Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, 9 May 2017

SALEENA COMPLETE

adsense here

1474463087186.jpg KHADEEJA CANDY MOBILE BLOG WELCOME TO MY WORLD YOUR COMMENTS AND CORRECTIONS ARE ALWAYS WELCOME ENJOY YOURSELF 💁 Menu Skip to content Home › SALEENA › SALEENA SALEENA Posted on September 22, 2016 by Khadeeja Candy — Leave a comment ​[8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: BISMILLAH RAHAMANIM RAHIM *SALEENA* Na Khadija Abubakar Alkali 1~ Gudu take cikin karan gero daga ita sai daura gaba, Numfashinta na kokarin daukewa Tanayi tana waiga bayanta Har taka karya kwana bata an karaba tajita kasa sakamakon kwara da da tayi da wata mota dake kokarin shigowa kwanar, Da sauri abdallah ya fito motar yana fadin ” subhanallahi ” ko kallonshi batayi ba ta tashi a firgice zata ci gaba da gudun, Ganin haka yasa Abdallah ya rikota da sauri yace ” malama tsaya mana mu gani bakiga kinyi kaura da motaba “? Kwana data fito kawai take kallon tana kokarin kwace kanta tace ” dan Allah sake karsu zo gasu nan tafe kasheni zasuyi rape dina zasuyi dan Allah kai taimaka min ” Abdallah ya shiga kallon kwanar shima yana fadin ” suwa mie kika musu “? Sai a lokacin ta kalleshi ta shiga nuna masa hanyar ” gasu nan tafe wasu ne kasheni zasuyi suyi min fyade ka taimaka min dan Allah ” cike da tashin hankali Abdallah yace ” cikin hankali kike baiwar Allah kodai kina hauka ne ? Cikin kuka tace ” wlh gasu nan zuwa biyo dan Allah ka sake ni ” bude mazaunin baya naga Abdallah yayi zai sakata Kokuwa ta shiga yi dashi tana kokarin kwace kanta tace ” dan Allah karka mayarda ni gurin su ka tausayamin plz ” ni ba gurinsu zan………… Bai karasa maganar ba ya saketa da sauri sakamakon wani mugun cizo data kaimashi a hannu Tana ganin ya sake ya juya zata ranci na kare cikin zafin nama Abdallah ya rikota da dayan hannun nasa ya bude mazaune baya yana kokarin sakata yace ” ni taimakonki zanyi ” da sauri ta karasa shiga motar tare da rufe ganbu shi kuma ya shiga driver seat yayi reverse da karfi, Wani irin gudu ya shiga yi kura sai tashi take harya tashi kade wani dan achaba, Mutane sai kallonsa suke kamar xai tashi sama Har itama ta farajin tsoro ta shiga masa ihu ” dan Allah dan Annabi karka mayarda ni gurin su karka cutar dani ka tausaya min ” Bai saurare taba saida ya shigo cikin gari sannan ya tsagaita gudun ya samu gefen t-t yayi parking, Ya juyo ya kalleta yace ” ni ba cutarki zanyiba na fada miki in kuma baki yarda ba ga hanya nan zaki iya fita ” Hawaye kaca2 a fuskarta tasa Hannayenta tana kare kirginta ganin ya tsareta da ido Saida yaga ta fara tsarguwa sannan ya dauke kansa ya maida kan motocin dake wuce wa yace ” karki bata min lokaci dan akwai abunda ya kawoni kauyen nan ” Da sauri tace ” no plz karka maidani cikin kauyenan wlh suna nan ciki ” yace ” to ina zan kaiki “? ” wlh nima ban saniba ni banida kowa garin ban san kowaba hasalima ni bansan inda nakeba dan Allah ka taimaka min “. Murmushi yayi yace ” wannan wace irin magana ce mie kike nufi ” ” dan Allah bawan Allah ka yarda dani wlh ban san kowa anan ba dan Allah ka taimaka min ” shiru yayi har na wani lokaci ganin haka yasa tace ” dan Allah malam mubar gurin nan karsu ganmu dan wlh har kai bazasu kyaleba ” Ajiyar zuciya ya sauke yace ” ok zan kaiki gidan mu gurin mummy na kuma…. ” bai karasa maganar ba tace ” no dan Allah karka kaini can wlh kocan zasu iya kamani dan photo na suke gwadi har a tv wlh ” juyo yayi ya kalleta ” waike mie kike nufi ne ina to zan kaiki gurin police ko gidan marayu tunda kice bakida kowa kewai ma suwaye ne suke binki mie kika musu “? Cikin muryar tausayi tace ” babu lokacin yi maka wannan bayanin amman dan Allah ka taimaka min ka samu wani lungu inda babu wanda zai ganni ka saukeni dan Allah ” Tabe baki yayi yace ” hakan ya fi miki kenan “? ” ae wlh ya fimin dasu kamani sumin fyade kyma su kasheni ya fi min ” Yayi har kusan minti 5 yana kallonta sannan ya kunna motar yaa hau t-t Bai dade yana tafiya ba naga ya shigo wata umguwa da babu mutane sosai sai gine2 kasa wani gefen kuma gidanar xamani ne naji da fadi. Da alamu dai sabuwar unguwace, Tafiya yayita kamar wadda zai bar unguwa sannan naga yayi parking. Bakin wani gida mai farin faiti da green gate fitowa yayi yasa key ya bude kwado da aka rufe gate din dashi ya wangale gate din, Sannan ya dawo yaja motar suka shiga ciki,,,, © Khadeeja Candy [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* Na Khadija Abubakar Alkali 2~ gidane plate maikyau da tsare bakin wata katuwar kofa yayi parking bayan ya rufe gate ya zakayo ya bude mata ganbo matar Alamar ta fito, Kalloshi tayi cikin fuskar damuwa “dan Allah karka cutardani dan Allah karka maidani gurinshi ka tausayi mun” kallonta yayi fuska a hade “ke bana son shashanci nayi miki kamada mugun mutun ne in baki yarda dani ba ga hanyan nan” Ya karasa maganar yana nuna mata gate fitowa tayi idonta a kasa kamar munafuka tace “yi hakuri” “Mtswww” yaja tsaki ya nufi kofar da sauri ta rufe ganbun motar ta rufa masa baya, Yana kokarin sakawa kofar key tace “nan gidan yayenka ne ka kawoni”? Ba tare daya kalleta ba yace “gidana ne ni kadai ke ciki sai ke dazaki fara zama yanzu” ya karasa maganar tare da bude kofar, Bai ce ta ita ta shigoba ya shige abunsa, Ita kuma tana tsaye tana kallon harabar gidan saida yayi kusan minti 7 da shiga sannan ta itama ta turo kofar ta shigo a hankali, Dube2 tayi shiga amman bata ga kowaba sai wata kofa data hango bude,. Nan ta samu gefen kujera ta rabe tana karewa katon parlour kallo da ya kawatu da kayan alatu, Tana ganin ya fito ta tashi tsaye da sauri tana kalloshi, Kujera ya nuna mata “zo nan ki zauna” Ba musu ta nufi inda ya nuna mata ta zauna sai a lokacin ya lura da dingishin ta take da kuma jinin dake zuba a guwarta, Wata kofar ya nufa ita kuma sai kalle2 take dan gani take kamar wani zai fito, Bai dadeba ya fito rike da gorar ruwa da cup wani karamin tebur ya janyo ya dora cup din ya zuba mata ruwa “dauki ki sha” yace da ita Ido ta sakar masa kamar tace bazata shaba ganin haka yasa ya dauki ruwan ya shaye ya dire kofin ya sake zuba mata wasu da sauri ta dauki ruwan ta shanye har tana sarkewa, Ta dire kofin tana maida numfashi Tabe baki yayi ya kalleta sama da kasa da sauri tasa hannu ta rungume kirjinsa Ciki2 yajs tsaki ya nuna mata wata kofar “kalli can bedroom ne akwai bathroom ciki ki shiga kiyi wanka” yana fadar haka ya juya Har yakai kofa ya juyo yace “amman karki taba min soso da brush soaps kawai na yarda ki taba” tashi tayi tsaye tana masa kallo tsoro “ina zaka kai”? A takaice yace da ita “gurin iyayena in kuma kina zuwa ga hanya muje”? Dauke kai kawai tayi batace dashi komai ba yana ganin haka ya juya ya fice, Saida taji tashin motarsa sannan ta nufi kofar ta ciro key din dake lake ta kulle daga ciki, Tana rufewa ta sauke ajiyar zuciya ta gyara daurin zanenta. Inda taga ya fito da ruwa ta nufa, Tana shiga taga kitchen. Dubi2 ta shiga harta hango wuka dake saman fridge da sauri ta nufi gurin ta dauki wukar, Saida ta buda wata kofar da tagani a kitchen din taga store ne sannan ta fito, Ta dawo parlour kai tsaye ta nufi wata kofa daga cikin kofofin dake parlour, Bedroom ne da toilet ciki saida ta duba har wardrobe da karkashin gado sannan ta fito. Ta nufi wani dakin, Haka tabi dakunan kusan daki 3 duk haka take musu saida taga babu wani sannan hankalinta yadan kwanta, Parlour ta dawo ta zauna tana share gumi tayi kusan 5 minute a haka sannan ya tashi ta nufi kofar da ya nuna mata. Rike da wukarta a hannu, Tana tura kofar taga bedroom kamara yadda ya fada mata zuciyarta na bugawa ta shiga, Nan ma saida tayi binciken kwakwanf taga bataga komai ba sannan ta nufi kofar ta kulle ta shiga bathroom din, Zanenta ta cire ta rataye bayan ta kunna shower ta dauki sabulu ta shiga cuda jikinta, A gaggauce tayi wanka ta fito daure da towel din tada gani cikin toilet din rike da wukarta zuciyarta sai bugawa take, dan har yanzu bata aminta da gidan ba, saman bed ta zauna tabi pictures dinshi dake manne jikin bango da kallo,,, © Khadeeja Candy [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* Na Khadija Abubakar Alkali 3~ tayi 2hr a dakin bayan ta kare kallon pictures ta koma yi mishi bincike2, da ta gaji ta bude kofar ta dawo parlour ta zauna rike da wukarta sai dube2 take, Tana haka taji parking din mota. da sauri ta tashi ta leka window tana ganin motar da suka shigoce ta sauke ajiyar zuciya ta dawo gurin da take ta zauna, Knocking yayi har sau 4 sai a na biyar ta taso taxo bakin kofar ta tsaya “wanene”? Daga can waje ya amsa mata “nine bude” Saida ta leka ta kara tabbatarda shine sannan nade wukar dake hannunta cikin towel ta bude kofar, Yana shigowa kallo 1 yayi mata ya dauke kai wata katuwar leda ya ware daga cikin ledodi dake hannunshi ya mika mata “karbi kije daki kisaka” Ba musu ta sa hannu ta karba ta nufi bedroom. Saman gado ta zazzage ledar tana dubawa. Dogayen riguna ne guda biyar da dogon wando biu sai katon hijab, Saida ta dawo ta kulle kofar bedroom din sannan tasa wando da bakar abaya ta bude kofar ta fito ba tare da tasa hijab din ba, Kujerar dake facing din tashi ta zauna gabanta sai bugawa yake Suna hada ido ya hade mata fuska yace “koma kisa hijab” har ta bude baki zatayi magana kuma ta fasa ta tashi ta nufi dakin. Ko minti 3 ba ayiba ta fito sanye da hijab din mai ruwan kasa brown color, Gefen kujera ta tsaya tana kallonshi yana kokarin saka safar hannu tace “na saka” kallonta yayi fuskarsa babu yabo babu fallasa ya nuna mata kasan carpet “zo na ki zauna inyi treatment dinki” Yi tayi kamar bata jishi ba saida ya sake kallonta sannan taje ta zauna inda ya nuna mata sai hadiyar yawun tsoro take, Saida ta janye rigar ta lankafe wando sannan ya shiga treatment dinta. Bayan ya kare ya tura mata ledar Takeaway da fruits da yogurt ya tashi ya kwashe kayan da yayi aikin dasu ya nufi kofa, Da sauri tace “ina zaka”? Batare daya juyo ba yace “gida” “ni kadai zan kwana nan”? Kai kawai ya daga mata ya fice. Tana jin tashin motarshi ta cire hijab din ta dora saman kujera ta sama kofar key. Kai tsaye tudun wada ya nufo yana ta sake2 aranshi har ya iso gida, Yana yin horn maigadi ya bude mishi gate ya shigo saida yayi parkin a parking space sannan ya nufo cikin gidan da sallama ya shigo parlor hajiya zainab ta amsa mishi fuskarta dauke da murmushi “amin a’alaikansalam Abdallah sai yanzu”? Zaunawa yayi kujerar dake kusa da ita yana fadin “ae wlh mummy aikin ne ba sauki ya gida”? “lafiya kalau amman kan kusha aiki bari na kawo maka ruwa” tana kokari tashi ya dakartarda ita “a’a mummy barshi kawai karki wahalarda kanki bari naje part dina ai akamin abincina can ko”? “ae tun daxu nasa hannatu takai maka” tashi yaya yana fadin “ni bari naje can har wanka ma nayi nadan kwanta dan nagaji sosai” murmushi tayi tace “to Allah maka albarka” ya amsa da “Amin” ya mata saida safe ya nufi part dinshi,, *** *** *** *** *** Washe gari karfe 8am da yan mintuna ya shigo part din mummy dining are ya tararda su suna karyawa, Su maryam da hannatu da ummul-khairi na ganinshi suka shiga gaidashi bayan ya amsa ya risina ya gaida mummy cikin far’ah ta amsa mishi tana mishi ya gajiyar jiya shima yana murmushi yace “gajiya tabi lafiya mummy” ya kalli maryam yace “hada min abincina” “Ba a’nan zakaci abincin ba”? Cewar mummy Duban agogon hannushi yayi “ae mummy akwai Patient din da zan duba da safe nan inna tsaya cin abinci gida zan iya makara” kai kawai mummy ta daga mishi ta kalli maryam “yi sauri ki hada masa” maryam ta tashi ta nufi kitchen da sauri , Kololi ta dauko da plas da plates ta zuba mishi duk abunda tasan yana karyawa dashi, Tasa mishi a kwando ta nufi motarshi ta sa mishi. Shiko yana tsaye kusa da mummy yana cin wainar kwai dake gabanta, Saida ta kawo kusa dashi sannan tace “big bros na samaka a mota fa”, Kai kawai ya daga mata yayi ma mummy sallama ya fice,,, tana kwance saman doguwar kujera taji tsayuwar mota da sauri ta tashi ta leka hangoshi tayi sanye da kananan kaya yana kokarin fitowa motar. Dawowa tayi ta dauki hijab din’ta tasa, Yana yin knocking ta tashi da sauri ta bude mishi kamar mai jira. Daga bakin kofa ya ya mika mata abincin. Hannu tasa ta karba tana mashi ina kwana ciki2 ya amsa ya juya ya nufi motarshi har yayi ribas tana tsaye bakin kofa tana kallonshi kamar wani bakonta, Hakan yasa shi fitowa ya kalleta daga can yake tambayarta “kina bukatar wani abun ne”? Batace dashi komai ba ta shige ciki ta turo kofa, Tsaki yaja ya shiga motar ya fice, ©Khadeeja Candy [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* Na Khadija Abubakar Alkali 4~ cire hijab din tayi ta janyo abinci gabanta ta shiga budawa farfesun kaji ne sai kwai da plantain da dankali soyayyu sai flas din tea da bread, Tsuwara abincin ido tayi tana wasu-wasin cin dan gani take kamar wani abu yasa mata ciki dan har yanzu zuciyarta bata gama aminta dashi ba. Tashi tayi ta dauko raguwar fruits din jiya ta shiga ci dan tafi aminta dashi sama da dafafen abincin, Can kuma naji ta sauke ajiyar zuciya ta janyo abincin tayi bismillah ta fara ci”””’ Sai kusan azahar Abdullah ya samu kanshi kacar ya iso gida saboda gajiya ko part din momi bai biya ba ya wuce part dinshi yana shiga ya fada bathroom ya sakarwar kanshi shower bayan ya kare wankan ya dora alwala sama ya fito, Wardrobe ya nufa ya fiddo kaftani ash color yasa ya feshe jikinshi da body spray, Ya shinfida carpet ya kabarta sallar a’zahar,””’ 2:40 ya fito dakin rike da hulla dsame color da kayan shi bayan ya fesama jikinshi wani turare mai tattausan kamshi. Ya shafe fuskarsa da wani mai2 maiko sajenshi sai sheki yake part din mummy ya nufo koda ya shigo parlor bai tarar kowa ba kai tsaye dining area ya nufa saida ya bude kololin dake gurin yaga abunda aka dafa sannan ya nufi kitchen ya dauko wasu madaidaitan kuloli ya shiga zubawa, Sai sauri yake yana yi yana kallon stairs. kar mummy ta fito dan ko ta tambayeshi bai san amsar da zai bata’ba. Yana karewa ya dauki abincin ya nufi mota, Yana shiga ya mata key yayi horn maigadi ya bude mishi gate. Kai tsaye gidan ya nufa yana isa ya fito motar ya bude ma kanshi gate, Bayan ya shiga da motar ya dawo ya rufe gate din. Dawowa yayi gurin motar ya bude ya dauko abincin sannan ya nufi cikin gidan. Yana taba kofar yaji’ta rufe tsaki yaja ya aje abincin ya shiga knocking, Nan ma sai da yayi har ranshi ya bace sannan ta bude, “sannu da zuwa” bai amsa mata ba ya duka dauki abincin ya ratsa gefenta ya wuce, Juyowa tayi laba2 ta xauna a kujer dake facing din tashi, Tsitt parlor yayi daga ita har shi babu wadda yace wani abu ita sai tsoron take tayi mishi magana yace mata wani abu sai satar kallonshi take, Shi kuma ya kafe ta da ido ala dole ita zata fara mishi magana. Can dai ta dago cikin tsoro ta kalleshi “ina wuni”? Jin yayi kamar karya amsa mata kuma wata zuciyar ta hanashi saida ya dauke kai sannan ya amsa “lafiya kalau ga abincin ki nan ” “to na gode Allah ya saka da alkhari” Tashi tayi ta dauki kulolin ta kai saman dining ta aje, Ta juyo ta nufi hanyar bedroom bata karasa shiga ba ya kirata “ke” juyowa tayi tare da amsawa “na’am” ya nuna mata kujerar data xauna dazu “zo nan ki zauna” Ba musu ta nufi kujerar ta xauna gabanta sai faduwa yake, Ba tare daya kalleta taba yace “ina son ki fada min wacece ke”?!!! Waje tayo da ido ta hade wasu yawu da karfi ba shiba ko ni da’nake dauko muku rahoto saida naji wucewar su, Kallon mamaki yayi mata suna hada ido tayi saurin kawarda fuskarta. tana maida numfashi, Shiru tayi bata ce dashi komai ba har na wani lokaci nan ya kalleta yace “kinji abunda nace or shall I repeat”?! Kara yin kasa tayi da kanta Muryar ta na rawa ta shiga mishi magana “su…na…na As…ma’u ni yar…kano ce sunan mahaifina shu’aibu amman ya rasu mahaifiya tama ta rasu a hannun kawu na nake shi yake rikona” Jinginawa Abdallah yayi jikin kujerar yana kallonta yace “to mie kika zo yi garin nan”? Sai a lokacin ya ta kalleshi “ina nake wane garine nan”? “kina cikin garin sokoto” kasa tayi da kanta tana rabon ido ta shiga zancen zuci “na shiga uku har sokoto ya kawoni” a fili kuma tace “babu abunda ya kawoni zuwa kawai nayi”, Gyara zamashi yayi yace “amman kince min bakida kowa nan garin kuma ke baki ma san inda kike ba ko kin manta”? “a’a wlh banida kowa nan kuma bansan kowa ba kawai dai nazo ne dan na samu tsiratarda rayuwata daga hadarin nake cikin kuma ina tambaya kar kyauyen da nake ne ba gariba” wani kallo yayi mata “to mie ya faru dake har kika zo nan dan tsiratarda rayuwarki kuma su wanene suke binki har kike cewa zasu miki fyade”? Kawarda fuska tayi tana tunanin wace karyar zata sake yi mishi ta tsira, Bata ankara ba tace yace “kodai karya kike min ne”? Tashi tayi tsaye da sauri tana kallonshi “wlh ba karya nake ba da gaske nake fyafe suke son su min kuma su kashe ni” Kara lan kafarda kanshi yayi jikin kujerar ya dora hannunshi saman bakishi ya nuna mata kujera, Da sauri ta zauna kamar mai jiran umarni tana mayarda numfashi da karfi,, Jin batace komai ba sai kalloshi take yasa yace “ina jinki baki bani amsa ba har yanzu”?! Saida tasa hannunta daya cikin dayan ta matse sannan ta shiga magana “ni yar jarida ce ina aiki da jaridar Corner news shine wata naje gidan su kawata babanta dan siya sane…….” sai kuma tayi shiru tana murzar hannun nata, wani kallo yayi mata na rashin yarda “ina jinki cigaba”, Idonta kasa tace “muna zaune garden da ita muna fira sai aka kirata ta tashi tace na bari tazo shine data fita ni kuma saina tashi ina zagayawa cikin garden din har nakai gurin windows babanta naji yana waya yana fadin akashe mishi wani dan siyasa sai na fitarda wayana nayi recording ba tare da yasaniba na fito….” kallonshi tayi ganin ya tsareta da ido yasa ta cigaba gumi sai karyo mata yake.. “kwana biu da faruwar hakan sai aka kashe dan siyasar ni kuma sai na fadawa manager mun har na nuna mishi record din shine wani daga cikin abokanin aikina, yaje ya fadawa baban kawar tawa shine shi kuma yasa akashe ni yanzu kusan wata 2 kenan sunason kasheni basu samu dama ba……….” nan maganar ta’ta ta sarke Murmushi Abdallah yayi bai bari ta ganiba sannan yace “har yanzu baki fada min abunda ya kawoki sokoto ba ya akayi kika taho? kuma ya sunan dan siyasar da aka kashe”?,,,,,,,, © Khadeeja Candy [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* Na Khadija Abubakar Alkali 5~ kawar da fuska tayi ta bata rai kamar zatayi kuka “sunan shi Alhaji3 umar dan jariri” shiru tayi Abdullah yace “ina jinki ” ” kuma da na gudo daga kano jos na fara zuwa gurin yayan mahaifina can ma ban tsiraba dan bansan wadda ya fada musu ba kawai sai naga ana nemana suka rika nuna ni a tv suna bada cigiyata da picture dina da number waya wai duk wadda ya gannin ya kira su, Da gurin police Haka yasa duk inda nabi sai a rika nuna ni shine yayan mahaifina yace na gudu naje duk inda nasan zan tsira haka naje tasha na shiga motar kebbi to kuma ka min mukai yan fashi suka tare mu nan ne kowa ya gudu nima na rika har na shigo wannan kyayen sai kuma na hadu da waddannan mutane da akasa su kashe ni…………” Tashi yayi zaune daidai fuskarshi dauke da tambayoyi yace “amman kamar baki isa ki fara aikin jarida ba dan a yadda na fahimta bazaki wuce 18year ba kuma…….. ” bai karasa ba ta tashi tsaye da sauri tana Girgirza kai “a’a wlh shekarana 24 jikina ne haka saboda ni bafulatana ne…..” kawarda fuska yayi yana motsa baki kamar mai cin wani abu, tana ganin haka ta koma ta zauna fuskarta dauke da damuwa dan gudun take karya ganota gashi kuma bata san wace tambayar zai sake jefo mata ba””””” Shidai Ya dadi a haka mamaki ya cikashi sai zancen zuci yake “to ke wannan bazaki bari na TV tambayar tawa ba hmm anya kina da gaskiya kuwa” Can kuma ya tabe baki ya tashi tsaye tare da saka hannayenshi aljihu yace “to nidai zan wuce in kinada bukatar wani abun ki fada min”? Wani sanyi taji ya ziyarci zuciyarta jin yace zai tafi dan dama tambayoyin sun isheta, kasa2 ta kalleshi “a’a bana bukatar komai na gode sosai Allah ya saka da alkhairi” Ido ya dan tsura mata sannan yace “amin” ya fice, Badan ya aminta da abunda ta fada mishi ba duk da zuciyarshi nason aminta da ita amman yana ji a jikinshi akwai abunda take boyewa,,,,, Tana jin tashin motarshi ta tashi da sauri ta rufe kofar ta fada saman kujera zauna tana dariya ta dafe zuciyarta “hmmn ashe na iya tsari hahaha2”,, Sauke ajiyar zuciya tayi tayi fari da ido “hmm wlh na iya acting kamar yar film ko wata marubuciyar littafin” dafe kanta tayi tana murmushi “OH my dear god na gode maka da ka bani damar yin haka Allah ka kara tsiratar min ds rayuwa kasa wannan mutumin ya rike ni da gaskiya kada ya cutar dani” kwasar dariya ta shiga yi tana yiwa Allah godiya,,,,, ………………washe gari da wuri2 Abdullah ya kawo mata abun karin tana ganinshi ga banta ya fadin ganin yazo da sassafe haka ta dauka ko wani abun ne, Shidai komai baice mata ba bayan gaisuwarta daya amsa. Ya shiga motarshi ya dauki hanyar office, Karfe 1:30pm ya tashi aiki direct kasuwa ya nufa kayan abinci ya siyo da fruits mai dan yawa, Sannan ya nufi welcome to China restaurant yayo mata takeaway ya hado da kayan sanyi drinks sannna ya nufo gidan, Wannna karon knocking daya yayi ta bude mishi a bakin kofa ya tsaya ya mika mata kayan “ga takeaway nan kuma ga wasu kayan abinci nan ya siyo miki kuma akwai wasu a kitchen in case kika ji yunwa kamin na zo saiki dafa tunda akwai ruwa dan ba koda yaushe zaki rika ganina ba ina da aiki a office ba hutu yanzu” Kallon tsoro tayi mishi “mie hakan ke nufi”? Yace “hakan na nufin a rana so daya zaki rika ganina”, kai kawai ta daga mishi ya juya ya shiga motarshi ya dauko hanyar gida, Yana isa yayi horn maigadi ya bude mishi gate parking space ya nufa yana yin parking ya saki murmushi jin muryar Sulaiman, Da far’ah ya fito motar ya nufo parlour……. Yana shiga ya saki dariya da sauri Sulaiman ya juyo suna hada ido ya tashi shima yana dariya suka rumgume juna, Abdullah ya kalleshi yace “humble yaushe ka dawo”? “jiya na shigo gari na kira wayarka ai ban samuba” “kasan matsalar Nigeria network din ma fama ake dashi ya hanya”? Ya karasa magana tare da zauna, Shima zaman yayi “lafiya kalau ya aikin naku”? “aiki yana nan sai abunda yaci gaba ba sauki” Sulaiman yayi dariya yace “na gani ai dan tun 12 muke fira da mummy naga baka dawo ba nace aikin ne kila ba sauki” Kasa Abdallah yayi da kanshi yana satar kallon mummy da sai yanzu ya ganta, Mummy tayi murmushi “au kinya kake ji yanzu kuma”? Dagowa yayi yana dariya “Allah mummy ban gankiba sai yanzu”! “to ya za ai ka ganin kaga Sulaiman” dariya suka har mummy, ……………………Sun dade suna fira dan Sulaiman gidan ya wuni sai kusan magariba yabar gidan””””””””””””” *** *** *** *** *** *** *** Abdallah na tsaye gurin wata katuwar rigiya, rizabuwa saiga wata matashiyar farar tunkiya ya nufo shi tana shissheka. Tana kawowa gurin shi da sauri Abdallah ya debo ruwan rijiyar ya zuba mata a wani koko nan da nan ta shiga sha babu sassauci, A hankali ya risina yana shafata, Can ta dago ta kalleshi yana mata murmushi ta shige jikinshi. Hannayeshi yasa ya dauke yana tashi tsaye ya hango wani mutum kamar buzu tafe saman jaki ya nufo shi fuska hade, Yana kawowa ya kalli Abdallah yace “wannan tunkiyar tawa ce ni na sayeta” yana cewa haka yasa hannun ya tura Abdallah cikin rijiyar!!! Shuuuuu kakeji kamar an sako abu daga sama,,,, …………………a firgice Abdallah ya farko numfashinshi na kokarin daukewa, da sauri ya taba bed din daya ke kwance yaji gado ne “inna’lillahi wa’inna ilaihi’raji hasbunallahu wani-imal’wakil” abubda ya furta kenan sannan yakai hannu ya kunna bedside lamp ya kara tabbatar da daki yake sannna ya sake yace “Alhamdulillahil lazi’ahyana ba’adama a matana wa’ilail-nushur A’uxubillahi minasheidanin’rajin” saukowa yayi ya dawo bakin gado ya zauna yana sauke ajiyar zuciya,,,,,,, ©Khadeeja Candy [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* Na Khadija Abubakar Alkali 6~ ya dade zaune a haka yana ganin mafarkin kamar a fili ya faru bachi ya gagara daukar shi, har aka kira asuba, Sannan ya tashi ya nufi bathroom saida yayi wanka sannan ya dora alwala sama ya nufi masallaci, Karfe 7:30 ya shigo gidan part din mummy ya fara zuwa saida ya gaisheta sannan ya nufi part dinshi, 8:30 ya sake nufo part din mummy bayan ya shirya cikin kananan kaya dark blue jean with black T-shirt koda ya shigo suna dining area zaunawa yayi a kujerar shi suka karya tare, Sannan ya fito ya nufi office. Yau ma kamar kullum aikin ba sauki hakan yasa shi kashe wayarshi dan kar adameshi, Bayan ya kare duba marasa lafiya ya shiga surgery kusan mutun hudu yayi theatre sannan ya fito ya cigaba da duba wasu marasa lafiya, Sai 4:30pm ya tashi aiki…….. A gajiya ya nufi parking space yana shiga motarshi ya mata key ya kama hanyar gida, Yana isa yayi horn maigadi ya bude mishi gate, Part din mummy ya nufa a garage ta yayi parking. Yana fitowa suka hadu da ummul-khairi da far ah tace “big big big bros sannu da zuwa” Murmushi yayi “yauwa uwar yawo ina aka fito”? Dariya tayi tana boxing da hannuwa “haba bigger than us haka yanzu humble yace min shikenan ni kullum nice kafar yawo”? Part dinshi ya nufa yana dariya “to ai gaskiya aka fada ina kika ga humble”? ” bai dade da tafiya ba gurin ka ma yayi baka hadu dashi ba”? Juyowa yayi “yau kike magana ko jiya”? “yanzu nan iyaka 38-35 minutes yace ya kira wayarka kashe kuma yana son magana dakai shine yace bari yaje can ya sameka tare ma da hannatu suka fita” “ina yace miki xaije”? “cewa yayi gidan ka zaije dan yasan ka isa tashi aiki yanzu” da karfi Abdallah yace “what!!!? Da gaske”? “wlh da gaske lafiya”? Da sauri ya nufi garage yana “hasbunallahu wani’imalwakil” da sauri ummul-khairi ta biyo shi “lafiya mie ya faru”? Bai tsaya bata amsa ba ya shiga motarshi yayi mata key yana fitowa garejin da karfi yayi ribas, Tun kamin yakai gate ya shiga horn maigadi mai gadi na bude mishi gate ya hau t-t kamar zai tashi sama …………………Cikon kankane lokaci ya isa gidan saboda gudun da yake, Yana ganin gate din gidan bude gabanshi ya fadi, koda ya kunnu kai cikin gidan yaga motar Sulaiman, Ko parking din kirki baiyiba ya fito ya nufi kofar. Tsaye ya tararda shi bakin kofar kanshi kasa yasa hannayenshi aljihu, Ajiyar zuciya ya sauke ganin kofar rufe. Ya karaso kusa dashi jiki ba kwari “humble lafiya dai kake ne mana haka”? Kallonshi Sulaiman yayi fuskar babu yabo ba fallasa “naje gida ban gan kaba kuma nasan ka tashi aiki shiyasa nace bari nazo nan wani abun ne”? Kai ya Girgirza “no yanzu ummul-khairi take fada min kana nemana” wani kallo Sulaiman ya watsa mishi “ae haka ne” “abdallah ya dan kawarda fuska “muje ko”? Ido kawai Sulaiman ya tsura mishi baice dashi komai ba kuma bai motsa daga inda yake ba har saida abdallah ya dago suka hada ido, “iya zaman da mukayi dakai bansan kayi aureba kuma baxai yiyu kayi aure ban saniba ko wani daga cikin family ku bai saniba, Dan haka ba aure kayi ba kuma ban sanka da neman matan banza ba abdallah”! Wani irin faduwar gaba yaji da sauri ya dauke kanshi daga kallon da yake mishi yace “mie ka gani hala wani abun ne”? Saida ya karaso kusa dashi sannan yace “mie yasa ka kawo mace gidanka mie ya hada ka da ita”? Abdallah hade numfashin dake son fito mashi yayi “macce kamar ya mace ka gani”? “ba makaho bane ni kuma abunda na gani zahirine kamar yadda ita ma ta ganni”! Soso kanshi abdallah yayi “amman… Wlh humble bana neman mata kafi kowa sanin haka” “to ita wannan mmie take yi anan mie ma ya hada ka da ita da har zaka kawota nan ka aje”? Dafashi abdallah yayyi “taimako take nema humble tana cikin matsala ne shiyasa” Sulaiman yace “kasan wacece ita da har zaka taimaka mata”? © Khadeeja Candy [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* Na Khadija Abubakar Alkali 7~ shiru abdallah yayi har na wani lokaci yana shafar sajeshi can ya kalli Sulaiman yace “ae nasan ta nasan wacece ita”! kallon tsoro Sulaiman yayi mishi ya Girgirza kai “kuma ka ajeta abdallah what is wrong with u kasan abunda ka aikata kuwa”? Nan gaban abdallah ya dan fadi jin abunda Sulaiman yace amman saboda dakewar zuciya irin tashi sai ya nuna bai damuba “to minene aciki nifa taimako nayi”, Tabe baki Sulaiman yayi ya nufi motarshi ranshi a bace ya fisgi mota yabar gidan, Yana fita abdallah ya shiga buga kofar yana “bude nine bashi bane ya tafi kinji asma’u”? Knocking ya shiga yi yana lallabata, tun yana bugawa a hankali har ya fusata ya dinga jibgar kofar yana kwala mata kira amman shiru ko motsinta bai jiba balle alamun bude mishi, Yana haka aka kira sallar magariba. tsaki yaja ya nufi motarshi Nan ma ya dade cikin motar yana kallon kofar wai dan ko zata bude, amman tsit!! Haka yasa shi yiwa motar key ya fice, ……………… Saida ya tsaya a masallacin dake unguwar su yayi sallah sannan ya nufo gida, Yana isa yayi horn aka bude mishi gate ko parking baiyi ba yaga mummy da hannatu, maryam da ummul-khairi sun fito sun nufoshi hankalinsu a tashe, Shima haka ya fito motar ganin yanayin fuskokinsu gabanshi sai faduwa yake a ranshi yana “Allah kasa dai ba humble yace musu wani abun ba” a fili kuma yace “lafiya dai mummy na ganku haka”? “ina fa lafiya abdallah ummul-khairi ta fada min hankali tashi kabar gidan nan kuma na kira wayoyinka duk a kashe gashi kuma hannatu tace Sulaiman ya kirata har zai fada mata wata maganar kuma ya fasa shine duk hankalina ya tashi “, rufe motar abdallah yayi ta zagayo gefen da take ya rungume ta yana murmushi yace “hankwantarda hankalinki mummy babu komai sai alkhari” ummul-khairi tace “to mie yasa ka fita hankalinka a tashi”harara ya watsa mata “in kina gulma ta saina fasa miki bakin nan”, Mummy ta ture mishi hannu “ai gaskiya ta fada ba gulma bane fada mun ina kaje kuma mie ya rada maka hankali”? Sosar kansa ya shiga yi yana yan kame2 “am…..mummy…… Humble wasu katardu zai karva gareni kuma masu muhimmanci ne shine na dauka koya wuce bai karba ba shine hankalina ya tashi” Ajiyar zuciya mummy ta sauke “to ai alhamdulillah wlh ni duk hankalina da ya tashi” Rika hannunta yayi suka nufi part dinta yana fadin “to ya kwanta mummy muje ki huta uwar yawo duk ta rikita min ke”, Su hannatu da maryam suka rufa mishi baya suna dariya, Ya dan dade yana fira bayan yaci abinci tare dasu mummy saida ta fara jin bachi sannan yayi mata saida safe ya nufi part dinshi, *** *** *** *** *** *** Washe gari koda 8:00 tayi Abdallah ya shirya, A gaggauce ya nufo part din mummy yana karyawa ya nufi office. ………………aiki kan ya shashi babu sauki sosai yaso ya samu dama ya takaita aiki amman ina, Sai kusan 3 rana ya tashi aikin. Azurce ya nufo gidan shi dan aikin kawai yake amman Asma’u tana cikin kwakwalwarshi tana yawo dan ya rasa gane kanta gashi maganar Sulaiman ta tsaya mishi a rai, Wannan karon bakin gate yayi parking bai shigo da motarshi cikin gidan ba Yana shigowa ya nufi kofar koda ya taba ya jita rufe kiran sunnata yake yana buga kofar a hankali amman shiru ko motsinta babu, knocking ya shigayi babu albarka ganin bata bude ba yasa dole ya nufi motarshi ya dauki hanyar gida, Yana isowa gida kai tsaye part dinshi ya nufa. Bathroom ya fada yayi wanka da tunanin Asma’u ya fito bathroom din kanshi a kulle yake da tunanin abunda ta boye mishi ga maganganu Sulaiman sun tsaya mishi ga gajiyar aiki duk sai abubuwan suka chakude mishi, Haka ya nufi wardrobe ya dauko short da jallabiya yasa, Gefen gado ya samu ya dan gincira nan da nan bachi yayi gaba dashi, “””””””””””””” 4:00 na bugawa alam din wayarshi ya fara aiki tashi yayi yana jan tsaki dan kwata2 bachi bai wuce 10-15 minutes ba bathroom ya nufa danyi alwala, Bayan ya kare sallar ya nufo part din mummy da sallama ya shigo bayan ta amsa mishi ya samu kujera ya zauna, Ganin ta rike baki tana Girgirza kai ya sashi tambaya “lafiya dai mummy”? Ajiya zuciya ta sauke “hmm wlh duniyar ce nan sai a hankali” “mie ya faru mummy”? Hannatu dake kusa da mummy tace “wai wata yarinyace ta kashe mijinta ta gudu” abdallah ya dora kafa daya saman daya yana fadin “indai wannan ne ai ba yau aka fara ba wannan ma ai ya zama yayi ga yan Nigeria” maryam ta nufo shi tana fadin “ka ganta bro mai kyau da ita kuma yarinya nidai gani nake kamar karya ne dan ta Whtspp aka turo picture dinta kuma 99% labaran Whtspp duk rumours ne” Karbar wayar yayi yana tabe baki ya shiga dubawa, Ba shiri naga ya tashi tsaye rike da wayar yana zaro ido,,,,,, ©Khadeeja Candy [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* Na Khadija Abubakar Alkali 8~ da sauri ya kalli maryam yace “da gaske kike abunda kika fada”? Kamin tayi magana ummul-khairi tace “bros ka santa ne?” kai ya Girgirza yana shafe gumin daya karyo mashi “a’a” Matsowa tayi kusa dashi da fuskar zolaya “to mie yasa naga kamar hankalinka ya tashi”? Kawarda fuskarsa yayi yace “a’a kawai naga tana da kyau ne kuma yarinya da ita haka ace tayi kisa”! Maryam tace “wlh nima dai shi nagani kasan mutane da sheri yanzu haka kagene” “aa ba wani kage mutane yanzu sai a hankali basu dauki kisa komai ba maybe gaskiya ne” cewar hannatu, Maryam tace “to mie yasa zata kashe mijinta inhar gaskiya ne”? Hañnatu taja tsaki “mtssw ke duk yadda ake fadin abu bazaki ganiba aisai kiyi ta gardamar” Abdallah da tun dazu ya kasa samun sukuni ya kalli maryam yana kokrin boye abunda ke ranshi “mie sunanta maryam kuma ina ne garinsu”? “sunan ta saleena kuma yar garin kaduna ce ayadda sukace fa”! Wani dakan 3’3 gaban abdallah ya shiga yi kamar zai fito, Dan ya kasa gane abunda yake ji da kuma gani tsayuwa ta gagareshi yana har yayi shirin zaunawa kuma ya fasa ganin yadda mummy take kallonshi, Kofar fita ya nufa hannatu da maryam na mishi magana bai jiba saida mummy ta kirashi “abdallah?” a firgice ya juyo “na’am mummy” “bakaji hannatu na maka magana bane”? “banji ba mummy cos hankalina yana wani gurin” kallonsu yayi kasa2 “sisters ku bari na dawo sai muyi magana”, Duk suka daga mishi kai suna mishi Allah ya tsare, ………………… Part dinshi ya nufa keys kawai ya dauka ya nufi gurin mota ko kayan jikinshi bai chanja ba, Hankalinshi a tashe ya shiga driving sai wani fisgar kai yake kamar wadda yake mishi majiyar, Kacar ya isa gidan yan ta sake sake aranshi.wata zuciyar na fada mishi anya ba turo ta akayiba dan ta shafa maka kashin kaji’ba, Bakin gate yayi parking ya fito ya nufi cikin gidan, Babbar kofar ya nufa Yana ta6a wa yaji’ta bude, haka ya kunno kai cikin parlor suna hada ido ta’tashi tsaye da sauri, Ganin yanayin fuskarshi ya tabbatar mata daba akwai wani abu dan bata taba ganinshi cikin irin wannan yanayinba duk da ba wani saninshi tayi sosaiba. Amman ta tsorata sosai ganin yadda ya hade fuskar, Yanayin forward tayi backwards gabanta sai faduwa yake, Tana leken bayanshi da kuma hannu dan a zatonta yana tare da makami ko wasu, Cikin tsoro ta shiga mishi magana “ya fada maka ko? yace maka wani abu ko?” abdallah a fasace yace “mie yasa kika min karya mie yasa kika boye min kinsan kinyi kisan kai kuma kike ce na baki masauki na cece rayuwarki dan kawai ki jefa tawa rayuwar cikin hadari”? Tunda ya fara maganar take yamusar fuska kamar mai shan madaci, can kuma ta kawarda fuskar jikinta sai rawa yake numfashinta na fita da karfi kamar mai shirin haihuwa, Tsawa abdallah ya daka mata ganin bata da niyar magana yayo cikinta “answer me”!!! Hawayen dake makale a idonta suka zubo Ba shiri taa fara magana “daman nasan wannan ranar zata zo ranar da asirina zai tonu ranar….. ” bata karasa maganar ba tayi shiru saka makon hannun da abdallah ya daga mata “babu produce ko director anan gurin ba film muke yiba dan haka bana son ki sarra famin halshe amsa kawai nake da bukata”,,,,,,,, ©Khadeeja Candy [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *Na Khadija Abubakar Alkali* *9*~ ja tayi da baya da sauri jikinta sai rawa yake “dakata zan fada maka gaskiya” sai kuma tayi shiru tare da hadeye yawun da suka cika matan baki, can kuma Ta kalleshi da raunaniyar fuskara tace “wallahi badan inaso na kasheshi ba bada son raina ba sherin zuciya ne!” wani irin bugawa gaban Abdallah yayi ba shiri ya fadi ya zaune yana “la haula wa’lakuwati illa billah da gaske kin aikata kenan?” hawayen dake makale a idonta ne suka fara zuba. Kai Ta daga mishi “na aikata tun lokacin dana aikata nake gudu” girgiza kai Abdallah yayi “mie yasa kika aikata kisa kinsan mie kisan kai ke nufi kuwa?” wasu zafafan hawaye suka zubo mata “ada kan ban saniba amman yanzu na sani babu riba aciki sai asara da danasani wallahi nayi nadama” “wai da gaske kike kodai wata karyar ce kika sake min ko kuma shari aka yimiki?” Kallonta ya sakeyi “kinyi kankanta da aikata kisa plz tell me the truth?” zubewa tayi kasan gwauwoyinta Ta nuna mishi hannayenta “na aikata da hannayena na kasheshi nice na aikatana kashe mijina” Kallon tsoro yayi mata “mi yasa kika kasheshi mie yayi miki?” “saboda bana sonshi name fadawa iyayena bana sonshi sukace ko zan mutu saina aurenshi kuma shima yasan bana sonshi amman ya dage sai ya aureni ya nunawa iyayena kudi suka auramai ni duk da inada wadda nake” lumshe ido Abdallah yayi ya sauke ajiyar ya dade a haka sannan ya kalleta yace “wacece ke?” dago kai tayi ta kalleshi ido cikin ido “suna *SALEENA* *IBRAHIM* ni haifanyar garin kaduna ce uwa da uba ciki na girma ibrahim mai ice shine mahaifina sa na ar saida ice itace sana ar mahaifna mu talakawa ne sosai dan wani lokacin. Abincin da zamuci wahala yake mana nice ta farko a gidanmu kuma ni kadaice macce kannena hudu duk mazane ina ajin farko a kyau shiyasa mazan unguwarmu duk hankalinsu yana guna har aka min lakani da star girl kowa ya taso ni zakaji yace yana so musamman yayan manya duk da yake ni talakace kullum burin mahaifina na auri mai kudi ko Allah zaosa mu fita cikin talaucin da muke ciki hkan yasa lokacin da Salman ya fito yana sona mahaifina yayi saurin amincewa kasan cewar mahaifinshi dan majalisa ne kuma shima babban Dr ne lokacin da ya tunkareni da maganar sai naga nuna mishi akawai wadda nake soyayya dashi saida shi kuma wadda nake soyayarda dashi ba mutunmen kirki bane hakan yasa mahaifina yaki aminciwa dashi ya auramin wadda bana so shima salman din na fada mishi bana sonshi amma. Ya dage shi sai yayi aureni wai ai shi tunda yana sona babu matsala zai iya hakuri da duk abunda zanyi mishi har lokacin da zanfara sonshi” ajiyar zuciya ta sauke tare da share hawayen dake zubo mata da gefen hannunta Sannan ta cigaba “baiyi zaton kiyayyar da nake mishi takai haka ba da bazai aureni ba. Kudi kan ya zuba su gurin aurena dan har gida saida ya saima mahaifina kuma komai shine yayi kayan dakina ma da tufafina daga dubai aka hado su, tunda mukayi auren ban taba kyautata mishi ba ko girki bana mishi hakan yasa ya dauki yar aiki komai cikin gidan itace takeyi iya kacina naci nasha nayi bachi, tunda nazo gidan kullum burinshi ya za aiyi yakai jikina ni kuma ban taba bashi hadin kai ba hakan yasashi kawarda kai ya daina ma nuna min, bazan manta. Ranar wata lahadi cikin drink yasa min maganin bachi ina sha na buge da bachi hakan ya bashi damar cinma burinshi akaina. Ni kuma tun daga lokacin naji. Tsanarshi ta kara shiga raina kullum burina ya zanyi na rama abunda yayi min shi kuma tun daga lokacin in banda nunamin kauna babu abunda yake nuna min akwana a tashi aka kwashe wata 3 babu abunda ya dake shiga tsakaninmu ba sai wata rana da dare ya shigo dakina ya zauna gefen gadona yanuna min shi hakkinshi yake so na bashi kallon rainin hankali nayi mishi naja tsaki hakan yasashi yin cikina da masifa waiina cin amanarshi ina Tauye mishi hakkinshi shi yadda gaji da hakuri xai iya jure komai amman banda wannan har yake tambaya na wace irin kiyayya nake mishi haka ne kallinshi nayi cike da takaici nace tsana Ta karshe nake maka wadda ko kasheka zan iya’yi dariya yayi yace Tho. Bismillah mana saiki aikata nake gani kamar umarnin shi nake jira na tashi cike da jin haushi name nufi kitchen na dauko wuka name nufo parlour” © *Khadeeja Candy* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *Na Khadija Abubakar Alkali* *10* “kai tsaye na kunno kai cikin dakin ina shiga na ganshi kwance rairam fuskarsa na facing dinna sai murmushi yake. tsaye nayi na cige baki wata zuciyar na ingizani inajin bazan iyaba ina haka ya dago ya kalleni yace bismillah mana zoki kasheni wata harara na watsa masa nace gani kake kamar bazan iyaba ko? Wlh zan iya ai katawa kara gyara kwanciyarsa yayi yace nifa ke kawai nake jira a shirye nake haka na rumtse ido nayi cikinshi da wukar ina kawowa kusa dashi ya yinkuro ya rikemin hannun ya murde ba shiri na sake wukar yana ganin haka ya daukeni ya jefani saman gado ya biya bukatarshi yadda ranshi yake so, ya tashi yana dariya yace indai haka nake so shi bashi matsala indai har sai yayi kokuwa dani zai samu biyan bukatarshi dan ya gane har yanzu ina tare da kuruciya yana cewa haka ya nufi kofa sai kwasar dariya yake yana saleena kenan. sosai abun yaban haushi haka na dauki wukar na nufeshi ido rufe na yanka masa ita a baya da sauri ya dafe gurin ya juyo yana min kallon tsoro nan take ya kwanke min fuska da mari biu ni kuma banyi wata2 ba na daba masa wukar a ciki naja har kasan mararsa” tana kaiwa nan Abdallah ya tashi tsaye da sauri yaja baya ya a mata kallon tsoro “haka zuciyarki tayi tauri? Ki kashe mijinki saboda kiyayyah” fashewa tayi da kuka “wallahi nayi nadama kuma nayi da nasanin aikata haka tun lokacin nake gudu ina ganin ya fadi na fito gidan da gudu mai gadi na ganina ya shiga tambayana lafiya ban tsaya bashi amsaba na bude gate na fito da gudu na nufo gidanmu duk da yake akwai tazara haka nayita gudu har na kawo gida a wahale. Ina isowa naci karo da mahaifina yana ganina ya koma cikin gida da sauri ya turo kofa. Kiran sunanshi na shigayi ina buga kofar daga can ciki ya amsamin da muryar kuka waishi bazai budeba wai nasom shima na kasheshine kuma na nemi wani uban bashi ba nace mas mamana nake son gani kamin yayi magana naji muyar mahaifita ta fashe da kuka kannenama suka kama daga nima naji kuka yaxo min mai karfi na jingina jikin kofar ina jin kukan mahaifiyata tana jin nawa muna haka naji an kira abbana da sauri ya dauka yace ae ranka ya dade wlh haka ne gata nan ma tho saikun iso inajin haka na shiga kiran mahaifina ina abbah bude min mama ce ya bude min inajin muryar kamnena suna fadin baba bude mata can ciki naji muryar mamana tana cemin ki gudi saleena karsu zo su kamaki ki gudu inajin haka na saki kofar ina fadin na tafi mama na tafi a inajin muryar kannena suna kirana, cikin muyar kuka nake amsa musu inajin kamar su bude min nan mamana ta katsamin tsawa tace nace ki gudu saleena kamaki zasuyi nace mata mama ina zanje tace duk inda zaki tsira da rayuwarki Allah ya tsareki tho. Kawai nace mata na nufi bayan gidanmu ina gudu har na kai bakin gulbi. hankalina a tashe kuma cike da gajiya na isa t_t sai rangaji nake kamar wadda tasha giya, Cikin sa ah wani mai mota yayi parking ya tambaye lafiya nake nan nace masa dan Allah ka taimaka min da girman Allah yace mie ya sameni nan na kasa bashi amsa yana ganin haka yace min na shigo motar kawai cikin sauri na shiga ina mishi godiya. Bayan munyi nisa yace min shifa wani gari zaije nan naji wani tsanyi na ziyarci xiciyata nace mishi na yarda muje duk inda zaije. Saida ya biya ya dauki wasu abokannensa yan shaye2 nan nima ina kallomshi na gane shima haka yake. Haka mukayita keta gari har nayi bachi na farka tun inajin tsoro har na farajin na samu aminci. muna isowa sai yasa akayi parking ya kalleni yace shifa baya taimako banza yadda ya taimakeni haka zan taimakeshi na yarda na bashi kaina nan na nuna masa ni bazan yarda ba sai yace to kuwa saidai ya saukeni nace na yarda sai kuma yace ya fasa sai yayi abunda yakeso dani sai ya biya bukatarshi dani kuma ya kasheni nan yace su shiga daji dani muna shiga ya shiga kokuwa dani har ya ciremin riga yace su bashi guri zai kebanta dani nan na samu sa ar buga mashi dutse na gudu da daura gaba gurin gudun ne na hadu kai wannan shine tarihin rayuwata” da kuka ta karasa maganar © *Khadeeja Candy* . 1474463087186.jpg KHADEEJA CANDY MOBILE BLOG WELCOME TO MY WORLD YOUR COMMENTS AND CORRECTIONS ARE ALWAYS WELCOME ENJOY YOURSELF 💁 Menu Skip to content Home › SALEENA › SALEENA SALEENA Posted on September 22, 2016 by Khadeeja Candy — Leave a comment ​[8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *Na Khadija Abubakar Alkali* *11~*girgiza kai Abdallah yayi yace “haka naganki kamar yarinya ashe ke monster ce” da fusakar tausayi ta kalleshi tace “nayi nadamar abunda na aikata ban taba aikatawa ba sai yanzu kuma wlh nayi da nasanin aikata hakan” “da nasaninki bazai haifar miki da komai ba saleena kin riga kin aikata kuma kinsan duk wadda yayi kasheshi za’aiyi ko?” rumtse ido tayi wasu zafafan hawaye suka zubo mata kallon tausayi yayi mata “nadamarki bazata haifar miki komai ba saleena kin riga kin aikata” cikin kuka ta kalleshi tace “dan Allah karka kaini gurin yan sanda” idonshi cike da hawaye yace “tsoro kikeji kar a kasheki ko ashe kina son ranki shima wacce da kika kashe yana son ranshi kika kashe shi baki dauki kisan kai sai abuba sai kikaga kamar kwanciyar hankaline ko hukuma bata kamaki bazaki taba samum natsuwa ba dan rai kika kashe Allah bazai barkiba in kin tsira nan. Bazaki tsira gaban Allah ba na rasa gane mie yasa mutane basu dauki kisan kai komaiba a dokar kasa. Mafa in kayi kisa kasheka ake balle musulunci shida ko kunne kika cire sai an cire naki fada min wace riba kikaci kika kashe shi?” “babu riba sai hasara” “kin cutarda kanki saleena dakinyi hakuri da kinci riba” “lokacin idanuna a rufe suke saboda bana son shi sai yanxu nake gane kuskure ne na aikata.. ” kika ta shigayi mi karfi kamar ranta zai fita. Ido Abdallah ya samata kamar ya rarrasheta wata zuciyar ta hanashi. ganin batada niyar daina kukan yasashi tashi ya nufi kofar fita dagowa tayi ta kalleshi.”gurin yan sanda zaka kaini ko?” tsayawa yayi cak ya rumshe ido kamin ya juya yace “a’a bazan kaikiba ba kuma zan fada musu ba sai inke ce da kanki kikai kanki gurinsu kin nemi na taimaka miki kuma na taimaka miki zan kuma cigaba da taimaka miki” hannunta tasa ta share hawayenta kamar ta sake masa wata maganar sai kuma ta fasa ta kawarda idonta badan ta gansu da abunda ya fada mata ba ganin haka yasa shi juyawa ya fice. Kai tsaye motarshi ya nufa yana shiga ya mata key da tunane2 ya nufi gida. Yana isa yayi horn. maigadi ya fito da sauri ya bude mishi hannu kawai naga Abdallah ya daga mishi yayi ribas ya dauki hannyar gidan Sulaiman Bakin gate yayi parking din motarshi ya fito ya shiga cikin gidan. Yana isa bakin kofar parlour yayi tsaye kamar mai tunani yafi minti biyar a haka kamin yakai hannu ya tura kofar parlour ya shiga da sallama Sulaiman na zauna saman kujera ya juyo ya kalleshi fuskarsa babu yabo babu fallasa ya amsa mishi “wa’alaikassalam” sosai jikin Abdallah yayi sanyi ganin abunda bai taba faruwa tsakaninsu ba Sulaiman baya farinciki gani shiba Kusa dashi ya xauna yana murmushin karfin hali “fushi kake dani ko abokina?” Sulaiman banza yayi dashi ya cigaba da kallon tv dafashi Abdallah yayi yace “haba abokina wlh ban san abunda ta aikata ba sai yanzu nace maka nasanine kawai dan banyi zaton abunda ta aikata yakai haka ba” wani kallo Sulaiman yayi mishi yace “kaban mamaki sosai Abdallah” “oh friend nace maka wlh bansan ta aikata kisa ba sai yanzu danni karya tayi min” nan ya kwashe duk abunda saleena ta fada mishi daga farko ya fadawa Sulaiman girgiza kai Sulaiman yayi yace “ai ko babu komai kebantuwar mace da namiji bashida kyau saboda komai zai iya faruwa ballantana ita da ta aikata kisa ai komai zata iyayi” daga hannayensa Abdallah yayi cike da kyamar abunda humble ya fada “wlh babu abunda ya taba shiga tsakaninmu kafi kowa sani ni wlh zina bata taba burgeniba” shima hannu ya daga mishi “a’a nifa bance ka aikata ba ina maka illar hakan ne” Abdallah yace “tho bamu aikata ba” “tho yanzu ina take ta gudu ko?” “a’a tana nan wai kai humble ina ka samu labarinne?” Gyara zamashi yayi yace “kasan kaduna nake zama abokina aka bawa case din a hannunshi na samu labari harma da picture dinta saida abunda yaban mamaki ya akayi ta iso sokoto?” Tabe baki Abdallah yayi ya fada mishi duk abunda saleena ta fada mishi Jinjina kai Sulaiman yayi yace “wlh haka ne ita ta kashe mijinta kuma wai har take tsoron a kasheta take gudun tsira da ranta” Abdallah yace “babu wadda yake son mutuwa sai dole humble” “uhmm. Amman ai tunda ta kashe dolene itama a kasheta” Abdallah ya sauke ajiyar zuciya “haka ne kan amman ni iyayenta nake dorawa laifi mie yasa suka aura mata wadda bata so” humble ya tabe baki “tho dan an aura mata wadda bata so saita kasheshi wannan ai rainin hankaline ma” “karka manta humble kiyayyah babu abunda bata sawa yadda kasan so na sa aiyi komai haka kiyayyah take sawa” Facing din Abdallah Sulaiman yayi yace “forget the past let us face the future yanzu kasan abunda zakayi” Girgixa masa kai Abdallah yayi “kawai ka mikata hannun police ko kuma ka bani dama name kira wadda aka bawa case din yazo yadda kamata” shiru Abdallah yayi alamar tunani can take kalleshi yace “I can’t humble mai riga name mata alkawarin bazan fadawa kowaba ba kuma zan tona mata asiriba” Kallon tsoro Sulaiman yayi mishi “what are yhu saying humble?” “I mean I really just can’t humble ba laifinta bane iyayenta ne suka jamata” Cikin daga murya Sulaiman yace “tho dan iyayenta ne suka Ja mata so what kai ina ruwanka a cikin?” fuskar damuwa Abdallah yayi “nifa bazan iya ba humble am so sorry” Cige baki Sulaiman yayi yace “sorry for yourself dan da alama sonta kakeyi kuma hakan bazai haifar maka da komaiba dai matsala” “no no ni ba sonta nake ba kawai dan na mata Alkawarine” Tsaki Sulaiman yaja “Alkawarin banza ina fa ji maka tsoron abunda zaije yadda dawo karka sa kanka cikin hadari” © *Khadeeja Candy* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *Na Khadija Abubakar Alkali* JAN HANKALI ni banyi labarinnan dan ya faru da wata ko waniba dan haka in labarina yazo daidai da abunda ya faru dake ko yar uwar tho kawai labarin ne ya zama daya badan nasan abunda ya faru da ke ko yar uwarki ba hasalima wannan labari nawa kirkirare ne dan haka ni banyishi dan cin fuskar wani ko wata ba!!! *12~* dafashi Abdallah yayi “babu wani hadari kaidai kamin fatar alkhari kawai” “ni ai daman fatan alkahari nake maka koda yaushe amman dai ina mai fada maka ka bada yarinyar nan hannun police” tashi yayi tsaye tare da daga mishi kai “owk zanyi tunani akai” ido kawai sulaiman ya bishi dasu harya kai kofa sai kuma ya juyo ya kalleshi “kar wadda yaji. Maganar nan plz humble” tabe baki sulaiman yayi yace “har gobe ni amininka ne Abdallah” murmushi kawai yayi ya fice *** Kai tsaye gida ya nufo cike da sakesake aranshi part dinshi ya wuce yana shiga ya fada bathroom yayi wanka bayan ya fito ya gabatarda sallar magrib bai fito dakin shiba saida aka kira i’sha sannan ya fito nufi masalaci, 8:30 ya nufo part din mummy da sallama ya shigo hannatu da maryam suka amsa mishi tare da gaisheshi dan mummy waya take. Kusa dasu ya zauna “sisters ya kuke?” “lafiya kalau yaya ya aikin” gyara zamanshi yayi tare da busarda iskar bakinshi “da godiya ina ummul-khari?” Maryam tadan wara ido “wlh bamu saniba dan muma muma sama koda ta fita” Hannatu tace “kedai gyara maganarki kice koda ta fita bama nan dan muma bamu dade da dawowaba” tsaki Abdallah yaja “wai ku bazai dai a fada muku magana kujiba ko? Ban hakaku ywon dareba?” maryam ta xunguri hannatu “ke wlh munafukace tunfa kamin ayi magrib muka dawo ita dai ce bamusan inda tajeba” bata jira mie zaice ba ta mirgudawa hannatu baki ta nufi stairs, Mummy na aje wayar Abdallah ya hauta da masifa “haba mummy so nawa zan fada miki kibarbari yarannan suna fitar dare ko namiji ma yaya kare bare mace kinsan lokacin da dad na nan wlh basu isa su fita ko’ina ba” waya. Mummy ta muna mishi “kaga tun dazu nake ta kiranta bata daukaba nimafa bason yawon daren nakeba tun biyar na yamma tabfita nace kartakai magrib tace min tho kuma kaga har yanzu bata iso ba Allah daima yasa lafiya” Mummy na rufe baki aka turo kofar parlour aka shigo da karfi saida hannatu ta zabura. Ummul-khari ce rike da gyale a hannu hannunta daya kuma rike da baren takalme, kai tsaye ta nufo mummy tana haki “Mummy mummy…… Mummy kinsan yarinyar nan dana nuna miki poton ta wadda ta kashe mijinta na ganta gidan yaya” wani irin faduwa gaban Abdallah yayi da sauri ya tashi tsaye ba shiri ya fisgota ta baya fuska a hade “ubanwa yasa ki kaiwa dare”? Sai a lokacin Ummul-khari ta lura dashi da hannatu dake parlour ya tsunta biu ta daga tana nunashi “yauwa yaya kasan yarinyar da kaga pic dinta wlh na ganta gidanka ta shiga da gudu….. ” wani. Wawan mari Abdallah ya watsa mata da saida ta fadi ta kuma fashe da kuka “bashi na tambayekiba abunda ya saki kaiwa dare nake son ki fada min” da sauri mummy tayi kanta “haba Abdallah ka barta ta fadi abunda take son fada mana” nunata yayi da yatsa “mummy karya take dan kawai karna dake tane tace haka” nan Ummul-khari ta tashi tsaye “na rantse da Allah mummy na ganta da idona” mummy tace “Ummul-khari dagaske kikeyi?” “mummy ta mie kike son narantse miki na ganta wace irin rantsuwa kike son na miki?” mummy tace “da Allah” “tho wallahi mumny na ganta idanuna” ta karasa maganar tana budewa mummy idonta, Nan mummy ta kalli Abdallah cikin rashin fahimta da sauri ya daga mata hannun “haba mummy ya za’aiki yarda da maganarta yarinyar. Da take kaduna mie ya kawota sokoto kuma fa a picture taga photon ta har zata iys ganeta a fili kuma cikin dare.kuma ni mie na hada da ita za har zataje gidana wannan ai ba maganar kamawace ba” mummy ta koma kan Ummul-khari “karya kike ummu tho mie ma ya kaiki can unguwar?” “mummy gurin kawata hafscyG naje kinsan unguwarsu daya da yaya ina fitows gidansu sai naga gate din yays bude na dauka yana ciki saina shiga na tararda kofar bude ina shiga banga kowa ba sai… ” nan Abdallah ya katsa mata tsawa mummyvta daga mishi hannu “bata ta cigaba inajinki” “saina shiga dakin banga kowaba sai kayan mata na fito na fito da sauri na jamashi kofar dakin da parlour bayan na shiga gidan har na hw tt saina hangota zata shiga gidan hankalinta a tashe harna haskata da mota ta rufe fuskarta ds hannayenta ni kuma nayo gida da gudu wlh na ganta mummy” mummy tace “kodai mai kada itace kika gani ummu?” “tho kodai ba ita bace nidai wlh naga macce ta shiga gidan kuma a dakin shima akwai kayan mata nasawa (tufafi)” Murmushin karfin hali Abdallah yayi zaiyi magana hannatu ta tashi tsaye tana mishi kallon rashin yarda “yaya ka karyatata mana kace karya take inhar abunda ta fada karyane” nan mummy ta kamo hannayen Ummul-khari ta kalli Abdallah “yes ka karyata min ita Abdallahi ka kalli cikin idona kace karya take!!! © *Khadeeja Candy* *DEDICATED TO MY SWEET FRIEND SUMAIYA BELLO (Smmy London,Sunsun)* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *Na Khadija Abubakar Alkali* *13~* dagowa Abdallah yayi suna hada ido da mummy yaji kanshi yayi mugun tsarawa da sauri ya kalli hannatu “ina ruwanki maie na tsawa mutane baki cikin magana dake akeyi ne ko goya mata baya zakiyi kema?” hanna’tu tace “babu wannan zancen yaya wannan ma maganar wasa bace kawai ka rantse ko kuma ke mummy kije gidan ki bincika da kanki” tana cewa haka wani tunani yazoma mummy da sauri ta dauki wayarta “ina zuwa” number Sulaiman naga mummy ta danna alamar kira, Bata dade tana ringing ba aka dauka nan da nan mummy ta shiga mishi bayani “lafiya kalau wata yarinyace yanzu ummul-khari tace min ta gani a gidan Abdallahi shine nake son kaje ka bincikamin” mummy na kawai nan yayi holding din wayar can kuma ya saki yana “hello hello” kamar wadda baya ji can kuma ya kashe. Nan mummy ta sake dannan numbersa jinta tayi Switch off sosai abun yaba mummy mamaki kallon Abdallah tayi “watou zance ummul-khari gaskiyane ko har sulaiman yasan da maganar yana min rufarufa” juyarda kansa yayi “wane irin rufarufa kuma mummy dan Allah kibar maganar nan wai ya za’ayi yarinyar da take kaduna mu hadu da ita sokoto haba mummy” bata bi ta kansa ba phonebook naga ta shiga tana binciken numbers saida takai ga wata number da akan rubutawa Dsp jamil hafiz dange sannan ta danna kira Abdallah ido ya sakar mata yan tunanin mie mummy take shirin aikatawa,. bata dade tana ringing ba aka dauka cikin rawar murya mummy ta shiga amsa gaisuwar da yake yimata “Allahmdulillah tho lafiya ba lafiya ba dan Allah gidan Abdallah nake son kaje ka dubamin ko za’asamu wani abu…… Ae yanzu plz owk yana nan a gangaren tudun wada can ciki number 7 gate din gidan green ne owk na gode saina jika” tana sauke wayar ummul-khari ta jefa mata tambaya “wa kika kira mummy?” Ajiyar zuciya mummy ta saukae kamin tace “dsp jamil ne” wani irin zallo naga idon Abdallah sunyi da karfi ya furta “wht?!!!! haba mummy ohh shett” ya juya da gudu zaibar parlour “Abdallah!!!! Kiran da mummy tayi masa kenan a firgice ya juyo ta nunashi da yatsa “ban yarda ba ka taka kafarka ba kabar gidan nan matukar ba part dinka zakaba bayan nan ban Amince kaje ko ina ba” mummy nacewa haka ta nufi stairs ummul-khari ta rufa mata baya, Hak ya juyo ya zauna ya dafe kanshi can kuma naga yasa hannu aljihu ya fido wayarsa ya shiga kiran Sulaiman amman ina wayar a kashe. Jifa yayi da wayar ya daga kansa sama “ohhh god” kallinshi hanna’tu tayi fuskarta dauke da damuwa tace “yaya kenan kasan Abunda yake faruwa?” Wata. Muguyar harara ya watsa mata cin tsawa yake mata magana “karna sake jin bakinki cikin maganata karki sake samin baki cikin harka” matsewa hanna’tu tayi cikin kujera kamar zata shige jin irin tsawar da yake yimata saida ya fice sannan ta sauke Ajiyar zuciya ta lumshe ido, Baifi awa daya da fita ba mummy ta fito sanye da gyale hankalinta a tashe ita da Ummul-khari da sauri hanna’tu ta tashi tsaye tana tambaya ta mummy lafiya na ganki haka ina zaki?” cikin tashin hankali mummy tace “gidan Abdallah zanje yanzu dsp ya bugo wayar wai nazo akwai matsala” Hanna’tu tace “subhanallahi tho Allah dai yasa lafiya” Ummul-khari tace “babu wani abu mummy yarinyar nan ce aka gani insha Allah” mummy tace “tho nidai muje koma minene ai in munje ma gani” da sauri suka fita ita da Ummul-khari hanna’tu kuma ta nufi stairs, *BAYAN HOUR 2* Abdallah na zaune dakinshi ya hade kai da guiwa abun duniya duk ya isheshi ya rasa yadda zaiyi roko daya yake Allah yasa Saleena ta gudu shidai fatan shi kar’akamata, Yana haka aka turo kofar dakin akan shigo da sauri ya tashi tsaye suna hada ido da mummy yayi saurin kawarda fuskarsa. ganin hawayen dake bin fuskarta tafiya mummy take kamar mai koyon tafiya har ta kawo kusa dashi cikin rawar murya tace “Abunda ka aikata kenan Abdallah?” Sanda kansa yayi kasa ya kulle idonsa gam. Haka yake ji kamar ya rufe kunnuwansa kar mummy ta fada mishi an kama SALEENA, Bai ankaraba yaji mummy ta furta mummunan abu ” *kasheta kayi Abdallah*”? Haka yaji maganar tana mishi yawo a kwakwalwa kamar mai mafarki da sauri ya bude idonsa yana yiwa mummy kallon tsoro. Can kuma sai ya saki murmushin rashin fashinta” ban ganeba mummy mie kike cewa ne?” tassssss!!! Mummy ta wanke mishi fuskar da mari saida yaga wata jar wuta ta sake watsa mashi mari haka ta wanke masa fuska da mari hudu sannan ta durkushe kasa ta fashe da kuka, Sosai Abdallah ya kadu dan yasan duk Abunda zaisa mummy tayi mishi mari hudu ta kuma fashe yi kuka ba karamin Abubane, Dukowa yayi ya dafa mummy “lafiya mummy mie ya faru?” ganin irin kukan da take yasan ba amsa zata bashiba, sakinta yayi ya nufi part dinta cikin tashin hankali, Ummul-khari dake bakin kofa tana ganinshi tashi da sauri ta matsa nesa dashi sai kuka take cikin sanyi murya Abdallah ya tambaye “Ummul-khari mie ya faru?” cikin kuka tace “yaya ta mutu” da sauri ya tashe kunnuwansa ya rumtse ido. Dsp jamil yace “babu tabbacin haka ta mutu ko bata mutuba sai an bincika” cikin tsawa Ummul-khari tace “ta mutu mana daga ganinta kasan ta mutu” Hanna’tu da itama kukan take tace “ina gawar take?” dsp jamil yace “mun aika da gawar asibiti dan tabbatarda bincike kafin mu mika case din kotu” hannu Ummul-khari ta dora saman kai “kotu kuma?” “ae mana wannan case din babba ne” Hanna’tu tace “dan Allah dsp karka kai case din kotu” ajiyar zuciya dsp ya sauke kamin yace “wannan case din ya wuce duk yadda kike tunani Dan kinga ita ta aikata kisa anzo kuma an samu gawarta a gidansa duk da yake bamu tabbatarda hakan ba” maryam dake saukowa downstairs da kuka tace “ni yayana bai taba aikata kisan kai ba kuma wlh bashi ya kasheta ba” dsp yace “bincike ne zan tabbatarda hakan ba ni ko keba” Abdallah dai yana nan dafe da kai rumtse da ido duk abunda suke jin yake kamar mafarki,,, © *Khadeeja Candy* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *Na Khadija Abubakar Alkali* *14 ~* dafa Abdallah Maryam tayi “yaya kace wani abu mana kace bakai ka kasheta ba” Ido kawai ya sakar mata kamar wadda bai san abunda take fad`i ba “muje Abdallah” abunda dsp jamil ya fada kenan yana nuna masa k`ofa. Lumshe ido yayi ya had`iye wani k`ololon bakinciki. wai yau shine ake sakawa gaba ya aikata kisa. Ya dad`e a haka kamin ya bude ya kalli hanna’tu “je ki kula da mummy” kai ta daga masa tana zubarda hawaye. Haka suka tisa k`eyar Abdallah gaba suka fice dashi. Mummy kwana sukayi ido bud`e sai zubarda hawaye suke. tunda safe mummy ta kira wayar Sulaiman cikin sa’ah ta shiga. Yana dauka ta fashi mishi da kuka. Ta fada mishi komai. Shima ba karamin kaduwa yayi ba. Koda 8 tayi mummy da duk y`an’gidan har Sulaiman suna station. Babu yadda basuyi ba akan abarsu su ganshi. ammn aka hana su. a haka dole sukayi hak`uri har dsp jamil ya iso. Yana ganin su mummy ya gaishesu cikin girmamawa. Bayan ya bawa Sulaiman hannu sun gaisa. Guri ya nuna musu suka bayan sun zauna. yasa akan fito da Abdallah. Wasu yan sanda biu ke biye dashi a baya. Har ya zauna. Sannan dsp jamil yayi musu nuni da ido. suka koma daga bakin kofa suka tsaya. Shima bayan ya gaisa da Abdallah ya basu gurin. “yaya akayi hakan ta faru Abdallah?” tambayar da Sulaiman ya jefa masa kenan. D`agowa yayi ya kalleshi da idonsa. da sukayi wani jurfi. “ka yarda da abunda ake zargin na aikata kenan?” Kallon mamaki Sulaiman yayi mishi “haba Abdallah ya kake wannan maganar kamar bakasan da wanda kake maganaba yanzu kana ganin ko duk duniya akace ka kashe zan yarda?” Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli mummy “wlh Sulaiman bansan yadda akayi hakan ya faru ba” “Kamar yaya ka sake jikinka kamin bayani mana” “tun rabuwar da mukayi dakai na dawo gida ban sake fita ba sai kawai naji wannan abun” “tho ya akayi aka gano gawarta gidanka har yan sanda sukasan da maganar?” Nan Abdallah y kawshe duk abunda ya faru bayan rabuwarsu ya fada mishi. Har kiran da mummy tayi mishi. Matsowa Sulaiman yayi d fuskarsa kusa da fuskar Abdallah. Kamar mai rada yake mishi magana. “karka kuskura ka fada musu kasanta karka ce musu kai ka basu masauki karka nuna musu ka taba ganinta ko kasan ta aikata kisa” Busarda iskar Bakin shi yayi. “an riga am gama Sulaiman sun min tambayoyi kuma ba riga na basu amsa tun jiya” Cike baki Sulaiman yayi kamin yace “mi suka tambayeka?” “sun tambayeni kona santa nace musu ae na fada musu farkon karya da tamun harna bata masauki” “yanzu ka nuna musu kasan ta aikata kisa kenan?” “a’a ban fada musu nasan ta aikata kisa ba duk da sun min wannan tambayar” “gud tho karka kuskura ka nuna kasan ta aikata kisa” Kai kawai Abdallah ya daga mishi ya kulle bakinshi. idonshi cike da hawaye ya kalli mummy da ita hawayen take. Zaiyi magana dsp jamil ya zo tare da officers din dazu. Kallon agogon hannun shi yayi “time yayi” Da sauri Ummul-khari tace “haba jamil ba baifa fi minti 20 ba” “a k`a’ida duk wadda ya ake zargi da aikata kisa ko kuma ya aikata ba’abari aganshi sai anje kotu matukar ba lauyansa ba ko kuma wani wadda kuma ta yarda yagani ba” Tashi Sulaiman yayi ya bashi hannu “mun gode sosai jamil nasan da hakan yanzu wane mataki ake?” “Yanzu mu munkare suk wani abu da zamuyi mun rubuta komai karfe 10 dr yace muzo mu karbi Result akan ita yarinyar so da zarar mun karba zamu tura abun kotu” “kotu!!?” Maryam ta furta da karfi. “dsp na fada maka wlh yayana bazai iya aikata kisa wlh baiyi kisan kaiba” Gyara tsayuwarsa yayi “tho ai na shiga ban dauka ba bata fidda b`arayo ai zuwa kotu ba wani abu bane illah kare kai” Kara fashewa tayi da kuka ta rungume Abdallah. Shikan duk abunda ake idonshi na kan mummy daketa zubarda hawaye. Haka dsp jamil yayi sallama da Sulaiman. Bayan. Ya bawa y`an’sanda umarnin ma yarda Abdallah A mota Ummul-khari babu irin kukan da batayi ba. Tana fadin ta shiga uku tasa yayanta cikin matsala matsala data sani da bata fadaba. Har aka kawo gida kuka suke ita da Maryam mummy ma ba’ah magana. Bayan sun iso gida. Sulaiman ya karbi number dsp jamil. Har zai fice mummy tace “Sulaiman mie yasa kika boyemin wannan sirrin mie yasa kikayi gangancin aikata haka?” Dawowa yayi ya zauna yana sauke ajiyar zuciya “wlh mummy nima bansan da yarinyar ba sai ranar da naje gidan na ganta koshi badan yaso ba” nan ya kwashe duk abunda ya faru ga fadawa mummy. “kuma wlh mummy babu yadda banyi dashi ba kan ya yarda mukai yarinyar nan gurin police ko kuma na fada dangin mijin da suke nemanta amman yake waishi yana ganin tausayinta” rumshe ido kawai mummy tayi tana zubarda hawaye. © Khadeeja Candy [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* Na Khadija Abubakar Alkali *15~* guraren 11am Sulaiman ya kira wayar dsp danjin mie result din Ya kunsa. Mamaki sosai Sulaiman ya cika dashi jin abunda dsp ke fada mishi. “mun karbo result din dr kuma ya tabbatar mana da cewar anyi mata fyade kamin a kasheta kuma murde mata wuya akayi har ta mutu” “Subhanallahi wai mike faruwa ne haka” busarda iskar bakinshi yayi kamin yace “yanzu wane mataki ake?” Dsp jamil yace “ae tho kaga yau laraba zamu duk abunda ya kamata kamin jumma’ah ranar littanin kotu kawai za’ah shiga” “owk zanzo anjima” ahaka sukayi sallama. 2 da rabi Sulaiman ya dawo gidansu Abdallah mummy da su hanna’tu na zaune parlour. ganinshi yasa mummy tashi tsaye “Sulaiman ansamu wani labarin ne?” Zaunawa yayi yana sauke Ajiyar zuciya “babu wani labari mummy saima karin abun haushi” “kamar yaya?” “wai result din ya nuna anyi mata fyade kamin a kasheta” “Innalillahi wai’inna ilahi raji’un” abunda suka furta kenan. “Wai nikan mie yake shirin faruwa da yayane haka?” cewar maryam. Sulaiman yace “kaddarori ne kinsan duk musulmi ana jarrabarshi saida jarabawar ta babbata shiyasa ake son kayi imani da kaddara mai kyau ko marar kyau” Mummy kan kuka kawai take. Sulaiman yace “mummy dan Allah kibar kukan nan addu’ah ya kamata kiyi mu samu mafita” “gaskiya kan mummy kibar kuka hakan dan Allah yanzu humble mie ake ciki” maryam ta tambaya. “yanzu kotu za’ah shiga ni zan tsaya masa lauya zanyi duk abunda ya kamata ranar littanin zamu shiga” ya kalli Ummul-khari. “Ke kuma ki shirya dan kinsan dole sai an tambayeki duk abunda kika gani shi zaki fada banda kari banda ragi dan labarinki yana nuna akwai wadanda suka biyota tunda har kike ta shiga gidan a guje” maryam tace “lallaikan dan duk wadda ya aikata mata wannan abun yasan tana umguwar ne” kai kawai Ummul-khari ta daga masa. Tashi yayi yana fadin “ni bari naje umguwar ko zan samu wani abu kamin naje gurin dsp” “tho Allah ya kiyaye ya bada sa’ah” ya amsa da AMIN ya fice. tun daga lokacin Sulaiman yake jirga jirgar zuwa gidan Abdallah. Yana bincike Waiko zai sami wani abu da zai zamo musu hujja a kotu. Daga gidan kai tsaye gurin Abdallah ya nufo bayan yayi mishi tsarabar kayan marmari da drinks. Zaunawa yayi Visitors room bayan yayiwa Security magana afito masa da Abdallah. Labalaba Abdallah yake tafiya harya kawo kusa dashi. “kaine kazo humble?” Kallon tausayi yayi masa. “nine Abdallah plz seat” haka ya zauna kamar marar lafiya. Tsarabar da yayo mishi ya mika mishi “dan Allah Abdallah ka rika cin abincin dubi yadda ka koma” “humble bazaka gane bane” “Kamar ya bazan ganeba insha Allah zamu samu mafita kasan duk mai gaskiya yana tare da Allah” Ajiyar zuciya ya sauke “haka ne Allah ya shige mana gaba” “AMIN yanzu inason ka fada min iya zaman da tayi gidanka da kuma lamarin data baka bata fada maka wadda yake binta ba ko wadda yake ungurin kasheta ba?” Kawarda fuska Abdallah yayi “haba humble so nawa zan fada maka wannan maganar” “yanzu koda acikin bachi baka taba jin ta fadi sunan wani ba bancin mijinta?” kai ya girgiza “bata fada ba koma ta fada tho bansaniba tunda ba gidan nake kwana ba iya kacina na kawo mata abinci” Sulaiman yace “kadaiyi tunani” “bata fada humble” “kuma kai iya shigar da kake gidan baka taba ganin wani yana kallonka ba ko leken gidan?” Shiru yayi alamar tunani “gaskiya ban taba luraba dan banyi tunanin har lokacin akwai wadda yake biyarta ba kuma kasan bata fada mi gaskiya ba sai daga baya” Sulaiman yace “yanzu bazaka iya tuno wani abu koda kadan ba cikin labarin da taba kaba?” “ae tho tadai fada min mutunmen da ya kawota nan Sokoto ya nemi yin xina da ita taki aminciwa har yace sai yayi mata fyade kuma ya kasheta na kuma taba fada maka haka ai” Ajiyar zuciya ya sauke “haka ne yanzu dai ka shirya gobe zamu shiga kotu so u have to be strong dan zaka yita samun Tambayoyin da bakayi zato ba da kuma zargi kalakala so dole sai kayi hakuri gurin bada amsa da kuma jure duk abunda zakaji kuma ina Kara jadaddamaka karka kuskura kace kasan Ta aikata kisa labarin data baka farko shi zaka fada” Kai Ya daga mishi “insha Allah” “kuma ka kwantarda hankalinka babu wata matsa insha Allah” Sai kusan biyar Sulaiman yadda baro guri. © Khadeeja Candy [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* Na Khadija Abubakar Alkali *16~* koda 8am tayi mummy da hanna’tu da Maryam, Ummul-kharida wasu daga cikin abokannin Abdallah da yan family dinsu suna kotu mummy dasu maryam anrafka uban tagumi. kowa kagani fuskarsa babu walwalah. Sulaima na zaune gaban wani tebur shida wasu louyoyi. sai 10 harda wani abu Alkalin ya shigo shida mukarrabansa. yana shigowa kowa ya tashi tsaye ya natsu. saida ya zauna sannan kowa ya zauna. yayi kusan minti uku da zama. sannan ya dago kansa yace “a gabatar karar farko” da sauri muhuti (mai yin kira) ya mike tsaye rike da wasu takardu hannun shi “kara ta farko itace wadda dsp jamil hafiz dange ya shigar bisa ga zargin Abdallah shu’aibu Esa a da kisan SALEENA Ibrahim” yana kaiwa nan ya juya ya mikawa Alkalin takardu dake hannunshi. Duba rakardun naga Alkali yayi kamin ya dago kai yace “agabarta wadda ake kara” Nan take aka wasu yn sanda su hudu suka shigo da Abdallah hanuwanyeshi sarks da handcuff fuskarsa tayi narai narai. Saida ya tsaya gurinda aka tanada dan aje masu laifi sannan suka cire mishi handcuff. Suban tsab Alkalin yayi mishi sannan yace “Abdallah ana zarginka da kisan SALEENA ko ka aminta?” Cikin ladabi Abdallah yace “a a ya mai girma mai shari’ah bani na kasheta ba” Dukardar kansa yayi yayi dan rubutu sannan ya dago “ina lauyoyin mai kara?” Wata kyayyawar budurwa ce naga ta mike tsaye cikin girmamawa. “Sunana barrister Sumaiya bello lauya mai gabatarda wadda ake kara. Tare dani akwai… Barrister Maryam Ibrahim dangaskiya (sis) lauya mai taimakawa mai gabatarda mai kara” suna cewa haka suka dan risina sannan suka zauna. Saida Alkali ya danyi rubutu sannan ya dago kai “ko akwai lauya mai kare wadda ake kara?” Tashi Sulaiman yayi cikin girmamawa “ae ya mai girma mai shari’ah Sunana barrister Sulaiman Muktar lauya mai kare wadda ake tuhuma” bayan yace haka ya rinawa Alkali ya koma mazauninsa. Nan ma rubutu Alkalin yayi sannan yace “ko lauya mai gabatarda kara nada tambayoyin da zaiyiwa wadda ake kara?” Tashi tayi cikin girmamawa fuskarta dauke da murmushi “ina dasu ya mai girma mai shari’ah” Matsowa tayi kusa da Abdallah tana yi mishi wani kallo “ko zaka fadawa kotu waye kai?” “Sunana Dr Abdallah Shu’aibu Esa” “Dr Abdallah Shu’aibu Esa” ta fada a hankade “Shin minene alakarka da Margayiya SALEENA?” “banida wata alaka da ita” “tho ya akayi aka samu gawarta a gidanka”? “saboda na taimaka mata ne” “ka taimaka mata kamar ya kotu nada bukarta sani?” Aziyar zuciya Abdallah ya sauke ya kwashe haduwarsu da Saleena da farkon labarin data bashi ya fada mata. Jinjina kai tayi “watou ka taimaketa ne dan kayi mata fyade ko kuma daka cinma burinka ka kasheta dan kar asirinka ya tonu ko?” Da sauri Sulaiman ya tashi tsaye “objection my lord ya kama abokiyar aikina ta gyara kalamanta ya daina dan ganta wadda ake zargin da kisad kai tsaye dan Ba’ah riga an tabbatar ba” “korafi ya karbu ki gyara kalamanki barrister” cewar Alkali. Murmushi barrister Sumaiya tayi ta dan risina “thank u my lord” sannan ya juyo gurin Abdallah “Shin da kaga Saleena gana gudu tana jin tsoro harta nemi ka taimaka mata mie yasa baka kaita gurin yan sanda ba ko gidan iyayenka saika kebeta daban agidanka a kuma unguwar da babu mutane sosai?” “Saboda ta bukaci hakan kamar yadda na fada miki tun farko tace tana jin tsoro” barrister tace “shin ko kasan saleena yar kaduna ce ba kano ba kuma ko kasan ta gudo ne danta kashe mijinta?” cikin natsuwa Abdallah ya amsa da “a’a ban taba saniba” fuskar mamaki tayi “amman jaridu dayawa sun wallafa kuma yayita yawo a social media sa…..” Sulaiman ya mike “ojection my lord ya kamata barrister ta gyara tambayarta dan abu ya watsu a jaridu ko kuma an zuba a social media bai zama lalle Abdallah yasani ba” Alkali ya dubi barrister “korafi ya kar6u ki gyara tambayarki” “na gode ya mai shari’ah” ta sake juyawa gurin Abdallah “Shin ko zaka fadawa kotu kwanan saleena nawa a gidanka?” “kawanan ta 9” juyawa barrister tayi tana facing din Alkali “ya mai girma mai shari’ah bisa ga duk kan alamu Abdallah yasan abunda margayiya Saleena ta aikata ya mai girma mai shari’ah babu wani da zai ga macce tana 6oyo a zamin nan na yanzu ya aminta ya kawota gidansa batare da wata manufa ba daman yayi hakan ne dan ya samu damar aikata mata haka jaridar Rariya ta buga a shafinta na 6 cewar wata amarya ta kashe mijinta ta gudu saboda anyi mata auren dole Aminiya ma ta buga shafinta na 9 hausa daily mata buga a shafinta na 4 Nigerian corne ma ta buga shafinta na 11 duk akan Saleena ta kashe mijinta Sannan anyi ta yadawa a social media Shin ta yaya Abdallah zaice bai san ta aikata kisa ba Tunda a birni yake ba kauyeba kuma Dr ne shi” tebur din lauyoyi ta nufa ta dauko wata takarda daga cikin takardun dake gaban Barrister Maryam ta dagata sama tana nunawa Alkali “ya mai girma mai shari’ah wannan takarda ce wadda tazo daga Special hospital likitoci sun tabbatarda cewa anyiwa margayiya Saleena fyade kamin a kasheta . tho wata kila Abdallah yayi anfani da wannan damar ne na taimakon da yayi mata ya nuna aikata alfasha da ita dataki aminta saiya aikata mata fyade ganin ganin asirinsa zai tonu saiya kasheta. a hukumance duk wadda ka kama kaga yana jin tsoro kamar yadda saleena take ance ka kaishi hannun hukuma qmman Abdallah duk baiyi hakan ba saboda mummunar manufa tasa sannan dsp jamil ya samu gawar Saleena a palon Abdallah. ya mai girma mai shari’ah inason wannan kotu mai a dalci data yankewa Abdallah Shu’aibu Esa hukuncin laifin daya aikata bisa samunsa wannan laifi na gode ya mai girma mai shari’ah” saida ta mika wa muhuti takardar shi kuma ya mikawa Alkali sannan ta koma ta zauna. saida Alkali yayi rubutu sannan ya kalli Sulaiman “ko kauya mai kare wadda ake kara nada tambayoyin da zaiyiwa wadda ke tuhuma?” Sulaiman ya tashi yana “ae ya mai girma mai shari’ah” © *Khadeeja Candy* dedicated to *Sumaiya bello (Sumsum)* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *Na Khadija Abubakar Alkali* *17~* Sulaiman ya matso kusa da Abdallah yana mushi murmushin gyarin kuwai . “Ka kwantardar hankalinka Abdallah wannan kutu ce mai adalci” kai kaiwai Abdallah ya jinjina masa. Sulaiman Yace “Shin ko zaka fadawa kotu kana ina da misalin karfe 7pm na ranar talata”? “ina gida tare da mummy da kuma kannena” “shin da misalin karfe nawa ka samu labarin mutuwar Saleena?” “da misalin karfe 10 harda wani abu” “shine ta hanyar wa ka samu labarin mutuwar ta?” “ta hanyar dsp jamil” sulaiman ya juya yana ficing din Alkali yace lya mai girma mai shari’ah idan kotu ta bani dama inason a kira dsp jamil danyi mishi wasu tambayoyi?” Alkali yace “kotu nada bukatar bukatar ganin dsp jamil a gabanta” Da sauri dsp jamil ya taso ya tsaya gurin da aka tanada dan bada shaida. Sulaiman ya matso kusa dashi. “kaine ka bada shaidar mutuwar Saleena ko muce kai kaga gawarta shin da misali karfe nawa kuka samu gawarta kuma ya kuka tararda gawar?” “da misalin karfe 8 da rabi da wani abu kuma mun samu gawarta ne cike da kazanta” “Shin koda kuka kaita asibiti tanada rai ko batada?” Da sauri barrister Sumaiya ta tashi “ojection my lord ya kamata abokin aikina ya gyara tambayarsa shin ta yaya dsp jamil zaisan ta mutu ko bata mutuba shi dan saandane ba Dr Dr ne kawai zasu iya tabbatarda hakan kuma sunyi” Alkali ya kalli Sulaiman “korafi ya karbu ka gyara tambayarka” Maida hannunshi yayi baya ya dan risina “thank u my lord” Sannan ya saka kallon dsp “Shin samame kuka kai a gidan ko wani ya fada muku tana cikin gidan?” Dsp yace “Hajiya Safiya mahaifiyar Abdallah ita ta kirani ranar tace tanason nakai ziyara gidan danta ko zan samu wani abu” Sulaiman Yace “good da misalin karfe nawa ta kiraka?” “da misalin karfe 8 saura kwata” Sulaiman ya kalli Alkali iyakar tambayoyin da zanyi masa kenan ya mai shari’ah saida inason kotu ta bani dama na kira hajiya Safiya danyi mata wasu yan tambayoyi” Saida Alkalin ya salami dsp sannan yace “kotu nada bukatar ganin hajiya Safiya” Tasowa mummy tayi tana sharar kwallah ta nufi gurin bada shaida ta tsaya. “dsp jamil yace kece kika kirashi da misalin karfe 8 saura kikace yaje gidan Abdallah kozai samu wani abu shin hakane?” tambayar da Sulaiman ya farayi mata kenan. Saida ta sauke Ajiyar zuciya sannan tace “haka ne nice na kirashi” “Shin mie yasa kika aikata hakan baki yarda da danki bane ko kina zargi wani abune ko kuma wani abun kikaji?” Cika idon mummy sukayi da hawaye ta kalli Abdallah cikin kuka ta fara magana “na yarda da dana 100% bana kuma zargin wani abu kawai ranar kanwarsa Ummul-khari ce tazo hankalinta a tashe tace taga wata ta shiga gidan Abdallah shine sai naji tsoro nakira yan sanda dan suje suyi bincike na hanashi fita” “kenan lokacin da kika samu wannan labarin Abdallah yana cikin gida kenan ko?” “ae yana cikin gida” Ganin irin kukan da take yasa Bai sake yimata wata tambayar ba. Juyawa kawai yayi gurin Alkali yace “iyakacin tambayoyi da zanyi mata kenan ya mai shari’ah” Alkali yace “zaki iya tafiya ki zauna Hajiya safiya” Saida ta zauna sannan Sulaiman yace “inada bukatar kotu ta kira Ummul-khari danyi mata wasu yan tambayoyi?” “kotu nada bukatar ganin Ummul-khari” Ana anbatar sunanta gabanta ya fadi idonta suka cika da hawaye ta taso jikinta na rawa ta tsaya gurin da taga mummy ta tsaya. Sulaiman ya matso kusa da ita “Hajiya safiya tace kece kikaxo kika fada mata kinga shigar wata yarinya gidan Abdallah hakane?” Saida ta hadeye yawu sannan tace “ae… Ae.. Ha.. Hakane.. Ne” Sulaiman yace “ki kwantardar hankalinki babu abunda za’ayi miki tambayoyine kawai” Muryrata cike da gargada tace “thom…” “shin ko zaki fadawa kotu yaya kikaga yarinyar?” “na ganta ta shiga gidan da gudu hanlakinta a tashe tana waiga bayanta harna haskata da mota ta rufe fuskarta da hannayenta” “sai kika shiga cikin gidan ko yaya kikayi?” “a’a ban shiga ba daman ina tukin mota ne sai na nufo gida cike da hanzari na fadawa mummy” “shin da misalin karfe nawa kika fadawa mummy” “da magriba ne” “shin lokacin da kika zo gida kika fadawa mummy Abdallah na cikin gidan?” “ae yana zaune parlour shida mummy na shigo a gansa ma na fada” “shin koda kika baro yarinyar tana da rai ko kuma ta mutu?” “tana da rai” Juya Sulaiman yayi gurin Alkali. “ya mai girma mai shari’ah bisa ga dukan alamu lokacin da aka kashe Saleena Abdallah yana gida. Dsp jamil yace karfe 8 saura hajiya rabi ta buga mishi waya sannan ya isa gidan karfe 8da wani abu sannan Ummul-khari tace da ganta da magriba har tazo gida ta fadawa hajiya safiya kuma a lokacin Abdallah yana cikin gida sannan hajiya safiya tace tunda aka fada mata bata bar Abdallah ya fita ko inaba sannan inason wannan kotu mai adalci tayi duba shin inda Abdallah yasan ya kasheta ta yaya zai yarda hajiya Safiya ta daga waya ta kira dsp jamil akan yaje yayi bincike. Abisa dukan alamu ya mai girma mai shari’ah an kashe margayiya saleena ne a lokacin da dsp jamil ya isa gurin” “objection my lord ya kamata abokin aikina yasan mie yakeyi yana kokarin zuya wannan shari’ah ne zuga dsp jamil bayan babu wani abu daya nuna hakan”……. Tarar numfashinta yayi.”ya mai shari’ah babu wata mace da za’ayiwa fyaden minta 10 ko 15 ya munana kamar yadda akaiyiwa SALEENA koda kuwa budurwace wadda bata taba sanin namijiba ko kuma ta taba sani abisa duk kan alamu koda an kashe saleena lokacin da Ummul-khari taga ta shiga gidan da gudu zuwa lokacin da dsp jamil ya isa gida ya nuna awa daya kenan. Thon zai xama anyi mata fyade ne da mintina 40 ko fiye da jakan ko kuma basu kai ba likitoci sun tabbatar anyiwa saleena fyade da yakai awa daya harda wani abu sannan kuma ba mutun daya yayi anfanin da ita ba so bisa ga bayanen da dsp jamil ya bayar ya nuna kodai ya isa gurin lokacin da anayi mata fyade ko kuma ya tararda maiyi mata fyade dan haka ina rokon wannan kotu mai alfarma data duba wadannan shedu nawa ta yiwa Abdallah daurin talala inso sai muci gaba da shari’ah” yana kaiwa nan barrister Sumaiya ta tashi tana “objection my lord babu wani da za’a kama da gawa gidansa sannan da kaifin aje mace da bakasan inda take ba asakeshi harsa shedu masu karfin sun tabbatarda hakan” Duk abunda ake alkalin na rubutawa. Saida ya kamala ya dago ya kai yace “kotu ta dage sauraren wannan kara har zuwa 24 ga wannan watan da muke ciki sannan kotu ta bada umarnin a cigaba da tsare Abdallah gidan kaso” yana kaiwa nan ya buga desk ya tashi kowa ya mike tsaye ana “koooooootuuuuuu” © *Khadeeja Candy* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *_Khadija Abubakar Alkali_* *18~* haka aka wuce da Abdallah mummy sai kuka take Har suka shiga mota gaba dayansu gida suka nufo har Sulaiman, Suna shiga mummy ta sake fashewa da kuka dafe kai Sulaiman yayi “haba mummy mie anfanin kukan nan dan Allah kinga fa mun fara samun nasara kawai addu’ah ya kamata ki tamamu” Ajiyar zuciya ta sauke “nayi marmarin Abdallah” Zaunawa maryam tayi kusa da ita “karki damu mummy very soon yay zai dawo insha Allah kawai kiyita mishi addu’ah” Kai mummy Ta daga mata idonta cike da hawaye Sulaiman yadda Tashi tsaye yana fadin “before na manta ummul-khairi ki shirya da wuri gobe zamuje gurin qawarki muyi mata yan tambayoyi ko zamu samu wani abu” Kai Ta Girgirza “owk insha Allah” Saida yace “good” sannan ta kalli mummy “ki kwantarda hankalinki mummy komai zai dawo normal” “Tho Allah yasa Allah fitar min da d`ana da duk musulmin” Dukansu sukace “amin” yayima mummy sallama yadda fice, *WASHE GARI* koda goma tayi ummul-khairi Ta shirya Sulaiman na zuwa suka kama hanya, tun cike mota Sulaiman ya kunne wata yar karamar rikoda bayan ya gargadi ummul-khairi akan karta kuskura Ta nuna tasan da zaman rikodar. Da isarsu yayi horn aka bude musu gate, Suna kokarin yin parking suka ganta Ta fito rike da wasu Takardu a hannunta Ta nufi parking space. Da sauri ummul-khairi Ta fita motar ta nufi inda take “wait wait hafscy” juyowa tayi cike da far’ah “ohhh, wa nake ji kamar ummul-khairi” “nice wlh ykk fita zakiyi ne?” “ae wlh zan dan shiga scul ne” Daidai nan Sulaiman ya karaso rike da wasu takardu suna hada Ido ya sakar mata murmushi “sannu” itama murmushin Ta mayar mishi “yauwa sannu” ta kalli ummul-khairi “wanene wannan ummul-khairi?” Zatayi magana ya tare numfashinta “uhm.. Sunana barrister Sulaiman muktar” “wow nice to meet yhu” Ta maida dubanta ga ummul-khairi “saurayinki ne?” “Nop Abokin yayana kuma shine lauyan da yake kareshi by the way munzo ne muyi miki tambayoyi” Kallon rashin fahimta tayi mata “about what?” Sulaiman ya karba mata “about kinsan kan da akayi a umguwar ku” Waje tayo da ido “what? Nifa banida hannu a ciki bansan komai akai ba” Ummul-khairi Ta dafata “kwantarda hankalinki friend babu abunda za’ayi miki kawai yan few questions ne” “tho miyasa saini baga mutane da yawa a umguwar ba I just don’t understand” “saboda ke muka Sani kuma munada tabbacin zaki fada mana gaskiya plz hafscy ki taimakawa yayana plz n plz” Ta karasa maganar tare da hade hannayenta guri daya, Sulaiman yace “and I promise yhu nothing is going to happen to yhu u can trust us” nan ta kalli ummul-khairi ta girgixa mata kai, Shiru tayi kamin Ta nuna musu kofar garden “shall we..” gira Sulaiman ya daga mata ya lumshe yana murmushi “yeah of course” A tare suka nufi garden din a tare, Bayan sun zauna Ta aje takardunta gefe Ta kalli Sulaiman “ina jinka? ” Saida ya fiddo biro daga aljihunshi sannan yace “ko kina nan lokacin da aka aikata kisan?” “Eh ina nan Amman ina cikin gida lokacin bansan anyi Kisanba sai washe gari koshi da maraice” “baki samu labarin komai akan kisan ba?” Ido Ta tsurawa Sulaiman kamar mai tunani, Can kuma Ta kwarda fuskarta “a’a bi ban samu labarin komai ba” Sulaiman yadda girgixa kai “plz Hafsa karkiyi mana haka kinga bawan Allah nan anrufeshi kuma za’a kasheshi akan laifin da bashi ya aikata ba” zubewa Ummul-khari tayi kasan gwuiwoyinta idonta cike da Kwala zata roketa, da sauri ta dakatar da ita “a’a friend babu haka tsakanina dake zan fada muku komai” saida ummul-khari ta zauna sannan ta kalli barrister Sulaiman tace “akwai wata yarinya da akan idonta komai ya faru tace taga komai ta kuma san wadda ya aikata dan sunyi zama unguwa daya da shi” da sauri ummul-khari ta dafata “Alhamdulillah ina yarinyar take ina zamu Sameta?” “yar nan unguwar ce gidan da suke gadi yana kallon gidan Abdallah” ummul-khari zatayi magana Sulaiman ya tari numfashinta “ko zamu iya zuwa gurin yarinyar yanzu?” “ae zamu iya ai gidan babu nisa” tashi sulaiman yayibyana fadin “muje ko?” bai tsaya jiran amsarta ba ya nufi gurin motarsa da sauri, suka rufa mishi baya. koda suka isa harya tada mota shiga kawai sukayi ya kama hanyar gidan, nesa da gidan sukayi parking suka karasa da kafa, “Assalamu alaikum” hafsa take salamar ita da ummul-khari bayan sunbar Sulaiman a waje, “Wa’alaikumussalam” daga can ciki ake amsa musu, wata matashiyar yarinyace naga ta fito daga cikin dakin. tana ganin hafsa ta saki far’ah, “anty hafsa keda kanki kikazo gidan mu? murmushi tayi “ae wlh rahama wani abu mukazo yi tare ma muke da bako a waje” “bako? lafiya dai?” “lafiya kalau kawai yana son ganinki ne” ta juya tana fadin “tho bari na dauko hijab dina?” bata dade ba ta fito sanye da hijab milk color, suka nufi fice. tsaye suka tararda shi yana karewa unguwar kallon yana ganinsu ya saki murmushi. saida ta kawo kusa dashi sannan ta kalleshi dan tunda suka fito kanta a kasa yake, “ina wuni tace dashi” “lafiya kalau qanwata ya gida?” “gida kalau” kallon ummul-khari yayi “kunyi mata bayani?” “a a kaine dai zaka yimata” hafsa ta bashi amsa “owk” ya kalleta “am sunana Sulaiman muktar ni abokin Abdallah mai gidan can” ya nuna mata gidan “wannan kuma qanwarsa ce so muna son sanin wani abune akan abunda ake zargin abokina da aikata shine muka ce bari muzo na unguwar mu dan bincika shine muka fara zuwa gidan na farko sannan muka fado gidansu hafsa shine nace ta rakomu gidanku dan muyi miki wasu yan tamvayoyi kema ganin kinma fi kusa da gidan” hafsa tace “dan Allah rahama ki fada musu gaskiya tsakaninki da Allah” kai ta girgiza “zan fada insha Allah duk abunda na sani bazanyi karya ba” © *_Khadeeja Candy_* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *_Na Khadija Abubakar Alkali_* *19~* Sulaiman ya gyara tsayuwar “good haka muke so ko zan iya samun gurin zama?” Juyawa tayi tan fadin “eh bari na dauko tabarma” Bata dadeba ta fito rike da tabarma. Ta nufi karkashin wani ice ta shinfida musu Bayan sun zauna ya kalleta yace “Shin da yaushe abun ya faru?” A hankali take bashi amsoshin tambayoyinshi har ta amsa mishi duk tambayar da yayi mata, Ummul-khari sai kwasar murmushi take tana gode Allah. Sulaiman ya kalleta “rahama mun gode sosai mun kuma jidadi Allah ya saka miki da alkhari” Kasa tayi da kanta “Amin nima na gode” Sulaiman Yace “am saidai muna neman wata alfarma daya” “owk kamar tame?” “an ko zaki iya bada shaidar nan a cotu?” Waje tayo da ido “kotu kuma……….a’a gaskiya” “ki kwantarda hankalinki ba wani abubane just shaida zaki bada dan taimakon wannan bawan Allah plz” tashi tayi tsaye “a’a nidai na fada muku abunda na sani dan Allah karka sani cikin matsala” Tashi sukayi suma Sulaiman yace “dan Allah ki taimaka mana wlh ke kadaice zaki iya fiddo shi daga cikin halin da yake yanzu kuma….” bai karasa maganar ba ta juya ta nufi gida da sauri. Dafe kai Sulaiman yayi ya busarda iskar bakinsa. Hafsa ta dan leki fuskarsa “ohh u don’t have worried zanyi magana da ita zamu samu solution calm down” kallonta yayi yana murmushi “yhu don’t have to tell me that nima namiji ne” dariya tayi “owk ni bari naje gida kar nayi lati a scul” “owk bari na Ajeki sai muwuce Ummul-khari muje ko?” sauri dakatarda su tayi “no zan karasa da kafa kasan babu nisa sai munyi waya kawai duk yadda akayi zakaji” kai ya daga mata yana murmushi “na gode da taimako” daga can ta dago mishi hannu “aha ur alwys welcom” murmushi Sulaman yayi hakan yaji ta burgeshi. saida ya gata shiga gida sannan ya shiga motar suka kama hanyar gida. har suka isa sulaiman murmushi yake. suna isa gida ummul-khari ta rumgume mummy tana dariya. “lafiyarki mie kike yiwa dariya?” “mummy mun samu mafita mummy munsamu yarinyar da tasan komai akan idonta kayi komai kuma ta fada mana komai” mummy ta daga hannu sama “Alhamdulillahi Allah mun gode maka” Sulaiman yace “saida matsala daya yarinyar taki ta yarda tayi shaida a cotu” ummul-khari tace “a’a nasan insha Allah zamu samu kanta kuma kaga ai Budurwarka tace karka damu ko zata samo solution” tashi yayi tsaye yasa hannunshi Aljihu “kibar wannan maganar ummu kuma inason wannan maganar ta yarinyar nan ta zama sirri kar wadda yaji” “owk insha Allah” saida yayiwa mummy sallama sannan ya fice, [7/29, 2:36 PM] Khαdeeja Cαndy: tun daga lokacin hafsa takr zirga zirgar zuwa gidansu rahama tana lallabata da bata kwarin gwuiwa babu abunda zai sameta, *bayan kwana biu* su mummy suna zaune parlour sulaiman ya shigo, da far’ah suka tareshi a tsaye ya gaisa dasu ya kalli ummul-khari yace “taso zamuje gurin qarwarki ta kirani” kallon rashin fahimta “oh.. ta kiraka?” “eh ya a’kayi?” murmushi tayi “a’a bsbu komai naga bakada number ta” shan mur yayi “shin zaki tashi muje ko sai kin bata min lokaci” tashi tayi hanna’tu ta mika mata gyalenta “ungo bama sai kin shiga dakiba” tana karba suka fice, tun kamin su kasa kaiwa gidan naga yayi parking ya ciro wayarsa ya dannan calling “gamu munzo amman daidai jaction muka tsaya.. owk ..” bayan ya sauke wayar ummul khari ta kalleshi “wai nikan ya akayi ka samu numberta?” yi yayi kamar bazai amsa mata ba can kuma yace “zuwana uku nan bayan zuwan da mukayi rarar nan” kai ta girgiza tana murmushi “owk nice” bai sakece mata komaiba har hafsa ta iso, tana sowa ta bude gidan baya ta shiga “muje gidansu amman kamin kakai zakayi parking” kai kawai ya daga mata ya tada motar suka nufi gidan, tun kamin ya karasa yayi parking hafsa da ummul-khari suka fita tare suka shiga cikin gidan, basu dade ba suka fito tare da rahama suka nufo motar, “Ina wuni?” “lafiya kalau rahama ya kike ya gida?” “Alhamdulillah” “am hafsa tace mun kin shirya kin kuma aminta zaki bada sheida a kotu haka ne?” shiru tayi kamin tace “eh aman iyayena basu saniba kuma bana son su sani har sai mun dawo” ummul-khari tace “kina tunani haka yafi miki kiyiwa iyayenki karya?” “matukar kuna son na bada shaida tho dolene sai nayi hakan dan bazasu taba amintaba naje na bada sheida a kotu ba amman kinga da mun dawo zan sanar dasu komai” ummul-khari zatayi magana Sulaiman ya tari numfashinta, “owk rahama mun gode sosai 24 zamu shiga cotu so ki shirya” kaibta girgiza “insha Allah” wani dan karamin abu naga ya ciro a aljihunsa “amman kamin nan inason nuna miki wannan” da sauri ta karba tana dubawa “ina ka sameshi?” “cikin gidan Abdallah na sameshi karkashin kujera” “shine fa wadda nake fada maka wlh shine” da sauri ummul-khari ta karba “mugani?” hafsa ma saida ta karba. ta dubi Sulaiman “gidan ka samu?” kai ya daga mata tare da karbar id din ya maida aljihu “shikenan ma taxo gidan sauki mun samu kwakwaran sheidu” cewar ummul-khari sulaiman yace “eh amman inason ya zama srrin tsaninmu daku plz” duk suka ce masa babu wata matsala kowa yayi alkawarin bazai fada ba, a haka sukayi sallama © *_Khadeeja Candy_* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *_Na Khadija Abubakar Alkali_* *20~* tun safe su mummy da su hannatu da maryam, ummul-khari da hafsa da rahama suka isa kotu, Karfe 10 alkali ya shigo da sauri aka ta’tashi tsaye bayan ya zauna suka zauna saida ya gama kintsawa sannan yace “a gabarda karar farko” Tashi muhuti yayi kire da takardu “yau 24 ga watan July zamu cigaba da sauraren karar Abdallah wanda ake zargi da kisan saleena wadda barrister sumaiya bello ke wakitar margayiya saleena Barrister Sulaiman muktar ke wakitar Abdallah” juyawa yayi ya mikawa Alkalin takardun sannan ya zauna, bayan alkalin ya duba takardun yace “a shigo da Abdallah” nan take aka shigo dashi cikin gaggawa bayan ya tsaya gurin da aka tanadar masa aka cire mishi handcuff alkalin ya kalli lauyoyin dake zaune gurin “kotu tana sauraren lauyoyi” nan barrister Sulaiman ya tashi “ya mai girma mai shari’ah idan kotu ta bani dama inason gabatarda sheidata ta farko?” alkalin yace “kotu ta baka dama” juyawa yayi yana kallon wani tsoho “baba dahiru mai goro” da sauri naga ya taso ya nufi gurin da aka tanada dan bada shaida, sulaiman ya nufeshi “ko zaka fadawa kotu waye kai da kuma shekaranka da kuma aikinka?” “sunana dahiru mai goro shekaruna 67a duniya aikina kuma shine gadi” “shin aka ina kake gadi?” “ina gadine a gidan Alhaji usman gidan dake kusa dana Dr Abdallahi” “Abdallah makocinka ne shinko zaka fada mana wanene Abdallah?” “Abdallah mutun ne na kwarai mai hankalin da sanin ya kamata” “shin da kasamu labarin cewar ana zargin Abdallah da kisan kai ya kaji?” “Objection my lord” barrister sumaiya ta mike, “abokin aikina yana kokarin batawa kotu lokacine kawai dan banga anfanin tambayoyin da yake yiwan wannan dattijon ba” Sulaiman yace “ya mai shari’ah bana nufi batawa kotu lokaci inason kotu tasan wanene Abdallah kuma Kuma wannan dattijon yana da masani akan kisan Saleena” Alkalin yace “korafi bai karbuba zaka iya cigaba da tambayarka” risinawa yayi “thank u my lord” sannan ya kalli dattijon “inajinka malam dahiru?” “gaskiya naji kaduwa na kuma yi mamaki ban kuma yarda ba saboda a gaban idona wasu maza uku suka shiga gidan da kafa wasu a mota bayan harshi Abdallah ya dade da fita gidan” barrister sulaiman ya gyara tsayuwarsa “kace maza uku suka shiga gidan shin ko zaka fadawa kotu su wanene?” “gaskiya ban sansuba amman inagansu zan iya nuna su” “kana gurin har police suka iso?” “ae bayan shigar police suka fito” “shin ya akayi ka gansu?” “lokacin da ita yarinyar ta fito gida ina zaune bakin gate din da nake gadi bayan kamar mintuna 30 na tashi na shiga cikin gida ana kiran magrib na fito dan suwa masalaci sai na ganta tana gudu da kafa tana kuka ina tsaye bakin gate saina hango wasu maza uku biye da ita rike da wuka wasu kuma a mota sai nayi saurin komawa cikin gidan na rika lekonsu ta gate ta nan na hangota ta shiga gidan cike da tashin hankali bayan kamar minti 10 haka suka bita har cikin gidan” [7/31, 7:30 PM] Khαdeeja Cαndy: “shin zaka iya fadawa kotu maza nawa ne suke cikin motar?” “gaskiya ban saniba dan ban tsaya na tantance suba amman dai wadanda suke tafiya kasa sukan zan iya ganesu” “so zaka fadawa kotu ya kaminsu yake?” “eh dayan yanada jiki da dan fadin fuska yanada saje da kuma jajayen idanu yana kuma siririne fari mai mai guntun gemo shima dayan bashida jiki bakine kuma kajere” sulaiman ya juya gurin alkalin “ya mai shari’ah iyakacin tambayoyin da zanyiwa malam dahiru kenan” Alkalin ya kalli barrister sumaiya “ko lauyan gobnati nada tambayoyin da zatayiwa malam dahiru?” “ae inada ya mai shari’ah” “shin ranar talata da misalin karfe shida da minti 58 kana ina?” “ina nan gidan da nake gadi” ta kalli alkali “iyakacin tambayar da zanyi masa kenan ya mai shari’ah” Alkalin yace “malam dahiru zaka iya zuwa ka zauna” bayan ya koma gurin zamansa ya zauna sulaiman yace “in kotu ta bani dama inason gabatara sheidata ta biu?” “kotu ta baka dama” Suleiman ya kira rahama cike da tsoro ta taso tazo tazo ta tsaya, Sulaiman ya kalleta yace “shin ko zaki fadawa kotu wacece ke da kuma shekarunki?” “sunana rahama ismail shekaruna 19” “shinko kin taba ganin margayiya saleena?” “eh na taba ganinta ranar da aka kasheta” “a ina kika ganta?” “na taso daga islamiya saina biya gidansu wata kawata ana kusan fara kiran magriba na fito gidan na nufo gida nan na hadu da ita layin dake kusa da mu tana gudu tana kuka harta fadi na da sauri na cinmata na tambayeta lafiya saitace min na gudu karna tsaya wasu zasu cutar da ita zan sake yi mata wata tambayar sai naga mota ta shigo gurin da gudu saina watsa nima da gudu na isa gida nasa sakata na rika lekon gate dan ganin ko sun biyoni” “shin bayan hakan kin sake ganinta?” “eh na sake ganin lokacin da nake leko saina ta taho da gudu tana waige waige har wata mota ta haskata saita shiga gidan da gudu” “shin bayan hakan ko wani abu ya sake faruwa?” “ae naga wasu maza sun shiga gidan su uku sai kuma wata mota baka ita ta shiga” “shin ko kinga fuskokin wadanda suka shiga gidan kin sansu?” “eh nasan fuskokin biu daga ciki dayan ne ban saniba” “dawa dawa kika sani kotu tana son karin bayani?” “nasan lasdom wani mai kauri da dan fadin fuska sai kuma jajayen idanuwa dayan kuma raizer farine siriri da gemo bamai tsayo sosai ba” “shin ya kayi kika sansu kika kuma ganesu?” “munyi zama unguwa daya dasu kuma ba ita kadai ba yakan kawo mata gidan wasu suna far’ah wasu kuma da kuka” “shin kinga fitarsa byan shigarsa?” “eh naga fitarsa lokacin da yan sanda suka shiga gidan” sulaiman ya kalli alkali “iyakacin tambayoyin da zanyi mata kenan ya mai shari’ah” © *Khadeeja Candy* 1474463087186.jpg KHADEEJA CANDY MOBILE BLOG WELCOME TO MY WORLD YOUR COMMENTS AND CORRECTIONS ARE ALWAYS WELCOME ENJOY YOURSELF 💁 Menu Skip to content Home › SALEENA › SALEENA SALEENA Posted on September 22, 2016 by Khadeeja Candy — Leave a comment ​[8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *_Na Khadija Abubakar Alkali_* *21~* Alkali. Ya Kalli Sumaiya “ko lauya mai kara nada tambayoyin da zatayiwa Rahama?” “banida su ya mai shari’ah” Alkali yace “rahama zaki iya zuwa ki zauna” Bayan ta zauna Barrister Sulaiman yace “in kotu ta bani dama inason gatarda shedata ta uku?” “kotu ta baka” Jikara dake gansa naga ya bude ya ciro id kat ya daga sama “ya mi shari’ah na samu wannan ad kat dinne a gidan Abdallah karkashin kujerarsa dake parlour ad kat din yana dauke da photon wani matashi baki mai dan kauri da saje da kuma manya ido kamar yadda malam dahiru da kuma rahama suka fada sunan da yake jikin wannan ad kat din shine hamisu lasdom” mikawa muhuti ad kat din yayi shi kuma ya mikawa alkali, “ya mai shari’ah inason kotu ta gane ba Abdallah ne ya aikata wannan kisan kan ba bisa ga bayanan rahama da kuma malam dahiru sannan kuma ga ad mun samu a gidan sannan dukan bayanai sun nuna dsp jamil ya tararda wanda ya aikata kisan nan ya mai shari’ah iyakacin shedu da nakeda su kenan” Yana kaiwa nan ya koma ya zauna. Bayan kamar minti 5-7 alkalin ya kalli barrister Sumaiya yace “ko lauya mai kara nada korafi ko shedu da zata gabatar?” “a’a banida su ya mai shari’ah” Rubuce2 alkalin ya shiga kamin ya dago kai yace “bisa ga dukan hujoji da kuma shedu da lauyoyi suka gabatar kotu ta bada umarnin sakin Abdallah shu’aibu esa” cika idon Abdallah sukayi da hawaye yayi saurin lumshe ido, “kuma kotu ta bada umarnin tsare dsp jamil da kuma umarnin kamo hamisu lasdom kafin zama na gaba wadda za ayi ranar 5 ga watan da zai shigo” Saida ya buga desk sannan ya tashi tsaye kowa ya tashi ana “koooooootuuuuuu” Alkalin na fita yan’sanda suka kama dsp jamil aka samishi handcuffs aka wuce dashi, Da sauri Abdallah ya nufi mummy dake Hawayen yiwa Allah godiya ya kama hannayenta “mummy kukan nan ya isa haka plz daman shi naketa tunani nasan na saki cikin matsala zakiyita zubarda hawaye akaina dan Allah mummy kibar kukan nan ki kuma yafemin” tashi kawai mummy tayi ta rumgumeshi. Bayan ya saketa ya rumgume maryam da itama kukan take “daman nasan gaskiya zata bayyana yay” Ta bayanshi ummul-khairi da hannatu suka rumgume, Sun dade a haka kamin Ta sakesu ya juyo ya kalli Sulaiman “kafi karfin amini agare kuma kafi karfin dan’uwa a gareni ina tunanin zuciya daya akayi mana aka saka maka rabi aka saka min rabi bansan kalmar da zanyi anfani da itaba name gode maka” Murmushi Sulaiman yayi ya jashi suka rumgume juna “no need for that Abdallah what is important now u are free” Bayan sun sake juna yayiwa malam Dahiru godiya sosai, Sannan ya nufo Rahama. Suna hada ido tayi saurin yin kasa da kanta ta sauke ajiyar zuciya, Murmushi Abdallah yayi yace “na gode sosai Rahama Allah ya saka miki da aikhari Allah kuma ya taimakeki” Saida ta hadeye yawu sannna tace “AMIN” Ta juya da sauri ta kalli Sulaiman “dan Allah ka maidani gida kar umma ta nemeni” Kamin sulaiman yayi magana Abdallah yace “AI babu abunda muke jira muje kawai” Tare suka fito harabar kotun suka nufi parking space suna kokarin shiga mota Sulaiman ya kalli Abdallah yace “bakafa cewa hafsa ka godeba kuma duk wahalar nan da mukayi tare muka yita tama fini shan wahala” Murmushi Abdallah yayi ya matso kusa da hafsa “na gode sosai hafsa Allah ya saka da alkhari” “haba yayana nifa kanwarkace bana bukatar hakan dan nayiwa yayana abu saiya gode min” Saida Sulaiman ya kalli Abdallah sukayi murmushi sannan kowa ya shiga mota suka kama hanyar gida, Koda suka isa gida sun tararda wasu makota da abokanin mummy dan tun a waya mummy ta sanar musu kowa sai barka yake musu duk da dai bakare case din akayi gaba daya ba. Abdallah sai phone calls yake samu daga yan uwa da abokanin arziki wasu kuma har fida suke kawo masa murnarsu, *bayan kwana biu* Abdallah yana zauna parlour shida Ummul-khari mummy hafsa ta shigo cike da tashin hankali tana haki, tashi Ummul-khari tayi ta nufeta “lafiya hafsa miya faru?” Fashewa tayi da kuka “na shiga uku Ummul-khari kasheni zasu sun kashe rahama yanzu akan hanyarta ta dawowa daga islamiya aka sinci gawarta gata can anyi asibiti da ita nima kasheni zasuyi Ummul-khari kasheni zasuyi” Da sauri Abdallah ya tashi tsaye “what?” Ummul-khari ta rumgumeta “bazasu kasheki ba Hafsa kibar kuka” Keys din dake gaban mummy ya dauka yana fadin “wace asibiti aka kaita?” Cikin kuka hafsa tace “husaini medical” Yana juyawa mummy ta rike masa riga “ban yarda kajeba Abdallah” Fuskar mamaki yayi “haba mummy kodai bakiji mie tace bane?” “naji amman ban aminta kaje kai kadai ba ka kira Sulaiman kuje tare” “dan Allah mummy ki barni naje kamin Sulaiman ya iso lokaci ya kure………” Kateshi mummy tayi “tho ban lamunta ba inhar bakaje da shiba ban aminta kaje ba” Ganin ba shida mafita yasashi daukar waya ya kira Sulaiman, Shima ba karamin kaduwa yayi ba cikin kan kanen lokaci ya iso gidan, Suka kama hanya haka ya rika gudu kamar zai tashi sama. © *_Khadeeja Candy_* HAPPY BIRTHDAYS FRIENDS. _inason inyi anfani da wannan damar na taya friends dina murnar zagayowar ranar haihuwarsu sumaiya Bello my sweet friend ina miki Addu’ah Allah yasa sawa rayuwarki albarka ya baki duk abunda kike nema Ina miki fatan ki fara sabuwar shekararki cikin jindadi da walwala my besty kema ina miki wannan fatan @Hauwa ya’u Zamau HAPPY BIRTHDAY TO ALL OF YOU LOVE U ALL_ [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *_Na Khadija Abubakar Alkali_* *22~* har suka isa asibitin Abdallah dafe yake da kanshi, Suna isa suka nufi emergency. Suna shiga Abdallah yayi karo da wani abokinshi da far’ah ya tare shi “dr Abdallah lafiya na ganka a haka?” Saida Abdallah ya sauke Ajiyar zuciya sannan yace “wlh wata yarinya aka kawo wai anyi kokarin kasheta” “subhanallahi yar’uwarka ce na ganta an shiga icu da ita but ban saniba ko ba ita bace amman dai da kashiga zakaga yan’uwanta” Da sauri Abdallah ya kunna kai cike da tashin hankali Sulaiman ya rufa masa baya, Yana shiga ya tarar baban Rahama tsaye shida wasu mata dukansu babu kwanciyar hankali a tare dasu, Abdallah na isa ya mikawa Baban Rahama hannun suka gaisa Abdallah ya dan risina ya gaida wadda yake zato mahaifiyar Rahama Banza ta masa sai wani zanzana take tana shawaye Sulaiman ma ya mika mishi hannu suka gaisa Sunfi 1 daya a haka sannan likitan ya fito Duk suka nufeshi har Abdallah suna tambayar lafiyarta Murmushi likitan yayiwa Abdallah “dr Abdallah I’m so surprised yar’uwarka ce?” “no time for that plz fada min yaya jikinta yake yanzu?” “dr ta mutu ko?” Mahaifiyar Rahama ta tambaya “a a ku kwantardar hankalinku tana da rai kuma abun yazo mata da sauki” Abdallah ya sauke Ajiyar zuciya ya nufi dakin Da sauri suka rufa masa baya “wait wait karku shiga tana da bukatar hutu” Maman Rahama tace “amman dr ya shi kabarshi ya shiga bafa dan uwanta bane mune iyayenta” “yafini kwarewa a aiki yasan yadda zai tafiyarda ita ku bari anjima sai ku ganta” A dole suka hakura suka zauna Abdallah na shiga yaja kujera ya zauna kusa da ita ya kura mata ido dake cike da hawaye, Haka ya tsareta bai fito ba saida yaji muryar mummy Yana fitowa ta nufoshi “Abdallah ya jikin nata?” “da sauki mummy komai na tafiya daidai” Mummy ta juyo gurin masu baban Rahama an kama wadanda suka aikata mata haka?” “a a har yanzu bamu da labarin komai sai in ta farka zata fada” Wani tunanine yazo ma Abdallah Da sauri ya nufi dakin dr Tarar dashi yayi yana rubuce2 kujera yaja ya zauna dr ya mika mishi hannu “dr ina tayaka murna akan abunda ya faru Dr” Murmushi Abdallah yayi “na gode amman dr me da me ke damun Rahama yanzu miye ka tarar anyi mata?” “bamu samu komaiba gaskiya inbanda Sukar wukar da akayi mata” “babu wani abu bayan haka?” “babu wani abun bayan hak gaskiya” Ajiyar zuciya ya sauke yace “Alhamdulilah” Dr ya kalleshi” lafiya?” “lafiya kalau babu komai” Nan dr ya dan jashi da fira kamin suyi sallam ya fice, Police mummy tasa ak kawo masu gadin Rahama duk abunda akeda bukata ita keyi sai kusan 11 dare ta koma gida bayan tayi2 da Abdallah yaki ya bita, Sai 2 da 40 Rahama ta soma motsi da sauri Abdallah ya riko hannunta, A hankali ta shiga bude ido dishi2 ta fara gani hakan yasa ta maidasu ta kulle, Hannu ta kai zata taba gefen cikinta da sauri Abdallah ya rike Fashewa tayi da kuka a hankali Abdallah ya shiga kiran sunanta “Rahama….” Banza ta masa saida yayita kiranta kamar bazai daina ba sannan ta amsa cikin kuka, “naam” “mi kike yiwa kuka?” “Cikina ba aga an fasa min ciki ba” “A a ba’a fasa miki ciki ba andai yankeki kadan kuma likita ya dinke” Bata sake cewa komai ba inbanda hawaye da take Haka ya ciro hankicin ya goge mata hawaye ta, “zakici wani abu?” “a a bana jin yunwa” Murmushi kawai yayi ya dauko lemo orange ya yanka ya matse mata a cup a dora daidai bakin “bude bakin kisha ruwan lemo” “a a bana sha…” Ba shiri ta shiga sha jin yana kwararo mata shi saida ta shanye sannan ya dire kofin yana murmushi “good gal yanzu bude idonki” A hankali ta shiga bude idon ta dade tana kallon silin kamin ta sauke idonta a kanshi Wani murmushi yake sakar mata daya karama fuskarsa kyau hakan yasa tayi sauri dauke kai “ina ummana?” “ummanki tana waje” “ina son ganinta” “au na manta tana bachi kinsan karfe 3 harda wani abu fa” Junkurawa tayi zata tashi da sauri Abdallah ya mayarda ita “ina zaki?” Buge mishi hannu tayi “sake ni ni gurin mamana zanje” “Haba Rahama baki an miki tiyata ba zakice ki tashi” Fashewa tayi da kuka “na shiga uku cikina wayyo na shiga uku” Dafe kai Abdallah yayi “ohh ai nine na shiga uku nida na fada miki” Haka sukayi ta rigima dakar Abdallah yaga safiya ta waye ya kira mata mamanta Kuraren sha biu yan sanda bincike sukazo suka shiga yi mata tambayoyi, “ya akayi abun ya faru?” “nidai na taso daga islamiya sai naga wani mutun yana bina harya zo kusa dani ya cika min wukar nayi kuwa na fadi ban sake sanin inda nake ba sai yanzu” Abdallah yace “saida jiya ko?” Kasa kasa ta watsa mishi harara a ranta tana. _ina ruwanka dan shishigi kawai_ A fili kuma tace “sai jiya” Murmushi Abdallah yayi shida dr dake kula da ita, “kinsan wanene yayi miki haka?” “a a ni bansan shi ban taba ganin shiba” “in kika gansa zaki iya ganeshi?” “eh zan iya” “ya kamainshi yake?” “bakine mai dan kauri da jajayen idanu” Nan suka tashi “mun gode zamuyi bincike insha Allah ki kuma kwantarda hankalinki” Kai kawai ta daga musu suka fice, Abdallah ya rufa masu baya shida dr ya dan dade sannan ya dawo dakin, Tana ganinshi ta wani hade rai Murmushi kawai yayi ya nufi kujera ya zauna “zakici abinci?” Dauke kai tayi “a a ni ka fita” “naje ina?” “nidai ka fita” “banzaje ko inaba” Fashewa tayi da kuka “na shiga uku wayyo ummana” Da sauri ya karaso kusa da ita “lafiya miya faru?” “tho ka fita dan Allah” “tho” da sauri ya juya ya fice yana murmushi © *_Khadeeja Candy_* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: [8/2, 4:33 PM] Khαdeeja Cαndy: *SALEENA* *_Na Khadija Abubakar Alkali_*. *23~* haka Abdallah yayita jinyar Rahama kullum sai sunyi rigima kwananta hudu a asibiti Abdallah yasa dr yayi mata transfer zuwa asibitin da yake aiki ya cigaba da kula da ita, duk wata da wainiya da ake mummy ce takeyi tun mahaifiyar rahama najin haushinta ita da Abdallah ganin sune silar komai daga baya ta daina ganin yadda suke hidima da ita da yarta suka dawo kamar yan’uwa a hankali Abdallah ya turo kofar dakin ya shigo “Assalamu Alaikum” amsa mishi tayi ba tare data kalleshi ba “wa alaikumsalam” da murmushi ya karaso kusa da ita “kinci abinci queen?” kai ta daga mishi “dazu nurse ta dubaki?” nan ma kai ta daga mishi dariya yayi “wai yau kurma kika tashi ne?” kasa ta karayi da kanta “kimun magana mana queen” banza ta masa murmushi kawai yayi ya bude durowa ya dauko alura da sauri ta kalleshi “eh eh mi kace ma mi kake son nace?” kyalkyalewa yayi da dariya zaiyi magana Sulaiman ya shigo shida hafsa. nan da nan rahama ta ware baki “sannu da zuwa anty Hafsa yanzu kuka zo?” rumgumeta tayi “yee rahama na kinji sauki kinga yadda kikayi kiba kamar ba mai ciyo ba?” rufe fuska tayi “kai anty hafsa” sulaiman yayi dariya yace “ai dole tayi kiba abokina ke kula da ita fa kinga ga kwanciyar hankali ga kuma s …..” bai karasa ba ya rufe bakinshi ganin rahama na shigewa cikin jikin hafsa duk suka kwashe da dariya Abdallah yace “kamar yadda ka maida hafsa ko” kallon junansu sukayi sukayi suka fashe da dariya sun ɗan ɗaɗe suna fira sannan suka fice, saida ana sauran kwana uku a koma kotu Abdallah ya sallameta bayan sunyi yargegeniya da mamansu rahama akan rahama zata cigaba da zama gidansu har sa an yanke hukunci dan tsaron lafiyar. dawowarta gidanne ta fara ganin ganin gata gurin mummy da su hannatu da maryam da ummul-khari Abdallah ma ba’ah magana dan kullum gida yana kula da ita haka yake ganinta kamar saleena duk inya tunata ranshi baci yake, ranar da za’ah komai kotu tun da wuri suka shirya har rahama. mota daya ta shiga ita da maryam da hannatu Abdallah kuma ya shiga da ummul-khari da mummy koda suka isun tararda hafsat da Sulaiman harda ma mahaifan Rahama cikin kotu bayan sulaiman ya taresu sun gaisa suka samu guri suka zauna ba aɗaɗe ba Allalin ya shigo shida mukarrabansa kowa ya tashi tsaye dan girmamawa bayan ya zauna aka zauna saida yayi yan mintuna da zama sannan yace “kotu nason ganin Abdallah da dsp jamil da kuma lasdom a gabanta” da sauri Abdallah ya tashi ya nufi gurin da aka saba tsayarda shi ya tsaya wasu yan sanda ne suka shigo dasu lasdom sanye da handcuff da dsp jamil suka tsayer dasu gurinda aka tana darwa masu laifi. alkalin yace “kotu na sauraren lauyoyi” tashi barrister Sulaima yayi yana gyaran riga “ya mai shari’ah idan kotu ta bani dama inson gabarta sheidata ta farko?” “kotu ta baka dama” juya Sulaiman yayi yana kallon wani dattijo yace “malam sani xaka iya tsayuwa gaban kotu” tasowa dattijon yayi ya tsaya gaban kotu Sulaiman ya kallesgi yace “ko zaka fadawa kotu waye kai da kuma aikinka da shekarunka?” “sunana malam sani sana’ahta itace sayarda tumatur shekaruna 64 a duniya” “shin miye akalarka da lasdom?” “banida alakar komai dashi in banda makotaka” “shin ko zaka fadawa kotu abunda kasani akan lasdom?” “eh lasdom mutun ne mai alkhari duk da yake bashi sakin fuska kuma baya daukar raine abu kadan zai iya cewa zai illataka” “shin ka taba ganin abunda baka yarda da shiba a gurin lasdom ko kuma jin wani abu?” “eh tho gaskiya yana yawan neman matan banza wani lokacin ma suda kansu suke zuwa ko shi yazo tare dasu amman abunda bana gasuwa dashi shine yakan kawo mata wasu nuna kuka suna neman taimako ya shiga dasu gidan kuma nakanji anacewa daman ya saba yiwa mata hakan kuma har kisan kai yanayi shine kawai abunda na sani” sulaiman yabkalli alkali “iyakacin tambayoyin da zanyi masa kenan ya mai shari’ah” alkalin ya kalli barrister sumaiya “lauya nada tambayoyin da zakiyiwa malam sani?” tashi tayi tsaye “eh ya mai shari’ah” ta kalli malam sani “shin da kaga abubuwan da baka yarda dasuba mie yasa vaka fadawa hukuma ba?” “saboda ina tsoron ya cutar dani ko iyalina” komai tayi ta zauna “na gode ya mai shari’ah” alkalin ya kalli malam sani yace “zaka iya zuwa ka zauna” sulaiman yace “in kotu ta bani dama inason gabatarda sheidata ta biu?” “kotu ta baka dama” sulaiman ya kalli yace “a shigo da dayyabu” nan take wasu yan’sanda suka shigo da wani matashi daga ganinshi dan shaye2 sai wani rabon ido yake aka tsayarda shi gaban kotu [8/2, 4:57 PM] Khαdeeja Cαndy: matsowa sulaiman yayi kusa dashi ya kalli alkali “ya mai shari’ah wannan sunansa dayyabu yaro lasdom ne kuma yasan komai akan kisan saleena harma da sukar wukar da kayiwa Rahama” alkalin ya kalleshi “kaji abunda ake zarginka shin haka ne?” fashewa yayi da kuka jikinshi sa rawa yake “eh haka yallabai amman wlh ni ban kashetaba ugana ne ya kashe ni ko tabata banyiba” “shin xakayiwa kotu bayanin yadda abun ya faru?” “eh wlh xanyi kafin magriba ne abun ya faru nidai ina zaune bakin gate din mai gidana ya fito yace na janyo mata zamuje wani guri banyi masa musu ba naja muka biyo ta unguwar da zimar zamuje wata unguwar har zamu fice sai kawai yace min na tsaya ina tsayawa sai ya fita ya leka wata kwana ya dawo yace mun ya nabi hanyar yaga yarinyar da yake nema sai mukabita tana ganin mota na binta ta shiga gudu ta koma bayan wani gida ta laɓe nan yafita da kafa yabita tana ganinshi tayi kuwa ta cigaba da gudu mun kuma muna binta a mota sai wasu daga cikin abokansa suka fita suka rika tafiya tare dashi akasa har ta shiga gidan suka bita nima na bita tana kokarin rufe kofar parlour ya tura da karfi ya shiga ya aikata mata fyade shida abokaninsa” “bayan ya karene ya kasheta?” “a a saida yan sanda suka zo lokacin duk tanada rai sai dan sanda ya ganshi yace masa miya aikata haka yace masa ya gudu dan turoshi akayi ya kamashi lokacin duk tanada rai har tana fadin a taimaka mata a kaita asibiti sai dan sandan yace aiko duk ta tashi yana cikin matsala tunda taji abunda yace kuma tasan wayanta suka aikata mata haka har yana tambaya minene mafita sai lasdom da abokaninsa sukace mafita kawai akasheta yana unkurin hanata ne lasdom ya murde mata wuya ya mutu amman wlh bani na kasheta ba” © *_Khadeeja Candy_* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *_Na Khadija Abubakar Alkali_*. *24~* “ance kanada masani akan sukar wukar da kayiwa Rahama shin haka ne?” “eh shine ya aika wani yaronshi yace ya kasheta ya fada mishi inda yake amman wlh bani bane” alkalin ya kalli lasdom yace “kasan wannan?” cewa da dayyabu lasdom ya daga kai “bude baki zakayi kayi magana ba daga kaiba” “eh na sanshi” “mie a lakarka dashi?” “yaronane” alkalin yace “kaji abunda ake zarginka kai da kuma abunda yaronka yace shin gaskiya ne?” shiru lasdom yayi har na wani lokaci kamar ba zaice komaiba saida alkali yace “nan kotu ce ba gidan hutu ba dole ne kuma ka bude baki kayiwa kotu magana” can ya dago kai da jajayen ido yace “eh gaskiya ne” nan take kotu ta yamutse kowa yana fadin albarkacin bakinsa saida alkali ya buga desk yace.”na kotu ce ba kasuwa ba dan haka kowa ya natsu” sannan fa kowa ya kama bakinshi Alkalin yace “kana nufi kai ka kasheta kenan?” “eh nina kasheta” “saboda mi?” Abunda dayyabu ya fada shi lasdom ya fada Alkalin ya jinjina kai yace “shin ina kasan margayiya saleena?” nan take yayiwa kotu bayanin haduwarsu Alkalin ya juya gurin dsp jamil yace “kaji abunda lasdom da dayyabu sukace da kuma abunda barrister yake zarginka akai?” Fashewa yayi da kuka “wlh nayi nadama” “da gaske ka aikata kenan?” “eh na aikata amman nayi nadama” “shin mi yasaka aikata hakan?” “lasdom abokina ne tun mana kanana muka taso tare shiyasa nayi unkurin rufa masa asiri amman na gane kuskurene” Rubuce Rubuce alkalin ya shigayi kamin ya dago kai yace “bisaga dukan hujjoji da sheidu da lauyoyi suka gabatar da kuma ansa laifi da masu laifi suka kotu ta gamsu ta yankewa Lasdom hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa da samunsa da lafin kisan saleena kotu kuma ta yankewa abokaninsa hukuncin daurin shekara 20 a gidan yari bisa da samunsu da laifin yiwa margayiya saleena fyade kotu ta hankewa dsp jamil hukuncin shekara koma sha biyar a gidan yari bisa da samunsa da laifin cin amana kasa kotu ta kuma yankewa dayyabu hukuncin shekara 5 a gidan yari bisa da samunsa da laifin yiwa dan ta adda aikin kuma kotu ta wanke Abdallah shu’aibu esa kuma kotu ta bada umarnin bayarda gawar saleena ga yan’uwanta” saida yayi rubutu sannan ya buga desk “koooooootuuuuuu” Alkalin na ficewa ka wuce da criminals Din Abdallah ya nufi famiy sa suka rumgume juna suna murya, sulaiman ya shiga gaisawa da mutanen dake bashi hannu suna masa murna harda wasu lauyoyi suka rika shigowa suna mana barka, sun ɗaɗe a haka sannan suka fito harar kotun yan jarida suka hau daukar photo suna wasu kuma suka hau fira dashi. daker ya samu suka rabu dashi ya isa parking suna kokarin shiga mota Abdallah ya kalli Sulaman yace “wace asibiti gawar saleena take friend?” Sulaiman yace “mi zakayi?” “inaso ganin gawartane” fuskar mamaki sulaiman yayi “mi zakayi da gawarta?” “plz sulaiman nidai fada min kawai” mummy ta matso kusa dashi ta dafashi “haba Abdallah kayi mi da gawarta kuma” “mummy plz” ajiyar zuciya mummy ta sauke tace “shikenan muje tare duk” sulaiman yace “a a mummy kuje gida kawai ni zan kaishi” haka mummy tayi tsaye ta kafe itakan saida ita dole tasa suka shiga motar su duka suka nufi asibitin koda suka isa sun tararda har an fito da gawarta za a saka mota da wata mata na tsaye gaban gawar tana kuka ita da wasu maza biu Abdallah na isa kusa dasu ya kalli namijin yace “su waye ku?” waddan yadan fisu manyanta yace “ni kawannin saleena ne wannan kuma mahaifiyarta ce” sulaiman yace “tafiya xakuyi da ita?” “eh tun shekaranjiya muke garin anan muna jiran a bamu gawarta” “ina mahaifinta yake?” “yana can gida ba lafiya” Abdallah ya matsa kusa da wadda yaji ance mahaifiyartace ya kalleta yace “mi yasa kuka mata auren dole miyasa kuka aura mata wadda bata so kinga yadda rayuwara ta salwanta ko kinga yadda aka kasheta ko duk sanadin kunyi mata auren dole ta aikata kisan kai duk saboda an aura mata wadda bata so yanxu wace riba kukaci?” in banda kuka babu abunda matar take, cike da sanyin jiki Abdallah ya nufi gawar ya bude mata fuska nan ta nan hawaye suka shiga bin fuskarsa hak ya shiga magana da ita kamar wadda aka ce masa tanaji “kin gudu saleena kinyi tunanin zan tona miki asiri da baki aikata kisa ba saleena da rayuwar bata shiga cikin haɗari haka ba kinyi gudun gara kin fadawa zago kowane bawa baya wuce kaddarasa ke taki kaddarar haka tazo miki saleena yau gashi kin koma ga mallacinki za’ah saki kabarinki daga ke sai abunda kika aikata naso ki rayu saleena naso ki rayu” nan ya durkushe ya fashe da kuka kamar mace, © *_Khadeeja Candy_* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *_Khadija Abubakar Alkali_* *25~* babu wadda jikinshi baiyi sanyi ba gurin Sulaiman ne ya dafashi ya tadashi tsaye, ya ɗaɗe yana kallonta sannan ya juya ya nufi mota sulaiman ne yayi musu Sallama suka kamo hanya koda suka isi sun tararda wasu yan uwa da abokanin arziki kamar marar lafiya ya shiga amsa gaisawa dasu suna masa barka. sai kusan Azahar ya nufi part dinshi yana shiga ya fada banɗaki yay wanka tare da Alwala yana fitowa ya kabbarta sallah bayan ya kare ya shiga lazimi . uku da wani abu ummul-khari ta shigo dakin da sallam “assalamu alaikum yay” saida yakai karshen carbin yayi addu’ah sannan ya amsa mata “Amin wa’alaikissalam sis” “naam yaya congratulations” murmushi yayi “congratulation too” “Allah ya tsare gaba yaya” “amin sis ina Rahama?” “tana can dakina tan shiri” “shirin mi?” “wai zata wuce gida tunda an kare” murmushi yayi ya tashi yana sa agogon hannunsa “kice ta sameni garden inta shirya” “owk yaya” ta fice da sauri, tana fita ya nufi mirrow ya dauki turare ya feshe jikinshi sannan ya nufo garden kujeara dake karkashin icce mangoro ya nufa ys zauna ya lumshe ido, saida yayi minti 30 da zaman sannan yaji sallamarta cikin sanyin murya, a haka ya amsa mata ba tare daya bude idon ba, “anty ummul-khari tace kana son ganina” sai a lokacin ya bude ido yana murmurshi ya kalleta “wow kinyi kyau wlh daman ummul-khari tace mun kina nan kina min kwaliya” da sauri ta zaro ido ta nuna kanta “ni?” “eh kefa gashi kuma bata min karya ba” “nikan bance kai nake yiwa ba” “oh karya take min kenan ko?” ta girgiza kai “a a nifa ko kwaliya banyiba hoda kawai na shafa ba karya take ba amman ..dai bance zanyi maka kwaliya ba” “ai kinfi min kyau a haka kamar na daukeke na gudu” kasa tayi da kanta nan yayi wata miskilar dariya “tho fadamin wa kikayiwa kwaliya haka?” batare data kalleshi b Tace “ta zuwa gida ce” “oh har kin gaji da ganina?” kamar zata fasa kukan tace “dan Allah ka bari bana so” “dan Allah ka bari bana so” ya kwakwayi muryarta, tashi tayi xata fice da sauri ya sha gabanta “sorri bari na bari bazan sake ba” saida yaga ta dan saki fuska sannan yace “muje ki fadawa mummy ko dan kinsan ba ke kadai zakiba?” kai kawai ta daga mishi suka fice, Rahama bata bar gidanba sai kusan 9 na dare bayan sun hada mata goma na arxiki Abdallah da Ummul-khari suka kaita har gida, Tun daga lokacin kusan Kullum Abdallah sai yakai mata ziyara tun tana jin kunyarsa har ta fara sakewa dashi, yau ma kamar kullum Abdallah na cikin mota yaji sallamar rahama cike da murmushi ya amsa “yauwa friend kin fito?” “eh na fito dr yasu mummy?” “suna kalau kinma tunani mummy tace na tamabayeki tunda kin kare karatu mi zakiyi?” fuskar mamaki tayi “mummy tace kodai kace?” shan mur yayi “kamar ya ni kuma” “tho naga kaine kake min wannan tambayar koda yaushe” murmushi yayi “Allah ka yafemin ai naga ba fadamin kike ba shiyasa nace bari na laba da mummy tun har yau kinki ki fadamin wacece kema fa” dariya tayi tace “tho xan fada maka” fitowa yayi ya jingina jikin motar yana kare kunnuwa “ina jinki queen” “tho ai nice nake jinka ka fara tambayarka” shiru yayi alamar tunani can ya kalleta yace “`WACECE RAHAMA?“` murmushi tayi tace Rahama Alhasan shine cikanken sunanta Malam Alhasan shine mahaifinta malama maimunatu itace mahaifiyarta tayi karatu a sokoto kuma na kammala karatuna saida ban cigaba ba kuma nice ta biu a gidan mu yayata tana aure da yaranta biu inada kanne hudu maza uku mace daya nan ne gidanmu kuma ina karkashin kulawar iyayena wannan itace rahama” murmushi yayi yace “a a ba shikenna ba?” “tho mi ya rage?” bari na karasa miki “Rahama black beauty ce mai dogon hanci da idanuwa masu jan hankali da tana da natsuwa da kunya da iya lafazi da gata da zakin murya kuma ta iya sata” da sauri ta kalleshi “mi? wa sata?” “ni mana kinmun babbar sata” “mina sata?” kirginsa ya nuna “zuciyata kika sace” murmushi tayi ta rufe fuska, sun dade a haka kamin ta kalleshi tace “tho fada min yanzu wanene dr Abdallah” “nawa zaki bani?” “zan baka miliyan biu” “a a ni ba kuɗi nake soba” “tho mi kakeso?” “zan fada mikibamman sa in kimmun alkawarin inna tambaya zaki ban?” “eh na yarda zan baka koma minene fada waye kai?” “Sunana Abdallah Shu’aibu esa ni dr ne mahaifina kuma ya rasu kin kuma ga mahifiyata ni dan sokoto kuma nine na farko a gidanmu inada kanne mata uku hannatu maryam da kuma ummul-khari shikenan” murmushi tayi tace “yayi kyau dr” “tho bani abunda kika min alkawari?” “tho ai kai zaka fada” jimmm yayi kamin ya dago ya kalleta suna hada ido yace “zuciyarki nake son ki bani” da sauri ta dauke kai tana murmushi jin tayi shiru yasashi cewa “kona maimaita?” kai ta girgiza masa ta nufi kofar gida, saida ta kusa shigewa sannan ta juyo tace “an baka” ta shige gidan da gudu murmushi yayi ya daga hannunshi sama “yesssss” ya ɗaɗe gurin yana kallon kofar kamar mai jiran fitowar ta sannan ya shiga motarsa ya dauke hanyar gida cike da farinciki, *_Khadeeja Candy_* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *_Khadija Abubakar Alkali_* *26~* Abdallah na kwance saman kujera yana waya da Rahama sai kwasar dariya yake yana ganin mummy yayi saurin yin salama da ita ya tashi zaune . mummy ta kalleshi tana murmushi tace “ai daka cigaba da wayarka ni kicin zanje ba gurin nayiba” tashi yayi yana murmushi “bari naje part dina nayi wanka mummy” “lailaikan kara kaje ku karasa wayar yafi” maryam ta fada tana saukowa downstairs juyowa yayi ya watsa mata harara ta kalli tace “mummy karya nayi?” mummy ta gizgiza mata kai “a a” da sauri ya fice yana dariya, *bayan wata 4* su mummy suna zaune parlour suna fira suakaji sallamar Sulaiman duk suka amsa mishi Abdallah ya bashi hannu suka gaisa sannan ya gaida mummy ya samun kujera ya zauna ya kalli mummy yace “mummy hajiya tace na fada miki ki shirya this monday zakuje tambayar auren hafsa” mummy ta washe baki “masha Allah kace mun girma haba ko kaifa Abu yayi kyau wlh Allah kaimu” Abdallah ya kalleshi “kana nufi kai da gaske?” dariya sulaiman yayi “ka dauka karya nake hala aina fada maka” ya kalli mummy “Ahh tho nima gaskiya mummy asan nayi nima ane mamin dan bazan yarda Sulaiman yayi ya barni ba” murmushi mummy tayi tace “Alhamdulillah ai daman wanna ranar nake jira zura maka ido kawai nayi naga gudun ruwanka zamu shirya komai insha Allah” Sulaman yasha mur “niko kaga Abdallah bana son gasa wlh baka tashi neman auren ba sai yanzu da kaga na nema?” Abdallah ya kalli mummy “ai koda kazo muna maganar ko mummy?” mummy tace “a a yanzu dai ka kawo maganarka” duk suka kwashe da dariya, sati daya da tambayar auren sulaiman aka tambayi na Abdallah Farinciki sosai Rahama tayi ita da iyayenta daman suma wannan ranar suke jira, legos mummy taje ta hado mata laifinta gani na faɗa, ana kai na sulaiman aka kai nashi wata uku suka sa Abdallah yasa mummy ta roka aka mayar wata biu saboda bukinsu yaxo daya dana Sulaiman danshi wata biu akasa basuyi gardama ba suka amince, ya zama 1 ga watan April, sosai mummy taji ɗaɗi su hannatubda maryam da ummul khari suka shiga shirye shirye mummy kuma tasa aka gyara mata gidanta komai saida aka chanja har fentin gidan sabuntashi akayi, ɓangaren Abdallah ma ba zama dan tunda lokacin yake kai da kawo dan ganin komai ya kammala abuja yasa aka bugo masa iv babu wadda bai gayyata ba har friends dinshi da yaɗaɗe rabonshi dasu ya saida ya aika musu iv ta ɓangaren mummy babu wadda bata gaiyata ba kaf family and friends babu wadda baisan da maganar ba, su maryam da hannatu da ummul-khari ma saida sukayi tasu gayyatar. *******××××××××××******** ranar talata akayi wankin amare hafsa da Rahama laraba sukayi arab day, alhamis akayi kamu abun kwanin ban sha’awa amare suka saka kaya irin daya gurin zamansu ma abun kallone, kowane fuskarsa dauke da murmushi anyi taro sosai harda an _Khadeeja candy novels_ sunci ado sai wani takun kasaita suke, ranar jumma’ah akayin walima _malama hafsat ibrahim dan gaskiya addmin din nisa’ul khari_ tayi wa amare nasiha akan zaman takewar aure _malama maimunatu ibrahim addmin din Macce abun son_ matayi musu tsokaci akan kwaliya da kuma girke2 taro yayi taro su serder ansha ado mrs shagari ba ah magana sai dauka pic take Ag frndy tana kura da ita sai wasar baki take peenah take away kawai take rabo, ranar asabar 9pm akayi dinner amare sukayi ankon farin riga gown amgwaye kuma farar shadda a hankali suke rausayawa ana musu barin kudi, bayan sun zauna yan _Classic ladies_ suka shiga Filin rawa suka fara aikinsu _pretty gal saida dan kwalinta ya fadi_ bayan sun kare suka yanka cake. sai kusan 12 aka watse, “`1 ga watan April da misalin karfe 11 aka daura auren Abdallah da Rahama Sulaiman da Hafsa a masallaci jumma ah na Abubakar maccido“` ranar na kasa banbance wadda yafi wani farinciki tsakanin Abdallah da Sulaiman kowa ka gani fuskarsa kamar an masa albishir da aljanna mummy ba bayaba sai hamdallah take yiwa Allah, *8:30* aka kai amare dakunnansu Kowane gida babu laifi specially na Abdallah babu karyar naira kuma yafi karfin talakka © *_Khadeeja Candy_* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *_Khadija Abubakar Alkali_* *27~* bayan Abdallah ya raka abokaninsa ya shigo dakin da salama cikiciki ta amsa mishi saboda sakewar da muryarta tayi akan kuka, kusa da ita ya zauna yana murmushi “dear kuka dadi kika ko?” bata ce komaiba saima kara fashewa da tayi da sabon kuka da sauri ya jata jikinshi ya rumgume yana buga bayanta alamar rarrashi, sun ɗaɗe a haka saida yaji ta ɗan tsagaita kukan sannan ya kalleta “tashi mu godewa Allah ko?” kai ta daga mishi ta tashi suka rage jayan jikinsu suka shiga bandakin tare sukayi alwala suka bayan sun fito sukayi nafila biu ta godiya ga Allah, da suka kare ya janyo kayan ciyeciye daker ya samu taci sai ya tabbatarda ta koshi sannan shima yaci, bayan sun kare yakai kayan kicin. koda ya dawo dakin ya tararda harta kwanta da kayan jikinta murmushi kawai yayi ya sanya kayan bachi ya kashe wutar dakin ya kwanta, washe gari da wuri mummy ta aiko ummul-khari da kayan karyawa haka tayi ta musu shegantaka, bayan fitar Abdallah abokanin amaryan suka rika kai mata ziyara, sai kusan magariba sukabar gidan koda Abdallah ya shigo ya tararda ita ta kwaɓa ado kiss taji an manna mata gefen kunne haka ya tabbatar mata da angonta ya shigo da sauri ta tashi tsaye tana zare ido murmushi yayi yace “ka kara ko?” “gaskiya kinyi min kyau amarya” da sauri ta rufe ido jan hannunta yayi ta fado kanshi ya rumgumeta yana dariya, a hankali ya fara aika mata kiss kamin ya fara yi mata abubuwan masu kwance kai saida taji yana kokarin wuce guri sannan ya janye jikinta ta shige ɗaki da gudu. dariya yayi ya rufa mata baya, daker ya lallabata suka dawo parlour sukaci abinci nan ya barta yaje yayi wanka ya saka yakan bachi ya nufo parlour kusa da ita ya zauna ya jata ya rumgume saida yaga hankalinta ya dauko kan tv sannan ya fara aika mata da sakwanni ya shiga kokarin rage mata kayan jikinta, daker ta kaci kanta ta nufi ɗaki tashi yyi a galaibaice ya nufi ɗakin. _a daren Abdallah ya maida Rahama cikankiyar macce,_ washe gari da asuba shiya taimaka mata tayi wanka sukayi alwala tare sukayi sallar sannan ta shiga masa kukan shagwaba shi kuma duk yabi ya rikice yana lallabata sai sa mata Albarka yake, *BAYAN WASU WATANIN* suna zaune suna cin abinci Abdallah sai aika mata da sakwannin soyayyah yake ita tana aika mishi har suka kammala zata kwashe kwanukan yayi saurin dakatar da ita “a a dear ni zanyi wannan kifa kika girka” da kanshi ya kwashe kayan yakai kicin. bayan ya kai ya aika mata kiss a wuya ya riko hannunta suka dawo saman babbar kujera ya zauna ya zaunarda ita gefensa ya rumgume, suka shiga aikawa juna sakwannin soyayyah sun dade a haka sannan ya kalleta da sleeping eyes yana shafa cikinta yace “babyna i love yhu so much Allah yayi miki albarka ya saukeki lafiya” murmushi tayi ta lakatar masa anci “amin dear Allah barmu tare” sun dade a parlour sannan suka nufi dakin cike da kauna. haka suka cigaba da soyyayyah abu abun burgewa a bangaren Sulaiman ma sai hamdallah basu da wata matsa kowa yabon zamansu yake, ranar wata monday Rahama ta tashi da wani mugun ciyon mara haka ta wuni taki ta fadawa kowa gashi ranar Abdallah bashi hutu sai kusan 9dare ya shigo, tunda yayi sallama yaji ba’ah amsa masaba hankalinshi ya tashi da sauri ya aje kayan kwalan daya siyo mata ya nufi dakin, kwance ya tararda ita a galabaice idonta rufe ta dafe ciki yana dagata yaga jini hakan ya tabbatar mishi da haihuwace. da sauri ya sata mota ya nufi asibiti, tun kamin ya isa ya kira mummy ya fada musu, can ita kuma mummy ta kira iyayen Rahama ta fada musu bai ɗaɗe da isa asibitin ba suma suka isa, tsaye sukayi bakin dakin haihuwa suna kai da kawo. Abdallah kuma yana ciki yana karbar haihuwar matarshi, cikin idon Allah ta haifo masa santaleliyar baby gal fada muku yadda Abdallah yake farin ciki ma bata lokacine su mummy ma ba’ah magana kamar su zuba ruwa kasa su sha, ranar suna yarinya taci sunan mummy Halima’tu aka mata lakani da Mannal babu abunda ba’ah raba ba kowa sai yabon buki yake saboda yadda Abdallah yayi mata gata saikace autar duniya, © *_Khadeeja Candy_* [8/6, 3:20 PM] Khadeeja Candy: *SALEENA* *_Khadija Abubakar Alkali_* “`LAST PAGE“` *28~* kowa yaga mannal zaibgane yar abdallah ce dan duk shita biyo babu inda ta ragoshi Rahama nayin arba’in ta koma gidan mijinta lokacin ne Abdallah ya kara sanin girmansa yanzu dai gashi ya zama uba kuma shugaba, Rahama maba bayaba dan kullum cikin yiwa Allah godiya take daya bata Abdallah a matsayin mijinta gashi da sanin darajar mace da iya tafiyarda rayuwa fagen kyau ma ba bayaba haka rayuwa ta cigaba da tafiya tsakaninsu kowanne na farin ciki da abokin zamansa, da far’ah Abdallah yashigo kamar kullum jin kuka mannal a ɗaki da sauri ya nufi ɗakin, saman gado ya tararda ita jin motsin ruwa a banɗaki ya tabbatar mishi da wanka Rahama take, hannu yakai ya dauketa ya shiga jijjigata, nan da nan tayi shiru dan daman tasan hannun abbanta suna haka Rahama ta fito daure da tawul tana murmushi “dear ka dawo?” bata mata fuska yayi “ban saniba ki shiga wanka ki barmin yarinya tana ta kuka haka?” hannu takai ta taba gashin kanshi kamar wani karamin yaro “sorri dear bazan sakeba” murmushi yayi yace “are u sure?” saida ta masa kiss sannan tace “yes” janta yayi ya rumgume “love u babyna Allah barmu tare” tace “Amin” NIMA NACE” *AMIN* ” “`TAMMAT BI HAMDILLAH“` *my words* auren dole ba fa’idaba so da yawa yaka zama alkhari so kuma da yawa yakan zama shaeri dan haka ni bance ba alkhari bane hakuri kuma maganin zaman duniya da saleena tayi hakuri ta zauna gidan mijinta da haka bai sameta so da yawa wasu akan musu auren dole kaga sun gudu sun koma zaman bariki wasu kuma su kashe mijinsu kamar yadda saleena tayi kuskuren aikatawa duk wannan ba abun yi bane hakuri ya kamata da kayi hakuri saka cinma riba mai yawa kuma ka samu rabo lafira kuma duk abunda hakuri bai kawoba rashin shi bazai kawo shiba, Rike gaskiya kuma yanada matukar amfani shine silar fitar Abdallah daga halin daya shiga duk ka rike gaskiya duk inda ka shiga sai Allah ya fitar dakai, taimako yanada amfani amman ana son mutun yayi taka tsansan, kurakuran da nayi ina rikon Allah ya yafemin no one is perfect oh Allah hope for your mercy. don’t leave me for myself. correct all of my affairs for me. *DEDICATED TO* Sumaiya bello (summy London, sumsum) my sweet friend Allah Barmu tare. *TUKUICINE* gareku masoyana a duk inda kuka ni daku Mutu kan raba na gode da kauna Allah barmu tare. *KUNA RAINA* momi aisha gusau momi fatima nura momi shafa gusau maman husna kawar arziki Hadiza babangida (umcy) hauwa zamau besty hafsat gusau (hafscyG) Manira mrs umar anty fatima dr hauwa dahiru aunty Fauziya d sulaiman Ag frndy aunty na Dr khadija Ibrahim kin nunamin kauna fiye da tunanina. *NA GAISHEKU* kdeey s.a azeez mai hancin roba kausar lov kina raina teema luff zee maman khady shafa’atu umar nafee anker sadiya afka my daughter Rashida Abdullahi kardam sis Rofaida umar Amrah hannefa usaman munay baqa Aysha one fati azlam rabi’ah sk mashi jeeddah aliyu zara bb Benazer omar *NA YABA MUKU* Nagarta writers Association *NA GAISHEKU*. wisdom Hausa writers Extreme Hausa writers Excellent writers Best writers group modern hausa writers Online hausa writers *BAN MANTA DAKUBA* yan group dina Khadeeja candy novels na whatsapp dana facebook, da classic ladies hadaku Perfect women’s da Doctor’s Group ina sonku sosai *All friends* are not True. But true friends are very few, Which includes U. my dear _Rose okkwafo (rosy lurv) u always stay by my side even the holy world are against me *KUNFI KOWA* son novel dinnan the world of novel’s da mace amana’ce doctor’s Group samira luff pretty gal miss indomi na gode sosai da kauna Harma da wayyanda ban Ambataba Khadeeja Candy tana godiya tana sonku kuma tana gaisheku _DOMIN GYARA KO KORAFI KO KUMA SHAWARA here is My Number ~08036126660~_ _ni Khadija Abubakar Alkali kece muku bissalam_ adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *