Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, June 15, 2017

TANA RAINA 3

adsense here

Sad-Nas [10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 37-38 Kaka yace eh nasan komai sabreen, mamminkine tace karna gaya miki ita zata gaya miki da kanta shiyasa nayi shuru😰. Sabreen tace to kaka amma dukda kasan hakan shine kabarta tazo guna akan me zatazo guna bayan ita da iyayentane nasadiyar kasancewata marainiya, juyawa tayi afusa ta sake hankad'a salma tana cewa kibar gidannan banason ganinki kuma bana buk'atan jin sauran bayaninki kawai ki fita a gidannan karki sake zuwa inda muke adalilinki mahaifina ya sadaukar da ransa😭, salma ma kuka takeyi tace kiyi hakuri sabreen ki saurareni, sabreen tace bana buk'atan jin komai kawai ki fita nace😰, salma tace haba sabreen nasan dama hakan zai faru amma dan Allah kiyi hakuri ki yafe mana hakan shiyasa nad'au alk'awarin taimakonki kota wani hanyane dan ki yafe mana, sabreen shiyasa na saudaukar da budurcina dan in taimakeki a hannun wannan MUTANE UKUN a tunanina hakan zaisa ki yafemin sabreen dan Allah😰. Murmushin takaici sabreen tayi tace kina nufin zan yafe mikine, to ai shi mahaifina RANSA ya baki saboda da haka ban yafeba kuma kibar gidannan salma😭. Shi kaka dayake yasan wacece salma da sauri yaje ya janyo sabreen yana cewa haba sabreen kefa musulmace bai kamata ki dinga fad'an hakanba mahaifinki kwanansane ya kare koda hakan bai faruba to a wannan ranan zai mutu. Da sauri sabreen ta cewa kaka da bazai mutuba kaka ka dena bin bayanta nidai ban yafeba salma kibar gidannan😭, kaka yace salma yi hakuri kije karki damu zata yafe muku dama bakuyi komaiba jeki kinji mun gode sosai banaso 'yan gidan su dawo suji me muke ciki. Kuka sosai salma takeyi sannan ta tafi tana fita daga wajen gate d'insu seta b'ace. Kuka sosai sabreen takeyi kaka yana ta rarrashinta tana cewa wayyo Abbana wayyo mammaina Allah ya jik'anku da rahama😭. Kuka tayi mai isarta sannan tayi shuru ta wuce d'akinta tanata tunanin abin a ranta, toilet ta shiga ta wanke fiskanta sannan ta fito zataje kichin ta d'aura abinci dare, wayartace ta fara kara ta duba taga yah kamal ne, ta dauka tare da cewa hello, kamal yace hello sabreen ina fata dai kin dena kukan yanzu? Murmushin karfin hali tayi tace EH nadena, yace to shikenan mun fitane dukkanmu hardasu mum amma zuwa anju kafin magrib zamu dawo kinji, to yah kamal sekun dawo nagode, yace sabreen kawar naki ta tafine? Eh tafi😠, ko to shikenan semun dawo, toh sannan ta katse wayar. Itadai bats ganewa yah kamal ba alamu dai ya Nuna sonta yakeyi, kuma gaskya yah kamal mutum ne nagari Wanda ko wace mace zatayi fatan samu a rayuwarta. Yana da kyawawan halaiya ga nutsuwa da Sanin darajan mutane, bugu da k'ari kyakkyawane shi sosai Dan yafi SUHAIL kyau gaskya, kawai dai shi SUHAIL farine tas kamar balarabe, shi kuwa kamal bak'ine sannan yana da saje mai kyau Wanda shi suhail Sam bayi da saje se gashin kai mai laushi. Kunsan kuma farin mutum da d'auke ido da kuma d'aukan hankalin 'yan mata gashi sun iya dressing sosai da iya d'aukan kamshi😘 kuma suhail yafi kamal tsayi sannan suhail baida yawan dariya kamar kamal, wannan shine bambancinsu. Sabreen tanata tunani a zuciyarta tana had'a abinci har ta gama tuwo miyan kuka yaji DRY FISH. 6:20pm su mum suka dawo gida lokacin sabreen tana kwance a d'akinta, mikewa tayi dan taji dawowarsu ta karasa Palo tace HAJIYA sannuku da dawowa, mum tace yawwa sabreen sannunki da gida ya fama da aiki, sabreetayi😊 tace alhamdulillah sannan tace ya kamal yah suhail sannunku da dawowa, sukai mata 😊sukace yawwa sannu da aiki, ta kalli HAFSAT sukaiwa juna murmushi tace sannu da dawowa, HAFSAT tace yawwa sannu sanna itama ta shige d'aki. Suhail yace muyi alwala ko semu wuce masallaci, kamal yace to Kaje ina zuwa sannan suhail ya wuce ya barsu a tsaya, sabreen ta juya zata koma d'aki se kamal yace sabreen inasonyin magana dake, sabreen ta juyo tana kallonsa tace toh yah kamal ina sauraronka, daga Inda yake tsaye yace baridai muyi sallan magrib tukunna kinji, tace to badamuwa, murmushi yayi mata sannan ya wuce d'akin suhail ita kuwa tanata binshi da kallo harya shige sannan tayi ajiyar zuciya ta wuce d'akinta. Bayan sun dawo daga masallacine suhail yace toni bari in ciga ciki seka shigo, OK kamal yace dashi sannan ya kira sabreen a waya yace mata yana tsakar gida acikin mota, tace to ina zuwa shi kuwa ya shige mota ya zauna yana jiran fitowarta. Saida ta sake fesa turare sannan ta fito bakowa a Palo ta wuce gun Motansa ta bud'e gaba tare da sallama bayan ya amsa sallamarne seta shiga ta zauna tare da rufe kofan tace gani yah kamal kanta na kallon gate d'in gidansu shi kuwa yana kallonta yayinda take ganinsa da gefen idonta.😜 Sad-Nas 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 41-42 Kamal yana komawa gida ya watsa ruwa a jikinsa sannan yayi shirin bacci, wayarsa ya d'auka ya kira mummynsa ya gaya mata komai akan sabreen. Farin ciki sosai tayi mishi tare da addu'oi tace kaga se'a had'a aurenku dana suhail, kamal yace insha Allah mummy sannan sukayi sallama seya kira sabreen. Ringing d'aya ta d'auka hello, murmushi yayi yace hello sabreen kardai har kinyi bacci, a'a idona biyu ka tafine? Eh natafi kodai kinaso in dawone, a'a kawai dai na tambayane😊, yace bakinki fitowa muyi sallama ba, bahaka bane yah kamal kawai dai... se kuma tayi shuru, yace kawai dai me, tace bakomai ka isa gida lfy, lfya lau mummyna tace ingaisheki sosai, murmushi tayi tace nagode ka gaisheta, zataji me kikeyi yanzu? Bakomai ina kwamcene, har zakiyi bacci kenan, eh tace dashi, yace ok to shikenan bari in barki ki huta kinji, to nagode seda safe, ehen "I luv you so much sabreen" kunya taji sosai bata ce komaiba, yace sabreen, tace na'am a hankali, ya sake cewa "i luv u" itama tace "i luv u too" cikin wata irin murya wanda yaji dad'insa, murmushi yayi yace "ok good night" tace ok sannan tayi saurin katse wayar tare da sauke ajiyar zuciya tana murmushi. Mikewa tayi ta fito palo da niyan d'iban abinci dama bata ciba, anan taga su mum sunata hira inda yah suhail yake cewa hafsat yakamata ki dinga zuwa kichine kina ganin yadda sabreen take girki dan kinsan bazata dauwama agidannanba dole wataran zatayi aure, mum tace ai nima yanzu na samu sauki dan haka zan dingayi. Sabreen tace dasu sannunku hajiya, mum tace yawwa sabreen se yanzu zakici abincin? 😊eh hajiya, sannan ta wuce inda ya suhail ya mike yayi gun daining d'in dan d'auko wayansa. Bayan ta gama d'iban abincinne ta juya zata koma se kafanta ya zame a tiles din saura kadan ta fad'i suhail ya tallafota da hannunsa biyu inda ta rike plate d'in da kyau suna kallon idon junansu🙄, sabreen taga kamar suhail yaso ya gane idanunta, da sauri ta mike tate da janye jikinta ta sunkuyar da kai tace nagode sannan ta wuce d'aki yanata binta da kallo🤔. Sabreen tana shigewa d'aki ta sauke wani ajiyar zuciya tare dayin murmushi tana jin dad'i a ranata😇 ta d'ayan b'angaren kuma kallon da suhail yake mata alokacin daya tallafota kamar kallon sani yake mata, tace to yanzu idan yah suhail ya gane idanuna fa, gaskya nayi kuskure bazan sake yarda mu had'a idoba. Shi kuwa suhail bayan ya d'auki wayansa ne seya fita waje zuciyarsa cike da waswasi akan sabreen, dan gaskya idanunta sunyi mishi kama dana wannan yarinyar🤔, kaka ya hango a tsakar gida suna hira da maigadi, ya karasa gunsu yace kaka nazo gurinkane. Kaka ya mik'e tare da cewa to muje daga can koh, gefe suka koma tagun ajiye motoci suka zauna a fararen kujeran roba, suhail yace kaka inaso in maka tambaya akan sabreen ne, kaka yace ina jinka. Suhail yace wato kaka gaskya bazan b'oye maka aduk lokacin dana kalli sabreen se inga kamar itace wannan yarinyar da neke nema mai nik'af d'innan dan gaskya bazan tab'a mancewa da idanuntaba, kakaji yaji k'irjinsa ya buga dan SALMA ta gaya masa komai kuma ta tabbatar mishi da cewa suhail shine wannan saurayin, kaka ya dawo daga duniyar tunani yace gaskya d'annan nidai jikata bata taba sa nik'af ba kuma ba'a mata fyad'eba sannan kasan babu yadda za'ayi ace an mata fyad'e kuma tab'oye mana kai kanka kasan bazai tab'a b'oyuwaba tunda kace MAZA ne harsu UKU kuma manya. Shi kansa suhail yabinda yake basa mamaki kenan yacewa kaka kwarai kuwa hakane to k'ila kamannine kawai idanunsun yayi, kaka yace eh zaiyu amma kai meyasa ka damu hakane d'annan? Suhail yace kaka bazan b'oye makaba wlh tun a wannan lokacin yarinyar "TANA RAINA" Allah ya d'auramin SONTA kaka fatana shine in sake had'uwa da ita dan in gaya mata sak'on zuciyata. Kaka yace kana nufin zaka aureta a hakan? Kwarai kuwa kaka don haka zuciyata take gayamin, kaka yaji dad'in hakan a ransa yace lallai sabreen tayi sa'an samun suhail a rayuwa gashi zai rik'eta tsakaninsa da Allah kuma jikarsa zata huta dan haka gobe zai sanar da sabreen komai sannan kuma zaice ta gayawa suhail d'in cewa itace wannan yarinyar kuma ba'a mata fyad'eba. Suhail ne ya katseshi da cewa shikenan kaka nizan shiga ciki seda safe, tare suka mik'e sannan kaka yace toh Allah ya tashemu lfy, suhail yace ameen sannan yayiwa maigadi sallama seya shiga cikin gida. Koda ya shiga su mum sun shiga bacci, sabreen ne ta fito da plate d'in abinci kanta ko d'ankwali babu dan tasan babu kowa a palo ta nufi kichine bata lura da suhail ya shigo palon ba, shi kuwa suhail gashin kanta kawai yakebi da kallo mai tsayi sosai dan batasa ribom ba yana baje a bayanta. Kichine d'in ya bita lokacin tana wanke hanunta akan sink yaje dab da bayanta ya tsaya, bayan ta gama wanke hannuntane seta juyo dan komawa d'akinta aiseta tsorata ganin mutum a bayanta har hannayenta sun tab'a kirjinsa inda ruwan hannunta ya jik'a mishi rigansa tana kallonsa cikintsoro😳 suhail yace wlh kece kece wanan yarinyar daga razanarki na gane kece dan bazan tab'a mantawaba😇 Sad-Nas 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 43-44 Murmushi sosai suhail yakeyi yana kallon idanun sabreen, da sauri ta matsa baya tana cewa me kake cewane yah suhail wata yarinya kenan kake magana akai, cicefa sabreen ba wata yarinyaba. Suhail ya dawo haiyacinsa tare da sosa k'eyarsa yace kiyi hakuri sabreen idanunkune sukayi kama sosai da nata kiyi hakuri kinji😔, kai zanba hakuri yah suhail dana jik'a maka riga😊, karki damu ba komai seya juya zai fita se sukaga hafsat tsaye a kofar kichine d'in🙄. Suhail ya tsaya yana kallon hafsat yace hafsat me kikazo d'auka, ta d'an wayance tace nazo d'aukan ruwane se naji murya a kichine shine na shigo ashe kune, tana kaiwa nan ta juya da sauri ta koma d'akinta, suhail yasan hafsat tasa wani abu a ranta, ita kuwa sabreen jikinta a mave yake dan hafsat ta gansu da suhail a kichine gashi da daddare, da sauri tazo gun kofan inda suhail yake tsaye tace dashi barin wuce, juyowa yayi yana kallonta ita kuwa kanta a sunkuye ya matsa mata yana kare mata kallo harta wuce sannan shima ya wuce d'akinsa da damuwa sosai a ransa. Hafsat ranta se tafasa yakeyi ita dai batan me sukaceba amma to me yah suhail yakeyi a kichine gurin sabreen bayan sam shi bayama shiga kichine😠 lallai zan koyawa sabreen hankali idan dai har tayi kok'arin shigewa suhail d'ina, kai ina bazai yuba gobe zanyiwa mum magana akan aurenmu da suhail😠. Ita kuwa sabreen mamaki takeyi akan ganeta da suhail yaso yayi, lallai akwai aiki gobe zan sanar da kaka lbrn soyayyata da yah kamal gara kawai ayi aurenmu kar azo a samu matsala, sannan ita kanta taga yadda ran hafsat ya b'aci tace toko son yah suhail d'in takeyi oho, kishine ya tokarin sabreen a k'irjinta tace Allah sarki yah suhail shikenan zan rasaka, kuma na tabbatar daka fara sonane yanzu nima kuma ina sonka wlh😥. Washe gari da safe sabreen bata fitoba dan basa karyawa da wuri kuma bata sallah. Harse 8:00am tayi wanka tasa riga da siket cikin kayan da kamal ya saya mata material ne blue ya mata kyau sosai ta fesa turare sannan ta yafa gyale a kafad'arta ta fito ta wuce kichin toasted bread tayi musu wanda tasa saidin a ciki se kamshine yake tashi ta sake soya egg sannan ta tafasa ruwan tea da kayan yaji taje ta shirya komai a daining sega hasat tayi wanka tasha english wears riga da siket tayi ado tazo har daining tana k'arewa kayan jikin sabreen kallo ita kanta tasan mai t'sadane dukda tasan cewa itama kyakkyawace amma kuma tasan bazata had'a kanta da sabreenba ko kusa. Ta k'arasa tace ke sabreen me kukeyi da yah suhail jiya a kichine? Sabreen ta juyo tace ina kwana hafsat, 😏hafsat tace ba wannan na tambayekiba ai, sabreen tace bakomai hannuna naje wankewa shi kuma bansan meyaje yiba, daidai lokacin suhail ya shigo palon lokacin hafsat tana cewa to wlh ki kame kanki ina gayamiki suhail shine mijin da zan aura dan haka ki dena wannan rawan kan naki😚sannan ta juya suka had'a ido da suhail ta wuce d'aki ko gaishesa bata yiba yanata binta da kallo. Jikin sabreen yayi sanyi dan maganan ya b'ata mata rai ta kalli suhail tace ina kwana yah suhail sannan ta wuce batare data jira amsarsaba ta d'auko abincincin su kaka dana mai gadi takai musu. Shi kuwa suhail yana tsaye agun yana binta da kallo harta fita sannan yayi sallama a kofar d'akin hafsat tazo ta bud'e yana tsaye fiskarta a had'e yace yau bazaki gaisheni bane hafsat, shuru tayi nad'an lokaci sannan tace ina kwana😏, yace lfy fushi kikeyi dani kenan ko? Ta marairaice murya tace gaskya yah suhail inaga lokaci yayi daya kamata muyi aure indai har kana sona😠, suhail yace to shikenan ki denayin fushi zanyiwa mum magana kinji, 😊murmushi tayi tace to nagode muje muci abinci to, shima murmushin😊 yayi mata yace to muje sannan suka nufi daining inda mum take zaune agun tana karyawa, dad'in ganinsu tare taji sosai suka zauna suna gaisawa. Sabreen kuwa bayan ta kai musu ta zauna agun kaka tana gaya masa yadda sukayi da kamal kuma ta amince. Kaka ayi ajiyar zuciya sannan yace sabreen shikenan tunda dai kina sonshi kema, amma shi suhail ya riga fara sonki tun lokacin da kuka fara had'uwa, sabreen SALMA ta gayamin komai kuma jiya da darema suhail yazo min da zancen yarinyar akan yanaga kamar kece ni kuma Sam ban gaya masa cewa kece d'inba, dukda dai shi atunaninsa an miki fyad'ene ahakan kuma yake sonki sosai sabreen. Sabreen ta sauke ajiyar zuciya tace kaka wlh Nima ina sonshi amma kuma yah kamal fa, kuma kaka hafsat tana son suhail sosai nan taba kaka lbrn abinda ya faru tas. Kaka ya tausayawa jikarsa sosai yace to shikenan sabreen shima kamal d'in ai mutumin kirkine Allah ya zab'a miki mafi alkhairi, tace ameen kaka maganan me kukayi da salman? Kaka yace mun dad'e Muna jiran zuwan salma da iyayenta tun bayan rasuwan mahaifinki da kwana 7 suka dawo suka gayamana gaskyar yadda mahaifinki ya rasu kuma suka bamu hak'uri sannan suka tabbatar mana da cewa duk lokacin da Muke buk'atar taimako zasuzo garemu nan kaka ya gaya mata cewa wannan macijin daya sari mamminkima salman CE ta kasheshi ba jama'an gariba babu Wanda yasan hakan saboda suba mutane bane ALJANUNE😳🙄😱 Sad-Nas 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 45-46 ALJANU, Aljanufa kace kaka, kana nufin salma aljanace shine nayita hankad'ata jiya? Kaka yace kwarai kuwa shiyasa naketa dakatar dake, danma kinyi sa'a salma tana sonki a ranta ne tace ranan tazo gunki a d'akinki ganin,yadda kika tsoratane yasa ta canja salon zuwa ta yadda kowa zai ganta dan karki tsorata, amma wannan maganan ya zama tsakaninmu mu uku kinji? Sabreen ta sauke tsorataccen ajiyar zuciya tace to kaka shikenan nizanje in karya, yace toh sannan ta fito har zata shiga palo se taji hon, bayan maigadi ya bud'ene se taga motar kamal ne yake shigowa, hon yayi mata tare da kunnan wutan motan yana hankata, murmushi tayi sannan ta k'arasa gun motan ta tsaya ta gefensa, fitowa yayi cikin farin shets da blue jeens yayi kyau sosai ga kamshi da yake tashi, "good morning my luv" yace da ita yana murmushi😊, kunya taji sosai ta kauda kanta gefe tace morng ya kake😊, lfyta lau kin fito gurin kakane? Eh nakai mishi abincine, ok to muje ciki kafin ya gama cin abincin se indawo gunsa. Ayate suke tfy yana kallonta tare da cewa gaskya wannan wankan yayi kuma na yaba😘, dariya tayi dai dai lokacin sun shiga palo tare da sallama, wani irin abu ne ya tokari suhail a k'irkinsa ayayinda ya hangosu suna tahowa, sabteen ta karasa ta gaida hajiya sannan ta wuce ciki sunaya binta da kallo dukkansu😍. Bayan kamal ya zauna ne suka gaisa sannan hafsat ma ta gaishesa tare da had'a mashi tea, suna sha suna hira. Anan ne kamal yake sanar da mum k'udirinsa akan sabreen, mum taji dad'i sosai kuma tayi farin ciki tace to ai gara dai kam kuyi aure zaifi, kaima suhail yanzu kam lokaci yayi da za'ayi aurenku da hafsat kamar yadda iyayenku sukeso. Wani irin dad'i hafsat taji a ranta tace kamar kina raina mum😊, suhail ya kalli hafsat yace mum tunda tana karatu a dai bari seta gama tundama saura 1year ne ta gama. Mum tace to shikenan Allah ya nuna mana, yace ameen, kamal yace to gaskya nidai zan rigaka dan banaso in wuce nan da 6 month, suhail yayi murmushi yace to Allah ya sanya alkhairi, sukace ameen. Ita kuwa sabreen tunda ta shiga d'aki taketa tunanin maganan da sukayi da kaka, nan ta kira munira ta gaya mata komai a waya. Munira tayi mamaki sosai tace yanzu bakya tsoro sabreen gaskya ina son ganinta, kuma inaso ta zama kawata wlh😀, sabreen tace lallai kam to idan ta sake dawowa zan had'aku. Munira tace to yanzu shikenan kin hakura da suhail d'in? Sabreen tace eh nahakura munna kawai zan auri yah kamal tunda ma kinga ga abinda hafsat tace min, munnira tace to shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi agareki k'awata, sabreen tace ameen ina abbakar sadiq d'inki? Munna tace yanan shimafa ya dage wai miyi aire se inci gaba da karatuna, sabreen tace eh tundai zai barki ai shikenan nima hakan zanyi, munna tace eyye ashe fa kina son kamal d'innan😜, sabreen tayi dariya tace bakida kyau fa munna nikam se anjuma ki gaida su mama😀, munna tace to nagode zasuji ki gaidamin "ango to bee" hmm zaiji sannan ta katse wayar tana dariya😃. Bayan su mum sun gama cin abincine kamal da suhail sukaje gun kaka kamal ya gaya masa buk'atarsa akan sabreen, kaka yaji dad'i sosai kuma ya tabbatarwa kamal cewa yabashi tunda dai sabreen d'in ta amince, murna sosai kamal yayi sannan sukayiwa kaka godiya suka tafi. Suhail da kamal ne suke tfya a cikin motansu suna hira, suhail yace abokina ka kusa ka zama angon sabreen, kamal yace bawannanba tukunna, kasanfa matsalata suhail yanzu in gayawa sabreen ne ko dai inyi shuru? Suhail yace ina kace nanda 6month kake son auren, kaga daidai kenan kafin lokacin auren komai zai daidaita kamar yadda doctors sukace insha Allah. Daganan kuma shikenan seka jah kaya abokina gaskya zaka morefa da wannan sabreen d'in naka😋😃, 👊🏽duka kamal yakai masa yana dariya tare da cewa kaima ai k'i kayi damunyi tare. Suhail yace abokina kafi kowa sanin cewa ban tab'a "SON" hafsat a matsayin matar aurenaba sedai "SO" amatsayin 'yar'uwata na jini, nidai wannan yarinyar "TANA RAINA" itace nake "SO" a matsayin matar aurena dan haka sedai in auri mata biyu a rana d'aya wannan shine burina, da zab'in mahaifina da kuma zab'i nah. Kamal yace "ar u serious?" Suhail yace wlh abokina shiyasa nake so ka tayani da addu'a Allah ya sake had'ani da "TANA RAINA" kamal yace tofa harka lak'ana mata suna kenan toh ai semu sake komawa k'auyen gobe ko Allah zaisa mu dace, suhail yace hakan za'ayi kuwa, kamal yana kallon abokinsa kallon mamaki da irin son da yakewa wanda akaiwa fyad'e, yace sekayi angon "TANA RAINA" dariya suhail yayi😃 yace eyyy angon sabreen sannan suka tafa✋🏻suna dariya nima "SAD-NAS" na tayasu😆😆😆 [10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 47-48 Washe gari bayan su suhail sunyi breakfast ne sukayiwa mum sallama akan zasu fita, mum ta musu fatan alkhairi sannan suka wuce tsakar gida gun kaka inda yakeba flawer ruwa, kamal ya kira sabrenn a waya dan yau tunda yazo baigantaba, sunata hira da kaka sega sabreen ta fito da himar har k'asa tana tafiya a hankali, juyowa sukayi suna binta da kallo, tunda kaka ya hangota yasan cewa tayi kuka. Ta k'araso tare da gaishesu kanta na gefe, daga kamal har suhail sunsan akwai wani abu a k'asa dan sam babu ko fara'a a fiskarta. Kaka yace sabreen lfy kuwa yana ganki haka? Hawaye suka zubo a fiskanta ta share da hannunta tace bakomai kaka, kaka yace bakomai kike kuka kuma gashi sam babu fara'a a fiskarki meya samekine? Kakana karka damu bakomai kawai dai mun d'an samu matsala ne da hafsat😥 kaka kasan cewa ina da hakui akan komai, amma kalamanta sunmin zafi sosai wanda idan na tuna tuna suna min zafi sosai, ta goge hawayenta ta juyo tana kallon kamal tare da cewa yah kamal dan Allah ka janye soyayyata kaje ka nemo daidai da kai, ni talakace 'yar kauye sannan jahila k'azama wanda take bin duk wata hanya koda ya sab'awa Allah ne taya yinshi dan ta janyo hankali yayyuna biyu da suke cikin gidan, akan suhail dai asirinki baiyi aikiba, shima bro kamal d'in ahankali asirin zai karye daga nan kuma ta k'are miki 'yar gidan matsiyata wanda bata da gatan uwa bare na uba😭. Kallon kamal da suhail takeyi har cikin ido tana kuka tare da cewa wannan sune kalmomin da hafsat ta gayaminsu saboda nazo yin aiki a gidansu, kaka yau da asuba danazo gaisheka ban gaya maka bane saboda nasan hakuri zaka bani, amma su yayyuntane na gaya musune saboda su zama shaida dan gaskya hafsat bazata sake gayamin hakan ban mayar mata da martani, gudun faruwan hakanne yasa nakeso mubar gidan kawai nida kakana masu girki suna nan dewa a gari na gwammace inci gama da zamana a k'auyenmu. Tana kaiwa nan ta juya da saurinta ta koma ciki tanata kuka. Gaba d'ayansu abin ya musu zafi, kaka yace karku damu da zaran ta huce shikenan😒. Ran kamal inyayi dubu ya b'aci, yace dama haka hafsat take🤔, suhail kuwa cikin gidan ya koma yana kwalawa hafsat kira, da sauri ta fito don jin muryarsa da karfi. Ta k'araso tare da cewa na'am bro suhail gani, ransa a b'ace yace meya had'aku da sabreen? Atake ta b'ata rai tace bakomai, suhail yace kamar ya bakomai, kimin bayani meya had'aku da ita? Hafsat ta b'ata rai tace bro yanzu saboda sabreen d'inne kake min ihu haka har kana b'ata rai, nifa kanwarkace kuma wanda zaka aura, hafsat ba wannan na tambayekiba dan ke k'anwatace seki aikata laifi? Tace laifin me kuma na aikata bro wato takai k'arata gunka kenan😣 harta samu fiskan kai kara agunka tabd'i to shisshigemin takeyi ni kuma bana son hakan shine nace mata ta fita harkata danni ba sa'arta bace😏. Suhail yace hafsat yaushe kika zama haka, wlh kinban kunya ban tab'a tunanin haka daga garekiba a irin tarbiyan da kika taso. Yah suhail waime ta gaya makane dahar ka yadda dashi haka kaketa min fad'a? Suhail yace abunda kika mata shita gayamana dan haka wannan ya zama na farko kuma na karshe kar in sakejin kin mata haka kina jina? Rai a b'ace tace naji sannan ta wuce d'aki kamar zata fashe😡. Mum ce ta fito tana cewa suhail meke faruwane kaida hafsat naji kamar fad'a kake mata? Suhail yace bakomai mum ki barni da ita kawai laifi tayi, laifi kuma, hafsat d'in laifin me tayi toh? Suhail yace sund'an sami rashi jituwane ita da sabreen kuma ita hafsat d'ince da laifi. Toh yau kuma hafsat da fad'a bari inje inji toh, se mum tabi hafsat d'aki shi kuwa suhail ya shiga d'akin sabreen tare dayin sallama. Tana zaune akan gadonta tana share hawaye da hannunta, mik'ewa tayi tare da amsa sallamar cikin muryan kuka kanta a sunkuye, hanki ya ciro a aljihunsa ya mik'a mata, wani iri taji sannan tasa hannunta ta karb'a tace nagode. Yana tsaye daga kofa yace sabreen dan Allah kiyi hakuri kinji, na mata magana hakan bazai sake faruwa kinji? Wani sanyi taji a ranta ta d'aga kai alamun toh, murmushi yayi yace toki dena kukan pls😊, kawai setaji tana son kallon fiskarsa seta d'ago da kanta tana kallonshi tace "thankyou"☺. Muryar nata yayi mishi kama dana wannan yarinyar wlh suna kallon juna har cikin ido setayi saurin sunkuyar da kanta k'asa saboda wani irin kaunarsa da yake ratsa jikinta, shidai baisan me zaiceba seya bud'e kofan ta d'ago da kanta sunata kallon juna harya fita. Sabreen ta sauke ajiyar zuciya tanaji dad'i acikin ranta😇 wani gefen kuwa cewa takeyi kawai zancewa yah kamal yafito muyi aure dan gaskya bazan iya jurewa soyayyar suhail ba matukar ina sashi a idanuna gaskya. Afili kuma tace suhail kai nakeso tun ranar daka zubar da jininka akaina nice fa sabreen nice yarinyar da kake nema😒 "I LOVE YOU SO MUCH SUHAIL😰". Suhail da yake tsaye a bakin kofa kuma dai yasan ba karya kunnensa yayi mishiba tabbas yaji abinda sabreen tace😳🤔😳... Sad-Nas [10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 49-50 farin cikine ko bak'in ciki suhail yakamata yayi oho, shikansa ya kasa ganewa, yana cikin jimamin abunne yaji tfyar mum zata fito daga d'akin hafsat, da sauri ya fita ya wuce gunsu kamal da kaka inda suke tsaye suna magana. Suhail ya k'araso yace kaka dan Allah kayi hakuri da abinda hafsat tayiwa sabreen yani mata magana hakan bazai sake faruwaba insha Allah, kaka yace haba suhail aida ka rabu dasu, nasan sabreen zata huce sarai. Daganan sukayi mishi sallama sannan suka tafi k'auyen su sabreen, tunda suke tfy suhail hankalinsa sam yana gun sabreen barema dayaji tace shi takeso. Kamal yace abokina yanaji kayi shurune? Suhail ya dawo daga duniyar tunani yace fad'an danayiwa hafsat ne yad'an dameni kasancewar ban tab'a mata fad'anba. Kamal yace barina kirata to, take ya kira hafsat kamar bazata d'aukaba se kuma ta d'auka tace hello, kamal yasa a hands free yace k'anwata kiyi hakuri da abinda yafaru dan Allah gashi tun d'azu suhail se tunanin fad'an daya miki yaketayi abin ya damesa. Wani sanyi hafsat taji a ranta kancewa suhail ya damu da fushin datayi😊 tace ina yah suhail d'in, kamal ya kalli suhail sannan suhail yace hello, dad'i taji tace hello yah suhail, yace na'am kiyi hakuri da abinda ya faru kawai banyi tsanmanin haka daga garekibane sannan kuma dan sabreen tana aiki a gidanmu bai dace mu tozartaba ina fata zaki fahimce, eh naji yah suhail nasan nayi kuskure amma kayi hakuri kuma zanje inbawa sabreen hakuri yanzu, dad'i yaji har cikin ransa sannan yace mata yawwa "my wife to be shiyasa nake k'ara sonki", karon farko kenan da hafsat daji kalma mai dad'i daga bakin suhail masoyinta, tace shikenan sekun dawo😊, yace yawwa byee sannan ya katse wayan. Kamal yace tofa soyayyarce ta tashi kenan😜? Suhail yayi murmushi yace eh d'ansa ido😃. Shi kansa kamal yasan kawai suhail ya furta hakanne dan hankalin hafsat ya kwanta amma bawai dan yana sontaba. Haka sukaita hira, amma shi suhail tunanin sabreen ne a ranshi yayinda wani sonta yake k'aruwa a ransa. Sun isa kauyen sun dad'e sosai sunata nema amma shuru, musamman ma kamal duk wanda yagani zaiyita masa kwatance amma se ace musu ba'a santaba, shi kuwa suhail yacewa kamal kawai kazomu tafi tunda bamu sametaba na hakura zan auri hafsat d'in kawai. Haka suka kama hanya suka dawo lokacin 2:40pm, sabreen ta fito kaiwa su kaka abinci kenan segasu kamal sun shigo. Kallonta sukeyi dukkansu biyu harta shige ta ajiye sannan ta fito daidai lokacin sun fito daga motan tace dasu sannunku da dawowa, suhail yace yawwa sabreen sannu sannan ya wuce gaba ita kuma suna biye dashi ita da kamal. My luv yakike ya gajiyan aiki, 😊bawani gajiya aina saba, kin tabbata? Eh sannan tace yah idan kaci abinci inason yin magana dakai, yace ok hope dai lfy koh? Tayi murmushi tace lfy lau, yace to idan na gama zan kiraki a waya kinji, tace toh sannan ta wuce d'akinta. Bayan ta kwantane munira ta kirata tana gaya mata cewa aisu suhail sunje k'auyensu yanzuma dagacan suka dawo sunje neman yarinya mai nik'af, sabreen tace toke waya gaya miki? Munna tace mutanen da suketa tambayane suka gayamin waiko nice, shine na tambayesu ina mutanen, se suka nunaminsu kawai senaga kamal ne da suhail ammasu basu ganniba. Sabreen tace nagode munna zansan yadda zanyi zan kiraki anjuma Sannan sukayi sallama sabreen tana ta mamakin abin aranta. Bayan su suhail sun gama cin abincine se suka wuce d'akin suhail suna hutawa, shi kuwa suhail kwanciya yayi tare da rufe ido kamar maiyin bacci. Kamal ya kira sabreen kuma yasa a handfree suhail yanajin komai, sabreen tace hello yah kamal, yace banace miki banason sunan nanbako, tayi murmushi tace to kayi hakuri ina kaje haka bakamin sallamaba? Am sorry luv naso inyi miki sallamanne se kuma kika tafi cikin fushi, 😊 to ina kaje inadai bagun wata kajeba ko? Kina kishinane luv, sosaima dan gaskya ina da kishi😏, dariya kamal yayi yace to shikenan karki damu ke kad'ai kin isheni my luv na raka suhail, ananne suhail ya bud'e kunnensa da kyau donjin me sabreen zatace, ina ka rakashi, hira na rakashi luv kuma bamu sametaba, shuru sabreen tayi se kuma tace ok mummy ta kirani d'azu gaskya naji kunya sosai wlh, kamal yayi dariya yace kunyanme kuma keda zan kaiki gunta, hahah to shikenan Allah ya nunamana ameen luv gaskya inaso ayi bikin da wuri wlh, sabreen tace nima haka, dad'i kamal yaji yace da gaske kikeyi luv? Tace wlh kuwa, yace ok dama nace nanda 6month ne amma zanje in samu kaka ince mishi nanda 3month nakeso hakan ya miki? Eh yamin😊, ok zanyiwa mijin mummyna magana danshine zai karb'a min auren, ok badamuwa ina yah suhail? Gashinan a gefena inaga kamarma yayi bacci, ok shikenan zanje in d'aura abinci bye, "ok my luv bye i love u", murmushi sabreen tayi tace "me too" sannan ta katse wayar. Kamal ya daki suhail yace tashi abokina angon "TANA RAINA" nanda 3month zan zama angon sabreen😃, suhail daya gama jin duk hiransu ya tashi yana cewa baka da kirkifa shine zaka tasheni ina cikin bacci😜, sorry angon "TANA RAINA" farincikine yamin yawa wlh😇. Bayan sunci abincin darene sund'an tab'a hira kad'an se kamal yasamu kaka da maganar aurensu da sabreen, kaka yace bakomai zaije kauye danya sanar da aminan mahaifinta, kamal yaji dad'i sosai sannan ya tafi da farin ciki a ransa. Suhail kuwa bayan mum ta shiga baccine ta barsu a palo shida hafsat suna hira sannan yayi mata seda safe ya tafi d'akinsa itama tayi nata d'akin tanata farin ciki😀 9:30pm suhail ya fito da jallabiya ajikinsa yaje kofan d'akin sabreen yana nocking, sabreen ta d'auka hafsat ce dan haka batasa ko himarba daga ita se kayan bacci, dogon wandone har k'asa se rigansa iya cinyanta mai guntu hannu kanta ba komai tayi parking seta zo ta bud'e kofan🙄 yah suhail ne a tsaye yana kallonta tun daga k'asa har sama gashi batasa bra ba "BUBS" d'inta suna tsats tsaye👀 Sad-Nas [10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 51-52 Yah suhail yacibaga da kallon sabreen ko kyafta ido bayayi, sabreen ta lura da irin kallon da yake mata tace dashi ina zuwa, sannan ta koma ciki ta d'auki himar d'inta tasa seta fito. Palo ya koma yana jiran fitowanta, bayan ta fitone lokacin yanata zagaye palon se tace yah suhai gani. Juyowa yayi yana kara kallonta sannan yace sabreen d'azu da safe bayan nabar d'akinki naji abinda kike cewa dagaske abinda naji? Bugawa k'irjinta yayi tace me kenan yah suhail? Ya matso kusa da ita yace naji kina cewa kece yarinyar da nake nema, 🙄a'a ba haka naceba wata yarinya kuma ya suhail ni sunana sabreen, hannunta ya rik'o dukka biyu take jikinta ya fara b'ari yace sabreen "pls tell me the truth" danna dad'e ina nemanta kuma dama zuciyata tanata waswasi akanki duk lokacin dana had'a ido dake sabreen, sannan wasu lokacin ina tuna muryanki dan Allah ki gayamin gaskya sabreen. Hawayene ya fara zuba daga idon sabreen tana kallon idonsa tace NICE yah suhail😪, sake hannunta yayi tare da juya mata baya yace "Ohh My Gosh" sabreen meyasa, ya juyo yana kallon idanunta cike da tashin hankali yake magana meyasa kikamin haka sabreen "why" meyasa baki gayaminba tuntini, yanzu gashi aminina ya wucemin gaba why sabreen kamar zaiyi kuka. Sabreen tace kayi hakuri yah suhail😓, hakurifa kikace sabreen taya zanyi hakuri bayan kinsani a cikin tashin hankali, sabreen kinsan yadda nake k'aunarki a raina kuwa, kanta ta d'ago tana kallonshi ji take kamar ta rungumesa dan yadda taga hankalinsa ya tashi, sake matsowa yayi yana kallonta cike da tausayi yace sabreen baki kyauta minba yanzu shikenan ya kikeso nayi da k'aunarki sabreen😔? Sabreen ta juya tana kallon bayanta dan bataso hafsat ta fito ta samesu, tace yah suhai kar hafsat ta fito ta ganmu barina d'auko wayana kasamin number'nka semu k'arasa a waya pls, kansa ya kawar gefen cike da damuwa, ita kuwa d'aki ta koma ta d'auko wayanta tazo ta mik'a mishi, ya karb'a yasa mata sannan ya mik'a mata tare da rik'o hannayenta yace kafin ki tafi inason jin kalma mai dad'i daga bakinki sabreen😒, kallon juna sukeyi tana hawaye tace "I LOVE YOU😢", wani dad'i yaji a ransa baisan lokacin daya janyotaba ya rungumeta a k'irjinsa yana jin k'aunarta na ratsa jinin jikinsa, kok'arin janye jikinta takeyi amma sam ta kasa dan yadda ya k'ank'ameta yana cewa "pls let me be sabreen" na wannan lokacin kawai sansan ya tsubaci bayan wuyan yana cewa "I LOVE YOU MORE SABREEN"😔. Kusan 3minit sannan ya saketa dan kar mum ko hafsat su fito, kanta a sunkuye dan kunya dataji, ya shafi kumatunta yace kimin flashin yanzu kinji? Kai ta d'aga batare datayi maganaba, murmushi yamata sannan ta juya da sauri ta shige d'aki sannan shima ya fafi. Koda ta shiga d'aki setaji sabon kaunarsa yana ratsa jikinta😪, himar d'in ta cire ta kashe wutan d'akin ta kwanta sannan ta kirashi harya fara ringing setaji ya katse ya sake kiranta. Hello sabreen, na'am, yanzu kaka yasan maganan? A'a kaka baisan komaiba yah suhail babu wanda na gayawa se k'awata munira, suhail yace tomesa baki fad'aba? Sabreen tace yah suhail nifa mutanennan basumin komaiba, suhail yace kamar ya basumiki komaiba sabreen? Sabreen ta sauke ajiyar zuciya sannan tabawa suhail lbrn abinda yafaru acikin yanayi najin kunya. Mamakine sosai a fiskan suhail yace to ita wannan d'in wacece? Sabreen tayi karya tace nima ban santaba wlh, kan suhail ya d'aure kuma ya kasa yadda da abinda sabreen ta gayamasa. Itama sabreen tagane cewa bai gamsu da maganantaba, tace yah suhail nasan bazaka yadda amma wlh gaskya na gayamaka basumin komaiba. Suhail yace sabreen kina nufin har yanzu ke cikakkiyar budurwace? Sabreen taji nauyin maganan nasa sosai amma seta daure tace "EH" hakane yah suhail. Idanunsa ya rufe yanata juyi akan gadonsa had'e da takaicin yanzu shikenan ya rasa sabreen, taji yayi shuru baice komaibane se tace yah suhail ya naji kayi shuru? Yace bakomai sabreen ina cikin damuwane kawai bansan ya zanyi da k'aunarki a rainabane gashi kin amincewa AMININA gaskya ina cikin damuwa sabreen. Sabreen ta tausaya musu dukkansu tace yah suhail ba kana eman hafsatba? Suhail yace sabreen hafsat had'in iyayenmune bawai don ina sonta bane kekad'ai ce a raina sabreen kinsan da wani suna kamal yake kirana? Tace a'a, yace angon "TANA RAINA" saboda na saki a raina sosai kuma da wannan sunan nake kiranki kullum. Sabreen tayi murmushi tace eyyah nima "KANA RAINA" tun bayan had'uwanmu yah suhail munira ma shaidace akan hakan, dad'i sosai yaji yace to yanzu me abunyi sabreen? Tace gaskya babu wani abunyi yah suhail bazan iya juyawa yah kamal bayaba tunda harna amince mashi, suhail kamar zaiyi kuka yace kina nufin ni in hakura kenan sabreen? Cikin muryan kuka tace "EH" hakan nake nufi ka auri er'uwarka suhail ka manta dani😓, yace bazan iyaba sabreen bazan iyaba😔. Zaka iya yah suhail seda safe😰, yace sabreen dan Allah karki kashe wayan, amma ina ta kashe tareda swiching nashi off😔😔. Sad-Nas [10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 53-54 Suhail ya sake kiran wayanta amma se yaji a kashe😓, kwallane yaji yazo masa ido. Ya goge kwallan yanata tunani me mafita yanzu, amma sam shi kansan yasan babu wata mafita dan kuwa bazai iya cin Amanan kamal ba. Itama sabreen kodata kashe wayar kuka sosai takeyi dan tasan suhail yana cikin wani hali, kuma itama haka dan sam bata son yah kamal, koda tana sonshi kuwa to dai suhail shine a ranta. Seda tayi kuka sosai sannan, bacci barawo ya kwashesu dukkansu biyu. Washe gari da asuba bayan su kaka sun dawo daga masallacine suhail ya sami kaka har d'akinsa ya gaya masa duk yadda sukayi da sabreen, kaka ya nuna mamakinsa a fili yace to gaskya dai na yadda da maganan sabreen dan babu yadda za'ayi maza har uku su mata fyad'de kuma ta dawo gida lafyanta lau, suhail yace hakane kaka ni yanzu mafita nake nema kasan yadda nake kaunar sabreen tun kafin insan cewa itace, dan Allah kaka ka taimakamin😔, kaka ya tausayawa suhail sosai yace shule babu abinda,zamu iyayi akai sedai hakuri kuma kaci gaba da addu'a, dan nariga dana baiwa kamal sabreen kuma nasan kaima bazakaso ayiwa kamal haka ba. Suhail yaji wani iri a ransa amma seya daure yace hakane kaka kamal amininane harma mun zama kaman jininmu d'ayane na hakura nayita addu'a Allah yasa hakan shine mafi alkhairi agareni. Kaka yace ameen sannan sukaiyi sallama suhail ya wuce gun mum d'insa a d'aki tana karatun Qur'ani maigirma. Bayan ta idarne suka gaisa tace yana ganka haka. Kamar bakajin dad'i? Suhail yace wlh mum ina da yar damunane amma dai insha Allah komai zai daidaita kisani a addu'a, mum tace toh agun aikine kodai, suhail yace eh kidai sani a addu'a kawai. To shikenan Allah ya yaye maka insha Allah zansaka dukda dai dama inani, to mum nagode zanje ind'an kwanta, to shikenan tanata bin d'an nata da kallo harya fita. D'akinsa ya wuce ua cire jallabiyansa ya kwanta tare da d'aukan wayansa ya kirana number'n sabreen, wani dad'i yaji lokacin dayaji wayar tana ringing, da sauri ta d'auka yace hello cikinc sassanyar murya, shima dad'a kasa da miryan nashi yayi yace hello sabreen kin tashi lfy? Lfy lau ya suhail ya kake, sabreen bana lfy ina cikin damuwa sosai wlh😔, tausayinshi ya kamata tace nima haka yah suhail wani sabon k'aunar kane yake shiga zuciyata tun daga jiyan😪, da gaske kikeyi sabreen? Da gaske nakeyi yah suhail "I LOVE YOU SO MUCH"😔, dad'i sosai yaji mara misaltuwa yace " i love you more sabreen and i will always love you till end", murmishi tayi tace pls amma karka sake kirana dan kar wataran yah kamal ya gani ko hafsat, suhail yace insha Allah sabreen zanyi kokari inga cewa na dena kiranki amma hakan bashine zai hanani dena sonkiba, nima haka yah suhail pls ka goge number a wayarka, ok sabreen I LOVE YOU byee, tace ok byeee sannan ta kashe wayar tare dayin deleting number'nshi tana mai tausayinshi. 9:30 suhai ya farka yaje yai wanka ya shirya ya fito palo mum da hafsat suna daining suna karyawa, zama yayi hafsat ta gaishesa tasha adon safe, ya amsa yana d'an mata murmushi😊 yace kinyi kyau, dad'i taji tare da jin kunyar mum😉. Suhail yace ya banga kamal yazoba har yanzu ko lfy bari dai nakirashi, bayan ya kira sun gaisane yake tambayarsa ko lfy, kamal yace wlh maigadine bayi da lfy da ciwon ciki ya tashi yau yanzu muka dawo daga asibiti bazan samu zuwaba seda rana, suhail yace subhanallah to Allah ya sauwaka nima ina zuwa yanzu ka gaisheshi, ok zaiji sekazo. Mum tace meya faru ne? Suhail ya gaya mata, tace toh Allah ya bashi lfy sukace ameen. Da wuri sabreen tayi abincin rana kamar yadda mum tace mata ta zubawa su kamal a kula suhail yakai musu. Sun dad'e sosai sunata ta hira har 4:00pm kafin nan suhail ya koma gida, kamal kuwa suna manne a waya da sabreen yace mata zaizo bayan isha. Haka dai rayuwarsu taci gaba da kasancewa, kaka yaje kauye ya gayawa aminan mahaifin sabreen zancenta da kamal, sunji dad'i sosai kuma sunyi farin ciki musammanma mahaifin munira yace dama munirama an aiko kuma wai suna son auren nanda wata biyu, shine aka yanke shawaran to abari a had'asu kawai nanda wata ukun. Kamar yadda kuka sani dai auhail da sabreen suna cikin damuwa duk sun fita hayyacinsu musamman ma suhail abun har damun mum yakeyi. Ana cikin hakanne akayiwa su suhail waya daga pakistan cewa ana da buk'atar mutum d'aya yaje a tsakaninsu, kamal yace zaije tunda dama shine da zuwa, amma sam suhail yak'i yace shi zaije kaika zauna kacigaba da shirye2 aurenka idan na dawo sekaje koda sati d'ayane sekaje kayi ka dawo. Haka kuwa akayi suhail ya shirya ya tafi pakistan, dan a tunaninsa idan baya ganin sabreen abin zai d'an ragu masa, amma inah seya gwammace dama baizoba gara yadinga ganinta koda bazaice mata komaiba. Duk iya k'ok'arin da suhail zaiyi domin ya cire sabreen a ransa yayi amma abin se gaba2 yakeyi domin kuwa "TANA RANSA"💘. Kamal kuwa se murna yakeyi ya kusa ya zama ango kullum yana tare da sabreen😎. Sad-Nas [10/22, 7:27 PM] ‪+234 803 863 6764‬: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 55-56 Sabreen tana kwance suna waya da munirane taketa ganin call d'in yah kamal yana shigowa, seda sukayi sallama sannan ta kira kamal harya tsinke bai d'aukaba. Kiransa ya sake shigowa ta d'auka tace hello, kamal yace dawa kike waya haka luv? Sabreen tace da munnira ne, yace ok ya take, sabreen tace lfyanta kalau. Kamal yace luv kamar yadda na gaya miki cewa akwai wani magana da nakeso muyi dake mai muhummanci sosai kina jina? Sabreen tace eh ina ji, kamal yace luv amatsayinki na wanda zan aura yana da kyau kisan komai tun kafin muyi aure, sabreen banaso kiji kunyata ki saurareni da kyau. Kamal ya fara da cewa sabreen na kasance ina da matsala a matsayina NAMIJI, tun lokacin da iyayenmu suke raye muke zuwa can pakistan ake dubani, likitoci sun tabbatar da cewa nan da wasu shekaru zan samu lfy yayin da nake shan magunguna, to yanzu dai acikin lokacin da suke gayamin saura 5month kenan, danaso se bayan lokacin da suka d'aukamin kafin inyi aure, toh amma se gashi yanzu aurenmu saura 2month shiyasa naga yadace in gaya miki a matsayinki na wanda zan aura. Shuru sabreen tayi gabad'aya kunya ya kamata🙉, kamal yaci gaba da cewa sabreen banaso in cutar dake shiyasa na gayamiki tun yanzu, zaki iya hakuri dani har tsawon 3month da aurenmu batare da....katseshi tayi da cewa "EH" zan iya yah kamal bakomai, dad'i yaji sosai yace nagode sabreen "i luv u", murmushi tayi tace nizanyi bacci seda safe😊, yace "ok luv gud night". Ajiyar zuciya sabreen ta sauk'e tare dayin murmushi da haka tayi bacci. Washe gari da safe bayan ta gama breakfast taje gun kaka suna hira se kaka yake cewa sabreen naso inje k'auyen mu a sayar da gidanki na gado domin a had'a miki kayan d'aki amma se kamal yacemin baya bukatan komai daga garemu dukya d'auke mana abun har kunya yake bani wlh, sabreen tace shikenan kaka kayi yadda kaga ya dace dai. Kaka ya kalli sabreen yace har yanzu kina son suhail ko? Sabreen tace har abada suhail "YANA RAINA" kaka katayani da addu'a Allah ya ciremin shi a raina😒, kaka yana tausayawa jikansa yace sabreen....salam sukaji ance daga waje, wslm suka amsa sannan sabreen ta mik'e ta fito dan ganin mai sallaman🤔 SALMA ce a tsaye tanayiwa sabreen murmushi😊, kaka yace yaya dai sabreen wayene, sabreen tayi shuru tana kallon salma😉 sega kaka ya fito😀a'a salma kece sannu da zuwa, salma ta gaisheshi cikin girmamawa sannan sabreen tace muje cikin gida. Suna tfya kaka yana binsu da kallo yanajin mamakin irin damuwa da salma tayi da sabreen yana cewa dama akwai soyayyane tsakanin mutum da aljan🤔? Bayan salma ta gaishe da mum ne se suka wuce d'aki, salam tace amaryan kamal kenan😊, sabreen dai tsoro takeji a ranta wai ita da aljanace haka kuma batayi mamakin jin haka daga bakin salmaba, tace hmm ya kike yasu mamanki? Salma tace lfyansu lau sunce ingaisheki, sabreen tayi murmushi tace ina amsawa, salma tace nasan kina jin tsoro ko, karki damu sabreen bazan tab'a cutar dakeba ki d'aukeni kamar kawarki munira😊, sabreen tayi karfin hali tace toh dama tace in gaisheki sosai, salma tace ina amsawa wataran zanje mu gaisa inhar kina son hakan, sabreen tace inaso kam dan munira ta dameni da zancenki sosai😊, salma tace to shikenan idan zanje zan gayamiki seki sanar da ita😀, sabreen tace to barina kawo miki ruwa, salma tace yi zamanki bana bukata😊. Shuru sukayi na kusan 2minit se sabreen tace salma mutane ukun nan da suka miki fyad'e shin kind'au wani matakine a kansu? Salma tayi murmushi kad'an sannan tace eh suna can suna fama da jinya gabansu ga kumbura suntum tare da azaba sosai da suke fama dashi wanda koda wasa bazasuso sake yiwa wata mace fyad'eba😏. Sabreen tace to amma meyasa bakiba ta wani hanyan dabanba har kika bari suka miki fyad'en? Salma tace sabreen kaddara tariga fataa domin abinda yazomin kenan a wannan lokacin inaga ta hakanne kawai zan iya taimaka miki😊. Har sabreen ta bud'e baki zatayi magana se salma ta mik'e tsaye tare da cewa nizan wuce sena sake zuwa kuma☺, sabreen ta mik'e ta rakata har gate tare da cewa nagode😀. Haka lokaci yaci gaba da tfy bikinsu sabreen saura 2weeks 3days kaka yacewa mum zasu koma k'auyensu don shirin biki, mum tace to su bari se zuwa jibi kafinnan suhail ya dawo, kaka yace to bakomai Allah ya dawo dashi lfy, mum tace ameeen. Sad-Nas 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 59-60 Sabreen ta sunkuyar da kanta tace bari na shiga ciki, ta juya kenan se suka had'a ido da suhail da sauri ya kawar da kansa itama sabreen haka ta wuce d'akinta. Bayan sun gama cin abincine kamal yace mum jibi zan wuce pakistan insha Allah suhail zanbar komai a hannunka pls ka kula min da sabreen bare kuma zasu koma gida itada kaka so pls kayi duk wani abu dakaga ya dace, tace bazatayi program ba, amma wanda zai auri munira k'awarta ya kirani munyi magana akan za'a had'a gabad'ayane zamuyi dinner zan baka number'nshi seku had'u. Suhail yace ok badamuwa, mum tace toh shikenan seku maidasu gida gobe donyi shirye shiryensu tunda yanzu sabreen ta koyawa hafsat girki harta kware😀, hafsat tace mum nima zan bisu raka sabreen😊, kamal yace shikenan zamuje k'anwata. Shidai suhail zuciyarsa ciwo take mishi amma seya daure sunata hira cikin farin ciki. Washe gari su sabreen suka shirya tsab suka fito, alkhairi sosai mum tamusu dama kuma kamal ya bud'e mata account tun suna gidanshi aciki yake sa mata kud'in aikinta ita da kaka, dan yana musu kyaitan kud'in kashewa sosai shiyasa bata tab'a na account d'in. Can k'auye kuwa munnira tayi musu girki mai kyau kuma mai dad'i ga fura da nono ta share tsakar gidansu tas dama k'asane sosai a tsakar gidan dan haka ta shareshi tas komai dai yayi. 3:10pm su sabreen suka iso k'auyensu, da sauri munna ta fito ta rungume sabreen tana murna sosai tacewa hafsat sannu da zuwa, hafsat tace yawwa sannu, sannan ta kalli su suhail tace angwaye marabanku da zuwa, sukace yawwa amare😀, kakane yace bisimillah ku shigo, su sabreen suka wuce ciki su kaka suna biye dasu. D'akin munna suna wuce ko ina a gyare, dukda dai su talakawane amma sam hafsat bata kyamacesuba gidan nasu ya burgeta ko ina tsab, k'auyen ya bata sha'awa sosai, munna ta kawo musu abinci da fura dukkansu sukaci tare sannan sukasha fura, sabreen tace hafsat kinga gidan namu koh😉, hafsat tace wlh nikam gurin ya birgeni dasu yah suhail zasu yarda su barni in kwana se gobe in koma😊, sabreen tace ko'in tambayesu? Hafsat tace eh ki gwada😀, tafawa sukayi suna murna. Bayan su suhail sunci abincine sun koshi sosai se baban munira ya kaisu gun aminan mahaifan sabreen suka gaggaisa tare dayi musu addu'oi sosai, suhail da kamal sunyi musu alkhairai dewa sosai ga kuma kyautar kud'i, sunji dad'i sosai sannan suka kira su sabreen akan hafsat ta fito su tafi. Sabreen ne ta fito lokacin suhail ne kawai ajikin mota yana tsaye, ta karasa gunshi tace yah suhail dan Allah kabar hafsat ta kwana nan zuwa gobe seta koma, kallonta yakeyi sama da k'asa yace wazai maida ita goben? Sabreen tana kallonshi har cikin ido tace yah suhail base kazo ka d'auketaba gobe, suhail ya kauda kai gefe yace sabreen bata gayawa mum ba kuma skul fa? Sabreen tace yah suhail zamu kira mum yanzu kuma hafsat bata da class gobe pls ka barta mukwana😉, to sabreen hafsat bata rik'e kayabafa, ya suhail inada sabon d'inki nasan zai mata pls, ok shikenanto zan dawo gobe in d'auketa, 😃nagode yah suhail, shima murmushi yake mata mai cike da kauna yace sabreen me ma'anar (SABSU)? Sabreen zatayi magana kenan sega kamal da kaka🙊. adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *