Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, November 7, 2017

son gaskiya complete hausa novel

adsense here
{{ SON GASKIYA }} part 1'
SALIM ya paka motarsa ya dubi wani shago ya
shige domin kiishi ya dameshi gashi da saura kan
yakai gida ya fito da roba ahannunsa abin
mamaki yaga wata ajingine amotarsa tana rusa
kuka mai sauti yayi sallama yace....malama lfy...
budurwar ta kalleshi ta durkushe akas tace ...ka
taimakeni don allah rayuwata ta lalace bani da
sauran jin dadi...salim meya faru ......... budurwar
tace...bani da kowa iyayena sun mutu duka ta
hanyar assident amota gashi bansan ina zani ba
kowa ya kini .....salim wane taimako kike so na
miki ......tace ka bani masauki rayuwata na daf
da rushewa kaima karka gujeni......salim gaskiya
zamani ya sauya ana tsoron taimako.... abokinsa
wanda ke saurarensu tunda suka suma tahir
yace...
ka taimaketa bada siffar zalinci allah na kaunar
masu taimako.... ya amince suka sata amotarsu
abaya suna tafe tahir yace..yan mata ya
sunanki...tace suna na MALIKA... ahaka suka
karasa hajiya babar salim da kannansa
AISHA,RAHMA suna zaune salim ya gabatar da
malika agurrinsu sam hajiya tace....salim bazai
yiwuba an daina taimako aduniya kaiya waye wai
karasama wacce zaka taimaka sai yar tsiya
talaka kasan yadda na tsani talaka kowa kamar
.....salim yace don allah ko kwana uku.....hajiya
tace uhm inka kama magiya kamarr maroki na
yadda amma ana ukun kasan yadda zakai da
ita...ta mike ta wuce bedroom rahma tai tsaki
tabi uwarta domin itama bata san talaka ko
kadan...
aisha ce ta kama malika tashi muje kiyi wanka
ko! malika ta bita ciiki salim ya kuura mata ido
yana mai tausayiinta FROM "musa hussaiini
aliyu" BAYAN KWANA UKU duk suna zaune afalo
malika tayi ado domin shadda aisha ta bata
sabuwa tasha aiki tasaka salim yana kallanta
anan ya tabbatar cewa malika kyakkyawace ta
gaban kwatance gata fara ga gashi yaya akai
kyakkyawa kamar malika ta samu kanta arashin
galihu?hajiya tace kai me kake kallo kana jina?
ya juyo yana jin kunya yace ba komai....hajiya
tace yaune wa'adin dana bawa wannan MARAR
ASALI ya cika ka fitar min da ita....salim yace
don allah hajja akara mata kwanaki ya zamo sati
in sadata da danginta ko yan uwanta wlh ba'inda
ta sani........ hajiya tace kasan bana taimako naki
mai taimakon talaka domin su illah ne ga
rayuwarmu mu attajirai dan me kai taimako
alhalin kasan bazan yadda ba..........
aisha tace hajja atausaya mata muji matsalarta
domin taimako na irin wannan akwai lada mace
ce kuma budurwa ina zata inta fada hannu maras
kyau ba.....rahama ta harareta tace to uwar
mumunai hajja kar abatta domin tsintacciyar
mage bata mage.....malikawacce ke zubda
hawaye na jinsu tace salim na gode kada ka
sabawa iyayenka bin umarninsu na da kyau haka
allah ya kaddara min rayuwa mai cike da azaba
da kunci na gode....ta mike......salimya mike
adimauce yace ina zaki?.....malika tace zan tafi
har allah ya hadani da kamar ku su taimaken
koda kwana daya ne..... {{ SALIM yasha gaban
malika yace....ba'indazaki harsai na nemo miki
danginki ko asalinki...yazu gun hajja ya durkusa
yace..kii ceci ne in muka barta ina zata kuma
lada ya wuce mu don allah ataimaka mata danni
ta zauna...hajja tace kai salim in zauna da ita ta
mureni bazan mureta ba ina tana FAKIRIYA...
aisha tace hajja ki kafa mata komai kike so tayi
miki muddin zata zauna na lokaciin tafiyarta....ha
jja tace na yadda ta zauna amma duk wani aiki
na gidannan itace zatai irin shara,wanki,girki,kai
komai kuma awata bazamu biya kiba tunda mun
baki ci da sha da mazauni....malika ta taku ta
tsugunna agabanta tana hawaye tace na amince
kuma godiya agareki..hajja ta wuce afusace
tabarsu rahma ta bita tana mai bakin cikin ajje
miskiniya agidansu BAYAN SATI malika ta lalace
ta rame ta kanjame saboda azabar wahalar aikin
da gayya rahma da hajiya suke kakalo aiiki mai
wuya kuma dole tayi gashi kaf aikin gidan ita keyi
bamai tausayinta agidan sai salim da aisha shi
yasa take kaunarsu rahama da hajja kamar su
kasheta don tsana summa hanata rabarsu wai
karta guga musu talauci tayi kuka inta tuna
rayuwarta ta baya kamar ranta zai fice wai yau
itace ake gudu....BAYAN KWANA UKU malika ta
tsugunna tace ina kwana...hajja lfy daban kwana
kya ganni maza gacen guga afalo kije kiyi ki
tabbatar kiin gama kaf....
tana guga cikinta na ciwo yunwa na damunta
salim ya shigo yace malika waya saki guga da
safe haka...malika ta hajja ce...salim yace kinma
karya kuwa...malika tace a'a ..salim yace tashi
muje ki karya.........malika tace bari...ya daka
mata tsawa yace bana san musu malika!!! ta
mike atsorace tai kittchen DA DADDARE aisha na
zaune afalo malika ta zauna akasanta tace sannu
anti...ta dubeta tana kan kushin mai laushi tana
karatu tace yauwa malika ya aiki?.. malika tace
da sauki anti meyasa hajja na kawu kayanta da
anti rahma wanki da guga amma baki taba
kawumin ba....aisha ta tausaya mata ga hakuri
ga biyayya domin daga gani ta girmeta sai dai sa
ar yayart rahma tace haba malika ai wahalar
karta illataki gashi kona magani ba'a baki aikin
da kike ku ma aikata uku yayi musu wuya kema
ina miki addu ar fita daga rayuwar nan.... rahama
ce ta tawu da kayan wanki ta watsa mata aka
tace...
tashi adarannan nake so ki wanke su tas!! kuma
wallahi su fita tas!!!........ tace haba rahama ta
gaji kuma dare ki tausaya mata da safe sai ta
miki...rahama tace tausayi wace kalma ce tausayi
bansan taba na fada miki aisha ba ruwanki kuma
wallahi sai tayi shi...hajja ta shigo falon tace
meke faruwa...rahamatace waidan nace
TSITACCIYAR nan taimin wanki yanzu shine take
min wa.azi in bari sai safe..hajja tace kanwar
uwarki ce ban hanaki shigemata ba wata ran ta
illataki ta gudu tunda mara tusheta wlh dake da
salim sai na dauki mummunan mataki akanku
akan wannan mai siffar mayyar ke!!tashi ki kuma
ayau aha!!...malika ta kwashe kayan tana
hawaye..rahama tace dubeta duk yadda akai
mayya cema...ta wuce toilet tana wanki tana
kuka tana tsanar wannan rayuwartata inama
mutuwa ta dauketa da tafi kowa jin dadi domin
ta gaji da duniyar...................
BAYAN KWANA UKU malika tana tsaye agarden
tana ba furanni ruwa salim na bayanta ya zuba
mata ido yana murmushi samunta agun nan take
ransa yai baki daya tuna azabar da ake mata dan
bashi da ikon hanawa ne malika ta karasu ta
gaidashi ya amsa yace malika gobe ki shirya
zamu je SAHAD STORE domin na lura kayanki
babu sai biyu kawai kike wanki daura ko...malika
kanta akas domin bata taba yin ido 4 dashi ba
tana jin kunyarsa tace haka ne na gode..salim
yace malika ya kamata ki sanar dani labarin
rayuwarki har yanzu bamusan ko ke wace ce ba
kinga iinna sani tabbas zanyi kokari in sadaki da
danginki ko yan uwanki...hawayemai zafi ya
zubowa malika tace haka ne tabbas labarina
babu dadi bani da kowa sai allah sai kai jigon
taimakona inna tunama hankalina tashi yake yi
kayi hakuri inada ciwon zuciya tabbas tuna
rayuwata dai dai yake da bugun zuciyata amma
insha allahu kanna rabu daku zaka san kuni wace
ce kuma kai addu ar allah ya kare dukkan
musulmi daga shigen rayuwata..
kuka ya kwace mata tai gaba bata saurari amsar
saba salim ya kama tunani wace irin rayuwa ta
gani?da gaske tana da ciwon zuciya? ya kasa
baiwa kansa amsa WASHE GARI su hajja da
yayanta na zaune afalo salim ya fito yana kiran
malika,malika ta fito da sauri tai wanka ta maida
shaddarta da aisha ta bata batai kwalliya
bakasancewar bata da komai na kwalliyar...hajja
tace ina zaku?..salim yace sahad store zamu je in
siyo mata kaya bata kaya...hajja tace yanzu da
wannan zaka tafi dubeka wato itace yar uwa
kamata siyayya banda su rahma..salim haba
hajja itace abar tausayi suna da kaya...hajja ta
mike tace wallahi inkaga kafita tare da shegiyar
nan to dasu rahma... MALIKA ta durkusa akas!
gabansa tace don allah kabi umarnin hajja don
allah ka dena bambamtamu koda zaka bambamta
ka wareni domin sune jininka ni kuma
bakuwa...cikin takaici salim yace to su
tawu...hajja ta harareshi tace ku tashi ku shirya
atafi daku abu naku..sai dasu rahama suka shirya
muka tafi muna zuwa sahad store na zama yar
kauye kaya iri iri salim ya bada umarni
kowaccenmu ta jida iya san ranta nan fa rahama
ta kama kwasa ni kuwa salim da kansa yake
debumin kayana kala 15 da takalmi,jaka,gy
ale,hijjab,kayan kwalliya,man gashi, turaruka
tamkar kayan lefe nayi mamaki irin kashe kudin
da yayi akaina dasu rahama haka muka tawu
amota rahama na hararata domin bata so aka
siyan komai ba muna kumawa na wuce dakina na
kwanta ina jin dadi rabona da farin ciki irin na yau
tun iyayena na da rai...........
a haka naci gaba da zaman hakuri BAYAN SATI
ina zaune nai shiru naji salim na kirana na tashi
tsam na same su afalo salim ne ya mana anko
dani dasu rahama harshi shadda puple taji aiki
conko gata galila yar dubai da takalmi,jaka,
gyale,duk puple sai da yaba su rahama sannan ya
mikomin nai godiya salim yace inaso gobe kuyi
kwalliya da ankonnan tahir ya dawo daga makkah
zamu je yi masa sannu da zuwa...suka amsa
amma hajja ranta abace bata so ya musu anko
tare da mara asali ba rahama kowa haushi ya
cikata asanyaye malika ta dau kayanta tai daki
tana tunanin wai meta tsare ne aduniya...salim
ma ya gano hakan amma sai ya basar ya wuce
dakinsa WASHE GARI aisha da rahama sunsa
ankonsu sunyi masifar kyau komai puple salim ya
shigo falon harta hula,takalminsa,agogo,duk puple
yayi masifar kyau domin dama shi
kyakkyawane..salim yace ina malika..aisha tace
inaga tana ciki..ya zauna akushin jiranta ahankali
malika ta fito take taku tamkar wahainiya komai
puple tai gwagwaro da dankwalinta ta zubo
gashinta har bayatamkar yar gwamna farinta ya
fito sosai rahama kamewa tai tana mamakin
kyanta tabbas alokacin ta gane tai gomanta
domin tamkar tocilance da wutar nepa takaici ya
kamata dama akwai wata wacce tafita kyau da
iya sa kaya da kwalliya waima abin takaicin yar
aikinsu cetana fama da wahala ya akai tasan
sirrin iya haduwa tabbas bazata iya binsu ba
wazai kalleta ga sarauniyar kyau agun..aisha kam
mamaki yakamata dama malika wayayyiya ce
wahala ce ta dakushe kyanta tabbas ta fimu
komai...salim kowa kura mata ido yayi ya kama
addu ar allah ya bashi koda bata kai rabin malika
ba...
malika ta karasu tana kamshi tamkar amarya.

{{SON GASKIYA}} Part 2
Har sai da malika tace yaya na gama...sannan
salim ya dawo hayyacinsa akunyace yace to
muje..da sauri rahama tace yaya cikina namin
ciwo bazan iya zuwa ba..salim bai damu ba
domin baisan zuwa da ita dama tunda ta tsani
malika aisha ma ta gane tai shiru kawai yayi waje
suka bishi malika da aisha..rahama na tsaye har
ta tabbatar sun tafi ta kuma cikin dakinsu da
sauri ta cillar da jakar hannunta tabbas malika
muddin zana zauna da ita sai ta kashe mata farin
jininta agun samari sun kuma kanta da tasan
haka ne tun farko da tayi tuggun kurarta gashi lkc
ya kure wata zuciyar tace dan bata kwalliya
shiyasa kyanta ya boya..hajja ta shigo tace
rahma ya kika dawo lfy..hawayen takaici ya
zubowa rahma da kunya tace malika ta gani ta
kureta afagen kyau da tsari da kwalliya alhalin
mara galihu ce amma ta bata kunya ita da take
birni sai tace haba hajja fisabilillahi ya dace yaya
ya maida malika tamkar yar gida tana mara asali
ya mata kaya iri iri kuma komai zai mana tare
tana mai mana aiki wai anko anguwama hadda
ita shiyasa na fasa wlh amkonnanma bada nawa
zanyi...
hajja tace abin na bani haushi me yake nufida ita
barni dasu wlh anko ya dena mata daku...rahama
ta kwanta amma ranta nasan gidan tahir dole ce
malika ke mata cikas..... G.R.A sun sauka
khaleesat matarsa ta amshesu afalo suka zauna
tahir ya fito suka suma gaisawa yace malika kin
waye ko..tai murmushi tahir ya kama salim sukai
dakinsa suka zauna yace salim haka malika ta
goge allah sarki maraici bani labarinta..salim
yace bata bani komai ba game da rayuwarta...tah
ir yace haba ka zauna da ita bata baka labari
baai kayi shirme...khaleesat tace to ko tawu muje
ko..aisha da malika suka bita cen katan dannie
table mai cin mutum goma abinci iri iri akaisuka
zauna..khaleesat ta shigo tacegwauro tasu na
hada muku dinnie....salimyace ok nine gwauro
zaki ga matata nan kusa...khaleesat tace karyar
banza ai mugani...tahir yace gara kimai ko yayi
zuciya yayi aure tashi muje muci abinci....
malika tai tagumi aisha tace malika dama ke
kyakkyawace haka abani sirrin abun meye na
tagumi salan ki bata kwalliyarki...malika tace
hankalina ya tashi gobe zan bar gidanku........
..aisha afirgice tace wace magana kike haka
ba'inda zaki...alokacinsalim da tahir suka iso
suka ja kujerasalim yace meya faru...aisha tace
wai so take ta tafi gobe...gaban salim ya fadi
tahir yace ba'inda zaki je har sai kin sanar mana
dake wace? ..aisha tace kada ki musamana ki
bamu labarin rayuwarki domin anan muke da
dama..hawaye ya zubowa malika. {{SON
GASKIYA}} Part 6 *musa hussaini aliyu dan
malam* MALIKA ta kama kuka kamar ranta zai
aisha ta da fata tace idan har mun bata miki
akan wannan maganar kiya femu..salim ya rasa
meke masa dadi aduniya yayi shiru.........malika
ta dubi aisha tace ba'abunda kukamin zan baku
labarin rayuwata domin zamana daku yazo badan
bana kaunarku ba har abada kuna raina rayuwata
na tuna da iyayena .................DA FARKO
SUNANA malika mahaifina ni kadai ya haifa don
haka iyayena keji dani sunan mamata sadiya
nake ce mata momi abbana alhaji abdallah
gaidam babana manager ne abankin FIRT BANK
yana da company akallah sunkai biyar bashi da
kowa sai kaninsa bukar mai yaya biyar duk mata
da kubura matarsa bukar da babanmu ubansu
daya na taso agata gaba da baya masu aikina
kula dani hudu duk inda zani su suke kaini daya
driver na biyu bodyguard daya dan aikena ko
kuda iyayena basasu ya sauka akaina bayan na
gama secondary ne abbana ya nema min
admission a A.B.u zaria bayan saukata ta al qurni
abbana ya kaini haddasu bodyguard masu
tsarona abbana ya hana kowa ne saurayi kulani
sainayi karatu don haka ku soyayya ban taba
yiba na taso da iya kwalliya ga ilimi dandanan na
tara masoya a b u amma bana kulasu..
tsakanin bukar da abbana basa jituwa
kasancewar allah ya azurta abbana muna abuja
suna kaduna saii ya tsani abbana duk alherin da
yake mai abanza sau tari innaje yayi ta zagina
wai an batani da gata yayansama kallona basayi
hakama uwarsu harmun jaye jikinmu dasu....ina
makaranta na dauki wayata galaxy na kara nace
momi ina kwana..momi tace yar auta ya zaria da
fatan zaki maida hankali ga karatu....cikin
shagwaba nace eh amma ga exam ta tawu
rabona da ganinku two month kenan..momi tace
yar auta toya kike so..malika niidai so nake ki
lallabi on sunday sai ya kawuki ki
gammu........momi kinsan halin abbanki inya
yadda nima na damu inganki....da daddare momi
ta fadawa abbanmu ba musu ya amince aka
sanarmin suna hanya ran lahadi ina jira shiru
shiru inna buga lambarsu akashe har yamma
motar bodyguard na gani yazo yacemin in tawu
muje nace lfy yace eh hankalina atashe na hau
motar nasan ba lfy.... gudu yake cikin dakiku
kadan na gammu akano naga ya wuce babban
asibitin malam aminu kano hospital ya paka
hankalina baya jikina na fito na zagayo naci
kwalar rigarsa nace me kake nufi dani?
daka daukoni azaria ka kawuni kano akanan ba
hospital..yace ranki ya dade wlh umarni akabani
muje ciki...na bishi ina tunanin meke faruwa
muka hau sama daki 16 muka shiga da da bukar
na fara tozali sannan abbana agado ranga ranga
jikinsaduk bandeji akafa da hannu karaya uku
kamar gawa motsi bayayi na kwallah kara jakar
hannuna nai jifa da ita na rungume abbana ina
kuka nace abba meya faru wayyo ni..bodyguard
dina naji yace akan hanyarsu ta kawu miki ziyara
school a.b.u babbar mota ta dannesu..hankalina
ya dimauce na manta da tambayar momina na
duru kasan gado ina kuka nace abbana kuya
feeni na shiga uku dana sani dabance kozu ba..da
kyar naji abba yace bake bace farin cikina allah
yayi tanan ne hanyar mutuwarmu malika kin
zama marainiya ki iya maraicinki ki yadda da
kaddara da hakuri karki sake ko bayan raina ki
dena neman ilimi domin shine ilimi na zaman
rayuwa kai kuma bukar ka rike malika amana
domin kai zaka zama madadina ka bata jin dadi
da abunda take so domin na tara dukiya da har
jikokinta sai sun barsu dukiyata ka rike mata
amana intai aure ka bata kayadda..ya tsaya yana
tari bukar yace insha allahu zan riketa amana..ina
kuka nace abba ka dena ce mini marainiya sai
naga kamar mutuwa zakai...abbana yace kinma
zama marainiya sai dai kiyi hakuri domin momin
da mota tabi ta kammu ko motsawa batai ba ta
zama gawa maza tashi akaiki ki mata addu a kan
'a kaita ki rungumi kaddara..na sake ihu bansan
lkc dana gwara kaina ajikin karfen gadon abbana
GAB!!!
kaina ya fashe jini ya wankemin fuska ban daba
na mike ina ihu na fika bodyguard shiya bini ya
budamin mota na fada ya jani kankace me na
gammu akaduna gidan bukar domin lkc da aka
samu assident azaria sai akakai gawar kaduna
domin yafi kusa amaimakwan abuja gidanmuwani
gida jar kasa aragaje anan motarmu ta paka nai
arba da mutane maza damkam akofar
gidan.............
ASIBITI muna fita bukar yaje yasawa kofa key ya
dauki Pillow yazo kan abbana yace wlh yau zaka
bakunci lahira kamar yadda na dade ina jiran
zuwan arziki be zuba wannan ce damata ta
karshe in kasheka..ya durawa abbana pillow tun
yana shure shure har ya zama gawa ya ajje
pillow agefe ya kurma ihun muna furci da kuka ya
nufi gun doctor domin sanar mai..

{{SON GASKIYA}} Part 3
DDa gudu na shiga wani daki ruguggujajje anan
nai arba gawar momina akwance an gama mata
sitira na tsugunna akanta na yaye likkafanin
fuskarta dangana da hakuri suka zumin alkc
hawaye na zubomin na kama mata addu'a ina
kuka shigowar matar bukar kubura naji tana
cewa..jama a wata sabuwa ana wata ga wata
yanzu aka turu allah yama alhaji rasuwa..jinai
gabana ya fadi zumbur na mike jinai jiri ido na ya
rufe nai wata irin kara na sulale kasa sumammiya
sai asibitin albasar dake kaduna aka kaini..
sai da aka kawu abbana aka suturta sannan
akaje akabinnesu agu daya..ni kuwa da kyar aka
samu lafiyata ciwan zuciya watana guda aka
sallamemu haidar ne dan bukar kemin komai
domin shine mai sona amma ba wanda yazu ko
dubiya ranar da aka sallameni ranar bukar ya
bada umarni muka kuma gidanmu dake abuja
basu tafi da komai ba afalo muka sauka bayan
mun huta bukar ya tara bodyguard da yan aikin
gidanmu su 25 ya musu kurar kare muna kuka
bakin ciki rabuwa domin mun saba kuma yace
sangartacciya wacce batasan wahala daga yau
zaki san kin shigo duniya makaranta domin komai
na gidannan ya dawo kanki..nai dakina ina kuka
na dauko hotanmu mu uku da abba da momi na
kallah ina kuka azuciyata ina cewa wayyo ni
malika rayuwata ta gama yawu mutuwa ta
sauyamin rayuwata..ya zamana nice mai yin
komai tunban iya girki da wanki ba na iya nai
sabo da wahala na rame na kude na kare duk
wankinsu ni keyi kai har shara mai makwan su
samu yar aiki don su ganamin azaba nima na
mutu suke min haka..
ina zaune na tuna da wasiyyar abbana na cewar
in nemi ilimi na samu bukar da maganar yace ina
na gama har abada aure zaimin..ba ai sati biyu
ba ya fitar da yayansa mata uku hajara,humairat
,hauwa,duk adukiyata ni kuma ya hadamu afalo
da sani yayan haidar bukar ya bukaci babban
dansa ya aureni sani yace allah ya tsare wlh nafi
karfin wannan yarinyar ni india zaka fitar dani in
nemo mata..haidar na yace ni inasan malika tun
tana yarinya ya dubeni wacce ke hawaye kina
sona na kasa magana sai hawaye waini ake
tallah nema min miji duniya kenan..bukar yace
zanje inyi shawara inkai ka dace ka aureta sani
kaine mijin..sani yace akai kasuwa..suna dakinsu
bukar yace aganinki waya dace ya ,auri
malika..kubura tace malam muddin muka aurawa
haidar malika wata ran sai ya dauremu ya maida
mata dukiyarta hannunta amma idan ta auri sani
tabbas harta mutu baza taga haka ba domin
shima yana yana da kwadayi dukiya amma haidar
mu gujeshi yana da tausayi........
bukar yace toya zamu yi domin bana so
dukiyarnan ta bammu..kubura tace idan ka sake
ka bari ta auri haidar to wlh kamar jin dadinnan
ya tafi amma in sani ne me irin halinmune..bukar
to ai sani baya santa.....kubura ko dan dako ne
abatasshi.....bukar yace na samu mafita zan
kasheta adarannan kamar yadda na kashe ubanta
a asibiti na samai pillow ya margaya..kuburatace
dama yafi asirinmu alullube muddin tana raye
itama fargaba ce agaremu amma inta mutu komai
namu..ina labe ta window ina jinsu hawaye ya
zubomin ashe shiya kashe abbana tabbas bani da
sauran makiyi kamarsa ya zama dole in tsira
daga sharrinsa adaran na hada kayana ajaka mai
gadi na bacci na fice gidan kawata mai sona
atika na shiga ina kuka na bata labari tace ina
zaki nace zan shiga duniya amma ga takadduna
sune shaidata sune arzikina ki ajjen abbana ya
nunamin takaddun filayensa da gidaje dana
company dana bankuna sama da dari uku tun
kafin ya mutu nasan gun ajiyarsu yana bayan
mutuwarsa na canza musu guri anan na bata
amanar takaddun munyi bankwana inda raban
saduwa..na bazama atiti nake kwana ina bara in
samu na abinci harna iso kano anan ne wata
mata ta daukeni yar aiki watana uku wata ran da
daddare aka mata sata ta kalamin sharri ta kureni
yan iska suka bini ina gudu anan na zubar da
kayana duk da kyar na boya awani kango da safe
ina bara na hadu dakai da tahir kuka
taimakam.................
nan malika ta tsaya tana hawaye suma su salim
sai hawaye suke aisha kam sosai take sun kasa
magana sai tausayinta suke... bukar yace toya
zamu yi domin bana so dukiyarnan ta
bammu..kubura tace idan ka sake ka bari ta auri
haidar to wlh kamar jin dadinnan ya tafi amma in
sani ne me irin halinmune..bukar to ai sani baya
santa.....kubura ko dan dako ne abatasshi.....b
ukar yace na samu mafita zan kasheta adarannan
kamar yadda na kashe ubanta a asibiti na samai
pillow ya margaya..kuburatace dama yafi
asirinmu alullube muddin tana raye itama fargaba
ce agaremu amma inta mutu komai namu..ina
labe ta window ina jinsu hawaye ya zubomin
ashe shiya kashe abbana tabbas bani da sauran
makiyi kamarsa ya zama dole in tsira daga
sharrinsa adaran na hada kayana ajaka mai gadi
na bacci na fice gidan kawata mai sona atika na
shiga ina kuka na bata labari tace ina zaki nace
zan shiga duniya amma ga takadduna sune
shaidata sune arzikina ki ajjen abbana ya
nunamin takaddun filayensa da gidaje dana
company dana bankuna sama da dari uku tun
kafin ya mutu nasan gun ajiyarsu yana bayan
mutuwarsa na canza musu guri anan na bata
amanar takaddun munyi bankwana inda raban
saduwa..na bazama atiti nake kwana ina bara in
samu na abinci harna iso kano anan ne wata
mata ta daukeni yar aiki watana uku wata ran da
daddare aka mata sata ta kalamin sharri ta kureni
yan iska suka bini ina gudu anan na zubar da
kayana duk da kyar na boya awani kango da safe
ina bara na hadu dakai da tahir kuka taimakam .
nan malika ta tsaya tana hawaye suma su salim
sai hawaye suke aisha kam sosai take sun kasa
magana sai tausayinta suke..KHALEESAT ce tai
karfin hali tace lallai kinga duniya wai jininka
ubanka da san ganin bayanka..aisha tace duniya
ina ribar cin dukiyar maraya..salim yace ba'inda
zaki je kina taare damu duk wuya duk rintsi zamu
taimakeki..malika tace a'a ina neman haddasa
fitina agidanku kuma ba'asan ganin motsi agidan
tabbas gara nai gaba kuna dace..tahir yace
malika kina tare damu har abada zamu
taimakeki..ya kamu salim yace zo muje
kaji..abincin da babu wanda yaci duk kawar da
akamai..suna dakinsa abakin gado tahir ya
dubeshi yace salim dole ka taimaki malika? salim
wane taimako kake tunani...tahir da zaka taimaka
ka aureta ina ganin wahalarta ta kare nasan zata
samu duk abinda ta rasa kuma ka maye mata
gurbin iyayenta..salimyace tahir tun ranar dana
fara tozali da malika zuciya ta kamu da tsananin
kaunarta ayanzu haka ba wacce nakewa SON
GASKIYA sai ita amma kunyarta ta hanani
furtawa gani nake kamar bazata yadda ba tabbas
hajja ma bazata amince ba...
tahir wannan mai saukine ka nemi yaddar malika
kawai sannan kaje kai tunanin yadda zaka
bulluwa hajja....anan suka fito sai dare su salim
suka kuma nan yaja aisha dakina cikin sirri yace
aisha wlh na dade da kamuwa dasan malika ina
shakkar fadamata hakama hajja kina gani zasu
amince..aisha tace amma naji dadi malika zata
amince sai dai matsalar hajja bazata yadda ba
amma ka tuntubi malika inta amince kawai kuje
gun kawu ka sanar mai domin shine mutum na
farko da hajja kejin tsoro..salim yace a'a idan nai
haka hajja zata ce na munafunceta na gujeta zan
nemi izininta ko..aisha tace to allah yasa
adace..washe gari malika na girki akicin tana
yanka doya salim ya shigo yana mata labarai tayi
mamakinsa domin in banda magana kawai baya
mata wannan wasan ko dariya daga cen yace
malika kinsan na dade da kamuwa da azabebben
ciwon sanki da kaunarki wlh inkin amince zan
aureki..gabantaya fadi akaro na farko data fara
ido 4 dashi..
agigice salim yace ko bakya sona ne sanar
dani..hawaye ya zubowa malika tace inna ce
bana kaunarka na yaudari kaina tabbas kana
raina bisa SON GASKIYA ba algus aciki amma
hajja bata kaunarta na rasa ganu lefina in gyara
ahaka kake tunanin auranmu dakai zai yiwu dani
talaka,mara asali,yar aiki don allah kada ka tuna
kowa yaji....salim yace wlh in kina sona zanyi duk
yadda zanyi in aureki. WASHE GARI bayan anyi
breakfast naji salim na kwalamin kira afalo ina
shigowa falon naga hajja,rahama,sa lim suna
zaune akushin gabana ya fadi na daure na zauna
akas! hajja tace me nene muna zamammu ka
kirata..salim yace hajja wlh ina san malika da
kaunarta don allah inkin amince...hajja ta tareshi
kanya karasa ta mike zumbur rahama ma ta mike
zumbur ransu abace aisha ma da salim tashi
tsaye sukai nice kawai adurkushe gabana na
bugawa..hajja tace kana da hankali dan iska
wawa shin asiri tama ko meye tun wuri ka fara
goge wannan mummunan sannaka domin bazata
sabuba wankan kuturu da sabulu..rahama tace
haba yaya duk matan duniyarnan sai wannan
sarauniyar munin wlh bazamu hada asali da
wannan ba duk yadda akai asiri tama ta
mallakeka..
TASS!!salim ya mari rahama da karfi yace sa
ankine ni mara kunya me bakin hali ina
ruwanki.....TASS!!hajja ce ta mari salim tace
karya kake ka mari yata akan wannan shegiyar
kuma wlh kaja mata maza tabarmin gida..salim
yana hawayen bakin ciki yace malika tashi! tashi
mubar musu gidansu nabar gidan..hajja tace ita
dai ta bari amma kai inka barshi saina tsitstsine
maka albarka..salim ya wuce afusace malika ta
bishi tana kuka..ran aisha beso ba ta kasa ma
magana..kai tsaye gidan kawu suka wuce(yayan
hajja ne uwa daya uba daya kuma malamine
aunguwar)a baranda suka sameshi yana karatu
suka zauna bayan gaisawa salim ya kwashe
tarihin malika da abinda ke faruwa ya zayyana
masa tas!
kawu yace allah sarki lallai hajja bata da imani
kamar yarinya bansan lkc da zatai hankali ba in
banda abinta taimakon marayu irinsu malika
akwai lada tana malika kina sanshi wlh kamar
anyi angama zaki ci gaba da zama agidana har
bikinku kin yadda..malika tana hawye tace na
yadda amma haka za'ai biki bani fa da
kowa..kawu yace ba damuwa ce ba nizan maye
miki gurbin uba kuma walinki..anan sukai sallama
salim ya tafi malika ta zauna gun matarsa cikin
jin dadi washe gari kawu yayi sammako yana falo
hajja ta shigo anitse nufin tana tsoron yayannata
ta gaisheshi yace yimin shiru bashi ya kawuni ba
meyasa har yanzu baki da hankali marainiyar
allah ki addabeta wai bata da asali ba yawan
dangi ko yan uwa bane asali mafificin asali shine
ka zamo musulmi kuma musulmi dan uwar
musulmine ke zakiji dadi bayan ranki adinga cewa
yayanki basu da asali..asanyayetace wlh kawu ba
haka nake nufi ba ai gara asan asali ko..kawu
yace sati me zuwa zan aura musu aure

{{SON GASKIYA}} Part 4
Kawu na gama maganar ya fice fit hajja ta rasa
ya zatai hankalinta atashe tai falo aisha,rahama
suna kushin azaune ta tawu kamar zatai bori
tana dukan kirji tace ni!!ni!!!ni!!! kawu zaiwa haka
ya amince ya auri mummuna yarinyarnan mara
asali....rahamata mike tace wlh indai yaya ya
aureta saina takura mata sai tayi dana sanin
auransa..aisha tace kawai hajja tunda kawu ya
yanke hukunci kema ki yadda kawai..hajja tace
ina salim ya gama dani....sati na zuwa ran
asabar aka kawu lefe tamkar na yar sarki akai
kamu da walima washe gari lahadi aka daura
aure inda tahir aminin ango ya kama musu hall a
tropical otel akai dinner party acen malika inka
ganta tabbas sai ka zubda yawu don azabar kyan
da tayi domin salim ya kashe sama da dubu dari
uku agyaran jikinta tai masifar kyau tasha
gwaggwaro da kayan kyalkyali anyi taron biki da
sauran danginsu salim da aisha amma hajja da
rahama ba'inda suka halarta ankai amarya
gidansu bangaranta daban dama ya dade agine
dakinta yayi kyau salim shiya mata komai bazata
manta dashi ba mijinta...
amary a malika ta lullube fuskarta tana kuka
salim yace meye abun kuka alhalin farin cikinmu
ya cika..malika tace ina farin ciki da ganin cikar
burina na samun miji mai yiwa matarsa SON
GASKIYA amma wani sashen zuciyata ina takaici
ace aurena guda ba wani dan uwa tabbas naso
ace iyayena sunga wannan ranar araye da naga
gata wacce ba duk yaba..
salim yace allah sarki,har kinsa zuciyata karaya
addu a zamu musu haka allah yayi ikonsa tashi
muyi sallah ko amarya..BAYAN KWANA UKU
malika tai kwalliyarta tasha shadda ga aiki
babbama sai kamshi take salim ya fito da tasa
dama anko sukai yayi kyau yace yau kwananki
uku amma baki taba zuwa ki gaida hajja
bako..malika tace am mantawa nake ta dauki
gyale ta yafa tace muje..suka fita hajja na falo tai
shiru suka shigo suka tsugunna suka gaisheta
hajja ta mike tsaye tace dakata bana so!! salim
yace don allah hajja me kike so..hajja tace abinda
nake so shine ka saki wannan shegiyar
matartaka..gabansa ya fadi malika ta mike tsaye
tace hajja don allah mena tsare miki arayuwa duk
abinda nasan zanyi domin ki soni nayi ku kinki ko
kinso yanzu kin zama uwata be kamata ki dinga
tsanata ba ki tallafi maraicina ki barni inyi bautar
aure...
ta rushe da kuka aisha tace tazo ta tsugunna
tace hajja bakyau kisa ai saki allah ya halatta
saki amma baya so akeyi. HAJJAH ta shiga
tunani tabbas inta tirsasa salim ya saki malika
bazata taji dadi gurin kawu ba adole cikin fushi
tace ku tashi bana san ganinku nan da nan suka
bar falo rayuwa mai dadi malika ta fara
kasancewar bangaranta daban sai taga dama
aduk sati take zuwa gaida hajja da rahama kowa
abun ya zama gaba ko magana basayi ita kowa
aisha kan zuwa wani lkc susha hira malika cikin
wata biyar ta murje tamkar ada tai fari
kasancewar rayuwar son junansu suke hatta
samu ciki wata biyu murna wajen salim kamar
yayi hauka su kuwa su aisha da rahama sunyi
kwantai domin sun rasa miji kai ko tayi ba'a
musu hakan yasa ran hajja ya baci domin ta fisu
suyi aure tunda sun gama karatu amma ko leke
ba'a taba yiba wai ana kiran wance..kwanci tashi
cikin malika ya tsofa da daddare nakuda ya
kamata salim adimauce ya kaita albarka hospital
kano dama asibitin tahir abokinsa ne tasha wuya
sosai amma wajen asubah ta haifi santalelen jariri
namiji mai kama da salim sak!
misalin goma na safe aka sallamesu suka kuma
gida aisha ke zuwa kullum taiwa jaririn wanka
safe da yamma da sauran aiki na maijego har
kwana hudu amma hajja da rahama ko suje ganin
da suna falo azaune aisha ta shigo ta zauna hajja
tace daga ina..aisha tace bangaran malika naima
baby wanka hajjah kinga da kyakkyawa don allah
hajja me yasa baki je kinga jikanki na farko
ba..hajja tace hmmm inaso inga jikana sosai
amma wannan bana kaunarsa tunda ya fito ta
asali mara tushe ina zanso sa.....rahama tace
allah ya raya ammani dannan bana uwa
dashi..aisha tai shiru gudun kar aduketa...ran
suna yaro yaci sunan babansu salim dama shima
ya mutu tun suna yara sunan kowa mahmud ake
kiransa halifa tahir ya kawu khaleesat da aka da
yamma suka juya..ahaka dai rayuwa ta tafi
amma malika ta ware ta zama katuwa har
shekaru biyu halifa ya girma yana magana an
sashima anursery 1 salim nasan matarsa sosai
cikin ikon allah ta samu wani cikin mai laulayi ya
dinga bata wahala officer dinsu salim aka mishi
transfer zuwa gombe three month zaiyi malika da
halifa suka rakoshi har mota salim yace my one
meye abun bata rai..
malika tace gaskiya gani nake kamar mun rabo
kenan wata uku yamin yawa..salim yace kamar
yaune agun rabbi kedai kimin addu a bisa samun
sa a..nan sukai bankwana yanaiwa halifa
bye..bayan awa uku aka kirata ana sanar da ita
salim yayi assident yana murtala hospital. labarai
MALIKA ta rugu da gudu suna falo ta sanar musu
suka mike suna kuka suna tambayar asibitin tace
murtala kano da sauri hajja da rahama suka fice
amotar hajja rahama ta jasu malika tai tsaye tana
kuka sai aisha tace bari inje in dauko gyalena mu
tafi ina halifa..malika tace nima bari in daukoshi
yayi bacci..ta juya da sauri..tana shiga bedroom
halifa na kwance yana bacci agado taji cikinta ya
murda da ciwo watan cikin biyar dama ta fiya
laulayi tunda ta sameshi ta dafe cikin ta
tsugunna akas!tana kuka batai wasa ba sai ganin
jini tayi na binta kamar ruwa ta tsunduma ihu ta
sulale ko numfashi babu na kirkiri ahaka aisha
tazo ta sameta itama ta kwala ihu ta janyeta sai
albarka hos domin yafi kusa dandanan aka kama
aiki kanta cikin emergency cikin jikinta ne ya
lalace ya zube aka bata gado domin ta zubar da
jini mai yawa ta kude daga nan aisha ta wuce
murtala anan ta tarar salim allah ya masa
rayuwa tunda akai assident din ahanyar gombe
rufe musu akai hajja da "yayanta kuka kamar me
aka kai gawar gida anan aka mata sitira aka
kaita tahir da khaleesat suka zo suka tambay
aisha ina malika tace wlh tana asibiti tai bari bata
samma anyi mutuwar yaya..
tahir yace wane hospital..tace albarka..anan ya
gane cewa sunsan albarka amma basu san
nashine anan yake ba inba marigayi salim nan
sukai sallama yana zuwa ya fara duba daki daki
ana6 ya ganta ta danji dama akwance tahir yace
bansan anan kike ba sai da naje
tambaya..hawayeya zubowa malika tace don
allah ina labarin mijina yana raye ko ya
mutu..tahir yace mutuwa yana nan..tana hawaye
tace ka fadan gaskiya domin mutuwa da kaddara
sun zame min jiki ka sanarmin ni nasan iko allah
yafi gaban komai allah na godema..tahir cikin
tausayi yace karya zan miki yananan ina fata
allah ya baki lfy muje ki dubashi..ya juya bai jira
amsartaba..washe gari akai sadakar uku aisha ce
ta rike halifa tamkar uwarsa da daddare bayan
kowa ya fashesuna falo hajjah tace awane
asabitimalika take..aisha tace albarka..hajja tace
meya sameta..aisha tace cikin jikinta ya bare
bata masan yaya ya mutu ba..hajja tace ke
rahama tashi kije ki sanar mata mijinta ya mutu
itama ta bishi..aisha ta mike zumbur tace a'a
hajja intasan ya mutu zuciyarta zata iya bugawa
ta mutu..hajja tace au bakyaso ta mutu gwana
yayanki ya mutu tabbas na fisu ta bishi wlh
inkika sake kika je sai na tsitstsine miki..rahama
tace kamar na fada ta fica. malika na kwance
taga rahama ta shigo gabanta ya fadi rahama
kanta tace munafuka!!muguwa!!to kisan gurin
zuwa amma ba gidanmu ba domin mijinki ya
mutu..
nan take malika ta kwallah ihu ta sulale acikin
wani hali tamkar matacciya rahama ta juya ta
fice..ahaka tahir ya sameta da kyar mata allurai
ta samu kanta yace what happen kin fara
warkewa kina neman dawo da komai baya..tana
kuka tace ashe mijina ya mutu yau kwana hudu
ban sani ba na shiga uku mai sona ya mutu
tabbas gara in mutu rayuwata gama yawu..tahir
yace waya fadamiki mutuwar..ta kwashe lbr
yadda suka kaya da rahama tahir yayi nazari
tabbas so suke so kasheta yace allah ya masa
rayuwa amma inaso ki yadda da kaddara me kyau
da mara kyau ya mata nasiha ta gamsu bayan
kwana uku ya kaita gidanshi dakinta daban
khaleesat ta rungumeta sosai kamar jininta..acen
kowa halifa inya tada rigima shi mominsa aisha
ce ke rarrashinsa ta kaishi shopping tamai
siyayya na alawoyi itama hajja yanzu tana san
halifa ganin malika batanan dama ita da take
gani shi yasa bata kulashi sunyi masifar kama da
ubansa salim shi yasa hajja ke kaunar halifa tana
ganinsa amadadin danta hatta abinci ita ke bashi
abaki..kwanci tashi malika ta gama takaba wata
uku tai kyau tai fresh saboda ba'abunda bata
samu ba na jin dadi domin tahir attajiri
asibitocinsa biyar babban doctor ne ama nigeria
gaba daya kuma matarsa ta riketa hannu bibbiyu
shekararsu biyar amma allah be taba baiwa
khaleesat ciki ba ko bari..rannan aisha ta fice
cikin sirri taje albarka hospital kai tsaye ofishin
manager na asibitin ta nufa tana shiga tai arba
da tahir ta zare ido tace tahir!
munsan kai babban doctor ne dama anan kake
aiki kaine oga bamu sani ba..ta samu kujera mai
kallansa ta zauna tahir yace wlh aibansan kuna
zuwa ba lfy..aisha tace lfy ya matarka..tahir yace
na nan kalau..aisha tace dama zuwa nai na
dudduba female room banga malika shine na
tawu domin in tambayi manager domin ya
dubamin list sai akai dace kaine waya dauketa
kuma tana ina..tahir yayi shiru cen yace aisha ai
malika ta mutu tun ranar da rahama ta fada
mata mutuwar mijinta.....aisha tana kuka tace na
shiga uku ta mutu tahir a'ina aka binneta..anan
asibitin akai jana'izarta domin kinsan bata da
kowa nina tsaya mata aka kaita kabarinta..aisha
tace allah sarki halifa shi nake tausaywa ya zai
tasu amaraya kamar yadda uwarsa ta taso
amarainiya..ta mike tana kuka ta fice.

{SON GASKIYA}} Part 5*
Rahama zaune agefe tana whatsapp awayarta
aisha na gefe tana ta rusa kuka hajja ta shigo ta
zauna akushin daf da aisha tace be kamata ace
dan mun samu lbr mutuwar malika ki zauna kiyita
kuka tun jiya inaga kukan da kike ko rabinsa baki
yiba akukan mutuwar ubanki...aisha tace haba
kenan ma baki damu ba..hajja tace ban damu ba
dama cen bana kaunarta..aishatana hawaye tace
sai yanzu gane cewa rayuwar asara muke
agidannan tabbas kun zalinci baiwar allah
marigayiya malika zalinci mafi muni ina takaici
dahar ta mutu baku nemi yafiyar taba kuma baku
dena gaba da ita ba domin ita tata ta kare kuma
kuma dole kuje inda taje..TASS!!!
hajja ta mari aisha tace mara kunya ni kike duba
kike fadawa haka wlh in kumaji mu zakiwa wa azi
ko....acen gidan tahir suna zaune afalo sunyi
kwalliya tahir ya fito da ledoji 2 ya raba musu
suna dubawa sarkace daham,murjani,diamond,da
mayuka,turaruka,doguwar riga blackberry,atamfa
bakwai,less da shadda uku uku da takalma suna
murna sukai godiya malika tace doctor na gode
amma abinda kake mana yayi yawa kullum daga
wannan sai wannan..tahir yace ba komai kuci
gaba da addu'a am!jiya aisha tazo nemanki nace
mata kin mutu..malika tace doctor aisha mai
kaunata ce da gaskiya meyasa kace mata na
mutu duk da bansan nufinka na haka ba..tahir
yace haka ne nufina anan kinga su hajja basu da
wani buri da yafi suga ance kin mutu shi yasa nai
haka domin idan sukaji kin mutu zasuyi murna
kina raye har lkc daya dace su ganki yayi zasu yi
mamaki kuma watakil in sunji kin mutu suyi
nadama...malikatace haka ne maganarka gaskiya
kana da tunani na gode...rayuwa mai dadi taci
gaba malika ta rungumi kaddara ta maida alhinin
mutuwar salim tahiri..rannan khaleesat na falo da
tahir ta kwalawa malika kira ta fito taci kwalliy ta
zauna tana gani..
khaleesat tace magana ce dani doctor,malika
kuna jina..tahir yace to matata muna ji..khaleesat
tace na yanke shawarar mijina tahir ya auri
malika domin na yaba da hankalinta da kirkinta
tabbas na amince bisa zuciya daya ka aureta mu
zama mu biyu dama kammu ya hadu...tahir yace
tabbas inasan malika nima bisa SON GASKIYA
domin na yaba da halinta amma sai nabar abin
araina domin gani nake ke matata bazaki yadda
ba..gaban malika ya fadi hawaye ya zubomata
tace in banda abinki kishiya ai dole babu
mahalukiyar da zata so ai mata kishiya na gode
amma bazan iya hada miji dake ba naci amana
kenan.. khaleesat ta kamu hannun malika ta rike
tana hawaye tace tabbas agareni da mijina baki
ci amana ba kuma ke yar uwata ta jini don allah
ki taimaka ki auri mijina domin ni bana haihuwa
bazan haihu ba mahaifa ta zama virus ki haifa
mana yara kyawawa kamarki tabbas ko baki auri
mijina ba sai wata bakuwa ta shigo kuma indai
baki auri mijina ba har abada nabar gidan
doctor..malika na kuka ta rungume khaleesat
suka saka kuka tace na amince tabbas ku yan
halak ne kamar mijina salim da kanwarsa aisha
kunmin halacci kun ceci maraicina...
sati mai zuwa aka daura auren tahir da malika ta
angwance part dinta daban har tai wata bakwai
agidan ta samu ciki wata biyar murna gun tahir
khaleesat kuda basasu ya tabata komai tana
zaune ake mata hatta takalmi ko kaya iri daya
suke sawa saboda shakuwa alkc hankalin malika
ya tashi tana so ta dauko halifa kuma ta ganshi
rabanta dashi tun mutuwar salim yau shekara
daya kenan ta nemi izinin tahir akan suje ya
barsu ita da malika suka shirya suka je afalo
suka samesu halifa ya rugo ya rungume malika
yana dariya itama tana dariya suka zauna su
hajja suka kama mamaki dama bata mutu ba
hajja tace malika dama kina raye..khaleesatcikin
gatse tace ta mutu ne ta dawo domin baku damu
da itaba..hajja tace ke yannan ba'a mutuwa
adawo da salim ya dawo..malika tace haka ne
hajja ban mutu ba sai randa kwana na ya kare
dama nazo tafiya da halifa ne........hajjatace don
allah kada ya dade domin idan ina ganinsa
tamkar salim nake gani kuma bana so ya rayu
agidan gori..malika tai murmushi tace uwarsa ma
agidan gori ta girma don an masa gori ba
damuwa domin dama gadan gidansu ne
gori...khaleesat tace au baku san tana da aure ba
gama ciki tsoho..aisha tace waye
angon..khaleesat tace mijina tahir shine
mijinta...gabansu ya fadi da mamaki hajja tace
shine malika har kiyi aure baki sanar mana
ba..malika tace am!sorry hajja na manta daku lkc
ina cikin dadi ne.....
aisha tace mudai malika inkin haihu ki tuna damu
karki mance..rahama tace wlh ko kuka damu da
ita me zata baku ko me zata muku...khaleesat
tace wata ran sai lbr kare ma da ranarsa balle
mutum ku tashi mu tafi..halifa yace bari in dauko
kayana..malika ta kamushi gyale musu kafi karfin
wannan kayan sai yan leda ko hada ko rike..suka
fice su hajja suka bisu da kallo suna mamakin
malika ta canza kamar baturiya alkc hajja ta fara
nadama abinda tai mata. kwanci tashi malika ta
haihu agida danta namiji kyakkyawa khaleesat da
tahir ba wanda ya kaisu murna anyi suna ansawa
yaro suna SALIM ana ce masa dadi aisha ta
halarci sunan inda ta labartawa hajja irin
makudan kudi da aka kashe..yaro sai da yayi
wayo harya isa yaye sannan ta mallaka khaleesat
dadi duka khaleesat tai murna dama halifa na
wajen su alokacinne tahir ya samu malika da
maganar ya kamata subi bayan bukar zai tsaya
koda kutu ya amsu mata kayanta malika tace a.a
tabarsu da allah tahir yace ina hakkin kine ki
amsa haka suka tafi abuja su biyu ta gane layin
gidansu atika suka biya atika har tai aure da yara
biyar tabbas atika ta cika kawa ta gari domin
takaddun suna nan ta bada har sunyi kura atika
da malika sukai ta kukan yaushe rabo atika tace
wlh idan kika ga bukar sai kinyi kuka ga dukiyarki
taci gaba amma basu da lfy ci ta gagara suna isa
gida kamar yadda ta sanshi ada ya karama kyau
tabbas kana gani kasan arzikin babanta ya ninku
abun mamaki suna isa falo da humairat suka gani
ta kude ta rame sai wari take S kanjamau ta
kwaso ta kalli malika da kyar amma ba bakin
magana haushi suka ji kamar na kare suka shiga
bedroom bukar ne agado tamkar dodo yana
haushi yuwa kare harshensa ya zazzago irin na
kare adaddaure da jikn gado ya zama baki kamar
gawa yi muryar tsohuwa muka ji tana cewa
suwaye tuni tsoro ya kamani nida atika kamar mu
gudu harmun fara hawaye amma tahir ko alamun
tsoro babu agareshi wata tsohuwa ce ta shigo
atakure ayakune fuskarta ta juye tamkar fata
jikinta wani irin kurjine manya manya har fuskata
ashe kubura ce tana kallona ta fashe da kuka ta
tawu zata rungumeni na daka mata tsawa nace
dakata!!
karki sake ki tabani muguwar tsohuwa ga yadda
karshen yayi gashi dukiyar taci gaba amma baku
da lfy amfanarta karshen alewa kasa tabbas
saina saku akundin tarihi na duniya yadda za'a
dinga tunawa da irinku domin ku zama izina ga
masu irin halinku allah ya raba dukkan musulmi
da irinku maza ki bani lbr meya sameku
haka..kubura ta durkushe akas tana kuka tace
bayan tafiyarki hajara da hauwa suka bude gidan
karuwai a algeria anan suka ta lalatarsu bamu
sani ba shugaban kasar yasa aka kamasu aka
harbe su domin haka akewa karuwai akasar da
kyar humairat ta dawo tana fama da kanjamau
sani kowa safarar miyagun kwayoyi da fashi yake
tuntuni bamu sani ba aka kamasu sunje
fashi..Taci gaba da cewa da sukai fashin shine
aka kamasu aka yayyankasu alkc labari ya
samemu nan take bukar ya haukace saboda bakin
ciki ya kama haushi tamkar kare ya dinga cisgar
fatar jikinsa yana ci danye da kyar sai da na tara
jama a aka daureshi kullum kwana yake haushi
baya ci bayasha idansama yanzu ko budewa
bayayi ya manne tabbas bukar gawa ce taki rami
ku rabani dashi kuna huta nima kuma haka kurum
idona daya ya zagwanye da daya nake gani kuma
ku dubi jikina wasu kurajene duk sun baibayemin
jiki malika munci zalinki allah ne ya tseratarki
daga sharrinmu ki yafee mana dukiya ta kice
fatanmu ki yafee tabbas akan san duniya mun
kashe mutane da dama..
ta tsugunna tana kuka tana neman gafara malika
na hawaye tace na yafee muku iya hakkina da
kuka cuceni koda allah da abinda kuka shuka
gashinan na bibiyarku tun aduniya ku kuka jiyo
dominni yanzu naci riba allah na godema..tahir
yace na gode miki matata yanzu ya zamuyi
dasu...atika tace yan hisbah da yan sanda da
malamai su zamu kirawu mu basu lbr sannan su
fita dasu asan yadda za ai dasu haka akai cikin
awa uku aka kira manyan malamai yan sanda
d.p.o su bakwai da yan hisbah sannan aka
labarta musu sunyi mamaki wani malami sheikh
adam mudassir yace ikon allah tabbas babu
abunda yakai azaba irin cin dukiyar maraya ga
dai izina nan ga yan baya allah yasa mu dace aka
debesu aka kai bukar gidan tarihi yana haushi
jama a na zuwa suna kallansa ana tsinemai wasu
na addu ar allah ya kare duk musulmi..humairat
kowa asibiti aka kaita satinta guda ta mutu ita
kowa kubura bara take atiti tana ganin
ishara...malikata sai da gidan miliyan dari saboda
ya fita daga ranta ta sai dan biliyan goma
tamkar gari guda ko karamin kauye ga kyau suka
kuma ciki dasu khaleesat ta tuna da yan aikin
babanta bodygurd ta gayyacesu walimar dawo
war sabuwar rayuwa ta yaushe gamu su talatin
kowa ta bashi aikinyi acompanonynta ta saiwa
atika karamin gida da mota ta sake musu mota
yar biliyan uku uku da tahir da khaleesat da ita...
rayuwar su hajja ina su rahama sunki auruwa da
kyar aisha ta sami mai wankau ta aura gidan
data tarema jar kasa ne wata ran yan fashi suka
hauro suka kwashe duk dukiyar hajja kuma su
kaiwa rahama fyade suka tafi..hajja ta dawo
talaka ga hawan jini,ciwan zuciya kuma ko zama.

{{{SON GASKIYA}}} Part 6
Ta zama gurguwa sai akeke ake turata har wuya
takai sun siyar da gidansu domin maganin hajja
kudin ya kare..rahama ce ke tura hajja akeke
suna bakin titi suna bara malika ta danno
motarsa ice colour ferrari ce motar agefe
khaleesat ce sunyi anko wani paper less iya riga
da karan miski dan india ne sunsha gwagwaro
dadine acinyar khaleesat kawai sai khaleesat taga
hajja da rahama suna bara ta paka motar tace ta
mika musu dubu gomarahama ta amsa tana
godiya..
malika tace hajja kin gane ni kowa nice malika
matar salim danki...da sauri hajja da malika suka
kalleta suka rushe da kuka domin ta canza kamar
baturiya domin ayanzu itace manager na
company goma khaleesat goma na akarkashinta
hakama tahir kuma duk mallakin malika
ne.........hajja ta kama kuka tana tuba tace
malika kiya feemi wlh ga ishararki nan mun
maida talaka mara galihu muma ga karshenmu
ya kare.............
rahama tace malika kiya feeni tabbas na cuceki
cuta ba karama ba ashe zaki iya taimakammu
duk muguntar da muka miki arayuwa tabbas ke
yar kwarai kece mai asali mai inganci mune
shegu na tuba kiyiminduk abinda zaki min ga
kaina ina tuba..malika tace badan ko zan taimake
kuba don allah na biyu kumadon salim mai
minSON GASKIYA ya soni amma allah yayi bamai
nisan kwana bane salim ya taimakeni alkc da
kowa ke tsanata alkc dana zama abar gori
agurinku ba tare daya gujeni ya taimaki maraicina
da SON GASKIYA ya aureni daga bisa ni ya mutu
yabarni tahir amininsa ya dura daga inda ya
tsaya ya shigemin gaba na amsu dukiya na zama
fitacciyar attajira wacce duniya kejidani yaya zan
manta da salim ta hanyarsa na samu komai ya
zama har bayan raina in nuna masa SON
GASKIYA in taimaki yan uwansa domin be
wulakantani ba in zama madadinsa gareku abinda
kukamin don kanku na yafe..
malika ta kwashesu ta siya musu gida me daki
hudu duk wata tana dire musu kayan abinci iri iri
aisha ma taba mijinta aiki ta sai musu gida..
biyayya kamar me haka su hajja sukewa malika
malika ta kara samun ciki ta haifi tagwaye mace
dana miji tasa sunan sa'adatu da abdallah
iyayaenta ake ce musu abba da momi bayan ta
yayesu suka tafi makkah ta biya musu da ita
tahir,khaleesat,atika,aisha, sukai umara da hajji
suka dawo again ta sake haifar yan biyu mata
khaleesat da malika shida kenan yayanta halifa
ya zama saurayi yana england yana degree dadi
mai sunan salim yana BUK yana kwas sunci gaba
da zamansu najin dadi da kaunar juna allah mai
iko yadda yayi da rayuwar hajiya malika kenan...
KARSHE..
ME ZAKU CE GAME DA WANNAN LABARIN? WANI
DARASI KUKA KOYA? WATA SHAWARA ZAKUBA
WANDA YAKE POSTING DIN LABARIN NAN?
MU HADU A WANI SABON LABARIN

Naku akoda yaushe sadeeq(cirobiyu✌🏼)

Whatsapp 09022133165

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *