Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 4 October 2017

farar haihuwa complete hausa book

adsense here
[8/22, 2:48 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°1

Bismillahir Rahmanir RahimKai kawo take tayi a siririn corridor din asibitin cikin tsananin tashin hankalin rashin sanin halin da kanwarta take ciki. Inna Uwale dake zaune a kan tabarma ta daga hannu sama idanunta duk sun ciko da hawaye tace Ya Allah ka bani farin jika ko wanne iri ne. Ya Allah fari kyakkyawa kamar ni. Zulai aminiyarta tace amin amin Uwale ai ranar sai munyi sadaka. Tani dake kai kawo da sauran matan da 'yan uwansu ke cikin dakin haihuwar suka zuba mata ido. Ta kuwa cigaba da adduar farin jika kamar yadda ta saba. Cikin kunar rai Tani tace amma Uwale baki da mutumci ko kadan. Kanwar tawa tana ciki rai a hannun  Allah kina wani fatan a haifa miki farin jika. Farin jikan yaci.....bullowar mal Yakubu yasa tayi shiru ta share hawayen bakin cikin da ke shirin sauko mata. Ita kuwa Inna Uwale tace ashe baki da kunya Tani? Ban girmi uwarki Baraatu ba? Ita dai Tani shiru tayi don tana gani mutumcin Mal Yakubu mijin kanwarta. Yayi gumi sharkaf saboda tafiyar da yayi zuwa asibitin a kafa bayan dan Tani din ya bishi gona ya sanar dashi halin da ake ciki. Ramlah da Sadi suna ganinsa suka mike suna murna suka tsaya a gabansa. Daukar Sadi yayi itama Ramlah tasa kuka sai an dauketa. Tana kukan bata sani ba ta taka kafar Inna Uwale. Wata kara ta saki kafin ta hankade ta ta fadi kasa. Matsa can gun yar uwarki, shegiya baka mummuna. Mal Yakubu yace haba inna a nan din ma. Tani ta dauke ta tana goge mata bakinta da yasha kasa. Yarinya sai kuka take. Yo ba kaine duk ka cuceni ba dan nan. Mata aka sami abin kallo jin yadda Uwale ta bude murya. Ta cigaba dube ni nan ga fari ga kyau haka Allah Yayi ni tun kuruciya don ma girma yazo. Ta daga siririyar kafarta ta hagu wadda shan inna ya shanye tace da wannan Allah Ya ragewa aya zakinta duk kyan dire na ban sami mijin arziki ba sai ubanka. Allah dai Ya jikansa. Babu irin adduar da banyi ba da cikin ka don ka fini sanin baki ne. Allah Ya taimake ni na haifo ka fari tas ga kyau. Sai hawaye shar suka sauko mata ya durkusa kasa don Allah Inna kiyi shiru. Sauran matan dake wurin suna ta kallo an sami labarin kaiwa gida yau. Yaron nan da yake mai bakin kashi ne ya rasa wadda zai aura sai yar maiduguri. Wallahi kunga wannan yayar tata ta nuna Tani har ta fita haske. Kalarta fa kamar dauda yadda dai kuka ga 'ya'yan nan. Ba yadda banyi ba har da kwanciya a asibiti duk don a fasa auren yaki jin maganata. Ga haihuwar balai duk shekara. Yanzu wannan cakurkurar, ta nuna Ramlah  zaayiwa kani na biyu. To ni mijina ba arziki har ya mutu shima dan babu. Ni kuwa kafin na mutu sai naje makka da kudin jika ko na mijin jika. Haka kawai yadda nake da kyan nan bazan bar baya bakikkirin ba. Mal Yakubu ya share hawayen idanunsa. Inda sabo ya saba da halin innarsa amma irin wannan a cikin mutane ta gama zubar masa da mutumci.

Goron bakinta ta furzar tace wallahi indai ta haifi fari ko fara nayi alqawarin yi mata wankan jego da hannuna. Ga mutane suna min shaida. Ni ban tsani Munari ba harkar bakar fata ahalin tsiya da talauci ne bana so. Tana gama magana wata nurse ta fito tace ina wadanda suka kawo Maimunatu Ado? Mal Yakubu yayi saurin matsowa gaba. Inna uwale ma ta cangalo kafa tace Nas fada min me aka samu. Fari ne? Ko kallonta nurse din bata yi ba tace masa ta sauka lafiya za'a fito da ita zuwa dakin hutu. Uwale tace tana zaro manyan idanunta ke yar nan karki min rashin kunya, ya ina tambayarki me aka samu zaki min banza. Ki fada min gaskiya fari ne ko baki? Don wadan can yaran ko irin farin nan na jarirai wallahi baa haifesu dashi ba. Nurse ta kalli mal Yakubu tace masa namiji ne tayi gaba abinta.

Zulai kawar uwale ta kama hanci ta rangada guda. Uwale ta kuwa make ta, to uwar kinibibi ai baki ga kalar dan ba zaki cika mana kunne.
Batul Mammanđź’–
[8/22, 2:50 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°3Mal Yakubu ya fito da dan kudi daga aljihunsa ya nuna mata. Kinga na ajiye saboda siyan rago amma tunda haka Allah Ya qaddara mana sai ki fada min abinda kike so na saya miki. Tasan duk don ya kwantar mata da hankali ne saboda abinda inna Uwale tayi mata. Tace haba baban Ramlah ka bari muje gida mana. Ya girgiza kai kinsan Allah maimunatu bana son Yaya Salihu yaji zancen nan. Kinga lokacin haihuwar Sadi da inna ta hana a yanka masa rago cewa yayi na sake ki ba dole bane auren. Maimunatu bazan iya rayuwa da wata mace ba bayan ki. Don girman Allah kada ki bari a raba mu. Murmushi tayi bata manta yadda ya rinka rokon yayanta ba har saida iyaye suka shiga maganar. Tace ni da kai Malam Yakubu mutu ka raba. Dariya yayi sosai sannan ya fita neman taxi da zata kai su gida.

A tsakar gida Inna uwale da zulai suka zauna tana ta bambami tun a hanya. Ni munari zata cuta? Ni uwale wallahi sai anyi min farar haihuwa a gidan nan. Sai naga jika mai kyau da daukar hankali zulai, sai jikana mace ko namiji yayi kudi. Ni banda abin namiji ma ina tsiya ina bakar fata. Munari fa banda hakora ni ban taba ganin wani abu mai haske a jikinta ba. Zulai dai sai bada baki take don tana samu a wurin aminiyar tata. Bayan sunci abinci Uwale tace ke ni a ina zaki samo min farar mace bazawara mai 'ya'ya ne.? Zulai ta ware ido farar bazawara mai 'ya'ya fa kika ce uwale. Eh saboda su hadu da dannan su haifi farare. Ko wacce iri ce indai fara ce ina so. Don ma duka yaranki sunyi aure ne ai da ko Sabuwa ya aura dama ita naso masa tuntuni. Zulai tace to zan duba Uwale gashi kinga Sabuwan ma suna ta fada da mijin gashi haihuwarta biyu. Dan karen kwadayi gare da zulai duk talaucin gidan Uwale sun fita arziki nesa ba kusa ba ga rashin abinci. Uwale tace ki barta a gidanta a samo wata saboda idan an kashe auren sai tayi idda fa. Ni kuwa so nake nan da sati biyu ma amarya ta tare. Zulai tace to bari na tafi kinsan da zafi zafi ake dukan karfe.

Gidan Sabuwa ta nufa ta tarar da ita da mijin suna fada saboda babu abinci a gidan ga yaranta suna jin yunwa. Zulai ta zakalkale kamar ba suruka ba yana ta basu hakuri suna zaginsa. Karshe zulai tace kaga Inuwa ka sakar min 'yata yanzu wallahi ko in hadaka da 'yan sanda. Yaro mara kunya haka ko yau ka saketa zata sami mijin aure. Ai farar mace kadara ce. Idan kaki kuma wallahi sharri zan kulla maka wanda zaisa ka raina kanka. Yace haba Gwaggo meyayi zafi haka? Ni bazan saketa ba. Sabuwa tace Gwaggo ban fa gaji da auren ba kawai don babu abinci sai kice ya sake ni. Ta zumburo baki. Zulai ta make bakin banza zan miki gata kina min fitsara. Zulai ta ja hannunta suka shiga daki ta fada mata hadin da take son yi. Kinga idan kika haifi farin da uwale ke jarabar so wallahi sai yadda muka yi da ita. Kina kallo dai yadda kike wahala nan ga fararen 'ya'yan shegen mijinki baya gani. Sabuwa ta bata rai Gwaggo nifa ina son sa gaskiya. zulai ta saki wata ashariya Sabuwa zan miki rashin mutumci fa. Bar ganin ni na haifeki bani da kyau a harkar samu. Ki tada balli a daren yau ya sallameki kawai.


Batul Mammanđź’–
[8/22, 2:51 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°2Da dafa bango Munari ta fito daga dakin nurse na biye da ita da jaririn. Tani ta gyara goyonta ta mika hannu zata karbi dan Uwale tayi saurin shigewa gabanta tace bani nan. Ni na haifi ubansa. Tana bude zani ta kwala ihu ta mikawa zulai dan ta kai goshinta kasa tayi sujjada. Allah nagode maka...ta kalli surukarta munari kin kwaci kanki wallahi. Ke dai Allah Yayi miki albarka. Da kanta ta rike Munari suka karasa dakin aka bata gado. Tani da mijinta suna ta yi mata sannu. Inna uwale ta sake karbar dan tana ta washe baki tace jamaa kunga abin arziki ko. Yarinya mai son gamawa da duniya lafiya kenan. Ashe tumatir da su mangwaron dana rinka siya miki yau kinga ranarsu ko. Ashe banyi asarar kudina ba. Zulai  ai na fada miki duk miyar kadi ko harkar daddawa sai da na hanata gashi kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu. Kiri kiri ta hana kowa daukarsa saboda tsabar murna. Zaninta taji zai kwance ta mikawa Zulai dan ba don taso ba tana magana. Ai sunan babana zaa saka maka yaro. Nima a nan na gado farin da kyau har kaima ka dandala. Zulai ta dan jujjuya yaron a firgice Uwale tace ya haka ne? So kike ya fadi? Zulai tace a'a fa Uwale gani nayi kamar baya motsi. Kinga fa ko kuka baiyi ba. Allah tsine mai karya ta fada tare da karbe dan. Ai kuwa abinda zulai ta fada gaskiya ne. Uwale ta juya shi shiru ba motsi. Yaro ga shi fari kato ga kyau amma bai zo da rai ba. Da cangala kafar uwale ta fita kiran nurse kuzo ku daba min dannan na shiga uku na ni Hadiza ina zan sa kaina. Nurse tazo tace a'a maimunatu baki fada musu yaron bashi da rai bane? Hawaye ne ya sauko mata tace yanzu zan fada. Tani ta zauna gefen gadon ta rungumeta. Yi hakuri Munari Allah Yasa mai ceton mu ne Ya yi masa rahma. Mal Yakubu ya ajiye  Sadi ya karbe yaron daga hannun Uwale ya kare masa kallo sannan ya rufe shi sosai da zanin. Uwale cikin kuka tace yanzu mai kyan ne ya mutu? To wallahi kasa a ranka Yakubu kamar kayi aure ka gama. Kan uba ni zaki yiwa haka munari? Ki haifi bakake digirgir farin kuma ya koma. Yar purse dinta ta dauka tace Zulai zo mu tafi gida. Daga bakin kofa tace tsakanin na dake munari Allah Ya isa, muguwa mai bakar aniya.

Suna fita Tani tace gaskiya baban Ramlah abinda Inna tayiwa Munari bata kyauta ba. Wannan wane irin rashin imani ne. Mace ta rasa danta a rinka binta da bakaken maganganu. Wallahi sai na fadawa Yaya Salihu ai ba daga sama ta fado ba tana da dangi. Munari tace Yaya Tani kiyi hakuri don Allah. Ya zaki bani hakuri bayan ke aka batawa Munari... mal Yakubu ya rinka bata hakuri. Yaya Salihu mutumin kirki ne amma akan yan uwansa bashi da kyau duk da kasancewar ba uwa  daya suke ba amma iyayensu na zaman lafiya. Jafaru ta kira danta mai kimanin shekaru takwas. Yana shigowa yace Umma Munari sannu. Ta dan murmushi yauwa dan albarka. Tani ta goya masa Sadi ta rike hannun Ramlah. Bari mu tafi munari yaran nan basu ci abinci ba na taho dasu. Mal Yakubu ya kara bata hakuri. Yanzu zamu taho muma zan nemo dan tasi ne saboda jikinta.
Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:00 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°4Sabuwa duk abin duniya ya isheta saboda yadda Zulai ta rinka yi mata fada. Tana kwance kan katifarta zuciyarta tana mata saka da warwara. Inuwa ne ya shigo dakin ya nemi kwanciya kusa da ita. Wani tsami ne ya daki hancinta ta mike cikin fada. Don wulakanci banda rashin abinci a gidanka kullum sai ka kwanta min kana wari? Don Allah ni ka tashi jiki sai tsami kamar kayi wanka da kwata. Ya tashi ya kai mata duka ta rike hannun sannan ta kwada masa wani kwantareren takalmi a ka. Cikin karaji ya biyota waje suna ta fada sai ta tuna hudubar zulai. Nan da nan ta fara zaginsa tana cewa ya saketa sanin cewa yana da saurin fushi. In sake ki ko Sabuwa? Ni kike cewa na sake ki ko? Ta eh in dai ka haifu cikin uwa da uba. Ransa ya kara baci har kin manta sakin da nayi miki kwanaki Zulai ta rinka hadani da Allah na mayar dake ko? Ai da kenan Inuwa yanzu kuwa na gaji bazan zauna yunwa ta kashe min 'ya'ya ba. Yayi dariya makota duk sun saba jinsu kije Sabuwa na sake ki saki daya amma wannan karon kada kuzo biko don wata zan nema. Kuma ki tafi ke kadai don a nan kika sami yaran ba dasu kika zo ba. Ita kalmar sakin kawai taji tasa kuka wallahi inuwa wasa nake don girman Allah ka mayar dani kafin kowa ma yaji. A zuciyarta fatan ta daya ya mayar da ita. Ina zata idan ta bar gidansa? Gwaggonta da kyar take ciyar da kanta gashi sauran yayyenta duk sunyi aure. Me ya kaita ma yarda da shawarar gwaggo. A wurin girki ta kwana washegari yayo fatali da ita da kayanta.

Cikin kuka ta karasa gida. Gwaggo Zulai na ganinta da kaya da kumburarriyar fuska ta tashi cikin sauri. Ya sake ki ko Sabuwa? Ai dadina dake jin magana. Sabuwa ta turo baki ta zauna kan tabarma yanzu Gwaggo baki damu da dukan dana sha ba sai saki ko. To ya sakeni amma wallahi idan baki yi min tanadi mai kyau ba sai na jawo miki magana a unguwar nan. Zulai ta rike baki lallai yar nan baki da kunya. To ki kwantar da hankalinki Yakubu zan tabbatar kin aura.

Tani duk ta zayyanawa iyayen su abinda Uwale tayi wa Munari. Babar su Tani Inno tace to ai inda sabo ta saba sai tayi hakuri. Shi kuma yaron Allah Ya jikan shi. Inna Ladi kishiyarta  babar su Salihu tace Allah Ya shiryeki Jummai. A fada miki abinda tayiwa auta shine zaki wani tabe baki. Allah Ya jikan Malam amma da yana nan bazai lamunci wannan abin ba. Bari Yayan ku ya dawo daga birni Tani da kanshi zashi gidan. Inno tace haba Yaya don Allah kada ma ya sani. Yanzu sai kiji yana cewa a sako masa kanwarsa. Inna Ladi tace to tashi muje gidan. Inno tace ni ba zani ba Yaya rigima ce bana so. Inna Ladi ta sabi mayafi suka fita ita da Tani bayan ta ajiye yaran wurin Inno.
Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:00 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°5A tsakar gida suka tarar da Munari tana iza wuta ga hayaki saboda yanayin damina icen duk ya jike. Inna Ladi tayi saurin zuwa wurin ta karba. Da kyar Munari ta iya durkusawa ta gaisheta. Inna Ladi tace haba mike...ina kike Uwale fito Allah Ya tona asirin ki. Yanzu yar ta haihu jiya, haihuwar ma mai ciwo tunda ba dan amma don tsabar wulakanci da kanta zata dora ruwan wanka da wannan icen haka? Uwale ta cangalo kafa daga daki ta fito. Idan kun damu da ita sai ku dora mata. Inna ladi tace tafiya muka yi jaje gidan kanin babanta garin kwari shiyasa tani bata same mu a gida ba . Dama tace jiyan ma ita ta dora ruwan. Haba Uwale rashin imanin naki har ya kai nan. Uwale tayi wani juyi ita ga mai kyau...ta tafa hannuwa yafi nan Ladi. Ki tambayeta abinda tayi min. Dan farin ne fa ya mutu sai wadan can gawayin kullum su nake gani a gidan nan. Sannan ace bazanyi fada ba. Inna Ladi tace Munari dauko gyalenki wallahi na gaji da wannan diban albarka. Idan yayanki ya dawo sai ayita ra kare. Tana gama magana Mal Yakubu ya shigo da dan guntun ragonsa kafi zuru. Jin abinda ake fada ya karasa gaban matarsa. Munari don Allah kada ki tafi. Inna Ladi ki rufa min asiri kada ku raba ni da ita. Hawaye ne taf a cikin idonsa Uwale na gani tace kwarankwatsa ka bari hawayen nan suka fito gaban surukarka sai na daga maka nono. Da kaji anyi zancen saki sai kuka kamar ka auri hurul...hurul me ma? .oho matan aljannah dai nake. To ka zabi daya ko ka sake tan ko kuma nan da sati biyu ka auri duk wadda na zaba maka. Da hanzari yace zanyi auren inna. Ya koma kallon Munari koma daki in dafa miki ruwan kinji. Kinga rago can na siyo zan gasa miki. Sosai Inna Ladi taji tausayinsa amma sai ta dake ni dai tafiya zanyi da ita mun gaji. Uwale tayi tsaki aikin banza kin saki baki kishiyar uwa zata kashe miki aure kin zata sonki take. Makirci ne kawai irin namu na mata. Munari sai a lokacin tayi magana.. Inna ki dena fadin abinda kika ga dama kan Innarmu don akanta wallahi zan....zaki me??? Kaji ko dan nan matarka zata zageni. Inna Ladi tace Tani dora ruwan wankan ko sake kallon Uwale bata yi ba taja hannun Munari suka koma daki.

Bayan kwana hudu da haihuwar munari Uwale na zaune karkashin bishiya tana shan fura Zulai ta shigo. Tana ganin furar yawunta ya tsinke. Ita kuwa uwale bata san tana yi ba kuma bata yi mata tayi ba. Can ta lura da kallon da Ramlah ke yi mata. Ta ja tsaki shegiya mayya duk ta kafa min ido zo ki karba. Yarinya ta taso daga wurin wasanta tazo gaban uwale. Dan yatsa ta tsoma cikin furar ta dangwala mata a harshe. Ramlah ta lashe tas ta koma wasa. Zulai dai abin duniya ya isheta sai ta fara tunanin abubuwan tausayi da suka sameta kamar rashin abinci da rashin tayin fura daga kawarta. Nan da nan sai ga hawaye Uwale ta tande baki tace lafiya zulai. Uhmm ina fa lafiya Uwale. Ina ta faman nema miki yarinyar da Yakubu zai aura jiya da daddare sai ga Sabuwa. Uwale tace fara gaya min zancen yarinyar kafin muyi zancen sabuwan. Zulai ta sha kunu Uwale baki da kara fa. Aurenta fa ya mutu. Ajiye ludayin tayi eyye kika ce me? Nace aurenta ya mutu. Ashe wata biyar kenan da mijin ua saketa bata fada ba ta zauna gidan tana son ya mayar da ita gashi har iddah ta kare. Jiya yayi mata korar kare. Sai wasu hawayen ke zubuwa daga idon Zulai ganin kudaje na bin kokon furar tasan sarai uwale na gani zata zubar da ita gaba daya. Uwale tace to ai ki bar binciken haka tunda har ta gama iddah kuma na tuna duk yaranta farare ne. Ki bar komai a hannuna ranar asabar zata tare a gidan wannan alqawari ne. Zulai sai murna , uwale tace ga fura ki sha. Kafin ta rufe baki Zulai ta janye kokon ta kafa kai. Mayunwaciya Uwale ta fada a sarari.

Tana zuwa gida ta sanar da Sabuwa yadda suka yi. Ni dai na fada musu kin gama iddah idan ba haka nayi ba kinsan uwale da rashin hakuri kamar zawo sai ta bashi wata. Sabuwa ta hadiyi yawo da kyar tace Gwaggo ina jin ciki gareni fa wata kusan biyu. Muhuci zulai ta kwala mata a ka. Baki da aiki sai ciki ne duk yunwar gidan inuwa. To bari kiji. Ranar asabar zaa daura aurenku sai kiyi shiru da bakinki. Idan kika haihu sai muce bakwaini[truncated by WhatsApp]
[8/22, 3:02 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°6Sabuwa ta ware idanu kai Gwaggo ai kinga auren babu iddah ma ba kyau ko? Zulai ta banza rufe min baki. Inji uban wa aka ce ba kyau. Aure kan aure ne ba kyau kuma dai ba shi zakiyi ba tunda ya sake ki. To cikin fa? Shi ciki ai ba matsala kinsan Uwale babu abinda ba zatayi ba akan farin jika. To nasan tana da gonaki biyu na gadonta kinga ko ita muka samu mun huta. Sabuwa dai bata gamsu ba tace Gwaggo zunubin fa. Ai dan zai zama shege...kul kika kira shi shege da ubansa fa. Ina fata bai san da cikin ba? Eh   bai sani ba. Zunubin kuma zamuyi ta cewa astangafirillah sai kiga Allah Ya yafe. Sabuwa tace Astagfirullah dai Gwaggo. To naji yanzu dai kin amince ko. Na amince Gwaggo. Sukq zauna suka kulla duk yadda zasuyi a gidan Uwale idan aure ya yiwu. Saar su daya kauyen da Sabuwa ke aure daban da nasu saboda haka da wuya yaji labarin auren.

Shirye shirye ya kankama na bikin Sabuwa da Mal Yakubu. Uwale da Zulai le kidansu da rawarsu don shi angon ko a ransa. Kullum yana rarrashin Munari ta kara hakuri idan ya sami kudi zai raba musu gida da Inna Uwale. Ana saura kwana biyu Yaya Salihu yazo garin Danmarka gaida iyayensa shi da matarsa Ruma. Tani na jin labarinsa ta tafi gidan ta zayyana masa halin da Munari ke ciki. Fada ya rinka yi iyakar karfinsa Inno tana bashi hakuri. Inna Ladi tace ni bazaka burge ni ba sai kaje gidan kayiwa uwarsa barazana yadda zata yi shayin takurawa 'yata. Kamar jira yake ya tafi gidan cikin fushi. A bakin kofa ya gamu da Mal Yakubu ya fara zazzaga masifa. Mal Yakubu duk ya tsorata yana ta bashi hakuri. Har gidan ya shiga sukayi ta da Uwale yace ke Maimuna dauko mayafinki ya kama hannun yaran..birni zamu tafi kai kuma ka biyoni da takardarta. Mal Yakubu dai harda kuka itama Munari tana yi. Da kyar Yaya Salihu ya aminci ya barta amma ya dauke Sadi dashi zan tafi. Mal Yakubu yace wallahi na bar maka shi don girman Allah kada ka rabani da matata. Yaya Salihu yace mata zan kaiwa Ruma kinji ko munari sai ta hada shi da Ali su shiga makaranta idan sun dan kara girma. Godiya tayi masa ya kawo kudi ya bata. A waje ya sake jaddadawa Mal Yakubu ya kular masa da kanwa sannan idan anyi  auren zai sa ido a kansa. Daidai da rana daya yaji zance mara dadi zai dauki mataki.

Ranar lahadi da karfe biyun rana bayan an idar da sallar azahar aka daura auren Mal Yakubu da Sabuwa. Dakinsa aka saka amarya ya zama bashi da daki a gidan sai na wadda take da girki. Da daurin gindin uwale Sabuwa ta goge da yiwa Munari wulakanci a gidan. Kullum hakuri take saboda yadda mijinta ke iyakar kokarinsa wurin kyautata mata. Watan Sabuwa biyu a gidan ta fara bayyana cikinta kamar yadda suka yi da Zulai. Uwale kamar ta lashe ta don so. Kullum Zulai tana gidan abinci safe ,rana da dare duk an mata kwano. Habaici iri iri Munari take sha idan suka hade kansu karkashin bishiya da yamma. Kirikiri Uwale ta hana Sabuwa girki kullum Munari keyi idan dare yayi kuma ta tubure tace sai Mal Yakubu ya shigo dakinta ranar girkinta.Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:02 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°7
Haka rayuwa ta kasance a gidan Mal Yakubu yau fari gobe tsumma a wajen Munari. Ba don soyayyar da suke ma juna ita da mijinta ba da tuni ta bar gidan.

Sabuwa na kwance a kofar dakinta da daurin kirji tana shan rake Uwale ta fito daga bandaki tace kai sabuwa ki raba kanki da zaki fa saboda nakuda. Kinji ki Inna kamar wata sabon shiga? Haihuwa ta uku har sai kin karanta min yadda zanyi? Ta yatsina fuska ke fa daya kawai kika yi ta tsaya miki cak. Munari daga cikin dakinta tace Allah Ya kara ta cigaba da yiwa yarta Ramlah kitso. Uwale har wani tsoron sabuwa take ta ajiye butar hannunta tace to Allah Ya baki hakuri uwar biyu. Wannan ciki naki badai girma ba. Gaban Sabuwa ya fadi ita bata taba ciki mai girman wannan ba ma gashi a karyar da tayi baifi wata bakwai ba. Bata sake tankawa Uwale ba don kada a ja maganar ta cigaba da shan rakenta.

Bayan sati uku wata rana Uwale da zulai sun fita unguwa tun safe nakuda ta kama Sabuwa. A muguntar Uwale kulle gidan tayi ta waje wai kada munari ta fita saboda taji Mal Yakubu yana cewa ta dawo da wuri tasan sarai unguwa zata. Da munari ta shirya ta shirya yarta zasu fita taji kofar a garkame. Ta gaji da ja ta dawo daki rai a bace. Dama gidan kanwar Inno zata je ziyara. Tana ajiye gyalenta taji kamar ana kiranta daga dakin Sabuwa. Shiru tayi ta tabbatar sannan ta fito cikin sauri. A kwance ta ga Sabuwa tana nishi da kyar duk ta hada gumi duk da sanyin gari. Munari jika na rawa don itama bata saba ba tace Sabuwa kinga Inna ta kullemu ta waje kuma saboda zurfin soro babu mai jinmu kiyi hakuri na dubaki. Cikin masifa tace kiji dadin kasheni ko...ki fita ki nemo taimako Munari don idan na mutu sai nayi miki fatalwa. Babu irin bugun da Munari batayi ba babu wanda yazo kashe reza ta samo a daki ta dawo kan sabuwa. Tace kiyi hakuri inajin bakwaini zaki haifa don kai ya fito. Da taimakon Allah Munari tana ta yi mata addua ta samu Sabuwa ta haihu. Yarinya ce santaleliya fara tas irin wadda Uwale take so. Munari ta yanke cibi ta taimaka mahaifa ta fito.  Kai Sabuwa wannan 'ya da takai wata tara ban  san irin girman da zata yi ba. Ruwan wanka ta dora ta wanke jaririya ta kaiwa sabuwa ruwan wanka. Sai bayan laasar Uwale da zulai suka dawo. Tun daga tsakar gida uwale ke yiwa Munari dariyar keta ta hanata fita. Munari ko a jikinta tace Inna kinyi kawa fa. Ko kulata bata yi ba harda tsaki zata wuce tace Inna nace kinyi kawa fa Sabuwa ta haihu. Zulai ta yi dakin cikin sauri Uwale tana binta tana cangala kafa. Allah Kasa fara ce, Allah Kasa fara ce. Haka take fada har ta shiga dakin. Baby ta dauka ta rungume. Yarinyar akwai kyau ga hasken da Uwale ke buri. Zulai ta rike yarta. Sabuwa bakwaini kika haifa? Me ya faru haka? Waya karbi haihuwar? Sabuwa tace nakuda ce ta kamani gashi kun kulle gidan. Munari ce tayi komai, Uwale ta rungume yar ta fita. Munari ta gani tana kwasar tuwo ta dan saki fuska nagode fa Munari sannu da kokari. Zulai da ta gama zige yarta a cikin daki ta fito da sauri wace godiya zakiyi mata uwale? Ashe kina fita ta kama Sabuwa da kokawa shine haihuwar tazo ba shiri. Ai don kada a kamata da laifin kisa ta karbi haihuwar. Uwale ta bata rai muguwa azzaluma da mai kyan zaki kashe min. To ta Allah ba taki ba baka mai bakar aniya. Tuwon ma bazata ci ba kada kisa guba. Kwashe abinki ki bace min da gani. Hawaye ne ya saukowa Munari ta je har kofar dakin ta leka Sabuwa na kwance a kan gado. Cike da takaici tace Sabuwa abinda zaki saka min dashi kenan ko? Allah na gani kuma baya bacci. Zulai tayi tsaki muguwa kinga farar haihuwa kina bakin ciki.

Mal Yakubu dai yayi farinciki daidai gwargwado yace to Inna sai asa mata sunanki ko. Tunda kan Ramlah kika ce kada asa sunanki. Uwale tace yo haka kurum zaka sawa wancan mummunar abar sunana? Ya jawo abarsa ya rungume suk yaransa yafi sonta. Inna tace  itama wannan bazaka sa mata sunana ba saboda kyanta. Akwai sunan gayu dana taba ji wallahi wata rana dana je gidan Harira jikanta ya kunna talabijin. Sabuwa tace ni fa Inna kada ki bata wa yata suna. Inna tace ni dai Hannan naji an fada ai ko yayi dadi ko? Sabuwa ta bata fuska Hannan kamar marowaciya Hanan ake cewa. Na yarda Malam a saka mata. Mal Yakubu yace to Allah Ya raya ya dauki Ramlah ya tashi yayi waje.

Ranar suna aka radawa yarinya suna Hanan. Uwale sa guda ta bayar aka yanka cikin shanunta uku. Anyi bushasha ranar suna kamar haihuwar fari. Yan uwan Sabuwa suna ta zuba habaici ga Munari. Ga 'ya mai goshin arziki an haifa. Haka dai akayi ta taro Munari da nata yan uwan suna daga cikin daki.  Yayar sabuwa na suyar nama ta bawa duka yaransu aka tsallake Ramlah. Ta rinka binsu da kallo har Uwale ta kula tayi tsaki ai idan baki bata ba Hanne yarinyar nan kamar mayya sai tasa ki kone da mai. Cillo mata kashi ta gwaigwaya. Hanne ta dauko wani guntun qashi ta jefawa Ramlah. Qashin bai zame ko ina ba sai bakin rijiya Ramlah ta bishi da dan gudunta. Tana zuwa bakin rijiyar takalminta daya ya zame daga kafarta santsi ya kwasheta sai cikin rij[truncated by WhatsApp]
[8/22, 3:03 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°9
Sai da cikin Munari yayi wata shida Uwale da sabuwa suka san dashi. Gaba daya Sabuwa hankalinta a tashe yake tana tsoron kada Munari ta sake haihuwa hankalin Mal Yakubu ya koma kan abinda ta haifa. Yanzu ma kamar yasan Hanan ba yarsa bace baya bi ta kan ta sai Inna Uwale ta dame shi. Ita kuwa kullum tana rike da ita a tsakar gida ko dakinta tana mata waka. Hannan farar jikar Uwale. Zaki auri mai kudi mai mota,zaki kaini makka da madina.

Duk wahalar da Munari ke sha saboda cikinta yakai watan haihuwa Uwale bata daga mata kafa akan girki ba irin yadda aka yiwa Sabuwa gata. Ganin aka Mal Yakubu ya siyo risho har biyu yasa a kitchen din. Uwale bata san dashi ba sai da ta fito da goyon Hanan tana ta cangala yar kafarta. Eyye me zan gani haka? Fito fiti kinibabbe ta kirawo Mal Yakubu daga daki. Wato don munafurci shine zaka wani siyo risho saboda matarka ta dena wahala ko? To ban yarda ba. Ni nafi son abincin da aka dafa da itace. Yafi dadi da inganci. Sabuwa tace a'a fa inna waye baya son sauki ni gaskiya nafi son rishon. To...to ai shikenan saboda kada fatarki tayi duhu a bakin murhu ba. Ta harari Munari kunyi sa'a uwar mai kyau tana son rishon ba don haka ba da kunga tsiya wallahi. Kamar kullum shi dai Mal Yakubu sai aikin bada hakuri.

Tun dare Munari ke fama da ciwon baya kadan kadan  tana daurewa. Zuwa asuba abin ya ta'azzara gashi ba girkinta bane. Da kyar ta iya mikewa ta bude kofar dakinta. Dakin Inna uwale ta nufa tana tafiya da kyar. Tana ta kwankwasawa Uwale na jin muryarta ta sake gyara kwanciya....aikin  banza haihuwa ta hudu ai zaki iya da kanki. Haka ta koma kofar dakin Sabuwa tana bugu. Mal Yakubu ne ya fito ya kamata zuwa dakinta yace Sabuwa ta tashi Inna su kula da ita sannan ya fita zuwa gidan makocinsa mai akori kura ya taimaka masa su tafi asibiti.  Yana dawowa daga bakin kofa ya jiyo kukan jariri. Da gudu ya karasa ya ganta kwance kan tabarma ita kadai da baby a gabanta. Duk ya rude yace bari na kira Inna...hannu ta daga masa barshi kawai Malam ga reza can dauko ka yanke cibiyar.

Su kadai suka yi abinsu su Inna ko leqe. Ya fita ya bawa makocinsa hakuri ya dawo ya buga kofar daki cikin fushi. sabuwa ki fito kafin na shigo dakin nan don wallahi na shigo jikinki zaiyi tsami. Ta fito tana mika...yanzu don wulakanci ince ki tashi inna ku taimakawa Maimunatu sai ku barta ita kadai? Inna ta fito dan nan ni kake cewa munyi maka wulakanci? To mungode Baba sai ka fadi me kake so muyi yanzu. Inna ni ba haka nake nufi ba amma ai ko sannu ayi mata. Sannu maigida to me aka samu? Mace ce ya fada ya kasa boye murnarsa.
Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:05 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°8Salati da ihun mata yasa su Munari fitowa daga daki. Mata na ganinta suka yi cirko cirko an rasa mai magana tana ta tambayar me ya faru. Uwale tace ni dai ba ruwana ,fa bani bace. Munari tace wai meye ne? Me kuke leqe a rijiyar? Wata makociyarsu ce tayi karfin halin fada mata...Ramlah ce ta fada.

Wata kururuwa Munari tayi cikin zafin nama ta nufi rijiyar ana rirriketa. Tani tace cikin rudewa garin yaya ta fada? Wata yar cin shinkafar sunan tace qashi ne Hanne ta jefa mata bakin rijiya shine ta bishi ta fada. Mal Yakubu aka fita kira a majalisarsu. Munari tun tana kuka da sauti har muryarta ta dashe....wayyo Allah kawai take cewa. Abin tausayi ta zama.

Mal Yakubu ya shigo yana tambayar me ya faru ake nemansa. Munari ta mike ta rije wuyan rigarsa. Baban Ramlah idan na rasa 'yata bazan zauna a gidan nan ba. Yi hakuri ki fada min abinda ya faru. Wani yaro yana cin nama yace 'yarta ce ta fada rijiya. Mal Yakubu yace Ramlah? Babbar riga ya tube zai shiga shima aka rike shi. Uwale ta soma kuka don Allah dan nan kada ka shiga kaima ka mutu. Suna haka Sabi mai hakar rijiya ya shigo da wasu maza. Igiya mai kauri aka daura masa ya shiga. Duk sakan a wurin su Munari tamkar shekara suke jinsa. Kamar wata zautacciya haka ta koma. Sai bayan kusan minyi goma ya fara jan igiyar. Cikin sauri aka jawo shi da Ramlah a kafadarsa. Mal Yakubu ya karbe ta ya kwantar akan tabarka. Cikinta ya danna ruwa y rinka fita ta bakinta da hanci. Munari ko wurin bata je ba tana zaune inda wasu mata suka riketa ta share hawaye Allah Ya jikanki Ramlah kawai take fada.

Duk yayi iya yinsa ya tabbatar yarsa ta rasu. Cikin kuka ya bude hannun da yaga ta damke sosai. Qashin data dauka ne ashe ba rabonta bane. Wace 'yar....din ce ta jefa kashin bakin rijiya? Jin kowa yayi tsit ya sake kunduma zagi cikin tsawa. Aka samu wata ta nuna Hanne. Kanta yayi kamar zaki cikin fushi wani abokinsa ya rike shi. A tsorace tace Uwale ce tace min mayya ce na jefa mata qashi  shine tautsayi yasa na jefa bakin rijiya. Suna wannan fadan Munari ta dauke gawar yarta ta kai daki ta fara shirin yi mata sutura. Taron suna ya koma na mutuwa ita dai Uwale tayi tsit don yau dan nata ya bata tsoro. Yana matukar son Ramlah sosai. Bayan an tafi kaita ne Munari tana zaune gaban iyayenta da suka zo ta fara jan numfashi da kyar. Mal Yakubu aka kira ya zo ya fitar da ita a rude. Ya kalli innarsa cikin bacin rai. Idan itama ta mutu yau zan saki Sabuwa kuma ta tafi da yarta bana so. Asibiti suka nufa inda likita ya tabbatar jininta yayi mugun hawa kuma tana dauke da ciki na wata daya. Duk da bakin cikin dake damunsa Mal Yakubu yayi matukar murna. Ta taga yake leken matarsa saboda ance a barta ta huta sosai. Yana adduar ta sami lafiya.

Bayan kwana takwas da rasuwar Ramlah Inna Ladi tazo gidan da sauran yaransu mata hada kayan Munari. Mal Yakubu yana ta bada hakuri yana zubar da hawaye. Inna Ladi tace kaga ka bari mu tafi ta laluma kafin yayanta ya zo kaima tunda baka ganshi ba kasan baya gari ne. Kiyi hakuri inna ya zan saki Maimuna a wannan lokacin ga rashin 'ya ga kuma rabo a tare da ita. Inna Ladi ta kalle  ta Munari da gaske ne? Kanta ta sunkuyar kasa sai hawaye. Yi shiru kinji kada ciwonki ya tashi. Ta dubi Uwale dake zaune tana yiwa Hannan rawa Sabuwa tana bacci a daki. Yakubu kasan kashe min jika akayi da gangan muka hakura yanzu haka zata zauna cikin bakin cikin rayuwa a gidanka? Kiyi hakuri inna babu fa wani yanayi mai dorewa. Zan kula da ita muddin raina bazan bari wani ya wulakanta ta ba,yana magana yana kallon Inna Uwale. Ta dago kai nasan dani kake dan nan ka cigaba da zargina don kawai yarka ta mutu. Ba ga wata Allah Ya baka ba? Girgiza kai yayi ya cigaba da bawa su Inna hakuri.

Tun daga lokacin babu me shiga harkar Munari a gidan saboda yadda iyayenta suka sa musu ido. Sai habaici daga gefe. Mijinta kuma yana nuna mata so da kulawa sosai suna ta rainon cikinta cikin sirri. Wata rana suna cin abinci tace ni kuwa Mal meyasa baka so su inna su san ina da ciki? Munari kenan ai ba murna zasu yi ba. Karshenta a rinka yin abinda zaa bata miki rai har ciwonki ya tashi. Ko kin manta Yaya Salihu yace duk ranar da jininki ya hau ko zanyi kukan jini sai na sakeki. Dariya tayi masa aikuwa gobe zanyi masa aike. Au tsokanata ma kike ko? Zan rama ne... yanzu dai kiyi ta sa hijab da zaman daki so nake kawai Inna taji haihuwa. Allah ba don darajar ta haifeni ba da tuni nasa an daure....hannu tasa ta rufe masa baki. Haba Mal? Ka manta Allah Yace kada mu fadi kalma mara dadi game da iyayenmu? Kada ka manta kwananta ne ya kare mu kuma hakurinmu shine ladanmu. Hakane Munari nima yau na dana. Allah Yayi miki albarka Ya saukeki lafiya. Amin M[truncated by WhatsApp]
[8/22, 3:06 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°10Inna uwale ta tabe baki sai mace ta takarkare ta haihu amma karshe kaga bakin jariri. Allah Ya raya dauko min abin na gani a nan bana son doguwar tafiya saboda kafa. Ba musu ya je ya dauko mata 'yar da kansa ya kawota. Ba yabo ba fallasa itama dai bakar ce amma ba sosai ba gata kyakkyawa kamarsu daya da mal Yakubu. Inna tana kallonta ta mika masa gata nan bari naje nayi sallah. Ita kuwa Sabuwa ko kallon yar bata yi ba ta juya zata koma daki. Dawo nan ya daka mata tsawa. Wuce kije  ki dora mata ruwan wanka. Inna uwale tace ka ma isa...ita da take da jaririya. Dama ai gasa ce tasa munarin haihuwa yanzu. Girgiza kai yayi cike da takaici yaje ya dora ruwan da kansa.

Daga ranar 'yan uwan munari ke yi mata komai. Ana saura kwana biyu suna tace Mal wane suna zaka saka mata ne? Haba munari ai shawara zamuyi dake. Ta sunkuyar da kanta kasa nasan wanda ya mutu baya dawowa amma inda hali a saka mata Ramlah. Murmushinsa ya fadada dama haka naso ina dai tsoron yi miki fami ne. Allah Ya raya mana ita. Tace amin. Uwale dake bakin kofar dakin ita da Zulai wanda dama gulma suka zo ji ta shigo tana matsar kwalla. Yanzu dan nan ko kara bazaka min ba kasa sunana sai zabin matarka. Inna ke fa kika ce ba kya so tun a haihuwar marigayiya. Akan Hanan ma kika sake cewa bakya so kika zaba mata wanan sunan. Ta dan fito da ido ni dan nan? Abin harda sharri? To ba damuwa ka saka mata sunan da kake so. Tana juyawa zata fita Munari tace haba Inna kiyi hakuri sunanki za'a saka mata. Ba haka inna uwale taso ba, so tayi Munari ta ce bata son sunan sai ta hadasu fada da Yakubu. Tsaki tayi ta fice Zulai na rufa mata baya. Duk da abin baiyiwa  munari dadi ba sai ta nuna wa Mal Yakubu jindadinta sosai.

Ranar suna aka radawa yarinya suna Khadija. wata  yar uwar baban Mal yakubu ce tazo ta karbi jaririyar wanzami yazo za'a cire mata beli. Uwale ta gama lura da yadda munari ke matukar kaunar jaririyarta sai ta fita wurin wanzamin tare da waziriyarta zulai. Basu dade da fita ba aka jiyo sautin kukan Khadija da katuwar murya kamar zata shide. Mata an sami abinyi suka yo soro da gudu. Tani ce kan gaba tana zuwa ta tarar uwale ta kwaye gefen fuskarta wanzan yana kallon kalangunta ya fara zanawa jaririya a gefen fuskarta na dama. Fizgota Tani tayi ta koma cikin gidan da sauri. Munari ta karbeta zata bata nono amma taki karba sai wani irin kuka take. Har dakin Uwale ta biyosu. Amma Tani baki da ta ido. Yanzu nace ayiwa yarinya kalangu zanen fulani irin nawa shine zaki dauketa. Munari tana hawaye tace yanzu Inna duk gidan nan wa aka taba yiwa zane a fuska shine zaki ce ayi mata. Au kema rashin kunyar zaki min? Bani ita a karasa mun barshi a zaune. Munari tasa zani ta goya yarta tana ta kuka. Wallahi Inna idan kinga anyi wa yarinyar nan zane a fuskarta to mutuwa nayi. Ya kike so nayi da raina ne? Matsalar yau daban ta gobe daban. Allah bari Mal ya dawo idan mutuwar aurena ce tazo sai dai na tafi da yata. Zanen nan fa Allah Ya tsinewa maiyi da wanda akeyiwa. Kuka wiwi Uwale tasa ita a dole anyi mata rashin kunya. Nufinki Allah Ya tsine min ko? To yau zanga wanda dan nan zai zaba cikin mu biyu.

Daga gefe wasu mata suka ce gidan uwale duk taron suna sai anyi dirama. Ai munari ta kyautawa kanta yau.


Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:09 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°11Wasa wasa har magariba ta gabato ana ta mayar da zance a gidan Mal Yakubu. Shi dai tun a kofar gida da labari ya riske shi komawa yayi ya kira wan babansa Baba Hadi.

A tsakar gidan ya tarar dasu gaba daya da sauran mata 'yan jin kwakwaf. Baba Hadi na shigowa yace duk su fice su bar gidan. Sum sum suka rinka fita daya bayan daya. Ba dai haka aka so ba don sun so jin yadda zata kaya aji dadin ba da labari. Suna fita Inna Uwale cikin kuka take labarta masa abinda ya faru. Baba Hadi yace ba matsala ke Munari bani yar . Ba musu ta mika masa jaririyar bayanta. Yace to Yakubu karbo yayarta ya nuna Hanan dake hannun Sabuwa. Bari na sa Yau ya kira wanzamin duk sai ayi musu. Shima Sadi idan suka zo gari sai a karbo shi a yi masa. Uwale ta wurgo kafa cikin sauri bangane ba Yaya Hadi wai harda Hannan za'ayi wa? Eh ya amsa a takaice. Dukkansu ba jikokinki bane? Tayi tsuru tsuru da ido...anya ayi harda ita? Sabuwa ta ce Al-Quran ba za ayi mata ba. Mal bani 'yata. Baba hadi yace au ita wannan da baki isa da uwarta ba shine zaki ce kada ayi mata, amma ita  munari ko kadan baki damu da lamarinta ba? To wallahi ki fita idona Uwale. Akan yadda kike takurawa matar yaron nan zan nuna miki ni ba marigayi bane. Shine yake jure halinki na tsiya. Kai ta sunkuyar kasa bata ce uffan ba. Ya mikawa munari yarta. Ki kara hakuri kinji Maimunatu. Allah Ya raya muku yaranku. Tana ta godiya ya fita Mal ya raka shi.

Tun daga lokacin uwale ta kara kunnawa Munari karan tsana. Duk lokacin da Mal Yakubu ya fita sai wulakanci kala kala. A can birni kuwa Yaya Salihu yasa Sadi a makaranta tare da yaransa. Lokacin da Ummita ta shiga wata na ashirin da haihuwa Munari tayi shirin yayeta. Wata rana tana kwasar tuwo Ummita tana ta zillo a bayanta. Tace haba mamana so kike na kona hannu ne? Uwale wadda tuni zulai ta bata shawarar yadda zata kori munari daga gidanta ta daga waje ni kuwa munari kin fiye kinibibi yaushe ta zama mamanki. Na zata sunan uwarki Baraatu. Munari tayi murmushi Inna ai kema uwata ce. To indai haka ne daga yau tunda dai nike da iko da kowa a gidan nan yarinyar nan zaa rinka kiranta Dijengala. Ni na tsani suna Ummita dinnan. Gara dai a kirata dijengala a gargajiyance. Munari tace to ba komai inna ai yadda kike so haka zaayi. Ba haka inna uwale taso ji don fada tazo takala. Sabuwa ta fito daga dakinta tace inna kinji da yadda ta amsa miki kuwa? Ai gatse tayi miki. Allah Ya kyauta uwar miji ace bata isa da surukarta ba. Ni kina ji ai sanda ta sawa tawa yar suna. Wannan ma idan na haife ita zata sa suna.

Munari dai bata kula ba don tasan neman rigimar tasu ne ya tashi. Da Uwale taga haka zama tayi a wurin sai da mal yakubu taji sallamarsa tasa kuka. Karya da gaskiya ta rinka hada masa Sabuwa na mara mata baya. Ganin ko kadan bai yarda ba tace kai na gaji so nake indai ba tare na haife ku ba ka saketa ta koma gidan ubanta. Munari ta soma hawaye tana bata hakuri. Ta tabe baki kyayi kya gama. Yau abincinki ya kare a gidan nan. Idan baka saketa ba yanzu a gabana ba wallahi sai na tsine maka albarka. Haba inna ya kike so nayi ne? Babu abinda kike nema da bana miki. Don Allah kiyi hakuri. Itama kukan tasa masa idan baka saketa ba Allah Yakubu zan maka mugun baki. Naki jinin bakar matar nan. Ka saketa yanzu.

Munari tace mal idan kana son gamawa da duniya lafiya kabi umarnin Inna. Yana kuka tanayi yace na sakeki saki daya. Wani kukan ne ya zo mata da karfi ta shiga daki dauko mayafi. Inna don ta kara kuntata mata tace kwanto goyon ai ba dashi kika zo ba. Dama yar ta isa yaye. Munari ta kalli mal yakubu yace Inna don Allah. .hannu ta daga Allah Ya tsi....da sauri munari ta kwanto yar da take matukar so ta bashi ta fita daga gidan cikin kuka.Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:10 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°13Da gudu ta karasa don yau akan wannan yar Mal yakubu yana iya karairaya ta. Tana dagota wani irin tari ta rinka yi har uwale ta jiyo su ta fito. To 'yar nema zaki fara sanaar tarin ne....kai lafiya sabuwa me ya faru? Wallahi Inna bansani ba. A cikin robar wanka na ganta. Na shiga uku na yau a gidan nan. Ba kuka zakiyi ba dauko gyalenki mu kaita kemis. Kila ruwa ta shaqa. Su 'ya'yan munari kamar kifaye kowa ya tashi mutuwa sai ya tsumbula ruwa.

Basu tarar da mai kemis ba dole suka wuce asibiti. A nan Mal Yakubu ya hadu dasu bayan dan aiken su inna ya riske shi. Likita yace gaskiya Mal akwai ganganci a tare daku. Yarinyar nan ba karamin kamu sanyi yayi mata ba tun kafin yau. Sannan idan ta tashi za'a sake yi mata wasu gwaje gwajen amma gaskiya a yadda na fahimta kunnuwanta sun tabu. Da kyar zata ji kamar da. Shi kam mal yakubu sarkin hawaye har ya fara. Sabuwa taci fada don ma inna ta tsaya mata ne. Karshe yace idan ta sake bari wani abu ya sami yarsa sakinta zaiyi ya hadata da hukuma.

Labarin abinda ya sami Dijengala ya sami su Inno. Hanawa sukayi a sanar da munari son kada tace zata taho tunda ta fara karatu a wata makarantar addini. Inna Ladi da ce taje gidan ta bukaci a basu ita tunda basa sonta. Bayan doguwar muhawara tace su jira shammaci daga kotu. Wannan kalami nata na karshe ne yasa Zulai ta bawa Uwale shawarar suje wurin wani malami a dauke musu hankali daga kan Dije. Anya ayi haka Zulai? Nifa gaskiya bana son inyi shirka. Haba Uwale malami ne fa ba boka ba. Ai irin malaman nan ba bokaye bane, suna da ilimin islama gashi idan kika je zaki ga littattafai da carbi kala kala. Sannan idan kika bari aka shiga kotu daurin shekaru zasu yi miki duk da tsufanki da yar kafarki. Tuni Uwale ta tsorata .A haka ta ja raayin Uwale suka je wurin malamin. Bukatarsu biyu ce. Mal Yakubu yaso Sabuwa ya hakura da abinda ya faru sannan Munari da 'yan uwanta a dauke musu hankali daga kan Dije da zancen zuwa kotun nan. Ya kasance munari ta manta ma da yar tata gaba daya.

Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:11 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°12Cikin kuka ta shiga gidansu da sallama. Inna Ladi ta ajiye butar hannunta ta taro ta. Me ya faru Munari? Ta shafa bayanta taji ba goyo. Ina 'yar? Ba dai ta mutu ba. Munari ta kasa magana sai kuka. Inno tace wai ba magana ake miki ba. Inna ya sakeni, inna uwale tace idan bai sakeni ba zata tsine masa. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Ita kuwa Uwale tana son gamawa da duniya lafiya? Ina ruwanta da zaman ku inji Inna Ladi. Inno dama bata saka baki a lamarin gidan yarta saboda kara amma yau bakinciki ya isheta. An sako mata 'ya da magaribar fari. Tace ina goyon. Munari ta sake fashewa da kuka tace ba dashi nazo ba. Inno tace Alhandulillahi in anyi duniya don Manzon Allah SAW kin bar gidan Yakubu har abada. Saurin dago kai tayi haba Inno wallahi ba da son ranshi bane. Na dai fada miki...munari ba fa sadakarki aka bani ba. Haihuwarki nayi kamar kowanne da. Kyautace Allah Ya bani to nayi hakurin da zanyi Allah Ya yanke miki wahala. Inna Ladi tace hakane amma kada muyi saurin yanke hukunci.

Sallama suka ji daga waje. Inna Ladi ta amsa don ta gane mai muryar tare da yi masa izinin shigowa. Yana shiga gidan ya zube a kasa yana basu hakuri. Inno tace ai ni so nake ka cike mata sakin gabadaya. Inno kiyi hakuri don girman Allah. Zan kama mata gida sai na mayar da ita can. Kaga tun ina ganin mutumci da kimarka ka bar gidan nan kafin ayi abun kunya. Yadda Uwale ta karbi Ummita to zan aikawa Yayansu ya dawo maka da danka. A'a inno na bar masa ki dena maganar nan don Allah. Ya kalli Inna ladi ki bata hakuri, ko kula shi bata yi ba taja hannun munari tana tirjewa cikin dakinta. Haka ya gaji da zama ya koma gida.

Washegari kafin azahar Inna Ladi ta aika Tani tazo da mai binta Shafa suka raka Munari birni gidan Salihu bisa umarnin iyayensu.

Haka Dijengala inji kakarta uwale ta tashi cikin kuncin rayuwa da wahala. Mahaifinta ne kadai gatanta. Tana da shekara biyu Sabuwa ta kara haihuwa. Dama ba wata kulawa Digengala ke samu ba hatta wanka sai babanta ya matsa ake yi mata. Watarana ya fita da sassafe Sabuwa ta kai ruwa bandaki a katuwar roba ta kira Hanan da Dijengala tayi musu wanka. Tana gamawa yarta tace muje in shafa miki mai tukunna. Dije wadda aka yiwa tsirara sai rawar dari take saboda sanyi tace Mama nima wanka. Wani mari Sabuwa ta gaura mata ta dauki yarta suka fita. Dije tana kuka ta taka sabulu ta zame ta fada cikin robar ruwan. Sai da sabuwa ta gama shirya Hanan bayan kusan minti goma ta dawo ta tarar da Dijengala ta kusa shidewa a robar ruwa.

Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:11 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°14
BAYAN SHEKARA 17

Cikin daga murya irin na wadanda basa ji sosai tace Inna ina kwana? Uwale ta sha kunu matsa can ni kada ki tofe ni da yawo kinzo kina min ihu a ka. Dijengala tace naam? Alamun bata ji abinda kakarta ta fada ba. Tsaki Uwale tayi tare da daga hannu lafiya nace. Murmushi tayi wanda yake kara mata kyau tace au banji ba ne. Dama ai ba jin kike ba. Ta sake daga hannu tashi ki bani wuri. To..to..to ta mike ta koma dakin su ita da Hanan da kanwarsu Zaliha.

Wata yaloluwar katifa ta nufa ta kwanta. A hankali idanunta suka ciko da hawaye. Ita meyasa bata da Umma? Ina dangin ummanta suke? Hawayen ne suka gangaro sai tari ya sarke ta. Zaliha ce ta ganta bayan ta dawo daga makaranta. Yaya Dije sannu ta dafe mata kirji. don idan ta fara tarin numfashinta har neman daukewa yake. Rashin kudi sosai yasa Babanta ke yawo da ita gidan masu maganin gargajiya, wasu suce sanyi wasu suce asma. Zaliha ta dago kan dije ta bata ruwa bayan tarin ya lafa. Ta daga murya Yaya Dije kuka kika yi ko? Tayi saurin girgiza kai tari ne Zaliha. Allah Yasa da gaske kike, bari naje na dauko mana abinci nasan yunwa kike ji ma.

Haka dokar Sabuwa ta koma  abincin Hanan daban, Zaliha da Dije tare ake hada musu. Tunda Dije ta gama secondary school wadda ba wani abin kirki ta iya ba saboda rashin kunne kullum sai ta jira Zaliha ta dawo zasu ci. A cewar sabuwa kada dije ta cinye abincin. Babansu bai taba sanin wannan dokar ba don har yanzu yana so da kula da lamuran yarsa. Shekararsu goma sha biyar da baro kauyensu suka koma birni da zama. Takurawar iyayen Munari kan sai an basu Dije yasa Uwale sayar da filayenta harda gidansu ta matsa masa sai sun tashi indai ba so yake ya kulleta a gidan yari ba. Tayi mamakin yadda aikin malam bai kama su ba sai dai kuma bata kara jin duriyar Munari ba tunda tasa Yakubu ya saketa. Aikin gini da noma yake yi a haka yake ciyar da iyalinsa yake saka su a makarantar gwamnati. Tun tafiyarsu wadda basu yiwa kowa sallama ba iyayen Munari suka sanar da ita duk abinda ya faru. Tayi kuka sosai saboda tana matukar son 'yarta kuma ta kara tsanar Yakubu akan guduwa da yayi da ita. Allah Yasa ma Sadi yana wurinta.

Hanan ta fara karatu a polytechnique ta garin kano tana ji da kyau da gayu. Duk gidansu babu wanda take so kamar kakarta Uwale saboda yadda take shagwabata tana kuranta kyaunta. Duk yar yaudarar samarin da take da izinin kakarta take yi. Tana kwance kan gadon uwale tana chatting Mal Yakubu ya shigo dakin. Wani wuntsulowa tayi da sauri zat gudu. Hannunta ya rike ya dawo da ita dakin munafuka ina zuwa. Ya zaka kirata munafuka dan nan ka kiyayeni fa akan Hannan wallahi. Inna kina bata yarinyar fa. Kalli wayar hannunta abinda take saurin boyewa kenan kada na gani. Uwale tayi murmushi zancen banza ai kudin dashi na na bata ta siya dashi. Hanan tace Allah Baba ita ta bani.bari saurin rantsuwa ni tsakanina daku shawara ce. Iya abinda zanyi miki nayi na tarbiya. Allah Ya shirya.
Ficewa yayi rai a bace ya tafi dakin yaran wurin Dije da Zaliha. Baba sannu da zuwa...yauwa Zulaihatu. Taba min yayarki nasan bata ji shigowata ba. Tsinkin tsintsiya Zaliha ta sawa Dijengala a kafa ta mike a firgice. Wayyo Allah...muryarta duk ta cika gidan. Tana ganin babanta ta matsa kusa dashi. Baba kaga Zaliha ko...zan zane ta fa. Guje guje suka rinka yi a tsakar gidan yana dariya. Yaran nan biyu kadai ne suke wanke masa bacin ransa da damuwa. Sune kuma Uwale bata so don abin mamaki duk farin Sabuwa haka ta haifo Zaliha baka har tafi Dije duhu. Shiyasa uwale bata shiga sabgarsu kamar babu su a gida.

Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:12 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°15
Ranka ya dade ga takardun filayen guda uku aka samu a wuri daya. Alh Sulaiman Hassan ya kalli sakatarensa Modibbo nagode dan fillo. Zanyi magana da  managers din sauran kamfanin sai muyi finalising project din. Modibbo yace hakan yayi ranka ya dade amma akwai sako daga wurin Hajiya fa. Murmushi yayi alamun yasan sakon Hajiyar yace nasan cewa tayi ka tabbatar yau na tashi da wuri ko? Shima Modibbo murmushin yayi ni dai umarni nake bi kuma lokaci ya riga yayi. Wai ni waye ke biyanka ne ni ko ita? Ai Alhaji da kai da kaya duk mallakar wuya ne. To naji ya fada tare da mikewa.

A hankali yake tuki don yau drebansa bai zo ba matarsa ta haihu. Karatun Al-Quran  yake ji kira'ar Sheik Khaleel Husary yana bi cikin nutsuwa har ya isa gidansa a unguwar bompai ta cikin garin kano.

A falo ya tarar da ita ta gama hade rai alamun tana fushi dashi. Mata ne biyu zaune tare da ita. ko da ya gaisheta da kyar ta amsa masa shima yasan yayi laifi bai matsa mata ba yayi hanyar bene tace cikin fushi Sulaiman ina zaka je kuma? Umma zan canja kaya ne na dawo. To kayi sauri yaran kawata ne suka zo gaisheni shine nace su jira kazo ku gaisa. To kawai yace a ransa kuwa harda dariya...umma kenan ta zama matchmaker karfi da yaji ita a dole sai yayi aure a wannan shekarar. Shima kullum yana adduar samun ta gari yasan kuma Allah mai jin rokon bayinSa ne.

Wanka yayi yasa kananan kaya ya sauko. Yana zama Umma ta mike to bari na duba abinda ake dafawa. Yasan so take ta basu wuri ya ce to kawai. Tana tashi dayar wadda take ta yi masa kirikiri da ido tace Yayanmu ni sunana Ainau wannan kuma kanwata ce Bilkisu. Ko kallonsu baiyi ba don basu yi kama da masu kunya ba ya zaro kudi a aljihunsa ya mika musu ga kudin mota nice meeting you. Sai anjima muje nasa dreban Umma ya kaiku gida. Ainau ta bata rai ai Hajiya tace mu jira zaka kaimu da kanka idan ka dawo saboda kaga gidan. Ashe ma doluwa ce yarinyar ya fada a ransa. Kinga naji ciwo a hannun bari a kaiku. Bani number dinki zan kiraki musamman. Kanwar tace nifa? Itama karbar tata yayi yana so suyi su fita kafin Umma ta dawo. Sai da yaga fitar motar daga gate din gidan ya dawo ya zauna. Muryar ummansa yaji tace Sulaiman ina su Ainaun suke. Ai sun tafi wai sauri suke yi...amma yaron nan baka da kirki. Wai so kake na mutu banga jika na ba shekarunka talatin da shida fa...jin ta fara shakar hanci yasan kukan blackmail ne ya tashi. Kiyi hakuri Ummana na sami mata ina jira mu gama daidaitawa ne. Ta washe baki hakoran makkanta suka bayyana. Da gaske Sulaiman? Da gaske Umma..to ai da kayi magana da wuri bazan kira yaran nan ba, dama nima duk basu yi min ba. Yadda tayi maganar yasa shi dariya sosai.

Modibbo da abokinsa Mal Yakubu suna zaune kofar wani gida da su mal yakubu ke aikin ginawa yace mutumina Alhajin kamfaninmu ya sayi wasu filaye manya guda uku. Ban dai san abinda zai gina a wurin ba amma naga so yake ayi ginin da wuri. Zanyi masa magana akan ka ka samu shiga cikin masu yin aikin. Nagode Modibbo Allah Ya bar zumunci. Wallahi kudin karatun yaran nan da ciwon Dije sune suke damuna. Kada ka damu in sha Allah zaka sami wani abin yanzu don Alh Sulaiman akwai kirki. Haka suka zauna suna ta hira har laasar tayi suka tafi gida tare.
Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:13 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°16
Hannu yaji ya sakalo masa wuya ta baya. Daddy oyoyo...tashi yayi ya daga Ammar sama yana ta dariya. Umma ta fito ni kun cika min gida da ihu abinda kuka iya kenan. Dariya suka sake yi mata Ammar yace Daddy dazu mamana tazo kafin ka dawo daga office. Umma ya kalla tace Ammar je ka daki ka dauko wa daddy tsarabar da tayi maka. Yana fita tace zuwa tayi ta sanar dani ta sami mijin aure. Ai gara tayi auren ta dade shekara shida ai ba kwana shida bane. Sulaiman yace Umma Allah Yasa dai ba fushi kike dani ba akan rashin aurenta. Gyara zama tayi ko kadan duk uzurin da ka bani na karba. Idan ka kai mata Ammar ranar jumaa sai kaji ko waye mutumin.

Alh Sulaiman Hassan shine da na biyu a wurin Haj Bintu. mahaifinsa babban dan kasuwa ne kuma yana da kamfanin yin kafet har uku a kasar. Shekarar Sulaiman ashirin da daya baban nasa ya rasu bayan yasha jinya yayansa Yusuf ya cigaba da kula da kamfanin baban. A lokacin da yake masters dinsa a fannin aikin banki , Yusuf ya rasu sakamakon hatsarin mota da yayi. Ya bar matarsa sakina da ciki wata biyar. Bayan ta haihu ne Umma tayi ta kokarin hadasu da Sulaiman yaki yarda a cewarsa bazai dena kallonta a matsayin matar wansa ba. Shekaru shida kenan sai yanzu ta sami wani zata aura.

Saboda matsin layin daga can baya Sulaiman yayi parking motarsa shi da Modibbo suka taka da kafa zuwa kofar gidan Mal Yakubu. Kwata ce a kofar gidan dole suka shiga daga dan zauren waje inda Uwale ke kiwon tumaki. Banda wari da zarni babu abinda ke tashi a wurin. Sulaiman ya gimtse fuska. Modibbo sarai ya gane warin ke damunsa yace yallabai kayi hakuri shiyasa nace ka zauna a mota na kira shi.
Ba komai Allah Yasa ya fito yanzu dai.

Wata kyakkyawar yarinya ce ta fito fara tas harda dan karin mai. Cikin yanga take tafiya. Gaba daya hankalin Alh Sulaiman ya koma kanta. Baba yace yana zuwa ta fada ba tare da tayi musu sallama ko gaishe su ba. Ciki ta koma tana taunar cingam.

Mal yakubu ya fito ya gaishe da Alh Sulaiman sannan ya gabatar da kansa. Alh Sulaiman yayi masa bayanin wurin da filayen suke ya kuma bukaci yazo kamfani ya same shi washegari.

Ihun da suka ji yasa su yin shiru Dijengala ta fito da gudu tana kuka. Murya can sama tace Baba kaga Mama ta hanani wanka yau ma wai zan karar da ruwa. Kaji yadda nake tsami kuwa...matsawa tayi gabansa tana daga masa hannuwanta har gashin hammata Alh Sulaiman yana gani. Kuma fa jinin wata na yazo tun jiya . Subhanallahi Dije sauke hannun mana ya kama hannunta zai koma cin gidan da ita. Tirjewa tayi Baba dukana fa zata yi kuma kullum Yaya Hanan tana yi da Zaliha. Duk kunya ta kamashi ya daga murya don taji abinda yake fada...muje nace zan mata magana. Burinsa kawai su koma cikin gida. Sai lokacin taga mutane tsaye...lahh baba modibbo sannu da zuwa. Sai ta rike baki au...duk kunji abinda na fada ko? Wayyo kunya ta dafe kai tare da komawa cikin gida. Alh Sulaiman kuwa  dariya ce ta kwace masa ganin yadda Dije take baragada a gabansu. Sai dai fa akwai wari dan kare.

Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:13 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°17Wani murmushin ya sake yi shi kadai Umma ta jefe shi da pillow din kujera kai ni dariyar me kake yi kamar kwancen hauka....wata dariyar ya sake yi sannan ya bata labarin Dijengala kurma. Itama dariyar tayi maimakon ka taimaka mata shine kake dariya. Ni mubar wannan zancen dai ya sunan yarinyar da kayi min zancenta ne? Ga mamakinsa sai yaji yace Hanan.

Daren ranar tunaninta ya rinka yi. Tana da kyau mai daukar hankali gashi da gani tana da tsafta ba kamar Dijengala ba. Wani murmushin ya sake yi da ya tuno yadda take magana. Daga nan har yayi bacci tunaninsa yana kan Dije yana dariya.

Ranar litinin duk ya kagu modibbo ya iso. Yana zuwa kuwa tambayarsa tayi ko anyiwa Hanan miji. Modibbo yadan yi turus...Hanan dai yar abokinsa ce amma ko kadan bata da hali. Ranka ya dade ba ayi mata miji ba a iya sanina. To ka sanar da mahaifinta idan ya amince zan nemi aurenta. Modibbo ya nuna farincikinsa a fili amma ba don yadda Dije ta tashi ba sai shirme da shiririta ga lalurar kurumta da ita zai so Alhajin ya nema.
*******************
Rana duk ta dami Hanan a kofar banki inda take jiran kawarta. Wata mota take ta kallo, ba karamin kyau tayi mata ba...duk mai motar nan ko ba'a fada ba mai kudi ne kuma mai kyau. Tayi dan tsaki ita kyau ma bai dameta ba indai akwai kudi. Tana zaune a wurin wani matashi ya fito ya bude motar. Gaba daya ya tafi da hankaliñta ta bishi da ido. Kana ganinsa kaga kudi don yawan shige shigenta tana gane mai kudi tana gane yaron mai kudi. Wannan matashin kam shine da kudin. Tashi tayi ta kade skirt dinta tayi saurin zuwa gaban motar inda yake shirin rufe kofa tace Alhaji kwana biyu. Ya dan dago kai a dakile yace ya kin sanni ne? Tayi baya yi hakuri sai naga kamar wani da na sani ne. Sai kashe murya take tana magana ciki ciki. Ya bata rai bashi bane to...matsa na rufe kofar. Kafin ta gama matsawa ya bugeta da kofar ya figi motarsa. Kafin ya bace ta gama haddace numbar motarsa.


Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:14 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°18Kawarta Hajara ce ta fito jaka cike da kudi. Sorry Hanan na barki jira ko? Gaskiya da mita zan miki amma na fasa. Wani kamu nayi mai kauri. Hajara tace haba a yana ina? Hanan ta fada mata yadda suka yi. Amma zancen gaskiya kawata yayi min akwai kudi. Ji nayi kamar kudin jikinsa yana kirana. Shegiya uwar son kudi nasan wannan mai cangala kafar zaki kaiwa. Allah sarki innata tafi kowa kaunata. Ni ba wannan ba Hajara ki rakani gidan Babba mana. Akan mutumin nan sai anyi aiki.

Dayake halinsu yazo daya shiyasa kullum a makaranta tare suke. Hajara da Hanan suka wuce gidan Babba wani malamin tsibbu. Don yanzu bin malamai harda yan mata. Allah Ya kara shirya mu. Bayan dukkan bayani Babba yace Hanan kin san sunansa? A'a amma ga numbar motarsa, ka taba yi min aiki akan wannan wawan malamin da numbar waya ai. Ba damuwa Hanan ga wanan turaren ki saka kan garwashi sai ki rubuta numbar motar a takaddu goma ki rinka dorawa akan wutar har su cinye duka. Sai ki lazumci zuwa wurin da kuka hadu na kwana goma. Idan baki ganshi ba to motar ba tasa bace. Godiya tayi sosai tace idan ciniki ya fada zaka ganni.

Bayan kwana uku Modibbo ya sanar da Mal Yakubu bukatar Alh Sulaiman. Murnarsa bazata misaltu ba ya sanar da Uwale. Burinshi dama tayi aure ya gaji da sintirin da samari ke yi masa a kofar gida. Sabuwa ma tayi murna har ta sanar da babarta Zulai. Cikin dare ta bawa mijinta shawarar ya aurar da Dijengala. Banda abinki Sabuwa ina Dije take da saurayi. Tayi wani murmushin keta...wani kurma ne dan uwan Zainab makociyarmu. Tace a kauyensu yake Kura. Hade rai yayi dakata malama ni 'yata bata gama kurmancewa ba kinji ko. Ki rike abinki rabonta na tafe. Kuma dama ina son yi miki magana Allah ranar da kika sake hanata ruwan wanka zaku yini a gidan nan ba ruwa. Yar hirar tuni ta watse ya juya yayi kwanciyarsa.

Gari na wayewa cike da zumudi Uwale ta sanar da Hanan zancen Sulaiman. Ta wani harareta jiya tasha uban hayaki akan wani yau a kawo mata zancen wani Alh Sulaiman. Kinga Inna ki bar maganar nan ina da wani. Haba Hannan mutumin nan fa kudi gareshi sosai. Mafarkina a kanki ne zai tabbata. Hanan ta wuce zata shiga wanka. Kinga Inna ki bar maganar nan ku bashi Dijengala ko Zaliha. Auzubillah uwale ta fada tana tofar da yawu. Dije ai ai musaki irinta. Yarinya ga baki ga muni.Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:14 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°19Hanan tayi sati daya tana zuwa bankin da suka je da Hajara tun safe har sai sun tashi amma mai motar bai dawo ba. Rai a bace ta koma gida duk ta kusa gama kashe kudin hannunta a hawa motar zuwa banki.

Dakinsu ta shiga zata cire kayanta tayi wanka Dije ta shigo tana waka da karfi. Hakan ya kara batawa Hanan rai ke rufa min baki banza kawai. Ta fice tana tsaki. Babanta ta gani a kofar kitchen yana magana da Sabuwa...yauwa zo hanan dama zancenki muke yi. Ta turo baki  gaba ta karasa gabansa ta tsaya. Nasan an fada miki maganar Alh Sulaiman ko. Wanda kuke aikin gini dashi baba? Eh ya amsa mata. A zuci tace tabdi magini zan aura? Allah Ya kiyaye, itama Mama tsautsayi  ya kawota gidan nan. Mal yakubu yace dama tafiya ce ta kamashi amma ya dawo zai zo yau da daddare inji modibbo. Uhmm tace ta wuce bandaki. Wallahi bazai sameta a gida ba ma. Me zatayi da talaka.

Haj Bintu tana ta kallon yadda Sulaiman ke shirin fita daga dawowarsa ko abinci bai ci ba. Ina zaka ne  don nasan wannan shigar bata zaman gida bace. Hular hannunsa ya gyara Umma gidansu Hanan zani amma da Ammar zan tafi saboda zan kaishi aski. Wato ka dawo zaka nuna min ban iya kular maka da danka ba ko? Yana dariya ya bata hakuri. To ina tsarabarta ko haka zaka tafi? Mata fa sai da ihsani. Zan biya na siyo wani abun a hanya. Hannun Ammar ya kama suka tafi yana ta yi masa hira.

Hanan ta rasa yadda zata yi ta fice daga gidansu tunda babanta yaki fita tun safe. In ba rashin aikin yi ba kakkarfan mutum kamarsa ya zauna a gida wuni guda....tayi tsaki. Zaliha tace lafiya. Hararar ta tayi ban sani ba ta bata amsa tare da fita daga dakin. Mal Yakubu na fita zuwa masallaci sallar magriba ta fice ba tare da sanin kowa ba.

Alh Sulaiman yana dosar gidan ya fara jin  warin kwatar kofar gidan. Shifa harkar warin nan baya kaunarta. Ya rasa dan aike gashi bashi da numbar wayar kowa a gidan.Ammar ya tura ciki ya sanar da zuwansa. Yaro ya shiga kai tsaye dakin da ya hango haske ya nufa. Uwale ce da Sabuwa suke kallo yace salamu alaikum wai daddy na yace ya zo. Sabuwa ta kalli dan kyakkyawan yaron kai kuma daga ina wa ya turo ka? Mal Yakubu ya shigo yace dan Alh Sulaiman ne mai son Hanan. Kirata Sabuwa yana jirantaa soro.

Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:15 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°20
Sau uku ta kira taji shiru. A zaune ta tarar da Dije tana gyangyadi kafin Zaliha ta dauko musu tuwo. Shureta tayi da kafa ke kurma tashi...a firgice ta tashi tace mama me ya faru? Ta dungure mata kai tare da rage murya ubanki ne ya faru. Dije ta bata fuska tana nuna kirjinta ubana? Ubana?? Sai hawaye...ke yi min shiru munafuka ana magana sai kiyi ta kallon bakin  mutane ina Hanan? Dije tace ta fita tun dazu. Kai yarinyar nan zata ja min masifa ta koma daki ta fadaw Mal yakubu.

Ransa yayi matukar baci gashi yar wayar tasa ma ba kudi bare ya kirata. Uwale tace yarinyar nan neman tona min asiri take ga wayata kirata. A kashe suka ji wayar. Bari na fada masa kawai ,ita kuma yau tamu ce ni da ita.

Jin Zaliha bata dawo daga dauko musu tuwo ba Dijengala ta duba kitchen bata ganta ba ga yunwa yana cinta. Ita kuwa Zaliha  cikinta ne ya kada ta tafi bandaki. Wata tsohuwar naira ashirin ta dauko a kasan akwatinta ta saci jiki zata je siyan wainar fulawa a gidan Zainab makociyarsu. Tana saka kafarta a soron aka dauke wuta, saboda duhu hannunta take mikawa kamar makauniya tana neman hanyar fita, wani mulmulallen abu mai dan gashi gashi  taji ta shafa ta tabbatar ba kan daya daga tumakin Sabuwa bane.  Ammar data tabawa kai ihu ya saka. Daddy kamani naji an taba min kai. Sulaiman yace ina zuwa Ammar wayata nake nema. Dije sake taba kan tayi don ta tabbatar da abinda ta taba, gashi tana jin kamar maganganu amma ta kasa gane me ake fada. Ihu tasa iya karfinta wayyo Allah baba nayi gamo. Sulaiman tuni ya gano muryar yar kazamar yarinyar nan yace ke rufa mana baki yana neman hannun Ammar su fita. Ta soma kuka Al'Quran naira ashirin ce a hannuna waina fulawa zan siyo a gidan Zainab yunwa nake ji. Gashi don Allah kada ku mayar dani kaza ko doya. Ba shiri sulaiman ya soma dariya...hannun dansa ya kama. Yana jin yadda Dijengala take tsalle da ihu. Mal Yakubu ne ya iso soron da yar fitila. Shima bai kula da su Sulaiman ba don ya zata sun tafi. Dije dena ihu nine...tana ganinsa tayi saurin matsawa kusa dashi tana magana da karfi, baba aljanu ne suke son bude min ido, dansu suka turo min shegu. Kul kike zagi dije...shima baba zuciyarsa ta kusa bugawa daya ji ance daddy mu tafi. Sai a hankali ya gane Alh Sulaiman ne da dansa.
Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:16 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°21Da kyar ya iya tsayar da dariyarsa yace Mal 'yar nan taka tana da abin dariya. Ai nima na tsorata don nayi tunanin kun tafi. Ammar ya nuna takalminsa ne ya kwance na tsaya daure masa sai aka dauke wutar kuma ina tunanin wayata tana mota. Sake sallama suka yi kafin Sulaiman ya gama fita yaji mal yakubu yana tambayarta ina zata.. wallahi baba yunwa ce kuma zaliha bata kawo abincin ba, dama wainar fulawa zan siyo ta ashirin. Dariya yayi haba Dije wainar ashirin ai sai da kiyi kuskurar baki da ita. Me kace baba? Banji ba. Muje na baki nawa abincin kici a daki kada sabuwa ta gani. Daddy mu tafi mana wari nan. Sai a lokacin sulaiman ya dawo hankalinsa yaja hannun Ammar suka fita bakin layin inda yayi parking motarsa.
****************
Ashir ya rasa abinda ke masa dadi. Tun washegarin zuwansa banki zuciyarsa ke masa radadi ya rasa dalili. Ji yake kamar ya koma bankin ya nemi yarinyar da ta yi masa magana amma shi ko fuskarta ma bazai iya tunawa ba don  bai kalleta da kyau ba. Wata biyu ya rage bikinsa amma yan kwanakin nan baya son ko jin sunan matar da zai aura. Dama dai auren baya gabansa don shine na uku ma. ba ya dadewa da mata suke rabuwa, hakan na damun yan uwansa shiyasa wannan karon babansa ya yanke shawarar hada shi da yar kaninsa da mijinta ya rasu shekaru shida da suka wuce, wato sakina mahaifiyar Ammar. Gidansu Ashir suna da rufin asiri dai dai gwarwado. Lokacin da ya fara aikin kwangila ga aikin office shine kudi suka zauna masa  sosai. Kasa nutsuwa yayi karshe ya yanke shawarar zuwa bankin a daren bayan yayi magriba a kofar gidansu.

Hanan na sauka daga adaidaita sahu suka hada ido da mutumin da take ta nema. Gabansa ne ya fadi yana ganinta. Banda kyawunta wani yanayi ya shiga mai wutar fassara. Idan bai auri yarinyar nan ba rayuwarsa tana cikin matsala. Har wani gumi ke keto masa. Karasawa yayi inda take ba tare da yayi mata magana ba ya mikawa dan sahu dubu daya yace mata zo mu karasa bakin motata. Ba musu ta bishi...lallai aikin Babba yayi kyau.

Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:16 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°22Bude mata yayi ta zauna a seat din gaba. Shima yana zama yace me ya fito dake a daren nan? Ta rausayar da kai tana kare masa kallo, ga kyau ga kudi.ready made kenan..kai ya kamata nayiwa wannan tambayar. Hmm ina jin abinda ya fito dani ne ya fito dake. Me kenan ta tambayeshi ciki da jindadi. Yana kallonta yace tunaninki mana. Duk kin hanani sakat...ina tunanin kema hakan take a wurinki. Ni fa kudi nazo dauka ba wurinka nazo ba. To fitar min daga mota indai hakane. Tsoron kada garin jan aji ta rasa shi yasa tayi saurin cewa wasa nake maka. Nima ka hanani nutsuwa tun ranar da muka hadu. Yaji dadin amsarta...ni sunana Ashir Sani. Ina aiki a NNPC sannan ina harkar kwangila sosai. A takaice dai i am a very busy man. Ina ruwanta da yawan aikinsa indai akwai kudi. Ta fada masa nata sunan daga nan hira suka rinka yi kamar sun dade da juna. Ganin tara ta wuce yace muje na kaiki gida.

Alh Sulaiman na fitowa daga layin gidansu Hanan ya hangota cikin motar wani. Ina taje a daren nan ya tambayi kansa. Motar na kara matsowa yaga kamar yasan mai tukin amma ya kasa tuna ko waye. Bai kawo komai a ransa ba ya tafi gida.

Cikin sati biyu soyayya ta kullu sosai tsakanin Ashir da Hanan. Ta sanar da uwale da sabuwa komai game dashi. Tuni ta sace zukatansu bare da suka ga irin hidimar da yake mata. Mal Yakubu dai ya nuna rashin amincewarsa. A cewarsa bazasu mayar dashi karamin mutum ba. Ya riga ya amsawa Alh Sulaiman har yace zai turo iyayensa don baya son a dauki lokaci. Uwale tace to dan nema mai toshe kofar arziki. Shi Sulaimanun nawa ya taba bata tunda yazo. Inna ki dena koyawa yarinyar nan son kudi, zuwansa uku fa kullum ba ta gida. Yau idan ta dawo sai naci mutumcinta. Shegen yawo kamar kaza. Uwale ta sha kunu bana son irin haka fa, ka manta tana karatu ne? Ni dai na gama magana yarinya Ashiru zata aura. Jiya da ya shigo dubu goma ya bani. Ni Uwale da dubu goma tawa ta kaina. Ka sallami wannan abokin ginin naka don bazan bashi jikata ba.

Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:16 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°23Abokin gini kuma Inna? Ni da na fada miki gini zanyi masa yana da kamfani. Sabuwa da tun farko bata yi magana ba tace haba Malam wai kai a dole sai ka nuna baka son yarinyar nan ne? Ya arziki na binmu kana sa kafa kana shurewa. Babu wanda ya isa yayi mata dole. Wanda take so zata aura. Idan kuma dole ne sai ks bashi Dijengala ai itama mace ce. Inna Uwale ta tuntsire da dariya...wa yaga barahaza. Ba yadda ya iya dole ya kyalesu idan suka hade masa kai don baya iya musu da Inna Uwale. A zuciyarsa ya gama yanke shawarar sanar da Modibbo ya bawa Alh Sulaiman hakuri. Dama can ba sa'an auren yarsa bane shima don yaga kamar auren zai hanata yawo ne.

Alh Sulaiman yana mamakin yadda duk lokacin da yaje baya samun Hanan kullum sai ace masa bata nan, gashi Umma duk ta kwallafa rai. Shi kanshi yana son ya kara ganin kyakkyawar fuskar Hanan din. Yarinyar akwai class. Yana dawowa daga office ya shirya ya tafi gidansu da yamma. kila don saboda zuwan dare yake shiyasa baya samunta. Yau tararta zaiyi kafin ta fita. Yana tuki Dijengala ta fado masa a rai. Shi kadai yayi murmushi Allah Yasa itama na sameta...a ransa har ya gama shawarar idan yau auri hanan zai ce ta taho da kanwar tata.

Yau ma can baya ta ajiye motarsa. Sabuwar benz ce  da masu kudi ke yayi ya shigo lokon a kafa. Farin yadi ne a jikinsa mai bula bula. Wandon da shafi amma babu a rigar, ana ganin farar vest din dake ciki. Takalminsa da hula duk ruwan toka ne. Yayi kyau sai kamshi ke tashi duk inda ya wuce. Bai ankara ba yazo daidai kwatar kofar gidan Mal Yakubu yaji an kwala ihu sai ruwan kwata ya gani ya fallatso masa ko ta ina a jikin kayansa harda gefen fuskarsa. Ransa ya gama baci sosai saboda shi mutum ne mai matukar kyankyami. Dijengala ya gani kafarta daya a cikin kwatar babu ko mayafi a jikinta tana kuka. Ganinsa a tsaye yasa kukan ya karu ta soma bashi hakuri da karfi. Don Allah kayi hakuri ban sani ba. Inna ce ta biyoni da bulalar doki. Kafin yayi magana wata dattijuwa ta fito daga gidan da ke kusa dana su Dije. Daga murya tayi yadda Digen zata ji...me ya faru Digengala? Ta sake wani sabon kukan sannan ta fita daga kwatar ta karasa wurin matar. Gwaggo, Inna ce tace yau bazanci abinci ba sai na debo ruwa bokiti goma. Kuma fa na debo shida amma yunwa nake ji. Tace na sa baba yaki siyo ruwa saboda sun hanani na wanka jiya daya fita.  Gwaggo taja hannunta kiyi hakuri kinji yar albarka  shigo kici abinci kiyi wankan. Ta kalli Sulaiman wanda ya zuba musu ido. Alhaji shigo kaima kuma kayi hakuri.

Ya kalli tsohuwar ba damuwa? Haba yaro ni da 'ya'yana biyar ne a gidan nan babu mace ko daya sai matar babban. Kazo ka dan gyara jikinka. Suna shiga daga bakin kofa ya tsaya aka bashi buta ya dauraye kafarsa yana ta dage hanci. Kadan ya rage burinsa ya koma gida kawai. Yana ta kallon yadda Dije ke cin abinci da sauri da sauri. Yace don Allah ina da tambaya gwaggo. Ina jinka ta amsa. Wai ita yarinyar nan wace ce ita? Kamar jira take ta bashi labarin duk abinda ta sani game da Dijengala da wahalar da Sabuwa da uwale ke bata. Sosai ya tausaya mata bata da wata damuwa sai ya cikinta. Yayi godiya zai fita Gwaggo tana yiwa Dije waka. Dijengala ta maigari, ba auren talaka ba. Yana bakin kofa suka ji ance sai auren musaki ba, kurma irinta.

Inna Uwale ce ta hau kan wata katuwar bambu ta ruwa da aka kifa daga gidanta. Sabuwa ta riketa ta tsaya don kar  ta fada ta leko ta katangar da ta hada gidanta dana gwaggo. Sulaiman har dan tsorata yayi sai kuma ya tsaya yana jin tijara irinta Uwale. Dije tuni ta tashi daya kan kwanon tuwon ta koma bayan gwaggo ta buya. Zaki shigo gidan ki same ni ne 'yar banzar yarinya, waye bawanki da zai debo ruwan. Gwaggo tace Ke dai Uwale kinji kunya wallahi...idan zaki shekara kina nunawa yarinyar nan tsana bazaki taba canjawa kanki suna a matsayin kakarta ba. Kuma wallahi idan kika sake min leqe da wannan shanyayyar kafar taki sai na tsire miki idanu. Cikin fushi tace ni kike fadawa haka...wallahi zan hadaki da hukuma su shiga tsakaninmu. Makotaka ai ba hauka bane duk kin samin ido inji uwale. Gwaggo tace anji kunya dai ace danki ma hakuri yake da halinki, duk kin bata masa gida da tashin hankali. Kin rabashi da matarsa da yake so kin hada shi da wannan makirar. Shewa uwale tayi kamar ba tsohuwa ba. Ai na isa ne.

Sabuwa ce taji cizon cinnaka a kafa ta saki Uwale ji kake timmm ta fado tana ihu. Gwaggo tace Allah Ya kara kadan ma kika gani.

Shi dai Sulaiman tunda yaji maganganun wanda basu san ma yana kofar soron ba sai tausayin Dijengala mai cin tuwo ya kam[truncated by WhatsApp]
[8/22, 3:16 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°24
Yana isa gida Ammar ya tare shi a bakin kofa...hmmm daddy wari. Umma dake zaune tana yanke farce tace daga ina haka. Itama ta kama hanci kai me ya sami kayanka. Ina zuwa umma bari na gyara jikina.

Bayan yayi wanka doguwar riga yasa ya sauko kasa. Yana zama ya fara yiwa Umma hirar dijengala. Yadda yake bayanin cike da nishadi kamar ba shi aka watsawa kwata ba. Umma tace wai ni Sulaiman kanwar kake so ne ko yayar? Murmushi yayi Umma yar nake so mana. Ita wannan Dijen zanso ki ganta. To ai yadda kake fada kamar babar hanan din ke takura mata. Ba don yar ka fara nema ba ai da sai ince ka nemi Dijen don naga tafi burgeka. Ahh haba umma kurma ce fa. Ta rike baki to sai me Sulaiman? Kurma ba mutum bace? Ni nafi son irin auren nan da zai kasance taimako ga wani.

Tun da Umma tayi masa magana sai kawai hankalinsa ya rabu biyu. Tabbas sau biyu yana tarar da rigima da Dije akan ruwan wanka. Kana ganinta kuma sam babu gyara. Yasan a kalla zata kai shekaru ashirin. Da wannan tunanin ya jira litinin tazo. A office ya sake yiwa modibbo tambayoyi akan Hanan. Wannan karon gaskiya ya gaya masa game da halayyarta. Kuma a yadda babansu ya fada min jiya wai kakar ta zata kaima aikin gini kake yi shiyasa suke son a bawa wani. Mal Yakubu har kunyar ka yake ji saboda yadda take ficewa daga gidan kafin kazo. Hmm wato sun dauka talaka ne shi yake fada a ransa. To idan ba damuwa modibbo ka sanar dashi zanzo gidansa zuwa karshen sati akwai maganar da zamuyi. Modibbo fata ya rinka yi Alh Sulaiman ya nemi auren Dije.

Alh Sani ya kalli dansa Ashir..yanzu da gaske ka fasa auren sakina? Ashir me kake son mayar dani ne. Haj Lami tace kaga duk wancan auren kai kake zaba masa kila shiyasa baya karko wannan karon don Allah kada kayi masa dole. Ai dama da saninki yake wannan wulakancin. Yanzu meye aibun Sakina? Haj tace bazawara ce fa. Ga budurwa ya samu son kowa. Har hotonta nagani. Alh Sani yace shi ma ai bazawarin ne...bazan tilasta masa aurenta ba kada ya bata mana zumunci amma wallahi Ashir idan ka kara sakin mace zan maka ba dadi. Shashasha wanda bai san mutumcin kansa ba. Shi dai Ashir ko tak bai ce ba ya tashi ya tafi gidansa. Me zaiyi da wata Sakina ana zaune kalau. Yadda son Hanan ke ci masa zuciya baya fatan a wuce wata daya bata zama matarsa ba.

Yau Alh Sulaiman da abokinsa ya tafi gidan Mal Yakubu bayan sun yanke shawara shi da Ummansa. Umar yace yanzu Sulaiman har lokon nan ka zo neman aure? Wannan yarinya ta ciri tuta. Yayi dariya sai ma ka ganta mutumina. Ai na iya zabe.

Goruba take ci a kofar gidan Gwaggo ita da kawarta. Kawar ce ta fara hango su Sulaiman tace ke Dijengala kinga wasu yan gayu can. Dije na ganin Sulaiman ta gane shi. Al'Quran shine mutumin dana watsawa kwata. Tashi mu gudu dan sanda ya dauko min. Na shiga uku.

Da gudunta ta tafi zata shiga gida ta kira babanta ya basu hakuri don taga kamar kayan jikin abokinsa na yan sanda ne. Bakaken kaya ne shirt da wando ne. A kokarin gudun ne dan katakon daya raba kwatar gidansu ya rufta da ita ta sake yi masa kwalliya da kwata. Rasa bakin magana yayi don takaici yana tunanin fasa abinda ya kawo shi. Ita kuwa Dijengala ta gama tsurewa don tsoro ta bare baki tana kuka, muryarta a sama.

Batul Mammanđź’–
[8/22, 3:16 PM] ‪+234 812 673 9684‬: FARAR HAIHUWAđź’°26Gwaggo ta dauko tabaryarta tayo hanyar soro. Tana ganinsu tace au Alhaji kaine...kaji shirmen Dijengala ko. Wallahi duk na zata da gaske take. Kallon jikinsa tayi...ba dai yau ma kwatar kuka fada ba? Murmushi yayi yace bata kula bane ta fada ciki.

Daga ciki suka jiyo Dije tana cewa ba dai sun tafi da Gwaggo ba. Na shiga uku me zan fadawa 'ya'yanta. Shigowarsu ta gani ta saki baki na tuba don Allah ku yi hakuri kaga ni bana ma ji sosai kaina bazai yi kudi ba. Gwaggo tace rufa min baki sarkin surutu.dauko musu ruwa a buta. Kema ki je ki gyara jikinki.

Bayan sun kammala gwaggo tace kai kuma kullum kuka hadu da Dije sai tayi maka wanka da kwata. Ba komai Gwaggo dama mahaifinta nake son gani. Bari naje nayi masa magana da kaina to, kasan halin yarinyar nan ina iya turata taki dawowa.

A wulakance su Uwale suka gaisa da gwaggo tace wurin Mal nazo. Sabuwa tace bacci yake yi. Mal yakubu ya fito suka gaisa. Tace dama kayi bako ne shine babu dan aike  nazo yi masa sallama da kai. Uwale tace haka dai aka iya gulma da sa ido. Gwaggo bata kula ba suka fito waje...mal yakubu bakon yana gidana fa. Yace sunansa Alh Sulaiman. Mal yace subhanallah wallahi har kunyarsa nake ji. Ya sanar da ita yadda suka akan maganar Hanan. Gwaggo tace to Allah Ya kyauta muje sai kayi musu bayani.

Umar ne ya gabatarwa mal Yakubu bukatarsu game da Dijengala. Sulaiman yace baba kada kaga kamar ina maka yawo  da hankali. Naga kamar Hanan din tana da wani ne shiyasa. Tamkar an mishi albishir da kujerar makka yace da gaske kake Alhaji? Kai zaka auri Dijengala. Sulaiman yace in har ka amince. Na fara sanar da kai ne don neman izini kafin na turo maka iyayena. Farincikinsa baya misaltuwa yayi godiya sosai. Umar ya bashi dubu ashirin yace baba ga wannan mungode.

Suna tafiya Mal ya dauki kudin ya bawa gwaggo ajiya dama ya saba shawara da ita. Yace yanzu zan sami nutsuwar amsawa wanda yazo neman auren hanan. Dama saboda na riga na amsa tun farko ne. Gwaggo tace ai gara tayi auren saboda Uwale kara bata ta take yi. Haka suka yi ta yan shawarwarinsu sanan ya kira Dije ta fito daga daki suka koma gida.

Ashir ya dage sai shirye shirye yake. Anyiwa gidansa sabon fenti an gyara ko ina. Dama ya kusa gama hada lefen Sakina saboda haka abinda ya rage ba yawa. Ya dai kashe kudi sosai don duk abinda Hanan tace ta zauna. A dan lokacin da suka hadu ya siya mata sabuwar waya ga kudi daya ke kashe mata.

Mal Yakubu ya sanar da uwale zaije gida ya sanar da kawunsa da nata yan uwan za'a zo neman auren Hanan dana Dije. Uwale da Sabuwa sam basu damu ba da jin Dije ta sami miji tunda Mal Yakubu yace wannan abokin ginin nasa ne zai aureta. Shima yana sane yaki fada don gudun kada su toshewa yar tasa hanyar arziki. Ita uwale harda cewa kyan da dama ya gaji ubansa, tunda ita mace ce gara ta auri mai aiki irin na ubanta.

Tunaninsa bai wuce ina ma Munari tana nan. Ina ma zata ga auren yarsu. Babu ranar da baya tuna su ita da Sadi. Amma gashi Inna uwale ta gargade shi ko sau daya yabi hanyar gidan su munari bata yafe masa ba.
Haka yaje kauyensu ya sanar da yan uwansa zancen auren ya dawo a ranar.
Batul Mammanđź’–

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *