Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, June 4, 2018

bintu complete hausa novel

adsense here
bintu complete hausa novel

BARKA DA SALLAH....!!!!

             ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

   (Ayimin afuwan rashin zuwan Yar Fillo, Allah bai nufa ba adalilin binciken da ba'a kammala yi ba akan abinda ya shafi sak'on da akeson isarwa. A cigaba da tayamu addu'a...Allah Yayi mu fidda litattafanmu.. Ameen..)
 

 
'Yar budurwa ce mai shekaru goma sha bakwai a duniya, kana ganinta ka san rainon k'auye ce. Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa holan. D'inki na zamani ya zauna d'abas a jikinta, maimakon ta d'ora d'ankwalin sosai, sai ta rufe gashinta gami da sak'alo jelolin d'ankwalin ta wuyanta ta k'ullesu. Fuskarta fayau babu ko d'igon kwalli, wannan ya janyo bayyanar 6acin rai k'arara a saman fuskarta. Ita kam an takura rayuwarta a birni, Mami ta hanata shafa ko hoda, a ganinta ta kai minzalin da ya dace ace tana kwalliya, tana tsayawa da samari kamar sauran k'awayenta da ta barosu a k'auye, duk domin a matsawa rayuwarta da karatun bokon da ta tsana, na islamiyyar ma da ya Innarta ta ke turata ballantana wani bokon nasara.
   Ta ja tsaki a daidai lokacin da ta k'araso babban falon Mami na saukar bak'i don kiran Anti Asma'u, kamar yanda Mamin ta umarceta. Saidai me? Ta yi turus ganin Anti Asma'u zaune tare da Yaya Ma'aruf a gefenta suna hira cikin murya k'asa k'asa.
  Ta gwalalo ido ganin Yaya Ma'aruf ya saki fuskarsa sosai sai faman doka murmushi yakeyi har hak'oransa sun gaza 6uya. Ta dubi tazarar dake tsakanin masoyan biyu, ba wata tazarar azo a gani ba, kai zaman ma da sukayi ya 6aci.
  "Tab! Ana iskanci a birni." Ta fad'a cikin k'ank'an da murya. Ta bud'e baki zatayi magana sai kuma ta fasa ganin Yaya Ma'aruf ya rik'o hannun Anti Asma'u, da saurinta ta sanya hannu ta rufe bakinta gami da k'ara la6ewa jikin kakkauran labulen dake a falon wanda ya hanesu ganinta, hakanan ko kad'an basu ji motsinta ba.
   Abin mamaki, Anti Asma'u ko a jikinta, sai ma dariya da takeyi har tana k'ok'arin fad'awa jikinsa.
   Aikuwa tayi wuf ta fito daga ma6oyarta.
   "Innalillahi!" Ta fad'a da k'arfi tana mai d'ora hannuwanta a ka, a firgice suka dubeta, sam basuji motsinta. Ma'aruf ya ja mugun tsaki. Sam! Ya k'i jinin yarinyar, bata da kan gado. Ita kuwa tuni ta soma ja baya zata fice, ai kuwa kamar yasan niyyarta ya yi azamar mik'ewa ya cafkota.
   Ta runtse ido. "Wayyo na shiga uku! Don Allah Yaya Ma'aruf kayi ha.."
  "Shii!!" Ya dakatar da ita ta hanyar sanya yatsu biyu a saman la66ensa. Ya zaro idanuwa yana dubanta fuskarsa a murtuk'e, ita kuwa  Anti Asma'u tuni ta mik'e tsaye ta zari mayafinta gami da gyara zamansa sosai a jikinta. Babu inda baya rawa a jikinta, tana bala'in tsoron Yaya Ma'aruf, domin ko kusa baya shiga sha'aninta. Tafison Yaya Rufa'i sau dubu akansa. Haka kuma sunfi shak'uwa.
  Durk'usawar da yayi a gabanta ne ya sanyata k'ara rud'ewa, kallo d'aya tayiwa fuskarsa tayi saurin mayar da dubanta ga Anti Asma'u wacce ke k'ok'arin ficewa, daga falon da saurinta, da alamun kunyar ganin da Bintu tayi musu a tattare da ita.
   Jin ya kama kunnenta da k'arfi ne yasa ta sakin k'aramin k'ara, k'afafunta suka d'auki rawa tana mai runtse ido don azaba.
  "Wayyo, don Allah kayi hakuri Yaya, wallahi bazan k'ara ba."
  "Tun yaushe kike mana la6e?"
Tuni ta soma hawaye, sai k'aramin tsalle takeyi amma bai saketa ba. Dakyar ta girgiza kai cikin muryar kuka ta amsa. "Ni ba la6e nakeyi muku ba, Mami ce ta turoni kiran Anti Asma'u, kwarankwa..."
  Ai bata k'arasa ba ya make bakin, bayan ya saki kunnen.
  "Ban hanaki wannan rantsuwar ba? Idan na k'ara jin kin min rantsuwa da kwarankwatsa sai na 6allaki. Sannan ki bud'e kunne ki saurari kashedin da zanyi miki."
  Ta bud'e idanu tana dubansa, sai kuma tayi saurin sadda kanta tana mai cigaba da kuka  ciki-ciki.
  "To." Ta fad'a, ya jinjina kai.
"Good." Ya mik'e ya koma saman kujera ya zauna kafin ya dubeta.
  "K'araso nan ki durk'usa."
  Ba musu ta k'arasa ta durk'usa fuskarnan kamar kace "Arr!" ta arce.

¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<02>>

Ya kwashi mintuna k'alilan yana mai danna wayarsa, ita kam ta k'agara ya barta ta tafi. Can kuma ta tsinci muryarsa.
  "Ko da wasa, ko da wasa naji kina bawa wani labarin abinda idanunki suka gane miki yanzu, sai na yanke kunnuwanki. Kinji abinda nace ko?"
  Da sauri ta gyad'a kanta, gaba d'aya jikinta rawa yakeyi.
   "Tashi ki wuce."
  Abinda takeson ji kenan, da gudu ta mik'e zata fita. 
   "Ke!!!"  Ta juyo a firgice. Ya rik'e kunnensa kad'an.
  "Ko Mami kada na sake naji kin sanarmata."
  Ta gyad'a kanta ta fice.
A falo ta sami Mami zaune tare da Anti Asma'u sai Yaya Rufa'i da 'yar uwarta Aisha da suke sa'annin juna.
   Ta k'arasa shigowa tana kumbure-kumbure, ga hawaye sha6e-sha6e a saman fuskarta, wannan ne ya katse hirar da sukeyi. Ita kuwa Anti Asma'u gaba d'aya ta rud'e, tsoronta bai wuce abinda zai fito daga bakin Bintu ba. Yarinya akwai fitina, kada ta tonamata asiri.
   "To sarkin kuka, ke da wa kuma?" Cewar Mami tana kallonta.
  Bintu ta k'arasa gefen Yayanta Rufa'i ta zauna. Bata kai ga magana ba sai ga Ma'aruf ya shigo fuskarnan a murtuke. Ya nemi waje ya zauna a d'aya gefen hannun Rufa'i.
   Mami ta dubeshi kafin ta k'ara duban Bintu. "Bintu keda wa? Me ka yi mata yau kuma?" Ta maida zancen kan Ma'aruf, sun san kukan Bintu, bai wuce adalilinsa. Shine kawai tasu bata zo d'aya ba a gidan, baya ragamata ko kad'an.
  Ya d'aga kafad'a "Rashin kunya tayimin, na kama kunnenta nayi mata kyakkyawan gargad'i."
  Bintu ta dubeshi ya harareta da sauri ta k'ara 6uya ajikin Rufa'i.
  "Haba Yaya, me Bintu zatayi maka mai zafi kayimata hukunci haka? Mami kinga yanda kunnenta ya fashe, da farce ya kama mata." Fad'in Rufa'i kenan bayan ya duba kunnen. Ransa duk babu dad'i da abinda yayansa ke yiwa  Bintu, kamar ba jininsu ba.
  "Zo mugani." Ta k'arasa ga Mami. Bayan Mami ta ga wajen, ta dubeshi cikin 6acin rai, "Kai dai baka kyautawa abinda kakeyi, to wallahi ka kiyayeni. Koda wasa kada ka k'ara yi mata hukunci irin wannan. Ni ban yarda ma da abinda ka fad'a ba, nasan halin yarinyar nan, bata da tsiwa..."
Sai kuma tayi shiru, ta girgiza kai ta kalleshi "Koda tana da tsiwar ai ba yi maka takeyi ba inace dai?"
   Yayi shiru baice uffan ba, ganin da gaske Mami ba shirun zatayi ba yasa ya mik'e ya dubeta.
  "Kiyi hakuri Mami." Ta kauda kanta kawai ta maida ga Asma'u.
  "Tafi da ita d'akina, akwai mentholata ki shafa mata."
  A kunyace Asma'u ta mik'e, Bintu na kallonta. A ranta tana fad'in.
  "Oh, dan Allah ji yanda take sunne kai yanzu, hum."
       Bayan shigarsu d'akin, ta janye hannunta daga na Asma'u. Anti Asma'u ta dubeta da murmushi sannan ta nufi gaban madubin Mami.
  Bintu ta hakimce saman stool tana kallonta. Asma'u ta dubeta ta madubi tayi d'an murmushi sannan ta juyo ta dawo gabanta ta durkusa. Ganin haka Bintu ta turo baki gami da dauke kanta, ita haushi take bata ma.
   "Bintu, bakisan Yaya Ma'aruf mijina bane?"
  Jin furucinta ya sanya Bintu dubanta baki sagale. Amma a 'yan iskan ma Anti Ma'u ta daban ce. Daman haka miji da mata sukeyi? To duk ba haka ba, ita bata da labarin anyi bikinsu ma, ballantana ta ga Innarta ta halarta. Wannan kawai k'arya ce, abinda Mami ta gayamata ko hannu namiji ya rik'e maka zakayi ciki ka haihu? Lallai ma.
   "Latsi." Cewar Bintu a fili tana mai jinjina kai gami da jan majina don har lokacin ta kasa sakin ranta. Abin ya kusan bawa Anti Asma'u dariya, ta gimtse. Shakka babu, an d'aura mata aure da Ma'aruf wajen watanni uku ma, akwai dalilan da yasa ba'ayi tariya dai. Ta mik'e sanin da tayi ba ganewa zatayi ba.  Ta lakuto man ta nufi kunnen tana fad'in "Yayanki mijina ne, ya ci ace a shekarunki na sha bakwai kinsan menene..." Sai kuma tayi shiru, Bintu babu kan gado, ba k'aramin aikinta bane ta nufi Mami da tambayoyi. Ita kam, ta fasa yini yanzu zata zo ta wuce tun kafin tayi mata wata ta6argazar.
    Kamar kuwa ta sani, Bintu gaba d'aya ta jefa kanta kogin tunani. Ta hau cin farcenta, wai aure, ta k'ara tunano abinda ta gani, ta girgiza kai kamar wacce ta watstsake daga bacci ta dubi Anti Asma'u. Ai da sauri itama ta dakatar da ita.
  "A'a, karki k'ara wata magana zan had'aki da Mami. Idan kiga bari ta ji wannan maganar dukanki zatayi, Mami ta tsani la6e."
  Ta numfasa kawai ta kyaleta.
                        * * *
  Zirga-zirga kawai Bintu keyi a d'aki, a fili take magana.
  "Na tambayi Yaya Rufa'i?" Ta girgiza kai. "Kai a'a, kada shima ya zaneni." Ta zauna gefen gado tana cin farce, cikin ikon Allah sai ga Aisha ta shigo tana kiranta. Ganinta yasa tace "Au, kizo wai zamuje siyo takalmin sallah inji Yaya Rufa'i." Ai da sauri ta mik'e, ta janyo hannunta.
  "A'i, au yi hakuri namanta, Aisha, gayamin wani abu."
  Aisha ta nutsu ganin yanda fuskar Bintu ta nuna dagaske tambayar zatayi babu alamun shashancin nan tattare da ita.
  "Mene?"

[7/20, 9:56 PM] Aysha Abe:  ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<03>>

"Anti Ma'u da Yaya Ma'aruf wai an d'aura musu aure?"
  "Lallai, baki da labari? Ai tun kafin ya tafi bautar k'asa akayi aurensu. Nan gaba zaayi biki. Ai Inna ta sani."
   Bintu dai bata gamsu da wannan kad'ai ba, saidai ta chanja akalar tambayar daga wacce tayi niyyar yi a farko.
  "To gayamin, ai Mami dagaske takeyi idan namiji ya kama hannuna zanyi ciki ko?"
  Aisha ta tuntsire da dariya, bata mantawa, itama Mami ta gayamata haka a baya, don kuwa ta zama budurwa tun tana da shekaru sha uku a duniya, watakila kuma hakan yana da nasaba da cimarsu da yanayin hutun da jikinsu ke samu, idan an ajiye wannan ma, Aisha Allah Yayi mata baiwar hankali, hakanan tana da ilimin addini daidai gwargwado, ana koyardasu duk wadannan hukunce-hukunce da sauran abinda ya dace su sani a addinance.
   "Ke Bintu, ana fad'a ne fa kawai don a tsoratar. Ni ki kyaleni da wadannan tambayoyin, Yaya na jiranmu kada yayi fad'a." Ta wuce da sauri don d'aukar mayafi.
   "Toh amma.." Ta katse maganar da tayi niyya sakamakon tunawa da gargad'in Yaya Ma'aruf gareta.
  "Ki dauko mayafi, zamu biya mu sauke Anti Ma'u a gida sai mu wuce."
   Dole ta nufi kayanta itama, bayan sun shirya suka fito, a tsaye suka sami Yaya Rufa'i da Mami, tana ba shi sak'o. 
   Aisha ta ja hannunta, "Zo muje wajen Anti Ma'u mu jira tana waje."
  Suka fito, saidai a 'yar baranda suka iskesu da Yaya Ma'aruf, da sauri Bintu ta tsayar da Aisha suka la6e kad'an. A ranta tana fad'in asirinsu dai zai tonu yau idan itama Aisha ta ga sunyi wani abin.
   Yaya Ma'aruf sukaji yana fad'in.
"Banyarda da wannan satar kallon ba na gulma, ke har yau kin kasa sakin jiki ki dunga kallon kwayar idanuna sosai..."

  Basu kai ga jin k'arashen ba, Aisha ta figi hannun Bintu suka koma baya.
  "Wallahi babu kyau la6e ba ruwana, kenan d'azu ma la6e kikayi ya kamaki ko?"
  Ta harareta  "Banza, so nakeyi kiga wani abu amma basuyi ba kika wani janyoni, zo mu koma kigani." Ta rik'o hannun Aisha, Aisha ta fisge ta k'ara janta baya.
  "Wallahi baruwana, bazamu koma ba."
  "Ke bakiji wani iskanci ba ma, wai ta kalli kwayar idanunsa. Nasan harararnan zaiyi mata."
  Aisha tayi dariya.
 "Ashe na fiki sanin abubuwa Bintu, lallai ke da sauranki. Ai kallon soyayya yake nufi. A shirin RAI DANGIN GORO naji Ahmad Isa yana fad'a, wai da saurayin ya kalleta saida ta ji yarr, wai ta sauke idanunta saboda ba zata jure kallon kwayar idanunsa ba."
   Bintu ta tuntsire da dariya. Yi takeyi tana k'arawa.
   "Rainin hankali. Kalleni to mugani."
  Ta gwalo mata idanuwanta, Aisha ta ja tsaki tana dariya.
  "Ke dallah, sai da namiji wanda kakeso."
   Bintu banda dariya ba abinda takeyi don abin dariya yake bata, suna tsaye sai ga Yaya Rufa'i.
   "Au, maimakon ku shiga mota kuka tsaya anan?"
  "Yauwa Yaya Rufa'i. Muga ida..."
  Da sauri Aisha ta toshe mata bakin tana dariya.
  "Ke wallahi ba'a sirri dake. Sirrine fa."
  Yaya Rufa'i yayi dariya.
 "Menene abin? Yau kuma ni kuke yiwa 6oye-6oye?"
  "Yaya ba haka bane, sirri na bata ai babu kyau fad'awa wani kuma."
  "Shikenan ai, ku muje, inaso naje amso d'inkuna na ne."
  Suka kama hanya, har lokacin Yaya Ma'aruf na tsaye da Anti Asma'u. Yaya Rufa'i ya tambayeshi "To, ko mu tafi zaka kaita?"
  Yaya Ma'aruf ya gyad'a kai, "Yeah kuje kawai."
  Bintu ta kalleshi, ya bita da harara ta dauke ido. Wai wannan idan Anti Ma'u ta k'ura mishi ido, ai sai ya sanya ta firgice.
  Koda sukaje nan ma Bintu saida ta tsaya ruwan ido, a k'arshe ta za6o mai shegen tsini, duk yanda Yaya Rufa'i da Aisha suka so hanata d'aukarsa ita kuwa ta dage lallai shi takeso. Dole suka kyaleta, ganin haka ya k'aro mata da wani flat mai kyau da rangwamen kud'i.
   Murna ya cika Bintu har gwalo take yiwa  Aisha.
  "Wani abin ma sai gobe."
 Aisha tayi dariyar mugunta "Zakiyi bayani ne."
                         * * *
             RANAR SALLAH...!
 
 
[7/20, 9:56 PM] Aysha Abe:  ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<04>>

Tun bayan sallar asuba, Bintu bata koma bacci ba.  Zama tayi tare da su Mami dake aikin girke-girken sallah tana tayasu da hira. Ko a k'auyensu babu abinda take tsinanawa innarta duk kuwa da faman da Innar zatayi, saidai tayi ta gaji. To zuwanta ne ma wajen Mami abin ya d'anyi sauk'i.
   "Mami, wai bazamu idin ba?"
Mami wacce ta riga ta gama gundura da wannan maimaicin tambayar da Bintu ke yi mata, ta bata amsa a fusace.
  "Bansani ba, ke wai bakisan abinda ya kamata ba? Tashi ki bar nan tun kafin na 6ata ranki."
  Ta mik'e tana zum6ure baki, Atine da Magajiya masu taya Mami hidima suna dariya.
  Tana shiga d'aki ta nufi wajen kayanta dake a goge a ninke.
   Bayan ta gama shafasu ta janyo takalminta ta gwadashi a karo na shida tun bayan da aka siyo.  Kwas kwas d'in da takalmin keyi ne ya tayar da Aisha daga bacci. Ta dubeta tana mutsistsika idanu kafin ta ja tsaki tayi mik'e.
  "Kedai wallahi kamar na kwasheki da mari nakeji, duk kin wani ishi mutane tun siyo takalmin nan."
  "Sai ki mareni idan kin isan."
Cewar Bintu tana k'ok'arin dafe bango ganin tana neman kaiwa k'asa.
   "Ki tashi ki shirya, Mami tace Abba ya shirya."
  Ai da jin haka Aisha ta mik'e zaune.
  "Dagaske? Ke meya hanaki wankan?"
  "Kaya kawai zan saka."
Hakan da ta fad'a yasa Aisha mik'ewa ta fad'a band'aki.
  Bayan fitowarta, itama ta soma k'ok'arin shiga. Daman batayi, wankan dai tafiso Aisha ta soma."
       K'arfe bakwai, sun gama shiri tsaf. Bintu dole ta bari Aisha tayi mata kwalliya da d'aurin d'ankwali, saidai duk da haka, saida tayi d'igo a goshinta hakan bai hanata fitowa tsaf tayi kyau ba. Shadda ce a jikinsu fara tas, ta sha aiki mai duwatsu. Aisha sai kallon Bintu take.
  "Ke sai naga kamar fa kin fini yin kyau."
  "To uwar ba'a, yanzun ma shi kikeyimin? Ke da kike fara tas, menene abin gani a yaba wajen bak'ak'e. Ai dole ma nan gaba na soma kwailin."
  "A wane gidan?" Suka tsinci muryar Mami wacce sam basu kula da shigowarta d'akin ba kasancewar k'ofar tasu a bud'e take. Ta k'araso ciki, itama shaddar ce a jikinta saidai kala da ta bambanta don ita ruwan k'asa ta sanya, iri d'aya da mijinta, bawani ado sosai ta yiwa fuskarta ba. Sunyi zaton fad'a zatayi, sai kuma ta saki fuska tana dubansu.
  "Inye, kaga 'yanmatan Abba, to ko ku fa? Bintu har kinso ki fini kyau ni d'inma. Kalarki mai kyau ce kada na k'ara jin kinyi zancen wani shafe-shafe."
  Bintu ta amsa da toh tana mai washe baki na jin dad'in yabon da Mami tayi gareta.
   "Toh sai ku fito ga 'yan uwanku da Abbanku duk sun kammala shiri."
  Kowaccensu ta dauki mayafinta wadatacce ta yafa. Aisha ta dubi Bintu baki bud'e ganin tana k'ok'arin zura takalmi.
  "Wai dagaske takalmkn nan zaki sanya?"
  "Me zai hana kuwa? Lallai ke d'innan kina wasa da Bintu."
  Tuni ta zura tana k'ok'arin daidaita tsayuwarta. Aisha ta girgiza kai. "Wallahi ki chanja ki sanya d'ayan nan, ina jiye miki ki fad'i."
  "Jikinki ko jikina? Kudai 'yan birni kun maida mutanen k'auye wasu da basu da wayewa. Tunda ke bazaki iya tafiya da shi ba sai ki bar wad'anda zasu iya suyi ai."
  Daga haka ta nufi k'ofa tana taku gaba d'aya a takure.
 "Ke muje."
  Suka fito.
 A nan farfajiyar gidan suka tarar da su Mami na k'ok'arin shiga mota. Abba yayi murmushi ganinsu. Suka gaisheshi.
  "Lallai, yaran Abba sun fito. Kamar ba ku ba." Sukayi dariya kawai.
  Ita dai Bintu da sauri ta fad'a mota sakamakon takalmin dake neman kayar da ita. Mami ta girgiza kai.
  "Bakya ji Bintu, kinason wahalar da kanki."
  Yaya Rufa'i yana dariya yace "Barta Mami, jiki magayi."
  Bintu ta d'ago ido da zummar kallon Yaya Rufa'i, saidai cikin rashin sa'a suka had'a da Yaya Ma'aruf, abin mamaki yau kam babu hararar, kallon sak, kallo d'aya ya maida kansa ga tuk'i. Motar tayi shiru sai kabbara da kowanne keyi a hankali, wato(Allahu Akbar Allahu Akbar, La'ilaha Illallahu Allahu Akbar, Allahu Akbar walillahil hamd) kamar yanda sunnah ta koyar.
Bintu wacce bata iya sosai ba, sai mus-mus da baki. A karshe sai ma ta matsa daidai kunnen Aisha.
   "Ke, wallahi Yaya Ma'aruf yayi min kallon arziki yau. Yayi kyau sosai."
   Aisha ta harareta kawai, hakan yasa ta dauke kai tana kalle-kallen gari. Takalmi kuwa tuni ta tu6eshi tana hutawa.
   
 
 
 
[7/20, 9:56 PM] Aysha Abe:  ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<05>>
  Kuka har da sheshshek'a takeyi sakamakon marin da ta sha a hannun Yaya Ma'aruf a dalilin take mishi yatsu da tayi da takalminta, Mami bata ce komai ba ta bi mijinta wanda ya rigasu shigewa gidan, ba'a gabanshi akayi marin ba. Ita kanta yau Bintu ta 6ata mata rai, har kusan fad'awa tayi kan wata tsohuwa wajen idi, tsohuwa ba hakuri tayita 6a6atu, saida Mami ta sanya baki tayi shiru. Mami ta dakawa Bintu tsawa akan maza-maza ta cire takalmin ta rik'eshi a hannu saidai tayi tafiyar haka.
  Bintu ta k'ara rushewa da kuka, tana murnar Mami bata doketa ba, yanzu gashinan ta takewa Yaya Ma'aruf yatsun k'afa ya mareta. Haka tayi cikin gidan, Rufa'i na kwala mata kira don ya rarrasheta amma ko juyowa batayi ba.
    Tana zaune tana kuka da jaye-jayen Allah Ya isa, Aisha kuwa banda dariya babu abinda takeyumi mata. Tun Bintu na jin haushinta har itama ta hau dariya tunanowa da yanda ta dage akan takalmin. Tayi kwafa.
    "Allah kuwa sai ma na tonamai asiri."
  "Asirin me?" Cewar Aisha.
  Bintu ta k'ara yin kwafa.
"Kedai ki zuba ido."
Kiran da Mami ta kwala musu ne ya katse hirar. Bintu tace ita babu inda zata je. Haka Aisha ta fice ta barta.
  Bata fita ba saida Mami ta shigo da kanta ta d'an yi mata fad'a kafin kuma ta sauko tana rarrashinta, haka ta fito tana zum6ure-zum6uren baki. Anan saman kafet ta tarar da kowa har Abba anyi zaman cin cin abinci. Ta dubi Yaya Ma'aruf ta dauke kai, a ranta tana fad'in.
  "Ai sai na tonamaka asiri kwanan nan, d'an iska kawai."
   Abba na murmushi yace "Haba Bintu, wanene ya ta6aki? Zo ki gayamin."
  Ta k'arasa ta zauna, saidai bata iya cewa komai ba ganin Ma'aruf.
   Suka soma cin abin, Abba na janta da hira har ta sake.
  Bayan sun kammala, ita da Aisha suka kwashe kwanukan suka nad'e ledar cin abincin sukayi kicin.
    Ranar sun sha yawo tare da Rufa'i.
                         * * *
   Washegari sai wajejan k'arfe goma Bintu ta farka. Ta kasa kunne sosai jin hayaniyar mutane daga falon Mami. Hakan yasa ta fito daga ita sai riga da wando na bacci. Ta d'an la6e, tana kyallara ido ta gane duk 'yan uwan Abba ne, babu wacce ta soma ganewa sai Anti Ma'u. Kwafa tayi, har cikin ranta ta ji dad'in ganinta, a fili tace "Yau asirinku zai tonu."
  Ta koma ciki ta fad'a wanka itama. Bayan ta fito tayi kwalliyarta harda jagira irin k'atuwar nan saidai nata yayi girma da yawa. Ta dubi matar jikin kwalin eye shadow, ta dubi kanta kafin ta ja tsaki, ba iri d'aya bane kwalliyarsu. Cikin ikon Allah, sai ga Aisha ta shigo. Tana kallon fuskar Bintu ta soma kyakyata dariya. Bintu ta hau tayata.
  "Don Allah zo ki yimin kwalliya wacce ta ci uban ta jiya. Yau zan nunawa wata bata da wayo."
  Aisha ta saki baki ta kama"Toh, wacece kuma?"
  "Baruwanki Malama, yimin don Allah."
  "Goge, ke wanke fuskara gaba d'aya."
  Da gudu-gudu ta fad'a band'akin ta wanko ta dawo ta zauna.  Cikin kwarewa irin na Aisha, da baiwarta da Allah Yayi mata na iya tsantsara kwalliya  tayi mata kwalliya gami da sanyamata eye-shadow wanda a baya sam Bintu bata amincewa ta sanya. Ai kuwa tayi kyau fiye da zato. Banda "Masha Allah, Subhanallah." Babu abinda Aisha ke ambata, ta k'arashe da "Wallahi kin fi koyaushe kyau tun zuwanki baki ta6a kwalliya irin na yau ba."
  Bintu tayi farr da ido, kai kace wata budurwar azo a gani ce.
"Nasani." Aisha ta kai hannu zata goge mata ta kauce tana dariya.
  "Au godiya zanyi fa."
   Aisha zata fita ta tsaidata.
"Aramin wayarki." Ta mik'a mata ta fita.
  Ta hau dannawa, gaba d'aya ta mance yanda Aisha ta koyamata daukar hoto. Ta dire wayar da zummar da zarar ta kammala zataje d'an dolo mai wankinsu ya koyamata don batason Aisha tasan abinda zata aikata.
   Ta had'e tsaf cikin atamfa ja da fara, d'inkin ya zauna d'abas a jikinta, tayi d'aurin d'ankwalinta na sabo, ta sak'alo jelun wuyanta ta k'ulle. Cikin sa'a sai ga Aisha ta dawo d'akin, tana ganin haka ta gyara mata. Bayan fitarta, Bintu ta fesa turare ta janyo flat shoe din da Rufa'i ya za6omata ta sanya. Aganinta bayar da kai ne ta fad'i a gaban Anti Ma'u, ita daman sam jininta bai had'u da ita ba, sai kuma yanzu ta k'ara gano silar rashin had'uwar jininsu, 'yar iska ce.
   Ta d'auki wayar Aisha ta fito da niyyar zuwa wurin d'an dolo.
  ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<06>>

  "A'ah Bintuuu!!" Fad'in 'yan matan kenan sa'anninta. Kasancewar gaba d'aya sun santa. Tayi musu murmushi kafin ta k'araso kamar wata mutuniyar kirki ta zauna. Nan suka gaisa, ko kallon Anti Ma'u batayi ba. Har saida Anti Ma'un tayi magana.
  "A'a, Bintu yau abin ba magana?"
Sai lokacin ta d'an yamutse fuska tace "Ina wuni."
  "Bazan amsa ba tunda saida na rok'a." Fad'in Ma'u cikin fushi, bata ga abinda ta tarewa yarinyar nan ba da ta tsaneta. Ta kusa daina shiga harkarta. Bintu ta mik'e tana dariya.
  "Ina zuwa."
  Bata saurari kowa ba ta fice daga falon tana wani jijjiga jiki a dole tafiyar Ma'u take kwaikwaya. Aisha dariya ta su6uce mata sakamakon ta fahimci ko da wa Bintun take. Ma'u ta gane saidai ta basar.
    Tana fita harabar gidan fa nutsu ta soma tafiyarta sak. Ta dubi hagu da dama, bata hango d'an dolo ba, dole tayi gaba wajen maigadinsu. Yana ganinta ya washe baki. "A'a, d'iyata, wannan cakarewa haka?"
  Bintu ta rik'e k'ugu tana murmushi.
  "Nagode Baba, kasan inda d'an dolo ya shiga?"
  "Ganinan!"
Cewar d'an dolo da babbar murya a sa'ilin da yake bud'e kyaure ya sanyo kai, hannunsa rik'e da mp3 yana jin wak'a.
  "Yauwa, zo muyi sirri."
  Tayi gaba ya bi bayanta har zuwa wajen shukoki. Ta dubi kusa da su babu kowa, ta mik'a mishi wayar Aisha.
  "Gwadamin yanda zan d'auki hoto."
  D'an dolo yayi dariya.
  "Kai, sau biyar kenan ina gwadamiki. Wane irin kwanya gareki?"
  Ta harareshi. "Malam idan bazaka koyamin ba, bani waya."
  "A'a yi hakuri." Ya soma nunamata yanda zatayi, kafin tace bari ta gwada. Ta nunoshi da wayar. "Gyara nayi maka hoto mugani."
   Yayi tsayuwar DAB&#128540;, ta kyalkyale da dariya kafin ta daukeshi.
  "Lah kaga ya yi."
   Suna cikin haka, Yaya Ma'aruf yazo wucewa. Ai da sauri D'an dolo yabar wurin. Ma'aruf ya bishi da kallo kafin ya maido dubansa ga Bintu cikin d'aurewar fuska.
  "Ke, banyi miki gargad'i ba akan wasa da yaron nan ba ne?"
  Ta turo baki, bata da niyyar magana don har lokacin bata bar jin haushinsa ba. Ya matso, ta matsa a tsorace. Ganin yana shirin cafkar kunnenta ya sanyata yin magana babu shiri.
  "Wayyo, kwa.. Au, wallahi abu ya nunamin. Kayi hakuri bazan sake ba."
  Ta k'arashe tana dafe da kuncinta. Ya zubamata ido cikin kallon raini. Ganin kamar bai wuce ba tayi magana.
  "Anti Ma'u ma ta zo."
  Jin abinda tace ya bashi dariya, hakan ya sanyashi murmushi mai ban sha'awa. Bintu bata ji. Tayi  sak'ale tana kallon abin kamar a mafarki har ta saki kuncinta. Ai kuwa ya mintsili kumatun ya ja.
  "Sa'anki ne ni?"
 Daga haka ya saketa ta juya sai gida. A ranta tana fad'in.
  "Yau zan sanyaka kuka ai." Ta k'arashe da dariyar mugunta.
     Nan ta zauna ta saki jiki anata hira, sai gashi ya shigo.
  Kowannensu ya gaisheshi. Bintu ta zubamusu ido kamar talabijin, sai wani murmushi suke sakarwa juna.
   K'arshe yayi mata wata magana k'asa-k'asa sannan ya mik'e ya fita. Fitarsa da mintuna biyu, ta mik'e ta bi bayansa. Gaba d'aya manya da k'ananan 'yan matan irinsu Bintu suka saki shewa. Mami ta fito daidai lokacin tana tambayar abinda yayi musu dadi.
  "Bakomai." Suka amsa. Bintu ta faki idonsu ta fice ta hanyar kicin. Yau kam komai zai shiga wayarnan. Kai tsaye ta nufi sashen Ma'aruf.
   Sad'af sad'af take takawa a barandar har ta kai jikin k'ofar. Ai kuwa ta ci karo da takalmin Ma'u. Ta numfasa ta waiwaya bayanta. Babu wanda ke tahowa. Taji k'arar kid'a, wannan ya bata tabbacin koda ta murd'a babu wanda zai ji cikinsu.
   Ta murd'a k'ofar ta tura a hankali. Ashe dagaske 'yan iskan abinda zasu kuma yi kenan. A tsaye ta hangesu ya yiwa Ma'u kyakkyawar runguma. Hannunta na rawa ta ciro wayar Aisha daga rigarta ta saita ta d'aukesu hoto. Har kala uku, ta ci sa'a akwai wanda fuskokinsu gaba d'aya suka fito sosai. A sannu ta mayar da k'ofar ta rufeta kamar yanda take. Babu wanda ya ji cikinsu sakamakon kid'an dake tashi.
   Saida tayi nesa kad'an da wajen ta hau kyakyata dariya har tana rik'e ciki.
  "Zakuyi bayani ne."
                       * * *
 Misalin takwas na dare babu kowa a falon Mami bak'o, dukkansu sune. Har Abba yana zaune tare da su ana hira. Can sai ga Bintu ta shigo, bayan tayi zaman dirshan akan gado tayita bincike har ta gane yanda ake bud'o hotuna. Ta dubi kowa tana murmushi. Babu wanda ta ji dad'in gani kamar Ma'aruf. Ya dubeta ta sakarmai murmushi, shima fuska a sake yake kallonta. A yau yana cike da farinciki baison abinda zai dagula lissafinsa.
  Ta k'arasa ta gaida Abba. Ya amsa fuska a sake.
   Can ana hira Bintu ta katse ta hanyar kiran sunan Abba. Kowa yayi shiru yana dubanta.
  "Na'am 'yar Abba, ya akayi?" Cewar Abban.
  Ta dubi Ma'aruf sannan ta dubi Mami sai kuma tayi shiru.
  "Bintu ya akayi? Yi magana mana." Mami ta fad'a.
  "Daman wani iskanci akeyi a gidannan nakeso yau kowa ya ganewa idanunsa."
  A tsorace Aisha ta dubeta, haka su Abba, abin ya basu mamaki.
   "Innalillahi, a gidana? Me kika gani?"
  Ta fiddo wayar Aisha ta bud'o hoton ta mik'awa Abba.
  "Kagani."
  Abba ya kar6i wayar yana dubawa. Nan da nan ya daure fuska gami da mik'awa Mami, mik'ewa kawai yayi ya nufi falonsa.
 ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<07>>
  Mami ranta ya 6aci, ga tsananin kunya da ta kamata. Ta rasa wa zata watsawa harara tsakanin Ma'aruf da Bintu wacce sam bata da wayo. Kunya ta sanyata mik'ewa bayan ta bar wayar anan ta bi bayan mijinta.
  Ma'aruf ya sanya hannu ya d'auki wayar, tuni Bintu ta ja baya a tsorace. Gaba d'aya fuskarsa ta sauya kwarai, farar fatarsa ta koma ja. Ya dubesu. Da sauri Aisha tayi magana.
  "Na rantse da Allah bansan abinda tayi ba, tace dai na ara mata waya."
  Gadan-gadan ya nufi Bintu, ya damk'eta kafin ya kwasheta da lafiyayyen mari. Ai tuni ta fasa k'ara.
  "Wayyo na shiga uku Innata!"
  "Ma'aruf!"
 Ya ji muryar Abba cikin tsawa.
 "Saketa!!"
  Dolensa ya saketa.
 "Zo inason magana dakai."
 Daga haka Abba ya koma ciki, Ma'aruf a kunyace ya bi bayansa.
 Rufa'i wanda wayar ta koma hannunsa ya goge hotunan gaba d'aya, shi kansa a yau Bintu ta k'ona ransa. Ya ja tsaki ya girgiza kai.
  "Bintu baki da wayo sam, bakisan ya kamata ba." Ya mik'e tsaye gami da duban Aisha.
 "Daga yau sai naga wanda zai k'ara baku waya tunda amfaninta kenan a hannunku. Banda abin Abba ma, ina ke ina rik'e waya a shekarunki. Mts." Ya fice bayan ya jefa wayar aljihun wandonsa.
  A can kuwa Ma'aruf ya sha fad'a kwarai. Abba yace dole Ma'u ta tare a d'akinta babu wani sai ta kammala SS3 kuma. Ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba, a k'arshe ya gargad'eshi kada ya kusa yace zai k'ara ta6a lafiyar Bintu, yarinya ce.
     Wajejan tara na dare, Aisha d Bintu suna d'aki babu mai kula juna cikinsu. Aisha tana fushi da ita akan ta sanya Rufa'i kwace wayarta, daman sam baya so aka bata wayar, ayau gashinan Bintu ta janyomata. Itama Bintu gaba d'aya haushinsu take ji ganin babu wanda ya goyi bayanta. Ga fad'an da ta ci sosai a wajen Mami akan d'abi'ar da takeso ta mayar da ita jiki, wato la6e. Kuma ta k'ara jaddada mata Ma'u matar Ma'aruf ce. Daga haka ta fice, ko uffan basu cewa juna ba da Aisha har bacci yayi awon gaba da su.
  Sai zuwa safiya Aisha ta sauko, daman bata kasance mai rik'o ba. Itama labari ta samo wajen Mami cewa za'ayi bikin Ma'aruf bayan sati biyu. Har sunyi magana da Hajiyar Ma'un, itama ta nuna jin dad'inta.
  Bintu ta mik'e zaune.
 "Wai da gaske ba'ayi musu fad'a ba?"
  Aisha ta ja tsaki.
 "Banza, ai bazaki ta6a ganewa ba. Bud'e kunne ki ji menene aure."
 Nan ta dunga yi mata karatu dallah-dallah. Bintu tayi shiru tana sauraro. K'arshe ta saki baki da mamakin inda Aisha tasan duk wannan.
  "A'i wai ina kikejin duk wadannan?"
 Aisha ta d'aure fuska.
 "Na gayamiki banason wata A'i."
 "Yi hakuri, gayamin."
 "Kinga ga Rai Dangin Goro. Kuma ga whatsapp na matan aure ina ciki. Maman Faruk sunana ma. Amma ko Mami batasani ba."
  "Kin shiga uku wallahi."
Aisha tayi dariya.
 "Kuma k'awata Safiya Bingel ta koyamin ba."
   Sukayi dariya kafin alamun tsoro ya bayyana saman fuskar Aisha.
 "Allah dai ya rufamin asiri na jima da ficewa ciki, da bansan me Yaya Rufa'i zaiyi min ba."
      Tun bayan faruwar lamarin, ko kallon inda Bintu take Ma'aruf baya yi. Hakanan baya amsa gaisuwarta, a k'arshe ma ya gargad'eta akan kada ta k'ara gaisheshi baya buk'ata. Sannan koda wasa ya k'ara ganinta a sashensu sai ya kakkaryata.
  Itama tun lokacin ta shareshi.
      Bayan sati biyu akayi 'yar liyafa sai yini na gida, Ma'u ta tare a gidan mijinta wanda babu nisa sosai da gidansu Ma'aruf. Hatta Innar Bintu wacce kanwa ce ga Mami, ta halarci bikin. Ta ji dadin ganin da ta yiwa 'yarta gaba d'aya ta chanja ta k'ara girma. Matsalar da Bintu ta gayamata guda d'aya, wato karatu. Ita ta gaji da zuwa makaranta gashinan kwata kwata bata da wani basira, bata mayarda hankali. Inna tayita yi mata fad'a, a k'arshe ta rarrasheta da nunamata wataran zata ji dad'in karatun. Jinta kawai tayi, amma sam bata so haka ba, a sonta Inna ta cewa Mami a kyaleta kawai. Babanta ma yazo, shima sai washe baki yakeyi ganin yanda Bintunsu ta koma. Yayita shi wa Mami da Abba albarka yana binsu da addu'o'i na alheri.
                     * * *
  Kuka sosai takeyi, ta fito daga cikin motar a guje ta rungume Mami.
  "Dan Allah Mami kiyi hakuri wallahi zanyi karatu, kada a kaini bodin bana so."
  Mami ta soma karaya, saidai tana so taga Bintu tayi karatun addini da boko. Shiyasa koda Ma'aruf ya kawo shawarar kaita Bodin batayi musu ba.
  "Kiyi hakuri Bintu, zaki dunga ganinmu lokaci zuwa lokaci, ga 'yar uwarki nan kuna tare. Kada ki damu kinji ko?"
   Aisha ta lek'o ta windo tana dariya.
  "Mami ki kyaleta, seniors zasu jibgeta a banza dole ta nutsu."
  Mami ta harareta. Dakyar ta rarrashi Bintu, ta shiga mota. Rufa'i ya ja suka tafi. Jss1 aka ajiye Bintu, zatayi repeating. Ita kuwa Aisha ta wuce Jss3.
                        * * *
       BAYAN SHEKARU BIYAR...!

[7/20, 9:56 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<08>>
  "Mamina!!"
 Budurwa mai shekaru sha tara cif a duniya ta fad'a cikin d'aga murya alokacin da ta shigo falon a guje.
  Mami itama da sauri ta fito daga kicin tana mai cike da murnar ganinta. Ai da sauri ta k'arasa gami da fad'awa jikinta tana dariya, Mami tayi mata kyakkyawar runguma tana murmushi mai bayyana hak'ora kafin ta d'agota.
 "Bansan yaushe zaki ajiye shiriritar nan ba."
  Budurwar ta turo baki.
 "Kingani ko? Daman nasan yanzu za'a soma takuramin a gidannan. To dai babu inda zan k'ara tafiya, atoh."
  "Inji wa? Sai mu turaki can k'auyen Rano kije can ki cigaba da haukanki."
 Cewar Rufa'i wanda ya shigo mata da akwati, Aisha na biye da shi.
  Sukayi dariya har Mami. Bintu ta dubeshi da fararen idanunta masu kyau manya da su. Ya harareta a wasance, ta dauke kai tana fad'in.
  "Tab, ai dai dad'in abin bana gudun Innata. Kuma matarka ai itama a k'auyenmu ka kwasota."
  "A'a malama, Hajara ta fiki kyau da wayewa. Kin manta da yanda kikayi karatun?"
  Duk wannan  maganar suna yinta ne a tsaye. Sai lokacin kuma suka zauna ana dariya.  Idan da sabo, ya saba da tsokanar da Bintu ke yiwa Hajara matarsa. Kasancewar kusan sa'anni suke, kuma itama 'yar gida ce. A yanzu ta kusa haihuwa, har lokacin kuwa Ma'u ko 6ari bata yi ba. Allah bai kawo haihuwar ba.
  Bayan shigarsu d'aki, Bintu ta dira saman gado ta saki k'aramin ihu.
  "Home sweet home, shikenan babu k'ara kwana a makaranta, ba wani takura kai da karatu."
 Aisha ta d'aka mata duka.
 "Karatu yanzu kika soma, wa zai je miki jami'ar?"
 Bintu tayi murmushi mai k'ara fiddo tsantsar kyawun fuskarta.
  "Ai gwara jami'a tunda jeka ka dawo zanyi, ke nifa banason kwanan makaranta, wai da yaya na kammala? Ni abu d'aya ma nakejin haushi yanzu."
 Ta yamutse fuska tana mai zame d'ankwalinta, hakan ya tona  asirin gashinta wanda ko kusa bata shafawa relaxer, yana d'aure da ribon, ya cika taf saidai babu tsawo.
   "Wannan yayan naki mai kama kwara."
  Aisha ta zaro ido, "Au, iskancin naki har ya kai ki kirashi da kwara? Lallai ma, baruwana."
  "Abinda yafi haka ma ai zan kirashi. Mutum babu walwala, sai wanda kakeso kad'ai ke ganin hak'oranka. Ji dan Allah idan yana gaban wannan siririyar matar tasa kamar a hure. Ke nan da kike ganina har na mutu bazan ta6a taka gidansa ba. Banje ba ina k'arama ba ballantana kuma yanzu da na k'ara sanin ciwon kaina? Hum um!"
  Aisha tayi dariya.
 "Kuma wallahi Anti Ma'u tana damuwa sosai akan rashin zuwanki. Amma tana tsoron rashin kunyarki ne shiyasa itama bata shiga harkarki."
  Bintu ta yiwa Aisha wani kallo.
 "Ita Ma'un ta gayamiki haka?"
 "Kai Bintu, Ma'u babu Anti ma?"

 Harararta tayi kamar idanun zasu fad'o.
  "Na fad'a d'in, munafus jeki ki gayamata. Toh wallahi ko mijinta ke kanki kin sani rabona da ganinsa tun ina Ss2 ballantana kuma ita. Kin tuna ko ancemin gashinan a falo bana fitowa indai ina gidannan nazo hutu ballantana wata matarsa. Amma gobe zakimin rakiya gidan Yaya Rufa'i, kinsan shine nawa."
  Aisha dake kallonta ta ta6e baki kawai.
  "Kanki akeji."
 Dariya kawai tayi ta mik'e a saman gadon ta hau rage kayan jikinta tana wak'arsu ta 'yan bodin na rabuwa da sukayi. Nan kuma hirar ta koma ta rayuwar makaranta, suna yi suna darawa abinsu.
                        * * *
   Bak'a ce, saidai bak'inta mai shek'i da kyawu ne, kana ganinta kasan tana hutawa. Doguwa ce ba can sosai ba, tana da 'yar k'iba hakanan tana da diri mai kyau da burgewa. Hancinta bai cika sirantaka ba, ba kuma zaka sanyata a layin marasa hancin ba(Lol). Tana da magana(Idanuwa) masu k'arawa fuskarta kyau. A yanzun tana da shekaru goma sha tara cif a duniya.
   Tana sanye da leshi ruwan madara, anyi mata d'inkin riga da siket da ya kama jikinta ya zauna d'abas. Taci kwalliyarta.
  Fuskarta a tur6une, tana tsaye daga bayan kujera.
  "Kinji abinda nace ko?"
 Ta kauda fuskarta daga kallon Mami.
  "Naji."
 Aisha wacce dariya ta so su6uce mata, dole ta maida shi sakamakon kallon da Mamin ta jefomata.
  "Shikenan, kuje, a kula da abin hawa."
 "To Mami, sai mundawo "
 Cewar Aisha, Bintu dai tayi gaba. Haka kawai Mami ta sanyata zuwa gidan Ma'aruf dole, ita kam batasan meyasa Mami ke son 6ata ranta akan wanda bai damu da harkarta ba itama bata damu da shi ba.
  A cikin adaidaita sahu, dole ta saki fuskarta tana hira sakamakon Aisha da ta tunano mata wautar da tayi a baya kafin tariyar Ma'u a gidan Ma'aruf. Itama dole ta biyemata suna dariya wanda suka saba duk sadda suka tuna wani abu cikin wautar da Bintu tayi.
  "Ke, ni sai yanzun ma nakejin kunya fa, hm, Allah Ya kyauta shirmena dai."
 "Amin, ai gwara ki dunga yiwa kanki addu'a."
  Ta ta6e baki.
 "Mu soma zuwa gidan nasa banaso mu dade, kinga sai mu fito mu nufi gidan Yaya Rufa'i."
  Aisha murmushi kawai tayi. Dayake ba nisa, nan da nan suka isa. Bayan sun sallami mai napep suka rankaya ciki.
  Maigadinsu ya bud'e suka shiga. Ta dubi harabar gidan, bashi da wani girma, amma yayi kyau don an k'awata shi da shuke-shuke. Suka k'arasa ciki.
  Falon ya had'u, abinka da 'yan boko (Lol), babu wani tarkace sosai amma fa an zuba kujeru masu tsada, hakanan kafet da labulaye. Babu kowa a falon sai Sa'ade yarinya mai shekaru goma sha uku dake taimakawa Ma'u da aiki. 
  Bintu ta zauna gami da d'ora k'afa d'aya kan d'aya sannan ta dubi Sa'ade.
  "Ke, masu gidan basanan ne?"
 "Suna nan."

 Aisha ta dubeta. "Mu jira, nasan sun ji shigowarmu."
  Ta ta6e baki gami da yin k'as da cingam dake bakinta.
  "Minti biyar, idan basu fito ba sai mu k'ara gaba zuwa gidan karamci."
  Harararta kawai Aisha tayi batace uffan ba. Bintu ta d'aga kafad'a alamun batasan tana yi ba ko a jikinta.
  Suna zaune har suka ci mintuna uku, a fusace Bintu ta mik'e. Ta rattaba sallama cikin d'aga murya. Har sau uku. Zatayi na hud'u ta ji an murd'a k'ofar dake a bayanta. Wannan yasa ta fasawa. Ta juyo duk a zatonta matar gidan ce.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<09>>
Fuskarsa ba walwala kamar yanda ta riga ta sani. Yana sanye da singilet bak'a da wando (three-quater) fari k'al. Rataye a wuyansa, tawul ne. Ganin yanda d'igo-d'igon ruwa ya d'an kwanta a fatarsa ya tabbatar daga wanka ya fito.
   Kallonta yakeyi ido cikin ido, hakanan itama fargaba ta hanata d'auke nata idon.
  "Yaya ina kwana."
Maganar Aisha ta maidoshi tunaninsa, kallon da yake binta da shi na rashin sani ne ko mantuwa. Yasan kamar dai fuskar ba bak'uwarsa bace, saidai bazai iya tunano ko wacece ba.
  Bintu ta koma ta zauna, maimakon ya amsa gaisuwar sai ya zarce ga abinda ya fito da shi.
  "Ke wane irin mugun d'abi'a ne wannan? Idan kunga ba kowa falon ba zaku iya hakuri har matar gidan ta fito ba. Wace iriyar k'awa kika samu haka?"
  Ya k'arashe yana maida kallonsa ga Bintu. Bintu ta dubi Aisha. Aisha ta amsa.
"Lah Yaya, Bintu ce fa."
Jin abinda tace ya sanyashi k'ara dubanta da mamaki. Ta cigaba da taunar cingam.
"Ina kwana."
Ta gaisheshi a tak'aice. Ya gyada kai.
"Ok, sabon rashin kunyar da kika koyo kenan a Boarding d'in? Toh ki kula, ina nan a Ma'aruf d'in da kikasani, ban chanja ba."
  Daga haka ya juya zuwa d'aki. Ta bi bayansa da harara cikin k'aramar murya ta amsa.
  "Nima Bintun da ka sani ce. Kuyi wani iskancin yanzu ku gani mana."
  Suka tuntsire da dariya ita da Aisha.
  "Kai Bintu, wallahi baki Smda kirki."
  Tayi kwai da cingam kafin ta fiddo ta mik'awa Sa'ade.
"Yardar min. Ke kuma malama tashi mu tafi."
  Ta mik'e ta soma kiciniyar yafa mayafinta. Kafin Aisha ta tanka, Ma'u ta fito cikin doguwar rigar atamfa, fuskar ta sha hoda da jan baki.
  "A'a ya da haka? Bintu ina murnar ganinki kina yafa mayafi. Oyoyo."
  Tana maganar ne cikin sakin fuska sosai. Bintu ta yamutse fuska.
  "Ai naga..."
  Sai kuma ta fasa maganar. Ma'u ga basu hakuri, suka gaisheta ta amsa kafin ta zauna ta hau tambayar Bintu game da makaranta.  Jefi-jefi Bintu ke amsawa don kacokam ta mayarda hankalinta ga danne waya.
  Ma'u ta maida hirar kan Aisha, wacce ke sanarmata sun d'anyi hutun makaranta. A k'arshe ta mik'e.
  "Kuyimin hakuri bari na had'awa yayanku karin kumallo."
   "Lah Anti bari mu tayaki."
  Cewar Aisha tana mai mik'ewa. Tuni Ma'u takai k'ofar kicin, tana dariya tace.  "Bari kawai nayi."
  Aisha duk da haka ta bi bayanta, ta juyo don ganin ko Bintu ta taso, saidai ga mamakinta kamar bata san wainar da suke toyawa ba, k'arshe ma talabijin ta nufa ta kunna ta dauki remote ta zauna ta soma controlling. Aisha ta shige kawai ta kyaleta.
   Hankalinta ya tafi a kallon wani series wai Saloni(gwalo) wayarta ta d'auki k'ara.
  "Suhail." Shine sunan da ta gani
Saurayi ne k'arami wanda koda zai girmeta bai fi ga bata shekaru biyu ba, aboki ga k'awarta, Maijidda. Ta dubi  k'ofar da Ma'aruf ya fito d'azu, babu alamun fitowarsa yanzun, hakan yasa ta d'agawa.
  "To sarkin takura rayuwa, kaidai bansan wane irin saurayi bane. Babu kud'i sai afkin kiran waya ka cikani da 6a6atu."
  Suhail daga d'aya 6angaren ya kyakyace da dariya, yana son bugowa Bintu ko don abin dariyarta.
"Amma kin raina ni wallahi, haba 'yanmata, a cikin samarinki goma da wuya ki samu biyu irina."
  Ta yamutse fuska kafin kuma ta saki dariya.
  "Waya gayamaka ina da samari da yawa? Kai d'aya ne na k'arfen."
  Farinciki ya mamaye Suhail. Sun jima suna hira da wasa da dariya kafin tace ya kyaleta ya isheta da zuba. Bayan ta ajiye wayar tayi magana a fili.
  "Banza, yaro da shi sai karambanin tsiya. Ni dama zai aikomin kati ya fiyemin wannan zantukan marasa alkibla."
  Tana d'ago kanta sukayi ido hud'u da Ma'aruf tsaye, saidai bai k'arasa fitowa daga d'akin ba. Sanye yake cikin shadda fara tas. Ya d'ora' bak'ar hula a kansa. Kallonta yakeyi kallon tuhuma, gaba d'aya ta tsorata. Ta had'iye miyau.
  "Yau babban yaya da la6e." Ta fad'i a ranta. Ya k'arasa fitowa ya zauna a gefenta kafin ya sanya hannu ya d'auki wayarta. Ya gama bincikensa a contact, abin mamaki sunayen da ta sanyawa samarinta ya bashi dariya sai murmushi kawai yakeyi.  Akwai Banki, Malam K'eya, Sarkin Nanaye, sai Suhail 6a6atu. Ya dubeta.
  "Abinda kikeyi kenan a makarantar? Duk a ina kuka had'u?"
  Ta sunkuyar da kanta tana wasa da zobunan yatsunta biyu kamar wata saliha.
  "Ni babu wanda na janyo."
Kamar yayi magana sai kuma ya barta, ya ajiye wayar ya d'auki remote.
  "Ina Aisha?"
Ta tsuke baki. "Tana taya Ma'u girki."
  Cikin tsananin mamaki ya dubeta.
"Ma...what?"
Sai lokacin ta tuna a inda take.
"Su6utar baki ne wallahi Yaya. Ina girmamata ai, Anti Ma'u."
  Baice komai ba har ya kamo Al-jazeera. Ta yamutse fuska, ta mik'e. Ta gwammace ta koma kicin wajen su Aisha da dai ta zauna kallon wani Al-Jazeera.
  "Zo nan."
Ta tsaya kafin ta juyo ta dubeshi. Shima ita d'in yake kallo. Gaba d'aya sai yayi mata kwarjini, ta tako a sannu ta zauna saman kujera inda ta tashi.
  "Gani."
Ya k'ara murya kad'an.
"Zauna, ki dunga fassaramin abinda suke fad'a naji ko da gaske yanzun kin iya (English)."
   Ta d'an dubeshi. Amma Yaya Ma'aruf ya raina mata wayo, lallai ma.
   "Ina jinki."

[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<10>>
  Ta muskuta tana duban talabijin. Yau zata rainamishi wayo tunda abin nashi hakane.
   Tayi tsai bayan ta gama fahimtar inda labarun ya dosa. Akan yara masu (kwashiorkor) ne, har gasunan ana nunosu ana jawabinsu. Ta turo d'ankwalinta gaba, kafin ta soma magana.
"Ana magana akan wad'anda k'iba tayi musu yawa ne, da ace duk zasu koma kamar wad'annan da kwarai sun ji dad'in rayuwa kuma..."
  Ba zato ya sakarmata rankwashi a tsakar kanta.
  "Banga amfanin karatunki ba. Tashi ki bani wuri kafin na kwasheki da mari. Dak'ik'iyar kawai."
  Ta mik'e da saurinta ta nufi kicin d'in, tana shiga ta kwashe da dariya, Ma'u da Aisha na tayata kasancewar suna jin abinda ke wakana tsakaninsu.
  "Baki da kirki wallahi. Kin raina mijina Bintun Mami."
  Bintu tana 'yar dariya ta amsa.
"Atoh, ya cigaba da takurawa rayuwata ya gani."
  Sukayi dariya. Sun riga sun kammala, ta ja kujera ta zauna  tana dubansu yayinda suke jerawa saman babban faranti.
Tana ta afkin girgiza k'afa, d'abi'ar da Mami ta hanata. Ma'u kawai take k'arewa kallo ganin yanda fatarta ta murje ta k'ara k'iba sosai.
  "Tab, Anti Ma'u wallahi ki rage k'ibar nan, nan gaba zaki iya illah."
  A mamakince suka dubeta.
  "Illa wace iri kuma?" Cewar Ma'u.
"Yanzu misali, Yaya Ma'aruf ya k'ara aure tsab zaki tomasheta,wannan duka d'aya da wannan mulmulallan hannun naki kin kasheta."
  Aisha ta ji hanjin cikinta sun kad'a. Yau Bintu ta janyomusu, mai fitar da ita sai Allah. Ma'u tayi murmushin yak'e.
  "Hum, ballantana ma bana tunanin Mijina na sha'awar k'ara auren. Sam, ba shi da wannan ra'ayin. "
  Ta d'auki farantin ta fice. Dukan da Aisha ta d'aka mata a cinya ne ya maido da idanunta gareta ga barin kallon Ma'u.
  "Kinsan abinda kike fad'a kuwa? Wallahi naga alama kina neman sanyamu cikin blacklist  d'in anti ma'u. Yau mun shiga uku."
  Bintu ta tsayar da ita ta hanyar yarfamata hannu.
  "Ke dallah can kyaleni, ta sanyamu mana sai me? Nifa ba tsoranta nakeji ba. Ai duk laifinku ne, saida nace bazan zo ba kuka matsamin. Maganin kar ayi kar a soma."
  Aisha dai tayi lamo kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.
  "Aisha!" Muryar Ma'u ya katse mata tunani. Ta zaro ido
"Shikenan, ta sanarwa Yaya."
  Bintu ta ta6e baki ta bi bayanta suka fito.
  "Kuzo ku karya mana."
Bintu ta girgiza kai.
  "Nidai na k'oshi, Mami fa cikamin..."
  Kallon da Ma'aruf yayi mata ya sanyata yin shiru.
  "Toh Aisha fa?"
Aisha ta girgiza kai.
"Na k'oshi Anti, mun karya kafin mu fito."
   Zama sukayi suna duban TV. Bintu sai afkin satar kallonsu takeyi. Sai hirarsu sukeyi akan abinda ya shafi ambaliyar ruwan da ake nunowa anyi a wani gari a Aljazeera.
  Can kuma tayi magana.
"Yaya zamu wuce."
Ba tare da ya dubeta ba ya jefo mata tambaya.
  "Daman ba yini kuka zo ba?"
"Eh, gidan Yaya Rufa'i zamuje."
Sai lokacin ya d'ago ya dubeta.
"Ba zaku bar gidannan yanzu ba tunda ba a kurkuku kuke ba, idan na dawo anjima da rana sai na saukeku."
   Ran Bintu ya 6aci, ta daure dai ta had'iye 6acin ran sannan ta koma ta zauna.
  Aisha bataso furucin Yayan ba, don gaba d'aya ta tsorata da Bintu, tana tsoron kato6arar da zata k'ara yi musu.
  Saidai Bintu ta bata mamaki, sakewa tayi kamar batace komai ba, itama Ma'un bata nuna komai a fuska ba. Saidai har zuciyarta ta ji ta tsani yarinyar, ta lura tantiriya ce ta bugawa a jarida. Dole tayi takatsantsan.
   Sai bayan da Ma'aruf ya dawo suka tafi. Bintu zaune a baya. Tana ji yana tambayar  Aisha ko itama tana kula samari. Tayi kamar batasan wainar da suke toyawa ba.
   Can ta d'ago kanta, suka had'a ido, ta sauke nata tana murmushi kawai. Ba koyaushe takeson magana ba.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<11>>
  Yana saukesu yayi gaba bayan ya basu dubu d'ad'd'aya. Sukaui godiya.
  Hajara uwar surutu, nan suka had'u sukayita zuba kamar ruwan famfo. Yaya Rufa'i baya gidan bai dawo daga ofis ba. Nan sukayita kyakyata dariyar abinda Bintu ta yiwa Yaya Ma'aruf da matarsa.
  "Ke dai Bintu zanso naga mijin da zai kwashi shiriritarnan ta ki." Cewar Hajara. Bintu tayi dariya irin ta rainin hankali.
   "Mijin Bintu? Tab, yana k'asar waje yana karantar masters yanzu."
  Suka gwalalo ido.
 "Waye?" Suka tambaya har suna had'a baki.
  Ta dubesu kafin  ta cigaba da rainamusu wayo
 "Yana nan, kulkum muna waya. Duk randa ya zo k'asar nan, zaku ganshi."
  "Mts, mak'aryaciya kawai."
 Aisha ta fad'a bayan ta d'agota.
  "Ina batun k'arya anan?"
 Aisha tayi murmushi tana duban Hajara.
  "Ai nasan halinta ciki da bai. 'Yar iska kawai, wallahi k'arya takeyi.'
  Bintu ya kyalkyale da dariya.
  "Ho ni, ranar aurena akwai rawa da gira d'aya." Suka dara.
 Ranar sun jima cikin nishad'i har dawowar Rufa'i. Shima ya biyemusu sukayi tayi, saida Mami ta kira wayarsu sannan sukayi azamar tafiya, Rufa'i da kansa ya kaisu gidan.
                        * * *
   Bayan watanni Bintu ta soma zuwa jami'a, business take karanta. Aisha lokacin ta shige level2, ita kuwa, Accounting take karanta. Alokacin Hajara ta haifi d'anta namiji, wanda ya ci sunan kakansa Abba, wato Umar suke kiransa Sadauki. Cikin iko da hukuncin Allah itama Ma'u ta samu ciki saidai bisa matsalar da likita yace mahaifarta tana da shi, ya sanya aka k'ulle mata bakin mahaifar da fatan samun cikin ya zauna.
   To fa! Bintu kai ya k'ara wayewa, an shiga jami'a. Kwalliya take ci har da na ban mamaki, a lokacin ta k'ara sanin rayuwa, tasan lallai ado shine mace. Hijabi idan ba don sallah ba, ko kad'an baya daga cikin suturunta na sanyawa ta fita, a cewarta yafi dacewa da gidan malamai. Aisha kuwa jefi-jefi takan sanya wataran ta fita makaranta.
   Abinda zai burge mutum da Bintu, ko kusa bata da kula kulan samari. Idan kuma ka matsawa rayuwarta, toh fa alokacin zatayi maganinka ta hanyar cin kud'in da k'arya-k'aryacen ankon biki da na katin waya. Ga duk saurayi mai hankalin da ya fahimci ba don Allah take sonshi ba, nan take yake yanke mu'amalarsu. Idan kuma ta gane da iskanci kazo, ta zageka tas ta kuma gargad'eka da babbar murya.
    A haka rayuwar ke tafiya.
  Watarana tana zaune a baranda, sanye da T-shirt ja da zanin atamfa, kanta babu ko d'ankwali, ta bararraje tana shan rake tana kallon wata wak'a a wayar d'an dolo dake zaune gefen kujera shima yana fisgar rake. Sai dariya suke 6a66akawa da hirar duniya, Mami batanan ta fita, Aisha kuwa tana kwance a falo tana jinsu.
  Babu zato Ma'aruf ya iso, sam basuji k'arar motarsa ba kasancewar a waje ya fakata.
  "Kai bari na tura wak'ar nan wayata, tayimin kyau."
  Cewar Bintu wacce hankalinta kacokam ya tafi akan wayar, gaba d'aya batasan da tafiyar d'an dolo ba. Hakanan batasan da zaman Ma'aruf ba a wajen.
  Kallonta yakeyi a matuk'ar fusace, yana takaicin wannan taurin kai irin na Bintu da bata da aiki sai hira da d'an dolo.
  Ya warce wayar kafin ya kai mata hauri da k'afarsa ya had'a da kai mata mari, da sauri ta kauce.
  "Don ubanki bana hanaki mu'amala da mutumin nan ba? Ina rantsuwa da Allah sauran k'iris ya bar gidannan!"
  Tuni ta soma hawaye, ranta ya 6aci, kamar ita k'atuwar budurwa wai Ma'aruf ke duka?
  "Ai ba hira mukeyi ba, wata wak'a yake gwadamin."
 "Wak'ar banza da wofi kai! Shashasha kin zauna kanki babu ko d'ankwali kina wagewa gardi baki. Zan sa6amaki wallahi!"
  Ta mik'e ta tattara wayoyin ta nufi ciki tana kuka, bata tsaya a falon ba ta zarce zuwa d'akinsu. Yaya Ma'aruf ya tsani ganin walwalarta, tun tana k'arama ya takurawa rayuwarta. Lallai zata bar gidan nan idan har ba zai kyaleta ba. Ta yi kwafa kawai.
   Mami koda ta dawo, bata goyamata baya ba, haka tayi mata fad'a ita dai a ganinta kowa ya tsaneta ne kawai.
    Hakan yasa ta dauki fushi da mutanen gidan. Daga gaisuwa bata k'ara cewa uffan ga kowa. To gidan ya koma babu dad'i garesu, daidai da ma'aikatan Mami suna jin dad'in zama da Bintu, da wuya kuyi hirar mintuna uku bata sanyaka dariya ba. Abba da kansa ya rarrasheta don kuwa samunsa tayi tace zata tafi Rano. Mami jikinta yayi sanyi, tana son Bintu, wannan ne dalili babba da ya sanya ta d'aukota daga wajen k'anwarta Dije.
    Nan ta shiga nan nan da ita har ta ware. Washegari ran Mami yayi fari k'al ganin Bintu ta shirya ta nufi  makaranta, don har makarantar ma yaji tayi masa.
                       * * *
   Bayan watanni tara, Aisha ta koma gidan Yayanta Ma'aruf domin taimakawa Anti Ma'u. Gaba d'aya daman an hanata aiki mai wahalarwa, cikinta ya girma cikin hukuncin Allah saidai a yanda likitan ya fad'a, cs zasuyi mata, har an sanya (Date).
  Suna samun hutu Aisha ta koma gidansa. Bintu ko daman  Rano takeson zuwa, rabonta da Rano tun kafin ta soma zuwa jami'a. Saidai zuwa yanzun tana matuk'ar tausayawa Ma'u musamman yanda ciki ya sanyata ramewar dole. Har mamaki Aisha da Mami kai harma da Hajara sukeyi idan sun ga yanda Ma'u da Bintu ke d'asawa. Kodayake, Bintu bata da raini a zahiri, barta dai idan ta so zata kwa6a maka magana a wasa. Tana da fushi amma bata da rik'o. Sannan a gaban Ma'u ta sha fad'amata. Ta k'i jinin mijinta, tafi k'aunar zuwa gidan Yayanta Rufa'i akan Ma'aruf. Da Ma'u ta fahimci halin na Bintu haka yake, sam bata da 6oye abinda ke ranta, yasa ta bar damuwa.
      Kwananta uku a Rano, aka yiwa Ma'u aiki.
  Suna zaune tsakar gida suna hira da yayanta Saifullahi, sai kannenta, Habib da Habiba, da Innarsu sai 'ya'yan abokiyar zaman innar, wacce suke kira Umma .
  Wayarta tayi k'ara ta duba. Ganin sunan A'i yasa  ta d'agawa da sauri.
   "Me muka samu?"
  "Baby Boy." Cewar Aisha cikin tsananin murna.
   Ihu Bintu ta saki tana mai tsananin farin ciki.
   "Ta haihu! Ta haihu!!"
 Haka ta hau fad'i. Nan su Inna suka shiga murna da hamdala.
 Washegari kuwa wajejan tara na safe, Inna da Bintu sai Saifullah suka nufi Kano.
  Tunda Bintu ta shaidawa Mami sun taho ta kashe wayarta.  Basu jima sosai ba a hanya (inji ni..lol) suka iso Birnin Kano.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<12>>
  Gida Saif yaso su soma nufa, saidai Bintu tace ita kam asibiti ya kamata su je su ga lafiyar baby da mamansa. Inna ta goyi bayanta. Bintu ta bud'e wayarta a lokacin da motarsu ta shigo harabar asibitin. Layin Aisha ta soma nema. Saidai yana ta k'ara ba'a d'aga ba. Ta kira lambar Mami, cikin sa'a ringing uku ana hud'un Mami ta d'aga.
  "Mami gamunan a asibitin, a wane 6angare kuke?"
  Ta ji shiru kafin ta ji muryar Mami a sanyaye.
  "Ku dawo gida mu ma gamunan a hanyar gidan."
  Kafin Bintu tayi magana Mami ta katse. Ta dubi wayar da mamaki.
 "Ya akayi ne?" Cewar Inna da ke tsaye tana jiran shigarsu. Bintu gaba d'aya jikinta yayi sanyi.
  "Bansani ba, wai an sallamesu, tace muje gidan. Mamin ce ta sanyayarmin da jiki, duk muryarta ta chanja."
  Inna tayi shiru tana ambaton innalillahi a zuci, tasan ba k'aramin abu ke sanya yayarta shiga wani hali ba. Ta soma kokarin shiga mota.
  "Ai sai mu k'arasa."
 Suka hau sai gida.
 
 Cikin fad'uwar gaba, suke duban k'ofar gidan ganin motoci fin uku.
 "Wannan motocin duk na barkan ne?"
  Cewar Bintu.
 "Ina tunanin haka."
 Baba maigadi ya bud'emusu kyauren suka shiga, anan ta ga su Abba tsaye tare da mahaifin Ma'u wanda ya kasance k'anin Abban, sai sauran 'yan uwansu.
  Suka gaisa sannan suka k'arasa ciki, Saifu ya bisu da akwatin Bintu. Gaba d'ayansu jikinsu a sanyaye. Kuka kawai kakeji daga falon Mami. Ai da gudu Bintu ta k'arasa, duk taron jama'ar dake a falon, bata kasa hango Aisha ba. Itama a guje ta k'araso ta rungumeta.
  "Munyi rashi Bintu, Anti Ma'u ta rasu."
  Ai ji tayi kamar an bugamata guduma a k'irji sakamakon wani bugawa da yayi.
  "Ke kina da hankali kuwa? Haka mutuwar take?!!"
  Ta fisge jikinta da gudu ta nufi wata 'yar uwar Ma'u da suke uwa d'aya uba d'aya.
  "Anti Zainab, ina Anti Ma'u?"
 Cikin kuka Zainab ta k'ara jaddada mata lallai babu Asma'u, Asma'u ta rasu."
  Kai Bintu ta ga tashin hankali. Da wayonta, batasan mutuwa ba. Kuka takeyi tana tambaya.
 "Haka mutuwar take? Innalillahi."
 
  Suna ji suna gani aka tafi da Ma'u makwancinta na gaskiya. Ko ta kan jaririn bata bi ba ballantana ta sanyashi a ido.
   Har magrib bata saki ranta ba, babu abinda take tunanowa sai yanda Ma'u ke hak'uri da dukkan abinda take fad'amata duk furucin da ya zo bakinta akan mijinta.
  "Allah Sarki, halinki na gari ya biki. Allah Yayi miki rahma. Aisha, ina Yaya Ma'aruf?"
  Aisha ta ja majina.
 "Yaya Ma'aruf yana asibiti, amma naji Mami tace sunyi waya da Rufa'i, yanzu zasu taho. Shi fa yana ganin an fito da ita bayan an shiryata ya suma. Har zuwa yanzu, bai k'ara sanin inda kansa yake ba sai yanzun. Yaya Ma'aruf ya ji mutuwa Bintu, yana son Anti Ma'u kamar ransa."
  Bintu hawayenta suka k'ara zubowa. Ta tunano baya, ta jinjina kai. Ita tasan yana k'aunar Ma'u.
  "Ina Bebin?"
 "Yana wajen Anti Amina. Ta amince zata shayar da shi, mijinta bai hanata ba."
  Tausayinsa ya mamaye Bintu. Ta mik'e ta fito zuwa wajen da Anti Amina take. Saidai ta tabbatar mata yana d'akin Mami yana bacci. Batayi k'as a gwuiwa ba ta nufi d'akin Mami. Can ta hangoshi cikin gadon jarirai yana baccinsa lafiya lau.
  Ta bud'e (net) d'in ta rik'o yatsunsa. Yaron sak mahaifinsa, babu abinda ya bari. Hawaye kawai take shatatarwa na tausayinsa. Shikenan ya zama mara uwa. Abin akwai tausayi. K'aunar yaron ya shigeta kwarai. Nan ta kwanta tana dubansa har bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita itama. Don jiya batayi baccin kirki ba sakamakon d'oki da son ganin Ma'u da bebinta da takeyi.
   A haka Mami ta shigo ta iskesu.
 "Wani abun sai Bintu, kya bud'ewa yaro (net) sauro ya cijeshi?"
  Bintu batasan ma tana yi ba. Mami ta gyara mishi rufin net din ta fita.
                        * * *
 Washegari da asuba Bintu ta farka babu yaro a gefenta. Inna ke sanarmata yana can wajen Amina a d'ayan d'akin. Suna cikin haka Mami ta shigo.
 "Mami don Allah kada a d'auke baby daga gidannan."
  Mami ta sauke ajiyar zuciya jin k'orafin Bintu.
  "Shi kansa uban  yaron bai amince ba, yace a samo mai shayarwa ko nawa ne zai biyata da dai yaron yayi nisa da shi."
  "Haka ma yafi wallahi Mami. Idan ya koma gidan Anti Amina ba zamu k'ara ganinsa ba fa. Kema nasan bazaki so ya bar nan ba."
 Mami ta d'auki hijabin sallarta wanda shi ya maidota d'akin daga d'akin Abba.
  "Bani da iko, sai abinda Abbanku ya fad'a. Bari dai muga yanda za'ayi."
  Daga haka  ta fice. Bintu ta fad'a bandaki tana fad'a a fili.
 "Banda mutuwa ma, me zai raba d'a da uwarsa? Kai, Allah Ya bamu kyakkyawan k'arshe."
  Inna daga saman darduma ta amsa da amin.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<13>>

  Bintu bata samu yiwa Yayan nasu gaisuwa ba sai wajejan sha d'aya na safe. Shi d'inma, aikenta Mami tayi akan yazo Abba yanason ganinsa, don gaba d'aya wayoyinsa a kashe suke.
  Da sallamarta ta tura k'ofar, ba'a amsa ba. Kansa kawai take iya hangowa kasancewar ya juyawa k'ofar baya, ta tako sannu kad'an yanda take iya hangen fuskarsa. Fuskarsa ruwan hawaye ne kwance yayinda ya zubawa k'aton enlargement na hotonsa da Ma'u tun ma na lokacin da aka d'aura musu aure  yana duba. Ta dubi hoton, ma'auratan sun dace matuk'a da juna. A dai fari da kyau, babu na yar wa. Allah Ya basu, kodayake jini d'aya ne.
  Tunda take a rayuwa, bata ta6a jin tausayin Yaya Ma'aruf ba sai a wannan karon da Anti Ma'u ta tafi ta barshi.  Ga duk wanda ya zauna da Ma'aruf da Asma'u, zai gane irin tsantsar so da kaunar da sukeyiwa juna. A yau ga mutuwa ta yi musu YANKAR K'AUNA.  Ta zauna a gefensa, ina ruwan Bintu, maimakon ta rarrashe shi sai kawai ta had'a kai da gwuiwa ta fashe da kukan itama.
  Sai a lokacin yayi niyyar motsawa. Ya ji shigowar mutum, saidai bai san ko wanene ba. A yanzu kuwa da ya ji muryarta, ya ganeta.
   "Nayi rashin madubi abin dubawa. Na rasa wani 6angare na jikina. Asma'u ta kasance wata fitila mai haskaka rayuwata, har abada bazan daina jin ciwon rashinta ba. Bani da tamkarta, a yanzu kuma bani da tamkar abinda ta haifamin."
  Yayi shiru sakamakon hawayen da ya haneshi k'ara magana.
  Bintu ta tsaida kukanta ta dubeshi cike da tausayawa.
  Kawai sai ta k'ara rushewa da ihun kuka. Ya tsayar da hawayensa ya dubeta a mamakince. Wai daman tana da tausayi har haka? Ikon Allah.
  Sallamar Mami da Abba ta katsesu. Itama jin shirun yayi yawa ne ya sanyasu biyo sahu don Abba har ya fito da zummar ganin abokansa da sukazo musu ta'aziyya.
  "A'a, menene kuma haka? Ke ba kiranshi nace kiyi ba?"
  Bintu ta mik'e tana sharar majina.
  "Kuyi hakuri, kuka ya sanyani."
 Abba ya girgiza kai sannan ya nufi wajensa ya zauna. Bintu ta fice daga d'akin. Nasiha mai ratsa jiki Abba yayi mishi. A k'arshe Mami ta d'ora sannan Abba ya umarceshi da yin wanka ya kimtsa ya fito amsar gaisuwa. Ya amsa da toh.
      Ita kuwa Bintu kan gadonsu ta nufa kai tsaye bayan shigarta d'aki. Ta kwanta ta soma rusa ihun kuka.
   "Allah mun tuba, Allah ka ji k'anmu ba don halinmu ba."
 Aisha ta amsa da amin.
 "Haba ke kuwa, ya dace kibar wannan kukan, duk masoyin Ma'u na hakika kamata yayi ya bita da addu'a koyaushe. Wannan kukan ba abinda zai rage mata."
  Bintu ta zauna sannan ta share hawayenta.
 "Hakane, Allah Ya jik'an Anti Ma'u."
   To a k'arshe dai bayan anyi sadakar bakwai kowa ya watse, lokacin itama Inna ta wuce Rano. Gidan ya zama daga su sai su, sai ko Ma'aruf wanda Abba ya k'i amincewa da komawarsa gidansa adalilinsa na tsoron halin da zai jefa kansa saboda damuwa. Sai kuma Malama Atine wacce ita ke shayar da Hanif, yaron Ma'u.
  Babu wanda ba ya ji da Hanif, daidai da 'yan uwan mahaifiyarsa sukan lek'oshi. Da wuya ayi sati batare da wani cikinsu yazo ganinsa ba. Bintu da Aisha kuwa, d'akin da yake nan ne wajen hirarsu tare da Atine muddin basu da karatu.
  Tsakanin Bintu da Ma'aruf kuwa, raina mishi wayon da ta saba yi, ta rage sosai ganin yanda shi kansa ya sanyaya.
    Saidai bayan watanni biyu ta fahimci ashe lam6o yayi ba wai ya chanja bane.  Abinda ya had'asu kuwa shine.
   Tana bacci gefen Hanif yaro mai watanni biyu, wanda saboda gata da kulawar da yake samu sai ka rantse d'an watanni hud'u ne. Cikin magagin baccinta ta d'ora mishi hannu a wajen hanci, ai kuwa yaro ya hau numfarfashi, Allah Ya taimaka Ma'aruf  yayi sallama ya shigo wanda sam Bintu bata ji ba, Allah Ya yi ta mai nauyin bacci. Atine suna falo suna hira da 'yan aiki. Lokacin k'arfe uku na rana. Babu zato ya kai mata wawan duka a k'afa. Ta mik'e a gigice tana sosawa.
  "Tsabar iskanci kashemin yaron zakiyi?! Atine! Atine!!"
  Ai da sauri ta yo d'akin. Nan yayita bud'emata wuta. Ya kuma gargad'eta koda wasa kada ta k'ara yarda Bintu tayi bacci a gefen d'ansa.
  Bintu ta turo baki tana dubansa. Ya danna mata harara.
 "Sai na yanke wannan bakin mai kama da na tsuntsaye. Tashi ki fita kafin na karyaki!"
  Ta mik'e cikin fushi ta bar d'akin.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<14>>
  Gadonsu ta fad'a, wani wawan bacci ya kwasheta tuni ta mance da haushin Ma'aruf da takeji. Ba ita ta farka ba saida Mami ta tasheta don gabatar da sallar isha'i.
  "Kwanakin nan kin zama wata kasa, baki da aiki muddin baku da makaranta sai bacci. Kina bani mamaki, wannan bansan me zaki tsinana a gidan aure ba."
 Tana jin Mami na faman maganganu har ta fice. Ganin da tayi wani sabon baccin na neman kwasarta ne ya sanyata mik'ewa da k'arfinta. Ta fad'a band'aki.
  Bayan ta gama uzurinta ta d'ora alwala ta fito. Saida ta idar da sallah sannan ta fad'a ta k'ara wani wankan sakamakon zafin da ya addabeta.
   Ta shirya cikin brown tshirt da siket bak'i. Bata bi ta kan d'ankwali ba, ita kam basa jituwa da d'ankwali. Gashinta tufke da ribbon ta nufi falon.
   Tayi mamakin ganin Sadauki tare da babansa. Gaba d'aya suke zaune har Ma'aruf da Aisha wacce  bata jima da shigowa gidan ba itama.
 Da gudu-gudu yaron ya nufota da tafiyarsa wacce batayi kwari sosai ba. Yana son Bintu, har ya ganeta, ita d'inma kasancewar tana mishi wasa sosai ne. Yaron yana da kwuiwuya idan yaso. Ganinta ne ya sanyashi warewa amma a farko yana nannad'e jikin mahaifinsa.
  Da sauri ta d'aukeshi ta cilla sama tana dariya.
  "Oyoyo my lovely son. Ummuah!" Ta sakar mishi sumba a le66ansa. Ya kyalkyale da dariya. Mami tace
 "Oh, kiga yaro, tun d'azu ya k'i sakewa amma ganin mutuniyarsa har da kyakyacewa."
  Rufa'i da Aisha suka dara. Bintun ma tana dariya ta k'araso zata zauna.
  "A'a, ban hanaki zama babu d'ankwali ba? Oya, koma ki d'auko." Cewar Mami.
 Dolenta ta koma tana d'auke da Sadauki har d'aki, bayan ta d'auko suka fito.
  Ko kallon sashen da Ma'aruf yake bata yi, ballantana ya saka ran samun gaisuwarta. Ta gaida Yayanta Rufa'i. Ya amsa cikin nuna jin dad'in ganinta.
 "Kamar kuwa kinsan inada magana da ke kanwata."
  Ta bar yiwa Sadauki wasa ta dubeshi fuska a sake.
  "Magana wace iri Yayan?"
 "Kema kinsani, maganarmu ta rannan har yau bakice uffan ba."
  Sai lokacin ta tunano, ashe fa ya sanarmata abokinsa Ukasha ya nuna yana sonta. Ta dubi gefen Mami, idanunsu yana kanta. Jikinta ya bata Ma'aruf ma kallonsu yakeyi. Ta yamutse fuska.
 "Ai don kada na fad'a kaga kamar na wulak'anta abokinka ne wallahi."
  Mami da Aisha har Rufa'in suka dara. Mami tayi kwafa, kafin ma Rufa'i ya sanarwa Bintun ita ta soma ji, daman tasan za'a rina.
  "A'aha, saidai idan ba Fatima Bintun da na sani bace. A komai sai ta kwa6a shiriritarta."
   Bintu ta dubeta da murmushi.
"Allah Mami ba zancen shiririta ba, ni ban fiyeson mutum mai sirantaka ba. Ka ba shi hakuri, Allah kuwa bana sonshi. Ai karatu ma nakeyi ko Mami?"
  Mami da Aisha suka tuntsire da dariya, hatta Ma'aruf wanda rabin hankalinsa ke a waya saida ya murmusa jin abinda ya fito daga bakinta. Rufa'i ya d'an d'aure fuska kad'an.
  "Wulak'ancin da zaki yiwa abokina kenan? Kinsan kusancinmu kuwa?"
  Kafin tayi magana, Mami ta rigata.
  "Wai ana so dole ne Rufa'i? Tunda yarinya ta nunamaka bata sonsa ai sai ka rabu da ita. Nifa banason takurawa mutum."
  Rufa'i yana jijjiga muk'ullin motarsa yace "Allah kuwa Mami kuna sangarta yarannan da yawa. Kamar wannan k'atuwar ace har yanzu wulak'anta maza takeyi, wataran sai kin nemi mashinshini kin rasa. Ukashat yafi k'arfin ajinki, don ma dai kawai so baruwansa."
  Ganin ya fusata, ya sanyasu dariya. Sai lokacin Ma'aruf ya tofa,
  "Toh kai menene na fusatar? Ni ai sun burgeni, idan karatun karatu, idan auren to ayi auren. Babu amfanin kula samari barkatai. A zamanin nan na yanzu sai ana kaffa-kaffa. Kodayake naga ita waccan boss ta kanta ce."
  Ya basu labarin sunayen da ya ta6a gani ta sanyawa samarinta. Rufa'i kansa saida ya dara. Ita kuwa ko a jikinta don bata huce da abinda Ma'aruf yayi mata ba, sai ma ta mayarda hankalinta ga yiwa Sadauki wasa. Ba zato ta ji an mako mata filo.
  Mami ce, cikin dariya take fad'in.
 "Jimin ja'irar yarinya, ashe abinda kuke aikatawa kenan? Eh lallai zan kwace wayoyinku."
  Bintu sai lokacin tayi dariya. Atine ta fito rik'e da Hanif wanda ta chanjawa kaya. Bintu ta bishi da kallo, taji wani sanyi, tun d'azun tunaninta yana kansa saidai batason shiga d'akin ganin Ma'aruf a wajen. Ga Ma'aruf kuwa, ya lura da fushin da takeyi da shi, abin mamaki, sai ya ji ya damu. Yana rik'e da Hanif, saidai jefi-jefi yakan dubeta, sai wasa takeyi da Sadauki tana hira da Rufa'i wanda dolensa ya saki ransa ganin Bintu bazata bar shi ba. Sunata hirar har Mami, can kuma Hanif ya soma kuka. Tayi saurin dubansa, ganin ta had'a ido da ubansa ta basar gami da d'auke kanta.
 Ita kam ko kukan yaron bata so. Tana gani uban ya mik'e ya sa6ashi a kafad'a yayi waje yana raino, ta bi fuskar yaron da kallo da murmushi kafin ta maido dubanta ga Sadauki.
  "Yayan, wai yaushe zaka kawomana Sadauki kwana? Mami ku lura bai ta6a kawoshi ba."
  Mami ta ta6e baki
 "Yaron yanzu kenan, son 'ya'yansu Bintu. Baki ganin ko yini zai kawoshi, saidai su yinin tare?"
  Rufa'i ya rufe fuska yana dariya.
 "Yaron nan fa ba'a yayeshi ba."
 "Mami rannan fa agabanmu yayita fad'a wai meyasa Anti Hajara ke bari ana fita da shi makwafta? Bayaso." Cewar Aisha.
 "Ai shikenan, yanzun ma ya tashi ya wuce da shi."
 Bintu tana dariya ta amsa.
 "Madara yafi sha kuma. Kawai dai Yayan bayason nesa da yaronsa."
  Mami bata k'ara magana ba, k'arshe ma ta mik'e ta bar falon. Hirar batayi tsawo ba, Rufa'i ya fice ganin hadari a garin.
  Bintu ta dawo ciki ta dubi Aisha.
 "Wai yayanki baisan ba'ason fita da yaro idan ana iska ba haka, don Allah jeki kice ya maidoshi ciki, kallesu can a harabar gidan."
  Aisha ta harareta.
"Tsawon baki na fiki ne? Jimin ke d'innan ma. Banda haka, mutum da d'ansa."
  Bintu ta ja tsaki.
"Banza mai fuskar buzaye." Daga haka ta fito Aisha na mata dariya.
 Ta lek'osu ta windon falon, suna tsaye ya rufe mishi kai da shawul, har lokacin ana iska, ganin da tayi iskar ta soma k'arfi yasa ta kasa hak'ura da saurinta ta nufi k'ofa. Shima a lokacin ganin iskar na yawa ya sanyashi yo hanyar falon. A fili take masifa.
  "Ya fita da yaro cikin wannan iskar kamar..."
 Sauran maganarta ta mak'ale a fatar bakinta ganinsa a gabanta. Ya zubamata idanu, haka kawai ta ji kallon ya sanyaya jikinta. Ta juya da sauri, ya dakatar da ita da fad'in.
 "Kar6eshi." Dolenta ta juyo tana wani cin magani.
 "Me d'in?"
 Yayi d'an murmushi a ranta tace "Ba saban ba."
  "Ina tunanin shi kikazo kar6a."
 Ta tsuke baki, idanunta suka kai ga shanyarta. Ta nuna da yatsa.
 "Shanyata..shanyata na zo kwashewa."
  Ya dubi kayan.
 "Daman ke kika saba kwasa?"
 "Ai d'an dolon bayanan."
  Bai bi ta kanta ba ya gota ya shige ciki ganin idan baiyi da gaske ba ruwan zai iya zubowa batare da ya koma d'akinsa ba.
  Ta rik'e k'ugu ta bi bayansa da kallo. Dolenta ta kwaso kayan gudun kada ya k'aryatata. Tana kallonsa da sauri sauri ya nufi d'akinsa. Itama da sauri tayi ciki don tuni ruwa ya soma sauka.
  A falo ta yasar da kayan ta nufi d'akin Hanif. D'aukar yaron tayi tana mishi wasa. Tana son yaron, kusan tare suke rainonsa da Atine. Haka ta wuni a d'akin har akayi kiran sallah.
                           * * *
<<15>>
Haka rayuwar ta gidan ke tafiya cikin jin dad'i da kwanciyar hankali. Idan an d'auke mage da 6eran gidan wad'anda basu fiye jituwa ba.(Ma'aruf da Bintu).
Sun bararraje a falo da k'anwar Ma'u, Hafsa wacce bikinta ya k'arato suna duban ankonta.
"Kai, wallahi yayi kyau. Bari na kaiwa Mami ta gani." Cewar Aisha.
Bayan tashin Aisha, Bintu ta muskuta kusa da Hafsa.
"Wai wa zaki aura?"
Hafsa tayi farr da ido.
"Ina da wanda yafi Bash?"
Bintu ta kya6e baki.
Yayi daidai da tahowar Ma'aruf, zaiyi sallama ya tsaya cak jin furucin da Bintu tayi wanda ya girgizashi. Ga abinda tace.
"Kema dai Hafsa, ke bakiga yanda akeyi ba. Idan yayata ta rasu, sai a bawa k'anwarta mijin? Saboda yaranta su samu gata. Wai Bash? Mts."
Hafsa ta d'aure fuska, daman wata kakarta ta ta6a yi mata wannan maganar. Nan take haushin Bintu ya kamata. Ta mik'e ta d'auki jakarta.
"Ni bana wannan ra'ayin, bana sonsa. Kuma aurena da Bash, in sha Allah babu abinda zai hana. Idan kinga damar zuwa ki zo, idan kuwa bakiga dama ba kada ki zo."
Daga haka ta nufi falon Mami na biyu. A fili Bintu ta rik'e baki tayi magana.
"Oh, ina laifin Yayanmu, Bash d'in da bai fi a dunk'ule a jefa aljihu ba tsabar gajarta?"
Daidai lokacin Ma'aruf ya fita baranda, saida ya kammala cin dariyar furucinta na k'arshe kafin ya shiga.
Ta mik'e da zummar barin falon itama da zummar k'ara fesawa Mami hangen da tayi sukayi kici6us da Ma'aruf. Ta amsa sallamarsa a tsorace. Bata so zuwansa yanzu ba Hafsa na nan, tsoranta kada ta sanarmishi kato6arar da tayi mishi. Ganin babu walwala a saman fuskarsa yasa ta azamar gaisheshi.
Ya amsa kafin yace.
"Ki zo ina nemanki."
Daga haka ya juya ya fita. Ta had'iyi miyau, to fa, yau kuma da wacce yazo? Hankalinta ya kasu gida biyu, tana son k'arasawa wajensu Hafsa, ga kuma kiran Yaya Ma'aruf.
"To idan dukana zaiyi fa?" Ta tambayi zuciyarta. Dabara ta fad'o mata. Bari ta tafi da Hanif, tasan yanda yake son d'ansa bazai iya yi mata komai ba. Da sauri ta nufi wajen Atine ta kar6eshi ta goya.
K'ofar a bude, ta shiga da sallamarta.
Yana tsaye gaban firij yana fiddo gwangwanin Maltina. Ya dubeta, murmushi ya saki har hak'oransa na bayyana. Ta k'araso ta zauna.
"Yaya gani"
Ya maida firjin ya rufe ya zauna yana fuskantarta. Itama shi take kallo, ta dauke idanunta. Ita kam tafi sabawa da hararar da yake danna mata akan kallon salama d'innan.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<16>>

 "A kanki nake zaune?"
 Cikin rashin fahimta ta dubeshi. Bazaka fahimci yanayin da ke a saman fuskartasa ba.
  "Yaya bangane ba."
 Ya ajiye gwangwanin Maltina bayan ya kur6a.
 "Me kika cewa Hafsa?"
 Gabanta ya fad'i, ashe yayi musu la6e? Oh, yanzu ya zatayi?
 "Ko baki gane ba?"
 Ta mik'e tana jijjiga Hanif wanda ke zullo shi a dole sai ta saukeshi.
  "Saukeshi."
 Ya fad'a, ta saukoshi ta rik'e.
 "To ai ni bansan abinda na fad'a ba."
  Shiru ya biyo baya, sai kur6ar lemunsa yakeyi yana dubanta rik'e da gudan jininsa. A hankali ya sauke ajiyar zuciya.
  "Munyi dake ki nemamin matar aure ne?"
  Yanda yayi zancen a sanyaye ya sanya ta d'ago dara-daran idanunta ta dubeshi, wani sassanyar kallo yake yi mata wanda yasa ta jin abinda tun da suke tare bata ta6a jinsa ba. A sannu ta sauke kanta ta maida ga Hanif wanda ke wasa da agogon hannunta.
   "Baki ban amsa ba, meya kawomiki tunanin nemamin auren Hafsa?"
  Gabanta ya soma fad'uwa ganin yanda yake maganar a sanyaye, ita fa tafi ganewa maganarsa a sama-sama yanda ya saba yi mata magana.
  Ta zubawa Hanif ido, tana matukar son yaron. Batasan sadda ta soma fad'in zahirin abinda ke cikin zuciyarta ba.
  "Tausayin Hanif nakeji. Kowane yaro yana so ya rayu tare da mahaifiyarsa, saidai Allah baiyi Hanif zai rayu da tasa mahaifiyar ba. Na sha gani yana faruwa a wasu wuraren, mijin yaya ya auri k'anwarta bayan rasuwarta saboda ta kula da 'ya'yan 'yar uwarta. Shine dalilina na yiwa Hafsa maganar. Kayi hakuri dan Allah."
  Ta k'arashe cikin rawar murya. Alal hak'ik'a tana tausayin Hanif, har ta sha fad'a a gabansu Mami, ita kam duk radda tayi aure da Hanif zata tafi. Aisha kan tsokaneta, ya zatayi idan Yaya Ma'aruf yayi aure ya damk'awa matarsa Hanif.
  "Wallahi idan muguwa ce, labari ya risk'eni ta ta6a lafiyarsa, ke zan biyo gidanki na kwasa muje muyi mata tsinannan duka."
  Wannan ne furucinta, har ma ya basu dariya.
  A wannan shirun da tayi, a nan ya samu damar nazartarta.
  Gaba d'aya bai fahimci kansa ba. A sannu ya kai duba ga yaronsa, bai iya furta komai gareta ba. Can kuma ya samu damar magana.
  "Nagode da wannan k'auna da kike nunawa d'ana. Amma ina mai gargad'inki, banaso ki k'ara yiwa Hafsat maganar nan. Daidai da Mami banason yaje kunnenta. Ni Ma'aruf bana tunanin aure yanzu, Asma'u..." Sai kuma ya fasa cewa uffan, ransa na sosuwa a duk lokacin da tunanin Asma'u ya fad'o mishi.
  "You can go."
 Ta mik'e rungume da Hanif tayi hanyar fita. Ta juyo kad'an ta dubeshi, idanunsa a kanta, tayi azamar d'auke kanta ta fice. Haka kawai ta rasa abinda yasa ta jin tausayin Ma'aruf a karo na biyu bayan rasuwar matarsa.
   A farfajiyar gidan sukaci karo da Aisha wacce ta yiwa Hafsa rakiya.
 "Ina kika shiga, Hafsa ta tafi."
 Ta numfasa, maimakon tayi magana sai kawai ta mik'a mata Hanif tayi gaba. Aisha ta bi bayanta da kallo. Anya kuwa lafiyarta kalau? Ta bi bayanta zuaa d'aki ganin da tayi bata falon.
  Ga mamaki, kuka ta tarar tana yi har da sheshshek'a.
  "Ke lafiya kuwa? Meyafaru?"
  Bata kulata ba, ganin tana niyyar zuwa kiran Mami ya sanya ta dakatar da ita.
  "Tsaya, wallahi Yaya ne ya tunamin Anti Ma'u, duk sai ya bani tausayi."
 Aisha ta numfasa. Bintu ta labarta mata abinda akayi bayan ta rok'eta alfarmar kada ya je kunnan Mami.
  Aisha tayi murmushi.
 "Allah Sarki, ai daman za'a sha wuya kafin Yaya ya amince yayi aure. Ashe Abba ma ya yi mishi zancen aure kwanaki, shine dalilin rashin lafiyar da ya yi a satin da ya wuce. Yanzu sai an had'a mishi da addu'a, Allah Ya sanyaya zuciyarsa. Ke nifa banga abin tashin hankali ba, duka-duka ko shekara ba'ayi da rashin Anti Ma'u ba, shima kingani ai Abban shiyasa bai k'ara maganar ba. Hum, wayasani ma ko 'yar gida zamuyi muku."
  Ta k'arashe da zolaya. Ai tuni Bintu ta mance da kukanta. A harzuk'e tace.
 "Wallahi yanzu zan d'ura miki ashariya, shegiya. Bakinki ya sari d'anyen kashi. Aka had'ani da Yaya Ma'aruf ai an nakasta rayuwata."
  Gane inda ta nufa ya sanya Aisha tuntsirewa da dariya. Bintu tayi kwafa.
 "Kya yi dariya mana, muguwa kawai.  Ke kafin ma ayi wani batun, ko hoto akayimana da shi ai an cuceni. Mutum kamar zabiya, tab. Ai wallahi mata ma kad'ai sun isheni."
 Aisha tana dariya ta amsa.
"Kuma bakisan wani abu ba, wallahi har zawrawa sonsa sukeyi. Kodayake ai ke shaida ce. Dubi k'awar Anti Amina, Iklima, da biyu matar nan ke kawowa Hanif ziyara. Mace babba mai shekaru talatin, kusan sa'arsa ce."
  Kwafa Bintu tayi. A rayuwa babu wacce tafi jin haushi kamar Anti Iklima. Ta lura wayewarta ya yi over, ga afkin bleaching, har fuskarta tayi tabo. Ita a dole son Yaya Ma'aruf take.
 "Ai ita wannan idan batayi hankali ba, wataran sai na koyamata hankali."
  "Me zai dameki da ita? Wajenki take zuwa?"
  Harararta tayi.
"Yaya Ma'aruf ai yayana ne inace? Shi kansa na kula baya k'aunarta wallahi. Daga ya ganta yakeyin kicin-kicin, ke dole ma na koyamata hankali."
  Aisha na murmushi,
 "Wai anya babu wata tsakanin..."
  Ashar d'in da Bintu ta lailayo ya sanyata yin shiru da azamar rufemata baki tana jan a'uziyya.
 "Baki da hankali?" Cewar Aisha.
 Ta fisge hannunta.
 "'Rainin wayo kai, na gayamiki babu komai tsakanina da Yaya Ma'aruf, sai kawomin k'abli da ba'adi kikeyi. Bar ganin kin fini jiki sai na zauneki na jibgi banza."
  Aisha ta ajiye Hanif ta soma k'ok'arin mak'ureta. Ai da gudu ta fice tana dariya, daman sai cika bakin, amma babu k'arfin.
                       * * *
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶
©Rufaida Omar
(July...2016)
<<17>>
A kwana a tashi babu wuya wajen Mai Sama,
har gashinan an shiga satin bikin Hafsa da
Bashir. Nan fa Aisha ta zama busy, koyaushe
da ita Hafsa ke shirye-shirye kasancewarta
aminiyarta. Da zarar Aisha ta taso
makaranta, bata yo gida sai can gidansu.
Duk yanda tayi Bintu ta dinga taimakonsu da
wani abin, tace ba ruwanta ita bata kalan
dangi.
Ana gobe za'a soma biki, Aisha ta koma
gidansu Hafsa da zama. Bintu ta k'ek'eshe
tace ba da ita ba, gad'a a mak'ota. Babu
inda zata, dole Aisha ta fice da fushinta. Ko
a jikinta, acewarta babu dangin iya bare na
Baba, zata dai lek'a bikin.
Washegari asabar, misalin goma ba safe,
tana zaune a falo tana karyawa kasancewar
bata jima da tashi ba. Mami na zaune tana
bawa Hanif maganin mura, Ma'aruf yayi
sallama ya shigo. Bintu ta dubeshi, ya gama
had'ewa cikin tsadadden yadi kalar ruwan
toka, hannunsa sanye da agogo ruwan silver
sai zobunan azurfansa biyu a kowane hannu.
Yayi kyau har ya gaji da had'uwa. Ya gaishe
da Mami, ta amsa da murmushi.
"Yau babu baccin safen? Ina zuwa haka?"
Ya gyara zaman hularsa idanunsa akan
Hanif.
"Akwai wani abokina ne bai ji dad'i ba
kwana biyu, shi nakeson lek'awa."
Mami ta gyad'a kai. Sai lokacin Bintu ta
gaisheshi, ya amsa ba tare da ya dubeta ba,
ta ta6e baki. Yanzu mamakinsa takeyi, tun
maganar Hafsa da sukayi, kusan sati da 'yan
kwanaki kenan, ya chanja mata. Bai fiye
shiga harkarta ba, ko meyasa? Bata da
amsar hakan. Maganar Mami ta katseta.
"A'a, ga Bintu ku je tare ka sauketa a gidan
walimar nan tasu."
Hakan yasa ta dubansa, shima ita ya duba
kafin ya dubi Mami fuska a yamutse.
"Ina direban ya shiga ne?"
Mami ta 6ata fuska.
"Ai nasan da zamansa nace kuje tare. Ka
sauketa, yau ba zai zo ba."
Ya dubi Bintu fuska a 6ace sai kuma ya
mik'e.
"Idan ta shirya tayimin magana."
Daga haka ya fice, yana ji Mami nayi mata
maganar tayi sauri. Bintu ta mik'e fuska a
6ace, ita kam bataso aka had'ata tafiya da
Ma'aruf ba.
Ta ci wajen mintuna talatin da wankanta da
shirin. Walimar ba ta anko bace, yini ne na
'yan mata. Don haka ta sanya material
ruwan k'asa, d'inki mai matuk'ar kyau akayi
mata. Ya zauna d'abas a jikinta. Ta murza
d'aurin d'ankwalinta bayan ta kammala fente
fuskarta da kwalliya. Ta feshe jikinta da
turaruka masu sanyin k'amshi don ko kusa
Mami bata barinsu amfani da k'arfaffan
turaruka.
Ta fito, d'akin Mami ta soma shiga tayi mata
sallama, Mami ta bata kud'i ta zura a
jakarta. Saida ta shiga d'akin Hanif ta
sumbaci goshinsa kafin ta fice.
"Kwas, kwas." Take takunta da takalminta
mai d'an tsawo, tana son takalma masu tsayi
duk kuwa da cewar ba gajera bace. A haka
har ta nufi sashen Yaya Ma'aruf.
Ta shiga da sallama, yana kwance saman
kujera idanunsa a lumshe. Ta zuba mishi ido,
kamar wanda aka k'arawa haske da kyau. Ga
sajensa ya kwanta luf-luf. Haka kawai ta
tsinci kanta da dubansa, a sannu ya bud'e
idanunsa suka sauka cikin nata. Da sauri ta
kauda idanunta.
"Na shirya."
Ta fad'a cikin in-ina. Ba shi da niyyar
mik'ewa, saidai bai maida idanunsa ya rufe
ba, ya cigaba da dubanta.
Jin shiru yasa ta jin haushi, ta juya zata bar
d'akin.
"Ki jirani."
Ta bi umarninsa ta tsaya a k'ofar d'akin, ya
fito ya rufe da muk'ulli. Suka jero.
Abba yana zaune a 'yar barandarsa yana
karatun jarida, yayinda Mami ke k'ok'arin
zuba mishi ruwa a kofi. Hankalinsa ya kai
garesu, a gaban idonsa suka jero har
Ma'aruf ya bud'e mota suka shiga. A hankali
yakejin wani tunani yana d'arsuwa a
zuciyarsa. Muryar Mami ta katseshi.
"Abban Aisha, ga ruwan."
Ya numfasa ya kar6a ya sha alokacin da
maigadi ya maida kyauren ya rufe.
Bayan ya kammala sha ya ajiye kofin gami
da duban Matarsa da murmushi d'auke
saman fuskarsa....
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<18>>
"Yaranki ne suka ban sha'awa."
Cikin rashin fahimta Mami ta tambaya.
"Wai Bintu da d'anka?"
Ya jinjina kai.
"Kwarai na ji musu sha'awar kasancewa tare k'ark'ashin inuwar aure, duba da abubuwa da yawa. Saidai ke d'ince bansani ba ko zaki iya bamu 'yar ta ki."
  Mami tayi shiru, ita kanta ta jima tana wannan tunanin, saidai sanin halin Bintu da Ma'aruf ne yasa ta danne sha'awarta, ta tabbatar da kamar wuya su amince da hakan. Musamman na ita Bintun.
  Tunaninta ya katse sakamakon rik'o hannunta da Abban ya yi.
  "Lallai idan hakan ya tabbata, ba mu ba, har su yaran zasuyi farinciki Fatima. Baki lura da yanda yarinyar ke tsananin k'aunar Hanif ba? Ki sanyawa lamarin albarka. Sauran ki barwa Allah, ni kuma zanyi k'ok'arin fahimtar da yaronnan."
  Ta dubi mijinta, annurin da ta gani kwance saman fuskarsa ya tabbatar mata lallai da gasken gaske ya d'auki lamarin har gashinan ya gaza 6oye farincikinsa. Batasan irin wannan k'auna da Abba ke yiwa Ma'aruf ba, tamkar shi kad'ai ne d'a a wajensa. Ta numfasa gami da zare hannunta cikin nashi
"Zan fi kowa farincikin k'ulluwar wannan al'amari, saidai karatun Bintu fa? A ganinka ita zata amince ta aureshi?"
  Abba yayi shiru kafin ya dubeta.
"Bana nufin tursasa musu, saidai yara mu muke da iko akansu ba su keda iko kanmu ba. Ballantana kuma na yiwa yarannan kyakkyawar shaida Fatima. Ina ji a jikina, in sha Allah, ba zasu bamu kunya ba. Batun karatu, ai aure bazai hanata karatunta ba. Ki bar komai a hannun Allah, in sha Allah zasu fimu jin dad'in wannan had'in."
  Mami dai hankalinta ya rabu gida biyu, a gefe guda tana mai jin dad'i idan ta misalta yau gashinan Ma'aruf da Bintu sun amince da auren juna wane irin farinciki zatayi? A gefe idan ta tunano rashin jituwarsu duk sai zuciyarta ta karye, bata hangen yiwuwar lamarin ko kad'an, abin ne da kamar wuya.
                      * * *
       A can kuwa, Ma'aruf da Bintu babu mai cewa wani uffan tun soma tafiyarsu. Motar tayi shiru ko rediyo bai kunna musu ba. Abinda sam Bintu bazata jura ba kenan, idan baza'ayi biyu ba to ayi d'aya. Ko suyi hirar ko ya kunna rediyo. Batason tafiyar kurame, hakan yasa ta fiddo wayarra ta hau k'ok'arin sanyawa kunnuwanta (Earpiece).
   "Ke baki iya hira ba?"
 Ta tsaya jin abinda yace, ta dubeshi hankalinsa na ga titi. Ta kauda idanunta.
  "To ai bansan abinda zance ba."
 "Bani labarin Banki da Sarkin Nanaye."
  Ya k'arashe da murmushi. Itama sai ta d'anyi dariya. Ya dubeta.
 "Ko ba sunayen nasu kenan ba?"
  Ta tsuke baki, to ta samu abinda take so.
   "Yaya ai sune suka fiye naci, na nunamusu bana sonsu amma wallahi sun addabeni. Ai Banki aure ma zaiyi yanzu, Sarkin Nanaye kuma ya gaji ya hak'ura."
  Ma'aruf na murmushi lokacin da ya sha kwanar da zata kaisu gidan su Hafsa sannan marigayiyar matarsa.
   "Kina da matsala Bintu, mijinki yana da aiki babba."
  Ta ta6e baki
 "Ni bana sha'awar aure fa a yanzu."
 "Sai me? Keda ga shi har soyayya kin iya kina yi."
  Tayi dariya.
 "Wannan sai A'i, ni bana soyayya. Na d'auketa 6ata lokaci wallahi. Shiyasa nake k'ara godewa Allah da bai ta6a sanyamin son wani namiji a rayuwata ba, son aure."
  Shiru ya biyo baya, can kuma Ma'aruf ya dubeta kad'an ya d'auke kai.
  "Ai nayi zaton bazaki k'ara shekara ba zakiyi aure. Kodayake banga namijin da zai iya da shiriritarki ba."
  Ta 6ata fuska.
 "Kuma a hakan fa wallahi sona ake..."
 Sai kuma ta fasa maganar ganin kallon da yayi mata. Ta muskuta.
 "To ai gaskiya ne."
 "Eh, irinsu Ukasha ba, amma sanin kanki maza ire-irenmu, munfi k'arfin ki."
 Ta dubeshi kad'an, wai me yake d'aukar kansa ne?
 Shi kuwa sam bai fad'a da wasa ba, ya fad'i iyakar gaskiyar abinda ke zuciyarsa ne. Baisani ba, furucinsa ya yiwa Bintu zafi matuk'a.
  Ya faka a k'ofar k'aton kyauren gidan.
  "Bismillah, jeki."
 Ta dubeshi lokacin da ta murd'a k'ofa. Kamar ta gasa mishi bak'a sai kuma ta fasa ta fita a fusace gami da banko k'ofar da k'arfi. Har saida ya firgita.
  Sai lokacin ya tunano furucin lallai zai iya 6ata ran mace mai ji da gayu irin Bintu. Yayi 'yar dariya kafin  ya ja motarsa. Ai kam da wuya, su had'u wuri d'aya da Bintu ayi rabuwar arzik'i.
   Ita kuwa haka tayi ta yiwa Aisha mitar abinda yace. Tun Aisha na sauraro har ta gaji.
 "Ke wai magana bata wucewa a wajenki? Menene abin jin haushi anan? Ni banga abin damun kai ba, kin mance da bakinki kin sha fad'a babu abinda zakiyi da kamar Yaya Ma'aruf?"
  Bintu ta numfasa cikin yanayin fushi.
 "To ai ni a nufina na fi k'arfinsa ne, ba wai yafi k'arfina ba."
 Aisha tayi dariya kawai, lallai ma Bintu, ta yaya zata had'a kanta da Yaya Ma'aruf? Kodayake ance mace ta fi namiji kyau watakil da wannan furucin na bahaushe take tutiya.
  Har aka tashi walimar bata saki ranta ba, ta ji haushin abinda yace mata, ta kuma ci alwashin ramawa.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<19>>
  Duk yanda Aisha ta so ta zauna ta kwana, amma fafur fa k'i. Dole haka suka rakota titi suka koma. Tana daf da kaiwa bakin babban titi inda anan take saka ran samun abin hawa, ta ji hon a bayanta. Ko tsayuwa batayi ba ballantana ta juyo ta dubi mai shi.
  Banda murmushi babu abinda yakeyi, bai so biyowa d'aukarta ba saidai babu yanda ya iya tunda Mami ta kira ta shaida mishi ya biya d'in sanin da tayi Bintu ba zata amincewa kwanan ba. Isarsa ne Aisha ke sanarmishi ko mintuna biyar batayi ba da tafiya, hakan ya sanyashi biyo titin sanin ana wuyar abin hawa a titin cikin unguwar ba lallai ne tayi sa'ar abin hawa ba.
  Hon da ya cika kunnuwanta ne ya sanyata tsayuwa gami da juyowa a fusace da niyyar yiwa mai shi rashin mutunci. Saidai ganin motar yasa ta fahimtar Yaya Ma'aruf ne. Ya bud'e murfin mota ta fito yana dubanta.
"Ke bakyajin hon ne? Taho mu tafi." Ta dubi gefenta, wasu samari ne zaune suna dubansu.
  "Alhamdulillah." Ta fad'i a ranta.
Cikin d'aga murya tayi magana.
"Wai kai Malam wane irin naci ne haka? Tun d'azu kake bina, na gayamaka bana sonka, ko dole ne?!!"
  A fusace ya nufota, tayi azamar d'aga hannu gami da ja baya a tsorace.
"Wallahi koda wasa kada kayi gangancin ta6a lafiyata, ana so dole ne? Ba gayamaka bana sonka!"
  Daga haka ta ja tsaki ta juya, tana jin sa'adda samarin suka kwashe da dariya har da masu fito. Ma'aruf ya rasa abin cewa, gaba d'aya ta d'aureshi da jijiyoyin jikinsa. Ya gaji da binta da kallo kawai ya fad'a motarsa a fusace ya ja.
  Cikin matsanancin gudu ya wuceta har yana tayar da k'aramar guguwa.
   "Yau naga ta kaina." Ta fad'a a fili. Anya zata koma gida? Kai babu batun kome, ta gwammace tayi kwanan gidansu Hafsa idan yaso gobe Mami ta tahomata da kayan buk'ata ko ta bayar a kawomata. Amma ai ta riga da tayi musu sallama. Kawai sai ta hau mota, kai tsaye gidan yayanta Rufa'i ta je. Suna zaune da Hajara sai ganinta sukayi kamar an jefota.
"Ke kuma lafiya?"
Ta zauna, hannu ta kai ta ja ruwan dake ajiye saman faranti akan center table ta kur6a.
"Anan zan kwana."
Rufa'i da Hajara suka dubi juna. Kafin su tambayi komai, ta kwashe abinda ya faru ta sanarmusu. Rufa'i mamaki ya haneshi cewa uffan, Hajara kuwa banda salati mai had'e da dariya babu abinda takeyi.
  "Wai Bintu baki da aljanu kuwa?"
Bintu ta turo baki.
"Lafiyata lau, ai shine ya ja. Cewa yayi fa wai maza ire-irensu sunfi k'arfin ajina."
  Rufa'i yayi wani murmushi tunano maganar da Mami ta gayamishi d'azun. Lallai akwai badak'ala.
"Banda abinki, kema kinsan broda ba shi da rufa-rufa. Idan ya fad'i abu iyakar gaskiyarsa yake nufi. Amma ni kaina ban ji dad'in abinda yace ba. Ai kinfi k'arfin ma ire-irensa."
  Hajara ta tuntsire da dariya.
"Yanzu kin sanarwa Mami kina gidana?"
Ta girgiza kai. Ya dauki waya ya kira Mami ya shaidamata.  Mami tace babu wani abu. Da kansa bayan ya fita da dare ya biya ya kar6o mata kayan amfaninta. Bai ko had'u da Ma'aruf ba ballantana ya ba shi hak'uri kan abinda Bintun ta yi.
                        * * *
   Ma'aruf fa???
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<20>>

Maimakon ya nufi gida, sai ya zarce zuwa gidansa. A fusace ya shiga falon gani da zama kan kujera ta zaman mutum uku wacce batayi k'ura ba sakamakon yana zuwa lokaci-lokaci yasa d'an dolo ya gyara ko'ina.
  Ya runtse ido yana huci, a sannu kuma abinda ya faru ya shiga dawowa kwanyarsa. Ba shakka Bintu tayi masifar rainashi. Kasa zaman gidan ya yi ya fito. Iyakar tsawon rayuwarsa, babu macen da ta ta6a yi mishi wannan wulak'ancin sai ita. Wai k'anwarsa, wacce ya d'auketa wata yarinya da batasan komai ba sai shirme da shiririta. Lallai idonsa idon Bintu, hum!
   Koda ya isa gidan, bai zarce ko'ina ba sai d'akinsa. Har wayewar gari Mami da Abba basu sanyashi a ido ba.
   Safiyar washegari, bai fito ba sai wajejan goma na safe.
  Mami na zaune a falon Abba suna hira sai gashinan. Ya shigo da sallama, duk suka dubeshi suna masu amsawa. Ya had'e cikin jeans blue marar nauyi, sai farar shirt, kansa babu hula gashinan nan yayi luf-luf. Zama yayi ya gaishesu har lokacin 6acin ran nan da Bintu ta jaza mishi yana nan mak'ale cikin ransa har ma ya shafi walwalarsa.
  "Ya akayi dai kakana? Akwai abinda ke damunka?"
  Maganar Abba ta sanyashi sakin fuska kad'an, ya zauna ya tankwashe kafafunsa.
"Babu komai Abbana."
Abba ya gyad'a kanshi. Zaiso a yanzu ya ji ta bakinsa, saidai rashin walwalar da ya gani tattare da shi yasa shi yin shiru.
  "To, Allah Ya rufa asiri, acigaba da hak'uri da rayuwa."
"Amin. Nagode Abbana, addu'arku muke buk'ata koyaushe."
  Abba ya gyad'a kai cikin jin sanyi a ransa.
"Kuna tare da shi a koyaushe in sha Allah."
  Haka suka cigaba da hirar duniya har Mami ta fita ta barsu. Saida Ma'aruf ya sake sosai sannan Abba ya numfasa.
   "Kakana, akwai maganar da nakeson muyi."

Gaban Ma'aruf ya fad'i, ya soma ambaton Allah.
"Ina saurarenka Abbana."
D'akin ya d'anyi shiru kafin kuma Abba ya soma magana. Saida ya soma na nasihohi masu nuni da muhimmancin yarda da k'addara kafin ya gangaro zuwa ga abinda yakeson fad'a.
  "Madallah, a matsayina na mahaifinka, ina mai neman amincewarka wajen had'aka aure da 'yar uwarka Fatima Bintu matuk'ar hakan bazai zamto cutarwa ba ga rayuwar d'ayanku. Ka sani, bani da burin tursasaka, ko a farkon aurenku ma kaida d'an uwanka  ban tursasa d'ayanku ba, saidai kowannenki da kansa ya za6i matar aure. A wannan karon ma, ba hakan nakeson ayi ba. Na baka nan da kwanaki uku, kayi tunani ka yanke abinda kaga ya dace. Idan baka k'aunarta, to lallai ka sani, ba zan tursasa maka aurenta ba, hakanan itama Fatima Bintu, dukkan abinda tace akan lamarin, to fa bazan takura mata ba. Daman zumunci na so had'awa."
Abba ya d'anyi shiru yana duban Ma'aruf wanda gaba d'aya ya gama shiga hali na rikita.
"Kana iya tafiya."
Ya mik'e jiki kamar ba nashi ba, haka ya bar d'akin a daddafe. Bai iya k'arasawa falon Mami ba, zama yayi a kujerar dake a barandar Abba ya zubawa farfajiyar gidan ido kawai. Bintu? Bintu fa?!! Ita kuma Abba ya hango mishi matsayin abokiyar rayuwa? Ya Ilahi! 
  Saida ya kwashi mintoci kusan uku kafin ya mik'e ya bar wajen. Abba ya sauke labule ya koma saman dardumarsa ya zauna gami da d'aga hannu ya yi addu'ar neman abinda yafi alheri. Fatansa ya ga wannan aure ya tabbata.
    A can kuwa, Ma'aruf fa ya shiga tara ba uku ba, kansa ya d'aure matuk'a. Meya kawowa iyayensa wannan tunanin? Su rasa wanda zasu hasko a matsayin matarsa sai Bintu? Yarinyar da kunya bata isheta ba?
  Ya runtse idanu sannan ta bud'esu, nan da nan suka kad'a.  A yau mutuwar Ma'unsa ta dawo mishi sabuwa fil! Ba don mutuwa ta mishi YANKAR KAUNA ba, yaushe iyayensa zasuyi tunanin aura mishi wata Bintu? A yau ya k'ara jin kewa mai d'umbin yawa na Ma'unsa. A gefe guda wani iri tsanar Bintu yake ji.
 
  ("Wai kai Malam wane irin naci ne haka? Tun d'azu kake bina, na gayamaka bana sonka, ko dole ne?!!")

 ( "Wallahi koda wasa kada kayi gangancin ta6a lafiyata, ana so dole ne? Ba gayamaka bana sonka!")

 Ya runtse ido ya bud'e duk a lokaci guda. Cikin zafin nama ya mik'e ya nufi firij, ruwa ya ciro ya soma kwankwad'a kafin wani sanyi ya ziyarci ruhinsa.  Lallai zai koyawa yarinyar hankali, zai tabbatar mata cewar ita d'in marar kunyar k'arya ce.
  Alokaci guda ya saki wani guntun murmushi.
                      * * *
  A gidan Rufa'i kuwa Bintu ta sake sai hada-hadar tafiya gidan yini sukeyi tare da Hajara wacce itama zata je. A ranar ne kuma za'ayi Dinner Party, ta kama dole da yamma ta koma gida don kwata-kwata Mami bata had'o mata da ankonsu na Dinner ba.
  Bayan sun kammala, Rufa'i da kanshi ya saukesu wajejan uku na rana. A can suka iske Mami itama da Atine har da Hanif. Nan ta hau tambayar Binti dalilinta na k'in komawa gida, dariya kawai Bintu tayi bata ce mata komai ba. Ganin bata da niyyar maganar ta kyaleta. Aisha kawai ta sanarwa, saidai alokacin ta fahimci jini d'aya ba wasa ba, don kuwa da gaske Aisha ta ji babu dad'in abinda ta yiwa Yayanta. Bintu ganin haka itama ta watsar da ita, saidai basu ci ko rabin awa ba, Aisha ta sauke fushinta, ita d'in ko kusa bata da rik'o.
   Da yamma  Mami ta had'a Bintu da direba domin zuwa d'auko kayanta na dinner. A karshe Bintun tace zata fito kawai daga nan gidan. Yana sauketa, ya juya wajen Mami don su d'inma zasu halarci Dinner, kasancewar har da iyaye.
   Ta dubi farfajiyar gidan, wani sanyi ya ziyarci zuciyarta ganin babu motar Ma'aruf wannan ya bata tabbacin baya gidan. Hankalinta kwance ta shiga.
   Wanka ta soma yi sannan ta d'ora alwala. Saida ta idar da Magrib sannan tayi zaman gaban madubi ta shiga fente fuskarnan nata da kwalliya.  A fili take fad'in.
 "Yau zan kece raini."
 Ta kammala shafe-shafenta sannan ta fiddo orange lace d'in da sukayi na 'yanmata, d'inkin doguwar riga(fitet gown) ta zura. Nan ta k'ara zaman tafkeken ribbons dinta sannan ta d'ora nad'in da sukayo akanta.
   Ta saki baki tana duban kanta a madubi, iyakar had'uwa ta had'u. Wayarta dake k'ara tun d'azu tana yankewa, sai lokacin tayi niyyar d'agawa.
 "A'i ya dai?"
 K'arar da ta ji ya bata tabbacin sun kama hanya.
 "Kin fito? Mami tace ki tsaya ga Yaya Ma'aruf zai taho ku fito tare."
 "Tab!"
 Da sauri ta katse wayar, ta jera da wa? Ita kuwa me ya kaita wannan gangancin. Da sauri-sauri ta had'a 'yar jakarta ta zura takalminta tana magana a fili.
 "Hauka nakeyi zan fita da Yaya Ma'aruf? Kasheni kawai zaiyi "
 Saidai me?

 

[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<21>>
  Bata kai ga bud'e k'ofar d'akin nasu ba ta ji hon d'in motarsa.
Ai take hanjin cikinta suka kad'a. Da sauri ta fito daga d'akinsu tana lek'ensa ta windon falon Mami. Tana kallo ya kashe motar ya kwashi wayoyinsa, akan idanunta sukayi magana da baba maigadi, batasan abinda suke tattaunawa ba, k'arshe ya yo ciki. Da sauri ta saki labule, kirjinta kamar ana lugude tsabar bugun da yakeyi. Shikenan kashinta ya bushe. Ta fito tana sand'a har ta iso farfajiyar gidan.
  "Ke!"
Ta ji an dakamata tsawa, a firgice ta juyo, yana tsaye jikin windon falonsa yana hangenta.
Ta zaro idanunta taba dubansa kafin kuma tayi narai-narai da fuska kamar mai shirin kuka.
  "Zo nan!"
"Shikenan na gama yawo." Tayi furucin a fili.
Daga haka ya sauke labule. Dole ta taka ta nufi d'akin, a ranta banda addu'o'i babu abinda takeyi. 
  Ta shiga da sallamarta. Ya amsa a ciki, yana tsaye a tsakar falon. Yayi mata kallon tsanake tun daga fuska zuwa yatsun k'afafunta daga inda yake tsaye. Fuskarsa sai ka rantse bai ta6a dariya ba. Batasan ya akayi ba ta ji ta tsugunna.
  "Yaya barka da dare."
Bai amsa ba.
"Ina zaki?"
"Di..di..nar Hafsa."
Ya d'anyi shiru.
"Mami bata ce kiyi jirana bane?"
  Ya fad'a cikin tsananin zafin rai, gaba d'aya yarinyar haushi take ba shi, ya tsani a rainashi. Abin ban haushin ma, wai ita akeson ba shi matsayin mata, wannan abu da me yayi kama?
   "Ta fad'a."
"Ok, itama kin rainata kenan?"
Ta d'an dubeshi, sai kuma ta sauke idanunta, gaba d'aya jikinta ya d'auki rawa. Fatanta Allah Ya mantar da shi abinda tayi mishi jiya kada yayi mata maganar. Ai kuwa dai alokacin baiyi d'in ba. Ya d'auki wayoyinsa ya shige d'aki. Nan ta zauna zaman jira, tun tana duba agogo har ta daina, idanunta tuni suka kawo ruwa ta soma zubar hawaye. Bakinciki da takaici duk suka bi suka addabeta, yana sane ya shanyata. Ta kwashi kusan rabin awa a zaune saman kafet d'in kafin ya fito daga d'akin. K'amshin turarensa ya daki hancinta, ta d'ago ta dubeshi ranta cike da jin tsananin haushinsa. Saidai kuma wani irin sanyin jiki ya ziyarci zuciyarta ganin yanda ya had'e iyakar had'ewa kai ka rantse injin matso kyau ya shiga. Sanye yake da farin boyel mai tsadar gaske, ya d'ora hula bak'a. Yayi kyau har ya gaji. Saidai ta gwammace bata dubeshi ba, don kuwa bai bita da komai ba sai harara. Baice mata uffan ba har saida ya nemi wuri ya zauna, takalminsa ya soma k'ok'arin zurawa.
  "Kina sane da laifinki ko?"
Ya fad'a ba tare da ya dubeta ba. Ta saci kallonsa, ita kam duk ta tsorata.
  "Don girman Allah Yaya kayi hakuri." Ta fad'a cikin muryar kuka, bil hakk'i ta tsorata ganin yanda koda wasa babu annuri a fuskarsa.
   Baice mata uffan ba har ya kammala ya soma kashe futilu, ganin haka ta fito tana sharar kwallah har da sauke ajiyar zuciya duk a hangenta ta tsira.
   Bayan sun isa wajen motarsa ta kama gidan gaba zata bud'e ya harareta.
  "Koma baya."
Ta koma babu shiri, ai ita ko boot ne zata shiga matuk'ar ba zaiyi mata wani hukunci ba.
  Ya saki kid'a lokacin da motarsu ta cilla titi. Tana kalle-kallenta a hanya, tun tana saka ran ganin sun iso Afficent har dai ta nutsu ta gane ba ma hanyar suka d'auka ba.
  Fargabarta ta k'aru, gaba d'aya hankalinta ya tashi.
  "Yaya ba hanyar muka yi ba kamar."
  Baice mata uffan ba sai ma ya k'ara volume na rediyo. Ai kuwa ta soma kuka. Ya dubeta ta madubi ya dauke kansa yana mai sakin murmushin mugunta.
  Bai tsaya ko'ina ba sai a wani k'aton gida wanda ko ba'a fad'a ba, kallo d'aya idan ka yiwa gidan zaka san akwai wani abu wai shi kud'i.
  Bayan ya shiga yayi fakin ya rage muryar kid'an dake tashi. Wayarsa ya fiddo ya danna kira bayan ya bud'e speaker.
  "Prince." Wata murya ta fad'a daga can 6arin, yayi wani murmushi na mugunta yana mai duban fuskar Bintu wacce take k'arewa gidan kallo ta madubi amma furucin da ta ji wata tayi ya sanyata maido hankalinta ga saurarensa.
  "Gani nan a waje."
Daga can ta saki ihun murna.
 "Wow!! Yau lallai ina da mugun sa'a. Ma'aruf da kansa a gidannan?"
  Ya d'anyi dariya kafin ya amsa.
 "Kika wuce 5minutes zan juya na koma inda na fito."
  Ai sai ta d'an d'aga murya.
 "A'a, na tuba don Allah. Ganinan fitowa."
  Ya katse wayar. Bintu ta rushe da kukan bak'in ciki, tsabar ma rainin wayo yau itace ta zama 'yar rakiyar zance?
   "Rufemin bakinnan."
 Ya fad'a a hankali, dolenta tayi shiru. Ya d'an karkato yana dubanta.
  "Ko tari ban yarda kiyi ba har mu bar gidannan wallahi, idan kikayi wani kwakkwarar motsin da ta fahimci kina motarnan sai kin raina kanki. Bani wayarki."
  Da sauri ta mik'a mishi tana kokarin danne kukan da ya taho mata, wata irin tsana da haushin Ma'aruf kawai take ji.
 Ya kashe wayoyinsu ya ajiye.
  Mintuna uku kawai, sai ga wata budurwa kyakkyawar gaske. Fara tas da ita, ta ci ado har ta gaji cikin wani rantsesan yadi. Tana taku cike da yanga. Bintu sai kuka ya tsaya cak, shakka babu ta had'u iyakar had'uwa. Ita kuwa budurwar ko kusa bata ganinsu kasancewar gilas din tint. Ta k'araso, Ma'aruf ya bud'emata gefensa ta shigo ta zauna.
   Nan ta bishi da wani sassanyar kallo.
  "Prince ka shayar da ni mamaki, na kasa gask'atawa. Don Allah mu shiga daga ciki mana."
  Ya d'an ja fasali kafin ya amsa yana wani yamutse fuska.
 "No, kiyi hakuri, ina da uzuri ne banason na jima. Don kin damu da ganina ne na daure na zo yau."
  Bintu fa ta ga abinda ya fi k'arfinta. Ashe daman haka mata ke yiwa Yaya Ma'aruf? Mamakin da takeyi bai wuce yanda wannan mace mai shegen yauk'i da ji da kanta ba ta marairaicewa Ma'aruf har tana rok'onsa ya dunga kulata ko yayane tunda mai sonka yafi mak'iyinka.
  Ta saki ido da baki tana duban yanda shi kuwa yake faman shan k'amshi. Gaba d'aya ta samu abin kallo ta mance da batun dinner. Wannan shine karon farko da ta ji Ma'aruf ya burgeta...!!
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<23>>

Yana zaune gaban Abba domin amsa kiransa. Abba ya dubeshi.
  "Ina sauraron ra'ayinka game da maganarmu ta kwanaki."
Ma'aruf ya k'ara yin k'asa da kanshi.
  "Na amince." Ya fad'a da kyar, Abba ya ji wani farinciki ya lullu6eshi. Ya yi hamdala a fili kafin ya bi Ma'aruf da kyawawan addu'o'i. A k'arshe ya sallameshi.
Ma'aruf ya mik'e jiki babu kwari ya bar falon.
  Kai tsaye falon Mami ya nufa. Tun kafin ya k'arasa ya jiyo dariyar Bintu da Aisha saidai na Bintun yafi na kowa d'aguwa. Takaici ya sanyashi fasa shiga ya juya ya koma sashensa. Wai meya kaishi amincewa auren wannan yarinyar ne? Wane su6utar baki ne haka?
  Kai gaba d'aya ji yayi ya tsani kansa, ya tsinci kansa cikin yanayin 6acin rai da damuwa matsananciya. Ganin ba wani sauk'i ya sanyashi barin gidan batare da ya d'auki motarsa ba.
                     * * *
   Bintu tayi shiru tana duban Mami wacce ke k'ok'arin zama gefenta a saman gado. Mamakinta bai wuce na kiran da Mamin tayi mata ba har da rufe d'aki da korar Aisha.
   Mami ta soma da kiran sunanta.
"Fatima Bintu, takwara kuma d'iya awajena."
  Bintu tana murmushi ta amsa.
"Na'am."
Shiru ya d'an biyo baya, ita kam tana jin nauyin ma gayamata maganar, saidai ba yanda ta iya tunda Abba ne ya sanyata jin ta bakinta.
  Cikin hikima irin ta manya Mami ta soma da kwantar mata da hankali da nunamata lallai ita mai k'aunarta ce, ba zata bari a cutar da ita ta kowane hanya ba. Tana k'aunarta tamkar yanda take k'aunar yaranta. A k'arshe ta sanarmata da buk'atar Abba ta son had'ata aure da Ma'aruf har ta k'ara da sanarmata cewa Ma'aruf ya amince da aurenta.
   Bintu ta ji gabanta ya mugun fad'uwa, Ma'aruf kuma?! Innalillahi!! Meyasa tunanin Abba zai kawomishi hakan? Ya zatayi da rayuwa idan har Ma'aruf ya kasance mijin aurenta? Idanunta suka ciko da kwallah. Mami ta kauda duba daga gareta cikin sanyin jiki tace.
  "Bazan bari a kwareki ba Bintu, zan jiraki daga nan zuwa kwanaki uku, matuk'ar baki k'aunarsa, kada ki kwari kanki, ki fito fili ki sanarmin, bazan ta6a bari a aura miki shi ba. Ki tsayar da tunaninki wuri guda, ki kuma dunga addu'a."
  Daga haka Mami ta fita daga d'akin batare da ta k'ara dubanta ba ballantana ta fahimci komai a fuskarta.
  Bintu ta zame ta zauna dirshan a saman carpet. Yaya Ma'aruf fa?!! Me ya burgesu har sukayi tunanin wannan had'in? A rasa ma wanda za'ayi tunanin had'asu aure da shi sai mutumin da ya k'i jinin walwalarta? Koyaushe burinsa ya k'untata rayuwarta?
  Abar batun haka ma, ta nunamusu wata alama na cewar aure take buk'ata ne? Eh lallai, sun bi son zuciyarsu kawai zasu yiwa d'ansu gata. To ai itama tana da nata gatan, don haka ba zata k'ara kwanan gidansu ba daga wannan rana, gobe Rano zata nufa.
  Gaba d'aya tunanin Bintu ya birkice, kukanma babu sai ruwan hawaye kawai. Ranta banda k'una babu abinda yakeyi. Ba Ma'aruf d'in kad'ai ba, gaba d'aya gidan saida ta ji ta tsanesu.
   A ranar haka ta wuni babu walwala, Mami na lura da ita saidai batace uffan gareta ba. Gaba d'aya itama ta ji ta damu, tayi da na sanin yi mata maganar nan, daman ita tasan da wuya abin ya yiwu. Da dai ace Rufa'i ne, wannan kam tana da tabbacin ba lallai ne Bintu ta k'i ba.
  Gidan bai musu dad'i ba ko kad'an,  daman Bintu ce mai rayamusu shi, yau ita kuwa babu kanta. Fuskarta tamkar an aikomata sak'on mutuwa.
  Washegari da wuri ta fito, ta lissafa kud'inta zasu isheta hawa motar zuwa Rano. Kai tsaye kuwa inda zata sami motar ta nufa maimakon makaranta.
  Inna suna zaune sai ganinta sukayi. Nan k'annenta suka hau murna. Umma kishiyar Inna batanan, hakanan Saifu da babansa suna kasuwa. Kallo d'aya Inna tayi mata ta fahimci babu lafiya. Abin akwai mamaki matuk'a.
 
   

[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<22>>
  Ya kwashi kusan rabin awa kafin yayi niyyar tafiya, a hakan ma budurwar wacce ya kira da Sa'a bata so ba, haka sukayi sallama tana rok'onsa da ya k'ara dawowa. Abin har ya bawa Bintu haushi, ta k'ulu iyakar k'uluwa, dubu yanda mace ba kunya take karya murya, shi kuwa sai shan k'amshi, haka kawai ta ji wata muguwar tsanar Sa'a ta dirar mata. Can kuma dai tayi tunanin me zai dameta?

Bayan tafiyarta ya juyo ya dubi Bintu wacce sai lokacin ne ta tunano inda suka nufa, ta turo baki ta 6ata rai. Murmushi kawai yayi baice komai ba, ai kwalliyar ta biya kud'in sabulu, yayi ribas maigadi ya bud'e mishi (gate) ya fita.
   Sun kusa Afficent ya tsaida motar a gefen hanya. Ta dubeshi, hannu yasa ya bud'e mazaunin gefensa.
  "Dawo gaba, don ba direba kika ajiye ba."
  Ta yi jim kamar kada ta fito sai kuma ta bud'e ta dawo ta zauna ranta a 6ace. Tsaf ta fahimci manufar kaita wajen budurwarsa, wato dai ya nunamata lallai akwai mata 'yan gayu da suka damu da shi fiye da zatonta.
  Ya dubeta ya maida kansa ga hanya lokacin da ya sha kwanar da zata kaishi d'akin taron.
  Suna isa ya mik'a mata wayarta, a fusace ta fice daga motar. Saida ya kammala kunna wayoyinsa sannan ya kashe motar ya rufeta ya shiga.
  Tun kafin ka k'arasa cikin hall d'in kana jiyo tashin kid'e-kid'e. Tana k'arasawa ciki kuwa ta daburce ganin taron jama'a. Mafi yawansu, dangin Abba ne. Ta dawo baya da zummar kiran Aisha a waya. Sai jin maganarsa tayi a dab da kunnenta sakamakon k'arar kid'an da bazai barta ta ji maganarsa ba.
  "Illar 'yan k'auyen kenan, ko shekara nawa zasuyi a birni, wayewarsu, suna ce kawai."
  Daga haka ya zarce ciki, kai tsaye 6angaren maza ya nufa. Ta bishi da kallon takaici. Ji tayi an dafa ta ta juya, ganin Aisha yasa ta sauke ajiyar zuciya, ta kasa magana kawai sai ta soma kuka. Ganin haka Aisha ta ja hannunta suka nufi waje.
 "Ke ina kuka tsaya? Ga Mami can cikin damuwa. Me Yayan ya yi miki?"
  Bintu tayi kwafa. Ta kwashe labarin komai ta bata, Aisha abin ya so bata dariya jin yanda take faman kushe Sa'a, ita kam tasan wacece Sa'a, d'iyar wani d'an majalisa ce, tun kafin ma ya auri Ma'u tana sonsa yanzu kuwa bazawara ce ma mijinta ya saketa adalilin shaye-shayen da takeyi ya zamar mata jiki. Tasan ko a mafarki, Ma'aruf bazai ta6a auren Sa'a ba ballantana kuma a farke. Saidai kuma jin abinda yace mata yanzun ne yasa jikin Aisha sanyi.
  "Kiyi hakuri, kinsan halin Yaya Ma'aruf, ba yau ya soma ya6amiki magana don kawai ya k'ular dake ba. Ke kika nuna kina da saurin fushi shi kuma anan yake samun damar yi miki son ransa. Ni yanzu ba wannan ba, muje Mami ta ganki hankalinta ya kwanta."
 Bintu ta share idanunta gami da yin kwafa kawai, Aisha ta gyara mata inda ya 6aci, tana janta da zolaya har Bintu ta saki ranta suka shiga ciki.
  Mami ta yi murnar ganinta kafin ta hau fad'an meyasa bata hau adaidaita ba tunda Ma'aruf d'in ya biya hira. Bintu tayi shiru da mamaki, ko kusa Ma'aruf baisan yayi k'arya ba babu kwakkwarar dalili.
  Har aka tashi taron bata sanyashi a ido ba. Tun kafin ma a tashin ashe ya tafi, haka ta ji a bakin Rufa'i sadda Mami ke cigiyarsa.
       Washegari da yamma aka mik'a amarya Hafsa gidan mijinta. Babu inda Bintu ta je, saboda makaranta, ranar a gajiye ta dawo lik'is. Agaban idanunta Mami suka wuce, tana kwance saman doguwar kujera bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita.
   Dab da magrib, Ma'aruf ya shigo. Dawowarsa kenan daga ofis, tuni ya yi wanka ya chanja zuwa k'ananun kaya na shan iska.
  Sam bai ko lura da ita a falon ba, duk a zatonsa, gaba d'aya gidan ne suka fice sai masu aiki ya rage da Atine da Hanif wadanda ya hanesu fita acewarsa, yaron ya gaji, kwana biyu kenan ana fita da shi.
  Saida ya shiga kicin ya nemi Iya da ta d'oramishi ruwan shayi, sannan ya doshi falon. Alokacin ne idanunsa ya kai gareta.
 Bacci takeyi, kallo d'aya zakayiwa fuskarta ka fahimci bata da wata matsala. Gashinta wanda ko kusa batason kitseshi ya mik'e tsaye kamar na mahaukaciya, ribon d'in kuwa tuni ya fad'i.
  Daga ita sai vest da dogon wandon da bai matseta. Ya ja guntun tsaki kafin ya d'auki filon kujera a gefensa yayi jifa da shi saman fuskarta.
  Bacci na Bintu fa, saida ya gwammace bai jefeta ba, juyin da ta yi yasa shi mik'ewa dole ya bar mata falon.
  D'ayan falon ya koma ya jinginar da kanshi saman kujera yana mai lumshe idanunsa. Wani yanayi ne, wanda tunawa da Ma'unsa kad'ai kan janyo mishi.
  Cikin k'arfin addu'a ya bagarar da tunanin ta hanyar buga game a wayarsa. Har Iya ta kawomishi ruwan shayin kamar yanda ya buk'ata.
  "Ki tashi mai baccin nan, lokacin sallah ya kawo kai."
 Ya fad'a yana duban Iya. Iya tayi 'yar dariya.
 "Au, mutuniyarka? Bintu ko rigima, ai saida na hanata bata fasa ba."
  Ta fice. Ta gabansa Bintu ta shige d'akinsu, bai ko dubeta ba. Bayan ta kimtsa ta k'ara fitowa cikin doguwar jallabiya da hula a kanta.
   Tayi kamar bata ganshi ba zata fice.
  "Ke bakisan ki gaida mutum ba?"
 Har lokacin haushinsa takeji. A ciki ciki ta gaisheshi bayan ta d'an russuna. Bai amsa ba, itama ta shareshi ta fice daga falon.
  Ya numfasa, har lokacin zuciyarsa ta kasa yanke tayashi yanke abinda ya dace. A gobe ne kuma zai bawa Abba amsa. Shi dai yasan Bintu ba ta daga cikin matan da yakeso, ina zai iya da shiriritarta? Ba k'aramin aikinsa bane wataran ya zaneta yayi mata raga-raga. Saidai kuma yanajin nauyin k'in amincewa aurenta. Da wane idon zai dubi Abba yace a'a? Mami kam, ya sani ba zata ji dad'i ba ko kad'an idan ya k'i jininta.
  Da wannan tunanin ya kammala ya fito. Zai fice ya hangota daga d'akin Hanif, rik'e da shi a cinyarta tana kai lomar abinci tana d'an lasa mishi miyar a baki, sai kuma ta kyalkyale da dariya. Sun burgeshi burgewa, yasan tana son d'ansa, yana girmamata a wannan wajen.
  Ya numfasa ya fice jin an soma kiraye-kirayen sallah.
[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<24>>
 Bayan sun shiga d'aki ta kora yaran zuwa tsakar gida. Bintu tuni ta soma hawaye.
  "Ke, sanardani meke faruwa? Ina Yaya Fatima, ya na ganki ke d'aya?"
  Inna ke jero dukkan tambayoyin nan cike da tsananin rud'ani. Bintu ta tsaida kukanta.
"Wai Mami ce, wai.." Kuka ya hanata k'arasawa. Inna ta soma fusata.
  "Ki gayamin mana, me yafaru?"
"Cewa sukayi zasu auramin Yaya Ma'aruf."
  Mamaki ya rufe inna, ta tsaya kyam tana dubanta.
  "Shi ne kikace musu me?"
Ta turo baki.
"Gudowa nayi don ni..."
Marin da Inna ta shek'a mata ya haneta k'arasawa. Cikin tsananin tashin hankali take dubanta, kamar ba wannan Innar mai sanyin hali kuma mai tsananin nuna k'auna gareta ba. Kallo d'aya ta hangi tsananin 6acin ran dake kwance saman fuskarta.
   "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!" Inna ta maimaita har sau biyu. Kawai sai kuma ta kece da kuka.
  "Kaico wannan rayuwa, ni Dije wane zamani muke ciki da d'an Adam ke saurin manta halacci? Da ace kinsan menene kawaici da girmamawa da lallai baki baro gidan 'yar uwata ba bisa wannan k'aramar maganar. Idan ban ta6a gayamiki ba yau ki sani, Yaya Fatima ko dukkan yarana ta nema na bata ta rik'esu zan iya, babu irin sadaukarwar da bazan iya yi dominta ba matuk'ar bai sa6awa addini ba. Ban taso naga mahaifiyata ba, Yaya Fatima nasani, bayan mahaifina, bani da wata gata sai ita. Idan nace zan tsaya gayamiki ire-iren abubuwa na kyautatawar da Yaya Fatima tayimin a rayuwa zamu iya cinye lokaci wanda bazan so hakan ba. Bazan so Yaya ta ankara da cewar nan kikazo ba, ban haifi d'iyar da zata k'i biyayya ga 'yar uwata ba, yanda banyi ba, to muddin ina raye ba zan aminta da d'ayanku ya aikata hakan ba. Kin bani kunya! Kin kuma shayar da ni mamaki kwarai, ko a mafarki banyi zaton 'yar uwata zata bijiro miki da wata buk'atar ba ki k'i amincewa. Bakisan fa dad'ina ba Bintu, Yaya Fatima ita ta yayeki, itace komai na gatanki. Tana sonki fiye da son da na nunamiki, a tunaninki, Yaya Fatima zatayi abinda zai cutar da ke da rayuwarki?"
 Inna ta k'arashe cikin sanyin murya. Ta ja majina
 "Tun kafin na 6ata miki rai nayi abinda ban ta6a yi gareki ba, ki tashi ki koma inda kika fito, idan kuma na isa da ke, ki amince da auren dan uwanki."
   Bintu ta mik'e jikinta a sanyaye, da alamu dai maganganun na Innarta sun shigeta. Har ta sanya kai zata fice, Inna ta kirawota ta mik'a mata dubu biyu akan ta k'ara kud'in mota. Ta k'ara da fad'in.
 "Ma'aruf yaro ne da yasan abinda yakeyi, yasan daraja da girman d'an adam. Miji ne wanda zakiyi alfahari da shi. In sha Allah ba zaki koka ba da kasancewarsa miji gareki. Ki koma ki yi biyayya ga uwarki mai k'aunarki. Kada ki sake ki sanarmata kinzo garinnan. Kije, Allah Yayi albarka ga rayuwarku, Ya shiga lamuranku. Ina miki murnar samun miji abin alfahari ga dukkan wacce ta sameshi."
  Bintu ta dubi innarta cikin zubar hawaye. Sai kuma ta juya a sanyaye ta gyara zaman jakar hannunta wacce ta fito da zummar zuwa makaranta ta yo Rano. Ta fice daga d'akin bata bi ko ta kan k'annenta ba dake yi mata magana ba ta bar gidan da sauri-saurinta.
   Don tayi sauri yasa ta hawan k'aramar mota peagout. A motar ma hawaye kawai takeyi. Gaba d'aya ta tsinci kanta cikin jin kunyar abinda ta so aikatawa Maminta mai k'aunarta da zuciya d'aya. Lallai ta kusa tafka kuskure babba, dad'in magabata kenan. Duk wanda a duniya ya rasa mai fad'a masa gaskiya shakka babu yana cikin garari na rayuwa. Tayi alk'awarin yin biyayya ga Abba da Mami, zata auri d'ansu ba wai don halinsa ba, saidai domin Allah.
  "To so fa? Kina sonsa?"
 Wata zuciyar ta jefomata tambayar da ta hautsina cikinta. Ai ita batasan ma soyayyar ba ballantana ta fahimci komai. Kodayake, a zamanin k'uruciyarta, Aisha ta ta6a shaida mata kad'an daga yanda kake gane ka fad'a son mutum.  Fad'uwar gaba, da wani kallon kwayar idanu.
 Ta ja k'aramin tsaki. Shirme kenan. Tsoro ke kawo fad'uwar gaba kawai, shi kuma kallo, kawai idan mutum yana da kwarjini zaisa ka ji bazaka iya duban kwayar idanunsa sosai ba. Banda wannan, sauran kawai tunani ne na marasa aikin yi da suka yarda suka amince da soyayya har ma suke wahalar da rayuwarsu.
    A haka tayita tunane-tunanenta har dai suka shigo Kano, kai tsaye tashar unguwa uku suka isa. Mintuna arba'in ne suka kawosu. Ta duba agogon dake d'aure a fatar hannunta. K'arfe uku na rana har da mintuna.
  Ta fito ta nemi abin hawa tayi mishi kwatance.
   Adaidai junction na titin Zoo road, wajejan Oasis Bakery motarsu ta tsaya cikin go-slow.
  Ma'aruf yana daga gefensu batare da zato ko tsammani ba, a gefensa abokinsa ne Hashim suna ta6a hira. Juyowar da zaiyi ya hangeta cikin adaidaita, fuskarta babu walwala, hankalinta gaba d'aya yana ga kallon gabanta, yayi daidai da basu hannu da akayi wanda ya janyo rabuwarsu. Mamaki kwarai ya kamashi. Daga ina take? Wajen wa ta zo a wannan unguwar? Abin mamakin kenan, sam bata da k'awaye ballantana yayi zargin ko wajensu ta zo. Haka ya 6oye mamakinsa ya maida hankali ga abokinsa da ya dage ba shi shawarar yanda zai tafiyar da zaman aurensa da Bintu har ma ya ladabtar da ita.
   Shi dai Ma'aruf baice uffan ba. Tunaninsa gaba d'aya ya tafi ne ga ganin da ya yiwa Bintun yanzu daga hanyar da zata sadata da unguwa uku. To ko dai Rano ta je? Yayi kwafa a ransa kawai.
   

[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<26>>
Rufa'i ya dubi Maminsu.
"Nadai lura 'yarki batason muna kiranta da wannan sunan ko Aisha? Kuma ai girman kujerarta ne."
Ya k'arashe yana maida dubansa ga Ma'aruf wanda yaji maganar k'aninnasa tamkar an soka mishi allura a k'ahon zuci. Ya maze kawai, babu damar ya bar musu falon saboda Mami ta nuna tanason magana da shi.
  Maganar Mami ta katse tunaninsa.
"Nikam zan hanaka zuwa gidannan Rufa'i, ka girma amma bakasan ka girma ba baka da aiki sai tsokanarmin 'ya?"
  Suna dariya hakan ya yi daidai da fitowar Bintu daga kicin. Mami  kirata.  Ji tayi kamar ta d'ora hannu a ka ta fasa, meyasa Mami zatayi kiranta a gaban wannan mutumin? Kodayake gaba d'ayansu ma haushinsu takeji ganin yanda suke faman dariya wato su kenan duniyar dad'i take musu. Tana mai tur6une fuska ita wai shagwa6a ta k'araso ciki, kai tsaye jikin Mami ta kwanta. Ma'aruf bai ko k'ara kallonta ba tun daga kallon da yayi mata fitowarta daga kicin d'in. A ransa har tsaki yayi, yarinyar kowane shiga ma idan ta so yin abinta takeyi babu wata damuwa kan hakan. Haka kawai baisan dalilin jin sosuwar rai ba.
   "Zaki fara ko? Aure fa muke shirin yi miki." Cewar Rufa'i. Ina, tuni Bintu ta kai wuya, ai kuwa ta fashe da kuka. Mami ta rungume kafad'arta, nan ta shiga yiwa Rufa'i fad'a, tace ya bar mata gidanta bazai zo ya hana 'yarta sakewa ba. Rufa'i jiki yayi sanyi ganin Bintu na kuka, shi kam gogan, ba zaka gane komai ba a fuskarsa. K'arshe ma ya mik'e ya ja gefe yana amsa waya.
  Nan Rufa'i ya hau bata hakuri.
"Haba tawan, kinsan bama haka dake. Ai ke tawa ce."
Da ire-iren haka ya samo kanta.
  Ma'aruf na waya saidai jefi-jefi idanunsa kan sauka akan Bintu, har haushin kansa ya soma ji don bai ma san lokacin da yake kai duban gareta ba.
   Ganin zaman falon bazai mishi bane, yasa ya d'auki wayoyinsa.
"Mami zan d'anyi wani aiki kafin wadannan su barmu muyi maganar."
  Anan ne Bintu ta saci kallonsa. Yayi kyau kam don kyau, saidai mamakinta bai wuce yanda batajin soyayyarsa ba kamar yanda Aisha ke son Ashir d'in. To kodai wannan 6ace 6acen ran da takeyi shine so d'in?
"Oho." Ta bawa kanta amsa. Ashe batasani ba har ya fice. Dariyarsu Aisha ta maidota cikin hankalinta. Ta mik'e zaune sosai cike da masifa tace.
"Wai ke Aisha banason rashin mutunci fa, ai Yaya Rufa'in zai tafi ya barmu a gidan wallahi sai na rama."
Aisha ta had'iye dariyarta sanin halin Bintun da son ramuwar gayya wanda babu kyau. Gashi kuma tayi rantsuwa, tasan Bintu bata wasa da rantsuwa.
  "Allah Ya huci zuciyar..."
Kafin Aisha ta k'arashe, Rufa'i ya amshe.
"Matar Yayanmu."
  Aisha ta dubeshi ita kam ba abinda ta so fad'a kenan ba. Dariya suka sanya, a fusace Bintu ta fice daga falon zuwa can baranda wajensu Sadauki. Mami ta nunawa Rufa'i k'ofa.
"Tashi ka barmin gida." Ya mik'e yana dariya, daman ficewar zaiyi don a wannan karon ya daure ya bar Sadauki ya kwana."
  "Ayi hakuri Maminmu."
Da haka ya fice bayan ya d'auki ragowar ruwan robar da ya sha.
                     * * *
   Da daddare misalin tara. Bintu na kwance a d'akin Hanif, tana yi musu wasa tare da Sadauki, a rayuwa tanason yara. Idan Hanif ya kyalkyale da dariya itama ta dauki dariyar marar sauti saboda Mami ta haneta dariya mai k'ara ko yawan nan.
   Can kuma ta tsinci Sadauki a gefenta ya watso mata tambaya.
  "Anti, ai dai zaki tafi da mu gidan Uncle idan kunyi aure ko?"
  Ta dubi yaron da baifi shekaru biyu zuwa uku ba da mamaki.
  "Waya gayamaku zan je gidan Uncle?"
    "Daddy."
Ta numfasa yayinda haushin Rufa'i ya k'ara kamata. Batace komai ba ta bagarar da zancen.
   Ga Ma'aruf kuwa, al'ardarsa ce baya kwanciya batare da ya zo ya ga d'ansa yayi mishi addu'a ba. Wannan na d'aya cikin burikan da Ma'unsa ta ci idan har ta haifi bebinta. Burinta duk dare ta tofe yaranta da addu'a kafin bacci. Har kishi ya kamashi alokacin da tayi wannan furucin shi a dole yafiso ta so shi sama da komai don ya lura tun samuwar cikinta magana d'aya biyu, to fa zata sanyo abinda zata haifa
   Hakan yasa shi k'ok'artawa wajen cikamata burinta, duk kuwa da cewar wani abin sai mace.
  Yayi sallama batare da ko a ka ya kawo zai isketa a d'akin ba.
  Ai kuwa sukayi ido hud'u tana kwance ta d'ora Hanif saman k'afafunta tana mishi wasa. Doguwar riga ce mai kauri ta bacci a jikinta. Kan babu kallabi. Kusan lokaci guda suka kauda kansu. Ta ajiye Hanif saman gado, da gudu ya rarrafa ganin zai fad'o yasa Ma'aruf d'aukarsa.
  Bintu ta mik'e zata fita, ya dakatar da ita ta hanyar jifanta da tambaya.
  "Ina Atine ne?"
Ciki-ciki ta amsa.
"Ta je kicin dafa fidar Hanif."
Tana k'ok'arin sa kai ta fice ya k'ara tsaidata.
  "Ke zo nan."
Ranta yayi wani bak'i, ita fa ko ganinsa ma batason yi, mugu da shi.
   Saidai dolenta ta dawo baya batare da ta zauna ba. Haushin kansa ya ji a fusace ya soma magana.
"Wato tun yanzu raini ya gilma tsakaninmu, banda kin raina mutane ya zanyi kiranki ki tsayamin a ka?"
  Ta had'iyi miyau na takaici kafin ta zauna. Yayi shiru yana duban Hanif kafin yayi kwafa a fili ya dubeta.
  "Shine kika cewa su Abba ni kikeso ko?"
  Ta zaro ido ta dubeshi, idanunta ya kawo ruwa.
"Lallai ma, wallahi ni ban ta6a ma sonka ba, ni kawai..."
  Ta soma hawaye. Ya harareta, yarinya sai tsabar iyayi da yarinta.
  "Idan ba ke kika nunamusu kin amince da aurena ba, ta yaya zasuyi tunanin had'amu? Wai ke bakiga irin 'yan matana  ba ne? Kin ta6a cin karo da mai shekarunki?"
Ya d'an fasali kafin ya cigaba da magana bayan ya lalla6a Sadauki ya bar d'akin gudun kada ya kwashi rahoto don lura da yayi yaron akwai wayo.
  "Me kika sani a aure ne? Bana tunanin ko girki da gyaran gida kin iya don ban ta6a ganin kina yin d'ayansu ba."
Sai kuma ya d'an ja tsaki.
"Kin d'ebo ruwan dafa kanki Bintu, ina tausayinki a gidana. Sai na kunce miki wad'annan notinan na kanki na saita miki su. Sannan daga yau na k'ara ganinki cikin shiga irin na d'azu sai na 6allaki, hakanan na kafa miki dokar d'ankwali, koda wasa na k'ara cin karo dake babu d'ankwali zaki d'and'ana kalar azabata."
   Ta mik'e ta goge fuskarta, gaba d'aya ta gama k'uluwa. Har zata fice sai kuma tayi tunani, ai idan ta barshi batare da ta ya6a mishi ba to fa bazata ji sanyi ba, gwara ta dunga ramawa kafin azo lokacin da ya riga ya zama miji gareta. Hakan yasa ta dawo da baya. Ya dubeta, ta kauda kanta gefe, ita ko kusa batason yawaita kallon kwayar idanunsa. Ta tsuke baki wanda ta saba yi idan zatayi rashin ta idon.
  "Dad'in abin dai nima k'ak'abamin kai akayi ba sonka nakeyi ba. Ni da ace zaka taimaka ka samu su Abba kace bana sonka da nafi kowa jin dad'i. Kaima kasan nafi k'arfinka. Maza nawa ne suke sona don ma soyayyar ba damuna tayi ba? Yanda kake shiryamin uk'ubobi nima haka nake shiryamaka don wallahi bana sonka, mugunta kawai kasani ba komai..."
  Mik'ewar da ta ga yayi ya sanyata fita a guje. Ran Ma'aruf ya 6aci ainun, tunda yake bayajin akwai macen da ta ta6a gasa mishi maganganu irin haka. Shakka babu Bintu ta k'ara rura wutar k'iyayyarta a zuciyarsa. Sai kuma alokacin ya k'ara jin wani kwarin gwuiwar aurenta, acewarsa, wannan kad'ai ne hanyar k'untatawa rayuwarta. Ya d'auki d'ansa ya fice zuwa sashensa.
  Da gudu ita kuma ta k'arasa d'akinsu. Anan ta tarar da Aisha dake faman laluben wayarta. A firgice Aishar ta dubeta.
  "Lafiya?" Bintu ta zauna bakin gado.
"Oho. Kekuma lafiya kika wani rikita mana d'akin?"
Aisha ta ja tsaki.
"Yauwa, bakiga wayata ba don Allah? Nasan Ashir yanata kirana bai samu ba."
  Bintu ranta yayi fari k'al. A fili kuwa ta ta6e baki.
"D'aukar miki waya nakeyi? Bangani ba."
  "Bani aron naki nayi kiransa."
Ta harareta "Kud'ina bana banza bane."
  Aisha ta ji haushi. Haka ta gama lalubenta, Bintu ta zura wayarta a cikin filo bayan ta kasheta ta kwanta ta rufe idanu. A ranta tana fad'in. "Yi iyakar bincikenki. Gobe kya k'ara kirana Matar Yaya."
   Tun tana sauraron shige da ficenta, har baccin gaske yayi awon gaba da ita.
  Sai a washegari ta damk'a mata da zasu fice zuwa makaranta.
  Bintu bata k'ara yarda sunyi arba da Ma'aruf ba, saidai fa acewarta ba tsoro bane!
                         * * *
             Bayan Wata d'aya da sati biyu....!!


 

 

[7/20, 9:57 PM] Aysha Abe: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<25>>
Ko da ta isa gidan babu wanda ya d'ago wani abu. Bayan ta idar da Azhar ta dawo falon.   Mami ta dubeta, ta sakarwa Mami murmushi kafin ta kwanta saman cinyarta.
"Wash! Wallahi nagaji Mami."
  Wani sanyi ya ratsa zuciyar Mamin ganin Bintu bata sanya komai a ranta ba. Ta dafa kanta.
"Sannu 'yar gidan Mami, amma yau baku jima ba."
  Ta lumshe ido tana mai jin dad'in susar kan da Mamin keyi mata. A haka Aisha ta shigo gidan daga gidan amarya Hafsa. Ganin Bintu tayi turus.
  "Har kin dawo?"
Ta harareta.
"Menene?"
Aisha na dariya ta zauna.
"A'a mamaki nayi dai. Haba Mami, kinason biyewa yarinyar nan wallahi. K'atuwa da ita sai shegen shagwa6a, wannan dai mijinki yana da aiki wallahi."
Ta ta6e baki ta muskuta.
"Wallahi A'i kin fiye sanye ido, dad'in abin ba ke zakiyi aikin ba. Mijina kuwa..."
  Shaf, ta mance da wani batunta da Ma'aruf harma take batun miji. Sai kuma ta ji nauyi, ta maze ta share batun ta hanyar sanyo wata hirar.
  "Ke ni bamu labarin gidan amarya."
  Nan fa ta soma zuba, tuni Bintu ta ware ta mik'e zaune. Har Mami suka had'u akayita hira, a k'arshe suka shige d'akinsu sukayi la'asar.
   Tana zaune saman darduma tana sauraron bayanin da Aisha ke faman zubawa yayinda take sauya kayan jikinta.
  "Ke ni har na soma tunanin anya ba zan ce Ashir d'ina ya fito ba, irin wannan soyayyar da na tarar a gidan  Hafsa da Bashir ai hum."
  Ta yi shiru tana dariya. Bintu ta ja tsaki.
  "Ke kuma babu soyayyar da ta burgeka sai ta wad'annan? Kwata kwata basu burgeni ba balle suyi abinda zai burgeni."
  Hafsa ta zauna gefen gado da d'aura k'irji tana murmushi mai bayyana hak'ora. 
   "Bakisan so ba, amma zan d'agamiki k'afa wuyarta dai mu mik'a ki d'akin Yaya."
  Ran Bintu ya 6aci ta danne saidai duk da hakan saida fa aikamata harara.
  "Dad'in abin ni soyayyar ba damuna tayi ba, ina bawa lokutana muhimmanci. Da soyayyar gwara a siyomin rake nayita 6alla ina shan abina."
   Hafsa ta kyalkyale da dariya, ta kai mata duka a kafad'a alokaci guda kuma ta mik'e.
   "Lallai akwai aiki awajen mata."
Da haka ta shige band'aki, Bintu ta bita da kallon baki da matsala. Ta kwantar da kanta  ta yi shiru. Wai daman damuwa tana kashe jiki har haka? Iko sai Allah, gashinan ayau sanadin wannan rikitaccen al'amari ta zama wata mai sanyi. Wayarta da tayi k'ara yasa ta d'aukowa, Innarta ce, bayan gaisuwa ta tambayeta ko sun isa lafiya. Ta tabbatar mata lafiya kalau. Ta k'ara binta da nasiha akan ta maida komai ga Allah, in sha Allah ta na ji a jikinta akwai alheri a aureta da d'an uwanta.  Bintu tayi na'am da hakan kafin daga bisani suyi sallama.
   Ma'aruf a 6angarensa yaso ya yiwa Bintu tambaya game da inda ta je saidai kuma zuwa yanzun bayason shiga dukkan lamuranta. Ai ya damu da ita kenan ma idan ya shiga.
     Kwana ukun da Mami ta d'ibar mata na cika, Mami ta ji daddad'ar magana bayan ta kirayeta don jjn abinda ta yanke. Dad'i yasa Mami ta rugumeta a jiki.
  "Alhamdulillah, Allah Yayi muku albarka."
  Bintu ta lumshe ido kawai ranta na k'una. Ita fa tasan rayuwarta zata yi babu dad'i ne muddin ta auri Ma'aruf.
Abin ya bata mamaki ganin Mami har da 'yar kwallar farinciki. Lallai sai yanzu take k'ara gaskata maganar Innarta. Ta kuma hak'ik'ance Mami dagaske tana son wannan had'in.
       Kafin sati biyu magana fa ta zagaya dangi. Tuni Abba da k'aninsa Mahaifin Ma'u wanda suke kira Alhaji, suka sun je har Rano sunga mahaifin Bintu an tsaida magana. Abun fa ya yiwa manyannan dadi. Nan suka yanke nan zuwa watanni biyu kacal.
    Haka suka dawo cike da tsantsar farin ciki. Ai Bintu tun daga ranar bata k'ara bari koda wasa sun had'u da Ma'aruf ba, hakanan shima tunda ya fahimci ta sani ya rage shigowa falon Mami ya yi dogon zama. Saidai idan Mamin ce ta nemeshi game da shawarar wani abun na biki.
                      * * *
   Wani yammaci ya kama lahadi, gaba d'aya gidan sun had'u a falon Mami suna hira har Rufa'i wanda ya zo da d'ansa, shima gogan yana zaune ya gama had'ewa cikin riga da wando farare tas, sunata hirar siyasa. Abba ne kawai bayanan sun fita taronsu na gida na manyan dattawa.(Family meeting). Alokacin Bintu ta fito sanye da riga da wando, rigar har gwuiwarta sai pencil jeans da ta sanya. Kanta kuwa ba'a ma batun d'ankwal, gashin ne dai ga shi nan an tufkeshi babu ko kitso. Biyun nan daman sam basa daga cikin tsarinta. Mami kad'ai ke tsawatar mata akan hakan. Kallo d'aya ta wurga musu gaba d'aya bata k'ara duban inda suke ba ta cigaba da tafiya.
   "Yayarmu." Ta tsinci muryar Rufa'i, daman tasan shi da Aisha ke kiranta da hakan idan sun so tsokanarta.
  Ta cigaba da tafiyarta ta shige kicin tamkar bata ji shi ba....
  [7/19, 9:07 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<26>>
Rufa'i ya dubi Maminsu.
"Nadai lura 'yarki batason muna kiranta da wannan sunan ko Aisha? Kuma ai girman kujerarta ne."
Ya k'arashe yana maida dubansa ga Ma'aruf wanda yaji maganar k'aninnasa tamkar an soka mishi allura a k'ahon zuci. Ya maze kawai, babu damar ya bar musu falon saboda Mami ta nuna tanason magana da shi.
  Maganar Mami ta katse tunaninsa.
"Nikam zan hanaka zuwa gidannan Rufa'i, ka girma amma bakasan ka girma ba baka da aiki sai tsokanarmin 'ya?"
  Suna dariya hakan ya yi daidai da fitowar Bintu daga kicin. Mami  kirata.  Ji tayi kamar ta d'ora hannu a ka ta fasa, meyasa Mami zatayi kiranta a gaban wannan mutumin? Kodayake gaba d'ayansu ma haushinsu takeji ganin yanda suke faman dariya wato su kenan duniyar dad'i take musu. Tana mai tur6une fuska ita wai shagwa6a ta k'araso ciki, kai tsaye jikin Mami ta kwanta. Ma'aruf bai ko k'ara kallonta ba tun daga kallon da yayi mata fitowarta daga kicin d'in. A ransa har tsaki yayi, yarinyar kowane shiga ma idan ta so yin abinta takeyi babu wata damuwa kan hakan. Haka kawai baisan dalilin jin sosuwar rai ba.
   "Zaki fara ko? Aure fa muke shirin yi miki." Cewar Rufa'i. Ina, tuni Bintu ta kai wuya, ai kuwa ta fashe da kuka. Mami ta rungume kafad'arta, nan ta shiga yiwa Rufa'i fad'a, tace ya bar mata gidanta bazai zo ya hana 'yarta sakewa ba. Rufa'i jiki yayi sanyi ganin Bintu na kuka, shi kam gogan, ba zaka gane komai ba a fuskarsa. K'arshe ma ya mik'e ya ja gefe yana amsa waya.
  Nan Rufa'i ya hau bata hakuri.
"Haba tawan, kinsan bama haka dake. Ai ke tawa ce."
Da ire-iren haka ya samo kanta.
  Ma'aruf na waya saidai jefi-jefi idanunsa kan sauka akan Bintu, har haushin kansa ya soma ji don bai ma san lokacin da yake kai duban gareta ba.
   Ganin zaman falon bazai mishi bane, yasa ya d'auki wayoyinsa.
"Mami zan d'anyi wani aiki kafin wadannan su barmu muyi maganar."
  Anan ne Bintu ta saci kallonsa. Yayi kyau kam don kyau, saidai mamakinta bai wuce yanda batajin soyayyarsa ba kamar yanda Aisha ke son Ashir d'in. To kodai wannan 6ace 6acen ran da takeyi shine so d'in?
"Oho." Ta bawa kanta amsa. Ashe batasani ba har ya fice. Dariyarsu Aisha ta maidota cikin hankalinta. Ta mik'e zaune sosai cike da masifa tace.
"Wai ke Aisha banason rashin mutunci fa, ai Yaya Rufa'in zai tafi ya barmu a gidan wallahi sai na rama."
Aisha ta had'iye dariyarta sanin halin Bintun da son ramuwar gayya wanda babu kyau. Gashi kuma tayi rantsuwa, tasan Bintu bata wasa da rantsuwa.
  "Allah Ya huci zuciyar..."
Kafin Aisha ta k'arashe, Rufa'i ya amshe.
"Matar Yayanmu."
  Aisha ta dubeshi ita kam ba abinda ta so fad'a kenan ba. Dariya suka sanya, a fusace Bintu ta fice daga falon zuwa can baranda wajensu Sadauki. Mami ta nunawa Rufa'i k'ofa.
"Tashi ka barmin gida." Ya mik'e yana dariya, daman ficewar zaiyi don a wannan karon ya daure ya bar Sadauki ya kwana."
  "Ayi hakuri Maminmu."
Da haka ya fice bayan ya d'auki ragowar ruwan robar da ya sha.
                     * * *
   Da daddare misalin tara. Bintu na kwance a d'akin Hanif, tana yi musu wasa tare da Sadauki, a rayuwa tanason yara. Idan Hanif ya kyalkyale da dariya itama ta dauki dariyar marar sauti saboda Mami ta haneta dariya mai k'ara ko yawan nan.
   Can kuma ta tsinci Sadauki a gefenta ya watso mata tambaya.
  "Anti, ai dai zaki tafi da mu gidan Uncle idan kunyi aure ko?"
  Ta dubi yaron da baifi shekaru biyu zuwa uku ba da mamaki.
  "Waya gayamaku zan je gidan Uncle?"
    "Daddy."
Ta numfasa yayinda haushin Rufa'i ya k'ara kamata. Batace komai ba ta bagarar da zancen.
   Ga Ma'aruf kuwa, al'ardarsa ce baya kwanciya batare da ya zo ya ga d'ansa yayi mishi addu'a ba. Wannan na d'aya cikin burikan da Ma'unsa ta ci idan har ta haifi bebinta. Burinta duk dare ta tofe yaranta da addu'a kafin bacci. Har kishi ya kamashi alokacin da tayi wannan furucin shi a dole yafiso ta so shi sama da komai don ya lura tun samuwar cikinta magana d'aya biyu, to fa zata sanyo abinda zata haifa
   Hakan yasa shi k'ok'artawa wajen cikamata burinta, duk kuwa da cewar wani abin sai mace.
  Yayi sallama batare da ko a ka ya kawo zai isketa a d'akin ba.
  Ai kuwa sukayi ido hud'u tana kwance ta d'ora Hanif saman k'afafunta tana mishi wasa. Doguwar riga ce mai kauri ta bacci a jikinta. Kan babu kallabi. Kusan lokaci guda suka kauda kansu. Ta ajiye Hanif saman gado, da gudu ya rarrafa ganin zai fad'o yasa Ma'aruf d'aukarsa.
  Bintu ta mik'e zata fita, ya dakatar da ita ta hanyar jifanta da tambaya.
  "Ina Atine ne?"
Ciki-ciki ta amsa.
"Ta je kicin dafa fidar Hanif."
Tana k'ok'arin sa kai ta fice ya k'ara tsaidata.
  "Ke zo nan."
Ranta yayi wani bak'i, ita fa ko ganinsa ma batason yi, mugu da shi.
   Saidai dolenta ta dawo baya batare da ta zauna ba. Haushin kansa ya ji a fusace ya soma magana.
"Wato tun yanzu raini ya gilma tsakaninmu, banda kin raina mutane ya zanyi kiranki ki tsayamin a ka?"
  Ta had'iyi miyau na takaici kafin ta zauna. Yayi shiru yana duban Hanif kafin yayi kwafa a fili ya dubeta.
  "Shine kika cewa su Abba ni kikeso ko?"
  Ta zaro ido ta dubeshi, idanunta ya kawo ruwa.
"Lallai ma, wallahi ni ban ta6a ma sonka ba, ni kawai..."
  Ta soma hawaye. Ya harareta, yarinya sai tsabar iyayi da yarinta.
  "Idan ba ke kika nunamusu kin amince da aurena ba, ta yaya zasuyi tunanin had'amu? Wai ke bakiga irin 'yan matana  ba ne? Kin ta6a cin karo da mai shekarunki?"
Ya d'an fasali kafin ya cigaba da magana bayan ya lalla6a Sadauki ya bar d'akin gudun kada ya kwashi rahoto don lura da yayi yaron akwai wayo.
  "Me kika sani a aure ne? Bana tunanin ko girki da gyaran gida kin iya don ban ta6a ganin kina yin d'ayansu ba."
Sai kuma ya d'an ja tsaki.
"Kin d'ebo ruwan dafa kanki Bintu, ina tausayinki a gidana. Sai na kunce miki wad'annan notinan na kanki na saita miki su. Sannan daga yau na k'ara ganinki cikin shiga irin na d'azu sai na 6allaki, hakanan na kafa miki dokar d'ankwali, koda wasa na k'ara cin karo dake babu d'ankwali zaki d'and'ana kalar azabata."
   Ta mik'e ta goge fuskarta, gaba d'aya ta gama k'uluwa. Har zata fice sai kuma tayi tunani, ai idan ta barshi batare da ta ya6a mishi ba to fa bazata ji sanyi ba, gwara ta dunga ramawa kafin azo lokacin da ya riga ya zama miji gareta. Hakan yasa ta dawo da baya. Ya dubeta, ta kauda kanta gefe, ita ko kusa batason yawaita kallon kwayar idanunsa. Ta tsuke baki wanda ta saba yi idan zatayi rashin ta idon.
  "Dad'in abin dai nima k'ak'abamin kai akayi ba sonka nakeyi ba. Ni da ace zaka taimaka ka samu su Abba kace bana sonka da nafi kowa jin dad'i. Kaima kasan nafi k'arfinka. Maza nawa ne suke sona don ma soyayyar ba damuna tayi ba? Yanda kake shiryamin uk'ubobi nima haka nake shiryamaka don wallahi bana sonka, mugunta kawai kasani ba komai..."
  Mik'ewar da ta ga yayi ya sanyata fita a guje. Ran Ma'aruf ya 6aci ainun, tunda yake bayajin akwai macen da ta ta6a gasa mishi maganganu irin haka. Shakka babu Bintu ta k'ara rura wutar k'iyayyarta a zuciyarsa. Sai kuma alokacin ya k'ara jin wani kwarin gwuiwar aurenta, acewarsa, wannan kad'ai ne hanyar k'untatawa rayuwarta. Ya d'auki d'ansa ya fice zuwa sashensa.
  Da gudu ita kuma ta k'arasa d'akinsu. Anan ta tarar da Aisha dake faman laluben wayarta. A firgice Aishar ta dubeta.
  "Lafiya?" Bintu ta zauna bakin gado.
"Oho. Kekuma lafiya kika wani rikita mana d'akin?"
Aisha ta ja tsaki.
"Yauwa, bakiga wayata ba don Allah? Nasan Ashir yanata kirana bai samu ba."
  Bintu ranta yayi fari k'al. A fili kuwa ta ta6e baki.
"D'aukar miki waya nakeyi? Bangani ba."
  "Bani aron naki nayi kiransa."
Ta harareta "Kud'ina bana banza bane."
  Aisha ta ji haushi. Haka ta gama lalubenta, Bintu ta zura wayarta a cikin filo bayan ta kasheta ta kwanta ta rufe idanu. A ranta tana fad'in. "Yi iyakar bincikenki. Gobe kya k'ara kirana Matar Yaya."
   Tun tana sauraron shige da ficenta, har baccin gaske yayi awon gaba da ita.
  Sai a washegari ta damk'a mata da zasu fice zuwa makaranta.
  Bintu bata k'ara yarda sunyi arba da Ma'aruf ba, saidai fa acewarta ba tsoro bane!
                         * * *
             Bayan Wata d'aya da sati biyu....!!


 

 

[7/19, 9:07 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<27>>
  Biki fa ya kankama, sai shirye-shirye kawai mutanen gidan keyi. Mami babu zama, itace can itace nan. Bintu kallon kowa kawai takeyi da ido, gaba d'aya ta rame saboda bata ta6a kawowa a ranta zatayi aure nan kusa ba. Tuni aka kammala had'a lefe da kayan kunshi da komai da aka sani na al'ada aka rankaya Rano. To abu na gida, babu wanda bai taya Fatima Bintu murna ba, a k'arshe Inna da kanta tace a mayar can Kano, Mami ai itace uwar amarya ita kam ango ne na wajenta. Haka da dariya da komai 'yan uwan junan suka rabu. Ga ango da amaryar kuwa babu wanda zai saurin d'ago wani abu tsakaninsu. Aisha dai tuni ta harbo Bintu, saidai ta san komai zai wuce bayan aure. Babu abinda yafi k'ular da Bintu kamar yanda Ma'aruf ya soma nunawa lallai dagaske sonta yakeyi agaban 'yan uwa. Ta k'ulu iyakar k'uluwa ta tabbatar sabon salo ne ya d'auko domin k'untata mata ga shi a wannan ga6ar ta rasa abin da zai zame mata ramuwar gayya. Ganin bata da mafita yasa ta ke k'auracewa duk wajen da yake. Ta yankewa kanta shiga d'akin Hanif, hakanan ta rage zama falon Mami saidai ta shige k'uryar d'akinta tayi zamanta.
   Ana sauran sati bikin ne, aka soma yiwa Bintu gyaran jiki, Mami ta tilasta ta sanya hijab da nik'ab idan zataje makaranta har ma da safa saboda kada rana ta 6ata gyaran da akeyi. Ana sauran kwana uku ne kuma ta daina zuwa makarantar acewar Mami ta bari a mik'ata d'akinta tunda ba jarabawa sukeyi ba.
     Ana gobe za'a soma biki, suna zaune a d'akinsu ita da Aisha, da Hajara harma da Jalila da Atika(yanuwansu wadanda suke sa'anni, suna zama a Rano). Amarya Bintu ansha lalle da kitso siri-siri.
   Hajara ta kama baki.
"Kai nifa nafi mamakin ramar da yarinyar nan keyi, daman akwai abinda zai ladabtar da Bintu haka? Kamar ba wannan shak'iyiyar ba."
Bintu ta kallera kawai saidai batace uffan ba. Su Aisha suka kwashe da dariya. Atika dake cin meatpie ta dubeta.
   "Wallahi ni kunsan me yafi burgeni? Bai wuce yanda naga Yaya Ma'aruf ke nan nan da ita ba. Ku duba kugani, yana ganinta zakuga ya soma zolayarta da amaryata amaryata. Hum, wannan a gidansu akwai kallo."
   Bintu ta harareta, me zasuyi ba dariya ba. Ta ja tsaki, kamar tayi magana, sai kuma ta fasa.
  "Yi maganarki, yar duniyar k'arya kinaso kina kaiwa kasuwa. Kodayake kin gama ciki bakin ke bakya soyayya." Cewar Jalila.
  Tsam ta mik'e ta koma wajensu Mami da iyayensu Atika wadanda suka kasance, 'ya'ya ga kishiyar uwar su Mamin. Nan kuwa babu mai tsokanarta saima hirarsu da sukeyi.
   Washegari aka soma shagalin biki. Can na hango masu aikin abinci, ciki har da Fauza ga Ummu Abdool a gefenta suna ta juya farar shinkafa a k'atin warmer. A gefe ga dangin Taskira suna ta wanke kwanukan rabo. Can kuwa, Su hanne da Batool kai harma da Sholingaye ke faman kula da miya. Can na hango Bingel da Faharty na fad'a akan k'ashi ganin Bayarabiya Asal mai d'aukar bidiyo ta nufo wajensu ne ya sanyasu nutsuwa.
Kai group na matan aure suma sunyi gefe suna hirar yanda zata kaya a gidan amarya Bintu wacce suka gama had'ata suka suburbud'a mata lakcoci acan falon Mami.
  Bintu ta sha kuka yanda manyan nan suka sanyata a tsaka suna faman yi mata maganganun da suka girmi kunnuwanta.
  "Nidai gaskiya banason aure." Su Aisha suka kyalkyale da dariyar jin abinda ya fito daga bakinta. 
    Ango kuwa a yanzu ya share komai, ya lura a hakan da yake nunawa Bintu son k'arya idan sun ke6e kuma ya guma mata rashin mutunci.
   Washegari misalin k'arfe goma na safe aka d'aura auren Fatima Bintu Muhammad da Ma'aruf Abdullahi...!!!

[7/19, 9:07 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<28>>
Idan kaga Bintu, ba  zaka ce itace amaryar ba domin kuwa tun safe take kwance saman gadon Mami, daga ita sai Sadauki don su Aisha sun hanata zaman d'akin da zolayarsu, wannan yasa Mami ta lalla6ata zuwa d'akinta.
   Har kuwa aka d'aura auren bata da niyyar motsawa daga saman gadon. Su Aisha sunason zuwa yi mata bud'i saidai Mami ta yi musu jan ido akan shiga inda take.
  Kuka sosai takeyi, saida Mami ta yi da gaske kafin ta shawo kan Bintu. Babban abinda kuwa yasa jikin Bintun sanyi bai wuce tambayar da Mamin ta jefomata ba na cewa.
"Bintuna kodai bakyason yaron nan tilastawa zuciyarki kikayi?"
Wannan ne silar daina zubar hawayenta kafin ta nunawa Mami ba haka bane tana kaunarsa.
   Bayan ta yi wankanta a d'akin Mami. Mami ta turo Hajara da Aisha domin taimakawa wajen shiryata kafin ango da abokansa su shigo bayan ta gargad'esu akan koda wasa kada su tsokaneta.
   Aisha ta fente mata fuskarta. Yayinda Hajara ta fiddo mata abin buk'ata. Bintu ta fito tayi kyau fiye da zato, ta had'e cikin shadda fara mai golden surfani. 
"Masha Allah!" Shine kad'ai abinda ke fitowa daga bakin Aisha da Hajara. Bintu dai ta bisu da ido kawai, ita kanta tasan ta had'u k'arshe. Fatarta ta k'ara murjewa tayi haske sakamakon gyaran da ta sha a kwanakin nan.
   "Wai ina amaryar ne?" Cewar wata gwaggonsu ta Rano lokacin da ta sanyo kai d'akin tare da sauran tsoffin. Har tsakar kan Bintu ta iso ta sakar mata bud'a.
"Ayuiririii!"
  Haka sukayi mata ca, banda haushinsu babu abinda takeji. Suka ja ta har tsakar falon Mami aka zaunar da ita saman kujera, tuni ta soma ruwan hawaye Aisha ta taimakawa wajen sharemata har itama tana tayata hawayen. Bata ta6a jin tausayin 'yar uwartata ba akan lamarin auren sai yanzu, da kuma tunanin rabuwar da zasuyi, daga yau shikenan bazata k'ara kwana tare da ita ba. Babu abinda ta tunano sai shak'uwarsu da yanda take rayamusu gidan da wasa da dariyarta. Allah Sarki rayuwa.
  Can kuma sukaji shewar ta juya baya. Ana fad'in ga ango! Ga ango!
   Har da abokansa kuwa. Yana sanye cikin dakakkiyar shadda fara k'al, sai shek'i yakeyi. Lallausan sajensa ya kwanta luf-luf. Ya had'u har ya gaji, kallo d'aya zakayi kwayar idanunsa ka fahimci lallai ya yi kuka sakamakon kad'awar da sukayi, ba kuwa don komai ba sai don tunano matarsa wacce k'aunarta ko kad'an bai ta6a raguwa ba a zuciyarsa. A yau da aka d'aura aurensa da Fatima Bintu, sai ya ji zuciyarsa tamkar anyi mishi fami. Haka suka kammala gaisawa da dangi, yana shirin ficewa wata abokiyar wasanshi ta janyoshi.
"A'a ango ya zakayi mana haka. Zo nan ka zauna sai fa anyi muku hoton tarihi."
Wajen akayi dariya. Bintu zata mik'e sai kuma wata ta maidata ta zaunar.
"Zauna, ina zaki gudu? Ke kuma matsa kin zauna kina taya 6era 6ari, kema muna dab da aurar da ke."
  Aisha ta matsa tana k'unk'uni. Daidai lokacin kuma aka zaunar da Ma'aruf a gefenta. Kusan lokaci guda gabansu ya fad'i, k'amshin turaren kowannensu ya bugi hancinsu. Ta muskuta ta ja gefe cike da jin haushin wad'annan matan.
  Abin haushi suka bud'emata lullu6i wai za'ayi hoto. Dakyar ta bari akayi d'aya duk ranta a k'untace kafin da gudunta ta kutsa ta fad'a d'akin Hanif kasancewar yafi kusa da inda take. Ma'aruf ko murmushi kawai yayi wanda shi kad'ai yasan ma'anarsa.
     Haka akayita hotuna da ango da abokansa. K'arshe akayimai da d'ansa fin kala biyar.
    Bayan Magrib kuwa aka soma shirin tafiya Dinner party wanda Mami ta shirya.
   Anan kuwa Bintu bata bayar da matsala ba, sosai ta ji fad'an Maminta. Ta gama had'ewa cikin gown lace ne mai adon golden da fari. Ta d'ora golden head sai 'yar jaka had'e da takalminsa da na mayafi.
  Su Aisha da sauran abokan karatunsu na sakandire da jami'a sai 'yan uwa sun yi ankonsu suma sun fito d'as cikin golden lace, yayinda mazan sukayi ankon farin boyel.
   Mami ta shigo ta d'ago ha6ar Bintu tana dubanta. Murmushi ta saki.
"Masha Allah, Allah Ya kauda idanun mak'iya akanki my daughter. Kinyi kyau, sai ki k'ara kame kanki banason rawa kinji ko?"
  Bintu ta amsa kawai da to. Ina ta ga wani dama ta yin rawa a auren da ba wani so da d'aukinsa take ba?
   Aisha ce tayi mata rakiya har motar angon. Ta saci kallon motar. Baka ganin wanda ke ciki, hakan yasa ta maida kanta k'asa. Kafin su k'arasa Bintu ta ja tsaki.
"Wallahi taraku nakeyi daga ke har su Anti Hajaran, zan rama d'aya bayan d'aya."
  Jin abinda ta furta yasa Aisha darawa.
  "Ashe fa d'an iska d'an iska ne ko? Oho dai, kafin kiyi mana ke muka soma yiwa."
  Bintu ta yi kwafa.
"Lokaci."
Daga haka bata k'ara cewa uffan ba tana jin dariyar Aisha.
  Aisha ta bud'e mata k'ofar ta shiga, wani sanyi ya ratsata had'e da k'amshi. Ta dubi gefenta, ajiyar zuciya ta saki ta kauda fuskarta. Ai 6ata lokaci ne ma idan tace yayi kyau, daman kyakkyawan ne. Saidai a yau kowa ya ganshi zai k'ara son ya k'ara kalla banda ita Bintun. Acewar zuciyarta kenan.
  Muryar Hashim dake zaune wajen direba ya katse tunaninta.
"Ina gaisuwa amarsu."
  Ta daure ta gaisheshi cikin sassanyar muryar da ya ba shi mamaki, ya saba jin Bintu da karad'i, bata da wani sanyi. Ya dai basar ta hanyar dariya kafin ya amsa ya had'a da fatan alheri. Bata amsa ba, alokacin kuma ya ja motar.
   Shiru ya biyo baya. Can kuma ta ji wayarta ta d'auki k'ara. Ta ciro ta duba. Text message ne daga unknown number. Ta bud'o ta karanta.
  "Kin ci nasarar zama matata, ina tayaki murna, fatan baki mance dukkan maganganun da na yi miki a baya ba?"
   Ta dubeshi kad'an bayan ta kammala, wani shu'umin murmushi ya sakarmata mai k'ara sanya yanmata matowa a kansa. Ta kauda kanta, abin da ya ba shi mamaki ganin batayi niyyar ba shi amsa ba, k'arshe ma ta kashe wayar gaba d'aya ta jefa jaka.
 Hashim ya danna rediyo nan kuma kid'a ya soma tashi jin da yayi shirun na motar ya isa. Haka har suka isa babu wanda ya k'ara cewa wani uffan sai shi da Hashim da ke d'an ta6a hira.

 
 
 
   
[7/19, 9:07 PM] ‪+249 99 715 2061‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<29>>

 Sun isa har dab da k'ofar shiga hall d'in sannan Hashim ya faka.
 "Ku jira kar ku fito, ina zuwa."
 Ya fita daga motar.  Ma'aruf ya dubeta, ba laifi kam ta yi kyau kamar ba wacce ya sani ba, duk kuwa da cewar ya ga wadanda suka fita a kyawun. Ya maida kansa ga kallon wajen. Yayi daidai itama ta juyo tana dubansa. Ji fa, namiji har namiji, amma zuciyarsa banda mugunta babu komai ciki.
  "Jikina ya bani ana kallona."
 Ta kauda kanta, a karo na farko tayi niyyar maida mishi martani.
  "Ni me zan kalla a fuskarsa wanda babu shi a wajen..."
  Bata kai ga k'arasawa ba sakamakon fisgo kafad'arta da yayi, wannan ya sanya fuskokinsu suka kusanci juna har suna jin hucin numfashinsu. Cikin kakkausar murya kuma mai k'aramin sauti ya soma magana.
 "Ki bar gangancin gayamin dukkan wasu kalmomi da suka fito daga bakinki, idan kuwa bazaki kula ba zan ladabtar da bakinki wallahi."
   Ya saki kafad'arta, ta matsa da sauri tuni ta soma k'ok'arin zubda hawaye. Ganin haka ya k'ara magana.
 "Lallai kukanki na nufin na ci galaba akanki tun kafin a je ko'ina."
 Jin abinda yace ya sanyata azamar share fuskarta.
 "Ai ba kuka nakeyi ba. Kuma ma.."
 Ta had'iye abinda tayi niyyar cewa tunano da abinda ya fad'amata a yanzun. Gane hakan da yayi ne, ya sanyashi murmusawa kawai baice uffan ba. A haka kuma sai ga Aisha tace su fito. Ashe kan 'yan matan da zasu shigar da su aka had'o. Can na hango dangin Rof na whatsapp a sun jeru suma babu wacce batayi anko ba, wannan ne dalilin da yasa dole aka barsu suka shiga jerin masu shigar da amarya.
  Bintu ta fito, har aka zagayo da ita angon bai da niyyar fitowa. Shi kam hawayensa ya tsaya d'aukewa. Babu wacce ya tuno sai matarsa Ma'u. Masoyiya agareshi, bayajin har abada zai manceta. Allah Sarki rayuwa.
  Hashim na shirin kwankwasa masa sai ya bud'|e ya zuro k'afafunsa ya fito. Bintu takaici ya hanata ma dubansa, idan yana wani yangar sai kace mace. Ita fa ta lura ajinsa har yayi yawa. Tayi kwafa a hankali kawai.
   Ba tayi aune ba, sai jin tattausan hannunsa tayi a cikin nata, bai tsaya a rik'on ba har saida ya sark'esu wuri guda. Ta d'aga kai ta dubeshi, sai hasken flasher suka gani, tuni ya soma tafiya ta bishi cikin wani irin yanayi na sanyin jiki da rik'on ya janyomusu duka. A haka suke taku. Da ka gansu sai kayi zaton wasu taurari masu haske fiye da sauran.
  Shi Ma'aruf yana takunsa cike da jin isa da k'asaitar shi d'in kyakkyawa ne kuma mai aji kwarai da kowace mace zataso ya kasance abokin rayuwarta. Ga Bintu kuwa, yangar daman ta zamto jiki agareta, haka tafiyarta take saidai ta yau ta bambanta da sauran. Sai wani shan k'amshi takeyi bata ko kallon mutane sosai ballantana ta damu da masu d'aukarsu hotuna. A haka har suka k'arasa mazauninsu.
    Sai lokacin ta soma k'ok'arin zame hannunta ganin ba shi da niyyar sakinta. Shaf shima ya mance da wai hannun Bintu ya ke rik'e da, ya saki hannun bayan ya kalleta kad'an kawai.
    Nan aka soma gudanar da shagalin biki, can na hango 'yan matan Zauren Karatu da DM har ma da Classic Ladies suna faman cashewa abinsu, kana ganinsu kasan basu da wata matsala asalima murna kwarai sukeyi game da wannan aure na Ma'aruf da Bintu. Bintu ta ja tsaki, wanda ya dira a kunnen Ma'aruf. Ya matso saitin kunnenta yanda zata ji abinda zai ce.
 "Kika k'ara tsakin nan tsaka zaki zama."
  Ta matsa gami da dubansa, ya d'aga mata gira kad'an da murmushin k'ularwa. Ta kauda kanta kawai tana mai tsuke bakin.
    Can kuma aka tsaida kid'an, akayi addu'ar bud'e taro, kafin kuma a soma hada-hadar cin abinci.
   Har aka kammala babu abinda Bintu ta sanya a bakinta sai lemo. Shi kuwa gogan babu laifi ya d'an ci abincinsa.
   A k'arshe aka umarci Ango da amarya su fito domin yanka (cake),  ya soma mik'ewa, abin mamaki ya k'ara mik'o mata hannunsa wanda ba k'aramin burge mutanen wajen sukayi. Ga iyalan Mami kuwa, su Rufa'i da Aisha abin ya basu mamaki matuk'a, haka suma su Atine su d'an dolo da suka san rashin d'asawar Bintu da yayanta.
  Ta dubeshi, kallon idanunsa ne bataso, sanyaya jikinta yakeyi.
  "Haba Amarya kina yanga, daure ki mik'awa angonki hannu." Cewar mai gabatarwar wanda ya bawa sauran jama'a dariya. Hum! Wai sai ga Bintu ta ji kunya. Ta d'aga hannunta ta d'ora a saman nasa ranta babu dad'i saidai jikin yayi sanyi. Ta mik'e suka soma saukowa. Mami ranta yayi sanyi matuk'a, addu'arta bai wuce yanda ma'auratan nan suka had'u ba, Allah Yasa aurensu yayi albarka.
     Adda Ummi ce mai mik'a wuk'ar yanka cake, Ma'aruf ya kar6a. Bayan ya yanko ya sanyamata a baki, aka d'au sowa. Itama dakyar ta iya sanyamishi a baki bayan ta daurewa zuciyarta, abinda ya bak'anta mata bai wuce yanda har ya k'ara wani rik'o hannunnata ba.
   Bayan sun kammala aka tsayar dasu, cikin fili, nan aka soma zuba musu ruwan kud'i. Can na hango matasan DM mazansu da matansu suna 6arin ruwan kud'i.
   A haka aka tashi amarya ta dage Maminta zata bi. Ba takura kuwa, Mami ta ja ta zuwa motarta suka tafi tare da wasu k'annen Mamin.
 Washegari aka gabatat da lakca, inda matan DDM da Khairin Nisa'i suka jagoranta. Da yamma aka shirya amarya za'a kai ta gidan mijinta...!
[7/19, 10:24 PM] ‪+249 99 950 1031‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<30>>
  Zo kaga kuka da turjiya wajen Bintu. Ta rik'e Mami da Aisha gam! Har ta kusa sanya Mami kuka, Aisha kuwa ai ba'a magana. Abokiyar hirarta zata tafi ta barta. Dakyar Mami ta ja ta ta sanyata a mota bayan ta k'ara mata da nasiharta akan ta Abba da mahaifinta.
    Har aka isa gidan kuka kawai takeyi. Haka Bintu tana ji tana gani kowa ya watse ya barta, ko k'awayen amaryar wadanda rabinsu 'yan uwana babu wanda aka bari bisa fad'in Mami.
  Jin shiru yasa ta bud'e idanunta. D'akin Asma'u a baya kenan wanda ya yau yake mallakinta. Anyi fenti mai kyau, kayanta masu tsada. Ta numfasa, jin tsayuwar mota yasa ta mik'ewa da azama ta rufe k'ofar da muk'ulli. A fili ta furta. 
"Naga abokan da zaka tattaro min su cikamin kunne da hayaniya."
  To shima Ma'aruf d'in babu wanda ya janyo rakiya sai Hashim wanda shi ya tilasta masa suka biya siyo KAZAR AMARCI da sauran kayan sha.
  Da sallama suka sanyo kai falon. Daman basu tsammaci ganin kowa ba a falon, don haka Hashim ya nemi wuri ya zauna. Ma'aruf ya harareshi ganin hakan.
"To me kuma kake nema?" Hashim ya sanya dariya.
"Ikon Allah, ka manta bisa al'ada abokan ango ke rakiya suma su tofa nasu addu'ar?"
  Ma'aruf wanda shima ya nemi wajen zama, ya cire hularsa ya yamutse fuska.
  "Look, ka tilastamin mun siyomata tarkace, ba kuma zan d'auki wani sabon abu ba bayan wannan kaji ko? Baruwana da wata al'ada. Malam ka tashi ka je Sally tana jiranka."
   Hashim tun yana d'aukar abin wasa don kuwa a auren Ma'aruf na farko, har Ma'un ya kawo falon idanunta a rufe ya yi musu 'yar nasiha. Ganin haka ya watsar, ya bishi da nasiha daga nan kuma ya mik'e.
  "To ai shikenan, mai yiwuwa kishi ke damunka. Bari na tafi, Allah Ya sanya alheri. A kuma ji tsoron Allah dai. Atoh."
  Wani kallo kawai ya bishi da shi baice uffan ba. Ya mik'e yayi mishi rakiya har wajen motarsa.
  Bintu tana jin dukkan abinda suke fad'a, ta ta6e baki, wai ma? Shi kansa bai isheta kallo ba yanzun balle kuma abokinsa.
   Ta cire laffayarta ta wurga saman gadon. Wani riga da siket na farin leshi d'inkin ya kamata kwarai hakan ya k'ara fiddo zahirin zubin halittarta.
   Ta fisge d'ankwalin, tana k'ok'arin zuge zip din rigar ne ta ji an murd'a k'ofar. Jin ta a k'ulle ya sanyashi soma bugawa a sannu.
  Ta harari k'ofar ta cigaba da abinda ta soma. Shima daga bugu uku bai k'ara ba ya bar wajen, daman ledar zai mik'a mata, haka ya sanyata a firij ya fice zuwa d'akinsa bayan ya kashe fitilu.
  Ita kuwa Bintu ta chanja kayanta zuwa riga da dogon wando ta nemi makwanci. A gajiye take sosai, hakan yasa ko mintuna uku bata ci ba bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita.
   Asuba nayi kuwa ta farka, wannan kuma sabon su ne, Mami ta sabar musu da tashi sallar asuba. Tana idarwa kuma ta lafke anan saman dardumar sai bacci, abinda ta kasa horuwa da shi kenan, hak'uri har fitowar rana.
   Cikin baccin ne ta ji ana bugun k'ofarta tamkar za'a 6alla. Bintu ba dai nauyin bacci ba. Ta mik'e a firgice. Ga rana har ta fito kyal. Ba shiri ta bud'e k'ofar.
  Ma'aruf ta gani sanye cikin farar jallabiya sai faman huci yakeyi.
  "Wane irin wulak'anci ne haka ina bugun k'ofa bazaki bud'e ba, banda wannan ma, wanene ya baki damar rufe k'ofa?"
Ta turo baki.
"Gani nayi d'akina ne."
Ya watsa mata mugun kallo.
"D'akinki, ni kuma gidana ne. Ki ka k'ara gangancin rufe k'ofa sai na hukuntaki. Ba ki da abinda zan nema."
   Ta dubeshi kawai cike da tsananin 6acin rai dangane da furucinsa. Ta kauda kanta tana mai tunanin abinda ya kamata tayi domin ramuwa. Ya katsemata tunani.
  "Ki kunna wayarki, Mami na son magana da ke. Ki kuma yi sallah, don banga alamun kinyi ba."
  Ya juya ya fice ya barta tsaye kamar an dasa ta. Ta ci alwashin Yaya Ma'aruf sai yayi dana sanin munanan kalamansa gareta. Tayi murmushi mai fassarori.
  "Bintu ce fa." Cewar wani sashe na zuciyarta.
Ta juya ta koma ciki ta rufe d'akinta, saidai bata sanya muk'ulli ba.
   Wayarta ta nufa kai tsaye ta kunnata. Kira ta dannawa Mami. Mami tana d'auka kawai sai ta fashemata da kuka.
  "Haba Bintu, kukan na menene kuma? Meyafaru?"
  Ta ja ajiyar zuciya.
 "Mamina kewarku nakeyi wallahi." Ta fad'a a shagwa6ance. Mami tayi murmushi mai sauti.
  "Muma munyi kewar Bintuna, saidai dole zamuyi hakuri saboda gidan mijinki shine babban gata da rufin asirinki. Shi kuma kad'ai ne wanda zai nunamiki so tamkar mu ko ince fiye da mu. Kinji ko?"
  Bintu ta share hawayenta, lallai ma Mami, batasan abinda ya yi mata ba yanzun. Amma ai bakomai, Inna ta haneta kai k'ara kasafai. Itama ai ba kanwar lasa bace. Shine abinda ta barwa zuciyarta. A fili kuwa ta nunawa Mami ta gamsu, ta hau rok'on a kawomata hanif amma Mami tace ba yanzu ba sai an kwana biyu. Dole ta hak'ura.
   Gama wayarsu, ta mik'e ta fad'a wanka. Bayan ta fito ta nufi akwatin da Aisha ta had'omata. Tsaki tayi, Aisha sai a barta, duk ta had'ata da manyan kaya bayan ta sani ko a gida ba damunta sukayi ba. Tayi ta d'age-d'agenta, can dai ta hak'ura ta d'auko wani atamfa ja mai adon fararen fulawoyi manya. Simple d'inki akayi masa na riga da siket saidai ya zauna sosai a jikinta. Ta k'ara fesa turare. Ta dubi kan gadon, kayan da ta cire babu linki, haka ta tattara komai ta linke ta gyara gadon gami da adana kayan sallarta.
  Har zata fita falo ta tuno da batun d'ankwali, ba k'aramin aikin Ma'aruf bane ya zubamata rankwashi a kanta, ba don ta so ba ta d'auka, saidai koda ta tashi yin d'aurin batayi na kirki ba, sai wani da ake kira da Ture Kaga Tsiya. D'ankunne kawai ta sanya sai zobunanta, babu sark'a da abin hannu. Fuskar fayau babu kwalliyar kirki, acewarta wa zata yiwa?
   Batayi tsammanin ganinsa a falon ba, saidai ga mamakinta yana zaune saman carpet yana karyawa abinsa. Mamaki tayi kwarai, ta shaida kulolin, daga gidan Mami suka fito. Ya dubeta duba na wacce bata isa ba ya kauda kansa fuskarnan tamkar wanda aka aikowa sak'on mutuwa. Shi fa ba'a kyauta mishi ba, ina shi ina Bintu ne? Wannan ta gama ganinsa ai ta cuceshi. Gwara suyita zaman doya da manja.
 Ganin irin kallon da yayi mata ne yasa tayi murmushin mugunta. Kicin ta shiga ta d'auko kofi da cokali bayan ta d'aurayesu ta dawo.
 Ta zauna d'an nesa da shi ta janyo flask na ruwan shayi fuskarta a sake.
  "Wane irin d'an iskan d'auri ne haka kamar wata ka..."
  Bai kai ga k'arasawa ba wayarsa ta d'auki k'ara. Saida ta kusan yankewa sannan ya d'aga tare da sanyawa a loudspeaker.
  "Hello."
 Bintu ta yagi kwai ta tura a baki batare da ta kalleshi ba.
  Daga can ita kuma wacce ke akan layi ta fashe da kuka. Kukan da ya sanya Bintu kusan sakin dariya sakamakon wata k'atuwar murya da ta ji marar dad'in sauraro tamkar ba muryar mace ba saidai ta cije.
  Shi kansa yayi mamakin jin ta da babbar murya haka, ashe kenan idan zasuyi magana da shi ne kawai take ragewa. Yau kam gayun murya babu shi.
 "Prince ka cuceni, ka ci amanar k'auna. Ashe daman aure za'ayi maka da 'yar uwarka shine baka sanardani ba? Na shiga uku."
 Sai lokacin Bintu ta gane ko wacece, itace dai wacce ta yi mishi rakiyar dole zance wajenta.
   Ma'aruf ya d'an rarrasheta ta kasa shiru har ya gaji, ganin zai kashe wayar dole ta sauko. Yace ta kwantar da hankalinta, shi aure ai nufin Allah ne. A k'arshe kuma tayita rok'onsa akan ya shigo tayi mishi kallon k'arshe don itama zata koma Kaduna wajen yayarta.
  Ya tabbatar mata zai shigo. Bayan sunyi sallama ya kwantar da kansa saman kujera ya lumshe ido kawai. Can ya tsinci muryar Bintu.
  "Yaya, wallahi wannan matar 'yar yaudara ce. Bakaji muryarta ba? Allah Ya kamata, ranar da na raka ka zance tana ta faman k'ank'ance murya, yanzu kuma dubi yanda ta bud'e murya tana zuba kuka tamkar ana ruwan sama."
  Yayi cak, ya kuma gaza bud'e idanunsa, gaba d'aya tunaninsa ya tafi ga matakin da yafi cancanta ya d'auka akanta. Ita kuwa wani sanyin dad'i ne ya dirar mata ganin ta kashe bakinsa. Ta kammala ciye-ciyenta a tsanake ta kora da ruwan shayi kafin ta mik'e ta kai kayan kicin.
   Kafin ta kai ga juyowa, ta ji an cakumi gashinta da k'arfi. Ai tuni ta soma ihu.
[7/20, 1:55 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<31>>
Tuni d'aurinta ya kunce.
"Wacece mai k'atuwar murya?"
  Ta sanya hannu ta rik'o hannunsa amma k'arfin ba d'aya ba, ko gezau yatsunsa basu motsa ba.
  "Zan mutu! Don Allah kayi hak'uri Yaya."
   "Daga yau kika k'ara kiranta mai k'aton murya ni da ke ne. Ke meye a muryarki?"
  "Wallahi muryata tafi... Wayyo!"
Ta kasa k'arasawa adalilin k'ara jan gashin da ya yi.
  "Au, ashe bakinki bazai mutu ba? Lallai idan zaman da kika za6a kenan muyi zaki d'and'ana kudarki."


  Tuni ta soma hawaye. Ya saki gashin. Ya kama hanyar fita yana fad'in.
"Ki kammala ki sameni a falo."
Ta tur6une fuska ta bishi da harara.
  "Duk abinda ka tanada nima shi na tanada gareka."
  Bayan ta kammala wanke komai ta ajiye ta d'auki d'ankwalinta ta d'ora shi tana fad'in, ba zata fasa murza d'aurinta yanda ranta ke so.
  Ta share fuskarta, ba fa zatayi saurin karaya ba, yanzu aka fara wasan tsakaninsu tunda bazai gaji da zaluntarta ba.
  Ta fito da wannan takunnata mai cike da yanga. A haka ta k'araso cikin falon, idanunsa a kanta yana duban ikon Allah. Ta zauna saman kujera. "Ganinan."
   Ya ja fasali sannan ya soma maganarsa.
  "Inaso ki kiyaye bakinki. Ki kuma kiyaye dukkan wani abu da zaki janyowa kanki na d'ora hannuna a jikinki. Banason raini, shine kuma babban abinda yafi had'amu kema kinsani. Sannan kina sane cewar Ma'aruf ba k'azami bane ko? Sai ki kiyaye ayyukanki, daidai da d'akina da toilet ban d'agamiki k'afa ba."
  Yana murmushi ya d'aga mata gira. "Ai amarya ce, bata buk'atar 'yar aiki yanzu."
   Takaici ya isheta, ta dauke idanunta ta turo baki.
"Ni ko a gida fa bana wankin band'aki, Aisha ke yi."
  Ya harareta. "Gida daban, gidan aure daban. Banason maimaici. Na gama maganata ok?"
   Ta amsa da toh sanin halinsa. Ta mik'e ta bar falon.
  Kan gado ta fad'a tana tunanin yanda zata soma rayuwar nan a gidan Ma'aruf.
   Bata kai ga tunanin komai ba har ta ji tsayuwar mota. Da sauri ta mik'e ta lek'a. Wani ihun murna ta saki ganin wadanda ke fitowa daga motar. A guje ta fito, bata lura ko da mutum ko babu ba a falon, ita dai burinta ta bud'e k'ofa ta ji ta ajikin 'yan uwanta. Ba zato ta ji an dakamata tsawa wanda ya sanyata juyowa ba shiri.
  "Menene hakan?!"
Kafin ta ba shi amsa suka jiyo sallamar mutane tun kafin su k'araso jikin k'ofar. Ta shareshi ta juya ta bud'emusu. 'Yan Rano ne, yanmatansu da iyaye amma duk ciki banda Inna. Da sauri ta rungume Aisha tana murna sai kuma ra fashe da kuka. Wata cikin su, mai suna Gwaggo Sadiya ta kama baki
"Haba kekuwa Bintu, menene abin kukan kuma?"
  Ma'aruf na murmushi ya amsa a kunyace.
"Shagwa6ar fa gwaggo?"
Suka k'araso ciki suna dariya. Aisha ta ja hannunta zasuyi d'aki saidai wata gwaggonsu ta dakatar da ita.
  "To kekuma haka akeyi? Baki bari ta gaishemu sannan kuyi sirrinku?"
  Aisha ta saketa suna dariya. Ta k'arasa ta fad'a jikin gwaggo Sadiya sannan ta gaishesu.
"Bintu da son jiki. Ashe sai abinda yayi gaba."
  Ita dai murmushi tayi kawai. Ma'aruf take duba yanda yake wani sunne kai shi a dole kunya ga surukai. Ya dubi Aisha.
  "Ke me ya hanaki tafiya makaranta?"
Ta sosa kai.
"To Yaya ai ba wani abun akeyi ba."
  Ya harareta.
"Kedai kinzo ki takurawa Amaryata da gulmace gulmacenku."
  Akayi dariya, Aisha dariyarta da biyu ce, har da mamaki. Ta dubi Bintu kallon ashe an shirya. Bintu ta murgud'a baki gefe kawai ta watsar. Ta lura wannan ce sabuwar kissar da Ma'aruf ya 6ullo da ita. Tayi kwafa, ai kuwa zata nunamasa ta fishi iyawa.
   Ta narke fuska tana mishi wani irin duba.
"Allah Yaya ba wata gulma zamuyi ba, kaima kasan tun jiya nake kukan kewarta."
  Bataji kunyar furucinta ba, sai gwaggonnin ne sukaji, 'yan matan kuwa sukayi makwas suna dariya ciki-ciki. Shi kuwa gogan ya maze, lallai ma yarinyar nan, kawai sai ya mik'e a kunyace yana murmushi kamar gaske ya bar wajen bayan ya jefeta da kallon zamu had'u. Ta bishi da murmushin da ta saba idan tayi wata muguntar. A ranta kuwa tace "Yanzu ka soma gani indai irin salon da ka za6a mana kenan."
  Bayan fitarsa, yanmatan suka kwashe da dariya, gwaggonnin kuwa mik'ewa  sukayi suka  zagaya d'akunanta biyu da kicin, daman basu zo ba.
Aisha ta samu ke6ewa da Bintu.
"Gayamin Tawan, ya lamura?"
Bintu tayi murmushi, ai itama tasan me takeyi, ko Aisha bazata bari ta gane komai ba.
"Ke na durzu a hannunsa, ashe daman duk wani jan ajin da yakemin na k'arya ne, ban dauka komai zai wakana ba tsakani."
  Aisha ta saki baki.
"To ya na ganki garau?"
Bintu ta ja tsaki.
"Kefa 'yar iska ce, wayagayamiki dole sai na kwanta ciwo? Saida fa ya had'a da kuka da magiya na amince. Ya kuma dauki alk'awarin daina musgunamin."
   Aisha dagaske ta yarda, ai sai tayi wata shewa da dariya. Atika ta dubesu.
"Anayi babu mu."
Aisha ta harareta. "Maganarmu ce ta aminan juna."
  Bintu tayi dariya kawai. Wannan Aishar ma karatun litattafanta ya tashi a banza.
"Amma da banason fallasa don Allah."
"Tsakaninmu babu haka Bintu, don Allah ki k'ara zage damtse wajen janyo hankalinsa. Ga k'ananun kayanki can acikin akwati da sauran kayayyakin ma, na had'omiki. Kada ki yarda ki ba shi (chance) na k'orafi."
  "Naji karki cikani."
  Aisha tayi dariya.
"Zan taho miki da books."
Bintu ta harareta. "Sanin kanki ko a gida bana karatun Hausa ballantana a gidan aure."
  Aisha ta k'ara numfasawa.
"Wallahi mamaki nakeyi, daman fa na zargi yaya yana sonki kawai yana k'ok'arin 6oyewa ne irin abinnan."
Bintu ta ta6e baki.
"Shiyasani."
Aisha tace "Bawani, kukasani dai, kema ai kina so kike wani sharewa."
  Dariya kawai Bintu tayi.
Basu jima sosai ba suka tafi. Bayan tafiyarsu shima ya fice ko sallama baiyi mata ba don dagaske yarinyar ta bashi mamakin furucinta.
  Har sukayi sati cikin wannan zama nasu na doya da manja. Ta koma makaranta abinta shima ya koma aikinsa. 
  A gajiye ta dawo gidan misalin biyar na yamma, bayan sun gaisa da Audu maigadinsu ta shige ciki. Anan farfajiyar gidan ta hangi motarsa a fake. Wannan ya bata tabbacin ya dawo. Ta k'arasa shiga ciki a zatonta ya k'ulle da muk'ulli saidai tana murd'awa ta ji k'ofar a bud'e. Baya falon, wannan ya bata damar zubewa kawai akan doguwar kujera.
"Wash!" Ta fad'a a fili cike da jin wata iriyar gajiya. Ta lumshe ido jin dad'in iskar fankar dake kad'awa. Ta kwashi mintuna kusan uku anan kafin ta mik'e ta k'arasa d'akinta. Ta rage kayan jikinta ta fad'a wanka. Saida ta fito ta shirya cikin riga mai k'aramin hannu T-shirt ja an rubuta Baby a jiki, da wando short bak'i ko gwuiwarta bai k'arasa ba. Wannan karon dai ta samu kitso wajen 'yar wata makwafciyarsu. An yarfa mata su k'ananu. Ta tufke da manyan ribbons biyu bak'i da ja. Hoda kawai ta shafawa fuskarta sannan ta fito zuwa kicin domin d'ora girki. Har lokacin baya falon saidai ta ji muryarsa yana amsa waya daga d'akin. Ta ta6e baki tayi kicin, tasan bazai wuce sauran cocaine ba(Sa'a). 
   Ta rasa me zata girka, a k'arshe dai ta yanke shawarar yin jellop din taliya. Ta soma aikin ne tana yi tana wak'e-wak'enta ta ji kamar motsin mutum a bayanta. Wannan ya bata damar juyowa ta dubeshi.
   Ganin haka ya nufi firij yana k'ok'arin bud'ewa.
 "Yaushe kika dawo?"
 Ta yi kamar bata ji ba. Ya gama shan ruwansa sannan ya juyo gareta.
   "Ban hanaki yawo babu d'ankwali bane?"
  Tayi narai-narai da fuska.
 "Wallahi Yaya d'ankwalin takura gareshi."
  Ya dubeta duban da ace ba matarsa bace bai kamatu ba.
 "Nikuma bazan d'auka ba a gidannan, sai ki wuce ki rufe kanki."
 Kamar bazata ajiye aikin ba, dole ta ajiye ganin ba shi da niyyar barin wajen. Ta giftashi ta fita. Ya sauke ajiyar zuciya, bai bita da kallo ba, don ba shi da jarumtar nan. Saida ya tabbatar ta shige sannan ya fito ya koma d'akinsa.
   Acan d'inma duniyar tunani kawai ya lula, saidai duk yanda zuciyarsa ta kai ga fahimtar da shi wani abu, sam ya k'i aminta balle kuma ya bata dama. Ya ja tsaki ya mik'e, bayason tunanin abinda bazai amfana da shi ba.
                          * * *
     

 
 
 

[7/20, 8:05 PM] ‪+249 99 715 2061‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<32>>
  Ta kammala tsaf ta zubo nata a filet bayan ta bar mishi nashi cikin flask. Kasancewar ba sallar takeyi ba, yasa ta zaman cin abincinta.
  Ta soma ci kenan tana kallon wata tasha da ke hasko wrestling. A haka ya fito da zummar tafiya masallaci. Yayi mata kallo d'aya ya cigaba da tafiyarsa baice uffan ba. Ta bishi da kallo, wataran rashin son yawan magana irin na Ma'aruf yakan bata mamaki matuk'a. Kodayake daman bashi da hayaniya, bar shi dai da son girma. D'an hayaniya sai mutuminta, Yaya Rufa'i.
  Bayan ya dawo ya zauna a falon alokacin ta kusa kammala cin abincin. Ya dubi abinda take kallo sannan ya dubeta.
  "Bani remote."
Ta narke fuska.
"Yaya don Allah ka bari na gama kallo."
  Ya yamutse fuska batare da ya dubeta ba don baya buk'atar cigaba da dubannata saboda dalilai.
"A matan ma bansan sunan da zan baki ba, me mace zatayi da wrestling idan na rashin abin yi ba? Malama bani na kalli abinda zai fissheni."
  Ta mik'a mishi remote d'in ta d'auki filet tayi hanyar kicin ganin ya kamo Aljazeera. Daman ai ba yau suka soma fad'a akan tashar kallo ba.
  "Ina abincina?" Bata ko juyo ba ballantana ta dubeshi ta amsa.
"Yana kicin."
  "Kawomin."
Ta had'o mishi komai ta ajiye, zama tayi gami da janyo wayarta.
"Malama tashi ki suturta jikinki kafin zuciyata ta tashi."
  Wani gululun bakinciki ya turnuk'eta, kai bafa zata amince da wannan cin fuskar ba. Dole ne tayi maganin Yayan nan.
   Ta fasa zaman falon ta koma d'aki. Batasan sadda ta soma hawaye ba, kewar Maminta da Aisharta suka mamayeta. Yanzu da ace tana gaban Mami da duk wani abu da zai mata ba dai yayi a gabanta ba. Gashi kuma babu damar kai k'ara, to tace me? Alhalin ta riga ta nunawa Aisha komai lafiya ke tafiya tsakani. Ganin zata sanyawa ranta damuwar babu gaira babu dalili ne yasa ta janyo wayarta. Whatsapp ta soma k'ok'arin downloading, a baya sam bata chatting, tana ganin yanda Aisha ke haukar karanta books da kutsawa groups na matan aure amma ita ko a jikinta. Wannan karon kam, tayi niyyar somawa don ya d'ebemata kewa.
    Bayan ta gama downloading, ya kammala updating contacts dinta da komai. Bata d'ora hotonta ba, tabar wajen fayau.
   Dad'i ya cikata ganin Aisha online, hakanan da yawa daga cikin 'yan uwansu na Rano da 'yan uwan Abban Aisha ma duk sunayi. Kai tsaye ta yiwa Aisha magana. Aisha harda 'yar rawarta na murnar ganinta. Nan ta sanyata a groups, na matan auren ma ta sanya (Admin) ta sanyata ciki.
   Nan ta soma ganin abubuwa, saidai tafi maida hankali a na 'yanuwansu na Rano. Suka isheta da shewa suna tambayar ya amarci. Ta biyemusu da dariya, koda suka tambayi mijin, sai cewa tayi gashinan yana mata tausa. Nan aka dauki dariya har da masu turo Audio. Kai Bintu ta rasa inda zata sanya ranta don dad'i. Ashe dai wataran zata ga amfanin chatting? Haka tayi ta biyemusu tana darawa.
   Shima Ma'aruf bai k'ara bi ta kanta ba. Misalin tara ta ajiye wayar ta fito. Fitilun a kashe, sai hasken tv saidai waya yakeyi. Ta fahimci da abokin aikinsa yake yinta, ta wuce zuwa kicin domin d'aukar ruwa. Bayan ta fito ne yayi mata nuni da hannu wato ta kwashe kayan abinci. Kamar bazata tsaya ba, sai kuma dai ta dawo da baya. Yana wayan yana binta da kallo sakamakon hasken tv da ya hasketa. Ita kuwa kamar tasan yana kallonta ta wuce tana wata rausaya wacce da gayya ta yi ta.
   Ai kuwa har da d'an mik'ewa zaune. Tuni kuma ya soma mance bayanin da sukeyi ta wayar. Ta gabansa ta shige da robar ruwa a hannunta.
  Ajiyar zuciya yayi, ya runtse ido. Dole ya yiwa abokin aikinsa sallama ya tattara ya kashe kayan kallo ya fad'a d'akinsa. Yarinyar nan zai gargad'eta, don bazai lamunci ta dunga yi mishi yawo da duk suturun da ta so ba acikin gidannan.
                       * * *
      Ita kuwa shigarta d'aki ta chanja zuwa kayan bacci doguwar riga mai d'an kauri saidai da kad'an ta wuce gwuiwarta, bata da nauyi. Daga haka ta kashe fitila ta kunna (gwamna ya gaza..lol)ta hau whatsapp bayan tayi male-male asaman gadonta. Kai tsaye group na matan aure ta lek'a, nan ta soma cin karo da sirrika kala-kala da akeson duk mace ta iya ta kuma sansu. Ta soma karantawa tiryan-tiryan. Ajiyar zuciya kawai ta saki, wai ana nufin itama zata iya yiwa Ma'aruf? Ta runtse ido ta bud'e, kai bata fatan har mutuwar aurensu wani abin ma ya had'asu. Ta yarda akwai sha'awa a rayuwa, soyayya ce dai ta kasa gaskatawa yana faruwa domin acewarta ita bai ta6a kamata ba.
  "Toh idan kuma kika soma son Yaya Ma'aruf fa?"
  Cewar wata zuciyarta. Ta ja wani iri. Kai Allah ma bazai jarabceta da wannan ba in sha Allah. Me zata so a wajen mutumin da baya sonta?
  "Ni mugani ma ko yana online."
Ta fad'a a fili sannan ta hau lalube contacts. Baya online, hotonsa ta gani a dp hakan yasa ta bud'owa. Saida ta furta "Wow" a fili tun bata kai ga k'arewa hoton kallo ba.
 
 

[7/20, 10:42 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<33>>
Ta bud'o hoton tana kalla.  Yana zaune cikin motarsa a mazaunin direba. Ya juyo har da wani tankwashe k'afafu, hannunsa na dama dafe da ha6arsa yana murmushi har da wani k'ank'ance idanu. Ya gama had'ewa cikin lemon-green na shadda ta sha aiki. Farar hula ce mai adon lemon-green a saman kansa. Ta bishi da kallon tsaf, tasan yanada kyau, bayan wannan ma, yana da wasu nagarta na mutunci da yake nunawa jama'a da dukkan wad'anda yakeso kad'ai, amma idan bai k'aunar mutum, to fa anan ka shiga uku. (Atunanin Bintu kenan).
  Sai kuma ta tsinci kanta da fad'awa kogin tunanin wanda ya d'aukeshi hoton. Ta k'urawa hoton ido, anan ta gane alokacin Ma'aruf da k'ibarsa wuyansa a cike ba kamar yanzun da ya rame ba. Hoton zai dan kwana biyu da alamu. To kodai Hashim ya d'aukeshi? Sai kuma ta girgiza kai, ba zai kashewa Hashim idanu haka ba. Ta yi jim, sai kuma ta ja  tsaki ta kashe wayarta. Me zai sanya ta damu kanta da tunanin abinda bai dameta ba. Ta lumshe ido a haka bacci yayi awon gaba da ita.
  Abinda ya bata mamaki bai wuce yanda tayi mafarkin Yaya Ma'aruf ba, wai gashinan ta tsareshi da tambayar wacce ta daukeshi hoto har ya kawo mata duka.
Koda ta farka, sai mafarkin ma ya bata dariya da haushi. Lallai jiya ta ci ta k'oshi.
        Washegari ya kama asabar babu makaranta, wannan yasa dukkansu babu wanda ya taka waje. Lokacin k'arfe sha biyu na rana ta kusa saidai Ma'aruf ko falon bai lek'o ba, haka itama Bintu, tana kammala gyare-gyaranta ta koma d'aki abinta ganin bai tashi ba ballantana ta gyara.
   Sai wajejan sha biyu da rabi ta ji fitowarsa falon. Anan kuma ta ji yana kwala mata kira. Ta ajiye wayar da take dannawa ta fito.
  Yana zaune ya hard'e kafafunsa a saman tebur, yayi wankansa yana sanye cikin riga ja da wando fari na jeans. Kallo d'aya yayi mata ya had'e rai. "Wai ban hanaki yin shiga anyhow a gidannan bane?"
  Ta dubeshi sannan ta dubi abinda ke a jikinta. Doguwar riga ce 'yar kanti saidai tana da fiddo halitta kwarai. Ta turo baki kad'an sannan ta zauna tana dubansa kad'an.
"Wallahi Yaya kaima kasan manyan kaya suna takuramin a rayuwa. Ko a gida bana sanyawa."
  Ya furzar da iska kawai, bazai iya fitowa ya sanarmata dalilinsa ba. Shi kansa yana jin ma kunyar tuna wai surar yarinyar da ya raina ke d'an hargitsa shi ba.
  "Kawomin breakfast."
Ta saci kallonsa tayi murmushi lokacin da ta mik'e. Ai tasan manufarsa ta hanata sanyawa. Ita fa ba yarinya bace. Tana shiga kicin tayi kwafa.
"Lallai zakayi ka bari." Ta ayyana a ranta. Ta k'udurta a ranta ba zata bar shiga irin yanda ta so ba don ko a can gida ma bata fasa ba.
  Ta had'omishi kayan kari ta fito. Ya sauke k'afarsa saman teburin ta ajiye sannan ta koma ta zauna. Ya d'an dubeta kawai ya basar, ya soma k'ok'arin had'a tea.
  "Yaya, baka kewar Hanif? Don Allah ka rok'i Mami su dawo nan."
  Ya d'an ji sanyi a ransa. Kamar bazai amsa ba sai kuma yayi magana.
"Munyi magana da ita jiya, zan iya tahowa da shi a yau."
  Haba Bintu ta hau murna har tana washe hak'ora.
  Yana lura da yanda tayita faman shige da fice, daga d'akin da Ma'aruf ya tanada don d'anshi kad'ai wanda aka k'awata da kwalliya da ya kamatu a d'akin yaro. Can kuma sai ta nufi kicin ta d'auko duster ta goge. Kallonta kawai yakeyi, hakanan kuma ya ji ta burgeshi. Yana so yaga ana son d'ansa Hanif. D'an soyayya kenan. Bintu kuwa, a wannan 6angaren ya tabbatar ba shi da matsala ko kad'an da ita. Tana son d'anshi.
  Yana kammalawa ya  fice gidan. Sai wajejan biyar na yamma Aisha ke tabbatar mata yazo ya taho da Hanif, zuwa lokacin ya sallami Atine da goma ta arziki, Atine har kuka tayi saboda murna.
Ai kuwa nan Bintu na jin sun taho ta mik'e ta fad'a kicin, har ta kammala tuk'a tuwon semovita miyar ku6ewa babu labarinsu.
  Can kuma sai ta ji k'arar bud'e gate wanda ya bata tabbacin shine.
  Ta bud'e k'ofar, bayan yayi fakin ya fito yana rik'e da Hanif a hannu. Yaron ya k'ara narka uban k'iba, ya k'ara wayo. Ga shi fari k'al da shi kamar mahaifinsa. A kammani kuwa, zuwa yanzu sai ka kasa bambance kamannin wanda yafi rinjaye, tsakanin babansa da mamarsa.
   Sunayin sallama ta amsa da saurinta ta kar6i Hanif ta cillashi sama ta cafe tana dariya. Shima Hanif d'in ganin haka ya kyalkyale da dariya. Tuni ta juya ciki tana fad'in.
 "Oyoyo d'an Mami."
  Ya shigo da 'yar jakar Hanif ya rufe k'ofar. Kallonsu yakeyi domin kuwa alal hakika sun burgeshi. Yana zama ta dauki jakar yaron sukayi d'aki. Ya shafi sumarsa yana murmushi, lallai Bintu ba k'aramin so take yiwa Hanif ba
[7/21, 9:23 AM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<34>>
Bintu fa ansamu abokin hira. Ai kuwa bata fito falon nan ba sai bayan sun gama wasa da Hanif. Tayi mishi wanka ta chanja mishi kaya bayan ta shafa mishi hoda a jikinsa da fuskarsa, sannan ta sanyamishi riga da wando jikin cotton, na baccinsa. Ta dubeshi tana dariya irin wacce ake yiwa yaro na wasa.
   "Inye, kaga bebina yayi kyau. Zo muje falo muci abinci."
Ta d'aukeshi, yana rik'e da d'an ball sai ihu yakeyi yana sanya bakinsa a jiki. Tayi mamakin ganin Ma'aruf zaune saman carpet ga filet a gabansa har ya kammala cin abinci ma. Ya hard'e k'afa yana kallon The Dr's a Mbc4. Ganinsu ya sanyashi juyowa. Nan ya mik'awa yaronsa hannu yana murmushi.
"Come to me my boy."
Bintu ta dire mishi yaron sannan ta d'auki filet tayi kicin. Jimawa kad'an sai gatanan ta fito rik'e da faranti itama ta zubo tuwo. Ta ajiye ta koma ta d'auko ruwan roba saboda Hanif, marar sanyi. Itama ta d'aukowa kanta pure water mai d'an sanyi-sanyi.
  Ta dawo ta zauna.
"Zo mu ci abinci." Ma'aruf ya tankwashe k'afafu.
"Juyo da abincin nan zan ba shi."
  Ta dubeshi, kai har takan yi mamakin irin wannan so da yake yiwa d'ansa. Ba musu ta juyo da filet din. Tana ci a yangance ne saboda wai tana gaban miji, ta ji ance ba'ason yin loma babba. A gida ma bata fiye yi a gabansa ba saboda tsoron fad'ansa, da dai Rufa'i ne, to shi kam babu kalar lomarta da baisani ba.
   Bayan ta kammala ta ja baya tana shan ruwa.
  "D'aukomin tissue a d'aki." Ta mike zuwa d'akin. Ta k'ara k'arewa d'akin kallo tamkar bak'onta. Zata d'auko ne, ta hangi BlackBerry dinsa da ke jone a chaji tana faman (vibrating) alamun dai kira ya shigo. Ta nufi wayar ta duba.
  "Lawisa" Shine sunan da ta gani kawai, babu wani sakaye. Ai kuwa bata manceta ba, k'awar Yaya Abida yayar Ma'u dake yawon zuwa gidansu neman soyayyar Ma'aruf tana fakewa da duba d'ansa. Ta rik'e k'ugu, yau zatayi maganin shegiya ashe. Ta d'aga.
  "Hello." Bintu tayi shiru. Sa'a ta k'ara magana.
"Haba Ma'aruf, so fa ba hauka bane da zaka dunga wulakantani,  don kayi aure shikenan sai kuma ka daina kulani gaba d'aya. Me zakayi da yarinya wacce batasan rayuwa ba?"
   "Uwarki da ubanki zaiyi dani."
Cewar Bintu a zuciye. Lawisa tayi shiru kafin tace.
"Ni zaki yiwa rashin kunya? Ina mai wayar?"
Bintu ta dubi k'ofa babu alamun mutum, ta cigaba da magana a hankali.
  "Ya shiga wankan sunnah. Ke wai bakyajin kunya ne Lawisa, don yau bazan kiraki antin ba. Babba dake, iskancinki ya rasa kan wa zai fad'a sai tatta6a kunnenki(cewar bintu, don Lawisa bazata fi talatin da wani abu, ta girmewa Ma'aruf). Toh wallahi kika k'ara kiran mijina sai na bazaki a duniya na kiraki karuwa. Ai ina sane cewar ba son Allah kikeyimai. Idan kuma don wannan ne, karki damu, mace mai karfin mata goma ce ni."
  Ta katse kiran da sauri jin Ma'aruf ya kwalamata kira.
"Na'am!"
Ta amsa murya a d'age, a fili tace.
"Shima Yaya Ma'aruf, ya rasa wacce zai kula sai Lawisa. Ai wallahi ko ni mace banga abin burgewa awajenta. Idan Yaya dan iska ne ya k'are a Lawisa ya ci baya wallahi."
  Ta zari tissue ta fito tana masifa a zuciya, a gefe d'aya kuwa, ta ji dad'in yanda ta ci mutuncinta, daman ba tun yau take dakonta ba.
    Ya jefata da wani irin kallo.
"Me kika tsaya yi?"
Fuskarta a sake tace "Babu komai."
    Kamar yayi magana, sai kawai ya fasa. Ya kar6a ya gogemishi inda ya 6ata a jikinsa da baki. Ta dauke filet d'in ta maida kicin sannan ta kawo ruwan wanke hannu. Bayan sun wanke ta kai kicin ta zubar.
   Ta tsaya tana dubansu, babu alamun dai Hanif yana jin bacci. Ita kuwa Allah Allah takeyi ta shiga makwancinta kafin ta6argazar da tayi ya fito.
  Ta zauna don tasan sai an kammala koda zai shiga d'aki. Hanif ya rarrafo wajenta, nan kuma tabar batun kallo ta k'ara shagaltuwa wajen yi mishi wasa. Ta dubi Yaya Ma'aruf wanda yake satar kallonsu.
   "Yaya, wallahi yanzu na rasa da wanda Hanif ke kama, idan na hango kamanninka sai na hango na mamansa."
  Ya lumshe ido ya bude da murmushi saman fuskarsa.
  "Kamannin wa kika fi hangowa?" Yayi furucin hankalinsa na ga tv. Ta k'urawa Hanif ido, sai kuma ta dago tana yiwa Ma'aruf kallon k'urillah. Sannan ta maido dubanta ga Hanif.
  "Kaga hancinku d'aya, bakinku ma haka, duk k'aramin baki gareki. Idanuwan ne dai kamar na Mamansa."
   Ya kwantar da kai jikin kujera yana dubanta da murmushi, Ma'aruf bai fiye hayaniya ba sai akan Bintu wacce ke sanyashi dole don muddin bazata kiyaye abinda baya so ba, to fa za tayita wahala a hannunsa.
Ta kauda kanta ganin ba shi da niyyar magana.
  "Ai dole yafi kama da ni don na fi sonshi akan mamansa dama."
  Bintu ta amsa.
"Allah Yasa dai kada ya dauko halinkuuuu. Allah Yasa da halayen Annabinmu (s.a.w) zaiyi koyi."
  Abinda ta fada a farko ya fusatashi saidai jin kalamanta na k'arshe yasa ta d'aureshi, babu abinda zai iya  ce mata.
  Ganin ta tsira yasa ta yi mishi saida safe. Zata shige ya dakatar da ita.
  "Ki kula, nasan kalar baccinki, muddin na lek'o naga kin danneshi ni da ke ne."
  Bata ce uffan ba ta fad'a dakinta. Bayan ta ajiye Hanif ta fita ta dauko jakarsa da ruwan zafi a flask wanda ta dafa saboda shan firisocrim dinsa.
  Kulle k'ofarta tayi harda mukulli, tasan yau ya shiga d'aki ya dauki wayarsa to babu abinda zai hanashi kusan ci mata zarafi.
  Acan kuwa Lawisa an k'ulu an kuma ci alwashi akan Ma'aruf ko babu aure! Daman kamar Bintu ta sani, abinda ta fi bukata kenan da shi bawai auren ba.
   
 
 
 
 
[7/21, 1:45 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<35>>
 A 6angaren Ma'aruf kuwa, yana shiga d'akin ya ajiye wayarsa k'arama marar tsada sosai k'irar Samsung, da ruwan shan da ya shigo da shi. Ya rage kayan jikinsa ya fad'a wanka. Bayan ya fito ne ya shirya cikin riga mai hannun singilet da wando iyaka gwuiwa na bacci. Alokacin ne kuma ya zare wayarsa daga chaji. Yayi mamakin ganin kira rututu na Lawisa. Kamar bazai kirata ba sai kuma ya kira, don baisan dalilin wannan yawan kiran ba duk da ba yau ta saba kiransa ba saidai muddin ta kira sau d'aya zuwa biyu bai d'auka ba bata matsawa kanta.
   Bayan ta d'auka, yayi mata sallama, ta amsa. Kafin ya kai ga tambayar ko lafiya ta hau magana.
 "Ka gargadi matarka ta kiyayeni, domin nafi k'arfin wulak'anci."
  Yayi shiru kad'an, menene had'inta da Bintu kuma? Ya had'e gira.
  "Idan zakiyi magana yanda zan fahimta kiyi, idan kuma bazakiyi ba, lokacina ba na shirme bane ok?"
   Nan ta shiga zayyane mishi dukkan abinda ya had'asu. Kusan dariya ya so yi sakamakon kalaman da Bintu ta jefata da su. Har yakai ga murmushin mamaki. Wato har tasan wani wankan sunnah? Hum. Shi fa yana yi mata kallon wacce batasan komai ba.
   "Kana jina kayi shiru!"
 Ta fad'a ranta a 6ace.
"Duk abinda matata ta fad'a hakane anyi, kiyi hakuri banji dai dadin zagin da tayimiki ba, zan gargad'eta. Ya dace zuwa yanzu ki bar rayuwata Lawisa, ni na gayamiki bazan iya biyayya ga abinda kikeso ba, ba kuma zan iya aikatawa ba. Lokaci yayi da zaki kyaleni, daman ina kulaki ne ba don komai ba sai don girmemin da kikayi da kuma kaunar da kike nunawa d'ana kafin ki 6ullo da wannan batun naki marar kyawun ji. Kiyi hakuri Bintu bata kyauta ba da ta zageki wannan kuma zan gargad'eta."
  Tayi shiru don takaici, kawai ta kashe wayar. Ya ta6e baki ya jona Samsung d'insa a chaji. Kamar ya je yanzun ya samu Bintu, saidai ya hak'ura zuwa gobe.
   Haka ya kwana zuciyarsa babu ko d'igon damuwa.
      Washegari tun tashin Bintu da asuba bata samu damar komawa ba adalilin Hanif, bataso ya tashi neman abincinsa. Tasan mai yiwuwa ya tashi cikin dare amma nauyin baccinta bai barta ta ji ba ballantana ta had'amishi abincinsa.
   Tana farkawa ta had'a ta ajiye yanda zai d'an huce kafin ya farka.
  Ta mik'e ta koma falon ta tsaftace har kicin, saida ta kammala komai misalin takwas da rabi ta d'ora abin kari. Kafin ta kammala Hanif ya tashi, ta koma gareshi, tana d'aukarshi tayi bandaki, daga zuwa cire famfas ta 6ige da yi mishi wanka, suna fitowa ta tuno da ruwan da ta dora. Da gudu ta direshi saman gado ta nufi kicin. Har ya k'one sauran kad'an, haka ta k'ara wani ruwan akai da Lipton. Ta fito tana jinjina kokarin mata. Haka suke fama ashe.
  Ta koma dakin ta shirya Hanif cikin riga fara mai adon purple da bakin jeans bayan ta sanyamishi wando. Ta sanya mishi safa mai fari da purple itama. Ta d'ora mishi bif a wuyansa gudun kada ya 6ata jikinsa. Haka ta daukeshi suka fito falon. Anan k'asa ta zaunar da shi, ta koma ta dauko abincinsa da ta dama ta ajiye saman tebur sannan ta fad'a kicin ta kashe ruwan zafi ta juye a flask. Daman shi kadai ya rage mata tayi.
  Ta jera komai saman faranti ta kawo ta ajiye saman tebur.
  Sai lokacin ta samu nutsuwar dawowa ga Hanif ta shiga ba shi a baki. Ai kuwa ya hau sha da sauri. Ya bata tausayi, ta tallafi kumatunsa.
  "Sorry bebina, na barka da yunwa."
  Fatansa ta cigaba da ba shi. Saida ya shanye tas har yana gyatsa sannan ta bashi ruwa ta gyara mishi bakin ta cire bif din.
  Bayan ta kammala ta mik'e. Saida ta gama gyara komai a kicin ta dawo  ta daukeshi zuwa d'akinta, kayan wasanshi ta dauko ta dire mishi kayan wasa kala-kala. Nan kuwa ya rikice yayita iface-ifacensa yana wasa.
     Ganin haka ta hau gyaran gado ta kwashe kayan wankinsu, saukinta akwai mai wanki. Ta ware na Hanif tunda kala d'aya ne bazai gagareta wankewa ba, ta hada nata a inda ta saba sati-sati ake wankewa.
   "Bari na shiga wanka bebina, banda rigima." Baimasan tana yi ba, sai wasansa yakeyi yana jik'a kayan wasan da miyau.
  Ganin su biyu ne kuma batason yayi rigima yasa ta bar band'akin a bud'e. Duk kuwa da cewar bata hangoshi, amma tafison ta dunga jinsa kada ya hau kuka.
   Saida ta kammala wankan ta hau wanke mishi kayansa da ta cire.
   Bangaren Ma'aruf kuwa, tara da mintuna ya tashi. Wanka ya soma yi ya zura jallabiya mai hula irinta 'yan Morocco sai dogon wando daga k'asa marar nauyi. Ayau kam koda zai fita baya tunanin fita da wuri.
    Yana fitowa falon ya shak'i iska mai dadi, a 'yan zaman da sukayi ya tabbatar Bintu ba yanda ya d'auketa take ba, ba mai son jiki bace wajen kula da gida.
  Ya hangi kayan kari a saman tebur, saidai kuma jin iface-ifacen yaronsa yana wasa ne ya sanyashi nufar d'akinta.
  Anan tsakar d'akin ya tarar da shi yana wasa, ya k'arewa d'akin kallo, kafin ya sanya hannu ya dauki yaron ya cillashi sama yana dariya. K'arshe ya sakar mishi kiss a le66ansa. Yaron sai k'amshi yakeyi.
  "Hey, ina Mamanka?"
 Ya tambaya cikin kunnen yaron. Hanif sai dariya yayi kawai.
  Jin dariyarsa yasa Bintu fitowa rik'e da rigarsa da ta matse, daga ita sai tawul, bai kai ga rufe cinyarta ba.
   Ido hud'u sukayi da Ma'aruf, tayi azamar komawa ciki.
 "Au Yaya kaine?"
 Bai amsa ba don babu k'arfin amsawar, ya juya kawai ya fita daga d'akin zuwa falo.
  Ya tsinci kansa cikin wani yanayi, lallai shi d'in bai zamo dutse ba, yana da buk'ata. Ganin Bintu a haka ya dagula lissafinsa, babu laifi yarinyar tana da abin gani a fad'a a jikinta.
    Ya kai kusan mintuna biyar anan yana waya da Abba da Maminsa kafin ta fito, ajiye wayar kuma yayi daidai da fitowarta.
  Kallonta ya jazamishi jin wani irin shock tun daga tsakar kansa har tafin k'afarsa.
   Ya gaza d'auke idanunsa daga kanta. Wata shegiyar riga ce a jikinta wacce ta matseta. Hannun rigar d'aya irinta vest, d'ayar kuma hannun 3-quarter. Ruwan toka ce rigar, sai wando shima iyaka gwuiwarta bak'i mai kamar roba, hakan yasa ya kamata ya fiddo da zahirin halittarta. Sai hula da ta rufe kan da shi.
  Ta sakarwa Hanif dake gefensa murmushi tayi kamar bata ga kallon da Ma'aruf ke binta da shi ba.
  "Bebina, bari na shanya kayanka ko?"
  A haka ta nufi hanyar waje. Sai lokacin ya dawo hayyacinsa.
   "Baki da hankali zaki fita a haka?"
  Ta tsaya, saida ta kammala murmushinta kafin ta juyo ta yi mishi wani irin narkakken kallo...
[7/21, 7:33 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<36>>
  "Ya Ilahi."
Ya fad'a a ransa. Baisan lokacin da muryarsa ta sanyaya ba.
"Kada ki fita haka please."
"Please?" Ta maimaita a zuciyarta da mamaki. Yau kuma Ma'aruf ke bata oda harda rok'o. Sai kuma ta ji jikinta yayi sanyi.
"To a ina zan shanya?"
Ya kauda kai ga dubanta.
"Jeki zan sanya a shanya. Sannan please ki ringa suturta jikinki saboda aljanu."
   Ta yi murmushi kawai sannan ta koma d'akinta. Tsalle tayi ta fad'a saman gado kafin ta tuntsire da dariya. Yaya Ma'aruf kenan, yana wasa da ita. Ta yi kwafa. Zaiyi bayani ne. Ganin ta soma jin yunwa ne yasa ta mik'ewa dole ta chanja shiga zuwa doguwar riga ta shan iska, jallabiyar mata. Ta fito, baya falon saidai ya sauke Hanif daga saman kujera. Abin ya bata dariya, ta had'a tea abinta ta soma karyawa tana yiwa Hanif wasa. Ranta fari sol, ganin mazan sun soma russuna, ashe ma abin a baki ya tsaya?
   A d'aki kuwa, Ma'aruf ya shiga wani hali, dole saida ya had'a da fad'awa band'aki gami da sakarwa kansa ruwa. Kusan shekara kenan, shi d'in dai mutum ne kuma mai lafiya. Tunaninsa ya soma kuncewa akan Bintu. Ya soma jin wani abu a ranta yana tunani. Eh! Tunani kawai yakeyi, don ba shi da tabbas. Kawai ya dauki abinda yakeji da wani suna na daban wato sha'awa! Banda haka babu wani abu. Acewar Ma'aruf Abdullahi. Wannan ne silar share maganar Lawisa baiyiwa Bintu ba.
      Da daddare tana ji tana gani ya shirya maida Hanif wajen Mami, ranta bai so ba saidai jarabawa zasu soma a makaranta gashinan babu mai rik'o. Akan hakan yace Mami ta nemar musu yarinya da zata iya rik'eshi su je makarantar tare ko su zauna gida har Bintu ta dawo.
    Tun faruwar hakan sai ya zamana Ma'aruf ya rage zaman falon lura da yayi na zata fasa shigar kananun kaya ba. Ita kuwa wani sa'in ba da gayya takeyi ba, sai don hakan ya zame mata sabo. Tun bata rufe kanta har ta zo ta saba adalilin yawan tunasar da itan da yakeyi ta hanyar rankwashin kan.
    Watarana tana zaune a falo, fitowarta kenan bayan ta idar da sallah. Ranar ya kasance juma'a. Sai ga shi shima ya shigo dawowarsa daga masallaci kenan. Tayi mishi sannu da zuwa.
"Shirya zamu fita."
Wani sanyi ya mamayeta, daman zaman ya gundureta. Tayi shiga ta manyan kaya. Leshi ne light blue dinkin riga da siket ya zauna d'abas a jikinta. Ta k'ara gyara kwalliyar fuskarta sannan ta yafa mayafi dark blue hakanan takalminta mai d'an tsini shima dark.
    "Kina ina?"
Jin muryarsa yasa ta saurin d'aukar jakarta wacce ta yiwa ciko sai wayarta.
"Gani nan."
Tayi mishi kyau kwarai, to babu damar nunamata, ya soma tafiya.
"Muje."

  Ta rufe gidan ta bi bayanshi. Gaban motar ta zauna shima ya shiga ya tayar.
  Ta saci kallonsa, sai kawai ta ji ya burgeta ganin kamar yau din yana cike da nishad'i.
  Tunaninta ya tafi a inda zasuje, sai ware ido takeyi. Shima baice mata uffan ba. Ganin sun shiga layin gidansu ta saki ihu murna.
  "Ke banason hauka!" Ya fad'a cikin fad'a-fad'a.
  Ta nutsu tana dariya.
"Wallahi Yaya wani dad'i ne ya rufeni."
  Yayi murmushi kawai batare da yace uffan ba. Ji takeyi kamar ta 6alle murfin motar ta fad'a ciki tun kafin maigadinsu ya bud'e gate.
  Ai kuwa yana shiga da fakin ta bud'e murfi ta fita da saurinta ko waigowa batayi ba ballantana ta rufe mishi k'ofar motar.
  "Mamina! Mamina!!"
  Ta hau kwala kira. Da Aisha suka soma cin karo kuwa, duk da cewar sun saba ganin juna a makaranta, amma yau ganin na gida daban yake da na koyaushe. Fitowar Mami ya sanya Bintu runtumawa a guje ta rungumeta. Mami itama rungumeta tayi tana mai cike da tsantsar farincikin ganin yanda d'iyarta ta k'ara k'iba da kyawu.
  Ma'aruf da Aisha sai abin ya burgesu, wannan k'auna da Mami da Bintu ke yiwa juna daga Allah ne kawai.
  Can kuma ta saketa tana dariya gami da kwantar da kai a kafad'arta.
"Wallahi Mamina nayi kewarki da yawa."
  Mami ta rik'e hannunta suka k'arasa suka zauna.
"Nima nayi Bintuna, amma nagode Allah da yanda na ganki kinyi kyau."
   Ya k'araso ya zauna gami da gaida Mami. Ta amsa cike da farinciki. Yau wani dadi takeji. Nan fa suma masu aikin suka hau murnar ganin Bintu abokiyar hirarsu.
  Abba ma yana shigowa ya zauna a falon ransa fari k'al. Hira sukeyi kamar ba surukanta ba. Bayan Abba da Ma'aruf sun shiga falonsa ne Mami ke labarta mata cewa ansanya ranar bikin Aisharta nan kusa.
  Baki ta saki da mamaki.
"Amman Aisha bata gayamin ba?"
Aisha ta harareta da wasa. Mami ta amsa tana murmushi.
"Kwana uku kenan da kawo kud'in, nan da watanni uku za'ayi."
  Kai, ranar Bintu ta yi murnar da ta jima batayi ba. Idan ka ganta da Ma'aruf a gaban iyayen saika rantse babu wata 6araka a tsakaninsu.
   Har takwas na dare tana gidan. Lokacin ne kuma Ma'aruf ya dawo daga 'yar unguwar da ya je. Ya zauna yana duban yanda ta yi filo da cinyar Mami ta d'ora Hanif akan ruwan cikinta tana shan cakulet tana lasa mishi suna hira a haka.
  Ya girgiza kai yana duban Mami.
"Mami kina son sangarta yarinyar nan, bansan dalili ba."
  Ta shafa kan Bintu tana murmushi.
 "Sunanmu d'aya, bani da kamarta."
  Bintu ta lumshe ido ta bud'esu akan Ma'aruf. Ya ji wannan ya basar.
  "Hakane. Sai ki taso mu tafi."
 Ta nark'e murya.
"Kai Yayana tun yanzu?"
Ganin gaban Mami ne yasa shi yi mata murmushin dole.
 "Au, da kwana zamuyi?"
Mami ta sanya baki. Haka Bintu ba don ta gaji da ganin Maminta ba ta shirya suka tafi bayan Mami ta yi mata alk'awarin zuwa.
       
 

   
 
 
 
[7/22, 3:58 AM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<37>>
A mota suna tafe ya dubeta.
 "Kinason Mami."
 Ta numfasa da murmushi dauke saman fuskarta.
"Tana sona shiyasa."
Kamar yayi mata wata tambaya sai kuma ya share. Ya dubeta.
 "Zakiyimin rakiya zance ne ko na mik'a ki gida?"
 Tambayar ta zo mata iya wuya, shima d'in ya fad'a ne don ya ga yanda zatayi.
  "Kaini gida." Ta fad'a kusan a k'ufule. Baice uffan ba ya kad'a kan motar zuwa gida. Tana ganin tamkar wasa yakeyi, saidai kuma ta gane lallai dagasken yakeyi don a k'ofar gidan ya faka motar gami da dannan mabud'i ta gefensa. Dubansa tayi, bai dubeta d'in ba, saidai murmushi da yakeyi na mugunta. Ta bud'e a fusace ta fice.
   Saida ya ga shigarta sannan yayi dariya kad'an ya d'agawa Audu maigadi hannu.
 "Ina dawowa yanzu."
 Daga haka ya bar layin. Wasa yakeyi mata domin kuwa abin motsa baki yakeson zuwa siyomusu.
  Bintu a fusace ta k'arasa ta bud'e kofar ta shiga. Ta kasa ta6uka komai, ta shiga safa da marwa falon bayan ta yar da jaka da mayafi da dankwali. A haka ta soma rage kayan jikinta. Ina Ma'aruf yaje? Wajen sauran cocaine(Sa'a) ko kuma Lawisa? Ran Bintu fa babu dad'i ta shiga wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa.
   To me hakan ke nufi? Me zai dameta da  fitar Ma'aruf zance?
  Ta zauna daga ita sai undies, a fili kuma tayi furucin.
  "Ai ba wani abu tsakaninmu, me zai dameni?"
  Ta kusan mintuna uku, ta kasa hakuri ta fiddo wayarta a jaka. Ta lalubo wayarta ta nemo lambarsa.
    "Angrybird." Shine abinda ta rubuta a sunan Ma'aruf. Haka ta danna kira.
   Lokacin yana hanyar gidan, ya d'auko wayar ya duba. Baisan lokacin da ya dara ba ganin Bintu ce. Bai d'aga ba har ta yanke.
  Sai lokacin Bintu ta ji haushin kanta sosai, ta ja tsaki gami da tattara kayanta zuwa d'aki. Haka kawai baya sonta sai ya zama ya dunga wulak'antata. Kawai ta soma zubar hawaye.
  "To me zai dameki wai?"
 Wata zuciyar ta k'ara jefomata tambayar da ta sanyata share hawayenta gami da mik'ewa. Wankan ma bazatayi ba, kawai ta bud'e cupboard d'inta ta d'auko rigar bacci doguwa har k'aurinta mai k'aramin hannu. Tana da (top) saidai ko bi ta kansa batayi ba,  haushi da wani mugun abu da batasan ko menene ma ya tokare wuyanta.
   Duk da 'yar yunwar da take ji, haka ta nemi makwanci. Babu yanda Mami batayi ba akan su tafi da abinci ya k'i, ashe don ya shiryamata mugunta yayi hakan. Tayi kwafa, zuciyarta tayi wani irin rauni, yanzu shi yana can yana dariya a gaban budurwarsa. Hawaye ta ji ya silalo mata. Ba zato kuma ta ji hon d'in motarsa.
 Ta mik'e da sauri ta lek'a, ganin dagaske shi d'inne yasa ta sauke ajiyar zuciya gami da goge fuskarta.
    Tana ji yana bugun k'ofar, saida ta d'an yi jim sannan ta mik'e ta fita ta bud'e. Ya had'e fuska gami da mik'amata ledojin hannunsa.
 "Au, daman kina ji kika shareni?"
 Batace uffan ba, ta kar6i ledojin ta ajiyesu zata shige d'aki.
  "Ina zakije? Na sallameki ne?"
 Ya fad'a yana dubanta. Dole ta dawo ta zauna tana 6ata rai.
   Dakinsa ya shige. Saida ya gama abinda zaiyi sannan ya dawo falon har ta kai k'ololuwa wajen 6acin rai.
  Zama yayi yana k'aremata kallo, lallai zaiyi maganinta tunda ba zata gaji da tsokanoshi ba.
    "D'aukomin filet da kofi."
 Ta tashi tayi gaba, cikin sauri take tafiya a fusace wanda ya ba shi damar k'arewa halittar kallo. Murmushi yayi, yasan hirar da yace zai tafi ne ya 6ata ranta. A ganinsa ko hirar ya je, me zai takura zuciyar d'ayansu?
   Bayan dawowarta ya umarceta da bude ledojin, ta ciro kaza wacce aka nad'e a foil paper, ta juye. Ta fiddo youghurt din data gani sai lemu.
    Tana kammalawa ta juya zata tafi, ji tayi mutum ya fisgota jikinsa.
 Ta ware idanu tana dubansa a tsorace, hakan ya k'ara fito da manyan idanunta masu kyau tana dubansa. Shi d'inma ita yake duba, zuciyarsu na bugu da sauri-sauri.  Ta soma kiciniyar zillewa, babu dama. Ya d'ago ha6anta, cikin k'aramin muryar  ya soma magana.
   "Hey, ba dai kishina kikeyi ba ko? Ban hanaki yimin shiga haka ba?"
  Ta ji gabanta ya fad'a, saidai kusancinsu yasa batason cewa uffan. Gaba d'aya ma jikinta rawa yake, abu ne da bai ta6a faruwa gareta ba, wai namiji ya rik'eta har haka.
    Da ace anan abin ya tsaya da saukinta ne, saidai kuma batayi aune ba ta ji ya soma isar ga sak'onsa a cikin mataunar abincinta(hhhhh.. Inji Tasleem.
Lol).
   Bintu ta rasa a inda take, gaba d'aya ta tsorata, jikinta kamar ana kad'awa. To ba ita d'in ba, shi kansa bai tsira ba. Da k'arfi ta fisge jikinta ta ja baya, da gudu kuma tayi d'aki ta rufe gam! Shi kuwa saman kujera ya zauna ya dafe kansa, idanunsa a lumshe. Ya kwashi tsawon mintuna a haka kafin yayi baya ya jingina da kujera.
   "Oh Allah, what's about to happen?"(Meke shirin faruwa?)
   "Very soft." Ya fad'a a ransa lokacin da hancinsa ya k'ara shak'o k'amshi na jan bakinta.
  "Kai, Bintu ce fa!" Wani sashe na zuciyar yayi mishi tuni. Ya bud'e idanunsa da suma suka chanja.
  Eh Bintun ce! Ai halaliyarsa ce. Ya bawa kansa wannan amsar cike da jin kwarin gwuiwa da kore kalmar da na sanin da wani sace na zuciyarsa ke k'ok'arin tursasashi wajen yarda.
  Saidai ba zai kashe kansa ba, ya shirya dambe da borin kunyar, har ya samu abinda gangar jiki da ruhinsa ke so suna kaiwa kasuwa. Don me zai bari shaid'an ya kusan cin galaba akanshi har ya ji zai iya amincewa da buk'atar Lawisa ya kai mata ziyara?
  A'a, shi d'in bai kasance cikin mazinata ba, don haka dole ayi d'ayan biyu. Gudanar da zaman lafiya tsakaninsa da matarsa, ko kuma auro wacce zata iya da buk'atunsa.
   Dakyar ya saita kansa ya rufe wannan tashar, zama yayi ya soma cin kazarsa hankalinsa kwance. Saida ya ci mai isarsa sannan ya sha youghurt ya d'ora mata sauran saman firij sanin da yayi na cewar dole zata buk'ata. Daga haka ya dauki ruwa ya kashe fitilu ya fad'a d'akinsa.
                      * * *
    Bintu fa???
[7/22, 2:02 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<38>>
A daki bintu tana shiga taji wani bakin ciki abinda yayiwa mata a zuciyarta hawaye hawaye hawaye hawaye hawaye hawaye hawaye hawaye hawaye suka dinga zubowa karshe ta shiga ta shiga kitchen ta dauko wuka ta cakawa kanta a ciki  take nan ta fadi ta mutu
 Ma'aruf Yana daki YA jiyo kara shima YA fito da gudu yayi kitchen yama zuwa yaga bintu ta gadi cikin jini YA dinga kuka YAna jijigata amma inaaa ta muta shima sai yayi tunanin mai zaije YA cewa mommy kawai shima YA dauko wukar YA cakawa kanshiiiii shima ya fadi mutuuuu. Kurunkus angama bintu 😏
 😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😜😜😜😜😜😜😜😜😜
[7/22, 10:42 PM] ‪+234 806 038 4145‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<38>>
A hankali ta zauna a k'asa ta jingina da gado yayinda ta takure k'afafunta da hannuwanta wuri d'aya. Har lokacin jikinta yana kyarma. Ta k'ara kai hannu ta share bakinta. Sai kuma ta fashe da kuka marar dalili. To ita kanta batasan abinda ya janyomata zubar hawayen ba, tasan dai ta tsorata sosai da irin abinda ya wanzu tsakaninsu. Can kuma ta mik'e ta koma kan gado gami da goge fuskarta. Lumshe ido tayi tana maida numfashi sannu-sannu. Abin mamaki sai kuma ta tsinci kanta da yin wani murmushi. Yaya Ma'aruf ya had'u, shine kawai abinda ta ayyana a ranta. Abubuwa da yawa sun tsaya mata a rai a d'an wannan rik'on da yayi mata da sak'on da ya isar.
   "Ban hanaki yimin shiga haka ba?" 
   Abinda ya fad'o ranta kenan, ta mik'e tsaye da saurinta ta nufi gaban madubi tana k'arewa jikinta kallo.
   Rigar kam babu laifi, da a gidan Mami takeyi ba zata barta ta sanya ba duk da cewar ita bata ga aibunta ba, amma ba laifi tayi shara-shara.
  Ta dauki top d'inta ta d'ora akai gami da zama a gefen gadon ta rik'e cikinta da ke wani irin kuwwa sakamakon yunwar da ta ji ta motsa mata. Saidai kuma batajin zata iya fita yana a falon, wai Bintu ce da jin kunyar Ma'aruf yau? Abin da ya bata mamaki kenan har yasa ta murmusawa.
   Haka ta zauna tana sak'e-sak'en zuci. Ta rasa yanda zata fassara hakikanin matsayin da ta ajiye Ma'aruf. D'an uwan ne ko Mijin? To ai kuwa tuni a matsayin mijin yake ko ta k'i kuwa. Saidai fa bata sonshi, shine babbar hujjar da ta kafawa kanta har take tak'ama da shi. Ya za'ayi ta mance munanan kalamansa a kanta? Ai ya nuna ita d'in yarinya ce babu abinda zaiyi da ita, to kuwa zai yi nadamar furucinsa, shiga kuwa na English wears, yanzu ta soma. Jikinta ne kuwa, ta daina bari ya maimaita wannan abu da yayi. Ta sauke ajiyar zuciya tayi shiru tana jira ya bar falon. Ta jima zaune kafin ta jiyo motsinsa wajen kicin sai kuma da jimawa ta ji ya rufe k'ofarsa. Saida ta bari aka d'anyi mintuna ta lek'o, ganin duhu a falon ya tabbatar mata lallai ya kwanta kenan. Kunna fitilar ta yi ta ware ido, babu ledojin a tsakar falo hakan ya sanyata nufar kicin, nan ta ci karo da su a saman firij.
  Haka ta koma dakinta ta rufe gam da mukulli bayan ta dauki komai na bukatarta.
                      * * *
    Washegari ya kama Asabar, abinda ya sanya Bintu jin babu dadi, tana son gasa shi, saidai ta lura ta soma d'an jin nauyinsa don abinda yayi, ashe daman da gaske ne da ta ji ana cewa ana samun wani sauyi a jiki idan irin hakan ta faru a lokacin? Ita kam sai yanzu ta gaskata. Bata mantawa akwai sadda suke hira da Aisha akan ire-iren lamuran nan, ta 6alli rakenta tana tsotsa gami da lumshe ido.
 "Banza kawai, jeki haukan soyayya ya kasheki kawai, gwara miki shan rake kullum kiyita sha kina nishadi abinki, da wata soyayya."
  Bata manta amsar Aisha alokacin.
  "Hum, bakisan menene ma'anar kalmar ba, kedai Allah Yasa wataran ki ji yanda..."
  Bata manta yanda ta toshemata baki wai kada tayi mata mugun fata. Aisha ta fisge hannunta tana dariya kafin tace.
 "Wallahi akwai abinda idan anyimiki ba zaki iya magana ba. Ke bakinki mutuwa zaiyi, zaki fahimci shegen kuri ne kawai kikeyi."
   Dariya tayi ta cigaba da shan rakenta kawai.
  Bintu ta numfasa ta mik'e cike da kwarin gwuiwa, ba fa zata bari tayi saurin karaya ba, lallai idan ta nunamishi sanyi da kuma nauyinsa da take ji zai fahimci yayi nasara akanta. Har alokacin tana jin 6acin ran zancen da yaje.
  Har ta fito ta kammala komai bai fito daga d'akinsa ba, daman bata tsammatar hakan tunda yau babu aiki. Ta koma d'akinta tayi wanka, har ta dauko kananun kaya sai tayi murmushi ta mayar, gaskiya a yau dai ba zata iya sanyawar ba amma hakan ba wai yana nufin ta bar alak'a da su bane tunda sun zame mata kamar atamfa.
    Ta sanya doguwar riga ta atamfa, hoda kawai ta shafa sai man le6e.
   A falo tana zaune tana karyawa sai gashinan ya fito. Ko wanka baiyi ba, daga shi sai riga da wando dogo na bacci na (pyjamas).  Ya zauna saman kujera. Bata ko kalleshi ba sai ma ta had'e fuska. Ido ya zubamata, haka kawai ya ji ta burgeshi yanda ta had'e fuskar. Ya bi d'an bakinnata da kallo kawai, shi kansa a yanzun sai yakejin kunyarta amma kasancewarsa namiji, ya maze har da wani had'e gira kad'an.
  "Ina kwana." Ya gaisheta da gatse.
 Sai kuma bataji dadin gaidashin da bata yi ba.  Ta gaisheshi, ya amsa kafin yayi umarnin ta had'amishi abin kari. Babu musu ta had'a ta ajiye a gabansa.
   Yana wani muzurai yana shan tea shi a dole kada yarinya ta ga fuskar rainashi. (Ikon Allah)
    Har ta kammala ta mik'e babu wata magana da ta k'ara shiga tsakaninsu. Ya bita da kallo, sai yaga kamar ma atamfar ta fi yi mata kyau sosai. Ya kawar da wannan tunanin kamar yanda ya saba kaudawar duk lokacin da ya taso.
     Haka suka ci hutun karshen satin kowannensu na kokarin nuna jarumtarsa a fuska, alamun fa babu wani abu a zuciya.
   Ranar litinin tana zauna a falo bayan ta dawo daga makaranta, bayan ya dawo aiki yake sanarmata da tafiyar da ta kamashi zuwa Lagos, bisa wani aiki da zaiyi a karkashin branch na kamfaninsu dake can. Ai a take ta soma washe hak'ora.
  "Yaushe ne tafiyar?"
 Ya zauna yana dubanta fuska a sake.
 "Oh, wato murna ma kikeyi?"
 Ta rufe baki adalilin dariyar farincikin da ya taho mata.
 "A'a, ai idan dadi yayi yawa kuka akeyi, nima bakinciki ne yayi yawa shiyasa ni darawa."
   Ya jinjina kai ya dubi gefe yana murmushi mai bayyana hak'ora kafin ya dubeta.
  "Bansan lokacin da raininki gareni ya k'aru har haka ba."
 Ya mik'e tsaye, ya soma tafiya  hanyar d'akinsa.
 "Gobe zan wuce in sha Allah, mungama magana da Mami, Aisha zata zo ta tayaki zama."
  Wani ihun murna ta saki wanda ya sanyashi juyowa. Da sauri tayi narai-narai da fuska.
 "Toh Yaya, Allah Ya kiyaye."
  Ya d'an zubamata ido sai kuma ya juya ya shige.
  Murna bai barta ta k'arasa abinda takeyi ba, ai gwara ya d'anyi k'aura daga gidan ko ta sha iska. Haba, Kullum mutum yana gida idan ya taso ofis sai kace ba shi da abokai. Ta ja k'aramin tsaki kawai.
  Shi kuwa mamaki ta ba shi ganin yanda take murna da tafiyarsa, wannan na nufin Bintu bata damu da shi ba? Ya tunano a baya idan wata 'yar tafiya ta sameshi yanda Ma'u ke damuwa har ta kai ga zubda ruwan hawaye na rashin son tafiyarsa. Amma yau ga Bintu ta zo matsayin matarsa, bata jin ko d'ar na tafiyar da zaiyi. Jikinsa ya d'anyi sanyi, haka kawai baiji dad'in yanda ta nuna d'in ba. Ya damu iyaka damuwa har saida ya gaza jurewa a ranar da zai tafi ya dubeta.
  "Meyasa bakiyi bakinciki da tafiyata ba?"
  Ta ji tambayar babu zato, sai kuma ta yi murmushi.
 "To ai kaima zaka huta da ni, tunda kace ina matsawa rayuwarka. Kuma kace ni ba komai ka d'aukeni ba ko?"
  Ya rasa kuma bakin magana. Ya watsamata wani kallo mai nuni da jin haushin kalamanta sannan ya sanya kai ya fita jaye da Trolley dinsa. Ta dafe bango da hannunta tana binsa da kallo gami da doka uban hamma. A hankali tace "Allah Ya kaika lafiya. Bari nayi baccina har na gaji ba takura."
 Ta rufe k'ofar ta koma ciki, lokacin bakwai da mintuna na safe. Abin ya yi mata dadi don kuwa bata da paper.
[7/23, 11:59 AM] ‪+249 99 715 2061‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<39>>
   Zuwan Aisha gidan ya yi musu dadi. Haka zasu zauna suyita hirar duniya idan ba makaranta. A kokarin Bintu bai wuce koyaushe ta nunawa Aisha lafiya lau suke da mijinta ba. Har takan dauki waya tayi kiransa saidai har wayar ta gama rurinta baya ko kallonta. Saidai a wayance tayita zuba zance don burge Aisha.
  Satinsa d'aya da tafiya, amma ko text bai ta6a yi mata ba, da zummar gaisuwa. A yanzu kuwa ta daina samun layinsa, saidai ta ji Aisha tace yayi kiranta ko kuma Mami. Jikinta yayi sanyi, haka kawai ta tsinci kanta da shiga damuwa. Kodai furucinta ya bawa Yaya Ma'aruf haushi? Ashe zai damu da ta nuna damuwa akanshi?
   Ta kai dubanta ga Aisha wacce ke kwance rigingine a saman gado tana amsa wayar masoyinta Ashir, sai wani narke murya takeyi da murmushi. Daga inda take ta zubawa wayarta ido kawai amma kunnuwanta suna ga Aisha tana sauraronta.
   Kawai sai ta ji abin ya burgeta, inama ita da Yaya Ma'aruf su dawo haka? Sai ta ji nauyi, kada dai ta kamu da son Ma'aruf ne? Ta girgiza kai, kokusa bata fahimtar abinda akeyi a group din nasu ta whatsapp ta tsinci kanta da komawa contact ta lalubo lambar Ma'aruf, har lokacin hotonnan ne akai bai chanja ba. Ta bud'o tana duba, a hankali takejin wani abu na yawo a zuciya da gangar jikinta. Tayi nisa a kallonsa ta ji Aisha ta makomata filo.
  "To 'yar is me kikeyi kika wani nutsu?"
   Bintu batajin wasa a yau, ta ajiye wayar ta dawo kusa da Aisha ta zauna.
   "Tashi ki bani wasu amsoshi don Allah."
   Aisha ta mik'e zaune ganin Bintu dagaske take ba wasa.
  "Ina sauraronki."
  Bintu ta muskuta tana fuskantarta.
  "Ya mutum zai gane ya fad'a tarkon so?"
  Me Aisha zatayi banda dariya. Ta d'aga hannu sama.
  "Allah na godemaka da Ka bani tsawon ran ganin wannan rana. Cabd'i!"
  Ta girgiza kai kad'an tana had'e rai cikin son kauda 'yar kunyar da ta ji.
  "Malama banason haka, idan bazaki bani amsa ba ki bar yimin dariya."
  Ganin Aisha bata da niyyar dainawa ya sanyata daukar wayarta a fusace ta shige d'aki. Kan gado ta fad'a tana murmushi, daman tasan hakan zata faru tunda ta riga ta gama cika baki a baya. Tana jin sadda Aisha ta shigo gami da zama gefenta, ta had'e rai. Aisha ta gimtse dariyarta ta soma magana duk kuwa da cewa Bintun ta juyamata baya.
   "Idan ka soma son mutum, zaka tsinci kanka cikin yawan tunaninsa, haka kuma da zarar ka ganshi kun had'a ido zaka ji kamar wasu kibiyoyi ke fitowa daga idanunsa suna shiga naka har suna haddasa maka wani kasala, har ka kasa jure kallon ka sauke idanunka. Komai na mutum zai dawo yana burgeka, ko muryar mutum ka ji sai ka ji wani sanyi na dadi. Babban abinda ke tabbatarwa ka kamu da soyayyar mutum shine KISHI. Nan duniya zakaji baka kaunar abokin takara a zuciyarsa. Ba kuma ka kaunar wani ya ra6eshi da sunan so. Ko yaya kaga ya sakarwa wani fuska ya kula da shi fiye da yanda yake kula da kai sai ka ji tashin hankali sosai, da damuwa da bakin ciki a zuciya. Matukar kina jin wadannan abubuwan da na lissafa, shakka babu (You Are In Love)."
  Bintu ta bud'e lumsassun idanunta tana duban fuskar gadonta, ta ji gabanta yana bugu da sauri-sauri. Ta kamu da son Ma'aruf yanzu? Kenan dukkan abinda takeji a ranta akansa soyayya ce?
  "Kenan alamomin da nakeji akan Yaya Ma'aruf suna nuni da cewar inasonsa?"
  Batasan sadda ta watsowa Aisha tambayar ba. Aisha ta rasa inda zata tsoma ranta don dad'i, don ta jima da gane cewar  babu abinda ya ta6a shiga tsakaninsu kawai dai ta barta a yanda ta so ne.
  "Idan har kina jin abubuwan da na lissafa akansa, to lallai kin fad'a cikin matsanancin soyayyarsa."
  Sai kuma ta ji wata iriyar kunyar Aisha, lura da hakan ne yasa Aisha mik'ewa ta fita da zummar d'ora musu girki. 
  Ta sauke ajiyar zuciya ta mik'e zaune.
 
  "Inason Yaya Ma'aruf." Shine abinda ta furta cikin siririyar murya.
                  * * *
  "Ina sonki Fatima Bintu." Cewar Ma'aruf kenan a yayinda yake kwance cikin kujera idanuwa a lumshe yana tunanin Bintu wanda ya zame mishi jiki tun zuwansa Lagos. Gaba d'aya kewarta ta dameshi, baisan ya damu da yarinyar ba sai bayan da ya nisanta da ita. Yana fushi da ita akan ta nuna halin ko'in kula da tafiyar da zaiyi, wato dai bata damu da shi ba. A rayuwarsa yana so yaga an damu da shi. Sai ya kai zuciyarsa nesa yake k'in daukar kiranta, lallai shi yana son tilasatawa ransa ya fiddata. Yanaso yabar tunanin wani abu nata da ita kanta. Yana so ya yakiceta a ransa. Wannan yasa ya yanke shawarar yin wata d'ayan da ogansu yace yayi acan batare da ko sau d'aya ya dawo hutun karshen sati Kano ba.  Sanin da yayi ma idan yazo ba wani abun zai samu awajenta ba. 
    Ya numfasa ya mik'e zaune. Kalmar nan ta "So" baiyi zaton zai k'ara furtata ba ballantana ya ji ta a ransa. Sai ga shi zuwa yanzu ya gama tabbatarwa ransa ya fad'a dumu-dumu cikin kogin son matarsa kuma 'yar uwarsa abokiyar fad'ansa Bintu.
 Sai kuma yayi murmushi sadda ya tunano rashin jituwarsu tun afarkon zuwanta gidansu har zuwa girmanta.
   Rufa'i ya dannawa kira, ya sanar dashi cewar wata d'aya zaiyi don haka ya dauki su Aisha ya maidasu gaban Mami. Daman ya kammala waya da Abba ya shaida mishi. Ya yiwa Bintu gajeran sak'o babu wani abin jan hankali ciki ya shaidamata su had'a kayansu Rufa'i zaizo ya tafi da su gidan Mami.
   Ta yi kasak'e tana duban sak'on alokacin suna tare da Aisha tana k'ara koyar da ita yanda zata shawo kansa. Ta sanarwa Aisha kafin su soma shiri. Ranta duk babu dad'i jin zai cinye wata d'aya a garin da basu da wani  addini sosai.
    Haka suka kammala shiri suka nufi gidan Mami.
   Saidai tana ganin Mami ta mance da batunsa ta hau murna. Ganin yanda ta d'an rame sai Mami tayi zaton ko ciki ne. Ta shiga nan nan da ita. Murmushi kawai sukayi ita da Aisha.
[7/24, 9:37 AM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<40>>
A wannan wata d'ayan, wanda aka ci sati uku kenan da Bintu tayi a gidan Mami, ta yishi  cikin kwanciyar hankali, duk kuwa da cewar babu wata mu'amalar arziki dake shiga tsakaninta da Yaya Ma'aruf face gaisuwa da take mik'a mishi ta whatsapp, shima wani sa'in za'a nunamata ya je kuma ya gani amma babu amsa. Sai sadda ta ci sa'a ne yake amsa mata, daga amsa gaisuwar kuma bai k'ara cewa uffan.
   Tun tana yi har ta soma gajiya, wani sa'in ta watsar.
  Shi kuwa ya d'auki hakan kawai a matsayin rainin hankali, tunda gwana ce wajen hakan.
    Ganin yana neman cutuwa sosai da bukatunsa, ya sanyashi farlantawa kansa azumin litinin da alhamis. Haka kuma da yawaita dauke hankalinsa da wani abu da ba zai jawo mishi motsuwarsa ba. Saidai iyakar dauriya yinsa kawai yake, akwai sadda Lawisa ta kusa cin galaba akanshi. Sukayi doguwar hira a waya mai ta6a sosai, a k'arshe suka yanke zata kawomishi ziyara har Lagos.
  Koda zuwanta da soma gudanar da abubuwa, tun kafin lamura su 6aci, ya dawo nutsuwarsa inda wata kyakkyawar zuciyarsa tayi mishi tuni da "Bafa matarka bace." Da sauri ya fisgeta daga jikinta ya mik'e yana kiran innalillahi a fili kafin ya fad'a ya wanke jikinsa. Nan ya taddata tana hawaye, bai bi ta kanta ba ya kama hanyar fita sai kuma ya tsaya batare da ya juyo ba, cikin kakkausar murya yace. "Kiyi hanzarin barin gidannan tun kafin na dawo."
  Yana shirin ficewa yaji ta rungumoshi ta baya, ya runtse ido, kafin ya juyo ya tureta.
  "Karki k'ara kusantoni! Ki rabu da ni Lawisa, please daga yau ki fita hanyata."
  Hannunsa ta rik'e a gigice. "Bazan fita ba, ka taimaki rayuwata Ma'aruf kada  ka barni ha.."
  "Ki kyaleni! Ki kyaleni nace!! Kafin na dawo ki tattara abinda kikasan mallakinki ne ki bar gidannan!!"
  Ya fad'a a tsawance kafin ya sa kai ya fice.
  Ranta ya 6aci sosai da wannan wulakancin da yayi mata, ita kuwa ko shine autan maza ba zata k'ara kallonsa ba. Ta dauki wayarta ta kira d'aya cikin mutanenta na Lagos. Nan tayi kwatancen inda take, a take kuwa Alhajin yasa direbansa zuwa d'aukarta. Ko wanka bata tsaya yi ba ta shirya tsaf ta bar gidan.
     Ma'aruf bai jima sosai ba ya dawo, ya ji dad'in rashin ganinta a gidan, ya zauna ya rik'e kai. Idanunsa sunyi ja sun kumbura adalilin kukan da ya ci, yau ga shi ya kusa tafka kuskuren da da ace ya faru ba zai iya yafewa kansa ba. A gefe kuma ga soyayyar dake azabtar da shi, ya ji haushin yanda ta bar turomishi sak'on gaisuwa ko don baya kulata sosai ne? Batasan cewa yana jin dadin hakan ba?
  Ajiyar zuciya ya saki, fatansa ya kammala aikinsa yaje ayi wacce za'ayi don ba zai zauna da cuta ba.
       Acan kuwa, Bintu bata k'ara bi ta kansa ba, ta danne abinda takeji a ranta dangane da shi. Ta nemi zuwa Rano ganin iyayenta tunda sun samu hutu. Kasancewar shima Rufa'i zai kai Hajara ganin gida, yasa Abba bai hanata ba ya kira ya sanarwa Ma'aruf. Allah Ya tsare hanya, shine kawai abinda yace.
  Farinciki ya rufe Bintu yau zata ga 'yan uwanta.
  Suma can sun shirya tarbarta sosai. Tare suka je har Aisha.
  Yan uwa sunyi murnar ganinsu. Inna ta shiga nan nan da su.
  Kwanansu uku suka soma shirin tahowa don Rufa'i zaizo daukarsu. Inna ta k'ara yiwa Bintu nasiha sosai akan rik'e hakkokin mijinta da sauransu. Ta yaba kwarai ganin Bintun ta yi hankali, ta zama wata mai sanyi da nutsuwa, batasan cewa soyayya ke nukurkusarta ba har ta ladabtar da ita ladabin dole. Aisha ta samu abubuwa sosai a wajen 'yar Rano kasancewar bikinta baifi sati hud'u da kwanaki ba.  Haka suka baro Rano cike da kewa.
    A safiyar asabar ne ta koma gidanta kamar yanda Mami ta umarceta. Tare suka je da Aisha sai 'yar yarinyar da aka samo mata da bata wuce sha uku ba da zata tayata rainon Hanif, har da Hanif din wanda suna isa Bintu ta goyeshi a bayanta. Suka gyara komai  don a ranar akesa ran dawowar Ma'aruf kamar yanda ya shaidawa Mamin.
  Kicin suka fad'a suka hau girke-girke. Suna yi Aisha na k'ara bata shawara.
  "Kwalliya fa zaki ci malama, irin wanda na gayamiki. Kada ki nunamishi fushinki Bintu. Kiyi hakuri, kece dole wajen yi mishi biyayya, amma fa ban hanaki jan aji kad'an ba, karkiyi yanda zai tsinke."
  Sukayi dariya, Bintu ta dafa kirjinta.
"Bakiji yanda gabana ke bugu ba, a tsorace nake fa. Kinsan Yayanki akwai disgawa."
  Aisha ta girgiza kai.
"Akanki ba, kuma kema kinsan abinda yasa yake miki hakan, kin nuna mishi baki da kunya."
  Bintu ta harareta. Aisha ta dara kad'an.
"Allah kuwa rashin girmamashi sosai ne yasa yakemiki wasu abubuwan. Ki tuna keda kanki kin sha yabon yanda sukeyi da Anti Asma'u, yana sakarmata fuska, wasa da dariya duka, koda kuwa a gabanmu ne. Yana da mutunci wallahi ba wai kuma don Yayana bane. Ita gaskiya fa a fad'eta."
  "Ya gasamin maganganu fa."
"Wannan kuma kinfini sanin ta sigar da zaki rama, saidai ina k'ara baki shawara, kada ki ja aji ta yanda zai tsinke wallahi."
  Murmushi kawai tayi, suka cigaba da aiki suna hira, anan ne Bintu ke labarta mata yanda sukayi da Lawisa. Me Aisha zatayi banda dariya, har da rik'e ciki. Ta jima tana dariya da k'arawa.
 "Kai wallahi kinyi daidai. Toh wallahi ko don saboda su ya dace ki bada kai bori ya hau kada kiyi sakiyar da ba ruwa."
 Aisha ta k'arashe tana mai kwafa.
"Bakisan wacece Lawisa ba. Yar iska ce, idan ma nayi kiranta karuwa banyi k'arya ba wallahi. Ki tashi tsaye karki bari su samu k'ofa."
 Bintu ta girgiza kai da gamsuwa da wani irin tsoro.
   Bayan sun kammala, Aisha ta yiwa Hanif wanka, itama Bintun ta fad'a band'aki.
 

 (Kuyi hakuri, ba da son raina na barku jiya ba.. Ba chaji ne)
[7/24, 12:57 PM] ‪+249 99 715 2061‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<41>>
Mintuna ashirin da kammala shirinta da komai, ta fito falon inda Aisha da Sarah mai rainon Hanif suke zaune suna kallo. Ba Aisha ba, daidai da Sarah saida ta saki baki wajen kallonta.
    Wani shegen siket ne bak'i mai shek'i amma ba shi da kyalkyali, tsaga gareshi tun daga gwuiwa har k'asa, sai wata riga ja mai igiyoyi wanda ya tafi X ko kirjinta bai rufu yanda akaso ba, bata da hannuwa sai na vest. Ta rufe kanta da jar hula mai wani laushi duk da hakan, tufkakkan gashinta bai kammala rufuwa ba.
   Ta rik'e k'ugu ta karkace kai kad'an yayinda ta d'an tsuke baki.
  "Ya?"
  Aisha ta had'e yatsunta biyu.
"Wow! Kinyi kyau wallahi."
  Ta k'araso tana mai yin farr da ido.
"Nasani."
  Aisha ta d'aka mata duka a cinya sukayi dariya.
"Yau dai da wuya Yayanmu ya d'auke idanunsa akanki."
Sai kuma jikinta yayi sanyi. Fatanta kada ya gwatsaleta.
  "I hope so."
"In sha Allah, kedai kada ki damu."
  Cewar Aisha.
Angonnata basu shigo Kano ba sai bayan Magrib. Tuni Aisha ta tattara ta wuce. Duk yanda Bintu ta so zamanta har zuwa sadda zai shigo amma fir ta k'i.
   Tana zaune ta rik'e Hanif tana mishi wasa ta jiyo tsayuwar mota. Ji tayi gabanta ya fad'i, ashe daman don batason Ma'aruf ne yasa batajin nauyin yin komai a gabansa?
  Tayi saurin duban Sarah.
"Shiga d'aki."
Sarah ta mik'e da sauri ta fad'a d'akin Hanif.
   Kwankwasa k'ofar da akayi yasa ta nufar k'ofar, Hanif yana rungume a jikinta bata ajiyeshi ba. A hankali take tafiya har ta isa k'ofar ta bud'e. Ido cikin ido suka dubi juna. Kowannensu yana kokarin isarwa d'an uwansa sak'o.
Sai kuma ya juya da sauri, Isa direban Mami ya tara gami da kar6ar akwatinsa.
  "Nagode Malam Isa."
  Ganin haka, yana shigowa ta sa hannu ta rik'o trolley din, shi kuma yayi amfani da hagunsa wajen amsar Hanif dake mak'ale a hannunta na dama.
   Wani shock sukaji gaba d'ayansu, ya narkar da idanunsa wajen kallon abinda ya fi tafiya da imaninsa a wajenta. Ita kuwa ta dauke idanunta. Murya na rawa ta furta. "Yaya sannu da zuwa."
Baki amsa ba har ta juya ta nufi d'akinsa tana rausayar da batasan yanda akayi ta soma ba, wannan kam yafi (natural) tafiyarta had'uwa da tada hankali.
   Baiyi k'asa a gwuiwa ba ya tura k'ofar da k'afarsa ya mara mata baya. A daidai k'ofa suka had'u, caraf ya rik'o hannunta ya ja zuwa ciki. Ta dubi yanda ya rik'e hannunnata gam kamar mai tsoron a rabasu, sannan ta dubeshi a tsorace, gabanta na bugu da k'arfi da kuma sauri-sauri.   Ya ajiye Hanif a saman gado ya jawota gaba d'aya zuwa jikinsa gami da yi mata kyakkyawan rumfa ruf. Gaba d'ayansu sun ji a jikinsu kuwa. Daidai kunnenta ya yi magana.
  "I'm in need of you Fati."
Yanda yayi maganar da irin muryar da yayi amfani da ita wajen yin ce ta sanya tsintar kanta cikin rawar jiki. Bata ankara ba ta jishi yana cigaba da abinda bazata iya jura ba.
   "A'a! Bintu, not so fast!"
  Da sauri ta daddage ta tureshi, bata bi takan Hanif ba ta fice a guje. Sai ma ta ba shi dariya, hakan ya sanyashi murmusawa.
   
   

 
[7/25, 12:04 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<42>>
Hankalinta ya tashi, ta fad'a kan gado tayi shiru. Ya akayi ta kasa danne zuciyarta? Ta ji haushin kanta, Allah Yasa dai bai gano lagonta ba.
  Bata kammala tunane-tunanenra ba ya shigo da sallamarsa.
  Ta daure ta amsa a nutse batare da ta dubeshi ba.
  Shi d'inma bai damu ba ya mik'amata Hanif.
  "Rik'eshi."
  Ta kar6eshi baki bar dubanta ba ya yamutse fuska kad'an. Kamar yace wani abu sai kuma ya fasa ya fice.
   Ta bishi da kallo tana murmushin takaici, wasu siraran hawaye suka sirnano daga idanunta. Iyakar saninta, tana da rik'o wani lokacin, amma ta rasa dalilin da yasa zuciyarta ke neman gazawa wajen rik'on abinda Yaya Ma'aruf yayi mata. Magana kam, ya gaggasa mata, saidai ta tsorata da abinda Aisha tace akan matan dake kawomasa hari zasu iya zamowa barazana a rayuwarsu.
  "Amma bai furta yana sonki ba. Kodai bukatar ce kawai yake nufi?"
  Ta ji zuciyarta babi dadi da wannan tunanin da tayi. Ta yi ringingine saman gado tana duban Hanif dake wasa da zobenta. Tunaninta bai wuce anya dagaske Ma'aruf yana sonta ba? Tafi bawa zuciyarta kawai bukatarta yakeyi. Ba don hakan ba ma bazai nemeta ba. Da bakinsa ya kushe halittarta, ya nuna mata nan duniya ya k'arfin kasancewa da ita. Ita kuwa ta yaya ma Aisha zatace kada ta k'i bada kai?
  Ta numfasa ta rik'o hannun d'an kamar shine uban take maganarta a fili.
  "Kai, bazan yi yanda yakeso da wuri ba, sai naji gaskiyar abinda ke zuciyar babanka."
  Hanif dai banda ihu-ihunsa da 6angale dariya babu wani abu da yakeyi. Ta d'an kama kumatunsa.
"Ni ce fa Bintun Mami! Zamiyi maganinsa ko?" Ta k'arashe da 'yar dariya. Ba ita ta fito daga dakin ba saida ya kwalamata kira. Ta janyo (After Dress) ta zura tana murmushi ta fita.
   Yana zaune saman kafet yana amsa wayar Abbansa, saidai hakan bai hanashi binsu da kallo ba har suka zauna.
   Hanif ta ajiye gefe sannan ta mik'e ta dauko komai na bukata wajen cin abinci. Ta soma zubawa ta ji muryarsa.
  "Fati." Bata amsa ba, ba kuma ta fasa abinda takeyi ba, saidai kiranta da yakeyi da Fati, yana sanyamata jin wani abu.
  Ya k'ara kiranta da murya da sigar da bazata iya ji ta kyale ba. Dole saida ta yi dagaske wajen saita tunani da nutsuwarta, ta d'ago fuskarta a daure, ba k'aramin namijin k'ok'ari tayi ba wajen dubansa.
    "Na'am." Ganin yanda ta tur6une fuska sai ya ji haushin kansa. Ya manta da cewar Bintu ce fa, yanzun d'an abubuwan da ya aikata zasu sanya ya janyowa kansa sabon raini.
  Ya sosa hanci.
"Kada dai ki dauki abin d'azu a matsayin wani abu, haka aure ya gada. Eh, kuma ba zai yiwu gida bai k'oshi ba a bawa na waje. Abar batun nan, ya wajaba lallai a gareni ni da ke mu zamto masu tsoron Allah mu dunga sauke hakkokin juna. Hakan zai fi mana kyau." Shi kam, bak'a sosai yaso yarfamata. Baisan ya akayi  ya kasa ba.
   Anzo ga6ar da zata maida martani, don haka ta tura mishi farantin abincin gabansa, ta dubeshi ta kauda kai tana murmushin mugunta.
  "Na farko dai ni bani da bukata, hakki kuma na yafe nawa, kuma Yaya ka manta kace babu abinda zakayi da jikina. Ka kuma ce kallona kan tashi zuciyarka. Ni ce fa wannan yarinyar da kake fad'a. To nidai bani buk'atar komai nagode da niyya."

  Ya rasa me zaice? Saidai ya maze ya sha mur. Kamar yayi magana sai ya fasa ya hau cin abinci yana ta nanata maganganunta a ransa. Lallai ma yarinyar nan, wato haka take da riko? Ya ji ta ba shi haushi, ya d'an dubeta da niyyar fad'a, saidai bazai  iya ba, wai wane irin muguwarl soyayyarta ce tayi mishi kamu har haka? Kallonta ma wani nishad'antar da zuciyarsa yakeyi. Ya daure batare da ya kalleta ba cikon sanyin murya yace. "Please leave me alone."
 Yanda yayi maganar baisa ta nuna tausayinsa a fuska ba, iyakar magana ai ya gasa mata. Ta dauki Hanif har da wani cillashi sama tana dariya. Daga haka ta shige dakin Hanif.
   Ji yayi ransa na k'una, wato ko a jikinta? Shi kuwa yaya zaiyi ne ta gane zuwa yanzu yayi nadama? Lallai so na sanya ladabin dole. Yau shi ke bin Bintu!
   Ya runtse ido.
                      * * *
  Tun daga ranar ya fita hanyarta, duk da cewar ta damu a 6oye, hakan baisa a fili nuna kamar batasan me yake yiwa fushin ba. Ta daure ta cigaba da walwalarta yanda ta saba babu ko nuna wata alama ta damuwa.
   Ranar da ta je gida wuni, shima ranar yana ajiyeta ya nufi gidan abokinsa Hashim.
  "Ya akayi ne wai? Please mafita zakaban banason dariyar banza."
  Hashim ya tsagaita dariyarsa.
"Sorry, mamaki dai nayi ne. Kamar ka ace ka auri wannan ficikar yarinyar har ma ka soma sonta? Abinda ko a mafarki bazakayi kuskuren gani ba kenan."
  Ya fahimci Hashim na tunano mishi furucinsa ne. Ya lumshe ido kafin ya bud'esu ya dubeshi ransa a 6ace, ya ja guntun tsaki.
 "Bazaka gane ba, banason tuna baya."
    Hashim ya numfasa ya gimtse dariyarsa. Daidai sadda Salimarsa ta shigo ta ajiye musu kayan motsa baki. Ta tambayi lafiyar Amarya. Ya amsa da murmushi.
 "Lafiya, ai kun kyauta tunda shi bai kawoki ba kekuma bakizo ba."
 Hashim da Sally sukayi dariya.
 "Tuba nake, zaku ganni very soon in sha Allah."
  Ya jinjina kai yana shafa sumarsa fuskar dauke da murmushi.
  Bayan fitarta daga falon, Hashim ya dubeshi. "Kai zakayi wannan yak'in har ka siye zuciyarta."
  Ya yatsine fuska yana dubansa.
 "Ta yaya kenan? A tunaninka zan durkusa na rok'eta ta soni? Never! Furuci d'aya nayi mata wanda a yanzu nake (regretting, I'm in need of her)."
   Hashim ya ja tsaki.
 "Kana da matsala, dole kuma ka sauke wannan ji da kai ko ince girman kan da kake nunamata wallahi."

 (Kuyi hakuri, banjin dadin jikina ne
.
Tears)
[7/25, 6:38 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<43>>
Hashim ya dubi abokin nasa da tausayi yace ma'aruff dole ka daure anjuma kaje kayi raping din bintu ko tana so ko bata so ....hehehe lol zuciyarta? Ta ji haushin kanta, Allah Yasa dai bai gano lagonta ba.
  Bata kammala tunane-tunanenra ba ya shigo da sallamarsa.
  Ta daure ta amsa a nutse batare da ta dubeshi ba.
  Shi d'inma bai damu ba ya mik'amata Hanif.
  "Rik'eshi."
  Ta kar6eshi baki bar dubanta ba ya yamutse fuska kad'an. Kamar yace wani abu sai kuma ya fasa ya fice.
   Ta bishi da kallo tana murmushin takaici, wasu siraran hawaye suka sirnano daga idanunta. Iyakar saninta, tana da rik'o wani lokacin, amma ta rasa dalilin da yasa zuciyarta ke neman gazawa wajen rik'on abinda Yaya Ma'aruf yayi mata. Magana kam, ya gaggasa mata, saidai ta tsorata da abinda Aisha tace akan matan dake kawomasa hari zasu iya zamowa barazana a rayuwarsu.
  "Amma bai furta yana sonki ba. Kodai bukatar ce kawai yake nufi?"
  Ta ji zuciyarta babi dadi da wannan tunanin da tayi. Ta yi ringingine saman gado tana duban Hanif dake wasa da zobenta. Tunaninta bai wuce anya dagaske Ma'aruf yana sonta ba? Tafi bawa zuciyarta kawai bukatarta yakeyi. Ba don hakan ba ma bazai nemeta ba. Da bakinsa ya kushe halittarta, ya nuna mata nan duniya ya k'arfin kasancewa da ita. Ita kuwa ta yaya ma Aisha zatace kada ta k'i bada kai?
  Ta numfasa ta rik'o hannun d'an kamar shine uban take maganarta a fili.
  "Kai, bazan yi yanda yakeso da wuri ba, sai naji gaskiyar abinda ke zuciyar babanka."
  Hanif dai banda ihu-ihunsa da 6angale dariya babu wani abu da yakeyi. Ta d'an kama kumatunsa.
"Ni ce fa Bintun Mami! Zamiyi maganinsa ko?" Ta k'arashe da 'yar dariya. Ba ita ta fito daga dakin ba saida ya kwalamata kira. Ta janyo (After Dress) ta zura tana murmushi ta fita.
   Yana zaune saman kafet yana amsa wayar Abbansa, saidai hakan bai hanashi binsu da kallo ba har suka zauna.
   Hanif ta ajiye gefe sannan ta mik'e ta dauko komai na bukata wajen cin abinci. Ta soma zubawa ta ji muryarsa.
  "Fati." Bata amsa ba, ba kuma ta fasa abinda takeyi ba, saidai kiranta da yakeyi da Fati, yana sanyamata jin wani abu.
  Ya k'ara kiranta da murya da sigar da bazata iya ji ta kyale ba. Dole saida ta yi dagaske wajen saita tunani da nutsuwarta, ta d'ago fuskarta a daure, ba k'aramin namijin k'ok'ari tayi ba wajen dubansa.
    "Na'am." Ganin yanda ta tur6une fuska sai ya ji haushin kansa. Ya manta da cewar Bintu ce fa, yanzun d'an abubuwan da ya aikata zasu sanya ya janyowa kansa sabon raini.
  Ya sosa hanci.
"Kada dai ki dauki abin d'azu a matsayin wani abu, haka aure ya gada. Eh, kuma ba zai yiwu gida bai k'oshi ba a bawa na waje. Abar batun nan, ya wajaba lallai a gareni ni da ke mu zamto masu tsoron Allah mu dunga sauke hakkokin juna. Hakan zai fi mana kyau." Shi kam, bak'a sosai yaso yarfamata. Baisan ya akayi  ya kasa ba.
   Anzo ga6ar da zata maida martani, don haka ta tura mishi farantin abincin gabansa, ta dubeshi ta kauda kai tana murmushin mugunta.
  "Na farko dai ni bani da bukata, hakki kuma na yafe nawa, kuma Yaya ka manta kace babu abinda zakayi da jikina. Ka kuma ce kallona kan tashi zuciyarka. Ni ce fa wannan yarinyar da kake fad'a. To nidai bani buk'atar komai nagode da niyya."

  Ya rasa me zaice? Saidai ya maze ya sha mur. Kamar yayi magana sai ya fasa ya hau cin abinci yana ta nanata maganganunta a ransa. Lallai ma yarinyar nan, wato haka take da riko? Ya ji ta ba shi haushi, ya d'an dubeta da niyyar fad'a, saidai bazai  iya ba, wai wane irin muguwarl soyayyarta ce tayi mishi kamu har haka? Kallonta ma wani nishad'antar da zuciyarsa yakeyi. Ya daure batare da ya kalleta ba cikon sanyin murya yace. "Please leave me alone."
 Yanda yayi maganar baisa ta nuna tausayinsa a fuska ba, iyakar magana ai ya gasa mata. Ta dauki Hanif har da wani cillashi sama tana dariya. Daga haka ta shige dakin Hanif.
   Ji yayi ransa na k'una, wato ko a jikinta? Shi kuwa yaya zaiyi ne ta gane zuwa yanzu yayi nadama? Lallai so na sanya ladabin dole. Yau shi ke bin Bintu!
   Ya runtse ido.
                      * * *
  Tun daga ranar ya fita hanyarta, duk da cewar ta damu a 6oye, hakan baisa a fili nuna kamar batasan me yake yiwa fushin ba. Ta daure ta cigaba da walwalarta yanda ta saba babu ko nuna wata alama ta damuwa.
   Ranar da ta je gida wuni, shima ranar yana ajiyeta ya nufi gidan abokinsa Hashim.
  "Ya akayi ne wai? Please mafita zakaban banason dariyar banza."
  Hashim ya tsagaita dariyarsa.
"Sorry, mamaki dai nayi ne. Kamar ka ace ka auri wannan ficikar yarinyar har ma ka soma sonta? Abinda ko a mafarki bazakayi kuskuren gani ba kenan."
  Ya fahimci Hashim na tunano mishi furucinsa ne. Ya lumshe ido kafin ya bud'esu ya dubeshi ransa a 6ace, ya ja guntun tsaki.
 "Bazaka gane ba, banason tuna baya."
    Hashim ya numfasa ya gimtse dariyarsa. Daidai sadda Salimarsa ta shigo ta ajiye musu kayan motsa baki. Ta tambayi lafiyar Amarya. Ya amsa da murmushi.
 "Lafiya, ai kun kyauta tunda shi bai kawoki ba kekuma bakizo ba."
 Hashim da Sally sukayi dariya.
 "Tuba nake, zaku ganni very soon in sha Allah."
  Ya jinjina kai yana shafa sumarsa fuskar dauke da murmushi.
  Bayan fitarta daga falon, Hashim ya dubeshi. "Kai zakayi wannan yak'in har ka siye zuciyarta."
  Ya yatsine fuska yana dubansa.
 "Ta yaya kenan? A tunaninka zan durkusa na rok'eta ta soni? Never! Furuci d'aya nayi mata wanda a yanzu nake (regretting, I'm in need of her)."
   Hashim ya ja tsaki.
 "Kana da matsala, dole kuma ka sauke wannan ji da kai ko ince girman kan da kake nunamata wallahi."
[7/26, 12:44 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<44>>
 Shi kuwa iyakar dauriyarsa kawai yayi, yana son kusantar tafi haka, saidai bayaso yayi gaggawar da zata fassarashi baibai. Watakil ba zata fahimci yanda yake so da kaunarta ba.
   Ya ji sadda tayi bacci, shi d'in kuwa ya jima kafin baccin yayi awon gaba da shi hakance ta sanya baiji kiran sallar asuba ba.
  Ta k'ura mishi ido tana kallon irin baiwar da Allah Ya bata na samun mutum mai kyau da kwarjini irin Ma'aruf, ba wayonta ba ba komai ba.
   Bacci yakeyi hankalinsa kwance, dakyar ta iya mik'ewa ta fad'a toilet.
 Saida ta kammala tsarki da alwala ta fito. Har lokacin bai tashi ba.
   Ta d'ora zani saman rigar baccinta tayi shirin tayar da sallah tsaf sannan ta tashe shi a hankali ta hanyar bubbuga k'afarsa.
  Ya waro ido yana 'yar mik'a. Ganinta da hijab, ya sanyashi azamar mik'ewa.
 Saida ya kammala sannan ya fice zuwa masallacin gidan dake kallonsu. Ita d'inma Sarah ta tayar, ta koma tayi nata.
  Ta jima da gama addu'o'inta da komai, har rana ta d'an fito, tana son ta d'an runtsa saidai tana tunanin Hanif.
  Zata fita sukaci karo zai shigo, ta tsorata, ai ta dauka babu abinda zai maidoshi. Ta gaisheshi ya amsa kafin ta ba shi hanya.
  "Ina zaki?"
Ta dubeshi. "Aiki zanyi."
 Ya ja hannunta ya rufe k'ofar.
"Aiki da asubar nan Fati? Bari zuwa anjima naga yau dai ba makaranta zaki ba.
   Bai bari tayi magana ba ya nufi ciki da ita. Har gado ya ajiyeta ya kashe fitilun ya zagayo ya kwanta gefenta.
  Ta runtse ido jin abinda yakeyi. Ya kuramata idanu yana murmushi.
  "Fati." Ya kira sunanta cikin sigar da ba zata jura ba. Bata iya amsawa ba.
 "Look into my eyes, please."
 Ta bud'e idanunta a hankali ta sauke cikin nashi, da sauri kuma ta maida ta rufe. Yayi murmushi ya soma magana ba tare da ya bar abinda yakeyi mata ba wanda ke kunce notinan kanta. 
   "Zaman da mukayi dake tare yasa na damu dake yanzun, kin samu wani babban gurbi a zuciyata Fati..."
  Sai kuma yayi shiru. Ba wannan takeson ta ji bani ta so ba, yanda ya soma bi da ita yasa ta soma fita hayyacinta, saidai da sauri ta mik'e zaune ya dubeta da soyayyun idanunsa. Da saurinta ta mik'e kafin ya ankara ta nufi k'ofa.
  "Tsaya!" Ya fad'a da 'yar muryarsa. Ta tsaya cak, ta sa hannu tana m'ara suturce jikinta, a yanzun shi kuma ya shiga matsanancin damuwa, Bintu bata son shi, shine kawai abinda yasa wa ransa.
  Hakan yasa shi mik'ewa gami da gyara rigarsa ya nufi inda take.
 "D'akinki ne. Baki kamata na takuraki ba."
   Daga haka ya fice. Ta bishi da kallo kafin ta lumshe ido tana murmushi. Ta yarda ta kuma gaskata cewar Ma'aruf fa yana sonta yanzun, saidai ta so yayi furucin da bakinsa ba wai yayita kwana-kwana ba.
 Ta koma ta kwanta gami da tattaro zanin gadon da filon da yayi matashi tana shinshina cike da jin sanyi a ranta. K'amshin turare Yaya Ma'aruf kawai ke tashi. Wasu ruwan hawaye suka kwaranyo mata. Ko a mafarki idan ance mata zata fad'a wannan hali na soyayya ba lallai ta gaskata ba, sai gashinan daga ita har Yayannata Allah Ya jarabcesu da fad'awa kogi na soyayyar juna, so mai wahalar da zuciya da gangar jiki kuwa.
 Shima a can, kasa bacci yayi, idan har bazai samu kan Bintu ba, to zai iya kamuwa da mugun ciwo kuwa don shi kad'ai yasan yanda yakeji a ransa. Yayi amanna cewar bazai iya son wsta ko kusantarta wata d'iya mace ba sai ita. Ita kad'ai yake so yake kuma buk'ata.
  Ya lumshe ido yana sakin ajiyar zuciya.
   Bintu kuwa har ta kammala komai ta bawa Hanif abincinsa tayi mishi wanka Ma'aruf bai fito ba. Ta gaji da zaman jira ta bar Hanif a hannun Sarah itama ta fad'a wankan. Har ta kammala ta shirya cikin doguwar riga d'inkin buba ta fito falon, shiru babu labarinsa. Hankalinta ya tashi, ta kasa daurewa kawai ta nufi d'akinnasa. Da sallamarta ta shiga, abin mamaki baya dakin, jin motsin ruwa ya bata tabbacin yana wanka ne. Hakan yasa ta fita. Saida ta kammala karyawa ta fiddowa Sarah keken Hanif baranda ta shiga turashi, ita kuwa zama tayi jugum har zuwa sadda ya turo k'ofar ya fito. Tasan yau babu aiki, to meyasa ya shirya cikin manyan kaya.
 Zama yayi a gefenta, duk yanda yaso ya nunamata yayi fushi, bai iya hakan ba, musamman ma ganin yanda ta ci ado, duk sai ya raina ajinsa, to ita d'inma hakanne a wajenta.
  "Fati." Ta narke fuska. "Nidai gaskiya ka daina kirani Fati."
 Yana murmushi ya jefamata tambaya.
"Why?" Ta turo baki "Sunan fa Mami ne, kacemin Bintu na yanda kwa ya sanni  da shi."
 "Ok, Bintuna, had'amin tea."

Ta dubeshi ido waje sai kuma tayi k'as da kanta don batason kallon da yakeyi mata, irin  kallon da Aisha ke gayamata a baya ta k'aryatashi, a yanzun kuwa ta gask'ata lallai akwai shi. Batayi aune ba ta ji ya tallafo ha6anta da hannunsa na dama kafin kuma ta ankara tuni ya soma mata  sak'o. Abinda ya keyi zai tabbatar ya mance a inda suke, wannan karon ba k'arfinta ne ya kwaceta ba sai wayarsa da ta dauki ruri.
   Alokacin ta ja gefe. Ya duba Abbansa ne, cike da girmamawa ya dauka. Abba ya hau fadan dadewar da yayi bai zo sun wuce ba. Ya bashi hakuri gami da mikewa, a tsaye ya kora tea din kadan sannan ya koma daki,  jimawa kadan ya fito cikin yadi maimakon shaddar da yasa a farko. Ta kauda kanta, yana murmushi yace"Saina dawo, zan fita da Abba. Ki shirya tarbata mai karfin mata goma."
  Ai a guje ta fad'a dakinta, ya fice yana dariya.       

 


 
(Nagode wadanda sukamin ya jiki, da ma wadanda basuyiba a rubuce amma sun kirani, da ma wadanda basuyi duka ba amma sun damu da hakan. Allah Yabar zumuncinmu..love oll)
[7/26, 11:45 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<45>>

Tana lek'ensa ta windo har ya bar gidan sannan ta sauke labulen gami da zubewa kan kujera tana dariyar farinciki.
  "Na sameshi!" Ta fad'a a fili kafin ta dauki ragowar tea din ta saita daidai saitin da ta ga ya sha ta hau korawa a cikinta tana mai lumshe idanu, wani irin  soyayyarsa na k'aruwa a ranta.
  Ta dire kofin bayan ta kammala, sai kuma jikinta yayi sanyi.  Baifa furta yana sonta ba?
 "Sannu bata hana zuwa." Ta ayyana hakan a ranta. Cike da nishad'i ta tattara kayan karin ta mayar kicin domin ji tayi gaba d'aya yunwarta ta kau.
  Ranar yini tayi da wani nishad'i marar misaltuwa. To shi d'inma hakan ce gareshi, don har Abba saida ya tambayeshi ko anyimishi albishir da aljanna. Dariya kawai yayi.
   Itama a ranar sunyi waya da Aisha, wacce shirye-shiryen biki ya 6oyeta don alokacin sauran watanni biyu da kwanaki. Nan Aisha ta sanarmata lallai a wannan daren tayi kokarin kyautatawa mijinta. Tayi shiri, irin shirin da tasan zaiyi saurin birkita tunaninsa.
   Sukayi dariya.
"Kinsan fa har yanzu ya k'i furtamin yana sona?"
  Tsaki Aisha ta ja.
"Kedai ki bada kai, wannan kuma sadda zai furta ma bakisani ba, kuma na gayamaki wallahi Yaya yana sonki. Ki bi dai shawarwarina. Na yarda zaki iya fin haka."
 Suka k'ara darawa kafin suyi sallama.
  Misalin d'aya na rana, ta dauki waya tayi kiransa kamar yanda Aisha ta gayamata. Saida ta kammala dariyar sunan (Angrybird) da ta sanyamishi. Saidai har ya kammala rurinsa baki d'aga ba. Bata sauke wayar data kunnenta ba sai gashinan ya kira. Ta shige d'akinta tana goye da Hanif wanda yayi bacci a bayanta.
 "Assalamu alaikum."
 Yayi sallama cikin tattausan muryarsa. Ta lumshe ido ta bude tana murmushi.
"Waalaikumussalam, Barka da rana Yaya."

 "Bintunaa! Ya dace a chanjawa Yaya suna, a k'ara mishi matsayi please."
  Tayi shiru batace komai ba, ya d'ora da fad'in.
 "To gayamin ya kike? Ina bebina?"
 "Lafiya lau, gashinan yayi bacci."

Ya jinjina kai kamar tana ganinsa.
"Masha Allah. Kinsan ina nake kuwa?"

 "A'a " "Gamunan tare da Abba munzo daurin aure Katsina."
 Ta zaro ido. "Katsina?"
Yayi 'yar dariya. "Hey, kin tsorata ko? Ba kwana zanyi ba ai, zanzo ki bani karfin mata goma."

 Ai tuni ta kashe wayar tana dariya, shima dariyar yayi cikin jin wani irin nishadi marar misaltuwa.   Bata motsa daga inda take tsaye ba ta ji shigowar sak'o. Ta bud'o.

 "Kina k'ara burgeni Bintuna, miss you! Ayi mana addu'ar dawowa lafiya."

 Ta karanta yafi sau biyar da wani, k'arshe ta zauna gefen gado tana cigaba da karatun. Wani sanyi ne takeji yana ratsa zuciyarta, wai kuwa dagaske Yayanta Ma'aruf d'inne kuwa? Wannan Ma'aruf din da suke yawan samun sa6ani har Mami kan kirasu mage da 6era?
Sai kuma ta ji tanason ba shi amsa.
   "Miss you too, Allah Ya maidoku lafiya YAYANA."

Ya saki ajiyar zuciya. Wai meke faruwa haka? Da ace ba gida guda suka task da Bintu ba, kuma baisan soyayya ba, zai iya rantsewa ko wani abin tayi mishi ya soma sonta har haka, irin son da babu wacce ya ta6a yiwa sai Ma'unsa.
       

Ita kuwa Bintu da wuri ta kammala ayyukanta don wajejan hudu na yamma   ya shaida mata sun taho. Ta k'ara gyara Hanif ta shiryashi cikin kana kaya marasa nauyi. Itama ta shiga da zummar wanka, ta zaro ido ganin abinda bata zata ba. Tayi shiru, ashe fa tuni aka shiga sabon wata. Hakanan ta hakura ta kimtsa jikinta ta fito.
  Batayi wani shiga mai birkitarwa ba kawai ta sanya yadinta marar nauyi mai hannu (3quater)  dinkin doguwar riga, saidai ya kamata.
  Haka ya dawo  gidan har da ledarsa ta kaza a hannu. Dariya ta ciyota alokacin da ta sanya hannu tana kar6ar ledar. Ya matso da ita.
 "Ya akayi?"
 Ta sunkuyar da kanta tana girgiza kai.
 "Bakomai." Tayi furucin a hankali.
 Yayi 'yar dariya. "Ashe inada maganin tsiwarki?  Lallai nayi sake a baya. Yau dai (the game will be over).
 Daga haka ya shige dali yana wani takun kasaita har batasan sadda tayi dariyar mugunta ba


(Kuyi maneji da wannan ..kuyi hkr wlh ba da son raina yake kadan ba.!!)
[7/27, 1:40 PM] ‪+234 806 038 4145‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<46>>

Bayan sallar Magriba, suna zaune yana wasa da Hanif ita kuwa ta dukufa tana zubamishi abinci kana ganin fuskokinsu kasan suna cike da jin nishad'i. Shi nasa na murnar yau zai samu abinda ya jima cikin tsananin so da bukata, yayinda ita kuma ya had'e mata biyu, ga hirar da sukeyi cike da nishad'i ga kuma na muguntar da Ma'aruf baisan da zamansa ba, har sai kuma ta ji ya bata tausayi.
  "Wai Bintuna duk me ya sanyaki wannan fara'ar?"
Ta dubeshi ta kauda kai tana murmushi.
"Bakomai."
Murmusawar shima yayi, zuwa yanzu ya gama fahimtar ita dinma tana sonshi, kawai dai jan aji ne irin na mata.
   
  Misalin goma da rabi na dare, suna zaune daga shi sai ita a falo, Sarah da Hanif sunyi nisa da bacci. Ta mik'e tsaye, ya rik'o hannunta wanda ta jishi har kwanyarta. Ta dubeshi, idanunsa a lumshe.
"Ina zaki?" Ya nemi sani da muryarsa wacce ta chanja sanadin tunaninta da ya fad'a.
Ta kuramishi idanu.
"Zanyi shirin kwanciya ne."

Ya saki hannun bayan ya sauke idanunsa akanta, ta kauda nata da sauri sai kuma ta shige.
 
  Bayan ya shirya ya sanya hannu ya dauki wayarsa ya kirata, tana gani ta k'i amsawa saboda wani nauyinsa da takeji.

Ta zubawa wayar ido yanata ruri, alokacin ne kuma ta ji shigowarsa dakin. Ta mik'e tsaye da sauri, sai kuma tayi k'as da kanta ganin ko riga babu a jikinsa. Ya dubeta daga sama har k'asa, sannan ya sauke ajiyar zuciya ganin irin shigar da tayi wanda shi kadai Allah Ya yarjewa gani.

"Meyasa bakya amsa kirana? Sai ma ido da kika zubawa wayar?"
Ta girgiza kai, baki bari tayi magana ba ya soma abinda ya matsu da shi.
  Har saida ta kaisu da zubewa a k'asa. Alokacin kuma ya d'ago ha6anta har numfashinsu na bugun hancinansu da sauri-sauri.
  "Tashi muyi sallah."
Shaf, ta mance da batun rashin sallarta sai alokacin. Ta lumshe idanunta, murya na rawa ta amsa.
  "Bani da sallah."
Ya saki ha6anta yana murmushi, duk a zatonsa wasa takeyi.
"Bari na gani."

Ya d'ago ya dubeta kamar yayi kuka, sai kuma ya mik'e ya fita kawai. Tausayinsa ya kamata, da kyar ta iya mikewa ta kashe fitilu ta kwanta. Babu jimawa da kwanciyarta, ta ji shigowarsa hakan yasa ta saurin rufe ido. Kwanciya yayi ya juyota jikinsa ya sumbaci goshinta.
  "Allah Ya tashemu lafiya."

Ta amsa a hankali. Cikin dare ya kasa saita kansa, haka yayita juyata son rai yana yanda yaso, kafin a karshe ya mike ya bar mata dakin. Ta bishi da kallon tausayi yanda yayi mata da kuma kalaminsa gareta har yana furucin bazai iya rayuwa babu ita ba.
  Ta lumshe ido tana murmushi a haka sabon bacci yayi awon gaba da ita.

Shi kuwa tun daga ranar ya rage ra6arta hakanan ya rok'eta da suturta jikinta duk sadda suke tare kada ya sa6a umarnin Mahaliccinsa.
   Idan kuma ya fita aiki, ta fita makaranta suna tare a waya, bini-bini ya kirata har itama ta saba da kiransa idan ta ji shiru. Baya dawowa gidan sai magriba, haka zasu zauna suyita hira, gaba d'aya yanzu ya sakar mata har ta daina kunyarsa. Hirarsu a yanzun ya bambanta da na baya don hirar soyayya ce da mutunta juna.
  Kamar dai a yau, tana kwance saman doguwar kujera tana lissafa kwanakin period dinta, a goben ne take da kwana bakwai cif wanda a kwanan zatayi wanka. Ta ji shigowar motarsa da tsayuwarsa. Saidai kafin ta motsa wayarta ta hau k'ara, ta dauka ta duba. Tayi mamakin ganin yayannata ne. Ta d'aga da sallama, ya amsa.
  "Ki fito, yau zance nazo."
 Abin ya bata dariya. Ta amsa da toh. 
  Dakinta ta shiga ta k'ara kallon kanta. Riga da siket na brown lace ne a jikinta, tayi kyau ya zauna d'as a jikinta. Ta k'ara feshe jikinta da turare ta murza jan baki. Mayafinta ta dauka marar nauyi ta yafa a kafad'arta, sannan ta zura takalminta mai tsini ta fita.
  Hanif na tare da Sarah a d'aki, bata bi ta kansu ba ta fita.

  Yana sanye da shadda sky blue, hularsa kuma dark blue. Dinkin boda, ya zauna sosai jikinsa, yayi kyau har ya gaji. Kafarsa d'aya ya tankwashe saman kujera, kansa kwance a kujerar ya zubawa hanya ido, a sannu kuma yana sauraron kid'an dake tashi a rediyon motarsa. Ido ya zubamata sadda ta fito tana wani irin taku na jan hankali, bata ganinsa sakamakon gilashin  ba haske, saidai jikinta ya bata ita din yake kallo. Yasa hannu ya bud'e mata gaban motar tun kafin ta k'araso. Ta shigo ta rufe. Tayi mishi sallama. Ya sauke ajiyar zuciya don baisan Bintu na da kyau haka ba saida ya soma sonta. Ya amsa yana tambayarta mutan gida
 Abin ya sanyata dariya.
"Wai Yayana menene haka?"
 Hannunta ya rik'o.
"K'ara'i, sonki ya sanyani Bintuna."
Ta zaro ido tana dubansa, baki ta6a cewa yana sonta ba, zataso a yau ya furta. Ya hura idanun.
 "Bakya sona ne? Yau fa baki zaki bude malama, hira ta kawoni, zan bayyana miki sirrin dake raina."

 Tayi farr da ido, ya kauda kai yana wani irin murmushi, ya kar6i wannan sak'on.
[7/27, 10:30 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<47>>

 "A baya, nayi zaton mace d'aya ce ta dace da ni, mace d'aya ta dace na mallakawa komai nawa. Nayi zaton yanda nake, ni d'in MIJIN MACE D'AYA ne, banyi aune ba, mutuwa tayi min YANKAR KAUNA da matar da na so na kuma fi sonta fiye da kowace mace a duniya."
  Ya d'an tsagaita kafin ya cigaba da magana.
"Na zo nayi biyayya bayan da na jajircewa zuciyata na yarda da KADDARA, na aureki."
  Ya k'ara matse yatsunta yana dubanta duk kuwa da cewar idanunta baya gareshi.
  "Bintun Mami, Bintun Ma'aruf. Kinsan me yafi had'ani dake?"
  Sai lokacin ta dubeshi ta girgiza kai gami da turo baki. Yayi 'yar dariya.
  "Bakya ji, na lura kina da fitina da tsokanar fad'a. Ba kuma sai na fad'amaki wanene Ma'aruf ba. Wannan shine ya kawo rashin jituwarmu. Kafin kuma na zo na had'u da jarabta ta sonki. Ban k'ara sanin ina sonki ba, sai bayan da na nisanta gareki har na kwanaki talatin da d'aya, zuwana Lagos kenan. Bayan na dawo nayi kokarin soma janyoki a jikina domin nuna miki irin so da kaunar da nakeyi miki a aikace batare da na furta ba."
  Ya d'anyi shiru yana mai cigaba da murza yatsunta, ta sauke ajiyar zuciyar tana kar6ar sak'on a sannu-sannu.
  "My Queen."
Yayi furucin da wata muryar da ta ji kamar ba ta shi ba.
"Ina sonki, ina kaunar na kasance tare da ke har abada. Kin shirya kar6ata matsayin miji kuma uba ga 'ya'yanki?"
  Ta sunkuyar da kanta k'asa. Gaskiya ne, da ba'ason zurfafa k'iyayya a addini, bakasan sadda zaka soma son abinda kake k'i ba.
  Ya d'ago ha6anta.
"A'a my queen, you have to answer me."
  Ta lumshe idanunta. Murya na rawa ta furta a hankali.
 "Na amince, ina sonka."
  Haka yayita aika sak'o kafin ya barta yana murmushi ya soma da bud'e kofofin.
 "Nagode my queen."
  Daga haka suka shiga ciki, ran kowannensu k'al.
  Ranar ma basu raba shimfid'a ba.

 Washegari kuwa da Magriba, yana shigowa ya risketa tana sallah a d'akinta. Ai baisan sadda ya washe hak'ora ba don farinciko sannan ya juya zuwa d'akinsa.
  Abincin daren nan dakyar ya ci. Ita kuwa gaba d'aya ta tsorata da yanda ya soma nunamata. Haka dai ta daurewa zuciyarta ganin ya riga ya gama matowa.
   A daren bayan sunyi sallar nuna godiya ga Mahaliccinsu yayi musu dogon adduoi.
       DAREN ALKHAIRI KENAN...!

                         * * *
  Kuka takeyi sosai, yana rarrashinta, dole tayi shiru ganin yanda duk ya bi ya damu kansa da kukannata.
   Da kansa ya taimaka mata ta tsarkake jikinta kafin ya barta ta k'arasa.
   Ranar ya tsinci kansa da wani irin farinciki marar misaltuwa. Lallai Allah Ya mishi babbar kyauta, a yau gashinan ga madadin Asma'u. Yau shi ya taimakawa Sauda da d'awainiyar gidan, ita kuwa kunya ce ta hanata fitowa ma.
  Tana jin shigowarsa d'akin tayi saurin ture kanta k'ark'ashin filo. Ya k'arasa yana dariya ya hau yi mata cakulkuli, babu shiri ta hau dariya gami da ture filon.
  Ya sumbaci goshinta, ta lura yanason yin hakan kafin ya kwanta ya soma yi mata wasu nauyayyun zantuttuka acikin kunnenta.  Zata mik'e cikin zafin nama ya janyota, tayi narai-narai da ido, kwalla suka cikamata idon.
  "Don Allah kayi hakuri."
 Ya kwaikwayi muryarta.
 "Don Allah ki nunamin karfinki na mata goma."
  Ai sai ta tura kanta jikinsa tana dariya. Yayi mata kyakkyawan runguma.
                    * * *
  Acikin wannan satin, ba'a cewa komai. Da ka gansu kasan suna cike da more rayuwa babu wata matsala a gabansu. Sai gashi wata muguwar shakuwa ta daban ta shiga tsakanin Bintu da Ma'aruf wanda ta bawa kowa mamaki.
  Akwai sadda da yamma suna zaune gaba d'aya a falon Mami ana hira har Hashim da Sally wadanda suka kawowa Mamin ziyara, lokacin sauran kwanaki biyar ya rage bikin Aisha.
  'Yar kwarewa Ma'aruf yayi, nan da nan Bintu ta rikice ta mance a inda suke ta hau shafa bayansa tana mai mik'a mishi ruwa. Cike sa tausayawa tace. "Sorry my king."
  Ya amsa, gyaran muryar da Rufa'i yayi ta farkar da su. Mami dai kauda kanta tayi kawai tana murmushi, yayinda Rufa'i da su Hajara suka sanya dariya. Ma'aruf ko a jikinsa sai ma ita Bintun ce ta dan ji nauyi.
 "Oh, Allah Hakim, yau 'yar Mami ce ke wannan rikicewar akan abin gudunta? Soyayya lallai tana dadi
"
  Mami ta mike don sai alokacin ta ji kunya. Daman ita Bintu ke kunyar, ai kuwa tana bada baya ta dubi Yaya Rufa'i.
  "To meye? Wasu ma suyi mana."
 "Lah, ni kike gayawa haka? Eh lallai, kinmanta sadda yake bulale ki nake yare miki? Aisha kinga halin d'an adam."
  Bintu na dariya ta zauna gefen mijinta wanda ke sauraronsu da murmushi dauke saman fuskarsa.
  "To ai bulala ce ta soyayya, yanzu ba gashinan tayi rana ba, ai hakane ko my king?"
  Suka tuntsire da dariya har Ma'aruf din.
 
 "Yes my queen, ashe kingane. Ku dai ku rike girmanku ba'a shiga tsakaninmu da queen, ko harshe da hak'ori ma haka suka ganmu suka kyale. Ato."
  Dariyar aka k'ara. Hashim ya d'ora da fad'in.
 "To d'an iska, dadin abin dai..."
 "Ya isa." Ma'aruf ya dakatar da shi ta hanyar mik'ewa yana dariya gudun kada yayi mishi iskanci.
  "Malam tashi muje ku gaisa da Abba."
 Haka suka wuni cike da jin wani irin annashuwa.

                         * * *
      BIKI BUDURI....!

((SAIRAN POST DAYA KO BIYU IN SHA ALLAH..!)
 

 
 
 
 
[7/28, 7:00 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<48>>

  A yau ake bikin sanya Aisha a lalle. Wannan yasa gidan nasu yake a cike da 'yan uwa, cikinsu kuwa har da mutanen Rano. Wannan karon har Umma abokiyar zaman Inna itama ba'a barta a baya ba wajen halartar bikin autar Mami.
   Bintu babu zama, sune wancan babban shagon na kayan kicin, sune acan shagon gyaran gashi.
Ya zamana ta dawo gidan da zama, duk yanda Ma'aruf yaso hanawa bai samu hakan ba kasancewar ta samu daurin gindi wajen Mami.
   A daren da akayi kamun Aisha, suna zaune a can d'akinsu tare da su Atika harma da Hafsa kanwar Ma'u wacce itama takanas ta zo kwana adalilin mijinta yayi tafiya, kasancewar gidansu basu da sa ido ballantana har abin ya zama wani babban al'amarin da zai shafi ZUMUNCI A YAU.
   Sai hira sukeyi suna kyalkyala dariya. Rabin hirar kuwa Atika ke basu akan matar saurayinta. Yanda yake bala'in shakkar daukar koda wayarta a gaban matar.
   Wayar Bintu da tayi k'ara ya sanyasu dubanta suna tsokana.
"Toh sarakan soyayya."
  Ta murgud'a baki tana dariya kafin tace suyi shiru ta d'aga da sallamarta.
  "My king, fatan dai ka bar fushin?"
"Idan kinaso na daina, zo ki sameni anan d'akina. Ta zaro ido.
"Lah, baka tafi gida ba? Karfe goma fa " Yayi 'yar dariya.

  "Kina wasa, ai na gayawa Mami saidai nima na kwana a gidannata."
  Ta hadiye dariyarta, suma tasu suka gimtse don kuwa a hands free wayar take.
  "Allah Sarki My King, shikenan ai, da safe Dan dolo sai ya mik'o maka kayan karinka. Allah Ya tashemu lafiya."
  Ta kashe wayar gaba d'ayanta, me zasuyi banda dariya. Aisha ta d'akamata duka a cinyarta.
"Wallahi kina daukar alhakin yayana, kinsan dai abinda yake nema."
  "Ai idan batayi hakan ba, babu mai kiranta da Bintu." Cewar Hafsa cikin dariya.
  Ta zaro ido.
"Lallai ma, kunyi zaton nima ina iskanci ko? Ba abinda na iya."
  Sukayi dariya. Kasancewar basusan labarin ba yasa Aisha fesa musu. Ai kuwa nan sukayita tuntsire dariya. Ranar kwanan farinciki sukayi, ita kuwa tana sane ta k'ular da Ma'aruf.
  Har washegari daurin aure da yini, babu abinda ya sake hadasu, koda tayi kiransa a waya sai ya k'i dauka. Hakanan ko sun hadu d'akin Mami bai ko kallonta. Jikinta yayi sanyi, da kanta ta soma neman shiri.
  Don haka ana ta shirye-shiryen tafiya dinner, itama ta shirya cikin ankon da sukayi kalar pink, ta ci ado har ta gaji da haduwa, jikinta babu dadi, daurewa kawai takeyi don tana bala'in son zuwa fatin.
  Ta dubi Aisha,
"Kuna iya tafiya, kinsan ni tare da King dina zan taho."
Sukayi murmushi kafin ta fita zuwa sashensa na gidan. Saidai yayanta Saifu ta iske, shi  ke sanarmata yana can gidansa. Haka Mami ta saka aka kaita don ta tafi kafe saidai su tafi tare.
  Da shigarta ta iskeshi saman doguwar kujera a kishingide yana amsa waya. Sam baiji shigowarta ba, ta karaso da sallamarta, alokacin ya ji ya amsa saidai bai ko dubeta ba. Ta zauna da sauri sanadin jiri-jiri da ke kwasarta, jikinta yayi zafi, ta tuna rabonta da abinci tun wajen k'arfe d'aya na rana da ta ci.
   Bayan ya kammala wayar ya mik'e zaune. Sai lokacin ya dubeta, tayi mishi kyau kwarai. Ya yi kamar bai ga kwalliyar ba ya kauda kansa. Ta marairaice fuska gami da mik'ewa tsaye. Babu shiri ta soma kokarin zubewa awajen, da azama ya tarbota.
  "Lafiya?" Ta soma kukan shagwa6a.
 "Kaine kake fushi da ni, duk ka tayarmin da hankali."
  Ya dagota.
"Abar wannan maganar, jikinki fa da zafi, kin kuwa ci abinci?"
  Ta girgiza kai. Ya mike yana fad'in "Ina zuwa."
  Ta kwanta a saman kujerar tayi lamo tana tunanin yanzu watakil ansoma shagalin fatin.
  Can sai gashinan ya fito cikin kananun kaya. Ya dagata zaune yana jan tsaki.
 "Wannan kayan ma ai k'arawa kanki wani nauyin ne Queen."
  Zai ragemata ta nok'e har da hawayenta.
 "Nifa wajen Dinner na biyo mu tafi."
Ya zaro ido.
 "Kina a wannan halin? A'a muje dai na nema miki abinci sai mu wuce asibiti."
  Ya nace, itama ta kafe harda kukanta, ya zaayi ma bataje dinar nan ba bayan ta ci buri akansa? Haka ya amince suka tafi, tayi-tayi ya chanja kaya ya k'i. Ta lafiyarta yakeyi.
   Yaso su soma zuwa asibitin, ganin haka nan da nan ta mike ta daure tace ita fa ta samu sauki daman yunwa ce.
  Ya girgiza kai kawai. Bintu akwai k'arfin hali.
  Sun shiga yana rik'e da ita har mazauni. Bayan sun zauna, ya sanya aka kawomata abinci tun kafin ma a soma ciye-ciye. Ta ci tayi nak ta ture, sai lalla6ata yakeyi, sun burge mutane da yawa musamman sarakan soyayya, wato 'yan ROF whatsapp.(lol).
  Fauza kasa jurewa tayi ta isa wajensu ta daukesu hoto, tana fatan kasancewa da habib dinta haka wataran. Sally ta k'ara kankame hannun Hashim dinta a kunne ta radamishi. "I love you." Shima ya ji sanyi, don soyayyar abokinsa da Bintu na burgesa.
  Ba'a je ko'ina ba ta soma shek'a amai. Hankulan mutane ya dawo kansu, Ma'aruf ya ja ta sukayi waje,  ma'aikatan wurin suka gyare wajen tsaf aka cigaba da shagali kowa hankalinsa yana ga Bintu. Ko meke damunta?
  Kai tsaye shi kuma yana kaita mota suka nufi asibiti harda Atika wacce yasa ta hau su je.
  Likita ya aunata ya buk'aci fitsarinta, ai kuwa result ya nuna tana da ciki. Hamdala kawai Ma'aruf yayi ta yi har suka fito hannunsa cikin nata.
  Suna shiga mota ya sumbaci goshinta. Hawaye suka zubomata na farinciki.
      Nan dai zance ya cika gidan ta bakin Atika cewar Bintu na dauke da juna biyu.
  Kowannensu ya hau murna, Bintu bata da masaniyar wainar da ake toyawa don yayannata cewa yayi gidanta zata kwana ta huta.
   Har aka kai Aisha babu inda ta fita, Mami ma ta goyi bayan Ma'aruf a wannan karon.
                      * * *
      SANNU BATA HANA ZUWA...!
[7/28, 9:29 PM] ‪+249 99 842 9948‬: ¶°°BINTU°°¶

      ©Rufaida Omar
         (July...2016)

<<49&50>>

A yau har ga Bintu ta cika watanni tara cif dauke da cikin bebinsu da Ma'aruf. Sai kuma a wannan lokacin ne ta shiga damuwa sosai, ba na komai ba sai na tsoron haihuwa. Sau da yawa Mami ke kwantar mata da hankali don tuni ta komo gidan Mamin duk kuwa da ba da son ran mijinnata ba wanda yaso ta zauna gabansa ta haihu.
  Takan ce, tana tsoron mutuwa kamar yanda Ma'u ta rasu. Ma'aruf da zarar ta soma zantuka haka har ma ta hau rok'on gafararsa, sai ya ji hankalinsa ya tashi, akwai sadda ya zubda hawaye yana rok'onta akan ta bar sanyamishi damuwa.
  Haka dai har wata ranar litinin da daddare nak'uda ta taho gadan-gadan. Babu shiri Mami ta kwasheta sai asibiti. Cikin ikon Allah, mintuna baifi arba'in ba da zuwansu, ta haifo d'iyarta mace santaleliya.
  Ma'aruf wanda ya zo tun wayar da Mami tayi mishi, suna tare da Mamin a tsaye suka ji kukan jaririyar. Sai kuma nos ta fito ta sanar dasu haihuwar.
"Ya lafiyar uwar?" Shine farkon abinda Ma'aruf ya nemi sani. Hankalinsa ya kwanta jin tana cikin koshin lafiya.

   Murna kam ba'a cewa komai, washegari haka yan uwa sukayita zuwa gidan Mami don a washegari aka sallamesu.

Abinda ya burge Ma'aruf ga Bintu, bai wuce ganin da kanta ta nemi a sanya sunan Ma'u ba, shi kam ya so sanya sunan Innarta. Haka nan aka yiwa yarinya hud'uba da Asma'u suna kiranta BINGEL(lol).
                       * * *
         BAYAN WASU SHEKARU...!


Barrister Fatima Bintu bakinta ya k'i rufuwa adalilin yau ake bikin yayesu daga makaranta. Tana rik'e da hannun Hanif da Bingel ta rungumosu Yaya Rufa'i ya daukesi a hoto. Ta k'arasa ta sumbaci goshin bebinta Amir mai sunan mahaifinta Muhammad dake rik'e a hannun Abida sabuwar 'yar aikinta. Nan ma ta kar6eshi akayi musu hoto, kafin ta k'arasa ta rungume Maminta tana hawayen farinciki.
  "Yau ga Bintunki ta fito a yanda kikeso, I am now a Barrister.'
  Sukayi dariya, itama Mamin ta sharce hawayenta na farinciki.
"Allah Shine abin godiya."
Sukayi dariya. Ta janyo Aisha wacce ke rik'e da d'anta Mustapha suka had'u suka sanya Mami a tsakiya aka dauki hoton.
  Daga bisani kuma gaba dayansu har Abba suka dauka. Bintu ta cika tayi fum saboda rashin zuwan Ma'aruf akan lokaci. Har da hawayenta. Koda Abba yayi niyyar kiran wayarsa, hanawa tayi.
Har suka bar wajen suka dunguma zuwa gida babu shi da labarinsa.
   Ganin an nufi gidan Abba bata damu ba ko kad'an, fushin da takeyi da mijinta yasa ta yanke koda kwana ta kama ta kwana anan ba zata k'i ba.
  Saidai ta cika da mamakin yanda aka faka motoci a kofar gidan, su d'inma anan sukayi fakin suka fito cike da mamaki tattare da su.
  Fitowar Saifu yayan Bintu dauke da d'ansa a hannu ne ya basu mamaki. Ya gaidasu Abba da fara'arsa, baice komai na daga tambayoyin da suke mishi ba yayita musu iso zuwa ciki.
    A babban falon na Mami suka tarar da mutane cike, Ma'aruf na tsaye gaban wani k'aton cake yana kunna kendir. Ya dago ya sakarwa matarsa murmushi, tuni dukkan wani 6acin ranta ya gushe.
  Nan fa bakin kowa ya gaza rufuwa ana ta murnar ganin juna.
  Bayan Bintu ta yanka cake tayi kamar zata sanyawa Ma'aruf sai tayi azamar turashi bakin Hanif, akayi dariya.
   Duk da iyayen dake a falon, baisa yayi dabarar yi mata magana ba.
"Ina sonki fiye da kullum. Babbar kyautarki shine, na biyamiki umrah."
Ta dago dara-daran idanunta ta dubeshi tana dariyar farinciki. Da ace akwai hali da ta rungume mijinta, kawai sai ta soma fidda hawayen farinciki tana dubansa. A haka Rufa'i ya daukesu hoto ana dariya.

       TAMMAT BI HAMDULILLAH

 Inda mukayi kuskure a gafarcemu. Nagode sosai yan uwana masoyana, shakka babu kun nunamin kauna, fatana Allah Ya hadamu haka a aljannarSa. Amin.

Godiya ta musamman ga Ummu Abdool, Bingel. Kun zamo wasu jigo a rayuwata, Allah Ya bar zumunci, amin

Ban manta 'yan ROF na Facebook da whatsapp, wlh ina kaunarku!

 Sai: DDM, DM(ciwon ido kenan), HDY(Abin Tunk'ahona), Fikrah Writers Association. Dss.

Da duk masoya masu kirana dain text, da kurame masu karantawa babu magana, fatana dai su tsinci sak'onnin..lol. Nagode gaba d'aya.
  Sai Allah Ya had'amu a goron babbar sallah in sha Allah...!
       ((RUFAIDA OMAR IBRAHIM M))


adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *