Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Friday, June 2, 2017

Kukan kurciya cmplt

adsense here

[2/9, 8:00 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 🐾KUKAN KURUCIYA...🐾 NA MUH'MD ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM {Bily}✍🏻 (Mrs Abdus'salam) Assalamu alaikum yaku 'yan uwa, muna farin cikin kasancewa daku a wannan d'an littafi namu, ALLAH yabar k'auna. Idan kin karanta ko ka karanta wannan littafi namu kaga abinda yay kama da rayuwarka, ba haushi zakujiba bakuma marubutan littafin zaku zagaba, A'a, kamata yayi ku bibiyi littafin domin magance taku matsalar ko gyara taku rayuwar, fatanmu masu kuskure irin wannan su daina, masu sha'awar yi karsu fara, shiyyasa muka kira littafin da suna "KUKAN KURUCIYA, MAI HANKALI NE KAD'AI YAKE GANEWA, to ALLAH yaganar damu ayayinda b'ata ya riskemu.🙏🏻🙏🏻 Page 1⃣&2⃣ Tafiya take tana had'a hanya, kai da kaganta kasan ba,a hankalinta take ba, dan kariyar ALLAH ce kad'ai ke tareda ita a bisa titin, takalmanta rik'e ahannunta, gata dai k'yak'yk'yawar mace dirarriya kuma fuskarta tana nuna alamun hak'uri, wani ihu datayi yasa muka maida kallonmu gareta, tacika hannu dak'asa ta watsa jikinta, tasake kwala ihu saini Ameeda, d'iyar malam dauda da iya Abu, d'iya d'aya tilo agurin iyayenna, nice tafari nice auta, yarinya mai farin jinin tallah. Bansan sanda hawaye suka zubo bisa kumatunaba, takuma kaikaicewa ta rabga ihu, na girgiza kai dan tabani tausayi matuk'a. Mai adaidaita sahu ta tare, cikin muryar 'yan maye ta ce, "gidanmu zaka kaini. Mai adaidaita ya yatsine fuska, toni nasan gidan kunne? kifad'i anguwar dazaki malama. Tayi shiru🤔 alamar tunani, can tađ'ago tana kallonsa da rinannun idanunta, ta ce, "kaga namanta sunan anguwarmu amma muje zan dinga nuna maka hanya. Mai adaidaita yaja dogon tsaki yana fad'in saboda nima makakkene irinki ko??, yaja adaidaitarsa yayi gaba. Ta tuntsure da dariya tana nuna babur d'in tasa, kaga mahaukacin mutum, amfad'a maka dan ina a bige kwakwalwata bata aiki ne?, jiri ya jata kamar zata fad'i, tayi saurin dafe wata mota dake bayanta. Indai tak'aice muku ta tsaida adaidaita kusan uku amma basu d'auketaba dan jin tamance sunan anguwarsu, da k'yar wani yad'auketa, tako ringa nuna masa hanya dalla dalla har kofan gida, ta zaro d'ari biyu acikin d'ankwalin ta tamik'a masa, yakarb'a yana fad'in toga canjin malama. Ta juyo tana kallonsa dan harta fara tafiya, ta ce, " sunana ba malamaba, kuma canji kaje nabar maka duka, tafad'a dad'an k'arfi. Mai adaidaita ya jinjina kai yana godiya ya ce, "ya ALLAH yashiryeki kinji. Muda muka biyosu abaya mukace amin ya RABBI. Cikin gidan tashiga tana tangad'i, iya Abu dake a tsakar gida tana aiki tabita da kallo cikin bacin rai. Ameeda tazube agabanta tana fad'in iya taimaka mini da abinci wallahi cikina kamar b'arayin duniya sunmin sata. Iya abu ta balla mata harara ke tsinanniya kada ki bata min rai in abinci kikeso ki koma ki ciwo daga inda kika fito , idan kuma kinje kibar tunawa dani, inkuma bahakaba wlhy yanzu jikinki zaya gaya miki. ameeda ta tuntsure da dariya harda bugun k'asa ta ce, "iya aii tsinannun nada yawa dankema tsinanniyarce, na tabbata kafin iyayenki su mutu saida suka tsitstsine miki albarka.. Kafin ta k'arasa iya abu tashiga jibgar ta tamkar ALLAH ya aikota, itako sai ihu take da kururuwa harda zagi, makwafta suna jinsu, babu wanda ya leko balle a shigo ceto, dan idan da sabo sun saba, babu wayewan gari dabaza'a daki ameeda ba, saidai idan bata kwana a gidanba, dan wata sa'in bata kwana agida, duka sosai iya abu tayi mata, saida taga ko yatsun hannunta baya motsi sannan tabarta tana cigaba da kalaman tsinuwa da d'ebe albarka ga d'iyar tata. Ahaka malam dauda yashigo yasamesu, azatonmu za'a samu rangwame daga garesa, amma saimukaji yana ambatar wannan shegiyar sai yanzu tadawo gida??. iya abu dake cin rai ta huro hanci ta ce, "yanzu tadawo zatamin iskanci nazane shegiya. Yayi dai dai,yasa k'afa ya shuri ameeda dake kwance A kasa matsiyaciya tashi kibawa mutane wuri, sai kaurin taba kikeyi asararriyan yarinya. Na rintse ido nabud'e danjin irin munanan kalami da iyaye ke yima d'iyarsu, lallai dole ameeda ta lalace indai har haka iyayenta suke mata tun tana karama. Itako ameeda tana kwance ko motsi batayiba bare ta amsa kalaman baban nata kota bi umarnin sa, ruwa ya d'ebo ya watsa mata, tabud'e idanunta dak'yar, ya ce, "bacewa nayi kitashi anan ba me kika tsaya kina kallona, ameeda ta mika masa hannu tana fad'in taimaka ka kaini d'aki baba wlhy duk jikina yayi tsami, waccan tsohuwar ta dakeni sosai, kafa yasa ya shureta da karfi yana zagi da tsine mata, ta maida hannunta tana fad'in bakaso natashi kenan, dan nikam bazan iya tashiba, duk cikin yanayin maganar bugaggu take maganar. Banza sukai mata suka cigaba da harkokinsu, saida taji rana tafara dukanta taja jikinta da k'yar tashiga dakinta a kofar dakin ta kwanta abinta.................✍🏻 Ku biyomu. Hikayarmu!!! 💖Abba gana💖 & 💞Bily💞 www.muhdabbagana.blogspot.com [2/10, 8:06 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 🐾KUKAN KURUCIYA.......🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM {Bily} (Mrs Abdus'salam) Page3⃣&4⃣ WACECE AMEEDA???. Ameeda diyace ga malam Dauda, iya Abu itace mahaifiyarta, ita kad'ai Allah ya mallaka musu, sun dade suna neman haifuwa a kwana a tashi Allah ya albarkacesu da Ameeda, sun nuna mata so da kauna da ya wuce misali wanda hakan ya jawo ta tashi a sangarce, tayi karatu har zuwa secondary kuma tanada kokari, ta samu tarbiyya dai dai gwargwado a wajen iyayen nata. Ameeda tun tana 'yar karama take talla, saboda tsantsan son kudi irin na mahaifiyarta tun mahaifinta malam dauda baya jin dadin tallar da ake d'oramata har ya zamana baya iya cewa komai dan iya abu ta mallakeshi sai abinda tace. AMEEDA k'yak'yk'yawace sosai, ga dogon hanci, tanada hak'uri sosai, dakuma tsoro. Duk da gatan da iyayenta suke mata wannan baihana mahaifiyarta duka da aibanta d'iyar ta taba, abu kadan ameeda zatayi sai mahaifiyarta ta hauta da duka da zagi, balle taje bata sayar mata da kayan sana'ar taba, aii ranar ta banu. K'yawun ameeda yasa takasance mai farin jini awajen samari, talakawa damasu kud'i, idan kaga motoci na layi a k'ofar gidansu saika d'auka wani taro akeyi, duk wanda yazo kuma dole taje balle idan yanada mota, inko tak'i zuwa mahaifiyarta tafara tsinemata kenan dayi mata gori, wai babanta talaka itama taje ta auri talaka, saisu dawwama a talauci. Wannan maganganu suna k'ona zuciyar ameeda, amma babu yanda zatayi tunda mahaifiyarta ce. Akwana a tashi wani saurayi mai suna Naseer yashigo rayuwar ameeda, Naseer d'an mai kud'ine sosai, gashi shima an sangartashi, dan shikadaine awajen iyayensa, kwata-kwata bashida tarbiyya ko kad'an, ya kware a fagen shaye-shaye da neman mata, tunda ya k'yalla ido akan Ameeda yaji yana buk'atar yayi tarayya da ita, amma saidai ameeda tak'i bashi had'in kai, yaja ra'ayinta da kud'i, amma ta bijirewa buk'atarsa. wani abokinsa Badaru shiyya bashi shawarar yakama k'afa da mahaifiyarta mana, yasan dole tasa ta kulashi , yakoji dad'in wannan shawarar tasa, dan haka sukayi shiga ta mutunci sukaje har gidansu ameeda, yanemi izinin zuwa wajenta zance, dafarko mahaifiyarta tak'i amincewa, dan ta ce, "baza'a kashewa d'iyarta kasuwaba tana tashenta, amma da Naseer ya ajiye mata d'aurin kud'i saita amince da sauri, harda alk'awarin mallaka masa ameeda. Tun daga nan Naseer yasamu damar zuwa wajen Ameeda, saidai tak'i bashi hadin kai, ganin wannan yasa yafara zuba mata benelyn acikin lemo, tun bata sha harta fara saboda tana ganin nan gaba shi zai kasance mijinta, Ahankali lemon dayake kawomata yafara tasiri a rayuwarta, har takanji idan bata shaba bata jin dad'i. Da Naseer ya kula tazo hannu, saiya koma kawo mata zallar benelyn, da sauran kayan saka maye, akwana atashi harta fishi kwarewa wajen iya shaye-shaye, ya kuma koya mata zuwa club, takanje ta kwana acan, ba tare da wani fargaba ba, Ameeda tayi suna a club saboda iya rawa, da d'ibar kayan maye, idan tana rawa dolene abata fili a club. Saidai abin sha'awa ga rayuwar ameeda, duk iskancin nata bata tab'a aikata zina ba, babu lallab'ar da Naseer bai mataba amma tak'i, bayanshi wasu dayawa su kan sha kawo mata hari amma tak'i, duk buguwar datayi baka isa kaja ra'ayin taba, bare kace zaka nuna mata k'arfi. Wasu samarin kuma suna tsoron Naseer ne saboda zarransa, yanzu Ameeda tazama cikakkiyar 'yar maye. Gashi iyayen nata sun tsaneta, suna kuma tofin ala tsine da k'addarar rayuwar data da baibaye d'iyar tasu. Yauma kamar yanda ta saba ta tashi tayi wankanta, tad'au kwalliya cikin wando da riga na fakistan, tayi matukar kyau, tafito tana goge takalmi, iya abu tafito daga kicin hannunta rikeda kwarya da gari, Ameeda ta ce, "iya yau babu abincine??. Iya abu ta watsa mata harara, tana fad'in tunda kin bani kud'in yi abinci basai ki danne ni ki kwataba. Ameeda tayi murmushi tareda jawo jakkarta, tazaro 'yan dubu dubu guda biyar ta mik"a mata, ga wannan kuyi cefane kafin nadawo. Jikin iya abu na rawa takarb'a tana washe baki, yauwa 'yar albarka, idan kina bada irin wannan mai zai sa muringa fada, kedai ALLAH yabaki miji nagari mai kud'i da mota. Ameeda tayi murmushi domin jin furucin mahaifiyar nata, tana mamakin kwadayi irin na mahaifiyarta, itadai indai kanada kud'i to komai mugun halinka zata zauna dakai, ahankali ta furta ya ALLAH ka shirye iyayena, kakawo mini canjin rayuwa mai albarka....... Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!. 💖Abba gana💖 & 💞Bily💞 [2/10, 8:09 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 🐾KUKAN KURUCIYA..........🐾 NA MUH'MD ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM {Bily}✍🏻 (Mrs Abdus'salam) Page5⃣&6⃣ AMEEDA tamik'e tana fad'in iya bari naje saina dawo, iya tajuyo tana kallonta ta ce, "to Yau kuma sai ina??. AMEEDA tad'an gyara tsayuwarta ta ce, "iya zanje wajen falmata ne, amma zuwa yamma zan dawo, zanbawa hashimu sako yakawo muku yanzu idan nafita. Iya ta washe baki tana fad'in to madallah, Ameedan baba, amma dan ALLAH yau kar a dawo a buge d'innan. Ameeda ta fice tana fad'in to inna, a zaure ta tsaya tana share hawaye, da alamun tana cikin damuwa, tad'an dad'e tana zubar da hawaye, daga baya tagyara fuskarta sannan ta fice. Gidan wata k'awarta taje falmata, itama dai falmata irinta ce, dan a club suka had'u, saidai falmata tana zaman kantane, wannan halinne ya banbantata da Ameeda, a hankali suka shaku har suka zama k'awaye mafi kusanci. sallama tayi ta shige ciki, Suka rungume juna cikin farin ciki, falmata tace kai Ameeda wlhy yau kinyi k'yau, ga idanunki yau dai-dai suke. Ameeda tayi dariya ta ajiye jakar ta a saman kujere, ta warware gyalen data nad'e akanta shima ta ajiye, ta kwanta. Falmata ta ce, "badai barciba Ameeda??, Ameeda tad'an yatsine fuska, ta ce, "barci tsiya nakeji, ga yunwa ya takurani yakamata abani abinci. Falmata ta ce, "to mizakici? Asiyo miki, kinsandai ni ba girki nakeyiba. Ameeda ta harari falmata tana fad'in ai ba abin kirki kikayiba. Falmata tayi dariya kawai, dan kullum Ameeda tana bata shawara akan tadage ta iya girki, saboda wataran dole subar shashancin nan suyi aure. Babu dad'ewa aka kawo musu abinci, suka zauna sukaci suka k'oshi, Ameeda ta kalli falmata ta ce, "wai babu komai yau agidan ne??. Falmata ta harareta, dan tasan kayan maye take nufi, ta ce, "plz Ameeda karki sha komai, ke wai bakya zama sai abuge, yakamata yau d ki dan huta, gashima zanyi bak'i daga abuja, shi yasama na ce, "kizo da wuri, danki tayani gyaran gida. Ameeda ta ce, kice dai kawai kin maidani 'yar aiki, amma wane irin bak'ine maza ko mata, idan mazane kema kinsan bazan zau....... Falmata tayi saurin katseta sannu ustaziya, nibansan randa zaki wayeba Ameeda, kishigo harka sosai dan ki wuce wajen, kifita daga tarkon talauci, ki fidda iyayenki. Ameeda ta had'e fuska tareda d'agawa falmata hannu, "kinsan nasha gargadinki akan wannan maganar, wallahi dana tara dukiya da kudin banza gwara na mutu acikin talauci, tamik'e a fusace taja gyalenta da jakka. Da sauri falmata ta tareta tana bata hak'uri, akan bazata sakeba, dak'yar tashawo kan Ameeda ta hak'ura ta zauna. Ameeda taje ma'ajiyar kayan mayensu takwaso kwalabe uku tadawo tazauna, dan sune kad'ai zasu gusar mata da b'acin ran da falmata tasakata, ta tsani kace mata tayi tarayya dana miji, haka tadinga korawa harsuka kare, tamik'e zata k'aro wasu, falmata tayi saurin tareta tana fad'in ya isa haka. Ameeda ta ce, "d'aya kawai zan k'ara, falmata ta ce, "A'a, bazaki k'araba wlhy uku fa kika sha, nan dai falmata tayita lallab'ar ta, harta hak'ura tashige bedroom ta kwanta. Falmata tabita da kallo tana girgiza kai, tana mamakin yanda Ameeda take caja kanta da kayan maye, amma bata yadda ta aikata wani fasikanci ba, zata iya cewa bata tab'a had'uwa da mutum irin Ameeda ba, dan sunsha yin fad'a akan hakan, koda yake tasan tunda Naseer ya gagara tursasa Ameeda dole kowama ya kasa. Dan idan har Naseer yasaka ido a kan mace tofa dolene tashiga tarkonsa, amma Ameeda ta gagareshi, yayi dai nasarar koya mata shaye-shaye, da zuwa club, amma sauran bad'ala ya gagara. WACECE FALMATA??? Falmata 'yar asalin barno ce, ita cikakkiyar babarbariya ce. Falmata yarinyar kirkice mai ilimi da addini, mahaifiyarta ta rasu wajen haihuwarta, daganan kakarta ta reneta tsawon shekara bakwai daga baya Allah ya karbi abunsa. Bayan rasuwar kakarta sai aka dawo da ita gidan mahaifinta, daga nan falmata tashiga tsananin rayuwa, dan matar babanta tana gallaza mata, bata sonta ko kad'an, amma agaban mahaifinta ta kan nuna mata tsantsar so da tausayawa. Wannan yasa mahaifinta yakasa fahimtar halin da falmata take ciki, gallazawar tayi yawa, dan har takai abinci yana gagarar ta agidan, wannan yayi matuk'ar tasiri wajen lalace warta, daga baya ta gudu zuwa garin kano, anan tahad'u da badaru abokin Naseer. Shiya siya mata gida, yake mata komai data buk'ata kamar matarsa. takaitaccen labarinta ....................✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!. 💖Abba gana💖 & 💞Bily💞 [2/11, 8:10 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 🐾KUKAN KURUCIYA....🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM {Bily}✍🏻 (Mrs Abdus'salam) Page7⃣&8⃣ Sai yamma can Ameeda ta tashi daga nannauyan barcin daya d'auketa, takai dubanta ga agogon dake manne a d'akin falmata, 5:56pm ta zaro idanu tareda fad'in nashiga uku ni Ameeda ko sallar azahar banyiba, ta zabura daga gadon tana maida numfashi, bandaki tashige tayi wanka tareda yin alwala. D'akin tadawo tafara ramuwar sallah. Bata bar wajenba har saida tayi sallar isha'i, tun tana kabbaran farko takeji ana buga k'ofa bayan ta kammala ta saka kayan falmata sannan ta bud'e d'akin tafito. Tayi turus dan ganin Naseer zaune, shima ayatsine yake kallonta yanata wani mazurai. Ta daure ta ce, "sannu da zuwa. Harara ya watsa mata taredajan tsaki, ya ce, " 'yar rainin hankali, shine kika wani kulle d'aki, anata bugawa kinyi banza da mutane. Ameeda tad'an tab'e baki kayi hakuri ina sallah ne. A'a d'awafi kikeyi, tun karfe 1 narana nake zarya agidannan falmata ta ce, "mini kina d'aki kwance, dan iskanci inata buga miki kinki ki bud'e. Lah wlhy barci nakeyi, kwata-kwata banjikaba, kaima kasan danaji zan bud'e aii. Harara ya zabga mata, yau kika fara shiga d'aki ki kulle ayita bugawa kiki bud'ewa, zaki kawomin wani tsarin banza. ka yi hak'uri, yanzu mike tafe dakai?? Saida ya kurb'i giya sannan ya ce, "nazone dama nafad'a miki gobenefa zuwa abuja d'innan, dan haka ki kwana da shiri, dan kinada matuk'ar muhimmanci awajen faty d'inanan, kinsan dai yanda nake da ANAS, baikuma dace ace babu baby na awajen birthday d'insaba. Ameeda tad'an murgud'a baki, nidai tun ranar nagaya maka bazan jeba, dan haka kabar zancennan kawai, banaso yakawo mana b'acin rai, tafad'a tana mik'ewa, ni bari na wuce gida dare yanayi. ke k'aramar 'yar iska har kin isa nabaki umurni ki bijire? kodan kinga ina lallabakine??. Ameeda tayi masa kallon sama da k'asa ta ce, "To Nas kai ubanane dabazan bijirema umar ninkaba, kaima kasan idan har na ce, "bazanyi abu ba, to bazanyi d'inba", dan haka ka saurara mini, ina sauran 'yammatan naka kad'auki d'aya acikinsu mana ta rakaka. Nas ya finciko Ameeda cikin xafin nama ya had'eta da bango, cizo ta galla masa ahannu, da sauri ya saketa, ta nunashi da hannu kai Nas kasan nasha fad'a maka, duk iskancinka kadaina gigin tab'amin jiki, wlhy kashiga hankalinka, idan har bazaka iya fad'a min magana daga nesaba to ka saurara, niba 'yar iska bace kajiko!!. tana gama fad'a ta fice, atsakar gida ta tarar da falmata itada bad suna hira, kallo d'aya tamusu ta d'auke kai tana tsaki, daga nesa ta ce, "falmata nawuce gida saida safe. Falmata ta ce, "kai Ameeda bazaki kwanan anan bane??, ko yau bazakije club bane?. Ameeda ta yatsine fuska tana fad'in bazanjeba, inaso naje gida dan nafad'ama iya cewa zan dawo dawuri. To shikenan saida safe, falmata tafad'a. Bad ya ce, "Ameeda abin ko gaisuwa?,. "O, sorry ban kula dakai bane ykk?". Ya ce, "lfy lau, ya garin. Gaba tayi abinta ba tare da ta amsashiba. Bad yamaida kallonsa ga falmata, wai ita wannan k'awar taki miye damuwarta, kodai Nas ne ya b'ata mata rai??. Falmata ta ce, "k'ila hakane amma dama tun d'azu ranta ab'ace yake, shine dalilin dayasama ta d'au caji. Bad ya ce, "wlhy dani nakeson yarinyar can datuni na shak'ama shegiya koken, nayi abinda zanyi, narasa mike damun Nas da har yarinyarnan tafi k'arfinsa. Hummm kajika dawata magana, tunda bataso yazaiyi, wlhy nakula Ameeda bata buk'atar wannan harkar, dan ALLAH ku barta, indai dan ALLAH yakesonta to ya aureta kawai, amma indai ta wannan hanyarne bazai tab'a samun Ameeda yanda yakesoba. Habawa falmata bakisan Nas bane kawai, na tabbata wataran sai yakaiga samun nasara, kedai kisa idanu kisha kallo kawai. Dariya kawai falmata tayi dan tasan hakan bamai yuwuwa bane, tasan tasha cin kud'in Nas akan yanaso ta shawo masa kan Ameeda ta yarda dashi, amma takasa. Aban garen Ameeda kuwa tana fita ta samu adaidaita ta hau, sai gida, sallama tayi tare da shiga cikin gidan babu kowa a tsakar gida, d'akin iya tanufa, amma babu kowa, saita wuce d'akinta kaiwai. Tacire kaya ta kwanta, babu dad'ewa ta fada duniyar tunani, tabbas indai tana tareda Nas bata tunanin zata shiryu, lokaci yayi dazata nisanta kanta dasu Nas, to amma iyayentama suna taka rawar gani wajen lalacewarta, kenan suma dolene ta nisancesu?, to inta bijire musu ta tafi ina zata?, a kano tatashi tayi wayo harta mallaki hankalin kanta, itadai batasan wasu 'yan uwansu dasuke nesaba, to miye mafita??. Zata cigaba da zama dasune?, kokuwa zata kama gabanta domin daidaita rayuwarta?, kullum shekarunta k'ara ja suke, tanaso tayi aure ta haifi yara, amma bata fata Nas yazama mijinta uban 'ya'yanta, wace hanya yakamata tabi domin gujewa auren Naseer??. Tajuya kwanciyarta zuwa rubda ciki, wayarta tad'anyi k'ara alamar shigowar sak'o, ahankali takai hannu ta d'auka, Nas ne yaturo mata sak'o. Ta ajiye wayar batareda sha'awar duba sak'onba, sai kuma ta d'auka ta duba. Ga abinda ke ciki.... Hy babyna Plz kiyi hak'uri da abinda nayi miki, nayi miki alk'awarin bazan sakeba, amma dan ALLAH kiyi hak'uri ki halarci birthday party d'inan, dan wlhy duk cikin 'yammatan kece mai kala, kin fisu aji, kuma kece nake burin ki zama uwar 'ya'yana, dan nasan zasuyi alfahari dake a matsayin uwarsu. Saina jiki. I luv u my dear. Naki NAS!!!. Tsaki tayi tana fad'in shasha sha ai wlhy duk dad'in bakinka babu inda zanje, kuma ni bana fatan kazama mijina, dan 'ya'yana bazasuyi alfahari dakaiba a matsayin ubansu. Taja tsaki tareda wurgar da wayar saman katifar ta. Iya talek'o tana fad'in Ameeda sai yanzu??. Ameeda ta tashi zaune wlhy kuwa iya, amma nad'an dad'e da dawowa na lek'a d'akinki bak'ya nan. Eh naje gidan malam D'anladi, matarsace ta haihu d'azu. Ayya ALLAH yaraya, mi'aka samu. Mace ta haifa tanana sarga d'ed'iya, iya tafad'a tana washe baki. Ameeda ta ce, "masha ALLAH. Kinci abinci ko, iya ta tambayi Ameeda??. Eh, kawai Ameeda ta ce, "mata. To aii shikenan, kinga bari naje nacinye wanda na ajiye miki dama wlhy bai isheniba. Ameeda ta girgiza kai kawai, danjin furicin iya abu, ta shafa cikinta tare da fadin a cikin ranta wlhy yuwa nakeji ba k'aramaba, dan tun safe rabonta da abinci. Kud'i ta d'auka tafice, wajen wani mai shayi taje tasiyo soyayyar indome da kwai, da shayi, tazo taci takoshi, sannan tasamu sa'ida. WASHE GARI tunda safe tashirya tabar gidan, dan tasan Nas zai iya zuwa yasa su iya su tursasata zuwa Abuja. Itako wlhy bazata jeba, gidan wata aunty ta tatafi, tawuni acan sai dare tadawo. ko hutawa batayiba iya abu ta shaida mata zuwan Nas, wai haryabasu kud'i, amma ransa ya b'aci daya tarar bata nan. Baki Ameeda ta tab'e ta ce, "matsalarsa ce kuma wannan, nidai tunda nace bazaniba ai dole a sauraramini. Tamik'e tashige d'aki tana mita...................✍🏻 Ku biyomu!!. ©2017 Hikayarmu!!!. 💖abba gana💖 & 💞Bilyn Abdul💞 [2/11, 12:11 PM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA......🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 {☆bilyn Abdul☆} Page9⃣&🔟 Ameeda ta juya ta sake juyawa akan 'yar yololiyar katifarta, gaba ďaya kanta akulle yake tama rasa irin tunanin dazatayi, da sauri ta mi'ke zaune tajawo jakarta ta hannu, kwalaben sirob taďakko guda uku taďan rintse ido tana mai ba'kin cikin yanda rayuwa da sakacin iyaye ya jefata, afusace tashiga 6alle marafan kwalaben kamar wadda ta tuna wani abu, jiki na rawa tashiga tuttula maganin abakinta kamar mai shan ruwa, kafin mu farga ta shanye kwalabenan ukku gaba ďaya,, abba ya girgiza kai yana jan numfashi da sauri,, tabbas yanajin tausayin halin da ameeda take ciki,, nikam kunsan mace da rauni saida nayi kuka. Tana gama sha ta 6ingire awajen tahau barci,, muma sai muka fito guywa a sanyaye. Ameeda bata farkaba sai bayan magriba, ta mi'ke zumbur tana kallon kanta kamar wadda aka sake, takai dubanta ga agogo, ido ta zaro dan ganin yanda lokaci yatafi idan zata iya tunawa tun 'karfe tara na safe take barcinnan, ta furta na shiga uku babu azahar bare la'asar, da hanzari tafice daga ďakin iya abu ce kawai atsakar gidan take tatar koko, ta shiga washe baki yauwa ameedan baba kin tashi??, kinga zoki 'karasa min tatar nan dama nagaji wlhy, ďan 'karamin tsaki ameeda taja ta wuce batarda tabi takan iya abu ba bareta tanka mata, iya abu ta ta6e baki 'yar kwaya tanaji ina magana tamin shiru kai ALLAH yawadaranki Ameeda, kai kawai na girgiza ina faďin ohni abba wanan wace irin rayuwace akeyi agidanan???, naďanja tsaki domin babu mai bani amsa tunda bily yau bata nan nikaďai nazo ďaukar muku rahoto. Ina nan zaune saiga ameeda tafito daga bayi da'alama wanka tayi, ruwa ta ďiba abuta tayi alwala, ďaki tanufa batareda takula habaicin da iya abu take mataba,, sallolin da'ake binta tashiga ramawa, tadaďe tana addu'a da ro'kon ALLAH ya shiryata tadena mugayen halayen datake aikatawa, dakuma ro'kon ALLAH yabata miji nagari mai sonta da gsky, ta shafa sanan tafito waje. Zuwa sanan iya abu tagama tatar kokon tana zaune tana walfar tuwo abinta, ameeda taja kujera 'yar tsugunno ta zauna agefen iya abu,, tana kallonta amma ta share tacigaba da cin tuwonta, ameeda taďan murmusa dan tasan tana fushine akan abunda tayi mata ďazu, cikin taushin murya ta ce, "iya ina nawa tuwon??, saida iya abu ta haďiye laumar tuwonta jikake kutttttt sanan ta harari ameeda cikin masifa ta ce, "ban dafa dakeba,, murmushi ameeda tayi ta ce, "babu damuwa iya, taďanyi shiru zuwa wani lokaci saikuma taja numfashi tareda faďin iya dan ALLAH inada tambaya??, iya tai mata banza bata tankaba. Ameeda tacigaba da faďin iya wai ina 'yan uwanmu ne??, gaban iya abu yafaďi duuuuum arikice taďago tana kallon ameeda data tsura mata idanu, sai fidda numfashi take da'kyar ga gumi yafara bin sassan jikinta kamar wadda tahaďi kwaďo,, Ameeda ta ce, "iya yayadai ko tambayata ta 6ata miki raine??, da sauri iya abu take girgiza kai saikace 'kadangaruwa, tashiga kame2 A'a ameeda babu komai tambayarki bata 6atamin raiba, miye abin 6acin rai awanan tambayar kawaidai naji xancen nakine abazata shiyyasa...... ameeda tayi saurin 'katseta to iya kibani amasa mana ina danginmu suke?, kuma mu 'yan asalin wane garine??, inane tushenmu na asali??, cikin sar'kewar harshe ta ce, "kibari ba yanzuba watarana zan faďa miki, to waima miye dalilin wanan tambayar???. Ameeda tagyara zama tana faďin babu komai iya,, kawaidai ina son sanine, ina kuma mamakin tunda nataso bamu ta6a zuwa wani gari danufin ziyarar danginmuba, sai nan kano kawai nasani,, ahankali kuma nafara fahimtar bawata dagantaka mai 'karfi tsakaninmu da 'yan uwanmu nan kano, musamman idan nayi la'akari da irin halin danake ciki basu ta6a nuna damuwarsuba bare su tsawatar mini. Jikin iya abu sai rawa yakeyi kamar mai jin sanyi, Ameeda tana kula da'ita, tana mamakin yanda iya abu tashiga wani hali daga tambaya. Lalai akwai alamomin tambayoyi akan iyayen nata,, akwai wani 6oyayyan abu gameda tarihinta,, lokaci yayi dazatasan mi iyayenta suke 6oye mata, lokaci yayi dazatasan inda danginsu suke, lokaci yayi dazata nisanta kanta ga iyayennata, tasan duk tsiya bazata rasa wanda zai ri'keta acikin dangin nasuba harta samu mijin aure,, tayi al'kawarin koda a'kauye dangin iyayenta suke zata zauna dasu kuma tasamu miji acikinsu tayi aure,, tagaji da wanan tam6elen datakeyi, tasan kuma indai tana gaban iyayenta bazata ta6a daidaita rayuwartaba,, ta mi'ke batareda ta tanka irin lallashin da iya abu take mataba akan taci tuwon data zubo mata,, gyale taja akan igiya tafice abinta......................✍🏻 Ku biyomu!! ©2017 Hikayarmu!!!!!!! 💖abba gana💖 & 💝bilyn Abdul💝 [2/14, 5:57 PM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KIRCIYA........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 {☆Bilyn Abdul☆} Page1⃣1⃣&1⃣2⃣ Babu daďe tadawo hannunta ri'ke da ledar indome, sanda tadawo iya abu ta tashi dan haka tashige ďakinta itama, tana tunane2 yanda iya abu ta ruďe lallai awai wata magana a'kasa,, amma zatayi 'ko'kari tonota insha ALLAHU. Hakadai tacigaba da tura indomi ďin badan tana mata daďiba, bayan tagama ci tafita wanko hannunta,, harta kai gab da 'kofa zata shige saitayi saurin jan birki danjin ana magana 'kasa2 a ďakin iya abu, ta matsa ahankali gefen 'kofar baba taji yana magana cikin ruďewa. Abu!! data tanbayeki mikika cemata??. Why malam bance mata komaiba saboda matu'kar razana da maganar ta sakani, iya abuce ke magana cikin rawar murya. Baba ya ce, "lallai wannan magana takai arazana, to wai ya akayima wananan yariyar harta iya wanan magana??, kodai Nasuru ne ya kitsa mata hakan??. Kai malam kaima kasan nasuru bazai faďaba, dan yanama abuja, nasan Nasuru bazaiyi irin wannan kato6ararba. Baba ya sauke numfashi tareda yarce gumin daya wanke masa fuska, ahankali ya furta lallai idan mukayi sakaki tofa allura zata tono garma..........da sauri iya abu ta katseshi haba malam daina yimana wanan fatan mana, ai har abada babu mai tono mana daďaďďen sirrinmu, wanda dagamu sai ALLAH saikuma hajiya. Baba ya jinjina kai, to ALLAH ya tabbatar mana zainabu. Tunda Ameeda ta'iso wajen tsaye take kamar gunki, zuface keta ambaliya adukkan sassan jikinta, maganganun su iya abu sun rikita mata kwakwalwa, tarasa yanda zata fassara zancen nasu dan ta fahimta. Da sauri tashige ďaki danjin motsin babanta zai fito, ta faďa saman katifarta tana fidda numfashi, afili ta furta wanne irin 6oyayyen sirrine su baba basa son nasani, minene ma'anar allura zata tono garma idan sukayi sakaki???, miyasa suke zargin kuma Nas shiyya sakata wanana tambayar???? Shin wai miya haďa Nas ma da sirrinsu??, kodai Nas yasan wani abu gameda family ďinsu ne???,, tadafekai tana jijjigashi kamar mai shirin hawa bori, hawaye suka fara silalowa akumatunta, itakam tana kallon rayuwa a baibai, lallai akwai mayan 'kalubale dake bibiyar rayuwarta ta baďini data zahiri,, yanzu tawace hanya yakamata tabi domin binciko boyayyen sirrin iyayen natane dasuke 6oye mata akan aslinsu da tushensu???, da sauri kanta yake sarawa kamar zai faďo 'kasa. Jakkarta ta raruma tafara zazzagewa amma bataga abinda take nemaba, ta koma cikin kayanta, cikin sa'a tayi tozali da kwalbar sirob guda uku, da hanzari take 6alle murafan ta juye maganin abakinta, ta yarda kwalaben gefe dan bai ishetaba, kwalaben ďazu ta đauka tana 'kara kalacewa anan barci yay gaba da ita. WASHE GARI. Da'kyar taiya tashi tayi sallah tayi wanka tana cikin shafa mai kiran falmata yashigo ta ďauka murya aďashe tana faďin falmata ykk??. Lfy lao Ameeda kema ykk?, ina lfya, dama sonake kizo kirakani wani waje dan ALLAH, okey babu damuwa dama shirin zuwa gidanki nakeyi,, to shikenan ina saurarenki. Bayan wani ďan lokaci tafito saye cikin atanfa zani da riga ta yafa mayafi, atsakar gida taga iya ta gaisheta sanan ta ce, "zanje gidan falmata saina dawo. Cikin rawar jiki iya tace to saikin dawo Ameedan baba, batabi takantaba tafice daga gidan. Koda taje sai suka nufi inda zasu, gidan wata 'kawarsu sukaje sukai mata ALLAH yasanya Alkairi, dan tayi aurene itamadai irinsu ce ALLAH ne yay mata gyaďar dogo tasamu miji tayi aure. Daga nan asibiti suka nufa domin yin dubiya, bayan sungama dubiya suka fito, arikice Ameeda taďago domin ji tayi karo da mutum lokaci ďaya suka ďago suna kallon juna, ahankali tafurta yi ha'kuri dan ALLAH. Ko motsi baiyiba saboda shiga wani matsanancin ruďani, kallonta yakeyi ko 'kyafta ido bayayi, falmata taja hannunta suka bar gurin................✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!!. 💖abba gana💖 & 💝bilyn Abdul💝 [2/16, 12:52 PM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA......🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 Page1⃣3⃣&1⃣4⃣ ........har suka tsaida adai2ta sahu suka shiga yana kallonsu, da hanzari ya tsaida wata shima ya hau, ya ce, "mai adai2ta wancan matan zamubi, to mai babur yafaďa, haka sukaita binsu Ameeda lungu da sa'ko har 'kofar gidan falmata, daga ďan nesa dasu suka tsaya, saida yaga inda suka shiga sannan yace mu juya kawai, mai adai2ta ya juya kan babur ďinsa suka koma. Koda suka koma asibitin bai iya shigaba sai kawai ya shiga motarsa ya fice, wani ďan matsakaicin gida yaiso, fakin yayi, cikin hanzari yashiga gidan, agurguje ya haďa 'yan kayansa kala biyu aďan 'karamin akwati, ya ďakko zuwa mota, komawa yayi ya kulle gidan sannan yadawo yayma motar key yafice daga anguwar,, babban titi yahau yarin'ka sharara gudu(araina na ce, "waishi wanan mike damunsane????). Hanyar kaduna yanufa daga kaduna yaďau hanyar abuja, 'karfe uku a abuja tayi masa saboda uban gudun dayayta shararawa ahanya, wata haďaďďiyar anguwa yashiga woow!! Nafaďa azuciyata lallai anguwar tahaďu masu karatu, hon yayi a'kofar wani 'katon gate, dagudu mai gadi yabuďe masa ya danna hancin motar ciki yana ďagawa mai gadi hannu, a yalwatacciyar harabar gidan yayi fakin ya sakko daga motar yana mi'ka dafaďin Alhmdullh, ya lankwasa yatsunsa sukayi 'kara sannan ya shiga cikin ainhin gidan. Da sallama yashiga 'katon falon daya tsaru da kayan more rayu babu kowa sai ac daketa faman aikinsa, tv falon ma tanata 6a6atu, ya wuce abinsa zuwa ciki,, nanma wani falonne tsararre annan ya tarar da mutanen gidan, dagu wasu yara 'kyawawa kansu ďaya sukazo suna faďin uncle oyoyo,, yataresu cikin farinciki tareda ďagasu ďai2 yana sumbatar kumatunsu, suma yabasu nashi suka sumbata, gaban wata matsakaiciyar dattijuwa yaje ya tsugunna yana gaisheta, ta amsa fuskarta ďauke da murmushi Muzzaffar ďina lafiya kuwa naganka agida kuma yau ba weekend ba??. Kansa yashafa yana murmushi, wlhy kuwa momy hakanan naji ina marmarin ganinku shiyyasa nataho,, kumani wlhy zaman kano ďinnan ya isheni sonake adawo dani nan kusadaku. Murmushi dattijuwar tayi tana tashi zaune daga kishingiďar datayi karka damu Muzzaffar insha ALLAHU kwanannan zaka dawo abuja da aiki, dan har nayima kawunka maganama, yauwa momcyna yafaďa yana kwantar da kansa gefen kafaďarta,, momy ta shafa kansa to kaga tashi kaje ďakinka kayi wanka saikazo kaci abinci ko??, dama kamar nasani nasaka hama ta gyara maka ďakinka,, fuska yaďan yatsine kai momy banace 'kazamar yarinyarnan tadaina shigar mini ďaki bane??, da'kuwa momy tayi masa kaci gidanku muzaffar bana hanaka wanan halinbane??, yaďan shagwa6e fuska tareda hađe hannayensa biyu yana faďin sorry momy bazan sakeba. Yauwa ďan albarka jekayi wankan kaji. Ďakinsa yanufa wanda ya tsaru shima komai na ďakin farine tas, na ce, "lallai kanada tsafta malam,, dan 'kazami baya maida komai nasa fari haka, ďakin sai tashin 'kamshi yakeyi, ya cire kayan jikinsa ya ďaura farin tawul yanufi bayi,, komai na bayinma farine tas masha ALLAH, babu 6ata lokaci ya salla wankansa yafito ya shirya cikin wando fari iya gwuywa da pink ďin riga 'karama, ya gyara sumarsa tareda feshe jikinsa da turare sanan yadawo falon. Dinning yanufa wanda aka cika taf da kayan abinci saikace zasuci su goma, 'yan yaran ďazu sukazo suka haye saman kujerun dinning ďin suna faďin uncle muma zamuci, murmushi yayi musu tareda jan hancinsu to my dota's, dakansa yazuba musu sukaci suka 'koshi bayan sun kammala suka dawo falon kusada momy suka zauna, suna nan zaune suna 'yar hira har aka kira sallar la'asar, tashi yayi yanufi masallaci suma su momy suka nufi ďaki domin gabatar da tasu sallar. Bayan yadawo kai 'tsaye ďakin momy yanufa tana zaune saman sallaya tana lazumi yawuce bakin gadonta ya kwanta saida ta idar sanan ya ce, "momy ina yini?, lafiya lao muzzaffar ya gajiyar tafiya??, to Alhamdllh momy,, masha ALLAH ai haka akesonji. Ya ce, "momy nifa wani abun mamaki nagano a kano yau, da sauri momy ta ce, "wane iri muzzaffar?, kasa yasakko ya zauna kusada ita, wlhy momy natafi zan shiga asibiti sainayi gamo dawata budurwa mai tsananin kama dake kamar antsaga kara an karya. Arazane momy ta ce, "muzzaffar da gsk kakeyi kokuwa wasa??, yaďan jinjina kai wlhy momy da gsk kinsandai ban ta6a kawo miki makamanciyar wanan maganarba, ta matso kusadashi cikin zumuďi ta ce,, "kasan daga ina take??, kai ya sake girgizawa A'a momy amma dai naga inda suka shiga itada 'kawarta,, masha ALLAHU yarona kayi "kyan kai, gobe idan ALLAH yakaimu zamu juya kano. Da sauri ya ce, "A'a momy bama saikinjeba kibari nagama bibiyar yarinyar, idan naďan ga wani abu gameda sirrinta saimuje harda dady, kinga babu dađi kiyi tafiya yanzu dady bai saniba ko???, shikenan muzzaffar kaima kakawo hanzari maikyau momy tafaďa cikin raunin murya. Labarai masu daďi yayta kwakwaloma momy danta saki jikinta, yansan yanzu saita burkice musu, dama kwanan suka samo kanta da'kyar akan wannan matsalar, saida yaga tasaki jikinta sanan yatashi yafice daga ďakin, daga nan addu'oi mamy tacigaba dayi ALLAH yatabbar musu da farincikin dasuka rasa na shekar masu yawa,, ALLAH yakawo musu'karshen wannan damuwa tasu. (Muka ce, "amin momy, dukda bamusan wacce irin damuwace ta dabai bayekuba). Itako Ameeda tunda suka koma gidan falmata tafaďa duniyar tunani kokađan fuskar saurayin dasukayi karo takasa 6ace mata, duk wani motsinta yana kan tuna fuskarshi,, har falmata saida talura da damuwarta, kusada ita tazo tazauna, cikin sigar lallashi ta ce, "haba Ameeda wai saiyaushe zakibar sakama kanki damuwa akan abinda bake kika ďorama kankiba???,, yakamatafa ki zubar dakomai agefe kiji daďin rayuwarki, dagafa duniya sai kaduna,, watarana bazamuyi abinda mukeyi yanzuba. Murmushi Ameeda tayi tana mai kallon fuskar falmata ta ce, "falmata ai bazamuyima ALLAH wayauba,, nida ke duk bamusan ranar da mala"ikan mutuwa zaizo kanmuba, wlhy ina matu'kar shiga cikin damuwa da halin danake ciki. Sai kuma wani SABON AL'AMAREE (littafin bilyn Abdul) dayake shirin faruwa agidanmu, amma bansan taya zan fassara shiba, ayau kuma na'kara gamo dawani abinda ya tsayamin zuciya acikin asibiti. Falmata ta gyara zamanta sosai,Ameeda miye yake shirin faruwa agidan naku?, miye kuma kikayi gamo dashi a asibitin??, shiru Ameeda tayi saikuma zuwa can ta nisa hannun falmata takama tana faďin karki damu zan sanar miki amma bayanzuba,, a asibiti kuwa mutumin damukayi karo da junane ďazu yaketa yimini gizo a idanu, bansan miyasaba nakasa mantawa da fuskarsa da kuma irin kallon kurillar dayake mini. Dariya sosai falmata tashigayi har Ameeda tafara jin haushi ta ce, "k kuma miya baki dariya daga cikin maganganuna???. Falmata ta tsagaita da dariyar tana bama Ameeda ha'kuri, wlhy 'kawata ganinayi kamar kin kamu da soyayyane?, tsaki Ameeda tayi ta ce, "kefa falmata watasa'in kanki a cunkushe yake wlhy,, wlhy abinda nakeji gameda mutumin ďazu yafi 'karfin soyayya, wani abu daban nakeji gameda shi, kinsan ban ta6a soyayyaba kuma har yanzu baga wanda zanyi soyayya dashiba. Falmata ta langa6e kai gefe kenan yaudarar Nas kikeyi??, tsakai sosai Ameeda tayi, "o, da ke atunaninki son Nas nakeyi?, to idanma kina tunanin haka kibari wlhy banta6a jin onason Nas azuciyataba,, k ahalin yanzuma jinake na 'kara tsanarsa da duk wasu halayensa. To shikenan Ameeda ALLAH yajishemu al'kairi, Ameeda ta ce, "amin 'yar uwa. Gaba ďaya yinin yau haka tayishi sukuku kuma cikin ikon ALLAH batasha komaiba har dare, agidan falmata takwana dan kwata2 bata sha'awar komawa gidan,, koda sukaje club da daddare batasha komaiba, bakuma tayi rawaba, gefe tasamu ta zauna abinta, kowa yasan budurwar Nas ce dan haka babu wanda ya matsa mata, dan sunsan halinsa sarai, kuma yana dawowa labari zai kai masa, ba'karamin aikinsa bane yakashe mutum. Haka rayuwar tacigaba da gudu da sauri,, babu abinda yacanja daga rayuwar ameeda saima kara ta6ar6arewa da yakeyi,, dan Nas yadawo mata dawani sabon salon na shaye2, gidansu kuwa ji ake da'ita yanzu su iya basa mata faďa bare duka, duk abinda takeso shi ake mata, ita lamarin nasu har mamaki yake bata matu'ka. Yauma haka taci kwalliya cikin doguwar riga ba'ka saidai daka ganta kasan abinda tasha bai gama sakintaba, haka tafito tana ďan dafe bango ayayin dataji zata faďi, cikin ikon ALLAH harta iso titi, tana tsaye domin jiran babur ko mota saiga wata dalleliyar mota tadawo da baya har zuwa gabanta dan da harya wuce. Ahankali aka zuge gilas ďin motar 'kya'ky'kywan saurayin ranarne ya bayyana, atsorace Ameeda taja baya tana tangaďi, yabuďe motar dasauri yafito, sorry yafaďa yana matsowa kusada ita, ta ce, "malam lafiya kuwa??, murmushi yasaki mai 'kayatarwa ya ce, "lafiya 'kalao 'yammata, ina zuwa haka??. Tai saurin dafe bangon wani shago danjin tana niyyar faďuwa, ina ruwanka da inda zani nikam banason yawan shishshigi gsky,, amamakinta saitaga yayi murmushi tareda haďe hannuwansa a waje guda yana faďin sorry madam, amin afuwa natsaya ne narage miki hanya naga kina bu'katar hakan,, harararsa tayi tana wani lumshe idanu irinna 'yan maye, to idan banasofa?, sai incigaba da ro'konki harki amince kishiga motata beauty. Murmushi tayi saboda jindaďin sunan daya kirata dashi, ta ce, "to muje ALLAH dai yasa karka sayar mini dakai,, buďe mata motar yay tashiga yana faďin ai ko sayar da kai nakeyi bazan saida na beauty ba irinki, dariya tayi tana faďin maza akwai daďin baki. Tada motar yay sukabar titin batareda yayi maganaba. Yajuyo yaďan kalleta yayinda sukayi nisa, beauty ina muka nufane??, taďan gyara zamanta ta ce, "muje zan rin'ka nuna maka hanya, okey yafaďa yana murmushi,, lafiya lau ta nuna masa hanya harzuwa gidan falmata yayi mamaki kwarai da gsk, azatonsa yanda take abigennan bazata iya komaiba, tafito tana masa godiya, ya ce, "yanzu nan haka zamu rabu ko number bazaki baniba??, taďan ta6e baki haba malam daga haďuwa yau saina ďauki no ďina nabaka??, ya murmusa A'a beauty kindai manta yauce haďuwarmu ta biyu fa, aikuwa na cancanta abani, kinga idan kinbani number ki duk sanda kika bu'kaci zuwa wani waje sainazo nakaiki, kinga kinsamu direba daga sama kenan. Dariya sosai tayi tareda mi'ka masa wayarta tana faďin sarkin wayo gashi kaďauka, yauwa ngd sosai yafaďa yana kar6ar wayar tata mai 'kyawun gsk, number sa yasaka sanan yakira tata yay save ďin tasa atata sanan yayitata atashi,, sallama sukayi yaja motar yatafi suna ďagama juna hannu, itama saita shige gidan falmata tana murmushi, jinta take cikin wani farinciki mara musaltuwa.............✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!!. 💖abba gana💖 & 💖bilyn Abdul💝 [2/19, 2:39 PM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul☆) Page1⃣5⃣&1⃣6⃣ .......Tunda tashiga falmata ke binta da kallo dan ganin wata fara'a mara kangado datakeyi, ta zube saman kujera tana lumshe idanu dan barcin bai gama isartaba, falmata data kasa ha'kuri ta ce, "Ameeda wai miye sirrin farin cikinki ne???. Murmushi Ameeda tayi tana kallonta hummm 'yar uwa yaumafa sake haďuwa da guy ďinnan nayi, shimane ya kawoni har 'kofar gidanan. Falmata ta saki baki tana kallonta, kai haba??, ALLAH kuwa, zama falmata tayi kusada ita tana faďin to ya akayi yasan gidanku??, k ahanya ya ďakkoni yayin zuwana nan gidan, kai kawai falmata ta jinjina ta na faďin to ALLAH ya jishemu alkairi. Haka rayuwar tacigaba da gungurawa yayinda da Muzzaffar yashiga rayuwar Ameeda sosai, koda yaushe suna ma'kale da waya, ko kuma su haďu awani wajen dan bata so Nas yagane tana tare da wani, cikin hikima yake janye ra'ayinta daga barin shaye2, idanma tasan zasu haďu bata shan komai kwata2, yauma tana zaune aďakinta sai wayarta tafara ruri, takai hannu ta ďauka dan ganin sunan Muzzaffar, cikin muryarsa mai daďi ya ce, "assalamu alaiki beauty, saida tayi murmushi sannan ta ce, "wa'alaikassalam yayana, ykk?, ya aiki??. Alhmdllh wlhy, yanzuma gani ina shiri tashi daga aikin, kefa kina inane??, gabanta ne yafaďin dan batasan yazata cemasaba, tunda suka haďu baisan inane gidansuba kullum a hanya suke haďuwa ko gidan falmata, shi azatonsama nanne gidansu, yaďan yi gyaran murya yana faďin yadai beauty??? koba'kya gidane??. Ajiyar zuciya taja ta ce, "ina gida zakazo ne??, eh indai kina bu'katar ganina sainazo??, sassanyar dariya tayi aini kozaka kasance dani koda yaushe zanso haka, amma yanzu kaga kayi aiki kagaji dan haka kaje gida kayi wanka kaci abinci ka kwanta ka huta. Murmushi yayi tamkar yana gabanta, murya 'kasa2 ya ce, "ina gwauro yaga duk wanan gatan beauty!!?, dariya Ameeda tayi sosai, wlhy kanada abin dariya, yanzu dakanka kake kiran kakanka gwauro??. Shima dariyar yayi, to aii gsky ce beauty, kinga da inada mata da yanzu kafin na isa gida an haďamin ruwan wanka, idan nayi kuma ga abinci yana jirana, kilama saboda gata abani abaki, to amma yanzufa?, dole duk abinda nalissafo nizanma kaina. Ameeda ta gyara kwanciyarta to yayana kadage kayi auren mana musha biki, kaga idan kayi aure to koda yaushefa ina gidanka ina taya aunty na aiki da hira kafinkadawo. Tofa yafaďa yana murmushi, beauty to idan kuma kece kika zama matar tawafa???, ido tazaro da sauri kamar tana gabansa, tabďija yayana bar wananan zance kaji yanzu dai bari nabarka sai anjima,, kafin ya farga ta kashe wayar gaba ďaya, yayita kira amma akashe, daga baya saiya ha'kura yanufo gidan falmata kawai. A 'kofar gidan falmata yay fakin yasamu yaro ya ayka dan akira masa Ameeda, shigar yaron babu daďewa suka fito da falmata, saida ta gaisheshi sanan ta ce, "ai tana gida yauma batazo nan gidanba kwata2, cikin mamaki yake kallonta ya ce, "dama tanada wani gida bayan wannan??. Lah bata ta6a gaya makabane, ainan gidanane nikuma 'kawartace, kai ya girgiza to shikenan, dan ALLAH kozaki iya yimin kwatacen gidanne??, babu damuwa ai bawani nesa baneba, kwatance tashiga yimasa, ta ce, "damma inada ba'ko dana rakaka kawai. Babu damuwa yafaďa yana tada motar, bankwana yay mata yatafi. Yazo gaf dazai fita layin ya haďu da motar Nas, bin motar yayi da kallo harta shige wanan ai Naseer ne mikuma yakeyi anan anguwar??, kardai ďan isakan yaronnan yazo yayta 6ata 'ya'yan jama'a a garinnan??. Da yayi tunanin yabi bayansa saikuma yafasa ya hau babban titi yanufi gida, yama fasa zuwa gidansu Ameedan kenan. Bayan kamar kwana biyu da faruwar hakan saisuka sake haďuwa da Naseer a anguwar, amma shi Nas baiga Muzzaffar ba, Muzzaffar ya ce, "Beauty dan ALLAH kinsan wancan guy ďinne??, cikin damuwa ta kalleshi ta ce, "miyasa kamini wanan tambayar ne??, saboda naga kina ganin shigowar motarsa kika kwantar da kujerar baya, kuma kin matu'kar shiga ruďani. Ajiyar zuciya taja tareda zubo da hawaye daga idanunta, ta ce, "karka damu dashi, a'a beauty dolene nadamu dashi dominkuwa nasansa nasan koshi waye, irikice take kallonsa cikin tsoro kuma, a ina kasansa dan ALLAH????. kansa ya maida ga titi yana faďin kifara sanar dani ala'karku sanan saina sanar dake nima,, cikin rawar baki tace shinefa saurayina danake gaya maka ďinnan, hazbinallahu wani'imar wakil yashiga ambata, arikice ya ce, "Ameeda yau inaso ki kaini ainahin gidanku. Nanma cikin tsoro take kallonsa ta ce, "badaga gidan namu mukeba yanzu,, kansa ya girgiza tareda yin fakin agefen titi, juyowa yayi sosai yana kallonta, Ameeda banan bane ainahin gidanku, nan gidan 'kawarkine falmata, amma idan kin bani dama yanzunnan zan kaiki ainahin gidanku inda mom & dad naki suke, yana gama faďa yatada motar. Gaba ďaya zufa ta wanke jikin Ameeda, tanajin kunyar 'karyar datayi masa gsky,, amma ba laifinta bane rayuwace tamaida ita haka. Tiryan2 yaringa bin hanya kamar yata6a zuwa babu indà ya tsaya sai'a 'kofar gidansu Ameeda, yajuyo yana kallonta beauty ga gidanku nan👉🏻🏚.................✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!. 💖abba gana💖 & 💝bilyn Abdul💝. [2/19, 2:38 PM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA.......🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul☆) Assalamu alaikum. muna mi'ko gaisuwa da fatan alkairi gareku masoyanmu aduk inda kuke,, kuyi ha'kuri dabaku pages ďai2 damukeyi kullum, littafin namu gajeren labarine,, insha ALLAHU muna gab da kammalashi,, mungode da 'kaunarku garemu,,, luv u oll😍😍😍😘😘. Page1⃣7⃣&1⃣8⃣ ..........jikinta sai rawa yakeyi cikin kuka take bashi ha'kuri dan bataji daďin yanda tayi masa 'karyaba, kayi ha'kuri yayana wlhy badan banida gskya yasa na 6oyemaka sirrinaba akwai wasu dalilai masu yawa,, amma ina ro'konka da ka gafar ceni, insha ALLAHU wanan shine nafarko na 'karshe dazan yimaka 'karya akan abinda yashafi rayuwata, ta ďago tana kallonsa sai taga shikuma hankalinsa yana kan babanta dake tsaye a'kofar gida yana cin goro. yayana!! tafaďa cikin sanyin murya, ahankali yajuyo yana kallonta cikin in ina ya ce, "beauty waye wancan??, babanane tafaďa cikin 'kwarin gwuywa. Tafďijan yafaďa azuciyarsa, Ameeda ta ce, "koshima kasanshi ne??, A'a yafaďa a ta'kaice amma idanunsa nacigaba da kallon malam dauda. Ameeda tabuďe motar tafice tana faďin to sai mun haďu gobe ko?, okey karki damu kijirani agida insha ALLAHU 'kar fe biyu zanzo miki da abu uwan mamaki, kinsan masu iya magana sunacewa KUKAN KURCIYA JAWABINE.......Ameeda ta'karasa da faďin "mai hankaline yake ganewa yayana, murmushi yayi tareda mi'ka mata dubu biyar ya ce, "sai kinjini, okey bye tafaďa tana ďaga masa hannu. Koda tashige gida yadaďe zaune amota yana karema malam dauda kallo, daga baya yafice yabar anguwar, gida yaje yay wanka yanufi filin jirgi sai abuja. Da wuri ya isa yauma mutanen gidan sunyi farincikin zuwansa, bayan yaci abinci ya huta, suka haďu afalon daddy, daddy ya ce, "Muzzaffar kace mana a kwai magana amma munjika shiru. Muzzaffar ya murmusa, tabbas daddy akwai magana, dan yau na'kara gano abin mamaki kamar yanda na faďa maka awaya, inaso ka shirya mana tafiya kano muduka harda hajiya babba. Bangane mikake faďaba Muzzaffar???, daddy zaka gane amma sai goben.........momy ta katse musu zancen da faďin a'a muje mu kaďai idan komai ya bayyana sai azo har inda take, kasan halinta sarai, kuma batason zuwa kano da kowa. Gsky ne daddy yafaďa, yanzu saimu kwana cikin shirin zuwa kano insha ALLAH. Washegari sukai 'kaura zuwa kano, dayake jirgi sukabi har saida suka huta agidan muzzaffar, kamar yanda yay mata al'kawari 'karfe biyu suka iso anguwar dan masallataima sunata sallar karfe biyu, amotar suka zauna babu wanda yafita sai muzzaffar, kansa tsaye yashiga cikin gidan saboda anyi masa iso, tunda yashigo iya abu tayi mutuwar tsaye, cikin in ina take nuna Muzzaffar Ameeda ina kika san wanan👉🏻🙎🏻‍♂??. Ameeda dake tsaye tana kallonsu ta ce, "iya Shinefa Muzzaffar ďin danake gaya miki, kumafa kece kikace ya shugo, ganin ta rikice da ganinsa sai Muzzaffar ya basar ya tsugunna har 'kasa yana faďin mama ina yini?, cikin rawar baki ta ammsa, baibi takantaba ya haye tabarmar da'aka shinfiďa masa ya zauna. Ana cikin haka baba ya shigo gidan shima yarikitu da ganin Muzzaffar amma sai muzzaffar ya fuske ya'ki bada kofa koďaya ta alamun yasansu, nanma rissinawa yayi ya gaida baba, atsorace ya amsa tareda faďin yaro mike tafe dakai ne???. Murmushi Muzzaffar yayi ya ce, "baba nidai sunana Muzzaffar nafito ne daga 'kasar kamaru, ALLAH ne ya haďani da Ameeda naji kuma inasonta, wani ďan aikine yakawoni Najeria saidai bansan ko inaba bankuma san kowaba akasar sai Ameeda dana fara karo da ita. Ajiyar zuciya baba da iya abu suja lokaci ďaya itadai Ameeda duk kanta a ďaure yake, tana mamakin miyasa yayi 'karya??, bayan ita yafaďa mata iyayensa suna abuja. baba ya ce, "yaro kana nufin kaiba ďan kasarnan bane??, eh hakane baba, niba ďan nan bane, domin a kamaru ďinma ba anan na girmaba a london na girma, lokaci ďaya suka washe baki iya abu ta ce, "masha ALLAH aimu wlhy sai kayi mana kama dawani damuka ta6a sani. Ayya aidama haka rayuwa tagada mama, saikiga baka haďa komai da mutumba amma kuna kama da juna, nima haka mutane sukecewa ina kama da Ameeda sosai tamkar jini ďaya muka fito????. Idanu suka zazzaro tareda haďa baki wajen faďi kuma???. Ya ce, "ai ikon ALLAH kenan kawaidai kamace, ya za'ayi muzama jini ďaya bayan tana Najeria ina kamaru koma nace london, wanan shine karo na farko dana ta6a zuwa 9ja. Ajiyar zuciya suka 'kara saukewa sukace eh gskyar ka kuma. Ya ce, "to nazo neman aurenta ne indai zaku bani, amma inaso asadani da ainahin iyayenta. Iyayenta kuma???? suka haďa baki wajen faďa suna kallon juna. Muzzaffar ya ce, "eh ina nufin kanin baba ko yayansa tunda sune masu ďaura aurenta. Eh kayi gaskiya yaro suka faďa suna sauke ajiyar zuciya. Muzzaffar yasake faďin saidai abinda yabani mamaki ko kaďan bakwa kama da ita anya kuwa ba sato................da sauri sukace satowa kuma yaro??????, nanama suka faďa suna dafe 'kirji. A'a bahaka nake nufiba, ina nufin kota sato kamannin wanine a danginku???. Ohhhhhh yaro kace wani abu, tana kamane da kanwar kakar baban babana ce. Ayya ammadai tayi 'ko'kari data ďakko gida, dan ance duk wanda yabar gida gidafa ta barsa, saidai inane asalin 'kauyen naku, dan can yakamata akai kuďin aurena. Kallon juna sukayi Yaro kauye kuma???,,, suka faďa suna haďa baki. Eh baba wai ina nufin asalinku, dan inaso na auri 'yar dangi mai asali kuma. To to to wannan magana da girma take yaro. Miye girmanta baba???, kodai dangin kune a abuja dan naga kamarsu da Ameeda, tayi kama sosai dasu. Abuja kuma yaro???? suka faďa kamar zasuyi kuka. A'a kukwantar da hankalinku nifa nayi muku hannunka mai sandane, yanzu ina tareda iyayena zasu shigo idan kun basu izini dan sunaso ku gana kamar yanda al'adar kasarmu kamaru take kenan, dan gobe idan ALLAH yakaimu zamu juya kamaru. To sushigo mana bari asaka musu tabarma. Duk abinnan da akeyi Ameeda tana zaune kamar gunki tana kallon alamomin rashin gsky kuru kuru a idanun iyayennata, lallai yau akwai abubuwan mamaki masu kamada almara agidannan, ita harma tarasa yanda zata fassarasu. Shin kodai ya Muzzaffar yasan wani abu gamedasune??, miyasa yakema iyayenta wanana tambayoyin ma wai??, miyasa sukan rikice aduk lokacin da yay musu tambayar ne???, gaba ďaya takula sun fita hayyacinsu.. Amota ya tarar dasu momy, ya kallesu yana murmushi, dady ina fatan kunajin duk yanda mukayi ta waya???, kwarai kuwa ďan kirki muna jinku, inagadai dukkan hasashenmu yazama gasky kuma ALLAH yakawo mana 'karshen damuwa ta shekara ashin da biyu dasuka wuce. Murmuahi yayi To ALLAH ya tabbatar iyayena, yanzu kamar yanda kukaji sunce ku shigo. To suka faďa suna fitowa. Duk wanan tanbayoyi da Muzzaffar yakema su iya abu wayarsa a kunne take, dankuwa kiran daddy yayi ya ajiye wayar komai sunaji har aka gama. Da sallama suka shiga gidan, iya abu da baba suna zaune yayinda Ameeda take zaune a inda suka barta kamar dutse. Tunda suka rangaďa sallama suka shigo kallo ya koma sama, dominkuwa tuni su iya abu sunyi mutuwar zaune, ko yatsun hannunsu sun kasa motsawa, Ameeda ta mi'ke zummbur dan tun shigowar muta nen biyu gabanta yake dukan uku2 tamkar zai fito waje, jinta take tamkar ba'a duniyaba, sai kawai ta yanke jiki tafaďi awajen batareda daliliba. Da gudu Muzzaffar yayi kanta yana kiran beauty! Beauty!!!. Ina beauty ta suma, jiki na rawa momy ta 'karaso wajen tana jijjiga Muzzaffar da Ameeda dake jikinsa. Acan kuwa tuni fitsari ya ji'ke wandunansu iya abu da malam dauda, tuni sunshiga cikin kogin kwadamin ruďani da kiďima, lallai yau kashinsu ya bushe, lallai yau itace ranar tonan asiri, lallai yau itace rana dubu ta 6arawo ďaya kuma tak tamai kaya, lallai yau itace rana mai firgitarwa, lalai yau itace rana ta cizon yatsa da ambatar dana sani. Lallai yau itace ake kira da 'karshen tuka tuki tikkk. Adai dai wanan lokacinne kuma Naseer yashigo gidan ko sallama babu, tofa shimafa mun lura 'kamewa yayi atsaye tamkar bishiyar da aka dasa awaje ďaya, gaba ďaya zufa ta gama wanke masa dukkan sassan jikinsa, jiyake tamkar ya saki kashi atsaye, lalaikam idan zomo na yawo tofa kerema yana yawo tabbas wata rana za'a haďu, yau itace ranar zadata girgiza mutane masu ďunbin yawa, wasu zasu rasa daula, wasu zasu rasa aure, wasu zasu rasa aiki, wasu zasu rasa mutunci, wasu zasu rasa girma, wasu zasu bakunci gidan yarinema, tofa tabbasa Nas yana ganin kila yana cikin masu ziyartar gidan yari, dan yau ranace mai kamada ranar hisabi amma na duniyyyyyyyya😜. Tofa wai miye sirrin wanan rikita2ne???, wai miye abinda ake tsoron yafarune??, wai miye dalilin shigar mutane masu yawa cikin ruďani haka?????, miye tsakanin su muzzaffar da Ameeda ne???, miye tsakanin Nas dasu muzzaffar ne???, waishin ma waye muzzaffar???, waye Naseer???, suwaye su iya abu?????, wacece Ameeda??????, miye matsayin momy & daddy awanana bada 'kala???, miye kuma ya haďa wanana ahali akarkashin runfar rikici ďayane??????????... Mukaďaine masu baku wanana amsar, dan haka ku kasance damu........................✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!!. 💖abba gana💖 & 💝bilyn Abdul💝 [2/24, 6:11 PM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA..........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul☆) Page1⃣9⃣&2⃣0⃣ .........Bayan an yayyafama Ameeda ruwa ta farfaďo, ya Muzzaffar ya zaunar da ita, ruwa dady ya mi'ka mata tasha tana hawaye, cikin kuka ta ce, "ya suwaye waďannan dan ALLAH???. karki damu 'kanwata ashirye muke damu sanar dake komai, dan haka ki kwantar da hakalinki. Dubanta ta maida gasu iya abu dake durkushe sunata rawar jiki harda kuka, ahankali ta matsa kusadasu tana faďi iya miyake faruwane agidabnan??, shin kunsansu ne?? Idan kun sansu suwaye su??. Babu wanda yabata amsa acikinsu saima rawar jikinsu dake 'karuwa, ta ďauke kai daga garesu ta maida kan Nas dake tsaye shima tamkar gunki daka gansa kasan arikice yake, jira kawai yake yasami hanyar dazai arce amma babu dama, dan tuni polis sun dunkare 'kofar gidan. Waya daddy yayi tareda faďin kushigo ku kwashesu dan yanzu zamu koma abuja acan zamuyi komai daya dace. Okey sir suka faďa suna ďirarowa cikin gidan tamkar tururuwa, tamau aka dam'ke iya abu da malam dauda da Naseer aka yayibesu sai mota, 'kofar gidan cike yake da al'ummar annabi sai kallo da dariya akema su iya abu, su mutane azatonsu wajen kwaďayin 'yarsu ta auri mai kuďi suka kwaso wanda yafi 'karfinsu, mota aka cimimiyasu suna kuka da ro'kon ayi hakuri babu wanda ya sauraresu saima wani ďansanda daya kwalama iya abu bakin bindiga a 'kafa, tako daddage ta kwala ihu. Acikin gidan kuwa tuni Ameeda ta ruďe tana kwasar kuka dakyar suka lalla6ata tayi shiru, momy ta ce, "idan kinada wani abin bu'kata ki ďauka dan daga nan har abada bazaki sake zuwa gidanan ba, cikin mamaki Ameeda take kallonta amma babu damar tambaya dan tana tsoron kar itama asaka 'yan sanda cimimiyar ta yanzunan. Kayanta ta haďo dady yakama hannunta haba baby indai sutturace abinda kike bukata kawai to kibarta mu tafi komai kike bu'kata zamu yimiki da izinin ALLAH kinji. Kai ta jinjina tareda ajiye jakkar kayan ta ďauki ďan abinda ba'a rasaba suka fice, har yanzu mutane suna tsaytsaye a kofar gidan dan su iya abu ana motar 'yan sanda, suna shiga motar polis suka take musu baya sai abuja garin naira. Koda suka iso 'yan sanda wucewa sukayi dasu iya abu polistion sukuma suka wuce gida. Aljannar duniya ameeda tafaďa azuciyarta, gaba ďaya tazama 'yar 'kyauye, taga gida tamkar baza'a mutuba, saida momy takamata ta zaunar sannan, mizzaffar sai dariya yake mata, tana kallonsa amma tayi burus dashi tanabin ko ina da kallo, ruwa 'yan aikingidan suka kawo musu tareda kayan motsa baki, ďaya acikin 'yan aikin ta rissina tana faďin momy akawo abincine??. Momy ta girgiza mata kai, a'a magajiya abarsa saimunyi wanka sanan, to hajiya afito lafiya. Muzzaffar yami'ke yana faďin kunga nayi nana. Momy ta ce, "to saura kuma ka kwanta barci, kanayin wanka kazo kaci abinci, karki damu momyna kibani minti talatin. Kai ta ďaga masa tana dariya, saida ya haye samansa sanan ta kama hannun Ameeda tana murmushi babyna zomuje kiyi wanka kinji, itadai ameeda tamkar makaho da ďan jagora haka takebin momy har zuwa ďakinta. Yasalam ameeda tafaďa azuciyarta, bedroom ďin yatafi da imaninta wani abin kallo sai a bathroom tamkar wajen cin abinci, bayin ya haďu, itadai haka tayi wanka tafito, saimada momy tanuna mata yanda zatayi sanan. Bayan futowarta momy ma tashiga wankan, bayan ta nuna mata kanayan kwaliya dakuma kayan sawa data ajiye mata akan gado. Tashirya tsaf cikin jar doguwar rigar mai adon fararen duwatsu abinka ga fara tayi mata ďas kamar dan ita akayi. Momy ma tafito tashirya, sukayi sallar la'asar dan tama ďan shige lokacinta. Afalo suka tarar da ya Muzzaffar da dady suna jiransu a dinning. Momy tazauna kusada dady, itama ya Muzzaffar ya nuna mata kusadashi, babu musu taje tazauna, aka haďama kowa abinci agabansa sanan sukai bismillah suka hau ci. Itadai ameeda akunyace takecin abincin har saida daddy yay mata magana, babyna kodai dakaina zan baki abincinnan dai?, hannu tasa tarufe fuska tana dariya a'a dady zanci da kaina. To yakamata kam, kisaki jikinki baby nan gidankune, bakida inda yafinan kinji, dummm taji kanta yayi, wai ita wane irin ruďani ake shirin sakatane??, tagaza gane wanan rikitaccen al'amarin??, ya Muzzaffar ya ta6ata, taďago tana kallonsa da ido yay mata alamar taci, ďan murmushin ya'ke tayi tacigaba dacin abincin. Su momy suna kallonsu. Dahaka dai suka gama cin abincin suka tashi, dady ya haye samansa sukuma suka zauna suna 'yar hira, wadda duk anayine dan ameeda tasaki jikinta. Momy taje ďakin daddy, ta ce, "Alhaji nifa yau tareda baby zan kwana nayimaka yaji, yay murmushi a'a hajiya ainima ban yardaba saidai tazonan mukwana tare, murmushi momy tayi ta ce, "to inaga hakan zaifi sau'ki kam. Ranar agado ďaya ta kwana da momy da dady, sukasakata tsakkiya, (araina nace kai 'yan boko sai abarsu, wananan gandamemiyar budurwar za'a kwana gado ďaya da ita in bandadai.........baridai nayi shiru, ALLAH yashiryemu).............✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!. 💖abba gana💖 & 💝bilyn Abdul💝 [3/1, 11:30 AM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA..........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul☆) Page 2⃣1⃣&2⃣2⃣ ........Washe gari bayan sun kammala breakfast suka nufi polistion, itadai duk abinda ake ameeda binsu kawai take da kallo cikin mamaki, tarasa gane kan wannan lamari, har yanzu bata fahinci inda suka dosaba, gashi kowa ya'ki bata damar tambaya, dahakadai suka 'karasa, tunda suka shiga 'yansanda suke 'kamewa daddy, watodai afahimtar ta daddy ďansanda ne kuma babba, shiyyasa yaja rundunar 'yansanda har kano suka yayibosu, towai misuka yimusu?, mi iyayenta sukai misu ne?, komadai miye ai yanzu zata gani, wani 'kayataccen office suka isa, mutummin dake saman kujerarsa ya mi'ke tareda sarama daddy, daddy yay masa umarni daya zauna, suma duk suka zazzauna asaman kujerun da aka 'kawata office ďin dasu domin saukar ba'ki, wanda suka tarar a office ďin yakira waya taraeda bada izinin shigowa dasu iya abu. Babu daďewa aka shigo dasu kallo ďaya ameeda tayi musu hankalinta yatashi, daka gansu kasan sunci ďan karen duka, duk raunuka ajikinsu, dareďaya sunyi wujiga2 kamar waďanda suka shekara akulle. Gaban dady da momy suka zube suna kuka da ro'konsa gafara, alhaji dan girman ALLAH kayi mana rai wlhy ka 'kara barinmu awajennan kashemu zasuyi, wlhy munyi nadamar abinda muka aikata, kuma ashirye myke mu faďa muku gskyar lamari, dan ALLAH kace karsu kashemu.......dakatar dasu dady yayi tahanyar ďaga musu hannu, ruf suka rufe bakinsu tamkar ruwa yacinyesu, office ďin yay tsit, dady yay gyaran murya tareda faďin musa ai inaga kawai zamu tafi dasu gidan dan kes ďin nagidane, dama nabari kakawosu nanne dansu dan nasan kai tsaye bazasu amsa laifinsuba sai sunji wuya, musa D.P.O yace babu damuwa sir bari nasa akai makasu, ai tun daren jiya suka faďi laifinsu kuma sunce basu kaďai bane suma sakasu akayi. Dady yajinjin kai ya ce, "shiyyasa nace zamu je gida dasu dansu nuna mana waďanda suka sakasu ďin dady yafaďa yana mi'kewa. 'Kara cimimiyar su iya abu akayi zuwa wani haďaďďen gida shima babu nisa da gidan dady, dady ne yafara shiga, da wata dattijuwa yafara karo, dakaganta kasan ba 'karamar masifaffiya bace, dan ko sallamar dady acinkushe ta amsa masa kuma cikin yanayin masifa, doguwace fara 'kya'ky'kyawa, tahaďu sosai dan tafi momy 'kyau nesa ba kusaba, daddy yazauna yana faďin ya gidan??, ta yatsine fuska tareda ta6e baki, yaukuma mafarkinmu akayi da sassafen nan??, ďan murmushi kawai daddy yayi dama sainayi mafarkinki nake zuwa ganinki, ba jiya dasafe nabar gidanba, nanma baki ta ta6e ai nasan idan kana gidan 'yar gold mantawa kake da kwa da komai, yanzuma da safennan sayeed yayo waya wai yana bu'katar kuďi, dady ya haďe fuska wane kuďi kuma yake bu'kata? Kofa sati uku banyi da tura masa dubu ďari biyarba, shin kuďin abincine??, bare ace suyakeci? Haba alhaji yanzu dan ALLAH dan yace yanason katura masa kuďi saiya zama abin faďa, sukenanfa ALLAH yabaka su biyu dukiyarnan fa tamkar tasuce tunda idan kamutu sune zasu gada, bare kace za'aci da ha'kkin 'yar gold, murmushi dady yasaki tareda gyara zama nibama wannan yakawoniba hassana, ta watsa masa kallon rainin hankali to da wacce kazo??, kodami kazo ashirye nake dakai alhaji ta'kare maganar cikin 'kufula. Kallon k kika sani yay mata sanan yaďauki wayarsa yay kira, kushigo kawai yace ya kashe, tami'ke tsaye afusace, wakuma ka kawomin har cikin gida, kaifa nakula kullum rainin hankalinka 'kara yawa yake, wlhy Alhaji har yanzu ina nan amatsayin hassanata daka sani, babu abinda yarage ahalina.............maganar ta kakare mata ama'koshi dan ganin masu shigowa, saikuma jikinta ya hau rawa dataga su iya abu, gabanta sai dukan tara2 yakeyi, tadaka musu tsawa kai kukuma daga ina? gayyar tsiya arna a idi, babu wanda ya kulata saima neman gurin zama dasukayi, Nasir ne 'karshen shigowa falon, ta gwalalo idanu tareda faďin Nasir kaikuma daga ina?, ina kasamo waďannan kara da kiyashin? Gaba ďaya aruďe take maganar, baice mata komaiba yanemi guri shima yazauna. Dady ya kalleta ya ce, "hassana yakamata kizauna, da'karfi tace bazan zauna ďinba munafuki, to wannan gayyar dakayomin ta micece??, tsawa dady yadaka mata tareda faďin karki zauna ďin, ai zaki zauna da tsiya, ana cikin haka saiga wani dattijo shima yashigo, shimaďin arazane yake bin mutanen falon da kallo, yanan tsaye wata tsohuwa tashigo tareda wani dabaikai su dady girmaba, saikuma mata su uku sumadai da'alama akwai dangan taka tsakaninsu da dady dan naga kama, sudai nakula kowa hankalinsa akwance yake. Duk guri suka nema suka zauna, hajiya hassana ce kawai a tsaye, da'alama tana samun hanya arcewa zatayi waje, saikuma dattijon nan dayaketa zufa da rawar jiki, sai kulmawa su iya abu idanu yakeyi, falon yay shiru babu abinda ake sai kallon kallo musamman ma Ameeda da kanta yake shirin tarwatsewa saboda mamaki wanan irin taron dangi haka duk na miye??.....maganar dady ce ta 'katseta, sallama yay musu tareda godiyar halartar kiransa dasukayi, kowa ya amsa. Tsohuwar nan ta kalli dady tareda faďin Hamza ina kasamo wannan yarinyar??, ta nuna ameeda, naga ita kaďaice ba'kon ido afalonnan gashi? kuma ina jin wani abu gameda ita"".. Dady yace mama ai akantane akai wannan taron, insha ALLAHU yanzu zamu fiddaku aduhu. Kallonsa ya maida gasu iya abu ya ce, "abu munason jin wani abu daga bakinki keda malam dauda, malam dauda yay saurin 'kar6e maganar da faďin wlhy alhaji banida laifi kona sisin kwabo, kaga wanan munafukar ya nuna iya abu, to duk wani kulli ita tasanshi tareda hajiya matarka da alhaji Tasi'u yayanka da matarsa, saikuma abokanka uku da 'kanwarka matarka hajiya sadiya, saikuma Nasir kanin matarka, duk wani bayani abakin waďannan mutanen dana lissafa zaka sameshi dan sune suka kulla abinsu, nima saboda hakane aka danneni da asiri nakasa ta6uka komai arayuwata. Dady ya ce, "malam dauda su waye abokannawa??, malam dauda ya ce, "alhaji safiyanu da marigayi alhaji lawan da alhaji mansur......atsorace dady yake kallonsa saikuma yazaro waya da sauri batarda yayi maganaba ya hau kiransu ďaya bayan ďaya da bu'katar son ganinsu, cikin minti goma sha biyar suka iso kusan atare, ba abunda sukayi zaton ganiba kenan dan haka dasuka shigo duk sai suka rikice bayan sun gama bin falon da kallo, dady ya ce, "kuzauna mana, amnafa kuyi ha'kuri bansanar daku dalilin kiranba. Tsohuwa ta katse musu zance da faďin wai mike faruwane, nifa sai "kara rikitar dani kukeyi da sakani aduhu,, kiyi hakuri mama yanzu zaki fahimci komai, abu bismillah...ina kika samu wannan ďiyar??????. Ďagowa tayi tana kallon ameeda, muryarta na rawa ta ce, "hajiya ce tabani.......................✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!!!. 💖abba gana💖 💝bilyn Abdul💝 [3/1, 11:30 AM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA.........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM (☆bilyn Abdul☆) Page2⃣3⃣&2⃣4⃣ .......gaba ďaya falon suka maida kallonsu ga iya abu, dady ya ce, "wace hajiyar? Ta ce, "hajiya hassana, gaba ďaya falon suka ďauki sallallami tareda tafa hannye, tuni hajiya hassana ta zauna jagwaf tana zufa, dady ya ce, ta yaya tabaki ita?. Iya abu ta matso hawaye sanan tafara bada labari daga tushe. Kamar yanda kuka sani hajiya hassana itace matar alhaji ta farko, sunkai tsawon shekara ashirin ALLAH bai basu haihuwaba, gashi kuma ALLAH ya azurta alhaji da tarin dukiya, yana cikin damuwa ta rashin haihuwa amma baita6a yin'kurin 'kara aureba, har saida mahaifiyarsa ta taursasashi, alokacin 'yan uwa sun goya masa baya da'kin amincewa dan bayason 'kara aure saboda 'kaunar dayakema matarsa hajiya hassana, saidai dukda haka acikinsu akwai masu goyama mama baya, akan alhaji ya 'kara aure, ba 'karamar fama akayiba kafin ya yarda ya 'kara aure, ya auri hajiya saliha wato momy, tunda ya auri hajiya salaha zaman lafiya ya 'kaura agidansa ta 6angaren hajiya hassana, kwata2 bata 'kyaunar tabuďe ido taga hajiya salaha agidan, abinda yasa duk nasan wanan shine tun ina yarinya aka kawoni wajen hajiya hassana amatsayin 'yar aiki daga 'kyauyen kokai, hajiya hassana tanada faďa sosai da kalolin shirya makirci iri2, to sai akayi sa'a halinmu yazo ďaya, ganin haka yasa tasakani cikin lamuranta sosai, duk wani mugun abu na asiri kona tsafi dazata kulla akan alhaji to da sanina harma da taimakona, ganin na kwarance awajen mugun hali yasa hajiya tasa dauda mai gadi ya aureni dan bataso nayi nesa da ita ko kaďan, dauda baya sona alokacin amma saida muka shiga muka fita yasoni, alhaji yabamu BQ Muka zauna, babu daďewa da aurenmu ya auro hajiya saliha. Wanan aure ba'karamin girgiza hajiya hassana yayiba dan tasan saboda bata ta6a haihuwaba aka saka alhaji 'kara aure, alokacinne muka 'kara haukacewa da bin bokaye da malam tsibbu, gaba ďaya magana ďaya suke gaya mana shine hajiya saliha zata haihu kuma zama daram agidan alhaji. Hankalinmu yayi matu'kar tashi domindai hangen hajiya hassana bai wuce dukiyar alhajinba, wadda take ganin tareda ita aka tara, amma tana ji tana gani zata zama 'yar kallo akan dukiyar, dan yana mutuwa 'ya'yan hajiya saliha zasu gajeta saidai abata tumilin takaba, duk da haka bamu daina bin malamaiba saima abinda yay gaba, akuma lokacinne nasamu ciki na sanar da hajiya hassana, tayi farinciki sosai da wanan ciki wanda har hakan yafara bani mamaki, amma saidaga baya tasameni da wata shawara itada alhaji Tasi'u yayanka. Sunce zasuce maka hajiya hassana tanada ciki, sunyima wani dector magana zai bata magani tazama kamar mai ciki, nikuma ina rainon ciki, idan nakusa haihuwa zatayi dabarar dazamu bar 'kasar na haihu acan sai ace itace ta haihu, nima na haihu ďan baizo da raiba, dafarko na nuna kin amincewata amma dasukace zasu bani miliyoyin kuđi bayan ankasheka saina amince. Kwana biyu da faruwar haka saiga zance yafito hajiya saliha tanada ciku, lallai alhaji yayi farinciki hakama sauran dangi amma banda mutum uku dakuma abokanka, daga nan muma saimukace hajiya hassana tanada ciku, dayawa wasu basu yadda da zancenba, amma dayake likita ya aiwatar da komai sai alamomi namai ciki suka bayyana ga hajiya saliha; tonikuma bama kowa yasan inada cikiba tunda bana zuwa ko ina, bakuma kowa k zuwa gidanba saboda bala'in hajiya hassana, bama kowa k gane inada cikiba saboda banida girman ciki, saima mai lurane zai gane. Mun gayama dauda dukkan shirinmu amma saiya'ki yarda ya ce, "bazai ci amanar alhajiba, damukaga zai kawo mana yawa saimukayi masa abinda bakinsa zai rufe ruf koda wasa bazai sake maganarba, ALLAH kuwa ya amince mana daga nan muka samu kan dauda harma yafara taimaka mana abisa kullin namu. Gallazawar da akema hajiya saliha tasa alhaji ya canja mata gida, hajiya taji haushin hakan matu'ka, dahaka wata tara tacika, zuwa sanan ko alhaji ba'a bari yaganni ita kuma hajiya kullum tana gama da tulin tsumma aciki, wata ranar talata natashi da na'kuda, cikin dare na haifi ďa naminji, wanan lamari yayima hajiya hassana daďi dan sanan alhaji bama ya 'kasar, asirinmu rufe muka gama komai, likita yabama hajiya magani ruwan nono yazo mata tashiga shayar da jariri, nikuma ina gefe ina jiyyar kaina. Kwana biyu da haihuwata hajiya salaha ta haihu saidai ďan baizo da raiba, anyi shagali a sunan ďana wanda yake amasa sunan ďan hajiya hassana ga wanda bai saniba, yaro yaci suna baban alhaji wato usman muna kiransa Sayeed, afirgice dady yake kallon iya abu da dukkanin muta nen falon, iya abu ta share hawaye tareda ci gaba da bada bayani. Watan Sayeed uku aduniya nasamu ciki, nayi murna sosai dan koba komai nima zan ri'ke ďa ahannu, haka naita rainon ciki har wata tara sanan na haihu 'ya mace, Alhaji yay mana hidima dan acewarsa mun zama 'yan uwa. Daga nan ban sake haihuwaba har hafsa takamu da 'kyanda ta rasu, nayi kuka sosai su hajiya nata lallashina, sai bayan shekara uku muka samu ciki tareda hajiya saliha, alhaji yayi farinciki da cikin hajiya salaha dan tahuta da gorin da hajiya hassana take mata na rashin haihuwa, ALLAH kuwa ya inganta mata muka haihu tare ni namiji ita mace, a wanan haihuwama anufin hajiya ce ta haihu baniba, aka sakama ďa sunan baban hajiya wato Abubakar shine sadiq kenan, itakuma hajiya salaha aka sakama ďiyarta Khadija....bayannanma tadaďe bata haihuba, hajiya hassana ta tsani khadija sosai bata 'kyaunar yarinyar, dan haka wani daren juma'a tabama yarinyar shinkafar 6era ta mutu.......hazbinannalahu wani imal wakil aka shiga amabata afalon, arikice dady yami'ke ya sha'ke hajiya hassana cikin wata irin murya maiban tausayi yake faďin dama kece kika kashemin yarinya hassana kin cuceni kin cuceni kin cucenu....dakyar aka 6an 6areshi daga jikinta ana lallashinsa, su hajiya ansha sha'ka sai wurga idanu take kamar kwaďo aruwan zafi, iya abu tacigaba dafaďin daganan ALLAH ya'kara bama hajiya salaha ciki ta sake haihuwar mace aka sakamata khadija itama. Itama hajiya taso kasheta amma ALLAH bai yardaba, daga nan suka shirya mitin itada alh Tasi'u, alh safiyanu, alh mansur, alh lawan, sai 'kanwarta haj sadiya, haj laure matar alh tasi'u, abu, sune suka yanke shawarar sace khadija daga wajenku, dan 'ya'yanta suci gado su kaďai konace 'ya'yana, anyanke shawarar nizan ďauke Ameeda muyi nesa da abuja nida dauda karmu sake koda tunanin zuwa, duk abinda muke bu'kata za'a yimanashi, sunce mu raini yarinyar cikin rashin tarbuyya dan anaso ta tashi abauďe, inda halima tazama karuwa dukdai wani halin rashin kirki yazamto tana aikatashi, tashi ďaya miliyan uku aka bamu, to mukuma bamu ta6a ri'ke ko dubu ďari biyu ba shiyyasa muka haukace muka ruďe, akaje kano aka nema mana gida, muka gudu, rana ďaya kuka nememu kuka rasa ko sama ko 'kasa, daga 'karshema saikuka ďauka sacemu akayi, saida muka tafi dakusan wata uku sananan aka sato mana khadija aka kawo mana shiyyasa baku ta6a zargin mune muka sacetaba, amma labari yazo mana akan irin rikicewar dakukayi na rashin khadija kunshiga ruďani sosai aka sanar damu dan Alhjima saida aka haďa da addu'a. Mukuma munacan muna rainon khadija wadda muka maidawa suna ameeda, ta taso a ta6are dan babu mai kwa6arta duk abinda tayi dai2ne babu mai cemata baiyi daidaiba, 'yar tallace sosai dan ta kware tun tana 'karamarta muke ďora mata harta girma. Munsata makaranta batareda sanin su hajiyaba, daganan tazama 'yar kanta, saidai bata bin maza ko kaďan wanan yasa hajiya hassana taturo 'kaninta Naseer yashiga rayuwar ameeda sosai yakoya mata abubuwa masu yawan gsk narashin arzi'ki, harda shaye2 dazuwa club wanan shine abinda yafaru ga ďiyarku kwara ďaya tilo ameeda, duk 'karshen wata su hajiya suna aikamana da kuďi danmuyi bu'katunmu................✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!!. 💖abba gana💖 💝bilyn Abdul💝 [3/4, 12:16 PM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA.........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul☆) Wananan page ďin nakune mmn twins & ummiyy kunfi kowa son littafinnan, mungode ALLAH yabar 'kauna😍😍😘😘 Kuyi hakuri dajinmu shiru babu posting Luv u oll😘😘😘😘😍😍 Page2⃣5⃣&2⃣6⃣ ......a haukace dady yami'ke ya sha'ke wuyan haj hassana yana kuka, yawancin mutanen falon duk kuka sukeyi musamman ma ameeda daji take tamkar ta tashi tahau su iya abu da duka, kuka take kamar ranta zai fita, jitake babu wanda ta tsana aduniya kamarsu yanzu, musamaman ma haj hassana data rabata da iyayenta tun tana 'yar 'karama, gsky bata zaton zata iya yafemusu koda nan gaba. hajiya tsohuwa ta ce, "wa ameeda zonan jikata naji ďumin jikinki kinji, dan jitake kukan da Ameedan takeyi tamkar aranta takeyinsa. Agefe kuwa ana kici2n kwace haj hassana daga sha'kar da daddy yay mata, da'kyar aka yakiceta sai hakki take da kakarin mutuwa, daddy ya ce, "wlhy kudukanku sai munshiga kotu daku babu fashi, sai an kwatar min hakkina awajenku, azzalumai, maciya amana, kekuma nasakeki sai uku!!!! Kibarmin gidana karna sake ganinki, nayi dana sanin kasancewarki matata mara imani....kuka ya sar'keshi yakasa cigaba da faďar abinda ke zuciyarsa. haj hassana sai kururuwar kuka take da bashi hakuri, Alhaji karkayimini haka dan ALLAH katunafa shekara talatin da biyar muna tare dan ALLAH karka gujeni alokacin danakeda bu'katar zama dakai, ka taimakeni alhaji ka tausaya mini....tasake rushewa da kuka tareda kama 'kafarsa, hankaďata yayi ya taka mata hannu harsaida yay 'kara yafice fuuuu...wata galabaitacciyar 'kara tasaki dan azaba, babu wanda yay yun'kurin taimakonta, bayan wasu 'yan mintuna saiga dady da gayyar 'yan sanda, yayibarsu aka sakeyi su bakwai akai ciki dasu. Bayan wasu 'yan awanni komai ya natsa, Ameeda tabasu labarin halin data tsinci kanta awajensu iya abu da yanda rayuwa tamai da ita adalilin Naseer, kuka suke sosai cike da tausayinta, ta ce, "ashe inada gata bansaniba??, ashe su ba iyayena bane?, shiyyasa suke cutar dani ta hanyar lalatamin tarbiyya, shiyyasa basu ta6a damuwaba da halin dana tsinci kaiana, ya Muzzaffar haďuwata dakai alkairine, bazan ta6a mantawa dakaiba, kataimakeni kataimaki rayuwata kacetota daga hali irinna gur6atattun mutane, ngd ngd ngd yayana abin alfaharina...ta kara rushewa da kuka, dady dake kusada ita yarungumeta yana lallashi saikace wata karamar yarinya. Tabasu tausayi kwarai da gsk, amma babu komai zasu sharemata hawayen shekara ashirin da biyu dataketa zubarwa, zasu maida ita 'yar gata kuma mai gata. Tun aranar tafara ganin gata na musamman ga iyayen nata, komai saidai ayimata, jinta take tamkar awata (SABUWAR DUNIYA littafina mai zuwa), lallai tayarda ita 'yar gatace kuma a bar so ga kowa, ranar agidan kaka ta kwana, tasha tarairaya. RAYUWAR AMEEDA A SABUWAR DUNIYA. tana zaune afalo cikin 'kayatacciyar kwalliya ta burgewa, 'yan tagwayen yarannan dabamusan ko 'ya'yan waye ba har yanzu suna gefenta suna mata surutu sai faman murmushi take dan tanason yara, ita indai yaro baida fitina to xata iya zama dashi, ya Muzzaffar yashigo falon da sallama, ta ďago manyan idanunta tana amsa masa, fuskarta cike da murmushi. Dagudu yaranan sukaje suka tarosa, ya tarbesu shima da farinciki, kusada ameeda ya zauna datake binsu da kallo cikin sha'awa da matu'kar birgewa zuciyarta na kissima mata abubuwa dayawan gsk, har yazauna kusada ita bata saniba, ya hura idananunta dake tsaye 'kyam awaje guda. Ajiyar zuciya tasaki tana murmushi, saikuma ta shagwa6e fuska kai yaya sokake idanuna su bushe??. Yay murmushinsa mai 'kayatarwa tareda juyowa sosai suna fuskantar juna, ya sanyaya muryarsa tareda faďin khadijah na mikike runanine??. Hannu tasaka tana rufe fuska ta ce, "babu komai. Hummm niko kinga nasan abinda kike tunani, taďago kai da sauri tana kallonsa to faďi naji idan kacanki gsky. Yaďan jinjina kai tareda latse baki, idan na faďa minene tukuycina??, ta rausayar da kai gefe duk abinda kabukata indai bai sa6ama shiri'a ba kuma inadashi zan maka, yasake yin murmushi mai sauti, kina tunanin inama ace su 'yan biyu 'ya'yanmune na cikinmu ya 'kare maganar da kashe mata ido ďaya, idanu ta zaro lah yaya nidai babu ruwana kuma ba haka nake tunaninba. Ya ce, "uhhmyiiim ban yardaba, kirantse indai ba haka bane, tashitai da niyyar guduwa yay saurin dam'ke hannunta, saikuma yay saurin saki, tajuyo ahankali tana kallonsa, saikuma ta tuna rayuwarta da Naseer, tatuna babu abinda yafi bu'kata arayuwarsa irin jikinta, kullum burinsa yaza'ayi ya mallaketa, ashe akwai sauran mutane masujin tsoron ALLAH da tsare dokokinsa??, ashe akwai masu gudun aikata alfasha komin 'kan'kantarta, jiki asanyaye takoma ta zauna, cikin sayin murya ta ce, "yayana inasonka ina 'kaunarka, kaine mutum nafarko dana faraso amatsayin masoyi, kaine mijin daya dace da rayuwata, kaine kaďai zaka iya saita sauran halayena dasuka nemi ku6cemin.....ta rushe da kuka mai tsuma zuciya. Xamowa yayi daga kujerar, ya tsuginna agabanta, banason ganin kukanki khadija nima nadaďe ma'kale da 'kaunarki araina kawai dan baki bani dama bane, nasan alokacin kina tsoron Naseee ne kawai, amma inaji araina kece uwar 'ya'yana, ahankali yakai hannu yana share mata hawayenta. Su momy dake la6e suna kallonsu cikin farinci da jin daďi, jisuke tamkar su tashi sama dan daďi, lalai za ayi bikin 'yan gata.........wata sallamace ta katse musu farincikin nasu, gaba ďaya sukajuyo suna kallonsa cikin mamaki da al'ajabi. Wani saurayine baki, dakagansa kasan arikice yake; kodai abuge kokuma yanada ta6un hankali, hannunsa rikeda bindiga...😳...............✍🏻 Ku biyomu. ©2017 Hikayarmu!!!!!. 💖abba gana💖 💝bilyn Abdul💝 [3/6, 2:39 PM] mrs bilkisu: 🐾KUKAN KURCIYA.........🐾 NA MUH'D ABBA GANA✍🏻 & BILKISA IBRAHIM✍🏻 (☆bilyn Abdul☆) Zaku iya samun book's ďin bilyn Abdul a blog kamar haka. https://Mrsbilkina.blogspot.com 🔚 Page2⃣7⃣&2⃣8⃣ ........Arikice Ameeda da ya Muzzaffar suke kallonsa, bindigarsa ya saita sosai akan ya Muzzaffar da Ameeda, hazbinallahu wani'imal wakil kawai suke ambata azuciyarsu, ya Muzzaffar yay 'karfin halin faďin Sayeed mimuka yimaka? Yaushema kadawo 'kasar??. Cikin sanďa sanďa daddy yabiyo ta bayansa ya daki bindigar ta faďi (karku manta daddy babban ďan sandane) mari ya wankama sayeed ya'kara wanka masa wani, tuni sayeed yazube awajen saboda zafin mari, da'kyar momy da Ya Muzzaffar suka ri'keshi saboda sai kaima Sayeed duka yake tako ina. Ya ce, "ku 'yaleni harni wannan ďan iskan yaron zai shigoma gida da bindiga?, to anufinsa nizai kashe kenan ko iyalina??, Sayeed ya fashe da kuka yana faďin nibanzo danna kashe kowaba dady, kaduba kagani babu bulet cikin binfigar, nazone gareka domin nayi maka godiya nakuma baka ha'kuri akan abinda maciya amana sukai maka. Tuni jikin daddy yayi sanyi da abinda yayma Sayeed, ya kamoshi dakansa yatayar zaune, to amma Sayeed miyasa zaka shigo da bindiga??, yanzu dakasa nayi maka abinda yafi haka aiban 'kyautaba. Murmushi Sayeed yayi karka damu daddy nayi maka uzuri, kobaka aikata komai akainaba 'yan sanda zasuzo su kamani yanzu babu daďewa. Atare suka ce, "yan sanda kuma???........ kafin surufe baki wayar daddy tafara wringing yaďaga tareda sallama, basu san mi akace masaba sungadai ya ajiye wayar. Yadawo da kallonsa ga sayeed, sayeed mika aikatane haka da zafi??, murmushi Sayeed yayi ya ce, "daddy nakafama maciya amana tarihine, na nuna musu kuskurensune, na harbi 'kafafunsu mamane da waďanda sukace su iyayenane, harda ďan iska Naseer. Harbi sayeed miyasa ka aikata haka??. Dady hakane yadace dasu, domin nina sun taka rawar gani wajen lalata min rayuwa nida 'kanina, munaji muna gani Sadiq yazama ri'kakken ďan fashi, nikuma kuga yanda rayuwa ta maidani, shaye2 ya lalatani, babu abinda nake aturmrai sai iskanci da shan giya da coken, yafashe da kuka, daddy su mama masifane adoron 'kada, sonaima nafasa kawunansu da bulet suyi muwar jakuna abola, amma saina canja shawara na hahharbe musu 'kafafu da hannuwa ta yanda bazasu sake moruwaba, koda wanan ba'kincikin nabarsu zanji sanyi, dan haka dady dan ALLAH ko ankamani karkayi belina kabarni acan na 'kare rayuwata gabaďaya, banaso kokaďan wani yasake taimakona, ya mi'ke dazummar ficewa amma sai ya Muzzaffar ya ri'keshi, haba Sayeed baikamata ka yankema kanka irin wanan hukuncinba.....murmushi Sayeed yayi tareda dafa kafaďar ya Muzzaffar ya ce, karka damu Muzzaffar abinda yadace damai irin halina kenan. Tun farko iyayena sunrigaya sun ruguzamu, sun sayar da rayuwarmu akan kuďi kuďinma daba nasuba, wlhy daza abarni ayanzu sana ida ďauke ragowar Numfashinsu kowa ya huta...ya fisge hannunsa yafice. Basuda za6i face take masa baya, yana fita 'yansanda suka cikuykuyesa, suma su dady mota suka shiga suka bisu. Tuni ankwasi su iya abu zuwa asibiti dan sayeed ya faffasa musu kafafu da hannaye da bulet abun babu 'kyawun gani, sai kuka da dana sani suke, nikam gsky banji tausayinsuba saika ALLAH ya'kara danayimusu. Su daddyma asibitin suka Nufa hankalinsu yatashi daganin 6arnanr da Sayeed yayi, (lallai KUKAN KURCIYA JAWABINE, sun raini abunda zai halakasu, sun gina ramin muguntar saka wani, sai duk suka afka batareda sun saniba, ALLAH sarki dady shine yabiya akai musu aikin cire bulet ďin. Bayan kwana biyu daddy yayi ciku2 aka fito da sayeed, saidai kasha Sayeed ya kashe kansa batareda kowa yasan yanda abun yafaruba, ALLAH sarki gsky bamuso hakaba domindai Sayeed abin tausayine ALLAH ya yafr masa), agidan dady akai masa sutura ananma akai zaman makokinsa, to ALLAH yaji'kan musulmai. BAYAN lafawar komai aka shiga shirin bikin su ya Muzzaffar da Ameeda, lallai naga bikin 'yan gata kam, dan shiri ake bana wasaba. Zuwa sanan an sallami su haj hassana daga asibiti, saidai suduka sun rada 'kafa da hannu, lallai suna danasani akan 6arnar dasuka aikata, kukakam sunyi harsun rasa hawaye. ALLAH yataimakesu ma haj kaka tahana daddy yakaisu kotu, amma kamar yanda Naseer yay hasashe hakane tafaru, domin kuwa abokan daddy duksun rasa aikinsu, ga haj hassana takar6i takardarta ahannu, komaidai ya lalace musu basuga tsuntsu basuga tarko, su iya abu kam aisunfi kowa asara, domin sun rasa 'ya'yansu duka biyu, Sayeed ya rasu Sadiq kam bama asan inda yakeba saidai gyaran ALLAH. BIKI BUDURI. dahaka dai aka fara shagalin bikin su Ameeda, Naseer yayi kuka sosai, har kano Ameeda taje ta gayyato Falmata, wadda itama ayanzu ta yanke shawarar yin aure, harma tafara istibira'i. Bikidai ya akan kama don yaune aka ďaura aure, bayyana muku yanda ake shagalinma aii 6ata lokacine ammafa anan kwasar shoki, bakin ango da amarya yaki rufuwa, hakama dady da momy daduk wani masoyinsu, aranar da daddare aka sada amarya da ďakin mijinta ya Muzzaffar. To masha ALLAH komaidai yayi dai dai dominko amarya da ango sun riski rana mai cike da farinci saimuce ALLAH yasanya alkairi. Itamaidai falmata ALLAH ya haďata da abokin ya Muzzafar wato Ahmad kuma sunyanke shawarar yin aure, dan haka dady yahanata komawa yari'keta awajensa, idan biki yataho zasuje har Barno wajen mahaifinta. To saimuce ALLAH yasanya alkairi baki ďaya. BAYAN WASU SHEKARU. Mun isa gidansu ameeda domin ziyara, amma sai abubuwa dayawa suka bamu mamaki, domin kuwa mun tarar da ameeda da yara har huďu duk tagwaye, mace da namiji sai maza kuma, abin sai wanda yagani yara 'kyawawa abin sha'awa da birgewa, muna nan zaune saiga falmata itama danata yaran har uku, lallai masha ALLAH aure yayi riba. Saimuce ALLAH yabar zaman tare da 'kaunar juna. A6angaren su iya abu kuwa komai ya lalace, dan tuni malam dauda yasaketa yakoma 'kyauyensu, itakam tana kano tana bara dan tazama gurguwa, hajiya hassana kam ciwon 6arin jikine ya kamata saboda ba'kincikin rashin cimma burinta, to saimuce ALLAH yakara, dama ance idan zaka gina ramin mugunta to saika ginashi gajere dan bakasan mai faďawaba, kuma KUKAN KURCIYA JAWABINE.....😁👌🏻. TAMMAT BI HAMDULLAH. Nan muka kawo 'karshen wanan ďan takai taccen labari namu, ALKAH yabamu ladar abinda mukayi dai2, Wanda mukayi kuskure ALLAH ka yafe mana. Muďinnedai naku masu sonku da 'kaynarku. MUH'D ABBA GANA. & BILYN ABDUL. muna mi'ka ďunbin godiya gareku masoyanmu saboda hakurin bibiyarmu da kukayi, ALLAH yabar 'kauna, saikunjimu asabon littafi mai zuwa. Mungode sosai❤❤❤❤❤😍😍😍😘😘😘😘. Hikayarmu !!!!!! ©2017 adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *