Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, 15 June 2017

TANA RAINA 2

adsense here

By Mmn Shureim (Sad-Nas) 23-24 Lokaci nata fty har aunty Rukayya ta gama koyawa sabreen girki na tsawo 2month, sannan babu abinda zakace sabreen ta dafa makashi wanda bata iyaba, ta k'ware sosai itama yanzu sedai ta koyar da wasu, harta snacks da drinks na gida wabu wanda sabreen taba iyaba. Yaune kamal ya sallami aunty rukayya da kud'ad'e masu yawa wanda nima bansan adadinsu, sabreen suke tsaue da aunty rukayya suna bankwana, sabreen tace aunty rukayya ki bani number wayanki dukka dai bani da waya amma zanso kiban number'nki kakana yace jibi zai sayo min waya, aunty rukayya tace to badamuwa nan ta ciro card d'inta tabawa sabreen sannan tace gaskya kinada hankali da dad'in sha'ani sabreen Allah ya baki miji na gari😊, sabreen tayi murmushi tace ameen aunty rukayya bazan tab'a mancekiba nagode sosai Allah ya biyaki😀, aunty rukayya tace ameeen sannan tayiwa su kaka da kamal sallama ta tafi. Duk hiran da aunty rukayya sukeyi da sabreen kamal yana jinsu, dan haka ya shirya zai fita se sabreen tabi bayansa tace yah kamal zaka fita ne, eh sabreen akwai wani abune, a'a dama inaso inyi maka godiyane akan girki dakasa aka koyamin nagode sosai😀, murmushi yayi yace bakomai sabreen nizan fita se dare zan dawo, ok dama inaso inje gurin munira ne tunda muka rabu bamu sake had'uwa ina kewarsu sosai☺, kamal yace to shikenan ki bari zuwa gobe semuje harda kaka koh, dad'i taji sosai tana maiyin murmushi wanda yake k'ara mata kyau tace nagode yah kamal Allah ya kaimu goben😊, ameen sabreen na tafi. Bayan kamal ya fitane ya kira aunty rukayya yake tambayarta ko sabreen ta tab'a gaya mata irin wayar da takeso, aunty rukayya tace eh toh akwai randa muke hira take cemin akwaia wayan malaminsu na secondary skul wai wayan yana da camera sosai idan ya d'aukesu hoto a ciki, tun daga ranan take son wayan a ranta samsung galacky x5, kamal yace toh shikenan nagode. Shagon waya ya tsaya ya saya mata sabuwar samsung x5 sannan ya wuce gunsu mum. Kamar kullum se yaban isha kamal ya dawo bayan yaci abinci ne yazo palo yasamesu sunata hira, wayan daya sayawa sabreen ya mik'a mata gashi sabreen wayane na sayo miki na miki charging sannan nasa miki sim d'in MTN aciki, karb'a tayi hannun biyu tana farin ciki tare da cewa nagode yah kamal Allah ya biyaka da gidan aljannah, ameeen sabreen Allah ya bamu dukkanmu sannan kakama yayi masa godiya yace kamal kaibaka gajiyane, kud'adenka zasu kare dan Allah ya isa haka ka dena b'arnatar da kud'inka akanmu zaman da mukeyima kad'ai ya ishemu wlh ka mana gata sosai Allah ne kad'ai zai biyaka, kamal yace haba kaka bakomai wlh ni zanje in kwanta saboda da safe nakeso mu tafi dan kud'an yini acan zuwa yamma semu dawo, kaka yace to badamuwa Allah ya kaimu, wayarsace tayi kara ya d'auka tare da sawa a hands free yace hello abokina, suhail yace eyyy yane gwabro kak'i dai kayi aure koh, kamal yayi murmushi yace wannan ai bani kad'ai kake tsokanaba harda kanka, dariya suhail yayi yace toh garin yasu mum, kamal yace yanzu na dawo daga gunsu lfyansu lau ya pakistan, suhail yace lfya lau wlh mummy ce take cemin wai munk'i muyi aure semu tsufa ai mun rasa matan aure😀, kamal yayi dariya yace aiseka yi kafin nima nayi dan haka kai nake jira, suhail yace zan dawo ran friday insha Allah ya maganan su kakane dan mum tacemin ran wenesday mai girkinsu zata tafi, kamal ya kalli kaka da sabreen yace eh nima d'azu danaje ta gayamin kuma na tabbatar mata da cewa ran talata zan kawo mata mai girki, suhail yace ok to yaushe zakaje garinsu kakan? Kamal yayi murmushi yace gobe insha Allah, suhail yace to nagode abokina ka gaida su kakan inkaje, kamal yace suna jinka, suhail yace me kace? Kamal yace sorry nace zasuji😉, bayan sunyi sallama ne kaka da sabreen suke ta dariya😀, kunya kamal yaji seya mik'e tare da cewa seda safenmu😉, har yanzu dariya sukeyi sannan kaka yace to Allah ya tashemu lfy yace amenn sannan ya shige d'akinsa. Washegari suka shirya tsab se k'auyensu, murna sosai mutanen k'aunuen sukayi da ganinsu kaka musamman ma nunna, tace sabreen me sirrin ne kin ganki kuwa yadda kika kara kyau se wani shek'i kikeyi, sabreen tayi dariya tace kema kin canjafa me sirrinne k'awas? Nan munira ta bata lbrn saurayin da tayi me suna ABUBAKAR SADDIQ shi doctor ne kuma yana da hankali sosai gashi yana kulawa da ita sosai kingama harya sayamin wayanmu galacky x5 sannan komai ya sayamin sena ajiyei miki naki kinga nan munira tayita nunawa sabreen kayan alkhairin da Abbakar yake mata harda iyayenta. Bayan ta gama ganine tace lallai k'awata kin paso gari Allah ya tabbatar da alkhairi ya kuma nuna mana bikin💃🏻munira tace amenn toya birnin bani lbr mana, sabreen ta kwashe lbrn birnin tun daga farkon zuwansu har karshe ta fad'awa munna sannan ta bata sayayyan kayan da kamal yayi musu harda k'arin jaka da takalmi nasu mama ma dabanne. Munna ta bud'e baki tana ganin abun duniya tare dayin godiya ita dasu mama sukaiwa kamal godiya sosai, munna tace kodai yana sonkine sabreen? Sabreen tace SO kuma, oho nidai bai tab'a gayaminba nima kuma bansa komai a rainaba, SUHAIL shine a raina amma kuma duk randa yah kamal ya furtamin cewa yana sona nad'au alk'awarin amince masa tare da bashi soyayyata danya cancanci hakan daga gareni kuma kowace mace zataso mutum irin yah kamal dan baida wata matsala wlh. Munna tace to Allah ya zab'a miki mafi alkhairi sabreen, ameen Amaryan abbakar mu zamu koma se wani lokaci kuma😀. Bayan sun komane kamal yace to kaka seku shirya jibi talata zaku koma gidansu suhail ran laraba mai girkinsu zata tafi sabreen zata fara girki ran alhamis yayinda suhail zai dawo k'asar ran FRIDAY. Daga kaka har sabreen basuso hakanba, shima kamal d'in babu yadda zaiyine amma sam bayason tfyarsu, kaka yace toba komai Allah ya nuna mana, kamal yace ameen sannan ya wuce d'akinsa suma sukai nasu d'akin da tunani kowannensu yayi bacci😲😵😲 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 25-26 Kamal ne dasu sabreen akan daining suna breakfast, babu wanda yake cewa komai gabad'aya jikinsu a mace yake tunba kamal ba. Bayan sun gamane sabreen ta koma d'akinta tana kwance akan gadonta suna waya da munira tana dariya, bayan sun gamane ta kira aunty rukayyama sukasha hira sosai dayake kamal yasa mata credit aciki. Wani number ta gani yana kiranta, ta d'auka tare da cewa hello, muryan yah kamal taji yace sabreen kamal ne na kirakine in sanar dake wannan number nane kiyi saving kinji, ok toh nagode ya kamal ka fita ne? A'a yanzu dai zan fita akwai wani abune, emmm dama inaso inje shago ne akwai abinda nakeso in saya, toh menene gayamin se in sayo miki koh, shuru tayi batace komaiba, yace "sabreen" tace emmm nafiso inje da kainane yah kamal😉, murmushi yayi yace toh shikenan fito muje kisaya, toh nagode sannan ta katse wayan ta dauki himar d'inta tasa tayiwa kaka sallama sannan ta sami ya kamal agun motansa, gaba ta bud'e ta shiga sannan yaja suka isa wani d'an babban shago, sabreen tayi saurin cewa yah kamal ka zauna kawai ni zanje yanzu zan fito, toh yace mata sannan ta fita ta wuce shagon, bayan shigantane kamal ya fito yana biye da ita a baya batare data saniba ya shiga. Part kawai sabreen ta dauka guda 2 sannan tazo gun biyan kud'in, mai karaban kud'in yace ki barshi kawai, tace yah za'ayi kace in barshi ungo karb'i kud'inka, mai shagon yace wani ya riga daya biya miki, tace wani kuma waye shi? Mai shagon ya nuna mata motan kamal, kunya sosai taji tace yanzu yasan abinda na saya kenan😁, k'in fita tayi tana tsaye a cikin shagon segashi ya shigo fiskansa a d'an d'aure yace baki gama bane sabreen, shuru tayi ta wuceshi ta nufin gun motan kunya kamar ta shiga k'atsa. Tunda suka fara tfy batace komaiba kanta na gefe, kamal yace sabreen ya kikayi shuru, tace bakomai, murmushi yayi yace aida kin gayamin in sayo miki me aciki muna sayowa hafsat ai nida suhail, kunya taji sosai tasa himar d'inta ta rufe fiskanta tana dariya batare dayajiba, shima dariyan yayi yace kidena kunyata sabreen domin ni bana kunyanki kinji koh? Batace dashi komai shima bai sake cewa komaiba har suka iso gida, bayan ya tsayane ta bud'e kofan tare da cewa nagode batare data kalleshiba, dariya yayimata wanda ya kara masa kyau yace bakomai na tafi gun mum se dare zan dawo, toh zallah ya tsare, ya ameeen sannan ta rufe motan ya tafi. 9:00pm kamal ya dawo gida, bayan yayi wanka yaci abincine seya kira sabreen a waya yace inason magana dake ina palo, doguwar rigan atamfane a jikinta da d'ankwalinsa da tayi lullub'i dashi yana hango gashin kanta harta k'araso gunsa sannan ta zauna akan kujera tace gani yah kamal, kamal ya gyara zama yace sabreen kin tab'a yin soyayya? Wani iri taji dan bata tsanmaci wannan tambayar daga garesaba, daurewa tayi tace a'a yah kamal, ya sake cewa amma dai nasan kina da masoya ko, tace eh akwai amma gaskya ban tab'a kula ko wani d'a na mijiba, kamal yace shin ko akwai wanda kikeso aranki? Ananne sabreen tayi shuru dan bata san me zata ce mishiba, sake maimaita tambayan yayi tareda cewa ina sauraronki sabreen, kanta a sunkuye tace a'a babu. Kamal ya sauke ajiyan zuciya yace ko zan iya sanin dalilin k'inyi soyayyar? Sabree tace babu wani dalili yah kamal, yace toh shikenan tashi kije😊, kallonsa takeyi har cikin ido shima haka sannan ta wuce d'aki. Murmushn jin dad'i kamal yayi tare da tashi ya shige d'akinsa da farinciki sosai aransa. Ita kuwa sabreen mamakin tambayoyin da yah kamal yayita mata takeyi har bacci ya d'auketa [10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 27-28 Ayaune sabreen zasu koma gidansu suhail, bayan ta gyara ko ina ta kimtsane tayiwa ya kaml girki ta ajiye a daining, da yamma yazo ya tarar dasu a palo suna zaune. Bayan yaci abincine yace to bari ind'an watsa riwa semu tafi koh, sabreen tace to sannan taje ta d'auki plate d'in ta wanke ta dawo ta zauna, daidai lokacin kamal ya fito daga d'akinsa se kamshin turare yakeyi yace toh kaka muje ko sannan ya d'auki kayan kaka ita kuwa sabreen ta d'auki nata suka tafi. Maigadi baiso rabuwansu da kakaba harma da sabreen domin mutanen kirkine suna da dad'in zama sosai. Tunda suka fara tfy babu wanda yace komai se wayan kamal ya fara ringing, ya d'auka tare da cewa hello abokina ya akayine, suhail yace ka d'aukosu kakan kuwa, eh na d'aukosu yanzu hakama muna dab da shiga gidane, suhail yace"thankyou dud" pls ka gaishemin da kaka, kamal yace kaka yana jinka, se kaka yace ina amsawa Allah ya dawo dakai lfy, suhail yace ameen kaka nagode, kamal yace to abokina zan kiraka anjuma, ok sena jika sannan ya katse wayar, dai dai lokacin kamal yayi hon aka bud'e gate suka shiga, tun daga wajen gidanma kasan gidan manyane bare kuma inka shiga ciki, bayan sun fitone kamal ya d'auki kayan kaka yana musu jagora har suka k'arasa da sallamarsu, mum ce da hafsat zaune suna kallon "THE GARDINERS DAUGHTER" wani series film ne mai dad'in gaske. Tun shigowarsu suka sawa sabreen ido suna ganin irin kyawunta ai atake kirjin hafsat ya buga da karfi, bayan sun zauna ne suka gaggaisa hafsat tace bro kamal kardai ince sune bak'in namu? Kamal yayi murmushi yace kwarai kuwa sis sune, wannan itace sabreen wannan kuma kakanta, shi zaici gaba daba flawer ruwa ita kuma zata dinga yin girki, mum tace Allah sarki sannu sabreen ya hakurin mahaifiyarki kuma, sabreen tace hakuri ya zama dole, mum tace to Allah ya jikanta ya jikan dukkan 'yan'uwa musulmai, gabad'aya suka amsa da ameeen. Se mummy tace toh hafsat tashi ki nunawa sabreen d'akinta ko, hafsat tayi murmushi tace taso muje, mikewa sabreen tayi tare da d'aukan akwatinta tabi bayan hafsat, shi kuwa kaka masaikin bak'i dake tsakar gidan ta gefe aka kaisa, d'akin harda AC da komai dakomai dai gwanin sha'awa. Bayan hafsat takaita d'akinne ta bud'e wall drop sannan ta karb'i akwatin sabrren ta ajiye mata a ciki ta juyo tace nan shine d'akinki, sannan ga toilet naki nan, idan akwai wani abu da kike buk'ata toki sanar dani kinji😊, sabreen taji dad'i sosai tace nagode hafsat😊. Bayan hafsat ta fitane sabreen ta k'arewa d'akin kallo tas d'an daidai ne bayi da girma sosai amma an zuba kayan duniya, kwanciya tayi tana ta tunanin yah kamal, tace oh yah kamal yau shi kad'ai a gidan bazaiji dad'iba hakama mai gadi. Bayan isha hafsat tazo ta kira sabreen wai kizo kici abinci, a baya take biye da hafsat har suka k'arasa daining, kamal na zaunne kusa da mum suna cin abinci, hafsat ta zubawa sabreen ta ajiye tare da cewa bisimillah zauna muci, sabreen tace zanje inci a d'aki, mum tace meyasa zakije d'aki bayan gamunan anan kodai kunyan d'an nawa kikeyine kamal, kamal yace kunyana kuma mum meyasa zataji kunyata kawai dai k'ila kunyanki tajeji, mum tace toh shikenan hafsat mik'a mata ta tafi d'akin tunda hakan tafiso, sabreen ta karb'a tare da cewa nagode emm kaka fa? Kamal yace kaka yana d'akinsa yanzu na kai mishi nashi abincin jekici abincin seki dawo muyi hira kinji, toh tace sannan ta wuce d'akinta taje ta zauna tana cin abincin, abincin yayi dad'i sosai dan haka taci sosai sedai bata cinyeba. Wani murya taji kamar daga sama an SABREEN, d'ago da kanta tayi tana kallon bakin kofan shigowa😳 wannan MACEN tagani a tsaye tana kallonta tana mata murmushi, itadai sabreen sam bataji an bud'e kofaba kawai ganin mutum tayi a tsaye, ahankali MACEN take takowa inda sabreen take, 😳😳🙆🏻ihu mai karfi sabreen ta sake tare da wurgi da plate d'in abincin hannunta tasss kakejin fad'uwan shi a k'asan tiles take ya tarwatse. Ganin yadda sabreen ta tsoratane yasa MACEN tayi saurin b'acewa segasu mum da kamal sun shigo da saurinsu, kamal dake waya da suhail yace abokina bani 2minit zan kiraka, da gudu sabreen taje ta rungume mum tanata kuka tare da waige waigen bayanta🙄😳🤔 [10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 29-30 Mum ta d'ago da sabreen tace lfy sabreen, menene, sabreen ya rasa me zatace se tace musu mammina na gani anan mammina tana nan d'akin naganta, kamal ya matso kusa da mum yace ki kwantar da hankalinki sabreen mamminki ta rasu ai ba yadda za'ayi ki ganta anan wanda ya rasu baya dawowa kinji "may be dai kin razana ne kawai" har yanzu dai sabreen waigawa takeyi tanata k'arewa d'akin kallo. Mum tace shikenan hafsat kwashe plate da abincin can, sabreen muje daining kici abinci. Da sauri tabi mum suka isa daining ta zauna mum ta zuba mata abincin, kad'an sabreen taci tace ya isheta, ruwa mum ta mik'a mata yasha sannan tace nagode mum, hafsat ce ta k'araso tace mum ko zamu kwana da ita a d'akina idan ta dena tsoron seta koma d'akinta, mum tace toh hakanma yafi sabreen ku kwana tare kinji, kai sabreen ta d'ago batare datace komaiba hankalinta yana gun wannan MACEN. Wayan kamal ne ya sake yin kara ya d'auka hello abokina, suhail yace meke faruwa ne a gidan? Kamal ya gayawa suhail komai, sannan suhail yace ina sabreen d'in bata wayan, sabreen da tayi nisa cikin tunani kamal yana ta mata magana tare da mik'a mata wayan amma sam bata jinsa, hafsat dake zaune a gefentane ta tab'a kafad'arta tace sabreen tunanin me kikeyi haka akanata miki magana bakyaji, se a lokacin ta dawo hayyacinta a zabure ta kalli hafsat sannan ta karbi wayan tasa a kunne tare da cewa hello, suhail yace sabreen naji abinda ya faru amma inaso kisani shi mamaci baya dawowa k'ila dai kinsa tunaninta arankine har kike ganinta a naki tunanin yakama ki d'auki kaddara kisa a ranki cewa ta rasu ba kuma zata dawo garemuba har abada kinji? Shuru tayi tana had'iyan kukanta batace dashi komaiba, suhail yaji tayi shuru batace komaiba seya kira sunanta "sabreen are you there"? Se alokacinne tace "yeah naji kuma na gode" sannan ta mik'awa yah kamal wayan, lokacin suhail nacewa sabreen muryaeki yamin kama dana wata yarinya, karaf a kunne kamal amma seyayi kamar baiji yace hello abokina yane, suhail yayi ajiyar zuciya yace bakomai nan dai sukaci gaba da hiransu har kamal yayi musu sallama ya tafi suma suka wuce d'akunansu donyi bacci. Kamal dai tunda ya koma gida tunanine cike a zuciyarsa game da sabreen da kuma abinda yaji a bakin suhail, da kyar bacci ya d'aukesa. Shima suhail acan pakistan kasa bacci yayi yanata tunanin wannan yarinyar mai nik'af, tabbas yanzu da yayi magana da sabreen seyaji irin wannan muryance datace mishi "Thankyou so much SUHAIL" yace toh kodai kawai dan nasata a rainane shiyasa naji muryanta irin na sabreen, da wannan tunanin shima yayi bacci. Itama sabreen kasa bacci tayi dukda kashen wutan d'akin da hafsat tayi amma sam ta kasa bacci, fiskan MACENNAN dai shiyake mata yawo a kwakwalwarta, tace dama na sani dabanyi ihuba tunda dama na dad'e inaso in sake ganinta domin inyi mata godiya, insha Allah duk randa na ganta bazan sake tsorataba zanso inji metakeson gayamin sannan nima kuma inyi mata tambayoyi, ta wani gefe kuwa dad'in kalaman suhail takeji har cikin ranta tana ta murmushi tare da mamakin suhail tana zamcen zuci, yanzu shi suhail kota muryata bazai ganeniba😊, murmushi tayi tana tuna lokacin da suke shak'ar numfashin junansu yayinda suke kallon idanun junansu, kyakkyawar fiskarsa take gani a idanunta tare da murmushin yayi mata😌 dad'i sosai take ji har cikin ranta tace koda wasa bazan sanar dashiba, kuma bazan tab'a bari ya ganeniba😊 da wannan tunanin itama bacci yayi gaba da ita. Bayan sunyi breakfast ne taje gun kakanta sunata hira har azahar kafin ta shigo dama bata sallah. A palo suke zaune sunata hira da mum da yah kamal da kuma hafsat sabreen dai dariya kawai takeyi tana sauraron tsokanar da yah kamal yakeyiwa hafsat, har la'asar bayan sunyi sallah ne kamal yace zai fita se dare zai dawo, mai girkinsu tana gama abincin dare d'anta yazo ya d'auketa, alkhairi sosai mum ta mata harma da hafsat sannan suka tafi. Bayan isha yah kamal yayi cefene sosai ya kawo gida saboda gobene alhamis sabreen zata fara girki. Washegari ta shiga kichine ta fara girki, dama kunsani base na k'ara maimaitawaba. Kowa yaji dad'in girkin nata harma da masu gadin gidan sunata cewa ai tafi nadama iya kirki wlh, dad'i kaka yaji har cikin ransa don yadda aketa yaba girkin jirarsa😊. Haka tayi na rana dana dare mum farin cikine a fiskarta sosai danko gaskya girkin sabreen bakarya, sun yaba sosai harda hafsat tana cewa gaskya zaki koyamin girki sabreen, yah kamal yace da lalacinkinne zaki koyi girki? Hafsat ta b'ata rai mum kinji abinda bro kamal yake cewa ko, mum tace rabu dashi zaki bashi mamaki kuwa, sabreem tace zan koya miki hafsat karki damu. Haka sukaita ta hira har suka gama cin abinci se yah kamal ya mik'e tare da cewa mum nizan tafi seda safenmu, mum tace yau da wuri haka babu hira kenan, kamal yace mum kinsanfa gobene abokina zai dawo, dan haka bazan samu zuwa da safe bama sedai zuwa yamma. Mum tace to shikena Allah ya bamu alkhairi, kamal yace ameen sannan ya wuce gun kaka sukai sallama seya tafi, su mum kuwa sun d'an tab'a hira sannan suka wuce donyin bacci, Hafsat se murna takeyi gobe bro suhail d'inta zai dawo, ita kuwa sabreen binta kawai takeyi da kallo tana mamakin hafsat, dan sam basa wani hiran kirki da hafsat d'in, amma gashi yanzu tanata murna tana cewa sabreen zakiga d'ayan bro na gobe kinji, sabreen tayi murmushi tace to Allah ya kaimu goben Allah kuma ya dawo dashi lfy😊, hafsat tace ameen sannan ta kashe wuta suka kwanta kowacce da tunaninda takeyi a ranta da haka har bacci ya d'aukesu... Sad-Nas [10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 31-32 Washe gari da safe safreen da hafsat suka kintsa gida tas ko ina se kamshi yakeyi, hafsat ce taje d'akin bro suhail ta wanke masa ta gyara ko ina tsab. Sabreen ta had'a musu breakfast bayan sunci ne taje gun kakanta suka d'an tab'a hira dayake bata da wani aiki se girkin kawai. Sabreen ne da mum a palo tana tambayanta Hajiya me za'a dafa, mum tace karki damu sabreen d'ana suhail babu abinda baya ci se gwaten doya da kuma duk wani juice na gargajiya da ake had'awa to baya sha, shidai a drinks coke yafi so. Sabreen tace toshikenan Hajiya yau zan koma d'akina da zama, mum tace meyasa, sabreen tace bakomai ai yanzu na dena tsoron😊, murmushi mum tayi tace to shikenan kiyi yadda kike so kinji, nagode Hajiya sannan ta tashi ta wuce d'akin hafsat ta kwashe kayanta tas ta mayar d'akinta sannan ta kwanta a gadonta tana jiran wannan MACEN ta sake zuwa, ganin ba wani abinda zatayine seta kira munira sunata hira abinsu, daga nan ta kira yah kamal tace kar yace ni bana kiransa. Ringing d'aya ya katse sannan ya kirata, murmushi tayi ta d'auka tare da cewa hello yah kamal ina kwana, lfy lau sabreen ya kike, lfyta lau yau bakazo kayi karin kumallo ba, eh wlh nasha tea nd bread karki damu zanzo da suhail bayan la'asar muci daddad'ar girkinki kinji, murmushi tayi tace toba damuwa se kun zo dama na kirane mu gaisa se anjuma, ok sabreen nagode sosai ki gaishemin da kaka, to zaiji insha Allah sannan ta katse wayar tayi baccinta. 20:00pm daidai sabreen ta farka tare da duba wayanta taga time, 🙄 wuce kichine tayi da saurinta domin had'a domin had'a abinci, peppe soup d'in kaza tayi da rice nd stew sannan ta hada cor-slow mai dad'i kuma yasha had'i, sannan ga friut salad. Da misalin 3:50pm ta gama komai seta zubawa kaka da maigadi kowa da nasa takai musu sannan ta wuce d'akinta tayi wanka tare da shafa mai tasa doguwan riga after dress batayi kwalliyaba sam se d'an turare data fesa ajikinta "WISAL" wanda yah kamal ya saya mata. Kichine taje ta d'ibi abincinta ta koma d'aki taci sannan ta mayar da plate d'in kichine ta dawo d'aki tana ta game a wayanta dan ya kaml yasa mata games masu yawa. 4:15pm motar kamal tayi hon a gate, da sairi mai gadi ya bud'e gate yana yiwa suhail maraba da dawowa sannan suka gaisa dukkansu seya k'arasa ciki. Hafsat ne ta fito d'auke da ado sosai a fiskarta tayi matukar kyau ta k'arasa gunsu da mirnarta tana cewa oyoyo bro suhail "yoir wlcum" murmushi suhail yayi yace wannan kwalliyar dukni akwai wa? Murmushi tayi tace sosai ma kuwa😊, kit d'insa ta karb'a a hannun ya kamal tace sannu da kokari yah kamal, yawwa hafsat, suhail yace gaskya naga wannan wankan naki yar'uwata kuma zan biya😊, dad'i taji sosai sannan suka wuce suna dauke da kaya a hannunsu. Mum tana mirmushi tace maraba da dawowa ya hanya, suhail yace Alhamdulillah mum kuna lfy, lfy lau sannunka da hanya, yawwa mum sannan ya wuce tare da cewa bari nad'an watsa ruwa, ok kamal yace sannan hafsat ta shiga da kayan d'akinsa. Bayan suhail ya fito ne ya wuce daining inda suke zaman jiransa, ya k'arasa ya zauna tare da gaishar da mum d'insa, sannan suka gaisa da hafsat yace ta zuba mishi aminci. Suna cin abinci dukkansu suna hira sega sabreen ta fito ta iso hargun daining tace ya kamal sannu da zuwa, ya suhail sannu da dawowa ya hanya? Kamal ne ya fara magana yace yawwa sannu sabreen yana mata murmushi😊, suhaila yace yawwa hanya Alhamdulillah ya karin hakuri kuma, sabreen tace hakuri alhamdulillah kanta na kallon hafsat, yace to allah ya jikanta, tace ameen seta kalli mum tace hajiya bari naje gun kaka, mum tace toh sabreen sekin shigo, murmushi tayi sannan ta wuce kamal da suhail sunata binta da kallo harta fita. Mum da hafsat duk sun lura da kallon da sukeyiwa sabreen ita kuwa sabreen batama san sunayiba, bayan fitantane suka maiyar da idonsu kan abincinsu, ita kuwa hafsat wani kishine taji har cikin ranta😬😁 [10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn shureim (Sad-nas) WASUNKU SUNA TAMBAYA KO NICE MAMAN SHUREIM DATA RASU WATO (ZARA'U BABA YAKASAI ALLAH YA JIK'ANTA DA RAHAMA AMEEN) TO GASKYA DAI NI BANKAI MATSAYINTABA DANNI BA BARUBUCIYA BACE KAWAI DAI ABIN YANA BAN SHA'AWA NE SHINE NACE BARI DAI IN GWADA, CIKIN IKON ALLAH WANNAN SHINE LITTAFINA NA UKU, NAGODE DA SOYAYYARKU. Love you all💞💐🌹🌺 33-34 Sabreen ta shiga gun kaka yana ta karatun Qur'ani mai girma, bayan ya idar ne ya juyo yana kallon sabreen data shafa addu'an a fiskanta tace ameeen kakana, kaka yace naji mai gadi yana cewa sannu da dawowa kardai har SHULE d'in ya dawowo, 😅dariya sosai sabreen tayi sannan tace kaka ba shule ake cewaba SUHAIL sunansa, kaka yayi dariya yace to ai sunan nasane da wahala gara dai shi kamal d'in nasan sunan, amma shi shule kam bamma tab'a jiba se agunsu. 😄kai kaka kaban dariya wlh EH yadawo, kaka yace dakike dariyannan se kikayi kama da mahaifinki sosai, 😰hawayene atake ya cikowa sabreen a idanunta ta fara magana Allah sarki ABBA NAH Allah ya jikanku da rahama ameeen, kaka naso ace ina tare da iyayena inga soyayyar da ABBA zai nunamin amma kai da mammi ne kawai na samu naku itama yau babu ita a duniya😭😭😭 har abada bazan tab'a mantawa dakuba "KUNA RAINA" kaka ma kwallaya yake sharewa a fiskarsa, ganin hakanne yasa sabreen ta tashi ta fita tana ta kuka harta shigo palon ko sallama babu ta wuce d'akinta yayinda su mum suke binta da kallo. Kamal yace hafsat jeki kiji meya sami sabreen take kuka, hafsat ta mik'e ta wuce lokacin sabreen ta kifu a gado tanata kuka babu irin tambayan da hafsat batayiwa sabreen ba, amma ko kallon hafsat batayiba bare tace mata wani abu. Hafsat ta dawo palo tace batacemin komaiba tanata kukanta, suhail yace hafsat jeki kirata, bayan hafsat ta gaya mata ne seta fito, sabreen ta dena kukan amma hawayene cike a fiskarta taja gyalen kayanta ya rufe mata ido taje ta zauna a kan kapet. Mum tace sabreen meya faru kike kuka, cikin wani irin murya mai cike da tausayi tace bakoma hajiya, wani iri kamal yakeji a ransa kamar yaje ya rungumeta. Sallamar kakane ya katsesu, bayan sun amsane kamal da suhail suka mik'e suka karsa gunsa dama basu gaisaba, wata yarinyace kakkyawa biye da kaka, bayan sun gaisane itama yarinyar ta gaishesu se kamal yace kaka meya samu sabreen ne? Kaka yace ta tuna da iyayentane shiyasata kuka😒. Suhail yace Allah sarki nayi tunanin hakan kuwa, kamal ya kalli yarinyar da take sanye da doguwar riga jah da gyalensa yace wannan fa kaka? Kaka ya kalleta yace dasu kawar sabreen ce tazo guntane, kamal yace ok shiga tana ciki, a nitse ta wucesu kamal yace sabreen kinyi bak'uwa, sabreen ta d'ago da kanta don ganin bak'uwan nata🤔🙄 wazata gani wannan MACENNE ta karaso tare dayin sallama taje ta zauna kusa da sabreen sannan ta gaida mum cikin girmamawa ta gaida hafsat sannan ta juyo tana kallon sabreen da mamaki ya cikata tare da d'an tsoro kad'an. MACEN tana murmushi tare da tab'a hannun sabreen tace kaka yacemin kinata kuka tare da d'aga mata gira😉ma'ana su shiga d'aki, sabreen tad'anyi murmushin karfin hali tare da wayancewa tace muje ciki toh, mik'ewa sukayi a tare suka wuce d'akin sabreen, shidai kamal idonsa nakan sabreen har suka shige ciki yayinda kaka yake lura da irin kallon da kamal yake yiwa sabreen... Sad-Nas [10/22, 7:26 PM] ‪+234 803 863 6764‬: 🌺💐TANA🌹RAINA💕💞 By Mmn Shureim (Sad-Nas) 35-36 Bayan su sabreen sun shiga d'akine MACEEN tasa key ta rufe, da sauri sabreen ta juyo tace meyasa kika rufe kofan? MACEN tace karki damu sabreen bazan cutar dakeba nazone dan inyi magana dake. Bayan sun zaunane macen ta rik'e hannayen sabreen dukka biyu ta fara magana suna kallon junansu. Sunana SALMA kuma ni kad'ai ne agun iyayena, tun kafin a haifeki mahaifinki ya rasu ata dalilin cetona. Wata rana nida iyayena muna zaune a cikin jeji suna koyamin harbi da kwari da baka, ina zaune daga nesa su kuwa iyayena suna tsaye agu d'aya mahaifina ya saita kwari da baka a daidai inda nake zaune akan zai gwada kona iya kwaucewa kamar yadda yake koyar dani, nima jira nake ya harbo in nuna masa kwarewata na kaucewa. Kawai sega wani bafulatani yana wucewa se idonsa yakai gun iyayena kuma yaga suna da niyan harbinane, bafulataninnan ya kalli lokacin ina zaune bazan wuce shekaru 7 ba, dai dai lokacin da mahaifina ya harba kwarinne se wannan bafulatani yayi sauri tare dayin tsalle danya tareni, amma se wannan kwarin ya sameshi a daidai setin zuciyarsa, nan take ya fad'i. Iyayena dani dukkanmu mukazo kansa lokacin jini nata zuba sosai daga jikinsa, hannuna ya kamo yana magana da kyar yana cewa haba bayin Allah wannan yarinyar kuma metamuku da zaku kasheta dan Allah ku kyaleta sannan ya juya yana kallona yace yarinya tashi ki gudu kinji ki gudu zasu kasheki, mahaifina ya share kwallan fiskarsa yace bawan Allah ba kasheta zamuyiba, hasalima 'yarmuce wannan na cikinmu gwaji kawai muke mata akan koyar da ita danayi, gashi abisa rashin sani na cutar dakai gurin kokarinka na ceton 'yata😰, dan Allah ka yafemin bawan Allah ba'a son rainabane. Bafulatanin yayi murmushi yace bakomai na fahimta, haka Allah ya tsaramin nikuma, ta wannan hanyar zan koma ga mahaliccina, nayafe maka har cikin zuciyata, sedai ina neman taimakonku, mahaifina yace taimakon me kenan? Bafulatanin yace matata tana gida d'auke da tsohon ciki ita da surukina suna can gida a wannan kauyen da yake gaba danan, inaso ku taimaka ku k'arasa dani gidana dan baajin zan iya karasawa da kaina dan yadda nakeji ayanzu. Dukda cewa mahaifina ya cire kifiyar daya soki bafulatanin, amma sam jini bai dena zubaba gashi daga gani yana shan azaba, haka mahaifina ya d'aukeshi mukaje har kauyenku, nan mutane suka taru a kanshi agun mai unguwa. Matarsa da surukinsa aka kira sukazo tana ganinsa ta fara kuka sosai, mai anguwa yace meya sameshi haka? Har mahaifina ya bud'e baki zaiyi gaya musu abinda ya faru, kawai se bafulatanin ya fara magana da k'yar yana cewa ina cikin tfy ne se nayi tuntub'e da wani abu, kafin in ankara se naji na fad'i akan wani abu mai kaifi kuma mai tsini, ban iya tashiba se naji mutane na zuwa, shine nace su taimakamin su kawoni kauyenmu, bafulatanin ya nuna mahaifina yace wannan shine wanda ya ciremin kifiyar data sokeni kuma ya kawoni gida. Hawayene sosai a fiskar iyayena dajin lbrn da bafulataninnan ya fad'awa yan kaiyensu. Matarsa da surukinsa suka fara kuka gashi asibiti se cikin garin, mahaifina ya d'aukesa yace muje asibiti, nan aka tashi da wuri domin zuwa asibiti, se mata mai cikinnan ta rike hannunsa tanata kuka tana cewa maigida karka tafi ka barni tun bakaga abinda zan haifa manaba, banaso abin cikina ya zama maraya dan Allah karka barmu. Bafulatanin ya rik'e hannun matarsa yana kokarin magana amma se mukaji yana salati tare da cikawa😰. Kuka sosai matarsa takeyi da kuma jama'an dake gurin musamman iyayena dani, matarsa kuka takeyi tare da rungume gawan mijinta kowa ya tausaya mata, da kyar mahaifinta ya janyeta ya kaita gidan makota inda nida mahaifiyata mukabi bayanta, bayan mahaifinta yakaitane seya koma gunsu mahaifina akayi mishi wanka tare da suturceshi akai masa sallah se gidansa na gaskya😭. Salma ta tsaya da lbrnta anan tana kallon sabreen da idanunta yayi jah dan kuka datakeyi😭 SALMA ta dad'a matse hannayenta acikin na sabreen tana kwalla itama tace sabreen bakowa bane wannan bafulatanin illa MAHAIFINKI dan Allah ki gafarcemu nida iyayena😰👏🏻. 😳🙄😭😭 idanu sabreen ta bud'e tare da tsananta kukanta sosai ta hankad'e Salma tare da mikewa tabud'e kofa ta fita a guje segun kakanta yana baiwa flawer ruwa, tunkafin ta karasa gunsa ya juyo ya tareta dan yasan komai. Sabreen tana kuka tana cewa kaka itacefa sanadiyan rasuwan mahaifina wannan ita da iyayenta sune sila kaka😭😭😭. Salma ta k'araso gunsu tana cewa sabreen kakanki yasan komai ke kad'aice baki saniba dama, sabreen da take kallon salma seta juya tana kallon kaka tace kaka wai kasan komai😡😰😭?? adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *