JARABABBEN KISHI part 9
Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:08
Ayau Sha Tara ga watan November Wanda yayi
daidai da ranan asabar ne, Dubban Mutane ciki
harda "senator na kano central", suka halacci
daurin auren *Suhayr kabir sulaiman da Angonta
Saheeb Garba Dan'koli* Bikine na manya bikine
Wanda ya amsa sunansa biki. Ba ai wani event
ba saboda suhayr tace bata iya jure kallon da yan
mata zasuyi wa mijinta ba, walima kawai akayi
bayan daurin aure. 'Suhayr tayi kyau dukda ba
wata kyakkyawa bace amma dayake ance ko
amaryar buzuzu ce ranan bikinta kyau takeyi,
Badon farar fataba inajin dasaidai akai kasuwa,
Suhayr gajerace badai sosai ba sannan tanada
idanu Wanda zamu iya kiransu da sexy eyes,
bakinta Dan karami Dan das, tanada jiki Wanda
bazamu iya kiranta da siririya ba, Saikuma hanci
kwarai batada hanci amma tanada kara. Da
misalin karfe Tara na darene yan daukan amarya
suka hallaro Domin daukar amaryarsu, motaci
uku ne Golf guda biyu sai wata space wagon
guda daya. Ga dunbin jama'a yan rakiyar amarya
kowa sai tofa albarkacin bakinsa yake Itako
suhayr fada ake mata sosai Wanda ko wacce
uwa takeyiwa yarta inzata kaita gdan miji. Ciki
harda fada akan jarabebben kishin data sawa
kanta, "Hjy ikilima ce ke magana da kakkausar
murya: "suhayr kishi a jininmu yake Kuma Allah
ne ke halittan kowani bawanda dashi, amma
saiyasa nawani yafi na wani Karki kasance me
nuna kishinki a fili yata ki sassauta kishinki, don
kishi ba hauka bane Wallahi indai kikayi koyi dani
toh tabbas suhayr zaki zama yar gaban goshi a
gdan saheeb". kuka suhayr keyi Wanda saida
tasa kowa na wajen kuka Wanda zan iya cewa
kukan yazame ma kowacce amarya al'ada,
dazaran zaa kaita gidan miji ta dinga kuka
saboda tunanin ta rabu da gida yan uwa da
abokan arziki, kenan saidai ziyara. Mahaifinta
shima yayi mata fada kwarai me shiga jiki. An fito
za'a sata a mota bawata mota mai tsada tanajin
abunda ake cewa Amma bataji komaiba illah
kosawa datayi akaita gdan saheeb, Acikin daya
daga acikin golf din akasa suhayr sai yan uwan
hjy ikilima, Dana mahaifinta suka cika sauran
motacin biyu..... Don ba kawa ko daya data shiga
motar kai amarya daman tun asalinta suhayr
daman bamai jaye jaye bace. *Ankaita gdanta
dake zooo road kowa ta watse saboda mahaifinta
yabada umurnin kar Wanda ya kwana," daga
suhayr sai saheeb aka bari acikin gdansu*
~Kubiyo yar mutan zazzau kuji labarin zaman
auren saheeb da suhayr shin wace waina zasu
toya ?????????gadaishi kowa ya watse ?KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 10 JARABABBEN KISHI part 10 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:11 A Daren yau hankali ya kwanta, suhayr taxama mallakin saheeb, "Suhayr ayaune zamu kafa tarihi a rayuwar mu, yaune muka kasance ma'aurata," Kunyarsa suhayr keji Wanda abaya ba haka takeji akansa ba. "Tashi muyi sallah ko?" Cewar saheeb Wanda farin cikinsa yakasa boyuwa, "toh" tace. Alwala suka dauro suka gabatar da sallah da godiya ga mahaliccinsu, Wanda ya kawosu zuwa wannan lokacin. Sun danyi ciye ciye daga bisani Suhayr ta tashi tahau gado ta kwanta a tsorace don tasan Daren yau shine Daren farko dazata kwanta gata ga namiji Wanda a yanzu shine annurin zuciyarta. Tuni bacci yayi awon gaba da ita, saida saheeb ya kammala ya tashi ya matsa kusa da ita yana mata rada a kunne "cutey kitashi ki cire wannan kayan kinsan sunada nauyi zasu hanaki bacci". Tashi tayi tana cewa "Umma Dan Allah ki kyaleni kinsanfa nagaji dayawa," tana bode Ido saitaga Ashe saheeb ne. Ya mata murmushi rungumeta yayi yace "yar umma daga yau kindaina kwana da umma", dariya tayi tace "hakane saheeb sabo ne kawai kasan bana iya bacci saida umma," 'Saheeb yace "gashi yau xakiyi bacci ba tare da umman ba" dariya sukayi duka, tashi tayi ta dauko kayan bacci tasa amma fah saidata shiga cikin toilet saboda kunyarsa data keji. A Daren yau saidai muce Alhamdulillah saboda saheeb ya cimma burinsa akan masoyiyarshi, Ya maida mugun yawunsa "Assalatun farko saheeb yatashi yayi wanka ya fita zuwa masallacin dake kusa dasu, Bayan yadawone yatadda Suhayr kwance sai faman kuka takeyi, Wanda hakan yaba saheeb tausayi, saboda yasan cewa yayi laifi. Amma hkr yaxama wajibi daman haka auren ya gada, haka ko wacce mace tayi going through. Daukanta yayi cik yakaita toilet ya hada mata ruwan zafi, yataimaka mata ta gyra kanta, tagabatar da sallah. Suka koma suka kwanta farkawa tayi ta shiga kitchen don ganin abunda zata iya dafa musu, Amma taga wayam hakan bai bata mamakiba saboda tasan mijinta bashi gareshi ba. Wani corner ta leka taga kayan garanta daki guda nan tafara tunanin abunda zata samfara amma babu kayan hadi, Tana cikin wannan nazarin ne taji ana knocking kofa, Budewa taje tayi Ali direba tagani yace ina "kwana uwar dakina ya bakon waje?," "Lafya" tace, yace "Daman hjy ce tace in kawo muku abinchi". Tace "shiga dashi mana," Coolers ne na abinchi ya shiga dasu ciki ya a falon. Juyowa yayi yace "sannan tace kiyimun lissafin abubuwan dakikeda bukata yanzu kasuwa nayi" tace "toh" sannab ta lissafa komai a littafi ta rubuta ta mikamai ya tafii. Tsayawa tayi tana tunanin irin sonda iyayenta ke mata, abunda iyayen saheeb ne yaka mata suyi mana wannan hidimar amma sai gashi umma ce dakanta, Duk yanayin da suhayr take ciki saheeb na kallonta. Jitayi an dafata da sauri ta juyo tace "my life sannu da tashi". Sam bata nuna mishi a wane hali takeba, "Suhayr tunanin me kikeyi?" Ya fada yans kallonta. Tayi saurin cewa "Lah my life ba komai kawai tunanin yadda zan faranta maka rai nakeyi". Dariya don yasan kwaskwarima tayiwa kala manta, tace "Kaji mijina muje dinning kaga abunda umma ta aiko mana dashi tace muhuta karmu dafa komai". Daukanta yayi suna dariya cikin nishadii da kaunan juna, Sunci sunyi kat suka koma falo suna kallon Indian film.KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 11 JARABABBEN KISHI part 11 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:14 Bayan wata biyu, suhayr ta kasance mace mai kiyaye duk wani hakkokin mijinta babu abin da ya nema ya rasa daga gareta, matsalarta daya a duniya kishi bata son kishiiya kuma bata kaunar duk wata mace ta rabeshi hakan yasa ta roki alfarmar mahaifinta ya bashi kudi ya ja jari ya bude shagon sai da hula da agogon maza, domin bata son yayi "white collar job" Da hakan zai kawo cudanyrsa da mata ko da kuwa yan uwanta ne bare Kuma nashi. kyawawan dabiunta da kuma son da ta ke masa yasa ta samu love dinsa 100pecent domin duk wuya duk dadi tana jurar yi masa komai, Tana zaune a falo taji ana knocking ta miqe taje ta bude kofar taga wasu yan mata kyawawa, sunsha mai da foundation, kallonsu takeyi shekeke Wanda haka yaba nimrah haushi tace wai ko baki ganeni bane?". Suhayr balla ma nimrah harara tayi tace "mekikazo yi gdana da wayannan masu kama da aljanun?" Suhayr ke magana cikeda isa sa fankama. "kut gaskiya nimrah matan wannan naki batada mutunci mine ma masu kamada Aljannu?" Suhailah ce ke magana tana taunan cingam. "Suhayr magana muke kina kallonmu", Dariya tayi tace "inajiran inji dukane saboda Nace muku masu kamada mami water". "Ke !!!!" Nimrah ce ta dakawa suhayr tsawa "dakata kiji karki ga kinama sauran mutane insunzo gdanki kice zakimun, danni nafi karfin yinki wallahi saidai inyida gyatuminki". Suhayr ce tace "Habawa Nimrah kinso ki tafka babban kuskure wajen tabamun iyaye Wanda nasan sunfimun naki iyayen sau miliyan, ai kinsan bakin rijiya ba gurin gadar makaho bane, Nimrah kafin inbude idona in rufe ki fitarmun da wayannan masu kamada yan ruwan inba hakaba I will surely sure you gals mah true colour". Nimrah tace "Aikam da wuya yau inba'a haifi da Mara Ido ba" inji nimrah Wanda ta runtse Ido bataji bata gani, don tsabar takaicin abinda Suhayr tsyi masu. "Mai gadii John" Yayi saurin shigowa yana cewa "yes mah hjy lafya irin wannan kira". Cikin bacin rai Suhayr tace "How many times have I warn you that I don't want to see any lady in dis house apart from my mum? Haven't I warn you?" John jiki na rawa yace "yes mah," "oya before the count of three I don't want to see any of this things infront of me". Da duka john ya rakasu ammafa nimrah baki yaki mutuwa "cewa tayi "yau kin nunamun gida nakine Suhayr amma saikinyi ladaman cimun mutunci shegiya yar matsiyata." Ciki ta koma ta harde kafa Ashe saheeb nanan suhayr ke cima nimrah da friends dinta mutunci, "Hayaniyyan me nakeji suhayr?" shuru tayi kaman bada ita yakeba can ta dago ts kalleshi tare da cewa "Pls saheeb ka gayawa kanwarka, nasa mata boundary da gdannan". Shima cikin bacin ran yace "kozaki iya gayamun dalili?". Tace "Dalili shine zan iya raunatata inta kara shigomun da kawayenta, masu suffan jinnu gdannan, Akan mema saitaxo gdannan nifa banason shisshigi ka gaya mata," Saheeb ne ke zaune kusa da ita yace "suhayr nimrah kanwata ce kiyi hkr da abunda zan fadi Nimrah nada ryt din zuwa inda nake". Tayi saurin dakatar dashi da cewa "dakata Saheeb inada kishi da banaso kayi tozali dawata mace inba niba, don haka ta kiyayi gidannan, don ko jaririyace ina matukar kayi mata murmushi bare baliga kaman nimrah." Yace "Amma dai kinsan nimrah muharramata ce?". Tace "Koma me CeCe nagama magana" tashi tayi tashiga daki. A ranan ya shiga wani hali ummansa ce ta kirashi tacimai mutunci, sannan da sharadin saiya kara aure ko yana so ko baya so.Home / JARABABBEN KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 12 JARABABBEN KISHI part 12 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:34 Tunani mai zurfi ya shiga amma bashida yadda zaiyi, Suhayr ta hanashi mu'amala da mata harma da yan uwansa, Gashi saheeb yana matukar kaunar matarsa bayason yaganta cikin damuwa, bayason ganin bacin ranta, Amma yana mamakin kishi irin nata, inda za'a bashi littafi da Biro tsaf saiya rubuta kishin suhayr gaba daya. Saheeb Yakama sana'a ba kana hannun yaro acikin manyan plaza dake kan hanyan Hotoro. Dayake wajen center ne inda manyan mutane ke wucewa, Gaba daya kayansa na wajene saidai kayan gida kaman su shadda, huluna, dadai sauransu. Amma fah koda yaushe akan waya sukeyi da sahibar tasa wato suhayr, arana saita kirashi fiye da sau talatin, saboda kishi dake dawainiya da ita Amma hakan bai hanashi yin budurwaba, Daman masu iya magana nacewa duk wayon amarya sai ansha manta, Haka shure shure baya hana mutuwa. Ranan yatashi da wuri daga shago ya kashe wayansa, saboda yanaso yaje family house dinsu ance ana Neman sa, don yasan inya gayawa suhayr saitasan yadda tayi ta hanashi zuwa, adaidaita yahau sai dorayi, Yana shiga aka yimishi cha mijin hajiya! Mijin hajiya!! Mijin hajiya!!!. Yadanji kunya kwarai amma ya maxe Yaga dangi kowa ya hallara abun yayi matukar razanashi, Zama yayi ya gaidasu, "yauwa saheeb abunda ya taramu anan shine gameda matarka suhayr Data hanaka sakat saboda kana zaune a gdansu sannan Kuma tabaka jari". Inna larai ke magana shuru yayi baice kala ba saboda yasan daman za'a Rina, "Dalilin taruwanmu shine munaso ka kara aure". Zare Ido yayi yace "aurefa kukace? Dan Allah karkuyimun haka dududu watanmu nawa da aure zaa kawomun zancen wani aure yanzu Haba Dan Allah kucanza wata shawarar amma ba wannan ba". Ummansa dake gefe tace "dole kayi aure don samun kwanciyan hankali". Bashi da yadda xaiyi dole ya amsa masu ba don xuciyarsa na so ba, a haka yakoma gida cikeda tunani iri daban daban, ta ina ma xai fara sanar da Suhayr wannan xancen?. Da shigarsa yaji kakarin amai da sauri ya yadda ledojin dake hannunsa, Da gudu ya shiga toilet suhayr yagani tafita hayyacinta. "Subhanallah cutie meke damunki haka"? Bata iya bashi amsaba, illah hawaye dake tsirarowa daga idanunta "Saheeb zan mutu ka kaini asibiti". Mota ya dauko yasata suka wuce asibiti. Likitane yace ashiga da ita, amma suhayr dukda ciwon da take bata sassauta kishinta ba, gam ta rike hannun saheeb tare suka shiga anyi mata test kusan kala uku, " congratulations yallaboi madam tana dauke da ciki wata biyar". Saheeb yayi saurin cewa "Likita wata biyar fa kace ya akayi bata saniba Kuma nima haka?" Likita yace "Tana iya yuwuwa inna farine baxata ganeba,haka kaima, amma ya kamata a kula da ita sosai musamman ma abinchi, tadinga cin kayan marmari irinsu zogale dama dai sauran kayan Karin jini A yanzu bata bukatar motsa jiki saboda Dan bai rigada yayi kwari ba". Murna wajen saheeb sai Wanda yagani don ji yake kamar ya hadiyeta don murna.KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 13 JARABABBEN KISHI part 13 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:36 An sallamesu, hjy ikilima musamman taxo don ganin yartata, Sunsha fira tsakanin ya da uwa tuni aka fara siyayyan kayan ahaihuwa. BAYAN WATA Uku ne lokacin cikin Suhayr yana wata na takwas, Dangi fah sun tashi haikan ganin saheeb yakara aure, Domin sunce suhayr tayi musu Kane Kane gashi yanzu arziki yaci uban Nada, sai a cika gida da iyali, Saheeb yafara Neman aure gadan gadan, amma duk abunda yakeyi suhayr bata saniba, Har ansa ranan wata uku duk ya maidata biri boko, makota tashi ga saiga wata mata tashigo, tana cewa, "ke ummu aiman Ashe makocinki aure zaiyi? Duk kishin da ake cewa matarsa nadashi". Ummu aiman sai siginal takewa indo amma itako sai zuba takeyi, Saidata gama tsaf suhayr taji wani irin ciwo na naman cin karfin ta tace,"Baiwar Allah kozakimun kwatancen gdansu yarinyar?". "Kwarai maizai hana". Inji indo. Nanfa indo tayita mata kwatance harta gane. "Ngd" tace tashi tayi taje gda, tace "yau saiya gane cewa, ruwa ba sa'an kwando bane, sai ya gane shayi ruwa ne saina nunawa saheeb cewa yayi kuskure namiji munafiki, ni xai munafurta? Ya qara aure? kabashi dukkan yardarka yacima amana". Gyale kawai ta chanja ta nufi Gidansu yarinyar tayi sallama da uban yarinyar, cike da mamaki ya fito yana kallon Suhayr. Tace "naji labarin cewa, zaka aurawa mijina yarka? toh Kasani yarka zatayi kwanan prison matukar tace zatayi kishi dani, Don saina aikata inda baxata kara jin kamshin mijina ba, sannan inkun shirya yarku tazo gdana, toh Ku kawota na nikafali, don sainayi ajalinta". Uban yarinya yace "aikin banza, kewacece? Aikam saimunyi Shari'a dake har yaumut tanadi". Suhayr tace "Mune gwannati kaje ka tambaya waye Alhj kabir sulaiman inajin kasanshi, toh nice diyarsa daya tilo, Inyazo shi mijin nawa kace yaci gaba da Neman aure nikuma, inci gaba da rusamai tsari". Tura cikinta tayi ta shige mota ta badamai kura, Uban yarinya yace "tab ai aure anfasa, baxai iya da wannan ja'ibar ba Daganinta zata aikata duk abunda tace. Saheeb yaje zance uban yarinyar Yace "karya sake zuwamai gida saboda matarsa taxo tayi barazanar kashe musu ya". Gda yadawo cikin bacin rai ya iske Suhayr yace "Suhayr hankalinki ya kwanta kin raba abunda Allah yahada, Tun kafin muyi aure kike abu daya haryanzu kinki ki daina". Tanadaga zaune tace "kamanta dakwai ranan danace ka kalli kwayar idona? nacema maika gani"? Kacemun *JARAB EL GHIRA? Flames of jealousy?* Toh I can do more than wat you are thinking saheeb, Bantaba Sanin cewa kai munafiki bane sai yau butulu kawai Wanda ke manta alkhairi, Bacin so baya dubi da nasaba da chanchanta, Yaushe zan aureka Saheeb? Amma shine zaka zaga bayana kaci amanata? Kayi hkr da kalamaina, nasan kai mijinane, dole infadi Nasan duk umma ce kesawa ka kara aure, Kuma Wallahi Allah ya saukeni lafya, sainaje har gdan tagayamun dalili, Inace ita kadaice wajen mahaifinka? Ohh shine saboda kiyyaya zatasa ka kara aure toh zan gani, Ga fili gamai doki Saura sukuwa". Mari taji ya sauka a kuncinta, "Karki sake yima mahaifiyata cin zarafi a gabana inke bakisan darajar iyayeba Toh ni nasani Kuma aure ba fashi sainayi Kuma ra'ayinane, bana umma ko Abba ba, Saina cika gdannan da zuri'a mai yawa, saidai ki mutu.SHI novels / JARABABBEN KISHI part 14 JARABABBEN KISHI part 14 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:38 Kuncinta ta rike tana mai kallon saheeb Ido cikin Ido, Cike da takaici tace "tabbas saheeb sai kayi ladaman marina saika San cewa ka mareni Akan wata yar iska? Kayi kuskure wannan. *So ne ko kiyayya*? (Na sanah s matazu,) Saheeb magana nakeyi kana jina, aikam inhar numfashi bakai ba kara aure acikin gdannan, Na yima rana shine zakamun dare"? Wasu zafafan hawayene suke kwaranya a cikin idanunta, Amma saheeb koh kallonta baiyi ba, bare Kuma ya tausaya mata saboda abunda take dauke dashi a cikinta. Fuuuuuu Saheeb ya wuce kaman zai tashi sama kuka suhayr keyi tana cije baki saboda wani ciwo datakeji, Tana cikin wannan halinne taji Sallama Ashe kawartace tashi tayi ta bude kofa "ah ah maraba da mutanen jigawa saukan yaushe ina yaran da oga?". Qawar tace "Tab suhayr uwar biyu kenan wannan ciki naki dakwai bayani". Dariya suhayr tayi a Falo suka zauna tasa mai aikin ta takowo bakuwa abinchi da abunsha, "Kawata naji dadin zuwanki wallahi, inada damuwa sosai", tas ta kwashe komai ta gayawa kawarta. Qawar tace "Tabbas suhayr keme lefi ce yazaki dinga yin Abu irin wannan? Bayan kinsan halin maza insuka so Abu sai sunyi ko'a boyene? Tunda nake da baban hydar ban taba cewa bazan zauna da kishiya ba, dama zai kara auren wallahi Nina shigemai gaba don ganin yayi auren Kuma gashi muna zaune lafya". Suhayr tace "Tab aini *Jarababben kishi*na bazai barniba, Akan saheeb zan iya rasa raina". Ummu hydar tace "Tab bari kiji kadan daga cikin wani littafi na matan aure Dana taba karantawa," Kila ya miki amfani don bance dole ba". " Idan har Kika yarda da cewa namiji ba zai qara aure ba suhayr to wllh kinyi wauta domin basu da tabbas a wannan bangaren, karki yarda namiji yayi miki alqawarin baxai miki kishiya ba, shi kanshi ai bai san me yake gaba ba, idan Allah ya rubuta sai yayi auren nan to fa ya xama dole yayi shi". Ta cigaba da cewa "Idan Kuma kika ce ba zaki rike dan Mijinki ba (dan Kishiya) Nan ma kin tafka shashanci babba, don Idan kin haifi naki 'Ya'yan babu tabbacin cewa xaki dawwama a gidan ko a duniyar ma, Idan kuwa kika ce namiji ba dan goyo bane kin zama sakarya, domin kin mance da cewa ai kece baki Iya yanda ake goyon namijin ba" Idan kuma kika ce Kishiya ba abokiyar zama bace ba, mijinki baxai qaro wata matar ba toh ke naki 'Ya"yan Idan kin haifa jere Za Kiyi dasu a dakin ki? Karki raina uwar mijinki domin tamkar uwa take a gurinki. Da dan numfasa snnan ta cigaba "Idan kina wulakanta dangin mijinki, Toh naki dangin waye zai girmamasu? Idan kika ce ke bakya son kishiya toh sauran Yan mata da zawarawan gari suyi yaya?. Suhayr tabbas yaka mata kifarka daga nannauyan baccin dake dibanki Suhayr shuru tayi don tasan dakaman wuya gurguwa da auren nesa, yadda takeda kishinnan aikam bazai taba yuwuwa ba, Ummu hydar taci gaba da cewa, "Idan kika ce ke bakya son Kishiya toh kisani, da yiwuwar ayi miki kishiyar waje wacce Idan akayi rashin sa'a Kishiyar nan taki ta waje ta aiko miki da "SAKON MUTUWA" (HIV Aids) SUBHANALLAH, Suhayr meyasa baxakiyi amfani da wannan hudubar ba ki gyra, lahiranki?". "Tabbas ummu hydar da kishiyar gda tabbas na kwammace ta waje Inta tashi ta kashemu mu duka". Ummu hydar tace "Kash yayan da kika Haifa Kuma fa?". Cewar ummu hydar. Suhayr kai tsaye tace "Suzama marayu" (Ni kam dai nace Suhayr kin fara bani tsoro)ISHI novels / JARABABBEN KISHI part 15 JARABABBEN KISHI part 15 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:39 Duk abunda kawar suhayr ke fade duk a kunnen saheeb, Hannu yadaga sama yace "Allah kasa suhayr tayi amfani da wayannan fatawa" Amma saiyaji akasin haka. A ranan ummu hydar ta tafi tabar suhayr da dumbin tunani. Shi kuma saheeb ya rasa yadda zaiyi, akullun yanada shaawar ganin ya tara mata domin ya tara yaya masu yawa. A haka suhayr taci gaba da tsula tsiyarta, duk inda taji yaje neman aure saita wargaxa, sai da tayi sanandin lalacewar auren daya nema guda 7. Danginsa suma sun bashi mata duk yadda akayi da boyewa sai da ranar daurin aure taje da bindinga tasawa waliyyin a goshi yana daurawa zata aika dan banza lahira. *CIGABAN LABARI* Nan yan'uwa aka fara cece kuce akan saheeb lallai suhayr tafi karfin shi, harta isa ta hanashi qara aure?. Saheeb ne ya juyo cikeda bakin ciki, dajin kunya ga dubban abokansa harda abokan cini kayyanshi Yace "suhayr am disappointed in you, you disgrace me in public? Had I know zaki zaman mu matsala a rayuwana, tabbas daban au........" "Saheeb dakata" wata murya yaji kakkausa Da alamu babu wasa acikin muryan. Juyowan da Saheeb yayi mahaifinsa yagani, Mahaifin nashi yace "Tabbas auren ka da suhayr alkhairi ne, Sannan bakada wata kallaman daxaka aibanci suhayr, Tacika mace jaruma, Sannan Wallahi tayima komai duk abunda akeso mace tadunga yiwa mijinta kasamu". Shidai Saheeb bakin ciki ne ya isheshi, yarasa makemai dadii yaci gaba da cewa" Kaida kanka Saheeb duk randa zan tambayeka cewa ya zaman takewanka da Suhayr? Kakan cemun babu wata matsala, Toh banga dalilin ka na kara aure ba tunda bata gaxa wajen kyautata maka ba". "Amma Abba".... "Bansanjin wani kalma daga bakinka ba ku tafi gida kawai". Sun koma gda ba Wanda yace ma kowa kanzil, Ahaka suka cigaba da rayuwa har Suhayr ta haihu baice da ita komai ba, ko barka bare kuma yadauki da yayi masa huduba tundaga asibiti daya kaita bai kara hada Ido da itaba. Bayan mahaifin Saheeb yazone ta gayamai halin da ake ciki, Yayiwa da huduba yasa masa sunan mahaifinta wato kabir Wanda tayimai lakabi na NOOR wato (haske). Murna a wajen Suhayr bai misaltuwa. Suhayr ta hana kowa zuwa mata barka daga danginta har na mijin, Sannan tafadi ma ummanta bazatayi suna ba kuma baxata koma gda wankaba, Abunda ya daurewa ummanta kai shine yadda Suhayr ke magana ba koh alamar shakka, ta kaleta tace "Suhayr meye dalilinki na Na cewa baxakiyi sunaba? Kuma kinsan yin suna yaxaman mana al'ada" Tace "Umma nace baxanyi sunaba' saboda bazan juri ganin mata acikin gdana ba Sannan meye abun doki dahar sai anyi suna bayan uban d'an baya maraba da zuwansa duniya". Tana magana tana zubda hawaye Wanda duk Wanda ya kalleta saiyasan cewa Rashin kulatan da Saheeb bayayi yana cimata tuwo a kwarya. Umma tace "Suhayr hakanan Saheeb bazai juya miki bayaba saidai inkin yimai laifi" Suhayr tace "Wani laifine umma nayi banda ya wuce naje na wargaxa mai auren da yake shirin karawa? Nibanyi fushiba daya munafunceni bai sanar dani cewan zai'yi aureba sai shi? Nikuma nayi amfani da kishina Wanda bashida maraba da leban wuta na ruguza komai, Kishiya a gdan Saheeb sai bayan raina". Umma Suhayr ce tace "kull inba hakaba zaki tafka kuskuren da sai kinyi Dana sani, wannan maganar inkikayi wasa yan Amin suka amsa toh Wallahi zaki mutu kuma yakara aure ke har hudu sai yayi".EN KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 16 JARABABBEN KISHI part 16 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:41 Duk abunda kawar suhayr ke fade duk a kunnen saheeb, Hannu yadaga sama yace "Allah kasa suhayr tayi amfani da wayannan fatawa" Amma saiyaji akasin haka. A ranan ummu hydar ta tafi tabar suhayr da dumbin tunani. Shi kuma saheeb ya rasa yadda zaiyi, akullun yanada shaawar ganin ya tara mata domin ya tara yaya masu yawa. A haka suhayr taci gaba da tsula tsiyarta, duk inda taji yaje neman aure saita wargaxa, sai da tayi sanandin lalacewar auren daya nema guda 7. Danginsa suma sun bashi mata duk yadda akayi da boyewa sai da ranar daurin aure taje da bindinga tasawa waliyyin a goshi yana daurawa zata aika dan banza lahira. *CIGABAN LABARI* Nan yan'uwa aka fara cece kuce akan saheeb lallai suhayr tafi karfin shi, harta isa ta hanashi qara aure?. Saheeb ne ya juyo cikeda bakin ciki, dajin kunya ga dubban abokansa harda abokan cini kayyanshi Yace "suhayr am disappointed in you, you disgrace me in public? Had I know zaki zaman mu matsala a rayuwana, tabbas daban au........" "Saheeb dakata" wata murya yaji kakkausa Da alamu babu wasa acikin muryan. Juyowan da Saheeb yayi mahaifinsa yagani, Mahaifin nashi yace "Tabbas auren ka da suhayr alkhairi ne, Sannan bakada wata kallaman daxaka aibanci suhayr, Tacika mace jaruma, Sannan Wallahi tayima komai duk abunda akeso mace tadunga yiwa mijinta kasamu". Shidai Saheeb bakin ciki ne ya isheshi, yarasa makemai dadii yaci gaba da cewa" Kaida kanka Saheeb duk randa zan tambayeka cewa ya zaman takewanka da Suhayr? Kakan cemun babu wata matsala, Toh banga dalilin ka na kara aure ba tunda bata gaxa wajen kyautata maka ba". "Amma Abba".... "Bansanjin wani kalma daga bakinka ba ku tafi gida kawai". Sun koma gda ba Wanda yace ma kowa kanzil, Ahaka suka cigaba da rayuwa har Suhayr ta haihu baice da ita komai ba, ko barka bare kuma yadauki da yayi masa huduba tundaga asibiti daya kaita bai kara hada Ido da itaba. Bayan mahaifin Saheeb yazone ta gayamai halin da ake ciki, Yayiwa da huduba yasa masa sunan mahaifinta wato kabir Wanda tayimai lakabi na NOOR wato (haske). Murna a wajen Suhayr bai misaltuwa. Suhayr ta hana kowa zuwa mata barka daga danginta har na mijin, Sannan tafadi ma ummanta bazatayi suna ba kuma baxata koma gda wankaba, Abunda ya daurewa ummanta kai shine yadda Suhayr ke magana ba koh alamar shakka, ta kaleta tace "Suhayr meye dalilinki na Na cewa baxakiyi sunaba? Kuma kinsan yin suna yaxaman mana al'ada" Tace "Umma nace baxanyi sunaba' saboda bazan juri ganin mata acikin gdana ba Sannan meye abun doki dahar sai anyi suna bayan uban d'an baya maraba da zuwansa duniya". Tana magana tana zubda hawaye Wanda duk Wanda ya kalleta saiyasan cewa Rashin kulatan da Saheeb bayayi yana cimata tuwo a kwarya. Umma tace "Suhayr hakanan Saheeb bazai juya miki bayaba saidai inkin yimai laifi" Suhayr tace "Wani laifine umma nayi banda ya wuce naje na wargaxa mai auren da yake shirin karawa? Nibanyi fushiba daya munafunceni bai sanar dani cewan zai'yi aureba sai shi? Nikuma nayi amfani da kishina Wanda bashida maraba da leban wuta na ruguza komai, Kishiya a gdan Saheeb sai bayan raina". Umma Suhayr ce tace "kull inba hakaba zaki tafka kuskuren da sai kinyi Dana sani, wannan maganar inkikayi wasa yan Amin suka amsa toh Wallahi zaki mutu kuma yakara aure ke har hudu sainovels / JARABABBEN KISHI part 17 JARABABBEN KISHI part 17 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:43 "Umma bazan iya jure jin kalamanki ba, Maiyasa bazaki bani goyon bayan yaki da kishiya ba? Wallahi umma kishiya ba abokiyar zama bace" Suhayr ke maganar cikin muryar kuka. Umma tace "Tabbas suhayr kishiya abokiyar zamace idan kikayi dace" Tayi saurin cewa "Umma kiji kalamanki? cewa kikayi idan nayi dace? Nikam kishiya ba kwai bace umma bare in kwankwasa inji irinta, Umma idan kishiya abunyi ce maiyasa bantashi naganta agdanmu ba? Idan kishiya dadii ce maiyasa bakice Abba yakara aureba? Idan kishiya dadii ce meyasa Yawancin marubuta na duniyar yanar gizo ke fada mana illolinsu? Ita kanta *"Humairah B Melody"* tana daya aga cikin victim." Umma tace "Suhayr Karki zurfafa kishi don koba jima koba Dade namiji mai son aure saiyayi, Allah ya hadaki da miji jarababbe saidai kiyi hkr" tayi saurin cewa "Hkuri umma? Nikuma zanyi amfani da jarabata da *jarababben kishina* inci gaba da wargaxa mai tsari". Itadai umman Suhayr cewa tayi "Allah yaganar dake hanya madaidai ciya, Amma duk abunda kike na kyautatawa, tabbas kici gaba Karki fasa namiji wawa ne?. An hado mata sha Tara na arziki harda k'yautan mota tsalleliya daga mahaifinta, Akwati biyar nata' uku na jariri NOOR, Sannan ga kudi masu yawan gaske. Rago biyu Saheeb ya yankawa yaro, mai aikice tayi gyran nama ta soyashi tsaf makota kawai tamikama suma ba dukaba, dangin Saheeb sunyi tsaigumin Rashin kawo musu naman dabatayi ba ( *Nida belly mukace kuma da shegen zalama kuke*) Saheeb yafara sauyawa, yadaina fushi da ita Sun koma kamar da amma fa burinsa yananan na kara aure. Wata safiyane aka buga kofa, Direban gdansu tagani, "lafya naganka da sanyin Safiya?". Driver yace "Eh Alhaji ne yace in sanar miki da cewa kishirya wani sati ansama miki makaranta a *NORTH WEST UNIVERSITY*" "Dan Allah?". Tayi murna sosai, saboda murna saida tabashi tukwaici. Saheeb na shigowa ta karbi ledar dake hannun sa, tayi mishi maraba Yayi wanka ya gabatar da sallah sannan take gayamai cewa ansama mata makaranta, yaji dadii Kwarai yace Allah yabata sa'a Shiri suhayr takeyi zata gdasu tun Asuba ake dauki Tare suka fita da Saheeb ta saukeshi a shago itakuma ta wuce da alkawarin inzata dawo zata biyo tadaukeshi, " I love you Saheeb" tace tana mai kallonshi, yayi murmushi yace "your love to me is like a priceless Gold" itama ta mayar masa da cewa "You are expensive in my life Saheeb I can go on without you in my world". Dariya yayi yace, "Suhayr kenan duk abunda kika fadii nima haka nakeji a zuciyana". Kissing dinta yayi yashafa kan Noor Yace "ka gaida grany da takwara" Har yayi nisa ta kirashi "pls Saheeb banda kalle kalle". Hancinta ya lakuta yace "I promise you dat my love". Akan hanya ta sauka tayiwa Umma siyayya, tufa ta saimata da kayan marmari. Rike take da noor saiga wata mata daganinta baxawarace don bazaka kirata da budurwa ba. Duk'da ba abun mamaki bane samun babban mace kamarta batayi aure ba.KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 18 JARABABBEN KISHI part 18 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:44 Kusada Suhayr ta matso tace "Sannu fah inason yaronki". Washe baki tayi abunka da mai yaro wawa "Tnx alot kin ganshi duk ya kosa yaje yaga grany". Matar tace "Ehyah inbazaki damuba Dan Allah meye sunansa dake kanki". Suhyr tace "Sunansa NOOR nikuma Suhayr". Daidai da an miko mata kayan data siya na kayan marmari. Tace "Dan Allah bawan Allah biyoni dashi". bayan boot ta bude ta zubasu. Tuni suhayr ta manta da wannan matar, motarta ta shige don Suhayr batason zakewa. "Baiwar Allah tsaya". Ina tuni suhayr ta figi mota..... Tana isa bakin gate tayi horn aka bude mata, Packing loge Ta nufa ta jera tata motar da sauran. Waya ta dauka don ta sanar ma Saheeb ta isa amma akasamu akasi yana waya kasar waje, don yayi odan kaya Ta kirashi yafi sau tulin gashin tinkiya amma shuru" Tuni zuciyarta tafara tafar fasa, cewa Saheeb da mace yake waya. K'ara k'ira tayi aka samu ak'asin a 'network' kiran yashiga wayar wata..... Bugu daya aka dauka Ba jira Suhayr ta fara bala'i ta inda take shiga batanan take fitaba "Ka tuna Saheeb you promise me cewa bazakayi waya da wata mace ba pls Saheeb kasan ko yadda nakeji yanzu?. Shuru taji Suhayr tace "mijina abun alfahari answer me pls" "Hello kiyi hkr ba mijinki bane" Damm!!!!!!!! Taji zuciyarta ta buga jin muryar mace Dayake shu'uma tasamu dukda bata Santa ba amma tana bakin cikin ganin mace ta hana mijinta sake wa Koh kuma mace mai shegen kishin tsiya. "Kinyi shuru nace ke wacece?" cikin zafin rai Suhayr take magana. "Islam ce Kuma ni budurwan mijinki ce, gashi kusa dani yana bacci daya tashi wanka zaiyi yayi sallah don bashida cikakken tsarki saimu wuce juffatu muyi shopping". Jiri Suhayr take gani idonta na juyawa, Karfin hali tayi tace "baki isaba yar iskama irinki harkin isa mijina yaxama abokin iskan cewar ki???? Karyarki tasha karya Wallahi kin gamu da ajalinki indai nice yar iska Mara mutunci Mara Sanin ciwon kai" Tsaki tayi tace "kinibibi sakarya indai mijinki ne ke kadai sai ingani. Katse wayan tayi. Mai gadi taba NOOR yashiga dashi tace tana zuwa Mota ta shiga Shagonsa ta nufa cikin ikon Allah yana ciki yana ta sallaman customers. Saida tabari ya sallami kowa tace "Saheeb kataimakeni ina cikin rudani wacece kaba wayanka?" Saheeb dafe kirji yayi yace "nooo Suhayr you most be dreaming tunda na shigo shago Wallahi ko waje ban lekaba". Mamaki duk ya cikata Kira wayar kiji cikin ikon Allah ta kira yadauka taji gashi dai muryan mijinta ne Duk sai taji kunyan ta kamata "Saheeb kayi hkriiii....." "Shhhhh!!!!! Karkiban hkr abunda nakeso dake shine./ JARABABBEN KISHI part 19 JARABABBEN KISHI part 19 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:45 "Abunda nakeso dake kizama mai yimun kyakkyawan zato, Kiyarda dani Suhayr " Suhayr tace "Saheeb kayi hkr amma kaji na rantse maka mace tadau wayanka". Saheeb yace "Haba Suhayr ana samun matsala daga network In mutun yakasa samun ka kawai sai suyi Diverting Call dinka saiya shiga wayar wani Inkuma dashi wacce ta dauka zata duba baxataga lambar ba" Tashi tayi tace "natafi don koh umma bata ganni ba" Saheeb yace "OK love you " kallonta Saheeb keyi Kaunar matarsa kawai yakeyi a ransa. Gida ta wuce ummanta tagani rikeda noor sai kuka yakeyi "Oyoyo umma" Umma ta tarbeta da cewa "dakata Suhayr narasa gane miki, wannan kishin ina rabaki dashi amma kinkiji." Suhayr tace "Umma menayi kuma" Suhayr tabata rai Umma tace "inajin duk Abunda ke faruwa shine kikaje shagonsa koh? kitadamai da hankalinki? In baki ba mijinki farinciki ba Suhayr mezaki bashi? nidai ina baki shaawara ki daina don bashida amfani, Amsheshi kibashi madara yasha". Haka sukayita hira har yamma gashi Abbanta baidawo ba, Tabar sallahu cewa tana gaidashi Zata dawo kafin ya koma. Saida tabiya ta shago ta daukeshi, Suna isa nimrah suka gani a bakin gate Sai cin magani take tana cika tana batsewa. Mai gadine ya bude gate suka shigo, Fitowa Saheeb yayi rikeda noor a hannun shi, ya kalli Nimrah yace "Nimrah lafya kike kuwa? Baki iya ki gaidani ba?" Nimrah tace "Dan Allah yaya kasan tun yaushe nazo gdannan? Kuma umma tace karna dawo saina ganka". Zaro Ido yayi yace "lafya?" Nimrah tace "Inafah kusan sati umma batada lafya bakaxo ka gaidata ba Koh kiranka akayi bakason dauka". Nimrah ta tabe baki ganin Suhayr taxo wajen Saheeb yace "Nidai banga kiranku ba gaskiya" Suhayr tace "nicenan nake kashewa, saboda muna cikin jin dadii ba Wanda ya isa ya hanamu sukuni" "keeehh Suhayr kinsan koh uwa tawuce gaban wasa? Yanxu da mutuwa tayifa? Saheeb ke magana cikin bacin rai. Suhayr tace "Dana shiga uku". Nimrah dake tsaye tana ballama suhayr harara , tace "kuma umma tace inna ganka mutaho tare". Suhayr tayi saurin cewa "Ba inda zashi sai gari ya waye" Nimrah tace "Aikam kinyi kadan inace kema wajen naki uwar kikaje? Kuma sainaga bai hanaki ba". Suhayr tace "ai uwata ce" Nimrah tace "shima Uwarsa ce" Kallonsu kawai yakeyi yana kallon son zuciya irinna Suhayr..... Baice da ita komai ba hannun nimrah ya rike taji kaman ta kurma ihu, tace "Saheeb ina kake shirin zuwa?" shuru yayi nimrah tace "gurin ummansa zashi" tafadi tana mata gwalo. Ciki Suhayr ta shiga tace "lallai sainayi maganin nimrah Saina nuna mata cewa ita karamar yar iskace", Kwafa tayi Sallah tafarayi Sannan ta shiga kitchen tafara girki. Taliyace macaroni ta Dafa Wanda yaji kayan lambu" Wanda ya hada da carrot, pea, harma da cabbage, Ga hanta Sai tadanyi pineapple juice Dan daidai. Farfesu tayi musu na kafan sa Tajerasu a dinning. Jikin mahaifiyanshi ya tsananta, Tuni yashiga rudu asibiti aka wuce da ita, Ruwa aka Samata. Dayake kusa da zoo road ne "Bari naje gda" yacewa kanninsa ya kawo musu abinchi Yana isa gdan yashiga Suhayr yake kwalawa kira Fitowa tayi cikin wasu yan iskan kaya Wanda bashida maraba da ace tsirara Take. Bata nunamai wani abu ba, Saima murmushi datake tana taku daya kan daya, Wanda tuni Saheeb yaji gaba daya jikinsa ya mutu, Kusa dashi ta matso "Wani irin kamshi yaji tuni ya sunkuceta ta sai daki kan gado ya ajeta. Yafara.HI novels / JARABABBEN KISHI part 20 JARABABBEN KISHI part 20 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:48 "Lafya yaya bai dawo ba har yanxu?" Cewar Sarah mai bima nimrah. "hmmm inkika bibiya wannan yar'iskan matar tasa ta hanashi ya fito" cewar Nimrah. Amrah dake zaune tana kallonsu Batace dasu uffan ba don arayuwarta ta tsani ayita cece kuce don ita tace Suhayr bata kai matsayin dazata dinga maganarta ba. Amrah hatsabibiya ce rigimanma don tace Nimrah batai komai ba. Nimrah tace "Amma bari na fita waje inje in siyo mana koda dankaline muchi". Nimrah ce ke magana daga ganin fuskanta kasan cewa akwai damuwa kwarai. Wata budurwace daganinta kasan tasha boko ta koshi tajiyo duk hirarsu. Tace daga gani da matar wansu suke Amma kuma sunban tausayi. Tashi tayi ta dafa kafadan Amrah tace "beautiful yanaga kin bata fuska? Kina neman ki bata kyawunki?" Amrah tace "Kamar yadda kika gani mahaifiyar muce ba lafya Kuma da yayanmu mukazo yaje ya kawo mana abinchi kinga bashi ba labarin sa Kuma baya rasa nasaba da matarsa don taki jinin mu balantana kuma umman mu Kila ita ta hanashi dawowa, yadda kikasan tayimai asiri". "Karki damu ya mai jinkin" ta cewa Nimrah. Nimrah tace "Da sauki bacci takeyi". "OK bari ina zuwa" flask taje ta dauko makare da abinchi ta kawo gabansu tare da cewa "Pls kannina kuci abinchi idan umma ta tashi kubata taci". Mamakin kirki irin nata sukeyi Sarah tace "inba zaki damuba inason Sanin sunanki". Budurwar tace "Ni sunana Atika". "Suna mai dadi" cewar Amrah. Har dare ya tsala Saheeb bashi ba alamansa, Haka suka kwanta a kujera sukasa Kansu a gefen gdon da ummansu take kwance. Washe gari kaman a mafarki Saheeb ya tashi, sai a lokacin yake tunawa da ummansa harma da kanninsa, tagumi yayi kawai sai hawaye Wanda nima Humairah bansan kona meye ba. Nashiga uku kallon Suhayr yakeyi wacce batasan me duniya take ciki ba Duka ya Dada mata ji kake tas!!!!! "tashi tabbas Suhayr zaki iya halakar danii bansan cewa kin kware a yaudara ba, bansan cewa bakida imani ba" Saheeb ke maganar cike da takaici. "Saheeb wat is the matter? You wake me up and you're insulting me? For goodness sake wat have I dont?". Suhayr ta fada itama da bacin rai. Saheeb yace "Ai daman baxaki saniba tunda kinyi succeeding nabar mahaifiyata da kanina da yunwa bayan nagaya miki cewa ummata tana asibiti kizuba abinci inkai musu". "Yanzu mekakeso kace Saheeb? Nabar mahaifiyarka da yunwa? Toh h you are wrong saboda hakkina dake kanka ka sauke, so i don't care". Ta fada tana mai niyyar komawa ta kwanta. Cikin bacin rai yace "Suhayr kafin in irga uku ki tashi kishiga kitchen kidafama umma abinci ki hadamun inkai musu inba haka ba Zan nuna miki true color na". Ya qarshe da tsawa. Haka Suhayr ta tashi Minti arba'in yayi yawa ta kammala. Ya dauki hanya sai asibiti, Yanata tunanin wace karya zaiyi ya gamsar da kanninsa? Yana shiga cikin asibiti wata ya hango ba wata bace Abeeda ce take ba ummansa abinchi a baki. Lokaci guda yaji sonta yashiga cikin zuciyarsa, "Inama Suhayr ce takewa ummata haka Danaji dadii" Abinda yake fada kenan a xuciyarshi. karasawa yayi yace "umma Ina kwana" koh kallonsa batayi ba Kanninsa ma kowa ya bata rai. "pls my sisters kuyi hkr wallahi........" Bai karasaba nimrah tace "nasan yaya tunkafin kaxonan kashirya irin karyar dazaka sharara mana Dan haka bamu da bukatar jin wani Abu daga bakinka" Umma dake kwance tace "kinyimun Daidai Nimrah kai dai kam kaji kunya wllh". Tsayawa yayi jikinsa duk yayi sanyi kunya duk tabi ta isheshi. "umma kiyi hkr tunda yasan yayi kuskure" Abeeda ke magana cikeda ladabi. "Umma albarkarku itace kadai ke tasiri a rayuwar mu Kishi mishi albarka sannan kidinga mishi Adu'a Allah ya tsareshi daga kaidin mace", takarasa tareda kallon Saheeb Wanda yayi nisa a fagen son Abeeda. (Tir kashi Abeeda dai kawar Suhayr ce amma batasan cewa saheeb mijin Suhayr bane kubiyoni donjin sauran labarin)novels / JARABABBEN KISHI part 21 JARABABBEN KISHI part 21 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 19:49 Kwanan su biyu a asibiti Amma ba suhayr ba labarin ta, abun yana damun Saheeb amma bashida yadda zaiyi, Washe garin ranan da zaa sallamesu Saheeb yace "suhayr bakije kin gaida umma ba gashi har za'a sallamesu" Koh kallonsa batayiba tace "pls Saheeb kadameni wai shin ina ruwana da Rashin lafiyarta? Koh inada matsala da hakanne? Pls Saheeb ka kyaleni, ask you can see am ready to school So inkaje ka gaidata ga abinchi a dinning bissimilah". Koh kallonta baiyiba yace "kitashi kidauko cooler kisamun nawa abincin xankai musu asibiti". "ah ah Saheeb wai meye amfanin su nimrah da bazasu gda su daho abinci ba Tika tika dasu?". Inji Suhayr "Ba matsalanki bane inkinji toh kitashi inkuma bakijiba Zan fita can waje insiya musu". Suhayr tace "Tafi nono fari Kasan da hakan ka tsaya jaka ta dafa ka kai musu?". Tashi yayi don yanajin inya cigaba dajin munanan kalamanta zasu tarwatsa zuciyarsa. Akan hanyansa na zuwa ne yayi musu adar abinchi sunci sun sha Daga bisani aka sallamesu, adaidaita suka hau har gda. Abeeda tayi missing dinsu amma batada yadda zatayi Sunyi exchange na number, Domin sudinga gaisawa, itqma Abeeda takamu da son Saheeb. A hanya suhayr ta hadu da Abeeda tana tafiya tana yanga Packing tayi tace "yanmata ran gari Takawarki lafya". Dariya Abeeda tayi tace " wata sabon gani suhayr". Suhayr tace "Shigo mana kinsan mun tsaya akan titine". Abéeda ta shiga sannan tace "suhayr yaushe kikayi aure?" Suhayr tace "Hmm last year badai ke kintsaya ruwan Ido ba? kinganni harda Dana noor" "Nyc name" inji Abeeda. Suhayr tace "Northwest University nake zuwa kefah" Abeeda tace "Aini poly nakeyi, Ina HND ne". "Allah ya taimakemu "Yasu hjy keko Abeeda nadade inason ganinki Inaso ki rakani wajen wannan malamin hajyan Akwai Marsala". Abeeda tace "Suhayr matsalar me dagayin aurenki koh 2yrs bakiyiba?". Suhayr tace "Abeeda kinsan koh kishin danake akan saheeb? Kinsan irin taaddancin dana dinga yi? Akan so ya kara aure? Kafin aurena saida narabashi da yan mata sunkai biyar, bayan aurenmu kuwa bakwai na lalata, Ke har wajen daurin aure" "Wat!!!!!" Zare Ido Abeeda tayi tace "tab Suhayr ke shu'umace". Ta tabe baki tare da cewa "ai nafi haka ke Niko uwarsa bata zuwa gdana bare kuma kanninsa koh yan uwansa" Abeeda tace "tirkashi Ashe dakwai bikin zuwa babu Zane" A zuciyarta tafadi "tabbas Saheeb yayan Amrah shine mijin Suhayr" "OH my God Suhayr kin kade sai kinyi dakinsanin fadamun sirrinki, saina shigo rayuwar Saheeb Na hanaki sakat" A baki tace "OK xan rakaki amma yaushe kika shirya?". Ta danyi jim tana naxari sai kuma tace "ummmm Abeeda mu barshi weekend kinga am free ba school". Abeeda tace "Haka zaayi". Ahaka sukayita hiran har takai Abeeda bakin poly sannan ta wuce nata makarantar. Cikeda farin ciki Suhayr tace "Saheeb bakaiba kara aure, Sai anyimun maganinka Saheeb bawai muzgunama nakeso nayi ba sonka nakeyi Banaso wata taBBEN KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 22 JARABABBEN KISHI part 22 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:07 Abeeda na isa gda tace da hajiya "Hjy kinsan meya faru yau Suhayr nagani Har tayi aure kinsan harta haihu?". "Iyeeh tabdi jam" inji hjy saude. Abeeda tace "Hjy ina Wanda nake baki labarin Rashin kirkinta ?" Hjy saude tace "eh" "Toh Ashe Suhayr ce Hjy duk yadda za'ayi inshiga gdan saina shiga koh ta halin kaka". Hjy saude tace "Yauwa yata haka nakesonki da jarumta, Karki sake ki karaya". Abeeda tayi dariya tare da cewa "Bakiji ba wai zan rakata gurin Malam ai kibari hjy (tsuntsu biyo zan jeho da dutse daya) Itace sakarya hjy" "Yauwa yata" hjy ta rungumo Abeeda tace", "Yar hjy, uwar hjy, yar lelen hjy, yar gaban goshin hjy, Kishiga ya auro hudu kuma ki zauna dasu, indai kisssace yanzu kai ya waye ba boka ba Malam iya ruwa fidda kai Wanda ya iya allonsa ya wanke". "Hjy yanzu zan kira Malam inyimai bayanin komai, yafara aiki tunda nasan a irin kallon da yakemun, hjy dakwai so a ciki" Malam suka kira tayimai bayani yace angama cikin kankanin lokaci zaki zama halak malak dinsa ammafa Saikinci damaran zama a gidan Saboda matar shu'umace duk yadda kike tunani tafiki Sannan ta mamayeshi kwarai Saboda yana masifan sonta Sannan gdan da suke ciki mallakin mahaifinta ne ke harta kasuwancin dayake kudinta ne". "Malam ai wannan duk ba wata matsala bace Masifa kuma ai saimuyita gwabzawa Mekarfi ya kwaci kansa". Malam yace "Angama" Washe gari tun safe Suhayr ta kammala aikinta, Saheeb yana zaune Tunanin Abeeda kawai yakeyi, duk Suhayr tana kallonsa da yanayinsa. Mai aikinta ta goge ko'ina Sun kammala. kusa dashi taxo ta haye kan kafarsa tace "Nurul-Q'alby Lafiyarka kuwa gaba daya ka canza? Kodai akwai matsalane a kasuwa?" Rungumeshi tayi har sunajin numfashin juna. "Talk to me Saheeb Your silence it wat I hate". Dagota yayi yace "my blood ba abunda ke damuna Saidai har yau nakasa cikama zuciyana burinta" "Zare Ido tayi tace "buri kuma? Wani burine Wanda ya wuce mu karasa rayuwar mu nidakai da yayana har abada?" murmushi yayi Amma na ciki na ciki yace "Hakane Suhayr Allah yabarmu tare" "Amin" tace "inaso zanje unguwa Amma bawani dadewa zanyiba Sannan a gda zan bar Noor". Saheeb yace "Amma Suhayr dakin tafi dashi inajin da hankalina yafi kwanciya" "Toh" tace tana dariya tace "your wish is my command". A hanya suka hadu da Abeeda, suka kama hanya sai wani kauye can gaban dawanau Gaban "kwa" in an wuce "Dungurawa" Wato "Doruwar shehu" Cikin unguwan suka shiga sai gasu a kofar gdan Malam din, Sunyi mishi bayani yace dubu talatinne ba yawa Da sauri Suhayr tafito da kudi zunzurutun kudin ta bayar. ( ni HUMAIRAH danida beelybadaru, akaba kudin muyita mata tsayuwar dare) Abeeda tace "Malam kar ayi sanya" yace "karki damu" Kallon suhayr takeyi tace "saikinyi dakin sani don saina maye gurbin duk abinda kika kasa Hakan zaisa nasamu matsayi a birnin zuciyan Saheeb" duk a xuciyarta take xancen. Sun kama hanya kowa da abunda yake sakawa Bayan sati hudu wata guda kenan, Saheeb yarasa sukuni har saida ya binciko gdansu Abeeda, Daga zuwansa yace aure yakeso nanda wata guda Sannan bayaso kowa yasani saboda karya koma kunnen matar sa. Soyayya mai ma'ana ce tashiga tsakanin su Baya iya barci sai yaji muryanta, Kullun saisun gaisa da yan uwansa, harma da umma lokaci guda ta asirce zuciyansu da akhairai. Shiko kanin Saheeb ba wadda yaki jini irin Abeeda, Don yace batai masa ba gwara Suhayr sau miliyan, So gamon jini" Kwatsam mustapha yaji ana zancen yayansa zaiyi aure kuma a boye musty yace "shikam bazai yarda a munafunce Suhayr ba," Gdansu Abeeda anata shiri biki saura satii biyu.I novels / JARABABBEN KISHI part 23 JARABABBEN KISHI part 23 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:11 Shiri akeyi gadan gadan, akalla saida Saheeb yayiwa Abeeda akwati biyar harda kit, Sadakinsa naira dubu hamsin Yabada komai na kawayen amarya. Saheeb ne tsaye yace "Abeeda daga yau baxaki sake ganina ba, sai ranan daurin aure". bata rai tayi "saboda me my Blood?" Yace "Saboda banaso Suhayr ta gane komai saboda tafara mun complain cewa Bata gane yanayina ba kinga karta dagoni" (Rikicin duniya damai rai akeyinsa) "hakane Amma dai zakazo dinner koh?" Cewar Abeeda. Yace "Eh zanzo karki damu" "Toh" tace ta juya tana jujjuya sassan jikinta komai na kadawa, Saheeb ya bita da ido har ta bace ma ganinsa. Shiko musty nazarin yadda zaayi a Raguza aurennen yake, Gashi yakasa zuwa ya sanar da suhayr, kwatsam saijin labarin dinner da aka shirya Yace "toh koh saina sanar da suhayr Kartace na munafunceta". Ayau ne daurin aure tun safe Saheeb ke shiri yakasa zaune yakasa tsaye. Suhayr duk tana kallonsa daga bisani tace "oh my God Dan Allah Saheeb safa da marwan me kakeyi? Saikace Mara gaskiya?" Da sauri ya juyo yace "suhayr kamanya wane irin zancene wannan" (Cewa tayi gulty conscious) " ! dole in tambaya saiwani rawan jiki kake kaman me shirin yin sabuwar amarya?". Dam gabansa ya fadi "Yauwa inaso ka kaini gdansu Abeeda kawata inyi mata godiya". "Godiyan me ????" Ya fada a dan tsorace, sai kuma ya maxe ya ce "Look suhayr yawonki yafara over fah kiyi hkr next week kyaje" tace "Allah yakaimu", Yana fita dagashi sai boxer, Daki ta nufa wata tsaleliyar shadda tagani bugagga Ga wata hula mai shegen tsada. mamaki ne duk ya cikata ina Saheeb zashi? Tab yau akeyinta (Rakumi da kayan tanka). "Saiko na hanashi zuwa koh ina falo ta dawo ta kalmashe kafa, Yazo ya wuce yasa shaddar sa fara kal, kitchen ta nufa da sauri ta debo miyar datayi na manja, fitowa yayi yana duba irin kyan da yayi Baiyi auneba ta taho da sauri Daidai da saheeb ya dago Gaba daya miyar ta kwaremai Gashi miyar da zafi". "Subhanallah!!!!!" Ta fadi tareda da cewa "swthrt am sorry it's a mistake " Kallonta yakeyi kaman yasa hannu aka ayita ihu!!!! "Suhayr kin kyauta kwarai" a zuciyarsa yace "Amma Daga gobe zaki gane kurenki". Daki ya wuce baice da ita uffan ba. Wata shadda yasa tsohuwa sawa daya Yasa hula ya fita, Abokinsa Marwan ne ya zo ya daukeshi a mota. Saheeb yace "My guy kaga abunda suhayr tayi mun? Miya ta watsamun a kaya" marwan yace "Mutumina gaskiya saika zama namiji inba hakaba Suhayr saita zamema annoba Saukinta ma Abeeda itama A ce". Andaura Aure kowa ya shaida, Abeeda sai murna take umman saheeb sai godiya take ga Allah, Yan uwa kowa sai barka yake mata. Musty ne Yakama hanyan zuwa wajen Suhayr don ya sanar da ita, saboda sauri yakalmi daban daban yasa Rigarsa a baibai. (Niko mexanyi banda dariya) take ya fada koh sallama babu "Lafya musty naganka hajaran majaran???". Musty yace "Ina lafya maye ya cinye amarya". zare Ido Suhayr tayi tace "a ina??ABBEN KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 24 JARABABBEN KISHI part 24 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:13 Musty yace "Aunty bafa nufina meye ya cinye Amarya bane Yaya Saheeb yayi aure". "What???" batasan lokacin data mike tsaye ba, tace "musty kana nufin Saheeb dina yayi aure?" Musty yace "Kwarai aunty har an daura ma nima dazu nakeji". Suhayr tace "Tabbas Saheeb yayi kuskuren boyemun komai, amma kuma ban makara ba Naji ma zaayi reception". Ah ina musty ya gaya mata shiri ta tashi yayi tana zubda hawaye, a gda tabar Noor wajen mai mata aiki. "Musty zo muje" motarta ta dauka ta dauki madoki abunyin golf tasaka a bayan boot. gudu takeyi har suka isa wajen da ake partyn. Dayake tinted glass ne bawanda ya ganeta, tace "musty kazauna a cikin motan karka damu bari na shiga don banaso afara komai". Ta fita ta shiga ciki Saheeb ta hango yanata washe baki, Wato yayi amarya, chan ta hango kawarta Abeeda bakaramin razana Suhayr tayi ba, " what!!!!! Abeeda itace ta auri Saheeb????" Take tambayan kanta amma idanunta kodai gizo suke mata. "Nooo in mafarki nakeyi yaka mata in tashi, Nooooo dis won't be possible". ji tayi ankira Saheeb da,amaryar sa Abeeda ai sakato tayi Basu ankaraba duka suka faraji tako ina da sandar golf, kuma gata da bindiga kowa yakasa tunkararta, Tuni Saheeb ya fadi sumanme, itako Abeeda tuni kamanninta suka canza, baki ya kumbura amma Suhayr duka takeyi baji ba gani. saida tayi nasaran sumar da Abeeda Hjy saude lbr ya risketa tuni ta tsure. Loudspeaker ta dauka Tace "ina ma kowa murnan zuwa gaggarumin bakin biki Wannan da kuke gani maciya amana ne, Abeeda kawata ce wadda na yarda da ita amma shine taci amanata, Shikuma wannan da kuke gani ba kowa bane illar mijina kuma uban yayana, nasan dayawa mutane zasu kirani da mahaukaciya tabbas basuyi karya ba, Indai akan miji nane. Wutan kishi na damuna kwarai Bansan wace jaraba bace kecin sa yayi mun kishiya kuma kawata?, Kadan kuka gani". ta fadi tana kallonsu koh motsi basayi. Tiryan tiryan ta sakko tana taku daya bayan daya tace "kafin in irga uku kowa ya bace" ta nuna bindiga, Kan kace me kaman anyi ruwa an dauke. Ta tsallake su tayi waje, Tashiga mota suka koma gda. Suhayr tayi kuka kaman ranta zai fita amma duk abunda tayi tace bata huce ba.KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 25 JARABABBEN KISHI part 25 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:14 Ambulance aka kawo aka kai Saheeb da Abeeda asibiti, Hankalin kowa saida ya tashi ciki harda umman saheeb. Abbansa yace "duk abunda ya faru Halima kece sila kuma ina gaya miki kisa kafar zuwa kashe gobarar da kika hada Da hannunki kuma a gdan danki Don ni ba abunda ya dameni wallahi " Shuru umman saheeb tayi, batace dashi uffan ba, Fuuuuuu tafita Suhayr ce tace "musty muje gdan naku". Hanya suka kama sai dorayi suna tafe kowa ba baka sai kunne A kan kwana ta ajiye shi Sbd kar ace tare suke, Koh Sallama babu Suhayr ta fada dakin umman Saheeb. "Ban taba Sanin cewa ke gurmi bace mai hada guri, umman innace miki uwar banza nasan wallahi banyi laifi ba, Umma tabbas kin saiwa kanki fetir din dasaiya konaki, Kin ziga Saheeb yayi aure don farin cikinki Bakisan akasin haka zaki samu ba, Zama da kishiya baxan iyaba saidai yau kitashi daga dakinnnan kibasu su zauna, sannan ki ciyar dasu Amma bada kudin ubana ba." Shuru umma tayi tarasa bakin magana. Suhayr tace "Dole kiyi shuru saboda kinsan baki shuka alkhairi ba Munafukar tsohuwa". "tub" tayi ta watsawa umma miyau tace "kadan kika gani saikinzo *zaman makoki (na Rashkardam*) Zaki gara ganewa idonki, Zakisan yadda zafin Kishi yake." Kai tasa zata fita kawai taci karo da Abeeda tsaye tace "zafin Kishi koh hauka????? Tambayanki nake?" Suhayr dago jajayen idonta tayi ta hankada Abeeda saida ta fadi. Suhayr ta taka wuyanta tace "ke in bakisan cewa ni yar taaddan mijina bace yau zaki sani, Kinyi gangancin shigowa hurumin daba nakiba, Saheeb is mine Abeeda mine alone" Kakari Abeeda keyi kaman zata mutu. Nimrah ce tace "tabbas bakisan darajar taki uwarba, dabaki zo har cikin gdanmu kinciwa uwarmu mutunci ba" A fisace Suhayr ta juyo tace "nimrah dake nake wayasa bakinki a ciki, oh baki sanni ba amma yau zaki sani bana daukan raini a wajen kowa bare ke" wanka ma nimrah mari tayi tace " Say a word again and I will show you the other meeee" tub tayi ta watsawa nimrah miyau. Kan Abeeda ta dawo tace "saidai wannan tsohuwar ta fita tabar muku dakin, amma badai gdan ubana ba Kinji". itama miyau ta watsa mata saitin bakin Abeeda. Sannan ta fice ta shige motarta saida tasa motar tayi gunji kannan ta figeta, don saura kadan ta take AbbanI novels / JARABABBEN KISHI part 26 JARABABBEN KISHI part 26 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:15 Juyowa yayi yace "tabbas wancan Suhayr ce Lafya take gudu kaman zata tashi sama?" Tabe baki yayi yace "Allah ya tsare." Tsakiyar tanka sheshen falonta ta tsaya tana huci, Tace "tabbas hakurina ya kare, Baxan iya jurewa irin abubuwan da Saheeb yakemun ba harya je ya aura kawata Koda yake bakomai Allah yana sama yana kallo ban gaxa ba, wajen yiwa mijina biyayya ba wajen sauke duk wasu hakko ki waje daya na gaza Wajen Rashin boye garwashin kishina, *JARAB EL GHIRA* (Akaro na farko da suhayr tafara karaya kenan) Saheeb baya ya farfado ya nemi Abeeda ya rasa, bai zarce koh ina ba sai gda koh a mutu koh ayi rai koda Suhayr zata yanka tsokanshi ne saiyaje ya fayyace mata komai. Abinchi takeci takeba noor abaki yana mata kwaranci, "Abba! Abba!!!" Kallonsa tayi tace "Abba baya sonmu karka sake kiran sunan Abba kaji." Hancinsa ta lakuta. "Saheeb yana tsaye yace "abbanka yana sonka sosai, karka sake kayi amfani da Kalmar umma She's rong" Dagowa Suhayr tayi da mamaki tace "what!!!!!? Mekazoyi gdannan? Kafin in rufe idona in bude Ka fit......." bata karasa ba ya rufe mata baki," *"Am going no whr suhayr you can do your worse but today you have to learn me your ears* Bantaba zatan zaki iya aikata munmunan aikin da kika aikata yauba". Hmmm wata dariyar mugunta tayi tace "koh ???". Saheeb yace "Ki tuna Allah subhanahu wata'ala yafadi acikin littafinsa mai tsarki, yace auri bibbiyu, uku uku hurhudu Sannan yace inbazamuyi adalciba muyi daya, Toh kinga inada kwakkwaran hujja ta kara aure". "Dakata Saheeb" cire hannu tayi daga cikin abinchin ta kira mai mata raino tace dauki noor kuje dakin wasa. Kusada Saheeb taxo tace "dole kasamu bakin yimun wa'azi tunda yanzu kasamu masu gdan rana, I don't blame you saheeb I never new that you are *Savege* till today, da baka da komai ai ka hkr da aure saboda jaraba dake cinka, na mamajo Saheeb inkaso kayi Hudu I don't care amma abunda nakeso Kasani, Inhar ka cuceni Daidai da kwayar zarra ban saniba toh Allah kadai zai isarmun ba mutum ba, Sannan indai anan gdan zakasa Abeeda toh bazan taba yarda ba, Sannan inaso muzauna Ayau muyi lissafi kabani uwar kudi kadauki riba, Saika ciyar damu dashi." TirkashiKISHI novels / JARABABBEN KISHI part 27 JARABABBEN KISHI part 27 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:16 Saurin juyowa yayi ya kalleta tace " kwarai yau za ayita ta kare tunda har ka iya kara aure, Nasan katsaya da kafanka kuma gdannan da kake gani na barshi nima Saidai ka kama mana haya mu biyu". Zare Ido yayi cikin rudani, nashiga uku meyasa Suhayr zata yankemun irin wannan hukuncin? "Pls Suhayr kiyi hkr kiyafemun," Tace "Ai ni bakamun ba amma kayiwa kanka, Inace kudi gareka? Kasani yanzu basai anyi nisaba, Zauna muyi lissafi gobe muje ka turamun a account dina". Saheeb bashida bakin magana Sai zufa yakeyi. Anyi lissafi ancire kudi naira miliyan biyu, Kudin da aka bashi jari, Saheeb yayi matukar mamaki ganin riba zunzurutun, riba har tafi uwar kudi yawa Baiyi mamaki ba saboda yasan cewa, ya San yadda yake tafiyar da kasuwancin shi, Murna ya dinga yi itako Suhayr bataso ba. "Toh ina saurare zuwa jibi Don baxan zauna a cikin gdannan ba, Gdanka nakeso inzauna bana ubana ba, Sbd ko wacce mace da gdan miji take takama ba gdan uba ba." "Toh" yace tunda yaga ta sauko, tashi yayi yace "zani gdan umma,Da sauri tace "Wace umma look man you are not going any whr we are sleeping together Harsai ranan daka sama mana gda mubiyu mu koma, In short koh shago bazaka budeba," Saheeb yana masifar son Suhayr shiyasa komi tayi yakanji haushi amma, sonta baya koh girgidi a cikin ziciyarsa. Gdansu Saheeb koh amarya tana chan tayi tsuru tsuru, sai hawaye ke zuba a idanunta. Kowa yaganta saita mikamai buhun tausayi, gaba daya halittarta Suhayr ta canza, Hatta hakoranta na gaba babu guda daya *"Nida ILILEE mezamuyi banda dariya, an maidata tsohuwar karfi da yaji"* Umman Saheeb ce ke lallashi, yan'uwan Abeeda duk sun zo. Umma tadinga basu hkr, Abeeda tace "yanzu wani mataki hjy ta dauka akan Suhayr?". "Wani mataki ta dauka kuwa suda sukeda sojaji da mopol da yan sanda? Ai sune gwamnati", cewa auntyn Zaria kanwar hjy saude ce aure ya kaita Zaria shiyasa ake ce mata auntyn Zaria. "Ke kinsan cewa matarsa yar iskace kika shigemai?" Abeeda tace "Aunty koda Suhayr zata kasheni ne naji nagani, zama da Saheeb ba fashi," Wage baki aunty Zaria tayi tace "Allah yabaku zaman lafya Kuzo mutafi, Ba Wanda yace kala, Sai kanwar babanta "inya samu gdan a kawo miki kayan dakin." "toh" Abeeda tace jiki ba kwari gashi ba Saheeb ba labarinsa. Musty ne yashigo yana waka, mai rabon shan wahala koh a karkashin gado yake saiya iskeshi, Kowa binsa yayi da kallo daga karshe ya fashe da dariya yace " ke kadan kika gani wahala yanzu kika fara sha, yanzu kika tsoma kafa indai Suhayr ce, kin kade, Ji yadda ta canza miki halitta wata rana kar yaki zatayi ta watsaki waje....." "Kai dakata" cewar ummansu "bansan shashanci".Home / JARABABBEN KISHI novels / JARABABBEN KISHI part 28 JARABABBEN KISHI part 28 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:18 Dariya yayi ya fice aguje. Saheeb yadamu kwarai Rashin ganin Abeedah haka itama. Neman gda yakeyi shida Suhayr suke zuwa koh ina, Anyi nasara ansamu gda a wajajen, kofar famfo. Flat ne kato mai falo biyu, akowani falo ana akwai dakuna biyu sai kitchen a ciki Suhayr tace "gda yayi kyau, yanzu zan dawo gdan mijina insakata in wala," kallon ta kawai Saheeb keyi. Yakasa cewa uffan, can yace "Yanzu hankalinki ya kwanta koh?" Juyowa tayi da sauri tace, "Ina ka taba ganin mai kishiya hankalinta a kwance? Ai har abada tana cikin tashin hankali har sai, saitaga tarabu da kishiyar nan lafya, ko kuma kishiyar ta mutu" Kasa cewa uffan yayi yace "muje insamo miki mai kwashe kaya" "Toh" tace acikin zuciyanta tace " hmmm na dauka zakayi magana ne Saheeb Dana fede ma bindi har wutsiya" Sun tare a gda daya Saheeb ya tarasu Don yayi musu fada, Sannan uwar gda ta fadi kwana nawa ta yanke? Zaa dinga raba kwana. "Dan Allah Ku hada kanku Suhayr banason tashin hankali, nayi aurene Don samun natsuwa da kwanciyan hankali, badon indinga raba fadaba,...... "Kai har kanada bakin cemun, kayi aure Don kwanciyan hankali? Daman duk zaman da mukayi daman zaman azaba kakeyi?" Saheeb yace "Ah ah Suhayr kinyi misunderstanding dinane ba haka nake nufiba".... " ai baka ba kwanciyan hankali, tunda ka iya kara aure, kwanciyan hankali sai dai kaji a makota, Kwana kuma kuya shafa kuna iya yankewa", fuuu ta tashi kitchen ta shiga tafara dafa abinci itada hawwa mai aikinta. Tuni kamshi ya bude koh ina gashi Saheeb yunwa yakeji, Tashi yayi ya fita duk akan idon Suhayr, Abu ya ruko a Leda guda daya.. " wato naka kaida amarya toh kayi kadan, kofar taje ta bude tace "Memuka samu ne Ango mijin amarya"? Bata tsaya ba ta amsa ledan taga kaza daya da kemuka, dagowa tayi tace "Ashe adalcin da kake ikirarin zakayi kenan........."HI novels / JARABABBEN KISHI part 29 JARABABBEN KISHI part 29 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:20 "Na dauki wannan ka koma ka siyo muku Wanda zakuci nima inada bakin cin kaza." bata tsaya ta kalli fuskanshi ba, ta wuce kara fita zaiyi Abeeda tace karka damu Mijina na hkr, (Tabbas indai haka zaa cigaba da zama tabbas ba adalci) Koh sauraran Abeeda baiyi ba ya fita yaje ya siyo mata wasu, Ya wuce dakinta dashi, Wani irin darene Wanda gaba daya sunkasa tantace irinsa, babu Wanda ke dokin wani cikin su, kowa bakinciki yakeyi, (Ni HUMAIRAH mezance saidai fatan azauna ayita hkr). Suhayr sallar dare takeyi kullun har kwanan Abeeda suka kare, Tana Neman tsari Allah ya kareta daga sharrin kishiya. Ya shirya tsaf zashi shago, ya fito yace "Suhayr zan fita," Tace "Allah ya tsare ya kiyayeka yabaka sa a." wani irin dadi yaji Wanda baitaba jiba, tuni ya rungumeta yayi mata"hot kiss "Zan aiko harisu anjima zai kawo muku kayan abinchi." "Toh" tace "nima zani school, kabari kawai inzan dawo zan biyo in kwashi Kayan," komai cikin gdan Saheeb yana tafiya Daidai amma fah baida wani sakewa, Saboda Suhayr ta tsaya kaida fata cewa bata yarda da cuta ba, Wata Safiyar juma'a ne Abeeda na kwance tajiyo Suhayr ta kure waka, *Romantic* na korede bello da tiwa savage Itakuma a rayuwa ta tsani jin wani sauti dazai dame jinta. Tashi tayi koh Sallama ta fada falon Suhayr direct wajen home theatre ta wuce ta zare socket din. Suhayr abun yabata mamaki, baki bude Suhayr tace "ke wace irin karyace mara sanin ciwon kai? Banshiga harkanki ba kishiga nawa? Meye matsalanki da wakana, You must be very stupid Abeeda, you heard me ryt?". Abeeda tace "Kin wani cika mana gda da sauti ki tuna nan gdan mijinane Suhayr ba gdan ubanki ba". Ta nuna Suhayr da yatsa. Tuni Suhayr ta karya Dan yatsan tace, "kinyi kuskuren sako ubana cikin wannan maganan". wayarta ta dauko ta kira Saheeb yana dagawa tace "Saheeb yanzu zanyi kulikulin "Saude" da matarka." Saheeb yayi saurin cewa "Suhayr meya faru???". Tace "Bari na gama da ita tukun sai insamu daman yimaka bayani" Yayi saurin cewa "Noo Suhayr pls don't do that." Karaf ta katse wayan Tace "yau zan nuna miki cewa nima gdan mijinane, bulala ta samu takama Abeeda tayi mata lilis da jiki tace " get out of my room" ta nuna mata hanyan fita. "Yau naji ikon Allah na hana akawoki da redio ne? Zaki takurama rayuwana Yaunaji masifa Banda kaddara data Riga fata ke kin isa in tsaya dake?". Ta dinga sababi ita kadai Saheeb ne yabaro shago yazo kafin yazo tuni Suhayr ta gama da Abeeda, Kiransu yayi gaba daya yace "Suhayr meye dalilin fadannan?" "Saheeb nan dakinane koh dakina ba" yace "kwarai naki ne". Tace "inada ryt din yin yadda nakeso koh banda shi?" Saheeb yace "kina dashi" "Shine wannan kyankyason zata zo har dakina ta kashemu wakar da nakeji?????" Saheeb ya kalli Abeeda yace "Abeeda meyasa kikeson shiga sabgar daba takiba? Karki sake koda wasa Don wallahi Suhayr bazata raga miki ba, Kowa ya zauna a matsayin sa". *Bayan shekara biyu* Saheeb arziki ya bunkasa har kasar waje yake zuwa ya daina bada sako. Lokaci guda ya kankara katon gda flat hudu , (Aiki ga mai yinka) Ga sasan yara Gana mahaifinshi, Gana mai gadi. Suhayr kam ta kammala karatu, Aiki take a GtBank. Abeeda tunda tayi aure narasa dalilin ta na tsayawa. Suhayr tuni ta kara haihuwa, yara biyu lokaci guda, da Sadiq da farouq, Itako Abeeda yarta daya mai sunan mahaifiyar Saheeb. Kwatsam Saheeb ya kara Neman aure, Suhayr tace Sam vada itama ba wata sha'awa dazata bashi, Nanfa Abeeda ta tsaya kaida fata. Itace ta shirya akwati, Suhayr tace "yau naga sabon salo tusa a loudspeaker Hmmm kishiya har wata abun zakwadi ce? Anyi aure komai normal suka koma sabon gdansu Komai na daki saida Suhayr ta canza, Harta TV irin katonnan tasa, Suhayr yace zaiyi musu kaya itada Abeeda tace bataso abata kudinta. Gida yayi albarka da yaya. Duk shekara sai Abeeda ta haihu haka ma amaryar maryam, Itakoh Suhayr tace tagama Allah shi raya mata ukun, Saida saheeb yayi mata hudu ya rufe kofa, yayi farinciki yakuma godewa Allah daya barshi a Raye ya cika burinsa,ISHI novels / JARABABBEN KISHI part 30 JARABABBEN KISHI part 30 Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:21 Kowa a cikin gdan yanabama suhayr girma, aunty kasa aunty sama. Har biyota sukeyi sasanta, Dukda tana Kishi amma daga baya taga Ashe abun ba haka yakeba, Inkayi Dacen abokan zama tabbas kayi babban sa'a Ana girma ana hankali, kannin Saheeb duk sunyi aure, haka Suhayr ta tsaya kaida fata, Amrah wan Suhayr ta aura Sulaiman, Rayuwar gdan Saheeb abun shaawa, Shikanshi girma yazo. *Noor yana Nile university dake Abuja, yanbiyu suna Turkish international college*, Ammafa fada tsakanin Abeeda da maryam anayi saboda maryam bata iya gani ta kyale, Suhayr ce tazama alkali, Maryam batada kunya haka takewa umman saheeb Rashin kunya, Suhayr tayi dariya tace "hmmm maryam kenan" ta dafata tace "Wata rana zaki bari nayi abunda yafi wannan Wallahi haka duk Rashin kunyanki nafiki, tunda kika ganni haka toh duniyace, ta horani, Naga ba sarki sai Allah abunda ake bazaa fasaba," Juyowan da maryam zatayi tace. "Bana bukatar wa'azinki, karki kuma shiga sabgan daba takiba". Suhayr ta mutu da manaki batasan lokacin data wanke maryam da mariba, tace "kinzo zamanin nayi sanyi kalau, Dabaki isa ki nunamun Dan yatsaba, Kaza kawai wacce bata gajiya da masifa Banda jaraba irinta maza me saheeb zaiyi dake? Yau nasan darajan iyaye baxan yarda kiciwa umma mutunciba, Never" ta tofa ma maryam miyau Abeeda tace "Suhayr antuna da kenan", babban abunda zatama ta wuce shine ya tofama miyau. Saheeb na tsaye yace "good Suhayr kinyimun Daidai". Da Sauri ya rungumeta. Yace "Duk cikin matana babu wacce rigimanta takaina Suhayr, tunda kikaga tayi sanyi toh Wallahi tayi Wanda yafi wannan muni, Kafin kizo." Nan ya tarsu yayi musu nasiha. Gda yadawo normal kaman da. novels / JARABABBEN KISHI part 31 the end
JARABABBEN KISHI part 31 the end
Posted by Bashir Sani Fesan on 17 Dec 2016 - 20:23
Inna-nallahi wa'inna ilaihir rajiun, Tabbas dukkan
mai rai saiya dandana mutuwa, Allah yayiwa
mahaifin Saheeb rasuwa, sanadiyan mashin daya
bigeshi, Banda yaxo da ajali, koh kujewa baiyiba.
Family din Dan-koli sunyi babban rashi inda
Saheeb yakasa zaune yakasa tsaye. Anyi bakwai
kowa ya watse, Musty shine ke kan komai na
dukiyar mahaifinsu, dayake basuda yan'uba
Bayan kwana biyu suhayr tadawo daga office
karfe shidan yanma, Tajiyo hayaniya dayake da
gajiya sallar kawai tayi ta fita, maryam tagani sai
tada jijiyan wuya take, Tana cewa "don kin tsaya
kaida fata a auroni shine me? Sai naga niba cin
amana nayiba keko, ananar kawarki kikaci kika
aure mata miji Kece keda rabon shan kunya
baniba," Suhayr takasa koda motsi kallon Abeeda
takeyi wacce take cikeda ladama, Muryar suhayr
sukaji tana cewa "maryam banda shirme irin naki,
dani da Abeeda mutu a raba takaimin kaxa, Indai
akan cin amana ne nayafe mata duniya da lahira,
Sanadiyyan aureta nayi ladaman wasu abubuwa
da dama, ciki harda. rage *JARAB EL GHIRA
(flames of jealousy)* Danayi nagane cewa Kishi
ba hauka bane, Nagane cewa kishiya abokiyar
zama ce, tabbas kaman yadda nayi dace Daga
baya Da Abeeda taxo da zafin kai daga bayaba
taga ba riba fadan da kishiya, Maryam inaso kiba
Abeeda hkr Sbd munriga munzama daya, tunda
munada zuri'a". Ana haka saiga zulaihat taho
cikeda isa da takama, Tace "tabbas aunty suhayr
kinyi gaskiya, Munrigada munzama daya saidai
fatan Allah yakara hada kan duk wasu kishiyoyi,
dake fadin duniya, yabamu hkr zama da juna
sannan ya sassauta Kishi a tsakanin mu". Gaba
daya suka rungume juna, daganan kowacce tarike
girmanta, Saheeb koh anzama Alhaji, Saida
yakaisu duka Makkah harda mahaifiyarsa, da
mahaifiyar kowace matarsa, Saheeb yana cikin
farin ciki, a cikin gdanshi burinshi ya cika,
kowacce kokarin faratamai rai takeyi.
********************* Tamat billahi ina godiya ga
Allah mekowa me komai daya bani ikon kammala
wannan Dan kankanin littafin dafatan mun karu
kuma zamuyi amfani da abunda ke ciki. COPY AND SHARED BY SAKEENAT USMAN AND MARYAM AMEERAT YOLAAA