbahar shi. "Ehh na tashi Mati, sai mu tashi mu fara haramar shiri ko?" Jatau ya fad'a cikin muryar bacci. Nad'e kayakin su sukayi sannan Mati ya ninke abun rufar da mutum jiya ya kawo masu, Yana ninkewa kuwa sai ga mutumin yazo, Bayan sun gaisa ne Mati yace "yanzu kuwa muke tunanin yanda zamuyi da zanin rufar nan naka, gashi kuma bamu san gidan ka ba sai gashi kuma Allah ya kawo ka", "Wallahi kuwa, kuzo muje gida na na saka an had'a maku abunda zaku karya dashi kafin ku tafi", Jatau yayi caraf yace "a'a ka barshi kawai zamu siya a hanya muci", Shiru mutumin yayi ba wai dan ranshi yaso ba. "Mati kaje masallacin can ka kawo min ruwa insha" Jatau ya fad'a yana kallon Mati. Tafiyar Mati Jatau ya fara surkullen shi na tsafi yana kallon wannan mutumin, take saiga wannan kibiyar tsafin tashi ta b'ullo ta shiga hannun shi, Jefa ta yayi a saitin zuciyar mutumin take ya tashi sama yabi iska, bai tsaya ko ina ba sai rumbun Jatau inda dodon shi yake, Zo kuga murna wurin *DODON JATAU,* yaji dad'in smaun jini a wannan lokacin duk da har yanzu matar shi bata saba da jinin mutane ba, tafi son tasha jinin dabbobi. Koda Mati ya dawo da ruwa a hannun shi ya mik'awa Jatau shi, Karb'ar ruwan yayi ya kalla sosai sannan yace "aboki na Mati ruwan nan bashi da kyau sosai, ka miyar dashi kawai na fasa sha", Bashi da yanda zayyi ya karb'a ruwan ya miyar sannan ya dawo suka d'auki hanya. Sosai Hassu ta samu sauk'i, sai dai al'ada da tazo mata cikin lokaci d'aya, A lokacin data fara ganin jinin hankalin ta yayi matuk'ar tashi, Hakan yasa ta samu mahaifiyar ta da maganar, "Goggo tun jiya ciki na yake min ciwo, shine na dafa sassakcen bagaruwa nasha na samu sauk'in ciwon, To kuma yau da safe shine naga..." tayi shiru sanadiyyar kukan da yaci k'arfin ta. "Kika ga me Hansatu? Fad'a min ki daina kukan mana" Goggo ta fad'a cikin tashin hankali, "Goggo jini naga yana bi mun cinya na" ta k'ara rushewa da kuka. "Na shiga uku ni Amina! Hassu al'ada kika fara kenan? Al'ada kika fara tun kafin a miki aure, wannan abun kunyar har ina? Tunda nake ban tab'a ganin an fara al'ada kafin ayi aure ba" ta fashe da kuka kamar wadda tayi abun kunya. (Al'adar k'auyen su kenan, wai ya zama abun kunya idan mace ta fara al'ada ba'ayi mata aure ba, hakan yana hana kowane namiji ya aureta, idan ma bai san ta fara ba ya aureta to sai ya wulak'anta ta sannan ya mata korar kare daga gidan shi, kuma yana da hakkin da zai kai k'arar iyayen ta gidan maigari a kore su daga garin saboda cin amana da sukayi, tirrr da wannan d'abi'ah) Itama Hassun kuka take sosai har Baffa ya same su a haka, ya tambaye su abunda ya faru Goggo tace "malam kaji abun kunya wai Hassu ta fara al'ada yau, mun shiga uku malam da wannan abun", Cikin damuwa Baffa yace "bana so kuna kukan nan Amina, idan kinayi to ita kuma Hassun tayi me? Fyad'en da aka mata ne ya jawo mata al'adar ta da wuri, kuma tunda taji sauk'i ai ina ganin ba wani abu bane, kawai mafita d'aya ce mu samu mu aurar da ita da wuri, tunda mu a al'adar garin mu dole sai an yima yarinya aure a gidan mijinta take fara al'ada, kawai mu dage da addu'ah muna sanar da ubangiji shine kad'ai yasan halin da muke ciki kuma shi zai fitar damu", "To Baffan su yanzu da kace a aurar da ita wa zata aura? Waye kake tunanin zai auri Hassu bayan kowa yasaa da maganar fyaden da akayi mata? Kuma ma idan an auretan mijin daga baya ya gane ta fara al'adah ya kake so ayi? Kasan dole zai wulakanta mana yarinya fa, A cikin wannan dajin da muke ciki wa kake tunanin zaizo har ya nemi auren Hassu?", "Ki cire wannan damuwar Amina, da yardar Allah Hassu zata samu wanda zata aura kuma mai sonta, ku daina wannan kukan dan Allah, ki koya mata yanda zata tsaftace jikin ta", Goge hawayen Goggo tayi sannan ta fara koyawa Hassu yanda zata gyara jikin ta. A Garu kuwa har yanzu Hard'o bashi da kwanciyar hankali, kullum sai yayi mafarkin Hassu tazo mishi tana kuka, Hakan yasa kwata kwata bashi da kwanciyar hankali, Abokin shi yazo ganin shi ya bashi labarin duk abunda yake damun shi, Shi kanshi abokin nashi hankalin shi ya matuk'ar tashi, Ya shawarce shi akan ya fad'awa baban shi cewa duk laifin shi ne maganar su Hassu, Amma sam Hard'o yace shi bazai iya tinkarar mahaifin shi da wannan maganar ba, Tafiya abokin nashi yayi cike da mamakin halin abokin shi, Tun tafiyar shi Hard'o yake tunanin shawarar da abokin shi ya bashi, tabbas gaskiya ya fad'a masa kuma ya zama mashi dole ya fad'awa baban shi wata k'ila hakan ne kawai zaisa shi ya samu kwanciyar hankali. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/27/2016, 11:14 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 2⃣4⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Afuwan nayi mistaking number ne. Mun sadaukar da wannan shafin ga 'yar uwar mu, yayar mu kuma masoyiyar mu *Aunty Mamu (Mrs. Jabo),* sak'on ki ya iso garemu kuma muna godiya da hakan, tabbas 'yan k'ungiyar *NAGARTA* kun zame mana wani jigo na rayuwar mu, bamu da abunda zamuce maku face mu k'ara godiya a gareku, *RAZ* na k'aunar duk masoyan su na nesa dana kusa.πŸ’“❤πŸ’• **** Da yamma mahaifin Hard'o ya shigo d'aiun da yake jinya ya same shi sukuku kamar kullum, Zama yayi a kusa dashi yace "hannu Hard'o! Ya jikin naka dai?", "Jiki da sauk'i Baba, dama tun d'azu nake jiran shigowar ka, akwai maganar da nake so muyi da kai", Cikin mamaki Baban nashi yace "magana kuma Hard'o? Lafiya dai ko?", "Lafiya k'alau Baba, akan maganar yarinyar nan ne Hassu" Hard'o ya fad'a cikin yanayin da baya son fad'in maganar. "Wacece kuma Hassu?", "Baba Hassu dai wadda na kawo maka maganarta cewa na kamata da namiji suna lalata har ka koresu daga garin nan ita da babanta da mamarta sai kuma k'anin ta d'aya", "To to to to nagane ta, ya akayi ne? Ince dai ba kana nufin a dawo dasu bane, saboda babu abunda zaisa in dawo da 'yar iska a gari na dan kar ta gurb'atar da tarbiyyar sauran yara". Kuka Hard'o ya fashe dashi sanadiyyar fuskar Hassu da yake hangowa yayin da take zo masa a mafarki, tabbas ya zama dole ya fad'i gaskiya saboda fad'in gaskiyar ne kawai zaisa a dawo dasu a garin, dan da alama suna cikin wani hali a duk inda suke. "Da kai nake ina maka magana kayi min shiru Hard'o", "Baba dama ba laifin su bane laifi na ne, nine nayi mata fyad'e na kuma gudu masu da shanu na tafi Yola dasu na siyar", Cikin mamaki Baban yace "kai Hard'o ka sani duk wata k'arya da zakayi ba itace zata saka ni dawowa dasu ba, ka canza wani salon dai ba wannan ba", "Baba dama nasan dole za'a wahala kafin ka yarda, wallahi baba nine nayiwa yarinyar fyad'e, ba ita kad'ai bama kusan duk 'yan matan da kake kora daga garin nan nine nake masu fyad'e, sai a yanzu nake nadamar abunda nayi, nadamar da bata da amfani saboda nasan da dama cikin wanda nayi ma fyad'en wasu ban san inda zan gano su in nemi gafarar su ba", "Hard'o har yanzu baka kawo min wata hujja wadda zata gamsar dani cewa kaine da laifi ba", "Baba kayi tunani da kyau, ya akayi nasan anyi wa Hassu fyad'e? Mesa nine kawai nake gane wanda akama fyad'e? Mesa nake kawo maganar wanda akama fyad'e bayan kuma ba nine kad'ai saurayi a garin nan ba? Duk daraja da kimar mahaifin Hassu mesa 'yarsa zata mik'a kanta ga namiji da gangan don kawai biyan buk'atar ta? Kar ka manta baba, duk rugar nan tamu fa babu malami kamar mahaifinta, a koda yaushe cikin bada fatawa yake, ya bama yaransa tarbiyya mai kyau har yaran rugar nan kowa tana son ace itace k'awar Hassu, kowane namiji yana so yaji ance shine saurayin Hassu, kaga kuwa ba abun mamaki bane dan nace nine nayi mata fyad'e" ya k'arisa maganar yana hawaye sosai. "Tabbas na yarda da maganar ka Hard'o, kuma sai da ka fad'a ne duk nake tunano hakan, Hard'o ka cuce ni, kasa na zama shugaban banza mai son kanshi, ka sa na zama azzalumi gana k'asa dani, ka fad'a min yanzu ina zan gano jama'ar dana kora? Ina zan gano su su dawo mahaifar su da zama? Shin mun san halin da suke ciki yanzu? Kar kayi mamakin da dama wasu sun mutu dalilin korar dana masu, saboda ba lallai su samu wurin zama ba, Allah gani gareka ya Allah, Allah ka yafe min ka had'ani da jama'ar dana kora domin neman yafiyar su" ya fashe da kuka shima cike da tsantsar nadama. Tun daga lokacin ciwon zuciya ya kama baban Hard'o, da yake basu da asibiti basu san wane irin ciwo bane, sai dai jik'e jik'en sassak'e kawai ake masa, Kwanan shi biyu yana jinya Allah ya karb'i rayuwar shi, A cikin kwanakin jinyar da yayi ya rok'i gafarar Allah sosai yayi nadama, Sosai mutanen garin sukayi mamakin sauyin daya samu, sai dai kuma sun kawar da mamakin su a lokacin da suka samu labarin rasuwar shi, Kenan dama mutuwar shi na gab saisa ya tuba ga Allah, kowanen su tunanin da yake kenan a ranshi. Bayan mutuwar baban Hard'o da sati biyu aka nad'a shi a matsayin shugaban rugar su, Sosai Hard'o ya samu lafiya har yawan mafarkan da yakeyi ya daina, ya sauya halayyar shi baki d'aya, Rugar Garu ta samu sauyi sosai tamkar ba ita ba, 'Yan garin sunji dad'in canjawar da garin su yayi. Bayan hawan kujerar Hard'o da kwana biyu ne ya saka ranar da za'a bi daji domin gano inda su Hassu suke dan shikam a iya tunanin shi yasan cewa basa cikin kwanciyar hankali, saboda yanda ya ganta a mafarki ya tabbatar da ba wuri maj kyau suke ba, duk da yanzu ya daina yin mafarkin baki d'aya. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/28/2016, 11:52 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 2⃣5⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 _Dan Allah mutane ku zama masu hak'uri, ku ringa duba shin idan nine akayiwa abu kaza zanji dad'i ko bazanji ba? Wallahi muna bakin k'ok'arin mu dan ganin mun farantawa mutane rai, duk da abubuwa da suka mana yawa hakan baya hana idan wasu sun nemi mu tura masu daga farko mu tura, amma wai duk da haka wasu basa gani, idan ma suka nema aka b'ata lokaci wurin turawa sai subi mu da zagi, shin zakiji dad'i inda ke akaima haka? Wannan abu dai dan Allah mukeyi ba dan ko sisin dake hannun ku ba, amma wai ba'a duba hakan sai zagi da bak'ak'en maganganu. Sannan kuma idan wasu sun nema da yawa muka tura a groups sai kuma mutane su ringa cewa ana k'ona masu data, kin san bakya so a k'ona miki data ne kika shiga group na novels? Ai duk wadda take group na novels dole tasan za'ana cin data d'inta, dan haka muke rok'on ku dan Allah ku zama masu adalci, mu ringa tunani kafin mu aikata wani abu. Idan akwai wadda wannan maganar ta b'ata mata rai to ta gafarce mu, d'an adam ajizi ne kuma tara yake bai cika goma ba a duk inda yake. Masoyan mu mugode sosai da soyayya._ ******* Sunyi tafiya mai nisa kafin suka isa Yola, Cike da farin ciki Jatau ya kalli Mati yace "garin zallar fulani kenan, nasha jin ana fad'in Yola garin fulani ne, fulanin asali masu kaaraa da kawaici", Murmushi Mati d'in yayi shima yace "ga alama nan na gani ai, tunda mukazo muke cin karo da fulani", "Yanzu dai sai mu gama hutawa mu yanka ta dajin gabacin mu, ina tunanin acan zamu samu babban dajin da zamuyi farautar mu da kyau", "Ehh kam, duk yanda kace ayi haka za'ayi aboki na Jatau". Bayan sun gama hutawa sosai suka tashi suka nufi dajin gabas, sunyi tafiya mai nisa kafin su fita daga cikin garin Yola, saboda Yola nada girma sosai, Sai yamma lik'is sannan suka isa wani daji wanda babu ko alamar akwai mai rai a cikin shi, gashi kuma dare ya fara yi, hakan yasa suka yanke hukuncin su kwana anan kafin gari ya waye su k'ara nitsawa cikin dajin sosai dan da alama zasu samu kayan farauta a cikin shi. Washe gari tun gari bai gama yin haske ba Hard'o da tawagar shi suka d'auro shirin neman su Hassu, Sun harhad'a komai sannan suka hau rak'uman gidan su Hard'o guda goma sai wasu akan jaki guda goma Hanya suka d'auka sai dai kuma kash! A maimakon suyi yamma sai sukayi kudu, Har suka fita daga dajin kudu babu ko alamar su Hassu, hakan yasa suka baro wannan dajin suka nufi dajin Yamma wato inda su Hassu suke, Zuwan su yayi daidai da isowar su Jatau wurin, Bukkokin su Hassu suka fara cin karo dasu a lokacin su kuma suna ciki saboda sanyin da akeyi, Ganin su Hard'o yasa su Jatau dakatawa a daidai inda suke sukaci gaba da kallon su, A gaban bukkokin Hard'o ya sauko daga kan rak'umin shi sannan suma sauran suka sauko daga kan nasu, Sallamah yayi a daidai bukkar da tafi girma d'in wato inda Baffa da Goggo suke, Cike da tsoro Baffa ya kalli Goggo itama ta kalle shi baki d'ayan su suna mamakin sallamar da akeyi masu, Amsa sallamar Baffa yayi bayan an kuma yin sallama a karo na uku, Cike da fargaba Baffa yace "lafiya dai ko?", "Lafiya k'alau malam, matafiya ne mu muna da tambaya ne" Hard'o ya amsa bayan yayi shiru yana tunanin kamar yasan wannan muryar. Baffa ya d'an samu kwanciyar hankali lokacin da yaji ance matafiya ne, Hakan yasa ya taso daga bisa gadon karan su ya lek'o yace "tambayar me kuke ne?", Saurin juyowa Hard'o yayi ya k'ara murza idon shi dan tabbatar da abunda ya gani d'in, Wata irin fad'uwar gaba Baffa yaji, take jikin shi ya fara kyarma lab'b'an shi na k'asa na gugar na sama, "Dan Allah Hard'o kuyi mana rai, wallahi munyi nisa da rugar mu, kuyi hak'uri zamu bar nan d'in ma gaba d'aya amma karku tab'a min iyali na" ya k'arisa maganar sosai hawaye ke fita daga idon shi. Shima Hard'on hawayen yayi yace "ka gafarce ni ya kai wannan dattijo, na sani ni da mahaifina masu laifi ne kuma dama ku muka fito nema domin mu rok'i gafarar ku" ya duk'a har k'asa yace "nine nayi wa 'yar ka Hassu fyad'e kuma naje nayi zugi ga mahaifina aka kore ku, a dalilin fad'in gaskiya da nayi ga mahifina yayi nadama ga duk zaluncin da yayi a baya, damuwar cutar da yayi a baya ce ta masa yawa har ya rasa rayuwar sa, kafin ya rasu ya umurce ni akan in neme ku duk inda kuke in dawo daku rugar mu kuci gaba da zama, sannan kuma in nema masa gafara a wurin ku kaida iyalinka". Cikin mamakin Baffa yake kallon Hard'o, tabbas da alama Hard'o yayi nadama don yanayin shi ya nunar da hakan. Suna cikin haka ne Goggo ta fito saboda duk tana jin abunda suke fad'i, "Hard'o munji kuma mun yafe maka duk abunda ka mana, shima kuma mahaifin naka mun gafarce shi, amma gaskiya ba zamu koma Garu da zama ba, nan ma da muke mungode Allah saboda muna cikin farin ciki da kwanciyar hankali" Goggo ce tayi wannan maganar tana kallon Hard'o cike da tsana. "Dan Allah Goggo kuyi hak'uri ku koma, nasan indai har baku dawo Garu da zama ba to baku yafe mana ba", "Hard'o ina son ka sani mun yafe maka har cikin zuciya ta, kawai dai komawar ce ba zamuyi ba, saboda nasan indai har muka koma Garu da zama tabbas Hassu ba zata auru ba saboda babban abun kunyar da ka saka ta a ciki". Tuni Hassu ta fito tana kuka sosai dan ji take tamkar an fama mata tsohon tabon daya dad'e da warkewa, Kuka take kamar ranta zai fita tana k'ara kallon Hard'o tana tuna lokacin da take masa magiya amma yayi kunnen uwar shegu da ita. "Tabbas Hard'o maganar da Goggo ta maka gaskiya ne, naji duk bayanan ka kuma na yarda da tubar da kayi, amma ka sani nasan inhar na koma Garu bazan tab'a auruwa ba kamar yanda Goggo ta fad'a, ka jawo min abun kunyar da har 'ya'ya da jikoki sai ya bisu, kawai ku tafi ku barmu anan" Hassun ta fad'a duk da kunya irin ta 'ya'yan fulani da gareta amma dole ta daure ta fad'i abunda yake ranta. Duk abunda yake faruwa a gaban Jatau da Mati ne, ya fara tuno kalaman Dodon shi cewa "duk 'yar fillon da ka fara cin karo da ita kawai ka aure ta" Caraf Jatau yace "karki damu 'yar fillo, ko menene ya same ki ni naji zan aureki in har zaki amince dani kuma bazan tab'a wulakanta ki ba". Baki d'ayan su suka dawo da hankalin su ga Jatau da har yanzu idon shi yake kyam akan Hassu da itama d'in shi take kallo tunda ya fara mata magana. Follow me @ my insta miss_amrahmashi Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/29/2016, 10:30 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 2⃣6⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 "Ehh k'warai da gaske nake zan auri Hassu indai zaku yarda ku bani aurenta" Jatau ya nanata bayan ya matso daf da inda Baffa yake tsaye. Cike da mamaki Baffa yake kallon shi, a ranshi yace "to shikuwa wannan wane irin mutumi ne? Duk da yaji ance Hassu tayi abun kunya wato bai damu da yaji wane irin abun kunya ne tayi ba, lallai kam da gaske wannan bawan Allah'n yana son Hassu kuma tsakanin shi da Allah yake sonta", Jin shiru babu wanda ya k'ara magana yasa Jatau nanata abunda ya fad'a, ya kuma k'ara da "Ni mutumin Bagu ne a k'ark'ashin wani gari mai suna Illaila cikin jihar Sokoto, ni mafarauci ne tate nake da aboki na Mati, ina so ku yarda dani zan rik'e 'yar ku da amana bazan tab'a ha'intar ku ba, ina da mata uku a halin yanzu duk suna Bagu da zama, yanzu ma ance mana ana samun kayan farauta ata wajejen nan saisa mukayo nan". Gyaran murya Baffa yayi yace "naji bayanan ka bawan Allah kuma na yarda da kai, amma akwai maganar da ta zama dole ace ka santa, ina so ka sani Hassu bata da budurci, an mata fyad'e a watannin baya, bana son na cuce ka na had'a ka aure da ita kuma daga baya idan ka gane ka wulak'anta min 'ya, kaga Hassu yarinya ce har yanzu amma gashi ta fara al'ada tun kafin a aurar da ita, kuma mu a tsarin garin mu ba'a haka, kuma babban abun kunya ne yin hakan, saisa ma nace ba zamu koma Garu da zama ba saboda abun kunyar nan, zaman mu anan shine mafi alkhairi fiye da na can duk da can ne mahaifar mu kuma garin mu na iyaye da kakanni". "Babu komai Baba indan wannan ne, ai kowa yasan k'addara kuma babu wanda ya isa ya k'etare ta, ko kai waye baka isa ka tsallake kaddara ba tana kan kowa, kuma koda ma ace da gangan ne ai rubutaccen al'amari ne, duk abunda Allah ya tsara babu *d'an adam* (Rufaida Omar) d'inda ya isa ya wuce shi, tabbas nasan ni da Hassu wani had'i ne daga Allah tsakani na da ita, naji k'aunar Hassu sosai *har a zuciya* (Sodangi) ta kuma ni babu ruwana da wani fyad'e da aka mata, ni tsakani na da Allah nake sonta ba dan wani abu nata ba, da yardar Allah bazab taba zame maku *tab'arya mai baki biyu* (Aunty Mamu) ba", (su Jatau kamar da gaske shi na Allah ne). Cike da jin dad'in kalaman Jatau Goggo tace "mungode sosai bawan Allah, tabbas ka nunar mana cewa kai d'an halak ne, mun baka auren Hafsatu", "Yanzu ma idan kana da sadaki ka kawo za'a d'taura aurenku da ita tunda dai ga shaidu da yawa, na baja auren Hafsatu, amma ka sani cewa Hafsatu *'Yar gata ce* (miemiece), bana son abunda zai tab'a min ita" Baffa ne yayi caraf yayi wannan maganar yana fad'in haka yana murmushin jin dad'i. "Kwarai kuwa akwai sadaki a hannu na" Jatau ya fiddo mak'udan kud'i ya bayar amma Baffa yace sunyi yawa, kad'an ya karb'a take aka d'aura auren shi da Hassu a gaban su Hard'o kuma sune shaida, Mati shi ya zama wakilin Jatau. Ita kuwa Hassun tama rasa a halin da take ciki yanzu, shin farin ciki ne ko kuwa bak'in ciki? Taya zata iya zaman aure da wanda ya girmi babanta? Amma kuma idan tayi la'akari da wani abun ma ai taimakon ta ne yayi, wa zai iya aurenta a halin da take ciki? Samun namiji irin Jatau a wannan lokacin ai abu ne mai wahalar gaske, ta kud'ura a ranta cewa zata zauna zaman aure da Jatau har k'arshen rayuwar ta, mutuwa ce kawai zata rabata dashi, zata iya daurewa kowane irin hali gareshi ta zauna dashi matuk'ar halinda yakeyi d'in bai sab'a ma addinin musulunci ba *(RAZ* sukace akwai aiki kenan kuwa) Ita dai fatan ta Allah yayi mata jagora ya shige mata gaba, Allah kuma ya tabbatar mata da alkhairi, zata dage da addu'o'in da Baffanta ya koya mata, dan tabbas duk wanda ya rik'e addu'ah bazai tab'a tab'ewa ba. Tsabar jin dad'in d'aurin auren yasa Baffa da Goggo suka amince zasubi su Hard'o su koma Garu, Shi kanshi Hard'on wani kishi yakeji yana tokarin zuciyar shi, amma bashi da yanda zayyi tunda rufin asiri ne Hassu ta samu, yaso ace sun koma garin su ya aureta saboda dama can ya dad'e yana sonta sai shaid'an ya libbace shi har ya aikata mummunan al'amari gareta kuma a lokacin yaji sam bazai iya aurenta ba, saboda babanta matsiyaci ne ba wani abu ne dashi ba, amma yanzu kam ya gane kuren shi, yaso ace Hassu matar shi ce, dan haka yayi k'ok'arin kawar da kishin dake ranshi ta hanyar nuna farin ciki ga wannan al'amarin. Kayakin su suka had'a baki d'aya sannan suka fito, Baffa ne yace "to Jatau ango zamu tafi garin mu, amma kuma ya kamata ace tare zamu tafi da kai saboda a samu wanda zasu biku, kasan babu yanda za'ayi mu d'auki 'yar mu ita kad'ai mu baka ka tafi da ita ba tare da ansan inda kuke ba ba wai dan bamu yarda da kai ba", "Hakane kam baba, hakan da ka tsara shine daidai, muje kawai". Jatau da Mati sukabi bayan Baffa dasu Goggo, suna tafiya yana satar kallon Hassu, ita kuwa kunya takeji sosai yasa har yanzu ta kasa had'a ido dashi sai kawar da kanta take idan taga alamar yana kallon ta. Haka kawai Jatau ya samu kanshi da soyayyar Hassu kuma tsakanin shi da Allah, Shidai yaji yarinyar ta burge shi kuma yana da sha'awar zama da ita tsakanin shi da Allah ba kamar yanda yayi aure a baya ba, A wancan karen kam duk dan su haifa masa yara ya ba dodon shi jini ne, yanzu kuwa soyayya ce ta tsakani da Allah yake mata, Bai san da wace fuska zai kalli dodon shi yace ya kamu da son Hassu ba. Haka sukabi hanyar Garu cikin farin ciki, Da yamma lik'is suka isa Garu dan dama su Hard'o sun dad'e da isa har yasa anyi shela akan ya dawo dasu Baffa da zama garin Garu saboda basu da hak'k'i aka kore su, Baki d'aya 'yan garin sunyi farin cikin dawowar su Baffa garin, saboda ba kad'an ba sukayi kewar su, koba komai sunyi rashin babban limamin garin. Kwanan su uku da komawa Goggo ta gayyaci danginta dana Baffa sukayi biki sosai duk da ba wani shiri amma Hard'o ya d'auki nauyin komai da za'a kashe, Washe gari mutum biyar suka shirya daga dangin Goggo dana Baffa, amarya tasha nasiha sosai Hard'o ya bada rak'umma wadatattu aka kama hanyar kai amarya. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/30/2016, 2:15 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 2⃣7⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 A hanya dare ya cimma su, hakan yasa suka yada zango a bakin wata babbar itaciya cikin wani k'auye, Har a wannan lokacin Hassu addu'o'i ne a bakin ta, 'Yar jakar kayakin addu'ar da babanta ya harhad'a mata a wata 'yar k'aramar jaka ta d'auko ta fara karanto wani lazimi na neman kariyar Allah daga wannan k'unzugun k'auyen da suke ciki saboda dama can kauyen yayi suna da mayun dake cikin shi, Haka ta raba dare tana jero addu'o'i duk da baccin da yake idon ta baisa ta daina ba, sai dai ta dib'a ruwa ta shafe idonta dashi idan taji bacci, Sai asubah sannan ta tashi abokanan tafiyar ta domin suyi sallah, Sunayi kuwa suka kama hanyar Bagu saboda yanzu saura kad'an su isa dan har sun wuce Zamfara ma. Sai da rana tayi tsakiya sannan suka isa garin Bagu, Babu haufi ko tsoron komai Jatau yayi masu jagora har gidan shi da duk fad'in k'auyen babu gidan mai kyanshi sannan ya fita domin ya raka Mati zuwa gidan shi, Su kansu 'yan rakiyar sunyi matuk'ar mamakin gidan Jatau, saboda tunda suke sudai basu tab'a ganin gida mai kyan wannan ba, sai tsoron gidan ma suka hau yi saboda fulani suna da wiyar yarda da mutane, sosai gidan ya burge su duk da yake ginin jar k'asa ne irin na k'auye amma fa sam a duk fad'in rugar su babu gida mai girma da kyan wannan. Da shigar su cikin gidan kuwa suka hau rangad'a gud'a da zazzak'ar muryar su, Dije ce ta fara fitowa daga d'akin ta domin ganin ko lafiya saboda gud'ar da akeyi d'in tayi yawa, Ganin manyan mata zagaye da Hassu da tasha lullub'i yasa Dije cin burki a inda take tana tunani a ranta ko su waye wannan haka. Itama Gaje fitowar tayi dan dama wani aiki ne takeyi yasa bata fito tun fara jin k'arar ba, "Bayin Allah lafiya? Su waye ku? Wa kuke nema" Gaje ta jero wannan tambayiyin a jere da juna. "Nima dai tambayar da nake shirin yi kenan amma mamaki ya hana ni yinta, malamai wa kuke nema?" Dije ta sake jefa masu tambaya. "Mun kawo amarya ne a gidan nan" d'aya daga cikin dangin mahaifin Hassu ta fad'a had'e da yin guntun murmushi, "Amarya?" Gaje da Dije suka fad'a a lokaci d'aya, "Barira fito ki jiye mana wani zance dan Allah" Gaje ta fad'a bayan ta tafa hannuwa cike da mamakin abunda waccan tsohuwar ta fad'a. "Ehh tabbas anarya muka kawo, 'yar mu Hassu muka kawo wacce mijin ku ya aura" k'anwar Goggo ta fad'a tana kallon Barira da fitowar ta kenan bayan su Gaje sun kira ta, tana cikin ban d'aki ne yasa bata fito tun shigowar su ba, saboda taji duk yanda sukayi da sauran kishiyoyin ta. "Bayin Allah gaskiya b'atan hanya kukayi, ba nan gidan bane kuke nema, ku fad'i dai sunan maigidan ko mun san gidan sai ku kwatanta maku shi" Dije tayi caraf ta fad'a tana binsu da kallon raini, *(RAZ* sukace "wai bak'auye ke raina bak'auye, hakane dama ko mahaukaci ya tsani a kira shi da mahaukaci, dan haka sai mu duba halin da muke ciki kafin mu fad'i aibun wani'). "Tabbas nan gidan ne ba wai wani gida muke nema ba, saboda tare muke da angon shine ya kawo mu kuma ya bamu izinin shigowa" waccan tsohuwar ta farko ce ta sake fad'a masu haka. "Kai a'a tsohuwa, lallai ba nan bane kuke nema, saboda mai gidan mu ya tafi farauta kuma bai dad'e sosai da tafiya ba, ya kuma ce shida dawowa nan ba yanzu ba zai jima acan, dan haka kunyi b'atan hanya ne ku tafi kawai tun kafin mu kira maku yara su kore mana ku" Bareera sarkin tsiwa ce ta fad'i haka yayin da ta turo d'ankwalin ta gaban goshi ita a dole masifaffiya. "Ke Bareerah baki da hankali ne?! Da uwar wa kike? Ki miyar da d'ankwalin nan da kika turo ko kuma in b'ab'b'alla ki a cikin gidan nan" Jatau ya fad'a saboda duk abunda suke fad'i a kan kunnen shi ne yana jinsu. A daburce ta gyara kallabin ta jikin ta sai rawa yake alamar tsoro, "Kayi hak'uri maigida wasa nake masu" ta fad'a bayan ta d'an rusuna k'asa alamar bada hak'uri. "Ehh tabbas wannan amarya ta ce na auro Hassu, kuma duk wacce ta nemi tayi mata wani abu ko kuma ta b'ata mata rai to ta tabbatar da ranar zata fad'i da hausar garin su, Hassu *'yar gata ce* dan haka ku kiyaye ni kar inji ko ingani, ina fatan kun gane?", "Eh mun gane" suka fad'a su duka ukun a tare cikin tsoro da fargaba. Izini yayiwa matan da su shiga wani d'aki wanda yafi ko wane d'aki kyau a cikin gidan, shiga da Hassu sukayi wacce har yanzu bata bud'e mayafin data rufe fuskarta dashi ba, A bakin k'ofar d'akin kafin a shiga da ita ta tsaya cak ta karanto addu'o'i sosai kamar yanda Baffa ya koya mata, Bayan ta karanto tayi sallamah ta shiga cikin d'akin take ta samu kanta da wani irin mummunar fad'uwar gaba, jikin ta sai rawa yake tamkar wadda aka fad'awa sak'on mutuwa. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [12/30/2016, 2:16 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 2⃣8⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 _Wannan shafin naki ne *QUEEN MIMI,* sak'on ki ya iso mana kuma mungode miki sosai, Allah ya baki abunda kike so duniya da lahira, Allah kuma yabar hannu da ido ya bar mana k'ungiyar NAGARTA._ **** Kakarta ta fahimci hakan yasa tace "Hassu! Lafiyar ki kuwa? Mesa jikin ki ke rawa?", "Babu komai Goggo A'i" Hassun ta fad'a wacce har yanzu jikinta bai daina rawa ba. Janta tayi ta zaunar da ita a 'yar k'aramar kujerar d'akin ita kuma ta zauna a k'asa, Kwantar da ita tayi akan cinyar ta ta ringa bubbuga bayanta a hankali tana fad'in "Hafsatutu na kiyi hak'uri kinji? Shi aure babu inda baya kai mace a fad'in duniyar nan, nasan tsoron da kikeyi kar mu tafi mu barki ko? To ki ajiye hankalin ki wuri d'aya ki saurari nasihar da zan miki" Goggo A'i ta sauke Hassu daga bisa cinyarta ta dawo da ita k'asa ita kuma ta koma kan kujerar ta fara da "kiji tsoron Allah a duk inda kike, ki sani cewa aure sunnah ce ta manzon Allah (SAW), kibi mijinki sau da k'afa, ki kula dashi, ki miyar dashi tamkar k'aramin yaro, idan kika san yana son abu kaza to karki barshi ya nemi abun, kiyi gaggawar nema masa shi ta yanda ranshi zayyi fari idan yaga abun, Kiyi masa biyayya kamar yanda sunnah ta nunar, nasan kin karanta kuma kin sani, Akwai hadisin manzon Allah (SAW) inda yake cewa "da ace an bada izini ayiwa wami sujjada bayan Allah mad'aukakin sarki to da mace ce za'ace tayiwa mijinta sujada", Wannan hadisin ya nunar mana da daraja irin ta miji kenan, A wani hadisin kuma yace "da ace mace zata lashe gyambo rub'ab'b'e mai wari na mijinta, ko kad'an bata biya ba", Kinga anan ma duk darajar miji ce aka nunar, dan haka ki kula da kyau, Ki kasance mai tsafta, ki tsaftace makwancin mijin ki, ki kasance mai gyara shimfid'ar mijin ki kafin yazo kwanciya, Koda ace mijinki ya b'ata miki rai karki zamanto mai rik'e shi a cikin ranki, Idan ya b'ata miki rai kiyi k'ok'arin fitar da komai cikin natsuwa da ladabi ki nunar mishi da bakiji dad'in abu kaza daya miki ba, Tabbas zayyi dana sanin abunda ya miki, kuma daga wannan lokacin bazai sakeyi miki wannan abun ba, Idan yana miki fad'a koda ace kinsan baki aikata abunba kiyi shiru ki ajiye hankalin ki wuri d'aya ki saurare shi, idan ya gama duka kice "yi hak'uri mai gida na baza'a sake yin hakan ba, dama wancan ma tsautsayi ne" wallahi dole jikin shi zayyi sanyi, kar yana magana kina magana sam wannan ba ladabi bane kuma kimar ki zata zube a idon shi, wani namijin koda ba mai dukan mace bane idan yana magana kina magana b'acin rai zai iya saka shi ya wanka miki mari ba tare daya san yayi ba, saboda *wasu mazan* zuciya ne dasu *wasu matan* kuwa suke koyawa mazan su duka. Idan kikaga ya nacema abu yana ta miki fad'a a kanshi kiyi k'ok'arin k'irk'iro hawaye ki sarrafa fuskarki yayin yinshi, ki ringa murmusa ido kina kuka, tabbas yin kuka a gaban miji ba zubar da kima bane d'aga daraja ce, wani irin tausayinki zaiji, zaiji kunyar fad'an da yake miki har daga k'arshe ya dawo rarrashin ki, Yanda kike yarinyar nan k'arama ki ringa zuba masa yarinta, ke koda ma ace ke babbace karki ringa miyar da kanki tsohuwa, miyar da kanki yarinyar k'arfi da yaji a gaban mijinki, tabbas bazaki tab'a zama tsohuwa ba a wurin shi koda ace kin tsufa d'in, Namiji nason mai kula dashi sosai, hakan zaisa ya zamanto tamkar kin masa asiri, duk abunda kika nunar masa da kina so zayyi saurin yi miki shi. Sannan kuma Hafasatu ki zama mai tausayi da jink'an mijin ki, ki kula da dukiyar shi bisa amana, karki zama almubazzara mai wulak'antar da dukiyar mijin ki, Ki sani cewa tausayi na k'ara k'arfafa soyayya, jink'ai yana k'ara dank'on soyayya, ina fatan kin fahimce ni" Cikin kunya Hassu tace "ehh Goggo", "Yauwa, game da kishiyoyin ki kuma ki zama mai yi masu ladabi, kinga kece k'arama a girme sun girme ki hasalima sun isa haihuwar ki, ki kula da rayuwar su, duk abunda kikaga zai iya cutar dasu ki kwatanta masu gaskiya cikin ladabi, nasan kin karanta kin san muhimmancin girmama na gaba, Bana so kiyi kishi dasu ko kad'an, ki d'auke su tamkar iyayen ki ko kuma yayyenki na jini, Koda sun miki wani abu ki koyawa zuciyar ki danne abun, kar ki ringa kai k'arar su a wurin mijin ki, Wasu matan sun d'auki kishiya abun k'yama ko kuma abun k'i, dan me mace zata haramta abunda Allah ya halalta? Allah fa da kanshi ya basu izinin auren hud'u idan zasu yi adalci, dan me mace zata hana namiji? Kedai kawoi abunda kika sani ko ince fatan ki ki zama tauraruwa a wujen mijin ki, to ki dage da faranta masa rai sai kiga kin zama abunda yafi tauraruwa ma a wurin sa, Ki dage da kwatantawa mijinki ibada, duk abunda kika sanar dashi kina da kwatankwacin ladar daya samu a kyakkyawan abunda ya aikata, Dan haka kema sai ki dage, duk sallar da zakiyi ki saka shi a addu'ah akan Allah ya tsarkake masa dukiyar sa, Allah ya bashi ikon ciyar daku, shayar daku da kuma tufatar daku ta hanyar halal, Sannan kuma naji yace bai tab'a haihuwa ba, karki matsawa kanki koda Allah baisa kin haihu ba, ita haihuw a ta Allah ce, kawai ki dage da addu'ah Allah ya shige miki gaba a raywar auren ku, zakiga komai ya tafi miki daidai". "Insha Allahu Goggo A'i zanyi amfani da duk bayanan ki, nagode k'warai Allah yabar min ke 'yar tsohuwa ta" Hassu ta fad'a cikin zaulaya bayan ta goge hawayen daya fito mata. Duk wannan bayanan da Goggo keyi akan kunnen Jatau ne, wani irin son Hassu yaji ya k'ara mamaye shi, Sai dai kuma a wasu bayanan gabanshi ya matuk'ar fad'uwa, yaji Goggo tace mata ta ringa saka shi ibada, gashi kuma Dodon shi ya hana shi duk wani nau'i na ibada, kuma tabbas bazai iya k'etare duk maganar da Hassu zata fad'a masa ba, Da wannan tunanin ne ya kama hanyar rumbun shi, saboda tunda suka iso garin bai shiga ba. Su Hassu kuma suka nufi yin sallolin dake kansu. *ku d'aure d'amarar ku masu karatu, saboda yanzu labarin GIDAN JATAU zai fara.* Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/1, 12:38 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 2⃣9⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Jiki sanyaye ya bud'e guntuwar k'ofar rumbun ya shiga, Sassauke kayakin wurin yayi kafin yaci karo da dodon shi sai matar dodon dake ta azabtuwa da ciwon nak'uda. "A gafarce ni ya dodo na! Tun d'azu muka iso ban samu halin shigowa ba" Jatau ya fad'a bayan ya rusuna k'asa cike da ladabi ya had'a hannayen shi biyu a bisa goshin shi alamar ban hak'uri. "Ba wannan ne matsala ba Jatau, naso in maka duba dangane da wannan amaryar taka duk da yake tun kafin kayi tafiya na gano akwai aure tsakanin ka da ita, matata tana cikin mawuyancin hali, tana nak'uda kuma daga ni har kai bamu san ya zamu taimake ta ba, sai dai mu zira ido mu gani saboda tun d'azu nake tsafi amma tsafin ya kasa taimakon ta, dole dai sai lokacin haihuwar yayi sannan zata haihu". Wata irin k'ara Doduwa ta saki a lokacin da kan yaron ya fito, da k'yar *dodon Jatau* ya iya saka hannun shi ya jawo mata yaron, Wani kan ne ya k'ara fitowa nan ma dodo ya jawo shi, A tak'aice dai Sai da ta haifi yara hud'u duka masu kamanni d'aya, Munana sosai abun k'yama gasu 'yan k'anana kamar 'ya'yan mage, Wani irin murmushi dodon yayi bayan ya d'auki yaran su duka hud'un yana mai mamakin wai yau shine ya rik'e yaranshi da kanshi, a ranshi yace "nima nayi tawa zuri'ar kuma dole mu yad'u a cikin garin nan, dole muyi b'arna mu k'aratar da duk mutanen dake garin sannan mu koma wani garin" ya k'ara rungume yaranshi cike daso da k'auna duk da k'azantar dake jikin su. "Jatau ya kamata a samo ma Doduwa jini mai yawa tasha saboda ta samu damar shayar da yaran mu da kyau", Shima Jatau d'in murmushin yayi tare da fita da sauri ya rufe k'ofar rumbun. K'ofar gida ya fita amma ya samu babu kowa a waje kasantuwar duhu ya fara anata kiraye kirayen sallar magrib kowa ya tafi masallaci, Wani irin haushi Jatau yaji, gashi kuma dodon shi yace masa yayi sauri ya dawo saboda yanayin halin da doduwa take ciki tana da buk'atar abunda zataci ta k'oshi, kuma ba wani abu bane face jini wadatacce da take so, gashi jinjiran ta suna ta faman kuka da k'arfi, shi tsoron shi ma kar wani yazo gittawa ta wurin rumbun yaji k'arar kukan su saboda yanda suke yinta da k'arfi lafiya lau duk wanda yazo gittawa zai iya ji. Ya kalli gabas da yamma kudu da arewa babu ko alamar mutane, yad'an k'ara gaba ko zaiga wasu mutanen amma har yanzu dai babu kowa, hakan yasa ya nufi gidan shi domin sanar da dodon shi cewa ba'a samu wanda za'a kashe abada jinin shi ba, sai dai ko idan an gama sallar magrib zuwa anjima sai ya fita ya samo mata. Shigar shi gidan yayi daidai da fitowar wata tsohuwa daga cikin dangin Hassu, yawu ya had'iya da k'arfi tare da bud'e tafin hannun shi, Idon shi ya zare sosai take idon nashi ya zama jajur kamar jan garwashi, harshen shi ya zazzalo waje wannan akaifar siririya ta fito daga yatsar shi, Tafiya yatsar ta ringayi har ta isa daidai bisa zuciyar tsohuwar, Da sauri Jatau ya shige rumbun shi jikin shi na rawa sam hankalin shi bai kwanta ba, gani yake kamar wasu sun ganshi, in banda ma doduwar shi tana buk'ace da jinin da bazai tab'a dangin Hassu ba, shidai baya son abunda zai b'ata mata rai ko kad'an kuma yasan inhar danginta wata ta mutu dole ranta zai b'aci, amma bashi da yanda zayyi sai hakan, baya son ya b'atawa dodon shi rai kodan kar asirin shi ya tonu, dan matukar ba'a shayar da jinjiran dodannin ba tabbas sai asirin shi ya tonu ta hanyar d'aga sautin kukan su da sukeyi. Ihu tsohuwar ta saki da k'arfi tare da dafe zuciyar ta, K'arar ihunta itace ta fiddo dasu Hassu daga d'aki a tsorace wasun su har sun fara sallah wasu kuma sun gama, "Baabah Bilki lafiya?" Hassun ta fad'a tana mata fufita da hijabin jikin ta, Bata samu damar bata amsa ba sai aman jini data ringayi sosai harda gullamar jini ke fita, Take idanuwanta suka kakkafe wuri d'aya, hancinta ya ringa zubar da wani farin ruwa mai had'e da majina, "Bilki ki fad'a mana me sameki? Fitowar ki kenan fa daga d'aki zakiyi alwala kuma lafiya kika fito, dan Allah ki fad'a mana meke damunki?" Goggo A'i ce ta fad'a harda d'an guntun hawayen ta. Shiru dai har yanzu tsohuwar ba magana ba kuma motsin kirki, Baki d'ayan su hankalin su yayi matuk'ar tashi, hakan yasa suka ringa k'walama Jatau kira suna neman agaji, "Jatau! Jatau zata mutu! Dan Allah kazo ka kai mana ita wurin magani" wata d'ayar mata ta fad'a bayan ta d'ora hannun ta bisa kai, Goggo A'i tace "kekam Kulu ai bana tunanin Jatau yana gidan nan, saboda sallah akeyi yanzu, mudaiyyi mata addu'ah kafin yazo sai mu kaita wurin magani tunda dai mu bamu san inda ake bayar da magani ba a garin", Jin maganganun su yasa Jatau ya tsaya tsaf, har ga Allah yayi niyyar fitowa amma kuma gwara kar ya fito d'in, saboda inhar baya gidan ba zasu tab'a zargin wani abu daga gareshi ba, "To amma kuma ya zanyi in fito? Tsaye da suke suna juran zuwa na, idan fa sukaga na fito daga nan ciki dole wata rana Hassu zata buk'aci sanin abunda nakeyi a ciki, kuma ma yanzu ai kowa sallah yakeyi ni kuma me zance masu idan suka ga ba daga masallaci nake ba?" Tambayar da yake yiwa kanshi kenan yana nanatawa. Komawa yayi cikin rumbun ya samu dodon shi cike da jin dadi har yanzu yana rungume da jinjiran shi munana, matar shi kuma ta smau jini sai faman sha take cike da farin ciki, ya fad'a masa halin da ake ciki, "Barsu, nasan yanda zanyi dasu, zan aika masu da guguwa ne duk iska ya jefar dasu, idan ka samu ka fita sai in tsayar da guguwar, kajeka kawai yanzu". Fita Jatau d'in yayi shi kuma dodo ya saki guguwar had'e da iska mai d'auko k'asa sosai, Fitowar iskarce ta jefar da sauran tsofaffi ukun dake tsaitsaye kusa da Baabah Bilki, Goggo A'i da Hassu kuwa sam iskar ta kasa yi masu komai, ko motsi basuyi ba sai addu'o'in da suka ringa jerowa suna tottofe Baabah Bilki dasu, su basu ma kula da wata guguwa da akeyi ba, wannan iko ne da kariyar Allah. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/1, 9:39 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 3⃣0⃣ Na *RAZ* ®NWA 2016 Suna cikin hakane Jatau ya lek'o kanshi waje amma da mamakin shi sai yaga su Hassu har yanzu akan Baabah Bilki suna mata addu'ah, Da sauri ya koma jikin shi na rawa ya fad'awa dodon shi halin da ake ciki, "Kawai kayi zamanka anan tunda kaga duhu ya fara, idan dare ya k'ara nitsawa sai ka fita cikin duhun ka koma bakin gida sannan ka sake dawowa, sai suga kamar a lokacin ne ka dawo, ni kuma akwai aikin da nake son inyi game da wannan amaryar taka, har yanzu ban san ya zamantakewar ku zata kasance ba kuma ya kamata ace mun san hakan a yanzu, dan haka yau aikin da zan kwana inayi kenan", "To barin jira har daren yayi" Jatau ya fad'a, har a ranshi yana fatan ace zamantakewar shi da Hassu mai d'orewa ce, baya son yaji abunda zai raba shi da ita ko kad'an. Cikin lokaci kad'an kuma iska da guguwar suka lafa, sauran tsoffin suka dawo inda su Hassu suke suna kallon sarautar Allah, Gata dai mutum ce amma kamar ba mutum ba, ta kasa aikata komai idonta har yanzu a kafe yake wuri d'aya har ya canza launi ya koma kalar d'orowa, k'wayar idon kuwa ta koma kalar k'asa, Jijiyoyin kanta baki d'aya sun fiffito bayyane duk da sumar dake kan bata hana ganin jijiyoyin ba, Addu'o'i sosai suke mata har yanzu, Wata fasaha ce ta fad'owa Hassu take kuwa ta zauna ta d'ora fuskar Baabah Bilki akan cinyar ta, Suratul-Yaasiin ta fara karanto mata k'asa k'asa a kunnenta, Gama karanta ta keda wuya jikin Baabah Bilki yahau karkarwa, lab'b'anta na rawa wasu na gugar wasu, ta ringa k'yafta ido da sauri da sauri, Cikin iko da hikimar Allah ba'afi mintina uku da gama karanta suratul Yaasiin ba aka zare rayuwar Baabah Bilki. Da yake cikin su babu wanda yasan mutuwa, hasali ma babu wanda yayi tunanin Baabah Bilki zata mutu dan basu bata mutuwa ba, sai gashi kuma ta mutu, Sukam dad'i sukaji a lokacin da sukaga ta rufe idonta sunyi tunanin ko sauk'i ne taji ta kwanta bacci, Hakan yasa sauran suka koma ciki, Goggo A'i da Hassu kuma suka tsaya kanta har yanzu basuga alamar ta mutu ba. Saida dare ya fara nitsawa an gama sallar isha sannan Jatau ya lallab'a ya sulale k'ofar gida, Yana fita kuwa yaci karo da Mati yazo wurin shi, "Ahh abokina Mati kaine a daren nan?", "Ehh wallahi Jatau nine fa, haka kawai nace gwara inzo mu gaisa in kuma ji lafiyar amarya", "Ka kyauta kuwa aboki na, mu shiga daga ciki" Jatau ya fad'a tare da nufar cikin gidan Mati na biye dashi. Sallamah Mati yayi suka k'arisa ciki, Da hanzari Hassu tace "sannunku da zuwa" ba tare da tasan ko su waye ba saboda bataji muryar Jatau ba, kuma gashi cikin duhu ne. "Yauwa Hafsatu, zaman me kuke a waje duk sanyin nan?" Jatau yayi naganar kamar baisan ko meke faruwa ba. Kunya taji sosai da taji muryar Jatau, ita dai kunyar shi take ji sosai, koda yake ba abun mamaki bane, ansan fulani da kunya, kaaraa da kuma kawaici (sis R. Tace fulanin daa keda wannan banda na yanzu). "Barin karb'o fitila d'akin Bareerah yanzu, naga kamar cikin duhu kuke" Jatau d'in ya fad'a bai jira ta bashi amsar tambayar daya mata ba. D'akin Bareerah ya shiga ya d'auko 'yar fitilar k'wan dake d'akin ta wadda keci kad'an kad'an alamar babu kalanzir a cikin ta, Haka nan d'in ya d'auke ta ya tafi d'akin shi da ita ya kashe sannan ya d'ura kalanzir ya sake kunnawa tayi haske sosai. Tsakar gidan ya koma da ita ya haska inda su Hassu suke har yanzu tana rungume da gawar Baabah Bilki, duk yanda tayi nauyi sosai itakam bataji ba, dan bata tab'a kawo mata mutuwa ba. "Ya akayi ne? Waye ne a kwance?" Jatau ya fad'a a rikice bayan ya k'arisa inda suke. "Rik'e min fitilar nan Mati aboki na" ya mik'awa Mati fitilar bayan ya zauna a daidai inda suke. "Me sameta ne?" Ya fad'a a rikice kamar da gaske, Goggo A'i ce tace "wallahi kawai fa alwalar magrib ta fito, shine fa daga fitowar ta ta fasa k'ara da k'arfi muka firfito, tun daga nan bata kuma magana ba sai fa yanzu da bacci ya d'auke ta", "To amma Goggo kunsan da haka mesa baku aika an kirani ba? Ai ba'a shiru irin wannan, ko kuma ai sai ku kira abokanan zaman Hafsatu tunda su sunsan mazaunar da nake zama, koda yake dai yau tun sallar magrib ina masallaci sai yanzu na fito" yayi masu k'arya. "k'addara dai ta riga fata, dama zaman jiran zuwanka muke ka kaimu inda ake bayar da magani a duba ta, wata k'ila ko maye ya kamata, tunda in ba maye ba me zaisa lafiyarta k'alau a lokaci d'aya ta fad'i? Koda shike kuma ikon Allah ya wuce ban mamaki" Goggo A'i ta fad'a hannunta bubbiyu a kumcinta tayi tagumi. "To abunda za'ayi ku d'auke ta mu tafi, akwai wurin wani boka ya iya duba sosai, zai duba mana abunda ya same ta", "Boka!?" Hassu da Goggo A'i suka fad'a a tare idanuwan su zazzare suna mamaki sosai. Kame kame Jatau ya fara kwata kwata ya manta da cewa sufa ustazai ne ba irin shi ba, ashe ba kowa ke zuwa wurin boka ba, "Ehh...wa..wasa nake maku dama dan inji me zaku fad'a, akwai wata mata tana bada magani sai muje can a duba ta, ku tallabe ta muje" Jatau ya fad'a a daburce yana dana sanin maganar daya fad'a a baya, sub'utar baki ce kawai. K'ok'arin kamata suka fara amma suka kasa saboda mugun nauyin da tayi, ganin sun kasa ko motsa ta yasa Jatau ya fara taimaka masu amma shima ya kasa d'aga ta, Idon shi zare yace "nikam fa kamar ba bacci take ba", "Idan ba bacci take ba me zaisa ta rufe idon ta kuma kamar tana bacci?" Goggo A'i ta jefo masa tambaya, "Goggo ki kalla fa kamar bata numfashi, anya tana da rai kuwa? Mati zo ka gani" Jatau ya kira Mati dan ya taya shi ganin halin da Baabah Bilki take ciki. Mati ya duba ya kuma tabbatar mashi da Baabah Bilki ta rasu, Kuka sosai suka fasa hakan yasa sauran ma suka fito daga cikin d'aki, hatta su Dije saida suka fito dan dama duk suna jin halin da suke ciki tun d'azu, tsabar kishi ne ya hana su fitowa su taimaka masu tun kafin Jatau ya dawo. Sai da sukayi kuka mai isar su sannan sukayi shiru, sunyi tawakkali ga Allah saboda mutuwa tana kan kowane bawa, kuma idan lokacin mutuwar mutum yayi babu dabara dole a duk inda yake sai ya tafi. Cikin wannan darenMati da Jatau suka sanar da mutane akan za'ayi jana'ozar ta da safe, Kwanan keso Baabah Bilki tayi Su Hassu suka kwana sunayi mata addu'ah, Washe gari limamin garin da kanshi yazo, Hassu da Goggo A'i suka mata wanka, babu jinkira aka kaita tabbataccen gidanta. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/2, 11:01 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 3⃣1⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 Bayan rasuwar Baabah Bilki da kwana biyu su Goggo A'i suka fara haramar komawa gida, Hassu ce zaune tayi tagumi saboda har yanzu jin mutuwar Baabah Bilki take tamkar a mafarki, wasu siraran hawaye suka ringa sauka daga kumcinta wanda bata ma san da fitowar su ba, ita dai kawai tasan tayi zurfi a tunani ne, "Hassu lafiyar ki kuwa?" Goggo A'i ta fad'a bayan ta jawo kujerar katako ta zauna tana fuskantar Hassu. Saurin share hawayen tayi ta d'anyi murmushin yak'e tace "lafiya lau Goggo, me kika gani?", "A'a ba lafiya ba Hafsatu, in lafiya me zaisa ki kalli gabas kina hawaye, Ina so ki kwantar da hankalin ki ki cire ko wace irin damuwa daga ranki, idan ma tunanin mutuwar Bilki kike to ki cireta a ranki, in banda abunki ke da k'ananan shekarun ki zaki ringa sakawa ranki damuwa? So kike wata cutar ta kama ki?", "A'a Goggo", "To ki daina kinji? Duk mai rai mamaci ne, idan ma kina tunanin kamar a silar kawoki ne Bilki ta rasu to ki daina, saboda koda ba saboda ke ba dole anan k'asar ta take, ki fawwalawa Allah komai kuma ki d'auka a ranki cewa ko ke da kike lafiyayya zaki iya mutuwa a kowane lokaci, dan haka addu'ah kawai zakina mata, ita kad'ai ce hanyar da zaki nuna soyayya a gareta ba wai kuka ba", "Insha Allahu bzaan sake yin kukan ba Goggo" tayi murmushi tana kallon ta. "Yauwa jikalle ta, dama ina son na fad'a miki ne muna son komawa garin mu gobe, in banda ma rashin da muka samu ai da tun shekaranjiya mun koma, ya kamata ace mu koma hakanan saboda kinsan nayi kewar mai gidana nima" tayi dariya tana kallon Hassu. "Lallai ma tsohuwar nan, ku har wata kewa kuka sani?" "Kiji min 'ya, wato kune kawai kuka san kewa ko?", "Ah nidai Goggo ban fad'a ba, gani nayi wannan tsohon miye abun kewa a ciki, nasan dai wasa kike ba wata kewar shin da kikeyi". "Bari dai ki gani, wannan yarinyar idan ba na tsuleta ba ba zata shafa min lafiya ba" Goggo ta fara zaro zaborin tsintsiya tana shirin tsulawa Hassu ita. Da sauri kuwa Hassu ta shige k'uryar d'akinta ta turo k'ofar tana dariya. Da dare Jatau ya shiga wurin su Hassu da fura a leda ya siyo masu, saboda ya fuskanci cimar su da tasu ba d'aya bace, dan haka yafi gane ma ya siyo masu fura da nono ya kawo masu su dama da kansu. Bayan ya gaishe da Goggo ya mik'a mata ledar hannun shi, "Jatau dama kuwa akwai maganar da nake so muyi da kai", Take jikin shi ya fara b'ari yayi zaton ko wani abu ne, neman wurin zama yayi yace "lafiya dai ko Goggo?" "Lafiya k'alau, maganar komawar mu gida ne, muna so idan babu takura gobe mu kama hanya, kaga ya kamata mu koma kodan mu sanar dasu mutuwar Bilki saboda basu sani ba har yanzu", "Sun sani kam Goggo, tun washe garin da akayi rasuwar na tura d'an aike ya sanar dasu, kuma kafin ya dawo saida yaga sun samu kwanciyar hankaki sannan, amma dai duk da hakan ya kamata ku koma ko hankalin su zai k'ara kwanciya, kai! Allah yaji k'an Baabah Bilki" ya fashe da kukan munafurci. "Kayi hak'uri kayi shiru mana Jatau, kaifa namiji ne ba mace ba, dan me Hassu zatayi kaima kuma kayi? Dan Allah ka daina mana", "Goggo dole nayi kuka, ta dalilin mu fa Baabah Bilki ta rasu", "Kar na kuma jin wannan maganar a bakin ka Jatau, ba saboda ku ta rasu ba, lokacin ta ne yayi kuma babu makawa sai ta tafi, koda ace a gidan take dole zata tafi, kayi shiru bana son in sake jin kukan ka", "To shikenan Goggo, gobe da sassafe kuke son tafiya ne? Dan akwai wanda nake son nayi ma maganar amalanken shanu idan zaku tafi, sai ya fitar daku daga nan ku samu abun hawa ku tafi, idan ba haka ba kuma dole sai dai ku taka da k'afarku har sai kun fita", "To da dai asubanci muke son muyi, amma tunda haka ne zamu shirya da safe, duk lokacin da yazo d'in tafiya kawai zamuyi", "To shikenan Goggo sai da safen, ya Hassun ko tayi bacci?" Jatau ya fad'a har da d'an rufe fuska shi a dole yaji kunya. "Tayi bacci tun d'azu, kasanta da bacci kamar kaasaa", "Ina jin kunyar ki Goggo, gaskiya ki daina kiranta da kaasaa" ya fad'a cikin zolaya, "Au! Dama kunyar k'arya kaji kenan? Lallai yaran zamani ba kunya, Allah ya shirya min kai Jatau". Da haka yayi bankwana da ita ya shiga rumbu wurin dodon shi. Da shigar shi kuwa ya samu dodanniya (munji kuma mun fahimci gyaranki sis, hausarce kin san kowa da kalar tasa, insha Allahu ba zamu kuma amfani da kalmar doduwa ba sai dodanniya kamar yanda kika shawarce mu) tana shayar da yaranta, abun mamaki kan nono hud'u gare ta kowane yaro d'aya yaja nashi kan, basu da kyan sifa, Itadai Kande har yanzu sai kallo, hatta da haihuwar da dodanniya tayi duk a gabanta ne, sosai take k'yamar su, ita a yanzu tama cire ranta da fita daga wannan rayuwar, dan tasan abu ne mai matuk'ar wahala ta fita d'in, Allah dai shine gatanta kuma shi take fad'awa matsalarta a koda yaushe, tun tashinta bata saba da rashin sallah ba, sai gashi yanzu rabonta da yin sallah har bata san adadin watanni ba, tun kafin Jatau ya sato ta ya kawo shi gidan ta. "Dodo na dawo ne akan waccan maganar, tun jiya kace baka ga komai ba amma yau abunda zaka wuni kanayi kenan, ince dai ko yanzu an dace", "Ba'a dace ba Jatau, har yanzu na kasa ganin komai barin in fahimci wani abu a tsakanin kai da amaryar ka, nayi k'ok'arin sanin dalilin hakan na kasa, dan haka dole muyi hak'uri, amma a tunani na akwai alheri a cikin tarayyar ku, zata hayayyafa, zansha jinin yaranta, zakayi arzik'i da jinin yaranta, zaka kuma k'ara samun d'aukaka sosai fiye da tunanin ka *(RAZ* dai sukace tirk'ashi!!!). "Haka nake son ji ya Dodo na", "Dije tana d'auke da juna biyu amma k'arami ne dan ko ita har yanzu bata san tana dashi ba, don haka ka aiko min dashi cikin daren nan, nida iyali na muna da buk'atar abinci dama", "To yanzu kuwa" Jatau ya fad'a tare da fita daga rumbun ya nufi d'akin Dije. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/3, 12:50 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 3⃣2⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 A cikin wannan daren Jatau ya nemi salwantar da abun cikin Dije da ko ita kanta bata san tana d'auke dashi ba. Wani irin natsanancin ciwon ciki taji ya turnuk'e ta, hakan yasa ta tashi zaune hannunta rik'e da marar ta, Hawaye ne kawai ke zarya a idonta, Tayi bakin k'ok'arinta dan ganin ta daure amma ta kasa, Da k'arfi ta k'walawa Gaje kira, "Gaje!", Shiru Gaje bata jita ba kasantuwar akwai 'yar tazara tsakanin d'akunan su, sannan kuma dama Gaje akwaita da nauyin bacci. "Gaje!!" Ta k'ara k'wala mata kira amma har yanzu shiru. "Dan Allah kuzo ku taimakeni zan mutu" ta fad'a da k'arfi tare da ciccije lab'b'anta cike da alamar ciwo da rad'ad'i. Shiru Hassu tayi dan ita a tunaninta ko mafarki take, jin har yanzu Dije batayi shiru da k'wala kiran ba yasa ta tashi zaune tana k'ara karkad'e kunnenta. "Ku taimakeni dan Allah zan mutu" ta k'ara fad'i da k'arfi. Caraf Hassu ta tsallako su Goggo A'i ta fito daga d'akin ta k'ara kasa kunnuwanta dan jin kota ina ne murya ke fitowa. Babu ko tsoro Hassu ke tafiya lungu da sak'o na cikin gidan, duk da duhun dake cikin gidan baisa taji tsoro ba, Sautin kukan Dije tajiyo a lokacinda ta tinkaro d'akinta. Da sauri kuwa ta shiga ciki, kasantuwar akwai duhu cikin dak'in yasa bata ganin komai dake cikin sa, "Waye ba lafiya ne?" Ta fad'a a hankali. "Nice bani da lafiya, cikina da marata kamar zasu fashe saboda ciwo, tunda nake ban tab'a ciwo mai azabar wannan ba, kuma ni nasan banida ciki barin ince ko b'ari ne zanyi, duk da b'arin da nayi da yawa ban tab'a mai irin wannan ba, bana tunanin b'arin ne ma" ta k'arisa maganar da kuka sosai. "Kiyi hak'uri Yaya, gashi kuma babu haske barin in d'ebo ruwa in miki addu'ah ko zaki samu sassauci" Hassu ta fad'a cike da tausayi. "Kinga wata gata nan kusa dani, barin lalabo miki ashana sai ki kunna, ki taimake ni dan Allah" ta fad'a tare da lalaben gefenta har taci karo da ashanar. K'yasta ta tayi take kuwa d'akin ya d'auki haske, karb'a Hassu tayi ta kanga ta ga fitilar k'wan take kuwa ta kama. Haskawa tayi ta fita da ita waje ta nufi randa, a rufe ta tayar da ita dan haka ta bud'e ta d'ibo ruwa kad'an a tasar shan ruwan su ta dawo d'akin Dije da ita. Bayan ta ajiye fitilar ne ta kanga tasar a bakinta ta ringa karanto addu'o'i tana tofawa a cikin ruwan, Ta dad'e tanayi kafin ta bama Dije ruwan tace "kisha da niyar kina neman waraka daga Allah, saboda shine kad'ai mai warkar da bawa". Karb'ar ruwan Dije tayi ta kuwa k'udura a ranta tana neman agajin Allah, ta kuma kad'aita shi domin babu mai bada waraka sai shi, ta kwankwad'e ruwan baki d'aya sannan ta ajiye tasar a k'asa tace "nagode sosai Hafsatu, kuma dan Allah ki gafarce ni akan abunda na miki ranar da aka kawo ki, *a rashin sani* (Ummul-Fadeelah) ne ban san haka kike ba, ban tab'a tunanin akwai ranar da zaki taimake ni ba, tabbas hausawa sunce "d'an hakin daka raina shike ji maka ciwo" gashi kuwa na gani, ki yafe min Hassu" ta fashe da kukan nadama saboda wani irin sassauci taji tana samu, a hankali ciwon marar da cikin suke raguwa. Rungumeta Hassu tayi tace "ki daina fad'ar kin b'ata min rai Yaya, ni ban rik'eki a rainaba, dan haka Allah ya yafe mana baki d'aya, Allah kuma ya baki lafiya". Haka Hassu ta zauna tare da Dije har saida ta samu sauk'i sosai bacci ya d'auketa sannan ta sake tofeta da addu'ah ta fito ta nufi nata d'akin, Bayan ta shigane da gudu *RAZ* suka sameta, Rabiatu tace "dan Allah kiyi hak'uri zamu d'an tsayar dake munga kamar bacci kike son kiyi kuma gashi muna son muyi miki wasu 'yan tambayoyi", Murmushi ta miyar mana dashi tace "babu komai *RAZ,* ba bacci nakeji ba kuyi tambayarku kawai", Zarah tace "waikam menene kika karanta ma Dije da har ta samu sauk'i lokaci d'aya ta daina jin duk ciwon da takeji bacci ya d'auketa?", Abune mai sauk'i na karanta mata, kamar yanda manzon Allah (SAW) ya shawarce mu da idan d'ayan mu bashi da lafiya mu ziyarce shi, sannan kuma mu karanta masa _As'alul-Lahul-Aziimu, Rabbal-arshil-Aziimu, anyashifiyaka_ idan kuma mace ce sai muce _an yashfiyaki,_ k'afa bakwai na karanta mata, Sai kuma na k'ara da _laa ba'sa d'ahuuran insha Allahu ta'ala,_ k'afa d'aya ita kuma, na tofa a ruwan na bata tasha". Ni Amrah nace "lallai kam wannan addu'ah ce mai kyau, munji kuma mun d'auka insha Allahu, sannan kuma zamu sanar da ita ga dubban mutane masu bibiyar labarin mu, muna fatan jama'ah zasu amfana da ita", Rabiatu tace "to mungode sosai takwarar *Hafsatul-Kiram,* tabbas kina da kyawawan hali tamkar mai irin sunanki, ki kwanta kiyi baccinki" ta sakar mata murmushi irin na farin cikin nan. "Ba bacci zanyi ba 'yan uwana, indai har zan kwanta inyi bacci a yanzu da dare ya raba tsakiya to kuwa da babu babbar asararriya kamar ni, a daidai wannan lokaci ne al'arshin Allah yake kusantarmu, anaso ko farkawa mutum yayi daga bacci yaci karo da wannan lokaci koda bai tashi yayi sallah ba daga inda yake kwance yayi salatin manzon tsira (SAW) koda k'afa d'ayane, sannan ka rok'i Allah buk'atunka na alkhairi ka koma ka kwanta, lallai zaka samu dace a wannan lokacin". "Kekam Hassu masha Allah! Iyayenki sunyi sa'arki, sun baki kyakkyawar tarbiyayya, kinada sani daidai gwargwado kuma gashi kina sanar damu, muna miki godiya sosai Allah ya saka miki da alkhairinsa, muma bari mu gudu muje mu rok'i Allah ya biya mana buk'atunmu" na fad'a tare da mik'ewa, suma mik'ewar sukayi sannan muka fito, Hassu kuwa ibadarta taci gaba dayi sosai har asubah tayi ta tashi su Goggo domin suyi sallah dan taji sunce asubanci suke son suyi. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/4, 11:21 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 3⃣3⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 HBD *Ruk'ayya Auwal Mashi,* Allah ya rayaki ya k'aro shekaru masu albarka. Allah ya kawo mana ranar da zamusha shagalin bikinki. Wannan shafin sadaukarwace gareki *Basman mai sanyinta,* sak'onki ya iso mana kuma munyi farin ciki sosai, tabbas samun k'awa kamarki a wannan lokacin yana wahala, Allah ya bar zumunci ameen. **** Washe gari da sassafe kuwa suka gama shiri, bayan sun zazzauna ne Dije ta shigo d'akin fuskarta a sake, Har k'asa ta duk'a ta gaishe dasu Goggo sannan tace "sannu Hafsatu, ya gajiyarki?", Murmushi Hassu tayi tace "kinjiki Yaya, wace irin gajiya kuma?", "Hmm! Nagode sosai Allah ya saka miki da alkhairi, kinga ashe juna biyu nake d'auke dashi ban sani ba, har ma yayi k'ok'arin zubewa amma kuma bai fitan ba, saboda tun sassafe na tafi gidan Tani mai magani, ta duba min kuma ta harhad'a min magunguna tace inci gaba da shansu insha Allahu babu abunda zai samu cikina bana, kin san haka muke mu, duk cikin da mukeyi bama haihuwarsa sai dai ya zube, idan munyi sa'a mun haifeshi kuma sai ya mutu". "Allah sarki! To bayan magungunan ma sai ki dage da addu'o'i ba dare ba rana kina sanar da Allah matsalarki, ki daure da tashin dare kina salloli da rok'on Allah, zakiga da yarda da amincewarsa cikinki ya samu lafiya ya zauna, nima kuma insha Allahu zan tayaki da addu'ar" Hassu ta fad'a tana mata murmushi. "Nagode miki kuwa sosai, sannan kuma ina mai k'ara neman yafiyarki, ki yafe min dan Allah", "Bana son kina wannan maganar Yaya, tun jiya kinyi min wannan maganar nace miki na yafe miki ki daina tadota, amma kuma kink'i ki daina, kin manta Allah ma muna masa laifi kuma mu rok'e shi gafara ya yafe mana? Danme ni zank'i yafe miki?", "to shikenan Hafsatu, Allah ya kawar da fitina a tsakaninmu, barinje nasan Gaje ta gama damun koko a kawoma su Goggo" ta tashi ta nufi waje. Bayan fitarta ne Goggo A'i ta tambayi Hassu dalilin godiyar da Dije keyi, tayi mata bayanin komai, Goggo tace "kin kyauta sosai kuma naji dad'in abunda kikayi, ina alfahari dake Hafsatu, kin gaji iyayenki sosai Allah ya miki albarka". Bayan sun gama karyawa duka Jatau yazo da wanda zai tafi dasu, Harda kukan rabuwa sukayi Hassu nata sheshshek'ar kuka Dije ke rarrashinta, Babu yanda ta iya a gabanta suka kama hanya a cikin amalanken shanu. Daga nan Jatau ya shiga rumbu, da shigarshi ko zama bayyi ba dodo ya kwatsa masa tsawa da k'arfi wadda saida ta gigitashi, Hankali tashe ya rusuna k'asa yace "me na maka ne ya dodona? Lallai nasan na maka wani babban laifi tunda har kayi min wannan tsawar, to sai dai kuma bansan ko wane irin laifi bane nayi" cike da tashin hankali yake yin maganar. "Karka raina min hankali mana Jatau! Tun jiya da dare munyi dakai zaka aikomin da jinin abun cikin Dije, kasa iyalina sun saka rai amma kak'i ka kawo masu, mesa idan kasan bazakayi ba baka fad'a min ba tun wuri? Kasa yara sunata kuka na rasa yanda zanyi dasu, ka b'ata min rai sosai Jatau!". Cikin rashin fahimta Jatau yace "nikam nasan na gama komai tun jiyan, na turo maka jinjirin cikinta, amma kuma bansan mesa kace baka ganshiba", Shiru dodo yayi yana nazari kafin yace "akwai rikitarwa a wannan lokacin, ni kaina nayi mamakin hakan, baka tab'a sab'amin maganaba, baka tab'a cewa zakayi kuma bakayiba, amma sai gashi jiya munyi magana ka sab'a", "Ban sab'a maganaba ya dodona, tabbas na aiko dashi saidai ko wata matsalarce b'oyayya wadda bamu santa ba" Jatau yayi maganar cikin girmamawa. "Bari zan duba zan gano matsalar yanzu" *dodon jatau* ya fad'a bayan ya fara 'yan tsaface tsafacenshi yana rufe ido, Bayan ya bud'e idonshi yayi bak'i k'irin babu ko alamar haske a cikinshi, Murza idon yayi sosai sai gashi ya koma sak idonshi yanda yake da, Sakeyin tsafin yayi ya rufe idonshi ya bud'e, yanzun ma dai bak'i k'irin yake kamar d'azu, Saida yayi har sau uku amma duka sakamakon d'ayane, Da k'arfi ya kad'a kanshi yace "akwai matsala! Akwai babbar matsala Jatau". Cikin firgici Jatau yace "matsala kuma? Tame kenan?", "Ta komai ma Jatau, na kasa ganin komai game da wannan matsalar, idona ya kasa gane min komai akan abun cikin Dije, Da zarar nayi k'ok'arin lek'a cikinta sai in ringa ganin wani farin haske ya dabaibaye ta, na rasa kome yake damuna". Shiru Jatau yayi cikin rud'ani kanshi ya sark'e gabaki d'aya, yama rasa abunda zayyi, shi kanshi dodon ya rasa abunda zayyi, dan haka su dukan sukayi shiru kowa da abunda yake sak'awa a ranshi. Can Dodo ya nisa yace "ina ganin wannan karen zan damk'awa matata wannan aikin ko zata iya, ta jima tana son na bata wani aiki amma ina k'i, tunda dai wannan ya gagareni k'ila ita zata iya, ka kwantar da hankalinka bana son ganinka cikin rashin walwala da jindad'i, kajeka gobe komai zai daidaita, karka dawo yau sai gobe da safe, tabbas zakaji labari mai dad'i. Juyawa yayi ya fita cike da farin cikin jin maganar da dodonshi yayi ta k'arshe, yanzu kam hankalin shi ya kwanta sosai, rufe rumbun yayi bayan ya fita ya nufi d'akin Hassu yana washe baki. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/5, 11:26 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 3⃣4⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 A daren ranar ne Jatau ya kusanci Hassu a matsayinta na matarshi, sosai yaji mata raunuka kasantuwar bai iya bin mace a hankali ba saboda sam baisan hak'k'in hakan ba, Sosai Hassu tayi mamakin yanda ya kusanceta bayyi addu'ah ko d'aya wadda akeso ango yayi ga amaryarsa, da kuma wadda akeyi yayin kusantar mata, Duk da rawarda jikinta keyi saboda tsoro bai hanata samu ta karanta addu'ar ba. Koda suka gama Hassu jiki babu kuzari da rarrafe ta fita daga d'akin, takalminta ta jawo da k'yar ta tattaka har ta isa band'aki tayi wankan tsarki sannan ta dawo d'aki. Da dawowarta ta tayar Jatau yayi kwanciyar ruf da ciki har bacci ya fara d'aukarshi, Bubbugashi tayi yayi saurin tashi had'e da yin mik'a, "Lafiya dai masoyiyata?", Shiru tayi taji kunya sosai saboda ko had'a idonta ta kasayi dashi, "Wanka nace bakayi ba maigida" ta fad'a kanta sunkuye k'asa tana wasa da 'yan yatsunta. "Wanka kuma? Wane wanka kike nufi zanyi cikin wannan daren? Ai saida safe ni nakeyin wanka" ya fad'a cikin muryar bacci. "Innalillahi wa innaa ilaiji raji'un!" Ta fad'a a asirce, "kardai jahili na aura wanda baisan hukuncin wankan tsarki ba, Allah gani gareka". "Wanka kikayine ke? Naga jikinki kamar a jik'e, kin samu sabulun da kikayi wankan dai ko?" Jatau ya fad'a yana mata kallon soyayya. "Maigida wankan tsarki nayi fa, ai ba'ayinshi da sabulu da soso" "Hm um, kece kikasan wannan nikam bansanshi ba" Jatau ya fad'a tareda komawa ya kwanta saboda shikam bacci yakeji a gajiye yake. Kwanciyar ruf da ciki ya sakeyi itakam Hassu tama rasa abunda zata fad'a, tana jin ana fad'in akwai jahilai a duniya bata tab'a had'uwa dashi ba sai yau, wai da girmanshi da tsufarshi amma baisan wankan tsarki ba, kenan duk zaman nan Jatau bashi da tsarki? Matanshi fa uku a halin yanzu, su kuwa duk wane irin jahilan matane wanda basa nunarwa mijinsu da hanyar gaskiya? Akwai matsala kenan, ya zama mata dole ta fara gyara gidan tun wuri ma. Sake bubbuga Jatau tayi, "menene kuma?" Ya tambayeta dan haushinta yakeji ta hanashi yin bacci kuma gashi yana tsananin son yin baccin. "Maigida wata kwanciya naga kayi wadda addinin musulunci ya haramtata" "Wace kwanciya kenan Hafsatu? Dama addini harda wata kwanciya ya halalta da kuma wadda ya haramta?" Jatau ya fad'a bayan ya tashi zaune. "K'warai kuwa akwaita maigida, kwanciyar nan wadda kakeyi ta ruf da ciki batada kyau ko kad'an, Saboda akwai wata rana da manzon Allah (SAW) tare da sahabbanshi suka tafi yak'i da sauran mutanen Madina da yawa, A wannan yak'in kafirai suka samu nasarar kashe musulmai da yawa musulman ma suka kashe kafirai sai ya zamanto gawarwakin kafirai dana musulmai sun had'e sun yamutse wuri d'aya. Bayan an gama yak'in ne wasu sahabbai suka samu manzon Allah (SAW) sukace "ya manzon Allah! Gawar kafirai dana musulmai sun had'e wuri d'aya gashi kuma muna son mu ware na musulmai domin a sallacesu, amma bamu san ya zamu tantance musulmai ba", Sai manzon Allah (SAW) yace "ku duba duk wanda sukayi kwanciyar ruf da ciki sune kafirai kar muyi masu sallah, wanda kuma sukayi sab'anin haka kuma sune musulmai su zaku kawo mu sallace su". Hakan kuwa sukayi, suka kwaso gawarwakin wanda basuyi kwanciyar ruf da cikin ba, masu ruf da ciki kuwa acn suka barsu saboda ba musulmai bane. Kaga kuwa malam ai kwanciyar ruf da ciki ba abun kirki bane, bai kamata mu musulmai mu ringa yinta ba saboda yanda manzo ya misilta masu yinta, ina fatan zaka gyara ka kuma fahimceni maigidana". Shiru Jatau yayi yana wani tunani, yasan matuk'ar dodonshi ya gano halayyar Hassu to tabbas zaisashi ya rabu da ita, saidai kuma har yanzu dodon ya kasa gane komai gameda Hassu. "To nagane Hafsatu, kuma bazan k'ara yinta ba" Jatau ya fad'a harda d'an guntun murmushinshi "Nagode sosai angona, sai kuma magana ta biyu kafin mukai ga babbar", Zamanshi ya gyara sannan yace "ina jinki amaryar" "Ya kamata ace kafin komai ya shiga tsakanin mu munyi alwala, munyi sallar nafila kamar yanda manzon Allah (SAW) ya umurci dukkan amarya da ango suyi, Sannan idan an gama akwai addu'arda akeyi, Zaka dafa kaina da hannun damarka kace "Allahumma inni as'aluka khairaha wamin khairuma jabaltaha alaihi, wana'udhu bika min sharriha, wamin sharrima jabaltuha alaihi". Sannan kuma a yayinda zaka shigeni zakace "Allahumma jannibnasshaid'ani ma, wa jannibnasshaid'ani ma razak'tana" daga nan kuma sai kayi duk abunda kake so sannan kuma zakabi a hankali saboda bi ta hanyar tsiya tamkar yin fyad'e ne". Sosai Jatau ya kasa hankalinshi yana sauraren Hassu kamar da gaske, ita kuwa da zuciya d'aya take sanar dashi, saboda wani hak'k'ine wanda ya rataya gareta, tunda ita ta sani shi bai sani ba fole zata sanar dashi cikin hikima. Ta nisa sosai sannan tace "abu na uku kuma shine babbansu wato wankan tsarki, zan maka bayanin yanda akeyinshi da kuma sharud'd'anshi" "To ina jinki". Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/6, 9:09 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 3⃣5⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 Tabbas duk wanda zai maka gyara akan wani kuskure wanda ya kasance kana aikatawa to babu kamarshi a doron k'asa, *Maman Affan* ta group d'in miemiebee, kin mana gyara ko kuma ince kin kawo mana k'orafinki akan munayin gajeren shafi wanda kuma hakan ne, bawai kece ta farkon kawo mana wannan k'orafin ba, amma kuma ta hanyarda kika kawo mana k'orafince tayi mana dad'i sosai saboda sak'one wanda kikayi amfani da k'walwa, hikima da kuma fasaha da kuma nuna tsantsar soyayya a garemu, *RAZ* sunji dad'in wannan k'orafi naki kuma sak'onki ya isar masu, saboda jindad'in soyayyar da kika nuna mana yasa *RAZ* suka sadaukar da wannan shafin gareki *Maman Affan keda baby'n mu Affan,* Allah yabarmana ke ya k'ara dank'on soyayya, soyayyarki ta shigar mana a zuci sosai. Mungode😘. ****** "Shidai wanka ya kasu kashi uku wato manya manyan da manzon Allah (SAW) ya kawo mana, Akwai wankan janaba, wankan haila sai kuma wankan bik'i (wanda akeyi idan jinin haihuwa ya d'auke). Bayansu kuma akwai wanka wanda suke na sunnah ne, ba'a wajabtasu ba amma kuma duk wanda yayisu yanada lada mai girma, misali wankan jumu'ah, sunnah ce yinshi saboda manzon Allah (SAW) yayishi ya kuma shawarci al'ummar musulmai suyishi, Yanzu dai mu koma kan wanda suke wajibi wato guda ukun dana kawo, Zan maka bayanin janaba saboda itace take taka, haila da bik'i garemu mata yake, da sannu zamu koma kan wancan d'inma duk zaka sansu. Janaba shine fitar maniyyi daga gaban namiji ko kuma mace, idan ruwan maniyyi ya fito koda baka sadu da mace ba wankan janaba ya wajaba, ya wajaba ga duk wanda ya fitar da wannan ruwa yayi wanka, wankan shine..." tayi masa bayanin yanda akeyin wanka sosai tun daga farillai, sunnah har zuwa mustahabban wanka. "Dan haka yanzu ka tashi kaje kayi wanka kayo alwala mu gabatar da sallar nafilarda manzon Allah (SAW) ya shawarcemu da muyi, ko yanzu lokaci bai k'ure ba". Tashi yayi jiki babu k'wari, ba wai kuma dan ya gamsu da bayananta ba, amma a yanda ya nunar tamkar ya gamsu da bayanan ne, hasalima bai rik'e abu ko d'aya data fad'a masa ba, Har ga Allah yana tsananin tsoron kar asirinshi ya tonu ga dodonshi, saboda alk'awari ya masa akan shida sallah har abada, shikam yanzu baisan yanda zayyi ba, gashi kuma bazai iya k'etare maganar Hassu ba. Shawara kawai ya yanke akan ya shiga rumbunshi har sai gari ya waye sannan ya fito, inyaso sai yasan abunda zai tsarama Hassu idan ya fito d'in da safe. Kai tsaye rumbu ya wuce, ya samu dodo zaune matarshi da yaranshi kuwa a kwance suna barci, Bayan ya shiga ya gaishe da dodonshi yace "Jatau kaine haka cikin daren nan? Lafiya?", "Lafiya k'alau ya dodona, na kasa baccine nace barinzo muyi hira", Murmushi dodo yayi, yayi shiru sannan yace "ba lafiya ba Jatau, akwai matsala", "Ba wata matsala fa, bacci yak'i d'aukana ne" Jatau ya fad'a yana murmushin yak'e. "To yayi kyau sosai, dama kuwa kamar kasan akwai maganar da nake son muyi dakai, amma kuma kafin nan, matata ta fara aiki akan abun cikin Dije, saidai kuma itama d'in ta kasa yin komai saboda har yanzu cikinta haske yake idan ta dubashi, Ta yanke hukuncin ta kashesu baki d'aya saboda akwai matsala, Dije ta dage da ibada da salloli yanzu, ina tsoro fa kar wani asirin dake tsakaninka da ita ya kare, saboda indai tana addu'ah dole za'a karb'a mata ita, dan haka kai ya ka gani? Za'a kashetanne ko kuwa a barta asiri ya kare ta fallasaka kowa yasan halinka?". Da sauri Jatau yace "a'a kawai a kasheta, yanzu ma idan ka shirya kawai ka kasheta d'in ya dodona". Dariya dodo yayi da k'arfi yace "a shirye nake Jatau, amma dayake banine zanyi aikinba matatace satayi, barin tasheta a barci yanzun nan tajeta ta kasheta ta kawo mana jininta, kaga musha riba biyu kenan, ga jininta dana abunda ke cikinta". "Tabbas hakane kam, a d'aukota kawai a kawota anan sannan a aiwatarda abunda za'a mata". Dije kuwa tana can ta d'aga hannu sama tanata kwararo addu'o'i akan kariyar Allah, tana fatn Allah ya kare mata abunda yake cikinta. (Batayi fatan Allah ya kareta ba saidai kawai ta abun cikinta take) Tana cikin yine matar dodo ta iso, tsayawa tayi cak ta kasa shiga d'akin saboda addu'arda Dije keyi a bayyane tana ambaton sunan Allah, Ta kasa yin komai tana tunanin ta tafi kota tsaya, amma kuma ba zata iya tafiya ba saboda tama mijinta alk'awarin duk yanda zatayi sai tayi dan ganin ta cika masa wannan aikin daya bata na farko koda ace zata mutu ne" Wata irin k'ara ta saki da k'arfi wadda ta saitata a daidai d'akin Dije, saboda ita kad'ai takeson taji k'arar bada kowaba, Da farko Dije bata ankara da k'ararba, sai a karo na biyu sannan ta jiyo wani irin sauti mai had'e da kururuwa a cikin kunnuwanta, Sosai hankalinta ya tashi, ta nemi addu'arma ta rasa sai rawar jiki take, sam ta kasa tuna sunan Allah ko d'aya tsabar tashin hankali da take ciki. Da hakan matar dodo ta samu damar shiga d'akinta, Da zahirin sifarta ta shigar mata, Kallo d'aya Dije tayi mata ta kawarda kanta tare da fasa ihu da k'arfin gaske, saidai kuma aikin banza babu wanda zai iya jinta, Tunda take bata tab'a ganin halitta mai munin wannan ba, gata bak'a k'irin jikinta duk gashine, hancinta da bakinta a had'e yake sai ido guda uku, hak'oranta hud'u kacal biyu sama sai biyu k'asa, Dije ta kasa fad'in komai har yanzu sai mik'ewa da tayi daga bisa sallayarta ta ringa ja da baya baya matar dodo na binta har ta isa bakin bango babu hanyar guduwa, Dariya ta saki da k'arfi tare da fizge hijabin jikin Dije ta jefar kan gadon kararta, Ta cire d'ankwalinta shima tayar, Da k'arfi taja ganshin kanta sama itama tayi sama suka fita ta rufin k'asar d'akin, Basu isa ko inaba sai rumbun Jatau, A daidai gaban *dodon Jatau* ta ajiye Dije sannan ta sunkuya tama mijinta sujada ta koma gefe wurin 'ya'yanta. "Tabbas kin cika jaruma, kinyi aiki mai wahala sosai, duk abunda ya faru na gani daga inda nake, kinyi dabara kinyi aiki da hankalinki, dan haka dole na miki kyauta, jinin farko na amaryar Jatau nakine, saboda muna daf da kashe yarinyar dan na fara tsorata da ita, na kasa gano komai akanta, saisa nakejin tsoronta har na fara ayyana wani abu a raina, ki koma kiyi kwanciyarki ki huta, idan na gama da ita ke kad'ai zakisha jinin abun cikinta". Jatau na zaune ko a jikinshi, dama bawai yana sonta bane barin ya damu dan wani abu ya sameta, bai tab'a jin yana son mace ba sai Hassu, koda yaji dodo ya ambaci za'a kashe Hassu wani irin haushi yaji a ranshi, amma kuma bashida yanda zayyi, koda ace yace zai kashe Hassu dole ya hak'ura, saboda bazai tab'a iya yima dodonshi musuba saboda shine abun bautarshi, baisan wani abun bautaba saishi, kuma ga wani sabon salo datake neman ta kawo masa, duk yanda yake sonta zai iya hak'ura da ita akan ya rasa dodonshi, dan yasan matuk'ar ya rasa dodonshi tofa tashi ta k'are, ya rasa komai kenan kuma dole sai asirinshi ya tonu. D'aga kanta tayi taci karo da Jatau, Sosai hankalinta ya tashi tana tunanin meya kawota nan? Me zasu mata? me had'insu da mijinta Jatau?, Batasan a bayyane tayi maganarba saida taji Jatau yace "abun bautana kenan, kasheki zamuyi saboda kina yin addu'ah kin hanamu fitarda abunda yake cikinki, kuma abun cikinki namune, bazamu tab'a barin d'aya daga cikin matana wata ta haihuba, a haka zasu dawwama babu 'ya'ya, kekam taki ta k'are yanzu, duk wanda yasan sirrinmu dole sai ya mutu" ya k'yalk'yale da dariya da k'arfi cike da mugunta. Kallonshi kawai take hawaye na mata ambaliya daga idanuwanta, a ranta tace "ashe dama Jatau shine yake kashe mana yara? Ashe haka addu'ah takeda matuk'ar tasiri? Tabbas addu'ar da Hassu ta koyamin itace ta kare min cikina, kuma tsayawarda nayi lokacinda naji wannan k'arar saisa har ta samu damar d'aukoni, kuma dama a addu'ar ai abun cikina kawai na nemarma kariya ban rok'a hardani ba, dole in dage da addu'ah ko Allah zai kub'utar dani daga hannun wannan azzaluman, kuma matuk'ar na fita saina tona asirin Jatau munafuki kowa yasan halinshi". Jin Dodo ya fara tsafi sosai yasata yin addu'ah da k'arfi tana kuka, Sosai ran dodo ya b'aci najin addu'arda takeyi, A fusace ya mik'ar da zungureriyar yatsarshi daidai fuskar Dije take ta sank'are wuri d'aya ta koma daidai inda Kande take, Tsaf yanda yayima Kande itama haka yayi mata, ta kafe wuri d'aya idonta ya tsaya cak ko motsi batayi. Cikin fushi dodo yace "wannan matar taka taso ta rusa min tsafina mai k'arfi, ban tab'a samun wanda yamin hakaba, bazan tab'a shan jinintaba, dole zaka hak'ura da ita da abun cikinta, zata dawwama a haka kamar yanda waccan yarinyar Kande zata dawwama". Jatau yace "kayi daidai ya dodona, kayi mata duk abunda kaga dama bazan tab'a ganin laifinka ba, duk abunda zakayi daidaine a gareni, haka kuma duk umurninda zaka bani dole zan bishi komai d'acinsa komai dad'insa". Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/7, 4:44 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 3⃣6⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 Baabah Haja ce zaune tayi tagumi baki d'aya ta rasa abunda ke mata dad'i, yau kimanin watanni shida zuwa bakwai kenan babu Kande babu alamarta, gashi kuma duk lokacin da Larai tazo ta mata maganar Kande sai ta b'ata rai tayi k'ok'arin kawar da maganar, sosai wannan al'amarin yake damunta, Itakam ta tabbatarda ba lafiya ba, dan inda ace lafiya Kande ba zata d'auki har tsawon wannan lokacin ba tare da tazo inda take ba. Shawara ta yanke kawai akan zataje gidan Mati duk da yake bata tab'a zuwa ba tunda take a rayuwarta, Tashi tayi ta yafa mayafinta ta kama hanyar gidan, tana tafiya tana tambaya saboda bata san gidan ba, kawai dai tasan unguwar. Wani yaro ta tambaya gidan take kuwa ya gwada matashi, Sallamah tayi taja tayi tsaye cak tana k'arema gidan kallo, ashe haka yake? Ita tunda take ko a mafarki bata tab'a tunanin zata zo gidan abokan gabarsu na iyaye da kakanni ba. Sallamar ta sakeyi a karo na biyu daidai fitowar Baseeru daga band'aki, Tsantsar mamaki ya hanashi amsa sallamar, sai gani yake kawai mafarkine yakeyi, "Yau Baabah Haja ce a gidanmu?" Ya tambayi kanshi a cikin zuciya baisan maganar ta bayyana ba. "Ehh nice Baseeru, nazo biko ne", "Ikon Allah! Biko kuma Baabah? Shigo dai daga ciki su Innah na d'aki". Bin bayanshi tayi ya isar da ita d'akin Innah, Bayan tayi sallamah taja tayi tsaye bata shigo ba, "Baseeru kaida wayene?" Larai ta fad'a tana lek'en 'yan hudojin asaberin dake jikin k'ofarta. "Innah ki rufe idonki zan baki mamaki ne" Baseeru ya fad'a yana murmushi. "Toh! Mamaki kuma?", "Ehh Innah mamaki, kawai ki rufe kiga ikon Allah", "Hmm! To na rufe" ta rufe idonta tam fuskarta d'auke da murmushi dan tasan halin Baseeru da shirme wata k'ila ma ba abun kirki bane. K'ofar d'akin ya koma yajawo hannun Baabah Haja ya shigo da ita ciki, daidai gaban Innah ya dakatar da ita yace "ki bud'e idonki kigani" Da sauri kuwa ta bud'e idonta taci karo da Baabah Haja, Cike da murna ta tashi ta rungumeta tana fad'in "yau kakatace a gidanmu? Lallai nafi kowa farin ciki, sannu sannu da zuwa" ta saketa tare da jawo tabarma ta shimfid'a mata. Shima Matin fuskarshi da murmushi yace "sannu Baabah Haja, munji dad'in zuwanki sosai", "Yauwa sannu Mati jikana" ta fad'a tare da miyar masa da murmushi. Ita kanta wani irin dad'i takeji wanda ta dad'e bataji irinshi ba, lallai shaid'an ya dad'e yana mata hud'ubar banza, tagode Allah da yanzu ta gane gaskiya, kuma zataci gaba da kula dasu har sai lokacinda mutuwarta ta d'auketa. "Gero da wake ne muka dafa Baabah, barin kawo miki yanzu" Larai ta fad'a bayan ta tashi tana k'ok'arin fita daga d'akin. "A'a Larai, ki kawo min ruwa kawai ya isheni", "A'a nidai Baabah gaskiya sai kin cishi, yaushe rabonda kici abincina? Tun na k'aramar sallah fa, ko babbar sallah bamu samu damar kai miki abinci ba, kuma daman k'uli k'uli ne akwai dad'i", "To naji uwar magana, jeki kawo min kad'an kuma ki dawo muyi magana". Madafarsu ta shiga ta nemi tasar data saba kai mata abincin sallah ta sako mata gero da waken kuwa a ciki, ta barbad'a k'uli k'uli da mai sannan ta kawo mata, Bayan ta ajiyeshi a gabantane tace "saura ruwa ya rage, barinje in kawo yanzu" ta fita, nan da nan kuwa sai gata ta ciko kofin tasa da ruwan tulu mai sanyin gaske. "Nikam ina yaran sukene? Baseeru kawai na gani" Baabah ta fad'a bayan ta bud'e tasar abincin tana k'ok'arin fara kai loma. "Sun tafi makaranta kuwa, shima Baseerun amai da gudawa yake saisa baije ba, amma suma d'in nasan suna hanyar gida yanzu" Larai ta fad'a tana kallon Baabah Haja. A hankali ta fara cin abincin cike da farin ciki da annashuwa, Mati da Larai ma wani irin dad'i sukeji wai yau Babah Haja ce a gidansu, wannan babban abun mamaki ne kuma abun farin ciki. Kafin ta gama cin abincin kuwa saiga Audu da Talle sun shigo, Audu rik'e da allonshi da hawaye sun fara bushewa a fuskarshi. Da sauri ya shigo d'akin yana kallon Mati yace "baba kaga wai kawai saboda malaminmu ya tura yaya Talle ajinmu ya koya mana karatu shine ya sameni ya ringa duka waishi a dole mai adalci, dan sauran 'yan ajinmu suce harni k'aninshi ma ya duka, kuma fa baba babu abunda na masa" ya k'arisa maganar da fashewa da wani sabon kukan. Jawoshi Mati yayi gabanshi yace "yi hak'uri Audu, sau nawa nake ce maka ka zama mai hak'uri ne wai? Ai Talle yayanka ne ko yankaka yayi yanada damar yin hakan, dan me zaka ringa fad'in wannan maganganun game dashi? Ka daina indai kana son karmu b'ata". Shiru yayi yana ajiyar zuciya kamar wani k'aramin yaro, sai yanzu ma suka kula da Baabah Haja dake kallonsu tun shigowarsu tana murmushi. "Ahh Babarmu ce a gidan namu?" Talle ya fad'a bayan ya jawo kujera ya zauna. Gaisheta yayi ta amsa kafin tace "yana ganku ku biyu? Kardai kuce min a hanya kuka baro 'yar k'anwar taku". Kallon kallo suka ringayi su duka dake d'akin dan sam basu fahimci zancen Baabah Haja ba, "K'anwarmu kuma? Wa kike nufi kenan?" Baseeru ya tambaya. "Kai karka rainan hankali fa, wace k'anwar gareku bayan Kande?". "Kande? Wacece kuma haka? Dama akwai wata Kande gidan nan ne bayan wadda ta mutu tunda dad'ewa?". Tsaye ta mik'e tana kallonsu d'aya bayan d'aya saboda tama rasa abunda zata fad'a, Wata tambayar banza taji suna mata, wai kodai basu gane abunda take fad'a bane? Ko kuma zaulayarta ce suke? Amma kuma ai basu janta wasa, Laraice kawai ke janta wasa yanzu kuma tamayi shiru tana tunanin itakam bata san wata Kande ba a yanzu. "Larai kiyi magana mana kinyi min shiru? Ina Kande take?" Baabah Haja ta fad'a cikin zafin rai. "Baabah kin manta cewa Kande ta mutu tunda dad'ewa?" Larai ta b'ata amsa cikin natsuwa. "Bangane Kande ta mutu ba, kai karfa ku miyar dani shashasha wacce bata san abunda take ba, yaushe Kande ta mutu da har baku sanar dani ba? Mesameta nece ku fad'a min ya akayi ta mutu?" A zauce tayi maganar muryarta na rawa saboda sosai hankalinta ya tashi. Wani irin juyi Audu yaji kanshi na masa, yana k'ok'arin tuna wasu abubuwa amma ya kasa, tabbas yasan Kande, ya kuma san ya daina ganinta amma kuma baisan lokacinda ta mutu ba. Da k'arfi Baabah Haja ta fad'i k'asa ta sume, Baki d'aya hankalinsu ya tashi, hankalinsu ya koma gareta, Larai na fad'in "Audu kawo min ruwa" Amma Audu baima san tanayi ba, yayi nisa a tunanin 'yar uwarsa wadda bazai iya rik'e komai nataba, ya manta kamanninta ya manta komai gameda ita. "Dakai fa nake Audu" Larai ta sake fad'i amma har yanzu baisan tanayi ba. "Wannan wawa ne dan Allah Baseeru ka kawo min ruwa in yayyafa mata ko zata tashi, wallahi ita kad'ai gareni, itace kawai ta rage min bana son ta tafi ta barni itama" ta k'ara fashewa da kuka. Mati ma a daburce ya ringa bubbugata amma shiru ne, ruwan Baseeru ya kawo aka yayyafa mata a fuska amma har yanzu ko motsa hannunta batayi ba, Hakan yasa Mati yace "ko zamu tafi da ita wurin magani ne? Bai kamata mu zauna da ita a hakaba, ki d'auko mayafinki mu tafi". Da sauri kuwa Larai ta d'auko mayafinta, saidai kuma tana zuwa ta tayar Baabah Haja ta farfad'o, A hankali take magana "wani irin ciwo nakeji wanda ban tab'a jinshi ba, nasan wannan ciwon bana tashi bane, tun daga k'asan zuciyata nakejin wani ciwo har zuwa bisa k'irjina, Mati ka yafe min tsawon lokacin dana d'auka bana shiri dakai ina gaba dakai, ku yafemin in akwai wani abu dana maku na sab'awa, nasan banida magani a halin yanzu, dan haka na mallaka miki komai nawa Larai, kuma ni inaji a jiki na Kande na raye bata mutu ba, kawai dai akwai wani b'oyayyen al'amarin ne wanda Allah kawai ya barma kansa sani, dan haka duk lokacinda Allah yasa ta dawo gareku ku rok'a min yafiyarta saboda d'an Adam ajizine, naso in sameta in rok'i yafiyarta saboda rabuwarmu ta karshe nasan na b'ata mata rai har tayi ik'irarin bazata sake zuwa inda nakeba, ashe kuwa hakan ne" ta kara fashewa da kuka. "bazaki mutuba Baabah, zafin ciwone kawai" Larai ta fad'a tana kuka a hankali. Suna cikin hakane kuwa malakul mauti ya ziyarci Baabah Haja, babu b'ata lokaci kuwa ya zare rayuwarta. Lokacinda suka gane ta rasu ba kad'an ba hankalinsu ya tashi, sun shiga tashin hankali sosai, kuma duk maganganun Baabah Haja baisa ko kad'an sun tuna da Kande ba, Audu ne kawai ya tuna da ita amma kuma ya kasa tuna komai a kanta. Haka aka kaita tabbataccen gidanta, Larai kamar zata zauce haka tayi, da yake batada yanda zatayi dole ta hak'ura ta mik'awa Allah lamurranta, sai addu'ah kawai data k'udura a ranta cewa zatana yima kakarta har lokacinda itama tata mutuwar zata risketa. **** Gaje ce ta fito daga d'akinta kasantuwar shirun da taji har yanzu Dije bata shigo inda takeba kamar yanda ta saba, D'akin Dijen ta shiga amma tajita shiru babu ita, hakan yasa ta k'arisa shiga ciki tana fad'in "yau matar d'akin nan jego takene?". Har yanzu shiru tajita hakan yasa tayi tunanin ko tajeta band'aki ne, Zaman jiranta tayi amma har rana ta fito babu Dije. Wurin sauran abokan zamanta taje ta fad'a masu bataga Dije bafa. Hassu ma tace tunda safe ta shigo ta dubata da jiki amma bata ganta ba. D'akin Jatau suka shiga su duka ukun, sun sameshi yana bacci bai tashi ba, "Maigida, maigida ka tashi" Gaje ta tasheshi. Zabura yayi ya tashi yana mitsitssika ido, "Lafiya?" Ya tambaya cikin muryar bacci. "Kasan inda Dije taje kuwa? Tun d'azu fa muke nemanta bamu gantaba", . "Mene? Baku gantaba? To ina tajene?" Ya tamhaya kamar da gaske baisan inda takeba d'in. Salati suka d'auka su duka ukun, Hassu tace "maigida ka tashi mu fara nemanta, gata kuma mun rabu da ita jiya batada lafiya, ba abun ayi shiru bane wannan fa". Tashi yayi suka ringa nemanta, har gidan iyayenta sukaje amma duk batajeta can ba, baki d'ayan inda suke tunanin zataje sunje duk bata nan, hakan yasa suka dawo gida a gajiye hankalinsu a tashe na rashin abokiyar zamansu, musamman ma Hassu da take jinta kamar 'yar uwarta ta jini. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/8, 3:48 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 3⃣7⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 Yinin ranar haka sukayishi babu walwala a tare dasu, Hassu kamar zautacciya ta koma, ta rasa abunda ke mata dad'i, wai ace mutum ya b'ata lokaci d'aya kamar wani cokali ko k'aramin abun anfani, wannan magana abun a dubace. Bareerah da Gaje ne zaune duk sunyi jigum_jigum kowa da abunda yake sak'awa ranshi, basu tab'a sanin matsayin Dije yakai har haka a cikin ransu ba sai yanzu da babu ita, lokaci d'aya duk sun susuce kamar basu ba. Zama Hassu tayi a daidai inda suke ta dafa cinyoyin Dije tace "ni a gani na bai kamata ace mun dawo mun zauna ba, b'atar mutum fa ba b'atar tufafi bane, ya kamata mu tashi mukai cigiya da sanarwa gidan maigari ko Allah zaisa a dace". Bareerah ta share hawayenta tace "lallai kin kawo shawara *mai kyau* (Mr. Smiles), amma wannan ai namiji ya kamata yakai wannan maganar gidan maigari ba mace ba". Gaje ta gyara samanta tace "maigida ne kawai ya kamata yaje amma kuma duk cikinmu babu wacce zata iya tunkararsa da maganar, dan haka ni a ganina k'wara kawai mujemu da kanmu gidan maigarin, tunda dai nasan zai sauraremu". Caraf Hassu ta mik'e tsaye tace "dan me zakuce babu wacce zata iya tunkararsa? Wannan fa babbar maganace ba k'arama ba, kuma dole sai namiji ya shiga cikinta saboda ba lallai bane maigari ya sauraremu barin har a d'auki wani matak akai, kuma ai matarsa ce dole zaijeshi yayi duk abunda ya dace". "Tab! Wayene mai zuwa ya tinkareshi da maganar? Bari kiji wani abu Hafsatu, duk abunda mukeso komai tsananin son da muke masa indai ta hanyar maigidane dole muke hak'ura, koda kike ganina da fad'a fa iyakacin fad'ana anan ne, ban isa inja da maganarshi ba, ko yana magana bai yarda wani yayiba, idan ma abinci mukeso dole mu hak'ura sai sanda yaga damar bamu, kuma bamuda yanda muka iya dole muyi hak'uri da hakan saboda tsarinshi kenan, kuma tun farkon zuwan kowace macen gidan nan yana gindaya mata wannan sharud'd'an kuma dole tabisu". Bareerah ce tayima Hassu wannan bayanin k'asa k'asa dan bata so Jatau yaji maganarsu. "Ai kuma wannan ya kawarda komai Yaya, taya za'ace Yaya Dije ta b'ata cikin daren jiya kuma muna nan zaune? Dole fa musan nayi, ni zan sameshi da maganar saidai duk abunda zayyi yayi" ta tashi da sauri ta nufi hanyar d'akinshi ba tare da shakkun komai ba. Ta sameshi kwance ko a jikinshi kan shanyayyar katifarshi, Bayan tayi sallamah ya d'ago kanshi cike da mamakin shigowarta, A ranshi yace "wannan kodai batasan dokokina bane? Anya kuwa tasan ba'a shigo min d'aki sai idan ni na bada izini? Koda yake ai laifina ne, nine soyayyarta ta hanani in fad'a mata dokokina har gashi tana neman aikata abunda babu macen data tab'a ko tunkarar aikatashi". Maimaita sallamar tayi kasantuwar tunanin da yayi nisa a ciki yasa bai amsa sallamar ba sai a karo na biyu da tayi. "Alaika_sshalemu" ya fad'a bayan ya tashi zaune yana kallonta, yana sauraren ta fada masa abunda ke tafe da ita. Wani irin haushinshi taji sosai a ranta, tsabar jahilci ma ko amsa sallama bai iyaba cikakkiya, lallai akwai aiki a gabanta ja, saboda tasha alwashin duk sai ta gyara masa komai, ta miyar dashi mutum, saboda yanzu kam mutum mutumi ne tunda baisan komai akan addininsa ba. Saitin inda yake ta zauna a k'asa tace "sannu da hutawa maigida", "Yauwa sannu Hafsatu amaryata" ya fad'a yana mata kallon soyayya, shi kanshi yana mamakin irin soyayyar da yake mata, soyayyarta ta hana ya gindaya mata kaf sharud'd'anshi gashi kuma har tana neman zarcewa hurumin da ba nata ba. "Maigida wata maganace nazo da ita idan ba zaka damuba". Ta fad'a kanta k'asa tana wasa da yatsunta. "Ina jinki masoyiyata Hassu" ya fad'a bayan shima ya sauko k'asan inda take ya fuskanceta ya rik'e yatsunda take wasan dasu ya ringayi nata da kanshi cikin soyayya. "Akan maganar Yaya Dije ne Maigida, kaga shiru har yanzu babu labarinta, shine nace me zai hana aje gidan maigari a bada cigiyarta ko Allah zaisa a dace?", "Hassu kenan, lallai ke yarinyace har yanzu, in banda abinki idan ma saceta akayi waye zai yarda ya saketa barin har a ganta idan anyi cigiya? Ya kamata ku sani Dije fa ba yarinya bace, ba wadda za'ace ta b'ata bane, ni a ganina kawai dai ta gudu ne da gangan, wata k'ila akwai wata manufane a ranta dama, a tunaninku waye zaizo cikin daren nan ya saceta? Ita kad'aice cikin gidan da itace kawai za'a sace? Mesa bamuji alamar wani ya shigo ba? Kawai dai guduwarta tayi" Jatau yayi k'arya. Shiru Hassu tayi, wani b'angaren na zuciyarta na fad'a mata hakan zai iya zama gaskiya, mafi rinjayen zuciyarta kuma na fad'a mata ba gaskiya bane, akwai dai matsala. "Nidai maigida wannan alfarmace na nema, dan Allah a taimaka aje akai cigiyar tata, kasan ba'a san inda za'a dace ba", "To shikenan Hassu zanje yanzun nan tunda dai kina so" ya fad'a dan baya son yaci gaba da musu da ita har ta fara harbo jirginshi. "Yauwa nagode da wannan alfarmar maigida, ga sallar magrib can ana kira kajeka masallaci, kaga daga can ma sai ka biya ta gidan mai gari ka sanar dashi d'in", "To babu damuwa barin tashi in tafi" ya mik'e ya jawo rigar sanyinshi daya rataye jikin katakon da yake rataye kayakinshi. Bayan ya sakane ya fita tabishi a baya, Bareera da Gaje kuwa mamaki suke sosai ta yanda Hassu ta shiga d'akinshi babu shamakin komai kuma suka fito harda murmushi yake mata, lalllai wannan amarya tashi kam ya d'auketa da daraja da kuma muhimmanci. Koda fitarshi bai tafi masallacin ba, wuri ya nema ya zauna yanata dariyar farin ciki, lallai matanshi wawaye ne, ya bugar dasu babu wacce ta fara ganin ko alamar gaskiya, amma da yake dama ya rigada ya asircesu, Hassunce kawai bai asirce ba, itama kuma dan tafi k'arfinsu ne, har yanzu dodo ya kasa yi mata komai, yama kasa ganin komai akanta barin har yasan abunda zaiyi mata. Saida yaga mutane suna gittawa alamar an gama sallah kenan, hakan yasa ya tashi ya kama hanyar gidan maigari, A daidai gaban masallaci yayi kicib'is da Mati ya fito, Cikin ladabi Mati yace "sannu Jatau abokina, kwana biyu ka b'oye, ko duk amaryarce ta b'oye mana kai??", Murmushi Jatau yayi yace "wallahi kuwa duk itace Mati, ai auren k'ananan yaran nan dad'i gareshi, ni'ima ce babba sau wanda yayi kawai yake ganewa, kaima ka gwada ka gani sai ka shimin albarka", "Abokina Jatau kenan, aini Larai d'ina ma ta isheni bana neman k'ari saboda bata rageni da komai ba, duk abunda nakeso tana k'ok'arin yiminshi, idan ina cikin damuwa tana k'ok'arin kawarmun da ita, idan inada matsala tana k'ok'arin gyara min ita, kullum burinta shine ta kawo min farin ciki a cikin gidana, kaga kuwa bana buk'atar wata mace ni, mena rasa? Ina samun komai daga gareta, ina iya auren wata ta kawo min tashin hankali a gida bayan kuma yanzu hankalinmu a kwance yake, wannan dai saiku Jatau", "Lallai Mati kai wawa ne, waya fad'a maka sai an rageka da wani abu kake neman aure? Ai zama da mata d'aya tsautsayine, yanzu idan Larai tayi tafiya, ko kuma tayi maka wani rainin hankali, kaga idan da wata wurinta kawai zakajeka ta kawar maka da komai, dan Allah karka bani kunya mana", "Hmm! Abar maganar kawai Jatau, yanzu dai ba wannan ba, dama akwai maganarda nakeson na maka, kasan kuwa kakar Larai ta rasu? Wannan tsohuwar wadda bata k'aunata", "To to to to to, nagane ta, wannan masifaffiyar tsohuwar wadda ta nemi ta hana aurenka da Larai, ta mutu kenan" Jatau ya tambaya dan sam bai san ta mutu ba. "Wallahi kuwa tsohuwa lokaci yayi, kawai wai matar nan tazo min da wata magana wai munada wata 'ya mai suna Kande, ni ban ma santa ba, kawai dai rud'ewar tsufane ya kamata, shine Larai tace mata kota manta Kandenmu ta rasu tunda dad'ewa? Wai tsohuwar nan tace itakam bata yarda Kande ta rasu ba, ta tabbatarda tana raye kuma wata rana zata dawo garemu, kaji faa", Hankalin Jatau ya soma tashi da wannan kalaman, cikin kid'ima yace "um...a...llallai kam tsufane yasa ta fad'in haka, wacece kuma Kande?", "Wadai ya sanar mata? Shine fa ta fad'i ta sume daga nan, bayan mun samu dak'yar ta farfad'o kuma sai mutuwa", "Wayyo ta mutu ashe?" Jatau ya sake tambaya dukda ya fad'a masa ta rasu. "Wallahi kuwa ta rasu Jatau, kuma saida ta nemi yafiyarmu sannan ta rasu, kuma tsabar rud'ewa da tayi fa wai harda cewa tayi idan Kande ta dawo mu rok'ar mata gafararta", A ran Jatau yace "aikuwa Kande ta tafi kenan har abada ba zata sake dawowa ba, amma da yake ta mutu ma shikenan ai, ta hutarma kanta", A zahiri kuma yace "to shikenan ai ta kyautawa kanta, Mati ko zaka rakani gidan Maigari ne? Matata Uwargida fa ta b'ata tun jiya cikin dare, yau mun yini muna nemanta amma bamu sameta ba, shine na yanke hukuncin zuwa gidan mai gari ayi cigiyarta ko za'a dace", "Subhanallahi! Dije ta b'ata? Abu bayyi dad'i ba kuwa, shine kuma kake nan hankalinka a kwance?" "To ya zanyi abokina, so kake inta rusar kuka?", "A'a ba haka nake nufi ba abokina Jatau, yanzu dai muyi sauri muje kar lokaci ya k'ure maigari yabar fada, kuma kasan idan ya koma cikin gida dole sai gobe sannan zai sauraremu", "To mu tafi" Jatau ya fad'a. Hanyar gidan maigari suka nufa kuwa, sunyi sa'a kuwa yana fada da sauran fadawansa. Har k'asa Mati ya duk'a ya gaisheda maigari banda Jatau da yayi tsaye k'erere yak'i fad'ar komai, Kasantuwar duhu ya fara yasa maigarin bai gane ko waye ba, dan haka yace "Mati kaida wayene?", "Nida Jatau abokina ne yallab'ai". Abun mamaki sai ga maigari ya mik'e tsaye yace "ashe kaine Jatau mai sa'a, ai ni ban ankare da kai ba, ka zauna mana" cikin ladabi yayi maganar kamar Jatau ne shugabanshi. A gatsine Jatau ya zauna, shima maigarin zama yayi, "Jatau akwai matsalane?" Maigari ya tambayeshi. "Ehh akwai" Jatau ya fad'a a tak'aice. Maigari ya sallami duk mutanen dake fadar ya zama daga shi sai Jatau da Mati, Bayan ya gyara babbar rigarsa yace "ina saurarenka Jatau mai sa'a, ince dai ba laifi mukayi ba?", "Ba laifi kukayi ba, Mati yi masa bayani". Bayani Mati ya masa gameda b'atar Dije, duk k'aryar da Jatau ya gilla masa saida ya fad'i bai rage komai ba, Shiru mai maigari yayi kafin yace "to in kuwa hakane Dije da kanta ta gudu kamar yanda kuma d'in kukayi tunani, tunda ai ba itace kad'ai a gidaba da har za'a shigo ciki a saceta, lallai akwai wani abu a k'asa, amma dai duk da haka za'ayi cigiyar, yanzu cikin daren nan ma za'a fara, kuma za'a jera kamar kwana uku zuwa hud'u anayi, daga nan indai babu ita sai a hak'ura a barma Allah komai". "To yayi daidai" Jatau ya fad'a tare da zira hannunsa cikin aljihu, babu komai a cikin aljihun amma da mamaki saiga kud'i yana zarowa d'aya bayan d'aya yana ajesu gaban maigari, shi kuwa ya washe hak'ora yana sud'ar leb'onshi. A gidan Jatau kuwa shiru sukajishi gashi kuma duk yinin ranar ba'aci komai ba, kuma ga yunwa suna ji, Tun fitar Jatau Hassu take tambayarsu inda kayan abinci suke amma sunk'i fad'a mata, saboda suna jiye mata tsoron kar ta zarce inda ba huruminta ba, ganin ta nace yasa Bareera tace "kinga wancan rumbun? Acan komai na abinci yake, saidai kuma ya gargad'e mu sosai akan rumbun, bamu kad'ai bama, tunda muke a cikin gidan nan bamu tab'a ganin wani ya lek'o rumbun can ba barin ya shiga ciki, Jatau ne kawai yake shigarsa, wani lokacin ma a ciki yake yini, mun rasa gane abunda yakeyi a cikinsa, ke wani lokacinma har kwana yanayi a cikinsa". Mik'ewa Hassu tayi tace "nikam bazan yarda mu kwana da yunwa ba, yanzu zanje in d'ibo mana abinci mu dafa" ta nufi hanyar rumbun. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/10, 10:02 AM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 3⃣8⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 Ta bud'e 'yar k'aramar k'ofar rumbun zata shiga kenan Jatau ya shigo, Baki d'aya ya susuce yama rasa abunnda zai fad'a lokacinda ya hangeta tana neman shigar rumbunshi, lallai Hassu wuyanta ya isa yanka, yanzu kam dole zai d'aukar mata hukunci duk da sonda yake mata. "Ke Hassu!" Cak ta dakata saboda yanayin yanda ya kirata bai tab'a yi mata haka ba. "Karki shiga! Nace karki shiga rumbun nan". Juyowa tayi cike da mamakin yanda yake yi mata magana, "Na'am maigida" ta fad'a tana kallonshi. "Waye ya baki izinin shiga rumbun nan? Abokan zamanki basu fad'a miki bana bari a shiga ciki bane" Jatau ya tambayeta a fusace. "Sun fad'a min maigida, gani nayi yunwa na neman kashemu, kuma gashi baka dawoba duk yinin yau bamuci komai ba, saisa naga gwamma in shiga in d'ebo mana mu dafa ko zamu samu sassaucin yunwar da mukeji, gashi kuma nice da girki". "Lallai baki da hankali Hassu" ya matso daf da inda take tsaye gaban rumbunshi "Ki shiga taitayinki dan naga kina neman zarcewa daga huruminki, ruwa ba sa'an kwando bane, kiyi k'ok'arin kawar da idonki daga al'amurrana, kiyi koyi da abokanan zamanki, ki tambayesu su k'ara miki bayani game dani, idan baki hankalta dani ba kuwa, hmmm!" Ya wuce d'akinshi fuuuuu cike da fushi. Bareerah da Gaje ne tsaye suna kallon duk abunda ke faruwa, kusa dasu ta dawo ta zauna ta fashe da kuka tace "wai yanzu shikenan muna matan gida amma bamu da wani 'yanci? Bamuda 'yancin d'ibo abinci mu dafa a lokacin da mukeda buk'ata?", "Kiyi hak'uri ki daina kukan, saida muka fad'a miki ai kika k'i yarda, wallahi kinji na rantse duk inda kike zaton Jatau ya wuce nan, sam baya tsoron Allah, burinshi a koda yaushe yaga ya tauye mana *Hak'k'i* (Ayusha Iliasu)" Bareerah ta fad'a tare da sharema Hassu hawaye. "Dan Allah inaso ku bani labarin Jatau, bansan komai game dashiba, cikin lokaci kad'an aka d'aura mana aure hakan yasa babu halinshi wanda na sani, dan Allah ku sanar dani abunda kuka sani a kanshi da kuma akan wancan rumbun nashi" ta nuna rumbun da yatsarta har yanzu bata daina zubarda hawaye ba. Saida Gaje ta kalli d'akin Jatau taga babu ko alamar fitowarshi sannan tace "ke! Ki rufawa kanki asiri wallahi, ina miki tsoron abunda ya faru ga Rabi kema ya sameki, dan itama shishshigi tayi a rayuwarsa", "Me kenan ya samesu? Dan Allah ki cire tsoronsa ki bani labari, harda tsoronshi da kuke nunarda kunaji yasa yake k'ara raina maku hankali, yakeyi maku duk abunda yaga dama", "Hassatu kenan, shi Jatau ina ruwanshi da wannan? Da muji tsoroshi da kar muji tsoronshi duk uwarsu d'aya ubansu d'aya, dan haka kima daina fad'ar haka" Gaje tayi wannan maganar bayan tayi murmushi kad'an, a ranta tana k'ara jinjina yarinta irinta Hassu. "Dan Allah ku fad'a min nidai karku barnu a duhu, ku nake saurare" Hassun ta sake fad'i a k'agare da taji *labarin Jatau.* Gajece ta fara da "ni da Dije mune matanshi na farko sai wasu biyu Amina da Rabi, duka a rana d'aya aka d'aura mana aure saboda kud'in da gareshi yasa kowane uba yake burin ya aurawa Jatau 'yarsa, suma kuma 'yan matan kowace takejin dad'i ace itace Jatau zai aura, Bayan an kawomu ne ya fara gindaya mana tsaurarrun sharud'd'anshi wanda har saida naji fitsari a lokacin da yake fad'insu, Ya kuma jadadda mana akan karmu kuskura mu rab'i rumbunshi barin har muyi gigin shigarshi, "Wallahi" ya rantse mana da duk lokacinda ya kama wata tana koda lek'en rumbun ne sai ya wulak'antata ya lalata rayuwarta sannan kuma daga k'arshe ya kasheta, Dukkanmu munji tsoro sosai muka d'aga kawunanmu alamar munji zancenshi, Umurni yayi mana da mu tashi mu tafi, kowa kuwa ta kama hanyar d'akinta. Munyi kamar wata uku da auren Jatau ya fita waje ya barmu a cikin gida, Rabi ta tashi tsaye tace "kai nifa wallahi ban yarda da wannan Jatau d'in ba, kunsan ni auren dole mahaifina yayimin dashi wai kawai dan Jatau ya gwada masa kud'i, kud'in banza da wofi gareshi tunda basu da asali, kuma rumbun daya hanamu shiga ni saina shiga inyaso yayi gunduwa gunduwa da namana idan ya dawo" ta tashi ta tafi. Da sauri na tashi na rik'o hannunta nace "kiyi hak'uri karki shiga ciki Rabi, tunda dai shi ya hana mu shiga to karki shiga, maganin kar ayi kar a fara, ki dawo ki zauna kici gaba da zaman hak'uri kamar yanda kowa takeyi a cikin gidan nan" "Ki sakeni Gaje, wallahi sai na shiga inyaso ya kasheni, ni nama huta da *Zaman tsanani* da nakeyi a cikin gidan nan" Babu yanda na iya dole na saketa, kai tsaye kuwa ta shiga cikin rumbun. Tana ciki bata fitoba kuwa Jatau ya dawo, Baki d'aya hankalinmu ya tashi hakan yasa muka mimmik'e tsaye jikinmu na b'ari mun kasa fad'in komai ga kaya a hannunshi amma tsabar rikicewa ta hana kowa karb'an kayan hannunshin harda Dije da ita keda aiki ranar. Da ganinmu yasan bamuda gaskiya, Cikin k'araji da fad'a yace "meya farune?", "Babu komai maigida" Dije ta bashi amsa har yanzu jikinmu rawa yake barin ma ita da tayi maganar. "K'arya kuke akwai abunda ya faru, ku fad'a min ko kuma in b'ab'b'allaku" sai bayan ya fad'i maganar ne ya tuna da baiga Rabi ba, "Ina Rabi take?". Rawar da jikinmu keyice ta k'aru jin tambayar daya mana, "Idan bakuyi maganaba duk abunda na maku ku kukaja" ya sake fad'i a tsawace. Da hannu Amina ta gwada mashi rumbunshi da yatsarta, kafinta sauke hannunta kuwa ya d'auketa da kyakkyawan mari har saida ta duk'e, Wannan duk'ewarda tayi shikenan saidai gawarta aka fitar, Ita kuwa Rabi tunda ya shiga cikin rumbun har maganar da nake miki yau babu ko labarinta, kuma har yanzu iyayenta basu mashi ko tad'in zancenta ba, bayan kamar sati uku ne ya auro Ladi da Bareerah lokaci d'aya, Ladince ya rabuda ita bada dad'ewa ba ya auro ki, tun abunda ya samu Rabi da Amina ne yasa muke jin tsoronshi, muka kiyayi duk wasu sharud'd'anshi, hanyar rumbunshi ma bamubi, saboda uwar mai tsoro akewa barka, ta marar tsoro kuwa sai jaje. Abunda nake miki gudu kenan Hafsatu, komai zai iya faruwa idan baki daina yi masa shisshigi ba saboda Jatau ya tsani a shiga harkarsa". Jinjina kai kawai Hassu tayi cike da mamakin mugaye da d'abi'un hali irin na Jatau, lallai batayi sa'ar miji ba kuma akwai babbar matsala. Mik'ewa tsaye tayi tace "kuma na d'auki alk'awarin saina shiga rumbuncan in ga abunda yake b'oyo wanda har yayi kisan kai akanshi koda ba yanzu ba, to kuma babu abunda aka masa dukda Amina daya kashe da kuma Rabi daya b'atar?" "Mefa aka masa? Kinsan a wannan lokacin wasu sun d'auki kud'i tamkar sunfi *d'an adam* (Rufaida Omar) daraja, har iyayenta basuji komaiba saboda kud'inda ya tilka masu, dan haka ki kama kanki Hassu, kibar maganar nan kawai dan bana son ki d'aukowa kanki abunda zaifi k'arfinki, kina zaman zamanki kiyiwa iyayenki asararki, ki dangana kawai ki mik'a lamurranki ga Allah, ki bashi zab'i shi zai zab'a miki duk abunda yafi zama daidai gareki". "Hmm! Yaya kenan? Taya zan zauna ban binciki abunda ke cikin rumbun can ba? Ai inhar na zauna a haka toko bazan tab'a samun natsuwa ba, amma idan na bincika koda ace babu komai zan samu natsuwa kuma kuma zaku samu, kuma addu'ah dolece gareni, zan hana idona bacci in fad'awa mahaliccina halinda muke ciki", "Hakane kam, amma kam ina shawartarki daki daina, kinsan hausawa sunce abunda babba ya hango yaro ko yahau tsauni bazai gani ba, dan haka ki dangana kawai tunda dai na baki shawara ki zauna lafiya" Gaje tabata Shawara saboda tausayinta takeji, bata son wani abu ya sameta kamar yanda ya samu Amina da Rabi. Shiru kawai Hassu tayi bawai danta gamsu da bayanin da Gaje tayi mata ba akan ta hak'ura karta shiga rumbun, tayi alk'awarin shigarshi kuma bazata sab'a alk'awarinta ba. "Wai to in tambayeku menene sana'ar Jatau? Me yake siyarwa da har yakeda wannan tarin dukiyar wadda duk fad'in k'auyen nan babu mai ita?", Baki Bareerah ta rik'e ido bud'e tace "ki rufa mana asiri kibar maganganun nan Hassu, idan ke bakya tsoro to mufa muna tsoro, kar ki ja mana mudai muna zaman zamanmu lafiya". "Dan Allah ku kwantar da hankalinku, bazai jimu bafa insha Allahu, ku bani wannan amsar daga ita shikenan bazan sake tambayarku ba". Gaje tayi k'asa k'asa da murya tace "babu wata sana'a guda d'aya tsayya wacce za'ace itace yakeyi, wannan dukiyar tashi Allah kad'ai yasan asalinta, wasu dai sunce wai gado mahaifinsa yabar masa ita, amma kuma abun tambaya anan shine; wane irin kud'ine wanda basu k'arewa kullum sai hab'aka suke? Bayan kuma ba wani juyasu yakeyi sosai ba", Shiru Hassu tayi cike da mamaki tana saurarensu, "Gashi da sa'a kuma, duk abunda ya tasa a gaba sai yayi nasarah, idan sana'a ya fara da wani to shine da samun riba wancan kuwa ya fad'i, abunda yake tutiya dashi kenan yace wai tanan dukiyarshi ke k'ara yawa bayan kuma ba haka bane, kawai dai akwai wata k'ulalliya wadda Allah kad'ai ya barma kanshi sani, Kuma kinga da zarar mun samu ciki sai ya zube, idan ma munyi sa'a mun haihu to take d'an yake rasuwa, kuma baki d'ayanmu matanshi hakanne babu wani canji, kuma tsabar tsoronshi da muke yasa muka kasa tinkararshi da maganar, babu wanda zaiso ya mutu baibar mai masa addu'ah ba, nikam harso nayi ma ya sakeni inje inyi wani auren ko zan huta amma bama zan tab'a iya tinkararsa da maganar ba, dan nasan idan ma na tunkaresa daya sakeni to tawa ta k'are daga ranar, Ladi ma daya saki wai kawai saboda al'darta ta d'aukemata ne kwata kwata yasan bazata sake haihuwa ba, shine fa ya rabuda ita sai kace shima haihuwar yakeyi, idan ma yanayi ai babu amfani tunda basa rayuwa abunda muka haifa d'in, ni ji nayi inama nice al'adar tawa ta d'auke kodan in fita daga wannan kurkukun da nake ciki, dan zama gidan nan wallahi yafi kurkuku tsanani, duk da tarin dukiyar dake cikinsa, kodayake ai dama hausawa sunce zaman lafiya yafi zama d'an sarki, kuma wallahi hakane, nikam na zab'i in zauna cikin talauci akan zama cikin dukiyar gidan nan amma babu kwanciyar hankali". "Kinga kuwa a daren jiya da muka rabu da Dije tacemin tana d'auke da juna biyu amma k'arami ne" Hassu ta fad'a tana kallon Gaje dukda duhu ya fara. "Ciki? Ciki fa kikace Hassu? Lallai sai yanzu na yarda da maganar Jatau, wata k'ila guduwa tayi dan bataso wani abu ya samu cikinta, inkuwa hakane to sam banga laifinta ba saima burgeni da tayi, gwara tajeta inda za'a kula da ita har sanda zata haihu wata k'ila zai rayu abunda zata haifa d'in idan ba'a gidan nan bane" Bareerah ta fad'a a hankali dan kar Jatau ya fito daga d'akinshi yaji abunda take fad'a. "Kuma kuma bai kamata ku zauna ba, addu'ah zaku dage da ita ba dare ba rana, Allah baya gyangyad'i, kullum yana karb'ar addu'ar bayinshi, kuma akwai hadisin manzon Allah (SAW) wanda yace "Allah yana saurin karb'ar addu'ar wanda aka zalunta" to kunga kullum cikin zaluntarmu yake, dan haka mu dage da sallar dare mu hana idanuwanmu bacci mu sanar da Allah matsalolinmu, insha Allahu zai sauraremu kuma zai zab'a mana alkhairi", "Gaskiyane Hassu, insha Allahu zamu dage da tashin dare, mu rok'i Allah sosai" Bareerah tayi maganar tana share hawayenda taji yana fito mata wanda batasan dalilin zuwanshi ba. "Akwai addu'arda zan baku yanzu idan na shiga d'aki na rubuce take da larabci sai in koya maku har ku iya tunda ba wani wahalane da itaba, amma kafin nan barin baku wata wadda idan ma wani sihiri yayi maku insha Allahu sai ya fara fita ta k'afarku a hankali har ya gama ficewa baki d'ayanshi. Idan zakuyi alwala kukazo wurin wanke k'afafuwa, Ku fara karantawa k'afar damanki Suratul-Nas, Falak' da kuma Ikhlas k'afa uku uku, sai ayatul-kursiyyu k'afa d'aya, salatin manzon Allah(SAW) k'afa uku, sannan ki wanke k'afar damar, itama k'afar hagun haka zakuyi mata kafin ku wanketa, Ku nemi ganyen magarya kuna wanka dashi kuna sha, yana karya sihiri shima, kuma yana hana wani sihirin shiga jiki idan akayi k'ok'arin sakeyi maku sabo". "Mungode sosai Hassu, kuma zamu fara daga yau insha Allahu" Gaje ta fad'a cike dajin dad'in samun Hassu a cikun rayuwarsu. (Abubuwan dana kawo ya kamata mu dage da yinsu, amma akwai sharad'in na alwalan, kunga yanzu an samu sauyi mutanenmu sunfi yin alwalwa a cikin band'aki, to indai zamuyi wannan addu'ar dole zamu fita waje muyi alwalar acan sannan muyi addu'ar, tana karya sihiri sosai kuma duk tsananin sihiri bazai tab'a shigarka ta k'afa ba, saboda akwai sihirinda akeyi na takawa, wani sihirin ma ba kai akayiwa ba kawai tako shi kakeyi, indai muka dage da wannan fa shikenan mun kub'uta, saidai mubi kanmu da addu'ah kawai. Shima na ganyen magaryar ya kamata mu dage dashi, mu ringa wanka da garinta sannan muna shanshi a ruwa muda yaranmu koda lafiyarsu lau, saboda wannan lokacin kana taka wasu na taka, Allah yasa mu dace, Allah kuma ya amfanar damu baki d'aya). Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/10, 7:25 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 3⃣9⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 Bayan sati biyu. A wannan lokacin ne Gaje da Bareerah suka ringa ibada tareda nemawa kansu tsari daga Allah, Kuma Alhamdulillah, yanzu duk wani tsoron Jatau da sukeyi sun samu sassaucinshi. Hassu kuwa ko d'akinta bai k'ara shiga ba duka gidanma ya bari, saboda bayan abun ya faru ya shiga ya samu dodonshi da maganarta, "lallai akwai matsala kam, wannan wace irin yarinyace ne wai? Batada tsoro ko d'aya sannan kuma asiri baya shigarta, ya zama min dole in dage dan inhar tunaninda nake ya zama gaskiya tabbas dagani har kai zamu shiga tashin hankali, saboda ni a ganina wannan yarinyar tanada wani b'oyayyen abu wanda ita kad'ai ta barwa kanta sani", "To yanzu menene abunyi ya dodona?", "Ka nisanceta na tsawon wani lokaci, akwai aikinda nake son nayi idan baka tare da ita, saboda na duba naga akwai soyayyarta sosai a cikin zuciyarka kuma matuk'ar kana tare da ita aikinda nake sonyi d'in bazai yiwu ba, dan haka ka nisanci gidan baki d'aya har sai lokacinda na nemeka, amma daga can d'inma ya kamata kana aiko mana da jini saboda samun k'warin guiwar aikin". Wannan dalilin ne yasa Jatau yayi nisa da gida, bai fad'awa kowa inda zaije ba saidai kawai suka daina ganinshi, Su kuwa ba k'aramin dad'i hakan yayi masu ba, koba komai zasu d'an sarara na wani lokaci kafin ya dawo. Zaune take tana kwab'a jan lallen gargajiya zata shafa a k'afarta saboda ita a tsarinta bata rabuwa da lalle, tun tana yarinya Goggonta ta saba mata da hakan, Wani irin bak'in luliyayyen abu d'an k'arami taga yana k'ok'arin shigowa cikin d'akinta, Kallo d'aya tayi masa taga yayi mata kama da bak'ar leda, hakan yasa tayi tunanin ko iskane ya kad'o da ita cikin d'akinta. Miyar da kanta tayi k'asa ga kwab'in lallenda takeyi. A hankali wannan bak'in abun ya ringa shigowa cikin d'akinta yana nufar inda take, Ita sam bata kula ba saima ci gaba da tayi da zuba lallen a k'afarta tana daidaita shi dan karya zaud'o sama. Sannu sannu har dunk'ulen abun ya iso daidai saitin kan Hassu, daga nan kuma sai yayi tsaye cak ya kasa tab'ata ya kuma kasa tafiya. Ko a jikinta zanen lallenta kawai take bata san abunda ke faruwa ba, Kamar tasan da wani abu a kusa da ita kawai ta fara karanto suratul Ikhalas kamar yanda ta saba indai tana wani aiki to wannan surar take karantawa, bata tab'a yarda bakinta ya zauna hakanan ba tare da tana karanta suratul ikhlas ba, A bayyane ta koma karantawa bayan ta gama sakama k'afar dama ta koma gata hagu, Fitt da k'arfi wannan bak'in abun yabar saitin kanta, ya ringa lilo bisa iska ya kuma kasa tunkararta yanzu, K'ara d'aga sautin karatun tayi cike da zazzak'ar murya, Da karfi abun yayi hanyar barin d'akinta, Bata kula ba saida ya fita sannan takai dubanta gareshi, Bata fahimci komai ba kawai taci gaba da abunda takeyi har yanzu kuma bata daina karatun ba. Wannan abun bai zarce ko inaba sai rumbun Jatau, Daidai gaban Jatau ya tsaya a hankali ya ringa saukowa, da mamaki sai gashi ashe d'aya daga cikin yaran dodone wanda aka haifa masa. "Ya ake ciki babban d'ana?" Dodo ya tambayeshi, "Ince dai kayi nasarah? Dan naga alamar kai jarumine gaba da baya, babanka jarumi kuma mamarka jaruma, nasan ka gama komai da izini na babanka". "Babu nasarah mahaifina, naso ace na gama maka da ita amma abu ya gagara, tana karanta wani abune wanda ya nemi ya illata min rayuwa, kaga jikina" ya fara nuna mashi fatar jikinshi, "Kaga duk ta tattalb'e kamar wanda ya k'one kawai sauraren abunda take fad'i d'inda nayi, saisa bansan lokacinda na barota ba, amma zan ringa bibiyarta idan naga bata fad'in abun zan illata maka ita, zatayi mutuwar wulak'anci sannan in kawo mana jininta muyi wandak'a dashi, amma kafin nan saina kawota nan ta tabbatarda ruwa ba sa'an kwando bane, mu munfi k'arfin taja damu". "Wannan haka yake babban d'ana, ina alfahari dakai sosai kuma nasan zakayi nasarah" dodo ya fad'a yana d'an bubbuga bayan d'anshi. "Zanma Jatau magana kuma ya had'aku da wanda zasuna baku jini kuna biya masu buk'atunsu, dan inaso mu hayayyafa mu yad'a zuru'ah sosai a cikin garin nan harma da wasu garuruwan dake kewaye da wannan garin". "Wannan shawarace mai kyau ya Babana, barin lek'a inga ko ta tsaya da abun" "To ka tafi d'ana, kana tare da kariyata, amma fa ka kula dan bana son wani abu ya sameka, ka kula da kanka" Dodo ya fad'a yana kallon d'anshi cike daso da k'auna. "Na maka alk'awarin zan dawo lafiya babu abunda zai sameni, kuma zanci gaba da bibiyarta har sai na kawo maka ita anan kayi abunda kaga damaryi da ita" ya koma dunk'ulallen abun nan bak'i kamar d'azu ya fita. Kande da Dije kuwa gabansu ne kawai ke faduwa, dan sun san watace suke neman takassarawa, a ran Dije tace "indama inada yanda zanyi in sanar da Hassu abunda suke shirin aikata mata da nayi, saidai kuma banida yanda zanyi". Bareerah da Gaje suna zaune suna taya Hassu fira saboda har yanzu bata wanke k'unshinta ba, Hassu tace "nikam dai baccin kun hanani shiga rumbun can wallahi da tuni anyita an k'are, taya zamu zauna da yunwa babu abincinda zamuci kuma babu kud'in siye? Sauk'inmu ma d'aya Yaya Gaje ana aiko miki daga gida aida tamu ta k'are, mugun yayi tafiyarsa ya barmu da fama da yunwa, Allah kad'ai yasan iyakar abunda shi yake cima cikinsa". "Koma dai menene bamu yarda ki shiga rumbun nan ba Hafsatu, zama lafiya dukiya, tunda dai ana kawo mana munaci d'in kawai gwara mu hak'ura har lokacinda Allah zai dawo dashi" Bareerah ta fad'a bayan ta kwance ledar da Hassu ta k'ulle k'afarta ta dama dashi, "Kinga wannan ya kama, saura k'afar hagunce itama nasan yanzu zatayi tunda dai wannan d'in tayi". D'an Dodo ne a dunk'ule ya ringa tahowa yana nufar Hassu saboda yanzu labari sukeyi itada abokan zamanta ba karatu take ba, Dad'i kuwa yaji sosai ya fara nufar inda take, Duk basu ankara dashi ba saboda d'an k'arami ya zama yanzu kamar girman sauro. Ringa zagayar Hassu yayi amma ya kasa tab'a ko fatar jikinta duk da ba addu'ah takeba, "Wai meke bina ne haka?" Ta tambaya bayan ta d'aga kanta tana kallonshi. "Saurone matsoraciya" Gaje ta fad'a tana kallon Hassu tana murmushi. "Ai sauron yanzu basuda kunya ko kad'an wallahi, da rana ma bin mutum suke basuko tsoron shiga mutane" Bareerah ta fad'a bayan ta ringa korarshi da k'yallen dake hannunta. Da mamaki ko gezau baiji ba, hasalima sai k'ara manne ma d'ankwalinta yake saboda ya samu ya tab'ata, "Kai Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wai ina dalilin sauro mai k'wak'wa? La haula wala k'uwwata illa billah!" Ta fad'a saboda gajiyar da tayi da korarsa bawai da wata manufa tayi ba. Da sauri yayi k'ok'arin guduwa aikuwa Hassu tasa hannunta da bismillah ta cafkoshi, "Shegen sauro Allah kad'ai yasan jinin mutanenda kasha, dan haka taka ta k'are yanzu zaka mutu kaima kaji idan mugunta tanada dad'i" ta k'ara matseshi a hannunta. Azaba sosai ta ishi d'an dodo, dan haka ya ringa mitsitstsike mitsitstsike yana neman guduwa amma babu hali, Muguwar matsar da Hassu ta masane a hankali ya fara komawa halittarsa yana k'ara girma, Da mamaki Hassu taji abu sai nauyi yake mata a hannu, Hankali tashe ta bud'e hannun nata ta sakeshi k'asa da k'arfi cikeda tsoro, K'yallen dake hannun Bareerah ta fizge da k'arfi ta bugama d'an dodo, Take kuwa ya ida zama kaf halittarsa, Baki d'ayansu hankalinsu ya gama tashi, sai faman runtse idanuwansu suke saboda rashin kyan ganin halittar, A hankali ya ringa k'ok'arin motsawa amma ya kasa, Sai can daga baya ya d'an motsa yana kallonsu d'aya bayan d'aya duk ya rikice shima yana gudun karta karanto masa abunda ta karanta d'azu, Da k'yar d'an dodo ya samu ya tashi yayi sama, Hassu tayi k'ok'arin daurewa dan ganin ta damk'oshi amma ina, ta kasa saboda tsabar tsoro gashi kuma har yayi nisa, Idonsu a kanshi har ya isa rumbu ya shige abunshi. Kallon kallo suka ringa yima junansu, kowace da abunda take sak'awa a ranta, "Ai dama na fad'a maku wallahi akwai abunda Jatau yake b'oyo a cikin mugun rumbun can nashi, Idan ba hakaba mesa wannan abun zai shiga can?". "Hakane nima na yarda da maganarki Hassu, tabbas akwai magana a k'asa, kuma ya zamar mana dole mu dage tsare kanmu" Bareerah tayi maganar bayan tayi tagumi cikeda tsoro. Gaje data kasa fad'in komai sai yanzu tace "to wai mema ya kawo wannan abun? Wurinwa aka turoshi? Me yazo yayi mana?", Caraf Hassu tace "ni a ganina wurina aka turoshi kuma akwai abunda aka turoshi yayi min, hmm! Basu san ina tare da kariyar Allah ba, a zatonsu mahaifina ya barni a haka ne? Ko nayi rantsuwa bazanyi kaffaraba, wlahi babu abunda zasu iya yimin, kuma nasha alwashin komeke cikin rumbun can k'arshenshi ya kusa zuwaatunda suka tab'ani, zan jira har lokacin da Jatau zai dawo in nemi izininsa, zanje Garu (k'auyensu Hassu), zan fad'awa mahaifina komai, idanma ta kama mu dawo tare tofa zaku ganmu tare dashi, idan kuma shawara zai bani yanda zanyi ma dai duk d'aya, insha Allahu karshensu ya kusa". "Mu kuwa munyi alk'awarin zamu baki goyon baya d'ari bisa d'ari, sai inda k'arfinmu ya k'are dan ganin kinyi nasarah, nikam jikina ma ya fara yin sanyi gameda rashin haihuwarmu, wama yasan koda jinin 'ya'yanmu mukecin abinci?" Gaje ta fad'a. "Kamar kinsan tunaninda nakeyi kenan nima, Allah kad'ai ya barma kansa sani, kuma da yardar Allah asirinsu ya kusa tonuwa, idanma shida wani keyi dai tasu ta kusa k'arewa kowa sai yasan halinda yake ciki" Bareerah ta fad'a tana k'ara mamakin wannan abun. Timmmm! d'an dodo ya fad'a k'asa gaban babanshi, A rikice yace "babban d'ana kafiya? Me sameka?", Dak'yar yake iya bud'ar bakinshi yana magana yace "asirinmu ya tonu babana..." yayi masa bayanin duk abunda ya faru. "Nasan tawa ta k'are baba, mutuwa zanyi, ni kad'ai nasan iyakar abunda nakeji, sun kasheni babana" "Ka daina fad'ar haka d'ana, ba zaka mutuba, ba yanzu zaka tafi ka barni ba" dodo ya fad'a a rikice. "Na shiga uku baba! Ko bayan raina ina rok'onka karka k'yalesu, ka d'aukarmun fansa, ka cikamin burina na kashe wannan makairar yarinyar itada kishiyoyinta" yana gama fad'in haka kuwa ya mutu. Da k'arfi dodo ya fasa kuka wanda har saida matarshi da sauran 'ya'yanshi suka tashi daga bacci, Hankali tashe ya labarta masu duk abunda ya faru, Itama matar tashi hankalinta ya tashi tace "shikenan sun kashe min babban d'ana, inda ka sani da baka sakashi wannan aikin ba, aikuwa harshi Jatau d'in saiya gane d'anmu ya mutu, suma kuma matan saisun gane kurensu, saboda bazamu tab'a barinsu zama lafiya ba, hatta da zaman gidan nan saiya nemi gagararsu kuma babu inda zasu tafi suna nan, sai mun gama wulak'anta masu rayuwa sannan daga k'arshe mu kashesu mu shanye jininsu, yanzu shikenan sun kashe mana babban d'a" ya fashe da kuka sosai. Hawayen nasu kanshi abun tsoro ne, bak'ik'irin dashi harda wani maik'o maik'o yakeyi, ga idonsu ya k'ara yin jajur tsabar kukanda sukeyi. Tsaye dodo ya tashi yayi wani irin juyi da k'arfi wanda mu kanmu *RAZ* saida muka tsorata, munyi mamakin tsawonshi dan duk tsawon rumbun nan saida dodo ya d'an duk'e bai isheshi ba, ga k'iba sosai da fad'i da gareshi. "Na rantse da naman kan daya zama halittata saina wulak'anta rayuwarsu, saina zama ajalinsu, sai sun san sun kashemin babban d'ana wanda nafiso fiye da rayuwata, zan cika maka burinka d'ana". (Ohh! Ashe babu dad'i dan anma mutum abubda yakema wani, lallai akwai aiki ja, inji *RAZ).* Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/11, 5:54 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 4⃣0⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 _Sak'on gaisuwa da jinjina gareku; Aunty Sdy Jegal, Ashnur Pyar, Maman Nusy (Marubuciyar labarin Husna), Queen Mimi, RAZ NOVELLA 1&2, Ummee Saddam, and Aunty Maijidda Musa, Allah yabar zumunci da zaman tare, RAZ loves you much._ ***** Sunyi kwana uku suna jimamin mutuwar d'ansu, wani irin haushi da takaici dodo yakeji, Har yanzu tunanin ta hanyar da zaibi ya kashe su Hassu yake, yama kasa yanke shawarar yanda zayyi dasu. Jatau ne zaune banda tunanin Hassu babu abunda yakeyi, cike yake da soyayyarta dan yanda yake jinta a ranshi ba lallai idan zai iya rayuwa idan babu itaba, Yana zaune sak'on kibiyar dodo ya iso gareshi, koda ganin kibiyar ya tabbatar da akwai dalili, Hakan yasa ya fara surkullen dashi kad'ai yasan abunda yake nufi, Yana k'walawa dodonshi kira da k'arfin gaske, A hankali iska ya fara d'aukar Jatau yana yin sama dashi, ya koma girmanshi kamar tsuntsu, Bai dira ko inaba sai cikin rumbunshi, Lokacinda Jatau yazo gittawa da sifar tsuntsu a gabansu Hassu ne, suna zaune suna furar jin dad'in tafiyar da Jatau yayi, Hassu kuma ta basu labarin ita ta k'agara ya dawo kodan ta rok'eshi ta tafi gida dan ta sanarda babanta halinda suke ciki. Gaje tace "nifa idan nice ke wallah bazan wani jirashiba, mugun mutum irin Jatau ma ai babu amfanin kice wai dole sai ya dawo kin nemi izininshi sannan ki tafi inda kike so". "Hmm! Yaya Gaje kenan, baki san komai mugun halin miji mijinka bane? Dole aljannata a k'ark'ashinshi take komai bak'in halinta, kuma ya zama min dole in bishi sauda k'afa kar in sab'a masa, koma dai ya halin Jatau yake ai mijinane kuma dole in nemi izininshi kafin inje ko ina". "Ehh kuma fa hakane"Bareerah ta fad'a. Rufe bakinta kenan Jatau yazo a wannan halittar, Akan idanuwansu ya shiga cikin rumbu, Hassu da hankalinta na kan abunda ke faruwa tace "kunga kuma wani abun ko? Ya Salaam! Allah dai ya kyauta". "Ameen" suka fad'a su duka duk jikinsu yayi sanyi. A hankali Jatau ya sauka daidai gaban dodo, Da sannu sannu ya ringa komawa halittarshi ta Jatau har ya koma duka, kafin yace komai cike da tsiwa matar dodo tace "Jatau! Jatau!! Jatauuuu!!", Hankali tashe Jatau ya d'aga kanshi ya kalleta, "Sau nawa na kira sunanka?", Da hanzari yace "sau uku". "Jatau matanka sun kashe mana babban d'anmu wanda mukafi ji dashi, suna neman su tona mana asiri, dan haka dole zamu d'auki *fansa,* a doron k'asar nan ba'ayi wanda zai tab'amu mu k'yaleshi ba ko waye, kai koda kaine Jatau!" Ta fad'a a tsawace. Cike da mamaki Jatau yace "sun kasheshi? Garinya hakan ta kasance?", Dodone yayima Jatau bayanin duk abunda ya faru lokacinda baya nan. Dama yasan za'a rina, babu abunda Hassu bazata iyayi ba, dan ya kula batada ko alamar tsoro a rayuwarta, "Nabar wuk'a nabar nama gareka ya dodona, kayi masu duk abunda kaga dama saboda wannan yarinyar ni tafi k'arfina, babu abunda zan iya yi mata" "Dama bamu buk'atar saka hannunka a cikin wannan aikin, kaidai kawai abunda mukeso ka baza idonka kasha kallo, ka kawar da jinka da ganinka", "Hakan za'ayi ya dodona" ya tashi ya fita daga rumbun. Babu haufin komai Jatau ya fita, su Hassu na zaune k'ofar d'akin Gaje har yanzu suna al'ajabin wannan al'amurran dake faruwa a cikin gidansu. Kallon kallo suka ringa yima junansu a lokacinda sukaga Jatau ya fito, Sosai suke mamakin yanda akayi ya shiga rumbun saboda sudai tun d'azu suke zaune amma basuga shigowarshi cikin gidan ba, "Towai kodai Jatau aljanine?" Suka tambayi kansu a cikin zukatansu. Bai tankawa kowa a cikinsu ba kawai ya shige d'akinshi, Hassu tace "nikam ina tababa anya Jatau kuwa mutum ne?", "Mutum ne mana Hassu, mesa kika fad'i haka?" Bareerah ta tambayeta. "Ki duba tun lokacinda muke zaune wurin nan, bamuga shigowarshi gidan nan ba, ta ina yabi ya shiga to idan ba aljani bane?" Hassu taba Bareerah amsa. "To kodai shine yazo da sifar tsuntsun nan wanda ya shiga rumbu?". "Anzo wurin, tabbas hakane dan nima tunanin da nayi kenan" Gaje ta fad'a bayan tayi ajiyar zuciya. "Idan kuwa hakane kenan maganata tana bisa hanya, lallai Jatau ba mutum bane, idan mutum ne kuma to babban matsafi ne" Hassu ta fad'a. "Maganarku gaskiyane, duk wani b'oye b'oye bazan sakeyi makushi ba, ni natsafine kuma mai satar mutane, ina satar mutane ina kawowa dodona dake cikin rumbuna" kamar daga sama suka jiyo muryar Jatau yana wannan maganar. Sakin baki sukayi suna kallon Jatau, shima kuwa ya tsura masu ido yana kallonsu dan yasan suna daf da mutuwa su duka ukun, "Ku daina mamaki kunji? ku d'auka a ranku cewa kuda barin gidan nan har abada, zaman gidan nan sai ya zamar maku tamkar kurkuku, kai zaman kurkuku ma sai yafi wannan dad'i, sannan kuma duk wanda zaku tunkara da wannan maganar da nufin tona min asiri shima sai ya mutu, Barin fad'a maku abunda baku sani bama, Dije data b'ata ba b'ata tayi ba ni na saceta yanzu haka tana cikin rumbuna lokacin mutuwarta kawai nake jira, Duk yaranku da kafin ku haifesu ko kuma bayan kun haifesu suke mutumuwa duk aikinane, jininsu nake bayarwa ga dodo sai in binne namansu a d'akunanku, Har wannan tsohuwar wadda ta mutu lokacinda aka kawo Hassu nine na bayarda jininta a lokacinda matar dodona ta haihu tanada buk'atar tasha jini kuma na fita ban samu kowa a waje ba, shine na dawo gida da nufin in fad'awa dodo ban samu jinin wanda zan kawo ba, kicib'us nayi da ita a lokacin ita kuma zata shiga band'aki, shine take na aikata ga dodona, Duk mutanenda zakuji sun b'ata a garin nan ba wani ya sacesuba face ni, Kad'an kenan daga mugayen abubuwan dana aikata a rayuwata tun yarintata har zuwa wannan lokacin, Har aurenki da nayi" ya nuna Hassu da yatsa "duk tsarin dodona ne, shi yace in tafi hanyar garinku duk 'yar fillon dana fara had'uwa da ita in aureta saboda na rabu da matata Ladi. Wannan abun wanda kuka kashe kuwa d'an dodona ne, kuma inason ku sani kun kasoma kanku masifa da bala'i, saboda dodona bazai tab'a k'yaleku ba, idan kuwa yayi tunanin k'yaleku to matarshi ma bazata k'yaleku ba barinma shima ba k'yaleku d'in zayyi ba". Yana gama maganar ya nufi hanyar fita waje. "Jatau!" Hassu ta kirashi ba tare da haufin komai ba. Juyowa yayi cike da mamaki, tunda ya auri Hassu bata tab'a kiran sunanshi kai tsaye ba, cak ya tsaya yana tunanin abunda zata fad'a masa. "Jatau ka sani Allah ya fiku, mu Allah muka rik'a kuma shi zai karemu, duk wani tsafinka da abunda zakuyi kaida dodon naka Allah ya fiku, muna tare da Allah kuma bamu fatan ranar da zamu nemi agaji da taimakon wani koma bayan Allah, dan haka kayi kuskure! Kuma da kake cewa bazamu tab'a fita daga gidan nan ba mun yarda, mun yarda da hakan amma kuma ka sani zakayi dana sanin rashin fitarmu daga gidan nan, sai zamanmu ya zame maku masifa da bala'i, dan haka mun yarda zamu zauna, kuje duk wani tsafi kuyi zamu zauna a gidan". "Hmm! Ke a zatonki akwai wani abu wanda zai iya tsayarda tsafin dodona? Babushi kuwa" ya fice abunsa. Hannu Gaje da Bareerah suka d'ora akai sai kuka suke, "Shikenan mun shiga uku, munsan tamu ta k'are yaukam, Hassu mesa bakida tsorone? Nikam gaskiya guduwa zanyi" Gaje tayi wannan maganar tare da nufar hanyar waje dan lokacin har Jatau ya fita. Tana fita kuwa tun daga zauren gidan ta ringa ganin ambaliyar ruwa tun daga zauren har k'arshen ganinta na cikin unguwar, Da zarar ta runtse idonta kuwa sai take ringa ganin namun daji mugaye suna k'ok'arin tinkarota. A rikice da gudu ta dawo cikin gidan, Ta samu Bareerah har yanzu kuka take ta kasa fad'in komai, "Mesa kika dawo?" Hassu ta tambayeta. "Babu halin fita Hassu, mun shiga uku! Yanzu shikenan abunda yake fad'a gaskiyane? A haka zamu dawwama cikin wannan uk'ubar?", "Ki daina fad'ar haka Gaje, nidai fatana mu rik'e addu'ah, addu'a bata tab'a fad'uwa k'asa banza, mu dage sallar dare muna fad'awa Allah natsalolinmu, ku daina nuna jin tsoronshi a gabanshi, harda hakan yasa yake maku yanda yaga dama, duk tsoronshin da kuke sai kuna daurewa". "Taya kike tunanin zamu bar jin tsoron Jatau Hassu? Jatau fa abun tsorone dashi da kaidinshi" Gaje ta fad'a cikin muryar kuka. "Hakane amma mu dage da addu'ah Allah zai fitar damu insha Allahu" Tana gama maganar suka ringa jin wata k'ara da k'arfin gaske kamar kunnuwansu zasu cire, Take hadari ya had'u a daidai iyakar gidansu, sai walk'iya da k'arfi had'e da cida, Bak'in hadarin ne ya kare hasken rana baki d'aya sai uban duhu daya mamaye gidan ko tafin hannunsu basu iya gani. Iyakar tashin hankali sun shiga, gashi kuma abun sai k'ara ta'azzara yake, k'arar hadarin kuma bazata tab'a bari aji kukansu ba barin har a kawo masu agaji. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/12, 7:21 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 4⃣1⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 _Wannan shafin nakine *Zee El-Kasim (Maman Khady)* sak'onki ya isar mana muna godiya sosai Allah yabar zumunci, masoyanmu wanda muka sani da wanda bamu sani ba muna mik'a godiya a gareku, muna fatan Allah ya had'amu a Aljannah._ ****** Sannu a hankali hadarin ya fara saukar da wani irin bak'in ruwa had'e da wasu k'ananan k'wari suma bak'ak'e wulik. Matuk'ar tashin hankali sun shigeshi, ga wani irin duhu tamkar dare ya raba tsakiya, basu ko ganin junansu, A hankali Hassu ta fara karanto Ayatul Kursiyyu da k'arfi, Tun tana sanin abunda take fad'i har takaiga batama san me take fad'a ba kawai dai tasan bakinta yana furta addu'ah, Amma kuma tamkar yi mata ita akeyi, wannan kuma ikone daga Allah. Jin addu'ar da take yasa Gaje da Bareerah ma da k'arfi suka ringa karanta bakin gwargwadon abunda suka sani. Wani irin haske had'e da k'ara ya gitta masu, cikin iko da hikimar Allah lokaci d'aya hadarin ya washe, ruwan ma ya tsaya, take komai ya zama daidai kamar babu abunda ya faru. Koda suka duba jikinsu duk tabbunane yayi burd'i sosai inda wannan k'warin suka ringa saukar masu, Har yanzu bakinsu bai tsaya da addu'ah ba, duk da ganin komai ya lafa kuwa. Cikin natsuwa Hassu ke kallon yanda suka dunk'ule wuri d'aya su duka ukun, Jikinsu rawa kawai yake har yanzu, Lallai dole suyi taka tsantsan da zama cikin gidan nan, saboda inhar basu dage da addu'ah ba komai zai iya samunsu. "Kamar yanda na fad'a maku a baya dole mu tashi tsaye wurin rok'on Allah, wannan halin da muke ciki Allah kad'ai ne zai iya fitar damu" Hassu ta fad'a tana share hawayen dake bin kumatunta, saboda tunda abun ya faru ko alamar kuka bataji ba, sai yanzu wai da komai ya lafa ne take jin kukan, Su Gaje kuwa kukan da sukayi ma bashi da iyaka, tun farkon had'uwar hadarin suke sharara kuka har yanzu. "Insha Allahu ba zamuyi wasa da addu'ah ba Hassu, idan ma mukayi wasa da ita ai tamkar muna wasa da rayuwarmu ne, kinga kuwa dole muyi taka tsantsan" Bareerah ta fad'a cikin muryar kuka. "Kad'an daga aikin *Dodon Jatau* kenan, wannan ba komai kuka gani ba saboda yanzu zaku fara, duk wata hanya da wani zai kawo maku ziyara na kasheta barin har wani yayi tunanin taimakonku, haka kuma babu halin fita daga gidan nan, abinci na nan na ajiye maku idan kunga dama zaku iya dafawa kuci dan bana son ku zauna da yunwa har ku mutu ba tare da mun gama azabtar daku ba" Jatau ne ya jefo wannan maganar had'e dayin murmushi sosai. "Kuma ba yanzu zaku mutu ba, baku tsoro kuwa yanzu zaku fara gani" yana gama fad'in haka ya shige d'akinshi. Shi kuwa dodo da k'arfin masifa ya fad'a cikin rumbu, jikinshi duk ya fara tattalb'ewa wurin yayi wani iri kamar ya k'one, Cike da k'arfin hali yake magana "binku da nayi ta hanyar sauk'i shine yasa kuka min haka ko? To lallai zan maku ta k'arfi da yaji dan ku gane ruwa ba sa'an kwando bane, ni nafi k'arfin ku kara dani", Matarshi dake gefe tace "na kula dakai kamar mutuwar babban d'anmu bata dameka sosai ba, idan kuwa ta dameka ai bazaka tab'a sassautawa wanda sukayi silar mutuwarshi ba, kaga idan kasan kai bazaka iya wannan aikin ba ni ka had'ani dashi kaga aiki da cikawa". "Ina son ki fahimci wani abune Matata, nafi son su gama wahala su azabtu sosai sannan su mutu, yanzu zan ringa tsoratasune, hatta baccin dare bazan tab'a barinsu suyishi ba, basu ba hutu har abada". "Nikam inda zakabi ta tawa kawai ayi masu cikin lokaci d'aya, kasan idan baka iya kama b'arawo ba shi zai kamaka", "Maganarki hakane, amma fa idan na kashesu a haka zanji bak'in ciki sosai saboda basu azabtu ba, amma idan na gama tsoratasu suka wahala sosai sai inbar miki wuk'a da nama, ki kashesu ta hanyar da kike so", "To tunda haka ka fad'a d'in ba damuwa aje a haka, zan taimaka maka wurin tsoratasu" dodanniya ta fad'a cike da masifa. Jatau ne ya shigo cikin rumbun hannunshi rik'e da wata babbar leda, Saida ya rusuna har k'asa sannan ya mik'a ledar ga dodonshi. "Meke cikin wannan ledar ne Jatau?" Dodon ya tambayeshi bayan ya fara k'ok'arin bud'eta dan duba abunda yake ciki. "Da'zu dana shigo kana bacci, munyi magana da dodanniya akan zan kawo mata wasu gab'ob'i na jikin gawar malami wanda ya mutu bada dad'ewa ba, tace akwai wani aikinda takeson tayi dashi, shine naji labarin wani limami ya mutu a bayan layinmu, bayan an kaishi an binne ni kuma nabi kabarinshi na tone na fitar da duk gab'ob'in data lissafa min tanaso d'in". "Me zakiyi dasune?" Dodon ya tambayeta cikin k'atuwar muryarshi. "Zan had'a wata halittane wanda zan aika masu da ita cikin daren nan" ta fad'a bayan ta karb'i ledar daga hannun mijinta tana dudduba abunda ke cikinta. "Yanzun ma kinga yamma ta fara gabatowa, ya kamata ace duk abunda zakiyi d'in kin kammala,saboda a aika masu da abun tunda wuri kafin baccin farko ya d'aukesu, kin san idan baccin farkon nan ya d'auki mutum ba lallai wani abu ya iya tashinshi cikin sauk'i ba". "Ehh hakane, karka damu yanzu zan gama komai" Ta fara tsaface tsafacenta had'e da busa iska daga bakinta, da zarar ta busa iskar sai wuta ta fito daga bakin tayi cikin abunda take had'awa, "Kasan dalilin da yasa nace dole sai malami zai ciro gab'ob'insa?" Ta k'ara busa wutar a daidai inda take had'ewa da k'wayar idonshi guda d'aya. "A'a sai kin fad'a" Jatau ya fad'a yana kallonta dan koshi baisan yanda zatayi ta had'a wannan abunba, lallai sai yanzu yake tabbatarda cewa kaidin mace yafi na namiji, gashi dai shine ya koya nata komai amma kuma har tazo ta zarceshi iyawa, ta fishi iya tsafi da komai ma. "Saboda idan malami ne babu wani abunda zasu karanta dazai iya yi mashi wani abu barin har ya tsaya da abunda yakeyi masu saboda dama ya rigada yasan komai" ta bashi amsa bayan tayi dariya mai cike da k'eta da mugunta. "Lallai ke babbace matata, na jinjina miki sosai da irin jarumta da basirarki" Dodon ya fad'a shima yana murmushin. Shi kanshi Jatau yayi mamakin wannan abu, duka duka yaushe dodanniya tasan duniya barin har tasan kalar wannan k'etar? Shidai nashi kallone kawai, fatanshi yaci gaba da basu jini suna bashi dukiya, bai damu da matanshi da zai rasa ba, saboda yasan ko ya rasasu yanada kud'inda zai iya ya auro hud'u ma a tare. Cikin lokaci kad'an kuwa ta had'a mutum mutumi, k'wayar idonshi d'aya a daidai inda hanci yake, d'ayar kuma a bisa goshi, Bayada hanci ko kad'an saboda dama banda hanci tacema Jatau ya samo mata, Duka tsawonshi bai wuce gab'ar hannu ba, Hannunshi d'aya sai k'afarshi ma d'aya wadda ko yatsu batada su. Ajeshi k'asa tayi sai gashi idan yayi taku d'aya sai ya furzar da wuta daga bakinshi, Idan ya sake yin wani takun kuma sai ya saki wata irin k'ara mai rikitar da rayuwa, Taku na uku idan yayi kuma sai komai dake wurin ya jijjiga, Jatau dake wurin tsayema saida yajishi can an jefar dashi cikin buhunnan abinci. A hankali ya tashi yana kallon wannan 'yar halittar, duk k'arantarta wai itace ta ringa jifa da abubuwa haka. Bayan isha'i Gaje da Bareerah suka dawo d'akin Hassu, saboda cike suke da tsoron gidanma baki d'ayanshi, Koda suka zaune da zarar sunyi k'ok'arin yin magana sai Hassu tayi masu gyaran murya akan suci gaba da ambaton Allah. Haka suka ringayi har dare ya fara nitsawa, hakan yasa suka fara haramar kwanciya bacci. "Ka tafi da izinina, ka dawo cikin yardata, ka tsoratasu amma kar kayi masu wani abu dan ba yanzu nakeso su mutu ba, ka tabbatarda sun tsorata sosai ta yanda bazasu yi bacci ba, koda sun rintse idanuwansu kai zasu ringa gani". Tana gama fad'in haka tayi tsafi tare da jefashi sama, hanyar d'akin Hassu kuwa ya nufa, Ya samesu duk sun kwanta mak'ale da junansu, hakan yasa ya dira k'asa a daidai kusa dasu daga can gefe. Taku d'aya kuwa yayi wuta ta ringa b'ulb'ulowa daga cikin bakinshi yana watsata a daidai fuskokinsu, Sake yin wani takun yayi sai k'ara da k'arfin gaske wadda har saida ta tashesu daga gajeren baccin daya d'aukesu. A rikice suka tashi har yanzu basu saki junansu ba, sunma rasa abunda zasuyi sai rawa da jikinsu yakeyi. Wani takun ya kumayi aikuwa da k'arfi d'akin ya ringa jijjiga da kanshi, katangar ta ringayi kamar zata fad'o masu sai kuma ta koma yanda take, Idan tayi kamar zata fad'o masu d'in har sai sun sadak'as cewa tasu ta k'are, sai kuma suga ta koma da kanta, Da k'arfi aka ringa jijjigasu har saida suka rabu da junansu. Sake yin wani takun yayi saiga wannan wutar taci gaba da fita da sauri da sauri, saitin Gaje ta ringa fita tana sauka a baki d'ayan jikinta, saida ya gama sannan ya juya ga Bareerah, Itama ringa harba mata wutar yayi tana sauka jikinta sai soshe soshe take wurin na damewa kamar dai yanda k'una keyi idan aka tab'ata. Bayan ya gama da itane ya juyaga Hassu, Daidai ya saki wutarne Hassu ta ringa ambaton sunayen Allah wasu b'oyayyu wanda ba kowa yasansu ba, da k'arfi take fad'insu tana kuka, wasu addu'o'i ne takejin bakinta na furtawa wanda tunda take a doron k'asa bata tab'a jinsu ba, batama tab'a sanin akwaisu ba, saidai wani lokacin tanajin makamantansu a bakin Baffanta, a duk lokacinda zasu kwanta bacci saiya tottofesu da ita. Cak ya tsaya hatta da wutar daya fara harbawa ta saitin Hassu saida ta tsaya, tsayawar da yayi d'in baisa addu'ar ta daina fita daga bakin Hassu ba saima k'aruwa da tayi. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/13, 5:37 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 4⃣2⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 A hankali ya fara kusantota, bataji tsoronshi ba ko d'aya saima k'ara k'arfafa addu'ar da bakinta keyi, Saida yazo daidai gabanta sannan ya sunkuya k'asa, guiwarshi guda d'aya a k'asa sai hannunshi guda d'aya ya had'e yatsun wuri d'aya tare da d'orasu bisa goshinshi alamar yana bata hak'uri, Har yanzu dai addu'o'i ne kawai ke fita daga bakinta bata ko miyar da hankalinta gareshi ba barin har taga hak'urin da yake bata, Sauke hannshi yayi ya dunk'ule yatsun wuri d'aya alamar jinjina, Har yanzu Gaje da Bareerah basu farfad'o ba, saboda tun lokacin da ya ringa harba masu wutar nan azaba ta sumar dasu. Sai yanzu Hassu ta d'aga kanta ta kalleshi, idonta yayi jajur sai hawayen wahala ke fita daga ciki, A hankali ya ringa rarrabewa daga jikinshi, saida ko wace gab'a da aka had'a ta rabe da jikin sannan ya ringa narkewa, Baki d'ayanshi ya narke kamar darma a cikin wuta, Bayan ya gama narkewar ne ruwan ya ringa zama k'ananan tsutsotsi, a hankali kuma wuta ta ringa kamasu har suka mutu k'urmus sannan wutar itama ta mutu. Shiru d'akin yayi kamar babu abunda ya tab'a faruwa a cikin d'akin. Wata irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, ta d'aga kanta ta kalli Gaje da Bareerah suna baccin wahala, Lallai sai a yaune ta k'ara tabbatar da addu'ah nada matuk'ar amfani, duk irin halin da mutum ya shiga kar ya manta da addu'ah, saboda indai ka rik'eta lallai kana tare da kariyar Allah, Gasu dai kalar abunda aka aiko masu, inda ace bata rik'i addu'ah ba da komai zai iya samunsu a cikin wannan daren, saboda babu mai taimakonsu idan ba Allah ba. "Alhamdulillah!" Kawai ta iya furtawa tare da mi'kewa tsaye, Duk da tsoron da takeji bai hanata sake yin addu'ah ta fita daga d'akin ba, Kai tsaye band'aki ta nufa, bayan tayi fitsari ta fito ta d'aura alwala sannan ta koma d'akinta, Har yanzu dai su Gaje basu farfad'o ba, Daga can gefe inda sallayarta take ta nufa, Kabbara sallah tayi, saida tayi raka'a goma kowace fatiha da suratul Ikhlas, duk bayan raka'a biyu takeyin sallamah, Bayan ta gama duka tayi addu'ah sosai, ta fad'awa Allah damuwarta, anan bisa dardumar sallar bata san lokacin da bacci yayi awon gaba da ita ba, Dama tunda abun nan ya fara faruwa ko kiran sallah sun daina ji, Sai dai kawai tayi amfani da fitowar alfijir sannan tayi sallah. Ganin alfijir ya keto yasata tashin su Gaje, "Yaya Gaje ku tashi lokacin sallah yayi", "Umm" kawai Gaje ta fad'a ta sake yin wani juyi ta koma baccinta. "Yaya Bareerah" ta d'an bubbugata "Ku tashi lokacin sallah yayi" Itama Bareerar baccinta ta koma alamar bacci yayi dad'i. *(RAZ* sukace oh! Ji wanda akace ba'a son su samu yin bacci amma gashi su baccin ma dad'i yayi masu, lallai addu'ah bata bar komai ba, saisa a kowane lokaci akeso ka nemi abokin zama wanda yasan abunda yake, saboda shine zai iya sanar dakai abunda baka sani ba, shine zai kareka ya kuma taimakeka a lokacinda kake da buk'atar taimako, yanzu inda ace Hassu bata san abunda take ba aida komai zai iya samunsu, sai gashi ta dage da addu'ah kuma Allah da yake baya gyangya'di ya amsa mata addu'arta a take, dan haka muke shawartar 'yan uwanmu musulmai akan mu dage da addu'ah, mu rik'i sallar dare kar mu yar da ita, kar kuma dan munyi addu'ah Allah bai amsa mana ita a take ba musa rashin hak'uri har muyi abunda ba shi bane, indai har mukaga hakan to tabbas akwai ajiyar da Allah ya mana, saboda a wannan lokacin da muke ciki kana bacci ne wani yana maka nasari, Allah ya karemu yasa mu d'auki wannan shawarar...ameen). Saida tayi masu tadi uku uku sannan suka tashi, Sukam tamkar a mafarki sukaga faruwar abun, A tunaninsu ma mafarkine sukayi kawai dan sun saka tsoro a ransu, Bayan sunyi Sallah Hassu ta k'ara jaddada masu akan su rik'i addu'ah itace makamin mumini. Ita kuwa dodanniya tana can hankalinta kwance, ita a tunaninta abunda ta had'a yana can yana tayar ma su Hassu da hankali ya hana masu bacci, "Yanzu nasan suna can babu kwanciyar hankali duk daren nan basuyi bacci ba, ai dama yanda nayi amfani da baki d'ayan tsafina wurin yinshi nasan ba'a banza ba, tunda na jishi shiru yana can yana wahalar min dasu kuma haka nake so". Dariya dodo yayi yace "kin fini mugunta matata, ke jaruma ce kuma ina fatan kifi haka jarumta, kinyi namijin k'ok'arin da ko ni mijinki banyishi ba, wannan abunda kika had'a ban tab'a tunanin ko a mafarki zan iya had'ashi ba, sai gashi ke kuwa kinyishi da kanki, kuma nasan babu wani abu wanda zasuyi da zai iya cinshi, sai ya gama abunda yake masu sannan zai dawo garemu, kinga ni kuma sai insan kalar abunda zan koya masa, dan yinin gobe yayi masu shi". D'an dodo ne yace "baba nima zan bishi goben, zan tayashi aiki dan nima kaga irin tawa jarumtar", "A'a d'ana, bana son ka tafi kaima ka mutu kamar yanda d'an uwanka ya mutu, ka zauna kawai shi kad'ai ma zai iya, kaga shi koda ace ya mutu ba zamuji komai ba tunda dama had'ashi akayi" Dodo ya fad'a yana bubbuga bayan d'an nashi. "Abunda na had'a fa yafi k'arfinsu, kama daina tunanin akwai abunda zasu iya yi mashi, zai gama ya dawo lafiya, kuma d'ana ka kwantar da hankalinka, goben tare zakuje dashi, saboda kaima ka fara koyon aiki, inason ka zama jarumi yanda koda mun bar garin nan zaka iya yin komai, babu abunda zai gagareka, saboda indai kuka gama da wannan mutanen zamu bar garin nan, zamu koma wani garin kuma tare da Jatau d'in". Shiru dodo yayi, shidai baya so d'anshi yayi aikin gobe, amma baya iya yin musu da matarshi, dan haka dole zai hak'ura suje aikin tare saboda shima abun alfaharinshi ne d'anshi yayi abun jarumta. Washe gari. Jatau ne tafe sanye da wani bak'in yadi maras ko kyawun gani, Sun saje shida yadin jikinshi kalarsu d'aya ba'a ko iya banbancesu, Bai tsaya ko ina ba sai bakin gidan Mati, Audu ne tsaye shida abokinshi suna fira, ganin Jatau yasa ya tsuguna har k'asa ya gaisheshi, Shima abokin nashi gaisheshi yayi sannan Audu yace "a kira maka baba ne?", "Ehh ka kira minshi, kace yayi sauri akwai magana ne muhimmiya" Jatau ya fad'a yana ma Audu murmushi, Ba komai yasashi murmushin ba face tunowa da yayi da Kande, kamar Audu da Kande d'aya kawai banbancin shi namiji ne ita kuma macece, shi harma mantawa yake da wata Kande daya takassara rayuwarta a cikin rumbunshi. Cikin gida Audu ya shiga gabanshi na fad'uwa sosai, haka kawai baisan dalili ba indai yaga Jatau sai gabanshi ya ringa fad'uwa sosai da sauri da sauri, D'akin babanshi ya shiga ya sameshi ya gama cin tuwo, "Baba ga kawu Jatau can waje yana jiranka, yace wai kayi sauri muhimmiyar magana ce zakuyi", "To gani nan zuwa kuwa yanzu", Fita audu yayi da sauri har yanzu gabanshi bai daina fad'uwa ba. "Kayi sauri ka tafi malam, idan kaji kira samu ne, dama yanzun nan kake maganar rashin sana'ar yi, ka dad'e fa rabonka da komai malam, ya kamata ka nufeshi da maganar koda ace ba itace ta kawoshi ba, sai kaji yanda zakuyi" Larai ta fad'a tana kallon mijinta, "Hakane Larai, nima tunanin da nake kenan, amma dai bari in fara jin dame yazo sannan in tuntub'eshi da maganar, ko ranta min kud'i sai yayi inyaso sai in biyashi daga baya, ko kuma inje wurin yaya Na'Allah ya ranta min sai in biyashi". Bayan ya gama maganar ne ya tashi ya nufi hanyar waje. Da fitarshi kuwa ya samu Jatau tsaye yana jiranshi, Har k'asa ya duk'a ya gaisheshi sannan Jatau yace "kwana biyu ka b'uya abokina, shine nace barinzo inyi biko", "Aikuwa ko jiya naje gidanka, saidai k'ofar gidan bata wutuwa saboda ruwane kwance male_male a kwance, kai kace ma wani k'aton kogi ne, kaima kuma bansan yanda akayi ka fito ba", "Ehh kasan ruwan da akayi shekaranjiya ne da yawa, to a tunanina shine yayi yawa har yayi wannan kwanciyar, na fidda wata k'ofar ta bayane na fito ta ita" Jatau ya bashi amsa. "Dama wata maganace nake tafe da ita Mati, bansan ko kanada ra'ayi ba". "To ina saurarenka abokina" Mati ya fad'a yana kallon Jatau. "Haka nace wai tunda dai ga damuna ta shigo sosai me zai hana mu had'a k'arfi da k'arfi mu fara aikin noma? Ni inada gonar ma, sai ka kawo abunda gareka mu had'a muyi duk abunda ya dace", "Kamar kasan abunda ke raina kenan kuwa, to yanzu dai ina son zanje gidan Yaya Na'Allah, zan nufeshi da maganar sai ya bani kud'i koda basuda yawa, kai saika ranta min cikon". "To babu damuwa Mati, kawai ka kawo wanda ka samu d'in babu damuwa ni zan cika maka sauran kyauta, sai muyi aikin nomar" Jatau ya fad'a kamar da gaske mutumin kirki ne, koda yake hausawa sunce munafukinka tabarmarka, wannan haka yake kam. Da wannan maganar suka rabu, Mati cike da murna, Jatau d'in ma cike da murna saboda wani tsari ne yayi, wanda kanshi kawai ya barma sani. Kai tsaye gidan yaya Na'Allah Mati ya nufa, ya fara fad'a mashi matsalarshi, Shiru Yaya Na'Allah yayi kafin yace "nikam Mati dama akwai maganar da nake son muyi dakai game da wannan mugun abokin naka Jatau". 'Daga kai Mati yayi cike da jin haushin maganar da yayanshi yayi mashi yace "ban ganeba Yaya, Jatau abokina fa mutumin kirki ne kuma yana k'aunata, ba mugu bane bafa" "Zaka gane yanzu kuwa, wato Mati an dad'e ana yin ruwa k'asa na shanyewa, ka ajiye hankalinka akan maganar da zan maka". "To yaya ina saurarenka, amma dan Allah bana son ka zama mai d'aukar zuga, idanma wasu mugayen ne suka kawo maka wata zuga game dashi to wallahi k'arya ne, Jatau me k'aunata ne, yana son ganin farin cikina a koda yaushe kuma yana son kaf iyalina" Reebee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/15, 8:19 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 4⃣3⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 _Masu karatu kuyi hak'uri duk jiya baku jimu ba, hakan ya faru ne saboda rashin wutar da muka samu, ayi hak'uri nasan an jiramu an jimu shiru._ ******** "Ka sani Mati, wannan Jatau d'in daka miyar mai sonka koma ince mai k'aunarka sam ba mai k'aunarka bane, bashida buri a rayuwarshi daya wuce yaga kaci baya a koda yaushe, Ka kula da kyau kuma kayi tunani, shin kai kad'aine mutum a duk cikin garin nan? Mesa yake nacewa dole sai dakai zayyi sana'a? Mesa a kowace sana'a kai kake faduwa shi kuma yake samun riba? Wannan mafa babban abun a duba ne Mati, ya kamata kayiwa kanka karatun ta natsu, ka ajiye hankalinka wuri d'aya, kai ba zaka iya yin sana'a da kanka ba dole sai ka had'a dashi? Wannan sam ba tunani bane, kuma ni ba wai bana son baka kud'i bane, wallahi idan yanzu kace min zakayi sana'a kai kad'ai toni mai baka ko nawa kakeso ne, ammafa indai kaida Jatau zakayi to ko sisina bazanyi asara ba dan nasan ba ribarsu zakaci ba saima rashi da zaka samu nasu, Dan haka ina shawartarka daka ajiye maganar Jatau, kazoka muyi sana'armu ta gado tun iyaye da kakanni". Shiru Mati yayi, ji yake inama yanada halin make yayanshi da yayi, yana jin haushi yaji an ambaci wani aibu na Jatau, shi a ganinshi bashida babban masoyi sama da Jatau. "Yaya kunefa baku gane ba, Jatau mutumin kirki ne kuma yana k'aunata, dan Allah ka daina aibuntashi". "Mati kenan, nidai ina shawartarka da ka daina saka Jatau a hud'd'od'inka, ka gwada yin wata sana'ar ba tare dashi ba, ina mai tabbatar maka da zakaga ribar abun". "To shikenan Yaya, na amince zanyi babushi d'in, amma idan nayi kaga wannan d'inma nayi asararshi ai zaka daina zargin Jatau abokina ko?", "Ehh zan daina Mati, kajeka ka dawo anjima zan baka kud'i, saima muje kasuwa ka zab'i duk abunda kake son kayi sana'ar dashi", "To nagode yaya, barin tashi in wuce" Mati ya fad'a bayan ya tashi tsaye. "Ka gaishe min dasu Kande" Yaya Na'Allah ya fad'a danshi baisan Kande ta b'ata ba. Shiru Mati yayi kafin yace "wacece kuma Kande yaya? Kadai manta Larai kake son fad'i ko?", "Kamar ya wacece Kande? Kaida 'yarka kace wai wacece, Kande dai 'yar autarka ita nake nufi". Mati yayi k'ok'arin tuna wacece ya kasa, hakan yasa yace "gaskiya nikam bansan wata Kande ba, Kanden da garemu ta mutu tun shekarun baya". Cike da tashin hankali Yaya Na'Allah yace "kai Mati karfa ka raina min hankali kaji, yaushe Kande ta mutu? Kai kodai bakada lafiya ne wai?", "Lafiyata k'alau yaya, kaine dai ka manta da Kandeta ta mutu kusan shekaru uku kenan da suka wuce". Shikam Yaya Na'Allah d'aukar abun yake kamar wasa, ganin Mati da gaske yake yasa hankalinshi ya k'ara tashi, Lallai akwai matsala, kajeka gida basai ka dawo ba anjima d'in ni zanzo gidan naka da kaina, sai inga idanma zaulayata kake". Tashi Mati yayi cike da mamaki yabar gidan, sau biyu kenan hakan ta faru, dama silar abunda ya kashe kakar matarshi Larai kenan wato Baabah Haja, tunda ta nemi sanin inda Kande take suka nunar dasu basu san wata Kande ba, daga k'arshe Larai tace ai Kande ta dad'e da mutuwa, shine dalilin da yasa itama ta mutu, Gashi kuma yanzu ma Yaya Na'Allah ya sakeyi mishi maganar Kande, Shikam ya shiga duhu, bai san ko wacece haka ba, ko a sauran danginshi shidai yasan bai tab'a yin wata 'yar uwa mai suna Kande ba, amma kuma su suna yawan kawo mashi zancenta. Da wannan tunanin ya tafi gida, kanshi a d'aure ya labartama Larai duk yanda sukayi da yayanshi, Ita kanta taso ta fad'a mishi kar ya saka Jatau a wannan sana'ar da zayyi, sanin halin mijinta akan yanda ya d'auki Jatau da muhimmanci a rayuwarshi ya hanata fad'a mishi hakan, dan tasan komai zai iya yi mata saboda Jatau mai sa'a, bai had'ashi da komai ba, saboda da a tab'o Jatau ya gwammaci a tab'o marigayi babanshi daya dad'e da rasuwa. Sannan kuma itama tayi mamakin maganar Kande daya bata labari, lallai akwai magana mai girma wadda su basu sani ba, Amma ta d'auki alk'awarin zata dage da addu'ah game da wannan magana ta Kande, idanma akwai wata b'oyayyar magana wacce ita bata sani ba game da mai wannan sunan to tana fatan Allah ya bayyanar mata da gaskiya. "Malam ni ina ganin kamar shawara mai kyau ce Yaya Na'Allah ya baka, Ka daure kayi sana'ar kai kad'ai a wannan lokacin, Jatau yanada sa'a sosai, koda ace ma babu abunda ya maka tayiwu daga Allah ne, amma ina shawartarka akan kabi shawararshi zaka tsinci ribarta a gaba". A fusace Mati ya mik'e "karki fad'awa abokina magana maras dad'i mana Larai, shimafa yaya Na'Allah abunda yasa nayi shiru da yana aibunta abokina Jatau kawai dan banida yanda zanyi ne, amma fa magana ta gaskiya bani son ana kawo min kushenshi, komai zan iya yima mutum idan yana fad'in magana akan abokina Jatau" Ya k'arisa maganar cike da fushi. Larai bata kuma fad'in komai ba kawai taci gaba da abunda take tare da k'udurar rik'e addu'ah, musamman akan yanda mijinta baya son a aibunta Jatau duk da munanan halayensa wanda sai a yanzu suke bayyana k'arara. **** Zaune take tayi tagumi hankalinta in yayi dubu ya tashi, Tunaninta d'aya fa kar aje wani abu ya samu mutum mutuminta, tunda gashi tun d'azu take zaman jiran dawowarsa amma shiru har yanzu babushi babu alamunshi. "Mijina ina jin tsoro kar wannan makirar yarinyar ta sake yimashi abunda tayiwa babban d'anmu" ta fad'a cike da fargaba tana kallon mijinta da shima d'in ita yake kallo. "Baki d'aya na rasa abunda zanyi, na rasa me zanyima yarinyar nan in huce da abubuwanda tayi min, ta fara fin k'arfina gava d'aya". Cike da jarumta dodo yace "ki daina wannaa maganar matata, bana so ki karaya, ina son ki d'auka a ranki cewa yanzu zamu fara yak'i da ita, a baya ba komai mukayi ba yanzu ne zamu fara aiki, kar kiga wai dan ta halaka miki abubuwa guda biyu wai zata iya karawa damune, munfi k'arfinta munfi k'arfin wanda ya fita ma, dan haka ki kwantar da hankalinki, barin dubo mana abunda ta mishi". Wani tsafi ya ringayi yana fad'in wasu kalamai dashi kad'ai yasan ma'anarsu, Duk kalma d'aya da zai fad'i sai bakinshi yayi wani irin bak'in kumfa mai cike da k'yama, Tofar da kumfan yakeyi cikin wani kwano na kayan tsafinshi. Da mamaki saiga kumfar tana duddunk'ulewa wuri d'aya, a hankali kuma ta ringa narkewa har saida ta zama tamkar ruwan mai, Bud'e tafin hannunshi yayi zara zaran yatsunshi suka mimmik'e, mugayen akaifunshi suka k'ara firfitowa ya bajesu a jikin kwanon, Cikin lokaci kad'an saiga duk abunda ya faru a daren jiya na d'akin Hassu an gwada masu, Har yanda abun ya ringa narkewa yana zama tsutsotsi duk saida suka gani. Matuk'ar tashin hankali sun shigeshi, hakan yasa yayi saurin malalar da ruwan a k'asa cike da takaici. "Lallai wannan yarinyar tayi k'ok'ari, ta zama abun a yaba mata saboda koba komai tayi namijin k'ok'arin karawa damu, amma fa ki sani yarinya munfi k'arfinki, idan kuma abunda kika d'aukarwa kanki kenan mu zuba dake". Duk yinin ranar su Hassu basuga Jatau ba, ga wata irin yunwa da sukeji gashi kuma har yanzu ba'a kawoma Gaje ba daga gidansu, saboda abincin da Jatau ya ajiye masu yace su ringa dafawa sun d'aukarwa kansu alk'awarin cewa koda ace yunwa zata kashesu saidai ta kashesu akan suci abincin haram, wato na jinin mutane. Cike da kasala Hassu tace "wallahi alhaki ba zai tab'a k'yale Jatau ba, ko barinmu da yunwa da yakeyi ma kad'ai babban zunubi ne barin munanan halayensa" ta k'arisa maganar tana kallonsu Gaje da Bareerah. "Hmm! Hafsatu kenan, ke kikasan wannan ai, shikam ina ya sansu? Ko kin manta cewa jahili ne baisan komai game da addini ba?" Gaje ta tambayeta. "Ki tuna mata kam dan da alama ta manta, me Jatau ya sani? Shi yama san wata kalmar zunubi ne barin har yasan illar yinta?" Bareerah ta fad'a bayan tayi hammar yunwa wadda take ba itace ta farko ba, dan zamansu hamnar da tayi ta yunwa takai goma sha. A cikin rumbu kuwa Jatau ne ya shiga bayan ya gaishe da dodonshi ko amsa mashi gaisuwar bayyi ba yace "Jatau akwai babbar matsala fa, kasan da cewa ta kashe mana abunda matata ta had'a a daren jiya?", Jatau bayyi mamaki ba, saboda sanin halin Hassu da yayi, "Ni dama bana son yi maku musu ne jiya da naji kunce wai babu abunda zata iya yi masa, amma fa yanda nasan halinta dama dole sai tayi mashi wani abu ba, idan ma bata kasheshi ba to dole akwai abunda zata mishi wanda zai illata". Har yanzu dai shiru matar dodo batace komai ba sai huci kawai da takeyi, "Ni nasan yanda zan masu a cikin wannan daren, zan kamosu in kawosu har nan ciki sai yanda mukaga damaryi dasu, sai inga sauran tsiya irin tata, saboda indai ta rigada ta shigo nan ciki tofa babu sauran wani abu da zata iya yi". "Kiyi komai matata, ke jarumace kuma nasan da wannan, inason ki zomin dasu a wulak'ance a cikin daren yau, tabbas idan hakan ta kasance zan k'ara jinjina miki, kuma zan baki sarautar *MASARAUTARMU"* (Next novel na *RAZ* insha Allah). Shiru Jatau yayi baice komai ba, amma fa yasan ko yanzu ba lallai idan akwai wani abunda zasu iya yima Hassu ba, yadai yarda cewa zasu iya wahalar da ita, ammafa bai yarda cewa zasu iya kamota sukai cikin rumbu ba. Da haka Jatau ya fita daga rumbun, kai tsaye d'akinshi ya nufa hankalinshi tamkar baya tare dashi, kawai gani yake asirinshi zai tonu, dan haka dole zai fita a cikin daren nan ya samowa dodo da matarshi jini kodan su k'ara samun k'arfin yi mashi aikin da yake so, wato a kashe mashi matanshi su duka ukun, dan yasan matuk'ar ba'a kashesu ba tofa tabbas asirinshi ya kusa tonuwa, kuma da zarar maganar ta fita waje to duk wani tsafinshi zai k'are, saboda tun kafin babanshi ya mutu ya tabbatar mashi da cewa duk ranar da maganar dodon ta fita waje tofa dole asirinshi zai tonu, kuma dodonshi zai wulak'anta, shima d'in kuma zai wulak'anta sosai, abunda baya fata kenan kuma. Fita yayi waje kuwa, yana fita yaci karo da Amadu d'an abokinshi Sani, tafe yake yana wasa da dokin kara, Caraf Jatau ya kamashi ya damk'e, Bai jira komai ba kawai ya shige cikin gida dashi, A gaban dodo ya kaishi, cike da murna kuwa suka shanye jininshi lokaci guda, d'an dokin kararshi Jatau yayi jifa dashi ta bayan gida, bai koyi tunanin kar asirinshi ya tonu ta hanyar dokin karar ba daya jefar d'in ba. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/15, 8:19 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 4⃣4⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 *DARE* Kwance suke su biyu sai Hassu daga gefensu rik'e da Al-Qur'ani tana karantawa, Gaje da Bareerah kuwa sunyi nisa a baccinsu, A hankali ta ringa jin wata irin k'ara k'was k'was k'was kamar doki na tafiya. Tun tana jin abun a hankali har ya ringa k'aruwa da k'arfi sosai, Jin abun take tamkar a mafarki, baki d'aya hankalinta ya tashi, Tun tana jin k'arar daga waje kuma yanzu ta koma kamar a rufin kwanon d'akinta ne ake yin tafiyar, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Kawai ta iya furtawa. "Kar dai yauma wani abun suka sake aiko mana", A hankali ta rufe Al-Qur'anin ta ajiyeshi a gefenta, Casbahar hannunta ta cire ta ajiye a kusa da dardumar sallarta. Cike da natsuwa ta ringa bubbuga Gaje, saidai tasha wahala kafin Gaje ta tashi daga bacci, Bayan ta tabbatar da ta tashi ta koma ga Bareerah, itama ta wahala kafin ta farka daga baccin. Wannan k'arar takun ce kunnuwansu suka fara jiye masu, dan haka sukayi firgigit daga magagin baccin da sukeyi. Take gabansu yahau dukan uku uku, hawaye suka fara kwaranya daga idanuwansu, lallai suna cikin tashin hankali, saboda wannan k'arar da sukeji tamkar saukar aradu suke jinta, Gashi duk taku d'aya da za'ayi sai sunji k'irjinsu yayi wani mummunar fad'uwa, kuma yayi nauyi sosai kamar an d'ora wani abu mai nauyi a bisa k'irjin. "Ba kuka na tasheku kuyi ba" Hassu tayi maganar k'asa k'asa, "Addu'ah zamuyi ko Allah zai karemu kamar yanda ya karemu a daren jiya". "Hassu taya kike tunanin zan iya yin addu'ah a wannan halin da nake ciki?" Gaje tayi maganar tare da fasa kuka da k'arfi. "Yaya dan Allah ki daina wannan maganar, ita addu'ah ai babu lokacin da ba'a iya yinta, dan Allah ku daure mu rok'i Allah, kunji dai yanda wannan k'arar take k'ara yawaita, saboda haka yanzu ba lokacin yin kowace magana bace" Hassu ta fad'a ita kanta tsoron takeji, amma ta dake ta nunar masu da addu'ah itace fiye da duk wani tsoro da zasuji. Kafin ta koma bisa dardumarta suka ringa jin ana jujjuya d'akin baki d'ayanshi kamar ginin zai zube, Sai a tallabeshi a miyar da saman ya zama k'asa, k'asa kuma ya zama a sama, Wani irin iska mai k'arfi ya figi rufin d'akin aka jefar waje, Ya zamanto babu komai a saman, suna hangen sama ma. Hankalinsu ya k'ara tashi sosai, Hakan yasa Hassu ta ringa neman Qur'aninta duk da yake har fitilar k'wan dake d'akin saida iska ya kasheta, A cikin duhun ta ringa lalubenshi amma bata sameshi ba, Sosai hankalinta ya k'ara tashi, Cike da kuka ta ringa karanto Ayatul-Kursiyyu idonta rufe tam dan bata son ganin abunda zai tayar mata da hankali har yasa ta tsaya da karatunta. Baki d'aya d'akin aka d'auka da hannu, Matsesu akayi da hannu d'aya tamkar yanda ake matse yakuwa, Da k'arfi kuma aka sakesu akayi jifa dasu wuri d'aya, Har yanzu bata daina karanta ayatul-kursiyyu ba saima k'ara muryarta da tayi. Saida ta karanta k'afa bakwai sannan taci gaba da karanta suratul Yasiin cike daddad'ar k'ira'arta tanayi tana shesshek'ar kuka. Cike da takaici dodanniya ta saki ihu da k'arfi sannan ta koma daidai halittarta ta tafi jikin rumbu ta tsaya tana huci. A hankali suka ringa jin komai yana komawa daidai, Hakan yasa Hassu ta d'an dakata da karatun ganin har hasken fitilar ya dawo, komai yayi tsaf tsaf kamar babu abunda ya tab'a faruwa a cikin d'akin. Daga can gefe ta hango Qur'aninta babu abunda ya sameshi, wurin yayi daidai dashi kamar dama acan ta ajiyeshi. D'an murmushin wahala tayi tace "alk'awarin Allah baya tab'a tashi, yayi alk'awarin zai kare littafinshi mai tsarki a kowane hali, gashi kuwa duk wannan tashin hankalin da yanda aka ringa jijjik'a d'akin babu abunda ya sameshi, lallai wannan ikone daga Allah. A hankali dodanniya ta fahimci Hassu ta dakata da karatunta, Har tayi niyyar komawa cikin rumbu kuma ta tuna da alk'awarin da ta d'aukarwa kanta na cewa lallai lallai sai ta kawo su Hassu a cikin wannan daren. Hakan yasa tayi kukan kura ta koma cikin d'akin Hassu batako canja halitta ba, a ainahin tata halittar taje. Da k'arfin gaske ta fad'o cikin d'akin, Jibgegiyar macece, saboda idan zata mik'e to tsayin d'akin ya mata kad'an, saida kuma siririyace ba kamar dodo ba. Cike da tsoro su Gaje suka farka daga baccin wahalar daya d'aukesu, Cin karo da sukayi da dodanniya yasa suka k'ara takurewa wuri d'aya, Sai kuka da k'arfi daya kufce masu, hankalinsu ya k'ara tashi matuk'a, yau kam sun cire ran samun nasarah, saboda tunda ake kawo masu hari basu tab'a had'uwa da mai tsanani irin wannan ba, saboda yau da sifarta tazo masu. Sosai gaban Hassu ya ringa fad'uwa, hakan yasa ta ringa yaren fulatanci tana kuka sosai Qur'ani rungume a k'irjinta, idonta a rufe take yin maganar, Baffa kawai take ambata idan ta fad'i kalma d'aya ta fulatancin, Bayan ta gama yaren ne taci gaba da karatu da k'arfi sosai yanda har wanda yake wajen gidan ma zai iya ji. Tun daga cikin rumbu dodo yake jiyo karatun Hassu, Haka yasa yayi tsafi mai k'arfi ya kira dodanniya akan ta dawo cikin rumbu, Cike da azaba ta samu da k'yar tayi tsafi tabar d'akin, Sai cikin rumbu ta b'ullo, Hankalinshi a tashe yace "haba matata kinaso su kasheki ne? Koni da nake nan ban tsira ba ji yanda aka jijji min rauni to inaga ke dakike tare dasu? Tabbas inda baki dawo ba yau ba lallai kiyi rayuwa ba, zan iya rasaki matata". Wani irin kuka mai had'e da kururuwa ta fasa, "Yanzu shikenan ban cika alk'awari ba? Ban cikawa kaina alk'awari ba da nace yau cikin daren nan zan kawosu cikin rumbu?" Ta sake yin kururuwar wanda shi kanshi dodo saida ya tsorata. "Kar kiji komai matata, nasan kinyi bakin k'ok'arinki na ganin kin cika wannan alk'awarin, amma ki bari ba yau ba, yaukam inhar kika koma ba lallai bane ki dawo" yana gama maganar ya ringa bubbuga bayanta a hankali har yanzu batayi shiru ba. **** "Baffa ka taimakeni, ina cikin wani hali, ina cikin tsananin buk'atar taimako, yana nema ya kasheni, matsafi ne Baffa, idan har bakazo ba komai zai iya yimin, nayi bakin k'ok'arina amma abun yana neman ya gagareni, idan sunayi ina yin nasarah nasan akwai ranar da sune zasuyi nasara bani ba, dan Allah kazo gareni Baffana inhar baka so ka rasa ni". Firgigit ya tashi daga bacci yana kalle kalle, Tabbas wannan ba mafarki bane yakeyi, tamkar a zahiri ne 'yar lelensa tazo masa tana kuka sosai tana da tsananin buk'atar taimakonshi. Hankalinshi ba k'aramin tashi yayi ba, Duk sanyin da akeyi amma shi gumi yake, hakan yasa yasaka tafin hannunshi ya share gumin daya keto a bisa goshinsa. "Tabbas wannan gaskiya ne, ba mafarki bane" ya sake maimaitawa a ranshi. A haka gari ya waye bai ko rintsa ba, ido kumbure su Goggo suka ganshi, Bayan ta gaisheshi tace "nikam malam me sameka ne? Na farka tsakiyar dare na ganka zaune kayi tagumi, kuma gashi yanzu idonka ya kumbura alamar bakayi bacci ba kenan, ince dai ko lafiya", Har yanzu gabanshi fad'uwa yake, da k'yar ya iya samun fad'in "nayi mummunan mafarki ne Amina, kinsan kuma manzon Allah (SAW) ya hanemu akan fad'in mafarki maras kyau, dan haka kedai mu saka Hassu a addu'ah, tana tsananin buk'atarta". Sosai Goggo ta rikice, Ta d'ora hannunta a kai tana salati, "Malam Allah dai yasa lafiya, dan Allah ka fad'a min me ka gani? Me samu 'yata?". "Tana cikin matsala iyakar abunda zan iya fad'a miki kenan, tana kuma da buk'atar addu'ah, dan haka sai mu tashi tsaye mu k'ara tashi tsaye, mu fad'awa Allah", Gabanta ta dafe saboda tsananin fad'uwar da yakeyi, ji take kamar k'afarta ba zata iya d'aukar gangar jikinta ba, dan haka ta nemi wuri ta zauna sai kad'a kanta take tana fatan Allah yasa babu abunda ya samu 'Yarta Hassu. Hassu kuwa har gari ya waye bata daina addu'ah da karatun Al-Qur'ani ba, runtse bata runtsa ba hakan yasa kanta ya ringa mata azabar ciwo kamar sai fashe haka take jinshi, Su kuwa Bareerah da Gaje suma sunyi tagumi tun lokacin da suka tashi daga bacci, Wannan wane irin hali ne suke ciki? Jatau ya zame masu musiba a rayuwarsu, su fata ma suke Allah ya d'auki rayuwarsu akan wannan wahalar da sukesha, babu kawanciyar hankali kullum cikin tashin hankali da masifa suke. "Ya Allah kai kad'ai kasan halin da muke ciki, Allah idan mutuwa itace alkhairi a garemu ina fatan ka d'auki rayuwata ko zan samu sassauci" Gaje ce ta fad'i haka tare da fashewa da kuka. Kallo d'aya za'ayi masu asan suna cike da tashin hankali, hawaye ya gama bushewa a fuskokinsu. Suna cikin haka Jatau ya shigo d'akin, Ganin halin da suke ciki yasa ya fashe da wata irin muguwar dariya, "Tashin hankali yanzu kuka fara gani, indai tak'amarku taurin kai to da tsaurin ido to baku ga komai ba sai yanzu zaku fara, Dan haka sai ku d'auri aniyar ja da matsafa irinmu, sai muga ko waye zayyi nasarah" ya k'ara fashewa da dariya tare da barin d'akin. A Garu kuwa yinin ranar haka Baffa yayishi cike da fargaba da tashin hankali, Lallai matsalace mai girma saboda ta yanda yaga Hassu tazo masa ya tabbatar da akwai damuwa, Hakan yasa ya samu Goggo zaune itama tayi tagumi cike da tashin hankali, Wurin zama ya nema ya fuskanceta, "Nikam ina ganin zan shirya in tafi wurin Hassu dan inga halin da take ciki, saboda bai kamata yanda na ganta kuma ace na zauna ba, dan haka zan tafi da kad'an daga cikin kayakin aikina, saboda inhar wani ke cutarta fa ba zan k'yaleshi ba, dan haka ki harhad'a min kayakina gobe zan kama hanya, zanyi mata aiki sai inda k'arfina ya k'are". Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/16, 5:47 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 4⃣5⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 Yinin ranar dai a haka nan su Hassu sukayishi, Ga yunwa ga gajiyar wahala, hatta da magana ta gagaresu. Suna cikin haka Jatau ya shigo ta k'ofar baya, Kamar yanda ya saba shi yake kawo masu abinci idan an kawo daga gidan su Gaje, Saboda babu wanda zai iya shiga gidan saishi, haka kuma babu wanda zai iya fita saishi. Bayan ya mik'awa Gaje abincin ya kwashe da dariya mai cike da k'eta da mugunta, "Zaku dawwama a cikin wannan rayuwar ne, sai nayi yanda nayi har abincin ma aka daina kawo maku, Yanzun ma abunda yasa nake bari a kawo dan bana son in shiga zargi ne, Saboda daina zuwa gidan da Gaje tayi, nace masu baki da lafiya ne kuma ciwo mai tsanani yanda babu wanda zai iya ziyartarki, Dan haka ne ma kullum idan an kawo abinci a k'ofar baya ake jirana sai idan naje nake karb'owa, kunga kenan babu wanda zai tab'a zargina da wani abu, mu cutar daku nida dodona yanda muke so, a k'arshe mu mu salwantar da rayuwarku" ya k'ara kwashewa da dariya. Hassuce ta tashi babu tsoro ko kad'an a idonta, Duk da tana jin tsoron amma tayi k'ok'arin kawar dashi, Kallon Jatau tayi cikin ido tace "bari kaji wani abu Jatau, Mu da ayar Allah muka dogara kuma insha Allahu akoda yaushe mune da yin nasarah, Saboda duk wanda ya rik'e Allah baya tab'a tab'ewa, kuma Alhamdulillah! Ko yanzu kasuwa ta watse d'an koli yaci riba, Ko yanzu rayuwarmu tazo k'arshe duk da nasan idan muka mutu daga Allah ne, duk cikinku kaida kayan tsafin naka babu wanda ya isa ya d'auki rayuwarmu sai Allah, To naci riba tunda nima na samu nasarah a kanku, addu'ah ta k'ona d'aya daga cikin kayan tsafinku, Sannan kuma duk iya tsafin naku ma na rainashi tunda idan nayi addu'ah guduwa kayan tsafin sukeyi, Dan haka kaja tsumman bakinka kayi gaba". Cike da fushi Jatau ya d'aga hannunshi zai mari Hassu, wanda yayi daidai da d'aga hannun Baffa yana addu'ah, "Ya Allah ka karemin yarinyar nan da kariyarka mafificiya, Allah da kai na dogara ya Allah, kai kace a rok'eka a duk lokacin da bawa yake buk'atar taimako ko agaji, Allah ga Hassu can kai kad'ai kasan halin da take ciki, Allah ka fitar da ita dan zati da hikimarka, ka fitar da ita kamar yanda ka fitar da manzonka (SAW) daga sharrin kafiran Makkah..." Yaci gaba da addu'ah sosai yana fad'in "Ya Rabbi, Ya Rabbi, Ya Rabbi" Kamar yanda yazo a cikin Hadisil Qudsi inda Allah mad'aukakin sarki da kanshi yace _"ina jin kunyar bawana ya anbaceni da wannan suna (Ya Rabbi) har sau uku ya rok'eni wani abu kuma ban amsa mishi abun ba"._ Sosai Baffa ke kuka tare da gurfana ya fuskanci gabas hannunshi duk biyun ya had'esu wuri d'aya. Cak! Hannun Jatau ya mak'ale, yayi yayi ya isar dashi ga fuskar Hassu amma ya kasa, sannan kuma yayi k'ok'arin ya dawo dashi daidai kuma ya kasa. A fusace hannun a mak'ale yabar wurin, Gaje ta kalli Hassu Bareerah ma ta kalli Hassu, "Wai kam baiwar Allah'n nan me kika taka ne?" Suka tambayeta su biyun a tare cike da mamaki. "Babu abunda na taka sai addu'ah, Addu'ah ce take karemu mu duka a kowane lokaci duk da yanzu ma banyi addu'ar ba, har sakin jikina nayi da niyar jin saukar mari kuma sai wannan abun haka ya kasance, dan haka daga Allah ne" Hassu ta fad'a itama kanta mamakin abun takeyi. Haka Jatau ya shiga rumbu har yanzu hannunshi bai saki ba, A hankali ya shiga cikin rumbun yana k'ara kallon hannunshi, Gaban dodo ya tsaya yace "kaga yanda hannuna ya koma ya dodona", Kallonshi dodo yayi sosai yace "garin ya hakan ta kasance Jatau?", "Na d'aga hannuna da nufin marinta ne, kawai saidai jinshi nayi ya mak'ale, har marin nata ma na kasa". Cike da takaici Dodo yace "wacece tayi maka haka!?" Da k'arfi yayi maganar yana k'ara kallon hannun Jatau daya mak'ale. "Har ma sai ka tambayi wadda tayi mishi haka kenan, ai bai kamata ka tambaya ba saboda kaima kanka kasan ko wacece" matar dodo ta fad'i wannan maganar itama d'in cike da fushi. "Wata irin k'ara dodo ya saki da k'arfin gaske yana jujjuya kanshi, nasan ba wanda zai aikarmta haka inba wannan makirar yarinyar Hassu ba, Wannan yarinyar wai wace irin yarinya ce? Yarinya tana neman tafi k'arfinmu, wai mema ta taka ne? Ya kamata fa mu k'ara tashi mata tsaye, muyi k'ok'arin kawar da ita". "Hakane mijina, abunda ya kamata kayi tun baya kenan, sai kace wai kafi so mu sakar masu da rashin kwanciyar hankali sannan ayi masu duk abunda ya dace, amma kaga yanzu idan akayi masu mai baki d'aya shikenan mun samu kwanciyar hankali" matar dodoce ta fad'i haka harda murmushin mugunta. "Ba zamuyi masu komai ba yau, bama zamuje inda suke ba, saboda idan ma tayi wani shiri yau duk shirin ya lalace, kunga idan bamuje ba yau ai gobe ba zatayi tsammanin zamuje ba, sai ta saki jikinta sosai tayi bacci, Daga nan ni kuma sai inyi tsafin da zanyi in d'aukota in kawo cikin rumbun nan, Idan na kawota shikenan tata ta k'are ba zata iya yin komai ba sai yanda mukayi a ita, duk ta wancan sauran matan mai sauk'i ne, cikin lokaci d'aya ma zamu iya gamawa dasu". "Wannan shawarace mai kyau ya dodona, kayi masu duk abunda kaga dama" Jatau ya fad'a, "Yanzu babu wani abu da za'ayi min hannuna ya gyaru?". "Yanzu zan gyara maka hannunka kuwa" dodo yayi maganar bayan ya runtse idonshi, Hasken wuta ya ringa fitarwa daga bakinshi yana isar dashi a hannun Jatau, Haka ya ringayi amma har yanzu hannun Jatau bai gyaru ba, Saida ya maimaita sau uku amma ko alamar gyaruwa hannun bayyi ba, K'arshe dai bud'e idonshi yayi yana mamakin hakan, Duk tsafin da yayi taya za'ace hannun bai gyaru ba? "Jatau hannunka bazai tab'a mik'ewa ba, tunda har nayi tsafin nan bai mik'e ba banga abunda zaisa ya mik'e ba". Kuka Jatau ya fashe dashi ya k'ara kallon hannun, Ya d'an lank'washe sai kuma yatsun sun babbandare baki d'ayansu, Shikenan a haka zai dawwama tunda dai dodo yace bazai tab'a gyaruwa ba. Koda Jatau ya fita daga gidan mutane kowa ya ringa tambayarsa abunda ya samu hannunshi amma cewa kawai yake ya buge hannun ne shine yayi haka A cikin wannan daren babu abunda yazoma su Hassu, Duk da zaman jiran da sukeyi amma har asubah tayi babu abunda yazo, hakan yasa suka fara tunanin ko an k'yalesu ne, Amma Hassu ita kanta tasan anyi masu dabarah ne kawai dan a samu damar zuwa masu gobe dan ansan zasu saki jikinsu. Tunda asubah Baffa ya fara shiri, Saida Goggo ta masa addu'ah sosai sannan ya d'auki kayakinshi ya kama hanyar barin garin, Yayi sa'a kuwa ya samu mashin ya kawo wani natafiyi, dan haka ya tsayar da mashin d'in ya kaishi har cikin garin Yola, Acan ne ya samu mota kai tsaye wadda zata kaishi har Sokoto, Abunka ga bak'auyen mutum duk inda aka shiga sai rarraba ido yake yana kallon abubuwan da bai tab'a gani ba, saboda shi tunda yake bai tab'a barin Yola ba. A b'angaren yaya Na'Allah kuwa yaje gidan Mati, ya samu yana zaune shida Larai, Shima zaman yayi ya fuskancesu, "Yaya ina yini?" Larai ta fad'a bayan ta rusuna k'asa. "Lafiya k'alau Larai, ya yaran?", "Lafiya lau basu dawo daga makaranta ba" ta bashi amsa tare da komawa wurin zamanta ta zauna. Shima Mati d'in gaisheshi yayi ya amsa, "Sannunku, kamar yanda na fad'a maka cewa zanzo shine d'in nazo, game da maganar Kande ne wanda ka nemi ka miyar dani shashasha wanda baisan abunda yake ba, Taya zakace wai kai baka tab'a yin wata 'ya mai irin sunan ba? Amma kuma kana tunanin ka tab'a yinta wai ta mutu tunda dad'ewa, sam wannan ba magana bace, idan ma siyar da ita kayi ko kuma b'atar da ita kayi dole ka fito fili ka fad'a min, ba wai b'oye b'oye ba, mun wuce lokacin da hakan zata shiga tsakaninmu, kai k'anina ne ni d'an uwanka ne, bakada wanda ya fini haka nima bani da wanda ya fika, Dan haka kar kaji komai, ka fad'a min gaskiya ni mai rufa maka asiri ne a kowane hali" ya k'arisa maganar bayan ya fuskancesu. Shiru Mati yayi yana k'ara nazari, shidai yasan har ga Allah iyakar gaskiyar kenan, baki d'aya ya rasa inda yaya Na'Allah ya dosa, Ita kanta Larai d'in hakane, tunda yake magana ta aje hankalinta wuri d'aya wai ko zata iya tuna wani abu amma ta kasa, Hakan yasa ta bud'e baki tace "Kayi hak'uri yaya Na'Allah amma fa ni kaina bansan inda zancen nan naka ya dosa ba, haka Baabah Haja kakata ta samemu da wannan maganar wanda hakan ne ya sama ajalinta, dan Allah kayi mana yanda zamu gane". Shiru Yaya Na'Allah yayi jikinshi sukuku, kar dai da gaske sukeyi basu san Kande ba, lallai akwai matsala babba, taya zaka haifi 'ya da cikinka kuma kace baka santa ba? Akwai dai wata b'oyayya a k'asa wanda Allah kad'ai ya barwa kansa sani. Bayan Yaya Na'Allah ya gama maganar zuci ne yace "Nidai fatana Allah yasa ba siyar da yarinyar nan kukayi ba, amma fa wannan maganar a dubace kuma a sakata a ma'auni a aunata, Kande fa 'yarku ta cikinku nake nufi". "Tabbas ni kaina na jima ina tunanin wannan al'amarin, tun lokacin da naji wani abu tamkar mashi ya soke min gefen zuciyata, tun daga lokacin na samu kaina da tunanin kamar na tab'a yin 'yar uwa Kande amma kuma nayi k'ok'arin tunata na kasa, kullum na kwanta bacci sai tunaninta ya fad'o min amma sai inyi k'ok'arin kawar dashi, lokaci d'aya kuma na samu kaina da mantata baki d'aya daga rayuwata. Sai bayan mutuwar Baabah Haja ne na sake ajiye hankalina, na samu malaminmu da maganar shine yace zaimin istahara akan maganar Kande, in sameshi bayan kwana uku, Bayan kwana uku na sameshi, yace inyi hak'uri yayi istahara amma baiga komai ba, Ya sake bani hak'uri cewa zaici gaba da yimin istahara insha Allahu yana sa ran Allah zai gwada masa komai, Haka na ringa zuwa wurinshi koda yaushe yana k'ara bani hak'uri, Sai yau naje wurinshi yake sanar min abubuwan daya gani a istaharar, Ya shaida min cewa Kande tana wurin d'aya daga cikin manya manyan shak'ik'an Babanmu, baiga inda take kai tsaye ba, ammafa wurin makusancinshi ne take, sannan kuma ya ajiyeta bai mata komai ba, saidai kuma tana cikin matsanancin hali, an kashe bakin kowa daga cikin dangin Kande, saisa kowa ya manta da ita, nima d'in an samu matsala ne wurin rufe bakina yasa nake d'an tunata kad'an kad'an". Audu ne ya jefo da wannan maganar tare da hawaye zafafa daga idonshi. Yaya Na'Allah ne ya mik'e tsaye yace "babu wanda zayyi haka sai Jatau mai sa'a, tabbas shine kada'i zai iya aikata haka", "Wallahi kawu ni kaina tunanin da nayi kenan, tun lokacin da malam yake fad'a min banyi tunanin kowa ba sai Jatau mai sa'a" Audu ya fad'a yana kallon Mati. Cike da tashin hankali Mati ya shak'e wuyan Audu, "Wannan wane irin sharri ne kake k'ok'arin k'ullawa Jatau abokina Audu? Me ya maka? Yanzu duk irin soyayyar da yake gwada min ni mahaifinka saida haka zaka bishi? Baka kyauta min ba Audu, bakaiwa Jatau mai sa'a adalci ba". Da k'arfi Yaya Na'Allah yaja Audu yace "Mati ka saki yaron nan nace!", Mati baida yanda zayyi dan dole ya saki Audu tare da komawa k'asa ya zauna cike da tsanar Audu. "Kazo mu tafi gidan Jatau d'in, yau yau d'in nan za'ayita ta k'are, duk inda yakai Kande sai ya fad'i, ko kuma yau k'arshenshi yazo" Yaya Na'Allah ya fad'a bayan ya kama hannun Audu sun fita. Larai ma hijabinta ta saka tabi bayansu, suma sauran Baseeru da Talle binsu sukayu, Ganin haja yasa Mati ma bin bayansu yayi, saboda baya son yayanshi ya aikata wani mummunan abu akan abokinshi Jatau. Isarsu k'ofar gidan Jatau tayi daidai da isar Baffan Hassu, da tambaya ya usa gidan a lokacin har magrib tayi. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/17, 6:08 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 4⃣6⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 _Gaisuwa ta musamman ga *Phertymah Xarah (Pherty),* muna jin dad'in yanda kike kula tare da bibiyar wannan labarin, tsakanin *mu da ke* akwai soyayya mai k'arfi, dan haka mun sadaukar da wannan shafin gareki, fatanmu a kullum Allah ya k'ara d'aukaka marubutanmu baki d'aya._ ****** Kicib'us sukayi a kusa da gidan Jatau, a hankali Baffa ya taka zuwa inda suke, Hannu ya mik'awa Yaya Na'Allah suka gaisa sannan yace, "Dan Allah malam tambaya nake", "To Allah yasa na sani" Yaya Na'Allah ya fad'a fuskarshi d'auke da murmushi. "Gidan Jatau mai sa'a nake tambaya" Baffa ya tambayi Yaya Na'Allah, "An kwatanta min wai ance ta nan ne gidan, ina nufin Jatau mijin Hafsatu, kwanan nan ba'afi wata biyar zuwa shida ba yayi sabon aure, ya auro wata bafulatana.." Yana neman ci gaba da bayani irin nasu na fulani Yaya Na'Allah ya dakatar dashi ta hanyar fad'in, "In kaso na gane wanda kake nufi, nima gidanshi zamuje ai, gashi can wanda yake fuskantarmu". Cike da mamaki Baffa yake kallon gidan, Gidane babba mai jyau sosai ginin jar k'asa, A duk k'auyen Bagu babu gidan mai kyau kamar gidan Jatau, Gaba su Yaya Na'Allah sukayi Baffa yana biye dasu a baya rataye da 'yar buhun bakonshi sai hukarshi hab'ar kada ya tattare gefenta, Wuyanshi ya sargafa makimanciyar sanda ya rik'e da hannun damarshi. A daidai k'ofar gidan Jatau suka dakata kasantuwar makeken fili da suka ringa gani a wurin, bayan kuma kafin su k'ariso suna ganin gidan lafiya lau. Kallon kallo suka ringa bin junansu dashi, "Nikam kodai idona ne yake gane min haka? Fili kawai nake gani kamar babu gida anan" Yaya Na'Allah ya fad'a had'e da waigen Baffa da shima d'in shi yake kallo. "Mu shiga ta cikin filin mu gani to" Audu ya fad'a yana kallon babanshi Mati cike da tsoro, dan yasan yau had'uwarshi da babanshi ba zata masu dad'i ba. Shawarar Audun kuwa sukabi, rankas sukayi k'ok'arin shiga filin saidai kuma me? Ruwa suka gani malale a cikin filin wanda ko k'arshenshi basu gani, Sake kallon junansu sukayi cike da mamaki, sun kasa shiga ruwan kuma su basu juya baya ba. "An samu akasi kuma, ni ban iya ruwa ba, hasalima tsoron ruwa nake saboda har jiri yake d'ibata idan na kusanci ruwa, dan haka saidai mu koma sai wani lokacin, ina jin harda yanayin damunar da ake ciki ne yasa ruwa yake kwanciya anan, barinma kuma dama gangarene wurin" Yaya Na'Allah ne ya fad'i haka tare da k'ok'arin komawa baya, Baya son ya fad'i wata magana ya b'atanci game da Jatau, sabida yana gudun ko Baffa makusancin Jatau ne. "Ni da nake fillo tsoron ruwan me zanji? Ku bari na shiga, idan na shiga sai inji mai zurfi ne ko naras zurfi? Kunga idan ba mai zurfi bane kawai sai kuma ku biyoni mu shiga, saboda nidai a tsananin buk'ace nake da ganin halin da 'yata take ciki, bana son in k'ara kwana ba tare dana ganta ba" Baffa ya fad'a bayan ya tsoma k'afarshi a cikin ruwan. "Kunga kuwa bashi da zurfi, ga iyakar inda k'afata ta shiga' ya gwada masu k'afar, hakan yasa suma suka tsoma tasu k'afar a cikin ruwan, Nan da nan kuwa sukaci gaba da tafiyarsu. Sunyi tafiya sunkai kimanin tsakiyar ruwan suka ringa ganin namun daji irinsu zaki, damusa, giwa da sauran nau'o'in dabbobin daji masu cutarwa, Take gabansu ya hau fad'uwa, Hankalinsu in yayi dubu ya tashi, duk suka mak'alk'ale junansu barinma Larai data gama firgicewa da ganin wannan dabbobin. Baffa kam ko a jikinshi, saboda wanda suka fisuma yasha had'uwa dasu, dan haka baiji tsoron komai ba yasa sandarshi ya ringa koresu da ita, Dama kuma sandar tashi tare take da ayoyin Allah, a kowace rana sai ya tofeta da addu'o'i da ayoyin Allah saboda gudun irin haka dama, saboda shi mutum ne mai yawan shiga daji iri iri, to kuma baisan kalar abubuwan da zaici karo dasu ba, dan haka baya barin sandarshi a haka. Take kuwa dabbobin suka ringa ja da baya, cikin lokaci kad'an sai gashi ko b'ushi b'ushinsu babu, Hakan ba k'aramin mamaki ya bama su Yaya Na'Allah ba, sunyi mamaki sosai saboda ko alamar tsoro Baffa bashida shi. Ci gaba da tafiyar sukayi a cikin ruwa har saida suka kai k'arshen ruwan dai babu alamar gidan Jatau, Tun abun baya basu tsoro har takaiga sun fara tsorata, wai gidan Jatau da dazarar an shigo kwana shine yake fuskantar mutum, amma sai gashi yau babushi babu alamarshi. "To kodai ruwa ya shafeshi ne?" Audu ya fad'a cike da natsuwa. "Wane irin ruwa ya shafeshi? Tsayuwarmu bawan Allah'n nan yana tambayarmu mafa ina hangen gidan, kai da sakel dai kam" Larai ta fad'a saboda itadai kam ta fara tsorata da wannan al'amarin, "Nidai gaskiya mu hak'ura mu koma gida". "Nima dai da abunda zan fad'a kenan kika rigani Innah, kar muje fa garin neman k'iba mu samo rama, muje mukai kammu ga halaka muna ji muna gani" Talle ya fad'a dan shima fa tsoron yake ji sosai. "Aradun Allah babu inda zanje ina nan saina gano inda 'yata take, saboda bazan yarda ta sake kwanta a cikin matsanancin halin da take ciki ba, kudai ku tafi, ku kwatanta min gidanku yanda idan na gano gidan zan nemeku fan in gwada makushi" Baffa ya fad'a bayan ya sauke jikarshi sabida ya gaji sosai. 'Yar gorarshi ya fiddo daga cikin jikar bako d'in, a hankali ya fara alwala suna kallonshi, Yanda yakeyi alwalar kanshi ya banbanta da yanda aka umurci bayi suyi. (Kallona sis R. Tayi tace "sis kiga yanda yake alwala kamar bai iyaba, kuma wai malami ne", Caraf Zarah tace "nima dai maganar da nake kenan da zuciyata, kun rigani a fili na rigaki a zuci" Murmushi na masu nace "wannan alwalar da yakeyi akwaita a sunnah, tazo a cikin wnai hadisi an kwatanta mana yanda zamuyita, itama kanta wata hikimar kariya ce, Sannan kuma mutanen zamanin manzon Allah (SAW) sunfi yinya a lokacin da suke neman agaji, ko kuma suke saurin yayin tafiya yak'i, ko kuma idan basuda wadataccen ruwa, Itadai alwalar ana yinta kamar haka; Zan dangwali ruwa makimanci a hannuna, sai in wanke tafukan hannuna duka biyun, Zan sake dangwalo wani in kurkure baki in tofar kamar dai yanda zanyi sananniyar alwala wadda kowa keyi, Daga nan zan shaka ruwa sannan in dangwali kad'an in wanke fuskata, Duka kowane shud'i guda guda ne, Daga fuska sai hannu, amma da ruwan dana wanke hannun dama ba sai na dangwali wani ba, da kufa kufanshi zan wanke hannun hagun, Daga nan sai inci gaba da dangwala ina wanke sauran guraben da suka rage har in kammala", "Lallai kam kinga ko yanzu mun k'aru da wannan" Zarah ta fad'a tana kallona). Suna kallon Baffa har ya gama alwalar ya fuskanci alk'iblah, su basu tafi ba ba kuma su nemi wurin zama ba, saboda gajiya iya gajiya sunyi ta, ko tafiyar da sukayi a cikin ruwa kanta mai tsawo ce. Bayan Baffa ya gama sallar ne ya d'aga hannunshi ya rok'i Allah sosai akan ya bayyana masu gidan Jatau, Ajiye hannunshi kenan kamar wasa ginin gidan Jatau ya ringa saukowa daga can bayansu, Ashe dama sun rigada sun wuceshi tun da jimawa, D'aga kansu sukayi kamar wasa kuwa sukaga gidan Jatau, hankalinsu ya k'ara tashi sosai, Saida Baffa ya gama addu'ah sosai sannan ya tashi yayi gaba suna biye dashi a baya, Baki d'ayansu tsoro ya gama mamayesu, shi kuma Baffa ba wai tsoro yakeyi ba, kawai dai yana mamaki wannan al'amarin ne, Babu wanda ya kuma fad'in komai face zuba idonsu da sukayi suna biye da Baffa da ko alamar tsoro babu a tare dashi, har yanzu dai yana mak'ale da sandarshi a kafad'a. Har cikin gidan suka shiga, Mati yayi mamaki sosai saboda bai tab'a shiga gidan Jatau ta k'ofar bayan nan ba saidai ta gaba, bai ma san akwaita ba sai lokacin daya fad'a masa tanan yabi lokacinda ruwa ya cika gidansa wai a cewarsa. Yanzu kam sun tabbatar da lamarin Jatau akwai sark'ak'k'iya a cikinsa, Harda Mati d'in kanshi ya gama tsorata da wannan lamarin, Idan ba gidan matsafaci ba wane gida ne zai ringa b'acewa yana b'ullowa, Akwai dau *b'oyayyen al'amari* wanda Allah kad'ai ya barwa kansa sani sai kuma shi Jatau d'in. Da wannan maganar suka k'arisa cikin gidan, Saidai kuma abun mamaki kamar kango haka suka ringa ganin gidan, Irin tsofaffin gidajen nan wanda an dad'e da shigarsu aka fita, Saboda ko rufi babu a jaf d'akunan gidan, sannan katangun wasu duk sun rushe. Duk wannan abubuwan dake faruwa Jatau na cikin rumbunshi hankali tashe dodo yayi tsafi a wata 'yar k'warya suna ganin su Baffa, Tun farkon zuwansu har yanzu da suka shigo gidan, Babban tashin hankalin Jatau bai wuce ganin Yaya Na'Allah da mutane da yawa ba, yasan tabbas akwai magana, idan ba hakaba me zai kawosu harda wannan gayyar haka? Shikenan yau asirinsu zai tonu. Dodo ne yayi k'ok'arin kwantar masa da hankali ta hanyar fad'in "Kar ka damu Jatau, na maka alk'awarin babu abunda zasu gani a cikin gidan nan, yanda sukazo a haka zasu tafu ba tare da sunga komai ba, ka saki jikinka kawai nama gama aikin". Hankalin Jatau ya d'an kwanta amma ba sosai ba, har yanzu jikinshi bai daina rawa ba, yana k'ara tuno furucin da babanshi ya masa kafin ya rasu, na cewa idan har yayi kuskure asirinsa ya tonu koda mutum d'aya ne yasan halin da yake ciki tifa tasu ta k'are. Bai ankara ba yaji hawaye suna sintiri a bisa goshinshi, Janshi dodo yayi ya d'ora a bisa cinyarshi, Amma tsabar girman dodon sai yayi kamar bai d'aura komai ba, Da sauri Jatau ya sauka daga bisa cinyar, saboda wasu k'ayoyi da suka ringa sukarshi. Su Baffa kuwa har Yaya Na'Allah yace kawai su haj'ura su tafi, ta yiwu ruwane ya cinye gidan suka tashi, Amma fa sam Baffa yace shi bazai tafi ba, saboda shikam jikinshi ya bashi nan ne gidan, dan haka saidai su su tafi amma shi yana nan. Mati yace "kudaici gaba da biyewa shirmen wannan bafulatanin, bayan kuma kunsan fulani da wauta, nan ina kukaga alamar akwai mutane a ciki da har zaku nemi kubi zancenshi? Jatau kam da alama ya tashi". Ganin har yanzu Baffa bashida niyyar binsu yasa Yaya Na'Allah yace "bawan Allah ka tashi mu tafi, babu kowa a gidan nan, gashi har duhu ya fara", "Ba wai nak'i ta taku bane, ammafa inaji a jikina 'yata tana cikin gidan nan" Baffa ya fad'a bayan ya nemi wuri ya zauna, "Ku samu kuyi sallar magrib kar lokacinta ya fita, kunsan ita k'aramin lokaci ne da ita, nikam nayi k'asaru tun a hanya na had'a da isha'". "Ehh kaima kuma kayi magana, amma kuma ina zamuyi sallah anan? Bayan kuma ko ruwa babu?" Larai ta fad'a tana kallon Mati mijinta. "Kudai dage bin maganar fulani, wanda babu magana mai ma'ana a tare dashi saidai shirme", "Haba Mati! Wannan wane irin cin fuska ne? Kasan kuwa cin fuska bashi da kyau a addini?" Yaya Na'Allah ya fad'a yana kallon Mati, Shiru yayi cike da tsanar Baffa, shidai haka kawai yaji mutumin bayyi masa ba, Shi kuwa Baffan murmushi kawai yayi ya kalli Mati, duk da Mati d'in ya girmi Baffa amma kuma ai ko tsakanin manya da yara akwai girmamawa, bawai dan kaga kaine babba a wuri ka ringa yima k'arami wulak'anci ba. ******* A hankali Hassu ke jiyo muryoyi wanda ta rasa ta inda suke fita, Tana jin muryoyin a kusa dasu ne sannan kuma tasan tasan muryar d'aya daga ciku, amma kasantuwar ba sosai muryar ke fita ba yasa ta kasa tantance ko ta wacece, sannan kuma a halin da suke ciki basu tab'a tsammanin akwai wanda zaizo inda suke ba, Hakan yasa ta kawar da tunaninta kawai, saboda su Gaje basu ma ji muryoyin ba, itace kawai take jin muryar mutanen. Jin muryoyin suna k'ara yawaita yasata mik'ewa tsaye, "Nikam zan fita inga ko meke faruwa", Cikin tsoro Bareerah tace "karki fita Hafsatu, baki san ko wata siga bace suka d'auko ta hanyar halakamu, dan Allah na rok'eki ki tsaya karki fita" ta fashe da kuka, "Idan kuma zaki fita to saidai mu fita tare dan ba zamu bari ki tafi ke kad'ai ba, duk abunda zai sameki ya samemu tare". "Maganarki gaskiya ne Bareerah, saidai mu tafi tare" Gaje ta fad'a tare da mik'ewa tsaye, saboda har yanzu Hassu bata zauna ba, gabanta mummunar fad'uwa yake saboda muryar da takeji. Hanyar fita d'in kuwa suka kama su duka ukun, ata inda sukaji muryar tafi k'arfi suka dosa, wato inda su Baffa suke. *_muna miki murnar kammala littafinki mai ma'ana Aunty Sdy Jegal, Allah ya k'ara miki baseerah, hazak'a da kuma d'aukaka, RAZ sun gaisheki sun kuma tayaki murna sosai_* Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/18, 9:07 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 4⃣7⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 _Wannan shafin naku ne 'yan *Zauren Biebie Isah,* zan iya cewa kunfi kowa son littafin *Dodon Jatau,* *RAZ* suna ganin sak'onninku kuma suna farin cikin hakan, suna k'aunarku sosai kamar yanda kuma kuke k'aunarsu, fatan alkhairi gareku baku d'aya._ ***** A hankali cike da fargaba suke tafiya ga fitilar k'wai a hannun Hassu da tayo gaba sai rarraba ido take, Cikin sand'a suke tafiya har suka isa inda muryar ke fita sosai, Cike da al'ajabi tace "Baffa!" Da k'arfi har saida ya jiyota, Da sauri ta saki fitilar hannunta k'asa ta k'arisa wurin Baffanta ta rungumeshi cike da farin ciki, Take kuma sai hawaye wanda ta rasa ko hawayen na menene. "Kiyi shiru Hassuna, ba gashi nazo gareki ba yanzu?" Baffan nata ya fad'a cike da rarrashi. "Baffa ashe Jatau mugune matsafacine aka aura minshi" ta fad'a tare da rushewa da wani kukan. Yaya Na'Allah dake tsaye saida ya zabura jin furucin Hassu, lallai biri yayi kama da mutum. Da sauri ya matso inda take yace "yarinya mesa kika fad'i haka? Ina Jatau d'in yake?", "Nima ban sani ba" kawaa ta iya furta masa sannan taci gaba da kukanta, a daidai lokacin su Gaje suka k'ariso inda suke hannun Bareerah rik'e da fitikar da Hassu ta saki. "Ki ajiye hankalinki wuri d'aya ki mana bayani kinji? Babu abunda zasu iya yi miki insha Allahu tunda gani tare dake" Baffa ya fad'a cikin sigar rarrashi. Cikin natsuwa kuwa Hassu ta sanar dasu kaf abunda ta sani tun daga farko har k'arshe bata b'oye masu ba, d'an abunda ta manta bata fad'a bama saida su Gaje suka fad'eshi basu rage ba. Mutuwar tsaye Mati yayi, yama rasa abunda zai fad'a sai kallo da yake binsu dashi, Sauranma dai duk kanwar ja ce, Audu kam bayyi mamaki ba saboda dama malaminsa ya fad'a masa hakan saidai bai fito zahiri ya fad'a masa komai ba. "To ya isa haka ya isa 'yata, ki daina kukan nan bana sonshi, Kinyi k'ok'arima sosai kuma na yaba miki, Lallai kunga muhimmancin addu'ah sosai, saboda inda ace babu ita da tuni nasan sun gama daku, ku k'ara dagewa sosai, Sannan kuma nasan tunda muka shigo nan ba lallai mu fita ta sauk'i ba, bama na tunanin zasu barmu mu fita har sai mun gama dasu, Dan haka kumu daure mu kwana anan kafin safiya tayi, saidai kuma sai an daure, saboda ba zasu k'yalemu haka kawai ba, Amma babu komai nasan abunda zanyi, kudaiyi k'ok'ari kuyi sallah, gashi inaji har isha ma tayi". "Maganarka gaskiyane Malam, matsafa irinsu Jatau dama ba sasu barmu mu fita daga gidansu ta sauk'i ba, ashe saisa gidan ya ringa zama abubuwa iri iri kafin mu shigeshi, lallai kuwa sai mun tashi tsaye, dole mu hana idanuwanmu bacci a wannan daren domin kariyar kanmu" Yaya Na'Allah ne ya fad'i wannan maganar cike da al'ajabin wannan al'amarin. Da sauri Larai ta matsa inda Hassu take, "Yarinya ko kinji labarin inda yakai kin 'yata? Sunanta Kande" cike da tashin hankali tayi wannan maganar tare da kama kafad'ar Hassu da hannunta na dama. "Gaskiya mama ban sani ba, ammafa kusan duk abunda zai samo a cikin wancan rumbun nashi yake kaiwa, ina miki fatan Allah dai yasa ba jininta ya bayar ga dodonshi ba". Kuka Larai ta k'ara b'arkewa dashi, hankalinta ya k'ara tashi sosai, Mati kam ya rasa abunda zai fad'a, yanzu kam ya yarda da maganganun da sukeyi, Sai kuma a yanzu yake k'ara tuno wasu abubuwan wanda suka faru a tsakaninu wanda suka tabbatar masa da hakan, lallai Jatau matsafi ne shine bai sani ba. Cike da al'ajabi suke har Gaje ta kawo masu ruwan alwala da tabarma, Take kuwa sukayi sallah suka sanar da Allah matsalolinsu. Bayan sun idar suka zauna kowa yayi jigum jigum yana tunani, Suna fatan Allah ya basu nasarah akan wannan azzalumin da kayan tsafinshi, koda yake hausawa sunce sarkin yawa yafi sarkin k'arfi. *(RAZ* sukace ba anan take ba). **** Jatau ne har yanzu hankalinshi bai kwanta ba, musammanma yanzu da yaga su Hassu sunje inda suke har sun labarta masu komai. "Shikenan tawa ta k'are ni Jatau, asirina ya tonu, na shiga uku!" Ya fad'a kamar zautacce. Shi kanshi dodo da matarshi kamar zautattu haka suka koma, sun rasa yanda akayi tsafin yak'i tasiri ga Hassu da kuma mutanen da suka shigo gidan a wannan lokacin. Ta 'yar k'aramar k'ofar rumbun Jatau ya lek'a, nan idonshi ya k'ara hango mishi su Baffa da har yanzu bai saki Hassu ba, k'ara kwantar mata da hankali kawai yakeyi. Dodo ne cike da tashin hankali da firgici yace "naji sunce wai anan zasu kwana, dan haka dole musan yanda zamu gama dasu a cikin daren nan, dan haka Jatau kayi k'ok'arin fita ka samo mana wadataccen jini a cikin daren nan, zamusha nida matata da yarana uku, na maka alk'awarin zan kawar maka dasu su duka dake wurin can, Jatau kai amanata ne, mahaifinka ya damk'a min amanarka dan haka dole in maka abunda kake so, dolena in faranta maka rai, bazan tab'a bari asirinka ya tonu ba, karka damu kaji?" D'aga kai kawai Jatau yayi ba wai dan hankalin nashi ya kwanta ba, har yanzu yana k'ara lek'ensu ta 'yar k'ofar yana tunanin shikenan su Hassu sun fad'a masu komai, gashi kuma harda Mati abokinshi da duk zamansu bai tab'a sanin halinshi ba, yanzu kam ya tabbatar daya sani. "To ya za'ayi in fita ya dodona? Saboda bana so su ganni, idan har suka ganni tofa komai zasu iya yimin" Jatau ya fad'a yana kallon dodonshi cikin rauni da fargaba sosai". "Ka runtse idonka kawai zaka fita, idan ka tashi dawowama kawai ka runtse idon naka, zaka dawo" Dodon nashi ya fad'a yana ma Jatau murmushi. Nan da nan kuwa Jatau ya dawo cikin rumbu, yana b'ullowa yara biyu ma suka b'ullo, harda leb'o dodo ya sud'a sannan ya fara yi masu aiki, Jinin yaro d'aya ya shanye sannan ya raba jinin d'ayan yaron kashi biyu, matarshi ya bama rabi sannan yaba yaranshi sauran rabin, hakan yasa suka samun k'arfi sosai tare da d'aukar alwashin yau yau d'in nan zasu gama dasu Hassu. _dan Allah kuyi hak'uri da wannan, wallahi mura nake duk ta kashe min jiki ta sakar min zazzab'i, baifi shafi uku bama littafin dukanshi ya k'are, muna k'aunarku masoyanmu na nesa dana kusa._ Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/19, 9:26 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 4⃣8⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 Da k'arfi dodo ya saki wata irin gigitacciyar k'ara wadda duka su Baffa saida hankalinsu ya tashi, Wani irin wawan juyi yayi mai had'e da hasken wuta, take gidan yahau jujjuyawa kamar abun wasa, Ga wuta tana b'ulb'ukowa daga k'asan ko ina na cikin gidan, Iua kad'uwa sun kad'u, ga azabar wutar da zafinta da yake shigarsu. Sake bud'e hannunshi yayi ya ware yatsunshi na hagu, da k'arfi ya yarfa hannun take wasu irin dogayen halittu masu kama da macizai suka ringa fita daga hannun barin rumbun da sauri da sauri, Saidai kuma ba macizai bane sabida su sirarane sosai gasu da sauri sosai, Duk kaurinsu bazai wuce kaurin tana ba, amma kuma sunada tsayi sosai kamar na maciji, sannan kuma bak'ak'ene sosai da jajayen idanuwa kamar jan garwashi. Yaukam Dodo ya d'auki aniyar yak'arsu kota halin k'ak'a, saboda ya kula kamar sauk'inda yakeyi shi yakeja har akeyi masu yanda akaga dama. Bayan abubuwa sunbar rumbun ne ya sake sakin wata k'arar ya bud'e bakinshi ya furzo iska mai k'arfi, Wani irin bak'in ruwa ya fito daga bakin nashi, tofar dashi yayi sai gashi ya zama wasu k'ananan k'wari suma bak'ak'e marasa kyawun gani, Da mamaki sai gasu suna tashi sama suna barin cikin rumbun, Isarsu tayi daidai da isar wancan dogayen abubuwan, Dan haka suka had'e wuri d'aya suka isa daidai inda suke, Shigarsu suka ringayi tako ina babu sassauci, In banda ihu babu abunda ke tashi a wurin, Baffa kuwa har yanzu yak'i sakin Hassu, babu abunda yafi damunshi face zafin wutar dake fita daga k'asansu. Dodo kuwa har yanzu tsaye yake yana kallon duk abunda yake faruwa, Ganin wancan d'in sun gama yasa ya sake juyawa ya saki wani iskan, Take iskan ya isa inda suke ya ringa yin sama dasu yana nanawa a k'asa, Wasu daga cikinsu duk suka jijji ciwo sai jini ke malala a wurin. Cikin k'arfi da azama Baffa ya saki Hassu ya mik'e tsaye, Dukda azabar wutar bata hanashi lalubar buhum bakonshi ba, Da hansari ya fitar da buzunshi ya shimfid'a akan inda wutar ke fita, Da ajiye buzun kuwa take wutar wurin tayi k'ara sosai tare da mutuwa, Sauran wutacen gefensu kuwa da haskensu yayi amfani ya zaro k'aranar gorarshi wadda keda sauran ruwa yayi irin alwalar da yayi d'azu a lokacinda suna neman gidan Jatau, Bayan ya gama alwalar yahau kan buzunshi, Alkah kad'ai yasan abunda Baffa yake karantawa a tsayuwarshi, ya jima kafin yayi ruku'i, Sallah raka'a biyu kacal yayi, amma sai kace wanda yayi raka'a talatin, saboda ya dad'e sosai yana yinta. Take baki d'ayan gidan ya fara jijjiga banda wurinda suke, Inda rumbu yake kuwa sai anyi sama da rumbun sai ya sauko k'asa, Sauran d'akunan gidan kuwa rushewa suka ringayi saboda azaba, Addu'ah Baffa keyi sosai a sujjadar da yayi ta k'arshe. Baki d'aya abunda ke faruwa su Yaya Na'Allah suna kallo, A tsorace suke sosai ga azabar zafi da rad'ad'in ciwo, Inda aka ciccijesu kuwa duk yayi wani irin burd'i sosai kamar wanda suka k'one. Dodo kuwa ganin yanda ginin rumbu yakeyi dasu yasa ya k'ara k'arfafa tsafinshi, Matarshi a fusace ta tashi ta jujjuya sosai ta zagaye kanta da yatsarta, Sai gashi wani abu ya zagaye baki d'ayan rumbun, Ya tsaya cak daga tashi samanda yakeyi. Ganin haka yasa dodo ya k'ara sakin wani tsafin saiga wani irin ruwa yana sauka, Ruwan k'unshe yake da k'wari irin bak'ak'en nan masu cizo sosai, Ga wani bak'in ruwa wanda idan ya sauka a fata sai ta tattalb'e tayi bororo sosai kanar k'unar wuta, Haka ruwan ya ringa sauko masu, k'warin kuwa duk wanda sukahau fatarshi ciki auke shigewa saidai su ringa ganin motsinsu a cikin fata, Duk abun har yanzu iya su kawai ya tsaya, Baijema Baffa dake sujada ba, Hassu kuma bakinta yak'i yayi shiru da ambatar sunan Allah tare da ayoyinsa. Tsafi sosai dodo tmya ringayi wanda koshi kanshi yayi mamakin yanda ya ringa yinshi, tunda yake a rayuwarsa bai tab'a yin tsafi mai girma da darajar wanda yakeyi yanzu ba, ga matarshi ma ta dage sosai ta rutrufe idanuwanta duka ukun sai surkullenta takeyi, Yaransu uku kuwa sun had'esu wuri d'aya, k'arfinsu ya zama na mutum uku hakan yasa suka k'ara girma sosai harma sunfi baban nasu girma, Da k'arfi halittar tasu guda d'aya ta b'ace daga cikin rumbun, A hankali iska mai had'e da guguwa ya tasi baki d'aya ya mamaye cikin gidan, Had'ewa iskan ya farayi wuri d'aya yana duddunk'ulewa, Ya jima a haka kafin ya zama halittar 'ya'yan dodo da suka had'e wuri d'aya, Jijjiga jikinsu sukayi saboda inda bai had'eba ya had'e, Baki d'aya jikinsu wasu irin siraran abubuwa ne kamar k'ayoyi kamar kuma k'usa, amma sunfi k'ata sirantaka, Wuta ke fita daga jikinsu baki d'aya, Kaf jikinsu kuwa babu inda babu ido guda d'aya, A hankali ya d'aga k'afar guda d'aya ya d'ora a takunshi na d'aya, Inda ya d'auke k'afar tashi yayi rami zurun zurun kamar an tonashi ne, Haka ya ringa taku da k'yar yake d'aga k'afarshi tsabar nauyi da jikinshi yake da, Da haka da haka har ya isa inda su Mati suke. Sosai tsoro ya mamayesu, babu abunda jikinsu keyi sai karkarwa, Yanzu kam sun sadak'as da tasu ta k'are, saboda tunda suke a rayuwarsu basu tab'a ganin abu koda mai girman wannan ba sai yau, Gashi kuma baki d'ayansu babu wanda ya iya furta wani abu daga ayar Allah. Har yanzu kuma Baffa bai d'ago daga sujada ba, dan haka baisan abunda ke faruwaba har abun yazo kusa dasu Gaje da Bareerah, Hakan yasa suka k'ank'ame juna gashi yanzu ba kusa da Hassu suke ba, ita tana daga can gefe inda Baffanta yake. Wata irin kururu abun yayi tare da zira dogon hannunshi ya jawo Baseeru da yafi kusa dashi, Matseshi yayi da k'arfin gaske yanda ba zai iya k'watar kanshi ba, Ihu Baseeru ya tsala na tsabar azabar matsar da aka masa, Wannan ihun nashi shi yaaa Baffa ya d'ago daga sujjadar dan ya tabbatarda akwai matsala, A zaman tahiyar ma ya dad'e kafin yayi sallamah, Kamar ance ya waiga aikuwa yaga abunda ke faruwa, Tashi yayi da sauri ya isa inda suke, Cikin zafin nama ya zungura sandarshi a daidai hannunshi inda ya kama Baseeru, Zabura yayi ya saki Baseeru yana mamakun abunda aka zunguri hannunshi dashi, Bai gama mamaki ba Baffa ya sake zura hannunshi a jikin hannun wancan, Aikuwa ya fasa wata irin k'ara yana duffuk'ewa cike da azaba, Baffa bai k'yaleshi ba sai ajiye sandar tashi da yayi, Ya dunk'ule hannunshi yana karanto addu'arda koni bansan abunda yake furtawa ba, Dudduk'ewa sosai wancan d'in yakeyi har ya isa k'asa, A hankali wannan k'ayoyin na jikinshi suka fara kakkaryewa suna fita daga jikin, Saida suka fice tas sannan Baffa ua bud'e idonshi, Sake dunk'ule hannun nashi yayi da k 'arfi ya bugashi a daidai tsakiyar kan abun inda yayi wani tsini kamar k'aho amma kuma guda d'aya ne, Da sauri k'ahon yayi k'asa wurin yayi rami, Sake rufe ido Baffa yayi yana kwararo addu'o'i bayan ya dafe wancan abun da hannunshi na dama, Duk da zafi da jikin abun yakeyi baisa ya sakeshi ba, Cikin k'arfi da kwaratsi abun yayi k'ara sosai, Hakan yasa Baffa ya sakeshi tare da yin shiru ya zurawa sarautar Allah ido, Dagargajewa sosai abun ya farayi, Take wurin ya d'ume da masifaffen wari, Saida suka rabe suka koma su uku d'insu sannan suka fara narkewa, Wani irin k'azamin ruwa suka ringa komawa mai kama da ruwan kwata, Ga wari sosai ga wasu mitsi mitsin abubuwa dake fita daga ruwan, A hankali suka ringa tashi sama suna nufar rumbun Jatau. Yana tafiya kuwa wurin yayi tsit kamar babu abunda ya tab'a faruwa, Har warin da yakeyi ma yanzu babu, Saidai kuma su sauran har yanzu hankalinsu bai kwanta ba, Cike suke da tsoro da fargaba. Ajiyar zuciya Baffa ya sauke tare da neman wuri ya zauna, "Banyi niyyar gamawa dasu ba, nafi son saa gari ya waye ido na ganin ido yanda sauran mutanen gari zasu ganema idanuwansu, Sannan harshi Jatau d'in musan abunda zamuyi masa" Baffa ya fad'a cikin halin ko in kula, saboda tunda abun ya fara faruwa ko kad'an d'in tsoro baiji ba, Saima dad'in da yakeji yana k'ara godewa Allah da kuma kakanshi wanda ya rik'eshi akan koya masa manya manyan abubuwa da yayi, Sai ayau yake k'ara morarsu, dukda wahala da yasha kafin ya koya. A fusace dodo, matarsho da kuma Jatau suke kallon abunda ke faruwa, Tun daga farko har k'arshe saida suka gani, Saidai kuma sun rasa yanda zasuyi domin suje su taimaki 'ya'yansu, Dan haka sai kallo kawai suka koma, ga wani irin takaici da yake mamayesu. Yanzu kam Jatau ya cire ran zasuyi nasarah baki d'aya, Saboda yanda yaga anyi da 'ya'yan dodo kuma ya kasa aikata komai, Kenan shima idan wani abu zai sameshi babu wani taimako da dodo zai iya yi masa tunda har ya kasa taimakon 'ya'yansa. A hankali k'ananan k'warin suka ringa shiga cikin rumbun suna sauka bisa jikin dodo, Yayyab'eshi sukayi baki d'aya kamar yanda zuma take lullub'e mutum, Sai k'ara da gumza da sukeyi, dodo dai kallonsu kawai yakeyi ya rasa gane manufarsu, Dan haka ya sakeyin wani tsafin dukda gajiya sosai da yayi, Yanada buk'atar hutu. "Jatau babu yanda za'ayi ka samo min jini yanzu? Idan ka smao sai in k'ara samun k'arfin da zamu gama dasu yanzu" dodo ya fad'a yana kallon Jatau. Cikin takaici Jatau yace "taya zan fita daga rumbu a wannan halin? Idan fa na fita suka ganni inyi yaya? Kasan zasuyi sauk'in kasheni", "Tsafi zan maka saika fita ai, kar kaji komai yanzu na k'arshe zamuyi masu, kaga wannan k'warin fa duk 'ya'yana ne suka narke suka zama haka, Kuma a tsafin da nayi yanzu naga idan na basu jini sukasha zasu tashi su koma daidai". "To naji, amma a ina zan samu wanda zan kawo yanzu? Darene fa sosai yanzu har asubah ta gabato, kadai bari idan asubar tayi kafin nan mutane sun fara fitowa sallar asubah, sai in samo maka wasu". "Lallai wannan shawarace mai kyau, hakan za'ayi babu damuwa, yaudai koda me suke tak'ama sai mun gama dasu ko zamu samu kwanciyar hankali" Dodo ya fad'a cike da fad'a, ya k'uduri munanan abubuwa a zuciyarshi game dasu Hassu. (To koya abun zata kaya? Sai mu had'u daku a shafi na gaba wanda shine na biyun k'arshe insha Allahu). _gaisuwa da godiya ga *Feedo Deedo da Meeshaluv,* munga sak'onku mun gode sosai, Allahu yabar soyayya da zaman tare._ Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/20, 6:48 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 4⃣9⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 Hakan kuwa Jatau yayi, ganin asubah tayi yasashi juyawa ga dodonshi yace "Ka fitar dani yanzu ina ganin har mutane sun fara fitowa, zanyi k'ok'ari in samu koda mutum d'aya ne sai kubi a hankali duk ku samu". "To shikenan Jatau, saisa nake sonka akoda yaushe, saboda kana bin maganata" Dodo ya fad'a tare da cigaba da surkullenshi kamar yanda yayi d'azu sanda ya fitar da Jatau daga rumbu. Nan da nan kuwa Jatau ya b'ace, bai b'ullo ba sai daidai 'yar kungun dake sada mutum zuwa masallaci daga gidanshi, Tsaye yayi a wurin da d'an mak'alallen hannunshi sai rarraba ido yake yaga ta inda zaiga wasu zasu wuce, Ya jima babu wanda yazo gittawa kafin daga baya wasu matasa su biyu sukabi ta lungun zasu tafi masallaci, Ganinsu yasa Jatau da sauri ya saki kibiyarshi da akaifar hannun hagunshi kamar yanda ya saba, Take kuwa kibiyar ta soki d'ayan saurayin, Haka yayima na biyun shima ta sokeshi, B'acewa sukayi duka garda Jatau d'in, sai gasu cikin rumbu sun b'ullo. Ciie da farin ciki dodo ya jinjinama Jatau, saboda yayi k'ok'arin yanda ya kawo mutum har biyu kuma ba'a d'auki wani lokaci mai tsawo ba. A b'angaren su Baffa kuwa babu wanda ya rintsa a cikinsu, Jin har an fara kiran slar asubah yasa suka tashi, alwala sukayi Baffa yajasu jam'i bayan sunyi raka'ataininl fajr sannan suka gabatar da sallar asubah, Anan ma sunyi addu'ah sosai, Baffa yayi adhkar d'inshi na asubah kamar yanda ya saba har saida gari ya fara yin haske, A lokacin kuma har syn shanye jinin mutum d'aya saura na d'ayan ne basusha ba suna jiran na farkon ya gama bin jikinsu sannan su gama da wancan. "To ku shiryafa, sai kunyi hak'uri kyn daure, saboda komai zai iya faruwa, za'a iya baku tsoro ta kowace hanya, amma ku kwantar da hankalinku komai na wannan lokacin ne kawaa da izinin Allah zamu samu nasarah, sai kuma kuci gaba da addu'ah sosai, Saboda so nake duk abunda yake cikin rumbun can yau ayita ta k'are sai mun gama dasu, zaluncin ya isa haka, bafa fin k'arfin wani sukayiba, tun a baya ma dan bansan abunda yake faruwa ba da abun bayyi tsayin haka ba, dama haske kawai nake jira gari ya fara, kunga a lokacin mutane sun fara wucewa, sai suga abunda macucin mai kud'in unguwarsu yakeyi" Baffa ne yayi wannan maganar bayan ya kurb'i sauran ruwan alwalarshi daya rage saboda k'ishin da yakeji kuma baya son ya fara aikin ba tare da yasha ruwa ba. "Kayi kuma muna tare dakai, insha Allahu zakayi nasarah, saboda wannan aikin alkhairi ne koma ince jihadi ne, Allah kad'ai yasan ladar da zai baka ta dalilin haka" Yaya Na'Allah ya fad'a cike da soyayyar Baffa, saboda shikam ji yayi Baffa ya burgeshi, samun mutum mai ilimin addininsa a wannan lokacin abune mai matuk'ar wahala. Jikarshu ya bud'e ya fiddo ruwanshi (idan masu karatu ba zasu mantaba a baya na fad'a maku cewa Baffa yana ajiyar ruwan saman farko idan shekara ta zagayo, to yanzu ma shine ya fitar), Mik'awa Yaya Na'Allah yayi yace "Karb'i wannan, dukda yake bashida yawa amma kubi a hankali zai isheku, ruwane mai d'auke da addu'o'i sosai da ayoyin Allah, Ku shashshafa a yatsun k'afarku dana hannu, sannan ku d'isashi a idonku, kamar yanda kuka d'isa a ido to haka zakuyi a kunnuwanku, Fa'idar yin hakan kuwa shine; kamar yanda na fad'a maku komai zai iya faruwa to hakan ne, Kayan tsafin nasu zasu iya fitowa a sifarsu, kuma idan har kuka had'a ido dasu komai zai iya samunku, zaku iya makancewa, Sannan kuma zasu iya yin magana kuji, idan har kukaji to zaku iya kurumcewa, Dalilinda yasa nace ku shafa a yatsunku kuwa saboda babu wuya sihiri, tsafi ko kuma sammu ya shigi mutum ta yatsunshi musamman ma akaifa, Amma wannan ruwan zayyi maganin komai, babu abunda zai sameku da yardar Allah, Karku manta ku rik'e addu'ah sosai a bakinku". Karb'ar ruwan Yaya Na'Allah yayi, kamar yanda Baffa yace masan kuwa haka yayi, D'aya bayan d'aya suka ringa shafawa har saida baki d'ayansu suka gama har ruwan yayi saura, Karb'ar abunshi yayi ya miyar a cikin jaka. Buzunshi ya sake kakkab'ewa sannan ya shimfid'ashi a k'asa yana fuskantar rumbun Jatau, Wata 'yar k'aramar kwalba ya zaro da jikarshi, Turarene a cikin kwalbar ya fitar, ya shasshafe jikinahi dashi sannan fuskanci alk'iblah ya gabatar da nafilah raka'a biyu. Kamar ance ya gama kuwa wani irin haske ya ringa tasowa daga daidai inda Baffa yake, Sosai hasken yake k'ara yawaita har saida ya mamaye baki d'ayan Baffa ya zamanto babu mai iya banbanceshi a cikin hasken, Addu'ah sosai yakeyi inda Hassu daga gefe ma ta dasa tata addu'ar, Kamar ance ta fara kuwa suma su duka suka d'auki addu'ar a bayyane had'e da sunayen Allah tsarkakakku, Baki d'aya hasken ya mamayesu, yayi kamar an zagayesu dashi, Sai kuwa duk gidan ya d'auki karatun Al-Qur'ani mai girma. Jatau da dodo kuwa sunacan sunata shirin shanye jinin d'ayan mutumin da Jatau ya sato, A hankali suka fara jiyi sautin karatunda duka gidan Jatau ya d'auka, Hankali tashe Jatau ya zaro ido, Dodon kanshi hankalinshi ya tashi, hakan yasa ya fasa shan jinin mutumin ya miyar da hankalinshi ga abunda ke faruwa. "Kardai ku fad'a min cewa wannan har ya baku tsoron tinkararsu, ka cire tsoro mu fita baki d'ayanmu, yau za'ayita ta k'are, zamu nunar masu da cewa munfi k'arfinsu" matar dodo ta fad'i haka a k'ufule. Dama kuwa tunda dodo ya bama 'ya'yanshi jinin mutumin farkon suka tashi, Tare suka futa daga rumbu harfa Jatau daya gama tsurewa, dauriyace kawai yayi amma harfa zawayi yakeji. Da k'yar da k'yar suke tafiya har suka isa daidai marabar su Baffa da haske, Tsafi sosai sukeyi amma ina, wannan hasken ya zama kariya gasu Baffa, gashi kuma har yanzu bai fasa karatunshi ba. A zuciye dodo ya k'arfafa tsafinshi, har yanzu dau babu wani cigaba saima azabtuwa da yakeyi, Yaranshi kuwa dama sun rigada sun lalace, jininda aka basune ya tayarsu saisa suna tinkarar haske suka fara narkewa suna zama k'ananan k'wari kamar d'azu, Matar dodo kuwa dauriya kawai take, ammafa iya azabtuwa tana yinta da hasken, Kallon hasken kawai zatayi sai idonta ya zubar da wani irin jan hawaye kamar wuta, Tashu tayi da niyyar mik'ewa hakan uasa ta manne a jikin hasken, Kamar yanda kukasan wutar lantarki tanayi idan aka tab'ata to haka matar dodo tayi, Ta manne a jikin hasken duk iya k'ok'arinta na ganin ta janye jikinta daga hasken ta kasa, Tsafinta kuwa da zarar ta fara sai ta kasa, A wannan lokacin har tsafin nata yak'iyin tasiri. Ganin haka yasa dodo ja da baya dan jar shima ya tab'a hasken, Aikuwa ya k'ara yin tsafi ya ware yatsunshi sai wuta ke futa daga yatsun suna tinkarar inda hasken yake, Amma kuma da zarar wutar ya isa ga hasken sai ta tsaya cak! Daga baya kuma sai ta ringa kimawa baya tana sake komawa a jikin Jatau, Iya azabtuwa yanayinta da zafin wutar, hakan yasa jikinshi ya ringa tattalb'ewa duk gashinshi yana fita a k'asa, Hakan yasa dodo ya miyar da yatsunshi ya tsaida tsafin wutar yana tunanin wanda zayyi yanzu. Bakinshi ya bud'e saiga ruwa yana kwarara shaaaaa kamar an kunna famfo, Saidai kuma abun mamaki ruwan kalar ja ne kamar jini, sosai yake kwarara kamar ba daga baki yake fita ba, Sauka ya ringayi k'asa take ya mamaye gidan baki d'aya amma kuma ya kasa isa inda hasken yake, K'ara k'arfin ruwan yayi sai gashi yanzu ya isa wurin hasken, amma kuma ya ringa yowa baya yana dawowa jikin Dodo har saida ya wuce wuyanshi duk girmanshi, Ganin yana neman hayeshi yasa ya rufe bakinshi ya tsayar da ruwan, Sauka ya ringayi yana raguwa wasu irin bak'ak'en kifaye na fita daga gareshi, Dad'in ganin kifayen yaji sosai, ya fara aikasu ga hasken amma ina, Sun jasa huda hasken barin har su shiga cikinshi, Hakan yasa suka dawo jikin dodo suka ringa cin naman jikinshi, Kokkoresu ya ringayi amma suna nan manne dashi basu daina cinshi ba Saida suka cinye kaf fatarshi ya zamanto ana hanye tsokar jikinshi maras kyan gani, K'yaleshi sukayi suka sauka daga jikinshi nan suka ringa narkewa suna komawa irin wancan ruwan, Duddunk'ulewa ruwan yayi inda ya ringa tinkarar bakin dodo yana shuga ta k'arfi da yaji, Yana ganin yanda dunk'ulen yake yawo a cikinshi yak'i narkewa, Duk inda ya tab'a a cikin nashi sai wata irin azaba yakeji da rad'ad'i a wurin. Matar dodo dai ta mak'ale har yanzu, Ga dodo kuma ya kasa aikata komai dan ganin ta sauko. Iya wahaka dodo ya wahala, duk wani salo da zayyi dan ganin yayi nasarah yayi amma babu sa'a, Yanzu kam ya hak'ura ya yarda cewa anfi k'arfinshi, Ya janye baki d'aya makaman yak'inshi ya ajiyesu, zai rok'esu gafara su yafe mishi dan yaci gaba da rayuwarshi, ya yarda kome zasuyiwa matarshi suyi mata indai shi zasu k'yaleshi, dama ai daga baya ya samu matar da 'ya'ya, kuma gashi yanzu duka 'ya'yan nashi babusu sun mutu, dagashi sai matarne, ya zab'i ya rasata indai shi zayyi rayuwa. K'ara ya fasa mai had'e da kuka sosai, Wata irin murya wadda ban sanshi da itaba ya fara magana, "Na yarda cewa kunfi k'arfina kuma bazan tab'a iya ja daku ba, kuyi hak'uri ku yafeni, bazan kuma aikata maku laifi ba, ku d'auki Jatau da matata kuyi masu duk abunda kukaga dama, amma bi ku k'yaleni". Jin ya fad'i haka yasa Jatau k'ara tsurewa, Kallon dodonshi yayi cike da tuhuma yana gwada kanshi wasu hawaye na fita daga idonshi, Yaukam *dodon Jatau* yaci amanar Jatau, Ya zab'i duk abunda zai samu Jatau hai damuba indai shi babu abunda sai sameshi. Jin maganar da dodo yayi yasa Baffa tsayawa da karatunshi, jin ya tsaya yasa suma sauran suka tsaya, Take hasken ya d'auke sai hasken rana kawai, Murmushi kawai Baffa yayi ya kalli dodanniya data fad'i k'asa tim, Sauran ruwan daya saka a jikarshi ya fiddo, Watsama dodanniya shi yayi a jiki d'an kad'an take tayi wata irin wantsala tana murje murje a k'asa, Sake watsa mata ruwan yayi aikuwa sai tahau rugurgujewa, Kowace gab'a tata ta ringa fita daban daban, Saidai kuma taurin rai irin nata suka ringa komawa suna had'ewa da junansu, Wats amata ruwan Baffa yayi a karo na uku, Aikuwa komai ya sake rabewa tare da nannarkewa suna zama tsutsotsi asalin yanda suke kafin su zama dodanniyar. Wannan shine k'arshen natar dodo, bari mu koma ga dodon. Ganin halinda matarshi take ciki yasa ya k'ara tsurewa, duk jarumta urin tata amma ta kasa aikata komai a hakin yanzu, gata har tata ta k'are babu saurin tsafi a tattare da ita, shikenan ta mutu an rufe shafinta. Ajiye ruwan Baffa yayi ya komai ya d'auki sandarshi, Singata yayi daidai inda dodo yake ya k'ank'ame jikinshi sai kyarma yake, A hankali haske ya ringa fita daga sandar yana sauka jikin dodo, Da zarar ya sauka kuma sai ya ringa wantsala alamar ciwo, jikinshi yana karkarwa dama kuma babu sauran fata a jiki sabida kaf kifayen nan saida suka gama da ita. Dukda haka Jatau k'ok'arin yin tsafi yake, amma kuma babu nasarah, sabida ya kasa aikata komai sai rad'adi da jikinshi yake masa. Matsawa Jatau yayi inda dodon yake, so d'aya tal ya watsa masa ruwan sannan ya damk'e hannunshi wanda da k'yar ya uya damk'ar tasa, Addu'ah Baffa ya tittifa a jikinshi sannan yace "Inason ganin duk abubda ka ajiye a cikin rumbun can, sabida ban yarfa dashi ba", Jikin dodo na rawa kuwa ya mik'ara da hannunshi, Take ginin rumbun ya rushe baki d'ayanshi duk abunda ke ciki ya bayyana, Kande da Dije ne tsaye kamar yanda aka miyar dasu tamkar gumaka, Ganinsu yasa cuie da mamaki Mati ya kalli Jatau bakinshi na rawa yana sonyin magana amma tsabar mamaku yas ya kasa, Aguje Larai taje ta rungume 'yarta cike da tashin hankali dan ganin halinda 'yar tata take ciki, Su Hassu ma wurin Dije sukaje suka sake fasa wani kuakn wnada suka rasa gane kona menene. "Ka fad'a min komai dangane dakai da Jatau, idan kamin k'arya kuma nasan maganinka" Baffa ya fad'a yana kallon dodo. "Bama san maka k'arya ba, gaskiya zan fad'a maka" ya fad'a cike da rawar murya sabida tsananin tsorata ya tsorata da Baffa, "Asalina...." ya kwashe labari tun daga farko har k'arshe bai rage komai ba ya fad'a, Wani abunda ya fad'a komua RAZ bamu sanshi ba. Salati suka d'auka su duka dake wurin, Koda muka d'aga kai ashe wurin ya cika mak'il da jama'ar gari kowa na kallon wannan abun al'ajabi. Da gudu Mati ya nufi inda Jatau yake ya cakumeshi da k'arfi cike da rikicewa, Ashe Jatau ya kashe masa har yaransa biyu, sannaj kuma ya miyar masa da Hassu tamkar mutum mutumi. "Karka tab'ashi Mati, inason har sai wannan wanda suka miyar haja sun tashi sun koma daidai, suga hukuncinda za'a d'aukarwa Jatau a gaban idonsu" Baffa ya fad'a tare da kamo Mati yana bashi hak'uri. Baffa ya tilastama Dodo lallai sai ya miyar dasu Kande halittarsu, amma ya tabbatar masa da cewa yanzu bashida k'arfin tsafinda zai miyar dasu daidai. Gyad'a kai kawai Baffa yayi, saboda shi yasan maganinshi, yasan yanda zayyi dashi. Rerbee'art sk❤ Amrah mshπŸ’“ Zarah bbπŸ’• *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION* [1/20, 6:48 PM] Xarah~B~BπŸ‘ŒπŸ».: [12:39pm, 20/01/2017] AmrahπŸ’“PinkyπŸ’“durling😘: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* 5⃣0⃣ Na *RAZ* ®NWA 2017 _Laifin dad'i k'arewa, wannan shine shafin k'arshe a cikin labarin *Dodon Jatau.*_ _wannan shafin naku ne *RAZ NOVELLA 1&2,* Allah yabar zumunci tare da had'in kai mai d'aurewa, mungode da goyon bayanku a koda yaushe._ **** "Zan kasheka ne yanzu, saboda mutuwa ita take kashe sihiri ko sammu, ko boka ne duk tsananin tsafinshi da zarar ya mutu tofa komai nashima ya mutu, dan haka kaga idan ka mutu sai halittarsu ta koma daidai" Baffa ya fad'a yana k'ara kallon dodo daya makure wuri d'aya sai azabtuwa da yakeyi. "Na rok'eka karka kasheni, bana son mutuwa ban tashi barin duniya ba, zan gyara maka su yanzu amma karkayi min komai" Dodon ya fad'a cikin muryarshi maras dad'in saurare, "Kai nake jira" Baffa ya miyar masa bayan ya k'ara yayyafa masa ruwa. K'ara da k'arfi ya saki cike da azaba, Da k'yar da wahala ya samu ya mik'e, Baki d'aya mutanen wurin saida suka tsorata da yanda dodon ya tashi, saboda ganin sukayi kamar zai nufi inda suke, A hankali ya taka har yayi juyi sannan ya furza wani iska daga bakinshi a daidai saitin Kande da Dije, Take kuwa iskan yayi sama dasu sosai sannan ya dawi dasu k'aaa timmm! A hankali kuma a tare jikinsu ya fara warwarewa, numfashinsu ya fara dawowa, idonsu ya fara k'yaftawa, bakinsu ya fara motsi, Kallon junansu sukayi suna tunanin shin abunda yake faruwa da gaskene kodai gizo ne?, A tare kuma suka d'agawa junansu kai alamar sun tabbatar da gaskene, Zumbur suka mik'e tare da rungumar junansu sai wani sabon hawaye ya ringa zarya daga idanuwansu, D'ayan wanda Jatau ya kawo masuma da sannu igiyar da aka nannad'eshi da ita ta ringa narkewa tana zubewa a k'asa, Mik'ewar shima yayi da sauri ya isa inda ya hangi mahaifinshi tsaye suna kallon ikon Allah. Dije ta nufi Hassu, Gaje da Bareerah ta rungumesu tana kuka sosai, Kande kuwa wurin iyayenta taje harma ta rasa me zatayi tsavar farin ciki, Yau rabonta dasu kusan shekara d'aya kenan, Jin bazata iya rungumar babanta ba yasa ta rungumi mamanta cike da farin ciki, ga kuka da takeyi wabda ta rasa dalilinshi, na farin cikine ko kuwa na bak'in ciki? "Allahu Akbar!!!" Kawai ke fita daga bakin mutanen wurin, Cigaba da addu'ah Baffa yayi babu ko sassauci, a hankali dodo ya fara canza halitta yana rage girma, Saida ya koma d'an k'arami asalin girmanshi kafin ya fara shan jini, Baffa dai bai daina addu'arshi ba, Tsutsotsi k'anana ya ringa komawa wata na fita daga wata, wata na fita daga wata har suka yawaita, Sake dunk'ulewa sukayi sai gasu sun koma asalin naman kan da Mani mahaifin Jatau ya ajiye, Ganin haka yasa Baffa ya dakata da addu'ar yana k'ara kallon yanda dodo ya canza ya zama rub'ab'b'en nama. Wata kabbarar aka d'auka kowa na mamakin wannan al'amarin, sai yanzu mutane suka game ashe duk b'atar da mutanen garin sukeyi Jatau ne yake sacesu yana kaima dodonshi. Gudu Jatau ya saka yana neman guduwa saboda yasan tashi ta k'are, a ganinshi idan ya gudu to ya tsira. Da sauri mutane suka nufi kamoshi, amma Baffa ya dakatar dasu, Babu musu kuwa suka dakata, Jatau kuwa har yana shirin barin gidan baki d'aya. "Jatau!!!" Baffa ya fad'a da wata murya wadda babu wanda ya sanshi da ita sai Hassu, itakam tasan idan ranshi ya b'aci yana yinta, kuma idan yayita baki d'ayansu sai sun gigice savoda tsoro, wannan kuma baiwace daga Allah. Cak! Jatau ya tsaya jikinshi sai b'ari yake, ya duk'ar da kanshi savoda tsabar kunya, baya ko iya had'a idonshi da kowa. "Ina zaku samo min kalanzir?" Baffa ya tambaya bayan ya isa inda Jatau yake, Wani mutumi ne daga can nesa dasu yace "bama kalanzir ba fetur zan samo indai wannan azzalumin mutumin za'a salwantar, ya kashe min 'yata Nafeesa, dan haka ku jirani yanzu zan dawo da yardar Allah" yana gama fad'in haka yabar wurin. "Hassu duba jakata akwai igiyar da nake nad'e bakun buhun, sai ki d'auko min sandata" Baffa ya fad'i yanama Jatau wani kallo irin na saika wahala d'in nan. Da sauri kuwa Hassu ta d'auko, da taimakon Yaya Na'Allah da Mati suka d'aure Jatau tam da igiyar, Jibgarshi suka hau yi sosai da sandar Baffa, idan wannan ya jibga sai wannan ya karb'a ya jibga, Jina jina sukayi masa sannan Baffa ya karb'i sandarshi ya ajiyeta a gefe, Suna cikin haka saiga mutumin da zai kawo fetur ya dawo, hannunshi rik'e da galan. "Zan iya samun taya ko guda d'ayace?" Baffa ya sake tambaya, Wani bak'o da yazo garin da mashin yace "Ko babu zan ciro ta mashin d'ina duka biyun" aikuwa ya fita ba jimawa shima ya dawi rik'e da tayoyi guda biyu. Ashana Baffa ya buk'ata da hanzari Hassu ta shiga d'akinta sai gata rik'e da ashanar, A jikin Jatau aka d'ira tayoyin sannan Baffa ya yayyafa masu fetur, ya zaro ashana zai k'yasta kenan da sauri Kande ta isa inda Baffa yake ta tsuguna har k'asa, "Dan Allah ina neman wata akfarma gareka, tun lokacinda 'yar uwata ta fara zuwa inda nake ta shaida min cewa Jatau ne ya kasheta nake burin ranar da zan d'auki fansa da hannuna, daga k'arshe kuma yazo ya miyar da rayuwata wata kala, dan Allah inaso ka bani ashanar nan in k'yasta mishi domin cikar burina". Murmushi Baffa yayi tare da mik'awa Kande ashanar, K'yastata tayi ta k'ura mata ido hawaye na futa daga idonta, Kuka da ihu Jatau keyi sosai yana rok'onsu akan suyi masa hak'uri ba sai sake ba, Zuciya mai tausayi da imani, Hassu ta hure ashanar ta kasa k'ona Jatau, da gudu ta koma wurin iyayenta kuka yaci k'arfinta. Dama Baffa yasan ba lallai bane ta iya, dan haka ya duk'a k'asa ya d'auki kwalin ashanar ya sake k'yastawa ya jefata ga Jatau. Wuta sosai ta kama a jikinshi, nan da nan dukanshi ya had'e da wutar ta ko ina tana cinshi. Kuka yake da k'arfin gaske yana murje murje amma ina, da haka har wuta ta cinyeshi tsaf saidai tokarshi. "Alhamdulillah! Masha Allah!! Lallai babu k'arfi babu dabara face daga wurin Allah, babu abunda yafi addu'ah a doron duniya, duk wanda ya rik'i addu'ah baya tab'ewa" mutanen gari suka ringa fad'in haka wasu sunyi tagumi sun tausayawa k'arshen Jatau, wasu kuwa farin ciki suke suna jin dad'in yanda k'arshenshi yayi. Kwashe tokarshi Baffa yasa akayi, da rub'ab'b'en naman kan daya zama dodo aka tona rami a daidai inda rumbu ya rushe, mai zurfi sosai ramin sannan aka zubasu aka binne. Wannan shine k'arshen *Dodon Jatau* da kuma Jatau d'in kanshi, Sunyi mummunan k'arshe a gaban d'umbin al'ummar garin. Mati ya tsuguna har k'asa yace "ka yafe min da cin fuskarka da nayi a baya, sharrin shaid'an ne", "Babu komai bawan Allah, komai ya wuce" Baffa ya bashi amsa fuskarshi d'auke da murmushin dattako. Matan Jatau kuwa wuri d'aya suka zauna inda suketa firarsu suna nuna jin dad'in nasarar da suka samu, kowace na jin haushin takabar da zasuyi mashi, saboda ya same masu dole suyi masa takaba dukda halinshi, wannan wajibine. Jinine ya b'allewa Dije sosai, babu jimawa saiga dunk'ule ya fito daga k'asanta, ashe b'ari ne tayi, sosai taji dad'in haka saboda koba komai ta rabu da mugun iri, yanzu kam babu sauran tunanin Jatau tunda tashi ta k'are. A hankali baki d'aya ginin gidan ya fara rushewa, da sauri aka ringa fita daga ciki, daga can nesa mutane suka koma suna kallon yanda gidan yake zubewa da kanshi, Saida ya zube baki d'aya ya koma k'aton fili. Babu Jatau, babu dodonshi da iyalinshi, babu dukiyar Jatau, babu rumbunshi, gida ya rushe, dad'in duniya kenan, gashi ya kasa tafiya lahira da duk kayan jin dad'in. ************************* Alhamdulillah, muma kuma daga nan sai ruwan biro d'inmu ya k'are, takardunmu suka cika, k'arfinmu ya k'are, da gudu muka baro k'auyen Bagu muka nufi wata masarauta da mutanen babban garin Bilba sukema take da *MASARAUTARMU.* ************************* Fatan an fad'akartu, nishad'antu an kuma ilimantu na wannan dogon labarin namu, masoyanmu wanda suka jima suna bibiyar wannan labarin mun gode sosai da kulawarku, Allah yabar hannu da ido ameen ya Allahu. [1:53pm, 20/01/2017] AmrahπŸ’“PinkyπŸ’“durling😘: *πŸ‘½....DODON JATAU....πŸ‘½* *FILIN GAISHE GAISHE* πŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ Na *RAZ* ®NWA 2017 Jinjina ga uwa mabada Mama, k'ungiya mai alabarka mai taken *NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION,* dole mu yabeku tare da jinjina a bisa namijin k'ok'arinku a koda yaushe, ba zamu tab'a iya biyan wannan k'ungiya ba, saidai fatan alkhairi a kowane lokaci. Godiya ga writer's groups kamar; Excellent writers, Online Hausa writers, Writer's Planet da sauransu. Jinjina ga shugabanninmu: Aunty Lubie, Adda Bena, M. Jabo, Aunty YBK, Ummul-Fadeelah, Chuchungaye and Bebeelo. Kunfi kowa son wannan labarin; Aunty Mamu (Mrs. Jabo), Feedo Deedo, Meeshaluv, Aunty Sdy Jegal, Ashnur Pyar Mera Dil, Aysha Takai (Maman Affan), Queen Mimi, Zee ElKasim (Maman Khady), Pherty, Maman Nusy, Ummee Saddam, Basman mai sanyinta, Safura Garba, Fadeelah Abubakar (Sakonki ya iso mana, muna godiya sosai), RAZ NOVELLA (1&2), ZAUREN BIEBIE ISAH, Da sauran mutane sosai wanda lissafoku ba abune mai sauk'i ba, saidai muyi maku fatan alkhairi. Mrs. Umar Novels group, Ililee's Novels group, Nafee Ankerh Novella, Maryama G Novels, Best Hausa novels, Stylish Hausa novels, Pherty Novels, Ummee Saddam Hausa novels, Da sauran wanda bamu ambataba kuyi hak'uri muna k'aunarku lodi lodi. 'Yan uwanmu marubuta; Autar Hajia, Kausarluv, Aneelurv, Stylish, Kdeey, Nafer anka, Pherty, Ummi aysha, Haneefa Usman, Munayshat, Biebie Isah, Miemiebee, Maryama Garba, Miss Hafsy, Asea B aliyu, Ayshat one, Mrs. Umar (matar soja) sahaf, Futha Pinky Durling (namesy), Damary, Jeeddah Aliyu, Khadija candy, Ayusher mohd, Ayusha iliasu, Kwaise, Qurratul-ayn (ina jajenki k'awallina, Nucyluv, Rash kardam, Ummeeterh, Ummu Abrar, Chuchu, Aneesa Didi, Basmah err lele, Asy Khalil. Bamu manta daku ba; Abdul Mr. Smiles, Raheem Jega, Sa'eed Bebeji, Ililee, AAJ, Abba Gana. Baki d'ayanku muna gaisuwa, munso ace kaf sunayenku sun fito, amma kuma ba abune mai sauk'i ba, saidai muyi maku fatan alkhairi tare da had'in kai da dank'on zumunci a tsakaninmu. Masoyanmu na nesa dana kusa, wanda muka sani da wanda bamu sani ba, muna mik'a sak'on godiya a gareku, kuci gaba da kasancewa a littattafanmu, Rerbee'art sk- *HARAMTACCEN ZAMA* Amrah msh- *WATA SHARI'AH* Zarah bb- *KADDARATA CE!* *DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI KO KUMA K'ORAFI, ZAKU IYA NEMANMU A WANNAN LAMBOBIN;* 08032133670 07037603276 08144410022 BLOG- www.babymsh.blogspot.com www.princessamrahh.blogspot.com www.zahrabb.blogspot.com *RAZ KE CEMAKU KU HUTA LAFIYA, ALLAH YA HAD'A FUSKOKINMU A ALJANNAH BAKI D'AYA* adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *