*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (MELODY)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*Xarah Bukar*
*Bismillahir rahmanir rahim*_
*(Praise be to ALLAH who made me to be alive gain to fill your heart with such a beautiful and interesting novel,*
*NOTE: _it is a fiction seems to be like a true life story, I didn't do it to curse or abuses somebody I guest if it comes across your life story am apologising I didn't do it bcos of you_👏🏻*
0⃣1⃣
Hadari ne gagarumi ya had'u daga gabas da yamma kowa sai gudu yakeyi yana neman inda zai fake tun kafin ruwan su sauko,
Cikin k'ak'k'anin lokaci ruwan sama mai tarin ni'ima yafara sauka, shaaaaaaaa...
Dishi- Dishi nake hangota acikin hazon ruwan saman, Wata matashiyar budurwace ke tafe cikin ruwan tana zubda hawaye, iskar dake tashi na kad'a mata Himar, ilahirin suranta duk ya bayyana saboda kashib ruwan datasha,
Rik'e take da zungureran trolley tana janta dakyar, a hannunta nake hango wani irin kyankywan kunshi wanda yasha rani yayi jajir, abinka ga farar macce sai zanen yafito tsintsa, haka zalika kafarta yasha kunshi daganinta kasan amarya ce, tafiya take tana d'ingishi ga dukkan alamu tagaji sosai, haka takejan trolley d'in kamar zata fad'i a hakadai harta karasa bakin kofar wani d'an karamin mai kyau, Tana isa kofar gidan, tarar kofar gidan a rufe, a hankali tasa hannu tana dukan kofar tana jan nunfashi jikinta sai kyarma yake saboda tsabar sanyin datakeji,
Tana jima tana dukan kofar, sai cen wasu samari sukafito su biyu, ganin dasukayi mata yasa d'ayan ya zare edo "anty ummi lafiya kuwa" yafad'a a tsorace,
A hankali ta kutsukai cikin gidan tasaki trolley d'in a bakin kofar gidan da kyar da iya furta "kushigo da jakar nan ciki" tana gama fad'a bata jira sukayi maganaba ta wuce cikin gida tana hawaye,
samari suka shigar mata da akwatin cikin gida,
Koda tashiga falon mutanen gidansu da wasu sauran 'yan biki suna zaune a a cikin falon suna breakfast, tayi sallama tashiga, suduka suke kallonta
Baki bud,e kowa ya tsaya kallon ikon Allah amaryar da akakai jiya-jiya, itace a gida yau safe?
Sai sallallami akeyi harda ragowan yan biki dabasu tafiba"
"Ummi" naji ankirata dashi,
"Lafya kika dawo gda?
"Wani abunne ya faru?
Kinyi shuru ummi? Kuka ta fashe dashii, taki cewa uffan.
"Aunty ki tsaya mama ta dawo kila ita tafad'i mata abunda ya faru?"
Bayan an idar da ruwan ne mama tadawo,
Nidai Humairah ina zaune inajiran inji abunda yake faruwa.??
" mama ummi tadawo gida munyi munyi tagaya mana meyafaru taki, ki shigo kila keta gaya miki.
"Nashiga uku ni Dije meyafaru, ummi?
Tana ganin mama tace umma ya sakeni!!!!!! " dam taji kirjinta ya buga.
"Ummi laifin me kikayi?"
Ummi tace " Mama kinji na rantse bansan menayi masa ba Wallahi ban saniba, ina tashi da safe kawai naga takarda a kan gado ina bud'ewa naga yasa",
*Ni 'MUS'AB nasaki ummi saki uku, aranan sha biyar ga wayan nuwamba 2016*
"Mama ga takardar"da Sauri mama ta amsa ta karanta tace tabbas babu karya" 'amma yaxama dole inje wajen uwarsa inji dalilin da zaisa ya sakeki kwana daya dayin aure",
Dasauri mama tazari 'Hijabi ta Zara sai tafita,
Bayan ta isa gidan Koh sallama babu ta shiga mai gadi yana tsaidata koh saurararsa batayiba",
Tawuce kai tsaye cikin falom tana fad'an "Hajiya Fatu! Hajiya Fatu!!!
Dasauri hajiya fatu tafita daga daki takaraso falo "'Lafya kiketa hayaniya hjy Dije? acewar hajiya Fatu
Mama tace Inafa lafya
d'anki yasakomun y'a, shiyasa nazo inji akanme akan wane dalili, kodan batada gata, Shiyasa zai watsa mana kasa a Ido? kuka mama ta fashe dashi tsabar takaici
Haj fatu tadafe kai ita abin yayi matukar girgizata, tad'aga edo ta dube sama tace "Oh ya Allah ka dubemu da idon rahma, bansan a ina wannan 'Dan ya samo wannan mummunar dabi'ar ba," sannan tasauke edonta kasa tadube mama tace "Hajiya kiyi hkr Wallahi banida masaniya akan wannan sabon al'amarin, amma zan kirashi duk abunda ake ciki zanxo in sanar dake, dan Allah kiyi hkuri kitafi, muje narakaki,???"
Mama tayi saurin d'aga mata hannu tana kuka "a a basai kin rakaniba " tana gama fad'a Da Sauri ta fita tabar gdan cike da bakin ciki, zuciyarta cike da fargabar kilama ya lalata ma 'yarta "BUDURCIN" ta domin kuwa shine kad'ai abinda yakeso...............
Dedicated to all youth🙍🏻🙍🏻♂
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (MELODY)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*Xarah Bukar*
0⃣2⃣
Tunda haj fatu takirashi a waya take tsaye a falo tana jiran isowarsa, ranta yayi matukar baci, zuciyarta harwani zafi take mata,
Kamar daga sama taji yafara kiranta tundaga waje Ammi! Ammi!! Ammi!!!
Tana jinsa tayi banza dashi saboda wani haushinsa datakeji,
Shigowarsa falo yayi anan yayo kicibus da ita a tsaye tana huci, mus'ab yace ammi kinanan nake kwalla miki kira kinyi". Ignoring dina????
Ammi tadaka mishi tsawa "dakata Son" ta cewa Mus'ab " banason jin komai daga bakinka, don bakada abun cewa, wlh mus'ab kabani kunya meyasa zakamun haka?" (Nayi zaton wuta a makera sai gata a masaka)
"Me ummi tayima zaka saketane " takarasa maganar cikin hargowa,
Dasauri takaraso wurinsa cikin bacin rai ta kamo Kwalan rigarsa ta chakumeta tana hawaye tace,
"Son irin tarbiyan da nayi maka kenan"?
Mus'ab shikam ko ajikinsa cikin gadara yace "Ummi batayimun komaiba Ammi, kawai naji banason zama da itane", batarai yayi yana gama magana yafirgi rigarsa yafice yabar ta tsaye, a tsakiyar falon tana kuka,
Batafi minti biyarba taji anyi sallama hakan ya sata dago fuskarta, mahaifin mus'ab ne yashigo ganin tana kuka yasa yayi tsaye sororo yana tambaya "hajiya lafiya kike kuka?"
Ammi tace "dole inyi kuka mus'ab ya saki matarsa, kwana daya dayin aure!!!!.
"wannan ai bacin sunane ace kamanni yaronnan zai watsawa kasa a Ido, yar aminina, yanzu me kike tunani hjy dije zatace, na wulakantata, saboda mijinta baya Raye?" mahaifin Mus'ab ne ke magana cikin karaji,
Sannan yakara maganar da kisan sunansa Mus'ab mus'ab!!!!!!
Ammi tace "Ina mus'ab yayi gaba, dole muyi Abu akai mai gda inba hakaba, zaici gaba da zubar mana da kima da mutunci a bainar jama'a..... .
"Kwarai hjy maganarki gaskiyane.
*********************
Hjy dije gda ta wuce inda tasamu ummi tanata kuka,
" yi hkr daughter karki damu Allah yasa rabuwanki da mus'ab shine mafi alkhairi,
Kituna "wani Hanin ga Allah baiwane, Karkiji komai 'yata Allah zai kawo miki mijinki anan gaba, Wanda saimunce' gwamma da akayi",
Juyowa ummi tayi tace mama Adu'arki a gareni itace mafita kawai kitayani da adu'a".
*BAYAN WASU WATANNI*
An shafe watanni ba mus'ab ba labarinsa harta gama iddarta,
Manema suka fito ciki harda abokin mus'ab,
"Kwatsam saiga ciki"
Abunda ya girgiza hjy Dije kanan'
"tayi bakin
ciki kwarai amma tayi farin ciki. Ummi dake zaune bayan sun dawo daga asibiti wajen gwaji"
Mama tace "dole ko sunki ko sun so su karbi wannan d'an amatsayin fansar budurci, shi kadai ya ishi mus'ab da iyayensa ishara, barina naje gidan"
Nan ta mike tafita,
*********************
Sallama hjy dije tayi cikin gdansu mus'ab ta kutsa har tsakiyan falo gdan"
"tace hjy fatu kinyi babbar bakuwa mai babbar sako.......
Dariya ta sakko tanayi duk boring kunya ya isheta, sai wasu yan kame kame takeyi"
"Inataso inzo inga diyata amma abun sai a slow banda sukuni yau ina Dubai sgobe muna UK, shiyasa.
" Zauna mana" ah ah niba zama naxoyiba, nazone inyi miki albishir dacewa 'yata, yarku, "tana dauke da cikin d'anku Mus'ab harna tsawon wata uku,
Amma tace "what??? Ta girgiza sosai,
Mama tace "Kwarai kina mamakine? Toh hjy fatu kidaina mamaki da ikon Allah kinga takardar inyaxo saiki sanar dashi,.
" batajira komai daga bakin Ammi ba ta fita abunta,.
*********************
Kusada ATM d'in Stanbic dake PZ na hangi motar mus'ab dagani ina cikin layin masu cire kudi.
Da Sauri na tsalako wata budurwa naga tayi packing motarta, bayan nasa,
" tasha uban gilashi daganinta, kasan tasha Hutu tayi dankam",
"Layi yana gab da yazo kan mus'ab tace excuse me Dan Allah kayi hkr inci arziki,
Am in a heast...........
Wani irin kallo tayiwa mus'ab ta kashe nasa edo saida ATM dinsa ya fad'ii......
*Dedicated to all youth🙍🏻🙍🏻♂*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (MELODY)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
0⃣3⃣
Sannan mus'ab yayi murmushi yace "Gaskiya nafi ki kaguwa, saidai kibari inci arziki inna cire saiki cire.
"Toh" tace tana taunan cingam, "Saida yagama tsaf yashiga mota sai a lokacin ya lura da wata mota a bayansa..
fitowa yayi yafara masifa " wane wawanne ya aje mana mota yasan cewa, ATM nazo ba dadewa zanyi ba"
Cikin isah da gadara ta fito daga cikin motar tana fad'an "Nice nan koh dakwai maganane? Sai wani muzurai Kake kaman kayiwa sarki karya???
Ran mus'ub yabace dasauri ya zufe kofar motarsa yazo gabanta "Ke dallah kiyi mun shiru kidauke, akwalar motarki kubar wurin nan tun Kafin insa ad,agaki daga ke har motar taki"
Cike da hargowa tanuna masa yatsa "Karya kake Dan matsiyata, karka kuskura, ka rainani don ka ganni a gabanka l, Am very expensive as you can see am from a wealthy family...."
Tun bata karasa maganarba ya kwasa mata wawan mari sannan yace daga yau nidake muzuba saikinyi dakin saniii" Niba irin samarin da kika saba yakushi bane kibarsu da tabo",
Ni damusane bana jira sannan banida tsoro, kuma baidai mace ba saidai namiji Wallahi".
Tuni ta shige motar tana kuka takunna tayi wani irin reverse saura kad'an ta tsallaka dayan length din,"
Sai bayan tatafi sannan yashiga motarsa Shima HK ya kunna motar cikin bacin rai, amma yarasa meyasa yake ladaman abunda yayi mata.......
*********************
Gida ya wuce direct inda ya taradda Ammi a falo zai wuce tace, SON dasauri yace naam Ammi ",
Dauki wannan takardar ka karanta,
Matarda daka aura ka saki, tana dauke da ciki,.......
"Dam kirjinsa ya buga, haba Ammi kwana daya awani ce ciki???? " this is unbelievable' "In possible wlh Ammi sunaso kawai suyi inheriting wani Abu daga arzikinmu ne kawai, amma cikinnan banawa bane......
Ammi tadaka masa tsawa "dakata karka maidamu kananan mutane, kai ka isa kaja hukucin Allah ne"
muryan mahaifinsa, ya katseshi yana kokarin fitowa daga dakina daman shi yake jira tundaga nesa yake cewa "Amma kasan dacewa, Kaine kafara saninta, a matsayin mace???? Banga dalilin daxaisa, kace ba cikinka, bane. sannan likitoci sunyi ittifakin cewa, mace tana iya daukan ciki daga tagama wankinta,....
Sannan da gabanin fara al'adanta, dan haka d'a nakane yaxama dole ka amsa, shuru mus'ab yayi yace , naji Abba na amsa, amma Ku rikeshi a matsayin d'anku amma, ba d'anaba, yana gama maganar yayi ficewar sa,
kulawa ummi tana samu sosai an mallaka mata kudi daga ciki har haihuwa, har rainon d'an.......
*********************
Da gudu tasauka tashiga tana kuka, wata mata nagani buxuwa gashinta har gadon baya ", ta tsayar da ita dacewa "
Lafyarki Ambil kinshigo kina kuka?
Kedawa,?? kinje kinyi halin naki na Rashin kunya?
Ambil tana kuka tace "Yanzu umma harni zai Mara bari Abbana ya dawo Wallahi kodan gdan uban waye sainasa an horamun shi"
Umma tarungumeta tace, "meyasa bakiyimai hkr ba, kinsan kowani D'an Adam da irin baiwan da Allah keyimai",
Bakisan inda rana zata fad'iba, kimun alkawari bazaki gayawa, 'Abbanki ba????
"Nayi miki umma"
Amina ta fadi tana cikeda shagwaba.......
*Waye Mus'ab*????
*Dedicated to all youth🙍🏻🙍🏻♂*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (MELODY)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
*Ina kiraga masoyana ina barar adu'arku, gobe insha Allah zan fara jarabawa. daga mai kaunarku har kullun HUMAIRAH BASHIR Melody👄*
*Love you ol😘*
0⃣4⃣
Mus'ab Ahmad rufa'i shine ainihin sunansa, d'a ne d'aya tilo a wajen mahaifinsa Alhaji Ahmad rufa'i ya fito daga karamar hukumar "Soba LGA" shararren D'an kasuwane a central market dake Kaduna, ya kware wajen saida gwala gwalai.....
Yana safara daga Dubai zuwa Nigeria"
'Mahaifiyarsa, hajiya Maryam sunan ta, anfi kiranta da Fatu (Ammi).
Yar asalin garin lere ce, tallan fura take kawowa, cikin kasuwar soba, inda yaganta ya aureta.
Ankai ruwa rana saboda, yan'uwan Alhj Ahmad, sunki jinin yan gdansu Ammi, "
Saboda tsananin bincike saida allura ta tono garma
Shiyasa Ammi batada wani farin jini acikn family din mijinta, Mus'ab shine d'ansu na uku yanada yayye biyu Wanda Allah yayi masu rasuwa sana diyyan gubar feshin gona dasuka Shaka.
A yanzu shine d'ansu Wanda suke masifarso, mus'ab dogone black beauty,
Gashinsa, luf luf" kaman Dan India, yanada Jan Lebe da idanu wadatattu,
Yayi karatun primary a therbow school secondary a ALBANI COLLEGE dake magume Zaria, daga bisani yasamu, Admission a crescent university Abeokuta, bayan ya kammalane yasamu aiki a kamfanin layin MTN.
Mus'ab Takadarine na karshe Wanda yayi kaurin suna a cikin birnin Zaria.
_Wannan kenan_
********************
*Cigaban labari*
Tashi tayi tashiga wajen abokiyar zaman umman ta tace, "Ummu ayman kinga yadda wani ya mareni koh,? Ammu wai ummata tace inyi hkr kuma gayen inaso akoyamai hankali, koya kika gani ummun ayman?"
Ammu tace "kwarai ki gayawa Abbanki inba hakaba gobema karawa, zaiyi"
Amina tayi tarike hannun ammu tana dariya tace "yes shiyasa nake sonki nake kara sonki," tana karasa maganar tasaki hannu ammu tatashi ta wuce a guje, tana jin dadi, Amma takasa, kawar da tunanin mus'ab acikin ranta......
Bayan tashigo d'aki tayi zaune gefen gado, still tunanin mus'ab ya fad'o mata, a zuci take cewa
"😡😡Hey was wrong with you Amina? Y do you have feelings on that "Margot" oh no am in for him noo bazansa daddy ya hukuntamun shiba",
Itada zuciyarta take, zance😡😡
Bayan takarasa zancen zucinta Tashi tayi ta fesa wanka, wasu kaya tasa shokin gefe a tampha exclusive taji dinki,.
Komai too match takalmi, da jaka, da hangles d'inta iri d'aya"
Hatta Dan kunnayenta masu kaman Green ne.
Keys d'in mota ta d'auka sannan tafito falo anan taci karo da umma,
Bayan takarasa wurin umma tace "umma zanfita naga gari,
Kinsan yau weekend ne, dey are alot of fun out there........."
Umma ta washe baki "tohm autana adawo lafiya, Amma dan Allah banda tsokana "
Amina tace "tohm umma " sannan tafara taku cike da kasaita, harta fita harabar gidan,
Motarta tashigo ta kunna tafice tabar gidan, akan tati Tuki take ta kure sautin kid'a, waka takeji Wanda saurayin HUMAIRAH ya tsantsara mata, Dayake beat din wakan akwai duma, hka kaji motar tad'au sauti dum, dum , dum. koh horn bataji, tafe take cikin motarta, kirar "Yarix",
Go slow ta hada a wajen "roundabout" d'in tudun wada, "nikaina danake Sauri saida na shagala da kallon Amina, bare wani da namiji,"
"" mus'ab ne ke bayanta, gashi bayaso yayi missing tseren dawaki da ake a polo club", fitowa yayi a fusace yana masifa yakaraso wurin kofar motar, saida ya buga mata glass sannna tabude, a daidai lokacin suka had'a edo, mus'ab yaja tsaki yace "Haba dole yar koyoce a cikin motar dole asamu, go slow I wonder Wanda ke barinki da mota Wallahi, tunda ke "yar" masu kumban susane, sai a hadoki da danjagora,"
Amina takasa cewa komai, kallonsa kawai takeyi cikeda, raini, tace, amma anyi asara, " kaida kace, badai maceba saidai namiji meye na tsayawa kayita kumfar baki akaina,? Kafin in irga uku ka matsamun, inba hakaba, intureka, inture banza,
Dan kauye, bakada maraba da d'an kauyen soba."
Sakin baki kyau yayi yana kallonta, azuci yake zancen " wannan yarinyar meyasa muke clashing da itane, Amma na lura ansangartata da yawa, zan koya nata darasii."
Shikadai yake zancensa na zuci"
*Dedicated to all youth🙍🏻🙍🏻♂*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (MELODY)👄*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
0⃣5⃣
Tabbas ran Amina yayi fari kal, amma cewa take "for goodness sake meyasa nake haduwa da wancan garan, ne?" Nidai cewa nayi na love,
Saida suka shafe kusan wata guda basuga junaba, hakan yafarune",
Saboda Rashin lafya da Mus'ab yakeyi Wanda saida ya kwanta a asibiti......
Amina tashiga damuwa kwarai kullun saita fito, don taganshi, amma shiru kakeji Malam yaci shirwa, shima Mus'ab yadamu da rashin ganinta, amma Dayake namiji ne, bai wani sama kansa damuwaba"
Tunda ya kwanta ciwo bakoma samun damar fita,
Yau takasance week end hakan yasa yayi wankansa cikin kananun kaya yad'auki key na motarsa yafita falo,
Anan yaci karo da umma tana zaune tana karatun jarida, yakarasa bashin kujera yazaune, sannan yagaida bayan amsa, ya dube yace "Ammi bari nad'an zagaya kozan samu fresh air"
Ammi ta janye jaridar datake karatu gefe ta dubesa tace "kaji shu'umi cikin gdan ba fresh air ne kagaNidai nakosa, inyi surikata "
Kusada ita yaxo yace "Ammi karki sawa kanki, damuwa very soon"
Ammi taji dadi kwarai saboda tana masifar son d'an nata ya kara aure,
Bayan yafito daga gida yahaura titi zuciyarsa na masa 'yan sake- sake akan amina,
Daidai wurin chicken republic dake opposite, ecobank na pz, ya hangota tana kokarin shiga wurin tabba yaganota,
da aauri ya juya kan motarsa, yana hangenta ta glass dayake yamma tafara yi, gashi yanzu longer nyt muke, shorter day.
Saida ya daidaici zata fito yashiga da saurinsa, ya bangaji ledar Ice-cream d'in dake hannunta, tuni ta watse a fuskanta, cike da masifa tasaka ihu kad'an sannan tace "What, who did dis, i guest he must be foolish for committing a crime lyk dis??..."
Mus'ab koh kallon inda take bai ba dayake yasan da gangan yamata,
Da sauri tasa hannu ta janyo bayan rigarsa dayake bata gane shiba, cike da hargowa tace " Malam kai makahone, zaka bangaje mutun kawuce, batareda, kaba mutun hkr ba???
After ol bacewa zanyi ka biyani ba don matsayin ka, a tip d'in Dan yatsana yake bakada wannan matsayin....." Nan taci gaba da masifa, kamar wata mahaukaciya, kansa yana soke a kasa yaki ko kallonta,
saida ta gama tsaf ya d'ago kansa, a lokacin sukayi edo hud'u tayi saurin sakinsa harda ja daba ta razana sosai da ganinsa, yayi murmushi ganin yadda taja baya, yace "hmmm inason Sanin wai me sunanki ne ma, da duk inda naje saikin biyoni"
Amina tad'an yi yake cike da takaici sannan tace "oh God wani yaxo yatayani, jin abun dariya, nicema nake binka, Shigowa zakayi nikuma, fita zanyi cikinmu wake biyo wani, nice ko kaine " takara maganar da nunashi da yatsa,
Mus'ad yayi tsaye yana kallon ta, the way yadda take furta lazafi a bakinta yadda bakin ke motsawa tana burgeshi, hakan yasa ya tsinci kansa da Kasa kawar da edonsa akan kallonta,
"Amina me kikazo yi naga dukkin bata jikinki da Ice-cream" wata matashiyar budurwa tafad'a wanda ga duk kan alamu tare da amina sukazo, tayi tsaye tana kallon yadda jikin amina yabace da ice cream,
Amina tatabe baki tana kallon mus'ub "Kinganshi nan shiya zubarmun dashi, Sannan yake cemun wai duk inda yaje Saina, biyoshi,.ke kanki kansan halina nayi kama da wacce zata dinga bin wannan chakus d'in"
Dariya suka kwashe da ita da Jidda(kawarta)
Jidda ta yatsayar da dariyarta tana kallon wanda yayi tsaye kamar gunki yana kallonsu tace "haba malam inbanda kai abunka "ina ruwan biri da hada???"
Amina tace "Tayani gani yar uwa,"
Jidda ta dube amina tace "kawata kodai yana cikine???" Takarasa maganar tana dariya,
Amina tatabe baki " Allah shi kiyaye, mezanyi da wannan d'an kauye jishifa ko wanka bai iya dubi rigar jikinsa, awajen yan baro yake siya fah" suka bushewa dadariya ita da jidda,
*Dedicated to all youth🙍🏻♂🙍🏻*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (MELODY)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
XARAH BUKAR
0⃣6⃣
Mus'ab duk yagama jin kunya, yakasa cewa komai, Sum sum zai wuce tace "ina zaka? Kake wani sand'a?"
Dariya suka kwashe dashi, harsaida yafara jin haushinsu ya tsaya cak guri daya,
Amina tace " naga bakasai komaiba tsaya koda snacks, ne ka tafi dashi,"
Mtwzzz mus'ab yaja tsaki, yajuyo a fusace yace "namiki kamada matsiyaci ne?
Dahar zaki siyamun, snack??You must be out of your sences" ya wuce wurin motarshi,
Jidda tace "kawata mubishi mukara cika masa ciki" suka kara kwashewa dadariya sannan sukabi bynsa, har waje motar sukabishi, Amina tana cewa "oh my dear meye na fushi ai basai matsiyaci ake saiwa Abu ba??Harda mawadaci mah'' tayi "stiring" dinshi,
Tayi saurin shiga gabashi tana murmushi, tuni Mus'ab yafara. Jin kaman ya rungumeta, "Don jsaiwani shagwaba takeyi. Dasauri yariko hannuta yajanyota tadawo daf dashi suna shakar nunfashi juna, a hankali yasauke murya yace "ina sonki amina "
Saida taji kamar anmata sock, duk jijiyoyin jikinta suka tsaya, tayi tsaye saranda takasa cewa komai,
Wani irin lallausan murmushi yasakar mata sannan yasa hannusa cikin aljihu yaciro katinsa sannan yakara janyo hannunta ya damka mata katin, duk tana tsaye kamar wata gunki,
Zagaywa yayi ta gefenta yawuce batare daya kara cemata uffanba, sai bayan yashiga motarsa yatafi sannan jidda tazo ta tabata sai alokacinta zabura tadawo hayyacinta, jidda tace "ai shikenan karshe fad'a yazo, saiki wuce muje gida" nana suka wuce suka shiga mota suka nufi gida,
*BAYAN KWANA BIYU*
""" soyayya mai karfi ce ta fara samun guri acikin zuciyoyinsu,
Inda suka zama tib da taya"
"Hankalinsu baya kwanciya inhar basuga junaba, " kowa yagansu saiyayi sha'awarsu, saidai kash me hali baya fasa halinshi,
"Sannan ba'a canzawa tuwo suna,
Magana tayi nisa har takaiga ansa musu rana, dayake duka family d'in guda biyu,...kowa ganin kud'ine
Babu raini.
"Mus'ab duk ya kosa ranar aurensu yazo,
Wata ranan larabane, da misalin karfe, uku na rana",
Amina takaiwa kawarta, ziyara, wato ummi.
" Ummi wucewa nazoyi nace bari na biyo yaushe rabo,? Ance har kinyi aure, kinfito.? Ummi kuma da ciki? Amina tafadi cikeda, jin tausayin ummi.
"Amma baida imani, Sam, Amina meye abun damuwa,wannan cikin dakike gani'
Masifar son sa, nake kallonta Amina takeyi, tace yanzu cikin nan har wani abun sone???? Ummi
" kwarai ai shine *FANSAR BUDURCINA* da'ace bulus yaci yasakeni babu ciki ai ya takaitani",
Ya cuceni, amma yanxu koh banza nasan za'a kirashi da sunan ubansa"..........
Amina ta jinjina kai tace "Kwarai Ummi kinyi gaskiya, tabbas da'ace kin fita babu ciki, daya kware ki, ya bude ki gal Sannan ya sakeki"?????
Allah ya rabamu da irin wannan auren..... Amin ummi tace.
Sannan amina tacitro katin bikin tamikawa ummi tace" yauwa katin bikina na kawo miki, shine nace bansaniba. Koh zakizo?"
Ummi takarba tana fara'a tace "Mezai hana? "Ai koh ina shiga nake da cikinnan tunda ba shege bane da ubansa,"
Kwarai kawata, ko gaida hjy idan ta dawo. Toh zataji
"Bayan fitan Amina ne ummi ta bude katinnan, sunan data ganine,ya tsoratata.........
A firgice tace "Mus'ab? Shine zai auri Amina??? Tab lallai "dakwai bikin zuwa babu zani"
Dole ne inyi duk yadda zanyi in hana "afkuwan wannan aure inba hakaba, tabbas cutar Amina zaiyi yadda, yamun.........
" Muryar hjy dije taji Mamanta, ta ruga falo ta tadda yan" uwanta, duk a zaune.
Tace mama Amina wazatta mus'ab zai aura dazu takawo mun, "invitation card" din bikin?Umma mamarta kawarkice pls kije ki fad'a mata cewa, Mus'ab mayaudarine,
Kul inji hjy "ba abunda ya shafeki, haka 'yan gdannan, Akanme kika sani ita ya zauna da ita???
Toh ina gargadinki, " bakinki kanin kafarki
Banason jin wata kalma daga bakinki, ummi tace toh mama.......... Tun daga ranar taja bakinta tarufe, saidai zuciyarta cike da tausayin amina,
A KWANA ATASHI
"Biki saura sati daya an had'a event kala kala, yayi inviting friends d'inshi,
Ya kashe kudi sosai a bikin"
"Amina koh sai murna takeyi, amma mahaifinta bayason wannan aure,
Saboda yaji kishin kishin a gari gameda mus'ab. Amma dayake Amina sunan mahaifiyarsa, gareta kome takeso shiyake mata, bayaso yaga bacin ranta" don hk nasashi yaji kaman zaibar duniya. Dukda ba ita kadai ya haifaba.
"Mus'ab zaune yake acikin garden din gdansu, shida abokinsa, Sani gambari.
Sani yace "Mutumina kakusa zama angogu don banace angoba, itama Amina waje zakayi da ita?
Mus'ab ya dube sani yace " Sani kenan ai andinga kenan, harsai naji bana numfashi,"
"Mutumina zata kai ga adaina baka aurefa, cewar Sani......
Sai inkoma saikuma.......
" yayi Shuru, ganin mai aikinsu, tace yallaboi ga coffee d'in.
Mus'ab ya kalleta awulakance yace "Kinci gdanku da Kofi ubanme ya kawoki,?? Muna fuka toh kisani inhar kika fallasa, sirrina, saina karar da duka danginki..........
*Dedicated to all youths🙍🏻🙍🏻♂*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (MELODY)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
*Dedicated this humble page to my sweet, loving, cooling, jumping, jiggling, swixting, *AYUSHA ILIYASU*😘bunch of love abundantly👏🏻.
You deserve more from me,".
0⃣7⃣
Shiru tayi batace komaiba,
Kallon sani yayi yace "abokina tashi mu tafi, na lura yarinyarnan so take ta batamun tsariiii"
Nan suka fita sukabar gidan
Indo kam abun ya dameta, azuci tace "Wato auri saki yakeyi, abunda Allah ya hana"
Duk abunda zaimun ya Dade sainaje na fada musu, karsu sake su aura mishi yarsu inba hakaba zataje ta dawo"
"Nidai cewa nayi duk inda takwana Shane"
Indo ana gobe biki taje gdansu Amina tasami uwar Amina tace Nazone na gargadeku karku sake Ku aurawa mus'ab 'yarku, auri saki yakeyi....... Auren d'and'ane.
" kowa Shuru yayi Amina ta fito tace karya kikeyi,
Mus'ab dina bazai aikata hk ba kila dai wasune suka biyaki, kud'i don kizo ki hanani auren muradina,"
Kafin in bude idona kifita kibar gdannan...
Babu yadda indo batayiba akan du amina su fahimce amma sam son mus'ab ya rufe mata edo, haka indo ta hakura tadawo gida,
Amina kuwa taci gaba da shirye shirye biki
YAU DAI an daura aure Amina da mus'ab, akan sadaki #150,
Da misalin karfe hudu na yamma aka wuce RAS akayi lunching...
Karfe bakwai akakai Amina gidan mus'ab daya sha kayan more rayuwa,',
"Nidai kayan har tausayi suka bani, itakanta Amarya abar tausayi ce.
Kowa ya watse ango aka shigo da abokai, anata dariya,
Misalin goma abokai suka watse,
" daga Amina sai mus'ab,
Bayan mus'ab yaje yarakasu yarufe dukkanin kofofin gidan, sannan yadawo d'aki wurin amaryrsa amina,
Kangado yazauna yana murmushi yace "my life matso kusa dani mana inji dumin jikinki, kinsan cewa ketawace......
Amina itama murmushin take tace "da dai ka tashi mnje muyi alwala muyi sallah mugodewa, Allah daya nuna mana wannan ranar"
Yace Toh amma ransa baisoba"
Suna idar da sallah kawai yafara rabata da kayan jikinta,
Daman a rikice yake,"
"Pls stop it meye hk Amina tace duk ya rude, Amma ina tuni yafara sarrafata, yadda yakeso har Allah yabashi ikon rabata, da kayan Adonta Wato *BUDURCINTA*.
tayi kuka kaman ranta zai fita" nidai nace kukama kadan kika gani",
Wani bacci ne mai nauyi ya debeta,
*Washe gari*
Tana farkawan taga
Babu mus'ab ba alamansa,
Tashi tayi dakyar ta shiga toilet tayi wanka ta gyra kanta,"
Tayi sallah har tagama, Shiru mus'ab bai baidawo ba, ta janyo wayarta takirasa wayansa a kashe,
Tayi jina Tana tunani , kamar daga sama taji ana buga kofa......
A hankali tatashi taje ta bud'e tazace shine saitaga bakon fuska,
" yallaboi ne yace gashi inbaki," yakaeasa maganar yana mika mata wata takarda
Tace toh jiki ba kwari ta amsa ta rufe kofa..
Kujera tasamu ta zauna ta bude, takaddar, abunda ke rubuce acikin takardar ne ya razanata, ta kwalla wani uban kara"
Tafadi kasa warwas.
9:30am har a lokacin tana kwance a tsakiyar d'akin somammiya, kwatsam sai tayi baki sukayi bugun kofar sukaji Shuri" watace Tayi dabaran bude slide din window taga Amina kwance bata motsi.....
""Nashiga uku meyafaru da Amina gatacan kwance, daga karshe balla kofar sukayi,
Kanwar mahaifintace tafara daukan takardar taga, saki uku. Babu kome"
Tayi salati ta sanar da ubangiji........
"Yanzu abunda yaronnan zaiyi mana kenan, cin amana????
Daman wata mata ana gobe biki tazo tafadii" aka maidata mahaukaciya" tabbas ga zahiri.
"Ruwa suka watsa mata suka kira aka taho da mota sai gda,
Mahaifinta kam yakasa zaune yakasa tsaye,......
Amina sai surutai takeyi, kaman ta haukace'
Mus'ab yanzu ka kyauta kenan??? Dan Allah mus'ab karkayimun hk.....
Allah sarki saida kowa yayi mata kuka, tayi kuka harna rashin kwatace saida aka had'a da adu'a sannan aka samu tadawo daidai
*Bayan sati d'aya*
akaje aka kwashe kaya...
duk Ammi batasan wainar da ake toyawa ba. saida tayi bakuwa tace Ashe hk Abu yafaru mus'ab yasaki Amina ",
Zare Ido hjy maryam tayi tace koda bakiji da kyauba.
Yanzu ya fita nace ya Amina yacemun tana lafya?? Ammi mezatayi banda kuka tace shikenan zai bata mana suna a gari........
" ngd kinji dabaki zoba da a ina zanji?
Allah ya shiryamun mus'ab. Amin
*********************
*BAYAN WANI LOKACI*
Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah saida mus'ab ya auri mata biyar,
Amma wasu Sbd kundinsa Dana ubansa suke aurensa"
"Daman kud'a garin kwadayi ake mutuwa",
Ammi ta damu kwarai gari sai gulmansu akeyi, daga karshe sukayi wani sabon gini, shuka koma, NAGOYI.
Inda bawanda yasansu
" Ammi ce kadai kewa mus'ab magana, banda abbansa.
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (melody)👄*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*ZARAH BUKAR*
0⃣8⃣
Kyankywar unguwace wacca ko wanne d'an adam zaizo zama cikin
Dayake sabuwar uguwace......
Alhaji Ahmad rufa'i ne zaune yana kallon talabijin, Daidai lokacin. Da ake sanarda mutuwan mahaifin, colonel sambo dasuki",
" Hankalinsa ya dauku, Daidai da shigowan, mus'ab"
Wucewa yayi "unfortunately "
Ya bugi wani table karan ne ya dawoda hankalin, mahaifinsa.
"Barka da gda yace ,amma abba bai daga idonsa akan mus'ab ba, wucewa mus'ab zaiyi.
Batare da ya juyoba yace "Kai dawonan kazauna" ba musu mus'ab, yadawo.
Abban yace " yanxu kaxabi ka batamun suna a cikin garinnan koh Kaikenan ka auri mace ka saka?Me ka maida mace, Riga yaukasa wannan gobe ka cire wannan? Abunda ka maidata kenan? Tabbas bakayo halina ba dabaka aikata wani Abu maka mancin wannan ba Amma inaso ka sani saikayi dana sani wata rana saika sa rigar dazata zamema kaya" rigarda zatayima wahalan fita.......
Mus'ab yakasa koh motsi, bayan rabon edo babu abinda yake, ganim baiyi maganaba yasa Abba yaci gaba dacewe ",
"Sannan nabaka nanda wata biyu kasamo mata wacce zata zamema garkuwa a Rayuwa," inba hk ba yafadi tareda tashi tsaye ya nuna mus'ab da Dan yatsa"
Zanyima zabi Wanda bakada tsumi bakada dabara. Dole ka amsa, husna zan aura maka wacce kafi tsana a rayuwarka itace zata zama matarka" Fuuuuuu abba ya wuce koh kallonsa baiba, a daidai lokacin ammi tafito tun a d'aki takejin fad'an Abba hakan yasa tafito,
Take mus'ub yajuy a fusace yana kallon abba,
Ganin Ammi yasa ya sassauta fuska.
Ammai takaraso wurinsa ita takai cinsa take , cike da gara tace " tabbas mahaifinka yayi gaskiya, nikaina halinda ka dauka. Yana damuna,
Kasa mutane a gari suna zaginmu, da mutunci mu.... To idan Baccin kake yaka mata kafarka inba hakaba za'a wayi gari agama komai kana bacci............... Ammi ce take magana ranta abace, itama tana gama maganar tafice tabar falon..
*********************
Mus'ab zaune yake shikadai, yarasa abunda ke masa dadii.
Amma babu alaman yayi ladamar abubuwan daya aikata." Sannan bashida niyyar dainawa.......
"Yanzu ina zanje in nemi aure bayan Abba yace dole sainayi aure nanda wata biyu??
Nooo impossible I have to leave to another country before something get spoiled hear"""""
"Yanzu wace yarinya zanje in nema a garinnan?
I will try my best inkuma nakasa samu yaxama dole ingudu inbar garinnan, don baxan taba yarda Abba ya auramun, Husnah ba don baxan taba barinta ta hada jiki daniba,........ I hate her!!!!!!!!
*Dedicated to all youths🙍🏻🙍🏻♂*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
0⃣9⃣
*********************
"Gaskiya yau yasmin garin akwai iska iskan kuma mai dadin gaske,"
" Wallahi kam kawata cewar Yasmin
" jiyannan ga rana gashi muka isa bakin gate Aka shanyamu, da yaune zama zanyi nasan har bacci sainayi, INTISAR ce ke magana cikeda yanga". Daidai lokacin suka kawo bakin gate,
Bude gate akayi tundaga nesa intisar ce ta hango mus'ab zauna a gefen motarsa,
Dasauri tajuyo ta kalli yasmin tace, "Yasmin juya ki kalli gayen can wlh ya had'u yanada kyau Sosai sainaji inama yazama mijina?!!! Intisar tafad'a tareda marairai cewa Yasmin,
Yasmin tasaki baki tana kallonsa tayi jim kamar mai tuna wani abu,
Intisar tace " bakice komai ba kinyi Shuru,"
Yasmin tace "Inty inaso intuna inda nasan wannan fuskanne, kamar nasanshi, bara nayi tunani"
Shikuwa mus'ab Ganin yadda 'yan matan suke kallonsa yasa yatashi yanufi cikin motara,Tunani Yasmin ta tafi har saida mus'ab yafito da motarsa, ya tafiyarsa, bata dawoba,
Inty takai mata dukan wasa tace "Oh Yasmin wane irin tunani kikeyi saikace, wacce tayi loosing komai???
Kinga harya tafi, kinkoga wani irin kallo daya mana, ai saida nashiga taitayina.
"hmmmm" Yasmin tace "intisar taho mutafi kinsan damabln irin masu kud'innan sun iya rainin wayo.
Kallon kowa suke a kaskance, Kinsan wannan dakike gani nataba saninshi, nasanshi a gyallesu
Wallahi auri saki gareshi"
Intisar baki bude tace auren dandane kenan, ba malam hudu yace mana Allah ya tsinewa mai auren dandane???? Kina nufin halinsa kenan, inty ta girgiza kai cike. Rashin gazgazata maganar yasmin sannan tace " Amma gaskiya Yasmin fuskarshi kaman natsatse, baiyi kama damasu irin wannan halinba"
Yasmin ta harareta tace "toh shikenan karki yarda da maganana, kedaman haka kike, wlh wannan dakike gani Humanizer ne, ( manemin mata)
Sannan kwana d'aya dayin aure zai saki yarinya yace tayi gdansu, kenifa kingani hanyannan ma mudaina bi Sbd karyace yanason d'aya daga cikin mu,
Don banaso nazama victim"
Intisar tatabe baki cike da rashin yadda da maganar yasmin tace "Nikam akan wani kato bazai daina bin wannan hanyarba, amma kina ganin cewa wata rana bazaiyi ladaman yin hakaba"
Yasmin tace "Intisar baida niyyar yin ladama Sbd har kungiya garesu,
" yan auri saki"
Intisar ta zare edo " Tirkashi Yasmin Allah yayi mana tsari dashi, saikuma intisar ta marairaice fuska tace " amma kuma Yasmin nasan cewa inna gaya miki wani Abu zakiji tausayi na, Wallahi nakamu dason bawan Allah nan kuma inada niyyan canza mishi duk wani hali nashi amma da taimakonki."
Cike da tashin hankali yasmin tace "Wa!!!! Ni!! a a kam ai idan kinganni a lahira kaini akayi, bani nakai kaina ba, mezai sani nashiga harkar wannan mutumen"
" Hahaha...... Yasmin kintaba ganin Wanda yakai kanshi lahira?
Ai Allah keyiwa kowa ajalinsa, Sai mutane sukai mutun kabari subarshi dagashi sai halinshi,." Intisar tafad'a tana dariya,
Yasmin tayi saurin rike hannunta tace "Kinga muyi Sauri karmuyi latti irinna jiya Malam hudu ya jibgemu.
Sauri- sauri gudu- gudu haka sukeyin tafiya, saiji sukayi antaka burki Daidai da zasu tsallaka titi. Kiiiiiiieeeeeeeeee!!!!!!
*Dedicated to all youths*🙍🏻🙍🏻♂
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)👄*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
🔟
Juyowan da zasuyi mus'ab suka gani,
Da Sauri intisar ta tsugunna muryarta na rawa tace,
"Dan Allah Malam kayi hkr" tuni yaji wani natsuwa, har cikin zuciyarshi,
Murmushi yamata "Tashi karkiji komai, nasan ba laifinku bane nawane, kuyi maxa karku makara". Da gudu intisar ta wuce Yasmin ma tabi bayan ta,
Sai gudu sukeyi.
Mus'ab kuwa mezaiyi banda dariya"
"Just take a look ganina duk sun zabura, motarsa yashiga yana kallon kyakkyawan fuskar intisar, tana dawo mai.
A zuci yace " Allah ya hadani da hasken idanuwana, yau gata karamar yarinya,
Sweet sixteen" yakarasa zancen zuci tareda shafa kasan gemunsa.
Tundaga ranan bai sake ganin intisar ba, yakasa cin abinchi yakasa, komai.
Bashida wani abunyi saina tunani",
Office dinma yadaina zuwa.
" Ammi tana sane daduk wani halin da mus'ab yake ciki, Amma tarasa yadda zata bullowa abun,
Yau mus'ab yana zaune a falo, yana kallon tv, amma hankalinsa kwata-kwata baya kan kallon, fuskar intisar kadai kemasa gizo,
Abba yaturo kofar falon yashigo, tare da yin sallama, ganin mus'ab zaune a falon yasa ya tsuke fuska,
Mus'ab yana zaune baimasan da shigowar abba ba sai maganar kawai yaji yana fad'an "saura kwana ashirin yaragema kafito da wacce kakeso,
Inba hakaba my "decision take place"
Bansan lokacin da na firgita ba, saura kiris, wayata ta fadii,
Sbd wani irin kara danaji mus'ab yayi.
"Hawaye kawai naga yanayi,"
A lokacin ammi tafito zata yiwa abba sannu da zuwa, a daidai lokacin mus'ab yasaka kara, saida ta firgita, hankalin Ammi ya tashi ganin, halinda danta yake ciki. Abba ko kallon ammi baiba dominshi ransa a bace yake ya wuce d'akinsa,
Ammi tayi tsaye a falon nad'an wani lokaci daga bisani kuma takarasa gurin mus'ab, zauna tayi kusa dashi ta dafashi tace. Son gayamun dalilin damuwanka,?"
Da Sauri yad'ago yace "Ammi zaki iya sharemun, hawaye na?"
Ammi tace "Kwarai my son inhar baifi karfina ba, Koda dukiyana gaba daya zai kare akanka, my Son."
Mus'ab yashare hawayensa yana kallon amma yace "Ammi dakwai wata yarinya Dana gani nakeso,
Amma narasa inda zan ganta kullun ina ganinta zata islamiyya, Amma kwana biyu bata ba lbrinta. Sai kawarta nake gani,
Gashi banaso kawar tasan inason kawarta. Sbd nataba ganin yarinyar a gyallesu,
Tana yawan zuwa gdan kakanninta
Banaso ta gayawa yarinyar halinda nake ciki."
Amma tayi ajiyar zuciya sannan tace ""Yanzu kana nufin yarinyar tasanka," mus'ab ya girgiza kai, ammi takara saukw nunfashi tace "Karka damu dani dakai zamuyi wannan farautan, Sbd muba Abbanka kunya"
( *Masu iya magana sunce hannunka baya rubewa ka yarda,*
*Haka duk lalacewar masa tafi karfin kashin shanu*)
*********************
"Umma yanzu haka zamu zauna da yunwa?
Kinga kausar yunwa takeji, tun d'axu take kuka umma," intisar tafad'a tana kallon ummanta,
"Intisar!!! Yanzu Yakikeso muyi babanku bai dawoba,
Kinsan yanzu dakyar zai shigo da kwatan gari. yanzu wata yayi nisa masu cefanen wata ba'a biyasu albashiba, kuyi hakuri yadawo sai mugani mezai zo mana dashi"
Cikin fuskar tausayi intisar tace " hakane umma, Allah ya rufa asiri, bari naje gdansu Yasmin inji ko sunada tsaki su sammaba,
Muyi dantama lele...!!!!!" Tana gama fad'a ta mike tsaye,
Umma tace "Toh saikin dawo"
Tana fita mus'ab ya hangeta daman yanzu kullun yana unguwar yana dakonta,, ganin gidan data fito a jagule yasa yafara zancen zuci yace " daman dakwai mutane acikin wancan gdan?
Kuma nan naga tafito?"
Yana karasa zancen yayi murmushi a Lokaci guda yace "abu mai sauki kamar ruwansha, zanyi saurin siye iyayenta da abun duniya( Wato kudi) dunda su talakawane amatse suke...
*Dedicated to all youths🙍🏻♂🙍🏻*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)👄*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
1⃣1⃣
Aiko Saina aureki," yana karasa maganar yashiga motarsa,
Bai zarce koh inaba sai gida, yana parking a harabar gidan yafito dasauri yanufi cikin gida yana kwallawa ammi kira"
Ammi!!!Ammi!!!!
"I have a good news for you,???
Whr are you???
Da Sauri ammi tafito daga d'akinta,
" wane irin good news ne wannan mus'ab" ammi tafad'a bayan ta isa wurinsa,
Mus'ab yana fara'a yace "ammi nasamo yarinyar, ashe 'yar talakawace"
Ammi taji dad'i sosai tace "masha Allah, yanzu meye mafita"
Mus'ab yace "yawwa ammi abu nafarko dazan farayi shine na tsaye iyayenta da imanin kafuri(wato kud'i) yanzu Ammi pls kije gdansu yarinyar kiyi musu magana, ga kudi kikaimusu,
Saboda naga mabukata ne"
Ammi tace " mus'ab bafa najeba daga baya kasa naji kunya, Dan Allah karka bani kunya?
Kaba yan uwanka kunya kowa sai gulmanka yakeyi."
Mus'ab ya shagwabe fuska kamar wani karamin yaro "ohhh ammi, karki damu insha Allah wannan itace ta karshe"
Ammi tace "to shikenan "
********************
"Yasmin Dan Allah kunada tsaki, kusammana Wallahi babanmu baidawo ba..
Gashi kausar sai kuka takeyi,." Intisar tafad'a tana kallon yesmin
"Intisar babu tsaki amma barina baki abinchi kikaimata...." Yasmin tafad'a tare da mikewa tashiga kichin tad'auko abinci acikin kula takawowa intisar, intisar tayi godiya sannan tafita tabar gidan,
"Akan hanyan ta na dawowa takara cin karo dashi,
Tana sauri- sauri ta wuce ta wurinsa domin har yanzu tsoronsa takeji, mus'ab yace salamu alaikum"lokacin dayasha gabanta,
Koh kallonsa batayiba, cikin hanzari tace " Dan Allah Malam kayi hkr kaga in babana yaganni dakai Wallahi yankani zaiyi",,tana karasa maganar tayi banza dashi ta wuce gida......
*********************
Ammi sallama tayi cikin gdan tace sannunku, da Sauri intisar ta ajiye shikafan datake bawa kausar,
Tatashi dasauri tana mata sannu tace "ga kujera, kizauna" bayan ta ajiye mata kijerar agabanta,
Sannan ta kwala umma kira " umma kinyi bakuwa,"
Umma tana cikin d'aki tace "Toh ganinan zuwa.
Bayan umma tafito daga d'akin tsaya tana kallo ammi, saidai bata waye taba, amma saita karaso kusa da ita tazauna "Sannu da zuwa" akasa umma ta zauna,
Ammi tace yawwa sannu, ya yara ya sanyi, ammi tana kallon gidan ya yatsine tace "Kuna kokarin zama a cikin gdannan ga sanyi, gashi rufin buhu ne.....
Umma tace "Hjy anata ciki waketa, rufi.."
Ammi tayi ajiyar zuciya sannan tace "bawani dogo lokaci nakedashiba daman Nazone da arziki sannan in nemi alfarma ki dakuma ta 'yarki,"
Ni???? Umma tafad'a cikeda mamaki,"
Ammi tayi murshi tace "Karki damu inaso muzama surukai ne,
'Yarki intisar nakeso Ku aurawa D'ana...... Wanda shikad'aine farincikina, yana cikin damuwa, akan intisar, idan zaku amince bamuso bikin ya d'auki wani dogon lokaci, inhar intisar zata aminche!!!!?????
*Dedicated to all youths🙍🏻🙍🏻♂*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
1⃣2⃣
Ga wannan zan dawo zuwa jibi inji sha'awaran dakuka,
Yanke.
Kudi ta ajiye musu mai tarin yawa, don saida umman intisar ta rude" har kofar gda ta rakata tayi mata fatan alkhairi.
"Intisar, tana fitowa daga daki ta hangi kud'i matsowa tayi kusa, da Sauri tace umma waya baki kudi cikin mamaki take magana,
Umma tana kirga kudin tace Wancan baiwar Allah nan dakika ga tafita itata ajiye mana wannan kudin........
Ihu intisar tayi tace yau akwai bidiri umma, zamuci shinkafa da miya",
Umma ta katsa mata farin ciki da cewa " Intisar inada magana dake, kiyimun biyayya insha Allah baxaki taba tagayyara ba,"
Intisar tayi danyi jim sannan tace" umma zan iya komai don ganin farincikin ki,
Koda haka zai kasance akasin nawa farin cikin..... "Tafadi tana zubda hawaye tunkafin ummanta tafadi, taji abunda hjyarnan data fita tafadi..
"Suna cikin hakane, saiga mahaifinta ya dawo",
Fuskarsa, cikeda damuwa' hannu rabbana yashigo.
Kawai tozali yayi da makudan kudi tuni ya wartsake..........
Samira ina kuka samu makudan kudi hk? Nanfa ta gayamai komai dayake iyayene masu kwadayi,
Abba yace "Ai taxo gdan sauki, insha Allah dasun dawo kice ta amince yaro kuma nabashi izinin zuwa zance........
"Cikeda tausayin kanta, tace umma, baba zanyi muku komai inhar zanga murmushi acikin fuskanku'
" banida wani buri saina ganin kuna cikin jin dadii.
Allah yasa shine mafi alkhairi a gareni'
Tana gama fadi ta tashi ta shiga cikin daki.......
"Allah ka hadani da, iyaye kwad'ayayyu, wayanda basa tunanin makomar rayuwata,
Amma ba laifinsu bane, tabbas na yarda talauci yana daya daga cikin yankin imani......
Intisar tabani tausayi kwarai" baniba harta mai karatu saiya tausaya mata.
*"Bayan kwana biyu,*
mus'ab yafara zuwa gdansu, intisar nan mutane sukayi cha akai, yanzu Malam magaji wannan Dan zaiba yarsa"
Wanda kowa yasan cewa auri saki yakeyi....????
"Amma hakan baisa, mlm magaji yakaraya ba.
"koda inty zata je washe gari ta dawo ba komai inhar zanyi ban kwana, da talauci.haka kawai malam magaji kefada
"Yasmin tayi mamakin labarin daya risketa, cewa inty zata auri, Mus'ab.
"Tayi bakin ciki Dan tasan wayanda suka fita,
Basusha ba bare ita.
Yar ta tsitsiya,
Amma "Duk tsuntsun dayaja ruwa shi ruwa kan duka,
Mudai 'yan musha bikine.
" intisar daman tana masifar sonsa amma sbd halinsa ne yasa, ta cireshi a ranta ta gujeshi.
Yau mus'ab ne tsaye a gefen motarsa shida inty suna zance,
Mus'ab yace "My love kinada kyau sosai, inasonki ina kaunanki, Bantaba jin son wata ya mace ya shiga zuciyana lokaci guda irin yadda sonki ya shigeni ba,
Gobe Abbana zasuzo Neman aurenki kuma a gobe zaa sa mana rana,
Lokaci guda annurin fuskanta,ya gushe, tuni mus'ab ya rude yace. Nashiga uku Nayi laifine wajen fadin hakan?
" Da Sauri tace ah ah ina farinciki, kwarai, da wannan albishir dinka,
Zan tafi gda sai anjima...
Yaro yasamu bayan tafiyanta, yace ungo mikama ta cikin gidannan", yaron ya wuce da ledoji niki-niki na kayan alatu,
A yaune asabar akasa ranan bikinsu, sati hudu.
Karkuyi komai cewar Ammi data dau son duniya ta daurawa Inty. "Toh sukace abun duniya baya boyuwa, gari ya karade da zancen mus'ab zaiyi aure.......
Kuma yar karamar yarinya zai aura,
Mu abunda munsan komai Wallahi Malam rabe talauci ne yasa mlm magaji aurar da yarsa,
Inba talauci ba yasan cewa yaronnan auri saki yakeyi yadauki yarsa, yar shekara goma sha takwas aurama, Gansanemen yaro sbd kudi Ku tsaya kuji ana biki yau gobe zaku ganta tadawo...
*Dedicated to all youths🙍🏻♂🙍🏻*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH ( Melody)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
1⃣3⃣
*Wacece intisar*
Intisar magaji shine sunanta na ainihi.
Inda mutane ke kiranta da Inty.
"Yarinyace kyakkyawa son kowa kin Wanda yarasa,
Yarinyace ajin farko, mai karatu har ajin karshe, takai..
Farace amma sbd wahala duk ta dafe.
"Asalinsu Fulani ne, don zan iya cewa haifaffun Nagoyine,
Kowa nasu anan yake,
"Samira shine sunan ummanta,
Da kuma Kanninta hudu,
Itace ta fari, sai usama shine na biyu sai unaisa da kausar itace auta.
" sbd talauci tundaga makarantar primary Inty bata cigaba ba", sai islamiya datake zuwa.
Shima nauyinta, malam hudu ya dauka.
*Cigaban labari*
Biki saura sati biyu biki umma ta hada 'yarta, babu irin abubuwan gyara daba tayiwa 'yarta ba,
"Ita a tunaninta, ko matanne basu gyara Kansu shiyasa yake sakinsu.
*********************
GDA yafara cika, har lere da soba, akakai goron biki,
Wasu sunce Allah ya kiyaye suje bikin da gobe zai sako mata,
Kowa da abunda yake fad'e.
"Itadai bata damuba danta ne jinintane, batada yadda, ta iya,
Da ikon Allah.
Yasmin ce kwance tana dannar wayarta, intusar tana gefenta a zaune,
Yasmin tad'an kauda kanta daga kallon datake ta dube yasmin tace waike bikinki babu party ne?
"Gaskiya babu" cewar intisar, "kinga walima zanyi.Yasmin inaso kisamo mun abunda zansha, jinin watana yazo, Sbd naci damaran zama gdan mus'ab kota hakin kaka"
Yasmin ta bushe dadariya tana kallon intisar tace "Hahaha kinjiki fa, wai kinyi d'amarar zama gidansa kota halin kaka, to idan ya koreki fah? Saiki zauna kamar wata Mara yanci?"
Intisar tasauke nunfashin tace " Yasmin insha Allah sainaba marad'a kunya, sainaba kowa mamaki, saikuma ankafa tarihi akaina, domin insha Allah bazanbar gidan mus"ab ba".Saina kwatowa duk matan daya aura yanci, sai na ansar musu *FANSAR BUDURCINSU*
Sannan insha Allah maza masuyin haka zasu dawo kan hanya madaidai ciya, kedai kawai kisa edo kiga irin nawa aikin, Yasmin adu'arki nake nema,
Sannan maganin nan nakeso. Saidai muje chemist mutambaya",
Kila mudace."
Yasmin tace 'to muje" nan suka tashi suka fita
Tafe suke suna hira wasu yan mata zasu wuce, sukace kinganta can " kud'a garin kwadayi yake mutuwa",
Ran Inty yabace tace eh naji kwadayinne Ku maiyasa bakuyi kwadayin ba...... Kokuma meyasa ya tsalake gdanku yazo gdanmu? Toh ahir dinku, inba hakaba yanxu zamuba hammata iska, yan iska muna fukai dagaku har iyayenku........
*Dedicated to all youths*🙍🏻🙍🏻♂
[11/21, 9:05 PM] +234 806 873 6032: *FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)👄*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
1⃣4⃣
Nan dai taci masifarta mai isarta yaran basu kara kulataba,
Yasmin taja hannunta suka wuce shagon mummy dake tsakiyan layi", Abun murna aunty mummy suka samu sukayi mata magana,".
"Daga bisani tabasu maganin suka wuce "
*********************
Ana saura kwana biyar biki,
Mus'ab yazo yayi musu albishir da cewa, an Gina musu gda subar Wanda suke ciki"
Daman haya sukeyi a ciki, mlm magaji kamar zaiyi fitsari don murna," gaba daya ya rude, fatansa dai Allah yabar yarsa a gdan mijinta,".
"Komai ansa musu acikin gdan na more Rayuwa, yan gulma sai zuwa sukeyi.
Akwatina goma aka kawo ciki harda sarkar zinare,
" Wanda a kiyasin danayi yakai naira dubu Dari hudu da hamsin"
"Yan kallo sai zuwa akeyi, komai na biki mus'ab yayi, amarya tasha lalle kaman ba iyaba,
Duk Wanda ya kalli intisar Wallahi ya dinga kallonta kenan,
Tazama kamar wata zinariya,
Koda yake baiki a kirata da " Apple of her parents eyes".
"Ranan biki akayi kaya taccen walima,
Wanda yasamu hallatan zaratan abokanan ango,".
Daganinsu bawanda zakacema, na banda.
" Ango sai sheki yakeyi, tuni intisar taji magani yafara aiki, daman ta shiryawa, zuwanshi.
*ladies care premium* dinta ta siyo don ance zatayi zuban jini sosai.
"Kallon Yasmin tayi mata signal da Ido, daga bisani ta kalli angon nata.
Wa'azi tace ayi mata akan masu auri saki,
Ai kuwa malamin ya koro aya an koro hadisi daya bayan daya aka nemi, abokan ango aka rasa,
"Ina abokan naka cikin Rashin gaskiya yace, sunada wani meeting ne, nima yanxu zan wuce.
Zamu dawo daurin aure nanda, karfe biyu.
"Ba musu da Sauri Yasmin tace, kinganiko basuda gaskiya, hmmm Yasmin, kingansu kaman mutanen arziki koh? Toh zanyi maganinsu daya bayan daya saisun gane cewa......
"Na banbanta da sauran mata",
Yasmin tace " kedai kibini asannu, don shafin banfara ba, bare in bude..... Sukayi tafi sukayi dariya sukayi shewa.
"Yan biki sai zuwa sukeyi. Gda yacika yayi dankam.
*********************
Ammi gaba daya tsoro takeji don kar mus'ab yabasu kunya,"
Alhj Ahmad kuwa abokansa, uku ya gaiyata, Wanda suma haka sukeyi......
"Andaura aure umma ta dauki sallaya ta hau sama ta jero salloli, ta daga hannu sama, takaiwa Allah kukanta...
*Dedicated to all youths🙍🏻🙍🏻♂*
[11/21, 9:05 PM] +234 806 873 6032: *FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
XARAH BUKAR
1⃣5⃣
*********************
Misalin shida Na yamma sukazo d'aukan amarya,
Tabbas gdanku ne, koda kasa kikeci yafimiki, kowani gda a fadin duniyannan.
"Sannan kuka al'adane, in amarya batayiba, sai ace da ita Marar kunya.
Tabbas kowa yayi mata fatan alkhairi"
Umma dake zaune kusa da l intisar tace "umma Dan Allah kiyafemun, adu'arki ita kadai bakeda bukata.... Adu'an uwa ga yarta baya faduwa kasa banza,
Umm tayi murmushi tace "Intisar bakiyimun komaiba Allah yayi miki albarka, yasa kizama zinayi acikin mata, Ki kasance mace mai biyayya da hkr juriya da Sanin yakamata, tsafta,kula da miji shine abunda zaisa ki kwatarwa kanki yanci, kiyiwa kowacce mace zarra" umma takarasa maganar tana hawaye, intisarma haka kukan take,
Nan dai Kowa acikin gdan saida yayi mata fatan Alkhairi,
Daga bisani aka dauketa sai gdan mus'ab babu Wanda ya kwana a gdan hatta kawarta Yasmin..........
*********************
Bayan an watsene saiga mus'ab da abokansa, suna tafe suna dariya,
"Wato banza tafadi gasassa"?
"Nikam nace dole mus'ab kamaida mugun yawu, domin intisar ta shirya zama dakai, tanajin tafiyarsu tayi saurin tashi ta rufe kofar d'akin,
Su mus'ab suna karasowa suka tura kofar sukaji a rufe, mus'ab Yayi yayi intisar ta fito amma ina tayi kunnen uwar tsinannu tace, ba sunnah bane miji yashigo da abokai fiyeda biyar don ganin amarya, don hk babu inda zataje.
" mamaki yacika mus'ab amma ya kwantar dakai, sannan ya juya wurin abokanansa yace taki fitowa. Akanme zatace bazata fitoba kasan tsarin kungiyarmu???? Cewar wani baki tittirna" dagajinshi daman baida imani.
Intisar tana labe tana kallonsu ta jikin kofar, wani Biro naga anmiko mai, mai masifar kyau"
Karka tsallake gobe inba hakaba kasan halin kungiya"_
Ihu takeda niyyan yi amma saita daure.
Rakasu yayi har bakin gate, yadawo yana wani mugun murmushi,
"Ba intisar ba harni saida naji cikina ya murda, dajin shigowansa. Koda yazo tabud'e kofar, Daki ya nufa, bayan yakarasa yazauna kusa da ita yace amarya kisha kamshi,
Sai wani sheki kikeyi kamar zinariya.
" murmushin karfi da yaji tayi tace Allah koh.
"Mai karatu zaiyi mamakin karamar yarinya kaman inty da dabara iri daban daban..... Wanka tashiga bandaki tayi tafito sanye da towel a jikinta. Yace yaka mata ki shirya muyi sallah muci abinci Koh?
" Kallonsa tayi tace hakane bari na gama shiryawa, tukunna saimu ci abincin saimu yi alwala Koh????
"Dariya mus'ab yayi yace amarya bakya laifi" yana wasar hauru, saida tagama shiryawa tsaf ta zauna tace bismillah. Abun yana bashi mamaki sbd sauran matan dayake aura, bahaka sukeba, d'ard'ar yafaraji.
" Anya ba aljana, na auroba. Kuwa?
Huramai Ido tayi tace, haba *chocolaty"* tunanin me kakeyi tunkafin ka Tara yaya?????
Ba komai my life, citake tana Adu'a acikin ranta. Allah yabata saa akan mus'ab takoyamai karatun daya Dade bai karanta irinsa ba.
"Tana gamawa ta haye gado, yatsaya yana kallon ikon Allah, me yarinyarnan take nifi danine?
Tashi muyi sallah mana"?
Nifa banda tsarki, sbd hka banga dalilin da zakace intashi inyi sallah ba_Liman saika maida wukan don bani na kasa zomon ba rataya ma baa baniba,
" intisar tana gama magana taja bargo, tabarshi zaune, yanata sake sake,
Tashi yayi ya buga uban tsaki, yafice abunsa, itako ganin hk yasa, ta tashi da Sauri, tabi bayansa,
Wani daki yashiga,.
"Alamun waya yakeyi,
Tana jinsa sannu2 yana fad'an mutumina,
Yarinyarnan fah batada tsarki, yazanyi"
Acen bangaren wanda yakira yace " duk ranar data gama, saika cika aiki, ka aikata gda....."
Yace " tohm sannan yayi sauri yakashe waya.
" intisar da Sauri ta koma daki, ta rufe kofa GAM da mukulli.
Bayan yagama yazo kofar d'akin ya tarar a kulle, yayi bugun duniya taki budewa, daga karshe ya juya yayi d'akinsa.
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (melody)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
I dedicated this humble page to ANEESA DIDI🍼🍼
1⃣6⃣
Adaren ranan mus'ab yashiga damuwa kwarai, amma daga bisani yayi wata muguwar dariya,
"Intisar bazaki taba tsallake tarkona ba,
Haka dole tacimma ruwa, " tir nidai cewa nayi ba abunda zaiyi tasiri inba'asa Allah aciki ba, komai yafada babu insha Allah acikin,"
Nikam nace aikin banza.
"Cikin Daren inty tayi alwala, dukda batada tsarki tadinga adu'an Allah yakawo mata dauki.
Daga karshe bacci mai nauyine ya dauketa, tashi tayi bayan gari ya waye, tashiga toilet tayi brush. Tafito tana hamma tareda yin mika mai tsawo tayi salati ta gaida ubangijinta. Bayan tagama tafito falo
Zagaye take acikin katon falonta, tana kallon tsaruwan, da gdan nata yayi,
Tsalle tayi ta fada kan kujera, ai da Sauri ta tashi",
"Donji tayi kaman kujeran na numfashi"
Nikam mezanyi banda dariya, cikinta taji yanata kiran ciroma.
Wasu kuloli ta hango masu sheki da tsada,
"Iya leke lekena, narasa inda na taba ganin, kulan nan",
Daga baya na tuna, gdan Ummeey zamfara nataba gani.
" Akalla kudinsa yakai dubu sittin,
"Bude kulolin tayi taga abinci, kala daban daban, aituni intisar tafara, zubawa, komai saida tasamu nasaran, ci.
" tanaci tana tunawa, dayan kanninta kome sukaci da safennan oho.
Tana gamawa, misalin karfe daya taji ana buga kofa,
Tuni jikinta ya hau kyarma,
"Da gudu ta tashi ta sanyo hijabi, dogo har kasa, ta bude, wata mata ta gani tsaye, gawani mutum abayanta dauke da wasu kuloli.
Hjy Ammi ce tace ga abincin, rana abada kwanonin dazu, da Sauri intisar ta washe baki tace, toh bismillah kushigo.
" Kan dinning suka ajiye komai, direba ya kwashi, kuloli,
Indo ce tsaye tace yarinya tabbas kincika diya mace, tabbas iyayen ki basuyi asaran zuwanki, duniyaba.
Naganki cikin murna da walwala, dafatan kinsan halin mijin naki, auri saki ne.
Zan baki wani sirri, zuwa anjima inmuka dawo kawo miki abinchin, dare.
Kallonta inty ta tsayayi tace, toh Allah yakaimu.
Amin indo takama hanyan ta wuce,
"Intisar yar albarka, taci tasha, tayi kashi,
Ta kwanta, tayi bacci.
*********************
"Samira kindaiji inty Shiru, tun safe nakesa, Ido inga tashigo amma Shuru?" Malam magaji yafad'a yana kallon umma,
"Hmm malam kenan, ai 'yarmu jarumace, sannan adu'armu bazata fadi kasa banza ba". Ummanta ke magana babu alaman damuwa, a fuskanta,
Kokuma d'ar.
*Dedicated to all youths🙍🏻♂🙍🏻*
*Dedicated to all youths🙍🏻♂🙍🏻*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)*👄*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
Dedicated to Aneeluv GRP, Humairah melody GRP, manshat nvl GRP, Rashkardam GRP, maman Abba nvl GRP, faxy nvl GRP.
1⃣7⃣
"Ka kwantar da hankalinka, zuwa jibi zansa, Yasmin taje gdan tajiyomun labarinta, yan unguwa, sai zarya sukeyi cikin gdan su akeyi, kokuma aturo yaya,
" da gayya umma kebarinsu suzagaya ko ina a cikin gdan.
*********************
Ammi na tsaye a far fajiyan gdan, taga dawowarsu, indo.
Da Sauri ta isa gurin indo, tace ya lafya?
Yakikaga walwalan intisar,? Dariya indo tayi tace, hjy ki godewa, Allah aduarki ta karbu.
Ban ganta cikin damuwa ba Sannan da alamu, mus'ab baya nan.
Hankalin ammi ya kwanta, kwarai, tayi murna,
Shiko Ahj Ahmad yana tsaye ya kasa kunne yaji ance mus'ab ya saki intisar matarsa. Da gudu ammi tanufi cikin gidan tana cewa
Alhj nazoma da sabon aibishir, intisar,Tananan, ba inda taje Sannan,
Babu wata damuwa a fuskanta." Bayan takarasa tazauna
Tuni Alhaji ya washe baki kaman gonar auduga, tabbas, indai intisar taci maganin zamada, mus'ab tabbas saitaji dadin dabata taba mafarkinsa, ba. Gashi akai mata anuna mata yadda zatayi amfani da ATM din, Sannan ga wayanan a kwali, akaima, mahaifanta.
Sannan ga nata tadinga amfani dashi.
Tabbas inhar intisar zata sasu farin ciki koda dukiyarsu zata kare kanta, toh tabbas zasuyi mata hidima.
"Maras adadiiii"
Kamar yadda Ammi ta daukanwa,kanta na ciyar da danta, da matarsa, saboda susamu, suci Amarcinsu, yadda yakamata.
Rashin sani akace yafi dare duhu, Ammi batasan wainar da ake toyawa ba a gdan mus'ab, batasan cewa amarcin ma ba'acishi ba, bare ma ayi tunanin moreshi.
Intisar ta sheka wankanta, sanye takeda, bakar jallabiya, taji duwatsu masu kalan red and yellow.
Tayi packing gashinta, baya tayi gammo dashi, ribbon din datasa, ya shiga da kalan jallabiyan datasa,
Tasa takalminta, "lowpers" tasa tadawo dinning ta zauna taci abinchi tayi k'at.
Daki ta koma tana wani tunani, ina mus'ab ya tafi? Abunda yakamata ango yana gda da matarsa. Tashi tayi tanufi dakinsa
A bakin kofar takaraso nan taji ana dariya, ana shewa, kuma idan zata gasgaza muryar dataji daga cikin dakin mus'ab muryar maccice,
Saida taji gabanta yafad'i
Tuni tace Wato abunda Yasmin ta gayamun, yazama gaskiya, cewa mus'ab manemin matane???
"Aiko sai nayi maganin, abun, nan ta gimtse bakin cikinta, sannan takoma dakinta dakinta aguje ta dauko, shampoo na wanke gashi. Sannan takara dawowa bakin kofar,
Ta kara kasa kunne, tana sauraronsu,
"ka tashi ka rakani, kaga yamma tana karayi Kasan kai angone amarya zata damu sosai cewar ina ka shiga" matar dake cikin dakin mus'ab tafada,
Mus'ab yace ". Merry banaso kitafi kibarni I really wants to be with you til tomorrow pls kikara kwana koda dayane........................
" ah ah jibi zan dawo tashi muje da Sauri intisar ta ruga aguje ta labe, "
Tazuba shampoo kaf a bakin kofar gashi kuma tayil ne,
Merry ce tafara fitowa kafin yagama kimtsa kansa, tafito cikeda yanga tana wani kwarkwasa, ga uban tulin attachment, akanta
Ai kuwa tsantsin shampoo yajata tafadi kasa warwas." Tasaka ihu,
Da gudu mus'ab yayo kanta yana fad'an marry lafiya,
Kafin yakaraso bakin kofar tuni intisar taballe mukulli kofar ta kulleshi a ciki. Yayi ta duka amma kofar taki budewa,
Intisar tajuyo tana kallon marry Wato ranta abace "woto kega yar iska koh, yau sainayi miki jina Nina. Kuma in watsa ki waje insa motar kwasan shara, tayi gaba dake"......
Sai a lokacin yaji maganar intisar cikin tsawa yace"Intisar kizo ki budeni,"
Intisar tace " aiko saidai ka mutu don saina gama da shegiyarnan zan budeka",
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)👄*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
1⃣8⃣
Dakyar merry ta iya bud'e baki tace "Pls madam kiyi hkr bazan sake zuwa miki gdaba,"
Hmmm tuni intisar tayi Sauri tasanyo wani gajeran wando, sakamakon taga merry bazata iya tashiba ,sannan
Tafito daga ita sai singlet.
Ta d'auko bulalarta mai shiga jiki, tadinga tsula mata,
Gashi kafarta ta karye sana diyyan, mummunan faduwar datayi..... Ihu takeyi babu mai cetonta, tana fad'an "baby pls help me"
Intisar tana dukanta tace "ai yau zakiga baby, shegiya kafura"
Mus' ab duk a firgice sai dukan kofar yake kamar zaiyi mata kuka "Intisar kizo kibud'eni Dan Allah kiyi hkr.
Intisar tana huci tace "Wallahi inkaga na bud'eka, toh tagama da wannan, yar iskan yau saina naga uban dayasata kwana gidana"
Sai da mus'ab yagaji da dukan kofar yaga intisar batada imanin bud'e, dasauri yaciro wayarsa yakira abokansa, sukawo masa d'auki,
ba'a dauki lokaci mai tsawo ba, sai gasu,
Tana cikin dukan merry taji ana bugun dayar kofar waje_ jitayi ana cewa " kizo ki bude kofar Dan Allah."
Tanaji tasan abokanan sane,
Dasauri Intisar taje kitchen, tahado ruwan zafi sannan tafito tazagaya ta d'ayan kofar Gidan,
Suna tsaye a bakin kofar sukaji tace "ganinan" ta bayansu, ganinta sukayi da ruwan zafi, da karfi ta famtanu ruwan zafin,
Takoyi nasaran watsa musu ruwan zafin" da gudu suka warwatse, tabisu da gudu har waje , bayan sunfita
Ta janyo gate ta garkame.
Takom ciki wurin merry takoma Ta dinga Jan merry har bakin gate,
Ta bude gate ta watsota waje tacema yara kuyita danta saikun kaita karshen, layi.
"Tadawo ta kulle kofa takoma ciki, bakin kofar d'akin mus'ab tazo " tace saura kai, yau kwanana daya zaka kawomun karuwa, sbd kaganni karama toh Wallahi badaganan takeba."
Cikin tsawa yace " Kizo ki bud'eni, inuwa ba hakaba wlh zan sab'a miki, wlh saina sauya miki kamanni, nizaki wiywa wulakanci"
Intisar ranta a bace tace " ok zanbud'eka inazuwa"
Dasauri taje kicin tad'auko wuka, sannan tazo ta bude kofar, taja baya tayi tsaye tana jiran fitowarsa, dagudu yafito ganinta da wuka yasa ya tsaya chak,"
Cikin zafin rai ta nuna masa wukar tace "wlh Kana tabani zanyima lahani"
"Ki ajiye wkar zamuyi magana, idan kuwa ba haka wlh zan sakeki" yafada cike da lallashi,
Intisar tace "Watoma Tunanin sakina kakeyi Koh, toh kadade, Wallahi.
Kadade baka sakeni ba kai zakayi asara babban. Baniba"
"Noooo Ba haka bane taya za ayi nasaki haba amarya " yafad'a yana dariya,
Intisar zatayi magana kenan sukaji muryar indo tana sallama tana dukan kofa,
Intisar tace " ina zuwa"
Dasauri mus'ab yace a a tsaya dan Allah inshirya infita, daga bisani saiki bude kofar, banason kowa yasan abinda ke faruwa"
dariya intisar tayi tace "toh miti biyu nabaka"
Dasauri yakoma dakinsa yachanzo kaya, yafito yafita ta kofar baya itakuma, ta bude kofar, indo tagani tasaki dariya tace.
Amarya yar shagali, irin wannan kwalliya ?
Ina angon naki, intisar tace yanxu yafita ta baya wai kunya yakeji.
Danladi zoka fita da kayannan kashigo da kulolin can dake bayan mota.
Hk tashigo dasu jirani inba uwar dakina sako mutafi.
Intisar ta washe baki
Indo tace "gashi Alhj Ahmad yace abaki surukunki, Abun cire kudi ne, Sannan ga wayoyi kikaiwa umman ki kikaiwa Abbanki,.
Sannan Ammi tace inkinason yar aiki akawo miki, koxata dinga debe miki kewa.
Intisar tace " indo inaso kitayani yi musu godiya, kwarai.
Kice musu ranan danayi kwana bakwai zanzo ingaidasu"
Indo tad'an matso kusa ga kunne inty, tasassauta murya tace "karki taba yarda mijinki ya kwanta dake, inba hakaba, daulannan dakike ciki saidai kiji a mak'ota, don korarki zaiyi, dan duk sauran matan hakan yake musu"
Intisar tayi gajeren murmushi tace "Ngd kwarai indo kigaida Ammi," cikeda tsoro Intisar tayi sakato, tana tunanin maganan da indo ta fadi mata,
Yanxu nice ke cikin gatannan, tabbas lallai duniya juyi juyice yanzu inazan ga Yasmin don bazan iya zuwa gdaba, sbd yan tsegumi sai suce ya sakoni ne.
Tunda mus'ab yafita bashi ba labarinsa,.
Itako intisar ko ajikinta, wai an tsikari kakkausa.
*********************
Washe gari
intisar tana cikin falo zaune bayan yauma saida sukayi masifa sannan yafita,
Tana zaune taji ana buga kofa, dasauri tatashi taje ta bud'e. Yasmin tagani
Wani irin tsalle tayi ta haye jikin Yasmin,
Yasmin ta kura mata edo tana kallon cike da mamaki "Intisar kinganki kuwa kwana biyu kinzama wata hamshakiya,"
Bayan sun kara sun zauna intisar tace "Meyafi raina, Yasmin inci mai kyau insha me kyau, inyi bacci inyi kashi, intakama inyi tusa." Suka bushe dadariya suduka,
Dariya Yasmin tayi tace "lallaine kawata, meye labari,?
Intisar ta tsayr dadariyarta tace "Komai normal, ya'akayine"
Yasmin tace Wallahi umma ta aikoni inzi inga Koh lafiya, kwana biyu taji shiru ba labarin saki?
Intisar tace " waiyo ummana ina kausar Dan Allah da usama duk suna lafya?
Yasmin tace lafya lau suke bafa dadewa zanyi ba, daman lafiyarki umma tace inzo in gani.
Intisar tace " to Kice mata ina lafya, babu wata matsala, taci gaba damun Adu'a.
Leda intisar ta dauko tace, Ga wayoyinan kikai musu, saimu dinga gaisawa.
Ga wannan kice sudafa, wannan kuma kishafa ma jikinki. Tamika wani tsadadden turare.
*Dedicated to all youths🙍🏻🙍🏻♂*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)👄*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
1⃣9⃣
Wasa farin girki intisar a gdan mus'ab,
Mutanen gari anata zura Ido amma.
"Intisar tana gdan mus'ab, hankali a tashe don ba nace a kwance ba"
*"Bayan sati guda"*
Intisar ta shirya tsaf tace, mus'ab gdan Ammi takeson zuwa ta gaidata" mukullin mota ya damka mata yace. Kije indai zaki iya tukawa, don babu inda zani.
"Toh tace bataki ba ta amsa, katon akwati ta dauka, yaji kaya,
Intisar tace inkasan wata toh bakasan wata ba", Wato kaiga wulakantacce?
" zanyi maganinka",
Keke napep inji yan Zaria " tasamu ta daura akwatin ta,
Tace mai napep ka rufemun labulen nan Dan Allah,.
Mura nakeyi, alhalin karyane", bataso yan unguwa suganta.
"Baa zarce da ita Koh inaba, sai layinsu mus'ab, dayake layin shurune haka tabuga aka bude mata, tashiga.. .
" Ganinta yasa Ammi tasowa da Sauri tace intisar lallai kin cika, alkawari..
Allah yayi miki albarka, ina mus'ab din?
Ammi ta tambaya,
Intisar tace "Yana gda cewa yayi intaho yananan zuwa", daki guda aka ware Mata akasa indo tashiga da kaya.
*********************
Shuru shuru zaiga shigowan, intisar amma ba ita babu alamanta,
Mus'ab dake zaune baida alaman tashi barema ya dubata.
Wayarsa ce ke ruri alamun kirane, batareda ya dubaba yasa a kunne.
Hello mutumina kaxo muje polo yau, dakwai wasa.......
Ah ah gambari yanaga ka canza layi?
Saikaxo kawai mutumina, tashi yayi ya hada, tabs dinsa, da wayarsa, GIONEE U:
Ya fice abun mamaki ba intisar babu labarinta,
Wato tafiya tayida mukullin motar koh?
Ciki Yakoma yad'auko,
Wani mukullin BNW dinsa, unfortunately,
Tayar motar ta sace.
Baiji dadii ba, ya tashi yakoma ciki ya d'auko wani mukullin,
Yana zuwa gaban motar yaga fetir din gaba daya ya tsiyaye.
"Ah ah wai ya haka?
Mota uku duk babu labari,"
A kallah motoci biyarne, a gdan amma hudu basuda lafya,
Sai guda d'aya kuma itace intisar taje da makullinta, girgiza kai yayi tare da cewa "zanyi maganinki"
*********************
Gata ake nunawa, intisar, hatta ruwan wanka, kai mata akeyi.
Kwance take dayake tasan ta'asar datayiwa,
Mus'ab ta kirashi bugu d'aya ya dauka,
Tace "ranka ya dad'e,
Tafadi tareda make murya, dafatan kasamu fitan koh ?"
Mus'ab yace "Bangane me magana ba,? "
Intisar ta bushe dadariya "Ai daman baso nake ka ganeba. Motoci biyarne a gidanka, wato sune adadin matan daka batawa budurcinsu, sai aka wayi gari yau gasy duk sun b'ace babu wanda take sanadinka,
D'ayar motar daka samu tanayi, amma kuma kanajinta ba Daidai ba, toh nice nan inhar ita zaka dinga hawa toh, ina maka albishir d'in cewa ka gamu da matsala, ba karama ba, dan haka malam sai anjima kayi tunanin wacece wannan motar"
Karaf ta kashe wayar,
Mus'ab mamaki yagama cika mishi zuciya,
Wacece wannan,????
"It most be intisar"
Amma I will teach her a lesson, DAT she will never forget" Wato tasan cewa auren d'and'ane nakeyi?
I most do something strange to keep her away from my house.
Da haka ya isa filin polo. Ransa ba dad'i,
*BAYAN SATI UKKU*
Satinta uku agdansu mus'ab, ammi sai leleta take, tasamu wata irin karya ta shararawa ammi cewa mus'ab ne yace taje gida saiya nemeta, shine amma tace tazauan nan sai ranar dayazo da kanshi nemanta,
Yau takama asabar da yamma, yashigo falon ammi nan yaganta zaune a falo, ta daura kafa d'aya kan d'ayi, cike da isa da kuma izza, yarinya takara kyau tayi fresh, yajima ya kallonta tabaya bata masan da shigowarsa ba,
Sai ji tayi kawai yace "wato ke mai wayo koh, shine kikazo kika tare, kuma kinsan dacewa da aure akanki, wato wajen Ammi yafi miki gdan mijinki koh?"
dagowa tayi ta watsamai wani kallon kamar takai masa duka " kashiga taitayinka, kayi harkar gabanka domin yanzu ni 'yar gatace"
Mus'ab ya watsa mata tsaki "idiot girl, kullum kara kurciya take" nan yafice Saman upstairs yake hawa yana surutai,
Intisar takara bushewa dadariya, harda tafawa,
Dakin ammi yashiga ransa abace yana shiga yafara masifa, "Ammi gaskiya bakimun adalciba.
Ya za'ayi kibar inty a gdannan kwana da kwanaki, tabarni da yunwa?Gaskiya kitashi kice ta hada kayanta taxo mutafi?!"
*Dedicated to all youths🙍🏻🙍🏻♂*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)👄*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
2⃣0⃣
Ammi tatashi tana murmushi tace tunda gaka kazo ai shikenan,
Muje tafe suke, koda. Suka karaso falon cikin ikon Allah babu intisar babu labarinta"
Ammi ta kwallawa indo kiri "Indo!indo!!!
Da sauri indo tafito daga kichin takaraso wurin ammi "Naam hjy"
Ammi tadubeta tace" ina intisar take?"
Indo tace "Eh toh naganta da akwati, itada jummai mai aikinta, sun tafi. Sun tari Dan adaidaita,"
Cikin zafin rai mus'ab yace " mai aiki kuma_ aikin banza, wlh yarinyar nan kullim cikin cazamun kai take" mus'ab yafadi yace, amma bakomai iya gobene tuni zan kad'ata gda!!!! Azuci yafad'i wannan zancen
Jin yayi shiru yasa ammi tace "Mus'ab kila tatafi ne bataso ka kaita, bari na kirata," ammi taciro wayarta takira inty bugu d'aya tad'auka,
Cikin gaggawa ammi tace "intyna kina ina"
Intisar tace "Ammi kiyi hkr banaso yakaini ne shiyasa nafiso yadda nazo nakoma dakaina, gani a hanyar komawa gida".
Ammi tayi murmushi tace " Intisar kenan, yar albarka. Kin kyauta, shima gashinan tahowa, kikulamun da mus'ab dina yadda yakamata. Kuma In dawata matsala kifad'a min,"?
"Tohm ammi babu komai gamuma har mun kawo gdan.............. "Ngd sai anjima yauwa, Ammi ta kashe wayan,"
Sannan tajuya gurin mus'ab tace "matarka takoma yanzu, kajekasameta, sannan kuma zansa direba yadinga zuwa yana koya mata mota".
Dasauri mus'ab yace Noo Ammi bayanzu ba kinga bafa wani girma gareta ba
Bari naje dare da karayi, kinsan unguwannan, da matsala yan daba sunyi yawa.
Nan yafice yabar gidan
*********************
Bayan ya isa gida, yasamu intisar kwance a d'akinta, kura mata edo yayi cike da sha'awa, karasawa yayi bakin gadon yafara shinshina kafarta kamar wani maye, bata akaraba taji yafara , taba jikinta, dasauri tatashi tana kallonsa " malam miye haka" uffa yakasa cemata saboda gabaki daya yafita hayyacinsa, yau kota halin kaka soyake yasamu intisar, tashi yayi yaje yarufe dakin sannan yakashewutar dakin, gab intisar yafadi, nan take jikinta yadau rawa "mus'ab wai mekake shirin aikatawane"
"Sonake yau kibani hakkina amatsayina namijinki,"
Duj da tsorace take amma saita daure tayi dariya tace "ai baka isa ba, nice zanbaka kaina, eheeelallai isak yana wahalar damai kayan kara, nidan Allah bani hanya nafita..." Kafintakarsa maganar ya sa hannu yaturata kangado, dasauri yahauro kanta, nan suka shiga kokuwa , danbe sukayi sosai , harsaida intisar tagalabai, tafara gamashi da Allah sarki,
Amma ina Mus'ab yayi babban nasara, wajen zubda mugun yawunsa a jikin intisar, Amma kuma yaji daban da sauran matan dayake aura, gashi kuma dolensa yacikama kunyayarsu alkawari., haka yakare da ita yatashi yakoma falo yakwanta bayan yayi wanka ya kwimsa kansa, sai bacci, intisar kuwa tana cen kwance akan gado ko nunfashi dakyar takeyi
Da Asuba intisar tasha kukanta, babu mai bata hkr tasan karshen zamanta a gdan yazo karshe, amma kuma taci alwashin zama daram acikin gdan.
Tashi tayi dakyar da zufan goshi ta isa toilet tayi wanka da ruwan zafi, bayan tagama tafito ta kimtsa kanta,
Saida tayi sallah sannan tafito falo kafin tafito Tuni mus'ab ya aje Mata takadda", akan table "
Batayi mamaki ba saboda tasan za'a rina
Daukar takaddar tayi taga tabbas sakine tallintal guda d'aya",
"Tayi kuka me isarta, daga bisani ta share hawayenta, taci damaran zama acikin gdan, tunda Allah bai haramtaba har kwalliya yace ayi ko miji zaigane kuskurensa, ya maida aure.
"Dayawa mata basuda wada tattacen ilimi, akan hakan," dazaran miji ya sakeki saiki wani kwashe kaya Niki Niki, sai gda, Wanda yin hakan kuskure ne,
"Mace tayi iddah acikin dakinta shine mutunci ba'a gdan iyayeba," Sannan yazama wajibi miji ya ciyar dake, ya tufatar dake", harta kayan kwalliya shiya kamata siya miki, ko wani baxawarin zai ganki yace yanaso",.
"Allah yasa mudace "
"Intisar ta dauki takaddar tayi mata mugun boyo, sannan ta sheka kwaliyanta mai rai da motsi, tafito suka fara aikin gda da jummai,
Bata nunawa jummai komai ba.
"Misalin uku ne saiga Mus'ab yashigo abun mamaki, ganin intisar yayi acikin daki tana sheka bacci,
Ruwa ya debo ya watsa mata,
Tuni ta mike tana salati tareda cewa, A'uzubillahi binash shaidanir rajim.
" kannan ta bude idonta, yace "Wato nine shedanin? Shinke
Bana baki takaddar sakiba? Mekike jira baki kwashe komatsanki kinvarmun gdana ba?
"Cikeda rashin fahimta tace, mekake nufi? Ganar dani ? Yaushe kasaeni, aini banga wata takardaba"
Mus'ab yace " wannan kuma ke kika sani nidai nace Ki kwashe kayanki ki tafi gda na sakeki."
Wani dariya ce ta kubuce mata Wanda yin hakan saida ya bashi tsoro."
"Lallai nema Mus'ab bakaji kyau ba, hannu ta mikamai, tace zubamunshi anan nikuma wallahi yanzu zanbarma gdannan ka."
Mus'ab yadubeta da mamaki " me yarinyar nan take nufi, ne?"
Intisar tace "Idan baka ganeba?
Cewa nayi biyamun BUDURCINA saina barma gdanka.
Inko baka biyani ba toh mutu ka raba nidakai, takalmin kaza,....
Kai kama rainani wallahi da BUDURCINA ka daukoni sannan yanxu kace intafi bayan ka bareni a Leda,?
Toh wallahi da sake, bazata taba sabuwaba bindiga aruwa ehe.!!!!!! Takarasa maganar da masifa, sannan tarike kugu tace "Ai ba sunan uwata saraiba, haka basunan ubana yautai ba"
Mus'ab yayi murmushi domin duk wannan haukar datake dariya take bashi, "Aiko karya kike cewar Mus'ab baki isaba,
Yana nunata dad'an yatsa, Saina yad'aki a duniya, cewar nasakeki. Idan yaso karkibar gidan"
Intisar Tace "nikuma in wallafaka a shafukan jaridu in karyataka,
Cewa karya kakeyi banga takadda ba" Inkuma kace ka sakeni tabbassai dauki *FANSAR BUDURCINA* aini ba jaka bacedazaka taka abanza, kuma saina yad'awa duniya cewa neman mata kake da aurenka, !!!!!!
Wani wawan mari yayiwa intisar Wanda saida tafara ganin taurari,
Dagowan dazatayi ta itama sharara mai mari tace " kul, karka sake kasake marina, inba haka ba,
Sainayi ma kare jini biri jini, domin yanzu ba'a igiyar aurenka nakeba" tana karasa maganar,
Fuuuuuu tafice kaman zatayi kuka tawucw d'akinta,
Tabarshi nan tsaye a falon ya dafe kumatunsa yan mamakin ikon Allah, yau macce tamaresa, kuma yakasa tabuka komai...
*Dedicated to all youths🙍🏻
♂🙍🏻*
[11/25, 6:58 PM] +234 803 934 4770: *FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
2⃣1⃣
Tabbas intisar abar tausayi ce, daga bisani na hangota tana dariya, ta tashi tafara duk abubuwan dake gabanta,"
Kullun haka take fesa wankanta,
Taci kwalliya, tasa kanana kaya, kuma ta zauna a cikin gdan, koda wasa bata taba bankad'awa kowa sirrinta, hatta kawarta Yasmin.
taci mai kyau tasha mai kyau, wayarta ce ke kara a hankali, infinix hot note,
Ce naga ta kara a kunne, hello Ammi ina wuni, nidai kasa kunne nayi saboda, bana iyajin maganar da Ammi takeyi,
Saidai naji intisar tace toh Ammi Allah yakawoshi lafya.
"Tsalle tayi tace yau zanje kasuwa insiyowa ummata abunda ransu keso, Dana iya ATM dinnan hmmmm ai sainayi wa mata zarra. " horn taji da Sauri ta dauko himar d'inta, tasa ta samu flat shoe tasaka bawani make up tayiba.
"Don duk Wanda yaganta zaice kamar matar manyace",
Tana fita
Bayan mota tashiga tacewa direba, Dan Allah inmukaje inaso ka kaini kasuwa......
" Toh yace babu musu, sun isa ATM machine suka kafa layi. Cikin ikon Allah machine din yana Sauri, tuni layi yaxo Kansu, ya nuna mata yadda zatayi komai.
Kudi ta cira masu shegen yawa, buhunan shinkafa tasiya daduk kayan datakeda bukata, abun gwanin ban sha'awa.
"Gida yakaita ta sauke komai nata tace yaje yakai ma iyayenta,
Sannan shima tayimai ihsani,
*********************
Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah, intisar tashafi wata daya Tana zaman *iddah*
Tareda mus'ab acikin gdan, gaba daya haushinta, yakeji, kullun cikin tashin hankali, suke dayake tarigada tazaman mai rigar karfe, shiyasa yake ganin dakwai abunda ta taka,
Falo ya sameta taci body hug, da wando pencil, ta kunna waka tana rawa, gaba daya ta tafi da tunanin sa.
" da Sauri yaje gaban TV ya kashe, ke wace irin dabba ce karya Mara zuciya,
Kin wani kure mana gda da music.?
Intisar ta kallesa a yatsine tace "Kaji bansan shiga shara ba shanu, bansan tsugudidi, kaji ina ruwan biri da gada, Dan Allah yita kanka, meye ke tsakanina dakai? da aurene kuma yanzu babu shi toh don haka, ka kyaleni inyi wandak'a, yadda nakeso.aa"
Cike da bacin rai mus'ab yace "Baki isaba wallahi tunda nandin ba gdan ubanki bane!!!!!!
Intisar tatabe baki "Oho dai zamane dai zaman iddah nakeyi kuma lokaci nayi zanbar ma gdan uban naka," itama da wayo tarama zagin dayayi mata, tana gama fad'a tabar wurin
tafiya take tana karairaya, gashi taci ta koshi, mazaunanta, sunyi bulbul,
Komai nata yaciko Fam.
Mus'ab tuni yaji gaskiya yanason matarsa, yaji duk duniya, babu wata mace dazai iya Rayuwa da ita imba,
*Intisar* ba.
A daidai kofar kichin tace "Jummai inkin gama abincin kikawomun daki, ki hada mun da yogot." Yadda tafadi saida nayi dariya, ita ala dole tayi turanci. Sannan ta wuce d'akinta
*********************
"Malam kaga abun arziki inji Dan hansin", kowa sai gulma yakeyi, wai boka mukebi da malamai?" Umma tafad'a tana kallon malam magaji dakecin abinci
Shinkafa Malam baban intisar yakeci duk abunda take fada baijiba, sai cewa yayi
"Wai banako manoma sun samu shinkafa kuwa? Itakuma umma tace " Malam inazasu samu shinkafa gashi kanata ziri"
"Sai a lokacin yasan cewa santi yakeyi, dariya kawai yayi sannan yaci gaba dacin abin cinsa"
**************###****
"Ammi ce zaune takira, mus'ab tace yau insha Allah inanan zuwa inga surikata,"
Dasauri mus'ab yace " mekikace????
Ammi tace "Cewa nayi kacewa intisar inanan zuwa.
Ai tuni ya daburce,
Daga wajen aiki yad'auki waya yakira intisar amma wayar tana ringing taki d'aga wa,"
Duk yabi ya rude hankalinsa duk yabi ya tashi. Gashi aiki yayimai yawa customers sai kira sukeyi.
Intisar tana zaune tana kallon wayarta dake ring tace aikin banza bazan d'aukaba. Koh ubansa zan masa oho, wawa kawai marar sanin darajar macci" saikuma taji tanason tad'auka taji mezai ce mata,
Tana gani kiran yakara shigowa, ta d'auka a fusace, tace
" Wani wawanne Mara tunani yake damuna da kira saikace wani batacce?
Sannan tayi shuru,"
Mus'ab yace "Nine mus'ab Ammi zataxo kiyi mata abinchi kuma karki sake kigaya mata!!!!!!
Intisar taja tsaki sannan tace "Mtwww, toh wai angaya ni irinka ce sakarya, ai wannan saikai tunda baka gaji dajin kunyaba,
Sannan babu abunda ya dameni da zuwanta.
Kuma karka sake kirana don fita zanyi yanxu,"
Wayarta ta kashe gaba daya, shiko mus'ab yarasa yadda zaimata ya wuce,
Nace uhum kadanma kagani, ai baa fara komaiba.
Da karfi ta kwalawa jumma kira bayan takashe, cikin hanazari jumma takaraso,
Intisar tace " jummai zo gyara koh ina bari nashiga kitchen. Ammi zataxo inkingama kisameni a kitchen," jummai tace toh hajiya"
Girki tazauna ta tsara na mutunci.
*Balangu tayi da guava drink, sai jollof din shinkafa, mai hanta, sai farfesun kifi ruwa, sai tadafa kuskus da taliya aka yimata miysn kabeji da Kara's.*
Abun baa magana,
Wanka tashiga tayi, towel ta daura, tanajin muryan Mus'ab, tajuya baya tana shafa mai
*Dedicated to all youths🙍🏻🙍🏻♂*
[11/25, 6:58 PM] +234 803 934 4770: *FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)👄*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
Ina kiraga masoya wannan littafi dasuyi hkr,sun jini shuru hakan yafarune sanadiyan exams danafara, amma insha Allah zaku dinga jini.
Ina kuma baran Adu'ar Ku. Love you all😘
2⃣2⃣
Banko kofar D'akin yayi afusace, kawai burki yaja ya tsaya, yana karewa inty kallon. Dayake tasan shine ita kuwa juyosa bata yiba,
Itako da gayya takeyin mai wani abun,
A fusace yace " Ammi taxo ?
Ko juyosa bata yiba taci gaba da kwalliyarta, cike da raini tace "Dayake kabani tsaronta dole ka tambayeni ita, taja dogon tsaki, mtwww...........
Sannan tamike tsaye tana wani rausayawa tana tafe tana juya maxaunenta, tana girgixa koh ina na jikinta," tuni mus'ab yashiga tashin hankali.
Yaji duniya yanason ya kasance tareda intisar amma ina, tayi masa nisa,.
Dasauri ya kawar da tunaninsa yayi saurin cewa " Dan Allah kisa jummai tayi mata abinchi."
Intisar tace "Bazaayi ba Koh ana dolene, a a, Jinan malam nayima iyaka da dakinnan, Sbd inhar zakana shigowa nikuma baxan fasa gayama duk maganar dataxo bakina ba.
Kamar daga falon suka fara jiyo muryar kamanna Ammi da Sauri ta karasa shirinta, ta fesa wani turare mai D'an banzan kamshi.
Bayan tagama shirinta Ta wucewarta, tabarshi tsaye kamar wani gunki,
Dariya inty tayi tana murnan ganin Ammi,
Har kasa ta duka tace, ina yini Ammi.
Lafya lau inty Nasameku lafya?
Ah lafya lau umma
Mus'ab tagani tsaye!!!!
" yace barka da zuwa yauwa yace. Ya aiki ana zuwa kuwa?
"Intisar dake tsugune ta tashi, tana kiran jummai
Kitchen tashiga tace maxa kikai ma Ammi kayan ruwa," toh Aranan Mus'ab yaga bariki tsantsa a wajen intisar.
Bata nuna cewa komai ya faruba.
Ta fuske tana ma Mus'ab wani shu'umin kallo, a zuciyarta tana cewa
" watan d'aya kwaram yake"
Ammi taji dadin hadadden girkin inty kwarai. Karfe ukun yamma Ammi takama hanya ta koma,
Makudan kudi ta ajewa intisar.
Tuni ta lamushe tayi d'aki dasu,
Bayan ammi tafita
Mus'ab ne yadawo dakin intisar, tana zaune bakin tana tunani, taji shigowarsa, a fusace yace "ke Dan ubanki dole kibar gdannan, sbd naga alama bakida niyya? Kambala iddar nan????
Intisar ta takallesa a yatsine tace "Toh kayi kadan uban kuturu yayi kadan bare na makaho,
Badai ubana ba saidai naka, kuma gda bazan barshiba, kaji ingayama, zaman gidan nan damar yanzu nafara eh, idan kaga Gda inna barshi toh ka biyani BUDURCINA, imba hakaba kofar takashi baxan fita ba"
Mus'ab ya yaja tsaki " Banza Mara zuciya, ana korarta taki fita"
Cike da hargiwa , inty tace gakanan babban banza, kai kashiga taitayinka, inba hakaba, sainasaka ka wuce ta akaifan wuka.......
Tsaki kawai yakara ja, yafice yabar d'akin,
*********************
*BAYAN WATA BIYU*
Intisar tayi wata biyu, abubuwa dadama sun fara kamar nadamar mus'ab, tuni mus'ab yafara jin yana masifar sonta,
Gaba d'aya ya rude.
Kullun safe saiya gaidata, itako taki amsawa, gashi wasu yan iskan kaya take sawa, Wanda dole duk namiji lafiyayye yayi sha'awar ta.
Yashiga wani hali sai ramewa yakeyi, kullun ji yake kaman ya saceta, anya bada gayya takemun wani abunba?
" Dole infito in gayawa intisar cewa inasonta kuma inaso na maidata dakinta,
Amma bansan yadda zatadauki magana ta ba.
"Nidai nace sai an gwada akansan na kwarai,
Gaba daya intisar tashiga damuwa, saboda Ganin Halinda, Mus'ab yake ciki, gashi itama sonshi takeyi, itama kaman ranta..
Ranan da Intisar tashiga wata uku, koh ince tayi jini uku,
Mus'ab yashigo yasameta zaune agaban madubi,
Sallama yayi abunda baitaba yiba,
Duk iya zamanta a gdan! " inty harkin tashi? Tayi banza dashi",
Maiyasa kike wulakantani ne intisar.......
Intisar tace Malam dakata inace nayima iyaka da dakinnan don haka yita kanka...
*Dedicated to all youths🙍🏻♂🙍🏻*
[11/25, 6:58 PM] +234 803 934 4770: *FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
2⃣3⃣
Mus'ab yace "Intisar Dan Allah kitsaya ki saurareni,
Kiji kalaman bakina,
Narasa samun sukuni, inty.
Intisar wallahi Ina sonki, inbazaki damuba, inaso inmaidaki a matsayin matata",
Juya baya tayi tana dariya tace yauwa daman wannan ranan naje jira!!!!!!
Kuma gashi taxo
'Yanxu zanyi yadda nakeso ganin ka d'and'ana yadda duk macen da miji yasaketa takeji, toh yau Mus'ab zan sakeka har saikayi ladaman abubuwan dakake aikatawa.
Afusace ta waigo tana tafi tace aikam kaga nikam gaba naci, saidai wata intisar d'in amma baniba,
Yau zamana a cikin gdanka yakare.
Iddah ce kuma nagamata ad'akina,
Akwatuna ta fito dashi, duka daduk wani Abu masu mahimmanci.
Sannan Takira direban Gdansu Mus'ab tace yazo da mota, ta kwashe komai, tacema jummai kije na sallameki, tayi mata sha Tara na arziki.
"Mus'ab magiya yake ina intisar tace batasan wannan ba,
Takaddar sakin tananan yauzanje in nunawa iyayena,.
" daga yau kuma indasa zawarcina yadda nakeso,
Cike da magiya mus'ab yace "Dan Allah intisar kiyi hkr kuka Mus'ab keyi Wanda saida yabani tausayi.
Inasonki intisar ina kaunanki, inkika barni zanshiga wani hali.
Intisar tayi dariya tace haka nakeso kashiga wani halin yadda sauran matan daka saka suka shiga wani hali.
" direba muje bin motar yake dagudu kaman ya haukace, itako intisar bata sake waigensa, ba, illama dukunnar dakai datayi tanajin ciwon rabuwanta da Mus'ab.
Da isarsu kofar gda, dayake ranan aikine kowa na wajen nemansa, umma ne taga akwatina, anata shigowa dasu,
Tsaya wa tayi taga ikon Allah.
"ntisar tagani lokaci guda taji gabanta yace ras!!!!!
Intisar dake kallon ummanta dariya kawai take da gudu ta rungumeta tace, umma inty ce kar kiji tsoro.
" Nan direba yakoma, Mus'ab tuni yafita kamanninsa, sai a lokacin yakejin son intisar har kokon zuciyarsa. "
Amma nace "is too late to cry when the head is already cut off"
"Sunbatu kawai yakeyi, baisan lokacin daya figi motaba, Allah ne yakaishi lafya imba hakaba. Dasai dai wani bashiba,
Horn yayi wanda kowa saida ya firgita, ana budemai yawani katse motar,
"Yana ihun kiran Ammi, da Sauri tafito yace ammi intisar ta tafi tabarni, Ammi nashiga uku???"
Dasauri ammi tace "Kai Dan Allah yimun shuru wani abune yasama Inty din??
Mus'ab yana kuka yace "Ammi nasaketa kusan wata uku, amma shine taki fad'a, Ammi lokacin data gama iddah naji baxan iya rabuwa da itaba lokacin intisar tace zamana da ita yakare....
Ammi kitaima keni wallahi inason intisar baxan iya Rayuwa imba da ita ba....
Kuka yakeyi wiwi!!!!!!
Kaman wani sauna.
Ammi tayi ajiyar zuciya sannan tace "tafi naji akeyi tuni , zanje..." Bata karasa magarba sukaji ana tafi ta bayan ammk, na waiga Ashe Alhaji Ahmad ne, dauke da murmushi a kuncinsa sannan yace "
Tabbas bahaushe yayi gaskiya dayace, "Ku gargadi mai Gina ramin mugunta.Allah nagode ma daka barni da raina da numfashina, dakabarni, inga wannan abun farincikin."
Mus'ab kuwa tuni yayi mutu a zaune tuni yanemi kukan yarasa. Mahaifinsa kawai yakebi da kallon.
"Yau mace taxaman ma rigar kaya, kacirema abun yaci tura!!!!
Bayan abba yakaraso wurinsu, yana murmushi yace "Kazo ka gaya mana kasaki matarka ne mujema biko?
Toh kayi kuskure. Bama karamiba, don dagani har hjy fatu babu inda zamu kaje kayi fafutukar,
Da kanka, inkayi nasara toh tabbas kai namiji ne.....
Tir kashi.............
*Dedicated to all youths🙍🏻
🙍🏻♂*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
2⃣4⃣
Inba hakaba Mus'ab saidai ka mutu, don babu inda zamu.
"Allah sarki tsakanin uwa da d'a
Tuni ammi taji tausayin d'anta ya kamata,"
Shiko Mus'ab tuni yanemi numfashinsa, yarasa.nan ya zube kasa somamme
hjy Ammi ta rude tana kiran direba, sai asibiti.
Likitane tsaye akan sa,
Bayan wasu mintuna likita yafito yadube ammi yace " gaskiya d'anki yana cikin matsanancin damuwa, tabbas ciwon zuciya na Neman kamashi.
Ga hawanjini,
Ammi tana kuka tace "Nashiga uku, Allah kataimakeni, ya Allah kaba Mus'ab lafya",
Nidai Dana ke tsaye nace Amin.
wasa wasa Mus'ab yad'auki, kusan sati biyu. Ana Abu daya bashi da wani magana inya farfado saina intisar,
Ga wasu hawaye, masu tsuma zuciya dake zubowa akan fuskarshi
"Allah sarki soyayya"
Tabbas mus'ab yayi wasa da damarsa gashi yanzu dama ke damar dashi.
Likitane ya shigo yaga mus'ab na kuka yace haba "Namijin duniya" da girmanka kake asarar hawayenka?
Nooo gayamun matsalarka nikuma zanyima ma ganinta,
Mus'ab yace " Doctor baxaka iya yin komai ba saboda batasona , ta tafi tabarni.Amma nasan cewa alhakine yake bina, Adaren ranar ummi matarsa ta farko, tadawo mai da dansa, dayake taji lbrn yana asibiti.
" Likitane yace lafya kika shigo mana babu wani sallama?
Ummi tace "Eh nashigo din aiba gurinka naxo ba gurin wannan mayaudarin nazo tamika masa yaronsa tace "'Ga danka, nadawo ma dashi jininka, Wanda duk duniya bakada kamarsa, wannan shine *FANSAR BUDURCINA*
Ta kalli yaron tace my love kaga abbanka nan, karkayi kuka zaikula dakai kamar yadda nake kulawa dakai.
"Sunansa, Ahmad" tagayawa mus'ab lokaci guda tafice, tabar shi yanata kuka yana kiran umma! Umma!!
Lokaci guda mus'ab yaji son dansa acikin zuciyansa. Likita yace mutumina dakwai wani boyayyen al'amari Wanda kake shirin boyemun?
" Bude kofar dasukaji ne yasa likita yayi shuru, ganin Ammi tsaye, yasa yace mus'ab Allah yabaka lafya....
Karage tunani daga bisani ya wuce.
"Ammi ce tayi saurin rungume, Ahmad tace waye wannan?
Mai kamada kai mus'ab??????
Ammi ummi ce tadawomun da Dana har cikin asibitin nan. Sai hawaye ke tsirarowa daga cikin idonsa.
" Ammi taji dadii kwarai ta rike jikanta, na fari.
Cikin sati na uku, aka sallami mus'ab.
Likita yabashi shawarwari, daga bisani sai ince Sun zama abokai.
********************
"Nifa umma yasakeni da dadewa, kindawowa nayi saidana fita iddah a d'akina Sbd yan gulma.
Umma tace Tabbas kinada baseerah inty ke macece mai hankali da tunani,
Tabbas kinciri tuta
Malam magaji dake gefe yace mu bamu taba tunanin cewa zakikai war haka ba.
Yan gulma harsun gaji da jiran dawowarki, kizo ga guri nan ki zauna Allah yamiki zabi na alkhairi. Amin cewar umma da Inty,"
Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah inty tashiga jerin zawarawa, masu aji.
Wata asabar ne intisar na zance a kofar gda itada wani Attajirin mai kudi.
Wanda akalla yayi sa'an baban mus'ab.
Sai zuba love sukeyi, mus'ab yace Dan Allah ji wancan tsohon banza?
Koh kunya yawani zo wajen yar karamar yarinya....
Jita itakuma sai washe baki takeyi,
Wucesu yayi yashiga cikin gdansu"
Yayi sallama ummace tayi mamaki daganin mus'ab tasan cewa yana cikin tashin hankali.
"Maraba barka da zuwa yauwa, yace yana dariya.
Akasa ya tsugunna"
Ina gaisheta,
Daga bisani yace umma nazone kiyafemun gameda inty gaskiya umma nayi ladama kuma nayi Dana Sanin sakinta.
Inaso umma kitaimakeni, inty takoma d'akinta,
Itakoh intisar sallaman sugar daddy dinta tayi tashiga cikin gdansu a fusace, "Ta nuna mus'ab da Dan yatsa tace meya kawoka gdanmu???
Mekazoyi?
Tsakanina dakai babu aure, har abada, kajina gayama.. " umma yaudararrki yaxoyi
Inty..........
Dakata mus'ab dakata bakada abun cewa, kuma gdanka bazan komaba.
*dedicated to all youths🙍🏻
🙍🏻*
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)👄*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
2⃣5⃣
Bani bakai kafin inrufe idanuna in bude ka fitan mana daga gda tunda ba gdan, uban wani bane!!!!!
Mus'ab yace "Dan Allah intisar kitaima keni yadda Allah yataimakeki, adaura mana aure ki koma d'akina, Dan Allah kiyimun rai Allah sarki SO baruwanshi da shekaru kankanta kokuma nasaba.......
" kuka mus'ab yakeyi kamar karamin yaro son inty kawai yakeyi, bugun zuciyar danakeji akan sonki inty wallahi babu Jada baya,"
"Banda sauran moriya inhar kikace baki sona", zan iya mutuwa.
Son mus'ab takeyi amma yaxama dole, ta kwatarwa kanta yanci, kugu ta rike tace Mus'ab inkaso ka mutu inkaso kayi rai, wannan duk matsalanka ne.
umma dai yar kallo taxama don takasa cewa uffan"
Umma Dan Allah kisa baki. Mus'ab yafad'a cike da magiya
Umm tace "Mus'ab banida abun cewa yau in intisar tace baxata koma gdanka ba, yanzu bazawara ce tanada damar dazata zabi Wanda takeso yaxama abokin rayuwanta. Don hk zamu tambayeta intanason zama dakai bamuda tacewa.............
Waigowan daxaiyi yace inty ki amince da soyayya ta a karo na biyu, kawai yanemeta ya rasa.
" tashi yayi yana kuka tashiga motarsa, yana tuki ahankali, abun duniya ya dameshi,
Tunanin yadda inty zata amince mashi akaro na biyu yakeyi....
Nidai Mus'ab bai bani tausayi ba, sbd lokacin dayake sheka ayarsa, ya manta da rana irin wannan zata iya zuwa.
"Rananda bashida tsimi bashida dabara.
"Da isarsa gda yanemi guri ya zauna Ammi ta kalleshi tace, tabbas Wanda yakiji bayaki ganiba.
Tabbas in kace zaka watsar da magansn iyaye toh bazaka taba sha da dadi ba",
Yanzu fisabilillah Mus'ab wagari ya waya?
Nidai banida abunda zanyi akai, indai intisar tace baxata dawo ba.........
Mus'ab yajuyo kamar zaiyi kuka yace "Ammi naje gdansu intisar abun bakin ciki tsaye take dawani saura yi, tsoho akalla ai yayi Abbana.
Ammi dariya tayi tace meye na kishin matar daba takaba?
Musa'ab yace "haba Ammi dolene nayi kishinta. Sbd inasonta ina kaunarta."
Ammi tayi murmushi tace" Aikin banza, kaji dashi, ciwon ajali adan yatsa,
Guri yanema ya zauna yace,
"Allah sarki tsufa inji kishiyar mai duwaiwai"
Ammi tace "Aini dazata burgeni nanda sati tayi aure,
Da nafi kowa farin ciki, kaga ko banza kayi kwatai," takaraa maganar dadariya
Mus'ab tashi yayi jiri yana dibansa, kamar zai fadi, maganar zuwa wajen auki koh yasha ruwa.......
Ba lafya ina zuwa aiki?
*********************
"Intisar meyasa baxaki koma gdan mus'ab ba tunda yagane kuskurensa?" Yasmin kefad'a tana zaune kusa ga intisar
" Yasmin kenan ai maxa sai ana yimusu haka, zasusan cewa mufa mata *DARAJA*
Garemu, kuma yaxama dole in kwatarwa mata yanci.
Sai Mus'ab ya shiga damuwa mai muni, akaina, zaisan cewa mace zinare ce kaffa kaffa ake da ita, saisan cewa, mace yar gatace........Yasmin nafiki son komawa gdan mus'ab amma shafin littafin nawa bai kareba da saura"
Yasmin tace tabbas ina bayanki intisar, maxa yanxu sun maida mata kaman Riga sucire wannan Susa wannan.
Sbd yanxu matan kamar jamfa a jos sake,
Matan yanzu suke bidar maxan dole kinga adinga mana cin kashi.
Intisar tace "hmm Ban musha kawata ashedai ingane, cewar inty, dole yanxu kowacce mace ta tashi tsaye, wajen nemawa kanta yanci imba hakaba, zata ga ni anayi a makota.
*********************
Wata safiyar Talata, Ammi taga mus'ab jikinsa babu sauki, ta saba Ahmad tace direba yakaita unguwansu, inty
A tsakar gida ta taddasu, suna hira.
"Tanaganin Ammi ta rungumeta tace sannu da zuwa, Ummar taku batanan ne?
Tananan tashiga makota, kausar jeki kira umma.
Ruwa inty tadebowa Ammi tabada kudi aka siyo mata hollandia,
Daman best dinta kenan.
" umma ce tashigo tana maraba lale sannunku Dan samari, gashinan cewar Ammi.
Kinganni ba shiri koh?
Toh muna bikone dukda Alhaji ya hana amma tsakanin uwa da da akwai tausayi.
Umma tace "Hjy a gaskiya yanzu intisar takeda daman tofa albarkacin bakinta, sbd yanzu tazama vazawara,
Ita zata zabi mijin da takeso.
zan kirata duk abunda tace hjy bamuda wata dabara, tunda yanzu tasan inda ruwa kemata yoyo.
~Dedicated to all youths🙍🏻🙍🏻♂~
*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
~Written by~
~Humairah (melody)👄~
~Story by~
~Ililee~
~Edited by~
~Xarah Bukar~
2⃣6⃣
Umma takira intisar,
Intisar tace Na'am umma tace zonan,
Da Sauri tashiga ta dukunna tace umma gani,
Umma tace "Ammi ce takeso ki koma gdan mijinki, a firgice inty ta dago tuni idanunta sukayi rau rau, tace a gaskiya bazan koma ba.
" yanxu hakama nace wani yafito kuma sati mai zuwa zasu kawo kudin tambaya, gaskiya Ammi kiyi hkr bawai cin fuska nayi miki ba." Umma tafada cike da gadara
"HAKURI na ayusha ILIYASU*
Yakamata muba zuciyoyinmu.
Kawai da gudu ta tashi tafice
Bawai don ranta naso ta gayawa Ammi hakaba.
Don ta samawa kanta yanci, dole taja ajinta yadda yakamata.
Haka Ammi ta tafi da sanyanyar gwiwa, Rayuwa tayi musu zafi dagashi har uwarsa,
Shiko Ahj Ahmad yana Dubai UAE baimasan wainar da ake toyawa ba.
Kullun sai mus'ab yaje gdansu inty, kullun da salon wulakancin datake yimai.
Har ya cire rai da samun inty,
Saboda Ammi da abbansa sunsamai Ido ne basuda niyyar taimakamai,
Gashi dukya kauracewa abokanansa......
*********************
Alhamdulillah ansa ma inty rana wata biyu, da wannan Alhajin da Mus'ab yace sa'an babanshi.
"Yan gari sai zundensu akeyi,
Wata majalissa naje na tsaya,"
Inda Naji ana gulman malam magaji,
Malam lado narasa kwadayi irinna magaji, ya aurawa yarsa me auri saki yanzu kuma tsoho??
"Hmmm garba kenan, kwadayine kawai saboda yaga yanada kumbar yakushi,"
Malam liti dake gefe yace, kufa na lura duk mahassada ne,
"Da ace daya daga cikinku yasamu wannan damar, toh tabbas nasan abunda, zakuyi sai kunce magaji ba komai yake ba.
"Malam liti duk irinku ne masu karamar kwakwalwa,
Shiyasa naga yarka Yasmin take shisshige musu......
Toh wallahi duk Wanda yahau matar kwadayi toh a tashar, kwadayi zai ajiyeku.... mtwww tsaki liti yaja yace kinga tafiyata banda lokacin tsaiguminku.
~Dedicated to all youths~🙍🏻♂🙍
🏻*FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
2⃣7⃣
Liti yana tafe yana surutai. Mutanen sai abarsu, wani fah yana nan Dan numfashin da kakeyi bakin ciki yakeyi.
"Intisar soyayya takeyi, sosai itada sugar daddy d'inta inda shima sonta yakeyi, tamkar tsoka daya a miya,
Yau sauna zaune da umma suna cin abinci umma tace " intisar na lura mus'ab yayi ladama amma kinki.
Ki tausayamai,"
Intisar tace "Hmmm umma kenan inaso in kwatarwa mata yanci ne, gurin mazajen da basu maidamu a bakin komai ba, Suke wulakanta mace, toh saiya Dan Dana kudarsa,"
Umma kai kawai ta girgiza Allah tatai maka,
Mus'ab yana zaune tare da ammi a falo suna kallon amma shi hankalinsa san vaya wurin yatafi duniyar tunanin intisar, saicen yasauke nunfashi, umma tadubesa tace "lafiya kuwa "
Mus'ab yace "Ammi nidai na hkr da samun inty, sbd na lura batada niyyan dawowa gareni, dukda na nuna nayi kuskure.Daman shi aure Nufine na Allah,"
(Khadija chafe)
Ammi tanisa sannan tace "Mus'ab daman kowani Dan Adam musulmi an sanshi da tawakkali........Kuma duk abunda yayi farko, zaiyi karshe, Sannan mutun ya tuba daga mummunar dabi'ar dayake, shima wani tsirane"
Mus'ab yace "Ammi wlh rud'in shaidanne, magana sukaji daga sama,
Kamar diran mikiya", tabbas yau nasan cewa Dana yayi hankali da har yake ladaman abunda yakeyi.
" Nayi farinciki, kwarai, da Allah yakawo mun wannan, rana.
Da gudu junior ya taho ya haye kan tsoho." Yana dariya.
Hjy waye wannan kamar Nina haifeshi??????
"Hmmm jininka ne Dan Dan ummi ne lokacin kana Dubai UAE ta dawo dashi zatayi aure. Alhaji Ahmad yayi murmushi yace, tabbas wannan dan shine farin cikinmu mus'ab.
Sana diyyanka mun rike jika, da ace zama kakeyi da matan da sbd jikoki gdannan ya mana kad'an.
" Ammi ina gaya miki, da mutun mai auri saki, inagaya miki gwamma mai aure aure. Mutum yayi hudu reras Wallahi yafi sau dari...cewar mahaifin mus'ab.
*********************
Biki yarage saura sati biyu, intisar, tana tunanin yadda zata bullowa Al'amarin,
Gdansu Yasmin ta nufa tayi sallama bakowa gdan sai Yasmin, tace Naji dadin ganinki kuwa.
Zo muje waje suka fita Yasmin,
In ajiye miki rashin auren nan daba kiyi ba, kuma tabbas ke kawar arziki ce,
Inaso ki auri, Alhaji Danjume donnni gdan mus'ab zan koma.
"Zare Ido Yasmin tayi, tace intisar kinsan tabbas baxai soni ba, kuma kinga musalle bazaiji dadii ba, zaice kudine ya rudeni na rabu dashi......
" Dallah musalle fah kikace. Toh ko kinaso kobakiso, shina zaban miki, saboda, inje inci gaba da rainon soyayyata tsakanina da mus'ab tabbas nasan yayi ladama ya zuwa yanxu.
Toh yazanyi?????
Cewar Yasmin da kowa yana iya ganin damuwa a fuskanta.
Intisar nida koh, bokati baa siyamun ba? Dame zaa kaini?
*Zancene buringi inji tusa*
Mekikeci na baka na zuba? Karki damu zakisha mamaki.
"Ana saura kwana hudu biki, aka kawo akwatina, kamar na budurwa, sha Tara na arziki.
Intisar kallon kayan takeyi, tace Yasmin duk nakine daga yau zuwa jibi.....
Kema zaki shiga sahu kifantama, yadda mata ke fantamawa, ke yasmin Allah yayi mana tsarida talauci
Amin.
Kuskus dinme kukeyi,? Bakomai umma kinga wayannan yara Allah ya shirya.
*********************
Mus'ab yakoma gdansa da zama ya rungumi kaddara, ya fidda rai da samun inty,
Ana gobe biki. Mus'ab yashiga damuwa yanata tunanin inty, kiran sallane ya tasheshi daga tunanin,
"Ya wuce masallaci, itako intisar tuni ta hada akwatin ta, takai can bakin hanya....
*Dedicated to all youths🙍🏻🙆
🏻*
[11/26, 5:16 PM] +234 9060041624: *FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
2⃣8⃣
'Dan napep tasamu, tashiga basuja birki ko inaba sai kofar gidan mus'ab, tasamu kofar a bud'e take_ ta biya mai napep tako shige cikin gidan, a tsakiyan falo, ta tsaya taga yadda gdan ya kurance,
"Tabbas mace itace gda, yanzu hk mus'ab ke kwana Allah shi kyauta.
Tana tsaye a falon taji anbud'e kofar falon an shigo, da sauri ta juyo sukayo edo hudu da mus'ab,
" Mus'ab ne yayi tsaye yace Inty ???
Cikeda mamaki itako juyowan dazatayi, saida ya firgita..
Sbd babu alaman wasa a fuskanta.
Cikin rawar murya yace "Ba gobe ne za d'aura miki aure ba?
Tayi taku biyu zuwa uku tace, in aureshi inkaimai mene tafadi cikeda tsiwa.
Ina BUDURCINA yake? Shiyasa kaganni a gdanka, toh nazone kabani BUDURCINA intafi inkaimai,
A rude mus'ab yace, intisar pls kiyi mun rai kitaimakeni, tuni ya rungumeta, ya matseta a kirjinsa, tana fitarda numfashi mai sauti,
"Intisar kiyi hkr kizauna dani, nayi miki alkawari, zan biyaki, *FANSAR BUDURCINKI*
Koda kuwa yin haka zaiyi sana diyyan mutu wata,
Da sauri intisar ta rufemai baki,"
Mus'ab inaso fansar BUDURCINA yakasance, ka gyra halinka, kayi ladaman abunda ka aikata, ka koma ga Allah katuba,
Sbd yanzu munriga da munzama *JINI DAYA NA ANEESA ABUBAKAR RIMI*
Dasauri mus'ab yace "Intisar na tuba kiyafemun, kara rungumeta yayi, yana sunbatarta"
Tako ina, yana kuka yana murmushi, duk a lokaci daya.
"Yakamata muyi gaggawan zuwa musanar ma su Umma cewa, mun maida aurenmu,".
Na maidaki. Ciwar mus'ab bayan yafito daga jikin inty, suka fita tare,
*********************
Gda ya rude Amarya ta bace ba ita ba labarinta, ana hakane, Yasmin ta shigo tasami umma tace umma intisar ta zabi komawa gdan mus'ab saboda shine annurin zuciyanta. Tabbas mus'ab yayi ladama kuma nasan duk inda suke suna tafe, don su sanar daku.
Bata gama rufe bakiba saiga inty da mus'ab tsaye,
Da gudu inty ta rungume ummanta, tace umma tabbas naxabi komawa ga tsohon mijina, sbd shine zabina.
"Tabbas mus'ab yayi ladama kuma yayi daya sani, yanxu na tabbata mijina, na kwarai ne.
Kowa tsaya wa yayi yana kallon ikon Allah, yanzu ya zaayi da Alhaji Danjume",?
Abune mai sauki, nakirashi yanzu zamuyita ta kare, na yarda na aminche.
Yasmin kawata tazama matarsa..........
*BAYAN WASU AWA UKKU*
Alhaji Danjume ya Aminche, daga bisani biki yakoma gdansu, Yasmin, inda mahaifinta yayi farinciki,kwarai yace mahakuci mawadacii............
"An daura aure, anyi komai an kai Amarya gdanta,
Duk abunda akeyi Ammi bata saniba, bayan sun fitone suka biya ta gda, suka sanarda, Ammi halinsa ake ciki tayi farinciki kwarai,
Sunji dadii........
*Dedicated to all youths🙆🏻🙍🏻*
[11/26, 5:50 PM] +234 9060041624: *FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)👄*
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
*Dedicated this page to you ILILEE And ABDUL smile😀*
2⃣9⃣
Gidansu suka koma, Rayuwa aure mai dadii. Ammafa inda kwanciyan hankali da wadatar zuci.
Mus'ab yaso abashi junior amma, Ammi tace Sam, bazata bashiba, tana musu fatan samun, wani danbada jimawa ba."
Waiyo soyayya Wato sai Wanda yagani, a gdan mus'ab soyayya sukeyi kamar baxa'a mutu ba,
Sukan farantawa junansu rai wajen nuna bajintarsu, A Rayuwa aure.
Nan mus'ab yakoma aiki gadan gadan, tagaiga koh, abokansa yagani a hanya", baya kulasu.
Kuma suma yana musu fatan su daina halinda suka ciki su komaga Allah.
******
Yasmin amarya kulawa babu wacce bata samu, awajen, mijinta. Dayake ya tsufa Baiyi aureba,
Shiyasa yasan yadda ake alkinta karamar yarinya, bayason baccin ranta.
Cikin ikon Allah Yasmin tasamu ciki,murna a wajen Alhj Danjume ba'a cewa komai",
Tuni aka rushe gdansu Yasmin, akayi musu sabon gda son kowa kin Wanda yarasa.
sukayi bye bye da talauci, harsuke taimakawa wasu.
"Mahassada kuwa sun dawo kan hanya dayake sunji uwar bari, sungane cewa hassada gamai rabo taki.
Yasmin kyautar mota akayi mata yanzu batada wani buri, saina taga takoma makaranta domin tayi yakida jahilci.
Tabbas burinta yacika kuwa.
Intisar kamar had'in baki itama ciwo takeyi, abun gwanin ban tausayi, mus'ab duk yabi ya rude, aka kira family doctor yayi musu albishir dasun samu karuwa.
Mahaifin mus'ab yayi farin ciki, ammi kuwa tuni tasa adawo da inty gdanta tayi rainon ciki. Itama koyon mota inty takeyi dukda batada wata cikakkiyar lafya.
Mus'ab yaxama uban yaya tunda sun tunanin samun Dana biyu.
Inty tarike junior tamkar ita ta haifeshi.
Zumunchi tsakanin Yasmin da intisar abun saiwanda yagani", hatta iyayensu haka abun yake.
*Bayan wasu watanni*
Intisar ta haifi 'yarta mace ranan laraba, Yasmin ta haifi da namiji ranar Alhamis.
Murna wajen mazajen ba'a magana.
Yaradai sunci sunaye kamam haka.
Samirah Mus'ab Ahmad (Imtihal)
Sai na wajen Yasmin
Nuraddeen Danjume.
(Anwar).
*Dedicated to all youths🙍🏻🙆🏻*
[11/26, 6:13 PM] +234 9060041624: *FANSAR*
*BUDURCINA*🏹
*Written by*
*HUMAIRAH (Melody)*👄
*Story by*
*ILILEE*
*Edited by*
*XARAH BUKAR*
THE END
3⃣0⃣
BAYAN SHEKARA
BIYAR
Intisar anzama manyan mata Wanda ake damawa dasu, Yasmin ce takawo mata ziyara suka zauna suna tattauna Yadda Rayuwa ta dinga kasancewa Ada.
"Tuna baya akace roko" yara sun zama yan gata, sunyi bulbul. Hatta iyayensu sun zama wasu dika dika.
Su intisar sun zama top of the town" kowa zancensu yakeyi.
Kowacce da kalar motar datake tukawa. Mus'ab yayi arziki hard a kai surikansa aikin hajji.
Kannin su intisar da Yasmin kuwa, sun girma, makaranta suke zuwa mai kyauda tsada......
Umman intisar Dana Yasmin sukace yaya masu rana, sanadin haihuwa gashi mun samu d"aukaka, yaya mata abun alfaharine duk abunda mace tasamu bata taba mantawa da iyayenta.
Ina ganin beken wasu saisuce wai sunfison yaya maxa
Hmm umman Yasmin nidai anan zance Allah yayima zuriarmu Dana ya yan mu albarka yasa sugama da duniya lafya.
Ni HUMAIRAH Melody nace ina kiraga Masu hali irinna mus'ab dasuyi ladama tunkafin lokaci ya kure musu.
Sannan su tuba zuwaga Allah donshi Allah maji rokon bawane.......
Anan zan tsaya da takaitaccen labarin dafatan yafadakar ya wa'azantar ya nishadantar.
Tammat
*Godiya ta musamman zuwaga masoya yan uwa da abokan arziki masoya wannan littafi mai suna FANSAR BUDURCINA.*
*Dole na jinjina maku ILILEE da mr smile😀 kun taimakamun kwarai Allah yabar zumunchi yabar kauna*
*Har kullun kuna raina, Aneesaluv, Ayusha, Rashkardam, Aneesa didi, Aneesaty, Mhix Cheerie daduk wayanda bansamu kiran sunanku ba, kuna raina.*
Jinjina ga marubuta.
Aneesa AR
Autar hjy
Aneesa didi
Ayusha
Mamam Shakur
Maman shaheed
Hajara yayana mijina
Nafeesa Anka
Al'eeman
Rashkardam
XARAH BUKAR
Feedo yar ficika
ILILEE
Mr, Smiles😀
Maryam slow
Beelybadaru
Daduk sauran daban kira sunansu ba.
Nice taku har kullun Humairah Bashir Melody👄
Saimun hadu a littafina na gaba
Wanda Allah yaso.....................