Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, 5 June 2017

MAFARKIN HAMA complete

adsense here

[12:02pm, 12/9/2016] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 Bismillahir Rahmanir Raheem,ina me miqa yabo da godiyata ga ubangijin daya bani ikon fara wannan littafi nawa lfya,sannan ina roqonshi daya bani ikon qarewa lfyaπŸ™πŸ½ya kuma sa mu amfana da lttafin. *SHARHI* Wannan littafi dae kamar yadda na fad'a it's base on *MY DREAM*,wani mafarki nayi wanda na jima ina jinsa a qwaqwalwata,shine nake son nayi amfani dashi don fad'akarwa da kuma nishad'antarwa,the only fiction kuwa shine sunayen wasu daga cikinsu saboda a mafarki ba kowa ne zaka iya recognising sunansa ba.Allah yasa mu dace.... ®WISDOM OFFICIAL WRITERSπŸ“ *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 01 Shekaru da dama da suka wuce,anyi wani sarki me suna *JAISUS*Jaisus nada mata biyu wanda yanxu haka uwar gidan sa nada ciki ya kai wata bakwae,sunanta *YAAYI*,sarki baya kulawa da ita kwata-kwata baya sonta baya son ganinta,kullum saeta sha baqinciki a gidan,ba wani abu bane kuma ya janyo hakan illa sab'awa umarninsa da tayi,yyi yyi da ita ta sallami wata hadimarta me suna *HAIMA* amma firr taqi,saboda yadda suka saba kuma a iya zamanta da hadimar bata tab'a bijire umarninta ba,suna matuqar son junansu,wannan dalilin yasa sarki Jaisus qara wani auren,wato amaryarsa ta yanxu me suna *WAHIYYA*,yana matuqar jida Wahiyya amarya sosae,bata ganin darajar Yaayi ko kad'an,itama ta tsani Haima wato hadimar uwargidan sarki Jaisus.. Jaisus neh da Hawiyya zaune a wani d'aki (wajen shaqatawar sarki da iyalensa neh),sai surutai sukeyi ba kai bbu qafa,ga wani abu kamar tulu a gabansu da cup a hannun kowannen su,wannan abu kamar tulun kuwa cike yake da barasa (giya),sae sha sukeyi suna ihu da sheqa dariya,a wannan yanayin Yaayi tazo ta samesu,koda ta ga hakan saetayi qoqarin neman gun zama ta d'au kofi itama zata d'ebi barasar,kwatsam taji sarki Jaisus ya riqe mata hannu gam,ihu tayi wanda shiyasa shi sake hannun duk yyi zanen jaa dake Yaayi fara ceh tass,a fusace ya miqe ya jata zuwa waje ya wurga,duk abunda ake yinnan Wahiyya na zaune tana binsu da ido,bayan ya jefa ta waje sae ya dawo ya zauna bece ko uffan ba sae d'aukan kofinsa da yyi ya kamfato barasar cikin abu kamar tulun nan,ya kalli Wahiyya wacce itama shi d'in take kallo,suka kwashe da dariya dukansu.. Yaayi kuwa da qyar da taimakon hadimarta data sa aka kira mata ta samu ta tashi,d'akinta ta maidata sannan ta shiga yi mata sannu,da qyar Yaayi keh iya amsawa hakanma da kai.Fifita Haima ta shiga yiwa Yaayi,a haka har bacci ya d'auketa.Sarki da amaryarsa kuwa bayan sun qare shan barasarsu agun suka kwanta sae barci,basu suka farka ba sae washegari da rana.. Wata mata ceh zaune a tsakar gidanta tana tsince hatsi wanda bazan iya cewa ga sunan shi nan ba,tanayi tana y'an waqe waqenta sae wata yarinya y'ar kimanin 7-8yrs ta shigo gidan,talle ta kawo mata,bud'an bakinta tace "shegiya gajeriya me kamada kunkuru",sae ta sheqe mata da dariya,mijin matar neh ya fito daga d'akinsu ginin kara ya dubi matar yace "haba Niyad,wannan wane irin abune haka,kullum yaran mutane suka zo saekin samu abunda zaki zagesu dashi?hkan bashida kyau wllh",a fusace ta miqe tana nuna shi da yatsa tace"kai Ja'i,sanin kanka neh cewa ba'a jaa dani in bari saboda haka ka rufa mun baki ka kiyayen idan kana son zaman lfya a garin nan",Ja'i dake mugun shakkar Niyad ya jaa baki yyi gum ya koma d'aki inda ya fito,yarinyar kuwa da sauri ta tafi ta bar gidan dan tasan jarabar Niyad sarae.. ©Hama G Muh'd [1:28am, 12/13/2016] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 02 Komawa Niyad tayi ta zauna ta cigaba da aikin da take,sae faman mita take da zage-zage wae inba rashin mutunci ba meyasa za'a ringa aiko mata yara cikin gida suna zuwa mata rashin kunya,haka tayi ta mita kamar tab'abb'iya.. *Waye Niyad da Ja'i?* Niyad da Ja'i dai mata da miji neh wa'inda tunda sukayi aure basu tab'a haihuwa ba,yanxu aurensu kimanin shekaru bakwae kenan kuma bbu ko b'ari,hakan yasa Niyad ta tsani ganin wani yaro ya rab'eta,da yara sunzo gidan sae zagi da hantara,gashi wani abun haushi tana son zagin halittar mutum dan kwae batada d'a.Har yau har gobe Niyad taqi yin tawakkali da rashin haihuwarsu,ga shegen kamanta mutum da kunkuru,daga tace baki kamar na kunkuru sae tace gajarta kamar kunkuru.. Sarki Jaisus neh ya tashi a firgice yana kalle kalle kamar wanda ya warke daga makanta,can ya hango Wahiyya kwance tayi shame-shame a gurin kamar wacce bata san dad'in jikinta ba,tashi yyi ya je inda take kwancen ya tasheta wae safiya tayi,da qyar ta tashi ta je d'akinta inda ake ta mata gaisuwar ban girma duk inda ta wuce,hadimarta na gani ta soma binta tana mata kirari,wae "gimbiya takawarki lfya,y'ar sarki jikan sarki matar sarki kuma uwar sarki nan gaba",kan Wahiyya ya huru fam sae bunqasa takeyi kamar qosasshiyar giwa,da sauri *AINA* ta bud'e ma Wahiyya wani abu shi dae ba qofa za'ace ba ba kuma labule ba,ta shiga sannan tabi bayanta,da taimakon ta Wahiyya tayi wanka ta sauya kaya sannan ta sake gyara mata gashin kanta saeta kawo mata fruits a kwando,Yailahi! Ban tab'a ganin irin wainnan Apples da ayaban ba,da kankana,fresh neh sosae gasu manya manya (ko dan sune favorites d'ina oho).. Bayan Wahiyya ta gama cin fruits d'in though ba wani sosae taci ba dan su mafi yawancin abincinsu barasa ceh (Allah ya kyauta),Aina ceh tayi mata rakiya zuwa fadar sarki,bayan sun iso Sarki Jaisus da ganin Wahiyya ya soma murmushi harta qaraso kujerarta dake gefenshi ta zauna cikin tinqaho,fadawan dake gurin kuwa duk suka shiga aikin gaisuwa itako dad'i take ji idan ana mata wannan ladabin,Aina na bayanta tana mata fifita.. Kullum Sarki Jaisus na tareda amaryarsa Wahiyya,ko kad'an baya waiwayar uwargidansa hasalima idan ta nemi tazo inda suke,wulaqntata yake a gaban mutane bbu ruwansa,wannan dalilin neh ma ya sanya yanxu bata zuwa wajen su.. Bayan wata biyu.. Yaayi ceh ke kwance tanata murqususu a qasa,Haima da wata tsohuwa na kanta suna tayi mata sannu,da gani haiwuwa ceh tazo mata,tsohuwar dake kanta kuwa zai wani abu take ta d'irka mata tana wasu maganganunta,can Yaayi ta haifo y'arta fara sol,wannan tsohuwar da Haima neh suka gyara Yaayi da y'arta,sae suka gyara wajen suka wanke kayan tass suka shanya,tsohuwar da knta taje ta sanarwa sarki cewa matarsa ta haihu,ko a jikin Sarki,bece komai ba haka tsohuwarnan ta tashi ta tafi,koda ta dawo gun Yaayi bata fad'a mata cewa sarki beyi murnan haihuwarta ba,haka ta cigaba da kulawa da Yaayi da y'arta har sukayi arba'in,Yaayi ceh tayi ma y'ar suna dan su a al'adarsu haka sukeyi,sunan y'ar *ZEEDAT*,Yaayi naji da y'arta sosae,haka rayuwarsu ta cigaba bbu kulawar sarki.... ©Hama G Muh'd [10:21am, 12/13/2016] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 03 Haima ceh tazo wucewa kwae saetaci karo da Aina,Aina ta fad'i a qasa,a razane Haima ta soma bata hauri kan bada saninta bane tayi haquri,Aina ta miqe a fusace ta kwashe Haima da mari,sannan ta soma zaginta "shegiya tsinanniya,mayya to baki isa ka kasheni ba in fad'a miki kinyi kad'an,kuma ki shirya fuskntar hukuncin sarki a kanki tunda kka bugeni na fad'i",Bbu irin haqurin da Haima bata bama Aina ba amma sam bata jiba saeda taje ta had'a munafinci agun sarki,shikuma be tsaya yabi kam maganar ba kwae yace ayi masa kiran Haima,bayan Aina tabar wajen sae Haima taje ta fad'awa Yaayi abunda ya faru,ana cikin haka wani bafade ya shigo yace sarki yana magana da Haima,gabansu ya fad'i barinma Yaayi,amma bbu yadda suka iya haka aka tafi da Haima,hukuncin da sarki ya yanke mata kuwa shine ta kwanta Aina tabi ta kanta har sau goma,karku manta fa Aina tafi Haima da komai,girma,tsayi,nauyi,shekaru duka tafi ta amma ba yadda zatayi dan sarki baya sake magana idan yyi ta.Haka bbu imani Aina tayi ta bin ta kan Haima har sau goma,da qyar da taimakon mutane Haima ta tashi aka rakata wajen Yaayi,koda Yaayi ta ganta kuka kwae ta fara yi,nan bayin nan da suka kawo Haima suka bamasu Yaayi da wancar tsohuwar labarin abunda ya faru tass,tsohuwar tace karta damu Haima zata samu lfya dama ita kamar likita ceh a garin.. Niyad ceh kwance a tsakar gidanta ta jiyo ihun yara a qofar gida,daga ji dae fad'a suke ko wasan banza,ran Niyad yyi mugun b'aci ace a rasa inda yara zasuzo suna iskanci sae qofar gidanta,da hanzari ta tashi ta fita,ai kuwa fad'an ta iskesu sunayi dan haka ta cakwamo su ta wurga cikin gidanta,ta dawo ta rufe qofa,banda had'iyan yawu bbu abunda yaran nan keyi dan sun san yau kashinsu ya bushe a hannun Niyad,nadamar zuwansu qofar gidan suka soma yi gashi dae yara neh amma sun san nadama,Niyad ta karyo wani qaton kara ta nufosu,dukansu ta shigayi saeda taji ta gaji gashi karan duk ya karkarye a jkinsu,yaran duk sun galabaita ta bud'e musu qofar suka fice a guje kamar basu aka gama jibga yanxunnan ba,Niyad ceh tayi dariya tace "shegun yara masu kamada kunkuru,ga yadda suke tiqan gudu kamar kunkurai",ta sake sheqewa da dariya kamar wacce ta zauce,Niyad kenan sae Allah ya shirya.. *Gidan Sarki*, Wahiyyace kwance duk a galabaice,yau tunda ta tashi take ta amai,yanxunma aman neh yazo mata da sauri ta tashi tayi waje Aina na biyeda ita tana mata sannu,amai ta shiga kwararawa kamar zata fitoda hanjin cikinta,duk ta sauya kama ta rame,bayan ta gama da taimakon Aina ta wanke jikinta sannan ta koma d'akin,Aina ce tasa akayi mata kiran Sarki,bayan yazo yaga yanayin da Wahiyya take ciki sae Aina tayi masa bayanin komai,Lkita yasa akayi masa kira,bayan tazo ta duba Wahiyya da kyau sannan ta sanarda sarki sakamakon rashin lafiyar matarshi.. ©Hama G Muh'd [10:22am, 12/13/2016] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 04 Sakamakon kuwa shine Wahiyya na d'aukeda ciki harna wata biyu, murna wajen Sarki kuwa ba'a magana dan har liyafa ya had'a na murnar samun cikin Wahiyya,anci naman dabbobi ansha barasa kamar ba gobe,duk sun bugu kamar tab'abb'u sae ihu sukeyi.. Har yau Sarki Jaisus be tab'a sa Zeedat a idonsa ba,yarinyar harta d'an fara wayo gata kyakyawa ta qarshe,har yau har gobe kuma wannan tsohuwar likitan tana zuwa duba Yaayi da y'arta kusan kullum dan ganin yaya lfyarsu take tareda tausan Yaayi kan abunda sarki ke yimata,Yaayi kuwa cewa take bbu komai ze wuce watarana. Bayan an gama liyafa kowa yyi tatur da barasa da qyar sarki ya iya dawowa gida shida Wahiyya,amma ita bata sha barasar ba saboda wancan taohuwar likitar tace ba'a so me ciki tana shan abun wae zae iya lalata cikin,gashi Sarki da Wahiyya na mugun son cikinnan kamar a haifeshi yau sukeji,suna shigowa d'akin Sarki ya zube kamar an sauqe kayan trailer tsabar irin yadda ya zube a qasa kamar asara,a haka nannauyan barci yyi gaba dashi,ita kuma Wahiyya ta d'an jima kafin tayi bacci duk ta gaji.Sauran mutanen kuwa duk agun suka zube suka shiga sharara barci kamar kasa,da asuba wasu suka shigo gidan sarki dan satar abinci saboda tsanin yunwa da sukeyi,wae a garin idan anyi noma rabinsa wa sarki ake kaiwa rabin kuma shine na mutum kuma dududu abinda suke nomewa befi buhu biyu zuwa uku ba shekara so baya isarsu da iyalansu,koda sukaga fadawa kowa yyi barci kwae sae suka shiga suka d'iba iya d'ibarsu suka gudu,kowa ya nemi wajenda zae b'oye nasa yadda ko anzo bincike baza'a samu ba.. Saeda rana ta fito rau a sama kafin fadawan nan suka tashi,koda d'ayansu kuwa yazo ta wurin ma'ajiyar abincinsu sae yaga an zuzzubar a qasa kuma ba haka aka rufe qofarba da dan haka sae yyi sauri ya janyo hankulan sauran zuwa wajen ya nuna musu,cikin kowannensu ya shiga qara dan sun tabbatar yau akwae daru da Sarki kuma wasu zae bama laifin zaece meyasa sukayi bacci har hakan ta faru.D'aya daga cikinsu neh yyi azamar bud'e qofar,yana jaa kuwa ta bud'e alhalin da sai mutane biyu zuwa uku sunji jiki kafin qofar take bud'ewa amma sae gashi yanxu mutum d'aya be sha wahala ba ta bud'u dan haka suka sake tabbatarwa anshiga d'akinnan da dare,koda suka leqa ciki sunga abincin yyi mugun raguwa,zufa kowannensu ya shiga sharewa bayan lokacin sanyi neh,haka suka tattara wanda ya zuzzuba suka had'a tareda refe d'akin sunata zullumin abunda yau zae faru idan sarki yazo yaga abincin haka bayan wancan satin dayazo yaga yawan abincin kuma baci sukeyi ba balle yace ko anci a gidan,daman sayarwa yakeyi ma garuruwan makwabtansu,kuma tun wancen satin daya wuce bbu wanda aka siyarma abincin kuma tabbas yau zaezo dubawa dan dama kowane qarshen sati yakan zaga gidan yaga meke wakana ciki kuwa harda d'akin abincin nan.. ©Hama G Muh'd [11:21am, 12/13/2016] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 05 Sae kusan yamma sarki ya fito zaga gida dan be tashi da wuri ba,aikuwa yana zuwa d'akin abincin nan qirjin su ya fara bugu da qarfi,sunyi sunyi su tuno dabarar da zasuyi kar sarki ya duba d'akin nan amma ina basu tuno ba dan haka kwae suka sadaqar,ana bud'ewa Sarki yaga d'akin duk a rame bbu kayan abinci,ya juyo ya kallesu sukuma suka sunkuyar da kai dan dokace duk wanda ya kalli idon sarki akwae hukunci me tsanani akansa,Sarki Jaisus yace "munyi baqi masu siyen abinci neh?",shiru sukayi bbu wanda yace qala sae b'ari da sukeyi,Sarki da ranshi ya fara b'aci ya daka musu tsawanda saeda suka ji kamar su nitse tsabagen tsoro,"ba magana nakeyi ba neh?",d'aya daga cikin fadwan yayi qarfin hali ya ceh "ran Sarki ya dad'e bbu wanda yazo ya siya abinci,muma tashin mu mukaga abun haka,na tabbatar shigowa akayi da dare aka sace saboda nauyin baccin da mukayi",ran Sarki ya sake baci,a fusace yace "wane irin barcine kuke yi da har a shigo ayi min sata baku ji ba?",kowannensu ya shiga cewa "ran sarki ya huce,ranshi ya kuma dad'e",wani bafaden yace "ran sarki ya jima barasar da muka sha jiya ceh tasamu wannan barcin amma tubanka muke nema ya me komi",Sarki yace "yafiyata kenan aje a nemo min wanda ya saci abincin nan,idan kuma ba haka ba zaku fuskanci fushina ba kad'an ba",kowannen su ya yarda da hakan,Sarki ya bar wajen tareda wasu mutanensa,aka bar wainnan fadawan da tunanin yadda zasu b'ullowa lamarin,daga qarshe dae suka yanke shawarar bi gida-gida dan yin bincike,suka raba kansu kashi-kashi,wasu suyi nan wasu suyi can,haka sukayita bincike gida-gida amma har dare basu gano ko gida d'aya ba,dan haka suka rasa yadda zasu tunkari sarki da wannan maganar.. Qarshe dai gidan suka koma suka sanarda sarki cewa sun fara bincike kuma gobe zasu gama zasu kawo mishi wanda yyi wannan aika-aikan,sarki ya barsu akan goben amma yace indae zuwa gobe basu kawo mishi wani bayanin ba to tabbas zasu fuskanci hukuncin shi,sukayi godia sannan suka tashi jiki bbu qwari suka fita.. ©Hama G Muh'd [10:10am, 12/16/2016] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 06 Suna fitowa suka d'anyi tafiya can bayan sunsha wata kwana sae suka zuba a wajen kamar asara,kowa tunanin mafita yake dan lallae idan zuwa gobe basu kaima sarki wani bayani ba to lallai zasu fuskanci hukun shi,ana cikin haka d'aya daga cikinsu yyi zumbur ya miqe yana cewa "na samo mafita,kuu na samo mana mafita",dukansu suka fara tambayarsa "wace mafita kenan?",yace "kun san ni gwani neh wajen iya gano shatin takalmi koh",suka d'aga kawunansu alamar eh suna dad'a zuba masa ido,yace "yace kuma ina iya gane takun da akyishi yau da jiya,saboda haka me laifin na duba mana shatin,takalman jiya zuwa yau,kunga idan kowa a cikinmu ya tantance nashi sannan muka tantance na Sarki,toh tabbas sauran na b'arawon Sarki neh tunda bbu masu wucewa tanan inba mu ba",wani ihu suka kurma dukaninsu suna cewa "sae kai",haka suka tashi suka d'unguma wajen dukansu,biyu daga cikinsu suka nemo takarta da al'qalamin rubutu suka kawo,ta gefe ya nuna musu suka tsaya dukansu,d'aya bayan d'aya yabi kan shatin takalman nan ya zanasu,kowannensu ya nuna nashi shatin sannan suka nuna na Sarki,sauran guda uku wanda basu samu meshi ba dan haka suka yanke hukuncin zuwa gidaje-gidaje suna duba me irin wannan zanen takalmin.Yanzu ma kamar d'azu,suka raba kansu kashi-kashi,way'annan suyi nan way'ancan suyi can,kowa ya bazama nema bayan kowane tawaga an basu irin zanen takalman da ake nema,a cikin tawagar nan kuwa wasu sun sami d'aya daga cikin zanen takalman yyi iri d'aya da takalmin wani mutumi dan haka suka jashi suka tafi dashi,koda suka had'u da sauran suma sun samu zane d'aya da yyi kama dana wani mutum,dukda dae basu samu na duka zanen ba,amma sun rage hanya tunda sun samu mutum har biyu,kuma su mutane biyunnan zasu iya fad'an sauran b'arayin. Haka suka ja mutane biyunnan zuwa fada,suka kullesu a wani d'akin hora masu laifi,suka fito suka je suka kwanta bayan sun bar wanda zena gadin su,a haka har gari ya waye musu,da safe bayan sarki yazo fada saeya sa amasa kiran way'annan fadawa masu gadin gidan,suna zuwa suka fad'i qasa suna masu miqa gaisuwa ga Sarki Jaisus,sarki yace "ina fatan kun cika umarnina?",d'aya daga cikin fadawannan yace "ran sarki ya jima,ae bbu wanda isa jinkirin cika umarnin ka,tabbas mun nemo b'arayinka a halin yanxu ma muna kulle dasu",sarki yyi wani dariyar qeta sai yace da wani bafaden aje azo masa dasu,haka bafaden nan ya tashi yaje inda aka kulle mutanen nan,yana zuwa yyi wata magana da me gadin wajen yace dashi sarki neh ya aiko shi yazo ya tafi dasu,bbu b'ata lokaci megadin yaje ya bud'e su ya taho dasu ya damqa ma wannan bafaden,bafaden ya riqesu sae ya sasu a gaba ya soma tafiya dasu zuwa fadan Sarki.. Niyad ceh tafe da wata qatuwar jaka zata kasuwa,ko meh zata siyo haka ohonta! Tazo daedae wani gida sae taci karo da wasu yara y'an mata su hud'u sunata carafke,da ganinsu saeta fara zaginsu kamar aiko ta akayi.. ©Hama G Muh'd [11:48am, 12/17/2016] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 07 "Shegu masu hana ayi ruwan sama,da shegen baqaqun qafafuwan ku kamar na kunkuru,ga guntancin tsiya sae shegen rashin mutuncin tsiya,idan baku tashi anan ba saena karkarya ku",da gudu yaran nan suka miqe suka shiga gida,Niyad kuwa ta kama hanya tayi tafiyar ta tana ta faman zage-zagen ta. Bafaden nan da Sarki ya aika ya kawo masu laifin nan neh ya shigo dasu,wurgasu qasa yyi saeya sunkuya ya gaida sarki yace "ranka ya dad'e,ga b'arayinka nan a gabanka",mutanen nan suka gaida sarki,sarki yace "kune kuka saci abincin sarki kou?",kowannensu ya kalli d'an uwanshi sai d'aya yace "ran me martaba ya dad'e mune amma bamu kad'ae ba",Sarki ya dube su yace "ku dawa ye?",sae mutumin ya shiga lissafo sunayen su,da sarki yaji haka sae yace lallae yaje ya nuna ma fadawan shi suzo dasu gaban shi,hakan kuwa akayi uku daga cikin fadawan sarki suka sa mutumin nan a gaba zuwa kamo barayin sarki.Koda suka jesu gidajen basusha wuya ba suka kamo b'arayin d'aya bayan d'aya, har gaban sarki suka je,b'arayin sun kai su goma duk aka sa sukayi layi a gaban sarki,Sarki ya d'ago ya qare musu kallo d'aya bayan d'aya sannan yace "kune b'arayin da kuka sace mun abinci kou?",kowannen su bece qala ba,sae wani bafade yace "wae bada ku sarki ke magana bane?"ranshi a b'ace yyi maganar,sae kuma ya jyo yana kallon sarkin yace "ran sarki ya jima ko tantama bbu,way'an nan sune b'arayinka",Sarki yyi gyaran murya sae ya ceh "lallae zaku fuskanci hukunci nah me tsanani",d'aya daga cikin b'arayin nan yace "ranka shi dad'e ayi mana afuwa mana,ba laifin me bane yunwa ceh tasa mu yin hakan,amma tuba muke yi",wani bafade neh ya buge bakinsa yace "ko kunya baka ji ba,har ka kalli idon sarki kace yyi haquri bayan wannan mumunan laifin da kuka aikata?",ya juya ya kalli sarki yace "ran Sarki ya jima hukuncin ka kwae suke jira",sarki yace "hukun da na yanke shine,aje a d'ebo mun dukkanin iyalanku wato matanku da y'ay'anku,ni nasan yadda zanyi dasu,ku kuma za'a fille muku kai".. ©Hama G Muh'd [11:49am, 12/17/2016] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 08 Gaban b'arayin nan ya soma fad'uwa dan sun san maganar sarki dutse neh,baya magana ya sauya ta,haka sarki yasa aka kwaso dukkanin iyalan b'arayinnan sannan aka filewa mazajen kai a gaban su,masu kuka nayi masu suma sunayi, bayan an gama sarki yace matayen sun zamo bayinsa haka nan yaran kuma za'a sayar dasu a matsayin bayi,tashin hankali suka shiga ba kad'an ba,lallae Sarki Jaisus da fadawan sa sun cika azzalumai na qin qarawa.. ★★★★★★★★★★★★★ Bayan wata takwas... Sarki da Wahiyya na zaune a d'akin hutawa sae Wahiyya tace mishi cikin ta na mata ciwo,da gaggawa yasa aka kira mishi likitan su,tana zuwa data duba ta sae tace ae haihuwa ceh tazo mata,da gaggawa aka maida ita wani d'aki inda anan ta sauqa lafiya,ta haifo d'anta namiji me kamada sarki Jaisus,nan da nan fada ya amsa ai matar sarki ta haifi d'a namiji me kama da sarki,koda zancen ya isa kunnen Sarki,yyi matuqar farin ciki ya samu me gadan sa,so da qaunar Wahiyya ya ninku a zuciyar shi,ya taso yazo d'akin Wahiyya dan ganin babyn shi,a kwance ya sameta d'an na gefenta da alamu barci yakeyi,ya qaraso inda take yyi mata sannu,bata ceh komai ba sai d'aga kai da tayi alamar yauda,ya d'au yaron yana kallo,wani sonshi neh ke ratsa shi ganin yadda yake kama dashi tun a jaririnsa ma kenan,bayan ya gama kallon yaron saeya kwantar da shi a gefen uwar sannan ya kwanta ta gefe shima. Yaayi ceh zaune da Haima a gefenta tana bata labarai,Yaayi ko sae dariya take dan labarin abun dariya take bata,Zeedat ceh ta shigo d'akin da gudu tana kiran mamanta,wae taga tsutsa shine take wannan ihun,da maganarta ta yara tace mama tsutsa,tanayi tana haqi,yarinya ceh y'ar kimanin shekara d'aya da watanni goma amma ta iya tafita ga kaifin tunani,tana da matuqar hankali da fahimtar abu.Yaayi tayi dariya tace "haba zeedat,ma tsutsa kke wannan ihun kamar kinga kura?",yarinyar tayi dariya kamar ta fahimci me uwar ta fad'i,Haima tajaa ta ta zaunar sae ta cigaba da musu labaran tare suna dariya.. ©Hama G Muh'd [11:50am, 12/17/2016] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 09 Koda labarin cewa Wahiyya ta haihu kuma d'a namiji neh yazo kunnen su Yaayi,Yaayi bata damu ba ko irin jin kishin ita ta haifi mace wancan kuma ta haifi namijin nan batayi ba,ita dae kwae fatanta shine y'arta ta taso da irin wannan halin nata kuma sarki ya gano kuskurensa. Washegari aka rad'a ma yaro suna *JAHEED*,anci ansha kamar ba gobe,tun safe ake d'aya har dare kafin aka gama,duk wani mutum a garin ya halacci wannan taron kuma kowa yaci ya qoshi har ya bar abinci. °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° Bayan kwana biyu.. Sarki da Wahiyya na zaune a fadar Sarki tareda fadawan sarki,fadawan sunata musu kirari su kuma suna jin dad'i,can saega Zeedat ta shigo da wata hadimar data rakota,hadimar ta tsuguna ta gaida Sarki sannan ta sanarda shi dalilin zuwansu "ran Sarki ya dad'e,babbar y'arka ceh ta matsa tace sae an kawota gun baban ta toh shine na kawo ta",lallae dama haka yarinyar take da kyau,sarkine ke ayyana hakan a ranshi dan yarinyar ta tafi dashi,kamarta d'aya da uwarta,wani irin hararar da Wahiyya tayi mishi neh yasa yace da hadimar ya tafi da yarinyar baya son ganinta.Bada son ranshi yasa aka fitar da yarinyar ba,tana kallonshi shima yana kallonta haka hadimar nan ta d'auketa tayi waje da ita,Sarki beji dad'i ba kwata-kwata amma beko nuna hakan ba sae ma sawa da yyi fadawan suka cigaba da hirar da suke musu,Wahiyya kuwa dad'i taji a ranta ganin yadda Sarkin ya nuna yarinyar bata dame shi ba. Koda hadimar ta d'auki Zeedat wajen Yaayi ta kaita ta kuma sanar da ita yadda sukayi a gaban sarki,da irin abunda ya nuna musu,ko a jikin Yaayi tace "koma miye dae shine ubanta ba'a canza ma miya suna dan haka ko ba dad'e ko ba jima sae yazo yyi alfahari da ita dan Zeedat ba qaramin baiwa ceh da ita ba",Haima ceh tayi ta kwantar masu da hankali har suka mance sukayi ta nishad'in su.. ©Hama G Muh'd [8:08am, 1/1/2017] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 010 Yau ma kamar kullum Haima na zaune da Zeedat tana mata wasa,Yaayi kuwa tuni tayi bacci.Bayan d'an wani lokaci Zeedat ta tashi ta fita waje,bata tsaya ko'ina ba sae sashen su Jaheed,tsayawa tayi cak ganin kallon da Wahiyya da Aina keyi mata,Zeedat yarinya ceh qarama amma tasan abunda ake nufi da wasa da kuma rashin sa,kafin Wahiyya ta bud'i baki sae Zeedat tayi saurin cewa "sannu da hutawa ranki shi dad'e",kamar Wahiyya bata ji abunda ta fad'i ba tayi gumm.. Ta kai kamar mintuna 2 zuwa 3 tana hararan Zeedat kafin tace "me ya kawo ki sashe nah?"fuska a d'aure,wani gajeren fitsari Zeedat taji yana shirin fito mata da qyar ta riqe shi tsaban tsoron Wahiyya da ta ji,bata iya ansa tambayar ta ba a maimakon hakan saeta tsura mata idanu,a fusace Wahiyya tayi mata magana wanda yafi na farkon tsawa tace "ba tambayar ki nake bane?",Zeedat tayi maza tace "ranki shi dad'e nazo wajen qanina neh muyi wasa"cikin muryar kuka tayi maganar,Wahiyya tace "to dama ae ko baki fad'i ba raena zae dad'e dan nafi qarfinku kiji in gaya miki daga keh har uwartaki a tafin hannuna kuke,sannan kuma waye qaninki anan?",Zeedat ansa "Jaheed",Wahiyya ceh tayi maza ta miqe tana fad'in "kambuuu,Jaheed d'inne qanin naki? To koda wasa ban yarda ba shegiya mayya me halin uwarta",hawayen da Zeedat ke maqale dasu suka soma zubowa,Wahiyya ta qaraso inda take taja hannunta tayi waje da ita ta wurga kamar kayan wanki.. ©Hama G Muh'd [8:09am, 1/1/2017] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 011 Zeedat ta kai 30mins a wajen tana kuka,can saega Jaheed ya zago ta gurin,tsayawa yyi cak ganin Zeedat a yashe tana kuka duk jikinta ya b'aci da qasa,ya qaraso wajen duk jikinshi bbu qarfi ya shiga lallamnta yana tambayar wanda yasa kuka,kamar a sama Wahiyya ta fito ta tsaya a kansu,da sauri taja Jaheed a jikin Zeedat tana ta faman huci tana zagin Zeedat wae mayya wato saeda ta lallab'a tasan yadda tayi taja mata d'a,to idan ta fito ta sameta agun saeta karya qafarta,taja hannun Jaheed tayi ciki dashi tabar Zeedat agun tana ta kuka abun tausayi. Da sauri Zeedat ta tashi ta nufa sashen su dan sarae tasan idan har Wahiyya ta fito ta sameta to lallae kashinta saeya bushe,koda ta fad'a ma mamarta,batace komai ba sae cewa da tayi tai haquri. Wahiyya ceh ta fito,ganin Zeedat bata gurin yasa tayi qwafa ta shige ciki tana mita,taje ta samu Jaheed yana ta kuka saeta shiga lallaminshi,da qyar yayi shiru Aina tana mishi wasa.Bayan wani lokaci,Sarki ya shigo cikin gida sae yake tambayar Wahiyya meya samu magajin sa dan yaga alamun yyi kuka dukda bacci yakeyi,nan Wahiyya ta fad'a mai qarya da gaskiya,abunda akayi dama wanda ba'a yi ba,ranshi yyi matuqar baci yace "lallae yau zan koya ma Yaayi da y'arta hankali,zan gwada musu ba'a tab'a magajin sarki a kwana lfya",yyi zumbur ya miqe ya fito waje yana neman bafaden dake gadin wajen. Fadwa sun kai suu hud'u way'inda suka zo suka durqusa gabansa suna gaisuwa,be ansa wa koda d'ayansu ba sae umarni daya bama d'aya daga cikin su na cewa aje azo mishi da Yaayi da y'arta,bbu b'ata lokaci ya miqe yana fad'in "maganar Sarki dutse neh,yanzu yanzunnan za'a kawo maka su,ran Sarki ya huce",yyi wuuf ya miqe da hanzari ya nufa sashen Yaayi dan cika umarnin Sarki.. ©Hama G Muh'd [7:56pm, 1/1/2017] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 012 Yaayi na kwance Zeedat na gefenta tana bacci inda ta gama kukan ta a gurin tayi bacci,maganar bafaden nan neh ya tashi Yaayi gashi lokacin Haima bata nan ta barsu suyi bacci neh,haka Yaayi ta tashi taje ta duba,koda taje saeta bafaden nan ya sanarda ita abunda sarki ya aiko shi yyi,bbu musu Yaayi tace "ba komai barin d'auko Zeedat d'in muje",yace "toh ranki shi dad'e".Ta juya kenan saega Haima ta dawo Yaayi tace "yauwa gara da kka dawo yanzu,muje ciki". Haima tasha jinin jikinta amma bata ceh komai ba sae bin Yaayi da tayi suka shiga ciki,nan Yaayi ta sanarda ita abunda ke tafe da wancen bafaden,Haima tayi mamakin dalilin kiransu da sarki yyi amma sae Yaayi tace mata ba abun mamaki bane dama tasan dole Wahiyya sae tayi musu wani munafincin agun sarki,Haima ta tausaya mata sosae amma bbu yadda suka iya haka Haima ta d'auka mata Zeedat sannan suka fito dan zuwa kiran da Sarki yyi musu.. Suna tafe bafaden nan na biye dasu har zuwa sashen Wahiyya,bayan sun isa sae Yaayi tace da Haima ta bar wajen kar ya had'a da ita in ya ganta.Haima taqi tafiya wae koma miye yyi musu tare dan bazata iya tafiya ta barsu a haka ba,da qyar Yaayi tashawo kan Haima har ta yadda ta bar wajen.. ©Hama G Muh'd [8:00pm, 1/1/2017] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 013 Bayan Haima ta bar wajen neh bafaden nan yyi magana da Sarki ya sanarda shi ya kawo su,bbu jimawa Sarki ya fito ya nufa fadan shi sannan yace da bafaden ya kawo mishi su,bbu b'ata lokaci bafaden nan ya sasu gaba yana biye dasu har fadan Sarki,bayan sun gama settling sae Sarki yyi gyaran murya sannan ya fara magana kamar haka "dalilin kiran ku dana sa akayi ba wani abu bane illa zantar da hukunci akan ku gwargwadon laifin da kuka aikata keh da kuma y'arki wanda ba saena wani b'ata lokaci nah wajen tunasar daku ba saboda ku kunfi kowa sanin laifinku",Wahiyya ceh ta shigo tana wata bunqasa tana jin kai,tazo kujerar dake gefen ta Sarki sae ta zauna tana wani shagwab'a irin ta makircin nan,Sarki kuwa tunda ta shigo yake wani kallonta yana murmushi kamar bazawarin da yyi kwantai ya samu mata. Bayan ta gama zama sae Sarki ya juyo ya cigaba da cewa "yanxu hukuncin dana yanke shine zaku kwana a d'aya daga cikin d'akunan horo (prison),sannan kuma sae an dubi d'aki mafi sauro da kuma duhu saboda ku ladabtu da kyau",ya juya ya kalli Wahiyya wadda itama shi take kallo tuntuni yace "wannan hukuncin yyi?",Wahiyya ta washe baki tace "wannan yyi,hukuncin ka wuqa me martaba"ta qarasa maganar tana sunkiye da kai alamar girmamawa,Sarki kuwa yaji dad'i ganin ya burge Wahiyya dan bashi da wani buri illa yaga yasa ta farin ciki ita da d'anta a kullum.. ©Hama G muh'd [8:04pm, 1/1/2017] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 014 Ba tareda wani b'ata lokaci ba aka kira bafade me kula da gidan yari (prison) yazo ya tafi dasu Yaayi dan cika umarnin sarki,bayan ya rufe su saeya dawo yazo ya sanar da Sarki cewa ya cika umarnin sa,Sarki yace mishi yyi kyau,Wahiyya ta kalle shi tace "kada a sake a basu abinci har sae an fitar dasu daga d'akin",bafaden nan ya ansa mata cikin girmamawa saeya fice,Sarki da Wahiyya suka tashi suka nufa cikin gida inda fadawa suka rufa musu baya. Bayan bafaden nan ya bar wajen bbu abunda Zeedat keyi illa kuka mamanta na rarrashin ta tana bata baki kan tayi haquri zaman kwana d'aya zasuyi kawae,Zeedat yarinya y'ar kimanin shekaru 8 da wani abune amma tasan cewa masu laifi ake kawowa nan wajen kuma a iya saninta bbu laifin da sukayi amma bbu yadda suka iya dole su kwana a wannan d'akin dukda darajarsu da martabar su. Da yamma lis Zeedat ta tashi daga bacci tana jin yunwa dan yau bata wani ci abun kirki ba,bata sanarda mamanta ba saboda bata son tashin hankalinta dan tasan cewa bbu abinci a halin yanxu,saedae tsakanin d'a da uwa ya wuce wasa Yaayi ta fahimci Zeedat najin yunwa qwarae,batace mata komai illa ciro wani d'an abun da ta ciro ta miqa mata tace "ga wannan kici dan nasan a halin yanzu yunwa kke ji",mamaki ya ishe Zeedat amma bata ceh komai ba illa qarb'an abincin da tayi dan yunwa take ji,abunka da masu sarauta bata wani ci abun kirki ba taji ta qoshi ta d'au ruwan ma tasha,Yaayin ma taci tasha ruwan ta qoshi suka rage wani,cikeda mamaki Zeedat tace "mama dama kisan zamuzo nan neh?",Yaayi tayi murmushi tace "ina fa,kwae dae sanin hali nasan hakan zata iya faruwa gashi kuwa ta faru". ©Hama G Muh'd [8:06pm, 1/1/2017] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 015 Zeedat ta rungume tana mejin dad'in kasancewar ta mahaifiya a gareta. Jaheed ko tunda ya tashi a barci Wahiyya ta hana shi fita dan karya gano abunda ake ciki,dan tabbas tasan idan ya sani to lallae saeya san yadda akayi aka fito dasu,dan haka ta tsare shi a gida ta hana shi fitowa dukda yadda ya matsa ya fito,a jikin shi yana jin akwae abunda ya faru bayan barcin sa amma bbu yadda ya iya dole ya haqura ya kwanta dan yasan ba barinshi maman zatayi ya fita ba. Koda dare yyi Yaayi da Zeedat sunyi barcinsu cikin jin dd'i bayan sun qarasa cin abincin su na d'azu,saedae cikin dare suka tashi saboda tsananin sauro da suka addabe su,duk tasu susa suke bbu sanya,a rayuwarsu kaff basu tab'a shan azaba irin ta wannan da suke ciki yanzu ba,alla alla suke gari ya waye amma ina gani suke kamar daren yau yafi na kullum jimawa,sun zamo abun tausayi dasu,ga sauro ga shegen duku dan ko idon mutum ba'a gani,Zeedat tayi kuka harta gaji tayi shiru. Saeda asuba suka dan samu sauqin yanayin,koda safiya kuwa tayi basu iya sun kwanta ba tsabagen rad'ad'i da jikin su ke musu duk jikinsu quraje neh jajaye gasu dama farare neh su. Saeda suka sake wuni kafinnan aka fitar dasu,Haima ceh tayi jinyarsu duk tausayinsu ya kama ta,bayan ta gyara Zeedat ta kawota ta kwantar bada jimawa ba kuwa tayi bacci,haka ma Yaayi bayan tayi wanka saeta kwanta tayi bacci.. ©Hama G Muh'd [8:16pm, 1/1/2017] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 016 Yaayi da Zeedat sunyi zazzab'in fiyeda sati sakamakon kwana cikin sauron da sukayi,gaba d'aya sun zamo abun tausayi bama yaZeedat da ita yarinya ceh,Haima ceh tayi ta musu jinya har suka fara samun sauqi.A kullum Yaayi qara son Haima takeyi,ta zame mata kamar yar uwa,itama Haiman tana son Yaayi da y'arta Zeedat. Wahiyya ko kullum cikin qulla munafurci take,tace anyi wannan tace anyi wancan,qarya ko a bakinta kamar tub'abb'en Sarki,tayi tayi ta raba Jaheed da zeedat amma inaa ta kasa dan ba kad'an ba Zeedat da Jaheed sun shaqu ga kishin juna da suke. Saedae yanzu Zeedat ta rage shiga ma Jaheed saboda halin mamarshi,Yaayi ceh tayi mata wannan nasihar gwanda abi komai a hankali sannan sae a zauna lfya da kowa lfya. Wahiyya na cikin bacce Jaheed ya saci hanya ya fito dan kar ta tambayi inda zai je,a hankali ya tashi kuma harya fita bata sani ba,yana fitowa ya nufa wajen wasu fadawa masu gadin gida,da zuwanshi kuwa saeya tambayesu "shin kunada labarin inda aka kai mun yar'uwa ta kwana biyu?",fadawan suka kalli juna cikin mamaki sukace "bamu da masaniya magajin Sarki",a fusace Jaheed yace "kun sani mana,idan kuma baku sanarda niba ku tabbatar kuna da munmunar hukunci agurin Sarki".. ©Hama G Muh'd [12:08pm, 1/3/2017] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 017 Daga jin haka sae jikin fadawan nan ya soma rawa sukace "ranka shi dad'e ae abun be kai har haka ba,sarki neh yasa a rufesu a d'aki me duhu da sauro na kwana d'aya daga cikin d'akunan horo",wani irin tausayin sune ya d'arsu a zuciyar Jaheed wanda hakan yasanya shi zubar da qwalla,gashi dae yaro neh d'an kimanin shekaru 6 ya'n watanni amma sarae yanada feelings akan abu,bece dasu komai ba ya juya ya nufa sashen su Zeedat,a ranshi yana tunano abunda zaece mata dan yasan,bbu tsoro ko kad'an a ranshi dan haka yasa kai ya shiga qofar. Mamaki neh da al'ajabi suka ishe Fadawan can kowa da irin abunda yake cewa,wani yace "kai amma yaron nan bbu tsoro a ranshi",wani yace "ina kaga tsoro kuwa tunda har iya tunkaro mu da wannan maganar",wani daga cikin su yace "gashi da tunani da kaifin basira in ba haka ba ta yaya akayi yasan cewa basu kwana a gidan su ba!",d'ayan yace "gashi d'an yaro,inba na manta ba befi shekaru shida bafa",sae d'ayansu yace "baka manta ba shekarunsa shida neh da y'an kai yanxu",d'aya daga cikinsu yace "kaii,akwae kallo nan gaba to,dan yanda yaran nan suka d'auko hanya bbu alamun gaba a tsakanin su dan haka zasu iya janyo ra'ayin iyayen ma",wani yace "haka neh kam",haka sukayi ta tsegumi tsakanin su... ©Hama G Muh'd [12:09pm, 1/3/2017] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 018 Yaayi na kwance tana bacci Zeedat ko na zaune suna ta shan hirarsu da Haima kamar wasu sa'anni dan yanxu ta samu sauqi bbu laifi,Zeedat ceh meyi wa Haima tambayoyi ita kuma tana bata ansoshin tambayar,bud'e qofar sukaji anyi,koda suka d'aga kai sai sukayi ido hurhud'u da Jaheed wanda shima kallo yabi su dashi,qarasowa yyi ya zauna kusa da Zeedat inda ya bata haquri kan abunda ya faru,Haima ko kallonsu kwae take dan ba kad'an ba yaran na burgeta yadda suke nuna kulawa a tsakaninsu ko a gaban waye dukda cewa iyayensu sunyi hannun riga.Zeedat tace dashi "bbu komai qanina daman baka mun komai ba,kuma dan baka zo ka taimake mu ba a lokacin a ba laifin ka bane,na tabbatar rashin sani neh don da ace kasani to daka zo inda muke,nagode da kulawarka",yace "ba komai",tace "yanxu abunda za'ayi ka tashi ka koma kar mamarka ta tashi ta neme ka bata samu ba kasan bazae mana dad'i ba koh",ya marairaice yace "nikam sae mamarki ta tashi na bata haquri dana tafi",Zeedat tace "aa Jaheed kasan halin ummar ka fa,yanxu idan ta farka bata ganka ba zata nemeka kuma idan tasan cewa nan kazo to zamu fuskanci fushinta",ta karya murya tace "ko kana so tasake sawa a hukunta muneh",da sauri ya girgiza kai.. ©Hama G Muh'd [12:09pm, 1/3/2017] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 019 Zeedat tace "tou ka tashi muje na raka ka idan Mamata ta tashi zan fad'a mata kazo kuma kace tayi haquri kan abunda ya faru",ta qare maganar da murmushi a fuskarta,shima murmushin yyi mata sannan ya tashi,itama ta miqe ta raka shi har qofa sannan ta dawo ta barshi ya tafi. Jaheed na komawa ya samu mamarshi ta tashi a bacci da gani kuma neman shi take bata ganshi ba,koda ta tambaye shi inda yaje saeya ce mata ya duba waje neh yaga ko baban shi na nan,tayi murmushi sannan ta kwad'a ma Aina kira,da hanzari Aina ta gabatar da kanka a gaban Wahiyya,tace "gani ranki shi dad'e",Wahiyya tace "Jaheed ke son ganin mahaifinsa dan haka nake so kiyi mishi jagora zuwa ga fadansa",tana qare maganar Aina tace "an gama gimbiya matar Sarki kuma uwar Sarki nan gaba",cikeda jin kai Wahiyya tace "a yanxun ma uwar Sarki nake",Aina ta murmusa sannan ta riqo hannun Jaheed ta d'orashi abayanta tana mai wasa saeta fito dashi zuwa fadar sarki,a hanya ko Jaheed yana ta jin haushin meyasa yace yana neman babansa,dama yace kwae ya leqa waje neh dan da gaske Jaheed baya son had'a hanya da babansa saboda ko kad'an baya son abunda yake yiwa yayar shi Zeedat da mamarta,don dae kwae bbu yadda zaiyi neh.Koda suke tafiyar kuwa kowa suka wuce sae yayi musu gaisuwar ban girma har suka iso fadan Sarki... ©Hama G Muh'd [12:58pm, 1/3/2017] Hamagee🌷: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 020 Sarki da Fadawan sa suna ganawa,a lokacin Aina ta shigo da Jaheed a bayanta,da ganin Jaheed ko fadwan suka fara masa kirari 'takawarka lafiya sarki me jiran gado,d'an sarki jikan sarki tattab'akunnen sarki,ta ko'ina d'an sarauta kke,ta uwa ta uba',Jaheed beyi wata wata ba yaje ya zauna a kujerar gefen babanshi,har lokacin kirari ake musu shida baban,shiko sarki wani irin dad'i yake ji gashi ga magajinsa dan ba kad'an ba yana mugun son Jaheed,shi kuma Jaheed be damu da kirarin da ake mai ba tunanin sa kwae Zeedat d'inshi,inda baban zae daena wulaqanta su toh daya fi kowa samun nutsuwa da farin ciki.Haka suka qare zaman su yau a fada,tareda sarki Jaheed ya koma cikin gida. Koda Yaayi ta farka a bacci sae zeedat ta sanarda ita zuwan d'an uwanta wato Jaheed da saqon daya bayar ta baiwa maman,har a ran Yaayi taji dd'i sosae amma saeta nuna ma Zeedat kamar bata ji dd'i ba,Zeedat yarinya ceh me kaifin tunani saboda haka ta fahimci sudden change dake fuskar maman dan haka saeta ceh "mama,meyasa kka b'ata rai?"kamar zatayi kuka dan ko kad'an bata son ganin fushinta,ganin hakan yasa maman tayi murmushi tace "aa Zeedat,ba komai kwae dae bana son kina yawan huld'a da Jaheed duk da cewar shi d'an uwanki neh amma gudun sake faruwar abunda ya faru a baya nake so ki jaa jiki da shi kinji",Zeedat ta fahimci abunda maman ta hango dan haka tayi murmushi tace "na gane Mama,nima bana son shiga mishi amma yau d'in shi yazo kinga kuma bazan kore shi ba kou",maman tayi murmushi tace "hakane y'ata",duk abunnan da akeyi Haima na zaune tana kallonsu a ranta suna burgeta matuqa,haka rayuwarsu taci gaba.. ©Hama G Muh'd [5:40pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 021 Several years ltr,, Zeedat da Jaheed na hango a gindin wani rafi kan dutse sunata wasa da dariya,sun girma sun qara kyau abunsu,Zeedat nada kimanin shekaru 21 yanxu haka,shikuma Jaheed 19years kenan.Daka gansu kaga y'an gida d'aya saboda yanayin jikinsu iri d'aya,dogaye neh kuma basuda jiki gasu farare tass ga kyau,saedae ita Zeedat kamannin mamarta tayo shi kuma Jaheed da babansu yake kama sarki kenan,wani in ya gansu ma zaece y'an biyu neh saboda kansu d'aya.Babban matsalarsu a yanxu itace rashin jituwar iyayensu dan ko had'uwar da sukeyi a waje ma bada sanin iyayen bane,saedae sum sha alwashin sae sun daedaeta tsakaninsu koba dad'e koba jima tunda yanxu sune masu tasowa iyayen kuwa gangarawa sukeyi. Suna cikin haka sae Jaheed yace "zaki wuce yanxu neh dan nikam na gaji gida zani yanxu",Zeedat tace "yanxun harka gaji,yaushe ma muka fito",Jaheed yace "ae idan baki manta ba mun riga ku fitowa ba anan kka sameni ba?",tace "haka ne kam amma ae lokacin kace baka jima kaima da fitiwa ba",yace "iyi,bakji yunwar da nake ji bane",Zeedat tayi dariya tace "yanxu naji magana,dama kwae kace mun yunwar kke ji mana",shima dariyar yyi sannan yace "kinga tafiyata sae kin dawo",Zeedat tace "toh saena zo dan nikam ba yanxu ba gaskiya",Jaheed ya miqe Fadawansa suka rufa masa baya sukayi gida.. ©Hama G Muh'd [5:40pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 022 Zeedat kuwa cigaba tayi da wasanta da ruwa,acikin hadimanta akwae wata wacce ta yadda da ita me suna *SUNAM*,Sunam yarinya ceh me mutunci da daraja babba,tasan hakkin dan Adam sosae kuma batada hayaniya,gata da gaskiya da rik'on amana wanda hakan yasa Zeedat ta yarda da ita. "Sanam",Zeedat ta kira sunanta,"naam"ta ansa da wata iriyar murna me shegen dad'in ji,Zeedat tace da ita "zoki gani,kamar mutum a can",sae tayi mata nuni da wani waje inda mutum yake tafiya shi kadae da gani kuma hunter neh,Sanam tace "kwarae kuwa naga mutum gashi can kamar ma maharbi neh",Zeedat tace "kaman dae kam",can da suka qure mishi kallo sae sukaga ashe inda suke yake nufowa,Sanam tace "gimbiya Zeedat mu bar wajen nan dan ko tabbas mu yake tunkarowa wataqil ma ganinmu yasa shi zuwa nan",cikeda rashin kulawa Zeedat tace "toh laifin me mukayi mishi da zamuji tsoron shi mu har wajen",Sanam tace "ba haka bane ranki shi dad'e ina jin tsoron mutane neh dan bamu sani ba ko mugu neh",Zeedat tace "ae koma miye shi bbu yadda ya iya damu tunda bamu shiga mishi hidima ba toh haka nan shima be isa ya shiga namu ba,ki dena tsoro bbu abunda zae faru"Sanam dae kwae tana jinta neh amma duk ta tsorata da zuwan mutumin nan.. ©Hama G Muh'd [5:40pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 023 Mutumin nan na qarasowa inda suke ya tsaya a daedae inda Zeedat take zaune,wucewa yazo yi amma ganinta ya sanya shi tsayawa.Bata ceh dashi komai ba iyakaci tasan ya mugun burgeta dan ba kad'an ba yyi kamada jarumi gashi fari kyakyawa kamar balarabe,infact shigarsa ma ta larabawa yyi,da kamar zae wuce sae kuma ya tsaya dan sosae Zeedat ta burge shi dukda cewa shi baya kula mata amna yau ya d'au aniyar kulawa,yace da ita "assalamu alaiki baiwar Allah",Zeedat ta shiga tunani aranta take tambayar kanta 'tooo menene kuma wannan daya fad'i,na biyun kuma Allah! Toh menene hakan yake nufi',Bawan Allahn ya fahimci rud'un data shiga dan haka yace da ita "ko baki jin yaren dana keyi neh?",Zeedat tace "naji wannan amma ban gane me kace daga farko ba kuma naji kace Allah,shin meyake nufi? Kuma ni y'ar Sarki ceh ba baiwa ba dan naji d'azu ka ambaci baiwa",cikeda mamaki yake kallonta,yaya za'ayi ace mutum besan Allah ba afterall shine mahaliccinmu kuma mamallakin mu gabaki d'aya,ya daure ya b'oye mamakin sa yace mata "amma keh ba musulma bace koh?",da wani sabon mamakin ta kalleshi tace "musulma!menene shi din?",wani irin mamakinta neh ya kamashi a ranshi yake fad'in 'lallae wannan jahilci yyi mata yawa,dama ashe akwae irin way'annan har yanzu a duniya,toh ae ko kafirai sunsan musulunci kwae dae aeki dashi neh bazasu yi ba,toh insha Allahu saena warkar da wannan baiwar Allahn daga wannan duhun jahilcin da take ciki,Allah ka bani iko da damar yin hakan'... ©Hama G Muh'd [5:41pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 024 Ya kalli Zeedat yace "ni sunana Abdulmud'allib amma ana kirana da Mud'allib",Zeedat tace "suna me dad'i,ni kuma sunana Zeedat",ya maimaita sunan "Zeedat",saeya kalleta yace "suna me dd'i,da zaki bani dama dana koyar dake addinin musulunci,addinin daya fi dacewa dake da kowa ma.Lallae had'uwar mu alkhairi ceh garemu baki d'aya",Zeedat tayi shiru tana sauraren shi,ita dae wannan baqo na burge ta matuqa dan haka take so ta bashi had'in kai don koyar da ita yanayin rayuwar shi ko zae taimaka mata itama,Mud'allib ya kalleta yace "toh malama Zeedat ni zan wuce garinmu,a nan kusada kuu muke dan haka gobe insha Allahu ina so mu had'u anan kuma keh kad'ae karki sanar da kowa zuwanki nan saboda bazan cutar dake ba dan mu addininmu yyi mana hani da mu cutar da d'an uwanmu",cikeda zumud'i Zeedat tace "amma zanso insan addinin nan naku da baya son wani ya zalunci wani dan babban abunda keh damuna kenan da mutanen garin nan akwae zalunci,kuma naji ka ambaci wani abu yanxunnan wae insha Aallhu,koh zaka sanarda ni abunda hakan keh nufi",Mud'allib ya kalleta yace "tabbas zan sanarda keh kuma zan koyar dake dukkanin abunda ya shafi addinin mu amma sae gobe in mun had'u kamar yadda nace kada ki sanarda kowa zuwanki nan ke kad'ae kuma zaki zo",Zeedat ta d'anyi jim na wani lokaci sae kuma ta fara magana kamar dae wacce ta tuno wani abun "abunda yafi yanxu shine karmu had'u anan,dan idan muka had'u qanina zae iya biyoni dan ya saba idan be ganni ba toh nan yake zuwa dan nice ma na sabar mishi da zuwa nan hutawa dan haka barin maka kwatancen wani wajen daban",Mud'allin yaji dad'in hakan dan haka tayi mishi kwatancen inda zasu had'u da kuma lokacin da zasu had'un.. ©Hama G Muh'd [5:41pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 025 Godiya Mud'allib yyi mata sannan sukayi sallama ya tafi,saeda Zeedat ta daena ganinsa kafinnan ta juyo ta kira Sanam tace da ita su tafi,suna tafe suna d'an hiransu kamar qawaye saedae duk yadda Sanam taso jin hirarsu Zeedat da baqonnan Zeedat taqi fad'a mata komai illa sunanshi data gaya mata,a haka har suka iso gida. Koda Mud'allib ya koma gida yau ba'a gane mishi dukda cewa ba mai magana bane dama amma yau ya fita daban,sannan be samu yyi bacci ba da dare yyi,tunanin Zeedat neh ya hanashi baccin,alla alla yake gobe tayi dan su sake had'uwa dan shi ya matsu yaga Zeedat ta zama musulma auren ta kuma yake sonyi dan tunda yake be tab'a ganin mace kamarta ba,gata kyakykyawa me kaifin basira dan daga gani qwaqwalwarta zata d'au abu da wuri,gata y'ar sarauta amma bata ji da kanta,wani abunda ya qara burgeshi da ita shine lokacinda tace mishi zata yadda ta abunda addinin shi yace saboda su garinsu bisa zalunci yake tafiya ita kuma bata son hakan.Saeda aka kira sallahr asuba Mud'allib be runtsa ba dan haka ya tashi yyi alwala yazo ya gabatar da nafilfilu sannan yaje massalaci yyi asubar shi a jam'i,saeda gari ya waye kafinnan ya idar da karatun kurani da yakeyi wanda hakan dabi'ar ceh tukunna ya dawo gida,sae a lokacin ya samu yyi bacci da niyyar qarfe goma zae tashi ya shirya dan zuwa inda sukayi da Zeedat zasu had'u dama 12 sukayi zasu had'un. A wajen Zeedat ma batayi baccin kirki ba sae tunanin Mud'allib takeyi,bata samu tayi bacci ba sae wajen qarfe 3 dan haka ba ita ta tashi ba sae qarfe 10:30,tana tashi tayi wanka ta shirya saeta fito ta gaida mamanta da Haima dake zaune kusada maman suna tattaunawa,bayan ta gaida sune saeta zauna tayi karin kummalon ta a wajen.. ©Hama G Muh'd [5:41pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 026 Kamar yadda Mud'allib ya tsara zae tashi qarfe 10,toh hakan ya tashi,bbu b'ata lokaci ya tashi yazo ya shirya yyi karin kummalo sannan ya fito yazo ya gaida Ummee dan haka yake kiran maman shi,babanshi kuma tun a masallaci suka gaisa dan haka be tsaya wata wata ba ya fita dan zuwa garinsu Zeedat,qarfe 10:30am ya fito bashi ya isaba sae 11:50am. Bayan Zeedat ta kammala karin lokacin 11:00am daedae dan haka bata motsa daga inda take ba ta zauna sukayi ta hira dasu mamanta sae 11:40am dot,ta lallab'a ta bar wajen,d'aki ta koma inda ta wata qofa ta fita lokacin 11:500am daedae,bbu nisa sosae da gurin da sukayi zasu had'un dan haka 11:58am ta isa. A daedae wajen ta sameshi yana jiranta,suka gaisa sannan suka nemi gurin zama sannan suka fara maganarsu kamar yadda yyi alqawarin koyarda ita musulunci haka yyi iyaka bakin qoqarinsa da fahimtarsa ya sanarda ita komai,kama daga yadda ake sallah,azumi da duk wani abun da ya shafi addinin islam,sannan ya bata tarihin annabawa da mutanen daa sosae,Zeedat kuwa tayi kuka harta gode Allah,a yanxu halinda ake ciki Zeedat ta musulunta,dan haka tare ma sukayi sallahr azahar da niyywr idan taje gida zatayi kamar yadda ya gwada mata (bayan tayi wankan tsarki kenan),yanxu sun yanke shawarar kullum zasu ringa had'uwa a wajen yana koyar da ita karatun alqur'ani me girma da wasu littafan musulunci.. ©Hama G Muh'd [5:42pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 027 Yau tun da safe Jaheed ke neman Zeedat,koda ya tambayi Sanam saeta ceh mishi itama bata ganshi ba da kamar zata sanarda shi cewa sun had'u da wani jiya amma saeta fasa,Jaheed ya damu matuqa gashi baya son shiga sashensu dan mamansu tace idan ya sake ya shiga sashen saeta yi fushi dashi,dan haka ya wuce zae fita,a qofar fita ya tambayi masu gadi ko sunga fitar Zeedat,d'aya daga cikinsu yace qwarae yaga sanda ta fita d'azun nan,Jaheed ya tambaye shi ko ya san ta inda tabi sae megadin yace gaskiya be sani,kai tsaye Jaheed ya bar gidan inda ya nufa wajen da suke had'uwa da Zeedat neh wato gindin wannan rafin. Yana tafe guards d'insa na biye dashi har suka iso wajen,ganinta yasa yaji relief ya qarasa inda take zaune tana jifan duwatsu cikin ruwan ya zauna,tana ganin shi ita kuma ta sakar mishi murmushi tace "sae yanxu ka fito",yace "iyi bayan nayi ta neman ki tun d'azu ban samu ba,meyasa kka fito keh kadae ga can Sanam a gida itama tana cikiyar ki?",Zeedat tace "kwae yau banjin ayi mun rakiya neh,kuma nasan kaima idan ka fito nan zaka zo",saeta sakar mishi wani murmushi,shima murmushin yyi mata.Basu wani jima sosae a gurin ba suka tashi suka koma gida,tun a mashigar gidan suka rabu karma wani ya gansu yaje ya fad'a ma Wahiyya.. ©Hama G Muh'd [5:42pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 028 Zeedat na shiga taje ta gaida mamanta da Haima dake zaune da ita sannan ta koma d'aki inda ta gabatar da sallah tareda bitan karatun da Mud'allib ya qara mata yau,wani sauyin yanayi take ji a rayuwarta kamar wacce aka cire ta cikin wani qangi,ko dayake qangin neh! Koda yaushe Zeedat ta tuno Mud'allib son shine yake qaruwa mata a rai,yana burgeta matuqa dan bata qi ace su kasance tare a koda yaushe ba.Shima Mud'allib haka yake a wajen shi yana son Zeedat matuqa saedae be fad'a mata ba,ya d'au alwashin gobe idan suka had'u zae sanarda ita abunda ke ranshi saedae besan ko zata amince ba. Washegari kamar yadda suka tsara zasu had'u hakan sukayi,bayan ya gama koya mata karatun neh ya sanarda ita abunda ke cikin ranshi na cewa yana sonta,itama ta amince mishi,godiya yyi mata kafin suka rabu bayan sunyi sallahn azahar tare.Ya d'an mata rakiya kafin ya juya ya tafi gida shima a ranshi yana mugun jin dad'i.. ©Hama G Muh'd [5:43pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 029 Yaukam Zeedat bata da niyyar zama a wannan wajen da suka saba had'uwa da Jaheed dan tasan lokacin la'asar ya kusa shiyasa kwae ta wuce abunda kai tsaye tayi gida. Sarki yanzu ya fara tsufa saboda haka ya rage biyewa Wahiyya kan wasu abubuwan da takeyi dan haka yanxu ta tsaneshi bata sonshi dan harta fara tura ma d'ansa qwalli d'aya wato Jaheed tsanarshi,ta sanarda Jaheed wasu abubuwa da uban yyi wanda duk wani me hankali zaiji ya fita a ranshi wanda kuma dukda had'in kanta akayi wasu kanma ita ta sashi yyi su,amma yanxu tana ware kanta. Saedae duk abubuwan nan bata nunawa sarki a idonshi cewa bata qaunarshi,a halinda ake ciki ma neman hanyar da mulki zae bar hannun shi ya koma na d'anta takeyi dan a ganinta a yanxu Sarki baida wani amfani a gurinta.Wahiyya kenan butulu!! Yaayi kuwa na nan hankalinsu kwance da y'arta Zeedat,basuda wata damuwa yanxu,dama damuwar kenan ta rashin kulawa daga Sarki wanda yanxu kam ma ya zame musu jiki dan ko kwata kwata ya daena damun su.Barinma Zeedat da daman tun haihuwar ta bata san miye gata da jin dad'in uba ba,a yanxu maganar sauya rayuwar dukkanin y'an garin neh a ranta zuwaga tafarki mafi gaskiya mafi b'ullewa wanda tana jiran lokacin da Mud'allib zai bata izini neh kwae.. ©Hama G Muh'd [5:43pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 030 Yanzu ya zame wa Zeedat da Mud'allib jiki,kullum sae sun had'u a wannan wajen yyi ta koyarda ita abubuwa masu tarin yawa gameda addinin musulunci wanda ita kuma take ta qara zurfafa a cikinsa,dad'in shi da ita kuwa komai ya koya mata bata mantawa yana nan a zaune,a halinda ake ciki yanxu ma harta kai izu 25 na qur'ani,kuma hadda ceh me kyau a kanta ba wae ko irin na muna hadda ba. Kullum maganar Jaheed a yanxu ita ce ina Zeedat ke zuwa kullum saeta tafi wani waje ta barshi,ita kuma saeta ceh mishi ae inta fito kafin yazo neh saeta d'an fara zagawa. Sarki na kwance a d'akin Wahiyya duk damuwa ta isheshi,tunanin Yaayi da y'arshi kawae yake yi da irin zaluntar su da yyi tayi a baya akan Wahiyya,motsin da yaji neh ya dawo dashi daga tunanin da yake yi,Wahiyya ceh riqeda kwarya da barasa a cikinta,tana wani kwarkwasa kamar yadda ta saba mishi sae tace "meke damun sarki neh?",Sarki ya dubeta yace "bbu komai sae tsufa",tayi murmushi irin nata na shaid'anun matan nan sae tace "ga me kore damuwa nan,abunda kafi son sha dan d'ebe kewa wato barasa,gata da sanyi",a take Sarki ya miqe ya zauna dan da gaske yana son shan barasa koda ba a cikin damuwa yake ba,Wahiyya ta miqa mishi ya qarb'a yasha,bayan ya gama sha ya kwanta a wurin duk ya bugu.. ©Hama G Muh'd [5:43pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 031 Aina da Wahiyya na zaune suna tattaunawa kan abunda suka aikata,dan Aina ceh ta kawo ma Wahiyya maganin data Saka ma Sarki wae dan ya nakasa a d'aura d'anta Jaheed a kan karagar mulki,Wahiyya na sanarda Aina cewa Sarki yasha barasar kuma yanzu haka yyi barci daga ji idan ya tashi aikinsu yyi,Aina ta kwashe da dariyar mugunta tace "lallae me jiran kujera ya zamo me ita zuwa gobe nasan Sarki zae tashi a nakashe kuma nanda wasu y'an kwanaki idan aka ga Sarki ba zae iya komai ba nasan za'a d'aura me girma Jaheed a kan kujerar Sarki",cikeda zumud'i Wahiyya tace "haka neh zancen ki". Bayan d'an wani lokaci,Wahiyya ceh ke magana da wasu fadwa da tasa aka yo mata kiransu,kome tace musu?oho! Nidae naga ta basu y'an silalla a jikin wata y'ar qaramar jaka,su kuma suna ta murna,su biyu neh fadawan,bayan ta basu sae suka fice suka koma bakin aikinsu. •••••••••••••••••••••••••••••••• Later at night,, Aina na kwance tana sharar bacci a d'akinta dan dama ba'a d'akin Wahiyya take kwana ba,wasu mutane neh suka shigo a hankali fiskokin su duk a rufe,sun saka baqaqen kaya kowannen su kuwa takobi neh a hannunshi,basu tsaya wata wata ba d'ayansu ya tashi Aina sae d'ayan yyi saurin sa mata tsumma ya toshe mata baki.. ©Hama G Muh'd [5:47pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 032 D'ayan na toshe bakinta sae wanda ya tashe tan yace mata "kin san *shi ramin qarya qurarre neh*,kuma hausawa sukan ce *idan zaka gina raminka na mugunta,toh ka gina shi daedae da kai dan tabbas wata ran kaine zaka afka cikinshi* saboda haka kin toni wanda yafi ki kuma bbu makawa haka zaki afku cikin shi,batare da wani b'ata lokaci ba gimbiya ceh ta aiko mu kashe ki wato uwargidan ki matar sarki Jaisus kuma biyanmu zatayi da abu mafi soyuwa a zuqatan y'an Adam,saboda haka yanxu zamu cika aikinmu",idanun Aina duk sun firfito waje da jin wanga batu,jikinta kuwa sae rawa yake yi,tuni ta tsulo fitsari a gurin,bafaden nan da ya toshe mata baki neh yyi maza ya fille kanta agurin bbu ko tausayi,ta kai kusan mintuna 20 kafin jikinta ya daina motsi,su kuma shegun tuni suka watse suka bar d'akin. Washegari da safe magana ya bazu a fada cewa anyi kisan gilla ma Aina,Sarauniya Wahiyya kuwa murna taji kamar meh dan a ganinta yanxu asirinta bazae tonu ba,saedae a gaban jama'a nuna tayi rashin Aina takeyi,koda aka tambayi sarki kuwa saeta ceh tun safe take tashin sa amma yaqi tashi sae surutai da yake tayi shi kad'ae,koda Jaheed yaji haka hankalinshi be wani tashi ba Wahiyya ceh tasa aka yo mata kiran likita tazo ta duba sarki. Bayan ta duba shi saeta tabbatar wa mutane cewa Sarki ya nakasa dan ko tashi da kanshi ba zae sake iyawa ba,murna wajen Wahiyya ba'a magana,sae dae cikin mutane tana nuna damuwarta.. ©Hama G Muh'd [5:48pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 033 Jaheed ya d'an tausaya ma sarki da yaji abunda ya sameshi qwarai,saedae idan ya tuno da abubuwan da yyi sae yaji kwae ya tsane shi.Labari ko da ya iske Yaayi da Zeedat basuji dad'i ba musanman Zeedat wacce tasha alwashin musuluntar dashi kafin ya koma ga Allah. Koda Zeedat da Mud'allib suka had'u yau,ya fahimci akwae abunda yake damun Zeedat dan haka ya tambayeta,ita ko bata b'oye mishi ba ta sanar mishi komai ta kuma fad'a mishi cewar tana son ta sa baban ta ya karb'i muaulunci,Mud'allib be musa mata ba yanxu kam dan a halinda ake ciki ya yarda da Zeedat kuma ya san ba kad'an ba yanxu tayi nisa cikin musulunci kuma imaninta ba zae bari wani ko wata su rinjaye ta zuwa ga kafirci ba.Ba tareda sun jima ba yace taje tasan duk yadda zatayi taga babanta dan musuluntar dashi kafin ace ya mutu,koda sukayi sallama bata tsaya ko ina ba dan yau Jaheed yace mata bazae fita ba dama,sae gida. Hamdala tayi data samu an mayarda baban can side d'inshi yanxu ya bar sashen Wahiyya kenan,koda ta shiga sae sarki ya fara koke koke yana neman yafiyarta,itama kukan ta shiga yi tana ce mishi ba komai ta yafe ae shi babanta neh kuma ta d'au mishi alqawarin nema mishi gafarar mamanta ma. Ko kad'an zeedat bata sha wuya wajen musuluntar dashi ba,nan ya sanarda ita *mafarkin* da yayi kwanan nan wanda shiyasa shi ya dawo sonta kamar rae,wae yyi *mafarkin* y'an garin nan suna cikin duhu wanda ko ganin d'an uwanka baka iyawa tsabagen duhun da suke fuskanta,wae sae tazo ta kawo musu haske wanda saeda tasa ma baban hasken kafin nan tasa ma sauran al'ummar.. ©Hama G Muh'd [5:48pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 034 Bayan ya gama bata labarin *Mafarkin* sae yace lallae wannan *mafarki* nawa ya tabbata dan kuwa gashi na gani,Zeedat bata bar sashen ba saeta ta tabbatar ta sanarda shi duk abunda ya kamata ya sani ta kuma mishi alwala sunyi azahar tare sannan tace koda bata samu ta dawo anjima ba saboda kar mutane su fuskanci wani abu to yyi sallahr shi daga kwance kamar yadda ta koya mishi. Zeedat bata tsaya ko ina ba sae sashensu inda ta tararda mamanta da Haima,Zeedat ta kwashe duk yadda sukayi da Sarki ta fad'a musu,a take suka karb'i musulunci suma,koda lokacin la'asar kuwa yyi sukayi alwala bayan sunyi wanka sae sukaje sashen sarki,basu samu kowa ba kuwa,suka gana dashi sannan sukayi sallahn la'asar d'in,inda sarki ya nemi gafarar Yaayi,ita kuwa tace ba komai ta yafe.Tare sukayi sallahr magrib da isha'i kafinnan suka koma sashensu bayan sun tabbatar yaci abinci kuma baya da buqatar komai. Wahiyya kuwa tunda aka maida Sarki sashen shi bata sake koda leqawa bane. Washegari kamar yadda Zeedat ta saba had'uwa da Mud'allib suka had'u,yaji dad'in nasarar da sukayi na ceto rayuka har uku daga kafurci zuwa musulunci,yauma basu wani jima ba suka rabu bayan ta biya mishi karatun yau.. ©Hama G Muh'd [5:49pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 035 Nasan kuma kunyi missing gidan Niyad da ja'i,to nima nafi ku missing dan haka bari d'an tab'o kad'an daga wajensu.. Niyad ceh zaune a tsakar gidan Ja'i na ta faman hura wutan dafa qwai (egg) wanda Niyad tasa shi dan yanxu komai shi yakeyi a gidan kasancewar Niyad nada ciki,yanzu haka cikin nada wata 7 kenan,saboda wannan yasa ta sake mishi duk wani aikin gidan yakeyi shi kad'ae,shima kuma Ja'in be damu ba saboda d'okin da yake,yanxun cewa tayi tana son cin qwan zabi shine yaje ya sayo yazo yake tafasa mata. "Wai kai har yanzu baka iya had'a wuta tana ci bbu hayaqi neh?duk ka cika ni da hayaqi",Ja'i yace "kiyi haquri yanxun nan zae kama kuma zaki daena jin hayaqin",tace "daka taimaki kanka". Bayan ya gama dafa qwan sae ya d'auki wani kwano ya saka a ciki sannan ya kai mata,ya ajiye kwanon a qasa yana b'are qwan sae tace mishi "haba Ja'i so kke saena mutu neh kafin ka gama b'are mun qwan?",Ja'i ya dubeta yace "haba Niyad duk saurin nan da nakeyi baki gani?",Niyad bata sake cewa komai ba harya gama ya miqa mata.A hankali take ci abunda,bbu wata damuwa a ranta,Niyad kenan sarkin jaraba!! ©Hama G Muh'd [5:49pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 036 Sarki na kwance wasu daga cikin fadawan shi suka shigo wajenshi,inda sukayi mishi batun murabus da zaiyi tunda wannan ciwo nashi bana tashi bane,sukace ya kamata ya barma magajinsa gadon mulki wato Yarima Jaheed,koda sarki yaji haka saeya ceh yaji amma a d'an bashi lokaci dan yyi nazari a kai tukunna,Fadawa sukace bbu komai ko zuwa nanda kwana uku zasu dawo dan jin sakamakon da ya yanke.Suka tashi suka fita aka bar Sarki da shiga damuwa,baya son Yarima Jaheed ya zamo Sarki dan tabbas muguwar uwarshi zata iya juya shi tasaka yyi zalunci saboda ya lura yanzu yana d'aukar maganar ta fiyeda daa.A halin yanxu Sarki ya san komai gameda abunda Wahiyya tayi da kuma wanda take kanyi yanxu,ya zuba mata ido neh kwae yaga gudun ruwanta. Bayan d'an wani lokaci Zeedat ta shigo dan taimaka wa babanta yyi alwala yyi sallah,bayan ya idar saeta bashi abinci yaci ya qoshi,bayan nan suna cikin hira sae sarki ya kira sunanta "Zeedat!!",Zeedat ta ansa da "naam me martaba",ya cigaba "ina son muyi wata magana dake wanda kuwa maganar nada matuqar muhimmanci gare mu baki d'aya,magana ceh wadda ta shafi kyautuwar al'ummar garin nan namu wanda idan akayi wasa gyaran da muke neman yi ko ince kke neman yi lallae zai b'aci" ©Hama G Muh'd [5:50pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 037 A rud'e tace "Allah ya baka nasara wace magana ceh haka?",sarki yace "ki kwantar da hankalin ki,idan har aka sab'a yin abunda nake so na fad'a neh shine za'a fuskanci matsala babba,d'azu daff shigowar ki waziri,galadima da kuma sarkin fada suka zo suka sameni kan maganar yin murabus a bama Yarima sarauta,ni kuma gaskiya nasan cewa idan har Yarima ya karb'i sarauta toh lallae irin sarautar da zaa cigaba dan koda ace yyi niyyar sauyawa bazae yiyu ba saboda Wahiyya bazata barshi ba dan ko nima ita tayi ta sani yin wasu abubuwan ballantana kuma d'anta,sannan tabbas rayuwarki na cikin had'ari shiyasa nace musu su bari nayi tunani akai tukunna",Zeedat ta d'an nisa sannan tace "toh yanzu me ka yanke? Kasan dole Yarima neh zae gaji sarautarka dan baka da wani magaji illa shi",Sarki yace "eh haka neh amma dole in samu mafita kafin nanda kwana uku da suka bani zasu dawo",Zeedat tace "toh Allah ya zab'ar da abunda zefi kasancewa alkhairi",Sarki yace "ameen",Zeedat tayi mishi sallama ta tafi,shi kuma sae tunani yakeyi. Koda su waziri suka bar sashen Sarki kai tsaye sashen Wahiyya suka nufa inda suka aiki wata baiwa ta sanarda ita zuwansu,koda baiwar ta fito saeta ceh wae su shiga.Bayan sun shiga suka zauna sannan suka karanto mata yadda sukayi da sarki,da jin hakan sae Wahiyya tace "koma miye dae bbu yadda zaeyi dan dolensa yyi murabus kuma Yarima neh zae hau dan bashida wanda yafi shi",sukace "wannan gaskiya ceh",sukayi mata sallama suka tafi.. ©Hama G Muh'd [5:50pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 038 2 days later,, Zeedat na cikin tafiya zata gurinda suke had'uwa da Mud'allib kwae sae taji kamar motsin mutum a bayanta,abun ya bada tsoro matuqa dan a iya saninta ko Sanam bata yarda ta biyota balle kuma wasu,yau kimanin kwana uku kenan kullum sae taji irin wannan gashi idan ta juya bata ganin kowa dan wajen cike yake da dogayen ciyayi gasu green abun sha'awa kasancewar lokacin damina neh saedae daminar bata shiga sosae ba dan ba kullum ake ruwan ba ma,tayi qarfin hali ta cigaba da tafiya amma duk hankalinta na baya,a cikin kwanaki ukun data fuskanci ana binta canza hanya takeyi taje wani wajen sae daga baya saeta je inda suke had'uwan amma yau batada niyyar sake hanya dan haka kai tsaye taje wajen abunta. Ba wani bane me binta illa wani bawa daga cikin bayin Jaheed wanda shi Jaheed d'inne yasa shi ya gano mishi inda Zeedat ke zuwa kullum kuma a irin wannan lokacin gashi kuma ya gano wajen dan haka ya koma ya sanarda Jaheed komai,Jaheed yace mishi ya gode gobe zae raka shi wajen,ba kad'an ba Jaheed yyi mamakin ko waye wannan wanda Zeedat take zuwa kullum su had'u kuma ko tad'inshi bata tab'a yi mishi ba,shidae ya barma ranshi cewa koma wanene zae ganshi gobe kuma idan ya gano cewa cutarda ita yake neman yi toh bbu makawa zaesa a fille mishi kai kuma ko wanene shi.. ©Hama G Muh'd [5:50pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 039 Bayan sun gama sae sukayi sallama Zeedat ta dawo gida,bayan ta shiga sashensu ta gaida maman saeta nufa sashen sarki kamar yadda ta saba kullum,ta gaida shi tayi mishi alwala yana kwance yyi sallah,haka itama tayi alwala tayi sallahr azahar,bayan sun idan ta saba sae sun d'anyi hira ta bashi abinci kafin ta tafi dan yanxu tace ma masu kulada shi cewa su barshi kwae ita zata ringa yi mishi komai dan ko kad'an Zeedat bata yarda da masu aikin gidan ba gani take kowa da maganar Wahiyya yake aiki bbu imani ko kad'an azuqatansu.Bayan ya gama cin abincin sae ya kirata "y'ata!",Zeedat taji dad'in wannan suna da ya kira ta shi saeta ansa mishi da "naam babana",ya cigaba "batun hukunci da nace zan yanke akan murabus neh,lallae nayi nazari sosae kuma na yanke hukunci cewa make zan barwa kujerata ta mulki bbu wata mafita idan ba ita ba",Zeedat cikeda damuwa tace "ni kuma baba?",yace "qwarai ke d'in,kuma inason ki karbeshi hannu bibbiyu dan hakan neh kwae zaesa addinin gaskiya wato addinin musulunci ya fad'ad'a a wannan garin,kuma na sanki da biyayya saboda haka nake roqonki don Allah karki qi,idan kuma d'an uwanki kke tunani toh ki daena dan na tabbatar bazae damuba saedae kwae Allah ya tsareki da sharrin Wahiyya",Zeedat da tuni ta fara kuka tace "ameen baba,kuma na amince zan karb'a amma saboda kare addini nah kad'ae",yace "Allah miki albarka amma kada ki fad'a ma kowa",tace "ameen babu meji insha Allah saedae Mud'allib dan bana iya b'oye mishi wani abu a kaina",yace "bbu damuwa",sukayi sallama sannan ta tafi.. ©Hama G Muh'd [5:51pm, 1/6/2017] Hamagee: 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 040 Washegari,, Da sassafe su waziri suka dawo mishi akan batun kwana uku da suka wuce,batareda b'ata lokaci ba Sarki yace dasu "na zauna nayi tunani da kaina kuma na yanke hukuncin zuwa nanda sati d'aya tak zanyi murabus kuma ba kowane me hawa kan karagar nan ba illa babbar y'ata wato Zeedat dan a iya tunani na bbu wanda ya dace face ita dan Yarima har yanxu yarone qarami be gama sanin zafin kansa bama balle yasan na al'umma",gaba d'ayansu suka cika da mamakin maganganun sarki dan su a tunaninsu bazae ko jaa da maganarsu ta bama Yarima sarauta ba dan a iya ganinsu yafi son Yarima fiyeda komai a kowa a duniya. Yau Jaheed tun sassafe ya shirya yake jiran fitan Zeedat dan binta yaga wanda suke ganawa dashi,be jima ba kuwa ta fito ita kad'ae ta tafi,seda ya bari ta d'anyi nisa kafinnan yace da bawan nashi su bita,tana tafe tana tsoron kar wani ya biyota kamar sauran ranakun amma sae taji shiru yau babu me binta dan haka ta saki jikinta tayi ta tafiyar ta har ta iso wajen,suka gaisa da Mud'allib sannan ta sanarda shi yadda sukayi da Sarki jiya,shikuma dajin haka sae yace "abunda za'ayi ina kince Jaheed d'in na jin maganar ki?",tace "eh",yace "toh ko zaki gwada mishi maganar shiga musulunci ko Allah zaesa ya karb'a kinga kin kub'utar da abu biyu,na farko zae musulunta kuma zae musuluntar sannan na biyu kin kare sarautar garinku dan zaeyi mulki neh bisa tafarkin addinin musulunci",tace "wannan gaskiya ceh amma ina tsoron mahaifiyar shi dan ta wuce inda kke tsammani,ina...."bata qarasa ba taji mutum a kansu,da juyawar ta sae sukayi ido hud'u da Jaheed....... Mu had'u a littafi na uku dan jin yadda zasu qare!!,taku har kullum Hamagee. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 041 Da sauri Zeedat ta miqe tana kallon Jaheed suprisely,Jaheed ma kallonta yake yace "dama nan wajen kke zuwa kullum shine kke b'oye mun",Mud'allib neh yace "ku zauna ku fuskanci juna mana",sae a lokacin Jaheed yasan dashi a gurin dan da idonshi kamar a rufe yake baya ganin kowa sae Zeedat. Jaheed ya kalleshi cikeda mamaki sannan ya juyo ya kalli Zeedat saeya nuna Mud'allib yace "wannan kuma waye Zeedat?"Zeedat ta dubi Mud'allib tace "wannan shine Mud'allib me taimako gareni,gareka kuma ga al'ummar wannan garin,shine wanda ya fitarda ni daga cikin duhu kuma kuma yake neman fitar daku zuwaga haske dan kuwa tabbas addinin islam addinin haske neh,saboda rayuwata a yanxu ta sauya don ni kaina ina ji a jikina,a halin yanzu Me martaba,mamana da kuma Haima suna cikin addinin dan haka nake so kaima ka karb'e shi domin mu tsira tare",Jaheed daya tsaya yana ta kallon Zeedat sae yanzu ya nisa yace "amma wannan wane irin addini neh da har me martaba ya amince dashi? Lallae ya zamo dole in karb'e shi nima dan tabbas bana son yadda rayuwar mu anan garin take tafiya". Cikeda farin ciki Zeedat tace "Alhamdulillah",Mud'allib ma godiya yyi ga Allah sae yyi sujada Zeedat ma ta bishi sukayi tare yanda suka karanto addu'ar da ake yinta yayinda mutum ya rizqi abun farin ciki saeya yita don nuna godiya ga ubangiji.Koda Jaheed yaga sunyi sujadan,shima sae yyi yadda suka yi... ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 042 Bayan sun d'ago sae Jaheed ya tambayi dalilin yin hakan sae Mud'allib yyi mishi bayanin komai.basu bar wajen ba saeda Jaheed ya musulunta ya karb'i dukkan cika cikan musulunci,bayan nan Zeedat ta sanarda shi hukuncin da Sarki ya yanke na cewa ita zae barma sarauta amma yanxu lallae Sarki zaeji dad'i kuma zae bar mishi karagar mulki in yaji cewa ya musulunta dan dama damuwar shi itace yadda mulkin garin zae cigaba kan koyarwa irin ta addinin Allah,addini mafi adalci,addini me koyarda mulki da yadda ake yin shi. Bayan sun rabuda Mud'allib wanda ya kasance cikin murna da farin ciki,sae suka nufa gida tare bawan da ya rako Jaheed na biye dasu,hira suke inda Zeedat take qara sanarda Jaheed wasu abubuwa gameda musulunci shi kuma yana jin dad'in hakan.A haka har suka isa gida,suna isa sashen baban suka nufa inda suka taradda shi kwance yana neman miqewa,da sauri Jaheed ya qarasa inda yake ya tayashi gyara zama,ya sa mishi matashi a ta kanshi sannan yace mishi sannu,Baban yace yauwa cikeda mamakin Jaheed da kuma farin cikin ganinsu tareda y'ar uwarshi,Zeedat ma ta qaraso tana mishi sannu,yaji dad'i sosae.. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 043 Bayan duk sun gaida shi sae Zeedat take sanarda shi gameda musuluntar qaninta wato Jaheed,Sarki yyi murna qwarai da jin hakan dan haka yyi ta saka musu albarka,bayan sun gama sae Zeedat ta kira sunan baban "Baba",sarki ya ansa da "naam",sae Zeedat ta cigaba da cewa "tunda yanzu Allah yyi d'an uwana ya karb'i musulunci,to ina ganin ya kamata a matso da wannan hidima wato nad'in sarautar shi,ya kamata a sanar a fada cewa gobe za'a nad'ashi sarki kaga daga nan addinin zae fara yad'uwa har ya gama zaga garin",sarki yana jin batun Zeedat yana girgiza kai alamar abunda take fad'i gaskiya ceh,sae bayan ta gama saeya ceh "wannan gaskiya ceh,lallae kinyi tunani me kyau,Allah ya kaimu goben",sukace "ameen",Sarki yace "yanzu muyi sallah dan naga lokacin azahar tayi,bayan mun idar kuma inaso kuyi mun magana da waziri dasu galadima dan in sanarda su samun su fara shirye shirye kafin zuwa goben",suka ansa da "toh". Jaheed neh yau kam ya taimaki baban wajen yin alwala kafin nan shima yyi nashi,Zeedat ma tayi nata sae dukansu sukayi sallah,Jaheed neh yaja su dan harya iya sallah yanzu kuma ya riqe surori har biyar a yau d'innan.Bayan sun idar sai suka fita Jaheed yaje yyi ma su waziri magana kan sarki na nemansu,bbu b'ata lokaci suka je,nayan sun gama tattaunawa sae Sarki yace da Jaheed gobe ya tabbatar Mud'allib yazo fada kafin a fara nad'in,Jaheed yace toh sannan yyi mishi sallama ya tafi.. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 044 Bayan su Waziri sun bar sashen Sarki sae suka fara gulma wae ya akayi Sarki ya sauya maganar shi a yau d'innan,su a tunanin su yarima neh yaje yyi mishi magana dan sun san tabbas Sarki na jin maganar yarima amma dukda haka sunyi mamaki da sarki ya juya lokaci guda dan su a iya saninsu idan yyi magana baya canzawa.Koda suka kai wannan labarin ma Wahiyya,taji dd'i sosae sannan ta musu alqawarin zuwa gobe bayan anyi nad'in sarautar akwae wani babban aikin da zasuyi mata saeta biyasu harda sauran na baya da bata qarasa basu ba duk zata had'a musu.Sukayi godiya sannan suka bar wajen sae Wahiyya dake ta saqa da warwara kan yadda zata cimma burinta gobe. Tana cikin hakan Jaheed ya shigo,ya gaida ta sae yyi shiru be sake ce mata ci kanki ba,saeda ta gaji saeta ceh "lallae yau yarima ka nuna mun cewa ni Wahiyya ni nayi naqudar ka na bi na haife ka dan ka nuna mun yanzu kana bin abinda nake fad'a maka,da badan kaje ka samu mahaifinka kan batun sarautar nan ba da yanzu wa y'aruwarka za'a bada amma yanxu ka qwacen ma kanka y'anci",tayi wani murmushin mugunta,Jaheed kuwa kallonta kwae yake a ranshi yana tunanin wanda yazo ya fad'a mata cewa shi yyi wa sarki magana.Lallae su waziri munafukai neh dan kuwa tabbas bbu wanda yaji maganar nan sae su sae kuma Zeedat,amma tabbas su sukayi mata gulmar dan kuwa ba Zeedat bace, Jaheed ya fad'a a ranshi.. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 045 Bayan Zeedat ta bar sashen Sarki kai tsaye tayi side d'insu,tana shiga ta gaida mamanta bayan sun idar da sallah dan lokacin data shigo suna sallahn azahar,bayan sun gaisa saeta sanarda ita duk abunda ake ciki.Maman tayi farin ciki matuqa da musuluntar yarima,ba ita kad'ae bama harda Haima tayi murna sosae. Lokacin la'asar nayi Zeedat,Yaayi da kuma Haima suka nufa sashen Sarki danyi mishi alwala sae suyi sallahr acan dan in ba hakan ba bbu meyi mishi kuma bazae iya da kanshi ba gwanda ma idan ruwan na kusada shi toh yana iya lallab'awa dan hannunshi na dama yana aeki,bayan sun shigo sae Zeedat ta taimaka mishi yyi alwala lokacin kuma su Yaayi suna yin nasu,bayan ta gama saeta barshi yyi sallah itama tayo alwalan,bayan ta idar saeta ceh ita kam zataje ta d'an huta dan ta gaji,sukayi sallama sannan ta fita,Yaayi kuwa ta jima suna hira da Sarki daga baya har Haima ta tafi ta barsu. Ba wata hira bace kuma illa ta duniya. Lokacin magrib nayi Zeedat da Haima suka dawo sukayi sallah tare kafin nan sukayi mishi sallama suka tafi,kafin yayi bacci ko yyi isha. Jaheed ma dake shi kad'ae neh a sashen sa yyi sallolin shi hankali kwance. Dukkanin su da tunanin gobe sukayi barci.. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 046 Niyad da Ja'i na hango a tsakar gidansu suna ta zuba drama,wae Ja'i ya siyo musu ragon suna neh dan yanzu haihuwar tazo kusa sosae dan yana iya zuwa yau koh gobe,shine Niyad take wannan shegen rigimar wae a dole saeya siya musu saniya koh raqumi dan ba zae yiwu ace shekara da shekaru basu tab'a haihuwa ba sae yanxu kuma ace ya sayi rago kad'ae,Ja'i yace "haba Niyad kowa ba daedae qarfinsa yake abu ba? Yanxu keh kanki shaida ceh a garin nan ba kowa yake ka da rago a suna ba,mafiya yawansu akuya ceh ko taure",a fusace Niyad tace "dakata Ja'i ban tambayeka abunda mutan gari sukeyi ba,kwae ina magana akan abunda ya dace muyi neh dan nuna banbancin mu dasu dan kuwa akwae,abunda yasa nace babanci kuwa shine su masu yanka akuya ko tauren ai kowacce shekara d'aya ko bibbiyu suke haihuwa,mu fa? Inace yanxu kimanin shekarun mu talatin da biyar kenan bamu samu haihuwar ba sae yanxu kuma ka cemun wae ga yadda y'an gari sukeyi",ta wani ja ta tsuke fuska,Ja'i yace "ba wae ina nufin semun yi yadda ya'n gari sukeyi ba,ina nuna miki cewa koda ragon muka yanka bbu meh ganin kashinmu neh"Niyad tace "Ja'i! Baka da wata magana da zaka mun fa tunda duk shekarun nan da muka d'iba bamu tab'a siyan koda kazar suna ba, toh lallae dole mu yanka sa ko raqumi dan yanzu yaci ace ka tanadin kud'in saboda baka tab'a haihuwa ba,idan kayi lissafin kud'in sayan akuyoyi na kowane bayan shekaru biyu tun auren mu ai yafi kud'in siyen raqumi ma",shidae Ja'i daya rasa yadda zaiyi da ita saeya bar gidan abunshi.. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 047 Ja'i be dawo gidan ba saeda yasan yadda yyi ya samo saniya,aro yaje yyi? Siya yyi? Ko kuwa satowa yyi,ohoo ko Niyad batada wad'annan amsoshin tambayoyin ita dae kwae tayi murna da yin hakan. Da dare yyi Ja'i yaje ya nemo musu abunda zasu ci na daren,bayan ya dawo sukaci kafin nan suka kwanta bacci. Washegari tunda sassafe Niyad take jin ciwon mara,daga ji kuma tasan haihuwa ceh tazo mata saeta sanar da Ja'i.Shikuma Ja'in saeya je ya kira likitar garin wato matarda take karb'ar haihuwa,koda ta zo saeta sa Ja'i ya kawo mata duk abubuwan da zasu buqata daman sun kammala siyayyarsu tun cikin nada watanni shida. Suna zaune can sae naquda tazo ma Niyad gadan gadan,ko magana Niyad bata iyayi ta koma abun tausayi,koda likitar taga haka saeta maida Niyad d'aki da taimakon ta Niyad ta haihu,d'anta Namiji ta haifo gashi qato fari kyakyawa,Likitan tayi qoqarin gyarasu duka sannan ta gyara d'akin,Ja'i na shigowa kai tsaye ya nufa wajen Niyad da jaririnsa,murna wajen shi bbu magana,nan ya sallami likitar da kud'i me yawa saedae kullum zata ringa zuwa tanayi ma me jego da jariri wanka dan bbu meyi musu,tayi godiya tayi musu sallama ta tafi bayan ta sanarda su yadda zasuyi komai kafin zuwa gobe ta dawo.. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 048 Bayan likitar ta tafi sae Ja'i ya tafasa ruwan zafi yasa a abun riqe zafi wanda Niyad zata ringa tsarki dashi kenan har zuwa goben,bayan ya gama saeya fita zuwa kasuwa,koda ya dawo da gashin nama ya shigo da yawa,ya kawo ya ajiye ma Niyad. Niyad taci gashin nan kamar bazata bar saura ba amma bbu yadda ta iya sada ta rage dan naman nada yawa sosae.Da dare yyi suka kwanta sukasa jaririn su a tsakiyar su suna wasa dashi har bacci ya d'auke su. Washegari da sassafe Ja'i yaje ya hura wutan ruwan wanka Niyad da jaririnsu kamar yadda Likita tace,can likitan tazo tayi musu wankan ta gyarasu sannan ta duba lafiyarsu taga ba wani abu da yake damunsu saeta tafi abinta. ………………………………………… Haka suka cigaba dayi kullum saeta zo ta musu wanka har ranar suna.Yau da wuri tazo ta shirya su sae aka kwantar da babyn yana bacci,su kuma suka cigaba da shirye shiryen su. Rana tayi har an rad'a ma yaro suna *YUZRAN*,mutane y'an suna har sun fara cika a gida,kowa yana mamakin irin wannan suna dan basu tab'a ganin sunanda aka yanka Saniya guda ba irin wannan,ga abinci ishashe. Niyad ceh ta shiga d'aki domin d'auko jariri wa y'an suna su ganshi,koda ta d'aga shi sae taji jikin shi a sake,saeta kai kunnenta wajen hancin shi,ina shiru kke ji,ta d'aura tafin hanninta kan qirjin shi amma ina bbu rai,wani ihun data kurma neh yasa jama'a tururuwa a d'akin... ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 049 *_Gidan Sarki_* ••••••••• Washegari da safe Jaheed ya nemi Zeedat suka je wajenda Zeedat suke had'uwa da Mud'allib,basu wani jima ba Mud'allib yazo dan dama sunyi akan yazo goben da wuri,bayan ya iso sae suka gaisa sannan suka nufa gida tare. Sarki na kwance sukayi sallama ya ansa sae suka shigo bayan ya basu umarnin shiga.Ko wannan su ya nemu guri ya zauna,Sarki neh ya fara magana "godiya da dukkan wani yabo ya tabbata ga ubangiji Allah,ina miqa mishi godiyata daya kawo mu wannan lokaci,kuma ya sauya mana rayuwa acikin qanqanin lokaci,kaima kuma ina maka godiya daka shiga rayuwar y'ata harya zamanto mun gano hanyar gaskiya kuma mun bita duk ta sanadiyyar ka,keh kuma Zeedat bbu abunda zance dake da kuma d'an uwanki sae Allah yyi muku albarka"dukansu suka ceh "ameen".Sarki ya cigaba "dalilin da yasa na taraku anan shine,na farko yau za'a rad'a sabon sarki a garinnan saboda haka nake kira gareka yarima,daka kwatanta gaskiya da adalci a mulkin ka,kuma ka tsara komai a hanya mafi gaskiya da dacewa dan haka nake so ka nad'a Mud'allib wazirin ka kuma limamin garin nan sannan ko bayan raina ban yadda ka bijirewa umarnin sa ba dan kuwa tabbas nasan ba zae saka a turba ta banza ba,na biyu kuma inaso ana gama nad'in nan a d'aura auren Mud'allib da Zeedat,aure kuma na har abada,idan kka sab'a umarnin mijinki Zeedat toh ki tabbatar da cewa ban yafe miki ba,na uku kuma gareka neh Mud'allib,na baka amanar y'ayana biyun nan da Allah ya mallaka mun idan,ka sani idan kaci amana toh lallae amana bazata barka ba.Daga qarshe nake cewa Allah ya had'a kanku baki d'aya ya kuma baku zuri'a ta gari sannan yasa kuci nasara wajen ceto rayuwar al'ummar garinnan",suka ceh "ameen",kowannen su ya d'au mishi alqawarin cika dukkanin abunda yace suyi,daga qarshe suka mishi sallama suka bar d'akin. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 050 Bayan sallahr azahar aka d'aura yarima kan karagar mulki,bayan an gama hidindimu sae Mud'allib ya koma garinsu akan gobe zae dawo da y'an uwanshi sae a d'aura musu aure da Zeedat. Bayan an gama komai sai Waziri da galadima suka je sashen Wahiyya dama tace anjima suzo tana neman su,suna zuwa ta fito ta samesu.Wasu y'an maganganu sukayi kafin nan ta sallame su suka tafi cikin murna dan ba kad'an ba ta basu abun arziqi kuma tace zata qara musu. ___________________________________ Ana yin sallahr isha'i Sarki yyi bacci dan a gajiye yake sae dae yana murnar burin shi ya cika tunda ya shaida magajin shi saura auren y'arsa wato Zeedat wanda ake sa ran d'aura shi gobe in Allah ya kaimu. Kamar a mafarki yaji mutane a kansa dan haka yyi saurin tashi dan ganin abunda yake faruwa,da bud'e idon shi sae yyi ido hud'u da Waziri da galadima sae sarkin fada kowan nensu bbu idon rahama a fuskar shi.Waziri neh riqe da adda ya sa a wuyan Sarki tareda mishi kashedin idan ya sake yyi musu ihu saeya fille mishi kai kafin lokacin yin hakan yyi,"Gimbiya Wahiyya wato amaryar ka,ta aiko mu nan dan mu qarasa ka dama ita ta nakasa ka idan baka manta,toh shine muke so muji ko kanada saqon da zaka isar mata kafin mu aika da kai" inji Waziri,Sarki dake ta b'ari yana addu'oi yace "bbu komai saedae ina roqon ku daku bani wata dama"Waziri yace "hanzarta damar miye?" Sarki yace "ina so ku bani takarda dan yin wata y'ar wasiyya ga y'ay'ana kuma inaso ku basu hannu hannu kar ku bama wani ko wata idan basu bane"Sarkin fada yace "an gama amma ka tabbatar baka rubuta musu wani abu da zae gane muna da hannu akan wannan kisa ba",Sarki yace yyi alqawarin hakan dan haka suka kawo mishi takarda,alqalami da kuma tawada a cikin wata roba qarama,suka taimaka mishi ya tashi ya zauna sannan suka damqa mishi kayan rubutun,saeya fara rubutu kamar haka: ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 051 *_Assalamu alaikum,daga farko dae ina me baku haquri kan mummunan labari da zaku iske amma ina so kuyi haquri kuma kuyi ta mun addu'a ko zan samu rabauta a ranar gobe kiyama.Bayan nan ina so na muku magana kan riqo da addininku sannan kada ku bijire mishi koda na qanqanin lokacin.Kai yarima ko ince Sarki inaso kayi mulkinka bisa addinin musulunci,kuma duk wani hukuncin da zaka zantar ya kasance haka addini ya tanadar,kayi mulkin ka bisa amana da jin qai kuma ka tabbatar dukkan al'ummar mu sun karb'i wannan addini.Keh kuma Zeedat,ina so ki zauna da mijin ki lafiya,yi nayi bari na bari shine kad'ae hanyar samun aljannar ki,Allah yasa mu dace ya kuma baku ikon riqo da gaskiya._* _Bissalam_ Bayan ya gama saeya nad'e ya ajiye a inda yasan zasu gani,su waziri dake jira ya gama suka ceh ya gama yace eh,a take a wajen ya fille mishi kai,shi kuwa Sarkin banda kalmatush shahada bbu abunda yake yi har yaji kanshi ya bar jikin shi dan sunkuyar da kanshi yyi a lokacin,koda suka gama aikinsu sae sukayi sauri suka bar d'akin kowannen su ya koma makwancin shi.Sarki kuwa jikin shi duk jini neh inda gangar jikin sa yake gefe haka kanshi ma gefe guda yake,jini duk ya rufe fuskar shi.(Allah ya jiqan shi nace sannan na bar d'akin).. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 052 Washegari da safe Jaheed da Zeedat suka fara shirye shiryen d'aurin auren,bbu wanda yasan da auren sae su sae maman Zeedat da Haima,suna cikin haka suka ji ana shela cikin fada wae an kashe Sarki a d'akinshi cikin dare kuma bbu wanda ya san su waye neh. A hanzarce suka nufa wajen,suka taradda gawar Sarki kwance a gaban bayin shi sunata rusar kuka,Jaheed yyi qarfin hali yace dasu su daena mishi kuka ba'a kuka haka wa mamaci sae dae ayita mishi addu'a,dukkan su saeda sukayi mamakin maganganun yarima na cewa wae suyi mishi addu'a dan su basu san wannan ba (Allah mun gode maka kuma ka raba mu da jahilci a duniya da lahira). Zeedat kam gabaki d'aya ta rasa na cewa,jikinta duk yyi sanyi a ranta tana tunanin wanda ya aikata wa ubansu wannan aika aikan.Da qyar suka bar gawar baban bayan sunyi mishi addu'oi. Har an d'auki gawar za'a a birne bayan matan shi duk sun ganshi,kwatsam saega Mud'allib sun shigo da y'an uwan shi,yace a dakata sae anyi mishi wanka an sallace shi,kowa ya tsaya yana mamakin abunda ya fad'a.Saeda aka mishi wanka sukayi sallahn gawa da taimakon y'an uwan Mud'allib d'in sannan suka kai shi makwancin shi,bayan sun sae Jaheed yace za'a iya d'aura auren yanxu sannan bayan an d'aura za'a bashi Waziri da kuma limamin gari sannan sae a fara aikin yad'a muaulunci a garin,amma kafin nan sae an gano wanene silar mutuwar Sarki,Waziri,galadima da kuma sarkin fada duk idonsu saeda ya raina fata,Mud'allib yace "da zaka bar maganar d'aurin aure da nad'innan sae zuwa nanda kwana biyu zuwa uku daya fi saboda a gano wanda yyi wannan kisar kuma a yanke mishi hukunci daedae da abunda ya aikata",Jaheed da jin hakan saeya ceh "ai duk yadda kace daedae neh,toh sae a bari sae bayan kwana ukun sannan daga yau za'a fara bincike",Mud'allin da y'an uwan shi duk suka goyi bayan hakan akan bayan kwana uku zasu dawo.. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 053 Bayan nan sae Jaheed da Zeedat sukayi musu rakiya suka tafi.Zeedat da Jaheed bayan sun dawo kai tsaye sukayi sashen Sarki,masu aikin suka yima tambayoyi kan waye na qarshen shiga d'akin sukace tunda suka bar d'akin bbu wanda ya sake shiga kuma basu ji motsin kowa ba da daddare,ran Jaheed yyi mugun baci dan a ganinshi sakacin su neh yyi yawa da suka zauna bacci basu san wanda ya shiga ba,Zeedat ceh tace "lallae shigowa akayi aka kashe shi,kun zauna kuna barci baku ma san wanda suka shigo ba,an san baku isa ku hana a kashe shiba amma ae da kuna lura da abunda keh wakana da kun gano wanda yyi wannan kisan",haquri suka soma basu su kuma suka wuce suka barsu a wajen,d'akin Baban suka nufa inda sukayi ta dube duben su ko Allah zaisa su gano wani abun,suna cikin haka Zeedat taci karo da wata takarda a tsakankanun shimfid'ar Baban,ta zaro takardar sannan tayi ma Jaheed magana "zo ka gani Jaheed",Jaheed yyi maza ya qaraso inda take yana fad'in "meh kka samu?",nan ta ware musu takardar suka bi suka karanta,kowannen su saeda yyi kuka saboda tsananin tausayin Baban,Zeedat tace "amma wannan wane irin azzalumi neh,harya jirashi yayi wannan rubutun kuma ya kashe shi,kai mutanen mu basuda imani",Jaheed yace "insha Allahu wanda yyi wannan abun saeya shiga hanu kuma bbu makawa hukunci saeta hau kanshi koma waye shi".. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 054 Bayan sun d'anyi jim na wani d'an lokaci,sae suka cigaba da binciken su,can Jaheed yaci karo da wani zobe,ya d'auko ya nuna ma Zeedat suka qare mishi kallo,Zeedat tace "bbu makawa wannan zoben sarauta ceh,ya zamo cewa a cikin fadawan gidannan neh wani ya shigo d'akin nan,kuma ga jini a jiki,tabbas sae mun nemo meh wannan zoben saboda a cikin gidan yake",Jaheed yace "wannan haka yake,kuma da gani na babban bafade neh dan su kad'ae ake mallakawa irin wannan abubuwan".Bayan sun gama tattaunawa sae suka yanke hukunci anjima a fada za'a tara dukkan fadawan gidan sae a tabbatar da zoben waye,a haka suka rabu Jaheed yyi sashen shi ita kuma tayi nasu sashen inda ta sanarda Maman ta komai,Maman tace "Allah ya tona asirin wanda yyi kisan",Zeedat da Haima sukace "ameen".Bayan sun gama jimamin suka tashi sukayi alwala sukayi sallahr azahar.Jaheed ma sallahr yyi a sashen shi. Bayan tafiyan su Mud'allib sae su Waziri suka jeh suka samu Wahiyya suka sanarda ita abunda ake ciki,Wahiyya tayi musu alqawarin zata hana Jaheed yin binciken dan idan harya gano toh lallae kashin su ya bushe,sae sannan su Waziri suka d'an ji sanyi a ransu saedae maganar da Jaheed yyi na cewa za'a nad'a Mud'allib Waziri yana damun Wazirin,amma ya bar maganar tukunna sae an kashe wancen maganar kafinnan ya d'ago wannan.. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 055 Wahiyya ta rasa ta yadda zata fara tunkarar Jaheed da batun ya janye bincike akan wanda ya kashe ubanshi,saedae bbu yadda ta ita dole ta san duk hanyar da zata bi dan hanashi aiwatar da binciken,dan haka ta tashi kai tsaye ta nufa sashen Jaheed d'in. Jaheed ya idar da sallah kenan bayan yyi addu'oi yana tunanin me zoben nan saeya ji muryar mamanshi dan haka yyi saurin miqewa ya nufa qofar d'akin ya bud'e mata ta shigo,tana kallon shi taji nikinta yyi wani irin sanyi ta rasa ta inda zata fara mishi magana,Jaheed ya lura da yanayim da ta shiga ciki dan haka ya tambayeta "ya dae na ganki haka?kinada wata matsala neh?",jin ya fad'i hakan yasa Wahiyya tayi amfani da wannan lokacin tace "bbu Jaheed kwae tunanin mahaifin ka nakeyi,ina tausaya mishi kan irin wannan kisa da akayi mishi",Jaheed yace "ki daena damuwa mama,insha Allah zae samu rahamar ubangiji",Wahiyya da bata fahimci abunda ya fad'i ba tace "ban fahimce ka ba",Jaheed yace "ba wani abu",Wahiyya tace "shi kenan,amma kasan miye?",yace "a'a",tace "ina ganin ya kamata ka janye maganar bincike da kke sonyi na mutuwar babanka,muji kwae da rashin da mukayi,bana so garin binciko wani abun a janyo wata babbar matsalar saboda haka yadda muka haqura kaima ya kamata ka haqura kwae dan ba gano komai za'a yi ba",ta wani sunkuyar da kai qasa alamar kuka yaci qarfinta,Jaheed ya matso kusada ita ya d'an kwantar da kanta a jikin shi yana lallashin ta sekace y'ar shekara 5.. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 056 A ranshi yana mamakin yadda akayi taji wannan maganar tunda bata wajen akayi kuma a iya tunanin shi bbu wanda zae fad'a mata a wajen,yace lallae akwae wani abu dake gudana wanda bamu san dashi ba,yyi gyaran murya bayan ya gama tunanin da yake sae yace "karki damu daga yanxu ma na daina",wani dariyar da Wahiyya ta sakar neh yyi mugun d'aure mishi kai,wae ace a kashe mijinta amma bata damu da sanin wanda ya aikata kisan ba saima so da takeyi a rufe maganar kuma har murna takeyi dan yace ya janye,lallae akwae wata maganar a qasa saedae ya barwa kanshi sanin hukuncin da ya yanke a kan hakan.Yyi murmushi shima yace "ina shikenan,hankalinki ya kwanta?",tace "eh,haqiqa ka nuna mun cewa inada iko akanka kuma zaka bi maganata akoda yaushe",yace "hakane mama",ta tashi ta miqe ta tafi tana me murna.Koda ta koma sashenta saeta saka aka kira mata su Waziri sannan ta sanarda su yadda sukayi da Jaheed d'in,suma sun d'an samu relief saedae har yanzu waziri na cikeda damuwar maganar Jaheed ta cewa za'a nad'a sabon Waziri,ya d'an nisa yace "ni dae har yanxu hankali nah ba'a kwance yake ba na cewa za'a nad'a sabon waziri",Wahiyya tace "damuwarka kenan? Toh bakada damuwa ana maka wannan maganar kai kana wata,ae indae muka samu wannan magana ta ruhu toh munyi meh wuyar daga baya ayi maganar nad'in,sannan kasan a yanzu idan na mishi maganar nad'in toh dole yyi tunanin wani abu a tsakanin mu",dukkansu sunaji suna girgiza kai alamar gamsuwa,daga bisani sukayi mata sallama suka tafi.Farin ciki gun Wahiyya ba'a magana. Bayan fitar Wahiyya Jaheed yyi ta jin mamakinta,meyasa bata son a gano wanda ya kashe baba? Meyasa daga jin nace na fasa ta fara murna jikinta na rawa?,duk wannan tambayoyin a zuci Jaheed yyi su,yyi maza yyi nafila raka'a biyu saeya roqi Allah ya gafarta mishi qaryar da yyi ma mamanshi,dan bazae iya yin yadda takeso ba,dole ya gano wanda ya kashe mishi baba.Bayan ya idar ya kwanta a haka har yyi bacci.. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 057 *Gidan Niyad* Mutane suka cika a d'akin kowa na tambayar ta lfya,bata iya basu ansar tambayarsu saedae kukan da ta cigaba dayi,ganin babyn kwance yasa wata ta tsuguna ta d'auko shi,a kid'ime take fad'in "yah mutu,wayyo d'an yah mutu",nan da nan gidan suna ya koma na makoki,masu farin ciki da masu taya murna suka koma baqin ciki da tausaya wa Niyad,lallaminta sukayi tayi masu kuka kuma nayi.Bayan Ja'i ya dawo aka sanarda shi,yyi baqin ciki kwarae da gaske,shi yanzu ma babban damuwar shi shine yadda ya karb'o bashin saniyar suna gashi baida kud'in biya,kuma gashi har an yanka yanzu ya zamo asara kenan,wani irin takaicin Niyad yaji saboda ita ta tursasa shi ya karb'o. *Gidan Sarki..* Washegari Sarki (wato Jaheed)ya tara dukkan fadawan gidan dan qarasa binciken da yakeyi,nan ya gano cewa wannan zoben na Waziri neh,Jaheed be nuna cewa ya gane komai ba kan kisar baban shi saedae a ranshi yana tunanin yadda zaeyi ya tunkari waziri da batun ko yanada wata masaniya kan batun.Bayan an watse da yamma Jaheed da Zeedat suka yanke shawarar tunkarar waziri tare dan dama Jaheed ya sanarda ita duk yanda akayi d'azu,bayan sun gama tattaunawa sae suka nufi wajenda waziri ke zama suka samesu tareda Galadima da sarkin fada kuma daga gani suna tattaunawa neh kan wani abu me muhimmanci ganin yadda fuskarsu ta nuna.Suka qarasa suka mishi magana,gefe suka jashi kafinnan suka fara mishi tambayoyi kan ta yaya akayi zoben shi yaje d'akin sarki,nan da nan jikin shi ya soma rawa ya qago wasu qarerayin shi ya fad'a musu.Sukayi sukayi dashi cikin hikima ya fad'a musu yadda akayi amma firr waziri yaqi kuma daga maganganun shi sun gano cewa sarae yanada masaniya kan kisan shiyasa suka qi barin shi. Saeda waziri yaga fushin jaheed sosae tukunna ya yarda ya fad'i gaskiya tunda ga kan nakasan sarki da mutuwar Aina har zuwa mutuwar sarki,tas ya kwashe ya fad'a musu dan sun mishi barazanar mutuwa sunce indae be fad'i gaskiya ba toh lallae zasu kashe shi.. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 58 Sun shiga cikin tashin hankali ba kad'an ba barin ma Jaheed da ya kasance mahaifiyar shi ceh tayi komai.Waziri kuwa yyi nadama sosae saedae *it's too late to cry...* Bayan kwana biyu,kwanaki uku sun cika cif,Mud'allib suka dawo shida y'an uwanshi,anyi musu tarba da kyau daga bisani aka d'aura auren su da Zeedat daman duka b'angare biyun a shirye suke.Bayan an kammala komai aka nad'a Mudallib Waziri tareda niyyar neman way'anda suka cancanta sae a basu galadima da kuma sarkin fada,bayan an gama hidindimu sae y'an uwan Mud'allib suka tafi da niyyar shikuma zae je daga baya tareda Zeedat d'in. Koda aka sanarda Mud'allib rabarin da waziri ya bayar saeya ceh hukuncin daurin rai da rai neh akansu,saboda haka Sarki yasa aka zo mishi dasu waziri dama tun ranan yasa aka kullesu saboda karma su fad'a wa mamanshi abunda ake ciki,koda suka zo sae Mud'allib yyi qoqarin musuluntar dasu,amma fir suka qi,dan haka bbu bata lokaci akayi musu hukunci daedae da laifinda suka aikata. Wahiyya dajin wannan labari tayi hauka,haka aka d'aukota aka kaita gidan yari amma sashen mahaukata.Jaheed yyi baqin cikin abunda ta aikata ba kad'an ba saedae kuma bbu yadda ya iya kuma hukunci dolene akanta dukda cewa itace ta haife shi,bbu yadda ya iya haka yyi tawakkali ya dogara ga Allah sannan idan ya tuna yanada Zeedat da kuma Mud'allib,sae yaji damuwar shi ta ragu dan Mud'allib ya zamo mishi kamar jini yanzu,bama shi kad'ae ba har ita Zeedat d'in shiysa take qara sonshi koda yaushe... ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 059 Bayan wasu y'an kwanaki,Allah yyi wa Wahiyya rasuwa,Jaheed yaji baqin ciki mara misaltuwa daya kasance ta mutu ba'a musulma ba saedae bbu yadda ya iya da ikon Allah,Zeedat,Mud'allib da kuma Yaayi da Haima sune sukayi ta lallamin shi suma sun tausaya mishi sosae da sosae. Bada jimawa ba suka fara aikin yad'a addinin musulci ma jama'a,saedae abun haushi bbu dayan su daya kula hasalima cewa sukeyi sarki na neman ruguza rayuwarsu da suka samo shi tun kakanu da iyaye,sunyi sunyi har sun gaji dasu,saedae sun d'au niyyar cika wannan alqawari da sukayi wa kansu na yad'a addinin. Bayan kwana biyu,Mud'allib ya d'auki Zeedat suka tafi garinsu da niyyar zasuyi kwana d'aya sae su dawo,zae kaita ganin dangin shine. Bayan tafiyarsu Jaheed baya jin dad'i kwata kwata,Yaayi ceh kad'ae me d'ebe mishi kewa dan yanxu ya riqeta kamar mahaifiya harma yana jin da ita ceh ta haife shi tun farko. Washegari da safe,Jaheed na zaune a fada suna tattaunawa da Yaayi kan yadda zasu fuskanci al'amarin,sae wani bafade ya shigo yace dashi yyi baqi,Jaheed yace ace dashi ya shigo.. ©Hama G Muh'd 🍁🌿🍁🌿 *MAFARKIN HAMAGEE 2* 🌿🍁🌿🍁 ®WISDOM OFFICIAL WRITERS *_In devotion to Sis Feedy_*❤ Page 060 Bafadennan ya fita yace da baqin su shiga sarki yace su shigo,koda suka shigo sae suka gaida shi cikin girmamawa kamar yadda akeyi wa sarki,Sarki yace "meke tafe daku?",d'aya daga cikinsu ya fara da cewa "haqiqa munyi nazari munyi tunani kan maganar da kai mana ranan,kuma mungano cewa addinin nan naku abun bi ne saboda da muka duba irin rayuwar da akeyi da a gidannan da kuma wacce ake yinta yanzu ba d'aya suke ba,da ana mulkin zalunci da son kai amma yanzu bbu wannan kuma da duk abunda sarki yaga dama ayi yinshi akeyi koda be dace ba amma yanzu gashi nan addini kke so ka koyarda mu amma baka tilasta mana ba,sae ma neman zab'inmu da kayi,saboda haka nida wanban d'an uwan nawa mun yarda munaso mu shigo cikin addinin koda kuwa zamu qarar da dukkan dukiyoyin mu neh",wani farin cikine ya ziyarci zuciyar Jaheed da Yaayi wanda basu tab'a shiga cikin shi ba,Jaheed yace "lallae naji dad'in wannan magana taku amma ku sani cewa ba'a biyan komai kafin a shiga cikin wannan addinin",nanda nan Jaheed ya musuluntar dasu. Bayan nan sae mutanen suka sanarda su cewa ae basu kad'ae bane akwae wasu a waje,yawansu yafi qarfin su shigo a tare shiyasa suka jira a waje yanzu suma sae aje a musuluntar dasu.Jaheed sunji dd'i sosae dan haka bada jimawa ba suka nufa waje inda suka ga mutane bila adadin,nanda nan suka karb'i musulunci suma,fadawan gidanma duka suka shiga,ranan dae tare sukayi sallahr azahar. Bayan sallahr suka zauna Jaheed yyi ta ilimantar dasu way'ansu abubuwan da ya kamata su sani as *muslims*, suna cikin haka su Mud'allib suka dawo,suma sunyi murnar taran wannan labari me dad'i.Haka rayuwarsu taci gaba kullum a jam'i sukeyin sallah matan kuma a gidajensu sukeyi,a kwana a tashi kuwa dukka y'an garin suka musulunta illa su waziri wanda har yanzu suke gidan yari. Rayuwar Niyad kuwa tuni ta sauya dan yanzu ta daena duk abunuwan da takeyi,suma sun kama addini bbu sanya... Anan na kawo qarshen wannan littafi me taken suna *MAFARKINA*,sae mun sake had'uwa a littafina na gaba wato *UNIVERSITY GIRLS* wanda already na fara rubuta shi,saqon gaisuwata ga dukkanin masoyana na fili dana b'oye,wanda na sani da wanda ban sani ba,Allah ya had'a mu a darussalam..Assalamu alaikum!! ©Hama G Muh'd adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *