Gude yake sosai saman dokinsa, fari tass dashi, dokin ba wani kwalliya aka masa ba, linzami ne
kawai sai sirdinsa, dokin shima da alama ya saba da maishi, sabida yanda yake bada had'in
kai ake gudu ba sassautawa, sai tsallake abubuwa yake, da kin ganshi kinsan yana cikin
nishadi, alamar baida matsalar komai a rayuwarshi, yayi gudu sosai, har saida yakai
dai-dai wata bishiya, sai kuma naga dokin ya tsaya da kanshi ba tareda mahayin ya ja
linzamin dokin ba, haniniya dokin yayi ya wani 'aga k'afafuwansa na gaba sama, sai naga guy
d'in da ke saman dokin yayi murmushi yace "bravo my maverick "(sunan dokin kenan) Ya
sauko saman dokin yabi wani sak'o yadan gangara kad'an dokin nashi yana biye dashi, sai
gashi gaban wani babban rafi, ya kalli ruwan yayi murmushi, ya tsinko wata flowers ya rik'a
wurgawa a ruwan a hankali har ya wurga ta k'arshe, ya bita da kallo saida ta k'ure ma
kallon sa, tsugunawa yayi gaban ruwan yana kallon su suna gudana, farare tas daga, daga
wani dutse suke fitowa suke biyowa hanyar suna wucewa, yakan zo nan ne, dan gun yafi
flowers, so ya fi sakashi nishadi, a hankali ya saka hannun sa a ruwan, ya d'ibi ruwan ya
watsa ma dokin sa a fuska, sai naga dokin shima ya matso ya shiga ruwan yasha ruwan
ya fito, ya mik'e tsaye, ya shafi dokin nasa sai kawai suka fito, ya tsinko wata flower, yana
tafe yana wasa da ita, sunyi tafiya mai d'an nisa shida dokin sa, sai da flower hannun sa ta
k'are sannan ya hau dokin sa, suka fara gudu bai tsaya ko inaba ba sai wani babban gida,
mai kamar gidan gona, ya shiga ciki kai tsaye, haniniyar dawaki kawai naji, it same like duk KARANTA CIKAKKEN LABARI