Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Thursday, 22 June 2017

’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU

adsense here

Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Novels villa Duniyan novels Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: +2347039625239 YAYA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. ﺍﻟﺒﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮ ﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮ ﺣﻴﻢ . ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻏﻔﺮ ﻟﻲ ﺫﻧﺒﻲ ﻛﻠﻪ، ﺩﻗﻪ ﻭﺟﻠﻪ، ﻭﺃﻭﻟﻪ ﻭﺁﺧﺮﻩ ﻭﻋﻼﻧﻴﺘﻪ ﻭﺳﺮﻩ. ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺻﻞ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭ ﻋﻠﻰ ﺃﺯﻭﺟﻪ ﻭﺫﺭﻳﺘﻪ ﻛﻤﺎ ﺻﻠﻴﺖ ﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﻫﻴﻢ . ﻭﺑﺎﺭﻛﺖ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺃﺯﻭﺍﺟﻪ ﻭﺯﺭﻳﺘﻪ ﻛﻤﺎ ﺑﺮﻛﺖ ﻋﻠﻰ ﺁﻝ ﺇﺑﺮﻫﻢ، ﺇﻧﻚ ﺣﻤﻴﺪ ﻣﺠﻴﺪ . GATARWA Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. Ina godiya a gare sh’i, ina neman taimakonsa, ina neman gafaransa, kuma ina neman tsarinsa daga sharrace- sharracen rayukanmu da mitagyn ayyuka. Wanda Allah ya sh’irye sh’i babu mai b’atar da sh’i, wanda kuma ya b’atar ba mai sh’iryar da sh’i. Ina shaidawa babu abin bautawa da gsky sai Allah, shi kad’ai, babu abokin tarayya gare sh’i. Ina shaidawa cewa Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne. Ya Allah kayi tsira ga wad’anda suka bish’i da ky’aky’awan kw’aikw’ayo har zuwa ranar kiyama. Kuma ka musu aminci, aminci mai yawa Ameen. SADAUKARWA Na sa daukar da wannan littafi mai sun YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU, ga Mummy’s d’ina Khadija’s. GODIYA godiya mai d’imbin yawa gareku, da bazarku nake taka rawa a duniyar Rubutu, Allah ya barmu tare. Maryam .S. Bello Maryam Alkali Mamu(Mrs Jabo). Page-1~5. Tari wanki ne a gabanta, sai faman wanke su takeyi, kalo d’aya zaka mata ga gane ta gala baita sosai, har k’arfin har bata jin karfin jikinta. Gwaggo ne ta taho da wasu kayan wankin ta kara mata, tace “Khadi maza- maza kiyi sauri ki wanke ma Beeba kaya, zata gidan Innarku. A wahale na d’ago nace “Inna ga wasu sabbin kayanta can na wanke su, sun bushe tasa su, kuma suna da ky’au, gash’i nayi wankin da yawa na gaji. Gwaggo wani uwar ashar ta narko, wanda ni Rash bansan lokacin da nayi baya da sauri ba. Shako ta Inna tayi tace”dan jakar ubanki ni zaki fad’a ma kin wanke wasu, kuma har kina iya cewa kin gaji. Eh! Lallekam yau zaki gwadan ke yar Zamani ce, ban isa dake ba ko?. Khadi cikin muryan kuka tasoma cewa”dan Allah! Gwaggo kiyi hak’uri wlh ba da wara manufa na fad’i hakan ba. Gwaggo kara shaketa tayi tace”ko uwar ki ma bazata mayar min da martani ba. Kafin Khadi tayi magana ji kake tass tass tass ta wanke ta da mari har sau uku, dukanta tafarayi ta kota ina. Wayyo ni kaina Rash na tausaya ma Khadi, don ga alama fuskan gwaggo nan bata da tausayi ko kad’an Taku a kullum mai k’aunar ku ﺭﺍﺷﻴﺪ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-6~10. Gwaggo sai da tayi likis ma Khadi kafin ta ky’aleta, tace”wlh sai kin gama wankin nan yau ko na miki dan banza duka, sha-sha kawai, mts tayi tsaki ta nufi cikin d’akinta. Khadi kam kuka tasha ga wani yunwan da ke murd’amata ciki. Kama cikin tayi ta tamke da d’an kwali abunka da Khadija maganin Maza cikin dakiyar zuciya ta fara wankin , da ikon Allah kafin akira Sallah la’asar ta gama. Gwaggo ta fito da abinci a d’an k’aramin kwano wanda ko d’an yaro bazai ish’esh’i ba. Ta turo mata kwanon ta juya tayi d’akinta ko tausayin Yarinyan nan bata ji ba. Ga uban aikin da ta mata a cikin gidan kamar jaka. Malam Ahmadu ne ya sh’igo da Sallamansa, in donsa ne ya sauk’a kan Khadi dake kwance tamkar wanda aka d’aura ma dutsin dala da gauron dutsi aka. Da sauri ya k’arasa gurinta cike da tausaya wa, ya tallabo ta yace “Mama na ya dai? Mai ya same ki na ganki haka? . Gwaggo ta fito cike da masifa tace”komai ne ya same ta ko zaka karb’a mata ne, sai in sani. Cike da b’acin rai Malam Ahmad ya nufo ta, yace”kee Hauwa wlh ki kiyaye ni zan sas-saba miki akan Khadija sam ba kya tausayin yarinyan nan. Gwaggo tace “ina ko zan tausaya mata ba sanin zafinta nayi ba bare na san miye tausayi. Malam yace”duk aikin da take yi a gidan baky’a gani ko?. Kuma ba ky’a sanya yar cikinki. Wannan yarinya Yata ke a gun mu, duk irin rikon da muka mata Allah zai tambaye mu, Hauwa kiji tsoron Allah. Gwaggo tace”ehehe wa’azi zakamin ai tsoron Allah kulum cikinta muke, yar wani ba yata bace nawa kawai na san, fuuu tayi d’aki in ka gama sai ka sanar min. Taku a kulum mai k’aunar ku ﺭﺍﺷﻴﺪ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-11~15. Cikin ta kaici yazo ya tallabi Khadi ya d’agata sai a lokacin ya kalli d’an abinci da gwaggo ta bata. Taburma ya d’auko a d’akinsa ya sh’in fid’a mata, ya zaunar da ita. Kular abincinsa ya kawo mata tare da juye ruwa mai zafi ya had’a mata Lipton ya bata da kyar ta iya sha. Abicinsa ya kara mata, sai da ya tabbatar ta kosh’i kafin ya ci sh’ima. Khadi ta mik’e jiki ba kwari ta nufi rijiya ta d’ebo ruwa ta nufi bayi, wanka tayi ta fito, ta sha fa mai kayanta masu d’an kyau ta saka ta dawo waje gun Malam don gudun bala’in Gwaggo. Malam yace”Mama nah bazan fasa miki nasiha ba, inaso ko kasance mai yawan hak’uri kinga halin Gwaggon ku kullum Addu’a nake mata Allah yasa ta gane gsky. Khadiya duk halin da kika samu kanki, ki kasance mai hak’uri zakici riban rayuwanki. Kai ta d’aga masa alamae Eh!. Heeba ce ta sh’igo da Sallaman ta, cikin fara’a ta k’araso gun su, sannu da gida ta musu kafin tace”Addah ina ta sauri inzo in tayaki aiki, da aka tash’i a makaranta, ban samu abun hawa ba, Gash’i har kin gama. Khadi tayi murmushi tace”ba komai k’anwata, ya makaranta?. Alhamdulilah! Ki d’auko abinciki kici to Adda. Malam yana jin dad’in yanda yaransa suka had’a kai, baran Beeba da sam bata gado halin uwarta ba, heeba ya rinya ce mai hankali kamar Khadi. Sabanin Rabi da ke ji da taken rash’in kunya, halinta sak na uwarta hatta kama da Gwaggo take kama. Gwaggo tafito tsawa ta daka ma Beeba kee mai kikeyi a gunsu, kin dawo ko sanar ni bazakiyi ba, ni bana son kina taraya da mai fiska kaman na muciya. Oh! Ni Rash nace”wannan Gwaggon wata irin macece ta fiye son kanta, anya ma idonta na gani kuwa?. Duk irin kyan Khadi tana zaginta. Ko beeba ma bazata gwada mata kyau ba don ta d’aran mata nesa ba kusa ba. Taku a kullum mai k’aumarku . ﺭﺍﺷﻴﺪ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺔﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-16~20. Jiki ba kwari Beeba ta nufi d’akin, don sam ita bata son irin yadda mahaifiyarta ke nuna tsana ma Khadi. Gash’i ko kad’an Khadi bata nuna damuwarta kuma hakan ba sh’i zai hanata biyayya ba.Allah yasa Gwaggo ta gane. Ya sh’irya mana ita Ameen. ‘Dakin su tash’iga Gwaggo ta balbaleta da masifa, Gwaggo tace”Beeba bana son ganin ki da wancan mai fuskan mujiyan, kema kuma sai niman kai kike da su. Ni har Malam da ke biye mata ba kyalesh’i zanyi ba, ko kad’an bana k’aunar in bud’e ido imganta a gidan nan. Beeba tace”haba Gwaggo ba kyau fad’an haka fa, kuma ae Addah tana iya k’ok’arinta gurin kyautata miki. Ita ne kulum cikin aiki bata hutawa ko ni bana miki aikin da take, nikam ina son Addah na tana da halaye mai… Bakinta Gwaggo ta make tare da wata harara tace”kee a kul d’inki kar na kara jin cewa kina had’a kanki da wannan yarinya, Ko kema ta shanye miki Zuciyan ne?, kama yanda ta shanye na Malam baya ganin laifita baya son amata fad’a. Beeba tace”ko d’aya Gwaggo gsky kenan Khadi tana da halaye mai kyau. Mts Gwaggo ta ja tsaki ga abinki can maza ki ci don zaki gidan Innan ku, zaki anso min aika a gunta. Beeba ta d’auko abinci zatafita gunsu Malam Gwaggo ta dakatar da ita, ba yanda ta iya dole yasa taci a d’aki badan taso ba, don ta fi jin dad’in kasancewa da yar’uwanta. Gwaggo tace”Beeba yi sauri ki sh’irya kije min gidan Inna ku. To ta amsa ta kammala cin abinci tayi wanka ta d’auko kayanta masu kyau ta sanya su, ra fes da ita. Gwaggo “nagama sh’irin ke nake jira kizo fad’an sakon, don inje kar dare ta min a hanya. Sai da Gwaggo ta d’auko sakon da zata kai ma Inna kafin ta bata kud’in mash’in tace”kice ta had’a miki duka aikan harda kayan da na saya d’in, to ta amsa ta fito sai da tayi sallama wasu Malam kafin ta tafi. Taku a kullum mai k’aunarku ﺭﺍﺷﻴﺪ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Notice Masu karatu na zansa sunan littafina daga KHADEEJATUL-KUBRAH zuwa YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU, cos Daman YAR’RIKO ne suna Da na fara sawa, sai aka samu wacce tayi. So yanzu namar dashi YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU. Yafi ma’ana kuma sakon littafin akan haka zai tafi. Pg-26~30. Ana kiran sallah tayi d’akin su ta kwanta, kasanewan garin da sanyi lokacin hunturu ne. Addu’a tayi ta kwanta ga yunwar da ke addabarta. Haka har bacci b’arawo yayi awon gaba da ita. Dukun-kune take a yar ta barmata gefe kuma katifar Beeba ne yar k’arama wanda mutum d’aya zai d’auka. Bacci take amma sanyi ya dameta. Kiran Sallah asuba ya farkar da ita da kyar ta mik’e ta d’ibo ruwa a randa sai d’ari take yi. Alwala tayi ta koma d’aki tayi sallah bayan ta idar ta fara azkar d’in safiya wani bacci ne ya d’auketa kamar daga sama taji an shek’a mata ruwa mai sanyi nan take ta fara d’ari-d’ari, duk da haka Gwaggo bata kyaleta ba wani ruwan ta k’ara kwara mata. Barin da takeyi ya tsananta, Gwaggo tace”ke har kimsami daman da zaki kwanta bacin safe, uban wa ya baki dama?. Malam yana karatun Al-qur’ani mai girma sai yaji kamar ana hayaniya jin maganan yayi yawa ya fito, yaji d’akin su Khadi ne da sauri ya sa kai cikin d’akin ganin Khadi ta fi luuuu zata fad’i yaje da sauri yana”Salati ya tare ta fad’a a hannunsa cikin k’unan rai ya d’ago ya kalli Gwaggo yace” in kin kasheta ae kin huta, kin san yarinya tana fama da Pneumonia kuma yayi mata yawa zaki kwara mata ruwan sanyi, haba hauwa anya kina tsoron Allah kuwa ae d’a ko ba kai ka haifeshi ba, bai kamata kina wula kanta ta ba.( Yan uwa mata kira gareku, kune jigon gida duk lokacin da gida yayi kyau kune, kusani Ya’ya da Dukiya, da Dabba ba’a mugun tar su. A rauwa ba kasan wanda zai taimake ba, sai kaga d’an da ka haifa da cikin ka wani lokacin bai jik’anka ba, wanda baka san zafin sa ba ya taimake ka kuma Ya’ya Rahmane dan Allah kuna kyautata ma yara ba sai naka ba ku d’auka duk d’aya suke a gunku). Gwaggo ko a jikinta tayi waje tana cewa”ni dai dole ta fito ta min aiki yau ko ta ji a jikinta. Malam ya kali Khadi ta idanunta suka kafe a sama da sauri ya d’auketa ya fita waje da ita. Beba da ta fito daga d’aki ganin halinda Adda ta ke ciki yasa tayi gun Malam da hanzari suka fita dake garin da sanyi da kyar suka samu mai Napep yace”Yaro Asibitin Murtala zaka kai mu, Malam da Beeba suka shigar da ita ciki suka d’au hanyar Asibitñ, sun d’anyi tafiya kafin suka iso asibitin, kud’in mai napep ya basa kafin ya d’auki Khadi suka shiga cikin Asibitin nurse suna hango su, suka tahoda sauri suka karb’eta. Emergency aka nufa da ita, Dr Abdul ke bakin aiki, da sauri “nurse suka sanar masa an kawo patient. Yace “ok! I’m coming now”. Bata dad’e da isa gun su Malam sai ga Dr Abdul nan ya iso. Dubata ya soma yi yaga tana wani yanayi numfashinta na shirin d’aukewa, tai makon gaggawa aka bata cikin ikon Allah suka samu numfashinta ya dai-daita. Magunguna ya rubuta ya mika wa Malam yace”Baba gashi kaje Pharmacy ka sayo, in ka dawo ka bawa nurse sai ka same ni a office d’ina. Malam ya amsa da rawar jiki ya nufi pharmacy. Taku a kulum mai k’aunar ku . ﺭﺍﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-21~25. Malam suna hira da Khadi Gwaggo ta fito wani sak’on kalon da Gwaggo ta aika ma Khadi, yasa ta mike ba sh’iri ta nufi kitchen ta d’aura girkin dare, sai da ta magama aiki Gwaggo tazo ta d’auke tukunyan d’akinta ta sh’iga dash’i duk abun da suke Malam na kalon su bai ce mata komai ba. A zuciyansa ya na mai jin-jina bak’in hali irin na Gwaggo, Malam ya mike ya fita waje zuwa gurin da suke d’aukan karatu. Rabi ce ta sh’igo tayi d’akinsu ta nufa ta dau naira goman Gwaggo tasa a wando ta fita waje, alawa ta siya sai da ta shanye kafin ta dawo gida. Gwaggo tazo d’aukan raina gomanta don a siyo mata sikari ta saka a surki, taga babu kud’i cike da masifa tazo ta danki Khadi tace”ke barauniya bani kud’i na da kika d’aukar min wato satan ma gadonsa kikayi a gun uwar ki. Khadi tace”Gwaggo ko d’akin ma ban sh’iga ba ina zaune a nan gurin fa. Gwaggo tace”oh! Sharri zan miki ko?. Ni a ya’ya na babu b’arawo ba mu gaji sata ba sai dai ko gun uwarki ne zuri’an barayi. Nan take Khadi ta soma hawaye jin takaicin yanda ake kiran iyayenta da suke kasa. Eyeh lalle kin samu gu dan ban dakaki ba shine kike kuka ko?. Gwaggo ta d’auko dorina tazane Khadi sai da taji hannu ta ya gaji tace”naira goman da kika d’auka a madadin abinciki na yau da kuma karin safiya. Gwaggo ta juya zata tafi sai ta dawo ta rike kunne Khadi tace”saura in Malam ya baki abunci ki karb’a ki gani ni dake yau a gidan nan. Ina son ana kiran Sallah ki sh’iga d’aki ban yarda ki leko waje ba, ina ga munanan kafarki a guri kin san sauran ta nufi d’aki. Taku a kullum mai k’aunar ku ﺭﺷﻴﺪ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-31~35. Malam ya sayi maganin dubu buyu da d’ari biyar ya nufo k’ofan Emergency ya mika ma nurse “Malam ya tambayi office d’in Dr Abdul nurse ce ta gwada masa, godiya ya mata nufi office d’in, da Sallaman sa ya tura k’ofar aka bashi izinin shigowa, Dr ya nuna masa gun zama Malam ya zauna. Sai da Dr ya gama yan rubuce-rubucen sa tukun ya d’ago da fuskansa tare da zare yar faran glass d’in da ke manne a kyakyawan fuskansa. Malam ya msa sannu da aiki,Cikin girmamawa ya amsa, kali Malam yace”Baba jikin Khadeeja yayi tsanani sosai, mai yasa kuke barinta tana aiki da ruwan sanyi?, kuma tana zama a inda ke da sanyi, mai ya kawo hakan bacin na sha fad’a muku illar hakan amma kun kasa koyayewa. Malam da jikinsa yayi sanyi yace”Dr in Allah ya yarda wanan karon zamu kiyaye fatan mu kawai yanzu ta samu lfy. Dr Abdul ya kallesa sosai tabbas ya gano damuwa a cikin idonsa ga alamar magana a bakinsa, amma tunda bai fad’a ba “ni dai zanyi iya kokarina ganin na taimaka mata, ya Allah kabata lfy ameen. Ya kalli Malam yace”shikenan zaka iya tafiya amma akula mata da shan magani. Kai Malam ya d’aga masa alamar eh!. ‘Dakin da aka kwantar ta ya yashiga Beeba ya gani a bakin gadon ta zuba mata ido ga alamar tayi kuka sosai. Da Sallama ya shigo Beeba ta masa sannu ya amsa tare da zama a d’aya daga cikin plastic chairs d’in dake d’akin. Yace”Beeba ya jikin Addah ki?. tace” da sauki amma har yanzu bata tashi ba, bacci take ya kalli Khadi yace”Allah ya baki lfy, cikin zuciyar shi kuwa cewa yake” ya zama dole in d’auki mata ki akan Gwaggo bazai yiwu Khadi taci gaba da wahala haka ba. Ya mike ya nufi k’ofar Asibiti ya sayo musu abinci ya dawo ya kawo musu nan Beeba ta karya, shima sama- sama yaci abincin. Gwaggo ne tafito daga bayi ta na zuwa d’aki taga ba Beeba ta duba d’akin su Khadi taga bata nan d’akin Malam ma baya nan, Rabi ta tambaya tace”kee ina Beebalo?. Rabi ta kalli ina tace” ba sun fita da Malam ba naga ya riko Adda Khadi, tsaki tayi ta leko titi basa nan, nan takama bala’i yau zaizo ya sameta akan me zai fita mata da yarta don wata marar galihu, ita yarta na galihu, cikin gida ta koma sai surutu take ita d’aya. WACECE KHADIJA?. khadijatu~Kubrah shine asalin sunan Khadi ya d’aya tilo ga Malam Adam. Malam Adam haifafen garin kano cikin unguwan Dakata gurin fire service. Yayan Malam Ahmad ne Ubansu d’aya ne. Tun Malam Ahmad na karami Allah yayi rasuwa Mahaifiyar sa, ya koma hannun Maman Adam wato Kakan Khadi kenan, ta yi musu rikon tsakani da Allah har suka girma. Adam shiya fara yin Aure kasan cewan shine babba sun shekara da yawa da matar sa Balkisu Allah bai basu haihuwa ba, sai daga baya ta samu ciki ya zo mata da laulayi haka tayi ta fama har tazo haihuwa, ta kwana biyi tana na kuda, kafin rannan ukun har ana shirin shiga da ita operation ta haihu ko juyawa batayi ba Allah ya karbi abunsa. Malam Adam yayi kukan rashin matarsa mai hankali da kirki, watan ta shida da rasuwa Baba Ahmad yayi Aure, ya auri matar sa Hauwa amma auren dangi sukayi yar kwan war Maman sa ne,(danganta karsu ta gun uwa kenan da haiwa). Hauwa macece mai masifa tun tana budurwa ta ki jinin Balkisu Maman Khadi ganin yanda Ahmad ke zama a d’akinta hakan yana bata haushi sosai. Cikin ikon Allah Khadi ta samu kulawa in ka ganta bazaka ce bata sha nono ba madara take sha bul-bul da ita ga ta da gashi ga kyau sosai, gwanin burgewa. Hauwa shekaranta 3 da Aure ta haifi yarta Beeba kar kuso kuga murna gunta, ta d’au son duniya ta d’aura ma Beeba, ta taso cikin kulawa ga hankali, in ka ganta sak Malam Ahmad kamar kakinta yayi, yarinya mai hankali da nutsuwa, jinin su ya had’u da Khadi tun Beeba na karama Khadi ke mata wasa komai ta samu zata kawo mata, amma in Gwaggo ta gani ta kwace ta yar ta daki Khadi, ana cikin haka wata ranan talata Malam Adam ya tashi da ciwon Ajali kwanasa biyar Allah ya karbi abunsa tun daga wannan rana Khadi ta dawo hannun Malam Ahmad da zama, nan Gwaggo ta samu daman galla za mata, sam bata kaunar ganin Khadi da Beeba sun zauna gu d’aya. ﺭﺍﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-36~40. Sam Gwaggo bata ‘kaunar ganin Khadik, da Beeba sun zauna gu d’aya. A kwai wani rana, da Khadi na wasa ma Beeba, Gwaggo na zuwa ta saka k’afarta ta shure Khadi, ta fad’i akan hannu ta, sai da ta gurd’e. Ranan ran Malam ba ‘karamin b’aci yayi ba, har sai da ya mari Gwaggo. Tun daga lokacin ta ‘kara tsanar Khadi, har zuwa girmanta, sam bata tausaya mata, duk aikin gidan Khadi keyi, Beeba kuwa bata son ganin Khadi cikin damuwa, in Gwaggo ta bata ma Khadi aiki, sai ta faki idon Gwaggo ta zo ta tayata su gama. Haka rayuwansu ya kasance dad’i da ba dad’i, Malam ya sanya su a Makaranta Khadi da Beeba suna ‘ko’kari, amma Rabee kam in ban da niman tsokana ba abunda take. A hakan har Khadi ta kammala Secondary school d’inta, ta barsu Beeba yanzu ke karatu har islamiya an yaye ta. Matsalar ta d’aya ne sam bata kula saurayi, ko sunzo Gwaggo koran kare take musu, wai baa su nimi mayya ba. Tana lashe zuciyar mutane, har ta lashe na Malam da yarta Beeba. Hakan sam bai damun Khadi,ita kulum da Malam addu’a su, Allah ya shiryi Gwaggo yasa ta gane. Wankin Gwaggo dana Ya’yanta Khadi ke yi, in tafara sai ta gama, bata isa tace”ta gaji ba Gwaggo zata fara mata bala’i, wani lokacin, abimci ma hana ta take. Back to lbr. Khadi bata farka ba, sai kusan k’arfe sha biyu, sai da Malam ya ga tasamu ta ci abinci, kafin ya musu sallama, akan zaije shi gd ya dawo, Beeba ta mishi adawo lfy, ya fita. Yana isa gd, Gwaggo ta taso cikin masifa, tana tambayar sa ina ya kai mata yarta?. Ko dun bai damu da ita ba ne, yana son wannan mayyar ta lashe mata kurwa, kamar yarda uwarta ta lashe zuciyan mutane. Sai da ta gama sababinta Malam bai bi ta kanta ba, abincin sa ya d’auka, ya fita tare da tabarma da pillow. Gwaggo na ganin ya fita, gyale ta d’auko ta fara binsa a baya, har taga ya nufi Asibitin Murtala, itama tace”ma me Napep su bi Malam, haka ko akayi, har ya shiga cikin asibitin, ta bisa a baya, har ‘kofan Ward d’in da aka kwantar da Khadi. Ta na labe taga ya shiga d’akin bai dad’e ba ya fito, ya nufi wani guri a cikin asibitin. ta na shiga, gadajen ta rink’a bi, har ta iso na su Khadi, wani mugun kalo ta sakar ma Khadi,da ke jin gine da pillow, tace”mayya kin lashe zuciyar mijina da yata, to bakiyi sa’a ba, tana zuwa kusa da ita, ta wanke ta da kyakyawan mari, nan take yan d’akin suka yi mata caaa. Kafin ka ce me, guri ya d’auka da hayaniya. Dr Abdul ne ya fito daga Ward d’in dake, kusa da na su Khadi, hannunsa rike da waya, da alamar waya yakeyi. A hankali ya ke tafiya, tun daga nesa ya ke jin hayaniya, yace”Dr Umar ina zuwa, naga kamar female ward na lfy, bai karasa ba ya iso gun hayaniya, yayi yawa, da kyar ya kutsa zuwa cikin gun, sam ya manta bai kashe wayar ba. Dr Umar shima bai kashe ba, dai-dai lokacin Malam ya iso gurin, ganin abunda ke faruwa ya soma jan Gwaggo da ta rufe Khadi da duka, sai zuba bala’in take. Dr Abdul ya iso yana “tan bayan lfy?. Gwaggo sai wani fin cikewa take, Malam ya d’auke ta da mari. Ta d’ago tana kalon Malam tace”ka mare ni a kan wannan banzan, mayyan mai kod’ade’en fuska. Ba zan yarda ba, sai na rama ta sake yin kan Khadi, itakam in banda kuka ita da Beeba sun rike juna. Dr Umar da ke jin duk abunda ya faro, duk da baya gurin amma ransa ya baci sosai, cikin zuciyarsa yace”duk da bansan maike faruwa ba amma wata irin macece haka?. Malam ya ransa ya baci mari ya sake wanke Gwaggo da shi, zafin yasa ta nutsu sosai, sai ta dawo ta fara jan Beeba, ita ko gadon ta rike, security aka kira suka fita da ita. Sai da guri ya lafa, Dr Abdul yace”Baba ka sameni a office d’ina ya fita, Malam ya nufi office d’in sa. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-41~45. Sai da guri ya lafa,Dr Abdul yace”Baba ka same ni, a office d’ina. Biyosa yayi, suka nufi office d’insa. Sai da Dr ya zauna, yace”Baba ka zauna, magana zamuyi da kai. Malam ya zauna, ya na fiskantan Dr, gurin shiru kusan, na minti biyu, kafin Dr ya nisa yace”Baba ina son in tan bayeka ne game da Khadija.miye alakarta da wannan matar? Kusan yawanci lokuta, in kun kawo Khadija ba ta da lafiya, matan nan sai ta mata abun da zai kunta ta. anya kuwa mahaifiyarta ce?. Malam ya nisa yace”gaskiya ba mahaifiyarta bane, Khadija yar riko ne a hannu mu, nan Malam ya kwashe tarihin Khadi, ya basa a takai ce, ba Dr Abdul ba, ni kaina Rash na tausaya mata.wayar sane tayi haske alamar kira ya yanke, d’agawa yayi, ya ga duration wajan awa d’aya da rabi, sai alokacin ya manta, bai kashe wayar ba. Dr Umar da ke jin, duk abun da ya faru da Khadi, tare da tarihin rayuwan ta, take yaji yana son tai maka mata. Ta bashi tausayi, da ace yana 9ja da ya san abunyi, kwanciya yayi, a lafiyayen gadon sa, fiskansa yana kalon silin, cike da tunani kala-kala, har bacci ya d’aukesa. Dr Abdul ya nisa yace”gsky Baba ya kamata ka d’au mataki, don yarinyan nan, tana yawan aiki da ruwa, ga wahala ya mata yawa. Malam yace”nagode in Allah ya yarda, zan d’au mataki, sallama ya masa ya koma, gunsu Khadi da har a lokacin, kuka takeyi sosai, ko da ya iso, ya kalleta cike da tausayawa, yace”Khadeejatu~Kubrah!, ki kara hak’uri akan na da, nasan ki mai biyyace, duk da Gwaggo tana cutar da ke, kuma kina hak’uri, ki ‘kara akan na da, kinji ‘yar albarka, kai ta d’aga masa alamar eh!. Sanna tace”Baba ka maida Beeba gida, tunda Gwaggi bata son zamanta anan. Murmushi yayi, yace”Beeba ba inda zata koma, har sai an sallame ki, Beeba ‘yatace nafi, Gwaggon ku iko akanta. Nan ya ta gaya mata kalamai masu dad’i, har ta mance da muwarta, dariya suke yi, ita da Beeban ta. Gwaggo ko da ta koma gida, taringa masifa da zage-zage, har Malam ya dawo bata daina ba, har tana cewa”kasake ni mana, tunda yarinyan ta lashe kurwanka, d’aki ya shiga, ya kyaleta ta gama sababinta. Kwanan su Khadi biyar, a cikin Asibiti aka sallame su, tun a hanya take far gaban, dawowa gida, don bata san dame, Gwaggo zata tareta ba. Dr Umar kuwa tunda yaji labarin,Khadi yaji yana son tai maka mata, yarinyan ta bashi tausayi. Wayarsa ya d’auka ya kira Dr Abdul bayan sun gaisa yace”ya aikin dai? Daga ban garen Abdul yace”Alhamdulilah! Aiki ba dad’i. hira sukayi sosai, Dr Abdul yake tambayar Dr Umar yaushe zaka kare course d’in nan?. Ajiyar zuciya yayi, kafin yace”saura wata shida mu gama, nima na damu in dawo 9ja, nayi missing abubuwa da yawa. Cikin zolaya Dr Abdul yace” harda Baby Sakina ko?. Mtss yayi d’an tsaki yace” ana ta kai, waya ke ta kaya. wannan mayyar yarinya, maras kamun kan, ina zan kaita?. Ae saninta ya fi nawa. Yauwa ranan wacece naji ana hayaniya akanta?. Rannan muna waya da kai, kamar a Ward d’in mata ne, sai da Dr Abdul ya d’anyi tunani kafin yace”ok! Khadijat ne, nan ya kwashe, labarinta ya basa. Dr Umar ba karamin tausaya mata yayi ba. Ya kuma kudiri aniyar, duk randa ya ganta cikin damuwa sai ya tai maka mata, duk da bai san ya kamani ta yake ba. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-46~50 Suna isowa gida, Beeba ta ba wa mai Napep kud’insa, ta d’auko su bargo, da pillow, suka nufi k’ofar shiga gidan. Khadi ta tsaya, Beebah ta juyo ta kali Khadi, Tace”lafiya naga kin tsaya?. Nan take idon Khadi ya kawo ruwan hawaye, tafara magana, cikin muryan kuka,”Beebah ina tsoron shiga cikin gida, don Gwaggo zata iya dukana, kinga Baba baya nan, Beeba ta kalleta cike da tausayawa, Tace”Addah muyi addu’a in Allah ya yarda bazata yi mana komai ba. Kalamai masu dad’i, da ‘kwantar da hankali, tayita fad’a ma Khadi, kafin ta yarda sukayi addu’a, tare da shiga gidan. Assalamu’alaikum! Gwaggo dake d’aki, tanata sababi, taji kamar muryan Beeba da sauri ta fito, har tana tuntube, tana fitowa taga su Khadi, wani uwar ashar ta narka mata, da kalon yau zaki sani. ‘Daki ta koma, ta d’auko wata zu’ke’kiyar bulalan ta, Gwaggo tace” yau sai na rama, marin da kikasa Malam yamin, kuma wahala yanzu kika fara, Mayya kawai, sam tsabar bala’i, bata lura da qofar window, dake bud’e ba, jikake Garamm Gwaggo ta gwaru da window, sai da ta fadi a kasa. Nan take, ta saki ‘kara, oh ni Rash nace”su Gwaggo ko d’an dauriya babu. Ihu take kamar qaramar yarinya, Khadi da gudu, ta iso gunta fiskanta, d’auke da hawaye, sannu take ma Gwaggo, cikin tausayawa. Gwaggo da ‘kyar, ta iya yin shiru, tana d’agowa kuwa, bakin ya kumbura sundum, ko danaga bakin, bansan likacin da nasaki dariya ba. Gwaggo d’aki tayi, ko magana bata iyayi, sabida bakinta, paracetamol ta sha, don ta ji sanyi ajikinta. Khadi kam d’aki ta shiga, ta takure gu d’aya. Tana cike da tunani, mai tasa Gwaggo ta tsane ta haka?. To mai iyayenta sukayi ma Gwaggo ta ke tsanar su haka, har ya shafeta?. Duk wayannan tambayan bata da amsansu, haka ta hak’ura, dan bata da amsan tambayanta. Gwaggo tunda baki ya d’anyi sau’ki, ta soma gana ma Khadi azaba, na yau daban, na gobe daban, wani saran da ta samu, in Malam nanan, bata cika gallaza mata ba, amma in Malam ya fita, Khadi sai ta gwammace kid’a da karatu. Khadi ta yanke shawaran samun Malam, Tace”Baba ina son, in fara zuwa gurin, koyan d’inki, yafi zaman da nakeyi. Malam ba k’aramin dad’i yaji ba, kuma hakan zai ragemata, yawan damuwa, sati guda ya nima mata, tafara zuwa, amma sai dai yana nesa da unguwansu. Gwaggo tayi bala’i ba ‘kadan ba, gani bata da mafita yasa ta hak’ura, tafara tunanin, sabon hanyan da zata, gallaza ma Khadi. Kwanaki sun tafi,Yau saura sati d’aya, Dr Umar ya kammala course d’insa, suna yawan waya da Dr Abdul. Khadi tana zuwa gurin k’oyan d’inkinta, gata da hazaka da basira, yanzu har ta fara had’a kayan yara, zata yanka da kanta ta had’a. Ganin haka yasa Malam ya sayo mata, keken d’inkin hanu, dontana, yan facin da sanda na mutane, tana samun biyar goma. Masu karatu karkuso kuga Gwaggo ranan, kamar zatayi hauka, dan bak’in ciki da takaici, Khadi kam kule kanta, tayi a d’aki, don Gwaggo tace yau ko ita ko Khadi. Fanz kumin hak’uri, na rashin jina, k’wana biyu, bama samun wuta ne. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-51~55. Gwaggo tun da taga Khadi, tana d’an samu a d’inki, hankalinta ya tashi, Gwaggo ta kudiri aniyar sai ta b’ata keken d’inkin. Beeba ko murna ganin Addah ta, tasoma iya d’inki yanzu zata bar kai d’inki, ana wulakanta ta, Gwaggo ko kulum sai ta zagi Beeba, akan yanda take, nuna zakewar ta ga Khadi. Haka rayuwa tayi ta tafiya, Khadi na cikin kunci da matsin Gwaggo, hak’uri takeyi da ita, kulum sai taci kuka, yanda Gwaggo ke zagin iyayenta.Yanzu har ta kai, yan’unguwa sunsan, Khadi yar riko ne a hannusu. In Gwaggo taga Malam baya gida ta hana Khadi zuwa gun d’inki, in makwabta sun kawo faci, Gwaggo ta korasu, ta hana su shiga cikin gidan. Khadi kusan sati bataje, gun koyar d’inki ba. Malam baya samun zaman gida, sabga sun masa yawa, gashi yau tafiya ta kamasa zuwa Jigawa, tunda asuba yatafi. Zaije ya sayar da Gona’nsa dake garin, don fara sayyan auren Khadi. Da wuri ta tashi tayi wanke- wanke’nta gama, ko karyawa batayiba ta d’au hijab da nikaf d’inta, ta fito cikin sand’a, takalmanta a hannu ta rike dan Gwaggi kartajita, cikin sand’ a ta fita, a qofar gida ta sanya hijab dinta. Sauri- sauri ta fara tafiya sai da tayi nisa ta duba jakanta, taga naira d’ari ya rage mata, Gwaggo duk ta amshe sauran kud’in. Mai Napep ta tsara, ta masa k’watancen gurin, Yace”tabada naira d’ari, nan tafara “rok’ansa ragi, da kyar ya yarda zai kaita a naira Saba’in. Ta shiga suka d’au hanya, ko da taje sai da mai koyamusu d’inki, ta mata fad’an rashin zuwanta, hak’uri ta bata.nan suka fara aiki har sai da karfe hudu suka tashi, din yau sun samu K’wangilan dinka uniform d’in wani school. Dr Umar ne ke waya, yana sanar da Mum d’insa zai da wo 9ja, girki na musamman Ummin sa ta masa, ko da jirginsu ta iso, driver ne da kanwarsa Iham sukaje d’auko sa. A hanya suke hira da ilham, yana tambayar ta, yan’uwa da abokan arziki, har suka iso gida, tun daga nesa nake hango securitys a qofar gidan, tabbas ko ba’a fad’amin ba, Umar d’an wani babban attajiri ne, ko mai mulki, don masu karatu, bazan iya tsara muku kyan gidan ba. Tundaga gate masu aiki, ke masa sannu da dawowa, har ya isa cikin wani falo, niko Rash ganin irin kyan gidan nace”bazan bari a bani labarin cikin gidan ba, da hanzari na sanya kaina cikin falo, yasalam masu karatu hmm wai in bakayi bamu guri, karkuso kuga cikin falon, sannu a hankali, nafara bin falon da kalo, komai na golden da brown ne, ko dana d’aga kaina wasu koyaye ne tamkar zinari, sai haskawa sukeyi a cikin falo. Gefe na samu na rab’e don yanda sanyin A.C ke bugani, ga wani sassayan kamshin da ke tashi, wata yar datijuwa ce, ta fito d’auke da fara’a, afuskan ta ta iso cikin falon, tana cewa”ur welcome my son. Cikin girmamawa yaje yayi hugging d’inta, yana fad’i” i miss u too my lovely mum. Kanshi ta shafa, tare da rike hannusa, my Son “muje ka watsa ruwa sai kazo ka ci abinci ka huta. Mikewa yayi ya nufi side d’insa, komai a canza masa na d’akin, wanka ya shiga, bayan ya fito ne ya nufi falo, nan ya cika cikinsa da abinci kala-kala, yana kammalawa kenan ya nufo falo, wani daga cikin security d’in yazo, yace”Oga kana tare da bako Dr Abdul, ya kalesa cikin girmamawa, Yace” barshi ya shigo ae ba bako bane shi d’an gida ne. Dr Abdul ne ya shigo, sai da ya gaida Ummin su Dr Umar, tukuna suka nufi side d’in sa, hira sukayi sosai kafin ya masa sallama, akan zasu had’u, sai da ya rakosa, har jikin motarsa yashiga sai da, Dr Abdul ya bar gidan, kafin ya koma cikin gida. Amin afuwa, har yanzu wuta bai tsaya ba, shiyasa kuke jina shiru. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-56~60. Yau kwanan Dr Umar 8 da dawowa, har ya koma bakin aikinsa, tun safe yake jin son yawo zai zaga gari, kuma bai son security ko d’aya yabisa, don shi daman bai cika fita da security’s ba, don Dad ke matsa masa baya son yana yawo haka, ko driver yana bari yana jansa, yana tashi a office karfe 3:30pm, gida ya nufa yayi wanka, yau sai ya tsinci kansa da son sanya jamfa, nan ya ciro wata shadda dark blue amata aiki, da surkin farin zare da blue, hularsa ma blue ce da surkin fari, ya d’auko ta kalminsa ya tare da agogo, tsayawa yayi a madubi, yana kare ma kansa kalo, gaskiya ya hadu ko ni Rash dana kalesa, sai da kirjina ya bada dumm, Umar mutum ne mai kyau ga kamala ga k’warjini, fari ne tass, yana da dogon hacci tare da karamin baki, kai in ka kallesa sai karasa da wani yare zaka danganta shi, India ne ko balarabe, ko Fulani. Tunda ya sauk’o falo falo, umma ta ga d’anta, sai murmushi take zubawa, tace”Baba na sai ina haka?. “Wananan wankan fa?. “Ko nayi surkace?. Don raboka da saka manyan kaya ka dade. Cike da murmushi ya kalli Umma, Yace” Ummana duk wannan tambayar ni kad’ai, bata surka Umma da saura tukun, zan dai zaga cikin gari ne. Cike da kulawa tace”Allah yasa futanka a samomin surka mai hankali da tarbiya, yar mutunci, cikin jin dad’i ya amsa da Ameen. Tace”Son Allah tsare a dawo lafiya, ka kuma tafi a hankali, to ya amsa ya fita, tun a harabar gidan ma’aikata ke masa sannu kud’i ya ciro a aljuhunsa wanda bai san nawa bane ya basu, ya shiga motarsa ya ja. Khadi tafe take, tana tunani yau ta kad’e, in cikin zuciyar ta tace” yau gashi malam baya nan, nikam na banu, bansan wani irin duka zata min ba. Hala yau kamma, k’wananane ya kare, nan tafara “Ya Allah ka yafe min, kasa na cika da imani, wasu hawaye ke bin fuskarta. Tafiya take sam bata san inda take nufa ba. Tsaban zance zuci, har ta hau kan titi, jama’ a dake hanyar sai kalonta suke, wasu na tausaya mata, gashi fuskanta da nikaf, jama’a na ta mata magana sam bata sani ba, bata ma san sunanyi ba,”wai kunu a wani gida”. Dr Umar na tafe a cikin motarsa, ya kuna qira’ar Ahmad Sulaiman, yana tafe cikin nutsuwa, ya wuce ran about baban gwari kenan ya d’auki hanya. Sam bai hangi yarinya ba, sai da yazo kusa ya ganta. Sai tafiya take a tsakiyar titi ga mutane sai kalota suke horn yayeyi da k’arfi, amma sam bata ji, gashi ya d’au gudu sosai, wani wawan burki da yata kane yasa dawo cikin hayyacinta, damar motan, ta gabanta ya tazo, suman tsaye tayi, dan tsaban razana ita bata fadi ba ita bata motsaba. Da sauri ya fito cikin motar, yana zuwa kusa da ita, yaga bata motsa ba ga idonta sun kafe, cikin dakiyar zuciya yave” ke lafiyarki klau kuwa kika hau kan titi?. Me kike tunani haka? Luuu yaga ta tafi zata fad’i cikin zafin nama ya tareta, ta sauka a jikinsa. Jijigata yayi yaga bata motsi, cikin sauri ya fincike nikaf dinta, sam bai ga fuskanta ba, juyaa yayi, ya kali wanda suka taru a gun, wasu na masa kalon mamaki, wani d’an tsoho yagani yace”Baba pls kazo ka taimaka min dan Allah. kamata sukayi, suka dawo da ita gefen titi, da sauri Dr Umar yaje da gudu ya bud’e motarsa, ya d’auko goran ruwa, yazo ya yayya fa mata, sai a lokacin ya kali fuskan, kasa d’auke idonsa yayi, yana furta”Sarki ya tabbbata ga ubangijin sammai da kassai, lalle ubangiji yayi hallita a gurin. a hankali tasoma bud’e idonta, tarass ta sauke su akan, Dr Umar da ya zuba mata na mujiya, ya kasa d’auke kansa ga fiskanta. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-66~70. Gwaggo cikin hayaniya da masifa, Tace”mai yasa baka tura, Beebah ko Rabee’atu, sai Khadi, to sai dai na k’ona kayan. Malam kasa magana yayi, tsaban takaicin dake damunsa, wannan wace irin fitinaniyar macece?. Gwaggo ta d’ibi kayan, tayi hanyan kitchen dasu, Malam na ganin haka ya bita, kafin ya isa, har ta fara sawa a wuta, kwacewa yayi tare da zaro na wutan, wani gyalens mai kyau, da sauri ya taka, da takalmin sa, wutar ta mutu. Wani gumun kalo ya mata, duk iskancinta sai da ta shiga taitayinta, ta fito a kitchen, koda tazo dai-dai gun Khadi shureta tayi da kafa, sai da Khadi ta fad’i, ta Beeba ne ta d’aga ta, rana mata sannu, Malam yace”Hauwa mai yasa baki da tausayi ne?. Kina tuna kema zaki mutu kuwa?. Ki sani fa duk inda, iyayen Khadeeja sukaje, kema zakije, kuma Allah baya kyaleki bane, kuma nima ba wai fa tsoronki nake ji ba, ina d’aga miki k’afa ne. Hauwa kisani ‘YA’YA DA DABBA, DA DUKIYA, BA’A K’ETAR SU, bakisan wacce irin baiwa Allah yayi ma Khadija ba, bakisana wani irin taimako, zata miki a rayuwan ki nan gaba. Gwaggo ta kali Malam cikin kalon da ban d’au maganar ka da muhimmanci ba, tace” ehehehe Khadi ne zata taimaken, ahir ahir, Allah ya tsare gatari da saran k’ota, ni da Khadi badai muzauna inwa d’aya ba. Malam ya kaleta yace”Hauwa da badun Allah bayason saki ba, to da yau tabbas sai kin bar gidana, kuma kinci albarkacin Khadi da ‘YA’AYAN da kika haifa. Koda Malam ya ambaci saki, sai da k’irjin Gwaggo bada sautin damm! damm!.. Amma cikin k’arfin hali, dake shaid’an ya mata kururuwa, tace”sai me in ka sakeni?.daman wani abu nake samu a gidanka, in banda gayyan tsiya. Malam ya d’aga hannu yace”Ya Allah kana jina, kana ganin abunda ke faruwa, Ya Allah ka azurta Khadi da abunda zata taimaki Hauwa’u. Yana dasa aya, Gwaggo tace” ba amin ba har abada, sai dai ku da wannan mayyan, talashe zuciyarku. Fuuuu Gwaggo takama hannu Rabee, tajuya ta kali Beebah, kee da ta lashe maki zuciya, saikiyi ta makale mata, suka shiga d’aki. Malam ya kama hannu Khadi, da Beeba ya kaisu d’akunsa, albarka ya samusu, ya musu nasiha, tare da k’ara bama Khadi hak’uri. Tace” Baba ba komai, ae Gwaggo uwatace, ita na bud’i ido na gani, ita na santa, kuma ina mata fatan Allah yasa ta gane Ameen ya amsa. Dr Umar kuwa, yana komawa gida, ya tarar da Mum d’insa, suna hira da Ilham, shima zama yayi, tare dacewa washh, Mum tace” daga ina haka Son?. Gyara zama yayi, ya kali Mum yace”daga gidansu Khadeejat nake. Kafin Mum tayi magana Ilham tace”bros nikam ina son gani Aunty Khadejat d’inana. Kulum sai labarinta mukeji, fuskansa cike da murmushi, yace”zaki ganta har sai kin gaji da ganinta ma. Mum tace” Alhamdulilah! Allah ya nunan ranan da Babana ya samu wacce yake so, sai fatan Allah ya kaumu lokacin biki, cike da zumu d’i ya amsa da Ameen. Dr Umar yace” Mum baki ga yarinyan bane, gata da hankali, kuma inkinji rayuwanta abun tausayi, nan ya basu labarin had’uwansu, da irin wahalan, su Mum da ilham sun tausaya mata. Ilham tayi karaf tace” bros to ina wacce katab’a ban lbr ta, itama wacce Khaji a agun Dr Abdul?. Ummm itakam har yanzu ba labarinta. Mikewa zai haura sama, yakali Mum yace”yau she Dad zai dawo daga Dubai d’in?. Umma tace” umm sai next week. Ok! Allah ya kaimu. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-61~65. Sai da ta dad’e kafin, ta d’an tashi, sannu suke mata, bata iya amsawa ba, sai da ta huta sosai, Dr Umar ya kaleta, cike da tausaya, Yace”yan’mata mai yake damunki haka?. Da har kike irin wannan tunanin?. Kasacewa komai tayi, sai da yamata fad’a sosai, Yace” ki tashi mukauki gida, sai a lokacin ta zaro ido, kai ta girgiza musu alamar a’a, bayanda basuyi ba, amma fir taki, daga k’arshe Dr Umar ya tsara mata Napep, nan ta bada kwatance gidansu, sai da tashiga Napep sun d’au hanyan, Dr Umar ma motarsa yashiga, har yayi hanyan gida, komai tuna ya juya kan motarsa zuwa Dakata, gudu yakeyi sosai, cikin sa’a ya hango Napep d’insu, a baya ya rinka binsu har suka kai k’ofar gida. Mai Napep ya tafi, ta tsaya a k’ofar gida, tana tunani shiga, gashi yamma tayi sosai, ga yunwan da takeji, da kyar ta iya shiga gidan. Ganin ta nufi cikin gidan ya fito daga motarsa yazo dai-dai zauren. Assalamu’alaikum ta fad’a cike da tsoro, kara shiga ciki tayi ganin Gwaggo bata kusa, da sauri Gwaggo ta fito,”kee karuwa yar’iska ina kika fito?. Cikin fargaba da zaro ido, Khadi tace” wallahi Gwaggo gun d’inki naje. “Karya kike dan ubakiki, dukanta Gwaggo tayitayi kamar ta samu jaka. Dr Umar tun daga, nesa ke jin murtan ta tana ihu, sai leke yaykeyi, zuciyarsa na tafarfasa, ganin Gwaggo ta d’auko muciya, Beeba da ke gefe sai kuka takeyi, tana bama Gwaggo hak’uri, Dr Umar dake cikin zaure, ganin Gwaggo, ta d’aga muciya zata kwada mata, bai san lokacin da ya shiga gidan ba, rike muciyar. Gwaggo cikin fushi, d’ago tana masa kalon raini, daga kai waye ne?. K’ok’arin fincike muciyar takeyi, Malam da ya dawo daga tafiya, yaji da sauri ya k’araso cikin gidan, ganin abunda ke faruwa yace”Hauwa mai kikeyi haka?. Nan fa tafara ba Malam labarin karya da gaskiya, ta d’aura dacewa”Khadi karuwa ce yar’iska, da sauri Malam ya dafe kansa, don harcikin zuciyan sa, yaji kalman ta dake shi. Cikin kunan rai, Dr Umar yace”wannan sharri ne wlh, nan ya kwashe abunda ya faru ya fad’a musu. Gwaggo nan ta tire, “sam ni banyarda ba, shine ya d’auketa suke iskanci tare, Malam ya mata kwalon uku saura kwata, hak’uri ya fara ba Dr Umar, tare da masa godia. Dr Umar yayi musu salma ya nufi gida, cike da jimamin rayuwan Khadi. Tun daga wannan ranan, Dr Umar yasamu gurin zuwa, gidan gun Malam susha hira sosai, wani lokaci Malam ya turo Khadi su gaisa, sam bainuna musu ko shi waye ba, kuma bai taba sayan wani abu ya basu ba. A hankali shak’uwa ta shiga tsakaninta da Dr Umar. Kamar kulum Dr Umar, yayi wanka cikin manyan kaya, yayi kyau sosai, sai da ya biya ta, Sahad store yayi sayya, kaya ya had’a ma Khadi, less da atamfa da shadda d’inkaku, da su takalma da jaka. A hankali yake tafiya, har ya shigo unguwan, cikin sa’a ya samu Malam na gida, sai da suka gaisa, ya bud’e boot din motarsa, buhun shinkafa biyu, na tuwo dana dafawa, sai taliya carton biyar da makaroni, harda su maggi star. Malam dake gefe, ya tsaya yana kalon ikon Allah. Sai da aka gama shigarwa, Yace”Umar mai yasa kayi irin wannan d’awainiyar, kai ya sunkuyar, Malam ae ba komai, kai mahaifi ne ae. Godiya yayi masa sosai, dai-dai lokacin, Khadi tafito Gwaggo ta aike ta, tazo wuce musu, ta gaida Dr Umar ya amsa cikin kulawa zata wuce, Yace”tsaya ki amshi sak’onki, don ina sauri yau, wasu manyan ledoji ya miko mata, Malam Yace” Umar d’awainiyan yayi yawa, bakomai Baba sauri nake, sai na dawo, godiya yayi masa Dr Umar yaja motarsa ya bar gidan, Khadi ne tafara shiga cikin gidan da laida, Malam na biye da ita. Gwaggo tana ganin laida a hannu Khadi, da sauri taso zata amsa, ganin Malam tace”yau samuwa mukayi haka?. Malam yace”eh! Wallahi wanda ya taimaka ma Khadi ne yayi mana alkairi, Gwaggo ta dafe k’irji lokacin ta zazzage kayan ciki, nan fa ta tsorata, “ae wallahi abunda bazai yuwuba kenan, wannan k’arya ne. Malam daman funa furci ka kula shine ka tsiri kai Khadi koyar d’inki, don kana son ta had’u, da wanda ya kawo kayan, mai yasa baka tura Beebah ko Raee’atu ba?. Sai Khadi, nan tafara tonan silili ma Khadi, cikin takaici Malam ke kalonta. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-76~80. Da sauri ya tareta, ta fad’a hannusa, sunanta yakira, Khadijat! Khadijat Khadijat… Pls ki tashi, kar ki tafi ki barni lokacin dana ke bukatarki, kene farin cikina. Pls Khadijat, yana jijigata, amma sam ko motsi batayi, Dr Umar ya fita a hayyacinsa, sai sam batu yakeyi, Gwaggo ko wani ruwan sanyi, tasake d’ebowa bata tsaya, wata-wata ba, ta k’wara ma Dr Umar. Duk da na da lafiya sai da ya razana, ajiyar zuciya ya sauke, nan take ya dawo cikin hayyacinsa, hannu sa ya kala, da sauri ya d’auketa, cikin mota ya sanya ta. Da gudu yabar unguwan. Asibitin Murtala ya wuce, yana zuwa ya d’auketa a hannu, Emergency yayi da ita. Kasancewar shi duty safe ke dashi, Dr Abdul ke duty kwana. Da sauri ya d’aga waya ya kirashi, “Dr Abdul dan Allah kazo Emergency, Khadija tace bata da lafiya, kazo ka taimka min, muryansa kaman zaiyi kuka, duk ya rud’a Dr Abdul, don bai kuma taba jin, Dr Umar cikin wannan, yanayin ba. Dr Abdul yace”Friend wacece Khadija?.cikin fushi yace”Malam in zakazo to in bazaka zo nakira, DR James, kashe wayan yayi, yafara kiran Dr Jame kenan, Dr Abdul ya turo qofar ya shigo. Da sauri yayi kanta, yana ganin Khadi ce, mamaki ya cikasa, tambayoyi yafara yi makansa,” daman Umar yasan Khadi ne?. “To mai yasa yarinka min tambayoyi akanta?. “Ta ya’akayi tazama Khadijansa?. Maganan Dr Umar ne ya dawo da shi, daga dogon tunanin daya shiga. Dr Umar Yace”kai Malam, lafiya kake mata, irin wan kalon?. Da sauri yazo ya kareta, cikin kishi da jin haushi, yake maganan. Dr Abdul bai cemasa uffan ba, cikin hanzari yasoma dubata, daman yariga yasan matsalanta, cikin ikon Allah, ansamu numfashin ta, ya dawo dai-dai. Sai dai bata farka ba, sun mata aluran baci, don ta samu hutu. Special room aka kaita, don hutawa ita kad’aine a d’akin. Dr Umar ya zauna, a bakin gadon ya zuba mata ido, ko kyaftawa ba yayi. Ji yake kaman ya k’arba mata ciwon, Dr Abdul ne ya shigo, yace”Ya mai jiki?. Da sauki ya bashi amsa. “Allah ya k’ara sauki. “In ka gama kasameni a office d’ina. Ok! Dr Abdul ya fita, office d’insa ya koma, ya zauna cike da tambayoyi, a fuskansa. Dr Umar sai daya kai, kusan kamar 1hrs, kafin ya kira nurse, yace”ta kulamasa, da patient d’insa. Da sallama ya shiga office d’in Dr Abdul, bayan ya zauna ne, Dr Abdul Yace”friend ina kasamu Khadi?. Ko dama ka santa tun-tuni, Dr Umar yace” kai ka santa ne?. Dr Abdul ya d’aga masa kai alamar eh!. Ajiyan zuciya Dr Umar yayi, nan ya kwashe labari, tunga randa ya fara ganinta, har yanzu, dayake fama da azaban sonta. Sai da Dr Abdul ya jijina kai, yace”Allah mai iko, to ae itace Khadijan, da ranan kaji ana case akanta. Cikin mamaki Dr Umar yace” mai kace ne ban fahimta ba. Nan Dr Abdul yabashi labarinta, iya yanda ya sani. Umar ya tausaya mata ba kad’an ba, wani Sonta da Qaunarta, suka k’ara shigansa. Cikin tsokana Dr Abdul yace” friend amma gaskiya, ka cika kishi, kawai don ina mata kalon sani, amma kawani tare, dariya Dr Umar yamasa, tare da kai masa dukan wasa. Malam dawowansa, daga kasuwa kenan, aka basa labarin, abunda ya faru bai iya shiga gidan ba, ya juya zai tafi kenan, yaga Beeba ta fito, duk ta rud’e hijab ma bai-bai tasa. Da sauri ta bisa, Napep ya tsara musu, suka nufi Asibitin Murtala. Zuciyan Malam sai tafasa yakeyi, yana tunanin wani kalan hukunci, zai yanke ma Gwaggo. Don abuntan yayi yawa,”to wai mai Khadi ta tsare mata a rayuwanta ne?. Da takeson ganin bayanta, tabbas zai Aura da Khadi, don ta huta da bala’in Gwaggo. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-71~75. Khadi kulum tana cikin k’unci, Gwaggo ta sata a gaba, baran in taga, Malam ya fita kasuwa. Gashi Dr Umar ya kwana biyu bai zoba, d’inki ma, tabar zuwa sabida bala’in Gwaggo, wai sai Malam ya saka su duka, don su Beeba su samu suma mai saya musu kaya. Malam ko yace”bata isa ba, tayi k’ad’an ta gindaya mishi sharad’i yabi. Tunda tun farko, Khadi ne tafara cewa tana so, dan haka ba zaisasu ba. Zaban tayar musu da hankali yasa Khadi ta samu Malam tace” Baba bana jin dad’i zan d’an huta da zuwa aiki, kafin wata sati, Tukun ya hak’ura. Dr Umar ko, bai da tunani da yawuce na Khadijat, so ya kemata, wanda shi kanshi, bazai iya auna shi, a mizani ba. Masu karatu zamu so musan, WAYE DR UMAR? Umar Adam Naira, shine cikaken sunansa, d’a, d’aya tilo girin Adam Naira. Adam naira haifafen d’an Kano ne, nan yayi karatunsa, har ya girma, ya Auri maransa Maryama, sun dade da aure, Allah bai basu haihuwa ba, sai daga baya Allah ya azurta su da haihuwan Umar, wanda yaci sunan Baban Mum d’insa, bayan shekaru da yawa, ta haifi Ilham, wacce itace auta, a yamzu haka. Alhaji Adam Naira yarike muk’amai, na gwamnati da dama. Wanda yanzu haka shine gwamnan Kano State mai ci. Ya kasance mutum ne mai kwatanta gaskiya da adalci, hakan yasa al’uman garin Kano ta Dabo suke sonsa. Tunda Umar ya taso, shi bamai son yawan, hayaniya bane, sannan bai kula yan’mata,sai wata yarinya, Sakina da ta makalemasa, sam bata cikin tsarinsa, don bata da kamun kai, yar’gidan, matai makin governor ne, gata da rashin kunya, shiyasa basa shiri. Yanzuma saukin da yasamu, ya dawo yasamu sun fita waje, ita da Mum d’inta. Iyayensa burinsu shine, yayi aure amma baya kula yan’mata. Tun randa ya had’u da Khadi, tunda yasanar da Mum d’insa, da murna ta, tasanar da His Excellency. Yayi farinciki ba kad’an ba. Yace” yana dawowa zasu samu iyayen yarinyan, ayi magana a sanya rana.wanna shine labarin Umar a takaice. Dr Umar zaune yau, sai tunanin Khadijat, da ya damesa. Key mutarsa ya d’auka, yana fitowa securitys, suka fara gaidasa, da gudu suka bud’e masa, k’ofar motan yashiga, gida ya nufa yayi wanka, dun zuwa gun Khadi. Yayi kyau sosai, ya shiga mota shi kad’ai batare da security’s ba, ya nufi gidan. Khadi ko tunda ta tashi, tashi tana son yin wanka, kayan da Dr Umar ya kawo mata. ta d’auko wani less, mai kyau purple da duwatsu farare a jiki. Tayi kwaliya sosai, ta kuma yi kyau. Kasancewan yanayi gari, da sanyi, gun sai yayi, bada yanayi mai kayatarwa. Gwaggo ta shiga makwabta, sai zuba take musu. Yaro ne yashigo”wai ana salama, da Khadijat inji Umar. Tace”kace ina zuwa. Yana fita ta d’auko hijab d’inta fari tasa, bakaramin kyau tayi ba. Cikin nutsuwa ta fito, tunda Umar ya hangota, zuciyar sa sai harbawa, ido ya k’ura mata. Gwaggo da tafito daga, gidan su abula, ganin Umar acikin k’atuwar mota, nan zuciyarta ya fara tafarfasa. Yau mai zanyi ma Khadi na huce?. Wata zuciya tace”kawai ki d’auko wuka ki burma mata. Mtss a’a za’a kamani, can shaidan ya tuna mata, kawai ki shek’a mata ruwan sanyi, tunda bata so. Da sauri ta koma gidan Abula, tace”dan Allah samin ruwan a fridge d’inki. Sam Abula bata kawo komai ba, ta iba mata, a karami roban plastic. Da sauri tayi gida, ta k’ara dana randa, kamar wata mahauk’aciya ta fito. Dr Umar ya shagala, da kalon Khadi, itako tana wasa, da yan’yatsun hannuta. Sai jin shaaa… sukayi, take idon Khadi ya kafe, numfashinta ya d’auke, ta tafi luuuuu zata fad’i kasa. Da sauri Dr Umar ya fito, yana kiran sunanta, tareta yayi ta fad’i a hannusa yana jijigata, amma sam bata ko motsi. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺗﻠﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-81~85. Malam sun isa Asibiti, direct office d’in Dr Abdul sukaje, Don tambayansa, ko nan aka kawo Khadija, don shi har yanzu, bai san a ina, Dr Umar yake aiki ba. Duk da yasan dai, shi likita ne, suna zuwa suka tarar da Dr Abdul a office, cikin yanayi damuwa Malam”ya gaidashi, ya tambayes ya aiki?. Alhamdulilah!, Malam yace”Dr dan Allah, ko nan asibitin, aka kawo Khadi?. Dr Abdul ya amsa masa da eh!. Barin rakaku d’akin da take. Sai da sukayi tafiya mai d’an nisa kad’an, kafin suka shiga, wani Ward mai kyau, kana shiga, falo zakagani babba, sai gurin da likitoci ke zama, gefe kum d’akin hutun likitoci ne. Sai d’akuna da suke jere, gwanin birgewa, gurin tsab da shi, kamar ba’a cikin asibiti ba. Kowani d’aki gado d’ayane a ciki, sai yar loka da ke gefe, Malam suka tura, qofar d’akin da sallamansu. Dr Umar ne zaune ya zabga tagumin gaban Khadi, sam bai masan sun shigoba, suka sake mai-maita sallama, amma shiru, Dr Abdul ne ya isa gunsa da sauri ya dafasa, yace”my friend, cikin razana ya d’ago, sai a lokacin yaga Malam, duk kunya ta rufesa. Mik’ewa yayi da sauri, yana musu, sannu da zuwa. Kalo d’aya Malam yayi ma Khadi, yaji wani mugun tausayinta, ya kamasa, tambayan kamsa yayi anya bayi da laifi, shima acikin cutar da Khadi, da Gwaggo takeyi?. Idonsa ne ya ciko da kwala, bakin gadon yaje, ya rike hannuta, cikin muryan damuwa, Yace”Khadijatu kiyafr min, duk nine silan saki, cikin wannan damuwar. Tabbas Hauwa watarana sai tayi nadama, mai d’umbin yawa, Allah ya miki Albarka, ya Allah kajikan Adamu. Duk wanda suke gurin saida jikinsu yayi sanyi, Beeba kam kuka takeyi sosai. Malam ya juya ya kali, Dr Umar yace”Umaru na rasa, da wani irin, kalma zan gode maka. Tabbas ka taimaki Khadijatu iya taimako, Allah ya bamu, abunda zamu saka maka dashi.Allah ya maku Albarka Cikin zuciyan Dr Umar yace”abida zaumin kad’ai kubani Khadijat, don zuciyata, takamu da azaban sonta. Gwaggo da ke gida, sai fatan take, “Allah yasa adawo, da gawan Khadi. Na tsani ganinta, kamar mayya, komai zakamata bata zuciya. Mtsss ina da daga nan, tashiga uwa duniya, in huta da fitinaniyan, yarinyannan. Ko da taji Beebah tabi Malam, sun tafi asibiti, bakaramin haushi tajiba. Tunanin kalan, rashin mutuncin da zan masu. Kwanan su Khadi, biyu a Asibiti, Dr Umar shi ke d’awainiya da su. Kulum yana hanyan Asibiti, yana tashi daga aiki bayan ya duba Khadi, shagon waya ya zarce, yasaya mata, iPhone 7, wayar ta had’u. Gida yanufa, yana zuwa, yayi wanka, ya fito dining, Iham ce tazo tazauna a gefensa, tana masa surutu, can idonta ya kyalo waya maroon, tace”bros wannan fa?. Tare da kai hannuta ta d’auka, “bros wayan tayi kyau, bai kaleta ba Yace”na Khadiyat ne, ihu tasa tare da cewa”wooow wayan tayi kyau. Barin samata number, nan harda WhatsApp, ta bud’e mata. Sai da yagama tukun ya amshi wayan yafita. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-86~90. Sai da yayi musu, sayya mai yawa, ya nufi Asibiti. Ko da ya shiga, sai da ya biya office dinsa, ya ajiye wasu files, kafin ya nufi ,d’akin da su, Khadi suke. Da sallama ya shiga, suka amsa masa. Beebah ne “ta gaida shi, cikin girmamawa ya amsa, “ya tambayeta ya mai jiki?. “Ba shi amsa da sauki Alhamdulilah!. Fita tayi ta basu guri, ya kali Khadi da ke kwance, “ta gaida shi, cikin muryan, marasa lafiya, “ya amsa mata, tare da tambayan ya jikinta?. ta bashi amsa da sauki. Ido ya zuba mata, har saida tasoma jin kunya, ajiyar zuciya ya sauke, ya kara lumshe idonsa, a hankali ya bud’esu, cikin wani salo, da karya murya, ya kira sunan Khadeejat!!!. Duk da rashin lafiyan da take fama dashi, sai da taji, jikinta yamata, wani iri,”Na’am ta amsa masa cikin siririyan muryanta. Ya kaleta, yace”Khadeejat!. Na kasa hak’uri akanki, Khadeejat!. Ki taimaki zuciyata, da take fama da azaban sonki, My Khady tun randa, na fara d’aura idona a kanki, nakamu da qaunar ki, ki taimaka in samu gurbi, a cikin zuciyarki. Duk maganan, da yakeyi Khadi, bata ce komai ba. Sai lumshe idonta datayi, kamar mai jin bacci, cikin kasa-kasa da murya, harda d’an sauk’owa daga kujera, Yace”pls Khadeejat ki taimaki rayuwata. Tabbas nasan ina aure ki, a matsayin mata, kuma uwar ‘YA’YA NA, nasan zasuyi alfahari dake, a matsayi uwa ta gari. Khadeejat!. Ki sani duk wani abunda akeso, mace ta gari ta had’a, kin had’a. Khadeey na!! I’m deeply in ur love,pla don’t let me go!! You d joy of my lyf, pls n pls Khadeey!!, ki samamin matsuguni, a zuciyarki, ko k’ad’an ne. Ganin shiru batace komai ba, Yace”Khadeetaul~Kubrah, in kin amince pls ko murmushi, kimin in samu sanyi, a zuciyata. Ganin shiru yasa yanayinsa ya canza, duk da idonta na rufe, tana iya ganinsa, amma shi bai lura, da hakan ba. “Wani lallausan murmushi ta saki, tare da rufe fuskanta. Ganin haka, ya sauke ajiyar zuciya, yayi godiya ma Allah. Juya masa baya tayi, duk yanzu kunyansa, ta soma ji, ya dad’e yana mata hira, ganin tana jin kunyarsa, ya ajiye mata waya tare da mikewa, Yace”yau k’anwata kunya na takeji, amma badamuwa, wataran zanyi maganin kunyan nan. “Ga wannan d’an ajima zamuyi waya, ya fita abunsa, a waje yayi sallama da Beebah. Ko da tashi go d’aki, lokacin Khadi ta mike, sai murmushi take zubawa, Beebah tace”Addah lafiya naganki cikin wannan fara’a?, cikin zumud’i ta labarta ma Beebah, itama tayi murna sosai,nan suka bud’e, kayan da yakawo musu, yasha addu’a kam, suna bud’e na waya, kalo ya koma kansa, sun yaba da kyan, wayan sosai. Sai can dare taji wayar na k’ara, ko da tad’aga wayar kasa d’aukan kiran, duk sun rasa ma ya’akeyi, Beebata tayi nata basiran ama ina! Har wayan ta yanke, sai can dai Khadi tace”tsaya inaga wannan, ruwan ganyen ne amsa kira, do d’azu jan ya katse ne. Tana jan ruwan ganyen, ta tafara jin magana. Assalamu’alaikum! Wa’alaikumusalamu! Ta amsa, sai tayi shiru, ” Khadeejat ya jikin?. “Da sauki Alhamdulilah!. Hira ya rinka janta dashi, har sai da yaji, kamar bacci na son d’aukanta, ya kyaleta. Kwanan Khadi 7 aka sallameta, tayi fress kamar batayi rashin lafiya ba, suna dawo gida, suka samu Gwaggo bata nan, suka shiga, harda Dr Umar ganin irin yanayi, d’akin da Khadi take kwana, ransa ba dad’i ya kira waya, ba’a fi minti talatin ba, sai ga mota da sabuwar Katifa, irin manyan nan, da filo da bargo, aka gyara d’akin fess, ya musu sallama ya tafi, ko da Malam ya dawo yayi godiya, ana haka sai ga Gwaggo. Yau kam ta cika kamar zatayi hakuka, don ba haka taso ba, taso a fitar da kayan amma Malam ya hana. Rayuwa sai tafiya yakeyi, soyayya tsakanin Khadi da Dr Umar sai abunda ya karu, kulum suna gaisawa da Ilham, harta sata a group d’in novel ta yi kawaye yanzu. Duk inda kake da jama’a, baka rasa yan gulma, acikin mukaraban, Dr Umar ansamu wanda ya sanar da Sakeenat, Dr Umar yana neman wata yarinya, yanzu haka ana kan shirin magana Aure, nan take hankalinta ya tashi, bashi ta biyo jirgi yau ta tazo 9ja. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-91~95. Karfe shidan yamma, jirgin su ya sauka, acikun garin Abuja. Bata bata lokaci ba, ta sake shiga jirgin Kano, ko da ta iso, anyi sallah magriba, ana shirin yin isha’i, taso yau taje taga yar gidan uban waye, Dr Umar ke sonta, kuma da me tafita da shi, da har zai aureta, tabbas yarinyan sai ta raina kanta, washe gari da had’a security dinta, wankan kece raini tayi, ta kira kawarta, Zulaihat tace”Zuly ki shirya kizo, zaki rakani, wani karamin unguwa, wai shi Dakata. Cike da tsokana Zuly tace”kawas mai zaki dakata acan, nan Sakeenat, ta sanar mata da komai, Zuly tace”ban minti kad’an ina zuwa ko ku biyo ku d’auken. Haka akayi, suka dauketa, cike da rashin mutunci a fuskokinsu. Khadi ko wanka tayi, sabi da tasan yau weekend, Ya Umar d’inta zaizo, tayi kyau kamar wata amarya. Suna tsakar gida suna tad’i’ ita da Beebah kasancewan, Gwaggo ta tafi gidan kawarta, shiyasa suka sami freedom yau. Tun daga nesa suke jin, wi wi wi wi, kukan jiniya alamar, wani babab yazo unguwan, har sai da aka zo qofar gidansu, tukun kukan ya tsaya, cikin mamaki suna jira suji maisu shigowa, Khadi tace”Beeba kardai police ne suka zo gidannan?. To wayayi laifi?. Tana wannan tunani ko taga masu bakaken kaya, suna shigowa cikin gidan, nan take hanjin cikinta ya kad’a. Sai da suka shigo, sun tsatsaya musu, wasu yan mata ne biyu, su ka danno kai cikin gidan, kalo d’aya zaka musu ka gane, sun san bariki, idonsu abud’e yake, ga fiskansu ta sha man bleaching. Cikin isa da taunar chewing gum, ta iso gaban su, sai da suka musu kalon, sama da kasa, kafi ta juya, ta kare ma gidan kalo. A tare suka kwashe da dariya, Zuly tace”kai yayan talakawa, a cikin ku waye Khadi ko Khadija, shiru ba wanda ya bada amsa. Cikin zafin rai suka sake magana, da kyar, Khadi tace” gani nice Khadi. Sai da suka kaleta sama da kasa, sai da gaban Sakeenat ya bmfad’i don sai yanzu ta lura da Khadi, tabbas yarinyan ta had’u, dole Dr Umar ya makance a sonta. Daurewa tayi, ta fara yi ma Khadi, “concrete warning, duk randa naji ance kin kula Umar sai na muki rashin mutunci, sai nasa an d’aureki, tabbas duk halin naka-naka ne, mai rashin kunya ma wataran yana da rana. Beebah da Khadi kasa magana sukayi, Rabee’at dake bacci a d’aki, hayanayi ya fitar da ita, jin yanda, aketa zaginsu, dana iyayensu ta karaso da gudu, ta kalisu Sakeenat, ta sama da kasa, ta nuna su da yatsa, tace”banza mai fiskan biri, kin wani sha bleaching, waye ke?. Da har zakina zagin iyayena, nan Rabee’at tashiga sauke musu, kwandon rashin kunya. Dr Umar yayi wankan sa ya nufo, gidan su Khadi, tun da ya shigo unguwan ya fara ganin motoci, har ya iso qofar gidansu Khadi, nan yaga security, gidan gwamnati, da sauri ya fito daga mota, ya kira wani body guard, tambayesa mai ya faru, nan yake basa bayani, Sakeenat ne a ciki, da sauri ya shiga gidan, dai-dai likacin da, Sakeena ta harzuk’o zata mari Rabee’at da sauri Khadi, ta shiga tsakanin su, sai jikayi tasss!!, karan saukan mari a fiskan Khadi, kafin ta motsa, sai nasojin wasu karan tass!! Tasss!! Tass!! Gar sau uku, Dr Umar ya mari Sakeenat. Ya juya ya kali security d’in, da sauri suka bar cikin gidan. Cikin fushi ya kali Sakeenat, Yace” kee waya baki izinin zuwa gidan nan?. Duk randa na k’ara, ganin k’afarki sai kinji ajikinki, ki kuma sani Khadeejat ta miki nisa, itace uwar ‘YA’YA Na, ita nakeso, itace rayuwa, farinciki na, in part rayuwata bazatayi dai-dai ba in ita, banza sakarya, ko ana soyayyan dole ne?. Nace bana sonki bana sonki, ba kuma zan soki ba. Cikin b’acin rai yazo, rik’o hannu Khadi yace”My wife kiyi hak’uri dan Allah, hannu yasa, ya share mata hawayenta. Ya rike hannuta, ya Sakeenat da bakin ciki ya isheta, kaman ta shid’e a gurin. Yace”kee Sakeenat! Kinga wannan ta fi minke komai, itace mahad’an rayuwa ta, tafiki kamun kai, da nutsuwa, in kin…… Da gudu ta bar cikin gidan tana kuka, wi-wi da hawaye. Tabbas yau taja ma kanta raini agaban, wayanda take takasu son ranta, yau Umar ya mata haka?. Tana fita mota tashiga, Zuly ma ta biyota, rake suka bar unguwan. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-96~100. Tana fita suka nufi gida, da gudu ta shige d’akinta, kuka ta rinka rusa sosai, Hajiyarta ne ta shigo, tace”Zuly mai ya sami k’awarki ne?. Zuly tafara bama labarin komai. Hajiya tanisa tace”Zulaihat ba ki ba ma kawarki, shawara mai kyau, tunda Umar baya sonta, sai ta hak’ura, ko ana son dolene, kusani a ko da yaushe mace, ita ke jan kimarta, nikam bazan goyi bayan k’arya ba. Kunutsu kusan mekukeyi kun fa girma fa, ae ko irin shigan da kukeyi, wazai so ku?. Inayi fad’a Abban su Sakeenah, yace nacika takura masu, ga irinta nan, nima ina goyon bayan Umar, matsawan ba canzawa kukayi ba. Kukan Sakeenat ya karu, sai buga k’afa takeyi, tana cewa”Hajiya ni baki sona, tunda bakison abunda nake so, “tsawa ta daka mata, ke bana son aakarcin banza da wofi fa, sai da tamusu ba dad’i, tukun ta bar d’akin. Dr Umar kuwa lallashin Khadi yayitayi, Gwaggo ne ta shigo da sallamarta, tun daga waje an fata rahoto, shiyasa take fara’a, tana ganin Umar, tace” eehehe duniya yau taimin dad’i, in dai a kanka ne, da Khadi naso da dukan tsiya suka mata, ka wani shigo mana gida d’an iska, wato karuwanka ne suka kasa hak’uri suka biyo ka nan?. Ran Umar in yayi dubu ya baci, don ba abuda yatsana kaman a danganta shi da mazinaci. Gwaggo ta zagesu tass shida Khadi, tayi d’aki, Beebah ko sai basu hak’uri takeyi, Khadi kam kuka takeyi, kafansa yaja jiki ba kwari ya bar gidan. Malam ya na dawowa ya samu labari, yajima yana tunani daga k’arshe, yace anya kuwa bazan dakatar, da Umar da zuwa gidan nan ba?. Haka ya ta sake- sake, har ya tsayar da amsa ma kansa. Bayan kwana biyu Umar yazo, tun a waje suka gaisa da Malam, nan ya fara ba ma Malam hak’uri, Malam yace”ba komai ya wuce, amma inaga ka hak’ura da zuwa kawai, tunda daman ba wata alaka bace a tsakanin ka da Khadeejat, cikin firgici ya d’ago, yanaso yayi magana ya kasa, Malam yajima yana zargin Umar na son Khadi, amma bai furta ba, shiyasa yayi hakan don ya tabbatar. Don zan bada dama ga mai sonta ya turo magabatan sa, ayi magar Aurenta kawai. Inaga hakan shine zai zame mata hutu, Umar duk ya rud’e, yakasa magana jiki ba kwari, yabar unguwan, gudu yakeyi Allah ne ya kaisa gida lafiya, yana zuwa ya tarar da Mum a falo, gunta ya nufa, ya kwantar da kansa, a kan cinyanta, sai ga hawaye. Cikin sanyin murya yace”Mum zan rasata, Mum ki taimaka min, pls dan Allah!. Cikin rashin fahimta Mum tace”wacece zaka rasata?. Ajiyar zuciya ya sauke, Yace”Mun Khadeejat ce, Mum tace”kamar yaya zaka rasata?. Nan ya kwashe labari, ya fad’a ma Mum komai. Tab lallae Sakeenat bata kyauta ba, amma ko da Dad d’inaka bai dawo ba zamuyi waya dole asan abinyi. A yan kwanakin nan duk Dr Umar ya rame, hakan yasa Mum, ta sanar da Dad d’insu, ko da sukayi magana dashi, yace”bazai samu daman dawuwa, a satin ba don haka zai sa mataimakinsa, yaje da kansa, Mum tace” ni a’a ban yarda ba, kasan Alhaji Bashir baya da sauki, akan yara , kawai inaga zamu nimi wani yaje, kuma kaga yanda yakeson Sakeenat, komai zai iya yi. Dad yace”shikenan duk yanda kukayi, Mum ta sanar da Umar komai yayi murna, sanna yace”shi yanaga a tura Baba Liman, don yana da halin dattaku. Haka ko akayi, Baba Liman yaje neman auren Khadi ma Umar, basu wani samu Matsala Baban Khadi ba ya amince. Nan suka zuba kayan mun gani anaso, da kud’in gaisuwa dubu 2k, Malam yaki karba yace sunyi yawa, amma Baba Liman ya dage sai da ya karba. Da murna yashiga gida, a zuciyar shi, yana mai cewa tabbas Khadijansa zata huta, don da alama Umar d’an manyan mutanene, kuma zai riketa da AMANA. da murna ya shiga gun Gwaggo, cikin zak’uwa takaleshi “Malam lafiya naga sai farin ciki kakeyi?. Hmm kedai bari kawai, ina cikin farin ciki, mik’omata su gidan goro da catoons d’in minti yayi, tare da d’aura mata damin kud’i akai, ido ta zaro su waje, “Malam wayan nan kud’in fa da kayan fa?. Cikin murmushi yace”na Khadijat ne, kud’in aurenta. Jakar uba! Ina bazai yuba, ina na Beeba ko Rabee’atu?. To ba a gidan nan za’ayi wannan abun ba, sai dai ko inda Beeba ne. Malam yayi dariya yace”Hauwa kenan wai meysa ba kya boye hassadanki a fili, ae ni na d’auka Khadi da Beeba da, Rabee’at, duk d’aya suke a gunki?. Allah ya sauwake, nawa-nawa ne. Kuma wannan auren bazai yuwuba, sai dai ko in zaka kawo na Beeba sai a had’a. Shikam dariya ta basa, don suk tagama fita a hayyacinta, ya d’ibi kayan ya kai d’akinsa. Khadi najinsu amma duk ta damu da taji wa Malam zai had’ata aure da shi?. Malam ne ya shigo d’akinta, ya zauna a kujera, cikin nutsuwa ya kira sunanta, ta amsa, sai da yamata nasiha, kamar yanda ya saba, tukun ya saida mata, Umar ya kawo kayan ,yagani yana so, ina fatan kin amince kina sosa?. Shiru tayi, daga yanayinta ya gane ta amince, albarka ya samata ya fita. Washe gari Dr Umar yayi wanka sa, yayi kyau sosai, sai da yabiya Sahad ya mata shooping mai yawa, tukun ya nufo gidan, yaro yasamu ya aika ta fito. Cikin nutsuwa take takawa, tana sanye da hijab ash yamata kyau, hannu tasa a aljihu yana kare mata kalo. Da sallama ta karaso bayan sun gaisa, yace”gimbiya Khadeejatu, murmushi tayi yace kali nan, tana d’ago fuska ya kashe mata ido d’aya, tare da d’aga mata gira, duk sai taji kunya ya kamata. Haka sukayi hiransu a zaure, sai dab zai tafi ya d’ebo mata, kayan saya mata, godia ta masa har zata tafi yace”tsaya barin yi surprising d’inki, murmushi tayi. Yace” pls close ur eye, ba musu ta rufe, ” miko hannuki, bata komai ba ta mika masa tana murmushi, wani zobe ya ciro sai kyali yakeyi, ya sanya mata a hannu, nan take hannuta ya d’au kyalu yana haskawa. Kiss ya kaimta a hannu, sai sukaji, la ha ila ha illalahu, uhu jama’a da sauri Gwaggo ta damke su duka. Ta kwalala jama’a ku kawon d’auki na kama yan iska yau. Ihu take kamar mahaukaciya, Khadi ko duk jikinta sai bari yakeyi, nan take hawaye ya fara zuba, Umar ko don takaici kasa motsi yayi. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: ’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-101~105. Cikin takaici ya fincike rigansa, kalon tsana yake mata, da sauri Gwaggo ta sha gabansa, yau fa sai na tona muku asiri. Wani mugun kalon da ya aika mata, yasa Gwaggo bashi hanya, Khadi da gudu tabar gun. Gwaggo ta ga kayan da Dr Umar ya kawo da rawar jiki ta d’iba tayi cikin gida. Beeba na ganin haka tace”Gwaggo mai yasa keke ma Addah Khadi haka?. Gwaggo cikin zumud’i tace”kee bari kawai ae ido da ido na kamasu suna iskanci, cil da cil ganin annabin tsohuwa. Beeba tace”kai Gwaggo gaskiya Adda Khadi bazatayi haka ba, zata taba zubar da mutuncinta ba, kuma na yarda da tarbiyan da Malam ya bamu. Cikin b’acin rai Gwaggo tace”oh to! to! Wato Malam shi ya kula da tarbiyan ku bani ba?. Beeba shiru tayi ganin Gwaggo ta d’au da zafi. Malam na dawowa Gwaggo da munafurci tazo ta fara labartawa Malam, Malam ya kaleta sama da kasa yace”tashi ki ban guri bana son gulma, a yanzu a kwai wani abunda zaki fad’an na yarda, bacin nasan irin tsanar da kikayi ma Khadija, yarinyan mai hankali, bataji ba bata gani ba, kna gallaza mata, jiki ba kwari Gwaggo ta bar d’akin. Dr Umar ko hankalisa kwance ke gudanar da aiki, yanzu Dad d’insa kad’ai ake jira a kawo sadaki, sai asaka ranar biki. Sakeenat kuwa sam Mum d’inta, taki goya mata baya. Hankalinta duk ya tashi, can ta tuno wata shawara, Zuly ta k’ira a waya. Tace” kqwara kina ina ne yanzu?. Zuly tace”gani a hanyan zuwa gidan ku. “Ok sai kin iso. Ta ajiye wayar tana zaman jiran zuwan Zuly. Ko da Zuly tazo bayan ta gaisa da Hajiyar Sakeenat, tashiga gun Sakeenat, bayan sun zauna Sakeena tace”kawa nifa bazan share mari da Umar ya minba gaskiya. Zuly tace”wani mataki zaki d’auka?. Sakeenat tace”na bayar a sayo min dorina hud’u masu kyau, zamuje unguwansu ba tare da securitys ba, in munga yarinyan ko mu aika tazo sai mu cazata.Zuly tace”good idea, haka zamuyi. Key motarta ta d’auka suka fita,nan idi security ya kawo mata sak’onta, ta karba suka ja mota sai Dakata. Sun dad’e a unguwan Khadi bata fito ba, can da suka gaji yaro suka tura yaro ya kirata, Khadi ko kamar bazata fito ba, amma can da yaron yasake dawowa, ta d’au hijab d’inta tace”Beeba ana kira na a waje barin duba ga wayata nan. Khadi na fitowa yaron yace”gasu can a wancan motar. Khadi tana ta raba ido, don Umar bai tab’a zuwa mata da irin motar ba. Sakeenat ko suka rike bulala kowa ne bibiyi a hannusu, sai da Khadi tazo kusa suka bud’e motar atare, suka nufota da gudu dukanta suke tak’o’ina. Khadi ihu take amma basu kyaleta ba, Beeba taji kamar muryan Khadi da gudu ta lek’o ganin ana dukanta, koma gida “Gwaggo dan Allah kizo, yaran ranan suna dukan Adda Khadi, Gwaggo tace”ha da gaske Beeba tace”eh!. Duka suka fito da gudu. Dukanta ko suke Gwaggo ta fara kukara mata, kunyi min dai-dai. Rab Beeba ya b’aci sosai, ganin ba mai ceton Khadi, gashi ba maza a gun, yasa ta tuna da Dr Umar. Da sauri ta duba call history, ta kira number, bugu biyi yad’aga, “hello hello Ya Umar kazo ga wasu na ta dukan Adda Khadi, wanda suka zo ranana. Cikin figici yace”what suwaye?. Kashe yawar yayi ya shiga mota gudu yake kamar zai tashi sama. Sakeenat ko ganin sun mata lilis, ga mutane sun soma taruwa da gudu suka shiga mota, suka bar unguwan. Dai-dai zasufita a layi motar Dr Umar yadanno kai ganin motar Sakeenat yasa yasha gabanta, ganin zai tsaresu yasa taja motar da k’arfi sai da ta buge masa glass d’in mota ta gudu. Da har zai bita sai ya tuna kowani hali Khadi take kuma?. Sai ya fasa ya kara gudu. Beeba ko ganin sun tafi dakyar wata makwabciyar su, ta taimaka mata suka shiga da Khadi gida. Karkuga fiskan Gwaggo fal farin ciki. Dr Umar na zuwa yaga mutane, da gudu yayi salama ya shiga gidan, Beeba ya fara karo da ita cikin damuwa ke tambayrta ina Khadija?. Hawaye ya k’ara zubowa “tana d’aki a kwance. Yana shiga yaga halin da take ransa ya b’aci sosai. Ya kira beeba yace” ki had’a ruwan zafi don tayi wanka, waya ya kira ba afi minti goma ba sai ga wasu ma’aikatan asibiti da kaya, da kanta yamata treatment, ya mata allura nan take bacci ya d’auketa. Yana fitowa yace”sistet Beebah barinje gida na dawo. Na mata allura ta samu bacci, in ta tashi ki kaimata ruwa ta watsa zataji dadi. Yana zuwa gida yasanar da Mum d’insa komai, cikin bacin rai takira His Excellency yana d’auka, tace” ranka shidad’e! Ya aiki?. Cikin jin dad’i His Excellency ya amsa. Nan ta sanar masa da komai, sai da ya jin-jina al’amarin yace”tun da Baba liman nanan zan sa a tura 1million sai akai sadaki, 2millions kuma a had’a kaya akai. Ina dawowa sai aure kawai. Mumcikin farin ciki tace”Allah ya ja kwanan mai girma governor, godiya muke Allah ya tsare mana kai, Ya amsa da ameen. Malam ko da ya dawo ransa ya baci, amma yace”duk hakan baza’a fasa auren nan ba sai anyi, duk mai hassada sai dai yayi ya gama. Dr Umar ko kulum sai yayi sawu 3 a gidan kula ta musamman ke ba Khadi. Yau da yazo bayan sun gaisa da malam ya saida masa “iyayensa zasu zo, za’a kawo sadaki. Malam yace”Alhamdulilah! Allah ya kawosu lafiya mungode. Washe gari Baba liman yazo ya kawo sadaki, Malam sai da ya razana, kin karban kud’in yayi yace”gaskiya Malam sunyi yawa a rage. Baba liman yace”sam bazan koma da ko si-si ba, mudai fatan mu Allah ya sanya alkairi. Baban Khadi ganin Malam ya girmesa, kuma bazai iya masa musu ba ya sa hannu ya karb’a. Yana shiga gida don ya ba ma Gwaggo haushi yace”Hauwa kawo min taburma nan kizo kiga ikon Allah. Da sauri Gwaggo ta fito har tana tun-tub’e, ta shin fid’a masa tabarma bayan ya zauna sai taga ya zaro da min kud’i har bunch biyar, ido Gwaggo ta zaro, “Malam ina kasamu wanna kud’i?. Murmushi yayi yace”Hauwa wato zakaran da Allah yanufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi. “Kuma d’an hakin da karaina wataran sai ya baka mamaki. Gwaggo tace”ni dik ban gane hausanka ba Malam?. Malam yace”hmm Sadakin Khadi aka kawo har naira na gugan naira million d’aya. Wayyo nashiga uku sadaki ina Malam d’an yankan kai ne ba fa zaiyuba. Nima sai ka samo ma Bedba miji, Gwaggo ta sha kwalan Malam, ihu take tana kuka, tana fad’in ya cuceta. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: ’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-106~110. Gwaggo ta sha kwalan malam sai ihu takeyi, ya sa hannu ya ban-bare rigansa, yazo zai wuce ta sake shan gabansa, “yaufa bazaka fita agidan nan ba, yau saika kawo ma Beeba miji. Ya matsa tabisa yazo zai shiga d’aki ta tare qofar, sai ya tureta yazo fita ya iso zaure, tazo da gudu ta kama rigansa saida ta yaga. Ran Malam in yayi dubu ya b’aci bai san lokacin da ya kikifa mata mari ba, ya hankad’ata ta fad’i akasa. Yace”Hauwa hassadakin bazaikai ki ko ina ba, wannan aure matsawan in ima raye ba fashi, sai dai ki mutu da bakin ciki. Ya juya ya nufi d’aki ya canza kaya, yazo ya wuceta, har ya fita ya dawo yace”kuma wallahi in kika kuskura kika tab’a Khadija, a bakin aurenki saki zan miki ba dawowa, kina dukanta kin san sauran, Yasa kai ya fita. Gwaggo abun duniya ya isheta, tabbas Malam tun da ya rantse sai ya aikata, jiki ba kwari ta koma d’aki tafara kuka, cikin zuciyarta ko cewa take”wanna mari ba zai sha banza ba tunda yace karna daketa, to ae dole tayi aikin gida, dan haka ba duka akwai zagi da wahala yankuma. Khadi tana d’aki kwace, tana group chatt da kwayenta, wanda suka had’u a WhatsApp ta lura suna da hankali, shiyasa nasu yazi d’aya. A group d’in Khaleesat Haiydar suka had’u na Facebook dake Khadi mayar karatun novel ne. Hiran Novel d’in KAINE SIRRI NA littafin Aisha Muh’od, Queen Neenah tace” Khadeejat kin karanta KAINE SIRRI NA? khadi tace”eh ina karantawa kai, gaskiya novel d’in ya had’u. Farhat B Haske tace” Queen Neenah n Khadeejat kun karanta MARTABA TA da MATAR MUTUM na Mrs Umar Soja kuwa?. Sukace “a’a bamu karanta ba. “Lalle an barku a baya ni harna gama karantawa, yanzu ina karanta YAR WAYE NE?.na Khairat S Panisau, da KUDAN ZUMA na Zee Hrt. Suka had’a baki tare da cewa”Farhat littafin ya had’u ne?. “Eh kai ana rikici kam, ku tamabi. Hajiya Jamila Aliyu Haiydar tana dashi sai ta tura muku. Queen tace”Khady bari na nemomana zan tura miki ina samu. Khady tace”ok amma fa nagode. Farhat B Haske tace”gaskiya ya kamata yanda muka saba musan juna, gashi mun shaku sosai, ae zumuncin bai kamata ya tsaya a chatt ba. Queen Neena tace” ae fa gaskiya kam, yanzu musa rana sai mu fara zuwa gidansu Khady. “Ko ya kuka gani yan’uwa?. Duka suka turo da haka za’ayi. Khadi taji dad’i amma tana tunanin yanda zasu zo Gwaggo zata iya cin musu mutunci. Salama sukayi akan ran Friday za’a had’u, a gidan Hajiya Jamila Aliyu Haiydar sai su taho. Gwaggo tana gama sake-sakenata tafito ta kwala ma Khady kira, “fito dan ubanki, mai fiska kaman na biri, kin lashe wa mijina zuciya kin rabani da yata, gashi kin samu d’an mutane, kinsa yayi sata sun kawo kud’in aure ko?. “To ni kam dai ahir d’inki. “Kurwata kur bazaki iya ci ba. “Ko uwarki ma haka tagaji ta barni don nafi k’arfinku. Nan take idon Khadi yaciko da kwalla. Gwaggo ta tattaro wanke-wanke ta tara mata, tashiga d’aki ta d’ebo kaya harda wankaku, duk ta had’a mata. “Maza-maza kiyi ki gama su yanzu, ki kuma tabbatar an girkan abicin kar yayi dare. “Kin san halina basai an fad’a maki ba aha. “Ni ce Gwaggo Munguwa No1, in kika kuskure min a aiki sai na miki ba dad’i, tsohuwar mayya kawai. “Mai son raba aure, amma kuma bazaki iya ba sai dai a fasa naki. “Kuma ina kan bincike duk randa na gano gidan saurayinki, sai naje na had’a duk wata manakisa ta, an fasa auren. Niko Rash”nace Gwaggo rashin sani yafi dare duhu, da kimsan Umar d’an waye da baki fara masa rashin mutunci ba, don yafi k’arfin raini. Khadi ta dunkufa aiki baji ba gani, duk da ta gaji amma bata son ta nuna bare Gwaggo ta zagi iyayenta, don yafi komai cin mata rai. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: ’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-111~115 Aiki sosai tayi, Gwaggo tana fita makwabta, Beeba ta fito tafara tayata aiki, Khadi tace”Beeba da kin bari nayi, yanzu in Gwaggo tazo ta samemu, ni zata zaga uwa ta uba. Beeba tace”karki damu Adda yanzu zamu gama aikin, Rabee’a ta fito sai mika takeyi, alamar daga bacci ta tashi, kitchen ta wuce ta duna tukunya, taga an kusa gama abinci, kwano ta d’auko ta d’iba. Beeba tace”Rabee wani irin iskanci kikeyi ne, kina kalo muna aiki amma kizo ki d’ibi abinci?. Baki ta murgud’amusu, Khadi tace”kyaketa Beeba, kinsan Gwaggo na dawowa saita huce a kaina. Aiki sukayi cikin ikon Allah dake, duna da zafin nama basu dad’e ba suka gama. Khadi ta raba musu abin ci suka ci, Gwaggi na dawoa tayi mamakin yanda Khadi ta gama aiki da wuri, d’aki tashiga kwano ta fito da shi, ta turo ma Khadi ga wannan masaran kina gama cin abimci ki surfa min shi, don yau surfen hannu nake so bana inji ba. Cikin girmamawa tace”to Gwaggo”. A gajiye tayi surfe ta gama ta wanke ta shanya shi. Yau takama jumma’a yau ne su Hajiya jamila da Queen Neenah zasu zo, yan kud’in da ke Hannuta ta had’a ta siyo kaya ita da Beeba sukayi girki. Ware dubu biyu zata basu kud’in Napep, ta gyara ko ina sukayi wanka ita da Beebah, sunyi kyau sosai. Gwaggo na ganin Khadi ta fito tace”mayya inda kinga fiskanki da bazaki na yawo cikin mutane ba. Rabee ta mata kalon sama da kasa, sa’a d’aya Gwaggo bata sasu aiki ba. Sai kusan karfe biyar, su Farhat suka kira waya, Khadi ta d’auka da “sallamanta kun isone?. Farhat tace”eh! Gamu a dai-dai gun fire servise”. “Ok gani zuwa”. Ita da Beeba suka fita, suna zuwa kuwata gansu, da murna suka tari juna, farhat tace”ikon Allah yau Allah yayi zamu gana. “Eh wallahi sannu ku da zuwa. Su hajiya Jamila tace”wanna itace Beeba ko?. Khadi ta amsa da”eh! Itace, har kin ganeta. Suna hira suka shigo da sallama. Gwaggo ta musu kalon sama da kasa, Khadi ko sai addu’a takeyi, d’akin suka kai su. “Gwaggo ta kwala ma Khadi kira” ta amsa da “na’am gani zuwa”. “Kee dan uwarki ina kika samu wayan nan?. Ko maitan ki ya dawo har gida kike lashe mutane?. “Kiyi hak’uri Gwaggo kawaye nane fa”. “Eyeh har wani daman kawaye kika samu”. “To yau zaku ci ubanku daga ke har kawaye”. “Dan Allah Gwaggo kiyi hak’uri ki bari in sun tafi kimin duk abunda kikeso”. “Kee ko uwarki bazata ban doka nabiba, bare kee yar karamar kwaro”. “Assalamu’alaikum Malam yayi sallama”. “Khadi ta amsa” Yana daga qofar d’akinsa yace”Khadejatu! ” Ta amsa da “na’am Baba”. “Maza kizo nan” Gwaggo cikin takaici ta ja tsuka. Sam bata so haka ba, taso saita wulakanta Khadi Malam ya dawo. Da sauri Khadi ta nufi gun Malam, da sallama tashiga d’akin, tsugunawa tayi tace”sannu da dawowa Baba” Cikin fara’a ya amsa da”yauwa d’iyata, naji dad’in ganin ki, a cikin wannan yanayi” “Ya jinin yau fatan lafiya ko?. “Eh! Lafiya lau, ga kwayena ma sun zi gaida mu yau”. “Ah madalla mun gode, in zasu tafi ki fad’amin”. “To baba” Da Murna tayi d’akin ta nan tayi sannu nasu Hajiya Jamila, Beeba ko har tayi serving d’insu. “Tace muje ku gaida Baba na” dukansu suka mike har qofar d’akin Malam sukaje suka gaida shi, ya sanya musu Albarka. Gwaggo ma tafito daga d’aki duka k’ara gaidata. A dakile ta amsa, suka koma d’akin Khadi, hira sosai sikayi, kafin suka mike zasu tafi don magriba yayi. Ta d’ibi kayan kwaliya, da sabulai, acikin wanda Dr Umar ya kawo mata, da turaruka tasamusu a laida. Sun fito Malam ya kirata yace”ga wanna kibasu su hau adai-daita. Ta karba ta “sukuma sukayi godiya”. Har bakin titi suka rako su ta mika musu tare da musu alkawarin zata zo ita da Beeba. Bayan kwana biyu Khadi na zaman hak’uri, kulum da kalan horon, da Gwaggo ke mata. Ana haka kwanwar Gwaggo da yaranta suka zo mata kwana biyu, kulum cikin kunci da matsi take, itaji sanyi to tana tare da Malam ko Beeba ko Dr Umar. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: ’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-121~125. Gwaggo ta buga k’irji tace”nashiga uku, anya kuwa ba Khadi mu bane. Matar tace”nan gidan mana”. Innna Yalwa tace”sannuku da zuwa ga gurin zama”. Cike da fara’a suka k’ara shigowa. Nan fa aka shigo da akwatuna, ko da aka shin fud’a taburma, hmm akwatuna bazai yiwu a bazasu, a tsakar gidan ba. Inna Yalwa tace”yan’uwa yana da kyau, kafin mu fara bud’e kaya, muyi addu’a Allah ya sanya alkairi, ya kad’e fitin-tinun dake ciki, ya kuma kawar da idon mahassada da makiya, dazasu kawo farmaki ma auren nan. Gwaggo tace”kee Yalwa wa zaiyi hassda ko makiyi nasan dani kikeyi, nan Gwaggo ta fara kwala, ko ta kanta basu bi ba, sukayi addu’a aka fara bud’e kaya. Yasalam masu karatu karkuso kuga kayan yawanci ready made ne, ga tsada, ko da ka zo kan takalma duk gulma na, na kasa k’irga yawansu, jakukuna da poss ba’a magana. Ko da aka bud’e na d’ankunaye hmm gwala-gwalai da fashion masu tsada, ga manyan balguls ba a cewa komai, can idona ya kyalo wani karamar a kwati acikin kayan, da sauri Inna yalwa ta d’auko, tayi-tayi ta bud’e amma ta kasa, wannan matar ne tace”kawo ki gani, tana tab’a qofar akwatin yafara k’ara sauti mai dad’i gashi da k’arfi. Tana bud’ewa yace Hello My Master, cikin wata tausasashiyar murya na mata, kai ka d’auka a fili mutum yayi wannan maganan ba. Wata mata da ke gefe, tace” a kula da wannan a kwatin, don White Gold ne a ciki, yana da matukar tsada sosai, kud’insa ya kai miliyan uku a kud’in 9ja. Inna Yalwa baki har kuni godia suka fara musu, sai suka d’auko d’an kayan da suka had’a musu suka mik’a. Inna Yalwa da dubu biyar a jikinta, ta k’ara musu yadawo 15k. San suki karb’a sai da su Inna Yalwa sukace”ko kun rainane?. Da fara’a sukace”a’a Allah ya sanya alkairi, wane mu da raina kyautan da zata fito, daga gidan surkan Gwamna, matar d’ansa d’aya tilo. Inna Yalwa cikin rashin fahimta tace” umm Hajiya bam gane kince Surkar Gwamna ba?. Matar tace” eh ko bakusan cewa Umar shine d’an Gwamna d’a d’aya tilo na miji. Inna Yalwa tace”sam bamu sani ba ya ma b’oye mana ko shi waye”. Take matar ta war-ware musu, aikafin ta rufe baki. Gwaggo tasaka ihu ta hau tsakiyar kayan tana watsi da su, tana cewa” wanna fa k’arya ne d’an yankan kai ne, Hajiya Suwaiba k’anwar Adam Naira cike da mamaki, tace”lalle tabbas yau naga halinki da’ake fad’a. “Bari kiji ga kayan Lhadijat nan abu d’aya ya bata sai mun miki rashin mutunci, kisani duk wanda zakana masa hassada da bak’in ciki, Allah kan masa sakayya, mugunta da kike mata ne Allah ta bata. Gwaggo tayi kanta zata cakumeta wani security ya kaimata naushi ta fad’i a kasa. Hajiya Siwaiba tace”ae da ka barta da yau na koya mata hankali, ni ba irin matan da suke d’aukan wargi bane. “Mtsss bamza sakarya marar imani. “Khadijat takusa hutawa da muguntanki. Gwaggo na ihu kamar mahaukaciya, tana cewa”sai kun kawo na Beeba da Rabee’ in ba haka ba zamana lafiya. Gwaggo hauka tuburan Inna Yalwa ta kali K’anwar Gwaggo tace”da fa kin kama yar’uwanki kartayi tsirara, tsabam bak’in ciki. Da kyar aka shigar da Gwaggo d’aki aka kule ta. Malam da yadawo, ko da yaji labari, Hamdalah yayi, ya k’ara gode ma Allah, tabbas Khadijat ta samu miji, don yana jin labarin halin d’an Gwamna. Kayan yasa ka aka d’eba a gidan aka kai gidan Inna Yalwa da daddare, ba wanda yasani, motar kuwa ya kai gun wasu masu ajiye mota aka ajiye masa. Yan’unguwa ko ina ka leka sai zance akeyi, wasu ko so suke su ga Khadi matar d’an Gwamna. Gwaggo tana d’aki sai zage-zage take, Beeba ko murna ba’a magana. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: ’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-116~120. A gidan su Dr Umar kuwa, sun gama had’a lefe nagani na fad’a, lefen nun ma sa’a. Cikin kayan harda key d’in mota, k’irar Honda CRV, Mum d’insa ta saka masa, Dr Umar shima ya karo wasu kaya aka saka, masu karatu kar kuso kuga kayan akwatina ma Set hud’u akasa, zannuwa kuwa ba kananu. Hmmm kayan d’an Gwamna d’aya tilo aidole ya zama abun kalo, Mum tace”Umar ka sanar da Khadijat jibi za’a kai kaya. Cikin murna ya shirya sai da ya je Store ya mata sayya, ya nufi gidan, bai wani b’ata likaciba ta fito. Sai da sukayi hiransu yace mata”My Khady!”. Cikin sanyin murya ta amsa da “na’am”. “Khadijat! Duk wani farin ciki na kene, ina matuk’ar qaunanki. “Alhamdulilah! Allah ya amsa min addu’a ta, na bani ke amatsayin mata. “Ki sanar da mutanen gida, In Allah ya kaimu jibi za’a kawo kayan lefe. Cikin jin kunya ta saki murmushi, tare da rufe fuskanta da tafin hannun ta. Hira sukayi mai cike da so da qauna, sai dab magriba, ya mata sallama ya tafi. Khady na shiga gida ko da Malam ya dawo, bayan ta masa sannu da dawowa, ta sanar masa da sak’on Dr Umar. Cikin farinciki ya yi musu addu’a. Washegari Malam ya aika ma dangin Mahaifiyar Khady, dangin Uba ya sanar ma wayanda yakama ta su zo karban kaya. Malam ya sayo kayan karban bak’i, harda yan kajin sa, guda biyar ya tura kasuwan kauye, aka sayo masa. Ya sayo multina da lakacera, kaya iya na talaka, Baba Yalwa k’anwan Maman Khadi su suka soya kaji, pepper meet sukayi, yayi kyau ko ina sai kamshi yakeyi. Gwaggo in banda harare-harare ba abinda takeyi, ko hannu bata samusu a aiki ba, karfe uku sun gama komai sun gyara ko ina sai kamshi yakeyi. Malam yaje ya d’an had’a kud’in da zai had’a na kasan akwati, ganin karamci irin na Umar ya samo dubu goma yaba ma Inna Yalwa yace a basu. Khady ko tayi wanka cikin kayan ta masu kyau, suka zauna a d’aki ita da Beebah don basa son yawo. Rabee’atu kuwa tana kusa da Gwaggo, sai lashe baki takeyi, don tunda taga ana soya kaji, yawunta ya kai. Su Inna Yalwa wanka sukayi, suka saka kayan su, mai kyau, suna zaman jiran baki. A gidan su Dr Umar kuwa, Mum kwanta ta kira da matan Baba Liman, sai Kwanwar Baban su Umar, bata tara mutane ba, sabida tasan yanayin gidan su Khady, kar suje su musu ba dai-dai ba. Milasalin karfe hud’u da rabi, suka d’au hanyan. Misalin karge biyar, cikin unguwansu Khady, ya d’au jiniya, motoci ne sukayi jerin Gwano ga securitys a motoci sun sanya sauran motan a tsakiya, suna shigowa take suka fir-fito dan gani mai zai faru. Motocin qofar gidan su Khady suka tsaya. Gwaggo dake d’aki taji jiniya mota, tace”ko lafiya naji karan motar yan sanda?. Rabee tace”ai inaga wanda suka daki Adda Khady ne suka dawo dukanta hala. “Don ranan da irin wannan suka zo. Gwaggi tace”Allah yasa sune, su dakata inga ta inda za’ayi auren. “Zo mu fita muga ya zasu kare. Suna fitowa dai-dai lokacin yan sanda suka shigo gidan da bindigansu, Gwaggo sai zare ido take. ana haka suka ga wasu Mata cikin shiga ta alfarma sun shigo. Gwaggo tace”lafiya dai naga kuna shigo mana gida?. Wata mata mai yar kiba tace”nan ne gidansu Khadijat?. Gwaggo tace”eh! Nan ne. “Lafiya dai?. “Lafiya klau, kafin tayi wani magana ansoma shigo da akwatuna. Gwaggi tace”wanna fa?. Matar tace”kayan Khadijat muka kawi”. Gwaggo ta buga k’irji tare da zaro ido. Nima Rash sai da wayata ta subuce don na tsirata da ganin yanayin Gwaggo. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: ’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-126~130. Hajiya Suwaiba suna komawa, suka sanar da Mum d’in Umar yanda sukayi, tayi mamaki sosai ashe da gaske haka halin Gwaggo yake. Nan tace” hmm ni gwanda His Excellency ma ya dawo ayi bikin, yarinya ta huta. Hajiya Suwaiba tace”yaushe zai dawo? Mum tace” nan da 5days zai dawo. Hira sukayi tayi da yanda biki zai kasance. Gwaggi ko ta hana su Malam bacci sai ihu take, ko sallah anki bud’eta tayi. Khadi tayi murna tayi godia ma Allah da zab’in da ya mata, take ta kira su Farhat B Haske ta fad’a mata, Farhat ma take bata labarin tayi sabon saurayi, Sunansa Abdul-wasilu Humble, Khadi ta mata fatan Allah ya dai-daita su. Tana kashe wayar ta kira Queen Neenah ita ta fad’a mata, daga nan takira Hajiya Jamila Abubukar ta sanar mata, tayi murna sosai da sosai, takuma bata shawarwari da yanda zata kula da Umar kasancewa Hajiya Jamila ta girmesu, tana kwance dasune don taga suna da hankali shiyasa. Malam ganin iskanci Gwaggo zai wuce gona da iri, da safe yaje ta windoq duk ta wargaza d’akinta, yace”Hauwa ki nutsu, wallahi kinji na rantse, matsawan baki bar haukan da kike ba to yau zan rubuta miki saki, don ba za’azo biki ina matsayina na Surkin Gwamna a ga mahaukaciya a gidana ba, kuma haukanta akan bakincin take ma Surkan Gwamna. Ni Rash nace”hmmm Malam da biyu yayi maganan nan, don ya kuna Gwaggo ne. Gwaggo tace” eh dole kace haka ae dama baka sona don yanzu kaga Khadi zata auri d’an Gwamna dole kamin haka. Malam yace” kene bazaki gane ba ina sonki sosai, halinki ne bana so, ya fita abunsa. Gwaggo jin saki ta nutsu ko da tafito, jummai k’anwarta tayi mata nasiha tace”Yaya matsawan baki kwantar da kai ba, ina fad’a miki zaki wahala don yarinyan nan tayi gaba. Kiyi hak’uri kawao. Gwaggo tundafa wannan rana ta dawo kamar bata gidan yanzu bata dai magana da Khadi, amma ta bar hantaranta ko sabganta tabar shiga. Khadi ko kulum suna mak’ale da waya ita da Umar, suna waya ne yace”gobe Dad zai dawo ki shirya, in ya dawo ke da Beebah zakuzo ku gaidashi. Cike da murna tace”sai mun tambayi Baba in ya barmu. “Kedai nasan Baba bazai hana kizo ki gaida Surkinki ba. Haka sukayita hiransu mai cike da ni shad’i. Washe gari da safe inna ta d’aura ruwa a hita, dai-dai kusa da d’akinta a kwai soket, ya tafasa ruwan ta kashe, taje d’auko boket kenan ta sukuya tana d’aurayewa, sai tebur d’in ya karye yana shirin zubowa akan Gwaggo. Khadi tafito da ga d’aki karaf idonta ya sauka akan tebur, “kira ta kwala ma Gwaggo, ganin bata gane mai take nufi ba, da sauri tayi gun don ceton Gwaggo. Tana zuwa ta ture Gwaggo ta hantsula gefe kagin ta kauce ruwan ya juye mata ajiki, wani razanane k’ara tasaki, ta fad’i agun tana shure-shure. Gwaggo duk ta rikice, Beeba da Rabee sai Jimmai kanwar Gwaggo suma ihu suka saki, ana haka sai ga Mal da gudu yayi kan Khadi, wanda azaba yasa ta suma, d’aukarta yayi waje yafita da gudu yashiga Napep, Gwaggo ma da gudu duka bisa, Beeba kam sai kuka take, tana fad’i”wayyo Adda na!. Gwaggo sai hawaye takeyi, tabbas yau Khadi ta gwada mata yar halak ce ita, gashi taje ceton rayuwana itakuma zata rasa nata. Tabbas yau na yarda da kalman nan ta ‘YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU, bakan wanda zai tai makeka ba. Suna isa asibiti Dr Abdul suka samu gani halin da take ciki, akayi Emergency da ita, wayan Dr Umar yakira. Dr Umar suna Airport shida Mum da Ilham sunje d’auko Dad d’insu, don har jirginsu ya sauka, Dad ya sauko kenan, sun rungume juna, wayar Dr Umar tayi k’ara gani Dr Abdul yasa yad’aga da sauri “hello yace”. Daga d’aya ban garen Dr Abdul yace”kana ina, kazo ba lafiya Khadijat ta kone bansam ko garin yaya bane, amma ina zati ko Gwaggo nane ta konata sabida halinta. “What ina bazai yuba sai na d’au mataki. Mum tace”Kai da wa?. Cikin muryan kuka ya fara basu bayani, His Excellency yace” what muwuce Asubiti yau matan na zata gane ita bakomai bane. Suna zuwa Asibiti ta ko ina ya amsa da jiniya. Dr Umar da Gwamna da gudu suka fita duka shiga Emergency, Umar na ganin halin da Khadi ke ciki, kara ya saki ya fad’i sume. Mum da Ilham sai kuka suke, Gwamna ya fita kiran Doctors suka d’au Umar shima. Yana fitowa yaga su Malam yace”ina Gwaggo da take?. Malam ya nunata da yatsa, His Excellency da gudu yayi kanta wani damka ya mata, ya fara kwara mata kyawawan mari, yace”wallahi in har na rasa d’ana d’aya tilo, da abar qaunar sa, to kema sai kinyi mutuwar wula kanci. Kisani ‘DA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU. amma ke munguwa nai bakin hali zaki gane kurenki. Ball yakeyi da ita, yana fad’an magan ganu, da kyar aka rik’e shi, sijoji yace atafi da ita CID agana mata azaba. Basu tsaya jiran komai ba Women police suka d’au Gwaggi sama aka sata a mota, aka nufi CID da ita. Ni ko Rash tsaban gulma ina leka motar naga bakin Gwaggo har ya kun bura, fiskan taji marin manya, tamkar ba Gwaggo mai bala’i ba. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam: ’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-136~140. Umar kuka yake ana haka har suka iso New Delhi, motane tazo ta d’aukesu har asibitin da za’a mata aiki, kasancewa a sanar musu, sun sanda suwansu, ana shiga da ita likitoci, suka hau bata taimak’on gagawa. Sun d’au awani suna mata surgery, Umar ya kasa zaune ya kasa tsaye, duka sun dun kufa sai addu’a sukeyi. cikin ikon Allah likitan ya fito cike da fara’a, hannu ya mika ma Gwamna, yace’ In Allah ya yarda musa tsamani komai normal” Hamdalah suka rayi, suna gun akazo aka wuce da ita zuwa d’akin da zasu ajeyeta. Khadi bata far-fad’o ba sai kusan 3:00am na dare, doctors aka kira duka dubata, Umat ko sai addu’a ke mata. Haka suka kasance cikin jinyan Khadi yau kusan watandu d’aya kuma yau ne za’a ware mata, bandage, doctor yace”suyi fatan Allah yasa aikin yayi nan aka shiga da ita, wani room don since mata, su Umar sai addu’a yakeyi. Awa d’aya ya d’aukesu, likita ya fito nan ya saida musu komai normal, zasu iya shiga su ganta, Umar da gudu yayi d’akin yana zuwa ya ganta kwance, suna had’a ido murmushi ya sakarmata, zuwa yayi ya rungumeta, ana haka su Malam suka shigo, sai da Dad yayi gyaran murya, tukun ya san sun shigo, cikin jin kunya ya koma gefe, sannu suka ringa mata. Tun daga wanna ranan Umar shike mata dressing d’in ciwonta, ya bata abinci abaki, ya mata alwala, da daddare kuwa kafin ta kwanta zai d’auko story book yana karanta mata, da joke masu dad’i tana dariya, har tayi baci, inyaga tayi nisa da bacci yazo ya ru gume matarsa haka rayuwansu, ya kasance gwanin dad’i. Ganin Khadi ta warke suka fara ahirin dawo 9ja don ayi biki kowa ma ya huta. Gwaggo kam taci a zaba, in har kasanta ada kaganta yanzu bazaka ganeta ba, tayi baki sosai, gashi har hak’urinta sun zube, tsaban duka da wahala, sai daga baya ne, Beeba ta sanar ma Dr Abdul gaskiya, shima ya fad’a ma Baban Umar, sai da sukayi bincike suka tabbatar da gaskiyan al’amarin kafin aka saketa, randa tashiga unguwansu, matasa suka tashi zasu mata duka da kyar aka kwaceta, Gwaggo tayi nadama ba kad’an ba. Kulum cikin saloli take, tana addu’an Allah ya tashi kafad’un Khadi. Yau jirgin su Khadi ya sauka 9ja, Umar ko sai wani rawan kai yakeyi, ko kunyasu Dad baiji, sai yawani rok’o hannuta, sai da Mum ta zo ta rik’e hannu yarta, Mum tace”Malam za’aban aron yata, zan tafi da ita kafin biki. Yace”bakomai ae Khadi takune. Suna isa gida ta kira Hajiya Suwaiba da Ameena tace”ga yata nan kuje a gyara min ita, banson Umar ma ya ganta sai biki. ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ [4:55PM, 5/25/2016] Rash Kardam : ’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU NA ©RASHEEDAH .A. KARDAM. Pg-141~145. Shirye-shirye biki akeyi ba sanya, su Hajiya Jamila.k’irjin biki, su Farhat da Queen Neena takanas suka koma gidan Hajiya Suwaiba da zama, abunda aka shirya za’ayi ran Alhamis kamu, sai Jumma’a Walima da daddare kuma dinner, washe gari asabar yini. Komai ya tsaru yanda ake so, yau ne ranar da za’a fara Kamu, da yamma ko kwaye sun shirya, har an kaisu gun jiran isowar Amarya ake, ba’a dade ba kuwa ta iso cikin wata lafiyayiyar mota, tun dana zuba ido ma Khadi kasa d’aukewa nayi, gaskiya tayi kyau, duk yan guri sai yaba kyanta suke, taro yayi taro, komai yatafi yanda akeso, sai kusan shida suka gama kamu, daga gun gidan, Hajiya Suwaiba aka sake kaita. Washe gari akayi walima shima tsaru daddare kuwa sukayi shirin dinner. Hajiya Suwaiba ta bada umurni akai Amarya gidansu daga can za’a wuce da ita Dinner har a kaita gidanta, wannan umurnin Mum ne. Masu karatu in bakwayi bamu guri, tundaga nesa na hango motoci jere suna d’eban mutane, sai da aka gama diban kowa, na hango wata maroon d’in lemo zeen ta perker, su Gwaggo da’ake leke, baki tasaki tana kalo, don tunda take bata tab’a, ganin irin motarba. Nan akace afito da Amarya Inna Yalwa ce ta rakota, ohoho sunan wani kalma waishi sorry!! Masu karatu karkuga Khadi, in har nace zan iya tsara muku kyan da tayi, wayana ba zai d’auka ba. A hankali suka isa jikin motar tashiga, ana tayar da motan taji an rik’o hannuta, a razane ta juya Umar ne yaaha kyau. Koda suka isa gun dinner duk wanda ya gansu sai ya yaba, haka taro ya kare kowa cike da murna. Da safe Malam ya kira Khadi, ya mata nasiha, yan’uwan Mamanta suma nasiha suka mata, Gwaggo da k’afarta tazo tana kuka ta roki Khadi yafiya, Khadi tace” ba komai ta yafe mata. Da daddare aka d’au Amarya sai gidan Umar niko Rash nace”fatan alkairi. Gwamna gida mai ji da kyau ya bamasu Mala adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *