adsense here
Idan zuciya ta gyaru 1-01
Posted by ANaM Dorayi on 07:28 AM, 27-Jan-16
Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU
______________Na
______Fauziyya D Sulaima
19/81992.
"Chalo! Chalo! Chalo!" Zazzakar muryar
hatsabibiyar yarinyar ta fadi, ko ba'ayi bayani
ba kasan abinda kalmar chalo take nufi, wato
tsokanar fada ne da 'yan wani layi ke yiwa wani
layin, ko 'yan wata unguwa zuwa wata unguwar.
Jama'ar dake gefen hanya masu saida rake zuwa
goba, da yalo da doya suka fara hada kayansu,
daya daga cikin su ke fadin, "Kowa ya hada
kayansa don shegiyar yarinyar nan tun da ta
ambaci wannan kalmar ta chalo, to kuwa wanda
yayi sakaci zai yi a..." maganarsa ta tsaya tsak
dai-dai lokacin da ya hango zugarsu sun nufo su
da gudu, sun biyo wasu, ya suri farantinsa
wanda aci bal-bal ke tsakiya na kifi, suma 'yan
uwansa suka rufa masa baya kowa na neman
inda zai adana kayansa. "Chalo! Chalo! Chalo!!!"
Muryar zugar yaran dake biye da Abu suka
cigaba da fadi suna biye da 'yan uwansu
wadanda suka biyo, sukuwa yaran da aka biyo
sai kuma kara gudu suke yi, domin kada a
badesu da barkonon tsohuwar da su Abu ke
wulwulawa. Toka ce ake hadata da citta da
barkono a dake sai a kulle ta a leda a sanya
dutse a tsakiya a sanya zare a dinga wulwula ta,
idan aka cillata daga nesa sai ta fashe kamar an
cillah tiyagas (barkonon tsohuwa), duk mutumin
da ke harabar gurin sai yayi tari ko ya shide,
idan kuwa akaci karo da mai cutar (ASMA) kuwa
sai ta tashi. "A cilla- A cilla." Muryar Abu ta
kuma futowa tana baiwa abokan ta umurni
kenan, dan ganin yaran da suka biyo sunyi
musu nisa, ai kuwa babu bata lokaci suka hau
cillah kullinan tokar dake hannun nasu ji kake
tush! tush! tush! Tana fashewa a tsakiyar yaran
dake neman tsira daga farmakin su Abu,
wadanda Allah ya taimaka sun tsere wadanda
kuma keda rabon shan wuya tokar ta fashe a
tsakiyar su don haka suka fara tari da atishawa,
hatta mutanen dake makota dasu suma sun hau
atishawa, balle maza dake zaune a kofar gidaje
ana hira duk suma sun hau atishawa. Su kuwa
su Abu dariya suka sanya gami da ihu suna
fadin "Eye! Eye! Eye! Munci gari ba namu ba,
munci gari ba namu ba- munci gari ba namu
ba, munzo gidansu mun cisu" Wani mai kanti
dake kokarin zuba kananzir dai-dai lokacin da
abun ya fashe, ya shide kalanzir din ya zube a
kasa ya hasala don haka ya shiga shagonshi da
sauri yana atishawa ya dauko dorina yayi kansu
yana fadin "Shegun yara masu kama da iblisai
ba a sati guda baku bada mana wannan jarabar
ba, wallahi yau duk wanda na kama sai na fasa
masa jikinsa da dorinar nan" Yayi kansu da
gudu, Abu ta fara hangoshi don haka ta kuma
fasa ihu tana fadin "Kowa yayi ta kansa! Nima
nayi ta kaina, kowa ya guje dai, nima na guje
dai, kowa yayi ta kansa." Ko batayi bayani ba
sun san abunda take nufi, wato wani ya taho zai
doke su don haka kowa ya gudu, wai ai kuwa sai
suka kama gudu mai kantin nan ya bisu da
wasu samari biyu, da suma ke cin abinci aka
bude su su da abincin da kura, basuyi nasarar
kama ko daya ba domin yaran sun fisu gudu
tamkar barewu don daman sun san za'a biyo
su. Don sun saba duk randa aka yi biki ko suna
a gidan wasu aka kai musu cingam din fati
akube-kube sai anyi fada, don haka iyaye da
yawa ke hana 'ya'yansu zuwa akube-kube (fati),
yauma haka dince ta faru domin 'yan layinsu
Abu (Hatsabibiya ce) ta gayyaci akube-kube (fati)
tofa shine wani dan bayan layin nasu ya
warcewa 'yar layin..
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
yauma haka dince ta faru domin 'yar layinsu
Abu (hatsabibiya ce) ta gayyaci akube-kube (fati)
tofa shine wani dan bayan layin nasu ya
warcewa 'yar layin su kwanonta na akube-kube
lokacin da suke tsaka da rera wakar akube-kube
sai walo, munje mun dawo sai walo, sannunku
da zuwa sai walo, ga kwanan fati sai walo. Tofa
shine Abu tace a futo da kwanon suka kiya
shine fa fada ya harke ana ta karawa sannan
aka bada oda a dauko bom, shine fa aka biyo
'yan bayan layi. A bakin wata makarantar boko
suka dinga zubewa suna haki don sun san sun
tserewa wadanda suka biyo su. Sai tillikar dariya
sukeyi suna mai da yanda akayi. Abu ta fito da
kifi a hannunta soyayye tace, banzaye nifa mai
kifin nan da yake gudu sai dana suri kifi daya
wanda ya fado, nan fa kowa yayi karaf yace
raba dai-dai (wato wata sarace ake kullawa idan
kuka kulla raba dai-dai to da kaga mutum yana
cin abu idan ka riga shi fadin raba dai-dai to sai
ya raba biyu ya baka idan shima yaga kana ci
yace maka haka to sai ka bashi kaima, idan
kuma mai cin abin ne ya riga fadin bazai bada
ba). Abu ta sha kunu tace "Dallacan wa zan
baiwa wa zan hana" Ta bare ta cire kayar ta
lunkuma a bakinta tana muzurai, kowa ya tsaya
yana kallonta don dai ita masifaffiyace tsoronta
ake ji, wani yaro ne a cikinsu yayi karfin hali
yace "Gaskiya mu kwance ke Abun nan." Ya
mika mata hannu "Idan kece kika ga mutum
yana ci kika ce raba dai-dai idan bai baki ba
warta kike yi, amma idan kece sai kiki badawa."
Ta cire dankwalinta taci dammara dashi tace
"Anyi din, duk wanda ya isa ya kwata wallahi"
Habu yace "Banza ai ba tsoronki ake ji ba, daga
yau mun kwance nima." "La-la-la, ni kake zagi
wallahi ba zan yadda ba." Ta danki kasa a
hannu biyu ta matsa gabansa tace "Gata tsiya
gata arziki." Ya tankwabe ta tsiyar ai kuwa sai ta
rarumeshi, nan fa dambe ya kaure sauran yaran
suka rude da ihu eyeh-eyeh-eyeh, sannu suna
musu wata waka, "Ku chasu arna ku chasu, ku
chasu ba mai raba ku, wanda ya raba su shi
yayi barna, kai ku chasu arna ku chasu, ku
chasu ba mai rabaku." Su kuma tamkar ana
kara zugasu sai dambe suke yi, da yake Abu
'yar dama-dama ce mai kiba gata da karfi da
karfin zuciya ta daga Habu ta naka shi da kasa,
aka kuma rudewa da ihu da kyar aka janye ta
daga kanshi tana fadin "Wallahi da kun barni
yau da sai na chas-chas karashi." Shi kuwa ihun
da ake masa ya sanya ya fashe da kuka yayi
hanyar gida, suma saura suka bishi ana masa
ihu, ita kuma Abu sai kuma masifa takeyi tana
tafa hannuwa tana fadin "wallahi mutum yaje
ya fada a gidansu wanshi yazo ya tabani gobe
nima na zane shi." Sauran 'yan fadan ta suna ta
zugata tana dariya, a haka suka isa kowa ya nufi
gidansu, Abu tace "Bari naje na dauko gyada ta
na kasa wallahi kuma naji yaro ya zageni ya
sani." Ta shiga gidansu har lokacin da
damararta, Babarta dake zaune wacce asalin
sunanta Salamatu ne suke ce mata Sala tace
"Yauwa 'yar albarka yanzu nake tunaninki tun
da kuka tafi akube-kube baku dawo ba." Ta
fashe da dariya tace yau na gaya miki Sala
wallahi na chas kara yaron nan Habu, daman ya
raina ni har kuka na saka shi wallahi ya tafi
gidansu yana ta kuka. Sala ta fashe da dariya
tace "Yata giwar mata, wanda ya tabaki ya tabo
ramin zuma, bana son sanya ki cigaba da chasa
duk wanda ya kawo miki wargi ni na saka ki."
Tayi dariya tana gyara kashin gyadar tata tace
"Ta nawa ce Sala?" Tayi dariya tace "Haba
maitsada (Sunan da take kiranta dashi kenan) ai
ke ba sai an kirga miki ba, ke ai me kan arziki
ce yanzu zaki dawo nasan kudina ba zasu bata
ba sai dai ma su karu, dauki kawai kije da dai
Karimatu ce mai kan kwantai (kanwar Abu ce)"
Abu tayi dariya gami da daukar farantin wanda
aci bal-bal ke tsakiyarsa tayi waje da kujerar
zamanta.
Can hanyar 'yar kasuwa ta nufa inda masu lemo
da agwaluma da rake ke saidawa, tun da ta fito
aka karbi kujerar wata kawarta Laraba, suka tafi
suna tafe suna hirarsu akan fadan da suka yi da
Habu, da kuma chalon su. Sanda ta isa bakin
'yar kasuwa ta ajiye farantin ta, samari suka
fara zagayeta kowa ya dauki gwangwani guda
yana ci ana hira, rabin hirar duk batsa ce,
amma da yake Abu ta saba jin irin wannan hirar
sam bata damu ba, sai dai ta sheke da dariya
tace shege wane, can wani Rosi yace "Ke ai
wallahi Abu har yanzu baki waye ba, ki duba ko
kwana bakiyi a waje kullum kina gida." Ta mike
tsaye tace "Kan Uban can, har zaka ce ban waye
ba, don Allah dubeka Rosi din nan kaifa wallahi
tsami ne, don dai yayana jarababbe ne wallahi
da nima kwana zan dinga yi kamar Laraba ko
yaya kikace kawas?" Ta bawa Laraba hannu suka
tafa
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
. Mudi Niga yace "A'a ba wani Laraba taso muje
muyi zancen mu bayan makaranta kada 'yan sa
ido su ganmu." Abu ta tabe baki tace "Wallahi
nima don jarababben yayana ya saka min ido
ne, yanzu da an ganni za'a gaya masa yaci
ubana, wallahi da nima acan zan dinga zancen,
amma zan yi maganinsa." Su Laraba dai suka
mike suka tafi ita kuma suka cigaba da hira da
su Rosi. Karfe goma da rabi sannan ta dauko
kayan tallarta tana ta mita a fili "Banza su Rosi
din nan shiyasa bana sakar musu fuska, da
Kwage ne ko Damisa ai da tuni sunyi mini juye
mtss!" Taja tsaki, yanzu da kwantai zan koma
gida? bari dai na biya gurin dan Oga dan nasan
shi dole ne kila ya siye yanzu. Ta nufi chemist
din nasa da fitilar kwai a bisa tebur, yana zaune
a bisa kujera mai kama da tsohon soja, babu ko
sallama ta bankade dan yalolon farin yadin dake
kofar da sunan labule ta shiga tana fadin dan
oga kana nan baka tashi ba? Ya mike cike da
murna yace Wow! Habu yanzu kana rena wallahi
ina son ka da gani (cikin gurbatacciyar muryarsa
yake mata magana) ita kuwa ta ajiye gyadar
bisa wannan tsohon tebur din ta hure aci bal-
bal din tace "Daman zan biyo yanzu ga gyadar
zaka siya duka ko?" Ya matsa jikinta yana cewa
"Habu Habu, wallahi kana da cho, ina ta sonka
da yawa, amman zaka kwana anan ko?" Ta zaro
ido waje tace "Kaifa baka da hankali wani
lokacin, idan na kwana a gurin ka nace me a
gida....." Ya jawo ta jikinsa yana mata abinda ya
saba duk da ba gamsuwa yake yi ba, domin dai
lalubeta yakeyi, don taki amince masa dari bisa
dari sai dai yayi abinda ya samu (Allah ya
shirya, jama'a ku duba diya mace ta futa har
zuwa wannan lokacin uwarta bata neme ta ba,
tur da irin wannan Uwa). .
…Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Can tace "Malam na gaji zan tafi kada
jarababban can ya biyo sahuna don ma nasan
Sala zata kareni sallameni na tafi." Ya mike yana
gyara riga yace "Habu-Habu, wallahi yarinyar
nan baka da cho kina yawo da akalina, amman
zan rama ne." Tayi dariya tana fadin "Dan oga
kenan." Ya miko mata Nairori har na Naira
ashirin tace "La-la nagode." Ta sunkuci farantin
gyadar ta fuce da sauri tana fadin "Duka gyadar
ma ta naira ashirin ce amman ya bani Naira
ashirin" Shi kuwa sai kiran sunanta yake yana
dariya har ta kulewa ganinsa.(Wallahi sai mun
zamo masu taka tsantsan da irin kabilun nan da
suke mu;amala da yaranmu)….Sanda ta isa gida
an turo kofar da tirmi ba'a kulle ba, don haka ta
tura a hankali ta shiga da kullin namanta na
naira daya da ta siyo don kudin dake hannunta
naira ashirin da shida ne ga kuma sauran
gyada. Ta shiga dakin Sala ta taddata abisa leda
tana ta sharara bacci kamar matacciya (Ku duba
irin wannan Rashin tunani, ki tura diyarki talla
tayi dare amma ko damuwa bakiyi ba, bacci ma
kikeyi hankalinki kwance!!) A hankali ta dinga
taba ta tana fadin "Sala! Sala! Sala! Na dawo."
Sala ta mike tana magagin har ta wartsake tace
"Diyar arziki kin saida ko?" Abu tayi hamma
babu ko rufe baki balle salati, sai wani nishi da
tayi hmmmammman har bakin ya rufe da
kanshi, sannan tace na dawo ga kudin nan da
sauran gyadar dai, Sala ta sha kunu tace "Haba
Abu, kince fa a kunga-kunga har ta kare...." Tayi
shiru da zancen da taga ruwan Nairori a
gabanta, ta debo su da sauri tana kirgawa sai
ga naira ashirin har da Uku. Ta washe baki tana
fadin "Diyar albarka lallai kice samuwa kika yi
daga sama, wannan fa shine riba biyu ga kudi
ga sauran gyada, na baiwa Shehu da safe ya
karasata idan kin tafi makaranta, kin siyo
naman? Domin mai nema idan baya ci wata
rana shi za'a tafi nemowa." Abu ta nuna mata
ledar naman ba tare da tace komai ba ta mike,
Sala tace "Gwara dai aje a huta don ai kin gaji
na sani, sai da safe mai tsada." Tace to Allah ya
kaimu. Ta fuce a tsakar gida taci karo da Sadiku
yayanta ya shigo yana huci, ke don Ubanki ina
kika biya naje bakin 'yar kasuwa ban ganki ba
kuma ban dade da barin gidan nan ba? Ta
murguda baki gami da harararsa tace "To ina
ruwanka dani eyeh malam...." "Ke don ubanki
rashin kunya zakiyi mini? To yau idan baki gaya
mini inda kikaje ba wallahi sai na faffasa miki
jikinki." Yayi kanta ai kuwa suka kwasa da gudu
tayi dakin Sala wacce sukayi karo a bakin kofa.
Cikin hargowa da bala'i Sala tace "Malam meye
haka zaka biyo mini diya da gudu salon taje ta
karye ka cuceni? Wallahi yaron nan ka futa daga
idona na rufe kaji ko? Kai waye ne da zaka
matsa mata eye? Ko kai ne uwarta daka haifar
mani ko kuma kai ne Ubanta eye?" Cikin
hargowa take bala'in, ita kuma Abu tana gefe ta
rike kugu tana murguda baki da gatsina fuska.
Ransa ya kuma baci yace "Haba Sala, yaushe
zaki rufe idonki kina ji kuma kina gani Zainabu
ta dinga kaiwa dare a waje kuma idan ance
za'ayi mata fada kice baki yarda ba, yanzu ki
duba agogo karfe sha biyu har da rabi na dare
ace sai yanzu yarinya mace zata dawo gida." "To
Ubana ai sai kazo ka rufeni da duka, nace kazo
ka rufeni da duka!" Ta fadi da hargowa, kana ta
cigaba da cewa "Ina ruwana da wani lokaci ko
karfe dubu na dare zata dawo bai shafeka ba, ai
ba kai ne ka haifar mini ita ba, kuma da kake
cewar neman kudi hauka ne inace kaima nan
kake shigowa kana rara gefe a sammaka abinci,
kato dakai ba don tana nemowa ba zakaci ne?
shi solobiyon Uban naku idan muka daka ta
tashi zamu rayune? tun yaushe ya bar gidan
nan tun asuba ya tsallakemu ya gudu har yanzu
bai shigo ba sai mun kuma wani bacci, to zamu
zauna ne mu mutu idan bamu nema ba?
Wallahi ka fita daga idona ka samawa yarinyar
nan lafiya idan ba haka ba ranka zai baci." Ta
kuma cigaba da masifa.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
A gidan nan dame zata ji, da tsanar ta da 'yan
unguwa sukayi ko ko da jarabarka, yanzu daga
safiya suwa yanzu kasan nawa ta samu tun safe
kake,zan bata maka rai wallahi." Ya kwantar da
murya duk da ransa a bace yake yace "Sala ki
fahimce ni, ba wai ina yiwa Zainab fada don
bana sonta ba, sai dai a matsayina na
dan'uwanta ba zanso ace ta lalace ba, ki dubi
yanda kowa ya budi baki a unguwar nan
maganarta zaiyi, idan tsokanace itace gaba, Sala
yaushe... Kai rufe mini baki sai kwarara zance
kake babu kwama babu fulsu tof, ratatata
kamar zubar ruwan sama. To tayi din uban wani
ya hana, wato kafi so a dinga koro mini ita da
duka ko? To ban haifi sallamammiya ba, kai
tunda sallamamme ne sai kaje kayi tayi, ta dubi
Abu mai tsada shige daki kici namanki kiyi
kwanciyarki kamar tsumma a randa, naga
shegen da zai kuma takura miki." Abu ta kuma
murguda baki gami da yin gatsine ta shiga cikin
dakin su ita da kannenta duka uku duk matane
ta haye bisa katifarta ta bude namanta tana ci
gami da kunna rediyonta da wani saurayinta ya
bata, wakar lagireto ta fara futowa a hankali.
Itama Sala daki ta shige tabar Sadiku a can
tsaye kamar ya hadiyi zuciya ya mutu yake ji
don takaici, me ake da irin wannan rayuwa ace
kiri-kiri an san gaskiya ake takewa saboda son
duniya? Yaja tsaki yana fadin "Allah ya ganar
daku gaskiya." Ya nufi dakin sa dake soro yayi
fakare cike da tunani, jin kidan dake tasowa a
rediyon Abu yake yi har cikin ransa, don dai
yana shakkar bala'in Sala ne da wallahi sai ya
maka rediyon da kasa uban kowa ma ya huta,
yana nan kwance ya jiyo ta kashe da alamu
bacci zatayi kenan. Ba'afi minti talatin da hakan
ba yaji alamun shigowa, ko ba'a fada masa ba
ya san Babansu ne, ya dubi agogo karfe daya
da minti goma sha tara, yaja tsaki cike da
takaici, yana jinsa ya rufe kofar gidan ya leko ta
tsakanin labule yana kallonsa takalminsa a
hannunsa suke sai sanda yake sadaf-sadaf! Da
haka ya nufi daki, daga inda yake yana jiyo
munsharin Sala da alama bacci yayi awon gaba
da ita, ya saki labulen ya koma ya kwanta yana
tunanin wannan mummunar rayuwa da suke yi
da iyayensu, a haka har bacci barawo yazo ya
sace shi.
Da sassafe ta tashi ta shiga bandaki tayo alwala
tayi sallah, sannan aka jawo kayan kwalliya aka
maka mai, hoda da jan baki wato dai tayi tsaka
tsami kenan. Jagirar nan da aka ja har ta kusa
taba kunne ga jambaki an saka shi an kawo baki
an zagaye saman leben dashi, anyi wani digo a
tsakiyar goshin akayi wani bisa hanci, ga gefen
haba,sannan aka bude adaka aka dauko wata
atamfa 'yar kaduna Nichem, aka sanya aka yafa
gyale a kafada bayan ta daura dan kwali disko,
ta kalli madubi tayi kyau matuka, tayi murmushi
ta futo tsakar gida. Sala dake can kicin tana
suyar funkaso da miya tace "A'a kin shiryo, to
maza a dauka mai kan albarka kada lokacin
makaranta ya kure gashi nan na zuba miki
naki," tace To, kana ta nufi gurin da aka ajiye
mata nata din cikin watan fanteka, da miya a
cikin bokitin fenti, ta dora a kanta su kuma
kannenta suna ta mikawa na kofar gida dake
zaune suna siya. To maza mai kan albarka kada
a dawo da ko guda daya kinji ko? Bata ce komai
ba ta fice da digirgire don gwana ce gurin
daukar kaya a kanta. A hanya suka hadu da
Laraba, itama tana dauke da waina bandashe
mai kuli da mai da albasa) suka tafa kana suka
rankaya bakin tashar 'yan kifi, suna tafe suna
shan hirarsu suna dariya. Karfe takwas da minti
arba'in ta dawo, Sala ta tareta tana cewa
"Yauwa diyar arziki maza sauke ki shirya kada ki
makara, na zuba miki kici ne?" Tace "A'a naci
acan bakin tasha." ta mikawa Sala kudin ta
shige cikin dakin ta sanyo kayan makarantar ta
bulu din uniform da farin hijab, amman bata
sanya hijab din ba sai cin damara dashi tayi ta
rumgume littafai a hannu ta fice. Sala tace "Ga
kudin mota." Tace, "Ina da kudi ki barshi kawai."
"To a dawo lafiya a dawo dai da wuri." Tace to.
Ta fuce da sauri, tana fita ta sami hayis ta haye
aka sauketa a kofar makarantar 'yan mata ta
G.G.S.S Dala. Sanda ta isa ana taron 'yan latti
ko ma nace an gama, don wadanda aka tare din
an tura su cikin makaranta tsintar bola, sai
Discipline master da prefect ne a bakin kofa.
Babu ko shayi ta nufi kofar tana taunar cingam
din ta kas-kas, malam Kabiru discipling master
ya dubeta da takaici sanda take shirin shigewa
ko kallonsa ma bata yi ba yace "Ke zo nan."
Babu ko shayi ta nufeshi tana taunar cingam. Ya
dubeta a kufule yace "Ni sa'an Ubanki ne da
zaki tsaya mini?" Ta murguda baki tana kunkuni
taki durkusawa, ya zanbada mata bulala yace
"Kade doron sha-sha-sha."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta murguda baki gami da cigaba da yin
kunkuninta ta durkusa "Me kike cewa?" "Uwarka
nace" Ta fada a hankali, da motsin bakin ta yaso
ya fahimci abinda tace yace "me kika ce?," Tace
"Ni fa bance komai ba malam." Yayi ajiyar
zuciya kana yace "Mai yasa ke kullum sai kinyi
latti ne eye? Idan baki son makarantar ki daina
zuwa mana sai kace an miki dole, shegiya tun
baki tafasa ba zaki kone, kina aji daya tal amma
kin gallabi kowa, to wallahi idan bakiyi hankali
ba sai an kore ki daga makarantar nan,tunda ta
uwarkace ba?" Ta fadi a hankali, yaso ya juyo
amman bai fahimci abunda tace din ba, don
haka yace "me kike cewa?" Ta dubeshi da
shagwaba "Haba malam ni fa ban ce komai ba."
Yace shikenan tashi kibi 'yan uwanki kuyi tsintar
shara. Ta ce "To shege." Ta fada a hankali,Ta
mike ta nufi inda ta hango dalibai sunbi, sai a
sannan ya hango hijabinta daure a kugunta "Ke!
ke!! ke!!! Zo nan." Ya kuma kwala mata kira
amman tayi banza "Ke! Zainab ba kiranki nake
yi ba?" Ta juya tace "Au ai naji kana cewa ke ne
bansan dani kake ba, gani malam." "Ki cire
hijabin nan ki saka a jikinki." Ta yamutsa fuska
tace "Gaskiya malam zafi nake ji, bazan iya
yafawa ba" Da haushi yace "Idan baki yafa ba
ko zan zaneki a gurin nan." Lallai Malam Kabirun
nan bai san Abu bane, ta murguda baki gami da
dafe kugu da hannu daya tace "Allah ko kasheni
zakayi ba zan yafa ba don zafi nake ji, haka
kawai ba za'a sanya kurajen gumi su futo mini
ba, dan babu mai sai mini magani." Ya hasala
sosai ya nufeta da fushi ya daga bulalar dake
hannunsa zai maka mata, amman ta rike ta
gam tace "Allah malam ba zan yafa ba." Can
wata firifet ta hasala tace "Malam ka barmu da
shegiyar yarinyar nan taurin kai ne da ita bata
da mutunci, kusan kullum haka muke da ita taki
ta daina yin latti," Bata gama mai maganar ba,
ya fisge bulalar daga hannun Abu ya tsula mata,
Ai kuwa sai ta fasa wata uwar kara kana tayi
kansa ta cakumu wuyar babbar rigarsa ta shige
ciki, ya rasa yanda zai yi da ita sai hargowa yake
yi yana fadin "futo don ubanki, kina ina ne?"
Tana ihu ya rasa yanda zaiyi da ita dole ya cire
babbar rigar data makale a jiki ya kalleta da
takaici yace "To tashi kije ki wanke bandakin can
na seniors." Ta wurgar da malum-malun din "ni
gaskiya ba zan wanke kashin wasu garada ba,
haka kawai?" Ya rasa yanda zaiyi da ita, yau
Allah ya hadashi da shegiyar yarinya mara tsoro,
duk yanda ake jin tsoronsa a makarantar banda
ita,ya mike ya nufi Ofis din principal yana fadin
"Yau zaki ci Ubanki wallahi," babu ko shakka ta
bishi wata firifet tace, Zaki ci ubanki yau, za'ayi
maganinki. Ta dalla mata harara tace "banza kiji
da wadannan hakoran naki masu kama da kaca,
"Ke ni kike gayawa haka?" Tayi kanta da bulala,
ita ko ta tsaya kyam tana jiran ta karaso ta huce
a kanta, wata ce ta rike ta tace ke me yayi miki,
Malam Kabiru ya kwala mata kira da yayi nisa,
ta debi littafanta dake hannu ta bishi kamar ba
zata taka kasa ba. Ya shiga Ofis din principal
dake zaune a wata katuwar kujera taci
kwalliyarta ta sha glass dinta, daga ganinta kaga
tsohuwar 'yar boko. "Yaya dai Malam Kabiru
lafiya ne na ganka rai a bace?" Ya sami kujera
ya zauna yana huci yace "Hajiya yau wata
fitinanniyar yarinya ce ta bata mini rai bari ki
ganta." Abu ta shigo Ofis din babu ko sallama ta
dubi principal din tace "Sannu Ma." Bata amsa
ba illa kara gyara glass dinta da tayi tana duban
Abu dake tsaye kerere tace "Kika tsaya mana a
kanmu kamar wasu sa'anninki." A hankali Abu
tace "Da fa?" Sannan ta tsugunna. Malam Kabiru
yace "Kinji ko da kunnenki?, tun dazu wannan
kun-kunin take mini bana jin abunda take cewa,
sai dai ina zaton zagina take yi." Hajiya Kubra
tace "Malam Kabiru sanar dani me ya faru
kwantar da hankalinka." Babu bata lokaci ya
zayyane mata komai tun daga farko har karshe.
Hajiya Kubra ta dubi Abu da harshen nasara
tace mata "Haka ne abinda yace?" Da yake Abu
jaka ce bata iya turanci ba, domin ba zuwa
makarantar takeyi ba sai taga dama, idan tazo
kuma din bata yin komai sai hatsabibanci, don
haka bata iya komai ba, hakan ce ya sanya ta
yiwa shugabar makarantar shiru tana guna-guni.
Shugabar makarantar ta hasala ta doka mata
tsawa gami da kara maimaita mata abinda ta
tambayeta da fari.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Abu tace "Maa nifa bana jin abinda kike fada
gwara kiyi mini da yarena, don ni bana jin
abinda kike fada." Tana wani fisge-fisge take
wannan maganar. Ran Hajiya Kubra ya kuma
baci, don haka ta dinga zagin Abu da turanci,
tana fada mata "Banza jaka, baki san komai ba
sai shegen iskanci da rashin mutunci, a haka
za'a gama karatu ba'a san komai ba sai a kare a
auren dan dako ko dan acaba."Kalma daya Abu
ta fahimta a duk cikin maganar Hajiya Kubra
wacce tace mata "donkey" wato jaka, hakan ne
ya sanya ta fahimci irin cin mutuncin da ake
mata dan haka ta kama guna-guninta tana
fadin "gaki nan babbar jaka, ki dubeki fa tamkar
kayan wanki." "Me kike cewa?" Shugabar ta
tambaya da dacin rai jin Abu na magana kasa-
kasa. Ta murguda baki tace, "Ni fa bance komai
ba." Hajiya Kubra ta dubi Malam Kabiru tace,
"Malan zane mani ita kafin na bata horon da
zan bata tukunna." Duk da gabansa ya fadi dan
yana gudun makalewar da Abu take masa,
amman sai ya daure yayi ta maza ya nufeta da
zabgegiyar dorina. Ai kuwa yanda tayi masa
dazu haka tayi masa yanzu, ta cukwikwiye shi
tana ta zabga ihu, amman babu ko alamar
digon hawaye a idonta, da kyar ya samu yayi
mata guda Uku yana mai da numfashi.Hajiya
Kubra tace "To maza dauki tsintsiya ki share
harabar malamai duka yanzun nan." Ta mike
tana guna-gunin nata tace "Oho dai! Ko yanzu
na wahalar daku,"Me kike cewa?" Ta tambayi
Abun wacce tuni tayi fucewarta, ta kuma duban
Malam Kabiru tana fadin "Lallai yarinyar nan
bata da mutunci, shegiya irinsu ne idan suka
hadu da maza jahilai irinsu suke lakada musu
duka." Shi dai baice komai ba, yayi godiya ya
fuce domin dai Abu ta wuce iyakacin tunaninsa.
Abu tayi zaton abun na wasa ne, sai gashi
wankin hula yana neman ya kaita dare, dan
bata kammala ba har aka fita tara (break),
sannan ta nufi Ofis din shugabar makarantar
(principal) tace "Maa na gama." Ta dubeta a
wulakance tace "Ki yafa hijab dinki, sannan kada
ki kuma yadda a kawo mini kararki Ofis dina,
idan ba haka ba sai na koreki ko kuma kizo da
Baban ki." Abu ta cire hijab din nata ta sanya
wanda daman dan mitsitsine tace "To!" Sannan
ta fice daga Ofis din. Hajiya Kubra tayi kwafa
gami da yin tsaki tana fadin "Dakikiyar banza,
bata san komai ba sai iskanci." Ita kuwa Abu
tana yin nisa daga Ofis din ta cire hijab din
daga kanta ta kuma yin damara dashi sannan ta
nufi ajinsu. Kawayenta ne suka tarota ana ta
ihu suka rungumeta suna mata kirarinta, domin
wadanda abun ya faru a gabansu sun basu
labari, da haka suka karasa aji suna shewa har
aka koma break. Sai dai da zamanta da rashinsa
kusan duk daya ne a ajin, domin dai bata
tambayi abinda akayi ba da bata nan ba,
sannan yanzu ma da malami ya shigo bata tsaya
ta saurareshi ba hirarsu kawai sukeyi da wata
kawarta, kusan sau uku malamin yana
gargadinta akan tayi shiriu amman batayi
shurun ba, har ya gaji dai ya tambayeta kamar
haka "Abu, tell me how many are types of
letter?" Yana nufin ta gaya masa kashe-kashen
wasika. Tayi tsuru-tsuru don bata fahimci
tambayar bama balle tasan amsar da zata
bashi, sai wani murguda baki kawai takeyi tana
guna-guninta. ganin bata da niyyar bada amsar
ne ya sanya ya kuma gargadin ta akan tayi shiru
ta saurareshi, dan darasin turanci yana da
amfani ga dalibai don ta haka ne zasu koyi
yanda zasuyi magana dashi, amman har ya fita
daga ajin nan Abu bata daina surutunta ba sai
dai ta rage murya ba kamar da farko ba.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Da aka tashi ma sai da sukayi fada da
kwandasta domin dai idan da sabo ta saba,
domin dai maimakon ta bashi naira biyar sai ta
bashi naira uku ba kuma don bata dasu ba, a'a
dan dai neman jidali kawai irin nata.
Kwandastan ya dubeta ransa a bace yace "Ke!
Malama cika mana kudin mu saura naira biyu."
Tayi tafi gami da doka cinya tana fadin ba zata
cika ko kwandala ba don haka kudin motar
yake. Nan fa rikici ya rincabe amman Abu ta
kekashe akan ba zata cika ko kwabo ba. Daga
karshe yace wallahi idan bata cika masa ba zai
warci dankwalinta, maimakon ta saduda ina sai
ma ta cigaba da tsiwarta tana tafa hannu,
kawayenta na ta zugata. Abin ya hasala direban
yace masa ya cire dankwalinta tunda bata da
mutunci, dan haka ya cire dan kwalin nata. Sai
dai abu da kwandastan bai sani ba shine tuni
Abu ta gama dana masa tarko, don haka da ta
sauka kafin ya hau motar tace masa "Malam ka
bani dan kwalina." Yace "Na karfi ne, idan kina
son dankwalinki ki cika mini naira
biyu.......Warce gudar Naira ashirin da fellewarta
da gudu ne ya katse masa zancensa, ya saki
baki galala yana kallonta tamkar zata tashi sama
dan gudu, don Allah ya yi mata baiwar gudu.
Direban ya hau masifa sanda ya ankara da
abinda ya faru yana fadin "Banza sakarai, kana
me wannan 'yar mitsitsiyar yarinyar ta warce
kudi a hannunka? ai sai ka shigo mu tafi." 'Yan
cikin motar banda dariya babu abinda suke yi,
shi kuwa cike da jin haushi yake fadin "Haba
Oga baka ga shammata ta tayi ba? An bani
murtala ina shirin bada canji ta fisga ba?"
"Kawai kazo mu tafi, shegiyar ta bamu a can"
Direban ya katse masa magana. Ya dubi inda
Abu tabi ko alamunta baya gani dan akwaita da
gudu tamkar filfilwa, hayaniyar fasinjoji ce ta
sanya shi shiga motar yana fadin "Ai na gane
wallahi duk ranar da Allah ya kuma hadamu sai
taci ubanta." Ya shiga mota har lokacin wasu
fasinjoji suna dariya abinda ya kara kular dashi.
Ita kam Abu tunda ta falla da gudu bata tsaya a
ko'ina ba sai a tsakar gidan su, ta zube a kasa
tana mai da numfashi. Sala dake kwashe wake
da shinkafa ta dago tana dubanta a rude tace
"Yaya dai Maitsada, lafiya kike wannan hakin
kamar wacce tayi tseren gudu?" Sai data
numfasa sannan ta kwashe da dariya harda rike
ciki, duk da Sala bata san ko dariyar me take yi
ba sai ta hau tayata tana fadin "Hatsabibiya,
yanzu haka tsiyar taki kika shuka tunda naga
kina wannan dariyar." Tayi kokarin tsagaita
dariyar sannan ta fara magana "Bari ke dai Sala,
yau wani shege na hadu dashi zai nuna mini
zara bai san na fishi ba....." Ta kwashe duk
abinda ya faru ta sanarwa da Sala din, gami da
karasa zancen da cewar "Shegen kinga ashirin
din dana warto, gobe ma ya kuma."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Sala ta kuma fashewa da dariya tana fadin
"Lallai kinyi maganin dan iska shege, banda
iskanci akan naira biyu sai ya warce miki
dankwali? Da ba'a cin arziki ai da bai sami
kwandastan ba tunda nasan ba motarsa bace,
amman maganinsa kenan kinga ai gobe ya
kuma. Maza tashi ki shiga wanka kada lokaci ya
kure Abulata mai kan alheri, ba irinsu O'o ba
mai kan kwantai Wato tana nufin Karima kanwar
Abun, domin dai ita bata da hali irin na Abun
dan tana jin irin nasihar da Yayansu yake mata,
dan haka ma basa shiri da Sala sam. Ta mike
har lokacin tana haki da dariya ta shiga
bandakin, kwandan wankanta daban ne, dan ita
sabulunta dankwali ne kamar yanda take cewa
giv da dai sauransu, ba irin nasu Karimaba dan
yanka. Bayan ta fito daga wanka aka kuma
zauna zaman kwalliya, Jagira kam da aka jata
har saida ta tabo kunne, ga kuma dige-dige da
aka yi a fuskar ko ina, leben nan kuwa yasha
baki sama da kasa, sannan aka cokala daurin
dan kwali ture kaga tsiya aka fito. Sala nayi
mata kirari ta nada gammo ta dora a kai, akayi
digir-gire da fanteka wacce ke dauke da wake
da shinkafa da robobi a gefe da mai da yaji duk
a kai, sai hannunta data dauki wani bokiti
wanda dashi take wanke kwanukan da sukayi
datti, aka fice babu addu'a sai da kirarinta data
bita dashi, sai da ta fice daga soron sannan Sala
ta bita da sauri ta leka duk rabin jikinta a waje
ta kwala mata kira ta juyo tana guna-guni. Sala
tace "Yi hakuri Abule na dawo dake, na manta
ban tina miki maganar makarantar allo ba kada
jarababben yayanki yaga ba kije ba ya hadani
da malam, wanda yake jin kamar ya jefani a
wuta dan dai nafi karfinsa ne kawai. Don ba dan
jarabar su ba daga bokon har allon daina zuwa
zaki yi tunda dai kin sami na sallah." Ita dai Abu
batace komai ba ta juya ta tafi tana kun-kuni
tana fadin "Kawai daman akan wannan maganar
kika dawo dani, wallahi da na san a kanta ne da
ba zan dawo ba." Sala din kuwa tace "Mai kan
arziki a kukkunga kada a dawo da ko kwalli
daya, na san ki, ai ba kya kwantai." To kawai
tace sannan ta wuce. Kai tsaye tasha ta wuce
tashar kofar Wambai, tana isa kwastomominta
suka yi mata caaa, domin akwaita da araha ga
sakin fuska da tsafta, idan kana so takai maka
har shagonka zata kai maka
Tun karfe hudu saura minti goma abincin nata
ya kare amman sai ta tsaya hira da samari da
wasan jakai da kawayenta 'yan talla. Can ta
hango Rodimasta, wani da take bi kudi tuntini,
ai sai ta cire gyalanta tace dammara dashi tana
fadin "Yau Allah ya kama tsinannan can, wallahi
idan bai bani kudina ba sai nayi masa rashin
mutunci wallahi, dan yau sai anyi bala'i a cikin
tashar nan wallahi." Laraba kawarta ta riketa
tana fadin "Haba Abu yawa ne, ki kyale shi
kawai kin san halinsa dan akuya ne..." Ta fincike
tana fadin "Dalla malama sakeni ai ya san
wadanda yake yiwa akuyancin nasa, ni idan ya
kawo raini ai sai inci (ta kunduma zagi)." Ta isa
gabansa yana shan tabar wiwi sai wani lumshe
ido yake yana rere wakoki kala-kala na gambara
zuwa wakokin 'yan dambe da na barayi, kai
gasu nan dai barkatai. Abu ta rike kugu tana
wani karkada kafa tace "Kai barawo bani kudina,
rannan na zuba maka abinci ka gudu baka bani
kudina ba, to yau Allah ya kama ka, ko ka bani
kudina ko nayi maka rashin mutunci wallahi. Ya
dubeta yana murmushin mugunta yace "Banza
ke wallahi karamar arniya ce, har kin isa kiyi
mini wata barazana, to na cinye na karfi ne ki
kwata." Ta tafa hannu tana fadin "Kan Ubancan,
lallai yau ka tabo ma kanka, yau zan nuna maka
kai karamin dan iska ne, dan ko sama da kasa
zata hade sai ka bani kudina." Ta kama kwalar
rigarsa ta cukwikwiye tana cigaba da bala'i. Shi
kuwa sai dariya yake yana fadin "Yarinya kece
mai aikin yi, in dai nine wallahi mu kwana a
haka." Ya cigaba da zukar wiwinsa yana lumshe
idanu. Jama'a sukayo gurin suna bada hakuri,
Abu tace wallahi ba zata cikashi ba sai ya bata
kudinta idan kuwa ba haka ba zata dauko masa
folis ita kam Laraba da yake matsoraciya ce sai
hakuri take baiwa Abun. Maimakon ta hakura
sai ta doka mata tsawa tana fadin "Dalla can
malama gafara daga nan, Uwarsa ta kauye ce
take bani jari ko ubansa na karkar....." "Ke Abu
don kazanki ni kike zagi?" Rodimasta ya katseta
a hasale dan ya fara kufula da rashin mutuncin
da take masa. Babu tsoro balle fargaba tace "An
zageka din, kai wanene da ba za'a zageka ba
eye?" Ya kuma hasala da zafin rai yake fadin "Ke
wallahi idan baki sakeni ba zan tattakaki a gurin
nan na farfasa miki jiki." Tayi shewa "Ahayye!
wallahi Bismillah dan halak ka fasa, don ka sani
duk mari daya a folissitashan naira dari yake,
don wata kila sai an hada da gonar kauye
sannan za'a biya kudin marin....." "Ke Abu dan
Allah kiyi hakuri ki sake shi, wannan ai ba
mutuncin ki bane kina mace kina fada da
maza."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta kalli mai maganar tana fadin "Kaga Baba mai
taba ina ginin mutuncinka dan kana biyana
kudina ba irin wannan dan bashin ba, dan haka
kawai ka bar gurin nan sai ya biyani kudina zan
sakeshi." "Kinga ya isa sakeshi nawa ne kudin
naki na biya, tunda shima ya rantse ba zai biya
ba dan idan rigimar tayi zafi har mu zaku jawo
wa tunda dai haka 'yan sandan can ke so a fara
fada suzo kame." Ta murguda baki tana fadin
"Ai wallahi nima ba zan sakeshi ba sai dai idan
ka biyani, naira biyar ne dan haka sai ka biya."
Ya dauko naira biyar a aljihun gaba rigarsa yace
"Gata shike nan rigimar ta kare ko?" Ta saki
rigar Rodimasta tana fadin "Banza matsolo
matsiyaci, yau Allah ya rufa maka asiri da yau
kaga karshen rashin mutunci." "Ke! Ya isheki
tunda dai an biyaki kudinki 'yar matsiyata, dan
wallahi kika zageni sai na tattakaki." Ya fadi
yana nunata da yatsansa. Ta tsaya ta rike kugu
tana wani girgiza tana fadin "Wanda bai fasa ba
baya kaunar uwale da ubale..." Laraba ta
janyeta tana fisfisgewa da kyar aka samu ta
kama hada kayanta tana cigaba da bala'i ta bar
tashar. Tana isa gida ta dire fantekat kayan ta
mikawa Sala kudin wacce ke washe baki, ta fada
daki ta kwanta. Sala taji shiru ta leka dakin ta
ganta a kwance ta bude baki da mamaki tace
"Au Abula kwantawa kika yi? Ke da zaki je
makarantar allo? kada jarababban yayanki yazo
ya ishemu da mita." Ta mike gami da daukar
allo ta fice tana kun-kuni. Miskili kafi mahaukaci
ban haushi, Sala ta fada tana dariya. ta dora da
cewar "Abula diyar Salamatu wani lokaci idan
kina shan kunu ko miskilancin naki ya motsa sai
na ganki kamar wata diyar wani sarki, sai da
lallashi Abula ta." Bata dai ce komai ba ta
ficewarta.
Makarantar dake kusa da gidansu, dan
tsakaninsu gida uku ne, koda taje dinma hira ta
kamayi da kawayenta sai da malam din ya doka
musu tsawa sannan suka rude da hayaniya wai
su nan dole karatu sukeyi. Da ya kirawo ta ta
biya allonta kuwa inda-inda ta kama yi, nan fa
ya hauta da fada, tayi kum da baki kamar ba
Abula diyar Sala ba, dan idan akwai wanda take
tsoro da shayi a duniya bai wuce malam da
yayanta ba, dan malam din bai mata ta dadiba
tun tana 'yar mitsitsiyarta kuwa, gashi babu
yanda zasuyi dashi dan shine kamar matsayin
kakanta na gurin Uba, ya kuma maimaita mata
ta karanta kuwa tsaf. Domin dai duk iskancin da
takeyi tana sane don da ace tana maida hankali
akan karatu da mai kokarice ita dan
kwakwalwarta akwaita da saurin rike abu, sai
dai shiririta da wasa da ta sanya a ranta, dan
yanzu data koma gida zata fita yawo da wasa
dan da kyar gobe zata iya biya yanda ya biya
mata, rudewar da akayi da karatun tashi ne ya
kwace ta. Ana cewa fatiha kowa ya mike yara
suna ta waka suna fadin "Tashiiii." Su Abu da
zugar kawayenta kuwa tsayawa akayi ana maida
yanda aka yi, dan wai wata Lantana tayi
gulmarta, wai yau zasu dirji bakin Lantana da
rubabben kwai. Ai kuwa suka saka ihu aka
sanya Lantana tsakiya tana kuka, sai waccan
tace nima kince mini kaza kince mini kaza, sai ta
tabe baki tana fadin, "Laaa! Ni din?" Sai kuma ta
sanya kuka, Laraba ce ta kuma tunzura fadan
da tace "Eh, nima rannan kince mini wai Abu
tana zuwa gurin Dan Oga mai kyamis, Kutumar
uban can, lallai yarinya a gulmar taki har da ni?
dan ubanki?" Abu ta shiga masifa tamkar zata ci
babu, taci dammara da gyalanta tana cigaba da
girgiza gami da ambaton sunan iyayanta tana
kunduma musu zagi gami da dungure mata kai
da lakuce mata hanci, yara sai ihu suke yiwa
Lantana wacce banda kuka babu abinda take yi.
Malamin sune ya farga da abinda ke faruwa
yayi kansu da dorina, ya samu daya ya caula
mata ta gantsare gami da fasa ihu, abinda ya
ankarar dasu kowa ya bazama da gudu dan
gujewa bulalar malam, wannan ne ya ceci
Lantana daga fasa mata baki da akayi niyya da
rubabben kwai. Ana idar da sallah Abu ta fito
daga gida tana rera wakar kiran wasa don tunda
ta taso itace ke kiran 'yan wasa don ita ce boss
din, don haka ko yara ne ba'a gani ba gidansu
ake zuwa nemansu Sala tayi ta bala'i. Ta fara
rera wakar wasa kamar haka: "'Yan wasa ku
futo wasa, idan baku zo ba ubanku yazo, bani
na fada ba bature ne, baturen ma na kasar
borno. 'Yan wasa ku fito wasa." Ai kuwa sai sai
ga yara suna fitowa daga gidajensu da gudunsu
maza da mata.Yayanta Sadiku dake shagonsa
yana jinta, ji yake tamkar yaje ya shaketa, sai
dai yana gudun jarabar Sala ne, don shi a
zatonshi tun da ya samar mata makarantar
gaba da firamare zata daina wannan wasan
haukan, amman sai yaga babu abinda ta daina,
dan haka yayi niyyar hanata da tsiya amman
Sala tayi tsalle ta dire tace Wallahi bai isa ba ya
kyale mata yarinya ta wataya.
"Aljana a kwaba ba tsari, aljana a kwaba ba
tsari....." Wannan wakar ce ta katse masa
tunanin da yakeyi, ya mike ya leko da sauri don
yasan wa suke tsokana. Ai kuwa yana hango su
sunyi zuga suna biye da wata karuwa da taci
kwalliya da wani matsats-tsan siket kanta babu
dankwali balle mayafi, tana tafe da kyar da
sauri tamkar siket din zai yage, kanta tamkar
tozon rakumi ga takalmi sakadale tumeme da
kafarta, amman sunki saurara mata sai binta
suke suna mata wakar da ihu gami da bula
mata kasa. Can wasu dattawa wadanda ke
zaune suma suna zabga uban musu, dan sunan
majalisar tasu ma majalisar 'yan musu, suka yo
kansu sanda suka ankara da duka.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Nan fa suka runtuma da gudu suna dariya, sai
da sukayi nisa sannan suka zube a kofar wani
gida sunata dariya. Can Abu tace "Laaa! Ku tsaya
kuji wallahi yau mu kai sumame gidan shegun
can Karuwai mun dade wallahi bamu je ba ko?"
Yaran suka amsa da "Eh! Wallahi mu badawa
shegu tiyagas din toka." Abu tace "To kowa ya
tsaya bari naje gida na samo toka da citta a
gurin Sala." Ai kuwa cikin kankanin lokaci suka
hada citta da barkono dakakku da kuma toka
cikin ledoji suka kulle da dutse a tsakiya suka
nufi gidan karuwai ta bayan layi don kada a
gansu. Sun yi sa'a kuwa da yawan karuwan
suna daki suna hira da lalatattun maza 'yan
uwansu, wasu kuma ma suna caca da masu
aikata babbar alfasha. Suka shiga cikin gidan da
sanda kamar wasu barayi, har tsakar gidan suka
isa, cikin daga murya Abu ta bada umurni, "A
fasa! A fasa!!.Ai kuwa ji kake tush-tush-tush,
nan da nan karuwai suka kama ihu da atishawa,
na daki suka yo waje da gudunsu wasu daga su
sai siket, wasu kuma sai zani, harda masu dan
kamfai. Su Abu suka fasa ihu suna dariya gami
da ficewa da gudu daga gidan dan kada a
kamasu, sai da suka isa wani kofar gidan can
nesa da gidan karuwan suka zube suna dariya,
suna hango yanda suke ta atishawa.
Hantsi ya dubi ludayi sanda Abu ta dawo daga
tallar waina. gashi anyi sa'a ranar babu
makarantar boko, dan haka ta zauna a tsakar
gida tana baiwa Sala labarin yanda sukayi da
karuwan jiya suna ta kwasar dariya, Sala kam
harda durkusawa tana rike ciki. Can suka jiyo
sallama, tun kafin sukai ga amsawa aka shigo,
mutane guda biyu da kayan 'yan sanda a jikinsu
riga da siket, sun daure kugunsu da bel. Sala ta
mike cike da mamaki tana tambayarsu "Yaya dai
bayin Allah lafiya ko? Don ganinki babu alheri."
Daya daga cikinsu ta fara magana "Hajiya munzo
mu tafi da 'yarki mara mutuncin can Abu,
domin dai ta addabi uban kowa a unguwar nan,
idan yaso idan munje folis sitashon kya ji abinda
ta yi." Abu ta mike da sauri tana tillika dariya
dan tasan kwanan zancen tana fadin "To muje
din mana, Sala kiyi zamanki yanzu zan dawo."
Sala tace "A'a ba zan iya bari ki tafi ke daya ba
muje." Ta dauko gyale akan igiya suka fice tana
fadawa Karimatu ta lura da abincin da ta dora
kafin ta dawo. 'Yan sandan suka fara kuluwa da
dariyar da Abu take musu, dan haka suka ce
wallahi idan bata daina ba zasu yi mata shegen
duka, ta gumtse baki tana yi a ciki don bawai
tsoronsu takeji ba, a haka suka isa har folis
sitashon din. Ganin karuwai sun jeru ne har da
'yan daudu ya sanya ta kuma tabbatar da
zargin da takeyi, kamar ta fashe da dariya
amman dan tana gudun sharrin 'yan sanda ya
sanya ta gumtse bakinta. Ta isa gindin kanta
inda wani dan sanda yake zaune da gashi buya-
buya a bakinsa wai shi nan sajan ne. Yana wani
muzurai ya dubi Abu yace "Ke mai ya sanya kika
je gidan wadancan masu zaman kansu kuka
barbada musu toka hade da yaji?" Abu tayi
shiru taki cewa komai, ya kuma maimaita mata
maganar amman taki tankawa. Wani kurtun dan
sanda dake tsaye ya daga kulki ya maka mata a
gadon baya, ta gantsare gami da fasa ihu tana
sosa gurin tana fadi "Wayyo Allah na na shiga
uku, wallahi idan ka karya mini kashin gadon
baya na bazan yadda ba." Ya kuma dagawa zai
maka mata amman mai mukamin sajan din ya
hanashi domin idan da sabo sun saba da halin
Abu, sannan ya maida dubansa gurin Abu ya
daka mata tsawa ya kuma maimaita tambayar
da yayi mata da gargadin idan ta kuma yin
shirun zasu saba mata. Ta murguda baki gami
da kallon sa kyar da idonta babu alaman shakka
ko tsoro tace "Wallahi ko zaku kasheni ba zan yi
magana ba sai dai muje gaban (D.P.O)." Sala
tace "Abu kiyi magana kada su tsamama miki
jikinki." Ta kuma hasala tace "Sala kiyi shiru,
haka kawai sai su kama dukana bayan basu
kama ni da laifin komai ba? Ai nasan 'yancina
dan haka ba zanyi magana ba sai dai muje
gaba." Ran 'yan sandan ya kuma baci suka yi
mata caa tamkar zasu cinyeta amman ko gezau
batayi ba, ana cikin haka sai ga (D.P.O) din ya
shigo,
Da mamaki ya dubi Abu yace "A'a, Abu lafiya na
ganki a nan?" Ai kamar jira take ya shigo sai ta
fasa kuka kamar wacce aka yiwa dan banzan
duka, amman fa idon nan nata babu alamar
hawaye ko digo sai dai burarin kawai da takeyi
tana rike bayanta . (D.P.O) din yace su shigo
daga cikin Ofishinsa su duka, Dan daudun dake
tare da Karuwan ya rike haba yana fadin "Oh!
Ni Hajiya Ladi yau na gamu da shegiyar yarinya
mai sharri, wallahi ko kwallaba nan ta ganki ta
kyale, ai wallahi ko mutuwa zakiyi ba kuka ba
sai kinci ubanki." Ya karasa maganar yana tafa
hannu da cinya. "Kai! keep quit kayi mana
shiru." Wani kofur ya doka masa tsawa. Yayi fari
da ido gami da fadin "Lalala! Ka manta wallah
Hajiya Ladi nake ba kai ba." Da haka suka shiga
ofishin D.P.O din. Mai tuhumar Abu Sajen
Barewa ya karantawa D.P.O tuhumar da ake
yiwa Abu, da kuma abinda ya faru. Ya dubi Abu
yace "Kina jin zargin da ake miki? haka ne ko ba
haka na ne?" Ta lankwashe murya cikin ladabi
tamkar mutuniyar arziki tace, "Yallabai karya
suke mini, ni jiya da daddare ma ina gurin
tallan gyada ta, har kazo wucewa kace na kai
maka gwangwani goma a majalisarku ko?" Ya
dubi karuwan yace "To ku kunji abinda wacce
ake tuhuma tace, ko kuna da wata hujjar da
zata nuna mana itace din ta bada muku toka?"
Hajiya Ladi ya tafa hannu yana fadin "La'ilaha
illallahu, Allah na yarda yarinyar nan shegiya ce
kwalba." "La-la-la ka zage ni?" Abu ta fadi ta
dora da cewar "Yallabai kana ji yana zagina a
gabanka hakama acan waje yayi ta zagina."
D.P.O ya doka masa tsawa yana fadin "Kada ka
kuma zaginta." Ya rike haba yana fadin "O! Ni
Hajiya Ladi na shiga uku, tuba nake Yallabai ayi
hakuri na daina zagin, amman kwaran-kwatsa
dubu jiya ina suyar doya na shiga bandaki dan
na rage marata, na jiyo hayaniyar su Abu, kafin
na farga har na fara tari da atishawa a cikin
bandaki da kokarin shidewa har zani na yana
faduwa, da kyar 'yar fisuwa ta kamoni ina
kokarin bankawa cikin masai. Ko ba haka ba
'yar fisuwa?" Ya kalli wata karuwa da taci uban
bilicin, kan nan tamkar tozon rakumi daga ita sai
gajeren wanda iyakacin gwiwa da riga tishet.
Tana tsaye rike da kugu tace "Haka ne yallabai,
tabbas yarinyar nan ce ta gayyato mana yara
suka watsa mana toka mai yaji, dan da muryar
ta ma muka gane ita ce" "Karya kike yi bani
bace, daga jin murya sai kice ni ce? Idan kuma
kin yarda ki rantse da Allah ko a kawo Qur'ani
ki dafa." Abu ta katse ta. D.P.O ya ce "Kunga
tunda dai abun nan baku da shaida zargi ne
kawai kuke yi, dan haka ki basu hakuri ke Abu,
idan yaso a gaba sai kuyi kokarin kama koma su
waye ke muku haka."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ya dubi Sala ya cigaba da magana "Ke kuma kije
ki baiwa sajan din da ya karbi laifin kudin shan
ruwa, na kashe case din kowa ya fita." Sam ba
haka karuwan nan suka so ba, amman tunda
dai basu da cikakkiyar shaida dole suka hakura
suka fice, ita kuma Sala ta baiwa Sajan Barewa
Naira hamsin tace ya sha ruwa. A harabar caji
ofis din suka kuma cin karo da karuwan da
Hajiya Ladi suna mai da yanda aka yi.Abu ta
dubi Hajiya Ladi tana dariyar keta har da gwalo,
Hajiya Ladi ya dalla mata harara yana nuna ta
da yatsa alamun kashedi, ta kuma sanya dariya
gami da sanya hannu a wuyanta ta ja shi alamar
yanka, sannan ta nuna Hajiya Ladi. Hajiya Ladi
ya saka Salati "La'ilaha illallahu, ni zaki yanka?
Lallai yarinyar nan baki da mutunci, to gwara na
koma na fada su zama shaida tun bamu bar
gurin ba." Yana magana da karfi yana tafa
hannu da buga cinya, gaba daya hankalin
jama'ar dake gurin yayi kansu. Abu ta
marairaice tana fadin "Dan Allah jama'a wa yaji
sanda na yiwa mutumin nan magana balle har
nace zan yanka shi? to muje din mana a kwatar
mini hakkina tunda abin naka sharri ne, tunda
dai kowa yana ji anan bance da kai komai ba."
Sannan tabi bayan Hajiya Ladi da sauri dan su
koma ciki tare. Hajiya Ladi ya tsaya da sauri
sororo yana kallon Abu, domin dai lallai ya hadu
da wacce tafi shi sharri da iya iskanci. Da zolaya
Abu tace "Yaya ka tsaya mu tafi mana." Ya
dallawa Abu harara yana fadin "Kwalba uwar
sharri, kada ki kuma kirana da kai sunana Hajiya
Ladi, idan kuma jurinki iskanci zamu kuma
gauraya sai na nuna miki ke din baki isa komai
ba wallahi." Ya tafa hannu gami da bugawa a
cinya yana wani murguda baki da karkafa ido,
ya dora da cewar "Kun ga kuzo mu bar harabar
police station tun shegiyar yarinyar nan bata
haddasa mana ciwon zuciya ba, kunga tafiya ta."
Ya gyara daurin zanin dake bisa wandonsa gami
da dane hannu yana tafiya yana wani yanga,
suka rufa masa baya suna mai da yanda aka yi.
Abu ta kyal-kyale da dariya gami da nufar gida.
Sala tana biye da ita itama tana dariya da yi
mata kirari, "Abula tawa, kowa ya ja dake yaji
kunya. Mahassada kun sha kashi. Yarinya mai
tsada kalar manyan maza."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
KANO 11 GA WATAN 6, 1993.
Rayuwa mai sauyawa, sai dai ga Abu sauyi da
aka samu kalilan ne, domin dai cigaban nata bai
wuce na daina daukar abinci akanta,sai dai a
dorawa dan dako tana biye dashi ba, sai kuma
chalo da ta daina zuwa da dibar 'ya'yan jama'a
a tafi tsokanar fada duk ta daina. Sannan
kyawun ta da kirar da Allah yayi mata mai
daukar hankali sun fara bayyana. Sai kuma Abu
mafi girma da za'a idar bai wuce daina tallar
safe ba, saboda shugabar makarantarsu ta
budewa Abu wuta saboda jarabawa da aka yi ta
shiga aji biyu na sakandire amman sai ya
zamana Abu ce ta dauki na karshe a ajinsu,
sannan ko a jikinta (wai an mintsini kakkausa).
Abun ya konawa Hajiya Kubra rai, don haka ta
sanya aka tara mata duk wadanda suka zo na
karshe na kowanne aji, ta sanya su a gaba tayi
musu kaca-kaca, sannan tace lallai sai kowacce
tazo da mahaifinta domin tana son jin dalilin da
ya sanya basu mai da hankali akan karatun ba
har suka zo na karshe, dukkansu yaran jikinsu
sai kyarma yake yi kowacce a tsorace take
amman banda Abu dake ta murguda baki tana
magana kasa-kasa, sarai Hajiya Kubra ta ganta
amman sai ta rabu da ita da zummar idan
mahaifinta yazo za tayi mata hukunci a
gabanshi, haka nan suka tashi kowacce ta nufi
gidansu tun lokacin tashi baiyi ba. Abu tana
shiga gida babu ko Sallama bagazan-bagazan-
bagazan ta yadda jaka da hijabin tana fadin,
"Wallahi Sala ba zan kuma zuwa makarantar nan
ba, don na gaji da masifar shegiyar principal
dinmu, sai kace wata uwata haka kawai ta tsane
ni." Sala ta dubeta da kulawa tana tambayarta
"Mai tsada yaya akayi ne? Mai ya faru naga ko
lokacin tashi daga makarantar bai yi ba." Ta
tabe baki kana tace "Wai kawai dan munzo na
karshe shine ta sanyamu a gaba tanata
zaginmu, baki ga sauran ba jikinsu har rawa
yake yi, ni kuwa duk abinda tace sai na bata
amsa amman dai a hankali, kuma tama yi sa'a
dan 'yan arzikin a kaina da saina rama," "Kinyi
mini dai-dai, sai kuma aka yi yaya?" Sala ta
katse ta. "Wai kuma duk cin mutuncin da tayi
mana bai isheta ba wai lallai sai mun zo da
Babanmu, ni kuwa wallahi bata isa ba ai dai ba
karatun shiga Aljanna bane."
Sala ta amshe "Wannan tsabar rainin hankali
ne, haka kawai dan kunzo na karshe sai ace
wani sai kunzo da Babanku? To ai ba laifinku
bane sune basu iya koyarwa ba, ai zuwa
makarantar ba dole bane kiyi zamanki kin huta
da tashin safe ma." Wannan ne ya sanya Abu ta
share gindi tayi zamanta a gida har kusan sati
biyu bata je makaranta ba, sai rannan da Sadiku
ya shigo da hantsi wajen karfe goma, shima ya
dawo makaranta sai kuwa suka yi kicibis, yayi
kanta da masifa yana fadin mai ya hanata zuwa
makaranta. Ta zura dakin Sala da gudu dan duk
iskancin Abu tana tsoron Sadiku dan bai mata ta
dadi, dan babu wuya ya lakada ta. Sala ce ta
fito tana hargagi gami da sanar dashi yanda aka
yi. Ya kuma kulewa yace maza ta shirya ya
maida ta idan kuwa ba haka ba sai dai idan ta
daina fita ne wallahi sai ya karya mata kafar
talla. Sarai Sala ta san halinsa dan haka ta
lallaba Abu dake ta kunci ta fita suka nufi
makarantar. Sanda suka isa ofishin (principal)
shugabar makarantar ya dinga bata hakuri yace
Babansu ne baya gari shi ya sanya ba'a kawo ta
ba, shi kuma bai sani ba yana makaranta sai
yau da ya dawo ya taddata a gida. Da farko
Hajiya Kubra tace ba zata saurareshi ba sai dai
idan ya nuna mata katin shaidar cewar shi
dalibi ne I.D card, tayi mamaki sosai da taga
abinda yake karantawa (Law) amman kanwarsa
muguwar dakikiya. Ta bashi guri ya zauna
sannan ta sanar dashi irin mugayen dabi'un Abu
da kuma dakikancin ta. Yayi kwafa cike da
takaici yace "Babanmu yace a baki hakuri
sannan yace kafin na bar Ofis din na kiyi mata
bulala guda hamsin, kuma yace daga yau
kowane irin laifi tayi a daina korata gida tunda
ba fada takeyi ba dan bata son karatun, a dinga
bata horo mai tsanani kowanne iri ne." "Karya
kake yi wallahi, yaushe har kaga Baban mu daya
fada maka haka?" Ta katse masa magana da
rashin kunya da hargowa. Mamaki da takaici ya
kama Hajiya Kubra, wato bata bar na gida ba
balle na waje ma. Shi kuwa Sadiku saboda
tsabar takaici kasa magana ma yayi, sai dai yaga
wata bulala a kan teburin Hajiya Kubra dan haka
ya dauko ya hau zabga mata, tun tana ihu da
makaleshi har ta gaza bakin nan nata sai da ya
mutu, gashi babu Sala mai kwatarta ita kuwa
Hajiya Kubra dama a cike take da ita dan haka
ko uffan bata ce ba, daman duniya idan akwai
abinda take tsoro bai wuce dukan Sadiku da na
Malam ba, domin basa mata na wasa, gashi
sune kadai zasu daketa a duniya su daki banza
dan babu abinda Sala zata iyayi, sai dai tayi
hargaginta ta gama dan ba zata iya rama mata
ba, su kuma bata isa ta dauko musu 'yan sanda
ba kamar yanda ta saba.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Yawan dukan da yayi mata ne ya sanya ran
Hajiya Kubra yayi haske, ta tabbatar lallai akwai
mai kwabar Abu jine kawai da bata yi. Bayan ya
jibgeta ya gaji ya dubi Hajiya Kubra yace "Hajiya
ki bata fartanya tayi noma da kuma wankin
bandaki." Abu dake kwance tana kuka ta kuma
kurma ihi tana fadin "Wayyo Sala na shiga uku
kizo da kanki,A zuciye ya kuma kai mata duka a
bakinta wanda ya sanya ta yin shirun dole dan
sai da bakinta ya fashe, amman bata daina
harararsa da murguda baki ba. Haka ya tafi ya
barta saida tayi noman nan da wankin bandakin
dalibai wanda yayi kaca-kaca da kashi babu
kyan gani, dan saida ta daure hancinta da
dankwalinta sannan ta iya wankewa, shi dai
Sadiku yayi tafiyarsa, amman yasan yau bala'i
sai yasha ya more gurin Sala. Ai kuwa haka din
akayi domin dai data dawo gida taga idonta da
bakinta sun kumbura ta zabura da sauri tana
tambayar abinda ya faru. Abu ta zube a tsakar
gida ta dora hannu a kai tana zunduma ihu
kamar wacce akayi wa mutuwa ko kuma a
sannan ake dukan nata tana fadin "Wayyo Sala
na shiga uku, wallahi bazan taba yafewa Sadiku
ba ko kabarinsa zai dinga balbala da wuta..."
"Wai me ya faru? na san za'a rina daman, me
yayi miki?" Sala ta tambaya a rude. Ta kwashe
duk yanda akayi ta sanarwa da Sala tana ajiyar
zuciya dan babu alamar hawaye ko kwalli a
idonta. Habawa ran Sala idan yayi dubu ya baci,
ta dinga sirfa masifa tana fadin "Ai makarantar
ba dole bace da har za'a kama ki da wannan
dukan a fasa miki baki da hanci, tunda kin iya
daurin dankwali ai magana ta kare, ladan ya isa
haka. Shi kuwa dan Baba zaizo ya sameni
wallahi sai nayi mummunan saba masa, sai ya
yabawa aya zakinta."
Haka nan ta wuni tana mita kamar zata ci babu.
Shi kuwa Sadiku yana sane yaki dawowa gidan
da wuri sai da ya bari dare yayi ya lallaba kicin
dan ya dauki abincinsa, ai kuwa tayo waje
daman lambo tayi tace dawa Allah ya hadamu,
donma dai ya wuce duka ne da ranar sai yasha
duka a gurin Sala, shi kam ko kala baice ba da
yaga ba'a ajiye masa abincin ba ya juya ya fice.
Ta bishi har zaure tana fadin "Babu zuciyar
nema sai ta ci, ita dai wacce ka tsana din ce ke
nemo abinda kake ci kuma wallahi ko ruwa ba
zaka sha a gidan nan ba, idan kayi zuciya ka
siya, wanda na san ko sisi baka da shi baya ga
tarin takardu da bakar zuciya." Shi dai dakinsa
ya shige ya kwanta ranar haka ya kwana da
yunwa, ita kuwa saida ta kusa kwana tana mita.
Wannan shine sanadiyyar daya sanya dole aka
daina tallar safe, domin dai Sadiku yace duk
sanda tayi laifi a daina turata gida tayi noma da
wankin bandaki, abinda ta tsana a rayuwarta,
ya kuma rantse idan ta daina zuwa makarantar
sai ya ballata yaga da kan da kafar da zata yi
tallan, dole kanwar naki aka hakura da tallan
safe dan ta dinga zuwa da wuri. Da farko Sala
tace bata yadda ba amman ganin da rana ma
ana samun ciniki mai yawa kuma ita Abu tana
tsoron bala'in Sadiku ya sanya dole suka
hakura, sai dai su Karima suyi tallan safen kafin
su tafi makarantar, amman ita da yake ba irin
halinsu daya da Abu ba takanyi hanzari ta saida
ta tafi makaranta, domin ita halinsu kusan irin
na Sadiku ne shiya sanya basa shiri da Sala
sosai kullum tana mata fada da cewar mai kan
kwantai.
Misalin karfe biyu na rana ta fito daga gidansu
dan dakonta yana dauke da fantekar abinci da
kwanuka da miya a kansa, ita kuma tana rike da
farin bokitin roba mai haske an yanka salak da
tumatir da albasa, daya hannun kuma kaji ne
soyayyu cikin irin farin bokitin, anyi wanka an ci
kwalliya, zanin nan an daurashi kwauri a waje
anja jagira lebe yasha jambaki da baki, sai dai
anyi kilin an daina dige-dige da kwalli, hatta
takalmi dan madina dake kafarta yasha wanki
sai sheki yake yi, ana tafe dagwas-dagwas
kamar mai jin tausayin kasa, domin tun can
daman Abu akwai tsafta da kwalliya balle yanzu
da aka fara zama 'yan mata, gwalli da feleke ya
karu, duk cikin kawayenta tafi kowa iya tsara
kwalliya, daman gata ba baya ba gurin kyau.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
zandakata a nan,insha Allahu Zuwa yamma
zamu dora,domindai aikin Littafin yayi bisa,Wata
tangarda ce ta hanani farayimuku a
ana,nagode..
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Idan Zuciya Tagyaru 1-02
Posted by ANaM Dorayi on 05:26 AM, 28-Jan-16
Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU
_________________ Na
________Fauziyya D Sulaiman____
Mustafa dake zaune kofar gidansu bisa farar
kujera karkashin bishiyar Umbrella, yana
karatun jarida kamshin Abu ya bugi hancinsa ya
daga kansa da sauri yana dubanta, kusan sati
guda kenan yake ganinta tana wucewa irin
wannan lokacin, kwarai yarinyar ta kwanta masa
a ransa, da kuma dai alamun ba za'a sha
wahalar samun kanta ba, kullum yana son yi
mata magana amman ya rasa ta yanda zai fara,
yau dai dabara ta fado masa dan haka ya fara
kwala mata kira. "Ke! Ke mai abinci! Kawo." Ta
tsaya turus gami da waigowa tana dubansa,
domin bata saba saida abincinta cikin unguwa
ba sai ta dangana ga tashar kofar wambai,
amman sai taga yayi mata kwarjini ba zata iya
kin saida masa ba, domin dai abincinta sai
wanda taga dama take saidawa, don haka ta
hau kwalawa almajirin dake dauke da abincin
kira "Kai Mudi! Kawo abincin za'a siya. Babu
musu yayo ribas ya juyo, ya isa gaban Mustafa
wanda ke zaune akan farar kujera mai tambarin
kamfanin coca-cola ya tsaya kerere. Ta galla
masa harara tana fadin "Kai fa tamkar jaki kake
komai sai ance kayi zaka yi ko? To sauke kayan."
Sannan ta dubi Mustafa tace "Malam na nawa
za'a zuba maka?." Yayi wani mayaudarin
murmushi yana mata wani duba na yaudara da
kwarewa a harkar iya soyayyar 'yan zamani yace
"Haba 'yan mata babu ko gaisuwa?" Tabbas yayi
masifar yi mata kwarjini, hasalima tunda suka
hada ido taji wani abu ya bugi zuciyarta wanda
ya sanya ba zata iya yi masa musu ba ko rashin
kunya, shi kansa ya gano hakan a kwayar idonta
ya kuma san haka nan Allah yayi masa kwarjini
da farin jini ga kowa, domin dai da wani ne
cewa zatayi, ban iya ba ko kuma tace baka kai
matsayin da za'a gaidaka ba din ne, amman shi
sai ta tsinci kanta da ce masa "To ina wuni?"
Yayi dariya yace "Ko ke fa, lafiya kalau, yaya
sunanki ne, dan kallon farko naga kin mini dari
bisa dari."
Ta kosa da zancan nasa ta daure dai tace "Ka ga
sauri nake kada rana tayi mini, na nawa za'a
baka? Dan kada kaja nayi kwantai." Ya kuma
murmushinsa dake kashe mata jiki yace "Haba
dai, ai kyawawa basa kwantai, ko domin kyanki
ai a sayi abincinki." "Ka ga nifa zan wuce kana
bata mini lokaci, wallahi dan kaine kawai na
tsaya." Ta fada tana yamutsa fuska. Ya kanne
mata ido daya yace "Haba dai ke kya soma
tafiya ban san sunanki ba? domin dai zaman
nan naki ne, dan tun randa na fara ganinki
Allah ya dasa mini tsiron sonki a raina wanda
kullum yake kuma girma, dan haka nake zama
kawai naga wucewarki naji dadi. Ta dubeshi cikin
ido, yanayin kallon da yake mata ya kashe mata
jiki ta gaza masa komai, amman sai ta dubi
Mudi da ya baza kunnuwa kamar na zomo yana
sauraran abinda suke fada tace "Mudi dauki mu
tafi yana bata mana lokaci." Mudi ya yunkura zai
dauka amman sai Mustafa ya dakatar dashi
yana fadin "Kai ajiye, maza nemo 'yan uwanka
almajirai ka raba musu, kyaky-kyawa kamarki ai
kin wuce tallan shinkafa, ke fa gimbiya ce."
Yana maganar yana dubanta da wani kallo daya
bambanta da wanda samarinta kucaku ke mata.
Mamaki ya cikata amman sai ta gaza cewa
komai tayi shiru kawai tana dubansa. "Kaje
mana ka kira 'yan uwanka ka raba musu ka
baza kunnuwa ka saki baki sai kuda ke fadawa."
Yace da Mudi wanda ya saki kunne da hangame
baki yana dubansu. Mudi dai gani yake kamar
da wasa yakeyi, amman da yaji ya doka masa
tsawa ya kuma nanata masa ya sanya ya fara
kwalawa 'yan uwansa kira. "Alalan Alalan
almajiri, Alalan Alalan kazoo kaci, Alalan Alalan
Alalan kai ba tumatiri." Ai kuwa nan da nan
gurin ya cika da almajirai, yace "To maza abi
layi." Ya kalli Mustafa dake kallon su. Mustafa
yace "Ka rarraba musu mana." Ai kuwa nan da
nan ya fara zubawa almajirai kafin kace kwabo
sai fanteka da bokitin salad. Abu na tsaye rike
da kugu cike da mamaki tana kallonsa, lallai
wannan mutumin dan rikice ne, ko tambayarta
kudin abincin baiyi ba yasa aka raba, zata yi
maganinsa kuwa yau, don wallahi sai ta tsuga
masa kudi masu yawa. Ya dubi Mudi yace "To
maza a hada kayan a koma gida uwar dakin
naka zata taho yanzu." Sai da yaga Mudi yayi
nisa sannan ya dubeta na dan wani lokaci tana
tsaye rike da kugu da alamun mamaki da
shakka a fuskarta. "Adon gari tunanin me kike
yi? Har yanzu baki fadi mini sunanki ba." Ta
yamutsa fuska tace "Sunana Abu......" "A'a
babban suna Zainabu Abu mai tagwayen suna
kenan, gaskiya Zainab baki dace da kalar tallah
ba, dubeki fine baby ace kina daukar tallah? to
gaskiya ni dai daga yau na soke tallar nan." Ta
dubeshi a tsiwace tace "Ka ji mu da mutum sai
kace wani Ubana? ko kai ne zaka dinga biyana
kudin da nake samu eye?" Yace "Eh mana zan
dinga biya ko nawa ne, don gaskiya bana son
rana tana taba mini kyaky-kyawar fuskarki,
kyanki hutu Zainabu."
Ta tabe baki don zancen bai gamsar da ita ba,
don tasan bai san yawan kudin bane shiyasa
yake wani cika baki amman yanzu zata yi
maganin firiritarsa. Don haka tace "Ka ga ka cika
ni da surutu bayan baka biyani kudin abincina
ba." Yayi dariya yace "Haba Zainab, baki yarda
dani ba naga alama, ko don kin ganni da dan
wando jeans da shet? kin san mu 'yan boko
bamu san kaya masu nauyi, amman nawa ne
kudin? Kila idan na baki hankalinki yafi
kwanciya." Ta murguda baki wanda ya zame
mata kamar al'ada sannan tace "Dari uku da
ashirin da biyar ne, sai nama na naira talatin da
biyu...." "A'a Zainab, duka zaki hade mini?" Tayi
dan duru-duru don tasan zulake tayi duka
kayan nata basu wuce na dari biyu da tamanin
ba, don haka ta kasa hadewa ta fadi don bata
iya lissafi ba (bata da Maths tab akin yara), da
ya fahimci halin da ta shiga sai ya zura hannu a
aljihunsa ya debo 'yan murtala (Naira Ishirin)
har na dari hudu yace, "Ga dari hudu ma ni na
kara miki." Mamaki ya cikata matuka, hannunta
har rawa yake yi gurin karba don tana ganin
kamar zai maida yace ya fasa ne. Sai da taji
dumin kudin a hannunta sannan hankalinta ya
kwanta ta dube shi da mamaki tace "To nagode!
Zan tafi gida." Yace "A'a ai dole na yiwa gimbiya
rakiya ko don naga gidansu." A wannan karon
bata yi masa musu ba don yayi mata ba zata,
don haka suka nufi hanyar gidansu, a kofar gida
yayi mata sallama yace sai gobe tace Allah ya
kaimu. Ta shiga gida da gudunta Sala na zaune
tayi tsuru cike da shakkun labarin da Mudi ya
bata, gaskiya tafi zargin bari kawai suka yi yace
wani wai juye wani saurayi dan gaye yayi mata.
Abu na shigowa ta mike da zakuwa tace, "Ke
maza sanar dani menene ya faru?" Abu tayi
dariya gami da nuna mata kudin da saurayin ya
bata, ta fizge daga hannun Abu da azama ta
hau kirgawa, Abu kuwa sai dariya takeyi. Sala ta
kammala lissafawa ne ta dubi Abu cike da farin
ciki tace "Diyar arziki yau kuma wane mai arziki
kika hadu dashi? Kai wannan diya da kan arziki
kike, shi ya sanya aka tsangwameki a unguwar
nan, ki dubi yadda su Sarai da Sakina kawayenki
suke kwantai kullum sai sun dawo da ragowar
abinci, sai dai a cinye ko kuma akai dakalin 'yan
kwantai da daddare abincin naira biyu a karyar
dashi naira daya koma sis daya. Abu tace "Bari
ke dai Sala, ni tunda nake ma ban taba haduwa
da mutum mai ban mamaki irin wannan ba."
Sala tace, "Yaya ne sunansa?" Ta tabe baki tace
"Oho!!! Ni ko tambaya ma banyi ba." "Kiji
sokuwa, arziki yana kiranki kina masa kutufo, to
gobe ki tambayi sunansa kuma ki saki jikinki
dashi, kin san su irin wadannan basu son ki
dinga dari-dari da su, idan abin ma gaba
daya....." Abu tayi dariya gami da shigewa
dakinta. … Allah ya shirya.
Washegari ma haka ce ta faru, Mustafa yayi
mata juye ya rako ta gida, sai dai wannan karan
ya tsaya sun dan taba hira duk da ya lura
sokuwa ce sam bata waye ba, da kuma alama
girman jiki ne kawai da ita babu shekaru, sai dai
ko menene shi dai yaji ya gani yana kuma so a
haka.
Yau da gobe sabo da shakuwa ya shiga
tsakaninsu har ya zama an daina fita da abincin
ko ina sai dai a bawa almajirai a gida. Abu an
daina fitowa kamar yadda Mustafa yace bai son
kyaky-kyawar fuskarta ta baci da zafin rana don
haka tana gida kullum. Wani abu kuma da
Mustafa ya koya mata shine cin dadi, yanzu
abincin kala-kala take ci ba irin wanda take ci
ada can ba, ga kaya da yake kawo mata na
kwalliya da na sanyawa, sai ga Abu ta kuma
futowa fes da ita kuma yanzu da motar Babansa
ma yake zuwa zance gurinta ko ta Mamanshi
don haka cikin motar suke zancensu. Ta futo
daga wanka tana tsakar gida bisa tabarma da
kayan kwalliya a gabanta ana ta kwalliya da
hasken wutar nefa, dan Mustafa na gab da
zuwa, Sala ta zauna daga bayan ta tana kallonta
cike da murmushi tace, "Kai diyar nan wallahi
akwai ki da kwalliyar daukar ido, dubeki kamar
wata sarauniya. Ai ba don bamu gama cin kudin
ba da kin auri yaron nan don ya dace dake, ga
kyau ga kudi, sai dai na lura kamar dai iyayensa
ne masu kudin ba shi kansa ba ko?" Abu ta
tabe baki tace, "Oho! Ni ban sani ba, ke idan
banda abinki ma Sala yaushe na isa aure? Ni
yanzu ma sai nayi digiri, don Mustafa yace mace
idan tayi ilimi wai tafi kyau da tsada. Ni fa yanzu
Sala dan-na-sanin talla ma nake yi, ki dube ni ki
gani yanzu kamar wata diyar wani basarake."
Sala tayi shewa gami da rangada guda tace, "Kai
Allah nagode maka, ai abinda nake ta nusar
dake kenan tun da can, ki sami samarin da zasu
dinga kashe miki kudi mu huta da tallan, yanzu
ba gashi munyi kyau ba? Ga kudi suna shigowa,
wannan shegen yayan naki yana saka mana
ido." Ta ja tsaki, "Mtsw! Wallahi idan ya sake sai
nayi masa baki, wai har ni zai kalli idona yace
mini sai Allah ya tambaye ni duk abinda muke
aikatawa, wai don kina zance a mota, wai 'yan
unguwa sai zarginki sukeyi gashi kin daina talla
ma a ina kike samun kudi yanzu? Nace a gidan
ubansa. Sai fa da nayi masa wuta-wuta sannan
na samu ya fice daga gidan nan, kuma nayi
masa barazanar duk randa ya kuma shiga
shirginki sai na tsine masa, idan muka biye ta
tashi zamu rayu ne? Da yanzu mun mutu,
Mtsw!" Ta kuma jan tsaki. Abu ta hasala ta
murguda baki gami da tsiro shi gaba tace, "Ki
fita harkarsa kawai Sala, na lura talauci ne ke
damunsa, kuma wallahi yayi sa'a shi yayana ne
da wallahi 'yan sanda zan dauko masa." Sala
tace, "Ai bake ba ni kaina ba don gudun abin
kunya ba da saka ido irin na tsinannun mutanen
unguwar nan, da wallahi sai na hadashi da 'yan
sandan sun lallasa mini shi." Sallamar da wani
yaro yayi ce ta katse musu hirar tasu tamkar
wasu kawaye, su kuwa sauran kannan nata duk
sun bazama tallar gyada a can kofar gida. "Kai!!
Meye ka ishemu da sallama?" Sala ta katse shi
cike da haushin katse musu hirarsu da yayi ba
tare da ta kai aya ba don ko amsa sallamar ma
bata yi ba. "A'a daman wani ne a mota ke
sallama da Abu..."
"Au! Yi hakuri na hauka da fada, kace tana zuwa
dan albarka, ka ji?" (HMMM) Yaron ya fice yana
fadin to. Ta dubi Abu da ta mike ta nufi daki
don sanya kaya tana dariya tace, "Yau dai naga
kwalliyar nan ta daban ce, kiyi sauri kada ki
bata masa lokaci." Ita dai bata ce komai ba ta
shirya ta fito sai kamshi take yi, kai tsaye ta fice
ta nufi gurin da Mustafa yake, yana hango ta ya
bude mata gaban motarsa wato kusa dashi sai
wani malalacin murmushi yake mata na
tsananin yaudara irin na gogaggun samari, ita
kuwa sokuwar sai wani kara zobara baki takeyi
tana wani yauki har ta shiga ciki ta zauna tana
wani fari kamar 'yar tsana. Ya shaki kamshinta
gami da lumshe ido, cikin mayaudariyar
muryarsa yace, "Kai Zainabu, kin yi kyau kamar
wata sarauniya." Tayi dariya cike da jin dadi
tace, "Haka ma Sala tace wai nayi kyau sosai."
Yayi murmushin jin wautarta, Ya riga ya gama
karantar halin Abu da Sala, don haka ya san ba
zai sha wahala gurin samun hadin kan Abu ba,
don haka ya mika hannuwansa ya kamo hannun
Abu yana wasa dashi yace, "Kai yatsunki akwai
ban sha'awa, dube su zara-zara. Dadi ya kuma
cika ta na yabon da yake mata tace, "Haka kowa
ke cewa, wai yatsuna da na hannu da na kafa
suna da kyau kamar ba nawa ba." Yayi dariya
yace, "Gaskiya haka ne, amman kyanki ai yaci
suma suyi kyau." Cikin dabara ya jata jikinsa
yana fadin, "Ya dace dai yau na shaki kamshin
nan naki da kullum ke ruda ni." Ga mamakinsa
sai yaga Abu ta saki jikinta har ma tana kokarin
taya shi, abin ya bashi mamaki don yayi zaton
sai yasha wuya zai sami kanta, sai gashi ya
same ta a ruwan sanyi, amman sai ya danne ya
dinga aiwatar da mugun nufinsa da zuciyarsa ke
ingiza shi. (Allah ya kiyashe mu da aikin assha.
amin).
Da ya tabbatar ba zai sami wata matsala da Abu
ba, sai ya lankwashe murya yace, "Abu ko zaki
rakani wata 'yar unguwa?, daga can kin ga sai
mu wuce nayo miki siyayya ko?" Tace "Babu
damuwa muje kawai." Ya dubeta ta dan hasken
dake cikin motar na farin wata da ya shigo yace,
"Kina ganin babu matsala idan Sala ta aiko bata
ganki ba? dan kada tayi fada." Ta tabe baki tace,
"Kada ka damu ba zata ce komai ba tunda dai
ta san siyayya zaka yi mini, kuma ta san ai
muna tare." Yaji dadin abinda tace dan haka ya
tada motar gami da karo sautin wakar dake fita
a cikin rediyonsa, muryar Bob Marley ce a
wakarsa ta One Love, duk da Abu bata jin
turanci wakar tana mata dadi musamman da
yake koda yaushe za kaji kaset din Bob Marley
Mustafa ke sanyawa, har ma ta iya bin wakar
tana girgiza kai duk da ba daidai take fadin
wasu kalmomi ba. Suna tafe a hanya suna hira
har suka isa wani hotel, kasancewar kaurin
sunan da hotel din yayi baka ganin jama'ar kirki
a cikinsa domin kada sunansu ya baci, wannan
ya kara baiwa 'yan iska damar cin karensu babu
babbaka, gurin shiru babu alamun jama'a, sai
ka shiga daga ciki zaka ga kamar tsakiyar rana
ce dan haske da tashin kida. Ya dubi Abu yana
murmushi yace, "Zainabu ya dace mu dan tsaya
a nan musha lemo mu huta, kafin na wuce yi
miki siyayyar domin har dan kunne da sarka na
gwal zan sai miki, kema ki shiga sahun manyan
mata ko?" Yana mayaudarin kallonsa yake
maganar. Tayi dariya cike da jin dadi tace "Babu
damuwa." Ya sami guri ya faka motar tasa, ya
bude ya fito sannan ya bude mata ta fito suka
jera, Abu jin kanta take yi da girma saboda ta
fito daga mota, a ganinta ta gama cinyewa.
Sanda suka isa cikin reception din hotel din sai
ta kama zare idanu cike da kauyanci, domin
tunda take bata taba ganin guri mai kyawun
wannan ba, ta saki baki galala tana kallo ga
hasken wuta ga fankoki suna juyawa ga A.C da
Tibi, ga 'yan mata nan kala-kala kowacce da
shiga ta rashin mutunci, sai taji ta raina kanta,
lallai ta yadda da Mustafa da yace zai nuna
mata rayuwar 'yanci da wayewa, gashi kuwa ta
fara gani. Sai ta kama muzurai kamar ta koma
gida ta sanyo atamfarta Wagambari da tafi
kowacce kyau da tsada, amman sai taga ai ko ta
sako ba zata yi kyawun wadannan ba, ta
shagala da kallonsu tana fadin dama itace
wannan, can kuma idan taga wata sai taji tafi
waccan tace, kai waccan zan zama, shi kuwa
yana can yana biyan kudin dakin da zai kama
musu. Ya kammala ya amshi makulli ya nufe ta,
sai yaga sam hankalinta baya tare da ita har
hannu take sanyawa tana taba duk abinda ya
burgeta, ya kama hannunta suka nufi dakin da
ya kama musu. Sanda suka shiga dakin kuwa sai
labari ya sha bamban, sai taga ai can wajen ma
ba'a sanya komai na more rayuwa kamar nan
ba, ta fada kan tumemiyar kujerar dake falo da
karfi tana fadin, "Kai bari muga za ta loma
kuwa?" Ta saka wata dariya ganin ko motsi
sosan baiyi ba, can idon ta ya hango mata wani
gilas dake dauke da ruwa da kifaye da wasu
'yan kananan bishiyoyi, ta mike da sauri ta isa
gurin, ta saki baki tana kallo da shafawa, can ta
kuma fashewa da dariya tana fadin "Wallahi
kifin da ransu kuma yawo suke kamar a teku."
Shi kam Mustafa yayi tsaye yana dubanta,
hannuwansa cikin aljihu yana dariya saboda
ganin irin kauyancin da take yi, lallai ya kuma
tabbatarwa Abu sokuwa ce mara wayo, sai dai
rashin kunyar, domin da ace tana da wayo ba
zata yi wannan kauyancin ba, ko kuma dan bata
da wasu shekaru da yawa ne? Can ya hango ta
tana kiciniyar bude wata kofa sai turawa take
iyakacin karfinta.
Ya karasa yana dariya yace "Dakin bacci ne, bari
kiga yanda ake budewa." Ya kama marikin kofar
ya murda a hankali sai gashi ta bude. Ta kuma
bude baki cike da mamakin ganin wani irin
katon gado kuma dan karami ba irin na Sala mai
rumfa ba, ta nufi gadon da gudu tayi tsalle ta
fada tana kyalkyala dariya har da rike ciki tana
kuma birgima. Can kamar wacce aka kuma
tsikara sai ta kuma mikewa da sauri saboda
hango wata kofa da tayi ta san lallai wani abin
kallon zata kuma gani, wannan karon bata sha
wahala ba ta bude domin taga yanda ya bude
waccan, ta rufe bakinta cike da tsananin
mamaki taca cewa "Na shiga Uku ni Abula,
menene wannan kuma?" A cikin kunnenta taji
yana mata rada, "Wannan bandaki ne gurin
wanka irin na 'yan gayu, idan kina son irinsa zan
gina mana." Ta juya tana dubansa da mamaki
dan bata yarda da abinda yace ba, yaya ma
za'a yi aga bandaki a cikin daki kuma ga wasu
irin abubuwa a ciki kamar daki ma? Ya daga
mata kai alamar haka ne da gaske, ta nufi gurin
kwamin wanka ta shiga sai ya sakar mata
shawa, ta firgita ta fito da gudu tana ihu,ta
kankame shi domin ta firgita, ya fashe da
dariya. Lallai Unguwarsu da manyan gidaje
amman bata taba shiga ciki taga yanda suke ba,
domin ita kam bata iya jure wulakanci ko kaka
yake, su kuwa 'ya'yan masu kudin unguwarsu
wulakanci ne dasu, sam basu kula su ko fita
zasu yi ma sai dai a mota, shi kansa Mustafa
sanda ya fara cewa yana sonta tayi mamaki
sosai, sai daya dinga yi mata kalamai masu dadi
da yaudara sannan ta yarda, har yana cewa
shifa so babu ruwansa da mai kudi da talaka
duk yana shigarsa, da haka ya samu kanta dan
wani lokacin har mamakin kanta take yi data
afka son wanda ta tsana a da can. Tasha yiwa
motocin jama'a faci domin ta tsani gudun da
sukeyi a layin suna kade kaji da akuyoyi wani
lokaci harda mutane, idan anyi magana sai su
biya dan suna da kudi, sai da takai duk kofar
gidan da aka ganta sai an koreta domin idan ta
kullawa mutum duk sanda taga mota a kofar
gidansa koda ta baki ce sai ta koma gida ta
dauka kibiya ta kitso ta sossoka a tayoyin, dan
masu gadin da sun ganta zasu bita da bulala. Ya
janye ta yana dariya saboda yanda ya ga ta
tsorata yace "Bari naje na samo mana abinci da
dan ruwan lemo." Bata ce masa komai ba illa
tafiya da tayi gurin wani abin tana tabawa. Ya
dawo dauke da wani katon faranti mai dauke da
abinci da manyan kwalabe na giya (wa iyazu
biLlahi) ya ajiye bisa tebur din dake falon kana
ya shiga ya kirawo ta, da kyar ya samu ta baro
bandakin tana cewa ya tsaya tana kallo, yace In
dai kina son kallon kullum zan dinga kawo ki."
Dadi ya cikata, da wannan dabarar ya samu ta
futo. Abinci ya mika mata mai dauke da naman
kaza zuku-zuku, ta amshe kuwa da azama ta
fara ci, shima yaja nasa farantin yana ci yana
kallon ta yana dariya ,Can ya dauko kwalbar
Shandy dinsa ya bulbula a kofi ya kafa kai ya
kyankyama ya dire kofin. Ta dubeshi da mamaki
a tsorace tace, "Kai Musty (haka take ce masa)
Giya ce fa? ba zata bugar da kai ba? Naga dan
tasha idan ya sha yayi ta maye har kwata yake
fadawa." Yayi murmushi gami da lumshe
idanuwansa kana ya bude a hankali, "Ai shi
karamar giya yake sha wato burkutu shi ya
sanya yake maye, amman wannan original ce
wato mai kyau din ce, bata sanya maye bari na
zuba miki ki sha kiji." Ta manne kafada da sauri
tana fadin "Kai bana sha tsoro nake ji ni dai."
Yace, "Haba dai tawan don Allah kisha wallahi
ba zaki bugu ba sai dai kiji karfi." Da kyar ya
samu ta sha kofi guda, can kuma sai ta wawuro
kwalbar ta kafa kai ta dinga kyankyama, ta dire
kwalbar bisa tebur din. Ya fashe da dariya gami
da tafa mata yana fadin Wonderful, wato
mamaki ta burge shi, ya zira hannu cikin
aljihunsa ya zaro tabar shedan wato wiwi) ya
kunna ta ya zuka kana ya mika mata, wannan
karon batayi gardama ba ta amshe da azama ta
zuka domin bata cikin hayyacinta, sai dai zuka
daya ta kware ta kama tari, ya tashi da sauri ya
nufe ta yana rike ta har tarin ya lafa.
Amman don ta saba maimakon ta hakura sai ta
kara zuka don abin ita sha'awa ma ya bata, don
ta dade tana sha'awar yanda ake shan taba
musamman idan taga wanda ya kware mai
fesar da hayaki ta baki ta hanci. Dadi ya kama
Musty sai ya kuma zaro wata cikin aljihunsa ya
kunna ta ya hau zuka. Ta fashe da dariya karan
tabar na tsakiyar yatsunta guda biyu shima ya
taya ta suka dinga dariyarsu da zukar tabar
shedan din har suka gama, sannan ne kuma
Abu ta soma tangadi tana zage-zage da yarfe
hannuwa. "Wallahi karya ne! Babu wani sauran
shege da zai raina mana hankali wallahi! Ha-ha-
ha." Ta fashe da dariya. Ya isa inda take da
azama yana fadin "Kwantar da hankalinki
yarinya." Ta fada jikinsa shabar tamkar kayan
wanki, ai kuwa ya sami yanda yake so don haka
ya shiga aiwatar da mugun nufin da zuciyarsa
ke kintsa masa, da fari bai samu matsala ba sai
da abu yayi nisa data fara jin zafi sannan ta
nemi kwace kanta, amman da yake a buge take
hakan bai samu ba har sai da ya cimma burinsa
a kanta (Wa'iyazu billahi). Duk irin iskancin Abu
da gantalinta namiji bai taba aike mata kai tsaye
ba don tana tsoro da gudun kar aji mata ciwo,
ko su Dan Oga da dan tasha da suke siyan
abincinta, basu taba samun hadin kanta haka
kai tsaye ba sai Musty, yau ya samu daga sama
don haka shine mutum na farko da ya fara
sanin Abu diya mace, abunda ba zata taba
mantawa ba a kundin tarihin rayuwarta. A nan
bacci ya dauke su don duk cikin su babu wanda
ke cikin hayyacinsa. Basu ankara ba sai da gari
ya waye tangararau, sannan suka farka a firgice
Abu ta saki kuka da ta tuno abinda ya faru a
daren jiya, shi kuwa Musty kwantar da kansa
yayi ya dinga bata hakuri harda guntun
hawayensa, karshe dai yayi mata alkawarin kaya
da zai sai mata kala-kala har ya samu ya shawo
kanta don ya lura muguwar kwadayayyiya ce, ya
samu ya lallaba ta ya hada mata ruwan dumi
cikin bahon da tayi kauyanci daran jiya ta shige
ciki. Shigar ta bandaki da kuma tuno irin
alkawarin kayan da yace zai siyo mata ne ya
faranta ranta har ma ta daina ganin aibun
abinda suka yi din, don haka da kwarin
gwiwarta ta fito shima ya shiga don ya shirya.
Sanda ta kammala shiryawa ne gabanta kuma
ya soma dafuwa tana tunanin me zata ce da
Sala yanzu don ta Babanta sam bata jinsa,
domin sam ba zai lura bata gidan ba, domin bai
shigowa gidan sai dare ya raba, haka nan daga
gurin Sallar Asuba yake wucewa majalisarsu,
idan ka ganshi a gida da rana to lallai Alhazan
da suke wa a dawo lafiya sun kawo musu zakka
zai zo yaci abincin rana a kudinsa, yakan ce sai
ya ci guminsa wai, sai kuma jarababban yayanta
da take tsoro kada ya gane bata kwana a gida
ba. Ya fito shima ya gama shiryawa, ya dubeta
sanda suke karya kumallo sai ya ga ranta har
lokacin a bace yake, gabansa ya shiga faduwa
domin shi yanzu ma yaji ya fara sonta, don
haka ya kwantar da murya ya kamo hannunta
yana fadi, "Wayyo masoyiya ta, mene ne? Har
yanzu fushin ne? Ko baki huce bane?" Yanda
yake maganar ya kashe mata jiki, ta dinga jin
soyayyarsa da kaunarsa suna ratsa jikinta, ga
wani shaukinsa, ta kwantar da kai tace, "Wallahi
na huce, ina dai tunanin yanda zan sanar da
Sala ne, don ka san ban taba kwana a waje ba."
Ras! Ras! Shima gaban sa ya fadi don sai yanzu
ya tuna ya fito da motar Mominsa gashi ya
kwana, me zai ce mata yanzu? Lallai yasan zai
sha fada a gida, amman sai ya dake domin dai
yanzu matsalar Abu ce a gabansa.
Ya kuma kwantar da murya yana wasa da
hannunta yace, "Kada ki damu za muje nayi
miki siyayya ta ban mamaki wacce zata faranta
ran Sala din, na san ba zata yi fada ba muddin
taga kayan, ga kuma kudi da zan baki, kada ki
damu kinji ko?" Tayi ajiyar zuciya gami da cewa,
"Shi kenan." Wani katon kantin sayar da kaya
suka je. Bayan sun shiga yace ta zabi duk
abinda take so. Lallai kam yaga hauka domin
dai haka ta dinga jidar kaya kala-kala tana
sanyawa cikin dan keken da suke turawa har sai
da taga babu gurin da zata sa ta hakura, dan
wani abun ma sam bata san amfaninsa ba take
dauka, in dai taga kwalin yayi mata kyau to an
gama, domin har abin aski na maza sai da ta
dauka, shi dai binta kawai yake yi da kallo cike
da mamaki, amman bai ce komai ba domin dai
lallaba ta yake yi kada yayi magana yayi laifi. Da
suka isa gurin biyan kudin aka lissafa aka gaya
musu, kudin tsababa ne amman shi ko a jikinshi
domin dai yasan ta cancanci ya sai mata abinda
yafi haka ma. Ita kuwa 'yar jidalin wani kallo
tayi wa mai karbar kudin tana fadin, "Kai malam
dan wannan kayan ne zaka tsugawa wannan
kudin wanda yafi na buhun shinkafa 'yar
gwamnati? Kawai kayi mana ragi idan ba haka
ba mu fasa saya wallahi." Ta karasa maganar
tana tafa hannu da doka cinya. Kunya ta kama
Mustafa dan dai ta nuna cikakkiyar 'yar kauye
ce ita wacce bata taba zuwa irin wannan wajen
ba. Ya dubi mai karbar kudin sanda yake ajiye
masa kudin yace, "Ka yi hakuri daga kauye aka
kawo ta." Cikin harshen turanci yayi maganar
dan haka sam bata ji abinda yace ba. Mai
karbar kudin yace "Babu damuwa." Tana kallo
ya biya kudin don ma kada tayi magana ya
kama hannunta suka fice yana fadin ma'aikatan
su biyo shi da kayan, kamar jira ake su fita sai
wadanda ke gurin suka kama dariya. Tana daga
can ta hango suna mata dariya dan haka ta
kutuntuma wani zagi tana fadin, "Lallai ma
wadancan mutanen 'yan rainin wayo ne, ni
sukewa dariya? Wallahi bari naje nayi
maganinsu." Ta nufi gurin nasu da sauri. Ya riko
hannunta yana fadin, "Haba Zainabu na kada ki
mai da kanki 'yar kauye mana, ki zama
wayayyiya." Tayi kwafa tana dubansa tana huci
tace, "Wallahi sunyi sa'a da yau sun gane
kurensu, ni kawai ka fasa siyan kayan ma ka
bani kudin kawai na rike abuna." Yayi murmushi
yace, "Don Allah kiyi hakuri in dai kudi ne zan
baki." Da haka ya lallaba ta suka saka kayan a
mota suka wuce gida. Bayan sun shiga motar ta
turo baki gaba tana fadin, "Gaskiya wadannan
mugaye ne, dan wannan kayan zasu ce kudinsu
kenan, wallahi zai sayi buhun shinkafa har da
na wake ma, kai zai iya kai mutun Makka da
Madina ma." Dariya ta kwace masa har yana
dukan sitiyari yace, "Kai Zainabu akwai ki da
wauta wallahi, koma dai nawa ne yawan kudin
ai kinfi karfinsu a gurina, fatana dai kawai ki
dinga bani hadin kai, zaki zama tauraruwar
mata gagara-gasa a cikin unguwarku, zaki zama
abin kwatance." Ranta yayi fari kal! Amma bata
ce komai ba har suka isa kofar gidansu ya
tsaida motar. Ta dubeshi bata ce komai ba
amman ya lura da fargaba take yi dan haka
yace, "Kin ga kada ki damu tsaya kiga dabarar
da zamu yi." Ya bude motar ya fito ya kirawo
wani yaro yace maza ya shiga da kayan cikin
gida zai bashi lada, nan da nan yaron ya fara
jidar kayan yana shiga dasu cikin gida, su kuwa
suka cigaba da hirarsu, har saida yaron ya gama
shiga da kayan ya sallame shi. Ya dube ta da
salon da yake kashe mata jiki yace, "Yaya dai
Zainabu ina fatan babu matsala." Bai jira ya ji
abinda zata ce ba ya zura hannu cikin aljihunsa
ya zaro wata sabuwar ambulan mai dauke da
sabbin murtala (N20) ya mika wa Abu yana
fadin, "Ga wannan kyautar faranta mini rai ce,
sai da daddare idan na dawo." Ta fizgi kudin da
sauri kamar wani ne zai kwace, ta bude murfin
motar babu ko sallama ta fada gidansu da
sauri. Ya girgiza kai cike da dariya sannan ya
tuka motarsa ya nufi gidansu amman gabansa
na faduwa dan bai ma san irin karyar da zai
shirya ba.
Abu ta fada gidan babu ko sallama kamar wacce
aka hankada, a tsakar gida ta tadda su Sala da
kannanta suna kallon kayan da aka shigo dasu,
fuskar Sala cike da annuri. Tana shigowa Sala ta
mike da azama ta rungume ta tana fadin "'Yar
albarka, jiya sam banyi bacci ba na dinga darura
da sake-sake ko 'yan yankan kai ne suka yi
gaba da ku, sai yanzu da naga ana shigowa da
kayan nan hankalina ya kwanta nace na san
dare ne yayi muku a inda kuka je kuka ki
dawowa saboda 'yan sa ido, ai gwara da kika
kwana a can din ma dan baki ga yadda
jarababban yayanki ya dinga sintiri ba, sai da
nace masa kina daki kina bacci sannan ya
hakura ya kwanta, shi ya sanya na dinga
fargaba kada ki dawo ki buga kofar yaji ya hau
surutu da wa'azin nashi tamkar dan sarkin
Limamin Makka." (Kuji fa irin wannan Uwa,
wacce ya dace a ce hankalinta ya tashi saboda
kwanan da diyarta tayi a waje amman ko a
jikinta saboda tsabar kwadayi da son duniya,
Allah dai ya shirya). Abu kam da taji abinda Sala
ta fadi sai taji hankalinta ya kwanta, don haka
ta share karya da ta shirya da zata fada, cewar
wai mota ce ta lalace musu a hanya da suka
dawo daga siyo wadannan kayan, sai da gari ya
waye sannan suka sami masu gyara. Sai kawai
ta dauko kudin da ya bata na ambulan tana
fadin "Sala har da kudi fa ya bani." Sala ta
amshe da sauri ta kama kiciniyar farke ambulan
din ta hau kirgawa, Naira dubu biyu cif! Nan fa
suka kama tsalle da murna Sala tana fadin, "Kai
wannan yaro dan arziki ne, dan haka Abu ki rike
shi da kyau, Ubangiji ya sanya ya gama da
duniya lafiya." Haka nan suka dinga murna,
ranar nan dai ko abincin sayarwa Sala bata dora
ba. ga Abu kuwa wannan daurin gindi da ta
samu daga gurin Sala shine ya kaita ga
fandarewar da duk wanda yake da hannu gurin
lalacewar tata sai yayi da-na-sani wata rana,
rana mara alkhairi a kansu gaba daya, da-na-
sani mara amfani. (ALLAH YA KIYASHE MU DA
SHARRIN SON ZUCIYA, WANDA BAHAUSHE YACE
“BACIN ZUCIYA” Ameen)
KANO: 22|12|1993
Rayuwar Abu gaba daya ta sauya daga fari zuwa
baki, idonta ya kuma budewa da harkar banza,
domin wannan dan lokacin ta iya shan tabar
shaidan ta hanci ta baki, sannan kowane dare
kai wata rana ma har da rana Mustafa sai ya zo
ya dauketa sun tafi hotel sun sheke ayarsu.
Amman fa a wannan dan tsakanin sun sami
kudi mai dama a jikinsa, wanda duk iyakacin
shekarun da Abu tayi tana talla basu samu ba,
karatunta na boko kam sai dai muce sam barka,
domin Mustafa mai son ilmi ne dan shi ma dan
boko ne, dan ya kan sanar da ita irin yanda
mutum kan zama idan yayi karatu, yana zama
wani a duniya. Karatun allo kuwa tuni ta watsar,
Malam yayi hargagin a banza dan ba sai ya
ganta ba ma sannan zai doka ba. Sai dai kullum
tayi wanka taci kwalliya tana taku daidai a
unguwa, su Larai duk ta raina su yanzu idan
tayi kwalliya takan zagaya su tana musu yanga
idan sun dawo daga tallah. Baba Abubakar ma
sanda ya isa da fuffukarsa da Malam ya sanar
dashi halin da Abu ke ciki, ya shiga gidan da
fuffukarsa yana yiwa Sala korafi. "Yanzu Sala ba
zaki dinga tsawatarwa da yarinyar nan ba tana
neman ta jawo mana magana a unguwar nan,
kina kallonta....." "Kai Malam rufe min baki!"
Sala ta katse shi, ta dora da cewar "Kai har wani
namijin arziki ne da zaka zo kana mini wata
maganar banza, to tsaya kaji na gaya maka,
wallahi babu shegen da zai takura wa Abula a
garin nan, tun da dai ba Uban wani ya haifar
mini ita ba, kuma Uban wa muka je muka ce ya
taimaka mana da abinda zamu ci? Ko uban
waye ke ciyar damu? don haka babu wanda ya
isa yace mata 'yar iska na kyale shi. Shi kansa
Malam din da yake wannan fuffukar 'ya'yan
nasa ba karatun boko suke suna sheke ayarsu a
can ba? Har makarantar kwana sukayi fa, don ni
Allah ya bani yarinya mai kashin arziki za'a saka
mu a gaba? To wallahi ba'a isa ba, kuma daga
yau idan ka kuma zuwar mini da irin wannan
maganar sai ranka yayi mummunan baci, soko
sobarodo da baka yin maganin sisi, sai yau zaka
hau ni da fada." Duk da tsananin hakuri irin na
Baba Abbakar sai da ransa ya baci da tijarar
Sala yau, ya dubeta a hasale sanda ta diga aya
yana fadin "Au dan na gaya miki gaskiya shine
kike mini wannan tijarar? Wato dan kinga bani
da shi ko? Don da ina da shi baki isa kiyi mini
irin wannan rainin hankalin ba, dan haka ki
shiga taitayinki, idan ba haka ba ranki zai yi
mummunan baci wallahi Salamatu." "Ahayye
ayyururuuuiii!" Ta rangada guda da tafa hannu
sannan tace, "Lallai yau mazantakar za'a nuna
mini kenan ko? To tsaya kaji Abbakar, wallahi
baka isa ba, ka yi kadan, idan kuma kayi wasa a
cikin daren nan sai mu baiwa hammata iska." Ta
kama cin damara da wani zani dake yashe a
gefenta tana wani girgije-girgije da buga kafa.
(Tambaya: wai shin akan samu masu irin halin
Sala a wannan Zamanin kuwa????)
Ya fi kowa sanin halin Sala, don a shekarun
baya gidansu kamar silima yake gurin kallon
dambensu, sai dai shi da jarabar ta ishe shi ya
sallama mata, don haka yanzu ma ba zai iya
biye mata ba, don haka yabi lafiyar gadonsa na
karfe yana fadin, "Kanki ake ji, wai mahaukaci
ya fada rijiya, da girmana da 'ya'yana aga muna
raba hali a titi, ki yi da wani ba dai dani ba." Ya
runtse idonsa duk da ba bacci yake ba. Ta ja
dogon tsaki gami da fadin, "Oho dai! Kai dai
kawai kace ka ji tsoro, wallahi da ka tsaya da ka
gane kurenka yau, munafuki kawai wanda ake
gulmar 'ya'yansa da shi maimakon ya hana sai
maya kara tunzira abin." Ta haye gadonta na
katako tana cigaba da mita, "Ba ku da aiki sai
zaman gindin bishiya kuna gulma, sam ba a iya
juya kwandala ta koma Naira, ba don Allah ya
bani mata masu daukar min tallah ba ai da
nasha haushi, ka dubi wannan yaron da ya
kwaso matacciyar zuciya irin taka, idan don taku
ne sai dai yunwa ta kashe mu." Haka nan take
ta bala'in ita kadai, shi dai bai kula ta ba har
bacci yayi awon gaba dashi don dare ya tsala,
domin bai shigowa gidan da wuri sai dare yayi
sosai. Duk yaran nasu suna jiyo abinda suke yi
amman basa fahimtar maganar da suke yi sai
dai hayaniya kawai da suke ji, Sadiku yafi kowa
tashin hankali don tun yana yaro yake takaicin
abinda iyayan nasa keyi don ma abokinsa Zaid
na bashi baki. Sai dai addu'a al'amarin nasu,
lallai ba a sakewa tuwo suna, haka nan ba'a
sauya iyaye, shi kam da tuni ya sauya da ace
suyo su ake yi, domin kowanne da tabonsa. Sala
masifaffiya mai shegen son kudi da abun duniya
da son 'ya'ya, yayin da Baba Abbakar ya
kasance mai matacciyar zuciya da gulma da
munafurci, don sana'arsa kenan kullum yana
gindin dirimi shi da abokanan sana'ar ta shi
(magulmata) suna ta sana'ar tasu, bai saida
komai balle ya sanya ran zai samu ya kaiwa
iyalansa, 'yar sana'ar tasa ta saida shayi ya
watsar tuni zuciya ta mutu, sai dai gulma a
gindin dirimi. Don haka a cikinsu akan rasa na
zaba, shi dai yana godewa Allah da ya sanya bai
dauko halin ko daya ba a cikinsu, amman dai
yana takaicin irin rayuwar da 'yan uwansa da
iyayensa ke yi, don haka ranar da bakin ciki da
takaici ya kwana, amman yayi alkawarin zai yi
maganin abun da kansa, koda kuwa Sala zata
tsine masa ne Allah dai yaga niyyarsa.
*******************
Karfe takwas na dare Mustafa ya tsaida motarsa
a kofar gidansu Abu, ya tura yaro ya kira masa
ita, kusan tare suka futo da yaron taci uwar
kwalliya da atamfa mai barewa, tayi daurin
Hindu Rufa'i, ana wani tauna cingam wai ita
dole ga 'yar gayu, leben nan ya sha jambaki a
sama baki da kasa, an ja jagira mai cin birki a
gefen kunne. Ta hasken wutar lantarki ya hango
ta kamar ya yi dariya, don kwalliyar tata kamar
'yar kauye tayi mata, sai ya dake don kada ya
tsokanowa kansa don yasa halin tsiwar Abu. Ta
isa ta bude gaban motar aka zauna irin a
karkacen nan ana wani fari da ido wai ita a dole
ga 'yar gayu. Ya kamo hannunta yana dariya
kasa-kasa yace, "Kai gimbiya, kin ga yanda kika
yi wani kyau kuwa? Irin wannan kwalliya ai
sai....." Finciko ta da aka yi ne ya sanya shi yin
shiru cike da mamaki da razana. Sadiku ne ya
finciko ta ya watsar a tsakiyar titi, sannan ya
kalli Mustafa dake kallon sa sororo cike da
mamaki yace, "Kai dan iska mara mutunci
wallahi daga yau na kuma ganinka a kofar gidan
nan sai nayi maka rashin mutunci, don haka ka
ja tsummar rayuwarka ka bar kofar gidan nan
tun ba sanya yara sun maka atile ba." Ya juya
kan Abu wacce ta mike tana goge jikinta wai ita
nan ya bata mata kwalliya, sai murguda baki
take yi tana kun-kuni wanda ya san zaginsa
kawai take yi, ai kuwa yayi kanta ya zabga mata
mari sannan ya sanya kafa ya haure ta. Ta zube
a kasa gami da rike cikinta ta fasa ihu gami da
fadin, "Wayyo Sala na shiga uku!" Ya kuma kai
mata duka amman ta yunkura ta mike ta kwasa
da gudu ya rufa mata baya da bel din
wandonsa da ya zare. A soro suka ci karo da
Sala wacce ta futo a gigice saboda jiyo ihun 'yar
lelenta da tayi. Ai kuwa Abu na ganin Sala din ta
zube a soron tana fadin, "Wayyo Sala na shiga
uku zai kashe ni cikina Sala, zan mutu na shiga
uku (Kuji Makirci). Sala tace "Na shiga uku, wane
shegen ne ya taba mini ke Abula?...." Shigowar
Sadiku yana huci ne ya sanya ta gano abinda ya
faru. Sala ta zaro ido waje cike da bacin rai tana
fadin, "Lallai ka cika mara mutunci, yarinyar
tana zancen ta kawai za ka kama dukanta, to
me tayi maka, mugu?" "Haba Sala wane irin
zance? Iskanci dai kawai. Waye a unguwar nan
bai san abinda yarinyar nan takeyi ba? Haka
kawai ta sanya ana zaginmu da raina mana
hankali, wallahi na kuma ganinta da shegen
mutumin nan sai na karya ta." Sala ta kuma yi
masa kallon banza tana fadin, "Sannu Abbakar
Ubanta da yayi cikinta, to tsaya kaji na gaya
maka, kayi kadan kai uban da ya haife ka ma
yayi kadan balle kai karan kada miya, haka
kawai ka takurawa yarinya ka hana ta rawar
gaban hantsi? Kai ne ka haifar mini ita ko kaine
ka halicceta, eye? Bala'in naka ya wuce na baki
har ka fara kai hannu kana dukan ta? Za ka zo
kana gaya min ana gulmarku a unguwa, ina
ruwana da wasu 'yan unguwa 'yan saka ido
sana'ar banza ana ruwa suna kirgawa, su bari
su koma sata yafi. To bari inyi maka mai gaba
daya ta mahaukata tunda naga abun naka yana
neman ya wuce gona da iri,Wallahi daga yau
idan ka kuma taba mini yarinyar nan ko ka
kuma shiga rayuwarta da sunan fada ban yafe
maka nonona da ka sha ba!" Sadiku ya dafe kai
cike da tashin hankali yana fadin, "Innalillahi wa
inna ilaihi raji'un, Sala mai yasa haka? Yanzu
dan ina gaya muku gaskiya dan gudun kada ku
fada cikin halaka ya sanya zaki tsine
mini....."gaskiya ko kuma munafurci da sanya
ido? Kai waye ya shiga rayuwarka? Kullum kana
yawo da kodadden wando jins da rigar gwanjo
kamar tsohon matsiyacin bature." Ya girgiza kai
cike da takaici yace, "Shike nan Sala Insha Allahu
kome Abu zata yi a unguwar nan da gidan nan
na daina yi mata magana, taje in dai duniya ce
ta ishe ta riga da wando, za ta koya mata
hankali." "Ka ga malam kada kayi mata baki,
koda yake ai ba kai ka haife taba balle bakin ka
ya bita ba, wadanda ma suka fika sunyi sun
gama babu abunda ya same ta sai ma cigaba
balle kai, don kurwar Abu kur! Maye yaci kansa."
Sadiku bai kuma cewa komai ba ya juya ya fice
daga gidan, don sai yaji gaba daya gidan ma ya
ishe shi. Sala ta kama Abu dake zaune dirshan
tana kallonsu don taji yanda Sala ke afke masa
ta wanke mata zuciya, Sala din tana fadin "Tashi
muje gida ki kwanta kinji? Koda yake Alhaji
Mustafan yana can yana jiranki. Goge idonki kije
ku cigaba da zancenku, ki gaya masa ya kwantar
da hankalinsa kamar tsumma a randa, nayi
masa maganin dan saka idon can, ba ku da
sauran mai matsa muku yanzu, muje na raka ki
ko yana kofar gida a labe bai tafi ba." Ta daga
ta tana goge mata idon ta wanda babu ko
alamun kwalla ko guda daya, daman kukan nata
na sharri ne bawai na zafin duka ba. Suka nufi
kofar gidan tare, sai dai babu motar Mustafa
babu alamarta sai dai filin wajen kawai, dan
yana ganin sun yi cikin gida ya ja motarsa yayi
gaba don kada Sadiku yazo yayi masa tijara a
cikin jama'a har asirinsa ya tonu, don haka ya ja
motarsa ya gudu. Ai kuwa suna ganin baya nan
ran Sala ya kuma baci suka koma cikin gida tana
ta masifa da bala'i, wanda har makota suna
jiyota, ita kanta Abun ma taji takaicin tafiyar
Mustafa dan ta saka ran ya bata wasu kudi yau
na ankon bikin Larai, dan haka dai sun dauki
laifi gaba daya sun dora akan Sadiku wanda ya
bar musu unguwar ma gaba daya. A daran nan
Sala batayi baccin kirki ba sai bala'i da masifa
kawai take yi har Baba Abbakar ya dawo tana
yi, shi dai yayi mata banza bai kulata ba dan dai
yasan 'yan bala'in ne suka motsa, idan kuma
suka motsa babu wanda take saurarawa dan
haka shi dai ya lallaba ya haye gadonsa na
karfe yayi lamo kamar mai yin bacci amman a
zuciyarsa Allah wadarai yake yi da halin Sala,
har ya tuno wata mata data wuce ta gabansi
dazu suna majalisa wani yayi subutar baki a
cikinsu yace "Ka ga wannan matar idan ta fara
bala'i sai ta kwana tana yi." Ashe matar nan ta
jiyo shi don haka ta dawo ta tsaya a kansu gami
da rike kugu tana kallonsu shekeke tace, "Mai
kuka ce, eye?" Wanda ya fadi maganar ya yi
murmushi irin na matsorata yace, "A'a Hajiya ai
yabonki muka yi nace duk unguwar nan babu
irinki a mutunci, ba irin babata ba 'yar bala'i,
idan ta kama masifa sai ta kwana tana yi." Jin
abunda yace ne ya sanya tace, "Allah ya so ka
wallahi, da yau na lakada maka duka a unguwar
nan na ga mai kwatarka, da sai kaga karshen
masifa ta." Sai da tayi nisa sannan suka fashe
da dariya suna zolayarsa sai yace, "Ku ai gwara
da na yi haka, dan wallahi yanda na ga tana
wata girgiza bata ki mu casu a tsakiyar titin nan
ba, ni kuwa ina zan iya da ita kana ganin mace
kamar bishiyar kuka? Ai irin wadannan sai da
lallashi." Lallai kam haka ne sai yanzu ya gano
gaskiyar Malam Sabo, masifaffu ba'a iya musu
sai dai a bisu da lallashi ko kuma ayi musu
banza kawai. Shi dai har bacci ya dauke shi bai
san sanda Sala ta gama masifarta ba.
Da safe ma da bala'in Sala ta karya dan Sadiku
ko koko da kosan da ake bashi ranar ba'a bashi
ba sam, shima bai nema ba ya tafi makarantar
sa da yake yana karatun Low ne a B.U.K,
karatun da yake matukar shan wahala a kansa
dan babu wanda ke taimaka masa a iyayansa
sai Malam ne ma yake taimaka masa wani lokaci
da kuma rufin asirin Allah, dan ya iya zane idan
ya samu ya kan yi, ko kuma idan bashi da lakca
ya tsaya shagon wani abokinsa ya taya shi aski a
bashi wani abu, da kuma tallafi na karatu da
suke samu (Scholarship), haka nan yayi
ficewarsa da yunwarsa gashi banda kudin mota
bashi da ko kwandala. Ita kuwa Abu 'yar mulkin
ko shirin makaranta bata yi ba, don kwanciyar
ta ma tayi tace kanta ciwo yake yi, yinin ranar a
daddafe tayi shi dan takaici, ita kuwa Sala sai
kawo mata kayan dadi takeyi kala-kala wai dan
ta kwantar mata da hankali. Yamma na
karatowa aka yi wanka aka ci uwar kwalliya ta
jiran Mustafa aka kame akan kujera, duk yaron
da ya shigo gidan sai taji kamar ita zai ce ana
kira, gashi ita yanzu ta daina kula samari dan a
ganinta ita kalar manya ce kamar yanda
Mustafa ke gaya mata. Sai dai me? Har kusan
karfe goma na dare babu Mustafa babu alamar
sa, har gajiya tayi da lekawa amman babu shi
babu alamunsa. Daga karshe dai ta sanyawa
Sala kuka tana fadin "Sala ina ga fa Mustafa
fushi yayi da wulakancin da Sadiku ya yi masa
jiya, dan baki ji maganganun da ya dinga gaya
masa ba, shi ya sanya ya yi fushi ya ki zuwa."
Sala tace, "Bari ke dai Abula ai wannan yaron ya
goga mana bala'i, yanzu idan yaron nan ya
daina zuwa ina zamu sanya kanmu? Ki duba ki
ga irin kudin da yake bamu a sama ba tare da
mun sha wahala ba, yanzu idan ya daina zuwa
sai dai mu koma abincinmu kenan." "Abinci
Sala? Cabdijam!! Wallahi Sala na fi karfin tallar
abinci yanzu, dube ni fa ki gani? Ni samari ma
tsami na daina harka da su balle wani tallah,
idan mutum bashi da kudi ko kallo ma bai ishe
ni ba." Sala tayi dariya tana fadin, "Ho Abulata,
kinyi gaskiya wallahi kin fi karfin talla yanzu,
tunda Allah ya baki abun neman kudi ai shike
nan. Ki sha kuruminki na ma sani zai dawo,
watakila wani abin ne ya tsre shi, dan na san ba
kowa ne zai sami kamarki ya yasar ba... Ke
kamar na ji karar mota ma." Sukayi shiru, can
Sala tace, "Allah karar mota ce." Suka bazama
suka yi kofar gida har suna karo da juna, sai dai
me? Kurar mota kawai suka gani ta wuce tuni,
haka nan suka dawo suna zaman tsammanin
warabbuka, Malam ya ki noma yana jiran
sadaka. Sai dai har suka fara gyangyadi babu
Mustafa babu alamarsa, haka nan suka hakura
kowacce ta kama makwancinta cike da takaici.
Abu kamar wasa karamar magana ta zama
babba inji Garba Sufa, dan yau kwanaki shida
kenan amman babu Mustafa babu alamarsa,
uwa da 'ya sun shiga tashin hankali, tun suna
tunanin zai zo har sun hakura sun fidda ransu
da zuwan nasa, shi kuwa Sadiku da har yau bai
daina shan bala'in Sala ba murna yake yi don
ko babu komai ya kori Mustafa, lallai barazanar
da ya yi masa tayi tasiri a kansa. Daran daya
cika kwana bakwai suka yanke shawarar zuwa
gidansu dan su bashi hakuri, domin dai kudi
sun fara musu karanci don ma su Karimatu
suna daukar abinci da funkaso, don ita macece
mai jarababban neman kudi dan tun tana
budurwa bata iya zama babu sana'a ba.
Washegari da yamma Abu taci kwalliyar ta duk
da kanta da yake mata ciwo, ana taku dai-dai
kamar ba zata taka kasa ba, aka nufi gidan su
Mustafa wanda yake can gangaren layinsu.
Sanda ta isa ta tsaya tana kallon gurin da yake
zama bisa farar kujera karkashin bishiyar
Umbrella, lokuta da dama da jarida a hannunsa,
sai dai yanzu babu ko alamarsa ko kujerar tasa
ma babu a gurin. Katuwar koface wacce ke
garkame, bata mantawa da can suna zuwa
tsokanar kare, idan ya biyosu su zunduma da
gudu ko kuma suyi ta jifansa, wata rana sun
taba fasa masa kai mai gadin ya bi su da gudu
ya kama daya a cikinsu ya zane, shine fa suka
kulla masa, ai kuwa rannan maigidan ya futo da
motar zai tafi sai kuma yayi mantuwa ya koma
cikin gidan, su kuwa daman suna fakonsa dan
haka suka dauko wani abu mai tsini suka soka a
tayar gaba ta sace, ai kuwa sanda mai gidan ya
futo ya gani ya dinga yiwa maigadin fada daga
karshe dai sai wata ya hau ya bar wannan a
nan, bayan maigidan ya tafi suka dinga yiwa
maigadin ihu da tsokanarsa, ai kuwa ya bisu da
gudu sai dai kasa kama kowa yayi dan 'yar
zilliya suka dinga yi masa, haka nan ya gaji ya
koma yana nishi, don haka yanzu take fargaba
kada ya gane ta. Ta daure dai ta kwankwasa
kofar, ya bude ta 'yar karamar taga ya leko dan
yaga wanda ke magana, yana ganin ita ce ya
zaro ido waje yace, "Me kike nema a anan,
eye?" Yana maganar fuskar nan tasa a murtike.
Ta rike kugu da murguda baki a hankali tace,
"Banza dan gadi, kai ba don ta kama ba ka isa a
wani tsaya ana magana da kai, dalla ka bude da
wani bakinka duk gansa-kuka." Ya kuma hasala
dan dai bai ji abinda tace ba amman da alama
zaginsa take yi, dan haka ya bude ya futo da
wata zungureriyar bulalarsa yana muzurai. Ko a
jikinta bata ji ko dar ba don ba dabi'ar ta bace
tsoro, ta kuma ayyana a ranta wannan tsohon
ya tabata zai gane kurensa dan wallahi sai ta yi
masa sharri, ta kuma gyara tsayuwa. Ya hasala
matuka dan haka da zafin rai ya fara magana,
"Ke yarinya bana son rashin mutunci, don a
haife kin san na haife ki ko? Don haka ki bar
gurin nan tun ban zane ki ba." Ta yi masa kallon
baka isa ba sannan tace, "Ka ga Malam ni ba
wani abu ya kawo ni ba Mustafa nazo nema,
idan yana ciki kace masa Abu tana magana da
shi, ka daina mini surutu kana feshe ni da
yawu." Mamaki ya bayyana a kan fuskarsa, mai
ya hada Mustafa nutsatstsen yaro da wannan
hatsabibiyar yarinyar? Amman bai san alakarsu
ba, dan haka ya dan saki fuska ya ce, "Mustafa
fa kika ce?"
Ta motsa fuska tace, "Ko kana mamaki ne?" A
ransa yace, "Kai wannan yarinyar 'yar bala'i ce,
gwara ya lallaba ta su rabu lafiya. Don haka ya
kuma gyara tsayuwa ya fara kora mata bayani,
"Ai Alhaji Mustafa ya koma don daman hutu
yazo da kuma ciwon Babansa da ya tashi na
hanta, dan a can kasar waje yake karatunsa,
yau kwanansa shida da komawa, kuma ba shi
da ranar dawowa dan tun da ya tafi shekara
uku sai wannan karon ya dawo." Ta dafe kirji
cike da tashin hankali ta ce, "Yanzu ya tafi wata
kasar babu daman na ganshi dan Allah?" "Af! Ai
kuma sai kiyi, mutumin da aka ce miki bai kasar
gaba daya ma, kinga komawa ta ma." Ya koma
ya garkame kofar tasa. Kafarta ta yi mata nauyi
ta kasa dagawa, yanzu yaya zata yi da
rayuwarta? Don Mustafa ya koyar da ita darussa
masu wuyar mantawa, yanzu waye zai dinga
bata shandy tana sha? Waye zai dinga bata
tabar shaidan tana sha? Waye zai dinga kai ta
hotel taci kayan dadi ta hau gado mai laushi?,
waye zai dinga bata kudi mai yawa irin na
Mustafa? amsar ita ce babu, babu wanda zai
maye mata gurbin Mustafa ko ta ina. Da kyar
take iya gane hanyar da take sanya kafarta duk
hankalinta a tashe yake, don ma Allah ya
taimake ta ba wata tafiya bace mai nisa, da
kyar ta samu ta lallaba ta isa gidan dan zazzabi
da ciwon kai sun hadu sunyi mata taron dangi.
Bisa wata tabarma da ta tadda a tsakar gidan ta
zube, wacce Sala ta shimfida ta shiga kicin dora
sanwar dare, ta zauna idonta na zubar da
hawaye, azaba biyu take ji a jikinta gata rabuwa
da Mustafa ga kuma ta ciwon da ke addabarta,
ta zame ta kwanta ta kama juyi da malailaikuwa
a tsakar gidan tana kuka mai ciwo da taba rai.
Sala ta futo daga kicin dan ta dan huta, sai dai
mai zata gani? Abu ce 'yar lelenta tana birgima
a tsakar gida tana kuka dafe da kanta. Ta isa
gurin da sauri tana tambayar ta, "Abula diyar
kirki yaya aka yi? Bai hakura ba ne Mustafan?
Idan bai hakura ba ni sai naje da kaina na bashi
hakuri. Kwantar da hankalinki, banda abun dan
yau ma ai saurin fushi ba nasa bane ba, idan
yayi mana haka ai yayi mana tsiya, bari naje da
kaina na bashi hakuri ina ne gidan nasu?" Ta
mike tana neman gyalen da za ta yafa. Abu da
taga da gaske take yi ta ruko hannunta, ta juya
tana kallon ta amman ta gaza cewa komai, cikin
kuka Abun tace, "Kada ma kije Sala, ko kinje ba
zaki same shi ba don baya nan wai daman a
kasar waje yake karatu hutu ya zo, yanzu ya
koma yau kwanansa shida da komawa. Wayyo
Sala cikina zan mutu." Ta karasa maganar da
kuka tana rike ciki. Sala ta rude sosai ta ruko
hannun diyar tata tana mata sannu gami da
lallashinta tana fadin, "Kiyi hakuri Abula na san
zai dawo ya nemeki komai dadewa, domin ke
din mace ce da duk namijin da ya ganki sai ya
rude balle shi Mustafa da yake sonki, share
hawayenki ki daina kuka kinji Abula ta? Na san
zai dawo komai dadewa." "Ni fa cikina ne yake
mini ciwo. Wayyo Sala ciki....." Sai ga amai kyah!
kyah! kyah! Tana kwararawa. Sala ta kuma
rudewa ta mike da azama tana neman fo don
taimakawa diyar tata, tun tana yin amai na
abinci da ruwa har ta koma na majina take yi,
da kyar suka samu aman ya fada. Sala ta
taimaka mata ta raka ta bandaki dan ta wanke
jikinta, ita kuma ta dawo dan ta gyara gurin
zuciyar ta na cike da tsananin tausayin diyar
tata, dan ta gano ta fada kangin soyayyar
Mustafa.
Haka nan ta karasa yammacin a kwance ga juwa
da tashin zuciya dake damunta, daga karshe dai
Sala tace bari ta je gurin dan Oga ta karbo mata
magani ko aman ya tsaya. Tana isa dan oga ya
kama wage baki yana fadin, "A'a mana ne?
Sannu ka da zuwa. Ina Habu ne dan bana ganin
shi yanzu?." Sala tace, "Abu tana nan, yanzu ma
ita na zo na karbawa magani bata da lafiya." Ya
kuma wage baki yana fadin, "Habu babu lafiya?
Bari a bata magani mama, ka bari kudinka ma."
Ya kama hada magunguna bayan ya kammala
yayi mata bayanin yanda za'a sha kowanne, ta
amsa da azama ta nufi gida. Sanda ta sha
maganin kamar gaske dan aman ya tsaya har ta
sami bacci, sai dai wajen karfe goma sha daya
aman ya kuma dawowa dan shi ma ya tashe ta
daga bacci, sai da ta amayar da duk maganin
da ta sha samman ta sami sa'ida, sannan ta
sami wani bacci ya dauke ta. Da safe kuwa sai ta
tashi jikin babu laifi dan aman ya tsaya, sai dai
jikin nata babu kwari daga kwanciya sai
kwanciya, har ta samu ta tsakuri abinci kadan ta
ci, Sala sai ta kama murna jiki yayi kyau. Sai dai
yamma tana yi amai ya dawo sabo, har dare
yayi ana abu daya, sai da aka kuma samo wani
maganin. Sala kam bala'i ta hau yi tana fadin,
"A'a na gamo lagon abin ma, wato marasa
mutuncin nan ne ke neman kama mini diya
(mayu), lallai kam zan yi maganinsu, don ga
alama nan ciwo baya tashi sai almuru yayi,
wallahi duk shegiyar matar da na san mayyace a
unguwar nan sai naci ubanta, za su san wannan
karon sun ciwo mai zafi, dan ba zan yadda da
rainin hankali ba, dan sun ga diyata ta taso bul-
bul da ita gwanin sha'awa ga farin jini shine
zasu lashe mini ita? To wallahi kurwarta kur! Kai
bari ku gani ma ba'a bori da sanyin jiki, ai mune
maganin mayu." Ta debo garwashi ta gumbuda
garin tazargade da wani maganin mayu, nan fa
gida ya tirnike da hayaki sai tari suke yi. Sannan
ta kuma jika tazargadan a cikin ruwa ta mikawa
Abun tana fadin, "Amshi nan shanye, mayu za
su ci kan ubansu yanzu a gidan nan." Cikin ikon
Allah har ta gama shanyewa ba tayi amai ba
don da duk abinda ya shiga cikinta sai ta
amayar da shi, amman wannan ya zauna. Sala
tayi dariya tana fadin, "Ahaf ai na sani, mu za'a
gayawa zancen banza? mu maita ma bamu so yi
bane, abinda ake saidawa a kasuwa." Haka nan
ta dinga mita da balokoko a tsakar gidan kamar
wadan da take zargin suna nan a tsakar gidan.
Cikin kwana biyu sai jikin yayi kyau, domin in
dai ta sha ruwa da tazargade a ciki bata yin
aman, hankalin Sala ya fara kwanciya da ita
kanta Abun, sai abu daya da ya dawo musu da
hannun agogo baya bai wuce dawowar aman
ba. Tana tsaka da bacci aman ya taso mata, tayi
kokari ta fita amman ina ya riga ya yunkuro dan
haka ta zauna a nan ta dinga kelayawa.
Kanwarta Karimatu ce ta mike ta yi dakin Sala
da gudu tana gaya mata, ai kuwa a rude Sala
din ta taho, ta rike Abun kam-kam tana mata
sannu har dai suka samu aman ya lafa ta dan
sami bacci. Sala ta koma daki ta kwanta, sai dai
ba'a yi awa guda ba Karimatu ta kuma komawa
da gudu taba buga kofar dakin Sala gami da
fadin aman ya dawo.
Sala ta tashi a rude, sai ta kalli Baba Abbakar
dake ta shararar bacci ta kuma hasala, ta
daddage iyakacin karfinta ta maka masa duka,
ya tashi a gigice yana ta soshe-soshe, ta galla
masa harara tana fadin, "Ka saki baki kana ta
sharara bacci bayan ka san Abula bata da lafiya,
ko sisi baka taba bayarwa kace a sai mata
magani ba sannan sannu ma ta gagara? To ka
zo muje ka ga jikin nata kada ta mutu." Ta shiga
gaba yana binta a baya zugui-zugui kamar
makaho da dan jagora, ai kuwa yanda suka ga
Abu hankalinsu ya tashi dan ta galabaita sosai.
Sala ta rude matuka ta saki kuka tana fadin,
"Wayyo Abula! Dan Allah kada ki mutu ki barni,
na shiga uku ni Salamatu." Baba Abbakar ne ya
dinga lallabata da kwantar mata da hankali,
zuwa gurin asuba kuma sai Abu ta fara suma,
dan haka gari yana dan kara haske aka samo
mota suka kwashe ta sai asibitin murtala
(Murtala general hospital). Sun yi sa'a suna
zuwa aka karbe ta, nan da nan aka rubuta musu
abinda zasu siyo, Baba Abbakar babu ko sisi a
jikinsa don haka ya zame ya gudu, Sala ce ta
kwance jakarta ta dauko kudin ta bada, nan da
nan aka daura mata karin ruwa, sai da babbar
leda ta shiga jikinta sannan ta fara dawowa
hayyacinta. Cikin ikon Allah kafin azahar ta
dawo hayyacinta, da taimakon Allah da
taimakon karin ruwan da aka yi mata. Sai
washegari da likita ya dawo yaga jikin ya dan
fara kyau ya rubuta mata gwaje-gwaje bayan
'yan tambayoyi da yayi mata, gwaji kala uku aka
rubuta mata, akwai na taifot da na maleriya sai
kuma wanda yake tantama a kansa dan ance
masa budurwa ce, amman dai ya zama dole a yi
din don ya tabbatar da binciken sa gwajin masu
ciki. Sala ce ta taimaka mata suka nufi dakin
gwaje-gwajen aka auna komai aka basu
sakamako cikin ambulan, suka ce ta kaiwa
likitan da ya turo su, suka koma dakin da aka
kwantar dasu suna jiran zuwan likitan. Sai da ya
gama ganin marasa lafiya sannan ya dawo dakin
nasu, ya fara bin gadaje yana dubawa har ya zo
kan na Abu. Ya gyara gilashin din idonsa gami
da kara tambayarta jikin nata, Sala ce ta amsa
sannan ta bashi sakamakon dake cikin ambulan.
Ya amsa ya farke yana dubawa, ya kuma gyara
gilashin din dake idonsa yana kallon Abu,
sannan yace da Sala, "Baba kika ce budurwa ce
ko?" "Fil ma kuwa a ledar ta. Don ko kudin toshi
ba'a kawo ba balle a sanya rana balle kuma ta
kai ga biki ba." Sala ta bashi amsa da sauri. Ya
girgiza ka ya ce, "Haka ne." Yace, "Baba ku
same ni a ofis dina yanzu zan baku sallama dan
ta warware." Bai jira jin amsar su ba ya wuce
gado na gaba. Sun dade tsugunne a kofar ofis
din nasa da kayansu a zube suna jiransa, har ya
zo ya bude ya shiga suka rufa masa baya, ya
nuna musu gurin zama sannan ya dauki wata
takarda ya fara rubuce-rubuce a cikinta
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Idan zuciya ta gyaru 1-03
Posted by ANaM Dorayi on 07:50 PM, 28-Jan-16
Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU
_________________ Na
________Fauziyya D Sulaiman_____
Bayan ya gama ya daga kansa yana kara kallon
Abu wacce tayi wuki-wuki, ya ma rasa ta inda
zai fara, can dai ya daure yace, "Baba wannan
diyarki ce?" Batayi mamakin tambayar ba don
jama'a da dama kanyi mamaki idan aka ga
'ya'yanta wanda sam basa kama da ita, dan
kamar mahaifinsu suke yowa wanda idan ka
gansu tamkar Larabawa suke, ita kuma gata nan
bakikkirin, don haka baki a hangame tace, "Ka
ga bamuyi kama ba ko? Ai mutane da dama na
mamakin ace 'ya'yana ne don idan suna yara
suna kuka a gidan biki har cewa ake na
maidawa uwarsu sai anga na ciro mama ina
basu tukunna ake yarda nawa ne, ai diyata ce ta
biyu. Ha ha ha" Ta saki dariya daga karshe.
Ya girgiza kai cike da takaici ya ce, "A yanda na
gani a jikin kati yanzu shekararta goma sha
hudu ko?" Ta kuma yin dariya tana fadin, "Haka
ne likita ka ganta gaba-gaba haka nan take da
girman jiki babu shekaru, ka ganta kamar 'yar
shekara ashirin ko? Girman jikin ne kawai
musamman yanzu da take cin kayan dadi sai
tayi wani fari da kiba kamar diyar wani
basarake, bul-bul da ita gwanin sha'awa."
Likitan yayi murmushi don ya gano inda Abu ta
samu matsala, wato rashin uwa tagari ne, dan
haka babu wani boye-boye ya ce, "Hajiya ke da
yarinyarki ta sauya kin tambayeta dalilin da ya
sanya ta sauya?." "Haba dai likita wace irin
tambaya ai jin dadi shi ke sanya mutum ya
sauya, ka ga dai yarinyar nan kullum da sai ta
dauki talla safe da dare, yanzu kuwa ta samu
mai ba ta kudin sai dai taci ta kwanta sai dai
makaranta." Ya girgiza kai cike da takaici ya ce,
"Haka ne, to tsaya na gaya miki diyarki tana
dauke da juna biyu, ma'ana ciki, dan haka
wannan sauyawar da tayi ba wai ta jin dadi
bace illah ta ciki....." Sala ta mike da tashin
hankali ta dafe kirji cikin karaji tana fadin, "Me?
Likita cika fa kace? Lallai baka san aikin ka ba,
dubi Abulan duka nawa take da zata yi ciki? Kai
dai ka kara dubawa ka gani ko katin wata ka
dauko." Ita ma Abu dake zaune tana jin caftar
da Likita da Sala ta dafe kirkji da sauri tana
fadin, "Na shiga uku ciki ne dani." Sai ta saki
kuka. Sala ma ta sanya kuka tana fadin, "An ya
likita ba karya ka fadi ba? Ko kuma aljanu ne
suka hura mata ciki ka ga kamar ciki ne da ita,
dan yaushe ma ta fara al'ada duka, ka dai sake
dubawa." Shi dai rubutunsa kawai yake yi akan
wata takarda, sai da ya gama sannan ya daga
kansa ya mika mata kayin yana fadin, "Ko ki
yarda ko kada ki yarda 'yarki tana da ciki, dan
haka idan baki yarda ba sai kije wani asibitin a
duba miki ita, na gama daku sai ku tafi, a gaba
a dinga kula da tarbiyyar yara." Ta kuma
fashewa da kuka tana fadin, "Don Allah likita ka
taimake mu, yanzu yaya zamu yi da wannan
abin kunyar? Na shiga uku ni Salame....." "Kinga
Hajiya ku fita can kuyi kukanku don na tashi zan
kulle ofis dina." Ya mike yana hada kayansa. Ta
tsagaita kukan tana fadin, "Likita yanzu babu
wani taimako da zaka yi mana?" "Kinga Baba
babu wani abu da zanyi bayan addu'a Allah ya
rabata da shi lafiya, kuje waje zan kulle ofis dina
nace." Yana magana yana kallon agogonsa. Haka
nan suka fice daga Ofis din Abu tana kuka Sala
kuma duk ta gigice, suka yi zaune turus a gaban
kayansu kowacce tana kuka, har yazo ya wuce
su bayan ya kulle Ofis din nasa. Can dai Sala ta
daure ta ce, "Wai ni Abula garin yaya kika yarda
har yayi miki ciki ne ma? Ai da kince yayi wasu
'yan dabarun da bazaki samu ciki ba" (Fauza
tace, kuji fa jama'a bata bakin ciki da lalata
mata diyar da aka yi sai ra samun cikin, shima
don tana jin kunyar idon jama'a ne, kai tir da
irin wadannan iyayen). Abu ta cuno baki gaba
tana wani kumbure-kumbure tace, "To nima na
san zan sami cikin ne Sala? gashi yanzu ya gudu
ya barni da ciki. Kuma na san 'yan gidansu ba
zasu yadda shi yayi ba, na shiga uku yaya zanyi
da gorin 'yan unguwarmu? Ga shi dama sun
tsane ni, yanzu idan suka ji ina da ciki zasu
dinga tsokana ta."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Sala ta fyace hanci wanda ke kwaranyo da
majina ga hawaye sun hadu sun cakude sannan
tace, "Au!! Gaya musu zamu yi? ai kama
bakinmu za muyi muyi shiru, ko Abbakar ba
za'a gayawa ba, dan kada dadin hira ya kwashe
shi a majalisarsu ya kwaza, kin san shi da
shegen surutu, kija bakinki ki yi shiru har mu
zubar da shi....." "Zubarwa Sala?" Abu ta fadi a
kidime. "Eh mana zubarwa zam yi, dan da
kunyar duniya gwara ta lahira, kuma ma ai ma
tuba kafin mu mutu. Goge hawayenki ni na san
ta inda zan bullowa al'amarin, ki sha kuruminki,
bari na samo mana mota mu tafi gida." Ta fita
ta samo musu mota suka loda kayanzu suka
nufi gida da sunan Abu ta warke. Tana isa gida
ta sanya aka samo mata madaci ta hada da
darbejiya da omo da kanwa ungurnu ta dafa su
suka dahu sannan ta kawo wa Abu daki. Tana
kwance lamo ta ce, "Abula na tashi ki kafa kai
maza ki shanye wannan." Ta mika mata kwanon
dake dauke da hadin. Babu musu Abu ta karba
ta kafa kai ta kama kyankyama tana rintse ido
saboda rashin dadinsa da daci kamar zai yanka
mata harshe, ko kofi guda bata sha ba amai ya
ciyo ta, ta yadda kwanon ta kama amai, gaba
daya hadin ya zube, wanda ta sha kuma ta
dinga dawo dashi tamkar zata amayar da
'ya'yan hanjinta. Sala tana tsaye ta yi tagumi,
sai dai tana ganin aman ya lafa ta kuma dauko
wani kwanon cike da maganin tace, "Maza Abula
na daure ki shanye wannan....." Ta girgiza kai
cike da fargaba tana fadin, "A'a Sala gaskiya
babu dadi, hanjina kamar zasu tsinke ji nake
kamar zan mutu." Sala ta waro ido waje tana
fadin, "To dama waye yace miki dadi ne da shi,
eye? Daman ai za ki sha ne dan ki rabu da
wannan jarabar dake tare dake, da don dadi ne
yaushe zan baki? Da dadi nake so kiji sai na sayo
miki kaza da madara, amshi ni ki sha tun raina
bai baci ba ko asirinmu ya tonu ba." Abu ta
amsa idonta na fidda hawaye ta amsa ta kafa
kai tana sha, ai wannan karon ko rabin kofi bata
sha ba aman ya kuma dawo wa, ta dinga
yunkuri kamar za ta amayar da 'ya'yan
hanjinta, hankalin Sala ya kuma tashi, haka nan
suka hakura dan babu yanda zasu yi suka yi
zugui-zugui da su cike da tashin hankali. Sadiku
ya shigo gidan da Sallama, Sala tace da Abu,
"Maza kwanta ki rufe idonki zan ce bacci kike yi,
Waye......? Tsaya ina zuwa." Bakinta yana
kyarma take fadin, ta fita da sauri tana kokarin
gyara daurin zani dake shirin faduwa. Ya dubeta
da mamaki dan ganin yanda ta fito a firgice,
idanuwan nata duk sun yo waje. Ya kalle ta da
damuwa a ransa ya ce, "Lafiya Sala ko ba ki jin
dadi ne?" Da sauri Sala tace, "Lafiya ta kalau me
ka gani? Jiya ne dai 'yar uwarka ta tashi da
ciwon kai har muka kai ta asibiti kana
makaranta, amman yanzu jikin da sauki dan har
an sallamo mu." Yace, "Allah ya sawake." Ya
dauki bokiti ya zuba ruwa ya shiga bandaki, ta
yi tsaye tana muzurai wai dan kada ya shiga
dakin, har ya gama ya futo daga bandaki. Sanda
ya futo har tsoro ya ji dan ganin yanda ya bar
ta haka ya tadda ta tana tsaye, ya dube ta da
mamaki ya ce, "Sala yaya dai, lafiya?" Ta gatsina
fuska ta ce, "Lafiya kalau, ina shan iska ne
kawai."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ya dubeta sosai ya ji gabansa ya fadi dan ganin
yanayin ta, amman sai ya dake kawai ya wuce,
har ya isa soro sai wani tunani ya darsu a ransa,
sai ya juyo har lokacin tana tsaye tana dubansa.
Ya kalle ta da kyau yace, "Sala kunje asibiti kika
ce? Me suka ce yana damunta?" Munje mana da
Baba Abbakar muka je ma jiyan ta sami sauki
yanzu haka bacci take yi. Bai yadda da abun da
tace ba, dan haka ya ce, "Ki bani katin na duba
ko da wani abu da suka ce." Kululululuuu!
Cikinta ya duri ruwa, amman sai tayi saurin
yanko karya tace, "Laaa! Ka ga sai yanzu ma na
tuna da katin, ai mun baro shi a can asibitin
wallahi, ai tama warke idan ka ganta kamar bata
yi ciwon ba ma." Kamar ya kuma yin magana,
amman sai ya ga rashin dacewar yi din dan
haka kawai ya juya ya fita ya nufi dakinsa, sai
dai ransa cike yake da zargi kala-kala amman
yana ta addu'ar Allah ya sanya abin da yake
zargin ya zama ba gaskiya ba ne. Sai da Sala
taga ya shige dakinsa sannan tayi ajiyar zuciya
gami da shiga dakinta da sauri tana fadin, "Oh!
ni Salame yaro sai shegiyar tambayar tsiya
kamar dan jarida? Koda yake an ce ai karatun
Lauya yake yi sun iya sharri, ai da na gaya masa
abinda ya faru na shiga uku da surutunsa
kamar wani ubana." Kusan daran nan a zaune
suka kwana suna sake-saken abinda zai fish-she
su, daga karshe dai sun yanke shawarar
komawa asibitin watakila su sami wanda zai
zubar musu da cikin tunda an ce ana zubarwa.
Amman sun yanke shawarar ba zasu je asibitin
Murtala ba za suje Kuroda ne dan kada Likitan
jiya ya tona musu asiri. Sanda suka isa asibitin
suka bi layi har ya kawo kansu suka shiga,
bayan sun zauna likita ya dubesu yana
tambayar abinda ya faru. Sala ce ta fara
kwantar da murya tana fadin, "Wallahi likita
tsautsayi ne ya faru da yarinyar nan, yarinya ce
'yar albar....." Ya dubi katin yana magana,
"Hajiya kece Zainabun ne?" "A'a ba ni bace gata
nan." Ta nuna Abu. Ya maida dubansa ga Abu
ya ce, "Zainabu me ke damunku?" Idonta ya
kawo kwalla ta dubi Sala tana matse idanu, Sala
ta daga mata kai alamar ta yi magana, ta
kwantar da murya ba kamar da ba da take
magana a tsiwace tace, "Daman kaina ne yake
ciwo da ciki na da kuma amai....." Ya dubeta da
kyau sannan ya maida kansa ga katin yana
rubuce-rubuce, ya daga kansa bayan ya gama
ya ce, "Hajiya zaki kai ta ayi mata gwajin fitsari
da jini." Ya dubi wata ma'aikaciyar jinya (nurse)
yace, "Sister nuna musu dakin gwajin jini."
Ma'aikaciyar jinyar ta mike tana fadin, "Hajiya
taso muje mana."
Abu ta kalli Sala wacce ko motsawa bata yi ba,
Sala kam wani busashshen yawu ta hadiya da
kyar sannan tace, "To likita ai daman a babban
asibiti anyi mata gwajin, an gano tana da ciki
ne.... Daman zuwa muka yi ka taimaka mana
kamar yanda Allah ya taimake ka ka zubar...."
"Me?" Likitan ya tambaya da mamaki, ya dora
da cewar, "Hajiya an gaya miki muna zubar da
ciki ne mu?" Bai bari ta bada amsa ba ya cigaba
da maganarsa, "To ki sani mu bamu zubar da
ciki a nan, idan kika kuma kasadar zuwa wani
asibitin na gwamnati da sunan a zubar miki da
ciki za'a iya kama ki a daure, wato kina jin
kunyar duniya ba kya tsoron Allah ko? Wato
kinfi jin kunyar duniya ba kya tsoron Allah ko?
Me yasa kika yi sakaci da tarbiyyar 'yarki har
tayi ciki? A ce kamar wannan karamar yarinyar
da bata gama sanin kanta ba balle ma ta san
mecece rayuwa ta yi ciki....." "Ai dai kaddara ce
ba ta wuce kanka ba kai ma." Abu ta katse shi
tana murguda baki da wani kyafta idanuwa. Sala
ta kai mata duka tana fadin, "Kin ci Ubanki
nace, ana neman ya raba ki da wannan kajagar
kina masa rashin kunya?" "Kin ga Hajiya ku tashi
ku fita na gama da ku, don ina da marasa lafiya
dake jirana." Likitan ya katse mata maganar.
Sala ta gurfana bisa gwiwowinta za ta fara roko,
amma ya katse mata hanzari ya daga mata
hannu yana fadin, "Hajiya I said get out of my
Office, (Na ce ki fita daga Ofis dina)." Jikin Sala
ya yi sanya ta mike duk da bata ji abinda yace
ba ta gane korarsu yake yi, Abun ce ma ta dan
gane wani abu tunda ta san (get out) dan haka
suka fice babu shiri. A bakin titi suka yi tsaye
cike da tashin hankali, dan duk iyakacin
dabararsu ta kare. Abu ta fashe da kuka tana
fadin, "Yanzu Sala shi kenan gorin da nake yiwa
Ladi mai danwake ta haifi shege nima haka za'a
dinga mini? Kin gani har hana ta fitowa muke
muna bula mata kasa idan ta fito, gaskiya
Mustafa ya cuce ni, Gashi ya gudu ya barni da
abin kunya." Sala ta matse ido cike da takaici
tace, "Bari ke dai diyar nan, na rasa inda zan
tsoma kaina da wannan abun kunyar, wallahi
yaron nan ya shammace mu, da ina ganin sa
yaron arziki ashe dan tsiya ne." Tayi kwafa gami
da fyace majina da hawayen dake zubo mata da
gefen gyalenta.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Abu ta dube ta tace, "Sala yanzu gida zamu
koma?" Sala tace, "Eh, to! Ko dai zamu je gurin
bokan can na kan tudu mu gani ko za'a sami
maganin zubar da ci....." "Sannu Hajiya." Wata
murya ta katse mata magana daga bayanta,
gaba dayansu suka juya da sauri dan ganin mai
musu magana. Ma'aikaciyar jinyar nan ce da
suka gani a dakin likita, wadda ya ce ta raka su
dakin gwajin jini. Ma'aikaciyar jinyar ta fara
magana, "Ina ta addu'ar Allah ya sanya daman
baku tafi ba, na dan tsaye bata lokaci ne dan
kada likitan ya gane ku na biyo. Ai shi na gaya
muku dan ka'ida ne ba ya zubar da ciki, yana
wani fama da gemu kamar gaske. Don ma bai
kama yi muku wa'azi ba, shi ya sanya sam
bama shiri da shi, amman daman ka'ida ce duk
asibitocin gwamnati ba'a zubar da ciki idan na
da matsala ba, sai dai zan taimake ku yanzu dan
kun bani tausayi, bai dace yarinya karama
kamar wannan rayuwarta ta lalace tun yanzu
ba." Fuskarsu ta fadada da fara'a Sala ta ce,
"Kai amman likita mun gode miki kuwa, Allah ya
sanya ki gama da duniya lafiya." Ma'aikaciyar
jinyar tace, "Amin." Sannan ta fara yi musu
kwatancen wani asibiti mai zaman kansa inda
za'a cire musu cikin. Sala ta dinga godiya kamar
ta kwanta don durkuso tana godiya.
Ma'aikaciyar jinyar ta ce, "Babu komai idan baku
gane ba dai ku fada mini, sai dai yanzu rana ta
yi gobe da sassafe za kuyi sammako kuje." Sala
tace, "Mun gane ma." Haka nan sukayi Sallama
suka tafi suna ta godiya. Daren ranar dai cikin
farin ciki suka kwana, sai zumudi suke yi gari ya
waye su tafi, dan abun da ya so tauye musu
farin cikin su ma da farko bai wuce rashin kudi
ba, sai dai da yake ance mai kadara ba
matsiyace bane, sai suka daga wasu kayansu na
sawa har da wani saitin dankunnen gwal wanda
Mustafa ya saiwa Abu suka kai kasuwar Rimi da
kasuwar 'yan tsaye suka saida, Cas suka amso
kudinsu, dan haka suka daina fargaba suka
kwana da farin ciki wanda rabon su dashi tun
ranar da suka ji Abu tana da cikin. Sai dai idan
za suyi magana kasa-kasa sukeyi dan sun lura
da Sadiku ya sanya musu ido, ko ma su kulle
kofar.
Da sassafe suka yi sammakon shiryawa suka
nufi kwatancen asibibin da Ma'aikaciyar jinyar
nan ta musu, basu wani sha wahala ba suka
gano a nan cikin Sabon gari yake. Sanda suka isa
suka cika da mamaki dan ganin wannan
Ma'aikaciyar ta jiya, ta tare su tana dariya tace,
"Kun gan ni anan ko? ai ina aiki anan ma sanda
bani da aiki a can. Dan haka ne ma ya sanya
nayi muku kwatancan nan din, kuzo muje gurin
likitan." Wani katon Inyamuri ne kansa da sanko
ya sha kot, idanuwansa jajir suke da alamun
shan taba a lebensa, ta cikin gilashinsa ya dinga
leken Abu yana wani lasar lebe. Cikin harshen
turanci Ma'aikaciyar jinyar ta yi masa bayani
duk abinda ke damun Abu. Ya yi dariya cikin
gurbatacciyar hausarsa ya ce, "O.k na gane,
Yarinya ka zauna mana." Yana magana yana
dubanta kamar maye. Duk rashin tsoro irin na
Abu sai da ta tsorata da ganin mutumin, dan
haka ta tsaya ta kasa zama. Sala ta dubeta da
kulawa tace, "Abula zauna mana, shine zai raba
ki da wannan kajagar da ke tare da ke." Ta
zauna tana cigaba da kallon sa har lokacin
hankalinta bai kwanta dashi ba. "Hajiya ciki wata
nawa take?" Ya tambayi Sala. Tace, "Ban sani ba
likita, sai dai ka duba ka gani." Ya Umurci Abu
da ta kwanta a wani gado da aka zagaye da
labule sannan ya shiga yayi mata awo. Sai da ya
kammala sannan ya fito ya dubi Sala ya ce,
"Hajiya yarinyarka tana da shiki na wata uku ne,
amman kada ka damu idan da akwai kudi za'a
cire shi yanzu." "Nawa ne kudin? Mun zo da
shi." Sala ta fada da saurinta. "Ka je can waje ka
biya za su gaya maka kudin." Sannan ya dubi
Abu yana fadin, "Ka sauko za muje da ke dakin
aikin yanzu." Sala ta je ta biya duk kudin da aka
caje ta suka bata takardar shaidar ta biya, duk
yawan kudin bata ji kyashin biya ba. Bayan ta
karba ta kai masa ya amsa ya karanta ya
umurci Abu da ta shiga wani daki ita kuma Sala
ta jira a can wajen shakatawa. Sai da ya sanya
ta tube kayanta sannan yace dole sai ya fara
kusantarta sannan zai mata aikin. Hankalin Abu
ya tashi matuka ta mike ta daura zaninta tana
masa wani duba na tsana da tsiwa ta ce,
"Sannu tsohon dan iska Bunsuru, bayan an biya
ka kudinka, to na fasa ai ba kai kadai bane mai
aikin ba, ka biya mu kudinmu mu tafi wani
gurin." Hankalin likitan ya tashi don ya kwadaita
da Abu dan ya jima bai yiwa yarinya karama
mai kyau da kyan sura irin tata aiki ba, dan
haka ya kwantar da kai da gurbatacciyar
hausarsa ya dinga lallashinta, amman fir Abu
taki yadda. Da dai ya ga ba zai shawo kanta ta
haka ba sai ya ce, shikenan ya fasa ta hau
gadon yayi mata aikin, bata yi musu ba ta
kwanta, tana ji ya zurkuda mata wata allura
wacce ko minti uku bata yi ba taji duk jikinta ya
mutu ko hannu ba zata iya dagawa ba, bakinta
ma ya kasa buduwa balle tayi magana, za mu
iya cewa tayi karamar suma ne,
Amman tana jin duk abinda yake faruwa sai dai
ba zata iya yin ko motsi ba dan allurar bacci
yayi mata da yake tana da karfin jini ya sanya
ba tayi baccin ba. Tana ji tana gani katon
Iyamirin likitan nan ya biya bukatarsa amman
bata da halin hanawa, sai da ya kammala dan
kansa sannan ya dauko kayan aiki ya fara yi
mata. Sanda ya tura karafunan da zai dagargaza
abinda ke cikin nata ji tayi kamar ana zare mata
rai dan azaba, amman ko motsi ba zata iya yi
ba, sai dai hawaye dake zubowa ta gefen
idonta. Shi kuwa katon kedarin ko a jikinsa, ya
sanya karfan ya burge abun da ke cikin kamar
yanda ake markada kayan miya, bayan ya gama
watso abinda ke cikin ya kuma sanya wani ruwa
mai magani ya fara wanke cikin, sai da ya
wanke shi tas sannan ya maida mata kafafunta
yanda suke. Azaba dai ta sha ta, hawaye sai da
ya jika gefen da take kwance, ajiyar zuciya kawai
take yi amman ba zata taba mantawa da
wannan azabar a rayuwarta ba har abada. Yayi
mata wasu allurai na rage radadi sannan ya tura
ta can dakin hutu, cikin dan kankanin lokaci duk
kamanninta sun sauya saboda tsabar azaba.
Sala ta isa kanta da sauri tana mata sannu
sanda aka sanar da ita an gama, sai a lokacin ta
sami bakin magana ta fashe da kuka mai ciwo.
Wannan Ma'aikaciyar jinyar ce ta shigo dakin
hannunta rike da magani ta yiwa Abu sannu
sannan ta ce, "Likita ya gama da ita babu komai
a cikinta dan haka nan da awa uku idan ta huta
zaku iya tafiyarku, sai dai Hajiya daga yau sai ku
daina sakaci ciki yana shigar 'ya'yanku, don ke
Zainabu yanzu kin ji azabar da kika sha, dan
haka gwara ku dinga rigakafi kafin ciki ya shiga."
Sala ta dube ta da mamaki tana fadin, "Dakta
yanzu akwai wani abu dake hana daukar ciki
dama?" Ma'aikaciyar jinyar ta ce, "Eh akwai
mana, allura ce da magani har da kulle mahaifa
ana yi, in mace tayi daya daga cikinsu ba zata
sami ciki ba." Sala ta amshe cike da mamaki a
fuskarta, "Oh! Ni Salamatu ki ji wata fasaha,
rashin sani yafi dare duhu, da mun sani da
yaushe za mu sha wannan wahalar? Kin ji fa
Abula." (Sala ba ta ji tsoron Allah ko yin nadama
da abin da ya sami Abu ba, ba ta hankalta da
isharar da Allah ya nuna musu ba har take
neman hanyar da diyar ta ba za ta kuma yin ciki
ba, hakan ke nuna daman tashin hankalin da
suka shiga na samun ciki ne ba na gyaruwar
zuciya ba. Menene amfanin irin wadannan
iyaye? Kai, tir! Da su, domin su ne tushen
gurbacewar al'umma a ganina).
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ma'aikaciyar jinyar ta yi ta musu bayani, Sala
tana ta girgiza kai cike da mamaki, ita kam Abu
ita kadai ta san abunda take ji, sai dai tana jin
dadin bayanin likitar, ta kuma yi alkawarin ba
zata kuma samun ciki ba, yanzu ma rashin sani
ne. "To, yanzu likita a ina ake samun maganin
tsarin iyalin?" Sala ta tambaya. Sister din tace,
"Ai ana samu a duk asibitocin da kika je, sai dai
su asibitin gwamnati suna da ka'ida, basu
bayarwa sai matan aure, ko kuma idan kinje da
mijinki, har wasu masu zaman kan nasu ma
akwai wadanda ba sa zubar da ciki saboda
rakiyar asara, amman kin ga mu nan babu
ruwanmu za ki iya zuwa ki siya ko a chemist
dina." Sala ta ce, "Kai likita mun gode da
wannan kirkin naki." Ta yi murmushu ta ce,
"Suna na Sister Asibi, ko da wata rana kunzo
neman wani taimako,ta yi musu kwatancen
gidanta ta tafi ta barsu cike da murna, dan
itama tana da nata kason, don ka'idar asibitin
nasu idan mara lafiya ya zo ta sanadiyyar ka
kana da kaso mai tsoka musamman ma zubar
da ciki. Karfe biyar suka koma gida, shatar mota
ma suka dauka, da kyar Abu take iya taka
kafarta, san da suka isa jama'a na ta kallonsu,
masu zargi na yi masu addu'a kuma na yi, da
haka suka shige gida. Da suka isa daki suka baje
Sala ta dauko naman da suka yo tsaraba da shi
suna ci suna mayar da yanda aka yi suna ta
dariya ta abunda suka dinga yi jiya har da
kukansu. Ita kuma Abu sai baiwa Sala labarin
irin azabar da tasha take yi. Sala ta ce, "Ai an
gama, da kin samu kwarin jikinki zamu koma su
yi miki allurar da suka ce din, tunda dai duniyar
ta sauya gwara mu fizgi rabonmu muma, dan
na san idan kika murje kika goge, Alhazan birni
ne zasu yo miki caaa, tun da dai kina da kyau
da sura mai daukar hankali." Suka kwashe da
dariya har da shewa. Sadiku da duk maganar da
suke yi a cikin kunnansa ya daga labulan ransa
a bace hankalinsa a tsananin tashe, nan fa suka
yi tsamo-tsamo kamar wadanda aka watsawa
ruwa, cikinsu aka rasa ko mai tari balle su yi
magana, dan daga ganin fuskarsa sun san ya ji
duk abin da suka ce. Shaf! sun manta basu rufe
kofa ba, ko su yi a hankali ba. Da kyar ya iya
bude bakinsa cike da takaici ya ce, "Sala yanzu
tsakaninki da Mahaliccinki Ubangijin da ya
halicce ki kun kyauta abinda kuka yi? ko tsoron
Abu ta rasa ranta a gurin zubar da cikin nan
baki yi ba, daman tun ranar da na ga kin gigice
na yi zargin wani abu na shirin faruwa koma ya
faru, na yi iyakacin iyawata a kan tarbiyyar
yarinyar nan har kina jin haushina. Sannan
wannan abu da ya faru bai zame muku ishara
ba sai ma kara kangarewa da Abu ta yi? Shin
Sala kun san sanda zaku mutu? Ba kwa tsoron
Allah? Ba kwa tunanin Ubangiji ya dauki
rayuwarku kuna cikin wannan mummunan
sabon? Da nayi niyyar fita daga harkarku sai dai
ya zama dole na tunatar da ku gaskiya koda
kuwa zaku tsireni ne nauyi ne a kaina, tunda shi
Babanmu ya gaza. Sannan ke Abu azabar da
kika sha ba zata zame miki ishara ba? dan bata
kai kashi daya cikin dubu ta azabar lahira ba,
dan haka ki hankalta ki san..." "Kai! Ya isa haka
malam." Sala ta katse shi. Ta dora da cewar,
"Ka wani saka mu a gaba kana mana surutu
mara ma'ana sai kace wasu 'ya'yanka, idan
aljannar ta ubanka ce ka hana mu shiga, sannan
idan kace za'a yiwa Abu azaba dan tayi ciki shi
kuma mai saka ido sana'ar da babu uwa babu
riba yaya za'a yi dashi? Ka saka mana ido
kamar wani Ubanmu, wallahi ba dan a tsakar
dakin nan na haife ka ba da asibiti ne sai nace
musanya miki kai aka yi, dan baka kaunarmu ka
tsane mu, to ta Allah ba taka ba dan saka ido."
Yayi wani murmushi mai cike da takaici yace,
"Sala ina kaunarku a matsayin wadanda bani da
kamarsu a duniya, wannan ya sanya ni nake
gaya muku gaskiya, dan wanda baya kaunarka
bai gaya maka gaskiya.......Malam ka ishe mu
haka, ba'a san gaskiyar taka soko shashasha,
har ni zaka ce zaka gayawa gaskiya? Tun kafin a
haife ka na san gaskiya. Bace min da gani tun
ban daga maka nono kabi duniya ba." Ya saki
labulen jikinsa sanyi kalau zuciyarsa tana suya.
Abu tace, "Sala kiyi masa kashedi kada yaje yayi
ta fadi a duniya yace nayi cikin shege mun
zubar." "Hakane fa." Sala ta fadi da sauri ta
daga labulan tana fadin, "To, saura naji wannan
maganar a bakin wani, ranka zaiyi mummunan
baci Sa'idini, sarkin sa-ido." Shi dai baice komai
ba don ko juyawa ma baiyi ba ya cigaba da
tafiyarsa ransa yana cigaba da suya. Sala kuwa
cigaba tayi da balbalin bala'inta tana fadin,
"Haka kawai an saka wa yarinya ido dan anga
Allah ya bata kirar da zataji dadin rayuwarta,
dan haka babu ruwan uban kowa koda sadaka
take bada kanta balle ma da makudan kudi
ne." (Ubangiji ya shirya mu har wadanda suka
bata, mu gane gaskiya kuma ya bamu ikon
binta, Amin).Ku ziyarci blog dinmu domin
karanta Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
KANO: 15/5/2003
Kyakykyawar budurwa fara tas, sai dai bata cika
tsawo ba dan haka koda yaushe zaka ganta da
dogon takalmi,ba ta da gashi mai tsaho amman
akwai yawan gyara shi, tana da dogon hanci
wanda ya fito da ainihin kyawunta, bakinta
kuwa irin dan karamin nan ne kamar na yara,
sai idanuwanta wadanda ke ruda 'yan maza duk
sanda ta kalle su da shi saboda girmansu da
kuma kyansu, har wata digon zaiba ce a ciki, ga
ta da dan karan yanga da iya kwalliya,
wadannan abubuwan suka hadu suka maida ta
irin matan da zamani ke yayi. Tana sanye da
riga da siket na atamfa wanda ya matse ta
tsam-tsam daga kugunta, 'yar kibarta ta yi cas-
cas cikin kayan, fatar jikinta na da laushi tamkar
'yar jaririya, tana sanye da katon takalmi mai
kama da tsani don tsaho, fuskar nan tasha ado
irin na wayayyu, sai ta shafa jambaki kalar
kayan jikinta, bata sanya kwalli ba, sai dai ta
zizara jagira cikin idon nata, gashin girarta ya
kwanta luf-luf gwanin sha'awa, daga yanayin
shigarta da tafiyarta kadai ya isa ya yaudaro
'yan maza dan duk inda Zainabu ta bi sai an
kalle ta. Kayanta kalar katuwar jakarta ce, ga
wani kamshi da ke tashi a jikinta kamar kana
kantin sai da turare, tana da matukar fizgar
hankalin duk wanda ya dora idonsa a kanta,
sannan hatsabibiya ce ta fannin mu'amala,
domin ta kware ainun a iyar tafiyar da namiji
don haka duk mutumin da ya kusance ta ko sau
guda ne sai ya kidima a kanta. Ta fito daga
dakin nata bakinta sanye da wata alawa mai
tsananin kamshi tana tsotsa, Sala dake shan
kayan marmari wanda Zainabun ta kawo musu
tsaraba jiya da ta dawo daga Abuja, zaune ta
bararraje a tsakar gida tana kallon Zainabu, duk
da ranta a bace yake sai da ta yi murmushi dan
ganin yanda Zainabu taci uwar kwalliya, tana
dubanta da fara'a tana fadin, "A'a 'yar albarka
kin fito? Sannu da fitowa." Zainabu ta yamutsa
fuska gami da amsawa. Salan tace, "Jiya na so
muyi maganar yarinyar nan sai naga kin dawo a
gajiye, ga shi kun yo dare....." "Wani Abu ne
kuma ya faruwa?" Zainabu ta katse Sala din
(don yanzu ta tashi daga Abu ta koma
Zainabunta). "A'a a kan dai maganar nan ce ta
kwanaki ta matsiyacin yaron nan da ta nacewa,
shi kuma wannan yaron dan saka ido yana ziga
ta kamar shine uwarta, to yanzu wai iyayansu za
su aiko, ni kam sam ba na son tayi auren nan,
me take da shi? Ita ko sha'awarki bata yi, koda
yake ko ba tayi auran ba ma bata da wani
amfani tunda ta ki yarda ta ciwo arziki, dan
haka sai kiga shegiyar tayi sati biyu bata da ko
kwandala, sai dai idan an yi musu albashi ya
sanmata, wanda duka albashin nasa bai wuce
kudin takalmi da jakarki ba."Zainabu ta yamutsa
fuska tana fadin, "Sala ki barta ta yi auran nan
taji, in dai Maza ne ai zata gane kurenta, banza
ana neman a samo mata mai maiko tun da ta
nace sai tayi auren tana ki tana wani rawar kai,
ki rabu da ita kawai, dan rannan baki ga wani
abokin Alhaji T.J ba yanda ya mato a kanta, har
na nuna masa ya rabu da ita kanwata ce, sai ya
rantse mini da cewar shi da aure yake sonta,
amman babu yanda banyi ba yarinyar nan ba
taki ko kula shi, haka ya hakura ya kyale ta don
ya yi-ya yi ya gaji, shi da mata ke sonsa kamar
me? Shine fa kwanaki ya bani kujerar Makka
guda ukun nan da na kai ku ke da Baba."
"La'ilaha Illallahu, kai amman yarinyar nan bata
da rabo, arziki yana kiranta tsiya tana janye ta,
ina ga fa matsa mata zamuyi ta aure shi kawai
ko ta tsiya ko ta dadi." "A'a Sala ina ruwanmu?
Ita ce fa zata zauna da mijinta, sannan yanzu
idan muka hada su haushinmu zata dinga ji,
gwara mu kyale ta ta yi hankali, ni bari na wuce
kada na yi latti, kin san nace miki muna da bikin
cikar Asma shekara ashirin da biyar, zan je mu
fara shiri saboda shi na dawo jiya." "To-to, Allah
ya kiyaye, zaki dauki shatar mota ne?" Zainabu
tace, "A'a Alhaji Danlami sabon kudi yana waje
yana jirana." "To Allah ya tsare, ya bada sa'a."
Tace, "Amin." Gami da ficewa. Yana cikin mota
zaune ya sha manyan kaya kamar wani
mutumin arziki, tunda ta fito ya zuba mata ido
tamkar maye, ita kuma tana tafiya tana rangaji
tamkar ganyen bishiyar da iska ke kadawa,
tafiyar dake dauke hankalin 'yan maza. Tana
isowa ya bude mata kofa yana murmushi gami
da fadin, "Barka da warhaka Hajiya, irin wannan
shanyar haka har na bushe?" Tayi wata
mayaudariyar dariya ta jan hankali, tace, "Lallai
kam, to waye ya gayyace ka? Ina ga kaine fa ka
sakani fitar nan, da ka gaji ba sai ka tafi abinka
ba na huta." Ya kanne ido yana mata wani kallo
yace, "Ni na isa? ai kina da tsayawa mutum a rai
Zainabu, kusan duk aikin da nake fa idan kika
fado mini bani samun sauran sukuni muddin
ban iso gareki na ji duminki ba, ko matana na
kasa zama da su kamar ke, anya Zainabu kina
tausaya mini kuwa? Dan Allah ki daure ki aure
ni mana ko na sami nutsuwa." Tayi masa wani
malalacin kallo ba tare da tace komai ba ta
kauda kai gefe, ya kuma rudewa ya matsa kusa
da ita jikinsa har rawa yake yi. Ta kuma
matsawa gefe tana harararsa gami da fadin,
"Haba Malam, ko dai dan bunsuru ne ka
saurara mu bar kofar gidan ubana da kuma
tsakiyar ranar nan, duk iskancina ban taba yi a
kofar gidan ubana dan ina mutunta gidan." Ya
ja baya yana shafa haba yace, "Kai Zainabu kina
juya ni wallahi kamar waina, amman babu
komai zan matsa lamba har ki zama mallakina."
Ya tada motar yana ta sumbatunsa, ita kuma
murmushi kawai take yi, ta gama kashe shi da
kissarta da kallonta gami da tsananin kamshinta.
Sai da ya kaita wani babban gidansa na
shakatawa suka gama watsewarsu sannan ya
cika mata jaka da kudi dan ya san Zainabu mai
tsada ce, sannan suka dauki hanyar gidan
Asma, har lokacin yana ta sumbatu a kanta da
yaba kyanta da iya mu'amalarta. Sanda suka isa
gidan Asma ya kwantar da murya kamar wani
abun tausayi ya ce, "Yaya dai Hajiya, karfe nawa
zan dawo na dauke ki?"
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta galla masa harara tana fadin, "Kai fa tsiyata
da kai kenan ba ka iya cin kwan makauniya ba,
to ai ni din ba matarka bace da zaka hana ni
sakewa." Ta kammala maganar tana murguda
baki. Ya lankwasar da kai yana fadin, "Tuba
nake Hajiya, kece din sai a hankali, amman na
hakura sai gobe zan bullo." Ta daga kafadarta
gami da fadin, "Kai dai ka sani, sautun
mahaukaciya." Ta fice daga motar. Har tayi nisa
yana kallonta kamar ya kuma binta yake ji.
Zainabu macece hatsabibiya mai tsayawa
mutum a ransa, ta san yadda take iya tafiyar da
shi kamar wacce ta karanci abun, ya rasa
abinda ya sanya matansa ba sa masa irin yanda
Zainabu ke masa, da zai sami mai masa kamar
Zainabu cikin matansa ai da babu abinda zai
sanya shi yawo ana wulakanta shi, dan yana ga
idan ya sami Zainabu ta aure shi yana jin ko
kofar gida sai anyi da gaske zai fita, da kyar ya
samu ya iya jan motarsa ya bar kofar gidan. Ta
shiga gidan da ihu babu ko sallama, Asma dake
zaune daga ita sai gajeren wando da 'yar rigar
mama tana busa tabar wiwi tana wani lumshe
ido, ta mike tana ihu suka rungume juna. Asma
ta ce, "Shegiyar, wallahi na yi zaton ba zaki zo
ba, da kin kwafsa mini." Suka zauna suna mai
da numfashi, sannan tace, "Haba Hajiyata ai kin
san dole na zo, yaushe zan yarda chasun nan ya
wuce ni?" Asma ta fashe da dariya tana fadin,
"Dan akuyan naki ne na san shi da jaraba ko
bunsuru ya rufa masa asiri, na san da kyar zai
barki ki dawo, ko da yake Zainabun akwai iya
iskanci, har tsoro nake ji idan na ga saurayina
yana kallonki, don har ta kafa sigina kike yiwa
namiji,suka fashe da dariya gami da tafawa.
Zainabu tace, "Wai ni yaya shirye-shiryen fatin
ne? Ina fata kin tanadar mana komai?" Asma ta
tabe baki tace, "Kin san akwai maza 'ya'yan
wahala wadanda iyayensu da matansu suka
sallama mana, sun gama komai. Senator Tanko
ya kama mana hotel dama komai da za'a ci a
gurin, sai dai shegen wai ba zai zo ba dan kada
'yan adawa su sami abin da zasu soke shi a
kafafan watsa labarai. Oho, ni ko a jikina dan
daman bana son ganin wannan mummunar
fuskar tasa wacce zata hana samari 'yan bana
bakwai isowa jikina mu sha minti, dan kin san
sun kwana biyu sai a hankali, dan wallahi duk
sanda na kalli fuskarsa sai ta tuno mini da wani
tsohon goggon biri." Suka kuma fashewa da
dariya gami da tafawa. Zainabu ta zira hannu
cikin jakarta da dauko kwalbar Shandy ta kama
tsotsa, ta jingina da kujera tana lumshe idanuwa
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Asma ta kalle ta gami da fadin, "Ke 'yar duniya
babu ko dandano? Kin kafa kai kina tsotsar
abun ki?" Zainabu ta dube ta da ido daya dayan
kuma ta kanne shi, "Malama kada ki matsa mini
ki bar ni na yi dif! Ina ce tadda ke na yi kina
busa tabar mulki kin mini tayi ne?" Ta kuma
matsawa gabanta tana kwantar da kai tace,
"Haba tawan ki yiwa Allah ki ba ni na kurba ko
sau daya ne, na kwana biyu ban tsotsa shandy
ba" "Amshi 'yar jaraba ba zaki bar ni na sha ta
ishe ni ba." Ta mika mata kwalbar giyar, sannan
ta dauko nadaddiyar tabar shaidan a jakarta ta
bata wuta, hayaki ya fara gauraye dakin, Asma
ta sakar musu kidan Bob Marley nan fa suka
tashi suna cashewa suna wani gantsare-
gantsare, daman Zainabu gwana ce gurin rawa.
Misalin karfe goma na dare motoci suka fara
sauke mata a kofar hotel din da zasu yi fatin,
sun ci uwar kwalliya sai dai babu wacce zaka
kalla kace diyar Hausawa ce balle Musulmai, don
duk irin shigar turawa suka yi, daga masu
gajerun wanduna sai masu damammnun kaya
da 'yan kananan wanduna. Dakin taron kuwa
kida ne kawai ke tashi kamar zai tsaga daki,
kowacce da saurayinta take shigowa. Shigowar
Zainabu da Asma ne ya sanya kallo ya koma
kansu, dan komai iri daya suka sanya, wani
gajeren siket suka sanya wanda ya tsaya
iyakacin gwiwarsu ya matse su sosai yana ta
kyalli, sai wata 'yar yalolowar riga mai rawa ta
zauna das a jikinsu, takalmansu har gwiwarsu,
sai gyaran gashi da suka yi, duk da Zainabu
bata fiye sanya gashi ba yau ta sanya, fuskar
nan ta dauki kwalliya sai wani kamshi ke tashi
daga jikinsu. Mai jawabi sai kwarara musu kirari
yake, "'Yan mata adon gari, 'yan matan da
duniya ke yayi, Asma ta Zainabu manyan Bebis
da duniya ke yayi, kun girmi kwailayen Kano,
kuna ruda mazan kano." Aka fashe da ihu.
Zainabu sarkin rawa sai ta hau taka rawa dan
daman yanda ka san mazari haka take, gaba
daya sai ta dauke hankalin mazan dake gurin
dan Zainabu daban ce, irin matan nan ne masu
kamar fitila duk inda suka je sai sun haske shi,
nan fa maza suka yi caa a kanta, ana ta mata
liki amman miskilar ko a jikinta dan babu wanda
ta baiwa fuska.Zainabu daban ce ko a duniyar
barikin tasu, dan idan namiji bai yi mata ba duk
kudinsa bai isa ko kallo a gurinta ba, tana jan
zaranta yanda take so, dan ta san Allah yayi
mata kirar daukar hankalin maza, an sha dambe
da yanke-yanke a kanta, ko waye kai idan zaka
kwana dubu kana mata magana ba za ta tanka
maka ba, musamman idan tayi dif da Shandy
dinta. Sai karfe hudu na dare aka tashi daga
fatin nasu, an rakashe an cashe an sha kayan
maye kala-kala, Zainabu kam tangadi take yi
dan ta cake da yawa, ganin haka ya sanya Asma
ta sanya ta a motarta suka nufi gidanta don ta
san 'yan gidansu basu san tana shan giya da
wiwi ba sai dai tana fita yawon gantalinta. Sai da
gari ya waye sannan ta dawo hayyacinta, bayan
ta farka ta shiga ta yi wanka ta yi ramuwar
Sallar dake kanta sannan ta yi shirin tafiya gida.
Tana sanye da doguwar riga ta atamfa super da
aka ciwa mutunci, dinkin ya kama ta tsam daga
kirjinta yayin da yayi baza daga kasa, hannun
rigar tamkar shimi yake, ta yafa karamin gyale,
sai tsireren takalminta mai kama da tsani, ta
sanya zobba na gwal kirar dubai, da wani dogon
dan kunne a kunnenta, kamshin dake daga
jikinta tamkar kamfanin turare dan Zainabu
ma'abociyar son kamshi ce. A adaidaita Sahu ta
sauka dan bata nemi dan rakiya ba, duk yawan
mazan da ta dauki hankalinsu daran jiya dake
neman shiga, ta shiga gidan nasu da sallama
muryarta tamkar sarewa. Sala da ke zaune ta
mike tana hangame baki gami da fadin, "A'a
diyar albarka har kun dawo? Har an gama fatin
kenan." (Kuji wannan Uwa fa, diya budurwa ta
kwana ta hantse a titi amman wai mahaifiyarta
tace har ta dawo? Hmmm, su Sala ko sai yaushe
za’a dawo kan hanya).
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta zauna jabar bisa tabarmar da Sala din ke kai
tana fadin, "Mun dawo Sala, wallahi fatin yayi
kyau.Yaya na ji gidan shiru ne ko duk ba sa
nan?" Sala ta tabe baki gami da fadin, "Yaran
dai basa nan amman Karimatu na nan, dan jiya
nayi wa yaron nan tas mai hure mata kunne,
nace kada ya kuma zuwar mini gida shine take
ta kumbure-kumbure, motarsa fa daya ce tal
Abula, mai na sama ya ci balle ya baiwa na
kasa, mtsw!" Ta yi tsaki cike da takaici. Zainabu
ta yi kwafa kana tace, "Ke ma Sala da son bata
ranki kike a banza, ina ce tun jiya mun gama
maganar, tunda ta dage sai shi ai sai ki rabu da
ita ta aure shi, kowa rai yayi ma dadi baya ga
mai shi ne." Sala tace, "Ai shike nan, kina ji ke
Karimatu sai ki gaya masa ya turo iyayen nasa
ko ma huta da naci kamar maye." Sala dai
kamar tsoron Zainabu take ko dan tana kawo
mata kudi? Duk hukuncin da ta yanke a gidan
babu wanda ya isa ya ja da shi koda yayanta
kuwa. Karimatu dake daki tana karatun Kur'ani
dan ta sami sassauci a zuciyarta saboda kwana
tayi tana kuka saboda yanda Sala ta bada ita ga
saurayin, wanda ko da ya aure ta ba zai kuma
ganin darajar Mahaifiyarta ba, tayi hamdala ga
Allah gami da yin Sujjada tana kara gode masa,
don Allah ya sani tana son Abbas kamar ranta,
shima yana masifar son ta, soyayya suke mai
tsafta, sai dai tun da ta kawo shi gidan da
sunan wanda zata aura Sala take aibata shi,
daman yaya lafiyar kura balle ta yi hauka? Don
daman basa shiri sam da Sala, dan tun tana
yarinya taso ta yi hali irin na Abu amman ita
Allah ya tsare ta shine fa Sala ta tsangwame ta
kamar ba diyarta ba, ko da harkar karatunta
Sadiku ne ke tallafa mata da komai,Don zamu
iya cewa kusan su kadai ne shiryayyu a gida,
dan kannanta dake bin ta maza duk sun fara
shaye-shaye, Sadiku ya yi dasu har ya gaji don
yana tufka Sala na warwarewa ne, su kuma 'yan
kannansu mata kanana guda biyu suma tallan
suke yi, kusan hanyar da Zainabu tayi rayuwa
suke kai, sai dai karamarsu ce ta dauko halin
Karimatu da alama sai kuma autansu. Bayan
Karimatu ta gama godiya ga Allah ta dauko
wayarta da sauri duk da tana jin nauyin Abbas
din amman haka ta yi kiransa, bugu daya ya
dauka don tun jiya yake neman wayarta har ya
gaji ya hakura, ita kuma ta rufe ne saboda
nauyinsa da take ji don ma kada ya kira ta bata
san mai zata ce masa ba kuma.
Gaba dayansu suka yi shiru kowanne yana jin
nauyin dan uwansa ita kam har da kunya ma.
Shine ya daure ya ce, "Yaya dai Karimatu, tun
jiya nake neman wayarki a kulle, har hankalina
ya tashi na yi zaton ko kin daina daga waya ta
ma." Tayi wata doguwar ajiyar zuciya kana tace,
"Abbas kunyarka nake ji ban san da idon da zan
kalle ka ba, don na sani Sala jiya tayi maka cin
mutuncin da ina jin ba'a taba yi maka ba, sai
dai ba kai tayi wa ba illa ni, don Allah ka yi....."
Kuka ya kwace mata ya hana ta karasa maganar
tata. Ya kwantar da murya yana fadin, "Kin ga
Karimatu ki kwantar da hankalinki, na riga na
san halin Sala tuntuni na kuma ji na gani don
babu gudu babu ja da baya a son ki, na san tayi
haka ne dan na yi fushi na rabu da ke, ni kuwa
sai na ji ma yanzu na fara son ki, dan haka ki
kwantar da hankalinki mu yi batu a kan abinda
zai fishshe mu." Ta dan ji sanyi a ranta dan
haka ta sami kwarin gwiwar gaya masa abunda
ake ciki, na yanda Sala ta amince ya turo da
iyayensa, abin ya bashi mamaki sai ya ga kamar
mafarki yake yi don shekara nawa suna fama da
Sala, amman ace lokaci daya ta amince? Sai
Karimatu ta nuna masa kawai karfin addu'ar da
suke yi ne ya sanya hakan ta faru, ya amince
da lallai hakan ne dan haka ya dinga hamdala
ga Allah, daga karshe suka yi sallama cike da
farin ciki. Abbas kam jin sa yake kamar yafi
kowa farin cikin zai mallaki Karimatu, duk da
sanda ya fara nuna wa abokansa yana son
Karimatu sun kwabe shi dan suna cewar waye
bai san iskancin da yayarta Zainabu ke yi a
unguwar ba ‘karuwar gida’ haka suke kiranta a
bayan idonta, yace shi kam ya ji ya gani dan ko
Allah bai kama wani da laifin wani, Tunda kowa
ya san halin Zainabu da na Karima ba daya ne
ba, don babu wanda zai ce gida daya suka taso
ma, sai dai kamar su da tayi daya baya ga
Zainabu gajera ce amman ba can ba, sannan
tana da dan jiki yayin da Karimatun ta kasance
doguwa siririya, Allah ya kuma sanya iyayensa
masu ilmi ne kuma wayayyu dan haka suka
goya masa baya gami da yi masa addu'a ta gari,
wacce ita ce ke dawainiya da shi a duk inda ya
sanya gabansa.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
*************
Ba da wani dadewa aka sanya rana ba wata uku
ne kacal, sai dai tun da aka sanya ranar Sala ke
mitar bata da shi, dan bata ga abinda Karimatu
ta yi da zata mata kayan daki ba, dan ko sanda
suka yi talla banda kwantai babu abun da take
yi, balle yanzu da bata da ko na sayen kwalli.
Shi kuwa Baba Abbakar ba'a ta tasa, don kudin
da aka kawo na zance ma so ya yi ya cinye sai
da Sadiku ya yi masa jan ido, shine ya ji haushi
shima yake fadin, "Ya ga mai yin gadon." Shi dai
Sadiku kallon su kawai yake yi yana ta kokarin
ya rufawa 'yar uwarsa asiri. Biki ya rage saura
kwana uku Sadiku ya shigo da kayansa na
katako irin wanda ake yayi, da kujerunsa masa
kyau da tsada. Maimakon Sala ta yi murna da
sanya albarka sai ta hau tabe baki tana fadin,
"Eh! Da yake Karimatu ce kayi mata kaya masu
tsada, da Abula ce da ka tsana da ko tsinke ba
zaka yi mata ba." Sadiku yayi murmushi ya ce,
"Sala kenan, da Zainabu da Karimatu duk 'yan
uwana ne, ita ma ta daina iskancin ta fito da
miji kin ga idan ban mata wanda ya fi wannan
ba." Zainabu da ke zaune tana yankan kumba
tana zaune bisa darduma ta doka tsalle tana
tafa hannu ta ce, "Wallahi karya ne, na fi karfin
na tsaya ka yi mini kayan daki, dan yanda kake
aiki nima ina yi, da kake ce mini 'yar iska ai na
gode Allah tunda ba na neman mata, ka duba
ka ga yanda yanzu mata ke neman....." "Dalla
can, rufe mana baki marar kunya, ki yi abinda
duk kika ga dama ai rayuwarki ce, na san komai
dadewa zaki gane kurenki, Karima dai Allah ya
rufa mata asiri, ba ta yi irin halinki ba, dan haka
kuka tsane ta gidan nan....." "Ahaf! Ahaf!, Wato
dai ni kake gayawa magana ko?" Sala ta amshe
da saurinta, "To ka ga fita daga gidan nan tun
ban bata maka rai ba, duka yaushe ka fara
samun kudin? Kafin ka fara rike dubu daya
Abula ta rike dubu goma, kuma duka albashin
naka nawa ne? Abin da ko kudin takalmi da
jakarta ba su kai ba? Ka da ka kuma furta mini
ko kala, fice ka bani guri tun ranka bai kai ga
baci ba." Ya gallawa Zainabu harara wacce ta
rama sannan ya fice, yana yiwa Karimatu
magana, "Ki lura da yanda za'a shiga da kayan
kada fentin su ya goge." Tana daga can zaune
gefen kicin tana yanka Salad da zasu ci abincin
rana da shi tace masa "To." kawai. Ai sai bala'in
Sala ya koma kanta, ina wuta ta jefa ta, zagi ta
uwa ta uba da gori tana fadin, "Dadin abin dai
da abincin da Abula ke ciyar da ke kika rayu ke
da shi din." Ita kam ko kala bata ce ba, dan
idan da sabo ta saba, ita kam aikin ta ma ta
cigaba da yi ko a jikinta. Zainabu ta ce, "Haba
Sala, ki yi shiru haka mana ka da muyi bakin
kunya." Ai kuwa tamkar ta ji wahayi daga
mala'ika ta yi shiru. Ita dai Karimatu dariya ma
abin ya bata ta ce, "Idan ka ki sharar masallaci
kayi ta rumfar kasuwa ai."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
CALIFONIA: 30/9/2003
Yana tsaye jikin window hannuwansa nannade a
kirjinsa, dogo ne ba sosai ba yana da dan jiki
irin na maza majiya karfi, jikin nasa a murde
yake, yana da kyau irin na gogaggun maza da
suka san duniya, bai cika fari ba amman ba
zaka sanya shi a layin bakake ba, yana da irin
gashin nan da samari ke ajiyewa a fuskarsu, ya
iya daukar kwalliya irin ta namijin duniya. Bai
fiye hayaniya ba, miskili ne ga wanda bai san
shaidancinsa ba, ma'abocin farin jini ga shan
yabo ga jama'a saboda faran-faran din sa da
sakin hannu (kyauta), amman a badini mutum
ne mai tsananin son holewa, sai dai yana da
matukar taka tsantsan don yana gudun bacin
ran iyayensa. Ransa a cunkushe yake, lokuta da
dama idan abin ya motsa masa sai ya ji kamar
ya zama tsuntsu ya bar garin, ya dade yana
tausar zuciyarsa a kan abinda yake gani ba
komai ba ne, sai dai yanzu abin yana neman fin
karfinsa da shallake iyakacin dauriyarsa. Abin da
ya faru dashi tsahon wasu shekaru da yake
ganin a can baya mara amfani da muhimmanci,
har idan ya tuno abin yakan kira shi da tsuntsu
daga sama gasashshe, sai dai tunda ya yi nisa
abin ya fara damunsa, da farko yakan ga kamar
abin nan ne da Hausawa kan kira 'Sabo tirken
wawa' sai dai da yaga duk kwanan duniya abin
yana kuma tsiro a zuciyarsa har ya kai matsayin
da ya cika zuciyar tasa babu sauran wani gurbi
na tirjiya da dauriya. Ya yi kwafa a karo da
dama ya juyo yana kallon kayataccen falonsa
wanda ya sha kayan alatu kamar ba za'a mutu
ba, ya isa dan gurbin shan lemo, ya zuba lemo
a kofi ya hada da shandy ya cilla kankara ya
daga ya shanye wai ko zai ji sanyi a zuciyarsa,
sai dai har lokacin abin yana nan, sai yaga
kamar ma karuwa ya yi saboda mutuwa da
jikinsa ya yi sabon tunani ya shige shi. "Me ya
sa haka ne?" Yayi wa kansa tambaya, wadda
tsawon lokaci yake yiwa kansa, ya dauko taba ya
kunna ta ya bata wuta a hankali yana lumshe
idanuwansa amman har lokacin bai ji sanyi a
ransa ba. Ya jawo takardar da ya bayar da irinta
a Ofis dinsu jiya ta barin aiki yana kuma
dubawa, wayarsa ta fara kara ya dauka da kyar
yake magana, abinda aka gaya masa kamar kara
hasala shi aka yi don haka da zafin rai yake
magana cikin harshen nasara. "Eh! Ni ne na
rubuta dan na yanke shawarar barin aikin nan
don jama'ar kasata na bukatar gudummawa ta,
sannan iyaye na sun damu da su ganni,haba
Mustafa kada ka yi mana haka, idan albashinka
ne ya maka kadan zamu iya kara maka mu." A
ransa yace, "A wannan karon babu wanda zai
hana ni tafiya dan zan biyawa raina bukatarsa
ne, dan idan na cigaba da zama a haka zan iya
asarar farin ciki da kwanciyar hankalina."
Amman a fili sai yace, "Oga kuyi hakuri ba zan
iya janye kudirina ba a wannan karon na tafiya
ko da nawa zaku kara mini, nayi muku alkawarin
dai duk sanda na sami dama zan dawo muku
gaba daya, amman yanzu hankalina ya yi
kasata." Dan Baturen da suke maganar ya sare,
dan 'dan zaman da suka yi sun san Mustafa
mutum ne kaifi daya, idan ya sanya abu a
gabansa babu wanda ya isa ya hana shi
aiwatarwa, dan haka ma ya rike aikinsa da
gaskiya da amana, dan haka suke masifar ji
dashi, shine zai bare inji ba tare da ya tsaya ya
kalli 'yar takardar bayani ba ya maida ya hada
shi kuma ya tashi tsaf, ba kamar sauran
Turawan da sai sun duba ba a rubuce, ya dai
daure yace, "Shike nan Mustafa muna maka
fatan alkhairi, sai mun hadu a Ofis din. Ya yi
ajiyar zuciya ya ce, "Shike nan Oga sai mun
hadun." Ya kashe wayar tasa gami da lumshe
idanuwansa, wata rayuwa ta dinga bijiro masa
wacce ta wuce shekarun baya wacce a da can
yake daukarta shirme, sai dai yanzu ya tabbatar
ita ce rayuwarsa mai cike da ainihin farin ciki da
sanya shi nishadi da dariya, sai dai duk sanda
yake tunanin wani abin mai fadar da gaba kan
fado masa, sai dai yana addu'ar Allah kada ya
tabbatar da wancan abinda ke fadar masa da
gaban. Washegari jikinsa babu kwari ya fito daga
Ofis din nasu dan alhinin rabuwa da abokan
aiki, sai dai daman haka rayuwa ta gada dole
wata rana za'a rabu, walau ta gurin zama ko
aiki ko kuma ta har abada ma (mutuwa). Daga
nan kai tsaye gurin neman Visa ya nufa ta
komawa kasarsa ta haihuwa wacce rabonsa da
ita tsahon shekaru.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
KANO-NIGERIA: 15/10/2003.
Bayan ya sauka ya dauki shatar mota tun daga
filin jirgi har gidan Mahaifinsa. Maigadi ne ya
fara ganinsa don haka ya zuro da gudu cike da
murna da doki yana fadin, "A'a Alhaji Mustafa
yau kake tafe? Marhabun lale, sannu da zuwa."
Mustafa yana murmushi yake amsawa ya
sallami mai tasin, sannan ya dubi maigadin ya
ce, "Malam Bala a shigar da kayan ko?" Daga
nan ya shige cikin gidan kai tsaye, ya yi sa'a
kuwa jama'ar gidan duk suna nan domin la'asar
ce. Da Mominsa ya fara cin karo tana zaune a
falo tana karatun jaridar Leadership Hausa, tana
sanye da (Medicated glass), ya shiga da sallama
bakinsa a washe. Ta daga kai cike da tsananin
mamaki, suna hada ido dai ta tabbatar da lallai
shine, ta mike cike da murna tana fadin,
"Babana! Da gaske kai ne ka iso garin ba tare da
ka sanar da mu ba?" Ya isa gaban Mahaifiyar
tasa cike da farin cikin ganin Mahaifiyar tasa don
ya kwana da dama bai ganta ba, dan ma wani
lokacin ta kan bi Mahaifinsa suje ganinsa, don
shi tunda ya tafi bai kuma waigo wa Nigeria ba,
wanda shi wai nan dabara ya yi dan ya manta
da abinda ke damunsa a ransa, a cewarsa idan
ya yi nisa da abin zai samu sassauci koma ya
manta gaba daya, sai dai yanzu ya gano
dabararsa ba za ta kai shi ko'ina ba. Ya ce,
"Momi barka da gida, na same ku lafiya?"
"Lafiya kalau muke sai dai mamakin dawowarka
yanzu babu sanarwa, Allah dai ya sanya lafiya."
"Momi Lafiya kalau wallahi, na so kwarai na ba
ku mamaki ne dan na sha sanya rana zan zo
amman bana zuwa, dan haka nace wannan
karon sai dai ku gan ni kwatsam." "Lallai kam ka
ba mu mamakin, bari na je na samo maka dan
abin tabawa." Ta mike ta nufi kicin din gidan.
Tana isa kicin ta tadda 'yan matanta suna ta
faman kacaniyar girkin dare, ta ce, "Albishirin
ku?" Gaba daya suka ce, "Goro Momi." "To
yayanku ya dawo yanzun nan, yana falo dan
haka sai a hado masa abin motsa baki kafin a
kammala girki." Gaba daya suka yi falon da
gudu suna murna suna ihu, sun ma manta da
abinda aka ce su dauka, ta yi murmushi sannan
ta dauka ta tafi da shi.
Yana ganinsu ya ce, "Lallai 'yan matan Momi an
girma, kalle ku don Allah." Suka kalli juna suna
dariya.
Ya so tun daran ya fita ya fara aiwatar da
abinda ya kawo shi garin, sai dai gajiya ta hana
shi dan haka dole ya hakura har gari ya waye.
Washegari ya shirya cikin manyan kaya wadanda
suka kara fito da kimarsa da martabarsa, duk
da zaman da yayi kasar waje bai daina sanya
manyan kaya ba, musamman yakan aiko a yi
masa, idan ya sanya turawan suyi ta sha'awarsa
musamman idan zai je gidan biki ko wani fati,
yawaita sanya manyan kayansa tun yana nan
gida ya kara masa martaba a idanun jama'a har
suke ganinsa wani mai hankali da tsantseni.
Motar Babansa ya hau dan na shi yayo Odarsu
ba su karaso ba, yana tafe yana jin wakar Bob
Marley don mutuminsa ne, sai kada kai yake
cike da nishadi, yau ce ranar da zai cikawa
ransa burinsa, yau ne zai je ga Zainabu Abunsa
karo na biyu da sunan soyayya, idan ya tuno
abinda ya faru a baya sai ya dinga jin wani farin
ciki da nishadi. Sai dai abinda ke fadar masa fa
gaba idan ya tuna anya Zainabun tasa ba tayi
aure ba? Idan aka ce Zainabunsa ta yi aure
kuwa lallai yana cikin tashin hankali da rashin
nutsuwa, dan ya gano yanzu itace rayuwarsa,
sai yake ganin nisan gidan nasu da yake su sun
tashi sun koma cikin G.R.A. Ya isa kofar gidan
yayi fakin yana kallon gidan, kusan yanda ya san
shi haka yake yanzu, sai dai wasu sauye-sauye
da aka samu, mutane ne a kofar gidan can da
can suna cikin kwalliya. Gabansa ya tsananta da
faduwa da ya ga Sadiku sanye da manyan kaya
da gani sababbi ne sai daukar ido suke ya zama
babban mutum mai kamala, sai fito da abinci
yake shi da wasu cikin farantai. Ya zubawa
Sadiku ido har lokacin gabansa na faduwa, ya
zuge gilas din motar a hankali yana kara kallon
jama'ar dake kai kawo kofar gidan. Can ya
hango wani maroki yabi Sadiku yana masa kirari
ya sanya hannu a cikin aljihu ya dauko kudi ya
ba shi, da alama yana cikin farin ciki, daga
ganin alamun babu ko tambaya aure aka daura
sai dai bai san ko na waye ba, ya yafito wani
yaro da yazo wucewa ta kusa da shi yana kallon
motar. Yaron ya karasa yana kallonsa a alamun
rashin sani a fuskar yaron, "Dan Allah yaro
daurin auren wa aka yi a kofar gidan ne?" Ya
nuna kofar gidan da hannunsa. Yaron yace,
"Daurin auren wannan din nan aka yi 'yar gayun
nan mai kwalliya ni na manta sunan ta ma." Ya
rasa gane wacce yaron ke nufi sai dai
hankalinsa yayi kololuwar tashi don yana ganin
kawai Zainabun sa ce ma, ammai sai yayi ta
maza ya ce da yaron, "Na gode ka ji abokina, un
go wannan." Ya mika masa Naira dari biyu,
yaron ya amsa cike da murna ya tafi.
Yana cikin mota yana ta sake-saken yanda zai
yi, shin kundumbala zai yi ya futo ya tambayi
wacce aka daurawa aure ko kuma hakura zai yi
ya koma.Tunaninsa ya tsaya cak sanda ya hango
wasu hadaddun mata sun nufo shi, dayar
doguwa ce sosai fara amman da alama ta dan
kara da na kanti, sai dayar gajera ce amman ba
can ba, tana da wani irin kyau na daukar
hankali, daga shigar ta har tafiyarta sun yi
matukar burge shi, yana hango su suna doso
shi, sai yaga mara tsahon da yawa fuskarta tana
masa gizo kamar ya santa. Suka zo suka gota shi
suna taku sannu a hankali, gaba daya sun tafi
da hankalinsa, wani irin kamshi ya ji ya bigi
hancinsa san da suka wuce, ya lumshe idonsa
saboda kamshin da ya ji
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
"Anti Abu ga wayarki in ji Sala ta ce kin manta
ta." Wata 'yar yarinya da ta fallo da gudu ce ke
fadin haka. Mustafa ya bude idonsa da sauri.
Wacce tafi tafiya da hankalinsa yaga an mikawa
wayar, ta amsa ta sanya a jaka, yayi wata
sanyayyar ajiyar zuciya mai cike da rudani yana
fadi a ransa, "Yanzu wannan Abu ce da ya sani
a can baya 'yar mitsitsiya da ko kwalliya bata iya
ba, 'yar tallan abinci da ya wayar da ita, ita ce
ta zama wata irin tauraruwar mata ta wuce
yanda duk yake tunanin zai gan ta?" "Ya Salam"
Ya fadi a fili. Ko da wasa ko a mafarki bai taba
zaton Abunsa zata yi irin wannan wayewar ba,
ya daukarwa kansa zai dawo Kano na Nigeria ya
auri Zainabu, ba don tsananin kyau, ilmi ko
dukiya ba sai dai dan tsananin sonta kawai da
Allah ya jarabce shi, sai dai abun mamaki da
tsoro sai ya ga Zainabu ta sauya ta wuce
iyakacin tunaninsa gaba daya. Tashin motar da
yaga sun dosa ne ya farkar da shi daga dogon
tunanin da ya fada, ya tada ta shi ya bi bayan
ta sun sai dai ina sun riga sun yi masa nisa, dan
haka ko hangosu baya iya yi, dan hala dole ya
dauki hanyar komawa gidan su dan ya ji kiran
wayar Dadin su. Karfe takwas na dare ya kuma
dawowa kofar gidan su Zainabu, don yinin ranar
haka ya yi shi sukuku, ya dinga tuno yanda ya
ga Zainabu na tafiya da kamshinta na yanzu,
musamman yau Babansa bayan sun gaisa sai
yayi masa maganar aure dan sun jima suna
masa maganar yana cewa suyi hakuri har yanzu
baiga wacce ta yi masa ba ne. Cikin wata shigar
ya iso ya yi kyau matuka, shaddar har wani kara
take yi saboda tsabar bugu da ta sha, sai dai ya
tarar da cincirindon mata a kofar gidan, sai
motoci ne ke diban su, sai dai addu'arsa Allah
ya sanya ba Zainabunsa aka daurawa aure za'a
kai dakin miji ba. Yayi fakin ya fito ya jingina da
motar yana kallon matan dake kaiwa da
komowa cikin hasken fitilar da ya haske kofar
gidan. Har ya gama kalle-kallen sa bai hango
Zainabu ba, wata budurwa mai shegen yangar
tsiya da take ta wucewa ta gaban sa ko zai taya
ya daure ya yafito, babu musu ta nufe shi kanta
ya kuma fasuwa don ga dan gayu mai
hadaddiyar mota yayi kiran ta zata buda gurin
'yan matan gurin, ta nufe shi tana kara salon
tafiya tana wani girgiza, duk da ba wani kyau ta
cika ba amman daga gani tana ji da kanta.
"Barka da yamma adon gari." Ya fadi da wata
mayaudariyar muryarsa, yayi mata kuri da
idanuwansa wadanda ke ruda 'yan mata. Tayi
wani far da idon ta da kyar kamar bata son
magana ta ce, "Yauwa ya kake?" Yayi dan
murmushi yace, "Kalau nake. Na ce banga
amarya Abu ba ko har sun wuce ne?" Ya shirya
hakan ne don ya tabbatar da gaskiyar abin. Ta
yi masa wani kallo mai cike da mamaki sannan
ta ce, "Hala dai mantuwa ka yi naji kana cewa
Abu, dan dai na san Karimatu ce amarya ba
Abu ba, yaushe Abu zata yi aure ita da ta
daurewa bariki gindi?" Ta karasa maganar tata
tana yatsina fuska da alamun kishi a muryarta
jin ya ambaci Zainabu don ta zaci cewa zai yi
yana son ta. Ransa yayi wani wasai cike da farin
ciki da yaji ba Zainabunsa ce aka yiwa aure ba,
duk da bai ji dadin abinda ta ce din ba amman
sai ya dake ya ce, "Kai na shafa'a ne, yi hakuri
Karimatu nake so na ce miki na manta." Ta dan
saki ranta tace, "Babu damuwa idan gurin fatin
za ka mu zo ka rage mana hanya mana ni da
kawayena?" "Me zai hana, ki shigo na kai ki
mana." Ya yi haka ne dan yayi amfani da
wannan damar ya ga Abun a can.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Idan zuciya tagyaru 1-04
Posted by ANaM Dorayi on 01:13 PM, 30-Jan-16
Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU
_______IDAN ZUCIYA TA GYARU_____
_____________ Na
_______Fauziyya D Sulaiman______
Dadi ya cika ta ta yafito kawayenta da ke can
tsaye suna kallon su da mamaki da sha'awar ina
ma ace su yace yana so. Ta shiga motar tana
fadin, "Ga kawaye na nan zaka rage musu
hanya." Yace, "Su shigo mana." Dadi ya kuma cika
ta tace musu, "Ku shiga baya mana." Ta umurce
su sanda suka iso jikin motar. Ta so ya dan ja ta
da hira sanda suka hau kan kwalta don ta kara
budawa a gurin kawayen nata, sai dai shi kaset
kawai ya kunnan na mutumin na sa, yana gyada
kai zuciyarsa na can ga Zainabu Abu yana
kwadayin yanda zai ganta ko da sau daya ne. A
haka suka isa har inda za'a gabatar da fatin,
hotel ne hadadde, tun daga waje za ka san fatin
na manya ne dan manyan motoci ne a gurin.
Sisters night aka rubuta da kyalli baro-baro
wanda ke haske a gurin. Fatin Abu ce ta shirya
shin don taya kanwarta murnar biki, Malam ne
ya daura auren sannan 'ya'yansa suka shige
gaba gurin bikin dan duk yawancinsu suna auran
masu hali ne suna tukinsu, don haka a motocinsu
aka dinga dauko mata ma. Bayan yayi fakin
sauran 'yan matan suka fice da saurin su, ita
kuwa 'yar gwallin ta tsaya tana wani yauki da
fari, har zai ce ta fita mana sai ya tuna yanda
take masa wani yauki da yanga. Dan haka yayi
murmushi ya ce, "Ga shi har zamu rabu ban san
sunan Hajiyar ba." Tayi dariya mai cike da nishadi
ta ce, "Sunan ai ba wani na ku zo mu gani ba ne,
sunana Salimat." Yace, "Lallai nice name, suna
mai dadi." Ya zaro kudi a aljihunsa ya mika mata
ya ce, "Ga wannan kya yi liki kafin na shigo zan
ga wani abokin da bai karaso ba, idan na shigo
zan gan ki." Yayi mata haka ne dan ta rabu da
shi. Ta yi wani fari da idonta don ta yi zaton da
gaske yake musamman da taga ya bata kudi
masu yawa, dan haka ta ce, "Babu damuwa,
amman fa ban ji sunanka ba." Da sauri yace,
"Sunana Mustafa." Don ya gaji da ganin ta ya
matsu ta bashi guri ya shiga ya ga rabin ransa.
Ta ce, "Shi kenan na gode Mustafa sai ka shigo."
Ta fita tana wata yanga. Ya bita da kallo har ta
kule sannan ya yi tsaki yana fadin, "Ki ga mace
kamar an zana one amman sai wani firirita da
iyayi take, ita wannan ko a kafa aka daura mini
ita ai zan yage ta na zura da gudu ne." Ya kuma
gyara fakin ya kwantar da kujera gami da kara
sautin wakar da yake ji, ya kunna taba yana sha
yana kada kai kamar kadangare, ta cikin hasken
gurin yake karewa matan da ke shige da fice
kallo. Ya dan jima a haka sannan ya bude motar
ya fice ya kukkullo ko ina, sannan ya nufi inda ya
ji kida yana tashi na Mahmud Nagudu don shine
yake taya su shakatawa. Gurin ya tsaru matuka,
mawakin ya dage yana ta rera wakarsa cikin
tattausan lafazi, amarya da ango suna tsakiyar
makeken filin suna takawa a hankali, yana daga
inda yake tsaye ya gane Karimatu dan ya santa
tun tana karama, sai dai daman can ita tafi
Zainabu hankali da nutsuwa. Ya sakale hannuwa
a kirji yana ta waige-waige, bai kula da matan
dake ta kallon sa wasu ma har sukan yi masa
sigina. Can ya hangota ta shiga filin rawar tana
sanye da wani irin material golden anyi masa
wani matsiyacin dinki da ya kama jikin ta tsaf
kamar a jikin ta aka kera shi, ta daura wani nadi
mai kyalli shima, wani dan ziririn gyale a kafadar
ta, sai wani katon takalmi da ta sanya mai kama
da tsani dan tsaho, ta yi kyau matuka, ta zaro
kudi daga jakar dake hannunta ta fara watsa
musu.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tana yi itama tana taka rawa a hankali, da yake
gwana ce gurin rawa sai abun ya kayatar da
jama'a da dama. Sai mawakin ya koma kanta da
waka, "An gaishe ki yayar amarya karkada tsiwar
ango, magajiyar uwa, manyan matan da duniya
ke yayinsu, Zainabu tauraruwar zamani mai
haske duniya, kin dade kina tashe har gobe ke ce
tauraruwa farin wata sha kallo." Kanta ya kuma
fasuwa ta dinga zaro kudi tana zuba masa, Asma
ta shigo filin da irin kayan Zainabun komai da
komai, ita ma tana shiga ta hau yiwa Zainabu
likin kudin. Ango ya kama hannun amaryar suka
fice yana dariya yana fadin, "Kada ta gaji ta isa
haka rawar." Suna fita ya kuma mai da kidan
kansu yana wakesu su kuwa sai rawa suke yi ta
burgewa. Mustafa dake gefe a tsaye bai san
sanda ya kutsa filin rawar ba don Zainabu ta
tsumo shi da yawa, yana shiga ya zura hannu a
aljihu ya dinga debo daloli yana manna mata, ta
dinga dubansa da mamaki sai dai tana ganin
kamar gizo idonta ke mata ko kuma mai kama da
shi ne, amman da yake miskilar kanta ce sai ta
dake kawai ta yi kamar bata gane shi ba, sai da
ta gaji don kanta da rawar sannan ta fice daga
filin, yana ganin ta fita shima ya bi bayanta, duk
wanda ke shirin yiwa Zainabu liki sai jikinsu ya yi
sanyi dan sun ga mai liki da daloli, gurin ya
kacame da ihi da tafi na burgewa. Ita kam can
wani tebur ta nufa dake can baya da jama'a,
Asma ta bita da gudu har suka zauna. Asma ta
dube ta tana fadin, "Shegiyar ina kika sami
wannan hadadden gayen ga kyau kuma ga
'ya'yan banki? Ya yarfawa 'yan mazan gurin nan
wallahi." Zainabu tayi mata wani kallon banza
sannan ta sanya hannu cikin jakarta ta dauko
tabar shaidan ta kunna ta, ta jingina da kujera
tana fesar da hayakin ranta ya dauki zafi. Lallai
ko a duhu taga Mustafa ba zata manta shi ba,
shine mutumin da ya fara lalata mata rayuwarta
kuma ya gudu ya barta a lokacin da take matukar
bukatarsa, ba ta taba son wani mutum kamar
Mustafa ba sanda ya nuna mata kulawa da
soyayyar da sai daga baya ta gane tsananin
yaudara ce, sannan a yanzu bata da wanda ta
tsana a mutane sama da shi din. Asma kam sai
maganar Mustafa take mata ita kuma zafi take ji
a ranta dan haka ta kulle idonta kam har Asma
din ta gaji ta yi shiru, a tunaninta ko ta bar gurin
ne don haka ta bude idon ta. Tsaye ta gan shi a
kansu ya nannade hannuwansa a kirji yana
kallonsu, babu wani abu da ya sauya na daga
kamanninsa sai kiba da haske da ya kara, yana
nan har yanzu a dan gayunsa, yanda ya kura
mata ido itama haka ta kura masa har lokacin
tana cigaba da shan tabarta ta shaidan, Asma ta
dinga kallonta tana kallon sa ta gaza gane abun
da suke nufi, ta dai tabbatar da lallai yau
kawarta ta hadu da daidai ita.
Ya jawo kujera dake kusa da su ya zauna sannan
ya jawo jakarta dake ajiya, ba ta ko motsa ba
balle ta yi masa wani abu, ya dauko tabar
shaidan shima ya kunnata, a hankali ya dinga
fesar da hayakin sannan ya kai dubansa ga
Zainabu wacce ke wurga masa wata uwar harara
kamar idon ta zai fadi kasa. Yayi wani murmushi
wanda ya kuma futo da haibarsa ya ce, "Zainabu
Abun Musty!" Ta ja tsaki kana ta mike a fusace ta
rike kugu bayan ta kashe tabar ta ce, "Malam
lafiya dai ko? Don ni ban sanka ba ko don ka ga
na kyale ka kayi mini liki kake neman zakewa da
yawa?" Ya yi murmushi ya ce, "Zainabu kenan,
kina tsammani ko a buge kike zan yadda baki
gane ni ba? Na san na yi laifi amman na san zaki
yafe mini dan Mustafa naki ne." "Ka ga Malam ni
fa ban sanka ba, ban san daga inda ka futo ba,
ka je can ka nemi wacce kaka nema, idan kuma
buguwa ka yi kwakwalwarka ke gaya maka
karyane to ka bari ka nutsu ka dawo hayyacin ka
sai ka nemi wacce kake nema." Yayi dariya sosai
wacce ta kara kular da Zainabu sannan ya dora
da cewar, "Haba Zainabu, ai kinfi kowa sanin giya
ko taba basa bugar dani, sai dai ke farin shiga
balle yanzu ma na daina shan giya dan haka ya
dace kema ki daina." Ta doki tebur gami da
fadin, "Karya kake yi wallahi karamin kwaro, ka
dube ni da kyau ban yi maka kama da wacce ka
sani ba a da, dan kuma baka bar gurin nan ba
zan sanya yanzu a yi maka rashin mutunci
wallahi." Asma dake kallon su ta zunguri Zainabu
wai tayi shiru, amman kamar ta kuma zigata sai
cewa ta yi, "Dalla Malama ki kyale ni, ba irin
wadannan ake saurarawa ba, wannan da kike
gani cikakken dan iska ne da bai dace a dagawa
kafa ba." Maganar tayi masa zafi a ransa amman
da ya tabbatar dai ta gane shi din tsiya ce kawai
sai yayi murmushi ya ce, "Ni dai na sani Zainabu
ko giyar wake kika sha ba zaki manta dani ba,
dan haka na dawo rayuwar ki bada wasa ba, ina
fatan zaki manta da duk abinda ya faru a baya."
"Wallahi karyarka ta sha karya, ka dube ni da
kyau, sama da kasa zaka ga ba Abun da ka sani
da can bace, wannan Zainabu ce, dan haka ka ja
tsummar rayuwarka ka bar nan gurin idan ba
haka ba zan rotsa maka kanka da kwabar nan."
Ta nuna masa wata kwalba da ke kan tebur din
da suke zaune ta lemo.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ya yi murmushi gami da gyara zama har lokacin
yana zukar tabar sa yana kallonta babu ko
kyaftawa. Ta san halinsa mutum ne mara tsoro
sannan duk abin da ya sanya kansa babu mai
hana shi, dan haka tasan babu wata barazanar
ta da zata bashi tsoro, idan har ta yadda suka
cigaba da zama guri daya komai zai iya faruwa,
dan haka ta ga barin gurin kawai shine mafita a
gare ta, dan haka ta dauki Jakarta ta bar gurin
tana huci. Ya bita da kallo har ta bace wa
ganinsa, yayi murmushi sannan ya dawo da
dubansa ga Asma wacce ta zuba masa ido kawai
tana kallonsa, ta san lallai kawarta ta debo mai
zafi dan barazanar da takewa maza suna tsorata
shi tayi masa amman ko gezau bai yi ba. Ya yi
dariya ya ce, "Kawarmu yaya gida?" Ta yi wata
wawiyar ajiyar zuciya dan maganar ta zo mata a
bazata, sannan ta ce, "Lafiya kalau." "Kinga
yanda muka yi da kawarki ko? Na san halin
Zainabu muguwar 'yar buyagi ce zata iya yin
abinda ya fi haka ma, sai dai ban damu ba ko
dar ma banji ba, don na gano tsagwaron sona a
cikin idon Abu" Ya nuna kirjinsa da yatsansa yana
cigaba da fadin, "Ni ne mutum na farko da ya
san wacece Zainabu, duk wani iskanci da Zainabu
ke takama da shi nine na koyar da ita, ba wai ina
alfahari da haka bane, a'a zuwa yanzu ma duk
sanda na tina ni ne silar lalacewarta na kan ji
takaici kuma na ji haushin kaina, don haka nayi
alkawari yanda na zama sanadiyyar lalacewar
rayuwar Zainabu zan kuma zama jagora gurin
ganin na shiryar da ita." Ya manta Allah shi ne ke
shiryar da wanda ya so, ga shi ya yi hasashe ba
tare da ya nemi yardar Allah ba. "Amman ki bar
ni da Zainabu ni da ita kar ta san kar ne, na san
na yi mata laifi amman zata yafe mini komai
dadewa tunda nine mutum na farko da ta fara so
a rayuwarta." Gaba daya ya gama burge Asma
har ma take ganin inama ace itace ke da wannan
hadaddan gayen, amman ta san tunda Zainabu
ce a gabansa ba zai kalli kowa da daraja ba
musamman da yace shine masoyin ta na farko,
dan haka da wuya ya kalli wata mace da daraja.
Don haka ta share wannan tunanin ma a ranta
dan ta san ba mai yuwuwa bane, yanda kuma
suke da Zainabu ma ba zata iya yi mata zagon
kasa ba, dan haka ta fara jan sa da hira ta
Zainabu kawai, ya ma manta da Zainabu 'yar
buyagi ya zauna suna ta hirarsu har aka tashi
daga fatin, sannan ya nufi gurin Zainabu wacce
ke ta hada kayan su na fatin da ta san nasu ne,
ya isa gabanta yana dariya ya ce, "Yaya dai uwar
dakina ko za'a taya ni kwana ne yau dan ina tare
da gajiya wallahi na yo doguwar tafiya mai nisa."
Ba ta kalli inda yake bama balle ya sanya ran
zata kula shi, ya cigaba da surutunsa don a
ganinsa dole zata bi shi don yanda dare yayi
kuma kowa ya watse a gurin har amarya da ango
dole ta bishi dan babu wanda zai dauke ta, don
haka nema ya share guri ya zauna yana ta cigaba
da surutunsa. Can wata dankareriyar mota ta
kutso kai harabar da suke zaune, Zainabu ta
mike tsaye gami da kallonsa sama da kasa ta ja
tsaki sannan ta ce, "Malam ina gargadinka karo
na biyu da ka fita daga rayuwar Zainabu, ka
kuma gane yanzu Zainabu nake ba Abu ba."
Tana gama fadin haka ta nufi motar da salon
tafiyarta na yanga da jan hankalin maza. Ransa
ya yi masifar baci har yana ganin ba zai dauki
wannan raini wayon ba, don yana da masifar
kishin tsiya. Don haka ya nufi motar da sauri cike
da bacin rai, amman ina tuni ta riga ta shiga,
bayan ta zauna ta kalle shi yana wani huci kamar
tsohon zaki, ta yi wata mayaudariyar dariya mai
kularwa sannan ta rufe murfin motar, yana kallo
suka fice a guje, ya ji kamar ya rufa musu baya a
guje amman ina sun yi masa nisa. Ya doki iska
yana huci gami da fadin, "Ba zan taba daukar
wannan rainin hankalin ba wallahi, zamu gauraya
ne." Ku ji fa karfin hali namiji da suna Hajara
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
. Suna daukar hanya DPM ya kalle ta yana wani
lasar lebe yace, "Yaya dai gimbiya za'a taya ni
kwanan ne mu wuce gidan shakatawa ta?" Ta
galla masa harara ta ce, "Au abinda kake yiwa
kenan shiya sanya ka nace daman zaka dawo ka
dauke ni? Tsaya ka saukeni dan ka san kuna da
yawa 'yan iskan garin zan sami mai kai ni gida,
dan ni na gaji babu wani abinda zan iya yi." Ya
ce, "Kai Zainabu ke fa 'yar buyagi ce wallahi,
daga dan tayi sai jidali, shi kenan na hakura muje
kawai." Bata kuma cewa komai ba ta jingina da
kujera ta lumshe idonta tana tuno abinda ya
faru, wani ciwo mai zafi da ya dade yana damun
zuciyarta ya fara taso mata, tsigar jikinta ta fara
tashi yar-yar kamar mai jin sanyi "Mustafa!
Mustafa!" Ta fadi a cikin ranta gami da girgiza
kai. Lallai ta sani abu ne gingimeme a gabanta,
dan Mustafa da ban ne a cikin maza a gurinta,
kuma tayi wa kanta alkawarin a can baya duk
sanda Allah ya hada su ko a hanya ne sai tayi
masa rashin mutunci, amman sai ga shi a
gabanta amman ta kasa aiwatar da komai a
kansa, sai ma wani abu da yake neman ya dawo
mata da shi. Har suka isa kofar gidan su bata san
sun iso ba don tayi nisa a tunani, sai da ya kai
hannunsa yana shafarta tamkar wani maye
sannan ta farga, ta yunkura da masifa ta
hambare hannunsa gami da dalla masa harara.
Ya kama sosa keya yana dariya ya ce, "Tuba nake
yi, ai na zaci ko kinyi bacci ne, Allah Zainabu sam
ba na gajiya da ke, ke din ta daban ce, kamshin
ki kawai kan tayar mini da hanlaki, yanzu ji yanda
kamshin ki ya cika motar nan tamkar ni ban
sanya turare ba, wai ni da wane turare ki ke
amfani ne ma?" Ta yamutsa fuska ta ce, "Su
kuma wadanda ka ajiye a gidan fa meye amfanin
su? Dan haka wallahi nake tsoron aure, sai ku
baro matan ku a gida kuzo kuna hurewa
kadangarun bariki kunne da naira, yanzu haka
matan ka suna can suna jiranka kana nan kana
gantali da wannan daran." "Ke rabu da
wadannan matan, babu wani abu da suka iya sai
jarababban kishi da shegen bin Malaman Banza,
burin su kawai su tara kudi, da kun hau gado su
yi maka wani sumbukaka kamar jakai, babu wani
salo da suka iya wai su kunya, sau da dama idan
nayi niyyar daina bin matan titi na zauna da su
idan suka gaza gamsar da ni sai kiga na dawo
ruwa, balle ke Zainbau daban ce wallahi kin san
kan da namiji matuka, ko makarantar kika yi ne
na kawo matan nawa ki koyar da su?" Ta yi
dariya sannan ta ce, "Matsalarka ce wannan,
wata kila kai ma da laifinka, kana shigar musu
gida ne tamkar mala'ikan tsaron wuta babu
fara'a shi ya sanya suke kasa sakin jikinsu, ni dai
yau duk jarabar ka nan gani nan bari, ka ga fitata
ma.
Ta bude kofar ta fice tana fadin, "Asuba ta gari."
Ya bita da kallo har ta shige cikin gidan na su,
yayi tsaki da damuwa gamida kifa kansa bisa
sitiyarin motar tasa, Zainabu ta zame masa
masifa a rayuwarsa, muguwar hatsabibiya ce,
muddin ka yarda ta lasa maka zumar ta a baki to
lallai ka shiga uku, idan ba kana da kwararriyar
mace mai iya salo-salo ba sai ka ji ka rainawa
matan ka.Ya figi motar tasa ya bar kofar gidan
tamkar mai tsere da iska, ita kuwa tana isa gida
ta tadda gidan shiru kowa ya gaji da kacaniya ya
yi bacci, ta shiga ban daki ta dauro alwala ta
sanya kayan ta na sallah, ta shimfida sallayar ta
wacce ke ta kamshin turare ta haye ta fara
gabatar da Sallah. Idan ka ga yanda take
nutsuwa idan tana Sallah zaka rantse idan aka
sanya mata hannu a baki ba zata iya cizawa ba,
dan duk iskancin ta bata wasa da Sallah, tunda ta
taba jin wa'azi akan Sallah da irin azabar da
mara yinta ke sha ta nutsu da yin sallah, wannan
shine kadai abinda zaka daga a rayuwar Zainabu
ta yi tutiya da shi. Mu dai bi ta a sannu don
duniya ai takaitacciya ce.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Mustafa kam da kyar ya iya komawa gida, ya
dade a dakin sa yana sintiri hannuwansa sakale a
bayansa, wani masifaffan kishi da zafin Zainabu
ke addabarsa, lallai yau da yana da hali da sai
yayi wa Zainabu da wanda ya dauketa dan
banzan duka, gaskiya ba zai iya lamuntar wannan
halin nata ba na kula kowa, lallai dole ta daina
harka da kowa indai tana son kanta da zaman
lafiya, ya dade yana sintiri da kyar ya iya
daurewa ya dan kishingida har bacci ya dauke
shi. Da safe ya so yaje amman ya san da kyar zai
sami ganin ta don hidimar bikin da sukeyi dan ya
ji suna cewa yau din ne yinin biki, dan haka ya
yanke shawarar sai dare sannan zai shiga. Karfe
tara na dare ya isa gidan nasu ya rasa ta yanda
zai yi ya ganta, sai can ya sami wata budurwa
yace ta kira masa ita. Ta dube shi ta ce, "Ai Anti
Abu tun da aka yi Sallar Magariba suka fice da
kawarta Asma." Ya yi mata godiya ya koma motar
sa ya zauna, Allah ya sanya jiya ya amshi lambar
wayar Asma din, dan haka bayan ya shiga motar
ya zauna ya fara neman layin Asma din. Da
yanga ta dauka a yauki take maganar sanda taji
kira, "Hello wa ke magana?" Ya yi ajiyar zuciya
sannan ya ce, "Mustafa ne, don Allah ina son ki
bani kwatancen inda kuke, amman kada ki sanar
da kawarki yanzu zan zo." Ta dubi Zainabu da ke
zaune tana zukar tabar shaidan ta dora kafa
daya kan daya, tunda suka iso gidan abun da
take yi kenan dan cewa ta yi ba zata je kai
amarya ba don ranta a bace yake su wuce gidan
ta ta sami hutu, amman tun da suka karaso din
ta gaza tabuka komai baya ga busa taba, dan
haka ta riga ta gano kawar tata tunanin Mustafa
ne kawai don bata taba dora hankalin ta ga
namiji kamar haka ba. Sai ta ce, "Shike nan zan
yo maka text." Daga haka suka yi sallama. Minti
talatin da biyar kacal ya kwashe ya iso gidan ya
danna kararrawar kofa, Asma ta mike da sauri
don ta san Mustafa ne. Zainabu ta bita da kallo
ta ja tsaki tana fadin, "Banza, kin gayyato mana
wani kwarton ko? Ni da nazo dan na huta zaku
dame ni, daman tunda naji kina magana kasa-
kasa a waya na san jarabarki ta motsa." Bata ce
mata komai ba sai dariya kawai da tayi ta nufi
kofar, yana tsaye sanye da kananan kaya, wando
ne na jeans bulu da shet fara tas mai taswirar
birnin London, da silifas na fata a kafarsa dan
gasken, sai agogo na azurfa da wani kwalelen
zobe shima na azurfar, ya yi kyau matuka. Suna
hada ido da Asma ta yi ajiyar zuciya sai taga yau
yafi kyau ma fiye da jiya, dan ta kuma yadda irin
gogaggun mazan nan ne ma, ta kwantar da
murya tana fadin, "Yallabai barka da isowa." Ya yi
murmushi gami da fadin, "Yauwa kawarmu ya
gida?" Tana amsawa ta bashi hanya ya wuce ciki,
sannan ta kulle. 'Yar buyagin tashi tana zaune
tana ta busa hayakinta bata ko kalli inda suke ba
balle ma ta gane waye ba. Ita ma Asma tana
shigowa kiran wayar Alhaji Buba ya shigo wayar
ta, yace ga direba nan ya turo su taho, dan shi
baya zuwa da kansa dan kada masu ganin sa da
daraja su ganshi girma ya fadi, dan haka sai dai
duk sanda ya bukace ta ya turo direbansa a kaita
can gidan sa ta kwana, dan haka dakin ta ta
wuce ta hado 'yan kayanta. Har ya isa kusa da
ita ya zauna bata san ya zo ba, dan tabar
shaidan din ta fara gaya mata karya, ta jingina
da kujera ta lumshe idanuwanta tabar tana
tsakanin hannunta.A hankali ya zare tabar dake
tsakanin hannunta, kamar wacce ya tsikarawa
allura ta bude idonta firgigit ta ware manyan
idanuwanta a kansa suka yi ido hudu, sai ta yi
zaton ko gizo yake mata kamar yanda yake mata
tun dazu. dan haka ta mai da idanuwanta ta
lumshe wai ta daina ganin gizon sa, sannan ta kai
tabar ta bakin ta da zummar ta kuma zuka,
amman sai taji wayam babu komai, ta bude
idonta da sauri a kansa, shine din dai da gaske
yana taya ta shan tabar tata. Haushi da takaici
ya cika ta tama rasa yaya za tayi masa, amman
ta san ba kowa ne yayi mata wannan iskancin ba
illah Asma, dan haka ta mike da bala'inta ta nufi
dakin kwanan Asma din, sai gata sun ci karo a
hanya, ta ci uwar kwalliya sai kamshi take zubawa
rataye da jaka a jikin ta. Ta rike kugu tana
harararta, ita dai Asma dariya ta sanya sannan ta
nufi Mustafa ta cilla masa makullin tana fadi cikin
harshen turanci "Take care, good night." "Wai
Asma wannan wane irin iskanci ne?" Zainabu ta
tambaya a kule. Asma ta daga kafada alamar Oho
sannan ta fice da saurinta tana dariya. Ta kulu
matuka, ta mai da kallonta ga Mustafa dake
kallonta yana murmushi ta ce, "Wai kai kana gani
kayi mini dabara ne, to ka sani a yanzu na girmi
wayo da dabararka, sanda ka yi kaci nasara dai
ka yi amman ban da yanzu, don haka sai ka
zauna ka jire mata gida." Ta dauki dan yalolon
gyalenta da jakarta ta nufi kofa. Sai dai ina ya
rigata dan mikewa yayi da azamarsa ya sanyawa
kofar makulli ya cilla makullin cikin aljihun
wandonsa. Ta yi tsaye tana kallonsa cike da
takaici da masifa, ya isa gaban ta ya tsaya cak ya
zira hannuwa cikin aljuhunsa ya ce, "Ga ni
gabanki kiyi mini hukunci daidai da laifina zan iya
dauka, amman ki yi mini alfarma ki daina gudu
na sannan ki dai na mini kallon kiyayyar nan dan
yana bakanta mini raina, domin Allah ya
jarabceni da son ki Zainabu, na gaza kallon
kowace mace da daraja a rayuwata, ki taimaka ki
yafe mini laifin da nayi miki nasan mai girma ne,
amman na yi ne ba da son raina ba." Ta rike
kugu tana kallonsa idanuwanta sun sauya launi
zuwa jawur, duk wannan farin da kyallin babu
saboda tsabar dacin ran da take ciki, tayi wani
yake wanda yafi kuka ciwo sannan tace, "Mustafa
na sanka tuntuni gwani ne kai gurin iya yaudara,
da irin wadannan kalaman ka sami nasara a
kaina a wancan lokacin hadi da kuruciya da
talauci da son kudi irin na Mahaifiya ta, sai dai ka
sani a yanzu Zainabu Abu ta wuce duk iyakacin
tunanun ka, baka da sauran kalmar da zaka iya
yaudararta da ita, baka da kudin da zaka iya
yaudararta dasu, domin ina mu'amala da
wadanda suka fika kama daga Gwabnoni sai
Sanatoci da Ministoci zuwa manyan 'yan kasuwa
dake rike da akalar Nigeria, dan haka yanzu ina
da kudi da farin jikin da nafi karfinka, a yanzu
idan na buga waya kadai duk abinda nake nema
zan samu, dan haka kaga baka da makamin da
zaka yaudari zuciyata a yanzu, duk da kana
takamar kaine silar fadawa ta a wannan muguwar
harkar da kullum nake tsinewa mara albarka."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ya kuma kwantar da murya ya ce, "Zainabu
tunda na diro garin nan na ganki nasan lallai ba
Abun da na sani da can bace, kuma ban dawo
rayuwarki dan na nuna miki kudi ko kyau ko
mukami ba, na zo ne da sunana Mustafa
masoyin ki nida zuciya ta kadai ina fata zaki yafe
mini abinda nayi miki can baya, sannan na mai
da matsayina da martaba ta a zuciyarki kamar
da, koma yafi haka don a yanzu Mustafa bai zo
da zummar fasikanci ba sai dai da zummar auran
Zainabu, domin a yanzu Ubangiji ya jarabi zuciyar
Mustafa da tsananin son Zainabu." Ta kalleshi a
lalace tamkar ta ga mahaukaci sabon kamu tace,
"So! So! Lallai ka hadu da mugun ciwo idan har
da gaske kake, balle na san karya kake yi, domin
kai mutum ne mai yaudara da karya, don haka
ka bude mini kofa na fice kawai, dan bana son ko
kallon fuskar ka domin kai ne mutumin da ya
sanya rayuwata a cikin fargaba da tashin hankali,
nasha azabar da har abada ba zan manta da ita
ba dan haka bude mini kofa na fita ko na daina
ganin azzalumar fuskarka!" Ta karasa maganar
tana hargowa. Ya hadiyi wani miyau mai daci,
maganganunta suna yi masa zafi da suya a cikin
zuciyarsa, dan haka da kyar ya iya buda baki
yace, "Zainabu ba zan bude miki kofar nan ba
har sai kin amince dani kin yarda yanzu ni ba
mayaudari ba ne..." "Ba zan taba yadda da kai
ba, ka bude mini kofa kawai na fita tun ban
maka rashin mutunci ba wallahi." Yana tsaye
kyam babu alamun zai ko motsa, ranta ya kuma
baci matuka, ta ga lallai da gaske yake dan haka
ta nufe shi da azama ta kama kokarin kwatar
makullin, nan fa suka fara kokawa amman ina
namijin duniya ne maji karfi dan haka ta gaza kai
hannunta balle ta iya dauka har karfinta ya kare,
tayi kokarin janye jikinta amman ya hana ta
hakan dan ta tuno masa da wani lokaci da wasu
al'amura da ke masa dadi da sanya shi nishadi a
duk sanda ya tuno. Tayi kokarin ta kwace amman
ta gaza sai ma wani abu da yake shirin jawo
mata dan shin din daban ne a zuciyarta ya san
kanta da yanda yake samun ta a sama, daman
haka yake so ta shiga jikinsa dole sai ta sakko
don dai shine ya santa ya san wacece ita, tayi luf
a faffadan kirjinsa mai kirar zaki ta gaza kasa
aiwatar da komai. Ya sami yanda yake so dan
haka yake da salon yaudarar da sace zuciya,
yanzu kam ya soma nasara a kanta dan tana jin
zafinsa a ranta amman tana matukar son sa, dan
haka komai ya kwance mata, Mustafa ne namiji
daya tal da idan tana tare da shi take manta
kowa, amman duk sanda take tare da wani sai ta
tuno shi da soyayyarsa, don haka bata da karfin
halin da zata kwaci kanta duk da haushinsa da
take ji, dan haka sai ta fashe da kuka kawai.
Jikinsa ya dauki rawa don yasan ba karamin abu
ke san ya Zainabu kuka ba, don tana da taurin
zuciya, dan haka cikin tausasa murya da rada ya
ce, "Zainabu don Allah ki yi hakuri ki yafe mini na
tuba....."."Me ya sanya ka tafi ka bar ni sanda
nake tsananin bukatar ka a rayuwa ta eye?" Ta
tambaye shi tana kuka. "Ki yi hakuri na san nayi
miki lafi, sai dai na yi miki alkawarin ba zan kuma
barinki ba har abada, ni din naki ne ke kadai, ba
zan iya kuma barinki ba Zainbau, ni kaina na sha
wuya, na yi miki alkawari." Ta yi luf ta gaza cewa
komai dan yayi mata yanda ba zata iya kuma
musa masa ba, anan suka baje suna shashancin
su. Sai karfe goma na safe suka sami sukunin
tashi suka fada wanka sannan suka yi sallah,
sannan Zainabu ta fada kicin da sauri don ta
samar musu abin da zasu karya dan yunwa suke
ji matuka. Ya bita kicin din tana sanye da wani
dan guntun siket, tare suka yi aikin suna ta
dariyarsu. San da suke karyawa yayi mata kuri da
ido yana kallo don Zainabu ta bashi mamaki, ta
wuce duk yanda ya santa, gaba daya ta gama
haukata shi a daran jiya, yanzu abu daya ya rage
masa ya auri Zainabunsa ya huta, kullum yana
manne a jikin ta shi kadai, sai ya ji wani kishi ya
kama shi mai tsanani dan bai san iyakacin adadin
mazan da ta yi mu'amala ba, sai yake da na
sanin tafiya da yayi ya bar ta, da shi kadai ya san
abarsa. Ita ma wani irin farin ciki take ji a cikin
zuciyarta, dan ta sha karo da maza kala-kala a
yawon iskancinta, amma bata ji wanda ya taba yi
mata dai-dai da Mustafa ba, don haka tana yin
bariki ne bawai dan dadi ba sai don neman abun
duniya(Allah ya kyauta), Zainabu hatsabibiya ce
ta kin karawa, dan haka maza da dama ke shan
wahala a kanta, yanzu ma mikewa tayi tsam ta
isa inda yake ta zauna cinyarsa, ta sakala
hannuwanta a wuyansa ta mika masa bakinta wai
ya sammata abin da yake taunawa (wainar kwai),
bai yi mata gardama ba dan shima gwani ne, dan
haka ya hada bakinsa da nata yana ciyar da ita
abinda ke bakinsa, da haka ta dinga kara susuta
shi tamkar wani karamin yaro ta mai da shi.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Bayan sun kammala cin abincin suka yi masauki a
doguwar kujera mai cin mutum uku. Ta kwanta
lamo a kirjin sa tana shafar sa tamkar mage,
cikin kunnensa ta ce, "Musty wai me ya sanya ka
tafi ka bar ni sanda nake tsaka da bukatarka?"
Yace, "Sai kin sanar da ni irin wahalar da kika ce
kin sha sannan zan sanar dake nima." Ta yi kwafa
tana fadin, "Labarina mai cike da abun tausayi ne
da takaici, domin daga ranar da na nemeka na
rasa na shiga tashin hankali, naje har gidanku
aka ce mini daman hutu kazo wai a kasar waje
kake karatu, na shiga tashin hankali da ciwo mara
misali, abu fa kamar wasa sai ciwo ya dinga yin
gaba, da farko na zaci ciwon soyayya ne, sai da
abu yaci tura aka gano ashe ciki ne dani....." "Ciki
da gaske Zainabu ko na wasa?" Ya tambaya da
sauri. Ta yi dariya tana fadin, "Da gaske Musty
wallahi ciki ne na gaske, kai ai munga tashin
hankali ni da Sala a wannan lokacin." "To yanzu
ina abun da kika haifa din?" Ya kuma tambaya.
Ta tabe baki tana fadin, "Cabdijam, ai tuni muka
zubar da shi." Ya dafe kai yana fadin, "Ya salam,
ai sam ban san kina da ciki ba, har na ji ina son
abuna wallahi Zainabu." Ta warware masa duk
abin da ya faru sannan ta dora da cewar, "Bayan
mun gama da wannan muna murna mun dawo
gida da kwanaki kuma sai ciwon ciki ya balle mini
ga zubar jini kamar jinina zai kare, amman da
muka je gurin shegen likitan da ya zubar mini da
cikin ya caje mu kudi masu yawa gashi a lokacin
bamu da komai duk mun saida 'yan
kadarorinmu, don haka yace ba zai taba ni ba,
sai nurse din da tayi mana hanya ce tace muje
asibitin kuroda tun da dai yanzu ba zubar da ciki
bane zasu karbeni, gahi an kwana biyu da zubar
da cikin sai nace ina da aure bari na yi, sai ta
shige mana gaba da sunan ni 'yar uwarta ce daga
kauye aka kawo ni. Amman duk da na Gwabnatin
ne ma sai da aka rubuta mana magunguna masu
tsada ga karin jini, sai yaya na ne ya bada jininsa
aka diba, sannan Sala ta je ta ciwo bashi aka sayi
magunguna, lokacin adadin kudin kusan dari
shida ne. Bayan na warke muka fara tunanin
inda zamu samu kudin da zamu biya dan daman
irin kayan nan na bashin watan nan ta amsa ta
karyar da su ta saida sannan aka sami kudin, don
ma matar tana shakkar Sala ba tayi magana ba,
da na samu sauki sosai Sister din nan ta bani
shawarar na dinga fita good evening (karuwanci),
cikin kankanin lokaci komai ya sauya domin dai
kasan ni ta daban ce." Suka yi dariya gaba
dayansu sannan ta cigaba da maganar, "Yaya
Sadiku kamar zai shake ni ya kashe ni don tsabar
tsana da yayi mini, don har cewa yayi da ya san
ci gaba zanyi da iskanci da bai yadda an kara
mini jininsa ba, gwara na mutu kowa ma ya huta,
sai da Sala ta tsawatar masa harda barazanar
zata tsine masa idan bai fita harka ta ba sannan
ya saurara mini. Sister ce tace na koma karatu
domin rayuwa babu ilmi tana tawaya don haka
Sadiku na komawa ya maidani makaranta wacce
na yi kusan wata shida banje ba, da farko yace
ba zai maida ni ba sai da nayi masa alkawarin ba
zan kuma yawo ba sannan ya yadda ya kwashi
katina da zai tabbatar da bani da lafiya ne
sannan muka wuce makarantar. Sanda muka isa
Principal dinmu ta ce ba za ta amshe ni ba
domin dai nayi wajen wata shida ban zo ba 'yan
ajinmu har sun zana jarabawar sake aji . Sadiku
ya marairaice yana bata hakuri, ji nake kamar na
harbe shi don haushi, daga karshe ya dauko kati
ya bata don ta tabbatar bani da lafiya ne. Ta
ware idanuwa domin dai duk da bata fahimci
abinda likitan ya rubuta ba ta fahimci kalmar
(bleeding after abortion), wato zubar jini bayan
bari, ta daga katin cike da tsana da takaici take
kallona sannan ta fara magana.
"Lallai yarinyar nan kin cika tantiriyar 'yar iska,
bayan iskancin da rashin kunya har karuwanci
kike tabawa, kamar ki ace an zubar miki da ciki?
Kai tir da halinki, Allah ya wadaran halinki." Sai
ta jefeni da katin akan fuska ta. Sadiku ya mike
jikinsa yana rawa domin bai san likitocin da
suka yi mini karin jini sun rubuta bari nayi ba
don bai san karyar da muka shirya ba, sannan
bai tsaya ya duba katin ba duk da ba komai zai
gane ba ma, ya fara magana da rawar jiki, "Don
Allah Hajiya kiyi hakuri kaddara ce da
tsautsayi....." "Da kuma sakaci da rashin
tarbiyya." Ta karbe daga bakinsa, sannan ta
dora da cewa, "Wallahi ka ji na rantse yarinyar
nan ta gama zama a makarantar nan, alfarma
daya zan iya yi maka na rubuta maka takardar
(transfer) canji zuwa wata makarantar, don ban
ga amfanin zama da daliba irin ta ba, ita ba
kokari ba sannan ga shegen iskanci ta addabi
dalibai da malamai tun yanzu tana matsayin
kwaila, ina ga ta zama babbar mace? (No i
can't) ina ba zan iya ba." ta karasa maganar a
hasale. Ni kuwa ina gefe na cika nayi fam,
domin Sadiku ya gaza rama mini cin mutuncin
da matar nan take mini, don haka na mike daga
tsugun nan da nake yi na dole, domin tun a
gida ya gargade ni na durkusa da munje kuma
na gaida ta don ta san na yi hankali. Ke! Ma ya
ishe ki haka, haka kawai zaki sanya ni a gaba
kina zagina kamar wata uwata? Ko abun da yafi
ciki nayi ina ruwanki, idan ba zaki karbe ni a
makarantar ki ba kawai kice ba zaki karbeni ba
amman kin saka ni a gaba kina zagina, ke
wayasan iskancin da 'ya'yanki suke..... Marin da
Sadiku ya dauke ni dashi ne ya sanya ni yin
shirun dole, na dinga dubansa da jin haushi
kamar nayi masa Allah ya isa, amman tunda
lallabashi nake yi ya sanya na hakura ina ta
kunkune dai. Kana ji a gabanka tana zagina ma
ko? To maza ku bar mini Ofis dina tun ban hada
ku da (security) ba, ta fadi a hasale. Ya dauki
katin da yake a kasa yace, Malama nagode, kiyi
hakuri hali ne kowa da irin nasa, sannan ya
dubeni yace idan kin ga dama sai ki taho mu
tafi. Bai jira abinda zan ce ba ya fice daga Ofis
din. Na dalla mata harara ina fadin, "Allah ya
sanya ba kece kika kawo ilimin boko duniya ba,
sannan Mangwafak ba dan gidanku ba ne, don
haka zanyi karatu a wata makarantar ko kina so
ko baki so....." "Ki fitar mini daga Ofis dan
ubanki ko na sanya a zane mini ke ko na hada
ki da 'yan sanda su kulle mini ke wallahi
shegiyar yarinya mara kunya kawai karuwa.....
Na ce, "Kin ga karuwa dai a gidanki ba niba."
Ina gama fadin haka na ficewata ina hangota
sanda ta zauna a kujera cike da bacin rai da
bakin ciki mara misaltuwa, na dai ji dadi don na
rama wulakacin da tayi mini. Bayan mun dawo
gida Sadiku ya yi kamar ya cinye ni don bala'i,
yace kuma babu ruwansa da ni, don haka na
rasa yanda zan yi na koma karatun, don na
gane idan mutum yana zuwa makaranta yakan
rage 'yan sa ido. Daga karshe dai Sister Asibi ce
ta yi mini hanya na koma Sheka da karatuna,
acan dai na kammala Secondary dina, bayan
sakamako ya fito babu lafi na samu admission a
FCE, domin a wancan lokacin ba'a tsaurarawa
gurin makin jarabawa, don haka da 2 credits 2
passes na sami admission. A wannan lokacin ne
na kuma wayewa na san lallai da kai na a duhu
yake, duk da dai ba wani karatun ne a gabana
ba, na hadu da malamai 'yan ban gishiri na
baka manda da taimakonsu na kammala. Dai-
dai lokacin da na kammala karatuna na hadu da
wani dattijo ma'abocin son holewa DPM ne a
wata karamar hukuma. don haka tunda ya
kyalla idon sa a kaina ya makale mini, shine dai
ya kawo min takardar fara aiki (upper) har gida
tun sakamako na bai fito ba, don haka na fara
aiki na, amman fa a kanyi wata banje Ofis ba
domin dai ina da manya a sama, sun ajiye ni a
cikin Sakateriya bangaren (Accountant), mai raba
kudi, don haka Salary bana wasa nake samu ba,
duk da ba abinda na karanta kenan ba kasan
Nigeria jaga-jaga inji wani mawaki, don wallahi
wadanda muka yi karatu dasu da dama basu
sami aiki ba har yau, kuma yawancinsu sune
masu kokarin sun fito da first class amman da
yake basu da wani a sama suna zaune, kai
Nigeria sai a slow wallahi." Ya yi dariya yana
fadin, "Wallahi ke din nan 'yar buyagi ce, ni
kaina wani lokacin tsoro kike bani, barin ma
yanzu, don haka ne ma na dinga jin tsoron
dawowa don kada kiyi mini buyagin naki." Ta yi
dariya gami da kai masa bugu na wasa, suka
kama dariya gaba dayan su, sannan ya gyara
zama yana kuma shinshinarta kamar wata diyar
mage sannan ya fara bata labari kamar
haka.Kamar yanda kika sani daran da yayanki
Sadiku ya yi mini wannan wulakancin na tafine
raina a tsananin bace, domin tun da nake ba'a
taba mini wulakanci kwatankwacin wannan ba,
don haka na kudirta a raina na hakura dake
tunda daman yace duk randa ya kuma ganina a
kofar gidan ku sai ya sanya an jefe ni, ni kuwa
bana son iyayena su san halin da nake ciki sam.
Sai da na koma gida ne ma sannan na tuna da
abinda ya kaini gurin ki, don muyi sallama ne ni
zan koma makaranta duk da na san ban taba
gaya miki hutu nazo ba. Sai da tafiyar ta kama
gadan-gadan sannan na ji wani irin masifaffan
son ki yana bijiro mini da kewar ki, amman na
dake don ina ganin da zarar na bar garin duk
zan daina ji, don haka na bar Kano da zummar
na bar Zainabu Abu na nufi birnin Califonia. Sai
dai tunda na isa garin na jini kamar wani mara
lafiya, surarki da kamar ki ta dinga bijiro mini
don haka na yi zaton ko kewar ki ce, don haka
na fara mu'amala da mata kala-kala masu kyau
masu ilimi har ma da masu dukiya, amman sun
gaza gamsar dani kamar 'yar kwaila Zainabu,
amman na dinga yaudarar kai na da lallai sai na
manta Zainabu, duk macen da na kalla sai naji
na raina ta burin yana ga Zainabu, na ki na
dawo hutu don ina ganin idan na dage zan
manta dake din, sai dai iyayena suzo mini hutun
can, har na kammala karatuna kina nan a raina
na kuma baiwa kai na wani lokacin na mantawa
da ke, don haka na fara aiki a can duk da ba
haka iyayena suka so ba, sai dai shi Mahaifina
mutum ne mai saukin kai da baiwa mutum
damar sa inda yaga babu cutarwa a kanta. Dare
daya na ji duk iyakacin dauriyata ta kare,
musamman da nake ta fama da yawan ciwon
kai da aka auna ni akace na rage sanya damuwa
a raina, na yadda muddin na cigaba da zama a
can ciwon zuciya yana gan da kamani saboda
yawan tunani, na yanke shawarar zan dawo
Nigeria na neme ki amman a wannan karon
auranki zan yi, don na gane kece kadai nake so
a rayuwa ta, na kuma yi kokarin jifan tsuntsu
biyu da dutse daya don daman iyaye na sun
damu da lallai na dawo nayi aure.Sai dai idan
na tuno ki sai naga kamar na rasa ki ko kin yi
aure, da zarar na tuno hakan sai naji duk
hankalina ya tashi, na yawaita sallah da rokon
Allah ya sanya baki yi aure ba, da wannan
shawarar na dawo gidan Nigeria, da zummar ko
a yaya na sameki zan aure ki, don ban yi zaton
Abun da na sani zata koma mace mai girma da
daraja da aji kamar haka ba, don dai a yanzu so
ne tsagwaransa a raina ba wata sha'awa ba. Sai
dai na sha mamaki a yanda na ganki a yanzu,
nasan tun a can baya kina da kyau don yana
daya daga cikin abunda ya sanya nayi mu'amala
dake, ga tsabta koda yaushe zaki wuce ta gaba
na sai na ganki tsaf dake, takalminki kamar ba
kya sakawa.Don haka Zainabu ba da wasa na
dawo ba da zummar na aure ki na dawo, don
haka bana son a dauki wani lokaci mai tsaho,
sannan dole ki daina kula 'yan iskan samarin
nan naki don ina da kishi mai tsanani, shi ya
sanya a wancan lokacin ma nayi kokarin ganin
baki kula kowa ba, don haka Zainabu gani
gabanki da kokon barata ina fata zaki amince da
bukata ta." Tayi dariya cike da jin dadi ta ce,
"Lallai Mustafa ka debo ruwan dafa kanka, ta
yaya zaka ce kai kadai zan dinga kulawa bayan
ba mijina kake ba? Ai hakan ba mai yiwuwa
bane ba." Ya mike zaune yana mata wani duba
idonsa fal da masifa ya ce, "Wallahi kina so ne
na fara rotse a kofar gidanku, don duk dan
iskan da yayi mini rainin wayo a kanki zan yi
maganinsa, da can sun yi yanda suke so, yanzu
kuwa mai guri ya zo kowa sai ya matsa ya bashi
gurin sa, duk mai neman kansa da arziki.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta makalkale shi tana dariya ganin yanda yake
masifa kamar zai rufe ta da duka, suka kama
dariya don tana masa irin salon ta da take siye
masa zuciyarsa. Bugun kofar da akeyi ne ya
fargar da su, Zainabu ta mike da sauri tana
fadin, "Ina zaton shegiyar nan ce ta dawo." Ta
dubi agogo sha daya da minti uku, sannan ta
nufi kofar da sauri tana kokarin budewa. Asma
ta shigo da gudu tana ihu da dariya tana fadin,
"Shegiyar ashe akwai mai maganin iskancinki,
gaskiya Mustafa ka ci a baka na daya, ya ci a
sara maka wallahi, don kayi mana maganin mai
shegen taurin kan nan." Mustafa ya mike tsaye
yana dariya sannan ya ce, "Daman ke muke jira
mu wuce." Ya mika mata makullin sannan ya
dubi Zainabu ya ce, "Ke madam sai ki shirya na
sauke ki a gida ko, don na san idan na tafi
wannan dan iskan ne zai zo ya dauke ki." Suka
fashe da dariya ita da Asma har da tafawa, yayi
murmushi yana fadin, "Lallai kwa yi mini dariya
don kun san kun kama wuya na, ni kam na
wuce mota kya tadda ni a can." Har ya kusa
kaiwa kofa sannan ya tsaya yana fadin, "Ahaf!
Hajiya Asma na gode kuwa zan gan ki." Tayi
dariya tana fadin, "A'a don ni kada ka damu
babu damuwa ai duk yiwa kai ne, don bani da
kamar Zainabu duk Kano." Yayi murmushi ya
ce, "Na dai gode din sai mun sake haduwa."
Sannan ya fice. Asma ta kalle ta gami da
fashewa da dariya su dukan sannan suka tafa
Asma ta ce, "Wallahi kawata kin iya iskanci, ki
dubi yanda kika juyar da zuciyar dan talikin nan
a lokaci kankani don Allah, don Allah yaushe ne
zaki sanar da ni sirrin nan ne?" Zainabu ta tafi
tana fadin, "Sirri ne abin." Asma ta bita da gudu
tana fadin, "Haba kawar, ki taimaka mini don
Allah." Zainabun tayi dariya sannan ta ce, "Ki
bari sai mun hadu kinga yanzu lokaci ya kure,
don zumana yana jirana a mota." Suka kuma
fashewa da dariya, sannan Asma tace, "Lallai
Mustafa ya ciri tuta don ban taba jin kin ambaci
wani namiji da ko sunan da iyayansa suke gaya
masa ba, daga shashasha sai dan wahala ko dan
akuyan can, amman Mustafa yaci Zuma gaba
daya ma." Zainabu ta zame da sauri ta falla da
gudu tana fadin, "Malama ki kyale ni haka nan,
kina bata mini lokaci." Sanda suka isa gida duk
'yan biki sun gama watsewa sai dai sauran
kwadayayyu, sun jima a mota suna sallama
sannan ta fita tana takawa da tafiyarta ta
daukar hankalin 'yan maza, sai da yaga shigarta
gida sannan ya ja motar tasa cike da tsananin
sonta, da wani nishadi da farin ciki.
Tana shiga Sala ta kama yi mata sannu da
zuwa, ta sami kujera 'yar tsugunne ta zauna
don cike take da nishadi. Sala din ta kama
murmushu don ganin diyar tata a cikin farin ciki
sannan ta ce, "Hala yau diyar tawa ta hadu da
mai barin dala ne naga bakin naki ya ki
rufuwa." Ta yi 'yar dariya sannan ta ce, "Sala
kin san abun mamakin da ya faru kuwa tun
daran jiya?" Bata bari ta bata amsa ba ta dora
da cewar "Mustafa ya dawo." Da mamaki Sala
din tace, "Mustafa kuma? Waye me wannan
sunan, ba dan dan banzan yaron nan da ya
cuce mu shekarun baya ba can?." Zainabu ta
bata rai matuka kamar zata yi kuka, ganin haka
ya sanya Sala din ta tsuke bakin ta, don ta yi
zaton zata yiwa Zainabun gwaninta ne, don ta
san irin alwashin da taci akan Mustafa. Ita kam
mikewa tayi tana fadin "Ashe daukar hakkinsa
muka yi daman, don ba laifin sa ba ne." Ta sha
ruwa a randa sannan ta dawo ta gaya mata duk
yanda suka yi da Mustafan. Sala din tayi dan
murmushi tana fadin, "A'a lallai bashi da laifi to
mun yafe masa." Zainabu ta ji dadin abunda
Sala din ta fadi, don haka ta mike tana dariya
sannan ta ajiye mata damin 'yan dari dari na
dubu ashirin tace, "Sala gashi nan kya kashe."
Sala din ta dauka tana dariya sannan ta ce, "Ke
Zainabu ba kya gajiya? Na ga fa kin sha
kacaniyar biki kwanan nan." Zainabu tayi dariya
tace, "Ai Mustafan ne ya bada ya ce a baki kya
sha ruwa kafin yazo bada hakuri da kansa." Sala
ta fashe da wata wawiyar dariya sannan ta ce,
"Kayya ki gaya masa ya kwantar da hankalin sa
komai ai ya wuce gashi kin ce daman ba laifinsa
ba ne." Ita dai Zainabu daki ta shige domin tayi
baccin gajiyar kwanakin da bata yi ba can baya,
kafin yamma tayi su hadu da zuman nata
************
Cikin kwanaki kalilan soyayya da shakuwa ta
kuma shiga tsakanin su, duk da suna rikici duk
lokacin da Mustafa ya ga Zainabu da wasu
Musamman Alhaji.... Dan haka duk inda tasan
zata gamu da samarin ta kan guje masa don
bata son ace kullum suna samun sabani da
Mustafa dan yana da matukar kishi, su kuma
sun gaza hakuri dan duk kusan namijin da ya
fara mu'amala da Zainabu bai iya daina wa dan
ta fiye fitina da yawa, sai dai idan Allah ne ya
kwato shi daga hannunta. Shi kam Mustafa
kullum hankalin sa a tashe yake dan bai kaunar
ya ga Zainabu da wani, dan haka nema suka
yanke shawarar yin aure a wannan lokacin. Shi
kam yana shakkar tinkarar Momin sa da
maganar auren nasa don ya san ta bata san
wargi sam ita, ga shi daman kullum tana masa
maganar ya zabo mace cikin 'yan matan gidan
ko kuma ya duba cikin 'yan uwa masu tarbiyya
dan bata son yayi zaben tumin dare, sai dai shi
a iyakacin ganinsa daga 'yan matan dake cikin
danginsu har na waje bai ga wacce tayi masa
kamar Zainabunsa ba. Yau ya tadda Momin
nasa a karamin falo, 'yan matan ta suna
karamin falo suna kallo sai musu a keyi tsakanin
'yan matan, don gidan nasu bai rabo da 'yan
mata na 'yan uwa dan su basu da yawa su biyu
ne kacal, gashi Momin su tana da son jama'a
dan haka koda yaushe gidan a cike yake banda
masu zama dindindin, banda kuma wadanda
aka aurar, dan haka tunda ya ga take-taken
Momin na su na son ta hadashi da wata a
cikinsu shi ya sanya ba ko da yaushe yake sakar
musu fuska ba. Ya shiga falon da sallama, ita
kadai ce don ya baro Alhajinsu a falo da baki, ya
isa gaban ta ya gaishe ta, sannan ya koma
babbar kujera ya zauna, ya dubi tibin inda yaga
hankalinta ya karkata. Yakin Falastinawa ne dai
da Isra'ilawa wadanda kanwa uwar gami
America ke daurewa gindi, ana nunowa a tashar
C.N.N. "Kai wadannan mutanen wallahi
azzalumai ne, ka dubi yanda suke kashe farar
hula da basu ji ba basu gani ba, sannan su yi
farofagandar basa taba farar hula, Allah dai ya
bi musu hakkinsu kuma ya nuna musu karshen
su, Amin." Hajiya Kubra ke fada da bacin rai.
Mustafa ya ce, "Haka ne Momi, sai dai idan kika
duba daman can zaki ga abun nasu bawai suna
yi bane don wani abu sai don su yaki addinin
musulunci kawai, yanzu fa idan kika shiga
kasashen turawa da gemu sai kaga an mai da
kai wani abin tsoro saboda sunyi farofagandar
batawa musulmi suna a idon duniya, dan ma
yanzu Allah yana nuna musu ishara mutanan su
turawa sai musulunta suke, musamman
matansu kamar su Kristian Barkeu da 'yar uwar
tsohon shugaban kasar Birtaniya Tony Blair,
Laurent Bothh wacce ma'aikaciyar jarida ce, da
sauransu, shine fa muke dan samun sassauci a
gurinsu, abun nasu dai sai addu'a." Ta amsa da
"Amin, ina wai ka shiga ne?, tun da safe nake
saka rai da shigowarka amman shiru." Gabansa
ya fadi, don yanzu sam bai zama a gida kullum
suna makale da Zainabunsa, amman sai ya
dake ya ce, "Momi kin san ina fafutukar fara
aikin tun da sun bani (offer), takardar daukar
aiki, shi ya sanya yanzu bana zama." Ta ce,
"Lallai kam haka ne, Allah dai ya taimaka ya
sanya a fara a sa'a." Ya ce, "Amin." Sannan ya
kama inda-inda don ya rasa ta yanda zai gaya
mata. Hajiya Kubra ta dube shi tana dariya tace,
"Babana duk yanda aka yi da magana a bakin
nan naka." Da yake sunan Baban ta ne da shi.
Ya yi murmushi yana sosa keya ya ce, "Momi
sirika na yi miki shine nake kunyar sanar da
ke."tayi dan murmushi dan ba hakan taso ba
taso ace anyi 'yar gida, amman sai ta danne
dan tana son yayi auren, dan haka tace, "Lallai
kam kace yau zanyi kwanan farin ciki, a ina ka
samo matar taka ko a can American ne?" Yayi
dariya ya ce, "A'a Momi a can dai unguwar da
muka taso take, can kasan layinmu na da,
sunan ta Zainabu." Ta ce, "Lallai kam, Allah ya
tabbatar mana. Waye kuma Babanta, a wane
gida take ne ma?" Da sauri ya ce, "Sunansa
Malam Abubakar." Tace, ai shike nan bari Alhaji
ya shigo sai a sanar da shi, amman dani na so
ace cikin 'yan uwanka da suke gidan nan ka
zaba, amman tunda Allah ya kaddara matar
taka a waje take ba zamu ja da ikon Allah ba,
sai dai muyi addu'a Allah ya tabbatar mana da
alkhairi kawai. Ya ji dadin abunda ta ce, yayi
mamakin kuma saurin shawo kanta da ya yi,
duk da saurin daukar zafin ta. Daga nan suka
cigaba da hirar su a cikin hirar nema take cewa
tana fatan zainabun tasa mai hankali ce da
nutsuwa. Ya ce, "Momi ko ke kika ga Zainabu sai
kinyi sha'awarta, ta kammala diplomarta yanzu
haka tana aiki ne." Tace, "To ai shike nan, na
san dai sai Baban ku ya sanya anyi masa bincike
don kada ayi zaban tumun dare." Kirjinsa ya
bada ras-ras, amman dai ya dake yace, "Na san
ma babu wani aibu da zai tadda ga Zainabu in
dai ya sanya mutanan kirki a binciken ba
munafukai ba." Tun daga sannan ya ji hirar ta
fita daga ransa gaba daya, don bai san irin
abinda za'a ce akan Zainabunsa ba, shi kam yaji
ya gani dan haka koma me zai faru sai dai ya
faru amman shi dai da ikon Allah sai ya aure ta.
Da haka yabar dakin mahaifiyar tasa ya nufi na
shi, amman yana cike da tunanin abunda zai
biyo baya idan suka san wacece Zainabu.
Kwanaki biyu shiru babu wanda yace masa ko
kala akan maganar, shi kam ya damu kwarai ya
ji anyi masa zancan, dan Baban sa ma da suka
yi maganar da Hajiya Kubran abinda ta fadi ya
maimaita, cewar zai sanya ayi masa bincike
sosai. Ya sami wani tsohon abokinsa acan
unguwar da suka taso ya ce don Allah ya bashi
amana ya binciko masa labarin wata yarinya
Zainabu diyar Malam Abubakar kamar yanda
aka ce masa, sai dai abokin nasa ya dan sami
matsala da farko dan duk wanda yace wa sun
san Zainabu diyar Malam Abubakar sai suce
gaskiya basu san taba, mutum hudu ya tambaya
amman duk ba'a dace ba. Sai da ya isa
majalisar da yake zama ya fara kawo maganar
neman Zainabu da yake yi, sai wani cikin
abokan hirar tashi yace, "Ko dai Zainabu diyar
Baba Abbakar mutumin Sudan din nan ake nufi,
in dai itace kuwa bai yi mata ba, domin dai
kowa yasan karuwar gida ce, duk da babu kyau
suka akan maganar aure amman tunda dai
amana ya baka sai ka sanar da shi gaskiya in
dai ita ce din, da dai kanwarta da aka yiwa aure
kwanaki ce ma da sauki dan ba halinsu daya
ba." Nan suka hau sanar dashi irin halinta dan
gaskiya shi ma'aikacine bai fiye zama ba sai
karshen sati kuma yawanci hirar siyasa suke yi
da matsalar da kasar ke ciki. Ba shi da wani ja
Zainabu diyar Baba Abbakar ce dai dan abokinsa
yake nema, dan haka ya je ya sanar dashi
yanda suka yi, daga karshe har kofar gidan su
Zainabun suka zo tare ya nuna masa. Haka nan
Alhaji Abdullahi ya koma gida jikin sa sanyi
kalau, domin dai ya tabbatar da lallai itace
wacce dansa ke so, shi kuwa duniya sam bai san
ya takurawa dan sa, yaso ace Zainabu da dan
sa yake so ta kasance kamila ce ba lalatacciya
ba, kafin ya shiga sallar Magariba ya kirawo
wayar Mustafa yace lallai idan an idar da sallah
yana son ganinsa,babu bata lokaci Mustafa ya
iso gidan dan kusan tare ma suka yi sallar Isha'i
da Baban nasa, ya dade a raka'ar karshe yana
addu'ar Allah ya sanya Zainabu ta zama
rabonsa, don yaji muryar Mahaifinsa kamar da
zafi shi ya sanya duk ya kidime. Ya riga Baban
nasa shiga gida, Momin nasa ta zuba masa
abinci amman ya gaza ci duk da uwar yunwar
dake addabarsa, dan kada ma Momi ta zargi
wani abu ya sanya ya dinga tsakurar kadan
yana ci har ma taso ta gane. Ta dubeshi da
kulawa ta ce, "Baba anya wani abu baya damun
ka? Na ga kwana biyu duk ka wani shiririce,
balle yanzu ka gaza cin abinci sai tunani." Ya
kakalo murmushi yana fadin, "Laaa! Momi me
kika gani? Babu komai gajiya ce dai kawai."
Ganin tana son ta gano shine ya sanya ya saki
jikinsa yaci abincin sosai, har Baban nasa ya
shigo, ya shige sashinsa ya kira Hajiya Kubra ta
wayar gida (land line) ya ce, "Baba ya shigo ne?
Idan ya shigo kuzo tare ke da shi." Ta amsa da
"Ya shigo, ga munan zuwa." Bayan ta ajiye
wayar ta dube shi duk ya sha jinin jikinsa ta ce,
"Alhaji yana kiranka." Sannan ta mike ta nufi
sashin Maigidan nata yana biye da ita a baya
har suka isa. Mustafa bai zauna akan kujera ba
a kasa ya zauna ya sunkuyar da kansa yana
gaida Baban nasa, fuskar sa babu annuri yake
amsawa, ba kamar yanda ya saba amsa masa
da sakin fuska ba, hakan ne ma ya sanya gaban
Mustafa ya cigaba da faduwa dan yana ganin
lallai wani abu yana shirin faruwa. Sun jima a
haka yana cigaba da duba jaridar leadership da
suka taddashi yana dubawa, labarin ya dauke
masa hankali wanda aka ce wai waye ya haifi
Obasanjo, sai da ya karasa shafin da yake
sannan ya daga kai yana duban Mustafa kur da
idonsa, abinda ya kuma fadar da gaban
Mustafa. Can ya daure ya ce, "Baba ka ce
yarinyar da kake nema acan kasan layin da
muka taso take har ma ta kammala karatunra a
F.C.E ko?" Bakinsa yana rawa yace, "Haka ne
Baba." Alhaji Abdullahi ya kuma gyara zama ya
ce, "To nayi bincike kamar yadda addini ya
umurci muyi a duk sanda aka tashi neman aure,
sai dai abun takaici duk mutanen da aka
tambaya wadanda ba zasu yi karya ba sun
sanar dani ko wacece Zainabu, dan haka sam
ban yarda da tarbiyyar ta ba da ta gidansu ba
ma gaba daya, don haka kaje ka nemo wata, ba
zan maka auren dole ba amman ya dace ace ka
samo mace mai mutunci da daraja a idon
duniya." Hankalin Mustafa ya yi mugun tashi
ransa ya baci, makwallaton sa sai kaiwa da
komowa yake yi, duk da sanyin A.C da fankar
dake dakin basu hana shi yin gumi ba, da kyar
ya iya bude bakin sa yace, "Baba kayi hakuri
bawai zan maka musu bane, ni na san Zainabu
diyar kirki ce, ka san halin mutanan yanzu ba
duka ne ke fadar gaskiya ba, dan haka ma
yanzu idan za'a yi aure ba'a cika zuwa a
tambayi mutanen unguwa ba, dan basu kaunar
wani ya cigaba, dan haka nasan zasu iya yiwa
Zainabu sharri dan haka ina neman yardarka
akan na auri Zainabu, watakilama ba wacce
nake so aka gaya maka ba." Alhaji Abdullahi yayi
dariya dan shi yana da hakuri da bin komai a
sannu ba kamar Hajiya Kubra ba mai saurin
daukar zafi ba da saurin fushi, sannan ya ce,
"Baba bana shakkar ba Zainabun da kake nema
aka sanar dani ba, amman bari nayi maka wasu
tambayoyi idan har ba ita bace shike nan." Ya
goge zufar dake tsats-tsafo masa ba tare da ya
iya cewa komai ba Baban nasa ya fara jeho
masa tambaya"Asali Abu ake ce mata sanda
tana yarinya, yanzu ne ake ce mata Zainabu
ko?" Ya ce, "Haka ne." "Kuma da can tana tallar
abinci da gyada da dai sauransu ko?" Ya hadiyi
wani yawu dan dai ya san lallai Baban nasa ita
ya gano, da kyar ya iya cewa, "Haka ne." "Tana
da wani Yaya mai suna Sadiku wanda shi ba irin
halinta gare shi ba, da kuma wata kanwarta da
aka yi mata aure kwanaki ba ko?" Yayi shiru bai
bada wannan amsar ba dan dai ya san Babansa
yayi bincike matuka akan Zainabu. Alhaji
Abdullahi ya cigaba da bayanin sa duk da bai
bashi amsa ba, "Babanta mutumin Sudan ne,
sunan shi Baba Abbakar, kuma ana kiran
Babarta da Sala....." "La'ilaha Illallahu! Yanzu
wannan karuwar yarinyar kake so Baba?" Hajiya
Kubra ta amshe zancen tun bai kai ga bada
amsa ba. Jikin sa ya kama rawa da rawar murya
ya ce, "Momi ba karuwa bace, don dai tana
aikine a (Local Govt.) ne shi ya sanya ake mata
kallon 'yar iska, wallahi ina sonta Baba kayi
hakuri don Allah, sharri kawai aka yi mata."
Hajiya Kubra ta amshe, "Sharrin gidan Uwar wa?
Ai ni sai yanzu ma na gane da ka fadi sunan
Mahaifinta Abbakar da sunan Babarta, yarinyar
da tun tana 'yar labubuwarta take iskanci, har
ciki aka zubar mata tana da shekara sha hudu a
duniya." Mustafa ya ce, "Kin ji ba Momi, sharri
ne aka yi mata dan ana....." "Sharrin Uwarka? to
tsaya ka ji na sanar da kai, na san Zainabu
shekarun da suka wuce, yarinya ce mara
mutunci kuma mara kunya dakikiya, ta addabi
kowa, duk wannan lami ne ma akan iskancin da
take yi." Ta dubi mijin nata tana magana, "Alhaji
idan baka manta ba na taba baka labarin wata
'yar iskar yarinya shekarun baya da tayi mini
rashin kunya har cikin Ofis dina, lokacin ina
makarantar 'yan mata ta Dala (G.G.C DALA), dan
ranar da tayi mini rashin mutuncin nan kasa
bacci nayi, don har sai da jinina ya hau, har yau
ina addu'ar Allah ya hadani da yarinyar nan
nayi mata rashin mutunci amman har yau Allah
bai hada mu ba, sai daga baya ma na ji 'yar
unguwar da muka baro ce a bakin wata 'yar
ajinsu, sai yanzu zaka ce kana son ta wai kuma
da aure ma? Ai ko da ku biyu kuka rage a
duniyar nan ba zaka aure ta ba muddin ina
raye." Ya dafe kansa idonsa ya kada yayi jajir
yana fadin, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
Dan ya riga ya gano Momi ta san komai, ta san
Zainabu farin sani, ashe ita ce wacce take bashi
labari din nan, sai dai ya rasa ta yaya zai sanar
da su wannan cikin da take tsanar Zainabu
saboda shi dan ta ne yayi shi, ta yaya zai ganar
da su shine ya fara lalata Zainabu tun a wancan
lokacin da take zarginta, duk da ya tadda
Zainabu da wasu muggan halaye amman shine
ya koyar da ita kashi saba'in cikin dari. Ya yi
tsamo-tsamo da shi kamar wanda kaza ta
fashewa a cikin sa, bashi da damar da zai kuma
musa musu abinda suka fadi, don idan yace na
Babansa sharri ne to na Momin sa fa wanda
Zainabu da bakin ta ma ta bashi labari, a sanda
take bashi labarin bai yi zaton Mahaifiyarsa bace
dan shi ko tambayar ta makarantar da take bai
taba yi ba balle har ya gano hakan ba. Alhaji
Abdllahi ya katse masa tunaninsa ta hanyar
fadin, "Baba ka sani ba wai muna kin Zainabi
akan kanta bane, A'a muna kin Zainabu saboda
halinta, don babu wanda zai so ace yau ya hada
zuri'a da lalatacce, da ace irin halin kanwarta
gareta babu abinda zai hana mu kyaleka ka
aure ta, dan haka ina baka shawara da lallai ka
koma ka sake nemo matar aure dan wannan
bata yi ba."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Idan Zuciya Tagyaru1-05
Posted by ANaM Dorayi on 08:00 PM, 03-Feb-16
Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU
_____________ Na
________Fauziyya D Sulaiman_____
"Yo to banda abunsa ma a gidan nan wacce irin
mace ce babu kuma masu tarbiyya da kyau idan
ma shine ya rufe masa ido, don haka ka kwantar
da hankalinka ka zabi wacce ta dace da kai duk
'yan uwanka ne." Alhaji Abdullahi ya amshe, "Ki
na ji Kubra, ba wai dole sai anan gidan zai zabi
mata ba don zai iya yiwuwa bai ga wacce ta dace
da ra'ayinsa ba, ya je ko ina ya samo mata in dai
diyar musulunci ce kuma mai tarbiyya." Shi kam
duk bai fahimtar duk abinda suke fada don sam
hankalinsa baya jikin sa, ji yake kamar ya dora
hannu a kansa yayi ta zunduma ihu kawai ko ya
ji sanyi a ransa. Alhajin na sa ya ce, "Ka tashi ka
tafi Allah ya zaba maka abinda yafi zama
alkhairi." Ya mike da kyar yake iya daga kafarsa
yana hada hanya tamkar wanda ya sha giya ko
kwayar sanya maye, idanuwansa sun kada sun yi
jajir da su kamar gauta, har ya fice basu ce
komai ba illa binsa kawai da suka yi da kallo.
Hajiya Kubra ta ja tsaki tana fadin, "'Ya'yan yau
ba'a iya musu, banda haka daga ganin yarinya
baka san halin ta ba ka dage sai ka aure ta, ni
abun ma mamaki yake ba ni, yaushe har ya
dawo garin nan suka kulla soyayya da
hatsabibiyar yarinyar nan har ta dauke masa
hankali haka? Duka baiyi ko cikakkaken wata
guda a garin nan ba, ni ko bayan raina ba zan so
ya auri diyar nan ba, Wallahi Alhaji dan baka san
ta bane sam bata da kunya da ladabi ko miskala
zarratin, tuntuni na tsaneta wallahi." Alhaji
Abdullahi ya kuma gyara zama cike da tashin
hankali dan dai yana tausayin dan sa, don ya
gane ba karamin so yake yiwa Zainabu ba ya ce,
"Ai haka Allah yake ikonsa, shi kadai yasan a inda
suka hadu, sai dai muyi masa addu'ar samun
mace ta gari, da addu'ar ita kuma Allah ya shirya
ta." Hajiya Kubra ta ce, "Amin dai." Shi kam
Mustafa da kyar ya iya kai kansa sashinsa saboda
tsananin tashin hankalin da yake ciki, dan Allah
ya sani duk duniya baya ga iyayansa babu
abinda yake so sama da Zainabu, ya sani
Zainabu wata tsoka ce a cikin jikinsa mai yawo da
jininsa, a da can baya yana daukar son Zainabu
shirme kuma shiririta a zuciyarsa, sai dai a yanzu
ya sani muddin bai auri Zainabu ba lallai kam
rayuwarsa tana tare da hatsari. Ya kwanta
rigingine a gadonsa ya rintse idonsa, ina ma zai
iya kuka da lallai yayi ko ya sami sassauci a cikin
zuciyarsa. "Zainabu! Zainabu!" Ya fadi a hankali
ko ya ji sanyi a zuciyarsa, ya sani hakkin Zainabu
da sauran matan da ya cuta ne Allah ya saka
musu ya jarabce shi da son macen da ya raina a
da can, lallai da iyayansa sun san irin yanda yake
son Zainabu da sun barshi ya aure ta ko yaya
take. Haka nan ya dinga juyi a gadonsa bai san
sanda bacci barawo ya silalo ya dauke shi ba,
don yana cikin tsananin tashin hankali. Da asuba
da kyar ya iya tashi dan jikinsa duk ya masa
nauyi, a masallaci ya jima yana addu'ar Allah ya
karyo da zuciyar iyayansa su amince ya auri
Zainabu, har gari ya waye yana ta lazimi, sam ya
manta da zuwa Ofis dan haka sai da ya makara.
Ko da ya isa dinma kasa tsinana komai ya yi,
banda kallon hoton Zainabu dake bisa tebur
dinsa babu abinda yake yi, ya sani muddin
iyayansa suka hana shi ya auri Zainabu to kuwa
lallai zai jima bai yi aure ba, kai babu ma rana.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ya nufi kujerar da ke Ofis din doguwa ya kwanta
yana neman layin wayarta, bugu daya ta dauka.
Ita ce ta fara magana, "Hello My honey, Zuma
ta."Ta fadi da wata irin murya mai tsananin fisgar
hankalinsa, wacce ta ke siye zuciyar 'yan maza da
ita. Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce, "Zainabu ina
tare da matsala mai girma, na rasa yanda zanyi
da rayuwata ba ni cikin hayyacina da walwala ta."
Ta ji gabanta ya fadi amman sai ta dake ta ce,
"Ayya Zumana ka kwantar da hankalinka komai
zai zamo da sauki Insha Allah, ka na ina ne
yanzu?" Ya lumshe idon sa kana ya bude ya ce,
"Ina Ofis yanzu amman na gaza komai, ji nake
kamar bani da lafiya ma." Ta kuma kwantar da
murya ta ce, "Kana jina ko zumana, ka kwantar
da hankalinka gani nan zan zo yanzu Ofis din
naka don bani son bacin ranka....." "A me zaki zo
ne?" Ya tambaye ta da sauri. Ta yi murmushi don
ta san Mustafan ta da shegen kishii ta ce, "Ka
kwantar da hankalinka zan zo a shatar tasi ne,
don nima ina Ofis yau." Ya ce, "Yayi kyau, ina
jiranki kada ki jima." Ta dubi abokin aikin nata da
yake kallonta tamkar maye sai dai duk iyakacin
jarabarsa da gulmarsa ya gaza jin abinda take
cewa, ta galla masa harara kana tace, "Wallahi
Oga kai mugun dan saka ido ne, wannan kallon
da kake mini fa kamar maye?" Yayi dariya yana
sosa keya ya ce, "Ke din Zainabu da tsokano
mutum kike, banda ni waye zai daure zama da
zukekiyar mace irinki yana kallonta..... yanzu dai
ina zaki naga kina shirin fita bayan yanzu D.P.M
yayo waya zai zo." Ta yamutsa fuksa tana fadin,
"Idan yazo kace masa na fita idan da dama zan
dawo." "Zainabu ki yiwa Allah ki tsaya idan
ba....." Ko kuma bi ta kansa bata yi ba ta fice
abunta ya bita da kallo yana girgiza kai sannan
ya ce, "'Yar jidali, yarinyar nan kina gara zama
wallahi, ko da yake kin isa ne." Ta isa Ofis din
nasu cikin wani ubansu leshi, zanin ya zauna
dam a kugunta rafa ne,rigar bata fiye girma ba
don da kadan ta iya wuce cibiyarta, sai dai
hannunta dogo ne, yanayin kirarta ta kalangu ya
fito sosai duk wanda ya kalleta sai ya kara sai dai
mai karfin zuciya, kamshinta ka dai zai iya sanya
ka kalle ta balle kyau da tsarin tafiyarta.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta murda kofar Ofis din ta yi sa'a kuwa a bude
take don yasan zata zo, ta san Ofis din dan kusan
tare suka tare ma, ta shiga da sallama, yana bisa
kujera yayi tagumi, har ta isa inda yake bai motsa
ba sai dai idonsa yana kanta har lokacin. Matuka
kwalliyar ta burge shi, ta isa ta zauna bisa
cinyarsa ta janye hannunsa daga tagumin da ya
yi, ta shafi gurin tana magana kasa-kasa,
"Zumana waye ya taba mini kai?, hankalina a
tashe na iso Ofis din nan." Ya daga idonsa yana
dubanta, abinda ya kuma bata tsoro don ganin
idon yayi jajir da alamar tashin hankali, ta kuma
shafar fuskar sa abinda ke sanya shi jin sanyi a
ran nasa ta ce, "Zumana ka sanar da ni abinda
ke faruwa wallahi hankalina a tashe yake." Ya
lumshe idonsa sannan ya fara magana har
lokacin tana shafar fuskarsa yace, "Hajiya Kubra
tsohuwar Shugabar makarantar ku ta G.G.C Dala
wacce kika yiwa rashin kunya itace Mahaifiya
ta....." Ta mike a zabure gami da dafe kirji tana
fadin, "Innalillahi wa inna ilahihi raji'un, na shiga
uku, Mustafa yanzu Hajiya Kubra Mominka ce?
Wayyo Allah na yanzu ya ya zan yi? Ina fatan
baka sanar da ita ko ni wacece ba?"Ya ware
idanuwansa wadanda suke jawur yana fadin,
"Zainabu babu hanyar fita, Momi ta sanki farin
sani kuma tasan kece Zainabun da nake so yanzu
a raina, Baba na ya sanya anyi masa bincike a
kanki matuka, ina sonki Zainabu amman iyayena
sun hanani auranki, abunda basu sani na yanda
Zainabu take haka ma dan su yake, amman na
rasa ta yanda zan sanar dasu abinda suke gudun
Zainabu saboda shi na dansu ne." Jikinta ya
dauki rawa dan ta shiga tsahin hankali matuka,
ya kamo ta ya tallafe ta a jikinsa yana shafar ta,
ta yi lamo a jikinsa tana ajiyar zuciya tamkar
diyar mage, ta ayyana a ranta wannan wace irin
masifa ce ta doso su, yanda suke son juna ace an
haramta musu auran juna, don dai duniya bata
da abin so kamar Mustafa, ta gama sallamawa
kanta a yanzu shine bango majinginarta, don ta
gaji da walagigin yawon iskanci da shan bakar
azaba ta saida mutunci a gurin maza, domin dai
ta lura yanzu ta sani babu abinda ke tattare da
bin maza sai bata da sai da mutuncin kai,
amman gashi wani katon abu na neman ruguza
mata wannan burin nata. Ta san halin Hajiya
Kubra mace ce mai kafiya da dagewa bisa duk
abinda ta sanya a gaba, wuya da dadi basa
sanyawa ta sauya daga kan ra'ayinta, bata manta
kirarin da malamansu ke mata lokacin tana
makaranta, "Mace mai kamar maza kwari ne da
babu." Sun yi shiru na tsahon lokaci kowa da
abinda yake sakawa a zuciyarsa, sun gaza sanya
kansu farin ciki kamar yanda suka saba a duk
lokacin da suka hadu don basu gundurar
junansu. Ita ce tayi karfin hali tace, "Musty
zumana yanzu yaya zamu yi, ko shike nan mun
rabu babu mafita?" Ya kuma rungumar ta tamkar
zai maida ta cikin sa kada wani ya kuma ganinta
sannan ya ce, "Zainabu abinda nake tunani
kenan tun daga daran jiya har zuwa yanzu
amman na gaza samun mafita, sai dai na sani
ruwa ko iska da duk wata azaba basu raba ni da
sonki, ko da an rabani dake a fili ba za'a iya cire
sonki a raina ba, son ki shine so na gaskiya mai
wahalar da ruhin Mustafa da zuciyarsa." Tayi
sanyayyar ajiyar zuciya mai cike da jin dadin
kalamansa, sannan tace, "Shike nan zumana kada
ka damu ka kwantar da hankalinka mu cigaba da
addu'a, sannan mu tsaya kan ra'ayinmu na son
juna duk wuya da dadi ina ganin zamu yi nasara
komai dadewa." Yace, "Hakane Zainabu kin kawo
shawara mai kyau, har naji raina yayi fari." Ta
kuma kwantar da murya tana fadin, "Kada ka
damu ka kwantar da hankalinka ni din taka ce
har abada." Ta fara masa salon nata na jan
hankali a cikin kunnensa take fadin, "Musty
zumana (I love you so much) Ina sonka da yawa."
Bai iya hakuri da Zainabunsa musamman idan
tana masa salonta na kauna dan haka sai ya
shiga maida mata martaninta, ya ma manta inda
suke.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
**************
Abubuwa sun hadu sun jagulewa Mustafa har ma
da Zainabun kanta, don dai yanzu ba ta iya
kallon kowanne da namiji da gashin arziki idan ba
Mustafa ba, wadanda take watsewarta dasu a da
can ma ta kisu yanzu, kawarta Asma tayi mata
lallashin duniya akan ta cigaba da harkarta ko da
a boye ne amman ta gaza, dan sai dai tayi mata
wani kallon ta ce, "Asma baki san Mustafa ba ne,
shine namijin da idan ya baki zumarsa baki iya jin
dadin ta kowa, shine namijin da ya iya soyayya
mai kwantar da zuciya, shine mai kula da duk
wasu bukatu na macen da yake matukar so,
shine ya sadaukar da kansa ga Zainabu, shin kina
tunanin yana gabana da ransa zan iya kula wani
da namiji? Ki barni kawai baki san Mustafa ba
kina kallonsa ne kawai." Don haka Asma sai dai
ta zuba mata ido kawai don ita da kanta ta san
Mustafa daban ne a cikin maza kamar yanda
kawarta ke fadi. Samarin ta da dama sun damu
da wannan sabon halin da ta bullo musu da shi
musamman Alhaji Jamilu da kuma D.P.M, don
haka ma ta kashe duk wayoyinta, idan kaga ta
kunnasu lallai Mustafa zata kirawo. Hankalin Sala
idan yayi dubu ya tashi, domin dai tana ganin
kamar ana son kashe mata jin dadin diyar tane
da walwalarta, dan da farko ma fada ta kama yi
mata tana fadin, "Haba maitsada yaushe zaki
zauna namiji kwaya daya yayi ta gare-gare da
rayuwarki a banza, ki dubi irin wahalar da kika
sha a baya, amman yanzu duk kin daga
hankalinki don uwarsa tace ba zai aure ki ba, ga
maza nan kala-kala suna binki wadanda suka
fishi komai kamar su cinye ki amman kin makale
masa, dan haka ki rabu dashi kawai tunda dai
yanzu ba da bace." Ita dai shiru kawai tayi tana
ayyanawa a ranta, "Sala baki san so bane shiya
sanya kike fadin haka, da kin san irin abunda
nake ji akan son Mustafa da kin tausaya mini, zan
iya jure rashin komai amman banda Mustafa,
wannan wata jarabta ce da Allah ya doro mini."
Da dai Sala taga fada da mita ba zasu yi magani
ba sai ta koma lallashi, amman duk a banza wai
talaka ya girmi Sarki, su kuwa abokan watsewar
ta sai kyauta ta bajinta suke mata wai ko zasu
shawo kanta, amman idan an aiko ma sai dai
Sala ta karbe tana godiya tace bata jin dadi ne
shiya sanya bata fito ba. Idan mutum ya fiye
matsa mata da aike kuwa fita take yi tayi masa
rashin mutunci, don dai muguwar 'yar buyagi
ce.Haka zaka tadda ta tayi dif da tabar shaidan
ko shandy din ta a gidan Asma dan can Mustafa
ke tadda ta suyi watsewarsu acan da lallashin
juna, don ma dai shi yanzu Mustafa bai son
shaye-shayen da take yi don shi kam baya ga
taba yanzu bai shan komai sai dai idan wani yana
shan tabar shaidan a kusa dashi ya amsa yayi ja
uku ko hudu, amman giya kam tuntini ya daina
sha, don haka take rage shan su don su kan yi
fada idan ya tadda ta tana sha. Al'amura sun
kuma tsauri a gare su, don Momi ta kama shi da
hoton Zainabu wacce tayi tunanin ya rabu da ita
tuntuni ya fara neman wata ma, ta yi matukar
girgiza musamman da taji kalaman da yake
furtawa akan Zainabu din. Ta yi neman wayar sa
ne ta sanar dashi sallahun da Babansa ya bari ya
kaiwa kanin sa Kawu Sale, amman duk wayoyin
nasa a kulle suke, gashi kuma ta ga motar sa a
kofar gida abun da ya tabbatar mata yana ciki
kuma dai lokacin babu yara a gidan don haka ta
nufi sashin nasa da kanta don ta sanar dashi
sakon Baban nasa. Ta tadda shi zaune bisa
kujera ya dora (laptop) akan cinyar sa ya kura
mata idanu wadanda suke rine saboda tsabar
tashin hankali, a fili yake fadin, "Zainabu yaya
zanyi da son ki a zuciyata, ni kadai na san irin
azabar da nake sha saboda raba mu da ake
shirin yi, na gaza ganin ko wace mace da kima da
daraja don kece kadai kika san Mustafa, ba zan
iya auran wata mace ba muddin kina raye a
duniyar nan ba, san yani a kafadarki ko naji sanyi
a raina, na zama mutum-mutumi sai yanda kika
yi dani Zainabu." Hankalin Hajiya Kubra yayi
mugun tashi da jin kalaman da Mustafa ke
furtawa, ta kuma jin tsanar Zainabu ta lunku a
ranta don sai taga kamar yanzu yafi son Zainabu
sama da ita ma daga yanda take jin kalamansa,
kai ita tana ganin wannan son da yake wa
Zainabu ma bana Allah bane asiri kawai tayi
masa, banda haka meye hadin shi da ita, don ya
fita komai a ganinta, ta nufe shi da sauri dan ta
bayansa take baiga shigowarta ba, sai ta tsaya
turus tana kallon abinda ya dauke masa hankali
har bai ji shigowar ta ba. Wani katon hoton
Zainabu ne ta dauka da wani yadin material (light
purple), mai yarfin fulawowi jajaye da ruwan
zaiba, tana sanye da wani dankunne na fashion
mai kyau, ta tallafe habarta da tafin hannunta
tana dariya, (dimple) dinta ya fito sosai, fuskar ta
yi fayau, gashin idonta ya tashi gazar-gazar,
girarta ta kwanta luf-luf, labbanta sun sha
jambaki kalar kayanta sai walkiya suke yi tamkar
ba a hoto ba, hoton ya dauko matuka don an
futo da ainihin kyan Zainabu. Lallai ba Zainabun
da ta sani da ba ci, don ta goge matuka tana
kuma da kyan da lallai zata iya yaudarar Mustafa
ya sota, sai dai ita kyanta baya gabanta tunda
bata da kyan hali. Zuciya ta dauke ta don ganin
wai har lokacin bai san ta shigo ba hankalinsa
yana ga Zainabu ne kawai, ta fisge laptop din ta
kwadata da kasa, ai kuwa sai gashi ta bare gida
biyu, da alama da kyar zata kuma moruwa gashi
mai kyau ce dan daga kasar waje ya taho da
ita.ya daga kansa a gigice dan yaga wanda yayi
masa wannan yankan kaunar sai yaga Momin sa
a tsaye tana ta huci ta cika fam, nan da nan gumi
ya fara karyo masa don yasan Momi babu wargi
ba iri Babansa bane mai sanyi ba. "Mustafa! (ta
kirawo sunan sa yau babu sayawa saboda bacin
rai), wato dama baka rabu da wannan karuwar
ba ko? to tsaya kaji na gaya maka ko mutuwa
zaka yi akan sonta ba zaka auro mana jaraba ka
kawo mana gida ba, da mun sakankance ka rabu
da ita, ashe 'yar jarabar tana tare da kai. Shin
wai ni me ka gani a jikinta da har tafi sauran
mata da ka kasa kalla da daraja ne eye? Kai
yanzu ba zaka ji kunya ba ace matarka tsohuwar
'yar tallan goro bace mara tarbiyya ba? Bata gaji
tarbiyya daga uwa ko uba ba sam?, to tsaya kaji
na gaya maka ta mahaukaci, ko bayan raina ka
auri Zainabu ban yafe maka ba, sannan daga yau
idan ka kuma zuwa gidansu ko inda zaku hadu
ban yafe maka ba." Ya runtse idonsa gami da
dafe kai hankalinsa yayi mugun tashi, babu
abinda yake fadi sai, "Innalillahi....." Ta kuma
kufula tana fadin, "Kai ko mutuwa zaka yi babu
kai babu Zainabu na gaya maka in dai nice na
haifeka dan halak." Tana gama fadin haka ta juya
ta fice sam ta manta da abinda ya kawo tama
sashin nasa. Ya zauna jabar a kujera har lokacin
bai cikin hayyacinsa, ya kuma fadin, "Ya Salam!
Ya Salam!" Har lokacin zufa tana karyo masa duk
da sanyin A.C da fankar dake dakin. Maganar
Momin ta dunga masa amsa kuwwa a kunnensa
sai yake ji kamar har lokacin tana tsaye a kansa
tana ta maimaitawa ne, don haka ya sanya
hannuwansa ya toshe kunnuwansa wai ko ya
daina ji, amman da yake abin daga zuciyarsa
yake fita sai ya cigaba da ji kamar ma karuwa ya
yi. Lallai ko yaki ko ya so yasan rabuwar sa da
Zainabu ta zo kenan, idan har ya kasance da mai
albarka, don dai ya san duniya bai hada
Mahaifiyar shi da kowa ba, ko da kuwa zai mutu
din kamar yanda Momin nasa ta fada din ya rabu
da Zainabu har abada.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
WAI WACECE ZAINABU-ABU MAI TAGWAYEN SUNA
NE?
Asalin Salamatu mahaifiyar Zainabu 'yar cikin
birnin Kano ce, ta tashi babu arabi balle boko,
bata da aiki sai dai ta dauki tallan soye (dan tayi
da ake cirowa daga dabbar da aka yanka na kasa
mata a kokuna sannan a jera a cikin faranti). Don
haka kullum da sassafe zata yi sammako ta tafi
Mayanka ta siyo dan tayin wanda zama suke
kusa da dabbar da ake yankawa da zarar an
hango da dantayi sai a kwasa da gudu, wacce ta
fara kamawa nata ne sai ta saka a kwanonta ayi
ciniki sannan su kuma matsawa gaba da haka har
ka tara na iyakacin kudinka, sannan sai ta tafi
gida a yayyanka shi a soya, a zuzzuba a kokuna
sannan a tafi tallanshi kasuwanni. Idan ta dauki
tallan tun safe sai yamma likis take komawa gida,
don haka bata da lokacin karatu, sai dai ran da
taso sai ta tafi makarantar dare ita ma bata
fahimtar komai dan banda gyan-gydi babu
abinda take yi, don an sha yawo an gaji, idan
kuma ranar alhamis da Juma'a ce a tafi gidan
amare a yita wasan 'yar carafke ko lido da
sauransu. Mahaifinta yana so tayi karatu sai dai
bai isa ba dan matar sa tafi karfinsa, don haka
yana ji yana gani 'yarsa ke wannan rayuwar babu
kwaba balle harara, sannan idan dare yayi wani
lokacin zaka ga samari sun cika kofar gidan anata
zance da shewa da kawayenta kuma bana aure
bane illah ayi shashanci da zancen batsa a watse,
amman babu na aure a cikinsu. A gurin da take
sai da soye wani mutumin Sudan sunansa
Abbakar, shayi yake saidawa irin na babbar butar
nan wanda ake dauka a hannu da biredi da
kofuna a faranti, Abbakar mutum ne mai kirki da
hakuri dan kullum Salamatu sai ta tsokane shi
dan hausar sa bata fita sosai, gashi kuma da
shegen surutu da son tsegumi. Duk danginsa
suna can Sudan, yaki ne ya sanya suka watsu
suka yo Nigeria da 'yan uwansa, sai dai tun da
suka zo kowa ya nemi masauki, shi kam yayi sa'a
ya fada hannun wani Malami Malam Nadabo
mutumin kirkine ya bashi gida inda yake saukar
baki ya zauna cikin almajiransa, yana fita neman
abincinsa don shine ma ya bashi jarin da ya fara
sana'a tun yana zagaye cikin unguwar har ya
koma yana shiga kasuwanni.Da yake ya iya
shayin sai ya samu kwastomomi dan irin na
larabawan nan yake yi, a haka suka hadu da
Salamatu ma, don Allah yayi shi mutum ne mai
shegen surutu da son gulma dan haka duk
abinda ya gani sai ya nuna mata ko ya tambaye
ta da haka har soyayya ta shiga tsakaninsu. Abu
kamar wasa sai gashi sun saba matuka, sai dai
tun a wancan lokacin tayi mugun raina shi tayi ta
masa masifa bai damuwa, domin yana da
matukar hakuri sai dai zancan gulama amman
sam baida abokin fada, sai dai mutane da dama
suna ganin abun nasu kamar ba zai yiuw ba don
shi fari ne tasa kamar balarabe gashinsa ma a
nannade yake sai dai wahala ta sanya shi ya dan
dafe, yayin da Salamatu take baka, amman bata
da muni, sai dai bata da tsawo gajera ce sosai
mai jiki. Malam Nadabo dai shine kamar matsayin
mahaifinsa don haka shine ya tsaya masa har aka
yi wannan auren, suka tare a nan gidan Malam
din da yake zaune da almajirai, wasu suka koma
shagon gidan wasu kuma suka koma daya gidan.
Ta addabi kowa a gidan don gidan kusan a hade
yake da na Malam kasancewarta masifaffiya ce,
su dai matan malam bata yi da su don sun ja
girman su haka malam, sai dai duk 'ya'yan gidan
'yan dakinta ne musamman matan, amman duk
kusan almajiran malam tayi fada da su don ma
malam yakan yi mata fada, don haka babu
wanda take shakka kamar malam don babu
wargi, a nan gidan ta haifi dan ta na fari Sadiku
wanda aka haifa rana daya da dan Malam Zaidu,
don haka rana daya aka yi suna Malam ne ma ya
rada musu sunansu duka. Sun tashe tare da
Zaidu da yake Sala bata wani damu dashi ba don
ita ta fi son ta haifi mace wai itace abokiyar
neman kudi, don haka kullum a cikin watangariri
yake a cikin gidan musamman da ta yaye shi sai
ta bar musu a can, don haka kusan a gidan nasu
ya taso.Tare Malam ya sanya su a makaranta Ma,
sannan ta kuma samun wani cikin tayi ta tanadin
kayan mata har su dankunne da awarwaro
amman sai gashi ta kuma haifar namijin, shima
din haka ya taso a gidan malam din, sai dai daga
kansa bata kuma samun haihuwa ba har ya
shekara biyar, sai wata annoba ta zo ta kyanda
shima yana ciki, ai kuwa dai wannan kyanda itace
ta yi ajalin Sabitu. Rashin samun cikin nata ya
sanyata fara tunanin wai matan Malam ne sukayi
mata asiri don ta fara haihuwar da namiji, su a
kan Zaidu suka fara haihuwar namiji duk mata
suke haifa, ita fadi take banzaye ni da ana
musanye da munyi don nafi son matan, sai dai
bai ya wata goma ba da rasuwa Sala ta kuma
samun wani cikin. Ai kuwa dai wannan karon tayi
sa'a a wannan karon ta samu abinda take so din,
don haka murna ba'a magana, sai da dauki son
duniya ta dora akan Zainabu sunan Mahaifiyar
malam din ya sanya mata kenan, da farko tace
bata yarda ba sunan Sima take son a sanyawa
diyarta, shi kuwa malan sunan matarsa ta fari ne
da ta rasu yana son sunan, sai da Abbakar yayi
ta lallaba ta sannan ta amince, akan Zainabu sai
tayi fada da uban kowa a kuma sannan ne
Abbakar ya kammala ginin gidansa da taimakon
malam, don haka suka tattara ya nasu-ya nasa
suka koma, amman banda Sadiku wanda sai dai
yaje gidan nasu ya koma gidan malam don
kamar ba Sala dince ta haife shi ba musamman
idan Zainabu tana kin ji yana mata fada, dan
haka shima bai fiye zuwa gidan ba sai da ya
shiga sakandire ne ma yake zuwa sosai.Sala kam
sana'a ta kafa sosai a gidan ta, don daman tun
tana gidan malam jarabar neman kudi ne da ita,
don haka ba ta zama kullum cikin neman kudi
take. Tun daga wannan lokacin shike nan
haihuwa ta bude a gidan nasu, sai dai yaran
suna tashi babu tarbiyya, da farko malam ya fara
kiran Baba Abbakar akan halin da yaransa suka
tashi da shi, don haka yayi masa nasiha mai
shiga jiki, sai dai idan aka ce namiji bashi da
katabus a gidansa babu tarbiyya, don haka san
da Baba Abbakar yaje mata da abinda Malam din
ya ce, tsalle tayi ta dire tana fadin, "Wallahi baka
isa ba, wacce tsiyar kake tsinana mana da har
zaka yi mini wannan tsarin (don a lokacin babu
ciniki a sana'ar ta shi sai dai yayi ta yawo bai
samun ciniki sosai, daga karseh sai ya koma
kame-kame)." Malam Nadabo yana ji yana gani
gidan Baba Abbakar ya koma yanda yake don dai
yayi har ya gaji, sai dai shifa duk wani abu na
tsawatarwa yana musu dan haka shi kadai suke
shakka a rayuwarsu, don duk wanda ya doki
Zainabu sai inda karfin Sala ya kare, amman idan
Malam ne sai ta ce, "Sai kiyi hakuri na gaya miki
ki daina zuwa gidansa mana." Shi kam Sadiku ya
sami karatu mai kyau don ya sami makarantar
firamare mai kyau da sakandire, daga nan ya
wuce kwalegin share fagen shiga jami'a, shi kuma
Zaidu da yake bangaren Arabic ya dauka yana
Jami'atu Ummul Qura dake birnin Makkah yana
karantar harshen larabci, wannan shine mafarin
komawar Sadiku gidansu don dai babu abokinsa.
Da kyar da sidin goshi Sala ta bar 'ya'yanta suke
makarantar boko da ta allo don Malam yana fada
ne da kuma Sadiku, sai dai duk da haka Zainabu
ba kullum take zuwa ba sai jefi-jefi. Sai dai da
yake ba karatun ne a gabanta ba sam bata yi,
Zainabu ta taso da hali irin na Babarta don haka
bata da wargi duk wanda ya taba ta sai ta rama,
don dai Sala ta bata ta tun tana yarinyarta, ga
fadan ta baya mutuwa kamar fadan kurma, don
sai tayi wata tana fada sai dai idan iyayen yaran
sun gaji su zo gidan a baiwa Sala hakuri sannan
za ta hakura, idan mutum yafi karfinta ba ta raga
masa don da cizo da yakushi zata kwaci kanta, ko
kuma idan ka doke ta tayi ta jifanku ko duk inda
kuka hadu sai fadan ya tashi. Wannan halin nata
ya sanya duk unguwar kowa yake shakkarta,
abinda ke farantawa Sala rai kenan don takan ce,
Abulata da na kai kararki gwara a kawo mini
wallahi, don haka duk wanda ya taba ki koda
gemunsa yana jan kasa kada ki kyale shi ki rama,
daga nan har ofishin kwamishinan 'yan sanda zan
iya zuwa a kanki Abulata. Don haka har siyan
fada take yi, duk wanda bashi da karfi Zainabu
kan sayi fadan ta casa wanda ake fadan da shi
don akwai ta da karfi, idan kayi gulmarta za ta
sanya a kama ka a tura ka lungun ka-ci-uwaka a
tura maka kashi a baki ko bara-gurbin kwai, don
haka ta addabi kowa a unguwar tasu. Ko fakin
din mota aka yi bai gamshe ta ba sai tayiwa
mutum faci a motar tasa, don haka duk kofar
gidan masu hali na unguwar da an gan ta masu
gadi zasu bita da gudu tana dariya. Idan aka tura
ta makarantar firamare kuwa masu kosai da 'yar
tsala na sadaka take bi da waina wadanda ke
yawo da almajirai mutane na siya suce su raba
wa almajirai sai an fita tara take tafiya
makarantar. Yawo kuwa ko kare ya gan ta ya
kyale, don kullum za ta hada zugar yara suna
shiga karkashin manyan motoci da ke fakin a nan
kan tudu, dan haka duk wanda baiga dan sa ba
yana tare da Zainabu, yawo bola-bola sun iya
shi, gashi babu dama kayi magana sai Sala ta
hau bala'i tana fadin, "Kun ga kada ku sanya
mini diya a gaba, waye Abula ta daurawa igiya a
wuya kowa na ga da kafarsa ya bi ta, don haka
duk matar da ta kara cewa Abula ta ja mata
'ya'ya yawo wallahi sai na dirji bakinta, duk
wacce ba ta son 'ya'yanta su je yawo ta daure a
kofar gida, kurwar Abula kur! Na gaya muku."
Wannan shine kadan daga cikin labarin Zainabu
Abu mai tagwayen suna.
**********Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ubangiji babu ruwansa yakan bar bawa ya sakata
ya wala ya yi sabo son ransa ba tare da ya matsa
maka ba a duniya, amman abu kalilan zai jarabce
ka dashi duk sai ka gigice ka ga ashe kai din ba
komai bane, ka koma abin tausayi. To, Lallai kam
hakan ce ta faru ga Mustafa, don bai taba zaton
zai shiga ko da kwatankwacin wannan matsalar a
rayuwarsa ba, Allah ya jarabce shi da son
Zainabu wacce ita kuma mahaifiyarsa ta tsana
kamar mutuwarta, Zainabun da ya raina a baya,
sai ga shi son ta yana neman raba shi da duk jin
dadin rayuwarsa, don wacce ta kawo shi duniya
ta yi musu katangar karfe a tsakaninsu. A da can
da suka hana shi auran ta bai damu kamar
yanzu ba, don yaka je gurinta ya kwanta a
kafadarta ta lallashe shi, amman yanzu babu
dama don haka abubuwa suka masa yawa, yanza
haka yana ofis ya hada tagumi da hannuwa biyu-
biyu kamar wani karamin yaro, wani inji aka ce ya
je ya duba amman ya gaza tashi, gashi yafi kowa
iya gyara a sashen nasu, yanda kasan maye haka
yake idan ya sanya gyara a gabansa sai ya ga ya
gyaru, don haka suke ji da shi.Yana nan zaune ya
ji kiran wayarta ya shigo, ya zabura da sauri ya
dauka ya kara a kunnensa. Da kashe murya da
shagwaba ta ce, "Zumana shiru kwana biyu babu
kai babu wayarka, ko Zainabu ta yi laifi ne bata
sani ba?" Ya lumshe idonsa gami da kwanciya
jikin kujera, ransa ya yi fari tas saboda jin muryar
Zainabu kawai da yayi, sai dai ya gaza bude
bakinsa ma balle yace wani abu. Hankalin ta ya
kuma tashi da jin shirun da ya yi mata, ta kuma
duban wayar ta ga lallai a kunne take, da tashin
hankali ta ce, "Mustafa ka ce wani abu mana, ko
dai ka manta da Zainabunka ne?" Hankalinsa ya
kara tashi don jin muryarta kamar za ta yi kuka,
ya daure ya bude bakinsa da kyar ya ce,
"Zainabu baki yi mini komai ba, illah dai
Mahaifiya ta ta kafa mini mummunan sharadi a
kan idan na kuma zuwa inda kike ko duk inda na
san zamu hadu, to lallai ba ta yafe mini ba....."
"Me ka ce Mustafa? Yanzu kana nufin shi kenan
mun rabu har abada? Yanzu yaya zan yi da
sonka a raina Mustafa na? Anya zan iya rayuwa
babu kai, Zumana?" Yayi kokarin jawo dauriya ya
sanyawa ransa ya kwantar da murya da lallashi
ya ce, "Kin ga Zainabu kwantar da hankalinki, ni
din naki ne har abada ba zan iya rabuwa da son
ki ba, sai dai dole zanyi biyayya ga maganar
Mahaifiyata don ina son na rabauta duniya da
lahira, na yi miki alkawari ni naki ne har abada,
sai mu cigaba da addu'a komai ya zo da sauki,
don ina ji a jikina ke matata ce da zan rayu da ita
cikin ni'ima da soyayya." Hankalinta ya dan
kwanta ta yi ajiyar zuciya tana fadin, "Zumana
yanzu yaya za muyi kenan? Don na san zan sha
walahar rashin ganinka matuka." Ya lumshe
idanuwansa wadanda yake jin suna masa nauyi
ya ce, "Ki bari zan ga Babana idan ya dawo zan
sanya shi ya lallasar mana Momi din, ina ganin
shi zai tausaya mini idan ya ga halin da nake ciki,
don yafi Momi saukin kai." Ta ce, "Shike nan
zumana, amman zan dinga jinka a waya ko?" Ya
ce, "Dole ne ai Zainabu na kiraki a waya, idan ba
haka ba zuciyata ai bugawa zata yi." Ta yi
murmushi gami da fadin, "Ina sonka matuka
zumana." Ya yi dariya ya ce, "Nima haka Zainabu,
sai dai ina son don Allah ki yi mini alkawarin kin
bar hulda da maza kamar kina ganina, don na
danka miki amanar kanki, ina jin kamar zuciya ta
zata babbake idan na ganki da wani, shin zaki iya
rike mini kanki da alkawari har komai ya lafa?."
Ta yi murmushi gami da fadin, "Mustafa ko da ba
kace ka ba ni amanar kaina ba ba zan iya hulda
da kowanne namiji ba, don kai din kayi mini
yanda ba zan iya kallon kowa da gashi ba, ka
kwantar da hankalinka a yanzu Zainabu taka ce
kai kadai." Da kyar suka iya rabuwa a wayar don
suna ta sanar da kawunansu irin son da suke
yiwa junansu ne kawai. Sai a sannan ya sami
karfin gwiwar da zai iya tunkarar aikin da ke
gabansa, don haka ya shiga dan wani daki ya
sauya kayansa daga na gida zuwa na aiki ya nufi
inda injin da zai gyara yake. Ita kuwa Sala ce a
kanta a tsaye tana rike da kugu jira kawai take ta
kammala amsa wayar, ai kuwa tana ganin ta
gama wayar din ta dirar mata da jaraba. "Yanzu
Abula shi kenan zaki zauna namiji daya tal yana
miki yawo da hankali? Ga wadanda ke son ki
kuma sai wahalar da su kike yi? Yanzu jiya Alhaji
Hayatu Tumbin kudi sai da ya kashe kunyarsa ya
zo ya sameni ya ce don Allah ki fito ko gaisawa
ne ku yi, shi da gaske yake auranki zai yi ma, ya
cake mini dubu hamsin a hannuna ke kuma ya ce
idan kin fita zai baki duk abinda kike so, amman
yarinyar nan kika bada mini kasa a idona, har
mutumin ya gaji da jiranki ya yi zuciya ya tafi, kin
kwallafa ranki a kan shegen mayaudarin yaron
nan, kin ki ki saki zuciyarki ki ci arziki ki bar arziki
a mazauninsa? Wallahi kin bani mamaki Abula
ban taba zaton zaki koma sokuwa a hannun
namiji ba, su da kike juya su kamar waina?."
Zainabu ta dinga duban Sala da mamaki da
takaici da kyar ta iya buda bakinta ta ce, "Sala
kin san So kuwa?" "Ban san shi ba sai ke diyar
zamani, ba kuma na fatan na san shi tunda shi
din masifa ne da jaraba, ki dubi yanda ya maida
mini ke, wallahi da zan gan shi shi So din dana
rade masa kai don Ubansa, tunda ya hana ki ki
zauna lafiya." Ta dafe kirji gami da jingina da
kujera tana fadin, "Sala ki kyale ni kawai tunda
dai kin ce baki san So ba, yanzu haka kirjina ciwo
yake mini, lallai idan na rasa Mustafa na san
mutuwa zan yi don Allah ya jarabce ni da
tsananin son sa, zan iya yin komai don na same
shi Sala, yanzu kam na gane so yana gaba da
kudi da komai, ki rabu dani kawai don na yiwa
Mustafa alkawarin ba zan kuma kula kowa ba zan
yi ta jiransa har ranar da Allah ya sanya iyayansa
suka amince ya aure ni din." Sala tayi Salati tana
tafa hannu tana fadin, "Shike nan an sammace
mini ke Zainabu, don in dai ba asiri ba babu
abinda zai sanya ki gaza hulda da kowa sai shi
kadai, kuma yanzu ba ya nan baya ganinki ba kya
ganinsa ma, amman kin ce ba zaki iya kula kowa
ba, to wallahi ya yi a banza, don ni ma ai ba'a
zaune nake ba, duk neman sa'ar da nake miki a
ce ya tashi a banza, bari na tafi gurin boka na
kan tudu zan sanya ya raba min ku, idan ya so
sai na ga karshen shegen So din, tunda dai shi
ciwon masifa ne." Zainabu ta riko hannun Sala
da ke shirin fita daga dakin nata tana fadin, "Sala
kada ki rabani da Mustafa idan dai ba so kike na
mutu ba, shin wai kin san abinda ya sanya iyayan
Mustafa ma suka hana ni aurensa? To ba wani
abu bane illa yawon da nake yi na bin maza
tamkar karya, kowa ya zo ya dauke ni a mota ya
je yayi abinda ya ga dama da ni kan kudi, sun ce
ni karuwar gida ce, yanzu me ye amfanin irin
rayuwar iskancin da na yi? Ni kam zuciyata ta
gyaru don haka na bar abinda kike so na yi." Sala
ta kuma shiga rudu ta ce, "Ahaf! Kinji ba? Ai na
sani asiri yayi miki, banda asiri ke da bakinki ki
dinga kiran kanki 'yar iska, yanzu kin yarda ke
din 'yar iska ce? Kalmar da da idan aka gaya miki
sai inda karfinki ya kare amman yanzu kike gaya
wa kanki, to ba karuwa ba ko ke mecece kinfi
karfin danta wallahi, idan tace kuma ke karuwa
ce shi dan nata ai karuwi ne tunda dai shine ya
watsa miki rayuwa, sai nayi maganinsu shi da
uwar tasa in dai sunana Sala." Ta warce
hannunta daga rikon da Zainabun tayi mata ta
nufi waje tana cigaba da bala'inta.... To, masu
karatu, mu hadu a littafi na biyu don jin yadda
Sala zata aiwatar da wannan mataki.
Take cewa kar ku damu na dayan tare suka fito
da na biyun,Mai kaunarku da yi muku fatan
alkhairi a kullum: FAUZANKU CE! Mrs Q for Q,
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Idan Zuciya Tagyaru2-01
Posted by ANaM Dorayi on 12:38 PM, 08-Feb-16
Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU
_________________ Na
________Fauziyya D Sulaiman_____
Zainabu ta zame ta kwanta ta lumshe idanuwa
tana hango hoton Mustafa a zuciyarta, yanzu idan
Sala ta raba su yaya za ta yi da sonsa? Hawaye
ya shiga malalowa ta gefen fuskarta, ji take
kamar ta koma baya da rayuwarta ta goge duk
abinda ta aikata, amman ina lokaci ya gama kure
mata da ba za ta iya gyarawa ba. A da can baya
takan ga wautar masu cewa idan basu samu
wane ba ba zasu iya rayuwa ba, sai ga shi yanzu
ya zo kanta ita ma. Asma ta fado mata a ranta,
wai ina ta shiga ne a duniyar ne don ta nemi
wayarta ta rasa? Yau sati biyu kenan da tayi
tafiya da wani saurayinta, sai dai ta gaza samun
wayarta, gashi ita kadai ce ke bata shawara idan
ta shiga tashin hankali. Ta kuma dafe kirjinta da
take jin kamar zai tsage don ciwo, wai yau ita
Zainabu Abu dake gara maza kamar gare-gare,
ita ce ita ma yau zuciyarta ke tamaula da son
wani, ta lumshe idonta tana fatan ta yi bacci ko
ta huta da azaba.Ku ziyarci blog dinmu domin
karanta Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
*******************
Kwanaki suna tafiya amman dokarsa tana nan ta
hana shi kula Zainabu, abin yana damunsa
matuka, don haka tafiya kawai yake yi amman
shi kansa ya san bashi da koshin lafiya, gurin aiki
ma sai hakuri suke yi da shi don yayi rahotan
bashi da lafiya, ya gaza cin abinci ya koshi sai dai
ya sha fresh milk kawai da safe da da dare. Abin
ma biyu ya hade masa, na farko raba shi da
Zainabu da aka yi sai kuma kin kula shi da
Mominsa ke yi, ko da gaishe ta ya yi bata
amsawa. Shi kam ya yi alkawarin ko me zata yi
masa ba zai daina gaishe ta ba. Yau ma ya shirya
cikin shadda koriya ta amshe shi matuka, sai dai
daga gani yana cikin tsananin damuwa matuka,
ya nufi dakin Momin tasa da zummar ya gaishe
ta duk da ba amsawa take yi ba. Tana ta hada
kayanta don makaranta zata tafi, kanwarsa
Sumayya tana gefe tana tambayarta a kan wani
aiki (assignment) da take yi tana gaya mata tana
rubutawa, ya shiga dakin da sallama. Ya sami
kujera ya zauna jabar yana fadin, "Washi." Kamar
wanda ya yi wani aikin. Sumayya ta dube shi da
kulawa tana fadin, "Ya Mustafa ina kwana?" Ya
ce, "Lafiya lau. Ina 'yan uwan naki suke
musamman aminiyar Zainab." Ta yi murmushi ta
ce, "Sauran sun tafi lakca dan duk ta safe suke
da ita, mu kuma muna da jarabawar gwaji ne ga
shi motarmu ta samu matsala, don haka Momi za
ta rage mana hanya, Zainab nake jira tana shiri."
Ya kalli Momin da ta zauna tana shan shayi ya
ce, "Momi ina kwana?" Ko kallon inda yake ba
tayi ba ma balle ya sanya ran zata amsa masa,
Sumayya da ke kallon Momi din ta yi narai-narai
da idanuwanta kamar za ta yi kuka tana fadin,
"Momi don Allah kiyi hakuri haka, ki dubi yadda
Ya Mustafa ya koma, na san share shi din da kike
yi ne kuma ya sanya shi komawa haka, don Allah
ki sassauta masa kin ji Momi?" Ta gallawa
Sumayyan harara wacce take ji da ita duk gidan,
don ita ce 'yar gaba goshi sannan ta ce, "Ina
ruwa na da wani hali da ya shiga? Ai shine ya
dorawa kansa, wannan halin kuma da ya shiga
ne ya tabbatar mini da lallai ban isa da shi ba,
don da na isa da shi da ya saki ransa ya hakura
da auren shegiyar karuwar yarinyar nan ya cire ta
ma daga ransa gaba daya." Kirjinsa ya shiga
bugawa da sauri kansa ya hau sarawa kamar zai
tsage gida biyu, lallai Mominsa uwa ce ta fi gaban
komai, don ban da ita babu wanda zai zagi
Zainabu a gabansa da sunan karuwa ya kyale shi,
amman Mominsa tafi Zainabu daraja da girma a
gurinsa da zuciyarsa gaba daya. Ya mike da
zummar ya tafi jikinsa sai rawa yake yi, ta kuma
galla masa harara sannan ta ce, "Baba in dai nice
na haife ka na baka kwana biyu ka fito da matar
aure, idan ka bari har kwana biyu ta wuce ba ka
fito da mata ba to lallai zan aura maka wacce na
ga dama, kana ji na ko?" Ya gyada kai da sauri
yana fadin, "To Momi na amince da duk abinda
kika yi a kaina, fatana dai ki yi hakuri ki dinga
kula ni ko zan ji sassauci a zuciya ta." Tausayi da
soyayyar danta ta shige ta, musamman yanda ta
ga ya amsa babu wata jayayya ba kamar yanda
ta zata da farko ba, sannan bai damu da
hukuncin da ta yanke masa ba sai ma rashin kula
shi da bata yi bane ya fi damunsa, ta ce, "Shi
kenan ya wuce, sai dai ka yi kokari ka cika
umurni na cikin kwana biyun da na ce, don idan
kai idonka bai gano ma mace ta gari ba, to ni
nawa garau yake ina gani tar, zan zaba maka
mace mai daraja ta kwarai." Shi kam bai kuma
cewa komai ba ya nufi kofa zai fita, sai dai gaba
daya idanuwansa sun disashe ba ya fahimtar
komai, bugun kirjinsa ya kuma tsananta fiye da
yadda yake a ka'ida, amman hakan bai hana shi
dauriyar cigaba da tafiya ba duk da
kwakwalwarsa na neman gaza aiki yanda ya
dace,Ya kuma daga kafarsa amman ya kasa sai
ma kafafuwan nasa da suka gaza cigaba da
daukar nauyin jikinsa, don haka a nan ya yanke
jiki ya fadi gaba daya ya daina fahimtar komai
don mai alhakin sanar da shi din ita ma ta sami
matsala, wato kwakwalwarsa. Sumayya ce ta fara
ankara ta mike da azama gami da kwala ihu ta yi
kansa, Momi ta ankara da abinda ke shirin
faruwa itama ta yi kansa da saurinta ba ta san
sanda ta yar da kofin shayin da ke hannunta ba.
Suka kama jijjiga shi suna fadin sunansa amman
ina, ko motsawa ba ya iya yi. Momi ce ta bazama
da gudu can harabar gidan tana kwalawa direba
kira, Allah ya sanya ya dawo daga kai 'yan
makaranta don haka shi da maigadi suka iso da
sauri suna tambayar abinda ya faru ganin yanda
take a kidime, kasa magana ta yi illa dakinta da
take nuna musu, suka shiga da saurinsu tana
biye da su a baya. Suna shiga ta fara magana da
azama, "Maza ku dauke shi mu wuce asibiti kada
ya mutu." Sumayya ma sai kukan take yi, haka
Zainab da hargowar Momi din ta fito da ita ita
ma kukan take yi, haka nan suka kwasa suka yi
waje da shi, shi kam Mustafa ya yi nisa, sam bai
san wanda yake kansa ba. Suna isa asibitin dakin
'yan hatsari aka yi da shi (A&E), na asibitin
Malam Aminu Kano, nan da nan likitoci suka rufa
a kansa domin matsalar babba ce. Su Momi suna
waje suna ta sintiri, gaba daya hankalinsu a tashe
yake, sai da kyar ta samu ta rarrashi su
Sumayya, da suka ga karfe daya ta yi suka wuce
masallaci suka yi Sallah suka zauna suna ta
addu'a, masu karatu kuma suna ta yi. Ranar kam
sun manta da wani abu wai shi abinci, balle
makaranta. Bayan sun kammala sallar suka dawo,
amman har lokacin likitoci suna ciki, abinda ya
fara firgita Hajiya Kubra har take ganin kamar
mutuwa ma ya yi aka ki sanar da su. Sai karfe
daya da minti hamsin da shidda sannan likitocin
suka fara fitowa, Hajiya Kubra ta bi babban
likitan da sauri tana tambayarsa ya ya mai jikin?.
Ya dube ta ya ce, "Ke ce mahaifiyarsa ne?" Da
sauri ta ce masa, "Eh! Ni ce." "Ina mahaifin sa
yake yanzu?" Ya kuma tambayar ta. Ta kuma
cewa, "Ba ya gari wallahi, yana can kasar Spain
ne." Ya yi dan jim sannan ya kuma cewa, "O.K,
shike nan, idan dai da hali ayi masa waya a ce
muna son ganinsa da gaggawa, idan kuma yana
da dan uwa sai a turo shi sai a yi masa bayani."
Ta kuma shiga damuwa da jin abinda likitan ya
fadi, ta dinga fadin, "Innalillahi wa inna ilaihi
raji'un." Sannan ta kama neman layin wayar
Alhaji Abdullahi na can garin. Bugu biyu ya dauka
ya ce, "Ya ya dai Kubra kowa lafiya ko?" Ta goge
hawayen da ke zubo mata ta ce, "Eh, to! Da
sauki. Amman idan da hali ka zo cikin satin nan,
ko gobe ma don wata matsala ce ta taso mai
karfi." Hankalinsa shima ya tashi ya ce, "Ko dai
wani ne ya rasu kike boye mini, eye?" Ta ce, "A'a
wallahi babu wanda ya rasu, ka dai daure ka zo
din." Da haka suka yi sallama.Haka nan suka
dinga sintiri a asibitin har dare, sai daga baya ne
ma da suka ji babu wanda za'a bari ya kwana a
gurinsa don yana bukatar kulawa daga
ma'aikatan jinya, ya sanya suka hakura suka
wuce gida. Washegari da safe suka kuma
rankayowa suka yo asibitin, amman basu sami
damar ganinsa ba har lokacin ba'a shiga inda ya
ke, sam! Abinda ya ba su mamaki bai wuce ganin
Alhaji Abdullahi ya iso wajen karfe uku na
yamman ba, amman sun san babu mamaki don
duniya ta kuma cigaba matuka ba kamar da ba.
Kai tsaye Ofishin likita ya wuce bayan sun gama
gaggaisawa da su Hajiya Kubra da yara, don ta yi
masa bayanin abinda likitan ya ce mata. Bayan
sun kammala gaisawa da likitan ya ce, "Kai ne
Mahaifin Mustafa kenan?" Alhaji Abdullahi ya ce,
"Eh! Ni ne." Likitan ya gyara zama yana
tambayarsa, "Daman yana da wani ciwo ne da ya
shafi ciwon zuciya tun yana yaro?" Alhaji
Abdullahi ya yi dan jim sannan ya ce, "Ba na jin
ya taba yin wani ciwo da ya danganci wannan
duk tsahon rayuwarsa, kuma ina fatan yanzu ma
ba shi bane ba." Likitan ya yi shiru kamar ba zai
ce komai ba sannan ya dauko wasu takarsu na
hoton kirji da aka yi yana dubawa, sannan ya
kalli Alhaji Abdullahi ya ce, "Alhaji (I am sorry to
say) ka yi hakuri da abinda zan gaya maka,
yaronka ya kamu da ciwon zuciya, don yanzu
haka zuciyarsa ce ta kumbura saboda yawan
bacin rai da damuwa da yake ciki, don haka ne
ma muka hana kowa ganinsa don yana bukatar
hutu da rashin hayaniya, amman ya farfado tun
jya da yamma." Alhaji Abdullahi ya fara fadin,
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, La haula wala
quwwata illah billah. Yanzu likita ya ya za'a yi
kenan?" Dokta Bukar ya ce, "Kar ka damu, tun da
yanzu mun samu ya farfado, sannan a gwajin da
muka yi masa yau da sauki a kan jiya, sai dai
kawai wani suna da yake yawan ambata idan
yana bacci....." "Likita za mu iya ganinsa ni da
Mahaifiyarsa?, don tana cikin damuwa matuka
kada a yi biyu." Ya katse likitan. Likitan ya ce,
"Babu damuwa, tashi mu je ka gan shi." Yana
kwance a gado yana bacci, amman a fuskarsa ta
fada matuka, ramar da ya yi ta bayyana, Hajiya
Kubra ma ta shigo, don an ce ta shigo, ta isa
inda yake tana shafa kansa a hankali hawaye
yana zubowa daga idonta, shi ma Alhaji kallonsa
yake cike da tausayinsa, ya kama hannunsa ya
rike. Ya yi wata ajiyar zuciya kamar wanda yake
ido biyu sannan a hankali ya fara fadin,
"Zainabu! Zainabu!! Zainabu!!!" Kunnuwansu sun
jiye musu abinda yake fadi, Hajiya Kubra ta janye
hannunta da sauri gami da kallon Alhajin, Ya
matsa kusa da ita sai ta fada jikinsa tana kuka
tana fadin, "Alhaji kana jin abinda yaron nan
yake fada? Ba ya ta lafiyarsa sai ta wannan 'yar
iskar yarinyar, ni kam na shiga uku da wannan
jaraba." Ya dafa kanta yana shafawa a hankali
yana fadin, "Ki yi hakuri Khadija, na san ba yin
kansa bane sharrin so ne, wanda ke ma kin san
shi, koda yake ke baki san wahalarsa ba sai
dadinsa kika sani, ki duba ki ga bacci yake
amman yana ambaton wacce ba ta kusa da shi
ma, so yana shiga zuciyar mutum ne ba tare da
neman shawara ko neman yarda ba. Ki dubi
halin da yake ciki, kin san me likita ya ce yana
damunsa?"Ta girgiza kanta alamar A'a. Ya ce, "To
ki sani danki Mustafa yana fama da ciwon zuciya
ne, yanzu haka kumbura ta fara yi shi ya
sanya......."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
"Me ka ce? La'ilaha illallahu, na gamu da masifa
ni Kubura." Sai ta kuma fashewa da kuka. Ya fara
lallashin ta yana fadin, "Ya isa kiyi shiru kada ki
tayar da shi daga bacci kin ga ance ba'a son ana
damunsa da hayaniya, don haka ma aka hana
kowa ma shiga inda yake, fatana ki kwantar da
hankalinki ki yi hakuri da duk abinda zaki ji yana
fada, kin ji ko?" Ta daga kai alamar, To.Ina
Zainabu? Tana can itama cikin tsananin tashin
hankali, domin dai tun jiya da safe take kiran
wayarsa amman ba'a daga ba, ga shi tana
ringing, ta tura sakonni su ma babu amsa, don
haka ranta ya baci hankalinta idan ya yi dubu
duk ya tashi. Daga karshe sai ta yi zaton ko ya
amince da maganar Mahaifiyarsa ne ta rabuwa
da ita, don haka ta ga ya dace ita ma ta rabu
dashi tun da dai ga wayarsa tana shiga ga
sakonni ta aika masa bashi da sauran bukatarta.
Ranar nan haka ta kwan cike da bakin ciki da
tashin hankali, domin dai ta san ba karamar
masifa za ta shiga ba saboda rabuwa da Mustafa
ba. Tana dakin ta a kwance lamo tamkar mara
lafiya tun da gari ya waye ta kasa tsinana komai,
Asma ta shigo dakin da ihunta kamar yanda ta
saba. Zainabu ta mike da sauri tamkar ta ga
maganin ciwon ta tana fadin, "Kawas ina kika
shiga ina nan ciwon so zai kashe ni?." Asma ta
zaro ido waje tana fadin, "Haba dai Babbar harka
Musty fa yana hannunki sai yanda kika yi da shi
meye zai dame ki, ko kuma kin masa buyagin
naki ne?" Ta rausayar da kai idanuwanta suka
ciko da kwalla ta ce, "Sanin da kika yi, don
Mustafa ya kuma yaudara ta karo na biyu, a
wancan lokacin ya yaudare ni da kudi ne, amman
a wannan karon da abu mafi ciwo da wuyar
mantawa ya yaudare ni wato soyayya, kin gan ni
kamar wacce aka yiwa mutuwa duk na gaza
tsinana komai a rayuwa ta." Asma ta sha kunu
tana fadin, "Don Allah ki bar gayan wannan bacin
ran ma, yanda kike din nan, Mustafan me? Maza
nawa ke neman ko da rabin sa'ar da ya samu a
kanki? Lallai ya yi wa kansa, wai ni yaya aka yi ne
ma? Ba ni labari don Allah." Ta kwantar da
bayanta jikin kushin din da take kai a zaune,
sannan ta zayyane mata duk abinda ya faru.
Asma ta dafe kai cike da takaici sannan ta
kunduma zagi tana fadin, "Ke kin ji ni da shegiyar
tsohuwa, ba ta tambayar kanta me ya sanya dan
nata ya makale miki? Ai sai ta nemi dalili, wallahi
mutanen mu suna bani mamaki matuka, namiji
zai tsula tsiyarsa son ransa a cikin unguwa kowa
ya sani watakila har ta kai shi ga yiwa wata ciki,
amman ba za'a gaza ba shi mata a cikin unguwar
ba, amman idan mace ta aikata sai ki ji an yi
mata caa kamar wacce ta yi ita kadai, ana ce
mata karuwa, shi wai ba za'a ce masa karuwi ba,
amman dai dadin abin duk laifinsu daya ne a
gurin Allah, babu ruwanSa da cewar wai iskancu
ado ne ga namiji, mts!" Ta ja tsaki daga karshen
maganar tata, sannan ta dubi kawar tata ta ce.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
"Wai yanzu yaya kike ganin za'a yi ne, eye? Ni fa
ba na zargin Mustafa ba zai iya gudun kiba, don
ni shaida ce da irin son da yake miki, akwai dai
abin da zai hana shi daukar wayarki, ya kamata
dai mu kuma bincika mu gani." Zainabu ta galla
mata harara tana fadin, "Allah ya sawake, ai
wallahi na fi karfin nan, ki bar shi kawai, idan
aure bai kawo shi ba ai saki zai kawo shi." Asma
ta ce, "Shike nan, bari mu ba shi lokaci mu gani,
amman yanzu ki tashi ki shirya mu zagaya club
don Allah, wallahi tun da na dawo garin nan nake
samun wayar wahalallunki." Babu musu ta mike
don ita kanta tana son ta dan sami shakatawa,
domin daman ta gaza sakewa ta tsotsi tabar
shaidan din tata balle shandy, don tana shakkar
yayanta don ya saka mata idanuwa tamkar
ubanta, don ma yana shakkar Sala ma. A bakin
kofa suka ci karo da Sala ta dawo daga yawonta,
ba ta yiwa Sala din magana ba ta shige
bandakin, Sala din ta tsaya tana kallonta cike da
murna har tana ganin aikin malamin da ta je
gurinsa ne har ya fara aiki, can sai ga Asma ta
fito daga dakin don su gaisa don ta ji muryarta.
Sala ta ce, "Ahaf! Ki ce ke ce kika zo 'yar albarka,
tuntuni nake neman ki ban samu ba, domin na
rasa yanda zan yi da kawarki, wani dan banzan
yaro ya zo ya janye mini hankalinta, ko kofar gida
fa Abula ba ta zuwa balle ta yi wata kwalliya, ta
zama kamar mai takabar kauye, Abula na sarkin
kwalliya ki gan ta cas-cas tamkar diyar gwabna."
Asma ta yi dariya tana fadin, "Sala kenan, yanzu
ma fadan da na yi mata kenan, ki kwantar da
hankalinki komai zai daidaita yanzu ma unguwa
za mu." Sala ta ce, "Yauwa, amman na ji dadin
zuwanki wallahi, kin gan shi nan na (ta rage
murya) kin ga wannan sunansa mantau, a gurin
boka na amso shi, ki san yanda za kiyi ki zuba
mata a cikin abinda za ta ci, domin yanzu sai ta
ga dama take cin abun hannuna, so nake ta
manta da shegen yaron nan sam, ga manyan
mutane nan suna ta sintiri a kanta me za ta yi da
shi?" Asma ta amsa tana fadin, "Shi kenan Sala ki
kwantar da hankalinki tamkar na zuba mata na
gama."Ta ji dadin abunda Asma din ta fada don
haka ta kuma rage murya tana mata gulmar
Mustafa wai kada Zainabu ta ji su, ita kam bata
ma san suna yi ba har ta fito daga wankanta ta
shigo don ta shirya. Ta shiryo kanta cikin wani
material bulu, da yarfin ruwan dorawa mai haske
da kalar zaiba a jikinsa, dinkin riga da siket ne,
rigar 'yarr figil da ita don da kadan ta dara
cibiyarta sai siket din dogo ne sosai ya kama ta
daga kugunta yayin da ya bada fadi daga kasa,
an tattare gaban da wata zuga, ta yi daurin da ya
zauna a kanta tsam, sai ta yafa wani dan yalolon
gyale kalar kayanta, sannan ta dauki jaka mai
kyalli da takalmi ta sanya wanda yake kamar
tsani, sai kamshi ke fita daga jikinta wanda ba za
ka iya tantance daga ina yake fitowa ba, kwalliyar
ta yi mata kyau don ta iya tsara kwalliya balle
dama ga kyan ta hada abubuwan da suke jan
hankalin maza kanta. Tana fitowa Sala ta dinga
dubanta, can sai ta fashe da dariya tana fadin,
"Ko ke fa mai tsada, ki dubi yanda kika yi kyau
don Allah, amman da kin wani kama zaman daki
tamkar wata matar liman. Ita dai ba tace komai
ba don ba ta son haka din da take mata yau, har
suka nufi hanyar fita daga gidan. Sala ta bisu
tana ta rafka musu addu'a, har soro ta raka su
sannan ta ce, "To idan dare dai ya yi ki yi
kwanciyarki kawai a can, don kada ki dawo dan
saka idon nan ya kama yiwa mutane jarabar ta
sa." Haka nan suka isa bakin titi Asma tana ta
mita, domin dai tunda suka fito motoci ke
tsayawa amman Zainabu ta dage ba za ta hau
motar uban kowa ba yau, don haka sai da suka
isa har bakin titi Asma sai mita take yi tana fadin
da ta sani ta zo da motarta, don wani saurayinta
ne ya kawo ta a mota, duk inda suka gifta sai an
bi su da kallo domin dai Zainabu akwai ta da
daukar idon duk wanda ya kalle ta, sai ka ji
kamar ace matarka ce, sai tasi suka tara ta kai su
gidan Asma din, sai da dare ya yi sannan suka
fita suka tari tasi ta nufi club din. Sanda suka isa
club din sun tadda shi dinke sai cashewa ake yi,
nan fa kawayensu suka yi musu caa a kansu ana
ta cafkewa don sun kwana biyu ba su gansu a
club din ba. Idan ka ga yanda gurin yake da irin
yanayin shigar su zaka rantse babu wacce ta san
Zo na kashe ka da hausa, balle a je ga addini,
domin gurin yana can cikin sabon gari cike yake
da tantiran 'yan iska kamar ba a garin Kano ba
ne garin musulunci ba . Wani saurayin Asma ya
isa ya kama kugunta suka shiga filin rawa suna
takawa, Zainabu ta yamutsa fuska sannan ta nufi
gurin shan barasa (wine station) tana wani taku
tamkar tarwada, ta jawo kujera ta zauna ta
amshi kwalbar mutuniyar tata ta balle bakinta ta
kafa kai ta kama sha babu ko kofi, sai da ta sha
ta ishe ta sannan ta dauko tabar shaidan ta
kunna ta dora kafa daya kan daya tana kallon
kowa daidai, can ta fara caji ga shi an sanya
wakar da take masifar so ta love is wicked, ai
kuwa ba ta san sanda ta yi tsalle ta fada filin
rawar ba, daman ga ta gwanar rawa musamman
an sanya wakar da take masifar so, sannan ta
dace da lokacin da take ciki, habawa nan fa 'yan
maza suka mai da hankalinsu gare ta, wani mai
karambani ya shiga da zummar taya ta har yana
kokarin ruko ta, sai kawai ta zabga masa wani
uban mari gami da yin taga-taga kamar zata fadi.
Gabadaya gurin aka sanya ihu da shewa har da
masu fito, ya dube ta cike da tsananin takaici sai
ya daga hannunsa da zummar ya rama, amman
sai ya ji an rike hannunsa gam. Ya waiga domin
ya ga wanda ya rike masa hannu sai ya ga wani
hadaddan saurayi ne, ya kalle shi yana dariya
sannan ya ce, "Haba yaya zaka taba mana
golding baby? Kai ne fa ka zo har inda take
bayan ba ta gayyace ka ba, ka ga matsa ka bamu
guri dalla." Ya yi kwafa ya bar gurin cike da
tsanani kunya. Ita ma sai ta fice daga filin rawar
don ranta ya baci da iskancin da ya yi mata, don
ba ta shirya kula kowa ba, zuwa ta yi kawai ta
sha abunda za ta sami sanyi a ranta, amman
wani dan iska yana neman bata mata rai. Gayen
da ya rike hannun wawan ya biyo ta sanda take
janyo kujera tana kokarin zama, ya kura mata ido
tamkar maye, ita kam da ta kalle shi sau daya sai
ta kauda kanta gefe. Ya rausayar da murya cike
da yaudara ya ce, "Barkan ki da hutawa golding
baby. Ta rausayar da kanta tana dubansa kawai
tana zukar tabar shaidan din ta, sai ma ta
lumshe idonta ta ki cewa komai. Bai damu da
hakan da ta yi ba ya cigaba da magana, "Sunana
Amir, tunda na shigo club din nan kika kashe
mini idona, domin dai ke ce tauraruwa mai haske
a gurin." Ta kuma kallon sa shekeke, sai dai ko
babu komai yana da kyau da iya gayu, sai ya fara
tsokano mata kamannin Mustafa ma, amman sai
ta dake ta ce, "To kai yanzu yaya za'a yi? Ni ka
ga abinda ya kawo ni na sha na ji sanyi a raina."
Ta nuna masa tabar dake hannunta. Ya kuma
kwantar da murya irin ta 'yan mazan da suka iya
sace zuciyar mata ya ce, "To ban da abinki ai duk
jirgi daya ya kwaso mu, ki kwantar da hankalinki
za ki samu duk abinda kike so a gare ni kin ji ko?
Mata da dama suna so na amman ke daya tal
kika mini, na san zan iya burge ki." Ta yi
murmushi kawai tana dubansa a ranta tana
fadin, "Malam baka san Mustafa ba ne ya fi ka
komai, ai za'a dade kafin a sami kamar sa a cikin
maza, amman tunda ya yadda ni bari na gwada
ka, ai da babu gwara babu dadi."Da wannan
shawara ta mike yana biye da ita suka nufi dakin
da ya kama don irin haka. Ta fuskanci Amir shi
ma hatsabibi ne irin ta, sai dai sam bata ji ya
burge ta ba, hasalima ji ta yi ba zata iya
mu'amala da shi ba, sai kamannin Mustafa suka
fara yi mata gizo duk da kwayar da take kanta
daram shi ta dinga gani a can bakin kofa yana
mata murmushin da yake kashe ta da shi, don
haka ta hankade Amir ta kwashi takalminta da
jakarta da gyalanta a hannu ta nufi kofa. Ya bita
da sauri yana fadin, "Oh! Baby kada mu yi haka
dake mana, zo ko nawa kike so zan baki, please
kada ki bar ni ki taimaka mini mana." Ta yakice
hannunsa daga jikinta da ya kamata ta galla
masa harara tana fadin, "Kai gaye ka rabu da ni."
Da tsawa take maganar don haka ya tsorata ya
sake ta da saurinsa. Ta fice fuu kamar
mahaukaciya, tana tafe tana hada hanya kamar
zata kifa saboda tasha ta fi karfinta. Shi kuwa
zaman dabaro ya yi bisa kafet din ya dafe kansa
cike da tashin hankali, shi a tarihin rayuwarsa bai
taba neman yarinya ta ki shi ba saboda yana da
kyansa da kudinsa ga ilmi, sannan shi din gwani
ne gurin iya soyayya, amman ya sami wacce ta
kwafsa masa, lallai Bebin nan ta shammace shi
matuka, ga shi ta tsaya masa a ransa, don ya
dade a bariki bai ga macen da ta hada komai
dari bisa dari kamar ta ba, amman babu komai
in dai kare yana yawo zabo ma yana yawo wata
rana za'a hadu, don haka ya fice neman wacce
za ta rage masa daren nasa. Ita kam haka ta nufi
hanyar fita tamkar zata kifa, takalmi da jaka da
gyale duk a hannunta, Allah dai ya taimaka Asma
ta hangota bayan ta futo daga watsewarta, don
haka ta nufe ta da sauri tana mata magana
amman ko kallonta bata yi ba, da dai ta lura
kawar tata tayi duf ta koma gurin saurayin nata
ta nemi alfarmar ya kaisu gidanta, babu musu ya
amince don yana ganin wata karin dama ce a
gare shi ma. Da kyar ta samu ta turata a motar
tana ta tirjewa suka nufi gidan Asma din, a falo
ta zube Asma ta fara tambayar ta abinda ya
faru, amman ko kala ba tace ba daga karshe ma
sai ta mike da kayanta a hannu ta nufi dakin
kwanan Asma din.Asma ta kalli saurayin nata
wanda yake tsaye yana kallonsu da alamun
rashin damuwa a idonsa, ya daga kafada yana
fadin, "Wannan kawar taki muguwar 'yar buyagi
ce wallahi, ki dubi yanda ta yi duf ta kuma ki
sauraron kowa, sai gasawa 'yan maza gyada a
hannu take yi, ki rabu da ita kawai ki zo mu
kwanta." Bata yi masa musu ba suka nufi daya
dakin baccin nata.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ita kam tana isa dakin baccin ta yi watsi da
kayan dake hannunta ta kwanta jabar a gado,
duk da bata cikin hayyacinta hakan bai sanya ta
manta da kamannin Mustafa zuman ta ba, harma
sai take ganin kamar sanda take cikin hayyacinta
tafi dauriyar rashinsa akan yanzu ma. Wani irin
ciwo mai zafi ya taso mata a kirjinta, ta ji
zuciyarta kamar tana tafasa, ta dafe kirjin da taji
yana mata zafi hawaye suka shiga wanke mata
fuskarta a hankali ta dinga fadin, "Mustafa mai
nayi maka ka guje ni, ka san yanda nake jin zafin
rabuwa da kai a zuciyata kuwa? Zo ka taba zuciya
ta kaji kai kadai ne ka mamaye ta, muddin ka
barni zan mutu ne kawai, bani son kowa sai kai,
kai ne rayuwar Zainabu." Tamkar yana gabanta
haka take magana, saboda kwayar ta dake gaya
mata karya wai gashi nan a gabanta zaune a kan
kujera, ta lumshe idanuwanta ta mika hannunta
tana fadin, "Ka daure ka taba zuciya ta ka ji,
domin na kusa mutuwa da sonka." Ta jawo fulo
ta rungume sai ta saki kuka mai ciwo, wai wacce
irin masifa ce ke barazanar daukar rayuwarta ne?
Ta yunkura ta wurgar da fulon ta nufi jakarta
domin wata shawara da zuciyarta take kitsa
mata. Ta kama binciken kayan jakar tana
watsarwa, har ta ci karo da abinda take nema
wato wayarta ta tafi da gidanka, ta kama laluban
lambarsa har ta yi sa'a ta samo ta da kyar tana
ganin dusu-dusu ta kama kokarin nemanta. Daga
can gidan Momi ce a kwance ta sanya wayar
Mustafa a caji wacce ta ci karo da ita a dakinta,
don anan ya yadda ta sanda ya suma, ta ji ta
tana kara ta mike da sauri don taga mai kiran,
don tana zaton ko abokansa ke nemansa ta sanar
da su bashi da lafiya. "Zainabu Zuma." ta gani
baro-baro a jikin gilashin wayar, haushi da takaici
sai ta ji kamar kada ta daga, amman sai taga
wannan ce damar da ya dace ta gargadi yarinyar
ta rabar mata danta kawai. "Musty zumana! Yaya
kake?" Daga jin muryar ta kasan tana cikin maye
ne. Hankalin Hajiya Kubra ya kuma tashi matuka,
don haka da bacin rai ta fara magana, "Ke! 'Yar
iska ba Mustafan ba ne, shegiya karuwa kin dafe
mini yaro kamar kaska, yanzu haka yana can a
gadon asibiti rai a hannun Allah saboda mallake
shi da kika yi tsafi da tsafi, to bari na gaya miki
ko da kinfi kuturu naci, kuma koda kuna tsafi da
kare ne baki isa ki auri Mustafa ba wallahi, domin
shi yaro ne dan mutunci da ya futo daga gidan
mutunci, kurwarsa kur!" Zainabu sai taji ta
wartsake gaba daya domin dai ko daga bacci ta
tashi ba zata taba manta muryar Hajiya Kubra
ba, ga shi kuma tace Mustafa ba shi da lafiya
yana can rai a hannun Allah, sai taji ko kusa
maganganun ta basu bata mata rai ba sama da
ciwon Mustafa, ta daure da kyar tace, "Hajiya ki
yi hakuri don Allah ki bani Mustafa mu yi magana
ban san bashi da lafiya ba, yana ina yanzu? ki
bani shi kada na mutu." "Ki mutu din mana, ai
da mun huta da bala'in da kika ja mana, shegiya
macuciya kiji yanda kike magana da alama giya
kika sha, Allah ya tsaremu da hada zuri'a da ku,
dangin na ayya gayyar tsiya." Ran Zainabu ya yi
matukar baci da jin kalaman Hajiya Kubra, lallai
ta yadda wani yana cin arzikin wani ko a lahira,
don haka Hajiya Kubra ta ci albarkacin danta,
amman duk da haka ya dace ta sanar da ita ko
da kalma daya ne, ta bude baki da zummar tayi
magana amman sai ta ji layin ya dauke, alamar
ta katse kenan. Ta kuma kiran layin amman sai
aka sanar da ita yana kashe ne ma, ta fada gado
cike da tashin hankali ga maganar da Momin ta
gaya mata ga kuma rashin lafiyar da aka ce mata
Mustafa yana yi, haba ta san haka kawai Mustafa
ba zai iya rabuwa da ita ba ashe bashi da lafiya
ne. Hajiya Kubra tana tsaka da wayar ta ji ta
mutu tana dubawa sai ta ga caji ne ya kare don
bata dade da jona wa ba, kuma sanda take
wayar ta goce daga cajin, ta yi kwafa gami da
wurgar da wayar cike da bacin rai, don yau ta so
ta gayawa yarinyar nan maganar da zata rabar
mata da danta dole, ta fada gado ta kwanta
amman sai taji bacci ya kauracewa idonta gaba
daya, ta mike zaune ta hada tagumi da hannuwa
bibbiyu. Wai yanzu wannan 'yar iskar yarinyar
Mustafa ke so? Lallai bata raba dayan biyu daga
ji a cikin maye take magana ma, tabbas komai zai
faru sai dai ya faru amman ba zata yadda danta
ya auri karuwa ba, ga shi ta lura kamar Alhajin
ya fara amincewa, don yanda taji kalamansa ta
fuskanci ya sauko daga kan kudurinsa, don dai
bai san wacece Zainabu ba ne, ita kam ta yi
mata farin sani.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Da safe ma ta kuma kiran layin nasa amman a
rufe yake, tunda ta idar da Sallah da asuba take
kiran layin nasa amman a rufe yake, yau kam ta
jima tana yiwa Mustafa addu'ar samun lafiya a
sallar ta, a bandaki ma gurin wanka ta jima tana
tunanin yaya za ta yi, har ta gaji da dukan
shawar amman bata sami wata ma futa ba, daga
karshe dai ta yanke shawarar ta ta tadda Asma
ta ji irin shawarar da za ta ba ta. Ta shirya cikin
koriyar atamfar Asma super wax, dinki ya kamata
sosai don tafi Asma din jiki, ta dora dankwalin ta
yayi das a kan nata, duk da bata da wadataccen
gashi ta kanyi kitso koda yaushe ko ka tadda ya
sha gyara, da yake kuma tana da saje na gefen
kunnen kuma gashin nata mai taushi ne sai kayi
zaton tana da gashi mai dama kasancewarta fara
tas. Fuskarta ta yi fayau domin babu kwalli balle
jan baki, sai ta futo a ainihin (natural) din ta,
hakan ma ta yi kyau matuka, don idanuwanta
daman masu kama da kalar zuma ne bata sanya
kwalli sai dai taja jagira kadan a cikinsa, don har
wani kore-kore yake yi tamkar na mage saboda
kyau da kyalli, masu irin idon nata kadan ne a
duniya ma, musamman idan ta so iskancinta sai
ta dinga wani lumshe su tana wani budewa sai ka
ga mutum ya sukurkuce mata. A falo ta tadda
Asma daga ita sai wando (three quarter) iyakacin
gwiwa tana karyawa gami da kallo, ta sami kujera
ta zube can kuma sai ta mike tana fadin, "Ina
fatan dai ba shegen dan daudun nan ne ya yi
miki girki ba don kin sanni ni ko a gidan mu da
kaina nake girki na don bana son jagwalgwalo."
Asma ta yi dariya tana fadin, "Ai kuwa sai dai ki
dafa wani don nasan halinki ni kam ina da mai
aiki babu abinda zai sanya ni shiga kicin." Ta ja
tsaki tana fadin, "Ai kya ci mara dadi da kazanta
,tashige ciki ta kama kacaniyar samarwa kanta
abinda za ta ci. Bayan ta kammala girka abinda
zata ci ta futo falon ta zauna ta kammala ci
sannan ta ce da Asma din, "Wai ina sha-sha-shan
naki ban ji motsin sa ba ko har kin gama da shi
ne?" Asma ta yi dariya tana fadin, "Shegen Ofi ya
wuce don da kunya dai yace zai koma gida shiri
sai dai yayi musu shigar dare." Ta ja tsaki tana
fadin, "Allah dai ya shirya shi." Sannan ta sauya
maganar da fadin, "Ke nifa jiya na kira wayar
Mustafa....." "Kai amman kin bada gayu wallahi,
ke da nace ki share shi har sai ya kawo kansa mu
gasa shi tamkar gyada?" Ta tabe baki sannan ta
ce, "Na so yin hakan amman na gaza, jiya ban
cikin hayyacina sosai nayi kiransa, don ban zaci
zan wayi gari ba, saboda wani irin zugi da
zuciyata ta dinga mini, kai Asma so masifa ne
wallahi, sai dai me, kin san Babarsa ce ta daga
wayar?" "Bar gayan don Allah. Ya ya aka yi
wayarsa ta je hannunta? Lallai ki ce kunyi babu
dadi." Zainabu ta dan tsuke fuska ta ce, "Allah
sarki zumana ashe bashi da lafiya, duk da dai
bata gaya mini ainihin abinda ke damunsa ba sai
cin mutunci da ta yi mini na san ciwon so na ne,
don haka maganganunta kadan suka yi mini ciwo
domin ta saba gaya mini irinsu, amman nayi
alkawarin da izinin Allah sai na auri Mustafa don
na nuna mata don ta haife shi ai ba ita ce ta
halicce shi ba, sai na nuna mata iyakacin
takamarta wallahi a kansa, maganganun da take
gaya mini yanzu ne zan nuna mata karuwancin
da nake yi ai da danta nake yi, ta ce daman
waye zai auri 'yar iska to dan ta ne zai aura da
iznin Allah, ni yanzu yanda zan yi na ganshi ne
ma ya fi damuna domin nasan ba karamin ciwo
ne zai sanya Mustafa ya gaza kirana ba." Asma ta
ce, "Lallai ki ce da walakin goro a miya, ni kaina
na yi mamaki da kika ce wai Mustafa ya bar ki,
amman dole ne mu binciki asibitin da yake mu je
mu duba shi, gama karyawa muje gurin
maigadinsu mu ba shi na cin goro muji asibitin da
yake." Karfe tara na safe likita ya shiga duba shi,
sai ya jiyo shi yana magana a hankali, ya matsa
daf da shi ya kara kunnensa daidai bakinsa sai ya
jiyo yana fadin abinda yake fada tun da ya farka,
"Zainabu! Zainabu!" Ya yi niyyar yi masa wata
allura amman sai ya fasa ya kara matsawa kusa
da shi ya fara shafar kansa a hankali yana kiran
sunan sa a hankali. Ya fara far-far da
idanuwansa alamar yana son ya bude amman ya
gaza, ya kuma matsawa dai dai kunnensa yana
fadin, "Mustafa kana son ka ga Zainabun ka?
kana son a kawo maka ita ka ganta? to maza
bude idanuwanka na gani." A hankali ya bude
idanuwansa yana kalle-kalle, likitan ya yi
murmushi sannan ya ce, "Msutafa Zainabu kawai
kake son gani yanzu? ka tabbatar idan ka ganta
ka warke kenan?." Bai iya yin magana ba saboda
bakinsa da yaji ya yi masa nauyi sai dai kawai
daga kai da yayi alamar eh!.Likitan ya ce, "To shi
kenan ka kwantar da hankalinka za'a kawo maka
Zainabu har nan gurin ka ganta kaji ko?" Da haka
ya fice waje ya tadda Alhaji Abdullahi da Hajiya
Kubra dake zaune suna jiran jin abinda zai ce
musu, ya dube su ya ce, "(Cogratulations), ina
taya ku murna, domin dai danku ya farka, Hajiya
Kubra ta daga hannu tana fadin, "Alhamdulillah,
mun gode likita." Ya kuma cewa amman akwai
wasu sharudda da zan gindaya muku, kai Alhaji
ka biyo ni Ofis ku kuma kuna iya shiga ku gan
shi. Dadi da farin ciki ya cika su saboda ganinsa
idonsa a bude yana ta kalle-kalle, suna shiga ya
bisu da kallo sai kuma ya yi murmushi don ya
shaida Mominsa ce da kannansa. Suka isa suka
zauna kusa da shi suna dariyar murna, Momin ta
hau shafar kansa tana fadin, "Babana sannu ka
ji, yaya jikin naka?" Ya bude bakinsa ya ce,
"Alhamdulillah, Momi yaushe aka kawo ni nan
ne?" Da lallashi ta ce, "Kada ka damu ka kusa
komawa gida tun da kai ka sami sauki, za ka ci
abinci ne?..... Ko da yake bari likita ya dawo mu
tambaye shi." Haka nan ta dinga jan sa da hira
cike da jin dadi da farin cikin farfadowar tasa.
Karfe goma suka isa dakin da yake, domin dai
sun ga Maigadin ya sanar da su asibitin da yake
har ma da dakin da yake don ya je ya duba shi,
sai dai ya roki alfarmar kada su ce shine ya sanar
da su. Sanda suka isa Momi ce ta fara ganinsu,
Zainabu ta ci kwalliya matuka da wani Swiss lace
haka ma Asma din, ko da daga bacci ta tashi ba
zata manta da kamannin Zainabu ba, don haka
ta mike a gigice da masifa. Shi kuwa Mustafa tun
da yaji muryarta ta yi sallama ya kura mata ido
da wani mayataccen so, ji yake kamar ya zama
tsuntsu ya isa inda take. "Ke! Me ya kawo ki nan?
'Yar iska karuwa, ina ce jiya na yi miki gargadin ki
rabar mini da da na, ko shi ne don masifa kika
kuma biyo shi." Mustafa ya runtse idonsa cike da
jin zafin kalaman Momi, ita kuma Zainabu kyam
ta tsaya kamar an dasa ta ta dukar da kanta
kasa. A tarihin rayuwarta yau ce rana ta farko da
wata ta zage ta tayi kurum ba tare da ta rama
ba, zuciyarta ta yi bakikkirin sai tafasa take yi,
lallai Momin Mustafa ta ci darajar masu daraja.
"Ba magana nake miki ba? Ki fice mana daga daki
in ba haka ba na yi miki rashin mutunci, ki dubi
irin zuri'ar mu kin san ko dagamu yaron nan bai
dace da ke ba, don haka ki rabu da shi tun da
girma da arziki, ba zamu yadda ya auri karuwa
'yar shaye-shaye ba muddin muna raye." "Momi
don Allah ki yi hakuri kin ga fa yanda Yaya
Mustafa ya rintse idonsa kada ciwon nasa ya
dawo." Ran Momi ya baci don haka da zafin rai ta
ce, "Ke rabu da ni idan wannan 'yar....."
Shigowar Alhaji Abdullahi ne ya sanya ta yin
shiru. Ya dubesu ran sa a bace ya ce, "Kubra kin
manta kuna tare da mara lafiya ne, eye? Ko so
kike yi zuciyar yaron nan ta buga ne, wannan
wane irin so ne kike yiwa danki? To ki yi hattara
in ka kashe shi sai naga wanda zaki kuma
matsawa haka."Ta kwantar da murya ta ce, "Ka
yi hakuri Alhaji ba da shi nake ba yarinyar nan ce
ta zo Zainabu ga ta nan." Ta nuna Zainabu,
"Shine na ce ta fita." Ya bi Zainabu da kallo
wacce kanta ke a kasa gefe da kawarta wacce ta
rikewa hannu, don Asma din ta so rama mata cin
mutuncin da aka mata amman ta rike hannunta
gam alamar kada ta ce komai, don haka suka yi
shiru gaba dayansu. Ya dube ta da kyau ya ce,
"Wannan ce Zainabun?" Ta ce masa "Eh." da
sauri. Ya ce, "To wuce mu je waje, ke Sumayya
taso mu je waje. Zainabu je ki ki ga jikin nasa."
Hajiya Kubra ta yi sororo cike da tashin hankali,
amman ganin babu wasa a maganar Alhaji
Abdullahi ya sanya ta bi bayansa shi da Sumayya
domin dai har sun nufi kofa su, bayan ta
zabgawa Zainabu harara gami da yin kwafa.
Zainabu ta yi murmushin cin nasara ta rufe kofa
da sauri ta nufi gurin Mustafa wanda har lokacin
idonsa yana runtse. Ta durkusa a gabansa ta
kwantar da kanta daidai kirjinsa ta kamo
hannunsa ta sakale cikin nata, ta matsar da
bakinta dai dai kunnensa, cikin wani salo da
kashe murya ta ce, "Musty Zuma please wake up,
ka tashi." Ya bude ido a hankali yana duban ta,
bugun zuciyarsa ya fara sauyawa zuwa daidai,
jinsa yake yi tamkar a wata duniyar daban, ya
dago hannunsa wanda ke rike a cikin nata,
wanda ba'a sanyawa karin ruwa ba ya
rungumeta sosai a jikinsa, cikin kunnuwanta yake
fadin, "Zainabu ke ce da gaske? Ina kika boye ba
ki zo ba na kusa mutuwa?" Hawayen dadi suka
dinga disowa daga idanuwanta suna sauka a
kirjinsa, wanda yake jinsu kamar ana yayyafa mai
dadi ne a kirjin nasa don yana wanke masa zuciya
ne. "Ba zan kuma barin ka ba, ina sonka ban san
ba ka da lafiya ba, nima ina can cike da zullumi
da fargaba, na yi zaton ka bar ni, ina matukar
kaunarka Musty, ina sonka da yawa
Mustafa."Wani farin ciki ya dinga shigarsa, ya saki
dariya a hankali sai ya ji kamar wani karfi yana
shigarsa, sun jima a haka kamar ba zasu rabu ba,
Asma na tsaye harde da hannuwa a kirji tana
dubansu cike da tausayi da sha'awa. Shi kuwa
Alhaji Abdullahi da ya fita kai tsaye Ofis din likita
ya nufa, ko bai yi magana ba ta san abinda yake
nufi wata ta bishi Ofis din, don haka ta bishi har
ofis din. Sumayya kuma ta sami guri ta zauna
bisa wasu kujeru ita da Zainab. Likitan yana
shirin fita ya shiga ofis din nasa da sallama, ya
daga da sauri ya dube shi yana tambayarsa ,
"Alhaji akwai wata matsala ne?" Alhaji Abdullahi
ya ce, "A'a babu wata matsala, ina dai so kayi
mata bayani ne kamar yanda kayi mini." Ya nuna
Hajiya Kubra da ta shigo Ofis din.
Likitan ya ce, "Ok sit Hajiya, na gane ki zauna
Hajiya."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Babu musu ta jawo kujera ta zauna, shima
Alhajin ya jawo kujerar ya zauna. Likitan ya
dauko file din Mustafa ya dan dudduba kana ya
kalle ta ta cikin gilashin kara gani, (medicated
glass) ya ce, "Hajiya gaskiya kamar yanda na gaya
miki tun da farko yaron ku ya kamu da ciwon
zuciyar har zuciyar sa ta fara kumbura. kuma a
binciken da aka yi muna zaton wata damuwa ya
sanya a ransa, mun yi iyakacin kokarin mu ya
fara samun sauki, sai dai mun lura ba zai koma
dai dai ba har sai da wata Zainabu, wacce
albarkacin sunanta muka samu yau ya bude
idonsa....." "Na shiga uku na lalace, gaskiya likita
ka sake magana, ka san kuwa ko wacece
Zainabun da yake fada? ka san halin....." "Ba
lallai sai mun san wacece Zainabu ba, fatan mu
dai tazo kusa da shi idan har zata amince, domin
ganinta ne zai sanya ya dawo cikin walwalarsa,
sannan ciwon yayi gaggawar barinsa, idan ya so
idan ya warke kome ya dace a yi sai a yi." Likitan
ya katse ta da dogon sharhinsa. Ta yi tagumi
ranta a tsananin bace, ta kuma daurewa ta ce,
"Yanzu likita bayan haka babu wata shawarar da
kake ganin zata inganta lafiyarsa? Dole sai dai
wannan din?" "Eh, shi ya sanya ma kikaji na ce
haka din, sai kuma kashedi na biyu dole ne a guji
bata masa rai, duk wani abu da zai zamana akwai
damuwa a cikinsa dole ne ya nisance shi, idan
kuwa ba haka ba akwai barazanar zuciyarsa ta
buga lokaci guda (heart failure), ya fadi ya mutu,
don haka ne a kiyaye ka'idojin da na gindaya
muku." Ya mika mata file din ya ce, "Ki duba nan
wata kila zaki fahimci wani abu tunda kina da
ilimi ai." "A'a bar shi kawai ba zan gane
jawabinku ba don rubutun likitoci ba kowa ne ke
ganewa ba....." "Ta shi mu tafi." Maganar Alhaji
Abdullahi ta katse ta, ta mike salo-salo ta bi
bayansa jikinta a sanyaye babu kuzari har lokacin
ranta a bace yake. Kai tsaye gurin motarsa ya
nufa ya kirawo Sumayya a waya ya ce ta
taddashi a gurin da yayi fakin din motar ta sa,
kusan tare suka iso da Sumayyan, Hajiya Kubra
ta shiga gaba ta kame zuciyarta na suya.
Sumayya ta leko ta windon gilas ta ce, "Ga ni
Dady." Ya dubeta gami da fadin, "Yau ki kula da
Dan uwanki zan turo direba ya kawo muku abinci
ke da bakin naku, sai da yamma zamu dawo da
mamanku, kin ji ko?" Ta ce, "To Dady a dawo
lafiya." Ya ce "Amin." Kana ya ja motar suka bar
harabar gurin. Sumayya da Zainab suka koma
dakin da Mustafan yake ta kwankwasa lokacin
Zainabu na gefensa rike da hannunsa suna hira
jefi-jefi, gabansu gaba daya sai da ya buga
domin sun yi zaton ko Momi ce ta dawo. Zainabu
ta dubi Asma ta ce, "Ki bude kofar mana." Asma
tayi jim kamar ba zata bude ba can kuma sai ta
mike ta bude.Sumayya da Zainab suka shigo
fuskarsu cike da fara'a suka gaida su Zainabu.
Zainabun ce ta fara magana, "Hala ke ce kanwar
tamu da Mustafa ke yawan bani labarinki?" Ta
dafa Sumayya tana fadin, "Don kamarsu da
Mustfa ta baci." Sumayya ta ce, "Eh nice."
Zainabu ta ce, "Allah sarki, yanzu kina wace
school ne?" "Ina BUK (Dep. Of Nigerian
Languages) bangaren harsunan Nigeriya, ina
karanta Hausa Ingilishi." "Allah ya taimaka, bari
mu tashi mu wuce gida don mun bar su Dady a
waje." "Laa ku yi zamanku yanzu ma sakon dadi
din ne ya shigo da ni yace ku zauna su sun wuce
gida sai da yamma zasu dawo, zai turo direba ya
kawo mana abinci, mu yanzu gurin wata
kawarmu zamu da muka yi secondarary school
zamu don tana (Catering Dept.) bangaren abinci,
za mu gaisa don kullum muna zuwa gwara na bar
Yayar tamu ta duba jikin (Big brother) sosai, don
daga ganinki har ya wartsake, amman da tamkar
gawa yake sai numfashi kawai." Suka yi dariya
gaba dayansu har da Mustafa yayi murmushi,
suka mike suka fice suna fadin sai mun dawo.
Asma ta ce, "Lallai kawata kin kasance mai sa'a,
ki dubi yanda komai ya zo da sauki, wallahi ban
yi zaton zamu sami ganin Mustafa a yau ba
yanda kika sanar da ni yanda kuka yi da Mominsa
jiya a waya." Zainabu ta dubi Mustafa tana
murmushi ta ce, "Abin a jinin mu yake, haduwar
jini ce Allah kadai ya san abinda ya boye a
tsakaninmu ko zumana?" Tana magana da wani
salo na sace zuciya. Ya yi murmushi kawai sannan
ya ce, "Zainabu dan dagani mana ki jingina ni da
fulo bayana ciwo yake yi." Ta kamashi sosai a
jikinta ta taimaka masa ya tashi ta sanya masa
filo a bayansa. "Yaya ko a hada maka shayi ne?"
Ya dan girgiza kai ya ce, "Sai dai ki je ki tambayo
likita idan yace na sha sai ki hada mini." Ta ce,
"Shi kenan bari na je na jiyo, kawar zo muje."
Suka fice gurin likita. Su kuwa su Alhaji da suka
isa gida kowa sashinsa ya shige, Hajiya Kubra
tamkar zata mutu don bakin ciki, ita gani take yi
kawai wata makarkashiya aka hada domin ta
hada danta aure da karuwa kamar yanda take
kiran Zainabu. Da wayarshi Alhaji Abdullahi ya
kirawo mai aiki yace maza ta shirya abinci ta
baiwa direba ya kai asibiti.Ta ce "To Alhaji an
gama." Nan da nan ta hada kayan abinci ta hau
girki, shi kuma babbar rigarsa ya cire ya haye
gado ya kwanta don ya sami hutu. Sai karfe daya
da kwata ya tashi ya watsa ruwa kana ya nufi
masallaci ya bi jam'in Sallar azahar kana ya shigo
gida, kai tsaye sashin Hajiya Kubra ya nufa. Tana
zaune bisa darduma da alama Sallah ta idar
itama, sai dai ta hada uban tagumi, daga ganin
yanayin fuskarta tana cikin tsananin damuwa ne.
Ya zauna a gefen gadonta ya kirawo sunanta, ta
juyo da sauri cike da mamaki tana dubansa,
domin ba tayi zaton zai shigo sasashin ta a
wannan lokacin ba. "Ina so mu yi wata magana
da ke, ina fata zaki nutsu ki yiwa magana ta
duba na tsanaki, kada ki sanya wata fassara a
cikin zuciyarki." Ta daga kai alamar to kawai. Ya
ce, "Yauwa, daman akan maganar yaran nan ne,
naga kamar kin kufula ko nace kinyi fushi da
abinda likitan ya yi miki jawabi. Na sani duk iyaye
ba zasu so ace dansu ya auri macen da ba ta
gari ba, sai dai mu yau Allah ya jarabce mu da
dan mu yana son irin wannan matan, abu daya
nake so ki kawo a ranki ko kiyi alkalanci shi ne a
ina Mustafa ya gano Zainabu? Wacce alaka ce ta
hada su har suka shaku haka har ya kamu da
ciwon zuciya don za'a raba su? Amsa daya ce,
abokin barawo dai inji 'yan magana barawo ne,
ba na raba dayan biyu can gurin shashancinsa ya
hadu da ita, ban taba zargin Mustafa yana
wannan harkar ba sai da ya furta da bakinsa zai
auri Zainabu, sannan na san lallai yana wannan
mu'amalar. Duka hukuncin Zainabu da Mustafa
daya ne a gurin Allah, don shi babu ruwansa da
jinsin mace ko namiji kamar yanda mu hausawa
muke cewa, wai iskanci ado ne ga da namiji to
shi Allah babu ruwansa, kuma ina zaton wata
jarabawa ce Allah ya dorawa Mustafa ta son 'yar
iska ko karuwa kamar yanda kike kiranta, domin
ya nuna mana shi babu ruwansa da wancan
magana ta bahaushe. Don haka ina son ki
kwantar da hankalinki muzubawa sarautar Allah
idanu,idan ya kaddara aure dan Allah zai iya
dora miki wata lalurar da kina ji kina gani dole
za'a yi wannan aure. Ki kyale shi ya auri Zainabu
don idan Allah ya kaddara matarsa ce duk irin kin
da muke mata sai ki ga Allah ya kaddara anyi
abin, idan kuma Allah ya kaddara ba matarsa
bace sai kiga sun gama soyayyar ya auri wata can
daban, ki yi masa addu'a da neman shiriya
garesu baki daya, domin shi da na kowa ne, ina
fatan kin gamsu da jawabi na? Amman fa kina da
damar da zaki aura masa wacce kike so daga
baya don kina da iko a kanshi ba wai ina son na
nuna miki karfin iko ba ne, a'a nayi haka ne
domin samun ingancin lafiyarsa da kwanciyar
hankalinmu." Ta yi doguwar ajiyar zuciya gami da
goge hawayen da ke sakkowa bisa fuskarta ta ce,
"Shi kenan Alhaji Allah ya zaba mana abinda yafi
alhairi, ni daman ba yarinyar naki ba illa
halayenta don babu wanda zai so ace yau a
zuri'arsa an samu batacce, amman shike nan
Allah ya shirya zamu ce, sai dai Allah ya sani
bana kaunar yarinyar nan har abada don tayi
mini abinda har abada ba zan manta da ita ba,
sannan idan Allah ya nufa ta auri yaron to babu
ruwana da harkarta, sannan zan aura masa
nitsatstsiyar mace kamar yanda nake da buri a
rayuwa ta." Ya yi murmushi ya ce, "Hadizatul
Kubra kenan, na ji ra'ayinki kuma ra'ayi ba gaba
bane sai dai ina son ki sassauta kiyayyar da kike
mata darajar danki don Allah." Ta tabe baki
kamar ba zata ce komai ba kana ta daure ta ce,
"Shike nan ya wuce, amman duk sanda za ta zo
asibiti ba zan je ba hasalima na daina zuwa da
rana sai da daddare don haka sai ta dinga zuwa
a lokacin kada mu hadu ban sani ba na gaya
mata mummunar kalma." Ya ce, "Shike nan,
yanzu dai a daure a bani abinci don cikina ya fara
kiran ciroma, don naga yau fishi aka yi dani ko
abinci ba'a yi mini tayi ba." Ta ji kunya ta kamata
ta mike da sauri tana fadin "Tuba nake, kaje
sashin naka yanzu zan kawo maka." Ya ce, "A'a
anan zan ci tunda dai sarautar ta motsa yau." Ta
yi dariya gami da ficewa dauko masa.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Cikin ikon Allah jikin Mustafa ya yi sauki, kullum
Zainabu na zuwa tana wuni a gurinsa, takan dan
zo masa da abin motsa baki, duk da kullum ana
kawo masa daga gidansu, wata rana su zo da
Asma wata rana kuma ita kadi take zuwa. Gaba
daya yanzu Hajiya Kubra ta daina zuwa da rana
sai dai da yamma ko da safe, don haka suka
sami damar baje kolin soyayyarsu. Sala ma tayi
mitar har ta gaji domin dai samarin Zainabu ko
nace abokan watsewarta tun suna sintiri har sun
gaji sun fara janye jikinsu, dan kudin da suke
kawo mata yanzu duk sun daina, ita ma Zainabu
yanzu babu kudi kamar da sai wata ya kare take
samun albashi, don ma Sadiku yana kawo mata
kayan abinci da kuma kanwarta Karima da ita ma
take dan kawo mata wani abun wani lokaci,
amman duk ta raina tafi son a dinga kawo mata
na banza(wai a banza,masu karatu kuyi alkalanci
abanza take samu?) shi kuwa Baba Abbakar yana
nan jiya iyau, tsufa yana kama shi amman ya
gaza tsinana wa kansa wani abin kirki. Kullum
yana gindin bishiya duk wanda zai wuce ko zata
wuce sai sunyi gulmarsa, idan mai kudi ne su
bishi da sai kayi ko a dawo lafiya ya hajjaji, a bisu
da naira dari biyar ko dari biyu-biyu suna
wawaso. Su kuwa sauran yaran sunan nan wasu
suna karatun wasu kuma suna nan suna ta
yawon talla, don babu wanda ya isa ya cirewa
Sala ra'ayin talla a jikinta.
An sallame shi cike da samun cigaba a lafiyarsa,
sai dai an kafa masa dokoki na shaye-shaye, dole
likita ya hanashi shan ko da taba ne balle kwaya
ko giya, amman tsakaninshi da shi yayi masa
kashedin don dai iyayan nasa basu san yana sha
ba da bamu san yanda Hajiya Kubra zata kuma ji
ba. Ya dawo gida cike da dardar domin dai bai
san yanda ake cikin akan maganarsa da Zainabu
ba, shin sun amince ne ya aureta ko kuma suna
nan akan bakansu ta dole sai dai ya nemo wata
ya aura? Shi dai bai cigaba da zuwa gidansu
Zainabu ba, sai dai sun cigaba da yin waya, a
wannan lokacin sai suka ji tamkar an daure su a
kurkuku ne, ga shi har yanzu iyayensa ba su ce
masa komai ba, har ya koma bakin aikinsa yana
zaman dar-dar.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
****************
Ranar wata juma'a wacce tayi dai-dai da sati biyu
da fitowarsa daga asibiti Alhaji Abdullahi ya yi
kiransa falonsa da yamma. Gabansa ya kama
faduwa don bai san kiran da yake masa ba, ya
isa falon idan zaka tsaga jikinsa tamkar babu jini,
ya zauna a kasa ya kuma durkusawa ya gaida
Baban nasa. Alhaji Abdullahi ya amsa fuskarsa
babu yabo babu fallasa, kana ya fara magana,
"To Mustafa ka ga dai abubuwan da suka faru
tun daga ranar da wannan al'amarin ya faru. Da
farko ni da Mahaifiyarka mun nuna bama son
auran nan har mun kafa maka wasu sharudda to
kuma sai gashi wannan ciwo ya bullo sanadin
dokar da muka kafa maka. Ba wai muna kin
Zainabu akan mu bane a'a sai dai muna kinta ne
saboda halayenta, amman a iyakacin tunanina da
kuma yanda ka dage kana son yarinyar nan duk
da illar da muke hange maka nasan akwai wani
abu da Allah ya boye a kasa kuma dai 'yan
magana suna cewa, abokin barawo dai shima
barawon ne. Don haka muka amince ka auri
Zainabu domin samun wanzuwar lafiyarka,
amman da sharadi, da farko dole ne ta zama
mace ta gari, abun nufi ta tsarkake daga halayen
ta miyagu, sannan ta sami tsarki, sharadi na biyu
kuma dole ne ka rintse idonka daga jin duk wata
magana daga mahaifiyarka don ta fadi bata
kaunar yarinyar nan, abu na karshe kuma tace
dole zata zaba maka wacce take so ka aura daga
baya, ina fatan ka amince da wadannan
sharudda? Tunda ya ji Babansa ya amince da
auransa da Zainabu ya ji wani irin dadi ya rufe
shi, tamkar ya shide don dadi, bakinsa ya kasa
rufewa don murna, ya bude baki cikin farin ciki
ya ce, "Baba nagode Allah ya saka, kuma Insha
Allahu zanyi aiki da abinda ka ce." Sam yama
manta da sharadin Hajiya Kubra da haka ya bar
falon cike da farin ciki. A hanya saka ci karo da
Hajiya Kubra, ta kalle shi kawai babu yabo babu
fallasa, ya dukar da kansa kasa yana fadin,
"Momi na gode." Bata ce masa komai ba ta
shigewarta cikin dakin, bai ji dadin abinda tayi
masa din ba, amman dai tunda ta amince shi
kenan, ya fice daga gidan cike da murna ya nufi
sashinsa. Sanda ya zauna bisa kujera ya kirawo
layin Zainabu ta daga wayar da sauri tana fadin,
"Zuma yaya dai kwana biyu?" Yayi murmushi
gami da kwanciya bisa kujerar da yake kai ya ce,
"Albishirinki?" Ta yi dariya cike da jin dadi gami
da kashe murya cikin kissa ta ce, "Goro fari kal,
na kuma baka kyautar Zainabu har abada." Ya yi
dariya ya ce, "Zainabu zuma kin gama da ruhina,
lallai da su Momi sun hanani ke da ban san
yanda rayuwata zata kasance ba, yanzu dai ina
miki albishir da cewa, Momi da Alhaji sun amince
na aureki, don haka ki shirya yau kina da babban
bako." Dadi ya cikata ta doka tsalle gami da
fadin, "Don Allah da gaske kake Musty, kai
amman naji dadi, har naji kamar na zo yanzu ma
na ganka, don baka san yanda raina ke kuna ba
akan rashin ka ba, ina sonka Mustafa zumana."
Tana magana cikin salon sace zuciya da jan
hankali. Duk ya wani sukurkuce tamkar ya tashi
ya tafi, da kyar dai ya samu yayi hakuri har zuwa
dare don bai san ya nuna zalamarsa a fili har
Mominsa ta ji haushi, gwara ya zauna ya ci
abincin dare kamar ko da yaushe yanda ko ya
dawo ba zata gane ba. Suna gama waya ta mike
ta fara shiri, ta dauko magunguna na mata ta
fara sha tamkar wacce mijinta ne yayi tafiya zai
dawo (Fauza ta ce, "wata masifa ce yanzu ta
same su ta 'yan matanmu ko nace karuwan gida
na shan maganin mata, zaka ga mace bata da
aure amman saboda an daurewa iskanci gindi sai
ka ganta da magani kala-kala, daga na mata
zuwa na tsarin iyali wai don kada su dauki ciki,
ya Allah ka shirya mana al'ummarmu ta wannan
zamani masu irin wannan muguwar dabi'u, idan
kuma ba zasu shiryu ba Allah kafi kowa sani, kayi
mana maganinsu don albarkacin Masoyinka
Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wa Sallam", Amin).
Sala ta fara murna ganin diyar ta ta fara
giringidishin shiryawa a zatonta ko ta hakura ne
da Mustafa zata cigaba da harkarta kamar da
can, don haka ta fara mata kirarin nata, ita kam
Zainabu murmushi kawai take yi, tana fadin a
ranta, "Sala kenan, ita dai kudi kawai sune
burinta idan babu su babu sauran zaman lafiya,
idan zaki hakura ki hakura Mustafa ya gama da
ruhina ba zan iya cigaba da abin da kike nufi ba."
Karfe takwas da kwata na dare wayarta ta fara
kira, ta mike da azama tana kuma gyara kanta,
tana sanye cikin wani leshi ne wanda aka hada
shi da yadin Swiss gurin dinkin, kalarsa purple ne
dark da fari, dinkin ya kamata tsam a jikinta riga
da siket ne matsatstsu tamkar zasu yage, kugun
nan ya fito cas-cas, ta yi kyau matuka kamshi
kam ba zaka iya tantance wanda take yi ba
takamai-mai. Ta nufi kofar gida tana wani yauki
da yanga, ya dinga kallonta cikin hasken fitilar
nefa da ta haska kofar gidan na su, tamkar ya
zama tsuntsu ya je ya tarota, ya lankwasar da kai
yana lumshe idanuwansa. Ta isa ta bude motar
ta shiga ta maida kofar ta rufe, ya maida
dubansa gurinta yana wani lumshe ido, duk ta
gama kacalcala masa lissafi, shi da yazo da wata
niyya daban. Ta rangwadar da kai gefe cikin kissa
da kisisina ta ce, "Musty zuma ka ganka kuwa
yanda ka hadu tamkar wani prince? Dan sarki,
shigar nan tayi mini wallahi." Ya ji dadin
maganarta har ransa, Zainabu daban ce tana da
salo na sace zuciyar mutane, ji yake tamkar ya
aiwatar da abinda zuciyarsa ke ingiza shi, amman
ya dake ya ce, "Zainabu dole ki daina wannan
shigar har zuwa lokacin da zaki zama mallakina,
idan ba haka ba zaki wargaza mana lissafi." Ta
dubeshi da rashin fahimta ta ce, "Ban gane
abinda kake nufi ba, na zaci kace komai ya wuce
ne." Ya kwanta jikin kujera ya lumshe
idanuwansa ya ce, "Zainabu mu din nan musulmi
ne diyoyin musulmi, dan haka ya dace duk
abinda za muyi mu yi shi bisa tsarin addininmu,
na sani muna sane muke take gaskiya saboda
son zuciyarmu, amman mu godewa Allah da ya
fargar da mu muna raye, Masha Allah, abin da
nake son na sanar da ke shine, Mustafa zai auri
Zainabu da kyakykyawar niyya da nufin samun
tsarkakakkiyar zuri'a."Ya dago gami da bude
idanuwansa yana dubanta wacce duka jikinta yayi
sanyi kalau, "Zainabu ba zan kuma kusantar ki ba
har sai kin zama mallakata, kin zama matata da
izinin Ubangiji, za ki yi Istibira'i, ma'ana zaki
tsarkaka muyi Istighfari mu fita daga fushi Allah
sannan muyi aure cikin kyakykyawar niyya, ina
fatan kin fahimci abinda nake nufi yanzu?" Ta yi
ajiyar zuciya, jikinta duk ya mutu wani Imani da
tsoron Allah ya shigeta, ta dukar da kanta kasa ta
ce, "Shi kenan Mustafa, duk abinda ka tsara ina
maraba da shi, na kuma ji dadi da ka tuno mana
da wannan hanya ta neman gafarar
Mahaliccinmu, sai dai ban gane yanda ake yi ba
ka fahimtar da ni." Ya ce, "Yauwa abinda ake nufi
da Istibra'i shine, idan mace tana sabon Allah
(Zina) ta kuma amince za ta yi aure sai ta tuba
ga Allah ta kuma samu tsarkin mahaifa, ma'ana
ta zauna ba tare da ta kuma hulda da wani
namiji ba har sai tayi jini uku, ba wata uku ba, a
wata mazhabar kuma ance jini daya ne, domin
dai yin jini shine hukuncin, don kin san wata
matar sai ta yi wata biyu sannan take al'ada
wata kuma wata hudu, don haka sai sunyi jinin
nan dai sau uku, kin tabbatar kin sami tsarki
sannan ki yi aure, muddin kina son yin
tsarkakakken aure, duk wacce tayi aure tana
sabon Allah (zina) ba tare da ta yi Istibra'i ba to
tamkar tana cigaba da aikata sabo ne in dai ta
sani, sai dai idan bata sani ba, amman shi Allah
babu ruwansa baya amsar uzuri da jahilci,
amman dai ilimina kalilan ne ban sani ba ko da
gyara, dan haka zan sami wani malami yayi mini
cikakken bayani, sai dai zamu fara lissafi daga
gobe ne. Za ki daina zuwa ko ina sai dai gurin
aikinki, shima ba zaki dinga mu'amala da kowa
ba, ni kaina ba zan dinga zuwa kullum ba saboda
gudun tunzirawar shaidan, sannan zan yanko miki
hijab gobe wadda dole lallai da su zaki dinga fita
duk inda zaki....Zandakata a nan,inshaAllahu
zancigaba nan ba dadewaba,amma a gaskiya
quick response dinku shi ke karamin kwarin
gwiya,kenan inna bukatar comment dimin
cigaba,Nagode.Naku ANaM Dorayi
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100
Idan Zuciya Tagyaru2-02
Posted by ANaM Dorayi on 06:34 PM, 09-Feb-16
Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU
______________ Na
________Fauziyya D Sulaiman_____
Sannan zaki sanar da iyayenki halin da ake ciki
domin su zama shaida ga alkawarinmu."Ta ji
dadin abinda ya ce har cikin ranta, don haka
babu musu ko jayayya ta ce, "Na amince Mustafa
Allah ya shige mana gaba." Ya dubeta fuskarsa ta
sauya kala zuwa bacin rai, bakin kishinsa ya fito
balo-balo a kan fuskarsa, har ya bata tsoro
kamar ba zai yi magana ba can dai ya daure ya
ce, "Zainabu ni mutum ne mai kishi kin sani,
balle ke da nake jin tamkar ruhin jikina, na baki
amanar kanki don girman Allah ki rike mini
amana kada ki ci amana don Allah, kada ki bata
mana aure ki amince mu yi tsarkakakken aure
don Allah." "Kada ka damu Mustafa, nayi maka
alkawari zan kare kai na, ba zan ci amanar ka ba
Insha Allahu." "Shi kenan ki shiga gida, amman
kada kije ko ina gobe har sai nazo." Ya zira hannu
cikin aljihunsa ya zaro kudi masu yawa ya mika
mata, "Ki rike wannan don bani son ki nemi wani
abu ki rasa." A karo na farko da Zainabu ta ji
kunyar amsar wani abu daga hannun namiji
kenan, ta ce, "Ka barsu kawai ina da kudi cikin
akawun (account)." "Ki amsa don bani son ki
cigaba da mu'amala da wadannan kazaman
kudin." Ta amsa babu gaddama ta bude murfin
motar ta fice tana fadin, "Zuma sai da safe." Ya
ce, "Allah ya tashe mu lafiya, ki kula da kanki sai
goben." Ya dukar da kansa bisa sitiyarin mota
don baya son shaidan yayi galaba a kansa, sai
fadin Innalillahi wa inna Ilaihi raji'un kawai yake
yi, don wata irin sh'awa yake ji tana bijiro masa
ta Zainabu wacce bai taba jin irinta ba, ya kuma
sani sarai shaidan ne ke tunzirashi don ya lalata
masa kyakykyawar niyyarsa, haka nan ya ja
motar ya bar kofar gidan jikinsa babu kwari
tamkar wanda aka yiwa duka. Itama da ta shiga
gado ta fada cike da kewar Mustafa, sai take
ganin watanni uku suna da tsaho, amman yaya
zasu yi muddin suna son yin tsarkakakken aure
dole ne su bi dokar Allah. Sai dai tana tunanin za
suyi rigima da Sala muddin ta ji zancen zata yi
aure, domin dai ta lura Sala sam bata son tayi
aure tafi son tayi ta watsewa, bayan babu abinda
ke tattare da karuwanci sai bakar wahala da
tozarci da wulakanci daga gurin maza, sannan
jama'a su dinga kallonka a watse. Za ta fara yiwa
yayanta Sadiku magana duk da ba jituwa suke yi
ba, ta san idan ta kawo maganar aure zai
amince. Tana zaune a dakinta tana yin game a
wayarta ta ji shigowarsa zai dauki abinci, ta
yanda ta gane ta mitar Sala ne tana fadin, "Kai
na gaji wallahi da wannan doguwar Sallamar taka
kana firgitani, don sai na yi zaton kirana ake zan
amshi kudi, don jaraba kullum ba zaka tashi
shigowa daukar abinci ba sai kusan goma na
dare?" Ya yi murmushi ya ce, "Sala kenan, kin
san dai daga makarantar dare nake, tun da da
rana bana samun zuwa saboda aiki, kuma ba'a
tasowa da wuri." "Oho! Kai ka sani can kaje ka
karata ni ba zaka gaya mini karatu ba, Allah dai
ya kusa raba yari da barawo, don ma iyayen
matar taka kananan mutane ne suka sanya rana
har wata biyar, da ba haka ba ai da tuni anyi
mun huta da saka ido."Shi dai ya dauki abincin
sa ya fice yana murmushi, idan da sabo ya saba
da mitar Babarsa, kuma wai duk don yace a yi
aikin kirki abi dokar Allah ne ya sanya take gaba
da shi. Sai da Zainabu ta kintaci ya gama cin
abincin nasa sannan ta yafa gyalan da take Sallah
da shi, don duk kayanta shine babba ta nufi
shagon na sa. Yana zaune bisa kujera yana duba
wani katon littafi na addini wanda ita kanta bata
san ko wanne ne ba, ta shiga dakin da Sallama.
Mamaki ya kamashi, don dai rabon da ta shiga
shagonsa har ya manta, balle yaji tayi sallama,
yarinyar ma da bata yi masa magana sai taga
dama, amman ya daure ya amsa sallamar dan
bai san meke tafe da ita ba. Ta zauna a daya
kujerar dake cikin shagon ta ce, "Sadiku gurin ka
na zo, ina son muyi wata muhimmiyar magana."
Yan dubanta da mamaki tamkar ya ce ta bar
masa shagonsa, amman tun da bai san da
maganar da ta zo ba ya hakura ya ji idan da
shirme ta zo masa ya fatattake ta, ya ce, "Ke
nake saurare, ina fatan dai lafiya?" Ta gyara
zama tana fadin, "Lafiyar kenan, domin dai na
yanke shawarar zan yi aure ne....." "Aure?" Ya
tambaya da mamaki. Ta ce "Aure zan yi Insha
Alla, zan auri Mustafa dan gidan Alhaji Abdullahi
tsohon saurayi na, mun yanke shawarar za muyi
aure duk da tirjiya da muka samu daga gurin
iyayensa, amman yanzu sun amince yau ya zo ya
sanar da ni, yanzu mun yanke shawarar zan yi
Istibra'i na tsarkaka sannan ayi auren, shine ya
ce na sanarwa da iyayena, to ni ina shakkar
sanar da Sala ne domin ban san yanda zata dauki
maganar ba." "Masha Allah, Alhamdulillahi." Ya
fadi da jin dadi, domin dai abinda ya dade yana
son ji kenan, ya kuma dade yana addu'ar gani, A
ce Zainabu ta shiryu ta yi aure kamar 'yar uwarta
wacce ke zaune lafiya gidan mijinta yanzu. Ya
gyara zamansa ya ce, "Ya ya za kiyi dole ne ki
sanar da ita, don tasan dole za kiyi aure komai
dadewa, duk da nasan tafi son kiyi ta watsewa,
amman tunda Allah ya shirye ki ya juyo da
hankalinki shi kenan, sai muyi wa Allah godiya, ki
sanar da ita yanzu idan kin shiga cikin gida ni
kuma gobe zan sanar da Baba idan mun fito daga
sallar Asuba, sai dai kiji tsoron Allah ki tsarkake
kanki, kada ki ci amanar wanda zaki aura da
mahaliccinki, domin ko ana ya gobe zaki kammala
Istibira'in kika yadda da wani namijin to kuwa
duk kwanakin da kika yi sun zube a banza, kuma
ba aure za kiyi ba illa zaman zina, duk kuma
'ya'yan da kika haifa zasu kasance shegu ne." Ta
ce, "Shike nan nagode." Ta mike ta nufi cikin gida,
daman da alwalarsa don haka ya dora goshinsa a
kasa yana tasbihi da kabbara gami da godiya ga
Allah da ya nuna masa wannan rana ta
shiryuwar Zainabu, duk da ya lura kwana biyu ta
dan daina fita yawon banzar nata, domin duk
wani takunta yana hankalta da shi. Da ta shiga
kai tsaye dakin Sala ta nufa, ta taddata zaune a
tsakar daki tana lissafin kudin gyadar da Umar
kaninta ya siyar, tana kirgawa tana gyangyadi
saboda bacci ne a kanta, amman dan jarabar
neman kudi ba zata kwanta ba, sai ta tafi luu
tamkar zata fadi sai kuma ta farka a firgice ta
cigaba da lissafin, da ta fara baccin zai kuma
daukarta a haka ta tadda ta, ta zauna a kusa da
ita ta tabata tana fadin, "Sala-sala."Ta farka a
firgice tana fadin, "Ba fa bacci nake ba ina jinki
mai tsada yaya aka yi ne? Yau ai kin faranta mini
rai, zuciyata kal da naga kin shirya kin ficewarki,
ina fatan kin samo kudi da dama don kinga
kwana biyu ina fama da rashin kudi wallahi."
Zainabu ta yamutsa fuska kana ta ce, "Kinga ni fa
babu inda naje ina kofar gida Mustafa ne ma ya
zo, kuma mun yanke shawarar za muyi aure, don
haka daga gobe ma zan fara Istibira'i Insha
Allahu." Ta yi watsi da kudin hannunta tana
fadin, "Kan Ubancan! Lallai yarinyar nan kin bari
Mustafan nan ya raina miki hankali da yawa,
yanzu don zai aure ki sai kinyi wani Istibra'i?
Wato bai yadda dake ba kenan? Yana zargin ke
karuwa ce kenan. To tsaya na gaya miki sam ban
amince ba, shegen yaro ya zo duk ya hargitsa
miki lissafi kamar aljani, yanzu kamar ke namiji
zai dinga juyawa tamkar waina? Duk kin sake hali
kin susuce, wannan idan aka yi auren ma ai sai
yanda yayi dake, don haka ban amince kiyi auran
nan ba." Zainabu ta ji haushin abinda Sala ke
fadi, ta yamutsa fuska gami da fadin, "Sala na
lura baki kaunar nayi aure kin fi son nayi ta
yawon gantali da karuwanci a titi, da zaki wani
hakikance ba zan yi Istibira'i ba kuma ai kin san
dai abinda nake aikatawa sarai, na yo zina na
kawo miki kudi babu ruwanki da irin wahalar da
nake sha, kije ki tambayi duk wacce ke sana'ar
karuwanci dole take yi, dan kullum kana cikin
fargaba ne na daukar mugayen cuwuka, ga
hatsarin da muke shiga na mu'amala da kowa
kada ka hadu da dan yankan kai, domin
kawarmu Saliba har yau ba'a san inda take ba
tun da wani Alhaji ya dauketa kwanan gida, ni
kam na gaji wallahi aure na zanyi kome za kiyi sai
dai kiyi amman aure babu fashi." Sala ta mike a
hasale tana huci tana fadin, "Kan Ubancan, Abula
ni kike gayawa wannan maganar akan wani dan
iska can? To wallahi Abu zan yi maganinki a gidan
nan, naga uban da zai daura miki auran in dai
ina raye." Masifa take yi babu ji babu gani. Ita
dai Zainabu bata kuma cewa komai ba ta shige
dakinta ta kullo kofa, sai dai jarabar Sala ta cika
mata kunnen tamkar zata koma gidan banda
karadin maganarta cikin dare babu abinda ka ke
ji.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
A haka Baba Abbakar ya iso gidan, tun daga
zaure ya fara jiyo hargowarta da ihunta, a fili ya
ce, "Yau kuma waye ya tabo 'yar bala'in nan?
Amman ko waye ya jawo mana masifa domin dai
da kyar yau zata kyalemu mu runtsa." (Tabdijan
Allah kabamu mata nagari)Ya dade tsaye a soro
yana fargabar shiga, domin da yana da inda zai
kwana tabbas da komawa zai yi can ya kwana,
haka nan ya daure yana addu'a ya shiga dakin.
Kamar daman jiransa take yi ta ce, "Yauwa
Abbakar daman kai nake jira, ka zo naji idan
kaine ka daurewa Zainabu gindi a gidan nan har
take shirin auran wanda nace mata bana kauna
saboda asiri yayi mata ba son Allah yake mata
ba." Maganar ta zo masa a ba zata don bai san
abinda take nufi ba don haka ya ce, "Ni fa
Salamatu ban fahimci abinda kike nufi ba sam."
Ta kara gyara zama ta ce, "To ka sani ko baka
sani ba bari na sanar da kai, Abula ce ta taso da
zancan zata yi aure yanzu, ni kuwa sam wanda
zata aura din bai kwanta mini a raina ba, dan
haka gwara ma idan da hannunka a ciki ka zare
dan banga dan kan uban da ya isa ya daura
mata aure da shegen yaron nan mayaudari
ba."Baba Abbakar yayi murmushi gami da fadin,
"Salamatu kenan, ai kunfi kusa da Zainabu,
amman dai ina ganin tunda Allah ya karkato da
hankalinta tana son yin auren ni gwara ki rabu da
ita ta yi, kinga ai mun huta da zagin da jama'a
suke ma....." Ta mike a fusace tana buga hannu
da dukan cinya tana fadin, "To sannu munafuki
algungumi, bashi da aikin da ya wuce gulma, ina
ruwana da wani zagun mutane? Su yi tayi, ai da
zagi yana kari da yanzu jikina da na Abula babu
ko masakar tsinke, to munsha tabara mun sha
yasin, mun sha fate-faten alatsine, kurwarmu kur
na gaya maka, . Maganar aure kuma babu ita
wallahi baku isa ba.... Kai nama lura bakinku
daya, ni kuma na isheku riga da wando....."
Masifa take yi tamkar zata rufe shi da duka,
Zainabu dake can dakinta bala'ain da masifar
Sala ya ishe ta, kai duk wanda ke gidan ma
bala'in ya ishe shi, shi dai Sadiku sai ya kunnan
rediyo kawai dan haka daina jin hargowar, ita
kuwa zainabu sai kaiwa da komowa take cikin
dakin zuciyarta na kuna. Kamar wacce aka
tunawa sai ta nufi jakarta da sauri ta dauko
kwayarta ta sanya a bakinta kana ta nufi kofarta
ta kulle gam ta kulle wunduna sannan ta dauko
tabar shaidan ta kunnata da ashanar bature
(lighter) ta zauna gefen gadonta tana zuka tama
lumshe ido, dakin ya gume da hayaki tamkar
tasowar hadari, dan duk mutumin da ya shiga
dakin muddin bai taba shan kwaya ko tabar
shaidan din ba sai yaji kansa ya juye, amman ita
babu ruwanta tin da dai 'yar caburos ce, sai da
ta cake sosai kanta ya dauki caji sannan ta yarda
tabar a gefe bayan ta kashe ta kwanta rigingine a
gado, kwakwalwarta na shirya mata abubuwa na
karya, yawanci kuma da Mustafa ne. Da safe ma
da bala'in suka karya kumallo, shi dai Abbakar
daga gurin sallar asuba bai dawo gidan ba ya
wuce gurin buga-bugarsa, shima Sadiku shiryawa
yayi ya fice sai dai ya turawa Zainabu sako a
wayarta. Zainabu kam da kyar ta iya tashi
saboda nauyi da jikinta yayi mata, kai tsaye
wanka ta shiga dan ta danji dadi, yau ko abin
karin da aka saba kawo mata ba'a kawo ba, dan
haka ta kirawo wani kaninta ya amso mata shayi
da wainar kwai gurin mai shayi, don yunwa take
ji tamkar zata ci babu, domin dai duk mutumin
da ke shaye-shaye yana da saurin jin yunwa
saboda fafare masa cike da take yi gaba daya.
Tana kunna wayarta ta ci karo da sakon yayanta
Sadiku dan haka ta shirya ta fita, dan yace su
hadu a gidan Malam. Tana kokarin kulle kofarta
ne Sala ta iso tana tambayar ina za ta, ta yi
murmushi da rashin damuwa ta ce, "Sala tun da
kike kin taba tambaya ta inda zani? Bayan kin san
yawon iskanci nake tafiya amman yanzu dan nace
zanyi aure duk kin gigice har kina tambaya ta ina
zani." "Au zagina za kiyi kenan ko Zainabu?." Ita
dai bata kuma cewa komai ba ta nufi kofar fita.
Sala ta yi kwafa gami da fadin, "Zan yi
maganinku a gidan nan zanga wanda ya daure
miki gindi." A zaune ta tadda Malam din da
Sadiku, har ta manta rabon da ta shiga gidan,
domin dai a cewar Sala ba kaunar su suke ba
balle Malam da take ce masa dan saka ido, dan
haka ko ta kofar gidan bata wucewa dan idan ta
wuce dole ta gaida shi saboda ta san shi babu
wargi, abinda ta tsana a rayuwarta ta gaida wani
dan haka bata bin kofar gidan da kafarta sai dai
a mota.Ta sami gefen tabarma ta zauna kanta
yana kasa kamar mutuniyar arziki ta gaida Malam
din. Ya amsa fuskarsa cike da farin ciki sannan ya
cigaba da magana, "Zainabu na yi farin ciki da na
ji zaki yi aure daga bakin yayan ki, wannan ba
karamin abin alhairi ba ne, amman na ji yanda
kuka yi da Mahaifiyarki, sai dai ku yi hakuri da
halinta, domin shi hannunka ba ya rubewa ka
yanke ka yadda, tuntuni ina bakin ciki da halin
da kike ciki, Allah ya sani na yi duk iyakacin
iyawata ta ganin na tsamoki daga halaka amman
abin ya faskara, na hakura daga karshe don na
san Mutum bai isa ya shirya dan uwansa mutum
ba in dai Allah bai nufa ba, na dai cigaba da yi
muku addu'a dan na dauke ku tamkar jinina, sai
dai babbar matsala tana ga Mahaifinku Abbakar
duk lalacewa daga gurinsa ne, duk wa'azi da
nasiha na yi masa amman a banza, dan haka
yanzu ina farin ciki da wannan aure da za ki yi,
ina addu'ar Allah ya sanya ya zama hanyar
shiryuwarki." "Yanzu Malam yaya za'a yi? Kana
ganin mu daina sanar da ita komai a yi a nan
gidan ka ko yaya?" Sadiku ya tambaya Malam
din. Malam ya gyara zama kana ya ce, "A'a babu
wata fa'ida a boye mata din dole za'a dinga
sanar da ita tayi mitarta ta gama, tun da idan ta
ji ma daga baya ma fadan za tayi ko tace an rufe
ta, amman kada ku sake ku sanya Abbakar cikin
wannan sha'ani don na san babu wani abu da zai
iya tabukawa." Ya maida dubansa ga Zainabu
wacce har lokacin kanta yana kasa ya cigaba da
magana, "Ke kuma ki sani yanzu ba irin da ba ne
dole ne ki kame kanki idan har kina son ki yi
tsarkakakken aure, ki kyautata zuciyarki domin
sai ta gyaru sannan dukkanin ayyukanki zasu
zama gyararru da jikinki kamar yanda Ma'aikin
Allah ya fada." Muryarta da sanyi ta ce, "To
Malam na gode." Ta mike kamar mutuniyar arziki
ta bar Malam da Sadiku suna hirarsu domin dai
mutuminsa ne. Sanda ta isa gidan ta tadda Sala
ta cika tayi fam kamar zata fashe, amman don
wai taci asirin da ta amso na mantawa da
Mustafa gurin Malami ya sanya ta dan saki ranta
ta ce, "Ga abincinki nan na rana, ina shirin miko
miki na safe kika fita." Bata ce komai ba ta amsa
ta shige dakinta. Ta bude abincin, shinkafa da
miya ce har da Salak da nama, sai dai ga
maganin nan kore-kore cikin miyar, Zainabu ta yi
dariya tana fadin, "Sala tawa uwa ta ta kaina,
bata san son Mustafa a jinina yake ba ko da naci
magani ba zai rabu da ni ba." Kawai sai ta dauko
cokali ta kama cin abincinta bayan ta yi Bismillah,
don tayi imanin babu abinda asirin Sala zai yi
mata in dai akan Mustafanta ne. (Daman dai 'Yan
magana sun ce tsafi gaskiyar mai shi, kuma sai
ka yadda da canfi yake maka ka).
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
*******************
Da yamma tana daki a kwance tana karanta
littafin Fauziyya na kaddara ko son zuciya, duk
jikinta yayi sanyi da halin da taga yarinyar ta
shiga sai take tunanin kada itama Mustafa yayi
mata haka, kan ubancan lallai da ta koya masa
hankali, domin dai idan ita 'yar iska ce shima shi
ne, littafin ne ya dauke mata hankali daga mitar
Sala har tayi ta gama, kiran da wayar ta ke mata
ne ya sanya ta mike zaune da sauri dan ta
shaida kiran Mustafa ne. Ta dubi kanta jikin
madubi, ta yi kyau matuka amman kuma idan ya
ganta a haka tasan ba zai ji dadi ba, tunda dai
yace ta daina fita da irin wannan shigar, don
haka ta dauko wani gyale mai dan girma da take
yin sallah da shi ta yafa ta fice, ta yi sa'a kuwa
babu kowa a tsakar gida, Sala tana daki tana ta
faman gyangyadi saboda rashin bacci da take
fama da shi, don asubanci take yi gurin tashi,
haka nan sai takai karfe goma sha biyu ba ta
kwanta ba saboda shegen neman kudi, sai dai
tayi ta gyangyadi har da dingurawa wani lokaci. A
kofar gida suka ci karo da Mustafa, abin ya
girmameta ya bata mamaki, domin dai basu taba
yin zance a waje ba sai a cikin mota ko da
yaushe, ko ma su bar kofar gidan idan suka ga
da 'yan saka ido su yi tafiyarsu inda zasu wataya,
har kwana suke yi wani lokaci, wani lokacin kuma
sai dare zai dawo da ita, nan din ma da kyar
suke rabuwa. Idonsa kyar a kanta har ta iso inda
yake, zuciyarsa ta hau azal-zalarsa, amman sai ya
dake ya kauda kanshi gefe. Ta iso cikin yanayin
tafiyarta ta jan hankali ta tankwashe muryarta
mai dukan kunnansa har zuciyarsa ta ce, "Musty
Zuma barka da zuwa." Ya dago kansa yana
dubanta yayi murmushi ya ce, "Zainabu yaya
kike? Kin ganni yau da yamma ko? Gani na yi
gwara na kawo miki da wuri alkawarin namu ga
shi." Ya mika mata. Ta sanya hannu ta amsa
yana mata bayanin hijaban ne da yace zai kawo
mata. Ya dubi agogonsa ya ce, "Zainabu bari na
wuce ko?" Ta dubeshi da wani yanayi kamar za
tayi kuka domin ganinsa ya sanya ta ji wani dadi
da nishadi a rayuwarta, amman ya ce mata zai
tafi, amman sai ta dake kawai ta ce, "Shi kenan
ka gaida gida." Ya dubeta kamar zai yi magana
amman ya fasa kawai ya juya ya nufi motarsa. Ta
yi tsaye sororo tana dubansa har ya shige
motarsa, sai da ya dubeta sannan ya figi motar
ya bar unguwar da gudun shi, jikinta babu kwari
ta koma gida, ji take yi kamar ta bishi ta makale
shi, tana son Mustafa tamkar zata lashe shi take
ji. Washegari da safe tayi shirin zuwa aiki ta
kammala kwalliyarta tsaf kamar yanda ta saba,
sai kuma ta dauko hijab dinta guda daya ta
sanya, ya kawo mata har gurin gwiwarta sai tayi
kyau tsaf da ita, ta kalli kanta a madubi tayi
murmushi, lallai ta yadda shigar mutunci ke fito
da darajar mace, don sai take jinta daban. A
tsakar gida taci karo da Sala tana gyaran wake da
zata dafa, tayi sororo tana kallonta kamar wacce
taga sabuwar halitta, can kuma sai ta hau salati
tana tafa hannu, "La'ilaha illallahu, Abula me zan
gani haka kuma? Haka ya maida ke? Lallai na
yadda yaron nan shaidani ne, wato baiwar da
Allah yayi miki ta kyau ma ya hanaki nunawa
duniya su gani bayan ba ubansa ne ya kera ki ba,
lallai Abula abin naki yayi nisa sai dai addu'a." Ita
dai bata ce komai ba ta nufi hanyar fita, sai da ta
kai kofa sannan ta tsaya ta juyo ta dubeta wacce
har lokacin bakin ta bude ta ce, "Na tafi Sala sai
na dawo."Ta yi kwafa gami da mai da kanta ta
cigaba da gyaran wakenta, yau ba a yi mata
kirarin da ake mata ba, Zainabu Abu mai
tagwayen suna, kowa ya ja dake ya sha kunya,
mahassada ku rufe idonku yarinya mai tsada ta
danno, yarinya wacce bata da kirar Allah ya isa.
Zainabu ta fice tana murmushi a ranta tana
fadin, "Wato yanzu an daina yi mini kirarin ma
balle a dawo lafiya, Sala kenan." Ta tare mai
adaidaita sahu ta hau, Mustafa da ke can gefen
layin cikin motarsa ya daga bakin glass cikin
motarsa yana hangota, ransa ya yi sanyi don
ganin ta bi umurninsa, a hankali ya dinga bin
bayan mai adaidaita sahun har ta isa (local
government) karamar hukumar da take aiki. Tun
daga bakin kofa aka fara kallonta, maigadi ne ya
saki baki cike da tsegumi yana fadin, "Allah
buwayi, yau kuma Zainabu Hijab aka sanya, lallai
duniya ta fara biyar da ita dubi kamar ba ita ba."
Da ta shiga cikin sakatariyar kuwa kallonta aka yi
ta yi, ita kam ko a jikinta wai an mintsini
kakkausa, kanta tsaye ta isa ofis dinta, gashi
daman ita ba kowa take kulawa ba a cikin
sakateriyar, a cewarta wai duk kazamai ne basa
wanka, dan haka nema da yawa ke shan kashi
gurin ganin sun sami ko da dariyarta ne. Oganta
yana bisa kujera yana ta rubuta bococi na kudi ta
shiga da sallama, ya daga kai yana dubanta baki
bude ya ce, "A'a Malama Zainabu sai yau ake
ganinki a ofis....." Ya so ya cigaba da magana
akan hijab din da ta sanya amman ganin ta hade
rai ya sanya ya tsuke bakin sa don ya san hali,
yanzu sai tayi masa wankin babban bargo. Ta
jawo kujera ta zanua tana fadin, "Wash, yallabai
kenan, yaya aiki kasan sakateriyar ce shigowarta
sai a hankali wallahi, idan da wani aiki kawo a
tayaka." Ya yi dariya ya ce, "Wane ni, ai ban isa
ba na saka manya aiki, sai dai wallahi rashin
zuwanki kwana biyu ya yiwa yallabai DPM karan
tsaye gashi yana ta neman lambar ki bai samu
ba, haka ma HOD na works suke ta sintiri, ke
harda mai gayya mai jama'a Chairam yana ta
aike, har sallahu ya bar mini na lambar wayar da
zaki neme shi, yace kuma yana daula hotel dan
gidanshi na shakatawa an dameshi baya sakewa
sosai.....""Haba Oga tunda na shigo ka tsinke da
surutu sai kace baure." Ta katse masa magana, ta
dora da cewar, "Kowanne shege ya kuma zuwa
nemana wallahi sai nayi masa rashin mutunci, sai
kace wata karuwa, idan iskanci za suyi ai ga
gidajen karuwai can a sabon gari, banzaye masu
shegen son matan tsiya, kai! Aiki a sakateriya ko
bala'i, kowanne banza kucaki dame warin baki da
me warin hammata ya ce wai zai nemeka, mts!"
Ta ja tsaki, "Wallahi zan yi maganin kowanne
shege." Oga Bala yayi dariya yana rubutunsa ya
ce, "Ho! Zainabu ai ke din wallahi duk wanda ya
ganki sai miyansa ya tsinke, ni kaina dan dai anki
kulani ne amman ba karamin sonki nake yi ba
tuntuni, to sai dai nasan ban isa ba, amman duk
randa kika shigo aiki ji nake yi kamar ki zama
tawa ni kadai, don daga shigarki har kamshin
turaranki mannewa suke a zuciyata, idan naje
gida sai na raina matana, kin san matsalar
matanmu na hausawa kadan ne ke gyara kansu
irin yanda kike yi, shi ya sanya kowa ya lashi
zumarki sai ya dawo, wallahi DPM tamkar zai
zautu dan rashinki, shi ko damuwa da zuwanki
aiki bai yi, shi dai burinsa ki zo ki cire masa gibin
da kika bar masa a zuciyarsa, amman da kina irin
wannan shigar ai kinga babu wanda hankalinsa
zai tashi, ki dubeki kamar wata matar liman yau,
nasan kalilan din maza ne zasu yi sha'awar ki sai
jarababbu irinmu." Ta galla masa harara tamkar
zata rufe shi da duka, Oga Bala takadirin dan iska
ne, shine akawu na (local government) karamar
hukumar, tunda ta zo aka turota ofis dinsa ba wai
dan cancanta ba sai don tana da hanya, don kyan
karatunta koyarwa, amman da yake Nijeriya ce
idan kana da kafa sai a kai ka inda baka dace ba
ko da zaka kashe jama'a kuwa, kamar a asibiti da
ake daukar wadanda basu yi karatun ba sam-sam
ga kuma wadanda suka yi karatun saboda basu
da hanya. Tun da tazo ofis din oga Bala ya kyalla
idonsa ya ganta ya fara mika kokon bararsa,
domin dai idonsa idon mata ne, gashi su babu
ruwansu ko da matar aure ce in dai zata yadda
da su (Wa iyazu billah) musamman masu neman
aiki ko a yi musu (promotion) karin girma sai kaga
suna amfani da wannan damar suna lalata
watsatstsun mata, sai masu tsoron Allah daga
cikinsu kiyi komai yanda ya dace da dokar aiki.
Ita kuwa Zainabu idan namiji bai yi mata ba duk
kudinsa bai isa ya kusance ta ba, balle oga Bala
da ta raina masa ajawali, bakinsa kullum da tikar
goro ko taba yana sha, hakoransa duk sun dafe
gashi kullum kamar an kwatoshi daga bakin kura,
irin katon kauyen nan ne mara fasali, don ma su
Baba sun taimakeni an sakani a makaranta da
yanzu muna gona, haka yake cewa da kanshi
idan suka hadu da abokansa shakiyyai, don haka
ya buga ya buga amman babu fuska ga Zainabu,
gashi ya lura bata da tsoro ko shakka ko daya, ko
DPM bata tsoro, dan haka ya gama barazabar shi
da girman kujerarsa ya dawo ta lallashi da kashe
mata kudi amman a banza, ko kallon tsiya bai
isheta ba balle na arziki. Duk da hararar da take
wurga masa baiyi shiru ba dan haka ta doka
masa tsawa "Kai! Oga Bala wallahi ka yi asara
kazo gurin aiki kana tonawa matanka asiri, ina
ma ace ina daya daga cikin matanka wallahi da
sai ka gane kurenka." Yayi wata shashashar
dariya har da dukan tebur yana fadin, "Ho!
Zainabu, ai irinku daban ne cikin mata, na sami
kamarki ai sai ma nayi da gaske zan fito, ki dubi
yallabai fa (chairman) irin matan da yake
mu'amala da su, amman a kanki duk ya susuce,
rannan da ya sanya aka kira ni kamar yayi mini
kuka wallahi." Ta kuma kulewa da Oga Bala irin
shakiyyan mutanen nan ne marasa mutunci da
kamun kai ga almundahana, duk wata cuwa-
cuwa da ake yi a karamar hukuma shine sila dan
shedani ne, ya iya rubuta bocha ta bogi har
akwai ta 'yan kwadin sakateriya da ta kadangaru
da karnukan dake gadi. Dan haka ta mike a kule
ta dauki jakarta tana fadin, "Kai dai wallahi dan
iska ne, gwara na bar ofis din, da man zagayowa
nayi gwara na tafi tun bata kaini da cuccusa
maka zagi ba." Maimakon yaji haushi sai ma ya
kuma fashewa da dariya yana fadin, "Dan Allah
kiyi hakuri wallahi har na tura a sanar da yallabai
DPM kin shigo kada ya zaci karya nake yi....."
Sallamar DPM din ce ta katse shi, ya kumshe baki
yana dariya, DPM ya kalli Zainabu da wani duba
tamkar ya cinyeta ya ce, "Zainabu idon ki kenan
ko, to ki taddani a ofis."Ya juya ya fita yana
kannewa oga Bala ido, oga Bala ya fashe da
dariya yana fadin, "Yallabai kenan, da girman
kujerarka." Ta kuma gallawa Oga Bala harara
tana fadin, "Wallahi oga ka shiga uku, Allah ya
shiyeka, ka kuma sani abinda kake zaton zaka
samu ba zaka samu din ba, domin na rantse da
girman Allah ba zai samu abinda yake so din ba,
ko da maye ne kuwa shi,ya toshe baki a tsorace
kamar zai zubo da gudawa a wando ya mike
tsaye yana fadin, "Don girman Allah ki yi hakuri
Zainabu ki rufa mini asiri har na sanya ran zan
samu 'yan canji da alfarma....." Bata kuma cewa
komai ba ta kada kanta ta bar masa Ofis din da
yanayin ta na jan hankali. Ya dafe kai gami da
komawa jagwab ya zauna yana fadin, "Kai
wannan yarinya anyi shaidaniya, yanda take yawo
da hankalin maza kamar wata ibilishiya, gata da
shegen shiga rai, balle a ce mutun ya dandani
zumarta ya shiga uku Inji DPM." Sai kuma ya
fashe da muguwar dariyarsa da ya tuno yanda
DPM ya mutu akan son Zainabu har ya kan ce
masa, Bala ka san Allah tunda nake ban taba
gamsuwa da mace irin Zainabu ba, wallahi tana
da wani irin maganadisu a jikinta dake jan
mutum gunta. Ta shiga ofis din babu ko sallama,
ya mike jikinsa yana rawa zai tarota ta dakatar
da shi tana fadin, "Ka ga yallabai kada ka taba ni
don Istibira'i nake yi aure zan yi ma, yanzu kuma
Allah ya shirya ni." Ya ware idanuwa waje cike da
fargaba yana fadin, "Ki yiwa Allah Zainabu ka da
kiyi mini haka, ki amince ki aure ni, ni na yadda
komai kike so zan miki, idan kuma ba zaki aure ni
ba to mu cigaba da mu'amalarmu a boye, tunda
dai ai kinsan shi mijin da zaki aura ba waliyyi
bane da zai hakura da ke kadai ba." "Yallabai ka
tsaya na sanar da kai, zan yi aure da
kyakykyawar zuciya, ka dubeni da kyau zaka san
na bambanta da Zainabun da ka sani can baya,
dan haka ina baka hakuri sai an jima....." Ta juya
ta nufi kofar fita.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Da sauri ya sha gabanta yana fadin, "Haba
Zainabu, kada mu yi haka da ke, kin san dai aikin
nan naki ba zuwa kike yi ba, dan haka idan kika
ki amincewa da ni zan sanya a baki (quarry) ko
ma na sanya a kore ki, kin san dai babu sama da
ni a Local government din nan, ko chairaman
karya yake, tunda dai shi dan siyasa ne zai iya
tafiya ya barni da ke." Ta ja tsaki cike da nuna
rashin damuwa ta ce, "Yallabai kenan, ko ka
barni ko kada ka barni wannan matsalarka ce,
domin dai kasan neman aiki ba abu ne mai
wahala a gurina ba, sai anjima." Ta kada kai ta
fice. Ya bita da sauri yana kira "Zainabu!
Zainabu!" Amman ko waige bata yi ba ta fice
daga ofis din, ya dawo ranshi a tsananin bace ya
dafe goshi, lallai yarinyar nan muguwar 'yar
rainin hankali ce wallahi, yanda yake jinta kamar
ya zace ta, amman babu komai zai bita har gida,
dole ne ya san yanda zai yi ya ruguza maganar
auren ta. Tana kokarin fita daga sakateriyar
motar chairaman ta ci birki a gefenta yana
kokarin shiga, ya leko ta windo babu kunyar
direban dake jansa, balle jama'ar da ke tare da
shi (ko da yake ai sun san hali). "Zainabu kace
nake gani ko idona ne ke mini gizo." Ta kuma
hade rai tamkar zata fasa kuka, ya langabar da
kai yana magana, "Kai Zainabu alkawari wallahi
baice haka ba, fafur kin gujeni, gashi babu damar
naje kofar gidanku saboda 'yan saka ido, na yi
waya kin ki dagawa, Don Allah ki koma zanyi
magana da ke.ta kalli agogo dake hannunta ta
ce, "Mai girma ka yi hakuri, wallahi yanzu akwai
inda zani, amman ai oga Bala ya bani address din
inda zan same ka, zan zo kada ka damu." (Ta yi
masa haka ne domin ya kyale ta). "Kada fa ki
jirgani Zainabu don nasan halinki, sau nawa na
aika da mota gidanku kika ki zuwa?" Ta
rangwadar da kai cike da yaudara ta ce, "Haba
Yallabai nifa nayi maka alkawari, "Za ki zo yau na
jira ki?" Ta ce, "Amman dai sai dare zan zo,
domin yanzu unguwa zani." Ya ce, "Shike nan zan
jiraki, bani lambar wayarki." Ta gaya masa lambar
bogi, ya saka a wayarsa, sannan ya baiwa
direban umurnin su wuce yana fadin, "Ina jiranki
Zainabu." Ta ce masa "To." Kawai ta wuce da
sauri, domin dai tana zancen zuci, "Wai me
wadannan mutane suke maida ta ne? Sai kace
wata tsinanniya kowa Zainabu kowa Zainabu?, to
zata gwada musu ba karya ba ce ita, banzaye
duk babu wata soyayya da suka iya ko su gyara
matansu, sai dai su fito suna kashewa
kadangarun bariki kudi, amman idan kaje kaga
matansu sai ka zubda yawu, da anyi magana su
ce matansu kazamai ne, to ita mace ai dole sai
an bata zata gyara kanta." Ta ja tsaki dai-dai
sanda take tsaida wani mai a daidai ta sahu.
Mustafa da yayi parking tun dazu yana jiran
fitowarta ya bi bayansu dan ganin inda zata
kuma, sanda ya ga ta shiga gida sai yaji ransa ya
yi sanyi, lallai ya yadda Zainabu da gaske take
zata kare kanta zata yi tsarkakakken aure, ya
aminta ta gyara zuciyarta.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
*****************
Rayuwa mai sauyi, lallai Ma'aikin Allah (Sallallahu
Alaihi Wa Sallam) ya yi gaskiya, da yace idan
zuciya ta gyaru dukkan jiki ya gyaru, idan kuma ta
baci dukkan jiki ya baci, to haka ce ta faru ga
Zainabu. Domin dai gyaruwar zuciyarta sai ta
gyara dukkanin al'amuranta, domin dai yanzu
Zainabu ta daina fita ko ina in dai ba da dalili ba,
gurin aiki ma tun ranar da abin ya faru bata kara
zuwa ba, da wata ya kare ma aka turo masinjan
ofishinsu ya kawo mata albashi ta yi mamaki
matuka, domin tayi zaton zasu koreta ne, amman
har lokacin maza basu daina sintiri a kofar
gidansu ba, domin dai a sati na biyu da fara
istibira'in nata Mustafa ya amshi wayarta har
layin (sim card) ya bata sabuwa da sabon layi,
don haka ba kowa ne ya san layin da ta sake ba,
don haka duk wanda ya kira tsohon layinta sai
ace masa a kulle take dan haka wasu suka
hakura, wasu kuma basu gaji ba suka cigaba da
zuwa kofar gidan su suna naci. Sala kam tamkar
ta shake Zainabu don takaici, amman ita ko a
jikinta, domin dai ta saba da mitar Sala, idan ta ji
Mustafa ya zo tayi ta surfa zagi, wani lokacin
yana jiyota amman sai ya ke nuna kamar bai san
tana yi ba, domin dai bai taba yiwa Zainabu
zancen ba. Ita kam Sala tayi fadan a banza,
domin dai Zainabu ba ta ce mata ko uffan,
domin daman duk iyakacin rashin kunyarta bata
yiwa Sala da Babanta, domin a duniya tana ganin
darajar iyayenta, kuma ko waye kai ka taba mata
su zaka gane kuren ka. Da Sala taga fada ba ci
bane sai ta koma ta asiri, shima dai a banza
domin dai duk 'yankudaden ta sun kare, daman
Zainabu ce mai bata kudi na banza, Sadiku kam
sai dai ya jibge mata kayan abinci komai da
komai,Idan ta ce ya bata kudi sai ya ce mai take
bukata ya siyo mata? Sai ta hau mita da dole sai
ya ji abinda za tayi da kudin, idan yaji haka sai
ya ajiye mata kadan ya wuce. Karimatu kuwa ta
bi mijinta can Aba domin can aka yi masa canjin
aiki (transfer). Shi kam Mustafa ya yarda da
Zainabu dari bisa dari, domin duk wata hanya da
ya san zai kamata da laifi yabi amman bai
sameta da laifin komai ba, yana kuma sane da
mutanen da ke zuwa gurinta bata fita sai dai Sala
ta fito tana basu hakuri, har takan ce asiri aka
yiwa diyar ta su taya ta da addu'a. (Ku ji fa irin
wannan azzalumar uwa wacce bata tsoron
haduwarta da Allah).
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
************
Cikin hukuncin Allah ta kammala Istibira'inta ta
tsarkaka daga fushin Allah da kazantar zina,
ranar jinta take yi kamar wacce aka yiwa albishir
din gidan aljanna, tun da ranan Mustafa yayo
mata waya, irin kalaman da ya gaya mata su
suka sanyaya mata rai domin dai har ta fara
zargin anya kuwa Mustafan ta bai sake ba?,
domin dai duk wadannan kalaman na soyayya da
kallon da yake mata yanzu duk ya daina, da ya
zo ya bata abinda zai bata sai yayi mata sallama
ya wucewarsa kamar bai wani damu da ita ba,
gashi sai yayi sati bai zo ba sai dai yayi mata
waya ya tambayi lafiyarta ya kashe. Tunda suka
gama waya take murna ta fada kicin da sauri
tana kokarin shirya masa abinda zai ci don yace
mata a nan zai yi dinner (abincin dare) yau, ta
kirawo kaninta Ila ta rubuta masa duk abinda
take bukata ya siyo mata. Sala kallonta kawai
take yi cike da mamaki amman bata ce komai ba,
da ta kammala girkin ta yi wanka ta shirya kanta
cikin wani riga da siket na leshi wanda ya amshi
jikinta, ta gyara gashinta ya sha mai tai parking
dinsa, duk da ba wani tsaho ne da shi ba, tayi
wata kwalliya ta daukar hankali. Rabon Zainabu
da irin wannan kwalliyar tun ranar da ta fara
zaman Istibira'i, Sala ta fara washe baki cike da
murna domin tayi zaton ko asirinta ne ya kama
Zainabu, domin ta baiwa kawarta Asma wani
magani ta ce ta zuba mata cikin nono don idan
itace ta bata ba zata sha ba, Asma din tayi dariya
kawai ta karba, sai da suka hadu da Zainabu
take gaya mata suka yi dariya kawai suka watsar
da maganin. Karfe shida saura wayarta ta fara
kira, ko bata gani ba ta san Mustafa ne don haka
ta mike ta kara fesa turaruka a jikinta ta yafa dan
yalolon gyalanta ta nufi kofar gida, daman ta
karbi makullin dakin Sadiku don haka can ta bude
musu tace da Ila ya shigo da shi. Sai da ya shiga
ya zauna a dakin sannan ta shiga, babu laifi
dakin gado ne karami sai loka mai cike da littafai
da kayan kallo bisa (TV stand) abin dora tibi, sai
kujera guda daya mai taushi, an malale dakin da
kafet, sai wani irin hanga da kayansa a sakale
kanana. Ta shiga dakin da sallama idonta yana
kasa, Mustafa ya zuba mata ido tamkar zai
lasheta, rabonsa da yayi mata irin wannan kallon
har ya manta, ya lumshe ido saboda kanshin
turaren ta dake dukan hancinsa. Ta zauna bisa
kafet ta tankwashe kafafunta, ta dube shi da
yanayin salonta na jan hankali muryarta mai
taushi ta ratsa dodon kunnensa, "Mustafa honey
ya gida?"ya yi murmushi ya ce, "Zainabu irin
wannan kwalliya da kika yi ai sai ki maida mu
ruwa, lallai dole na bude wuta a yi bikin nan nan
da sati daya." Ta kalleshi tana wani kashe ido ta
ce, "Haba dai, kamar bikin wata 'yar tsana? Ka
dai bari ayi ko wata hudu ne ma ko biyar....."
"What, me? Wallahi ba zan iya wata guda ba tare
da na mallake ki ba, Zainabu kin san yanda nake
jinki a raina kuwa?, Zainabu kina wasa da irin son
da nake miki, ban san yaya rayuwata zata
kasance ba." Ta rangwadar da kai tana dariya
mai dauke hankali, ya taso tsam ya matso kusa
da ita ya kwantar da kai kamar wani maraya. Ya
kwantar da murya ya ce, "Zainabu kamshinki
yana da dadi ko na dan shaka ne....." Ta mike
tsaye tana dariya ta koma can nesa da shi ta ce,
"Haba nawan, kada muyi tuban muzuru mana,
kasan ance sharuddan tuba da nadama da kuma
daina aikata aikin sabon." Ya koma ya jingina da
kujerar yana dariya ya ce, "Ho! Zainabu wayo,
daman gwada ki nake yi, ni yaushe zan yadda na
kuma shan azabar da na sha na rashinki?" Kiran
sallah ne ya katse musu hirar tasu, ya mike ya ce
bari ya je masallaci ya dawo, ta ce shi kenan sai
ya dawo, ta shiga itama zata gabatar da tata
Sallar. Duk da bata da wani wadataccen ilimi na
addini tana da kokarin yin sallah a kan lokaci.
Tana shiga Sala ta rike haba tana dubanta ta ce,
"Oh ni Abula kin hada kanki da wahala, yanzu
kina nufin duk uwar kwalliyar nan domin yaron
nan Mustafa kika yi? Da nayi zaton kin gano
gaskiya ne, ke ba kya ganin yanda kawarki
Asma'u take fantamawa, ina jin jiya kuna hirar
tana kasar waje da saurayinta." Zainabu ta kulu
iyakacin kuluwa, yau kam ta gaza jure
maganganun Sala, ta dubi Sala da takaici a
fuskarta ta ce, "Haba Sala, wai kin fi so nayi ta
karuwanci ina kawo miki kudi Allah yana tsine
mini da jama'ar gari? Yanzu ba zai zama abin
alfahari a gurinki ace nayi aure ba, duk fa abinda
mutane suke fada akan mu gaskiya ne, ba kya
tsoron fushin Allah akan mu balle cutukan
zamani da azabar da ake sha gurin karuwanci, ki
gaya mini karuwar da kika taba ganin ta ci riba a
rayuwarta, karshen su dai tallan taba ko hauka
ko bara, ko kuma mutuwar wulakanci a tsakiyar
titi, don haka na tsarkake zuciya ta zanyi aure da
kyakykyawar niyya, idan zaki sanyawa aurena
albarka shi kenan idan kuma ba zaki sanya ba
Allah yana gani." Sala ta hau salati tana tafa
hannu, "La'ilaha illallahu, yau ni kike zagi a gidan
nan Abula? To tsaya na gaya miki har abada ban
son auranki da Mustafa, idan auran za kiyi ga
masu kudi shahararru da ke sonki har da
gwabnoni amman ki tsaya ga wannan karamin
alhaki, wallahi kinji kunya." Ita dai Zainabu
bandaki ta shige ta bar Sala tana mitarta. Kiran
da wayarta tayi mata ne ya sanya ta mike domin
ta san Mustafa ya dawo kenan, ta dauki abincin
da ta shirya masa ta nufi shagon Sadiku. Tana
shiga ya mike ya tarota ya amshi tiren abincin
yana tsokanar ta "A'a 'yan mata ban yarda da
daukar irin wannan kayan ba, ai sai kirjinki ya
bude."Ta yi dariya tana masa wani duba ta ce,
"Kai honey wallahi kana shagwaba ni." Ta jawo
tiren ta zuba masa abinci a faranti ta mika masa.
Ya kanne mata ido yana kallon abincin ya ce,
"Lallai ashe amaryar tawa ta iya girki, ina sane
nace a shirya mini abinci, taso to mu ci." "Ka yi
hakuri wata rana za mu ci kaji honey." Ya manne
kafada kamar wani yaro yana fadin, "Na ki
wayon, in ko ba zaki ci ba nima ba zan ci ba, kin
manta da da kike bani a baki ma." Ta ce, "Shi
kenan bari na taso." Ta zauna daga gefensa suna
ci suna hirarsu mai tsarki, sai da zai tafi ya sanar
da ita jibi mutanen gidan su za su zo neman
aure. Ta ce shike nan zata sanarwa da Yayanta
Sadiku domin dai a gidan Malam za'a kai komai,
da kyar suka rabu kamar kada su rabu.
KARSHEN TIKA-TIKA-TIK. Ranar Juma'a da
daddare kanin mahaifin Mustafa da wansa da
abokinsa suka kawo kudin zance har da
sadakinsu gidan Malam, Sadiku da Malam da
wani dan uwan Malam din ne suka karbe su, aka
gaisa a mutunce da daraja juna. Sun yanke sati
hudu ne bikin daidai da na Sadiku, su kam iyayen
Mustafa sati biyu suka soo, domin haka angon ya
ce musu, amman jin so ake a hada guda biyu ya
sanya suka hakura, suka yi sallama a mutunce da
ganin darajar juna. Bayan sun tafi Malam ya
kuma kirga kudin kamar yanda suka kawo, dubu
Hamsin na sadaki, dubu hamsin na kayan sanya
rana, sai dubu Ashirin na gaisuwar uwa da uba.
Da fari Malam ya ce yayi yawa, suka ce yayi
hakuri ya karba, domin da kudin jimlarsu dubu
dari biyu ne Mustafa ya bada suka rage ya koma
haka, domin auren da ba'a tsawwala ba yafi
daraja. Sun rabu akan a bar kudin gurin Malamin
duk da ya so Sadiku ya tafi da su yace a'a ya rike
a gurinsa. Sai dai wajen karfe goma da rabi Baba
Abbakar ya dira a gidan Malam akan ya zo ya
karbi kudin nan sun yanke shawarar da su za'a
cika a yi mata kayan daki. Malam yayi jim kamar
ba zai ce komai ba, can dai ya shiga gida ya fito
da dubu saba'in ya baiwa Baba Abbakar yana
fadin, "Wannan zan iya baka, amman sadakin
Zainabu a hannunta zan bata domin hakkinta ne,
duk ranar da aka daura mata aure." Baba
Abbakar yace, "Shike nan Malam babu komai." Ya
amshi saba'in din ya sanya a aljihunsa, suka yi
sallama ya nufi gida. Sai da ya yiwa kudin
kyakykyawan boyo sannan ya shiga cikin gidan
yana muzurai, da yake Sala a kule take domin
har gidan Malam ya zo yayi mata bayanin duk
abinda ya faru, tsananin kwarjininsa ya sanya ta
kasa cewa komai sai da ya tafi tayi ta mita tana
cewa, daman tasan bakin ciki ake yi diyarta ta
sami gidan hutu, shi ya sanya aka yi mata asiri ta
auri wannan da ba wani bane, don haka koda ya
shigo ko kallon tsiya bai isheta ba balle na arziki,
dan haka ya wuce ya kwanta yana kuma makale
da kudinsa. Washegari da sassafe ya ficewarsa ya
baiwa Sala naira dari biyar yace a siyawa yara
koko,ta karba tana mamaki, ta kasa jurewa ta ce,
"Lallai yau anyi abin kai, ina jin dai Abbakar
tsintuwa kayi, rabon da ka bada kudin abincin
'ya'yanka ai kusan shekara ashirin da biyar
kenan, lallai zan dorar yau." Yayi murmushi kawai
ya fice, domin dai baya son ta ja su da nisa don
kada ta dagoshi, ya ce zai kashe kudin domin dai
ai diyarsa ce, komai ta fanjama-fanjam, domin
dai a doke dai ba zai doku ba. Can gurin mai
shayi ya nufa ya sanya aka hada masa shayi da
wainar kwai da biredi da bota na dari biyar, ya
gyara zama ya kwashi gara yayi gyatsarsa ya
koma majalisarsu, ranar wuni suka yi yana sai
musu gyada da ruwa zuwa tsire da balangu, duk
wanda ke wucewa ta gabansu su kansu ranar
sun san Baba Abbakar yayi samu, da rana ta yi
kuma otal (hotel) ya tafi ya ci abinci har da
kazarsa. Sati uku cif suka wuce, shirye-shiryen
biki ya kankama domin dai gidan su Mustafa sun
kawo kayansu na lefe, duk da sai da aka yi bacin
rai domin dai Hajiya Kubra tace babu wani daga
danginta da zai sanya hannunsa cikin wannan
bikin, dan haka ba zasu je kai kayan lefen ba.
Ran Alhaji Abdullahi ya baci amman sai ya danne
zuciyarsa ya dinga lallashinta, da yake bata iya
ketare maganar mijinta sai ta hakura ta sanarwa
da kanwarta Hajiya Saratu da kuma Yayarta, tun
gurin duban kayan Hajiya Saratu ta fara korafi
kayan sun yi yawa, yarinyar da aka ce 'yar talla
ce za'a kaiwa wannan dukiya? Ai dole a rage,
Hajiya Kubra ta ce, "Hakane kin kawo shawara
gaskiya." Dan haka suka fara kwashe manyan
atamfofi su exclusive da super da aura, suka bar
holland, vlisco da england, ghana da shaddodi da
lesuna kanana. Hajiya Saratu 'yar duniya ce, sam
ba halinsu daya da yayarta ba, Ma'aikaciyar
banki ce, irin matan nan ne masu isa da izgili da
hassada, yayarta ma ba kyaleta tayi ba don dai
ba biye mata take yi ba, don haka ta dubi Alhaji
Abdullahi ta ce, "Haba Alhaji wannan yarinyar da
'yar talla ce, diyar matsiyata jahilai za'a kaiwa
wannan dukiyar? Ai ba za ta iya amfani da su ba,
ko da yake ta danyi yawon....." "Ke Saratu ni
sa'anki ne da zaki dinga gaya mini wannan
maganar? To wallahi zan saba muku gaba
dayanku, koma me cece shi ya ga abarsa yace
yana so, kuma kuna da 'ya'ya mata baku san me
zasu zama ba, fata na gari lamiri."Ya yi fada
sosai sannan ya fice. Tsananin kwarjini da rashin
hayaniyarsa da rashin shiga abinda ba nasa ba
ya sanya kowa ke shakkarsa, don haka kowa yayi
tsit, sai da ya fita ne sannan Hajiya Saratu ta
dauki jakarta tana fadin, "Lallai Kubra an dauko
miki ruwan dahuwarki, kinga sai bala'i yake, akan
wannan kucakar yarinyar Alhaji yake mana
wannan cin mutuncin har da yiwa 'ya'yanmu
baki, to ba dani ba, babu hannuna cikin wannan
sha'anin." Ta nufi kofa a kufule. Hajiya Kubra ta
rikota ta ce, "Haba 'yar uwa kada kiyi mini haka,
kin san dai yanda naki jinin mutuwa ta haka naki
jinin auran nan da yarinyar nan karuwa, idan kika
ce kin zame hannunku waye zai taimaka mini mu
ga bayanta? Ki yi hakuri ki rabu da Alhaji a
ruwan sanyi zan shawo kansa, wuyarta dai a yi
auren." Da haka ta samu ta lallaba Hajiya Saratu
suka tafi kai kayan. Sun so su tata rashin mutunci
sai dai da yake a gidan Malam ne yayi musu
kwarjini, saboda ganin mata masu mutunci da
sanin darajar kansu, 'ya'yan Malam kyawawa ne
masu ilmi don haka duk manya suke aure, duk
ya sanar da su maganar biki, sune kuma kamar
dangin uban su Zainabu, don haka suka gaza
iskancinsu, amman duk da haka sun yada
maganganu. Sanda Mustafa ya ji an rage kaya
daga bakin Sumayya ransa ya baci, amman ya
bar abun a ransa ya tafi ya siya kayan da suka
cire ya baiwa Zainabu yace ta sanya cikin kayan
lefen, za tayi magana ya hanata yace tayi kawai
yanda yace din, sai lokacin ta gane abinda ya
faru don tayi mamakin ganin kayan sun ragu
amman dai tayi shiru ne kawai. Saura sati guda
Sadiku yayi kiran Zainabu dakinsa ransa a
tsananin bace kamar wanda aka aikowa da sakon
mutuwa. Ita kanta da taga yanayin fuskarsa sai
da gabanta ya fadi, ta dubeshi a tsorace ta ce,
"Yaya Sadiku lafiya ko?" Ya ja tsaki kana ya ce ta
zauna, sai da ta zauna sannan ya ce mata,
"Zainabu akwai wadanda suka kai mu takaicin
rashin iyaye na gari a zamanin nan? babu su
tabbas, ba muyi dace da iyaye na gari ba, sai dai
Allah ya shirya mu ba wai don tarbiyyarsu
ba."Gabanta yana faduwa domin ta san tunda
yake fadin wannan magana akwai wani
mummunan abu da ke shirin faruwa, ta ce masa,
"Wai me ya faru ne?" Ya yi kwafa sannan ya fara
zayyana mata, "Kamar yanda kika sani Sala ta ci
alwashin ko cokali ba zata yi miki ba, ta fada a
gabana ta fada a gaban ki, kuma ko bikin Karima
ma haka tayi duk da irin tallan da kuka sha yi
mata, balle Baba da daman ba a zancensa gwara
kowa da shi. To jiya da daddare na yanke
shawarar na sami Malam mu yi magana akan
kayan da za'a siya miki, kin san nima da hidima a
kaina gashi ba wasu wadatattun kudi nake da su
ba, wanda nake dan tarawa ne a banki, sai na
dauki dubu tamanin a ciki da zummar na bawa
Malam a hada da kudin zance da dukiyar uwa da
uba ya zamana dubu dari da hamsin a yi kayan
gado da kujeru, dubu hamsin dinki ta sadaki a
baki abarki a hannunki, idan ya so kayan daki kya
san yadda za kiyi ki hada na jere. Da na jewa da
Malam da maganar sai ya cika da mamaki ya ce
mini, "Sadiku wanne kudi kuma, bayan tun ranar
da aka kawo Mahaifinku ya zo na bashi duka, sai
nace a'a dubu Saba'in zan bashi dubu hamsin sai
an daura aure zan baki a hannunki, domin sadaki
hakkin mace ne, sai ya ce mini ai kun yanke
shawara da su zaku cika kuyi kayan daki." "Ina jin
haka raina yayi masifar baci don na san Baba ya
kashe kudin nan, baya jin kunya balle tsoron
Allah, bai sauke nauyinsa namu da ke kansa ba
wanda Allah ya dora masa ba, amman ya koma
yake karbar hakkinmu, domin kada na bada mu
na watsawa Mahaifinmu kasa a ido, don nasan
duk lalacewarsa shine ubanmu, ya sanya na
dannen fushi na na rufa masa asiri na ce da
Malam, shi kenan zanje mu yi maganar da shi
naji ina kudin, Malam ya bini da to kawai,
amman daga irin kallon da yake mini na san ya
san ba za'a sami kudin nan a hannun Baba ba,
domin ya fimu sanin halinsa." "Don haka na
yanke hukunci da kaina yau na zauna naki yin
bacci, na dinga karance-karance har karfe biyu
da rabi sanda Baba ya shigo gida, ina jinsa yana
kokarin kulle kofa ya sanya na leka, shi kansa
yayi mamakin ganina, ya ce lafiya Sadiku baka yi
bacci ba?" Na ce "Baba ka shigo daga daki na ina
son yin magana da kai bana son Sala ta ji, babu
musu ya biyo ni ya tsaya daga bakin kofa yana
wani muzurai ya ce, "Lafiya dai ko?" "Na zayyane
masa yanda muka yi da Malam, na dora da
cewar, yanzu ya bada kudin gurin nasa a cika a yi
miki kayan daki." "Na gaya miki sai gashi ya kama
gumi jikinsa ya dauki rawa ya kama inda-inda,
daga karshe sai ya ce wai ya karbi kudin yana
tahowa a hanya 'yan sane suka yanke masa
aljihu, to yasan idan ya fada ba za'a yadda ba ne
shi ya sanya yayi shiru, yanzu haka neman kudi
yake ido rufe ya biya." "Daga yanda yake
maganar zaki tabbatar bashi da gaskiya, raina ya
baci na ce, Haba Baba mai yasa ka karbi kudin
nan, tun da muka taso baka san cinmu ba balle
shan mu, duk wani fadi tashi Mahaifiyarmu ce ke
yi, don haka duk wani hali da 'ya'yanka suka
shiga kai ne ja gaba, mun kyale ka don babu
yanda za muyi amman yanzu ace an kawo kudin
auren diyarka ka bi ka amshe bayan kai ko tsinke
ba zaka yi mata ba? Wanne abin gori kake son
bar mana, yanzu idan sirikan Zainabu suka ji
wannan zancen da yaya kake ganin zasu kalle
ta?." "Maimakon yayi nadama, a'a sai ma ya
kama fada, ta inda ya shiga ba ta nan yake fita
ba yana fadin, ai nasan Babarku ce ta sanya kuka
raina ni, amman banda haka ta yaya zan fadi
magana ka karyata ni, duk lalacewata ai nine
ubanku dai ba a sakewa tuwo suna....."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
"Fada dai babu makama, kamar an tashi Sala sai
muka jiyo muryarta daga cikin gida tana fadin,
Wai waye ke mana hayaniya a daran nan, kin san
ita ba lokaci take dubawa ba ta zaci dare ne
sosai, ta iso zauren ta ga Baba a kofar dakina a
tsaye, shi kuwa jikinsa sai rawa yake. Da mamaki
ta ce, Abbakar lafiya na ganka a nan, me ya
faru?" Da in-ina yake fada, "Fada nake masa ya
bar kofar gida bai kara ba, kada awaki su shigo
su yi miki barna." Yana magana yana kanne mini
ido wai kada na fada, da yake ranar babu 'yan
magana a kanta sai ta yamutsa fuska ta juya
kawai, ya bita da sauri, shine duk na ji raina ya
kuma baci, wallahi bacci sai dai barawo jiya ya
sace ni."Ran Zainabu idan yayi dubu ya baci, ta
dafe kai tana fadin, "Oh ni Zainabu mun shiga
uku, yaushe zuciyar iyayenmu zata gyaru su san
Annabi ya faku? Sadiku duk fa wani iskanci da
yawon tallan da nayi Baba ya sani, amman a
matsayinsa na Mahaifina bai taba kirana yayi
mini fada ba, Balle Sala da ke kuma tinzirani,
shin suna zaton Allah zai barsu haka ne? Addu'a
kawai zamu cigaba da yi musu sannan mu binne
wannan maganar a tsakaninmu." "Domin ka san
idan Sala taji wani bala'in ne zai tashi, don nasan
ko ruwa ba zai sha a gidan nan ba, kuma sai ta
sanar da kowa, daga karshe dai mu ne da abin
kunya domin su ko a jikinsu, daman dangin
Mustafa musamman Babarsa ba auren nan take
so ba, balle haka ta faru taji ai na shiga uku da
gori, dan haka kawai mu ja bakinmu mu yi shiru,
Allah ya sanya ina da kudi a account dina, kada
ka damu idan anjima zan fito maka da dubu dari
biyu, duk abinda ka ga ya dace daga kujeru zuwa
gado ka siya, amman ni na sayi komai na jere da
na kicin zuwa labule, kayan katako ne kawai ban
siya ba, ka bar kudinka kawai tunda kai ma kana
da taka hidimar, na gode." Ya ce, "A'a, nayi
niyyar baki dan haka sai a sayi kayan gadon da
su. Ta ce, "Shi kenan na gode,Ta fice daga dakin
nasa amman har lokacin zuciyarta tafasa take yi,
ina ma wani ne can yayi mata haka da yau ya
gane kurensa wallahi, ita da take neman fada da
kudinta balle ya zo?, don dai Mahaifin ta ne, ta
kuma yi alkawarin ba zata yi masa magana ba, ta
barshi da kansa zai gane bai kyauta ba komai
daren dadewa.
Mustafa kam idan ka ganshi tamkar wanda aka
yiwa albishir da gidan Aljanna, duk da irin
maganganun da Hajiyarsa ke gaya masa yayi
kunnen uwar shegu kamar baya jin ta, hidima
yake yi sosai, an shirya biki na garari. Ranar
kamu ma a central hotel aka shirya za'a yi, an
yiwa gurin kamun kwalliya mai kayatarwa,
Mahmud Nagudu yana cashewa, amarya ta shigo
cikin wani irin Sari na Indiya (Golden colour) kalar
kyalli, har da irin sarkar nan tasu ta goshi ta yi
kyau matuka, da yake Zainabu akwai iya tsara
kwalliya, nan fa aka fara cashe rawa, sam ta
manta ita amarya ce, domin yanda ka san mazari
haka take gurin rawa, sai da Asma tayi mata
rada a kunne sannan ta tuna ta koma ta zauna
tana dariya, kawayenta kuwa suka yi mata ca da
liki, gaskiya sunyi mata kara. Sanda dangin mijin
suka iso sai da gabanta ya fadi don ganin irin
kallon da Hajiya Saratu ke mata, tabbas a halitta
bata da makusa duk iyakacin hassadar mutum,
dan haka ne ma ya sanya ta dinga kallonta a
wulakance, Rungumar da Sumayya kanwar
Mustafa ta yi mata ne ya sanyaya mata rai, nan
fa Anti Binta ta fara fesa mata turare (Diyar
Malam ce tana koyarwa a makarantar Legal), nan
fa kida ya kuma barkewa, sai karfe takwas aka
tashi. A motar Asma suka zo gurin kamun dan
haka bayan an watse ma suka fita da zummar
hawa, sai dai sakon da ya shigo wayarta ya
tsaidata tana karantawa, ta yi murmushi ta leka
ta windo tana fadin, "To ke an hutar da ke
domin dai ga ango na can yana jirana a mota au
haka za kiyi mini 'yar iska zan rama wallahi."
Tana dariya ta nufi gurin motar Mustafa domin
ya gaya mata inda yake a tsaye. Tunda ta nufo
shi yake kallonta ta hasken fitilar da ta haske
kofar hotel din, ji yake kamar ya fita da gudu ya
taro ta, amman dai ya dake ta karaso, ita kuma
har wani sauya salon tafiya take yi. Ta shiga
motar tana murmushin jan hankali, ya riko
hannunta yana fadin, "Kai Zainabu wannan wane
irin kunshi ne sai kace na indiyawa?" Ta kanne
ido tana dariya ta ce, "Kai dai kawai kace yayi
kyau wace ni nayi irin na Indiyawa?" Ya dinga
murza hannun nata yana murmushi ya ce, "Ai ni
a guna yafi na Aishwarya Rai da Pretty Zinta da
Kajol da duk wata macen indiya da ke tashe,
domin yanda nake jinki tamkar mafi kyan
duniya." Ta yi dariya sosai domin jin dadin
kalamansa, amman sai ta canja maganar tana
cewa, "Wai yaushe ne kazo nan nema? Na yi
mamaki da na ji kace kana kallona na zo ka
maidani gida." Ya kishingida da kujera har lokacin
yana rike da hannunta ya ce, "Kina fitowa daga
gida na isa aka ce kun wuce a motar Asma'u,
shine na biyo bayanki, komai akan idona aka yi,
can baya na labe inda ba zaku ganni ba, amman
sanda naga kina taka rawa dauriya ta ta kusa
karewa na fito na hanaki, domin sai naga kamar
mai kidan da yaransa ke kawai suke kallo, sai
Asma'u tayi maki gata tayi miki rada a kunnen
kika daina.""Tuba nake ba zan kuma ba, kasan ni
da rawa....." "Mu bar wannan caftar, yanzu ina
muka nufa?" Ya tambaye ta. "Gida zan koma, don
mai yi mini dilka da halawa tana jirana." Ya tada
motar yana fadin, "A'a ai dole na kai ki a gyara
mini jikin nan, ki duba tun yau yanda kika fara
zama, fatarki ta zama wata mai taushi da kyalli."
Yana magana yana cigaba da murza hannunta
dayan kuma yana tuki da shi. Ta janye hannunta
tana fadin, "Kada ka sanya mu yi hatsari."
Amman bai saki din ba dole ta hakura tana
tsokanarsa har suka isa gida. Zainabu tana da
wani sirri da ke sanya maza matowa a kanta,
wato gyaran jiki, na farko dai duk nacinka ba
zaka taba ganin gashi ko kwaya guda a gabanta
ko a hammatarta ba, kullum cikin askewa take da
(shaving powder), domin a cewarta sune gidan
tsami dake sanya jikin mace wari duk irin turaren
da ta sanya, sannan na gaban kan rike kwayoyin
cuta wanda ke hassadawa mace cutuka kala-
kala, baya ga tauye mata ni'ima da yake yi,
sannan ba ta da sanya gurin shan magunguna
'yan gaske ba irin na macuta ba, don haka yanzu
da zata kwanta sai da tayi hadin ta ta sha kamar
haka. Hadin nikakkiyar aya wacce aka jikata ta
jiku aka markado da dabino jikakke, bayan an
surfa ayar a hadin aka markado da kanumfari
kadan sai a sanya madara ko nono da suga ta
sha, sannan ta kuma dauko wani dakakkan garin
hadi wanda aka hada garin kanumfar da
dakakkiyar 'ya'yan kankana da dabino da garin
aya tankadadde da kirfa da gero da hakin daka
da mazarkwaila da sassaken banna aka dakesu
lukwi ta sha da yoghot na roba. Sannan ta dauko
wata buta can bayan gadonta wacce take jike da
ruwan bagaruwa din-din-din, ta zagaya bandaki
ta yo tsarki dashi da ruwan dumi a cikin flask da
ta kara, bayan ta dawo ta dauko auduga ta
dangwali garin fas da ta kwabashi da man zaitun
da itacen asuwaki ta matsa shi a gabanta, yayi
kamar minti biyar sannan ta cire ta koma ta
feshe jikinta da turaruka ta sanyo rigar bacci ta
kwanta. Zainabu kam tana da sirrikan da take
siye zuciyar maza da shi a banza ma balle mijinta
abin son ta Mustafa, don haka tayi alwashin zata
yi gyaran da zata gigita shi.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Gurin Dina ma tayi kyau matuka tamkar itace tayi
kanta, Mustafa duk ya wani rude ga wani irin
kamshi da take yi, domin dai idan ta yi wanka
takan shafa mai mai hade da turare sannan ta
sanya turare mai maiko, ta kawo (body spray)
turaren jiki ta shafa sannan bayan ta sanya kaya
ta kanyi amfani da turare kusan kala shida, don
haka sai ka rasa gane wanne irin turare ta sanya.
Ranar Asabar 20 ga watan Shida 2004 aka daura
aure mai cike da tarihi na Mustafa Abdullahi da
Zainabu Abbakar, jama'a kam tamkar ana bikin
sallah, gaskiya daurin auran yayi jama''aA kuma
ranar aka je aka yi mata jere, Zainabu kam ta
fidda kanta kunya, domin tayi kaya na gani na
fada, duk girman gidan Mustafa an jere ko ina,
ga gara da aka jibga mata komai da komai, abin
dai gwanin sha'awa, su Malam kan sunyi mata
kara, sun zame mata gata da 'yar uwarta
Karimatu wacce itace ke tsaye akan komai na
bikin na su, tun da Sala tace babu ruwanta, sunyi
sa'a dai Sala bata yi bala'i ba faran-faran da
kowa ta ci kwalliyarta kamar gaske.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Idan Zuciya Tagyaru2-03
Posted by ANaM Dorayi on 08:07 AM, 11-Feb-16
Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU
_______________ Na
_________Fauziyya D Sulaiman____
Amman har lokacin tana nan kan bakanta na sai
ta raba auran, duk da babu wani abu na
kushewa da zata iya cewa daga Mustafa, Kayan
lefen Zainabu duk kawayenta babu wacce ta
samu kamarsu, ita dai tafi son Zainabu ta
cigaba da bin maza tana kawo mata kudi, babu
tsoron Allah a zuciyar ta balle nadama. Ranar
lahadi da misalin karfe goma sha daya da
mintuna aka shigar da Zainabu dankareren
gidanta na masoyinta, gidan kam ya hadu duk
hassadar mai hassada. 'Yan kai amarya sun
watse cike da tsegumin gidan, har wata a cikin
matan na fadin, "Oh ni Maryam, zamani ya
canza, ki ga mace ta gama iskancinta da
watsewarta amman daga karshe sai kiga mai
kudi ya aureta, nawa muka gani a wannan
zamani? Ki dubi gidan da Zainabu ta shigo, haka
nan wata a bayan layinmu Ummi Caransi ka da
ki so kiga iskancin da tayi, karshe na gaya miki
wani minista ne ya aure ta, yanzu baki ga
arniyar motar da take murzawa ba wallahi."
Abokiyar maganar tata tayi kwafa tana fadin, "Ki
ji Maryam da wani zance, to menenen abin
mamaki a ciki? Ko kin manta ayar Allah ta cewar
(Mazinaci baya aure sai mazinaciya ko fasika)?
don haka idan kika bincika za ki ga wata kila
daman can abokin fasikancin ta ne ta aura, ko
kuma shima yana yi a can itama tana yi a can
Allah ya hadasu, su kuma matan kwarai da basu
auran manya Allah ya ga zuciyarsu don haka sai
ya hadasu da salihan bayi 'yan uwansu
talakawa, ko kuma masu kudin na gari, wanda
yanzu sai kinyi da gaske za ki samo su." "Idan
kuma kika yi nazari zaki ga 'yan iskan da ke
auran masu kudin suna ganin sunci riba, gaba
zasu girbi abinsu ko da akan 'ya'yansu ne, idan
Allah ya sosu da rahama idan kuma basu da
rabo sai Allah yayi musu talala sai a can, dan
haka shi iskanci bashi da wata riba ga mace ko
namiji, fatanmu dai Allah ya shirya mana zuri'a,
sannan mu dage da tarbiyyar yara, domin
amana ce Allah ya ba mu komai dadewa za mu
yi wa Allah bayanin yanda muka yi kiwonsu,
idan sun zama na gari su zame nana sadakatu
jariya bayan ranmu, duk aikin da suka yi na
lada mu samu rabo, idan kuma mun watsa su
zamu yi wa Allah bayanin sakacin da muka yi da
kiwon da ya bamu." Maryam ta yi ajiyar zuciya
ta ce, "Haka ne kuma, a yanzu dai sai mu baza
kunnen mu ji abinda zai biyo baya kenan da
auran Zainabu.......a'a ki daina fadin haka, ai
shi Ubangiji Gafurur Rahim ne, kuma da zuciya
yake amfani, idan zuciyar Zainabu ta gyaru sai
Allah ya saka mata da mafi alkhairi, tun da dai
shi sarki ne mai yafiya, kuma idan ka gorantawa
dan uwanka wani aiki na sabo da yayi, ko zina
ko sata da dai sauransu, sai kiga Allah kaima ya
dora maka, tunda abin jarabawar ce, kuma
muma ba wayonmu ko dabararmu bace ya
sanya Allah ya shirye mu ba illah Rahamarsa,
don haka sai a yiwa wadanda suka kauce
addu'ar shiriya." Maryam ta ce, "Haka ne kam,
Allah na tuba." Suka rufe zancen nasu domin jin
motar da zata mai da 'yan kawo amarya ta
dawo.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
BURIN MASOYA.....
Burin masoya lallai bai wuce ganin su tare ba,
bisa aminci na aure ba, lallai haka ce ta faru ga
Mustafa da Zainabu, domin dai ko wasu 'yan
siyan baki bai zo da su ba, sai abokinsa kuma
amininsa Alkasim, shima daga kofar gida suka
rabu yana zolayarsa. Yana shiga ya kukkulle ko
ina na gidan ya nufi dakin amaryarsa cike da
doki da murna. Ita kam tana zaune bisa
tafkeken gadonta wanda ya sha kayan shimfidu
na alfarma, ta sha wani hadadden leshi da
kudinsa ya tasamman dubu hamsin, bashi da
nauyi sai dankaran taushi, light purple ne ya
sha duwatsu da cin baki da fari, ya amshi jikin
Zainabu, sai sarka da dan kunne na zallar
daimond kirar dubai da ta sanya da zabba da
awarwaro, an kuma nadeta da wata laffaya
wacce ta sha turaruka kala-kala, kamshi ne
kawai ke tashi kala-kala daga jikinta, gashin nan
ya sha gyara duk da ba ma'abociyar sanya
gashi bace a wannan karon an mata kitso da
shi, ta yi kyau das tamkar amaryar larabawa,
domin Zainabu tana da kyau matuka, duk da
fatarta bata fiye haske ba, hancinta da idonta
ya kara fito da kyawunta, sam bata shafa man
bilicin domin tana son kalar fatarta kalar alawa,
sai dai fa akwai ta da amfani da mayukan
gyaran fata. Sai ta hada mayuka na dubu sittin
har fiye da haka, don haka kullum ka ganta
tamkar diyar tarwada tana sheki da sulbi, balle
ka taba jikinta, wani silbi yake yi da taushi, ta
yadda ta kashewa jikinta ko nawa ne, don haka
ba a banza take siye zuciyar 'yan maza ba. Da
gaggawa ya isa gabanta ya zauna sosai bisa
gadon saboda kamshin dake shiga hancinsa, ya
daga laffayar a hankali, ta dago tana masa
murmushinta mai kyau kumatunta ya lotsa
(beauty point), ta kwantar da murya da kissa ta
ce, "Mustafa honey yaya gajiyar biki?" Ya lumshe
ido cikin wani salo da kallon da ya saba sace
zuciyarta, da wata irin murya wacce shi kansa
bai san yana da ita ba ya ce, "Zainabu yau kin
zama tawa ni kadai, yau wane farin ciki kike
zaton zanyi? Bana jin wata gajiya sam, ki cire
wannan laffayar na ga adon naki." Ya kama
warware mata laffayar, shigar da ke jikinta ta
fito ya kuma rudewa. Da kyar ya iya dauko fresh
milk da nama ya ce su ci domin kada su ji
yunwa, babu musu ta ci amman tana jikinsa a
makale kamar zata gudu, ita da kanta ta san
tayi rashin zumarta Mustafa. Ba su kammala cin
abincin ba komai ya kacame, domin ba zai iya
hakuri da Zainabu ba, wani salo take nuna
masa da yake haukatar da shi, tana daga cikin
mata ajin farko da suka amsa sunansu,Sai dai
wani abu da ma'auratan basu yi ba shine, sallar
da Ma'aiki ya koyar da mu ta samun
tsaftatacciyar zuri'a da samun zaman lafiya a
aure ba, saboda sun kwadaitu da juna kamar
basu san juna ba. Da kyar suka iya rabuwa da
juna da safe, amman sun yadda lallai aure yafi
komai dadi, domin babu fargaba a zuciyarsu ta
wani zai gansu ko kuma ta suna aikata sabo,
dan haka suka sakata suka wala. Karfe goma na
safe suka fito babban falonsu suna sakale da
hannun juna, kananan kaya ne a jikinta, duk
sanda ta taka kafarta sai jikinta yayi rawa, wata
irin halitta ce da Zainabu ta daukar hankali,
bata dai ta tsaho sosai amman tana da siffa irin
mai daukar hankalin nan, don haka idan ta saka
kananan kaya sai ka ganta tamkar wacce da su
aka halicce ta.shima Mustafa ba baya ba, yana
da tsaho da kirar karfi, yana da faffadan kirji da
yake birge mata da su, yana da kyan fuska irin
ta maza ajin farko hancinsa dogo ne, shi kam
yana da duhun fata sai dai ba can ba, yana da
saje dan siriri wanda ya fito da kyan fuskarsa
sosai, gashinsa yana da taushi saboda gyara da
yake samu. Suka fito rike da hannun juna cikin
nishadi da soyayya, kafin su karaso kukunsu
Emmanuel ya kammala shirya komai, domin tun
yana saurayi shi ke shirya masa abinci a can
gidansa na shakatawa, ya iya girki matuka
domin abinda ya karanta kenan. Ya zauna ya
zaunar da ita bisa cinyarsa, ta kalli abincin da
mamaki ta ce, "Honey waye ya dafa....kai
Zainabu har kin manta da mutumin naki Ema?,
ai da shi na taho nan gidan ma, don ya dinga
taimaka miki gurin aikinki." Ta yi murmushi ta
ce, "Ba mantawa nayi da shi ba, gani na yi ban
gane shi ba, ka sanshi da shakiyanci, nasan idan
ya gama abinci ya kan zauna a gurin har mu fito
yana mana shakiyanci." Ya ce, "Ai da kika ce
yanzu ya san da bambanci, na gargade shi da
kada na ganshi a cikin gida idan ba lokacin
aikinsa ba ne, da zarar kuma ya kammala ya
fita, domin kin san ina da tsananin kishi
musamman a kanki, ba zan so ya dinga kalle
mini ke ba." Ta yi murmushi sannan ta ce, "Ai
dole zai tafi ma don ban yadda wani yayi mini
girkin mijina ba." Sannan ta debo abinci a cokali
ta sanya masa a bakinsa, ya lumshe ido yana
dariya ya amsa, haka nan suka dinga ciyar da
juna. Sai wajajen karfe goma sha biyu yayi shirin
tafiya gaida su Hajiyarsa, ta ce masa ya dace ya
raba kayan gara biyu ya kai musu nasu. Ya
dube ta ya ce, "Haba dai me za su yi da wani
kayan abinci, ai suna da shi da yawa a sito
(store)." Ta kwantar da kai tana masa wani duba
ta ce, "Honey haka ne ka'idar ai, dole idan aka
kawo kayan gara sai an kai gidan iyayen miji,
suma ba ci zasu yi ba zasu rabawa 'yan uwa ne
maganin gori ga matar, domin kasan
mutananmu sun dauki garar nan da girma."ya
yamutsa fuska ya ce, "Kin san Allah? Wallahi da
an yi shawara da ni da babu wata gara da za'a
kawo, domin ni ke nake aure ba gara ba, duk
namijin da kika ji yana gori ko habaici don gara
to lallai matsiyace ne na karshe, su kansu masu
goranta garar daga dangin angon suma zuciyar
talauci ce da su duk arzikinsu, domin mai
wadatacciyar zuciya a gurin Allah yake nema bai
saka rai da na wani ba." Ta ce "Haka ne ga
wanda ya gane, mu je mu raba kawai lokaci
yana kurewa baka je ka gaida su ba." Kusan
komai daidai suka raba ta sanya gyalanta ta
taya shi shigarwa a mota, wasu kuma sai da
Ema ya sanya musu, bayan but din ya cika taf
da kaya, tana kallonsa tana daga masa hannu
ya fice daga gidan. Ta koma falo ta zauna
zugum tana kallo, sai taji kewar maigidan nata,
sai kuma ta tuno da shandy dinta, da ma tayo
guzurin abinta domin ta lura kamar Mustafa
yanzu ya daina shan komai sai taba, don haka
ta shige daki ta dauko ta tana zuka tana lumshe
idanunta kamar mai cin naman kaza, sai da ta
ishe ta sannan ta fadi jagwab a gado tana
ramuwar baccin daran jiya. Shi kuwa sanda ya
isa gidansu ya tadda kanwarsa Sumayya da
Zainab 'yan matan Hajiyarsa suna kallo, da
girmamawa suka gaishe shi, ya zauna bisa
kujerar yana amsawa da sakin fuska. Zainab ce
ta mike ta ce, "Ya Mustafa bari a kawo maka
abinci da ruwa ko?"Ya ce, "A'a Zainab ki barshi
a koshe nake." (Da yake suna dasawa da
Zainabu, duk cikin 'yan matan gidansu tafi kowa
tarbiyya, gashi tana da sunan masoyiyarsa,
lokuta da dama yakan tsokane ta da mai sunan
darling su yi dariya). Ya kuma dubansu ya ce,
"Yaya dai 'yan matan gidan mu ina Momin taku
take naji shiru babu motsinta?" Ta ce, "Wallahi
gajiyar bikin nan ce bata sake ta ba, amman ta
tashi bari na kirawo maka ita." Ta mike ta nufi
sashin Momin nasu. Ya kalli Zainab wacce gaba
daya hankalinta yana kan kallon fim din da suke
kallo na wani Indiya mai suna Ghajini, ya ce,
"Yaya dai mai sunan darling, ke fa akwai ki da
son indiya dan naji wani lokaci har fassarawa
kike, a bani labarin wannan fim din." Ta yi
dariya ta ce, "Ya Mustafa ai wannan fim din
labarinsa ba zai badu ba domin ya hadu karshe
wallahi, sai dai mu baka aro ka gani." Ya yi
dariya ya ce, "A'a bani da lokacin kallo sai dai
na baiwa takwararki ta kalla, domin naga ita ma
tana son kallon, idan yaso sai ta bani labarin
naji." Ta yi dariya ta ce, "Yaya kenan, kana son
Yayar nan tamu da yawa wallahi, zan so muje
mu gaishe ta kuwa." Ya ji dadin abinda ta ce
har ransa, shi ya sanya hirarsu take tsaho da
Zainab, domin tana son Zainabunsa ya ce,
"Lallai yarinya zaki ga Zainabu kuwa, za kuma ki
san ba a banza nake sonta ba, domin tana cikin
mata sahun farko, ke ni fa a iyakacin yawo na
da nayi a duniya har yau ban ci karo da macen
da ta hada qualities din Zainabu ba." Zainab ta
sanya dariya cike da mamakin irin son da Yayan
na su ke yiwa Zainabu, tun da take bata taba
jin ko labarin irin soyayyar su ba, shima dariyar
ya kama yi a haka su Hajiya Kubra suka tadda
su. Dadi ya kama ta domin a rayuwarta tana
son taga ya saki jiki da 'yan uwansa yana hira,
amman shi miskili ne sai ya so, sai dai ta lura
suna dasawa da Zainab ko don sunan 'yar
mulkin tashi ne da ita Oho? Ya tsagaita dariyar
yana duban ta ya ce, "Momi barka da safiya, na
shigo ban ganki ba na ke tambayar 'yan matanki
suka ce kina ciki." Ta yi murmushi ta ce, "Lallai
kam ka yi sa'a yau basu da lakca ta safe shi ya
sanya aka zauna kallo." Zainab ta mike da
zummar barin falon, Hajiya Kubra ta ce, "A'a ina
zaki Zainab? Zauna ku cigaba da kallonku, ai
hirar da ku za'a yi." Ta koma ta zauna amman
hankalinta yana kan fim din gaba daya, hira
suke yi sosai shi da Hajiyar tasa kamar babu
wani abu a tsakaninsu, har kusan awa guda, can
ya mike ya ce zaije ya gaida abokansa yayi
musu ban gajiya. Sai a sannan Zainabu ta fado
mata, ta hade rai ta ce, "A gaida su." Kamar
kada ya fita ganin yanda ta sauya lokaci guda,
amman gudun kada ya tsokanowa kansa fitina
sai ya sanya yayi shiru ya juya ya nufi kofa,
Zainab da Sumayya suna yi masa a gaida
Antinsu, ta galla musu harara basu kula da ita
ba. Sai da ya fita sannan ya tuna da kayan
garar dake cikin motarsa, ya kirawo mai gadi ya
ce ya shiga da su ciki, shi kuma yana saukowa
da su. An shiga da buhu biyu maigadin ya ce,
"Wai Hajiya ta ce ka shiga tana son ganinka, a
daina shiga da kayan."gabansa ya yanke ya fadi
amman ya dake ya shiga yana addu'a a
zuciyarsa. Tana zaune inda ya barta, sai dai tayi
kicin-kicin kamar ba ita ba, har lokacin su
Zainab suna nan suna kallonsu.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
"Momi gani maigadi ya ce kina kira." Ta yamutsa
fuska tana kallonsa ta ce, "Na ga ana shigo da
kayan abinci shine na ce bari naji daga wa, don
naga har da dubulan da alkaki?" Gabansa ya
cigaba da faduwa, ya daure yayi ta maza ya ce,
"Momi daman kayan gara ne Zainabu ta ce a
kawo......" "Kai!" Ta doka masa tsawa, ta dora
da cewar, "Kaga munyi kama da wadanda za su
ci kaya daga hannun matsiyaciyar matarka? Me
take da shi da zata bamu? Bana raba daya biyu
wannan kayan garar da kudin haram aka siye
su, don haka yau ce rana ta karshe da zaka
kuma kawo mini wani abu da ya shafi matarka,
kada ka manta na sha sanar da kai bani
kaunarta na tsane ta, domin na santa na san
wacece ita, kai ne aka linke a bai-bai, don haka
ka hada kayanka ka fice da su, tun basu sanya
jini na ya hau ba, zan kuma sanar da kai
kashedi na karshe, ko da wasa kada ka yi gigin
kawota gidan nan, domin wallahi sai ta
gwammace bata taba gani na ba balle ta auri
jini na, domin kasan sirrinta kaf yana tafin
hannuna, idan kunne ya ji jiki ya tsira." Sororo
yayi tsaye yana jinta cike da tashin hankali, bai
taba zaton kiyayyar da Mominsa ke yiwa
Zainabu ta kai nan ba, amman yaya ya iya dole
ya fara kinkimar kayan yana fita da su. Zainab
da Sumayya dake zaune jikinsu yayi sanyi,
domin basu son abinda Momin ke yiwa Yayan
nasu akan matarsa sam, amman basu da ta
cewa don haka suka ja bakinsu suka yi shiru. Shi
kuwa da ya gama jidewa ya dawo ya durkusa a
gabanta ya ce, "Ki yi hakuri Momi ba zan kuma
yin abinda zai bata miki rai ba da sani na Insha
Allah, na barki lafiya." Ya mike ya nufi kofa. Ta
yi tsaki cike da kuncin zuciya ta ce, "Bacin rai
kuwa ai yanzu ka fara gani tun da ka kwaso kara
da kiyashi ka ajiye a gidanka, koren juji wanda
Manzon Allah ya hori sahabbai da su guje shi,
wato kyakykyawar mace a gida mara tarbiyya."
Kanwarsa Sumayya ta ce, "Haba Momi ya dace
ki yi hakuri zuwa yanzu tunda dai Allah ya
kaddara sai anyi auren nan....." "Ke rufe mini
baki, ni zaki yiwa wa'azi? Da ban yarda da
kaddara ba zan amince ya aure ta ne? Ai na
sani ita din mummunar kaddara ce a gare mu,
amman nasan babu alkhairi ga Zainabu har
abada."Ta mike ta nufi dakinta tana mita.
Zainab ta dubi Sumayya ta ce, "Kin ga da Momi
tana fadan nan sai naji duk hankalina ya tashi,
abinda ba halinta ba ne, na rasa irin laifin da
Anti Zainabu ta yi mata haka da zafi ta tsane
ta." Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Kin san tsohuwar
dalibarta ce, kuma ta san halinta sarai, gashi
munafukai sun kawo mata labarin gidansu gaba
daya, mu da ba shiga harkar 'yan unguwar nan
da muka tashi nake ba sai da aka so ayi mini
tseguminta, na ce ina ruwana meye nawa a ciki,
wanda yace yana sonta yafi kowa sanin halinta
kuma shine zai zauna da ita meye nawa a ciki,
ita kanta Momi na so ace ta kauda kanta." Haka
nan suka dinga tattauna matsalar, su kansu ba
su son wannan sabanin tsakanin Momi da
Yayansu. Shi kuwa Mustafa da kyar ya iya fita
daga gidan da motarsa, yaje ya yi parking can
gefen hanya, ya dora kansa bisa sitiyarin ya
runtse idonsa zuciyarsa tana zafi, ya rasa wacce
irin kiyayya Momi ke yiwa Zainabu, ya dace ace
zuwa yanzu da ta zama matarsa ta sassauta.
Amman ina saima karuwa da tayi, domin
matakin da ta dauka yana nuna alamun ba za
ta yi wata mu'amala da ita a matsayin sirikarta
ba, tunda ta ce ko gidan bata kaunar tazo balle
kuma ace ta zo wata sabgar, shi kam bai san
inda zai tsoma rayuwarsa ba, Zainabu kam wani
ginshiki ce na rayuwarsa da ba zai iya rabuwa
da ita ba, sai dai kawai ya cigaba da addu'a
Allah ya daidaita tsakaninsu da Mominsa, domin
wannan kiyayyar tana ci masa tuwo a kwarya.
Rayuwa ce mafi dadi da soyayya suka gudanar a
cikin sati biyu da suka yi na hutunsu na amarci,
dukkaninsu sun yadda ba suyi zaben tumin dare
ba. Domin Zainabu ta bada kaimi sosai gurin
ganin ta faranta ran maigidan nata, tayi sa'a
kuwa lallai ta gama da zuciyarsa kaf, bai ganin
kowacce mace da gashi, don haka bini-bini yana
gida har abokansa suna masa tsiya. Ranar
lahadi da daddare suna falo a zaune, ita tana
zaune bisa kafet ta mike kafafunta shi kuma ya
dora kansa bisa cinyarta tana wasa da gashinsa,
har kitso take masa suna dariya, domin ji yake
kamar tana masa susa. Ya ce, "Zainabu na gobe
fa zan koma Ofis dan kin san hutun sati biyu
kacal suka bani." Ta sha kunun karya ta ce, "Kai
honey har hutun ya kare? Ai kamata yayi su
baka wata guda gaskiya." Cikin shagwaba da jan
rai take maganar tata. Ya rungumota jikinsa
yana hada hancinsa da nata ya ce, "Haba my
honey ki yi dariya mana, dole ce nima ta sanya
zan koma, kin san aikin gwabnati babu daga
kafa, amman kin san duk inda nake kina raina."
Ta ce, "Shi kenan nima goben na fara zuwa
aikina tun da zaman kadaici zai dame ni....."
"What, me? Aiki Zainabu? A'a babu ke babu
zuwa aiki." Ya katse mata magana. Ta ji
maganar tasa a bazata don haka ta ce, "Haba
dai, da wasa kake kaima kasan ba zaka rabani
da aikina ba, kai da iyayenka suke kirana da
'yar matsiyata suka ga na kuma share gindi na
zauna a gidanka bana nemo na kaina ai sai su
zaci kwadayi ne ya sanya na aureka, kuma
kasan sarai iyayena ba wasu bane dole zan
dinga taimakawa 'yan uwana, don haka kama
sake batu aiki kamar da kasa zan koma gobe ni
ma domin ba muyi da kai zaka hana ni aiki ba."
Ya tashi zaune yana mata wani duba tamkar
wanda aka aikowa da sallahun mutuwa, sai wani
hura hanci yake yi da zafin rai ya ce, "Kin san
Allah Zainabu, ba zaki kuma zuwa wannan
matsiyaciyar Sakateriyar da sunan aiki ba, ko
kina zaton bani da labarin samarinki a can? To ki
bude kunnanki da kyau ki ji, duk wani ko wasu
da kike mu'amala da su can da to yanzu na
yanke ta."Yanda yake maganar da gadara da isa
itama ya hasala ta, don haka da tsiwa ta ce, "Au
kace daman ka aure ni da wata manufa daban
ne, to tsaya na sanar da kai Zainabu kaifi daya
ce, wallahi da ina da niyyar kuma kusantar wani
namiji da wallahi baka isa na aure ka ba har na
zauna wata uku cur ina Istibira'i ba, don haka
ka ji da kunnenka Zan koma aikina, duk abinda
zuciyarka zata sanar da kai kai ka sani." Tana
gama fadin haka ta nufi cikin dakinta ranta yana
suya. Shi ma nashi ya kuma suya ya kama lallai
ya sani Zainabu fitsararriya ce, amman ya yi
zaton a matsayinsa na mijinta kuma wanda take
so zata rangwantawa, ya koma ya jingina da
kujera ya lumshe ido zuciyarsa na cigaba da
suya, wallahi komai zai faru sai dai ya faru
amman ba zai taba yadda ace yana nan sake da
baki matarsa na mu'amala da wasu 'yan iska
ba, ya fi kowa sanin halin shegen DPM din nan
da chairman din da kuma sauran ma'aikatan
dake sakateriyar, domin yayi bincike mai kyau a
kansu, don haka komai Zainabu za tayi ba zai
barta ta koma aikin nan ba, idan ta so tayi
(resignation letter) takardar barin aiki shi kenan
idan kuma bata yi ba ita ta sani. Haka nan ya yi
ta zama a falon har kusan karfe sha biyu na
dare, ga dai TV a kunne amman hankalinsa ba
ya kan kallon, ya dai gaji ya kulle ko ina ya nufi
dakin baccin na su,tana kwance a gadon da
alama ta dade da yin bacci, tamkar mai bacci a
cikin ruwa haka nan fuskarta tayi kyau, sanye
take da wata yaloluwar rigar bacci duk iyakacin
surarta a bayyane take, ga wani kamshi da ke
tashi daga jikinta, yayi saurin kashe fitilar dakin
wai don idonsa ya daina gano masa surar
Zainabu domin yayi fushi da ita yana son ta
gane yayi fushin,can karshen gado ya kwanta
nesa da ita, sai dai kamshin Zainabu ya addabe
shi da kewar lallausar fatarta, ya runtse idonsa
wai bacci ya dauke shi dole, amman da kyar ya
samu bacci ya iya daukarsa, domin dai cikin
kwanakin nan ya shagwabe da kwana jikin
Zainabu, ko tana kwance lamo bisa kirjinsa
kamshinta yana dukan hancinsa. Da wurwuri ya
tashi domin dai baccinsa rabi da rabi ne,
sashinsa kawai ya nufa don shiryawa a can. Sai
da ya kammala shiryawa ya fito ya zauna a
tebur din cin abinci shiru yana tunani, domin ya
saba da cin abincin Zainabu a 'yan kwanakin
nan tana bisa cinyarsa tana masa shagwaba
tana sanya masa a baki, a haka sai ya ci mai
yawa ya koshi. Ya dafe kai kamar ba zai ci ba,
can ya daure ya hada shayin kadan ya sha da
soyayyar wainar kwai da soyayyan dankali. Ya
dauki brief case jakar zuwa aiki ya nufi sashin
Zainabu domin ya san halinta tun da ta dage sai
ta fita lallai zata iya din. Ya duba falonta bata
nan don haka ya wuce dakin baccinta kai tsaye,
can gaban madubi ya hangota, daga ita sai dan
micicin tawul iyakacin cinyarta da alama daga
wanka ta fito, cinyoyinta sun fito sambal masu
sulbi gwanin sha'awa, tana shafa mai, ta cikin
madubi ta hango shi amman sai tayi kamar bata
ganshi ba. Yanda ya ganta sai yaji wani abu ya
tsirga masa, ya daure ya kauda kansa gefe ya
kirawo sunanta, bata dube shi ba balle ta amsa
masa ba, ya kulu matuka don haka da zafin rai
ya ce, "Ke! Zainabu kina jina ina kiranki kin mini
banza ko, to daman kashedi na zo nayi miki,
wallahi ko da wasa kada ki fita gurin aikin nan,
idan kina son zaman lafiya.....Idan bana so
kuma fa?" Ta tambaya sanda ta mike tsaye tana
kada kugu, wato komai ta fanjama fanjam
kenan.Ya kawo iyakacin wuya, ya nunata da
yatsa ya ce, "Kada ki yi mini rashin kunya don
naga baki da mutunci, ni kike yiwa wannan
tsiwar? To ki nutsu ki sani mijinki nake ba
dadiro ba, in dai kuma ina da daraja irin ta miji
wacce Allah ya bani to ban yarda ki fita ba, idan
kuma kece ke iko da kanki to Bismilla....." Yanda
yayi maganar ta sa ya sanya taji ba zata iya
masa musu ba, don haka har ya fita bata kuma
cewa komai ba, tana jin alamun tashin motarsa
ta leka ta windo da sauri, da gudu ya figi motar
tamkar mai shirin tashi sama, shi kansa
maigadin tsaye yayi yana kallonsa cike da
mamaki, domin ya san ba hakan ubangidan
nasa yake ba. Ta koma ta zauna jabar gefen
gado ranta yana suya da zafi, anya kuwa zata
yadda wannan mutumin ya raina mata hankali?
Ta ayyana a ranta, wato daman akwai abinda
yake tunani a ransa shi ya sanya yayi mata
lambo bai taba maganar zai hana ta aiki ba,
lallai bai san ta bane labarinta yake ji, amman
dai lallai ya ci darajar aure, don wallahi ba don
hakan ba babu abinda zai hanata fita yau.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tayi kwafa gami da nufar jakarta ta kayan
cakunta, domin yanda take jin zuciyarta idan
bata busa hayaki ta tsotsi ruwan shandy ba sam
ba zata ji dadi ba. Tabar shaidan din ta fara
kunnawa ta dinga bulbula hayaki kamar mai
shirin hada hadari, sai da taji ta caku sannan ta
hakura, ta dauko kwalbar shandy ta tsotsa
iyakacin son ranta tayi dif abinta sannan ta baje
a gado, idanuwanta suka yi mata nauyi don
haka dole ta lumshe su, sam ba bacci take yi ba
sai dai sake-sake na karya da zuciyarta ke mata
wai gata can cikin hazo tana yawo cikin fararan
kaya da kambu a kanta, Mustafa na rungume
da ita bisa faffadan kirjinsa, ta yi tsaki gami da
mai da kanta gefe don bata son tayi tunaninsa,
amman ina banda shi babu abinda ranta ke iya
gane mata.Sai da tayi kusan awa daya da wani
abu sannan ta ji dan dama dama, ga wata
azababbiyar yunwa, domin duk mai yin shaye-
shaye yana da saurin jin yunwa, shi ya sanya
wadanda basu da kudi irin 'yan iskan titi suke
saurin haukacewa saboda yunwa ga buguwa
sunyi. Wani dan wando three quarter iyakar
gwiwa ta sanya, da riga iyakacin cibiya mara
hannu, bata daura komai a kanta ba, haka nan
bata yi wata kwalliya ba, amman da yake tana
da kyau sai ta fito fes da ita. Kai tsaye ta nufi
tebur din cin abincin su, tayi zaune shiru kamar
ba zata ci ba, domin dai kewar Mustafa ta fara
taba ta, musamman kirjinsa faffada da yake
mata filo ko bargo da shi, ta lumshe manyan
idanuwanta wadanda ke yi mata luu kamar ba
zasu budu ba, sannan ta bude da kyar idonta
ya kai kan wani hotonsa da ya dauka yana
murmushi, tamkar ka kirashi ya amsa, ta
zubawa hoton ido kewar mijinta ta dameta,
haka nan ta danne ta yafini abinci ta ci kadan
sannan ta koma doguwar kujera ta kunna TV
wai ko ta rage kewa.
Shi kam daga nasa bangaren kasa hasala komai
yayi a Ofis din sa sai faduwar gaba yake yi
domin yana fargabar kada Zainabu ta fita,
domin dai ya san halinta da kafiya gami da
taurin zuciya. Ya kasa samun nutsuwa, don haka
dole ya mike da zummar zaije ya ci abinci ya
dawo, sanda yayi hon maigadin ya leko cike da
mamaki domin yasan da kam idan maigidan ya
tafi aiki sai karfe shida yake dawowa amman sai
ya wangale kofar da azama, ya shiga yayi fakin
can rumfar da aka tanada don ita.ya nufi gidan
kai tsaye da saurinsa, bisa doguwar kujera ya
hangota da remote a hannunta bacci ya dauke
ta. Yayi ajiyar zuciya cike da jin dadi bata ki jin
maganarsa ba, wani son ta ya kuma shiga
ransa. Ya lumshe ido cike da jin dadi sannan ya
nufi firji ya dauki lemo mai sanyi ya fincine kan
ya kafa baki yana sha, sai yaji gaba daya ya
huce daga fushin da yayi da ita, ya kuma
amince da lallai zai shawo kanta ta hakura da
aikin cikin ruwan sanyi. Ya kuma dubanta,
shigarta tayi masa kyau matuka, ya karasa
gabanta ya durkusa ya kai hannunsa kamar zai
taba ta amman sai ya fasa domin bai son ta san
ya dawo, don haka ya mike ya fice ya nufi Ofis
din nasa can Deport na hotoro. Karfe shida
saura ya dawo gidan, bai ji motsinta ba bai
kuma nemeta ba, domin yana sauri ya tafi
masallaci daga can ya biya ya gaida da iyayensa
don kada yaki zuwa yayi laifi gurin Hajiya, domin
ka'ida ne kullum sai yaje ya gaishe ta, sam
kuma ya manta bai sanar da ita yau zai koma
aiki ba. Ya dan jima a gidan nasu suna hira da
Hajiyar tasa har ya ci abincin dare a can, sai
wajen karfe goma ya iso gidan. Zainabu kam ta
cika fam domin a tunaninta wani sabon salon
wulakanci ne ya tsiro da shi, tana zaune a falo
sanye take da wata doguwar riga ta shadda
wacce ta kamata tsam daga kirjin ta, ta dora
dauri tamkar gwargwaro, ga wani dankunne
masu kyau da ta sanya sai kamshi take yi, kallo
take yi amman hankalinta ba a can yake ba. Ya
shigo da sallama da saurinsa don ya san yayi
laifi, ta dago dara-daran idanuwanta tana
kallonsa, sai kuma ta dauke idonta ta maidasu
bisa TV, duk da akwai gajiya a tattare da shi sai
da ya zauna kusa da ita.ya dubeta yana dan
murmushi ya ce, "Madam tuba nake na yo
dare, tun wajen shida na shigo banji motsinki
ba, gashi ana ta kiraye-kirayen sallah don haka
na wuce masallaci, da na fito kuma naje na
gaida Hajiya don bata san na koma aiki yau ba,
na san kin sha kadaici ko?" Ta yamutsa fuska
gami da wani kada ido, abinda ya kuma kara
mata kyau, ya mike, "Bari naje nayo wanka, ko
zaki taya ni?" Ya dubeta yana dariya. Ta kauda
kanta gefe cike da takaici, lallai ma ya raina
mata wayo. Ya iso gabanta ya tsugunna ya
kwantar da kai. "Haba zuma ta ki tayani wanka
mana, kin shagwabani ba zan iya cuda bayana
ba yanzu kinji ko?" Ta dubeshi kamar ta kwada
masa mari yanda yake wani narke mata ta ce,
"Don Allah Mustafa ka rabu da ni kada ka sanya
zuciyata ta buga." Ta janye hannunta daga rikon
da yayi mata. Ya kuma sanya dariya kana ya ce,
"Shi kenan, bari na je na yo wankan don jikina
har wani danko yake yi, sai na fito na lallashi
zuciyar don idan ta buga nima tawa bugawa za
ta yi." Ya nufi sashinsa yana murmushi, ta bishi
da harara domin haushinsa take ji. Can ta mike
ta shige dakinta ta fada wanka ta fito ta shirya
kan ta kamar yanda ta saba, kamshi kamar a
jikinta aka yi shi, ta sanya wata yaloluwar rigar
bacci mai hade da diras, iyakacin mazaunanta
ta tsaya, don haka kana ganin komai na jikinta,
ta haye gadonta ta lumshe idanuwa har lokacin
zuciyarta cike take da takaicin Mustafa.Ya shiga
dakin yana duban ta, gaba daya sai ya ji
dauriyarsa da fushinsa sun kare, daman shi
fadan ya ishe shi don jiya bai yi baccin kirki ba,
ba zai so yauma a kwata ba. Ya hau gadon yana
mata magana "Sleeping beauty ba dai har kinyi
bacci ba, kai zumata kada ki zamo raguwa
mana, yanzu fa ko sha daya bata yi ba." Tana
jinsa amman tayi masa bakam taki tankawa,
domin ta lura rainin hankali zai mata irin na
'yan maza, sai sun gama kunsa maka bakin ciki
da rana idan dare yayi kuma suce suna neman
wani abu, kamar ba shine ya rufe ido dazu yayi
mata rashin mutunci ba. Ya jawota jikinsa yana
mata wani salo da yake tsokano ta da shi yana
fadin, "Haba Zainabu kada muyi haka da ke, na
zo kaina bisa wuya tuba nake." Ta hankade shi
gefe tana fadin, "Don Allah ka rabu dani, wai
me ka maida ni ne? Ko ka manta abinda ka yi
min dazu ne, ka kyaleni kawai kowa yayi
harkarsa." Ya kuma matsawa jikinta yana mata
salonsa da yake sace zuciyarta tun a can baya,
cikin kunnenta yake magana, "Haba Zainabu, ki
yi hakuri tawan mu bar fadan haka ya isa,
dauriya ta wallahi ta kare da kyar na iya bacci
daran jiya, ni dai na yadda makaman, ki bari
daga baya mayi maganar aikin." Yanda yake
maganar kamar rada da kuma salon da yake
mata ya sanya ta gaza hankade shi, don haka
cikin shagwaba take magana, "Ni dai gaskiya ka
rabu dani, bayan kasan kai ne mai laifi sai kace
ba ni ba dazu kamar zaka doke ni.....Haba dai
duka, ni na isa na doki mai raina? Don Allah kiyi
hakuri kaina bisa wuya, haba honey sweet din
Musty." Yanda yake maganar gaba daya ya
gama kashe mata jiki, don haka dole ta share ta
fara gwada masa lallai itama tayi kewar sa, nan
suka lalace.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
**************
Da wayo da dabara Mustafa ya hana Zainabu
aiki, sai dai bai rageta da komai ba, don tafi
wata mai yin aikin ma, sannan ya bude mata
katuwar super market da sunanta, haka nan ya
bata jari mai dama ta fara kasuwanci. Don haka
ta kwantar da hankalinta tayi zaman ta a gida
domin ta lura sam bai kaunar ta fita ko ina, sai
dai kawayenta dake sintiri a gidan, don Asma
kusan kullum tana gidan har tana sha'awar
inama ace ita ce ta sami irin wannan rayuwar ta
Zainabu. Ranar wata Juma'a da asuba suna
kwance makale da juna wayar Mustafa ta fara
kira, da azama ya dauka domin ya san kiran
Momin sa ne, ai kuwa ita ce din, hankalinsa a
tashe ya ce, "Yaya dai Momi lafiya ko?" "Ka
hanzarta zuwa Alhaji ba shi da lafiya, ciwonsa
ya tashi don jiya ba mu yi bacci ba....Innalillahi
wa inna ilaihi raji'un." Kawai ya ce sannan ya
ajiye wayar ya hau saka kayansa. Zainabu da ta
tashi firgigit don jin salatinsa ta yi kansa tana
tambayarsa abinda ya faru. Cikin tashin hankali
ya ce mata, "Zainabu ciwon Alhajin mu ne ya
tashi don dama yana da ciwon hanta." Ita ma ta
shiga firgici sosai, har harabar da ake ajiye
motoci ta raka shi, sai da taga ya fita daga gate
din gidan sannan ta dawo cikin gida cike da
fargaba. Shi kuwa yana isa suka sanya Baban
nasa a mota sai asibitin Malam Aminu Kano, kai
tsaye A & E dakin gaggawa aka shigar da
shi,sanda suka yi hoton cikin abin ya tsorata
likitocin, domin hantar ta shi ta kuma kamuwa
fiye da da can, nan fa suka fara kokarin samo
kan ciwon, sai da suka ga ya samu bacci sannan
suka kyale shi. Hajiya Kubra da Mustafa dai
suna waje hankalinsu ya kai kololuwar ta shi, sai
da aka tabbatar musu ya samu bacci sannan
suka sami kwanciyar hankali, daga nan aka sake
masa daki zuwa Aminity, aka bashi kwanciya.
Wajejen karfe tara asibitin ya cika da 'ya'ya da
'yan uwa, duk da an hana kowa shiga gurinsa,
Mustafa ya samu ya koma gida domin yayo
wanka. Ya samu Zainabu har lokacin bata cire
kayan baccin ta ba, yana shiga ta tashi da sauri
ta tare shi ta rike shi gam a jikinta tana
tambayarsa jikin Alhajin nasu. Har ransa ya ji
dadin kulawarta ga mahaifinsa, cikin kwantar da
hankali ya sanar da ita ya sami sauki, ya ce
wanka ma ya dawo ya yi. Bata sake shi ba ta
ce, "Bari naje na taimaka maka sai mu wuce
asibitin tare." Wajen karfe goma sha daya suka
nufi asibitin, Zainabu tayi dan girkinta na
dubiya, sai dai kirjinta yana ta bugawa, domin
yau ne zasu yi ido biyu da Hajiya Kubra tun
bayan da ta auri danta. Sun isa asibitin cike
yake har lokacin da jama'a, duk yawanci suna
waje gindin bishiya sun shimfida kafet, ya isa
tana biye da shi a baya. Tun da Hajiya Kubra ta
hango Zainabu ranta yayi mummunan baci, ta
bata rai matuka don haka ko da ta karaso gurin
ta gaisheta bata ko kalleta ba balle ta amsa, su
Hajiya Saratu kuwa har sun fita hade rai, don
har tsaki ta saki ta kauda kai gefe. Ran Zainabu
yayi matukar baci, don ta manta rabon da ayi
mata wulakanci irin wannan, shi da kansa
Mustafa kunya ta kama shi kamar kasa ta tsage
ya shiga ciki yake ji, amman yaya ya iya tunda
dai iyayansa ne. Kanwarsa Sumayya ce ta ce,
"Anti ga guri ki zauna mana." Domin dai ko
gurin zama ba'a bata ba. Su Hajiya Saratu sai
aka sake babin hira tana ta aibata mata wai
masu bin maza don talauci, kowa a gurin ya
fuskanci inda zancen nata ya sanya gaba, don
haka babu wanda ya kulata illa Hajiya Kubra da
taji ranta yayi wasai domin dai ta san da
Zainabu take. Ita kam Zainabu ji take yi kamar
ta tashi tayi musu rashin mutunci, sai dai
darajar Mustafa zata iya hakuri da duk wani cin
kashi da za'a yi mata, don haka ta dukar da
kanta kawai tana wasa da yatsunta, shi kuwa
Mustafa gurin likitan ya wuce domin yaji yaya
jikin Baban nasa yake, amman dai daurewa
kawai yayi ya tafi ya bar Zainabu a nan gurin.
Sai da suka yi awa uku babu wanda yace da
kowa kala sai dai 'yan matan Hajiya dake jan
Zainabu da hira domin su janye hankalinta daga
kan su Hajiya Saratu. Ta yi kokarin biye musu
amman hankalinta gaba daya yana kan su
Hajiyan, domin dai duk abinda Hajiya Saratu ke
fadi ta san da ita take. Dawowarsa ya sanya taji
dan dama-dama, domin cewa yayi ta tashi ya
maidata gida ya dawo, kamar wacce ke kan
kaya don haka ta mike da saurinta ta ce, "To
Hajiya mun tafi Allah ya kara sauki." Ba su tanka
mata ba har lokacin, har sun dan fara tafiya
Hajiya Kubra ta kirawo Mustafa ya dawo ya
durkusa a gabanta.Da daga murya ta kama yi
masa fada, "Bance maka kada ka sake ka kawo
matar ka duk inda nake ba? Ko ka manta da
kashedi na ne, eye? To tsaya kaji na gaya maka
har yanzu wannan dokar tana nan, don haka
bana bukatar na kara ganinta a asibitin nan,
idan kuma ka kuma zuwa da ita to kai ka jawa
kanka ko me nayi mata." Ya mike jikinsa babu
kwari ransa idan yayi dubu duk ya baci, domin
dai yasan sarai Zainabu taji duk abinda Hajiyar
ke fada, da kyar yake iya daga kafarsa, takunsa
na uku ya kuma jiyo maganarta. "Kai, wannan
warmers din wa kuka kawo wa? To ka dauki
abincin ka domin wallahi ba zamu ci ba, sai dai
mu zubawa karnuka." Ya juyo ya durkusa ya
dauki warmers din ya nufi mota, ta ja tsaki tana
fadin, "Gayyar tsiya arna da idi, haka kawai ina
fama da ciwon mijina yazo ya kuma bata mini
rai." Har suka isa gida babu wanda ya ce da dan
uwansa kala, shi ya rasa me zai ce mata, dama
ba a gabanta ta fadi maganganun ba to da
sauki, domin sai yasan dabarar da zai yi ya
hanata zuwa asibitin amman yanzu aikin gama
ya riga ya gama, domin anyi a gabanta taji, don
haka bashi da sauran hanyar kariya ko wani
boye-boye, shi kunyarta ma yake ji wallahi.
Sanda suka isa gida tun bai gama fakin ba ta
balle murfin motar ta fice, ya bita da kallo
kamar ya kirawota amman sai ya fasa ya kifa
kansa kawai bisa sitiyarin yayi shiru yana sake-
sake, kusan minti ashirin yayi a haka sannan ya
nufi cikin gida.Shiru falon babu kowa don haka
kai tsaye ya wuce cikin daki, sai ya taddata ta
kunna taba tana sha, duk tayi facali da kayan
jikinta daga ita sai dan siket iyakar cinya da
rigar mama, sai busa hayaki take yi tamkar
wacce ke shirin tada karamin hadari ko ta sami
tabin hankali. Gabansa ya yanke ya fadi domin
dai yayi zaton ta daina shan taba, amman sai
gashi yau ya gani da idonsa. Hankalinsa ya tashi
matuka, don haka yana isa ya kwace tabar dake
hannunta ya sanya bisa (ash tray) ya kashe. Ta
dago idonta da ya sauya kala ta dalla masa
harara kana ta zaro tabar ibilis (wiwi) a jakarta
ta kunnan ta fara zuka. Ya kuma hasala ainun
domin dai bai san ta inda ta samo wadannan
abubuwa ba. "Ke Zainabu kinyi hauka ne?" Ya
fada a hasale. Ta daga ido ta kuma wurga masa
harara, ya kai hannu zai kwace tabar shaidan
din amman bata yadda ba sai ma daga masa
hannu da tayi tana fadin, "Enough, ya ishe ka
haka." "Akan me zan yadda ki sha abinda zai
cutar da ke, ke ko kunya ba zaki ji ba ki zo
tsakiyar dakinki na aure kina shaye-shaye, eye?"
Ta mike a kufule tana nuna shi da yatsa tana
fadin, "Malam ya ishe ka ka rabu dani, dame
kake so naji ne, eye? Iyayenka sun bata mini rai
kace ba zan sha abinda zai sanyaya mini zuciya
ba?" "Wallahi ka sani, wannan matar Hajiya
Saratu naji suna fada ko wa, taci darajar aure
da wallahi yau san nayi mata rashin mutunci,
shegiya matsiyaciya, ko ta zaci ban san ta bane,
ai duk wasu manyan gwamnati samarinta ne
duk da tana takama da aure, kuma duk wanda
zai bata kwangila sai ta bashi kanta, ko diyar ta
ba tana can kasar waje tana karatu da
karuwanci ba.....ya ishe ki Zainabu, kina son ki
bata mini rai da yawa ne eye?" Ya katseta cikin
hargowa. Ta rike kugu tana girgiza gami da
fadin, "Lallai ka dade ranka bai baci ba, domin
ni ai daga bola aka tsintoni shi ya sanya da ta
zageni baka rama mini ba, banza karuwar gida
wacce ke bin maza da aurenta da 'ya'yan
ta.....Ya dauketa da wani wawan mari wanda ya
sanya ta zube bisa gado, ta mike da azama tana
kokarin kamo rigarsa, ya kuma hanbareta ta fadi
bisa tsakiyar gado, ya kuma hasala sosai. Cikin
bacin rai yake fadin, "Duk lalacewar dangina ina
sonsu, don haka idan kinga zaki iya hakura da
abinda suka yi miki to idan ba zaki iya ba kiyi
abinda kika ga dama amman ba zan lamunci cin
mutunci ba wallahi." Ta dago da jan ido tana
dubansa ta ce, "Wallahi Mustafa zaka san ka
mareni, kuma ko zaka kashe ni ba zan daina
cewa Hajiya Saratu karuwar gida da aure ba,
sannan kai ma da suke zagina a kanka ai dan
iskan ne, kuma taba da wiwi yanzu na fara sha
domin dai kai ne ka koya mini, idan ka kuma
tabani kuma wallahi ka doki aurenka domin
baka auri jaka 'yar iska ba." (Fauza tace tsiyar
auren bariki kenan babu daraja balle mutunta
juna). Maganarta ta karshe ce ta sanya ya tsaya
sororo ya kasa aiwatar da komai a kanta, sai dai
jikinsa sai kyarma yake yi, kawai sai ya juya ya
bar dakin ya shige dakinsa ya fada bisa gado
ransa na suya, gaba daya yau sun bata masa
rai, wai shin da me zaiji ne da rashin lafiyar
mahaifinsa ko kuma da fitinarsu? Da kyar ya iya
yin wanka ya ci abincin dake cikin warmer din
ya fita daga gidan. Ita kuwa kullo kanta tai cikin
daki ta fara cakewarta abinta.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Har dare da ya dawo bai ganta ba, bai neme ta
ba domin ransa a bace yake har lokacin, sai da
safe ne ma da ya tashi yaji yana kewarta don
haka ya leka dakinta ya taddata ta ci kwalliya da
wani wando fela da half vest tayi kyau matuka,
kamar ya shareta sai ya takalo zance. "Ina
breakfast, karin kumallo na?" Ta daga idonta
wanda ke gigitashi idan tayi masa dubanta na
yauki, idanuwan Zainabu na daya daga cikin
abinda ke kashe masa lakar jikinsa, gasu da
girma da kyau tsakiyarsu kamar an diga zaiba,
musamman idan bata kora shandy ko ta sha
tabar shaidan ba sunyi kyau matuka. Ta karkace
kai gami da murguda dan karamin bakinta ta ce,
"Ban yi ba ko da magana?" Abin ya bashi dariya
domin ya lura masifa kawai take ji, shi kansa ya
san ba karamin karfin hali tayi jiya ba dan sam
bata tankawa Hajiya Saratu ba, shi abinda tafi
bashi haushi tabar da ya tadda tana sha, domin
da niyyar rarrashinta ya shigo daki, ta kuma
kara da zagin kanwar mahaifiyarsa. Sai yayi
dariya kawai ya ce, "Shi kenan naje na ci a hotel
tun da ban da matsayin da za'a dafa mini a
gidana." Bata tanka masa ba illa cigaba da tayi
da sauya tashoshin tauraron dan Adam, ya juya
ya ce, "Sai na dawo." Sai da yayi nisa ya jiyo
muryarta tana cewa, "A yiwa Baba sannu da
jiki." Ya ji dadi har ransa domin yasan lallai ta
damu da ciwon tsohon nasa, don haka ya ce,
"Zai ji Insha Allahi in dai ya farka zan sanar da
shi." Sanda ya isa asibitin yayi sa'a jikin na sa
yayi kyau don har yana gane mutane, ya isa ya
zauna a gefen gadon yana gaishe shi.Alhaji
Abdullahi yayi murmushi yana amsa gaisuwar
dan nasa har yana tambayarsa Zainabu. Ya yi
murmushi jin Alhajin na ambaton Zainabu, ya
ce, "Ta ce ma a gaisheka jiya ai da ita muka zo
lokacin kana bacci." Cikin ikon Allah da
hukuncinsa randa ya cika sati guda a asibitin aka
sallame shi, jiki yayi kyau sai dai an kafa masa
tsauraran matakai na daina cin duk wani protein
abinci mai gina jiki, kamar nama da kaza ka
kwai soyayye da madara da hanta har sai ciwon
ya lafa sosai. Gaba daya iyalansa sun sami
kwanciyar hankali don ganin jikin Mahaifinsu
yayi sauki, sai dai Mustafa wanda har lokacin
Zainabu fushi take yi da shi, yayi yayi ya shawo
kanta amman ya gaza. Yauma da kyar ya
rarrafa ya kai karfe hudu a Ofis, kome yake yi
Zainabu yake gani, sai yake ganin kamar ya
shekara bai tare da ita ma, don haka ya hada
komatsansa ya nufi gida. Tana zaune a falo
sanye da wata doguwar shimi iyakacin gwiwa
mai hannu irin siririn nan, ta kama ta tsam a
kirjinta kamar rigar mama, kugun nan ya matsu
tsam sai kuma ta bada fadi daga kasa, kan nan
ya sha gyara ta yi parking dinsa da ribon duk da
ba wani yawa ne da shi ba, sai wani kamshi ke
tashi a falon na ta. Ya ajiye brief case dinsa ya
fada kujera yana fadin, "Washi, na gaji wallahi."
Ko kallonsa bata yi ba balle ya sanya ran zata yi
masa magana, sai wani taunar cingam take kas-
kas, wanda ke kuma tsokano shi. Ya dubeta
sanda yaji wani abu ya tsaya masa a wuya ya
ce, "Zainabu manyan mata, har yanzu ba'a
huce bane? Tuba nake." Bata ce komai ba sai
murguda baki kawai da ta yi, tana wani fari da
ido abin da ya kara mata kyau. Ya ce lallai
wannan yarinyar 'yar rainin wayo ce ke, kina
nufin haka za muyi ta zama bari nazo nayi
maganinki. Ya mike da azama tayi zaton
zolayarta yake sai da taji ya makureta tayi tayi
ta ture ta gaza, har mintsininsa tayi amman ko
gezau, don haka ta kama yi masa kukan
shagwaba wanda ya kuma tsokano shi, dole dai
ta saki jiki ta nuna masa Zainabu tayi missing
dinsa itama, wannan ne ya sanya suka shirya
dole, don ya san ta yanda yake samo lagonta
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
*****BAYAN SHEKARU BIYU*****
Aurensu yayi shekaru biyu har da wani abun
amman ko batan wata Zainabu bata yi ba, abin
har ya fara damunta, domin yanzu 'ya'yan
Karimatu kanwarta guda uku, ga 'ya'yan gwanin
sha'awa, sannan matar Sadiku ma ta haihu
yaron har yayi wayo. Shi kansa Mustafa ya fara
damuwa don haka ne ma suka fara yawon
ziyartar likitoci, sai dai iyakacin gwaje-gwajen da
aka yi musu ance shi kam bai da matsala sai dai
ita ce ke da matsala amman an bata
magunguna ta sha da zummar duk abinda ta
gani ta koma. Duk da Hajiya bata shiga zancan
sa da Zainabu yanzu ta fara yi masa gori, wai
ya auro wacce ta karar da kwayoyin haihuwarta
a titi gurin zubar da ciki, don haka ya shirya
aure don ta kusa aura masa diyar mutunci wasu
abubuwa ne kawai suka tsaida ta, don haka
hankalinsa ya kuma tashi suka bazama neman
haihuwa ido rufe. Ranar wata asabar ya tashi da
wani mugun ciwon ciki, ya dinga kwara amai
kamar ba zai yi ba, Zainabu tace a kai shi asibiti
ya ce, A'a a yiwa likitansa waya kawai. Ai kuwa
haka aka yi, yana zuwa ya sanya masa drip
karin ruwa, sannan ya sanya masa allurar amai.
Tana nan zaune tana gadin ruwan Sumayya ta
yo mata waya akan tana neman wayar Mustafa,
ko ya manta yau ne birthday din Zubaida diyar
Hajiya Saratu da ya ce zasu je tare. Zainabu ta
ce, "Ayya kin ganshi nan kwance babu lafiya ana
masa karin ruwa." Hankalin Sumayya ya tashi
tace gata nan zuwa. Suna gama wayar ta sanar
da Hajiyarsu, duk da gabanta ya fadi amman sai
ta tabe baki ta ce, "Allah ya sauwake" kawai. Ita
kam Sumayya mota ta shiga ta taho dubasa.
Sanda taje dubashi jikin nasa yayi dan dama-
dama, don haka daga nan gurin birthday din ta
wuce, a can take sanarwa da 'yan uwa abinda
ya sami Mustafa. Ai kuwa ana tashi daga fati
aka yo gayya zuwa duba Mustafa, ita ce motar
karshe da Hajiya Saratu da suka taho da diyarta
Zubaida, sanda suka iso sauran sun komawarsu
gida. Suka zauna suna masa sannu, yana
amsawa don lokacin ya farka. Zainabu ta shigo
don daman tana kicin ne, tana sanye da atamfa
super tayi mata wani dinki na daukar magana,
ko mahassadi ya ga Zainabu sai ta burge shi,
domin siket din ya zauna daram a kugun ta
kamar sai da aka gwadata aka yi, wuyanta da
kunnenta white gold ne kirar dubai ga warwaro
kirar Saudiyya da ta sanya da zobuna, tayi kyau
matuka sai kamshin nan nata take yi tamkar
fure.Ta shigo dakin da sallama, ta dube su ta
ce, "A'a sannunku da zuwa." Sumayya ce kawai
ta amsa, Hajiya Saratu da Zubaida yamutsa
fuska kawai suka yi. Ta zauna gefen Mustafa ta
tallabo shi tana bashi fresh milk don ya ce ta
bashi, bayan ta kashe ruwan sosai ta
rungumeshi a jikinta ba da niyyar komai ba.
Amman sai Hajiya Saratu ta kulu, domin ganin
yanda Zainabu ta koma tamkar diyar sarki ya
hasalata, babu wanda zai kalleta yace Abu ce
diyar Sala da Baba Abbakar, don haka taja tsaki
tana fadin, "Kai har yanzu Allah bai kawo 'yan
dugwi-dugwi a gidanka ba, sai dai a cika maka
masai da kashi." Zubaida tayi dariya ta ce, "To
ke Momi banda rigima irin taki, yaushe uterus
mahaifar da tayi condemn ta lalace zata iya
haihuwa?, naji fa ance matar tasa sai da ta
gama sheke ayarta sannan suka yi aure, kinga ai
babu zancen haihuwa sai dai a hole kawai." Ran
Zainabu idan yayi dubu ya baci, don haka ta
janye fresh milk daga bakin Mustafa don kada
ya kware bata gani ba, ta kwantar da shi ta
saita karin ruwan kamar yanda likita ya nuna
sannan ta gyara zama ta ce, "Kinsan shi gwano
ai baya jin warin jikinsa, gwara wanda ya nemi
'yan uwansa bakar fata da wanda yake iskanci
da turawa wadanda kowa ya sani duniya sune
ke da kanjamau, kinga ni ai haihuwa ce kawai
zan rasa, wata kuwa bayan rashin haihuwar har
kanjamau ce da ita, don jiki ya nuna kiga mace
tamkar sillan kara babu dan abin yanga, ai da
gani da magana. Ran Hajiya Saratu da Zubaida
ya baci matuka, ita kuwa Sumayya ji tayi
Zainabu tayi mata daidai domin dai ta tsani
Zubaida da halayenta daman, su kuwa sam
basu taba sanin Zainabu ta san sirrin su ba, don
haka Hajiya ta kuma hasala. Ta mike tsaye tana
nuna Zainabu da yatsa tana surfa mata ruwan
bala'i da gori tana fadin, "Ke wallahi
hawainiyarki ta kiyayi rama ta, shegiya 'yar
matsiyata 'yar tallan shinkafa da wake. Ke
banda kaddara me Mustafa zai yi dake, an
gama yawan gantali bin tasha-tasha tallan goro
da rogo, duk samarin kasuwa sun gama
kwakularki, wallahi idan kika yi wasa zan miki
abinda har ki mutu ba zaki manta ba, ko kina
zaton bamu san asalin balbela bane, su tsoho
ana can gindin bishiya ana maula da bara, su
Inna kuma ana gindin murhu suyar gyada da
wake da shinkafa ana dorawa kanne su ma ana
kwakulesu a shaguna, an dai yi asara." Ran
Zainabu idan yayi dubu ya baci, hankalinta ya
tashi, Mustafa dake kwance cewa yake,
"Zainabu don girman Allah kiyi hakuri ki rabu
dasu, zan sanar da Baba duk abinda suka yi
miki." Amman ina shi kansa ya san ko kusa ba
zata kyale ba, don haka ta mike tsaye tana huci
ta ce, "Kaga Malam babu ruwanka ai Uba baifi
Uba ba, kuma uwa bata fi uwa ba, balle kai
kanwar Uwarka ce." Ta maida dubanta ga Hajiya
Saratu tana fadin "Alhamdulillah, don duk
wanda zaice Zainabu tayi iskanci sai dai yace
tayi kafin aure, amman a yanzu ina zaune
zaman aure sunna zuciyata da gangar jikina sun
gyaru, ke kuwa da waye bai san abinda kike yi
ba da yawon siyasarki da ake kwana dake a
hotel da kuma yawon kwangilarki da sai anyi
fasikanci dake sannan za'a baki kwangila da
aurenki kuma, wa ma ya sani ko duk 'ya'yan
naki na kwangilar nema.....""Kan ubancan, dan
abu ta kazar ubanki ni zaki yiwa sharri? wallahi
yau sai kinci ubanki." Ta ci damara ta nufi
Zainabu gadan-gadan. Mustafa da yaga abin zai
baci ya fincike karin ruwan ya shiga tsakani
yana baiwa Hajiya Saratu hakuri wacce tunda
take ba'a taba mata irin wannan cin mutuncin
ba, bata san yanda aka yi Zainabu ta san
sirrinsu haka ba. Ita ma Zubaida da ta kama
zage-zage tana fadin wallahi yau sai sunci uban
Zainabu, Sumayya ce ke janyeta, ita ma Zainabu
bakinta bai mutu ba, sai da Mustafa ya turata a
daki ya kulle sannan su Hajiya Saratu suka fice
tana fadin wallahi ba zata yadda ba don tasan
shine ya sanar da matarsa sirrinta har take
mata gori. Ya bita yana rantsuwa har yana
fadin, "Hajiya yanda kika samo sirrinta ban sani
ba itama haka ta samo naki babu hannuna, don
wallahi ni ban taba jin wannan zancen ba ma sai
yau." Bata bi ta kansa ba suka shige mota
Sumayya na tuka su. Kai tsaye gidan Hajiya
Kubra suka shiga ta fasa ihu tana fadin Wallahi
kotu ce zata raba ta da Zainabu matar Mustafa,
tunda tace duk 'ya'yanta har wadanda suka
mutu shegu ne basu da uba, bayan kowa ya san
Ubansu. Hajiya Kubra ta tareta hankalinta a
tashe, domin dai sam bata fahimci abinda take
nufi ba. Nan ka kwashe karya da gaskiya ta
fadi, sannan ta ce wai kawai dan sunje dubashi
basu kulata ba ta kama gaya mata wadannan
maganganu, tana fadi tana kuka, domin abin
yayi mata ciwo matuka, daman 'yan magana na
cewa idan baki ya san abinda zai fada bai san
abinda za'a mai da masa ba. Sumayya da aka yi
komai a gabanta ta ce, "A'a Anti Saratu gaskiya
ba haka aka yi ba, Momi wallahi ita ce ta
fara....." "Au! Kema kina bayansu? Daman nasan
daman Kubra kece kike sanya 'ya'yanki su yi
mini rashin kunya." Hajiya Saratu ta katse ta,
itama ta ce "A'a Hajiya ba haka....." "Rufe mini
baki, kina nufin 'yar iskar yarinyar nan ba zata
yi abinda aka ce tayi ba?" Ta kalli Hajiya Saratu
tana cigaba da fadin, "Saratu ko me aka ce
matar Baba tayi wallahi zan yadda, tun da bake
ba ni kaina yarinyar nan ta zageni, yanzu ma
abinda ya sanya take rangwanta mini don taga
tana auren dana ne, sai dai wallahi ba zan
kyaleta ta ci miki mutunci ba, don ke 'yar uwata
ce uwa daya uba daya, ki zo muje gidan ki ga
abinda zan yi, zan rama miki abinda tayi miki."
Sumayya ta dafe kai cike da tashin hankali, don
bata san abinda zai faru ba. Shi kuwa Mustafa
da ya ga su Hajiya Saratu sun fice ya nufi dakin
da ya kulle Zainabu ya bude ya tadda ta tsaye
tana huci tamkar kumurci. Ya galla mata harara
yana fadin, "Kin kyauta Zainabu, yanzu ko don
ganin halin da nake ciki ba zai sanya ki yi hakuri
ba? Yanzu na tabbatar lallai baki so na.....In dai
a zagi iyayena na kyale shine so to ban sonka
kai tsaye kaji na gaya maka Mustafa. Wallahi
don na zauna da kai ba zan yadda a ciwa
iyayena mutunci ba don duk lalacewarsu sune
suka haife ni, na kuma gaya maka duk shegiyar
matar da ta kuma zagin iyayena a gidan nan ko
gemunta na jan kasa don girma sai na dake ta,
aure hauka ne? Nayi kama da wacce zan zauna
akan namiji ana gasa ni, ka sani zan iya rabuwa
da kai in dai akan Baba Abbakar ne da
Sala,domin su ne suka kawo ni duniyar da har
ka ganni ka aura. Don haka idan har kana son
zama da ni dole ka kare darajar Iyaye na, Ni
Zainabu ka aura don haka wanda ya ga dama
ya zageni yace mini karuwa zan iya hakura idan
na so, sai dai duk wanda ya zagi Sala da Baba
Abbakar sai inda karfina ya kare wallahi."
Maganganunta suka kashe masa jiki, ya sani tun
can baya Zainabu mai son iyayenta ce, kuma
bata yadda da duk abinda zai taba mutuncin
iyayen nata ba, don haka yaga bashi da abinda
zai kuma cewa illa ya fice daga dakin, don kansa
ya soma juyawa. Yana zama a falo ya jiyo
shigowar mutane, kafin ya ankara har sun
bayyana a falon. Hajiya Kubra da Hajiya Saratu
da Zubaida ne, hankalinsa ya kai kololuwar
tashi. Ko zama basu yi ba Hajiya Kubra ta fara
surfa fada, "To sallamamme wanda aka asirce,
to tsaya kaji idan Zainabu ta asirce ka ka kasa
katabus a kanta ni wallahi sam baka isa ba,
domin ban hada 'yan uwana da kowa ba."
Hargowar Hajiya ta jawo hankalin Zainabu ta fito
falon. Ko dar bata ji a jikinta ba don dai tasan
karshen abin dai bai wuce ace ya sake ta ba.
Muryar Hajiya Kubra ta cigaba da karade falon,
"Don haka in dai ni ce Hadiza Kubra na haifeka
to yanzu ka rabu da yarinyar nan!" Gumi ya fara
karyowa Mustafa, ya ma rasa mai zai ce yaji
dadi a zuciyarsa, ya kalli ina Zainabu ke tsaye
yaga ko a jikinta itama, ya kalli iyayan nasa da
suka tsare shi da ido, kawai sai ya dauko biro
da wata (jotter) dake kan TV ya rubutawa
Zainabu saki daya ya mika mata. Ta amsa
shekeke tana fadi, "Wallahi tafi nono fari. Su
Hajiya Saratu zasu kuma yin magana Hajiya
Kubra ta ce, "Kinga magana ta kare ku wuce mu
tafi." Babu musu suka wuce domin dai ta
nunawa Zainabu sun isa. Zainabu ta hada
kayanta a trolley ta zuba a motarta ta nufi gidan
Asma, don da kunya ta nufi gidansu ta ce
Mustafa ya sake ta. Shi kuwa daki ya shige ya
dafe kansa tamkar wanda wani na shi ya mutu,
ji yake kamar jin dadin rayuwarsa ya kare tunda
ya rabu da Zainabu, ya rasa wane irin so yake
yiwa Zainabu a rayuwarsa ma. Rabon da ya sha
wani abin maye har ya manta, baya ga taba
yanzu babu abinda yake sha tun da Mahaifinsa
ya taba kama shi dumu-dumu da kayan maye,
ya ga bacin rai wanda bai taba gani daga gurin
Mahaifin nasa ba tunda ya zo duniya, daga
karshe ya ce yayi masa alkawarin ba zai kuma
shan wani abu na sanya maye ba ya yi masa
alkawarin, amman banda haka babu abinda zai
hana shi yau ya kora shandy ko wisky, don haka
taba kawai ya dauko ya dinga sha kamar wanda
aka yiwa gorin ta. Su Sumayya da Zainab kam
suna gida hankalinsu a tashe yake, domin sun
san ba za'a yi mai dadi a gidan Yayan nasu ba,
ai kuwa da su Hajiya suka dawo suka ji abinda
ya faru sun girgiza, sai da suka kebe a daki ne
ma Zainab ta kalli Zubaida tana fadin, "Zubaida
kin san wani abu? Wallahi wannan sakin auran
da yaya Mustafa ya yiwa Anti Zainabu kunyi
aikin banza, don wallahi komai dadewa sai sun
koma, domin na dade ban ji irin soyayyar su ba
ko da a film ko a littafi balle a gaske." Zubaida
ta kuma hasala, gashi daman basa shiri da
Zainab, domin ita diyar kanin Alhaji Abdullahi ce
uwa daya uba daya, kuma halinsu sam bai zo
daya ba, don haka ta rike kugu tana fadin, "Oho
dai su suka sani koma meye, tunda dai an bata
red card ai ni burina ya cika wallahi, kune
daman ai 'yan kanzaginta." Sumayya ta ce,
"Gaskiya Zainab ta gaya miki, kije ki rubuta cikin
diary dinki zaki sha mamaki wata rana." Zubaida
tayi tsaki kawai ta bar dakin don daman ta san
halinsu daya da Zainab da Sumayya, babu
wanda ya isa ya shiga tsakaninsu.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Sanda ta isa gidan Asma tana falo a kwance bisa
doguwar kujera tana waya da wani saurayinta.
Ta shiga gami da wurgar da jakarta can gefe
guda ta kayan. Asma ta mike cike da mamaki a
fuskarta, tayi kokarin sallamar wanda suke hirar
sannan ta ce, "Zainabu me ya faru, kin ganki
kamar wacce aka koro." Ta ja tsaki gami da mika
mata takardar sakin da Mustafa ya bata. Asma
ta karba da sauri tana karantawa, ta dago kai a
razane ta ce, "Zainabu da gaske kike Mustafa ya
baki saki? Kai ban yarda ba, kina son kice mini
duk son da yake gwada miki ya kare?" Ta
lumshe ido kamar ba za ta ce komai ba, can dai
ta tasahi zaune sosai ta kwashe duk abinda ya
faru ta sanarwa da Asma. Asma ta banka wani
zagi tana fadin, "Lallai wadannan mutanen basu
da mutunci, wato gwano baya jin warin jikinsa,
yarinyar da kike fada Zubaida ba bu iskancin da
bata yi a garin nan, duk gayun garin nan sun
san da zamanta, don daran jiya ma sai da na
ganta a night club wai ana birthday dinta, lallai
na sani Mustafa zai kawo kanshi ki kwantar da
hankalinki 'yar uwa. Zainabu ta yamutsa fuska
gami da yin kwafa sannan ta ce, "Asma kin san
Allah tun da aka zagi iyayena naji auran Mustafa
ya fita daga raina, domin nasan da haka kawai
ya sake ni sai nayi ciwon zuciya saboda son sa
da nake yi amman yanzu ko dar ban ji ba,
kawai zan gyara gidan da na siya kwanaki na
koma can da zama don ba zan koma gidanmu
ba sai Sala tayi mini dariya da gori." Asma ta ce,
"Haba Zainabu ki bar fadin haka ma don nasan
dole Mustafa zai nemeki ki bashi one week sati
guda ki gani......."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Zaharaddeen Shomar
whatsapp 08168575100
Idan Zuciya Tagyaru2-04
Posted by ANaM Dorayi on 07:37 AM, 12-Feb-16
Under: IDAN ZUCIYA TA GYRU
______________ Na
________Fauziyya D Sulaiman_____
Book 2
page 4
"Kinga barni da zancen nan Asma, idan kina da
shandy bani na tsotsa ko na rage bacin raina.
Kwanaki biyu suka yi Mustafa bai cikin
hayyacinsa, don bai san yana son Zainabu ba ma
sai yansu, gashi Alhajinsu bai nan da zai shawo
masa kan Hajiyarsa don ta dauki zafi da yawa,
daman yaya lafiyar kura balle tayi hakua, don
daman Zainabu a wuyan ta take. Ranar da ta cika
kwanaki uku ya gaza hakuri sai gashi a kofar
gidansu da karfe takwas na dare, Ya yi sa'a yana
yin parking kaninta Ilu na fitowa daga gidan, don
haka ya kirawo shi. Yaron ya taho da gudu don
ya gane ko waye, tun bai kai ga magana ba Ila
ya fara magana "Laa yanzu Anti Karima ta dawo
daga gidanku ance Anti bata nan wai ta tafi
unguwa kwanaki biyu." Ya ji maganar wani iri don
haka ya ce da Ila "Bata zo nan ba kenan yau?Ya
ce "Eh ta dade bata zo gidan mu ba ma, kuma
naji Anti Karima tayi mata waya ma tace wayar ta
a rufe take." Yayi shiru yana tunanin inda
Zainabu ta tafi, amman sai ya tuno da gidan
Asma don haka ya raya lallai tana can don haka
kai tsaye ya nufi gidan Asma din. Kai tsaye ya
shiga da motarsa har cikin gidan yayi parkinga
saboda mai gadin nata ya san shi daman, ya nufi
falon kai tsaye ya bude ya shiga, a falo ya ganta
zaune ita kadai sanye da dogon siket da riga da
ta kama jikinta ya shiga da sallamarsa. Ta daga
kai tana kallonsa ta tsaya da shan fate din da
take yi da cokali, ko me ta tuna kuma sai ta
kauda kanta gefe ta cigaba da kallonta. Ya isa ya
zauna a gefenta ta kuma matsawa gefe, ya kuma
matsawa har suka dangana da karshen kujera,
yayi murmushi ya ce, "To mun kai karshe sai
yaya Zainabu." Sai kuwa ta mike ta bar masa
kujerar ta koma wata, ya kuma tashi ya bita, ta
hasala matuka don haka ta kuma mikewa da
zummar barin falon, ya riko hannunta gam, tayi-
tayi ta kwace amman ta kasa, ta juya fuskarta
tana harararsa, yayin da shi kuma yake mata
murmushi gami da mayataccen kallon nasa. Ta
kuma hasala don tana ganin rainin wayo ma yake
shirin yi mata, da zafin rai ta ce, "Malam ka sake
ni ko ka manta ni ba matar ka bace yanzu, ka
fita daga harkata." Ya saki dariya gami da jawota
ta fada jikinsa, sai ta kama kokarin kwacewa
amman ta kasa, cikin kunnenta yake magana
"Zainabu har yanzu ai ke matata ce, tun da dai
saki daya nayi miki, sannan baki kammala idda
ba, yanzu haka ma na maida ke dakinki, kinga
magana ta kare kenan.""Ba zai yiwu ba Mustafa
kama janye wannan magana, domin dai na gama
auranka har abada, haka kawai zan zauna ana
wulakanta mini iyaye? Da kuma kake cewa ka
maidani yaya zaka yi da Mahaifiyarka tunda ita
ce ta baka umurni ka sakeni?, kasan ta ji wannan
maganar ma ba za ta yadda ba." "Zainabu abin
da ya kawo ni kenan, don Allah ki fahimce ni,
wallahi kina da girma a zuciyata ba zan iya
rabuwa da ke ba, ki dubi kwanaki uku kacal
yanda na koma, balle ace rabuwa ce ta din-din-
din, na yanke shawarar zan mai dake dakinki ki
zauna a gidana na farm center, idan Baba ya
dawo zan sanar da shi kuma nasan shi zai shawo
kanta Insha Allah, please Zainabu kada kice a'a,
kin san ina sonki da yawa." Yanda yake maganar
cikin kunnenta da sanyi da taushi da kuma salon
da yake gwada mata ya sanya ta kasa kwacewa,
jikinta ya mutu amman har lokacin bata yadda da
batun sa ba, shi da kansa ya lura da hakan. Ya
kuma riketa gam yana cigaba da fadin, "Haba
zuma (honey), ki na gani zamu yadda mahassada
su yi galaba a kanmu? Wallahi tun can daman
Hajiya Saratu bata kaunata, ita kanta Momi ba
sonta take yi ba, banda hassada da kyashi babu
komai cikin ranta, don ba sosai suke shiri da
Momi ba, abin ne aka yi shi kan gaba don Momi
daman bata son aurenmu, idan kika yadda muka
rabu za su yi mana dariya don sunyi galaba a
kanmu kenan, kada ki ce a'a Zainabu." Kalaman
nasa sunyi tasiri a zuciyarta, don haka ta kwanta
lamo a jikinsa yana shafata tamkar diyar mage.
Ya kuma kai bakinsa daidai kunnenta yana fadin,
"Please Zainabu say something, ki yi hakuri
Zainabu ki ce wani abu. Muryarta da sanyi ta
fara magana, "Mustafa ka sani bana son
wulakanci ko kadan, da ace Mahaifiyarka ce ta yi
mini wannan cin mutuncin zan iya hakura, domin
nasan ita ta kamani da laifuka da na cancanta
haka a gunta, sannan ita mace ce kamila dole
zata kyamaci irinmu, amman wata can Hajiya
Saratu wacce ta fini iskanci daga ita har diyar
ta....." Ya toshe mata baki yana fadin, "Ya wuce
don Allah ki manta da ita, zan dauki mataki mai
kyau a kanta Insha Allah." Bata ce komai ba tayi
shiru domin dai ta huce din, don itama cikin
kwanakin nan uku tayi rashin zumarta Musty,
daurewa kawai take yi, musamman idan Asma ta
tafi tabar mata gidan sai taji yayi mata fadi, ta yi
kallo har ta gaji, ko abinci take ci sai Mustafa ya
fado mata. Da dai ya lura ta sakko din ya fara
nuna mata lallai yayi rashin ta din da gaske, bata
yi sanya ba don ya san Zainabu babu wasa, ta
shiga mai da masa martaninsa, a nan gidan ya
kwana domin Asma bata nan. Da safe ne da ya
gama shiri bayan ya karya ya ce ta shirya da
yamma idan ya taso daga Ofis zai zo su wuce
gidan na sa, zai sanya a gyara shi kafin yamma,
tana makale da shi har jikin mota tana masa
salon dake kokarin hana shi fita, sun dade a jikin
mota can ya ce, "Anya kuwa Zainabu ba zan fasa
zuwa Ofis din nan ba kuwa yau?" Ta kwantar da
kai tana dariya ta ce, "Haba dai, ina nan ina
jiranka har ka dawo, babu mai gutsirar maka ni,
zaka same ni guda." Suka yi dariya gaba dayansu,
ta bude masa motar ta tura shi tana fadin, "A
dawo lafiya mai rai na."Ya yi dariya ya ce,
"Zainabu kin gama da ni, sai na dawo." Sai da
motar ta bacewa ganinta sannan ta koma cikin
gidan, wani nishadi da soyayyar Mustafa ke bijiro
mata, sai take ganin tayi wauta da can da take
cewa zata rabu da shi, ta san ko ta baru da shi
son sa da soyayyarsa ba zasu bari tayi wata
mu'amala da wani namiji ba, domin shi ne namiji
kwallin kwal da ya santa ya iya tafiyar da ita da
soyayyarsa da lallashi. Haka nan ta wuni har rana
ta yi tana tunanin Mustafa da soyayyarsa har
Asma ta shigo daga yawonta. Zainabu ta galla
mata harara don ganinta a wani birkice ta ce,
"Kai Asma Allah ya shirya ki, ya dace wallahi ki
hakura da iskanci ki yi aure, duk lalacewar aure
yafi wannan iskanci da kike yi wallahi." Asma ta
yadda jaka bisa kujera tana fadin, "Wash Allah
na, wallahi duk jikina ciwo yake." "Ba dole ki yi
ciwon jiki ba kinje katon banza ya lugwigwita ki
kwana da yini....."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Asma ta fashe da dariya tana fadin, "Shegiya don
Allah ya tsamar dake zaki dinga mini gori, wa kike
zaton zai aure ni da gaskiya yanzu kamar yanda
kika samu? Kuma ni ba abunda kike nufi ne ya
gajiyar da ni ba illa damben da muka ci da
shegen dan iskan, ke yanzu har kin manta da
naki iskancin da kika yi ko?" Zainabu ta kuta ta
ce, "Wallahi kin san ko da nayi yawo babu shegen
namijin da ya isa na zauna yayi ta lugwigwita ni
kwana da yini, kin san sai na ga dama, kuma
lokacina a kayyade yake, idan kuma na washeka
ko dubu nawa zaka bani baka isa na kuma
mu'amala da kai ba, ya dace ki yiwa kanki fada ki
zama International karuwa ba local ba shine za
kiyi daraja, ki duba yanda kika wani birkice kamar
wacce tayi kwanaki tana jinya, mutum daya kacal
ya more ki a banza da wofi." Ta ja tsaki gami da
yarfe hannu ta ce, "Malama na fa gaya miki ba
wannan ne ya wahalar da ni ba, dokuwa muka yi
da shege dan rainin wayo, kai karuwanci masifa
ne, shege dan akuya da matarsa ce yayi mata
haka? Ashe na gaya miki ba ni kadai ce a gidan
ba da wata a wani daki, idan ya fita daga guna
sai ya shiga gurinta, a dare daya fa don jaraba
da masifa, daga karshe da ya fice nace bari na
leka naga me yake yi ne yace mini wai wisky yake
shawowa kawai, sai naga ya shiga wani daki ina
shiga na ganshi da wata shegiya, kishi da haushi
ya cika ni don ban sani ba ko tana da shegiyar
HIV, don irin kucakan nan ne wallahi baki ganta
ba sai kin zubda yawu, shine fa da na kulu na
kwala masa wata flower vase a gaban goshinsa.
Bai ji ciwo ba amman dan jaraba sai yayi kaina
da duka yana kuma dura mini zagi, nan fa ya
kama duka na kamar ya sami jaka, da naga zai
halaka ni na daga wani glass na maka masa a
kansa sai ga jini ya tsinke, ashe shegiyyar da taga
muna fada ta kirawo police 'yan sanda don kin
san lambarsu yanzu available take, sai ta gudu
abinta, suna zuwa suka taddamu a haka shine fa
suka kwashe mu a daran nan sai police station.
Daga can aka kaishi chemist dakin bada magani,
har dinki aka yi masa sannan aka dawo da shi
muka kwana a bayan kanta...""Shi yafi damuwa
domin dan iskan yana gudun kada iyalansa su ji
don haka ya dinga roko 'yan sandan su kashe
case din anan kada su kaimu kotu kamar yanda
suka ce, ni kuwa wallahi ko a jikina tunda na san
bariki na fito ba karatun allo ba balle ace nayi
abun kunya. Daga karshe dai sai da suka caje shi
dubu dari, jiki yana rawa ya bada, da suka dawo
kaina nace a'a nan fa daya ni ko kudina ma bai
biyani ba, da dai suka ga zan musu tijara don
sun san kar ta san kar ne suma din shegune
suka sake mu tare. Shine na koma gidansa muka
kama wata rigimar wai ba zai bani komai ba don
naji masa ciwo, yanzu shi bai san me zaice da
iyalansa ba. Da na lura munafuki ne mai tsoron
matansa na ce wallahi idan bai bani ba kuwa har
tsakar gidansa zanje nayi masa tijara, shine dan
iskan ya wurgo mini dubu ashirin, kamar kada na
karba amman ganin yamma ta yi ga yunwa ina ji
ya sanya na kyale shi shege dan akuya, kinga
gobe ai ba zai kara ba." Zainabu tayi tsaki tana
fadin, "To don Allah meye abin riba anan yanzu?
Kin san Allah ni yanzu ko rabuwa nayi da
Mustafa wallahi ba zan kuma wannan
mummunar harkar ba, don kina ganin Tinda da
Zara yanda kanjamau ta maidasu yanzu ko a
gidansu babu mai kulasu balle bariki da bata da
amana, kowa gudunsu yake yi har da wadanda
suka gwagwada musu don su suna da kudi suna
cin kaji da choculate ta kanjamau gasu nan
jikinsu kamar basu da ita, wallahi sai dai na
koma business Allah, ke ni yanzu ma dan kaina
nake son gani kada ka mutu baka da mai maka
addu'a." Asma tayi dariya ta ce, "Lallai kawata
kinji duniya, mu kan a taya mu da addu'a, yanzu
yaya za'a yi da mutumin namu Mustafa babu
waya ba zuwa, ko binsa Ofis za muyi? Zainab ta
galla mata harara tana fadin, "Haba dai ajinmu
ya wuce nan, ki dube ni da kyau bani da makusa
ko siffar da zanyi kwantai, ko Mustafa ya kini ina
da masoya balle shi yayi kadan ya rabu da ni don
yau anan muka kwana......." "Shegiyar, Zainabu
kina sha'aninki wallahi, yanzu har Mustafa ya
kawo kan shi?" Ta mike ta koma kusa da ita ta
dafa gwiwarta ta kwantar da murya tana fadin,
"Ki yiwa Allah ki bani sirrin nan naki Zainabu da
ya sanya duk namijin da ya kusance ki bai iya
hakura, wallahi har yau samarinki na bariki na
kwalaficinki, akwai wanda ya ce muddin na
lallaba kika cigaba da mu'amala da shi zai bani
miliyan guda, ya ce shi babu ruwansa da
aurenki, to nasan ko baki da aure yanzu baki san
mu'amala da kowa sai Musty balle da aurenki,
don haka na bashi hakuri, na dinga hillatarsa da
gwalangwaso ko zai kyasa ni, daga karshe dai na
samu shiga, sai dai tun daga sannan bai kuma
kirana ba, ya ce Zainabu daban ce." "Ki yiwa
Allah ki gaya mini sirrin nan Zainabu." Zainabu ta
yi dariya gami da mikewa tsaye tana fadin, "Ai
kinfi kowa sanin sirrin nawa, kawai gyara ne da
iya kwanciya, sannan da baiwa daga Allah, ki
dubi dan karamin bakina kin san akwai abu a
nan." Suka yi shewa gami da tafawa. Zainabu ta
ce, "Ba zaki bata mini lokaci Mustafa ya taddani a
haka ba tun kwalliyar safe ba, sai na fito daga
wanka." Ta nufi bandaki. Ita ma ta mike ta ce,
"Nima din ai wankan zan yi don duk jikina ciwo ya
ke, shegen wallahi ya jibgeni da yawa, koda yake
nima na yi masa tabo"Zainabu ta shiryo cikin
wani wando gajere ne sosai da wata 'yar
makalalliyar riga, kugunta ya fito das, shape dinta
kuwa tamkar zai tsinke da siranta, tayi parking
gashinta, fatarta tayi likwi-likwi gwanin sha'awa
tamkar jikin jariri, Zainabu tana da kyau da iya
kwalliya da ke kuma sanyata shiga zuciyar duk
wanda ke tare da ita. Tana nan a falo tana kallo
Asma na ciki tana shiri ya shigo falon, da saurinta
ta mike da gudu ta fada jikinsa tana masa abinda
ta saba, ya daga ta cak kamar wata 'yar tsana
sannan ya manneta a jikinsa. Cikin kwantar da
murya ya ce, "I miss you Zainabu." Ta kwantar
da kanta a jikinsa tana fadin, "Me too Zumana."
Suka yi dariya gami da fadawa kujera. Can ya ce,
"Maza ki hado kayanki mu wuce kada dare yayi
ina jin yunwa da yawa." Ta mike ta shige ciki don
hado kayanta, doguwar (after dress) ta sako akan
kayanta ta fito janye da troley dinta, Asma na
biye da ita a baya. Bakinta cike da fara'a ta ce,
"Da girman kujerarka yallabai, ni dai na san
tsakaninka da Zainabu bata baci ko kadan, duk
wanda ya shiga tsakaninku zai sha haushi da
kunya.'' Dadi ya cika shi ya dubeta yana wani
washe baki ya ce, "Lallai Asma kin gano lagonmu,
kawar taki ce ba a wasa ba, irinsu a wannan
zamanin kadan suka rage, idan na rabu da ita
zan dade ina lalube ban sami rabinta ba." Dadi
ya cika Zainabu da yabon da mijinta ke mata, ta
kwanta a kirjinsa tana tsunkulinsa kamar wani
dan yaro. Ya yi dariya yana fadin, "Asma kin gani
ko?" Ta ce, "Zainabu tafi gaban nan, ni dai a
taimaka a karasa gida don Allah Zainabu kada ki
sanya ya manta hanyar."Suka yi dariya gaba
dayansu sannan ya kama troley din suka fice
Asma na biye da su, sai da ya shiga mota ya ciro
kudi naira dubu hamsin ya mikawa Asma ya ce,
"Gashi nan ladan rike mini zumata da aka yi." Ta
amsa da sauri tana fadin, "Yallabai ina godiya, a
sha soyayya lafiya." Ta juya ta koma cikin gida. Ya
juya yana kallon Zainabu da ta kwanto da jikinta
rabi jikinsa tana masa wani duba, Yayi murmushi
kawai ya tada motar ya nufi gidansa na farm
center. Dan babba ne amman bai kai wancan
gidan nasu ba, don shi ko maigadi babu, shi ya
fita ya bude musu sannan ya shiga da motar ciki
ya faka suka fice, suna rike da juna kamar daya
zai gudu ya bar dayan. Washegari ta kirawo
kanwarta Karima ta ce tana gidan Mustafa na
farm center, don ya sanar da ita taje can bata
same ta ba, ta ce gata nan zuwa kuwa don tana
son ganinta magana ce mai muhimmanci. Ai kuwa
ta gane kwatancen da tayi mata ta iso har nan,
maigidan ta ne ya sauketa ta tura gate din ta
shiga, yace da yamma zai dawo ya dauketa.
'Ya'yan ta Jidda da Sulaiman suna makaranta sai
na bayanta Salim, ta shiga falon da Sallama ta
tadda yayar tata tana kallon dish. Bayan sun
gaisa ta mike ta ce, "Anti yunwa fa nake ji haka
na koma kamar rumbu, Dadinsu Jidda har
tsokanata yake yi, bari na samo abinci a kicin
dinki." Zainabu ta yi dariya tana fadin, "Ke dai
fadi gaskiya ko dai kin harbu, don cikin ku babu
wuya, tun da dai Salim yayi wata goma ai
magana ta kare kila an gamu."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta dan tsaya tana dariya ta ce, "Au Anti ke ma
haka zaki ce, ai wannan karon kam sai na huta
Insha Allah, ulcer ce kawai ke damu na." "To
Allah ya sawake, kije ki gani ina jin farfesu kawai
ya rage wanda ya siyo jiya, baki ne mu a gidan
babu komai sai yau zai shigo da su." Ta fito
dauke da farfesun a plate da biredi da lemon
gwangwani ta zauna gefenta, suna ci suna hira.
Sai da ta kammala sannan ta fara maganar da ta
kawo ta. "Anti maganar yaran nan ce, ya dace
irin rayuwar da muka yi ta wahala da talla a ce
kannanmu basu yi ba, tunda dai Allah ya hore
mana, ki duba yanda Lubabatu ta girma amman
wai fada suke yi da Sala dole sai tayi talla tunda
taki kula samari ta samu kudi, ita kuma Jamila ba
ki ga iskancin shigar da take yi ba sai zaginta ake
yi a layin, ga samari 'yan iska na rashin mutunci,
to yanzu da ita Sala ke shiri, idan kika ga yanda
take kyarar Lubabatu tamkar 'yar riko, ga yaran
nan da kyau, maimakon ta goya musu baya su yi
karatu a'a nema take ta watsa rayuwarsu, Yaya
Sadiku ne ya zo gidana yana sanar da ni nace zan
sameki mu san yanda zamu bullowa al'amarin."
Zainabu ta yi kwafa gami da fara magana cikin
zafin rai, "Sala sai dai addu'a, har yau taki tayi
nadama ta san Annabi ya faku, meye bamu yi
mata ba? Dan da tace rashi ne yanzu kuma
menene, tunda dai kayan abinci wani har tadda
wani yake yi, ga kudi ana bata, sannan har gida
ake zuwa siyan abinci da waina da safe, ai ya
dace ace ta saduda haka, wato so take suje su
kwaso mana ciki ko?" (Wanzami bai son jarfa,
ance daman duk mai iskanci baya son ace wani
na shi nayi) Don haka ran Zainabu ya baci sosai,
ta dinga fada babu ji babu gani, daga karshe ta
ce da Karimatu, "Ki kyale ni da ita, don nice
maganinta don tasan halina, su kuma zan gaya
musu irin abinda ake ji a karuwancin don wallahi
wahalarsa tafi dadinsa yawa, musamman yanzu
da kanjamau tayi yawa." Da wannan shawara
suka rufe zancan Sala suka fada wani, Karimatu
ke sanar da Zainabu mijinta ya biya musu kudin
Hajji don haka bana tare zasu tafi. Zainabu ta ce,
"Lallai ina murna, idan kin tashi tafiya in dai
Mustafa bai biya mana ba sai ki kawo Salim na
yaye shi, don kewa da rashin haihuwa sun fara
damuna ki tayani da addu'a Karima, nasan
abinda nayi can baya ne Allah ya nuna mini
iyakata tun a nan duniya." Fuskarta ta sauya
zuwa damuwa karara. Karimatu ta lallashe ta, sai
da yamma maigidanta ya zo daukarta ta hada
mata kayan kwalliya da jakunkuna guda biyu irin
wanda take saidawa.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
*** *** *** ***
Kwanasu goma sha uku a gidan su (Farm center)
Alhaji Abudllahi ya dawo, Mustafa ya fi kowa
farin ciki da dawowar tasa, ita kuwa Hajiya Kubra
ta yi zaton ko ya hakura da Zainabu domin ta
sanya ana masa rokon Allah a kanta, bata san
suna tare ba ma, don haka idan ya zo gidan take
nan-nan da shi. Sai da Alhaji ya kwana biyu
sannan ya same shi a falonsa da zancan na su,
cikin ladabi ya kwashe duk abinda ya faru da shi
da Zainabu da Hajiya Saratu har zuwa sakin da
Mominsa ta sanya ya yi mata, bai boye komai ba
Sai kai ta gidan sa na (farm center) kawai ya
boye bai sanarwa da Alhajin ba. Ran Alhaji yayi
mugun baci musamman da yaji abin akan Hajiya
Saratu ne, daman shi sam baya shiri da ita
musamman da ya san halinta da abinda take yi,
musamman harkar siyasa da take yi da auranta
tana kuma bin maza a titi, don ta mallake mijin
nata, don haka sam baya son ta haushinta yake
ji. Don haka ya kirawo layin wayar Hajiya Kubra
wacce daman tana shirin zuwan ne, ta shigo
dauke da faranti na abinci ta ajiye a gefe sannan
ta zauna tana fadin, "Yanzu nake shirin kawo
maka daman." Sam bata lura da Mustafa ba sai
da ya ce, "Barka da yamma Momi." Ta kalli inda
yake, sai jikinta ya bata da wani abun ganin
yanda Alhaji yayi kicin-kicin, ta amsa kawai
sannan ta mai da hankalinta ga maigidan wanda
yake kallonta, can yayi gyaran murya ya fara
magana.Khadija yaya kuka yi da yaron nan ne?
Yanzu sai da kika san yanda kika yi kika raba
auran nan, ina ce kinfi kowa sanin fitinar 'yar
uwarki eye? Idan da gaskiya ai sai ki tsaya ki
saurari bayanin kowa, wai ni me kuka dauki aure
ne? Daga wannan 'yar magana shi kenan sai saki
kin sani fa da shine halak din da Allah baya so,
wato saki dan haka kin farantawa shaidan rai,
kinyi abu ba da tunani ba." Duk da taji haushin
kawo kararta da Mustafa yayi, amman ta gano
itama bata kyauta ba, don haka ta kwantar da
murya don ganin mai gidan nata ya dauki zafi
abinda yakan dade bai yi ba ta ce, "A yi hakuri
nayi kuskure, amman raina ne ya baci a
lokacin....."don idan da daraja matar Mustafa ba
zata rama ko me Saratu tayi mata ba tunda dai
'yar uwa ta ce uwa daya uba daya." "Haba
Khadija iyaye ai sun fi gaban komai, duk iyakacin
hakurin ka aka zagi iyayenka da cin mutuncinsu
in dai kai dan halak ne ka tanka, balle har da
diyarta suka je suka yi mata cin mutunci, don
Allah ki dinga adalci akan yarinyar nan, kada
kiyayyar da kike mata ta sanya ki jawowa kanki
fushin Allah." "Shi kenan Alhaji ya wuce ba zan
kuma ba, sai dai ya kwabeta wallahi ta iya
bakinta." Da sauri Mustafa ya ce, "Ita ma kanta
ta gano bata kyauta ba yanzu tace a baki hakuri
ma." Ta galla masa harara cike da jin haushi, a
ranta tana fadin ashe yana tare da ita har yanzu,
kai wannan yarinya ta zama matar jaraba, shi
kuwa ganin irin kallon da take masa ya sanya shi
sunkuyar da kanshi jikinsa na rawa. Alhaji ne ya
ce, "Ka tashi ka tafi ya wuce sai dai a kiyayi
gaba." Bai tashi ba kansa yana kasa ya ce, "Ka
nemar mini izini gurin Momi na mai da Zainabu,
ko har yanzu tana kan bakanta....." "Neman izinin
me za'a yi nawa abinda kana tare da ita kaje
kayi ta yi, ai kowa rai ya yiwa dadi baya ga mai
shi ne." Hajiya Kubra ta katse shi. Alhaji Abdullahi
yayi dariya don ya lura har yanzu bata huce ba
ya ce, "To ai cewa yayi na nemar masa alfarma,
don haka na nemar masa alfarma, don haka na
durkusa a gabanki Khadija ina neman alfarmar
Mustafa ya mai da matarsa Zainabu dakinta na
sunnar Ma'aiki.Yanda yake maganar ya bata
dariya don kamar wani danta ya koma, don haka
fuskarta a sake ta ce, "Komai ya wuce ya maida
ta, sai dai kuma ina da magana nima da muka yi
can baya ta auran da zan ba shi, domin yarinyar
tana karatu ne yanzu kuma ta kammala digirinta
don haka nima ina so mu tsaida magana yanzu ta
biki." Gaban Mustafa ya fadi amman sai ya dake
don kada ya tsokanowa kansa, sai dai gumi kawai
yake hadawa duk da sanyin AC da fankar dake
kadawa a dakin. Alhaji Abdullahi ya ce, "Ina jinki
Khadija wacce yarinya kika zaba masa don idan
ba aurawa Mustafa wacce ranki ke so aka yi ba
rigimar ba zata kare ba." Ta yi murmushi gami da
gyara zama ta ce, "Ba wata bace illa diya ta
Zainab, don daman tuntuni nake masa tanadinta
don yarinyar mai tarbiyya ce wacce muka rene ta
da tarbiyya da tsantse ni." Hankalin Mustafa idan
yayi dubu ya tashi, a ransa ya dinga maimaita
Zainab! Zainab! Sai yaji inama ace mafarki yake yi
ba gaske ba, tunda yake bai taba kawo wa zai
auri Zainab ba yarinyar da ya dauke ta tamkar
kanwarsa yake ganinta, kai Momi ta baro masa
jidali lallai, don Allah ya sani ba zai iya son wata
mace kamar Zainabu ba, don haka sai yake ji
kamar ya ce ba zai aura ba. Ran Alhaji Abdullahi
yayi dadi domin dai yana son shima ace an hada
zumunci tsakaninsa da Dan uwansa wanda su
biyu ne kacal a duniya, gashi kuma daman
yarinyar yana matukar kaunarta kamar shi ya
haifeta, don tun da ya daukota gidansa bai taba
jin wani abu na aibu a tattare da ita ba, yarinya
ce mai matukar hakuri da kawaici ga biyayya,
don haka da fara'arsa ya ce, "Kai tsohuwar nan
rigimarki bata karewa, amman ai kece uwarta don
haka ba zamu watsa miki kasa a ido ba, zan sami
Salisu (Mahaifin Zainab) mu tattauna."Ya maida
dubansa ga Mustafa yana fadin, "To kai ka zama
na Zainabu da Zainab, mata masu suna iri daya,
don haka sai ka rike amana don 'yar uwarka mai
halin kwarai ce." Jikinsa sanyi kalau ya ce, "Ba
damuwa Baba na gode." Ya mike yana musu
sallama kamar wanda aka bigewa kwauri, jinsa
yake wani iri daban, amman ya sani ko ya sha
giyar wake bai isa ya ja da maganar auran nan
ba don wanda ke goya masa bayan ma ya bada
goyon baya (100%) dari bisa dari, don haka
sallamawa ce kawai tashi. Haka nan ya shiga
motarsa cike da tunanin abinda zai biyo baya duk
randa Zainabu ta ji wannan zancan, Zainabu mai
shegen kishi ko sunan mace ta gani a wayarsa in
dai ba 'yar uwarsa bace rannan sai sun kwashi
adashin tsiya, balle ace wai shine zai yi aure,
kuma ma kanwarsa Zainab, kai abinda kamar
wuya fa gurguwa da auren nesa, hakan nan ya
isa gida da taimakon Allah don bai san da yanda
yaje ba. Sanda ya isa ya tadda Zainabu ta ci
kwalliya tamkar 'yar tsana, sai ya ji damuwarsa
kashi saba'in ta ragu, ta taho da gudu da dafe
shi, yayi wani taga-taga kamar zai fadi amman da
yake dirarran namiji ne ya tsaya kyam, ya daga
ta yana wani wulwulata kamar Bebi. Sai da suka
shiga daki sannan ta kula da yanayinsa, duk
yanda Mustafa ke cikin damuwa Zainabu na
lakanta saboda yanda take ji dashi a ranta, don
haka ta kama tambayarsa abinda ya dame shi.
Kamar ya sanar da ita gaskiya, amman bai san
yanda zata dauki maganar ba, don haka ya
wayance kawai ya ce kansa ke ciwo, nan fa ta
bazama ta samo masa magani tana wani lelensa
kamar 'yar bebi har bacci ya dauke shi.
Cikin kankanin lokaci Iyayansu suka gama komai
na sanya rana da biki gaba daya, wata biyu kacal
aka sanya, kowa yaji dadi a dangin musamman
dangin mijinta wadanda suke sonta sai ta kuma
samun wani matsayi don tana kyautata musu
matuka domin macece mai kirki da kyauta, illar
ta daya akwai ta da saurin fushi kuma sam bata
son raini balle wargi. Sai da aka sanya rana
sannan Zainab ta ji labari, jin abin tayi kamar
mafarki kamar kuma wasa, don haka ta tadda
Sumayya daki ta zauna gefenta hankalinta a
matukar tashe ta ce, "Sumayya wai don Allah da
gaske ne an sanya ranar aure na da Yaya
Mustafa ko zolayata Fatima ke yi?" (Wata 'yar
uwar Babanta da ke gidan). Sumayya ta kalleta
cike da tausayi don ita kanta bata so aka yiwa
Zainabu haka ba don sunyi alkawarin ba zasu
auri namijin da son su yafi nashi ba duk son da
suke masa kuwa, sai sun sami namijin da son sa
yafi nasu, sai gashi yanzu za'a aura mata wanda
bai sonta kwata-kwata hankalinsa yana kan
watanta. Sumayya ta dafa ta idonta itama cike da
kwalla ta ce, "Zainab wallahi ni kaina sai yau nake
jin wannan labarin, wai kuma Momi ce ta hada
auren, don daman tace sai Mustafa ya auri wata
cikin 'yan uwa, wallahi ban taba zaton ke Momi
zata ce ba nayi zaton Zubaida zata bashi don
naga ita ce ke son sa da Babarta suke son ya
aureta tuntuni, dalilin da ya sanya suka tsani Anti
Zainabu ma kenan." Zainab ta fasa kuka mai ciwo
ta ce, "Yanzu Sumayya babu wani taimako da
zaki yi mini a janye maganar nan, ba zan ce miki
bana son Yaya Mustafa ba don yayi haduwar da
duk wata mace zata so shi, sai dai muddin na
yadda na shiga gidansa zan zamo mace mara
daraja da samun kulawar mijinta, ki taimake ni
gwara a hadani da ko waye da ace Yaya Mustafa
zan aura, don yayi nisa a son Anti Zainabu." Ita
ma Sumayya idon ta ya ciko da kwalla ta
rungume Zainab tana lallashinta gami da yin
magana, "Zainab ki kwantar da hankalinki, Insha
Allahu zanyi iyakar kokari na naga na shawo kan
Momi, amman idan Allah ya kaddara ke matar
Yaya Mustafa ce babu tsumi babu dabara sai kin
aure shi, sai dai muyi addu'ar Allah ya zaba
abinda yafi zama alkhairi." Sun jima suna
jimamin su har gari ya waye, suka shirya suka
tafi camp, domin sun fito bautar kasa suna camp
ba'a yi posting dinsu ba. Shi kam Mustafa ya fi
kowa shiga tashin hankali da sanya ranar nan,
har ya zama ko kaunar ganin Zainab bai son yi,
don haka sun jima sam basu hadu ba, sai dai
daga karshe zuciyarsa ta bashi shawarar abinda
ya dace ya yi, dole ita Zainab din zata sami
Momin na su ta ce a fasa auren, don haka bai
shirya gayawa Zainabu ba har sai ya aiwatar da
abinda ke ransa tukunna. Su kam bayin Allah
basu san abinda ake ciki ba, da yamma suka
dawo gida domin su Babansu ne ya ce bai yadda
su zauna a camp din ba, aka yi sa'a kuma yana
da abokai daga sama, daman Nigeria wa ka sani
ne wa ya sanka, don haka ya sami yanda suke
so. Tun da suka doso falon gidan suke jin
hayaniya, suka kalli juna cike da tashin hankali
sannan suka shiga da sauri, sun tadda 'yan
matan gidan kowacce tayi tsuru-tsuru, sai
Zubaida da ke wata kujera a zaune tana matsar
ido ga kuma Hajiya Saratu tana surfa
bala'i."Kubra ko kin fadi ko baki fadi ba aikin ki
ya nuna baki kaunata balle zuri'ata, domin tun
karon farko na auran Mustafa na nuna bana son
hadin nan kika watsa mini kasa a ido, sannan
kullun kina kurin sai kin raba auren ki masa
auren zumunci, sai gashi yarinyar nan Zainabu ta
zageni tatas kina kallo ta dawo gidan Mustafa,
sannan don cin fuska da kika tashi nemar masa
aure kika samo a dangin mijinki saboda kinfi
kaunarsu da mu, idan abin naki gaskiya ne ai da
Zubaida ya dace ki hada su tun da dai kin san ita
yake so tunda farko, ko kuma nace ta nuna
alamun tana son shi, taki kula kowa saboda
Mustafa amman ki mini irin wannan cin
mutuncin." Hajiya Kubra dake zaune ta yi
murmushi da nuna rashin damuwa da maganar
'yar uwar ta sannan ta fara magana, "Saratu ina
ce da Zainab da Zubaida duk 'ya'yana ne, kuma
idan da gaskiya a duniya ba zan fifita Zainab
akan Zubaida ba, ki yadda Allah da Zainab ya
kaddara auran don wallahi ban taba sanin
Zubaida na son yaron nan ba, kuma ita kanta
Zainab din sai da aka sanya rana ta sani don
haka kinga bai dace ki zargeni ba ko ki kullace ni
ba....."
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
"Kullata da zargi kam har abada ba zai rabu a
tsakaninmu ba, don dai da arziki a garinsu gwara
naki kuma a gidanku a dakinku a karkashin
gadonku, kuma in dai har kamar yanda kikace ba
zaki fifita Zainab akan Zubaida da gaske ne to ki
san yadda za kiyi ki warware sanya ranar da aka
yi musu ki maida ta da Zubaida, don yanda
Zubaida ke fadi tunda ta rasa Mustafa karo na
biyu ita da aure har abada, kinga kin dirar mani
rayuwar diya da ka......Hajiya Kubra ta dubi
Hajiya Saratu da mamaki ta ce, "Haba Saratu ai
imanin dayanku bai cika har sai ya so wa dan
uwansa abinda ya so wa kansa, yanzu kina ganin
idan aka yi haka anyi adalci? Sannan da wane
idon zan kalli Babansu na ce wai a warware
sanya ranar nan, kema kin san ba abu ne mai
yiwu wa ba zan jawa kaina abin magana ne da
gori ga....." "Shi kenan kin gama magana kin
gama nuna mini kinfi kaunar Zainab da jininki
Zubaida, sai dai yau ce rana ta karshe da zaki
kuma ganin kafarmu a cikin gidanki, kuma daga
yau ki cire ni a jerin 'yan uwanki balle wata
sabgarki ta tashi ki sanya ni a ciki." Ta maida
dubanta ga Zubaida ta ce, "Ta so muje, ki
kwantar da hankalinki Allah zai musanya miki da
miji na gari, su dai su yi mu gani don wallahi
nasan karuwar matarsa ba zata barshi ya zauna
da Zainab din ba, daman kece daidai ita." Suka
fice daga falon a fusace. Ran Hajiya Kubra idan
yayi dubu ya baci, ta yi tagumi cike da damuwa
ta rasa abinda ya sanya Saratu ke bakin ciki da
duk wani abu da ya kasance na farin ciki ko na
cigabanta, idan ta ce bata son Zainabu don
mugun halinta ita kuma Zainab meye laifinta,
kuma tunda take bata taba mata maganar hada
auren Zubaida da Mustafa ba sai yau don
tsokano fitina, tun suna yara haka take mata
gashi dai uwarsu daya ubansu daya amman tana
bakin ciki da duk wani ci gaba ko farin ciki a
rayuwarta. Su kam 'yan matan gidan tsuru-tsuru
suka yi, Itama Zainab ji tayi kamar ta sanya
hannu a kanta tayi ta zunduma ihu, musamman
irin bangazar da Zubaida tayi mata da gayya da
zata wuce gami da ja mata dogon tsaki har da
mutsitsike dan yatsa, daman can bata jituwa da
Zubaida balle wannan abin ya biyo baya,Sumayya
ce ta jata suka yi dakinsu itama Hajiya Kubra ta
shige dakin baccinta domin ta daura alwala ta
bada farali amman har lokacin hankalinta a tashe
yake. Karfe takwas da minti hudu Zainab taji
wayarta ta fara ruri na neman agaji, ta dauko ta
da sauri, sunan Mustafa ta gani baro-baro Ya
Mustafa, gabanta ya yanke ya fadi, sai jikinta ya
hau tsuma don bata san mai zai ce mata ba. Tayi
dai ta maza ta danna madannin amsa kira ta
kara a kunnenta gami da yin sallama. Da kyar ya
iya amsawa sannan ya ce, "Ke kina jina? Ina falon
boys quarters ki zo yansu, kuma bance kizo da
wata ba ko ki sanar da wata nazo ba, don nasan
halinki." Yana kaiwa nan ya kashe wayar. Ta yi
tsumu-tsumu tana kallon wayar, kamar ta tsaya
ta sanarwa da Sumayya wacce ke wanka amman
sai ta tuna da gargadin da yayi mata don haka ta
mike jikinta na rawa ta nufi sashin yaran, daman
tana shirye tsaf gyale kawai ta dauka. Yana
zaune bisa kujera ya hade hannuwa, fuskar nan
ta sa babu alamun fara'a, ta yi sallama ta shigo
har lokacin jikinta rawa yake. Tunda ta shigo ya
zuba mata ido, yau ce rana ta farko da ya tsaya
yayi mata kallon tsaf, doguwa ce amman ba can
ba kuma itama fara ce ba tas ba, tana da kyau
daidai misali don duk inda mace take ji da kanta
ta kai nan, tana da gashi mai tsaho sannan tana
da kirar mata ta burgewa, sai dai ko kusa bata
kamo Zainabu a kyan kira da jiki ba. Har ta
zauna bai dauke idonsa daga kanta ba, abinda ya
kara tsurar da ita, shi kam so yake yaga abinda
zai kushe Zainab da shi a ransa amman har ya
karaci kallon kurillah nashi bai gano ba sai dai
yace Zainabun sa ta fita.Ita kam sai rawar jikinta
ya kuma karuwa don ganin duban da yake mata
babu ko kunya, ta daure ta zauna kamar wacce
zata zauna bisa garwashi. Yayi shiru bai ce mata
kala ba, ita kam tsoro ne ya hanata cewa komai,
amman don kada ta kara laifi sai ta daure da
kyar kamar mai yin rada ta ce, "Ya Mustafa ina
wuni.....Kinga ba wannan ce ta kawo ni ba kina ji
ko? Zuwa nayi naji dahir daga bakinki, shin ke ce
kika ce kina sona har aka hada auran nan?"
Ranta ya dan sosu, sai taji dauriya tazo mata,
don ba zata lamunci yayi mata cin fuska ba, don
haka ta danne ta ce, "Kai ma ka san hakan ba
zata faru ba, ni a matsayin Yayana na dauke ka,
don haka kama daina tunanin nice naje na ce ina
son ka aureni." "Wonderful, haka nake son ji
daman, don haka yarinya kin kwaci kanki muddin
kika sanar da Momi baki sona, ni bance bani
sonki ba sai dai soyayyar mu bata aure bace, ina
ganin ke 'yar uwata ce daman..... don haka ina
son ki sanar da Momi baki sona a janye maganar
auran nan, idan kika yi haka kin kwaci kanki, don
kin sani Zainabu ce kadai macen da nake so har
abada, raina ba zai iya rayuwa da wata can ba
bayan Zainabu." Ita kam tunda ya fara maganar
bata ce ko kala ba har yayi ya gama, sai da yaga
bata da niyyar cewa komai sannan ya kuma
cewa, "Banji kince komai ba, don bana son asan
na zo gurinki ma balle ayi zaton ko ni na sanar
da ke, ki nuna ba kya sona ne kawai don kanki,
hakan ma zai fiddani daga zargin Momi. Ta kuma
daurewa kashi na biyu ta ce, "Hakan ba mai
yiwuwa bane, yanda kake tsoron bacin ran Momi
nima haka nake tsoro, kuma yanda kake gudun
zargi nima haka nake gudu, don haka wallahi da
bakina ba zance da Momi bana sonka ba, sai dai
kai kaje ka fada idan ba haka ba kuwa sai dai a
yi auran....Kinga Malama kina wata maganar ba
zaki je ki fada ba ni ke nake tausayawa, domin
idan kika sake aka yi auran nan kin san ke ce a
hannu don zan sanar da ke ba zan iya shiga
dakinki da sunan kwana ko auratayya ba,
hasalima ba zan iya miki duban da na kewa
Zainabu ba, don haka idan kin fada kanki kika
ceta, idan kuma kika yi sakaci har aka daura kin
shiga rayuwa mara ma'ana da daraja, don kin
san har abada ba zan iya sakinki ba hakan kamar
na yanki tikitin salwantar da zaman lafiya da
Momi ne na har abada, don haka zan zauna dake
wani irin zama ne da ba zan iya bashi suna ba."
Idanuwanta suka ciko da kwalla, hankalinta yayi
mugun tashi da jin kalaman Mustafa, amman ta
san ko da zata koma matsayin da har abada bata
da 'yanci ne a gidan sa ba zata iya cewa da Momi
bata son danta ba gaba da gaba, "Zaka iya yin
komai kaga dama, amman wallahi har abada
Momi ba zata ji kalmar kin ka daga bakina ba, na
shirya zama baiwa a gidanka, domin shege shi ke
manta alkhairi ba dan halak ba, Momi tayi mini
abinda har na mutu ba zan manta ba....." "Shut
up, rufe mini baki!" Ya fadi a fusace san da ya
mike tsaye don ganin hakarsa bata tadda ruwa
ba, wannan itace dabara da ta rage masa ta
karshe, don haka ya gama saddakarwa da lallai
auran nan babu fashi, amman zai nunawa
yarinyar nan namijin duniya ne shi da ba'a isa a
yi masa auran dole ba.Ya nuna ta da yatsa ya ce,
"Ki shirya fuskantar bakar rayuwa mara fasali a
gidan Mustafa da Zainabu....." Yana kaiwa nan ya
fice daga falon yana wata irin tafiya kamar zai
balla tayal din da ya malale falon. Sai da ya fice
taji kuka ya kwace mata, ta hada kai da gwiwa
tana kuka sosai, haka nan Allah ke tsarawa bawa
abinda ya so ko da son ransa ko babu, ita kam
ko a mafarki bata taba zaton zata zama matar
Mustafa ba don ta riga ta san yayi nisa a son
Zainabu, ita kanta ta san Zainabu macece da
kishi da ita zai iya zama bala'i da masifa domin
babu ta inda ta rago ga mijinta, daga fannin girki
har fannin kwalliya, balle kissa da iya tarairayar
miji, takanas suke zuwa gidan daukar kwas kuma
duk sanda suka je sai sun ga wani sabon salon da
zai basu mamaki da sha'awa. Ita kam ta yadda
rayuwarta a gidan Mustafa rayuwa ce zata yi
mara 'yanci da cigaba ma, ta mika al'amarinta ga
Allah tunda shine ya tsara mata wannan rayuwa
ta san zai bata mafita, don Allah ya ce, "Baya
dorawa rai abinda yafi karfinsa." To tasan zai kai
mata dauki, ta yaya ne bai bata sani ba za dai ta
mika kukanta gareshi. Sai da taci kukanta ta koshi
sannan ta mike kamar wacce aka yiwa duka da
kyar take takawa duk jikinta ya mutu murus ta
nufi gida tana jan kafafu. A tsakar daki ta tadda
Sumayya ta zauna tana kallo, tana shigowa ta
dubeta da sauri, daga gani babu tambaya kuka
take don farin idonta ya rune zuwa ja har wani
kumbura kuma idanun nata suka yi, fuskar nan
duk tayi wani luhu-luhu abinka da farar mace.
Sumayya ta mike da sauri tana tambayar ta,
"Zainab me ya faru? Ina kika je? Tun dazu nake
nemanki ga wayarki kin barta a daki, Ko Ya
Mustafa ne....."Ta daga kai ta kalleta da sauri
saboda tambayarta ta karshe amman ta gaza
cewa komai. "Na ma san shine, Me yayi miki? Me
yace miki? Yace baya son ki ko? Zan sanar da
Momi yanzu kuwa....." Ta rike ta sanda ta ga ta
nufi kofa da sauri. "Kada ki fada mata na sani
zata kirashi tayi masa fada ne, shi kuma zai yi
zaton nice na sanar da ita don daman yace ko
me aka yi mini sai na sanar dake, don Allah ki
bari kada ki gaya mata ni baice mini komai ba,
bai ma zo ba fa." Tana maganar tana
sheshshekar kuka.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Sumayya..... ta ce, "Haba Zainab naga Ya Mustafa
da idona wallahi, don na fita amso sako gurin
Baba Maigadi dana aike shi na ganshi ya fito
daga boys quarters ransa a bace, yana wata
tafiya kamar tunzirarre har ya fice a motarsa bai
ganni ba, ni kuma na kyale shi don naga kwana
biyu kamar haushina yake ji." "Ni dai don Allah
kada ki gayawa Momi, ki rabu da shi kawai Allah
yana sane da ni." Sumayya ta warce hannunta
tana fadin, "Wallahi sai na yi mata maganar akan
auran nan ko da banyi mata ta Ya Mustafa ba,
kina ganin irin cin mutuncin da Anty Saratu ma ta
tayi dazu, Zubaida kuma har da bangazarki da
taka miki kafa, ina kallo don kada nayi magana
ne ace ina goya miki baya ne, shi ya sanya nayi
shiru, me yayi zafi haka kawai kina rayuwarki a
zo a matsa miki bayan baki sanya a ka ba, dame
zaki ji da kin da Ya Mustafa ke miki ko da
kiyayyar Zubaida ko kuma da kishi da Aunty
Zainabu, gwara yaje ya auri Zubaidar sa tantance
tsakaninta da Anty Zainabun, bani waje na sami
Momi din." Ta nufi dakin Momin nasu.Zainab ta
fada gado ta kuma fashewa da kuka mai cin rai,
lallai kam tana cikin matsala babba, wanne ne
baya cikin wadannan matsaloli guda uku, dama
ace ta samu Ya Mustafan yana sonta da sauki
amman mutumin da yake ganin ina wuta ya jefa
ta. Sanda ta isa dakin ta tadda Momi da wasu
fayal a gabanta tana cikewa, tana sanye da
(medical glass) dinta, ta isa ta zauna gefenta
Momin ta ce, "Ya dai aka yi na ganki duk ranki a
bace." Ta kuma hade girar sama da ta kasa ta ce,
"Momi akan maganar Ya Mustafa da Zainab ne
tunda kinga ita bata son shi shi baya sonta gwara
a hakura, ga kuma Anty Zainabu a gida kinga ba
zai ga wata mace da daraja ba tunda yana ganin
Anty Zainabu, ni a ganina gwara a maida auran
kan Zubaida tunda ita tana son shi, kinga ita zata
iya da ita, kar ce ta san kar." Hajiya Kubra ta
zare glass dinta gami da rufe fayal din tayi
murmushi sannan ta ce, "Sumayya tunda aka yi
maganar auran nan naga take-takenku ke da
Zainabu na san lallai Zainab bata son Mustafa, ba
wai kuma bata son sa don komai ba ne illa don
tana tsoron matarsa, lallai kam matarsa abar
tsoro ce, sai dai kiyayyar da nake mata ba zata
sanya na rufe ido na yi mata sharri ba, a iyakacin
binciken da nayi a kanta babu wanda ya ce mini
tana mu'amala da malamai ko bokaye, don haka
zargin da nake yi da na cewar asiri tayi masa ya
kau a zuciya ta. Yanzu na gano tsantsar iya
duniyanci ne da kissa ya sanya Zainabu ta tafi da
Zuciyar Baba, don haka Zainab macece itama
zata iya duk abinda Zainabu tayi ko ma tayi sama
da nata din, don duk mace tana da kissa da nata
wayon nasan wata rana zai yi alfahari da auranta
Insha Allah,wannan ne ma ya sanya na jajirce
naga anyi auran nan, don da can na zaci asiri
take yi naji tsoron kada na hada auran a nakasa
mini diya, amman tunda kissa ce da iya zama da
miji to itama zata iya wuyarta dai a yi auran.
Maganar Zubaida kuma kada ki kuma tunanin zan
amince Mustafa ya aureta, don idan na bari ya
auri Zubaida ba a rabu da bukar bane an haifi
Habu, don wallahi gwara Zainabu sau dubu da
Zubaida, ita din da har neman mata take yi,
sannan duk irin rayuwar da tayi a makaranta ina
sane da ita, sai dai tun da na fara sanar da
Mahaifiyarta ta nuna bata son gaskiya na zuba
musu ido. Ki sani ina son yayi auran mace salaha
kuma ta gari ne, wacce ko bayan ransa zata iye
rike masa zuri'arsa da tarbiyya, amma daga
Zubaida har Zainabu zuaciyarsu bata gyaru ba
balle gangar jikinsu ta gyaru su gyara wani ba,
kuma Allah ya sani ba wai ina kin Zainabu don
sunanta ko don gidansu ba, ina kinta don halinta
na banza ne, don haka ina neman kema ki
taimaka dan uwanki ya ajiye salihar mace mai
gyararriyar zuciya a gidansa, wacce zata haifa
masa zuri'a dayyiba masu nagarta. Jikin Sumayya
yayi sanyi ta kuma gamsu da bayanin Momi, sai
dai tana ganin kamar Momi tayi son kai, don tana
son danta ya sami zuri'a dayyiba sai ta aura
masa mace ta gari bayan shi din zuciyarsa bata
gyaru ba, tunda kowa ya san yanda ya auri
Zainabu ita Momin din ce bata san komai ba,
idan har akayi wannan aure lallai an tauye
Zainab mai kamala da kamun kai, amman babu
yanda za ta iya sanarwa da Mominta wannan
maganar, don haka ta mike kawai ta nufi kofa.
Momin ta ce, "Ki dinga tausar Zainab, gobe kuma
zanje kasuwa zan siyo mata wasu littafai da zasu
taimaka mata, ki bata hakuri don ni yanzu
kunyarta nake ji don na san naso kaina, amman
Insha Allahu yanda tayi mana biyayya Allah ba
zai kunyata ta ba komai dadewa." Sanda
Sumayya ta isa dakin ta tadda Zainab bisa sallaya
ta yi sujjada tana ta addu'a, duk da bata jin
abinda take fadi tasan kukanta take kaiwa rabbi
don haka itama tayi alwala ta fara taya ta neman
yardar Allah
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
. *** *** *** *** ***
kwanaki sun fara ja na biki sai shirye-shirye ake
yi a ko ina daga bangarorin iyayan amarya da na
ango, amma ango gaba daya a birkice yake,
Zainabu ta shiga damuwa kwarai ganin halin da
ya shiga, don haka ta yiwa kanta alkawarin ganin
ta magance masa abinda ke damunsa. Ya dawo
gidan yau karfe tara na dare, don yayi mata
waya ba zai dawo da wuri ba, wani inji ne ya
tsaya na zuba mai, don haka shi yake gyara shi
don kananan injiniyoyin duk sun gaza. Tana
zaune a falo tana kallon tashar Zee Aflam ya
shigo, tana sanye da dogon wando fela da ya
kama ta tsam ta sanya wata riga mai huda-huda
wacce ana hango kalar rigar kayan sun yi mata
kyau matuka, sai wani kamshi take yi mara
fasaltuwa. Tana jin shigowarsa ta nufeshi da
gudu, ya daga ta kamar kullum ya manne a
jikinsa, ta shiga aiwatar masa da abinda ta saba,
ya shagala matuka don Zainabu ta san kansa da
kyar ta jashi zuwa bandaki, ita ce ta kusa yi masa
rabin wanka suka fito nannade da tawul yana
dauke da ita kamar wata 'yar tsana, don da yaga
dama zai dauketa tsaf yana tsokanarta, yace
kamar roba take babu wani nauyi da yake shi din
kakkarfa ne, musamman da yake yana aikin
karfi.,sunyi shiru a kan gado, ya rasa ajin da zai
ajiye Zainabu don ta gama masa komai, gaba
daya kusan rayuwarta gurin kyautata masa
kwanciyarsa take karewa bata taba gazawa da shi
ba, duk sanda yazo da bukatarsa ta gamsar da
shi ko da tana al'ada ne ta kan san yanda za tayi
ta biya masa bukatarsa ba tare da ya kusance ta
ba, Zainabunsa zuma ce. Sai da ta tabbata ta
gamsar da shi sannan tayi lamo a kirjinsa tana
wasa da cikin salonta na kuma sace zuciyarsa ta
ce, "Zuma yau dole ka sanar da ni abinda ke
damunka, idan ka shigo sai na ganka duk ranka a
bace, ko Ofis ake taba mini kai ne?, nifa ban son
abinda zai dinga tsunkulinka, ka sanar da ni kaji
ko kana so nayi kuka?" Ta karasa maganar da
kissa da wani salo da ya sanya shi kusan
shidewa, sai dai duk da haka kirjinsa yana
bugawa kamar zai fito waje. Ya tashi zaune har
lokacin tana jikinsa kamar zata koma cikinsa ko
kuma a maida halittarsu tare, don haka ne ma
duk sanda suka raba shimfida (idan sunyi fada)
ya shiga damuwa matuka, don muddin yana gida
Zainabu na makale da shi tana goga masa
lallausar fatarta, abinda ke kara mata martaba a
idonsa, don yana son hakan da take masa, kai
duk wani abu da yake so ma Zainabu nayi masa.
Ta kuma narkewa tana shagwaba ta ce, "Allah ka
sanar da zanyi zanyi kuka, ko kana son nima na
fara damuwa kamar yanda kake.....ya toshe
mata bakinta kirjinsa hr lokacin yana bugawa, ya
ga gwara ma ya sanar da ita tunda yanzu bikin
saura sati biyu kacal kada ta ji a wani gurin ta
zarge shi, sai dai ya san yau kam zai gamu da
tashin hankali. Ya daure yayi ta 'yan maza ya ce,
"Zainabu tuntuni nake son sanar da ke abinda ke
damuna, sai dai ban san yanda zaki dauki
lamarin ba, ke din mutum ce mai muhimmanci a
rayuwata wacce har nake ganin da na rasa ki
gwara na rasa raina, kuma wallahi har abada ko
kina raye ko baki raye ko muna tare ko bamu
tare ba zan iya son wata sama da ke ba don ke
din rayuwa ce ta jin dadi, sai dai akwai wani
matsayi da mutum yakan kai da duka mai neman
cikawa da imani ba zai bijirewa maganarsu ba,
ma'ana ina nufin uwa kenan." Tana jin ya ambaci
haka taji gabanta ya yanke ya fadi don jin ya
ambaci Mahaifiyarsa, don tana zaton ko cewa tayi
sai ya sake ta, tana ganin in dai haka din ne ta
shiga uku don kamar yanda yace itace rayuwarsa
shima din shine rayuwarta, amman sai ta gaza
cewa komai illa bugawa da kirjinta ya kama yi ta
kuma kankameshi tamkar za'a rabasu da karfin
tsiya. Ya cigaba da magana a hankali cikin mafi
taushin lafazi da zaben kalmomi, "Don haka
Zainabu, ko me zance ina son ki fahimceni don
kinsan ke ce kadai nake so zan kuma cigaba da
so har daukewar numfashi na. Ba wata magana
bace illa Momi ta ce lallai sai na auri kanwata
Zainab har ma an sanya rana bikin saura sati
biyu, tun daga sannan ban kuma samun
kwanciyar hankali ba......" "Kai! Ya isheka haka
Malam." Ta fadi da karfi da zafin zuciya sanda
take janyewa daga jikinsa tana masa wani duba
da tsana da jin haushi. Ta dora da cewar, "Ni
zaka rainawa wayo ka maidani 'yar iska? To baka
isa ba nafi karfin ka hada ni da wata saboda ban
aureka dan kudi ko wani abu ba illa so, da na so
auran kudi da sai naje na auri mai mata, don
haka sai dai ka zaba ko ni ko wacce zaka aura,
kazo kana mini wani rainin hankali, mtsw!" Ta ja
tsaki gami da fadawa kujerar da ke dakin ta dafe
kai,Hankalinsa ya kai kololuwar tashi, ya san haka
zata faru daman don haka ya so ya yakice
maganar auran nan ko ta halin kaka amman sai
da ta tabbata, yanzu yaya zai yi da rayuwarsa da
rigimar Zainabu? Ya daure ya kuma kwantar da
murya ya ce, "Haba Zainabu ya dace ki fahimce
ni, kin san dai bayan ke ba ni da abar so, wallahi
ki yadda wannan auran zan yi ne don biyayya ga
iyayena amman ba don ina son yarinyar ba,
hasalima ita kanta yarinyar ta san ke ce dai kadai
nake so, don Allah ki kwantar da hankalinki mu
fahimci juna." Ta galla masa harara gami da
kauda kai gefe, zuciyarta sai wani irin tukuki take
yi, ji take kamar ta rufe shi da duka, ita ko sanda
tana bariki namiji bai isa ya hada ta da wata ba
balle ace wai mijinta da take so ta ware shi
daban a ranta fiye da kowa. Saboda tsabar
takaici ma sai ta kasa cewa komai illa idanuwanta
da ke zubda hawaye tamkar famfo. Jin ta yi shiru
ya sanya shi mikewa ya isa gabanta ya tsugunna
ya kuma kwantar da murya ya ce, "Zainabu ki
yiwa Allah ki dauki abin nan da sauki, ki kuma
zira ido ki ga irin zaman da zan yi da yarinyar
nan don na gaya mata ta sani ba zan taba sonta
ba....." "Ka rabu da ni malam ka ji ko!" Ta fadi da
tsawa gami da mikewa tsaye tana huci tamkar
wacce tayi tseren gudu, ta dora da cewar, "Ka na
ji ko? Ba ka isa na zauna da kai kana tare da
wata 'yar iska ba, don haka na gaya maka sai dai
ka zabi daya. Da me zan ji? da kiyayyar da
danginka ke mini ko da kakaba maka diyarsu da
suka yi? Don haka sai ka zauna da wacce aka
zaba maka ake son ka zauna da ita amma ba ni
ba." Tana kaiwa nan ta fice daga dakin da
gudunta don kuka ya ci karfinta.....Tofa,karshen
tika tiki tik..Labari ya dakko gakums takaddunsa
sunkare,yaya za'ayi kenan, saidai ko muhadu a
littafi nagaba kuma na karshe........(KO INA
LABARIN SALA DA BABA ABBAKAR DA KUMA
SADIKU DA KANNENSA? KO SALA TA GANE
KUSKURENTA KO KUMA TA KARA ZURFI CIKIN
BATAR TA? KO WANNAN AUREN ZAI YIWU KUWA?
DON JIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU
HADU A LITTAFIN NA UKU
Mai kaunarku da yi muku fatan alkhairi a kullum.
FAUZANKU CE! Mrs Q for Q,
adsense 2 here