Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, November 7, 2017

Darajar yayana complete

adsense here
DARAJAR 'YA'YANA1-01
Posted by ANaM Dorayi on 11:41 PM, 08-Mar-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
___________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Cikin sauri sadiya take yin komai dan bata son
mai gidanta ya dawo ya sameta ba yanda idonsa
yake bukata ba.Tuwon (semo) tayi mashi miyar
kubewa danya, sai farfesun kafar sa, sanan ta
tanadifura da nono, tasa a cikin fridge don tana
bukatar yayi sanyi.Ta share ko ina na gidan fes ta
wada tashi da kamshi turare, taje ta fesa wanka
sanan ta bata lokaci a gun kwalliya.Kankwasa
kofar da taji ne ta tuna da 'yan yaranta, da sauri
taje ta bude musu, kai tsaye ban daki tace su
nufa.Wanka ta sake yi musu sanan ta shirya su
cikin sababin kayansu masu kyau ta feshesu da
turaruka.Ta dawo dakinta inda ta rasa wane
kayane ma zata saka, a karshe ta yanke shawarar
saka wani jan material riga da siket.Ta dubi
kitsonta kanana da ta yarfa a madubi, sanan ta
kashe daurin dan kwali. Tasan yau zata burge
mijinta, musanaman da ta kalli lallen hannunta
na fulawa da aka zana mata.Ta kalli agogo karfe
shida da kwata, wayarta wadda ta dauke saboda
rashin chaji, ta jonata chaji.Ashe garin sauri bata
sa dai dai ba, don haka bata samu chajin ba har
aka dauke wuta.
banda haka da taji yanzu mijinta yana dai dai
ina?Kwnkwasa kofar ne ya dawo da ita daga
haushin rashin cajin da wayarta bata da shi, ita
da yaranta suka diba da gudu don taryo
mijinta.Tana bude kofar shine tsaye, sanye cikin
kayan yansanda, daga ka ganshi kasan babban
jami'ine, ta fada jikinshi tare da rumgume shi,
amma me?Sai taga ya sabule tare da cewa sannu
da gida.Cikin mamaki ta amshi ledar hannunsa
tare da jakarshi, ya tsugunna yana sha kan yayan
sa cikin jin dadi da kewa, sadiya ta tsaya cike da
mamakin saboda al'amari da take gani a gurin
me gidan nata.Abin da tasani a duk lokacin da ya
dawo yakan iso ne a marmatse cike da kewarta,
da ya shigo burinsa kawai ya rungumeta tsam a
jikinsa kafin yaran, amma yau sai taga ita ce ta
rumgume shi har yana sabulewa, lallai wanan
sabon al'amarine a gurinta.To ko dai gajiya ce
take damunsa?Kokuma fushi yayi ya gaji da
kiranta bai samu ba?Ta dubi kanta, kokuma
kwaliyarta ce batayi ba?Ta sake wai wayawa ta
kale su inda yake rungumarsu daya bayan
daya.Da kausar ya soma, sanan Al'amen, sai
mama ta tuno yanda yake mata a duk juma'ar
da yazo, ya kamata ya fi dokinta a wanan karon
da ya hada saty biyu bai zoba.Abin duk ya
dameta, tana tsoron kada wata masifa ko annoba
ta ratso cikin kyakkawan zaman nasu, tana tuna
da yadda take makale a gefen damansa sannan
ya dauki mama da hannun hagunsa har cikin
falonsu.Yanxu dai ba zatace ganin yara bane,
domintasan yaransu sun taso sun samesu cikin
wata rayuwa da suka shinfida ta shakuwa da
kaunar juna.Sun saba ganinsu rungume da juna,
sun saba ita da yaran suyi ta kokuwa a jikinshi,
basa yin wani abu da zai kawo matsala ga
tarbiyar yaransu, amma sukan rungumi junako
yin falo da junan ana hira.Sun rigata shiga falo,
ta shigo nan ma ta sake kallonshi, mamaki ganin
ya zauna shi da ke zarcewa dakinsa, can suke
zuwa ya basu tsarabarsu.
Sanan ya basu ta iya ya ce su kai mata, sanan
kada kudawo in na huta zanzo in gaidata, sai mu
dawo tare.Su ce to Abba, su tafi suna
tsallensu.Shi kuwa suna fita wata ran ko wanka
baya yi zai rungumota ya ce Dear my choice a
matse nake.Ya wancin lokacin sai ya samu
natsuwa kafin ya ci abincin ba yan yayi
wanka.Dan Aliyu mutum ne mai matsanan ciyar
bukata.Cikin damuwa ta isa kusa dashi.Yaya Ali
yau kagaji sosai ko?Ya dubeta me kika gani?Ta
ce, baka saba zama cikin falo ba.Ya miko hannu
bani ledar nan in sallami yaran nan.Ya fada ba
tare da ya bata waccen amsar ba.Ta miko masa
kanta daure ta nufi dakinsa da jakarsa, ya ba
yaran tsarabarsu, kayan ciye ciye ne da na wasa,
sanan ya mike ya nufi dakin sa.Kausar tace, abba
yau ina tsarabar iya?Sadiya daga cikin dakinta ta
kaso kunne taji amsar da zai ba da.Ba tare da ya
waiwayo ya dubi kausar ba, yace kinga magariba
ta kusa, bari in anyi sallah sai muje ko?Ya shiga
daidai lokacin ta shiga ban daki dan hada masa
ruwan wanka.Ta fito yana zaune bakin gado yana
kwance igiyar takalminsa ta iso gurin.Da sauri ta
tsugunna tare da cewa abba kausar yau kuma
harda aikina zaka shigar min?Ta ci gaba da
kwance takalmi tana cewa, yau duk na ganka
wani iri daban, ko duk gajiyar ce?Ya ce gajiya
saikace ba jami'in tsaro ba?Ta soma balle masa
maballen riga, to baka jin dadin jikinka ne ko?
Yaja tsaki, dan Allah ki bar ni da tambayoyinnan
naki please, gabanta ya fadi, ta dubeshi da gaske
yake yi fuskarshi daure.Jikinta yayi sanyi, ta gama
balle botiran, ya mike ya nufi ban daki ta mike
zata taimaka mashi kamar yadda ta saba, ya
shiga sai ya banko kofar zata tura sai taji karar
makulli yana kulle kofar.Cike da tsoro taje dakin
tana kallon kanta a madubi, ko dai batayi kyau ba
ne yau?Ta duba ba wata makusa, ta kara jan
baki da turare sanan ta fito ta same shi yana
shafa mai,ta isa gurinshi, ta ciro masa kaftani da
wando na shadda mai ruwan sararin samaniya,
ta ciro hular da zata dace da kayan ta ajeye
masa, amma sai taga ya janyo jallabiya mai
dogon hannu fara sol ya saka.Daga nan sai ta
koma ta jingina da bango dan jiran ganin
sarautar Allah.Ya fita, ta bishi ganin zai fita waje
ta ce, tabban kausar abincin fa?A sanyaye tayi
maganar.Ba tare da ya waiwayo ba ya ce, sallah
zan yi tukunna.Kausar ta ce,Abba ina kayi sallar
ka dawo kaje damu gidan iya, kada kaje daga
can.Ya dubi yaran da murmushi zan zo muje
kunji?Suka ce to Abban mu, bari muyi muma
sallar.Ko da tayi sallar sake zama tayi gaban
madubi tayi sabuwar kwalliya sanan tayi canjin
kaya daga jan yadin zuwa leshin ruwan dorawa
mara nauyi .Ba kamar ko yaushe da yake kashe
waya baina zasu ci abinci wayarshi kunne kuma
jifa jifa yana amsa kira.Guri daya taji dadi ya
zage ya kwashi abinci kamar yanda yake yi ko
yaushe, haka nan
haka nan 'ya'yan shi yana ta surutu da su.Amma
ita ya dauke wuta da lamarinta har ta kasa cin
abincin ma, so take ta tuno kurun laifin da tayi
masa dan kawai ta bashi hakuri.Bata saba da
wanan yanayin da suke ciki ba, zuciyarta ta ce ko
ya ta kiran wayarki ne ba a ji?Da sauri ta dube
shi.Abban kausar nasan kayi ta nema na layi naa
kashe ko?Ya dubeta ban nemi layinki ba, ba wuta
ne ta ce eh ba wuta.Kutashi muje gidan iya,suka
mike cikin murna,Ku ziyarci blog dinmu domin
karanta Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Kausar ta ce,Abba, momi bata dauko hijabinta
ba.Ya ce, bata son zuwa ne, tayi aiki ta
gaji.Wanan ya nuna mata ba a son zuwa da ita
tunda ba a tambayeta ba bare a ce ita ce tace ba
za ta je ba.Sun barta cikin tunani da jimami, ta
gyare gidan musanman gurin da suka ci abinci,
tayi ta jiransu tana zaune a falo tana kalon TV
amma inda zaka tambayeta abinda ake yi a TV
din ba zata fada maka ba.Ita burinta kawai ta
san laifinta, amma ina ta tuna da cewa anjima da
yazo dole zai sauke ko mai dan tasan cewa ba
zasu taba kasancewa gado daya da shi ba ya iya
kauda kai daga gare ta.Itama zata ja aji lokacin
har sai taji dalilinsa, ganin sun kai har sha daya
sai kurum ta cire tayi shirin bacci, kayan baccin
bakake masu matukar daukar hankali, ta dora
hijabi saboda da yara zai shigo.Kausar ce kurun
batayi bacci ba, Al-Amin yana sabe a kafadar
dama, mama a ta hagu, kausar din tana biye
dashi suka shigo.Kai tsaye dakinsu ya nufa da su,
tabi bayan su yana kwantar da su, ya fita ita
kuma ta gyara su, sanan tayi musu adu'a taja
musu kofa.Dai dai lokacin kausar tana cewa
momi sai da safe, sadiya tace, Allah ya kaimu
kausar.Dakinta ta nufa ta sake fesa turare, sanan
tanufi fridge don ta dauki furarshi wadda ta riga
ta dama.Shiru ta tsaya dan ya riga ya dauka, ta
nufi dakin shi.Yana zaune bakin gadonshi sanye
da kayan bacci, laptop ce a gabanshi kan dan
tebirin da ake ajeye mai fura.Kofin yana
hannunshi yana kurbar furar, idonsa sanye cikin
farin gilashi ta ce, tace ashe har ka dauko furar
ka?Ba tare da ya dubeta ba ya ce eh.Ta zauna
kusa da shi wai abban kausar nayi laifi ne da ake
ta share ni?
Ban gane na neke ta share ki ba?Ta ce na gane
yau duk ka canza ko na ce abubuwa sun canza
kamar ba mijina ba maita rairayata?Ya dago ya
dubeta baki min komai ba.Ta dora hannunta a
kan cinyarsa, abba kausar to naganka ne ni yau
irin kamar banyi kyauba din nan.Ya kalleta Dan
Allah ki barni ina yin abu mai muhimmanci ne.Ta
ce, amma dai da aka saurare ni bai fi abin da ka
ke yi muhimmanci ba?Ga mamakinta sai kawai
taji ya daka ma tsawa,kin san me kike fada kuwa
dan Allah tashi ki bani guri a nan,ta zaro ido,
mikewa tayi ta nufi kan gado ta kwanta a ranta
tana cewa ka gama kazo ka same ni ina nan
kwance.Abin ta'ajibi ranar dai haka ya raba dare
yana harkokinshi a internet sabon abu ga Sadiya
mutumin da in yazo satin karshen mako hatta
wayoyin shi kashewa yake suna manne da juna
har sai ya tafi yana cike da kewarsu.Ko da ya
kashe laptop ya kwanta juya mata baya yayi,don
Allah babban kausar me yake faruwa ne?Dan
Allah in wani abu ya faru ne ka sanar dani zan
baka hakuri, ban saba da wanan rayuwar
ba.Cikin zafin rai wanda banta ba ga ni ba ya ce,
nace bakiyi mini komai ba, kina son dole sai nayi
maki karya ne?Dan Allah ki bar ni in huta ki barni
na ce.Ta rike kai to banyi maka laifiba me yasa
ka canza min?Nasanka kai mutun ne mai bukata
a marmatse ka ke zuwa in kayi saty daya, wanan
satyn har saty biyu kayi amma sai naga kazo
bana gabanka.Ya zoro ido to yau ban da bukata
ko dole ne?Ya ja tsaki, tashi dan Allah taf dakinki
bana son jaraba kada ki dameni.Kuka ne ya
subuce mata, ta fita a dakin tunda aka kawota
gidan yau ce rana ta farko da zata kwana a
dakinta ita daya.Dan ko haihuwa tayi basa raba
makwanci, ta fito falo ga mamakinta sai taga
kausar tsaye a falo tayi saurin dai daita fuskarta
tare da share hawayenta ta nufi kausar.Me kika
fito yi?Kausar me kike so?Ta ce, mome naji abba
ne yana fada ne, me kika yi masa?Ta kama
hannun yariyanyar suka nufi dakin yara.Kan
katifarsu ta kwantar da ita ta kuma ta kwanta a
bayanta tare da rungumeta, kausar ta sake
tambayarta momi kinyi laifi ne Abba ya ce ki fita?
kasa magana tayi don al'ajabi ne ke dankare cikin
ranta, ta danne hawayenta ta ce kausar laifi nayi
masa.Kausar ta ce, momi ki bashi hakuri
mana,'to' Sadiya ta ce zan bashi sai da safe in ya
huce kinji?Kausar tace, eh.Sadiya ta ce ki daina
tashi cikin dare kin ji, tadinga shafa kan yarinyar
tana lallashinta hartayi bacci ita kuma ta koma
duniyar tunani tuno farkonsu.Iya mahaifiyar Aliyu
ya ce ga mahaifiyata, uwarsu daya ubansu
daya,su 'yan asalin jahar jigawa ne, a karamar
hukumar Hadeja.Mahaifiyarsu ta rasu ta barsu su
hudu mazabiyu mata biyu, kawu Adamu da kawu
Dauda duk iya ce babbar su.Lokacin da
mahaifiyata ta na budurwa, dan haka iya ta
dauketa lokacin suna zaune a Dutse da mai
gidanta da yaranta hudu.Yaya sulaiman
yayazakari, yaya sani, sai cikin yaya Aliyu.Mijinta
ma'aikacine a ma'aikatar gona ta jahar Jigawa,
daga baya yayi ritaya inda ya dawo kaduna da
zama sana din dan uwansa dake noma.A
unguwar mu'azu ya sai gida madaidaici a ciki aka
haifi Aliyu kuma a nan aka aurar da mahaifiyata
inda ta auri mahaifina wanda yakasance
ma'aikacin gidan Raidio kaduna.Amma dan zariya
ne kuma zariyar aka kaita,yana da mata biyu da
yara kusan goma, ko a lokacin.Maimuna
mahaifiyarta ta kasance mai hakuri da juriya, duk
da cewa bai kasance mutum mai cika hakkokin
iyalansa ba.Amma bata taba kawo kararshi gurin
iya ba,don tasan iya tana da fada sam bata da
wasa.Shekarar da yaya sulaiman yayi aure
shekarar ce mujin iya Allah yayi mai rasuwa,sunji
mutuwar ta farat daya yana cikin sallah yayi
sujjada a masallaci har aka idar bai dago ba.An
dago shi sai gawa, ashe mutuwar kenan.Yaya
sulaiman koyarwa yake yi a makarantar yan mata
dake Tudun wadan wada wato Sai yaya zakari
kasuwanci a babbar kasuwar kaduna, duk da
cewa ba wani babban dan kasuwa bane,Sani
kuma da ya gama secondary sai kurum ya shiga
wurin gyaran motoci dan a lokacin babu halin ci
gaba saboda yanda karatu ya zama a kasarmu sai
yayan masu shi.Talaka yana so yake hakura.Ya
Aliyu karamin su kuma suna tallafa mashi don
ganin ya samu karatunshi, kwanci tashi suma duk
suka yiyyi auransu.Lokacin da mahaifiyata tana
dauke da da tsohon cikina don ta jima bata haihu
ba, har lokacin iya bata gane yar uwarta tana
cikin matsala ba, sai bayan ta haife ni.Lokacin da
taga komai babu, abin ci a gidan gashi ya sake
yin aure ya ciko mace ta hudu,iya ta same shi ta
ce, yanzu tsakanika da Allah Abubakar hakan da
kake yi dai dai ne?A ce ka ajiye mata babu
kulawa ba abinci badai baka da shi ba sai don
zalunci?Ya ce ai za a siyo.Tace, gara ma ka siyo
don ba zan dauki zama da yunwa ba, in an ganka
a waje kwas kwas har da mshin din hawa gareka
amma a gidanka da yunwa.A daddafe akayi suna
inda aka rangada min Halimatu Sadiya, iya ta tasa
mahaifiyata ta tafi da ita, tace ba za a bartaba
haihuwar fari ba kulawa ba,Ita kenan gareni dan
wadan can yan uwan namu sai munyi tafiya mai
tsawo kan mu gansu.Sai da mahaifiyata tayi
kusan wata shida lokacin ni da ita munyi bulbul
tamkar kada iya ta bari mutafi, amma yanda
mahaifina ke ta suntirin zuwa yana kuma turo
mutane don baiwa iya hakuri sai ta hakura tace
mu koma.Amma ta ja masa kunne sosai, to dan
saukin yanzun ba kamar da ba, hakan yasa ki
shiyoyin jin haushinta suna ganin ya fifitata shi
ko tsoron karr a dauke ta ne don iya ta tabbatar
masa in tazo taga ba daidai ba to zata tafi
damu.Shakarata biyu ta sake samun wani cikin
tun yana karami take fama da laulayi iya tana
zuwa tare da yayanta akai akai suna duba
mahaifiyata tare da kawo mata abubuwa.Iya taso
ta tafi dani amma lokacin an ce inna da kalafucin
uwa, kulafaci gareni sosai ta hakuraKu ziyarci blog
dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Gurin haihuwarta kuma taji jiki da kyar ta haifi
yar bubu rai.Sanan itama jini ya balle mata ya
dinga zuba kafin aje Asibiti rai yayi halinsa, ance
iya taji mutuwar nan kaman me.Bayan anyi
bakwai aka raba dan abinda ta bari sanan iya
tace ba zata barni ba dani zata tafi da kyar
mahaifina ya yarda don shima yaji mutuwar yayi
kuka tamkar ranshizai fita , to mafarin zamana a
gun iya kenan.Na taso cikin gata da tarbiya duk
da irin son da iya take yi min, bai sa ta kasa bani
tarbiya ba.Lokacin da aka kawoni gidan yaya Aliyu
yana shekararshi ta karshe a makarantar kwana
ta barewa kwaleji dake zariya.Sam yaya Aliyu
halinsa ba iri daya bane da yayyansa, don su
suna da sakin fuska da fara'a, amma shi kullun
rai a hade ta bakin iya in tana masa tsiya takan
ce na rasa inda ka gado wanan halin naka na
shegen miskilanci, kullun cikin bacin rai sai kace
jakadan yan wuta. Tunda nake gidan bai taba yi
mun wasa ko hira ba, magana in ta hada mu to
bata wuce yazo bai ga iya ba, yace Sadiya ina
iya?Tare da haka ba shi dai raini ko rashin kunya,
sai dai kafi ya ga saurin fushi gami da zafin
zuciya. Yanada matsananciyar tsafta da ibada Iya
na yaba masa a nan, tunda na taso Allah baitaba
nuna mun bacci iya na dare ba, sai dai na rana,
bayan azahar. Duk lokacin da na farka zan ganta
tana yin nafilfilu.
Yaya Aliyu akwai iya saka kaya, bani manta
kawayena in sun biyo mini makaranta suka ganshi
sai kiji suna cewa, sadiya yayan nan naki dan
kwambo ne, ya cika yanga gashi baya
fara'a.Nakan ce kurufa mini asiri kada yaji.Burin
yaya Aliyu aduniya bai wuce ya zama police ba,
kalmar da Iya ta tsana duk lokacinda ya ce mata
shifa in ya gama karatunshi zai shiga makarantar
horar da yansanda.Sai ta ce masa ya daina
wanan tunanin don ita bata son dan sanda, wai a
nata ganin sharri kullun ake koya musu, kullin
suna kan titi suna karbar cin hanci.Wani lokacin
tace, dan sanda da aka ce ko ya mutu gawarsa
tana fita da ban, dan baki take to ban amince
ba.Shi kuma sai yace, iya kiyi min adu'a buri na
kenan zancen zancen ace kaza kaza duk sharri ne
babu ma'aikatan da babu na gari, kuma babu
inda ba battace.Kimin adu'a in zama mai kawo
gyara a cikinsu kuma in na zama dan sanda in
sha Allahu sai kinyi alfahari dani.Takan tabe baki
ta ce, uhm ni rabu dani da wanan zancen, ni dai
insuna yi sauraransu kurun nake yi, don sam in
yaya Aliyu yana fira da iya bana sa baki, domin
tsawa zai daka min ko ya harareni, haka nake
rayawa a raina ba wai dan haka ta taba faruwa
ba.Iya tana yin wainar saidawa a cikin gida,
muna yin ciniki sosai, wani lokacin har da
sha'anin buki suna ko walima duk muna yi da
sana'ar ta take yi mana dawainiyar karatu ni da
yaya Aliyu, sai dan abin da sauran yara suka
kawo mata.Dan suma yanzu ko wanensu yana
nan da dawainiyar iyalansa, karatun ya Aliyu
shine mai cin kudi, dan Alokacin yana karatun
digree sa ne a jami'ar Ahamadu bello dake
zariya.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Yana karantar (Engineering) ban san yanda zan
kwatanta muku ra'ayinsa ba, amma shi mutum
ne mai babbancin hali da ra'ayi.Bayan ya
kammala karatun sa ne ya dagewa iya yayyinsa
shifa sai yaje police Acadamy, wato makarantar
horar da manyan yansanda dake wudil jahar
kano, dakyar ya sha kansu.Ko da yake har sai da
kawunsu kannan iya dake Hadeja,Kawu Adamu
ne yaje har gida ya lallashi iya.Bayan ta yarda
tace, to ita fa bata da kudi,yaranta kuma suna
fama da iyalansu, dan haka yaje ya nemi
kudi.Aliyu ya ce, iya ai na fada miki asaida gona
ta, ta gadonmu da aka raba mana.Nan ma da
kyar ta yarda kawu Adamu shineya saida gonar
Aliyu yaje ya amsa, haka yayita zirga zirga
tsakanin kano da kaduna har sai da yayi nasarar
shiga police Acadamy.Ranar farko da yaxo ni
kadaice ina cikin wanke kayan waina bayan mun
tashi, iya bata nan taje kai kudin kayan miyan
wainar gobe, sai kurum naji sallamar sai naga
mutum tsaye kyam da kayan dan sanda riga blue
mai haske wando baki, ga wanan takalmin na su
da hula.Nikuwa dama gani da tsoron Dansanda,
sai naji cikina yana kugi, fuskarshi daure yace,
bakinki yana ciwo ne, bakya iya amsa sallama ko?
Cikin in-ina nace, wa...alai...kassalam.Ya zuba
min harara, yau ne kika fara ganina ne da har
zaki tsareni da idanu ko na can za maki ne?Na
sunkuyar da kai, a'a ya nufi dakin nace bata nan
ta je wurin Isa mai kayan miya, ya ciji ya tsa to


dauko min makullin dakina najena duba inda na
san iya tana ajewa na dauko masa da zan bashi
sai da na dan rusuna.Ya amsa ya nufi dakinshi
nazo na karasa wanke wanken na gyara gurin ya
fito cikin gajera wando da yar T-shirt irin ta
yansanda,Ina cikin kicin zan dora tafashen kashin
waina, yace baki san mutun yazo kiyi mai tayin
abinci ba, kenan ina ganin rowa zakiyi?Nace nayi
zaton ko kana azumi ne, na ga kullun kana yin
azumi,yace, oh, dama kina samun ido ne har kika
san cewa kullum ina Azumi?To yau ban yi.Nace,
duk abincin ya kare sai sauran tuwo kuma baka
cin dumame, sai dai in ko na dafa maka wani
abu.Yace barshi nasha cornfilakes,ya juya ya nufi
dakin sa.Na sauke ajiyar zuciya ban san meyasa
ba yaya Aliyu in yana guri bana so in tsaya a
gurin sai in ga duk ya cika gurin,gashi tsananin
tsoransa nake bai dai taba duka na ba watarana
ne dai da yake iya gadanga take ce masa sai tace
in kira mata shi, ni kuma naje nace iya ta ce kazo
gadanga.Wata tsawa da yayi min kadan ya rage
in saki fitsari, ya dora yatsinsa a dan manuni a
goshi na.In kika sake ce min gadanga sai na
zaneki tas kinji ko?Jikina yana bari nace, kayi
hakuri.Don tsoro lokacin har fitsari nayi a
wando.Lokacin da iya ta dawo tai murna da
ganin autanta, nan suka zauna suna yin fira, cikin
hirar ne naji tana yi masa zancen aure, inda ta ce
gadanga dan Allah ka nemi matar aure kasan
shekarunka nawa yanzu?Yayi dan murmushi ni
kwan nasan shekaruna, muke nan kullum cikin
rubuta date of birth ba dole in rike shekaruna
ba?Talatin da uku ne kacal.
Iya tayi dariya talatin da uku shine kacal?Ai dai
cikin sa'anninka ina tsammanin kai kadai ka rage
ba kai aure ba.Ya ce iya ba ni kadai na rage ba,
kin manta da usman?Ta ce, usman bikin shi kafin
Azumi ba kuyi waya bane?Aliyu ya zaro ido, iya
da gaske?Tace, ko jiya na kira shi na fada masa
yau zan shigo shi ne zai ki sanar dani?Iya ta ce
kila sai kazo din za ka ji zancen.Ya ce, iya kiyi
adu'a kawai amma ayanzu ba mata a ga bana,
kokari na in hada wanan course din nawa.Ta ce,
Allah ya taimaka.Ya ce sauran mu wata shida.Ta
ce, to Allah yasa a gama cikin nasara, ni dai fata
na ka zama mai gaskiya da amana, kayi aiki a
kasarka da kishi.Ya ce in sha Allahu, na gode.Duk
ina jin su har suka gama ya dube ni ita waccen
sunyi jarabawar J S. C.E din?Iya ta ce, tin yau she
har sun amso yan zu kici kicin shiga SS din ta
muke yi, ya ce zo ki bani saka makon na ki in
gani, dan nasan bawata kwanya ce da ke ba.Iya
ta ce, in ji wa?Sadiya boko da islamiya tana da
kokari.Na dauko gaba na yana faduwa na bashi
ya duba sanan ya kalleni babu laifi, amma kina
jin turanci?Na sunkuyar da kai, amma ban iya
bada amsa ba.Ya ce shirmen yaran hausawanmu
kenan, kuna jin tsoro ne kada kuyi ba dai dai ba
ayi muku dariya, to ai gara ayi muku dariyar
sanan a gyara muku.To ni dai daga yau kada ki
kara mun hausa.Har in koma duk kuma zuwan
da zanyi in baturanci zakiyi mun ba bana son jin
maganar ki.Iya ta ce, kuji mun fin karfin hali
gurin gadan ga, wanan ai mugun horo ne.Yare ba
na uwarka ba, ba na ubanka ba kace dole sai tayi
maka magana da si.Ya ce, in ba haka ba yau she
zata iya ga yanda zamanin namu ya zama sai da
karatu, ko da ta gama scondary zaki mata aure?
Iya ta ce, tana samun miji zan sallamata, don
haka kar ka takura mata.Ni dai nayi ciki na barsu
nan suna ta jayayya, yana cewa ilimi ko dan
tarbiyar yara ai ko ni ba zan auri matar da bata
ta shiga jami'a ba.Iya ta ce Allah ya taimaka ni
tawa tana samun miji zan turata can gidan
mijinta shi ne babbar jami'ar ta.Ku dai yan
zamani baku da magana sai dai in kun tashi aure
kun fi son yan boko sabo da tarbiyan yayan ku.To
amma kada ka manta ni banyi boko ba, amma
duk in da kuka shiga yabon ku akeyi ana sha
awarku.Aliyu yayi dariya, to iya in kin lura ai
baban mu yayi boko, kefa kika ce mun lokacin su
yaya sulaiman suna yara sun zo da home work
shi yake musu.Nima lokacin da na taso sune suke
yi mun ba, tace to wanan ce tarbiyar?Ban ce ilimi
baya cikin tarbiyya ba, amma bashi ne
gundarinta ba.Gun darin tarbiya shi ne ka dora
dan ka kan hanyar Allah da monzo (S. A. W) su
rinjayi komai a kan mazaunin shi.Sanan ka cusa
musu Tauhidi su iya rike Amana,Cika
Alkawari,Tausayin na kasa da taimakonshi,
Girmama na sama, in dan ka ya san wanan sai
ka hada masa da ilimin zamani da na adini shi
ne tarbiyya.Kai in dan ka ya san wadancan ya
rike ko bai je boko ba zai yi rayuwa
ingantacciya.Aliyu ya ce, haka ne zancen ki Iya,
Allah ya sa muma muyi tarbiyar yayan mu kamar
yanda kuka yi mana.Ta ce ameen.Ina da ga ciki
ina jin su na ce, in dai Iya ce duk musun ka da
gardama tana yi maka baya ni sai ka
fahimta.Abin da ya bani al'ajabi da mama ki, da
dare na je kai masa abinci dama fakon sa na yi
tayi dan ba zan yar da wata magana ta hada mu
da shi ba, tunda ya ce sai da turanci, niko dan
tsinta tsinta na iya.Dan haka ina ganin shigarsa
ban daki na dauki abincin na nufi dakin sa na
ajiye zan fita sai na hangi wata mujalla can kan
katifar sa, ni kuma da shegen son kalon hotunan
yan film.Na zata irin tasu ce yan fin din India, sai
na koma na dauko na bude jiki na ya dauki
tsuma ganin mata tsirara.Da sauri na rufe wato
dai mujallar ta tsiraici ce, na sake bude wani
shafin da sauri na rufe, ina fitowa yana isowa
kofar dakin.Ya ce cikin harshen turanci me kike
so na cecikin hausa, dama abinci ne na kawo
maka.Ya matso ya damki kunne natamkar zai cire
shi.Ba na ce kada ki kara yi mun hausa ba?Nayi
shiru dan ina tsoron yi masa turanci ya ji ba dai
dai ba ya ci uba na.Ya sake matse kunnan, cikin
turancin da zaniya na ce yayi hakuri.Ya saki kin ci
sa'a daga yanzu ba hausa tsakanina da ke.Duk
cikin turanci yake maganar.Ni dai nayi daki ina
Al'ajabinshi, mutum kamar na Allah ashe dan
iska ne, ya tasa hotunan batsa yana kallo.Shi
kuma da ya shiga dakin sai yaga kamar an jawo
mujarlar daga inda ya ajiyeta, a ranshi yace wato
dai yarinyar nan ta bude mujallar nan kenan,In
ko haka ne ban ji dadi ba, amma sai wata zuciyar
ta ce, kada ka zargeta, domin bata da rawar kai,
tsoranka ma takeji ba zata taba maka komai ba,
sai kurun ya samu natsuwa tare da gaskata
hakan.Kwana biyu yaya Aliyu yayi ya tafi, niko
cikinkwana biyun nan binshi nake da kallon
mamaki.Bayan tafiyar shine na samu ci gaba da
karatu na a makarantarmu ta maimuna
gwarzo.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Kwanci tashi su yaya Aliyu an kammala wanan
karatun, buki sosai akayi ko na ce walima dan su
yaya Sulaiman su har can suka je nan gidan mu
kuwa mun aikatu.Anyi wainar shinkafa, da su
zobo da kunun zaki, daga can suka turoshi
kaduna (headquarter) a matsayin A. S. P Aliyu
Tukur.Ranar da ya zo gida na jima a uwar daki
ina tunanin fitowa saboda tsoron maganar da zan
masa da turanci, gashi a fallon iya suna fira.Na
zauna ina bitan abin da zan fada masa da turan
ci, can iya ta kwalo mini kira na amsa, ta ce me
kike yi?Na fito, ya kalleni dama tana ciki, kin wani
kunshe kamar wani munafiki?Na ce, sannu da
zuwa. Cikin turanci na yi maganar, shi sai lokacin
na tuna mai da batun wani turanci.Ya kalli iya
sanan ya kalle ni ya amsa, na ce ina taya ka
murna, ya ce ya gode.Ya tambayi nawa karatun
na ce lfy lau.Da sauri nayi waje ina tsoron kada
ya daukowani zancen da va zan iya amsawa ba, a
rai na na ce, baka sanan wannan ba na fi sati ina
haddar su.Bayan na fita ya cewa iya, to kin ga
dai yarkita soma zama baturiya, iya ta ce, eh, ai
hakan yana da kyau.Tunda ya dawo kullun
zancen shi da iya ba ya wuce kayi aure gadanga,
ka fito da mata sai dai in bai zo gidan ba,
kokuma bai zo mata fira ba.Har ta kare ta ce yaje
gidan hajiya talatu ya nemi diyarta Jamila, yace
iya kiyi hakuri har inga wacce ta yi mun da idona,
bana son cushe cushe.Ta ce, duk fadin unguwar
Mu'azu har yau baka ga wacce kake so ba?Sai ya
ce, ina nan dai ina binkitawa, har dai ta hakura
ta zura mashi ido.Daga baya naji suna hira da
yaya sulaiman wai ta sama mashi magani tana
ganin kamar bashi da lafiya, niko da naji wanan
xancen lokacin cewa nayi a raina, ras yake kila
ma neman matan shi yake yi a waje tunda mai
ya hada mara lafiya da hotunan tsiraici?Kuma
bayan nan ina zaton yana kalon fina finan tsiraici,
don lokuta da yawa in yana kallon in nayi sallama
dakin zai kai abinci ko wani abu sai yayi sauri ya
kashe, sanan ya ce in shigo.In kaset din arziki ne
menene na kashewa?Amma na sa a raina wata
rana sai na kama shi.
Haka kuwa watara na xan kai masa abinci darana
lokacin aikin dare yayi da safe ya dawo,Iya kurun
ya gaisar muna aikin waina ya shige daki ya
kwanta.Sai kusan sha biyu sanan ya farka,
lokacin Iya ta tafi gurin sabo mai shikafar waina,
ta ce in ya farka in kai masa ruwan zafin shida
waina in kuma bredi zaya ci to in kai masa.Ya fito
ya shiga wanka, da sauri na dauki dan flask din
sa na ruwan zafi na nufi dakin, ko mai a kashe
yake amma na san zan kunna in gani tunda
wanka ya shiga saboda shi mutum ne mai
dadewa a wanka.In dai ya shiga tamkar zai canza
fata, don haka ina lokacin sallah ya katato xai
shiga ban daki iya kance bari muyi alwala dan in
ka shiga sai lokacin salla ya fita baka fito ba.Na
jona komai ya kawo na ce oji bulumme can kasa
dan muna funci aikuwa CD yana gama login sai
ga mata da maza tsirara suna aikata masha'a.Da
sauri na kashe na fita naje na ci gaba da aikina
abin da na gani ya girgiza ni kuma naji haushin
kaina da karan bani na.Na fito na dauki waina da
bredi naje nayi sallama ya ce in shigo na shiga na
ajiye xan fita ya ce tsaya, me kika shigo yi nan
dakin?Gaba na ya fadi na ce ni flask na kawo, ya
ce daga nan sai kika yiyi me?Cikin in ina na ce,
banyi komai ba ya Ali.Ya tsareni da idanu, bashi
da tabbacin nayi wani abu amma yana shigowa
yasan an shigo.Ya kalleni, jiki.Na fita sanan na
harari dakin na tafi.A raina na ce dan iska, amma
wani lokaci sai ya kure wa'azi sai kace na Allah.
Kwanci tashi ba wuya, muna cinye kwanakinmu
har mun kammala (SS3) mun zana jarabawa
kuma lokacin ya zo dai dai da saukar karatun mu
na alkur'ani.Munyi komai cikin nasara, kuma nayi
walimata a gidan mu inda iya ta matsawa ya
Aliyu sai ya buga mun memo wanda zan rabawa
kawaye na.Sauran yayyansa ma sun taimako,
baba na kuwa da naje zaria na fada masa dubu
biyarya bani wai inyi hakuri da yake ina zuwa
danhutu can wani sa'in iya tace inyi sabon dinki
da kudi na.Dangi kam sun xo babu laifi, har yan
uwa na na zariya, babanmu ya zo da su komai
na yayi babu laifi.Da yamma ni da kawata Aisha
muna kwashe kujerun da muka zauna akai
mukayi walima a waje da kawaye na.Mun hada
su guri daya sai naga guda biyu wanda ya Aliyu
da wani abokin sa suka zauna su na hira.Ta ce,
kije ki amso wadancan cikin zolaya tayi maganar,
don tasan ina jin tsoron shi.Na ce, ke kije ki
amso.Tayi yar dariya bari inje.Tayi tamkar zata
nufi gurin sai ta fasa.Muyarshi ta katse maganata
da zanyi lokaci daya kuma gaba na ya fadi, Ke!
Na wai waya, zo nan.Naje na rusuna na gaida su
cikin in ina ya ce, ke daga jin maganar ki baki da
gaskiya ko?Na ce, a a.Ya ce, to me nene nayin in
ina din?Nayi shiru, ya kalli abokinsa ga ta.Abokin
ya ce, ina yi muki murna da yin saukar alkur'ani
mai girma, Allah yasa anyi na tsoron Allah.Na ce,
amin.Ya Aliyu ya ce, jeki dama murnar zaiyi
maki.Ina tafiya ya kalli Aliyu ya ce, kanwar nan
taka tayi fa.Ya Ali ya ce, ok, iskancin naka har
agida ma zaka yi?Auwal ya ce bada wani abu na
ce ba, cewa nayi tana da kyau.Kai da ma ka
shiga kayi yar gida tunda duk matan dake sonka
baka kallon su.Ali ya ce don me zan tsaya kallon
yayan mutane, alhalin na san cewa ba auran su
zanyi ba?Auwal ya dan yi masa dukan wasa a
kafada tare da cewa, ko jiya munyi gulmarka da
Sajen Bello, wai ina ma shine mata keyiwa wanan
shishshigin, da sai ya more kuriciyarshi son
ranshi, amma kai kullun cikin Azumin dole, in
kaga mata sai kace kaga Abokanan gaba.Aliyu ya
ce, ban ga anfanin zina ba, koda ba haramun
bace mutum ya gujeta, ya kyamace ta, dan kare
kansa daga cututukan zamani.Ina fada maka ina
da kyama ba zan iya hada jiki da wayan can ba,
kuma dole in naga mata in hada rai tun da ba
halali na bane, kuma ba muharramai na
bane.Kullun dai ina adu'a Allah ya bani mace ta
gari mai kamun kai, kuma da kuke bin matan
Allah ya shiryeku, kai gashi kayi auran ma amma
ba ka daina ba.Kayi hattara duk abin da ka shuka
shi zaka girba, kana kallo wani can zai bata
rayuwar yayan ka yadda ka fada ta yayan
wasu.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa


Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Auwal ya ce , ka samu cikin adu'a abin ne
dawahalar bari, mata ne nishadin rayuwa, hira
da su ma a kwai dadi ne.Tsaki Aliyu ya ce in kaso
kaji dadin ba?Ni kuwa bana fatan in ji dadin fira
da mace wadda ba tawa ba, ina nufin
halalina.Auwal ya mike, bari ni in tafi kai dama
malami ya kamata ka zama ba dan sanda
ba.Sam Aliyu be mike dan raka shi ba, daga nan
suka yi sallama.Shi kam tunani ya shiga, shima
yana sabo wajen kallon fina finan batsa da
karantar mujallan batsa, duk da cewa bai taba
aikata zina ba ya san wanan laifi ne babba.Kuma
in mutum bai daina ba wata rana zai kai ga
aikata zinar, kuma tunda Allah ya rufamini asiri
tsawon lokaci yana yi ba wanda yataba ganinshi,
ya kamata ya daina.Ya tuna lokacin da ya fara,
wata rana yaje dakin su Auwal da rana lokacin
suna jami'ar Ahmad Bello ta Zaria, ya ga wani
novel a dakin ya dauka ya karanta, ashe na batsa
ne.Daga lokacin sai yaji yana so ya gani, ya ko je
wani shago a kasuwa ya siyo kaset din tare da
mujallar tun daga nan lokaci zuwa lokaci sai ya
siya ya kalla, sanan ya kona su ya sake siyan
wani.Shi da kanshi ya sha fada wa kanshi cewa,
yanda yayi Imani zai tsaya gaban Allah haka yayi
imani za a tambaye shi yanda yayi ya sami kudi
da kuma hanyar da yabi gurin kashe su.Me zai ce
game da wanan kudin da yake sawa yana siyan
batsa?San nan baya karanshi da komai sai karata
da masu hankali?Lallai wanan abune da ya
kamata yayi makansa tun kafin ya mutu.Ya mike
tare da kudircewa daga yau ya tuba,ba zai kara
ba.
Dai dai gwargwado ba xa a ce bani da kyau ba
tunda Allah bai halicci mumuna ba matsawar
mutum yana da kyan hali, balantana a ce mutum
musulmine.Aina ya ga kyau sai dai kuma in ba
tsafta, ni fara ce sol amma bani da dogon
hanci.Wanan baisa fuskata muni ba, haka
idanuwa na matsakaita ne, ni mutum ce mai
tsananin kwalliya ko alwala nayi sai na sake
sabuwar kwalliya.Haka nan iya bata gajiya da
siyan mun kayan kwalliya, sanan bata ganin
bekena duk lokacin da zan bata gurin kwalliya.A
cewarta ya mace doki ce sai da kwalliya, abinda
kawai bata yarda da shi ba shi ne, ayimini dinkin
da zai nuna surata, nan ne zata ce ba zata bada
kwamasho ba gurin yada zina.Ta ce, shigar da
yawancin mata keyi ita ce ke haifar da zinace
zinace sannan zata zuba ko nawa ne ta yankan
mini yadin hijabi amma mayafi dai sai dai inyi
asusu in siya.
Shima din ban isa in siya karami ba sai babba,
kuma mai kauri ban taba jin haushinta ba dan
nasan tana kare nine daga afkawa cikin
shaidan.Dai dai misali ina da farin jinin samari
masu sona, dan ma iya bata bari in fara fita
zance da wuri ba sai da na kai SS2 duk masu
zuwa gurina da aure suke sona.Sai dai ni cikinsu
banga wanda yayi mini ba irin injishi kane kane
cikin raina din nan ba, fada haka iya take cewa
maza ki tsaya ruwan ido daga karshe kowa ya
gudu kizo kina nema.Ai yanxu lokacin ya mace
mai hankali ake dubawa wanda yake da hali mai
kyau sanan ba jahili ba kuma ya kasance yanada
yar sana'ar da zai rikeki, to ki kamashi.Allah
shine mai azurtawa, in da rabo sai kuyi arzikin
tare, ke in ma baku samu anan ba to ya baku na
gobe kiyama.Yawan yi mun wanan nasihar yasa
nake ganin zan iya tsaida Idris kuma zan iya
auransa amman sai mun zauna da kawata
aminiyata Aisha.Mun zauna da ita ita ma tace,
gaskiya duk cikin masu sona babu kamar Idris a
hankali.Mun yanke shawarar in tsaida shi ita
kuma dama akwai makocinsu Bello dake sonta.Ku
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Wata safiya Iya tana kwance ba lafiya dole na
fasa zuwa makaranta tunda mun riga mun hada
kullun waina, sai kuma ciwon cikin dare.Ya Ali ya
shigo da shirin fita, don bai san bata da lafiya ba
sai da ya shigo dakin, ya girgiza da ganinta
kwance cikin bargo dakyar take magana.Arude ya
ce, ya babu lafiya ne?Tace, eh, yace meyasa ba a
tashe ni ba a gida fa na kwana?Ita wacen
sakaryar ba sai ta fada min ba.Iya ta ce ni na
hanata ta ce bari ta taso ka, ya cire hula, bari
muje Asibiti, bari in samo mota, ta ce, a a naji
sauki.Fita yayi sai gashi da likita wani dan nan
unguwar ya duba ta sai gashi hadda ruwa a dora
mata.Ranar dai bai fita bahar rana, bai taba
birgeni ba irin ranar, duk wani abu sai yayi, hatta
bata magani a baki da abinci sai gurin la'asar
sannan ya fita.Su yaya Sulaiman,Zakari da Sani
duk sun zo da matan su, sanan makota na ta
zuwa.Da yaje gurin aiki ya bada uzirin shi sai ya
dawo kusan shabiyun dare, jikinta yayi sauki.Ina
jiyo hirarsu,rokonshi take yayi aure ta ce Aliyu
bani da wani burin da ya wuce inga auranka, kai
na fuskanci kafi son sai na mutu sanan zakayi
aure.Jikinshi yayi sanyi, dan ya kasa tuna ranar
da ta kira shi da Aliyu, cikin tautasar murya da
lallashi ya ce, zan yi iya, in sha Allahu kina
raye.Ta ce, kayya, gadanga kullun haka kake
cewa, ni dai ai tuni na cire rai ka tashi katafi na
yafe maka Allah yayi muku albarka kai dasauran
yan uwanka.Yarinyar nan sadiya dan Allah ko ban
tashi ba kada ku bari ta koma zaria ta zauna
gurin wannan yaron hardai ta sami miji kuyi mata
aure.Ya ce, iya ke ce da kanki zaki aurar da ita
insha Allahu, ta ce shi kenan tashi kaje ka
kwanta.Hankali tashe ya fita bayan ya tai maka
mata ya kawota cikin daki, na tashi idona
naxubar da hawaye, na taimaka mata muka
kwanta.Ina kuka kasa-kasa ta ce,Sadiya lafiya?
Tace iya bana so inji kina cewa zaki mutu ki barni,
ta ce in fada ko kar in fada sadiya ba zan kara
lokaci ba sai dai in ajalina bai zo ba.Da kyar bacci
ya daukeni, lokacin iya tayi nisa da bacci.Shima
Aliyu tun da ya koma dakin shi fa ya kasa ko
zama, lallai dole ne ya nemi mata, sai dai
matsalar shi ta ina zai fara?Bai taba yin budurwa
ba, bai taba soyayya ba, shi kuma yana ganin
kamar raini zai ja masa in yaje kofar gidan su
yarinya.Amma bari gari ya waye yaje wajen
usman amininshi.Kafin ya wuce masallaci sai da
ya fara lekowa dakin mu ni da iya duk muna
sallah, sanan ya wuce,dan Allah ya kawo mata
sauki a cikin daren daga masallaci gidan Usman
ya wuce, ta wya ya kira shi cewa gashi a kofar
gida,Usman ya ce, lafiya?Aliyu ya ce, lafiya ba lau
ba, fito kaji.Da sauri usman ya bude gida ya fito,
sama sama suka gaisa.Usman ya ce, aboki lafiya?
Aliyu ya ce ina fa lfy, jiya tsohuwa ba lafiya, ta
fara bar mun wasiya, sannan tayita jaddada min
burinta kawai nan duniyar shine inyi aure.Usman
yace aboki ba ita kadai ba, ni kaina buri na
kenan, to tunda kaga tsohuwa ta tsananta gara
kayi ko kwa rabu lafiya.Aliyu ya ce, ai baka sani
ba, tunani na yanzu ina zanje nemo mata?Na
rantse maka banda budurwa...


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp  08168575100



DARAJAR YAYANA1-02
Posted by ANaM Dorayi on 08:55 PM, 09-Mar-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
___________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Usman yayi yar dariya sanan ya ce, ni da zakaji
shawarata wanan sadiya ta gidanku?Aliyu yace,
ah haba?Usman yace, naga yanda ake yabon
hankalin yarinyar, ko a gida tana da matsalane?
Aliyu ya ce, sam ko a gida bata da matsala
gaskiya, amma ban taba jin koda alamar sonta
ba, to wanan yarinyar ma ina ganin ta tsaida
wanda take so, in ma ba ta tsayar ba sai inga ta
yi mun yarinya.Shekarunta sha bakwai fa yanzu
in ban cika ma ba, usman ya ce, dai dai.Nafi son
wacce ta shiga makarantar gaba da scondary a
kalla ta mallaki hankalinta, ta san yadda zata kula
dani sai nine zan koma in kula da ita.Usman ya
ce, ba yaran yanzu ba, tunda kaga bata yiba in
kaga wata da tayi maka ko a unguwarku ko a
kafatanin unguwar mu'azu ka fada min yanxu
anjima sai muje, kaga yanxu sai kaje wa iya da
kwarin gwiwa.Aliyu yayi shiru yana tunani can ya
ce, aboki kasan Allah?Nifa ba wai ina kallon mata
bane, na layinmu ma ban sansuba balle na
unguwa.Usman ya ce, to aboki ka tsaya a Sadiyar
mai hankalice,Sadiya tayi.Aliyu yace inda ta kaicin
yake sai kuma in kirata ince ina sonta?Usman ya
ce in baka iyawa bi ta sama mana ka samu iya
ka fada mata kana son Sadiya, nasan zatayi
murna.Aliyu ya ce, aboki daina cewa ina sonta,
zadai ayi aure amma ba wai ina sonta ba, Aliyu
yace kuma ba zanyi karya ba tunda banji cewa
ina sonta ba,har Aliyu yaxo gida tunani yake anya
kuwa zai amince cewa yana son auren sadiya?
Lokacin da ya shigo dai dai na bare magani na
mikawa iya, ta afa tare da kora ruwa, ya tsaya ya
rike kugu yana kallon mu, tunaninshi a wanan
lokacin lallai babu wanda ya dace ya auri irina,
bisa hujjarshi tacewa ba zai sami matsala ba
wace take tsakanin iya da matan yayanshi ba.Iya
tana kuka cewa cikinsu matar yaya Sulaimance
kawai ta san darajarta, kuma tabbas hakane
domin sai suyi wata uku basu zo sun gaida ta
ba.Ita ba wai tana kwadayin abin hannunsu ba
ne, a a ko ba komai taga yan jikokinta yayi,
amma Sadiya bata da uwar da ta wuce iya.Dan
haka yana nan ko baya nan zata zamo a
karkashin kulawarshi, burinshi yaga ya daukewa
iya duk wani matsalarta, su kuma yayinshi suji da
iyalinsu.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tunaninsa ya katse lokacin da iya ta ce, gadanga
ka shigo ne?Yayi firgigit, na shigo iya.Na gaida shi
na fita, shima a ranar bai iya yi mata zancen ba,
karshe ma tunani yayi ya samu yaya sulaiman
suyi shawara.Haka kuma bayan sallar isha'i ya
nufi gidan yayan nasa bayan sun gaisa sai ya
sanar dashi abinda ke tafe dashi.Yaya sulaiman
yaji dadin zancen da Aliyu yazo dashi, sanan yace
sai ka samu yarinyar ku daidaita, Aliyu ya ce, ina
ga ba sai na sameta ba, indai iya ta amince shi
kenan.Yaya Sulaiman ya ce, iya ba zata ki ba,
yarinyar ce abinji, in ta ce bata sonka fa?Aliyu ya
ce, ai nima ba wai ina sonta bane, dacewar
auren kurum nake dubawa, shi yasa.Ya Sulaiman
ya ce, shirme kenan, to kai in kaje wajen iyar ce
mata zakayi ba sonta kake ba?Aliyu yayi
murmushi ce mata kurum zanyi ina so na auri
Sadiya, Sulaiman ya ce, Allah yayi mana zabi na
alkairi.Ka bari zanje gurin iyar, duk yanda mukayi
zakaji.Aliyu ya ce to.Yayi godiya yayi masa
sallama ya tafi..Sulaiman ya sami iya cike da
karfin gwiwa, ganinshi babu wanda zaikai iya
murna kai yasan har goron albishir zata
bashi.Amma ga mamakinshi yana gama labarta
mata dalilin xuwansa sai yaga tayi kicin kicinda
fuska ta ce kaine kaga sun dace ka bashishawara
koko shine ya sameka da zancen?Yace, a a dazu
ya zo mun da zancen sai kuma naga dacewar
haka.Ta ce, to ka koma ka fada mashi ban
amince ba, kace mashi ya nemo matarshi can
itama ta nemo nata mijin.Jikin Sulaiman yayi
sanyi ya sake tausasa murya ya ce, iya ban san
dalilinki ba, kokuma akwai abinda kika hango
wanda ba na Alkairi ba?Ta ce, na farko dai kasan
halin gadanga, zuciya ce dashi ga saurin fushi, ga
miskilanci tsiya, ga shegen jin kai.Sanan na sha ji
ko in ce ya sha fada min cewa shi yar jami'a yake
son aura.Niko tawa ko secondary din bata gama
ba.Sulaiman ya ce, iya in kin duba tunda shi din
ya ce ta mashi ai ina ganin ba za a sami wata
matsala ba.Fir iya ta ki zancen, duk ta inda
sulaiman ya bullo sai iya tabi ta wata hanyar,
haka nan yaya sulaiman ya hakura ya fita rai
babu dadi.Aliyu ya sunkuyar da kai yana
sauraron sakonshi a gurin yaya sulaiman, sam bai
zaci jin haka ba, amma sai ya ce, ba komai Allah
yasa haka shine mafi alkairi, na shi ganin ba zai
damu ba, tunda dama ba wai yana sonta
bane.Sai dai kuma yanda ya tsammaci abun yafi
haka, samun kanshi yayi da shiga damuwa, ko ba
ya son yarinyar hakika ya tsananta dason
aurenta.Ya samu iya da kan shi wata safiya yaxo
gaida ta bayan yayi shirin fita cikin dakin sa.Ya
ce, iya me yasa ba zaki bani auren sadiyaba? Ta
lissafo mashi dalilinta kamar yanda ta lissafawa
yaya Sulaiman takuma fada masayaje ya nemo
mata can.Ranshi ya baci amma bai nuna ba, sai
dai cikin sanyin murya ya ce, to shikenan iya na
hakura, amma ba zan taba xuwa ko ina neman
aure ba saboda ina da munmunan halayen da
ban can canta a bani mataba,tace, ni ban ce
ba,ya ce to iya tunda ba a bani a gida ba in naje
nema a wani gida suka bani na cutar dasu tunda
ba su san hali na ba,yana kai aya ya mike tare
da cewa, sai na dawo.Ita kuma lafuzan nashi
suka hanata magana.Ita zahiri ba wai bata son
auren ya Aliyu da sadiya bane, na farko ta san
halinsa, sanan tana tsoron ta tursasa min.Kullun
Aliyu sai yayiwa iya naci amma taki ko ta ga zai
dauko zancen sai ta hade fuska.Wata safiya ina
kwance kangado ina fama da matsananciyar
ciwon mara, dama mun rabu da yin waina tunda
iya tayi rashin lafiya.Ya Aliyu ya ce, a daina yin
wainar duk wata nake wanan ciwon marar.Yaya
Aliyu ne ya shigo gaida iya, bayan sun gaisa ta
ce, har ka shirya fita kenan?Ya ce mata eh, akwai
wani case a hannunsane yana son ya kammala
dashi kafin fitowar(AC) ta ce, to Allah ya taimaka,
a can zaka karya?Ya ce, eh.Sanan yayi shiru ta
ce, da magana ne?Ta sani in har yayi haka to da
magana a bakin sa, ko da yake ta san zancen na
sa daya ne, bai wuce na sadiya ba.Kuma tana
son Sadiyar ta ji ma kunnenta in ta amince
ruwanta don haka ta ce yaya autana?Yace iya dai
maganar Sadiya, Allah iya ba maganar yabon kai
ba, ina da kamalar da za'a bani mata, ya ko ta
gidan waye 'yar taki ai ba kyau tafini ba,ya fada
cikin sigar wasa, ta ce,duk da haka ba zan baka
ba, kai ita fa tarigata fidda mijinta.Yace dan Allah
iya ki fada mata kinji?Ta ce, au, nice ma zan fada
mata?Lallai ba ma son auran nata kake ba.Ya ce,
ni iya in na fada mata sai naga tamkar zata
rainani ne.Iya ta ce, kun ji girman kan ba?Don
Allah kayi hakuri nifa ka tayar dani,ba zan yarda
ba.Aliyu da ya gaji ya fita.Tun daga lokacin da
naji ya Aliyu ya ambaci sunana na mike zumbur
hankalina atashe,ni Sadiya yaya Aliyu yake nufi
ko wata?Kai in ko nice na more, dan gaskiya yaya
ba irin mijin da zance bana so bane, tab!Wanan
shine tsintar dami akala.A a iya kada kyi min
bakin ciki, ina jin fitarshina fito da sauri ina
kallon iya, ko zata ce wani abu, amma sai ta
shareni, na ta nufintadaga yanda na dauki
al'amarin tunda ta tabbatar naji.Ko daga irin
fitowar da nayi, ganin iya ba zatayi magana ba
sai na ce iya ta dubeni, wai ya Aliyu wa yake so?
Ta tabe baki dan Allah rabu da shi, wai ke, na
dafa kirji da karfi na furta da gaske?Ta ce, zan
maki karya ne?Na ce to iya shine zaki ce mashi
ina da wanda nake so?tace, au.Sharri nayi maki
kenan?Ina ce ke naji kina cewa kin tsaida Idris?
Na ce, ai ban fada mashi ba.Ta ce, meye nufinki
yanzu?Kina so ki ce min kina son Gadanga?Nayi
shiru tare da hade fuska, mamaki ya cikata, ta
ce, Sadiya dama can kina son Gadangan ne?Na
ce, nifa ban ce ina sonshi ba, amma ke meye
dalilin da kika ca baki yarda ba?Iya ta shiga tafa
hannu tana salati.Kin tirke nine lallai sai kinji?To
ba wani dalili bane sai na kare mutuncinki,
gadanga yana da zuciya, gadanga yana da fushi,
sanan ga miskilanci,ina tsoron ki shiga matsala,
gaki karamar yarinya, shi kuma shekaru sun dan
soma ja.Da sauri na ce iya in dai dan wanan ne
na yarda kinji?Ta ce, wai me ya burgekine a dan
sanda duk jikinki ya hau bari?
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Na ce, to iya gaskiya ya Aliyu ba irin mutumin da
za a ce ba a so bane .Ta ce, ni dai na ce a a ban
yarda ba.Na mike cikin fushi na fita tsakar gida,
da kallo iya ta bini, matuka ta ji mamaki
musanman ta sanni bani da rawar kai.Ni kuma
kicin na shiga na zauna banyi aune ba sai kurum
naga hawaye suna zuba a ido na, ni kaina har


naji mamakin kaina.To da bai ce yana sona ba
fa?Ranar haka na yini har dare, kusan mutum
uku suka aiko kirana naki fita, iya duk tana lura
dani tana kallona ranar bai dawo gida ba sai sha
biyun dare, sanan tunda a subahi ya fita.Yau
sam na kasa sukuni, iya sai kallona takeyi tana
salla, can bayan ta idar ta ce sadiya!Nayi shiru, ta
ce, nasan kina jina ta shi kawaiki tashi, na tashi
zaune ta ce, sadiya ina ganin baki gane nufina ba
game da zancenkike da gadanga shi yasa har kike
fushi dani.Gadanga bahogon mutum ne, ni na
haifeshi na sanshi tun yana dan karamin shi,
gadanga bashi da dadin lamari, amma in kinji
Allah ya baki sa'a.Sai dai ina so ki sani in da
wanda zaiyi farin cikin aurenki da gadanga to ya
biyo baya na,sai dai duk da haka ba zan kasa
fada maki gaskiya ba.Shawarar da zan baki kuma
ki rage rawar kai in ya fahimci kina doki kimarki
ta zube.A zaton iya zan hakura amma sai taji na
ce, in sha Allahu ba zan sami matsala ba.Ta tsura
mini ido haka kika ce?
Nayi shiru ta ce shi kenan, to da sharadi ba zuwa
kawo kara.Da sauri na ce, to,da kallo tayi ta bina
ni dai na tashi na koma makwancina ina
murna.Na zaci da safe zata neme shi ne ta fada
mashi ayi sai kurum ta share, ko da dai ya fita
da wuri, wasa wasa sam taki zancen inaji lokaci
da yawa da ya dauko zancen zata ce don Allah ya
rabu da ita.Sai dai abinda ke bani mamaki,
kullum yanda yaya Aliyu bai can za min yanda
yakemin ba , amma nakanyi uziri cewa kila sai
iya ta amince sanan za mu soma yin tadi.Cikin
haka ne har aka dauki tsawon lokaci muka shiga
shirin zana jarabawa (SSCE) duk na kori samari na
babu wani mai zuwa tunda na fada musu na
tsaida miji.Shikam ya Aliyu bai san na sani ba,
kullum ya zo gurin iya sai yayi mata nacin shi fa
yana nan yana jira ita kuma takan ce mishi kar
ya dame ta, ba ya ce ya fi son yar jami'a ba?Ya
je ya nema.Ni kuma in ya tafi wani sa'in in ce iya
don Allah ba kince kin hakura ba, tunda na
yarda?Sai ta ce min sakarya, dubi fa ko kallo baki
isheshi ba, amma duk kin tsamgwami kanki don
fitina, ni dan kare mutuncinki nake kin abin nan.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Usman abokinsa yaji shiru batun maganar Aliyu
da sadiya, sai ya zo gurinshi musanman don
zancen , dama ya kirashi a waya yaji cewa yana
nan.Bayan sun gaisa usman ya ce, aboki wai
haryanxu ban sake jin batunka da yarinyar nan
sadiya ba, in mun hadu baka yimin zancen ba, ni
kuma ban tambaye ka ba.Aliyu ya gyara zama
yayi sanan ya lumshe ido don haushi ya ce,
kabari kawai abokina, haushin maganar nake ji,
shiyasa ban taba yi maka zance ba.Ya miko
hannu ya dafa gyiwar usman abokina ban taba
samun abinda ya bani matsala ba kamar
maganar yarinyar, ni abin haushi duk lokacin da
nayi kudirin hakura dazancen sai na kasa.Kullum
adu'a ta Allah ya yaye min ita daga raina, amma
abin ya faskara.Ko son yarinyar ne ya kamani?
Usman yayi murmushi lallai sonta kake yi, Allah
yasa ita ma ta soka hakan.Aliyu yace ina ruwana
da ita?Iyace kurum damuwata, in da ta amince
shi kenan, amma baiwar Allah nan wai zan cuci
yarinyar ita ba zata bani yarinya karama
ba.Ranar harda cewa na tsufa.Usman yace zanje
in sameta aboki, kada kadamu.Aliyu ya ce, ko
kaje matarnan ba zata yarda ba, na dai fada
mata ni na hakura da yin auren.
.Usman yayi ta dariya tare da zolayar Aliyu da
cewa, aboki ka dai shiga da yawa, to da ka ajiye
duk wani girman kai ka dinga kiran yarinya hira
in taga haka zata fi yarda cewa da gaske kake
yi.Aliyu ya ce ka yarda ni ba zan taba iya kiran
yarinyar ba, ko ba Sadiya ba, kuma sanin kanka
ne ban taba ba, so bansan ta ina zan fara ba.Ba
ta ita fa nake ba, in iya ta yarda tayi hakuri ta
aureni dan da cewa auren sai kuma ya ja tsaki
kada ma ta hakura.Tama ji dadin zancen ta samu
miji irina, Usman ya ce, yabon kai?Aliyu yayi
dariya aboki ka fadi gaskiya, ni da ita wa yafi
kyau?Bai jira amsa ba ya ci gaba na farko dai
kaga ita fari ne kurum ya ceceta..... Usman ya
katsishi au, wai dama haryanzu akwai
mummuna?Ni dai yanzu na daina ganin
mummunaai tunda naga alamun kai ya waye, ba
a zama da kazanta, Aliyu ya ce, haka ne, amma
wani wan wani ne a kyau.Usman ya ce, duk da
ka fi ta kyau dai ita zuciyarka ta zaba, zanyi
maka kokari, zanje in samu iya.Aliyu yace tunda
ka dage jeka din, duk yanda kukayi zamuji.
Kamar yanda Usman ya alkawarta yazo ya samu
iya wajen la'asar ina yi mana tuwo, itakuma tana
zaune a kofar dakinta.Na gaida shi sannan na
dauko masa tabarma ya zauna, na kawo masa
ruwa sanan naje na ci gaba da aiki na.Daga inda
nike ina jiyosu suka gaisa sanan ya fara yi mata
zancen da ya kawoshi.Iya dama akan batun
abokina ne da yar uwarsa sadiya, iya dukkan su
naki ne, a ganina wanan abin farinciki ne.Iya ta
tsuke fuska,Usman ina ganin kimarka, zaifi kyau
ka bar zancen nan bana jin cewa zan
amince.Usman yayi shiru yana tunanin yanda zai
bullo mata.Can ya ce, to shi kenan, amma na so
ki amince domin yana cikin wani hali na son
yarinyar nan, nasan halinshi kin san halinshi,baya
daga cikin mutane ma su magana biyu.Yayi mun
rantsuwar ba zai taba aure ba in ba Sadiya ba,
duk duniya ita yake so.Zaman shi haka nasan
yana damunki.Ta ce in duk duniya Sadiya yake so
ita Sadiyar ya tambayeta ta ce tana sonshi? Nifa
ba zanyiwa yata auren dole ba, don in faranta
masa.Daga inda nake a kicin na da ga hannu ko
nace ya tsa tamkar mai bada amsa a cikin
ajinmakaranta, sanan na kwalawa iya kira!!Ta
kalleni tare da yi mun da kuwa, shi dai baisan
dalilin dakuwar ba, tunda ya bani baya, ita kila
ya zaci laifin nayi mata.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Usman ya fahimci nufin iya, shi yasa ya ce mata
Aliyu ya dinga kiran yarinyar suna fira.Ya dubi
iya, to in sha Allahu za mu tuntubi yarinyar, idan
bata amince ba shike nan.Yana fita ya dauko
waya ya kira Aliyu, bugu uku ya dauka. Usman ya
ce, Aboki da farko fara bani goron albishir.Cikin
sauri Aliyu ya ce kada dai ka ce mun
tasaurareka? Usman ya ce, in sha Allahu munyi
nasara Aliyu ya ce shi kenan sai na xo aboki,
gidanka zan sauka kaitsaye daga office yanxu ina
kan wani aiki.Suna cin abinci a falonsu Usman
yana koro mashi bayani duk yanda sukayi a
karshe yace yanzu kaga tana nufin ta yarda sai
dai amma tana so ka kira yarinyar ka nemi
amincewar ta.Aliyu ya tsirawa Usman ido, sanan
ya ce, ai wanan shine mai wahalar, gaskiya a boki
ba zan iya kiranta ba.Usman ya ce, tsoronta kake
jine?Raini ne bana so, yanxu dai kai kaje ka
sameta kuyi magana.Usman ya ce, nima ke nan
zan yi maka yakin neman sonta?Aliyu ya ce, duk
yanda ka ce amma ni in na kira tafa ba ra'ayinta
zanjira ba, umurni xan bata.Usman ya ce, shi
kenan ka bari xanje.Bayan sallar isha'i muna
zaune ni da iya muna cin abinci tare kamar
yanda muka saba, yaya usman yayi sallama shi
da matarshi Anty Abida da yaran shi guda
biyu,tsam na mike daga cin tuwon ina yi musu
sannu da zuwa, suka zauna na kawo musu abinci
da ruwa, sukace yanxu suka tashi daga kan cin
abinci.Na koma tsakar gida bayan na dauki
yarinya wato Ummulkhairi, yarinyar tana da wayo
yar mai kyau taji kitso, na ce Ummulkhairi kina
makaranta? ta ce eh mana, kuma Abban mu yake
kaini har ma da Abulkhairi, nace, iye, to koya
mun karatu.Ta ce, na islamiya ko na boko?Na ce,
a a islamiya dai.Ta gyara zamanta a cinyata ta ce,
in miki sunayen Allah kyawawa?Na ce, eh,ta fara
kenan babanta ya fito, ya kallemu karatu kuke yi?
Na ce, eh, tana koya mun ne.Yayi dan murmushi
ya ce ummu jeki wajen umman ki, ki ce mata ta
jira ni ina zuwa.Ta na shiga daki ya ce, kanwata
zo mana.Na mike na bishi zuwa kofar gida,
nasake gaisheshi nayi , bayan mun tsaya ya
ce,Sadiya nasan ba zakiji mamakin kiran da nayi
maki ba ko?Na ce ba wani mamaki, kila zaka
aikeni ne.
Yyace bahakabane na kiraki ne dan in sanardake
wani abun alkairi, ko da yake ban san yanda zaki
amshi abun ba.Na gane zan cen ya Aliyu, ya
duba duk cikin matan da ke garin nan yaga babu
wadda tayi masa sai ke, tamkar bai san zancen
ba na furta da karfi so!!!Usman ya ce ba wani
abun mamaki bane, dami ne kika tsinta a kala.A
raina na ce lallai ma yaya usman din nan, to bari
in latsa shi.Na ce, ya Usman ka ce masa yayi
hakuri kawai dan na riga na tsaida mijin aure
wanda nike so.Ya Usman ya ce, kin kai shi gida
ne?Na ce, gobe ne iyayan sa zasu shigo gidan
mu.Usman ya ce, in har zan baki shawara ki
yarda zan so ki dakatar da su domin kowa zaki
aura na tabbata bai kai Aliyu ba, samunsa sai an
tona, ko na ce irinsa.In kika sameshi a matsayin
miji tabbas zakiyi alfahari samun muji kamarshi,
mata da yawa suna sonsa, kila sun fahimci
nagartarsa, amma ba matsi in baki sonshi zan
koma in fada masa cewa baki sonshi da aure.Na
kalleshi bance bana sonshi ba, saboda duk
abinda iya ta haifa dole ne in soshi, kai ko wani
ne can ba danta ba in dai ya mutunta ta to zan
soshi bare dan cikinta, na riga na zabi wani
ne.Usman yayi shiru, ya zaci da yayi mun
magana zan amsa da murna, can ya ce, to yanxu
mai zanje in ce masa?
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Na ce, ka fada masa zanyi tunani zuwa gobe. Ya
ce, shi kenan, zan kiraki amma kiyi shawara da
kawarki wadda ta sanshi, na san zata fada maki
qualitie din Aliyu. Na ce, ba damuwa. Ya ce, shi
kenan gobe zanzo naji. In kin shiga kicewa Abida
su fito mu tafi daman na sallami iya. Na ce, to.
Bayan tafiyar su iya tashiga yi mun fada wai ai
gashi nan saboda bai daukeni da muhimmanci ba
abokinsa ya turo min, ta san jikina yana bari na
ce na yarda. Na vata fuska tamkar zan saki kuka
na ce, ni fa iya banyi fa rawar jiki ba, ce masa
kawai nayi zanyi shawara zuwa gobe. Ta ce, ato
in kin kimanta kanki yaga darajarki in kuma kinki
ni dai na fada maki babu zuwa a kawo mun kara.
A waya Aliyu yaji duk yanda mukayi, mamaki ya
dinga yi wai wanan yarinyar ce zata ce sai tayi
shawara, dawa zata yi? Kuma ita ce wa? Usman
ya ce ita ce mace. Aliyu ya ce, shi yasa kaga ba
zan iya kai kaina ba ga wata ya in ce ina son ta
ba, bare tayi mun yauki, nidan oya-oya ne.
Usman ya ce ka barni da itakawai na san jan
ajine zamuyi nasara cikin jin haushi Aliyu ya ce,
in taki ka kyaleta kawai, yarinya sai kace wata ta
gold sai ga ruwa nake yi a kanta. Ya ja tsaki nan
ya kashe wayar ba tare da ya sake jin mai
Usman zai ce ba. Kwana Aliyu yayi da zullumin
halin da zai tsinci kanshi, in yarinya taki
amincewa da shi. Da safe ina shara ya fito daga
dakinsa ban san me ke sani faduwar gaba a duk
lokacin da na ganshi ba.Na gaida shi ya amsa
cikin isa, kuma a ta kaice kamar yanda ya saba.
Sanan bai ko kalleni ba sai dai nice na bishi da
kallo. Namiji ne sosai ko tafiyarshi ta shaida
haka, daga ganinshi baka ga rago ba, dama abin
da ya dace dashi kenan jami'in dan sanda. Iya
daga daki ashe tana kallona ta ce, in kin gama
kallonshi sai ki ci gaba da sharar ko? Cikin kunya
da shauki na ci gaba da sharata. Da rana naje
gidansu Aisha kawata nake bata labari duk yanda
muke ciki, tace, tabbas! Sadiya idan zan fada
maki gaskiya ki amince kawai, kada ma ki tsaya
wani jan aji,sau nawa nake fada maki Aliyunku
unique ne?Allah in kika yi sake kin tsaya yauki
kya zo kina na dama, kin san shi da zuciya ya ce
yafasa.Kash!Ina ma nice ya ce yana so?Jin haka
yasa na kagu dare yayi.Har na debe tsammanin
xuwansa dan tara ta kusa, duk na tsure kar dai
ya Aliyu ya hakura da gaske.Can sai na tsinkayi
muryar wani yaro yana sallama ni ina cikin daki a
kwance kan kujera.Iya ce ta amsa salamar don
tana tsakar gidan, ya ce an ce sadiya ta zo inji
wani a waje.Ka fin ya rufe baki na mike, zaraf na
suri mayafi na fita.Iya ta ce, kai jama'a!Kai
jama'a!!Ni wanan yarinya ko dai zaki kai kanki
ne?Na ce ban fa san ko wane ne ba, ma ai
iya.Cikin gatse iya ta ce, ina zaki sani, shiyasa
kike ta sintiri tun daxu kin kosa ko wanene maya
zo?Na ce, sai na dawo.Ta ce, kada ma ki dawo ki
kwana can.Usman yana tseye a gurin da muka
tsaya jiya, na sameshi da sallama, muka gaisa ya
ce to kanwata nazo jin me kika yanke?Na danyi
shiru kamar mai nazari, ya ce, kada ki damu in
har baki sonshi ya ce babu komai.Na ce, ai ba
zan iya cewa bana sonshi ba ko dan iya, don
haka ka ce masa na amince.Usman ya ce,
Alhamdulillah, sai kin ji mu.Ranar nayi farinciki
har nafila nayi don godiya ga Allah, iya ta ce yau
kuma ibadar ce ta motsa har da nafilar dare?Ni
dai ban tanka mata ba, ta ci gaba, Allah ya sa a
dore, ina ta samun gadanga ce akayina san daga
yau shi kenan.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Washe gari yaje ya samu yaya zakari da yaya
Sulaiman yayi musu bayani, su kuma suka sami
dan uwan mahaifinsu dake nan layin kasuwa, a
nan unguwar mu'azu.Nan dai suka sa ranar zuwa
zariya gurin mahaifina don jin zance, Aliyu da
zasu tafi ya bada dubu hamsin ya ce har sadaki
duk yanda ta kaya shi kenan.Mahaifina yayi
murna har yana cewa wannan abu ai da ba sai
anxo ba, ita iya Sadiya tata ce, Aliyu ma nata ne,
da ba shi kenan ba sai dai muzo a yan
gayyata.Kawu ya ce, a a kun wuce haka, kuma
dole abaku hakkinku.Baba yayi ta godiya kafin
daga bisani ya ce bari ya kira dan uwansa.Sun
yanke sadaki dubu talatin sanan aka basu na
gaisuwa goma, sai dai suna dawowa suka fadawa
iya duk yanda akayi.Iya ta ce sam yarta tafi
talatin, su kawo goman nan hamsin ne sadakin
yarta, sanan gadanga ya ciko goma kudin
gaisuwa.Da kyar suka shawo kanta ta amshi
goman, sadaki arba'in kenan.Aliyu dai yana
zaune yana jin su yana kallonsu amma bai ce ko
mai ba.Suka ce an tsaida rana watan tara sha
biyar da shi, lokacin kuma ana watan shida.Aliyu
ya ce yaya Sulaiman lokacin nan bai yi tsawo ba
kuwa?Anawa ra'ayin nafi son wata biyu, iya ta ce,
har ka gama shiri ne zaka ce wata uku yayi maka
kadan?Aliyu ya ce, wane shiri ne mai zafi?Ba lefe
bane ko meye ne kuke cewa ya rage ba?Ta ce,
kana da gurin zama kenan ko nan zaka gyara mu
zauna?Ya ce, a haba dai, zan nemi gurin zama
duk a cikin wanan lokacin.Ta kalli Sulaiman ni fa
in nayi auran nan zataci gaba da karatunta ku
shaida wanan, in ya ce a a za a jimu.Aliyu ya ce,
na sani iya, nima ina son ta ci gaba da
karatun.Ta ce, to batun aure a barshi wata ukun,
sai kaga lokacin ya zama ba ka kammala da wani
abun ba har kake raina lokacin.Ya ce Allah ya
kaimu.Ina zaune cikin ajinmu bayan mun gama
zana paper din mu ta karshe, ina kallon yanda
yaran ajinmu suke ta jin dadi da murna tun da
muka baro hall din.Ta gumi na zabga ina
mamakin irin halin ya Aliyu, yau kusan sati hudu
da sa muna rana amma ko sau daya bai taba
kirana ba, haka nan kuma ko cikin gida ya shigo
ban isheshi kallo ba.Nima fa yanxu na soma
sarewa, anya kuwa mutumin nan yana sona?
Kullum iya sai tayi min gori, yau kam zanje in
nemi ya Usman.Bayan nan na cewa Anty Abida in
yadawo tace ya zo, ina son magana da shi, ta ce
to zata fada masa na ce ina su Ummulkhairi?Ta
ce suna makaranta.Da daddare kuwa sai gashi
ana sallama dani, na mike har ina tum tube.Iya
ta ce, sai karaftu kike sai kace a dakin Ajantina,
na san dai ba wanda kike son gani bane, dan
nasan shi ya fi karfin ya kiraki.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Nace, iya to ai ina so ne na ga ko wanene.Ta ce,
oho ke dai kika sani.Ina fita yaya Usman ne
kamar yanda nayi tsamani bayan mun gaisa ya
ce, Abida ta ce kin zo nema na.Na ce, eh.Na
sunkuyar da kaina ina wasa da yatsuna, na ce
dama nazo ne a kan maganar mu ne da ya Aliyu,
in abin ba zai yuwu ba gara mu hakura tun
yanzu.Ya gyara tsayuwa wani abu ne ya faru?Na
ce to ya Usman a haka ne za mu fahimci juna in
san abinda baya so yasan abinda bana so?Na ci
ga ba, bai taba kirana da sunan muyi zance dashi
ba, ko gida ya shigo ban ko isheshi kallo ba, shi
bashi da wani lokaci ne sai na aikin shi?Usman
yace ba wai zan goyi bayan shi bane amma
ninasan kina ranshi,ki fahimce shi, shi mutum ne
mai kishin kasarsa da aikin sa, shi yasa baya
samun lokacin kansa.Amma da zarar kin zama a
gidansa na san dole ya baki dukan lokacinki.Nayi
shiru kamar maganar ta shigeni, ammada na
tuna ko kallo na bayayi na ce, yaya Usman ka
san Allah ba dan aikin shi bane, ko kallo fa ban
isheshi ba.Usman ya ce, to bari zanyi mashi
magana.Na ce, don Allah kada ka ce nayi maka
magana, kada yayi tsammanin na damu da shi
ne.Usman ya ce, zanyi masa maga na da ma ai,
ba zan ce kece kika sani ba.Kusan sha dayan
dare Usman ya daga wayar Aliyu tare da yin
sallama, bayan sun gaisa Usman ya ce aboki
dazun ina ta kira baka daga ba.Aliyu ya ce, bari
kawai aboki, lokacin ina tsakiyar wani case ne
abin nan yana matukar daga hankalina tare da
bani mamaki.Ka san wani mutum dan kimanin
shekara arba'in aka kama yayi wa yar shekara
hudu fyade.Usman ya zabga salati tare da cewa,
wai aboki wanan wace irin masifa ce?Ko dai wani
tsafi ne?Aliyu ya ce, wa ya sani?Wannan fyaden
na kananan yara yayi yawa.Kullum sai mun sami
wanan case din wlh yanda abin nan ke mun zafi
a raina zan iya kashe irin wadannan mutanen,
don mugaye ne.Idan mata ne su je mana ga
karuwai nan,Usman ya ce, to Allah ya shirye su,
ya tsare mana daukacin musulmi.Aliyu ya ce,
amin aboki to kaji halin da nake ciki, lokacin da
ka kirani lafiya lau dai ko?Lafiya lau dama zance
ne ya kamata mu shirya muje muyi hira da
yarinyar nan ko?Aliyu ya ce, wace yarinya ke
nan?Usman ya ce, sai karinka yi kamar baka san
da zancen ba bayan nasan tana ranka.Aliyu ya
ce, tsakani da Allah sai ka tuna min.Usman ya ce,
ok, tunda yanxu iya ta yarda dole ka manta.Aliyu
ya ce subuhanalla? Dama wai Sadiya kake
magana?To wacce hira kuma zamuyi tun da na
rigaya an gama magana, sai jiran lokaci.Usman ya
ce, ai duk da haka za aje ayi hira ta san abinda
baka so don a samu zaman lafiya.Aliyu yayi yar
dariya.To ni ba haka tsarina ya ke ba, ina zaton
in har zanje gurin budurwa zan jene don ina
tallata kaina in in samu shiga,tonina riga na
samu shiga babu dalilin da zan matsawa
kaina.Usman ya ja tsaki kai dai bahago ne wlh, to
sai ka sai mata waya ko ta waya kunyi
magana.Aliyu ya ce, to yan zu dai kaine sarkin
yakinta ko?Suka sa dariya.Usman ya ce, da gaske
nikeyi, akwai wata waya da ake saidawa mai kyau
nan kusa daoffice din mu (MTN OFFICE) ya ke
aiki.Aliyu ya ce, ka suyo mata in kazo sai na baka
kudin, sanan kai zaka bata don har karshen satin
nan ban san lokacin dawowata, kafin ita ta tashi
na fita.Usman ya ce shi kenan.Washegari da
daddare ya usman yazo ya kawo mun waya wai
iji yaya Aliyu, inyi hakuriza mu rinka waya aikine
yayi masa yawa.Bani da zabi dole na hakura
tunda ga waya har da layin (MTN) ko da na nuwa
wa iya baki ta tabe sanan ta ce Allah ya sa
alheri.Tun da na karbi wayar ko flashing ba a
taba yi mun ba, ga dai lambarshi a ciki ya usman
ya samun duk da cewa har da kudi a layin nawa
nima cewa nayi ba zan kira shi ba.Sai dai in ta
kiran kawaye da yan uwa wadanda nake da
number su.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Wata rana da dadare naji Iya tana yi masa fada
cewa yana zaton haka za ayi auren ba lefe, biki
saura wata daya da kwanaki, amma ba a ga yana
motsi ba.Ya ce, abin ne ya shige masa, amma
gobe zai je ya sami matar ya sulaiman.Ita da
matar Usman Anty Abida sukai ta zaryar zuwa
kasuwa, saura sati biyu lefe ya kammala da dinki
da komai.Iya ta ce ya Aliyu ya bada kudin mota a
kaisu zariya, ni kuma nan kawaye na sun matsa
da batun anko, lokaci yana tafiya gashi ba zan iya
yi mashi magana ba.Aisha ta ce, kiyi wa iya
magana.Na ce, iya kwana biyu bata sana'a , bata
da kudin anko?Tab! Ba zai yuwu ba.Wayata na
dauka inyi kamar zan kira shi in fasa, Aisha ta
amsa na ce kada ki kira shi dan bai taba kira na
ba, ba wani kiranshi da nima zanyi Allah aisha ni
auren nan tuni ya fitan min daga rai.Ace kai kafi
karfin kazo sai dai abokinka?Aisha ta ce, Allah sai
na rubuta masa tex.Ina kallonta ta rubuta
masa.SALAM.INA FATAN KANA LAFIYA?KAYI
HAKURI KILA YANXU KANA CIKIN AIKI NA TSAIDA
KA, DA MA NAYI MAKA WANAN MESSAGE DIN NE
DON NA TAMBAYEKA A KAN MAGANAR ANKO,
DONKAWAYENA SUN DAMU SABODA LOKACI YANA
KAREWA.NA GODE, KA HUTA LAFIYA.Tana gama
rubutawa ta tura masa, maji amsa-maji amsa
shiru, nace kin gani ko?Ke ayi biki haka bani kara
masa batun anko.Aisha ta ce, niko yanda yake
nashi salon birge ni yake, na ce, au!Wulakancin
da yake min din ne yake burgeki?Tayi dariya, ai
ba wulakanci bane rayuwar sa ce haka.
Lokacin yana office din commissiner ya je a kan
nemansa da yayi tsam ya kame kamar yanda
yake al'adar yan sanda, sanan ya soma magana
cikin natsuwa ranka ya dade an ce kana nema
na.Commissioner ya dube shi cikin natsuwa
sanan ya ce da ma na kira ka ne a kan maganar
barawon shanu din nan da aka ce kaki yarda a
bada belinshi.Aliyu ya sunkuyar da kai don
girmamawa, yace ranka ya dade haka ne, naki
bada belinshine saboda bincike ya nuna shi din
ba karamin mai laifi bane.Daji suke shiga da
motoci suna kora shanayen fulani suna kwashewa
su kai kudu su saida, wanan kamawar ita ce ta
goma sha uku amma ba a taba mikashi kotu ba,
azzalumine na gaske,Commisioner yayi dan
murmushi sannan yazo ya dafa kafadar Aliyu ya
bubbuga alamun jinjina, san nan ya ce, Dan
Sanda mai kishi, lallai kasan aikin ka da ka tsaya
binciko wannan files din, ka tattarosu ka miko
min nan, ni nasan yanda zan kawo karshen
lamarinsa.Zan shigo gurinku anjima kaje.Aliyu ya
sara masa, sanan ya fito.Gaskiya in son samu ne
case din nan ya tsaya a hannunsa dan kam zaiyi
gogaiya da zalunci.Shigarshi office din sa kenan
sako ya shigo wayarsa, sai da ya zauna sanan ya
duba.Murmushi yayi bayan ya karanta, a fili
kumaya ce, ko me nene anko?(hahaha,kunjifa
dan rainin hankali inji,shin kuna ganin zai yuwu
ace baisan Ankoba,ai dai kayan yansanama
Ankone,kuma kala biyu, wasu su sa baki
kawai,wasu kuma baki da light blue ko? Cewar
ANaM Dorayi)
Ya kira layin Usman bayan sun gaisa ya tambaye
shi ko menene Anko? Usman yayi murmushi wato
kai dai in kaje ka shige caji ofis dinku shi ke nan
baka tuna meye a cikin garin.Aliyu ya ce, aboki
mu kuwa dake wanan ofishin mu muke da
labarin abunda ke cikin garin, amma ba wanda
ya shafi biki ba.Usman ya ce zaka bata kudi ne
kurum ta shiga kasuwa da kawayenta su zabo,
haka su ke yi.Aliyu ya ce, gashi ni kuma bana son
yawo bare kuma xuwa kasuwa, in dai zani ne in
zan je gidan zan tsaya nan wani super market in
sayan masu, guda nawa ake siya?Usman ya ce,
da ka basu kudin.Aliyu ya ce, ba zata kasuwa ba,
wanan shine ra'ayi na, zan siyo musu zani.Usman
ya ce shi kenan, sai ka suyo musu mai kyau.Aliyu
ya ce ina ruwa na da zabe, ni dai kawai in dau
zani.Don haushi Usman ko sallama babu ya
kashe wayar.Aliyu ko da wuri ya bar office din ya
bi ta kasuwa ya sai zaunnuwa kala uku ko
wanneguda bibbiyu ya nufi gida.Iya tana zaune
tana yankan kubewa ni kuma ina daga kicin ina
kwashe tuwo ina mulmulawa a leda ina sakawa a
kula ya Aliyu ya shigo da sallama.
Kusan kwana hudu ban sashi a ido na ba , da ya
zauna yana gaisheta.Ta amsa ya ce, ga zaunnuwa
anko ne suka ce ko menene ma?Ta dauki ledar
tana cirowa ta re da fadin kaine ka siyo ankon
gadanda da kanka?Ya ce, to duk ba zani bane,
shi nan sai su zaba.Ina kallo daga ciki kuma ina
jin su, tun kafin in fito zaunuwan suka tafi
dani.Ya ce, naki ne da nata.Iya ta ce, to mun
gode, da ma ina so inyi maka zancen gidan ne, a
ina kasamu?Ya ce, to ni dai nafi so a can kasan
layinku, gefen makabarta din nan, to ba a samu
ba sai na dawo neman na siyarwa, kudina
dakekasa yanxu za su iya semin gida, amma
albashin wanan watan da na wancan watan hada
mana za ayi.To ganin kurewar lokacin sai kurum
na barshi yanxun anjima zamuje mu ga wani gida
da yaya Sani da Usman wai ciki da falo sai kichin
da ban daki dubu dari da hamsin.Iya tayi shiru
tana nazari, can ta ce ina nufin kasan gidan su
babba ne?Ya ce ciki uku ne da kicin da ban daki
sanan ga filin da mutum zai iya fakin din mota
har biyu.Iya ta ce kuma nawa?Da sauri ya ce wai
miliyan daya da dari takwas.Ta ce, ina ganin zaifi
ka siya gidan in yaso sai a daga bikin.Ya dubi iya,
ai saboda bana son dagawar shiyasa na hakura
da siyan gidan.Iya ta ce siyan xai fi maka sauki
ka huta da biyan haya, auran kurum za a daga
ba.Ya ce ba dagawa za'ayi ba, abinda ya sa in an
daga za ayi asara da yawa.Abokaina sun kashe
kudi gurin kati mai tsada tare da wasu abubuwan
abokan aikina suma sun kashe kudi gurin shirya
bukin.Iya ta ce to, kana ji ko, yanda za ayi kawai
a daura auren da buki, sai ta zauna gida kafin a
gama gyara tunda dai nan a gida ne ba a dawa
ba, bana so ka rasa gidan nan ne muhalli a bariki
ba karamin rufin asari bane
Aliyu ya ce, shi ke nan sai ayi haka din bari zan
kira yaya Sani sai muje dake ki ga gidan sai a
biya.Lumshe ido nayi cikin jin dadin an fasa daga
bikin, kai naso in tare a gida na ranar amma baji,
buri na dai a daura auren, amma da iya ta so
kwafsawa wai a daga.Ya mike ya juya da nufin
fita ida nunsa sukasauka a kichin a inda nake, da
sauri na ce ina yini?Sai da ya dauke kai sanan ya
ce, lafiya.Har ya fita ina kallonshi.Iya ta katse ni
da cewa, wata rana sai kin gaji da kallon shi.Na
sunkuyar da kai kunya ta rufe ni, ban santana
kallona ba sa karya, in dai gadanga ne gaki ga shi
nan.
Pink din muka zaba ni da Aisha, sai dai muna
zuwa kasuwa aka ce dubu uku ce gashi kudin
aisha bai kai ba.Sai muka dawo gida da kyar
mamanta ta cika mata muka koma muka
siyo.Muka roki mai shagon ya ajiye mana da mu
siya da yawa.Yamma tai mana a kasuwa gashi
ana wahalar mota.Muna tsaye a kan titin kano
Road, na ce bana son magariba tayi mana tun
daya muka fito gashi iya ba ta san mun koma
unguwar mu'azu mun dawo kasuwa ba.Aisha ta
ce, sai dai muje mushiga dambancen ko za mu
samu, na ce zamuje.Ta kan legas street wani
lokacin ba a wahalar mota.Muna tafe wai wani
mai mota ya tsaya, 'yan mata kuzo mana.Na ja
tsaki tare da kara sauri, Aisha ta ce, lafiya?Ya ce
rage muku hanya zanyi.Na ce Aisha, kema kika
tsaya tambayarshi.Haka mutumin nan ya ci gaba
da bin mu yana magiya, duhun magariba ya
shigo na ce Aisha ko dai mu tsayar da mutumin
nan ya kai mu gida?Don ina tsoron fadan iya.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tace, nima hakan zan ce,dai dai lokacin ya sake
cewa ku kuwa tunda na ce Allah ya kamata ku
saurare ni, dan kun san mugu dai ba zai yi muku
sallama ba.Aisha ta ce unguwar Mu'axu muke.Ya
ce, ai hanya ta ce ni kuma Nasarawa zanje.Cikin
far gaba muka shiga motar ya ce mun a'a ke
dawo gaba dai ki nuna mun hanya , na koma ga
ba.Ya tam bayi sunayen mu, ina shirin xollo masa
karya sai naji Aisha daga bayana ta ce, ita Sadiya
ni kuma Aisha .Ya ce, masha Allah , sunaye masu
ma'ana.Ya dube ni, Sadiya dan ke fa nake ta
wanan bibikon sai aka ci sa'a kina da sunan
matata, ni sunana Auwal.Hakika jin sunanki ya
kara samun sonki Halimatu duk wace ta amsa
wanan sunan takan zama mai hakuri da hange,
bata rani bata daukar raini, macen rufin asiri zan
so na sake samun ki.Na ce matar taka ta hada
duk wanan halin shine zaka yi mata kishiya?Ya ce
jin dadin halinta yasa zan kara.Aisha ta ce bakai
mata adalci ba, au, ke fa sunan uwata ne ke da
zaki tayani yakin neman shiga?Aisha ta ce, nan da
sati biyu ita ma tana dakin angonta.Da sauri ya
ce, da gaske?Ta rantse mashi tare da fada mashi
ashobe muka zo siya.Daga nan nayi shiru bai
sake magana ba harya shigar damu layin kasuwa,
na ce sauke mu a nan ma mun gode.Sai mu
karasa.Ya tsaya muka fito, ya ce marya ba
godiya?Na dawo dai dai saitin shi na ce, mun
gode, na ce kayi hakuri muna sauri ne dare
yayi.Ya ce shi kenan, Allah ya baki zaman
lafiya.Juyawar da zanyi in tafi tare da cewa amin,
sai maganar ta tsaya, sa kamakon ya Aliyu da
nagani tsaye yana kallon mu.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347




Zaharaddeen Shomar
Whatsapp  08168575100



Darajar Yayana 1-03
Posted by ANaM Dorayi on 10:51 PM, 14-Mar-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
__________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Duk da kasan cewar duhun magariba ba zai sa in
kasa gane bacin ran sa ba.Gaba na ya fadi, irin
wanda ban taba yi ba.A fili na furta na shiga
uku!Aisha ta ce, me nene?Bakinta yayi shiru
sakamakon ganindatayiwa abin da nagani.Kusan
minti biyu yana kallo na, ko da banga fuskarshi
sosai ba na san a daure take .Sai yaja tsaki sanan
yayi babban titi abin shi.Muka kwashi sauri ni da
Aisha inayi ina waiwaya shi, a zuciyata ina cewa
yau na kade, Aisha ta ce muyi wa ni kin ga da
sauki tunda mama ta san mun xo mun koma
ne.Munyi sallama iya tana tsaye tsakar gida tana
cewa, kai ni wadan nan yara ko ina suka shige
ne?Kai Sadiya bata da hankali, ki fita tunda
hantsi har magariba, to ko kasuwar kwari ta kano
suka je?Ko jiran mu gama sallamar bata yi ba
bare ta amsa ta hau fada, Aisha ta shiga jero
mata dalilan mu, ta ce ku refa mun baki, ko
kasuwar kano kuka je ya ci a ce kun dawo tadubi
Aisha ta ce uwaki ta ganki hankalinta ya kwanta,
masu shegen rawar kai.Ta bini ke kuma, sai ki
jira xuwan gadanga don tun yamma yake shige
da fice bai ganki ba, har dai ya kare ya ce ita
wanan yarinyar ina tayi ne?Ina son ta hada mun
abin shan ruwa ina azumi, na dafa kirji na ce, to
me kika ce masa?Ta harare ni karya zan masa?Ce
masa nayi kinje kasuwa sayan anko, yayita fada
me yasa na barki don baya son xuwanki kasuwar
ne yasa shi siyo ankon dakansa.Na ce, na
kade.Na dauki buta dan yin auwala, a xuciyata
inatuno yanda ya ganmu muna fitowa a motar,
da nayi salla nayi addu'a Allah ya yayyafawa abin
ruwan sanyi.Da a zamar sa ya shigo da sallama
ga ba naya fadi da sauri, don haka ma ban iya
amsa sallamar ba, dakinsa ya shiga bayan wasu
mintina ya fito tsaf tsaf cikin shirin fita.Ban taba
ganin dansanda da kaki yake masa kyau matuka
ba irin ya Aliyu, kan cinya ta na dora fiskata
ganin ya nufo dakin Iya.Ga zato na da ya karaso
zai zabga min mari,ina jiyoshi yana cewa iya ya
tafi sai da safe, ta ce, can zaka kwana?Ya ce eh,
ta ce, Allah ya tsare mun kai, ya kuma bada sa'a
ka yawaita adu'a.Ya ce to ina yi iya, zan kara
kulawa.Ya sake wuce ni ya nufi fita, da kallo na
bishia raina na ce, zaki na maza sarkin jin
kai.Nan ya tafi ya barni da kamshin sa sai dai da
dukkan alamu yana fushi dani.Da dare ina cikin
daki kwance kan gado, juyi kawai nake zuciyata
tana mun nazari a kan kallon da ya Aliyu zai
mun, ganin da yayi mun a motar wani kamar in
kira shi in bashi hakuri, sai na fasa.Na rubuta
sako kamar haka:YA ALI DON ALLAH KAYI
HAKURI IN NA BATA MAKA RAI.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ban jira amsa ba don nasan ba samu zanyi ba,
amma ga mamaki na sai naji sautin shigar
sako.Da sauri na bude na soma karantawa.KUL!
BANA DAYA DAGA CIKIN MUTANEN DA SUKE
DAUKAR LOKACIN AIKINSU, SUNA HADA SU CIKIN
LAMURANSU NA DABAM.SAI KI RIKE WANAN DAN
GABA.Na lumshe ido ina son yin nazari a kan
kalaman nasa, na san dai kul! Dan gargadi ne ya
yi mun kenan ba ya bukatar a shigar masa
lokacin aikin sa.Nayi juyi ina mai yiwa kaina jajen
auran ya Aliyu, yanxu auren ya fi ban tsoro fiye
da birgeni.Washegari sukuku na tashi,Iya ta ce
jiya kuna can kuna gararin yawon ku mahaifinki
ya zo yayi ta jiranki har ya tafi.,na ce kash!Ko da
yake na san dole ya dawo kafin bikin.Ta ce ba
dole ne ba , kudi ne ya kawo sadakin ki da akayi,
sai gudumawar su dubu hamsin.Na ce hamsin
iya?Yaushe hamsin zatayi mun kayan daki?Ta ce,
ina laifi, mahaifinki fa yanxu ba aiki yake yi ba,
tunda yayi ritaya sai dai dan noma.Shi ko noma a
kasarnan yanxu dai ba a dauki maiyinsa da
mutunci ba, shine koma baya a gurin gwamna
ti.Su ba ga taki ba ba ga tallafi ba, dan
gurarenda suke nomawan ma kwanaki
yakecemun gwamnati ta ce zata amshi wurin.Na
ce iya gurin da ma ba nasu bane?Ta ce, Sadiya
kenan, dama talaka yana da guri ne a a wanan
karnin?Sai wanda Allah ya taimaka ya kuma tsaga
da rabonsa.Gurinka da takardu da komai za a
amshe maka,dubu hamsin ai yayi kokari.Na ce
haka ne Allah ya rufa asiri, duk abindaza ayi dai
dai karfinmu za muyi.Iya ta ce, in sha Allahu sai
kin zaba yata.Jugun nayi ina kallon Iya, baiwar
Allah nan tana sona fiye da yayan da ta haifa,
abin da take min ko ita ce ta haifeni sai
haka.Kusan duk dare sai bacci na ya katse, in yi
kiri kiri ni kadai cikin xullumi irin zaman da zanyi
gidan ya Aliyu.Na gama duk hashashen da zanyi
ban hango jin dadi ko kulawa a cikin auren ba, sai
yanxu na gane nufin iya ta guje mun wahala ne,
gashi lokaci ya kure mun bani da damar in ce
bana so.Kusan karfe uku na rana ina zaune ina
yankan farce na tare da gyarawa, sautin shigowar
sako naji, sharewa nayi amma naki dubawa don
nasn MTN ne.Sai kuma wata zuciyar ta ce mun in
duba, gaba na ya fadi ganin sunan ya Ali, na
duba cewa yayi.KI SAMENI A DAKI NA
YANXUN.Duk da cewa ina fargaba sai da na dan
sakemurza hoda tare da man lebe, sanan na
fesaturare.Iya ta kalle ni tana zaune gefe tana
gyaran goron ta da yayi tsutsa
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta ce, to mai aljanun kwaliya don a sarar turare
ana zaune kin hau feshe feshe.Na ce, iya yaya
Aliyu ne yake kira na, ta ce ya shigo ne?Na ce ina
zato, amma ta waya ya turo min.Na suri hijabi na
na nufi dakin gabana na matukar faduwa.Nayi
sallama ya amsa, na shiga kallo daya nayi mashi
yana sanye da gajeren wando da(t-shirt) fara sol
na sunkuyar da kai sanan na tsugunna tare da
cewa gani yaya.Sam bai ko kalleni ba, hasalima
danna wayarsa yake abinsa, nayi kusan minti uku
sanan ya ce (ba tare da ya kalli inda nake ba).Ya
sunan saurayinki da na ganku jiya ya sauke ku a
mota?Ban san lokacin da na zauna ba don tsabar
tsoro.Sanan na ce, ba saurayi na bane.Lokacin ne
ya dubeni cikin wata irin harara da murya ta isa
ya ce, ba karamin zunibi ba ne wajen dan sanda
mai laifi yaki amsa laifinsa.Kar ki raina hankalina
kokaryata ni, sunansa kurum na tambaya.Murya
ta ta soma rawa alamun kuka zai kubuce min, ya
dora yatsansa dan manuni akan leben shi ta re
da cewa, shhhhhi!Kul!Kika min kuka, ko rawar
muryar nan bani son ji.Ya ci ga ba duk da
dadewarku da shi baki san sunan shi ba?Nayi
kokari na kalaci miyau na hadiye shi tare da
kukan da ke son kwace min.Na ce, yau ne na
soma ganin shi, yana ta binmu yana rokon mu
wai mu tsaya muka ki, toda muka ga duhun dare
muka yarda ya kawo mu, don ana wahalar mota
kuma kudin mu ba zai ishe mu mu hau achaba
ba.Ya maida kanshi ya kwanta rigingine, ya kuma
ci gaba da danna wayarshi.Kusan minti biyu
sanan ya ce, wa yake so cikin ku da yake ta
binku?Da dama yana ta binku ne kawai ya rage
muku hanya duk da dimbin jama'ar da ke jiran
mota a gurin?Tsoro ne da faduwar gaba suka
karu gareni, cikin in-ina na ce, am.. Em.. Haka ya
ce wai ni yake so.Da sau ri ya tashi zaune, cikin
daga murya ya ce, menene?Da sadakin nawa a
gurinki?Da sauri na ce, ai Aisha ta ce mashi aure
za ai min.Ya zuro kafafunsa kasa, oh, da ke baki
fada mashi ba?Na ce, ta rigani yin mga na ne
shine dalilin da ya tsareni da idanunsa.To me
yace da ta fada masa?Haka ya ce Allah ya sa
alkairi.Ya sake komawa ya kwanta.Jeki zan
bincika, in na samu zantukanki ba gaskiya sai kin
sani.Zaraf!Na mikexan fita sai ya sake cewa, me
ya fada miki lokacin da zaki tafi ya kiraki?Na ce,
ya ce ne ba godiya?Shine na ce mun
gode.Tamkar ba shi na bawa amsa ba, don bai
komotsa ba bare ya dubeni.Ina ta tsaye har
lokacin da ya kula dan kansa, sanan ya ce, kina
da wata maganar ne?Na ce, a a.Ya ce, to kin
tsaya min a kai.Na tabe baki a raina na ce,
masiffafen ikon ka zan dauke shi kuwa?Tsuntsun
dayaja ruwa......ANaM)Na fice, duk da ba lokacin
zafi bane jikina sharkaf da zufa, kan kujera na
zauna ina maida numfashi.Iya ta ce, me ya ce
miki ne?Ko abinci zai ci?Na ce a'a mun dai yi hira
ne.Ta ce, shine kika yi wujiga wujiga sai ka ce
kunyi dambe?Sakon da ya kara shigowa wayata
shi ne ya hana ni baiwa iya amsa, ko da yake
dama bani da amsar.Sunan shi na kara gani na
bude sakon, cewayayi.NA MANTA BAN
GARGADEKI BA, DOMIN KE TAWA CE TUN KAFIN
NA BADA SADAKI, BARE NA BIYA KUDINKI.Naaje
wayar a gefena, na zari buta zuwa ban daki ba
don zanyi wani abu ba sai dan inkaucewa tam
bayoyin iya.Sauran sati daya biki iya ta zauna da
duk yayanta, sun shirya yanda za su gabatar da
komai cikin tsari.Ina tsakar gida ina jiyo su, iya ta
kwala min kira sadiya!Na amsa, zo kije gidan
Hajiya Umma Rimaye matar Likita Hassan ki ce
mata tayi wa maiyin alkaki magana?In sunyi
maganar nawa ne kudin?Na ce to.Na shiga dakin,
kaina sunkuye dan harda ya Aliyu a gurin, ta ce
maza-maza ki dawo, dukkwanakin nan na kula
baki son aike.Ina shiga uwar daki na tura mashi
sakon cewa iya ta aikeni, ya bude ya gani amma
sai ya ajiye wayarsa, sanan bai ce mun kala
ba.Neko sai nayi zamana gefen gado, jin shiru
ban fito na ta fi ba iya ta ce, kin tsaya kwalliyarki
ta jaraba ko?Na ce, a a.Ya san shi nake jira, sai
ya ce ba aikenki akayi ba kina jiran menene?Na
fito na tafi.,ya Usman ne ya kawo mun katinan
bukin a ranar da dare.Lallai su na kula biki zasuyi
na sosai.Farko zasuyi walima bayan daurin aure,
sai kuma dinner, sanan akwai police day, shi
kuma washe garin daurin aure zasuyi shi,
damisalin karfe uku.Ni da Aisha da Fatiman ya
Sulaiman muka shiga rabon kati.Ana saura kwana
hudu biki, Anty Abida matar Usman ta kirani ta
waya naje, bayan mun gaisa ta ce, kina dan
gyaran jikinki ko?Na ce da me?Ta ce dan shirye
shiryen mu na mata.Na ce, a a ni bani da kudi
anty.Anty ta ce, baki tambayi ango ba?Na ce
anty, ni ba zan iya tambayarshi ba.Nan take ta
kira wayarshi ta sa handsfree, ya daga tare da
amsa sallamarta, ya ce madam ya akayi ne?Ta ce
ango, ango ka sha kamshi.Ya ce bansha ba
tukunna.Suka yi yar dariya, ta ce dama maganar
gyaran jikin amarya ne, ka san anayi.Ya ce ban
sani ba gaskiya wane irin gyara kenan?Ta ce
dogon bayani ne yanzu dai kudi muke bukata.Ya
ce nawa ne?Ta ce talatin ne kacal ba yawa.Ya ce
madan kuna so sai kun tsotse ni tas! Ya fadi? Ta
ce tashi muje gidan Hajiya Umma Rimaye.Na ce,
a a, ita ce mai gyaran jikin?Ta ce, eh.Nace na ga
iya gurinta ta aikeni in kai kudin alkaki.Ta ce, eh,
ai kawarta ke yin kayan buki, ita dai ke gyaran
jiki.Na ce gaskiya tana da kirki.An hada kayan
dilka masu kyau an lailaye ni da su, duk da
kasantuwata fara ba karamin kyau nayi ba,
kwana uku zanyi ina zuwa.Kuma ran na uku za
ayi mun lalle.Iya da kanta tayi ta yabon kyan da
nayi, haka naita zuwa ranar da na cika kwana
uku ta kira mai zanen lalle inda aka zuba min
fulawa.Abinka da fara, kowa sai tanka ni yake ta
ce,tunda gidan su yana da girma kawaye na suzo
nan a yi masu na su lallan na ce, to na
gode.Abida ce ta amso kudin ta bada, Usman
shine ya bamu kudin walimar mu.Wani abun da
ban gane ba duk dare sai iya ta dama mun wata
fura wace ita ta hada kayan hadin da kanta,
sanan ta va inno yar sokoto ta daka mata.Furar
tana da danko, furar sai kace magani gashi duk
yawanta in ta dama sai ta tsare nina
shanye.Sanan da safe ta xuba gero a turmi ta
surfe shi, wai zata tara na dama kunun safe
saboda yan buki, amma tana gamawa zata wanke
shi ruwan farko ta tsareni sai na shanye ina kuka
ina komai.Tun ana jibi daurin aure wasu suka
soma sintirin taya aiki, makota dangi duk sun cika
gidan, yan gefen su iya da na baba na.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
An yi mini kamu inda aka feshe mu da turareni
da kawaye na kamar yanda muke yi a nan
Kaduna.(Ina yan kadunan,yakukeyi kubamu
Labari,ANaM) Gidan matar yaya sani mukakwana.
Zariya za a daura aure amma an ce ni ba saina je
can ba, tunda ba tarewa zan yi ba.Na nufo gida
dan kwasan kayan da zanyi anfani da su in nayi
wanka.Su ya Aliyu na ta shirin tafiya gurin daurin
aure, an kawo motoci.Ya Aliyu ba ya gurin sai
abokanan sa sun taru a kofar gidan mu, kunya ta
kamani, na ja gefen hijabina na rufe fuskata.Ina
jin wani cikin su amaryarmu ki bude idonki kada
ki fadi mana.Sai naji muryar Usman yana cewa,
sarkin kunya kenan.Zan shiga soro (zaure) naji
mun zabga karo da wani, da sauri na bude
fuskata, gaba na ya fadi.Ya Alyu ne har wayarsa
da ya na magana tafadi.Da saurina tsugunna dan
dauke, tare muka hada hannu zamu dauki wayar.
Hannunshi ya taba nawa.Ba ni kadai ba, na kula
harshi yaji abin da naji, tamkar wutar lantarki ta
jamu.Shi ne ya janye hannunsa, na dauki wayar
na mika masa tare da furta kayi hakuri.Kala bai
ce ba, sai amsar wayar da yayi ya tafi, na bishi
da kallo yayi matukar kyau cikintsaleliyar shadda
mai ruwan suminti, tana tamaiko.Kamshinsa ya
cika zauren, a fila na ce na more muji, na juya na
nufi ciki.Sai tsiya ake min Amarya-amarya.
Munyi walimama inda nai ta canjin kaya, kusan
karfe hudu Aisha ta miko min wayata, sa ko ya
shigo na bude kamar yanda na zata ya Aliyu ne,
in da ya ce, "Alhamdulilla" na kalli Aisha dubi
abin da ya ce, ta karanta da murmushi ta dube
ni, kin zama tashi dole yayi hamdala ga
Allah.Nace, Allah ya sa haka yake nufi, wanan
danjin kan?Sakon shi ya sake shigowa musalin
karfe bakwai na safe, na idar da sallah ke nan,
ya ce kije gidan Usman da ga can za a dauke mu
ni da ke dan zuwa dinner, kawayenki kuma su
xama cikin shiri su tsaya a kofar gidan mu,
please, banda marasa hankali, bayan sallar isha'i
za a tafi.Na ce, Aisha kinji mutuminki ko?Ta da
fani, me ya ce?Na mika mata wayar ta karanta ta
dube ni.Ki dauki kayanki da zaki sa ki tafi can ki
shirya, ni kuma zan kula da sauran kawayenmu a
nan dan mu shirya cikin tsari.Kinsan su ya Aliyu
masu aji ne ba irin tarkacen nan suke so ba.A
gidan Abida nayi salar isha'i sanan na shirya da
taimakon abida da yake ita ma in dai kwalliya ne,
matirial ne na saka riga da siket ruwan madara
da ratsin kore.Sai nesa kore takalmi da jaka duk
koraye, sarka kuma ja sai muka yi anfani da ja a
kwalliyar fiska ta gashi ya sha gyara, da ta shiga
fesa mun turare sai da na soma atishawa, kaloli
ta samun masu kamshi.Da na kalli kaina a
madubi sai na ce Alhamdulillah ni ce haka?Ita ma
sai yaba ni take yi, ta shirya, sun zo daukarmu
Usman ya ja motar suna gaba shida Abida ni
kuma a ka bude mun baya ashe ya Aliyu na cikin
motar.Sanye yake cikin lallausan yadi ruwan
madara, kalar kayana ke nan hular kube ce kai
yayi kyau matuka, sam bai kalleni ba.Waya ma
yake yi motar tana tashi wutar motar motar ta
dauke dai dai lokacin kuma ya gama wayar.A
hankali motar ke tafiya motar shiru sai sanyin
(AC) da wani dan sauti dake tashi a raidiyon
motar mai sanyaya rai, ban san ko wacce zabiya
bace mai wakar ba, tunda ba sauraran wakar
turanci nake ba.Sai dai wakar tamasoya ce,
kalamar zabiyarsun haddasa min shiga wani irin
yanayi, na lumshe ido tare da jingina baya na a
kujerar motar.Kamar daga sama naji saukar tafin
hannunsa a saman nawa, da sauri na ware
idona, a zatona bayanan zabiyar ne suka sani
dan karamin mafarki.hhhhh,kujita da shiririta..
Amma sai naji yatsunsa suna ratsa tsakiyar nawa,
lokaci guda kuma ya matsatse su tsam.Na dube
shi da sauri sam ba zaka ce shi bane.Don har
yanxu yana fuskantar inda dama yake fuskanta,
na kalli hannuwa na ma duk da cewa a kwai
karancin haske bai hana ni ganin sarkakun
hanuwan namu ba.Na sake mai da baya na jikin
kujerar tare dasauke yar karamar ajiyar
zuciya.Lumashe ido nayi ina tuno karon da
mukayi dashi da zun, goshi na da hanci na suka
dakikirjinsa.Na tuna hanuna da nasa suka hadu
wajen daukar wayar.Hannuwa na farare sun sha
lalle, na lura da yanda ya tsurawa hannuna ido
na yan sakwanni a lokacin. A raina ina ta mamaki
da tam bayar kaina, shi wanan ya canza daga jin
kan ne?Koko isa ce tasa shi yin haka?Wata zuciya
ta ce koma me nene mijinki ne a yanzu.Tsayuwar
motar ne yasa ni bude ida nuna.A zatona in zai
fita dole ya sakar min hannu,amma har muka fito
hannuwan mu sarke, a haka yayi ta daga waya
na kalli gurin da muka zo, an rubuta Cristal
Garden da wani rubutu mai yi kala kala na
wuta.Usman ya shiga ciki ya fito sanan muka
shiga tare.Dam gurin ya cika da mutane an
wadata ko ina da kayan ciye ciye da na shaye
shaye, naga muta ne manyan mutane da banyi
tsammani ba.
Anci ansha kuma anyi wasa da kudi, sai dai duk
yanda abokan ya Aliyu suka so muyirawa yaki ko
mikewa tsaye.Dan haka duk wanda ya matsu da
ya yi mana liki sai dai ya ishe mu a kan kujerar
mu, abokan shi da kawaye na sun sha rawa.Sai
kusan sha daya a ka tashi, mu kam sai sha biyu
sanan muka tafi don sai da aka kwashe kowa.A
kofar gidan mu motar ta tsaya, na yunkura zan
fita, sai naji ya dafa hannuna, wato ya dora
hannunshi a kan nawa.Na kalleshi shima ya kalle
ni, dai dai lokacin Usman ya fita, da ma mun
sauke Abida a gida.Aliyu ya ciro wayarshi ya
haska fiska ta, ya cire hannunshi da ke kan
nawa, ya dora a kan kuma tuna ya shafa har
zuwa dokin wuya na.Sannan ya juya bayan
hannunshi ya shafi haba ta, dole na lumshe
idanuna abin sai kace a mafarki.Ya tsansa dan
manuni ya saka ya gewaye lebuna na, na bude
ido ina kallonshi, murya kasa kasa ya ce, ki bar
wayarki a kunne zan kira ki.A jiyar zuciya na
sauke, sanan na amsa a kasalance to.Tsakar
gidan mu cike da mutane duk sunyi shinfida sun
kwanta, kasancewar lokacin damina ne amma
anyi kwana biyu ba ayi ruwa ba.Don haka gari
duk ya dauki zafi.Na nufi uwar daka, nanma duk
jama'a ne kwance, gado na dai ba kowa.Na cire
kayan jikina nai daurin kirji sanan na fada kan
gado.Iya can na varo ta a falo tana yin sallar
nafila, a rai na na ce iya koda biki ba a daga
kafa.Filo na dauka na rumgume ina tuno
abubuwan da suka faru yau, tamkar almara ji
nake yau na zama mace sosai.Karar ringing din
waya ta shi ne ya dawo dani cikin hankali na, na
dauka cikin faduwargaba na ce salamu a
laikum.Muryarshi can kasa kasa ya amsa sanan
yace ke da waye ne a nan?Na runtse ido dan
yanda muyarshi take ratsa dodon kunnena, na ce
ni da mutane amman sunyi bacci sunyi shinfida
ne a kasani a gado nike, ya ce ok, kin san me
yasa na kira ki?Na ce a a ya ce, saboda mu
fahimci juna...
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347.
A raina na ce abin da ya kamata a ce shine a
farko ya koma karshe.Tamkar ya shiga raina.Ya
ce kila kiga abun babu tsari ko?Kafin na bashi
amsa ya ci gaba.Ni irin nawa tsarin kenan, kina
jina?Na ce eh.Yace to yanxu sai ki fada mun
dokokinki kafin kiji nawa.Da sauri na ce ya Aliyu
ai bani da wata doka sama da ta Allah da
manzonsa, wada suka tsara ita ce abin bina doka
ta ni kadai in bika.Gud to me kike so me bakya
so?Zan so in soma jin naka yaya, tunda kaine
babba.Ya ce, to da farko dai bana son kazanta,
duk inda zan shiga a gidan bana so in shaki wani
wari.Kuma bana so in ganki babu tsafta ko in
shaki wani wari daga jikinki, sannan ina son
komai a kan lokaci.Na san kin fi kowa sanin ni
dan oya oya ne, komai cikin hanzari bani son
kasala, bana son musu ko gaddama.Abu na kusa
da karshe bana son duk wani abu da zai shiga
lokacin aiki na, ina fata kin fahimta?Na ce eh.Ya
ce yan zu sai inji naki.Na ce, ni dai bai wuce uku
ba, duka da zagi ne bana so.Sai nayi shiru.Ya ce,
ina jinki, saura daya.Na ce imm.... Bashi kawai
ma.Ya ce a a, ki fada in nayi maki cikin rashin
sani fa?Bana son mu munafunci juna,fadamin
duk abinda ke ranki da xuciya daya.nace
amm...dama kishiya ce bana so dai,kuma bamuyi
sabo daxan fada maka ba.shi kanshi shiru
yayi,nasan yana mamaki ne don bai zaci jin haka
ba,a zuciyarshi shi kamshiru yayi saidai bai ji
wani mamaki ba saboda yasha samun case din
mata akan kishiya.ganin kishiya ce abu na karshe
da mata suka tsana.nima shiru nayi gabana yana
ta faduwa,tsai din dana ji araina na raya cewa
magana xai dankaramin mara dadi,can yace ba
xan yi miki alkawari ba in na duba cewa komai
na rayuwata rubutaccene tun fil'axal kamar
yanda yake ga kowa.kifahimta,baxan taba yi miki
karya ba,don kawai kiji dadi.sai dai shawara daya
xan baki,kiyi kokarin tsare duk hakkokina,ta yiwu
in kinyi hakan bazaki rage gurbin wata ba
Kuma kila baxan ji sha'awar karawa ba.(Lallai
yaya kazama abokona,muna da ra'ayi daya
dakai, dan haka me sona nima namiki nasiha
makamanciyar ta Yaya Aliyyu,kiyi kokarin
kyautatawa,tayanda zaki rufe idanuna daga ganin
dukkanin wata mace da matsayi irin na soyayya
bayan ke. ANaM Dorayi)
Nayishiru tabbas nasan gsky yafada,amma kishi
ne daninasan wanan tundaga ranar da kunnena
yaji ya Aliyu ya furta yana son aurena.can kasan
xuciyata tunani ne kada wata rana yace xai so
wata har ma ya aureta.duk sauran samarina da
duk wanda yaxo da niyyar aurena nakan fada
mishi koda na aure ka banason kishiya fa.Toh shi
xakin nawa ina naha fuskar fada masa,shine sai
yanxun...ya katse tunanina da cewa,nasan baki
fahimce ni ba akan batun kishiya,don haka a aje
zancan gefe muyi mai amfani.nima naji abinda
bakiso zan kuma kiyaye insha Allahu.kiyi baccinki
sai dasafe kar ki manta gobe akwai ranar yan
sanda.bikin da suka shirya mana,ina fatan zakiyi
shiri?muryata sarke nace Allah yakaimu goben.
shine ya katse wayar sannan nakashe tawa na
kwanta,kalamansa ne ke yawo cikin kaina na
damu da bai min alkawari cewa baxai min
kishaya ba har bacci yayi gaba dani.(kabwata duk
lokacin da saurayi yace bazaimiki kishiyaba to
kisani hakan mafificiyar karyace a hasashena,pls
kabwata karkisa saurayin yayimiki wannan
alkawari kawai dan gudun bacin ranki,ANaM)
Ya aliyu ya iya magana cikin natsuwa,kai inason
gayen sosai.
Dasafe kin fitowa nayi ina yin sallah asuba dama
komawa nayi nacigaba da bacci. da Iya ta tashe
ni sai na langabe nace mata kaina ciwo yake yi
nan ko banason tashine in ta aiki ga mutane. sai
kusan sha biyu sannan na tashi nayi wanka na
karya.Aisha taxo muka sha hira anan ma muka
xabi kawayanmu da zamu je bikin anjima
dasu.yau kam shigar Green da Golding nayi
nawani leshi mai kyan gaske,abinka da farar
mace kayan sun dauke ni duk da cewa wai farin
ne yacece injiwasu
Duk yau ban sa shi a idona ba sai yanzun da za
mu tafi., yau kam gadanga kusar yaki kakinsa
yasha na yansanda, ya iya aje hularsa a kai
tamkar sai da ya yi course din sata,wani dan
sanda ne ya jamu zuwa wajen, guri yayi
guri,Usman shi ya taho da sauran kawayena,
Police band sai tashi take ga wasu yan sanda
suna ta bin kida fareti. gurin zamanmu na
musamman muka nufa înda masu kidan suka
dafo bazanmu da kida. ya Ali da abokansa da
fareti suka yi tafiyar har zuwa gurin zaman har
wani yana cewa yakamata matar dan dan sanda
ta îya fareti itama . sun yi wasa kala kala har
wani wasan su wai lokacin suna makaranta suna
cin garin kwaki,anci ansha anyi rabon
abubuwa.sai bayan magriba muka dawo
gida.karfe sha biyun dare dai dai wayata ta soma
ruri da sauri natashi nadaga yace xo mana
natashi xaune na kalli shashin da Iya take, tadan
rumtsa kafin lokacin sallarta ya karato,Na tashi
sadaf-sadaf tamakar munafuka nafita, a kofar
daki nayi sallama, ya amsa na shiga.Kwance
rigingine na same shi yana danna wayarshi,
jikinsa sanye da farar singileti tareda gajeran
wandonta.Nayi saurin dauke kaina don kunnyar
ganinshi a haka.Na rusuna kaina a kasa ga ni
yaya ba tare da ya dube ni ba ya ce, tun cake
din da kika bani a baki dazu gurin party nan ne a
ciki na,yun wa nake ji.Na dube shi me zaka ci?
Shima sai lokacin ya dube ni, me kika ga ya dace
in ci?Na ce, ko za ka fara shan ruwan zafi tun da
ka jima baka ci abinci ba, saboda cikin ka
yawarware?Ya ce to yaya za ayi, na samu ruwan
zafin?Na ce sai na dafa maka, na mike tare da
ajiye wayata a gefe na nufi kicin, ina kunna risho
naji takun tafiya, sai ga iya tsaye a kaina ta ce,
na farka ban ganki ba lfy kika kunna risho?Na ce,
yaya ne ya kirani a waya wai yana jin yunwa shi
ne zan dafa mashi ruwan zafi , ta ce, hum!Ki dai
kiyayi kanki, kuma ri rage wanan barin jikin,
sanan kiyi maza ki dawo daki na ce, to.Ina
komawa dakin dauke da dan flaks dinsa na
ruwan zafin na same shi yana danne danne cikin
waya ta, na juyo na jawo kofi zan zuba masa ya
dube ni baki da numbata a she?Na ce ina da ita
mana.Ya ce in gani.Ya ciro number ya miko min
wayar, na amsa na danno sunansa inda na sa ya
Ali, ya ce ok, bani ruwan zafin, na zuba a kofi na
hada masa sanan na mika masa.Sai da ya amsa
ya kurba sanan ya ce, amma na zaci cewa na
wuce wanan matsayin na yaya.Na kalle shi eh
haka ne.Ya dauko wayarshi ya danna ya nunu
min numbata a wayarshi.Yayi saving dinta da
suna my choice, a fili nafurta my choice, ya ce
nima sai a canja min suna ko?Muka kalli juna
cikin ido sannan na soma danna wayata, ya ce
zauna sosai mana, sai kace ba dakin mijinki ba?
Na zauna sannan na soma rubutawa na sa
honey, sai na goge na sa darling, shima na goge
sai kuma na rubuta sweet Aly.Zan goge yayi zaraf
ya amshe wayar ta re da cewa in gani me kike
rubutawa kina gogewa?A fili ya ce sweet Aly.Yayi
dadi ki barshi haka.Ni kuma tuni na sunne kaina
cikin cinya ta don kunya.
Ya ce ai babu wani sauran kunya tsakanin mu,
kinyi alkawarin za ki rinka kirana sweet dinki har
gaban kowa?Na dubeshi cikin kunya sanan na
sunkuyar da kai ina wasa da gefen hijabina na ce
ba dai ga ban muta ne ba, yace to ni gaban kowa
zan ce maki my choice, sunan ya da ce?Na saka
yatsa a bakina ina dan wasa da shi,na ce me
yasa ka zabi ka sanya min zabin ka?Ya dan kara
matsowa, dan duk duniya ke kurum zuciyata ta
zaba har mamakin ki tai lokacin da muka taya
wai saida kikaimana yanga kafin ki amsa.Na
yunkura bari inje in kwanta, ya ajeye kofi bakya
jin dadin firar tamu ko?Ya ci gaba, kiyi hakuri
dani ban taba fira da mace ba shi yasa, na dube
shi tare da dan zare ido ya ce baki yarda ba ko?
Nace naga kana dan sanda ka ce baka taba fira
da mace ba?Amma ba wai ban yarda bane yayi
dariya gaskiya bana yi, tsakanina da mace sai dai
in matsalar da ta shafi aikina ne ta hada ko har
yanzu baki yarda ba?Na ce na yarda na mike
tsaye ya ce, firata ba dadi ko?Na ce, da dadi
mana.Ya ce to shi yasa kike so ki gudu? Iya ta ce
kar na dade,yace ta manta ni mijinki ne ya ce ok
sai da safe?Na ce tam, har na kai bakin kofa
yace, gaki dai baki son kishiya sai ina ganin ba
zaki iya kula dani ba.Ina tsoron kada hakan ya ja
maki kiashiya. Cak!Na tsaya cikin wata murya
wacce ban san ina da ita ba na ce, sweet Aly,
Allah zan iya kula da kai fa ka ji?Kasa amsa ni
yayi don jin irin muryar da nayi anfani da ita.Na
ruga da gudu cikin kunya shi kam shiru yayi yana
mama kin mata.Lallai mata abokan nishadi ne,
dubi yar hirar nan da yayi da yarinyar nan ya
shagaltar dashi ya koma kamar sakarai, yayi
murmushi sanan ya kwanta.Nima kwanciya nayi
ina tuno abin da ya faru tsakaninmu duk da
kallon da Iya ta bini da shi, da na shigo sai dai yi
nayi kamar ban lura ta ji haushin dadewar da
nayi a wurin yayan ba.Washegari ban tashi da
wuri ba sai wajen tara lokacin baki suna ta shirin
tafiya gida jen su.Sha biyu kowa ya kama gaban
shi, sai mu munata aikin gyaran gida ni da
iya.Kusan karfe uku na yamma ya kirani wai a
kwai fura ko?Don anzowa iya da fura da nono
lokacin biki, na ce masa nono yayi tsami, sai dai
in ya siyo yogot ya shigo da shi ya ce to.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tunda na idar da la'asar na zauna zaman zabar
kayan da zan saka iya dai tana kallo na na sauke
akwatuna na zabo atamfa cikin kayan aure na.Da
na idar da sallar isha'i kuwa na shiga zabga
kwalliya ina ta feshe jikina da turaruka.Iya ta
shigo ta zauna bakin gado ta tsareni da idanunta
ko da bata fada ba nasan abinda kallon nata
yake nufi.,don haka nakoma nima bakin gado na
zauna tare da ajiye dan kwalin da na dauko zan
daura.Ta ce sadiya ni ba wai ina hanaki ki lura
da mijinki bane ko ki shige masa a ana fi so ki
bari sai kin tare, shi fa namiji babu ruwan sa da
zancen kunya, in baki ji nauyi na a matsayin
mahaifiyar Aliyu ba ai kyaji kunya na a matsayina
na uwarki.Saboda iya shege ko watsewa yan biki
basu tafi ba kin tafi dakin miji kin raba dare
saboda rashin kunya?Na sunkuyar da kaina rai
bace a zuciya ta na ce, har ga Allah shi yasa na
so in tare a daki na, ta ce daina bata rai, daraja
nike nemamaki da kima in kin tsare kanki har sai
kin tare kifi kima a idonsa, ga dai misali a gidan
ku.Kiji tsoron abinda ya faru da yar uwarki ta
zariya Harira ya faru dake, kan ta tare tayi ciki a
gidan mijin nata ya shiga yi mata wulakanci.Kin
manta banda ubanku tsayaye ne ai cewa zaiyi
cikin ba nasa bane, shi yasa in andaura aure ba
a tare ba mace ta mika kanta ba karamin so
mijin keyi mata ba za ya daraja ta.Wani dama
sha'awa ce ta kawosa gurin mace da ya biya zaiji
baya sonta, amma in tana gidansa fa?Ai yasan da
kunya ya ce yayi aure sati daya ya kori
matar.Jikina yayi sanyi, tabbas babu ja a batun
iya,kuma haka ne batun Harira, tayi goyon ciki a
gida ta haihu a gida ba ta tare ba.Kuma ya
saketa da kyar ya amshi cikin amma har yanzu
dan yana hannun uwarta agidan mu ita kuma
tayi aure a Hunkuyi.Na saka kaya a sanyaye na
zauna ina kara nazarin abubuwa.Har dakin iya ya
shigo suka gaisa ya ce, ina yarinyar nan?Ta ce,
tana ciki.Kamar daga sama sai naji ya ce, my
choice.Na fito da sauri tare da amsawa, duk da
nasan iya bata san me yake nufi ba.Amma tana
da saurin dago abu, zata san cewa suna ne na
musanman ya sa min, na amsa sannu tare da
gaishe shi.Ya miko min yoghot din in kin gama ki
kawo min.Na ce to,ya dubi iya bari nayi wanka.
.Na shiga da sallama, yana zaune kan sallaya da
alama salla ya idar, na ce baka sami jam'i bane?
Yace, shafa'i da wutiri nayi.Zan tsugunna ya ce
zauna a bakin katifa mana.Kina yi ya ce, sai kace
ba dakin mijinki ba.Ya gyara zama kan sallayar,
sanan ya dauko wata laide dake gefe ya bude ya
ciro kunshin takarda ya warware yana fadin.Kin
ganni da son kilishi shi yasa na saimuku
Balango.Ya dauki daya ya saka a bakin shi, zo in
baki a baki. Nace na koshi ni na ci abinci tun
dazu.Yace wanda kika ci da ban nawa nama ne,
matso kiji.Na dan sunkuyo ban sauka daga kan
katifarba, shima ya matso ya miko nannu ya sa
min abaki, na amsa tare da rufe fuskata cikin
tafukan hannaye na.Ya ce fada min gaskiyarki, ni
dake yanzu ba wani batun jin kunya. Kin kosa ko?
Na daga kai alamun eh, yayi yar dariya kinyi kyau
da wanan kwalliyar ta wace?Nasake makale kaina
cikin cinyoyi na, na ce eh.
Ya matso sai kurum naji ya kama ka fada ta, ya
saka dan yatsansa yana bin zanen fulawar, jikina
ya dauki bari don ji nake tamkar susa yake
min.Shima nasan yaji abin da naji don naji
muryarshi ta dan sarke.Ya ce wata gwana ce ta
zana maki wanan fulawar?Na ce wata yarinya
ce.Ya ce, yayi kyau.Ina son farar mace na dan
ware ido ina duban shi.Me yasa?Ya saki kafada ta
Ra'ayi nane kawai ba dan komai ba, ke fa?Na
sun kuyar da ka, kalar ka nafi so a cikin
maza.Yayi yar dariya, wace iri ce kala ta?Na ce,
wankan tar wada baka cikin farare kuma fara
cikin bakake.Ya tashi daga mazaunin shi ya dawo
kusa dani kan katifar.Kina nufin duk mun dace da
zabin mu?Ban iya amsawa ba saboda yanda ya
kusance ni, jiki na da na shi har suna haduwa.Ya
saka hannun shi a kafada ta ya manno nijikin sa,
fada mini gaskiya can dama kina sona?Duk da
halin da nake ciki na faduwar ga ba sabo da irin
yanda ya makale ni, bai hana ni tunanin wanan
mutimin ya cika tam baya.Ko yana zaton nima
mai laifin ce?Ya dago fuska ta, kalli cikin ido na ki
fada mun. Zan gane in kinyi karya kwa yar idonki
xata nuna mun.Naji mamakina lokacin da nake
furta can dama ina son ka kai fa kana sona?Cikin
wata ma yaudariyar murya nayi maganar.Kurum
sai na fuskanci le bunan shi a kan nawa yana yi
mun sumba, lamarin ya zo min sabo, ko na ce
bako.Ya dinga yi mun wasu abubuwa masu
firgitani har na zama bani da karfi.Tsoro na daya
kada ya gota daga haka, saboda ina tsoron
Iya.....zandakata Anan,muhadu a lokaci nagaba
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp  08168575100



Darajar Yayana1-04
Posted by ANaM Dorayi on 10:48 PM, 16-Mar-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
_______________NA
_____HALIMA K MASHI
Nayi karfin halin zame jiki na daga na shi,
yakwanta rigingine na mike sai da safe.Ya miko
hannu ya riko nawa hannun, cikin wata rikitaciyar
murya ya ce, ki zo nan mu kwana.Da sau ri na
ce, tab Iya ba zata yarda ba.Ya ce, ina ruwanta,
ni ba mijinki bane?Na ce to ai ban tare ba.Ya saki
hannu na.Da sauri na fice.Na tabbata in na shiga
daki haka iya zata fahimci wani abu, don duk
kwalliyar fiskata ya goge min.Don haka sai na
bige da sabar buta na nufi bandaki, na zo nayi
alawala.Ina shiga uwar daki ta bini da kallo tana
kwance kan gadonta.Na cire kayan jiki na dauko
rigar sallata nayi shafa'i da wutiri.Ta tabe baki
bata dai ce min komai ba ko takula duk na
tsargune?Oho.Da kyar na samu bacci ya soma
dauka ta sabo da tunanin abubuwan da suka
faru tsakani na da shi.Shigowar sakonshi dan
sautin ya farkar dani, na bude na duba cewa
yayi, kin hanani bacci my choice kixo ki taima ka
min please.A raina na ce mai zanyi maka sweey
Aly, ka dan bani lokaci mu tare, kiranshi ne ya
katse tunanina,sa sauri na farka dan ina tsoron
kada ringing din ya farkar da iya, duk da cewa na
san tana jina don bata da nauyin bacci.Can kasan
makoshi na nayi sallama ya amsa muryarsa a
raunane, har mamakinsa nake ina girman kan?


Ina isa da jin kan?A she dai mace dai ita ce
namiji.In ba mace rayuwar namiji ragaggiya ce.Ya
katse mamaki na da cewa, kizo kinji?Ba zan iya
bacci ba ki taimake ni.Nace iya fa tana jinmu ka
bari sai tayi bacci.Ya ce dagaske zakixo in jira ki?
Na ce eh.Sai ya yanke niko gaba daya ma sai na
kashewayar, na amsa masa cewa zan xo ne
kurum amma ba dan zan je din ba, sai don ya
barni.Kuma ko ba dan iya ba ina tsoro, tunda
ban san yanda abubuwan suke ba.Na makele fulo
ina tunanin ko a wane hali yake ciki yanzun, na
jima kafin bacci ya tafi dani.Nayi mafarki kala
kala masu dadi wai muna ta shawagi a cikin wata
duniya ni da ya Ali.Ku ziyarci blog dinmu domin
karanta Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Da safe kuwa fuskarshi a murtike, don ko amsa
gaisuwata baiyi ba, lokacin da yazo gaida Iya ina
gai da shi,hakan bai yi min dadi ba, na kunna
waya ta na tura masa sakon ban hakuri tare da
ce masa jiya naso inzo Iya ce bata bari na fito
ba.Ko ya gani ko bai gani ba oho, bai dai bani
amsa ba, na dafa ruwan tea na kai mai na same
shi ya gama shirin fita yana daura ta kalmi.Na
shiga da sallama ciki ciki ya amsa, ina shiga ya
dubeni fuska daure ya ce, lfy?Cikin wata murya
irin ta a salin jarumin maza.Jiki na ya dauki bari
na ce, dama....dama tea ne.Ya ce fitan min da
shi ina azumi, fargaba na ya karu, iya ce jiya ta
fash....Ke!Ya katse ni, fita a nan dan Allah.Na fita
da sauri, zugun na zauna ina tunanin yanda ya
Ali yake canza launi tamkar hawainiya...
Kimanin kwanaki uku kenan yayi mun dif, inna
gaida shi baya amsawa, haka nan in abinci na kai
mai ko yaushe sai ya ce yana azumi.In iya tayi
mashi magana ke nan, in nice ma na kai mishi ni
abu sai ya koro ni, ina girki a kicin iya ta fita
lokacin sai ga Aisha kawata.Naji dadin zuwanta ta
tayani,muna fira na bata lbr duk halin da nike
ciki na kara da cewa, ya Aliyu gaba yake dani, iya
ta sa ido sosai dan ganin ban bada kai ga miji na
ba, ba tare da mun tare ba.Don Allah Aisha ki
bani shawara, ta ce, ni dainawa ganin in har zan
fada maki gaskiya kibi mijinki, daga lokacin da
aka daura muku aure da shi dukkannin hakkokin
shi sun hau kanki.Nayi ajiyar zuciya tace, nasan
kin san komai ma kina yi ne kamar baki sani ba
nace Aisha nasani,Iya fa idonta yana kanmu.Ko
daki na shiga sai kiga tana kai kawo, in na fito
kuma tayi ta yi mun kallon tuhuma, to ki bashi
shawarar ku fita wani wurin mana.Nace tap nice
ma zan bashi shawarar?To an ce maki iya za ta
barni in fita ne?Aisha ta ce, yanda kika gani,
amma in nice zan bi miji nane.Rayuwar nan ta
yanxu mata suna bin maza har inda suke,
balantana mijinki dan kwas irin wanda basu da
yawa a cikin jama'a?Ku ziyarci blog dinmu domin
karanta Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Na ce nima ina tuna haka, shiyasa wlh ban so ba
da ban tare ba, kamar yarda ko wace Amarya
take tarewa a dakinta. Ki tayani da adu'a don sun
sani a tsakiya ita tana kallo na a mai rawar kai
na shige masa,shi yana kallo na mara
biyayya.Aisha ta ce, abu ne fa mai sauki ke ce
kika dauke shi da zafi, in kin bi mijinki kinga dole
ta barku.Na dubi Aisha ta ce, fa ba zai dubi
mutuncina ba, Aisha ta ce, in bai sameki a
mutuncenba ba?Kin bi maza ne?Na kai mata
duka, kinji ki da wani zance, in na bi tare muka
bi kenan.Ta ce ke ce da wani shirme, in kin ga
namiji yaga rashin mutuncinki ya sameki kin bi
wasu....(Biri fa kuma yayi kama da
mutum,watakila irin haka tafaru da yar uwarki da
Zaria,shiyasa mijin yayi inkarin kasancewarvcinkin
a matsayin nasa,hartakai ga saki ANaM Dorayi)
Kalu bale ga masu saida mutuncinsu a banxa.
Aliyu tukur ya tsaya a gaban shugaban shashin su
na binciken manyan laifuka, mataimakin
Commissioner.Ya ce ASP Aliyu zanfi so idan kana
tsayawa a kan aikinka, ina nufin ka rinka
dakatawa a madakatarka.Sanan ka rage kishin ka,
domin kasar mu a yau in kace haka zakayi lallai
ba zaka kai ko ina ba.Ina yi maka magana ne a
kan barawon shanu din nan, mutumin mai girma
commissioner ne, na tabbata da yana gari baza
ka kamashi ba bare tsarewa.Inma kayi nasara ka
kama shi, ba zaiyi minti talatin a tsare ba kai ba
a taba kama shi ba, yaranshi kurum ake
kamawa.Da sunyi waya da commissioner zaisa a
sake su, nayi mamakin ma da commissioner bai
tsawatar maka ba, ya ce kawai ka bar case din a
hannunsa.Ran Aliyu ya baci, shi da ya shiga aikin
dan sanda kishin kasarshi da kawo gyara, sai
kuma su rinka ganin barna suna kauda kai?Ya ce,
yallabai ina rantsuwar da mukayi da alkur'ni
cewa zamuyi aiki tukuru bisa amana da gaskiya,
idan dannanda bai zama mai kishi da gaskiya me
za a kirashi?Idan dan sanda zai rinka amsar cin
hanci yana hulda da manyan azzalumai yana
daurewa barayi gindi suna zalunci, za a kirashi
mai tsaron lafiya al'umma.AC ya dagawa aliyu
hannu, dakata ASP, wannan tambayoyin zasu fi
dacewa kayiwa CP su, ni shawara na baka.Da
akwai mutane irinka da yawa wadanda suka
nuna kishi, wasu anyi musu canjin gurin aiki zuwa
wasu garuruwan da ba zasu sami irin wanan
barnar ba bare suyi gyara.Wasu anyi musu sharri
an koresu, kai wasu sun mutu yayin da wasu da
yawa suka ajiye hularsu.Ban hanaka yin kishi da
gaskiya tare da kin karbar cin hanci ba, sai dai
ina mai baka shawara ka dinga tsayawa ga
kananan masu laifi, jeka abinka.
Aliyu yana zaune a office din shi, kansa ya dauki
zafi yana tuno sa'insa da sukayi da Barawon
shanun, inda barawon yace, kai yaro wanan ba
wani bakon abu bane satar shanun da muke
yi.Haka nan mu nan Headquarter gidan mu ne
kaine mutum na farko da na taba bawa cin hanci
ya maido mini.Nafi tunanin kana daga cikin
mutanen da basu da rabo, amma kai bako ne
ko?Aliyu ya ce, ba jin tarihi ko maganar cin hanci
na xo ba, nazo nan ne dan in kama ka,a
matsayinka na mai laifi, ni kuma na hukuma.Duk
wadan nan baya nan zasu biyo baya in munje
office, yaranka muka kama kuma suka ja
sunanka.Barawon ya zaro ido tare da daga murya
ya ce, kai bako ne shiyasa baka sanni ba amma
muje.Aliyu ya ce nasan ko ban sanka ba, bako ne
ni bako ne wannan ba damuwata ba ce.Ku ziyarci
blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Sun san Aliyu bai san wanene wanan barawon
ba, shi kanshi barawon cewa yayi zakayi da
nasanin kamani.Aliyu bai ce kala ba, ya nufi
Office din sa zuciyarshi cike da son nunawa
wanan baron cewa hukuma bai bar
kowaba.Amma me? daidai lokacin da yake bada
ummarnin ashigar da kara ne shugaban shashin
su AC ya ce, kajira tukunna sai an sami ummurni
daga commissioner.Dafawar da akayi mashi itace
ta dawo dashi daga dogon tunaninsa.Ya dago
kai.Insperctor kamal kaita ne ya ce Sir, ka daina
damuwa da irin wadan nan matsalolin, sanan ka
ci gaba da yanda kake, Allah zai kawo maka
dauki dan yana tare da irinku.Sai dai dama baku
cika farin jini ba a cikin yan sanda, saboda kowa
yana ganin cewa zaku toshe masa kafar
samu.Shawarata ka bar batun Barawon nan ko
ba komai kayi namiji tunda ka kamo shi, ka kuma
tsare shi.Sanan Allah ya doraka a kan CP bai
dauki zafi a kanka ba.Aliyu ya mike tsaye, na
shigo aikin dansanda cike da kishi da buri, gami
da kwazo.Manufata insamu waddanda zasu
fahimci niyyata don mu kawo gyara cikin
hukumar yan sanda.Na tabbata ko cikin
headquarter din nan akwai masu kishi da yawa
wadanda suke jin irin abinda nake ji yanxu a
zuciyata. Inspector ya ce, hada dani, sai dai ina
mai bakin cikin sanar da kai cewa ba zamu kai
labari ba, tunda daga sama a ake tadiye mana
kafa.Aliyu yace inko haka ne zaya ci gaba da
faruwa, watarana zan iya ajiye hulana.Inspector
ya ce, ranka ya dade kada kasaka haka a ranka
tun yanxun, kaji a cikin xuciyarka cewa burinka ya
cika, Allah yana tare da mai gaskiya.Ranka ya
dade ka duba tashin farko bin diddiginka yasa
sashinmu na bincike suke shakkarka, ina son
mutum irinka.Aliyu ya lumshe ido tare da cewa
zantukanka sunyi mun allura inspector, zan kara
kaimi.Da wanan ya cigaba da aikin sa.Daf da zai
tashine aka shigo da wani da ake zargi, ya kalle
gobjejen mutumin sanan ya dubi yan sandan.Me
yayi shi kuma wanan? Sajan Ado ya ce, ranka ya
dade, kato kamar wanan aka kama yayiwa yar
shekara takwas fyde,ran Aliyu ya tunxura, ya
runtse ido cikin takaici, ya ware ido ya kalli
mutumin cikin tsana ya ce, wai wane irin
zaluncine wanan kuke yiwa jikokinku?Cikin rawar
murya mutumin ya ce ranka ya dade na rantse
maka ba ni bane, sharri sukayi min, na rantse
maka.Aliyu ya harareshi, ba kowa bane yake
amsa laifinsa da sauri.Ya kalli yan sandan suwaye
suka kama shi?Sajan ya ce ranka ya dade ga
mutanen da suka kawoshi can, sune suka
kamashi da yarinyar a shagon shi tana ihu.Yace
ina yarinyar yanxu?Sukace an tafi kaita Asibiti.Ya
kalli mutumin yaja tsaki ya ce, ya ce ku rufe shi,
yanxu ba wani sausauci ga irin mutanen nan
masu cutar da kananan yara ta ta hanyar fyade
Ya koma office din sa cikin ta kaicin fyadan nan,
kullum sai sun samu irin wanan case din da yar
da jarirai yafi yawa, amma yanzun yanaga zasu
xo daidai.Ya kira sajan ya ce, ya kawo masa
takardar tuhumar (statement) da ya duba tsaki
yaja, ya dubi sajan.Kullum dai abin iri daya ne.Ya
tabe baki, sanan ya dubi a gogonsa, yau shida
zan bar nan, duk wanda ya nemeni
saidasafe.Sajan ya sake kamewa tare da fadin
yes sir!Sai kuma wanan mutumin yaya za ayi da
shi?Aliyu ya ce, ba maganar beli ko wani ya zo
zuwa gobe za a hada bincike a turashi kotu.Sajan
ya sara masa sanan ya fito.Da dunbin wanan
damuwar ya iso gida, daga ganinshi kasan akwai
abin da yake damun shi, kan katifarshi ya zube
rigingine bata re da ya cire koda ta kalmi
ba.Lokacin da ya shigo ina zaune a kan kujera a
kofar daki ina karatun wani littafi (SIRRIN BOYE)
na Anty Bilkisu.Ga al'adarshi in ya shigo dakin Iya
yake fara shiga kafin ya dawo dakinsa, ya cire
kaya in sun gaisa.Ya shiga wanka.Amma yanxu
tunda ya shigo shiru, iya ta fitodaga bayi (ban
daki) na dubeta na ce, yaya fa?Ya dawo yanayin
shi kamar na mara lafiya, ko baya jin dadi ne?Ta
ce, ba wani ke dai kina sonzuwa gurin mijinki ne,
kuma ba zan hanaki ba.Na hade fuska, Allah iya
nifa ba wai zanje bane fa.Ta ce, kije ki duba ko
lfy,naki tashi, dan dama ina tsoron inje yayi mun
wulakancin shi, ya ce nafita shiyasa naki
zuwa.Ganin da iya tayi tabbas ba zan shiga ba
kuma tabbas bai fito ba sai ta shiga dakin. Yan
da ta ganshi warwas a katifa batare da ya cire ko
takalmi ba, sai abin ya bata tsoro.Cikin saurin
muyar ta ce, Gadanga!Ya dago kai da kyar ya
dubeta, wani matsanancin ciwon kai ke damun
sa.Ya ce na'am Iya sannu.Ya tashi zaune,
ciwonkai ne ya hanani shigowa ciki.Ta ce,
matarka nema ni take ce mun ka shigo cikin wani
yanayi, bari a kawo maka magani ka sha.Yace
zanje Asibiti in anjima bayan magariba.Duk
kwanakin nan da haka nake ta yawo da ciwon
kan nan.
Ta ce, to kasha maganin yan xu sai kayi sallar da
dan karfin jikinka, kaje asibitin da dan kwari.Ya
ce, to.Ta kwala min kira Sadiya.Na amsa ta ce,
dauko min magani panadol kizo da ruwa.Naje har
gabanshi na ajiye da ruwan ina yi mashi sannu
yaya, ya jikin?Ko kallo na baiyi ba bare ya amsa,
mamakin yanda naga iya tan gutsi gutsi da
maganin, ta dubeni dauko mun cokali.Na dauko
ta jika ta bashi a baki tare da fadin, shiyasa nake
fargaban ciwonka gadanga.Duk da dai ba yawan
ciwon kake ba, amma kin maganinka shi ke
wahalar da kai a ciwo dai dai yake da na yaron
goye.Shi yasa duk lokacin da katashi ciwo bama
jita dadi.Ya sha ya koma ya kwanta, dai dai
lokacin aka kwada kiran magariba.Ta dube ni,
bari inje inyi sallah, nima na biyo bayanta.Ta
dakatar dani da cewa, jira tukunna muga yanda
jikin zaiyi.A raina na raya cewa dan ta ga ina
fashin sallah, shi kuma bashi da lfy.Shi kam yana
kwance, na isa gurinsa gabana yana ta faduwa,
duk da ina zaton zai daka min tsawa ban fasa yin
abin da nayi niyya ba.Gabansa na tsugunna ina
kwance masa takalmi, na cire su na aje gyafe,
sanan na kwashi kafafunsa na zubasu a kan
katifar.Har lokacin idanunsa biyu amma suna
lumshe, haka nan hannunsa yana dafe da
kai.Kusan minti shabyar ina zaune can gefe, ya
tashi zaune yana kici kicin cire rigarsa, na taso na
balle masa boturan, sanan na sabule rigar sai
farar singiletin, ita ma ya kama ya cire.Na kalli
kirjinshi gashi ne kwance na kauda kai don sai da
naji wani iri.Ya sabule wandonshi, sai gajere na
ciki, shima na kwashe su na zaba su a cikin
kwandon da yake zubawa.Naga yana kokarin
tashi nace mai zaka dauko in dauko maka?Ka
zauna kawai.Ya ce, bani jallabiyata.Na bashi fara
kal mai dogon hannu, ya mike zai fita, na ce ina
zaka je?Ya ce masallaci.Yana fita na shiga gyaran
dakin, ban taba yi masa gyaran daki ba sai
yau.Ko yaushe da kansa yake yin gyaran dakinsa,
nayi zaton zanga mujallun da na taba gani da, sai
kuma ban gani ba, har na gama.Iya ta idar da
sallah, ta sake lekowa ko ya tashi, na ce ya je yin
sallah, shiru shiru ashe daga can ya tafi
asibiti.Har kusan tara gashi bai fita da waya
ba.Iya da kanta ta fita har masallaci layin mu,
wanda suke sallah tana nemanshi.Duk wanda ta
tambaya sai su ce mata tare dai suka idar da
sallar isha'i.Da ta dawo sai na ce mata ko dai
yatafi Asibintin da ya ambata ne?Ta ce zata iya
yuwuwa ya tafin, tun da ya ambata.Nan dai
muka zauna zaman jiran tsammani,mun kasa ko
cin abinci.Sai sha dayan dare da yan mintuna
dan acaba ya sauke shi, ni da iya har rige rigen
fita muka yi, shi ne muka yi masa sannu ya
amsa, iya ta ce, muna ta neman ka.Ya ce, natafi
Asibiti ne shi yasa ciwon kai ya matsa min da
yawa.Amma na sami allura da magunguna, kuma
na kwanta canne kamar yanda likitan ya ce in
dan huta, Alhamdulillahi kai yayi sauki.Ta ce to
me zakaci yanzun?Ya ce, nasha tea a can kafin
ayi min allura, muka shiga dakin shi ya zauna
bakin gado.Iya ta fita nima na mike zan fita, sai
ta ce ki dan tsaya ke saboda dare ko?Na koma
na zauna ya kwanta tare da lumshe ido.
Wayarshi tayi ringign, ya daga ya kalla sannan
yaja tsaki, bari na kashe wayar nan ina so in dan
huta.Har zai kashe sai ga ma bari yayi anfani da
wanan damar ya nunawa sadiya anafa ribibin shi
har da take masa yan ga.Don haka sai ya daga ni
dai naji yana fadin yaya mati na me ya faru ne?
Ban zaci jin muryarta ba, ashe ya saka
hanfree.Sai kurum naji ta ce, lafiya lau sir, ban
gankaba ne an ce ka tashi tun six, ya ce akwai
wata matsala ne matina?Ta ce babu, naso in
ganka kawai, kayi hakuri kasan ganinka kawai
yana cire min damuwa dayawa, dayawa, amma
sir sai kanayi kamar baka san haka ba.Yace
matina yanzu bani da lafiya ne, ban dade da
dawowa daga Asibiti ba in nafito da safe zamuyi
maganar.Ta ce to Sir, nagode Allah ya kawo
sauki.Raina yayi mugun baci, a gabana yake
magana da wata arniya har take ce masa ganin
shi yana sata sukunni da kwanciyar hankali?Yana
ajiye wayar ya kalleni, na hada rai matuka na
mike ya ce, ina zaki?Nace zanje in ci abinci ne, da
kyar nake magana.Ya ce, au dama baki ci abinci
ba?Kamar in kai masa duka don ta kaici.Mutumin
da yayi nasa guri bai fada muna ba muka yi tsuru
tsuru cikin damuwa.Shine zai ce dama ban ci
abinci, ya mai maita tambayar nace um, ya ce
kina ciwon baki ne?Nayi shiru yace in kin ci ki
dawo, tunda Allah yasa yau naji da kunnena ba
iya ce take hanaki zuwa wurina ba, karya kike yi
mata.Ban tanka shi ba na wuce, a raina na ce ba
zan dawo baCan kusan daya saura ina ta tubka
da warwara na kasa bacci, ni nasan kaina ina da
mugun kishi, sai ga sako ya shigo cikin wayata
cewa ba zaki dawo bane?Na tura masa amsa da
cewa eh, ka kira Matina.Yana ganin haka yayi ta
dariya, sakonshi ya kai ke nan, don haka shima
kurum sai ya kashe wayarsa ya kwnta.Da Asubahi
iya taje dubashi ta sake shiga dan duba shi, sai
ta samu jiki yayi sauki, har ma ya tafi
masallaci.Don ya Aliyu ba rago bane namiji ne, ga
juriya da izza, matsalarsa daya in yana ciwo kin
magani,yayi tawa iya shagwaba sai kace karamin
yaro, shi a dole auta.Nikam har gari yayi haske
ban tashi daga makwanci na ba, tunda ina fashin
Sallah ba wai ina bacci bane kurum takaici ne ya
hanani tashi.Jiya ko baccin kirki banyi ba, saboda
takaicin ya Aliyu.Iya ta shigo, ke ba zaki tashi kije
ki gano mijinki ba?Ko da nafito kin xuwa nayi na
debi ruwa na shiga wanka.Ina fitowa nayi zaman
shafa mai duk ina jan lokaci ne don yayi abinda
zaiyi ya kama gabanshi.Bana ma ko son ganinshi,
lokacin da na shirya na nufi kicin a tsammanina
ya fita.Ina tsakiyar kunna risho sai naga mutum a
kofar kicin tsaye.Na rasa dalili in zan ga ya Aliyu
sai gabana ya fadi.Na kalli fuskarshi, gaskiya har
ya dan rame na ce ina yini?Ya ce ban yini ba, ni
yanxu zafiya ce, sanan ba zan amsa ba tunda
baki san hanyar daki na da bazakije ki gaida ni
ba.A raina na ce ina matina?Ita batazo ta duba
ka ba?Ya katse tunanin da cewa,ruwan zafi nake
so zanyi wanka.Na kalleshi, ban taba ganin yayi
wanka da ruwan zafi ba, nace to bari in dora
yanzun, bai ce, kala ba ya koma daki.Da yayi zafi
na sirka na kai masa ban daki, sai naje na ce
masa ga ruwa can.Lokacin yana waya, da hannu
yayi min alamar cewa in je yaji.Na tsargu da wa
yake waya, don haka da nasaki labule sai na
tsaya.Ji nayi yana cewa, kada ki damu, yanzu
zanfito.Jikina yayi sauki, ai da tunaninki na kwana
araina.Na girgiza kai tare da yin kwafa.Tabbas da
matina yake yin waya, nayi kicin ina yin magana
ni kadai, na ce to ita wanan shegiyar matinar me
ke tsakaninsu?Nemanta yake yi ko me?Wata
zuciyar ta katseni da cewa, ba kina gudunsa ba?
Ai ga Matina zata maye gurbinki. Jikina ya sake
mutuwa, na shiga tambayar kaina mafita.Wunin
ranar sukuku nayi shi, na kasa tuna yanda zan
bullowa abin.Duk jin su iya nake ko da can da
suke cewa ba ruwanshi da mata, ni nasan da
ruwanshi tunda ni naga mujallun batsa a dakin
shi.Wanda baruwanshi da da mata me ya
ruwanshi da irin kallon tsiraici?Dole ke nan inyi
yakin rabashi da matan banza.Wata zuciyar tace
haka ba zata yuwu ba, sai in zakiyi aikinki a
matsayin matarsa, lallai saikin mika kanki a fili na
ce ya na iya?Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Muna zaune a falo da iya washe gari da safe,
yazo yiwa iya sallama zai fita, nima na bude
baki da nufin ce masa sai ka dawo.Amma da
yake matina ce a raina sai kurum naji na ce
masa ka gaishe mun da matina.Har ya juya sai
naga ya tsaya cak, sanan ya waiwayo fiskarsa
dauke da murmushi ya furta cewa zataji in sha
Allahu.Ya juya ya tafi, ni kam kamewa nayi
tamkar gunki, a zuciyata tambayar kaina nake
dama mutun na iya kuskuren magana ya furta
abinda ke son zuciyarshi ya bar na saman leben
shi?Kash!Ban so nayi zarar bunun nan ba, abin
takaici harda murmushi na ambaci sunan
masoyiyarshi.
Kwana uku suka shude ina cikin damuwa,na san
Iya ta lura banza kawai tayi mun,narasa abinda
ke yi min dadi, ni ba fita nake ko ina ba, ba TV
Garemu ba bare nayi kallo, ta lalace ni kuma ba
ma abociyar radiyo ba.Wani kayan haushi ko
littafi na dauka da sunan karantawa sai in kasa
fahimtar komai.Na san kaina ina da shegen kishi
na ban mamaki, ko saurayina naga suna yawan
gaisawa da wata budurwa hankalina kan tashi,
bare a ce miji na.Tabbas da Ya Aliyu ya skar min
fuska da tuni na same shi munyi ta, amma ya
Aliyu ya wuce haka.Ku ziyarci blog dinmu domin
karanta Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Cikin sauri sauri ya Aliyu ya shiga shashin su, ya
kalli sajan Ado ina barawon?Suka kaishi ya
shiga.Ya tsura mutumin ido, aransshi ya ya ce
kai wanan mutumin baiyi kama da barawo
ba.Ya kalli Sajan, kawo abin zama, sai da ya
zauna sanan ya kalli mutumin.Kaine barawon fili
ko?Hawaye suka soma kwarara daga idanun
tsohon, don bakin cikin sunan da aka kirashi.Ya
ce cikin rawar murya, ranka ya dade ni ba
barawo bane, ban taba sata ba.Aliyu ya juya
kulkin dake hannunshi ya dan jefashi, sanan ya
cafke.To baba ya akayi har ka mallaki filin da
kake gini?Ya ce, ran ka ya dade filin nan na
gajeshi ne a gurin mahaifiyata, don mahaifinta
manomine.To ina zaune a gidan haya ga iyali,
ina da mace daya ga yaya takwas.Yan samarin
yara na a makota na roka sunakwana, ganin
kullum nauyi na karuwa, sai nayake shawarar
gina fili na ko da daki biyu ne rak.Na soma gini
ni da yaya na, dan sana'ar mu ke nan ta
leburanci da yaran.Mun soma ginin kawai sai
ganin yan sanda nayi sun xo kamani, ban san
abinda nayi ba.Aliyu ya ce, to baba naga
takardar bayanin laifinka, naga cewa ana
zarginka da laifin yingini a filin da ba naka ba,
filin tsohon jami'in dan sanda ne.Tsoho ya ce,
dana wlh wanan filin nawa ne, kowa ya sani a
unguwar mu ina da takarduna ina da
sheduna.Kuma ni da aka kawoni nan ba a
tambayeni ankawoni nan aka jehoni ne
kawai.Babu wanda yaji ta bakina.Aliyu ya ce ka
tabbata kana da takardu da shedu?Tsoho ya ce
ina dasu ranka ya dade.Aliyu yace zamu mikaka
kotu kuma in sha Allah zan tsaya maka sai kayi
nasara.Cikin izza ya nufi wajensu Sajan Ado,
yace sajan, yace Sir, bayan ya kame.Aliyu yace
waye ya kawo wanan mutumin?Sajan ya ce,
barawon fili?Aliyu ya ce, eh shi.Sajan ya ce CP
ne yasa a kamo shi.CP da kanshi?Ya tambaya
cikin mamaki.Yace shi, amma AC ne ya tura.Kan
Aliyu ya daure, ina takardar bayanan da kuka
bani dazu?Sajan ya sake daukota, Aliyu ya kalla
ya sake karantawa, wanan rubutun kofur bala
ne ai, sajan ya ce, eh, Aliyu ya ce kira min
shi.Ya juyya ya koma office din shi.Ya tsare
kofur da idanun shi waddanda basadaukar raini,
kainne ka rubuta wanan takardar ko?Ya kame,
eh, nine Sir, ya juyya mishi baya, amma ai baka
tambaye shi ba ka rubuta da yawun shi.Ko
menene dalilinka?Kofur cikin daburcewa ya
ce,Sir ai nima AC ne ya ce na rubuta haka, sabo
da raini mutumin yake so ya kawo wa tsohon
mataimakin IG.Aliyu ya daga hannu da nufin
dakatar dashi, tsaya min kowa ya cuta sai a ari
bakinsa a ci mai albasa?Ya ninke takardar ya
zura cikin aljuhunsa, yace dauko wata kazo muje
ka sake rubuta ainihin bayanin da yake daga
bakinsa, mu masu kare Al'umma ne da
rayukansu ba masu danne masu hakkin ba ne
da kuma kashe su.Kofur dake biye dashi ya ce,
sir, wanan tsohon mataimakin IG yana yawan
kawo mana matsalolinshi a nan, kullum
maganarshi bata wuce an cuceshi.Ku ziyarci blog
dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu ya ce dan ya taba zama jami'in dan sanda
bazaiyi anfani da wanan damar ba, sanan yayi
anfani da mu.Alkawari na daukarwa kaina ba
zan bar zalunci ba, matsawar naganshi zanyi
yaki dashi.Aliyu ya tsananta bincike kuma cikin
kwanaki kadan yagano cutar tsoho wanan
jami'in ke son yi, don hakka ya tattara dukkan
bayanai ya turasu zuwa kotu.Gobe da safe ya
tabbata in anje can tsohon zai sami hakkinsa,
saboda bayanai da hujjojin da Aliyu ya
hada.Yana tsaye a bakin titi zai hau a caba zuwa
gida Inspector Kamal ya sameshi a gurin, ya ce
ranka ya dade zuwa yanzu yakamata a ce ka
mallaki abin hawa ko da mashin, amma in san
samu ne a ce kana da mota.Aliyu yayi
murmushi, kada kadamu, ko mai lokaci ne, ya
ce in dauko maka na aiki mana ba sai ka sha
mai ba?Aliyu ya ce, a a na aiki anyi shi ne dan
aiki kawai.Ispector ya ce, kana birgeni Sir, komai
kana barinsa a muhallinsa.Lokacin da aka raba
mana mashina baka zoba.Aliyu ya ce, ko ina
nan ba zan amsa ba, don bana son bashi.Ya
karasa zancen tare da tare dan acaba.Wayyarshi
ta dauki tsiwa, ya cirota cikin hanzari ya daga
saboda ganin sunan AC, hakuri ya baiwa dan
acaban, sanan ya komaciki kamar yanda AC ya
bukata a cikin officeya same shi, kai kawo yake
ransa a bace ya dubi Aliyu.Me yasa ba bada
damar a kai barawon filin nan kotu?Aliyu ya ce,
angama bincike ne sir, sanan doka ta hana a
tsare mutum tsawan lokaci ba tare da an kaishi
kotu ba.AC ya ce, na san dai na rigaka sa kaki
ko?Bai jira amsa ba ya ci gaba da cewa, don
haka kasan na rigaka sanin doka.Ya koma
kujerarshi ya zauna.Wanene ya hada binciken?
Kai kasan ma da wa yake rigimar?Kasan filin
wayake son kwacewa?Aliyu ya ce, nine da kaina
nayi binciken sanan nasan rigimarsu shi da
tsohon IG ne, kuma CP ne ya sa a kawoshi.AC
ya ce, gud, to zan sake mai maita maka, in an
kawo mai laifi da umurnin CP dan Allah ba
ruwanka da shi, in zaya shekara.Ran Aliyu ya
baci, ya ce, Sir, amma ba akan haka mukayi
rantsuwa ba.AC ya daga masa hannu ban ce
maka inason tunatarwa ba, sai dai ina son
kasani ka kusan kai CP bango, dan kana son
shiga cikin lamarinsa.Sanan kayi hanzarin cire
kanka daga cikin lamarin tsohon, ka barsa yayi
nashi binciken.Shiru Aliyu yayi, amma ji yake
tamkar ya kama da wuta don zuciya.AC ya ce,
ka iya tafiya.Aliyu ya fice da kunan rai.Matina ta
hangoshi cikin sauri ta bishi, yana tsayawa a
bakin titi tana tsayawa, ta ce barka da warhaka
yallabai.Ya furzar da wani huci mai zafi, sanan
ya ce barka dai.Tace ina tuni yallabai ya runtse
ido don yanason saita zafin da zuciyarshi ke
yi.Baya so ta fahimci yana cikin damuwa, sanan
ya budesu sun kada sunyi ja, sanan ya ce
matina zanfiso mu zauna a matsayin abokai, na
fada maki bani da sha'awar auran mata
biyu.Ina yi maki adu'ar samun mijin da ya
fini.Ta ce, samun kamarka ne yallabai sai an
tona, kunyi karanci a cikin al'umma.Ba duka
namiji mace kamata zata bashi kanta ya kauda
kai, har yanxu ina tuna ranar, ranar da na fada
maka ni da kai muyi soyayya koda bamuyi aure
ba.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Na fada maka cewa wata gara basa da zan
maka shi ne, zaka iya yin duk yadda kake
sodani na mallaka maka kaina, amma sai kayi
mun nasiha ka kuma nuna min cewa addininka
ya yi hani da hakan.Na sami kaina da sonka
tare da son addininka, sanan cikin aikinka kowa
yasan kana kwatanta gaskiya da amana.Ina
tsoron in auri wani cikin masu addininku ya sake
ni, dan ku hausawa ance kuna da sakin aure
amma kai nasan ba zakayi haka ba.Aliyu ya
kasa kallonta dan ta daureshi da jijiyoyin
jikinsa.Ya ce, Matina ki amshi addinina da zuciya
daya, sanan kisa a ranki zaki sami mijin da ya
fini, nima zan tayaki da adu'a.Ta gyara tsayuwa
kada ka damu, ni zan ci gaba da zaman samun
irinka, alfarma daya nake roko in zaiyuwu, in na
kiraka ka daga wayata.Sanan in kazo nan muke
rinka gaisawa.Ya ce dan mun hadu mun gaisa
ba damuwa,abin da zaiyi dan wuya ki rinka
kirana ina da mata, nasan bazata so hakan
ba.Ta rausayar da kai gefe, cikin raunaniyar
murya ta ce, na gode,ka fadiwa matarka cewa
ta rikeka da kyau, dan tana cikin matan da
sukayi sa'ar zuwa duniya.Murmushi yayi duk
lokacin da kuka hadu saiki fada mata da kanki,
na barki lfy.Yana kan mashin yana tunani ko me
yasa yake samun irin wanan matsalar?Mata suyi
ta sonshi suna binshi, amma shi bai damu da
su ba.Matina yana kulata ne saboda musulantar
da take sha'awar yi, ya san in yazama sanadiyya
zai sami ladan hakan.Daga nan tunanin sa ya
koma kan matsalarshi ta office, in dai da irinsu
AC da PC anya kasar nan zata gyaru?Lallai
kasarsa Nageria tana cikin wani hali, kullum
burin nasama ya danne na kasa, sam ba a son
gaskiya.In ka tsayawa halas dinka sai mutane su
rinka yi maka kallon dan kauye.Ya girgiza kai
sakamakon tuno tsohon nan da yayi, shi da
gaskiyarshi da filin sa da komai ba a tausaya
masa ba, kasancewarshi mai rauni ana neman a
zalunce shi.Mai dama yana anfani da damarsa
gurin cutar mai rauni, yasan in ba wani ikon
Allah ba tsohon nan ya rasa filinsa kenan, in
yasamu ya fita da ransa kenan.Duk lokacin da
irin wanan ta faru sai yaji tamkar ya bar aikin
dansanda, amma da ya tuna kudirinshi na kawo
canji da gyara, sai ya hakura, da wanan sake
saken ya isa gida.
Niko tun lokacin da na furta masa cewa ka
gaishe da matina cikin kuskure, ban sake yarda
mun hadu dashi ba.Kusan kwana uku wasan
buya muke yi har iya ta fahimci cewa na guje
masa, amma bata nemi jin ba'asi ba, yi tayi ma
kamar bata san me ni ke yi ba.Sam ban zaci
dawowarshi a wanan lokacin ba, domin cikin
kwanakin nan sai dare yake dawowa.Ni kadaice
a gidan,Iya tun bayan la'asar sun tafi Asibitin
dutse duba wata makociyarmu da bata da
lafiya.Sun tafine da ma da sauran
makotanmu.Na wanke hijabaina da na Iya ina
shanyawa,daga ni sai best, zanina kuma iyarshi
kugu.Ina shanya ina mitar cewa iya sunje sunyi
zamansu, nasansu da son tafiyar kafa, yanzu
haka ma da kafa suka tako.Banji sallamarshi ba
sai dai naji ya ce ina suka tafi?Na waywaya na
kalle shi, da gudu na shige daki dan kirji na duk
a waje yake.Dan murmushi yayi sanan ya shige
dakinsa.Ina zaune bakin gado ina kallon jikina
sai ganin shi nayi tsaye a gaba na har uwar
daki.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Naja hijabina, ya ce ina tambayar iya kina gudu?
Ya hade fuska tamkar bai taba dariya ba.Tsoro
ya darsu a raina, cikin in ina na ce,Asibiti suka
tafi.Ya ce, dan kada ki bani amsa shine kika
kwasa da gudu?Nayi shiru, ya ce kin min
banza.Nace yi hakuri dama zan dauko dan kwali
nein daura.Ya ce, ok, ni zaki boye min gashin
kanki?To ajiye hijabin in ga gashin tunda halas
dina ne.Gabana ya soma faduwa, na zame
Hijabina ya ce ashe ma ba wani gashi kike dashi
ba, cire hijabin daga jikinki in gani.Na kalleshi da
sauri ya kauda fuska yana yatsina baki, sai kace
zai ga abin kyama.Na cire hijabin na ajiye cikin
sauri kuma na sa hannuna na rufe kirjina.Ya ce
cire hannunki.Na cire tare da runtse idanuna.Sai
kurum naji yasa hannu ya turani baya, na fadi
rigingine na bude idanuna da sauri ina tsoro,
yasa hannu ya janyo best din sai ta yage, kirjina
ya bayyana.Tsayawa yayi yana kare mun kallo,
ya tabe baki, dama best din taki rubabiya ce?
Sallamar iya ta tsakar gida ce ta sani tashi
zumbur, na dauki hijabi saka.Cikin tsoro mai
tsanani na ce ga iya nan.Shi kam ko a jikinshi.Ya
tabe baki tare da daga gira sai me?A zato na bai
fahimci nufina ba, don haka sai nayi nufin
fahimtar da shi katafi da sauri kada ta ganka a
nan tayi zaton ko wani abu ne.Sai naga kurum
ya zauna bakin gado, na zaro ido dai dai lokacin
da ta shigo falo tana cewa Sadiya ina kika shige
ne?Kin ganmu sai ynzu?Da sauri na fito cikin in
ina na ce gani nan, kun...kun dawo?Eh, lafiya
na ganki a hargitse?Ta ce ba ko mai.Na yi
waje.Ita kuma ta nufi uwar daki, gabana yana
faduwa.Tana shiga ta ganshi zaune bakin gado
yanawaya, ta ce au, ka dawo?Ya ce, eh, na
dawo tun dazu, waye babu lafiya kika tafi
asibiti?Tace matar mai besfa ce a asibiti mukaje
duba ta.Ya ce, Allah ya bata lafiya.Ya mike bari
in karasa masallaci.Sai tin kunne na naji
maganar shi, a hankali yace sarkin tsoro.
Sam ya kasa bacci abin da ya kalla daga
yarinyar kurum yake tunanowa, juyi yayi har
gari ya waye sai ya dauki waya da nufin kiranta
dan yana togon cewa ita din halas dinsa ce.Sai
kuma ya tuna cewa yarinyar ba zatazoba, sanan
ga iya, kai!Shi fa ba zai iya jira sai sun tare
ba.Da safe naje kai masa abin kari, lokacin ya
gama shirin fita kawai zaiyi, ya amshi kofin daga
hannuna ya kurba.Sanan ya kalleni kin kawo a
latti, kin san da wuri nake fita. Na ce, a
shanarmu ce ta jike shi yasa, sai da masu shago
suka bude iya ta fita ta siyo.Ya ce my choice.Na
kalleshi zan sunkuyar da kai, ya ce a a kada ki
sunkuyar da kai, kalli cikin idona, bana son
wanan sunkuyar taki tana cutar dani.Na kalli
idon shi, ya ce yau ina bukatarki, na gaji ina da
mata kullum nine cikin azumi.Nayi kwalkwal zan
soma kuka, ya tsareni da idonshi, ya kuma
hanani sukuyar da kai.Cikin raunaniyar murya
na ce, kasan dai iya ba zata bari ba.Ya ce daina
karya da iya, na gano ma ba ita take hana ki ba
tun da ranar nan in an ji ta ce ki zauna da ni,
lokacin bani da lafiya.Ya mika min kofin tare da
cewa, zan fada mata, jeki abinki.Na tafi ina
mamakin shi, musanman da naji ya ce zai
fadawa iya zanso inji ko me zai ce mata na kasa
karyawa don zullumi, ina ta juya biredin dake
gaba na, kamshin turarenshi ne yasa gabana
faduwa.
Ya ce, iya na tafi.Ta ce to auta na, Allah ya
tsare.Ya ce, amin.Yana wucewa na sauke a jiyar
zuciya.Cikin jin dadi na gutsire biredi, na dago
kofin shayi na kurba sai naji takun sawunsa ya
dawo, take naji shayin ya sane.Ya ce au, na
manta iya.Ta ce, na'am iya za a zo a dauketa
taje ta gaida matar oga, ko bani ba wani zaizo
daukarta. Na kalli iya, shi dama vai jira amsaba
ya tafi, ganin kallon da take min sai na tsargu,
na taihashashen baki muka hada.Don haka na
ce, iya ke ce masa ba zanje ba,Allah ni bana son
xuwa.Ta harareni, bakya son zuwa ne kika bari
ya tafi baki ce ba zaki ba, sai nice zance karki
je? Bayan kun kitsa abinku?Ta taba baki haba
yayan nan, na fa rigaku zuwa duniyar har da
kuke son maidani wata sakara. Na ce iyya Allah
ba haka bane, ba mu kitsa komai ba, ni bansan
ko mai akai ba, ban san da wata magana ba sai
da yayi yanxun. Ta ce kwaji da shi, nifa bance
kada kije ba, ke da mijinki zan hana ki?Ta fada
cikin gatse sanan tayi tsakar gida tabarni zaune
cikin damuwa.Da naga har la'asar babu wanda
yazo nemana, kuma shi bai dawo ba, sai naji
dadi kuma na dan saki jikina. Cikin haka wayata
ta fara ruri, na daga a raina ina adu'ar Allah
yasa ya ce an fasa.Sai naji ya ce ki shirya
Usman zaizo ku taho.Sai da na daga murya
yanda iya zata jiyo, sanan na ce, yaya, Allah iya
ta ce bazanje ba. Iya daga inda take ta ce, a a
ba ruwa na ni Sa'adatu, ban hanaki ba ni ko
baku hada baki ba ni yar bada shawara ce.Yace
to najiyo abinda iya ta fada, don haka na baki
minti talatin ki shirya.Sai ya kashe wayarshi.Na
ce na bani yanxu yaya zanyi?Don Allah ku bani
shawara, inbi mijina ko in nunawa iya
harshashenta ba haka bane?
Taku Halima K/Mashi kemuku godiya. Awanna
gabarma Kanwarku Sadiya tana neman shawarar
ku, Saimun hadu a cikin littafi na biyu.Ku ziyarci
blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347

Darajar Yayana2-01
Posted by ANaM Dorayi on 09:52 AM, 20-Mar-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
___________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Assalamu'alaikum, barkanmu da warhaka fatan
kuna lafiya,nasan kunjini shiru a cikin wannan
littafin,lallai kam kusan incemuku babu wani
kwakwkwaran dalili face rashin kulawa daga
gareku,saidai dayake ni nayi niyya dole
incigaba,da wannan nake bawa masu yawan
bibiyata hakuri,In Allah ya yarda da sannu zamu
kai har karshen littafin,
Na tashi na shiga wanka ina yan kun kunai,ko
kallona Iya bata yi ba, sosai nayi gayu atanfa fara
da sirkin purple ne. Haka takalmana da mayafina
duk purple ne, na fesa turaruka sosai.Iya ta
kalleni ta ce, da ma na san kun hada bakine shi
ne za a gwada min bariki, in dai namijine kuje
Allah ya taimaka. Ni dai nayi sororo raina babu
dadi, sannan bani da mifita.Har cikin gida Usman
ya shigo suka gaisa da Iya, sanan yace zamuje ne
ta gaida Ogansu Aliyu.Iya ta ce, menene na
shirya karya Usman ku da matarku.Nina haifeku
fa har da kukega zaku yi mun wayo, a gaida
Gyambo karshen girma kenanko? Usman ya
sunkuyar da kai yana dan murmushi cikin jin
kunya, ni dai na ce sai na dawo.Da mota yazo na
shiga, gidansa muka fara zuwa ya ce inga Abida
matarsa minti biyu. Ina yin sallama ta amsa,
sanan ta ce kai Amarya kin tsula kyau sosai, taja
hannuna zuwa bedroom din ta. Zo muyi yar
shawara,Bakin gado muka zauna.Ta kalleni a da
banyi zaton zaki zama mai taurin kai ba.Na zaro
ido ina kallonta, ta ce, ranar juma'a da daddare
mijiki nan ya ci abinci tare da mijina, ina daga ciki
ina juyo su mijinki yana fadawa mijina halin da
yake ciki na takura.Gashi kinki ki bashi hadinkai,
har yana cewa wani dare da kika ki sauraranshi
har ya dagawaya ya kira wata yar sanda dake
nacin sonshi ta kuma sadaukar da kanta
gareshi.Har ta daga sai kuma tsoron Allah ya
shige shi, Allah ya taimaka ya tashi ya shiga yin
nafila, daba dan haka ta faru ba, me kike
tsammani?Na ce, wai Allah, daga nan sai
zina.Tace kina da kwamasho ko baki da shi?Na
ce, ina dashi.Madallah.Ta dafani yanxu abinda
nakeso dake, kinga ke yar zamani ce, ki rike
mijinki, in ba haka ba sai wasu su rike maki
shi.Na ce, anty iya ce, Allah ba dan Iya ba zanyi
duk abin da yake so.Ta ce, to baga shi yau zaku
fita ba, in kin dawo Iya ganewa zatayi?In ba ke
kika fada mata ba.Nayi shiru ta ce, to kisani kina
cikin tsinuwar ubangiji, in yanxu kika mutu mijinki
yana cikin wanan halin sai kin hadu da fushin
Allah, ma tsawar ba shi ya yafe maki ba.Gabana
ya shiga faduwa, na ce, Allah anty nitsoro nake ji
ban san yaya abubuwan suke ba, nima bansan
yana fushi dani.Tayi murmushi ba wani
wahala.Ta girgiza kafadarta, ki amince da mijinki
a duk lokacin da ya bukaci haka na rokeki.Na
raunana muryata, in na sa muku aure ba?Na ce
eh.Ta ce ki ceci kanki daga halaka fa, kin san
komai ke ba jahila bace....Muryar Usman ta
katsemu da cewa wai me kike kitsa mata ne?Zo
mutafi kinji.Ta ce, jeki kada yajimu basusan naji
firarsu ba, dan Allah ki kama mijinki hannu
bibbiyu ko bakya son shi?Na sunkuyar da kai ina
sonshi mana, bari dai in gani ko zan iya ina
tsoro.Na fita muka tafi.,ban san ina muke tafiya
ba, don kaina yana sunkuye ne ina wasa da
yatsuna.Har zuwa lokacin da motar ta tsaya.Ina
daga kaina COMMAND GUEST na gani.Ya ce jirani
kadan ina zuwa.Gaba na ya shiga faduwa, koda
ban san ko inane nan ba na tabbata Hotel ne
tunda naga an rubuta guest.Bayan wasu lokuta
ya dawo yana waya, danhaka da hannu ya yafito
ni, na fito a baya nabishi yana ci gaba da tafiya
tare da tin waya.Kuma na fahimci kamar da ya
Aliyu suke magana, dan naji yana fada mai ga
mu nan yanxu zamu shiga cikin hotel din.Kuma
ni zan wuce ne dan Allah kayi hanzari muka ratsa
falon muka nufi jerin dakuna yasa makulli yana
bude wani daki.Dai dai lokacin sako ya shigo cikin
daki wayata, na ciro na duba.Cewa yayi kishiga
kijirani kadan my choice.Na kalli Usman yayi
murmushi ba da jimawaba zai zo, yanzu zaki
ganshi.Na shiga cikin dakin ina dari dari, tare da
yankalle kale, ya tako ya shigo dakin.Kada ki
damu ya dauki remote ya kunna TV, kiyi kallo ga
tashar India nan abin sonku mata.Ya nuna mata
wata takarda.In kina da muradin wani abu ga
wanan takardan ga numbe waya ki kira ki zabi
dayadaga nau'in abincin da kike so ko na sha, za
a kawo miki.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Har ya kai bakin kofa sai kuma ya dawo, ya ciro
wallet dinsa ya bude ya ciro katin MTN ya miko
min.Gashi ki loda a wayarki.Ya sake juyawa ya
tafi, tare da cewa ki kulle kofar in yazo zai
kwankwasa sai ki bude, na barki lafiya.A sanyaye
na ce, na gode.Tunda ya fita ta gumi na hada,
tunani da zullumin abu biyu ne na farko in ya zo
mai zai faru?Sanan yaya zan kare da fada iya in
na komagida?Ban ma san takaimaimain lokacin
da zamu bar nan ba.Fim din da ake yine ya dan
shagaltar dani, don haka ban lura da lokaci ba,
sai da na kalli a gogo na rude, shida dai dai na
yamma.A raina na ce tafiya zanyi.....kwankwasa
kofar ya dakatar dani, na bude cike da faduwar
gaba, a zatona shine ashe ma aikacin gurin ne
yake tambayata ko zanci wani abu?Na ce a a yace
kada ki damu Oga ya na nan zuwa, ban tanka shi
ba na maida kofar na rufe.A raina nace wato har
sunsanshi tunda gashi suna cewa yana zuwa.Na
ce wa yasani ma ko yana zuwa da mata.....na
katse zancen da cewa a'u'zubillah, ba kyau
munmunan zato.mikewa nayi ina ta kai komo a
tsakar dakin, tunanina wa zan kira wanda
zaikaiwa iya waya in mata bayanin cewa yaya
nake jira mu dawo.Can na tuno da Bello, na kira
wayarsa dan akwi number shi a wayata, kuma
yana kiran Aisha itama tana kiranshi da layi
na.Muka gaisa, na ce dan Allah Bello in kana
kusa ina son magana da Aisha ne, tayaya zaka
taimaka min?Ya ce bani minti hudu zuwa biyar a
kai mata. Na ce nagode. Sai da na bari kusan
minti shida sanan na kira cikin sa'a kuwa ta
daga.Na ce,Aisha taimako nake nema a wajenki,
don Allah.Ta ce na me?Na ce, kin sani ne?Mun
fita har yanzu bamu dawo ba, shine nakeso kije
kicewa iya don Allah kada taji shiru mun nan
dawowa.Ta ce, keda wa kuka fita?Na turo baki
tamkar ina gabanta, nace da wanan ya Aliyun
mana.Da sauri ta ce, au, ke da mijinki kika fita?
Bata jira amsa ba ta ci gaba da cewa, to ba zan
fada mata ba, na zata ma ke da wata ce, to in
shekara ma zakuyi ina ruwanta?Ta ja tsaki.Dan
Allah malama in zakiba mijinki kulawa ki bashi
kulawa kawai, sai an jima ta kashe batare da
nasake jinta bakina ba, nayi sororo ina kallon
wayar.Shi kuwa ya Aliyu daidai wanan lokacin ya
isa gidansu iya.Tana girki yayi mata sannu da
gida, ta ce yauwa ina yar tawa?Ya ce, yace yanxu
zanje in sameta in nayi wanka daga gidan oga
xuwa gidan sauran Abokai na.Murmushi iya tayi
ta ci gaba da cewa, wai ni za'a yiwa wayo, nifa
na haifesu, ni fa duk abinku kar nake kallonku.
Shiri yayi ango sosai, sai zuba kamshi yake yi, ya
nufi masauki na comman bayan yayi tsarabar kaji
da lemuka da kalolin madara masu tsafta. Ya
gaisa da masu tarbar bakin inda wani daya yake
tabbatar masa da cewa a jiyarsa na nan a ciki,
sun lura da ita yanda ya kamata.Kwankwasa
kofar ta re da muryarsa naji, inda yake cewa
Dear my choice.Jikina ya dauki bari, naje na bude
kofar tare da yi masa sannu da zuwa.Na amshi
ledojin hannunsa, kallo yake tayi tunda ya shigo
har ya maida kofar ya rufe, na ajiye ledar na
zauna kan kujerar dake kusa da gadon.Kai tsaye
yazo ya zauna kan hannun kujerar.Dear my
choice kinjini shiru ko?Yayi maganar cikin wata
laulausar murya
Na kalli a gogo gabana ya ci gaba da faduwa,
nace gashi har magariba ta karato, yanzu iya
tana can aiki yayi mata yawa, tana kuma jira
na.Ya kama hannuna me zakiyi mata da zata
jiraki?Na ce abincin dare mana.Ya hada tafin
hannuna da nashi ya sarke.Sanan ya dan matsa,
in kin tare a gidanki wane zai dinga yi mata aiki?
Cikin raunaniyar murya na ce, zan ke aika mata
duk abin da naci.Idanu na suka kawo ruwa don
tunanin rabuwa da iya.Ya dago fiska menene na
kuka?Na ce, ina tunanin rabuwa da iya ta ne.Ya
kwantoni jikinsa.Yi hakuri kanwata, ai ba wani
nisane tsakanin mu da iya ba, kullum nasan
zatazo ta duba ki, in bata zoba kuma mu
zamuje.Na kalli cikin idanunshi, da gaske zamuje?
Ka min alkawari fa.Ya ce, in sha Allahu.Ya ciro
fari kar din hankici mai kamshi daga aljihunsa ya
soma share min hawaye.Tashi kiyi alwala muyi
sallah sai muci abinci.Gurin da na idar da sallar
ya sameni, ya bajekomai gani da shegen kwadayi,
amma fargaba ya hana ni ci.Duk hankalina tashe
yake, ya lura da haka, sai ya soma lallashi
na.Haba Sadiya my coice, me nene naga duk kin
damu?Nifa mijinkine na sunna.Nace, to ai iya ta
ce kada wani abu ya faru tsakanin mu, har sai
mun tare.Ya ce to zata sani ne, ko ke zaki fada
mata?Na soma kuka, ina kallon fuskarshi.Wlh
yaya zata gane.Zumbur ya mike daga kusa dani
ranshi a bacce, ya soma yin magana cikin daga
murya.Kina fakewa da Iya ne kurum dan kawai ki
cucheni, ba fa haramun zan aikata ba.Kinsan ina
kyalekine ina lallabaki, in nace zan gwada maki
isa ba zaki iya kwatar kankiba ko?Jikina ya soma
bari, yaya don Allah kayi hakuri.....Yi mun
shiru.Ya katsane, sai wahala kike bani kina wani
inyi hakuri, ba zan hakura ba, haka nan ba zan
matsa maki ba, amma ki sani baki ba komawa
gida ko da zamu shekara a nan harsai kin yardar
min a bin da ya halasta min.Na fara kuka wiwi
shi kuma ya fice ya zare makulli ya kulle ni ta
baya.Na fada kan gado ina kuka, wata zuciya ta
ce mun gara fa kiyarda dan sai kin dibi kunyar da
bakiso a hannunki, don dan shi namiji babu
ruwansa.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Dasauri na dauki wayata na soma kiran layin
sa.Tayi ringing kusan sau biyar sanan ya daga,
cikin kuka na ce, yaya dan Allah kazo na
yarda....Da zafin rai ya ce, bana so, ke har kin isa
mzacen da zaki ja raina?Bari kiji wani abu, baki
son ki dade kada iya ta zargeki ko?To ina mai
shaida maki cewa nan zaki kwana, in yaso in kin
koma gida sai inga maizai faru.Ya kashe wayar,
ransa ya baci dani sosai.Daya wayarsa ta soma
ruri da sauri ya cirota don in yaji ringingi din ta
daga office ne, duk da ba ganinsa yake ba sai da
ya nutsu da ya daga ya ji muryar.Cikin sauri
sauri yake magana.ASP kana ina ne?Aliyu ya ce,
ina nan kan titin waff Road.Ya ce, yauwa kana
kusa ma, yi hanzari ka iso nan (headquarter) ka
kwashi yara ku nufiunguwar rimi layin dan marina
gida mai lamba tara, yan fashi sun shiga gidan
sunyi fashi.Sanan sunyi gaba da babban yaron
mai gidan.Ga ni nan zuwa ranka ya dade.Aliyu ya
amsa cikin izza, a duk lokacin da aiki ya taso
Aliyu yakan mance da duk lamarin dake gaban sa
matsawar ba salla ba ce.Sun isa gidan da yan
fashin suka shiga, Aliyu tare da inspector Adamu
da sajan Musa, sai kofur Bala.Cikin natsuwa Aliyu
ke kallon ko ina, kafin ya soma magana.Hajiya
sannunku da juyayi.Ta ce, yauwa.Cikin kuka da
rawar murya ta amsa, ya ce ina mai gidanki?Ta
ce, baya nan, kuma dama sunce shi sukazo
nema.Ya kalli kofur wanda tuni ya soma rubuta
komai, ya sake maida kanshi ga Hajiyar.Ta ina
suka shigo?Ta ja majina, sanan ta ce ta kofa.Ta ci
gaba, sun ga Yusuf ya shigo a cikin motar baban
su to sunyi tsammanin shine tunda gilashin mai
duhu ne.Don haka sai suka biyo shi.Aliyu ya ce,
shi Yusuf din daga ina yake?Ta ce, daga masalaci
ya ke, babansu yayi masa waya, cewa yaje ya
dauko motarsa.Don ni ya soma kira wai in kira
masa Yusuf ya dauki motar, sai na ce ya kira
layin sa ya fita masallaci.Kuma ba lallai bane
daga can ya dawo gida ba, Aliyu ya gyada kai
alamun gamsuwa sanan ya ce, motar ta samu
matsala ne?Ta ce, a a.Sau biyu ana biyo shi ana
kai masa hari a motar da dare shi ne dalilin da
yasa sam bayason karfe tara tayi masa a motar
na dare.Yau ma mitin ne zasuyi da ya taso musu
da gaggawa kuma bai san lokacin da zasu tashi
ba.Aliyu yayi taku zuwa tagar ya daga labulen
windon yana kallon harabar gidan haskenta
kamar duhun magariba baiyi ba.Ya waiwayo ya
dubeta wace mota ce daga cikin wayan nan
motocin guda uku?Ta karaso ta daga dayan
labulen windon wanacan (hondar ce) baka CRV.Ya
saki labulen yanzu mai gidan ya sani?Ta ce, a a
yana kashe duk wayoyin shi ne in zasuyi
mitin.Ina ne gurin aikin nashi?Aliyu ya bukata
cikin rawar murya ta ce, shine manaja a first
bank.
Aliyu yayi shiru kamar mai wani nazari, can ya ce
zaki iya fada mun kamannin yan fashin?Ta ce,
eh, zan iya.Babban su baki ne dogo kuma kamar
yanada yare, don hausarshi bata goge ba.Sai dai
kila muslmi ne, sauran kuma biyu fararene ina
zaton fulanine, biyun dake waje ne ban tantance
su ba.Aliyu ya jefeta da wata tambayar, yaya kika
yi tsammanin musulmine? Ku ziyarci blog dinmu
domin karanta Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta ce, haka kawai naga kamar musulmine.Aliyu
yayi guntun murmushi.Bari mu barki haka, yanxu
bari muje mu dora bincike.Ta sake fashewa da
kuka.Ran ka ya dade ka taimake ni yanzu yaya
za'ayi mijina ya samu labari dan kada ya fito
sukama shi?Aliyu ya ce, kada ki damu, zamu
bashi kulawa da tsaro, sanan ki saurara sosai
nasan zasu kiraki ina zaton garkuwa zasuyi
dashi.Kiyi mana saving din number, in kuma ba
number ki kiramu ki sanar da mu.Ta ce, to
yallabai na gode.Ya ce ba komai kiyi adu'a.Suna
fita ya kira AC ya koro masa komai, AC ya ce, to
yanxu ku fara ji da maigidan nata, sanan kunsan
yanda zakuyi ko?Aliyu ya ce, yes Sir!Sai dai ina
kake ganin za a bashi mafaka tunda ba dama mu
barshi ya koma gidansa?AC ya ce kuxo nan dashi
daga nan sai a kaishi inda ya dace.Aliyu ya kara
cewa yes sir.Ya dubi yaran kumaje first bank.Sha
biyu da minti ashirin, Alhaji auwal ya fitoa rikice
daga cikin banki, gama mitin dinsu ke da wuya
police commissioner ya kira shi bayan ya kunna
wayarshi.Ya fada mashi cewa ga yarana nan zasu
taho dashi dan kare lafiyarsa.Alhaji auwal ya ce
saboda me ranka ya dade?Commissioner ya ce,
masu bibiyara ne suka shiga gidanka, amma ka
kwantar da hankalinka za a kama su.Suna tafe
cikin mota Alhji sai adu'a yake yi yana tunanin
me ya tarewa wadan nan bayin Allah?Kofur ya
ce, Alh kaji cewa sun tafi da yaronka?Aliyu yayi
mashi tsawa da cewa kofur?Da sauri kofur yace
yes sorry sir.Alhaji Auwal ya ce ranka ya dade
wane dan nawa dauka Yusuf? Aliyu ya ce kada ka
damu, in mun isa can zakaji komai a bakin
yallabai, kuma duk abubuwan zasuxo da sauki.
Alh. Auwal ya ci gaba da adu'a.
Ofishin commissioner yayi tsit tamkar babu
mutane sai karan (ac) da na fanka.CP ya kalli
Aliyu dake kame, ya ce nasan kana da kwazo
Alhamdulillahi,yanzu sashin binciken mu na
takama da kai.Domin aikinka kanayinsa da
karsashi gami da izza.Ya kalli Alh. Auwal kada ka
damu Alh, babu abin da zai samu yaronka.Zamu
baka kula shi kuma zamuyi dauki badadi da
su.Alh, ya ce, kana ganin ba zasu kashe shi ba?
CP ya ce, ai kudi zasu nema munsan irinsu, sai
dai yanda tayi kwatancen shi ina zaton bako ne
kila kuma ya jima yana yi bamu taba arba dasu
ba ne.Amma wanan karon in sha Allah za mu
hadu.Ya kali Aliyu ASP aje ayi shiri yanda ya
kamata.Ina bukatar barayin nan tako wane hali
sai dai banda kisa zan saurari wayarka a ko wane
lokaci kwa iya tafiya
Sai da Aliyu ya tunkari gida sanan ya tuno da
wata Sadiya, amma duk da haka bai wani damu
ba dan yasan zata sami kulawa yan da ya
kamata.Ya sake ciro waya ya kira, jim kadan aka
daga, ya ce Ibrahim dan Allah ajiyata na nan?Aiki
ya rike ni da safe zan turo aboki na ya tafi da
ita.Ibrahim ya ce ba ko mai yalla bai.Sun saba da
Ibrahim ne sakamakon wata matsala da ta taba
tasowa a Hotel din su Aliyu suka bincika case
din.Ibrahim shine me kula da dakunan kwana na
cikin Hotel din.Motar yansanda tayi faking a kofar
gidansu Aliyu ya shiga gidan da hanzari.Sai da ya
gama shirinsa sosai sanan ya nufi dakin iya.Tana
kokarin fitowa suka ci karo, yace iya na kama
hanya zantafi wajenta aiki ya taso.Usman zai tafi
ya daukota ko da gobe ne.Kar ki damu canma
gida ne gidan Oga ne.Haushi ya hanata magana,
Aliyu ya dafa kafarta, ki min adu'a iya da yan
fashi zamuyi arta bu, kin san aikin mu bakin rai
muke yin shi.Ta ce Allah ya baku sa'a.Gudu gudu
ya fito.Da kallo ta bishi har ga Allah bana son
aikin dan sanda amma bata so ta bata rai a kan
haka, dan kada ta tauye shi.Ta tabbata adu'ar ta
ita ce daukakarshi, fushinta zai iya tauye shi a fili
ta furta, Allah ka yi wa yaran nan Albarka
dukansu, ka dorasu a kan hanya ma daidaiciya
amin.Nikam a a lokacin ina can tsoro, fargaba da
bakin ciki sun isheni.Kai har da nadama.Naji
haushin kaina da naki bin umurnin mijina, gashi
yanzu ya tafi yana fushi dani.Nasan mala'iku ma
ba zasu raga min ba, kuma iyar da nake cewa
zata yi mun fada in taga na dade, to sai dai ta
kashe ni.Dan ina ganin tabbas nan zan kwana.Da
na bi umurninsa kila da yanxu mun tafi gida cikin
jin dadi.Kila ma yayi ta shi min albarka, mala'ku
suna amsawa.Naja tsaki tare da cewa, kash!
Nima ban yi ba wlh.Haka nayi kwanan zaune,
danma na rage daren da yin nafilfili, sai da nayi
sallar asubahi sanan na kwanta.Bacci ya tafi dani,
ban farka ba sai kusan sha daya.Kwankwasa kofa
ne ya tasheni, nazo na ce wanene?Ya ce, Ibrahim
ne.Na ce, ai ya rufe dakin ya tafi da makullin.Ya
ce, ba ko mai ga wani makullin, me kike bukata?
Nace ba ko mai, akwai abinci a nan dakin dayazo
dashi jiya.Ibrahim ya ce, to shi kenan.Ina jin
takun tafiyar sa, na zauna a gurin dantsabar
takaici, bani da ma ranar tafiya gida ke nan.Shi
kam dai dai wanan lokacin yana gidan Alhaji
Auwal cikin falonsu inda yake sauraron bayani
daga bakin Hajiya.Yanda sukayi da yan fashin da
suka kirata.Ta ce, kamar yanda kayi zaton zasu
kira sunkira ni yau ya da safe.Aliyu ya ce, karfe
nawa?Ta ce takwas da rabi dai dai suka ce kudi
suke so naira miliyan uku da rabi.Sun ce in har
ba a sami kudin ba zuwa jibi zasu kashe shi,
kuma sun ce basa son jami'an tsaro su shigo ciki,
kuma basa so a nemi ragi.Me kika ce musu?Ta
ce, ni kuma duk abin da suka ce da to nake ta
amsa musu. Ya gyara zama ya ce, ina suka ce a
kai musu kudin?Wai filin golf.Ina number da suka
kiraki?Ta dauko wayar ta fito da namber ga ta
nan.
Ya amsa ya dauki number sanan ya fita harabar
gidan yana sanar da CP halin da ake ciki.CP ya
ce, ka tafi da layin kamfanin su, wane layi ne?
Aliyu ya ce (MTN) ne.CP ya ce, maza ka tafi dashi
ka tambatar kayi abin da ya dace da wuri, dan
kila cire layin zasuyi ko kuma anjima su kira da
wani layin da ban.Aliyu ya ce, an gama sir.Sai da
yaje office din Usman sanan ya tuna da
Sadiya.Bayan sun gama magana akan abin da ya
kai shi, dama usman MTN yake aiki, sanan ya ce,
wanan yarinyar mai shegen tsoron tsiya, kuka
tayi ta min na barta na tafi abina.Idan ka tashi
dan Allah katafi ka taho da ita don ni ko ganinta
bana son yi.Usman yayi murmushi, sanan ya ce,
kayi mata uzuri, kasan yarinya ce sai a
hankali.Usman ba da bata lokaci ba ya sanar da
manajan su, nan take aka soma gudanar da
bincike a kan lambar.Sun gano layin a yanzu baya
kan waya, amma sun hada komai yadda da an
dora shikan waya zasu gano inda mai layin
yake.Nan take kuma ya kira CP yayi masa
bayani.CP ya ce, good! Kara zage damtse in kuma
kana bukatar yara duk sanar dani.Yes sir!Inji
Aliyu.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Na idar da sallah azahar ke nan sai naji alamun
ana bude kofa, fatana Allah yasa yaya Aliyu ne,
in sha Allahu yanzu nan zan bashi mamaki
Sai dai kashi!Ya na budewa sai naga yaya Usman,
ya ce tattaro kayanki muje gida.Na dauki jakata
da mayafi, sanan na gaishe shi, ya amsa tare da
cewa ki kwaso lemukanmana.Na ce, na kishi da
su. Ya ce, ai kya kai wa iya tsara ba ko kina nufin
gidan Oga ba a baki ko mai ba duk da cewa kin
kwana?
Yayi tambayar cikin zolaya, na dawo na dauka,
har ya taya ni sai lokacin naga Ibrahim din da
suke nagana, gajere ne baki.Sai da muka tsaya
Marhaba Store ya kara min tsaraba wai harda
turmin zani matar Oga ta ce a ba Iya.Da zan fita
nace masa nagode, ya gai da anty Abida, ya ce
zata ji.Sanan ya ce, ki saki jikinki don kada ta
gane ba can kika je ba.Ina yin sallama iya tana
zaune, cikin faduwar gaba na isa gurinta ina yi
mata sannu, ta amsa fiska daure.Jikina yayi
sanyi, nayi karfin halin cewa.Iya kin ganni sai
yanzun?Tun da yaya ya kaini ya Aliyu bai zo ba
har sai da na kwana, wai suna aikin wani case ne
a hannun sa.Iya ta ce, kai ma dallah da jin haka
sai nayi shiru, don na san zance na bai shiga Iya
ba, na mika mata leda.Gashi inji matar ogan yaya
din wai in baki tana gaida ke.Sai naga iya tayi
murmushi ta girgiza kai, sanan ta ce an gode.Tun
lokacin ban sami bakin magana ba sai daki da na
shige na kwanta.Har yanzu haushin kaina nake ji,
da na sani nabi umirnin miji na, gashi wanda
naki don ita bata yarda ba, kuma nayi imani ko
da mezan ran tse ba zata yarda da ni ba.Aliyu
yayi nasarar kama dan fashin nan tare da
taimakon masu layikan wato network na
waya.Don yan fashin sunyi anfani da layika
dabandaban, ya kama oga tare da wani yaronsa
guda daya, jim kadan bayan an basu kudi sun
saki yaron.Sun dauki hanyar kawo da a lamun
zasu bar Kaduna ne, ya harbi tayarsu sanan ya
harbi ogan a kafa.Sauran sun gudu shi kuma
dayan tsayawar da yayi zai dauki kudin daga but
din motar shi ya kawo Aliyu yayi nasarar kama
shi.Wanan gaggarumar nasarar ta sa an karawa
Aliyu girma daga ASP zuwa DSP, inda aka tara yan
jaridu suka watsawa duniya.
Duk kwanakin nan da aka dauka sam Aliyu baya
shiga harka ta, in na gaida shi zai amsa amma ko
kallo ban isheshi ba.Haka nan har daki na same
shi don inyi masa murna kan karin girman da ya
samu, amma sai ya ce dan Allah in fitar masa
daga daki.Har Iya ta na ce mun Allah ya kara,
tun da na ba da kaina ba loka cin da ya da ce ba
ai yazama dole in jure wulakanci, bani da hujjar
yin musu dole in yi shiru.Gadan gadan ya tada
aikin gidan sa, da alamu ya sami kudi, ranar
wata a Abar bai fita da wuri ba.Sai da suka shirya
sanan sun fita hanya sanan ta soma yi masa fada
me yasa yake yiwa marainiyar haka?Ya ce, bata
jin magana ne, gara ma ki mata fada tun yanxun
don ba zan dauki gaddama ba.Sunje iya nata
santin gidan, ta ce gobe kawo kayanta ko?Aliyu
ya ce, amma na dakin anjima zan kwasosu har
da TV da su Radiyo, kema na sai miki TV.Ta rinka
godiya.Washegari makota da yan uwa tare da
matan yayan mu sukazo suka yi mun jere, da
dddare kuma aka yi mun rakiya.Iya tayi mun
fada sosai, kuma ta kara nanata mun cewa tunda
ni na dage da son ya Aliyu lallai in lallaba
halayanshi.Don bata so in kawo mata wani kara'i
sananta sa mana Albarka tare da yi mana adu'a
tagari.Kowa ya tafi sai ni daya, nayi sallar isha'i
da shafa'i da wutiri, sanan nayi wanka, kwalliya
sosai nayi duk da cewa ina cike da fargaba zai
kalleni ko ba zai kalle ni ba.In ma ya kalleni ni
me zai faru?Goma da wani abu naji ana
kwankwasa kofar gidanmu.Da sauri naje na bude,
shi daya ne kuma sanye da kakinsa na dan
sanda, ke nan shi Abokanai ba zasu rakosa ba
kamar kowane ango.Na amshi kayan hannunsa,
jakace da leda tare da yi masa sannu da zuwa,
ban zaci zai amsa ba, amma ga mamakina najini
a jikinshi ya rumgumeni tsam.Sanan ya amsa da
yauwa sannu.Ina makale a kafadar shi ya kulle
gidan mu.Ina mamakin halin yayan mu sosai,
tamkar bashine yake gaba dni ba.Abaki yayi ta
bani kazar da ya shigo da ita tare da madarar
holandia.Duk fargaba ya cika ni, amma haka
naita sha har sai da yaga kamar zanyi amai, ya
ce, kin koshi?Na ce eh.Munyi Sallah inda ya dafa
kaina yayi mun addu'a.Bai bata lokaci ba gurin
ibadar aure, wasanninsa sunyi mun nauyi.Don
haka na soma rokonsa yayi hakuri, mai makon
haka sai yaji kamar wata sarewa nake busa
mashi.Nasha wahala a wanan daren nawa na
farko, domin duk wani haushinsa sai da ya huce
shi, sanan ya dawo yana tausaya min.Don shi da
kanshi bai sai saita kanshi ba.Shi ya taima ka min
na gyara kaina.Ku ziyarci blog dinmu domin
karanta Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ba mu jima da kwanciya ba aka kira sallah, ya
tafi masallaci nima nayi tawa sallar.Naso
kwanciya amma sanin cewa zai fita da wuri yasa
ni shiga kincin don hada abin kari.Lokacin da ya
dawo zatonsa zai sameni a kwance, sai ya ganni
kicin.Ji kawai nayi an rumgumeni ta baya.Na
gaida shi ya amsa ya ce, naje nayi bacci don
yasan ina jin bacci, na ce ba komai inya fita zan
kwanta.Tare muka karya, sanan ya ce, inzo in
cuda masa bayan sa tun ina jin kunya har na
gyare don kuma yariga ya tsomani cikin
ruwan.Tundaga ranar komai tare muke yi, wata
masifafiyar soyaya yake nuna min har na dinga
mamaki, sai dai ina gyaruwa wajen kwanciya.Don
ya Aliyu mabukaci ne fiye da zatona, rana, safe,
dare office ma sai ya dawo, haka nayi ta jurewa,
saboda yana ririta ni kamar ya hadiye ni.Satin
mu biyu nayi fari fiye da da, fatata ta goge,
amma na rame.Dan Almajirin da ya so min shine
ke min aike, kullun sai na saka mai abinda muka
ci ya kai ma iya.Ranar da nacika sati biyu ranar
iya tazo, dukinda nayi iya tana da ido, bayan na
bata ruwa da abin tabawa sai na zauna kusa da
ita ina cewa iya nayi kewarki sosai ke fa?Ta ce,
Sadiya kewa ai ba a magana.Amman kuna zaune
lafiya?Na ce lafiya lau, Iya.Yaya na ji dani, baki
gani ba.Tace Sadiya ni sai naga kin rame, kina cin
abinci kuwa?Na ce, ina ci mana.Aka kwankwasa
gidan, na ce gashi nan ma.Da sauri naje na
bude, ya manneni a jikin sa na ce iya tazo.Ya ce
tana nan?Na ce eh.A zatona zai sake ni amma
har fallon mu saida ya zauna sanan na zame na
barsu suna gaisawa da Iya.Na kawo masa ruwa
da abinci, yace my choice ba zan ci abinci ba,
dama nazo ne in dubaki kawai don na kira
wayarki a kashe.Nace yanzu aka kawo wuta, ka
kuma san batir din baya rike chaji.Ya ce, haka
ne.Zan chanja maki wayar ma, Iya ma in sai
mata.Tace ni yanzu gadanga in ka hada ni da
waya ban san yaya zanyi da ita ba.Na ce, zaki iya
mana, mun gode yaya.Yayi murmushi tunkafin a
siyo?Ta ce, ai nasan tunda ka furta zaka
aikata.Iya ta ce, gadanga kai naga kayi bul ka
kara kiba ita ko yar tawa duk ta rame.Ya kalleni,
ashe bani kadai nake ganin wanan ramar ba, to
ko Asibiti zamuje?Na ce, yaya babu inda yake
min ciwo sai muje Asibiti?Yace rama ciwo ne My
choice, zasu baki magani.Iya ta ce, ni da na zaci
ko rigima kuke.Ya ce, haba dai, ai yar taki tana
da biyayya.Iya tayi murmushi sanan ta ce, haka
nike so,Allah yayi muku albarka, ya baku yaya na
gari.Yaya ne, ya amsa da amin.Tare da dago
haba ta.Iya ta ce bari na tafi.Naje daki na dauko
dubu daya na ce, iya gashi, ta ce ina kika sami
kudi?Na ce, in abokan yaya suka zo suka bani, ko
na bashi sai ya ce in ajiye abina.Kuma ni ko katin
waya shi ke loda min.Ta amsa tare da ce min
Allah ya anfana.Na ce, Iya da kin dan bari sai
anjima.Yaya ya harareni ke zakiyi mata aikinta a
gida?Na ce, (cikin shagwaba) ba ina kai mata
kullum ba, ia yana isarki ko?Ta ce har ma in rage
in ba wani.Sai dai duk da haka ina yin girkin
saboda almajirai ko yan ciranin nan na
mokatanmu.Na ce, har yanzu iya kina ci dasu?Iya
ta ce, wanda ka bada shine naka.Nace to ki tsaya
zanyi da yawa sai in sa miki.Aliyu ya kawo hannu
ya dan mintsineni gefen ciki na, tare da cewa
sauran aikin ke zakiyi mata?Iya ta nufi hanyar
fita tana fadin Sadiyayyena kina in zauna shiko
gadanga korata ma yake.Da sauri kuma cikin
dariya ya ce, lah, iya bankoreki ba, nima yanxu
zanfita nazo duba ta ne kawai, kuyi zamanku ni
bari na tafi. Duk muka sa dariya, Iya ta ce a a
yayan nan ni dai naji dadin yanda na sameku
haka, fatana Allah ya kauda shedan tsakanin
ku.Ta bude kofar gidan ta fita, ya bita nikuma
nayi mata alkawarin xuwa inyini in an
kwanabiyu.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Bayan ya dawo daga yi mata rakiya ya sameni
ina gyara gurin, ya makaloni jikinsa ya dago
fiskata.Sarai kinsan abinda ya kawoni, shine kike
rokon iya ta zauna ko?Gaba na ya fadi, amma sai
nayi yake tare dafadin ba haka bane.Muka nufi
dakinsa.Na rasa duk lokacin da yaya zai zo mun
da wanan batun gabana ya dinga faduwa
kenan.Na kasa sabawa.Ko shi ke sani rama?
Oho.Kawaye na duk wace tazo sai tayi zancen
ramata, haka Aisha, ta damu da son jin dalili
Na dage kan cewa ba ko mai, tunda bai kyautu in
fada mata yanayin mijina ba.Munje Asibiti likita
shima ya sha mamakin jin banda matsala kuma
ba inda yake min ciwo, amma na rame.Sai dai ya
ruvuta mana magunguna masu sa cin abinci,
amma duk da haka sai a hankali.Wani dare anty
Abida ita da Usman sun kawo mana ziyara
munata hira, sai Aliyu ya kawo batun ramata, aka
danyi zancen har Usman yana tsokanata da cewa
ina tsoron kishiya ne ki daina tunani, aboki na
naki ne ke daya.Nayi dariya sanan na ce, nasan
haka shima yasan haka.Yaya Aliyu yayi dariya.My
choice ban maki alkawari ba fa.Na ce, yaya kaima
kasan ko bakai min alkawari ba kai nawa ne ni
daya.Abida taja ni bed Room dina muka zauna
bakin gado, ta kalleni wai me yake damunki? Na
ce, ba ko mai wlh.Ta ce, ki fada mun ban sani ba
ko zan iya taimakonki.Nayi shiru ina nazari, can
nace anty ba ko mai, Allah sai dai ina zaton ko
dan yaya yana da yawan buka ta ne?Kin san
Allah anty na yaya bashi da hakuri hatta kai da
na ganshi ya dawo gaba na ya dinga faduwa ke
nan.Ta kada kai zancen ke nan, amma wanan ba
abin damuwa bane, da farko ki daina tsorata har
gabanki ya dinga faduwa.Kisa haka aikin da ya
zaman maki dole, aure bauta ne, in zakiyi sallah
gabanki na faduwa?Na ce, a a.Ta ce aikin gida fa?
Na ce, a a.Ta ce, wanan ma kisashi cikin dolenki,
tunda zama ne ba na kare ba.Gashi baki son
kishiya.Tayi dariya sai dai zan fada maki wasu
abubuwa da zasu taimakeki, dauko biro da
takarda.Na ce, to.Na tashi na dauko memo, ta
soma bayani kamar haka:
ki samo Dabino,Zuma,Aya, da Cukui zaki maidasu
gari ne, sanan ki dinga zuba madara peak da
zuma kina sha kullum safe da yamma.Kinji daya?
Na ce eh, na rubuta.Ta ci gaba, ki samu,kankana
ki dinga yawan shanta har kwallon,na ce gashi
kankana bata dame ni ba, ta zaro ido to kuwa ta
dame ki, kuma kya iya yanyankata ki zuba mata
madara peak ki dinga sha shima har
kwallo.Sanan a kai na kan Akuya, ki dafa shi da
romo, sai dai bazaki zuba mashi mai ba,
maimakon mai ridi zaki zuba da yawa ki cinye ke
daya.Haka kuma zaki sami garin dabino ki fasa
kwai da madara peak ki juya ki shanye.Nace wai
zan iya duk wanan?Ta ce, ki gwada tun gobe zaki
sanya ya nemo maki amma karki fada masa
dalilinki na son kayan, kawai kice zakiyi anfani da
su ne.
Kan batun ramarki kuwa, ki canza abin kari, da
me kike karyawa?Na ce,Tea ne sai Bread da Kwai,
watarana inyi kunu da kosai, ko indomie da
kwai.Ta ce ki koma cin dankalin turawa da
agada,ko doya da kuma kwai, in da hali harda
farfesu.Shayinki kuma ya zama yaji sugar da
bota, milo da madara.Ki zuba sosai yayi kauri
kisha.Sanan kirinka baccin rana shima baccin
yana sa kiba, sanan da daddare kici abinci
sosai.Na ce, to anty na gode.Ta ce, ba komai, ke
dai kada kiyi wasa, in kinyi su da kyau na tabbata
sai kin dawo neman wasu.Ko da yake ban fada
maki na tafin hannu ba,kin san hannu yana daya
daga cikin mai aikawa da sakonni.In mijinki mai
yawan kama maki hannu ne, ki samu zautun ki
kwaba da suga ta narke, kullun in zaki kwanta ki
rinka shafe hannunki.Sanan ki rinka shafawa a
lebunanki, nace to na gode anty sosai.Sallamar
yaya ce ta katse mu, ya ce, me ta baki kike ta
godiya?Nace abubuwan karin kiba ne wanda zan
rinka karin kumallo da su.Ya kalli Abida dama
zaki iya wanan taimakon amma kika share mu?
Muka sa dariya harda shi.Ya ce, mun gode.Ta ce,
ba wani abu bane wanan har da za ayi mun
godiya.Kai dai ka dage da siyo wa.Ya ce, in sha
Allahu ko su ke nan kudin za a siya, me nene da
me nene za a siya?Na ce, na rubuta zan nuna
maka.Yayi murmushi, to da kyau, yace kizo, abiki
yace zaku biya ta gidan yar uwarki ko?Ta ce, eh,
tare da mikewa na shiga dube duben me zan
bata, turare na bata mai kyaunace ta kaiwa
Ummulkhairi.Ka fin ya dawo da ga rakasu, har na
gama rubuta abinda ta ce na rinka karyawa da
shi,ya ce agada da dankali sai da safe, nayi
godiya da cewa Allah ya kaimu.Cikin satyn na
hada duk wani abu da anty Abida ta fada mun,
na shiga anfani da su.Kafin wata daya naga canji
sosai, yanzu bana wahala da duk dawainiyar da
miji na yazo mun da ita.Sanan nasoma cika ina
cika kayana gwanin sha'awa.Shi kanshi yaya wani
sabon ji dani ya sake ko mai tare muke yi in har
yana gida ni dashi mun zama abu daya.Ko tari
nayi sai ya tabbatar ba na cutarwa bane, haka
nima ina binshi sau da kafa, da ya nuna ra'ayin
abu zan masa balle ya ce my choice ina son
kaza.Ai in na soma sai ya gundire shi, duk abinda
bai so na kiyayeshi har abada.Shinfidar da muka
yiwa rayuwar mu ba zan iya bada labarinta ba,
kowa yana mamakin mu tamkar mun shafe
shekaru goma muna soyayya kafin muyi
aure.Muna cikin wata na uku iya ta matsa masa
wai sai ya maidani makaranta, form din (N.C.E)
ya sai min bada bata lokaci ba na zama daliba a
makarantar horas da malamai dake riga
cikun.Aliyu ya ce, ya zama dole in nemi avin
hawa ko don ke.Na ce Allah ya bada iko.Ba da
jimawa ba kuwa ya ,mallaki motarsa dai dai ta
talaka.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Don haka bani da matsala sai dai yanayin aikin sa
ya ce in ya sami lokaci zai rinka koya mun, na ce
to.Ban jima ba na iya mota, sau da yawa ni ke
kaishi gurin aiki in dawo, sanan in tafi
makaranta.Kai yaya ya nuna mun dukkan gata, a
lokacin jini ke babu matar da ta kaini sa'ar zuwa
duniya a zamaninnmu. Wata safiya na farka da
zazzabi, mura, ciwon kai da sauran su, gashi
ranar yaya ba gida ya kwana ba, saboda wani
case da ke hannunsa.Bana kiranshi in dai yana
wurin aiki, amma shi in ya sami lokaci yana kira
na.Ina kudindine a kan gado naji ringing waya ta,
da kyar na lallaba na dauko, na daga.Ya ce, my
choice kin wuni lafiya?Cikin wata murya na ce,
lafiya lau.Ya ce, me ya same ki naji ki haka?Wani
dan kukan shagwaba ya subuce mun na ce,
zazzabi.Nanfa ya rikice sai gashi a gida bayan
minti ashirin.Banyi ko wanka ba ya sani a mota
sai asibiti, gwajin farko ciki ya bayyana, murnar
da ya Aliyu ya dinga yi ta rinka bani mamaki.Kula
da tarairaya ina ganinsu gurin sweet Aly na da
iya, cikin ya sa ni yin kyau, duk da na sha wahala
kafin yayi kwari.Sanan na bude nayi kiba gwanin
sha'Awa.Lokacin da cikin ya tsufa sai kuma na
kumbura abin da yayi matukar daga hankalin
yaya.Duk da cewa likitan ya ce babu
matsala.Cikin haka aka chanja yaya zuwa kogi,
ranarda ya zo mun da maganar na sha kuka.Duk
da ya zaci dama zanyi rigima bai tsammaci har
haka ba.Yayi ta lallashina da cewa, sadiya my
choice,ki kwantar da hankalinki.Ai duk matar mai
kaki San sanda ko Soja da sauransu, dole ta
kwana da sanin akwai yawon zaga duniya.Banzaci
zan dade haka ba tare da an canzani wani gari
ba.Na shafa cikina yanzu baka nan zan haihu?In
katafi yanzu sai yaushe zan sake ganinka?Ya ce
da na sami sarari zanzo, na kwanta a jikinshi.Ni
dai zanbika sweey Ali kaji yaya na?Ganin yanda
na rikice sai ya ce, to shi ke nanmu tafi tare ko?
Na ce, to sanan nayi shiru.Ana gobe zai tafi yaje
suka hada baki da iya,na zage ina ta hada kaya
har yana taya ni, sai ga iya tayi sallama.Na ce,
sweet yaya na dubi iya tazo kamar tasan zamuje
sallama.Iya ta shigo har cikin daki na, ta kalli
kayan da akwatinan ta ce, wanan fa, kwalima ce?
Na ce iya kin manta gobe ne fa zamu tafi can
jihar kogi inda aka tura yaya.Iya ta ce, zakutafi ko
zai tafi?Ina zaki tafi da wanan katon cikin ga
kumburi?Na kalli yaya na wanda ke ta aikin jera
min kaya na a cikin a kwati.Ni ina kwasowa daga
cikin sif.Kin kallona yayi, sai da na ce yaya!Ya
kalleni na ce, kaji kuma wai ba tare zamuba, inji
iya?Ya ce, eh, a a ai kinji ta ce saboda cikinki na
ce, tabdi jan!Ni kam ba zan zauna ba.Iya ta ce,
lallai Sadiya ba inda zakije yar dadi muji, ni yanzu
ma zuwa nayi in tafi dake.Na saka kuka, iya
sororo tayi tana kallona, shi kuma sai ya tashi
tsam ya dawo kusa dani.Iya kije gida zan kawo
ta.Iya ta mike ai ba wani lallashi ba in zata zo
dan ma kada ka sake yi mata karya.Ke ko yanxu
ance ki bishi kya je?Na ci gaba da kuka na iya dai
ta tafi tana cewa sai kiyi ta yi.Tana fita ya
rungumeni, haba my choice ni na lura iya tafimu
gaskiya.Ki bari in kin haihu sai muje, ina zo zan
tafi dake.Yanzu kinga dole inje in ga yanayin
garin.Na ce, yaya dama na san cewa baka damu
dani ba, can na san baka sona.Ya manneni a
jikinsa, inji wa yace bani sonki?A zaman da
mukayi baki fahimci matsanancin son da nake
maki ba?Na ce, to me yasa zaka tafi ka barni?Ya
ce, ina canne amma na rantse maki zuciyata tana
tare dake.Yanxu ni dake bamu san haihuwa ba,
gashi yanayin aikina ba na za,ma bane bugu da
kari ba mu san kowa ba in haihuwa ta zo maki
bana kusa yaya ke nan?Nayi shiru a raina na
tabbata haka ne, amma damuwa ta daya, yaya
na nasan ba zaka jure zama ba mace ba, don
nasan yanayin ka.Ina tsoron matan zamani.Ya ce,
au, dama dan wanan ne?Nayi maki alkawarin ba
zan kalli wata ya mace da sunan so ko wani abu
ba, baki tunabaya ba?Na tsare kaina kuma Allah
ya tsareni, ba wanan a raina, nace to ya ya
zakayi?Ya ce, azumi mana, ko can shi na tayi ta
irin na annabi dauda.Inyi yau gobe in huta, kada
ki damu ki kyautata min zato, bani da sha'awar
aikata kazamin laifi irin su zina da
makamantansu. Na kalleshi na yarda da kai
mijina, kuma ni da kai mutuwa ce zata raba
mu.Zan jira dawowarka, amma za ka dinga
yawan kirana?Yace, kema na yarda ki kirani duk
lokacin dakike so, nace to amma dai mu kwana
abinmu a nan da safe in katafi sai na tafi nima.Ya
ce, sammako zanyi, na ce, eh, duk da haka, ya
ce shi kenan, sai muje da daddare mu kai
kayanki ko?Na ce, eh.
Hakika yaya na sweet Ali ya tafi ya barni da
tsananin kewarsa. Kafin ya kai munyi waya yafi
sau goma.Haka nan na hakura na saba da kwana
ni daya, daran wata lahadi na farka da wani
matsanancin ciwon ciki da baya.Kafin in tashi iya
yaya na soma kira, ya daga a rude na ce yaya
zan mutu ka yafe mun, nayarda wayar saboda
ciwon mara da ya murdo min.Kalamaina suka
farkar da iya, tazo tana cewa haihuwar ce Sadiya?
Yaya ya kashe ya sake kira a rude, iya ta daga ya
ce Iya don Allah............Kuyimin hakuri indakata
anan zuwa lokaci nagaba sai mudira daga inda
muka tsaya,fatan zanga comment dinku
rututu,kafin nan nake cewa zaku iya ziyartar blog
dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347



Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100



Darajar Yayana2-02
Posted by ANaM Dorayi on 09:51 PM, 02-Apr-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
_________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Irin tarbar da kikayimin ta mutunci shi yasana
boye kalatata,boye kishinki zaifi alheri, sama da
bayyanashi don yanda na yi mani bakikaini son
mijinki ba, haka na yi imani na fi ki kishin sa,in
kina musu lokaci zai tabbatar miki dahaka. Kije
kiyi aikinki sannan ki kunna min T.V Na harareta
tare da jan tsaki na nufi dakin yaran. Sun gama
cire kayan, Kausar tana linkewa, Al'ameen ya
ce,'Mama wace ce wannan??? ..... Na ce 'Bakuwa
ce, Na kunna musu T.V dinsu, na ce kar su fito
sai an kira sallah. Nima na shige dakina na fada
kan gado. Maganganun yarinyar sun ratsa ni, har
na rasa tunanin dayakamata inyi. Ina buqatar
shawara, domin na lura da 'yar iskar matar nan
batazo dawasa ba. Wa zan kira don neman
shawara? Aisha ko Abida? Aisha ba ta san d
wannan zancen ba, bari kawai in kira Anty Abida
tunda ta san da matsalar. Ringing na uku ta
dauka na ce, 'Anty Abida ya gida da yara. 'Ta ce,
Lafiya lau. Na kwashe komai na fada mata, ta
cika da mamaki, sannan ta ce, 'Shawarar da zan
ba kikar ki bari ta gane lagon ki kar ki nuna
fushinki, kuma kar ki kulata kuyi tashin hankali,
ballantana ta yi furucin da yaranki za su gane,ki
jira zuwan shi muji hukuncin da zai yanke. Na ce,
'To shi kenan Allah yayi mana jagora.'Ameen, Ta
ce. Na kashe wayar ina nazarin maganganunta.
Ita ko 'Yar Gwari, Mujidat tuni ta ciro wayarta ta
soma chatting da abokanta. Murfat ke
tambayarta wai yanzuntana ina? Mujidat ta ce
tana Kaduna. Murfat tace, 'Ashe muna kusa ni
ina Abuja jiya muka zo tare d Alhaji Karimu zai yi
meetina na kwana biyu.. Mujidt tace lallai kina
cikin kudi, murfat tace sosai ma, abokinshi Alh
muslimu ya tambayeki .Mujidat tace yakiranima
bandaga wayar ba, kinsan ina ina yanxu? Murfat
tace ba kin ce kaduna b? Mujidat tace ina gidan
officer Aliyu,Murfat tace kina hauka ne? Zaki je
gidansa? sai matar sa ta kasheki a banxa?
Mujidat tace ai matar tashi wawiya ce, har ruwa
ta bani nasha, bayan na gaya mata cewa mijinta
ciki ya min, tace ina baki shawara ki cire cikin
nan kixo gurin masu sanki, officer ba sanki yake
ba. Mujidat tace , ni inasonshi, zan tsaya nai fada
a kanshi, saboda ko nadawo zanta tunanin shine,
bazaki fahimta bane saboda bakitaba shiga
tarkon So ba, ni kuma na shiga tarkon So mai
tsanani.Murfat tace to yaya akayi kika gane
gidan?ina kwance Hotel ba lafiya , sai ga wayar
direban shi wai Ogafa an canxa shi zuwa Abuja,
yanxun haka ya tafi in gaya miki duk sai na rude,
take na miqe ina roqon Adewale ya taimakeni ,
yace sai nabashi kudi, bani da kudi sai dana roki
samarina , suma shegu ban samuba sai dana
musu alqawarin basu kaina, ina bashi kudin yace
naje kaduna zai turo wani dan sanda daga can
Headqurter su, yayi Tanbaya kan Aliyu Tukur aka
fada masa sunan unguwar su, sannan na nufo
Kaduna, nasha wahala kafin na iso, sabida motar
dana shiga me arhace, inazuwanan na samu wani
dan sanda da Adewale ya hadamu , shima akwai
kudin da akayi alqawarin xan bashi, sai daya dafe
shi,sannan yayi min jagora zuwa unguwar su
Aliyu, nan ya bar ni wai in nemi gidan, wai in
mun shig unguwar tare, asirinsa zai tonu, na
Adewale ma haka,nadade ina yawo, sannan na
samu gidan mamanshi, na shiga bata nan, sai
nace a kai ni gidan matarshi, Murfat tace ke yar
neman bala'i ce, bari tasa miki guba a abinci kici
ki mutu, mujidat tace shi yasa bazan taba cin
abincita ba,Murfat tace kidai yi ahankali, garinsu
kikazo, tace a garinnasu sai in karbe mijin kuma
na zauna lafiya.haka suka yita chat har xwa wani
lokaci, Niko munyi sallar magariba har na zubawa
yara abinci, 9 da yan mintina yya Aliyu ya iso
gida,da ita ya soma cin karo a falo, ckin zafin rai
yace me zakiyi agidana?itam cikin daga murya
tace goyon cikin dakayi min, abinda naji kenan,
na miqe ina kallon yarana,Kausar ce kawai idanta
biyu tana yin homework dinta, na miqe na fito da
sauri, dai-dai lokacin yana cewa, zan nuna miki
kurenki na biyoni gidana yar iska
karuwa.nakamashi ina fadin yaya yara fa? itama
tace yan iska dai, namijin karuwa. na dafa kaina
dan takaici, yar bariki tana zagin mijina da nake
girmamawa a gabana, najashi zuwa dakinsa,
nace, haba yaya, kamanta cewa kana da yara a
gidan nan?dubi yanda yar bariki tazo har cikin
gidanka tana zaginka?sabida mutuncinka daka sai
da,ai dama haka ne, dukwanda yabar maganar
ubangijinsa dole ya fadawa dana sani, da wace
rana zaka iya hada yau a gurinka dan bakin ciki?
ni dai a gurina babu, ya dago kai ya dubeni,
Sadiya nayi nadama sosai wallahi, ba sai ta
kanjamau kadai Allah yake kama mazinaciba, in
Iya taji batunnan na shiga uku, nasan bazan kara
yin daraja ba, kila ma ta cireni daga yayanta, ga
wannan matsiyaciyar da alamu fallasa tazi
min,nace to yanzu dai nema mata masaukin da
zata kwana, in yaso da safe sai mu zauna da ita
mu kafa mata sharuda,ya kama hannuna,
wadanne irin sharuda za'a kafa mata?kara min
haske, sai musa mata sharudan cewa ka yarda
zaka amshi dan,amma za'a rufa asirin cewa ba'a
son kowa ya ji, dan haka za'a ce mijinta ne ya
rasu, iyaynta suka koreta saboda ta
musulunta,na tabbata duk wanda yaji haka zai
tausaya,to inta haihu sai ta bamu yaron ta tafi
abinta,yace wazai rike yaron?nace ni mana, Yya
ko ban aure ka ba ai xan rike maka da, bare
kuma ina matarka na kasa rike jininka? yadan yi
shiru yana nazarin batuna , can yayi dariyar yake
yace,Sadiya baki tunanin me mutane zasu ce?in
sun gammu da jariri?me zamu fadawa yaran mu?
idan sun tambayemu nan gaba? nace ai zamu
fada musu dan mu ne, amma bani na haifeshi
ba, tunda dama a musulunci bai da
gadonka,kaga ba zamu sami matsala ba, ya sake
yin shiru, can yace ina ganin fadin gaskiya kawai
shine mafita, saboda duk rintsi karya bata kaiwa
ko ina baki tunanin cewa nan gaba zata zo nemn
danta?kuma asiri zai tonu? nace Allah zai rufa
asiri, kai dai da safe mu sameta da batun muji
yanda za'ayi.yace shikenan, Allah ya rufa asiri,to
yanzu ina zata kwan?ka kaita dakinka,yace a'a,
sai dai yara su dawo dakinki, ta kwanta acan ,
amma bazata kwanar min a daki ba, araina nace
yanxun ba, amma da ai tare kuke kwana ma.
yace kota kwana a falo? a'a ,bari in kaita dakin
yaran.haka kuwa akayi,muka kaita can.Da safe
dana kai mata abin kari sai tace a'a, tanada
maltina da kuma biredinta, bata cin abincin
kowane guri, da kanta takeyi, nace good, sannan
na fita.mudai sama-sama mukayi bacci, kuma
sama-sama muka karya, duk sai tunani muke,
yaya kuwa sai nadama yake, dan dadin da yabi
na watanni yaja masa zubewar mutunci na kila
tsawon shekaru.misalin sha dayan rana yace in
kirata ,muka zauna yara suna makaranta lokacin,
ta fito sanye da riga da siket na jeans, kanta
babu dankwali, cikinta kuwa har ya turo, ta
zauna tana taunar cingam, yaya yace Mujidat
dama mun kira kine don mu tattauna dake,
shawara ta farko zanbaki dubu dari biyu ki zubar
da cikin nan,ta daga masa hannu, ban amince ba
,koda zaka bani duniya da kayan cikinta, inbaka
mantaba nafada maka, badan kudi nake tare da
kai ba, sonka da kauna ce kawai, kuma cikinnan,
(tasa hannunta ta shafa cikin)ribar soyayya ce,
taya zan zubar dashi?kawo wata shawarar dai
muji,kalamanta sun konan raina tamkar in tashi a
gurin,amma sai na shanye.yace to naji, zaki
zauna damu ki haihu, amma da sharadin baxaki
fadawa kowa komai ba,duk abin dana fadawa
mutane zaki tsaya akan haka ne?ta dan yi tsai
tana tunani can tace ,zan yarda, amma idan na
haihu meye makomata? zan tafi da danne?ko
kuwa zan barshi anan?sai lokacin nasa baki , zaki
tafi ne kibar yaron a wurina, sai ki tafi
abinki,wata ran,xaki iya xuwaki ganshi duk bayn
wani lokaci, tayi min wani kallo, tare da yin kwai
da cingam dinta kato, sannan ta fasa shi taci
gaba da tauna duk muna kallonta, tayi yar
dariya, in naki fa? cikin zafin rai Aliyu yace , sai ki
tafi da cikinki, danma kin samu zan amsa? nasan
uban dayayi miki? tace , ka manta dararen daka
yi ta kwana dani?cikin bacin rai yace in baki yarda
ba malam kizo ki fice min daga gida kije kiyi duk
abunda zaki yi. tace zan fi son haka , dan zama
gidan mamanka ze fimin wal-wala, dan haka zan
je na fada mata ina dauke da jikanta, ta bani
masauki, ni dashi muka kalli juna, yace kije man ,
zanfi san haka.nace , a'a ,kedai barshi a wancan
tsarin,tace in dai har za'a barshi cikin sirri,
tonima zan kawo nawa sharadin?Aliyu kam takaici
ne ya hana shi daga kai, ban taba ganin shi cikin
wannan yanayinba, na takaicida bakin ciki.nace
fadi sharadinki muji?tace sharadina sai dai in na
haihu zai AURE NI.... kalamanta na karshe suka
tafi da numfashina, tsawon kiftawar ido, huhu,
nayi nasarar janyo nimfashi na,idanuwana suka
futo sukayi jajir, zufa ta ketomin, ta tuntsureda
dariya har Aliyu ya dubeta, nima lokacin na
dubeta, tace ,ya kika yi saurin firgita?naga keda
mijin naki kamar tagwaye, shawarar ku daya, kun
burge ni, kuma nasan yana sonki, kuma nima ina
san shi dan nasan qualities dinshi, na baku zuwa
gobe kuyi shawara.
(Uhm!Allah yakayuta,ANaM Dorayi)
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu ya harareta, Allah ya kiyaye ni Aliyu na
aureki,ai ko zan yiwa matata kishiya na nemo
mata yar mutunci bake ba karuwar titi,tir Allah
ya tsareni, ya miqe, na baki awa daya kibar
gidana, ko kuma yan sanda su zo su fita dake, da
kyar na miqe kafafuna sunyi sanyi, dakina na
nufa don ko ganin gabana banayi,zuciyata tamkar
ta faso ta fto,rigijif na fadakan gado, inasan yin
kuka amma na kasa, lallai kuka ma rahama ne,
tunda idan kayi shi zaka samu sauki,
Hannuwanshi naji a gadon bayana, ji nake tamkar
ya doramin wuta,zuwa,yanxu nasoma tsanar
yaya Aliyu,gaskiya hakurina yana son ya kare,
danzan iya danne komi, amma banda batun
kishiya ,zan iya hakura ya aureta, amma kuma
zan juri zama da ita?(Mata kenan,da kishiyar
gida!..Allah ka karemu daga bin soye-soyen
zukatanmu.....Ameen.ANaM Dorayi) Birkitonin da
yayi shine ya katse min tunanina yace, haba My
choice, kada wannan ya dameki, zanyi waya
yanxun xa'a turo min yara su tafi da ita, xuwa
ynxun ban damu duk duniya tasan cewa na mata
ciki ba, ai nima dan Adam ne kamar kowa, ban
wuce kuskure ba, nace aika riga ka tafka
kuskure,dole ne ka aureta, kuka ya subucemun,
naci gaba da magana cikin kuka wane hali Iya
xata shiga in taji wannan labarin?ita da ba
cikakkiyar lafiya ba, me zaka cewa y'ay'anka ?
wadanda tun jiya suka damu dasan sanin wacece
wannan bakuwar? y'an 'uwanka, wane idan kake
dashi da zaka kallesu?su da sukeyimaka kallon
mutunci da kima? ga abokai da sauran mutan
gari?kada ka manta, shi fa mutunci madara ne,
in ya zube sai dai a kwashi kasa,ka riga kayi
abinnan da hausaw ke cewa TSALLE DAYA ME
JEFA MUTUM RIJIYA....ya rike kanshi, sadiya na
yarda duk wanda ya bar layin da aka ja masa a
matsayinsa na musulmi dole yayi nadama mara
amfani,danasan abubuwa zasu zama haka da
banbi san zuciyata ba ,dam malamai suna gaya
mana zuciya wata tsoka ce ajikin dan adam me
hadari in kabi sonta sai ka halaka, ya dube ni,
yanxu kin yarda? kinaga ba wata mafita sai ta
auren ta? nace to inban yadda ba ya xanyi ,nasa
masa kuka ina fadin na amince ka aureta,
,kallona ya dinga yi tamkar na zame masa wata
sabuwa a sanyaye yace"nasan kin hakura ne
saboda ni, amma nasan bakya san kishiya,amma
kina ganin cewa nan gaba bazaki damu ba?na
runtse ido, zuciyata tana wata irin tafasa nace,
batun zan damu ko bazan damu ba a ynzun ba
shine mafita ba,na bude jajayen idanuwana ina
kallonshi, sai dai ina fatan daga baya ba zka
canzamin ba? ya rungume ni, Sadiya kada kiyi
tinanin haka kada kiyi fatan haka, ki tayani
addu'a Allah ya bani ikon yi miki irin halaccin
dakikayi mini,banda kamar ki har abada,kuma ke
kadai nake so ke daya kwal. Haka ya yi ta fada
mini maganganu masu dadi da kwantar da rai,
har zuciyata ta dan sauka. Yaya ya fito ya fita,ni
kuma na kira Anty Abida na fada mata, ta ce
hakan ya yi in ta haihu ya aure tan zai fi sauki a
bakacin ta haihu ta ba ku yaron. Na ce, To ya zan
yi tunda shi ya janyo. Nan dai muka yi sallama
nafito na kuma dora abinci,sai dai ina gamawa
ita ma ta soma dora nata,ban damu ba tunda
neman sulhu muke. Misalin hudu yara suna
Islamiyya suka shigo shi da Usman falo suka
zauna, na kawo ruwa da abinci.Usman ne ya sha
ruwan shi kam gogana har wata 'yar rama ya yi,
ya kalle ni ya ce, Kira yarinyar nan. Na ce to. Na
daga labulen dakin yara tare da yin sallama, ba
ta amsa ba sai dai ta dago ta dube ni,rufdaciki ta
kwanta kan katifar su Kausar tana chatting, na
ce, Ki zo in ji Mijina. Ta yi min kallon kishi zan ce
ko na tsana, sannan ta ja tsaki. Ni dai na juya na
ce musu tana zuwa. Zan tafi Yaya ya ce in zauna,
na samu guri na zauna. tafi minti shida sannan
ta fito,munyi jugum-jugum kamar masu zaman
makoki, ta tsaya kerere , gani. Ya harareta
.Kizauna mana kin ce wani gaki? Ta zauna tare da
fadin .yau kuma da wacce aka zo? Duk muka yi
shiru, irin zaman nan da ake cewa mutuwa ta
ratsa. Can Aliyu ya ce"Usman wannan ita ce
Mujidat,kuma na maka bayanin komai,dan haka
sai ka dan ce wani abu".Usman yace"bani da ta
cewa,sai dai ke.ya nuna Mujidat,karkisake kice
zakici zarafin wannan baiwar Allah ko nan gaba
"yakalli Aliyu"ya kamata wannan ya xama cikin
sharudan da zaka gindaya" Aliyu ya kalli
Mujidat"na yarda in kin haihu zan aureki, amma
ki sani so daya tak inayiwa matata ne,dole ki
bata girma da daraja,musamman data soma
bazaman aure ba, sannan zaman haihuwarki ina
gani can wani waje zan nemamiki haya" cikin
sauri na ce ban yar da ba, ai ta zauna anan,
kada a dinga zagayawa "Usman yace "haka ne
kuma,amma kina ga batakura? Na ce "bakomai"
Mujidat dadi ya rufeta ,kuma nan take ta nuna
murnarta, ta kuma sake bayyana tsantsar san
data ce tanawa mijina,dan haka dole tazauna
dani, ban bari ta kai karsheba natashi nayi kicin
abina.tsayawa nayi tsakiyar kicin shuru,anya
kuwa ban yi wautaba?ban zalunci kaina ba?ban
debo rvmuwan dafa kaina ba?amma sai wata
zuciyar tace kedai kada kiyi wannan tnanin, tunda
kin sadaukar da kimai ne dan asirin mjinki y
rufu,Allah ya sani Zuciyarki daya da ita,kuma
Allah zai shige miki gaba. Nasauke ajiyar xuciya
nace Allah gani gareka,sai da suka fito ne naji
muryar Usman na cewa"Madam na tafi"nace "ka
gaida min su Ummulkhairh dasu walida"yace
xasu ji.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
A ranar Aliyu ya koma Abuja,sabida an dameshi
da kira,gida ya koma sai ni da ita saikuma
yarana,a daren nan naje na fadawa Iya yanda
muka tsara zancen,tayi ta tausaya mata,tare da
shiwa yaya albarka tace ai gara daya taho da
ita,tace in an barta sai ta koma ruwa, tabar
musulinci, nace "ai shine" Iya tace Allah sarki,
naxo in yi mata ta'axiyya,banda abinku, daba
nan kuka kawota ba? Tunda ni kadai ce?nace"Iya
ki barta can kawai,sabida bata jin Hausa sosai"
tace"to shkenan ,kema Allah ya biya ki" na ce
amin.
Daren ranar mun kusa rabashi a waya yaya yana
shimin albarka tare da yi min alkawuruka kala-
kala na riqe ni amana,tare da kyautatamin daji
dani duk wani dadin zaman aure,har sai da aka
kira shi, yace minxai fta gurin aiki1 nce Allah ya
tsare.
Haka muka zauna da Mujidat,bata min
magana,sai dai ni in mata.innayi kamar in
shareta,sai na tuna da haramcin gaba,dan haka
in lokacin sallah yayi tana falo sai in ce
mata"lokacin sallah yayi" wataran
tace"to"wataran tayi min banxa ,sai dai ko ta
amsa ba dole ne ta tashi tayi sallar ba.abinci
kuwa,da kanta take yi,takanyiwa yara
magana,amma ba wai wasaba, sai dai in tana
san abu tace kai bani kaza, ko ke bni kaza. Sun
dameni wai yaushe wannan bakuwar zata tafi?
bata da kirki su suna san ta tafi,nce musu bazata
tafib,Antyn su ce baban su ya kawota ,kuma tana
da kirki,dan dai yanxun bata da lfy ne
shiyasa.suka yi shiru badan sun fahimce ni
ba,intaji fita tana san zaga gari sai dai kawai inga
ta fice bako mayafi. Sai dai nayi masa waya nce
ka fada mata in zata fita ta dinga saka hijabi ko
mayafi, saboda an ce ta musulunta, in tana fta
haka asiri zai tonu.ya ko kirata yace ta
kiyayeshi.kar ta bari tayi abinda zai toxartata,tace
ita bata da hijabi.yayi min waya wai in bata
hijabai guda 2, sannan yace ya hanata fta,kuma
ta sani ya zuba masu sa mata ido a unguwar,
dan kar tai xaton cewa xata fita wani gantalinta
ta dawo masa gida,ko kuma zata yo wani mugun
abun.tace karya damu,dama ita burinta aurenshi,
kuma tunda ta samu bata da matsala da wani
namijin can waje, tana zuwa matsa jikine.
Duk wani zaman kunci na dauka a zaman
Mujidat, sai dai ban damu sosai ba.ganin Aliyu
baya sakar mata fuska sosai.komai tace masa
tana so sai yace ta tambaye ni,bai cika zuwa
gidan bama, sai daiyazo ya debemu da yara mu
tafi can Abujan, akwai lokacin da sai da muka yi
sati uku saboda yara sun samu hutu. Ranar da
muka dawo har da shi ,mun samu ta tana kuka
wiwi, wai bata da lafita,nce masa muje Asibiti,
amota fadi yake Allah yasa ckinnan ya fta, na ce
dan Allah kabari, ka mata addu'ar alkhairi, bayan
dogon bincike likita ya gano tana shan maganin
tari na yara,wanda mata da maza kan sha sabida
su yi maye. Likitan ya ja kunnanta da cewa in ta
ci gaba d sha za ta kashe danta. Muna hanyar
dawowa gidan na ce, Ki daina kada ki je ki yi
sanadin rayuwar danki. Na dube shi. Kayi mata
magana ta daina shan pakalin. Ya ce, 'Ina
ruwana, ta yi ta sha indazata mutu ma kina
ganin ba zan fi son haka ba? Ta ce, 'Eh, na san
dama haka za ka ce, kuma sai na haihu lafiya. Na
ce, 'Inma banda ke mene ne abin sha cikin
maganin mura? Ya ce, 'Ai ba za ta daina rayuwar
bariki ba. Ta yi shiru tana nazarin dalilinta na
sha,tsabar son shi ne da take yi. Shi kuma ya
kwashe Iyalan shi suka bar mata gidan shi yasa
take sha sabida rage damuwarsa, ga shi ashe za
ta janyo makanta ne, 'Yar shigarda ta samu a
watse, don ta san in cikin nan ya zube shi kenan
korarta zai yi batada sauran garkuwa za ta jure
ta ci darajar dan da za ta haifa. Ta shiga wata
bakwai lokacind ta cewa Yaya a waya wai tana
son ta fara zuwa awon ciki, ya ce ta fadan in ta
matsu.kin fada min ta yi sai shi ne ya tambaye
ni. 'Mujidat ta yi miki batun awo? Na ce, 'A'a,ya
fada min yanda suka yi na ce 'Ka bari sai ka zo
sai mu yi zancen gani gata, in ya so sai a je
Asibitin a kuma sayi duk wani abu d ake buqata.
Bai amsa min ba ya canza zancen da cewa,
'Akwai wani bincike dazai kawo ni Kaduna me zan
samu? Na ce, 'Duk abin da ka ke so. Ya ce,
'Yanzun ina takura sosai a gidana in na zo zan
dauke ki mu fita a wani masaukin bakin mu dan'
huta. Na ce, 'Yara fa? Ya ce, 'Ga gidan Iya. Na
ce, 'To ma tafi mu bar mai ciki, kar a yi na
wancan karon. 'A yi ta yi mana, ina ruwana,
daman na san haka za ki ce. Ya ja tsaki tare d
kashe wayar shi. Na sani tabbas rayuwarmu ta
canza yanzun, amma wayaja? Shi ne. Allah yasa
mu dace, ameen. Wata Asabar Aliyu ya nufo gida,
yana karya kwanar unguwar su sai ya ga jama'a
cirko cirko tsaitsaye gungu gungu, wadansu kuma
suna ta maida yanda aka yi,yayin d kunnan shi
ke dauko masa sautin wasu muryoyi suna ihun
neman dauki. Kasancewar shi jami'in dan' sanda
dole ne ya bincika, don aikin shi ne kare rayukan
al'umma da dukiyoyinsu, ko da ba a unguwarsu
ya ga hakaba, dole ya tsaya.
Don haka ya gangara gefen titi yayi Parking din
Motarsa,yana fitowane wasu matasa sin tsaya
suna dan tattauna batun,Aliyu ya usa gurinsu
fare da yi musu salllama,suka amsa,ya
fambayesu abindake faruwa,daya matshin
yagane Aliyu dan haka yace "yallabai wallahi 'yan
sara sukane" Aliyi yace 'yan sara suka kuma?
Yace eh! Wasu matasane ance daga hayi suke
suka fada layinnan suma sara da sukan duk
wansda suka ganiyanunamasa inda
cincirindonbjama'a ke tsaye yace 'can
meshayinnena Buba suka soka,sannan suka sari
me lemun kysa dashi"
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu ya isa gurin daidai ana kokarin sashi amota
yace "bakuyiwa yansada wayaba" ?wabi yace "tin
dazu muka sanar dasu" Aliy yadagawaya yana
sake miran yansanda yana shedamusu cewa a
turomasa mota sabida 'yan sara suka sun sgigo
ungywarshi ,shine yavasu damar kai masu jikin
Asibiti sannan shikuna yacigaba da gudanar da
bincike jafin isowar yansanda.
Tanbaya yaitayiwa mutaben gari kan yansara
sukan;kasancewar mutanwnmu akwai tsoro da
rashin cikakken wayewa ga wasu sai zuka mi
bashi cikakaken hadinakai.sannanda yanufi
motaesa dan karasa gida,sai yaji wasu matasa
biyu suna magana,dayan yanacewa, "kasan Allah
Aminu su Dawa Adone suka jamana wannan
bala'indashi da Bangis Kauri" Aliyu yace "Kanina
kananyfin Dawa Ado din tsokanarsu yayi?
Duk suja waiwayo suka kalli Aliyu,ganinshu da
nayan Yansanda sai sukace a'a bamusaniba,suka
juya da nufi.n tafiya Aliyu yace tsaya kuji absan
cewa kunsan wani abu,dan Allah kubani
hadinkai.Dayan da akakira Aminu yace,'mufa
zabcenmu daban, 'yansanda basu da
amana,dazarar kafadi wata magana sai reshe
yajuye da mujiya a kama mutum a tsare"
Aliyu yace ba gaskiya bane,shaci fadine da shrri
irin na wasu mutane suke jifan jami'an tsaro
dashj,mu masu kare rayukan Al'ummane da
dukiyoyinsu bawai masu sharrib,kudinga bamu
hadin kai,tahakane zamu iya gano bara gurbin
al'umma."
Dayan wanda kebada labarin yace, yallabai
yallabai tsorona kada a kirani shaida,suganeni
insun fito suzo su sassareni".
Aliyu yace "sam sunanka bazai fitoba, vabu
wanda yasan munyi haka dakai." Yadafashi.
"Kagama zo nan mushiga daga mota dan kar
wasu sugane kaine kafadamin,kayarda ba
cutardakai zanyiba,taimako zanyi,kaga in ba'a
dauki matakiba zasu iya dawowa.Zaka iya sanin
ko kanwa tsautsayi zai fada?nasan kanada
dangi,da mahaifanka, sannan ga kanka ko
kanada yakinin cewa bazasu dira kankaba?
Saurayin yace "hakane yallabai"
Syka shiga Mota harda saurayin da dayan yace
Aminu.
Aliyu ya kalleshi yace 'kanina kai ya sunanka?
Nasandai abokinja shine naji ka kira da Aminu"
Yaron yace "Buhari'
Aliyu yace 'Buhari wane Dawa Ado?'
Buhari yace "Dan dabane,sunada yawa a
ungywarnan,saidai su da bangid sune sukai kauri
suna a ungywarnan"
Aminu yace, "wasuma sunce gudansu Dawa Ado
ana siyar da wiwi,wasu yarsu dake zaman kanata
agubta yake ajiyewa".
Aliyu yace "to mene labarin wannan fadan?"
Buhari gace,"to nidai mundawo Masallaci jiya da
Magriba dayake layinmu daya da Dawa Ado,sai
naganshi zaune tare da wasu yandaban,
,yaranema wadanda basufi shekara sha shida sha
biyarba,yana fada musu cewa zamu fadawa 'yan
hayi har naji ya anvaci sunan wani dan daban
hayin yanacewa lallai yanaso ayimasa yankan da
bazai tashiba,ko yatashi kada ya moru.Nidai na
wuce nabarsu,saidai ina zaton kan wiwi ne sjke
fadan, dan naji yanacewa "ankawo mishi kaya
kafin yazo shi wancan ya siye"
Aliyu ya girgiza kai alamun gamsuwa yace, to
yanzu kuyimin kwantabcen gudansi Dawan
dakuma Bangis din, ' sukace to.
Nan sukayimasa kwatance yacuro kati mai dauke
da lanbarsa a jiki ya basu,.
"Gashi kusa lanbobina a cikin wayoyinku,sai ku
kirani ko kumin flashing inkira dan insamu taku
lanbara,kunsan dalili?
Sukace a'a. Yace dan kucigaba da bada gudun
mowa cikin hnguwar nan,duk lokacin da kukaga
wabi abu mo kukaji makamancin wannan sai kuyi
maza kukira daya daga cikin wadannana
lanbobin. Ya sanya hannu ta baya yaciru yan
dubu dubu guda biyu ya mika musu tare da
cewa,"Ba cin ganci vane kyauta
nabaku,aikinmuma dazakuyimin ba na kudibane
taimakon kaidakai zakuyi."
Da murna suka karba, sunyj masa godiya,take
nan suka bashi lanbobinsu,sannan suka gangara
inda suja nunamasa gidansu Dawa Ado da
Bangus Kauri.sanna ya gan ga ra ya ajiyesu ya
wuce hidansa.
Likacin d na ji kwankwasa kofar ina kicin ina
kokarin dafawa yara Indomie, don ni a koshe
nake Iya ta aiko min da dambu, nacishi sosai
bayn La'asar shi yasa. Na nufi kofar cikin raina
ina tunanin ko waye? Ina bude kofa na yi sororo
don bai fada min zai zo ba. Na ce, 'Oho! Abin
'Yar haka ne? Ya shigo, sannan ya rufe kofa, ya
kamo ni ya rungume, na karbi jakarsa muka nufi
ciki. Mujidat tana zaune a falo ta ce, Sannu. Ya
ce, 'Yauwa. 'Ba tare d ya kalletaba. Muka nufi
dakinsa ina fadin. Kausar, Al'amin ga fa babanku.
Da gudu suka fito dga dakina, muka dunguma
dakinsa mu duka. Na ce daka fada min kana
zuwa Allah d tuni na yi maka abnci na
musamman. Ya ce, 'Ai rikici na tarar a unguwar
shi yasa da tuni na iso. Na ce, 'To yanzun me za
ka ci? Ya ce, Me ki ka dafa? Na ce, Ban dafa kmai
ba, yanzu daizan yi wa yara indomie,sai dai
muna da miya a fridge sai na dafa maka farar
shinkafa. Ya ce, 'A'a ku tashi muje gidan cin
abinci. Na ce, 'To ka canza kaya mana, ko kuma
ka yi wanka. Ya ce, 'Duk yanda ki ka ce. Na dubi
Kausar 'Mu je in ciro muku kaya ki sa musu sai
ke ma ki sa.'Na dube shi. 'Bari in ba su kaya.
Gira ya daga min na fita. Na dawo na taimaka
masa ya yi wanka. Ya shirya, nima na canza
kaya, duk Mujidat tana zaune a falo tana
kallonmu, sai na ji tausayinta ya tsirga a raina,
na ce, 'Ki tashi muje cin abinci. Saida ta yi min
wani kallo, sannan ta ce, 'To. Mun fito sai ya
Aliyu ya ganta, ya ce, 'Ke fa? Da sauri na ce,
'Tare za mu je mana. Tsaki ya ja,sannan ya ce,
'Ni yanzun ba nida damar sakewa kenan? Ban
tanka masa ba, a raina na ce wa yaja? Lokacin
dakuke shanawar ku ai ba ka ce an hana ka
sakewa ba. Da farko yaso mu ci a can,amma
yanzun sai ya ce kawai mu yi take away sabida
bai so zuwanmubada Mujidat. Daga nan sai ya
nausa da mu can gurin kasuwar Bacci, wani katon
shagon saida kayan wuta, na ce me za mu yi
anan? Bai kula ni ba don na lura ya ji zafin
zuwan Mujidat. T.V ya sai mana ta bango
(Plasma),mai kyau sai tsada,sannan ya sayi
resiba,ban san inda zai sa ba. Sannan muka je
wani babban store ya kwasarwa yara kaya har da
keke ya saiwa Al'amin. Yara sunata murna muka
isa gida. Ita dai mujidat duk inda muka je da Ido
take binmu, tare da yatsina fuska,jifa jifa tana
tabe baki tare da tsaki. Ni dai muka yi ciki ta
zauna a falo.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Dakina ya kai T.V, na ce ba na ka ba ne? Ya ce,
'A'a naku ne,don na lura ke da gidanki,amma kin
bar wa wata falon ki. Na tsura masa ido, 'Yaya
na gode. Ya harare ni, Lokacin fa dakika samin
suna kin yi alkawarin kirana Sweety Alinki,amma
yanzu sam kin daina na manta rabon da ki kira ni
dawannan sunan. Na ce, Yi hakuri Sweet dina. Sai
na ji su Kausar da Al'amin sun sa dariya.Kausar
ta ce, Momy Abba ne Sweet? Muka kalli juna cikin
dariya na ce, 'O.K, waton kun tsaya jin mu ne?
Al'amin ya katse zancen da cewa, Abba wai ita
Anty bakuwa sai yaushe za ta tafi? Kausar ta
zabga masa harara, 'Ina ruwanmuda wata can
Anty Bakuwa. Muka sake kallon juna cikin
mamaki. Na lura fa Kausar ta tsani matar nan.
Nace, Kausar ai ba tafiya za ta yi ba ita ma ta
zama 'yar nan gidan. Kausar ta zaro ido, 'Ta
zama 'yar gidan mu kumma? Ta tura baki,ni dai
Abba ta koma gidansu, kullum sai ta dinga
hararata, ko kuma tayi ta hana mu kallon T.V. Na
ce to ba ga shi Abbanku ya siyo mana wata ba?
Ta yi shiru. Na ce, 'Kar ki sake yin haka. Ranta a
hade ta ce, to Momy. Mun ci mun sha muna ta
hira har yara suka yi bacci, sannan muka gyara
masu kwanciya, sannan muka nufi dakinshi.Yayo
alwala tare d cewa. Je ki yo alwala muyi Isha'i.
Na yi murmushi , sannan na ce, Wanka zan yi
don ina fashin sallah. Ya runtse ido tare d fadin,
kash! Ga shi gobe zan tafi. Na ce, Kar ka damu
zan yi maka irindabarun da muka sabayi da.
Dariya ya yi, sannan ya ce, shi kenan. Da safe ni
mkadai ce na fito na hada abin kari, sannan yara
suka ci suka fito. Babansu yana kwance na ce
'Bari in kai su makaranta. Ya mike. 'Yau ba
Lahadi ba? Na ce, 'Hadda suke zuwa Asabar da
Lahadi. Ya ce, 'To ki yi sauri ki zo ki kara yin wata
dabarar. Na yi masa hararar wasa. 'Bashi yasa na
ce amAuran Mujidat zai taimaka maka ba ya
hade rai, sannan ya koma ya kwanta. Na dauki
makullin motarsa. Bari in ari motar ka. 'Nan ma
bai tanka ba. Lokacin da muka tafi Mujidat tana
soya kwai a kicin, na cewa Kausar su je su gaida
ta. Kullum dama sai na sa su sun gaishe ta,
kamar kullum sai d ta yatsina fuska sannan ta ce,
Lafiya. 'Na fita abina. Mujidat tana ganin fitar
Sadiya da yara sai ta maida kofar ta rufe,sannan
ta nufi dakin Aliyu yana kwance sai ya ga mata
tsaye a kanshi tana girgiza. Zumbur ya mike tare
d fito falo, don gudun kar ta kara janyo masa
wani laifin a kan na da. Ita ma ta biyo shi tana yi
masa kallon banza kana tsoro kada matar ka ta
dawo,shiyasa ka fito kar ta same mu tare.ta yi
'yar dariya. 'Ai ka gama kuskure tunda har kayi
ajiya a jikina na zo in yi maka gargadi ka rage
nuna tsana da kyama gare ni, in ba haka ba na
rantse maka zan je gidan mahaifiyarka in tona
komai. Aliyu ya ce,'Ai har abada ba zan so ki ba,
kin ci darajar matata data dage sai kin zauna da
mu, banda haka ke din banza. Ta tuntsire da
dariya, 'Ai ba ka san wani abu ba, ai ita kan ta
matar taka sa'a ta ci d ta kasance mai son
kwatanta adalci, banda haka wallahi da sai ta
raina kanta a wannan zaman da nake yi a gidan
nan, don sai dai inmu dinga kwana da kai gado
daya.ya harare ta, Ni kuma da yake zan tsaya ne
ina kallon ki har ki shigo mini daki,kuma ki sani ni
Allah ya shirye ni. Ta ce, 'Oho! Yanzun kana
tsammanin cewa kai wani shegen mai imani ne?
Ta yi murmushi mai sauti,sannan ta girgiza kai.
'Abu daya zan fada maka shi ne ka gode min da
na kawo shawarar auren ka,sannan ka godewa
matarka da ta yarda da in aure ka,ta samawa
kan ta lafiya don wallahi da sai dai ta sallamawa
kan ta domin matsawar ina numfashi duk inda ka
ke sai na bi ka,kuma sai ka yi duk yanda naso. Ya
gyara zaman shi sannan ya ce, 'Kin yi kadan
shaidaniya. Sannan ya kautar da kai.sam bai
tsammaci zuwan ta ba,sai dai ya ji ta a jikin shi
'yar barikin ta san lagon shi,wanda baya iya
bijiremata, zuciya muguwar nama har za ta
amince,amma sai Aliyu ya yi ta maza ya hankade
ta duk d tana da ciki, sannan ya ajemata mari a
fuska,ta shafa kumattun tana kallon shi bayan ya
mike yana mata kallon banza,ta yi 'yar dariya.
'Dubi yanda idanunka suka canza launi, ban da
cikin jikina da sai na tabbatar maka cewa in ina
nan dole ka rayu da ni,Kasa ba ta amsa ya yi kai
tsaye ya nufi dakinsa ya shiga ya kullo
kofa,sannan ya zauna bakin gado tare da rike
kan shi ya ma rasa wane irin tunani zai yi.Can
kasan makogwaron shi 'Hasbunallahu Wani'imal
Wakil yake fadi can a hankali ya ji kmai yana
warewa, ya kwanta rigingine ya tabbatar cewa
Mujidat shaidaniya ce, za kuma ta yi duk abin
data fada, auranta kam shine mafita, inbahaka
ba zata jashi zuwa wuta,tunda in tana raye bazai
fasa zinaba.Yadauko wayar shi ya soma kiran
layin matar shi.
Ina daf da gida naji wayata tasoma ruri, nayi
kwana,sannan na daga. 'Yaya dai Sweety Aly? Ya
ce, 'Ina kikene? Kin san dai daga ni sai wannan
shaidaniyar a gida. Gabana ya fadi, sam ban tuna
haka ba,nace 'ga ni nan yaya ina daf da gida. Ita
ce ta bude min gida lokacin da na buga,sai dai
tana bude min ta juya a raina na ce, 'Hakan ma
nagode. Na aje mota,sannan na nufi ciki. Zaune
na same ta tana sanye da dogon wando na jeans,
sai 'yar best yanayin shigarta na bata min rai,
musamman in yaya yana gari. Na murda kofar
na ji ta a kulle, na kwankwasa ya bude na bi shi
da kallo, don son in fahimci wani abu, amma ban
gane ba, don haka nace. 'Lafiya? Ya dube ni, 'Me
ki ka gani? na ce, 'a'a bakomai.naga kakirane na
dadene? Ya ce, 'a'a, kin san ina jiranki ne a sake
yi min irin dabarar jiya.nayi dariya, 'ai bana
batun dabara barima inyi wanka don ina zaton
anjima zan yi sallah. Damurna yace, 'Haba? Na
ce, 'Allah. Ya ce to shiga ina jiran ki. Saidai kuma
ina fitowa na same shi zanzare cikin kakinsa yana
daure takalmi, sororo na tsaya cikin mamaki kafin
nayi magana sai wayarsa ta soma ruri,ya dauka
da sauri. 'Buhari inajinka. Daga inda nake na jiyo
wanda ya kira da Buhari yana cewa,Yallabai
muna zaune ya wuce kamar yanda nasoma
fadamaka dazun, shi Dawo Ado, malun malun
yasa yana riqe da Adda sannan malun malun din
ta jike sharkaf da jini. Aliyu ya ce, 'Dan uwanka
Aminu ya kira ni ya fada min wai 'yan sara sukan
nan sun ce za su sake shigowa anjima, zan fito
yanzu. Yana 'aje wayar ya dauki dayar ya kira
headquater ya buqaci a turo masa 'yan sanda
mota biyu. Ina mamakin yanda Yaya keda izza
cikin aikinsa, yanzun nan ya rikide daga soyayya
ya kma zakin maza,ya kama kofa zai bude nace
"Sweet aliy ka manta daniko?" ya waiwayo da
sauri, sannan ya dawo ya rungumeni jikinsa ya
sumbaci kumatuna"ya za'ayi na manta dake?
Ashe zan iya mantawa da kaina kenan?ya dago
fuskata"sai na dawo"na saki murmushi"Allah ya
tsare min kai mai sona"ya sakeni ya fta da sauri.
Sun kama Dawa Ado,Bangis Kauri, sannan suka
dinga fadin sunan yan daban suna kama
su.kazalika sun dire hayi,inda can ma suka
kamasu da yawa,ya mikasu yakuma basu
shawara cewa suyi bincike kan yaran
sosai.sannan su tabbata sun mikasu kotu.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Hakanan da dare ina Sallah a dakina,misalin
takwas wanda yanzun yazama na yara,Kausar da
Al'ameen suna kwance ruf da ciki suna
Homework ,Aliyu ya shigo da Sallama,suka amsa
tare dayi masa sannu da zuwa,ya kalli Mama
dake bacci can gefe yace"wai shin mamana tayi
nata Homework din ne? Kausar tace"eh Abba
sunyi tare da mumy"dai-dai lokacin na kammala
addu'a ya tayani shafawa, na kalleshi"sannu da
zuwa" cikin murmushi nayi maganar
yace"yawwa,sannu matata"muka sa dariya, ya
rusuna saitin kunnena yace "kisa yarannan suyi
bacci da wuri" kafin in bshi amsa wayar shi
tasoma ruri.ya daga da sauri,nji yana fadin "Yes
Sir" nace Allah yasa ma zaiyi kwanan gdan yau.
Ilai kuwa, yana gama wayar ya kalleni"
yanzunnan zanwuce Abuja" na zaro ido"Abuja
kuma da daren nan?" yayi dan yake"aikinmu
kenan, ahaka muka yi rantsuwa babu dare ko
rana,duk lokacin da aikin yataso zamu fuskance
shi"na lumshe Ido ahankali nace"yanayin aikinku
yana shafar rayuwarku"ya mike zumbur"muje ki
hada min kayana" Kausar ta tashi zaune"Abba
bari muxo mu rakaka motarka"nace "a'a , ci gaba
da Homework dinki in yashirya zaizo har nan sai
ku raka shi," tace to. Tara dai-dai ya kammala
komai,dan ban amince ya tafi bai samu nutsuwa
ba, sabida tsoron kada shaidan ya sake ribatarsa
ya kuma kyallo wata,lokacin da muka zo gurin su
Kausar tini duk sunyi bacci. Ya tsuguna duk ya
sumbaci kumatunsu, sannan ya dauki hanya,na
raka shi mota,sai daya tashi sannan na koma
,ban tsaya wani tunani ba na kwanta don Inda
sabo na saba da tafiyar Yaya cikin dare, sai dai
Adduar Allah ya kare min shi.
Kusan sha biyun daramen wata litinin na jiyo ihu
cikin baccina, na tashi da sauri ashe nakuda ce
takama Mujidat. Da gudu na fada cikin dakin tana
zaune dirshan tana juyi da ihu, na ce ta kwanta,
bari na gani ko mota ta da mai. Kafin na dawo
har kan da ya fito sai ihu take har su Kausar sun
tashi nace mota ta ba mai bari in kira Iya. Na
kira ta na fada mata, tacebari ta taho tind dare
bai yi Sosai ba. Kai Mujidat akwai raki, har
nadaina Jin tausayinta, sai dai haushi.Kafin Iya ta
shigo dan ma Ya fito, masha Allah jariri
sambalele, sai dai abin ya yi ta fadar da gaba na
yadda naga yaron tamkar Yaya. Iya ce ta yanke
cibi sannan muka gyara ta tsaf da danta. Kusan 3
dare suka samu bacci, Ni da Iya muka koma
dakina. Ta dubeni. "Sadiya!" na kaleta da
faduwar gaba. Tace, "jaririn nan baki fahimci
komai ba?" Na girgiza kai "A'a iya ban fahimta
ba. Bashi da Lfy ne?" Tace, a'a kama naga yana
yi da mijinki sak, tamkar an tsaga kara, ko
'ya'yanki basu yi kama da shi ba kamar wannan
yaron, tsorona daya Kar dai ace Gadanga ciki
yayowa wannan yarinyar. "Nayi saurin cewa,
"a'uzu billahi! Iya ba kyau ayiwa mutum
mummunan zato, kin San wannan ba halin Yaya
bane". Ta ce 'eh, to haka ne, amman fa mutum
yakan canja daga halinshi da aka San shi dashi."
na ce, a'a fa iya ita fa wannan da mijinta, kafin
ya mutu mun sha gaisawa da shi. Kuma shi
kamanni hakayake sai kiga baku hada komai ba
amman Kuna kama." ba don Iya ta gamsu ba
tace to Allah yasa hakanne. Na ce ameen. Nan
mukayi alwala muka kama nafila, addua ta Allah
ya rufawa mijina asiri Kar duniya ta gane wannan
matsalar.
Da safe lokacin da na shiga dakin tana zaune da
danta a hannunta ta tsura masa ido tamkar ba
ita bace tayi ta kurma ihu ba. Na ce 'kin tashi?"
ta ce, 'eh mun tashi, kin ga yarona sai kace
Babanshi, naji dadin haka,Dan bazai sake min
musu cewa ba cikinsa bane." da sauri na ce,
'kibar maganar nan mana, yanzu bari kuyi wanka
in na kai yara makaranta sai nazo na kai ku
Asibiti." ta yatsine baki "kin sanar da mjnki?"
nace, a'a kin San Iya tana nan ba dama in masa
zancen ki.' ta dauko wayarta tana cewa, "ina
ruwana da Mamansa taji. Layinsama a kashe
yake.' tayi tsaki ta jefar da Wayar, Ni dai na fice
na kama aiki na raina bace, ban cika ganin
laifinta ba Dan shine musabbabin komai.
Da zamu Asibiti na sauke Iya a gida na wuce
dasu. An duba su ance duk suna lfy, muka tsaya
kasuwa na siya abubuwan da basu da shi,sannan
muka nufo gida.
Tsakiyar gado na zauna sannan na soma Kiran
layin mijina, bugu biyu ya daga, nayi Sallama ya
amsa tare da cewa. "Yaya na jiki cool da yawa?"
Na ce, 'Yaya budurwarka ta haihu." budurwata
kuma? Ya fada cikin sauri. Na ce, eh Mujidat
danta yana nan namiji......zandakata a anan zuwa
wani lokacin kuma,fatan zaku kara hakuri dani
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347



Zaharaddeen Shomar
Whatsapp  08168575100



Darajar Yayana2-03
Posted by ANaM Dorayi on 04:31 PM, 23-Mar-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
_________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Ta soma kwalla a kwai su, amma sun zo sun
kasa kamo barawon.Ya ce, to daga sun zo ne
zasu kamo barawo kamar suna da Allahn
musuru?Ina ganin ki hakura kawai in ba a kwai
wanda kike zargi ba.Ta ce, cikin jaka ta yake a
dakin na, ni na tafigidan kawata, mama ta tana
shigowa sai kanena sun ce kuma basu ga wanda
ya shigo cikin dakin ba.Aliyu ya tabe baki.Shirme
kenan, sai ki hakura kawai.Ta mike tana share
hawaye, shi ke nan nagode.Sanan ta tafi.,har ya
gama shirin sa tsaf zai tafi sai ga wayar
commissioner yana neman sa yana isa aka dan
ka wani aiki a hannunsa.Dole ya fasa tafiya ba
don ranshi ya so ba.Washe gari ranar goma dai
dai dawowar shi ke nan daga wurin motsa jikin
da yaso xuwajiya hakan bata samu ba sai yau.
Waya ta buga daga bakin gate ne, mai gadi ya
ce, yallabai bukur jiya ce ta dawo.Cikin damuwa
take oga.Dan sanda ya kara da haka ne don don
tunanin cewa in ta fito yau ma zai sami
kwaleliyar dubu daya tamkar jiya.Aliyu ya ce ka
ce mata zan fita ne ta dawo da yamma, bata jin
dadin haka ba amma me nema yana tare da
samu, don haka sai ta hakura ta tafi.A ranar ta
saka hotonta da ainihin sunanta aaccount din
da ta bude kuma Aliyu ya amshia botar ta.Da
yammancin ranar bata zo ba domin ta dana
sabon shairi, sha biyu zuwa karfe dayan dare ta
san lokacin da take ganin shi a online ne, don
haka sai ta hau.Cikin sa'a yana nan ta soma da
tura masa hotonta a inbox, yana ganin hoton ya
gane ta.Ya ce, oh, daman ke ce kika yi mun
basaja don in karbeki?Ta ce, naga in ba haka
nayi ba ba za ka kulani ba.Kuma ina da matsala
kai ne nake ganin zaka magance mun.Aliyu ya
ce matsalar me?Ta ce, kafin in fada maka
matsalar tawa, ka fara kallon hotunan nan.Aliyu
ya ce, to.Duk a tunanin sa matsalar ta ta shafi
aikin sa ne.Matsalar farko sassan kirjinta ne,
haka ta turo gabobi duk tsiraicinta ba inda ta
babu inda ta rage.Ya ce me nene ma'anar
hakan?Ta ce, ka duba hotunan da kyau?Ya ce,
eh.Dama ina so ne ka gani da kyau don in nayi
maka saimatsalar tazo da sauki, domin tun
ranar da na ganka na haukace da sonka.Ka
taimake ni.Aliyu ya rasa me zaice don ta kaici
da bakin ciki, sai kawai yayi blocking din ta
amma mehotunan da ta turo sun hau cikin
hotunanshi.Ya dinga bin su da dai dai yana
sharewa, amma da yazo kan na farkon na
kirinta sai ya tsaya yana ci gaba da kallon hoton
har ma ya kasa goge shi.Cikin daren tunaninsa
ya soma gurbacewa, da safe karfe shida wayar
bakin gate ta shigo, bai dauka ba don lokacin
bacci yana kanshi.Don baiyi wani bacci ba can
kuma a bakin gate din shi kanshi mai gadin
yana son wanan bakuwar ta samu shiga sabo da
ya san in ta fito zai samu wani abu.Ya ce,
madan me yasa jiya da yace ki dawo baki dawo
ba?Ta lallaba jakarta ta ciro yan dubu guda
biyu, gashi kasa kati.Da sauri ya amsa ya tura a
aljihu kamar yana tsoron kada wani ya amshe
masa, ko kuma ita ta ce ta fasa.Ya shiga zuba
mata godiya, ta ce, tunda jiyaya ce na dawo ban
dawo ba me zai hana in shiga kawa yanzu?Dan
sandan ya zaro ido oga yana da ka'da sai dai in
yayi fada zaki fiar da ni?Tayi masa fari da
idanunta, kada ka damu inyayi fadan zan wanke
ka.Tun da shiga falon ta ke ta kalle kalle, falon
nashi ya birgeta duk da cewa ba wani
kayanalatu ya zuba ba.Ta zauna kan kujera ta
bude jakarta ta dauko hoda da turare ta sake
gyarawa.Sanan ta cire rigar sanyin dake jikinta
saura singilrti, ta ajiye mayafinta ta gyara gashin
dokin dake kanta.Sanan ta dauki wayarta ta
soma kiran wayar ne ya tasheshi, wata isaka yaji
tana kadawa tamkar za ayi ruwa.Windo ya nufa
ya daga labule kamar yanda ya zata, hadari ne,
yaji dadin haka ko don yakara mikewa.Wayar ta
sake kacamewa da ruri, yana dubawa yaga
number yarinyar, tsaki ya ja tare da yin jifa da
wayar kan katifar sa.Ya bude kofar nifinsa yaje
kicin ya samu abin tabawa, cak ya tsaya sabo da
ganin yarinyar gaban shi ya soma faduwa,
lokacin da zuciyar shi ke tuno mashi hoton.Yayi
karfin halin daure fuska, sanan ya ce, da izinin
wa kika shigo min gida?Ta mike ta nufosahi, da
izininka masoyi na, ka manta ka ce in dawo jiya?
Ban sami dama ba shine na dawo yau.Ya ce, to
fita a gidan nan fita, ya nuna mata hanyar
waje.Ta zauna a hannun kujerar dake kusa da
ita,da ma ka bari mun fahinci juna.Ya juya ya
shiga dakinsa a fusace, durowa yaje ya dauko
bindiga nufinsa yayi mata barazana.Ya fito da
ita ya saita ta, kwashi kayanki ki fita.Hakika
gabanta ya fadi don bindiga ko makerinta yana
shakarta.Amma duk da haka sai ta jajirce, ta
runtse ido hawaye suka soma zuba,zanfi so ka
kasheni feye da ka barni a raye amma baka
amshi soyayyata ba.Zanyi alfahari in ka kashe ni
da kanka, kuma kacewa jami'an tsaro ni na yafe
maka ko sun tsinci gawata a gidanka.Aliyu ya ce,
muje ki fita ni bana son jin komai daga
bakinki.Sun isa bakin falo Ruwa ya tsuge mai
karfi wanda hakan ya sa ya kyale ta.Ya shiga
daki ya adana bindigar, sanan ya hau katifar sa
ya kwanta.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Gurbataciyar zuciyar sa ta shiga kitsa masa wasu
abubuwa, dauko wayar sa yayi yana kallon
hoton da yarinyar ta turo masa.Cikin jikinsa
sanyi yake ratsawa na ruwan dake
sauka.Mujidat turo kofar dakin ta shigo, kasa
magana yayi lokacin da ya waiwayo yaga ta raba
jikinta da tufafi.Yayi ta maza ya daka mata
tsawa, mai makon ta fita sai ta nufo gurinsa da
gudu ta fada masa.Shedaniyar shu'uma ce
yarinyar, don haka bata samu matsala sosai ba
gurin amincewa da gayyatar da tayi masa, zuwa
ga fadawa tafkin zunubin shedan ya sake
kawata abin ga zuciyar Aliyu.
Har yake ganin haram ta shigeshi fiye da
halalinsa.Mujidat ta amince Aliyu ne irin mijin
da take so ta samu.Duk runtsi ba zata barshi
ba, sai da kanwa takar tsami kwannafi ya
kwanta.Aliyu ya shiga jin cewa bai kyau ta ba.Na
dama ta shigeshi, ya mike cikin bakin rai ya nufi
ban daki zuciyar shi yar bakin ciki tana tunanin
shi cewa, wanan wankan da zaiyi anya zai fidda
mai da dattin zunubin daya kwasa?Ya fito ya
same ta kwance, haushinta ya kamashi sosai.Ya
dauki makulli ya bude durowarshi ya ciro kudi
batare da ya irga ba yan dubu dubu sabbi ya
mika mata.Gashi an gama ruwa ki tashi ki tafi
na rokekikar ki sake dawowa gidan nan.Ta
kalleshi cikin damuwa an ce maka neman kudi
nake yi?Ta mike ta soma saka tufafinta, so da
kauna kurun nake nema a gurinka baka da
kudin da zaka iya bani.Ta fice ta dauki jakarta
yana tsaye a tsakiyar falo yana kallonta ta fita
tare da cewa sai ka sake jina.
Ranar Aliyu yajima bai fita ba, na shi ganin
mutane zasu gane abin da ya aikata, kuma sam
baya son ya tuna.Sai istigifari yake yi, in dai
haka mazinata suke ji lallai zina bala'ice, ya
gargadi masu gadinsa lallai kada su sake barinta
ta shiganmasa gida.
Mahaifiyar mujidat yar asalin wani kauye ne a
Ilorin can jahar kwara, an ce dai asalinsu fulani
ne, amma yarbanci suke yi kuma yarbawa suke
kiran kansu.Musulmine su amma musulincin
nasu sai a hankali.
Mahaifiyar Mujidat mai suna Bukolatayi aure da
Mahaifin Mujidad hakimu bayansun haifi yayan
Mujidat dan suna fari kenan, mai suna
Latif.Wanan al'adar yarbawa ce mace taje aure
amma sai ta haihu za a daura, tasu hikimar wai
a gani in mai haihuwa ce.Bayan Latifa sun sami
Sikirat sanan Mujidat, mahaifin su mujidat
direban taxi ne, mahaifiyar su kuma tana da
shago a bakin kasuwa.Tun tasowar Mujidat bata
ji sam yar karya ce da son bobo, tunda ta lura
tana da kyau ai sai ta mai da kyawun nata
tamkar abin kasuwanci. Tun tana shekara tara
ta soma amsar kudi tana fansar da mutuncin ta,
haka ita mahaifiyart fitina gareta ko yau she
tana biye da mata wanan ya sa ko karatun kirki
bata yi ba, tana secondary idanunta sun gama
budewa, manyan mutane suke daukanta.Da
farko iyayanta sunda mu don mahaifiyarta ta
sha yi mata duka sanan tayimata tsarki da
ruwan barkono, amma da ga baya da ta soma
harka da manyan mutane tana kawo musu kudi
sai suka shiga shi mata albarka.Haka nan basu
damu tayi wata bata zo ba in dai zata yi musu
aike.A zuciyar su tafi yan uwanta Latifa da Sikira
wadda take aure a garin Ilorin.Kuma dalilin
ziyarar da ta kawowa anty sikira ta hadu da
Aliyu.Kuma har ta koma gida so da kaunar Aliyu
yasa ta ta dawo Ilorin don samun muradin ta.Jin
kai da jan aji irin na Aliyu shi ne ya sake burge
ta, amma sai gashi tashin farko ta same shi
cikin sauki.Tabbas in ta nace ba da dadewa ba
zai zo hannunta.Karfe tara na dare ta kira
numbar wayan mai gadin gidan Aliyu wanda ta
amsa dan bukatar kanta.Bayan ya daga ta
tambaye shi ka ganeni?Ya ce, a a ban gane ki
ba.Ta ce, sanana Mujidat daga nan cikin gari ni
ce wace na amshi numbar ka jiya bayan na fito
gurin Oga ya ce, ok madam ce ko?Sorry madam
na gane ki, ta ce oganka ya shigo?Ya ce, eh, tun
bakwai yana gida kuma naga alamar ba zai fito
ba, sai dai yayi mun kashedin cewa ko kinzo
kada in barki.Mujidat tayi shiru tana mamaki,
me zai sa ya tsaneta haka?Duk da ta mika masa
kanta kyauta, amma sai tayi wani
murmushi.Indai kissa tana magani to zatayi
mun, ta ceda me gadi in na baka dubu biyar
yaya zan samu in shiga?Yayi shiru yana
nazari.Lallai yana bukatar kudi don yasha kan
matsalarshi da maman Bilikis, amma dubu biyar
yayi masa kadan.Yace madan zan iya dabara in
kin ban dubu goma, zan fadawa Oga cewa
mamana ba lafiya nasan zai barni in tafi.Don
haka ta ba faruwa amma nasan kafin inbar
wurin sai an kawo wasu lokacin ke zaki samu
shiga dan su basu sanki ba.Kuma kafin in tafi
zan lalata wayar cikin gidan, ta ce hakan yayi
zan sameka da kudin in ka kamla komai ka
kirani.Yana kashe wayar yaga Aliyu tsaye a
bayan shi
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Dfarko ya rude sai kuma ya tuna cewa duk sun
yi maganar ne cikin yarensu na yaroba.Aliyu ya
ce, ina ta kiran waya baka daga ba?Ya ce, oga
jikin mama ne ya tashi shine dan uwa na ya
kirani.Aliyu ya ce, jikin ta ya sake tashi?Wani
ciwo ne ke damun ta?Ya ce hawan jini ne, Aliyu
ya sa hannu ya lalubo dubu biyu ya mika mashi
tare da cewa, Allah ya kara sauki. Ya kara da
cewa kaje ba sai ka jira wasu ba, bari nayi waya
su zo.Da murna mai gadi ya fita ya kira mujidat
yace, tayi sauri kafin wasu masu gadin su
zo.Cikin sa;a ta tura kofa ta shiga, haka nan
cikin sa'a ta riske shi a cikin falo zaune da yar
shirt fara irin mai kama jikin nan.Sai gajeren
wando, kalkon labarun kasa yake yi NTA, turo
kofar ne yasa shi waiwayawa, zunbur ya mike
yana nuna mata waje.Fita la'ananiya, ta saki
jakarta ta nufeshi, haba masoyina, ina sonka
sosai tsaya kaji.Ta kai hannu zata taba shi ya ja
baya.Ki fita kawai, ta zauna kan kujera, ba zan
sake barin gidan nan ba ko zaka kashe ni.Ya
biyota ta zagaya ta fada bedroom dinsa.Ya rasa
me zai yi mata, sai kurum ya kira yaransu daga
headquarter, jin haka dama tariga ta tanaji
dabararta.Taciro wayarta ta danna wani hoto ita
da shine suna tsaka da aikata masha'a ta
dauko.Kalli hoton nan ka gani, ina da irinsu da
yawa har na kati na wanke.Aliyu ya fizgi wayar
ya kalla, duk da ya girgiza amma bai nuna mata
ba ya ce, yace amshi wayarki ba kati ba in kin
gadama in kin tashi ki sa shi a kan profile din ki
na fcbk,ko a jikina.Ke ce mace mutuncinki sai
yafi nawa zubewa.Tayi shiru ta rasa me zata ce,
ya ce fita.Ta daga hannuwa biyu, naji naji zan
fita, ta matso gunsa amma ya kamata a ce
kanayiwa mesonka kallon mutunci da kima.Ta
soma kuka, ka tuna ba nice na dorawa kaina
sonka ba, ya kamata ko baka sona saika fada
min magana mai sanyi.Ya runtsa idanu, burinsa
ta fita domin zuciyarshi ta soma
tausayinta.Sanan ga shi dan can gefe yana rada
masa wani abu.Ya bude ida nunshi, shi ke nan
naji ban kyauta ba amma dai yanzu ki fita
kawai, domin ni da ke ba hurumai bane.Ki tuna
da abin da ya faru ni dake she karanjiya laifi ne
babba, kin sani.Ta matso ta kama hannuwansa
ka min afuwa sonka ne ya sani haka.Yanzu ina
jin yunwa ko zaka tai maka min da wani abu in
ci sai in tafi?Ya ce, duba kicin sai dai in bread za
ki ci.A kicin tayi ta zagayawa tana tunanin me
zatayi ne don ta samu ta kwana a gidan.Ta
dauki wuka ta dauko bread wai za ta yanka,
amma sai ta kulle ido ta sharbi yatsanta da
gangan, sanan ta saki kara.Cikin hanzari ya nufi
kicin da ganin yanda jinike zuba ya sa shi shiga
da sauri ya rike ya tsan nata.Kasancewar yana
da yar akwatinshi ta taimakon sai ya gyara mata
ya rufe shi sanan ya ce, muje a maki Allura sai
ki wuce inda kike.Ta soma rawan sanyi wai ba
zata iya tashi ba, barinta da yayi ta dan
warware shi ne ya kawo kwananta a
gidan.Domin tuni shedan ya ribace shi, duk da
yana zargin ta yanka kanta ne dama don kada
ta tafi, tun daga ranar ta zama gidan tamkar
matarsa, wanan ne yasa ko da ya koma gida
sadiya taga canji.
Wata hudu kenan da soma shiga matsalar mu
da ya Aliyu, amma tamkar na shekara biyu, duk
na rame na lalace har bana so inyi baki don
kada suce lafiya?Cikin wata hudu ya zo so hudu
duk karshen wata ke nan kwana dai dai yake yi
ya tafi sam baya kulani in yazo magana fiska a
daure yake min.Ya manta da wani hakki nawa
da yake kanshi, domin nima mutun ce ba ice
ba, ina shan wahala da kewarsa.Darare da yawa
ina zubar da hawaye don kunci da kewa, gashi
yayi mun sabo da yanayin sa na rashin
hakuri.Usman da Anty Abida sune kawai suka
san halin da nake ciki, ko iya da amininiyata
Aisha sunyi juyin duniya amma ban shaidar
musu da ko mai ba.Usman ya ce, duk lokacin
da nake bukatar wani abu bai min ba in
tambaye shi, ni gaskiya ina da jin nauyi.Yau in
na ce gashi gobe in ce gashi ba zai yuwu ba,
abin da kawai na tsana shi ne inga arana babu
makaranta, amma don abin anfani kamar su
abinci ina maneji.Tunanin kama sana'a ya
shigeni, na ce lallai ina bukatar in kama sana'a
don in samu in kare DARAJAR YAYA NA,
wadanda a yanzu sunfahimci tsakanina da
baban su a kwai matsala.Ba kausar ba hatta
Al'amin ya san cewa mahaifinsu ya canza, don
watarana da ya shigo daki ya same ni ina kuka,
sam banji shigowarsa ba sai naji an dafa ni.Nayi
ta maza na share hawaye na na kalle shi da
murmushi, ranshi a dagule ya ce, momy waye
ya saki kuka?Na ce Idona ke ciwo.Ya ce, mama
Abban mu ne ko?Na ce, a a Abbanku bayanan?
Yace, shi ne mana, ya ce ki barshi in na girma
zan maki duk abin da kike so, in kaiki maka, in
sai maki komai.Na rungume shi tare da cewa, to
yarona naji dadi na gode kaji.Ya ce momy ki
daina kuka kin ji?
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Bayan fitar Al'amin ne na shiga sabon tunani,
lallai matsala tsakanin miji da mata tana kawo
rabuwar kan yaya, tana tauye yara.Domin zuwa
da nayi open day din su a makaranta nan
malamarsu take yi mun korafin cewa yarinyata
Kausar sam yanzu bata da hazaka kamar
da.Bata da kuzari sam, ta ce kowa ya san
Kausar Aliyu Tutur a makarantar nan ya san ta
da kokari ga surutu, ga wayo.Haka nan duk
wanda ya yi mata bata kyalewa, amma daga
wancen term zuwa wanan tazama tamkar
doluwa ba karatu.Bata iya rama fada, karamin
yaro sai ya doke ta ta tsaya kuka, sanan tsaftar
su ta ragu, a da yaran suke zuwa na daya a
tsafta wanan karon sun koma na biyu.Don haka
kiyi kokari ki canja kila matsalar daga wajenki
ne.Afili na ce, lallai daga gurin mu ne,
matsalarmu zata maida yaranmu baya, dole in
kawo canji duk yanda zanyi gidan mu ya koma
gidan farin ciki kamar da da taimakon
Allah,Wayata na dauko na soma ruga sako
kamarhaka.KALMOMI SUN YI KARANCI
TSAKAKKEN YANAYI, FADIN YI HAKURI KADAI BA
ZAI GAMSAR BA.AMMA DUK DA HAKA INA ME
BAKA HAKURI, BA DAN NAYI LAIFI BA, SAI DAI
INA DARAJA DANGATARMU FIYE DA
SHEKARUNA.DA WANAN SAKO NAKE SAKE BAKA
HAKURI TARE DA AIKO MAKA DA ZUCIYATA KA
AMINCE DASHI DON SAKE DAWO MIN DA
FARINCIKI NA.INA FATAN ZA MU KOMA FIYE DA
DA, ZUMA TA ALY NAYI KEWARKA, INA TSNANIN
SONKA.
Na tura mashi ina tsammanin ganin sako kokira
amma shiru, duk wani tunani ko dabara nayi
amma babu nasara.Wata laraba da yamma su
kausar an koro su kudin islamiya, gashi dama
abincinmu ya kare, nafita hannuna da Nera Dari
na siyo garin rogo da suga.Nufina su sha da
dare, duk da ina tunanin yaya zan sha kansu su
sha gari da dare, sai lokacin da nake dawo wa
yana ba yana a mota direbanshi yana janye da
shi.
na shigo gidan zan Rufe sai naga mutum kamar
daga sama ya nufo gida, gaba na yayi muguwar
faduwa.Sam yanzu bana son ganin shi, don
tsananin tsoron sa nike ji, ko sallama baiyi ba ya
fara da ce mun, daga ina kike?Cikin in ina na ce
sha....shago baje can gurin hadi.Yin me?Na ce,
gari na suwo da suga.Gari?Ya tam baya tare da
zaro ida nu.Na sa dan yatsa na akan le buna na
tare da fadin yi hakuri yara suna ciki.Sai me? Ya
katse ni, na ce sai me in yara suna ciki, wato
sabon salon zubar da mutunci wanan kika samo
ko?Kamar ni a ce matata tana zuwa shago siyan
gari?Na nufi ciki raina a dagule, in ya bamu
abinda zamuci ishashshe ai ba zan fita siyan gari
ba, na raya hakan cikin raina.Kai tsaye daki na
shige na ajiye garin na fada ban daki don gudun
kada yara suji, da gudu suka rungumeshi suna
mashi oyoyo, al'amin da shi da mama, Kausar
tsayawa tayi tana kallon su.Ya dube ta ke
Kausar ba zakiyi min oyoyo ba? Ta ce sannu da
zuwa Abba.Ta juya ta nufi dakin su.Da kallo ya
bita cikin mamaki, me hakan yake nufi?Ta soma
yiwa yaran sa fanfo ne?Ya mike ya nufi dakin ni
kuma jin shiru sai na fito ina shigowa falo najiyo
muryar sa.Kausar ina tambayarki kin yi mun
shiru na ce me nene kike fushi?Sai na jiyo
muryarta tana cewa, Abba ni bana so ka dawo,
sabo da in kana nan kullum cikin fada da momy,
ni bana son tana kuka.Itama ta soma kuka, na
zaro ido cikin mamaki yarinyar,na saurara inji
me zai ce, fatana Allah yasa zancen Kausar
yazama sanadin fahimtar shi.Muryarshi ne ta
katse ni, ok wato uwarku tana kitsa muku
magana a kaina ko? Mamanku ta shirya muku in
nazo ina cutarku ko?Ya sake tambayarta cikin
daga murya, ban san lokacin da na fada dakin
ba ina fadin haba yaya.Yanzu me ya kawo
wanan tunanin?Tayaya za kayi mun wanan
zaton?Na kalli kausar fita.Ta fita na maida kofar
na rufe yana tsaye rai bace yana kallo na.Nayi
kasa da murya tare da tausasa ta, yaya wanan
sauyin da kakawo mana cikin gidan nan wlh ba
sai na kintsawa Kausar ko mai ba.Tana ji tana
gani, duk kokarin da nayi dan cewa basu
fahimta ba amma hakan bai samu ba.Saboda ka
kasa gyarawa, har takai ko a makaranta yaran
sun koma baya.Hawaye suka soma zubo min
masu zafi, na taka na isa inda yake tsaye nafada
jikinshi na kan kame shi.Yaya ka taimaka kayi
hakuri ka zubar da makamanka ka dawo mana
da farincikin mu.Ya ban bareni tare da hankade
ni har sai da na fadi, ya soma magana cikin
ihu.Tayaya kike so in yarda dake cewa bake
bace kike bata ni a wrin yarana ba?Yar wanan
yarinyar da bata gama sanin kanta ba shine har
zata san matsalar wani? To ni dake dasu munsa
hannu tunda kin zabi haka.Shiyasa sam bana
son zuwa garin nan, saboda takaicinki, kin zama
saikace sanda don Rama.
Kullun mahaifiyata tana tuhumata cewa bana
kula da ku, yanzu dan zubar da mutunci wai
kinje shago siyan gari.Na fashe da kuka yaya
yaushe rabon ka ajiye mana abinci?Tun zuwan
da ka tawo da wanan matsalar.Ya daga hannu
rufe min baki, yanzu ina yi maki magana ne a
kan shiga tsakanina da yarana.In zandau komai
ba zan dau wanan ba, ya kamata ki sani.Ya juya
ya fita bayan ya bude kofa.Kuka sosai nayi na
tsawon minti daya, sanan zumbur na mike na
fita.Mama tana kwance a tsakar falo tana ta
tsotsan yatsanta, ita bata san me ke
faruwaba.Ahmad yana zaune kan kujera ya
takure, Kausar na shiga raba ido in gani, can na
hangota gefen kujera ta makure tare da toshe
kunnuwanta, tana nufin bata son jin abinda ake
yi, ga kuka tana yi.Tayi sharkaf da majina,
dakinsa ya shige shikam naje na rumgumo
Kausar nazo na hadasu da Al'amin ina
lallashinsu.Duk da cewa nima hawaye ke
kwaranya a idanuwa na, Al'amin yazo yayi mun
rada a kunne, ki hada shi da Iya kinji Momy ta
rama maki(don duk zatonsu ni iya ta haifa ba
baban su ba) Najasu muka koma dakinsu, na
ce, Kausar Al'amin kuyi hakuri ni da Babanku za
mu koma kamar da, ba da jimawa ba kunji ko?
Kausar ta dago kai, yaushe momy?Na runtsi ido
hawaye na kwaranya na ce, bada jimawa ba
Kausar kinji?Duk suka makaleni, Al'amin yasake
cewa kin hada shi da Iya ne, da sauri na ce a a
ko ku kada ku fada mata, ba na ce muku bata
da lafiya ba?Kuna so in taji da muwa ciwonta ya
tashi?Duk sukayi shiru, nace kuna so ta mutu?
Da sauri suka ce, a'a,na ce to in kun fada mata
zata mutu.Kausar ta ce, bazamu fada ba.Na
share hawayena sanan na kallesu.Muna ciki har
aka kira magariba, na taso su mukayi salla.Tinda
na fito banga Mama ba, nasan tana gurinshi,
suna ciki ko sunfita oho.Na jika musu gari suka
zauna, Allah ya taimakeni suka kama sha.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Kausar tana cewa,Momy in nazama babba zan
dinga siyo mana kayan abinci.Al'amin ya ce,
momy ba na rigata ba.Yaya kausar nine
zandinga siyan ma Momy ko mai, na ce to tun
yanzu nagode, Allah ya raya ku, ku girma cikin
aminci da Albarka, suka ce amin.Raina yayi
sanyi yar firar nan da muka yi da ya rana sai
gashi sunyi sallama shi da mama tsam ya tsaya,
ganin suna cin gari.Na lumshe ido na hadiye
takaici na, sannan na ce sannu da zuwa.Bai
amsa ba yayi ciki, kamar in zauna sai kuma na
bishi.Ya aje mama ya zauna bakin gado tare da
dafe kai, na ce, ina maka sannu.Ya dubeni
idanu jajur.Yaya na ke cin gari da dare?Na ce,
to yaya bamu da komai ne.Na dubi mama,
zomuje ki ci gari.Ya daka min tsawa, ki daina
kira min sunan garin nan, ba zataciba.Ko
Inyamuri ya sha gari da daddare? Wanan shine
na karshe in ba haka ba rai zai baci, ban ce kala
ba na juya, cirko cirko nagasu Kausar a
falo.Kausar ta toshe kunne, Al'amin na tsaye
cikin damuwa,nakamasu muka koma na ce su ci
garin amma sai suka ce sun koshi.Kausar ta
kwanto kan cinyata, Al'amin ya kwanta kan
kujera na kwantar da kaina nima a hannun
kujera.Wai ta wace hanya zanbi gidana ya dawo
kamar da?Wa zai ban shawara dan ni ina ganin
tawa basirar ta kare kan haka.Allah ka bani
mafita.Muna nan har aka kira isha'i, na tashi
naje nayi sallah suma sukayi sai ga mama ta
shigo da nama da Holandia, na ce, suci.Al'amin
dai ya ci amma Kausar kin ci tayi waita ta koshi,
na rungumo ta, Kausar kina fishida Abbanki ne?
Tayi shiru, na ce ki fada min.Ta ce, eh momy
shima yanzu ya daina sonmu nace, a a yana
sonmu fushi yake yi in ya huce zai dawo kamar
da.Sai kurum naji ta ce, wane ne yayi masa
laifimomy?Na ce, ni ce, ta ce, bakiyi mashi ko
mai ba, ba ma kullun kina bashi hakuri ba
tunda yaki yayi hakuri ya daina sonmu.Bani da
bakin magana sai shiru ina mamakin Kausar,
yar wanan yarinyar har tana fahimtar abubuwa
kai abin da mamaki sosai.Haka na lallaba su har
sukayi bacci na kulle mana kofa sanan nima na
kwanta na fada kogin tunani.
Wa she gari da wuri na tashi nayi salla da
wanka, sanan nayi musu shirin makaranta, duk
a dakinsu.Nace suje su gaida baban su.Kausar
ta noke tare da daure fuska za ta soma kuka,
na ce, haba Kausar, kuje ku gaida Babanku
mana.Kina so ne ya j haushi irin jiya?Jiya ma kin
ki sakar mashi fuska ne shi yasayayi fada.Ta ce,
to momy yanzu tsoronshi nake ji.Na ce, daina jin
tsoro kinji Kausar, yana sonku.Daga nan ki bashi
hakuri.Ta ce, to.Amma sam fuskarta ba wani
annuri, ina biyeda su har kofar, Al'amin ya
kwankwasa daga ciki yaya ya ce, wanene?Mama
da jin muryarshi sai ta ce, Abba.Ya ce mama.Na
bude kofar suka shiga, yana kwance kan gado
da waya a hannunsa, da Alamu cht ya ke
yi.Kausar ta dan tsaya nesa dasu kanta a
kasa.Al'amin ya zauna bakin gado,Mama ta
hayekan gado, ya rungume mama da Al'amin
sanan ya tashi zaune.Al'amin ya gaida shi,
Mama ma cikin hausarta mara dadi ta gaida
shi.Ya kalli kausar daga inda take.Zo nan.Ta tafi,
ya janyota zuwa jikinshi, ta ce ina kwana?Ya ce,
ba zan amsa ba Kausar har sai kin fada mun
me mamanku ta ce maku nayi, kuke jin haushi
na?Kausar ta ce ba ko mai Abba, Al'amin ya ce
ta ce ne fa muzo mu gaida kai.Ya kalli Kausar,
yanzu kunfi son mamanku fiye dani ko?Al'amin
ya ce, muma ka daina son mu Abba.Ya ce, ok,
haka mamanku ta fada muku?Kausar tayi saurin
cewa momy bata fada mana haka ba, ta ce ne
kawai muje mu gaida ka.Ya dungurewa Kausar
kai yar karama da ke kin iya munafunci, ba zan
kara yi maki tsaraba ba.Ya kalli Al'amin, in ba
ka daukar maganar mamanku zan sai maka
keke kana so?Al'amin ya kama murna ina so
Abba.Ya kalli mama, mama na ke kuma in se
maki motar ki ta wasa ko?Na juya kicin ina kuka,
mutumin nan zai raba mun kan yara, zai kafa
min jam'iya yan partyn shi da nawa.Jin takun
Kausar yasani share hawaye, cikin sheshekar
kuka ta ce, momy kinji Abba zai sayawa su
Al'amin da mama tsaraba ban dani.Na tsugunna
na rungumota jikina ina shafa mata kai, yi
hakuri Abbanku wasa yake yi miki zai siyo miki
kinji?Ta ce, Allah momy da gaske yake yi ba ya
cein fitar masa daga daki ba?Na ce, yi shiru zai
sai maki.Da kyar tayi shiru.Na bata jug na ce,
kije wajen Iya ki ce mata in ta dama koko ta
baku, karfa ki ce mata wani abu ya faru kinji?Ta
ce to.Ta tafi nikuma na zauna a kicin cikin ta
gumi.Kausar ta sami Iya kwance ta gaida ta, ta
ce kausar menene?Ta ce, wai in kin dama koko
ki bamu, iya ta ce shine aka turoki ba Abbanku
ya dawo jiyaba?Me yasa bai rakoki ba?Tayi shiru
Iya ta ce to muje in se maki koko gidan ladi me
koko dan kulluna jiya ya kare, kice mata na ce a
jika maku gero tunda jifa jifa kuna shan kokon,
ban cika son abin siya ba.Sam iya bata fahimci
bamu da komai a gidan bane, tunda lokaci zuwa
lokaci sukanje su amshi kokon.Ta samu masu
kosai sanan ta rakata har kusa da gida.Tanaji
tana fadan turota ita kadai a wanan safiyar, ta
ce da uwarku tana tattalinku amma yanzu duk
ta canza,na rasa me ke damunta.Suna shan
koko da kosai kausar tana fada min sakon Iya,
na jika gero na ce to za a jika,suka gama na
dauki Mama na nufi kaisu makaranta, kusan
wata guda a kafa nake kaisu makaranta, don
mota tuni nayi fakin dinta gefe na rufe ta don
ba mai ba na da kuma kudin siya.Ina dawowa
na tarar da shi da Usman zaune yana
karantowa Usman laifuka na.Na gaida Usman na
shige daki, na hau gado na kwantawa,bawai don
bacci ba ko don hutu, sai don tsabar ta kaici.Can
na jiyo muryarshi yana kira na, ya kalle ni.Kin
san na fada maki ba zan dauka ba ki rabani da
yara na ba.Jiya na shigo gidan nan wai Kausar
tana yin fushi dani yar karamar yarinyar
nan.Al'amin yana fada mun na daina son su,
tayaya zan yarda wanan tunaninsu ne?Usman
ya daga mishi hannu saurara aboki na, ka barni
in gama magana ta don kada kakatse ni.Usman
ya kalleni,Sadiya me yake faruwa ne?Na runtse
ido don ta kaici, yaya Usman duk abin da ya
faru Abban kausar shine sila.Na koro mishi
komai tun daga farkon rigimar har zuwa
yau.Sanan na ce yaya Usman tsakani da Allah
kullun yaran nan suna kallon muna fada, ko
ince daga yazo sai shiga tashin hankali zasutashi
da tarbiya me kyau?Ya ce, a a.Na fada musu
yanda mukayi da malamansu. Ga rashin abinci
wane laifi na masa, ni dai yanxu tunda gani
gashi kurun ya fada min laifi na, wlh zan bashi
hakuri mu koma kamar da yaran mu suma su
sami natsuwa.Usman ya kalli Aliyu, aboki kaji,
sai ka fada mata laifinta don matsalar tazo
karshe.Aliyu yayi mun wani kallo ke dai kawai
baki son zaman lafiya ne, duk ki dauki damuwa
da bakin ciki kisawa kanki.Sau nawa zan fada
maki baki yi mun komai ba?Usman ya ce, to na
rokeka aboki ko mai ya wuce.Ya runtse ido tare
da fadin shi ke nan.Na dube shi nima in sha
Allahu ko mai ya wuce.Usman ya ce,
Alhamdulilla, yanzu sai ka tashi mushiga kasuwa
don nima abincin gida na ya kare.Nan dai suka
fita.A cikin mota Usman ya kalli Aliyu.Aboki ka
canza fa,Aliyu ya kalleshi wacce irin canzawa
nayi?Usman yayi murmushi sanan ya maida
hankalinshi titi.Kayi kiba sanan dabi'un ka sun
canza.Aliyu ya kure Usman da ido, zaiyi magana
kenan wayarsa ta soma ruri, ya ciro ya kurawa
Screen din ido,sha wara yake ya dauka ko ya
yanke,Usman ya kalle shi, daga mana abokina,
Aliyu ya katse kiran sanan ya kalli Usman,daga
jin kira sai kace in daga ba tare da kasan me
kiran ba?Usman ya ce, jami'in tsaro zai ji
shakkar daga kiran koma wanene.......Kiran
yasake shigowa, sai kurun Aliyu ya dagadan
kada Usman ya dago abinda ke faruwa.Ya ce,
yaya?Mujidat ta ce, muryarka nake sonji, nayi
kewarka da yawa, don Allah ka dawo yau.Tana
magana kamar zata yi kuka, salon dake narkar
masa da zuciya,take ya manta da wa yake tare
har ya furta cewa.Kada ki damu gobe kamar
yanzu muna tare,ta ce, to Zaki na sai mun hadu
a internet.Sai da ya salameta sanan ya tuna
yayi baram barama.Ya dubi Usman wanda bai
ce kala ba, ya soma nade tabarmar kunya.Wata
abokiyar aikina ce, muna gabatar da wani
aikine.Usman yayi murmushi sanan ya ce, sau
da dama in mutun ya shiga aikata rashin
gaskiya sai kaga ya zama makaryaci.Ita ko karya
illar ta da kayi so daya kafin ka fitar da kanka
sai kayi kusan sau goma.Aliyu ya kalle shi, me
ya kawo wanan zancen?Usman yayi dariya, ka
tsargu ne?Aliyu ya kalli gefe, intsargu da me
kuma?Usman ya hade rai, tsayar da halayenka
haka nan Aliyu.Ya gangara gefe titi yayi fakin
dazu nake ce maka dabi'unka sun canza ko?
Aliyu ya kalli titi muje zuwa da maganarka, in
wani zai fada mun aboki ba zan yarda ba,
amma gani ina zar ginka cewa kana hulda da
matan?Aliyu ya kalleshi da sauri, haba aboki,
nasancewa zaka iya bada shaida cewa ban
kasance mai shiga lamarin da mata suke ciki ba,
bare har inyi hulda dasu.Usman ya ce to amsa
min wadan nan tambayoyin.Aliyu ya cire hankici,
ya share zufar fuskarsa sanan ya ce, ina
jinka.Usman ya ce, na kira layinka sau uku wata
macece take dagawa.Na farko da dare ne gurin
karfe dayan dare, don in fada maka rasuwar
kanwata, sai kawai wata mace ta daga wai ka
shiga wanka.Na biyu da safe wata jumma'a don
mu gaisa ta ce ka fita gurin masu gadi, na uku
gargadi tayi mun in san lokacin da zan
dingakiranka yanzu kana cikin halin da bazaka
iya daga waya ba.Sai na soma lissafi giya kake
sha da har ba zaka iya daga waya ba, koko
menene?Sanan ita wanan matar yakuke da ita
har zata kasance a inda kake ciki tsakar daren
nan .In zuciyata ta zargeka sai wata ta shaideka
da cewa ba aikin ka bane, abin da bakayi ba
kana yaro ba na zaton cewa zakayi shi da
girmanka.Amma yau da matarka take fadin
yanda ka kaurace mata, sai na amince kana
neman mata, don kai ba me hakurin zama baka
tare da mata bane.Aliyu ya hade rai tare da
duban Usman, me cece shaidar ka ta zahiri?Duk
abin da kafada bai zama shaidar da zaka
amince ina bin mata ba.Ba zan iya zama ba
mace ba, shekaru nawana dauka can baya babu
auren?Usman ya ce kila lokacin baka san
amfanin matan ba,amma ni shawara daya zan
baka, inma zakayi harkar bariki to bai kamata ka
wulakanta matarka ta sunna ba.Aliyu ya ce, dan
Allah mu rufe wanan firar.Usman ya ce kafin
mu rufe sai nayi maka nasiha duk da cewa bani
da tabbas akan zargin da nake yi maka.Na san
mutun yana canzawa kamar yanda wahainiya
take canzawa zuwa duk kalan dataso.Nasihata
gareka in ka canza daga fari zuwa baki don
Allah ka saki wanan layin ka koma dai dai ko
don gudun zunubi, ko don tsoron azabar
Allah.Ko don kare mutuncin yayan mu, ko don
kare lafiyar ka daga cututukan zamani.Sanan
maganar zubewar daraja da kimarka a idon
wayanda suka san kanayi. Aliyu ya runtse ido
cikin in ina yace, muje aboki don Allah.Suna tafe
yana share zufa, lallai zancen Usman ya shige
shi.
Ko mai na abinci zuwa kayan tea sun hada
muna, lokacin da suka dawo ina kwance
kangado ina karanta littafin gidan zahra.Sau da
yawa in ina karanta littatafan Hausa sukan debe
min kewa halin da nake ciki, har na sha cin karo
da irin matsala ta.Sun ajiye min kayan abinci
suka sake ficewa, na fada kichin na shiga girki,
yarama da suka dawo makaranta sai murna
suke sun sami lafiyayen abinci.Yaushe rabon
muyi girki da kifi ko nama, yau gashi har
farfesun kan rago mukayi.Da daddare na fada
ban daki na sake wankana sheka kwalliya duk
tunanina yau za a shalabari.Sai dai muka
kwanciya ya juyya min baya, na gaji hakurina ya
kare don haka na ajiye kunyata na fada masa
cewa, yau ni ina son a faranta min.Ya ce, shi
gaskiya baya jin zai iya wani abu yanzu don duk
a gajiye yake.Nace, haba yaya, nima fa mutunce
kamar kowa, sama da wata hudu ka juya min
baya.Baka tsoron sharrin shaidan?Ya tashi
zaune a fusace, kina nufin zaki bi maza? Iye?
Fadamin zaki bi maza? Nasauka daga kan gadon,
ban ce zanyi zinaba yay, amma zuciya bata da
kashi, in na kasa jurewa fa?Na durkusa kan
gwiwowina, yaya ka taimake ni ka fiddani wanan
yanayin, ka tuna ni ban taba gudunka ba.Ya
mike ya dauki filo.Sai da ya kai bakin kofa
sanan ya ce, ina ganin kina cikin fitunananun
mata bari naje falo in kwana. Rufda ciki na
kwanta a kan gado ina kuka, wani mai kunci
daga bisani na dangana na fada ban daki na
sakarwa kaina ruwan sanyi yayi ta zuba tundaga
tsakiyar kaina.Ban fito ba sai da naji sanyi yana
ratsani, na fita naje kan gado na dukunkune sai
zazzabi da ciwon kai.Haka na kwana har safe da
kyar nayi Sallah na sha magani, sanan na fita
kicin.Shi kam a ranar ya koma kusan karfe biyu
ina kwance ya tsaya kaina wai ni fa zan tafi.Ba
tare da na dago ba, na ce Allah ya tsare, ya
ajiye kudi a gefe na tare da fadin, motarki an
gyara na ce uhm.
Duk da cewa Aliyu yana kirana a waya mu gaisa
yanzu duk abinda muke bukata yana
kamantawa, sai dai ya barni cikin kewa.Haka
nan ko a waya da mun gaisa shi ke nan sai ya
ce in bashi yaranshi suyi magana,ba wata hirar
soyaya ko ta rayuwa bare in sa rai zamu koma
kamar da.Duk da cewa yanzu yaran nan sun
dan saki jikinsu sai dai duk da haka da sun
ganni cikin takura ko damuwa yanzu zakaga
sunyi mun narai narai tamkar zasuyi kuka.Ni dai
a bisa halin da nake ciki gara ace bukatun ya
dai na yi mun ya bani kulawa da soyayya sunfi
mun duk wani abin duniya da zai sai min.Na
hakura ne saboda DARAJAR YAYA NA, sam bana
so in zube su inyi gaba.In ban rike suba naje
can inyi wahalar yayan wasu.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Wata rana naje kitso inda nake zuwa a can layin
zage-zagi wani gida, gidan haya ne maidauke da
matan aure da dama.A kulun naje gidan ina
karantar abubuwa na rayuwa da dama a gurin
matan gidan.Farko matar dake yi mun kitso, sau
da yawa mijinta in yadawo bata iya sakin kitson
taje gurinsa.Haka zai gaji da zama ya fito ya
dauki bokiti ya ja ruwa yaje yayi wanka.In kuma
da abinci ya ci ya fito in ya ciro kudin cefane ya
bata sai ta amsa a raine, yauma da nazo kitson
hakan ne ta kasance.Ya bata dari biyu ta juyata
sanan ta maida masa tana fadin gaskiya malam
bazata isa ba.Ya ce ba da garin tuwo ba, kuma
naga manja?Ta ce yau kwana uku muna tuwo,
ta kalli yaranta dake gefe suna wasa.Habu kunji
babanku wai yau ma tuwo sai suka rugo da
kansu gaskiya baba yau bazamuci tuwo ba.Ya ce
to me ni dai kudin nan ke nan.Ta ce, ko tuwon
ne ma kudin nan ba isar muzaiyiba, ya ce haba
Tasallah, ba kifi ba nama kice dari biyu baza tayi
miya ba?Ya shura takalminsa yayi gaba.Ta daga
murya sai dai ayi maka ciko kuma kana zuwa
zaka bani kudi na.Yaran suka hau mita, shi
baban nan kullun tuwo.Na kalleta cikin mamaki
sanan na ce, na kusan daina zuwa kitso gurinki,
ta ce zaku tashi ne?Na ce a a na ce nagaji da
yanda kike daukar mijinki ba a bakin ko mai
ba.Dubi yanda kike sa yaranki suna yi ma
mahaifinsu rashin da'a da raini, wanan tarbiya
ke nan?Tayi yar dariya hajiya kenan, Allah hajiya
ba haka bane, ace mutun kullun ba ci gaba, ba
ya neman wata sana'a a caba yake.Na ce, na
lura baki da godiyar Allah ta salla. Ranan fa ina
kallonki da yaranki kuka ce masa kun gaji da
shinkafa, san nan baki sanin mijinki ya dawo ki
bishi daki ba.....
Allah sarki Rayuwar Aure,kowadai da tasa
matsalar,damadai haka Rayuwar take,tanada
manyan matsaloli guda hudu wadanda duka
daya takan haddasa rashin jin dadi daga
bangare daya,Immadai -:
Mijin baya jin dadin zama da matar,misalin
Tasalla me kitso da Mijinta,kokuma...
2:Matar ake zalunta ,Misalin Aliyu da
Sadiya,Kokuma ...
3:Suna zaune lafiya a junansu, Amma dangin
matar ba kaunar mijin,shima Wannan Babbar
matsalace a auratayya,Wacce ke Haifar da Babar
Matsal..kokuma...
4 angin mijine basu son Matar, wanda nasan
da yawanku kunfi sanin wanna matsalar,..
Lallai dukanin gidan auren da suka samu kubuta
daga dukkanin matsalolinnan nazama wajibi Su
godewa Allah,akarshe Dukkani gidan Auren dake
da matsalar makamanciyar wadannan Ya Allah
ka kawo musu agaji,mukuma Ya Allah
kahadamu da abokan zama nagari
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347


Zaharaddeen shomar
Whatsapp  08168575100


Darajar Yayana2-04
Posted by ANaM Dorayi on 06:34 PM, 29-Mar-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
___________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Assalamu'alaikum, fatan kuna cikin koshin
lafiya...
Sagir Ali, Shamsusdden Usman,Fatima
Ahsan,Maman Ummi,Shamsiyya,Ummi
Amal,Aisha and Aisha Kaka Zanna nagode da
kulawarku,sannna inna jin dadin yanda kuke
kulawa da shige da ficena,shirun da kukaji
yafarune sakamakon ayyuka da sukaimin
yawa,fatan zakucikaba da bibiya dakuma hakuri
dani. nagode zamu Dora yanzu.....
Ruwan wanka sai dai ya diba yaje yayi, wanan
rashin dabi'ar har ina?tasake yin dariya, to ni in
nashiga dakin in ya dawo me zan masa?Na ce,
auran kiyayya aka maki?Ta ce, a a ni na kaishi
gidan mu, ta ci gaba kin sani ni gaskiya ko ya
dawo bana shiga, shi yanzunnan zaice zai
rungume ni, niko na tsani haka,ka debo rana ka
wani ce zaka rungume ni, salon su Habu su fado
dakin?na ce menene dan yaranku sun ganku
rungume da juna?Kai ke dai baki da dabi'a,irinku
ne ake kwacewa miji cikin sauki,daga baya kizo
kina ya ci amanar ki,ni dai in baki canza haliba
zan daina zuwa,ta ce;to Hajiya za'a sake, ai ku
hajiya cikin daula kuke baku da matsala.Nayi
murmushi Tasalla kenan.Shiyasa na ce, kina da
hange, ki kalli kasanki mana,Misali waccan
Maman Rashidan kuke ce mata ko wa?Tunda
nake zuwa gidan nan bai fi so nawa naga ta
daura tukunya ba.Kullun in kazo zakaga yaranta
suna cin dumame, ko garin rogo amma ban taba
ganin mijinta ya dawo ta barshi ya dibi ruwan
wanka da kanshi ba, ko ta shareshi taki shiga
daki.Sanan sau biyu na taba ganin mijinta nasan
yayi sa'ar mata, duk cikinku 'yan nan sasan da
na taba ganin shigowar mazajenku da fitarku ita
kadai ke yi wa mijinta sannu da zuwa da yi mashi
addu'a in zai fita.Tasalla tayi yar dariya, hajiya
kenan, ita waccen ai bata san kimarta ta ya mace
ba, in banda haka yaushe zan zauna babu
abincin kirki.Amma kina like da mutun kullum sai
tayi wankan asuba don jaraba.Na ce, tafi ku
godiyar Allah ne da biyayya.Sanan zakuga
cigabanta kuna nan, sanan yaranta sunfi naku
tarbiya da tsafta.Tasalla ta bata rai,Hajiya mu bar
maganar nan, amma ko su maman Auwal zaki
tambaya matarnan tana shiryawa yaranta kinaya
ne don in mutane sunzo su rinka gaidasu don a
ce suna da halin kirki.Na ce, ba wani bayan aike
ma ina kallon naku yaran amma baku aikensu
don kunsan cewa bazasuba, sai dai ku kira
nata.Daga nan Tasalla tayi kus, niko na ce in sha
Allahu duk randa zan kuma zuwa sai nayi wa
yaranta kwalima tunda naga yaranta basu fi
girman su Kausar ba, a raina na raya hakan.Ina
Mota na kusa isa gida da motar dama naje gidan
kitson da mota ne, sai ga kiran Aisha aminiyata,
cikin hanzari na daga ina fadin.Kin haihu kenan?
Tayi dariya yau andace kullun na kiraki zancenki
daya ne kin haihu?To ga yarki nan a gado.Na ce,
Alhamdulillahi ga ni nan.Na kira layin Abban
kausar kamar yanda na zata har ta tsinke bai
dauka ba, na sake kira.Muryar mace naji cikin
harshen turanci tace wakike nema?Sai da sitiyarin
ya kusa kufce min, na samu na tsaya tunda cikin
unguwa ne, na sake yin sallama cikin rawar
murya.Ta ce kina bukatar taimako ne?Na katse
layin zufa ta soma tsatstsafo min.Na rude
matuka, na kifa kaina a kan sitiyarin ina fadin
Allah yasa mafarki nake yi.Na kuma kallon wayar
ina shawaran in sake kira ne ko in barshi, sai ga
kiranshi ya shigo da sauri na daga amman na
kasa magana, Muryarshi ne yanzu ya ce hello!!
Dazun bakiyi magana ba sai wata irin muryanake
ji.A sanyaye na ce dazun ba kai bane wata ce ta
daga.Da sauri ya ce wata wa?A wayata?A'a sai
dai in network ne yasa ki kika ji haka.Ya saki
zancen da cewa, lfy dai?Na ce eh dama ina
dawowa daga gidan kitso ne sai Aisha ta kirani ta
haihu.Ya ce wace Aishan?Na ce, ta mamana.Ya
ce, Allah ya raya, kin cika son yawo.Na ce to yaya
in banje yanzun ba dole in sake fitowa don inyi
gabadaya.Ya ce to shi kenan ina yaran?Na ce
sunje yiwa iya wuni, ya ce ban son fa kina tafiya
ke daya fa.Ko mama bakya iya yawo da ita sai ke
daya tsura?Na ce, to yaya sun kwana biyu ne
basu je sunyi mata yini ba.Ya ce, to shi kenan
kardai kiyi dare don na sanku in kuka sami surutu
na ce to.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Bayan ya kashe wayar ya nufi gurin Mujidat da
ke zaune kan kujera tana dafe da kumatu, inda
Aliyu ya watsa mata mari sakamakon shigowa da
yayi ya ganta ta daga masa waya.Ya kalleta in
kika kara yi min gangancin daga min waya sai na
mugu saba maki, don zaki koma inda kika fito.Ta
mike tsaye kana jin tsoron matarka ne don kar
tasan muna tare ta ce ta fasa aurenka?Cikin
gatse Aliyu ya ce haka ne.Don haka kada ki kara
daga min waya.Ya juya ya shiga dakinsa rai a
bace.Mujidat ta mike tsaye tana kai kawo, wai
mutumin nan yana nufin duk son da nake masa
yafi son matarshi a kaina?In ma yana boye mata
ne sai nayi sanadin da zata sani, in sha Allahu.Sai
dai ta mutu ko ta bar mun shi, don na yi imani
na fita son shi, zanyi komai don naga na rabasu
da makircina kawai,ta hada yatsanta babba da
na tsakiya taja suka yi kara, wanan wata Alama
ce da take yi duk lokacin da ta ma kanta
Alkawarin aikata wani abu cikin izza.Ni kam
kwana nai da motata zuwa gidan Aisha, amma
zuciyata cike take da wasi wasin abin da kunne
na yaji wai netwok ne.Anya kuwa ba binne ni
yaya yayi da rai na ba?Nayi murna da ganin
Aisha cikin koshin lafiya tare da jaririnta.Na dauki
yarainyar ina juyyata, mashaAllahu,Bello ya fiki
karfin jini daga ita har Najib shi suka biyo.Na ce
haka dai su mama suka ce, na ce, ina angon
karnin?Ta ce ya fita na kwantar da yar na kalleta
a Asibiti?A gida kafin ya samo mota har kai ya
fito.Innarsu da mamanmu da ma suka zo sai
kurum suka amshi haihuwar, na ce shi kenan
Allah ya kawo shi cikin sauki.Na nufi wata kula
dake gefe, na ce me suka barararaka miki?Na
bude kular, ta ce tuwo ne, miyar kuka, kinsan
tsaffin nan sai suce wai maijego sai da
tuwo.Muka sa dariya, na ce a ni na horu da tuwo
gurin Iya, haihuwar kausar har wani baki nayi
nayi muni dan uban nan.Muka sa dariya.tace, ai
daga baya Anty Abida ta hada maki sabulu, na ce
ai ta min kokari yanzu ba abin da bana hadawa
da kaina.Ta ce zaki hada min sabulunma nace to,
haka mukai ta fira har shida, sanan mukayi
sallama naje gidan Iya na kwashi yayana muka
tafi gida.
Na kasa bacci cikin dare sai juyyi nake kaso
hamsin da daya na zuciyata, yaya Aley yayi
min.Tabbas zan zama wawiya in ban amince yaya
yana neman mata ba.Yaushe rabon da ya dora
yatsansa kan nawa?Kullun dare ina kwana da
kewa, hawaye na suna kwaranya.Na tashi zaune
in ko haka ne wane mataki zan dauka.Zuciyata ta
dauki zafi ina fidda wani huci, lallai in ya kasance
haka zamuyi rigima ba karama ba, don ba zan
dauki wulakanci a kan matar banza ba.
Washe gari da safe ina ta tunanin yanda zansake
cewa yaya zan sake komawa gidan Aisha, saboda
in na haihu kulun tana hanyar har ayi
suna.Amma ni ko haihuwar Najib dinta banyi
mata wani sintiri ba, yaya hanawa yayi.Kuma
bana son fita batare da izininshi ba.Don nayi
imani shi baya kallona Allah da ya halicceni yana
kallona.Text na tura mashi cewa zanje gidan
Aisha lokacin suna tare da Mujidat suna
karyawa.Ya dauka ya karanta, sai ko ya hade rai
ya soma kiran layi na na daga.Tunkafin in karasa
sallama na ji ya ce, ban amince ba kullum fita,
saboda ki dinga kallon maza ko? Na zaro ido na
mike da sauri na nufi daki dan su Kausar suna
nan gida don anyi musuhutu.Kuma bana so suna
jin matsalar mu.Ya ci gaba da fadan shi, na ce
wacce irin magana kake yi yaya?Don in dinga
kallon mazaje fa ka ce?Kana nufin in na fita haka
nake yi?Ya ce, oho miki, amma ban yafe ba in
kika leko waje, nace naji ai tunda ka hana ba zan
fita ba, amma cewar da kayi wai ina kallon mza
nike son inji hujjar ka.Kana ga don ka shuka
fulawa ta fito kaki kayi mata ban ruwa sai ta
mutu?Na ci gaba, haka ne zata mutu amma
kasani ni nasan DARAJAR YAYA NA.Ko don su zan
kare mutuncina kai shaidane budurwa gar ka
bare ni a leda, ka san haka kuma kullun ina
Adu'a Allah ya kare ni daga sharrin zamani.Ban
jira amsarshi ba na kashe, sanan na fada kan
gado ina kuka.Sai kurum naji hannun kausar a
baya na tana fadin.Momy kiyi hakuri ki kyale
shi.Da sauri na share hawaye na taso kausar
bana ce in ina waya a daki ba ku daina biyo ni?Ta
ce momy ki daina daga wayar Abbanmu, ko ya
kiraki ni bana so yana saki kuka.Na ce naji muje
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Kwana uku da yin sunan yar gidan Aisha ya ta ci
sunan Fateema, sai ga yaya da rana tsaka ina
mamakin yanda yanzu yake son yimin dirar
mikiya.Ko yana zargin ina fita ne?Oho.Nayi masa
sannu da zuwa ya amsa na ce, baka fada ba
gashi banyi abincin rana ba.Jiya sun bar
shinkafar da na dafa da dare, sai kawai nasa a
firiza yau na duma ma, amma bari in maka ko
macroni ce.Ya ce barshi bani da yunwa, in na fita
zan siyo fura.Sai da yayi bacci sanan ya tashi yayi
wanka ya fita.Duk ina dakina ina karanta littatafi
,tinda nalura bai bukatar ganina kusadashi, nima
hakan yafi min sauki don in yana gari nafi jincewa
nima macece in kwana cikin kewa.Washegari ya
fita zuwa gidan su Iya na dauko jakarshi, don
kwashe kayan wanki wanda ya dawo dasu kamar
yanda na saba.Ina daga suit din shi zan rataye
wata takarda ta fado, na dauka har zan maida
masa cikin Aljihun rigar sai wata zuciyar ta ce
bude mana ki gani, na bude.Yar wasika ce aka
rubuta da harshen turanci, ga abin da yake
rubuce.ZUMA NA KA TAFI DA TUNANINA, HAR
KAJE KADAWO KASANI ZA KA BARNI CIKIN KEWAR
LALLAUSAR FATAR JIKINKA.BA ZAN GUSHE BA HAR
SAI KA DAWO KA SAME NI CIKIN KEWAR LEBUNAN
KA MASU SANTSI TARE DA (YAWUN) KA ME
ZAKI.ALLAH YA DAWO MUN DA KAI
LAFIYA.....Kafin na kai karshe tuni na jike da
zufa, ina gamawa na ga gari yana juya min, ban
an kara ba sai dai naji ni a kasa ribin jikina a
gado rabi a kasa.Kusan minti biyar sanan na tashi
zaune sa sake karanta takardar ina kuka wiwi har
da majina tabbas yaya mata yake bi,domin
takardar ta nuna haka, mata ce kawai ya dace
tayiwa mijinta irin rubutun nan, wata zuciyar ta
tambaye ni ko dai ya sake aure ne?Duk da uban
kishi na sai nasami kaina da cewa inda ma auran
yayi zanfi son haka, da bin matan banza.Na soma
kaikawo cikin gidan ina tunanin matakin da zan
dauka.Shawarar wa zan nema?Na shiga dakina
na fada kan gado na dauki wayata na shiga
kiranshi, amma sai wani tunani ya fado min.Bari
kawai in kira Hajiya Baida'u, marubuciyar littafan
da nake karantawa danneman shawara.Dan ita
bata sanni ba balantana inyi zaton zancen zai iya
yaduwa, sanan tana da basira nasan zata sani a
hanya.Ringing na biyu ta daga, ta daga muka
gaisadama na saba kiranta, na ce Anty ina
nemanshawara ne.Leta na gani a jakar me gida
na wanda ke Alamta cewa yana tarraiya da wata
mace.Ta danyi shiru na dan lokaci.sanan ba yan
wanan letar kina da wata shaidar?Sanan can
dama halinsa ne?Na ce, a to a da can ba na
zarginsa, sai da ga baya na soma zarginsa domin
Anty kwata kwata ya kaura ce min kusan wata
shida zuwa bakwai yanzun,kuma Anty shi mutum
ne mai zurfin sha'awa, ba zai iya daukar ko
kwanaki ba ba tare da mace ba bare watanni.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ta ce kuma ba gudan sa kike ba har hakan ta
faru?Na ce wlh Anty Allah ya sani ban ta ba juya
masa baya ba, har matsalar nan ta shigo.Ta ce,
kuma kina gyara jikinki ba ji yayi kin zama wata
iri ba?Na soma lissafo mata abubuwan da nake
hadawa, ta ce, lallai kina kula da kanki.Na ce,
anty yanzu in yazo in fada mashi takardar don
yasan na sani?Ta ce, a a tunda kinga zarginsa
kike yi kenan baki da tabbas, ki boye takardar
kuma ko a idonki kada yaga damuwa.Ki bishi a
hankali, ki boye sirrin nan tunda uban yayanki
ne.In shaAllahu sai kiga Allah ya dawo maki dashi
kan hanya, na ce,Anty zanyi yadda kika ce, amma
zan ci gaba da bincike.Ta ce, za ki iya amma ki
sani tsananta bincike shima matsala ne, don zaki
iya ganin abinda zai saki hawan jini, na ce anty in
na tabbatar da gaskiyar zan tunkareshi ne in
nuna masa nasani.In ma zai aureta ne gara ya
aureta da zaman banzan nan, ta ce haka ne,
amma kada ki manta da adu'a, na ce insha
Allahu, ina magana cikin kuka.Ta kwantar mun da
hankali da cewa, ki daina kuka, na ce anty me
nene maganin bakin ciki?Ta ce karatun Alkur'ani
zuciyarki zata wanke sarai.Na ce, to anty na
gode.Muka yi sallama na kwanta nayi kuka sama
da minty biyar sanan na tashi na boye takardar
na ci gaba da aikina ina kuma ci gaba da
kuka.Wanan wane bala'ine Abban kausar ke son
jefa ni, ni da 'YA'YA NA?Ya manta cewa duk abin
da kayi da Dan wani kaima sai anyi da naka?Da
na koma daki sai naji komai nasa kyama yake
bani, shi kansa yanzu kyamarsa nake ji, na
karasa kwashe kayan nasa ina yi musu kallon su
kansu suna dauke da zunubin zinar da yake
yi.Tunda su Kausar suka shigo naga sun tsura
min ido ita da Al'amin shine ya soma
magana.Momy me yasameki a ido?Na ce, ba
komai, ciwo yake min.Sai naga sun kalli juna.Na
tsugunna tsakaninsu menene?Na tambaye su
tare da yin dan guntun murmushi da na kirkiro
ko nace yake.Al'amin ya ce, yaya kausar ce tace
bata so Abba yazo in yazo yayi ta saki kuka, kuma
fa ko an tambayeki sai kice ba komai shi ne nace
ai yanzu ya daina.Amma muna zuwa sai muka
sameki kinyi kuka, ku,ma muka tambayeki sai
kice ba komai.Kausar ta ce, na canka ko Al'amin?
Abban nan ni bana sonshi yanxu.Al'amin ya bata
fuska, nima bana sonshi, bakin ciki ya turnike ni,
bana son kallon da yara suke yiwa
mahaifinsu.Nace kausar ku daina cewa bakwa son
mahaifinku,bana fada muku in kunyi Sallah ku
rinka adu'a Allah ya kawo sauki cikin lamarinba?
Allah yana amsar adu'ar kananan yara, sukace
munayi sosai Momy kullum.
Ko da ya shigo kasa kallonsa nayi, ganinake zan
iya cin kwalarsa, don haka na sa kaina a daki na
rufe tare da sa sabon kuka.Ya kalli su Kausar, ina
mamanku?Al'amin ne ya ce, tana dakinta, yazo
ya buga kofar kamar kada in bude amma sai
nafasa na bude
Ya tsura min ido lafiya?Na kalleshi, me ka gani?
Ya ce, fuskarki na gani a kumbure, na taba baki
sanan na shafa fuskata.Kila baccin da nayi dazun,
ya ce wanan kumburin baiyi kama da bacci ba,
ya fi kamada wanda yayi kuka.Na mai wani irin
kallo.Don yanzu bani wani ganin girman shi, na
ce ai ban san tsawon lokacin da kuka na zai
dauka ba kafin ya tsaya.Ya ce to Allah ya kyauta,
ya juya tare da fadin to a zo a bani abinci.Sai da
na dan bata lokaci sanan naje na shirya komai na
dawo abina.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta
Littatafai masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Washe gari ya fita, sai dai duk Aliyu a dame ya
bar garin ya rasa gane kukan da Sadiya take
zabgawa, nashi ganin bai san yayi mata wani abu
ba tun zuwan shi.Rashin kulata ai ba yanzune
farko ba, to kukan na menene?Dole Akwai wani
abu, abin da yasake birkita masa lissafi yanda ko
wayarta yakira sam bata iya dagawa.Rana ta
hudu da komawarshi, ya gaji ya kira kayin Usman
ya fada masa halin da ya bar Sadiya, da kuma
rashin daga wayarsa da take yi.Yamma likis
inayiwa kausar kalaba na wanke mata kai ina
cewa sai gobe zan kaita kitso, sai ga Usman.Muka
gaisa sannan na ce, shigo falo, kausar kuma nace
suyi wasa a nan tsakar gida.Usman ya kalleni,
mijinki ya ce baki daukar wayarshi, kuma ya tafi
ya barki cikin kuka.namike naje na dauko mashi
takardar da na gani cikin kayansa.Shi kanshi
Usman kasa dago kai yayi ya dube ni, can ya ce,
lallai abin da nake zargi ya tabbata, amma don
Allah ki kara hakuri kuma in sha Allahu ko mai zai
wuce. Yanzu bari inje da takardar nan saboda
bincike, na ce yaya kayi hakuri kabar takardar
nan a hannuna saboda ta zama shaida a duk
lokacin da na masa zancen ya musa.Usman ya ce
nima da ma don hakan naso na aje ta guri na,
amma ajeta gunki, na amsa sannan mukayi
sallama.Ya kira Usman dan jin yaya?Usman ya ce
ta ce mun ba komai tana bukatar hutu ne da
dago waya, Aliyu yayi shiru, mamaki yake ji,
kuma yana ganin kamar da wani abu sun hada
bakine ita da usman.Aliyu ya ce, amma bakayi
mata fada ba, in ita ta manta cewa mijinta nake
ya kamata kai ka tuna mata. Usman ya ce, aboki
yanzu kaga aikinike, kasake kirana wani
lokacin.Ya katse wayar ba tare da ya jira amsar
Aliyu ba.Afili ya furta cewa, tabbas akwai wani
abu.
Tabayanshi Mujidat ta rungume shi.Dear wai me
ke faruwa ne?Tunda ka dawo na kasa gane
kanka.Ya kalleta cikin zargi kin sake daga wayar
matata ko?Tayi rau rau, wlh Honey ban daga ba,
ta somayi masa wadan su wassan ni tana rada
mishi a kunci me yasa ba zai mata irin son da
take yi masa ba?Ita fa zata iya mutuwa a kansa,
amma shi yafi son matarsa da ita.Ya hankadeta
tare da fadin dan Allah barni ta yaya ma zaki
hada kanki da matata?Matar sunna wacce ke
zaune don ni kadai, ta soma kuka tunda na hadu
da kai na daina hulda da kowa, nima ina zaune
nan ne dan kai daya.Aliyu ya ce, ban tabbatar da
hakan ba, tunda dana fita zaki iya fita, ta sake
dawowa ta rungume shi, na rantse bana bin
kowa kai daya nake so da kauna.Kuma bazan
daina sonka ba har na mutu.Aliyu ya zauna kan
kujera tare da rike kai, itakuma ta kwanto a
kafadar shi.Tunani take yi a zuciyarta yanda zata
ban bare ma'auratan.
Ina zaune ina danne dannen wayata, nima ina
son bude shafin nan na fcbk don ganin me
duniya take ciki?Aisha kawata da Anty Abida duk
suna ciki har Aisha tana bani labari wai da akwai
malamai sosai.In shiga nan in shiga nan dayake
ina da karanbani sai gani na bude fcbk, banyi
anfani da sunana ba ko adareshi na.Bayan kwana
biyu sai ga Aisha ta zo mun yawon Arba'n, na
nuna mata ta ce, ai na gani kin turo min sako, na
ce yau she?Ta ce duk wadan da kike da numbar
su za su gani, in kin bude, na zaro ido, har da
Abban kausar?Ta ce sosai ma, amma ba lallai ya
lura ba tunda bakiyi anfani da komai naki ba.Ta
nuna min yanda zan dinga komai, bayan tafiyarta
da dare ina kwance, na shiga fcbk nan na shiga
frnds, dinsa, mace daya na gani Mujidat.Na shiga
profile dinta hotunan da tasa nata yana daga
cikin wadan da sukayi like wani gurin ma har
yana cewa kin yi, sanan ga hotunan shi kala kala
cikin photos din ta wasu ta rubuta one an only,
wasu ta rubuta my Husband.(Tofa)
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Na tashi xaune wai ya aure ta ne? take kaina ya
sara, duk da ina cewa gara ace auranta yayi fiye
da ya neme ta sai na samu kaina cikin wani
tashin hankali mai tsanani.Na soma kiran layin Ya
Usman ba tare da na damu cewa dare ya dan
soma ba,cikin kuka nike cewa ya Usman ina ganin
fa auranta yayi bai fada mana ba. Yace,Habadai
wacece? Na karanto masa komai yace, kiyi hakuri
ki kwanta zan bincika,kada ki kara hawa fcbk
din,kurum ce masa nayi to amma muna yin
sallama dashina tura mata frnd request, cikin
sa'a ta amshe ni, da yake ita ma na ganta online.
Nace ban ga tasa marriage ba amma naga hoton
mijinta, ta ce eh za dai suyi auren ne, nace ni yar
kano ce ita fa? tace Lagos, amma yanzun tana
Illorin a gidan wanda zata aura.Kuka wiwi na
dinga yi yanzun menene abun yi? na tambayi
kaina, ta tambayeni ina da miji? sai nace mata
bama tare, tace ayya, yakamata mu daidaita.Ita
in sunyi aure bazata taba yarda su rabu da
mijinta ba don tanaji ko uwà r da tahaifeshi bata
kaita sonshi ba,ai ina gama krt na sauka daga nrt
na soma rero kuka tare da yin danasanin wannan
bin diddigin.Alwashi na sha duk randa yazo za'a
yi mai yuwuwa. Ba zan zauna ina wulankanta ba
haka kawai a debo ciwon zamani a kawo min
yarana su zama abun tausayi,na sake zama cool
ko yaushe cikin krt alkurani yana wanke min
zuciya, don haka yanzu bana daga wayarsa sai
dai in yaransa na kusa ya kira na mika ma
Kausar nace ta dauka.Ranar Kausar har tambaya
na take Mommy meyesa ba ka daga wayar Baban
ko yana mki fada ne? Nace a'ah munyi maganar
cewa yake in Kundawo zai kira ku ne,a haka
muka kwashe wata, ranar kwatsam sai gashi,
mamaki da naji banda Mama ko Al'amin bai je ya
masa oyoyo ba?nima batare da na Kalle shi ba
nace sannu da zuwa, yace Yauwa ya dubi yaran
yace Al'amin baku ganin bane, nukamun ganka
Abba sannu da zuwa.Yayi cik ba tare da ya amsa
ba ransa ya baci sosai da wannan ko in kula din
iyalanshi suka mishi,don haka ya dauri aniyar
Cima Sadiya zarafi yau dinnan, nasan dole zai yi
wannan tunanin dan haka na hada ma yara kaya
na kwana daya nace suje gidan Iya su kwana
tunda sati ne gobe, suna fita na kulle gidan na
shiga fall na kulle kaina na cire key din na nufi
daki,ya cire kaya sai gajeren wando zai shiga
wanka,nace toh Abba kausar yau fa zamuyita ta
kare a gidan nan ko ni ko kai?ya juya yana min
kallon mamaki sannan yace ke ina zaton kin soma
shan fakalin ko?nace 'eh wai don ma ba Zina
nakeyi amma ka bani kunya, ba tsoron Allah ba
kunyarshi baka tunanin darajar yayana ka aje
karuwa a gidanka Kuna fasikanci,saukar Mari naji
tau,sannan yace in ji wane makaryancin, na rike
kuncina ka mareni Akan wata 'yar iska, toh bazan
iya zama da fasiki ba ka dinga azabtar dani a kan
karuwa na warware gefen zani na ciro yar
takarda na mika mishi, ga aikenta zuwa gareni,
sannan na dauko wayata na same shi yana krt
takarda duk jikinshi yayai sanyi, nayi maza na fito
da pics dinsu da nayi saving, wannan ma karyace
ba hoton ku bane?na soma kuka ka cuce ni ka
cuci yarana haka kake nufin ayi ma Kausar?ya
daka min tsawa kina hauka ne kike ambato sunan
yata cikin wannan maganar?nace ba dadi kake
ma yar wasu?Na sake fashews da sabon kuka ka
bani takarda ta, bazan iyazama da kai ba!kina
haukane zaki ce na sake ki,toh bazan iya ba me
Zancewa Iya?nace in itace matsalar ka bazan fada
mata komai ba in baka sake ni ma zanje yanzu in
fada mata! hanklainshi yatashi ya dauki jallabiya
ya sa nikam ficewa nayi naje dakina na sure hijab
na bude Kofan falon ya rike ni kina hauka ne zaki
je ma Iya da wannan zancen?nace me zai
hana,ya kamoni na kwace nayi waje na bude
kofar gida kafin na bude ya daukoni cak,dakina
ya jefa ni kan Gado yace kina hauka ne?yace nayi
laifi kiyi hkr ki nutsu Muyi magana, nace kai ni fa
na daina Sonka kuma girmanka ya zube a gurina,
ganin zanga-zangar tayi yawa sai ya kulle ni ta
baya ya daga waya ya kira Usman yace don Allah
yana son ganinshi yanzu a gida,ina jinsu a falo
yana fada ma Usman shi bai San ina ji ba wai
duk na daga hankalinta har wai ina kwacewa ni
dole sai naje na fada ma iya.Usman yace aboki
tambaya daya zan maka kayarda kana aikata
laifin nan?yayi shiru ,Usman yace in har ka iya
amsarwa shine zai kawo karshen matsalar, yace
toh ai na fada mata cewa naji na kuma amsa
laifina don haka ta tsaya Muyi magana
taki,Usaman yace a'uzubillah, Aboki me yarude
ka ka fada wannan harka?wlh aboki kurum na
tsinci kaina a wannan halin, ka San zuciyata bata
da Kashi ga kuma sharrin shaidan, Usman yayita
masa nasiha sannan yace a jira ni na fito fuskata
suntum nace Nifa Usman na gaji ba zan zauna
ba,Usman yace yi hakuri nasan kinyi hakuri kuma
inshaAllah bazai kara ba,na kalleshi nasan zai
chigaba kawai ni gara ya aureta in son aure
suke,inkuma matan da yake bi da yawa toh ni
bazan iya zama ba.Usman ya Kalle shi gaskiya ne
Aliyu yace ita kadai ce muke tare wlh kuma itama
tsautsayi ne, Usman yace ko kayi nadama sanin
zaka koma can ku sake haduwa shi yasa ta kawo
shawara cewa taje tayi istibrai in ya so sai Kuyi
aure.Aliyu yace ina bazan auretaba ni nakuma yi
miki alkawarin cewa mun rabu da ita inshaAllah,
a gaban mu yayi waya ya kira maigadinsa yace a
fitar da Mujidat daga gidan kafin ya dawo, itama
ya kirata yace mata ya gode da wasikar da ta sa
mishi a cikin kaya don ta raba shi da matarshi
don haka maza ta bar mishi gidanshi,bai jira
takare kanta ba ya kashe dukkan phones dinsa.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ni Sam bai wani Burgeniba,suna cikin gidansuna
ta bani baki har magrib,suna fitowa nayi wanka
na sha magani nayi sallah ina zaune kan
dadduma har sai da nayi sallar Isha dama banyi
girki ba,na hau gado abuna na chigaba da kuka,
na soma barci naji ana shafa ni a wuya abunda
na jima ina kewa amma sai naji tamkar ana
shafa min kaya.Na ture hannunsa a kunne ya
rada mincewa'My choice zan zame miki sweet Aly
dini har abawa ba zan sake chanzawa ba,natashi
zaune muna kallon juna cikin ido nace yaya Sam
yanzu in ka fadi magana bana yarda matsalar
mutum ya kama karya kenan har a gane shi,na
sauka daga kan Gado naje na jingina da bango
ina kallosnshi shima ni yake kallo nace yaya ni fa
nadarmarka bata shige ni ba don nasan dole sai
Kun sake haduwa da yarinyar aurenta kawai shi
ya fi dacewa da kai,ya nufoni amma ina ce an
gama maganar nan,bazan iya auaran ta ba har
ta Haifa min yara na gari Domin ba uwa ta gari
bace,itace tayi ta bibiyata har sai da komai ya
faru kinga kuwa in na aure ta ta kuma ganin wani
shima xata iya cewa tana sonshi,ya kama
hannuna ki yafe min mukoma kamar da, Abban
Kausar na hkr amma sai Kamin rantsuwa cewa
bazaka kara aikata wannan halin ba?
Cikin sauri yace'na rantse ba zan sake ba nayi
alkawarin, nace toh shi kenan na zame hanuna
naje na kwanta sannan nace yawuce, ya Tako ya
zo ya hau gado ya kawo nizuwa jikinshi na tashi
zaune yaya kayi hakuri bazan sake iya hada
shinfida da kai ba har sai kaje kayi gwajin cutar
kanjamau!!!!! Zumbur ya mike tsaya tare da rike
kanshi Sam baiyi tunanin wani HIV ba tunda yake
tarayyada yarinyar, ya fara sintiri a tsabar
dakin,nace da baka yi tunanin haka ba ko?ya
sauke ajiyar zuciya 'ban yi wannan tunanin ba
wlh Sadiya amma bana zaton tana da shi,tunda
tsawon zamnmu ban taba ganin tayi wani ciwo
ba,nace ba a nan take na, Ance mace tana yin
shekara goma ciwon bai nuna ba,kawai kaje kayi
gwaji in ma tanashan magani a boye wa zai sani?
zufa ta rufeshi sai lumshe ido lallai kamar yana
ganin ta tana shan wasu kwayoyi har ya taba
tamabayar tace na family planning ne,fita yayi da
sauri na tashi na biyo shi ina cewa ina zaka
Abban kausa'r yace'koma asibit zanje yanzu
nan........
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
toh fa sai ku biyo ni cikin Kashi na uku don Jin ya
xata kaya shin Aliyu yana da ciwo?taku Halima K/
Mashi

Zaharaddeen shomar
Whatsapp   08168575100
adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *