Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, August 25, 2018

A WANI GIDA COMPLETE - DANDALIN HAUSA NOVELS

adsense here
A WANI GIDA COMPLETE - DANDALIN HAUSA NOVELS
COMPILED BY
ESHAAT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS
DOCUMNTS
WASAPP 08066360176 FOR MORE







 🏡🏡 A WANI GIDA🏡🏡
          😭😭😭

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 [email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey

Bismilahir Rahmanirrahim

Ina farawa da sunan Allah me rahma me jin kai. Yanda zan fara littafin nan lafiya Allah yasa na gamashi lafiya.

       GODIYA!!!

Sakon gaisuwa ga dukkanin masoyana, ina mika jinjina agareku da godiya ta musamman, Allah yabar kauna

     SADAUKARWA!!!!

Na sadaukar da wannan littafi nawa ga dukkanin iyaye MATA da MAZA, dafatan zukatanku zasuyi koyi da abu me amfani na cikin littafin, kuma zasuyi watsi da marar amfanin ciki.

Banyi wannan littafi dan inci zarafi wani ko wata ba, nayishi ne domin maslahar kowa da kowa, ina fatan zaku fahimci manufata. Nagode.

        Part 1 ⏩ 5

Gidan Alhaji Bature gida me dauke da mata biyu, kuma babban gida ne wanda ya ginashi domin iyali biyu, kowacce da nata bangaren, nashi kuma yana tsakiya, haka akowane bangare akwai kofar dazata sadaka da falonshi, kuma kowace mata da kuna biyu ne a bangarenta.

matarshi ta farko sunanta Hauwa'u, tana da yara 3,  biyu maza daya mace, kuma yaran gidan suna kiranta da mama. Matarshi ta 2 sunanta Jamila, tana da yara 2, daya namiji daya mace, yaran gidan suna kiranta da Inne, shikuma megidan suna kiranshi da Malan.

Alhaji Bature principal ne a makarantar maza datake garin Mani jihar Katsina. Allah yayi shi da son ilimin boko shiyasa sam baya wasa da duk yaron da yakasance baya maida hankali a karatunshi.

Daya daga cikin matarshi 'yar garin Mani ce wato uwar gidanshi mama, ta biyun kuma 'Yar Mashi ce. Malan  yana matukar son yaranshi masu kokari, kuma akayi sa'a yaran Uwar gidanshi suna gane karatu sosai.

mama mace ce meson aso nata, kuma tana da nuna banbanci atsakanin yaranta, kasancewar Malan yana matukar son yaranta yasa takara jin ita din wata ce. Danta na farko shine Farouk, na biyu kuma Fahad, se macen kuma Farida.

Yaran Inne kuma na farkon sunanshi Faisal, se macen Fatima. Ra'ayin Malan ne san yama yaranshi suna me farin harafin (F), kuma ya hana a boyema kowa sunanshi, shiyasa ma besa sunan iyayenshi kona matanshi ba, kawai yazabi sunayen ne bisa ra'ayinshi.

Farouk yana Primary 6 a wata Private School dake Mani, shi kuma Fahad yana a primary 4, se Farida tana Primary 2. Kasancewar yaran Inne basu da kokari sosai, hakan yasa Malan ya ciresu daga makarantar kudi ya maidasu ta gwamnati, domin Faisal tsaran Fahad ne amma so biyu ana mashi repeating, hakan yasa haryanzu yake primary 3. Itama Fatima sa'ar Farida ce, amma yanzu a primary 1 take, saboda itama so biyu ana mata repeating, ko nursery da kyar ta wuce.

Haka ma a islamiya sam basa maida hankali, shiyasa sauran suka wuce su. Wannan rashin kokari nasu bakaramin batama Malan rai yake ba, domin shide yana da kokari sosai, shiyasa yake ganin laifin Inne ne da yaranta suka kasance marasa kokari.

Domin yana ganin ita Mama da suka dade tare da ita tasan yanda yake tafiyar da al'amuranshi, wannan dalilin ne yasa yake fifita yaran Mama kan na Inne. Kuma ganin yana asarar kudinshi yasa ya ciresu daga makarantar kudi yasasu ta gwamnati.

Duk da mutanan gari suna yawan yin tsegumi akan abinda yayi, sede sanin halinshi yasa babu wanda yataba tun kararshi da maganar. Malan da iyalanshi suna zaune a Quarters ta garin Mani, Mahaifinshi yarasu, se Mamarshi wadda yara suke kira da Kakaji ita kuma tana zaune a unguwar Kangiwa.

Itama tana matukar son yaran Mama, kuma haka take nuna banbanci atsakanin yaran Inne. Sede duk wannan abun da sukeyi Inne bata taba magana ba, kasancewarta mata me matukar hakuri, inda sabo tasaba, tun kafin ta haihu take ganin banbanci atsakaninta da Mama.

Domin Mama tafi Inne kyau sosai, kuma ta iya kwalliya da kissa, ta iya jan hankalin mijinta, wannan shine yakara mata kima da daraja awajen Malan, kuma haka ta koyama yaranta duk wani salo na kissa, yanda zasu saka soyayyarsu awajen mahaifinsu.

WANNAN SHINE TAKAI TACCEN TARIHIN MALAN BATURE DA IYALANSHI.


Zaune Mama take tana yima Farida kitso domin gobe monday akwai makaranta, Farouk kuma yana wanke ma kannanshi safar na makaranta domin tun ranar juma'a da yamma Mama take sasu su wanke kayansu su goge.

 yayin da Fahad yake share masu bangaren su. Bayan yagama Mama ta duba agogo ganin Malan yakusa shigowa tace ma Fahad yi sauri yaje ya share kofar falon Malan.

Daukar tsintsiyar yayi ya nufi kofar falon Malan yafara sharewa, duk da Faisal ya share tun dazu da yayi sharar kofarsu, amma saboda kissa ta Mama tasa Fahad yatafi ya share saboda taga lokacin dawowar Malan yayi.

Da sallama Malan yashigo,da sauri Farouk ya ajiye abinda yake yanufi awajenshi, shima Fahad aje tsintsiyar yayi ya nufi wajenshi, suna zuwa kowa ya karbi kayan daya shigo dasu suna fadin Malan sannu da zuwa ya aiki? Murmushi yayi tare da dafa kansu yana fadin yauwa yarana, aiki Alhamdulillah, Allah de yayi maku albarka.

Sakin kan Farida Mama tayi suka tashi tare suna fadin Malan sannu da zuwa ya aikin? Yace lafiya lau Mamar yara, kema sannu da kula da gida, tace yauwa Malan ai kaine da sannu kaida kafita tun safe domin kanemo mana abinda zamuci.

Murmushi yayi tare da zama, mazan suka fara matsa mashi kafarshi, wannan al'adar da Mama ta koyamasu ne. Ruwa ta miko mashi duk da ba ita bace da girki, domin shi atsarinshi idan yadawo duk wadda yafara haduwa da ita yakan zauna sudan gaisa kafin ya nufi dakin me girki. Shiyasa Mama ta maida harabar gate din wajen zamansu inde akace maka yamma tayi, kuma alokacin ne kawai take zama.

Kuma yana karbar ruwa daga wajen duk wadda yasamu a aharabar gidan. Kallon Fahad yayi yace sarkin shara, kaide baka gajiya, Allah yabaka kaima wadan da zasuyi maka fiye da abinda kamun, Fahad yace amin Malan, muma Allah yakara mana karfin da zamu temakeka.

Sosai yake jin dadi aduk lokacin da yaran sukayi mashi irin wannan addu'ar, sabanin yaran Inne, ita bayan sannu da zuwa bata koyama yaranta yanda zasu shiga jikin mahaifinsu ba, asalima basu saba zama dashi ba, kowani abu suke bukata cikin dari dari suke tambaya.

Shikuma aganinshi itace takeson koya masu tsanarshi, kuma take janyesu daga jikin 'Yan uwansu. Ita ko Mama a duk lokacin da Malan yake tare da yaranta tana kokarin sasu su kira su Faisal amma se Malan yahana, yakance ta kyalesu tunda haka Uwarsu ta koya masu.

Bayan sun gama gaisawa yatashi yanufi bangaren Inne, zuciyarshi tana me cike dajin haushi. Yana shiga ya sameta zaune daga ita se daurin gaba tana tsefe ma Fatima kai. Kallonshi tayi tana murmushi tace sannu da zuwa Malan.

Kallonta yayi cike da haushi yace duk yinin yau wai mutum yazauna dagashi se daurin gaba, kuma gobe monday amma se yanzu kike ma diyarki tsifa gashi yamma tayi. Ya tsina fuska yayi yace yauwa sannunki da zama ba kaya.

Faisal ne yafito daga falo, kusa dashi yaje yace sannu da zuwa Malan, murmushi yayi yace yauwa sannu sarkin yawo, ai nadauka yau ma baka gida? Tashi Faisal yayi yashige daki.

Fatima tace sannu dazuwa Malan, yace yauwa sarkin kazanta, yanzu ke se yanzu ake tsefe maki kanki saboda shiriritarki, ga Farida can ita kitso ma ake mata amma ke seyanzu ake tsefewa. Wai summa wanke kayansu? Inne tace yanzu nakeso idan nayi sallar magriba in wanke masu.

Tsaki yaja yana fadin yanzu duk kwana biyun nan be isa ace kin wanke masu kayansu kin goge ba se yau ne zakice wai zaki wanke? Idan kuma basu kawo wuta ba fa dame zaki goge masu? Ko dayake kinsaba samasu haka sutafi makaranta Kamar wadan da zasu tafi ALMAJIRANCI.

Dayake Farouk me tsafta ne, tuni ya wanke masu ya goge masu, yanzu haka wankin safuna yake masu, shi kuma Fahad yana share mani kofar falo na, amma ke kin hana Faisal yaje yasamu lada. Inne tace wallahi tun dazu nasashi yashare.

Malan yace kika sashi yatafi yawo de, ai kullum haka kike fada, kuma idan nadawo se in samu wani yana sharewa, wallahi Inne kinji tsoron Allah, duk abinda kika koyama yaranki dashi zasu tashi, kuma wata rana ke abun ze dama bani ba, domin ni Allah yabani wasu.

Da'ace su kadai gareni shine zanshiga damuwa. Mutum yadawo daga aiki amma bakisan ki kawo mashi ruwan sha ba, kima iya tashi kimatso kusa dani ya gagara, ko dayake ba laifinki bane, kema kinajin kunyar daurin gaban da kikayi.

Haba Inne, sekace ba mace ba, kullum se nayi maki korafi akan wannan daurin gaban, to bari kiji, wallahi daga yau idan nakara shigowa na sameki a haka wallahi ranki seya baci. Bantaba nuna maki fushina akan wannan daurin gaban ba shiyasa kika kasa denawa.

To kowane lokaci idan naga dama zandawo, kuma idan na sameki ahaka nida kene. Shigewa falonshi yayi ta kofar da take bangarenta domin yayi alwala yatafi masallaci.

Yana fitowa yasamu su Farouk suna jiranshi abakin kofa, murmushi yayi yakama hannunsu suka nufi masallaci, sam be kula da Faisal da yake cikin masallacin ba, domin shi ya saba yana ganin lokacin sallah yayi yake tafiya masallaci, kuma ana sallamewa yake dawowarshi gida.

Amma kullum Malan cikin fada yake mashi wai bayason zuwa masallaci, kasancewar Faisal bame son magana bane yasa baya iya musama Malan duk abinda yace sede yabashi hakuri ya wuce. Su Fahad kuwa basa taba tafiya masallaci se idan Malan yana gida, kuma kullum se sun jirashi koda antada sallah, kuma betaba cewa surika tafiya ba idan sunga an tada, saboda yanajin dadi yaga yajero da yaranshi sun nufi masallaci.

Tagumi Inne tayi hawaye suna fita daga idonta, tabbas tana cikin tsaka me wuya, taya zata gyara wannan matsalar da take fuskanta? Tasan sarai batason saka kaya, amma meyasa yake ganin laifinta? Yanzu ba lokacin soyayya bane ita da ta aje yara har 2.

Lokacin kula da yaranta ne, meyasa Malan baze gane hakan ba? Shiyafiso kullum seyaga yaranta sunyi abu agabanshi sannan zeyarda sunayi? Ita kuma bataso tayi gasa da Mama, domin yaranta ne sukeyin haka. Goge idonta tayi tace inde nice daga yau nadena zama da daurin gaba, amma yarana bazasu rika aikin ganin ido ba.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[2:54PM, 3/27/2018] ‪+234 806 677 6651‬: 🏡🏡 A WANI GIDA🏡🏡
          😭😭😭

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 [email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 5 ⏩ 10

Cikin sauri Farouk ya kamo hannun Farida da Fahad ganin Malan yafito zetafi makaranta, ko abinci basu gamaci ba, amma saboda Malan yace Mama tana kokarin shirya yaranta da wuri yasa ta juye masu abincin tace sutafi dashi.

Duk da lokacin tafiyarsu beyi ba haka nan take sawa suna tafiya tare da Malan, wannan abun data keyi bakaramin dadi Malan yakeji ba, shiyasa kullum suke tafiya tare da yaranta. Yaran Inne kuwa se karfe 7:30 suke tafiya makaranta, kasancewar babu nisa shiyasa suke tafiya akafa.

Malan kuwa karfe 7 yake fita. Bayan yaleka wajen Inne domin yayi mata sallama, da sauri Faisal ya fito ya duka yana gaisheshi, kallonshi Malan yayi yace lafiya lau sarkin bacci, yanzu haka ko sallar asuba baka jeba? Faisal yace wallahi naje.

Malan yace bawani nan, kullum haka kake fada amma kuma bana ganinka amasallaci, idan ma kana zuwa meyasa baka jirana muna tafiya tare? Dukar da kanshi kasa yayi bece komai ba. Malan yace to yau zaku fara jarabawa, idan ka sake naga zero a takardarka kasan Allah sena zaneka.

 Kai ko haushi ma bakaji kannanka sunfi ka kokari, ina Fatima? Cikin kuka yace tana bandaki, Malan yace to kafada mata, matukar kuka bari kukaci zero wallahi dukan dazan maku seyafi na baya.

 Yara kamar wadan da shedan yayima fitsari akai, wallahi nide bakuyi hali na ba, sam ba haka nake ba, tashi kaje kashirya. Tashi Faisal yayi yana kuka.

Inne ce tafito tana fadin Faisal tashi kaje ga abincinka can kaci, kallon Malan tayi tace haba Malan, meyasa kakeson gwalashe yaran nan, irin wannan abun da kakeyi fa beda kyau, kuma zaka iya darsa wani abu a zukatansu.

Wani lokacin wallahi Faisal har tausayi yake bani, gashi de haryanzu yaro ne, amma yasan damuwa, soda yawa nasha kamashi yana kuka, amma idan na tambayashe seyace mun babu komai, kuma duk lokacin dazeyi kukan kode daga wajenka yafito ko kuma idan yadawo daga makaranta.

Inafa jin zafin abinda kakema yarana, kawaide inayin shiru ne domin gudun fitina,haka kacire yaran nan daga makarantar su Fahad, yaran unguwa har tsokanarsu sukeyi idan sukaga sunfito da kayan makarantar gwamnati.

Idan har bazaka iya biya masu gaba daya ba, to sauran ma ka maidosu tasu Faisal mana, kuma rashin kokari ai basu suka dorama kansu ba, suma da suke da kokarin ai ba rawa sukayi ma Allah yabasu ba, kuma maganar zuwa masallaci waye yafada maka Faisal baya zuwa, kaide kullum abinda ka gani dashi kake amfani.

Dago kai Malan yayi fuskarshi a daure yace KOTU ne ni, domin kinsan itace take amfani da abinda tagani, ke Inne kishiga hankalinki dani, wai meyasa kika rai nani haka, kodan kina ganin ina kyaleki? To tsaya kiji.

Wallahi daga yau idan kika kara tara ta da irin wannan maganganun banza se ranki yabaci, munafuncin banza, kede a kullum idan baki nuna hassada ga yaran can  ba sam bakijin dadi.

Tun da bakisan darajar kudi ba ai dole zakice na cire yaranki daga makaranta, haka zan zauna in rika asarar kudin makaranta kullum ana maidosu baya, 'yan unguwar sun dade basuyi masu dariya ba, duk shegen da yaji ze iya to ya tareni da maganar.

Duk abubuwan da kike koyama yaran nan babu wanda bansani ba, idan ma kinaso kisa masu kiyayyata azuciyarsu to kinyi karya, domin kowane Da yana alfahari da Ubanshi. Kuma kome zakiyi ina me tabbatar maki wata rana se sun fahimci irin mugun halinki nason rabasu da 'yan uwansu da kuma mahaifinsu.

Kina nan kin tasa yara agaba kina sane da yau zasu fara jarabawa amma hankalinki akwance kin hanasu tafiya da wuri, aiseki tayi wata rana dole zaki saduda, aikin banza. Naira 20 yabata yana fadin gashi nan kibasu tunda yau 12 zasu taso.

Juyawa yayi yafita yana masifa, hawaye ne suka zuboma Inne, Faisal ne yazo yana share mata yace kiyi hakuri Inne, idan na girma bazaki kara kuka ba, kuma bazan temaki Malan ba. Fatima tazo tana goge mata ido tace aide Inne Malan baya son mu ko? Yafison su Yaya Farouk.

Murmushi Inne tayi tace ku ma yana sonku, kawai de yafiso kuma kurika zuwa na daya amakaranta, Faisal yace to ai ni tsoro nakeji shiyasa idan zamuyi jarabawa nake kasa rubutu sosai.

Kinga konayi kokari Malan baya yaba mani, shiyasa idan Malamar mu tabani jarabawata se inji tsoro nasan kona rubuta da kyau Malan baze ce nayi kokari ba. Inne tace kadena jin tsoro kaji, kutashi muje kada ku makara.


Tafe suke a mota shida su Fahad, Farouk ne agaba sauran abaya, Malan yace Farouk yaushe ne zaku je common intrance din taku? Farouk yace se ranar Thursday, amma fa se mun gama exam zamu dena zuwa makaranta, kuma ranar saturday za'a yimana speech and price giving day.

Malan yace da kyau yaron kirki, kaga idan kagama zanyi kokarin sama maka Science school ko? Farouk yace nide Malan nafiso asama mani waccan Police acadame din naji wani abokina yace za'ayi exam din shiga makarantar ranar monday ta sama.

Malan yace to zanyima malamin makarantar magana ai abokina ne, se a yasa maka form din kaje kayi jarabawar, amma duk da haka gara araba kafa, Farouk yace insha Allah ma zanci ta. Malan yace zakaci kam, nasanka bakada wasa ai.

Bayan ya ajesu yabasu naira 30 yace kowa yadauki 10 saboda 12 zasu taso. Haka suka nufi cikin makarantar suna cike da farin ciki, shi kuma ya wuce makarantar da yake aiki.


Zaune Faisal yake ya tasa takardar jarabawarshi agaba, hawaye ne kawai suke zubo mashi, malamin su ne ya matso wajenshi, domin yana yaba hankalinshi, duk cikin yaran ajin shine beda hayaniya, kuma duk ya girmesu dan de kawai Malan yace abarshi a aji 3 amma yawuce class din.

Dafashi malamin yayi yace Faisal ko baka da lafiya ne har yanzu ka kasa rubuta komai? Dago kai yayi yana share ido yace malan ina tsoron kada in rubuta amsa ba dede ba inje banci maki dayawa ba, wallahi Babana duka na zeyi.

Murmushi Malamin yayi yace babu abinda zeyi maka, yana baka tsoro ne saboda kada kaki yin kokari, kasan kowane Uba yanason yaga yaranshi suna zuwa na daya a makaranta. Faisal yace ai mu Babanmu inde mutum beci duka ba baya yabonshi.

Kuma baya bashi kyauta, Malamin yace yanzu de kaga lokaci yana tafiya, ka fara rubutu bazaka fadi ba, jinjina kai Faisal yayi tare da fara rubuta amsar ajikin takardar, zama malamin yayi kusa dashi yana kara karanta mashi tambayar.

A hankali Faisal yafara rubuta amsa dede, yanda malamin yake mashi bayani a hankali yasa yaji dadi, haka yarika rubuta amsa har yagama, lokacin sauran 'yan ajin harsun gama, bayan yabada tashi yafita ya nufi ajin su Fatima.

A bakin kofar ajin ya sameta tana ta kuka, da sauri ya karasa yace Fatima lafiya waya tabaki? Dago kai tayi tace Yaya nasan Malan seya dakeni, ban bada amsa dede ba. Murmushi yayi yace waya fada maki baki bada amsa dede ba? Tace malamar muce mana da tana tambayata har seda ta dokeni, tana cewa wai banda kokari.

Kamo hannunta yayi yace zomuje wajen shugaba,  office din head master suka nufa, suna zuwa suka samu wasu malami a ciki, sallama Faisal yayi suka amsa mashi, head master yace Faisal lafiya? Shigowa sukayi.

Dukawa kasa yayi yace malan dama malamar su Fatima ce ta doketa wai dan bata fadi amsa dede ba, kuma idan muka koma gida Baban mu dukanmu zeyi idan yaga batayi kokari ba. Head master yace wace malama ce? Fatima tace malama Zainab.

Tsaki wani malam yayi yace wai meyasa Malama Zainab take haka, dama wancan satin naga ta bigi wani yaro wai dan ta tambayeshi be bata amsa ba. Head master yace kiyi hakuri kinji, Fatima tace to ai Babana dukana zeyi.

Murmushi sukayi yace baze dokeki ba, kuma kirika dagewa kina bada amsa dede kinji? Daga kai tayi, yace yauwa, to maza kuje kuyi break kada akoma aji. Bayan sun tafi yasa aka kira malama Zainab.

Bayan tazo head master yace haba malama, ya zaki rika dukan yara saboda basu baki amsa dede ba? Baki ganin yara ne, kuma dama jarabawar baki se mutum me hakuri yake iya yinta, saboda su kananun aji dama dole sede ayi masu jarabawar baki.

Kuma idan kina dukansu to zaki rasa yaron daze baki amsa dede, domin duk yaron da zezo yana tunanin idan yabaki amsa ba dede ba zaki iya dukanshi, saka tsoro acikin zuciyar yaro yana hanashi tsayawa ya fahimci abinda kikeso ya fahimta.

Duka bayasa yaro ya koyi abu, haka ma fada bayasa yaro ya fahimci karatu, jawo yaro ajiki shine yakesa yaro yayi kokari. Malamin su Faisal yace wannan haka yake, domin babbar matsalar wadannan yaran shine rashin kulawa.

Tsoron Babansu yariga yashiga zuciyarsu shiyasa sam basa fahimtar abinda ake koya masu, ni unguwar mu daya dasu, wallahi idan kaga yanda yake nuna banbaci tsakaninsu da sauran yaranshi masu kokari abun zebaka mamaki.

Badan komai ba sedan basu da kokari, wannan dalilin ne yasa yamaido su nan yabar sauran waccan makarantar. Head master yace insha Allah zanyi kokarin aikamashi da takardar nema idan yazo zamu tattauna akan matsalar.

Malamin yace lallai bakasan kowaye Malan Bature ba,wallahi gara kaja bakinka kayi shiru domin amsar dazaka samu daga gareshi se ranka yabaci sosai. Head master yace kaide kabari, ai ba'a saurin yankema mutum hukunci, kila yanda sauran mutane suke tararshi da maganar ne yasa baya sauraronsu.

Zaki iya tafiya malama, amma dan Allah ki kula, yaran nan amana Allah yabamu, kuma duk abinda kika koyama yaro har ki mutu baze mantashi ba. Malama tace nagode insha Allah zan gyara.


Salamu alaikum, salamu alaikum, wai ko Inne bata ciki ne? Fitowa Inne tayi tana amsa sallamar tana fadin wallahi ina ciki ina aiki, sannu da zuwa Salamatu kishigo. Bayan sun gaisa Salamatu tace ina yaran nawa ko basu dawo daga makarantar ba? Inne tace e amma yanzu zasu dawo naga 12 ta kusa.

Salamatu tace naga kamar Mamansu Farida bata nan ko? Inne tace inaji da leka makota, Salamatu tace inafatan de yanzu babu wata matsala? Inne tace uhm abinda yazama dole Salamatu ai bansan ranar da za'a dena wannan abun agidan nan ba.

Salamatu tace duk yanda akayi Inne baki dauki shawarar dana baki ba, Inne tace wallahi bazan iya abinda kika ce ba, domin ni arayuwata banason gasa. Salamatu tace haba Inne, yazaki zauna ana ci maki mutunci kamar ba mace ba.

Wallahi kin ganni nan babu macen data isa inzauna tana sani kuka acikin daki. Kamar yanda ta nuna maki ita 'yar duniyace kema kinuna mata kinfita iyawa, Inne mace fa ita take maida kanta baya agidan mijinta.

Mijinku mutum ne meson aiki da abinda yagani, wannan matar tariga da tagama sanin halinshi shiyasa tabiyo mashi ta haka, kamar yanda take sa yaranta suna yin abinda Malan ze gani kema kirika sa naki haka.

Inne tace wallahi bazanyi ba, haba Salamatu, ina amfanin mutum yarika aikin ganin ido, wata rana fa wanda kake koyama haka shine ze cutu, domin tariga da ta saka ma yaranta aiki dan wani yagani, kuma har abada haka zasu tashi.

Ko amusulunci babu kyau mutum yarika aikin da wani ze yagani, wannan abun shi ake kira da RIYA, nariga nasa araina zan cigaba da hakuri da abinda ake mani, insha Allah nasan komai me wuce wane, domin babu wani abu da yake dauwama arayuwa.

Banta ba magana ba akan abinda ake mani se yau, shima rai nane yabaci, kuma insha Allah daga yau bazan kara ba, zan cigaba da bama yarana hakuri, kuma ni bazan bata Ubansu awajensu ba, domin idan ma nayi nice na kwaresu.

Allah ba azzalumin sarki bane, baya bacci wata rana ze nuna ikonshi akansu, kuma idan suna da rabon yin kokari wallahi zasuyi ne. Salamatu tace haka ne, kema kin kawo magana me amfani, kuma nima na dauki shawrarki insha Allah zanyi kokarin koyama yarana irin wannan akidar, duk da banida kishiya amma zan koyi haka daga gareki.

Inne tace Allah yasa, kuma Allah yakara mana hakurin zama da mazajen mu. Salamatu tace amin, bara intashi inje indora girki.

Bayan an taso makaranta da dare Faisal yashiga wajen Malan, dukawa yayi yana fadin sannu da hutawa Malan, takardar ya mika mashi yana fadin head master ne yace in kawo maka. Karba yayi yana fadin yanzu haka bakuyi kokariri a jarabawar  yau ba.


Tashi kaje,  wallahi gobe idan na samu labarin kunyi wani laifi nida kune, yara kamar akanku aka sauke dakikanci, illar ka auri mata marar kokari kenan komin kokarinka se yaranka sunyo gadonta. Allah yakaimu goben.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[2:54PM, 3/27/2018] ‪+234 806 677 6651‬: 🏡🏡 A WANI GIDA🏡🏡
          😭😭😭

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 [email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey
             
           Part. 10⏩15

    Zaune Malan yake a office din Head master, bayan sun gama gaisawa Head master yace dama bawani abu bane yasa na aika maka takardar gayyata, inaso ne kazo mudan tattauna akan matsalar yaranmu.

Malan yace wane yaranmu fa? Murmushi Head master yayi yace ina nufin su Faisal da Fatima. Kasan yanzu yaran se hakuri, zakaga wani yaron duk yanda zaka koyamashi seya dade bedauki abinda kake koya mashi ba.

Kuma agaskiya Malan, Faisal yana da kokari, kawai de akwai wani abu dana fuskanta agareshi, yariga yasaka tsoro sosai azuciyarshi, kuma wannan tsoron shine yake hanashi tsayawa ya koyi abinda ake koya masu.

Tsoronshi yafi karuwa ne alokacin da akace za'a fara jarabawa, kuma inajin bawani abu bane yake sakashi tsoro illa barazanar da kake mashi na horo idan yafadi jarabawa. Ita kanta Fatima akwai tsoro tare da ita.

Kuma wannan abun ba karamar matsala ze jawo masu ba, abinda nake gani  hakuri zakayi koda basuyi kokari ba kadena tsangwamarsu, kasan shi yaro horo baya yimashi, dole seda lallashi.

Yanda yaranka suke matukar tsoronka yakamata karika jawosu ajiki kana nuna masu cikin hankali kwance abinda kakeso su rikayi, kuma kai malami ne, zaka iya zaunawa dasu ka kara duba jarabawarsu ka nuna masu yanda yakamata suyi.

Kumashi yaro kobeyi kokari ba bekamata ace ana dukanshi ba, yakamata arika yaba mashi ko yayane, wallahi Malan da kana zuwa sauran azuzuwa zakaga yanda wasu yaran ko iya rike pencil basuyi ba.

Hakan kuma bayana nuna gazawar malaman bane, a'a su kwata kwata kwakwalwarsu bata daukar karatu, irinsu zaka gansu abnormal, amma duk da haka iyayensu suka kawosu makaranta domin sunada yakini akansu.

Wasu iyayen ma sukan dauki yaransu masu irin wannan lalurar su kaisu makarantar kudi, kuma haka suke biyamasu batare da gazawa ba, domin kowane Uba yana so yaga danshi yana karatu.

Bare kuma kaida yaranka sun iya rubutu, kuma baze yuwu ace wai sunyi jarabawa acikin subject 10 ace basuci kodaya ba, duk subject baze yuwu ace sunci 0 over 100 ba, dole zaka samu sunci kadan daga ciki.

Idan kana yaba masu bisa kokarin da sukayi hakan zekarasa masu kwarin guiwar dagewa, amma suna ganin sauran yan uwansu suna makarantar kudi, sannan idan suka kawo jarabawarsu kana masu kyauta.

Su kuma sede kayi masu duka ko ka tsangwamesu, dole wani abu ze shigar masu rai, kasan fa yaran yanzu, ko abu karaba masu na wani yafi yawa da kadan haka zakaji suna fadin an bama wane meyawa.

To bare kuma ace kana masu haka. Nide ina roko agareka yanda kake malamin makaranta kazauna da yaranka ka kara sanin matsalarsu, kuma kajasu ajiki hakan zesa tsoronka ya fita aransu, da fatan zaka fahimceni? Dago kai Malan yayi tare da kankance ido.

Gyara zama yayi yace lallai kuwa na gama fahimtarka, ai be kamata kacemun wai ka kirani mutattauna ba, kamata yayi kace ka kirani nan kabani umarni hakan zefi sauki. Wai ko kamanta ni Principal ne? Babu irin matakin daban tsallake ba inde na koyarwa ne.

Kuma yarana ni nasan yanda nake tafiyar dasu ba seka kirani kana koya mani yanda zan tafiyar dasu ba, na tabbata kafin kasan meye dadin Da ni nasanshi, kaga kuwa kai baka isa ka koya mani yanda ake tafiyar da yaro ba.

Kuma kaci sa'a ina ganin girmanka, wallahi da sena maka rashin mutuncin da bazaka kara shiga harkar iyalina ba. Tashi yayi yana fadin idan ma yan gulma ne suka turoka ka koma kafada masu korafinsu be karbu ba, fita yayi yana masifa. Jinjina kai Head master yayi yace ikon Allah.


Wasu yara ne su 3 suka rugo da gudu suka shiga wani gida da yake kusa da nasu Faisal, yaran gidan Alhaji Bala ne, su 4 Allah yabashi 3 maza ne, 1 mace sede ita tunda aka haifeta bame lafiya bace, irin yaran nan ne abnormal, ita ce ta 3 amma haryanzu ko rubutu bata iya ba,sede tana magana amma haryanzu batasan ta girma ba.

 kuma a haka iyayenta suka sata makarantar kudi, duk da bata gane komai, amma Babanta yace abarta yafiso yaganta a makaranta, akalla zata kai shekara 12 amma har yanzu a aji 2 take, har kaninta yana aji 3. matarshi daya me suna Maryam, kuma shi dan kasuwa ne, kuma yaranshi  makarantar su daya dasu Fahad.

Da gudu suka shiga suna rige rigen mikama Babansu takardar da aka basu ta jarabawar da sukayi jiya. Babban cikinsu me suna Mannir wanda yake aji shidda shine yafara zuwa yana fadin Baba wallahi yau na cinye jarabawata duka.

Dayan kaninshi me suna Abba yace nima haka Baba, dariya Baban yayi ya kalli autansu me suna Saddik wanda yake ta bata rai yace a'a ni bazan kalli ta kowa ba sena fara ganin ta autana.

Dariya Saddik yayi hada masu gwalo ya ruga ya mika mashi, mamansu se dariya take masu. Yana karba yaga yaci 40 over 60 a English, dariya yayi yace kai yarona, gaskiya kayi kokari sosai.

Kaci pass, rungumeshi Saddik yayi yana dariya, Baban yace amma ya akayi nan malamar ta samaka zero? Saddik yace kawai na tsaya ina tunanin amsar ne tace insa duk wadda nasani shine nasa wannan.

Dariya Baban yayi yace yauwa to kuzo nan muga yanda akayi yafadi, Maman Saddik matso anzo fanninki kinsan ni idan ba kasuwanci akazo ba bana magana, kune yan boko mukam tun daga secondary muka yardata.

Dariya tayi tace kai Baban Saddik baka rabuwa da tsokana, yace ai gaskiya nafada, shiyasa nakeso yarana suyi ilimi. Turo baki Abba yayi yace Baba mufa? Jawoshi yayi yamasa rada akunne, dariya yasa yace E hakane, Yaya taho muga aikin Saddik.

Wata takarda Baban yadauko da pencil yabama Mannir yasake rubuta mashi tambayoyin da beci ba, haka suka rika nuna mashi ahankali suda Mamansu yana fitar da amsar harya gama. Dariya sukasa Abba yana fadin kai Baba wallahi ya rubuta dede.

Tafi Baban yayi yana fadin yauwa da kyau, kunga yanzu kunzo dede kenan, kowa yayi kokari, dan haka yau akwai tsaraba idan nadawo, amma kasan wani abu Saddik? Girgiza kai yayi yana murmushi.

Baban yace jarabawar gobe inaso kada kabari asa maka zero kaji, yace e kuma bazan bada ba idan bangama ba, Baban yace yauwa yarona, Allah yayi maku albarka

Amira ce tafito daga daki tana murtsike ido tanufo wajensu, murmushi Babansu yayi yace yauwa Mamana zo inji jikin naki, haka yake kiranta da yake sunan mamanshi aka samata Halima, su kuma suna kiranta Amira.

Matsowa tayi yakama hannunta tare da dora hannunshi ajikin wuyanta yana fadin zazzabin ma ya sauka. Mamansu tace ai shiyasa na hanata zuwa makaranta dan jiya dashi ta kwana, Baban yace ai naso abarta taje kinga ta rasa jarabawar yau, damma de na fadama Auntyn su gobe nasan zatayi mata.

Murmushi Mama tayi tace wallahi  Baban Saddik kawai dan kaki ta tawa ne, Amira bata fahimtar komai, da munyi hakuri mun barta agida, kudin da ake kashe mata ya isa ayi wata hidimar dasu, amma ina amfanin arika kashe mata kudi kuma bata fahimtar komai, haka Allah yayita se mu rungumi kaddara.

Bata fuska Baba yayi yace zaki fara ko? Idan ke kina kallon Mamana wacce bata fahimtar komai ni ina kallonta me kokari, kuma tunda muke dake na taba cewa kitayani biya mata kudin makaranta? Idan kinaso mushirya to kidena fada mani irin wannan maganar. Kutashi kucire kayan kuci abinci kafin akira sallah.

Bayan sun gama cin abinci sukayi alwala, suna fitowa Mamansu tace Babanku yana bandaki yace kutafi kada ku rasa sallah idan yafito ze biyoku, hannunsu Mannir yakama suka nufi masallaci.

Gidan Alhaji Bala kenan, haka yake rayuwa da iyalinshi cikin kwanciyar hankali da farin ciki, yana matukar son yaranshi kuma yana jansu ajiki, duk da beyi ilimin boko me tsawo ba hakan be hanashi kula da yaranshi ba.

Kasancewar matarshi tayi N,C,E yasa take temakon yaransu,sede be barta tayi aiki ba, danshi yafiso tazauna ta kula da gida, kuma duk wata bukatar ta yana mata, idan kagansu bazakace a kauye suke ba, suna da tarbiya da hazaka, kuma basa shiga gidan kowa sede su hadu awajen wasa ayi wasa, ana tashi kuma su tafi gida, idan kagansu agidan wasu to aikensu akayi.


A yau Juma'a aka bada hutun third term, in da kowane yaro ya karbi sakamakonshi yataho gida, wasu suna cike da farin ciki na kokarin da sukayi, wasu kuma suna kuka. A ciki hada Faisal da Fatima.

Zaune suke a falon Malan kamar yanda suka saba a duk lokacin da akayi hutu, Faisal da Fatima suna daga gefe idanuwanshi duk sunyi ja saboda kuka. Kallonsu Malan yayi yace ai kunsan bakuyi abun kirki ba shiyasa kuka rabe daga nan.

Fatima tace Allah Malan duka takarduna babu wadda aka samun zero duka, wasu duk naci. Faisal yace nima haka kuma jarabawar English ma 2 kawai na fadi. Malan yace aikin banza kenan.

To ai ba abun kirki kayi ba dan kafadi 2, kalli takardun Fahad, duk wanda na daga Excellent ake samashi, kalli hada kyauta aka basu, Yayanku gashi nan yagama makarantarshi kalli irin kyautar daya samu.

In da baya yin kokarin taya za'ayi yasamu haka, kuna gani gobe zamuje bikin yayesu da za'ayi, inda kuna kokari ku ma ai dole aje daku, kalli kanwarka Farida primary 2 take amma bata faduwa. Towai so kake abude kanka azuba maka karatun aciki.

Sauran yaran batare ake koya maku ba? Cikin kuka Faisal yace dan Allah Malan kayi hakuri wallahi zan gyara. Malan yace kullum haka kake fada ai, dauko dorina yayi yana fadin gara jikinka yafada maka hakan zesa ka gyara da kyau.

Mama ce tashigo tana murmushi tace kaga Malan da yaranshi, zama tayi kusa dashi tana fadin haba yau de zanshiga maganar nan, ayi masu hakuri kodan darajar yaran nan da suka kawo kyaututtuka masu yawa, kuma gobe ma nasan za'a basu wasu.

Malan yace kina ganin abinda suka kawo mani, babu wadda tafi bani haushi ma kamar Fatima kali takardunta, Allah ko bazan bigi Faisal ba sena zaneta, cikin kuka Fatima ta saki fitsari.

Dariya Farida tayi tana fadin Lah! Kalla Malan tayi maka fitsari asaman kafet dinka, saurin tashi yayi yana kokarin kamota, ai a zabure tayi waje cike da tsoro dariya sauran suka samata, Mama tace kadawo tunda ta gudu kuma kofar gida tayi kada ku raba mana abun kunya a unguwa.

Dama ga unguwar nan da iya gulma. Dawowa yayi yana fadin ai gidan zata kwana, icce tun yana karami ake lankwasashi, idan banyi mata haka ba bazata rika maida hankali ba, da ace mu iyayen mu sun yimana sako sako ai da bamuyi kokarin ba.

Na koyar da mutane sunfi akirga hada wadan da basa gane komai, amma da tsanani na seda sukayi kokari inda wasa nayi masu baza suyi kokari ba, akwai wadan da har yanzu da girmansu amma idan suka ganni se sun duka mani.

Saboda sun ga ribar horon danayi masu lokacin dana koya masu, mutanan waje ma natsaya kai da fata seda sukayi kokari sannan ace acikin gidana yarana suna kawo mani zero ai baze yuwu ba, idan zaka gyara ka gyara, zan kara maka dama zuwa next term matukar baka gyara ba ina me tabbatar maka Almajiranci zan kai ka.

Dariya sosai su Fahad sukema Faisal, shikuwa se kuka yakeyi. Malan yace babbar kyautar ka Farouk zan siya maka keke kuma......... maganar mutane sukaji awaje ana fadin ina Malan din yake? Tashi yayi yana fadin ganinan lafiya zaku shigo mani gida haka.

Yana fitowa Alhaji Bala yace lafiyarce ta kawo haka, kun bar yarinya tafito daga gida tana kuka bata kula da mota ba ta kade ta. Zaro ido Malan yayi yana fadin ina Fatimar take? Wani yace wanda ya bigeta ya dauketa sun nufi asibiti domin ba'san irin ciwon da taji ba.

Saurin shiga ciki Malan yayi yadauko mukullin mota, ko hula be dauka ba yace muje , Mama tace ka nutsu dan Allah kada kaima kaje ka bige wani. Inne ce tafito cikin tashin hankali dan Faisal yaje yafada mata.

Bata tsaya jiran komai ba tabi bayan Malan, tana zuwa ta bude motar tashiga tana kuka, haka suka nufi asibiti.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
馃彙馃彙 A WANI GIDA馃彙馃彙
          馃槶馃槶馃槶

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 [email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 15 鈴� 20

  Malan gaba daya hankalinshi yatashi, se zagaye yakeyi a gaban dakin  da aka shigar da Fatima, Inne kuwa tana zaune waje daya se kuka takeyi, kusan mintuna 30 likita yafito daga dakin, kai tsaye office dinshi ya wuce.

Haka Malan da Inne suka bishi jiki a sanyaye, bayan ya gama yan rubutunshi ya dago kai ya kalli Malan yana fadin kune iyayen wannan yarinyar? Malan yace kwarai kuwa. Jinjina kai likita yayi yace wato ta bugu ne akai, domin motar data bigeta ta kai ta daketa.

Munyi mata dressing wajen da taji ciwon kuma munyi mata allurai, sede zamu turaku zuwa katsina domin ayo hoton kanta, saboda bamu da tabbacin abinda yasamu kan. Amma daga nan zuwa lokacin da zata farka zamu kara sanin yanayin da take ciki.

Malan yace to zuwa yaushe zamuje ayo mata hoton? Likita yace zuwa ranar litinin, tunda yau juma'a inba asibitin kudi zaku kaita ba. Malan yace amma da wuri ake bukatar hoton? Likita yace i to gaskiya inaso inga wace irin matsala ce, idan zamu iya da ita shikenan, idan kuma tafi karfinmu kawai zamu maidaku can babban asibiti, kasan idan akace an bige mutum ta kai ba'a wasa.

Malan yace nagode, abinda za'ayi zamu barta anan zuwa ranar litinin din kawai zamu tafi can katsinar gara musan cewar awaje daya muke. Likitan yace shikenan zan hadaku da wani likita, Allah yakara sauki.

Yanzu tana bacci zaku iya zuwa dakin da aka kaita na yara kafin ta farka. Godiya sukayi mashi suka fito. Wanda ya bige Fatima ne yace Malan dan Allah kayi hakuri kasan tsautsayi baya wuce ranarshi. Malan yace musamman idan mutum yana tukin ganganci ba.

In ba tukin ganganci ba taya zaka shigo cikin unguwa da gudu se kace kana tuki akan titi, irin wannan ciwo anfi samunshi a babban hadari wanda akayi a babban titi, amma ai harda kunya ace acikin uguwa ne aka bigeta.

Batun hakuri ma betaso ba, inaso in fada maka kwandalata ba zatayi ciwo ba, duk abinda ake bukata kaine zaka biyashi, kamar yanda ba'a taya mutum azumin kaffara kasan Allah haka bazan tayaka biyan ko sisi ba.

Daga gobe se ka kara shigowa cikin unguwa da gudu, in ba da niya ba meyasa seda ka wuce gidanka sannan zaka kwaso da gudu, wato kukan dan wani sarewa ko, tun da jifa tawuce gidanka baka damu ta fada gidan kowa ba.

Zaka iya tafiya, amma ina me tabbatar maka idan har Fatima ta farka da wata matsala to kashirya zuwa katsina ranar monday. Sakin baki Labaran yayi yana kallon Malan cike da mamaki. Duk da kowa acikin uguwarsu yasan rashin mutuncin Malan amma be dauka ya kai haka ba, yadauka a iya karatun yaranshi kawai ya tsaya.

Jinjina kai yayi yace bakomai, Allah ya bata lafiya, kuma Allah ya kaimu ranar litinin seka fada mani lokacin tafiyar. Malan ya miko mashi waya yana fadin samani number ka. Bayan yagama sa mashi yabarsu yatafi cike da mamakin hali irin na Malan.

Kallon Inne yayi yace dan Allah ki rufe mana baki, nifa shiyasa banso na dauko kowa ba, da abu kadan yafaru shikenan kuyita mana kuka, cemaki akai mutuwa tayi ne, addu'a ai ita yafi kamata ayi mata. Wuce muje can dakin nasu.


Zaune Alhaji Bala yake shida iyalanshi suna ta murnar result din yaranshi da aka kawo, Mannir shine yazo na daya a ajinsu wanda ada na 3 yake zuwa Farouk dan gidan Malan yazo na daya, amma wannan karon shine yazo na daya.

Abba kuma a ajinsu yazo na 2, se Saddik dayazo na 4, Amira kuma kamar kullum itace ta karshe. Kayan dadi kala kala yasiyo masu suna zune sunaci gaba dayansu. Bayan sun gama yadauko kyautar daya siyo masu guda 4.

A jewa yayi yana fadin yauwa kowa yatashi yabi layi, kowa yasan na nawa yazo a makaranta ko? Sukace E, yace yauwa, zan rubuta number ajikin wannan takardar kowa zezo ya dauki na number da yazo a makaranta.

Dariya sukasa suna tsalle, Mannir ne kawai ya gane abinda Babansu yake nufi,haka kowa ya dauki nashi Amira se tsalle takeyi tana dariya anbata kyauta. Bayan kowa ya dauka Baban yace yauwa to kowa yazauna.

Duk wanda yakeso yarika daukar babbar kyauta to ya dage wani term din yazo na daya, kunga yanzu Mannir ze fita zaku rage ku 3, banaso position dinshi yatafi wani gida, nafiso yadawo gidanmu. Kuma gobe zamuje bikin yayesu da za'ayi inaso kowa yatashi da wuri.

Abba yace ai Baba daga wannan term din kullum na daya zan rikayi, Saddik yace nima haka. Amira tace nima Baba zan rika kokari, yace yauwa Mamana haka nakeso kinga kema zan rika baki babbar kyauta.

Murmushi Mamansu tayi aranta tana fadin wahala de, naga ranar da Amira zatayi ko na 10 ne balle na daya. Tashi tayi tana fadin Amira muje kicire kayanki kiyi wanka. Kallonta Baba yayi yace yau kada kidafa komai da dare party zamuyi. Mama tace lallai kam, wanda yayi kokari shikadai yakamata ace anayima kyauta.

Amma kai ka hadesu gaba daya kayi masu kyauta taya zasuji haushi har suyi kokari. Baba yace ai ba dole se an hana yaro kyauta yakeyin kokari ba, anaso arika karfafa mashi guiwa hakan zefi saurin sashi ya maida hankali.

Naga alama keda kikayi karatu a fannin koyarwa sam baki amfani da abinda kika karanta. Mikewa Mama tayi tana fadin da kabarni naje nayi aiki da kasan ina amfani dashi ko banayi. Baba yace nikam bade agidana aiki ba, abinda nake maki idan be isheki ba shikenan.

So nawa ina baki jari amma kin kasa yin sana'ar kirki, kuma duk da haka ban rageki da komai ba, ko bakiyi aiki ba ai zaki iya tsayawa ki koyama yaranki. Mama tace ai ina koya masu, kai de kawai abar maganar. Baba yace an barta.


Maman su Farida ce ta iso asibiti, ta na zuwa ta kira Malan awaya tace ina aka kwantar da Fatimar? Fada mata yayi ta nufi hanyar dakin hannunta rike da ledar data sako cooler abinci.

Bayan sun gaisa da Inne tace ikon Allah, har yanzu bata farka ba? Malan yace wallahi kuwa, kilama ranar litinin Katsina zamu koma. Mama tace ashede abun babba ne? Malan yace ciwon akanta yake ai, har dinki akayi mata fa, shiyasa likita yace yanajin tsoron kada ace wani abu yasamu kwakwalwarta.

Dafe kirji Mama tayi tana fadin Allah yasa kada tasamu wata matsala a kwakwalwarta dama ya lafiyar giwa. Malan yace amin, amma Labaran ai ya gama cutarmu. Mama tace wai dama Labaran ne ya bugeta? Malan yace shine mana.

Ai nace ko sisi bazan kashe ba shine zeyi komai. Mama tace wallahi da gaskiyarka, gara aljihunshi ya fada mashi, Allah de yabata lafiya. Ga abinci nan na taho maku dashi nasan kila Inne baki dafa abinci ba tunda nasan bada wuri kike dorawa ba.

Kallonta Inne tayi duk da tasan da biyu tayi maganar amma setace mungode. Mama tace Malan ai gara ka koma gida tunda yau juma'a kayi wanka kada akira sallah. Malan yace haka ne, bara inje idan ta farka se kuyi saurin kiran likita ko nurse.



A firgice Fatima ta farka tana fadin kayi hakuri Malan. Saurin riketa Inne tayi tana fadin Maman Farida kirawo likitan, kuka kawai Fatima takeyi tana fadin kayi hakuri Malan.

Bayan likita yazo ma kukan yasamu ta nayi tana kiran Malan, gaba daya afirgice take jikinta se rawa yakeyi. Likita yace kode wani malaminsu amakaranta ya doketa ne ko kuma tana matukar tsoranshi? Inne tace a'a kawai sunan.......

Mama tayi saurin fadin ai kasan halin yara, daga makaranta de suka dawo kafin su shigo gida aka bigeta bakaga kayan makaranta ma ajikinta ba. Likita ya jinjina kai yace haka ne, kamo Fatima yayi yana fadin tsaya kiji babu abinda Malan zeyi maki kinji.

Kina bacci ma malan din yazo dubaki kuma yace kiyi hakuri baze kara dukanki ba. Haka likita yayita mata wayo har seda yaga ta nutsu tabar kukan sannna yafara yimata yan tambayoyi domin yagane ko abinda yake tunani yafaru.

Haka yasa Inne tarika mata tambaya akan gidansu da duk wanda tasani, ganin kome suka tambayeta tana bada amsa yasa likitan yayi ajiyar zuciya, dago kai yayi yace Alhamdulillahi abinda nake tunani ma bashi bane.

Kuma naga jikinta bawani ciwo bane kawai wannan ciwon na goshinta shine se sauran gurjewar datayi, idan malan din yadawo zaku iya tafiya ma, amma idan yazo ina son ganishi a office.


Zaune Malan yake a office din likita, bayan yagama fada mashi abinda yafaru bayan farkawar Fatima yace zaku iya tafiya da ita, domin bana tunanin akwai wata matsala, idan yaso ranar juma'a se kumai dota akwance dinkin da akayi mata.

Amma gaskiya kajama malamin da Fatima take fadi kunne, ba'aso arika tsorata yaro har yarika firgita saboda tsoro, ai bada haka ake koyawa ba, garama idan baze iyaba ka dauketa daga makrantar ka maidata wata.

Amma na tabbata bakaramin tsoronshi takeji ba, irin haka ne fa yaro yake shiga cikin matsananciyar damuwa, daga karshe ma yadena fahimtar abinda ake koya mashi. Jinjina kai Malan yayi yace mungode. Haka suka nufi gida.

Sunzo shiga ciki suka hadu da Labaran, karasowa yayi yana fadin Malan yanaga kun maidota gida? Malan yace to dama so kake muyita zama asibitin? Ai wallahi kaci sa'a babu wani abu da yasameta da aljihunka yafada maka.

Ga wannan takadar magungunan da zaka siyo ne, sauran kudin kuma na asibiti da alluran da akayi mata duk na biya saboda bakazo ba, amma zaka bani naira dubu daya da dari biyar.

Amsar takardar Labaran yayi yana murmushi yace to Allah yakara sauki, hannu yasa aljihu yaciro dubu 2 yabashi yana fadin dari biyar din asai mata lemu, yanzu zanje insiyo magungunan. Wucewa  ciki Malan yayi be kulashi ba.

Da dare malan yana zaune adakin Mama bayan ya gama cin abinci Mama tace kasan wani abu? Yace sekin fada, tace wallahi wannan likitan da son jin kwaf yake, wai fa dan Fatima ta tashi tana kuka tana fadin kayi hakuri Malan shikenan ya tambaya wane malan.

Wallahi har Inne ta bude bai zata fada mashi abinda yafaru nayi saurin gyara maganar, to ai da kunya ace Babanta ne ta farka dashi, ita da ba'a gabanta akayi abun ba, narasa ko ina taji. Malan yace akwai wanda ze fada mata da ya wuce Faisal.


Mama tace nikam bazan iya fadar sirrin gidana ba, koma menene ai maganar cikin gida ne, meye na fadama wani likita. Malan yace keda kikasan wannan kece zaki iya gyarawa, ai kamar nasan za'ayi haka nace kizauna a asibitin.

Amma dama ita babu abinda takeso kamar kowa yaga gaza wata, shiyasa akullum take nuna ma yaranta nidin ba komai bane awajensu, kuma ni ba kinsu nake ba, amma matukar danka baya maida hankali wajen karatunshi to kada kace zaka rika yimashi lako lako yanzu ze sangarce.

Mama tace ai koda Farouk yazo na 3 wannan karon seda naji haushi damma de yagama makarantar, kuma seda nayi mashi fada sosai bayan tafiyarku dan naga bakayi mashi fada ba.( anya wannan maganar haka take mama?馃).


Murmushi Malan yayi yace ai dan mutum ya aikata laifi so daya ni bana mashi fada, kuma nasan halin Farouk kila akwai dalilin daya hanashi zuwa na daya shiyasa kika ga banyi mashi magana ba.

Gobe zamuje bikin yayesu da za'ayi se kishirya da wuri kinsan de bana son jira, Mama tace ai dole mushirya da wuri amma nasan Inne bazata je ba tunda Fatima bata gama warkewa ba. Malan yace wannan sarkin bakin cikin ko batada marar lafiya ma ai bazata je ba.

Murmushi Mama tayi tace kai ko malan bansan me Inne tayi maka ba, tsaki yayi yace nima bance tayi mani wani abu ba,  kawai de ina son mutum yazamo me kulamun da yarana shiyasa. Mama tace to Allah yabamu ikon kula dasu, yace amin.

Washe gari bayan sun gama shiryawa Mama tashiga ta duba Fatima da jiki tayi mata sallama, Inne tace adawo lafiya da Fatima lafiyarta kalau ai da naje. Tabe baki Mama tayi tace ai kinga kin huta da kallon kayan haushi, ko nice ma bazani ba, danni bana iya tsayawa ina kallo ana bama wasu yara kyauta ba nawa ba.

Juyawa tayi tafita tana dariya, girgiza kai Inne tayi tace Allah ya kyauta, cigaba tayi da bama Fatima magani. Malan ne yashigo da sallama yana shigowa Fatima ta bata fuska ko kallonshi batayi ba.

Inne ce tace Malan har kafito? Yace wallahi kuwa zanje wajen bikin yaye su Farouk, kinsan yana da matukar kokari nasan ze karbi kyauta da yawa. Ina Faisal fa? Inne tace yana daki bejin dadi shima. Malan yace ai ko dan kada ince yazo mutafi kyace bejin dadi.

Kallon Fatima yayi ya duka kusa da ita yana fadin Fatima ba gaisuwa? Ya jikin naki? Dukar da kai takara tana fadin Malan ina kwana? Yace lafiya lau, yanzu ina yake maki ciwo? Kwallace ta cika mata ido tace ba ko ina.

Tashi yayi yace sannu, idan nadawo zan siyo maki lemu kinji, juyawa yayi yana fadin idan Faisal yatashi kibashi maganin zazzabi. Inne tace to adawo lafiya yace Allah yasa.

Kallon Fatima tayi wadda take share kwalla tace me kuma yafaru? Dago kai Fatima tayi tace wallahi bana son Malan, saboda shima baya sonmu, kuma idan na girma kome nasamu bazan rika bashi ba.

Hannu Inne tasa ta goge kwallar data zubo mata, kamo hannun Fatima tayi tace kinaji ko, daga yau kada inkara jin kin fadi haka, Malan yana sonku, idan ku naso yarika maku yanda yake ma sauran dole kuma ku dage kuyi kokari.

Badan ya rika yaba maku ba, sedan kada ku girma ku zamo tamkar wasu marasa galihu, domin shi ilimi da kike ganinsa yana kara daukaka darajar mutum, kuma baya taba bari mutum ya tabe, kuma mutane basa wulakanta me ilimi.

Matsowa Faisal yayi wanda tun dazu da Malan yafita yatashi, zama yayi kusa da Fatima yana goge mata fuskarta yana fadin kiyi hakuri kinji, gaskiya Inne ta fada kuma insha Allah Inne daga wannan karon bazan kara bari abarni abaya ba.

Kuma tunda Malan yace kada mukara kai mashi result din mu bazamu kara kai mashi ba. Shafa kanshi Inne tayi duk yanda taso ta boye kwallarta kasawa tayi, seda ta zubo.

Faisal yace kingani ko Inne, kema kullum se Malan yasaki kuka, idan nayi kudi daukeki zanyi daga gidan nan. Murmushi Inne tayi tace Allah yasa Faisal, nide abinda nake fada maku kada ku kullaci 'Yan uwanku.

Domin ba kuda sama dasu aduniya, duk yanda wani zeso ya rabaku kada kuyarda, kuma banso koda wasa kusaka kiyayyar Mahaifinku aranku. Yana sonku rashin kokarinku ne yasa yake maku fada.

Kuma yanaso kuji haushi kuyi kokari shiyasa yake maku haka. Faisal yace in Allah ya yarda Inne zamuyi kokari kinji. Dariya maganarshi ta bata, tana mamakin  Faisal, idan yana magana kamar wani me shekaru da yawa, maganarshi cike take da basira.

Inne tace tashi kadauko abincinka kaci kasha magani. Faisal yace aini lafiyata kalau, kallonshi tayi tace kuma kace mun baka da lafiya dana tasheka dazu? Murmushi yayi yace kawai banaso Malan yace inje makarantar su Yaya ne.

Girgiza kai tayi tace bade kana jin haushin za'a bashi kyauta bane? Dago kai Faisal yayi yace Allah Inne banajin haushi dan Yaya ze karbi kyauta, kawai de banaso muyi tafiya tare da Mama ne.

Inne tace me take maka? Faisal yace bakomai kawai de banaso muyi tafiya da ita tare da Malan. Shiru Inne tayi domin tariga da tasan Mama itace take kara zuga Malan akan duk abinda yake masu, kuma tanajin dadin yanda sam Faisal baya kawo mata gulmar abinda Mama takeyi.

Kallonshi tayi tace to Allah ya kyauta, Mama de kamar mahaifiyarka ce tunda matar Babanka ce, kada kabari wani abu yashiga ranka, kuma kada ku manta kullum ku rika addu'ar dana koya maku kunji? Suka ce E.

********** **********

 Bayan sati 4 jarabawar su Farouk ta fito ta Science school da yayi, cikin sa'a yasamu sunanshi ya fito a Science Faskari ta maza, sede jarabawar da yayi ta police acadamy be cita ba. Sosai ranshi yabaci.

Yaso ace yasameta domin yawancin yan ajinsu duk can zasuje, kuma Mannir Bala yaci makarantar. Mama itama ranta yabaci haka tayita mashi masifa tana fadin dama ai tunda naga bakazo nadaya ba nasan kafara saka wasa a karatunka. Kodan kaga bamuyi maka fada ba shiyasa, har cema Malan nayi namaka fada, ashe zaka kara faduwa.

Yanzu nasan halin malan yanda be yima kowa alfarma shima bazeje neman alfarma awajen kowa ba, domin yasan ko yaje baze samu ba, munaji haka zaka tafi uwa duniya wai Faskari, bama cikin garin Funtua ba.

Sallamar Malan ce tasa ta yinshiru ta saki murmushi, bayan yazauna tace ina nan ina taya Farouk murnar samun Science Faskari. Murmushi Malan yayi yace ai nafada maki Farouk akwai kokari, sam bandamu ba dan beci waccan makarantar ba.

Dama Science School ai ta masu kokari ce, bakowa ake dauka ba, ita kuwa waccan Federal ce mutum ze iya bada kudinshi ma adauki danshi, ni kuma kinsan neman alfarma baya cikin tsarina.

Mama tace to ina ma neman alfarma yake da dadi, duk wanda yaje neman alfarma dole ne ya iske wulakanci, shiyasa nake alfahari da mijina baya zuwa yana kaskantar da kanshi awajen kowa.

Murmuhsi yayi yace nagode da wannan yabo, Farouk tashi kaje mota zakaga wata leda kadauko Uniform dinka ne, domin saura sati 2 akoma makaranta nafiso kaje da wuri. Mama tace haba de, ko wadan da suke cikin makarantar ai basa komawa da wuri.

Baresu da suke sababbin dauka kasan dole se ahankali zasuyi yawa, ka mashi hakuri nan da sati 4 seya koma, kawai aje ayi mashi registration kaga an koma da sati 2 se yatafi.

Malan yace kinsan fa banason ace yarona yayi latti, Mama tace ai ba latti zeyi ba, idan akaje aka gama mashi komai daya tashi kawai komawa zeyi. Malan yace kede kice bakison rabuwa dashi, kuma dole ku rabu dan nafison yarana suyi boarding School zasufi sanin me rayuwa take ciki.

Mama tace haka ne, nide ina neman alfarma, murmushi yayi yace tunda kece anyi maki, tace nagode sosai. Suma su Fahad ai se an sake masu kayan makaranta tunda sabon aji zasu shiga, nasan su Faisal ma kayansu sun tsufa se asake masu gaba daya.

Murmushi yayi yace wallahi kina burgeni, ina jin dadin yanda baki gwada banbanci tsakanin yaranki dana Inne, sede ita ban taba jin tace ayima yaranki wani abu ba. Mama tace to ai bakomai da yaranta da nawa duk wa ya haifesu? Kai ne, kuma ni kai nakeso dole inso duk wani abu daya shafeka.

Dariyar jin dadi malan yasaki yana fadin Allah yayi maki albarka, shiyasa nake kara sonki wallahi, kina son yarana, ni kuma duk meson yarana ina sonshi sosai. Mama tace tunda Farouk yafita kozaka maido Faisal makarantarsu shida Fatima banaso mutane surika ganin kamar nice nasa afiddasu.

Daure fuska Malan yayi yace dan Allah kada kisa rai na yabaci, nifa duk maganar da za'ayi matukar za'a sako mutane aciki wallahi batamun rai take, nifa ba ruwana da mutane, koma meza suce suje suyita fada, aide ansan yarana ne ko, kuma ina sonsu, nasan abinda nakeyi, hakan danayi masu zesa suji haushi suyi kokari nan gaba. Mama tace Allah yasa yace amin.


********* ********

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, tunda aka koma wannan term din kowa ya maida hankali wajen karatunshi, in da Farouk yatafi Faskari, Faisal kuwa sosai yake dagewa wajen karatunshi, kuma yana kokarin nunama Fatima duk abinda bata sani ba, haka kuma duk abinda be gane ba yana zuwa wajen malaminsu yana koya mashi.

Ko aiki aka basu baya tafiya ko break ne seyaje ankoya mashi, sosai malamansu suke yaba mashi kuma suna matukar sonshi dan yana da natsuwa ga hankali, alokacin yana aji 4 ganin yana gane abinda ake koya masu yasa Head master ya maidashi aji 5 kuma yace kada yafada ma Babansu.

Fatima ma aji 4 aka maidata, Faisal ko agida akwai wajen wani Copper da yake zaune agidansu Saddik wanda yakasance dan Uwansu ne, kuma yana yimasu lesson hakan yasa Inne taje ta roki alfarmar yaranta surika zuwa, Mamansu tace bakomai suzo.

Duk ranar alhamis da juma'a yake masu lesson din, duk abinda ake Mama da Malan basu sani ba, ko su Fahad ma basu sani ba shiyasa be hanasu zuwa ba, domin yace inde sun san basuyi kokari ba kada su kara kawo mashi takardunsu.

Hankalin Inne yafara kwanciya domin yanzu taga yaranta sun fara gane abinda ake koya masu, kuma tana kokari wajen kyautata ma mijinta, sede sam har yanzu bata yarda dayin wata kissa ba wai dan ta burge mijinta, ita aganinta kamar zata koyi irin na Mama ne, kuma  bata shiga harkar Mama, sede in wani abun jaje ne yafaru take shiga tayi mata kona murna.



A gidan Alhaji Bala kuwa Mannir shima yatafi makarantar Police acadamy saura su Abba da Saddik, se kuma Amira, wanda yanzu tashiga aji 3, shima haka nan malaman suka sata bawai dan ta cancanta ba.



Haka rayuwa tacigaba da tafiya, sam Malan yadena kula harkar karatun su Faisal, aganinshi bazasu taba canzawa ba, shiyasa yayi masu haka amatsayin horo yasan wata rana zasu canza idan sukaji haushi.

 Kuma dama tunda yaga Fatima taji wannan ciwon asanadiyar dukanta dayace zeyi yaji tsoro kada sukara jin tsoronshi musamman da akace mashi ta farka da sunanshi abakin ta.

Koda sunyi jarabawa basa kaimashi result din, yace duk ranar da sukayi kokari se su kaimashi, ita kuwa Mama dama haka takeso yadena kulasu, hakan yasa takara dagewa wajen canza salo kala kala na dauke hankali.

Har suka gama primary 5 zasu shiga 6 Malan baya karbar result dinsu, alokacin Fahad ya gama Primary 6 inda yaci Science Dutsinma, kuma shima can yatafi, Mama sam ba haka taso ba, taso ace yaranta yanda suke da kokari ace sun tafi makarantar kudi a Secondary ma.

Amma da yake tasan halin Malan yasa batayi magana ba. A lokacin da Head Master ya tura sunan yaran da gwamnati tace abada zasuyi jarabawar scholarship hada sunan Faisal yasa, duk da yasan kokarinshi be kai yashiga cikin masu yin jarabawar ba, sede yanayin kwazonshi da jajircewarshi tasa yasashi.

Haka yabashi takardar yace yakaima Malan, lokacin daya kaimashi masifa Malan yarikayi ya akayi Faisal yashiga aji 6, Faisal yace Head master ne ya maidani. Malan yace shikenan tunda yayi gaban kanshi, kuma ni bazan bata lokacina wajen zuwa wata jarabawa ba.

Dama ace kana maida hankali dana shige maka gaba, amma ina jin kunya amatsayina na Principal ace naje irin wanan waje kuma yarona beci ba. Kaje tunda yace shine ze kaiku Allah yabada sa'a.

Sosai wannan abu yayima Faisal zafi, haka yafito yana kuka, ran Inne yabaci sosai, taso taje tayi mashi magana amma kuma setayi hakuri tasan ta na iya zuwa takara jawo wata fitinar.

Itace taje wajen Head master tayi mashi bayani, yace bakomai, ai nasan halin Malan. Kuma insha Allah Faisal zeje yayi jarabawar ki dage da addu'a.

***** *******

Bayan shekara 1 Faisal ne yashigo gida da gudu yana murna, kai tsaye wajen Inne ya wuce yana zuwa ya rungumeta yana fadin Inne kitayini farin ciki naci jarabawar da mukayi a Katsina.

Inne cike da farin ciki tace da gaske? Yace wallahi kin gama takardar da malamin mu yace in kawo ma Malan, dama ai kinsan nafada mashi yace shi ba ruwanshi yasan koyaje baci zanyi ba.

Goge kwallar data zubo mata tayi tace Allah nagode maka, yanzu shikenan Faisal Abuja zakatafi kayi karatunka? Yace wallahi kuwa Inne, ashe nima zanyi farin ciki a gidan nan. Amsar takardar tayi tace nakosa Malan yashigo yaji wannna abun farin cikin.

Bata fuska Faisal yayi yace Inne nasan ko yaji ma bazeyi farin ciki sosai ba tunda baya sonmu. Inne tace zeyi farin ciki domin irin haka yakeso kazama. Faisal yace ni kuma koyayi farin ciki bazanji dadi ba, tashi yayi yashige daki yana kuka. Cike da mamaki Inne ta bishi da kallo zuciyarta cike da tsoron kada ace abinda take gujema Malan ne yashiga kan Faisal.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
馃彙馃彙 A WANI GIDA馃彙馃彙
          馃槶馃槶馃槶

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 [email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 20 鈴� 25

 Da dare Malan yana dakin Inne, bayan ya gama cin abinci suna zaune suna kallo yace wai inasu Faisal ne? Inne tace suna ciki suna kallo. Malan yace kamar yanda kikeso de haka ne ta kasance, bakiso yarana su saba dani kuma gashi nan kinci riba.

Inne tace me kuma nayi? Yace ba abinda kikayi, amma kisani ba'a raba hanta da jini, kuma idan baki sani ba da Uba ake ado, ko ina mutum zeje baze iya canza sunan Ubanshi ba.

Murmushi Inne tayi tace Allah yabaka hakuri, in da kasan yanda nake kokarin nuna masu muhimmancin ka har ma dana 'Yan uwansu wallahi da bakace haka ba. Malan yace in da kina masu ai dana gani. Mamansu Farida inde ina wajenta bata taba barin Yaranta suje wani waje muna tare dasu.

Fatima ce tashigo da sallama, Inne ce ta amsa tana zuwa ta duka fuskarta babu walwala tace sannu da zuwa Malan, kallonta yayi da yanda fuskarta tayi duk seyaji babu dadi, yarinya karama har tasan daurewa.

Murmushi yayi yace yauwa Fatima, kallon Inne tayi tace Inne ina littafin dana baki dazu na islamiyata? Inne tace kinga ko na manta gashi can asaman tebur dazu dana shigo na ajeshi anan.

Tashi tayi taje ta dauka zata fita. Malan yace Fatima kawo ingani yanzu kin fara iya rubutun ko? Takowa tayi ta mika mashi, bayan ya bude yayi mamakin yanda yaga rubutun ta na larabci kamar wani ne yayi mata.

Murmushi yayi yace lallai ashede Fatimar ta farajin fadan da nake mata, bara inga wane darasi ne, bangon littafin ya duba. Zaro ido yayi tare da tashi zaune, domin abinda yagani sosai ya tsoratashi.

FATIMA INNE, shine abinda aka rubuta ajikin bangon littafin, kara budewa yayi ya kalli rubutun dake ciki, iri daya ne dana bangon littafin. Mikama Fatima littafin yayi jikinshi gaba daya yayi sanyi.

Bayan ta fita Inne tace Malan lafiya de naga kamar akwai wani abu? Kallonta yayi idanuwanshi sunyi ja sosai, seda ta tsorata da yanayin data ganshi ciki, ya dade kafi ya kalleta yace lallai Jamila, ban taba sanin kiyayyar da kike mani ta kai haka ba.

Yanzu har ya kai kisa yaranki su canza sunana zuwa naki, saurin kallonshi tayi cike da mamaki tace Malan yaushe kataba ganin Uwa ta sa yaranta sun maida sunanta ama dadin Ubansu? Wallahi bantaba kokarin sasu suyi wani abu marar kyau ba

Malan yace amma gashi ai nagani ajikin littafin islamiyar Fatima, wanda kafin infara gani kece kika fara amasar littafin tunda gashi tazo nema awajenki, saboda ma ki nuna mani shiyasa kika kawoshi falona kika aje.

Kwallace ta zubo ma Inne tace wallahi, wallahi, wallahi idan har ka yarda da wannan rantsuwar tawa amatsayina na musulma to ban taba ganin abinda yake jikin littafin ta ba, wannan littafin ma daka ganshi nan dazu da yamma sun dawo islamiya zan shigo inyi shara anan tabani tace induba taci aikin da tayi jiya.

Bayan na amsa na ajeshi asaman tebur dinka nafara shara dan magriba takusa, ina gamawa natafi nayi alwala wallahi ko duba littafin banyi ba. Kayarda dani bazan taba saka Fatima ko Faisal su aikata maka wani abu marar kyau ba.

Kuka takeyi sosai duk seyaji beji dadi ba, duk yanda yake da zafi sam be iya muzguna ma mace ba, sede idan yanajin haushinta kawai ya shareta. Hannunta yakama yana fadin shikenan ya isa, ai na dauka kece kika sata.

Kira mani Fatimar, harta tashi Malan yace ko kuma barshi, nasan yanda yaranki suke jin zafina kona kirata idan zan kwana ina mata magana bazata cemun komai ba, karshe ma kuka zatasa kamar wadda aka duka.

Amma inaso zuwa gobe ki tambayar mani ita domin inji dalilin ta na saka sunanki. Inne tace insha Allah. Tashi tayi ta dauko mashi takardar da Faisal yabata, bayan ta zauna tace Malan albishirinka? Yace goro.

Mika mashi takardar tayi tana fadin bude ka duba da kanka. Amsa yayi yana fadin Allah yasa inga alkhairi. Kara gyara zama yayi ganin abinda aka rubuta ajiki. Murmushi yasaki yana kallon Inne yana fadin wai da gaske ne abinda ido na yake gani? Inne tace da gaske ne mana.

Hamdala yafara yana fadin kin gani ko? Dama nafada maki babu jaki acikin yarana, ban kasance marar kokari ba yarana bazasu kasance haka ba, shiyasa na fada maki jan yaron da baya maida hankali ajiki bashine gata ba, hakama lallashi bayasa yaro ya maida hankali akan karatunshi.

Matukar mutum ze dage wajen hora yaronshi dole ne yasaka tsoro aranshi har ya maida hankali akan abinda ake koya mashi. Da ace banyi masu haka ba, baza suji haushin komai ba, kuma baza suji tsoro ba aduk lokacin da basuyi kokari ba, domin sun san kosunzo baza'ayi masu fada ba.

Yanzu wai Faisal ne zetafi Abuja under Scholarship? Ikon Allah, ina mutanan unguwa da suke ganin laifina dan nayi masu Faisal haka? Lallai wannan abun nuna wane, dole in nuna masu abin alkhairin daya samu dana.

Ada nayi tunanin Farouk ko Fahad sune zasu samu irin wannan abun se gashi wanda na raina shine ya samu. Tashi kije ki kira mani shi, bara inkira Hauwa itama taji abin arziki.

Zaune suke hada sauran yaran da yake kowa yazo hutu, Mama tace wai Malan wane irin abun farin ciki ne ya samu haka naga kayi mana kiran gaggawa? Malan yace kede bari sauran suzo zakiji komai.

Da sallama Inne dasu Faisal suka shigo, gefe guda suka samu shida Fatima suka zauna. Fahad ne cikin zolaya yace waini Faisal kaje Interview din makarantar ku? Kallonshi Faisal yayi fuskarshi babu walwala bece mashi komai ba.

Farida tace makarantarsu ai yawa garesu, Fahad yace emana wancan karin da mukaje seda aka gama mana sanna akayi masu kunga yawansu yama za'ayi su iya karatu da wannan yawan.

Murmushi Mama tayi tace kai ku kam bakwajin magana, dama yaza'ayi ku hada makarantarku da tasu, ai akwai banbaci. Malan yayi murmushi yace ya isa, kallon Faisal yayi yace matso nan yau ai kaine atsakiya domin kaine za'a karrama.

Cike da mamaki Mama da yaranta suke kallon Malan, tashi Faisal yayi ya matsa tsakiya sede har yanzu babu alamun fara'a a fuskarshi. Malan ya daga takardar hannunshi sama yana fadin wannan takardar Scholarship ce ta Faisal.

Yana daya daga cikin yaran da sukaje Katsina yin jarabawar da gwamnati take shiryawa duk shekara, dama kuma wannan jarabawa yaran da suke karatu amakarantar gwamnati kadai ake daukar sunansu.

Wannan dalilin ne yasa Head master dinsu ya bada sunan Faisal, danni bam masan yashiga aji 6 ba, a tunanina yanzu ne zeshiga, to ashe malaminsu yamaidashi aji shidda.

Lokacin da Head master ya aiko mani da maganar zuwa jarabawar nace ni ba ruwana nasan Faisal bawani ci zeyi ba, se gashi cikin ikon Allah yasamu wannan jarabawa, yanzu haka gwamnati ta dauki nauyin karatunshi tun daga Secondary har zuwa jami'a idan har yaci jarabawar gama SS3 to itace zata biyamashi zuwa jami'a.

Kuma a Abuja ne makarantar take, wannna babban abun farin ciki ne ace acikin gidana yarona yasamu wannan makaranta. Kallon Faisal yayi yace ku nawa ne kukaci wanna jarabawar a garin nan?

Dukar da kai Faisal yayi yace mu 2 ne, nida dan gidan Baba Labaran Nura. Jinjina mai Malan yayi yace da kyau, Allah ya baku sa'a, gaskiya naji matukar dadin da bantaba jinshi ba. Dole ayi maka babbar kyauta wadda ba'a taba yima wani ba.

Jikin Mama kamar wadda aka watsa ma ruwa, gaba daya zufa ce take keto mata duk da fankar datake aiki afalon. Haka fuskar sauran yaran gaba daya ta canza.

Kallon Mama Malan yayi yana fadin kinji dalilin da yasa na taraku nan. Ajiyar zuciya ta saki tare da kirkiro murmushi tace kai gaskiya naji matukar dadi da wannan labari. Ashe dama Faisal zeyi kokari haka ba musani ba.

Ni na tabbata da ace su Faouk a makarantar su suke babu abinda ze hana basuci wannan jarabawa ba, kaga da ance yan gidan nan sun zama yan baiwa, da su 3 ne zasu tafi Abujar. Lallai yakamata amaida Farida can domin nasan za'a bada sunanta.

Kallonta kawai Inne takeyi cike da mamaki, duk wanda yaji maganarta yasan hassadace kawai aciki, ganin Malan yayi shiru yasa tayi saurin canza magana da fadin gaskiya mune zamuje mu kaishi har makarantarsu.

Ai dole ashirya mashi dan karamin Party. Murmushi Malan yasaki jin abinda tace. Kallon Faisal yayi yace Faisal fada mani duk abinda kakeso in baka amatsayin kyauta ta? Kara dukar da kai Faisal yayi wahaye suna zubo mashi.

Malan yace fadi duk abinda kakeso kaji, tashi Faisal yayi yace babu abinda nakeso, fita yayi da sauri yana kuka. Tashi Fatima tayi tabi bayanshi itama, sakin baki Malan yayi yana kallon kofar da suka fita.

Kamar Mama zatayi dariya ganin abinda sukayi mashi. Cikin salon yaudara tace kai lallai Faisal wanna duk farin ciki ne haka, kasan dole yayi farin ciki dan betaba tunanin wannan ranar zatazo ba.

Kabarshi nafiso mubashi mamaki kawai asiyo mashi kyauta. Jinjina kai Malan yayi yace haka ne, shikenan zaku iya tafiya. Tashi yaran Mama sukayi cike da bacin rai suka fita. Malan yace kawo mani ruwa, komawa yayi ya kwanta sede har yanzu yanajin wani iri azuciyarshi.


Zaune Mama take da yaranta Fahad hada kukanshi, Farouk ne yace to kai meye na kuka? Dan Faisal yaci makarantar Abuja ai bawani abu bane, kaima alokacin da aka maidashi waccan makarantar ai da kace kanaso, amma sekazo kana mana kuka.

Kaida yakamata ace ka tayashi murna ma. Mama tace dalla rufe mani baki, kai dama ai haka zakace, kaida yake bakada kishi, duk cikin ku babu wanda zeyi irin makarantar da Faisal zeyi amma kake fadar haka.


Ku barshi idan ma head master dinsu ne yasaka sunanshi bawani ci yayi ba ai za'a gane, domin wannan makarantar tamasu kokarice, duk wanda ya fadi korarshi sukeyi, kuma kun san Faisal beda kokarin dazeyi waccan makarantar.

Muna nan zamuga ankoroshi. Fahad yace insha Allah Mama se ankoroshi ma, Farida tace Allah yasa, kuma Mama itama Fatima yanzu a islamiya baki gani ba tana kokari, jiya malamin mu har naira 20 yabata data bada amsa.

Mama tace kada kudamu ni nasan bazasu taba kamo ku ba, kuma ke Federal Daura zansa Malan ya kaiki ma. Dariya Farida tayi tana fadin yauwa Mama, kinga nima zanyi makarantar 'yan gayu.

Mama tace kutashi kuje ku kwanta kada ku makara masallaci tunda yau Malan ba anan yake ba. Tashi sukayi suna fadin seda safe. Mama ta dade zaune tana tunanin yanda akayi Faisal yaci wannan makarantar, kode tasa Malan ya maida Farida makarantarsu.

Kai kawayenta dariya zasuyi mata, amma ba komai zanje wajen Maman Sultan in nemi shawara, tashi tayi tana fadin Allah kasa yana zuwa akoroshi.


Washe gari da safe bayan Malan ya fita Inne ta kira yaranta, bayan sunzo ta kalli Fatima tace wayace kisa sunana ajikin littafinki na Islamiya? Dukar da kai tayi kasa tana ciccira idanuwa kamar zatayi kuka.

Kamo hannunta Inne tayi tana fadin niba dukanki zanyi ba, amma jiya Malan yagani kuma ranshi yabaci, meyasa kikayi haka, ba kisan ba'a canza sunan Uba ba? Hawaye ne suka zubo ma Fatima.

Inne tace a littafin bokon ki ma kin canza? Grigiza kai tayi, Inne tace yauwa kinaji ko, kidauko littafin da kikasan kin canza sunan ki gyara, kin taba ganin wanda aka kirashi da sunan mace? Kinaso kawayenki surika maki dariya suna cewa bakida Baba? Girgiza kai ta karayi.

Inne tace kidena kinji, Malan yana sonku, gashima jiya kinji yace ze saima Yayanki babbar kyauta, kuma ai kinga yadena dukanku ko? Daga kai tayi, Inne tace to daga yau kada ki kara jin haushin shi, ko kinaso Allah yasaki wuta? Girgiza kai tayi.

Inne tace to kinyi alkawarin bazaki kara ba? Fatima tace amma Inne malan baya son mu, meyasa baya daukarmu amotarshi yana kaimu makaranta? Kullum baya wasa damu, kuma baya kallon jarabawarmu.

Gashi yana wasa dasu Farida, kuma yana kaisu makaranta amma mu baya kaimu, kuma su suna makarantar 'Yan gayu mu kuma seya ciremu, ai de Inne Allah ne be bamu kokarin ba ko? Kwallace ta cikama Inne ido.

Tabbas tasan Fatima yarinya ce, amma gashi tana rike da abinda akai masu, kamota tayi ta rungumeta tana fadin kidena wanna maganar. Fatima tace kuma a islamiyar mu na tambayi malamin mu meye hukuncin Baban da baya ma yaranshi wasa sede yayi ma wasu,

Dago kai Inne tayi tana kallonta, Fatima tace kinsan me yace mani? Cewa yayi Allah ya hana arika nuna bambanci acikin gida, kuma Allah ze kama duk wanda yake yin haka. Da aka tashi shine malamin yakirani yace mun a ina naga Baban da beyi ma yaranshi wasa.

Shine nace mashi Malan ne baya mana wasa kuma baya bamu kyauta. Rike baki Inne tayi jin abinda Fatima tace. Faisal yace ki kyale Malan kinji muma idan muka girma lokacin ya tsufa baza mu rika bashi komai ba.

Kuma naji dadi dan Head master yace babu abinda iyayenmu zasu siya mana komai gwamnati ce zatayi mana, kinga base Malan yakara kashe mani komai ba, shiyasa dazu nace bana son komai, ai de Inne ada baya bamu komai.

Kuma malamin mu yace duk wanda beyi maka wani abu dan Allah ba duk ranar daya baka saboda wani dalili kada ka karba. Hawaye ne sosai suke zubo ma Inne, ashe dama yaranta suna kullace da Malan? Dama irin wannan ranar take mashi gudu.

Yanzu ma kenan, Allah yasoshi basu gama girma ba, da ace har girmansu yana masu haka da ba'asan me zasuyi ba, amma tasan dasun girma zasu manta komai, domin zuwa lokacin tasan Malan ya gyara kuskurenshi.

Goge idonta tayi tace Faisal kada in karajin kafadi haka, kuma inaso daga yau kada ku kara tambayar kowa akan abinda Malan yayi maku, yanzu komai ya wuce daga yau zakuga canji awajenshi, dama yana maku haka ne saboda kuji haushi kuyi kokari, kuma gashinan yanzu kunji haushi kunyi kokarin.

Faisal ya goge kwallar data zubo mashi yace amma Inne ai malamin mu yace ba dole se an hora mutum yake kokari ba, kuma ni ba saboda Malan nayi kokari ba, saboda ke nayi kokari, kuma idan naje makarantar kawana ma saboda ke zan cigaba da kokari.

Komai zanyi saboda ke zanyi, nima amakaranta seda na tambayi malamin mu idan ana maida sunan Mama acire na Baba yace mani ba'ayi da tuni na maida sunanki. Idanuwa kawai Inne ta tsura mashi, abun yadena bata mamaki ya koma bata tsoro.

Tashi tayi tana fadin kuje kuyi aikin islamiyarku bari inje gidan Momyn Teemah indawo. Hada baki sukayi wajen fadin sekin dawo.

Tana fita ta hangi Mama tashiga gidan Maman Sultan, murmushi tayi dan tasan dama dole yau taje wajen Maman Sultan domin itace kawar shawararta aduk lowcost dinsu, shiyasa sam bata hudda da ita.

Duk da sunfi mutane da yawa dadewa a unguwar amma bada kowa take hudda ba, asalima kawayenta biyu,daga Salamatu se wata amarya da aka kawo bata dade sosai ba a unguwar sunanta Farida diyarta daya me suna Fatima ana ce mata Teemah.

Itama ko wata 5 batayi da haihuwa ba, ganin yanda takema su Faisal da Fatima kirki yasa Inne take kulata, kuma ko tazo gidanta bata kawo mata gulmar kowa, hakan yasa Inne tasaki jiki da ita, duk da tagirmeta amma tana neman shawara awajenta dan ance ba girma bane tunani.

Shiyasa take neman shawara awajenta domin duk tafi matan unguwar ilimin boko gashi taga tashiga islamiya kuma bata shiga gidan kowa se idan wani abu yafaru. Hakan yasa su biyu kadai take neman shawara a wajensu.

Bayan sun gama gaisawa da Momyn Teemah Inne tafada mata abubuwan da suka faru da yanda yaranta suka kullaci Malan. Momyn Teemah tace ai gaskiya abun da ciwo, yaro ma kenan, inaga ace babba ne akema wannan abun.

Allah yaso  Malan din yafara fahimtar illar abinda yakeyi da seyayi kuka da idonshi nan gaba, amma tunda yara ne ai da sauki, yanzu ne zasu fara sanin meye duniya tunda yanzu ne ita Fatima zata shiga aji 6 ko? Inne tace aji biyar de,  Farida ce zata shiga aji 6.

Momyn Teemah tace niko meze hana kije kisamu Head master dinsu ya maida Fatima aji 6 tunda de kince yanzu tana gane karatu. Kinga se sutafi J.S.S 1 tare da Farida domin wani yaron yana girma yana kara kokari, kila idan tashiga Secondary kokarinta yakaru.

Inne tace shikenan zanje insameshi, nima banaso kowa yatafi boarding abarta ita kadai agida. Amma wallahi Momyn Teemah wannan abun yafara damuna, da kin kalli idanuwan yaran zakisan da gaske suke sunajin haushin abinda Malan yayi masu.

Momyn Teemah tace kada kidamu ai yara ne, zasu manta komai, kuma nasan shima Malan din yanzu zerika jansu ajiki, kuma Inne ki kara daurewa kamar yanda Mama take tura yaranta jikin Malan kema kirikayi.

Idan ma ance na ganin idon ne ba komai, idan zasu tafi masallaci surika jiranshi suna tafiya tare, hakan zesa yasan cewar suna zuwa suma, kuma idan aiki ne kirika barin yana ganin lokacin da sukeyi, tunda de shi haka yake kibishi ahaka se azauna lafiya.

Murmushi Inne tayi tace hakama Salamatu tace mani, amma zanyi kokarin yin abu daya, inde muna zaune zan rika kiransu suna zama kusa dashi. Amma abu biyu ne bazan iya ba. Bazan iya sasu surika aikin ganin ido ba.

Kinsan illar da hakan yake janyowa? Yanzu matukar malan baya gida to yaranta basa zuwa masallaci, duk wani abu da sukeyi idan yana nan basa yinshi, hatta da karatun Qur'anin da sukeyi idan yana gida basayi.

Yanzu de Farouk shine babbansu ko? Amma wallahi ba kowace sallah yakeyi ba, idan ma yayi maki to sede ya hada, amma idan akace maki Malan yana gida shine gaba wajen zuwa kofar falon Malan yana jiranshi.

Meye amfanin haka, yanzu ba boarding suka tafi ba, kinga yanzu ne zataga illar sasu suyi abu na ganin ido, domin shi yaro duk abinda ka koya mashi dashi yake tashi, Allah kadai yasan ko yanayin sallah biyar arana acan makarantarsu ma.

Ni kam banajin Faisal, wallahi yanzu bade kiji nace mashi yatafi masallaci ba, kinga kuwa ko yatafi makaranta banida fargaba, nasan duk inda yaje zeyi addini. Jinjina kai Momyn Teemah tayi tace kuma hakane.

Gaskiya naji dadin wannna bayani naki, kuma nagode da kika haska mani wannan abun, Allah yayi mana jagora, kuma kicigaba da nuna masu Malan yana sonsu nasan wata rana zasu manta da abubuwan da yayi masu. Inne tace nagode, bara in tafi indora abinci, agaishe da Teemah idan ta tashi.


Har Inne tazo shiga gida Mama da Maman Sultan suna kofar gidanta suna fira. Mama tace kin ganta can daga gidan momyn Teemah take, Maman Sultan tace dan Allah kalleta kamar ba mace ba, wani idan ya ganku seyace kece amaryar.

Daga haihuwa biyu mutum yafara tsufa. Dariya Mama tasa tana fadin bakida dama, bari intafi nasan malan yakusa dawowa, kuma nagode da shawararki, kawai zance abar Farida a makarantarsu inyaso se insashi ya kaita Federal din. Sallama tayi mata ta tafi.

***** *****

Bayan hutu yakare haka aka shirya kowa yatafi,  Malan yace ze maida Fatima makarantar su Farida tunda tana ganewa yanzu, Inne tace dan Allah kabarta acan, idan itama tana rabon zuwa makarantar su Faisal kaga ka huta.

Malan yace nide kibarni kawai, lokacin da Fatima taji kuka tasa tana fadin ita bataso, da Malan yaga da gaske take yace shikenan yabarta tunda tafison hakan .  Malan da Labaran suka dauki yaransu suka nufi Katsina dasu domin ance su kaisu daga can za'a kaisu makarantar. Faisal yasha kukan rabuwa da Inne da Fatima.

Sosai Inne tayi mashi nasiha tasashi kuma yashiga yayi ma Mama sallama, lokacin da yashiga bayan ya gaisheta ta kalleshi ta mutse fuska  tace idan ka dage subarka, idan kuma kayi masu jakkan cinka muna nan muna jiran dawowarka.

Agaida makaranta, juyawa yayi fuskarshi adaure kamar yanda yashiga yafito, bayanshi ta biyo har suka iso waje, kusa da Malan taje ta bashi  dubu daya  tana fadin gashi kasiya mashi wani abu na bashi yaki karba.

Murmushin jin dadi Malan yayi yace Faisal meyasa baka karba ba to? Kallonta kawai Faisal yayi bece komai ba, Malan yace gaskiya naji dadi, domin saboda ni kikayi haka kuma nagode, kallon Inne yayi yace kinga abinda tabashi.

Inne tace to angode, Malan yace kema se ki koyi haka daga gareta, zanji dadi inga kinyima yarana abun kirki, murmushi Inne tayi, domin ita bata taba bari yasan tana bamasu Fahad wani abu ba.

Duk da Mamar tasani amma itace ta hana su nuna mashi tana basu. Inne tace insha Allah zan koya. Haka suka tafi Faisal yana ta kuka. Lokacin da suka isa Katsina haka Malan yabashi kudi yace yarike. Faisal yace Malan kabarshi ance komai acan za'ayi mana.

Malan yace nasani ai, amma ai nine na baka, karba yayi yana fadin nagode, kallonshi Malan yayi yace wai meyasa bakason sakin jikinka dani, ko magana zakamun baka dariya meyasa Faisal? Dukar da kai yayi yace bakomai.

Malan yace to kadage kayi karatu, kaga yanzu ka girma bazan dokeka dan bakayi kokari ba, amma nasan abinda zanyi maka matukar ka kawo mani result marar kyau, kuma wannan makarantar korar mutum sukeyi idan baya kokari. Faisal yace to.

Haka yajuya yatafi ko kallon Malan beyi ba, bare yayi kuka, shi kuwa Yaron labaran Nura rungume Babanshi yayi yana kuka sosai harseda Labaran shima yayi kwalla yana lallashin shi.

Komawa gefe Faisal yayi yana kallonsu, Malan ma kallonsu yakeyi yana kara kallon yanda Faisal yakoma gefe ya daure fuska ko kallonshi ba yayi. Da kyar Labaran ya lallashi Nura suka tafi. Suna tafiya Nura yana juyowa yana kallon Babanshi, amma Faisal tunda ya juya bekara juyowa ba. Kwalla ce ta cika idon Malan.

Sosai yaji bejin dadin abinda Faisal yayi mashi ba, ka dafa maganar mutane ta tabbata na cewar rashin jan Faisal da Fatima ajiki da beyi ze iya dasa kiyayyarshi azuciyarsu? Saurin girgiza kai yayi aranshi yana fadin ba haka bane, yara ne su babu abinda suka sani. Haka suka juya suma suka tafi.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
馃彙馃彙 A WANI GIDA馃彙馃彙
          馃槶馃槶馃槶

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 [email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 25 鈴� 30

Kwance Malan yake a dakin Mama, sam yakasa bacci tunanin abinda Faisal yayi mashi kawai yakeyi, har a zuciyarshi yana tsoron kada Faisal ya saka tsanarshi a ranshi. Mama ce tashigo da kofin ruwa a hannunta.

Zama tayi gefen gadon tana fadin bade har ka kwanta tun yanzu ba? Tashi yayi ya jingina yace kawai ina hutawa ne naga kin dade baki kawo ruwan ba. Mama tace wallahi Farida na samu ta farka wai tsoro takeji shine na kai ta wajen Inne nace su kwana da Fatima.

Malan yace ai dama abinda yakamata kenan, duk lokacin da nake dakin wata to arika hada yaran waje daya suna kwanciya tunda yanzu gidan ya zama saura su biyu. Kallonshi Mama tayi tace wai ni Malan tunda kuka dawo daga Katsina nake ganin kamar kana cikin damuwa.

Malan yace wallahi wani abu ne yake damuna. Mama tace kamar mefa? ....... yanda suka rabu da Faisal ya fada mata. Mama tace to meye abun damuwa a nan? Malan yace inajin tsoro kada yaran nan su girma da bacin raina azuciyarsu.

Kina kallon Fatima kamar bani ne mahaifinta ba, duk wanda yashigo gidan nan idan yaga yanda nake sakewa dasu Fahad ze dauka su Faisal ba yarana bane. Rabon da inga Faisal ko Fatima sunyi mani dariya har na manta.

Duk lokacin da zasu zo wajena kamar sunzo wajen wani dodo, har kosawa suke su gama gaisheni su tafi. Gaskiya abun yana damuna sosai, kalli yanda Fatima ta dage sena barta a makarantarsu, kamar Fatima har tasan zuciya, ina jin tsoro wallahi.

Ruwan Mama tasa mashi abaki, seda ya shanye sannan ta hau saman gadon tare da kama hannunshi tana wasa dashi a hankali tana matsa mashi ya tsunshi, lumshe ido yayi bece komai ba.

Murmushi tayi tace na fada maka daga Faisal har Fatima basu da wayon da zasu rika maka irin wannna abubuwan, yanzu ko Farouk idan ya girma baze iya tuna abinda akayi mashi yana yaro ba, bare kuma su.

Wayonsu be kai ace sun san meye zuciya ba, sede kasan kowane Da yafi daukar maganar Uwarshi, duk yanda Uwa taso yaronta ya kasance haka yake kasancewa, domin Uba beda wani tasiri sosai awajen yaranshi.

Saboda a kashi 100 na yinin kullum Uwa ce take daukar kashi 80 da yaranta, Uba kuwa befi ya dauki kashi 10 a ciki ba, sauran goman kuma na malamisu ne. Kaga kuwa kowane irin yanayi Uwa takeso ta maida Danta zata iyayi.

Koda ace Uba yana sake sabon gini kullum hakan bazesa Uwa taki rushe nashi ta dora nata ba. Musamman idan akace Uwar tanajin haushin Uban. Dora kanshi tayi saman kafarta tana shafa mashi kan ahankali.

Murmushi ta kara saki tana fadin Malan kafi kowa sanin halin gidan nan, be kamata karika barin wani abu yana bata maka rai ba, Allah yasani ban dauki kowa da wani abu agidan nan ba, kome zanyi saboda kai na keyinshi domin kai ne ka kawoni gidan nan.

Kuma irin soyayyar da  mu kayi dole zan girmama duk wani abu da zaka dauko ka kawoshi gidan nan koda ace abun ze iya halaka ni inde yafito daga wajenka ne kuma kace kanaso in zauna dashi dole zanyi kokarin zama dashi lafiya.

Tunda kake so nawa kaga Inne tashigo bangare na? Nasan beda yawa, a tunaninka Inne zata iya yin abinda nayi ayanzu dan ka wai diyarta tana jin tsoro ta kasa bacci? Yanda na dauki Inne azuciyata nasan ba haka ta daukeni ba.

Kaga kuwa ina girmama ta tamkar itace uwargida, amma sam Inne bata gani, na tabbata bazaka iya kirga so nawa kana gani na a bangarenta ba. Haka kuma na dauki yaranta tamkar nawa, sede bansan dalilin da yasa sam Inne bata jan yarana ajiki ba.

Hannu tasa kamar tana share kwalla, ganin idonshi a kulle yake yasa ta danyi sheshsheka kamar tana kuka, saurin bude ido yayi takara dukar da kai tana fadin nima fa Uwace, zanso ace nima ana kula yarana hakan zemun dadi.

Saurin tashi yayi ya kamota yana fadin haba Hauwa, kinsan fa ba nason bacin ranki, yazaki rika bata hawayenki saboda wata banza can. Wallahi wannan maganar taki takara haska mani irin abubuwan da suke faruwa agidan nan wanda ni sam ban kula dasu ba.

Har kinsa Jamila ta kara fice mani arai, to meza'ayi da mutumin da kullum burinshi ya tar watsa maka gida. Maganarki gaskiya ce, tabbas tunanin su Fatima be kai ace suna mani irin wannan abun ba.

Amma ki barni da ita, dama na dade ina tarata, abinda Faisal yayi ne yasa ya wanke laifinta awajena, amma yanzu haushinta yadawo sabo azuciyata. Ba tasan dama kawai hakuri nake da ita ba.

Me ake da macen da batasan kwalliya ba, ita dama bawani kyau gareta ba amma tace ba zatayi kwalliya ba, masu kyan ma ya suka kare idan basuyi kwalliya ba, bare ita. Wallahi darajar yaranta kawai takeci ada, amma yanzu tunda naga alamar ta naso ta rabani da yarana tabbas zan dauki mataki.

Kwanciya Mama tayi asaman kafarshi tare da shafa fuskarshi tace ina bayanka Malan, idan baka dauki mataki da wuri ba tabbas nan gaba idan Faisal ya zama wani abu ko kallonka bazeyi ba, bare kuma yanzu yasamu wannan makaranta, kasan komai gwamnati ce zatayi mashi.

Me kake tunani duk ranar da akace ya gama karatun jami'arshi? Kasan dole gwamnati ta bashi aiki me tsoka, ni wallahi ba kowa nakeji ba se sauran 'Yan Uwanshi, sam banajin dadin yanda bata barinsu suna shiga cikinsu.
Kullum yarana suna hanyar zuwa bangarenta domin suyi fira sa yaranta amma suna shiga ko minti 5 basuyi se inga sun fito, idan na tambayesu se suce wai Inne tace su Faisal karatu sukeyi baza suyi wasa ba.

Ni ban taba sani ba ashe har waresu takeyi tana kaisu gidan Maman Saddik ana koya masu karatu, yanzu dan Allah idan nice zan ware yaranta in kai nawa? Haba Malan wannan wace irin kiyayyace Inne takemun? Kuka tasa sosai.

Malan da zuciyarshi take tafasa yace lallai rashin mutuncin Jamila ya wuce tunani na, kada kidamu zan kamata da hannuna, wallahi duk ranar da tabari na kamata tana aikata wani abu to tabbas daga ranar zamana da ita yazo karshe.

Cije lebe Mama tayi, sam ba haka taso ba, amma seta saki murmushi aranta tana fadin zako ka kamata kwanan nan. Tashi tayi tana fadin amma de ina fatan yanzu kacire damuwa akan abinda Faisal yayi maka ko? Murmushi Malan yayi yace ai idan kina kusa dani damuwa bata zama a zuciyata.

Mama tace nafiso gaba daya ta fitar maka, banaso idan baka kusa dani tadawo. Malan yace kar ki damu, na yarda da abinda kikace, da sun girma zasu manta da duk abinda ya faru, kuma idan har na sallami Uwarsu ai tarbiyarsu hannunki zata dawo, kinga kuwa dole zasu soni. Dariya tayi tana fadin nagode.

***** *****

Haka rayuwar gidansu ta cigaba da tafiya, Inne taje tayi ma Head master magana kuma yamaida Fatima aji 6, sosai yanzu take kara fahimtar abinda ake koya masu, gashi kuma duk alhamis da juma'a tana zuwa lesson, sam bata shiga bangaren Mama, haka kuma bata wasa da Farida.

Domin Farida kullum dariya take mata, haka kuma tasa kawayenta surika tsokanarta hakan yasa bata shiga wajensu, idan kaga Fatima tana wasa to da Amira ce, duk da ta girmeta da kadan amma haka suke wasansu kasancewarta me lalura.


Zaune Maman Saddik take tana yima Amira kitso, Saddik da Fatima suna wajen lesson domin yanzu su biyu kadai suka rage dan Mannir da Abba suna boarding kuma dukansu a police acadamy suke.

Mama ce tashigo da sallama, amsa mata maman Saddik tayi tana fadin kishigo, murmushi tasaki tana fadin Maman Farida ce? Mama tace wallahi kuwa nice, kwana biyu nace bari de yau inshigo mu gaisa.

Maman Saddik tace bismilla ga kujera. Bayan sun gama gaisawa Mama tace Amira 'yan mata kitso akeyi? Dariya Amira tayi tace ina wuni, Mama tace lafiya lau Amira ya makaranta? Tace lafiya lau.

Maman Saddik tace makaranta ko shiririta, ni banga abin sawa amakaranta wajan nan ba. Mama tace kuma har yanzu ba ta gane abinda ake koya mata? Tabe baki Maman Saddik tayi tace inafa ganewa, har yanzu fa ABCD zuwa karshe kawai ta iya rubutawa, amma bata iya rubuta maki kalmar data wuce 5.

To ba laifi yanzu ta iya rubuta sunanta dana Babanta, amma duk da haka gani nake asarar kudi kawai akeyi, su kuma yan makarantar da yake kudin sukeso sun kasa bama Babansu shawara akan yacireta.

Mama tace lallai kam, ina laifin ma ya maidata ta gwamnati, kinga ko shekara nawa zatayi bazaku damu ba, domin ba kudi ake badawa ba. Shiyasa fa lokacin dasu Faisal basa ganewa na bama Malan shawarar ya maidasu can.

Kinga gashi da yabi shawarata gashinan yanzu sun fara kokarin. Maman Saddik tace aiko Fatima da Faisal akwai kokari, ina jinsu ai idan ana masu karatu, kuma Malaminsu ma yana fadin kokarinsu da nutsuwarsu, shiyasa naji dadi da akace Faisal yasamu wannan makaranta.

Tabe baki mama tayi tace kema meze hana kibama Baban Saddik shawara ya maida Amira makarantar su Fatima, kinga kudin da ake biya mata sekuyi wani abun dasu, amma asarar tayi yawa.

Maman Saddik tace wallahi kema kin fada, duk da Amira diyata ce amma nasan haka Allah ya halicceta bazata taba fahimtar komai ba, tunda harni dana haifeta na hakura na zauna da ita yanda take mezesa shi baze hakura ba.


Nasha ganin irinsu wallahi babu abinda suke fahimta, wasu ma iyayensu ko makarantar gwamnatun basu saka su haka nan suke zaune agida. uhm kede Maman Farida ki godema Allah, wallahi duk macen da Allah ya jarabta da haihuwar irin su Amira tashiga 3.

Gashi ita kadaice mace, kinga kuwa ko aure irinsu basayi. Mama tace kinsan Allah dan de ke mijinki yasamu, amma idan Amira diyata ce babu inda zan bari akaita, karshe ma acan makarantar yara janta sukeyi haka nan amaida maki diya karamar mahaukaciya.

Sufa ba'aso ma arika matsama kwakwalwarsu, domin haka Allah yayisu da karamar kwakwalwa. Maman Saddik tace da gaske? Mama tace wallahi kuwa, idan kikayi wasa matsalar da zata samu nan gaba setafi ta wadda take ayanzu.

Mamam Saddik tace inko hakane daga yau Amira tadena zuwa makaranta. Mama tace gara de ki dage. Baban Saddik da tun dazu yake tsaye yana sauraronsu wanda basuji zuwanshi ba, kara hade rai yayi yashigo tare da sallama. Saurin tashi Mama tayi tana fadin kin ganni daga shigowa mu gaisa har da zama.

Baban Saddik ina wuni? Fuska a daure yace lafiya lau, wucewa ciki yayi be ko kalleta ba. Mama tace toni natafi tunda me gida yadawo. Maman Saddik tace to nagode ki gaida gida sena shigo. Mama tace aike baki shiga gidan mutane, shiyasa ma yau nace bari in leko. Maman Saddik tace wallahi zanzo ai naji dadin wannna shawara taki. Ki gaida gida.

Bayan Mama ta tafi Baban Saddik yafito fuskarshi a daure, kallonshi Maman Saddik tayi tana fadin sannu da zuwa, yau naga kadawo da wuri. Zama yayi yana fadin daga yau bana son in kara ganin kafar wannan matar agidan nan.

Duk fadin Quarters din nan babu wanda besan halin ta ba. Kuma duk naji firar da kukayi, idan har kina ganin zaki gwada abinda tace maki to bismillah, amma kisani niba Malan bane, kuma ni babu macen data isa ta juyani.

Shiyasa nayi kokarin tsayawa da kafafuwana kuma na tsare hakkin iyalina, dan haka idan kinji zaki kulla kawance da ita ga fili ga me doki. Ni kuma zan nuna maki asalin waye ni. Kada kiga ina zama cikin gida ina sakin fuska muna yin wasa da dariya nida ke da yara.

Ina yin hakan ne badan komai ba sedan banaso gidana yazama kamar nawasu, wadan da gida jensu yake zama kamar gidan makoki a kullum, idan kinga suna dariya to sun fita waje ne.

Ni kuma tsarina ba haka yake ba, banaso kamar yanda nataso bansan farin cikin iyaye ba suma yarana su tashi haka, domin haka na tashi bansan iyaye na ba, kinga kuwa dole zanyi duk abinda zesa yarana farin ciki.

Kuma inaso gidana akoda yaushe yazamo cikin farin ciki hakan zesa yarana su saki jiki dani ta yanda baza suji tsoron yimani kowace irin tambaya ba, kuma bazasu kasa fada mani damuwarsu ba.

Haka kuma banaso na zama daya daga cikin irin mazajen da suke daure fuskarsu a wajen matayensu, idan suna dariya sede da matan waje. Wannan dalilin shine yasa kika ga ban cika yin fada agidana ba.

Kuma kema sheda ce, bawai dan bakya mun laifi ba, inayin hakan ne dan in kawo zaman lafiya, amma na tabbata aranki kina dauka kamar tsoronki nakeji. To bari kiji, duk da kece kika haifi yaran nan wallahi bazan bari ki kawo wani abu daze tabasu ba.

Kome zaki mun zan iya hakuri amma mutuncin yarana, iliminsu bazan lamunci hakan ba. Mamana nasan haka Allah yayi ta, amma da yayita haka ai AMANARTA yabamu, kuma bece mu nuna banbanci a tsakaninta da sauran yaran ba.

Da ace lalurarta ta kai ta yanda bazata iya magana ba, ko kuma bazata iya tafiya ba shine zamu ajeta agida, amma mu gode ma Allah lalurar me sauki ce, idan Allah yaso wata rana zata iya warkewa.

Idan muka dan kwafeta agida yakikeso rayuwarta ta kasance? Ai abun zeyi mata zafi. Ko da ace shiga aji kawai take bata koyon karatu zama cikin yara ya isa ya dauke mata wata  kewar.

Kamar yanda zan kashema Saddika kwabo ita ma haka zan kashe mata, idan ke kina ganin asara nakeyi ni kuma nasan riba nakeci domin yau ko iya sunanta kawai ta iya rubutawa har ta mutu bazanyi bakin ciki ba.

Domin duk inda tashiga zata iya rike biro kuma ta rubuta sunanta, kinga kuwa wannan kadai abin alfahari ne. Bare kuma Mamana ta wuce rubuta sunanta, tunda zata iya rubuta duka 26 alphabet sannan tasan 1234, kinga ai naci riba.


Na dauka nine zanyi irin abinda kikeyi, kasancewar duk wata Uwa tana bala'in son duk abinda yafito daga jikinta ko da ace Kadangare ne, se gashi ke kwata kwata baki son cigaban diyarki, da ace yau bake kika haifi Mamana ba wallahi da tuni mun rabu.

Kuma wallahi bazanyi kaffara ba, ko duniya muka haifa dake idan har kikace shawarar waccan matar zaki rika dauka zamu rabu dake, kuma daga yau idan har kika sa kafa kika fita kikaje wajenta zakiga abinda ze faru.

Idan da dayar matar zakiyi mutunci ban hanaki ba, amma koda kinje gidan idan kikaje bangarenta zaki sani. Tashi yayi yafita be tsaya jin abinda zata fada ba. Hannu Maman Saddik tasa ta goge idonta tana fadin kaji mani mata zatazo tasa inshiga 3.

Tunda nake da Baban Saddik be taba yi mani fada ba, amma gashi ta dalilinta yau yana fadin zamu rabu. Idan ko hakane daga yanzu na yanke alaka da ita, dama can bayi nake ba, yau ne data shigo zata kawo mani jaraba.

Kan Amira ta shafa tana fadin kiyafe mani kinji, naso inyi wauta, bansan duk yanda Allah yayi mutum ba akwai wata baiwa da ke boyewa ajikinshi. Allah ya baki lafiya kuma yakara maki budi a kwakwalwarki, insha Allah daga yanzu bazan kara fadar abu marar kyau agareki ba, domin nasan bakina ze iya tasiri akanki.

Da ace tunda na haifeki ina fadar alkhairi akanki kila da yanzu kinfi haka, Allah ka yafe mani nagode da wannan kyautar  da kayi mani, nasan wasu suna neman haihuwar ma basu samu ba, amma gashi ka bani ina rai nawa.

*** ***

Tun daga wannan rana Maman Saddik ta fita harkar Mama, ko haduwa sukayi akan hanya sede su gaisa amma bata tsayawa suyi fira, haka kuma bata sakar mata fuska, akwai lokacin data kara zuwa, Maman Saddik tana jin itace tashige daki, haka Mama tayi ta sallama ta kyaleta.

Kuma tasamu Baban Saddik ta bashi hakuri, kuma yaji dadin abinda tayi damashi bame riko bane, hakan yasa ya yafe mata.

 Tun daga lokacin takara dagewa wajen koyama Amira karatu, wanda ada ko littafinta bata dubawa, ko home work aka bata sede tasa Saddik yayi mata. Kuma ahakan Amira takara fahimtar abinda Mamanta take koya mata.

***** ******

Faisal kuwa yana matukar fahimtar abinda ake koya masu, dan yanzu yana cikin masu kokarin ajin, sam beda hayaniya, abokinshi daya Nura, koda yaushe yana duba abinda ake koya masu, domin yariga daya kudurci seyayi kokari badan komai ba saboda Inne.

Haka kuma jam'i baya wuceshi, ko wa'azi akeyi zaka sameshi shine agaba, idan beda aiki da wuri yake zuwa masallaci yayi shara, duk da akwai masuyi amma yana zuwa yayi domin yasamu lada. Faisal yana da gaskiya, hakan yasa malamai suke sonshi, kuma sauran seniors ma suke son shi, domin shi be yarda da yayi karya ba dan aso shi, kome zeyi iya gaskiyarshi yakeyi koda kuwa za'a bigeshi ne.

Duk abinda be gane ba har office yakebin malaminsu yana kara tambayarshi, wanna abun da yakeyi sosai yasa yashiga ran malamansu. Idan abokansu suna zaune suna firar gida kowa zakaji yana fadin Babana kaza, Dady na Kaza, Abbana Kaza, Momy na Kaza, amma banda Faisal.

Idan ka ji yana labarin gida to mutum biyu yake ambata, daga Inne se Fatima, abokansu har sun ganeshi. Wata rana suna zaune suna fira shi kuma yana daga gefe yana assignment wani dan ajinsu me suna Salim wanda yakasance dan Katsina ne yace Faisal yau baza ayi mana firar Fatima da Inne ba? Dariya sauran abokan sukayi.

Murmushi Faisal yayi yacigaba da rubutunshi, dama bawani shiga firarsu yake ba se idan yana cikin raha. Matsawa Salim yayi yana fadin dan Allah kayi mana firar Fatima da Inne. Faisal yace Salim wai meyasa kacika zolaya ne? Salim yace e naji nide kazo kayi mana fira.

Kai kullum idan muna labari bakason kashigo. Wani yace amma Faisal meyasa mu muna fadar labarin Baban mu amma kai baka fada ko Babanka ya rasu ne? Nura yace yana nan me kuka gani? Salim yace amma ai bamu taba jin ya ce Babanshi ba.

Nura yace kude kun cika shirme, ina ruwanku da Babanshi, to idan baku sani ba, Babanshi Principal ne, kuma ya iya koyawa sosai, kuma yana matukar son yaranshi. Dago kai Faisal yayi yana kallon Nura fuska adaure.

Dariya Nura yasa yana fadin nayi shiru, Salim yace ai de yau munji labarin Babanka, dariya sukasa wani yace kutashi mutafi kwallo.
 Tashi sukayi suka fita da gudu, Nura yace Faisal zo muje kallon kwallo, Faisal yace bazani ba, kaje kawai. Bayan Nura yatafi Faisal ya goge kwallar data zubo mashi.

Rufe littafin da yake rubutu aciki yayi, tagumi yayi yana fadin Allah sarki Inne da Fatima yanzu kome sukeyi ma? Kara goge kwallar yayi yana fadin kowa Babanshi yana sonshi amma banda mu. Allah kabani kokari me yawa nima Malan ya gane ba jaki bane.

*** ****

A makarantarsu Farouk da Fahad kuwa yanzu sam basa maida hankali wajen karatu, Farouk yafi maida hankali wajen koyon dinkin hula da wasu 'yan ajinsu sukeyi, duk da yana fahimtar abinda ake koya masu amma yanzu be cika zama yayi karatu sosai ba.

 Amma ya iya dinka hula sosai, kuma duk wani gyara yana yinshi, wannan abun da yakeyi shine yake dauke mashi hankali awajen karatu. Haka kuma sam bedamu dayin sallah ba, idan kaga yayi sallah a masallaci sede idan kora akayi.


Fahad kuwa in banda wasa babu abinda yakeyi, gashi abokanshi duk yaran masu kudi ne, koda yaushe idan ba'a aji to suna wajen kwallo, ko assignment aka basu basayi sede su saci na wanda yayi su kwafa, yana cikin 'yan iskan ajinsu sam basa jin magana. Maganar ibada ma se sunga dama sukeyi.

*** ****

Mama ce ta shigo bangaren Inne da dare, tana zuwa tace Inne naga yau kece da girki, to kisani yau Fatima bazata kwana dakina ba, kamar yanda Malan yace murika yi, ada de nabarta tana kwana amma yau gaskiya sede kibarta anan ta kwana domin fitsari take mani.

Inne tace Fatimar ce take fitsarin kwance? Ai ko tunda na yaye Fatima bata fitsari sede bacin rana, kuma dama can ni bana son zuwan da takeyi, ada da take kwanciyarta ita kadai meya sameta? Dama kece kika kawo wannan shawarar saboda wani dalili naki na daban.

To kisani bafa tsoronki nakeji ba, daga yau Fatima ta dena zuwa dakinki ta kwana. Juyawa Mama tayi jin alamar tafiya, kuma ta tabbata Malan ne dama saboda shi tazo gurin Inne.

Kasa Mama tayi da murya tana fadin yanzu Inne ni kike fadama dama bakiso Fatima tana zuwa dakina kwana? Inne da zuciyarta ta gama baci tace e nafada, nafa san duk irin abubuwan da kikeyi, kuma ba tsoro bane yasa nakeyin shiru.

Kawai banason fitina ne, hakan yasa banason yarana suna zuwa bangarenki domin banaso su koyo irin halin banzanki, tunda aka waremu acikin gidan nan nida yarana, bakomai zamucigaba da zama haka, suma bazasu kara kallon kowa amatsayin dan uwa ba.

Idan suka zauna ahaka zasuyi rayuwa me kyau, amma ina amfanin wannan hali na wannan gidan, wallahi nayi dana sanin auren mijinki, kun shayar dani bakinci amma kusani 'ya'ya na bazasu sha wannna bakin cikin ba.

Kuma daga yau Fatima tadena leka kofar dakinki bare taje ta kwana. Kuka Mama tasa tana fadin shikenan, Allah yaga abinda nayi maki, idan har kince nayi maki wani abu to yana gani. Dama kuma ai ba nice nace surika kwana tare ba, kawai umarni ne na bi.

Kuka sosai Mama takeyi, tsayawa Inne tayi tana kallon ikon Allah, matar data shigo mata da bala'i amma itace take kuka haka, to kode wani munafurcin ta shirya mata? Kafin ta bama kanta amsa taga Malan a tsaye ya hade hannuwanshi akan kirjinshi fuskarshi a hade. Sautin kukanta takara ganin Malan ya bayyana. Jinjina kai Inne tayi yanzu ne ta gane dalilin da yasa Mama take kuka.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
馃彙馃彙 A WANI GIDA馃彙馃彙
          馃槶馃槶馃槶

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 [email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 30 鈴� 35

    Juyawa Inne tayi ta koma ciki ganin irin yanda Malan yake mata wani irin kallo. Murmushin mugunta Mama ta saki domin tasan tarkonta yakama kurciya. Juyawa tayi tana girgiza kai tare da goge ido.

Sam bata nuna taga zuwan Malan ba, domin shi yana tsaye ta wajen falonshi, ita kuma setabi ta hanyar da zata sada ta da bangarenta, tafiya take tana ta girgiza kai har  ta wuce Malan yana binta da kallon tausayi.

Cike da bacin rai ya shiga falon Inne, lokacin tana zaune  saurin dago kai tayi jin yanda Malan yashigo a fusace. Mikewa tayi tana kallonshi. Kallonta yayi tare da jan tsaki yace dama irin wannan ranar nake jira.

Na dade ina jin irin abubuwan munafuncinki na gidan nan amma bantaba ji da kunne na ba se yau. Kuma dama na dade da yanke maki hukunci akan duk lokacin da naji abubuwan da kike aikatawa da kunnena.

Kin dade kina cutar da rayuwata a gidan nan, kin rabani da yarana, kin raba tsakaninsu da 'yan uwansu. To kisani duk wanda yaraba zumunci ranar lahira ze karbi hukuncinshi a hannunshi.

Kuma yarana da kika rabani dasu to kisani zasu iya barinki amma bazasu iya rabuwa dani ba. Domin nan gidansu ne, kefa? Gidanku yana Mashi, kinga tsakanin Mashi da Mani akwai tafiya dole kafin suzo wajenki se sun hau abun hawa.

Dago idanuwanta da sukayi ja tayi tana kallonshi, domin yanzu tafara fahimtar inda kalamanshi suka dosa. Juya baya yayi yana fadin kije na sake ki saki daya. Zabi yarage naki idan zakiyi amfani da koyarwar musulunci zaki iya zama dakinki ki gama iddar ki.

Idan kuma tafiya zakiyi wannna damuwarkice, kuma kisani kamar yanda na auroki ke daya haka zaki tafi kedaya, kibar mani yarana Allah yabani mata me kirki dazata iya zama dasu batare data raba kansu ba. Idan zaki zauna ni banida matsala.

Zan cigaba da ciyar dake kamar yanda nakeyi har ki gama kitafi. Tafiya ya farayi zebar dakin. Inne ta share idonta tace kafin katafi yakamata katsaya nima kaji abinda zan fada maka.

Da farko de ni bana bakin ciki da sakin da kayi mani. Domin shi aure da kake ganinshi rai ne dashi, duk lokacin da kaga an rabu to Allah ne yasa lokacin rabuwar yazo, domin babu wani abu dayake faruwa a duniya batare da sanin Allah ba.

Kuma shine yake bada iko akan komai. Duk da nasan haka manzon Allah yace muzauna agidajen mazajenmu muyi Iddah, amma ni bazan iya zama ba, gara intafi ko zakaji dadin zama tare da yaranka  kuma ka saka masu sonka azuciyarka.

Idan har abinda kafada gaskiya ne, ina me tabbatar maka wata rana gaskiya zatayi halinta, kuma idan har nice nake kokarin rabaka da yaranka idan natafi zaka gane hakan. Kuma ni bana bakin cikin barin yarana.

Domin duk inda suke nasan bazasu taba mantawa dani ba, kuma duk inda nake addu'ata zata iso masu. Allah yabaku zaman lafiya, kuma Allah yakara hada kansu fiye da komai.

Daga karshe kuma inaso ka rubuta sakin da kamun atakarda domin yazama sheda. Tsaki Malan yaja yana fadin aikin banza, fita yayi ya nufi dakinshi, be dade ba yadawo takarda dauke a hannunshi.

Wurga mata yayi yana fadin ki kwashe komai naki domin banaso kiyi tunanin zan maidoki gidana, dan wannan  dakin yarana maza zasu koma. Fita yayi yana kumfar baki. Zama Inne tayi tana wani irin kuka.

Ita sam sakin be bata mata rai ba, yanda yaranta zasu cigaba da rayuwa da wannan matar shine yake damunta. Tabbas tasan dole zasu fuskanci munafurci da kissa kala kala a wajen Mama.

Gashi de su yara ne bazasu iya kaucema kaidin ta ba, duk yanda tayi dasu haka zasu tafi, shi kuma Malan ba mutum bane me tsananta bincike kafin ya yanke hukunci bare yarika gane kaidinta.

Tashi tayi tafara hada kayanta acikin akwatinan ta, domin bazata bar komai nata ba, koda cokali tace bazata bari ba tunda yace yana da matar da zata zauna dasu tabasu kayanta. Katifa ce daya zata bari itama saboda Faisal zata barta.

Ta dauki lokaci kafin tagama hada kayanta, kayan Fatima tasa mata cikin akwati guda, shima Faisal ta hada mashi nashi kayan, rufe kofar dakinta tayi tafita ta nufi gidan Momyn Teemah.

Kuka kawai Momyn Teema takeyi data gama jin labarin da Inne ta fada mata, itama Innen kukan takeyi, Salamatu ce tashigo domin Inne tayi mata waya akan su hadu gidan Momyn Teemah.

Sosai itama tashiga tashin hankali dataji abinda yafaru da Inne. Salamatu tace lallai wannan mata Kaidinta yana da girma, me take nema a wannan duniyar dazata rabaki da yaranki da gidan mijinki?  Sekace anfada mata cewar zata dauwama a duniyar.

Dan Allah Inne kiyi hakuri, kada kibari wannan abun yashiga zuciyarki ya hanaki zaman lafiya arayuwarki,nasan yanda ciwon rabuwa da yara yake, dole sekin daure, kidauka yaranki kamar sun tafi wata makaranta ce me nisa.

Duk ranar da Allah yasa suka tsaya da kafafuwansu wallahi base kin nemesu ba, kuma base wani Malan yace suzo ba. musamman idan aka ce maki Faisal, alokacin daze girma ze iya daukarki yamaidoki kusa dashi.

A ranar da Malan beda ikon daze iya hanashi, haka kuma Fatima, daga ranar data bar hannun Malan daga ranar tazama taki, domin setazo wajenki so 3 bataje wajen Malan so daya ba.

Allah yabaki ikon hakuri da wannan al'amarin, kome Maman Farida zatayi ma yaranki tamkar tana horar dasu ne, domin wuya bata kisa, nasan karshen wahalar dazata basu bata wuce duk wani aikin gida ya koma kansu ba.

Kuma ma ai boarding Faisal yake, itama Fatimar ta kusa tafiya, zamansu agida se idan sun dawo hutu ne. Kada kidamu da duk abinda zatayi masu, wata rana setayi kuka da idonta.

Momyn Teemah tace wannan haka yake, idan kikayi hakuri wata rana zakiyi farin ciki, hakuri shine yakeda wahala, amma da mutum yayishi shikenan, kuma insha Allah yaranki zasu daukaka.

Kuma Malan seyayi kuka da idonshi tunda bakida hakkinshi, idan kuma yana ganin rabaki da yaranki shine zesa yaranshi su so shi ze gani, kuma Inne dan Allah inaso kamar yanda Malan yace kada kisa ran ze maidoki inaso idan kinsamu miji kiyi aure dan Allah.

Inne tace nikam bazan kara aure ba. Salamatu tace kada kice haka, domin kuwa duk namijin daya saki matarshi babu abinda ya tsana kamar ace tasamu miji tayi aure. Idan kikace baza kiyi aure ba gani zeyi kamar jiranshi kikeyi.

Nasan kowace Uwa bataso taraba kan Yaranta, amma wani lokacin dole takesa ayi haka, amma nide shawarata dan Allah idan kin samu miji kiyi aure, domin alokacin ne Malan ze gane bashi kike jira ba.

Share kwalla Inne tayi tace shikenan naji shawararku, kuma bazanki daukarta ba, domin duk unguwar nan kune kadai abokan shawarata. Ga yarana nan duk abinda sukayi ba dede ba dan Allah ku tsawatar masu.

Salamatu tace wannan base kin fada ba, Allah yabamu ikon rikesu. Momyn Teemah tace amin. Inne tace bari inje insamu akira mani me mota in dauki shata ya kai ni gida, sauran kayan nawa zuwa gobe za'a turo motar daukar kaya ta kwasar mani.

Sun sha kukan rabuwa, domin sun saba da juna, haka Inne ta fita tana kuka, tana shiga gida Fatima tashigo ta dawo daga lesson dan karfe 6 na yamma tayi, tana zuwa tace Inne sannu da aiki. Inne tace yauwa Fatima har kungama lesson din? Fatima tace mun gama Inne.

Daki tashiga domin ta cire hijabinta kuma ta aje littafinta, saurin fitowa tayi tana fadin Inne yanaga kin kwashe kayan falo dana dakin duk kin tadasu tsaye? Kwallace ta zubo ma Inne, Fatima tace ko wani gida zamu koma ne? Shiru Inne tayi batace mata komai ba.

Zama Fatima tayi kusa da ita, dukar da kanta tayi tana leken fuskar Inne dominta dukar da kanta. Fatima tace Inne waya dukeki kike kuka? Jawo Fatima Inne tayi ta rungume tare da sakin wani irin kuka.

Ashe dama haka kowace Uwa takeji idan zata rabu da yaranta? Na dauka yawancin matan da ake saki da suke haukan se an basu yaransu basu da aikin yine, ashe suna da gaskiya, su kadai suka san abinda sukeji aransu.

Ganin tayi shiru batace komai ba Fatima da itama ta fara kuka tace dan Allah Inne waya dukeki? Inne tace babu wanda ya dukeni Fatima, kawai zan tafi gidanmu ne. Fatima tace amma tare zamu tafi ko? Inne tace Fatima inaso ki bude kunnenki kiji abinda zan fada maki.

Ina ne gidanku? Fatima tace nan ne mana Inne. Inne tace ni ina ne gidan mu? Fatima tace yana Mashi. Inne tace da kyau, waye Babanki? Malan ne. Ni kuma waye Babana? Yana Mashi Baba tsoho ne.

To Fatima Malan yace in koma gidan mu da zama, yanaso keda Faisal kuzauna awajen Maman Farida, kuma daga yau wajen ta zaku koma, itace zata rika maku komai, hada abinci. Amma kece zaki rika wanka kamar yanda kikeyi anan.

Kuma inso kome ta saki ki rikayi kinji? Kai Fatima ta daga, Inne tace kuma kome tayi maki kada kisake ki fadama Malan, kiyi hakuri kinji, kinsan rannan kin fada mun malaminku yace duk me hakuri yana tare da Allah ko? Kai Fatima ta daga mata.

Inne tace to kome tayi maki ko su Farida kiyi hakuri, bana son rashin kunya, kuma ki rika maida hankali wajen karatunki, kuma kada kibari aiki yarika hanaki sallah kinji ko? Fatima tace naji, amma Inne yaushe zaki dawo? Murmushi Inne tayi tace bazan dawo ba Fatima.

Amma idan kunyi hutu nasan Malan zerika kai ku wajena. Fatima tace Inne itama Mama wata rana zata koma gidansu? Murmushi Inne tayi tana goge kwallar data zubo mata, hannun Fatima takama tana fadin nima bansani ba.

Kuma banaso kirika irin wannna maganar da kowa, haka kuma banaso kifadama kowa labarin cikin gidanku, duk wanda yake fadin labarin gidansu to sakarai ne, duk abinda akayi acikin gidanku ki barshi acikinki idan ba haka ba za'arika cewa ga Fatima me gulma.

Fatima tace babu ma wanda zan fada mawa, dama ni,bana bada labarin gidanmu. Inne tace yauwa, kuma duk wanda yakira ki acikin unguwar nan ya tambayeki abinda yafaru agidanku kice mashi kema baki sani ba, kome zece maki kice baki sani ba, idan ya matsa maki kice Allah ya hana gulma.

Haka Inne tayi ta yima Fatima nasiha cikin wayau da dabara har lokacin da me mashin yazo tare da me motar da tasa aka kira. Haka tarika daukar kayan tana aje mashi yana dauka ana sawa amota har suka gama.

Duk abinda sukeyi Mama tana labe tana ganinta, dariya kawai take mata, dan Malan tunda ya saki Inne yabar gidan. Fitowa Mama tayi tana dariya ta kalli Inne tace daman nafada maki, inde nice sekin bar mani mijina, domin bana kishi da irinku.

 Nasan yanzu kindauki darasin koyon zama da kishiya, nan gaba idan kinyi wani auren zaki iya daukar irin tsarina, domin zakiyi saurin kwace mijinki.

 Idan kuma akwai abinda yashige maki duhu nasan kina da numberta, kuma kinsan gidana zaki iya zuwa neman shawara. Kada kimanta dani wajen rabon alawa idan kinsamu wani mijin. Dariya tasa tana tafa hannu.

Inne kuwa ko kallonta batayi ba ta juya, Fatima se kallon Mama takeyi domin bata gane abinda take fada ba, amma de duk taji me tace, kuma sosai taji haushin yanda takema Inne dariya. Haka suka gama Inne nata kuka tace ma Fatima taje wajen Farida, itama Fatimar kuka kawai takeyi, haka su Inne suka tafi.

Fatima tana shiga wajen Mama ta sameta tana wata irin dariya, waje tasamu ta zauna tana share kwalla, Mama taja hannun Farida tana fadin kinga wadda bata zuwa wajenki yanzu tazo ko? Farida tace Mama ina Inne ta tafi to? Mama tace ta koma gidansu da zama.

Farida tace kema Mama zaki koma gidanku? Mama tace ni ina nan tare daku, itama laifi tayima Malan shiyasa yace ta tafi gidan Babanta, ni ko ai bana ma Malan laifi saboda haka ina nan tare daku.

Farida tace yanzu idan yaya Faisal yadawo shima nan ze dawo da zama? Mama tace ai yanzu ni kadaice Mamar kowa, amma tunda basu sonku ku ma baruwanku dasu. Ko kinason wanda be sona? Farida tace a'a.

Mama tace yauwa da kyau, yanzu kinga kinsamu wadda zata rika wanke maki safar makarantarki kuma tana tsefe maki kai ko? Farida tasa dariya tana fadin wallahi dama haushin wankin safa nakeyi.

Mama tace ai har pant dinki da kannan kayanki  duk itace zata rika wanke maku, damma kuna da me wanki da guga. Farida tace amma Mama batare zaki rika  samana abinci ba ko? Mama tace haba Farida, bafa daya kike da ita ba.

Idan kuna nan bazakuci abinci tare ba, amma Malan yace idan afalonshi zakuci asa maku tare. Farida tace to amma bazata hau mana gado ba. Mama tace akusa da gadon zata rika kwanciya. Tashi Fatima tayi tana kuka  jin ankira sallah.

Kallon Mama tayi tace Mama zanyi sallah, dariya Mama tayi tace ita uwarki bata bar kofarta abude bane? Fatima tace ta kulle kofar. Mama tace wuce kije kiyi ai nasan gobe zatazo ta kwashe kayanta wallahi can zaki koma kina amfani da bandakinta ba zakizo nan ki bata mani nawa ba.

Domin Uwarku gadon kazanta gareta nasan dole kunsha ajikinta. Wucewa ciki Fatima tayi tana kuka, Farida tace Mama kada Malan yazo ya sameta tana kuka fa. Mama tace ai se yayi isha'i ze dawo, kafin nan kuma kun kwanta. Tashi kije kidauko abinci kici.


Zaune Malan yake afalonshi yana cin abinci, mama tana zaune agefenshi, Malan yace inasu Fatima suke? Wani haushine yakama Mama, wato baze ce inasu Farida ba se wata Fatima.

Murmushi tayi tace ai suna cin abinci na barsu suna wasa ita da Farida, kasan Farida akwai son abokiyar wasa, yau ba kaga yanda take cikin farin ciki ba. Ita kanta Fatimar cikin farin ciki take, da ka ganta zaka gane yau tasamu sake.

Wasa sukeyi har bacci ya daukesu shine na tsaya gyara masu kwanciya asaman gadona nayi masu addu'a na rufo masu kofar dakin. Wallahi na dade rabon da naga farin ciki afuskar Farida irin na yau.

Shide yaro yana son yaga yana da abokin wasa, ita kanta Fatimar ba kaga yanda take wasa ba, araina nake cewa ashe dama Fatima tana dariya haka? Murmushin jin dadi Malan yayi yace ai dama na fada maki.

Suna matukar son shigowa cikin 'yan uwansu kawai munafuncin waccan matar ne, yau kadai jinake kamar ancire mani  kayar data shekara akafata. Me ake da irin Jamila, mace kamar wata Ku膽膽a.

A yanzu zansan ina rayuwa me dadi, amma da an maida mani yara kamar wadan da nake riko,tsakanina dasu iya gaisuwa ce. Yanzu ne zan gyara duk wani abu da aka sa masu azuciyarsu.

Ina me tabbatar maki tunda na rabasu da Uwarsu yanzu ne zasu so ni, kuma zasu cireta aransu, domin su duka yara ne, nagode Allah da yasa muka rabu da ita tun kafin su girma, dama abinda ba'aso ka rabu da mace yaranta suna manya.

Bazaka taba goge haushinka aransu ba, amma yanzu yara ne,kuma yaro baya rike abu me tsawo aranshi, kafin zuwa wani lokaci zasu manta da komai, kuma nasan zaki rikesu tamkar Farida. Mama tace kama dena fadar haka, ai ni babu abinda nakeso kamar ace anshigo gidan nan anrasa gane yarana.

Kaga Fatima da Farida kusan tare zasu tashi, sede Farida ta wuce Fatima da aji daya amma duk da haka babu nisa atsakaninsu, ina me tabbatar maka se mutane sun kasa gane ba uwarsu daya ba.

Haka ma Faisal da Fahad suma tare zasu tashi domin ajinsu daya, dan haka kama dena tunanin komai. Malan yace nagode maki, hakika kece matar aure, duk wanda ya sameki ya more. Kuma kiyi hakuri da irin cin mutuncin da Jamila tayi maki.

Mama tace haba ai komai ya wuce, dama nide fatana kai ka gane gaskiya kuma ka gane, kaga yanzu se mu bude sabuwar rayuwa. Malan yace wannan haka yake. Idan ta kwashe kayanta inaso in maida 'yan mazan can.

Tunda daki biyu ne se Faisal da Fahad su dauki daya, shi kuma Farouk tunda babba ne se ya dauki dayan, amma se kin rika kula da tsaftar bandakinsu kinsan halin maza. Mama tace haba kada kadamu ai ni yarana kasansu da tsafta, ko bance suyi ba zasuyi ne.

Yace nasan haka, dayan dakinki kuma se ki barma Farida da Fatima, zan siyo masu babbar katifa kinga kema kin rabu da yara adakinki, suma bandakinsu akula dashi dan kinsan na cikin daki ne, idan ba'a gyarawa da anshigo falon za'a gane.


Mama tace Malan kenan kamar kamanta wacece ni, kada kadamu akan yaranka, inde ina raye zakasha mamaki, amma suma mazan se ansaya masu katifa. Malan yace wannan badamuwa bane, kafin su dawo zan gyara masu komai. Mama tace Allah yabaka ikon yi, yace amin.

**** ****

Washe gari tunda safe Yayan Inne da wata yarta wadda take aure a Mashi sukazo da motar daukar kaya, suna zuwa suka shiga suka bude dakin, dama Inne duk tayi masu bayanin abubuwan da zasu dauka da wanda zasu bari, alokacin su Fatima suna makaranta.

Mama tana jinsu amma bata fito ba, haka suka gama kwashe komai suka bar mukullin kofar ajiki, har zasu fita Mama ta leko tana dariya tana fadin baiwar Allah ai yakamata kishigo mudan gaisa ko.

Koba komai ai zan rike maku yara yakamata arika bani girmana. Wani bakin ciki ne ya tur nike Yayar Inne, kallonta tayi tace kidena dariya domin wata rana wannan dariyar seta zamo maki kuka. Shewa Mama tayi tana fadin ai nida kuka har abada, tunda nayi kukan rashin iyayena kuma nagama.

Sede idan Malan ne akace ya mutu ko cikin yarana, gida kuma nacinyeshi, nida Malan mutu ka raba takalmin kaza, duk wani munafunci da kuka koya mata tazo ta saukeshi bataci riba ba, kuma zata girbeshi akan yaranta data koya mawa. Tsaki taja tashige ciki tana masu wakar habaici. Fita yayar tayi cike da bakin ciki suka tafi.


Tun daga wannan rana rayuwar Fatima ta canza, wahala kala kala Mama take bata, idan kaga tana janta ajiki to Malan yana gida, anan zakaga kamar zata goyata, ita de Fatima tarasa gane kan Mama.

Haka ma Farida take mata, idan Malan baya gida tayita hantararta, kuma basa cin abinci tare da rana sede da dare shima idan ranar Malan yadawo gida da wuri. Gashi bata kwanciya saman gado sede ashimfida mata wani tsohon zani ta kwanta.

Kuma kullum seta wanke ma Farida safarta, hatta da wondonta idan tayi wanka nan take barinshi itace zata wanke mata. Abinci kuwa ko bata koshi ba haka zata tashi, amma idan su biyu ne haka za'a cika masu kwano har su rage.

Duk yanda Malan yake janta ajiki har yanzu ta kasa sakin jikinta dashi, inde ze shigo gidan to se yasiyo masu tsaraba, yana matukar nuna damuwarshi akan Fatima. Wanna abunne yafara yima Mama ciwo.

Wato takashe maciji amma bata sare kan ba. Hakan yasa tasamu Malan tace mashi idan har kana yawan nuna ma yaran nan gata dayawa wallahi zasu rage kokarin da sukeyi. Yanzu fa Farida har zero ake samata a littafinta.

Wanda ada bata cin zero, amma yanzu saboda kanaso kajawo Fatima ajikinka gashi duk ka sangartasu. Ka sande banason in sangarta yarana, kuma duk abinda ake ma Fatimar har yanzu tana maka wani irin kallo.

Kasanfa wani lokacin yaro yana rike abinda babba baya rikewa, idan kana mata haka zataga ada bakayi mata ba se yanzu da mamarta bata nan, kuma kaga zata iya saka wani abu aranta, kazo kai baka gyara komai ba kuma asamu matsala.

Kawai kabarsu ni idan basa zaune kusa da kai ma nafi ganin suna sakewa, amma kaga Fatima ko dariya batayi idan suna falonka. Murmushi Malan yayi yace to yi hakuri uwar gida ran gida.

Duk yanda kikeso haka za ayi, ai nasan kina matukar kokari wajen kula dasu, kuma daga yau  nima zan gyara. Mama tace yauwa ko kaifa.

Haka Mama tasamu nasarar hana Malan kula Fatima itama Farida seta hanata zuwa wajenshi, wani lokacin kuma tasa Fatima ta kwanta da wuri, Malan yana dawowa setaja Farida sutafi falonshi.

Idan ya tambayi Fatima setace ai kasan Fatima dama akwai saurin bacci, shiyasa kawai da tace mun bacci zatayi nake gyara mata gado ince tayi kwanciyarta kada tajira Farida. Sosai Malan yakejin dadi idan Mama ta fada mashi haka.

Da haka ne Mama tayi nasarar kawar ma Malan tunanin Fatima, kuma ta hanata zuwa inda yake sosai, befi asati ta zauna dashi so 2 ba, shima a hakan a takure take dan har yanzu Fatima bata saki jiki dashi ba.

Inne kuwa kullum tana cikin tunanin Fatima, sosai take damuwa da Fatima, domin tasan Kaidin Mama, kullum cikin yimata addu'a take akan Allah ya kare mata ita. Daki guda Babanta ya ware mata agidan.

Duk abinda takeso shi ake mata, sosai Mamanta take tausayinta, kasancewar Babanta yana da hali yasa sam bata neman komai ta rasa, dama kuma itace auta agidansu, domin su 3 ne iyayensu suka haifa.

Idan kaga yara sede yaran 'yan uwa ko jikoki. Bata da wata damuwa se damuwar yaranta, kuma suna waya dasu Momyn Teemah tana tambayarsu ko Fatima tana zuwa makarantar boko da islamiya.

Koda yaushe suna fada mata tana zuwa, kuma suna kara karfafa mata zuciya, dan Salamatu cemata tayi ta kwantar da hankalinta yanzu Malan yana jan Fatima ajiki, a mota ma yake kaita Makaranta sanna ya wuce da Farida. Haka de suke kwantar mata da hankali har seda suka ga ta kwantar da hankalinta.



Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, Mama tana cin duniyarta da tsinke, hatta da lesson din da Fatima take zuwa seda ta hanata, sede duk da haka kokarinta be rage ba, karama kokari takeyi.


Maman Saddik taso taje taji ko lafiya Fatima ta dena zuwa lesson, sede tana tsoron abinda Baban Saddik yace mata agame da Mama, domin gaba daya unguwar babu wanda besan ansaki Inne ba.

Hakan yasa ta sameshi dan ta tambayeshi taje ta jiyo lafiya. Kallonta yayi yace Maman Saddik kenan, yanzu idan kikaje kinsan mezaki samo? Kada fa kimanta Fatima ba diyarta bace, taya zata barta tacigaba da zuwa wajen datake karuwa bacin ta tsani mamanta.

Abinda yafi kawai mubi Fatima da addu'a, idan Allah yasa zatayi kokari ko babu wannan lesson din to zatayi shine, domin Allah yana bama bawansa duk abinda yaga dama alokacin da yakeso. Yanzu kalli Mamana, kin taba tunanin zata iya fahimtar kalma daya ta ilimi? Amma gashinan da Allah yaso har rubutu tanayi.

Itama Fatima insha Allah wata rana seta zamo abin kwatance, domin duk wanda yace ruwan wani baze tafasa ba, to nashi ko zafi bazeyi ba. Fatan mu de Allah yasa muna da rabon ganin girmansu zakice na fada maki.

Maman Saddik tace haka ne, shikenan Allah ya kwatar mata hakkinta, shi kuma Malan Allah yabashi ikon gane gaskiya. Baban Saddik yace amin. Domin Malan ba irin mutanan da ake fadama gaskiya bane. Gara ka barshi duniya tabi dashi, wata rana ze gane muhimmancin jan yaro ajiki ko da kuwa akanshi aka saukar da dakikancin duniya.

**** ****

A yau ne yara suke cike da farin ciki musamman masuyin Boarding School, domin yau itace ranar da kowa ze tafi hutun first term, iyayen yara da yawa sunje daukarsu, yayin da wasu zasu tafi a motar haya.

Tun jiya da dare Malan ya yanke hukuncin ai kama Farouk da kudin mota domin zeje ya dauko Faisal da Fahad tunda su a waje daya suke, dansu Faisal motar makaranta ce zata dauko duka yan Katsina ta kawosu daga nan kuma iyayen kowa yaje ya dauki danshi.

Fahad kuma a Dutsinma yake shiyasa Malan yace idan yaje ya daukoshi se sujira a Katsina kafin su Faisal su karaso. Hakan yasa tun ajiyan ya ai kama Farouk kudin mota, sam Mama bataso haka ba, taso yaje ya dauki Fahad se sutafi su dauko Farouk idan yaso Faisal yataho da 膽an gidan Labaran.

Amma Malan yace a'a saboda su duka sababbin zuwa ne, shi kuma Farouk ya zama dan gari, hakan yasa ta hakura. Tunda safe Malan ya shirya ya nufi Dutsinma, bayan ya dauko Fahad suka biya katsina seda sukayi kusan awa daya kafin suka iso.

Da gudu Nura yaje ya rungume Babanshi, se murnar ganin juna sukeyi, Malan kuwa bakinshi yaki rufuwa, hango Faisal da yayi cikin kayan makaranta ya goyo jakarshi, seyaga yakara mashi girma, sosai kayan sukayi mashi kyau.

Tunda Faisal yataho beyi dariya ba har ya iso, yana zuwa yadanyi murmushi tare da dukawa har kasa yace Malan ina kwana? Murmushi Malan yakara saki yana fadin Faisal an girma.

Haba Faisal shine ko azo arungumeni bakaga yanda kowane yaro yakeyi da Babanshi ba? Murmushi Faisal yayi yakara dukar da kai, kamoshi Malan yayi ya dora hannunshi akanshi yana fadin to ya karatun ina fatan babu wata wahala? Faisal yace lafiya lau.

Fahad da yake gefenshi se hararshi yakeyi fuskarshi adaure, tunda yaga suna fitowa daga mota yaga yanda kayan makarantar sukayi masu kyau gaba daya haushi yagama kamashi, duk seyaji kunyar kayan makarantarshi.

Saleem ne da wasu yan ajin su Faisal  suka karaso suka gaida Malan, Saleem yace Faisal na dauka ai da Inne da Fatima zaza'azo daukar ka? Saurin kallonshi Malan yayi cike da mamaki, Faisal ya wurgama Saleem harara.

Dariya Saleem yayi yana fadin kai ma dan gidansu Faisal ne? Malan kuwa kallon Fahad yayi wanda Saleem ya dafa yana tambaya, ture hannun Saleem Fahad yayi tare da kara daure fuska.

Gaba daya se Malan yaji beji dadin yanda yara kanana suka san labarin Inne da Fatima abakin danshi ba amma basu san labarinshi ba, gashi acikin 'yan uwanshi ma Fatima kadai yake ambata.

Saleem yace natafi Dady na yana jira na dama cewa nayi bari inzo inga Babanka kila tare sukazo da Inne da Fatima ashema ba'azo dasu ba. Idan kaje kace ina gaishe dasu. Faisal yace zasuji se mun hadu next term.

Sallama sukayi da abokanshi Saleem se kara kallon Fahad yake yana nuna kayanshi yana dariya. Sosai ran Fahad ya baci, kallon Malan yayi yace Malan mutafi gida dan Allah. Malan yace to Faisal mutafi ko.

Gaba Faisal yayi ko kallon Fahad beyi ba yaje yashiga bayan mota ya zauna, shima Fahad ya bude gaba ya zauna yana wani bata rai. Tsaye suka bar Malan da sakin baki cike da mamakin su.

Wasu kwallan bakin ciki ne yaji sun zubo mashi, wai ace 'ya'yanshi ne suke ma juna haka? Gaskiya babu abinda zecema Jamila sede yace Allah ya isa, kin tar watsa mani iyalina. Hannu yasa ya goge idonshi ya nufi motar yana fadin zakaje ka iske wadda kakeso ai bata gidan dole ka saki jiki dani, kuma inde ina raye bazan taba barin kuje wajenta ba harse kun gama karatun ku, zuwa lokacin nasan nacire maku ita aranku nasaka soyayyata data 'yan uwanku aranku .

(馃 Niko nace anya ze yuwu araba hanta da jini).

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263.

馃槝馃槝 Jinjinar ban girma ga masoyana 馃憤馃徎馃憤馃徎
馃彙馃彙 A WANI GIDA馃彙馃彙
          馃槶馃槶馃槶

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 [email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 55 鈴� 60

Malan kasa kiran Alhaji Mansur yayi, domin yana matukar jin nauyinshi, zama yayi ya tsara mashi message ta yanda ze fahimci abinda yake nufi cikin ruwan sanyi, dan yana tsoron yayi mashi rashin mutunci kuma aikinshi ya samu matsala.

       Assalamu Alaikum.

Ya gida kuma ya aiki, nasan zakayi mamakin wannan sako dana rubuto maka. Bawani dalili bane se dan inaso in toshe wata matsala da take shirin fitowa daga gidanka.

Kamar yanda kasani ni tsohon mijin matarka ne, kuma akwai yara guda biyu atsakanin mu, matarka tayi matukar kokari wajen raba tsakanina da yarana.

Kwata kwata yarana basa sona saboda mahaifiyarsu, bayan mun rabu da ita daga lokacin nafara samun soyayyar yarana. Amma yanzu sena samu labarin tafara bibiyarsu tana so takara raba tsakaninmu.

Kuma zuwan datayi wajensu tabbas naga sauyi daga wajensu, domin sabuwar hudubar datayi masu tashiga zuciyarsu, kuma tayi matukar tasiri, yanzu dariyar da suke mani ma sun dena, basa zama kusa dani.

Basa son sauran 'yan uwansu, babban abinda yafi daga mani hankali shine abinda Faisal yayi. Kamar Faisal har yasan yayi fada da mata ta, wallahi da za kazo da kaga yanda ya nausheta a ido.

Nasan yanda Hauwa take matukar sona shine ya hanata kai Faisal wajen 'yan sanda, bakaga yanda idonta yayi ja ba. Ita kanta Fatima da take karama idan ta sata aiki batayi.

Wannan abu yayi matukar tada mani hankali, shiyasa nace zan maka magana domin kajama matarka kunne. Wallahi Alhaji ina matukar ganin girmanka shiyasa nakasa kiranka.

Da ace wani ne ba kai ba Allah kadai yasan matakin dazan dauka, da zaka tambayi mutanan unguwar mu na Mani zasu fada maka halina. Amma kai kana da girma a idona bazan iya maka rashin kirki ba.

Kuma matarka taci darajarka,kuma bata isa inkirata muyi maganar ba, kawai na fada maka dan kaja mata kunne. Kada takara zuwa wajen yarana, abinda nake siya masu ya ishe su.

Kuma ina matukar kokari akan yarana, babu abinda suka nema suka rasa. Idan kuma taki daukar maganata, to zan iya cire duka yaran daga makarantar in maidosu nan kusa dani suyi Day, idan nayi hakan nasan bazata iya tasowa tazo gidana wajensu ba.

Ina fatan zaka fahimci abinda nake nufi? Nagode.

                    Principal,
             Science Faskari.
           Malan, Bature Mani.


Malan ya karanta message din da yayi yafi so 5 kafin ya tura, domin bayaso ya rubuta wata kalma marar dadi wadda zata batama Alhaji rai, domin shide aikinshi yakeji.

***** *****

Lokacin da message din yashigo Alhaji yana kwance kusa da Inne suna fira, Inne ce ta miko mashi wayar tana fadin gashi anyo maka message. Alhaji yace nifa bana son duba message, yanzu haka campany ne.

Amsar wayar yayi ya bude, saurin tashi zaune yayi ganin wanda ya turo mashi sakon. Murmushi yayi yace Innen yara ga mutuminki yayo mani sako.

Inne tace to akaranta mana muji. Alhaji yafara karanta mata tana sauraro, seda yagama sannan ya juyo yana kallon Inne. Hawaye ne suke zuba daga idonta. Murmushi yayi yace wannan kukan kuma na meye? Kara fashe tayi da kuka.

Lallashinta ya farayi yana fadin haba Innen Yara, meye abin kuka anan? Daga ganin yanda ya rubuto wannan sakon kema kinsan yana jin tsoro.

Kuma tunda baze iya kirana ko yazo yasameni muyi magana baki da baki dashi ba ai yayi abanza. Kuma babu wata shari'a data raba tsakanin Uwa da 'ya'yanta, koda kuwa basa tare da Ubansu.

Kuma wannan maganar banza ce yake fadi, sede kamar yanda yabani girmana, kuma ya nuna yanajin nauyi na, nima bazan bada kai naba. Kiyi hakuri da hukuncin dazan yanke yanzu.

Kamar yanda ya bukaci kidena kula mashi yara dole zamu samo wata mafita, domin ya gane baki zuwa wajensu, sede kuma ba kamar yanda yafada abun ze kasance ba.

Zan tura mashi message na ban hakuri, kuma zance inde nine mijinki bazaki kara zuwa wajensu ba. Sede zamu sake salon kai masu ziyara, haka kuma zamu jama su kunne akan kada su sake su fadama kowa kina zuwa.

Idan zakije ganin Fatima gidan Principal zamuje kamar munje wajenta, kinga zata sa akira Fatima tazo gidanta batare da Farida ta sani ba. Na Faisal kuma me sauki ne, domin babu wanda ze fada mashi kinje.

Kiyi hakuri, duk wannan abun da yakeyi na lokaci kadan ne, da yaran nan sun girma komai zezo karshe, domin ayanzu ne kawai yakeda iko dasu. Ina me tabbatar maki akwai ranar da se yazo wajenki yana rokon kisaka baki domin surika zuwa wajenshi.

Kuma banaso wannan maganar tashi ta dameki, tunda ni yayi ma magana ki bar mani komai a hannuna, domin da dan gari akanci gari. Murmushi Inne tayi tace nagode Alhaji, bansan da wane baki zan gode maka ba.

Alhaji yace kin gama mani komai, domin kin rike mani marayuna tsakani da Allah. Lokacin da mamansu ta rasu kukan da nayi hada na tunanin matar dazan aura, wane irin riko zatayi masu.

Ga sude yara nasan idan ban samu mace tagari ba shikenan rayuwarsu zata shiga matsala, kina ganin se yanzu Ansar zeje secondary, ita kuma Khairat tana primary 4, kinga ko ai za'a kwaresu idan basu hadu da marikiyar kirki ba.

Inne tace ai bakomai, kowa yarike dan wani ze samu lada me tarin yawa, bare kuma marayu, wadan da ko kansu ka shafa kana da lada. Wallahi banajin bakin ciki dan ina rike yaranka da kyau ni kuma nawa ana wulakantansu. Allah yabani ikon cigaba da kula dasu. Alhaji yace amin, kema ai kin kusa sauka. Murmushi Inne tayi.


Faisal gaba daya ya canza agidansu, idan kaga yana magana shida Fatima ne, haka idan yana dariya da ita duk wanda yazo yake denawa, tsakaninshi da Malan gaisauwa ce kawai.

Haka ma Mama gaisuwa kawai take hadasu. Fatima ma sam tadena kula kowa, duk aikin da tasan tanayi bata bari ayi mata magana, tana tashi take yin abunta. Haka idan rana tayi zataje ta tambayi Mama abinda zata dafa.

Sosai Fatima ta iya aiki da girki, domin Mama abincin safe kawai takeyi, amma komai Fatima ce keyi, tun tana nuna mata yanda zatayi har ta dena. Farida kuwa sede adafa taci, bata aikin komai se zama cikin manya.

Ko wankin da Faisal yake ma Farouk yanzu ya dena, shima Farouk din yadena bashi, kuma shikadai ne yake kula su Faisal, kasancewarshi bame son magana ba yasa ba koda yaushe yake masu magana ba.

Fahad kuwa yafi kowa rashin mutunci agidan, Malan kadai yake tsoro, amma baya daga ma kowa kafa hatta da Mama, kuma duk tafi sonshi shida Farida, kuma sunfi kowa rashin kunya.

Bayan kwana biyu Alhaji ya maido ma Malan amsar sakonshi. Sosai Malan yaji dadin abinda Alhaji yace, kuma yaji dadi daya fahimceshi, dama tunda yatura sakon yake cikin zullumi, musamman da yaga anyi kwana biyu be maido mashi da amsa ba.

Mama yakira yace dama nafada maki zan dauki mataki akan zuwan Jamila wajen su Fatima, dazu Alhaji ya maido mani da amsar sakona, kuma yabani hakuri sosai, yace besan haka abun yake ba da be barta taje ba.

Kuma yace baze kara barinta taje wajensu ba matukar shi take aure. Dariya Mama tasa tana fadin yanzu haka shima yafara gano bakin halinta, ina nan da kai ya kusa korota daga gidanshi.

Malan yace ai shima yana da yara, kuma awajenta suke, yanzu haka tafara kokarin rabasu dashi kuma wannan message din danayi mashi shine ze kara haska mashi asalin boyayyen halinta.

Mama tace ai naji dadi, kaga yanzu yaranka zasu dawo kamar da. Malan yace na manta ma ban fada maki ba, kifadama yara nan su shirya gobe zamuje Mani tunda saura sati biyu su koma, Hajiya tana maganar ban kaisu sun gaisheta ba.

Mama tace ai nima abinda naga yafi tunda de ka kusa aje aiki, kuma lokacin da zaka aje aiki Mazan ne kawai suka gama karatu, kawai da anyi hutu murika tafiya Mani, tunda kaima idan akayi hutu ba aiki kake zuwa ba.

Kaga fa tunda suka dawo basuje islamiya ba, kuma ni nafison islmiyarsu ta Mani, gara murika tafiya can, suna komawa hutu semu dawo nan, suma kansu sunfi sabawa da unguwarmu ta can.

Gashi akwai yaran da zasuyi wasa acan, kuma ni nafi yarda da tarbiyar yaran can. Malan yace ba naki taki bane, inajin tsoron su Faisal surika zuwa Mashi wajen Kakanninsu, tunda de yanzu Uwarsu ta bar garin amma akwai iyayenta ai.

Mama tace matukar kaja masu kunne nasan bazasuje ba, kuma yaushe rabonsu da garin, bama zasu iya gane gidan ba. Malan yace yanda kikace haka za'ayi, kawai ki sasu kowa ya hada kayanshi se amaidasu can, idan yaso se mubar namu tunda zamu dawo.

Cike da farin ciki Mama tace nagode. Zuwa tayi ta fadama Yaran suje su hada duka kayansu gobe zasu koma Mani. Wani murmushin farin ciki Faisal yasaki, har seda hakoranshi suka fito.

Ita kanta Fatima seda tasaki dariya, sauran yaran kuwa ihu sukasa hada tsalle. Ido kawai Mama ta zuba ma Faisal, wato yana son akoma can shima, tsaki taja aranta tana fadin kunci sa'a nima inaso murika zuwa saboda ina son garin.

***** ******

Washe gari tunda safe Mama taje yima Zulai sallama ta fada mata nan da sati 2 zasu dawo. Zulai tace kawaide kinyi mana wayau, Mama tace haba ba haka bane, kawai ina kewar gida ne. Zulai tace to Allah ya tsare, ayo mana tsarabar Mani.

Haka suka kulle gidan suka tafi, acikin mota Farida da Fahad se wasa sukeyi suna dariya, Fatima kuwa tana kusa da Faisal yana bata labarin Saleem. Se dariya takeyi, tace ai da mun koma zan fadama Lubna kuna tare da Yayanta, dama ta fada mani Yayanta yana makarantarku. Duk haushi ya gama cika Mama ganin yanda suke labari suna dariya.

Lokacin da suka isa Abba da Saddik suna kofar gida suna wasa, da gudu Abba yashiga gida yana fadin Amira fito gasu Fatima Da Yayanki Faisal. Abinci Amira takeci alokacin, ai da gudu ta tashi tayi waje, duk kiran da Mama take mata tadawo tasaka hijab amma bataji taba.

Su Faisal suna fidda kaya yaji an rungumeshi ta baya ana dariya. Fatima ce tace lah, Yaya Amira ce, saurin juyowa su Malan sukayi suna kallonsu, juyowa Faisal yayi yana dariya ya kama kafadarta yana fadin Amirata ashe kinji nazo.

Sakin baki Malan yayi shida Mama yana kallon yanda Faisal yake wata irin dariya cike da farin ciki, shi betaba ganin farin ciki akan fuskar Faisal irin na yanzu ba. Saddik ne yace Fatima angirma.

Dan kwalinta ta buga mashi suna dariya, acikinsu babu wanda ya kula su Fahad, se murnar ganinsu Faisal sukeyi. Amira tace dan Allah Yaya kada ka kara tafiya ka barni, Faisal yace bazan karaba kinji? Kai ta daga tana murmushi.

 Mama ce ta buga masu tsawa tana fadin dalla sakar masu yarinya, ko an fada maka Fatima ce da kuke ciki daya zaka rika taba ta.

Saurin sakin Amira Faisal yayi tare da hade fuska, turo baki Amira tayi tana fadin aide shima Yaya nane. Malan yace haba Hauwa meye haka? Ke bakisan yara ba, kuma bakisan yanayin da Amira take ciki ba.

Mama tace idan ita bata da hankali aishi da hankalinshi, meye amfanin riketa da yakeyi, kai dalla kuwuce yanzu mukazo zakuzo kudame mu. Hannun Amira Abba ya kama tana ta hararar Mama suka wuce, idonta har ya cika da kwalla.

Haka suka shiga da kayan ciki ran Faisal a abace. Fita Malan yayi yana fadin zanje wajen Hajiya nasan yanzu gyaran gidan zakuyi. Mama tace gaskiya kam, saboda yayi kura. Yana tafiya tasa su Faisal da Fatima su share gidan, wani kuma ya goge.

Farouk yace kai Fahad kaje ka gyara mana dakin mu ni kuma in gyara dakin Malan. Mama tace bazeyi ba, ai kanajin wadan da nace suyi aikin shine kai kuma uban iyayi zakace yaje ya maku shara. Farouk yace gaskiya Mama abinda kikeyi baki kyautawa.

Allah fa yana kallonki, yanzu kanar Fahad da Farida ba zasuyi aiki ba, kuma ai Malan yace arika sa kowa aiki. Kuma wallahi idan basuyi ba sena fada ma Malan, juyawa yayi yashige falon Malan ya fara sharewa.

Sakin baki Mama tayi tana kallonshi, yaushe yaron nan yafara rai nata? Wato yanzu bayansu Faisal yakebi kenan? Idan ko haka ne zata dauki mataki. Kallon Fahad tayi tace yi hakuri kaje ka share maku dakin.

Kaji de yace ze fadama Malan, kuma Malan zaneka zeyi, kabari zan kamashi, Fahad yace kaji Mama, to tsoronshi kikeji, nide bazan share ba, sede kishare mana. Mama tace haba Fahad, nima zan gyara mana kayan mu ne, kayi hakuri zan baka naira 100 ka kashe.

Da kyar ta shawo kanshi yatafi yaje yafara sharewa. Haka suka gyara gidan yayi fes, sannan kowa yaje yayi wanka, Malan ya aiko da cefane, haka Mama tasa Fatima ta dafa masu taliya.

Zaune Faisal da Fatima suke agidansu Amira, se wasa sukeyi, Faisal da Amira kuma suna gefe ta dauko mashi littattafanta yana dubawa, sosai yaji dadi ganin yanda Amira ta iya rubutu, kuma tana karanta duk abinda ya rubuta mata.

Maman Saddik da Baba sunji dadin dawowar su Faisal, dan kullum Faisal yana gidansu suna wasa da Amira, kuma yana koya mata karatu, da Maman Saddik ta fada mashi za'a kai Amira Secondary sosai yaji dadi.


Mama sosai takejin haushin zuwan su gidansu Amira, tana so ta fada ma Malan kuma tana tsoron kada yagane tana jin haushinsu ne, hakan yasa ta kyalesu, sede Fatima bata cika zuwa ba, sede idan Mama ta fita, dan ko taje se Mama tasa ankirata tasa ta wani aiki.

Sosai su Momyn Teemah sukayi mamakin girman Faisal da Fatima, domin sunje har gida sun gaishe su, har seda Momyn Teemah ta kira Inne ta hadasu suka gaisa. Ana bama Fatima wayar ta sama Inne kuka.

Duk abinda akayi masu seda tafada mata, hada dukan da Mama tasa Malan yayibl masu seda tafada mata, kuka sosai takeyi tana fadin dan Allah Inne kizo kidauke ni. Itama Innen kuka takeyi.

Haka tarika lallashin Fatima kuma ta fada mata yanda Abbansu yace, kuma tace kada takara bama Farida komai, kuma kada tabari tasan tana zuwa. Fatima tace bazan fada mata ba.

Faisal ne ya karbi wayar, shima seda yayi kuka, Inne tace kanaji ko, kada ka kara fada da Mama, itama Mamanka ce tunda tana kula daku, kaga Farouk da yake maka kirki bazeji dadi ba idan kana ma Mamanshi rashin kunya.

Duk abinda tasaka karikayi, kuma kadena rai nata, wata rana komai ze wuce, kayi hakuri kaji? Faisal yace to. Nan shima tafada mashi abinda Abbansu yace, haka suka yita fira, domin itace ta bugo.

Bayan sun gama gaisawa sukayi sallama dasu, godiya tayima Momyn Teemah. Abinci tasa masu sukaci sannan suka tafi. Suna komawa suka iske su Farouk zasuje gaishe da Hajiya.

Haka Malan yace sutafi gaba daya su gaisheta. Sosai Hajiya taji dadin zuwansu, Mama tace ai Hajiya daga yanzu nan zamu rika hutu. Hajiya tace ai haka yafi, amma ace ya daukeku gaba daya wai se dogon hutu sannan zakuzo.

To ya gidan, kuma ya hakuri da yara? Tabe baki Mama tayi tana fadin Hajiya kinsan ai yanda zama da Dan da ba naka ba yake, sede hakuri kawai, amma inashan wahalarsu Faisal. Kwanakin baya har naushi na yayi a ido.

Kalli wajen har yanzu be gama washewa ba. Hajiya tace shi Faisal din? Mama tace wallahi kuwa, ai da gashi har Fatima sun rai nani, ko aiki na sasu basayi. Hajiya tace ja'irai masu hali irin na Uwarsu.

Kunnan Faisal dana Fatima takama ta murde tana fadin, idan kuka kara mata rashin kunya se nasa Malan ya maidoku wajena, se inga koni zakuyi mani rashin kunyar. Mutanan banza, ko kunyar Diyanta bakwaji kuke mata rashin kunya.

Seda Fatima ta fara kwalla sannan ta sakar masu kunnan. Haka Mama tayita fada mata karya da gaskiya tana kara batasu awajenta. Sosai ran Hajiya yabaci, haka ta yita bama Mama hakuri, kuma tace idan suka kara ta kirata ta fada mata.

Zatasa Malan ya maidosu wajenta. Haka suka wuni aranar, su Farida se wasa sukeyi, shiko Farouk yama tafi wajen abokanshi, Faisal da Fatima jisukayi kamar sutafi, dande Malan yace zezo ya daukesu, ko abincin da aka basu beda wani yawa.

Lokacin da Malan yazo daukarsu haka Hajiya tayi mashi fada akan yarika tsawatar ma su Faisal akan rashin kunyar da suke ma Mama, kuma tace idan suka kara ya maidosu wajenta. Malan yace ayi hakuri Hajiya, nima na nadauki mataki, kuma bazasu kara ba. Haka sukayi mata sallama ta bama yaran Mama kudi tana fadin bazan ba marassa kunya ba, seda Malan yaji ba dadi abinda Hajiya tayi, haka suka tafi.

****** *****

 Lokacin da hutu yakare haka Malan yayima kowa provision, har Faisal seda ya siyama wasu abubuwan kasancewar shi basa zuwa da komai na abinci amma seda ya siya mashi sabulun wanka dana wanki da omo, mai hada turare da maclean.

Sosai Fatima da Faisal suke cikin farin cikin komawa warsu, dan Fatima duk ta rame, shima Faisal duk ya yi baki ya rame. Amira kuwa tasha kukan tafiyar Faisal, shima seda yayi hawaye, dan yanda Amira take kuka.

Faisal ya rigasu tafiya  dan tare suka tafi da Nura, Baban shine yakaisu Katsina,  seda Fatima tayi kuka daze tafi. Su Fahad se dariya suke mashi dansu se ranar lahadi suke komawa, su kuma asabar shida su Fatima.

Kafin Malan yaje yadawo haka Mama ta kwashe kusan rabin kayan Fatima ta karama Farida, kuma ta sama Farida sauran abubuwan data siya mata, babu wanda yasan ta kwashe dan Fatima tana dakinsu kuma sun gama hada kayansu sun kulle komai.

A cikin jakar Farida Mama tasa mata dubu daya tace kada tabari Malan yasan ta bata idan ba haka ba baze kara mata ba. Haka Malan yazo suka saka kaya amota, seda Mama ta rakosu sannan ta bama Fatima dari 200 tace gashi ku kara ko, kema Farida ga taki Dari biyun, se ku kara da wanda Malan ze baku, adage ayi karatu kunji.

Sosai Malan yaji dadi kuma yayi mata godiya, haka suka tafi Farida tana kuka. Lokacin da suka isa malan ya basu dubu dai dai kuma yayi masu nasiha akan su kara dagewa. Kallon Farida yayi yace kada kimanta da addu'ar dana baki, kullum kirikayi duk abibda kikeji zaki dena, kuma kokarinki ze dawo.

Kallonshi Fatima tayi, wato Farida kadai ze bama addu'a banda ita, kwallace ta cika mata ido, shi kuma Malan anufinshi saboda yana tunanin anyi mata asiri. Ita ko Fatima se ta karajin haushin Malan.

Haka yayi masu sallama yatafi, da gudu Lubna tazo ta rungume Fatima tana dariya, itama Fatimar dariya tayi tana fadin ashe kin dawo? Lubna tace tun dazu. Tsaki Farida tayi ta dauki kayanta tana fadin aikin banza.

Zinatu ce tazo tana fadin ga kawata, rungume juna sukayi suna dariya, haka suka nufi hostel. Lubna ce tace Fatima amma rashin lafiya kikayi ko? Kwallar da Fatima take boye wace ta zubo.

Kamata Lubna tayi tana fadin mutafi kada aganki kina kuka, haka suka dauki kayan suka tafi........... Duk abinda Mama tayi masu seda Fatima ta fadama Lubna, sosai Lubna taji tausayin Fatima, har seda tayi mata kwalla.

Hakuri tayita bata, haka suka fara fiddo kaya dansu jera a loka. Tsayawa Fatima tayi tana kallon kayanta, fashewa tayi da kuka tana fadin wallahi ba haka Malan yasiyo mana ba. Mama ce ta kwashe mani kaya, ai dama tunda tace intafi daki nasan kayana zata kwashe.

Lubna tace kiyi hakuri, taje tayi ta kwashewa, kinga wannan jakar, Inne ce jiya tazo takawo mani tace inkawo maki, shima Yaya Saleem ta bashi ya kaima Yaya Faisal. Dariya Fatima tasa tana fadin dagaske? Lubna tace wallahi kuwa, kuma tace kada kibari Farida tasan ankawo maki.

Fatima tace kai nagode ma Inne na, jinake kamar in watsar da wadan nan kayan ma. Dariya Lubna tayi tace ai seki watsar. Zama Fatima tayi tace ashe Yaya Saleem da Yaya Faisal abokai ne? Lubna tace emana nima shine yake fada mani.

Kullum seya dameni wai inbashi labarin shagwabarki. Dariya Fatima tasa tace lallai ma nice me shagwabar, Lubna tace sosai ma, kawai bakisan kinayi bane. Ga jakar sweet ma yace inkawo maki.

Fatima tace haka fa yabama Yaya Faisal yakawo mani da akayi hutu, nima idan zaki tafi zan siya mashi wani abu. Lubna tace to tashi mu hada kayan.

***** *****

Haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya, sosai Fatima da Lubna suke maida hankali a makaranta, lokaci guda Fatima ta maida jikinta, kuma yanzu babu ruwanta da Farida.

Koda akayi visiting Fatima bata damu da abinda Mama takawo mata ba, bayan kwana biyu kuma Inne da Alhaji suka zo gidan Principal, haka ta aika aka kira Fatima Da Luban, sosai Fatima tayi murnar ganin Inne.

Haka suka sha fira kuma takawo mata kaya masu yawa hadasu Inner wears, haka tabata kudi, Fatima takara bata wasu tace tasa mata a asusu, haka suka dauki kayan sukayi masu sallama suka tafi daki.

Tun daga wannan rana Inne take zoma Fatima Visiting a boye, kuma Farida bata gane ba, hankalin Inne yanzu ya kwanta dan tana ganin yaranta, kuma tanajin dadi ganin Fatima se girma takeyi tana kiba.

Fatima tafi jin dadin rayuwar makaranta, har bataso ace an kusa hutu, domin tanajin dadi sosai. Farida kuwa bata karatu, sede wasa da maza, gata da son aikama wani tana sonshi, yan ajinsu duk sun ganeta, idan suna zaune da kawayenta komai tayi masu labarin aure. Zinatu ce kawai take biye mata sunayi.

**** ****


A yaune Inne ta haihu, inda tasamu diya mace me kyan gaske, sosai Alhaji yayi farin cikin samun diya mace, dan yanason yara mata, su Ansar ma se murna sukeyi, ba kamar Khairat, dan tasamu abokiyar wasa. Haka Inne ta buga ta fadama su Salamatu.

Ranar suna yarinya taci sunan Amatullah, dan Alhaji yace yanason sunan, sosai Inne tayi mutane, su Momyn Lubna sune akan gaba, dan zumuncinsu yakaru sosai. Su Momyn Teemah da Salamatu ma duk sunzo.

Taro yayi kyau, Inne takara zama babbar Hajiya, tayi kyau takara gogewa tazama 'yar birn, idan ka ganta ba zakace Innen daka sani bace ada, dan yanzu ta waye sosai.

Kamar yanda Alhaji yace idan ta haihu ze biya masu makka kuma ze koya mata mota, haka yasa aka fara koya mata mota lokacin da tayi arba'in,  kuma yace zasuje Makka tunda saura wata bakwai atafi, kafin lokacin Amatu takara girma, seta ajeta idan ta dawo tacigaba da shayar da ita.

***** *****

Abubuwa da dama sun faru, yara sun kara girma, Fatima tazama yan mata, tagama horuwa da aiki yanzu sam bata bari Mama tayi mata fada, sede idan Mamar taso yin fadan ne, Farida ta zama kwarkwar, gashi abun bakin cikin anyi mata repeating yanzu Fatima tana gabanta.

Duk tayi sanyi bata da sauran rawar kai a cikin kawaye, hatta da Zinatu yanzu ta wuceta. Lokacin dasu Faisal sukayi JSCE da za'azo ma Lubna visiting seda Saleem yazo, hakama Faisal seda Malan yace su shirya shida Fahad atafi dasu.

Sosai sukayi murnar ganin junansu Saleem da Faisal, Fahad kuwa sakin baki yayi yana kallonsu dan ko magana basayi da hausa, lokacin dasu Fatima sukazo sosai tayi murnar ganin Faisal.

Saleem kuwa ido ya kura mata, itama shi take kallo, Lubna tace Yaya Saleem wato baka ganni ba ko? Dariya yayi yana fadin am sorry Lil sis, ya makaranta? Faisal yace bata amsawa, kyaleshi Lubna zo kifada mani labarin makarantar ku.

Duk maganar da sukeyi da turanci sukeyi, Mama da Farida da Fahad sun zama yan kallo, sosai haushi ya gama kama Mama, dan tunda Fatima ta gaisheta suka ware dasu Faisal.

Farida kuwa kuka tayi ta mama tana fadin acanza mata makaranta, Mama hakuri tabata tana fadin kinsan de halin Malan, baze taba canza maki ba, gara ki kara dagewa, yanzu kina ganin se Fatima ta rigaki gamawa. Narasa meke damunki keda Fahad, so kuke ayi mani dariya.

Haka ta yita bata hakuri, lokacin da zasu tafi seda Fatima tayi kuka, shima Saleem seda idonshi yayi ja, wani zobe dake hannunshi yabama Fatima, su Faisal da Lubna se tsokanarsu sukeyi. Momynsu kuwa se dariya take masu, haka suka rabu cike da kewa.

Bayan koma warsu SS1 ne Fahad yafara biyema abokan banza, kuma anan ne suka fara koya mashi shan taba, tun yana sha yana kwarewa har yasaba, daga taba se kuma abun yaci gaba, kullum da dare se sunje bayan makaranta sunyi shaye shayensu kafin su dawo.

Lokaci guda ya kware, kuma ya kara zama dan iska, lokacin da akayi hutu Mama tace wai Fahad me yake damunka, duk kayi baki karame? Kallonta yayi yace mefa, kawai wahalar makaranta ce, haka ta dage tana bashi abun dadi dan yasamu yaciko.

Gashi yanzubsam yama dena kokari, kuma Malan yadena masu fada akan rashin kokari tunda Mama tace asiri akayi masu, hakan yasa ya zuba masu ido, duk zasu koma seya kawo ruwan addu'a yace surika sha, sede baya ba su Faisal, saboda suna kokari, besan kuma hakan da yake ba kara hura wutar kiyayya yake azuciyarsu, dan sun dauka bayaso suyi kokari ne shiyasa yake bama sauran.

Kullum idan Fahad yafita baya dawowa da wuri, kuma da dare ma seyayi shaye shayenshi sannan yake shigowa gida, gashi hada dauke dauke yakeyi, duk abinda yakeyi babu abinda Faisal be sani ba.

Shiyasa yanzu yake lallabashi, dan abu kadan yake harzuka Fahad, har da Farouk dambe sukeyi, Mama tarasa inda Fahad yasamu wannan zuciyar. Faisal yaso ya fadama Farouk dan yanzu suna mutunci sosai, se kuma yaji tsoron kada Mama tace sharri yake mashi.

Dan shi yanzu Farouk babu abinda yasa agaba kamar dinkin hularshi, sosai yazama gwani a dinkin hula, kuma da yayi saidawa yakeyi, sosai yake samun riba, kuma ba laifi yanzu yana maida hankali dan tun wani lokaci da Faisal yabashi shawara akan yarika maida hankali idan yasamu yagama karatun se yayi dinkishi sosai.

Tun daga lokacin Farouk yake maida hankali, kuma yana zuwa masallaci dan inde suka zauna suna fira da Faisal to seya yimashi wa'azi cikin dabara, dayake Farouk beda girman kai haka yake daukar duk abinda Faisal yake fada mashi. Amma tsakaninshi da Fahad fada ne kawai, dan yanzu Fahad sosai yakejin haushinsu.

Shakuwar Amira da Faisal ta wuce wasa, domin yanzu Amira takara girma, yanzu tana JSS3 itama, kuma takara dagewa wajen karatu, sede har yanzu akwai yarinta atare da ita saboda yanayin datake ciki.

Amma ita da Faisal abun ba'a magana, sosai yake sonta, duk abinda yasamu ita da Fatima yake bamawa, kuma ga Lubna itama sun shaku da ita, Baban Saddik har cemata yake Matar Faisal, itako tayita dariya.


Inne kuwa yanzu ta zama Hajiya Inne, motar datake tukawa kanta abun kallo ce, duk da mijinta ya aje aiki amma yana da hanyar samu sosai, ita kanta shagon saida kaya ya bude mata yazuba mata kaya kuma ya mallaka matashi, haka tasamo wani dan Uwanta a Mashi yake tsare mata, sosai tayi arziki,

Kuma ba ta manta da kawayenta su Salamatu ba, ita da Momyn Lubna sun zama tamkar yan gida daya, Ansar da khairat ma anzama manya duk sunje secondary, Amatu kuma tana nursery, sede daga ita Inne bata kara haihuwa ba.

Wata rana da Momyn Teemah ta haihu lokacin ana hutu, haka Inne ta sako yaranta amota sukazo suna, ba karamin kyau sukayi ba, lokacin da tashigo cikin unguwar kowa seda yabita da kallo.

Maman Sultan da Mama sun taho zasuje wajen sunan su kaga tsayuwar mota.Tsayawa sukayi suna kallon wanda ze fito. Inne tana fitowa Salamatu ma tafito daga gidanta.

Cike da farin ciki tace ga Hajiya Inne oyo oyo, saurin kallon Inne su Mama sukayi, tabbas itace, ido Mama ta tsura ma Inne, tanajin zuciyarta kamar zata fashe, Fatima da Amira suna zaune suka hango Inne, ai da gudu suka rugo suna murna.

Fatima tana zuwa Inne ta rungumeta, Amatu tana rike da hannun Khairat se dariya takema Fatima, dan sun saba, da ita. Daukar Amatu Fatima tayi tana mata wasa, Khairat ma ta rungume Fatima.

Su Faisal ne da Abba suka karaso yana ta dariya, Ansar ne ya rungumeshi yana fadin Yaya ina wuni? Faisal yace lafiya lau Ansar ina Abba? Yace yana gida.

Takawa Inne tayi har wajen su Mama tana murmushi, Salamatu tana binta abaya, kallonsu tayi tana fadin Maman Farida ina yininku? Maman Sultan ce ta amsa da kyar, Mama kuwa mamaki da haushi sun hanata, magana.

Murmushi Inne tayi ta juya tana fadin Salamatu muje wajen sunan ko, haka ta juya tana takawa cike da takama. Mama kuwa kasa shiga gidan sunan tayi, haka ta juya takoma gida kamar zatayi kuka saboda bakin ciki.

Kalli yanda Inne ta koma, itako gata nan yanzu kaya masu tsada ma bata dasu, tashin hankalin Farida da Fahad ya hanata yin kiba. Haka ta koma gida tana me cike da bakin ciki.




**** ****

BAYAN WANI LOKACI

Farouk yagama makaranta inda su Fahad suka zana jarabawar shiga aji shidda, dansu makarantarsu se wanda yaci jarabawa yake shiga aji shidda. Kuma akaci sa'a Fahad baci ba, hakan yasa aka mashi repeating.

Ya dawo mate din  Fatima, dan itama Farida tun suna aji 2 akayi mata repeating, yanzu Fatima tana gabanta, duk da lokacin Mama taji haushi haka nan ta hakura tunda de tasamu ta rufe bakin malan da cewar Inne ce tayima yaranta asiri, kuma shima ya yarda da hakan.

Lokacin da suka gano jarabawar Fahad kuka yayi tayi yana fadin baze koma makarantar ba.Malan yace aiko be isa ba seya koma, dama ai nafada maka. Kallonshi Malan ya karayi yana fadin wai ni tsaya ma, baka da lafiya ne? Fahad ya dago jajayan idonshi yace lafiya kalau.

Malan yace amma kalli bakinka, duk yayi baki, kaima kanka kayi baki kuma ka rame.. Fahad yace kawai nadanyi zazzabi,ne. Malan yace ni kake fadama kawai? Mama tace haba Malan kayi hakuri mana, kaima daga gani ai kasan  bayada lafiya, kallifa yanda yarame.

Malan yace to ai seku shirya mukaishi asibiti. Mama tace, tashi kaje Fahad, haka yatashi yana wata 'yar iskar tafiya yafita. Malan yace nifa ina zargin yaron nan. Tashi Mama tayi tana fadin a'a Malan kada kafara fadar irin wannan maganar akan yarana.

Me kake nufi da kana zarginshi? Nifa banaso kana ma Fahad haka, na lura da dadewa kafara tsanarshi acikin yaranka, to wallahi zamu fara batawa matukar kana mani haka, fita tayi tare da bugo kofar.

 Murmushi Malan yayi yace Hauwa kenan, kowa yaga Fahad yasan halin dayake ciki, amma tunda bakiso infadi gaskiya nabarki dasu, na dade da sanin kina goyon bayan yaranki, amma tunda haka kikeso zan sa maki ido. Allah ya shirya.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
馃彙馃彙 A WANI GIDA馃彙馃彙
          馃槶馃槶馃槶

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 [email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 60 鈴� 65


Kwance Mama take a dakinta tun bayan fitowar ta daga wajen Malan, zuciyarta se zafi take mata. Wannan wane irin bala'i ne haka? Yanzu Malan yadena kula da yarana kamar yanda yakeyi ada.

Tunda Inne tabar gidan nan soyayyar da Malan yake ma yarana ta fita daga zuciyarshi. Kenan saboda zaman Inne agidan yake son yarana? Meyasa ma nasa yasaki Inne? Gashi yanzu ita ta cigaba ni kuma ina nan kullum se kara tsotsewa nakeyi.

Gaba daya tafiyar Inne daga gidan nan haske ne akan yaranta, ni kuma duhu ne ya mamaye ni da yarana. Shi kanshi Malan yanzu arzikinshi ba kamar da ba. Amma kalli irin motar da Inne take hawa.

Kalli kayan jikinta, gashi ta rike 'ya'yan mijinta tamkar itace ta haifesu. Yaranta sun zamo abin so ga kowa, kansu ya bude yayin da kan nawa yaran ya toshe gaba daya. Duk kokari irin na Farida da Fahad be hana anyi masu repeating ba.

Nida naso ace yaran Inne ne ja baya akaratu, lokacin da  zasu fara karatun jami'a yarana sunyi nisa alokacin kuma gashi Malan ya aje aiki. Se gashi  kuma anyima yarana repeating, gashi Faisal gwamnati ce take daukar nauyin karatunshi.

Ita kuma Fatima zata riga Farida gamawa, nasan duk sauran kudin Malan akansu ze kashe, tunda zasu rigasu shiga jami'a. Allah na rokeka kasa Farouk shi yaci jami'a, koshi kadai nasamu yayi karatu nasan seya riga Faisal gamawa.

Idan yasamu aiki nasan ze kula da sauran. Hawaye ne suka zubo mata, tabbas maganar Malan gaskiya ce, yanayin Fahad ya dade da canzawa, narasa meke damunshi, gashi yanzu duk abinda na aje se inga andauke, wanda ada ba haka ake mani ba.

Kadde ace Fahad yafara sata? Saurin girgiza kai tayi tana fadin, ina, acikin yarana babu barawo, domin duk dangin mu babu barawo. To kode yafara shaye shaye ne? Kara girgiza kai tayi tana fadin hakan ma baze yuwu ba.

Domin Fahad tun yana karami baya son warin koda sigari ce. To meya samu Fahad? Tabbas nasan akwai sa hannu acikin rayuwarshi, kuma koma wanene senayi maganinshi, kuma daga yau duk abinda za'a kawo na kayan dadi nashi seyafi yawa.

Bazan zauna ina kollo yarona ya lalace ba, duk yayi baki yarame, tabbas kafin ya koma sena ginashi. Hannu tasa ta goge idonta ta tashi tana kwalama Farida kira.


Shigowa tayi tana fadin kai Mama, wannan kira kamar kin makance. Mama tace wato nice ma na makance ko? Dariya Farida tayi tana fadin ai naji kina ta kwala mani kira ne. Mama tace nasan Fatima tana can gidan su Amira.

Jeki dora farar shinkafa idan ta dawo setayi miya. Farida ta turo baki tana fadin lallai ma, ai kin sande itace take aiki taya zakice inje in dora abinci? Mama tace Farida kinga yanzu kin girma, inaso kifara koyon aiki domin wata rana aure zakiyi.

Farida tayi murmushi tana fadin ai kamar kin sani, muna gama makaranta aure zanyi nida kawata. Zaro ido Mama tayi tana kallonta, Farida tace kinsan yanzu samarina nawa? Su 2 ne, damma suna tsoron Malan shiyasa basu taba zuwa gidan nan ba.

Mama tace rufa mani baki, ke yanzu har kinsan maganar aure? To bari kiji in fada maki, yanda kowa zeyi karatu a gidan nan kema sekinyi karatu. Haba Farida, so kike bakin cikinku ya kashe ni? Kina ganin yanzu shima Fahad yadawo baya.

Kema kin koma baya, Farouk ne kawai acikin yarana yagama Secondary, so kuke wadan can yaran su zama wasu manya agidan nan, ga uwarsu ta zama babbar Hajiya, suma suzo suyi kudi, shikenan ni kuma na zama baya kenan.

To kima cire tunanin aure aranki, matukar ina raye se kinyi karatu kamar kowa. Kuma daga yau zan raba maku aiki keda Fatima, idan ma bazaki iya shara da wankin bandaki ba, wannan ba matsala bane.

Nide fatana ki iya girki, sauran ko baki iya ba badamuwa domin akwai masu aiki, amma shi girki kyan mace ta iyashi, idan na dare kikeso to, idan kuma na rana zakiyi duk daya seki zaba.

Farida tace Allah Mama bazanyi ko daya ba, tunda de Fatima takeyi kawai ki barta ta cigaba, Mama tace haba Farida, meyasa bakison farin cikina? Kuka Farida tasa tana fadin ai dama yanzu naga kindena son mu.

Gashi Malan kullum seyayi mana fada, se wadan can kawai yakeso. Kuka sosai Farida tasa tana dire dire. Jawota Mama tayi tana fadin yi hakuri, ni na isa ince bana sonku? Kawai inaso in koya maki girki ne, tunda bakiso shikenan.


Je ki kira mani Fatimar tazo ta dora, share hawayenki, bakida mesonki sama dani. Murmushi Farida tayi tace anjima zanje gidan 'yar makarantarmu daga can zanje ingaishe da Hajiya. Mama tace to jeki kira mani Fatima an jiman seki tafi.


Abinda Mama bata sani ba shine, inde Farida ta tafi wajen 'yar makarantarsu da gidan Hajiya to haduwa takeyi da wani saurayinta Salisu, yana da shagon provison, kuma hade yake da dakin da yake kwana.

Tun wata rana da Farida taje siyen sukari ashagon suka hadu, tun daga nan suke soyayya, kuma Farida tana bala'in son shi, saboda yace ze aureta, ita kuma babu abinda takeso kamar maganar aure.

Sanin halin Malan yasa be taba zuwa gidansu ba, sede tayi dabara taje shagonshi, wani lokacin ma dakinshi suke shigewa suyi fira, sosai Farida ta sake dashi, duk lokacin da taje haka yake gama tabeta ya kawo kudi da kayan zaki ya bata.

Haka take boye kudin tace ma Mama sauran kayan agidan kawarta aka bata. Ta saba da abubuwan da yake mata sosai, hakan yasa duk bayan kwana 2 setaje wajenshi, daga can seta wuce wajen Hajiya dan kada tace bata zuwa.

Kuma sosai Hajiya take jin dadin zuwan da Farida takeyi, har cewa take ita da Fahad sune yan gidanta, domin shima da gidanta yake fakewa yatafi yawon shaye shayenshi.

***** *****

Bayan sun koma makaranta first term, Faisal na SS 3, Fatima da Fahad kuma SS 2, yayinda Farida take SS 1, ba laifi Fahad ya ciko, yayi kiba kuma lokacin da zasu tafi seda Malan ya kara mashi fada sosai akan rashin maida hankalin da bayayi, kuma yace idan har aka kara mashi repeating to ze maidoshi Day.


Haka suka tafi Fahad kamar ze fashe, Mama duk bataji dadin abinda Malan yayi mashi ba, haka ta dauki fushi da Malan dan yanzu haushin shi takeji sosai, duk wata kissar da takeyi ada yanzu babu, abu kadan se fada.

Shi Malan ma dariya take bashi, shiyasa baya biye mata, idan kuma ta kureshi haka zeyi mata tass, dan shima Malan akwai fada, sanin halinshi ne yasa take jin tsoron yi mashi wani abun, koya bata mata rai ma sede ta dauki fushi dashi, idan ta gaji kuma ta sauko.

Yanzu gaba daya Malan ya canza, baya ma yaranshi fada, babu abinda yake fata kamar ya dedeta tsakaninshi dasu Faisal, dan ya dade da gano tsantsar tsanarshi a idanuwansu, sede har yanzu be yarda cewa ba Inne bace ta rabashi da su ba.

Haka sam yadena ma yaran Mama fada, ya kyalesu kamar yanda bataso yana masu. Kuma har yanzu yaki barin su Faisal suje wajen Inne, suma kuma sun dena mashi maganar, domin basu da damuwa tunda suna ganinta, shi kuma Malan ya dauka sun fiddata daga ransu.

Jarabawar su Farouk ta fito, ba laifi yaci, sede be samu English ba, gashi mark dinshi na JAMB be kai ya tafi jami'a ba, kuma duka subject 5 yaci, Math, Biology, Geography, Hausa se islamic.

Sosai Mama taji haushin rashin samun mark din daze tafi jami'a, samun Malan tayi tace abarshi zuwa shekara me zuwa se ya kara sake JAMB din kuma ya nemi English idan yaso seya tafi jami'ar.

Murmushi Malan yayi yace kina da tabbacin shekara mezuwa zeci duka abinda kikace? Mama tace amma de kasan ai Farouk ba jaki bane, duk da banso ya gama karatu tare da kannanshi ba, amma dole inyi hakuri ya sake jarabawa tare da Faisal.

Malan yace to kimayi addu'ar yasamu direct a makarantar dazan samar mashi, domin tunda naga beci JAMB sosai ba na siya mashi form din Isa Kaita Collage Dutsinma yaje yayi N.C.E, kinga yanzu beci English ba.

Kinga kuwa basa bama mutum direct N.C.E se yana da Maths and English, zanje inji idan zasu daukeshi, idan kuma bazasu daukeshi ba sede yayi PRE N.C.E.

Mama kamar zatayi kuka tace kasan Allah, Farouk bazeje wanan makaranta ba, makaranta kamar gidan biki, duk wanda yataso se kaji yace can zeje, gaskiya gara ya hakura yayi zaman shekara guda, zuwa wata shekarar se yasake jarabawa yatafi jami'a.

Tashi Malan yayi yana fadin, idan ke kike da iko dashi zaki iya hanashi tafiya, kuma wallahi iname tabbatar maki matukar Farouk betafi wannan makarantar ba, wallahi bazan kara nema mashi wata ba.

Fita yayi yana masifa. Kwallace ta cika idon Mama, Farouk kuwa da yake tsugunne yayi shiru yana sauraronsu. Mama tace Farouk kana jina ko? Duk yanda Malan zeyi kada ka amince da wannan makarantar.

Idan ka nuna kanajin tsoronshi shikenan an maidaka baya, kai ne babba agidan nan kai yakamata ace anfi daukakawa amma yanzu ace wai waccan banzar makarantar zaka tafi. Ai ko Fahad da kafi kokari bazanso yaje can ba.

Dago kai Farouk yayi yace gaskiya Mama nide zan tafi kawai, koma menene nine na jama kaina, Allah yabani kokari amma na tsaya biyema abokai muna shiririta. Da ace na dage nasan zanci duka jarabawata.

Babu amfanin inzauna jiran wata shekara, domin banida tabbacin zanci jarabawar dazan sake,nide kiyi hakuri kawai zantafi. Hannu tasa ta daukeshi da mari tana huci, hannu Farouk yasa ya dafe kuncinshi.

Mama tace tunda haka kace se kaje katafi, kuma naira 1 tawa bazata kara ciwo akanka ba, tunda yanzu kaima ka koma bayan Malan da wadan can banzayen yaran sekaje kayi tayi,wata rana kai ne zakayi kuka da idon ka.

A lokacin da Fahad da Farida zasu tafi jami'a kai kuma sede ka kare da alli kaga kayo gadon ubanka. Tashi kabani waje. Mikewa Farouk yayi yafita yana kuka. Duk abinda sukeyi Malan yana jiyosu.

Har Farouk yakai kofar gida Malan ya kirashi, sosai yaji tausayinshi, hannunshi yakama suka bar gidan. A cikin mota Malan yace Farouk duk naji yanda kukayi da Mamarku.

Kada kalamanta su tsorata ka, kuma tunda yanzu ka gane kuskurenka inaso kasani lokacin gyara baya kurema mutum har se mutuwa ta riskeshi, kuma kai namiji ne, kayi hakuri da duk abinda ze zo maka arayuwa.

Kada ka dauki wannan karatun da zakayi da wasa, kuma kada ka rai nashi, idan ka dage kayi karatun kana cikinyi ma zaka iya sake jarabawa ka nemi English din, kaga duk lokacin daka gama karatunka ko kana aiki ne zaka iya tafiya ka karo karatunka.

Shi karatu da kake ganinshi ba'a rai nashi komin kan kantarshi, kuma inaso kadage idan kashiga makarantar domin ka gyara kuskurenka, inaso kadawo da kokarinka na da. Farouk yace insha Allah. Malan yace Allah yayi maka albarka. Yace amin.

**** *****

Cikin sa'a Farouk yatafi makaranta inda suka bashi Pre N.C.E ze karanci Biology/Geography, haka Malan ya shiryashi babu abinda be sai mashi ba, Mama kuwa ko sisi bata bashi, da kyar ma tace Allah ya bada sa'a, haka yatafi yafara karatunshi.

Sosai yake maida hankali wajen karatu, kuma yana dinkin hularshi, idan yagama ya kaima Malamai, cikin lokaci guda Malamai suka sanshi dan Farouk ya iya dinka hula, sosai yake ciniki a cikin makaranta har ma da wajen makaranta.

Kuma acikin aji sosai yake dagewa, duk abinda akayi masu baya bacci seya karantashi, gashi yanzu yana son addini sosai, sam baya wasa da sallah.

Wata rana sunje cikin gari shida wani abokinshi Hamza da yamma, yaje siyo kayan dikin hularshi, haka suka taho akasa se sauri sukeyi dan ankusa magriba, da yake ranar asabar ne babu class.

Ta wajen makarantar su Fahad suka biyo dan babu nisa daga makarantarsu zuwa tasu. A gefen katangar makarantar sukaga wasu 'yan makaranta kusan su biyar a jikin katangar makarantar, hayaki ne kawai yake tashi daga inda suke.

Hamza ne yace dan Allah Farouk kalli wadan can kamar ba 'yan makaranta ba, ace wai yaro tun yana secondary ya bude hun hunshi da hayaki, zuwa gaba kuma me kake tunanin zasu zama.

Juyawa Farouk yayi danshi bema kallesu ba. Karaf idonshi ya sauka akan Fahad ya daga wata farar takarda daya kunna yana zuka yana fesar da hayakin sama se daruya suke mashi.

Murtsike ido Farouk yayi domin ya tabbatar da abinda idonshi ya gane mashi. Tabbas ko a amafarki yaga Fahad ze iya ganeshi, wasu hawaye ne yaji sun zubo mashi, Hamza yace Farouk lafiya de? Hannun Hamza Farouk ya kama suka nufi inda su Fahad suke.

Daga sama Fahad yaji muryar Farouk, dede lokacin ya zuki wiwi dinshi, ido yazaro lokacin da sukayi ido biyu da Farouk, zumbur ya mike tsaye, kwarewa yayi hakan yasa hayakin yarika fitowa daga bakinshi.

Saurin wurgar da sauran wiwin yayi yana kara kallon Farouk, sauran abokanshi ma duk suka mike.  Kwalla ce kawai take fita daga idon Farouk, Hamza ne yace wai Farouk ka sanshi ne?  Share idonshi yayi yace Fahad din gidammu ne.

Cike da mamaki Hamza yakara kallon Fahad din. Fahad cikin sanyin jiki yace Yaya? Girgiza kai kawai Farouk yayi ya juya baya yana fadin ashe halin da kasa kanka kenan Fahad? Dama na dade ina zarginka ashe zargina gaskiya ne.

Ka cuci kanka, kuma kanka zaka lalata ma rayuwa, tun kana yaronka zaka bata hun hunka da hayaki. Cikin kuka Fahad yace dan Allah Yaya kada ka fada ma Malan. Murmushi Farouk yayi yace Malan kadai kake tsoro ko? Baka tsoron Allah.

Kuma baka tsoron lafiyarka. Shikenan, bazan fadama kowa ba, duk abinda kayi dan kanka. Hamza muje anfara kiran sallah. Fahad yace Yaya dama anan kake? Farouk yace E, kuma ka tabbatar ka koma makaranta.

Juyawa sukayi suka nufi makaranta, zuciyar Farouk kamar zata fashe wai Fahad ne yake shaye shaye? Dama yasha zarginshi akan hakan, dan wani lokacin idan yadawo da dare se yarika jin warin sigari ajikinshi.


Hamza ne yace dan Allah Farouk kada kabari wannan abun ya dameka, tabbas nasan akwai ciwo,amma hakuri shine zefi, kuma kamar yanda kace ba zaka fadama Malan ba, wannan ba shawara bace.

Domin ba'ayin shiru a irin wannan yanayin, Fahad yaro ne, idan har ba a dauki matakin hanashi wannan shaye shayen ba to tabbas idan ya girma abun zefi haka. Gara kabata dashi akan kace zaka rufa mashi asiri dan yaji dadi.

Farouk yace ina tsoron yanda Malan ze dauki maganar ne, Malan yana da zafi, kawai zan fadama Mama nasan zata iya shawo kan matsalar. Hamza yace amma Malan zefi yimashi ta zafi akan Mama.

Farouk yace baka san halin Malan bane, kawai kabari zan fadama Mama. Hamza yace to Allah yasa ya gane, kuma Allah ya shiryeshi. Farouk yace amin. Haka suka nufi makaranta.

Fahad kuwa gaba daya hankalinshi yatashi, tsoro yake kada Farouk yafadama Malan, wani abokinshi ne yace haba abokina, meye na wani damuwa? Ai tunda kaga be dauki wani mataki sosai ba shima be rasa afawa.

Koda ya fada agida kawai kace masu ka dade da denawa, amma taya zasu hanaka jin dadinka, kai bakaji yanda kakeji ba idan kana sha? Nima lokacin da aka kamani agidan mu inasha kawai dan fada ne akamun.

Kuma na nuna masu nabari, shikenan kuma se aka koma ana jidani. Haka suka yita yima Fahad hudubar banza, kafin subar wajen seda wani yakara kunna mashi yabashi yasha sannan suka koma makaranta hankalinshi kwance.

****** *****

Lokacin da akayi hutu malamin su Farida ya bama Fatima takarda ta kawo ma Malan, saboda an kama Farida da wani yaro da dare acikin class suna 'yan tabe tabe, alokacin malamin shi kadai ya kamasu, haka ya zanesu kuma yace seya kaisu wajen Principal.

Kuka suka rikayi suna bashi hakuri, seda ya farfasa masu jiki sannan yace suyi mashi alkawarin bazasu kara ba, haka sukayi alkawari suna kuka. Lokacin da akayi hutu shine ya rubuta takarda ya bama dan uwan kowa yace su kaima iyayensu.

Yasan idan yaran yaba bazasu kai ba, duk da be fadama kowa ba seyai tunanin ai kama iyayensu domin sukara ja masu kunne, kuma yafada masu idan suka sake korarsu za'ayi.

Bayan Malan ya dauko su sam Fatima ta manta da takardar, haka su Fahad da Faisal suka dawo, gidan kowa se murnar ganin dan uwanshi yakeyi. Farida tace shikenan yanzu batare zamu rika dawowa da Yaya Farouk ba? Mama tace Yaya ai yana gidan biki.

Farida tace ina ne gidan biki kuma? Mama tace Isa Kaita mana. Farida tasa dariya tana fadin N.C.E zeyi shi kuma? Mama tace shida Malan sukace sun amince, base yaje yayi tayi ba.

Kude ku dage kutafi jami'a. Fahad ne yashigo yana fadin Mama ina abinci na? Mama tace Oh! Ni, yanzu ya akayi cikinka ya bude haka? Da de baka da cin abinci, ko kun dawo makaranta se kowa yaci kake cin naka.

Fahad yace yo Mama mutum ya kwaso yunwar makaranta ba dole ya nemi abinci ba. Mama tace to kaje kacire kayanka kayi wanka sekaci, dan Allah kalleka kamar ba senior ba, duk kazama kazami wallahi.

Dariya Farida tasa, kafa Fahad ya kai mata yana fadin zanci Uwarki wallahi. Dukewa Farida tayi tana kuka dan taji zafin harbin da yayi mata a cinya. Mama tace bana son sakarci fa, ya daga dawo warku zaku fara fada abinda bakuyi ada.

Tun dazu take son kadawo kuma shikenan kana dawowa zaka hauta da duka, wai meyasa yanzu kake da saurin zuciya ne Fahad? Kuma ko kunyata ba kaji zaka zagi Uwarta, to bayan ni akwai wata Uwar da kuke da ita ne? Juyawa Fahad yayi yana fadin wallahi Mama duk kece kike bata yarinyar nan.

Wallahi idan kikace zakimun wannan rashin kunyar taki Uwarki zanci, fita yayi yana zaginta. Rike baki Mam tayi tana mamakin canjin halayen Fahad, ada yafi Farouk son Farida, amma yanzu shine yake dukanta hada zagi.

Fatima ce da Faisal suka shigo tana rike da hannunshi suna ta dariya tana fadin Allah Yaya seka bani alawata, ai Yaya Saleem ni yace akawo mawa. Faisal yace ai nafada maki sekin biyani zan baki. Kwace hannunshi yayi ya ruga dakinsu itama ta bishi da gudu suna dariya.

Wani bakin ciki ne ya kama Mama, kallon Farida tayi tana fadin yi hakuri kitashi kiyi wanka kici abinci. Farida tace ni da nayi wanka ma gidan Hajiya zanje. Mama tace a'a kibari se gobe, yanzu kizauna ki huta.

Farida tace kai Mama, nide kibarni intafi. Mama tace kinsan de yanzu Malan ze dawo kuma nemanku zeyi, ki bari kawai se gobe. Farouk ne yashigo da sallama hannunshi dauke da jaka.

Farida ce tasa ihu tana fadin ga Yaya oyo oyo. Murmushi yayi yana fadin Farida yan mata, ashe har kundawo? Amsar jakar tayi tana fadin tun dazu ma. Murmushi Mama tayi tana fadin ashe kaima kana hanya? Farouk yace wallahi kuwa.

Gani nayi duk an tafi week end shine nace nima bara inzo nasan 'yan makaranta sun dawo semu gaisa. Mama tace sannu da zuwa, yace yauwa na sameku lafiya? Tace lafiya lau. Shiga ciki inzubo maka abinci.

Yana shiga Faisal yace la! Yaya yaushe kadawo? Farouk yace yanzu nashigo, ai nasan zaku dawo hutu shiyasa nace bara indawo mugaisa. Fatima tace Yaya sannu da zuwa, yace yauwa Fatima ya karatu? Tace Alhamdulillah.


Zaune Farouk yake a dakin Mama bayan yagama cin abinci tana ta tambayarshi yanda makarantar take,Farouk yace lafiya lau Mama, tace to wa yake maka girki kuma? Farouk yace ai na iya tun ina Faskari, Mama tace da kyau.

Dukar da kai kasa Farouk yayi yana wasa da hannunshi. Mama tace wai ni tun dazu nake ganinka kamar baka da lafiya, ko wani abun ne yake faruwa? Kwallace ta cika idon Farouk. Kara matsowa Mama tayi tana fadin kafada mani mana.

Fatima ce tayi sallama, amsawa Mama tayi tana fadin lafiya? Shigowa Fatima tayi tana fadin dama Malaminsu Farida ne yabani takarta yace inkawo ma Malan, shine na manta dazu a mota ban bashi ba.

Mama tace kinji gulma kai, ba anjima Malan din ze taraku gaba dayanku kowa yakawo takardunshi ba, bazaki iya ajewa anjima ki bashi ba? Fatima tace ai batawa bace ta Farida ce. Mama tace ita meyasa be bata ba? Se ke uwar rawar kai? Dukar da kai Fatima tayi kasa. Domin ta karanta abinda yake cikin takardar, kuma ta nuna ma Faisal.

Shine ma yace kada tabama Malan ta kaima Mama dan yasan Malan ze iya dukan Farida, sosai sukayi mamakin abinda Farida tayi, Faisal yake tambayar Fatima yace dama kinsan tanayin haka ne? Fatima tace nide naji ana maganar tana yawan cewa tana son maza.

Amma gaskiya bansan lokacin da tayi wannan abun ba, kuma ma kaji malamin yace be fadama kowa ba. Faisal yace Allah ya kyauta, ina fatan kede ba ruwanki? Fatima tace wallahi ni ba ruwana da kowa.

Cikin tsawa Mama tace to Uwar me kika tsaya kinayi, kitafi kibani waje, idan Malan din yadawo seki bashi. Farouk ne yadago kanshi yace kawo nan mugani, mika mashi tayi ta fita. Mama tace ai da baka amsa ba.

Bude takardar yayi Mama tana fadin karanta mani inji abinda yace, lokacin da Farouk ya fara karantawa seda hawaye suka zubo mashi, kasancewar da turanci malamin ya rubuta yasa Mama bata fahimci duk abinda ya karanta ba.

Sede ganin yana karantawa yana kuka yasa tagane akwai matsala. Mama tace bade korarta sukayi ba ko? Girgiza kai yayi yace wai meyasa komai yake zuwa mana a haka ne? Mama tace wai me yake faruwa? Farouk yace malamin su Farida ne yakawo karar ta.

Mama tace kamar ya? Nan Farouk ya fada mata abinda yace, sosai hankalin Mama yatashi, amsar takardar tayi ta yaga tana fadin baza'a fadama Malan din ba, nida kaina zan ja mata kunne.

Wannan bala'i dame yayi kama? Farouk yace shikenan kowa da tashi kaddarar, shi Fahad ga halin daya jefa kanshi, ita kuma ga abinda take aikatawa. Mama tace bangane ba? Cikin kuka Farouk ya fada mata halin da Fahad yake ciki.

Sosai hankalin Mama yakara tashi, kuka kawai takeyi, wannan wace irin jaraba ce tashigo mata gida? A fili tace Allah ya isa tsakanina dake Inne, burinki ya cika kin lalata mani yara. Farouk yace haba Mama, me kuma Inne tayi maki? Inne bata da laifi laifinsu ne.

Mama tace wallahi banyarda ba. Kuma inaso kaja bakinka kayi shiru, wallahi idan kabari naji wannan maganar a wajen wani sena bata maka rai, kasan de yanda Malan yakejin haushinsu Fahad, idan yasamu wannan labarin shikenan sun zama abun kyama awajenshi.

Ka barni nasan matakin dazan dauka, bazan bari Malan yaji wannan maganar ba bare ya maida mani yara saniyar ware. Nasan halinshi sarai, shi kullum wanda yakeyin abun kirki shine mutum awajenshi, dan haka bazan bari yasan komai ba.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263

馃彙馃彙 A WANI GIDA馃彙馃彙
          馃槶馃槶馃槶

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 [email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 70  鈴� 75

A cikin mota Malan se kame kamen labari yakeyi Zulai kadai take biye mashi. Sun kusa shiga Katsina Malan yace Zulai nide akwai maganar da nakeso inyi, sede bansan yanda zaki dauke ta ba.

Zulai da tun dazu ta dade da harbo jirginshi tayi murmushi tace haba Malan, ai babu wata magana daza ka fada mani in kasa fahimtar ta, kai fa namiji ne, kawai kafadi maganarka. Murmushi Malan yayi yace to shikenan bara mu isa.


Zulai ce tayi mashi kwatance har suka isa kofar gidan Yayansu. Malan yace Malama Suwaiba kishiga ciki zan danyi magana da Yayarmu. Murmushi Suwaiba tayi tace to bakomai mungode ka gaida gida.

Bayan ta tafi Malan yace Zulai dama ba wani abu bane, inaso in hada iri dake. Murmushi Zulai tayi tace to Malan Allah yasa alkhairi ne. Malan yace dama akan maganar Suwaiba ne, nide ina rokon abani dama inshigo cikin mane ma.

Amma ke nakeso kishige mani gaba dan naji kince bata son kula samari, bare kuma ni da nake tsoho. Dariya Zulai tayi tace haba Malan, ina wani tsufa anan? Kawai dan de kana zaune da mace ba 'yar zamani ba.

Duka yaranka biyar fa, wallahi kabari Suwaiba ta amince da kai nasan zata canzaka, domin Suwaiba akwai son gayu. Malan ya washe baki yace Allah ko? Zulai tace sosai mana. Malan yace amma ya kike gani ta wajen Hauwa gashi ke kawarta ce.

Zulai tace haba Malan, ai Hauwa cutar da kai kawai takeyi, na tabbata itace take kara tsufar da kai, domin Hauwa shu'umace, se mutum me zurfin tunani yake iya gane kai dinta. Amma shawarar da zan baka kafara sa mata ido musamman idan tayi baki.

Ko kuma lokacin da yara suka dawo gida hutu. Kuma ni badamuwata bace dan ka auri Suwaiba, domin ni ba garin nake ba. Kome zatace banida damuwa, idan kuma duniyanci takeji dashi na fita.

Kuma tabbas nayi maka sha'awar auren Suwaiba, kuma nasan itace zata maye maka gurbin Inne, domin kayi asarar mace ta gari, kuma ba kowa bane yayi silar rabuwarka da ita se matarka.

Idan kabi komai a sannu zaka fahimta da kanka. Kada kadamu zan samu Suwaiba, kuma nasan zata amince da kai. Malan yace amma nagode Zulai, samun Number dinki domin inji abinda ake ciki.

Bayan ta samashi number ya ciro dubu 5 yabata yace ta bama Suwaiba, dubu 2 yabata yace tayi kudin mota. Sosai Zulai taji dadi, godiya tayi mashi tana fadin aduba mejikin. Malan yace ai dama nine me jikin, kuma yanzu naga likitan gakinan azaune, maganin kuma yana ciki, idan kika amso mani maganin seki aika mani dashi. Ni yanzu gida zan koma. Dariya Zulai tasa ta bude kofa tana mashi asauka lafiya.


Bayan Mama ta gama gyaran gida tayi bakuwa wata 'yar uwarta da take aure a Shargalle, sosai Mama taji dadin zuwanta, bayan sun gama gaisawa Mama tace bara tashiga kitchen ta dora masu abinci, Matar me suna Amba tace muje mana nima ai banason zama ni kadai.

Haka suka shiga suka dora girki, bayan sun gama suka zauna suna fira. Har Malan yadawo Mama bataji karar motarshi ba, domin a waje ya ajeta, kai tsaye falonta ya nufa yana kiranta, yazo shiga yaji ana magana alamun mutum biyu ne.

A lokacin kuwa Mama tana bama Amba labarin irin abubuwan da tayi ta jawo hankalin Malan, da kuma yanda tasa ya saki Inne, da yanda takema su Faisal, har zuwansu Fatima Makaranta da abubuwan da take mata. Komai de seda Mama ta fadama Amba.

Sosai suke dariya, Amba tace amma Hauwa ke ta da bance, babu boka ba Malan kin kwace komai na gidan, kuma kin kama Malan a hannunki, Mama tace wallahi kuwa, ai yanzu ne nake iya daga mashi murya.

Shima gani nayi ze maida mani yara Saniyar ware, niko duk abinda mutum zemun zan iya jurewa, amma idan mutum yafara tabo mani yara wallahi anan zega bacin rai na. Damma de waccan munfukar matar ta shiga ta fita ta saka ma yarana rashin kokari, ai da har yanzu yarana su ke haskawa agidan nan.

To shi kuma Malan yanda halinshi yake, sam baya tunani da kwakwalwarshi, shi akullum duk yaron daya kasance me kokari agida to shine abun so awajenshi, haka kuma duk wanda yaga yana mashi aiki ko kuma yana wani abu da yakeso agaban idonshi to shine tauraro a wajenshi.

 Irin wannan halin nashi nayi amfani dashi wajen saka kaunar yarana azuciyarshi, domin inde yana gida yarana komai sune sukeyi, kuma basa tafiya masallaci seda shi. Haka kuma na saka kiyayyar yaranshi a zuciyarshi, kinga ko ai nayi mashi babban aiki.

Nasan har yaran nan su mutu bazasu dena ganin bakin Malan ba, domin basu taso da soyayyarshi ba, ko yanzu da yake kokarin jawosu ajiki da kinga yanda suke mashi kinsan basu saba ba.

Ganin yanzu yafison yaranta da nawa yasa nake mashi masifa, domin naga idan na tsaya wannan kissar to nice zan kwana ciki, dama saboda wa nakeyi, saboda kishiya ne, kuma tunda na koreta ai se in kwatar ma yarana 'yancinsu.

Kinga yanzu na zamar mashi kargen kafa, domin yanzu Malan baze iya kallon wata mace yace ze aura ba, nidin de nice abokiyar zaman tashi. Amba tace gaskiya agaisheki, ai ban taba jin labari me abun al'ajabi ba kamar naki.

Idan zaki shiga gidaje goma masu kishiyoyi to da wuya ki samu masu irin halinki, domin abinda kowa ce mace ta yarda dashi na hanyar da zata mallake mijinta ko kuma ta kori kishiyarta to hanya daya ce, wato Boka.

Segashi ke cimin ruwan sanyi kin gama da komai. Mama tace aini dama can a rayuwata banyarda da wani abu waishi boka ba, ai duk macen data isa to wallahi base taje wajen boka ba zata kwaci kanta, aini abun da na dauki boka marar aikinyi.

Kuma idan kura tana maganin zawo tayima kanta mana. Kullum yanda kika sanshi ahaka zaki sameshi, sekiji yayi aikin miliyoyi amma idan kika kalleshi kome aikinki bazaki hada dashi ba.

In banda cutar da mata babu abinda sukeyi, su kwanta dasu, kuma su kwace masu kudi, daga karshe su kafa masu sharadin daze halakasu, domin duk wani boka idan yabama mace magani daga karshe sekinji yace idan ta kuskure kaza aikin ze dawo kanta.

Kuma abun haushin se yace mata ciwon daze sameta beda magani, kinga kenan suna sane suke aikata masu haka. Sede har yanzu su Matan basu gane ba, domin zuciyarsu ta mace akan bokansu.

Amba tace wallahi da gaskiyarki, gara mutum yayi amfani da kwakwalwarshi ya kwatoma kanshi 'yanci. Mama tace gani nan de ina zaune agidana lafiya. Amba tace kinga kada dare yayi mani gara intashi in tafi. Mama tace haba ki bari kiyi la'asar mana.

Amba tace ai zan tsaya Mashi. Tashi Mama tayi ta hado mata wasu kayanta dazata bayar da sabulun wanka ta bata da dari biyu tace ta kara tayi kudin mota. Malan da jikinshi ya gama mutuwa haka yaja kafa yashige dakinshi.

Har bakin kofa Mama ta rakata Amba tana ta mata godiya, ganin motar Malan yasa Mama tace ashe Malan din ma yadawo, bara in mashi magana ku gaisa. Amba tace dakin barshi ma. Mama tace kede kibari in mashi magana kila ma ki kara samun na mota.

Yanajin Mama ta taho yayi saurin shigewa bandaki, koda tazo taga yana bandaki seta fita tace tashigo yana bandaki. Amba tace Allah kibarshi wucewa zanyi. Mama tace toshikenan ki gaida gida da yaran.

Malan kuwa wanka yayi yafito, adaki ya iske Mama tana jiranshi, kallo daya yayi mata ya dauke ido, gaba daya tsanarta ce tashigar mashi zuciya, fuska a daure ya zauna. Murmushi Mama tayi tana fadin Malan har kadawo? Amma kayi sauri.

Be kalleta ba yace E, tashi tayi ta kawo mashi ruwa da abinci, alokacin yana kwance ya rufe idonshi. Mama tace Malan tashi ga abincinka, be bude idon ba yace kibarshi idan natashi zanci bacci nakeji.

Mama tace ko inzo in tayaka baccin? Bude ido yayi yace dan Allah kifita banason surutu. Tashi Mama tayi tana tsaki tace dan ma nace zan ta yaka shine zaka kore ni, anjima zaka gani idan ka nemeni ko zanzo, fita tayi tana masifa.

Runtse ido yayi lokaci guda wasu zafafan hawaye suka zubo mashi. A ranshi yana fadin Hauwa kin cuceni, Allah ya isa tsakanina dake, kin gama tarwatsa mani gida, amma kisani wallahi kema sekin dandani irin bakin cikin da kika sani. Kuma yanzu ne zan kara dagewa wajen karo aure.


***** ******

Tun daga wannan ranar Malan ya canza ma Mama, ita kanta shakkarshi takeyi, domin yanzu ko zama gidan bayayi sosai, daya dawo yaci abinci ze kwanta, ana la'asar kuma ze fita, kusan kullum ya kwanta seyayi kuka.

Babu abinda yake damunshi irin rashin mutuncin da yayi ma Inne, yanzu gashi Inne tayi mashi nisa da babu abinda ze hana yaje ya maidota, gashi kwata kwata su Faisal basa sonshi, basa son zama dashi.

Sauran yaran daya saba dasu yanzu sun canza hali, Farouk ne kadai yake ganin hankali yana shigarshi, ya ma rasa ta inda ze fara. Gashi ya aje aiki, tunani yayi akan ya ciro kudinshi da yake tarawa a banki ya gina babban shago a wani karamin filinshi da yake cikin gari, idan yaso se ya zuba provision da kayan masarufi.

Se ya rika zama da kanshi dama yana gajiya da zaman rashin aikin yi, danshi ba ma'abocin zama majalissa bane, saboda yanayin shi yasa beda wasu abokai da yawa.

Wayarshi ce tayi kara, har ta kusa katsewa ya dauka, sunan Zulai yagani hakan yasa ya katse kiran ya kirata.  Bayan sun gama gaisawa Zulai tace albishir na bugo in maka. Murmushi Malan yayi yace ai na kosa inga kiranki, daurewa kawai nayi yasa bankira ki ba.

Zulai tace kasan halin Suwaiba, da kyar ta amince, sede tace ya za'ayi da aikinta? Washe baki Malan yayi yace haba wannan ai bawani abu bane, inada hanyar da zansa ayi mata transfer.

Zulai tace to babu damuwa, kuma nayima Yayanmu magana shima yaji dadi kuma ya amince da maganar sede yana son ya ganka. Malan yace wannan badamuwa bane, zan shirya zuwa gobe inje, amma kituro mani number Suwaiba bazan jira se zuwa gobe inganta ba.

Zulai tace toshikenan, godiya Malan yayi mata ya kashe, tana turo mashi number yakira Suwaiba.



Washe gari haka Malan ya caba ado kamar me shirin zuwa hawan sallah, sallama yayi ma Mama yanufi hanyar fita. Binshi Mama tayi tana fadin ina kuma zaka Malan? Kallonta yayi fuska adaure yace haifata kikayi ne? Cike da mamaki Mama tace bangane ba.

Tsaki Malan yayi yace dole duk inda zanje sena fada maki? Tunda nayi maki sallama aikin ki kice mani Allah ya kiyaye, in ba kuma yanzu kin dena Kissar ba. Juyawa yayi yafita.

Sakin baki Mama tayi tana kallonshi. To me yake nufi da wanna kalmar? Komawa falo tayi ta buga uban tagumi. To wai meyake samun Malan? Tunda yadawo daga Katsina gaba daya ya canza, sam yanzu baya mata fara'a.

Kuma baya son zama agida, gashi yanzu abu kadan se masifa. Gyara zama tayi tace to kode Inne tashiga tsakanina dashi ne? Mikewa tsaye tayi tana fadin wallahi bazan barta ba wannan karon, idan har Malan yaci gaba da yimani haka sena yimata babban tabon da bazata manta shi ba, kuma. Ba akan kowa zan dau fansa ba se akan Fatima.

**** *****

A cikin kwana biyu Malan da Suwaiba suka kulle, sosai suke zuba soyayya, gaba daya Suwaiba ta fara canza Malan, yanzu sam baya damuwa dan Mama batazo dakinshi kwana ba, haka suke kusan kwana suna waya.

Idan kuma yaga ranar tana jin kirki to baya dawowa gida da wuri seya gama wayarshi da Suwaiba sannan, gashi duk bayan kwana biyu seyaje Katsina, sam Mama takasa gane kanshi.

Gefe guda kuma ya fara gininshi na shago. Haka yaje ya samu Hajiyarshi da maganar aure, Hajiya ta rufe ido tana ta masifa tana fadin me ka nema karasa a wajen Hauwa? Mace me kirki, ai kaga yanda ka kare da kayi wancan auren, kuma yanzu zaka zo mani da maganar aure.

Malan yace Hajiya bakisan ko wacece Hauwa ba, nima se kwanan nan nasan asalin halinta................. Labarin duk abinda yaji tana fadama Amba ya bama Hajiya, sosai hankalin Hajiya yatashi.

Babu bata lokaci tace ta amince, kuma kada yafada mata  zeyi aure yabari ta gani daga sama, domin ta cuceshi, kuma zata samu Kawunshi suje domin suyi magana da Yayan yarinyar. Sosai ran Hajiya ya baci, haka tayi ta masifa, haka Malan ya yi ta bata hakuri yayi mata godiya ya tafi.


Haka Kawun shi da wani abokinshi suka je Katsina wajen Yayan Suwaiba bayan sun gaisa suka ba da kudin neman aure, sosai sukaji dadin yanda Yayanta ya amshe su, kuma yace idan sukayi shawara suka tsaida rana zasu aiko masu, godiya sukayi masu sukace zasu aiko da kayan sa ranar.

Sosai Malan yaji dadin labarin da suka fada mashi, haka ya cigaba da shirye shiryen aurenshi ba tare da Mama ta sani ba.

A ranar visiting kuwa da Mama tayi mashi magana cewa yayi ta shirya masu kayan zeje masu shi kadai, sosai tayi mamaki, data taso mashi da masifa yace idan ita takeda iko da kanta se taje.

Haka yakawo mata kayan miya da nama yace tayi masu miya, kuma ta sama kowa tashi a cooler da abinci da ban. Haka yayo masu provision kowa da kwalinshi, dakinshi ya wuce dasu ko gani batayi ba.


Lokacin data gama hada masu komai ya dauka yasa mota, dakinshi yake ya dauko kayansu ya saka mota se kallonshi takeyi, haka yashiga mota yana fadin bakida sakon da za'a kaima Farida? Saboda mamaki kasa magana tayi haka ya tafi.

Kasa tsayuwa tayi, haka ta jingina tana tunanin kode Malan yasan wani abu daga cikin abun da take yima Fatima ne? Jin jina kai tayi tace tabbas Fatima itace ta fada ma Malan, wannan dalilin ne yasa ya canza mata lokaci guda.

Idan ko hakane wallahi zata dauki mataki, komawa tayi ta dauko hijabinta  ta wuce gidan Maman Sultan.


Lokacin da Fatima taji ana ne manta tasha mamaki da akace babanta ne yazo masu visinting, Farida ta rigata zuwa itama tayi mamakin ganinshi, har take tambayarshi Mama, yace tana gida baki tayi shiyasa.

Haka suka gaisa yabama kowa kayanshi ya basu kudi, haka sukayi mashi sallama, har sun tafi ya kira Fatima, juyowa Farida tayi tana kallonsu duk bakin ciki yagama kamata, meyasa ita ba'a kirata ba? Tsayawa tayi tana kallonsu.

Malan yace Fatima nasan kinajin haushi na ko? Girgiza kai tayi tana dukar da kai kasa, Malan yace kiyi hakuri nasan Hauwa tana rage maki kayan abinci, shiyasa ma yau nazo da kaina, kuma daga yau bazata kara zuwa maku visiting ba.

Fatima tace to, murmushi yayi yace zan tafi kidage da karatu, juyawa Fatima tayi aranta tana fadin kaji malan, da can besan ana mata haka ba seyanzu da yaga takusa gamawa sannan zece haka, kuma gashi Innenta tana gidan me kudi shi kuma ya aje aiki shiyasa yanzu zece yana son mu.

Gaba daya ma ranta baci yayi haka ta wuce wajen Lubna, tana zuwa ta bata labarin abinda yafaru. Lubna tace kiyi hakuri Fatima, tunda ya fadi haka kila da gaske yakeyi be sani ba. Tashi Fatima tayi tana fadin Lubna bakisan ko waye Malan ba. Wallahi zan iya cika littafi da labarin gidanmu. Dariya Lubna tayi tace ai seki fara.

***** ****

Haka Malan ya dage da gyaran bangaren Inne, kuma ya tada wani gini me dakuna biyu daga bayan dakunan gidan, kasancewar daga can baya dama yabar fili saboda yanaso ya gina ma yaranshi maza dakuna hakan yasa yanzu yake gina dakuna biyu.

Ita de Mama kallonshi kawai takeyi, dan lokacin da tayi mashi magana cewa yayi ina ruwanta, ba gidanshi bane, tace to ai naga bangare daya kake gyarawa, yace kisa ido kiyi kallo idan zaki iya.

Bayan angama gyaran dayen part din yace itama ta kwashe kayanta da maida dakinshi za'ayi gyara, haka ta kira Maman Sultan ta ta yata suka kwashe. Maman Sultan tace anya Malan ba aure zeyi ba? Mama tace haba de aure.

Ai wallahi babu matar data isa takara shigowa gidan nan, kuma Malan sam beda son mata, ko bayan rabuwarshi da Inne cewa yayi dama rabo ne kawai yasa ya aureta amma shi beda ra'ayin mata biyu.

Kawai de yanaso yayi gyara ne saboda kinga su Farida sun zama 'yan mata kila bangaren su Fahad ze maidasu su kuma ga dakunansu can ana masu abaya. Maman Sultan tayi murmushi tace Allah ya temaka.


Bayan angama mata gyara ta maida kayanta shima aka gyara mashi nashi part din, cikin lokaci kan kani aka gama ginin dakinsu Fahad, kowane daki da banda kinshi, daya Fahad da Faisal, dayan kuma na Farouk ne. Haka ya maida masu gadonsu da kayansu ya kulle part din Inne.


Daga Katsina kuma suka aiko masu da sa rana nan da wata 2, amma idan sunaso akara to, babu bata lokaci sukace yayi. Kudi Malan ya bama Suwaiba yace ta hada lefenta da kanta dan bayaso ya bama wasu su siya mata kayan da bataso.


**** ****


Lokacin da biki yarage saura sati 3, a na saura kwana biyu hutu.  A ranar laraba aka kama su Fahad shida abokanshi sun dira gidan wani malami da sukayi tafiya shida iyalanshi, lokacin da dare ne, Vice Principal shida wani malami sun dawo da school area bayan kowa ya tafi daki wajen karfe 10 na dare.

Vice Principal ne yafara ganin yaro na karshe daya dira katangar gidan, nuna ma malamin dasuke tare yayi, cikin sauri yace yaje yakira masu gadi guda biyu, haka ya nufi kofar gidan.

Masu gadin suna zuwa Vice Principal yace kawai su shiga, haka suka dira, da Fahad suka fara cin karo ya dauko wata bakar jaka hannunshi daya kuma ya kunna wiwi yana zuka.

Sauran ma kowa da abinda ya dauko sunata shan wiwinsu wasu kuma suna shan sigari, Fahad yana fadin kuyi sauri mufita, lokacin da suka fito su kuma masu gadin sun boye, suna zuwa zasu haura katangar Vice ya dallesu da fitila.

A kidime suka zubar da kayan suka fara neman hanyar guduwa, masu gadin ne sukayi saurin cafkesu. Gaba dayansu hankalinsu yatashi, saurin yadda abinda suke sha sukayi.

Vice yace kowa yadauki abunshi, haka suka dauka jikinsu yana rawa, sawa yayi dayan malamin ya haska mashi su, haka ya matso da kayan da suka yarda akusa dasu ya daukesu hoto.

Kuka sukasa suna rokonshi yayi hakuri, yace bade kune 'yan iskan makaranta ba, daga kanku wasu bazasu kara marmarin aikata irin wannan laifin ba, kushigo har cikin gidan malami ku rika sha mashi wiwi da sigari saboda ku 'yan iska ne.

Megadi, kutafi dasu su kwana a wajenku, domin gobe za'a yanke masu hukunci. Haka suka tafi dasu se kuka sukeyi, ba kamar Fahad, dan yasan ya shiga 3 awajen Malan.


Washe gari ranar alhamis bayan malamai sun gama meeting aka kada assembly, gaba daya makarantar kowa ya taru, kowa da abinda yake tunani, wasu ma suna fadin ko hutu za'a bada. Principal ne da Vice suka hau saman step din, sauran malaman kuma suna gefe.

Haka masu gadi suka fito dasu Fahad gaba dayansu sunyi zuru zuru, agaban mutane aka ajesu daga sama, kowa se dukar da kai ya keyi. Gaba daya 'yan makarantar kowa da abinda yake fadi, domin da yawa mutane sun san halinsu.

Hannu Vice ya daga hakan yasa kowa yayi shiru, bayan sun gaishesu yasa akayi addu'a, bayani yafara kamar haka:

Ina fatan kowa yaga wadan nan yara da suke agabanku, kuma kowa yasan suna daya daga cikin daliban makarantar nan, wasu daga cikinsu suna SS 2, wasu kuma SS 3, ajiya da dare nida Malan Shu'aibu muka kamasu sun haura gidan Malan Bala, kasancewar basa nan sunyi tafiya.

Bayan nakira masu gadi muka shiga gidan, ace bayan sata hada shaye shaye sukeyi, kuma ba sigari kadai ba, wiwi muka kamasu suna sha acikin gidanshi saboda rashin tarbiya.

Wayarshi ya daga sama yana fadin hotunansu suna nan ciki kuma zamu nuna ma Uban kowane yaro, bayan nan kuma daga yau su ba daliban wannan makarantar bane, mun yanke wannan hukunci ne saboda hakan yazamo jan kunne ga sauran Dalibai.

Kuma daga yanzu duk wanda aka kama yana mana shaye shaye acikin makaranta, ko a waje, tabbas shima ze fuskanci irin wannan hukunci. Me kuka sani arayuwa da zaku jefa kanku cikin irin wannan rayuwar? Me zaku iya zama nan gaba idan har baku dena wannan banzan halin ba.

Iyayenku sun kashe kudi abanza sun kawoku makaranta amma da abinda zaku saka masu kenan, to wallahi ko suwaye iyayenku daga yau kun bar makarantar nan, sede kowa ya koma gida iyayenshi su sake mashi wata makarantar.

Kuma kowannansu ze karbi bulala 20, kuma daga nan kayanku kawai zakuje kudauko Principal ya bada School bus domin akai kowa gida, badan komai ba saboda mu damka ku a hannun iyayenku kamar yanda suka kawoku suka damka mana ku.

Kuma mu nuna masu irin ta'asar da kukayi. Alhamdulilahi anyi sa'a acikin ku biyar mutum 3 a Katsina suke, suran biyun kuma daya dan Mani ne, dayan kuma dan Kaita ne, dan haka bayan kun amshi bulalarku masu gadi zasu raka ku kudauko kayanku kuzo mutafi.

Ina fatan wannan ze zama darasi agareku. Masinja aka kira wanda dama shine yake ma duk wani me laifi bulala, wata katuwar dorinace a hannunshi, haka Vice yasa masugadi suka rika turosu daya bayan daya ana zanesu.

Ihu kawai sukeyi, wasu daga cikin 'yan makaranta sunji tausayinsu ganin yanda suke kuka, jikinsu duk ya fashe, haka aka gama zanesu sannan aka sallami yara masugadi suka tasa su zuwa daki domin su dauko kayansu.

Da kyar suke tafiya haka kowa ya dauko kayanshi suka saka a mota, Vice da wasu malamai guda biyu ne suka shiga motar suka tafi dasu. Acikin mota se kuka sukeyi, anan ma Vice fada yayita masu.

Haka suka fara kai 'Yan Katsina su 3, kowa seda suka ga mahaifinshi, kuma suka nuna mashi hotonsu sannan suka damka mashi takardar kora, duk mahaifin da aka mikama danshi da takarda se yayi kuka.

Bayan sun gama da Katsina suka wuce Kaita, daga karshe suka dauki hanyar Mani, Fahad in banda kuka babu abinda yakeyi, Vice kuwa se fada yake kara mashi, domin yasan Malan, haka suka shiga cikin garin Mani nan suka tambayi Fahad ya nuna masu hanyar unguwar, yana kuka yana nuna masu.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
馃彙 A WANI GIDA馃彙馃彙
          馃槶馃槶馃槶

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 [email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 75  鈴� 80

Malan ne ya fito daga gida yana shirin tafiya sabon shagonshi da aka gama ginawa domin ya duba aikin da akayi, Mama tana biye dashi abaya tana ta masifar seya fada mata dalilin da yasa yanzu baya kulata, kuma baya sakar mata fuska.

Shikam yayi banza da ita bayan ya fitar da motarshi ya koma domin rufe gate din. Mama tace Malan da fa kai nake magana. Malan yace ina ganin kin fara samun tabin hankali, domin babu wata mace me hankali da mijinta zefita ta biyoshi da irin wannan haukan da kike yi.

Ina a gidan nan na kwana? Me ya hana tun jiya da dare idan kina son magana da ni bakizo dakina kikamun ba? Saboda kina tashen iskanci shiyasa kikayi kwanciyar adakinki dan kina tunanin idan na damu dake dole in biyoki.

Se kuma yanzu dan rashin hankali zan fita ki biyoni har bakin gate kina daga mun murya. Idan kece kike iko dani dan Allah kicigaba da yimani irin wannan iskancin wallahi zakiga matakin dazan dauka.

Mutuniyar banza wadda duk kissar da take takama da ita irin ta jahilan mata ne. Gate din yarufe yabar Mama da sakin baki. Har zeshiga mota yaga School Bus ta Dutsinma tana karasowa.

Maida murfin motar yayi ya kulle, tsaye yake har suka karaso, haka nan yaji gabanshi se faduwa yakeyi. Vice yafara ganin yafito hakan yasa yasaki murmushi, shima Vice din murmushi yayi se kuma duk yaji babu dadi.

Sanin abinda yakawosu. Malan yace ikon Allah kaga mutanan Dutsinma, yau kaine da safen nan. Sauran malaman ne suka fito se kuma ga Fahad yafito yana dauke da jakarshi se katifarshi a kulle.

Fuskarshi duk a kumbure take, jikinshi duk datti sannan ga sahun bulala awuyanshi da hannunashi. Kurama Fahad ido Malan yayi jikishi duk yayi sanyi, bayan sun karaso Vice ya kalli Fahad yace shiga daga ciki.

Hannu yabasu suka gaisa Malan yana fadin kushigo daga ciki mana. Vice yace kai bama se mun shiga ba, Malan yace haba ai bazamu tsaya anan ba, dan Allah kushigo. Zaune suke afalo Malan yasa Mama takawo masu ruwa dan ita bama tasan Fahad yashigo ba, dan yana shiga yayi part dinsu yana Kuka.

Bayan ta gaishesu ta tashi zata fita Vice yace ai Hajiya da kin zauna wajenku mukazo gaba daya. Malan yace to Vice Allah de yasa lafiya, dan ban gamsu da ganin da nayima Fahad ba, gashi kuma se gobe ne hutu yan Fedaral ne kawai zasuyi hutu yau.

Yanzu ma fitar da nayi zanje shago ne daga can inwuce in daukosu kuma se gaku? Gyara zama Vice yayi gaba daya kunyar sanar da Malan abinda danshi yayi yake, amma babu yanda ya iya haka ya zayyane mashi duk abinda yafaru har zuwa hukuncin da makaranta ta dauka, kuma ya nuna masu hoton daya dauka.

Kuka Mama tasa tana fadin wallahi bazan taba yafe maki ba, muguwa azzaluma me bakin hali, gaba daya kin gama lalata mani yarana. Malan da zufa ce kawai take zubo mashi ya daka mata tsawa yana fadin tashi kibar wajen nan.

Saurin tashi Mama tayi tana kuka ta nufi bangaren su Fahad. Malan ya dade beyi magana ba, da kyar ya iya bude baki yace Innalillahi wa inna ilaihirraji'un. Sosai yabama sauran mutanan da suke falon tausayi.

Vice ne yace Malan kayi hakuri, nasan kai babban Malami ne, asalima karike mukamin Principal, nasan kasha haduwa da irin wadannan laifukan har ma da wadan da suka fisu, na tabbata ko kai ne iyakar abinda zakayi kenan.

Kayi hakuri dama haka duk wasu iyaye suke fuskanta musamman idan akace sun tara zuri'a, dole se sunyi hakuri da duk wata kaddara tazata fado masu. Inde mutum yana da yara dole seya hada da addu'a musamman yaran zamanin nan.

Tunda har Allah yasa yana SS 2 abinda zefi ka maidashi Day, koba komai kullum agabanka ze tashi kuma ya kwana agida, zakafi samashi ido fiye da idan baya gabanka, kuma kada kace zaka dauki mummunan mataki akanshi.

Domin irin wadan nan ba'a juya masu baya alokacin da suka kauce hanya, alokacin ma yakamata afi jawosu ajiki, idan Allah yaso sekaga sun shiryu, amma idan aka watsar dasu wallahi abinda zasuyi se yafi na baya.

Yawanci manyan barayin da muke dasu da yara masu shaye shaye idan kaduba karuwar lalacewarsu hada sakacin iyayensu, domin wani Uban daga inda akace ya kama danshi da wani mugun hali shikenan se ya dora mashi karan tsana.

Wasu korar yaran suke daga gidansu, wasu kuma shikenan daga ranar yaran sun zama abun kyama da kyara agaresu, gaba daya se su fara nuna masu banbanci tsakaninsu da sauran yaran gidan, ko shawara za'ayi basa kiran su.

Gaba daya se kaga sun zare hannunsu daga kansu, idan karatu ne bazasu tsaya su kula da sunje ko basu je ba, yawanci Iyaye mata sune kadai zaka samu suna janyo masu irin wannan hali ajiki, domin Uwa tafi Uba tausayi.

Daga irin haka kuma se asaka ma yaron wani tunani na daban, idan be shan wani abun ma dalilin banzatar dashi da akayi se yaje yakara haduwa da wasu mugayen abokan sukara koya mashi wani abun.

Kuma shima daga lokacin daya fahimci an cireshi daga layin sauran yara shikenan shima baze kara shiga cikin sauran 'yan uwanshi yazauna ba, daga lokacin ze fara kebe kanshi, se kuma tunani kala kala yarika shigarshi.

Kadaici se yafara damunshi, idan ba'ayi sa'a ba yafara shan kwaya shikenan kuma ya gama kashe kanshi, ga damuwar abinda aka mashi, ga kuma aikin kwaya, shikenan se kaga yaro ya kangare, daga karshe idan be koma babban barwo ba, to kwakwalwarshi zata tabu.

Kaga duk abinda yaje ya aikata dan gidan wa za'ace? Dole akira sunan mahaifinshi ko mahaifiyarshi, kuma har ya mutu baza 'a cireshi daga cikin gidansu ba. Haka zalika duk iyayen daka ga wai yaransu yana cikin irin wanna halin sun ce sun manta dashi wallahi karya ne.

Kai koda tafiya yayi yabar gidan har abada bazasu taba iya cireshi daga zuciyarsu ba. Kaga kuwa babban rigakafin da yakamata iyaye suyi shine surika kokarin jawo yaransu masu irin wannan hali ajiki.

Hakan zesa yaro yarika jin kunyar aikata wani abu marar kyau. Kasan Allah, akwai wani abokina dana sani Allah ya hada yaronshi da wasu mugayen abokai, haka suka koya mashi shaye shaye na fitar hankali.

Kasan matakin daya fara dauka daga lokacin daya kama yaron yana shaye shaye? Makarantar da yakeyi yafara cireshi, dama makarantar kwanace, Day ya maidoshi, kuma duk inda zeje tare yake zuwa dashi matukar baya makaranta.

Wani lokacin ma shi yake aike zuwa wani wajen, kuma koda yaushe suna tare agida, haka idan dare yayi baya barinshi yafita yawo idan ma shima Uban baze zauna gida ba, haka yake jan yaron sufita waje.

A hankali se yaron yadena shan abubuwan dayake sha, domin koda yaushe suna tare da uban, kuma gatan da yake nuna mashi ada seya linkashi, idan wata shawara zeyi to seya sakoshi aciki.

Koda sauran yaran kowa yafadi ra'aryinshi sekaji Uban yace ajira wane yazo. Irin wannan abubuwan da ake mashi sune suka kara sashi farin ciki, kuma yaga babu wanda yake tsangwamarshi saboda yana shaye shaye.

 Wallahi Malan cikin ikon Allah wannan mutumin yana addu'a kuma shima yana kokari wajen temakon yaron Allah yasa yaron yashiryu.

Yanzu haka maganar da nake maka yaron ya gama karatun degree dinshi a fannin likitanci, idan ba an fada maka ba bazaka taba cewa ko goro yasha ba. Kaga me yajawo haka? Saboda iyayenshi basu banzatar dashi ba.


To bare kuma kai, duka Fahad shekararshi nawa? Kasan wani lokacin kowa da irin yarintarshi, wasu manyan mutanan idan da za'a tono yarintarsu wallahi abun baze fadu ba, dan haka ina rokon ka kada kabari zuciya ta debeka kayanke danyan hukunci wanda ze saka danasani nan gaba.

Yana da kyau ka nuna mashi fushinka, amma dan Allah kada kazamo kamar sauran wasu iyayen. Ka kokarta kayi da jikinka, kamika ma Allah sauran, Allah yana karbar addu'ar bawansa aduk lokacin da yarokeshi.

Allah yashirya mana zuri'a baki daya, kuma yabamu ikon tarbiyantar dasu. Se alokacin hawaye suka zubo ma Malan, sosai yake kuka kamar karamin yaro, haka suka yita bashi hakuri. Wayarshi ce tayi kara, yana dubawa yaga wani malaminsu Fatima ne yakirashi.

Hannu yasa ya goge idonshi sannan ya daga wayar, bayan sun gama gaisawa Malamin yace dama yarane sukaga haryanzu ba'azo daukarsu ba, kuma sauran yaran duk sun tafi. Malan yace dan Allah Malan kamun wani temako, bansani ba ko suna da kudin mota a hannunsu.

Nima har nashirya zan taho wata matsala ta tsaidani, amma idan suna da kudi ka temakeni kadorasu a motar Mashi, nasan idan sukazo zasu iya kowa kansu Mani. Malamin yace badamuwa, idan ma basu da kudin za'a basu. Malan yace to nagode.

Kallon Vice yayi yace nagode da irin bayanin da kayi mani. Kuma tabbas koda nine nasamu irin wanna case din to irin matakin da kuka dauka zan dauka, babu abinda zance sede ince Alah yasaka da alkhairi, kuma Allah yashirya mana yaranmu.

Kuma insha Allah zanyi amfani da shawarar daka bani. Tashi sukayi suna fadin Allah ya tsare gaba, godiya Malan yayi masu suka tafi. Kasa fita yayi haka ya koma ya kwanta yanajin wani bakin ciki yana shigarshi.

Dama shi yadade da zargin Fahad yana shan wani abu, sede yanda Mamarshi ta dage akan babu abinda yakesha hakan yasa ya kyaleta. Tashi yayi ya nufi dakin Mama domin yaga Fahad din.

Yana saka kafarshi afalo yaji Mama tana kuka tana fadin, haba Fahad, yanzu seda kajawo mani abun kunya ko? Duk irin gargadin danayi maka baka jiba ko? Ai na dauka tunda Farouk ya kamaka kana shaye shaye yazo yafada mani nayi maka fada kuma nace bazan fada ma Malan ba nasan yana iya tsanarka zaka dena.


Ashe daka koma makaranta ma se abun yafi na da, yanzu ya kakeso inkasance acikin unguwar nan? Kasande ba kai kadai bane dan garin nan a makarantarku, karewa ma hada dan unguwarku a makarantar.

Kuma dole gobe wannan maganar ta fasu a garin nan har ma da unguwar nan, shikenan kasani jin kunya,ko wata sabga akeyi bazanji dadin shiga cikin mutane ba, duk inda nashiga haka za'a rika nuna ni.

Dama kowa yasanni da iya yada magana idan aka samu yaron wata yayi wani abun, se gashi yau Dana ne aka kama wai yaje sata, kuma yana shaye shaye, daga karshe kuma an koreshi daga makaranta.

Haba Fahad baka kyauta mani ba, meyasa duk yanda nake kokari wajen kareku daga fadan Malan baka gani? Bani da wani buri agidan nan kamar inga cewa kune asaman kowa, kuma kune nagaban goshin Malan, amma kai baka gani.

Dama yanzu Malan baya sona, kaga yanzu ka kara debo wata mganar shikenan komai akai na ze kare, duk yanda naso ace yaran Inne sune suke cikin irin halin da kuke amma abun ya gagara.

Ka duba lokacin daka jima Faisal ciwo, saboda in kareka daga fadan Malan nasa shi yace faduwa yayi, ko lokacin da Malan yace mun yana zarginka tabbas nima alokacin naga alamun shaye asheya a wajenka, amma saboda banason laifin ka haka na rufe ido nace banyar da ba.

Kalli yanda aka maida maka jikinka kamar wani jaki. Cikin kuka Fahad yace dan Allah Mama kada kibari Malan yakara dukana, wallahi jikina ciwo yakeyi, bulala 20 akayi mana, kuma da katuwar dorina.

Mama tace niyanzu banida bakin magana, amma insha Allah baze duke ka ba, sede nasan tabbas daga yanzu kai ne ja baya acikin yaranshi, yanzu Faisal ze amshe ragamar gidan shida Fatima.

Fahad yace shikenan yanzu Malan baze kara sona ba? Mama tace bazan taba bari hakan yakasance ba, kamar yanda Inne ta lalata mani kai, nima sena saka tsanar Faisal da Fatima a zuciyar Malan.

Idan yana tunanin kai kadai ne wanda yake shaye shaye, to shima Faisal din zamu san yanda zamuyi Malan yasamu wani abun ajakarshi, kaga koya rantse mashi baya sha baze yarda ba. Ita kuma Fatima nasan sharrin da zan ja mata.

Ka kwantar da hankalinka babu abinda ze faru da kai, idan ma tsanar ce to sede ya tsaneku ku 3. Tashi kaje kayi wanka kazo kaci abinci kasha magani se in shafa maka magani ajikinka.

Murmushin takaici Malan yayi seya fasa shiga dakin kawai ya juya ya koma falonshi, aranshi yana tunanin wane irin hali Hauwa take dashi haka? Mace kamar wadda bata da tunani, ashe dama tasan Fahad yana shaye shaye amma ta boye mashi.

Shima Farouk ya sani amma yayi shiru. Ko dayake ba laifinshi bane, dama dole ita ze fara fada mawa, kuma duk umarnin da tabashi dole yabi. Amma tunda haka ne ze kyaleta dashi.

Kuma baze taba yimata maganar Fahad ba, idan kunya ne se ta fishi jin kunya tunda itace take shiga cikin mutane, shikam yasan babu wanda ze tareshi da maganar, idan ma za'ayi maganar sede bayan idonshi.

Kuma shi dama bame shiga cikin jama'a bane. Murmushi yayi daya tuna sharrin da takeso tajama Faisal da Fatima, aranshi yace wannan kuma tsakininki da Allah ne, domin kin cutarsu dasu da yawa, kuma Allah baze barki ba.

Idan kuma kina tunanin Malan din da kika sani ne ada wanda baya bincike to kin makaro, Allah ya kaimu lokacin da zaki ja masu sharrin, dadin abun ma Faisal baze dawo hutu ba, Fatima kuwa da nayi aure tabar dakin ki.


Se wajen azahar su Fatima suka iso, Farida da gudu tashiga gida tana kwala ma Mama kira, fitowa tayi da fara'a tana fadin ga yan makaranta, rungumeta Farida tayi tana fadin wai meyasa Malan beje ya dauko mu ba? Mama tace kede muje kicire kayanki.

Baki yayi shiyasa. Fatima ce tashigo tana goye da jaka, sosai takara kyau, kamar ba makaranta takeyi ba, tayi haske tayi kiba, kyanta seya kara fitowa, lokacin data shigo Mama harta juya tajiyo sallamarta.

Juyowa tayi tare da amsawa, sakin baki Mama tayi tana kallonta, gani tayi tazama cikakkar budurwa, gashi tazama me kyau, kamar ba a kauye take ba, jikinta kanshi yayi kyau se sheki yakeyi.

Risnawa Fatima tayi tana fadin Mama ina wuni? Seda ta maimata so biyu sannan Mama ta farga da maganar da take mata, daure fuska tayi tace lafiya. Juyawa tayi tashige ciki gaba daya bakin ciki ya gama kamata.

Saboda ba zaka hada Fatima da Farida ba awajen kyau, ita Faridar ma duk seta rame takara duhu. Wucewa Fatima tayi dakinsu domin ta cire kayanta tayi wanka, Farida kuwa tana dakin Mama, sosai Fatima tayi bakin cikin rashin dawowar Faisal, tasan wannan hutun zata yishi ne kawai amma bazataji dadin komai ba.

Amira ce da Saddik suka shigo da gudu, kai tsaye dakinsu Fatima suka shiga, suna shiga Amira ta rungume Fatima tana dariya, Fatimar ma dariyar take tana fadin Amira, Saddik yace Fatima an girma, hararshi tayi tace wallahi ka rai na ni.

Dariya yayi yace to sannu da zuwa, ai de mun rigaku dawowa. Fatima tace muma de ai gashi mun dawo. Amira tace ina Yaya na? Fatima tace ai Yaya baze dawo ba se hutun sallah. Turo baki Amira tayi ta saki Fatima ta juya tana kuka.

Dariya suka sa mata,Saddik yace yau akwai rigima, kinsan Mama tace tun jiya duk abinda aka bata seta ragema Yaya, yanzu haka bataci abinci ba wai shitake jira, ganin ba taji karar mota ba yasa tace inzo in rakata wai tsoron Mamar su Farida takeyi.

Fatima tace nima wallahi duk banajin dadin rashin dawowarshi. Saddik yace ai se hakuri bara inje inji dramar da takeyi, har yanzu yarinya tana SS 2 amma batasan ta girma ba. Fatima tace Amirar ce yarinya? Kasan de ai ta girmeka. Saddik yace ada ba. Dariya suka sa yafita.

A can gida kuwa rigima sosai Amira takema Mama wai Yaya bedawo ba, se kuka takeyi, da Mama tagaji da lallashinta ta dauko bulala tace wallahi ko kimun shiru ko inzaneki, wai ke se yaushe ne zakisan kin girma? To Yayan baze zauna yayi karatu ba? Tashi ki bani waje.

Baban Saddik ne yashigo yana fadin haba Maman Saddik, ya zaki hada mata zafi biyu, amma de kinsan tun jiya take dokin dawowarshi ko? Mama tace tun jiyan inda kafada mata gaskiya ai da yanzu bata ji ciwo sosai ba, amma ka biye mata kana fadin yau ze dawo, ai gashi nan bedawo ba.

Baba yace taso Mamana Yaya zedawo daya gama karatu, kuma ai zedawo hutun Sallah kinji? Haka yayita lallashinta da kyar ta hakura.


Zaune suke gaba dayansu a Falon Malan, bayan sunci abinci sunyi sallah suka shigo gaishe shi dan tunda sukazo basu ganshi ba. Fahad kuwa kasa fitowa yayi dan ko abincinshi sede Mama ta ai ka mashi dakinsu na can baya, datace yafito yace baze fito ba.

Bayan sun gama gaisawa,  Malan ya tambayesu ya makaranta, sukace lafiya lau. Tambayarsu result dinsu yayi, Fatima ce ta fara mika mashi nata, gaba daya ta cinye subject dinta, duka excellent.

Farida kuwa da kyar ta mika result dinta, murmushi Malan yayi ganin irin result din data kawo mashi, kallonta yayi yace tabbas idan kika cigaba da kawo mani irin wannan result din, to bazaki wuce wannan ajin ba.

Kinsan de halin makarantarku, basa barin mutum yawuce haka zasuyi ta mashi repeating, to kisani hukunci daya zan yanke maki, matukar wannan karon baki wuce SS 1 ba, to kinbar makarantar kenan, zan maidoki Day, idan kina fita kinashan rana da tafiya zaki fi maida hankali. Kutashi Allah yayi maku albarka.


Lokacin da dare yayi haka Malan ya nufi dakin Fahad, lokacin Fahad yana zaune ya gama cin abinci ya kunna sigari yana sha, tunda Malan ya doshi dakin yafara jin wari, yana isa kofar dakin ya daga labulen, ido biyu sukayi da Fahad.

Da sauri Fahad ya wurgar da guntuwar sigarin ya mike tsaye, hannu Malan yasa ya kamo hannunshi tare da take sigarin suka fito waje. Kai tsaye falonshi suka nufa Fahad se zare ido yakeyi, dan tunda yadawo basu hadu da Malan ba.

Zaune Malan yake asaman kujera yayin da Fahad yake duke agabanshi. Kallon shi kawai Malan yakeyi, duk ya rame yayi yayi baki, bakinshi ya dafe kamar wanda ya dade yana shaye shaye.

Fahad! Malan yakira sunanshi, kasa dago kai Fahad yayi, Malan yace irin rayuwar daka daukarma kanka kenan ko? Yanzu wace riba kaci da aka koreka daga makaranta? Shikenan sauran yaran da kuka shiga makaranta tare sun wuceka.

Haka zasu gama karatunsu su zama wasu manya kai kuma ka lalata rayuwarka. Kana karaminka amma kasan kasha abinda ze bugar da kai. Shin kana sallah kuwa? Kara dukar da kai Fahad yayi, Malan yace gaba daya ka zanca.

Kuma ni bazan duke ka ba kamar yanda kake tunani, sede zan baka shawara kayi kokari kabar wannan halayyar da kakeyi, kada ka biye ta Mamanka, domin bata baka shawara me kyau.

Idan aka koma hutu zan maidaka Day kuma zanyi kokari su daukeka a SS 3, nasan ba'a gama registration na WAEC da NECO ba, idan suka yarda se inyi maka kazauna kasamu kayi jarabawarka kaga seka gama tare da sauran 'yan ajinku.

Idan kadena duk abubuwan da kakeyi zakaji dadin rayuwarka nan gaba. Kuma inaso ka koma islamiyar da kukeyi ada, dan nasan tunda kuka shiga makaranta kadena zuwa, amma Mamar ku tana fada mani kullum kuna zuwa. Tashi kaje, amma duk ranar dana kara ganinka kana sha mani sigari ko wani abu agida to aranar zakaga fushina.

Tashi Fahad yayi rai abace yafita,  danshi maganganun Malan ma bata mashi rai sukayi, taya zece yadena biye maganar Mama, bayan yanzu ita kadai take son shi. Daki ya koma ya dauki wani abu kawai yazo ya fice. Yazo fita ya hadu da Farida, dariya tayi tana fadin Yaya yaushe ka dawo? Harara ya buga mata, dariya takara sawa tana fadin Yaya kalli wuyanka sahun duka waya dokeka? Kafa yasa ya harbeta yana fadin zanci uwarki wallahi. Ihu Farida tasa yafice yabarta.


Tun daga wannan rana Fahad yade zaman gida, kafin kace me labarinsu ya baza gari, mutanan unguwa se gulma sukeyi, duk yaron da yayi ma Fahad maganar korarshi seya dokeshi, haka yarika fasama yara baki.

Ganin irin illar da yake masu yasa suka fara tsoranshi, sede suyi maganar bayan idonshi, amma idan yafito babu me mashi magana. Sam baya zama gida, haka kuma baya dawowa da wuri. Maganar shaye shayenshi kuwa se abinda yaci gaba, domin inda suke haduwa da sauran abokanshi idan yadawo hutu can yake zuwa.

Gaba daya Mama tshiga damuwa, lokaci kadan duk ta rame, ta rasa abinda yake mata dadi, gashi Malan beyi mata maganar Fahad ba bare tasan yanda za'a bulloma abun, gashi Fahad baya zama gida, idan yadawo to abinci zeci.

Gashi yanzu seyaci abincin mutum 3, saboda shi yanzu takara yawan abincin gidan, dan idan be koshi ba seta sa Fatima ta dafa mashi wani abun, ita ko Fatima ba ruwanta dashi, dama can bata shiga harkarshi.

Farida ce kawai take shiga harkarshi, itama tunda yayi mata wani bugu tadena mashi magana. Gashi yanzu iskancinta ya kara yawa, kusan kullum tana dakin me shago, yanzu abubuwan da sukeyi ma yafi na da. Fatima so biyu tana kamata tafito daga dakinshi, amma sanin halin Farida dana Mama yasa taja bakinta tayi shiru, tunda taga Mama bata fadama Malan laifin da Farida tayi amakaranta ba wancan karin.

Malan kuwa ya saka ma Fahad ido, ganin Malan yaki ma Mama magana yasa ta yanke shawarar ta samehi da maganar, shiko Malan hidimar bikinshi kawai yakeyi.


Bayan su Fatima sun dawo hutu da kwana 4 yakirata yace tashirya ze kaita wajen Inne tayi hutu. Saboda mamaki kasa magana tayi, wani farin ciki ne ya kamata.

Haka taje ta hada kayanta taje ta fadama Mama, wani kulu kulun bakin ciki ne ya taso ma Mama, wato yanzu Malan ya canza, har ma hutu ze kai Fatima. Tana murnar aiki zemata sauki shine dan bakin ciki ze dauketa.

Farida ma sosai taji haushi, yanzu Fatima birni zata tafi gidan 'yan gayu amma banda ita, jitayi kamar tace itama zataje, amma saboda bakin ciki yasa tayi shiru. Ganin Mama batayi magana ba yasa Fatima ta tashi ta fita.

 Mama kuwa jin Malan yashigo yasa ta tashi domin tana so tayi mashi maganar Fahad. A bincinshi ta kai mashi bayan ta zuba mashi ta zauna, kallonta yayi dan yasan akwai magana tunda tazauna, dan data kawo mashi abinci take fita.

Shiru yayi yana cin abincinshi, ganin bazeyi magana ba yasa tace Malan wai naji shiru tunda Fahad yadawo bakayi mani magana ba. Murmushi Malan yayi yace maganar me zanyi maki Hauwa? Ke da kika rigani sanin halin da Fahad yake ciki ai kece yakamata ki fara mani maganar.

Uhmm, Hauwa kenan, a tunaninki duk abubuwan da kikeyi agidan nan bansa ni ba? Wato kece kika hana Farouk ya fada mani halin da Fahad yake ciki, saboda bakiso nayi mashi fada.

Yayi kyau, ai ko yanzun da aka koreshi banyi mashi fadan ba, na barki dashi tunda zaki iya kula dashi, nide amatsayina na Uba zanyi kokarin sauke duk wani nauyi da yake kai na, kuma zan kara sama mashi wata makarantar yaje ya zana jarabawa kawai.

Sede a Day zan sakashi, kuma zanyi kokari wajen nema mashi duk abinda yakamata, idan ya tsaya yayi karatu yatemaki kanshi, sauran kuma nabar maki, tunda kina tunanin kece kikafi iya kula da yara ba se kinyi masu fada ba.

Mama tce ai shikenan, dama na dauka bazaka nema mashi wata makarantar bane, amma kasani wallahi irin wannan ban bancin da kake nunawa Allah seya tambayeka, yanzu gaba daya baka son yarana.

Gashi dan munafurci ma wai Fatima zaka kai hutu Katsina, wannan ai salon kwadai ne, dan kaga Uwarta tana gidan masu kudi shiyasa zaka kaita. Da can meyasa baka taba kaisu ba tsawon shekaru da dama? To yaran nawa daka tsana insha Allah sune zasu daukaka.

Malan yace dan Allah tashi ki bani waje tun kafin rai na ya baci, ba zakisan kin shiga damuwa ba senan gaba, kin tsani wasu kina nunama yaranki soyayya, kuma zakisan cewar kin dorasu akan turba marar kyau.

Tashi Mama tayi tana fadin kai zaka ga abun kunya agidanka, amma wallahi yarana sunyi gaba. Mugu kawai, murmushi Malan yayi aranshi yana fadin duk tsiyarki wallahi bazan sake ki ba, domin sakaran namiji ne yake sakin matar data cuceshi.

Kina nan tare dani, bazan sake ki kibarni da bakin ciki ba, yanda kika jawoshi gidan nan haka zaki zauna kishashi.馃ぃ


***** *****

Washe gari da safe haka Malan ya tafi da Fatima su Farida kamar suyi hauka saboda bakin ciki, Fatima kuwa ko sallama batayi masu ba, dan taga Mama tun jiya take masifa. Haka suka tafi zuciyarta tana me cike da farin ciki.

A mota Malan yace insha Allah shima Faisal zanyi kokarin zuwa makarantarsu lokacin da za'ayi bikin yayesu, domin ban taba zuwa mashi visiting ba,duk da ba laifina bane, idan naso zuwa se Hauwa ta hanani. Fatima nasan akwai abubuwan da Hauwa tayi maki kiyi hakuri, kuma daga yanzu zan rika barinku kuna zuwa wajen Inne.

Kafin ki dawo ma zaki samu sabuwar Inne, kuma dakinta zaki koma da zama. Kallonshi Fatima tayi, yace E aure zanyi, bakiga na gyara dakinsu Faisal ba? Dukar da kai tayi batace komai ba. Dan ita har yanzu jitake kamar de Malan ba gaskiya yake fada mata ba, duk lokacin da ta tuno irin dukan da yayi masu se tsanarshi takara shiga zuciyarta, shiyasa kome zeyi mata bata farin ciki, yaune kawai tasan tayi farin ciki.

Wai sabuwar Inne, ai yanzu babu wata mace da zata kara yarda da ita amatsayin matar Malan, domin tasha wahalar Mama, dan haka bazata kara yarda da duk matar da Malan ze kawo ba, idan ada tana yarinya anyi mata abubuwa yanzu babu macen da zata kara dukanta. Allah yakawota lafiya,wai zeje ma Yaya visiting, dama can rashin sone yasa baya zuwa amma kaji zeje wai laifin Mama, kawide dan yaga yanzu mun girma shiyasa yakeso yajawo mu ajiki,  ganin Malan ze dameta da surutu yasa ta kwanta.



A kofar gidan Malan ya ajeta, domin yasan gidan Alhaji, kuma yace ta gaishe mashi da Inne, sannan tace mata tayefe mashi. Ita de Fatima ta amsa ne kawai, haka tafita tabarshi dan har yanzu bata saba dashi ba.


Ihun su Khairat da Ansar ne yasa Inne tayi saurin fitowa. Tsayawa tayi tana kallonsu yanda suka rungume Fatima, kara murza idonta tayi dan ta tabbatar da abinda take gani. Da gaske itace. Ya akayi Malan yabarta tazo? Kuma ai Fatima batasan gidan nan ba.

Matsawa tayi ta kamota tana murmushi tace da gaske kece Fatima? Fatima tace nice Inne, kuma tare mukazo da Malan, amma yatafi. Inne da ta cika da mamaki tace mushiga ciki.


Bayan Fatima taci abinci ta bama Inne labarin abubuwan dasuke faruwa agidansu, hada labarin abinda Farida tayi amakaranta, kuma ta bata labarin abunda su Fahad sukayi har aka koreshi, kuma ta fada mata auren da Malan zeyi. Sosai Inne tayi mamakin Fahad.

Dama kuma duk cikin yaran Mama shine yakeda wata zuciya, kuma shine tafi sangartawa. Inne tace Allah ya kyauta kuma ya shiryasu, ashe su Hauwa za'a samu wata kishirya kuma. Fatima tace yanzu Inne kozaman gida Fahad bayayi, gashi da anyi mashi abu yayita zagin mutum, bakiga irin dukan da yayima Farida ba.

Inne tace kede ba ruwanki dashi, Fatima tace ni dama bana shiga harkarshi, Inne tace ina Farouk fa? Fatima tace Allah sarki Yaya me kirki ba, yana makaranta wannan karon bezo week end ba. Inne tace ai zan samu numbershi ince yazo mugaisa, haka sukayi tafira, abubuwa kala kala Inne takawo ma Fatima, da yamma kuma suka shiga kitchen tare.

 Lokacin da Alhaji ya dawo shima yayi mamakin zuwanta, anan Inne tabashi labarin da Fatima ta bata, hada maganar auren Malan, sosai shima yayi mamaki, addu'a yayi shima yace Allah yashiryasu. Allah yasa kuma su Fatima suji dadin matar daze aura.


**** ****

A na gobe daurin auren Malan Farouk yazo gida sunyi hutun mid semister, dan yanzu suna a second semister ne, sosai yakara girma, gashi yakara hankali, bayan sun gaisa da Mama yaci abinci take fada mashi halin da ake ciki.

Sosai yayi bakin cikin abinda yafaru, yace kin gani ko Mama, shiyasa tun wancan lokacin naso kibari afadama Malan, domin Fahad yana jin tsoron Malan yanzu ga irin abinda yajawo ma kanshi.

Mama tace dan Allah kada ka bata mani rai, shege me hali irin na Ubanshi, abun bakin ciki yasamu Dan uwanka amma ka tsaya kana fadar maganar banza, to de abun kunya ba akan Fahad aka farashi ba.

Kuma ni nasan wadda tayi mashi haka, kasa ido kayi kallo wata rana akan yaranta asirin ze koma. Farida tace Yaya yanzu kana dinkin hular? Hararar ta yayi yana fadin bansani ba, sakarai ya kawai, inda Fatima ta fiki kenan.

Kina kallon mutun bazaki iya mashi sannu da zuwa ba bare ki gaisheshi, seyanzu zaki tambayeni abinda be shafeki ba. Mama tace tashi kabani waje, Fatimar taje tayi ta finta seme? Ai de har abada bazaka canza Farida ba.

Kuma Fatima bazata taba zamowa jikinka sosai ba, domin rabin jininka ce, Farida itace take cikakkar jininka. Fatimar da kake fadi yanzu ma tana ajen Uwarta, kaga kuwa dole ka rungumi Farida tunda a inuwa daya kuke zaune.

Sakarai wanda baya kishin yan uwanshi da ni kai na, wallahi idan kace irin wannan halin zaka kawo mani zakasha wuyata, domin bazan lamunci karika tsanar yarana kana fifita wasu banzaye can ba.


Tashi Farouk yayi rai abace, saboda halin Mama yasa ko week end bayason zuwa, mutum yadawo daga makaranta yana farin ciki amma daga zuwanshi ko hutawa beyi ba an fara zaginshi, ya kamata ace yanzu tadena zaginshi agaban Farida.

Shiyasa da akayi hutun waccan semister yayi zamanshi makaranta, dan dinkin hularshi yafiye mashi yazo gida, seda ana saura kwana 3 adawo sannan yazo gida. Dakinshi ya wuce yaje yayi wanka lokacin Malan yadawo yashiga suka gaisa.


Sosai Malan yaji dadin ganin Farouk dan duk wanda yaganshi seyaga nutsuwa atare dashi, komai cikin nutsuwa yakeyi, anan Malan ya mashi maganar Fahad kuma yace meyasa be fada mashi ba. Farouk yace kayi hakuri Malan.

Naso infara fada maka se Mama ta hana, Malan yace ai shikenan, amma daga yanzu duk abinda yake faruwa banaso karika boye mani, nafiso kome zaka fada kataho wajena muyi magana, kaga kaine babba idan ba ka sakin jiki dani kana fada mun komai  ai sauran yan uwanka bazasuyi koyi da kai ba.

Farouk yace haka ne, kuma insha Allah zan gyara. Malan naga anyi mana dakuna, Allah yasaka da  alkhairi mungode. Malan yace bakomai, wancan dakin ma gobe za'a kawo amaryata. Farouk yayi murmushi yace Malan aure zakayi? Malan yace ko na tsufa? Farouk yace a'a, amma Mama bata sani ba ko? Malan yace zata sani amma se an kawota. Farouk yace Allah yasa alkhairi.

Malan yace amin, kaima Allah yayi maka albarka, nan Malan yafada amshi ya bude shago, haka suka yita fira, daga karshe yajashi suka fita dan yaga shagon.

***** ****

Washe gari wajen karfe 12 Malan yashirya cikin babbar riga se kamshi yakeyi ko sallama beyima Mama ba haka yatafi dauri aure, Mama bata san wainar da ake toyawa ba, hatta da mazajen unguwar sunje daurin auren amma babu wadda ta fada mata.


Salamatu da Momyn Teema sosai wannan aure yayi masu dadi, Maman Sultan ma batasan zeyi aure ba dan mijinta baya gari.


Bayan angama daurin aure kowa ya nufi wajen da za'a ci abinci, domin suna gamawa zasu dauki amarya su taho da ita, dan yanzu andena daukar amarya da dare. Kowa yaga Malan yasan yana cikin farin ciki. Bayan sun gama reception sukayi la'asar sannan aka basu amarya.


Farouk ne yashigo dakin Fahad domin tun da yadawo basu zauna dashi ba, dan har yanzu Fahad yana jin haushin Farouk, ko magana baya mashi, har Mama seda Farouk ya fada mawa, amma babu abinda tace se cewa tayi tunda kaima ka tsaneshi ba dole ze kyaleka ba, jin abinda Mama tace yasa Farouk ya kyaleta.

Warin wiwi yaji daga bandakinsu, fita waje yayi yana jiranshi yafito. Fahad yana fitowa ya jawo dakinsu dan fita zeyi. Koda yaga Farouk be kalli inda yake ba haka ya nufi hanyar fita.

Farouk ne yace wai kai Fahad meyasa bakada hankali ne? Yanzu dan rashin mutunci acikin gida zaka rika mana shaye shaye? Duk irin abinda yafaru da kai be zamar maka darasi ba? Yakamata ace kaji kunyar abinda ka aikata har yasa aka koreka daga makaranta.

Wallahi inda nine kai daga ranar da aka koreni daga ranar nabar shaye shaye, domin shine silar jefani cikin halin da nashiga. Amma dayake kai ba kada tunani shikenan seka dawo kabude sabon iskanci agida.

Fahad yace na bude dan Ubanka, ai gidan banaka bane, nima ina da gado aciki, kuma naje nasha wiwin, idan dakinka nashiga nasha se kayi mani mgana. Da aka koreni kuma ai ba kai aka kora ba zakazo kana zagina banza kawai, wallahi yanzu na tsaneka.

Daukeshi da Mari Farouk yayi yana fadin ni kake zagi? Dun kule hannu Fahad yayi ya kaimashi naushi a hanci seda jini ya fita.

Haka suka fara kokowa suna ta dukan junansu. Farida ce ta taho kiran Farouk, ai tana ganin an danne Fahad a akasa ana duka ta ruga da gudu tana kiran Mama. Da kyar Fahad ya ture Farouk lokacin daya watsa mashi kasa a ido.

Yana tashi ya hangi wani karfe babu bata lokaci yadaukoshi ya caka ma Farouk aciki, dede lokacin da Mama da Farida suka zagayo, hannu Mama ta dora akai ta fasa ihu tana fadin Fahad bakada hankali.

Farouk kuwa tuni ya sume awajen. Kuka kawai Farida takeyi, haka Fahad ya fice yana huci, yana fita yaga motoci suna parking akofar gidansu, ko kallonsu beyi ba yayi gaba, Malan da yake fitowa daga mota yabishi da kallo.

Mutanan unguwa se lekowa suke suna kallon masu kawo amarya, da gudu Mama tayi waje domin ta nemo wani yazo akai Farouk asibiti. Tana zuwa bakin gate ana shigowa da amarya se guda akeyi.

Tsayawa tayi tana binsu da ido, da Zulai suka fara hada ido, ko kallonta Zulai batayi ba haka suka wuce wasu mata suna fadin Suwaiba kin samu gida dankari. Daskarewa Mama tayi a wajen tana maimaita sunan Suwaiba abakinta.

Farida ce tafito da gudu tana fadin Mama wallahi jini se zuba yake a cikin Yaya, zubewa Mama tayi awajen a sume dan batama san abinda Farida take fadi ba.


Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263

馃槝馃槝馃拫馃拫 Ina mika godiyata agareku, kucigaba da kasancewa dani. Love u all

.馃彙馃彙 A WANI GIDA馃彙馃彙
          馃槶馃槶馃槶

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 [email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 80 鈴� 85

Da gudu Farida tayi waje tana ihu ganin halin da Mama take cike, wasu mata da basu karasa shigewa ciki ba sukayo kanta, hankalin mazan da suke waje ne yadawo kan Farida, cike da bacin rai Malan ya taho ganin yanda Farida take kuka tana ihu.

Yana zuwa takara fashewa da kuka tana fadin Malan Yaya Farouk ya mutu, Mama itama ta fadi kuma bata numfashi. A rikice Malan da wasu abokanshi suka shiga cikin gidan, da Mama suka fara cin karo mata duk sun zagaye ta.

Malan yace ma Farida Ina Farouk din? Tace yana can baya, Malan da Labaran suka nufi bayan, jikinshi ne yafara rawa ganin Farouk kwance cikin jini. Babbar rigarshi yacire ya bama Farida, haka ya dauko Farouk gaba daya gaban rigarshi seda ya baci da jini.

Haka suka nufo waje dashi. Mama kuwa an sa mata ruwa ta farfado tana zaune se raba ido takeyi, ai suna ganin Malan dauke da Farouk tayi saurin mikewa. Ko mayafi babu ajikinta haka ta bi bayan Malan.

Suna fita hankalin jama'a yadawo kansu, nan wani ya bude mota aka saka Farouk aciki Malan yashiga gaba, Mama tazo zata shiga Malan yace Hauwa ki nutsu, kije kidauko hijabinki ga Labaran nan seya kawo ku asibitin.

Tada motar wancan yayi suka nufi asibiti Mama kuma ta koma ta dauko hijabinta ita da Farida ko kulle dakin batayi ba haka suka fito Labaran ya dauke su. Sauran abokan Malan sukace ayima matan dake ciki magana su fito zasu koma, haka kowa yafito yana jimamin abinda yafaru, babu wanda aka bari.

Suwaiba duk hankalinta yatashi, se rokon Zulai take akan ta tsaya ta kwana, Zulai tace kibari gobe zan dawo, nan Suwaiba tasa kuka, ganin haka wata Yayar Mamansu tace Zulai ta tsaya tunda de ga halin da ake ciki basu sani ba ko Malan din baze dawo ba. Haka kowa yatafi aka bar Zulai da Suwaiba.


Su Malan basu tsaya asibitin Mani ba, kai tsaye suka nufi Katsina dashi dan sun san ranar asabar ne, sosai direban yake gudu, cikin minti 15 suka isa Katsina, asibitin medical center suka nufa dashi.

Lokacin da sukaje likita yace wannan case din yana bukatar dan sanda, haka su Malan sukayi ta rokonshi akan ya karbeshi dan yadade yana zubar da jini. Da kyar likitan ya karbeshi suka nufi emergency dashi.

Su Malan basu dade da zuwa ba se gasu Labaran dan basu san Katsina suka taho dashi ba seda wani yace masu yaga sun nufi hanyar Katsina, kafin su karaso Labaran yakira wanda yatuko su Malan ya fada mashi asibitin da suke.

Mama se kuka takeyi, Malan ne yaje yace dan Allah ki rufa mana asiri, insha Allah babu abinda ze sameshi, kinga de cikin jama'a muke. Mama tace dalla can rufe mana baki, azzalumi ma ha'inci, wallahi se Allah ya tozar taka.

Labaran ne ya kama Malan ya janyeshi gefe guda. Se alokacin yayi da nasanin cewa ataho da ita, shi sam yama manta da yayi mata laifi na rashin fada mata zeyi aure. Haka suka zauna kusan minti 30 har aka fara kiran magrib likita be fito ba.


Labaran ne yaje ya karbi babbar rigar Malan da take hannun Farida tun dazu, kawo mashi yayi yana fadin Malan kacire wannan rigar saboda duk ta baci da jini seka saka wannan muje muyi sallah.

Karba Malan yayi ya cire waccan yasamu leda yasa ya mika ma Farida  suka nufi masallaci. Mama kuwa se kuka takeyi, bakin ciki goma da ashirin ya isheta, ga bakin cikin Malan, kuma ga halin da Fahad ya sasu.

Se wajen karfe 7:00 aka fito da Farouk, har lokacin kamar gawa yake, sede an nade cikinshi da bandeji, haka aka kaishi wani daki aka jona mashi ruwa. Mama da Farida suka tashi suka shiga dakin.

Lokacin dasu Malan suka dawo wani yace likita yana son ganinsu a office. Zaune suka sunyi shiru, seda likita ya gama rubutunshi sannan yadago kai yana fadin waye mahaifin yaron da aka kawo? Malan yace nine.

Jinjina kai Likita yayi yace gaskiya wannan yaro yayi sa'a, kuma kwananshi yana gaba, amma karfen da aka caka mashi ko kuma wukar da aka caka mashi to tana dauke da tsatsa, daga gani ta dade a aje.

Inda Allah ya tsare kuma makamin be karasa shiga can ciki ba, da se yataba mashi hanji. Amma yanzu muyi mashi dinki kuma munyi mashi TT, ansa mashi ruwa insha Allah nan bada dewa ba ze farfado.

Amma waye ne yayi mashi wannan ta'asar? Malan da zufa tagama jikashi yace wallahi Likita nima bana gida, yaune aka daura mani aure mun dauko amarya daga nan garin muna zuwa kofar gida muka samu wannan danyen aikin.

Koma menene sena koma wajen iyalina sannan zan san abinda yake faruwa. Likita yace da alama fada sukayi, domin naga sahun naushi a fuskarshi. To Allah de ya kyauta, amma gaskiya seka kara kula, dan yanzu yawancin fadan da zaka samu matasa sunayi da wuya asamu ba'a jima wani mugun rauni ba.

Wasu ma daga haka zuciya take dibarsu su hallaka abokan fadansu, kuma wallahi ba komai bane yake kawo irin wannan zuciya ta matasan yanzu se wannan shaye shayen da sukeyi, shine abinda yake samasu zafin zuciya, abu kadan kaga an kama fada.

Allah ya kara kare mana zuri'armu. Malan yace amin nagode likita. Takardar magunguna data biyan kudi Likitan ya mika ma Malan, kuma yace koya tashi kada abashi komai zezo ya dubashi. Godiya sukayi mashi suka fita.

Suna fita Malan yace Labaran ina ganin zaku iya tafiya, zuwa anjima nima zan taho tunda ga Hauwa da Farida se su kwana dashi, idan kuma be farfado da wuri ba ina ganin anan zan kwana.

Idan kaje ka kara duba mani gidan dan ina zargin wannan yaron, kaga kada yadawo yayi ma Suwaiba wani abu, amma zan kirata ince su kulle gidan idan nadawo to, idan kuma ban dawo ba shikenan.

Labaran yace to shikenan, Allah yakara sauki, Malan yace amin, dayan abokin Malan daya tukosu shima Malan yace mashi sutafi Kawai. Mukullin motar yabama Malan yayi mashi Allah ya kyauta suka tafi a motar Labaran.

Kafin Malan yaje dakin Farouk seda yakira mijin Inne, seda Alhaji yayi mamakin ganin kiran Malan, yana dauka suka gaisa anan Malan yake fada mashi halin da ake ciki. Alhaji yayi mashi jaje yace idan akayi sallar isha'i zasu zo.


Seda Malan yaje ya siyo magungunan da aka rubuta mashi sede kudin basu kai ba na wanda ze biya na aikin da akayi ma Farouk, shine ya koma yayi ma Likitan bayani, likita yace ba komai, kafin asallameku seka biya.

Dakin da Farouk yake ya nufa, gaba daya agajiye yake. Yana tura kofar dakin Mama ta kauda kanta gefe guda. Kujera yasamu ya zauna, fuskar Farouk ya taba duk ta kumbura, sosai yaji tausayin Farouk, dan yasan beda hayaniya.

Kiran Farida yayi yace meyafaru? Nan ta fada mashi taje takira Farouk ta samesu suna fada, kafin ta kira Mama sukazo suka iske Fahad ya caka mashi wani karfe, kuma Fahad din ya gudu.

Runtse ido Malan yayi, dama tunda likita yace an caka mashi wani abu kuma fada sukeyi yayi zargin Fahad ne, wannan wane irin masifa ne haka? Malan yace shikenan zan ga Fahad din ai.

Mama tace ade rika bincike kafin a yanke hukunci, babu wanda yasan abinda ya hadasu, kasan Farouk da son girma,da saurin hannu, yanzu haka wani abun yayi mashi shi kuma yaji baze iya kyalewa ba shine suka fara fada.

Ai dama tunda Farouk ya dawo yake jin haushin Fahad, ni kaina seda yazo ya kawo mani karar Fahad wai baya kula shi, ni kuma nace dama inde mutum yaga an banzatar dashi agida ai dole yake ware kanshi.

Malan yace dan Allah kiyi mani shiru, in ma Fahad kashe Farouk yayi aide duk 'ya 'yanki ne, yau da ace Faisal ne yayima Farouk haka gaba daya duniya se tasan yayi mashi haka. Amma dayake dan gwal ne, dole zaki fadi haka.

Kuma ni bana jin takaici domin ciki daya suka fito, babu wanda zece bakin ciki ne yasa daya yayima daya haka, kuma idan kin goyama Fahad baya wannan ba damuwata bace, amma kisani matukar Farouk yagane kina fifita Fahad da  Farida akanshi, tabbas zakiyi babban kuskure.

Mama tace kamar yanda kayi ba, ai babu wanda yayi kuskure arayuwa kamar ka, domin kai ne ka nuna banbanci atsakanin yaranka tun suna yara, gashi nan nasan har su mutu bakin cikinka baze goge a zuciyarsu ba.

Kuma da kaje kayi aure kana tunanin hakan ze dameni ne? To kasani aurenka ko a kwalata be dameni ba, tazo taci abinda akeci agidan, nide na tabbata duk macen da zata shigo gidanka to saurana zata kwasa.

Malan yace Farida jeki waje, bayan ta fita Malan yace shiyasa naga ai wata ta suma alokacin da taga ana shigowa da amarya, ai wallahi nasan ba saboda Farouk kika suma ba. Da saboda shine kika suma tun acan zaki suma.

Amma seda kikazo bakin gate kikaci karo da masu kawo amarya sannan kika zube awajen saboda abun yazo maki daga sama. Shiru Mama tayi tana mazurai. Malan yace koma me amaryata zata iske aide nidin nine zata samu.

Kuma mu maza ba'a daukar sauran wani sede mu muyi gori akan duk wanda ya auri matar da muka saka, domin kullum shi namiji kara sabunta yakeyi. Ko yanzu kika rabu dani bazaki samu wanda ze aureki da sauri ba, domin kowa yasan saurana ze kwasa.馃ぃ

Idon Mama ne ya ciko da kwalla jin irin cin mutuncin da Malan yake mata.  Murmushi Malan yayi yace kuma idan kina tunanin zan rabu dake ma kidena, domin niyanzu nadena sakin mace, gara ta zauna ta rike yaranta.

Tashi Mama tayi tashige bandaki tana kuka, sosai abun yaba Malan dariya, wato ta dauka shidin kanwar lasa ne, shiyasa tafara fada mashi magana son ranta, dama idan baki yasan abinda ze fada ai besan abinda za'a maida mashi ba.

Wajen karfe 8:00 su Inne suka iso hada Fatima dasu Ansar, Amatu tana rike da hannun Fatima domin yanzu tagirma sosai shekararta hudu da rabi. Alhaji ne yakira Malan yace suna cikin asibitin.


Fitowa Malan yayi domin yatafi dasu, tun daga nesa ya kafa ma Inne ido, shi rabonshi da ita tunda tazo kawo ma Mama alawar bikinta. Lallai idan a hanya suka hadu baze iya gane ta ba.

Duk kunya ta kamashi ganin matar da yayima wulakanci amma yanzu itace tazo duba danshi, yaron matar data ke wulakanta mata yara. Kanshi akasa ya isa wajensu, hannu Alhaji ya mika mashi suka gaisa.

Inne tace ina wuni? Malan da kanshi yake kasa yace lafiya lau ya gidan, shiru Inne tayi batace mashi komai ba, sauran yaran suka gaishe shi, haka suka nufi dakin da Farouk yake. Gaba daya Malan jiyake kamar ya nutse kasa.

Shine yafara shiga yace ma Mama tasa hijabinta ga baki nan zasu shigo, ko kallonshi batayi ba ta dauki hijab dinta tasa ta koma kusa da Farouk ta zauna. Da sallama suka shigo ko kallonsu Mama batayi ba tade amsa masu sallamar.

Seda taji muryar mata sannan ta daga ido dan taga ko suwaye. Karaf suka hada ido da Fatima da Inne, mikewa tsaye tayi gaba daya annurin fuskarta ya bace. Murmushi Inne tayi tace kin ganmu daga sama ko? Murmushin yake Mama tayi tana fadin sannunku da zuwa.

Bayan sun zauna Mama ta gaishe da Alhaji, amsawa yayi yana murmushi yace yame jikin? Tace da sauki. Inne tace Maman Farida ina wuni? Mama tace lafiya lau, yame jikin? Tace da sauki.

Fatima tace Mama ina wuni? Ko kallonta batayi ba tace lafiya lau, sauran yaran ma duk suka gaisheta. Farida kuwa tana daga bayanta kamar munafuka ko kallonsu ta kasayi. Ganin Malan yana kallonta yasa tafito ta gaishe da Alhaji da Inne.

Kallon Fatima tayi tana sanye da wata doguwar riga ja me hade da mayafinta tayi rolling dashi akanta, fuskarta dauke da kwalliya, sosai tayi kyau, sosai ran Farida ya baci ganin yanda Fatima ta koma 'yar gayu.

Fatima kuwa ko kallonta batayi ba se kallon Farouk sukeyi. Alhaji yace Malan wai faduwa yayi ne? Malan yace wallahi fada sukayi da dan uwanshi, kasan halin yaran yanzu, kawai yadauki karfe ya caka mashi aciki.


Alhaji yace ikon Allah, lallai ya auna arziki, to Allah ya kyauta, ammade an dinke wajen ko? Malan yace E, kuma sunyi mashi allurar TT, kuma likita yace insha Allahu babu wata matsala, yanzu ma jiran farfadowarshi mukeyi.


Inne tace Allah ya sawake, Khairat ta bama basket din da sukazo dashi ta mika ma Mama, se kuma plask din ruwan zafi da cups se kayan tea, hada wata leda me cike da fruits, duk se kunya ta kama Mama, murmushi tayi tace hada wahala haka? Inne tace meye abun wahala ga mutumin da yake rike maka danka,

Ai yima kai ne, kuma Farouk yaron kirki ne, bawani abu dan bazan iya  mashi ba. Mama tace to angode. Motsi Farouk ya farayi alamun ya farka. Saurin tashi Malan yayi ya rike mashi hannu yana fadin yi ahankali kada ka fama ciwonka.

Kallon Mama yayi yace rike mashi hannun bara inkira likitan. Fita yayi be dade ba se gasu sun shigo da likitan, Alhaji yace a'a Dr. Ashe kaine me dubashi? Murmushi likita yayi yace Alhaji barka da zuwa, ashe patient din na wajan ka ne? Alhaji yace wallahi kuwa, kamar Da yake awajena.

Wucewa likita yayi yana fadin ikon Allah, abun auna mutum yasa ya duba Farouk, sannan ya duba sauran ruwan da aka samashi. Kallonshi yayi yace Farouk yanzu ina ne yake maka ciwo? Farouk yace cikina ne yake ciwo se kuma inajin tsakuwa acikin idona.

Likita yace ko an watsa maka kasa ne? Farouk yace E, jinjina kai likitan yayi yace kada kadamu cikin zebar ciwo, zuwa gobe kuma idan baka dena jin tsakuwar ba, zamuyi maka wankin ido.


Amma kome zakayi ka rikayi ahankali domin dinkin da akayi maka aciki ne, kuma bayason yawon motsi, Farouk yace to. Dago kai Likitan yayi yace Alhaji zaku iya bashi tea da abu marar nauyi tunda aikin be shafi hanjinshi ba, ammade kada yaci yakoshi tayanda cikinshi ze turo.

Malan yace to mungode, likita yace babu damuwa, kuma akwai nurse da zatazo domin ta dubashi, idan ma ruwan yakare duk itace zatayi komai. Zuwa goben zanzo in ga yanda jikin nashi yake, kuma maganar idonshi idan be dena jin abinda yake jiba kawai zamuyi mashi wankin ido. Malan yace to mungode.


Hannun Alhaji likita yakama suna kara gaisawa sukayi waje. Inne ce tace ma Fatima ta hadama Farouk tea ganin Mama tana jin kunyar taba kayan. Tashi Fatima tayi tana fadin sannu Yaya, yace yau Fatima.

Shine kika gudu ko? Murmushi tayi tace ai kune baku dawo ba, daga kai har Yaya Faisal, gidan duk babu dadi. Murmushi yayi yace ai gashi nadawo. Hada mashi tea tayi ta mika mashi  tana fadin gashi.

Mama ce ta kamashi yadan jingina da pillow ta karbi kofin ta fara bashi, dakin seyayi shiru se Amatu ce take ma Fatima magana, Malan kuwa kamar ruwa ya cinyeshi, jiyake kamar yanitse saboda kunyar Inne.

Kofar dakin akaturo, Alhaji ne yashigo yana fadin to kutashi mutafi Hajiya, Malan Allah yakara sauki, kudi ya mika ma Mama yana fadin Allah yakara sauki, Mama tace angode,tashi Malan yayi yana fadin amin nagode,Amatu ce taje takama hannun Malan tana fadin da kai zamu tafi ne? Murmushi yayi yace E zaki tafi dani ko? Kai ta daga mashi ta kamo hannun Fatima tana fadin Aunty mutafi.

Da kallo Farida ta bisu, ko kallonsu Fatima batayi ba taja su Khairat tana fadin Yaya na Allah yabaka lafiya se nazo gobe. Farouk yace amin Fatima. Haka suka fita Inne tana fadin to Allah yabaka lafiya Farouk se mun kara dawowa, Maman Farida Allah yakara sauki.

Mama tace amin mun gode, ya za'ayi da kwanukan kuma? Inne tace ai gobe Fatima zata zo takawo maku break seta tafi dasu. Mama tace mungode, haka suka fita Malan yana biye da Alhaji yana kara mashi godiya.

Har bakin kofa ya kaishi, shine ma yayi saurin bude mashi kofar, seda yashiga sannan Malan ya rufo kofar yana fadin mungode sosai. Hannu Alhaji yabama Malan sukayi sallama ya saka mashi kudi.

Malan yace haba Alhaji hada wata wahala? Alhaji yace bakomai, nasan yau kasha hidima ba lallai bane ace kana da kudi ajikinka, kawai karike wadan nan kafin inzo gobe, kuma na biya sauran kudin. Malan yace nagode sosai.


Haka suka tafi Malan yana tsaye har suka fita gate. Shafa kai yayi yana fadin gaskiya naji kunya, wai yau nine nake budema mijin matar dana saka kofa, kuma shine yake biya mani kudin Dana, matar dana saka itace tazo takawo mana abinci, badan su ba da sena fita nasiyo mana abinci.

Allah ka yafe mani abinda nayima baiwarka. Haka yakoma dakin ya samu su Mama an baje ana cin shinkafa da miyar kaji an bude lemun roba, murmushi yayi yace Farouk ka koshi ko? Kai Farouk ya daga yana fadin Malan kazauna kaci abincin.


Malan yace to Farouk nagode, zama yayi yajawo cooler abincin yazuba, Mama data cika baki da nama tana fadin kada ka kawashe nama duka zan kara abincin. Banza yayi da ita yazuba miyar ya faraci.


Lumshe ido yayi, yaushe rabon da yaci girkin Inne, harara Mama ta buga mashi tana fadin wallahi babu de kyau, karika tunanin matar wani dan kaci abincinta shine zaka wanu rufe ido, Malan yace naje nayi, idan kuma zaki hanani ne to? Girgiza kai Farouk yayi jin yanda Mama take ma Malan masifa.

Mama tace ko kunya bakaji ba ka kira mijin tsohuwar matarka dan kasan yana da abun duniya yazo ya kawo maka abinci, abun haushin ma hada matarshi yataho. Malan yace da basu zo ba ai da ba ki samu inda zaki cika baki da naman kaji ba.


Koma menene ai Uwar yarana ce, alaka bazata taba yankewa atsakaninmu ba, kuma mijinta abokina ne, gashi munzo garinsu dole inkirashi tunda bansan kowa ba. Idan kuma kina kishi ne ai be kamata ki taba abinda takawo maki ba, tunda ke bakida wata alaka da ita.

Nikam kowa ze iya fadar Uwar yarana ce, kefa? Mama tace ai ko ita tafada da bakinta cewar ina rike mata yara, kaga kuwa nima ina da alaka da ita. Farouk yace dan Allah Malan kuyi shiru kaina yana mun ciwo. Malan yace yi hakuri kaji.


Haka suka gama cin abincin, lokacin Farouk har yayi bacci Malan yace ina daga wancan falon zan kwanta, idan ya motsa ki kirawoni, nasanki da bacci kada yatashi bakiji ba. Mama tace ai da ka kira amaryarka kunzo kunci amarcin a asibiti, ai wallahi ni naji dadin wannan ciwo na Farouk.


Nasan ji ka ke kamar zaka mutu saboda an ruguza maka amarci, tsaki Malan yayi yace idan angirma de asan angirma, agaban yaranki kike wannan maganar, kuma kada kimanta nan asibiti ce, damma babu me jinki, amma wani lokacin za'a jiki, fita yayi ya barta.


**** ****

Washe gari wajen karfe 8:00 Inne tasa wani direban Alhaji ya kawo Fatima dasu Khairat asibiti suka kawo ma su Mama break, sosai sukayi kyau haka suka shiga, da Malan suka fara cin karo, risnawa sukayi suka gaishe shi. Fuskarshi dauke da murmushi ya amsa yana tambayar mutanan gida.

Bayan sun shiga suka gaishe da Mama, da kyar ta amsa saboda tsabar bakin ciki. Malan ne yace waya kawoku Fatima? Fatima tace direba ne. Tsaki Mama taja tana fadin aikin banza, har abada de da gidan Uba ake takama.

Farida tace ai AGOLANCI ma takeyi agidan ko Mama? Mama tace sosai ma, ga kuma kwadayi ba. Dariya Farida tasa, Malan da yake zaune ya harareta nan take ta nutsu, sam baya son yayi fada agaban su Khairat hakan yasa bece komai ba.

Fatima kuwa da haushin Malan ya gama cikata a ranta tace dama ai bazakayi magana ba, gashi agabanka ana ci mani mutunci amma kayi shiru. Tashi tayi tace abamu kwanonin jiya.

Mama tace Farida mika mata kayan jiya, tunda yanzu Inne ta samu me aiki ai dole ta huta, idan ma baki sani ba to inaso in fada maki, har abada yaran da Uwarsu ta barsu a tsohon gidan ta basa taba tasiri awajenta bayan tayi aure ta haifi wasu.

Rufin asirinki ma kidawo gidan tsohonki domin shine rufin asiri, dan da Uba ake ado ba rigar aro ba inji wani mawaki. Amsar basket din Fatima tayi ta kalli Farouk da hawaye suke zubo mashi tace Yayana Allah yabaka lafiya. Kai kawai ya iya daga mata ko sallama batayi masu ba suka fita.

Khairat tace Aunty kada mukara zuwa wajen wannan matar, bata da hankali, ga Yaya se kuka yakeyi amma se masifa takeyi, Fatima tace nima bazan kara zuwa ba, dama saboda Yaya nazo, tunda ba taso bazan kara zuwa ba.

Tashi Malan yayi ya hadama Farouk abinci, sam be kula Mama ba dan yaga Farouk yana hawaye, kuma yasan akan abinda tayi ne, shiyasa be kulata ba kada su dameshi da hayaniya.

Bayan ya gama bama Farouk abinci ya rakashi bandaki bayan sun fito shima yaci abincin, sannan likita yazo ya duba Farouk, tambayarshi yayi yanda yakejin idonshi. Farouk yace har yanzu akwai tsakuwar.

Likita yace cikin naka fa? Farouk yace da sauki sede zafi kadan, Likita yace bakomai insha Allah zafin ma zedena. Kallon Malan yayi yace zamuje ayi mashi wankin ido, zan turo wasu nurse suzo da gadon da za'a turashi.

Malan yace to nagode, bayan yafita sega nurses sunzo da gado, kama Farouk sukayi aka dorashi suka fita, wayar Malan ce tayi kara, yana dubawa yaga Suwaiba ce, dan dazu yakirata bata dauka ba ya naso ya fada mata Labaran ze kawo masu kayan break.

Dan tun da Faisal da Nura suke makaranta daya suke mutunci da Labaran. Dauka yayi yana me murmushi, Mama kuwa harararshi kawai takeyi dan tasan matarshi ce ta kira. Tsaki tayi tace jaraba kawai, kina mace kuma amarya ki rika neman miji.

Wama yasani ko sauran maza ce. Malan yace ranki yadade kin tashi lafiya? Dazu nakira baki dauka ba nace ko kina bacci ne? Ok yakawo maku break din kenan? Shikenan nima anshiga da Farouk dakin wankin ido, da sun fito zanzo gida inyi wanka in canza  kaya.

Toshikenan, ki kularmun da kanki, amin nagode amaryata. Mama jitayi kamar ta shako Malan, Farida kuwa se zumbure zumburen baki takeyi. Mama tace koma me zakayi ai de kafin ayi mata seda akamun, kuma wallahi dadin,abun nice nafara bareka aleda.

Dariya Malan yasa jin abinda Mama tace, ita sam ba ta ma kunyar Farida, tashi yayi yabar dakin. Mama tace munafuki ai dole zaka fita. Farida tace Mama Malan din ne munafuki kuma? Shiru Mama tayi ba tace komai ba dan tasan ta kwabo ta.

Kusan mintuna 15 aka fito da Farouk, se alokacin yaji dede a idonshi, dan tunda Fahad ya watsa mashi kasa yakejin babu dadi. Bayan sun kwantar dashi aka kara jona mashi ruwa. Malan yace likita zanje gida indawo.

Likita yace to akwai wanda zaku bari ko? Malan yace E ga Mamanshi nan, nima ba dadewa zanyi ba, kawai zanje iyo wanka ne in sake kaya. Likita yace shikenan shima yanzu zeyi bacci ai.

Ina fatan an bashi magungunan shi? Malan yace an bashi, likita yace to Allah yakara sauki, ina fatan Alhaji ya fada maka ya biya kudin nan?  Malan yace yafada mani, nagode Allah yayi albarka.

Bayan likita ya fita Malan ya tashi yana fadin zanje gida inyi wanka, se ku kula dashi, akwai abinda kike bukata intaho maki dashi? Mama tace kai de kace za kaje kasha amarcinka, to ga Farida nan kutafi tare ta kullo mani dakina kuma zata hado mani abinda nake bukata.


Ke Farida, kina zuwa kada kibari kidade kifito kutaho. Farida tace tunda wanka zeyi nima ai senayi. Mama tace to naji, amma kiyi sauri. Kuma kidauko mani kayana da brush da maclean, kuma ki kullo mani kofar bangarena.

Kinsan yanzu an kawo mana jaraba dole murika kulle kofa dan danginsu Zulai suna da gadon Sata. Girgiza kai Malan yayi yafita. Haka Mama tace ma Farida kada tabari ta dade, kuma tace ma Fahad ya dafa abincin da zeci.

Farida tace amma de Mama kinsan bana ma Yaya Fahad magana ko? Kuma inje inyi mashi magana nima yayi mani irin abinda yayima Yaya. Ai yana da abokai yaje can yaci, domin babu abinda ya iya dafawa. Fita tayi tana fadin semun dawo.



Lokacin da Fatima ta koma gida haka tace ita ba zata kara zuwa asibitin ba, Mama tace meyasa? Nan ta fada mata abubuwan dasu Mama suka ce. Inne tace ai shikenan, se direba ya rika kai masu.

Nima bazan kara zuwa ba, dan rabon da afada mani magana har na manta, Allah yabashi lafiya. Fatima tace amin. Inne yau fa zanje gidansu Lubna kinga itama tazo. Inne tace to kije ki tambayi Abbanku. Fatima tace to.


Su Malan suna zuwa gida ya nufi bangaren su Fahad, a kulle yasamu dakinshi, aranshi yana fadin ai,baze kwana gida ba yasan ya aikata babban laifi. Bangaren Suwaiba ya wuce.

Seda yayi sallama Zulai tace yashigo sannna yashiga. Bayan sun gaisa Zulai tayi mashi yame jiki, yace da sauki ai. Zulai tace wai fadama  wani abu yayi? Labarin abinda yafaru Malan yabasu, Zulai tace ikon Allah, lallai wannan yaron abun tsoro ne.

Gaskiya Malan seka saka ido akan Suwaiba, domin bakuwa ce batasan komai na gidan nan ba, gashi daga zuwanta har ta fara cin karo da tashin hankali, wasu ma se su camfata ai, jiya bayan mun rufe gida haka wani yazo yana ta bugawa, mude tsoro ya hanamu budewa har yagaji yatafi.

Malan yace inaji Fahad ne, ai yasan yayi laifi shiyasa bedawo da wuri ba. Insha Allah babu abinda ze faru da ita, yanzu hakama wanka nazo inyi sena koma, ina fatan zaki zauna mata? Zulai tace gaskiya nima gobe zan koma.

Sede in bika mutafi yanzu idan yaso se wata tazo ta zauna tunda akwai yaran yayanmu kuma hutu akeyi se Zainab tazo ta zauna kafin akoma, zuwa lokacin ai nasan kun dawo gida. Malan yace hakan ma yayi.

Mungode Allah yabar zumunci, Zulai tace amin. Tashi Malan yayi yashiga dakin Suwaiba, hakan yasa ta bishi, hakuri yakara bata tace bakomai ai Da na kowa ne, kuma dole kazauna acan dan jinyar namiji se namiji. Malan yace nagode, ni zan shiga wanka, tace to afito lafiya.


Part dinshi ya nufa domin yayi wanka. Farida ta rigashi gamawa haka ta hado ma Mama kayanta ta kulle part dinsu tazo waje tana jiran Malan, bayan ya gama kimtsawa yashiga part din Suwaiba yace Zulai ta fito.

Sallama yayima Suwaiba yace tazo ta rufe kofar, haka suka fito tana sanye da mayafinta, Farida tana ganinsu tayi saurin fita. Kiranta Malan yayi, tana zuwa yace baki iya gaisuwa bane? Bata fuska tayi tace ina kwana.

Zulai tace Farida kenan, lafiya lau, haka suka tafi  Farida se bakin rai takeyi, Malan da Zulai kuwa se labarinsu sukeyi amota. Seda suka fara biyawa ya aje Zulai sanna suka wuce, tana ta mashi godiya kuma tace za'a kai Zainab can wajen Suwaiba anjima.


**** ****

Kwanan Farouk biyar aka sallamesu, akwanaki biyar duk Inne ce take aiko masu da abincin safe har zuwa dare, sede bata kara zuwa ba direba ne kawai yake kawo masu. Duk da haka Mama bata bar tsine mata ba.

Malan da yaga abun nata bana karewa bane yadena biye mata dan ya lura Farouk yana shiga cikin damuwa. Lokacin da aka sallamesu Malan yayi ma Alhaji waya akan Fatima tashirya sutafi tare dan hutunsu yakare.

Haka Inne ta hada mata duk wasu kayan amfani tasa direba ya dauketa ya kaita gidansu Lubna ta kai mata kayan tace ta tafiyar mata dasu, suna dawowa sega motar su Malan. Kallon Mama yayi yace ya kamata kishiga ki kaimata kayanta kuma kiyi mata godiya.

Mama tace kaide kace kana son ganinta kawai, Malan yace kinji nace maki zanshiga? Alhajin ma ai gashi nan fitowa, Mama tace to babu inda zani. Farouk yace haba Mama Inne fa tayi mana abunda babu wanda zeyi manashi, meyasa bazaki shiga kiyi mata godiya ba? Mama tace to Ubana, ai seka sani inje.


Isowar Alhaji ce ta sata tayi shiru, bayan sun gaisa yace kushiga daga ciki mana. Haka Mama tafito Farida kuwa dama so take tashiga taga yanda gidan yake, Farouk ya fito yabi bayansu.


Inne tana zaune tana kallo ita da yaranta a tankamemen falonsu, gefenta kuma plate ne na fruits tana sha, Fatima tana gefenta. Da sallama suka shiga, Mama se sakin baki take tana kallon daula.

Murmushi Inne tayi tace sannunku kushigo ga wajen zama. Inne tace ina kwana? Da kyar Mama tace lafiya lau, dan jitake kamar zuciyar ta zata buga saboda bakin ciki, Farouk ya gaishe da Inne, tace lafiya lau Farouk ya jikin naka? Yace da sauki.

Fatima tace Yaya ina kwana yajikin? Murmushi yayi yace lafiya lau Fatima, hutu kuma yakare jibi se makaranta. Tace wallahi kuwa, tashi Mama tayi tana fadin kutashi muje koma hutu be kare ba ai dole mutum yatafi gidan Ubanshi da ya tsaya yana AGOLANCI.


Murmushi Inne tayi tace da zama wani gidan Uban ai gara AGOLANCIN, musamman idan mutum yana da 'yanci agidan, gashi kuma babu kishiya bare asamu me mata gori. Hannu Mama ta cije jin abinda Inne tace.

Farouk yace Inne mungode da hidima, Inne tace haba Farouk ai kawuce haka, Allah yakara baka lafiya, fita Mama tayi tana huci, Farida kuwa se kara kallon Falon takeyi. Fatima tace Inne se nadawo wani hutun. Inne tace to Fatima komai naki ai Lubna zata taho maki dashi.

Kallon Farida tayi  saboda ita tayi maganar dan kada ace Fatima bata koma da komai ba. Fatima tace Inne jibi kisoya mani kaji Lubna ta taho mani dasu. Inne tace komai zan hada maki, kudinki kuma zan samaki asusu tunda kince sun isheki.


Haka Farida ta saki baki tana kallonsu, Fatima tayima Inne sallama su Khairat suka rakota har bakin mota, juyawa Farida tayi tabi bayansu kamar zata mutu, dubu biyu Alhaji ya mika ma Farida, ai kamar jira take tayi saurin sa hannu ta karbe.

Har ta wuce Malan yace baki iya godiya ba? Juyowa tayi tana yake tace angode, dukawa Fatima tayi tana fadin na tafi Abba, murmushi yayi yace to Fatima adage ayi karatu, dan nurse nakeso kizama kinji? Tace to Abba,


Haka suka shiga mota su Khairat, Ansar da Amatu se kuka sukeyi, ita kanta Fatimar saboda kukansu seda ta zubar da kwalla. Mama tayi shewa tace ikon Allah, yau ina ganin barikanci.


To gidan kikeso ki koma da zama? Tsawa Malan ya daka mata yana fadin wallahi na kara jin muryarki Hauwa se kin sauka, sede ki taho amotar haya, ke da yake sam baki aiki da tunaninki. Gum Mama tayi tana hararar Fatima.



Suna isa kowa ya sauka, sun jima suna bubbuga gidan kafin Zainab tazo ta bude, Mama tace haka nefa, wato ansamu gida har wani kullewa akeyi, an dako mata 'yar riko, to wallahi babu macen da zata rika rufe mana gida, idan irin gidan da amarya take kullewa kikeso ai marar mata ya kamata ki aura.


Tureta Malan yayi yashige ciki dan ta bashi haushi, haka suka wuce tana ta masifa, Farouk kuwa aranshi yana fadin Allah jibi makaranta ze koma, haka yashiga ya nufi dakinshi. Fatima tana shiga Malan yace tayo nan da kayanta, kuma taje ta kwaso sauran kayan.


*** ***

Zaune suke afalon Malan Mama tana daga gefe se huci takeyi, Malan yace Alhamdulillahi, Allah nagode maka daka nuna mani wannan rana. Hauwa wannan itace amaryar da nayi, sunanta Suwaiba, koda yake base nayi maki bayaninta ba dan kin santa.

A salima Yayarta aminiyarki ce, inaso kowa yazauna da dan uwanshi lafiya, kuma babu maganar yin abinci tare, kowa zerika abincinshi, sannan kwana biyu zan rikayi idan nagama kwana 7 a dakin Suwaiba.

Bana son fitina, duk wacce na samu taje part din wata har sukayi rigima to itace bata da gaskiya, kuma zan dauki mataki akanta, Suwaiba Hauwa itace uwar yarana, kuma itace uwargida, inaso ki bata girman ta.

Bana so ki kawo mani fitina agidana, dan bama tashin hankali agidana, kema Hauwa kiriketa kamar kanwarki, tunda kanwar aminiyarki ce, duk abinda tayi ba dede ba ki gyara mata, idan kuma wani ne ya zalunci wani to bana so mutum ya dauki hukunci da kanshi, abari idan na dawo a fada mani.

Ina fatan kowa ya fahimci abinda nake nufi? Shewa Mama tayi tace Allah mun tuba, wai yau nice akema duniyanci anan gidan, koma me zakace, nide babu ruwana da maciya amana, wallahi ko kofar dakina naga mace senayi mata rashin mutunci.

Kuma bance arika aikar mani yara ba. Malan yace ya isa haka nan, itama na bata Fatima zata koma bangarenta kema kizauna da yaranki. Mama tace wannan ne baka isa ba, in rike yarinyar tun tana karama se yanzu ta kawo karfi zaka kwace mani ita, wallahi baze yuwu ba.


Malan yace idan Farida ko Fahad na dauka ai seki hana ni, tashi kibani waje, tashi Mama tayi tana masifa da zage zage. Malan yace ma Suwaiba kiyi hakuri, nasan kina da ilimi zaki iya zama da ita. Kuma ina fatan zaki rike mani Fatima tamkar ke kika haifeta? Suwaiba tace ai bakomai.


Na iya zama da wadan da suka fita hauka ma, kuma nasan komai akan labarin Fatima da Faisal, insha Allah zasuyi zaman jin dadi a wajena. Allah yabani ikon rikeso. Malan yace amin nagode, suma ai gobe zasu koma makaranta.

Ke kuma transfer dinki zuwa monday ta sama za'a kawota, kuma sekinyi sati 4 zaki fara zuwa aiki, tunda kin iya mota se kirika tafiya atawa danni shago kadai nake zuwa. Suwaiba tace nagode sosai.

**** ****

Washe gari haka Malan yasa Suwaiba ta shiryama Fatima kayanta kuma yakawo mata kayan miya suka shiga kitchen ita da Fatima suka dora abincin da zata tafi dashi.

Mama kuwa duk yanda taso Farida ta zo suyi aiki kiyawa tayi, bayan tagama hada kayanta shima da kyar ta hada ta tafi wajen saurayinta, seda suka gama lalatarsu sannan yakawo kaya yabata da kudi, haka tazo a boye ta saka cikin kayanta.


Suna gama shiri Malan yace su fito, haka Suwaiba ta bama Fatima kayan biki hada kudi sosai Fatima taji dadin yanda Suwaiba tayi mata, godiya tayi mata suka fito, ko kallon bangaren Mama batayi ba, dan ita tunda suka dawo ta dauko kayanta bata kara shiga part din ba.


Sallama taje tayima Farouk yace shima anjima ze tafi, Fatima tace haba Yaya ka bari ka kara samun sauki,mana. Farouk yace Fatima bazan iya cigaba da zaman gidan nan ba, kawai gara intafi. Fatima tace to Allah yakara sauki.

Haka suka tafi Farida se kuka takeyi wai Mama bata bata kudi ba, ita kuma bata dasu, tun amota Malan yace ta rufe mashi baki. Haka Fatima ta fada mashi abubuwan da Suwaiba ta bata, sosai Malan yaji dadi.

Bayan sun tafi Mama ta zauna tana tunanin inda Fahad yake, tunda suka dawo bata ganshi ba, kuma da alama tun tafiyarshi be kara dawowa ba. Tashi tayi ta nufi gidan Maman Sultan, duk da tana fushi da ita saboda bataje dubo su ba, amma haka ta tafi dan itace babbar aminiyarta a unguwar.

Dama kuma babu wanda yaje dubosu saboda basa shiri da Mama. Bayan sun gama gaisawa da Maman Sultan cikin borin kunya tace Maman Farida kin ganni shiru ko? Wallahi Sultan ne beji dadi ba. Mama tace nide ko nace, nasan haka nan bazaki kasa zuwa dubiya ba.

Maman Sultan tace ina amarya, ashe Malan aure zeyi shine kika boye mani? Mama tace ni yanzu ba wannan maganar nazo muyi ba, Fahad nazo nema, daga baya zan dawo muyi wannan maganar, danni ma Wallahi yanda kika ganta haka naganta, har fa suma nayi.

Dariya Maman Sultan tayi tana fadin kai dan Allah? Mama tace dan Allah bakiga Fahad ba? Maman Sultan tace wallahi banganshi ba, ni yaushe rabona dashi. Salati Mama tayi tana fadin to ina yashiga?

Maman Sultan tace kije gidan Hajiya kila baze wuce can ba. Saurin tashi Mama tayi tana fadin kinga har na manta da gidanta wallahi, bara inje kome kenan sena dawo.


Zaune take gaban Hajiya, bayan sun gama gaisawa Hajiya ta rufeta da masifa dan tasamu labarin abinda Fahad yayi, kuma lokacin da yazo gidan ta rufeshi da fada tayi, haka yayi mata rashin kunya ya tafi, kuma tun daga ranar be kara zuwa ba.


Sosai Hajiya take ma Mama fada, daga karshe tace yanda kikayi kokarin lalata yaran wata, gashi nan naki ne suka fara lalacewa, kadan ma kika gani, saura Farida itama , dan an fara kawo mani labarin abinda takeyi.

Wace irin mata ce ke Hauwa? To bari kiji , ni rabona da Fahad yau kusan kwana 6, nan yazo dan nayi mashi fada yayi mani rashin kunya yatafi, ko Malan ban fada mawa ba nasan da se yasha zana.

Tashi Mama tayi rai abace tace shikenan, yanzu kowa baya sona baya son yarana, idan ma wani mugun abun kuke nemansu dashi Allah yana gani, kuma  yarana bazasu lalace ba, insha Allah yaran Jamila sune zasu watse.

Kuma Fahad namiji ne, duk inda yaje nasan ze dawo gida, juyawa tayi ta fita tana masifa. Sosai Hajiya tayi mamakin yanda tayi mata, a fili tace Allah ya shirya, inde duniyace wanda bezo ba ma tana jiranshi.



Tun kafin ta karasa gida ta hango taron yara hada almajirai, sauri kawai take domin taga mesukeyi awajen. Tana karasawa ta ga mutum akwance kuda se binshi yakeyi, matsawar da tayi taga ashe Fahad ne, salati tasa tana fadin me yasameka kuma?

Wani yaro yace wasu matasa ne suka kawoshi nan suka kwantar dashi, Mama cikin kuka tace dan Allah ku kama manishi mushiga ciki, gaba daya yaran kowa ya watse da kyar tasamu wasu almajirai suka kama shi, suna shiga suka ajeshi adakinta, se wari yakeyi da zarni, naira hamsin ta basu suka tafi.

Kuka kwai take tana rufe hanci, kallon Fahad takeyi yanda ya koma, gaba daya yayi baki, Farouk ne yashigo, tace yauwa Farouk zo ka kama Fahad muje ayi mashi wanka, gashi nan se bacci yakeyi.

Juyawa Farouk yayi yana fadin gaskiya jikina be gama warkewa ba, sede kije kiyi mashi, kinsan,likita ya hanani daukar abu me nauyi. Ko kuma kibarshi idan ya farka yayi da kanshi. Sakin bakin Mama tayi tana kallon Farouk har ya fita.


Kuka tasa tana fadin nashiga 3, wannan wane irin bala'i ne haka yake shirin faruwa dani?馃檰馃徎馃槶.

Nikam nace shafa kiji馃槒馃し馃徎鈥嶁檧


Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263


馃彙馃彙 A WANI GIDA馃彙馃彙
          馃槶馃槶馃槶

              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

 [email protected]
Facebook...Nabeela Ladeey

        Part 85  鈴� 90

Kuka kawai Mama take tana fadin Fahad katashi dan Allah, amma ina Fahad bema san ta nayi ba, ruwa ta debo ta zuba mashi, da kyar ya bude idanuwanshi da sukayi jawur, sede ko hannunshi yakasa dagawa.

Kiranshi ta karayi amma yakasa amsawa, kafin wani lokaci idonshi yakara rufewa ya koma bacci, ruwa ta debo tana ta kwara mashi amma koya farka baya iya motsi.

Kamashi tayi tashiga bandaki dashi, da kyar ta cire mashi kayanshi tayi mashi wanka hada abun kashi ajikinshi, haka tagama mashi wanka amma baya motsin kirkiri, fito dashi tayi ta dauko wata karamar katifa ta kwantar dashi.

Fita tayi taje ta dauko mashi kaya tazo tasa mashi, har yakara komawa bacci, kuka tasa tana fadin wai Fahad wannan wane irin bacci ne haka? Kowane irin bacci mutum yakeyi matukar yayi wanka yana warwarewa.

Bandaki ta koma domin ta jika kayan data cire mashi, wani abu taji a aljihunshi, tana saka hannu ta ciro wata kwaya packet guda, kara dubawa tayi ta ganta kana na, saka rigar cikin ruwa tayi tana fadin ashe baka da lafiya ga maganinan a rigarka shine baka dawo gida ba.

Komawa tayi ta kara zuba mashi ruwa, yana bude ido ta ballo wannan kwayar data gani guda 2 ta saka mashi abaki ta zuba mashi ruwa, da kyar ya hadiye ya koma ya kwanta. Kallonshi tayi cike da tausayi tace sannu Fahad.

Tunda kasha magani nasan zuwa anjima zaka warware, bani da Panadol ma da na kara maka dashi, amma bara malan yazo seya siyo maka. Fita tayi domin ta dora girki.


Malan yana dawo wa dakin Suwaiba ya nufa, tana ganinshi ta taso tana mashi sannu da zuwa, karbar kayan da yazo dasu tayi tana fadin Allah sarki 'yan makaranta ana can. Malan yace wallahi kuwa.

Ruwa ta dauko mashi bayan yasha yace bani wannan ledar babbar ciki tasu Hauwa ce, wannan kuma ni dake, kifin Dan nakola ne nagani shine nasiyo. Suwaiba tace Allah sarki mungode Allah yakara budi, yace amin.

Nima nagode da wannan addu'a, tashi tayi tana fadin muje kaci abincinka ko, yace to bara na mika mata. Yana shiga falon Mama ya sameta ta tasa Fahad da yake ta bacci ta buga tagumi,

Murmushi yayi yace su Hauwa kuma tagumin me akayi? Saurin dago kai tayi ta daure fuska tace ai duk wata Uwa tagari dole taji ciwon halin da danta yake ciki, haka kuma duk wani Uban da yasan ciwon haihuwa dole ya damu da halin da danshi ya shiga.

Malan yace wannan kuma ke kika sanshi, ledar hannunshi ya mika mata yana fadin gashi keda yaranki, kuma Farouk anjima ze koma makaranta, saboda bakin halinki Dan cikin ki yake gudun ki.

Wallahi Hauwa kiji tsoron Allah, ya kamata ace zuwa yanzu kin saduda, zuwa yanzu kadai kina ganin yanda Allah yafara nuna maki ishara, ko wannan yaron da yake gabanki kadai ya isa ya zama aya akanki.

Nikam nagode ma Allah da yasa na fita daga makircinki, Allah ya haska mani duhun da nake ciki, wallahi Hauwa idan baki tuba daga abinda kike mani nida yaran Jamila ba hakika wuta itace mako marki.

Mama tace wallahi kaine za kaga wuta bani ba, kuma cikin nida kai za'aga wanda zeyi dana sani. Malan yace shikenan Allah ya nuna mana wannan rana. Shi kuma wannan baccin me yakeyi bayan anyi sallar azahar? Mama tace in da ka damu dashi kana shigowa shi zaka fara tamabaya.

Yaushe rabon daka ganshi amma ko so daya baka tambayeshi ba, kuma kasan baya kwana gida. Malan yace tunda ya aikata laifi ai dole ya gudu yabar gida, ba dan Farouk yana da sauran kwana agaba ba ai da tuni ya kashe shi.

Mama tace koma menene beda laifi, tunda kun juya mashi baya ai dole yashiga kowane hali.  Kasan awane hali na sameshi dazu? Hannu tasa ta goge idonta tace bayan na fita nemanshi haka nasamu wasu sun kawoshi ko motsi bayayi.

Haka suka yardashi akofar gida suka tafi, da kyar nasamu wasu almajirai suka shigo mani dashi, ajikin kayanshi fitsari ne da kashi, haka nace ma Farouk yazo ya daukeshi yayi mashi wanka amma se yace mani  wai likita ya hanashi daukar abu me nauyi.

Idan na zuba mashi ruwa daya bude ido yake komawa bacci, da kyar na kaishi bandaki na cire mashi kaya nayi mashi wanka da ruwan sanyi, amma duk irin ruwan dana sa mashi bacci yakeyi.

Seda na duba aljihun rigarshi naga fakitin wani magani kanana, ashe ma beda lafiya, da kyar na zuba mashi ruwa ya bude idonshi na samu na balli wannan maganin na bashi guda biyu, yana gama sha yakara komawa bacci.

Kuma bani da Panadol da na kara mashi dashi, amma shine za kazo kana fada mani bakaken maganganu akan Dana, koma me Fahad ya zama ni ba na takaici, domin shi namiji ne kuma wata rana komai ze wuce.

Tunda ta fara magana Malan yasaki baki yana kallon Fahad, cikin sauri yace ina maganin da kika bashi? Tashi Mama tayi ta dauko mashi maganin. Malan yana dubawa ya dafe kai, Salati kawai yakeyi tare da cire hula.

Kallonshi Mama tayi tana fadin lafiya? Malan yace lallai Hauwa ban san baki amfani da ilimin secondary da kikayi ba se yau, ace mutum ya dauki muguwar kwaya irin wannan ya bama danshi kuma har guda biyu? To idan baki sani ba wannan kwayar itace yaje yasha tafi karfinshi yake wannan baccin.

Kuma ke gashi kinzo waccan bata sakeshi ba, kin kara dura mashi wata. Dafe kirji Mama tayi tana fadin kwaya kuma? Tsaki Malan yayi yama rasa me zece mata. Juyawa yayi yana fadin dole mu kaishi asibiti.


Dakin shi ya nufa ranshi abace, yana shiga besan lokacin da wasu hawaye suka zubo mashi ba. Wannan wace irin masifa ce take samunshi? Ko de alhakin Inne da yaranta ne yake binsu?   Tabbas yasan alhakinsu ze iya kamasu.

Domin ya kunta ta mata, haka kuma yayi rashin adalci ga yaranta, se gashi tun a duniya Allah yafara nuna mashi ishara, yaran da be dauka da muhimmanci ba sune su kafi kowa agidan, wadan da ya fifita kuma gasu nan sune suka koma ja baya.

Farouk ne kadai yaron kirki acikinsu. Hannu yasa ya goge idonshi ya dauko wayarshi ya kira Labaran, bayan sun gaisa yafada masa idan yana gida yanaso ya rakashi asibiti. Labaran yace lafiya de? Nan Malan ya fada mashi halin da ake ciki.

Labaran yace babu damuwa gani nan zuwa. Yana kashe wayar ya shiga dakin Suwaiba, saurin tashi tayi tana fadin Malan lafiya na ganka haka? Girgiza kai yayi yana fadin ina fa lafiya.

Shikenan daga wannan masifa se wannan, labarin abinda yafaru ya fada mata. Suwaiba tace ikon Allah, ita kuma bata tsaya karanta abinda yake jikin maganin ba kawai ta kara dura mashi? Malan yace jahilcin fa.

Suwaiba tace haba Malan, taya zaka kira matarka uwar 'Ya'yanka da jahila, kada kamanta fa mu duka amana ne awajenka, idan har baka iya dedeta tsakaninmu ba hakika bazaka taba ganin dede agidanka ba.

Yanzu ka zo gabana ka kirata da jahila, me kake tunanin shedan ze ai yana mani azuciyata? Kada kamanta a duk inda muke shedan yana biye damu, kuma yana aiki da muna nan halayenmu wajen jefa mu cikin masifa.


Zaka iya samun macen da tayi karatu amma ba lallai bane ta iya gane sunan ko wane magani, kawai kuskurenta anan da ta dauki maganin da ita kanta bata taba ganinshi agidan nan ba ta bashi.

Kasan yanda Uwa take son Dan ta kuwa? Kowace Uwa idan taga Danta beda lafiya jitake kamar ta dauke ciwon ta maida kanta, kuma bazata bata lokaci ba wajen nema mashi magani, a yanayin da ta iske Fahad kowane irin temako zata iya mashi.

Kuma kai ma Malan kana da laifi, halin da Fahad yake ciki, wallahi mace bazata iya tafiyar dashi ba, tunda nazo gidan nan banganshi ba, haka kuma ban taba jin kayi maganarshi ba, kuma kana sane da baya kwana gida.

Kai da kanka kace yasan yayi laifi shiyasa ya gudu, da ace guduwar da yayi yafada mugun hannu me kake tunanin ze zama? Wallahi duk da ban taba haihuwa ba, bansan ciwon Da ba, amma ina tausayin halin da Fahad yake ciki.

Har yan zufa da kyar idan ya wuce shekara 20, kaga kuwa har yanzu hankali begama shigarshi ba, dan shekara 30 ma da yake cikin irin wannan yanayin ya aka kare dashi bare kuma yaro.

Nide shawarar dazan baka katsaya ka kula da Fahad, Hauwa bazata iya kula dashi ba, domin mu iyaye muna da tausayi, koda wani abu me wahala akace muyi ma yaranmu tausayi shine ze hanamu.

Shiyasa bazata iya nuna ma Fahad kuskurenshi ba, amma kai da kake namiji kaine zaka iya tsayawa ka nuna mashi kuskurenshi, domin yawancin yara sunfi shakkar mahaifinsu a kan Uwa.

Yanzu ne ya kamata ace kayi kokarin magance matsalar Fahad, wallahi idan yakara shekara daya nan gaba sede wani iko daga Allah, amma zaman gidan nan seya gagareshi, gani zeyi kuna takura mashi gara yatafi wani wajen.

A katsina akwai asibitin da zaka kaishi kuma zasu iya sama mashi magani, kada ma kace zaka kaishi asibitin garin nan, kawuce dashi Katsina kuma kada ka boye masu komai kafada masu abubuwan da yakeyi.

Dan Allah Malan ka daure ka gyara kuskuren da ka aikata abaya, babu abinda bansani ba na gidan nan, domin Hauwa aminiyar Yayace, kuma ta fada mani komai, duk da ita taso inshigo gidanka dan in wulakanta Hauwa.

Amma ni bani da wanna burin, kazauna da kowa lafiya arayuwa shine dede, gaba daya duniyar nawa take? Kai kanka kasan ka aikata kuskure tun akan yaranka da kuma kan Inne, saboda haka kada kayi sake ka kara maimaita abinda kayi abaya.

Yaro ko ya yake shima Da ne, me lafiya, marar lafiya, me hankali, marar hankali, me kokari marar kokari duk daya suke, kuma hakkin iyaye ne su tsaya su dedeta tsakanin yaransu, duk da ance wanda yafi maka biyayya yafi soyuwa awajenka.

Amma matukar baka adalci atsakaninsu tabbas kaima ba zaka ga adalci ba idan suka girma. Amma kayi hakuri idan akwai abinda na fada wanda ya bata maka rai. Hawaye ne kawai suke zuba daga idon Malan tunda Suwaiba ta fara magana.

Jawota yayi ya rungume yana kuka sosai, ita kanta seda kwalla ta cika mata ido, ya dade a haka kafin ya saketa yace nagode Suwaiba, hakika ke mace ce tagari, naso ace aurenki da nayi ya zama abinda zan kunta ta ma Hauwa.

Se gashi kin fini hankali da hangen nesa, naso in kara maimata kuskuren da nayi abaya ta dalilin aurenki, se gashi Allah be baki ikon biye mani ba. Nagode da shawararki, kuma insha Allah zanyi kokarin gyara kuskure na.

Bara muje mu kaishi asibiti Labaran yace gashi nan zuwa. Suwaiba tace to zauna kaci abincin kafin ya karaso sannan ku tafi, Malan yace kawai bara muje, Suwaiba tace Allah bazaka fita ba seka ci ko kadan ne, nasan idan katafi ba lallai bane kaci.

Zubo mashi tayi ta zauna tana ta lallashinshi yana ci. Turo kofar falon akayi da karfi, Mama ce tsaye tana ta huci, kallon Malan da Suwaiba tayi tana fadin to munafuka, wato yazo daukar mukullin mota yakai Dana asibiti shine kika rikeshi kina nuna mashi karuwanci ko.

In da Danki ne zaki tsareshi kice se yaci abinci? Banza kawai wadda batasan ciwon Da ba, kai kuma mijin ta ce ka biye mata kazauna kana cin abinci, koda yake baka da laifi. Ciki kawai ka iya se sayen ragon suna.

Da ace ku ma maza kuna dandana zafin nakuda koda na minti 2 ne da bazaku taba banzatar da abinda kuka haifa ba. To kusani wallahi idan Fahad ya mutu gaba dayanku senayi kararku, maciya amana kawai daku.

Juyawa tayi tana masifa. Malan yace aikin banza, mace kamar tababbiya. Murmushi Suwaiba tayi tace wallahi kaima hada kai, ko nice ai abinda zanyi kenan, yi sauri katashi kutafi, murmushi yayi yace ko kece abinda zakiyi kenan? Tace emana, amma bazan zageka ba.

Sede zan nuna jin haushina na rashin tafiya da wuri, amma yanzu ka tashi katafi, ruwa yasha sega wayar Labaran, tashi yayi yana fadin kin ganshi nan ma yazo. Sallama yayi mata tana fadin Allah yatsare kuma ya bada sa'a, yace amin mata ta.


Mama ya iske zaune da hijabi ajikinta tana jiranshi, yana zuwa ya dauki maganin da ta bama Fahad yasa aljihu ya daukeshi, tashi Mama tayi tana fadin ina kuma zakaje da maganin? Zuwa zakayi ka tona asirin Danka kace ga abinda yasha? Lallai Malan baka da tausayi.

Shiru yayi ya kyaleta ya nufi hanyar waje, biyoshi tayi tana fadin ai se ka jira in kulle dakina mutafi, komawa tayi tana rufe dakin, tana zuwa bakin gate sede kurar motar ta iske. Tsaye tayi tana masifa cike da bacin rai.

Ta san idan Fahad ya farfado Malan masifa zetayi mashi, amma da tana kusa ganin idonta bazeyi ba, jitayi kamar ta bisu sede ba ta da kudi a hannunta, kuma ba tasan wane asibiti zasuje ba, komawa tayi tana fadin wallahi zaka zo ka sameni.


Tafiya suke suna labarin abinda yafaru, Labaran yace dama kana fada mani zamu kaishi asibiti nace idan nazo zance mutafi dashi Katsina, saboda akwai wani likita dana sani akan irin  wannan case din yayi karatunshi.


Malan yace ai nikam nashiga wata jarabawa, wannan yaro ya fita zakka acin yarana, wallahi kunyar zuwa asibitin ma nakeyi. Labaran yace kunyar me? Wannan ba abun kunya bane a wannan zamanin, domin abinda yazama ruwan dare ne.

Wallahi duk wanda kaga yana maka dariya ko yana gulmarka akan yaronka ya zama haka to besan inda yake mashi ciwo ba, domin wannan zamanin duk yanda ka kai da tarbiyantar da Danka wallahi se yanda Allah yaso dashi.

Duk da Allah yana kallon zuciyar mu, amma wani lokacin yana gwadamu ta dukiyoyin mu, ko ta zuri'armu, ka ga kuwa babu wanda zece Allah baze jarabce shi ba. Abinda yafi kawai ka dage ka tarbiyantar da yaranka, ka mika ma Allah sauran.

Kuma matukar kaima baka TAKA DOKAR ALLAH ba to shima ze dubi lamuranka, amma gaskiya Malan kayi kuskure abaya, lokacin inaso in fada maka gaskiya sede yanda ka dauki kan ka yasa bana maka magana.


Allah ya hadaka da muguwar mace, amma kai sam baka fahimci haka ba, taso ta ruguza maka gida Allah ne kadai ya kareka, amma tunda yanzu ka gane kuskurenka to se kayi kokarin gyarawa.

Wallahi akwai mutanan da suke samuna akan tunda muna mutunci da kai in sameka in baka shawara akan tunda kayi aure ka rabu da Hauwa. Kasan kowa da irin tunaninshi, ai ba'a gyara da barna.

Shiyasa nace masu suzo da kansu su baka shawara, da su kaji haka suka fara zarewa. Murmushi Malan yayi yace kasan mutane da shegen sa ido,  ai wallahi koda Hauwa tayi mani abinda yafi haka bazan sake ta ba.


Ai ina ganin kuskuren wasu mazen wai dan mace tayi masu wani mugun abun su saketa su auro wata. Ai wallahi bazan sakeki ba, da ace ma ban haihu da ke ba, shine zan sakeki, amma na haihu dake, kuma kin lalata mani yara.

Lokacin dazan sakeki cewa zakiyi bakizo da kowa gidana ba, haka zata tsallake ta barni da abinda ta bata. Ai ko ana sakin mace to ba irin su Hauwa ake saki ba, domin abinda tayi mani yakamata ace ta zauna agabanta taga kuskuren data aikata.

Yanzu da ace na saketa, kuma Fahad yaje yayi wannan danyen aiki, shikenan fa ita tana can, kilama tayi aurenta acan gidan wani tayi nadamar kuskuren da tayi se tayi gyaranta acan su cigaba da zamansu lafiya ni kuma ta barni da masifa.

Daga karshe duk matar dazan aura se tace bazata iya zama da yarana ba, saboda an riga an lalatasu, idan ba Allah ya tsare ba se kaga na kasa samun matar aure, shikenan se inzauna da yara bakin cikinsu yakasheni.


 Wallahi ba za'ayi wannan abun da ni ba. Yanda ta bada gudunmuwa wajen lalacewar yaranta haka zata zauna muci bakin cikinsu tare, kome sukayi mu hakura murikesu. Amma babu maganar saki atsakanina da Hauwa wallahi.


Dariya sosai Labaran yayi, danshi tunda yake be taba cin karo da mutum me irin halin Malan ba, shidin na daban ne. Kallonshi yayi yace lallai Malan kai din na daban ne, hakika wannan magana taka abun dubawace.

Wallahi ko ni mata ta tayi mani irin abinda Hauwa tayi maka matakin dazan dauka shine saki, amma tabbas ayanzu na dauki darasi daga wajenka, wani sakin baya warware matsala sede ya karata. Kuma ina goyon bayanka Allah ya baka ikon jure duk wani abu da zatayi maka har ta gane kuskurenta.

Malan yace amin, shiyasa ai na dage na kara aure, domin bazan iya zama bakin ciki ya kashe ni ba, kasan ance gida biyu maganin kashe gobara. Idan na shawo zafi acan kaga zan samu sauki anan.

Musamman da Allah ya hadani da mace tagari, kasan Allah Labaran, ada dana auri Suwaiba naso in muzguna ma Hauwa, se gashi ayau Suwaiba ta fada mani maganar data tsaya mani arai, hakika auren mace me aiki da ilimi babban jari ne.


Bawai auren mace me ilimi shine jari ba, ka samu wadda take aiki dashi shine babban jari. Allah ya yafe mani abinda nayi abaya, kuma yabani ikon gyara kuskure na. Amma ina matukar farin ciki da auren Suwaiba.


Allah ne ya temakeni, da yaso seya hadani da wata muguwar macen, domin alhakin Inne nasan baze barni ba. Amma se Allah ya saka mani da mace tagari. Labaran yace ai  haka al'amarin Allah yake, duk yanda yaso haka yakeyi da bawansa.


Shiyasa kada kashiga tsakanin Allah da bawansa, domin shi Allah gafurur rahim ne. Fatan mu de Allah yabamu ikon cikawa da imani. Malan yace amin.


Suna isa Psychiatric hospital Labaran yayima abokinshi waya, cikin sa'a yace yana office, dan shima be dade da zuwa ba dan yau asabar yazo duba wasu Patient dinshi.


Malan ne ya dauko Fahad, suna shiga wasu ma aikata suka kawo gado aka dorashi sukabi bayansu dashi, cikin office din likitan suka shiga dashi, bayan sun gama gaisawa Labaran yayi mashi bayanin abinda yake tafe dasu.

Likitan yace afada mashi asalin abinda yake faruwa............. nan Malan ya fada mashi komai babu abinda ya boye mashi, daga karshe yadauko maganin da aka bashi yamika ma likitan.


Sosai likitan yayi mamakin inda yara kana na suke samun irin wannan muguwar kwaya. Kallonsu Malan yayi yace lallai wannan ba karamar kwaya bace. Allah kadai yasan ko nawa yasha har ta kaishi ga shiga wannan condition din.

Maganar gaskiya wannan kwayar tayi mashi karfi sosai, dan ba kana nan masu shaye shaye bane suke shanta, wasu ma irin masu aikin karfin nan ne suke shanta, suma kuma komin girman mutum baya shanta da yawa.


To shigashi yashata da yawa, kuma anzo ankara dura mashi har guda biyu batare da waccan ta sake shi ba. Allah ya kyauta, amma gaskiya yana cikin hadari, yanzu dole zaku barshi nan, sede mu bama bukatar me jinya.

Kawai zaku biya kudi ne kubarshi, mu zamu tsaya iya kokarinmu domin muga mun shawo kan matsalar, idan Allah yaso da rabon yadawo dede wata rana seka ga kamar ba'ayi ba.

Domin nayi irin wannan cases din da yawa, hada wanda yafisu kuma cikin ikon Allah ina yin nasara, wallahi kusan kullum se kaga mutanan da muka zauna dasu wadan da suka warke sunzo gaishe ni.

Wasu ma saboda sabon da sukayi basa iya barin asibitin kwata kwata, akwai wasu daga cikin leburorin mu patient di na ne, bayan warke warsu suka nemi abarsu anan surika aiki, kuma zaka samesu wallahi ko goro ba saci.


Wasu daga lokacin da suka warke ko warin sigari basa sonji, gasunan kala kala, wasu kuma idan matasa ne zakaga sun koma makaranta sun natsu sunyi karatunsu, daga karshe zaka samesu kamar wani abu be taba faruwa dasu ba.

Babu yanda Allah baya jarabtar bawansa, shiyasa ba abun kunya bane wai dan Danka ya shiga irin wannan matsalar ka ji kunyar kawoshi asibiti. Akwai wasu da Dansu yasha wata muguwar kwaya.

Lokacin da suka kaishi wani asibiti se suka boye asalin abinda yasha, su kuma dama ba likitocin fannin mu bane, kawai suka yimashi wani treatment din daban, wallahi wannan shi yayi sanadiyar mutuwarshi.


Da yake Baban yaron abokina ne, lokacin da na je gaisuwa yake fada mani asalin abinda yake faruwa, sosai nayi mashi fada, duk da Allah yasa bazeyi tsawon rai ba, amma da ace asibitin mu suka kawoshi ko da basu fadi abinda yasha ba ina kallonshi zangane halin dayake ciki.


Kuma bazamuyi kuskuren da wadan can sukayi ba, duk da bazamu hanashi mutuwa ba, amma ko yaya ne zamu iya gano kan matsalar. Labaran yace ai haka mutane suke, wasu suna ganin abun kunya ne dan Dansu yana shaye shaye.

In da kowa yana tashi tsaye wajen nema ma Danshi magani ai da an samu saukin wannan masifa. Allah yayi mana tsari da wannan zamani. Suka ce amin. Dauko masu form likita yayi Malan ya cike sannan ya basu bill din da zasu je su biya.

Godiya sukayi mashi, Malan yace ka bani number dinka to, likitan yace to kuma zamu ne meka shiyasa muka baka wannan form din kacike dan akwai address da komai aciki, amma de ga tawa kayi saving.


Bayan sun gama komai sukayi mashi godiya kuma likitan yace zasu iya zuwa duk lokacin da sukeso domin ganinshi, amma yanzu seya farfado sannan. Sosai sukayi mashi godiya suka tafi.


Malan yace wallahi tsoron ganin Hauwa nakeyi, se naji dama mun taho da ita taji wannan bayanin nasan ba zatace komai ba, amma yanzu duk yanda zan fada mata ba zata fahimta ba, saboda ta riga da ta sama ranta bana son yaranta yanzu.

Labaran yace dole zakayi hakuri amatsayinka na namiji, dama kuma idan ana fada tsakanin mata da miji dole miji ne yake fara sakkowa, domin su mata ba'a biye tasu, idan kace kai ba zaka sakkoba to tabbas za'ayi danyen aiki.

Shiyasa Allah ya daukaka mu sama dasu, kuma yasamana zurfin tunani sama dasu, ka dena biye mata kuna cacar baki, hakan shine ze kara jawo rai ni asakaninku, komun masifarta idan taga tana maka ba ka kulata zata gaji ta bari.

Malan yace ban da Hauwa, domin ba ta taba dena masifa, idan kuma taga tana mani ina kyaleta ji zatayi kanta yakara fasuwa, har ta rika gadarar ina jin tsoronta. Ni kuma kasanni bana kyalewa, domin mata zuma ne seda wuta.


Dariya Labaran yayi yace kaine kake ganin haka, amma mace tamkar flower haka take, duk yanda kayi da ita haka take kasancewa, kawai abinda zaka sama ranka shine hakuri, se me dan tace kana tsoronta? Bade kace ba zaka saketa ba? Kaga kuwa dole kasama kanka hakuri.

Matukar kana so ka zauna agidanka lafiya to dole ka sama zuciyarka ruwan sanyi. Ka sameta cikin hankali kwance kayi mata bayani yanda zata fahimta, kuma kada ka nuna mata case dinshi babba ne.

Kace likitan yace ze zauna awajenshi ne dan ya rabashi da abokansa da suke bashi irin wannan kayan mayen. Kasan Uwa da son Danta, wallahi matukar kayi mata bayani cikin kwanciyar hankali zataji dadi, kuma zata fahimceka. Malan yace shikenan zan kokarta, Allah yasa in iya danne zuciyata. Dariya Labaran yayi yace amin.



Malan ya dade kafin yashiga falon Mama, da kyar yasamu yashiga, zaune ya sameta ta buga uban tagumi, da sallama yashiga yana fadin uwargida ran gida. Saurin tashi Mama tayi tana duba bayanshi.

Dariya yayi ya kamota yana fadin Fahad kike nema ko? Kawai na saidashi. Duk yanda ta daure fuska seda tayi murmushi, kwace hannunta tayi tana fadin ni dan Allah kadena sani murmushi.

Ina Dana yake? Zama Malan yayi yana fadin kizo ina baki labari me dadi akan Fahad, saurin zama tayi tana kallonshi. Malan yace insha Allah daga wannan karon matsalar mu akan Fahad tazo karshe. Mama cike da zumudi tace me yafaru?..........

Nan Malan yafada mata duk yanda Labaran yace yafada mata, daga karshe yace kinga abokanshi ba zasu kara ganinshi ba bare su maidashi ruwa. Mama tace shikenan acan zeta zama? Dafe kai Malan yayi yace baki fahimce ni ba.


Lokacin daze dawo insha Allah ya tsani duk wani abu na shaye shaye, kinga koya dawo sukazo wajenshi baze iya tarayya dasu ba, domin baya bukatar warin komai, kinga shima zeyi rayuwa kamar sauran yara cike da farin ciki.

Dariya Mama tasa tana fadin da gaske? To yaushe zamu je ganinshi? Malan yace likita yace kwayar da yasha tana da karfi, kuma idan mutum yashata yana yin bacci sosai, to yace idan ya farfado ze kirani. Mama tace to ya sunan asibitin daka kaishi? Malan yace Psychiatric hopital ne. Mama tace na mahaukata kenan?Mama tace haba.

 Malan, Allah yasa ba karya kake mani ba馃檴. Nafa san halin ka sarai, nasan yanzu ba ka sona nida yarana, kila kawai bakaso mutanan unguwa surika ganin Fahad suna maka surutu akanshi shiyasa ka daukeshi ka kaishi asibitin mahaukata.

Kuka tasa tana fadin yanzu ta ina kaga Fahad yana hauka da zaka kaishi waccan asibitin? Wallahi kaji tsoron Allah, nide ka maido mani yarona, gara inzauna dashi yana shaye shayen yafi mani da a kaishi asibitin mahaukata.


Macuci kawai, insha Allah aniyarka sede ta bika, amma yarana baza suyi hauka ba, tashi Malan yayi ranshi abace yace bazan daukoshi ba, idan kina tunanin kin isa kije ki daukoshi, sakarya marar tunani, duk yanda naso in ganar dake ba ki ganewa.

Se kije kiyi abinda zakiyi, kuma kika fita daga gidan nan zakiga abinda zanyi maki. Hanyar fita ya nufa yana masifa. Murya Mama ta daga tana fadin so kake infita ka sakeni saboda ka yi aure, kuma wallahi babu inda zanje.

Dama ai naga take taken ka so kake inyi wani laifi da zaka fake dashi ka sakeni domin kasamu damar cin amarcinka, to wallahi nida kai mutu ka raba, ina nan kuma dole ka kaini inga Fahad. Murmushi Malan yayi daya fita aranshi yana fadin ni ba saki nake nufi ba, ai nida ke mutu ka raba.

**** *****

Haka rayuwar gidan Malan ta cigaba da tafiya, wata rana ayi dadi wata rana ayi rashin dadi. Shide Farouk ya koma makaranta, yace idan lokacin koma warshi asibiti yayi zeje daga can.

Da yake Malan yasan dalilin da yasa ze koma siyasa be hanashi ba, haka ya bashi kudi masu yawa yayi ma Suwaiba sallama, itama ta hada mashi kayayyaki tabashi, wanda ko Mama bata taba bashi ko ashana ba dan ze koma.

Sheda Fahad yayi sati guda kafin kwayar da yasha ta sakeshi, sede tunda ya farka ya koma kamar wanda aka zarema lakka, duk abinda zeyi a sanyaye yakeyinshi, duk yanda yaso yasamu koda sigari ce yasha abun ya faskara.

Dan ko fita bayayi shi kadai, duk inda zeje akwai wanda ze rakashi koda bandaki ne, kuma kafin yashiga se an cajeshi sannan, wata rana har kuka yakeyi, sosai yakeso yasamu wani abu yasha.

Sede sam likita ya hanashi, duk wata kofa ya tosheta, haka yayima su Malan waya ya sanar masu Fahad ya farfado, godiya yayi mashi ya tambaye shi halin da yake ciki, nan likita yayi mashi bayani, Malan yace zasu zo amma yanaso ya kara warwarewa yafiso Mamanshi ta sameshi da sauki. Likitan yace toshikenan.


Duk yanda Mama taso suyi tashi hankali da Suwaiba taki ta kulata, haka ta fara zuwa wajen aikinta kuma Malan ya bata motarshi tana zuwa aciki. Ba karamin tashin hankali Mama tashiga ba, bala'i kala kala takeyi akan Malan ya bama Suwaiba mota.

Itama tace dole seya koya mata, Malan yace shima ai bashi ya koyama Suwaiba ba, kuma itama saboda zataje aiki ne yake bata motar. Mama tace wallahi sede itama ya koya mata. Masifa kala kala haka Mama takeyi, gaba daya ta tashi hankalin gidan.

Ganin masifar taki karewa yasa Suwaiba ta roki Malan akan ya koya mata. Ranar da yake dakinta yace tazo suje ya koya mata, fara'a da haibaici awajen Mama abun ba'a magana, haka taci kwalliya tasa riga doguwa suka fita tana ta ma Suwaiba habaici.

Aranar farko da suka fara koyon motar Mama hada kukanta, wai Malan so yake ya kasheta, rokonshi tayi akan su koma gida ta hakura da koyon motar, Malan yace ai tunda suka fito seta koya, kan titi ya hau ya fito yace ta fito ta tuka akan titi dan dazu a wani fili ta fara tukawa.

Kuka sosai Mama takeyi tace idan baze maidata ba wallahi zataje ta hau mashin ta koma gida, inde mota ce Suwaiba taje tayi ta hawa, insha Allah itace zata zama ajalinta, amma ita ta hakura da koyon.

Ganin da gaske takeyi yasa Malan yana dariya suka koma gida, ko takan Suwaiba bata bi ba haka ta wuce daki. Malan daya fadama Suwaiba yanda sukayi da Mama sosai tayi dariya, dama tasan rigimace irin ta Mama.


Tun daga ranar Mama bata kara tada maganar mota ba, se kuma ta bullo da wata masifar, wai Malan idan yana dakinta dawuri yake fita kasuwa, amma idan yana dakin Suwaiba yana dadewa.


Malan yace Suwaiba da take tafiya aiki taya zan dade adakinta? Idan kinga na dade se idan kwananta yazo a week end, kuma dole inzauna agida in bata hakkinta, domin kema idan ina dakin ki bana fita se wajen 11 amma saboda masifarki zakice bana dadewa.

Mama tace amma ita ai baka fita se wajen azahar, Malan yace tunda week end ne ai dole in kai haka, kema idan week end ai bana fita se azahar. Ganin zata bata mashi rai yasa yabar mata gidan.


**** *****

Lokacin komawar Fahad asibiti haka yakira Malan yafada mashi, yace to seya dawo, bayan yaje likita ya dubashi yabashi wani magani daze rika shafawa acikin saboda yace yanajin kai kai, godiya yayima likita yanufi gidan Inne.

Sosai Inne taji dadin zuwanshi, dama wancan ranar taso ta karbi number dinshi amma ganin Mama yasa bata karba ba. Amatu hada tsallen ta sekace ta sanshi sosai, haka Inne ta cikashi da abubuwan motsa baki.

Kuma tace anan ze kwana tunda azahar tayi, idan yaso gobe seya tafi da wuri yasamu class. Sosai Farouk yaji dadin irin yanda Inne tayi mashi. Haka yaci abinci suka zauna shida Amatu suna ta wasa.


Lokacin da Alhaji ya dawo shima yaji dadin zuwan Farouk, haka suka zauna dashi suna ta firar rayuwa, anan Farouk yake fada masu Fahad yana nan Katsina a Psychiatric, sosai sukayi jimamin halin da yake. Alhaji yace to Allah ya shirya kuma ya bashi lafiya.


Washe gari haka Inne ta tashi da wuri ta soyama Farouk doya da kwai da dankalin turawa kuma ta soya mashi wainar kwai, haka ta dafa mashi farar shinkafa tayi mashi miya me yawa dama tana da kayan miya dafaffu a fridge, haka ta samashi naman kaji.


Acikin plastic ta juye mashi miyar ta zuba mashi shinkafar a cikin babbar cooler da doyar, haka Alhaji yace taje store ta dibar mashi danyen abinci. Sosai suka hada mashi shatara ta arziki.

Dubu 2 Inne ta bashi haka yayi mata godiya suka tafi da Alhaji ze kaishi tasha, Amatu kuwa bata san tafiyarshi ba tana can tana shirin makaranta. Bayan Alhaji ya ajeshi yaciro dubu 3 yakara mashi kuma ya biya mashi kudin motar, godiya Farouk yayi mashi, Alhaji yace kada fa kadena zuwa, inde kasamu hutu bazakaje gida ba kazo nan. Farouk yace insha Allah, haka yatafi cike da farin ciki, yana godema Allah da yasa ya gane gaskiya yadena wulakanta su Faisal.


**** ****

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya 'yan makaranta suna can kowa yana karatunshi, Farida yanzu sam bata maida hankali a makaranta, soyayya kawai tasa aranta, duk wanda taga yayi mata ba tajin kunyar aika mashi da wasika tana sonshi.

'Yan ajinsu har sun ganeta, gashi ta samu wata kawa wadda suke lalata da ita adaki, saboda itama ta koma kwanar su, kuma duk senior din da tace tana sonta ba ta jiran komai take amincewa, wani lokacin har zuwa daukarta ake kwana.

Duk abinda takeyi Fatima da Lubna sun sani, Lubna ce ma ta matsama Fatima akan suje suyi mata magana domin yin shirun beda amfani tunda 'yar uwarta ce. Lokacin da sukayi mata magana haka ta zage Fatima kuma tace kada takara shiga harkarta.

Tun daga ranar Fatima bata kara kulata ba, koda akazo visiting su duka Malan yazo dasu, kuma agabanshi aka hada komai na kayansu shiyasa Mama bata samu damar rage kayan ba.

Suwaiba itace tayi masu miya Mama ta dafa masu abinci, dan alokacin ranar girkin Mama ne ita kuma tace ba zatayi hada aikin visiting ba, hakan yasa Suwaiba tace zatayi masu miya.

Sosai Fatima taji dadin zuwan Suwaiba, bayan sun gaishe su ta koma kusa da Suwaiba tana fadin Aunty kinga mun kusa yin hutu, Suwaiba tace kice na kusa samun abokiyar fira? Fatima tace ai sati daya zanyi maki inyi ma Inne sati biyu. Suwaiba tace kai Fatima.

Mama da take gefensu tayi tsaki tace aikin banza son iyawa, idan mutum yanaso yazauna da Danshi ka mata yayi ya haifa, amma angama yawon karuwanci atiti ya za'ayi asamu haihuwa. Murmushi kawai Suwaiba tayi dan Mama batasan tana dauke da ciki ba.

Haka Farida ta rika fadama Mama karya da gaskiya, Mama tace ki rabu da ita, wata rana zamusha dariya ne. Farida tace Mama dubu daya zaki bani. Mama tace ke nifa yanzu banda kudi, kinsan bawani abu nake saidawa ba, se abinda Malan yaga dama yabani, yanzu ba kamar da bane.

Zumburo baki Farida tayi tace yanzu Mama baki so na sosai, Mama tace waya fada maki, kema kinsan bandasu ne, amma zan tara maki kafin kidawo, da kyar Mama ta lallasheta, haka suka tashi tafiya Suwaiba ta basu dari biyar biyar.

Mama tace waya san ko nawa kika bama Fatima dan agaban ido na ne zaki hadasu kibasu gaba daya, wai dan kisamu shiga awajen miji, inde wannan kissar ce duk na yita gashi daga karshe inda ta kaini, kema zakiyi kibari ne.

Suwaiba de batace mata komai ba, aranta tana fadin taki kissar ai taganin ido ce kikeyi, ita kuwa kissa ba dole se agaban wanda kakeso kake yinta ba, idan yasan kana wani abu abayan idonshi ma sekafi daraja awajenshi.


Bayan sun gaisa da Malan yabasu dubu dai dai kuma yakara masu nasiha akan su dage, haka sukayi masu sallama suka tafi.


**** ****

Jikin Fahad ya fara yin sauki, sede sam baya magana da yawa, gaba daya ya koma kamar wanda beda kuzari ajiki, duk yanda likita yaso ya sake kamar sauran bun ya gagara, domin kwayar tariga ta taba kwakwalwarshi.

Lokacin dasu Malan da Mama suka zo dubashi haka Mama tayi ta kuka tana fadin an maida mata yaro mahaukaci, sekayi mashi magana so biyar kafin yabaka amsa, kuma amsar so daya ze baka.

Da kyar likita yayi mata bayani, kuma yace kwayar daya sha ce tayi mashi illa, ga wiwin da yake sha itama tayi tasiri a kwakwalwarshi, dole se ahankali sauki ze sameshi. Mama tace itade abata Danta ta tafi dashi.

Malan yace babu inda za'a kaishi, abarshi nan idan yakara samun sauki se adaukeshi, da kyar likita yasamu ta hakura akan nan da wata 2 zatazo ta daukeshi. Haka suka tafi Mama se masifa takeyi.


**** ****

'Yan hutu sun dawo, seda Fatima tayi sati guda sannan Malan da Suwaiba suka shirya suka kaita gidan Inne, Mama kamar zata mutu ita da Farida saboda bakin ciki, dan Fatima tunda suka dawo so daya taje ta  gaisheta, sam bata shiga bangarenta, haka Mama tayi ta masifa Malan yace idan zataje tazo sutafi.

Tace Allah ya kyauta, ita bata iya kwadayi ba, haka suka tafi suka barta. Sosai su Khairat sukaji dadin zuwan Fatima, Inne ma taji dadin zuwansu, sede Malan be shiga ba ajesu kawai yayi yatafi.


Inne da Suwaiba kamar sun saba haka sukayita fira, kuma sam Suwaiba ba tayima Inne maganar Mama ba, seda taci abinci sannan tayi mata sallama dan zataje gidan Yayanta daga can Malan ze dauketa su tafi, musayar number sukayi Inne tana fadin inde kin haihu ki fada mani, Suwaiba tace insha Allah. Haka Inne tabata turaruka da sabulai kuma tasa direba ya kaita inda zataje.


Ana sauran kwana biyu su koma Makaranta Fatima ta dawo, sosai Suwaiba taji dadin dawowarta su duka yan gidan suka maidota hada Inne dan itace ma ta tukosu. Bangaren Suwaiba kawai suka shiga, duk abinda sukeyi Mama tana jinsu.

Bakin ciki duk yagama cikata, wato ita zasu hade ma kai, Farida kuwa ba ta gidan tana can shagon saurayinta. Ana haka sega Zulai itama tazo, sosai Suwaiba tayi farin cikin zuwanta. Bayan sun gaisa dasu Inne Zulai tashiga daki.

Haka Inne tace zata tafi dan zasu biya gida daga can zasu wuce. Suwaiba ta bama su Amatu da Khairat kudi da kyar suka amsa ta hada masu da biscuit, sosai Inne taji dadin abinda Suwaiba tayi masu.

Haka suka fita hada Fatima suka nufi gidan Maman Saddik, Amira da gudu tazo ta rungume Fatima suna murna, haka suka gaisa da Maman Saddik Inne tayi mata godiya akan abubuwan da takema Fatima da Faisal.


Mama tace haba ai babu komai, Amira tana nan kullum setayi rigimar rashin Yayanta Faisal, Inne tace wannan soyayya tasu tana nan, Mama tace wallahi kuwa, ai abun ma se karuwa yakeyi, dan har yanzu Amira takasa manta Faisal.

Inne tace Allah ya nuna mana lokacin da zamusha biki, Mama tace kema kin dauki wannan maganar dagaske? Inne tace haba Maman Saddik, ai insha Allah Faisal seya auri Amira. Mama tace to Allah yasa muna da rabon gani, Inne tace amin.

Sabulan data kawo masu ta bata kuma ta bama su Amira kudi, sosai Maman Saddik tayi mata godiya suka fita, gidan Salamatu sukaje, acan ma sun sha fira daga can taje gidan Momyn Teemah,bayan sun gama gaiswa ta bata tsarabarta haka tayi masu sallama ta tafi.

Fatima hada kukanta, itama Innen seda tayi kuka su Khairat da Amatu sukace abarsu wajen Aunty Fatima, Inne tace Mama zata rika dukanku, sukace sude abarsu, da kyar Inne tayi masu wayau suka tafi.


Mama kuwa jin maganar Zulai yasa ta tashi dama tana jiran irin wannan rana, haka taci dammara tashiga falon, tana zuwa ta rufeta da ruwan masifa tana fadin shegiya maciya amana. Tashi Zulai tayi tace ke Hauwa.

Ba fa tsoronki nakeji ba, duk irin abinda kike ma Suwaiba ina sane, itama kuma bawai toronki takeji ba kwai tana baki girmanki ne, kuma tafiki ilimi, ai matar data isa itace take zama agidan mijinta ba tare da ta bari wata tashigo mata gida ta kwace mata miji ba.

Idan ana maganar maci amana har zakisa baki? Keda aka baki amanar yara kika kasa rikewa kikaso ki lalata rayuwarsu, se gashi da yake basuda alhakin ki yaranki ne suka lalace, Fahad yana can saboda shaye shaye an kaishi asibitin mahaukata.

Ita kuma Farida tana bin maza, ai  kukan ki yana gaba, duk ranar data dauko maki abun kunya aranar zaki gane kuskurenki, banza kazama, wadda batasan yanda ake kissar zama da miji ba.

Kin dauka irin kissar da kikeyi itace kissa, bakisan hauka kikeyi ba, kizo ki koyi kissa awajen Suwaiba, domin ke taki ta ganin ido ce, ita ko ba tayin abun da wani ze gani.

Kuma kome kakeyi matukar  dan Allah kake yinshi bazaka taba tabewa ba. Hannu Mama tasa ta wanke Zulai da mari, hannu Zulai tasa ta cakumo Mama suka fito tsakar gida dan kada ayima Suwaiba barna.

Suwaiba kuwa hankalinta yatashi se hakuri take bama Zulai, kada ace tazo har gidan Mama tayi fada da ita, amma sam Zulai bata saurareta ba, haka suka fara fada da Mama, sosai Zulai ta na kada ma Mama duka.

Har seda ta zubar mata da hakora biyu na gaba, ganin fadan nasu bana karewa bane Suwaiba takira Malan, cikin sauri yazo, da kyar ya rabasu, Mama taji jiki sosai dama so take arabasu.

Dakinta Malan ya kaita ya kulle, Zulai kuwa bandaki tashiga ta wanke jikinta ta dawo falo ta zauna tana huci. Malan yace haba Zulai, da girmanki zaki biyema Hauwa? Zulai tace ai ba nice na jata fada ba.

A salima har inda nake tazo, nice ma najata muka fito waje dan kada ayima Suwaiba barna, kuma itace tafara mari na. Malan yace kiyi hakuri dan Allah, haka Hauwa take, bansan lokacin da zatayi hankali ba.

Seda Zulai taci abinci rana sannan tace zata tafi, Suwaiba tace ba kwana zakiyi ba? Zulai tace idan na kwana ai se ayi danyen aiki, kin sande bazan kyaleta ba matukar takara jana, gara intafi shine zefi.

Kema kidena kyaleta, shurun da kike mata yasa take dauka kina tsoronta ne. Murmushi Suwaiba tayi tace har abada Yaya idan kayi hakuri baka taba tabewa, kuma akoda yaushe me hakuri shine yake da riba.


Ni nasan wata rana komai ze zama tarihi, nide bana zuwa bangarenta, kuma ita bata zuwa, sede idan masifarta ta ciyota, kuma ni bana zaman gaba da ita, inde muka hadu ina gaisheta, amma fa bata isa naje har dakinta nayi mata magana ba.

Zulai tace to ai shikenan, Allah ya kyauta, ke kuma Allah ya saukeki lafiya, Suwaiba tace amin, haka Zulai ta tafi. Malan kuwa daukar Mama yayi ya kaita chemist aka bata magunguna, kafin su dawo bakinta ya kumbure. Da Malan ya kalle ta se yasa dariya, sosai abun ya kular da Mama, gashi bata iya magana dan zafi takeji.


A ranar Farida se wajen magriba ta dawo gida, kuma surayinta yasamu damar rabata da budurcinta, sosai tayi kuka, amma daya lallasheta ya bata kudi masu yawa kuma yace idan ta dawo ze siya mata waya haka tayi shiru.

Chemist yaje ya siyo mata maganin ciwon jiki, Farida tace amma idan nayi ciki fa? Dariya yayi yace aike yarinyace baki isa daukar ciki ba, kuma kinga kina gama makaranta auren mu zamuyi. Farida tace ya akayi naga kayan shagonka duk babu? Yace mata karewa sukayi se gobe zeje yasiyo wasu.

Da kyar ya samu ya lallabata ta tafi, da kyar take tafiya, ita tsoronta ma kada Mama ta gane, shiko jira yake ta tafi dan aranar ya hada kayanshi yatafi Lagos, dama dalilin da yasa ya saida kayan shagon shi kenan saboda abokinshi yace ya shirya su tafi Lagos.


Wannan dalilin ne yasha alwashin seya fanshe kudin shi ayau kafin yatafi. Farida tana zuwa gida taci sa'a Mama tana baccin wahala, haka tashige kitchen ta dora ruwan zafi taje tayi wanka taci abinci tasha magani ta kwanta.


Washe gari ma bata bari tayi wata tafiya sosai ba, kwanciya tayi tace bata da lafiya, da kyar Mama taje  ta dora masu girki, data gama ta kai mata dakinta, Farida tace kitafi idan na tashi bacci zanci, haka ta fita, tana fita ta tashi taci takara shan magani ta kwanta, dama sallah bata dameta ba.

Washe gari haka suka shirya kayansu suka koma makaranta, har Mama tana tambayar Farida me yasameta take dangyashi? Tace kafarta take ciwo bigewa tayi, haka suka tafi makaranta kasancewar third term suka koma.


Inda su Faisal  sunyi nisa da fara jarabawarsu, dan tuni sunyi Jamb kuma sunci maki me yawa, abokanshi suna ta cewa waje zasuje suyi karatu, hada Saleem, Faisal yace shi a Katsina zeyi karatu, Saleem yace meyasa bazaka je waje ba bayan kasan daukar nauyin mu za'ayi? Faisal yace idan suka dauki nayin mu muka tafi karatu waje.


Idan muka lalace kana tunani zasu dauki nauyin mu ne? Sede su bar iyayen mu da cizon yatsa, kuma shikenan munyi asarar rayuwarmu, idan aka koro mu kaga sede mudawo gida abanza, mutane nawa ne suke zuwa waje karatun amma basa yin karatun sede harkar banza? Nide nafiso inzauna gida inyi karatu na.

Saleem yace ai ko a ina ne mutum se yaso ze iya lalacewa, ko agidan ne ma. Faisal yace bazaka taba hada kasar turawa da gida ba, domin idan mutum ya tafi can jiyake kamar shikadai ne aduniyar, duk abinda zeyi yasan babu me ganinshi, amma agida fa? Dole yaji kunyar idon wasu.

Kuma duk yanda mutum ya kai ga kamewa, turawa shegun mutane ne, kaide idan zaka tafi kaje, amma ni ina gida wallahi. Saleem yace gaskiya, maganar akwai abun dubawa, kuma nima ina tare da kai, Allah yabamu ikon cinjarabawar, Faisal yace amin.


Farouk kuwa ya gama PRE N.C.E dinshi sede be dawo gida ba, kasancewar akwai wanda suka saba dashi a katsina shima yana dinkin hula kuma a shago yake kwana hakan yasa Farouk yace ze zauna a wajenshi, yace babu damuwa yazo har seya kara koya mashi dinkin hular.

Dan yanzu Farouk sosai ya kware a dinkin hula, hada mayan mutane yake kai mawa, kuma Alhaji ya hadashi da wasu, duk yanda Inne taso yarika yawan zuwa gidanta baya zuwa, dan abinda ya dauka idan kana zuwa da marmari yafi, shiyasa bece zeje gidanta yazauna ba.

Sosai yake samun kudi, sede baya kashe haka , tarawa yakeyi danshi beda burin daya wuce yasamu ko karamin gida ne kafin yagama karatu yasiya dan Mani ta fitar mashi arai.


***** *****

A yau ne su Malan suka dauko Fahad, ba laifi jikinshi akwai sauki, dan yanzu baya shan komai, kuma likita yace su sa ido akanshi, idan ba haka ba ze iya komawa shaye shayenshi, shiyasa yaso abarshi yasamu ko shekara daya ne kafin yakoma gida. Amma Mama ta rufe ido tana masifa tana fadin saboda ba Danka bane shiyasa zakace haka.

Ganin irin rashin mutuncin da Mama takema likita yasa ya sallami Fahad, godiya Malan yayi mashi kuma yabashi hakuri, haka suka tafi Mama se fada take amota.


Tun da suka koma ta maidashi dakinta komai ita ke mashi, sede sam baya magana sosai, wanka ma seta ce yatashi yayi, haka ze zauna yayi shiru, kamar karamin yaro, Malan ma yana kula dashi, kuma ya hanata tabarshi yafita koda masallaci ne, yace yarika sallar agida.


Gaba daya Mama ta rame saboda masifa da damuwa, tayi baki kamar ba ita ba, kawarta Maman Sultan ma yanzu bata zuwa gidanta, dan da mijinta yasamu labarin irin abubuwan da Mama takeyi yacema matarshi idan tana son zaman gidanshi to bayason yakara ganinta da Mama.

Tun daga lokacin ta dena kulata, ko Mama tazo gidanta tana jinta take kyaleta, daga karshe ma tace mijinta ya hana ta zo mashi gida. Haka Mama ta yita masifa tana fadin ai seta fadama wanda beda gidan, munafukar banza, haka sukayi kaca kaca ta tafi.


Shiyasa yanzu bata da kawar shawara, koda yaushe tana gida, gaba daya zaman unguwar ya fitar mata arai, kullum tana gida, shiyasa damuwa ta hade mata, ga rashin lafiyar Fahad.


Seda cikin Suwaiba yafito sannan Mama tasan tana da ciki, aranar jitayi kamar zata mutu, habaici take ta mata tana fadin ki rasa da wanda zaki haihu seda tsoho, wama yasani ko ba cikinshi ba ne? Dan kowa yasan Malan ya dade rabon daya haihu, se gashi kinzo zaki kawo mana kazanta acikin gida.

Sosai ran Suwaiba ya baci, tashi tayi ta zage Mama da turanci daga karshe tace idan tana ganin tsoronta takeji tazo su buga anan zata gane kurenta. Juyawa Mama tayi tana fadin in gaskiya ne abun kiyi da hausa mana馃ぃ, amma kin canza harshe kina zagina ashe tsoro kikeji.

Suwaiba tace kidawo muyi yaran da jiki ai shi babu yaran da bayaji, Mama tace saboda in zubar maki da ciki ki jamani dauri kusamu damar sakewa keda mijinki, ai ni yanzu nabar fada na bar maku ku yara. Suwaiba tace da aka maidaki tsohuwar karfi da yaji ba.

Ai wallahi da kinzo sena karasa zubar da sauran hakoran, Mama de tafiya tayi ta kyaleta, dan tasan ba zataci ribar fada da ita ba, dan Suwaiba akwai girma.

Tun daga ranar Suwaiba ta samu saukin Mama, sede habaici da gori haka zatayi ta wake wake acikin gida tana habaici, ita ko Suwaiba bata biye mata, dama da safe tana wajen aiki sede idan ta dawo.

Duk wanda yazo wucewa kusa da gidansu se yajiyo muryar Mama, tana waka ko tana habaici, wasu ma cewa suke kode tana da tabin hankali. Malan kuwa yanzu yadena biye mata yaga abun nata bana hankali bane.

***** *****

Bayan komawar su Fatima makaranta da sati 3 aka fara azumi, haka Farida ta fara rashin lafiya, zazzabi kasala da yawan amai, duk yanda kawarta taso suje clinic kin zuwa tayi, haka tayi ta fama da ciwo duk ta rame se tayi wani irin haske.

Lokacin da akayi sati 3 ana azumi ciwonta yayi tsanani, senior din dakinsu ce ta sa aka yi mata wanka suka kaita clinic, duk tambayoyin da nurse din tayi mata Farida ta bata amsa dede, jinjina kai tayi tace gaskiya se an kaita asibitin cikin gari domin za'ayi mata awo.

Rubutu tayi ta bama senior din tace ta kaima principal, bayan taje Principal tace takira hajiya Lami tazo sutafi tare, dan itace shugabar ma aikatan makarantar masu kwana da yara.


Suna zuwa ganeral hopital awon farko akace tana da ciki na sati 5, sosai matar ta girgiza, duk da itama tayi zargin haka, haka suka dawo makaranta, Farida batasan abinda ake ba. Principal dataji sosai hankalinta yatashi, tsoro take kada ace acikin Malamanta ne ko kuma cikin student.

Haka suka tasa Farida akan ta fada masu dawa ta taba lalata? Cikin kuka ta basu labarin saurayinta na gida, ajiyar zuciya Principal tayi jin ba daka wadan da take zargi bane. Sosai tayi mata fada, kuma tace korarta za'ayi dama dokar makarantar ce.

Babu bata lokaci tasa Hajiya Lami ta rakata ta hado kayanta, nan take Pricipal tasa aka kira meeting yara duk suna class. A meeting din ne malamin daya taba kamasu ya fadama Principal shima ya taba yimasu fada.

Principal tace dama can yarinyar ba tajin magana, nima nasanta, kuma dole zamu koreta dan hakan yazamo darasi ga sauran yara, aje akada mani assembly.

Kowa da abun da yake fada, haka aka dora Farida saman step se kuka takeyi tana dukar da kai. Hankalin Fatima seda yatashi ganin Farida asaman step. Nan principal ta masu bayanin abinda tayi, ai gaba daya wajen ya cika da surutu.

Kuka sosai Fatima takeyi, anan principal tace an koreta daga makarantar kuma Hajiya Lami ce zata kaita har gida. Kowa da abinda yake fada, Fatima kuwa kuka kawai takeyi, haka Lubna ta jata suka tafi class.

Nan Principal ta bada school bus aka saka kayan Farida suka tafi, se kuka takeyi.


Kwance  Malan yake a falonshi dan Suwaiba keda girki kuma tana wajen aiki shi kuma baya fita da wuri saboda azumi hakan yasa ya kunna tafsir yanaji.

Warin sigari ya faraji daga bayan falonshi, tashi zaune yayi yana fadin waye kuma ya keshan sigari ana azumi, kode hayakin icce ne? Har ya koma ya kwanta kuma yaji abun yana karuwa, tashi yayi ya nufi dakin Mama ya tambayeta kota kunna wani abu ne.

A falo ya sameta, tambayarta yayi kota kunna wani abu, tace ita babu abinda ta kunna, yace ba kijin warin sigari? Mama tace to yanzu agidan nan wakeshan sigari, kuma yanzu ma da ake azumi ina zaka samu meshanta, kila de wani gida ne aka kunna icce.

Malan yace ina Fahad fa? Mama tace na aikeshi yasiyo mun kati tun dazu ma nake jiranshi kaga bedawo ba. Cike da tashin hankali Malan yace tashi muje bayan, Mama tace me kuma zamuyi abaya? Fita yayi be tsaya sauraronta ba, tashi tayi tabi bayanshi.

Fahad suka iske yana zaune wajen dakinsu yana ta zukar sigarinshi yana lumshe ido, hannu Mama tasa akirji tana fadin nashiga 3, me zan gani haka Fahad? Da sauri ya wurgar da ita ya mike tsaye.

Malan kuwa kasa magana yayi, idanuwanshi ne kawai sukayi ja, juyawa yayi bece komai ba. Kamo hannunshi Mama tayi suka nufi cikin gida. Malan yana zagayawa ya iske Farida da wata mata suna ta sallama.

Seda gabanshi yafadi yasande saura kwana 3 ayi masu hutu, me yamaido ta gida? Da kyar ya amsa masu sallamar, Mama da suka karaso yanzu tace Farida lafiya ko har anyi hutun? Hajiya Lami tace kuyi hakuri mushiga daga ciki batada lafiya ne.

Ajiyar zuciya Malan yasaki suka shiga falon Mama, Fahad yana daga gefe se zare ido yakeyi, Farida kuwa kuka kawai takeyi, nan Hajiya Lami tayi masu bayanin abinda yake faruwa kuma ta mika ma Malan takardar korarta da ta awon da akayi mata.

Tashi tayi tana fadin Allah ya kyauta gaba nizan koma, fita tayi tana tausaya masu. Mama yanda take a zaune haka ta bingire asume, Malan kuwa ba zaka iya gane halin da yake ciki ba, dan ko motsi bayayi, sede idanuwanshi abude suke sun kara kadawa sunyi ja. Farida ce ta matsa kusa da Mama tana kuka tana jijjigata.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263.
adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *