Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, August 25, 2018

A MAKABARTA AKA HAIFENI CMPLT HAUSA ROMATIC NOVEL

adsense here
A MAKABARTA AKA HAIFENI CMPLT HAUSA ROMATIC NOVEL
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]
     
      Bismillahir Rahmanirrahim, inafarawa da sunan Allah megirma da daukaka. Yanda zanfara rubutun nan lafiya Allah yabani ikon kammalashi lfy.
     
    GARGADI..... Banyarda wani ko wata su juyamun littafi naba, ko kuma su canzamun labarina. Allah yabada ikon kiyayewa.

     GODIYA.....Ina mika godiya ta ga dukkanin masoyana wadanda nasani dama wadan da bansani ba, nagode da irin kaunar da kuke mani, duk da bazan samu damar binku inyi maku godiya ba, amma nayi amfani da wannan dama ga duk wanda yakaranta yazama amatsayin sakon gaisuwa zuwa gareshi. Allah yakara dankon zumunci.

 Season 1⚜5
        Babban mutum ne, kuma kyakkyawan dattijo wanda akalla baze wuce shekaru 50 aduniya ba,  acikin keken guragu aka turoshi wanda da alama yana fama da mutuwar shanyewar barin jiki, daga dakin gashi aka fito dashi bayan angama gasa mashi jikinshi, wanda ake masa duk bayan kwana 3.

    Sarki Qaseem ne yashigo dakin  wanda yakasance kanine ga dattijon dayake bisa kujera. Sannu Yaya yakarfin jikin? Kwalla ce tacika idonshi, wadda tariga da tazamar mashi sabo aduk lokacin dazeyi magana, Babban bawan dayake kusa dashi wanda yazama shine hadiminshi yasaka kyalle yayi saurin goge mashi idonshi.

Hannu Sarki Qaseem yadaga, nan take kowa yabar dakin. Zama yayi kusa dashi yadafa kafarshi, fuskarshi cike da damuwa, yace Yaya dan Allah kayi hkr, yakamata ace zuwa yanzu kayi hkr da abinda yafaru shekaru 18 dasuka wuce. Akullum semunsa manyan malamai sunyi addu,a akan damuwar datake cikin masarautar nan. Kuma kasan ba,a fidda rai da rahamar Ubangiji. Murmushi yayi tare da girgiza kai, yana kallon kaninnashi, wanda yake so sosai, kasancewar shikadai gareshi kuma Uwa daya Uba daya suke.

    Sarki Qaseem shima murmushin yayi ganin Yayanshi yanayi, yace tabbas Yaya yau naji dadin ganin murmushi afuskarka, wanda rabon dakayi hakan tunkafin karasa farincikinka. Segashi yau kayimun murmushi.

Dariya ce tafito daga cikin dakin, wanda wasu manyan mata ne, zaune acikinshi. Daya daga ciki tace, ai wlh Medaki kema kinsan bazan taba barin aci mana fuska acikin gidan sarauta ba, kamar yanda kikazo kika sameni acikin gidan nan shekarata nawa kika sani muna tare da Memartaba, kuma nayi hkrn zama dashi, harkikazo kika sameni, kekanki dabakiyi biyayya ba, ai da tuni nayankar maki Ticket nabarin duniyar baki daya.

 Dariya Medaki tayi tace haba Gimbiyar Babbar Gida, aini kinganni nan, tunda nataso haka Allah yayi ni, bandamu dasena zama babba ba, inde zanzama 'yar kore kuma inkarbu toni banida damuwa, zan iya yinkoma menene. Dan haka kada kidamu, koda yanzu bamune matan sarki Qaseem ba, aide kanin mijin mune. Kuma aide haryanzu muna cikin masarautar.

Gimbiyar Babbar Gida tadauki apple tasa abakinta, ta maida kallonta gurin Jakadiya, wadda take mata tausa tace, Jakadiya bamu labarin cikin gida. Jakadiya ta gyara zama tace Allah yatemakeki Babbar Gimbiya, wadda babu kamarta, ba,ayi ba, kuma baza,a tabayin kamarki acikin gidan nan ba. Allah yakara tsawon kwana. Babu wani labarin daze firgitaki acikin gida, kinriga dakinsan Gimbiya Shuwa haryanzu bata yarda dani ba. Narasa dalilinta nayin haka, ace mace duk wani hali irin na mijinta Sarki Qaseem tadaukeshi. Kodan ita tata sarautar gado ce, shiyasa bata yarda da kowa? Medaki tace haba Jakadiya atunanina babu wani abu daze baki tsoro acikin masarautar nan, kinsan ketamu ce, muma haka. Dariya tayi tace hakane, Gimbiya, karku damu asannu zakusha labari.

Zaune take cikin wasu kodaddun kaya, acikin wata bukka ta kara, wadda take daga gefen wata tsohuwar MAKABARTA. Wani  tsohon kwanone ahannunta,abinci ne, aciki wanda gaba dayanshi bewuce rabin kwanonba. Kyakkyawar matashiyace wadda bazata wuce shekaru 18 aduniya ba. Akusa da ita wata dattijuwa ce, wadda itama bazata wuce shekaru 38 aduniya ba, da kaganta zakasan tana cikin yanayi na hauka, gaba daya kamanninta sun bata. Jawota diyarta tayi tana mata magana irin ta kurame, tana mata nuni da kwano alamun taci abinci.
     Dariya Uwar tayi cikin halin hauka tace a,a Babyta yau bazanci abinci ba, kece zaki faraci, dariya yarinyar tayi mata, dan taji abinda tafada, sede kawai maidawa ne bata iyayi (KOMEYE DALILI🤔 OHO🤷🏻‍♀ MUJE ZUWA).  Matsawa Wadda naji ankira da Baby tayi kusa da Mamanta tasa hannu tafara bata abincin, itama hannu tasa tana bata abinci. Kwalla ne, suka zubo ma baby tayi saurin gogewa.

Wani Kyakkyawan Matashi ne, me kama da Larabawan Shuwa, baze wuce shekaru 25 aduniya ba, da Sallama yashiga dakin kyakkyawar matar, wacce take kishingide abisa kafet din dakin. Murmushi tayi tace, Yarima Arif sannu dazuwa. Kwanciya yayi kusa da ita yace yauwa Momy na, sannu da hutawa. Kallon bayin cikin dakin tayi, lokaci guda suka fita, Madarar shanu tamiko mashi, ya amsa yana murmushi, yace Momy naje gurin Abba ance yana dakin ganawa da baki, kuma inason magana dashi. Kanshi tashafa tace to ai sekayi hkr kajira yagama ko, wace irin magana kakeson yidashi? Momy dama akan rashin lafiyar Baffa ne,tunda nadawo naga yakamata ace anfitar dashi waje ko za,a dace. Murmushi tayi tace Arif bakasan komai akan ciwon Yaya ba, Abbanka yana kokari sosai amma koma menene idan yafito zamu gana dashi. Kwallan idonta tagoge.
   
     Kubiyoni domin jin labarin masarautar.

Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
    (Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ...🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 5⚜10
    Zaune suke adakin memartaba sarki Qaseem, Areef yadora kanshi asaman kafar Abbanshi, Gimbiya Shuwa Momyn Areef tana kusa da Sarki tana gyara mashi Inibi tana mika mashi. Sarki yashafi kan Areef yace Yarima inajinka wace magana kakeson kafadamun?

Tashi zaune Areef yayi yadauki inibi yasa abakinshi yace Abba dama akan maganar Baffa ne, naga yanda nabarshi haka nadawo nasameshi, shine nace meze hana afitar dashi waje koza,a dace. Murmushi Sarki yayi yace wlh Yarima nafika son inga Yaya yawarke, kozamu samu damar yin bincike akan babbar matsalar datayi sanadiyar shigarshi wannan halin. To amma Abba baka ganin fitar dashi ze iya temakawa gurin samuwar lfyrshi tunda acan sunfimu kayan aiki?

Hakane Yarima, amma babu yanda banyi da Yaya akan yabari afitar dashi ba, yakiya gashi ba magana yakeyi ba, sede yana jin duk abinda muke fada, yana ganin kamar gara abarshi yayi tazama haka, wanda kuma hakan bashine mafita ba, dole se mutum yana da lfy yake iya komai arayuwarshi, ni babban damuwata wadancan munafukan matan nashi, danni wlh haryanzu banyarda dasu ba. Gimbiya tace hakane Me martaba, sede kasan bamuda wata hujjar dazata nuna mana sune sanadiyar faruwar komai agidan nan, kamarde yanda kace acigaba da addu,a hakan zamuyi, fatanmu de Allah yasa Fulani da abinda ke cikinta koma menene, yasa suna raye, kuma cikin koshin lafiya.

  Sarki yace amin. Kallon Areef yayi yace Yarima yanzu angama karatu gashi zaka fara aiki kaga dole ace kaima kashigo sahun manya ko? Kwantar da kanshi yayi saman cinyar Gimbiya ya lumshe idonshi, shiru yayi bece komai ba. Gimbiya tace Yarima yanaji kayi shiru kode boye mana surikar tamu kakeyi? Murmushi yayi sosai wanda har seda dimple dinshi ya lotsa duka 2, yace Momy kubar maganar nan, niharyanzu banga macen danakeso ba. Sarki yace aiko Yarima yakamata ace kafara nemanta, dan kasan bazamu barka kazauna haka ba, atsarin masarautar nan kasan baza,a barka kazauna haka ba, damma de Yaya beda lafiya, ai da tunkafin kadawo anduba maka acikin 'ya'yan sauran masarautun ansama maka mata.

Dariya Areef yayi yace haba Abba niko aure zanyi ai banason yar gidan sarauta, nafison insamu mace wadda bata tashi acikin sarauta ba, kuma nibanason mace wadda zatazo tarika rainamun iyaye, kawaide akaramun lokaci ahankali zansamo wata wadda ra,ayina yayi dede da ita.

Harararshi Gimbiya da Sarki sukayi atare, Sarki yace uhm Yarima idanma mafarki kakeyi to kadena, acikin masarautar nan babu yanda za,ayi kashigo mana da bare, dole se yar sarauta, kana ganin yanda Momynka dani kaina muka fito daga gidan sarauta, jininmu gaba da baya cike yake da sarauta, kai kuma yanzu sekafara zuwa mana da wani batu. Ka godema Allah Yaya beda lfy, da kila seyafini daukar zafi akan wannan magana taka.

Duk da shima matar daya aura ta 2 data 3 basu fito daga cikin gidan sarauta ba, amma kowa yayi mashi uzuri, matarshi ta 2, agidan nan kowa yasan yanda akayi ya aureta, haka ma ta 3 dole ce tasashi ya aureta, sekuma babban rabon daya shiga tsakaninsu, bayan wannan babu abinda zesa Yaya ya auri wata mata wadda ba,a gidan sarauta ta taso ba.

Gimbiya tace Allah yahuci ranka Me martaba, banason ranka yana baci akan wannan maganar, abinda bamu taba yima Yarima agidannan ba, Fada shine yau da bakinka kake mashi, kaima kasan Yarima mebin duk wani umarninmu ne, ai base anbata mashi rai ba, sekasashi shiga damuwa, wanda kuma betaso acikinta ba, karka manta mungina rayuwarmu abisa soyayya dan Allah kada kabari zafin zuciya yacanza maka zuciyarka. Sarki yakamo Areef wanda idonshi har yayi ja dan bacin rai.

Kwantar dashi yayi saman kafarshi yana shafa kanshi yace ba ina nufin bata maka rai bane, kaji, kawai ina maka tuni da ra,ayin masarautarmu ne, banaso kasa wannan aranka haryadameka. Hawayene suka zubo daga idon Areef, cike da damuwa Gimbiya tamatso kusa dashi tace kagani ko, kalli abinda kajawo mashi, yaushe rabon da Yarima yayi kuka agidan nan? Inajin tun yana yaro, jawoshi tayi tamaidashi saman kafarta tace Ya isa haka Yarima na, kasan Abbanka yana sonka baya son bacin ranka yishiru hakanan.Sarki yace ya isa haka maganar tawuce kaji, amma kaima kaje kayi tunani.

Lumshe ido Areef yayi, aranshi yana fadin akwai babban aiki agabana, kuma gaskiya yanda ra,ayina yake bazan taba canzashi ba, bana bukatar yar sarauta, duk da haryanzu bansamu wadda nakeso ba, amma zantajira seranan dana samu sannan, nasan suna sona, dole zasu barni na auri ra,ayina. Amma dole nacirema su Momy wannan ra,ayin nasu.

Anesa da masarautar Sarki Qaseem, wani dankaramin gidane, me kyau, duk da karami ne, amma anyi mashi gini mekyan fasali. wani tsoho ne, fari, yafito daga cikin gidan, daka ganshi zaka gane ba asalin bahaushe bane, yafi kama da irin larabawan dasuka baro garinsu sukazo nigeria har zama yakamasu anan, zama yayi bisa wata kujera dake kofar gidanshi ya kunna redio yana kokarin kamo tasha.

Tundaga nesa yahango fadawan sarki suna zuwa, murmushi yayi, cikin hausarshi wadda bata gogeba, yace aikin kenan, kullum azo adameni da kira, kuma haryanzu ankasa samo mani Diyata, da abinda ke cikinta. Kwallar data zubo mashi ce yasa hannu yagoge. Da sallama suka karaso gurinshi, ahankali ya amsa masu. Daya daga cikin fadawan yace Barka da hutawa Baba, yace yauwa sannunku, yauma wani kiran neko?

Murmushi Bafaden yayi yace a,a Baba, dama Sarki ne, yace muzo mukawo maka kayan abinci. Murmushi yayi yace to madalla, nagode, yajikin me martaba? Bafaden yace to Baba dasauki zamuce, kasan sauki sede agurin Allah, fatanmu de Allah yanuna mana inda Gimbiya take ko zamu samu Hankalin kowa ya kwanta. Baba yace addu,a kam kullum munayinta, sede haryanzu acikin raina nakasa yarda cewa Rayhana itace tabar gidan Sarki da kanta, kuma nakasa yarda cewa bata raye, inaji ajikina wata rana zamu gana da ita, fatana de Allah yasa kome tahaifa ace yana raye. Sukace amin Baba, bara mushigar maka da abincin ciki, yace tonagode, dama gashi bayin dasuke dafamun abincin sungama aikinsu suntafi, kushigarmun dashi ciki.

Jakadiya ce take tafaman Sallama abangaren Gimbiyar Babban Gida, daga ciki akace shigo mana Jakadiya, tace Gafaranku de, ai nadauka ko bacci kikeyi, Allah yatemakeki Babbar Gimbiyar Sarki, Allah yakaramaki lafiya da tsawon kwana, Allah yabaki muma musamu awajenki, ke kadaice Babbar mata agurin Sarki, duk wanda yazo sede yabiyo bayanki. Daga gefe Gimbiya me Daki tarika wurga mata harara jin irin kirarin datakeyi ma Kishiyarta.

Murmushi Gimbiyar Babban Gida tayi tamata nuni data zauna, guri tasamu tazauna sannan takalli Gimbiya medaki tace Ina gaisuwa ranki yadade. Murmushi tayi tace sannu Jakadiya, daga ganin bakinki akwai magana, meke tafe dake?

   Babban labari ne yake tafe dani kuwa Gimbiya. Dazu nazo wucewa tagefen Dakin memartaba Sarki Qaseem, senaji yana magana kamar yana fada, dajin haka nayi saurin daukar tsintsiya nayi kamar ina shara, sede na boye fuskata, gudun kada aganni tunda ansan ba,a bangarensu nake aiki ba, asalima nice mebada umarnin ayi aikin........ nan takwashe duk abinda taji sunfada ta fada masu.

Tashi zaune Gimbiyar Babban Gida tayi, tace gaskiya naji dadin wannan labari naki Jakadiya, dan haka kina da kyauta me tsoka. Washe baki Jakadiya tayi tace godiya nake Gimbiya, Allah yakara girma. Amma Me daki wace irin shawara kike ganin yakamata mubi don mu samu muyi amfani da wannan dama?.

Gyara zama tayi tace, inaganin tunda har Sarki ya furta Bayason Yarima ya kawo mashi bare, meze hana kisamo daya daga cikin matan gidan sarautarku kimaidota gidan nan. Murmushi Gimbiya tayi tace Medaki kenan, kina tunanin Gimbiya Shuwa zata bari Yarima yaso wata data fito daga bangare na? Kinfi kowa sanin bama ga maciji da ita, dan haka wannan shawara taki bata karbu ba. Jakadiya kawo mana mafita.

Kara hade rai Medaki tayi jin ba,a karbi shawararta ba, sede yata iya, tunda bata da karfi agidan, dole tabi asannu kodan tasamu fada. Jakadiya tace Gimbiya inaganin tabayan gida yakamata mubiyo masu, tunda bazasu taba karbar abinda yafito daga gurinki ba,kamar yanda mukayi da farko yanzuma hakan yakamata ayi. Kayataccen murmushi Gimbiya tayi tace haka nake sonki Jakadiya. Allah yakaimu.

Yarima Areef ne kwance adakinshi, shida abokinshi Haisam, suna fira, Haisam yace Yarima yanaga kamar wani abu yana damunka? Yamutsa fuska Areef yayi yace kawai kabari Man, wlh jiya Abba da Momy suka kusa samun hawan jini. Dariya Haisam yayi yace uhmm nasan wasa kakeyi, yanda Abba Da Momy suke sonka, harzasu iya bata maka rai, kaifa agurinsu haryanzu yaro ne, dan haryanzu baka girma da hawa cinya ba. Areef yace banason sharri, idan wasu sukaji kace hawan cinya ai sesu dauka rungumeni akeyi.

Dariya suka saka, Areef yace wlh Man ba maganar wasa ba, aide kasan irin burina akan matar danakeso na aura ko? Yace E, yauwa to jiya daga nafada masu kalar matar danakeso shikenan, suka rufeni da fada, kasan ai ra,ayin momy da Abba duk daya ne, kuma nasan wannan magana dasuka fada harcikin ransu. Haisam yace kada kadamu, kaida ko matar ma baka samuba, meye naka na damuwa?.

Areef yace kaide ai dole nadamu, kasan me kwarmin ido dawuri yake fara kuka. Haisam yace abinda nakeso dakai, addu,a zaka cigaba dayi domin itace mafita, nikaina bana maka sha,awar auren macen gidan sarauta, kasan mata da sarauta, basu iyata ba, nafison kaje waje ka auri wata daban, hakan zebaka kwanciyar hankali sosai. Areef yace nima ai jinsu nakeyi, dan bansamu wadda nakeso bane, shiyasa nayi shiru, amma duk lokacin dana samu, agskiya sede kowa yayi hkr, dan bazan iya biyayya anan gurinba. Haisam yace muje mugaida Baban Umma fulani kwana 2 bamuje ba, tashi Areef yayi yana fadin wlh nima yana raina, dan bakaramin tausayi yake bani ba, ace mutum yazo gari da iyalinshi amma yanzu beda kowa, matar ta mutu diyar kuma babu wanda yasan halin datake. Muje mudawo, dan dazu waziri yake fadamun gobe zamuje  darazo wai Abba ze aikemu. Haisam yace kai gsky zanje, nima inason zuwa Darazo, fita sukayi suna dariya.

Washe gari tunda safe suka dauki hanyar bauchi, daga can suka wuce darazo,  tare suke da Jakadiyar Gimbiya Shuwa, dan itama garinsune shiyasa tabiyosu tanason tayi kwana 2. gidan wani babban malami sukaje, kuma dama shine malamin dayake masu addu,a akan batan matar Sarki Fulani. Bayan sungama gaisawa, suka fadi sakon Sarki, malam yace haryanzu muna nan muna addu,a sede kuma babu abinda ya nuna mana bata raye, akullum muna ganin tana raye, kuma akusa damu, danni abinda nake gani tafi kusa dani akan inda kuke, to Allah shine masanin gaibu, shikadai yafimu sanin gsky. Zamu cigaba da addu,a har Allah yasa mudace.

    Ruwan addu,a yabada akaima Tsohon Sarki, godiya sukayi mashi, Waziri yasa fadawa suka shigo da kayan dasukazo dasu. Waziri yace to muzamu koma. Malam yace tonagode, kallon Jakadiya yayi yace ammade Jakadiya ke anan za,a barki kidan mana kwana 2 ko? Tace E Malam, dama cewa nayi inzo inganku. Yace to ai yayi dede kishiga daga ciki. Tashi tayi tace to Yarima Allah ya kiyaye. Yace amin sekin dawo.

    Bayan suntafi wani tsoho yazo yace yanason ganin malam, malam yace ashigo dashi, bayan sungaisa Malam yace Baba meke tafe da kai? Tsohon yace wlh wata magana ce take tafe dani, nadade inaso inzo insameka amatsayinka na babban malami agarin nan, duk da ba,a cikin gari nake ba, amma inada labarinka, nine megadin MAKABARTAR datake wajen gari. Akwai wani abun mamaki dayake damuna, wanda yadade yana faruwa, sama da shekara 18, akan wata mata da diyarta. Malam yace Baba inajinka bani labarin abinda kasani.

   Kubiyoni zakuji yanda komai yake. Nagode da kaunarku.

Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
   (Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 10⚜15
      Malam yace inajinka Baba, dama Allah gafarta malam, tsawon shekaru 18 dasuka wuce nakasance ina gadi a MAKABARTAR bayan, gari, akwai ranar danayi rashin lafiya har kimanin tsawon sati guda banje gurin gadi ba, arana ta 8 danaje, inadan zagaya MAKABARATAR. Can daga nesa da ita naga wata rumfar kara, wadda daga gani kasan bata dade dayi ba, kuma gsky malam rumfar bawata rumfar arziki bace, dan ansha yin ruwan sama tana yacewa, sede abun mamaki da gari yawaye zan iske anmayar da ita.

   Ganin wannan rumfa danayi bakaramin tsoro naji ba, dan tunda nake gadi rumfata ce kadai agurin, matsawa nayi abin mamaki malam senaji kukan jariri aciki. Bayan nayi addu,a sena karasa gurin. Inazuwa daga ciki nahango wata babbar mata me alamun tabin hankali tana rike da yarinya ahannunta.

Da sallama nashiga gurin, saurin dagowa matar tayi tana kallo na, guri nasamu nazauna, nace baiwar Allah mekikeyi acikin MAKABARTA kuma hada yarinya jaririya?  Kawai senaga tanamun dariya, malam abinda na lura wannan yarinyar diyarta ce, dan agabana naga tafiddo nono tana bata.

Ganin wannan mata bazatayi mani magana ba, kawai sena fita , cikin rumfata naje nadauko abincin danaje dashi nakoma nakai mata. Inazuwa na iske yarinyar hartayi bacci, matar namika ma abinci, segashi ta amsa tana dariya, zama nayi harta gama namika mata ruwa tasha, kallonta nayi nace baiwar Allah kozaki bini gidana inkaiki keda jaririyarki? Saurin kallona tayi tana girgiza kai, nace ba cutarki zanyi ba, amma akwai hadari azamanki gurin nan.

Kuka naga tafara tana kara rike diyarta, haka nayita lallashinta hartayi shiru, ganin idan nakara mata magana zatayi kuka yasa nafita nabarta. Ganin har magriba tayi duhu yakarayi se tausayinsu yakamani, komawa nayi nasameta rike da diyarta, sun kwanta. Maganar dazu nakara yimata. Amma abun mamaki seta samun kuka, kamar daga sama naji wata murya tafara magana.

Yakai wannan bawan Allah me tausayi, kasani kamar yanda kayi niyar temakon wannan mata da diyarta, muma haka muke temakonta, kuma kaci sa,a dakazo da niyar temako, dan munyi alkawarin duk wanda zezo da niyar cutar dasu bazamu kyaleshi ba. Wannan mata haka Allah ya kaddaro mata rayuwarta agurin nan, kuma tunda ba,a sonta mu muna sonta, dan haka babu wanda zamu bari yadauketa agurin nan. Kabarta, Allah yana tare da ita, kuma muma muna tare da ita, amma tunda kaima mazaunin gurin nan ne, zaka iya temaka mata. Bakasan komai game da ita ba, mune muka sani, dan haka munaso kabarta kamar yanda ka ganta, shiyasa aduk lokacin daza,a kawo wata gawa babu wanda yake cin sa,ar ganinta.

Malam tunda naji wannan magana na tabbatar ma kaina lallai ba Bil,adama bane suke magana aljanune, hakan yasa na kyale matar nan, dan sunce basu san na matsa mata da tambaya, haka muka cigaba dazama a MAKABARTA tare dasu, yanda suka umarceni kada infadama kowa, haka nayi shiru ko medakina ban fadamawa ba, sede yan kayan diyana mata harma dana medakina idan naga sun tsufa nakan dauka ince mata wasu zan kaimawa.

Tun ina tsoron zama dasu har muka saba sosai, kuma ina kokarin bata abinci, sede duk sanda naje inasamu kamar taci abinci, dayake akwai rafi agaba damu, haka nasamu bokiti ina kawo masu ruwa ina aje mata, dan naga ita kezuwa tana dibar ruwan dakanta, kuma acikin wata karamar robace. Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya, har wannan yarinya tayi wayo, da kaina naje nace tadena bata nono, nadauki yarinyar nafara bata abinci, daga nan tafara cin abinci.

Aduk lokacin dana tafi daniyar fadama wani wlh malam dana dawo zan iske bata gurin, setayi kwana 2 ko 3 bata dawo ba, haka suka kara jamun kunne akan inyi hankali, tunda har aka haifi yarinyar nan agurin to nanne gurin zamansu, duk ranar dana kara kokarin fadama wani duk abinda yafaru dani ni najama kaina. Haka na hakura mukaci gaba dazama, amma harcikin raina na kudurta sena temaka masu, dan abinda suke masu ba temako bane, duk da agurinsu suna ganin kamar temakonsu sukeyi, amma abinda nagani taya za,ayi dan adam yazauna a MAKABARTA kuma ace anan ze rayu.

Ganin idan nacigaba da matsa masu zan iya rasasu kuma bansan inda zasu kaisu ba, yasa naja bakina nayi shiru, dannasan wata rana zantemakesu. Haka muka cigaba da rayuwa, munyi sabo dau sosai, diyarta tayi girma sosai, ganin yarinyar tayi girman daza,ace tafara sanin addinita yasa nace bari infara koyamata daga cikin abinda nasani, duk da nima bawani ilimi mezurfi gareni ba, amma Alhamdulillahi inada dede gwargwado. Dayake tunbayan daya kamata ace yaro yafara magana yayi, amma shiru ita yarinyar wadda Innarta tarada mata Baby, amma nikuma ina kiranta da yar Baba sbd munshaku da ita sosai, tun lokacin dana gane bata iya magana, sena lura da idan Innarta tayi mata magana tanaji, kuma nima haka, tun alokacin nagane yarinyar tanada matsalar rashin magana, wanda bansan dalilin hakan ba, dan duk kurman dana sani inde ba harshenshi ne yadatse ba, zaka sameshi bayaji, kuma baya magana, amma ita nata seyazo dasabani.

Haka muka rika maganar kurame da ita amma idan itace zatamun magana, amma idan nine zanyi mata lafiya lau zanyi tunda tanaji. Dun daga wannan lokacin muka fara karatu tundaha sarki harzuwa sallah da karatun da akeyi, sede nine kawai nake koya mata, idan bata gane ba, tanamun alamu.

    Mahaifiyarta wani lokaci se inga tazauna tana ta kuka wanda idan tafara batayin shiru seta dauki lokaci, konaje zan bata hkr yar Baba zatamun alamu da in kyaleta, alokacin da girma yazo ma Yar Baba haka nazaunar da ita nakoya mata yanda zata gyara jikinta, da abinda zata bari na ibada, da kuma yanda zata tsarkake jikinta idan lokaci yazo. Wlh malam hankalin yarinyar da natsuwarta kadai ya isa yasa tashiga ranka.

 Hatta da kitso wannan matar ita take yimata, sede ita matar bata bari agyarata, shiyasa idan kaganta zakaga gaba daya tafita hankalinta. Ko ciwo yasamesu nine nake samo masu magani, amma wadannan aljanu basu barin ko matar tabar cikin MAKABARTAR, iyakarta bakin rafi, shima tunda nake dauko masu ruwa tadena fita.

Akwanakin baya nayi rashin lafiya wadda ta tadamun hankali, banyi tsammanin zan tashi ba, kullum tunanina yazanyi da wadannan bayin Allah. Inacikin ciwon nasamu na tafi MAKABARTA gurinsu, haka naje nasamu Yar Baba duk tarame, kuka kawai takeyi, tana ganina ta taso da gudu tazo tana murna, alokacin nagane dalilin kukanta, harta da ita Matar marar hankali seda tayi ta murna. To malam bayan nawarke kuma nafara tunanin yanda zanyi, shine nasamu labarinka, nikuma nayi alkawarin zanzo gurinka, duk da ayanzu bansan wane mataki aljanun zasu dauka akaina ba, kuma zamuje musamesu, ko kuwa sun daukesu. Wannan shine babbar damuwar dana taho ina tunani.

Salati malam yafarayi, da tasbihi jin wannan al,amari. Gyaran murya yayi yace tabbas Baba kazo da magana me ban al,ajabi, kuma kaima kayi kokari sosai, wanda bakowane ze iya abinda kayi ba, lallai duniya babu gsky, tsoron Allah yayi karanci aduniyarmu da zukatan mutane, yanzu dan Allah ina wanda yakeda alhakin haukatar da wannan mata zesa dumbin zunuban daya dauka nata ita da yarta har na tsawon shekaru 18?.

Innalillahi Wainnailaihirraji'un. Yanzu Baba abinda nakeso da kai, ka kwantar da hankalinka, insha Allahu babu abinda ze sameka, kuma zamuje musamesu a inda kabarsu, addu,a zata temakemu akan wadan nan aljanu, kuma zanyi magana dasu, dan suma basuda niyar cutar dasu, asalima suna temakonsu ne. Bara inkira sauran dalibaina su shirya muje musamesu, amma ai bazamu bar bayin Allah acikin daji ba, kuma a MAKABARTA. Kodan lafiyar ita yarinyar.

   Tashi yayi yakira yaranshi yafada masu su shirya zasuje wani guri, koda yadawo, yasamu Baba yana jiranshi, haka suka dauki mota yasa aka kira Jakadiya da matarshi suka shiga, dan sutemaka masu gurin daukosu. Baba addu,a kawai yakeyi Allah yasa su samesu, agurin.

  Nima nace amin Baba.

Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
  (Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 15⚜20

   Hankali tashe Baba yafito daga motar yanufi inda rumfarsu take, amma abun mamaki babu ita babu dalilinta, idan ba wanda yasan da ita ba, babu wanda zece mutane sun taba zama agurin. Wasu irin zafafan hawayene suka fara zarya afuskarshi yan fadin Innalillahi wainna ilaihirraji,un. Zama yayi adede inda rumfar take yana kuka.

Malam ne, yakaraso gurin yadafashi yace Baba ba kuka yakamata kayi ba. Insha Allahu nizan dawo dasu duk inda sukaje, dama munsaba da aljanu, masu taurin kaima ina gogawa dasu, har kafiran cikinsu muna fama dasu, bare kuma wadannan da alama musulmai ne. Baba yace wlh malam, da,a ace sun dauke su Yar Baba bansan inda suke ba, gara ace banfada maka ba, muyita zama dasu anan har mutuwa tazo tasamemu. Tsautsayi ne, da kuma tausayi yasani karya dokar dasuka saka mun.

Shiru malam yayi, can ya kalli daya daga cikin yaranshi yace daukomun shinfida acikin mota kataho mun da gorar ruwa, bayan yakawo mashi ya amsa yafara alwala, shikuma ya shinfida mashi abin sallah. Kallonshi yayi yace kacemasu Jakadiya sukoma mota suzauna harsenace sufito.

Sallah yafara yi, kowa yana kallonshi, seda yayi raka,a 4 sannan yazauna yafara karatu, da yayi seya tsaya yayi adduo,i sannan yacigaba. Seda yadauki tsawon minti talatin, sannan wata kura ta taso kafin wani lokaci sega rumfar su Yar Baba ta bayyana agurin datake. Hamdala malam da Baba sukayi, dasauri Yar Baba ta iso kusa dashi tana dariya. Daya daga cikin yaran malam, wani yace Tsarki ya tabbata ga mahaliccin dayake tsara halittun bayinshi. Anya wannan yarinya mutum ce? Aini tunda nake bantaba ganin yarinya me kyanta ba, damma wai tana cikin rashin galihu, wannan da,a birni take gidan masu kudi ai se anrika boyeta.

Dariya nakusa dashi yayi yace kaima kenan dakake iya magana. Baba se shafa kan Yar Baba yakeyi yana murmushi, ita ko tashige jikinshi don da alama tsoron mutanen gurin take, dan atsawon rayuwarta bata taba ganin kowa aduniya ba, daga Mamanta se Baba. Mamanta kuwa kasa fitowa daga runfar tayi, se kuka takeyi.

Malam yace Alhamdulillahi, Allah mungode maka, kallon gefenshi yayi yace bayin Allah, meyasa bakuso atemaki wadannan mutanen? Kowa yafara kallon inda malam yake magana, sede babu alamun kowa agurin, maganar mutum daya tafara tashi me cike da alamun ladabi.

Allah yagafarta malam, mundauki tsawon shekaru 18 muna tare da wadannan bayin Allah, mune muka temaki wannan mata, alokacin da takusa halaka, wanda babu wani dan adam daze iya temakonta, semu, kuma ga dukkanin alamu munga kamar hadari ne, ya jefota gurin datake, sede koda muka bincika bamuga alamun mota tayi hadari ba, asalima mugunta akaso ayima wannan mata. Shiyasa muka temaketa, sede haryanzu Allah bebamu ikon gano dalilin daya kawota nan ba, kuma babu wani asiri ajikinta, wannan lalurar datake tare da ita da alama kode ajikinta take, ko kuma buguwar datayi ne yakawo mata ita. Malam yace naji, amma me kuka sani game da ita? Tsawon shekaru 18 dasuka wuce wata rana da dare muna zaune afadarmu.

      Se kawai mukaji fadowar wani abu akusa damu, sede abun mamaki, muna dubawa semukaga mace ce da tsohon ciki, kuma cikin ikon Allah babu abinda yasamu cikin, anan muka kara dubawa semukaga tabbas bil adamace, anan nasa yarana dasu dubamun ko hadari ne akayi, dayake akasan wani rami muke, hakan yasa nayi zaton ko hadari ne, dan wani lokacin idan akayi hadari mutane suna fadowa nan. Bayan yadawo yace mun babu wata mota datayi hadari, kafin mu ankara semukaji wannan mata tana nishi da karfi, nan take nagane haihuwa zatayi, anan nasa akayima me dakina magana.

Allah gafarta malam, ita dasauran wasu jinsinmu suka temaka mata harta haihu, sede koda ta haihu bata cikin hayyacinta, haka suka gyarata ita da diyarta, aka samo kaya aka samata, anan nace su kwantar da ita kusa da mahaifiyrta. Dayake safiya takusa, haka muka tashi mukabarta agurin ita da yarinyarta, anufina idan gari yakara haske kila wasu suganta sutemaketa.

      Bayan dare yakarayi muka sake dawowa fadarmu, abun mamaki kuma bamuga wannan mata ba, senayi tunanin wasu sun daukesu, muna nan zaune sega daya daga cikin yarana yazo yacemun ahanyarshi tazuwa nan yaga anyi wata runfa agefen wata MAKABARTA sede yar karama ce akayi, daya kara matsawa seyaga wata jaririyace kwance acikin rumfar, saman hakukuwa anshinfida mata zani tana bacci, daga waje kuma wata mata ce kwance agaban rumfar, dan tayi masu kadan bazasu iya shiga su 2 ba, asalima rumfar yara ce, abinda yabashi tsoro yaga wata halitta daga cikin jinsinmu sede basa cikin zuri,armu wato musulmai, yaganta tana kokarin daukar yarinyar.

Shine yaje gurin dasauri, to dayake sunsan kowaye kuma suna tsorona, yana ganinshi yayi saurin bacewa. Shine yazo yana fadimun, koda nasa adauko munsu senaga wannan matar ce tajiya, nan take tausayinta yakamani, anan nayi alkawarin kareta ita da yarta kuma babban dalilin dayasa nabarsu aMAKABARTA, sbd bazeyiwu nakaisu cikin jinsina ba, haka kuma nagane bil adama basuda tausayi harsuka iya barin wannan mata ita da yarta acikin daji babu metemakonsu, shiyasa nasa yarana suka yimata rumfa babba wadda zata isheta ita da yarta, kuma nasaka yarana suzama masu gadinsu.

Kasancewar bata da hankali yasa abubuwa da dama mune muke temakonta dasu, tundaga abinci dakuma ruwa, na hana yarana subarta tafita daga MAKABARATAR, sbd ina gudun kaidin bil adama, ko gawa aka kawo babu wanda yake iya ganinsu, nina zaba masu suyi rayuwarsu ahaka. Aranar da megadi yazo lokacin yarana suna sallah, basuyi tunanin wani zezo ba, hakan yasa shima yayi sa,ar ganinsu.

Danaga shima yanada zuciyar imani hakan yasa na kyaleshi yacigaba dazama dasu, sede banyarda yafadama kowa ba, dan nasan zuciyar kowa daban take, kuma yayimun alkawarin baze fada ba, mune muke daukesu aduk lokacin dayayi niyar fadama wani. Koyanzu yaci sa,a kaine yafada mawa, amma daba kai bane, yanda muka daukesu nayi niyar bazan ajesu anan kasar ba gaba daya, gara nakaisu wata kasa inda babu wanda yasansu, nasan zasu temakesu. To malam wannan addu,ar dakayi ita kadai tadawo damu. Kuma nayima Baba hakuri tunda naga alkhairi yakeson su dashi, yanzu Malam kome kayanke zamubi umarninka, amma kasani duk inda zaka kaisu kada karabasu dan yarinyar nan bazata iya zama awani guriba batare dasu ba. Kaima Baba kasan yanda kuka shaku.

Malam yace naji dukkan bayaninka, kuma naji dadi sosai daya kasance kaine katsinci wadannan bayin Allah, nasan irin halin temako dakake dashi bazaka taba barin wani abun cutarwa yasamesu ba. Allah yabiyaka kaida yaranka, hakika zakaran da Allah yanufa da cara, to ko ana muzuru ana shaho seyayi. Tabbas wannan yarinya Allah kadai yasan irin alkhairin data debo kuma shine yaraya abunshi. Yanzu abinda nakeso infada maka, gaskiya zaman yan adam agurin nan beyi ba, saboda rayuwar gaba, kaga wannan yarinya tagirma, yakamata ace tashiga cikin mutane, dan kada wata rana tafi haka girma ace zata koma cikin mutane abun ya gagara, kalli yanda take cike da firgici sbd ta ganmu wanda banga laifinta ba, nasan bata taba ganin kowa ba, se mutum 2.

Dan haka nayi maka alkawarin zandaukesu zamuje mu sama ma wannan mata magani, duk da kace ciwonta babu asiri ajiki, zamukaita asibiti aduba lafiyarta, kuma nizan rikesu tamkar jinina. Nagode sosai daka fahimcemu. Godiya sosai Malam yayima wannan shugaban aljanu sannan yabace.

Malam yace to Baba kajide yanda mukayi dashi, yanzu yakake ganin za'ayi? Baba yace naji dadin abinda kayi, kuma dama abinda nake fata kenan arayuwata inga ranar dasu Yar Baba zasu bar gurin nan, shiru yayi yana goge kwallan idonshi. Malam yace yanzu kutashi muje gida semusan abinyi. Jakadiya da matarshi yasa sukamo maman Yar Baba, tana ganin zasu dauketa tafara kuka sosai, da kyar suka kamata, shima seda Baba yaje yakamota yarike hannunta dana Yar Baba sannan ta bisu, gurin shiga mota kuka Yar Baba tasa masu, tsayawa tayi takishiga motar, duk tarike Baba, dakyar yasamu tashiga, haka suka nufi cikin gari.

Zaune suke afadar Sarki Qaseem, Waziri yamika gaisuwa tare dafadin Allah yatemakeka, munje kuma mun isar da sakonka, malam yace afada maka sunanan suna addu,a insha Allahu za,a dace, kuma yace afada maku Fulani tana nan araye, sede haryanzu Allah be gwada mashi inda take ba. Ga wannan ruwan addu,a ne yace akawo na me martaba.

    Areef ne ya amshi addu,ar ya ajeta agefen Sarki. Gyaran murya Sarki yayi yace to Alhmdullh, inaganin muma semucigaba da addu,a nasan wata rana Allah ze bayyana mana Fulani da kuma abinda tahaifa, addu,ar mu Allah yasa kome ta haifa ace shima yana raye. Waziri yace maganar gashin jikin memartaba, meze hana a maidashi yazamana duk bayan kwana 2 sbd inaganin hakan zefi temaka mashi. Sarki yace hakan ma yana da kyau, muje abashi maganin. Areef yatashi yadauki maganin suka nufi gurinshi.

Gimbiyar Babbar Gida suka samu agurinshi tana bashi kayan marmari, sallama Waziri yayi, daya daga cikin fadawan yaje ya sanar da ita zuwan me martaba. Komawa yayi yamasu iso sannan suka shiga, bayan sungaisa yatambayeta mejiki tace dasauki, tashi tayi tafita, jakadiya ta mara mata baya.

Duka sauran bayin suka fita, se Babban Hadiminshi ne, kuma wanda sarki ya aminta dashi ne kadai yarage, karbar robar Sarki yayi yazauna kusa da Yayanshi, yace sannu yaya, Malam yace yana gaisheka, kuma yace abinciken dayayi yagano Fulani tana raye bata mutu ba, insha Allahu zecigaba da addu,a za,a ganta. Kokarin dago kanshi yafarayi jin anyi maganar Fulaninshi, cike da farin ciki Sarki da Waziri suka temaka mashi yajingina, wani murmushin farin ciki ne, ya bayyana afuskarshi. Shima Sarki dasauran mutanen dakin kowa farin ciki ne, yacika fuskarshi.

Sarki yace hakane Yaya bata mutu ba, ga wannan maganin yace abaka kasha, dan Allah kada kaki karba, kaga yau shekara nawa ana kawo magani baka sha, ayau naga farin cikin dana dade bangani afuskarka ba, inaso kasha maganin nan, kaga kaima zaka samu karfin yimata addu,a.

Babu bata lokaci yabude baki, Sarki dakanshi yabude robar yayi bismillah yafara bashi maganin, tas yashanye, aka dauko dayar robar Sarki yace wannan ajiki za,a shafa maka, kallon Waziri yayi, babu bata lokaci yakama keken yaturashi suka nufi daki. Cike da farin ciki Areef yafita yanufi bangaren Momynshi. Dede zewuce alambu yahadu da sarkin Fada, kara hade fuska yayi, sarkin fada yamatso dasauri yana washe baki yace Allah yatemaki mejiran gado. Hannu kawai Areef yadaga mashi yawuce, da harara Sarkin Fada yabi bayanshi, kwafa yayi sannan yayi gaba.

Bayan sunje gida dakyar Yar Baba tasaki Baba Jakadiya takamata ita kuma Ladidi matar Malam takama Maman yar Baba suka shiga ciki, haka yaran gidan suka rika sakin baki suna kallon Yar Baba, itam seboyewa take ajikin Jakadiya. Daki takaita tazaunar da ita, haka suka kama Mamanta suka nufi bandaki da ita, da kyar sukayi mata wanka, sun sabata yafi so 5, haka suka fito da ita se kuka takeyi.

Dakin Ladidi suka kaita, sannan Jakadiya tariko Yar Baba takaita bandaki, kintsayawa tayi, dan bata taba ganin irin shiba, seda Jakadiya ta tsaya takoya mata yanda zata wanke jikinta da soso haka tasata tayi wanka tawanke mata kanta, sannan suka fito, kallo daya zakayima yar Baba kagane tsanin kyan datake dashi, dan kamatake da larabawa.

Bayan sungama shiryasu suka basu abinci anan maman Yar Baba takwanta se bacci, yar Baba kuwa tanajikin Jakadiya takwanta tayi shiru, ita kuma tana gyara mata gashinta, wanda yaji mai se kyalli yakeyi, daga haka itama tayi bacci. Malam ne yaleko yace idan sungama sufito suji abinda ya yanke akan su Yar Baba.

Ur's

NABILA RABI'U ZANGO
  (Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 20⚜25

     Malam yayi gyaran murya ya kalli Baba yace nataraku anan dan infada maku abinda nayi tunani akan wadannan bayin Allah, da farko de dakai zanfara Baba, kaga kamar yanda akayi mana bayanin akan 'Yar Baba, bazata iya rabuwa da kai ba, shine nace meze hana idan har kanajin zaka iya zama dasu, kayi hkr da waccan sana'ar taka kadawo nan cikin gari kaida iyalanka nikuma namaka alkawarin gurin zama harma da aikinyi aduk inda kake so.

Amma Baba kaduba kagani mekace? Gyara zama yayi yace agskiya Malam, nikaina banajin zan iya hkr da rashin 'Yar Baba akusa dani, nayi sabo da ita sosai wanda basauki bane ace za'a rabamu, kuma kamar yanda nayi alkawari zankula dasu nayarda zanbar aikina da muhallina indawo nan mucigaba dazama.

Malam yace gaskiya naji dadi, kuma insha Allahu zaka samu aiki me kyau, duk da acan ma aikin lada kakeyi nan ma wani aikin ladan ne, tunda temakon bayin Allah zakayi. Zamucigaba dazama dasu anan kuma gobe zamuje asibiti mukai ita wannan mata domin a aunata asan wace irin kalar hauka gareta, idan maganin asibiti ne, se adorata akan magani, idan kuma na hausa ne, semudawo acigaba dayi mata addu'a.

Jakadiya tace Yaya, dayake kanwarsu ce itace auta, tunda mijinta yamutu bata kara aure ba kuma bata taba haihuwa ba, shine Malam yasama mata aiki agidan Sarki, ta dalilinshi Gimbiya Shuwa tabata Jakadiya dan tace ta aminta da ita. Kallonta yayi yace inajinki meyafaru? Saddar da kanta kasa tayi tacigaba da magana.

Dama wata alfarma ce nakeso zannema agurina kaida Baba, amma dan Allah kada kucemun a'a. Wlh tun da muka dauko bayin Allan nan naji 'Yar Baba tashiga raina, musamman dazu datake kwance akan cinyata senake mata kallo kamar 'Ya ta dana haifa da cikina, duk da Allah be bani haihuwa ba, amma ayau naji inada sha'awar samun diya tabbas da za'a bani 'Yar Baba zanfi kowa farin ciki da hakan, kuma zantafi da ita can gidan Sarki mucigaba dazama da ita, amma Yaya mekace?.

Shiru yayi yana kallon kanwar tashi, yana ganin lokacin datake goge kwalla afakayce dan tasan yahanata kuka akan rashin haihuwa. Tausayinta yakamashi, kallon Baba yayi yace Baba mekace game da maganarta? Baba yace ai Malam kai muke saurare duk abinda kayanke dede ne, nide fatana kada akawo wani abun dazeyi sanadiyar nisantani da kuma mahaifiyar wannan yarinya daga 'Yar Baba. Allah yasani nidanake cikin hankalina zanshiga damuwa sosai, bare kuma ita wadda ta haifeta.

Malam yace shikenan gobe idan mundawo daga asibiti mukaji bayanin likita nikuma zan fada maku abinda nayanke, amma Baba dan Allah kada kacemun a'a aduk abinda zan zartar, kuma kaima insha Allahu babu abinda ze rabaku da Yar ka, duk inda taje kaima zakaje. Bayan kowa yatashi Malam ya kwanta yana kara tuno yanda wannan aljanin yafada mashi yanda suka tsinci wannan mata, rufe idonshi yayi yakara tuno lokacin da Sarki yake fada mashi halinda Fulani take ciki alokacin dasuka nemeta suka rasa. Ajiyar zuciya yayi yatashi cike da tunani aranshi yana addu'ar Allah yasa tunaninshi yazamo gaskiya, amma koma  menene yace zeyi istahara da dare.

     Wai lafiya Yarima naganka cikin farin ciki haka? Murmushi yayi yace wlh momy yau Baffa yayi murmushi, kuma yasha maganin damuka karbo mashi agurin Malam na Darazo, Tashi zaune tayi cike da annashuwa tace lallai ga dukkan alamu kunzo mashi dawani bayani me dadi ko? Nan yafada mata abinda Malam yace, hamdala tayi tace ai insha Allahu Allah zebayyana Fulani da ita da abinda akema bakin ciki agidan nan, kasanni tausayin Baba nakeyi, shiyasa banason haduwa dashi sede nayi mashi aike.

Yarima yace Momy niduk lokacin damuka hadu da Sarkin Fada kawai se inji raina yana baci, kawai nide mutumin be kwantamun arai ba, ganinshi nake da siffar munafukai. Momy tace Allah sarki, kaine kake ganinshi haka, amma aduk cikin fadar Sarki ai inaji babu wanda yake maka son da sarkin Fada yake maka tun kana yaro, kama cire wannan abun daga ranka kawai shedanne yake maka wasiwasi azuciyarka. Shiru Areef yayi amma sam zuciyarshi bata yarda da abinda tafada ba.

Bayan sungama shafa mashi maganin ajikinshi bacci yadaukeshi, kamashi sukayi suka kwantar dashi bisa gadonshi suka rufo mashi kofar, Sarki yace insha Allahu Allah yakusa kawo mana karshen wannan halin da muke ciki. Waziri yace da alama wannan maganin zeyi aiki ajikinshi dan tunda naga yasha naga wasu alamu. Sarki yace Allah yasa, suna fita sukaci karo da Jakadiya, kara gaishesu tayi, Sarki ya kalleta yadauke kai, Waziri yace zaki iya tafiya dan me martaba baya bukatar wani abu, kuma ma yasamu bacci, Jakadiya tace to ai shikenan Allah yabashi lafiya, juyawa tayi ta tafi tana me hararar Waziri tagefe.

   Da Sallama tashiga falon Gimbiya ita kadai tasamu se bayin dasuke mata hidima, zama tayi tana fadin Allah yatemakeki, Allah yasa kifi haka, murmushi tayi tadaga mata hannu, Jakadiya ta kalli sauran bayin dasuke falon, lokaci guda sukayi hanyar waje.

Gimbiya tace da alama akwai magana abakinki? Tace kwarai ma kuwa Gimbiya, waigawa tayi tace amma rankishidade banga Gimbiya karama ba, ko lafiya? Yamutse fuska tayi tace oho kinsanta da nawa yanzu haka tana can tana shiryawa kinsan yau ita zata karbeni. Gyara zama Jakadiya tayi tace ai me martaba ma yasamu bacci, kuma da alama ya karbi maganin dasuka bashi, dasauri Gimbiya ta tashi zaune, tace haba Jakadiya wane irin labari ne marar dadinji kike fadamun haka?

Allah yahuci ranki Gimbiya 'Yar Babbar Gida, kaina bisa wuya, banga amfanina aduniya ba idan har nazamo daya daga cikin masu bata maki rai, agafarceni Gimbiyar Sarki mace daya tamkar da dubu, kedayace me haske agurin me martaba, duk sauran matanshi bayinki ne Gimbiya me mulki gaba da baya. Wani kayataccen murmushi Gimbiya tasaki, ahankali tace inajinki menene shawara?

 Nagode Gimbiya, amma aganina meze hana mubi shawarar dana fara kawowa daga farko inaganin ita kadaice hanyar dazata bulle mana, dan mutanen nan suntashi tsaye akan wannan al'amari inajin tsoron abinda zedawo. Maganar Gimbiya medaki sukaji tana fadin wannan shawara taki Jakadiya tayi dede, amma ina ganin kamar haryanzu Yaya batayi na'am da ita ba.

Zama tayi tare da daukar apple tafaraci. Jakadiya tace Allah yatemakeke Gimbiya, barka da fitowa, hannu tadaga mata tamaida kallonta gurin Gimbiya tace Yaya dan Allah wannan karin kada kice zaki ki karbar shawararmu, wlh ayanzu kissa da tuggu basuci kawai mubama Jakadiya dama kamar yanda tanema daga farko.

Wani kallo Gimbiya tabita dashi, sannan tace wai meyasa kuka kasa fahimtata, koda yake ba laifinku bane daga ke har ita babu wanda yakeda jinin sarauta ajikinshi. Tashi tayi ranta abace tashige daki, da kallo Gimbiya medaki tabita, Jakadiya ko cikin sauri tabi bayanta jiki na bari. Karamin tsaki Gimbiya medaki taja ta tashi itama tabi bayan Jakadiya tana Allah wadai da wannan kaskancin datasa kanta ake mata.

Washe gari bayan sunje asibiti likitoci suka taru akanta, anyi mata gwaje gwaje kala kala, bayan sungama likitan yakira malam office, seda yayi rubutunshi sannan yakalli malam yace, agsky munyi duk wani bincikenmu kuma sakamako daya yake bamu, wannan mata lalurarta acikin kanta take, kuma mtsalace mesauki, sede kafin asamu abinda zedawo maka da hankalinka shine aiki, abinciken damukayi mungano cewar buguwa tasamu akanta, komade hadari ne, ko kuma akwai abinda yabugar mata kai, wanda shiyayi sanadiyar haukacewarta.

Amma abu mafi sauki shine duk ranar data kara samun makamancin abinda yafaru da ita, kota bige ko kuma ace arika nuna mata abubuwan datayi tarayya dasu kafin tasamu matsalar to zata iya dawowa hankalinta. Dan haka yanzu gida zaku koma da ita, akwai magungunan dana rubuta sekuyi mata amfani dasu. Godiya malam yayi mashi yakarbi takardar maganin yafita.

Koda sukaje gida ajikin Jakadiya Yar Baba takwanta hartayi bacci, dan yanzu tafara sakin jikinta, sede daga Jakadiya bata yarda da kowa agidan se ita. Adaren ranar bayan sallar isha'i malam yakara tarasu, hada Baba dan yaje yadauko iyalanshi yazo anan malam yabashi daya daga cikin gidajenshi suka sauka aciki kuma yasa aka zuba mashi kayan abinci dana amfani.

Malam yace to Baba kajide abinda likita yace agame da ciwon wannan mata ko? Dan haka nayanke shawarar za'a bama Jakadiya su ta tafi dasu can masarautar datake, dan Sarki mutumina ne, dazu munyi waya da waziri, kuma nafada mashi komai sede banfada mashi tarihinsu ba, kuma Baba wannan tafiya hada kai za'ayita, acan zaka samu aikin dazakayi idan yaso daga baya idan komai yadedeta zaka iya zuwa kadauki iyalinka.

Sede Baba banaso kafadama kowa labarinsu, kasan mutane akwai son zuciya nafiso kabarshi atsakaninmu wata rana zasuji labarinsu, kuma abangaren Jakadiya Waziri yace zasu zauna, kasan kuwa bangarenta yana daga bayan lambun gidan, bakowane yake zuwa ba, sede kai tunda sunsan kowaye kai zaka iya zuwa aduk lokacin dakakeso. Allah yabaka ikon rike sirrinku, sekayi ahankali da gidan sarauta, ba,a aboki agidan, kowa da halinshi yake zaune, dan haka kazama cikin shiri gobe insha Allahu zakutafi da safe. Allah yakareku daga dukkan sharri.

Baba yace amin, kuma naji dadin abinda kamun, ga iyalai na nan, nasan zaka kulamun dasu Allah yabaka ikon zama dasu lafiya, amma taya zamurika magana da kai? Murmushi malam yayi yace kada kasamu damuwa akwai waya ahannun Jakadiya, kuma iyalanka zasu zauna cikin kwanciyar hnkl, fatana Allah yabaku sa'a. Haka kowa yatashi Jakadiya tanacike da murna, harta tashi yace Jakadiya kisameni adaki, Bayan sun shiga naji malam yafara magana, akwai abubuwa da dama da zuciyata take sakamun akan wannan matar, shiyasa ma nace zakutafi tare. Kara rage murya yayi yana mata bayani,akan yanda yakeson abubuwan sutafi, sede duk yanda naso inji abinda suke fada ya gagara, haka nadawo inajiransu sufito, sundauki kusan awa daya suna tattaunawa sannan tafito.

Washe gari dasafe Malam yabada mota akadaukesu suka nufi babbar masarautar Gombe.

To jama,a bara muji menene asalin labarin wannan masarauta.

Tuna baya,

Asalin Labarin.

MASARAUTAR BUBAYARO.

Muhadu a page nagaba.

Ur's

NABILA RABI'U ZANGO
   (Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 30⚜35
     
      Qaseem yayi saurin fadin haba Yaya kasan mekake fada kuwa? Sarki yace koma menene Qaseem nasan baze wuce tace in....... kara kamo rigarshi datayi ne yasashi yin shiru yamai da hankalinshi gareta. Bawan Allah ga 'Yata nan, ita kadai Allah yabani, mahaifinta yarasu nikadai narage mata, kuma nima gashi Allah zerabata dani. Daga cikin wancan kauyen muka fito, mutanen garin suka koromu sbd kawai wani yayi ma mahaifinta kazafi, sakamakon hakan ciwon zuciya yayi ajalinshi.

Mu kuma suka koromu komai basu bari mundauka ba. Inarokonka kobayan babu raina kada kabari Nafeesa takoma garinmu, kamar yanda kamun alkawari inason rayuwar Nafeesa tayi albarka dan Allah kadaure ka auri Nafeesa.

Qaseem cike da bacin rai yace dalla malama kifadi abu meyuwuwa kinko san dawanda kike magana?  Idan baki sani ba, to........ tarin daya taso matane yasashi yinshiru suka maida hankalinsu kanta bakaramin shiga tashin hankali Sarki yashiga ba, ganin tana wani irin aman jini, Nafeesa ko se kuka takeyi, Sarki yatashi yace ma Waziri adauketa ko akan doki ne, mutafi da ita asibitin cikin gari.

Wani bafade Waziri yasa yadaukota, Haka Nafeesa ta tashi tana kuka. Cak bafaden daya dauketa ya tsaya jin jikinta yakara nauyi, Waziri yace muje mana katsaya kana bata lokaci, Ranka yadade ade zo aduba wannan baiwar Allah naji jikinta yasaki, dasauri Sarki yadawo dabaya, suna zuwa Waziri yataba hannunta yaji yadawo, yasa hannunshi gurin hancinta yaji ba numfashi, sam yamanta da diyarta agurin yace Rankai dade inaji fa ta mutu. Wani kara da Nafeesa tasaka nan take tafadi kasa sumammiya. Sarki cike da damuwa yasa Fadawa suka dauketa da mahaifiyarta aka dorasu akan doki aka nufi gida dasu, Qaseem kanshi jikinshi yayi sanyi yatausaya ma Nafeesa sosai.

Ko kafin sukai gida maman Nafeesa harta saki, dan akwai dan tafiya, suna zuwa sarki yasa aka kira Jakadiya nan Waziri yayi mata bayanin komai aka shiga da gawar cikin gida. Ita kuma Nafeesa aka kira likitansu domin yadubata.

Babu bata lokaci aka gama shiryata akayi mata sallah tasamu jama'a sosai, haka aka kaita gidanta na gaskiya, jikin Sarki yayi sanyi sosai dan yasan yariga da yadauki alkawarin da dole yacikashi. Bayan sundawo yakira Waziri dan suyi magana, bebi takan Qaseem ba, dan yasan baze bada goyon baya ba.

 Sosai Waziri yakara karfafa mashi guiwa kuma yakara tunasar dashi muhimmanci alkawari, da kuma irin jihadin dazeyi, Waziri yace kobaka aureta ba, kasama mata miji acikin gidan nan ko awaje hankalinka baze taba kwanciya ba sbd bakasan irin rikon dazeyi mata ba. Sarki yace bakomai ai itama mutum ce, kamar kowa kuma yin hakan dazanyi baze ragemun wani abuba, sede Allah yasani atsarina banida ra'ayin auren macen da bata fito daga gidan sarauta ba, kuma wannan ra'ayi nane shiyasa Qaseem yakeda irin ra'ayin, segashi nashi haryafi nawa. Nasan zeji haushi na, amma dole incika alkawarin dana dauka dazaran Nafeesa tasamu sauki za adaura auren banason tashiga cikin damuwa. Allah yabani ladar abinda nayi.

Bakaramin tashin hankali Gimbiya Zakiyya tashiga ba da Jakadiya takawo mata maganar auren Sarki ba, duk da batason Jakadiya amma daga ranar tafara sakar mata fuska dan tasan zatayi mata amfani. Koda tafada ma mamanta shawara daya tabata, kada tasake tanuna bacin ranta akan auren, kogurin Sarki banyarda ki nuna bacin ranki ba. Da wannan shawarar Gimbiya tasamu sauki aranta. Koda Jakadiya taga tafara samun sakin fuska agurin Gimbiya seta kawo mata shawarar kozata kaita gurin bokanta.

Dawani kallo Gimbiya tabita, cike da bacin rai tace waiku meyasa bakuda tunani idan zakuyi magana. Ko anfada maki gidan sarauta gidan hauka ne? To kada kikara zomun da wannan maganar banzar. Jakadiya cike da ladabi tace Allah yahuci zuciyarki, kiyi hkr insha Allahu baza'a karaba, tace tashi kije idan kinsamo wata shawarar wadda tayi dede da tsarina zaki iya dawowa.

Wacece NAFEESA?

   Diyace ga malam Audu da Uwani sunkasance talakawa ne, sosai mal. Audu beda wata sana'a data wuce Caca haka Uwani muguwar masifaffiyar mata ce, dama cirani yakawosu kauyensu alakocin Nafeesa tana da shekara 15, Uwani macece mesan kudi sosai hakan yasa take dorama Nafeesa tallar gyada, duk sanda taje talla acikin tasha dakin wani saurayinta take zuwa yasiya duka yabiya bukatarshi da ita. Seda tayi ciki har so 3 suna zubarwa, kuma Uwani bata cemata komai, shikuwa mal. Audu dama babu ruwanshi dasu.

Gaba daya sun dami yan garin, ana haka wata rana mal. Audu yayi Caca aka cinyeshi beda abinda ze bada hakan yasa yaje gidan wani mutum yasato rago, yana fitowa aka kamashi, anan mutane suka haushi da duka har gidanshi, seda sukayi mashi raga raga sannan abokanan Cacarshi sukace sutashi subar gidan dasuke ciki zasu sayar sudau kudinsu.

Uwani da Nafeesa bakaramin shiga tashin hankali sukayi ba, suna zaune suka farajin hargowar mutane, Mal. Audu yana kwance ko tashi be iyayi yaji mutane sun shigo sunfara yimasu wurgi da kaya, nan take zuciyarshi ta buga ya mutu, koda mutanen suka zo gurinshi se suka  samu ya mutu, anan suka fadama Uwani sukayi tafiyarsu, kuka suka saka Uwani tana fadin shikenan katafi kabarmu da tashin hankali.

Da kyar suka samu wasu daga cikin abokananshi suka yimashi wanka da sallah suka kaishi makabarta, duka basufi mutum 10 ba wadanda suka kaishi. Bayan kwana biyu da rasuwarshi Uwani tafara rashin lafiya, gashi basuda abinci bare kudin magani, haka Nafeesa tayita jinyarta, koda taje gurin saurayinta yabata kudi tasiyo mata magani korarta yayi dan alokacin ma tare da wata tagansu, haka tadawo tana ta kuka. Lokacin da akayi 7 da mutuwar mal. Audu masu siyan gida sukazo, anan suka koresu, duk inda sukaje neman temako babu me temakonsu dan babu wanda besan halin Nafeesa da uwani ba. Daga karshe suka baro garin har suka hadu da Sarki.
   ××××××××××

     Bayan kwana 7 da rasuwar Maman Nafeesa aka daura aurenta da sarki, mutanen garin sunyi matukar mamakin aurensu, sede wasu suna cewa auren tausayi ne Sarki yayi. Duk wasu kayan aure Sarki ne yayi mata, aka gyara mata bangarenta aka hadata da bayin dazasu rika yimata hidima. Haka Sarki yasa Jakadiya takoya mata duk wasu al'adu na masarautar.

Seda Nafeesa tayi wata 1 agidan sarki Jakadiya tana gyarata sannan takaima Sarki ita, bakaramin kyau tayi ba, dan gyara akayi mata bana wasa ba, fatar jikinta kanta seda ta canza. Abubuwa da dama Jakadiya takoya mata, wanda aciki harda biyayya ga gimbiya dan tafada mata ko ita wacece kowa binta yakeyi. Haka kuma ta bata Gimbiya Suhailat  agurin Nafeesa.

Aranar da Sarki ya kwana da Gimbiya Nafeesa yasameta bata da budurci ajikinta, yayi mamaki sosai, bayan sunyi sallar asuba yadawo yasameta tana kuka, zama yayi yafara tambayarta lafiya, cike da kissa tace kayi hakuri rankai dade dama nasan tunda Mama tarasu bata ida baka labarina ba, nasan dole zaka fahimci wani abu, nasan kagane banzo da budurcina ba, hakan yasamo asaline ta dalilin barayin dasuka shigo mana gida ana gobe za'a koremu daga garinmu, sune suka yimani fyde wanda shine dalilin ciwon Mamana dan Allah kayi hakuri, naso ace tunkafin adaura auren mun samu dama nayi maka bayani dako daya daga cikin bayinka kahadani dashi.

Tausayinta yakara kama Sarki yace bakomai Nafeesa, kada insake inji wannan maganar abakin kowa, kibarta tsakaninmu nayafe maki kinji, tace tonagode.

Haka zamansu yacigaba da tafiya, Sarki da kyar yasamu yashawo kan Qaseem dan tunda yayi aure yake fushi dashi. Gimbiya Shuwa da Gimbiyar Baban Gida da Gimbiya medaki kwata kwata basa shiri, shiyasa babu me shiga  harkar wani, Su biyu sunware Gimbiya shuwa, basa sata acikin harkarsu, sede itama Gimbiya madaki wato Nafeesa awulakance take agurin Gimbiya babba, se abinda tace takeyi, ita kuma tana kaskantar da kanta ne, kawai dan tasamu fada agurinta, dan Gimbiya Shuwa bata kulata, sbd akidarta na tsanar wanda ba dan sarauta ba.

Sarkin Fada ne, da jakadiya zaune alambu. Sarkin Fada yace waini Jakadiya haryanzu acikin matan Sarki babu me ciki ne? Yamutsa Fuska tayi tace inaji fa Sarki beda rabon samun da aduniya, bare aje ga maganar magaji, kaga ko mutuwa yayi ai sede abama Kaninshi. Sarkin Fada yace kinko san banason Qaseem ya anshi mulki kinsan yafi Sarki mugun hali, towai meze hana muyi masu kullalla. Jakadiya tayi dariya tace lallai Sarkin fada baka da dama, aini nafison ace sunbata shida kaninshi, shiyasa lokacin dayayi fushi dashi dan zeyi aure naji dadi, sede dayake akwai kauna atsakaninsu kaga basu wani dade ba, suka shirya.

Sarkin fada yace amma Jakadiya babu wata hanya dazakibi kishiga jikin Gimbiya Shuwa? Zaro ido tayi tace ni? Rufamun asiri, kana ganin sbd tsabar jinkai irin nata haryanzu bata yarda da kowa ba, sede mijinta. kai de kawai ayi sha'ani amma ina nan ina shirya masu gadar zare kaide kawai ka tsaya kayi kallo. Matso kaji wata magana. Ko kasan cewa nice nan na hana Gimbiya Zakiyya haihuwa agidannan?  Sarkin Fada yace lallai Jakadiya nasara maki. Tace uhm kawai ka kalleni kabarni akwai sauran abubuwan bam mamaki atattare dani. Kaide muje zuwa, da sannu sena tarwatsa farin cikin masarautar nan, haka nake bani da kyau, banki kowa yarasa ba, tunda har Allah yasa nazo a Jakadiya.
   
Muje zuwa danjin sauran labarin. Nagode da kulawarku.

Ur's

NABILA RABI'U ZANGO
 ( Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 25⚜30

Masarautar BUBAYERO, babbar masarauta ce mecike da tarihi, ashekaru 18 dasuka wuce Sarki HASHEEM shine Sarki amasarautar, yana da Kani wanda suke Uwa daya Uba daya, su 2 iyayensu suka haifa, kafin iyayensu surasu mahaifinsu shine Sarkin agarin.

Sakamakon hatsarin jirgi dasukayi shida mahaifiyarsu wadda ita kadai ce matarshi kuma uwar yaranshi, shine yayi sanadiyar mutuwarsu. Bayan kwana biyu da rasuwarsu .Waziri wanda shine mahaifin wazirin sarki Qaseem, shine yatara jama,a domin anada sabon sarki, ananne aka zabi Hasheem yayan Qaseem aka nadashi Sarkin masarautar Bubayero. Kuma shima Waziri yasauka daga mukaminshi yamika ma babban danshi wato Wazirin Sarki Qaseem.

  Alokacin Sarki Hasheem yanada Matarshi 1 mesuna Zakiyyah, diyace ga Sarkin Yobe, kuma abokine ga mahaifin su Qaseem, shiyasa suka hadasu auren zumunci, duk da Sarki Hasheem baya sonta haka yayi biyayya ya aureta. Mahaifiyar Zakiyya   takasance su 3 ne agurin mijinsu Sarkin Yobe, amma dayake macece wadda tasan kissa da iya tuggu hakan yasa tazamo yar gaban goshi agurin mijinsu, baruwanta dabin boka ko malam, tayarda da kanta.

Hakan yasa Zakiyyah tadauki duk wasu halaye nata. Kuma da wannan halinne tajawo hankalin Sarki Hasheem har yabata babban matsayi azuciyarshi. Alokacin da aka nada mijinta Sarki bakaramin dadi taji ba, sede babbar matsalar datake damunsu haryanzu basu sami haihuwa ba, ko batan wata bata tabayiba. Sede yanda takeyima Sarki yasa baya nuna damuwarshi akan haka.

Jakadiya itace babbar baiwa datakema Sarki Hasheem hidima tunkafin yazama sarki, ita kadai yabama amana aduka bayin gidan, hakanne yasa lokacin dayahau kujerar mulki yanadata Jakadiyarshi, ko Matarshi batasan wasu sirrinkanshi ba kamar yanda Jakadiya tasani, shiyasa kwata kwata basa shiri.

Bayan kaninshi yagama karatunshi akasar misrah yadawo gida, alokacin Sarki yasa aka gyara mashi part dinshi anan cikin gidan, kuma alokacin yazo mashi da maganar matar dayakeso ya aura, Yayanshi bakaramin dadi yaji ba, dan yana son kanin nashi kamar yanda shima yakesonshi. Daya tambayeshi wacece yace mashi diyar Sarkin Misra ce, atare sukayi karatu.

    Babu bata lokaci yasa waziri yashirya masu tafi sukaje neman auranta, koda sukaje sunsami tarba me kyau, kuma anan take aka bama Qaseem auran Gimbiya Suhailat, Bayan sundawo aka fara shirin biki.

Sati 1 akasa yanazuwa akaje akadaura aurensu, suka taho Gombe, sede Sarki Hasheem yace base anbasu bayi ba suna da isassun bayi, haka aka kawo amarya akasata part dinta. Tunda suka hadu da Gimbiya Zakiyya taji ta tsaneta, hakan yasa bata sakan mata fuska, kowa yanaji da kanshi, ita Zakiyyah tana ganin ita diyar Sarki ce, kuma matar Sarki, hakan yasa mulkin yayi mata yawa. Ita kuma Suhailat tana ganin masarautarsu tafi tasu Zakiyyah.

Bayan kwana 2 Sarki yasa Jakadiya tadebi bayi masu yawa takaima Gimbiya Suhailat tazabi wanda takeso, bayan tazaba Jakadiya tace tazabi amintattar baiwa acikinsu, wani kallo tamata tace aini bana zabar amintattiyar baiwa alokaci guda, dan haka ki kama gabanki idan ina bukatar hakan basekin fadamun ba. Jakadiya taji zafin maganar haka tajuya tawuce ranta abace, sede dayake ta iya duniyanci bata nuna mata afuska ba. Tsaki Gimbya taja, dan ita duk wanda befito daga gidan sarauta ba gani take beda wani matsayi, shiyasa ra'ayinsu da mijinta yazo daya, dan shima sarauta tashiga jikinshi dayawa yana bata muhimmanci.

    Sarki Hasheem yakasance mutum ne mesaukin kai sosai, sede shima yana daraja sarautarsu sosai, kuma baya son kai acikin masarautarshi, duk wanda ya aikata laifi ana yanke mashi hukunci dede dashi.

Dalilin aurenshi da matarshi ta 2 kuwa yasamo asaline, wata rana yafita rangadi shida Waziri da Kaninshi da fadawa, sunzo wajen gari nesa da cikin gari, se suka hadu dawasu bayin Allah agefen hanya uwa da diyarta, yarinyar bazata wuce shekaru 17 ba, tana zaune kusa da uwar tana ta kuka. Tsayawa sarki yasa akayi yasa aka kirawosu, sede yarinyarce kawai tazo dan matar tana cikin halin rashin lafiya bazata iya tashi ba. Tanazuwa tafadi kasa, Waziri yatambayeta meyasa suke zaune anan haka?.

Tana kuka bata basu amsa ba, Qaseem ya daka mata tsawa yace waike ba magana ake makiba kin tsaida mutane, Kallonshi Sarki yayi dan yasan abinda kaninnashi ya tsana kenan, murmushi yayi yamaida kallonshi kan yarinyar. Ihun matar dasukajine yasa babu shiri Sarki da Waziri da sauran fadawa suka sauka daga dokinsu suka nufi gurinta, yarinyar tarigasu zuwa gurinta.

    Jinine yake fita daga hancinta da bakinta, haka tarike hannun yarta hawaye suna fita daga idonta, akusa da ita Sarki ya tsugunna, fuskarshi cike da damuwa, yayi bakin cikin dabasu fito da mota ba, kallon Waziri yayi yace yazamuyi da ita, yakamata akaita asibiti. Hannun matar yaji takamo babbar rigarshi, dasauri fadawa suka matso dansu cire, amma yadakatar dasu. Kara dukawa yayi yace baiwar Allah kibari mukaiki asibiti kina zubar da jini.

   Kai tashiga girgizawa, ahankali tafara magana, babu inda zanje dannasan rayuwata tazo karshe, sede ina neman wata alfarma agurinka. Sarki yace inajinki, kadubi girman Allah, kamar yanda Allah yadauka kaka, yafifitaka sama da sauran bayinshi badan yafisonka ba, nasan matsayinka ya girmi alfarmar dazan fada maka, sede inason kayi jahadi domin ka ceci marainiyar Allah daga fadawa wata rayuwa.

Sarki yace inajinki, kifadi koma menene nikuma namaki alkawarin zanzamo mecika makishi. Waziri, Qaseem sukayi saurin kallon Sarki jin abinda yafada batare dayasan me matar zata fada ba.

Ur's
  NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
  08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 35⚜40

Zaune suke a falon Malam Bello na Darazo, Sarki ne, se Qaseem da Waziri. Malam Bello babban malami ne, kuma attajiri, duk da yamanyanta amma sbd ilimin dayake dashi idan kaganshi zaka dauka shekarunsa basu kai nashi ba. Shine babban malamin garin Darazo malamin sosai, yana temakon mutane dayawa agarinsu, mutanen garin suna matukar sonshi da girmamashi.

Hakan yasa yagina katon gida me bangarori dayawa, ko yaranshi maza 2 dasukayi aure acikin gidan suke zaune da matansu, da yaransu, dama kuma beda yara dayawa yaranshi 4, maza 3 mace 1, itama tayi aure acikin garin bauchi. Matarshi daya uwar yaranshi, se kanwarshi kuma autar gidansu, tunda mijinta yarasu bata kara aure ba, dama kuma bata taba haihuwa ba, hakan yasa tace bazata kara aure ba, itama ta manyanta akalla zatayi shekara 35.

Mutane dayawa idan sukazo garin basuda masauki yana basu guri acikin gidanshi, ko idan ya musuluntar da wasu yana basu gurin zama, yana da dalibai dayawa dayake karantarwa. Haka kuma baya aiki da aljanu, sede yana fitar dasu kuma suma sunajin tsoronshi, kuma duk wanda aka kawo marar lafiya yana temaka mashi, hakan yasa mutanen garin dana wajen gari suke girmamashi.

Yadade yana yima masarautar Bubayero hidima tun lokacin mahaifansu Qaseem, dan masarautar bata yarda da malamin duba ko boka ba, hakan yasa koda iyayensu suka rasu basu yarda shiba, duk wani temako kowata shawara sukan zogurinshi, kuma Sarki baya aiko kowa gurinshi kode yazo tare dasu Qaseem da Waziri ko kuma ya aikosu su 2, yauma sunzo domin neman wani temako.

Bayan sungama gaisawa, Malam yasa ankawo masu kayan motsa baki, dan sunyi waya da Qaseem tun jiya yafada mashi suna hanya. Qaseem ne, yafara magana cike da ladabi. Allah gafarta malam, kamar yanda muka fara magana dakai jiya awaya. Dama bawani abu bane akan matsalar rashin haihuwar Yaya, tun tuni naso muzo shine yake hanawa, shine nace ai koma menene yanada magani, shine mukazo muji daga gareka.

Gyara zama malam yayi yacire glass din dayake idonshi yace, hakika nima nadade ina tausaya ma, memartaba, kuma dama tun kwanakin baya damukayi magana dakai, nafarayin istahara akan al'amarin. Kuma alhamdulillahi dama kobakuzo ba nayi niyar kiranka, infada maka abinda nagani.

Sede inaso kusani bakomai ne, ake fada ba dan kayi istahara, amma tabbas akwai abinda nagani amma nabarma kaina, kuma insha Allahu abinda ake so ahana za,a sameshi, sede muyita rokon Allah, babu abinda yagagareshi. Kamar kullum abinda nake fada maku kuyi hankali da mutanen da kuke tare dasu bance kuyi bincike ba, amma kada kayarda dakowa kuyarda da kanku, shine zaku zauna lafiya.

Abinda nakeso kusani insha Allahu memartaba yanada rabon samun haihuwa, sede abinda zan fada maku agsky ayanzude rabon dana gani zesamu ba'a agurin matanshi yake ba. Amma koma menene nasan zesamu haihuwa insha Allahu, sede adage da addu'a inafatan kunfahimci bayanina? Waziri yace munfahimceka malam, kuma mungode Allah yasaka da alkhairi, muzamuzo mukoma.

Malam yace tonima inada wata alfarma danakeso kuyi mani, Qaseem yace haba malam ai kawuce komai agurinmu kafadi koma menene. To kamar yanda kuka sani akwai kanwata kuma autarmu, kunsan mijinta yadade da rasuwa kuma taki yarda tayi wani auren, shine nakeso dan Allah kozaku tafi da ita can tarika temaka ma matan sarki dawasu aiyuka inaganin yafi zamandatakeyi anan tunda can akwai jama,a dayawa.

Sarki zeyi magana Qaseem yayi saurin fadin agaskya malam naji dadin wannan magana taka, kuma inaso abani ita inkaima Suhailat, dan mundade muna neman wadda zata zama mekusanci agurinmu, kasan ni bakowa nake yarda dashi ba, itama haka, amma tunda daga gareka tafito, kuma jininkace nayarda da ita sosai.  Kuma dama tana da tsohon ciki inata tunanin wadda zata zauna mata. Mungode Allah yabamu zaman lafiya. Ya sunanta? Malam yace sunanta Safeeya.

Murmushi Waziri yayi yace mungode malam Allah yasaka da alkhairi. Sarki yace mungode malam, kuma insha Allahu zamu riketa amana. Malam yace nikeda godiya, bari inje infada mata tashirya.

Daki yakira Safeeya, sundade suna tattaunawa banji abinda suke fada ba, haka tafito tashirya tayima Matar malam sallama da sauran matan gidan, hada kukansu, haka suka shiga mota suka dauki hanya.

Gimbiya Suhailat taji dadin zuwan Safeeya, dan tanajin labarin malam agurin Qaseem, shiyasa tajata ajikinta sosai, dan har karatu take kara mata, hakan yasa suka saba dawuri, duk wata shawara Gimbiya Suhailat tanayi da Safeeya, haka kuma baruwanta dashiga part dinsu Gimbiya Zakiyyah, asalima basu san dazuwanta ba,  kamar yanda babu wanda yasan tana da ciki harya tsufa, shiyasa taji dadin zuwan Safeeya. Dan Waziri yahana anuna Safeeya acikin gidan, har seda Sarki yace meyasa Waziri yace yallabai dan Allah abarta, Qaseem yace shikenan yanda kace Waziri.

Haka rayuwar gidan tacigaba da tafiya, Cikin Gimbiya Suhailat harya shiga watan haihuwarshi, Qaseem da Sarki suna farin ciki da cikin, dan kamar Sarki yafi Qaseem farin ciki da Cikin, kuma betaba fadama matanshi ba, dan gani yake kamar sun sani kuma beso suga kamar shima yadamu darashin haihuwar.

Jakadiya dasu Gimbiya sun hada kansu, Gimbiya Zakiyya babu abinda takeso kamar haihuwa, ayanzu bata da abokiyar shawara se Jakadiya, duk wani sirrinta Jakadiya tasani, sede haryanzu bata karbi gurguwar shawarar Jakadiya ba. Ita ko Gimbiya Nafeesa dama tasan bazata kara haihuwa ba, dan tunzubar da cikin datayi har so 3, likita yace mahaifarta tasamu matsala. Shiyasa bata da damuwa agidan, itade burinta kawai tasamu ta tara abin duniyarta, shiyasa takebin Gimbiya Zakiyya soda kafa, sede tabangare guda kuma sun hade kansu ita da Jakadiyya.

Zaune Jakadiya take afalon Gimbiyar Babbar Gida, kallonta tayi tace inajinki Jakadiya wace shawara kika kawo? Gyara zamanta tayi takara rage murya tace Gimbiya bawata shawara bace dama wata dabara nakawo, nace meze hana kicema Memartaba kina da ciki. Saurin tashi Gimbiya tayi tace bangane mekike nufi ba. Wace irin magana kikeyi haka, dama ana cikin karya ne? Murmushi Jakadiya tayi tace Allah yahuci zuciyarki, bahaka nake nufiba. Kinga yanzu ku 2ne matan Sarki, kuma kece Babba taya za,ayi muyarda wata tashigo daga baya ace ta haihu ke baki samu naki ba.

Jiya mukayi magana da Sarkin Fada kinsan mutumina ne, agurinshi nasamu labarin Sarki yace daya samu da namiji tofa lallai shine zegajeshi, shine nace meze hana kawai kice mashi kinada ciki, idan yaso sekirika saka tsummuna idan lokacin girman cikin yayi, kinga semuje gidan marayu mudauko yaro namiji kinga kema kinyi na..... marin da aka dauketa dashine yasata tayi shiru.

Dasauri tamaida kallonta gurin Gimbiya datake ta huci sbd tsananin bacin rai, cike da tsawa tace kitashi kibacemun daga nan. Kuma ina me tabbatar maki da duk ranar dana kara ganin kafarki acikin part dina wlh sekinbar masarautar nan.
     
 Cike da bacin rai Jakadiya tafito, hanyar lambu tanufa inda suka saba haduwa da Sarkin Fada, wata baiwace tafito dagudu zata wuce, dasauri Jakadiya ta tareta dan tagane baiwar Gimbiya suhailat ce. Ke lafiya kike gudu haka? Wlh dama sauri nakeyi inje inyima Sarki Albishir Gimbiya tasauka lafiya tasamu da na miji. Kara goge kunnanta Jakadiya tayi tace bangane mekike fada ba. Dama Gimbiya ciki gareta? Kwarai ma kuwa, aiko Sarki yasan tana dashi. Wani mugun murmushi Jakadiya tayi, tace ki koma za'a isar mashi da sako.

Dasauri Jakadiya tanufi gurin Sarkin Fada, sundade suna magana daga baya tafito tana dariya tanufi bangaren Sarki. Bakaramin dadin Sarki yaji ba, nan take yayima Jakadiya kyauta metsoka, Qaseem ma seda yabata kyauta, dan yana gurin aka fadi haihuwar.

Kafin wani lokaci gidan Sarki ya sheda haihuwar Gimbiya Suhailat, Qaseem boye farin cikinshi yarikayi, dan bayason Yayanshi yashiga damuwa. Bakaramin tashin hankali Gimbiya Zakiyya tashiga ba lokacin da labari yazo mata. Har kuka seda tayi, gashi takori Jakadiya, haka tasa aka kira Gimbiya Nafeesa ita tarika bata hkr, dan ita ko akanta.

Duk wata hidima Safeeya ce take mata, yaronta me kyau sosai, tun yana jariri dayayi kuka se dimple dinshi ya fito. Bayan kwana 7 akayi suna, Sarki da kanshi yasama yaron suna, dan Qaseem yaso yasaka sunan Yayanshi amma Sarki yace yabari zesa mashi suna, shikuwa yayi haka ne, dan yabama matar kaninshi hakkinta ko akwai sunan datakeson tasama yaron. Lokacin dayasa Safeeya ta tambayeta sunan datakeso asama yaron tace tanason asamashi Areef, dan sunan kaninta ne, daya rasu. Sarki yaji dadin tambayr dayasa akayi mata, koba komai yasan ba,a shiga hakkinta ba.

Qaseem yayi mamakin sunan da Sarki yasama yaron, koda yabincika yagane shine yasa atambayi matarshi, bakaramin jin tausayin Yayanshi yayi ba, kuma yakara jinjina adalci irin nashi.

Bakaramin taro akayi ba, hatta da yan uwanta seda sukazo suna, su gimbiya Zakiyya sunga yanda ake mulki da kuma dukiya, haka suka saki jiki kamar bakomai akayi suna lafiya, se alokacin suka san da zaman Safeeya, dan sunga komenene Gimbiya zata sa sede takirata, gashi kuma ita batada uniform bare suce baiwace, alokacin sunan ne Gimbiya Zakiyya tashirya da Jakadiya, dan tasan koba komai tana mata amfani sosai.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, duk yanda suka so susamu wata hanya dazasu kunta tama Gimbiya suhailat babu dama. Jakadiya da sarkin Fada kuwa kansu ahade yake, dan sarkin fada seda yasan yanda yayi yarika shiga bangaren Qaseem, yanuna yana matukar son Areef hakan yasa yashiga jikin Qaseem sosai, duk lokacin da aka kawo Areef Fada, Sarkin Fada shine yake karbarshi yayita renonshi harseyayi kuka sannan amaidashi.

Bayan shekara 1 Areef yakara wayau sosai, kullum afada yake wuni tare dasu Sarki, kowa yasan irin son da Sarkin fada yakema Areef, hakan yasa itama Gimbiya suhailat take mashi kyauta akai akai.

Lokacin da Areef ya cika shekara 1 da rabi aka yayeshi, dan baya zama agurin Gimbiya yafi zma afada shiyasa kawai ta yayeshi. Duk wani makircin Jkadiya da Sarkin Fada babu wanda yasani, wata rana suna cikin lambu suna makircinsu, Sarkin fada Yace wlh Jakadiya idan har muka bari wannan yaron yagirma kashinmu yabushe, Jakadiya tace meze hana mukawar dashi kowa yahuta. Murmushi sarkin fada yayi yace shawararki tana kan hanya. Shiru yayi jin motsi akusa dasu, saurin juyawa yayi yanufi inda motsin yake, caraf yariko hannun wata baiwa wadda tazo wucewa taji suna magana ta labe tana jinsu.

Kuka tafarayi tana fadin wlh, banji komai ba, kuyi hkr, dankwalinta yacire yashaketa dashi harseda ta mutu sannan, Jakadiya tace kaga shegiya, muzaki tonama asiri. Yo da asirinmu yatonu ai gara kowa yamutu. Sarkin fada yazamuyi da gawar, kasande idan aka duba ba,a ganta ba dole ashiga nemanta. Murmushi yayi yace kada kidamu mubarta anan ko anzo anganta babu wanda zece kasheta akayi, daukarta yayi yajefata cikin swimming pool din gurin suka tafi.

Da gudu Jakadiya tashiga bangaren sarki tana kuka, Waziri yace lafiya ke kuma zakishigo mana haka? Tana kuka tace wlh nazo wucewa naga kamar mutum acikin ruwa shine nazo infada maku, ai dasauri suka mike suka nufi gurin, fadawa waziri yasa suka cirota, koda suka duba suka iske tamutu.

Sarki da Qaseem sun shiga damuwar abinda yafaru, haka akayi mata wanka aka rufeta, koda akayi bincike wata kawarta baiwa take fadin dama tana tsoron ruwa lokacin da aka aiketa lambu daga lokacin bata kara ganinta ba, sese akace ta mutu. Sarki yace kila zamewa tayi tafada kuma babu wanda yaganta. Da haka akarufe maganar, hankalinsu Jakadiya ya kwanta.


Wasu mutanene guda 2, tare da wani Dattijo daka ganshi zakaga beyi kama da hausawa ba, yafi kama da larabawa, gefenshi. Kuma wata kyakkyawar matace, fara tasss da ita, itama babbar macece, gefenta wata santaleliyar budurwace kyawunta yawuce afadeshi, daka gansu kaga larabawan asali, yarinyar bazata wuce shekara 19 ba, tare suke da kayansu suna tsaye ajikin wani dankaramin gida me kyau.

Mutane 2 dasuke tare dasu daya daga ciki yace to Baba yakaga gidan yayi maka? Cikin hausarshi wadda bata goge ba, yace e gida yayi tunda akwai dakuna 3 aciki kuma kowane da bandaki nashi aciki ai yayi dede. Dayan yace yauwa Baba kamar yanda muka fada maka zaka rika bamu dubu 50 ashekara sune kudin hayar gidan. Baban yace shikenan babu damuwa, amma akwai wutan nefa ko? E Baba akwai komai har ruwa bamuda matsalarshi.

Baban yace toyanzu kaine zakazo kadaukemu anjima muje cikin kasuwa muyi siyayyar kayan amfani ko? E Baba kome kakeso zanyi maka, kuma zan kaika inda zaka samu kaya masu kyau. Yace toshikenan yaro nagode bari mushiga daga ciki mu huta.

Wadan nan mutanen bawasu bane kamar yanda kukaji ankira dattijon da Baba. Asalin sunanshi ABRAHAM ne, kuma shi mutumin saudiya ne, yatabayin zaman Nigeria har so 2, yayi aiki da hausawa agarin Bauchi, bayan yakoma saudiya ne, ya yanke shawarar dauko iyalinshi yadawo dasu Nigeria, kasancewar yaji dadin zamanshi ABauchi gurin wani mutumin kirki, bayan yatafi seda yayi wata 2 bedawo ba, se wannan dawowar dayayi tare da iyalinshi, sede yayi rashin sa,a yana zuwa Bauchi yasamu labarin rasuwar mutumin.

Yayi kuka sosai, dayake akwai Babban yaron Alhajin atare sukayi aiki, kuma shi dan Gombe ne, hakan yasa yanemi address dinshi yazo nan yasameshi, kuma shine yayi mashi hanyar samun gidan dazasu zauna, dan yace tund yariga da yabaro garinsu baze koma ba, shiyasa yace zezauna agurinshi sucigaba da kasuwancin tare.

Matarshi daya da yarsu daya, mesuna Rayhana, suna matukar sonta sosai, tana da ilimin boko dana addini, gata da natsuwa baruwanta da hayaniya, tanason iyayenta sosai. Bayan sun huta, dayamma akazo akadaukesu suduka suka tafi kasuwa.


Jerin motocin Sarki ne suka shigo cikin gari suna jiniya sundawo daga Yobe, tacikin gari suka shigo dansu gaisa da jama'a mutane se daga masu hannu sukeyi, dan mutanan Gombe suna son Sarki Hasheem sbd yana masu adalci.

Rayhana ce da Umminta suka fito daga wani store na kayan kitchen, Mahifinta kuma yana daga dayan bangaren tare da wanda sukazo suna siyan wasu kaya, Rayhana takamo hannunn Umminta dansu tsallaka titi, yaran dasuka dauko masu kayan suna binsu abaya.  Wata irin kara da Baba yaji ne, tasashi saurin juyowa dashi da mutanen dake gurin. Innalillahi Wainna ilaihirrajiun, shine abinda mutane suke fadi da gudu Baba yarugo dan ganin abinda yake faruwa. Dasauri sauran motocin suka samu guri sukayi parking suka fito domin ganin abinda yake faruwa.

To jama'a muje zuwa anext page danmuji meyafaru.
   Tnx alot for ur concern to me, my luvly friends.

Ur's

NABILA RABI'U ZANGO
 (Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 40⚜45

Rayhanace rike da Umminta akasa ta rungumeta tana wani irin kuka yayinda jini duk yabata mata jiki. Babanta ne, yakaraso gurin ganin abinda yake faruwa shima yaduka ya rungumo matarshi yana kuka, babu alamun rai ajikinta, dan tunda motar tabigeta nan take tacika.

Driver daya kadeta ne, ya iso gurin, abayanshi kuma su Sarki ne da tawagarshi suka nufo gurin dan yana daya daga cikin motocin gidan sarki. Isowarsu tayi dede da Rayhana tamike tana kuka tanufi drivern motar tashakeshi tana kaimashi duka tana kuka. Dasauri Waziri dasu sarki suka karaso gurin, Waziri ne yayi kokarin cireta daga jikinshi yana bata hakuri, komawa tayi gurin Umminta tazube tana kuka gwanin bantausai.

Qaseem da Wazirine suka isa gurin, shikuwa Sarki tunda yadora idonshi akan Rayhana yaji wani abu ya soki zuciyarshi, da kyar yasamu ya dedeta kanshi ya karasa gurin, amma duk da haka yakasa dauke idonshi akanta.

Waziri yaduka kusa da Baba yakamoshi yana fadin kayi hakuri Baba muje akaita asibiti. Dago kai Baba yayi yana kallonshi yace wane asibiti kuma, bayan tarasu. Cak numfashi Rayhana ya tsaya jin abinda Babanta yafada, nan take tasume. Mamaki ne, yakama mutanen gurin lokacin dasuka ga Sarki yadauki Rayhana yayi hanyar mota da ita, ganin haka Waziri yace ma Baba yatashi sutafi asibitin, Waziri da kanshi yadauketa suka nufi mota, Qaseem dayake bin Yayanshi da kallon mamaki shima yanufi mota suka nufi asibiti.

Suna zuwa aka karbesu, dan danan aka fara bama Rayhana temakon gaggawa, Umminta kuwa koda suka aunata anan suka gano ta jima da rasuwa, anan sukayi masu bayani, Seda Su Waziri suka rike Baba lokacin dayaji bayanin likita, abisa kujera suka zaunar dashi, anan Waziri da Qaseem suka shiga bashi hakuri. Baba yace ashede kasarki anan take, jiya mukazo garin nan ashe bazaki rayu damuba. Haka yayita sambatu, suna bashi hakuri.

Sarki kam hankalinshi yana kan Rayhana, yakasa tsaye ya kasa zaune, Qaseem ya maida kallonshi gurin Yayanshi, tausayinshi ne, yakama shi, dan tunda yake betaba ganin Yayanshi cikin wannan yanayin ba, tashi yayi yanufi gurinshi. Kafadarshi yadafa, juyowa yayi, yana kallonshi, hannunshi yakama suka nufi wata kujera suka zauna.

Qaseem yace Yaya kanutsu Fadawa da mutanen gari suna kallonka, kuma kowa yasan bamuda alaka dasu kada suyi tunanin wani abu. Sarki yace Matar tarasu ko? Kai Qaseem yadaga mashi, Sarki yace Allah kaceci baiwarka kada itama ta tafi. Qaseem yayita bashi baki.

Mintuna 30 Rayhana tadauka kafin tafarfado, alokcin har antafi da Umminta gidan Sarki, dan Sarki dayaji cewar bakine agarin shine yaroki Baba akan suje masarautarsu ashiryata ayi mata sallah acan se arufeta. Baba yaji dadin yanda yasamu mutanen kirkin dazasuyi jana'izar  matarshi. Suna zuwa gidan Qaseem yawuce part dinshi yacema Safeeya tafito akaita asibiti zata zauna da wata kafin sudawo, haka yasa driver ya kaita yarakata har dakinta shi kuma yakoma.

Koda Rayhana tafarka wata mata tagani akusa da ita, cikin Hausarta marar dadi wadda suka koya agurin Babanta danshi zaman dayayi anan yasa ya iya hausa, kallonta tayi tace Ina Ummi na? Matsawa Safeeya tayi takamota tace kiyi hakuri tana daki, kai Rayhana tashiga girgizawa tana fadin ance ta mutu ai. Kuka tasaka marar sauti, sede daka jishi zakasan yana ci mata zuciya. Ahaka aka turo kofar dakin, tana daga kanta taga Babanta ne da wasu mutane, shima idonshi yayi ja sosai. Dasauri yakaraso gurinta ya rungumeta shima yasa kuka, tsaya su Sarki sukayi suna kallonsu cike da tausayi.

Ganin tasamu sauki likita yasallamesu. Bayan sunfito Rayhana tana jikin Babanta hawayene kawai suke fita daga idonta, Baba yakalli Sarki yace Yallabai inaganin Zamu koma garinmu gobe, banga amfanin zamana anan ba, dama nazo daniyar zama anan, amma tunda narasa matata gara mukoma nida yarinyata. Mungode Allah yasaka da alkhairi, kuma munyafe ma wanda ya banketa, sede yaje yayi azuminshi.

Shiru Sarki yayi yanajin wani zafi aranshi, kasa magana ma yayi ya tsaya yana kallon Rayhana. Qaseem ne yayi saurin fadin a,a Baba yanzu kaga dare yafarayi, muje gida koma menene semu tattauna.

Part din Gimbiya Suhailat Qaseem yace Safeeya tawuce da Rayhana, shikuma Baba suka nufi bangaren Waziri dashi, Part din Sarki Qaseem yawuce dan tunda suka shigo yawuce part dinshi. Kwance yasameshi abisa gadonshi yana kallon sama. ( Niko nace Kadde ace su Sarki anshiga layi ne😉).

Zama Qaseem yayi yadafashi cikin sanyi murya yace Yaya tundazu naga kashiga cikin damuwa, wanda kuma bahaka muka taho da kai ba, damuka dawo Yobe, kafadamun damuwarka, idan baka fadamun ba, wazaka fada mawa? Tashi Sarki yayi yakalli Qaseem yace shikenan yanzu Qaseem tafiya zasuyi? Ai yakamata ace tunda harsunzo daniyar zama garinmu kuma sukayi rashi tadalilinmu yakamata ace mubasu muhalli akusa damu suzauna, wlh Qaseem haka nan araina naji banaso sutafi. Murmushi Qaseem yayi yace kada kadamu Yaya munyi magana da Waziri bazamu bari sutafi ba. Sarki besan lokacin da wani Murmushi ya kwace mashi ba. Tashi Qaseem yayi shima yana murmushi yace Yaya bari inwuce seda safe. Harya kai bakin kofa yajuyo yace Yaya Allah tabbatar da alkhairi. Dasauri yafita yana dariya. Murmushi Sarki yayi ya girgiza kai yanajin wani sanyi yana ratsashi.

Rayhana kuwa tana falon Gimbiya Suhailat sunata lallashinta. Cike da tausayi Gimbiya tace kiyi hakuri kinji, daga yau munzama yan uwanki, bazakiyi maraicin Uwa ba, kinga nima ba'a nan kasar nake ba. Daga yau kinga nasamu yar uwa, haka sukayita lallashinta hartasamu taci abinci tayi wanka suka nufi dakin Safeeya suka kwanta.

 Washe gari Baba yasa aka kira mashi Rayhana tana zuwa suka fara kuka, Waziri yace suje fada Sarki yanason ganinsu. Bayan Sungama gaisawa Sarki yakara yimasu ta'aziya. Anan waziri yafada ma Sarki sunyi magana da Baba yace ya hkra zasu zauna, sede yafiso yakoma gidan daya kama yazauna aciki.

Qaseem yace Baba dan Allah kayi hkr kazauna tare damu kaga Rayhana zatafi jin dadin zama anan saboda akwai mutane, amma acan daga kai se ita, kuma daka fita zata zauna ita kadai, kaga kadaici zeyi mata yawa. Baba yace shikenan naji zanbarta anan amma nikam nafiso nazauna acan. Waziri yace shikenan Baba munyarda, amma zakayi hkr kadawo kusa damu, kaga can yayi nisa kuma zakayi nisa da 'yarka, akwai wani gida nesa kadan da masarautar nan za'a gyara makashi se asaka maka wadan da zasu rika yimaka hidima seka zauna, kaga koba komai kana kusa damu. Baba yace to nagode sosai, Allah yakara budi.

Kallon Rayhana yayi wadda tayi lamo ajikinshi, cikin larabci yayi mata bayanin komai, shiru tayi tana kuka, kai tashiga girgizawa tace ita bata yarda ba, da kyar yasamu yashawo kanta. Haka yayi masu bayani ta amince, bakaramin dadi Sarki yaji ba, tagefen ido Qaseem yakalleshi shima yayi murmushi ganin farin ciki kwance afuskar Yayanshi.

Haka aka gyarama Baba gidan aka zuba komai, yakoma ciki, Qaseem da kanshi yazabi bayi maza da mata dazasu rika yimashi aiki. Rayhana kuwa ankawo mata kayanta, kuma Gimbiya Suhailat da Qaseem sunce agurinsu zata zauna.

Gimbiya Zakiyya da Gimbiya me daki bakaramun jin haushin abinda akayi sukai ba, baram ma Gimbiyar Babbar Gida, gani take kamar anmaidata saniyar ware,Jakadiya wadda itace take kawo masu duk wani labari daga fada. Kallon Jakadiya Gimbiya tayi tace agskiya jikina bebani zaman wannan balarabiyar agidan nan akwai alkhairi ba. Kawai ni tunkafin inganta wlh naji na tsaneta, tsana ma ta sosai, dan haka dole musan wane irin kulli zamuyi mata tabar gidan nan.

Jakadiya tace Gimbiya da ace Gimbiya suhailat tana daukar zuga kuma tana bani fuskar shiga gurinta danaje mata dawani kaidi wanda na tabbata setayi sanadiyar fitar wannan yarinyar agidan dan sena nuna mata mijinta akwai dalilin dayasa yakawota gidanshi tazauna.

Gimbiya medaki tace kai amma Jakadiya kinkawo shawara me kyau, kuma dole sekin san yanda zakiyi kisamu kishiga jikinta. Gimbiya Zakiyya tace ni nasan me za'ayi, ina Sarkin Fada, ai mutuminta ne, dan haka tagurinshi zamu samu damar aikata abinda mukeso. Jakadiya tace angama ranki yadade. Murmushin farin ciki tayi takoma ta kwanta tana fadin seyanzu nafara jindadin aiki dake, dan kinfara kawo shawara irin tamasu tunani, wato yan gidan sarauta. Kallon Gimbiya medaki Jakadiya tayi, suka hada ido, su duka sunji zafin maganar data fada masu, amma haka nan suka hadiye bacin ransu.

Kwance Gimbiya Suhailat take ajikin Qaseem yana wasa da gashinta, Gimbiya tace Hubbi kasan mene? Yace sekin fada, wlh naji dadin zuwan Rayhana gidan nan, naji dadi sosai daka kawomun ita part dina, inajinta ajikina sosai. Qaseem yace nasan zakisota, shiyasa nakawo maki ita, kinsan nasan duk wani abu daya dace dake. Kinma san menene? Tace a,a inaso kikara kula da ita sosai, dan inaji ajikina Yaya kikema kiwo. Dariya suka saka tace kai Hubbi da gske? Yace sosai ma, kodazu munyi maganar da waziri, shima ashe yagane abinda Yaya yake ciki. Kai amma naji dadi, aikuwa zankoya ma Rayhana yanda zata kwace Yaya daga gurin wadan can matan nashi.

Jinjina ta musamman gareku masoyana. Nagode sosai, sekunjini a next page😘
.
Ur's.
  NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 45 ⚜50

Sarkin Fada ne zaune afalon Gimbiya Suhailat, Areef yana bisa cinyarshi yanata wasa yanacin biscuit, Murmushi Gimbiya tayi tace Sarkin Fada kaida mutumin naka ne? Washe baki yayi yace barka da fitowa ranki yadade uwargidan Yallabai.

Zama tayi, bayan sungaisa Areef ya mika hannu alamun tadaukeshi, murmushi tayi tace a,a nibazan dauke ka ba, ai nadauka kamanta dani, kara wangale baki yayi kamar yaji abinda tafada. Hannu tamika mashi segashi yataho.

Lafiya de Sarkin fada naganka awannan lokacin? Kanshi yadan sosa ahankali yace lafiya lau, dama wani dan labarine naji awaje shine nace bari inzo inji daga uwar dakina ko haka zancen yake, dan abun yashafeki, nikuma aduniya babu abinda zanji dangane dake ace nabarshi.

Inajinka, E to, to dama de akan wannan bakuwar balarabiyar ne datake zaune agurinki, shine naji mutane suna cewa wai yallabai Qaseem ne yakawota, koshima zebi sahun Memartaba ne yabi Sunnah. Kuma da alama itace ze aura ko? Wani murmushi Gimbiya tayi takara kallon Sarkin Fada, gaba daya babu natsuwa atare dashi, kozama yakasayi.

Kara murmushi tayi tace tonagode, amma nibani da labari, sede kazauna inaji yakusa shigowa semuji daga gareshi, zaro ido yayi yace haba Gimbiya rufamun asiri, ina ni ina zama inyi irin maganar nan da Yallabai, nifa dama ban tabbatar ba, kawai kinsan bazanso arika maganarki ina guri ba, shiyasa nace gara inzo inji da kunnena. Murmushi tayi tace gaskiya kam ka kyauta, to bahaka maganar take ba. To harnaji dadi, aini bazanso ayima uwar dakina abokiyar zama ba. Tonizan koma, ahuta lafiya. Mikama Areef hannu yayi nan yataho suka fita.

Murmushi tayi ta girgiza kai, kallon wata baiwa tayi tace takira mata Safeeya. Bayan tazauna ta fada mata abinda Sarkin Fada yace mata. Shiru Safeeya tayi nadan lokaci, sannan tace nifa Gimbiya dama nafada maki banyarda dashi ba, ina yawan ganinsu tare da Jakadiya, amma kikace kinyarda dashi. Gimbiya tace bakomai Safeeya ki kyaleshi ni haryanzu ina mashi kallon mutumin kirki, kila da gaske yaji maganar, kinsan gidan nan akwaisu da gulma, bare sunga ankawo yarinya mekyau dole surika tsegumi. Safeeya tace amma duk da haka kirika kula sosai Gimbiya, ba'a saurin yarda da mutum, nasan kuma wannan halin kine, amma naga kinyarda dashi. Tace shikenan Allah yashige mana gaba, tace amin.

Haka suka cigaba da rayuwa, su Gimbiya Zakiyya duk yanda sukaso su hada tuggu akori Rayhana sunkasa. Sarki kuwa Son Rayhana yayi girma azuciyarshi, gashi baya ganinta dan bata fitowa sede idan zataje gaida Babanta ita da Safeeya, ganin abun zedameshi ya yanke shawarar fadamasu Qaseem.

Waziri ne da Qaseem Zaune afalon Sarki, su dukansu cike suke da murnar abinda Sarki yafada masu, dama kuma abinda suke jira suji yafada kenan, dan Waziri yace ma Qaseem yabari shida kanshi yayi masu maganar.

Waziri cike da murna yace agskiya naji dadin wannan labari, nima tunda naga yarinyar kawai naji ta kwanta mun arai, duk da bata fito daga gidan sarauta ba, amma inaganin aurenku akwai alkhairi aciki. Amma mekace Qaseem? Murmushi yayi yace aini nakasa magana sbd farin ciki.

Duk da inada ra'ayin kin auren wadda bata fito daga gidan sarauta ba, amma nikam nayima Yaya sha'awar auren Rayhana, sbd mune muke tare da ita nasan halinta mekyau gashi babu ruwanta, tana da addini, Allah ya tabbatar da alkhairi.

Sosai Sarki yaji dadin maganarsu, kallon Waziri yayi seyayi shiru. Waziri yace to ai ba tsayawa zamuyi ba, zanyi magana da Malam domin yayi mana addu'a akan al'amarin, kome yafada semuyi magana da Baba. Qaseem yace wannan yayi dede, Allah yate maka. Waziri yace amma inaso abar maganar anan, harse komai ya tabbata, kasan halin mutane. Sarki yace wannan yayi dede.

Bayan kwana 2, malam yakira Waziri suka yi magana akan istaharan dayayi. Waziri yaji dadin abinda malam yace, sundade suna kara tattaunawa akan masarautar, sannan sukayi sallama. Qaseem yakira yafada mashi komai, sannan suka fadama Sarki. Sosai yaji dadi, waziri yace zasuje suga Baba.

Gimbiya Suhailat da Safeeya sunji dadin maganar, sede Rayhana batasan abinda akeyi ba. Da dare Gimbiya  Suhailat takirata, bayan tazo Gimbiya ta sheda mata dalilin kiranta. Sunkuyar da kai tayi tana murmushi bata ce komai ba, Safeeya tace Rayhana kiyi magana mana kin amince? Da gudu ta tashi tana dariya tashige daki. Dariya Gimbiya tayi tace Allah mungode maka, gaskiya naji dadi sosai. Allah yashige mana gaba. Safeeya tace amin, amma ina tausaya mata gata karama babu ruwanta zata shiga cikin matan Sarki.

Gimbiya tace kinsan yanda Yaya yake sonta kuwa? Betaba auren Soyayya ba seyanzu zeyi, kinsan baze bari wani ya wulakanta taba, kuma akusa dashi za'a ajeta, bakiga ana kara gyara part dinshi ba? Nasan de kawai su Gimbiya Zakiyya zasu sha kayan haushi sede suyi hakuri. Nikam yanzu zan kara koyama Rayhana zama dasu, kuma dole ayi mata gyara na musamman, nasan dawuri za'ayi bikinta amma duk da haka daga gobe zata fara amsar gyara.

Bayan su Waziri sunje gurin Baba sukayi mashi bayanin daya kawosu, sosai Baba yaji dadin maganar, nan take ya amince, masu suka bada kudin neman aure dubu dari biyar. Anan aka yanke rana sati 2. Godiya sukayi mashi kuma suka fada mashi basu bukatar komai.

Zaune Jakadiya take afalon Sarki, Bayan sungama gaisawa yakalleta cike da girmamawa, danshi yana matukar girmamata, dan sunyi sabo sosai, komatanshi bayajinsu kamar yanda yake jinta, sun share shekaru tare tun farkon zuwanta gidan, take mashi hidima, shiyasa yabata amana sosai. Kallonta yayi yace dama nakiraki ne dan inbaki sako kifada ma su Gimbiya Zakiyya da Nafeesa maganar aurena nan da sati 2.

Akwai Yarinyar da take zaune gurin Suhailat wadda mukazo da mahaifiyarta nan akayi mata sutura wadda driver na ya kade harta rasu. To itace nakeso na aura. Washe baki tayi tace  amma naji dadi sosai, kallonshi tayi tace Rankai dade da alama naga kana son Rayhana sosai, bantaba ganinka cikin wannan farin cikin ba alokacin da zakayi aure ba, se wannan karon. Ko aurenka na farko banga wannan farin cikin atare da kaiba. Murmushi yayi ya sosa kai, dan yanajin Jakadiya kamar mahaifiyarshi dan tagirmeshi, yace wlh Jakadiya ina mata son daban taba yima wata mace ba. Dariya tayi tace Allah ya shige mana gaba, kuma anan danaga ana gyara za'a ajeta ko? Yace haka ne.

Murmushi tayi tace gskiya nafi kowa farin ciki da wannan al'amari, sbd yanzu Uban gidana zesamu abinda ranshi yakeso. Dan haka zan daukota domin akoya mata zama agidan sarauta. Kallonta yayi yace ai inaganin kamar Suhailat tana koya mata, babu damuwa nasan zata kula da ita sosai. Jakadiya tayi murmushin yake tace toshikenan bari inje infada masu Gimbiyar. Check yadauko guda 2 yace takaimasu kowa dai dai. Wasu kudi yadauko yamika mata yace ga wannan kema kirike ahannunki. Godiya tayi mashi tafita.

Gurin Sarkin fada tawuce, abinda yafaru tafada mashi, sosai suka shiga tashin hankali. Sarkin Fada yace kina ganin Sarki baze iya samun haihuwa da wannan yarinyar ba kuwa? Kinsan fa ance larabawa albarka garesu. Jakadiya tace kada kadamu nasan abinda zanyi, damma Sarki yace ba,a gurina zata zauna ba da tunkafin tashiga gidanshi zanyi kokarin hanata haihuwa, amma kasan ni amintattar Sarkice dan haka kome nakai zesata taci, dan haka kada kadamu inde ina raye bazan bar Sarki yaga kwanshi aduniya ba. Shekarata nawa ina mashi hidima amma haryanzu nakasa zama wata acikin gidan nan, haka zankare a Jakadiya?.

Sede inzama fitila ina haska wasu ni ina kona kaina, ai rashin gata ba hauka bane, dan haka gara kowa yayita zama ahaka, shima wannan yaron dande ka hanani dayanzu na aiwatar mashi. Sarkin fada yace kiyi hakuri wannan yaron yashiga rai na, Allah yasani badan so nafara daukarshi ba, amma daga baya yashiga raina sosai, dan haka kibarshi, ninasan ko Sarki yamutu sede Qaseem yahau kujerarshi bade Areef ba, dan haka mutsaya akan sarki da matanshi. Yanzu kije ki kaima Gimbyar Baban Gida mugun labari, dannasan ita kadai zata shiga damuwa, banda Medaki, itakam ai tamu ce. Dariya Jakadiya tayi tace wlh bakada dama. Yace Allah kuwa kinsan daza,a bani Gimbiya medaki ai dana more, tun lokacin datazo gidan nan miyau na yabiya kawai senaji wai Sarki ze aureta. Jakadiya tace ai naga alamar itama yar hannu ce, amma matso kaji. Wata dariya suka kwashe da ita Sarkin fada yace kina ganin haka za,ayi? Tace sosai ma, amma bayanzu ba senan gaba idan komai ya zama dede.

Wani uban gumi ne yake fitowa daga jikin Gimbiya Zakiyya, kara kallon Jakadiya tayi tace yanzu jakadiya har saurin zuwa ki kawomun wannan bakin labarin kikeyi? Jakadiya tayi kasa da kai tace Allah yahuci zuciyarki, shima Sarki ba sonta yake ba, kawai tallarta Babanta yayi mashi, kuma kinsan Sarki dasaukin kai shiyasa ya amsa, amma dakanshi yafadamun ke kadaice macen dayakeso aranshi, duka sauran ya auresu ne abisa lalura. Dan haka ki kwantar da hankalinki.

Komawa tayi tazauna, saurin zuba mata ruwa jakadiya tayi tamika mata. Bayan tasha tace yanzu ya za'ayi kenan? Jakadiya tace Ranki yadade kamar yanda kika saba, hakan zakiyi, kinsan Sarki yana yabonki akan halayyarki tarashin tada hankali aduk lokacin dazeyi aure. Yace shiyasa yake kara sonki. Murmushi Gimbiya tayi tace shikenan, amma wannan karon bazan kyale wannan yarinyar ba. Jakadiya tace ai bazamu barita dadeba.

Ita kuwa Gimbiya medaki duk da taji haushi kadan amma ana bata magudan kudi tamanta da fushin. Jakadiya tace dama nasan bazaki damu ba, se waccan sarkin kishin, ita tana ganin kamar ita kadai sarki yakeso dan tafito daga gidan sarauta. Medaki tace aisetayi tayi nikam inde da kudi ya auri 10 ina ruwa na, nasan kawai zanrasa kulawar danake samu duk bayan kwana 2 , nasan hakanne kawai zedameni dan Sarki akwai iya shiga rai. Dariya Jakadiya tayi tace ai Gimbiya nasan matsalarki, kuma wannan badamuwa bace kede kawai kirikeni zaki samu yanda kikeso. Sarkin fada ma yanzu yaganni zanshigo nan yace ingaisheki, kinsan ke kadai yake gaidawa aduk matan gidan nan gaskiya yanaji dake. Medaki tayi dariya tace ai yana da kirki damma kada ace wani abu ai daya rika rakoki munashan labarai. Murmushi Jakadiya tayi tace ah, tunda kinaso ai angama.

Sati 2 Gimbiya Suhailat tadauka tana gyara Rayhana, takara kyau, sosai kyanta haryaso yayi yawa, tasha gyara sosai. Duk wata kissa Gimbiya ta koya mata, dayanda zata zauna da matanshi, babu abinda bata koya mata ba.

Duk wanda yakwana yatashi agarin Gombe babu wanda besan Sarki zeyi aure ba, gaggarumin biki aka shirya gidan kanshi yasha gyara, hankalin Gimbiya Zakiyya bakaramin tashi yayi ba, dan tagano irin son da Sarki yakema Rayhana, tun daga dukiyar dayake kashewa da kuma irin hidimar da taga Qaseem yanayi, wanda tasan shikanshi yana murna da bikin.

Taso ta tadama Sarki hankali akan auren, amma mamanta tanaji tahanata, tace bakida hankali Zakiyya? Kina ganin akan abinda yakeso baze iya wulakantaki ba? Tunwuri idanma wasu ne suke zugaki togara kidawo hanya, kina ganin nice karama acikin matan Abbanki amma yanzu nice nazama babba, dan haka banyarda kikara tada hankalinki akan auren nan ba. Kuma banyafe maki ba, idan har kika yarda wata tajaki kukaje gurin wani malami ko boka. Hakuri Gimbiya Zakiyya tayi ta bata kuma tayi mata alkawarin bazata je gurin kowa ba, kuma bazata kara tada hankalinta akan auren ba. Da haka ta kwantar da hankalinta, sede tayi alkawarin idan har tuggu da kissa suna sa mutum yaci riba zatayi amfani dasu takori Rayhana daga gidan Sarki.

Ayau ne miliyoyin jama'a daga jahohi daban daban da manyan sarakuna na garu ruwa suka halarci bikin Sarki Hasheem da Rayhana, wanda aka daura akan sadaki million 1, kowa yasheda wannan auren Soyayya ne Sarki yayi, ankashe dukiya sosai, anci ansha maroka da mawaka sun sami kyauta sosai. Adaren ranar Sarki da sauran Sarakuna da manyan masu kudi sukayi kayatattar walima ababban dakin taron masarautar Bubayero.

Bayan sungama kowa yanufi masaukinshi, kuma ranar aka kai amarya Rayhana dakinta dayasha dukiya kamar ba,a nigeria ba. Yayin da wasu suka cika da farin ciki alokacin Gimbiya Zakiyya tarasa inda zata sa kanta sbd tsabar bakin ciki. Jakadiya kuwa jan Sarkin Fada tayi suka nufi part din Medaki acan suka zauna suna bikinsu.


Nima nace yakamata abar amarya da Ango su sha amarcinsu.
   Nagode sekunji ni a next page.😘.

Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
  08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 50⚜55

Washe gari. Basu suka tashi ba, se 8:00, dasauri Sarki yatashi ganin ko sallah basuyi ba, gaba daya kunyar fita yakeyi dan yasan kowa nagidan yasan baya fashin sallah amasallaci, babban abin kunya ma abokananshi sunce zasu biyo sugaisa da Amarya kafin su wuce, gashi nan yamakara.

Kallon Rayhana yayi wadda take kwance fuskarta tayi haske ga sahun kwallan datayi jiya nan kwance afuskarta. Murmushi yayi yashafi gashinta wanda ya hargitse, ahankali yace kece farin cikina GIMBIYA FULANI. Kiss yayi ma goshinta yatashi yaje yayi wanka yana fitowa yatada sallah, bayan yagama ya dauko Waya  yakira Qaseem, yana dauka yace ai Yaya dayanzu zankiraka ince bakifa suna Falo harsun kusa gama karyawa. Sosa kanshi yayi yakara kallon Fulani yayi murmushi yace Uhm ka aika Safeeya taje takiramun Jakadiya tazo gurin Fulani nizan fita gurin baki.

Shiru yayi sannan yace amma Yaya meze hana kamaidata dakinta se inturo Safeeya tazo ta kula da ita, kasan bazata yarda Jakadiya ta kula da ita ba, tunda basu saba ba. Murmushi Sarki yayi yace shikenan to bari in maidata dama dan naga Jakadiya ita kadai keshiga dakina shiyasa nace haka amma yanzu zan maidata dakinta. Kashe wayar yayi kunya duk takamashi yanzu yazecema mutane.

Bayan yamaida Fulani dakinta wanda kofa ce kawai tarabasu da falon Sarki, duk abinda yakeyi tana jinshi kunya ce tahanata bude ido. Zama yayi yana kallonta, can kuma yatashi yafita yanufi gurin baki, akofa yahadu da Safeeya, cike da girmamawa ta durkusa tagaisheshi, amsawa yayi yana me mata fara'a. Yace yauwa Safeeya idan tashirya kaya suna nan su zata saka zasu gaisa da baki. Da to ta amsa mashi yayi waje, yana fita fadawa suka mara mashi baya suna kwasar gaisuwa.

Duk wanda yaganshi aranar yasan yana cikin farin ciki, dan duk yanda yaso yaboye fara'arshi kasawa yayi. Yana shiga falon baki suka fara yimashi tsiya, sosai yake dariya dayake yashigo cikin abokanshi. Wani Sarki yace gskya Hasheem bantaba ganin wannan farin cikin atare da kai ba, kada muna skul baka wannan fara'ar. Lallai baseka fada ba, kowa yasan yanzu ne kayi auren soyayya. Wani yace aidole yayi farin ciki wlh auren so daban yake, shiyasa banyi aure ba seda nasamu wadda nakeso. Haka sukayita barkwanci suna dariya, wani yace kaga kada muyi rana gara afiddo mana Amaryar data hanaka sallah amasallaci muganta muga wane irin zabe ne kayi haka. Dariya yayi yace a gaskiya sede muje Falona babu wanda ze fitomun da mata tana amarcinta tafito waje. Dariya suka saka yafita.

Abakin kofarshi yahadu da Jakadiya, saurin dukawa tayi tana mashi kirari, murmushi yayi yace Jakadiya kina lafiya? Tace lfy lau Rankai dade, dama tundazu naso inzo induba yakuka kwana sekuma naji ance badakai akayi sallah ba, shine nace to kobaku tashi dawuri ba?.

Murmushi yayi yace hakane, ai har Safeeya tazo tana gurin Fulani. Fulani? Jakadiya takara maimaita sunan aranta. Murmushi tayi tace to ai shikenan, bara inje ingyara dakin yace to. Dakin Fulani yawuce, tunkafin ya isa wani da daddai kamshi ya dakar mashi hanci wanda yayi sanadiyar saukar kasala ajikinshi. Lumshe ido yayi aranshi yanakara jin son Fulani.

Kwankwasa kofar yayi, da sauri Safeeya taje tabude. Dukawa tayi tana fadin ai har angama, murmushi yayi yace nagode, Jakadiya zata kawo maki tukuicinki. Godiya takara yimashi tafita. Yana shiga yayi mutuwar tsaye, ganin irin kyan da fulani tayi kamar ba mutum ba. Tasbihi yafarayi aranshi yana kara yabon irin kyan Fulani.

Zaune take tunda taji shigowarshi ta dukar da kanta, hannunshi taji ya zagaye mata kafadu dasu, saurin rufe ido tayi, mikar da ita yayi suna fuskantar juna, murmushi yayi ya matso da fuskarshi dede ta ta harsunajin numfashin juna, ahankali yace Fulanita babu gaisuwa? Saurin kwantar da kanta tayi bisa kirjinshi tana murmushi, kara rungumeta yayi sosai kamar ze maidata ciki, kamshin turaren da Gimbiya Suhailat tabama Safeeya tasa mata duk yafara rikitashi.

Sassanyar muryarta ta doki kunnanshi dafadin Ina kwana. Seda ya hadiyi miyau sannan ya amsa tare da lalubo lips dinta yahade danashi. Sun dade ahaka har yana neman wuce gona da iri yaji karar kofa. Dagata yayi yace kinga kinmantar dani mutane suna jiranmu, gaskiya senayi da gaske kada kirika sani jin kunya afada. Kamata yayi suka fito.

Akofar falon ya tsaya  yakara gyara mata mayafinta, yace gskiya dande kada suce namasu rowa dabazaki fita kowa yakallemun ke ba. Ahaka suka shiga falon tana jikinshi, kallo ne yadawo kansu, kowa seda ya yaba da zaben Sarki, anan suka rika yimashi tsiya, itade sede murmushi, ko fuskarta kasa dagawa tayi, ahaka suka gama gaisawa, kyaututtuka da dama suka bata, daga masu kudi se zinari wasu hada kyautar mota. Tasamu zinarai dayawa da kudi, wasu kayan ma an nadesu bansan ko menene ba. Sallama sukayi mata, Sarki yace bari inmaidata daki kada tayi tuntube. Gabada sukasa dariya.

Qaseem da Waziri tare da Sarki dasauran fadawa suka taka masu hargurin motocinsu, kowa yaji dadin haduwar dasukayi haka suka tafi suna cike da farin ciki, dan sundade basuyi irin wannan haduwar ba. Bayan sungaisa  dasu Waziri yawuce part dinshi dominsu karya.

Da Jakadiya yahadu tagama gyara mashi daki ankawo abinci tashirya masu, yace sannu da kokari Jakadiya, tace sannu da dawowa, Yace yauwa kije falon baki akwai kayayyakin Fulani kyautace da abokanai na sukayi mata, akwasosu ki kawomun su dakina, hannu yasa a aljihu yaciro kudi masu yawa zasu kai 100k, yabata yace yauwa gashi kibama Safeeya tukuicinta ne ayi mani godiya da irin gyaran datayi ma Fulani dazu. Amsawa tayi ta tashi tawuce.

Wani irin kululun bakin ciki ne, yarufe Jakadiya, ganin irin kudin da Sarki yabama Safeeya, aranta tace wato mutanan nan so sukeyi sucireni daga jikin Sarki, ayanzunne yakamata insamu dukiya daga gareshi ta dalilin Amaryarshi nasan akanta ze iya yima mutum kyautar mamaki, amma dan bukulu suka turo wata tazo tayi aikin da nice nakeyinshi aduk sanda Sarki yayi aure. Tabbas sena tashi tsaye akan Safeeya naga alama nan gaba Sarki ita zemaida yar gaban goshi.

Ninasan mezanyi, anfada maki sona da yakeyi haka nabarshi. Tsaki tayi tawuce falon domin kwaso kayan, mamaki da tsoro ne, suka cikata lokacin datayi arba da irin kayan da tagani afalo. Gaba daya tarikice ganin irin wannan dukiya. Aranta tace badan Sarki yaga kayan nan ba, wlh dasenayi nawa. Wata babbar jaka tajawo tasaka kayan duka aciki tadauka tanufi dakin sarki dasu. Bata samesu afalo ba, da alama abincin ma adakinta suke ci. Tsaki taja tace shikenan kuma za,a maida mana Sarki bita zai zai, yo aduk matanshi akwai wadda yataba shiga dakinta ma? Lallai Gimbiya zankai maki labarin daze tarwatsa zuciyarki, wanda zesa ki karya akidarki ta rashin zuwa gurin boka, ai wlh tunda nabace dole insamu abokan tafiya. Murmushi tayi lokacin data tuna yanda Sarkin fada yafara samun shiga gurin Medaki. Kwafa tayi tajuya tafita.

Wasu zafafan kwalla ne, suke fitowa daga idon Gimbiya Zakiyya, duk irin jiji da kanta, yau gashi agaban Jakadiya tana kuka, damma Jakadiya takori sauran Bayin. Lallashinta Jakadiya tacigaba dayi tana kara kwantar mata da hankali.

Gimbiya hakuri zakiyi, amma dole sekintashi tsaye, wlh bakiga irin makudan kudin da aka bama Fulani ba, dan sunan danaji Sarki yakirata dashi kenan. Babbar damuwata yanda taki barinshi yafito fada, abinci ma adakinta sukaci. Infada maki...... Marin da taji ya sauka akuncinta ne, yasata saurin hadiye sauran gulmar data kwaso. Cike da tsoro takara dukar da kai tana neman gafara.

Ke wace irin dabba ce? Wlh bansan ke dakikiya bace se yau, anfada maki gidan sarauta gidan bayine? Inbanda rashin sanin darajar sarauta taya zakizo kina fadamun irin wadan nan sakarkarun maganganun irin na jahilai irinku. Ina cikin damuwa zakizo kina fadamun abinda bantambayeki ba. Bance kifadamun abinda sukayi ba, kawai na tambayeki ina Me martaba shine zaki wage sakaran bakinki wanda yasaba dashan bakar kuka da daddawa kizo kina fadamun maganarsu.

Daga yau kika kuskura kika kara fadamun abinda banice na tambayeki ba, wlh, kinji narantse maki sekinbar masarautar nan. Kara dukawa Jakadiya tayi, tana bata hakuri, tashi tayi ta tureta tashige daki, tana fadin karna kara ganin kafarki anan sena nemeki. Wasu hawayene suka zuboma Jakadiya, diyar cikinta saboda kudi da mulki yau itace take zaginta da cin mutunci har haka. Tashi tayi tana fadin yo idan har nabarki kikaci ribar zaman gidan sarauta ai ba macece ta haifeni ba.

Qaseem ya kalli Gimbiya Suhailat yace ni kaina yau ina cikin farin ciki bansan abinda yasa ba, Yayana yana cikin farin ciki dole in kasance acikin farin ciki, inama ace Rayhana itace matar Yaya ta farko, nasan har abada baze kara marmarin kara aure ba. Kamar yanda nasamu farin cikin raina banajin zan iya kara aure, shiyasa akace auren soyayya yafi komai dadi.

Murmushi tayi ta kara shigewa jikinshi tace nikaina ina farin ciki da auren yaya, inajin Rayhana kamar kanwata, insha Allahu ajikinta zamu sami babban rabo. Rungumeta yayi yace inafatan haka, inaso inga jinin Yaya agidan nan shine babban farin cikina. Fatana Allah yadoramu akan duk wasu makiyanmu, dannasan munadasu dayawa acikin gidannan, sede Allah ne kawai yasansu. Gimbiya tace babu abinda zasuyi mana domin munrigasu munce Allah. Jawota yayi yace yakamata fa kiyima Areef kanwa dan kinsan ina son mace. Murmushi tayi tace nima haka ina addu,ar Allah yabani mace, yace to tashi muje daki ai ba,a samun mace abaki. Dariya tayi yadagata suka nufi daki.

Afalon Medaki Jakadiya tasamu Sarkin Fada suna zaune yanashan kayan marmari, medaki tana kusa dashi har jikinsu yana gogar na juna, kofar da aka turoce tasasu saurin matasawa, dan Medaki takori duk bayin. Murmushin jin dadi jakadiya tayi ganinsu ahaka, aranta tace kema kinshigo hannu.

Medaki duk kunya takamata, Jakadiya tace rankiyadade ashe mutumin yana nan? Shiru tayi, Jakadiya tace uhm kisaki jikinki kinganni nan nimafa haryanzu ina dan taba duniyancin nan ai mace fitila ce bata aiki dole seda batir. Dariya Sarkin Fada yayi yace da gaskiyarki Jakadiya, ainafada mata nidake da ita munzama aminan juna, akwai amana atsakaninmu, dan haka bakinmu adinke yake muci tare mu tashi tare babu wanda zeji kanmu.

Medaki tace amma gaskiya nagode, tunda nasan yanzu munzama saniyar ware aidole musami abokin fira. Anan Jakadiya tafada masu rashin mutuncin da Gimbiya Zakiyya tayi mata. Sarkin fada yace kirabu da ita, wlh kotana so ko bata so seta aikata babban laifin daze jamata kisa ko dauri acikin gidan nan, ita da anyi magana seta nuna mana sarauta da mulki, zamu gwada mata bakomai sarauta take bama mutum ba. Kibarta mucigaba da binta wata rana zata dawo garemu, kuma kada ki kara zuwa gurinta, da kanta zata nemeki. Ai ba ita takawoki gidanba, karewa ma kinfita matsayi agurin Sarki, kawai agurin shinfida zata gwada maki. Dariya suka sa gaba daya.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, babu ruwan wani da wani, Jakadiya tadena zuwa gurin gimbiya Zakiyya, ko aikenta sarki yayi dataje zata fadama Babbar Baiwarta tajuyowarta. Sunhade kai da Medaki, Sarkin fada tuni yasamu shiga agurinta, wata rana har kwana yakeyi agurinta, kasancewarshi babban mutum me karfi hakan yasa Medaki takejin dadin mu,amala dashi. Baruwanta da daga hankalinta, sede idan ranar girkinta yayi taje tayi kwana 2 tadawo.

Sarki yana kokarin yin adalci atsakaninsu, sede Fulani daban take agurinshi, duk ranar girkinta kowa seyasan ita keda girki dan ko fada baya son zama sosai. Gimbiya Zakiyya kuwa kissar datake mashi ce take dan kara sanyata aranshi. Medaki kuwa hakanan yake zama da ita dan bewani gamsuwa da ita, shiyasa wani lokacin idan kwananta ne ba kullum yake kusantar taba.

Bayan shekara daya, aka saka Areef makaranta dan alokacin yana da shekara 3, har lokacin Fulani bata samu ciki ba, duk da Sarki yafara damuwa amma sbd son dayake mata, ko maganar betaba yimata ba, akullum yana addu,ar idan har haihuwa alkhairi ce agareshi to Allah yabashi me amfani, idan kuma babu alkhairi Allah yasa mashi dangana.

Jakadiya tazo shiga part din Gimbiya suhailata taji suna maganar cikinta har yakai wata 5. Bakaramin tashin hankali tashiga ba, cikin sauri tajuya tanufi gurin Medaki da Sarkin fada. Suma hankalinsu yatashi dajin labarin, anan Sarkin Fada yace yakike ganin za,ayi? Jakadiya tana huci, tace na rantse da Allah baza ahaifi cikin nan agidan nan ba, ai nafada babu wanda zekara haihuwa agidan nan, dan haka gobe zanyi tafiya, kafin indawo ina me tabbatar maku cikin zezube. Dariya sukayi Medaki tace kinyi dede Jakadiya, Allah yabada sa,a. Bari indauko maki tawa gudunmuwar.

Safeeya ce tafito da gudu tana neman dauki, karo sukaci da Waziri zeje fada. Lafiya Safeeya naganki haka? Wlh Gimbiyace bata lafiya se zubar da jini takeyi, naga alamar ma kamar barine tayi, cikin sauri yadaga waya yakira Qaseem, sannan ya aika wani bafade yakira driver.

Likitane, yafito daga wani daki yace su sameshi office. Bayan sunzauna yakalli Sarki da sauran mutanen, sannan yace Rankaidade agaskiya sede kuyi hakuri domin abinda ke cikinta yafita. Sede munyi bincike bamu gano dalilin fitar saba, sede muce daga Allah ne. Qaseem yace likita yajikin nata? Yace dasauki babu wata damuwa anjima kadan za,a sallameta. Sarki yace innalillahi wa inna illaihirraji,un. Waziri yace se hakuri, Allah yamaida mafi alkhairi.

Bayan kwana 2 jikin Gimbiya yayi sauki sosai, sede haryanzu tanajin zafin barin datayi, kallon Safeeya tayi tace wlh ina mamakin abinda nagani acikin baccina, wanda shine yayi sanadiyar yin bari na. Kinsan jiya nace maki nagaji bacci kawai nakeji, harkikacemun inje inyi alwala kafin inkwanta nace maki nide nagaji zanyi addu,a kawai, to wlh ina kwanciya bacci yadaukeni, banyi addu,ar ba, kawai cikin bacci naga wasu irin mugayen halittu marassa kyan gani masu ban tsoro sunbiyoni ina gudu kawai nafadi, suka zagayeni, daya gada cikinsu yataka cikina, shine kikaji wannan karar daniyi kawai senatashi naga jini yana zuba.

Safeeya tace tabbas Gimbiya rashin addu,ar dabakiyi bane yasa wannan al,amari yafaru dake, kinsan addu,a tana da matukar mahimmanci arayuwa, kuma alwala kafin mutum yakwanta bacci tana da matukar tasiri ajikinshi. Kodazu munyi magana da waziri shima seda yayi mamakin al,amarin. Kuma yafadama malam, yace ajirashi nan da kwna 2. Gimbiya tace koma menene Allah yamana tsari dashi.

Bayan kwana 2 Fulani da Sarki sukaje asibiti Waziri da Qaseem ne suka rakashi, babu wnda yasan inda zasuje sesu Gimbiya Suhailat. Bayan likita yasa anyi mata test aka kawo result, cike da farin ciki yasanar dasu abinda. Yakejikin takardar. Kasa Sarki yasauka yayi sujada yana me godema Allah da kyautar da yayi mashi, kowa dakin seda yaji tausayin sarki ganin kwalla tana fita daga idonshi, duk sunyi farin ciki da wannan labari, itako Fulani kasa dago kanta tayi.

Qaseem yace likita wata nawa ne? Wata 3 ne, Hamadala Sarki yayi yakara yima Allah godiya. Waziri yace lallai likita anjima zakaga sakon tukuicin wannan albishir me tsada. Sede munaso kada kabari kowa yaji wannan maganar. Likita yace insha Allahu.

Suna fita Qaseem yakira malam yayi mashi albishir, shima yayi farin ciki, kuma yace kada subari kowa yasan da cikin, dan abinda yagani akan barin da Gimbiya Sauhailat tayi yabashi tsoro, dan haka akillaceta kada tarika fita har wani yaga cikin, yace ze rika aiko da rubutun dazata rika sha harta haihu insha Allahu, Allah zekare cikinta. Godiya sosai yayi mashi sukayi sallama.

Bayan sunkoma gida yafada masu abinda Malam yace, Waziri yace wannan haka yake, nima nayi tunanin haka, kunsan babu wanda yasan zuciyar mutane, abar maganar anan, kuma mucigaba da addu,a Allah yasauketa lafiya.

Nikam nace amin Waziri.

Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 55⚜60

Haka Suka cigaba da renon cikin Fulani, babu wanda yasan da cikin agidan, duk wata hidima Safeeya ce take zuwa tana mata, Waziri da kanshi yahana kowace baiwa shiga dakin Fulani, sede komenene akwai wani amintaccen bawan da waziri ya yarda dashi, shi suke bama sakon yashiga yafada mata, matakin tsaro sosai Waziri da Qaseem suka dauka akan cikin Fulani, Sarki har mamakin kulawar dasuke bama Fulani yakeyi, hakan yasa yakara basu babban matsayi aranshi, yanajin Waziri tamkar yayansu.

Gimbiya Zakiyya abun duniya yafara isarta, gashi tayi fada da Jakadiya, tanaso takirata amma girman kanta yahanata. Ganin itace meso yasa ta aiki wata baiwarta takira mata ita, alokacin suna part din Medaki ita da Sarkin Fada. Dariya Jakadiya tayi tace ai nafada maku wlh babu wanda zekara samun da acikin gidan nan, kuma banida haufin Boka ya iya aiki. Sarkin Fada yace ai naga alama, tunda kikayi nasarar zubar da cikin Gimbiya, gsky na jinjina maki.

Karar buga kofa sukaji, dasauri Sarkin fada yamike yashige daki, Jakadiyace ta tashi tabude, gaishe da ita baiwar tayi sannan tafada mata sakon Gimbiya Zakiyya. Murmushi Jakadiya tayi tace kice inazuwa. Komawa tayi tace seka fito matsoraci, dariya medaki tayi tace ai da gaskiyarshi, duk munfiki tsoro kekam kinci dubu, tace wlh kuwa.

Abinda baiwar tafada mata take fada masu, dariya Sarkin fada yayi yace ai gara ki koma, Medaki tace nimade bana shiga gurinta sosai, amma tunda zaki koma nima zan koma, Jakadiya tace bara naje inji dame tadawo.

Zaune take afalo bayan sungama gaisawa Gimbiya takara kallon Jakadiya tana yamutsa fuska, tace wai naji ance Gimbiya suhailat tayi bari? Murmushi Jakadiya tayi tace haka ne,  ranki yadade. Gimbiya tace ammade nasan akwai abinda yafaru ko? Dariya Jakadiya tayi batace komai ba, dan bata manta da irin zagin data sha ba. Gimbiya tace bani labari idan ko har naji dadinshi kinada babbar kyauta.

Jakadiya nan tasaki baki tabata labarin abinda yafaru, tace wlh kuwa Gimbiya ai nafada maki tunda de baki haihu agidan nan ba, amatsayinki na babba acikin gidan nan ke kadai yakamata ki sama mana da agidan nan. Wani murmushin jin dadi Gimbiya tayi tace gsky kin bani labari medadi, hannu tasa tadauko kudi masu yawa tabata amatsayin tukuici.

Godiya sosai Jakadiya tayi, Gimbiya tace kina de saka ido akan Rayhana ko? Tace e sosai ma, itama haryanzu babu komai atare da ita, Gimbiya tace yayi kyau, aikinki yana kyau.

Har cikin Fulani yashiga wata 8 da sati 2 babu wanda yasan da cikin, alokacin yafito sosai. Rungume take ajikin Sarki yana bata kankana abaki tana tayi mashi shagwaba, kallonta yayi yace Fulanita idan kika haifi mace wane suna zamu samata?

Murmushi tayi tashafo fuskarshi tace idan namiji ne fa? Hancinta yaja yace harga Allah inason diya mace shiyasa bantaba tunanin haihuwar namiji ba, nasan mutane dayawa sunamun kallon wanda beda magaji, nikam nikeda babban magaji, dan koda ace inada namiji ko mutuwa tazo mani zan bada wasiyar abama Qaseem sarautar.

Dan haka koda banida namiji bazan damu ba. Ko kinason haihuwar namiji? Kai tagirgiza tace nima inason mace sosai, Allah yabani mace, yace amin. Kura mata ido yayi, hura mashi iska tayi tace wannan kallon fa namenene? Jawota yayi ya rungumeta sosai harseda tayi kara ya sassauta mata, kallonshi tayi idonshi yayi ja sosai, tashi tayi niyaryi yakara riketa, ahankali tace akwai abinda ke damunka ko?.

Kai ya girgiza yace kwana 2 ina wani mafarki wai muna zaune kintashi kin ruga inata kiranki amma kinki kidawo, kuma har kika bace bankara ganinki ba. Jikinta taji yayi sanyi tace insha Allahu babu abinda zerabamu kai nawa ne nima haka. Yace Allah yasa.

Karar buga kofa sukaji, Sarki yace shigo dan yasan inde aka buga kofa to wannan bawan ne,shine kuwa yashigo yaduka kasa yace rankai dade Jakadiya ce, Sarki yace to kuma shine kabarta awaje, tashi yayi cikin sauri yafita. Fulani tace bari inshiga ciki kafin ku gama, riketa yayi yace haba kiyi zamanki mana kinsan yanda nake da Jakadayi ai, tace amma kasan malam yace..... bata karasa ba Jakadiya tayi sallama, cak ta tsaya ganin Fulani atsaye da katon ciki, Sarki wanda be kula da halin data shiga ba yace shigo mana Jakadiya.

Saurin seta kanta tayi ta shigo, tana zuwa tazube tana kwasar gaisuwa, zama Fulani tayi bayan sun gama gaisawa, kwata kwata Jakadiya bata gwada taga cikin jikinta ba, kallon Sarki tayi tace dama shigowa nayi inj ko akwai wani aiki da za ayi maka?.

Kai yagirgiza yace babu komai Jakadiya kije kawai, dariya tayi tace toshikenan afito lafiya, kallon Fulani tayi tace Gimbiya ahuta lafiya, fita tayi zufa tana fito mata. Sarki yace ai nasan Jakadiya bata iya daga kai ta kalleni, bare kuma ke, kinga batama kula da abinda ke jikinki ba, nasan data gani zatafi kowa murna, dan tana daya daga cikin wadan da suka shiga damuwa akan rashin haihuwata. Shiyasa naso abari infada mata amma su Qaseem da Waziri suka hana. Fulani tace idan na haihu ai zataji, yace to Allah ya kaimu.

Hartuntube Jakadiya takeyi sbd sauri, jikinta har rawa yakeyi sbd bacin rai. Ko sallama batayi ba tashiga falon Gimbiya Zakiyya, suna zaune ita da Medaki, Gimbiya tace lafiya Jakadiya zaki shigo mana guri babu sallama bare neman izini? Zubewa kasa tayi tana haki tace Allah yahuci zuciyarki, wlh wani bakin labari ne yake tafe dani, sede inajin fargabar fadin shi, amma idan kinmani izini zan iya fada. Gimbiya tace yi maganarki.

Abinda tahani ajikin Fulani tafada masu, cike da firgici Gimbiya Zakiyya ta mike, wata irin zufa tafara keto mata, Medaki tayi saurin tashi tariketa suka zauna. Gimbiya tace wlh baze yuwuba, haba Jakadiya meyasa jakiyimun haka? Amma mekika cemun kince babu komai ajikin Rayhana? Jakadiya tace kigafarceni, wlh tun lokacin da kika hanani zuwa gurinki alokacin naso infada maki bana ganin Gimbiya Fulani kona shiga gidan bata zama falo,  shiyasa bana sanin halin datake ciki.

Medaki tace toyanzu mekike ganin za,ayi kinsan de baza'a barta ta haihu ba. Gimbiya Zakiyya tace idan har nabar Rayhana ta haihu agidan nan to wlh nikuma aranar zanbar gidan nan, kai kuma ce niba 'yar halak bace. Jakadiya meye shawara? Jakadiya tace Gimbiya hanya daya ce, amma bazaki jita abakina ba, nasan bakisonta, amma zanje insamu Sarkin Fada kinga shi namiji ne, yafimu zurfin tunani, zanje inji yanda zamuyi. Gimbiya Zakiyya tace banason kidau lokaci, kuma kintabbatar Sarkin Fada ba munafuki bane, kina ganin yanda yake shige ma Qaseem da matarshi, yaronsu ma agurinshi yake zama. Jakadiya tace Sarkin fada mutumina ne, banida wani abokin shawara aduk gidan nan se shi, banida haufi akanshi, dan haka kibarni dashi anjima zakiji abinda muka yanke dashi. Amma bazamu bari tahaihu agidan nan ba. Gimbiya Zakiyya cike da bacin rai tace kaini harzamanta agidan nan banaso, sede kinsan banason maganar boka atsarina.

Sarkin fada kanshi seda yashiga tashin hankali dayaji labarin cikin Fulani, mikewa tsaye yayi yace tashin hankali, lokaci yayi dazamu fara aiwatar da aikinmu agidan nan, babu wani yaro daza,a kara haifa amasarautar nan, dan haka kicema Gimbiya idan har ta amince anjima da dare zanzo semu tattauna idan zata amince da shawarata, kuma kifada mata babu wani batun boka ko malam aciki. Jakadiya tayi ajiyar zuciya tace yanzu naji natsuwa, bari inje insameta infada mata seka jini. Yace kigaishemun da Gimbiyata.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 60⚜65

Zaune suke afalon Gimbiyar Baban Gida, wani shu'umin murmushi Gimbiya tayi, tashi zaune tayi daga kishingiden datake, alokacin data gama jin bayanin da Sarkin Fada yayi masu. Ahankali tace lallai dole nabaka kyauta me tsoka saboda wannan shawara daka kawo,lallai kayi tunani mekyau.

Gaka de kafito daga cikin matsiyata talakawa, kuma kazo gidan nan amatsayin bawa, kafin daga baya kasamu yanci, amma kana da tunani irin na yan sarauta. Kodayake ance kunfi wasu mata zurfin tunani, naji dadin wannan shawarar taka kuma ita za'abi, dan haka kaje kayi shiri kamar yanda kace zaka samu abokan aiki, bana son inkara jin labari mekama da Rayhana bare kuma cikin jikinta.

Asalwantar da ita idan samune tabar duniyar gaba daya. Badamuwata bace, inde nizan rayu to kowama yamutu banida matsala, dama can bata fito daga jinin sarauta ba, niko duk wanda baya daya daga cikin jininmu, wato sarauta, dashi da kaskantattar dabba duk daya suke agurina, koda kuwa na nuna mashi so, to bana gaskiya bane, koyakikace Medaki?

Gaba daya falon yayi shiru jin irin kazaman kalaman da Gimbiya Zakiyya take fadi akan talakawa, kallonsu tayi taga gaba daya fuskarsu tacanza, se alokacin ta tuna baram baramar datayi, cikin sauri tace shiyasa nake godema Allah daya hadani da mutanen kirki irinku, daban kuke agurina, kunfi kowa matsayi azuciyata acikin gidan nan.

Murmushin yake Jakadiya da Sarkin Fada sukayi, can Sarkin Fada yace bakomai Gimbiya muma muna tare dake, kuma dasannu zamu nuna maki muma muna cikin masoyanki, kinsan bawa akwaishi da amana. Murmushi tayi tace yayi kyau.

Shima murmushin mugunta yayi ya kalli Jakadiya da Medaki yakanne masu ido. Medaki tace yanzu yazakayi kasanfa dole aikin yakasance ranar da Sarki baya dakinta. Gimbiya tace kabari seyadawo gurina dan nasan Medaki bawani sanin yanda zata dauke mashi hankali tayi ba, kasan jinin sarauta ako ina daban yake, dan haka kabari nan da jibi. Yace angama ranki yadade.

Fita sukayi shida Jakadiya, acikin Lambun gidan suka sami guri suka zauna, Jakadiya wadda acike take da bacin rai ta kalli Sarkin Fada cike da bacin rai, tace yanzu haka zamu cigaba da zama tare da Wannan matar, diyar cikinmu tana mana cin kashi akullum? Wlh dole mugwada mata talaka ma, yanada yanci, kuma zata gane bakomai bane jinin sarauta suka sani, mune acikin gidan nan, dan haka zamu gwada mata munfita sanin gidan nan.

Dariya Sarkin fada yayi yace dadina dake saurin hawa, kalli nan, aljihunshi yayi mata nuni dashi, sede banga komenene aciki ba, lekawa tayi, tace meye amfanin hakan? Dariya yayi yace kisa ido kawai malama, zakiga yanda akeyin duniyanci, kinganni nan bana yarda da jinin sarauta, duk yanda ka kai dayi masu hidima wata rana dole sumaka butulci.

Shiyasa acikin aikina bana barin sahu, ko kuma baya da kura, dan haka kizuba ido kigani wata rana dole Gimbiya tanemi juya mana baya, alokacin zan nuna mata asalin kalata. Dariya Jakadiya tayi tace amma naji dadi, ai nadauka duk zagin datayi mana zetashi abanza? Yace tama isa, haba Sarkin Fada fa nake, kinsan yanda akayi nasamu wannan matsayin kuwa, nikaina ina tsoron kaina, bari infada maki abinda babu wanda yasani agidan nan seni kadai, sekuma marigayi ya matata, itama dalilin sanin abinda na aikata yasa nakara mata iska, wanda haryanzu babu wanda yasan da mutuwarta, kowa yadauka yanda nace guduwa tayi sbd bata haihuwa nikuma nace zanyi aure shine tagudu.

Har yanzu maganar ahaka take, alokacin Sarki dakanshi yarika bani hakuri, Waziri da Qaseem kuwa cewa sukayi kada insake inje bikonta, dama ba'a garin nan take ba, nace masu ai tama tafi garinsu.

Murmushin jindadi Jakadiya tayi tace inajinka bani labari insha, kara gyara zama yayi yace alakocin da za'a nada sarautar Sarkin Fada, mu 3 aka tsaida, sede yanda mutane suka zabi sauran biyun suka barni hakan yayi mani ciwo, shiyasa nashiga damuwa saboda nasa rai akan sarautar, bayan an kara kuri'a aka tsaida mutum daya acikin su biyun.


Hmmm kinsan menayi? Tace seka fada, cikin dare nashiga dakin Mati wanda shine za'a nada washe gari, dama kuma tare suke kwana da abokin takararshi, inazuwa na saka wuka nakashe Mati, Kallah yana baccinshi besan abinda yake faruwa ba, haka na debi jinin Mati duk nashafa ma Kallah ajiki harda fuska, kuma nadauki wukar nasaka mashi ahannu, haka najuya nafita.

Inazuwa gida nayi saurin dibar ruwa domin nima jikina duk yabaci da jini, hanyar bandaki na nufa kawai senaji maganar matata ta faramun salati, tana fadin inakaje da wannan daren, dama muna kwance naga sanda kadauki wuka ka boye awondonka kafita, kuma gashi yanzu kadawo jikinka duk jini. Anya megida ba wani abun kaje ka aikataba?.

Aje bokitin nayi najata zuwa daki, anan itama na shaketa, nan take ta mutu, haka na hada duka kayanta na kullesu adan kwali, naje cikin bayan lambun nan na haka rami sannan naje nadaukota ita da kayanta narufesu aciki, namaida kasa sosai, yanda babu wanda zesan anrufe wani abu nazuba, dama kuma gurin ba'a shigarshi sosai ai kingani.

Washe gari da safe naji ana kururuwa, ina fita naga mutane sunzagaye Kallah yanata kuka jikinshi duk jini ga wuka ahannunshi, yana fadin wallahi banine na kashe shiba. Haka aka jashi zuwa fada, bayan anyi bincike aka gane sahun hannunshi ajikin wukar, nan take shima aka yanke mashi hukuncin kisa. Sede babban abin ban haushi wannan shegen Wazirin wanda yakeda dogon hangen nesa, da zurfin tunani, shine yaja Sarki daki, bansan mesuka ceba, Sarki yazo yace hukuncin kisan daurin rai da rai agidan yari za,ayi mashi, bahaka naso ba, amma sanin kowa yaji hukuncin nasan baze taba fita ba hakan yasa hankalina ya kwanta.

Bayan kwana 2 kawai naji ance niza,a bama sarautar. Dadi sosai naji, sede ban gwada afuskata ba, Sarki yake cemun meyake damuna haka, anan nafada masu karyar kwanana 4 banga medakina ba, dama mundade muna rigima, shine kawai natashi naga takwashe kayanta tacemun garinsu zata tafi. Nace masu nayi neman harnagaji banganta ba. Anan kowa yatausayamun sukayita lallashina, dahaka washe gari akamun sarauta. Kuma daga ranar babu wanda yakara tamabayar medakina, asalima Waziri cewa yayi kawai inkara aure, nikuma nace tunda bana haihuwa bazanyi aure ba, shiyasa suka kyaleni.

Tokinji babban sirrina, kuma nafada makine, saboda nasan bazakici amanata ba. Wani irin murmushi Jakadiya tayi nikaina bangane kona menene ba, tace haba aini taka ce, cikinmu daya. Sarkin Fada yace kisamomin maganin saka mutum bacci, amma na fesawa, tace angama.


Fulani ce zaune afalo ita da Babanta sunata fira, tundazu yazo sundade suna fira, yakasa tashi yatafi, itama bataso yatafi, kallonta yayi yace Rayhana inaso bayan kin haihu idan abinda kika samu yayi kwari, zamuje gida domin mugansu, kuma suga abinda kika haifa, kinga zasuji dadi. Tace nima Baba inason zuwa gida, insha Allahu dana haihu kamar da wata 7 semutafi ko? Yace hakan yayi, amma kibari sekin haihu sekima mijin naki maganar.

Hannu yasa a ajjihunshi yaciro wani zobe mekyau, yamika mata, sakashi tayi ahannunta, ta kalli Babanta tace wannan fa? Kwallan idonshi yagoge sannan yace zoben mariganyi yane, nima jiya ina duba kayanta, kinsan tunda tarasu bandaga kayanta ba, to acikin wata jakarta naganshi shine nace bari inkawo maki kisaka ahannunki. Itama kwallan ta goge tace nagode Baba, yace bakomai bari intafi yamma tayi, tace Baba kabari se anjima mana, yace a,a ai na dade, gara intafi sena kara dawowa. Har bakin kofa tarakashi idanunta sunkasa dena zubar hawaye, shikanshi kwallace tacika mashi ido. Sun jima abakin kofa yana lallashinta kafin yatafi.


Gimbiya Suhailat ce da Safeeya sukazo duba Fulani takawo mata farfesun yan ciki, zaune suke tanaci sunata fira, Gimbiya tace kinde kusa haihuwa kihuta, nasan insha Allah nan da kwana 7 zaki cika wata 9 dede, nasan kozaki kara kwanaki bazaki kara dayawa ba. Fulani tace nima nagaji nakosa in haihu, sede bansan abinda yasa ba, yan kwanakin nan se intaji yawan faduwar gaba.

Safeeya tace kada kidamu kirika fadin Innalillahi Wainnailai Hirraji'un, insha Allah zaki samu sauki, kuma koma wani abune zesameki zezo maki dasauki. Tace shikenan nagode, Gimbiya suhailat tace bari mutafi nasan yanzu Yaya zeshigo, Fulani tace ai banan yakeba. E duk dahaka aidole yazo yaganki kafin ya kwanta. Fulani tace Allah banaso kutafi, to kibar Aunty Safeeya ta kwana anan tunda nikadai zan kwana. Dariya Gimbiya tayi tace a,a kibari kawai mutafi.

Kamar zatayi kuka tace dan Allah Aunty. Safeeya tace to bari inje idan yatafi seki kirani sena taho, murmushi tayi tace yauwa nagode, haka suka yimata sallama suka tafi.

Suna fita tashiga daki ta kwanta, ba dadewa Sarki yashigo dakin, kusa da ita yaje yakwanta ta bayanta yarungumota yana me tusa kanshi cikin wuyanta, murmushi tayi tace sannu da shigowa, yace yauwa, inacen sunrikeni afada, nikuma duk nakosa inzo kada kiyi bacci bamuyi sallama ba, tace kaima kasan bazan iya bacci bankarbi sakon seda safe daga gareka ba.

Kara rungumeta yayi, yace aide jibi kamar yanzu muna tare, tace sosai ma, kallonta yayi yace kinyi kyau sosai Ummin AMATULLAH. Dariya tayi takara shigewa jikinshi tace wato harma kasan mace zan haifa, kuma kasa mata suna? Yace sosai ma, tace ai nadauka sunan Ummanku zakasa? Yace naso insaka sunanta, sede yanda na dade ban haihu ba, kuma Allah yabani yanzu shiyasa naga yadace insaka wannan sunan kinsan idan akace Amatullah ana nufin amintattar Allah, idan kuma namiji ne, tozansa AMINULLAH. Shima fassarar duk daya ce.

Murmushi tayi tace kayi gaskiya, idan Allah yakara bamu wasu se asaka, yace hakane, zatayi magana yahade bakinsu guri guda, sundauki lokaci me tsawo ahaka, ganin yafara fita hayyacinshi yasata saurin sakinshi ta matsa. Runtse ido yayi yana maida numfashi.

Ahankali cikin mutuwar jiki tace nasan Gimbiya Yaya tana jiranka adakinka, yakamata katafi, bude idonshi yayi sede idon yayi ja sosai, maidawa yayi yarufe, sega kwalla sirara suna saukowa, dasuri tamatsa kusa dashi tace meyafaru? Saurin rungumeta yayi yana fadin dan Allah kada kibarni kinji, wlh kece farin cikina, duk ranar da babuke akusa dani rayuwata bata da amfani.

Saurin rufe mashi baki tayi tana fadain wai meyafaru kake wannan maganar? Murmushi yayi yace bakomai, kawaide ina fada maki ne, tun safe yau nakejin faduwar gaba, addu,ar danakeyi ce tasa nakejin sauki.

Tace babu abinda zefaru se alkairi, katashi katafi kada tayi fushi, yace wlh da ace Medaki ce, nasan zata iya saidamun kwananta, amma Zakiyya ko duniya zan bata bazata yarda ba. Tace a,a nima banaso nafison kwanana yazo da kanshi.

Murmushi yayi yace bazaki gane yanda nakeji bane shiyasa, tashi yayi yace muje kirakani to, tace to kuma idan katafi waze sani bacci? Yace kai namanta, jawota yayi yakwantar da ita akusa dashi, tausa yafara yimata ahankali yanayi yana mata fira medadi, tun tana bashi amsa haryaji shiru.

Zama yayi yana kallonta yadauki kusan minti 30 yana kallonta, daga karshe ya sumbaci goshinta, wuyanta da bakinta sannan yatashi yafita jikinshi asanyaye.

Washe gari tunda asuba, Sarki yatashi dawani irin firgici, sakamakon mafarkin dayayi, Gimbiya Zakiyya tace lafiya naga kana zufa? Tashi yayi bece mata komai ba,yanufi part din Fulani. Turus ya tsaya ganin bata cikin dakin, kuma dakin duk ahargitse, karar ruwan dayaji ne, abandaki yasa yaji hankalinshi yadan kwanta, juyawa yayi yaje yayi wanka ya nufi masallaci.


Tare dasu Qaseem da waziri suka taho, Waziri yace lafiya rankaidade naga tundazu kamar kana da damuwa? Kallonshi yayi, yace wlh wani mummunan mafarki nayi kuma da Fulani nayi mafarkin, shine nashiga dakinta da asuba sede naga dakin ahargitse, kuma Fulani bata yima daki haka, sede karar ruwan danaji abandaki yasa hankalina ya kwanta, amma kuma haryanzu gabana yana faduwa.

Waziri yace to kayi mata magana abandakin kaji ta amsa? Yace a,a Qaseem yace Yaya mudeje ka kara dubawa ko? Waziri yace haka yakamata.
    Part din suka wuce, sede afalo suka tsaya shi kuma yawuce dakin. Karar dasukaji ce tasasu saurin shiga dakin, Sarki suka gani kwance kasa da alama faduwa yayi, hawaye suna zuba a idonshi, dasauri Qaseem yamatsa kusa dashi yana fadin yaya lafiya?

Da hannunshi yayi masu nuni dawani guri, jini suka gani agurin, ga kofar bandaki abude ruwa na zuba a famfo, babu alamun mutum aciki. Da kyar Sarki yake fadin babu ita wlh bata nan, Waziri yafita waje dasauri, haka yarika bin masu gadin gidan sede babu wanda yace yaga wani abu yafaru cikin dare, abu kamar wasa har rana tafito babu Fulani.

Gaba daya gidan antaru ankira hukuma ansanar da ita sede haryanzu babu wanda yakira yace ansamu wani labari akanta. Sarki kuwa tun faduwar dayayi haryanzu akwance yake tun maganar dayayi da farko bekara cewa komai ba. Gimbiya Suhailat da Safeeya se kuka sukeyi, Baban Rayhana kuwa zaune kawai yake, idonshi harsun kumbura sbd kuka, yakasa cewa komai.

Abu kamar wasa har dare yayi babu Fulani, yan sanda harsungaji da nema, hankalin kowa atashe yake, banda munafukai, sede Jakadaiya tana zaune kusa da Sarki, idonta itama ya kumbura dan kuka, mutane se hakuri suke bata. Waziri yakira malam yayi mashi bayanin halin da,akeciki, shima ya jajanta masu. Yace sujirashi zuwa washe gari.

Washe gari tunda asuba. Malam yakira waziri yace mashi agaskiya Fulani tana cikin mawuyacin hali, sede besan inda take ba, amma kuma tana raye, za,a cigaba da addu,a. Anan yafada mashi halin da Sarki yake ciki, anan malam yace bakomai nan da kwana 2 zezo se asan abinda za,ayi.

Jikin sarki babu sauki, ko abinci bayaci se dakyar suke matsa mashi yaci kadan, Ranar da Malam yazo ne, suka shiga suka tattauna da mayan fada, kuma suka yanke hukuncin nada Qaseem amatsayin Sarkin masarautar Bubayero. Lokacin da Qaseem yaji kin amincewa yayi.

Da kyar suka shawo kanshi, washe gari aka nadashi Sarki. Bakaramin tashin hankali Gimbiya Zakiyya tashiga ba, se fada take tana fadin wannan ai shine kai kai koma kan mashekiya, wato munyi abu kuma yadawo kaina, kai bazeyuwu ba yanzu shikenan natashi daga matar Sarki? Wlh dasake. Jakadiya tace haba Gimbiya najifa ance rikon kwarya ne aka bashi, da sarki yasamu lfy zemaida mashi mulkinshi.

Haka sukayita bata baki, da kyar ta hakura, abu daya ne yasata kara yarda mulki zedawo hannunsu dataji ance Qaseem yace baze dawo gidan Sarki ba.

Bayan anyi nadi malam yakoma Darazo, haka akacigaba da nema ma Sarki magani da adduo'i, ankaishi asibitoci dayawa amma jikinshi babu sauki, matsalar shanyewar barin jiki ne tasameshi, hakan yasa aka fara yimashi gashin kashi, sede babu yanda basuyi ba akan afitar dashi waje, amma sarki yaki yarda koda suka fadama malam, seyace su kyaleshi, babban abinda zesa yadawo dede to ganin Fulani ne, hakan yasa suka kyaleshi aka cigaba da yimashi maganin gida.

Medaki kuwa cin duniyarsu sukeyi da tsinke, ita da Sarkin fada. Duk wani munafunci yadawo daga Jakadiya se Sarkin Fada. Gimbiya suhailat da Safeeya haryanzu sunajin kadaicin rashin Fulani, Babanta kuwa tundaga ranar yadena zuwa ko ina kullum yana kofar gida, sede masu aiki suzo suyi mashi aiki sutafi.

Wannan shine asalin labarin Masarautar Bubayero. Zamucigaba da cigaban labarin anext page. Nagode

Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 65 ⚜70

Tafiya sukeyi amota, Jakadiya Safeeya, kallon Wannan mahaukaciyar kawai takeyi, tana kara tuno maganganun da malam yafada mata ana gobe zasu taho, waigawa tayi takara kallon Yar Baba wadda tayi lamo ajikin Baba tana ta bacci.

Aranta tace tabbas suna kama sosai ma, sede kawai wahalar duniya zatasa baza,a iya gane kamar suba. Dole nayi yanda malam yace idan har muna son musami abinda muke so. Tunawa tayi da abinda malam yafada mata akan Waziri, aranta tace tabbas da ace kowane Sarki zesamu mutum me amana kamar Waziri dayaji dadi, addu,a tayi akan Allah yate makesu akan mutanen masarautarsu.

Alokacin dasuka isa Masarautar Bubayero Jakadiya Safeeya tayima Waziri waya akan sun iso, alokacin gurin karfe 12 , Waziri yace togani nan zuwa. Yana zuwa yabada umarnin abude masu gate, direct gurin part din Sarki Qaseem suka nufa, dayake ranar asabara ce, kuma azahar batayi ba, babu kowa awaje se bayin dasuke kai da kawowa.

Suna fitowa Jakadiya Safeeya takama matar, shi kuma Baba yakama Yar Baba Waziri yayi masu jagora zuwa bangaren Jakadiya Safeeya, dayake, dakuna ne, guda 2 se falo da kitchen, kuma kowane daki akwai bandaki aciki, idan kaga yanda Gimbiya Suhailat tasa aka gyara ma Jakadiya Safeeya part dinta zaka dauka nawata mekudice, babu abinda ba,a zuba ba na kyale kyale afalon, dakunan ma haka, gidan yayi kyau sosai. Duk da abangaren Gimbiya takecin abinci amma a kitchen dinta ma akwai kayan girki da kayan abinci.

Bayan sun shiga Waziri yakalli Baba yace sannunku da hanya, Baba yace yauwa munsameku lafiya? Yace lafiya lau, Waziri yace Alhamdulillahi Baba gashi kazo masarautar mu, kuma insha Allahu zakaji dadin zama damu, sede akwai abubuwan danakeso ka kiyaye kuma ka kula dasu, na farko de nasan malam yafada maka yanayin yanda gidan sarauta yake, dan haka abu daya zan fada maka shine akwai Wani mutum Sarkin Fada, inaso duk yanda zeso yashiga jikinka kada kabari wata magana wadda tashafeka tahadaku, zan kaika gurin Sarki amatsayin wanda malam yaturo domin kazauna tare damu, ka kula dashi sosai dasauran mutane, idan muka fita zan kaika gurin Baban Gimbiya Fulani, mutum ne, nagari kuma shima dattijo ne, nasan zakaji dadin zama dashi, koba komai daka zauna kana fira da mutanen gidan nan gara karika zuwa gurinshi kuna fira.

Baba yace nagode sosai, kuma insha Allah zaka sameni merike alkawari, fatanmu de Allah yabama wannan baiwa tashi lafiya, suka ce amin. Waziri yace muje ingwada maka masaukinka kafin Sarki yafito, kallon Jakadiya Safeeya yayi yace nasan akwai abubuwa da dama dasuke bukata, anjima kamar da yamma zankawo maki kudi, sekije kasuwa kisiyo masu kayan amfani, game da sutura ma, duk kisiyo masu, idan yaso seki hado da dogayen riguna surika sawa kafin tela ya gama dinkawa. Kallon Yar Baba yayi yace daga cikin gidan nan kada kifita ko ina kinji? Ta daga mashi kai, yace yauwa, dakin fita akwai mutanen dazasu kamaki, saurin boyewa tayi bayan Jakadiya safeeya jin abinda Waziri yafada. Murmushi yayi yace tsoro kamar farar kura.

Tashi sukayi shida Baba, yace Sena dawo anjiman, tace to mungode, nima abinci zan dafa masu kafin inshiga gurin Gimbiya. Yar Baba tashi tayi ta matsa kusa da mamanta wadda take zaune akasa tayi shiru tana ta wasa da kafet din falon, kwanciya tayi bisa cinyarta, tana mata murmushi, dankwalin kanta mamar tacire, tafara yimata wasa da gashin kanta, ita kuma se lumshe ido takeyi. Jakadiya Safeeya tana kallonsu tace ikon Allah, Uwa da Diya se Allah, gaba daya sungama burgeta, murmushi tayi tace Allah yasaka maki, akan duk wanda yayi maki wannan abun. Tashi tayi tanufi kitchen.

Waziri ne, zaune afadar Sarki, bayan sungama gaisawa yafada mashi Jakadiya Safeeya ta dawo, tare da wani tsoho, malam yace sutaho tare, yazauna anan, amma nabashi masauki abangarena, shine nace bari infada maka. Murmushi Sarki Qaseem yayi yace, Waziri ai duk abinda kayi dede ne, babu laifi, kazaba mashi duk aikin daze iya mesauki kasan abinda zaka rika biyanshi ai? Yace hakane, godiya muke.

Sarki Qaseem yace Waziri akwai maganar danakeso muyi akan Yarima, kasan yagama karatunshi kuma yacemun shi aikin gwamnati yakeson yayi, to munyi magana da abokina harma an daukeshi , ranar litinin zefara zuwa, anan gidan gamnati, sun bashi assistant director. Kuma nasan saboda abokinshi ne yanace yanason yayi aiki acan, dan shima acan yake aiki.

Kasan wani magana dayazo mani da ita? Munyi mashi maganar aure, Momynshi tanaso tayi mashi maganar diyar yayarta datake can kasarsu, amma seta fara tambayarshi koyana da wadda yakeso, budar bakinshi se cewa yayi yafison yasamu wadda bata fito daga gidan sarauta ba. Haba Waziri yama zece haka, ko Yaya daya auri mata 2 ba yan sarauta ba, ai matarshi tafarko daga gidan sarauta tafito, shine mukace bamu yarda ba, amma zaka iya kiranshi ka karaji daga bakinshi, kasan banason bacin ranshi, inaso kanuna mashi nayarda yafara auren yar sarauta daga baya se ya auri zabinshi.

Waziri yace wannan ba wata matsala bace daza'a bata rai, kabarni dashi zanji tabakinshi tunda beriga yasamu wadda yakeso ba, ai dasauki, kuma zanga abokinshi Haisam nasan shima zeyimashi magana. Murmushin jin dadi Sarki Qaseem yayi yace. Hakan yayi kyau, muje muga jikin Yaya.

Jakadiya Safeeya ce zaune afalon Gimbiya Suhailat, Gimbiya tace bakiji yanda naji ba, yan kwanakin nan dabaki nan, idan Sarki yafita sede inta zama nikadai, dariya Jakadiya Safeeya tayi tace nima duk banji dadi ba, ya Sarki da jikin? Gimbiya tace jiki kam dasauki, da ranar dasu Waziri suka kawo mashi magani, dakuma maganar da malam yayi akan Fulani ranar har murmushi seda yayi, kuma nantake yashanye maganin, inasha Allahu zesamu lafiya. Jakadiya tace Allah yabashi lafiya, ina dana Yarima?.

Hmmm Yarima rigima, kinsan abinda yazo mana dashi kuwa? Tace a,a. Nan tafada mata yanda sukayi dashi, tace kuma nibazan amince mashi ya auri kowa ba, se jinin sarauta, Jakadiya tace kiyi hakuri, ita harka ta aure ba,aso ana tsanantawa acikinta, addu,a yakamata kiyi mashi amatsayinki na mahaifiyarshi se Allah yayi mashi zabi nagari.

Gimbiya tace hakane, amma nafison yabi zabin dana yimashi, diyar yayata nakeso ya aura,duk da ban fada masuba, banaso infada masu Yarinyar tasa abun aranta, nasan bayanzu zatayi aure ba,shiyasa nayi shiru harseya amince, sannan nayi masu magana. Jakadiya tace bakomai Allah yashige mana gaba, nima zanyi mashi magana tunda de besamu wadda yakeso seya auri zabinku, idan yaso daga baya seya auri zabinshi. Gimbiya tayi murmushi jin dadi tace shiyasa nake sonki. Allah yayi mana zabi nagari.

Da yamma kamar yanda Waziri yace, haka yasa driver yadauki Jakadiya Safeeya yanufi kasuwa da ita, acan tasiya masu kayan amfani dayawa, sede yawan siyayyar duk ta Yar Baba tafi yawa, kananan kaya ma duk nata sunfi yawa, dasauran kayan amfani na yan mata. Data gama suka wuce gurin tela, anan tayi mashi bayanin yanayinsu tabiya kudin dinki yabata ranar karba.

Jakadiya Karima ce zaune afalon Gimbiyar Babbar Gida tare da Medaki, Gimbiya tace waini Jakadiya kina kula da Suhailat kuwa? Kada fa ta shammacemu kamar yanda Rayhana tayi mana. Jakadiya tace haba Ranki yadade ai ita da haihuwa sede alahira, kada kidamu bazan baki kunya ba. Murmushi tayi tace, haka nakesonji.

Medaki tace bari intashi inje nasan yanzu angama shirya Sarki inje induba jikinshi, yamutsa fuska Gimbiya tayi ta kauda kai, Jakadiya tace afito lafiya Gimbiya. Tana fita Gimbiya taja tsaki tace aikin banza kamar wata tsiya zata iya yimashi, ni wannan mata tsau tsayi ne kawai yasa Sarki ya aureta, shide talaka duk yanda akayi dashi baya iya sakewa. Shiru de Jakadiya tayi bata ce komai ba, tashi tayi tace bari inje gurin Sarkin Fada.

 Koda Jakadiya Safeeya takoma part dinta har lokacin maman Yar Baba bata tashi daga baccin datakeyi ba, saboda acikin maganin da likita yabata akwai mesa bacci, dan yace idan tana yawan bacci kwakwalwarta zatafi samun hutu, YarBaba kuwa tana zaune tana kallo.

Jakadiya tace Yar baba zokiga wani abu, tashi tayi tamatsa kusa da ita tazauna tare da jingina da jikinta, jakadiya Tayi murmushi tace, hmmm ke kam mage ma nan taganki tabarki inde gurin sonjiki ne. Dariya Yar Baba tayi takara kwantawa jikinta.

Kayan tafiddo tafara nuna mata, hada inner wears duk tarika gwada mata yanda ake saka su, se murna Yar Baba takeyi, Jakadiya tace zankoya maki yanda ake amfani dasu duka, kuma kinsande nafada maki banason kazanta ko? Kai ta daga mata, tace yauwa, yanzu tashi muje ciki kiyi wanka semu fara.

Ranar litinin Areef yafara zuwa office, aranar duk macen data ganshi se miyanta ya tsinke, sbd kyawun da yayi, tare suke da Haisam, Areef yace nifa nafara tsarguwa, naga se kallona akeyi. Dariya Haisam yayi yace kada kadamu sunga dan saurayi me kyau ne. Duka ya kaimashi yana fadin kai dan iska ne, yace emana kasani ko anan kasamu zabinka tunda babu yar gidan sarauta acikinsu.

Areef yace Allah ya kyauta, anfada maka ni matata zatayi aiki ne, lallai ma, kai bakasan irin macen danake so na aura ba. Kawaide katayani da addu,a. Haisam yace ato idan kuma nizan rigaka aishikenan,Areef yace nima zanfi son haka, da haka suka isa Office dinsu.

Jikin Sarki Hasheem yafara sauki sosai sbd yanzu yanashan magani tunda yaji maganar da Malam yayi, kuma yana cin abinci sosai, hakan yasa Sarki Qaseem yace afara fita dashi fada hakan zerika rage mashi zaman kadaicin dayakeyi.

Haka suka cigaba da rayuwa agidan Sarki, babu wanda yasan dazamansu, aduk lokacin da Baba yaso ganin Yar Baba yakanje yaganta susha fira, har mamakin ganin yanda tacanza cikin lokaci kadan yakeyi, gashi tsafta agurinta kamar da ita aka halicceta, akullum setayi wanka so 3 kuma ko sallah tayi setayi kwalliya, Jakadiya safeeya kam har mamakin saurin fahimtar datake da ita take, kome takoya mata ba wuya tadaukeshi.

Akullum da dare kafin su kwanta se sunyi karatun littattafai, dan zaman datayi takara sanin abubuwa dayawa agurin Jakadiya safeeya, harta da girki tafara koya mata, sbd tace idan bata nan setarika dafa masu. Duk da ankawo dinkunansu amma bata son saka atamfa ko less, tafison tasa kananan kaya, Mamanta kuwa tunda takeshan magani, yanzu haukanta da sauki, batayin komai, sede tazauna tayi shiru idan kuma kaga tana dariya to ita da yarta ce, duk da baccinta yafi yawa akan idonta biyu.

Zaune Areef da Haisam suke acikin lambu suna hutawa, babu kowa agurin, danshi Areef becika son fadawa suna binshi ba, yafison daga shi se Abokinshi Haisam wadda yakasance da ga dupty gvernor na gombe, kuma tare sukayi karatu dashi.

Yar Baba tana gama kwalliya tafito dasauri dan ta nuna ma Jakadiya dan tasan bata fita ba, tana zuwa falo taga bata nan, kitchen tashiga nan ma bata ganta ba, turo baki tayi dantagane tafita, hanyar dataga tana bi tashigo ko tafita tabi, tana zuwa ta tura kofar cikin sa,a tajita abude, murmushi tayi tafita.

Cike da tsoro tafara takawa tana bin cikin lambun, swimming pool tagani kallonshi tayi. Taci gaba da tafiyarta, can taji dawisu yafara kuka, ai batasan lokacin data juya dagudu zata koma inda tafito ba, cikin rashin sa,a tayi tuntube da dutse kawai tafada cikin ruwan.

Su Areef dasuke zaune nesa da ruwan sukaji karar wani abu acikin ruwa, koda Areef yakai kallonshi ga ruwan kawai yaga mutum yana ta daga hannu da kafa acikin ruwa. Cikin sauri yatabo Haisam yana nuna mashi, duk da basu san kowaye ba, Dasauri suka nufi bakin ruwan.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady )
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 70 ⚜75

Babu bata lokaci Yarima Areef ya fada cikin ruwan, yana zuwa kusa da ita yadaukota, alokacin tasha ruwa harta suma, fitowa yayi daga ruwan tana rungume ajikinshi, abisa kafet din dasuke zaune yakwantar da ita yadora kanta saman cinyarshi, Haisam yana biye dashi duk sun rude.

Kallon tsoro, mamaki suka farayi mata, addu.a duk wadda tazo bakin Areef yinta yakeyi danshi gani yake kamar ba mutum bace. Haisam yace Areef bakada hankali kana ganin kamar ba mutum ba amma zaka dorata akan cinyarka? Tunda de kacirota tashi mutafi, fara jan hannun Areef yayi.

Areef da jikinshi yagama mutuwa sbd tsabar firgici bema san yanayi ba. Da karfi yajashi sannan yadawo hankalinshi, katashi mubar gurin nan, nidama can nafara zargin gurin, gashi yanzu munfara gani. Areef yafara girgiza kai, yamaida kallonshi kan kyakkyawar fuskarta, sannan yace ba aljana bace, duk da bantaba ganinta amasarautar nan ba, amma kalli kafarta babu alamun tako ajiki. Haisam yace anfada maka aljanu basa fitowa asiffar mutane? Hmmm kaga malam wannan yarinya kyanta yayi yawa, wlh zantafi inkira mutane ko katashi mutafi.

Idanun Areef suka cika da kwalla yakalli Haisam yace dan Allah, katsaya ni nayarda mute maketa ta farfado, kaga zamu fidda kanmu daga zargin da muke mata. Haisam yace naji, idan ma Mutum ce daga ina tafito? Areef be tsaya bashi amsa ba, kawai yaduka tare da saka bakinshi cikin nata yafara hura mata iska, shiru yaji, yamike yana kara kallonta.

Kamshin jikinta duk yagama cika mashi hanci, Haisam yace kadanna cikinta, hannu yasa, jikinshi se rawa yakeyi yafara danna cikinta, can sega ruwa yafara fitowa ta bakinta, haka yayi tayi, harseda tagama fitar da ruwan datasha.

Tari tafarayi hakan ya tabbatar masu data farfado, cike da firgici ta tashi ta shige jikin Areef, duk ta kanan nadeshi, tafara kuka. Areef kasa magana yayi, dan duk tasakan mashi kasala ajiki, dukawa Haisam yayi yace ya isa haka, tashi muji daga ina kike.

Kintashi tayi, sede tadena kukan datakeyi , tayi lamo ajikin Areef kamar wata yar baby, Areef kuwa kallonta kawai yakeyi, bemasan abinda Haisam yake fada ba, ganin haka yasa Haisam ya bugi kafadar shi, dasauri yamaida kallonshi gurinshi, gira yadaga mashi yana fadin kallon fa nameye?.

Kabari mutambayi yarinya daga ina tashigo amma kawani rungumeta kamar kana shirin bata mama. Murmushi Areef yayi yana sosa kai. Dagota yayi, ahankali ta tashi tana kallonshi, sede taki barin jikinshi, se rawar sanyi takeyi.

Areef yace daga ina kike, meyakawoki nan har kika fada ruwa? Hannu ta daga tana mashi nuni da hanyar part din Jakadiya Safeeya. Haisam yace baki iya magana ne, kinaji ana maki magana zaki tsaya kina mana maganar kurame, kuma gashi alamu yanuna kinji me yace. Komawa tayi jikin Areef zata kwanta, dan gaba daya wani zazzabi takeji, sanyi sekara shigarta yakeyi.

Dasauri Haisam yajawota yana fadin yau ko sunanki mage senaga karshen son jiki. Areef yace haba bros kabita ahankali mana, kama hannun Areef tayi tarike sosai tafara kuka. Tsaki Haisam yaja yace toni zantafi.

Areef kamar zeyi kuka yace plsss kabari muji daga bakinta. Kallonta yayi, yace Beauty tashi kifadamun daga ina kike kinji, kinga kada yatafi yabarni kuma nasan mutane zekira kuma kamaki zasuyi, ai dasauri ta tashi tarike hannunshi, shima tashi yayi yana murmushi.

Haisam yace daganinta batada gaskiya gashi daga yin maganar kamawa tamike. Hannu tasa tana kara nuna mashi hanyar data fito, Areef yace baki iya magana ne? Kai tadaga mashi, tare da fara janshi zuwa hanyar. Atunaninshi ko sanyi ne yahanata magana, hakan yasa yafara binta. Da har Haisam ya kyaleshi se kuma yayi tunanin kada ta cutar dashi seyabisu.

Sunkusa zuwa gurin sukaci karo da Jakadiya tafito daga cikin gida hankalinta atashe. Cak ta tsaya tana masu kallon mamaki, kara kallon Yar Baba tayi, nan hankalinta yafara tashi ganin kayanta ajike, sede ganin wanda suke tare, yasa taboye tashin hankalinta. Da gudu taruga ta rungume Jakadiya Safeeya, janta tayi zuwa cikin gida, suma suka bi bayansu.

Seda tashiga da ita daki tasata tacire kayan tace tasaka wasu kafin tafito, juyawa tayi takoma falo. Bayan sungama gaisawa, Areef yace Aunty ashe beauty agidanki take? Kawai muna zaune nida Haisam agurin lambu semukaji karar wani abu acikin ruwa, muna dubawa ashe ita ce tafada, koda nacirota, ta suma, da kyar ta farfado. Shine tabamu tsoro, dan bamutaba ganinta agidan nan ba, gashi kuma kyanta ya kai akirata da aljana.

Koda muka fara tambayarta bata bamu amsa ba, sede kuma tanajin abinda muke fada, shine daga karshe tajawo ni muka taho nan. Ajiyar zuciya Jakadiya tayi jin bayanin da Areef yayi mata. Murmushi tayi tace Allah sarki sannunku nagode sosai, inbadanku ba kila data halaka, mantawa nayi ban kulle kofar ba, kuma nasan nitafito nema dan banyi mata sallama ba dazantafi.

Shirun dakaji tayi ai bata iya magana, tunda aka haifeta ahaka take, sede tanajin duk abinda aka fada. Tausayinta ne yakamasu, jikinsu duk yayi sanyi bakamar Haisam. Areef yadaga baki zeyi magana kenan tafito, baki yasaki yana kallonta, gani yake kamar ba ita bace, tasaka riga doguwa me siririn hannu tayi mata kyau sosai, kalarta Ja ce, gashi bata daura dankwali ba, fuskarta tasha kwalliya kamar meshirin zuwa gasar kyau, hannunta rike da comb, tana zuwa tafada jikin jakadiya ta mika mata comb din.

Murmushi tayi tace Uhm Yar Baba sarkin kwalliya yanzu seda kika kara wata kwalliyar? Kwantawa tayi jikinta takamo hannunta tadorashi akan wuyanta, jakadiya tace kai naji jikinki dazafi, ko ruwan dakika shiga ne, ze sakar maki Zazzabi?.

Kai tadaga mata, tana lumshe ido, Haisam yace Aunty ai dama yakamata abata magani tasha, kada yarufeta. Jawo hannunta takarayi tana mata nuni data sharce mata gashinta, fara Sharce mata tayi tana fadin kuma gashi babu magani agidan nan, sede inje gurin Gimbiya kozan samu.

Haisam yace a,a bari kawai idan muka fita semu siyo mata, kallon Areef yayi yace kai kuma mr. Watching seka tashi mutafi musiyo magani, shiru yayi mashi yana kallon yanda tarufe ido tana bacci, ga gashinta daya gama tafiya dashi. Dan bakinta yasha red janbaki, tayi mashi kyau sosai. Dukan dayaji akafadarshi ne yamaido dashi tunanin dayakeyi.

Hararar Haisam yayi, gwalo yayi mashi yana murmushi. Areef yace Aunty amma bansanki da diya ba ina kika samota? Tace tare muka dawo da ita daga Darazo, acan gidan Malam take, diyar Dan uwanmu ce. Zekara magana Haisam yace katashi muje musamo mata magani bata lafiya, idan mundawo seka idasa tambayar taka. Tashi yayi yana sosa kai yana murmushi yace Aunty semun dawo.

Kallonshi tayi tace dan Allah banason inji wannan maganar agurin kowa, koda kuwa Gimbiya ce, ko Sarki, kuje kudawo zakuji dalilina nafadar haka. Suka ce to, fita sukayi Areef yanayi yana waige, bugewar dayayi da kofa ce tasashi saurin dafe goshin shi. Dariya Haisam yasa hada rike ciki, suna fita Areef yakai mashi duka yana kara dafe goshin shi. Haisam ya tsagaita dariyarshi yana fadin sannu abokina ai bansan kaji zafi ba. Areef yace kacigaba lokacinka ne dariya ma yanzu kafara yimani inde akan beauty ne. Haisam yazaro ido yace akwai wata a kasa kenan? Areef yayi murmushi yace a,a sede asama dan iska. Dariya suka saka kafin suka nufi hanyar parking space.

Cak sarkin fada yatsaya ganin abinda beyi tsammani ba, adede lokacin dayake fitowa daga part din Medaki, daka ganshi kasan baya cikin nutsuwarshi. Wani irin kallo Waziri yake binshi dashi, cikin tsarguwa Sarkin fada ya matso yana washe baki yace rankaidade barka da fitowa, nima yanzu nafito zani fada shine Jakadiya Karima take shedamun Gimbiya Medaki tana nemana. Toyanzu nashiga ko minti 3 ma banyi ba, tambayta tayi shine kaga nafito. Muje fadar ai can kayi ko? .

Da ido Waziri ya kafeshi, bece mashi komai ba, kifce kifce yafarayi yana fadin ai semu wuce ko? Murmushi Waziri yayi ya girgiza kai yace muje, haka suka nufi fada cikin Sarkin fada duk ya duru ruwa, se addu,a yake Allah yasa Waziri be harbo jirginshi ba.

Baban Fulani ne zaune akofar gidanshi tare da Baba suna ta fira, dan  zaman dayayi bakaramin sabo sukayi ba, Baba yace gaskiya ina tausaya maka halin daka shiga, tabbas ka hadu da jarabawa, sede kuma hakurin dakayi gashi nan Allah yabarka da lafiyarka, kuma dama anason me hkr aduk lokacin da wata jarabawa tasameshi. Baban Fulani yace hakane, nima ada nayi niyar komawa kasata, sede ganin irin karamcin da mutanen nan sukayi mani da kuma rashin sanin Rayhana tana raye ko mace, wannan dalilin shine babban abinda yahanani tafiya, amma insha Allahu nasan za,a ganta tunda de anfada mana tana raye. Baba yace ai Allah baya bacci, koma a ina take wata rana zata dawo.

Koda su Areef suka koma jikin Yar Baba yarikice, Zazzabi ya saukar mata sosai, dan bata tabayin zazzabi mezafinshi ba, se kuka takeyi dama kuma gata raguwa, kwance take ajikin Jakadiya Safeeya suka shigo bakinsu dauke da sallama, dasauri Areef yazauna kusa da Jakadiya yana fadin Aunty bade jikin bane?.

Tace wlh kuwa, tunda kuka fita ta kwanta shikenan zazzabi yarufeta, Haisam yace Aunty kawai kutashi mutafi asibiti, zaro ido tayi tace A,a kawai ku kawo maganin inbata nasan zata samu sauki, kaga abincinma taki ci. Zata kara magana kenan taji motsi adakin Maman Yar Baba, saurin tashi tayi ta kwantar da ita bisa kujera tace inazuwa bari inshiga bandaki, Yarima kabata abinci kila taci seku bata maganin nasan zata samu bacci, bari infito.

Abakin kofa tasameta, dama tasan lokacin cin abincinta yayi jira take Yar Baba ta kyaleta taje ta tadata tabata abinci tasha maganinta, saurin kama hannunta tayi tasama kofar key suka koma ciki, bandaki tajata seda ta wanke mata baki tayi fitsari, sannan suka dawo tazauna dan tabata abinci.

Abincin yadauka ya matsa kusa da ita, hannu yasa yadagota, tana tashi ta lafe ajikinshi, zama yayi akan kujerar, hakan yasa takara shigewa jikinshi. Dariya Haisam yayi yazauna yana fadin wlh Beautyn Areef keda mage bansan wanda yafi wani son jiki ba, Areef yace kaga malam kabarta taci abinci tunda ba,a jikinka ta kwanta ba. Haisam yace ato adebi ahankali dan wlh kosannu bazan cemaka ba idan kacemun,,,,,,, gira yadaga mashi yana murmushi yace ai kagane?.

Areef yace kaide kasani dan iska kawai, kamata yayi ya rungumeta  ahankali yace kinajina ko beauty? Kai tadaga mashi tana turo baki, murmushi yayi yace yauwa idan bakiso inkira mutane sukamaki to kici abinci inbaki magani zaki warke, ai dajin haka tabude baki. Dariya Haisam yayi yace anya beauty bata tsoron mutane kuwa? Wannan shine karo na biyu danaga tana tsoro idan ance mutane. Areef yace haka ne, nima nalura da haka, kuma inaso Aunty tafito tadan bani labarinta, dan ban gamsu da bayaninta nadazu ba, yarinyar nan tafi kama da diyan larabawa.

Haisam yace shiyasa naga kuna dan kama , harararshi yayi yace ta ina? Haisam yace wlh ba batun wasa ba, dazu data kulle idonta na kalleta naga kundanyi kama, musamman tagurin idanunku da bakinku. Areef yace kaji dashi, nibanga wata kama ba, kyaleshi yayi yadauki cokali yafara bata abinci.

Hankalinshi gaba daya yana gurin kallon yanda take cin abincinta, shikanshi abun burgewa ne, tana jikinshi ahaka tagama cin abincin, shiko Haisam kallonsu kawai yakeyi, yafiddo waya yana daukarsu vedio, sun bala,in burgeshi, gani yake kamar atare aka halicce su. Magani ya ballo sede da kyar tasha, shima seda yayi mata wayo, tana gamasha ta koma jikinshi ta kwanta, kallonta yayi yace bacci zakiyi? Kai tadaga mashi, tare da lumshe ido, ko minti 5 ba,ayi ba. Bacci yadauketa. Areef yace beauty bakida matsala, yarinya cekace jaririya acikin minti 5 harkinyi bacci.

Bayan tagama bata abinci tabata magungunanta, sannan tajata zuwa bandaki, wanka tayi mata, bayan sunfito tagoge mata jiki, ta dauko wata doguwar riga tasa mata, kwantar da ita tayi bisa gado. Idanu ta kura mata ganin yanda dan kwanakin dasukayi tasake sosai, kara kallonta tayi, gabanta taji yana bugawa dasauri, matsawa tayi kusa da ita dan takara tabbatar da abinda tagani. Tabbas wannan matar zargin malam yazama gaskiya, wasu hawayen farin ciki ne, suka rika fito mata, zama tayi takama hannunta tana fadin ita ce, wlh itace, dama nasan malam baze taba fadin abu yazama ba haka ba, aiko ayau Sarki zeji labari medadi.

Waya tadauko takira Malam, bayan sungaisa, yace Safeeya yanajiki cikin farin ciki haka? Wlh malam tunaninka yazama gsky, dama kace kana tunanin wannan matar kamar Gimbiya Fulani, wlh, itace, nadade dafara tunanin haka tun akan diyarta, kamarsu da ita nake gani afuskarta, sede bakowane ze gane hakan ba, amma nide wlh yanda nasan Fulani kamarta bazata iya bacemun ba.

Hamdala Malam yayi yace nadade da tunnin haka, sede kinsan irin wannan al,amarin ba,a saurin yanke mashi hukunci, dole muyi ma Allah godiya, kuma zansa ayi sadaka, sede akwai abu daya danakeso daga gareki, wannan maganar daga ni seke se Waziri mukasanta, shima yanzu zankirashi infada mashi zarginmu yazama gaskiya, ammafa dole muyi shiru da bakinmu, kinsan idan har baka iya kama barawo ba, toshi seya kamaka, acikin gidan sarautar nan, akwai munafukai dayawa, idan bamubi asannu ba, bazamu iya kamasu ba.

Dan haka nasan haryanzu babu wanda yasan dazamansu agurinki, inaso kicigaba da rike sirrinmu, har ranar da Allah zebama Gimbiya lfy, bincikenmu zefi tafiya dede. Shiru tayi can kuma tace amma malam akwai mutum 2 dasuka san Yar Baba tana gurina, Yarima da abokinshi, yanzu haka suna gidan nan,,,,,,,,, kwashe duk abinda yafaru tayi tafada mashi, malam yace babu damuwa inaso kibarshi ayanda kika fada masu, sede kada kibari suga Gimbiya tunda dama kince bata fitowa falo,sallama yayi mata yace zekira Waziri.

Falo tafita ta iske su zaune, murmushi tayi tace kuyi hakuri nabarku dajira. Areef yace bakomai, hartayi bacci ma, Jakadiya tace kwantar da ita muje nima fita zanyi nasan gimbiya tana jirana, Areef yace a,a muje inkaita daki ahaka ai seta fado. Daukarta yayi kamar baby ya nufi dakin jakadiya, saman gado yadorata, juyi tayi takara rungumoshi, harseda yafada mata. Wani yarrr yaji ajikinshi, murmushi yayi yacire hannunta yajawo pillow yasa mata, nan take tarungumeshi, tsayawa yayi yana kallonta, dukawa yayi ya sumbaci goshinta, tare da fadin Allah kasa Momy da Abba sukarbi zabina. Juyawa yayi yafita.

Bayan malam yakira Waziri sundade suna magana, bakaramin dadi Waziri yajiba dayaji bayanin malam, haka suka dade suna tattaunawa, daga karshe Waziri yace akwai wani sirri dana fara ganowa agidan nan amma inaso inkara tabbatar dashi kafin infada maka. Malam yace Allah yayi mana jagora, insha Allah komai yakusa zuwa karshe, zan aiko da maganin me martaba. Godiya Waziri yayi mashi sukayi sallama.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 75⚜80

Waziri ne zaune tare da Sarkin Fada, Waziri ya kalli Sarkin fada yace, kasan nifa nafara gajiya da masarautar nan, bamu samun komai se wahala, shi wancan Yana zaune, jaririma yafishi dadin sha,ani, shikuma Sarki Qaseem bawani aiki yake ba, kullum da anyi magana yace Yayanshi, kawai idan bazasu iya ba, yakamata sumika ma nawajenka.

Amma kuma zamusha shiririta, dan nasan Yarima kwata kwata sarauta bata dameshi ba, shiyasa kozaman fada bayaso. Wata irin dariya Sarkin fada yayi, da alama antabo mashi inda yake mashi kai kai, baki ya karkace yafara zuba, ashede kaima kana layina, yoni idan tanine ai dayanzu an dade dashafe babin wadannan sarakunan 2.

Aduniya babu abinda natsana kamar inga wadannan mutane 2 suna farin ciki, shiyasa bakaramin dadi najiba alokacin da akace Sarki ya samu matsalar shanyewar barin jiki. Naso ace Sarki Qaseem be anshi sarautar ba, nasan kila da kai za abama.

Amma kana maganar wani Yarima ai har abada bazeyi sarauta ba, sede idan ubanshi ya mutu, ai akwai dalilin dayasa bayason sarauta, anfada maka son danake mashi nabanza ne? Nifa banason wani daga zuri'arsu yaci gaba da mulkin nan. Waziri yace amma nasan duk ranar da akace angano inda Fulani take nasan daga ranar Sarki zewarke.

Dasauri Sarkin fada yace ina, ai har abada kuwa baze warke ba, dan bana tunanin Fulani tana raye, saurin kallonshi Waziri yayi yace kamar ya kenan?  Rufe baki yayi yafara in ina, yace a,a kagane bawai ina nufin tamutu ba, gani nayi yau shekaru nawa da batan ta, inda tana raye ai da anganta. Wani murmushi Waziri yayi yace dama musami labarin mutuwarta ai dayafi, Sarkin fada dasauri yace wlh kuwa da kowa ya huta. Tashi yayi yace bari inje gurin mutuniyata, waziri yace wakenan?.

Jakadiya Karima mana ai kasan duk gidan nan banida aminiya kamarta, wato matar nan tasan takan duniya, sallama yayi mashi yayi gaba. Wata irin zufa ce tafara fitoma Waziri, ahankali yace Jakadiya Karima? Tasan takan duniya? Aminiyarshi?. Murmushi yayi yace nasamu daya, saura na biyu. Waya yaciro yakira malam, sun dade suna magana kafin yakashe yanufi fada.

Areef ne kwance akafar Momynshi Jakadiya Safeeya tana gefe suna fira, ahankali Gimbiya tashafi kanshi tace Yarima haryanzu naji shiru tunda mukayi maganar aure baka kara cewa komai ba, kasanfa kabar Abbanka cikin damuwa. Wani murmushi yasaki tare da lumshe ido, ita yakara gani aidonshi alokacin dayake bata abinci, ahankali yace beauty.

Momy tace wacece kuma Beauty? Saurin bude ido yayi yace kawai Momy inason mace me kyau, shiyasa kikaji nace beauty, murmushi tayi tace to kasamu kenan? Kai ya girgiza mata yace nade kusa samu kitayani addu,a. Momy tace Allah yasa irin zabin muce? Bata fuska yayi yamike tsaye yace Momy wai haryanzu baku cire wannan ra,ayin daga ranku ba? Nifa agskiya bazan auri yarinyar data taso gidan sarauta ba, duk wata al,ada tata da dabi'unta duk na sarauta, nidan sarauta itama yar sarauta towazeyi mulkin kenan?. Shiru Momy tayi tana kallonshi, tashi Jakadiya Safeeya tayi takama hannunshi tace haba dan autan Gimbiya, tomeye na bata ran? Zomuje gida kafadamun abinda kakeso, amma nima zanfada maka wanda nakeso, kayarda ? Kai yadaga mata taja hannunshi suka fita, da murmushi Gimbiya tabisu, aranta tana fatan Allah yasa ya amince.

Gimbiya Zakiyyah ce take tafaman masifa akan jakadiya Karima, wai ke wace irin mata ce, harni zakizo kirika fada ma, wai Sarkin fada yana gaishe ni. Toshi wanene dazemun wannan aiken, ko anfada maki ni baiwace dazakizomun da wannan maganar. Amma balaifinku bane, dan kunsami sakin fuska daga gurina ne, shiyasa kuke fadamun abinda kukaga dama, inda narike mulkina wlh ko kusa dani akace kizauna baza kizoba.

Kuma inaso kifadamun akan wane dalili Sarkin fada yace kigaisheni? Kasa tayi da kai tace Allah yahuci zuciyarki, wlh bada wata manufa yace nagaisheki ba, dama ganina yayi zanshigo nan shine yace ingaisheki, amma ai be isa yayi maki irin gaisuwar dakike tunani ba, agafarceni Gimbiya. Zama tayi tana huci tace, wannan shine karo nakarshe dazaki kara batamun rai, idan bahaka ba, wlh sekin fuskanci hukunci na. Godiya nake ranki yadade uwargida agurin Sarki, mace daya tamkar da dubu, fitila me haske zuciyar Sarki, Allah yakaramaki lafiya da daukaka aduniya, Allah yasa kifi haka. Murmushi tasaki sannan tadaga mata hannu tace muje kirakani gurin Medaki inaso indubata. Zaro ido Jakadiya tayi tace Eye, na'am , mekikace? Wata harara tasakar mata tace kina nufin bakiji menace ba? Nima yau inaso inje bangarenta. Wani miyau medaci Jakadiya tahadiya, dan ta tuna sanda zatazo nan sunhadu da Sarkin fada kuma zeje gurin Medaki. Tashi tayi jiki asanyaye suka nufi bangaren Medaki, bayi suna take mata baya.

Koda suka shiga azaune suka sami yar baba tana kallon casset din da Jakadiya ta kunna mata, tana ganin Areef tashiga sakin murmushi, shima murmushin yasaki, tare da sakin ajiyar zuciya, kusa da ita yazauna yana fadin beauty jiki yayi sauki ko? Matsowa tayi kusa dashi tadora kanta saman kafadarshi tare da daga mashi kai. Girgiza kai jakadiya tayi aranta tace dole in nuna ma Yar Baba matsayin kowane namiji agurinta, wato ita atunaninta yanda take hawan Baba kowama zata mashi haka? Dole musake sabon karatu. Tanaso tace mata ta tashi kuma bataso Areef yadauka dawata manufa, zama tayi akasa tace zonan yar Baba inji jikinki.

Tashi tayi taje tazauna kasa tare da dora kanta saman cinyarta, hannu tasa ajikinta tace ai zazzabin ma yatafi ko? Kai ta daga mata tana maida kallonta gurin Areef. Itama Jakadiya shi ta kalla, aranta tace tabbas kuna kama daga idonku har gurin bakinku, saukowa yayi shima yazauna akasa,ya kalli Jakadiya yace.

Aunty kina ganin idan nafitoma Momy da Abba wadda naji zuciyata tanaso, kuma bata kasance yar sarauta ba, kina ganin zasu ansheta? Murmushi Jakadiya tayi tace kwarai ma kuwa, amma dole sekayi abinda zanfada maka idan bahaka ba to sede ka auri mata 2, nikam banaso ka hada macen da kake so da wata, kana ganin yanda Sarki yakasance alokacin daya samu wadda yakeso, jiyayi dama beyi aure ba, da babu abinda zesa yakara aure bayan ya aurin zabinshi. Kuma kasan yanda sharrin matan sarauta yake, idan har sukaga mijinsu yana nuna fifiko atsakinsu yanzu zakaga anfara shigo da hassada.

Kuma nibanason kayi wani abu daze zo yaraba zumincin dake tsakanin iyayenka, duk da bangama gano wacce kake so ba, amma inaso yanzu kafada mun. Shiru yayi yana kara kallon beauty, itama shi take kallo, yace Aunty zanfada maki amma banaso beauty taji. Ai tanajin abinda yafada tafara dirza kafa akasa, tana turo baki tare dayin bayaninta da hannu na kurame. Dariya suka saka, yace metace wai?.

Jakadiya tace a,a ni baruwana kaine dakayi magana take wannan borin. Kallonta yayi yace beauty ai wannan maganar manya ce shiyasa nace banaso kiji, tashi tayi tadauki pillown kujera takwada mashi tashige daki tana dira kafa, dariya yayi hada rike ciki. Wayarshi ce tayi kara, yana dauka yace kasameni gidan Aunty.

Jakadiya tace hala Haisam ne ? Yace ai kinsan seshi, shikadai ne abokina aduniya nayarda dashi kamar yanda ya yarda dani, shiyasa bana tsoron yasan komai daga gareni. Sallama sukaji, Areef yace kashigo mana katsaya kamar kazo gidan surukai.

Zama yayi bayan sungaisa da Jakadiya yamika ma Areef hannu suka gaisa yana fadin ai garani bagidan surukan nazo nazauna ba. Dariya suka saka, Areef yace yauwa Aunty inajinki menene abinda kikeso inyi? Zama ta gyara ta kalli Haisam tasake fadin abinda tafada da farko, sannan takara dacewa abinda nakeso da kai yanzu kafadamun wace yarinya kakeso kuma a ina take, daga nan ni kuma zanfada maka mezakayi.

Sarki Qaseem ne zaune afalon gimbiya suna fira tana mika mashi kankana, kallonshi tayi tace Hubby, kayi hakuri nayi wani hukunci kuma bansanar da kai ba. Jawota yayi yasata ajikinshi sannan yace bakida damuwa kome kika yanke nasan zeyi dede da ra,ayi na, kinsan muna tafiya akan tsari daya. Murmushi tayi tace haka ne, dama bawani abu bane, munyi waya da Yaya nace mata tashiryo Ayman tadorota jirgi gobe ta taho.

Naga alamar Yarima yakasa samun wadda yakeso, nayi tunanin baya shiga cikin yan mata ne, shiyasa besamu wadda yakeso ba, amma idan Ayman tazo zansata tarika yimashi duk wata hidima, kuma surika fita tare nasan yin hakan zesa su shaku har soyayya tashiga tsakaninsu. Murmushi Sarki yayi yace, shiyasa nake sonki dayawa, kinyarda ra,ayinmu yana tafiya dede? Kai tadaga tana wasa da hannunshi. Yace amma ina fatan baki fadama Ummin Aymana dalilinki nasan tazo ba ko? Tace kamar kasani, banaso mushiga tsakaninsu harsesun shirya kansu sannan.

Yace da kyau, nafison kamar yanda naganki naji inasonki kema haka banaso mushiga hakkin Areef, duk da idan ya gwada bazebi zabinmu ba, bazanyarda ba, amma ko ita kada kifada mata dalilin sawa tazo, kawai kibarta, nasan zasu saba. Rungumeshi tayi tana fadin nagode hubby na. Kiss yayi mata akumatu, yana fadin bari inje gurin yaya yau likitan daze fara yimashi gashi zezo daga,
U.S, Tace Allah yasa adace, amma anan zezauna ko? Yace e zeyi kamar wata guda, kuma insha Allahu munasa ran nasara. Tace Allah yasa.

Da sallama suka shiga falon Medaki, sede bata nan, cike da fargaba Jakadiya karima tace rankiyadade kizauna bari inje indubota, zata shiga kenan tafito tana fadin ashe yau manyan baki garemu, Gimbiya Yaya da kanki aida kin aiko nazo. Ya mutsa fuska tayi tace kawai nima sha,awar fitowar nakeyi.

Zama tayi Jakadiya sebinta da idanu takeyi jikinta yana tsima, wata baiwa ce tashigo hannunta rike da katon faranti medauke da kayan marmari, jakadayi tace barka da fitowa Gimbiya, tace yauwa sannunki. Jakadiya tace ina fatan wannan kayan marmarin nadazu da aka kawo marasa kyau anfitar dasu ko? Medaki ta kalli Jakadiya, tayi murmushi tace ai basu dade bama. Gimbiya Zakiyyah tace shiyasa nakeso arika duba kayan daza,a kawo base ankawo ba ace basuda kyau.

Jakadiya tace kwarai ma kuwa, ai tunda basu cikin gidan nan hankalina ai yakwanta. Gimbiya Zakiyyah tace se akara kula. Medaki datake dariya aciki takara kallon Jakadiya wadda jikinta yayi sanyi, aranta tace lallai Jakadiya yar duniya ce, aifa sekayan marmarin, Sarkin Fada ai yamafisu komai. Gimbiya Zakiyyah tace yanzu fa idan Sarki yafadi ya mutu shikenan munzama yan kallo agidan sarauta ko?

Medaki tace nima nayi wannan tunanin anya babu saka hannun kaninshi arashin warke warshi kuwa? Ace ciwo shekara 18 harda watanni amma be warke ba. Kiduba fa kiga yanda yaki yarda afitar dashi waje, kullum seyarika fadin wai yace baya so, to mutumin da baya magana taya zece bayaso?

Jakadiya tace nizan fada maku haka, nida ake komai agabana, aduk lokacin da za,ayima Sarki gashi ko za,a bashi magani, daga Sarki Qaseem se Waziri kadai suke shiga dakin, nima nasan akwai abinda suke kullawa, kalli yanda Waziri da Sarki suka hade kansu, kullum yana manne dashi, Sarkin fada beda wani anfani agurinsu.

Gimbiya Zakiyyah tace, to gaskiya bazan yarda ba, daga yanzu inaso kirika saka idanu akan duk wani abu dasukeyi, tunda kowa yasan kece makusanciyar Sarki, dole subarki kizauna tare dashi. Jakadiya tace angama Gimbiya, tashi tayi tace nizan koma. Medaki tace nagode, kigaida gida sena shigo.

Inajinka Yarima fadamun kasande babu abinda bazan iya yimaka ba, dan farin cikinka. Shiru yayi yana sosa kai, Haisam yace Aunty wlh beauty yakeso, tunda nake da Areef bantaba jin yayi maganar wata ba, amma aranar dayafara haduwa da beauty beda magana se tata, kumani tun alokacin nagane yafada soyayyarta, amma sanin halin iyayenshi yasa yayi shiru.

Jakadiya Safeeya tace, na jima dasanin haka, sede akwai abinda nakeso kasani, idan har kanason yar Baba dole Kaboye ma Iyayenka harse zuwa wani lokacin daya kamata, banaso azo ahada tashin hankali, wanda zeyi sanadiyar rushewar zumunci. Areef yace Aunty akwai wani zumunci atsakaninki dasu Abba ne? Saurin girgiza kai tayi tace bahaka nake nufi ba, kaide kawai kayi yanda nace, kawai kanuna masu kana nema nan da dan lokaci komai zezo karshe.

Areef yace amma Aunty yanaga kamar beauty ba irin ta yan nigeria bace, gsky kyanta yawuce misali. Rasa mezata ce mashi tayi, tace kasan dangin mamarta ba yan nan bane, buzaye ne. Areef yayi murmushi yace haba shiyasa. Amma haka aka haifeta bataji, tomeyasa ba,a kaita asibiti ba? Jakadiya tace gsky ba,a kaita asibiti ba, kuma banaso kace zaka kaita ayanzu, idan lokaci yayi seka kaita, nima inaji ajikina kamar zata warke. Haisam yace mungode Aunty Allah yabiyaki, tace amin, tashi yayi yace bara inje inbada hakuri.

Jakadiya tace, a,a nasan tayi bacci kabarta kawai anjima sekadawo. Haisam yace malam muje akwai inda nakeso muje, sallama sukayi mata suka fita. Ajiyar zuciya tayi tace Allah katona asirin mutanen dasukayi wannan abu kowa yahuta, nasan Gimbiya zakifi kowa farin cikin zabin da Yarima yayi, sede ina tsoron zuwan Ayman kada ahada rigima, nasan duk mun son da kikema Fulani bekai na yar uwarki ba. Tashi tayi tashiga dakin Fulani.

Zama tayi takura mata ido tana kwance tana bacci, tace tabbas wahala tana canzama mutum kamanni, nayi mamakin yanda banganeki ba tun farko, amma ba abun mamaki bane, sbd irin wuyar da kikasha ashekaru 18 ko Sarki baze iya ganekiba. Fita tayi tanufi dakin beauty.

Jawota tayi tana fadin haba yar leleta, yihakuri, yace zedawo anjima ai, kobakison yadawo? Kaita girgiza tana turo baki, dariya Jakadiya tayi tace, shikenan, tashi muyi wata magana me amfani, tashi tayi tazauna tare da dora kanta bisa kafadar Jakadiya, murmushi tayi tace Sarkin son jiki, to kinsan menakeso infada maki? Daga yau banason inkara ganin Yarima yazo kinhau jikinshi, ko hannunshi banaso kitaba, kinsan nafada maki babu kyau kataba namijin da ba,a maku aure ba ko? Dan haka yanzu yace yana sonki, kuma aurenki zeyi.

Tokinga duk macen da akace anaso bazata kara bari saurayinta yataba taba harse an daura aure, kinji ko? Kai tadaga tana rufe fuska, Jakadiya tace kobaki sonshi, dasauri tayi mata alamun a,a dariya tayi tace kamar gaske keda bakisan wani so ba. To inde kinasonshi idan yazo kirika zama nesa dashi kinji? Ta daga kai. Jakadiya tace yauwa tashi kidauko Fikhu mucigaba da karatunmu.

   Shiru Sarkin fada yayi yana jin bayanin Jakadiya karima, harta gama yayi dariya yace lallai, wato nine ma kayan marmarin? Amma kinhadu, wlh kamar nasani inazuwa nace mata sauri nakeyi. Ita kuma Gimbiya dan tasamu ance ana gaisheta zata fadamun haka. To wlh tunda miyau na yabiya da ita kota halin yaya senasha romonta. Jakadiya tace wlh bakada dama, wato duk matan Sarki seka more? Yace kede muje zuwa kawai.

Washe gari tunda safe aka shiga da Sarki Hasheem dakin gashi, inda sabon likitan yafiddo kayan aiki masu nagarta yafara yimashi gashi dasu, Sarki Qaseem da Waziri se addu,a sukeyi Allah yasa adace. Jakadiya Karima ce tayi sallama tashigo falon, bayan tamika gaisuwarta da tambayar me jiki, tace dazu naga wani bature shine nace ko bako mukayi ne?

Waziri yace abokin Sarki ne, tace aiyo, nace memartaba ko wanka akemashi ne? Waziri yace dan Allah kifita koma menene idan angama za,a kiraki, tashi tayi tana cewa to to afito lafiya, da harara yarakata aranshi yana fadin tabbas abinda zuciyata take fadamun akanki yafara zama gaskiya, amma muje zuwa nasan lokacin yataho. Sarki yace meyasa baka fada mata gaskiya ba, kasan aduk gidan nan babu wadda Yaya yakeso kamarta, Yanda muka dauketa kamar Uwa take agaremu dan mundade da ita. Waziri cike da takaici yace nasani, kawai banason yawan magana ne kasan addu,a mukeyi shiyasa nace mata haka dan karta katsemu. Kallonshi Sarki yayi badan ya yarda da abinda yafada ba.

Sarkin fada ne zaune adakinshi hannunshi rike da wani abu yana kallo yana murmushi, yace Gidan sarauta babu gsky, nasan wata rana dole asirinmu zetonu, akullum idan bayi suka hada kai da yan sarauta karshe sune masha wuya, nasan mu munfi bayi matsayi, amma kuma kaskantattau Gimbiya take daukarmu agidan nan, ranar tonan asiri aranar zakamun rana. Dariya yayi yamaida abun cikin jakarshi yana fadin wai Sarkin Fada? Kode Sarkin tsiya? Wata dariya yayi yace koni ina tsoron kaina.

Seda Ayman takwana 1 dazuwa sannan suka hadu da Areef, yafito da yamma cikin shirin fita afalo yagansu zaune, Areef yace kai, Momy yaushe Ayman tazo bansani ba? Murmushi tayi tace kana can gurin Haisam kuma sanda kadawo tayi bacci, dasafe kuma kafita aiki bata tashi ba, dama cewa nayi zaka ganta da idonka. Dariya yayi yazauna yana fadin mutanen misrah tace Yaya Areef inakwana, yace lfy lau, kinzo lafiya ya yan gidan? Tace lafiya lau suna gaisheka, yace to ina tsarabata? Tace tana nan, yace yauwa bari inje Haisam yana jirana idan nadawo zan karba.

Momy tace inazakuje? Yace wlh kawai zamufita garine, tace to ai dakuntafi tare itama taga garin, yace hakanefa taso muje kiga birni, dariya tayi tace wane birnin kuma, fita sukayi suna fadin semun dawo Momy. Da kallon sha,awa tabisu tana murmushi, tare da fadin Allah kasa su hada kansu amin.

Tare suka jero har bakin motar da Haisam yake tsaye yana jiranshi. Idanu Haisam yaware yana kallon Ayman wadda taketa dariya ita da Areef, gaba daya tagama tafiya dashi, suna zuwa gaban motar Areef yace yi hakuri kaga wadda ta tsaidani nan, se alokacin itama ta kula dashi. Idanu itama tazuba mashi tana kallonshi cike da burgewa, gaba daya yagama tafiya da ita. Areef ya tsaya yana kallon Haisam wandda bemasan abinda yakeyi ba, juyawa yayi yakalli Ayman, itama mamaki tabashi yanda ta tsaya tana kallon Haisam, dariya Areef yayi ya harde hannuwa akirji tare da jingina jikin mota yana fadin ikon Allah.

Nima nace Ikon Allan gaske, Areef tayani gani.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 80 ⚜85

      Da karfi Areef yabugi kafadar Haisam yana dariya,  cikin sauri Haisam da Ayman suka dawo cikin hankalinsu, kunya duk takamata ganin Areef yagane kallon dasukeyi, cikin dakewa Haisam yace wlh kai dan iska ne, ni nayima haka lokacin dakaga Beauty?.

Dariyar da yakeyi ya dena yana fadin ai gani nayi kunmaida ni dan kallo, Haisam yajuya yakara kallon Ayman wadda ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsunta, murmushi yayi yace yaushe kukayi bakuwa bansani ba?.

   Areef yace kaide kashiga mota muje, kuma kabani key din, Haisam yace saboda? Areef yace kaima kasan bazan shiga tukinka yanzu ba, idan ko zaka tuka to wlh sede acire center mirrior. Dariya Haisam yayi ya cilla mashi key din, yana fadin ai se inzauna baya kaga nahuta da waige.

Tunda suka fara tafiya Haisam yakasa zama dede, ita ko duk kunya takamata, da kyar ta iya gaishe shi. Haisam yace lfy lau kinzo lfy? Tace lafiya lau, Areef yace malam yazaka barni ina tuki karika juyawa gurinta anbarni sekace driver. Dariya Haisam yayi yace Allah yabaka hakuri Yaya Babba.


Dariya Areef yayi, yace kaji munafunci, zakayi bayani ne. Wani gurin shakatawa sukaje, bayan yayi parking suka sami guri suka zauna, haryanzu Haisam yakasa dauke idonshi akan Ayman. Jan Areef yayi gefe, anan yace dan Allah abokina ina kasamo wannan me kyan? Dariya Areef yayi yace diyar Yayar Momy ce fa, jiya tazo, nima seyau naganta shine Momy tace mufito tare. Ajiyar zuciya yayi yace Allah yasa wani beriga ni ba, kasan Allah? Alokacin dana ganta jinayi numfashina yana neman tafiya.

Bantaba haduwa da macen data tafi dani alokaci guda ba, se Ayman, kuma yanzu ba se anjima ba, zanshigar da kaina. Areef yace ai bazaka sha wahala ba, dan naga itama ta kyasa. Haisam yace muje munbarta ita kadai, Areef yace kawaide kutashi mutafi gida nima wlh beauty na nakeson gani. Haisam yace dan Allah kabani 5 minutes ya isa.

Cikin wani shopping complex Areef yashiga, haka yayi ta daukarma Beauty kayan lashe lashe. Zama Haisam yayi akan kujerar datake fuskantar Ayman, shiru yayi yana kallonta har nawani lokaci, ahankali cikin murya mecike da so yakira sunanta da Angel. Seda taji wani Yarrr alokacin dataji sunan, kara dukar da kanta tayi tana murmushi.

Kara kiran sunan yayi, ganin bazata dagoba yace haba Angel, ko rowar fuskar ake mani? Wlh bazan boye maki ba, tun lokacin danayi ido biyu dake, kika tafi da zuciyata, Allah yasa babu kowa ataki zuciyar kamar yanda tawa take empty? Wani dadi ne yaziyarci zuciyarta jin abinda yafada.

Angel kode in hakura akwai wani dan uwanki kuma dan kasarku wanda yarigani. Batasan lokacin datace a,a ba, dariya yayi yace kina nufin nasamu karbuwa kenan? Kai tadaga, wani sanyi yaji aranshi, hannu yamika mata yace tobani wayarki insa maki number ta.


Yana cikin sawa Areef yadawo hannunshi dauke da manyan ledoji guda 2, yace kai wlh nagaji zantafi kuma sede kunemi mota. Haisam yace ai mungama harna kashe boss. Dariya yayi yace ainasan dama bazaka sha wahala ba. Ayman cikin hausarta wadda bata goge ba, tace Yaya tsaraba kasiyomun?.

Dariya yayi yace haba Ayman ai yanzu kinfita daga hannuna, nima iyalina nasiya mawa. Turo baki tayi tace kai Yaya yaushe kayi aure? Yace keyanzu aure kikayi dana ganki kina fira? Murmushi tayi tare da saddar da kanta. Haisam yace Angel tashi muje kizabi abinda kike so, Areef yace oho de, aide seda nayi sannan kuma kuyi sauri.

Jikin Sarki Hasheem yafara sauki sosai, dan yanzu yafara motsa hannunshi da kafarshi dasuka dena amfani ada, bakaramin dadi Waziri da Sarki Qaseem sukaji ba, sede haryanzu befara magana ba, kuma akullum tare suke fita dashi fada, sede idan yana bacci.

 Acikin matanshi babu wadda take zuwa gurinshi da sunan wani abu, tsakinsu dashi sede su shiga su duba jikinshi, amma ko abinci Waziri ko Sarki Qaseem suke bashi.

Gimbiya Suhailat ce, zaune tare da Sarki, kallonshi tayi tace kasan hubby Ayman da Yarima sunfita yawo, bakaga lokacin daya ganta ba, yanda yake fara,a, itama haka, wlh bakaji yanda naji dadi ba. Sarki yace lallai munkusa shan biki agidan nan, sede inaso abari har yaya yakara samun sauki sannan. Tace hakan ma yayi, Allah yakara mashi lafiya, yace amin.

Suna dawowa, suka nufi gidan jakadiya Safeeya, sede Areef yace ma Haisam sujirashi yashiga yayi magana da Aunty, kade gane menake nufi? Haisam yace hakane gskiya jeka bari muzauna alambu.

Bayan sun gaisa yayi mata bayanin abinda yake tafe dashi. Wani irin dadi ne, yashiga zuciyarta, sede bata fada mashi dalilin zuwan Ayman ba,kallonshi tayi tace gskiya naji dadin wannan maganar kuma Haisam mutumin kirki ne, nasan ko kanwarka yanuna yana so zaka bashi, dan kafi kowa sanin halinshi, amma akwai wani abu guda danakeso infada maku daga kai har Ayman.

Kada ku kuskura kubari Gimbiya ko Sarki wani yasan tarayyarsu da Haisam, kasan dalilin dayasa nafada maka haka? Saboda kasan ra,ayin iyayenka akan sarauta, kubar abin aranku, nan da wani lokaci komai zeyi dede, kaima alokacin zanyi masu maganar Yar Baba, kaga se ahada datasu Ayman, kaje kakirawosu, bakomai nasan idan nace ma Ayman kada tafadama kowa Yar Baba tana gida bazata fada ba. Areef yace Aunty kamar akwai wani abu dakike boyemun dan Allah kifadamun, kinsan halina babu wanda zan fada mawa.


Kai tagirgiza tace babu abinda nake boye maka, kaide inaso kayi biyayya da duk wata magana dazan fada maka, nafika sanin masarautar nan, dan haka kabi abinda nafada maka, kasan bazan taba cutar da kai ba. Kirawosu inyimasu jawabin dana maka, inaso inshiga cikin gida. Waya yadauka yakira Haisam yace su shigo.

Bayan sun gaisa Jakadiya Safeeya tayi masu irin bayanin datayi ma Areef, kallon Ayman tayi tace inafatan kingane abinda nake nufi? Idan har kunaso burinku yacika to kubi abinda nafada, bance soyayyarku akwai matsala ba, sede kuyi hakuri na wani lokaci zaku gane abinda nake nufi. Ayman tace mungode Aunty kuma bazan fadama kowa ba. Tace naji dadin haka, bari inshiga cikin gida. Yar Baba tana shiryawa ne. Kasan mutuniyar ko bacci zatayi setayi kwalliya.

Areef yace ai haka akeso Aunty, wai niko Aunty Beauty bata iya rubutu ba, inaganin kamar tunda tanaji ai zamu iya fira ta waya, muna rubutu ko kuma ta takarda. Shiru tayi kafin tace , kasan tunda tagirma aka gane bataji, shiyasa ba,a sata makaranta ba, amma karatun addini tasan abubuwa da dama kuma Allah yabata wata baiwa tasaurin fahimtar abu, kome aka koya mata cikin lokaci kadan zata daukeshi, har mamakin kokarinta nakeyi, ni kaina danayi boko da hada rubutu zan rika koya mata.

Haisam yace, abu me sauki kenan, ina ganin Areef kafara koya mata rubutu, ahankali sekurika shiga cikin karatun boko, kuma nan gaba za,a iya daukar mata me lesson. Areef yace hakane, tunda tana saurin fahimta, insha Allahu setayi karatu, Allah yayi mana jagora, Aunty kirata, se mubar mata Ayman muje muyi sallar magrib.


Bayan tafito, tazauna kusa da Ayman, tana ta murmushi, Ayman ma murmushi tayi tare da jawo hannunta, ai kamar jira take tadora kanta saman kafadar Ayman, dariya duka  suka saka, jakadiya Safeeya tace naga ranar da zaki dena son jiki kekam, daga ganin mutane, baki santa ba amma kin hayeta. Daga ta tayi tana murmushi, Ayman takara jawota tace Aunty kibarta, kinga dama bani da kanwa yanzu nasamu, kwantawa tayi saman cinyarta tana murmushi.

Haisam yace tashi muje masallaci kada Abba yace beganmu ba, Jakadiya tafita tace sekun dawo, akwai abinci akitchen idan kundawo, suka ce to. Areef yaduka kusa da beauty yace wato yau kinga yar uwa shine ko ki kalleni ko? Kai tagirgiza ta tashi ta kalleshi. Dariya Haisam yayi yace beauty bakida matsala, kome akace kiyi sekiyi, gaskiya nan gaba zankoya maki bakomai zaki rika yiba. Duka Areef yakaimashi yana fadin todan bukulu, ai seka hanata, Allah yakashe yabani idan munyi aure base narika magiya ba shine zakace wani tadena. Haisam yace sosai ma, har wannan son jikin duk sena hanata. Dariya Areef yayi yanufi hanayar fita yace tunda kaine mijin ai se ingani, aini naji dadin wannan abu, sonjiki. Ai shine abinso, fita sukayi suna dariya.
Ayman tace sister da kikayi wanka kinyi alwala ko? Kai tadaga mata, tace yauwa tashi muje kiyi sallah nima inyi alwala inyi, hannunta takama suka nufin daki.

Sarkin fada ne tsaye abakin kofar Gimbiya Zakiyyah se waige waige yakeyi kamar marar gaskiya, wani abu yadauko aleda yasa a idonshi, kafin yashiga gidan, alokacin tagama sallah tafito falo, da sallama yashiga, cike da mamaki tace kai? Waya baka ikon shigowa part dina? Ko kuma wani yace maka ina nemanka? Kai yadago suka hada ido, wani irin abu taji ya tsikareta, saurin rufe ido tayi, ganin halin data shiga yasa yayi murmushi aranshi yace anzo gurin. Kallonta yayi yace nadauka ai kinason ganina shiyasa nazo amma bari inkoma.

Saurin bude ido tayi tasaki murmushi tace ni na isa nace ka koma? Shigo sannu da zuwa, zama yayi abisa kujera, tace a,a muje daga ciki kada wasu suganka. Murmushi yayi yatashi yana lashe baki aranshi yana fadin wayyo ni. Daki suka shiga tace meza,a kawo maka? Murmushi yayi yace bakomai zoki zauna kawai fira nazo muyi, wani irin yanayi taji tashiga, tahowa tayi kusa dashi tana wani girgiza, kusa dashi tazauna tace togani, kallonta yayi yakamo hannunta yace babu wanda zeshigo ko? Lumshe idanu tayi alokacin taji wani bakon yanayi yashigeta, tace ina zuwa bari inbada sako akulle mun gidan kuma kada abar kowa yashigo, yace akulle gida nida ba nan zan kwana ba, wani irin kallo tayi mashi tace, kama isa, ai tunda kashigo sede da asuba kafita. Dariya yayi yace duk abinda kika fada dede ne rankiyadade, murmushi tayi tafita. Wani irin tsalle yayi na farin ciki, hannunshi yasa a aljihu yaciro wani abu aranshi yana fadin saboda tsaro.

Bayan sundawo daga sallah part din Jakadiya Safeeya suka wuce, anan suka samesu afalo beauty tana kwance kan cinyar Ayman ita kuma tana ta wasa da gashinta tana bata labari, da sallama suka shiga, Haisam yace to wlh baze yuwu ba, wannan matar taka zata sama Angel dina taurin cinya, Areef yace wlh kai dan iska ne, agaban beauty kake wannan maganar sokake ka kangararmun da ita, bacin kasan yarinya ce. Ai dasauri beauty ta tashi jin abinda Areef yafada, kafafuwa tafara durzawa akasa tana turo baki tana kunkunai.

Dariya Ayman da Haisam sukayi, Ayman tajawota tace yi hakuri, shine yace maki yarinya ko? Kai tadaga tana kara turo baki, kamar zatayi kuka, ai ganin haka yasa Areef ya matso yaduka kasa kusa da ita yana fadin yihakuri beauty na wasa nakeyi kinji? Kai ta daga tana murmushi, Areef yace yauwa beauty na, tashi muci abinci in baki tsara barki. Tashi tayi tanufi kitchen.

Haisam yace gsky kaci sa,ar mata wannan saurin sauka haka, to wlh kaji tsoron Allah, Areef yace da tsoronka nakeji? Sarkin sa ido kawai, kuma badakai zanci abinci ba, nida beauty zanci. Haisam yace Allah nagode maka nima daka hadani da abin sona ayau, nadana shiga 3 agurinka, Angel muma tare zamuci ko? Kai tadaga tana murmushi, lokacin da beauty tafito tasan alokacin ake bama mamanta abinci, harta nufi dakinta se kuma ta tuna da maganar Jakadiya Safeeya,,,,,,,, kada kisake kishiga dakin can idan akwai mutane agidan nan, idan ba haka ba, kamata zasuyi bazaki kara ganinta ba. Maganar Areef ce tadawo da ita, beauty mezakiyi awannan dakin kuma?

Juyowa tayi tana murmushi ta girgiza kai, tanufo gurinsu, ansar abincin yayi ta koma tadauko sauran, atare yazuba masu yamika ma Haisam yace ganaku nan, dariya yayi yajawo yazuba masu, Areef yace taho beauty na muci, zama tayi kusa dashi, sede bega ta jingina dashi ba, murmushi yayi aranshi yace su beauty anfara girma kenan, abaki yafara bata tanaci, shima yace nima bani zakiyi ko? Kai tadaga tana murmushi, haka sukarika cin abincinsu sun manta dawasu Su Haisam.

Dariya Jakadiya Safeeya tayi jin abinda Gimbiya  Suhailat tafada, tace ai sundawo tundazu suna gidana, acan nabarsu suna cin abinci ma. Wani murmushin jin dadi Gimbiya tayi tace ai nasan Yarima zeso Ayman, gashi lokaci guda har sun saba, wato kunyata sukeji shiyasa suka tafi can. Jakadiya tace emana agida na za,ayi firar ai, kinsan Yarima. Naguri nane, ai, gimbiya tace aise suyita ta tafiya nima haka nakeso, Allah yabama Yaya lafiya musha biki. Kallon agogo Jakadiya tayi tace bari inje gida seda safe Gimbiya.

Kallonta tayi tace haba de tunyanzu sallar isha,i ma yanzu za,ayi, wai meyasa yanzu bakison zama anan sosai, musammamma da dare? Gaban Jakadiya yafadi, aranta tace nasan Fulani tana can takusa tashi ai dole inkoma kada su Yarima suganota. Dasauri tayi murmushi  tace ai dole intafi inje inji inda aka tsaya amaganarsu, murmushin jindadi Gimbiya tayi tace hakane fa, Jakadiya tace nikam yanzu ai nasamu yan fira tunda de kunya tahanasu zama anan, dan yarima ma cewa yayi bayaso kusani harse Sarki yasamu lafiya yasan dayayi maku magana za,a sa rana. Gimbiya tayi dariyar jin dadi tace kibarni dasu, zamu gwada masu bamusan komai ba dakanshi zezo mana da maganar, bari hubby yadawo infada mashi, sosai Jakadiya taji dadin maganar Gimbiya, sallama tayi mata tafita.

Koda taje kowa yana zaune tare da masoyiyarshi, Areef yanata koyama beauty rubutu da karatu, kitchen ta wuce ta dauko abinci tace sannuku da aiki, Yarima yace Aunty har kindawo? Tace bari inshiga ciki inci abinci inyi wanka sukace to afito lafiya.

Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya babu wanda yasan abinda yake tafiya atsakanin masoyan. Abangarensu kuwa soyayya me karfi tashiga tsakaninsu, akoda yaushe suna part din Jakadiya Safeeya, Areef yadage sosai yana koyama beauty karatu da rubutu, suna dawowa office beda gurin zama se gurinta, dayake itama tanada basira kome yakoyamata take daukeshi, ayanzu har rubutu ta iya, dan tana hada kalmomi.

Ganin haka yasa hankalin Jakadiya yafara tashi, samunta tayi tafada mata kome Yarima ya tambayeta kada tabashi amsa, idan ba haka ba, duk ranar da yasan labarinta bazata kara ganinshi ba kuma zesa akoresu, kada kisake kice mashi A MAKABARTA AKA HAIFEKI, kawai kifada mashi abinda nafada mai, kinji ko? Ta daga kai, da wannan hankalin Jakadiya Safeeya yadan kwanta, kuma akaci sa,a shima be cika yimata tambayoyi ba.

Abangaren Gimbiya Zakiyya kuwa ta kwace ma Medaki Sarkin fada, dan duk dare agurinta yake kwana, wani irin sonshi takeyi, har bataso yayi nisa, sosai Medaki tashiga damuwa sede tunda Jakadiya Karima tayi mata bayanin komai, shima Sarkin Fada yace mata yayi hakane dan kawai yarama irin cin mutuncin datayi masu ne, kuma kudinta yakeci sosai, kuma yana kawoma su Medaki, hakan yasa hankalinta ya kwanta idan yasamu lokaci kuma yana zuwa gurinta.

Haka rayuwar gidan tacigaba da tafiya Waziri akullum yana kara sakama Sarkin fada ido, dan sunyi waya da malam yace mashi yayi kokari yagama hada duk wata sheda daza,a fara tuhumar Sarkin fada yana nan zuwa tunda jikin Sarki yafara sauki, yanaso akawo karshen matsalar gidan.

Gimbiya Suhailat ce tafito tana neman Ayman, ganin bata ganta ba, wata baiwa tace sunfita bagaren Jakadiya Safeeya. Murmushi tayi tace yaude bari inje da kaina inga wata wainar ake toyawa, kuma in nuna masu nasan abinda suke boyemun, ai gara azo ayi bikin nan kowama yahuta. Allah nagode maka da zaka cikamana burinmu, bari indawo in bama Yaya albishir medadi, itama nasan zataji dadi ace Ayman dinta zatayi aure.  Fita tayi wasu bayi suna take mata baya, suka nufi bangaren Jakadiya Safeeya.

Zaune suke afalo, Areef da beauty suna zaune bisa doguwar kujera, sungama karatu, yana bata biscuit abaki, suna ta firar su gwanin ban sha,awa, Haisam da Ayman suma suna zaune kasa yana bata ice cream tana ta zuba mashi shagwaba.

 Jakadiya kam tana dakin Fulani tagama yimata wanka tana sa mata kaya, tayi kyau sosai, hutun datake samu kyanta yafito har kiba tayi. Jakadiya tace insha Allhu komai zezo karshe da malam yazo kema kije gurin mijinki koze samu sauki.

Wazirine da Sarki Qaseem suka fito zasuje bangaren sarki Hasheem, dede gurin part din. gimbiya Zakiyya zasu wuce, sega Jakadiya da Sarkin Fada sunfito daga gidan, Sarkin Fada se gyara wando yakeyi, suna fitowa suka kwashe da dariya, hannu yamika mata suka kashe, yace kai wlh yau nasha roman Gimbiya, sosai, kinsan tundazu naso infito ta hanani, ashede haka Sarki yakejin dadinshi. Jakadiya tace ba dole sunemeka ba, tunda kana dauke masu nauyin abinda musakin mijinsu yakasa ba, ai wlh..........

Maganar ce ta makale sakamakon idanu data hada dasu Waziri. Hannu tasa ta tabo sarkin fada dayake shirin yin magana. Wata irin zabura yayi alokacin da idanunshi sukaga abinda take nuna mashi, wani irin kallo Sarki da Waziri suke binsu dashi,,,, kuttt suka hadiyi wani miyau me daci, ga wata irin zufa datake fito masu.

 Shinko su waziri sunji firarsu? Kubiyoni anext page danjin abinda yafaru.


Ur's.
 NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 85 ⚜90

Idan ran Sarki Qaseem yayi dubu to yabaci dajin irin kalaman Sarkin fada da Jakadiya Karima, Waziri ne, yajuya ya kalli Sarki Qaseem, shi kanshi ya tsorata da ganin yanayinshi. Cikin sauri yataboshi, yana kallonshi yayi mashi alamu da ido.

Juyawa yayi murmushi dauke afuskarshi yakalli su Sarkin fada yace dama gurin memartaba zamuje kuma segashi munhadu, ko kuma daga can kuke? Dasauri Sarkin fada yace wlh kuwa shinema mukashiga gurin Gimbiya muyi mata albishir naganin halin da Sarki yake ciki.

Gaskiya munji dadi sosai, jikinshi yayi kyau, yanzun nan nashiga ko kinti 2 banyi ba, shine ma muka fito da Jakadiya. Amma ai kuma yanzu kukazo nan, ko kun dade tsaye anan? Waziri yayi murmushi yace ai ko second 2 bamuyi anan ba, kuka ganmu, bari mukarasa. Wata irin ajiyar zuciya suka saki, har suna hada baki gurin fadin to adubashi, Jakadiya Karima tajuya tanama Sarki Qaseem kirari, hannu yadaga mata tare da kakalo murmushi sannan suka wuce.

Sarkin Fada yace wai! Allah yasomu damun kama kanmu ashema basujimu ba, Jakadiya tace kaide bari, nidama nasan dakyar idan sunjimu, dan Sarki Qaseem mutum ne wanda beson jin abinda bedameshi ba. Sarkin Fada yace haka ne, shima ai Wazirin na Allah ne, babu ruwanshi dajin gulma, akwai addini, muje gurin Medaki itama inkwashi rabona. Jakadiya tace to amma gaskiya yau nima inaso muje dakina.

 Wani kallo yayi mata, sannan yace haba Jakadiya da girmanki kike fadin haka, ai kibarma Gimbiyoyin Sarki, ke kam yanzu ai kinwuce wannan matsayin. Hade rai tayi tace amma ai duk tsufa na ban kaika ba ko? Dariya yayi yace haka ne, amma kinmanta namiji baya tsufa? Kawai kibar wannan maganar muje inyi abinda zefishsheni.

Wani guri kafin akai part din Sarki Hasheem suka samu suka zauna, idanuwan Sarki Qaseem har rufewa sukeyi sbd bacin rai, da kyar ya iya daga baki yace, dan Allah Waziri kace abinda naji ba gsky bane, nabama mutanen gidan nan amana musamman wadannan 2, acikinsu Yaya yafison Jakadiya Karima, nima haka, dan Allah Waziri. Wani irin tausayinsu ne yakama Waziri, ganin idanun Sarki Qaseem sunyi ja yasashi matsawa kusa dashi tare da dafashi yace.

Memartaba wane irin matsayi kabani azuciyar ka? Kallonshi Sarki yayi yace aduk gidan nan kaine mutumi nafarko damuka fara aminta da kai, kawuce kowane irin matasayi agurinmu har ka kai matsayin dan uwa agurinmu. Bari kaji aduk fadin duniyar nan kai kadai muke iya fadama sirrinmu, shiyasa bama jayayya da duk wata shawara dazaka kawo mana.

Kawai kafadi abinda ke ranka namaka alkawarin komenene zankarbe shi, nasan bazaka taba fada mana abinda ze cutar damu ba. Gyaran murya Waziri yayi, fuskarshi cike da annurin kalaman dayaji daga bakin Sarki Qaseem, ahankali yafara fada mashi duk irin abubuwan daya fara gani agurin Sarkin fada, har firar dasukayi seda yafada mashi, daga karshe yace zakayi mamakin idan nafada maka Gimbiya Fulani tana cikin gidan nan tsawon watanni 3?.

Seda Sarki yakusa kwarewa saboda firgita, kai waziri yadaga alamun da gaske yake, sannan yacigaba, akwai abubuwa da yawa wanda bakusansu ba, daga ni se Malam, se Jakadiya Safeeya kadai muka sansu, amma inaso abari se gobe idan Malam yazo zeyi maku bayanin komai, sede abinda nakeso kasani bawai munboye Fulani da wata manufa tamu bane, a,a wannan umarnin Malam ne.

Kuma alokacin da muka kawota gidan nan, babu wanda yasan itace, dan tun lokacin data bace tsawon shekaru 18, har zuwa yanzu tana cikin yanayi na hauka, kuma wahala data sha ne yasa muka kasa ganeta, acikin yan kwana kin nan dayake tana samun kulawa agurin Jakadiya Safeeya, dan agurinta take zaune, tofa alokacin ne, tafara dawowa kamanninta, sbd tana samun tsafta, shine Jakadiya ta ganeta.

Bayan tafada ma Malam, yace kada tafada ma kowa, kuma yakirani yafada mun, nima yace kada infada ma kowa, dan wadan da suka aikata mata wannan laifin suna cikin masarautar mu, dole semunbi asannu zamu iya ganosu.


Ajiya mukayi waya dashi yace mun zezo gobe domin yanaso yakawo karshen halin da masarautar mu take ciki. Babban abin farin ciki tahaifi cikin dake jikinta, Allah ya azurta ta dasamun diya mace, aranar data bar gidan nan kamar yanda su Malam suka sami labari daga gurin wadan da suka tsinceta, to aranar ta haihu, kaga yanzu Yarinyar tana da shekara 18 da watanni.

Babban abinda yasa nataboka alokacin damu kaji abinda su Sarkin fada suke fada shine, kasan idan baka iya kama barawo ba, to shine zekama ka. Nadade dasanin halin da Sarkin fada yake ciki shida matar Sarki Medaki, suna aikata kazamar harka, kusan kullum agurinta yake kwana, nasamu wannan bayanin ne daga gurin daya daga cikin bayin dana sa ya kular mun da duk wani motsi na waziri.

Dan haka ayanzu base gobe ba, inaso kabani dama nasa akama Sarkin Fada da Jakadiya akullesu har zuwa gobe, idan Malam yazo se afito dasu, nasan idan aka maimaita masu laifin dasukayi, zasu tona duk abinda sukayi. Hawayen dake idanun Sarki Qaseem yagoge, saboda bakaramin kaduwa yayi dajin labarin Waziri ba.

Da ace beji abinda suka fada dazu ba, kuma ace ba waziri bane yafada mashi dabaze taba yarda da abinda aka fada ba, kallon Waziri yayi yace ayanzu bani da sauran bakin magana, da kai da Malam nabaku damar ku aiwatar da duk wani abu da yayi dede da hukuncin masarautar nan, sede abu daya nakeso, inaso akawo ma Yaya Fulaninshi yagani, kila ta silar haka yasamu sauki, banaso afadi wani abu harse yasamu sauki, dan yaji duk irin abinda mahintan makusantanmu suka aikata. Waziri yace godiya nake, bara inje insa akama su, kafin wani tunanin yashige su sugudu. Sarki Qaseem yace shikenan bara inshiga gurin Yaya kada yaji shiru.

Da sallama su Gimbiya Suhailat suka shiga falon Jakadiya Safeeya, adede lokacin da Beauty tana karbar biscuit ahannun Areef shi kuma yana ta mata wasa da hankali, se dariya sukeyi, hannu tasa zata karba, cikin rashi sa,a tafada jikinshi. Kwanciya tayi saman cinyarshi tana ta dariya shima haka.

Cak Gimbiya ta tsaya da sauran Sallamar data fara, tsayawa tayi tana kallonsu cike da mamaki, da takaici, sam bata kula dasu Ayman ba, sede kawai taji dariya agefenta, saurin kallon gurin tayi, ai jitayi kamar tazube dan takaici, Haisam ne, yake kokarin saka ma, Ayman sweet abaki, sunata dariya abinsu.

Kamar daga sama sukaji wata irin tsawa, wadda tasa beauty saurin kankame Areef, tayi,wani Uban ashar Gimbiya tasaki, wanda ita kanta batasan ta iyashi ba. Gaba dayansu hankalinsu atashe suka juyo suna kallonta, cike da kaduwa Haisam da Ayman suka sauko kasa, shikam Areef sam abun be daga mashi hankali ba, kara rungume Beauty yayi saboda kukan datasa mashi, sam bata taba jin wata aba wai ita tsawa ba, tunda take, hakan yasa tayi mugun tsorata.

Gimbiya cike da bacin rai tace kai dan Ubanka bazaka saketa ba, kabani hankalinka? Jakadiya ce tayi saurin fitowa daga dakin fulani, dan dama tayi bacci ta tsaya gyara mata dakinne kafin tafita, tana cikin gyara taji wannan hayaniya.

Alokacin data fito saura kadan tazube saboda kaduwa, cak ta tsaya bakin kofa tana zaro ido tare da kallon Gimbiya. Areef yakama beauty suka sauka kasa, dan shima alokacin da Gimbiya tamashi wannan zagin bakaramin kaduwa yayi ba, dan tunda yake betaba jin irin zagin abakin momynshi ba, ko fada bata taba yimashi ba.

Wani irin murmushin takaici Gimbiya tayi, ta kalli Jakadiya, rai abace tace sannu munafukar Allah, mayaudariya, maha inciya, ashe dama abinda kike kullawa kenan? Kinaso ki batama yarona tarbiyya tunda ke baki dashi? Wato duk ginin da nakeyi kece kike rushe shi? Kinje kinsamo wata matalauciyar yarinya kin hadata da Yarima, ita kuma diyata kin hadata da abokinshi.

Ashe dama duk zaman damukeyi zaman munafurci ne ? Wai meyasa duk wanda be fito daga gidan sarauta ba, zaka sameshi maci amana ne? Lallai zamanki yazo karshe agidan nan, bazan kara amincewa da banzan halinki ba. Kai kuma Haisam kake kowa? Inaso kasani Ayman Yarima zata aura, garama ka tattara soyayyarka kayi waje da ita, ko kuma kaima kaje kasamu diyar dan siyasa ka aura, danmu bama auratayya da yan siyasa, domin Sarauta gado ce, kuma ajininmu take, kufa?.

Mulki ne, da lokacinku yacika ko kunaso ko bakwa so, dole kusauka kubama wanda yaci, dan haka kada inkara ganinka agidan nan, bare kuma tare da Yarima ko Ayman. Ke kuma kisaurari hukuncinki, matsawa tayi ta ture beauty wadda tundazu take kuka.

Hannu Areef yasa yariketa sosai shima hawayene suke zuba a idonshi, da kyar yace Momy dan Allah kiyi hakuri wlh beauty itace rayuwata, idan kika rabani da ita mutuwa zanyi, ture ta tayi takama hannunshi dana Ayman wadda itama kukan takeyi, Haisam ne kawai medauriya acikinsu, amma har jakadiya kuka takeyi.

Jansu tarikayi kamar yara har suka fita daga falon, dasauri Jakadiya ta matsa takamo beauty ta dagata zasu shiga daki, kuka kawai, takeyi harda sheshsheka, tana tashi takoma tazube kasa sumemmiya.

Abakin kofar falon Areef ya toge, duk yanda Gimbiya taso tajashi kasawa tayi, hannunshi ya fisge alokacin dayaji Jakadiya tasa wani irin kuka tana fadin munshiga 3 Yar Baba dan Allah kitashi, dasauri yakoma falon, Gimbiya tabishi tana fadin kadawo nace maka ko. Yana zuwa yaga beautynshi kwance akasa babu alamun rai atare da ita, wata irin kara shima yasaki tare da dafe kanshi yazube kasa asume.

Urs.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 90⚜95

Da gudu Gimbiya da Haisam sukayi kansu, tana zuwa takama Areef hankali tashe tafara jijjigashi tana kuka, Jakadiya Safeeya ma beauty tarika jijjigawa tana kuka. Haisam ne yayi kokarin fita waje yakira wasu bayi maza, suka dawo tare.

Su suka dauki Areef shi kuma yadauki beauty suka fita, Jakadiya, Gimbiya da Ayman suna binsu abaya, cikin mota yasakasu, Jakadiya tashiga tare da Ayman ya kulle kofar ko kallon Gimbiya beyi ba yaja motar suka barta nan tsaye dan babu halin tabisu, tunda Sarki Qaseem besani ba.

Komawa tayi part dinta tana kuka, kara tunano kalaman Areef tayi,,,, Momy wlh kika rabani da beauty nima mutuwa zanyi. Hannutasa tarufe duka kunnuwanta tana fadin bazaka mutu ba Yarima, kaine farin cikina, dan Allah kar kamun haka. Saman kujera tafada tana kuka bayinta se hakuri suke bata.

Waziri ne, tare da wasu manyan bayi maza suna binshi abaya, hanyar lambu suka nufa dan yafi zaton suna can, koda sukaje basu same su ba, tunawa yayi da Medaki, hakan yasa suka nufi can.

Alokacin Sarkin Fada da Medaki suna cikin daki, ita ko Jakadiya Karima tana zaune falo tana kallo ta tasa farfesun kaji tanaci. Wata baiwa ce tashigo falon, ai dasauri Jakadiya tace Uban wa yabaki izinin shigowa? Bana hanaku idan muna gidan nan kushigo ba?.

Dukawa tayi tace Allah yabaki hakuri, dama Waziri ne, ya tambayeni ko keda Sarkin fada kuna ciki, shine nace masa kuna nan, shine yace amaku magana. Cikin Jakadiya ne yayi wani kara, nan take zufa tafara keto mata, batasan lokacin data saki cinyar kazar datake hannunta ba.

Cike da tashin hankali tace ubanwa yace kifada masa muna ciki? Innalillahi wainnailaihirraji,un. Munshiga 3 kada de ace asirinmu ne yake shirin tonuwa? Tashi kiba mutane guri munafuka. Hanyar dakin Medaki tanufa, har tuntube takeyi, tana zuwa tafara bubbuga masu,alokacin sunyi nisa cikin harka, dade sukaji bugun yayi yawa, shine Sarkin  Fada yayi saurin zira babbar rigarshi, ko wando besa ba, haka yaje yabude.

Ai yana fitowa Jakadiya tajawoshi tana fadin munshi 3 gasu Waziri can abakin kofa suna jiranmu. Zaro ido yayi yana fadin waya fada masu muna nan? Tace kaide kawuce muje, bawannan bane agabanmu, yanda zamu kare kanmu bakamar ma kai, danni wlh tawa mesauki ce, tunda ni macece kuma kowa yasan inada hakkin shiga duk inda nakeso amasarautar nan.

Sarkin fada yace kiwa Allah kije kice ke kadai ce, bakisan inda nayi ba, nasan zasu kyaleki. Zaro ido tayi tare da dafe kirji tana fadin Jar Uban nan, ai wlh baka isa ba, ai gara ma kai, kome akayi maka kasha dadi, nifa? Menasha, kun hadani da naman kaza da kallo kunshige daki, ai wlh inde nafita kaima seka fita.

Bugun kofar falo ne, ya sasu saurin kallon gurin alokacin Medaki tayi saurin fitowa da daurin gaba ajikinta, kanta ko dan kwali babu, tana fadin wai meke faruwa haka? Shigowar Waziri ce tasata yinshiru, idanu 2 suka hada dashi, hakan yasa yayi saurin kauda kanshi, ai dasauri takoma daki, kallon Sarkin Fada yayi wanda ko rawani babu akanshi, dagashi se babbar riga,, jikinshi kam ko wando babu.

Hannu Sarkin Fada yadora akanshi yana fadin shikenan yau kuma ahaka tazo mani. Waziri cike da bacin rai yasa fadawa sukamashi, Jakadiya Karima tace ai dama kullum ina fada maku kune bakwaji, yau ga irin ta nan, nikam baruwana, Allah yakara, hanyar waje tanufa tana shirin fita. Wani kallo da Waziri yayi mata yasa dole taja burki tana raba idanu.

Wazirin yace ku kamosu dukan su akaisu kurkutu zuwa gobe, kuma inaso kusaka kwakkwaran tsaro agidan nan, yanzu zan fadama sauran masu tsaro, kada abari kowa yafita daga gidan nan koda kuwa matar Sarki ce, koma waye dole akirani kafin yashigo ko yafita. Haka aka tasa keyarsu zuwa kurkutu. Medaki kuwa tana daki tarasa inda zata sa ranta.

Suna zuwa asibiti aka karbesu akayi emergency dasu, kowa aka fara bashi temakon gaggawa, cikin lokaci kankani Areef ya farfado, sede beauty ko alamun motsi batayi, hakan yasa likita yace akai Yarima dakin hutu, nan suka cigaba da duba Beauty.

Tunda Areef ya farfado yafara kiran beauty, kuka yasakama Haisam da Jakadiya Safeeya, se lallashin shi sukeyi, Areef yace wlh idan wani abu yasami beauty na, nima Momy zata rasani. Haisam yace kadena fadin haka Areef insha Allahu zata warke. Karar wayar Haisam ce ta katsesu, Areef yace idan Momy ce kace mata ban farfado ba dan Allah.

Yana dagawa tace Haisam yaya jikin Yariman? Wani irin haushi yaji, wato ita ta danta ma kawai takeyi. Ahankali yace Momy Areef yana cikin wani yanayi, addu,a kawai zakitayashi. Cike da tashin hankali tace ina likitan banishi, yace suna can akanshi suna bashi temako.

Dan Allah Haisam kace ma likita yayi duk yanda zeyi kada dana yarasa ranshi, ko wani abun yasameshi dan Allah. To kawai yace mata, yakashe wayar. Runtse ido Haisam yayi yana karajin haushin kalaman Momy, Areef yace hankalinta yatashi ko?.

Kai kawai yadaga mashi, yace ina ganin matsalar mu zatazo cikin sauki, sbd Momy tana sonka sosai, dan haka dole muhada mata plan. Murmushi Areef yayi yace haka ne, abokina nagode, yanzu muje inga jikin beauty na.  Jakadiya Safeeya tace a,a Yarima ka kwanta jikinka babu kwari, likitoci suna kanta suna nema mata sauki. Komawa yayi yakwanta zuciyarshi tana zafi.

Sarki Qaseem ne, afalonshi hankalinshi tashe da abinda Waziri yafada mashi sungani apart din Medaki, haka yazauna yadafe kanshi da hannu 2, jin haryanzu shiru bega Gimbiya Suhailat tafito ba, yasa yatashi yanufi dakinta, kwance yasameta tana ta kuka, cikin sauri yakarasa gurinta tare da kamota ya rungume.

Kara rungumeshi tayi tasaki wani sabon kuka, shafa bayanta yafarayi yana fadin meyafaru kike kuka haka? Kanta tadago, tana share hawaye tace shikenan munshiga 3 Hubby, zamu rasa danmu guda 1 da Allah yabamu. Cike da tashin hankali Sarki yace bangane mikike nufi ba, meyasamu Areef din ? Ko hadari yayi? Kai tashiga girgiza mashi, tace yana can asibiti likitoci ma sunkasa samo kanshi. Sarki yace dan Allah kitashi kifadamun abinda yafaru, wlh zuciyata gab take da bugawa, bakisan irin tashin hankalin daya sameni ba, kifadamun abinda yafaru tunkafin nima kirasani.

Ai dasauri Gimbiya ta tashi tana kallonshi, se alokacin ta kula da yanayinshi, idanunshi sunyi ja sosai,cike da kaduwa tace hubby dan Allah meyafaru, kallonta yayi dan yafara kulewa da ita, tureta yayi cike da bacin rai, yace ya ina tambayarki kina tambayata dan kin rai nani, kawai kifadamun abinda yafaru idan bahaka zanbar maki gidan. Matsowa tayi ta rungumeshi tana kuka, dan tunda suke betaba yimata irin wannan ba, asalima bata taba ganinshi cikin irin wannan yanayin ba.

Dagowa tayi tajawoshi suka zauna bisa gado, kanshi tajawo tadora saman cinyarta tana ta shafa kanshi, lumshe ido yayi, yana sauke ajiyar zuciya. shiru sukayi nawani lokaci, jinyayi shiru yasa tadagshi ta tashi takawo mashi ruwa mesanyi, dakanta tabashi, kofi guda ya shanye, sannan takara jawoshi yakwanta akan cinyarta.

Ahankali tana shafa kanshi tace hubby karika fadin Innalillahi Wainnailaihirraji,un, kayi haka harso 5, sannan infada maka abinda yafaru, amma ina fatan bazakamun fada ba idan kaji abinda nayi?

Cike da fargaba Medaki tashiga falon Gimbiya Zakiyyah, alokacin tana zaune tana hutawa, kallonta tayi tace kekuma lafiyarki zaki shigo mani gida ahaka, ko Sarki ne ya mutu? Medaki tazauna tace ai da mutuwa yayi zefi sauki da halin dazamu shiga nida ke, da su Jakadiya, cinkin lokaci kadan.

Tashi tayi daga kishingiden datake tana yamutsa fuska tace bangane abinda kike nufi ba? Anan tafada mata duk abinda yafaru, har halin datake ciki ita da Sarkin Fada seda tafada mata, dan ita tariga da tagama yarda da ita, tunda taga halinsu daya ne. Wani irin miskilin murmushi Gimbiya Zakiyyah tayi,  tayi mata wani irin kallo, tace.

Lallai bansan ke Jahila bace se yau, wato keda Sarkin fada kundade kuna aikata alfasha, saboda kinga Sarki beda lafiya, kai, wama yasan tun lokacin da kuke tare? Hmmmm dama nafada, shiyasa duk abinda yafaru daku wlh bazanji tausayinku ba, kema kijira sammaci anjima ko gobe, dan tunda Waziri yakamaku da kanshi, kema kinsan hukuncin kisane akanki.

Tir da ke, kina matar Sarki kinabin maza, mazan ma wai Sarkin Fadan Mijinki. Kodayake ba laifinki bane, dama shi talaka kome akayi dashi, seya baka kunya, yanzu tayaya wanda yafito daga jinin sarauta ze aikata irin abinda kikayi?

To wlh bari infada maku dake dasu gaba daya, daga yau babu ni babu ku, kuma koda kunbude baki kunfadi abinda nasa akayima Rayhana, babu wanda zeyarda daku, dan bakuda sheda, kuma ni daga gidan sarauta nake, zan iya amfani da karfin mulkina inkwaci kaina, dan kunsan atsari na sarauta ba,a yanke hukunci dole seda sheda bayyanan na, ku kam bakuda wata shedar dazata nuna akwai sa hannuna aciki.

Kitashi kibani guri tunkafin azo aganki agurina. Cikin kuka Medaki tace dan Allah kada kinmani haka, nabaki duka yarda, banda kowa aduniyar nan kece silar jefani cikin wannan harka dan Allah kada kice zaki juya mun baya, kinsani duk wani abu da muka aikata shawararki mukebi, saboda kece babba. Hannu tadaga mata tamike tsaye tace nace kitashi kibani guri kada inkara ganin kafarki agidana.

Ni nabi shawarar kiyi zina da kaskantaccen talaka kuma yaron mijinki? Kafin asirinku yatonu kintaba fadamun halin dakuke ciki? Dan haka wlh kinji narantse maki baruwana acikin harkarku, fita nace. Tashi Medaki tayi tana kuka tafita waje. Wata irin dariya Gimbiya Zakiyya tasaka tace, uhmm dani kuke magana, anfada maku sarauta haukace? Kaima sarkin fada nasan kana tunanin katona asirina.

Ni kuma zan nuna maka bakada wayau,duk duniyar nan babu wanda zeyarda da kai dan kafada masu munyi harka tare, domin kuwa babu wanda yasan munyi daga ni sekai, kuma agidan sarauta ba,a karbar shedar mutum daya, kuma shedar ma tabaki. Dariya tasa tashige daki.

Saurin tashi Sarki Qaseem yayi yana kallon Gimbiya Suhailat, bayan tagama bashi labarin abinda yafaru. Kai yafara girgizawa ta kalleshi tace dan Allah kayi hakuri, wlh banyi haka dan in cutar dashi ba, kuma ni bansan Son dayake mata ya kai haka ba, kuma gani nayi nida kai munzaba mashi wadda ze aura shiyasa nayi haka.

Murmushi Sarki yayi yace kinzaba mashi de, kuma ita Ayman din ai tasamu wanda take so, to koma bata samu ba, yarinyar dayakeso ita zanbashi sede ita Ayman tazo ta 2, domin kuwa kinso ki tabka babban kuskure, ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba, yarinyar da kika gansu tare da Areef jinina ce, kuma shima jininshi ce, bari inje asibitin inga halin dasuke ciki.

Kuma kisani tunda har Ayman tasamu wanda takeso to bazata auri Areef ba, da ace tana sonshi, to zanbashi shawara ya aureta, amma tunda haka tafaru, kowa ze auri zabinshi. Kuma kisamu kalaman dazaki bama Jadiya Safeeya hakuri dasu, dan kinci mata mutunci, matar da ta sadaukar da jin dadinta domin takaremu.

Matar da tabaro kowa nata, badan tana cikin talauci ba, a,a kawai dan tazauna damu da gaskiya. Juyawa yayi yanufi kofa zefita, da gudu tarugo tarikeshi tabaya tana kuka tace, dan Allah hubby kayi hkr kada kamun irin wannan horon, naji nayarda da duk abinda kace, kuma nahakura Yarima ya auri koma wacece amma dan Allah kafitar dani duhu, kuma kada kayi fushi dani kasan bamu saba haka ba.

Murmushin jindadi yayi, sede bejuyo ba, yace ki kwantar da hankalinki, danki ze auri irin yarinyar da mukeso, yar gidan sarauta, albishir daya zan maki, wannan yarinyar da kika gani ba kowa bace se diyar Yaya da Fulani. Kuma wani abun farin cikin yanzu haka Fulani tana cikin gidan nan, sauran bayani sena dawo zakiji, yana fadin haka yayi waje. Wani irin yanayi tashiga, gaba daya tarasa mezatayi, ga kunyar abinda tayi yadameta, musamman idan ta tuno kalaman data fadama jakadiya, komawa tayi daki tana tunani.

Cikin sa,a da kwarewa tare da temakon Allah beauty ta farfado, numfashinta ya dedeta, sede haryanzu bata bude ido ba, kuma bugun zuciyarta be dedeta ba. Likita yace sukaita dakin hutu, nan da wani lokaci zata dawo dede akwai abinda ya tsoratata shiyasa tashiga wannan yanayin.

Adede lokacin Sarki da Waziri suka iso asibitin,kai tsaye office din likita suka wuce, bayan sun gaisa yayi masu bayanin halin da ake ciki. Sarki yace amma yaya jikin yarinyar? Likita yace insha Allahu babu wata damuwa, zata dawo dede. Amma Yarima jikinshi dasauki. Godiya suka mashi yasa aka nuna masu dakin Areef da beauty.

Seda Sarki yafara shiga gurin beauty, kwance yasameta kamar matatta, Jakadiya Safeeya tana gefenta se kuka takeyi, sallamarsu ce tasa tayi saurin goge idonta, ta tashi tana mika gaisuwa, da kyar ya amsa, hankalinshi yana kan beauty, sak kamarta da Fulani da Areef yake gani afuskarta, wasu hawayen farin ciki ne, suka zubo mashi.

Kusa da ita ya matsa, fuskarta ya shafa ya kalli Waziri yace tabbas ita ce, ko ba,a fadamun ba nasan wannan jinin Yaya ce, Allah sarki, Allah maji rokon bayinsa, insha Allahu ayau Yaya zesamu babban albishir, ayanzu base gobe ba. Kallon Jakadiya yayi yace kifadamun Ina Fulani take, inje da kaina inkaima Yaya ita?.

Se alokacin Jakadiya ta tuna sunbarta agida, damma tasan barci takeyi, sede tana duba agogo taga lokacin tashinta yakusa, gashi basu kulle gidan ba, cike da tashin hankali ta kalli Sarki tace Rankai dade tana gida kuma yanzu zuwa wani lokaci zata iya farkawa, gashi bankulle gidan ba, ina tsoron tafito, koza,a sa amaidani gida kada tafito?.

Waziri yace babu damuwa, muje muga jikin Areef semuwuce tare. Sarki yace a,a tunda ance jikin nashi dasauki kawai. Muwuce, Jakadiya tace to bari inma Ayman magana seta dawo nan tazauna kada tafarka. Waziri yace rankaidade muje gaba daya muga jikinshi semu wuce.

Areef da Haisam suna cikin tsara yanda zasu hada plan, Ayman tana gefe duk tashiga damuwa se kallon Haisam takeyi tana tunanin idan aka rabasu bazata iya. Hakura dashi ba. Turo kofar da akayi ne. Tasa su saurin kallon kofa, Areef suna hada ido da sarki yayi saurin komawa ya kwanta tare da rufe ido.

Dariya yakusa bama Sarki, bayan sun shigo Sarki ya matsa kusa dashi yace lallai yarona kai ragone tunda har zaka iya kwanciya asibiti saboda mace, to danazo ince maka na amince da zabinka amma tunda naga baka warke ba, nafasa, ai dasauri yamike yariko hannun Sarki yana fadin wlh nawarke koyanzu ma asallameni. Gaba daya dakin seda suka sa dariya, hada Ayman me kuka. Sarki yace ka kwantar da hankalinka babu wanda ze hanaka auren zabinka, kuma jininka, bari muje gida mudawo, kallon Haisam yayi yace ka kula dasu, ke kuma me kukan soyayya sekiyi shiru tunda zaki samu abinda kikeso, kitashi kije gurin Diyata kizauna zamu dawo yanzun nan. Juyawa yayi yafita suma suka bisu abaya.

Cike da Mamaki Areef ya kalli Haisam yace Jinina, kuma diyar Abba? Tome yake nufi? Kafada Haisam yadaga alamun shima besani ba, yace mujira sudawo maji daga garesu.

Jakadiya Karima se kuka take tana fadin tsakanina da Gimbiya Zakiyya Allah ya isa, muguwar mata tasamu cikin bala,i kuma gashi yanzu mune akulle, bamuda wata sheda dazata nunama mutane tanada hannnu  acikin  abinda muka aikata. Kaicona ni Karima, ban rike amanar da mutanan nan suka bani ba, naci amanarsu, nima kuwa Allah baze barni ba. Yanzu shikenan haka za,a yanke mana hukunci muna kallo abar Gimbiya?.

Wata irin dariya Sarkin fada yayi yace kidena bata hawayenki abanza, waye yace maki itama zata kubuta? Aini bana barin baya da kura, inde zanyi aiki to dole se nasamu madafa nake farashi, ko anfada maki nima irin kwakwalwar jinin sarauta nakeda ita wadda bata da seti? Kawai malama kizuba ido kisha kallo gobe.


Suna zuwa gidan afalo sukaci karo da ita tafito se raba idanu takeyi. Cak Sarki ya tsaya yazuba mata ido, tabbas ita ce, sede tarame, hannu yadaga sama yanama Allah godiya, Waziri yace Jakadiya kamota muwuce. Hannunta takama suka nufi waje.

Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 95⚜100

Da sallama suka shiga falon Sarki Hasheem, yana zaune abisa kekenshi yana sana,ar tashi wato tunanin Fulaninshi, matsawa kusa dashi Sarki Qaseem yayi.

Kafadarshi ya dafa ahankali yadago yana kallonshi, wasu siraran hawaye suka fito daga idanunsu su duka biyun, alamu Sarki Hasheem yayi mashi da lafiya? Murmushi yayi mashi yakama kekenshi yafara turawa.

Seda yakawoshi kusa da su Waziri sannan ya sake shi, shide kallonsu kawai yakeyi, Jakadiya Safeeya takamo hannun Fulani wadda take boye abayanta, tafito, adede lokacin dasuka hada ido da Sarki Hasheem Fulani taji kanta yayi wani irin sarawa.

Shi kam Sarki Hasheem besan lokacin daya mike tsaye ba bakinshi yana motsi yana nuna Fulani da hannu ba, itakam nan take ta kwala wani irin ihu tafadi kasa, shima jikinshi ne, yafara rawa yazube kasa idanunshi suna fitar da kwallah.

Dasauri suka isa gurinshi, Jakadiya Safeeya kam gurin Fulani ta nufa, sede tana tabata taji babu alamun numfashi atare da ita, Waziri yakama Sarki Hasheem yadora kan cinyarshi jikin sarki se rawa yakeyi yana kara nuna Fulani da yatsa, da karfi yace Fulani.

Jakadiya Safeeya takalli su Waziri tana kuka tace bata numfashi fa. Sarki Qaseem wanda duk yagama rudewa, yama rasa ina zeje, ya kalli Waziri yace yazamuyi ne? Waziri yace kawai muwuce dasu duka asibiti ina ganin zefi sauki.

Sarki Qaseem yace ma Jakadiya taje takira Suhailat tazo sutafi tare, anan Waziri yakira wasu fadawa suka kama Sarki aka kaishi mota, Sarki Qaseem kuwa da kanshi yadauki Fulani ya kaita mota. Waziri yatara manyan fadawa kusan guda 20 yace nabaku umarnin bayan fitarmu kada wani ko wata yakara fita koya shigo masarautar nan, harse mundawo idan nabada umarni.

Jakadiya Safeeya kam tana zuwa part din Gimbiya Suhailat, jikinta yafara rawa, dan batasan dawane ido zata kalleta ba, ganin zata bata masu lokaci yasa kawai tashiga, alokacin Gimbiya  tana zaune falo tabuga tagumi. Saurin tashi tayi tana kallon Jakadiya cike da fargaba tace.

Dan Allah kada kicemun narasa Yarima dan Allah, sunkuyar da kai tayi tace baki rasa shiba, sede memartaba ne yace infada maki kifito mutafi asibiti. Ai dasauri taje tadauko hijabinta tafito suka nufi mota, tana zuwa suka shiga wata mota ita da Jakadiya, su kuma suka shiga dayar Wazirri jasu zuwa asibiti.

Azaune, Areef yake bisa gadon beauty ya rike hannunta idanunshi suna fitar da hawaye, kara kallonta yayi yace dan Allah beauty kitashi haka nan, wlh zan iya samun matsala idan har baki farka ba. Haisam ne ya matso kusa dashi yadafa shi, yace kayi hakuri abokina zata samu lafiya, bagashi kana kallo numfashinta yna tafiya dede ba. Addu,a zaka yimata zata tashi.

Suna zuwa aka nufi emergency dasu, sede shi Sarki wani daki aka kaishi tunda dama likitan yasan cesa dinshi, akan Fulani likitoci suka taru suna bata temakon gaggawa.

Gimbiya Suhailat da tambayoyi suka cika cikinta, gashi tana son ta tambayi Jakadiya Safeeya amma kunya ta hanata, ganin haka yasa Jakadiya tace Gimbiya muje kiga jikin Yariman mana, kamar jira takeyi ta tashi cike da kunya tace muje de infara ganin jikin surikar tawa ko?.

Bakaramin dadi Jakadiya taji ba, dajin furucin Gimbiya, tace to muje, Gimbiya tace dan Allah kiyi hakuri da abinda namaki, wlh idona ne yarufe, har na furta maki wadan nan maganganun, amma kiyafe mun, kuma Hubby yayi mun bayanin komai nagane.

Tabbas soyayya baruwanta dawani mulki ko sarauta, kudi ko talauci, wlh nayarda da zabin Yarima dari bisa dari, ada kam nayi kuskuren cewa dole dan sarauta seya auri jinin sarauta, segashi tun ba aje ko inaba Allah ya nunamun ishara, kuma nayarda da abinda nagani.

Murmushi Jakadiya tayi tace haba ai babu komai, nice yakamata innemi yafiyarki, dan na rufe maki abubuwa da yawa wanda ba laifina bane, amma muje kiga jikin nasu, daga baya zakiji komai.

Hannun beauty dake cikin na Areef ne yafara motsi, saurin kallonta yayi yana fadin Haisam wlh beauty motsi takeyi, kara matsawa kusa da ita sukayi, Ayman tace aiko Yaya ga idonta nan yana juyawa, Areef yace beauty bude idonki nine akusa dake, babu wanda ze rabamu, dan Allah kitashi Abba ma yana dubaki kuma shima ya amince. Kallon Ayman yayi hawaye suna zuba a idonshi yace dan Allah kuce ta tashi.

Adede lokacin da su Gimbiya suka turo dakin babu wanda ya kula dasu dan hankalinsu yana gurin beauty, tsaye Gimbiya tayi tana kallonsu, gaba daya tausayinsu yakamata, gani takeyi duk itace tasasu awannan halin, matsawa Jakadiya tayi kusa dasu.

Adede lokacin beauty tabude idonta, bata sauke su akan kowa ba se akan Gimbiya Suhailat, ai kawai gani saukai ta tashi cikin tsorata ta kwala kara daga karshe tace Mama............ gaba daya dakin seda suka firgita dajin abinda beauty tayi, saurin shigewa jikin Areef tayi jikinta yana rawa, kara rungumeta yayi yana shafa bayanta.

Se alokacin ya juya yaga Momynshi ce ashe beauty tagani, saurin daure fuska yayi yace Momy dan Allah kifita, kina ganin yanda beauty ta tsorata daga ganinki, tunda beauty take bata taba magana ba, amma ayau ta dalilin tsoranki datakeyi gashi magana tafito abakinta.

Dan Allah kifita tunkafin takara ganinki tarasa ranta, wlh nima mutuwa zanyi. Cike da tashin hankali Gimbiya tajuya tayi hanyar waje tana kuka, Jakadiya tayi saurin kamota tana fadin kada kifita kidawo zanyi mata magana, kai kuma Yarima ka nutsu kasan dawa kake magana.

Jawota tayi suka matso kusa da gadon beauty wadda take kwance ajikin Areef, ahnkl Jakadiya ta dafa kafadarta tace tashi kiji wani abu Yar Baba kinsan de bazan cutar dake ba ko? To idan har kinyarda da hakan inaso kitashi kuma kada kiji tsoron komai, Gimbiya tazo dan tadubaki kuma tafada maku tayarda zakuyi aure keda Yarima.

Ai dajin haka beauty ta tashi sede bata rabu da jikin Areef ba, shikam murmushi kawai yakeyi, yana kallon Momynshi. Kusa da beauty Gimbiya ta matso takama hannunta, tace diyata kiyi hakuri kinji wasa nakeyi maku, babu wanda ze rabaku, nima inasonki, jawota tayi ai kamar jira takeyi tashige jikin Gimbiya, ai gabavdaya dakin aka sa dariya.

Da wani irin ihu Fulani ta farka tana fadin  wayyo nashiga 3 zasu kasheni, haka tayi ta ihu, ganin taki natsuwa likitocin suka leka suka kirawo su waziri, addu,a Waziri yayi ta tofa mata shida Sarki Qaseem, cikin lokaci kankani ta nutsu, sede gaba daya afirgice take.

Wani likita yace da alama tunaninta yadawo, sede agskiya atsorace take, kila mutanen dasukayi mata sanadiyar shigarta wannan halin sun tsoratata sosai, dan haka shawarar dazan baku idan har akwai malami, to ku kaita yayi mata addu,a insha Allahu zata dawo dede.

Waziri yace mun gode sosai, amma kana ganin za,a iya sallamarta ayau? Likita yace kwarai ma kuwa, ai babu sauran wani abu dayake damunta, dan ta dade tana shan magani, duk da ba mune muka bata ba, amma mungane ana bata magunguna masu kyau. Sarki yace mungode bari muduba jikin Yaya.

Shima Sarki Hasheem jikinshi yayi sauki, dan soyake abarshi yaje yadubo Fulaninshi, amma likitan yahana, turo kofar dakin sukayi tare da sallama, aibyana ganinsu Sarki yace ina Fulani ya jikinta? Gaba daya seda sukayi mamakin maganar data fito daga bakin Sarki, dan yau shekaru 18 da watanni beyi magana ba. Da sauri Srki Qaseem yaje gurinshi yana murmushi ya rungumeshi yana fadin Yaya wlh itama ta warke ayau ma zamu koma gida.

Cike da fara,a Sarki Hasheem yace da gaske? Waziri yace sosai ma, runtse ido yayi wasu hawaye suka zubo mashi yace Allah nagode maka daka dawomun da Fulanita, ya Allah katona asirin duk wanda yayi ma Fulani hakan ni kuma nayi alkawarin wlh bazan barshi ba.

Likita yayi gayran murya yace Alhmdull, dama nace maku yawancin irin wannan matsalar idan har mutum yahadu da ita ta dalilin rasa wani abunda yakeso, to aduk lokacin daya ga wannan abun alokacin da beyi tsammanin ganinshi ba, to inhar Allah yaso ze iya samun sauki.

To hakane yafaru da memartaba, jikinshi yasamu lfiya, nan da wani lokaci zefara tafiya kamar kowa, amma kada yayi garaje, gurin fara tafiya, yanzu haka zamu bashi sanda wadda zata temaka mashi gurin tafiya. Kuma zaku iya tafiya ayau, sede dole seyasha magungunan dazamu bashi, suna zasu temaka mashi jikinshi yayai kwari.

Sarki Qaseem yace yanzu kam tunda farin cikinshi tadawo ai ba magani ba, komai zesha. Dariya suka sa gaba daya, Sarki Hasheem yace yanzu de ku kaini inga Matata ko kuma intafi da rarrafe, dariya sukayi likita yace a,a ga kujera nan kuturashi yaga farin cikinshi.

Kwance take idanunta akulle, amma ba bacci takeyi ba, tanaso tayi tunanin,sede data fara setaji kanta yana sarawa, da sallama suka shigo, lokaci guda ta bude idonta, bata sauke su ako ina ba, se akan mijinta, jan jiki tayi ta tashi zaune, fuskarta dauke da murmushi, turashi sukayi har kusa da gadonta, sannan Waziri yakamo hannun Sarki Qaseem sukayi waje.

Hannunshi yasa yakamo nata, fuskarshi dauke da murmushi, saukowa tayi daga bisa gadon ta durkusa kusa dashi ta shige jikinshi tana kuka, kara rungumeta yayi yana shafa bayanta.

Dakin beauty suka nufa, azaune suka samesu se fira sukeyi, suna dariya, beauty kuwa tana jiin Gimbiya, se dariya takeyi, sede haryanzu tun maganar datayi tafarko bata kara cewa komai ba, Areef ma kasa matsawa yayi yana manne da ita, wani irin farin cike ne yaratsa zuciyar Sarki Qaseem ganin yanda yasamesu.

Sarki yace waini ina Areef marar lafiya ne, munje dakinshi mabu ganshi ba? Dariya suka saka, Areef yace Abba ai nawarke, Gimbiya tace ba dole ya warke ba, tunda yasamu abinda yakeso, dariya sukayi. Waziri yace ai seku tashi mufara shirin tafiya gida tunda kun warke dare yayi sosai. Sarki yace gaskiya kam, yaude asibitin tazama ta masoya.


Haka likita yabasu sallama tare da magungunan Sarki Hasheem dana Fulani, suka kama hanya zuwa gida, sede haryanzu Sarki Hasheem bega beauty ba, dan seda suka fara shiga mota sannan suma suka fito. Lokacin dasuka isa gida kuma dare yayi sosai, hakan yasa Gimbiya taja Ayman da beauty tace ma Jakadiya kema kitaho mukwana anan kisan de Yaya baze baki Matarshi ku kwana tare ba. Dariya tayi tace hakane, muje kawai. Kallon su Areef tayi tace Haisam kaima kafada ma su hajiya anan zaka kwana gurin budurwarka kada suji shiru.

Rufe fuska yayi yana dariya yace ai nafada masu, tace yauwa maganata tayi dede kenan? Adede lokacin da motar su Waziri da su Sarki tashigo harabar gidan, suna haskawa jikin wata bishiya suka haske fuskar Medaki, ai dasauri takara labewa, domin ta dade agurin jiran dama kawai takeyi tasamu tagudu, hannunta rike da dan kullinta, sede babu wanda yaganta daga Sarki Qaseem , se Waziri wanda dama shine yake jan motar, Sarki da Fulani suna baya, wani murmushi Waziri yayi , yawuce.

Bayan yayi parking motar yayi saurin fita yakirawo masu gadin gidan, ai Medaki tana ganin haka tayi surin komawa part dinta, kara jaddadamasu yayi akan su kula da tsaron gidan, kuma akulle kofa babu wanda ze kara shigowa bare fita.

Haka suka raka Sarki da Fulani har falo, Fulani ta kalli Waziri tarike kanta kamar me tunanin Sarki yace lafiya Fulani ko kanki yake ciwo? Kai ta girgiza, can kuma tayi saurin bude ido tace ina yarinyata? Sarki yace kina nufin kin haifi cikin jikinki kuma yana raye? Kai ta girgiza tace dan Allah kubani diyata wlh nasan na haihu, kada kucemun ta mutu.

Waziri yace ki kwantar da hankalinki, diyarki tana nan, araye asalima babu abinda yake rabaku, atare kuka zauna, babu abinda yasameta, sede yanzu tana gurin Gimbiya Suhailat, kuma nasan sun kwanta kinga dare yayi kibari seda safe zaki ganta.

Murmushin jin dadi tayi ta daga mashi kai, sallama sukayi masu suka fita. Sarki yace turani muje daki muyi wanka, murmushi tayi tafara turashi, atare sukayi wanka tana temaka mashi, bayan sunfito sukayi sallah sannan suka kwanta suna me cike da farin cikin ganin junansu, sun rungume juna kamar za,a rabasu.

Suna fita Waziri yakalli Sarki yace kaga abinda nagani kuwa? Sarki yace nagani, kabari kawai Allah yakaimu gobe nasan zamu gano sauran munafukan gidan nan. Sallama yayi mashi kowa yanufi part shi.

Washe gari da misalin karfe 10 Malam na darazo ya iso, aka saukeshi amasauki, bayan yagama cin abinci aka kawoshi fada, alokacin su Sarki Hasheem da fulani sun iso gurin tasha kyau sosai, tana zaune agefen Sarki, bayan sungama gaisawa da Malam, ya tambayi jikinshi yace Alhamdulillahi ai jiki yaya sauki, dama akwai dalilin dayasa kuma yanzu nasamu maganin akusa dani.

Dariya malam yayi yace to mungodema Allah, amma abinda nakeso da akai, sekayi hakuri da duk abinda zakaji ko zaka gani, ayanzu, nasan zaka shiga cikin damuwa, amma munaso mukawo karshen muna fukan gidan nan, kuma kaima nasan zaka so kasan wadan da sukayi ma Fulani haka.

Sarki yace hakane, babu komai, Allah yasa inji alkhairi. Malam yace amin, adede lokacin su Gimbiya Suhailat dasu beauty, Ayman, Jakadiya , Areef da Haisam suka shigo, ai beauty tana ganin Mamanta da gudu taruga tafada kanta tana dariya.

Itma tana ganinta tayi saurin rungumeta tna fadin yarinyata, Sarki da mamaki ya kamashi dasauri ya kalli fulani yace wannan ce diyata? Kai tacdaga mashi, besan lokacin da kwalla tacika mashi ido ba.

Waziri yabada umarnin afito dasu Jakadiya Karima, sannan yasa Jakadiya Safeeya takirawo su Gimbiya Zakiyyah da Medaki, wani bafade yasa yakirawo Baban Fulani da Baban Darazo, kowa yasamu guri yazauna yana kiran abinda za,ayi.

Nima nace bara in anje alkalamina injira shigowar su Sarkin Fada.

Ur's
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 100⚜105

Cikin isa da mulki Gimbiya Zakiyyah tashigo, ko sallama ma da kyar tayi, guri tasamu gefen Sarki tazauna, dan batasan yasamu lfy ba. Kallonshi tayi fuskarta dauke da murmushi tace barka da asuba memartaba yajikinka?.

Sanin ko anyi mashi magana baya amsawa yasa tadauke kanta bata kula da motsa bakin dayayi ba. Kallon malam tayi tace malam barka da asuba, yace yauwa kintashi lfy. Medaki ce tashigo jikinta duk yayi sanyi kamar antsamota daga ruwan zafi.

Akusa da bakin kofa tazauna duk tagama rudewa, cikin rashin jindadin abinda tayi Sarki Hasheem yace medaki dawo nan mana. Ai Gimbiya Zakiyyah batasan lokacin datace yaushe kafara magana memartaba?.

Murmushi yayi kawai yayi shiru, haryanzu babu wanda ya kula dasu Fulani, bayan medaki tazauna kusa da Gimbiya Zakiyyah, kallonta tayi tadan duko kusa da kunnanta tana murmushin mugunta tace ina fatan kinyi kwanciyar karshe agidan sarauta? Seki shirya karbar hukunci.

Sallamar su Sarkin fada da Jakadiya ne tasa Medaki tayi saurin tashi tana hawaye. Wani murmushin jindadi Sarki Hasheem yayi, ganin Jakadiyarshi, dama yana so ya tambayeta domin ita yakeso yayima albishir na samun diya da yayi, domin yasan tana daya daga cikin masu son yasamu karuwa.

Da fara,a yace Jakadiya matsonan infara baki albishir medadi, ai jitayi kamar yan hanjin cikinta zasu fito, kamar ance Fulani tadago kai, ai tana dagowa sukayi ido 4 da Sarkin fada. Wani irin ihu tasaka ta ture beauty, tashi tayi kamar zata ruga tana fadin gashi nan yazo zasu kasheni.

Waziri da Sarki Qaseem bakaramin mamakin abinda take fada sukayi ba, duk da dama suna zarginshi. Jakadiya Safeeya da Gimbiya Suhailat ne suka rike Fulani, Sarki Hasheem kuwa jiyayi kamar yatashi, gaba daya jikinshi rawa yakeyi, ganin haka Sarki Qaseem ya matsa kusa dashi yadafashi yana bashi baki.

Gimbiya Zakiyyah kuwa batasan lokacin data mike tsaye ba tana nuna Fulani, Medaki kuwa kukanta har yafito fili, duk da sanyi da falon yakedashi be hana zufa keto mata ba. Gaba daya sauran mutanen Falon sun shiga rudani,  Areef kuwa matsawa yayi kusa da beautynshi yari keta sosai, yadora kanta saman kafadarshi, dan yasan batason hayaniya, ita kam kuka tasaka tunda Fulani ta tureta.

Malam da kanshi ya matsa kusa da Fulani datake kwance akan cinyar Jakadiya tana ta kuka, addu,a yafara yimata yana tofa mata. Sarkin fada kuwa da Jakadiya zaman yan bori sukayi suna rarraba idanu.

Sarki Qaseem ne yayi gyran murya sannan yace ya isa, kowa yasamu nutsuwa kuma azauna domin muyi abinda yakawomu. Malam yadade yanama Fulani addu,a kafin tasamu tadawo cikin nutsuwarta. Sarki Hasheem kam gaba daya kanshi yagama daurewa shiru kawai yayi yana karanta addu'oi, hakan yasa yafara samun nutsuwa, sede haryanzu idanunshi suna kan Jakadiyarshi data kasa kallonshi.

Bayan kowa ya nutsu Waziri yatashi yace ma malam yabude masu taro da addu,a. Bayan angama Waziri yafara magana. Alhamdulillahi da farko zanfara dayima Allah godiya daya kawomu wannan rana mecike da farin ciki da kuma bakinciki.

Da farko zanfara gabatar da matar Sarki, kuma amarya agurinshi wadda akafi sani da Fulani. Bayan shekaru 18 da wasu watanni bata gidan nan, inda aka samu wasu marassa imani suka shigo har cikin dakinta suka dauketa........ Sallamar Su Baban Fulani ce ta tsaida Waziri daga jawabin dayakeyi.

Fulani tana ganin Babanta ta tashi tanufi gurinshi, ai shima yana ganinta yabude hannuwa tashige jikinshi tana kuka. Shima kukan yakeyi seda suka bama kowa tausayi. Bayan sun natsu suka zauna, Baban beauty kuwa gaba daya mamaki yagama cikashi ganin abin al,ajabi.

Waziri yaci gaba da magana. Kamar yanda nace ba,asan wadan da sukazo suka dauke Fulani ba, amma tunda Allah yasa gata tadawo kuma tana cikin hankalinta. Kuma zata iya nuna wadanda suka aikata haka akanta to duk wanda yakasance cikin masu laifi, tabbas ze fuskanci hukunci me tsanani, kuma kowane irin matsayi gareshi a masarautar nan.

Ai kamar daga sama sukaji Medaki ta tashi tana fadin shikenan munshiga 3 wlh, ba laifina bane, duk kutsaya wlh zanfadi iyakar gaskiyar dana sani. Gimbiya Zakiyyah tayi wani murmushi aranta tace lallai zaki sha mamakina,ni nasan babu wanda zeyarda idan kikace hadani.

Waziri yayi murmushi yace rankiyadade munajinki. Tashi tayi tana kuka tafada masu duk abinda sukayi itadasu Gimbiya Zakiyyah, akan batan Fulani, sede bata fada masu abinda suke aikatawa da Sarkin fada ba.

Gaba daya falon aka dau salati, Sarki Hasheem kuwa zama yayi kamar dutse, kallon Jakadiya Karima kawai yake idanunshi na zubar da ruwa. Waziri yace da kyau, tashi Gimbiya Zakiyyah tayi tafara magana cike da mulki.

Inada ja agame da maganar Medaki, wannan maganar datayi kawai tafa deta ne sbd wani dalilinata, amma kowa yasan bana shiga harkar talakawa taya za,ayi inhada baki dasu mu aikata irin wannan shirmen.

 wanda kowa yasan duk wanda yafito daga gidan sarauta bazeyi haka ba. Idan kuma har tace dani, ni nayarda sukawo sheda, idan har aka sameni da hannu aciki nayarda da duk wani hukunci daza,amun.

Waziri ya jinjina kai, alamar gamsuwa, ya kalli Medaki yace kina da wata shedar dazata nuna mana tana da hannu acikin abinda kika fada? Wata zufa ce takara keto mata, hawaye suna zuba a idonta tafara girgiza kai, tace a,a amma wlh dama tace zan gani....... kamar daga sama Sarkin fada yace nine shedar akwai ta acikin wannan aiki.


Kusan ma itace shugabarmu domin ita tasamu yin wannan aiki, kuma ni inada shedar dazata nunama kowa abinda ma bakusani ba, dama na ajeta sbd irin wannan rana. Ai Gimbiya Zakiyyah batasan lokacin data sauko kasa daga kan kujerar datake ba.

Anan Sarkin Fada yatashi yace tabbas ni nasan ayau asirina yagama tonuwa, dan haka banga dalilin bata maku lokaci ba, nasan Allah ya dade yana aramun rana, sede inaso kuyi hakuri da duk abinda zakuji, bakomai bane yasani aikata haka se SON ZUCIYA.

Wadda azamanin nayanzu shine abinda yake dawainiya da mutane da dama, wanda kuma bakowa bane yake saka mana son zuciya se shedan, da kuma mu kammu idan muka kasa tsarkake zuciyarmu.

Ban kasance mutum nagari ba a masarautar nan, na dade ina aikata abubuwa da dama, sede babu wanda yasani, harzuwa yanzu. Alokacin da aka haifi Yarima Areef, babban dalilin dayasa najawoshi jikina shine dan insalwantar da rayuwarshi, yazamana beda amfani arayuwa gaba daya.

Ada nayi niyar kasheshi sede shakuwar damukayi tahana ni, duk da Jakadiya Karima taso akasheshi, nine na hana. Babu irin maganin da ban bashi ba dan kawai inga yazamo dolo agidan nan amma hakan beyuwu ba, abu daya nasan yayi tasiri ajikinshi shine yanda bedamu da sarauta ba.

Alokacin daya girma se abun yadawo kaina, tunda yadawo daga karatu na lura bayason ganina, hakan yasa naja baya dashi. Amma sanin naci ribar cire mashi sarauta aranshi hankali na ya kwanta.

 Wannan kenan.

Bayan Jakadiya Karima tazo tasameni akan Gimbiya Zakiyyah tana nemana, bayan naje ita da Medaki suna zaune tafadamun abinda takeso inyi, sunaso insan yanda zanyi inhallaka Fulani da abinda ke cikinta. Aranar da dare itace agurin Sarki, hakan yabamu damar shiga dakin Fulani mu biyu, nina fesa mata abinda yake sa mutum bacci, sede ban fesa mata ba sebayan muntasheta, alokacin taganni seta fara kokarin yimana ihu, hartaji mani ciwo afuska, ganin za,a jimu ne yasani fesa mata maganin, nan take tayi bacci.

Kamata mukayi muka fita da ita, muka sata mota, dama munhada baki da masu gadin gate su 2, wato Lado da Mati, hakan yasa suka bude mana kofa muka fita. Munyi tafiya menisa dan seda mukaje wani daji dayake bayan garin Darazo kusa da wata Mabarta, anan muka wurgata cikin wani rami.

Sede wanda muka aikata laifin dashi banganshi anan ba, amma inaso ashigomun da amintaccen bawan Sarki Hasheem me kula da komai nashi nacikin gida, shine wanda yatemaka mun mukayi wannan abun.

Sarki Hasheem runtse idonshi kawai yayi yana karanto addu,a dan zuciyarshi zafi takeyi, jiyake kamar zata fito. Ganin haka Malam yasa aka miko mashi ruwa yayi addu,a aciki yabama Sarki Qaseem wanda shima kukan yakeyi, yace yabashi.

Dakin yayi shiru sautin kukan mutane kawai akeji, jisukeyi kamar almara ce ake fada masu. Bayan anshigo da bawan, anan yaxube yana kuka, yace dan Allah kumun rai wlh Son Zuciya ne da kwadayin abun duniya suka kaini da aikata wannan abu. Waziri yace haka kowa yake fada Son Zuciya, Ai kowa yasan son Zuciya bacinta.


Sarkin fada yafiddo wata karamar waya daga aljihunshi yamika ma Waziri yace wannan shine shedar dazata nuna maku akwai sa hannun Zakiyyah acikin duk wani munafunci da akayi, bazan kirata Gimbiya ba sbd tazama tamkar mata agurina. Saurin dafe kai Sarki Hasheem yayi dajin abinda Sarkin fada yafada.

Wata waya waxiri yaciro yajona ajikin wayar yahada da T. V ya kunna kowa yamaida hankalinshi akan t,v. Tun daga lokacin dasuke zaune afalon Gimbiya Zakiyyah tana fada masu yanda za,a kawar da Fulani, da duk wani munafunci dasukayi, harzuwa lokacin daya fara neman Medaki, tunda Sarki yaga sunfara aikata masha,a yarufe idonshi, aranshi yana fadin wato dama karya medaki tamashi babu wani fyaden da akayi mata, dama can yar iska ce. Areef kuwa yahana beauty ma ta kalli abinda akeyi, ya kwantar da ita akan cinyarshi yana shafa mata kai, daga haka tayi bacci.


Babban abinda ya dagama kowa hankali lokacin da aka nuno sanda suka fara aikata masha,a da Gimbiyyah Zakiyyah. Salati kowa yafarayi, hakan yasa Sarki yabude idonshi, sede yayi dana sanin ganin abinda matarshi da bafadenshi suke aikatawa. Waziri yasa hannu yakashe wayar.

Shiru kowa yayi se kukan Gimbiya Zakiyyah dana medaki kawai akeji. Jakadiya Karima ta tashi tace wlh shima akwai abinda befada maku ba, idan bazaku manta ba, alokacin da za,a nada Sarkin fada bashi bane aka zaba ko? Waziri yadaga kai. Nan Jakadiya tashiga basu labarin da Sarkin fada yabata.

Mamaki yakama kowa jin irin abinda sarkin fada ya aikata. Hayanice tacika falon. Bayan kowa yanutsu, Waziri yace lallai babu abinda zamuce sede muyi godiya ga Allah wanda shine yake tsaremu aduk inda muke.

Tabbas akace dazama da makiyi gara zama da barawo, kuma dama ance makusan cinka shine makashinka. Tabbas kunso kashe abinda Allah yaso yafito duniya, sede babu wanda ya isa ya aikata wani abu seda izinin Allah. Matar da kukaso kashewa da diyarta gasunan araye. Kallon Areef yayi yace daga matar taka kowa yaganta.

Murmushi yayi dan seyanzu yafara fita daga duhun dayake ciki, tashin beauty zeyi Malam yace abarta, zata tashi da kanta. Kowa mamakin ganin beauty yakeyi wai itace diyar Fulani, Sarki kam wani irin sanyi yaji yana ratsashi duk da damuwar datake ranshi.

Waziri yace akwai bayanin da Malam zeyi mana kafin afadi irin hukuncin daza,ayi ma kowa. Amma zamuje hutu daga nan zuwa bayan azahar dan sallah tagabato, wasu fadawa yasa suka tasa keyar su Gimbiya Zakiyyah, Medaki dasu Jakadiya yace atsaresu.  Kuma yasa suhada da mati da Lado.

Kuka kawai sukeyi. Sarkin fada kuwa murmushi kawai yakeyi.
Matsawa yayi kusa da Gimbiya Zakiyyah yace kinsan akullum tunanin yan sarauta akullum iya karshi harshe, dan basa amfani da tunaninsu sede na bayinsu. Kinga koyanzu ya isa kigane banbanci tsakanin Bawa da me mulki. Kuka tasaka, aka turasu zuwa kurkutu.

Nima yakamata inhuta haka kafin sudawo.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady).
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 105⚜110

Zaune suke gaba daya harda masu laifi, zuwa wannan lokacin idanunsu haryagaji da zubar hawaye. Sarki Hasheem ya kalli Gimbiya Zakiyya, duk tafita hayyacinta, har seda tabashi tausayi dan yasan halin mahaifiyarta idan hartaji abinda tayi tabbas zata saba mata.

Kawar da kanshi yayi ya kalli beauty wadda take haryanzu ajikin Areef, tunda Fulani ta tureta haryanzu taki kara kallonta kuma koda aka dawo sallah agurin Areef ta tsaya, shikam dama haka yakeso, yariketa kamar ance za,a kwaceta. Dan bemanta da halin data shiga ba lokacin da Momynshi tayi mashi fada.

Malam yayi gyaran murya yace Alhamdulillahi Allah yakawomu abinda na dade ina fatar Allah yakawomana karshen shi, tabbas masarautar nan tashiga tashin hankali da rudani, wanda zance bacewar Fulani agidan nan tamkar saukowar wani haske ne wanda yazo ya haske duk wani duhu dayake gidan nan. Kuma ya haska duk wasu munafukai dasuke tare da mutanen gidan.

Abin mamaki wai ace wanda kayarda dashi yanzu aduniya shine yake cutarka. Gaskiya nayi matukar girgiza dajin wadanda suka aikata wannan ta,asa wai makusantan Sarki ne, acikinsu kaf babu wani bare.

Dama haka duniya take, duk wanda zakayima hassada tamkar kana kara kusan tashi da ubangiji ne, domin tunda annabi yasamu makiya to babu wani dan adam din daze iya kubuta daga sharrinsu.

Sede abinda nakeso inkara tunatar daku, shine addu,a domin itace makamin mumini, duk da ake cewa bawa baya iya kaucema kaddararshi, amma idan muka rike addu,a babu abinda bazata yimana ba.

Addu,a takan canza sharri yazama khairi, kuma tanasa tsanani yazama sauki, dan haka koda Allah ya kaddaro maka wata kaddara marar kyau, idan har karike addu,a abun ze iya zo maka dasauki. Arayuwa baka taba gane makiyinka, harse ranar da asirinshi yatonu.

Agskiya Sarkin Fada kabamu mamaki sosai, da irin abubuwan damukaji ka aikata, ba kowane me imani bane ze iya aikata abinda ka aikata. Kaci amanar kanka, addininka, iyayenka, matarka, da kuma Ubangidanka.

Duk irin halaccin dayayi maka arayuwa, seda ka ha'inceshi, kashiga gonarshi har 2, duk da haka bata isheka ba seda kayi sanadiyar rugujewar farin cikinshi, tahanyar kauda abinda yake matukar so, kaso ka halakar dasu amma Allah be baka iko ba.

Ko kasan ta dalilinka irin ukubar da Fulani da diyarta suka shiga? Mezaka cema Allah aranar gobe kiyama idan yatambayeka akan amana? Ko kasan kalar abincin dasukaci atsawon shekaru 18 acikin MAKABARTA?


Ta dalilinka matar da babu ruwanta, bata yima kowa komai ba, amma saboda SON ZUCIYA irin taku kaida mabiyanka kunsa baiwar Allah tahaihu a MAKABARTA. Yarinya ta tashi a MAKABARTA. Bata san kowa ba se Mamanta da kaburbura, da bishiyoyi.

Wancen bawan Allah da kuke ganinshi agidan nan badan kowa yake zaune ba sedan farin cikin yarinyar da kukaso ku hanata zuwa duniya. Shine mutum na 2 daya temakeso, wanda badanshi ba haka Yarinya zata girma har shekaru 18 amma batasan komai ba, kuma ita ba hauka ba, barashin lafiya ba.

Kawai saboda tsabar SON ZUCIYA irin taku, bara infada maku abinda bakusani ba, kuma zakusan cewar duk zakaran da Allah yanufa da tsara to ko ana muzuru ana shaho se yayi.

Idan bakusani ba aranar da kuka wurgar da Fulani acikin dare kuka wurgata cikin rami, to aranar ta haihu, kunsan suwa Allah yaturo mata kawai dan yanason yanuna maku baya bacci? Wasu bayinsa ne, kuma yan uwa musulmai, wadan da suka fito daga jinsin aljanu.

Akusa da fadarsu kuka wurgata, kuma cikin ikon Allah alokacin suka temaka mata harta haifi diyarta acikin koshin lafiya. Zakusha mamaki idan nabaku labarin da daya daga cikin aljanun, wanda yakasance shugaba agurinsu, shine yabani labarin abinda yafaru. Bara kuji....

Kaf duk abinda Malam yasani seda yafada masu, gaba daya falon babu wanda beyi kuka ba saboda tausayin Fulani da beauty, kowa ya tausaya masu yanda sukayi rayuwarsu acikin MAKABARTA. Fulani da Beauty sunfi kowa kuka, dan ita beauty tade taso taganta a MAKABARTA.

Atunaninta nanne muhallinsu, kuma Fulani ita kadaice wadda tasani, mace, se kuma Baba wanda shima shikadai tasani namiji. Kuka takeyi sosai ayau dataji labarinta, ashe inda take tunanin muhallinsu ne, take cewa acan aka haifeta, ashe muhallin matattune, segashi yanzu ana fadin AMAKABARTA AKA HAIFETA.

Malam yace ga Baba nan, shine megadin MAKABARTAR da suke zaune, kuma shine mutumin daya zauna dasu bisa gaskiya da amana, kuma ko matarshi betaba fada mawa ba, harseda yaga lokaci yayi daya kamata yafada mawani, alokacinne yazo yasameni yafadamun.........


Duk abinda Baba yafada mashi seda yafada masu, da irin dawainiyar da yayi dasu. Hakanne yasa alokacin da yagama bani labari, mukaje muka daukosu duk da seda wannan aljanu suka rokemu akan mukula dasu idan har wani yakara yunkurin cutar dasu bazasu kyaleshi ba.

Tundaga ranar damuka daukosu, nafara tunanin tabbas abinda nagani acikin istaharata yana shige da wadannan bayin Allah, idan baku manta ba Waziri, azuwan da kukayi nafada maku naga Fulani akusa dani, kuma tana raye, sede bansan awane waje take ba.

Hakan yasa nafara zargin wannan mata da diyarta zasu iya kasancewa matar Sarki da diyarshi. Amma gudun kada inyi saurin fadar abinda zuciyata take fada mun hakan yasa lokacin da Safeeya tazo mani da alfarmar abata wannan yarinya ta taho da ita nan gidan yasa nayi tunanin barinsu suzo, sena cemata dole sutaho su duka.

Hakan yasa naroki alfarma gurin Baba nayabar aikinshi yataho tare dasu. Adaren dazasu tafi nakira Safeeya daki nake cemata ina zargin wani abu akan mutanen nan, itama tace mun zuciyarta tafara saka mata irin abinda nake zargi, dan ita tasan Fulani sosai, amma tacemun bazata iya cewa ita bace dan alokacin ko Sarki yaganta baze iya ganeta ba, tsawon shekaru 18, gashi bacikin hankalinta take ba, kuma bagurin jin dadi ba, babu wankan kirki, babu sallah, ba lallai bane a iya ganeta.

Shiyasa nace ma Safeeya sutafi tare, ta ajesu agurinta kuma kada tabari kowa yasan dazamansu idan har tasamu nutsuwa da tsafta zata dawo cikin kamanninta, idan kuma ba ita bace shikenan nace munyi temako.

Alokacin nakira Waziri mukayi maganar, dan aduk fadin masarautar nan mutum 3 nafi yarda dasu, kuma yana daya daga cikinsu, Sarki Qaseem, da Sarki Hasheem. Babban dalilin dayasa banyi maganar da Sarki Qaseem ba, nasan yanda halinshi yake, baze taba iya hakura abi abun asannu ba, kamar yanda nashirya, shiyasa ban fada mashi ba.

Bayan Safeeya takirani tafadamun tagano wannan mahaukaciyar bakowa bace se Fulani da diyarta, alokacinma nace mata taboye abun harse angano wadanda suka aikata mata haka. Nakira Waziri nafada mashi, kuma alokacin yake fadamun yafara zargin Sarkin Fada.

Ni nace mashi yacigaba da bibiyarshi harse ansamu cikakkiyar shedar dazata bada damar kamashi sannan, kuma nafada mashi bashi kadai bane dole akwai wata ko wani makusancin Sarki. Alokacin seyake cemun shifa yana zargin Jakadiya Karima.

Nima nayarda da abinda yafada, hakan yasa nace mashi ya zuba masu ido su duka biyun. To Alhamdulillahi yau gashi damukayi hakuri Allah yanuna mana makiyanmu afili.

Sede kuma akwai abu daya danakeso intambaya Waziri. Ina wannan bafaden da Sarkin fada yajama sharrin kisa, ina fatan ba,a yanke mashi hukuncin kisa alokacin ba? Gyara zama Waziri yayi yace, alokacin kam Sarki ya yanke mashi hukuncin kisa.

Sede ni ajikina bansan meyasa banyarda da hukuncin da Sarki ya yanke ba, kuma zuciyata takasa yarda da cewar shine yayi kisan, amma alokacin kuma zuciyata bata zargin Sarkin fada, sede kawai taki yarda da wanda akace yayi kisan.

Hakan yasa naja Sarki falo tafada mashi da kada ya yanke hukuncin dazezo yadameshi daga baya, nine nabashi shawarar daya yanke mashi hukuncin daurin rai da rai. Kuma haka akayi, haryanzu yana nan akurkutun gidan nan.

Sede tun lokacin dana fara zargin Sarkin fada da rashin gaskiya acikin gidan nan, tun daga ranar nafara kaimashi ziyara, mukan zauna muyi fira,acikin zaman damukayi ne, nakara yarda dabashine yayi kisan ba, kuma akwanakin  baya ne nasa aka canza mashi gurin aiki, harda gurin zama.

Kuma tunjiya nasa aka fiddoshi yanzu haka yana masauki. Malam yace kasa akirashi yazo nan. Waziri ya aiki daya daga cikin fadawan gurin. Malam yace wannan shine iyakar abinda nasani agame da rayuwar Fulani da diyarta. Wadda haryanzu babu wanda yasan sunanta.

Abinda Baba yake kiranta dashi shine Yar Baba, wanda yacemun ada yaji Fulani tana kiranta da Baby, jin sunan zeyi mashi wahala ne, yake kiranta da diyarshi. Amma ayanzu tunda gashi sundawo gida, za,a iya saka mata sun

 kuma Waziri se muji daga gareku wane irin hukunci zaku yankema wadannan maciya amanar.

Sallamar bafaden da aka aika ne tasasu kallon kofa, tare suke da wanda aka likama kisan da Sarkin Fada yayi, zama yayi yana kwasar gaisuwa, daka ganshi kasan yajigata, atsawon zaman dayayi akurkutu shekaru dayawa.

Kallon Sarki Qaseem da Sarki Hasheem Waziri yayi, domin jin abinda zasu fada. Sarki Qaseem yayi gyaran murya yace, ni babu abinda zance, sede kawai inma Allah godiya daya kawomu karshen wannan matsala damuke ciki. Tabbas wadan nan mutane, kunsamu cikin tashin hankali, babu abinda zance maku se Allah ya isa.

Sede abu daya nakeso kusani, hakan da kukayi bashine ze samurika tsoron mutane ba,ko kuma mudena jawo su zuwa jikinmu ba, ai ba,a taba taruwa azama daya, idan wani yazo daniyar cutarka, Allah ze aiko maka dana gari, wanda ze zauna da kai badan komai naka ba, sedan son dayake maka domin Allah.

Idan kuka kalli Jakadiya Safeeya da Malam,da Matata da kuma matar Yaya wato Fulani, daga baya muka kara samun Baban Darazo da abokin Yarima wato Haisam. Duka wadan nan dana lissafo babu wanda muka hada jini dashi, kuma babu wanda muka tashi dashi acikin gidan nan.

Asalima bamu taba tunanin zasu shigo cikin rayuwarmu ba, sedaga baya muka sansu, kuma duk da basu kasance yan uwa agare mu ba, sun zauna damu tsakani da Allah, babu wanda yakeda niyar cutar damu.

Idan muka kalli Malam da kanwarshi, bawai dan sun rasa abinda zasuci bane yasa suka shigo jikinmu. Jakadiya Safeeya tazo gidan nan badan kowa ba sedan bin umarnin yayanta, kuma duk da haka tarika kaskantar da kanta agaremu, wanda inda dan kudine zatazo, ninasan babu abinda ze kawota, dan aduk fadin garin Bauchi, darazo, Gombe, harma da makotanmu mutane dayawa sunsan Malam, kuma kowa yasan babban mutum ne.

Idan har kudine, bayada damuwa dasu, asalima yakan dauko wasu suci akarkashin shi. Amma duk da haka suke zama tare damu abisa gaskiya da amana. Wannan kadai ya isa yanuna ma kowa cewa wanda baku hada komai dashi ba, ze iya yimaka abinda makusancinka baze maka ba.

Yanzu ku kalli irin cin amanar da akayima Yaya, Gimbiya Zakiyya kinci amanar sarauta, kuma kinci amanar iyayenki, amatsayinki na Uwar gidan yaya amma aka hada baki dake, aka cuceshi, koba komai, mahaifinki da Abbanmu abokan junane sosai, kuma dama sune suka hada aurenku, alokacin Yaya bayasonki amma nayi imani da Allah haryanzu betaba fada maki keba ra,ayinshi bace.

Haka yakarbi zabin iyayenmu kuma yazauna dake da gaskiya da amana, segashi daga karshe kinzama butulu, bayan butulci ma harseda kika hada da cin amanar aurenku. Wa iyazubillah, kina matar aure amma kika aikata wannan babban zunubi agidanki. Amma kanki kikai mawa, kuma wlh. Kowace irin alaka ketsakinmu bazata hana ayanke maki hukunci dede da laifinki ba.

Kuka tasaka tana fadin natuba, dan Allah kumun rai, wlh duk abinda kuka fada gaskiya ne, amma niban aikata abinda kukagani da son rai na ba. Nide nasan babu abinda na tsana kamar zama guri daya da talaka, kuma ni tunda nake wlh wannan aikin da Sarkin fada yamun shikadai ne, yataba hadani dashi harmukayi magana. Akwai sanda jakadiya Karima tazo tacemun wai Sarkin Fada yana gaisheni.

Wlh ku tambayeta idan har zata fadi gaskiya zata fada maku irin cin mutuncin dana mata akan abinda tazo mun dashi, wlh babu wata alaka datake tsakanina dashi, ko aranar danasan munfara aikata sabo dashi, yana shigowa da masifa narufeshi, amma bansan ya akayi daga baya harna bashi hadin kai ba.

Dan Allah Sarkin fada kafada masu ba laifina bane. Wani malalacin murmushi Sarkin Fada yayi yadauke idonshi daga kallonta. Sarki Qaseem yace wannan kuma yarage naki, kinsan masarautar nan bata yanke hukunci seta tabbatar da sheda tazahiri, kuma ba mutum daya ba, kowa gurin nan yaga abinda kuka aikata, dan haka ki adana kalamanki.

Kallon Medaki yayi, yace kenarasa ma mezance maki, kinfi kowa zama cikakkiyar butulu, kinfi kowa sanin dayanda aka aureki da irin halaccin da Yaya yayi maki, duk da nibanyarda da labarin da mamanki tabada ba, amma sbd sanin girman alkawarin da yaya yadaukar mata, haka mukayi hakuri ya aureki.

Amma kirasa da abinda zaki saka mashi se irin wannan cin amanar, kema zakiga sakamakonki. Kuma abinda nakeso dake inaso kifada mana wacece ke? Da kuma asalin garinku.

Cikin sheshshekar kuka Medaki tace wlh nima bansan inane asalin garinmu ba, nadesan ayawon damukeyi daga wannan kauyen zuwa wani iyayena suka haifeni. Kuma sanin dana yima iyayena basu bani tarbiya tagari ba, babu ilimin addini bare na boko, to sukansu ma basu damu danasu addininba.

Nikaina nafara sanin Sallah ne alokacin dana ke bin wata kawata islamiyarsu, anan nafara sanin addini na, harna fara fahimta sosai, sekawai innata tafara doramun talla, domin ita macece meson kudi.

Aduk lokacin dana saida tana siyamun duk abinda nakeso, nima tundaga ranar son kudi,yashiga raina. alokacin kuma na hadu da wani saurayi shine yakara huremun kunne, haryayi nasarar ciremun budurcina, seda muka zubar da ciki har 2, kuma Innata bata tabamun fada ba, wannan shine sanadiyar lalacewar mahaifata.

Mahaifina dan caca ne, bedamu da ya rayuwata takeba, shiyasa nakasance tamkar dabbar daji, banida wani takunkumin daze hanani aikata abinda naga dama. Sanadiyar Caca mahaifina yarasa ranshi, mutanen gari suka koremu harmuka hadu daku, Innata tafada maku karya har kuka yarda damu.

Tabbas nasan naci amanar mijina, wanda yarufamun asiri, duk da yagane banje da budurcina ba, amma be tsaneni ba, asalima cikin laluma ya tambayani, shima nafada mashi fyade akamun wanda karyane, amma haka ya yarda dani, kuma yacemun beyarda infadama kowaba.

Dan Allah kayafe mani, nasan bankasance mace tagari ba, naci amanarka dan Allah kuyafemun. Kuka tasaka wanda seda wasu daga cikin mutanen falon sukaji tausayinta,,,,, hayaniya sukaji awaje, Wazirine da fadawa suka leka.

Wani kodaddan mutumi suka gani wanda beda kyan gani, sunata rigima da masu gadi. Waziri yace ku kyaleshi yakaraso, haka yataho yanata zare ido. Yana zuwa yace wani nake nema agidan nan nayi mashi aiki be bani kudina ba. Kuma nafada mashi idan har bebani kudina ba zanzo intona mashi asiri.

Murmushi Waziri yayi yace kashigo semuji wa kake nema. Kowa mamakin ganin mutumin daya shigo yakeyi, banda Sarkin Fada wanda yaketa muzurai. Waziri yace munajinka wakake nema?.

Yace sunanshi Sarkin Fada, kuma ya kasance daya daga cikin mutanen danake yima aiki, duk wani aikinshi nine nakeyi mashi, anan yarika fadin duk irin asirin dayasashi yayi, harda wanda yayima Areef, dana Jakadiya Karima wanda tazubarma Gimbiya Suhailat ciki kuma aka daure mahaifarta, har yakawo asirin karshe dayayi mashi.

Yace aranar yazomun akan yanason inbashi maganin mallakar zuciyar Matar Sarki, Zakiyyah, yacemun yadade yana sha,awarta amma yasan bazata taba bashi kanta ba, hakan yasa yazo inbashi magani, alokacin yacemun beda kudi amma yasan idan yasamu sa,ar kusantarta yamallake zuciyarta zesamu kudi.

Tun ranar dana bashi bankara ganinshi ba, shine yanzu nazo inkarbi hakkina. Salati kowa yakeyi, sbd wani abin al,ajabin dasuka karaji yabullo. Murmushi Waziri yayi yace kaima seka samu guri kazauna kajira naka hukuncin tunda Allah yakawoka. Zaro ido boka yayi yana fadin aishikenan kuma wlh nayafe mashi kubarni intafi.

Seda yabama kowa dariya, nan fadawa suka zaunar dashi. Se alokacin Sarki Hasheem yayi magana, jikinshi asanyaye yace Malam, kafadi irin hukuncin daya kamata ayima kowa abisa koyarwa ta addinin musulunci, kamar yanda yazo a Qur'ani. Dan nagaji da kallon fuskokin wadannan mutanen.

Dan duk acikinsu nafijin haushin mutum daya, bakowa bace se Jakadiya Karima. Allah ya isa tsakanina dake, kin cuceni, wlh zan iya yafema kowa agurin nan amma banda ke, bazan taba iya yafe maki ba. Mundaukeki Uwa asheke makiyarmuce nida dan uwana..... kuka yasaka tamkar karamin yaro.

Alokacin hatta da Malam seda yazubar mashi da kwalla sbd yanda yakeyin kuka kowa yasan abun yana cimashi rai sosai. Sarki Qaseem yana kuka yace Malam dan Allah ayanke masu hukunci kada ciwon Yaya yadawo.

Malam yace Alhamdulillahi, kamar yanda kuka sani duk wani laifi na duniya babu hukuncin da Alku'ani da hadisi basu kawo ba, dan haka zamu duba muga irin hukuncin da Allah yace ayima masu irin laifinku. Zanfara daga kasa zuwa sama, wato daga masu karamin laifi zuwa babba.

Zan fara da masu gadi, mati da Lado, tabbas kun aikata babban kuskure, domin da farko kunci amanar masarauta, sannan kunbada gudummuwa gurin aikata fasadi, dan haka hukuncinku anan shine zakuyi zaman kurkutu natsawon shekaru 2, domin aladabtar daku, sannan baku bakara aiki awata masarauta.

Se amintaccen bawan Sarki Hasheem, kaima kaci amanar Uban gidanka, sannan kazamo daya daga cikin wanda yatemaka ma Sarkin fada kuka sace Fulani. Dalili daya ne bazesa ayanke maka hukuncin kisa ba, saboda Fulani bata mutu ba, kuma Qur,ani cewa yayi wanda yakashe akashe shi, sbd haka kaima za,a daureka akurkutu na tsawon shekaru 5, tare da aiki metsanani.

Gimbiya Zakiyya, kinkasance matar aure, wadda aka kamaki da laifuka biyu. Nafarko kina da sa hannu abatan Fulani, wanda dakunsami dama kasheta zakuyi. Nabiyu kuma laifin aikata zina. To hukuncin zina anan yakasu kashi 2, akwai na wadda bata tabayin aure ba, wato budurwa, akwai kuma na wadda ta tabayin aure.

Idan budurwa tayi zina, kuma aka tabbatar dashedu, za,a yanke mata hukunci bulala 100, idan abokin yinnata shima saurayine, hukuncinsu daya.

Matar aure. Duk matar datayi zina kuma tanada aure, ko ta taba yin aure. Hukuncinta kisane, tahanyar jefewa da duwatsu, wanda yara ne zasu jefeta harta mutu, za,a rufe duka jikinta cikin rami abar kanta shine za,ayita jifa harta mutu.

Idan abokin zinarta yataba aure, hukuncinsu daya, idan kuma shi beda aure, to nata daban nashi daban. Abisa shedar da muka samu daga gurin wanda yayi maki asirin da kika fada wannan alfasha.

Kamar yanda yazo a arba'una hadith, mazon Allah yace INNALLAHA TAJAWAZILI AN UMMATI➡➡ Lallai Allah yagafarta ma al'ummata,  AL,,KADAHA... abinda sukayi da  KUSKURE.  WANNISIYANA... abinda sukayi da MANTUWA.  WAMASTUKURUHU ALAIHI... da abinda AKA TURSASASU AKANSHI. Rawahul bukhari wa muslim.

Abisa duba da wannan hadisi, sarkin Fada yayi amfani da karfin asiri ta hanayar mallakeki har kika biye mashi kuka aikata alfasha. Abisa wannan hadisi, anan bakida laifi agurin aikata wannan zina. Dan haka bazaki dauki hukuncin zina ba anan.

Sede hukuncin dazaki dauka na aikata laifin cin amana gurin niyar salwantar da rayuwar Fulani, dan haka zakiyi zaman kurkutu shekara 5. Saura hukunci kuma yarage ga mijinki.

Tunkafin yacigaba Sarki Hasheem yace Malam da ita da Medaki duk nayanke igiyara aurena akansu, dan haka kacigaba da yanke hukuncinka. Hannu Zakiyyah ta dora akai tana kuka.

Malam yace Medaki, kema hukuncinki biyu ne. Amma tunda nakarshen megaba daya ne, to hukunci daya zamu yanke maki, naki hukuncin kisa ne, tahanyar jefewa, tunda ke kin amsa kece kika bama sarkin Fada hadin kai da kanki. Dan haka hukuncin kisa zaki dauka.

    Jakadiya Karima kema hukuncin kisa ne akanki, sbd kin aikata kisan kai domin kinsa anzubar da cikin Gimbiya Suhailat. Anyanke maki hukuncin kisa daurin rai da rai akurkutu, tare da horo metsanani.

Boka, kaima hukuncin kisa ne, ta hanyar rataya, tunda ka amsa laifinka, kuma Allah kadai yasan iyakar ta,asar dakayi.

Hukuncinmu na karshe akan Sarkin fada, kai kam da ana mutuwa adawo to da seka karbi duka hukuncinka. Amma hukuncinka anan shine kisa ta hanyar rataya.

Anan muka kawo karshen wannan hukunci na MASARAUTAR BUBAYERO. Inafatan hukunci yayi maku, idan kuma akwai wani abu kuna iya fada, yajuya yana kallon Sarki. Sarki Qaseem yakalli Yayanshi. Kai yadaga alamun hukunci yayi, sannan yace kuma agobe za,a aiwatar da wannan hukunci.

Ihu Gimbiya Zakiyyah tasaka kamar meshirin shiga hauka, Medaki da Jakadiya ma kuka kawai sukeyi kamar ransu zefita. Haka aka kara tasasu zuwa kurkutu kafin gobe.

Nima nace Allah yakaimu goben da rai da lafiya.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 110⚜115

Kusa da Baban Darazo Fulani ta matsa, idanunta haryanzu basu dena zubar da kwalla ba, dukawa tayi har kasa tace, Baba hakika banida bakin dazanyi maka godiya, kayimun abinda bakowa ne dan Adam bane ze iya yimani shi.

Tabbas kazamo daya daga cikin mutane masu muhimmanci arayuwata, kuma daga yau inaso kadaukeni tamkar diyarka ta cikinka, inaso kadauko duka iyalanka kudawo nan dazama dan suma sunzama yan uwana.

Baba yace babu komai Fulani, duk abinda nayi maki nayi shine dan Allah, banyi dan wani abu naku ba, asalima bansan wane irin matsayi gareki ba. Hakika naji dadin yanda kika dauke ni, kuma nagode Allah yasaka da alkhairi.

Haka kowa yatashi yanufi bangarenshi kafin gobe da safe. Haisam ya kalli Areef yace abokina nizan tafi gida, amma dole gobe indawo in kalli wasan daza,ayi agidan nan. Tabbas nakara daukar darasi agidanku.

Allah yakara mana karfin imani kuma yacire mana SON ZUCIYA. Areef yace amin, nima kaina abubuwan gidan nan sun gama daga mun hankali, naji tausayin beauty na sosai, ta dalilin masu SON ZUCIYA tarasa ingantatacciyar rayuwa da kowane dan Adam masu galihu suke samu.

Tarasa cikakken Ilimin addini dana Boko, batasan kowa acikin yan uwanta ba, batasan yaya mutane suke ba, har seda Allah yakawota cikin gidan nan. Kalli Umminta, tasamu kanta acikin hauka harna tsawon shekaru 18. Agaskiya mutane basa kyautawa.

Nayi alkawarin zan jiyama beauty rayuwa medadi, wadda batayi irinta abaya ba. Zan sama mata makaranta me kyau wadda zata samu cikakken ilimin addini dana boko. Fatana Allah yabani tsawon rai in cika wannan burin dana dauka. Kamar yanda Sarkin fada yake ikirarin yasa anciremun son sarauta azuciyata, to be cuceni ba.

Kanshi ya cuta, kuma naji dadin hakan, zanyi amfani da damar dana samu dan insamu lokacin beauty na, nasan inda inason sarauta bazan iya samun lokacinta ba, bare incika mata burin dana dauka, dan haka zan rokisu Abba ayi bikinmu akusa dan bana tunanin zama da beauty akasar nan.

Zantafi da ita wata kasa harseta samu ilimi me kyau sannan mudawo. Haisam yace gaskiya ka kyauta, sede kasan da kyar idan su Abba zasu yarda, yanda beauty bata taso agidan nan ba zasu so ace sun sami lokacin zama da ita. Areef yace katayani addu,a insamu shawo kansu.

Washe gari da misalin karfe 10 na safe tawagar Sarkin Yobe wato mahaifin Zakiyyah da mahaifiyarta suka iso masarautar BUBAYERO. Dan tun ajiya Sarki Hasheem yasa Sarki Qaseem yafada masu halin da ake ciki. Ba karamin tashin hankali suka shiga dajin wannan labari, ba kamar mahaifiyarta datasan ta dalilin haka zata zama abin tsangwama acikin kishiyoyinta.

Zaune suke afalo, sede Familyn gidan ne, kawai aciki, tare dasu Mahaifan Zakiyyah, se kuma Waziri, malam da Jakadiya Safeeya. Agefe guda kuma Zakiyyah ce zaune atakure guri guda se kuka takeyi.

Mahaifinta ne yayi gyaran murya yafara magana. Hakika Zakiyyah kinbani mamaki da irin abinda kikayi, saboda kawai kishi irin naku na mata, yanzu inda Allah yabaku sa,a kunsamu damar kashe  Fulani da shikenan kema kinza me kisan kai ko?.

Ko agidanku dakika taso acikin kishiyoyi kika samu mahaifiyarki, kintaba ganin ance ta harari wani acikinsu? Duk da takasance karama acikinsu amma hakan besa ta rainasu ba. Agaskiya banji dadin abinda kikayima kishiyarki ba.

Kuma naji dadin hukuncin da aka yanke maki, wannan shine dede ga duk mutumin da yace Son zuciya zerika bi arayuwarshi, koyanzu da kikaga munzo bawai munzo bane dan ke, munzo ne, kawai dan inbada hakuri agurin mutanen da kika zalunta, babu ruwana da hukuncin da aka maki, haka zaki zauna tare da sauran masu laifi har shekaru 5, idan Allah yasa har lokacin ina raye nibazan hanaki zama gida na ba, amma kisani kina dawowa zan aurar dake ga duk wanda naga dama.

Dayake Sarki Hasheem yace kada wanda yafada masu abinda suka aikata da Sarkin Fada hakan yasa basusan maganar ba. Dan Sarki yace yanajin kunyar mahaifinta shiyasa yahana afada masu abinda tayi, duk da ba laifinta bane.

Kuka sosai Zakiyyah takeyi ta matso kusa da Babanta takama. Kafarshi tace dan girman Allah Baba kayafemun, wlh nikaina nayi nadamar abinda na aikata, babu irin shawarar da Umma bata bani ba, amma nabiyema hudubar shedan na aikata abinda yazubar da kimar masarautarmu, dan Allah kuyafe mani koda mutuwa zata riskeni acikin kurkutu.

Seda kwalla tacikama mahaifinta ido, damma bakin glass ne a idonshi, juyawa tayi kusa da Ummanta takifa kanta bisa cinyarta tasaka kuka, tarasa bakin magana, itama Ummar kuka takeyi sosai, seda suka bama mutanen falon tausayi.

Mahaifin Zakiyyah ya kalli Sarki Hasheem da Fulani, yace iname neman gafara agurinku, tabbas Zakiyya ta aikata kuskure dan Allah kuyi hakuri, muzamu koma seku aiwatar da duk hukuncin da kuka yanke ma kowa, kada tausayi ko wani kusanci ya hanaku cika umarnin Allah da Manzonsa.

Tashi yayi yana goge kwallar data zubo mashi, yanufi kofa yana fadin Zakiyyah nayafe maki duniya da lahira, Allah yasa wannan abu daya faru yazama kaffara agareki, idan munkara haduwa zanyi farin ciki da haka idan kuma ta Allah takasance se ince Allah yasadamu da alkhairi, haryanzu kinada lokacin tuba, kada kiga anyanke maki hukunci ki kasa cigaba da neman gafara agurin Allah.


Yana kai nan kuka yaci karfinshi yayi waje, fadawanshi dake bakin kofa suka mara mashi baya. Tashi Umman Zakiyyah tayi itama zata tafi, Zakiyyah tariketa tana kuka, tace Umma bakice komai ba, dan Allah kimun magana kada in mutu da fushinki. Jawota tayi ta rungumeta tace.

Nayafe maki Zakiyyah Allah ya yafe maki, insha Allah zanrika kawo maki ziyara harkifito, idan kuma na mutu, addu,ar ki nake nema, idan kinrigani mutuwa, addu,a ta zata sameki har kabarinki. Sakinta tayi tanufi waje dasauri tana kuka.

Da gudu Zakiyyah tabita, sede kafin ta isa harsun tada mota sun nufi gate, haka taruga da gudu, tana binsu, suna fita aka kulle kofar, anan tazube tana kuka, duk mutanen gidan suna kallonta.

Acikin mota kuwa Umman Zakiyyah se kuka takeyi, haka Sarki yajawota yana lallashinta. Tace shikenan yanzu kowa seyasan abinda Zakiyya tayi, shikenan yanzu banida sauran kima agurin mutane. Sarki yace namaki alkawarin babu wanda zesan abinda Zakiyyah tayi, sede idan tadawo gida, zamusan abinda zamu fada. Kwanciya tayi tana fadin nagode.

Tunda suka fita Sarki Hasheem yake kuka, yakasa denawa,gaba daya tausayin Zakiyyah da iyayenta yakamashi, kuka yakeyi kamar karamin yaro, gaba daya jijiyoyin kanshi sunfito, ganin haka Waziri yayima Likitansu waya, yazo.

Bayan yagama dubashi yayi mashi wasu allurai kuma aka bashi magani, ko minti 5 bekara ba yayi bacci. Likita yace jininshi ya hau sosai, kuma zuciyarshi tana bugawa dasauri, saboda tashin hankalin daya shiga, zeyi bacci na tsawon awa 8 kafin ya farka, idan yatashi ayi kokarin mantar dashi duk wata damuwa dazata kara dawo mashi. Sallama yayi masu yafita. Anan suka kulle mashi dakin suka fita.

Sarki Qaseem yace Malam muje agama abinda za,ayi kozamu dena kallon fuskokin wadancan munafukan. Waziri ya kalli Areef yace kaja beautyn taka kubar gurin nan banaso taga komai, idan zaka dawo kayi kallo to ita de kabarota acan.

Haisam ya kalli Ayman yace kema wuce mutafi banason kirika mun kuka, murmushi tayi tace aini babbace kuma nafi Beauty sanin matsalolin rayuwa. Dan haka kabarni in kalla, hakan ze karamun imani dajin tsoron aikata kowane irin zunubi. Murmushi yayi dan yaji dadin kalamanta.

Gaba daya mutanen masarautar harma da mutanen waje seda suka cika babban filin da ake wasan dokuna na Masarautar BUBAYERO, dan kowa yanason yaga yanda za,a aiwatar da wannan hukunci.

Hada manyan malaman masarautar suma sun halacci gurin, haka aka fito da masu laifi kowa yasaka kayan yari ajikinshi, gaba daya kunyar mutanen gurin sukeji, gani sukeyi kamar duka mutanen duniya ne, aka tara agurin ganin irin yawan da mutanen suke dashi.

Kowa neman boyewa yakeyi bayan dan uwanshi, Zakiyyah duk tafi kowa jin kunyar jama'an gurin, jitake kamar kasa ta tsage tashige. Duk abinda takeyi Malam yana kallonta, besan lokacin da kwalla tazubo mashi ba.

Bawai tausayinta yasa shi kuka ba, kawai daya kalli yanda take boyewa dan kawai taga yan tsirarrun mutane, wadan da ko rabin garin Gombe basu kai ba, amma shine take jima kunya. To inda ranar lahira ce Allah ya tadata agaban biliyoyin mutane yazataji? Wannan tunanin shine abinda yasaka Malam kuka.

Bayan sun tsaya agurin da aka tanadar masu, kowa yasamu nutsuwa, sannan Malam yahau kan wani guri medan tudu shida Sarki Qaseem da limamin masallacin masarautar, tayanda kowa ze iya ganinsu.

Seda Malam yasa liman yabude masu taron da addu'a sannan yafara magana. Har yanzu hawaye basu dena fitowa daga idonshi ba, musamman daya hau sama yaga mutane sun nutsu gefe guda kuma ga masu laifi suma sun tsaya suna kuka.

Kyalle yasa ya goge idonshi sannan yafara magana. Alhamdulillahi, kamar yanda kowa yasan dalilin taruwar mu agurin nan, kuma naji dadi matuka da Allah yasa naga Mata da Maza, Yara da Tsofaffi, sun halacci gurin nan.

Saboda kowa ze kalli yanda kowa ze amshi hukuncinsa. Nasan yawancin mutanen gurin nan masu hankali, wannan taron kadai ya isa ya tunatar da kowa tashin kiyama, da kuma tsayuwar hisabi.

Da farko inaso indanyi amfani da wannan dama inyima jama'a tunatarwa akan rayuwar duniya data lahira, hakika wannan abu da mutanen gidan nan suka aikata yasa mutane dayawa zasu koyi darasi.
Zanyi magana akan abu 2.

AMANA, da ZINA.
   
Wa iyazubillah. Hakika mutane dayawa sun shagala azamanin nan gurin Cin AMANA. Basajin kunyar ha'intar makusantansu. Dama Manzon Allah (s.a.w), yace idan karshen duniya yazo amana zatayi karanci, bawa ze iya cin amanar Uban gidanshi, kamar yanda Da ze iya cin amanar mahaifanshi.

Ayanzu halin damuke ciki kenan mutane basu dauki cin amana abakin komai ba.

(1) Kamar yanda yazo acikin hadisin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi. Inda Abdullahi bn Abbas (RA) yace. Lallai kyawawan aiyuka suna sanya mutum hasken fuska da na zuciya da yalwar arziki da karfin jiki da soyayya daga bayin Allah.

Kamar yanda sabon Allah yake sa fuska da zuciya duhu da raunin jiki da tawayan arziki da kiyayya daga mutane.
    Rawahul  Muslim.

(2). Allah ta'ala yana cewa. Kuma wadanda sukayi kokari ga nemar yardarmu. Lallai muna shiryar dasu ga hanyoyinmu, kuma lallai tabbas Allah yana tare da masu kyautatawa.
(Suratul Ankabut, Aya ta 69).

(3) Allah ta'ala yana cewa. Babu wata musiba dazata sameku, face sai sakamakon abinda hannuwanku suka aikata.
    (Suratul Al shuura Aya ta 30).

Sadakallahul Azim.

Kai jama,a, ina zamu kai wannan girman zunubi damuke daukar ma kanmu? Hakika Allah baya yafe laifin wani akan wani. Baka tunanin idan kaci amanar wani Allah yadauki ranshi ko ranka batare daka nemi yafiyarshi ba? Jama'a yakamata mutuba zuwa ga Allah, wlh duniyar nan tafiya takeyi.

Kada muyarda wasu subamu amana mu ci masu, ayanzu wanda ka yarda dashi shine wanda yake cutarka. Allah yasa mufi karfin zuciyarmu. Kowa da anyi magana seya ce Shedan. Kada kumanta shifa Shedan seyasamu kofar shiga jikin dan Adam yake iya shiga har yasamu damar yimasa mummunar huduba.

Idan har mukayi riko da gaskiya da Amana, muka koma ga Allah, tabbas ze cecemu daga sharrin shaidan. Idan baku manta ba, duk yanda shedan yakai ga hallakar da bayin Allah baze taba samun nasara agurin wadan da Allah ya tsare ba. Ba kuma tsayawa zakayi harse kasamu tabbacin lallai Allah ya tsareka sannan zaka rika addu,a ba.

Manzon Allah dakanshi yana neman tsari daga sharrin shaidan, wanda kowa yasani yafi karfin shedan, Allah yariga da ya haramta ma shedan kusantar manzonsa. Amma duk da haka Annabi be kwanta ba yace Allah yatsa reshi baze nemi wani tsari daga gareshi ba.

To kai waye dabazaka nemi tsari daga sharrin shaidan ba? Yakamata kowa yadage da yaki da zuciyarshi, ita kadaice hanyar dazata tseratar damu. Allah yasa mudace.

Magana ta biyu akan ZINA. Innalillahi Wa inna ilaihirraji'un. Wannan abu itace abinda yake damun mutane dayawa, babu yara, ba manya, marasa aure, har masu aure. ZINA wata musiba ce acikin al'umma.

Allah ya haramta zina, shiyasa ma yace kada ku kusanceta. ZINA tana tarwatsa duk wani mutunci na dan Adama, tana sa talauci. Shiyasa Allah yakawo hukuncin ZINA acikin alkur'ani me girma.

Dan haka ayau kowa zega irin hukuncin daya kamata ayima duk wanda ya aikata ZINA. Allah yashiryar damu da iyalanmu, baki daya. Kafin afara akwai jawabin da Sarki zeyi maku.

Komawa baya Malam yayi yana share kwallan idonshi, Jama,a da dama agurin seda suka zubar da hawaye akan jawabin da Malam yayi. Sarki Qaseem yafara magana, shima daka kalli idonshi zaka gane kuka yayi.

Alhamdulillahi, kamar yanda Malam yayi mana jawabi, nasan mutane dayawa sun kara sanin me ake ciki arayuwa. Kamar yanda zamu fara aiwatar da wannan hukunci, ina me fada da babbar murya, daga yau, duk wanda aka kara kamawa acikin kasata, dumu dumu da laifin aikata ZINA ,  kowani laifi, tabbas se hukunci yahau kanshi.

Ko wanene, kuma ko wacece, kowane irin matsayi mutum yake dashi, zamu buga tambari wannan doka zata fara ayau. Kuma naji dadi sosai da dokar zata fara daga cikin Masarautar mu, acikinta ma hada masu sarauta aciki. Karewa ma, hada matan Sarki Hasheem guda 2. Tunda har muka iya aiwatar da hukunci akansu.

Babu wanda za,a kara daga ma kafa idan ya aikata zina, watakila hakan yakawo mana sauki acikin kasarmu. Daga karshe ina yima Allah godiya daya nuna mana wannan rana. Sauka yayi idanunshi suna fitar da kwalla.

Anan Waziri yasa aka cire Zakiyya da Jakadiya Karima, dasu Mati da Lado gefe guda, kuma aka fadama mutane irin hukuncin da aka yanke masu. Medaki se Kuka takeyi. Tanufo gurin su Gimbiya Suhailat da Fulani, wadanda suma kukan sukeyi.

Har kasa ta duka sede takasa yin magana saboda kukan datakeyi, hannuwanta biyu kawai tahada alamun neman yafiya tacigaba da kuka. Kamota sukayi suka rungumeta suna kuka.

Seda suka saka kowa kuka agurin, wasu mata sukazo suka kamata, seda tayi addu,a sannan aka sata cikin ramin aka rufe jikinta akabar fuskarta. Tunda su Fulani sukaga haka suka bar gurin suna kuka, mata dayawa seda suka bar gurin, hatta da Sarki Qaseem fada yakoma yana kuka, kasa tsayawa yayi agurin.

Bayan anyi mata addu,a akasa yara suka fara jifarta, ahaka harseda ta mutu😭. Wa iyazubillah. Allah ka tsaremu daga aikata ZINA. Amin.

Zakiyyah agurin tazube asume saboda tsabar kaduwa, Jakadiya kam kuka kawai takeyi. Haka wasu suka dauketa aka shiga da ita ciki.

Boka da Sarkin Fada aka kira. Idanun Sarkin Fada sunyi jajur saboda kuka, haka shima yaje gurin Waziri, da Sauran mutane, yana kuka yana neman yafiyarsu. Bayan anyi masu addu'a aka dorasu saman wani table, aka samasu bakar hula afuskarsu sannan aka ture su daga kan table din. Haka sukayita lilo har suka mutu😭. Sannan aka tasa keyar sauran masu laifi zuwa kurkutu, alokacin Zakiyyah ta farfado itama aka hada da ita.

Gaba daya mutanen dake gurin babu wanda bezubar da hawaye ba, jikin kowa yayi sanyi, tsoro yashiga zukatansu. Haka aka taru akayi masu sallah aka wuce dasu makabarta.


INNALILLAHI WA INNAILAIHIRRAJI'UN😭😭. Allah kasa mufi karfin zuciyarmu. Bazan iya cigaba. Da typing ba se zuwa gobe idan Allah ya kaimu. Abinda nafada da kuskure Allah yayafe mani.
   Nagode da kulawarku, sekunjini anext page insha Allah.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[23/08, 1:48 p.m.] Nabeelert Lady: ..🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
AMAKABARTA AKA HAIFENI
🛤🛤🏕🏕🏕🛤🛤🛤
  (The story of hard kingdom)
              Nah
   Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)
  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)
 [email protected]

        Season 115⚜120
LAST PAGE

      Washe gari Sarki Hasheem yasamu karfin jikinshi, da misalin karfe 10, gaba dayansu suka taru a babban falo, bayan anbude taro da addu,a anan aka fada ma Sarki Hasheem duk abinda yafaru jiya, sosai ya tausaya ma Medaki.

Malam yace to Alhamdulillahi, muna godiya ga Allah daya nuna mana wannan rana, inafatan wannan abu da yafaru agidan nan ze zame ma kowa darasi, abinda yarage mana shine mucigaba da neman tsari daga sharrin masu sharri, kuma kowa yadage da addu,a, kada kuyi la'akari dacewar wani yana maku addu'a.

Idan har zaka iya saka wani yamaka addu'a to kai meyasa bazaka iya rage wani abu daga cikin darenka katashi karoki mahaliccinka ba? Allah da kanshi yake fada akwai wani lokaci acikin dare wanda yake sakkowa daga sama yazo ya karbi addu'ar bayin da sukayi awannan lokacin. Da aka tambayi manzon Allah wane lokacine wannan? Yace daga karfe hudu zuwa asuba.

Duk wanda yatashi awannan lokacin yayi sallah tabbas Allah ze karbi addua'arsa. Ina me maku nasiha da ku daure kurage jindadin duniya kusami lokacin ganawa da ubangijinku acikin dare, ibadar rana kadai bazata isheka ba, saboda duk yanda kaso kebewa da rana kace zakayi ibada ta tsawon minti 30 kadai, dole se wani abu yashigo maka katashi.

Amma idan akace maka da dare ne, kana da lokaci me yawa. Kuduba manzon Allah, shifa yariga dayasan anyi mashi albishir da aljanna, amma duk da haka yakan tashi cikin dare yayi ta ibada. To kai waye dabazakayi koyi dashi ba? Wanda aduk cikinmu babu wanda yakeda tabbacin shiga aljanna. Dan manzon Allah yace akwai wadan da zasu dade suna aikata aikin alkhairi, amma karshen wuta ce makomarsu. Kamar yanda wasu zasu dade suna aikata zunubi amma aljannace mako marsu.

Dan haka aduk lokacin da kukaga wasu suna aikata alfasha, kada kabata lokacinka gurin aibantasu, kai zaka cinye ladar daka tarama kanka, amai makon haka kayi masu wa'azi idan har kaga zasu dauka, idan kuma abin yafi karfinka to kabisu da addu'a.

Manzon Allah yace aduk lokacin da wani bawa ze rokama wani dan uwanshi abu agurin Allah, batare da sanin wancan ba. Mala'iku zasuyi rika yimashi addu'ar duk abinda yarokama wancan shima.

Daga karshe, ina kara maku nasiha dakuji tsoron Allah, kuma kucire son zuciya a zukatanku, Allah ze temakeku aduk inda kuke, kuma kuzauna da kowa da zuciya daya, idan shi bahaka yake zaune daku ba, wata rana Allah zetonashi kowa yaganshi, kamar yanda yayi ma wadan da suka wuce. Ina fatan kowa zerike duk abinda nafada maku.

Gyaran murya Sarki Qaseem yayi yace, hakika munji dadin irin fadakarwar da malam kayi mana, akwai abubuwa da dama daka tunatar damu, wadanda munshagala dasu abaya, hakika mutum yatashi yaroki Allah da kanshi shine abinda yafi, domin idan kadogara da wani, wata rana Allah yana uya daukeshi, shiyasa akace daka bama mutum kudi yasayi abinci. Gara ka bashi gona yayi noma, haka kuma daka bashi kudi gara ka sakashi makaranta.

Wata rana seya temaki kanshi da al'umma. Mungode kwarai da kulawarka agaremu, Allah yabar zumunci, kuma insha Allahu zamu kawo gyara sosai amasarautar nan, ta yanda zamu temaki sauran bayin dasuke cikin masarautar nan, suma susami ilimin addini kada rayuwarsu takare abauta.

Malam yace idan kukayi haka tabbas zaku kawo cigaba a masarautarku, kuma yin hakan zesa wannan masarauta ta daukaka, harma wasu masarautun suyi koyi daku. Ni kuma nayi alkawarin turo manyan yarana suzo suma subada tasu gudunmuwar, kaga ahakane, suma bayi zasu gane cewa suma mutanene, kamar kowa. Ina rokon Allah ya amshi wannan niya taku, kuma yasama abun albarka. Ina ganin ayau zanzo in koma.

Waziri yace mungode sosai Malam, Allah yasaka da alkahairi, kuma ina ganin kafin kawuce, zamu zabeka amatsayin wanda ze daura mana sabon Sarkin Fada.

Malam yayi murmushi yace, to inaganin yakamata abama wanda yakamata abama sarautar tun farko, kafin aci amanarshi. Koba komai, zeji dadin hakan, kuma sauran mutane zasu kara yarda dacewa duk zakaran da Allah yanufa da cara, to ko ana muzuru ana shaho seyayi, yasha wahala ta dalilin sarauta, ya kwashe shekaru dayawa acikin kurkutu. Tabbas babu wanda ya dace da wannan sarauta se shi.

Kallon Sarki Hasheem yayi yace, inaso inji wane suna kasama diyar tawa, kafin inkoma? Murmushi yayi yakara kallon Fulani sannan yace agaskiya tunkafin a haifeta dama nazaba mata suna, badan komai nazaba mata sunan ba, sedan inyi godiya ga Allah abisa kyautar da yayi mani nasamun karuwa.

AMATULLAHI, shine sunan dana zaba mata. Lumshe ido Areef yayi jin yanda sunan ya burgeshi. Malam yace Alhamdulillahi wannan suna yayi dadi, AMINTATTAR ALLAH kenan, to Allah yasa albarka acikin sunanki da rayuwarki gaba daya. Kowa yace amin.

Waziri yace Malam inaganin zaka kara dawowa nan kusa domin kadaura mana aure amasarautar nan, Murmushi yayi yace lallai kam nima naga alama, dan tunkafin inzo nasan da wannan labari, zuwana kuma yakara tabbatar mani da hakan, dan Yarima yafi kowa kaffa kaffa da diyar tawa, yanda kasan ance za'a kwace mashi ita. Dariya suka saka gaba daya. Anan Baban Fulani shima yayima Malam godiya sannan yakara yima Baba na Darazo godiya.

Sarki Qaseem yace ai basu kadai ba, gawasu masoyan nan agefe, dan haka tare za,a yi muhuta gaba daya. Kowa dariya yayi. Malam yace to Allah ya nuna mana, amma banaso asaka danisa, gara tazauna da mijinta, hakan ze sa tasamu kwanciyar hankali. Anan aka rufe taro da addu'a.

         
Kwana 3 aka dauka a masarauatar ana zaman jimami, jikin Sarki Hasheem yayi sauki, sede haryanzu yana cikin damuwa, kuma befara takawa da kanshi ba, dole seda sanda, hakan yasa Sarki Qaseem da Waziri suka nemi shawarar likita, shine yace idan ze yarda afitar dashi waje.

Zasuyi mashi wani gashi, insha Allah ze dawo dede. Bayan sun sameshi da maganar babu musu ya amince, hakan yasa Waziri yace dashi za,a tafi. Sarki Hasheem yace amma da Fulani zamu tafi ko? Murmushi sukayi sukace ai badamuwa.

Lokacin da Sarki Qaseem yasamu Gimbiya Suhailat da maganar cewa tayi suyi hakuri abarta akwai abinda zatayi mata kafin sudawo angma. Yace a,a kinsan Yaya baze yarda ba, kawai kibashi matar shi. Da to kawai ta amsa mashi.

Amma azuciyarta tayi alkawarin bazata bari sutafi tare ba, dan Fulani tana bukatar gyara sosai, shekaru 18 acikin hauka, kuma har haihuwa tayi. Dole ma tayi duk yanda zatayi tahana atafi da ita.

Zaune suke afalo ana tashirin tafiyarsu, dan anjima kadan zasu tafi,Fulani datake zaune agefen Sarki, tayi saurin rike cikinta. Dasauri Gimbiya Suhailat tace lafiya de Fulani?

Nana hankalin kowa yadawo kanta, Sarki Hasheem yace adauketa muje asibiti mana. Gimbiya tace a,a inajin baciwon asibiti bane,birin ciwonmu ne, na mata bari muje cikin gida. Sarki Hasheem yace ina ganin za,a daga tafiyar nan kafin tasamu lafiya.

Waziri yace a'a Memartaba, kada wannan yadameka, tafiyarmu bazata wuce kwana 10 ba, inaganin kayi hakuri tunda har angama komai kuma agobe za,a fara gashin nan, kaga likitan yace akwai inda zeje, saboda kaine yadaga tafiyar.

Kayi hakuri muje domin neman lafiyarka, nasan ayanzu kanajin babu dadi kowa yana hidimarshi amma kana zaune, guri guda, idan zajayi tafi seda sanda. Sarki Qaseem ya matso kusa dashi yace dan Allah Yaya kada kaki yarda ayi tafiyar nan, wlh Allah kadai yasan halin damuke ciki akan rashin lafiyarka. Shiru yayi, hawaye suna zuba daga idonshi.

Hannunshi Sarki Hasheem yakama shima idanunshi sunyi ja, yace karka damu dan uwa na, acigaba da shiri,Allah yasa ayi asa'a. Murmushin jindadi yayi yarungume Yayanshi yace nagode Yaya. Sarki Hasheem yakalli Beauty yace zo Amatullah mu gaisa mana.

Murmushi tayi ta tashi tanufi gurinshi tana zuwa tazauna kusa dashi ta dora kanta saman kafarshi. Hannu yasa yashafi fuskarta tace yauwa Amatullahi, Allah yabaki lafiya kema kirika magana kamar kowa. Areef yace Amma Baffa tayi magana so daya a asibiti.

Waziri yace insha Allahu wata rana zata yi magana, dan likita yace matsalarta ne sauki ce, kuma base an kaita asibiti ba, zata iya yin magana akowane,lokaci, yace idan har taga wani abu daya tsora tata bakinta ze iya budewa. Sarki Hasheem yace insha Allahu zata samu lafiya. Kuma da mun dawo za,ayi maganar bikunku, Yarima seka fadama abokinka dan ahada tare, ko Ayman? Murmushi tayi ta tashi tafita.

Lokaci yana cika suka fito domin tafiya, seda aka kai Sarki Hasheem gurin Fulani sukayi Sallama, sannan suka nufi air pot. Suna zuwa aka fara kiran sunaye, haka suka rungume juna shida Kaninshi, har kua seda sukayi. Yana kallonsu har jirginsu yadaga sannan suka dawo.

Dariya Gimbiya Suhailat da jakadiya Safeeya sukayi, Gimbiya tace ai nadauka Fulani bazakiyi yanda nace maki, ba, dan kina tausayin mijinki. Fulani tayi murmushi tace, duk yanda nake tausayinshi ai gara inzauna indawo da martabata ni kaina wani lokacin kyan kyamin kaina nakeji, kiduba fa kigani duk wata kazanta damuke fitarwa haka zanyita ingama babu wani wanka. Kai gaskiya mutanen nan sun cutar dani.

Jakadiya Safeeya tace wai ahaka ma kinsamu bakar da ba, kuma kinga acikin kwana goma zaki samu gyara sosai, wanda Sarki zeyi farin ciki da haka. Gimbiya tace ai wannan gyaran na musamman zakisha, suma Yarana nasu nadabanne.

Kallon Jakadiya Safeeya tayi tace akwai wani abu danake so inhada, amma anjima idan hubby yadawo zamuyi maganar, kema yakamata, ai ko? Jakadiya tace bangane ba? Murmushi Gimbiya tayi tace a'a bakomai dama gani nayi Waziri tunda matarshi ta mutu be kara aure ba, kuma dama diyarshi daya sunyi mata aure. Shine naga kema mijinki yarasu ai.

Dariya Fulani tayi tace kai amma wlh Aunty kin iya hangen nesa. Tashi Jakadiya tayi tana murmushi, Gimbiya tace, ina kuma zakije? Fita tayi bata cemata komai ba. Gimbiya tace Allah da gaske nakeyi, kuma insha Allahu wannan abu seya tabbata, zansa Hubby yafadama Malam, kinga se ayi tare dana su Amatu. Fulani tace Allah yasa.

Zaune suke acikin lambu, beauty Amatullah tana zaune agefen Areef yana koyamata karatu, su Haisam suma suna gefe guda suna firarsu. Areef ya kalli Haisam yace wai abokina ya kukayi da Dady akan maganar Ayman?.


Murmushi yayi yace yafi kowa mafarin ciki shida Momy dasukaji maganar, yace idan Baffa yadawo zasuzo. Areef yace ai gara azo a aurar damu kowama yahuta ko Beauty na? Kai tadaga mashi tana murmshi. Haisam yace Beauty bahaka zakice ba, a,a zakice.

Hararshi Areef yayi yace todan bukulu ai seka hanata, kuma wlh wannan sunan yafita abakinka, tunda de ansamata suna kawai ka kirata da Amatullahin ta. Haisam yace bazan kiraba, ni nariga dana saba.

Murmushi Areef yayi yace shikenan, nina zanrika kuran Ayman da Angel. Apple din dayake kusa da Haisam yadauka ya jefeshi dashi, dasauri ya cabeshi yana dariya, Haisam yace wlh baka isa ba. Areef yace tokaima kadena fada mata beauty. Haisam yace nayarda, dannaga alama nizakafi kwara.

Dariya suka saka Areef yace dade yafi maka, amma ni inkirata. Beauty kaima haka, ai bazeyuba. Haisam yace towai kai yamaganar fitarku waje bayan aure? Areef yace wlh har yanzu banyi maganar dasu Abba ba, amma yau zanje insamesu. Idan har sukaki zan hadasu da Malam. Haisam yace insha Allah ma zasu amince, duk da nima bazanso kamun nisa ba, amma saboda cigaban Amatu kawai zan hakura, nima inaso inga tadawo kamar kowa.

Gimbiya Suhailat tana kwance ajikin Sarki Qaseem suna fira, tace Hubby, dama wata shawara ce, nace bara infada maka kafinsu Yaya su dawo se afada masu aji mezasu ce. Kara yawota yayi yace fada inajinki. Anan tafada mashi abinda takeso.

Murmushi yayi yace wlh kamar kinshiga zuciyata, na dade ina wannan tunanin, kawai ciwon Yaya ne, yahanani fada amma tabbas idan suka dawo zansamu Waziri da Yaya da maganar. Wannan abu ne me kyau. Kema Allah yabiyaki da kika kawo wannan shawarar.

Sallamar Areef ce ta katsesu, abakin kofa ya tsaya, dan dama al'adarshi ce duk inda yaje baya shiga se anbashi izini kida gidansu ne. Murmushi Sarki yayi yace Allah yayi maka albarka Yarima, hakika ina farin ciki da irin halayenka da kuma tarbiyarka, ace mutum yaje kasar waje yayi karatu amma duk da haka tarbiyarshi bata lalace ba, asalima karuwa tayi. Babu abinda zanma Alkah se godiya, domin nasani shine ya tsare bawansa.

Bayan sun gyara zamansu ya amsa Sallamar yace shigo Yarima, shigowa yayi yazauna kusa da Abbanshi tare da dora kanshi saman kafarshi yace sannunku da hutawa Abba. Shafa kanshi Gimbiya tayi tace yauwa sannu Yarima. Sarki yace zanga ranar dazaka girma Areef, ace haryanzu kana hawa cinya.

Dariya yayi yace ai babu rana Abba, yace akwai mana, nan da wata daya kam ai zaka zama megida. Kafin kaima kasamu naka dan, kaga saka barmashi ko. Gimbiya tace ai anan zasu zauna ko? Abba yace emana, ai bama son muyi nisa da juna, zamansu cikin masarautar nan zefi.

Tashi Areef yayi yana sosa kai yace Abba dama wata alfarma nazo nema, yace fadi duk wata alfarmarka, ni kuma zanyi maka. Anan yafada masu abinda yakeso. Shiru sukayi, yace dan Allah Abba.

Sarki yace bawai naki bane, ina duba yanda Yaya zeji, kasan yanada bukatar ganin Amatu akusa dashi, amma se ace ana daura aure zaku tafi. Areef yace wlh Abba koni dole ce zata sani yin nisa daku, kuma ina me tabbatar maku shekara 3 zamuyi, niba burina beautytayi zurfin karatu ba, kawai inaso tasamu karatu me kyau, dan koda tayi karatun ni bazan barta taje wata University ba, kawai tasamu karatu kodan sbd rayuwarta data yaranta.

Gimbiya tace gaskiya kayi magana me kyau, kuma nima nagoy bayanka son dazamu nuna mata kenan mubarta tasamu ilimi me kyau, kuma tunda saudiya zakuje, nasan zata samu ilimi me kyau, kaga daga kai har ita kunje kusa da gida, kafin kudawo zaku zagaya dangi.

Sarki yace shikenan, idan Yaya yadawo zamuyi maganar dashi. Areef yarungume Abbanshi yayi yana dariya. Gimbiya tace ammafa zaku rika zuwa bawai zama zakuyi harseta gama ba. Sarki yace dama ai baza,ayi haka ba.

Haka suka cigaba da shirye shirye, Amare suna shan gyara, dan masu gyara na musamman daga meduguri aka dauko, Fulani daki guda aka ware mata ita da ne gyaranta, tunda tashiga bata fito ba, akoda yaushe suna cikin gyara, sallah kadai da cin abinci suke tadasu.

Bakaramin kyau takarayi ba, tadawo tamakar wata yarinya, komai nata yadawo kamar da. Beauty kuwa masu gyaran har mamakin kyanta sukeyi, gashi dama tunda aka fara gyaransu su Areef suka dena ganinsu, duk ya gama shuga damuwa.

Ayaune, masarautar BUBAYERO tacika da mutane, anata gyara da shirin tarbar Sarki Hasheem. Kowa kagani cikin masarautar cikin farin ciki yake. Fulani tasha kwalliya kamar meshirin zuwa zaben sarauniyar kyau, tayi kyau harta gaji, haka suka kaita dakinta dayasha gyara har yafi ranar da aka kaita kyau.

Motoci harma da mashina ne, suka je dauko Sarki. Ana bude kofar jirgi mutane suka fara fitowa, sarki Qaseem yazuba id kawai yaga ta yanda yayanshi zefito. Waziri yafara hangowa, daga bayanshi ya hango Yayanshi cikin shiga ta alfarma yayi matukar kyau, kamar bashi bane yayi ciwo abaya ba.

Da kafafuwanshi 2 yarika saukowa daga jirgi, ai Sarki Qaseem kasa hakura yayi ya karaso, cike da murna ya isa gurinshi uka rungume juna. Kowa na gurin seda suka burgeshi. Haka suka nufi gida cike da farin ciki.

Suna zuwa Sarki Qasee yajashi zuwa part dinshi, yace Yaya kashiga kashirya kada kafito seda dare, Fulani tana daki tana jiranka, nasan kagaji dayawa. Murmshi yayi yace shikenan nagode, sena fito. Har falo yakaishi sannan yafito fuskarshi dauke da annashuwa.

Tura kofar dakin Fulani yayi, lumshe ido yayi dan wani da daddan kamshine ya bugar mashi hanci. Da sallama yashiga, ai cak ya tsaya ganin Fulaninshi, da gudu tarugo ta rungumeshi, hannuwanshi 2 yasa ya rungumeta, wani irin farin ciki sukeji dukansu.

Sun dade ahaka kafi tajashi zuwa cikin dakin, riketa yayi yana kallonta, yace anya ba masanye akamun da Fulanita dana sani ba? Murmushi tayi tace kila, jawota yayi, yace gaskiya nagodema Allah dayasa bantafi dake ba, gashinan an maidomun da mata kamar yar shekara 18. Murmushi tayi tacire jikinta daga nashi tana fadin sannu da hanya, muje kayi wanka kaci abinci.

Murmushi yayi yace nikam bazan iya cin abinci ba, tunda naganki, dariya tayi tace a,a muje de. Haka tajashi zuwa bandaki. Bayan yafito ya shirya takawo mashi abinci, da kanta tarika bashi yana jingine jikinta, kamar karamin yaro, yahanata sakat. Da haka tagama bashi abinci, yaje yayi brush yadawo yana fadin taho kimun tausa, bacci zanyi.

Murmushi tayi tanufo gurinshi, yace amma kicire wannan kayan zasu damenim tace amma naga bacci zakayi, ina ruwan kayana da kai, kanne mata ido yayi yace e sonake musami AMINULLAH. Dariya tayi yajawota shima yana dariya.

Koda Sarki Qaseem sukaje fada da dare, Sarki Hasheem befito ba, ganin haka Waziri yace abari se gobe, azauna, akwai gajiya atare dashi, Sarki yace a,a amarci kawai yakesha. Waziri yace kaima ai sekaje kasha naka. Murmushi Sarki yayi yace kaima nan da wani lokaci kaza fara shan naka. Dariya Waziri yayi yace seda safe, Sarki yace to Allah yakaimu.

Areef ze zaune afalon Jakadiya kamar zeyi kuka ya kalleta yace haba Aunty dan Allah sokukeyi inshiga wani hali, kinfi kowa sanin damuwar danake ciki, shikenan ace kullum so daya zanga beauty gaskiya bazan iya ba.

Ina gyaran nan danni akeyishi? To nide abarmun ita haka banaso. Dariya Jakadiya tayi tace yi hakuri bara inturo maka ita karkamun kuka, fita tayi sega beauty tafito. Tsayawa yayi yana kallonta, tana zuwa tazauna kusa dashi tana murmushi, yakamo hannunta yace haba beauty nan shikenan sekirika guduna.

Kema bakison ganina ko? Girgiza mashi kai tayi, yace yauwa kokefa beauty na, hannunta yasaki, yace jeki dauko mani abinci yunwa nakeji, tashi tayi tadauko mashi, akasa tadameshi, nan tazauna tazuba mashi. Atare suka fara cin abinci, yana bata tana bashi, har suka gama sannan suka zauna yana mata fira.

Washe gari se bayan azahar sannan aka taru afada, atare Sarki Hasheem da Fulani suka fito, daka gansu kasan suna cikin farin ciki. Bayan angama gaisawa, aka bude taro da addu'a.

Sarki Qaseem yace Alhamdulillahi, munama Allah godiya daya kawomu wannan rana Yaya yasamu lafiya, komai na masarautar nan yazama dede, ina rokon Allah daya kara tsaremu damu da yaranmu baki daya. Dan haka inaganin zanmika ma Yaya kujerarshi, dama amatsayin rikon kwarya na amsa.

Sarki Hasheem yayi murmushi yace, a,a ai kuma nida mulki har abada, wanda nayi abaya ya isa, kaine zaka cigaba da mulkarmu, kafin Yarima yakawo karfi se abashi, amma wannan maganar ma kabarta.

Waziri yace wannan magana haka take, munriga da munyanke zaka cigaba da zama Sarkin Gombe, har Allah yakaimu lokacin dazaka sauka. Allah yatayaka riko.


Waziri yace magana ta 2 akan maganar bikinsu Yarima ne, munsami labarin mahaifin Haisam zezo gobe da jama'arshi neman auren Ayman, dan haka nan da sati 2 za'ayi bikinsu in Allah yakaimu.

Kallon  Baffan beauty yayi yace akwai wata magana da Yarima yazo mana da ita, jiya Sarki  Qaseem yake fadamun. Anan yafada masu alfarmar da Yarima yake nema. Shiru Baffan beauty yayi bece komai ba. Can yadago kai yace ai hakanma yana da kyau, Se ayi magana acan kasar asama mashi aikinyi kafin itama tagama karatun nata. Allah yasa aje asa'a akuma samu abinda akeso.

Sarki Qaseem yace kuma akwai dayar maganar, aure danakeso inyi, dama akan Waziri ne da Jakadiya Safeeya, ina ganin insha Allah nan da sati 2 tare danasu Yarima za,a daura. Dago kai Waziri yayi yasaki baki yana kallon Sarki Qaseem. Baffan beauty yayi murmushi yace lallai kamar kashiga zuciyata.

Dan Allah Waziri kada kace komai, kawai kayi fatan alkhairi, kasan baza zaba maka abinda zakayi dana sani ba. Sunkuyar da kai Waziri yayi yana murmushi. Sarki Qaseem yace ai ya amince, Allah yakaimu musha biki.

Shirye shirye ya kankama agidan su Yarima, iyayen Haisam sunzo anyi magana, kuma har can misra an fada masu, kuma sunce zasuzo. Baba Fulani ma yakira yan uwanshi yafada masu, wasu daga cikinsu sunce zasuzo. Duk wani shirin tafiyarsu Areef angamashi, anyi masu visa, da takardar shedar zama akasar, kuma an sama ma Areef aiki acan har gudan dazasu zauna ansamu. Dayake abun namasu sarauta ne. Babu wani bidi'a dazasuyi abikin, hakan yasa aka kira me wa'azi yazo yayi masu.

Ayau ne  dubban jama,a suka halarci daurin auren mutane, 3 nagidan sarautar BUBAYERO. Daurin aure ne daya tara mutane dayawa, daga garuruwa daban daban, harma daga kashashe. Bayan daurin aure akayi babbar walima, anci ansha, kowa seda ya yaba da irin auren wannan Masarauta. Gashide auren yaransu, abin sonsu akeyi amma kuma babu wata bidi'a da akayi. Mutane dayawa abin ya burgesu.

Adaren ne kafin azo daukar Ayman, Sarki yatarasu duka domin ayi masu nasiha. Nasiha meratsa zuciya sarki yayi masu, bayan yagama Baffan beauty ma yayi masu. Yace Amatullahi, kiyi hakuri kinga gobe da safe zaku tafi, babu ruwanki da kowa, bakisan kowa ba se mijinki.

Kada kiyarda wasu suzo maki dawani abu, yanda baki magana, karkiyarda kibiyema kowa, kuma kimaida hankali akan karatunki, inhar kinaso kidawo kusa damu, amma idan bakiyi kokari ba, acan zakuyi tazama. Ko kinaso kuzauna acan? Kai ta girgiza yace yauwa, Allah yayi maku albarka. Kema Ayman, kindega abinda yafaru azuwanki gidan nan, damma kinci sa,a gidanki daban ne, amma duk da haka bana son kisaki jiki da mutane, dangin mijinki kirikesu da hannu 2, kowa kizauna dashi da zuciya daya, Allah zetemakeki akan makiyanki. Allah yabaku zaman lfy. Anan Waziri shima yayi masu tashi nasihar, se yan uwan Ayman da dangin Fulani dasukazo, kowa seda yayi masu nasiha.

Se kuka sukeyi, bayan angama masu Sarki Qaseem yace kuje, yanzu za,azo adaukeki. Bayan suntafi, Sarki yace Waziri kaima yanzu zamu kawo maka taka amaryar. Dariya suka saka, gaba daya. Da misalin karfe 9 aka dauki Ayman, wanda Areef shima yadauki beautynshi amota suka tafi rakasu.

Bayan kowa yatafi yarage daga amarya da ango se su Areef. Haisam yace abokina yakamata muje inrakaku. Duka Areef yakai mashi yace wlh kai dan iska ne, wlh se ince ba inda zani, Haisam yace da kyau, ai akwai wani dakin, indarabon asamu dan gidanmu kuma shikenan.

Areef yace a,a ni baruwana kaine dan iska nikam nafison dan saudiya. Haisam ya kalleshi yace wlh abokina banason tafiyar nan taku, shiyasama bazan je rakiya ba, amma zamu zo dan acan zamuyi honey moon dinmu, Areef yace bakomai nasan sanda zamu tafi ma baku tashi daga baccin gajiya ba.

Dariya Haisam yayi yace ammade ai munyi sallah ko, Areef yace tobara mutafi nasan beauty na tagaji gara muje ta huta, mike wa sukayi, Haisam ya rungume shi idanunshi har yakawo ruwa. Shima Areef seda yazubar da kwalla, sun dade ahaka, kafin suka saki juna.

Har bakin mota suka rakasu, Ayman da Beauty se kuka sukeyi,da kyar Areef yacire beauty daga jikin Ayman. Ayman tace Yaya yanzu shikenan gobe zaku tafi? Kallonta yayi zeyi magana kuka yataho mashi, kawai jan beauty yayi suka shiga mota.

Amota yayi ta lallashin beauty, da kyar tayi shiru, haka suka nufi gida shima duk bayajin dadin rabuwarsu da Haisam dan bakaramin sabo sukayi ba. Beda wani aboki se shi, dashi kadai yasaba. Har dakinta na bangaren Jakadiya Safeeya ya kaita sannan yatafi.

Kwallan data zubo mata ta goge, takalli Jakadiya Karima tace yanzu kalli yanda duniya tajuya mani baya, kamar ni da mulki na da matsayina amma kalli yanda kowa yamanta ni acikin gidan nan, biki akayi ayau amma banida damar fita inje gurin. Jakadiya Karima tace, Zakiyya kenan, idan zakiyi hakuri ki aje wata sarauta ki rungumi kaddara kiyi.

Har garama ke, zaki iya kirga kwanakin ki,nifa? Sede afitar da gawata. Saboda haka kinganni nan namaida gurin nan kamar gidana, idan harzaki rika yimani maganar wata sarautarku, ina me tabbatar maki zanbar maki dakin nan, kuma bazaki kara ganina ba, dan kinsan babu wanda zezo yazauna tare dake. Shiru Zakiyya tayi tana jinyanda Jakadiya take fada mata maganganu. Murmushin takaici tayi tace duniya kenan.

Washe gari tunda safe aka fito rakiyarsu Areef, idanunshi sunyi ja sosai, dan tunjiya yakema iyayenshi kuka, Abbanshi har cewa yayi kode afasa tafiyar ne, yace a,a Abba, nasan damun tafi komai ze wuce.

Haka suka shiga mota aka nufi air pot dasu, ko acan da kyar aka ciresu daga jikin iyayensu, suma seda sukayi hawaye, suna kallo har jirginsu yadaga, sannan suka juya zuwa gida. Acikin jirgi kam lallashin beauty Areef yayi tayi, mutane se kallonsu sukeyi, dan sunga suna kama sosai, gashi dama beauty da kyar tashiga jirgin, shiyasa tashige jikin Areef, ko ido takasa budewa. Shiyasa kukan nata yazama 2.

Suna sauka dama mota tana jiransu,daukarsu tayi suka nufi gidansu, gida ne, mekyau, yaji komai, kayansu aka shigo masu dasu. Wanka Areef yace suje suyi, rufe fuska beauty tayi tana murmushi. Cak yadauketa bema tsaya jiran yardarta ba. Haka sukayi wanka suka fito, dakanshi yashiryata aka kawo masu abinci.

    Da dare ma kawo masu abinci akayi, bayan sungama yadauketa suka nufi toilet, wanka sukayi tare da alwala, sallah sukayi sannan yajawota suka nufi gado.

Washe gari da safe dakanshi yashiga kitchen yahada masu break, bayan sungama yajata zuwa daki suka koma bacci, seda azahar suka tashi, wanka sukayi sukaci abinci suka fito falo, takarda da biro yadauko yajawota suka zauna falo, yace beauty yau labari zamuyi fa.
Haka yayita rubuta mata yana bata tana rubuta mashi abinda tasani, idan ta manta ya tuna mata.

Haka suka cigaba da rayuwarsu acikin gidan gwanin ban sha,awa, akullum suna yin waya da yan gida, satinsu guda sannan suka fara fita, aranar yakaita makaranta shi kuma yawuce gurin aiki, seda yayita lallashinta kafin ta hakura, yace dasun tashi zezo yadauketa.

Rayuwar Areef da Amatullah gwanin ban sha,awa, suna matukar son junansu, akullum tare suke fita ya kaita makaranta, shikuma ya wuce aiki, se da yamma suke tashi, dayake makarantar hade take da islamiya, shiyasa sesun kai yamma, kuma Beauty tana gane karatun sosai, babu ruwanta da kowa, karatunta tasa gaba.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, suna da wata 3 dayin aure, ciki yafito ajikin beauty, bayan sunje asibiti akayi test aka gano ciki dan wata 2,  bakaramin murna Areef yayi ba, haka yakira gida ya fada masu, suma sunyi murna sosai. Tunda suka koma gida yake riritata, damma cikin beda laulayi,

Haka yakira Haisam yayi mashi albishir, shima alokacin yake fada mashi Ayman ma tana dauke da ciki itama wata 2, Areef yace amma naji dadi, zamu fara cika ma su Abba gida da jikoki. Haisam yace idan muna da rai muma semu hada zumunci. Areef yace Allah ya kaimu. Amma wai yaushe zaku zo, kasanfa muna son zuwa ziyara gurin yan uwa, gurin dangin su beauty, danasu Momy. Haisam insha Allah zamu shirya muzo. Yace to Allah yakaimu

   Baffan beauty ya kalli Fulani, datake kwance ajikinshi, dawowarsu daga asibiti kenan, fuskarshi dauke da murmushi, yace babu abinda zance maki Fulanita, sede godiya, tabbas ke haske ce acikin rayuwata.

Ashe inada rabon ganin yarana, aduniya. Ina rokon Allah ya saukeki lfy. Murmushi tayi tace amin. Yace ina ganin Gimbiya Suhailat zata rigaki haihuwa ko? Kai tadaga mashi, tace wlh ni kunya nakeji, yace kunyar me kuma?.

Tace haba dan Allah, yanzu kana ganin Amatu ciki gareta, Ayman ma haka, ga Aunty, yanzu kuma ace nima haka, kuma suk kusan tare zamu haihu. Dariya yayi yace kin manta dayar ai, tace wa kuma? Yace matar Waziri mana.

Tashi tayi fuskarta dauke da mamaki, tace da gske Aunty Safeeya tana da ciki? Yace da gske mana, dazu yake fadamun, nace kinga ikon Allah ko? Tace gaskiya kam, wama yayi zaton Aunty zata haihu, yanda ta dade bata taba haihuwa ba.

Yace aishi Allah babu ruwanshi, yana yin abunshi aduk sanda yaso,babu ruwanshi da tsufanka ko yarintarka. Fatanmu Allah yasa mugama da duniya lfy. Tace amin. Amma de ba gida su Yarima zasu dawo ba idan zata haihu ko? Dariya yayi yace wai naga duk kinbi kin damu, ina ruwanki dasu?.

Kinsande muna da inda zamu ajesu ko? Kuma zamu sami masu kula dasu, dan haka ki kwantar da hankalinki. Shiru tayi bata ce komai ba. Jawota yayi yace dazu Yarima yake fadamun zasu je ziyarar yan uwa. Murmushi tayi tace kagani ko,

Nibanje ba, ga jikarsu nan har zataje, yace karki damu kema zakije, Allah yasaukeki lafiya. Tace Amin.

Zaman Haisam da Ayman, zama ne na so da kauna, yana kula da ita sosai, itama haka, kuma tana daraja yan uwanshi. Acikin satin ne, yagama shirya masu visa suka daga zuwa saudiya domin zumunci.


Bakaramin dadi su Areef sukaji ba, da ziyarar dasuka kaimasu, kuma agidansu suka sauka, ko abinci basa tsaywa girkawa, sede sufita suci awaje, dagacan suwuce gurin shakatawa. Dayake Beauty suna hutu.

Sun zagaya gurare dayawa, sannan suka shirya dukansu suka nufi misra, yan uwansu bakaramin dadi sukaji ba. Kwanansu 3 sannan suka wuce garinsu Fulani, suma sun tarbesu sosai, sun sha gata, kwanan su 3 acan ma, sannan suka dawo gida.

Kwana 2 su Haisam suka kara sukace zasu wuce, har kuka sukayi dasuka rakasu, da kyar Areef yacire beauty daga jikin Ayman, haka jirginsu yadaga suka dawo gida yana lallashi.


Bayan wasu watanni Gimbiya Suhailat ta haifi diya mace, ansha hidima sosai, sede su Areef basu jeba, dan beauty tana Exams. Yarinya taci sunan mahaifiyarsu Sarki Qaseem Fatima, ana kiranta da NOOR.

Bayan wata 2 da haihuwarta Fulani ma tahaihu yan biyu, mace da namiji,gaba daya gidan seda kowa yasan anyi haihuwar yan 2, Sarki Qaseem bakaramin dadi yaji ba, ganin Yayanshi yana samun haihuwa yanzu. Alokacin beauty tagama Exams dinta, shima yadauki hutun shekara.

Hakan yasa suka nufo gida, bakaramin farin ciki mutanen gidan sukayi ba, apart dinsu da aka gina masu anan suka sauka, wata dattijuwa aka kawo ma beauty wadda zata rika temaka mata, ana cemata Ladingo.

Ranar suna akasama namijin sunan Mahaifinsu Sarki, macen Kuma sunan Mahaifiyar Fulani. Ana kiransu da AMEER DA AMEERA. Anyi shagali sosai, su beauty da Ayman da Jakadiya Safeeya sunata fama da tsohon ciki.

Bayan suna da sati daya Ayman da Jakadiya Safeeya suka haihu, Ayman ta haifi Namiji itama Jakadiya Namiji. Beauty kuwa kuka tasaka dataji ance Ayman ta haihu. Areef yatambayeta lafiya awayarta ta rubuta mashi ita fa tsoro takeji, dariya yayi uajawota yace ki kwantar  da hankalinki, babu wata wahala kinji ko? Kai tadaga mashi tana murmushi.

Adaren itama ta tashi da nakuda, dama beauty ga tsoro, gaba daya taki sakin jikinta se kuka takeyi, tun Ladingo tana kokari harta gaji, Areef kuwa kamar shine yake nakudar, kallonshi Ladingo tayi tace agaskiya Yarima ina ganin sede fa akaita asibiti, idan bahaka ba, za, iya rasa abinda ke cikinta.

Cikin rudewa yace to kihada kayan bara infada ma su Momy. Cikin lokaci kankani aka nufi asibiti da ita, hankalin kowa yatashi ganin yanda beauty tafita hayyacinta. Suna zuwa aka nufi labour room da ita. Kowa yakasa zama, Areef kuwa kuka yasaka, Haisam ne yajashi suka fita waje yana lallashinshi.

Areef yace kasan Allah daga wannan haihuwar beauty tagama haihuwa. Dariya maganar tabama Haisam sede ya dake ganin halin da akeciki. Haisam yace addu,a zaka rika yimata, yace haba Haisam kalli fa yanda take shan wahala, baiwar Allah wlh da ana karbar haihuwa dana karbar mata. Amma anyi na farko anyi na karshe, banason yaran dayan dazata haifa ya isa.


Haisam yace duk wannan ma bata taso ba, kaide muyi Addu,a Allah yasauketa lfy. Areef yace amin. Amma......... sunanshi yaji ankira cikin wata irin murya da Yaya Areef,, cak ya tsaya da magana dazeyi, yajuya yana kallon inda yaji muryar tafito. Ai dasauri yanufi cikin asibitin Haisam yabi bayanshi.

Suna zuwa kusa da labour room din suka jiyo kukan jariri, da gudu Areef yanufi dakin, cikin sauri Haisam ya rikeshi, yana fadin maza basu shiga, kajira afito da ita. Areef yana hawaye yace kasakeni, wlh duk da bansan muryar beauty ba amma nasan ita ce ta kirani, kasakeni inje inga beauty na.

Da kyar su Waziri suka hanashi shiga, Momynshi ta matso tace haba Yarima kayi hakuri mana, kallifa yanda ake kallonmu. Zonan kazauna kaji, yanzu za,a fito da ita. Wani likita ne yafito fuskarshi dauke da murmushi yanufo gurin. Sarki Qaseem ya tarbeshi yace yaya jikin Amatullah?.

Likita yace Alhamdulillah tasauka lafiya, tasamu baby girl, kuma duk suna cikin koshin lafiya. Sarki yace Alhamdulillah. Likita yace yanzu za,a kaisu dakin hutu, idan kungama kusameni office, akwai wani albishir din. Godiya sukayi mashi, yawuce. Areef yariga kowa shiga dakin da suke, kotakan jaririyar be biba, gurin beautynshi yanufa.

Hannunta yakama yarike sosai yana sannu beautu na, nine ko? Murmushi tayi mashi, yace sannu bazan karaba kinji? Kamar daga sama yaji tace Yayana ga babynmu. Surin dago kai yayi yana kallonta. Itama shi take kallo, cikin farin ciki yanunta yama kasa magana, kai tadaga mashi.

Ai yama manta da mutanen dakin kawai ya rungumeta da karfi, harseda tayi dan kara. Momy tace lfiyarka Yarima? Saurin sakinta yayi yajuyo yana sosa kai yace wlh Momy beauty tayi magana.

Suma mamaki ne yakamsu, suka nufi gurinta. Murmushi tayi tace Momy. Cike da farin ciki Momy ta matsa kusa da ita tace da gaske ne, ashe? Ikon Allah, lallai Fulani zatayi farin ciki. Allah mungode maka. Sarki yace Sannu Amatullah, cike da kunya tace yauwa Abbah, yace bari muje gurin likita mudawo.

Zaune suke a office din likita, bayan yagama rubutunshi yacire glass dinshi yace albishir din dana ce maku kilama idanunku sungane maku? Sarki yace tabbas yau munga abin farin ciki, sede muyi ma Allah godiya. Likita yace haka ne, dama nafada maku, akowane lokaci maganarta zata iya budewa, sbd akwai irinsu, kasan akwai wani zakaga kurma ne, bayaji baya magana amma sakamakon wani tashin hankali bakinsu yana budewa.

To itama Allah yasota gashi ta dalilin haihuwa bakinta yabude. Kuma jikinta babu wata matsala, zuwa anjima idan tahuta zaku iya tafiya, ga magungunan dazatayi amfani dasu anan. Allah yabada lafiya. Godiya sukayi mashi suka fita.

Segurin karfe 11 na dare suka koma gida, gaba daya murna tacika gidan, Ayman jitake kamar itama tadawo gida, dan Haisam yace tazauna tunda hidima tayi masu yawa, agidan. Kowa cewa yake yarinyar tana kamada Areef, shiko bakinshi yaki rufuwa, yamaki fita daga dakin, seda Momy tayi mashi da gaske sannan yafita.


Haka akayita shirin suna, Momy tace ma, Haisam yamaido Ayman gidan ayi suna gaba daya,daga baya sesu koma. Aranar suna bakaramin taro akayi ba, diyar Beauty aka samata Khairat, dan Areef da kanshi yace babu sunan wanda zesa, shi khairat yajeso.

Yaron Ayman shima Haisam be tsaya saka sunan kowa ba,yasa mashi Fahat. Waziri kuwa sunan Baffan beauty yasaka ma yaronshi wato Hasheem, ana kiranshi da Karami. Bakaramin dadi Baffan beauty yaji ba da irin karar da waziri yamashi ba. Sarki Qaseem shine yasayi komai na jariri harda ragunan suna.

Gaba daya masu laifin gidan aka fiddo haka aka raba masu aiki, kowa danashi, Zakiyya abangaren masu abinci aka kaita, tanayi tana kuka, ahaka suka gama, aka sallamesu kowa aka bata nata.

Bayan kwana biyu mahaifiyar Zakiyyah ta kawo mata ziyara, sunsha kuka sosai, ayanayin data ganta, kallonta tayi tace Zakiyyah kinga irin abinda nake fada maki ko? Yanzu ina sarautarki da mulkinki gashi nan kinkare a gidan kurkutu, acikin talakawa marasa galihu. Cikin kuka tace wlh Umma nayi dana sanin shiga wannan bakar rayuwar dana shiga, kuma insha Allahu na dauki darasi. Umman tace bakomai ai kin kusa fita kema kidawo gida. Allah yayi maki sauyi da miji nagari. Ta dade kafin ta tafi, takawo mata abubuwa dayawa. Zakiyyah se kuka takeyi.

Seda suka sami wata 2 kafin sukayi shirin tafiya, visa Sarki yasa akayima Ladingo yace sutafi da ita seta rika temaka mata. Haka beauty tacigaba dazuwa makaranta tare suke tafiya da Ladingo, idan zasu shiga aji seta barmata Khairat. Yanzu karatun yana mata sauki sosai, dan har larabci tanaji tana maidawa.

After 2 years. Beauty ce tafito hannunta rike da takardu tana ta farin ciki tanufo gurin Areef da khairat dasuke tsaye jikin mota suna jiranta. Khairat tayi wayo sosai, sede haryanzu ba,ayi mata kanwa ko kani ba. Tana zuwa tafada jikinshi tana murna. Kara rungumeta yayi yace congratulation my beauty na. Allah yanufa yau kingama karatunki.

Khairat tace Dady nima kadaukeni, dariya suka saka yace yi hakuri yau ranar Mimie ce, janta yayi suka shiga mota suka nufi gida. Party sosai suka shirya aranar, dan beauty hada qur'ani tasauke, gashi aharkar boko yanzu sede takoyama wani.

Bayan kwana 2 suka fara shirye shiryen komawa gida dama tuni yagama hada komai na aje aikinshi. Bayan suje sunyi tsaraba washe gari suka dira a nigeria. Kowa yayi farin ciki da dawowarsu. Haisam kamar ze zuba ruwa akasa dan farin ciki. Beauty ta kalli Ayman wadda cikinta har yafito kadan tana dariya tace Aunty yanaga haka?

Hararta tayi tace kema zakiyi ne ai, haka suka nufi gida. Babbar tarba, kowa yana cikin farin ciki.

Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya acikin masarautar, Areef yakoma aikinshi, suna zuwa cikin wanciyar hakali shida Haisam.

Iyalen Baban darazo sunajin dadin zaman gidan sarautar, babu abinda basa samu ta ko ina.

Ayanzu cikin masarautar karatu akeyi sosai, dan Malam ya aiko da malaman dasuke koya masu karatu, gaba daya bayin dasuke gidan, harma da masu laifi, ana fidda masu ranar karatu. Sosai suke jin dadin abinda ake masu, gaba daya canji yasamu agarin Gombe, duk wanda ya aikata wani laifi, ana yanke mashi hukunci dede dashi.

Bayn shekara 2 beauty takara haihuwar da namiji, ana kiranshi da Faisal, Ayman ma yaranta biyu, mace da namiji, macen sunanta Labiba.

Ayau ne Zakiyya tafito daga kurkutu, rungume suke da juna ita da Jakadiya Karima, kuka kawai sukeyi. Zakiyyah tace Allah yada fuskokinmu, da ace ba,a gidan nan kike ba, dazanyi maki alkawarin kawo maki ziyara.

Amma yanda zanbar gidan nan bana fatan inkara dawowa. Kiyafemun abinda namaki nima nayafe maki. Jakadiya tace nayafe maki. Allah yabaki miji nagari kema kiyi aurenki. Da kyar suka rabu sunata kuka. Sallama tayima sauran mutanen gurin tafito.

Mahaifyarta ce, tazo daukarta, haka suka nufi fada kallo daya zakama Zakiyya kasan tafita hayyacinta, gaba daya tayi baki ta rame. Azaune suka iske iyalan masarautar, kowa fuskarshi cike da annuri.

Kallonta sukeyi cike da tausayi. Zama tayi bayan sungama gaisawa, ta kalli Baffan beauty, suna hada ido ykara daure fuska ya dauke idonshi daga kanta. Wasu hawayene suka zubo mata, ahankali tace

Nasan banida bakin dazan rokeka gafara, amma duk da haka bazan yi kasa aguiwa ba, dan girman Allah kaya femun abubuwan dana yimak. Hakika naga rayuwa, kuma hakan kadan ya isheni darasi. Banaso in mutu da hakkinka kayafemun.

Kuka ne yaci karfinta. Shiru yayi kamar bazeyi magana ba, can yace bakomai nidama nadade da yafe maki. Allah ya shiryeki. Matsawa tayi kusa da Fulani, takamo hannunta, tana kuka tace Fulani dan .... saurin rufe mata baki tayi tana girgiza kai, hawaye suna fita daga idonta tace nayafe maki. Allah ya yafe mana baki daya.

Haka tayita rokon mutanen falon tana kuka, har seda tasa wasu kuka. Tashi sukayi auka masu sallama, har bakin mota aka rakasu, amma banda Sarki Qaseem, Waziri da Baffan beauty. Seda suka tafi sannan suka dawo.


Bayan kwana biyu da komawar Zakiyyah gida tadan murmure, mahaifinta yakira Ummanta da ita suna zuwa, ya kalleta yace, zakiyya ina tayaki murnar fitowa daga gidan yari. Basena kara tunatar dake rayuwa ba. Nasan azaman da kikayi kin kin koyi darussa da dama. To Alhamdulillahi dama arayuwa ana son idan mutum yayi kuskure yayi kokarin gyarawa.

Shiyasa Allah da kanshi ya saukar da hukuncin daza,ayi ma masu laifi, domin yazama darasi agaresu. Mutane dayawa ta dalilin wannan hukuncin suke shiryuwa. Naji dadi sosai danaga kin koyi darasi.

Abunda yasa nakiraki dama kinsan nace dakin fito zan aurar dake,somin zamanki agidan nan babu abinda ze amfana maki, se tarin bakin ciki. Dan haka nazaba maki miji, amma idan beyi maki ba, kinada ikon canza wani ba dole zanyi maki ba.

Goge hawayen idonta tayi tace, babu wani zabi dazakamun inki binshi, nayarda da duk wanda kazabamun. Murmushi yayi yace naji dadi, kuma bakowa bane se Wazirina. Shikadai ne, nasan zerikemun ke da amana kobayan rai na. Sede kinsan matanshi 3, sekiyi hakuri da abokanan zamanki. Wannan asabar din za.a daura auren akaiki dakinki. Allah yayi maki albarka.

Tashi tayi tana hawaye tanufi dakinta. Zama tayi tabuga tagumi, tana fadin kaicona dana kasa yin hakuri agidana, Allah yamun ni,ima amma na butulce mashi. Yanzu gashinan zan shiga cikin matan da suka haifeni inyi kishi dasu. Allah kabani ikon cin wannan jarabawa daka jarabceni da ita.


Kwance take ajikinshi sunata fira, Areef yace beauty na, yakamata fa ace akamar yanzu kinada yaran 3. Murmushi tayi tace a,a 2 ma sun isa, kaidama kace daga daya bazan kara ba. Dariya yayi yace nima bansan yanda akai kika karaba my beauty.

Kallonshi tayi tace habibina yakamata ka canzamun suna haka nan, kanaji rannan Khairat tacemun beauty ko, dana tambayeta ce tace wai Auntynsu ce itama take cemata beauty, data tambayeta meyasa tace mata haka setace ai tana da kyau ne, shine yan ajinsu suke cemata beauty, ahine Fahad yaketa kuka wai meyasa zasu rika cemata haka shine zerika fada mata haka ai.

Se nace mata tomiyasa tacemun beauty? Kasan metace? Wai nima inada kyau shiyasa kake cemun haka. Dariya yayi yace ai bata fadi karya ba. Kuma nibazan iya dena cemaki beauty ba, domin sunan yadace dake, alokacin dabansan sunanki ba, kawai naga beauty ne kadai yadace dake. Kuma Fahad da gaskiyarshi, nima bakiga lokacin da Haisam yana cemaki beauty ba nahanashi.

Ai sunan dakake kiran masoyinka dashi, kai kadai yakamata ka fadeshi. Murmushi tayi tace Allah yanuna mana muga girman su fahad, Areef yace aini tunyanzu nabama Fahad Khairat.

Dariya tayi tace duniya komai mewucewa. Allah ne yayi zanrayu, gashi yanzu wai harnice da yara 2. Kamar banice aka haifa AMAKABARTA BA. Daure fuska Areef yayi yace banaso inkarajin wannan maganar abakinki, kinaso au Khairat su san wannan labarin ne? Duk wani da nagari bazeso yaji wannan bakin labarin ba, kuma ace da mahaifiyarshi yafaru. Daga yau na kashe wannan labarin na AMAKABARTA AKA HAIFEKI.

Murmushi tayi takama kunnanta tace afuwan Habibina, insha Allahu daga yau bazan kara cewa AMAKABARTA AKA HAIFENI ba. Jawota yayi ya rungumeta yana fadin yauwa BEAUTY NAH!!!!!!


ALHAMDULILLAH!!!

Ina godiya ga Allah (s.w.a)  daya kawoni karshen wannan littafi nawa na AMAKABARTA AKA HAIFENI.

Abinda nafada da kuskure Allah ya yafemani, kuma banyi wannan labari ba, dan cin zarafin masu aikata irin wannan laifi. Nayishine domin yazama darasi ga mutane.


Ina mika sakon jinjina da godiya ga duk kanin masoyana, Allah yabar zumunci da kauna, nagode da irin kaunarku agareni.

Se kunjini alittafina nagaba me suna . DARAJAR MUHALLI.

SADAUKARWA GA FAMILIES OF LATE RABI'U IDRIS ZANGO

UR'S.

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *