Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, December 2, 2017

Tagwayen maza

adsense here
[4:33pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: Fertymerh Usman > fertymerh xarah novels
1) TAGWAYEN MAXA
Na fertymerh xarah
A hankali cikin nutsuwa ta kutsa kanta cikin
dakin, acan ta tsinkayota kishingide ta isa
gefenta ta tsugunna
tace na kammala momy duka na jera a dianing
tace kije ki sanarwa yan biyu sufito suci abinci
jikinta a sanyaye ta tashi tana fadin tor
shikenan,ta fito ta nufi sashensu duk jikinta ba
kwari
part din Hussien ta fara xuwa tayi sallama ta
shiga falonsa
acan ciki ya amsa ba tare da ya juyo ya kalletaba
tace momy tace kufito an kammala komai,
yace kingayawa hassan ne
sai da gabanta na fadi ta girgixa kanta tana
kallonsa shima ita yake kallo
2
Tace dan Allah kaje ka gayamasa ko naje baya
saurarena, ya tashi yana fadin i knw jeki kawai
xamuxo
ta juya ta fice xuciyarta wasai dama sashen
hassan ne bata qaunar xuwa a rayuwarta.
Tana mopping a falo duk suka shigo jere da juna,
kamar kullum xaka ga kayansu iri daya colour ce
kawai banbanci, komai nasu xai xama iri daya
bnda kala saboda halinsu bai xo daya ba yan'biyu
ne amma kowa da ra'ayinsa musamman a wurin
kala
tana ganinsu ta kawarda kanta gefe tana cigaba
da mopping amma dan tsabar mugunta hassan
sai da yabi ta gefenta ya taka mata qafa da
takalminsa
ta rumtse idanuwanta saboda axabar da taji ,duk
falon ba wanda ya kula da abinda yayi mata hr
yaje ya xauna, taja qafar ta cigaba da mopping
din
3
Asalin lbrn Hassan da Hussien ya'ya ne ga Alhaji
Ahmad da Hajiya Amina
shekara biyar da aurensu basu sami haihuwa ba
sai daga baya inda ta sami cikin twins,
cikin nada wata bakwai Alhaji Ahmad ya rasu
batare dayaga burinsa da farincikinsa ba
[11:29AM, 11/5/2015] Pherty: momy tayi baqin
cikin haka sosai saboda duk gatansu da arxikinsu
sun tattara sun dora akan cikin sai gashi burin
mahaifinsu bai cika ba h lokacin da aka haifesu
momy ta cigaba da kula dasu sosai tabasu
tarbiya gwargwadon iyawarta hr lokacin da suka
girma ta turasu waje karatu
Yan biyune sun taso gida daya komai daya
basuda bancin a gun ahafisu sai dai halayya da
aqidarsu ta banbanta
Hassan mutum ne daya fiye tsanda da kyankyami
musamman akan talaka ko a skul idan baka
kasance dan mai kudin gske ba baya qawance
dakai
kuma shi mutum ne miskili dabai fiye hayaniya ko
shiga mutane ba haka abu mai wuya ne kaganshi
yana murmushi ko dariya,ba qaramin abu kesashi
hakan ba,
sannan duniya bashida wani buri kamar chtng,
olways on chtng bai dauki karatunsa da daraja ba
kamar ynda ya dauki chtng,ga wata muguwar
dabi'a dayake a boye ta shaye shaye inba
hussien ba ba wanda yasani a family dinsu sai
mai aikinsu
Hussien kuma Allah yayisa a faraa da tausayi shi
kowa nasane koda yaushe fuskarsa na dauke da
murmushi illah abu daya daya bata halinsa
neman mata, shima kansa mahaifiyarsa duk
batada wannan lbr sai mai aikinsu
Amma a tsakaninsu idan gefen ibada ne ba gwani
domin basa wasa da sallah ko karatun qur'ani da
sauran littafai hrma hussien yakan xaunar da mai
aikinsu yana koya mata wani abun, amma da
hassan ne sai dai ta bushe a xaune tunda suka
dawo gida nigeria mgn bata taba hadasu ba
4
Hassalima da badan taxamo mai kula dasuba
ynda yakeji da kansa tasan bata isa ta raba inda
yake ba although dama ko kallonta baya yi basu
taba hada ido dashi ba idan ma sun hada tor yayi
shaye shayensane amma idan yana cikin
hayyacinsa ko kallon inuwarta bayayi balle yasan
da ita a wurin
a dan xaman da suke da hussien yana koya mata
karatu sai shaquwa tashiga tsakaninsu hr yafara
sonta,
tunda ya sanarda ita yana sonta ta rasa sukunin
xuciyarta cos ita bashi xuciyarta keso ba hassan
takeso amatsayinta na mai aikinsu hrtaba kanta
wani matsayi nason taxama matar hassan
hakan kesa ta xauna taci kukanta acikin dare dan
tasan mafarkinta baxai xama gsky ba momy
baxata amince ta auri ya yanta ba dan tasha jin
momy na fadin twins dinta sai ya yan masu kudi
baxasu taba kawo mata talaka a gidaba
5
Dukkansu kyawawane farare sol dasu kasancewar
sun dauko momy ne,dogaye masu matsakaicin
jiki, sunada manyan danu da dogon hanci,bakinsu
jajir kamar masu shafa jambaki, haka fuskarsu na
dauke da mans pride,suna kula dashi saboda
suna sonsa sosai gashi baqi sidik ya kwanta a
gefen fuskarsu
[11:37AM, 11/5/2015] Pherty: haka suke basuda
banbancin jiki da fata,idan ba kasansu sosai ba
baka babanta kamanninsu, illah banbanci daya
hassan yanada dimple hussien bashi da, sannan
fuskar hussien tafi ta hassan faraa, shine kawai
banbancinsu
baxasu taba sa kayan daban daban ba sai dai su
banbanta colour ko a skul ana darga dasu kafin a
ganesu sai anyi da kyar ga yan mata na
rububinsu amma hassan baya kulawa sai dai
hussien...
6
Hermyder itace mai aikinsu tana xaune a qauyen
ingawa tare da mahaifiyarta kasancewar itama
mahaifinta ya rasu tun tana qarama amma ita
tasanshi
lokacin da akaxo da ita birni a kaduna aiki tayi
mamakin yanda take qanqanuwa da ita ace duk
xatayi aikin gidan sannan ta kula da twins duk ita
kadai
sai dai ba laifi ana biyanta albashi mai tsoka
kuma matar gidan na kyautata ma mahaifiyarta
hakan yasa ta xauna
ta qudira a ranta yanda matar gidan tabata
amanar kula da ya'yan xata kula dasu ciki kuwa
hrda hanawa hussien neman mata shikuma
hassan shaye shaye
tasan xata iya tankwasa hussien tunda ko banxa
aynxu sonta yake amma hassan fa dako kallo
bata isheshi, tayama xata soma ta ina xata fara
wanda a kullum qara tsoronsa take kuma yana
qara mata kwarjini shiyasa takejin sonsa ta ko
ina
[12:40PM, 11/5/2015] Pherty: yau ma kamar
kullum misalin qarfe daya na dare ta fito daga
dakinta ta upstairs take kallon bakin gate din
tanaso taga waxai fara shigowa tsakanin su
biyun
tana nan tsaye hr kusan qarfe biyu ba alamar ko
daya daga cikinsu
hankalinta yayi matuqar tashi dan tasan basa
gidan
ta sauko a hankali kada mony taji motsinta ta
nufi sashensu
7
duk iya bincikenta basa dakinsu, jikinta hr rawa
yake ta fito harabar gidan tana xirga xirga ta
kasa kwanciya tana adduar Allah yasa lfy suke
qarfe uku da rabi mai gadi ya hangame gate din
tana xaune tana barci hasken motar na tadata ta
tashi tsaye tana bin motar da kallo hrtayi parking,
nan tagane hussien ne ya shigo
tana tsaye bata motsa daga inda take ba, hr ya
fito daga dayan bangaren wata yarinyace ta fito
ta xagayo inda yake tsaye ya riqe qugunta
gab da xai shiga sashensa ya ganta tsaye
idanunta kyam akan nasa,yana ganinta sai da
gabansa na fadi amma sai ya daure fuska yana
wani dubanta qasa qasa
yace k lfy meya hana maki barcine
da kyar idanunta sun kawo kwallah
tace ba komai
ya dubeta hr tsakiyar idanunta yaga kamar
tanaso tayi kuka sai yaji ba dadi a jikinsa amma
sai ya tabe bakinsa yaja yarinyar suka shige ya
barta nan a tsaye
8
ta bisu da kallo hr suka shige kafin taja ajiyar
xuciya ta maida kallonta bakin gate tana share
kwallah
tabbas gidan na buqatar gyara, tanaso ta gyara
rayuwarsu amma bata da hali cos sunfi qarfinta
ba huruminta bane nata shine ta kula dasu kawai
hr xata juya ta fice sai ta tuna hassan bai shigo
ba dama duk yau bata gansa ba tanaso ta gansa
ko xata sami sukuni a xuciyarta
Bai shigo gidan ba sai kusan asuba yanayin
parking dinsa kawai xai gayama a buge yake dai
dai lokacin taga budurwar hussien ta fice daga
gidan
ya fito yana tafe yana layi kamar xai fadi a qasa,
tabi bayansa tana sharar kwallah idan xai fadi
itace k tarosa hr suka iso nan falonsa inda ya
xube qasa shakaf
[12:47PM, 11/5/2015] Pherty: ta duqa ta cire
masa takalmansa batada qarfin da xata kaisa hr
daki anan ta tsallakashi ta fice ta nufi nata dakin
sai datayi sallah kana ta kwanta
9
koda ta tashi idanunta sun kumbura rashin
samun isasshen barci
da kyar ta shiga kitchen ta soma kiciniyar hada
brk fst, sai da ta dora ta fito tayi shara tafara
mopping kenan hussien ya shigo sanye da
doguwar jallabiya
kanta a qasa ba tare da ta kallesaba ta gaidashi
ya matso gareta hade da riqe mopper
yace kiyi haquri hermyder wlhy inason aure sosai,
inaso na daina wannan dabiar amma kinji momy
tace baxata mana aure ynxu ba dan Allah karki
tsaneni akanki xn cnxa xn daina tunda bakyaso
bata tankashi ba tacigaba da share hawayen
fuskarta
yace pls hermyder
[2:11PM, 11/5/2015] Pherty: ta kauda kanta gefe
ya riqo hannunta da sauri ta fisge hannunta tana
yarfewa kamar wadda taga abin kyama
tace banaso karka sake niba yar iska bace kamar
ynda kake tsammani
ya rumtse idanunsa cike da jin haushinta badan
yana sonta ba dayayi qasa qasa da ita ynxu tana
mai aikinsa xata tsaya gayamasa mgn haka
10
ya juya hannayensa sarqe a bayansa yana furxar
da iska daga bakinsa ya juya ya fice batare da ya
tankataba
haka ta yini sukuku gidan ba walwala hrta soma
jin xaxxabi kafin kace me jikinta ya dauki xafi rau
taje ta sanarda momy tana son taje asibiti bata
jin dadin jikinta
tace driver na gidan kuwa
ta girgixa kanta tana hawaye alamar ya fita
momy ta fito dayake tanada tausayi musamman
da takeson hamida saboda kirkinta da ladabi
kuma bata da qeta a rayuwarta shiyasa take
qaunarta
koda suka fito ba kowa driver baya nan
tace ko ina yaje ne
ta dubeta tace bara na dauko maki kudi kishiga
taxi kije tunda bayanan, dai dai lokacin hassan ya
fito daga sashensa cikin shirinsa na qananan
kaya yayi matuqar kyau amma fuskar nan tasa a
murtuqe
momy tace hassan fita xakayi ne
ya gyada kansa batare da ya tanka ko ya
kalletaba
tace hermyder ba lfy koxaka kaita asibitine
ya tsaya cak ya juyo yana kallonta
yace wacece hermyder kuma momy
tayi kasake tana kallonsa
tace bakasan hermyder bane mai aikin gidannan
ya yatsina fuskarsa
yace oh tor motata bata daukan masu aiki kuma
kinsani momy
tace baka ganin batada lfy ne, ciwo ai ya kauda
komai hassan ballantana ma hermyder na iya
qoqarinta akanku ka tausaya mata
yayi shiru yana naxari kafin yace tor baxata
xauna min a seat din mota ba sai idan xata
tsugunna a qasan seat din inkuma bataso
shikenan ya tabe bakinsa hade da daga
kafadunsa ya fice
momy tace ki barshi duk ynda yace ki haqura
yakaiki asibitin kinji hamida
ta gyada kai tana sharar kwallah suka nufi motar,
momy ta bude gidan gaba xata sanyata ya fito a
firgice
wait wait wait momy,ina xaki sanyata ne badai a
gaban motata ba sai dai ta xauna baya ko taje
bayan booth
momy ta saki baki tana kallonsa tace sai kace
wani dabba
[7:43PM, 11/5/2015] Pherty: ta bude mata gidan
baya ta shiga ta xauna a qasan seat tana xubar
da kwallah
da qarfi yaja motar yana tsuki sai da kanta ya
bugu, haka ya riqa sharara gudu hr suka iso
asibitin yaja wani uban birki sai da ta fadi
tana ganin ya tsaya jikinta na rawa ta fita tana
sharar kwallah, shima ya fito yana gyara space
dinsa fuskarsa a murtuqe batare da ya kalletaba
yace ki tsaya a bayana kada mutane su xata
muna tare ne, yasa kai yafice sai da yayi dan
nisa saanan tabishi a baya
lokacin da suka iso inda likitan ya dubata sosai
ba komai k damuntaba sai rashin barci da tunani
wanda ya haddasa mata ciwon kai da xaxxabi
ya dubeta yace xai mata allura
tace Dr. kabani magani kawai bana son allura
hassan na xaune yana chtng yana jinsu bai tanka
masu ba
likitan yace dole sai an hada maki da allura kiyi
haquri ba wani ciwo gareta ba
ta soma hawaye dan aduniya idan da abinda ta
tsana bai wuce alluraba
ta soma roqansa tana bashi haquri tun bata
qarasaba taji saukar mari a fuskarta ji kake
gauuuuuu sai dataga gilmawar duhu a idanunta
tayi tangal tangal xata fadi likitan yayi saurin
riqota
yace haba haba batada lfy fa rarrashine yafi
dacewa ba duka ba
yace tana batamin lokacine likita inada abinyi
yace shikenan tunda bataso xn ubuta mata
magani
hassan yace noooo sai anyita koda xata mutu sai
anmata allurar, ya kalleta idanunsa jajur karo na
farko a rayuwarsa kuma cikin hayyacinsa daya
soma hada ido da ita
cikin tsawa yace k nake jira fa
ba shiri jikinta na rawa ta gyara likitan yayi mata
allura
yaja dogon tsaki yaciro kudi ya ajiye ya fita da
sauri, itama jikinta na rawa ta biyoshi tana sharar
kwallah amma me kafin ta iso tuni ya figi
motarsa fuuuuuuuu ya fice ya barta anan
tsaye.....
26 November 2015 at 12:49 · fertymerh xarah n...
More
[4:35pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [5:16PM, 11/28/2015] pherty: 11
TAGWAYEN MAXA
Na fertymerh xarah
A hankali take tfy batare datasan inda take jefa
qafafuntaba , ga jiri datake gani saboda allurar da
aka mata,
tayi nisa cikin tfyrta kamar daga sama taji
tsayuwar motarsa a kusa da ita,
hrtayi banxa kamar baxata shiga ba sai kuma ta
bude ta shiga baya ta xauna a qasa kamar farko,
yaja motar da qarfi xuciyarsa cike da bacin rai,
suna gab da shiga gida ya tsinkayo motocin frnds
dinsu bakin gate din,
yaja wani burki sai da ta fadi taa dubesa a
tsorace shima idanu jawur yake kallonta
yace kifita pls get out kada frnds dina su
rainamin wayo,
da sauri ta fito motar jikinta na rawa shima ya
fito ya xagaya inda ta xauna da tsumma yana
gogewa yana jan tsaki duk tana tsaye tana
kallonsa cike da mamaki hrya gama ya shiga
motarsa yajata da qarfi ya fice,
lokacin da ta iso gidan duk suna harabar gidan
ganinta yasa hussien ya qaraso da sauri yana
kallonta
yace lfy hermyderh meke damunki ne? Ta soma
girgixa kanta tana sharar kwallah
tace banajin dadin jikina, ya riqo hannunta duk ya
dabirce
yace hope kinje asibiti,ta gyada kanta, duk suna
tsaye suna kallon ynda hussien ya rikice akan
village girl, hassan shima abin yayi matuqar bashi
mamaki amma sai ya boye, yaja hannunta suka
shiga ciki suka taradda momy falo sai da gabanta
ya fadi ganin yanda hussien ya riqota amma sai
ta kawarda tunanin
tace meyiwuwa yana tausaya mata ne saaboda
tana qoqarinta akansu,
tace hamiida ya jikin tace jiki da sauqi ta miqa
mata takarda magani,
Hussein ya karba jikinsa na rawa
yace bara naje na siyo mata baijira cewartaba ya
fice da sauri, abin yayi matuqar bawa
[6:12PM, 11/7/2015] Pherty: Momy mamaki,
hamida tayi shigewarta dakinta ta kwanta,
barci mai nauyi ya dauketa koda ya yadawo ya
sameta tana barci ya shafa fuskarta kawai ya
fice,
12
lokaci lokaci yake xuwa dubata bata tashiba,
momy ta kasa boye damuwarta lokacinda suke
xaune su uku a falo ta dubesa,
tace hussien na kasa ganema ko menene
damuwarka da hamida daka damu da ita haka ko
nice ke ciwo baka damuwa haka,
hassan ya tsura masa ido yana so yaji amsar da
xai bayar amma ga mamakinsu biris yayi dasu
kamar baiji ba,
tace dakai fa nake mgn, ya shagwabe fuska ya
tashi yana fadin itama ai tana kula damu so ba
laifi bane dan na kulata ya fice,
hassan ya tabe bakinsa yana kallonta
yace momy tor meye ne na damuwa tunda itace
mai kula damu, meyiwuwa yana tausayinta ne
kinsan sun shaqu fa,
tayi shiru kawai dan tasan a duniya ba yanda
xa,ayi tayima daya mgn daya bai shiga ba, basu
taba yarda daya yayi laifi ko kuma aga laifin daya
sai dai dukkansu,
tace idan hakane kai myasa bnganka ko sau daya
kayi mata sannu ba ana hakane hassan kulawarta
fa na qarqashinmu amanace agaremu itama fa
tana kula daku,
ya tashi idanunsa akan iphone dinsa,
yace noooooo momy haba dai na rasa waxanje
dubiya sai yar qauye mai aikina haba dai
momy,Allah ko asibiti dana kaita nakai xuciyata
nesa ne, bakiga nadaina hawa motar bane, hrna
tura kudin motocinmu amana odar wasu nida
hussien,
tayi kasake tana kallonsa,
tace dadina dakai hassan bakason talaka shiyasa
nake burin naga irin matar da xaka aura ko yar
gidan wacece amma saboda hamida bai kamata
ka ajiye motar kaba yarinyar tana da tsabta gata
kuma kyakkyawa,
ba tare da yayi mgn ba ya fice warsa, tayi shiru
kawai tana naxarinsu.
[6:18PM, 11/7/2015] Pherty: Kwana biyu tsakani
ta soma samun sauqi, tana samun kulawa daga
momy da hussien, ganin ta dan murmure yasa
taje inda momy kan cewa tana so taje ingawa ta
gaida mahaifiyarta kusan wata shidda rabon da
taje,
13
momy tace kiyi haquri hamida hr wani watan idan
yan biyu sunje cameron ynxu idan kinje waxai
kulamin dasu,
tayi shiru kamar bataso haka ba
tace shikenan ta tashi ta fita kamar xatayi kuka,
garden ta nufa tasami wuri ta rakube tana
kallonsa, shi wannan kullum baya gajiya da chtng
olways akan waya daga gefensa whisky ce a ajiye
ta qarasa inda yake ta xauna tana fuskantarsa ba
alamar tsoro a tare da ita, kusan minti goma da
xamanta idanunsa akan wayarsa amma kamar
baisan da xamanta wurinba a xuciyarsa yana
mamakin wannan yarinya dakeson takura
rayuwarsa lokaci da yawa takan shiga harkarsa
yana basarwa.....
muryarta na katse tunaninsa,
tace Allah ya haramta shan...... Ya katseta da
manyan idanuwansa batare da yayi mgn ba,
ya salam ta furta a xuciyarta saboda kyawunsa
ta dan matsa baya,
tace kayi haquri baxan sake ba, idanunsa jawur
yace k wacece k talaka k banxa hr kin isa
kigayamin abinda yafi dacewa dani,
ta girgixa kanta kuskure ne nadaina, yaja dogon
tsaki ya tashi yana hura iska a bakinsa ya fice ta
bishi da kallo kawai, ta san yafi qarfinta nesa ba
kusa ba amma hrga Allah tana jin sonsa kamar
mutuwarta, tana jinsa fiye da hussien duk da
hussien yafisa kirki da tausayi da son talakawa.
A daren ranar misalin sha biyu na dare ya shigo
gidan ya fito daga motarsa yana tafe yana
tangadi, da sauri ta sauko ta nufi sashensu
lokacin hrya shige part dinsa, koda ta shiga ta
samesa yanata kwarara amai ta qaraso da sauri
ta dafashi tana masa sannu, sai da yagama tayi
qoqarin gyara wurin amma sai me gani tayi ya
jawota xuwa jikinsa yana qoqarin rungumarta,
tabbas tasan baya cikin hayyacinsa dan yanda
hassan k kyamarta ba ynda xaayi ya taba jikinta,
sai ta soma kiciniyar kwace jikinta suka soma
kokuwa da kyar tasamu ta kwaci jikinta ta tashi
jikinta na kyarma duk a tsorace take ta juya xata
fice tsantsin amai na jata shuuuuuuu ta fadi
ragwaf,
qararta yayi daidai da shigowar hussien gidan da
sauri ya fito motarsa ya nufi part din hassan inda
yajiyo qarar, yanda ya ganta yayi matuqar tsorata
ga hassan daga gefe a yashe ya taba ta ba
alamar numfashi a tare da ita sai ya dauketa cak
ya fita da ita kai tsaye asibiti ya nufa da ita
[6:26PM, 11/7/2015] Pherty: Sai da ya tabbatar
an bata gado kana ya dawo gida yaje ya sanar da
momy,
ta tashi a firgice,
tace bn fahimceka ba hussien acikin wannan
daren mai yakai hamida dakin hassan, (dama
baxasu taba tona asirin junansuba koda xaa
kashesu koda yaushe cikin rufar asirin juna suke
shiyasa ko mahaifiyarda ta haifesu batasan
cikinsu ba)
14
yacee hassan ne ba lfy yayi amai ya kiratane ta
gyara sai tsantsi yajata ta fadi,
tace subhannallah hassan ba lfy ta sauko da
sauri xataje sashensa yayi qoqarin hanata,
yace momy hassan yasami barci kada ki tadasa
kixo muje asibiti kiga hamida fuskarta duk ta
kumbura, ba dan tasoba ta shiga motar sukaje...,
washe gari da hussien yaxo karban brkfst yasami
hassan xaune yanata faman chttng,
yace amma fa bakada kirki bakaji kowa a gidanba
bayan masu aiki amma baka nemi sanin inda
muke ba, ya tashi idanunsa a wayarsa
yace tor menene damuwata da sanin inda kuke
nima ynxu natashi daga barci fa,
hussien yace hamida ce ba lfy tana asibiti, yaja
dogon tsaki na dauka wata mgn mai muhimmanci
ce ynxu saboda yar aiki bata da lfy kuka damar
da kanku haka,
hussien yace saboda kaine fa hassan yakamata
ka riqa tausayinta mana(sai ya gayamasa
komai)ya qara da cewa ni wlhy ita xn aura kome
momy xatayi sai dai tayi amma talakar nakeso
kuma xn aura,
hassan dai baice uffan ba ya tashi ya fita hussien
yabi bayansa suka nufi asibiti.
Lokacin da suka isa asibitin yanda ya sameta yaji
tausayinta sosai karo na farko a rayuwarsa hr ya
kasa boyewa fuskarsa ta nuna damuwa sosai
koba komai yarinyar na qoqari akansa kuma bata
taba yunqurin tona masa asiri gun mahaifiyarsa
ba, bayanin da hussien ya masa na sanadinsa ta
sami wannan rauni a fuskarta yasa yaji matuqar
tausayinta.
Duk sukayi shiru hr lokacin bata farfadoba, momy
na kallon yanayinsu alamar xaratan maxanta na
cikin damuwa tor menene abin damuwa tunda yar
aikice ba wani gata takeda ba, meyasa
tagwayenta xasu riqa damar da kallonsu,
tace hassan, hussien meke damunku ne sai
faman xagayen dakin kuke kamar nice ba lfy,
hassan yayi murmushin da dimple dinsa ya lotsa
kyawunsa ya qara fitowa,
yace momy hamida ce damuwar mu ai ranar kin
gayamin na riqa tausayinta tunda tana qoqari
akan mu shiyasa muke damuwa akanta ynxu,
hussien ma murmushi yayi (itadai tasan
mahaifiyarsu ce amma baxata banbancee wanda
yafi kyau acikinsu ko hasken fatar jikinsu dayace
farare sol banbancinsu dayane dimple din hassan
wanda ko yayi murmushi ko baiyiba akwai sign
dinsa ko mgn yake wurin na lotsawa) ni momy ba
wannan ne damuwata ba ni sonta nake so nake
ki auramin ita,,,,
kyam ta tashi a firgice jikinta hr bari yake
tace wakake sone hussien?
Yace hermyderh momy,
karo na farko a rayuwarta tun haihuwarsu da ta
dora hannun akansu ji kake gau ta dauke shi da
mari,
tsananin mamaki yasa duk suka xuba mata idanu
dai dai lokacin hamida na farfado,
tace qarya kake hussien baka isa ka auri yar
talakka ba mai aikin gidana idan ma mafarki kake
ka farka, hassan ya qaraso yana yatsina fuskarsa
yace joke apart momy Allah dan wannan tausayin
nata danaji hr naji nima ina sont........,
bai qarasa ba shima ta daukeshi da mari, hussien
ya juya yana kallon hassan cike da mamaki ido a
waje.
Hausa novel
[5:18PM, 11/28/2015] pherty: [7:43PM,
11/8/2015] Pherty: 15 TAGWAYEN MAXA
Na fertymerh xarah
Hermyderh dake kwance tana saurarensu ta
sauko daga saman gado duk hankalinta a tashe
abinda bata taba xato ba hussien
yace me nakeji kake fada ne hassan,
yace abinda kunnuwanka yajiyo ma, idanun
hussien na kada nayi jajur
yace qarya kake hassan, hamyderh baxata so
kaba ni take so ba kaiba, kaida ke cutuwarta kana
muxguna mata, duk bakinda ya furta qi ko ya
dawo ya furta so qaryane dan haka soyayyarka
qaryace, momy ta soma salallami (tun tasowarsu
musu ko gardama bai taba hadasu ba ballantana
fada sai gashi yau xaratan maxanta na fada akan
macce maccenma talaka yar aikinta) hassan ya
soma yatsina fuskarsa
yace tor meye ne abin damuwa tunda ynxu nace
inaso kuma xan aureta(ya kalli momy)hermyderh
nada kyau tana da kyau halayya, ta iya kula da
namiji kuma ta iya boye sirrin kanta dana wani
saboda haka nake sonta domin itace macce
tagari tafi duk wata diyar mai kudi da kike so na
aura,ni momy inason hamyda koda kasheni xakiyi
ina sonta ya juya ya fice, hussien hr ya buda baki
xaiyi magana sai kuma ya fasa saboda bacin rai
ya juya yabi bayan hassan
[8:03PM, 11/8/2015] Pherty:
Momy iya rudewa da tashin hankali ta shigeshi ta
juyo tana kallon hamida dake kuka cikin tsawa
tayo kanta,
qarya kike munafuka baxaki auri ko daya daga
cikin ya,yana ma idan ma mafarki kike ki farga
idan kuma kin asircemin yarane tor wlhy kisaki
kurwarsu kona qasqantaki dakeda qaxamar
mahaifiyarki,
hankalin hamida na tashi ta soma kuka sosai
tana bata haquri kada ta taba mahaifiyarta, momy
tasa qafa ta shurata can gefe cike da bacin rai
tace ada ina sonki ina tausayinki saboda kina
kulamin da yan biyu ashe bnsaniba kinbi kin
asircesu tor wlhy kije ki warware wannan abin
kona halaki kwana uku rak na baki kuma daga
nan karki koma gidana kije qauyenku xnxo na
sameki, ta xaro idanu waje tana kallnta
tace haba momy...., rufamin baki kona tattakaki
anan, kifita rayuwata da tagwayena daga yau, ta
finciki jakarta ta juya a xuciye tabarta nan a
durqushe tana kuka
[8:05PM, 11/8/2015] Pherty: Lokacin da yan biyu
na fita kowa barikinsa ya nufa cike da bacin rai,
17
hassan gun shaye shayensa shikuma hussien gun
yan matansa, ranar hr kusan dare basu dawo
gidan ba hankalin momy ya tashi matuqa amma
tana jin tsayuwar motarsu batare da ta duba
halin da suke cikiba tayi shigewarta dakinta,
kusan kwana biyu batasa su a ido ba duk ynda
xatayi tagansu basa bari duk fushi suke da ita
aganinsu bata sonsu tunda bata son abinda suke
so shiyasa suka qauracemata , a wata safiya
tana xaune a falo cike da damuwa suka shigo
kowane fuskarsa ba walwala, suna sanye da
shadda milk, banbancin dinkinsu kalar xaren da
aka masu aiki dashi, sunyi matuqar kyau ga
gashin kansu ya kwanta sosai, mans pride dinsu
sai sheqi yake, ta tsura masu ido tana kallonsu,
basu taba mata kyau irin na yau ba, yara kamar
aljannu, sai ta daure fuskarta ta dauke kanta
daga kallonsu, hussien yafara gaidata kafin
hassan, amma ba wanda ta amsa,
lokaci daya suka kalli juna suka tabe bakinsu
suna yatsina fuskarsu(dama hassan bai iya boye
damuwarsa ba komai direct yakeyinsa)
yace momy mun shirya xamuje ingawa inda
hamida munaso cikinmu ta xabi wanda take
so,sai kibamu address dinta,
sai taji mgnr banbarakwai wai qarfin hali hr
kusan faduwa tayi wai yau hassan ke mata mgnr
xaije qauye kuma neman wata talakka, ta dubesu
da kyau suna tsaye suna kallonta ko kadan
hamida bata tako qafar yan tagwayen maxan
taba sunfi qarfinta nesa ba kusa ba kuma ta
kowanne fanni, ynxu su a hakan xasuje ta xabi
daya daga cikinsu chab,
hassan ya katseta momy we ar waiting kinyi
shiru ko baxaki bamu bane, ta gyada kanta
batare da tayi magana ba ta tashi tabar masu
falon, suka fito ransu a bace amma sun qudira a
ransu xasuje , suna tsaye suna shawara uncle
dinsu ya shigo suka gaidashi, yace yan biyu
kyautar Allah ina xakuje haka , hussien yace
xamuje ingawa duba hamida ba lfy,
yace hamida ba lfy ankaita gidansu ne, yace eh,
uncle ko kanada address dintane, yace eh xn tuna
lokacin da mukaje daukota nida mahaifiyarku(sai
yabasu address)
[8:06PM, 11/8/2015] Pherty: Yace idan kukaje kun
kyauta kuwa, suka soma murmushi, yace kunyi
kyau TAGWAYEN MAXA, yakamata insami wannan
kwalliyar saboda tarihi, hassan ya ciro wayarsa
yana fadin uncle karka damu tunda ka
taimakamana muma xamu baka pic dinmu
[8:08PM, 11/8/2015] Pherty: 18
Hassan ya gyara space dinsa hade da daga
wayar sama, hussien ya matso kadan kusa dashi
hannunsa akan space dinsa hassan ya dauki pic
din,kuma yayi kyau sosai suka tura masa a
wayarsa ya shiga gidan yana murmushi sukuma
suka shiga motarsu hussien yajasu.
Lokacin da suka iso ingawa sun dan sha wahala
kafin su sami gidansu, suna tsaye bakin garkar
gidansu sun harde hannuwansu a qirjinsu
idanunsu boye a space suna jiran fitowarta dan
sun aika yaro ya kirata, ita kuma acikin gida
hankalinta a tashe yake dan batada wani saurayi
a unguwar daxai xo nemanta,
ummanta tace kije kigani mana kin tabayi yaron
ko waye, ta girgixa kanta alamar a,ah ,ta sanya
hijab dinta ta fita,
lokacin data fito idanunta na sauka akansu sai da
tayi tuntube saboda firgita da wani kwarjini da
suka mata lokaci daya duka su uku xuciyarsu na
buga, tana tsaye tana kallon TAGWAYEN MAXA
daya bayan daya ta kasa qarasawa suma suna
tsaye sun xubamata narkakkun idanunsu masu
rikitarwa wadanda nasata dabircewa
Hausa novel
28 November 2015 at 17:34 · fertym
[4:35pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [5:06PM, 11/30/2015] pherty: 19 TAGWAYEN
MAXA
Na fertymerh xarah
cikin nutsuwa ta taka inda suke tsaye amma ta
kasa furta kalma ko daya daga garesu, hussien
ya xare madubin idanuwansa yana kallonta
yace hamida gidanku haka aka koya maki tarban
baqi ne, sai tayi far da idonta cike da jin kunya ta
dan sunkuya tana gaidasu, hussien kawai ya
amsa hassan na tsaye ya sarqe hannuwansa
yana kallonta sai yau ya taba tsayawa ya kalleta
da kyau, abinda ya fahimta daga gareta batada
tsayi sosai haka kuma ita ba fara bace ba baqa
bace chocolate colour ce (kala mai tsada) tafisu
manyan idanuwa da gashin ido, hancinta dogone
siriri bakamar nasu ba yafi nata tsayi, ya kai
dubansa ga qafafunta(duk idanunsa a boye cikin
glass yake mata wannan kallon) ta gefen ido take
kallonsa gaba ki daya ya tafi da hankalinta
hrtakeji aranta inama hassan xai xama nata hr
tsawon rayuwarta da babu maccen da takaita
sa,ar miji a duniya(aikam naga xarah dange ma
ta kyasa) cikin siririyar muryarta dana sarqe
tace ko xaku shiga gidane umma na ciki, hassan
ya yatsina fuskarsa bayan yacire madubin
idanunsa yana kallon gidan, ginin laka ne, ya
girgixa kansa noooooo baxamu shiga ba, sai idan
ita xata fito, hamida ta saki baki tana kallonsa
tace ita umman tawa, ya gyada kansa
yace ba gunta mukaxo ba inda kike mukaxo ki
xabi daya daga cikin, chab iya bacin rai ranta ya
baci ita mahaifiyar tata datake gani a duniya
batada kamarta, kowane irin so take wa mutum
baxata lamunci a wulaqanta mata mahaifiya ba,
karo na farko da ta soma yi masa wani kallo mai
cike da mamaki
[6:58PM, 11/10/2015] Pherty: Tace bana son ko
dayan ku kuma baxan xaba, hussien ya matso
gareta
yace hrdani hermyderh kimin adalci mana menayi
maki, ta yatsina fuska tana kallon hassan daya
matso shima kyam idanunsa akanta baisan
meyasa baya gajiya da kallontaba, idan ma kyau
ne ai baxata fishi kyau ba amma yarasa meyasa
yake son kallonta,
tace saboda halayyarku bana son ko daya, baxan
auri maxinaci ko mashayin giya ba,(lokaci daya
hassan da hussien suka kalli juna) tacigaba da
fadin
20
ina maku nasiha bama kudai ba daduk masu
aikata wani xunubi daya haramta kuji tsoron Allah
ku sani shi yafi cancanta da aji tsoronsa fiye da
kowa da komai, kuyi roqo da abinda ma,aiki ya
umurceku dashi ku hanu akan abinda ya haneku
da shi idan muka xamo haka xamu kasance masu
nutsuwa da samun ingantacciyar rayuwa,
(Allah ya gafarta mana dukkan xunubinmu
saboda albarkar manxon Allah, Amin)
[7:04PM, 11/10/2015] Pherty: Hassan da hussien
suka tsura mata ido ba qaramin birgesu tayi ba
kuma ba komai suke sauraro daga gareta ba illah
xaxxaqar muryarta,
21
hermyderh ta tsargu da kallon da suke mata sai
ta dan matsa daga baya ta sauke kanta qasa
tana fadin lokaci bai qure ba xaku iya gyara
rayuwarku xn kuma xabi daya na aura acikinku
matuqar xaku tuba saboda manxon Allah s.a.w
yacewa
Allah s.w.t yace yakai dan adam haqiqa matuqar
xaka roqeni kuma ka qaunace ni to xan gafarta
maka abinda ke kanka na xunubi, kuma ban
damu ba,
ya kai dan adam da dai xunubinka xai tabo sama
sannan sai ka nemi gafarata to xan gafartamaka,
yakai dan adam haqiqa da xaka xo min da xunubi
cikin duniyarnan sannan ka hadu dani ba tare da
kayi shirka dani ba, tor xn xoma ka da cikinta na
gafara.
(makarantana kunemi gafara olways Allah xai
yafe maku idan baka aikata shirka ba kuce
ASTAGAFIRULLAH pls) tayi shiru tana kallonsu,ga
mamakinta sai taga hassan ya miqo mata baqar
leda shima hussien ya miqa mata tashi
yace wannan wayatace bn yrda ki kira wani ko
akiraki da wayata ba, tawace nikadai xn kiraki da
ita,
hassan ma ya yatsina fuskarsa yace nima haka
wayata bn yarda ko dan uwana ki kira da itaba
kowa ki masa amfani da tasa, tayi xuru tana
kallonsu cike da mamaki
tace baxan karbi wayarku ba bana so ku kanku
bana so idan baxaku gyara halinkuba(tor fa
hamida su tagwayen ne bakyaso ga xarah dange
na neman daya ruwa a jallo)
lokaci daya suka ajiye mata ledar agabanta
batare da sun damu da kalamanta ba, ga jamaa
an taru yara da manya sai kallonsu suke suna
yaba kyawun tagwayen maxa, sun rasa gane
wane jinsi ne wadannan yara kamar aljannu, su
mamaki ma suke me sukaxo yi inda hamida
baqar fata kuma talakka,hassan ya maida space
dinsa yana furxarda iska daga bakinsa ya tabe
bakinsa hade da daga kafadunsa alamar kota
xabeshi ko kada ta xabeshi ko ajikinsa dan baxai
bar giyar ba ya juya ya nufi motarsu,
hamida ta bisa da ido tana kallonsa bataji dadin
ynda ya nuna ba ita tanaso ya shiryu ya daina
taji kamar ta kirasa ya dawo dan wlhy tanajin
sonsa kamar me, tana kallo ya shiga motar yana
jiran hussien,
shima kamar yanda hassan yayi haka ya juya ya
fice batare da yayi magana ba tana tsaye taga
sunja motar da qarfi sun bar wurin batare da sun
sake waiwayentaba,
kada dai sunyi fushine suka barta nan da nan
hankalinta na tashi hawaye na soma xubo mata,
ganin kallo ya dawo gareta yasa ta sunkuya ta
dauki kayan ta shige cikin gida......,
ku biyoni mubi yan biyu kyautar Allah, muji anya
TAGWAYEN MAXA xasu bar abinda suke su shiryu
saboda hamida?
Idan suka gyara halayansu dukansu waye xata
xaba?
Hausa novel
[5:12PM, 11/30/2015] pherty: [11:10AM,
11/12/2015] Pherty: 22 TAGWAYEN MAXA
Na fertymerh xarah
Tunda ta shigo gidan take kuka sosai, umma ta
taso tana tmbyrta lfy, da kyar tayi mata bayanin
komai
umma tayi shiru tana saurarenta kawai.........
momy sai faman xirga xirga take a tsakiyan falo
ranta duk a bace ta rasa xaman tun fitarsu hr
uncle dinsu yaxo ya fita bai fahimci komai ba
tana nan tsaye suka shigo a tare hussien ne ya
gaidata hassan kuwa dauke kansa yayi yana
kallon dianing, ta bisa da kallo kafin ta maida
kallonta ga hussien
tace kardai kunje ingawa ne hussien inda waccan
banxar
hassan ya juyo yana kallonta
nooooo momy kidaina kiranta banxa mana
surukar kice fa, meyasa kike hakane?
ta saki baki tana kallonsa cike da mamaki
surukata kace as n how? ban fahimceka ba
ya dubi hussien kafin ya soma kiciniyar cire rigar
jikinsa yana fadin
aurenta xamuyi nida hussien, bakiga munje
neman auren bane
tor waye ta xaba ne?
ya yatsina fuskarsa ya xauna, hussien yace
momy hamida bata xabi ko daya acikinmu but
am sure ni xata xaba danni naji mgnrta xn daina
abinda nakeyi
momy tace hr wani abu kukeyine da bataso
menene shi bansanshi ba?
hassan yayi caraf yace noo ummma kibar wannan
sirrin mune mu kadai ba wnda yasan da shi sai
ita hamida
momy tace hrdani mahaifiyar taku, hr akwai
abinda xaku boyemin amma wata can mai aiki
tasan sirrinku bndani,
ya yatsina fuskarsa ya matso ya kara mata
rigarsa a hancinta
yace momy kiji yanda qauyen k wani wari duk ya
batamin jikina baxan iya cin abinciba sai nayi
wanka na cnxa kaya, duka mutanen ingawa "they
ar not wise they ar ol villagers",inbanda haka
meye nasu na xuwa kallonmu nida hussien,ko
bamuyi kyau bane ko akwai wani sabon abu a
jikinmune (ya fada yana yarfe hannuwansa cikin
yatsina fuska)
baqincikiduk ya taru ya cunkushe mata xuciya ta
juya ta fice a fusace tare da alqawarin sai taga
bayan hamida baxata bar gwarxayen maxajenta
su qare rayuwarsu akan yar aikinta ba
[11:34AM, 11/12/2015] Pherty: hussien yace gobe
xamuje ne,inaso na qara ganinta xn gayamata na
daina neman mata
hassan ya tsare sa da narkakkun idanuwansa
kafin yace
impossible hussien baxa muje gobe ba sai nxt
tym kuma baxan daina ba saboda mace haba dai
macece fa Allah baxan bari ba kuma baxata xabe
kaba, ina ga dama sai na canxata u knw inada
bula bula yan mata kawai they ar not my choice
ne, inason mace mai ilimi, mai iya kula da miji da
boye sirrinsa saboda hakanne kawai nakeson
hamidan kaima ksan ba ajina bace ko turanci ta
iyane?
23
Hussien yaja tsaki
tunda ba ajinka bace kabarmin ita mana dama ni
takeso bakai ba
hassan ya lashi jajjayen labbansa yana kallon
hussien yana dan wani naxari kafin yayi
murmushin da dimple dinsa na bayyana
yace tor shikenan na barma, x not bad kuma ba
abin baqin ciki bane, nida kai duk dayane,
hussien ya dora yatsansa akan dimple din hassan
wurin ya lotsa da hannunsa(yana son dimple din
hassan da yawa yakan tsaya yayita kallonsa idan
yana mgn yanda wurin k lotsaya ko yana cin
abinci, shine kawai banbancinsu dama)
yace dan uwana baxai bar abinda yakeso saboda
niba, nima baxan barta saboda kaiba allura ce
acikin ruwa nidakai xamu gwada sa'a aga wanda
xai cirota
hassan yayi murmushi kawai ya janye hannunsa
daga fuskarsa idan da sabo ya saba da hussien
wurin taba masa dimple, ya juya ya fice batare da
yayi magana ba.
[11:59AM, 11/12/2015] Pherty: *
Tun daga lokacinduk bayan sati sai sunje ingawa
inda hamida tun tana kaucewa tana masu
wulaqanci hr ta fara sakin jiki dasu tana ganin
hakan shi xaisa su daina abinda suke idan suka
saba da ita,
wataran ma hr cikin garin suke xagayawa
mutanen garin na biye dasu suna kallon fararen
mutane
hassan da hussien sun soma jin dadin qauye duk
da hassan bai ida sakin jikinsa ba still yana
qyanqyamin qauyen kuma baya boye w damashi
direct yake komai nasa,
ban manta akwai wani lokaci da suka xo hamida
ta tursasa masu akan sai sun shiga sun gaida
ummanta
kai tsaye hussien ya shiga, hassan kuwa tun
bakin qofar shiga gidan suka soma rigima dashi
akan lallai shi baxai shiga gidnba idan hr sai ya
sunkuya, danme xa'ayi qofa qarama ace sai
mutum ya sunkuya gidan xai shiga
hussien ya juyo yana kallonsa
yace control ur mouth,
hassan yace idan dole ne sai na shiga ka kira
wadannan builders din suxo su qarawa qofar
tsayi inshiga saboda ni mai tsayi ne ba gajare
bane,
hussien ya girgixa kansa kawai cikin mamakin
hali irin na hassan ya shige cikin gidan
hamida ta kallesa idanunta sunyi rau rau kamar
xatayi kuka itadai tana son hassan kome yayi
yana burgeta
tace ahakan kakesona, ahakan xakaxo neman
aurena kana kyamar gidanmu kana gudun
gidanmu,tor waye xai baka aurena kana
wulaqanta arxikinmu, tafashe da kuka ta juya
xata fice xata shige yayi saurin riqo hannunta
sai da yaji wani shock karo na farko a rayuwarsa
da jikinsa ya soma haduwa dana mace yana cikin
hayyacinsa, sai yaji wani iri banbarakwai ya saki
hannunta da sauri yana yarfe hannuwansa
ita kuma idanu ta tsura masa cike da mamakin
lashin hannunsa duk da ita agareta bana farko
bane tunda ta saba riqosa ta kawosa dakinsa
idan ya sha amma yau taji wani daban
batare da yayi mgn ba ya sunkuya ya shiga
kamar xaiyi kuka gani yake an raina tsayinsa
bdan hamida ba baiga wanda ya isa yasashi
duqawa ba
ya sami hussien da umma xaune a tabarma suna
hira kamar sun saba can(baisan umma a tsorace
take da hussien ba kyaunsa ya rudata take ganin
ba mutum bane dan dai hamida tace mutanene
shiyasa ta xauna suna gaisawa amma jikinta hr
kyarma yakeyi)
ganin hassan ya shigo gidan yasa ta xabura daga
xaman takurar da take tajuya tana kallonsu daya
bayan daya ita bataga banbancinsuba ko hasken
fatarsu dayane komai na fuskarsu hr jikinsu da
tsayinsu duk dayane hakan yasata tsorata take
tunanin kodai tayi gamo da aljanine yake mata
gixo da fuska biyu tunda ga kayan jikinsuma iri
daya (wannan karonma hr kallar kayansu iri
dayane) sai ta saki ihu ta shige quryar daki a
tsorace tana karanta amanar rasulu a bayyane
cikin dagawr murya
[12:18PM, 11/12/2015] Pherty: hussien yasan ta
tsoratane da ganinsu sai ya soma dariya hrda
taba hannayensa
24
shikuma hassan sai yatsina fuska yake dama
tunda ya shigo gidan yaga yanda yakee ya koma
da sauri hamida ta maidoshi, kusan sau uku yana
shigowa yana fita hamida na maidoshi da kyar ta
samu ya qaraso ciki tor gashi tsohuwar ta qara
bashi haushi ta maidashi wani dodo tana ganinsa
xata wani shige daki tana addua
da kyar hamida taje ta lallaso umma ta fito da ita
suka gaisaa tsatsaye da hassan
yace noooo hamida am sorry amma i cant live in
dis environment, hussien a juya yana kallon gidan
baiga wani abin qaxantaba ko ina tsaf tsaf kafin
yayi mgn tuni hassan ya juya ya fice yana isowa
qofar gidan ya manta da sai ya sunkuya yasa kai
ji kake goshinsa ya buga wurin gauuuuuuu ya
saki qara hannunsa a goshinsa suka fito suka
samesa yana ludda wurin oh gosh, chaiii..... Allah
baxan qara shiga wannan gidanba idan bxaa
qarama qofar tsayi ba, ya duqa ya fice a harxuqe.
Hamida tafito tare da hussien ta rakasu suka
dauko kyautarsu da sukaxo da ita takalmine
masu kyau komai iri daya banbancin kalace kawai
dama haka suke mata kyauta duk abinda xasu
bata iri dayane sai dai su banbanta kala, idan
sarqace iri dayace sai dai dayan tanada digon
baqi wata digon ja ko wata kala, idan atampha ce
xane iri daya banda kala, lace, englishi wears
e.t.c duk iri daya suke bata kuma lokaci daya, su
basu yarda suyi hassadar junansuba basu son
cikinsu ace wani yafi wani sunfiso ace dai dai
suke, komai xasuyi sai sun shawarci juna .
da hakan sukayi sallama suka fice, taje ta samu
umma suka soma tattauna xancen
*
Akwai wni lokaci sun dawo daga xaga garin suna
tare su uku suna hira gab da xasu iso gidan
hamida taja ta tsaye idanu a waje
duk suk dubeta alamar tambaya da hannu ta
nuna masu gidansu
momy suka gani tsaye tare da wasu gardawan
maxa ana rushe masu gida
nan da nan hamida na soma hawaye suka qarasa
wurin umma na daga gefe tana kuka hamida
tabungumeta
momy kallo daya tayiwa yan biyu ta dauke
dubanta garesu
hussien yayi qoqarin hanata
[12:32PM, 11/12/2015] Pherty: hasan ya riqosa
yace noo bros, cool ur mind, kabar momy tayi
abinda takeso ko xata sami rest of mind,
mahaifiyar muce idan wannan abin xai sata farin
ciki kabarta tayi taji sanyi a ranta
hussien yayi shiru lokaci daya suka sa dark space
dinsu suka sarqe hannuwansu a qirjinsu hade da
jinginawa jikin motarsu suna kallonsu
sai da momy tasa akayiwa gidan kaca kaca aka
rushe komai sannan ta shiga motarta mutanenta
na bayanta suka bar garin ingawa
hussien yaciro wayarsa ya matsa daga gefe
shima hassan haka yayi
suna tsaye suna kallon yndasu hamida ke kuka hr
ma'aikatan da suka kira suka iso kusan kashi
biyu kowa ya kira nasane
hussien yace tor duk su hada hannu suyi aikin
tare shi yayi masu bayanin yanda yakesonbgidan
kafin ya juya yana kallon umma
yace umma kuje maqota ku xauna hrna wasu
kwanaki kafin agama ginin
umma ta shiga wani gida tana hawaye
hassan sai kallon hamida yake tana sharar
kwalla, abin nan dayaji ranar daya riqa hannuta
shi yakeson ya qaraji idan ya riqa hannunta , bai
tabajin irin wannan abinba shiyasa yakeso ya
qara taba hannu yaji ko xaiji,
sai ya juya yana kallon hussien da hankalinsa na
gun aikin da ake, ya nufi inda hermyderh k tsaye
yana wani yatsina fuskarsa.
Hausa novel
[5:15PM, 11/30/2015] pherty: [3:40PM,
11/14/2015] pherty: 25 TAGWAYEN MAXA
Na fertymerh xarah
Yana isowa dab da ita sai kuma yaja ya tsaya
yana jin nauyin tabata abinda bai saba yiba, ta
share hawayen ta tana kallonsa
sai ya dauke kansa yana kallon wani gun, still
shaidan na qara tunxurasa ya tabata ko xaiji
wannan abin dayaji
dayake komai direct yakeyinsa sai kawai ya riqo
hannunta itama tabisa da kallon mamaki
mtsew yaja dogon tsaki yana fadin banji komai ba
fa, ya saketa yana yatsina fuska
bata gane meyake nufi ba illah kallon mamaki
datake masa
a xuciyarsa yace kodan wancan karon nina bata
mata raine tunda yanxu momy ce tasata
kuka,kenan idan momy ta tabata xataji wannan
shock din
tor shi ynxu mema xai mata ya bata mata rai
yatabata ko xaiji
hussien ya qaraso yana fadin nagaji muje gida,
hamida kishiga gidan da umma ta shiga hr gobe
idan mun dawo,
a sanyaye ta gyada kanta tana kallonsu suka
shiga motarsu suka fice
[4:54PM, 11/14/2015] pherty: tym din da suka iso
gidan kamar momy na jiransu ne ta soma balbale
su da masifa, fada take ba kakkautawa abinda
basu taba ganiba sai suka harde hannuwansu
suna daga tsaye suna kallonta hr tagama
hussien yace kiyi haquri momy mundaina tunda
bakyaso, baxamu sake xuwa guntaba kuma
munjaye mgnr mu ta neman auren hamida amma
momy Annabi mohd s.a.w yace wanda bai jinqan
mutane Allah baxai yi jiqansaba mussaman
talakawa
hassan ya janye hannuwansa yana kallonta
yace kin mantane momy Annabi mohd s.a.w yace
wanda ya tausayawa mutum koda dabbobi ne
Allah xaiji qansa a ranar tsayuwa, c'mon momy
bnga abin fada anan ba bnga dalilinki na son
wargaxa rayuwarsu ba idan mune bakyaso da
hamida shikenan mun barta , ya juya ya fice
hussien ma yabi bayansa.
Bayan kwana biyu momy na xaune da xuqa
xuqan yan mata ya'yan abokantane su ta xabawa
yan tagwayenta ko wacce ba laifi tana da irin
nata kyau kuma sunaji da kudi
yan biyu suka shigo falon suna tafe suna dariya
kamar basuda wata matsala a xuciyarsu
gabaki daya yan matan sai da suka rude basuyi
tsammanin kyawunsu da kwarjininsu xai rudasu
haka ba sai kowacce ta sallamawa xuciyarta
basu kulasuba suna tafe suna hira abinsu gab da
xasu shige sashensu momy ta kirasu ganin ko
kallonta basuyiba
cak suka tsaya suna saurarenta batare da sun
juyo ba
tace kuxo nan nace ba mgn nake maku ba, suka
dubi juna suna yatsina fuskarsu kana suka tabe
bakinsu suka juyo suka dawo tsakiyan falo sunyi
tsaye sun xuba mata idanu
tace kun shigo ba sallama baku gaidani ba
ballantana kusan da yan'matan dana xaba maku
ku aura
abinku da manemin mata yaji ankira mata sai ya
juya yana kallonsu da sauri hussien kenan
hassan kuwa tabe bakinsa yayi shi bai kallesu ba
kuma shi bai dauke dubansa ga momy ba
hussien ya maida kallonsa gareta
yace momy wadannan fa
ta soma murmushi tana fadin
ka xabi daya hassan ya xabi daya nxt mnth sai
ayi aurenku
ya cije jajjayen labbansa
yace ni bana son ko daya(sai da yan matan suka
tsorata)ba wacce tayimin ban saniba kodai
hassan, ya fada yana kallonsa
hassan ya qara tsuke fuskarsa shi ajin nasa ma
ya hana ya kallesu gani yake girmansa ya fadi ya
tsaya kallon mata
ya dafe goshinsa da hannunsa
gosh" momy kamata xaki nemawa macce kenan
tallata kike
ta harxuqa
tace kada ku maidani wata shashasha mana
kagayamin aibun wadannan yan mata daxakace
ba wadda tayima, kai kuma kake gayamin mgnr
banxa alhali baka dubesu ba
ransa ya qara baci ya juya yana girgixa kansa
yana yarfe hannayensa
yace baxan kalli ko dayaba kuma banason ko
daya
hussien ya tabe bakinsa yana qara qare masu
kallo kamar xai taya dayar bawai da aure ba sai
kuma ya fasa ya juya yabi bayan hassan
iya jin kunya momy taji kunya.musamman da yan
matan suka soma roqonta akan ta lallashesu
sudai tunda suka gansu sunji suna so(yar baqa
ma tayi naci ta barsu)
momy tace karsu damu nan da lokaci qanqani su
dubesu gidansu
yan matan mai suna maryam da salma suka tashi
cike da murna suka fita, momy ta tashi a harxuqe
ta nufi sashensu amma tana murqa qofar falon
tajita qarqame alamar sunsa key
tayi bugun qofar su bude sunajinta sukamata
banxa hrtagama fadanta ta hayewarta sama.
26
kwanaki kadan hr an kammala ginin gidan ba laifi
duk ingawa bamai irin ginin gidansu hamida sai
gashi mutane sun soma bibiyarsu ba kamar da da
ake hantararsuba
ranar da suka shiga gidan an kammala komai
ansa kujeru da duk wani abu na qayata gidan a
ranar kuma yan biyu sukaje batare da sanin
momy ba
wannan karon ba gardama hassan ya shiga gidan
tunda an masa qofa dai dai tsayinsa
mai hali baya barin halin ranar da sukaxo ranar
aka bude gidan su hamida suka tare gadai gida
sabone ko ina tsaftsaf tayis sai sheqi yake ga
qamshi natashi a falon umman amma hassan sai
yatsina fuska yake yn kakkama rigarsa karta
dauki datti
[5:30PM, 11/14/2015] pherty: sai wani kyankyami
yake nunawa hamida na lura dashi ta rasa gane
murdadden raayi irin na hassan
yayi tsaye bakin falo umma dasu hussien nadaga
ciki
umma sai godiya take tana sharar hawaye dan
bata taba tsamani ko mafarkin irin wannan gidan
xai xama nataba
hussien yace ba komai umma Allah xaki godewa
shine yayi maki ba muba
ta juya tana kallon hassan a dan xaman da tayi
dashi ta soma gane halinsa shidai daban ne ta
lura sai wani shan qamshi yake yana qarawa, a
dabi'unsa take banbanceshi da hussien bayaga
haka baxata iya banbantasu ba
tace hassan baxaka xauna bane
yayi rau da idanunsa yana kallon hamida
taxo ta riqa hannunsa da niyar taje ta xaunar
dashi, gogan kuwa sai yaji irin abinda yakeso
yarrrrrr tsikar jikinsa hr tashi take kasala ta
saukar masa hr kusa da umma ta xaunar dashi
duk jikinsa amace ya tafi duniyar tunani wannan
riqonsa kawai tayi yakejin wannan abin tor idan
ta rungumesa fa mexaiji chab sai ya soma
murmushi wanda yaja suke kallonsa cike da
mamaki
dawowar tunaninsa ya dubi inda yake xaune kusa
da umma a hankali ya matsa daga kusa gareta
tace hassan me xn kawo mane
yace ba komai umma nagode
tace a'ah kyautar Allah kagayamin koma menene
xn baka shi inaso ne kasaki jikinka dani kamar
hussien
yace tor tunda kin matsamin kibani hamida ni ita
nakeso
tayi shiru tana naxari idan aurene tafi sha'awar
hamida ta auri hussien yafishi faraa da son
mutane baya kyankyami ko wulaqanta mutum
kamar hassan shiyasa hrta yankewa xuciyarta
hukuncin hussien tabawa hamida ko bayan ranta
shikuma hussien sai yabkwashe da dariya
yace wannan ce matsalar ka hassan
hassan ya harxuqa ya tashi
olryt shiyasa naga umman tamin shiru tunda
baxaku bani ba shikenan kafin suyi mgn tuni ya
fice
hamida ta tashi tabiyosa hr harabar gidan
tace hassan meyasa kakemin hakanan
ya juya yana kallonta
tor menayi daman nasan keda ummanki baku
sona hussien kukeso tor meye abin damuwa
tunda jininane shi kije nabar masa ke
tace meyasa kake wannan mgnr me nayi nida
ummana
yace ai tunda nace ina sonki kema ai bakice kina
sona ba hussien kike so
ta girgixa kanta tana hawaye ba haka bane
kayarda dani ina sonka hassan
yace tor shi hussien fa kina nufin bakyasonsa?
tayi xurr da ido tana kallonsa
tace shima ina sonsa
yayi murmushi alamar yaji dadi
daxu kin riqani naji dadi ynxu kuma ina son ki
rungumeni ingani mexanji(tor fa ikon Allah)
a tsorace take kallonsa idanunta waje
tace in rungume kafa kace....
ya gyada kansa yana murmushin da dimple dinsa
ya bayyana abinda ke qara burgeta dashi kenan
shifa har a xuciyarsa he mean it bai iya boye
abinda k xuciyarsa ba shiyasa yakeyin komai
direct
ta girgixa kanta
baxai yiwuba kadaina wannan tunanin
yace nooooo hamida karkice haka pls bana
neman abu na rasa just for you to hug me inaso
naji wani abune pls
wannan karon jikinta har rawa yake uwa uba
gashi ya tsareta da narkakkun idanuwansa yana
kallonta.......
Hausa novel
[4:37pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: 27
TAGWAYEN MAXA
Na fertymerh xarah
Ta soma ja da baya tana girgixa kanta
tace ai ni ba yar idka bace.....
ya tabe bakinsa hade da daga kafadunsa
yace tor shikenan tunda baxaki bani ba
itama tabe bakinta tayi dai dai lokacin hussien ya
fito yana kallonsu fuskarsa dauke da murmushi
yace hamida kishiga gida umma na jiranki
itama tana murmushi take kallonsa
tace tor shikenan, ta juya xafa fice sai hassan ya
kirata
keeeey.....xo nan, ta juyo tana kallonsa cike da
mamaki kamar baisan sunanta ba
ya qaraso inda take tsaye yavriqo qaramin
yatsanta ya sanya mata xobe, hussien na ganin
haka shima ya tuna danashi yaxo ya riqo
hannunta da hassan k riqe ya sanya mata xoben
a yatsan da hassan ya samata
sai ta saki baki tana kallonsu taya xobe biyu xai
xauna a yatsa daya
hussien yace kada kiciremin xobe kibarshi inda
nasa maki
hassan ya furxar da iska daga bakinsa
yace nima kada ki canxashi daga yanda nasa
maki shi.......lokaci daya suka juya suka shiga
motarsu suka fice
tabi yatsun hannunta da kallo xobe biyu a yatsa
daya wannan ai haukace
[5:16PM, 11/19/2015] pherty: *
Momy sai faman kaiwa da kawowa take a
tsakiyan falonta tasani ba wata hanya daxata iya
raba yan biyu dinta da wannan yar iskar yarinyar
idan har bata halaka ta ba,
mafita daya ce taje ta basu haquri akan abinda ta
masu kana ta roqi alfarmar hamida ta dawo aiki
gidan tana ganin ta haka xata cimma burinta
xata tarwatsa fuskar hamida taga yanda yan biyu
dinta xasu sota suso rayuwa da ita.
Haka kuwa akayi bayan kwana biyu ta shirya aje
gidan da siyayyarta taje inda umma kamar da
gaske hr qasa ta tsugunna ta bata haquri akan
abinda ta masu akwanakin baya
saboda darajar yan biyu dinta yasa umma ta
haqura hrta amince da hamida xata bita amma hr
a qasan xuciyarta bata so hakan ba tayine dan
yan biyu
hr suka xo gidan momy na cike da mamakin
ganin gidansu hamida ginin xamani duk qauyen
ingawa bamai gini kamar nasu abin yabata
matuqar mamaki ta kuma san aikin yan biyu
dinta ne, ta girgixa kanta kawai cike da takaici
tana tuqin motar.
28
Tym din da suka iso gidan yan biyu na falo lokaci
daya suka tashi tsaye ganin hamida da momy
momy na murmushi tace ga hamida nadawo da
ita xata cigaba da kula daku kamar da
hussien ya rungumeta yana dariya farinciki fal
axuciyarsa
yace momy kin kyauta mungode sosai
itama murmushin yaqe kawai take tana kallon
hassan amma ga mamakinta fuskarsa a daure
take sai faman lasarjajjayen labbansa yake yana
wani dauke kansa
hamida hr lokacin bata tantance a wane yanayi
take cikiba batta farinciki da dawowarta gidan
kawai tabi umarni mahaifiyartane
[5:43PM, 11/19/2015] pherty: momy ta shige
dakinta ta barsu nan shima hassan yabi bayanta
tana shiga dakin yana shiga rufe qofar dakin ne
ya sanyata juyowa tana kallonsa cike da mamaki
yana sanye da dark space fuskarsa a daure
hannayesa acikin aljihunsa
kwarjini yayi mata sosai dole yan mata su rude
akansu hr yau bata taba ganin muninsu ba
ta gyara tsayuwarta fuskarta a daure
tace wane salo ne ka bijiro da shi hassan, hrta
kai ka shigo min daki ba sallama
yace noooooo momy keep dat aside inaso
kigayamin dalilinki na dauko hamida kixo da ita
tace bayan kula daku ba wani dalili da xaisa
nadawo da ita
ya xare madubin idanunsa ya kafe ta da manyan
idanunsa
yace ba gsky bane momy, i knw u hate her nasan
ba saboda mu kika dawo da itaba kinada wata
manufa akanta
29
ta nunasa da yatsa cike da mamaki
tace ni hassan kake qaryatawa, ni xaka tasa gaba
saboda mace am.......ya dora hannunsa a bakinta
yace kiyi shiru momy xokiji, yajata suka xauna
bakin gado yana riqe da hannuwanta
yace momy karki cutarda hamida, tana son
tagwayenki tana kula dasu shiyasa tafiki sanin
sirrinsu akan keda kike mahaifiyarsu,
hamida nada ilimi tana samu akan hanya kawai
boko ne dabata qarasaba daxaki taimaka da
kinsata momy,
pls momy karki cutar da ita Allah ya hana na
tabbata a yanayin danaga hamida bada son ranta
ta biyoki ba kamar an mata dolene shiyasa hr na
xargeki,
hamida na neman halal dinta shiyasa hrtaamince
ta biyoki kuma tayi gsky domin annabi s.a.w
yace DALABU HALALU WA JIBBU ALA KULLI
MUSLIM( neman halal dole ne akan kowane
musulmi)
sannan ma momy ki duba dabi'un hamida
kigayamin aibunta da bakyason mu aureta
kigayamana wani abu cikin halayenta dabashi da
kyau wanda Allah ya haramta
[6:33PM, 11/19/2015] pherty: tayi shiru kawai
tana naxari cos babu ita kanta tasani hamida
bata da aibu, hamida yarinyace amma tana da
kyau hali kuma ta sami tarbiya duk da tataso
cikin maraici da quncin talauci amma duk da haka
baisa ta canxa daga kyawawan dabi'ubtaba
hassan yacigaba da fadin momy muna sonta
kibarmu mu aureta ba inda Allah ya hana auren
talaka ki janye wannan aqidar taki pls
ta janye hannunta daga nasa tana firgixa kanta
ganin haka yasa yayi rau da idanunsa kamar xaiyi
kuka
pls momy, ina sonta itace mace ta farko dana
fara so arayuwata idan kin cutar da hamida koma
ki hanamin aurenta am sure nima xn cutu
ta janye hannunsa tana fadin xnyi tunani akai
ya sumbaceta a goshi yana murmushi
yace amma momy ynxu hamida xata rage aiki a
gidannan ko tunda kin qaro maaikata sai abarta
ta kula da mu kawai
nan ma qara tsuke fuskarta tayi ta cire gyalen
jikinta da dan kwalli
tace shima xnyi tunani akai, dai dai lokacin
hussien ya shigo
ta dubesu tana bata fuska bana son wata mgn
kufita pls kada ku dagulamin lissafi
hussien yace dame xamu dagula maki lissafi
momy
kai tsaye hassan yace wai dan nace kada ta cutar
da hamida muna sonta
momy ta dora hannunta a goshinta hassan baida
sirrin kanshi komai xaiyi direct ne
tace dan Allah kufita kuje ku bani wuri
hussien ya fara fita hassan na bayansa.
30
Bayan kwana biyu tun xuwanta gidan taga kamar
komai ya lafa daga yan tagwayen shan giya da
neman mata hrta soma jin dadi sai dai batada
gwani aciki tunda kowane da ranarsa da irib
soyayyarsa a xuciyarta duk da tafison hassan
amma umanta tafison hussien hr ynxu bata
tantance waye nata a cikinsu ba
a wani dare tayi sati biyu da xuwa gidan ta tashi
xatayi nafila kamar ance ta duba window sai ta
tsinkayo hussien na bude gate din gidan ahankali
da sauri ta sauko ta nufi gate din dai dai lokacin
yana riqe da hannun yarinyarsa xasu fita gidan
dan gr ya fitar da mota
jin motsin saukowar hamida ya tayar da momy
daga barci sai ta tashi ta hankade labulen
dakinta tana kallonsu
hamida ta finciko yarinyar daga hannunsa
idanunta jawur ya juyo yana kallonta cike da
mamaki xuciyarsa na bugawa
yace menene haka hamida
tace ashe kai maqaryacine bansaniba ko kasan
alamomin munafiki shine wnda idan yayi mgn
yayi qarya idan yayi alqawari ya saba idan aka
amince masa yayi yaudara,
kamin qarya hussien kaine kafaramin alqawarin
ka daina duk da hassan baimin ba, ka karya
alqawarinka na amincema ka yaudareni sai ta
fashe da kuka
abinka da dare duk abinda suke mgn momy
najinsu kuma tana ganinsu
hussien yace ynxu ni munafuki ne kike nufi
hamida
tayi shiru tana cigaba da kukan da take
yarinyar tace wai cwty wannan wacece who x
she, meyasa take gayama mgn haka bakaa dauki
mataki ba,
hamida ta dubeta da jajjayen idanunta
tace ke wacece dakike wannan mgnr wayeke
menene dalilinki na biyo saurayi hr gidan ubansa
a wannan lokacin kina mace,
mace mai mutunci yar gidan tarbiya a irin wannan
lokacin tana gidan ubanta idan kin gurbata
rayuwarki meyasa kikeson lalata tashi
rayuwar.......keeey ta dakatar da ita
bai lalataniba nixan lalatashi, shine baida tarbiya
bani..........gau kakeji ya dauketa da mari sai ga
bakinta na jini
olryt yau nine bnda tarbiya ko ni xaki dubi
idanuna kigayamin haka
[7:09PM, 11/19/2015] pherty: now get out frm dis
house tun banyi qasa qasa dake ba
ta janye hannunta daga kuncinta tana kallonsa
ranta abace
for now dole ka dakeni ka korani waje saboda ka
gama cin moriyar ganga tunda can farko da kake
xuwa dani nan gidan ai agabanta muke wucewa
meyasa tun lokacin bata hanakaba sai yanxu
saboda itama kanason ka gurbanta tata rayuwar
kamar yanda kamin ko
31
cikin tsawa yace dan ubanki kigayamin waya fara
saninki kafin ni a fankonki na sameki akan
barikinki kece ma kika bata tawa rayuwar saboda
dake kawai nake mu'amala tun muna karatu
england kika tursasani kika hanamin kula ko
wacce mace sai ke, wannan da kike gani itace ke
iya qoqarinta na ganin na dawo kan hanya na
daina abinda nake amma ke ba maccen xama
bace ke ja'ira ce kuma shaidaniya tir da halinki
bilki
ta fashe da kuka kawai batare da tayi mgn ba ta
juya ta fice daga gidan shima ransa a bace yayi
shigewarsa part dinsa
hamida ta jinjina kanta kawai wato itace ma ta
batasa itace tasashi a wannan hanyar, koda ace
ba itace tasashiba ai shi namijine kuma kome
yayi adone agaresa amma ita da take mace fa?
momy dake can sama tana tsinkayosu tana jinsu
ta cika da imani wato abinda suke aikatawa
kenan tabbas ta yarda da hamida 100% ta yarda
ita kadai xata iya canxawa tan biyu dinta halinsu,
xamnta dasu batasan suna wannan abinba kuna
hamida bata taba faya mata ba, lallai dole su so
hamida suso kasancewa da ita sai taji matuqar
tausayin hamida musamman dataga tayi tsaye
bata shigo gidan ba, tor shi kuma hassan wane
abu ne yake aikatawa?
bata qare tunanintaba taga an hangame gate din
motar hassan ce ta shigo
wannan karon bai sha ba amma ya jibgosu xai
shiga da su gida yayi kicibis da ita
ya bata fuska hade da jan tsaki
yace mekikeyi haka sata nayo ne da xaki wani
tare ni haka,
tace tor meye banbanci da sata tunda baka
aikata abinda kake da raa sai dare ya raba
ya dauke kansa yana wani cije labbansa ya raba
ta gefenta xai wuce bai ankaraba ta sa
hanneyenta ta bige kwalaben dake hannunsa
gabaki daya suka xube suka tarwatse...
keeeey cikin tsawa ya dago yana kallonta
idanunsa jawur baiyi wata wata ba ya dauke ta
da mari kafin ya dafebkansa da hannuwansa duka
biyu yana safa da marwa a harabar gidan
xuciyarsa cike da qunci kamareta da duka yakeji
bata damu da marinba duk da taji xafinsa sai
cewa tayi
idan kullum xaka dakeni kadaina shaye shayen
nan na yarda,
shut up stupid, banxa kinsan ko nawane nayi
asara anan kinsan iyakar kudin dana kashe ne
kinsan kudin kwaya daya da kika fasa
ta girgixa kanta
tace ban san iya kudinsuba amma kagayamin kai
kasan iya adadin xunubin dake kanka akan sune
yace wannan matsalarkice not mind ina maki
mgn akan kudin danayi asara ne?
tayi shiru kawai tana sharar kwallah yaja dogon
tsaki cike da takaici ya juya xai fice sai ga momy
tsaye a gabansa idanunta jawur sai da gabasa na
fadi.
u
[4:37pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [7:48AM, 12/16/2015] Pherty: 31 TAGWAYEN
MAXA
Na fertymerh xarah
Ya dauke kansa daga kallonta yana wani cije
fuska kai tsaye batare da tunanin komai ba ta
wanke fuskarsa da mari ba hamida ba shi kansa
hassan ya tsorata
ya xuba mata manyan idanuwansa da suka rine
xuwa ja,
tace ashe daman haka kuke, ashe abinda kuke
aikatawa kenan bayan idona
[hayaniyarsu na fito da hussien ] kunci amanata
kun yaudari tarbiyata dana maku, hussien
yace momy me akayi n......, bai qarasaba shima
ta wanke fuskarshi da mari, a harxuqe
hassan yace but mum a....... Rufemin baki ta
fada cikin tsawa, kai kanada bakin magana ne
duk abinda k faruwa duk akan idona, sai yau na
yarda hamida alhairice agareni ynxu na fahimci
komai akanta duk qoqarin datake akanku bata
taba gayamin aibunku ba tabbas ta cancanci ta
xamo surukata na janye duk wata aqida tawa
akan mai kudi da talaka amma kasani hassan
bakai ba hamida baka dace da rayuwartaba xn
nemawa hussien auren hamida......,
shima hassan a harxuqe ya katseta look mum
mekike nufi did you hate me for now? Meyasa
xakice haka menayi ne? Ko angayamiki ni bana
sonta ne,
tace a hakan kake sonta kana sonta kake
dukanta,
oh gosh ya dafe kansa da hannuwansa duka biyu
ya juya ya dawo yana fadin nooooo mum ina
sonta wlhy akanta na fara so itace na fara shiga
damuwa akanta pls karkimin haka,
tace duk yanda xakayi sai dai kayi amma baxan
aurama hamida kaje kana cutar da itaba hussien
yafika sonta akanta naga ya haqura da
yarinyarsa hr ya korata waje amma kai saboda
wadannan abin hr xaka daketa ka nuna sunfita
daraja,
33
Tacigaba da fadin, yanxu ina son hamida saboda
son da take maku da kuma son gyara maku
halayya da takeyi shiyasa baxan so cutarda
rayuwarta kamar yadda na qudira a farko ba
tabbas hussien kadai xai iya riqeta amana,
ya soma yarfe hannuwansa yana fadin mistake ne
mum but i promise baxan sake dukantaba kiyi
haquri ina sonta mum pls sai ya fashe da kuka
abinda rabon dataga kukansu tun suna yara,
hankalinta na tashi bama kamar hussien ba da
shima ya riqo hassan din yana kuka,
tace dama kabar kukan hassan nariga na yanke
hukunci xaka auri salma hussien kuma hamida
gobe ma xnje ingawa neman aurenta tare da
uncle dinku
[7:59PM, 11/20/2015] pherty: Cikin daga murya
yace bana sonta nace bana sonta who is she?
34
Ya soma marin kansa da hannun daya mari
hamida ita kanta
hamida a rude take ta fashe da kuka tana fadin
momy pls ki dakatar dashi, xuciyar momy sai
tafarfasa take tana jin xafin halin da hassan dinta
ke ciki amma ta kasa tsayar dashi badan komai
ba dan karyaga karayarta,
hamida ta janye kawaicin dake damunta taje ta
riqe hannunsa dayake marin kansa,
tace me kakeyi haka hassan kadaina pls ya
fincike hannunsa fuskarsa har tayi jawur abinka
da farin mutum,
ya hankade hussien daga jikinsa batare da ya
waiwayesu ba yaje ya shiga motarsa ya finciketa
da qarfin tsiya ya bar gidan, hankalin momy a
tashe
tace kabishi hussien kada yaje ya halaka kansa a
banxa sai ta fashe da kuka,
hussien ya shiga mota ya bishi jikinsa har rawa
yake
hamida kuwa durqushewa tayi qasa tana kuka
kamar ranta, tun fitowarsa gidan yake kuka tuqi
yake batare dayasan inda xaijeba hankalinsa
yatafi qoluluwar tunanin yanda xai iya xama da
wata ba hamida ba ita ya fara so gashi har
akanta yana jiyo wasu feelings da bai taba jiba
tayama xaa kwaceta daga gareshi aba hussien ya
tuba ya daina dukanta baxai qara ba,
ya fashe da kuka qeeeeeeeey yayi qoqarin tsaida
motarsa dataso ta bigi motar gabansa, yayi
qoqarin kwacewa yayin da motarsa ta nufi daji,
gab kakeji ta bigi wata qatuwar itaciya,
hussien yaja wani birki tsakiyan titi ya saki qara
ya nufi motar hassan gashi darene........,
Hausa novel
[7:51AM, 12/16/2015] Pherty: [10:40AM,
11/27/2015] pherty: 35 TAGWAYEN MAXA
Na fertymerh xarah
Mutane suka rufawa motar baya yanda hussien
yaga hassan yasa numfashinsa ya sarqe ya fadi
ragwab sumamme,
nan da nan aka kwashe su subiyu aka nufi asibiti
da su, tym din da hussien ya farfado gadon
hassan ya nufa duk jikinsa jinine ya soma kuka
sosai kamar ransa fadi yake
hassan kada ka mutu kabarni, munxo duniya
atare kabari mukoma atare baxan iya rayuwa
bakai ba, kamar yanda muka xo tare muka rayu
tare kabari mu mutu tare, idan hamidace wlhy na
barma nixan auri saalma pls...,
ya fashe da kuka mai tsanani,
washe gari dole ya buga ya sanarda momy,
aikuwa a rude ta iso asibitin hamida na bayanta
ko mayafi babu
[10:42AM, 11/27/2015] pherty: 36
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine abinda
momy ke maimaitawa,
hamida kuwa a qofar dakin ta xube hannunta
dafe a bakinta ta fashe da wani matsinancin
kuka,
momy tace nooooo hassan, katashi pls idan
hamida ce gaka gata, meyasa xaka nemi halaka
kanka kan abinda kafi qarfinsa , hamida ta tashi
ta qarasa wurin da yake kwance qafafunsa da
kansa duk jinine dai dai lokacin dr.merah ya shigo
tare da hussien, ya dafe kansa da hannuwansa
duka biyu yanaa girgixa kansa cike da tausayawa
yace saai an masa x_ray saboda jinin dak) fita a
kanssa but actually ya sami matsala a qafafu da
kyaarne idan xai sake tfy akansu
[10:47AM, 11/27/2015] pherty: Lokaci daya duk
suka juyo suka xuba mashi ido cike da tashin
hankali,
momy tace qaryane dr. Dole hassan dina ya tashi
baxai xauna ba qafafu ba, inada kudin daxan fita
dashi waje ayi masa magani, ta fashe da kuka ta
cakumo rigarsa tana girgixashi cikin wani irin
kuka mai tsuma xuciya,
37
da kyar dr.merah ya banbareta daga jikinsa yana
fadin hjy a waje nayi karatu kumaa a waje)nake
aiki ina xagayowa nigeria kasancewarta
mahaifata kuma family dina suna xaune anan
idan kuka cire matata da ya'yana, duk abinda xaa
iya masa acan insha Allah xn iya kuma xn gwada
qoqarina akai
(magana yake cikin isa da qasaita da kyar ma
suke jiyosa yanayi yana yatsina fuskarsa amma a
xuciyarsa kallon hussien yake yana kallon hassan
cikin boyayyen dark space dinsa ya rasa gane
banbancinsu tagwayen kamar aljannu ko taya
suke gane abinsu oho ya tabe bakinsa ya juya ya
fice)
hussien da momy suka soma kuka kamar ransu,
hamida kuwa fita tayi ta nufi office din dr.merah
ta samesa kishingide yana juyi kan kujerar da
yake xaune,
sallama tayi a qasan xuciyarsa ya amsa batare
da ya kalletaba, da hannu ya nuna mata wuri ta
xauna, tace
38
Dr. Da gaske hassaan baxai sake tfy ba, ya gyada
kansa yana kallonta qaramar yarinyace ko meye
damuwarta akansa,ta soma share hawayen
fuskarta ,
yace ko meye damuwarki akansu by main looking
bakiyi kama dasu ba nasan ba qanwarsu bace ke,
kanta a qasa
tace ni mai aikin gidansu ce amma ta dalilina ya
sami wannan matsala, ya xuba mata idanuwansa
cike da mamaki bayan ya xare madubin idanunsa,
(cikin lokaci qanqani ta bashi lbrin komai batare
da shayin saba saboda tasan Dr.Aiman merah taji
labarinsa ga ummanta da momy, taji lbrin
mulkinsa da qasaita)
nan take yaji yana tausayin yarinyar itace mace
ta uku daya soma tausayi a rayuwarsa bayan
matarsa Affiya, sai Dr.fulani da ita
[10:51AM, 11/27/2015] pherty: Yace hermyderh
kada kidamu baxamu iya yimasa abinda Allah bai
nufaa ba, kiyi masa addua -kiroqi Allah bashi lfy
namu shine mu taimaka masa,
39
But i promise u insha Allah xai sami lfy yayi tfy
da qafafunsa kada ki damu
hamida,murmushi tayi tana kallonsa tana
mamakin girman mulkinsa da qasaita tana
mamakin yanda yake furta magana da kyar kamar
bayaso, duk mgnr dake fitowa bakinsa idanunsa
akan laptop bawai kallonta yake ba,
idan bata manta lbrn yarima aiman ba data
qaryata sarautarsa da qasaitarsa(duba mulki ko
sarauta)ta tashi tafice
tana fadin nagode Dr. Ta juya ta fice da sauri
yabita da kallo kafin ya girgixa kansa ya maida
kallonsa ga laptop ,
tana fita office din asibitin tabari ta nufi ingawa
cikin tashin hankali ta sanarwa ummanta abinda
ke faruwa taje taxo da kawunta akan xasuje
asibitin,
harda maigari taaje ta roqa akan yabiyota asibity
abinka da babban mutum saai yaje da mutanensa
ciki hrda liman,
abin yayi matuqar daurewaa umma da kawunta
kai saai dai basu tankataba har suka shigo mota
suka xo asibitin,
har lokacin bai farfadoba sai dai sun sami iyayen
salma ma sunxo salma sai kuka take sosai,
hamida da mutanenta yabawa kowa mamaki
kamar mutuwa akayi, kai tsaye ta nufi inda
hassan ke kwance ta riqo hannunsa tana kuka,
40
tace ina son hassan xn iya xama dashi a kowane
hali koda yaxama nakasasshe bnsoshi dan wata
dukiyarsa ko kyawunsaba sai dan yana hassan
akwai wata kissa inda wani mutum yaxo inda
manxon Allah yace ya manxon Allah shiryardani
xuwa ga wani aiki wanda innayi shi Allah xai soni
mutane kuma xasu soni,
sai Annabi yace guji duniya
[10:52AM, 11/27/2015] pherty: Allah ya soka
kuma ka guji abindake hannun mutane,mutanen
xasu soka,
shiyasa naxo da wakilina kawuna ga mai gari da
limaminsa, inaso a dauramin aure da hassan,
dam xuciyar hussien na buga gabaki daya dakin
aka xuba mata ido bama kamar hussien da salma
dana tsinci kansu cikin wani tashin hankali
ba.........
Hausa novels
[7:56AM, 12/16/2015] Pherty: [4:47PM,
11/30/2015] pherty: 41
TAGWAYEN MAXA,
Na fertymerh xarah
Duk dakin akayi shiru aka xuba mata ido cike da
mamaki, ganin haka yasa ta qara fashewa da
kuka ta girgixa kanta ta qarasa gurin momy dake
tsaye ta riqo qafafuwanta tana wani irin kuka mai
narkar da xuciyar mai sauraro nan da nan jikin
momy nayi sanyi,
umma ta dubeta cike da mamaki
tace hamida har ynxu ban gane inda kika dosa ba
inaji kin daukomune dan mudaba marar lfy ko?
Hamida ta dago manyan idanuwanta dana rine
xuwa ja tana kallon mahaifiyarta
tace harda auren hassan umma, yana sona yana
son halaka kansa saboda ni dan Allah ku
tausayamasa,
nan da nan ran umma na baci ta murtuqe fuska
cike da takaici ta fisgota daga tsugunne datake
itama hamida ta tsorata da ganin yanayin da
umman nata take ciki
[4:54PM, 11/30/2015] pherty: Mekike fada ne
hamida qara maimaitawa inji inajin kunnuwana
basuji da kyau bane,
hamida ta tsorata ta xare idanuwanta tana
kallonta tana girgixa kanta cike da tsoro,
42
umman ta sake saura qiris ta fadi ta juya ga
kawun hamida
tace bn amince da wannan auren ba ban yarda
hamida ta auri mutanen da basu da kirki basu da
tausayiba,
lokaci daya xuciyar momy da hussien ta buga duk
suka dubeta a raxane,
umma tacigaba da fadin hamida ya'ta ce jinina
ce ban yarda ta auri ko daya daga cikinsuba
saboda mahaifiyarsu batada mutunci tunda har ta
iya toxartamu ta wulaqantamu saboda Allah bai
bamu ba, hakama ya'yanta..........hussien
ya katseta da hanxarinsa,
yace umma kimin adalci kinfi kowa sanin yanda
nakeson hamida, wlhy ina sonta dalilinta nadaina
aikata duk wani abu marar kyau, sannan
mahaifiyarmu bai kamata ki jefeta da wannan
kalamaiba idan kikayi la'akari da irin halaccin
datayi maki a rayuwa bawai gori nake maki ba,
43
mai gari yayi gyaran murya kafin
yace Asmau(umma) ba iko xn maki ba abinda na
fahimta anan duk su biyu suna sonta kibarta ta
auri wancan da baida lfy ina ganin hakan shine
dai dai,
umma ta girgixa kanta cikin tashin hankali
tace bana son hamida ta auri hassan nafi yimata
sha'awar hussien shine yafi sanin darajarta shi
nakeson ta aura,
wasu xafaffun hawaye suka xubowa hamida
bawai batason hussien bane tana sonsa amma
xuciyarta tafi rinjaye akan hassan din,
ahankali taja qafafuwanta daga dakin ta fita tana
fitowa ta tsinkayo Dr.merah na fitowa theater
yana tafe yana xare handgloves cikin isa da
qasaita ga fadawa birjik a asibitin, guards dinsa
suna biye dashi a baya,
yana tafe yana yatsina fuska ma'aikatan asibiti
sai xubewa suke suna gaisuwa nurses da likitoci
sai dai ba wanda ya kula ballantana ya amsa,
cak suka ga ya tsaya harabar asibitin suna ganin
haka fadawan da guards suka san akwai matsala
tabbas akwai abinda ya fadi daga hannunsa
daman hakane duk abinda ya fadi hannunsa baxai
taba magana ko ya nunaba sai dai ya tsaya
masu more masa baya suje su duba ,
haka kuwa akayi da yawa suka juya suga ko
menene ya fadi suna isa cikin asibitin suka sami
turban dinsa ne har wata nurse ta dauka xata
kawo masa da sauri suka karba suka fito ,
hamida na tsaye na kallon sarauta wannan tor
dame yake taqama MULKI KO SARAUTA?
tana kallo aka bude masa mota ya jima tsaye
kafin acire masa labcoat din jikinsa aka musanya
masa da alkyabba suka nada masa turban dinsa
kana ya shiga motar sukajata ahankali kamar
masu tfy a hanya,
kusan motoci biyar suka morama motarsa baya
suka fice, ta sauke ajiyar xuciya ta tuna cikin lbr
da aka bata
akwai wani lokaci da sarki merah ya sauka daga
sarautarsa aka nada Aiman, saboda tsabar
sarauta da ji da kai a daren ranar yana tare da
mai dakinsa Affiya xasuje
[4:59PM, 11/30/2015] pherty: Lambu,
kunama ta cijesa a dan yatsan qafansa, amma
saboda qarfin mulkinsa bai fada ba ko raxana ko
wata alama da xai nuna illah tsayuwa da yayi
cak a xaton fadawan ya yarda wani abinne sai
suka shiga dube dube anan suka ci karo da
qatuwar kunama dai dai inda yake tsaye nan take
suka kasheta hankalinsu a tashe suka juya suna
kallonsa yana tsaye inbanda xufa ba abinda yake,
44
iya rudewa affiya ta rude ta rungumosa tana
tambayarsa inda kunamar ta cijesa amma yaqi ya
fada hassalima dauke dubansa yayi daga garesu,
fadawan cikin rudani suka xube qasa suna
roqansa ya fadamasu amma fafur yaqi tankawa
saboda gani yake idan ya nuna rakinsa tabbas
girmansa dana sarautarsa ya fadi,
Affiya nan take ta fashe masa da kuka ganin
kunama ce fa ta cijesa ta juya xatabar lambun
sai ya riqo hannunta yasa dayan hannunsa ya
xare space din idanun sa da idanu yayi masu
alama da yatsantsa......
Cabdi wani mulkin,sarauta da qasaita sai kun
duba littafin MULKI KO SARAUTA?shima littafin
fertymerh xarah ne.
kukan salma ya dawo da hamida daga xurfin
tunanin da take, sai a lokacin ta tuna halin da
take ciki tadawo da kallonta ga salma idanunta
sunyi rau rau ta koma cikin asibitin gab da xata
shiga dakin taji muryar momy cikin kuka tana
fadin
abar hamida ta auri hassan, hussien xai iya
haqura da hamida amma batasan ya rayuwar
hassan dinta xata kasance ba idan ba hamida,
umma tace nafison hussien akan hassan, nafi
ganin girmansa mutuncinsa tarbiyarsa sosai akan
hassan saboda haka na xabawa yarinyata hussien
ta aura,
ta juya a raunane tana kallon limamin idanunta
taf da hawaye
tace ga wakilin hamida shine kawunta tunda baa
sanarda yan uwan hussien ba inaso mai gari ya
xamo wakilinsa a daura auren hermyderh da
hussein yanxu ba sai anjima ba tunda TAGWAYEN
MAXA baxasu auri hamida dukkansuba dole
dayane xai xamo mijinta kuma hussien,
nan take hamida na xube da gwiwoyinta qasa
tana rusa kuka mai tsananin gaske.
Hausa novel
16 December 2015 at 08:05 · fertymer
[4:39pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [4:57PM, 12/22/2015] Pherty: 45
TAGWAYEN MAXA
Na ferty xarah
A raunane hussien ya matsa yana kallon hassan
da har lokacin bai farfadoba,
yana tausayin dan uwansa yana son dan uwansa
kuma komai xai iya akan dan uwansa,
tabbas yafison rayuwar dan uwansa akan hamida,
mace baxata taba xama sillar rabuwar
xumuncinsuba,
yau gashi duk kudinsu kyawunsu da ajinsu suna
neman rasa abu a duniya, komai na hassan
nashine, kuma komai nashi na hassan ne tor idan
hakane dan me baxai iya barwa dan uwansa
jininsa abinda yake soba,
ya rumtse idanunsa yanason hamida tamkar
ransa kuma yaxama wajibi yabarwa hassan
shikuma ya karbi salma a matsayin matarsa,
ya girgixa kansa yana hawaye ya kalli umma
yana share hawayen fuskarsa sai kuma ya juya
yana kallon liman kafin yajashi gefe sukayi wata
magana batare da kowa yajiyosuba kana hussien
ya dubesu
yace xaije ya dauko uncle dinsu dole shi xai xama
wakilinsa saboda shine ubansu a yanxu,
ya juya ya fice yana fitowa yaci karo da hamida
tsugunne a gefe kallo daya yayi mata ya dauke
dubansa gareta tana ganinsa ta taso da sauri ta
taryesa, ya murtuqe fuskarsa, hakan yasa jikinta
yayi sanyi ta langabar da kanta tana hawaye,
tace nasan tunaninka xai baka cewa bana sonka
wlhy ina sonka hussien, tausayin hassan da
kasancewarsa dan u.... Ya katseta ta hanyar
daga mata hannu
yace qaryane hamida qarya kike kice kina sona,
maganarki ba gsky bace duk hasashe ce ba tun
yau nake ganin soyayyar hassan atare dake ba
idanuna na kanki hamida, kada kidamu hassan
din da kikeso xaki samesa sannan duk wata
kulawa da damuwa da kika nuna akaina nagode
ya juya ya fice ransa a bace tabisa da kallo cike
da tashin hankali da rashin fahimtarta da baiyiba,
46
kusan minti talatin da fitarsa sai gashi tare da
iyayensa maxa kusan uku sun shigo asibitin kai
tsaye aka nufi dakin da hassan k kwance,
sun raxana da halin da suka sami hassan dan
basuda lbr hr sun juya xasu rufe momy da fada
ganin suna raye Dan' yayansu yana neman rasa
rayuwarsa basuda labari yasa momy tayi saurin
katsesu muryarta a sarqe tana kuka ta koro masu
bayanin komai
[11:18AM, 12/1/2015] Pherty: Nan da nan iyayen
maxa suka juyo da kallonsu ga umma suka dubi
hassan matsayinsa kudinsa kyawunsa da ajinsa
amma ace shine ya koma hakan saboda mace
macen ma yar talakawa to menene amfaninsu a
duniya idan baxasu iya samawa TAGWAYEN
MAXA abinda suke so ba,
amma abin tambaya da mamaki anan yanda duka
xaratan maxan suka kafe akan mace daya kuma
kowane daga cikinsu na buqatarta duk da basuga
yarinyar ba, sannan basajin ta ummanta saboda
sunada kudin da xasu nuna mata FIN QARFI akan
yarta(chabdi)
hussien ya katse tunaninsu xuciyarsa a raunane
yace a daura auren amma duka iyayen mata su
fita daga dakin,
47
uncle ya katsesa yace wane irin daurin aure ne
wannan hussien sai kace bakuda gata a duniya,
wane irin aurene xaa daura a asibiti kamar wasu
marar galihu, bamu yarda da wannan daurin
aurenba,
tabbas kamar yanda duniya tasan da mahaifinku
kafin ya rasu tasan da xaman kyawawan maxa
kamarku dole sai kowa yasani kuma ya shaida
auren TAGWAYEN MAXA a doron qasar nan,
bamai gari ba hatta liman da kawu sai da jikinsu
na dauki rawa wato abin na manya ne,
uncle ya cigaba da fadin kuma xaa cigaba da biki
baxaa dakatar ba saboda munada tabbacin
yaronmu yana raye da ixinin Allah kuma xai tashi,
Alhaji jafar da Alhaji ismail sukayi murmushin jin
dadi lokaci daya kafin su fita a tare uncle na bi
bayansu,
umma jikinta a sanyaye takalli kawun hamida
tace kada ka manta hussien na bawa hamida
dashi nakeson tayi rayuwa,
kawu ya gyada kansa kawai suka fita gabaki
daya hussien ya juyo yakalli dan uwansa har
lokacin baisan abinda ke faruwa ba ya girgixa
kansa kawai yana hawaye ya juya ya fice
[11:26AM, 12/1/2015] Pherty: Gidajen radio, t.v,
jaridu e.t.c aka shiga yadawa da sanarda daurin
auren TAGWAYEN MAXA,
hassan da hussien, cikin mintunan da basu wuce
arba'in ba qatoton harabar gidan
Alhaji jafar ya cika da mutane iri iri kala kala
tundaga yan uwa, abokan arxiki, qawaye ba
wanda bai hallara ba, nan take aka daura auren
HUSSIEN DA SALMA, HASSAN DA HERMYDERH,
wanda hussien ne ya nemi wannan alfarma ,
48
An dade ana kacaniyar daurin auren kafin su
qaraso asibitin hr lokacin matan basu san ya
daurin auren ya kasance ba illah hankalinsu dake
tashe saboda farfadowan hassan yana aman jini,
Dr.merah naganin yanayinsa yasa aka shiga dashi
emergency da gaggawa, yana tafe da sauri ana
cire masa alkyabar jikinsa tunda baxai iya cirewa
dakansa ba dole sai ancire masa saboda girman
qasaitarsa,
gab da xai shiga dakin emergency suka gama
sanya masa labcoat dinsa suka bude masa qofar
ya shige duk suka tsaya a waje suna jiransa,
hankalinsu a tashe sunyi tsaye cirko cirko ko
wane xuciyarsa bugawa take kamar xata bullo
qirjinsa tafito,
da sauri duk suka juya suka bar asibitin suka nufi
masallaci, arwallah sukayi suka shiga domin kai
buqatarsu da kukansu ga ubangiji talikai,
Allah ka biya mana buqatanmu ya rabbi!, awa
biyar cur suka dauka kafin su sami numfashinsa
ya dawo dai dai Alhmddlh komai ya dai daita sai
dai yasami barci,
kai tsaye aka nufi aminity dashi qafafuwansa duk
daure da bandage, ganin komai ya lafa yasa mai
gari ya tarasu duka yayi mgn da tattausan lafaxi
tareda bawa kowa haquri akan yanda auren ya
kasance dan shima a ganinsa hakan yayi dai dai,
umma kamar ta hadiye xuciya taji, wuf ta tashi ta
fice daga asibitin ta nufi ingawa,
salma kuwa dadi kamar ta mutu dama batada
gwani aciki kowanensu tana so, yayinda fargaba
tasa hamida a gaba jikinta sai faman rawa yake
har wani xaxxabi takeji ganin ummanta batayi
maraba da auren ba.
49
Sati biyu jikin hassan ya soma sauqi sai dai har
lokacin daga kallo bai furta ko wacce kalma ba
hassalima baisan meke faruwa ba illah ya tsani
kowa a asibitin ba kamar momynsa da hamida ba
wanda yake ganin ta dalilinsu ya tsinci kansa a
wannan halin,
ganin samuwar sauqinsa yasa Alhaji jafar da
Alhaji ismail suka tada mgnr bikin aure ,
anata shirye shiryen biki anyi biki kala kala
ankashe naira,
ranar da xaa kai amaren xuwa gidajensu uncle
yayiwa hassan bayanin komai sai dai ga
mamakinsa hassan bai nuna wata alama tajin
dadi ko rashinsa ba illah lumshe idanuwansa da
yayi kawai,
daren ranar da xaa kaisu ake dinner taro yayi
taro a qaton hotel din kaya iri daya amaren suka
sa wanda uncle yayi masu kayan biki
shikuma Alhaji jafar ya gina masu qatoton gidaje
guda biyu komai iri daya ciki da waje hatta kayan
dake ciki duk iri dayane sai banbancin kala wanda
anan ra'ayinsu ya banbanta,
gidajen suna kallon juna basuda tserayya mutane
har xuwa kallon tagwayen gidajen ake masu
matuqar kyau da tsari,
Alhaji ismail shi ya dauki nauyin auren tun daga
kan sadaki,lefe kayan aure da sauransu duk shi
yayo odarsu a waje,
taro yayi taro suna xaune su uku sun sanya
hussien a tsakiya duk acikinsu salma ce kawai k
farinciki yayinda xuciyar hussien a dagule take na
rashin dan uwansa a kusa dashi ana hidimar ba
hassan,
hamida ajima ajima take sharar kwallah
musamman idan ta daga kanta ta dubi hussien
da tashi amaryar ita kuma banata angon bugu da
qarima ance baxai iya tfy ba,
ta fashe da wani matsinancin kuka dai dai lokacin
taji wurin ya dauki shiru lokaci daya taga hussien
ya miqe tsaye tare da salma,
sai ta janye hannunta daga fuskarta itama ta
miqe ta maida kallonta dai dai inda taga jamaa
na kallo,
yana tsaye kishingide a mota hannunsa riqe da
sanda irinta masu mulki idanunsa boye acikin
dark space ya xare madubin fuskarsa ba yabo ba
fallasa,
hussien ya isa wurinsa da sauri yana dariya ya
rungumesa yayinda hamida ta rasa yanda xatayi
lokaci daya tasaki kuka da dariyar farinciki.
Hausa novel
[5:00PM, 12/22/2015] Pherty: [5:09PM,
12/12/2015] Pherty: TAGWAYEN MAXA
Na fertymerh xarah
A hankali ya dauke dubansa gabhamida yamaida
kallonsa ga hussien dake rungume dashi
hussien ma kallonsa yakeyi
yace hassan meke damun kane meyasa kake bata
rai, yau ranar farinciki ce kasami lfy kuma hamida
ta xama matarka
hassan ya bata fuska yana yatsinata
yace ashe dakai xaa hada baki aci amanata
hussien ya saki baki cike da mamaki
yace ban fahimci inda ka dosa ba
[5:27PM, 12/12/2015] Pherty: yace meyasa aka
aura min hamida, meyasa aka bani ita bayan
ance bnda mutunci bnda tarbiya bata dace dani
ba,( hawaye fal a xuciyarsa ya nuna qirjinsa da
dan yatsansa)yana fadin
ni ake wulaqantawa akan mace, macen ma yar
talakawa wadda nafita da komai, ni ake
gorantawa tarbiya ake cimin fuska dan kawai
nace ina son yar aiki, tor na fasa bana.......huss
ien yayi saurin toshe masa baki cike da bacin rai
idanunsa sunyi jawur yake kallonsa,
tun kafin yayi mgn hassan ya janye hannunsa
daga bakinsa a fusace cikin tsawa yace kabarni
nayi magana ina ruwanka dani ne?
cikin fusata hussien yace na barka kayi magana
ka fadi duk abinda kakeso ka fada, ka toxarta
aurenka a idon jamaa, ka nunawa duniya cewa
dole akama ba raayinka bane.....
51
Hamida dake qarasowa inda suke cak ta tsaya
lokacin da kalaman hassan na farko na daki
kunnenta,
nan da nan farin cikin fuskarta na kau, ta tsaya
cike da mamakin kalaman da hassan ke jifarta
dasu
duk qoqarin data nuna akansa, da irin soyayyar
da take masa, da son hussien data danne a
xuciyarta saboda qaunar da take masa amma da
abinda xai saka mata dashi,
ta juya taga jamaa sai kallonsu ake ta sunkuyar
da kanta tana share hawayen idanunta cike da
takaici ta juya tabar wurin
hassan yaja numfashi tare da iska kafin ya furxar
yana wani huci cikin takaici
yace tor meye damuwarka konayi, meye naka
idan na wulaqantar da aurena da kai aka hada
baki akaci amanata
hussien yace auren hamida shine cin amanarka
ofcourse ya bashi amsa idanunsa akansa
cikin bacin rai hussien
yace control ur temper,
yace anqi ayi
cikin tsawa yace qarya kakeyi, qaryane kace
bakason hamida a ynxu, qaryane kace xaka cutar
da yarinyar danakeso tamkar raina na barmaka
ita,qaryane kace xaka taxarta hamidata a idon
jamaa kuma qaryane kace xaka qaryata soyayyar
da kake mata qaryane! qaryane!! qaryane!!!(ya
cakumo wuyan rigarsa) stop pretending,now tell
me why did u betrayed her?
[5:48PM, 12/12/2015] Pherty: hassan yayi
qoqarin janye hussien daga cakumar rigarsa da
yayi nan kokuwa ta barke tsakaninsu(na shiga
uku)
mutanen dake gurin sukayo kansu da kyar suka
rabasu, uncle ya qaraso wurin cikin tsawa ya
dakatar dasu cike da bacin rai yaja hannayensu
ya nufi mota dasu kai tsaye gida suka nufa a falo
suka taradda momy, yanda tagansu yasata
faduwar gaba ta tashi daga inda take xaune tayo
kan hassan tana tmbyrsa lfy meya samesa shida
baida lfy sai kuma tayi kan hussien tana tmbyrsa,
duk suka dauke kansu daga gareta kowanensu
fuskarsa ba annuri
52
cikin tsawa uncle yace kunmin tsaye duk ku
xauna, lokaci daya suka xauna kamar basu so
suna tunxure tunxure
yace hjy kigayamin dama yan biyu na kokuwa da
juna ne?
hankalinta yayi matuqar tashi ta xaro ido cike da
tsoro tana kallonsu jikinta hr rawa yake kafin
tamaida dubanta ga uncle
tace a'ah sau daya ne kuma tun suna yara amma
bn sani ba ko sunayi a skul xamansu a cairo,
fada sukayi ne?
yace kunji kunya sakarku,kun ban mamaki kuma
kun nunamin ku cikakkun yan iskane bama kamar
kai hassan(ya nunasa da yatsansa)
hassan ya tunxure baki yana sunkuyarda kansa
yace ka tashi ka dakeni ko kuma nima kayi
kokuwa dani tunda kayi da hussien tunda ya
gayama gsky,yafi kaxauna kanamin qunquni,
kuma wlhy summa tallahi tunda na rantse ko
kaso ko kaqi sai ka xauna da hamida kuma a yau
xaa kaita gidanka idan kuma kaqi wlhy bani bakai
kada ka sake kallona a matsayin qanin
mahaifinka, ya juya ya fice daga gidan
hassan ya tashi yana daga kafadunsa
yace so what, tor sai me tunda kai ba ubana
bane me k..........yayi shiru sakamakon marin da
momy ta daukeshi dashi, ta cakumosa ranta a
bace
tace menakeji hassan, mekake fadine, shi uncle
din daya xama uba agareka hr kake butulce masa
kake gayamasa mgn irin wannan inda yaji
mekake tsammanin xai faru
[6:06PM, 12/12/2015] Pherty: ya fashe da kuka
hade da janyeta daga jikinsa,
tor mexai faru,kowa damuwarsa yasani bnda
tawa,kowa kansa yakeso bandani,dan kawai nayi
accident nasami tangarda a qafana ina dingirsa
shine baa sona ynxu komai nayi bnyi dai dai ba
har akemin kallon nakasasshe xaa aura min yar
aiki, nace banayi ko dolene?
saboda tsananin raxana da mamaki jikinta hr
rawa yake bakinta a bude ta juya tana kallon
hussien daya xuba mashi ido, tana qoqarin gyara
xaninta dakeson kwancewa saboda raxana
tace hussien meke faruwa me hassan ke nufi, ban
fahimcesaba
cikin tausasshiyar murya hussien ya bayyana
mata komai dake faruwa kamar yayi kuka saboda
bacin rai
ta juya tana kallon hassan idanunta fal da
hawaye
tace hassan kodai lasami matsala ne
a.kwakwalwa, ko giyar da kake sha ta taba
kwakwalwarkane?
garau nake momy,
hawayen da take maqalewa suka xubo mata
tace sakayyar da xaka mana kenan, duk halaccin
da akama id....ya katseta
kiyi shiru momy hamida munafukace hussien take
so bani ba nagani a kwayar idanuwanta duka su
biyu suna so suci amanar aure nane
hussien ya xaburo xaiyi cikinsa momy ta taresa
tace kabar shi hussien kabrshi, ya nunosa da
yatsa yana huci yace karda kasake kiran
hamidata munafuka, kaine munafuki mayaudari
wanda baisan darajar soyayya ba baisan haqqin
dan adam ba, idan batason ka sai me? k....momy
ta rufe masa baki
53
Tace kayi shiru hussien, hamida ynxu tana da
aure matar dan uwankace, bai dace ka danganta
wasu kalamai akantaba a ynxu,kabarshi idan
kasheta xaiyi yaje ya kasheta amma idan na isa
garesa kuma ni mahaifiyarsa ce inaso ya xauna
da hamida a matsayin matarsa,
sai a lokacin hawaye suka xubowa hussien,wani
iri yakejin kansa yau shine yayi fada da dan
uwansa hrda kokuwa kuma akan macce,ya
girgixa kansa yana cigaba da hawaye
yace nadaina momy daga yau, insha Allahu baxan
qara mgnr hamida ba baxan qara shiga lamarin
hamida da hassan ba koda ya cutar da ita,kuma
daga yau duk wani abu da ya danganci hassan na
daina shigarsa nafita hanyarsa shima yafita
nawa,ya kyaleni baruwansa dani kuma yafita
rayuwata kamar yanda xnbar rayuwarsa a duk
abinda ya shafi rayuwarsa, ya juya ya fice momy
na kiransa amma yayi mata banxa kamar baijiba
ya fice da sauri yana kuka
[6:44PM, 12/12/2015] Pherty: ta juyo tana
kallonsa ranta abace amma shi ko ajikinsa ya
qara daure fuskarsa
yace momy idan kun sake haduwa dashi
kigayamasa nafita rayuwarsa yafita nawa,nima ba
ruwanshi dani ko a hanya kada ya sake ya nuna
ni dan uwansa ne ko inada alaqa dashi saboda
na kwance ta aynxu shima ya juya ya fice
TAGWAYEN MAXA sun mata abinda bata tb
tsammaniba,taya xata yarda su raba kansu
bayan tare aka haifesu suka xo duniya suka rayu
tare komai tare sukeyinsa sai ynxu saboda mace
xasu raba kansu xasu yanke dangantakar junansu
ina baxai taba yiwuwa ba baxata aba yarda ta
xuba masu ido ba, jikinta a sanyaye ta nufi
bedroom dinta cike da tashin hankali
54
*
da dare kamar ynda uncle yace haka kuwa akayi,
a qaton gidan cikin jerin tagwayen gidajen aka kai
kowacce amarya gidanta, tym dinda alhaji
jafar,ismail, da uncle sukayi neman angwayen su
masu nasihohi basu samesu ba sai daga baya
suka sameau daya daya suka masu badan komai
a basuson su haduba sai dn kr suga junansu
bayan qawaye sun raka angaye kowane gidansa
sun watse, hussien yayi qarfin hali shiga inda
salma yayi mata sallama hade da ajiye mata
ledar da ya shigo da ita kana ya juya ya fita
yabar dakin kai tsaye dakinsa ya nufa, ya fada
kan luntsumemen gadonsa yana tuna hamida
batashi bace ynxu taxamo ta wani hr yake
wulaqantata...yayi saurin kauda tunaninta cos
ynxu taxamo matar wani,ya qudundune tamkar
wani mace acikin lallausan blanket
[6:55PM, 12/12/2015] Pherty: *
Gogan kuwa da kwalbar giyarsa ya shiga gidan,
yana tafe yana sha, tun bayan watsewar angaye
da qawayenta ta sauko tana kallon gidan
bata taba ganin gida mai kyau da tsari irinsa ba
ta window ta tsinkayo dayan gidan suna facing
juna komai iri daya ba banbanci tagwayen gidajen
sunyi matuqar birgeta, amma me batajin dadin
gidan tunda mai gidan ya nuna tsanar ta a fili
bayan a baya ya nuna mata so fiye da tunaninta,
ta boye damuwata ko ummanta bata gayamaba
tunda dama bata son hassan kuma umman ta
gargadeta tunda ta kafe akan hassan lallai idan
matsala ta taso tsakaninsu kada ta tunkareta
kada taxo mata da wata matsala indai akan
aurentane da hassan,
tuno wannan kalami na ummanta yasa ta sullale
na qasan falon tana kuka kamar ranta
tana cikin kukan ne ya shigo yana tangadi,
yanayinsa ya tsoratata batayi xaton an koma
gidan jiyaba a tunaninta komai ya kau ya daina
shaye shaye ashe kallon kitse takewa rogo, daga
inda take tsaye yaxo shiga sashensa ya taka
mata qafa da takalminsa
ta dan saki qara cike da xafin dataji amma bai
kulataba yi yayi da dai da duniya kamar babu
halittarta ya shige part dinsa ya bugo qofa jikake
gau.....
Hausa novel
[5:04PM, 12/22/2015] Pherty: [9:59PM,
12/14/2015] Pherty: TAGWAYEN MAXA
NA Fertymerh xarah
Da jan qafa ta isa dakinta, tsakiyar dakin ta xube,
kuka take sosai kamar ranta xai fita,
washe garin ranar ta kira ummanta kusan sau
uku koma fiye da hakan bata daga ba hankalinta
yayi matuqar tashi sosai, tafito daga wanka
daure da towel taji ana buga gidan da sauri ta
xira qaton hijabinta ta fito,
bata bude falon ba sai da ta tambaya waye,
muryar maigadi taji na magana cikin hanxari ta
bude masa qofar tana kallonsa bayan ta gaidashi
breakfast ne momy ta bada akawo masu ta karba
tana godiya, ya juya ya nufi bangaren hussaini.
tana jera kayan kan dianing taji motsin
saukowarsa kan step
da alama tashinsa daga barci kenan, kayan
barcine ajikinsa pyajamus,
ta dauke dubanta garesa tana cigaba da aikin da
yake
isowarsa wurin yasa ta dakatar da abinda take ta
gaidasa a raunane
bai amsaba bai kuma kalletaba illah yatsina fuska
da ya somayi yana kallon dianing
waye yayi girkin?
momy ta bashi amsa a taqaice
yace fyn an gud kana ya xauna ya soma ci batare
da ya kulata ba,
tsayuwa ta gagareta hakan yasa ta juya a
sanyaye ta nufi dakinta cike da mamaki itadai a
iya tunaninga batasan tayi masa wani laifiba
batasan dalilinsa na tsanarta a ynxu ba alhali ta
sadaukar da farin cikin mahaifiyarta saboda shi,
tana hawaye ta shige dakinta
56
Wata biyu ba abinda ya cnxa daga xamanta tare
da hassan kullum tana xaune cikin kadaici ba,
lokaci daya duk ta xame ta xama wata iri sanda
take yar aiki ma tafijin dadinsa akan yanxu dan
ma salma na xuwa ta debe mata kewa amma ita
konan da falo baya barinta xuwa ballantana
sashen salma
tana mamakinrashin jituwarsa da hussien duk da
batasan mafarin fadan ba amma ayanda tasan
tagwayen maxa batayi tsammanin akwai abinda
xai hadasu ba duk da abin ya shafeta ko taga
hussien ta gaidashi baya amsa mata hassalima
ko kallonta bayayi sai dai yayi shigewarsa ya
barta
ummanta kuwa da alama ta mantata duk yanda
takirata bata dagawa gashi hassan ya hanata
xuwa ko ina gwandama momy na xuwar masu
idan tasami lokaci
xaman ta da hassan sai dai muce Allah ya gyara
cos hali bai cnxa ba yana shan giyarsa, idan ya
fita aiki baya dawowa sai 6 idan ya dawo ba
ruwansa da ita baya kulata xai qara wanka yayi
shirinsa ya fice sai dare wataran ma batasanin
dawowarsa, duk ta rame taxama wata iri gwani
ban tausayi hrta soma dana sanin xabensa da
tayi
[10:16PM, 12/14/2015] Pherty: kamar kullum
kusan magrib salma ta shigo gidan itama a boye
take shigowa hussien ya hanata,
tace hamida ga wannan kiyi amfani dashi yana da
kau kuma yana gyara jiki
cikin rashin fahimta tace menene wannan?
tace na matane yana tada shaawa sosai idan
yaxo kishiga jikinsa koshi qarfene dole ya kulaki
amma kin xauna a gida kamar dutse bakida
mamora ke kika kyalesa wlhy, nima hussien ya
dauko min wannan rashin mutunci amma sai
dana saki jiki na shigesa sosai kinga duk
duniyarnan ba macen da yakeso kamar ni
dam gaban hamida na soma faduwa tayi rau rau
da idanu kamar xatayi kuka
tace salma ni ba wannan ne damuwata ba sakin
fuskarsa nakeso inaso yadawo da kulawarsa
gareni kamar da inaso ya taimakamin wajen bawa
ummana haquri, nifa bana cikin dadin rayuwa
baga miji ba baga uwata ba
salma tasaki ajiyar xuciya cikin tausayawa
hamida
tace nasani hamida mun xama daya nidake
banason na cigaba da ganinki haka, kuma namiki
alqawari gobe xnje inda ummanki insoma bata
haquri, amma inaso kisani shima hassan yanada
haqqi akanki kamar yanda kike da nasa, dama
xaman aure haka ya gada dole sai ana samun
haka, idan shi ya hau kesai ki sauko
hamida ta sunkuyarda kanta kawai
salma ta cigaba da fadin, inaso ki kwaci yancinki
da kanki hamida, kisha wannan maganin wlhy
baxan maki abinda xai cutar dake ba, kiyi wanka
ki feshe jikinki da taurare mai sanyin qamshi kije
dakinsa kijirasa....
hamida ta xaro idanuwa tana kallonta
tace so kike nayi kwanan asibiti yau
salma tayi shiru kawaikafin tace baki yarda dani
ba kenan baki yarda da abinda nake gaya maki
ba kenan kinason ki dore a hakan bakida wani
amfani a gidan dake da babu duk daya a gunshi,
kina xaune watarana xakiji yayimaki kishiya
nan da nan hamida na soma hawaye batada wani
xabi illa ta amshi maganin tasha
57
sun jima nan xaune salma nabata shawarwari
game da xamantakewar aure, kiran sallar.magrib
ya tadasu salma ta nufi sashenta da sauri kada
hussien yaxo bai sametaba, itama hamida ta
haura sama duk jikinta ya fara sanyi idanunta sai
lumshewa suke
[10:27PM, 12/14/2015] Pherty: A daddafe ta
qarasa sallah, wani irin yanayi takejin kanta, abu
takeji tun daga tsakar kanta hr tafin qafafuwanta,
tunda take bata taba tsintar kanta a irin wannan
yanayiba, shaawa ta tasomata sosai, ta kwanta
sai faman juye juye take kafin ta fashe da kuka
da tasan haka maganin yake da bata sha ba, ita
a tunaninta na gyara ne kamar yanda salma ta
fada mata, ta sauko daga saman gado, kitchen ta
nufa ruwa kawai takesha ba adadi, ba sauqi abin
hakan yasa ta fito harabar gidansu dai dai
lokacin mota ta kunno kai harabar gidan,
yana fitowa ta nufesa, idanunta a juye sunyi
jawur ta qanqameshi tana kuka tana roqonsa ya
taimaketa
hankalinsa inyayi dubu ya tashi ya soma kiciniyar
kwaceta daga jikinsa cikin tsawa
yace keee hermyderh me kike hakane kinada
hankali kuwa, hussien ne ba hassan ba ki bude
idanunki
kwata kwata bata cikin hayyacinta bata fahimci
komai daga maganarsa ba illah qara fashewa da
kuka datayi tana qoqarin shiga jikinsa dai dai
lokacin motar hassan na shigo gidan
nan hankalin hussien na tashi musamman lokacin
dayaga hassan ya fito daga motarsa, ya soma
kiciniyar rabata da jikinsa amma sai qara manne
masa take a harxuqe cikin bacin rai ya kai mata
wani gigitaccen marin da ya janyo hankalin
hassan garesu
qara tasaki sosai sai ga salma ta fito a guje,
ragwaf ta fadi wurin a sume bakinta na fitar da
jini,lokaci daya hassan da salma sukayo kanta a
rude.....
Hausa novel
22 December 2015 at 17:22 ·
[4:39pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: Edit · Delete
Fertymerh Usman > fertymerh xarah novels
[1:50PM, 12/26/2015] Pherty: 58 : TAGWAYEN
MAXA
Na fertymerh xarah
Hussien yaji uwa ya dora hannu aka ya saki ihu
ya shiga tashin hankali hr xufa ke karyo masa
mussaman lokacin da hassan ya dauki hamida
cak ya nufi motarsa da ita, salma na biye dashi
hankalinta a tashe sai hawaye take
wani kallo da hassan yayi mata yasanya ta
dakatawa da nufin shiga motarsa
tana kallo ya figi motar a xuciye saura qiris ya
kwasheta yabar gidan
salma ta qarasa gun hussien ta cakumo wuyan
rigarsa
tace kagayamin mekayiwa hamida meyasa ka
daketa? ya janyeta daga jikinsa kwata kwata
baya cikin hankalin kansa halin da hamida take
ciki yake kallo duk wani tsumi nata ya taso masa
sabon feelings yakeji game da ita ayau da jikinsu
na hadu
cikin mutuwar jiki ya bude motarsa ya shiga
itama salma da sauri ta shige......
[9:05PM, 12/19/2015] Pherty: *
kusan minti talatin kafin ta farfado lokacin momy
ma ta iso
tace sannu hamida, hamida ta lumshe
idanuwanta tana tunano abinda yafaru
salma taci amanarta ta cuci rayuwarta datasan
qudirin salma kenan akanta da bata amince da
itaba, gashi abinda ta janyo mata(hawaye suka
xubo mata)
meya sameki hamida,kukan me kike?acewar
momy
salma taxo ta riqa hannunta
tace laifinane amma kiyafemin hamida bnyi dan
cutardake ba
hassan ya qaraso fuskarsa a murtuqe yake
kallonta
yace laifinkine, kigayamin mekika mata
mekikayiwa matata wato baki kuka hada da
axxalumin mijinki dan acutar da matata ko?
ta girgixa kanta tana hawaye hussien na tsaye
bai tankaba amma ransa yayi matuqar baci
momy tace salma mekika mata ne?
ta soma sheshshekar kuka tana inda inda,
hamida ta tashi xaune ta xare drip din da aka
samata bata damu da jinin dake xuba a hannunta
ba ta sauko
menene haka ina kuma xakije?
cikin kuka tace gidanmu xnje inda
ummana,inason ummana inajin saboda tana fushi
danine na rasa jin dadin aure, naxabi hassan akan
ummana amma ya yaudareni sai ta fashe da kuka
hassan yace nooooo hamida ba yaudararki
nakeyiba c'mon momy kice tadaina wannan
kukan banaso ina fushi da itane saboda hussien
58
Amma hamida kigayamin gsky meye tsakaninki
da hussien meyasa naganki yau ajikinsa?
ba hamida ba gabaki dayansu tmbyr ta girgixasu,
baki bude idanunta na xubar da kwallah take
kallonsa
hussien yace sharrin da xakamin kenan, bayan
qiyayyar dakakemin hrta kai kamin sharri da
matarka
hassan ya yatsina fuska hade da daga masa
hannu
yace bada kai nake magana ba matata nake
tambaya kamin shiru? ya juya yana kallonta
yce hamida kigayamin gsky meyasa naganki yau
ajikinsa me...... momy ta katsesa a harxuqe
tace yimin shiru banxa, mekake nufi kada kace
kana xargin dan uwankane da matarka, na shiga
uku ni Asma'u sai ta fashe da kuka
stop crying momy,ba qaxafi bane nagansu da
idanuna i knw hamida baxata ci amanata ba
saboda nasan halinta, shikuma halinsane neman
mata.....
hussien ya soma hawaye xike da qunan rai ya
kasa gasgasta cewa dan uwansa ne hassan yau
k hantararsa, duk fadan da suke da hassan haquri
yake yana jure rashinsa amma baxai iya rayuwa
bashiba yariga yaxamo wani bangare na jikinsa
amma gashi hassan ya tsanesa saboda mace
yakasa yardarwa xuciyarsa ya rufe fuskarsa da
tafin hannuwansa duka biyu ya xube yana kuka,
kuka mai tsuma jiki hr cikin xuciya hassan kejiyo
kukan amma saboda bacin rai yasa yaqi nunawa
cikin wani irin yanayi salma ta riqo hassan
tace ba laifinsu bane laifinane kada ka xargi dan
uwanka da matarka wlhy hussien baisan komai
ba
[9:20PM, 12/19/2015] Pherty: da qarfi ya finciketa
yace angayamaki kowama dan iskane kamar
mijinki da xaki taba jikina idan bakisan aure ba ni
nasan darajjarsa kuma kije duk wanda yaci
amanata nabarshi da Allah ya juya ya fice yana
sharar kwallah
jiki a sabule cikin rashin dadi hamida taja
qafafunta danayi mata nauyi tafita daga asibitin
duk basu ankaraba
tana fitowa ta nufi motar ingawa....
59
Lokacin da ta iso ingawa kusan qarfe goma na
dare ta shiga gidan
kamar daga sama umma ta ganta nan da nan ta
daure fuskarta tayi shigewarta cikin daki
hamida batayi qasa da gwiwa ba ta bita hr dakin
ta tsugunnan daga can gefe idanunta fal da
hawaye
tace umma ya gida
shiru ba amsa
umma na sameki lfy
nan ma shiru
a sanyaye tace
umma dan Allah kiyi haquri ki yafemin
laifin me kikamin dakike neman gafarata,
ta qara matsowa gareta
tace kiyi haquri umma kiyafemin nagane fushin
kine ya janyomin halinda nake ciki dan Allah
kiyafemin kidaina fushi dani kona samu sassauci
a xuciyata
umman tace a yau kika tuna dani ynxu kikasan
dani saboda kin auri hassan kin sami abinda
kikeso mai kyau da kudi sai ynxu xaki tuna dani
cikin kuka tace Allah umma kina raina kece
xabina banida kowa a duniyarnan face ke, dake
na soma rayuwata koda natashi ke nasani taya
kike tunanin xn manta dake kiyi haquri umma dan
Allah
fuska a daure umman tace hamida tashi kibarmin
gida kitashi nace banason kalamanki
ta fashe da kuka mai tsanani tana roqonta amma
fafur taqi sassautamata akan sai tabar mata gida
ta koma can ga hassan din data xaba
umma hassan baya raina ynxu yafice min daga
xuciya ki tsaya ki saurari kukana ba wanda xai
tausayamin a duniyar nan face ke, ba wanda xai
sharemin hawaye kamar k da kike mahaifiyata
dan Allah kiyi haquri ki saurareni
nace hamida ki fita tun banyi mugun kalami
akanki ba......
a sanyaye hamida ta miqe tana kallonta tana
hawaye ta fito daga dakin
qofar gidan ta nufa ta xauna ta hade kanta da
gwiwa biyu tana kuka mi tsanani kamar ranta,
hassan shine sanadiyar batawarta da ummanta
tunda bata sonshi, hussien shine sanadin
tarwatse mata jin dadin aurenta
tabbas tayi dana sanin kasancewa da tagwayen
maxa, sun mata abinda baxata taba mantawaba,
bata taba kuka kamar irin wanda tayi a dalilin
tagwayen maxa ba kowane ya cutar da rayuwarta
tabbas tagwayen maxa sun mata illah a
rayuwarta
ta qara shigewa jikin cinyoyinta tana kuka sosai
kamar ranta........
sick ur prayer needed.
Hausa novel
[1:53PM, 12/26/2015] Pherty: [4:08PM,
12/22/2015] Pherty: TAGWAYEN MAXA
Na fertymerh xarah
Tunani umma tayi mai xurfi na ganin rashin
dacewarta akan abinda tayiwa yar ta koba komai
hamida kadai takeda a duniya kuma tabbas
fushinta xai janyo rashin kwanciyar hankalin
hamida
gashi batasan dalilin xuwanta ba a wannan daren
sannan ta korata idan hr hassan korata yayi tor
ina xataje a wannan daren
da wannan tunanin umma ta tashi ta fito a
hanxarce sai tasami hamida rakube taxo ta
tsugunna a gefenta hade da dafata
hamida ta dago da sauri tana kallonta idanunta
sharkaf da hawaye
umman ta kasa furta komai illah riqo hannunta
datayi suka shiga cikin gida.
*
Bayan fitar momy daga asibitin a harxuqe itama
sai salma ta janyo hannun hussien suka fito a
harabar asibiti suka sami hassan ya hada kansa
da motarsa da alama ya jima wurin
salma na jan hussien yana gocewa suka iso wurin
da qarfi ya fincike hannunsa daga gareta ya
nunata da yatsa dai dai lokacin hassan ya dago
kansa jin motsi a kusa dashi idanunsa jawur
saboda bacin rai
salma ta juyo da kallonta ga hassan
dan Allah kayi haquri ka saurareni wlhy badaniya
ko dan neman fitina nayi ba,
bai tankataba ya maida kansa jikin motarsa,
ganin haka yasa salma ta gayamasa gskyr komai,
ba hassan ba ko hussien sai dayayi matuqar
mamaki
tana kuka ta durqusa qasa tana roqonsu akan su
shirya kodan kwanciyar hankalin mahaifiyarsu
duk tagwayen suka dauke kansu sama lokaci
daya suka juyawa juna baya.
61
Kamar daga sama suka jiyo muryar momy na
fadin
maganata ta qarshe daku idan hr baxaku sasanta
kanku ba kudawo yanda kuke kamar da babu ni
babu ku xn yafe ku nafitar daku daga cikin
xuciyata koda kuwa sonku shine ajalina
[4:37PM, 12/22/2015] Pherty: Hassan ya soma
hawaye yana fadin amma momy ni....... ta daga
mashi hannu bana son jin komai daga gareka ba
xabi nake baku ba umarni nake baku idan hr
baxakuyi bane sai kuyi gaggawar sanardani ynxu
hussien yaxo da sauri ya rungume hassan, shima
baiyi qasa da gwiwa ba ya rungumosa amma
xuciyarsa a dagule take tunda baiga hamida ba
atare suka saki juna ya dubi salma yana fadin
hamida fa....
sai a lokacin suka lura bata nan hussien yace
inaji taje gida ne....
bayan dawowarsu gida suna tare su biyu hassan
ya dubesa
yace koyamin ynda ake soyayya ynda kakeyiwa
salma
hussien ya dan dubesa ta wutsiyar ido kafin
yace sai na koyama ne kai baka iya ba, tun
xamanku gidan mekake mata
ya yarfe hannuwansa yana yatsina fuska
yace komai bana yi mata shiyasa take fushi ban
taba xama tare da ita bane sannan itama inaji
bata iyaba tunda taqi ta koyamin
hussien ya kyalkyace da dariya, dariyar da ya
jima baiyitaba tun fadansu da hassan
ganin haka yasa hassan ya ciro masa wasu india
films yana fadin xn fara kallonsune nima na iya
soyayya
ya qara tuntsirewa da dariya, hassan ya tunxura
xai tashi ya riqosa yana fadin dan uwa maidasu
tukunna sai munje munyo bikon hamida xaayi
komai....
62
A cikin daren sukaje gidansu hamida duk da basu
sami hamidar ba amma umma tayi mamakin
ganinsu a daren
yau sai ga hassan anje inda umma an durqusa hr
qasa ana gaidata abin yabasu mamaki matuqa
hrdai ita ummar
hussien yafara mata mgn kan abinda yakawosu
umma tace duk da hamida taqi tagayamin dalilin
dawowarta nace baxata koma gidan hassan ba
dan bnsan wane irin xama take dashi ba
hassan yace umma ba abinda nake mata fa kawai
dan bana mata mgn ne ina fita gidan sai naga
dama nadawo shikadai nasani ko hussien ya juya
yana kallon hussien
haushi kamar ya shaqe hassan yakeji sunxo
gyara ya bata lamarin koda yake ya tuna halayyar
dan uwan nashi bai iya boye damuwarsa ba ko
sirrinsa shi komai direct yake yinsa
yacigaba da fadin amma umma ayi haquri xn
gyara nama gyara baxan qara barintaba duk inda
xamuje tare xnje da ita, ya tashi yana fadin ina
takene umma tana daki
kafin umma tayi magana tuni ya shige daki
tabishi da kallo cike da mamaki wai surukine
wannan, baki bude ta dawo da kallonta ga
hussien wnda saboda kunya kamar ya nutse
wurin
sai gashi ya fito janye da hamida tana gocewa
yana roqonta hr falo da qarfi ta fincike hannunta
ranta abace take kallonsa shikuma ya mariraice
fuska wai shi lallashi yake
ganin abin ba dama umma tace hamida dauko
mayafi kibisa gobe hussien yaxomi. dake inason
magana dake
ta gyada kanta tana hawaye taje ta dauko
hijabinta a harxuqe tafita yabi bayanta
umma tadawo da kallonta ga hussien hr a ranta
tasan hassan bashida nutsuwa shiyasa tayi
shaawar hamida ta auri hussien
[4:42PM, 12/22/2015] Pherty: shima ya tashi yayi
mata sallama ya fice, a waje yasamesu suna fada
shi lallai sai ya rungumeta a wurin ita kuma ta
kafe taqi
hussien yace kabari aje gida mana wai
meyasameka hakane
yaja dogon tsaki ya shiga motar itama hamida
tashiga baya suka fice
63
Suna isa gidan bata sauraresu ba tayi shigewarta
gida
sai suka kebe da hussien cikin mota......
daya shigo gidan yaje sashenta ya sameshi
garqame da makulli sai ya dawo ya xauna anan
falon ya ciro films dinsa yana kallo
[4:51PM, 12/22/2015] Pherty: washe gari cikin
shirinsa ya fito na xuwa office yaje sashenta yayi
saa a bude falonta yake sai dai bata ciki sai ya
nufi dakinta
tana xaune da littafin adduo'i ta ga shigowarsa
sai ta dauke kanta daga garesa
yace hamida baki shirya bane mekike jirane?
da mamaki take kallonsa
shirin me xnyi
yace office xamuje tare bakiji mena gayawa
ummanki bane nace baxan sake barinki ke kadai
a gidaba duk inda xanje tare xamuje
tace hrda office din?
yace eh mana kuma hamida u ar not a caring
wife ko dan girkinnan da mata kewa mijinsu da
safe bakimin ba ko bakya sona ne?
ta ajiye littafin ta tashi tana fadin tun farko
danakeyima ai bakaci ynxu kuma danme xnyi
yace yauwa hamida jiya kinqi bari na rungumeki
nasan kina kunyar hussien ne, kibari na
rungumeki ynxu i just want to feel dat thing.... ke
bakima sani ba ranar danaje gidanku na riqa
hannunki bakiji abinda naji bane shiyasa kikemin
wulaqanci
ya ajiye briefcase dinsa yana fadin come an hug
my hermyderh.......
Hausa novel Pherty: 64 TAGWAYEN MAXA
Na fertymerh xarah
Hermyderh ta dauke dubanta daga garesa
ya maida hannayensa ya sarqe
yace xakije?
ta girgixa kata ba tare da ta kallesaba hakan
yasa ya dauki briefcase dinsa ya juya bai sake
kulataba
bayan fitarsa ne da awa biyu hussien ya shigo
tunda taxo gidan sai yau ta ganshi cikin gidan
ya dubeta wani iri yace ki dauko mayafi kixo muje
inda umma kamar yanda ta buqata a jiya
hrta juya xata dauko sai kuma tadawo tana
kallonsa
tace bangayawa hassan ba,nima bnsan ynzu
xamuyi tfyr ba
yace karki damu kidauko kixo muje munriga
munyi mgnr dashi
ta juya taje ta dauko koda tafito hrya fita sai ta
samesa a mota tashiga
tym din dasuka xo ingawa bayan sun gama
gaisawa da umma sai ya fita yabasu wuri domin
su xanta
lokacin umma ta dubeta da kyau
tace hamida gayamin matsalar da kike ciki
gameda aurenki,gayamin meya dawo dake jiya
hamida ta sunkuyarda kanta qasa tana tsoron
gayawa umma abinda hassan ke mata tunda ko
banxa batasonshi sannan idan sukaxo suka
shirya suka daidaita tasan umman xata dore da
fushi da hassan sannan qiyayyarsa ma gareta
xata qaru haka yasa baxata gayamata ba....tace
kinyi shiru hamida kigayamin duk duniya bakida
wacce tafini bakida wacce xata share maki
hawaye kamar ni
Pherty: Duk da Allah s.w.a yace LA TAJASSASU
WALA YAGTABBA ADUKUM BAADAD kada kuyi
bincike kuma kada sashenku yariqa cin wani
sashe ma'ana kada wasu mutane su xauna
gulmar wasu mutane musamman akan binciken
mata da miji.
hamida ta dubeta da hawaye a fuskarta
tace umma ba komai, mun sami matsala ne kuma
jiya bayan.mun koma yabani haquri
umman tayi murmushi
tace naji wannan hamida duk da xuciyata bata
amince ba amma hasashenki najiya dakike fadar
dole ya sakeki baxaki xauna dashi ba karna sakeji
a bakinki
saboda haramunne mace tanemi saki a gun
mijinta batare da wai sababi ba sabod manxon
Allah s.a.w duk matar da ta nemi mijinta ya
saketa batare da wani laifiba tor ba ita ba
aljanna.......
ina gayamaki wannan ne ynxu saboda lokacin da
kikayi auren ban gayamaki ba kiyi biyayya tare da
qauracewa duk wani abu da kikasan baiso
wajibine mace ta yiwa mijinta da'a manxon Allah
yace duk mijinta daya kira matarsa xuwa
shimfida sai ta qi xuwa hr ya kwana yana fushi
da ita tor mala'iku xasu yita tsine mata hr xuwa
wayewar gari, namiji dan lelene kamar yaron goye
dole sai da rarrashi ballema miji irin naki da
shagwaba tayi masa yawa dole sai kinsa haquri a
xuciyarki da hakan xaki cimma ribar aure.
65
Ki tsare gsky aduk inda kike Annabi s.a.w na
cewa na umarceku da yin gsky domin ita qofae
acikin qofofin aljanna kuma na haneku da qarya
domin qoface acikin qofofin wuta kuma mutum
baxai kasance mai gsky ba hr sai an rubuta
mashi a wurin Allah shi mai gasky ne
kuma baxai kasance mai qaryabahr sai an rubuta
mashi a wurin Allah shi mai qaryane sannan ita
gsky da amana suna sawa mutum qima da
kwarjini a wurin jamaa,
inaso kiriqe gskyrki hamida ki kumasa tsoron
Allah a duk abinda xakiyi.
Pherty: Duk danasan kinada tsabta inaso ki qara
akan wadda kike da
ALLAH S.W.T yace shimai tsarkine kuma yanason
masu tsarki kuma baya karbar aiki sai mai tsarki
shi kuma tsarki bayayiwuwa sai ga mai tsabta
duk mutumin da bayada tsabta tor addininsa
akwai matsala
Allah s.w.t yace acikin al qur'ani
yaku dan adam kuriqe adonku yayin ko wacce
sallah, wato anaso idan mutum xaiyi sallah yayi
da kaya masu kyau masu qamshi saboda idan
kana sallah kana tare da mala'iku su kuma
tsarkakkune basa son qaxanta (tsabta nada
muhimmanci jama'a)
hamida ta dago tana kallon umman tata
tace nagode umma kin gayamin abinda ba
wandaya gayamin shi ina alfahari dake umma
umma tayi murmushi tana fadin hussien na jiranki
waje idan kindawo watarana xn qara gayamaki
wasu abubuwa gameda xamantakewar aure.
ta tashi tana murmushi
tace tor umma....tayi mata sallama suka fice.
66
Tunda ta iso gidan bata xauna ba
sai da ta tabbatar ta gyara gidan yanda takeso,
ta kammala girkinta ta jera a dianing kana ta
shiga wanka
Pherty: sanda tagama wanka ta shirya t fito falo
sai ta samesa ya fito sashensa da alama
masallaci xashi ynda taga yana sauri
tace barka da dawowa
da hannu ya amsa mata ya fice da sauri sai
itama ta koma daki dan yin tata sallar....
tana kan sallaya taji motsin shigowarsa ta tashi
ta fito falon tasamesa xaune
tace kaxo ga abinci....
ya dauke kansa daga gefenta yana fadin kyaleni
ai na kyaleki ko kema ki kyaleni
tayi murmushi ta xagayo ta bayansa ta
rungumesa a kunyace ta dora kanta a wuyansa,
ai kuwa saboda murna dadi kamar ya kashesa ya
tashi yana kallonta da dariya
yace wayace ki rungumeni ne?
tayi far da ido tana kallonsa
tace xokace abinci tukunna
taja hannunsa suka nufi dianing a kusa da ita ya
xauna ya shagwabe akan shi baxai ci abinci ba
sai dai tabashi yaci haka kuwa tayi sai da ta
tabbatar yaci ya qoshi ta tilasta masa xuwa yin
wanka
koda yadawo falonta batanan sai dai falon a
gyare yake hr qamshi k tashi mai kashe jiki
ya nufi dakinta yana lumshe idanuwansa yanajin
sonta a xuciyarsa
can ko ya hangota tsakiyar gado ido yasamata
yaga tayimasa wani irin kyau da kwarjini sai
sonta k fisgarshi
da sauri ya isa gareta ya hau gadon ya fada
jikinta
cikin murya qasa qasa ya soma magana
hamida ina sonki kece rayuwata
yakai bakinsa a kunnenta yana fada mata
maganganu masu ratsa xuciya da jiki(nidai pherty
banji komai ba amma tunda tsegumine halamcy
xata iya jiyoshi)
ya sumbaceta a kunne tsigar jikinta taji yana
tashi qamshin turarensa da sanyin dadi ya soma
kashe mata jiki ko banxa yau yayi matuqar
yimata kyau
tanaji ya soma shafata yayi qoqarin kai bakinsa
kan nata tayi saurin janyewa
a raunane yace menene hamida pls hamida
karkimin haka kece rayuwata karki barni tunda
bakyaso i promise baxan sake miki ba amma
kibarni na kwanta a jikinki
tausayinsa taji ya kamata kuma koba komai
mijintane yana da iko akanta,gaba daya ya karya
mata xuciya taji wani sabon sonshi na fisgarta
ta jawo hannunsa kamar qaramin yaro
xo twiny(yanda take kiransa),xo ka kwanta
nan ta dora kansa akan cinyarta tana shaqar
qamshinsa yayinda ya damqe daya hannunta ya
hada da nasa ya manna a fiskarsa
tausayinsa taji kamar tayi masa kuka ahakan hr
barci mai nauyi ya daukesa tana kallonsa tana
tunani...sai da barcin yayi nauyi sosai sannan ta
xame jikinta daga nasa ta kwantar dashi hade da
lulluba masa blanket kana ta sauka taje ta
kukkule ko ina ta dawo dakin ta kwanta kamar
mai jira ya jawota ya hadata da jikinsa
Asuba ta gari
Hassan & Hermyderh
Hausa novel
27 December 2015 at 08:18 · fertym
[4:40pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [11:08AM, 12/26/2015] Pherty: 67 TAGWAYEN
MAXA
Na fertymerh xarah
Washe gari da kyar ta xame jikinta daga nasa taje
tayi wanka ta shirya ta nufi kitchen sai da ta
kammala komai sannan ta nufo dakin lokacin ya
tashi daga barci
ta hau gadon tana fadin
tashi muje ayi shirin office na shirya maka
bathroom saura wanka
kallonta kawai yake yana murmushi,ta langabar
da kanta
pls mana my twiny
ta fada cikin muryar shagwaba
ya lumshe idanunsa batare da yayi mgn ba,
cikin murya qasa qasa tace twiny meyasa
kakeson hamida haka ita ba kowa ba bamai kyau
ba ko kudi amma kai gaka fari kyakkyawa bugu
da qari mai kudi HANDSOME SMART WITH A
GREAT PERSONALITY bayan xaka iya samun
dukkan irin macen da kakeso
ya jawota yana shaqar qamshin jikinta dana
gashinta
yace nikaina bansaniba but nasan hamida ta mai
kirkice tanada tarbiya da ilimin addini tanada kula
da boye sirrin mutum bayanshi bansan komai ba
amma ina sonki hamida promise to be with me
and make me happy forever
tayi murmushi kawai hr acikin xuciyarta taji dadi
ta riqo hannunsa suka sauko.......
bayan fitarsa ne salma ta shigo gidan, a dan
xamansu sunyi hira mai tsayi hr salma k fadin
bani labarin yadda akayi hamida mekikaji
cikin rashin sani mgnrta
tace lbrn mi
tace kina nufin komai bai auku jiya ba naganki
normal.fa gayamin baimaki komai bane hr ynxu
hamida tayi shiru kafin ta dubeta
tace salma bari nagayamaki wani abun da baki
saniba koda ace abin yafaru kobai faru ba baxan
gayamaki ba cos sirrin mijina ne
manxon Allah yace mafi sharrin mutane wurin
Allah ranar alqiyama sune namijin da yake biyan
buqatarsa da matarsa itama ta biya buqatarta da
mijinta sannan dayansu ya watsa sirrin dayansu
68
Amma wannan abin yaxama ruwan dare a ynxu
da yawa yan mata amare idan sunyi aure xakaji
suna baiwa qawayensu lbrn abinda yafaru d
mijinsu,
ynxuma grup ake budawa na matan aure xallah
aciki xakaji kowacce macce na fadin yanda ta
kwana da mijinta(ba wai nace duka grup na
matan aure ba)sannan inbanda mata suke mata
ke bakisan mutum ba bakisan ko wacece ba
haduwar internet xakije kina gayamata sirrinki
kikasan ko ita wacce irice kikasan mayyace ko
aljana saboda mutum ynxu baa shaidarsa hrdai
wanda baka sani ba but for now mata sun dauki
trust dinsu sunbaiwa matan internet suna dauka
yanda suka kwanta da mijinsu suna gayamasu tor
wlhy kudaina kuji tsoron Allah
[11:35AM, 12/26/2015] Pherty: hamida tayi ajiyar
xuciya tana kallonta
tace nasani salma kinfi kowa damuwa da aurena
kinaso na daidaitu da hassan amma ke meyasa
bki gyra taki rayuwar aure meyasa kike hangen
nawa auren bayan naki baki gyaraba, inafa sane
keda bakinki kika gayamin hussien na nemanki
kina qi
tor meyasa kike haka meyasa kike hana masa
haqqinsa alhali kinasonsa kika aureshi shine ma
baya sonki
annabi yace haqqin miji akan matarsa kada ta
qauracewa shimfidarsa ta kubutar da ratsuwarsa
sannan tabi umarninsa kuma kada ta fita sai da
ixininsa sannan kada ta shigo masa gida da
abinda yake qi
a wata fadar ma yace mafificiya daga cikin mata
itace maccen da mijinta idan yayi dubi xuwa
gareta sai ta faranta masa rai ma'ana tayi masa
murmushi idan ya umurceta sai tayi masa daa
idan bayanan sai ta tsare kanta da dukiyarta....
69
Sannan kin furta da bakinki cewa bakya masa
girki sai dai kisa wata mai aiki tayi masa akan
me salma
duk abinda kikawa mijinki lada ne, kallonsa lada
ne, murmushi lada ne,ki gyara masa shimfida
lada ne, ki masa girki lada ne, kiyi masa
shagwaba lada ne, kimasa kuka lada ne
annabi yace idan mace ta wanke tufan mijinta
Allah xai rubuta mata kyawawan ayyuka guda
dubu ya shafe mata miyagu guda dubu duk
abinda rana ta fudo akanshi yana nema mata
gafara sannan a daukaka darajarta sau dubu
Allah kabamu ikon yi amin
k bakiji wata kissa ba inda Aisha R.A take cewa
ya manxon Allah menene mafi haqqi acikin
mutane ga mace?
annabi s.a.w yace mijinta
a wata fadar ma nana aisha r.a tace annabi ya
kasance yana horo na da in daura towel yayi
xoxayya dani alhali ina cikin jinin haila, dan haka
mukula da haqqin miji akanmu musan irin yan
dabarun nan na mata......
amma meyasa macce dan anmata auren dole ta
riqa gallaxawa mijinta acewar wai dan bata
sonshi, k namiji ya furta yana sonki ya
wulaqantaki ballantana keda kika furta bakisonsa,
aure anriga an daura ba yanda xakiyi ki rungumi
qaddara ki rungumi mijinki ko kin rabu dashi
kinxama qaramar baxawara kuma yasha dake
koda bai maki komai ba
[12:07PM, 12/26/2015] Pherty: ballantana
wannan rayuwar duka duka nawace xai mutu ya
barki ko keki mutu kibarshi idan mijinki baya
yarda dake kin mutu kinje lahira dame xakiyi
taqama, duniya makarantace ba gida ba an
turomu karatune duk wanda yayi karatu mai kyau
xaiga da kyau a lahira dama rayuwar aure xomu
xauna xomu saba dole sai ankai xuciya nesa anyi
haquri sannan komai xaixo da sauqi
70
Akwai inda annabi ya taba cewa da yar'sa fatima
idan bakiyi hankaliba fatima sai wata macce anan
gefen madina ta rigaki shiga aljanna
fatima ta shirya taje gidan matar nan da nufin
taje ayi mata kitso nan kuwa taje ne kawai don
taga matar
anan fa taga yanda matar take tsananin biyayya
ga mijinta saboda da farko dataje
tace naxone kimin kitso
sai matar tace koma sai nagayawa mijina
fatima ta koma da mijin ya dawo ta gayamasa
yace haba dai kiyi mata mana diyar shugaban
halittace fa.
da fatima ta tashi dawowa sai taxo tare da
hassan
sai matar tace a'a ai ban gayamasa da hassan
xakixo ba sai ku koma sai nagayamasa,daya
dawo tagayamasa yace ya yarda
da nana fatima ta tashi dawowa sai taxo da
hussaini amaimakon hassan
sai matar tace aini da hassan nagayamasa xakixo
bada hussien ba dan haka kikoma sai
nagayamasa,
da mijin ya dawo ta gayamasa sai
yace koda da duk yan gidansu xataxo tor kimata
kitso
da fadima taxo aka fara kitso sai ga mijin nan ya
dawo matar ta turata daki ta rufe labule
tace shige kada ki ganar min miji,fatima na kallon
yanda matar ke girmama mijinta da tarairayarsa
kuma annabi s.a.w bayagayawa fatima cewar
matar xata rigata shiga aljanna dan ita fatimar
bata biyayya bane aa sai dan ta dada sanin cewa
girman miji agun matarsa ba abune mai sauqi ba
(kuma ku qara akan ynda kuke masa)
bama mace kawai ba hrku maxa annabi yace
namiji shine mai tsayuwa akan matarsa shike da
iko akanta
a wata fadar ma yace ku tausayawa mata kuma
ku kyatata masu babu wulaqantacce face mai
wulaqanta mata,sannan babu mai girma face
wanda ke gimama mata
a wata fadar kuma antabayi annabi shin xama
tare da iyalinka shi yafi maka ko kuma xama a
massalaci? sai yace maxa sa'a guda kacal tare
da iyalina shiyafi soyuwa gareni daga ittiqafi a
masallaci.......
salma ta dakatar da ita tatashi tana fadin ina
xuwa saboda koda naxo nan gidanki batare da
ixininsa bane idan yadawo yabarni anjima
xandawo
kafin hamida tayi mgn tuni ta fice sai ta bita da
kallo kawai
[1:42PM, 12/26/2015] Pherty: [1:37PM,
12/26/2015] Pherty: *
71
Tundaga tym din hussien yaga canji daga salma
irin kulawar da take bashi yaxamana ya manta da
hamida a xuciyarshi ya dawo ba wadda yakeso
kamar matarshi salma
Hassan an sami abinda akeso kullum ana maqile
da hamida komai hamida ko ina yaje hamida
farinciki kwanciyar hankali daukaka ya sauka a
TAGWAYEN MAXA
bama suka dai ba hr iyayensu kuma suna masu
yi masu fatan alheri da addua Allah ya cigaba da
kawo masu farinciki a rayuwarsa
salma ta fara haihuwa tasami duka mata twins,
wata biyu tsakani hamida ta haifo nata twins
aka sami wasu TAGWAYEN MAXA
ranar biki anga qawaye iri iri bama kamar
halamcy da baa gayyataba, amma su sady, miss
aysher, xarah dange, matar saif, ammi lurv, kdeey,
baby aysher da kausar,unique da hssina, mamu
da namcy, sally,m.boy, mahasin da nusee da duk
wanda ban fada ba yayi haquri ban manta dashi
ba yana raina hrdama masoyan tagwayen maxa
da duka members dina gabaki daya duk a
hangosu
HAUSA NOVELS 1,2&3
NISA'UL JANNAH 2
MATA MASU DUNIYA
TASKAR MARUBUTA
MATAN KWARAI
UNIQUE NOVELS
duk ban barku baya ba da duk wani grups ma
Na sadaukar da wannan littafin ga Ammi Bari'ah
marubuciyar AMARYAR PHERTY da PHERTY
72
Shin addini yayi gsky da yace ba lallai bane ka
sami duk abinda kakeso ba arayuwa ka xauna lfy
kamar yanda ta faru da SERLYMERH
(makauniya)......
Yaushe ne soyayya takeyin tasiri a xuciya ta
wanxu batare da sanin juna ba wanda daga
humayd hr afra baxasu iya fassarata ba a littafin
AFRA HUMAYD.....
Soyayya ba lallai ta faru a sanda akaso faruwarta
ba
ita wata irin abace daba ruwanta da lokaci
matsayi da dangoginsu
abuce wadda k faruwa a duk sanda taso ta
gudanar da tunani ta sarrafa gngar jiki kamar
yanda tayiwa ZARAH da Dr.Saifullahi Bakori
Ta taso cikin tarairaya gaa da shagwaba a gidan
arxiki mulki da bunqasa , babu abinda tasani sai
taqama isa da wulaqanta dan adam
haduwarta da Bilal ya sauya mata raayi inda duk
isarta mulkinta dataqamarta suka xube a qasa
IHSAN
Haduwar kan hanyace ta xamo haduwar xuciyar
Abdulsalam da Falmata ,aminci, tausayi, soyayya,
ha'inci da xalunci sune suayi gingimemen gini a
rayuwar ALMAJIRA
Abin tambaya acikin rayuwar JIDDAH meyasa
kowacce bata auri wanda takeso ba amma ta
samo soyyaya a gidan aurenta mami da jidda
Soyayya ko sadaukarwa wanene yafi rinjaye a
rayuwar AFNAN tsakanin Adnan da Affan
Pherty tace xata iya fassara ta ta soyayya da
defination mai yawa a LABARINA wanda neither
Dr.fulani Gafai nor Marhoom experience it.
Dariya take sosai ba kakkautawa kafin ta tsaida
dariyar tana kallonsa
tace ka ceto ni daga cikin wani hali dana shiga
duk da cewa kaine sanadin haukata kuma kaika
dai nakeso nake kishi baxan iya kwatanta ganinka
da wata macce ba....
Humayd Danbatta yayi murmushi hade da
rungumota yace ba wadda nakeso nake qauna a
duniyarnan kamar ke bakida kishiya ke kadai kin
isheni rayuwa kuma bake ba hauka har abada ina
sonki HERLYMERTU
Menene sirrin pherty, miss aysher da serdy daya
janyo suka xamo taurari masu haske da walqiya a
xukatan xaratan maxajensu koda yake sun
auresune bisa tubali na soyayya SADTEEYASH
TAGWAYEN MAXA ne,kamanni daya amma
mabambanta a halayya da dabi'a duk da
kasanvewarsu gida daya amma they ol acting
according to their experience,xamansu da Hamida
ta sauya tunaninsu daga marar kyau xuwa mai
kyau....
Daga inda pherty take xaune ta maido hankalinta
ga jinin sarauta inda taji yana roqon Affiya kiyi
haquri na tuba kece rayuwata qasaita ta a waje
take baa gida, idan a gidane affiya keda qasaita
ita keda ragamar komai nawa.
ta juyo tana kallonsa da murmushi tace hrda
MULKI KO SARAUTA? ya gyada kai yana
murmushi
ALHAMDULILLAH
Qarshen littafin TAGWAYEN MAXA
Much luv to.masoyan littafaina da duka members
dina na pherty Novels
adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *