Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Tuesday, 22 January 2019

BURIN HAFEEZ COMPLETE HAUSA NOVELS

adsense here
BURIN HAFEEZ COMPLETE HAUSA NOVELS
[11:47AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
           
               By

©MUNAY

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

Bismillahir-Rahamanir-Raheem.

Episode 1⃣


Tasss!! Kakeji ya wanketa da kyakyawan mari, cikin hargagi da tsananin masifa yanuna ta da d'an yatsa yace "ke dabbar inace? Kina gani lokacin da nake 'ko'karin kauce miki amma saboda tsabar dabbanci da 'kauyanci irin naki shine kike 'ko'karin shigemin, salon naje nabugeki kijawomin zuwa asibiti"

A gigice ta ri'ke 'kuncinta wanda yakemata tsananin rad'ad'i da azaban ciwo, batareda ta kallesa ba, cikin sassanyar muryanta tace "kayi ha'kuri, nima ba a son raina hakan yafaru ba, kaina ke tsananin min ciwo, hajijiya ce ke d'awaniya dani bansan lkcn da na tunkari motanka ba, kayi ha'kuri"

Tana fad'in haka tudu'ka tad'auki bokatin awaranta wanda yazube a 'kasa, ta ratsa ta gefensa tawuce, sakin baki yayi yana binta da kallo, cikin zafin rai yace "ke!!!! Zonan"

Batare da ta kalli inda yake ba tajuyo jiki asanyaye, qarasowa tayi gamida duqe kai cikin sassanyar muryanta tace gani, wani irin iska mai d'aci Hafeez yafurzar gamida xaro manya-manyan idanunsa fuska a hargitse  yace ke waye ubanki agareni nan? Da har adalilina xaki xubar da kayan tallanki amma kikasa budan baki kice nabiyaki, damekike taqama stupid grl?
Wasu irin xafafan hawaye ne ke kwaranya akan kod'ad'iyar fuskarta, cikin nuna rashin jindadin kalamansa tace" kai kuwa bawan Allah kai wanne irin mutun ne? Naga tunfarko nabaka hakuri sannan kayan sana'ata da suka xube bana buk'atar kabiyani" meka dauki kanka?

Toh bari kaji niba irin yan'matan nan bane masu son cece kuce akan titi ba, sannan kana mgnr cewa waye ubana' umhm ubana shi ba kowa bane, kmr yadda kasani baxai iyaja da mnya kmr Ku ba. Tana fadin haka ta gyara jemammen silifas dinta wnda yake qoqarin fita a qafarta tacusa qafarta ciki tafara tafiya cike da sanyin jiki' cikin xuciyarta kuwa wani irin baqinciki da qunci gamida d'umbin damuwa ke d'awainiya da ita.

Abangaran Hafeex kuwa ko k'wak'waran motsi yakasayi sbd tsananin mamaki da ya kamashi kasancewar tunda yake ganin yan mata kala-kala masu aji da marasa ajin babu wacce ya tab'a ciwa mutunci ta maida mishi da marta sai wannan jamammiyar talakar yarinyar" cikin tsananin fushi Hafeez ya fara takawa da nufin isa gurin wannan yarinyar, ae kuwa da sauri wata kyakyawar matashiyar yarinya tafito acikin motar da sauri gamida riqo hannunsa tace "plss Yaya Hafeex don't do dat 4god sake, tundaxu ina kallonku fa kasanar da ita laifinta Kuma wannan baiwar Allahn ta amsa laifinta har tabaka hkri" plss yaya kaxo mutafi gda ni ynwa nakeji gabadaya am vry tied,
Fuskan nan ta Hafeez kuwa kokad'an  babu fara'a yace look Balkisu pls ki k'yaleni inje inkoyama yarinyan nan tarbiyya,sbd na lura kokad'an bata da manners, cike da shagwab'a Balkisu tafara bubbuga qafafunta kmr xatayi kuka "plsss yaya nidai ka kyaleta kaxo mutafi gda," Hafeez yasake waiwayan wannan yarinya amma tuni tab'acewa ganinsa..wata uwar kwafa yayi gamida Jan tsaki ba haka yaso ba dan haka bashida wani xab'i dayawuce yashiga mota sutafi.cikin qasan xuciyarsa kuwa wani irin haushine yacikasa sbd gabadaya haushin knsa ma yakeji da bai qara marinta ba.

Al'asfar Restaurant yawuce da ita kai tsaye, sbd Hafeez Sam bai qaunar ganin Balkisu na complain akan yunwa, abinci kala-kala masu kyau da tsada yasa aka kawo mata. Taci sosai"shikuwa Hafeez sbd b'acin rai koh abinci yakasaci, babu yadda Balkisu batayi akan Yayan nata yaci abinci ba amma Sam yaqi., hakanan Balkisu tadaure itama tadanci abincin ba wai don ranta yaso ba..

Jiki a sa6ule suka nufi gda, shigarsu keda wuya Hafeez yanufi sashensa cike da 6acin rai' abangaran balkisu kuwa nadama ne gamida Danasani fal acikin xuciyarta.domin kuwa ita kanta tasancewa itace silar wannan fushin nasa
Sbd tahanashi aikata abinda take ganin shine dai-dai,

Acikin wannan dare kuwa daga balkisu har Hafeez babu Wanda yaruntsa, sbd kowa da tunanin da yakeyi cikin zuciyarsa. Abangaran Balkisu kuwa talashi takobi gamida alqawarin sai tanemo wannan yarinyar a dukk indatake, sbd tabama yayanta damar cikar Burinsa.

Da wannan tunanin nannauyan bacci yyi awon gaba da Balkisu.
 ®NWA
[11:47AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode2⃣

K'aran alarm din k'aramin agogon dake cikin d'akin ne yafara amsa kuwwa, mai nuna alamar lkci yayi' Balkisu nadaga cikin bargo tamiqo hannunta dan tsaida wannan k'aran kasancewar agogon na gefen gadonta.hannu tasa ta danna wani abu sannan k'aran yatsaya, a hnkli ta zuro qafafunta daga kangadon datake kwance yayinda idanuwanta ke lumshe, tanufi toilet, tana shiga ciki tayi brush sannan tadaura alwala, bayan tafito tafara gabatar da sallahr asubanta kasancewar lkci yayi
Balkisu na idar da sallah kamar wadda aka tsikara ta tashi  da sauri tafada toilet tayi wanka, dasauri-dasauri ta shirya tsaf cikin atamfarta mai ratsin orange da lemon green, Balkisu dukk da bawata doguwar kwaliiya tayiba amma kayan sunmatuqar amsarta, gyalenta tadauko Wanda yyi matchn da kalar kayanta tayafashi gamida daukar handbag dinta tanufi hnyar falo.

Daniel! Daniel!! Whr ar u? Dasauri Wanda Balkisu takira da Daniel yafito daga cikin kitchn sanye da kayanshi na kuku' dasauri ya iso gaban Balkisu cike da rissinawa Daniel yace yes madam gani, Balkisu tadubi Daniel sannan tasake duban dining area kafin tace wani abu tuni Daniel yafuskanci abinda takeson tambaya" dasauri yace am very swry yau nadan makarane bnsamu na kammala brkfst din da wuri ba. Balkisu tadanyi jimm kmr baxatace komiba chan dai tanumfasa tace "it okey ynxu dame dame ka kammala"? Daniel yace madam sos din kwai ne sai ruwan xafi na tea ynxu ne nakeson daura ferfesun, Balkisu tace okay jeka kawomin tea da sos din its OK.

Dasauri Daniel yashiga kitchn yaxo gaban Balkisu yacika umarninta nan da nan yahada mata breakfast, balkisu na kammalawa ta dauki handbag dinta gamida kallon agogon dake daure  atsintsiyar hannunta 7:30am tagani Dan haka dasauri takira Daniel tabashi umarnin yayi sauri ya kammala brkfst din sbd ynxu Yaya Hafeez xai fito yin breakfst...cike da bin umarnin ta yace okay.

Parkn space tanufa kai tsaye tadauki wata jar mota k'irar jeep, dasauri mai gadi yabude mata gate ta fice a gdan" Balkisu bata nufi ko inaba sai bolori anguwar da suka hadu da wannan yarinyar, tanashiga cikin anguwar tafara tunanin ta ina xataga wannan yarinyar   tayaya xata fara nemanta. Nan take dibara yafado mata, gurin mai sai da biredi da shayi dake cikin unguwar tanufa Wanda dukk abunda yafaru jiya a gabansa ne Dan haka tayi tunanin xuwa gurinsa koh Allah xaisa yasanta.
Daga gefen hanya kadan tayi parking motarta bayan takulle sannan tanufi garesa.

Balkisu na isa gurin mai wannan shayin  yaganeta, cike da rissinawa Balkisu tagaidashi kasancewarsa dattijon mutum, Cikin sanyin mgn Balkisu tace baba Dan Allah kokasan wannan yarnyar tajiya da wannan Abu yafaru jiya, maishayi yyi shiru cikin ransa yace"anya kuwa yadace nasanar da ita gdansu domin kuwa bnsan wanne irin tashin hnkli xataje ma wannan baiwar Allah dashi ba?" Mgnr Balkisu ce takatse mishi dogon tunanin da yatafi, baba karka damu inason ganin yarinyar ne sbd inbata hkri akan abinda yafaru jiya, mai shayi yyi murmushi yace auu toh ae shikenan, nan mai shayi yyi mata kwatance gdnsu wannan yarinyar "yace daxarar kinshiga cikin kwanar kikace anunamiki gdan Yaganaa mai awara toh babu wnda baisaniba, Balkisu tayi mishi godia tanufi inda ta ajiye motarta dasauri tanufi cikin kwanar da wannan mai shayi yyi mata kwatance, Balkisu sai murmushin mugunta takeyi domin kuwa
ayau tayi alqawarin saitadauki wannan yarinyar takaita gurin yayanta yacika burinsa koh xaisauqo daga fushin da yakeyi.

Balkisu nashiga cikin kwanar tanemugun parkn, sannan tafito daga cikin motar gamida kwalama wata yarinya kira keee!!"xo yarinyar dake qoqarin wucewa tagaban Balkisu tatsaya indatake batareda taqaraso wajen maikiranta ba, ganin yarinyar batada niyyar qarasowa wajenta yasa balkisu tafahimci akwai alamar tsoro atattare da yarinyar, murmushi kawai tayi gamida jehoma yarinyar tambaya tace kokinsan gdan Yagana mai awara?? Yarinyar ta gyada kai gamida nunamata gdan da danyatsa tace gashi chan gdan maibishiyar mangwaron chan.

Balkisu tagyada kai gamida murmushi alamar tagane, godiya tayima yarinyar dai dai lkcin tasa key tarufe motarta sannan tanufi gdan cike da Burin son ganin wannan yarinyar
. Balkisu nashiga gdan tafara jiyo ihun mutun alamar ana dukanshi, Balkisu batasan lokacin dataqarasa cikin gdan da saurinta ba gamida riqe hannun wannan mata dake dukan wannan yarinyar. Dasauri yagana tadannawa balkisu wata uwar harara gamida tambayarta kekuma fa?? Waye ke daxakishigo min gda babu sallama bare nema ixinina, Balkisu tayi murmushi gamida cewa kiyi hkri nasan bankyauta ba.Amma wannan dukan dakikeyima wannan yarinyar ne yad'agamin hnkli banmasan lkcin dana shigoba, Dan Allah baiwar Allah kiyi hkri kimata afuwa kidena dukanta haka.

Dasauri yarinyar da ake duka tamiqe tsaye Dan ganin wacece tashigo cikin gdansu Dan cetonta daga hannun yagana domin kuwa iya tsawon rayuwarta idan Yagana nadukanta qa'idane babu wani mutum da ya Isa yaxo yabata hkri ko yaceceta daga dukk wata axaba daxa'a gwada mata, Dan haka tamiqe daga duqen datake don ganewa idanunta. D'agowan daxatayi kuwa idanunta sukayi toxali da wannan yarinyar wanda fad'a yahad'ata da yayanta. nan da nan jikin wannan yarinyar ya hau rawa bakinta narawar sanyi tadubi Balkisu gamida had'a hannayenta alamar Neman gafara tace Dan Allah baiwar Allah kiyi hkri inba haka ba kuma kawai kikaini police station domin kuwa nasan abnda yakawoki kenan.

Abin yamatuqar bama balkisu dariya gamida tausayin yarinyar, a hnkli Balkisu taja hannunta suka nufi waje, yayinda jikin wannan yarinyar yacigaba da kad'awa alamar sanyi domin kuwa gabadaya illahirin jikinta a jik'e yake jagafff!.
®NWA
[11:47AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode3⃣


Batare da Balkisu tace uffan ba,haka taja hannun wannan yarinyar har inda tayi parkin din motarta,suna isa Balkisu tadubeta cike da kulawa gamida tausayawa gareta. Cikin nutsuwaa Balkisu tace "Baiwar Allah inasoki kwntar da hnkli ki abinda kike tunani bashi naxo aikatawa a gareki ba sbd kedin baki chan-chanci haka ba"inaso kiyishiru, kidaina kuka,kisanar dani ya sunananki"?Wata sassanyar ajiyar xuciya tayi sannan tashare hawayenta tadubi Balkisu tace,"sunana AMEENATU amma anfi kirana da Meena" Balkisu tayi murmushi, mai k'ayatarwa cikin kulawa ta dafa kafadan Meena tace"gashi sunanki mai dadi da ma'ana, ke kuwa Meena mekikayiwa mahaifiyarki haka har takemiki irin wannan mummunan dukan"???

Wasu zafafan hawaye ne suke zubo mata, sbd tambayar da Balkisu tayimata baqaramin tab'amata zuciya yayi ba.Meena tasaddakanta qasa gamida hadiye wani kakkauran yawu tace Dan Allah baiwar Allah kigafarceni amma baxan iya sanar dake lbrina ba sbd sanin lbri na babu abnda xaiqareki dashi, sai dai abinda kika tambayeni baxanqi baki amsa ba sbd ko ba komai kinceceni a lkcin da bantsammaci hakan ba,
Wani dogon numfashi Meena taja gami da qara tattare xaninta Wanda yake ajiqe, tadubi Balkisu tace wannan abun yafarune sbd laifin danayimata wanda cikin tsautsayi awaranta yaxube wato ajiye da abin nan yafaru toh shine tace lallai sai nabiyata kudinta nikuma gashi banda kudin biyanta shinefa yau da safee Aleesha tayi fitsarin kwance tadaura laifin akaina alhalin tasan cewa baninayi ba shine tad'ebo ruwa masu sanyin gaske takwaramin ajikina dukk dai hakan baimata bashine taqara da dukana kuma nasan tayi hakane dan tafanshi kudinta. Meena nafadin haka tadubi Balkisu da murmushi maicike da baqinciki da qunci,"tace nayi mamakin ganinki cikin gdanmu domin kuwa ni bantaba ganin wani mutum yaxo da nufin ceto naba sai ke kuma naji ddi ngd" Balkisu mamaki ne yagama Lullub'eta domin kuwa acikin lbrin Meena tabbas akwai alamar tambaya aciki? Dan haka Balkisu batayi qasa a gwiwaba wurin sake tambayar Meena, a hnkli Balkisu tace amma dai Meena Yagana ba itace aenahin mahaifiyarki ba koh?

Dasauri Meena tace a'a itace mahaifiyata banda wata mahaifiya da ta wuceta, Balkisu ta jinjina kai cikin rashin gamsuwa da mgnr Meena tace amma Meena ga dukkan alamu sun nuna.....balkisu bata qarasa abinda takeson fadiba Meena tayi saurin zame hannunta daga riqon da Balkisu tayi mata,dasauri tafara barin wajen gamida Yiwa Balkisu godiya tace Baiwar Allah ngde da taimakonki gareni dan Allah kimin afuwa bayan abinda nasanar dake ynxu bnsan komai ba.kiyi hkri nixankoma gda ayyuka na nan najirana, Meena na nafadin haka tasa kai tashige gda..

Balkisu kam shiru tayi cike da yin dogon nazari agame da rayuwar Meena domin daga dukkan alamu yarinyar na fuskantar k'alubalin rayuwa',cikin zuciyar Balkisu kuwa taqudurta axuciyarta tabbas sai ta taimakawa Meena domin kuwa yarinyar na buqatar taimako, Dan haka yaxama dole insan komai agameda rayuwarki.

Balkisu nafadin haka tashige motarta, gda kawai tanufa kai tsaye domin kuwa xuwa ynxu kwakwalwarta tagama daukan xafi, dafarko tadauka abin xaixo mata dasauqi amma daga bisani Balkisu taga sa6anin haka,
Domin kuwa har yanxu dan'uwan nata bai sauqo daga dogon fushin daya dauka ba.

Tagane hakan ne sbd talura ko fitowa baiyi daga cikin dakinsaba, dan haka dasauri ta ajiye handbag dinta tanufi dining area tadauki plate tahad'a mishi breakfast maisauqinci wnda tasan shiyafi so, dakinsa tanufa domin kuwa tasan baici komai ba. Sanin halinsane yasa ynxu taquduri anniyar qin biyemasa gwnda tabishi da lallashi kasancewar tasan baida ishashiyar lfy...
Kai tsaye ta nufi dakinsa ta kwankwasa gamida tura qofar' Balkisu nashiga cikin dakin tasaki plate din abincin dake hannunta da gudu taqarasa cikin dakin tanafadin inalillahi wa'inna ilaihiraji'un....®NWA
[11:47AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode4⃣

Cikin tsananin firgici Balkisu taqarasa cikin dakin, hnklinta gabadaya ya tashe ganin Hafeez kwance a qasa tamkar gawa. Dasauri taqarasa gareshi dakyar tasamu ta gyara mishi kwnciyarsa kasancewar bisa hannayensa yake a rigingine, Balkisu kam gabadaya tafita hayyacinta sbd tsananin rud'ewa sai faman sharar kuka take tanafadin"yayana plzz katashi dan Allah katashi kada kamutu kabarni kasancewa bani da uwa bani da uba kaine uwata kaine Ubana kaine dangina" plss Yayana katashi, nan Balkisu tashiga jijjigasa tanata faman sambatu' chan kuma ta tashi tafice waje da saurinta falo tanufa tadauki wayarta hannunta na makarkata dakyar tasamu tasaita kanta tak'ira family doctor dinsu, doctor muh'd najin abinda Balkisu tafadi mishi yyi saurin katse wayar gami da cewa gani nan tafe.

Dasauri Balkisu ta wurgar da wayan takoma dakinsa da gudu, ruwa tad'ibo masu dan sanyi tafara shafawa Hafeez a fuskanshi, Balkisu na cikin wannan halin tajiyo sallaman Dr muhd dasauri taqarasa gareshi tana nuna masa irin halin da yayan nata ke ciki.

Dr Muh'd ba tareda yace da Balkisu uffan yanufi kan Hafeez da saurinsa, yar qaramar jakar da yashigo da ita, ita yabude ya dauko abubuwan gwaje-gwajensa, Dr Muh'd yajima yana wasu yan gwaje gwajensa akan Hafeez Wanda daga bisani yadago kai yadubi Balkisu yace "pls Balkisu stop cryn sbd wannan kukan dakikeyi bashine zai basa Lpy ba hasalima sai dai yaqaramasa ciwon dake tattare dashi" domin kuwa a hali ynxu Hafeez baibuqatar kukanki, kulawarki kawai yake buqata,"ki kwantar da hklinki insha Allahu babu abinda xaisameshi" Dr Muh'd yaja dogon numfashi gamida cire gilashin dake sanye a fuskarshi yace amma Balkisu ya akayi kika bari hakan tafaru? Sbd nasha fada miki kidaina barin hafeez na dogon wasu tunanin wnda xasuke jefa xuciyarsa cikin mawuyacin hali, domin kuwa a Halin ynxu xuciyarsa na daf da bugawa dan Allah kiyi qoqarin bashi kulawa kamar yadda kika saba, Balkisu wadda kuka yaci qarfinta tadubi Dr Muh'd tace "Dr wlh nikaina wataran yaya Hafeez nafin qarfina akan irin wannan tunane tunanen nashi sbd ba tare muke bacci ba dakinsa daban dakina daban sbd haka wasu yan tunanin da Yaya Hafeez xaikeyinsu wlh banda masaniya"

Dr Muh'd yadauki jakarsa yarataya gamida xuba hannayensa cikin aljihunsa, yadubi Balkisu yace kuma fa hakane but dearis only one way inaga idan har munbi to tabbas Hafeez xai kasance cikin walwala da kuma samun ishashiyar kulawa.
Dasauri Balkisu tace Dr plss sanar dani.

cikin nutsuwa Dr Muh'd yabar dakin, yayin da Balkisu tarufa masa baya da saurinta.
Suna Isa cikin falo Dr Muh'd yadubi Balkisu yace"hanya dayace asamu ayiwa Hafeez Aure" dam! gaban Balkisu yabuga da qarfi, cikin tsaninin tashin hnkli ta xaro mnyan idanuwanta waje tace "Dr kamanta BURIN yaya Hafeez? Ni ina ganin wannan shawaran abune mai wuya.

Dr Muh'd ya danyi murmushin yaqe yace I thnk dix is d only way out! Balkisu tace tabbas hakane amma insha allahu xangwada sa'ata koh Allah zaisa adace.

Dr Muh'd yayi murmushi yace"any way nizan koma i'm in hurry" Balkisu tayi mishi godia sosai. Daga bisani takoma cikin dakin yayan nata don bashi cikakkiyar kulawa.

*************************
Daren ranan nan Balkisu bata samu ta runtsa ba, sbd irin tunanin da ya addabi zuciyarta a gameda rayuwarsu da irin k'alubalin da suka fuskanta cikin rayuwarsu.
Balkisu ganin cewa yawan tunanin babu abinda zai haifar mata sai damuwa da b'acin rai kawai  tayanke shawarar tashi tayi nafilfilu don nemawa yayan nata sauqi agurin ubangiji. Hakanan kuwa ta tashi tafada toilet tadauro alwala tafara gabatar da nafilfilunta. 'Balkisu da xarar ta idar da sallah haka xata tashi taje tadubo irin halin da yayanta ke ciki.har ynxu Hafeez baisamu ya farka daga nannayan baccin da yakeyi ba kasancewar alluran da akayi mishi don yasamu kwakwalwarsa gamida xuciyarsa ta huta.

Abangaran Balkisu kam Haka nan wannan dare ya xame mata tamkar gari baxai waye ba, Adua kawai takeyi har tadan samu bacci b'arawo yyi awon gaba da ita.

Kmr yadda Balkisu tasaba hakane yau ma alarm din da tasaita shine yafarkar da ita daga nannauyan baccinta, ae kuwa dasauri ta tashi tafada toilet tadauro alwala tafara sallahn asuba. tana idar wa ta tashi tanufi dakin Yayan nata dan ganin yanayin dayake ciki.
®NWA
[11:48AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode5⃣

Balkisu na fita kai tsaye tanufi d'akin yayan nata. A hnkli ta tura k'ofan gami da sallama, cikin nutsuwa tashiga cikin d'akin koh da shigarta bata ga kowa cikin d'akin ba. dan haka da sauri tak'arasa cikin d'akin, don tabbatarwa idanunta. Da shigarta ciki tajiyo motsin ruwa daga cikin toilet alamar akwai mutun aciki' Balkisu batasan lkci datayi wata sassanyar ajiyar xuciya ba. A hnkli taqarasa bed dinshi nan tahau gyara masa d'akinshi, cikin qanqanin lkci kuwa Balkisu ta gyara d'akin tsaf!.

Hafeez ne ya fito daga toilet, towel daure a kirjinshi da wani d'an k'aramin towel dinkuma yana tsane kansa.fuskan nan tashi tayi fayauu da ita kai dagani ba tambaya kasan yana jin jiki. A hnkli yake tafiya har ya xauna bisa gado bai lura cewa akwai mutum a cikin d'akin ba har sai da ya yaye qaramin towel din da ya yane kansa dashi. Balkisu yagani tsaye a gabansa tanayi masa murmushi.

Shima murmushin yayi mata Yace"yaushe kika shigo"? Balkisu tace ban dade da shigowa ba...sannan Balkisu tadan numfasa kadan tace"yayana ya jikin naka hope kaji sauqi? Hafeez yyi murmushi yace"am fyn Qanwata naji sauqi sosai ynxuma sallah zanyi" Balkisu taji dadi sosai har tabud'e baki xatayi mgn kome tatuna kuma sai tafasa, cikin murya mai nuna alaman tausayawa Balkisu tace"yaya kayi sallah ka kimtsa barin je indawo, kai kawai ya gyada mata,Da sauri ta fice a d'akin. Kai tsaye tanufi kitchn ita da kanta tahada masa brkfst kunun gyada ta hada masa da sos din kwai (wannan shine abinda Hafeez yafi qauna ya karya kummalo dashi) bayan tagama hadawa tajerasu bisa babban tray tanufi d'akinsa dashi.

Koh da shigarta ta tarar da yayan nata cikin shirinsa tsaf tamkar ba shine yakejin jiki ba, Balkisu kam tayi matuqar farinciki daganinsa haka, Dan haka da fara'arta taqarasa ciki gamida ajiye tray din a gabanshi. Hafeez dai sai kallonta yake tamkar wata baquwa,ita kuwa Balkisu sai qoqarin servn dinshi takeyi.

Tana gamawa ta miqa mishi plat da cup Wanda taxuba kunun gyada, Dasauri Hafeez ya zaro idanunshi gami da sake kallon Balkisu yace"Balkisu dukk waye xaici wannan abincin? Cike da shagwab'a Balkisu taturo dank'aramin bakinta tace"yayana kai xakaci mana kamanta tunyaushe rabonka da abinci, Hafeez murmushin yaqe yayi yace xan daici Wanda xan iya" Balkisu tace toh naji amma kaci sosai ga magagungunan ka chan barin dauko ma, Hafeez baice da ita komai ba sai binta  kawai yakeyi da kallo.

A hnkli ta tashi tanufi site bed dinshi tadauko ledan magungunansa, ajiye masa tayi a gabanshi sannan tafice a d'akin.

Site dinta tanufa tana isa ta rufe kanta cikin d'aki da gudu tafada kan gadonta. Gamida riqe kanta Wanda ke tsananin sara mata gaba daya kanta ya gama kullewa, "cikin xuciyarta tace tabbas ina buqatan neman shawara toh amma wajan waxan nema? Shiru Balkisu tayi nadan wasu dak'ik'u chan kuma ta tashi tsaye tafara safa da marwa.

Babu abinda Balkisu ke tunani sai shawaran da Dr Muh'd yabata, tabbas babu mai iya bama Yaya Hafeez kyakyawar kulawa face matarsa ta sunna, toh amma taya hakan zata kasance bayan tasan cewa cikin tsarin yayan nata babu mgnr aure aciki sbd wani BURI nasa da ya kwallafa aransa.

Wasu irin zafafan hawaye ne suke gangarowa bisa kuncinta tausayin rayuwarsu kawai takeyi, sai a ynxu ne take k'arajin kewa da muradin mahaifan nasu a kusa. Sai  dai babu hali...

Tunanin rayuwarsu na bayane yadinga dawo mata jitake tamkar ynxu abubuwan suke faruwa.

*waye Balkisu da Hafeez*?
[11:49AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode6⃣

Alhaji Abdullahi Shariff shahararren d'an kasuwa ne a fannin sai da filaye da motoci da gidaje, wannan itace sana'ar da Alhaji Abdullahi Shariff keyi tuntasowarsa na samartaka dukk da kasancewarsa goggen d'an boko amma sam aikin gwamnati baya basa sha'awa shiyasa tuntasowarsa yake yan buga Bugansa har Allah yasa sana'ar takarbeshi sosai Wanda sunansa yayi fice cikin qasashe da ma nan gda najeriya, Alhaji Abdullahi Shariff d'an asalin jarha borno ne cikin maiduguri, yana da mata daya Hajiya Hauwa da yaransu uku wato Hafeez shine babba sannan Balkisu da kuma yar auta Aysha wacce suke kira da Ameerah, wannan familyn na Alhaji Abdullahi da hajiya Hauwa suntaso cike da qaunar junansu.

Hafeez kyakyawan saurayi ajin farko,matashine dan kimanin shakara ashirin da takwas(28yrs)d'alibi ne a makarantar gaba da secndry wato jami'a(university of Maiduguri) yana karatu a fannin lawyer inda yanxu suke qoqarin xuwa bautar qasa,(NYSC)

Inda akatura Hafeez chan kudancin najeria wato Lagos. A lkcin da Hafeez xaitafi Lagos dan gudanar da bautan qasanshi Balkisu tashiga damuwa sosai kasancewar yadda suka shaqu da yayanta da kyar da lallashi ta daina kukan rabuwa da yayanta,.. hakanan Hafeez yatattara loage dinsa yayima mahaifan nasa sallama inda Abban nashi yayi masa nasiha akan abubuwan da suka shafi al'amuran rayuwa na yau da kullum hakanan Hafeez yyima iyayen nasa alqawarin kare mutuncinsa da addinninsa, Hajia Hauwa kam hakanan tasama d'an nata albarka gamida yimishi adua na fatan alkhairi,.

Har parkn space suka rakoshi inda drivansu ke qoqarin fito da mota dan kai Hafeez zuwa airport, Balkisu tanaji tana gani yayan nata yashige mota suka fice a gdan..Da fitarsu kafin suyi nisa Hafeez ya umarci drivan nasu da yafara kaishi federal lowcost. Babu musu kuwa Ali driva yajuya kan motarsa yanufi anguwar da aka umarcesa.
Kafin su isa tuni Hafeez ya fito da wayarsa don kiran wacce yakeson xuwa gareta.cikin daddad'a muryansa yafara mgn "hloo baby na gani nan shigowa anguwanku plss kifito inason naganki kafin nawuce" yana fadin haka yakatse wayar dai dai lkcin ne kuma driva yyi parkn alaman sun iso knan.

Kmr shud'ewa minti biyar na hango wata kyakkyawar yarinya sanye da hijab dinta har qasa, tafiya take tamkar mai tausayin qasa a hnkli cikin tafiyarta mai cike da qasaita taqaraso inda motarsu Hafeez ke parke, da sauri Hafeez yafito daga cikin motar hard'e hannayensa yayi gamida qura mata ido tamkar zai had'iyeta, "Assalamu alaikum ,shine abnda tafurta lkcn isowarta" yayinnda Hafeez yyi firgigit alamar yatafi dogon tunaninsa, a hnkli yyi wata nannauyan ajiyar xuciya gamida Amsa mata sallamarta.

Hafeez ne yadubi wannan yarinyar duba maicike da kewa, a hnkli Hafeez yace "toh Rafee'at am on ma way" Rafee'at tad'ago da idanuwanta Wanda sukayi rau rau alamar tanasonyin kuka, dasauri Hafeez yace no Rafee'at plss karmuyi haka dake karki manta cewa a dukk inda nakasance zuciyoyinmu natare da juna so pls stop worrn, ga waya i will always tray to call u kmr yadda nasa ba so plss no need to worry.

Rafee'at tad'ago jajayen idanuwanta a hnkli ta sauqesu akan Hafeez cikin wata irin dushashiyar murya tace"wannan shi ake kira a dakeka a hanaka kuka Haba my man yakake tunanin cewa baxan shiga damuwa ba karkamatanta cewa Kaine dukkan wani farincikina da walwalata kariga kasabarmin daganinka a koda yaushe ynxu kenan idan kayi wannan tafiyar sai dai kawai inkamajin muryanka? wasu zafafan hawayene suka dinga kwaranya a fuskar Rafee'at hakan kuwa baqaramin d'agawa Hafeez hnkli yayi ba.

Dole Hafeez yadaurewa xuciyarsa ya shiga aikin rarrashinta dakyar yasamu tayi shiru, sannan yyi mata sallama ya nufi airport xuciyarsa cike da alhenin rabuwa da abinda yafi komai qauna.

Hakanan Hafeez ya Isa cikin garen Lagos tamkar wani marar lafiya. Da isarsa kuwa Camp dinsu yanufa kai tsaye, yana xuwa yanufi dakin kwanansu, Hafeez sai da ya tabbatar yasamu ruwa ya watsa yayi sallahn azahar dinsa sannan yaxaro wayansa yafara kiran mutanen gda yana mai sanar dasu cewa ya isa lafiya. Sanda Balkisu ta Amshi  wayan suka fara tadinga jansa da surutu gami da jero masa tambayoyi akan yadda garin Lagos din yake.

Waje yafito yaxauna yana ta waya da Balkisu sai biye mata kawai yakeyi yakasa katse wayar, cikin hakan ne Rafee'at tayita kiran layinsa user busy har wajan awa daya Amma still busy Dan haka Rafee'at ta qufula sosai nan da nan tatura masa msg.

Hafeez na cikin tsaka da waya yaji wata yar qara tashigo cikin wayarsa a hnkli yaxame wayar daga kunnensa don duba Wanda yaturo sak'on sunan Rafee'at yagani Dan haka da sauri yakatse wayar da yakeyi ya shiga inbox din don duba sak'on nata:®NWA
[11:49AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode7⃣

_tabbas my man jikina yana bani cewa tunkafin tafiyar tayi nisa zaka mance da wata Rafee'a da wakake yin waya haka? da har akasamu damar daukemin hnkalinka alhalin kasancewa zan nemeka tabbas zuciya ta tana cikin qunci_.

Wannan saqo na Rafee'at baqaramin d'agamasa hnkli yayi ba, da sauri kuwa yashiga contact dinsa ya lalubo nmbn ta nan yafara kiranta. Wayan yayi ta ringing amma sam taqi d'agawa Hafeez kam bai fasa kira ba hakanan yyi ta kiranta koh Allah xaisa tad'aga amma daga qarshe Rafee'at kashe wayanta tayi, Hafeez nakira yaji swtch up.ae kuwa bai san lkcin da yayi wurgi da wayansa ba...Wata murya yaji kamar daga sama ance "fushi bai dace da kai ba. Kamata yayi kayiwa dukk wani da kake tare dashi uzuri kasancewarka mutum mai cikkiyar kalama, da sauri Hafeez ya d'ago kansa Dan ganin mai yimasa wannan shishigin, wata gajeriyar matashiyar yarinya yagani duqe a gabansa yayin da take qoqarin daukar wayarsa a hnkli tad'ago tamiqa masa wayar gami da yin murmushi tace" ni sunana Suhailat Mas'ud 4rm taraba state.

Murmushin yaqe Hafeez yayi gami yimata godiya yasa hannu zai amshi wayarsa da Sauri ta janye hannunta gami da girgiza masa kai alamar A'a, Hafeez cikin mamakinta ya dubeta da alamar tambaya a fuskarshi? Suhailat tayi murmushi wnda kumatuta suka lotsa wani lumshe idanuwa tayi gami da cewa baka sanar dani sunanka ba gashi kana qoqarin amsar wayarka daga hannuna.

'Hafeez' kawai yace mata a d'an tak'aice, Suhailat tayi yar dariya har da buga k'afafunta cike da zolaya tace Mallam Hafeez wannan dukk fushi ne haka? Hafeez sororo yyi yana kallon zak'ewa irin na wannan yarinya. Dan haka tashi kawai yyi da nufin bar mata wurin, da sauri tasha gabansa tana fadin am srry sir! Ga wayanka afuwan, tana Miqa masa wayan tabar wajen cikin sauri.

 Hafeez kam d'akinsu yanufa, yana xuwa yafada bisa yar qaramar katifansa, wani uban tsaki yaja mtssw! 'Cikin Xuciyarsa yana maijin haushin d'abi'un wasu matan.
Chan Kuma kamar Wanda aka tsikara daukar wayansa yayi yacigaba da Neman layin Rafee'ansa.

           "Hafeez dakyar yasamu layin Rafee'at yashiga xuwa ynxu har ta sauqo daga dogon fushinta, tadauki wayan cikin lumana Hafeez yyi mata bayanin cewa da Balkisu yakeyin waya ba da kowa ba.hakanan ya lallashi abarsa abinka da masoya tuni sunmanta komai.

Abangaran Suhailat kuwa qarqashin wata darbejiya tasamu ta xauna taxuba wani uban tagumi, zuciyarta cike da kwad'ayin son sake ganin wannan kyakyawan saurayi domin "kuwa lkci daya Suhailat taji bata da wani abin so da qaunar gani face Hafeez"
          Tundaga wannan lkci ya kasance Suhailat tafara bibiyar Hafeez gami da cusa kanta a gareshi dukk da cewan bata ga alamun wargi a tattare dashi ba.Amma kullum tana cikin yi masa wasu yan d'awainiya.

Zuwa ynxu kuwa kwalliya tafara biyan kudin sabulu  domin kuwa Suhailat tafara samun Hafeez yadan fara kulata ba kmr da dayake yawan shareta ba.

*Wacece suhailat*
Suhailat kabeer Musa yar asalin jalingo ce cikin taraba state, mahaifin Suhailat wato Alhaji kabeer musa shahararren dan siyasane ya hau muqamai da dama anan cikin jaharsu, matansa biyu Zainab itace uwar gda sannan sai Saffiya itace mahaifiyar Suhailat.
   Suhailat ita kadai Allah yabawa mahaifinta kasancewar uwar gdansa bata haihuwa, shiya Saffiya da Alhaji Kabeer suka dauki son duniya suka k'wallafashi akan tilon yarsu, hakan yasa tuntasowar Suhhailat bata ta6a Neman abu tarasa ba shiyasa takeyin yadda taga dama, dukk wani gdan club dake cikin taraba babu wnda Suhailat bata sani ba.Kasancewarta mai yawan son chasu da kuma wasu yan shaye shayenta masu saka maye.

Koh karatun da takeyi  a ynxu kudi da Isa ne yasa take taka dukk wani matsayi datake son takawa acikin rayuwarta."Suhailat Tasha haduwa da samari kala kala wadanda take furta musu kalmar so wasu su amince don dukiyarta wasu kuma su amince don samun jikinta.
     Iya tsawon rayuwar Suhailat bata taba ganin saurayin da takeyiwa zazzafar qauna ba kmr Hafeez Wanda shikuwa bai ma san tanayi ba.

           Wannan kenan!
 
®NWA
[11:50AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode8⃣

Shak'uwar Suhailat da Hafeez a kullum k'ara ha6aka takeyi, yayinda Suhailat tacigaba da nunawa Hafeez tsantsar so da kulawa. Wanda abangaran Hafeez bai ta6a zaton abin haka yake ba. Rayuwa suke gudanarwa mai cike da fahimtar juna.

Hafeez ne da Suhailat zaune bakin baranda suna hirarsu kmr yadda suka saba, Hafeez ne yadubi Suhailat yace sis nikuwa intambayeki mana. Suhailat tayi wani fari da ido gamida muskutawa tadubi Hafeez tace okay inajinka. Hafeez yyi gyaran murya gamida yin murmushi yace akwai wani abu dake dauremin kai agame dake, dammm!! Gaban Suhailat yabuga cike da fargaba tace"jst go street 2 ur qstn pls" Hafeez yace olryt dama abinda kedauremin kai shine naga kina amsa suna biyu wato Suhailat mas'ud koh Suhailat Kabeer, wata irin sassanyar ajiyan zuciya Suhailat tayi yyin da tuni gumi yagama wanke ta.

Cike da fara'arta tace aff! Dama wannan ce tambayarka? Gyad'a mata kai Hafeez yyi gamida kallonta, Suhailat tayi murmushi tace"Ma'ud sunan wan mahaifina ne nataba zama a gdansa ashekarun baya so gsky yana matuqar jidani shiyasa wasu har suke zaton cewa koh shine mahaifina, Hafeez ya bude baki kenan da niyar qara jeho mata wata tambayar kawai sai phone dinshi yafar ringin da sauri ya zarota daga cikin aljihunsa' sunan da yasanyawa mahaifinshine ya bayyana akan screen din wayarshi"ABBA" da dauri yadauka gamida yin sallama.

Abba ne keyiwa Hafeez mgn cikin nutsuwa yace "Hafeez kanajina? Cike da ladabi Hafeez yace inajinka Abba, Alhaji abdullahi yayi murmushi mai cike da dattijantaka. Sannan yace Hafeez jiya munyi magana da Mahaifin Rafee'at yanunamin cewa yana son ya aurar da diyarshi toh kasancewa xa'ayi birthday din yar'uwarka Balkisu shiyasa nayanke shawaran cewa ranar birthday dinta sai ayi engaged dinku kaga lkcin mutane suntaru sai ayi abu daya kowa ya shaida. Wani irin farinciki ne marar misaltuwa Yakama Hafeez baimasan lkcin da yayi wani tsallen farinciki ba. Cike da zumud'I Hafeez yace Abba komai yayi dai dai tabbas hakan ma yayi.

Hafeez yanufasa yace Abba birthday din Balkisu on 28 ne koh? Abba yace"eh on 28 ne. Hafeez da qarfinsa ya furta yesssss! "Abba ne yace lfy kuwa? Hafeez yadanji kunya amma kasancewarsa tsayayyen namiji yace no Abba kawai naga abin ne yaxomin a yadda nakeso sbd on 27 zamu kammala komai namu mu mudawo gda.

Abba ma da kansa yaji dadin wannan labarin sbd yana matuqar son kasancewa tare da d'an nasa. Dan haka yasamishi albarka gamida yimishi kyakyawan fata.
    Hafeez dai sai yak'e hakura yakeyi.

Yayin da Suhailat tayi shiru tana kallon Hafeez itama sai murmushi takeyi, sbd tasan tabbas akwai abunda aka fadamishi Wanda yasashi farinciki.

Hafeez naqare wayan yamaida dubansa ga Suhailat fuskan  nan tashi d'auke da farinciki marar misaltywa, Suhailat tawani lankwashe kai gami da lumshe idanu a hnkli tasauqesu akan Hafeez tace "Hafeez mai yasanyaka farinciki haka"? Hafez yasake murmusawa yace "Suhailat I have a surprise 4 u, amma not now sai on 28.

Cike da D'auki da Farinciki Suhailat tace olryt Allah yakaimu.

Ameeeeeeen kawai yace, a hnkli yatashi Yakoma makwancinsa nan ya fara dialin numbn Rafee'ansa inda tadauki wayan sukayi tahiransu cike da kulawa da qaunar junansu.
®NWA
[11:50AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode9⃣

Hafeez ne sanye da kayanshi na NYSC wnda sukayi matuqar amsarshi, zaro wayarsa yyi wacce take gefen aljihun wndonsa. Numban Suhailat yakira wayan bata jima tana ringin ba Suhailat tadauka yace da ita yana son ganinta, cikin k'ank'anin lkci kuwa sai ga Suhailat gata ta baiyana agaban Hafeez. Cikin nutsuwa Hafeez yace yauwa Suhailat dama so nake muje kirakani kasuwa kinsan nafadi miki cewa za'ayi birthady din Balkisu da kuma surprise din da nace xan miki, so inaso kikaini shagon da xansamu kayan mata kmr su less da atamfa da sauransu kinsan tafiyan mu yana daf da gabatowa

Cike da mamakinsa tarik'e ha6a tana kallonsa, cikin muryan zolaya tace a'a Hafeez waza'a ayima siyayya haka? "Hafeez yace ba nafada miki cewa I have suprise 4 u ba. So jst watch me, Suhailat ta gyad'a kanta gami da gyara wani dan yalolon gyalenta tadubi Hafeez da murmushi tace olryt mutafi am ready.

Taxi suka tara ya kaisu wani tamfatsetsen shago dake cikin garin Lagos, da shigarsu Hafeez yafara yin abinda yakawosu wato zab'en kayan da yasan xasu matuk'ar amsar Balkisu, ita kam Suhailat tsaye tayi tana kallonsa dukk farinciki ya isheta. Hafeez ne yajiyo ya dubi Suhailat cikin zolaya yace Suhailat plss zabamin kayan da kikasancewa sunyimiki a matsayin zab'inki less material atamfa dukka kizab'amin choice dinki masu kyau, wani irin farinciki ne ya mamaye xuciyar Suhailat domin wani tunani nata na daban datasa acikin
xuciyarta.
      Nan fa Suhailat tashiga za6en wasu danqara danqaran less masu kyau da tsadar gaske, da zarar Suhailat taza6o kayan sai tanunawa Hafeez tace "wannan yayi kuwa"? Hafeez kawai sai yace nidai kiza6amin kalar skin dinki wanda kikasan zai Amshi kalar jikinki. Nan fa Suhailat fara washe baki tana murna farinciki da jin kalaman Hafeez

"Hakanan takasance dasu Hafeez har suka gama siyayyarsu suka koma masauqinsu"

*************************
Yau yakasance ranar Saturday Wanda yayi daidai da ashirin da 27 ga watan Nowamba(27-November) hakan takasance ranar da wadansu daga cikin d'aliban xasu koma gda..
   Hafeez ne tsaye agaban trolley bag dinsa, da ganin alamunsa tsaye yake yana jiran wasu.

Suhailat ce tafito tsab cikin shirinta na dark blue din atamfa itama tafe take tana jan jakarta cikin sauri taqaraso gaban Hafeez tana murmushi , abinda Hafeez yafara  tambayarta shine ya daddy ya amincewa tafiyarki kuwa? Suhailat tayi wata irin ajiyar zuciya tace wlh yabarni but yacemin only 2days ana gama birthday din inkoms gda, Hafeez yace woww vry gud har naji dadi, sbd ticket din mutum biyu nayi bookin.

Airport suka nufa kaitsaye da xuwansu basu fi 30mnt  ba jirginsu ya d'aga sai borno.

Su Hafeez na sauqa drivansu na xuwa Dan haka shiga kawai sukayi suka nufi gda, suna cikin tsaka da tafiya sunxo daf dashiga anguwarsu wata akuya tadan gifta musu take anan drivan yadan ja birki da sauri Wanda hakan yyi sanadiyar zubowan kayan dake cikin handbag din Suhailat, waiwayowan nan da Hafeez zaiyi idanuwansa sukayi tozali da wasu munanan abubuwa wnda suka fado daga cikin jakar Suhailat.

Cikin tsananin tashin hnkli Hafeez yazaro idanunsa gameda nunata. Dam! Gaban Suhailat yabuga.
®NWA
[11:50AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode1⃣0⃣

Gabadaya hankalin Suhailat ya gama tashi, nan take tafara had'a zufa dukk da kasancewar sanyin AC n dake ratsa kowanne sassa Na cikin motar. Cike da mamaki Hafeez ke dubanta ji yayi bakinsa ya masa nauyi murya qasa-qasa yace Suhailat miye wannan nake gani acikin jakarki? Dasauri "Suhailat tafara sosa kanta gamida neman mafita cikin in'enar mgn ta dubi Hafeez tace amm uhum! Ae kasan Rukky wacce muke daki daya da ita wlh itane take shan wadannan syrup da kwayoyin toh na hanata tak'i ji shiyasa nikuma nakwashe kayan mayen nata na boye ajaka, gashi Sam namanta banzubar ba am swryy plss.

Suhailat nagama fadin haka Hafeez yayi wata irin nannauyar ajiyar zuciya gamida yin murmushi yace" huuu wlh Suhailat u really scared me!" Wani irin murmushi Suhailat tayi kai da gani kasan qaqaroshi tayi. Dasauri tasa hannu takwashesu tabude window da nufin ta zubar, Hafeez ne ya dakatar da ita yace"tabarsu anan cikin motar zai zuba su a shara.

Suhailat kam shiru tayi gabadaya jikinta yayi sanyi hnklinta ya gama tashi,sbd gabadaya gani takeyi Hafeez yagama harbo jirginta. Qarar horn din da driva ya danna ne ya fargar da Suhailat daga dogon tunanin da ta tafi, kmr daga sama tajiyo muryan Hafeez yace Suhailat"mushiga daga ciki koh? Dasauri ta bude murfin mota jiki a sanyaye, ta ziro qafafunta jitayi gabadaya sunmata nauyi. A hnkli tafito suka fara nufar cikin gda. Ae kuwa sai ga Balkisu da gudunta tanufosu, jikin Hafeez tad'ale tamkar wata qaramar yarinya, oyoyoo yayana! Nan tabashi pick agoshi, a hnkli Balkisu ta maida dubanta ga Suhailat cike da zumud'i tasaki hannu Hafeez takoma wajen Suhailat wani murmushi Balkisu tayi tace kece anty Suhailat koh? Suhailat tadan saki fuskarta tadafa kan Balkisu tace eh nice Billy, Balkisu ta k'yalk'Yale da dariya jin ance mata billy, tadubi Suhailat tace anty Suhailat kema Billy xakicemin irin na uncle ma'aruf?.Hafeez ne ya ja hannun Balkisu yace oya parrot mushiga daga ciki am very eager to c my mum, da sauri suka shiga cikin falon gami da sallamarsu.

Mahaifan nasa ne suka fito daga d'akinsu atare, cikin shigarsu ta alfarma kai dagani kasan yau rana ce ta farinciki a garesu. Da sauri Hajiya Hauwa tafito fuskarta dauke da fara'a, Suhailat tafara tarbo (kasancewar sunsanta awaya suna gaisawa, sannan Hafeez ya sanar da su zuwanta) Suhailat dukk farin ciki yagama dabaibayeta ganin yadda iyayen Hafeez suka tarbeta tamkar dama suntaba haduwa.

Bayan sungama gaishe gaishensu da nuna farinciki da kewar juna, nan Hajiya Hauwa ta umarcesu da suje dining area suci abinci, Balkisu najin ance haka taja hannun Suhailat "anty xomuje nan taja hannunta Suhailat suka nufi dining, yayin da Hafeez yarufa musu baya tunkafin su zauna Balkisu keta zuba mata surutu" Suhailat kam wani irin son Hafeez ne ke qara shigarta ganin yadda families dinshi suka karb'eta hannu bibbiyu.

Abincine kala kala aka tanadar musu, Suhailat dai tace sinasir take so ae kuwa Balkisu tazuba mata sinasir din mai yawa tace da ita sai tacinye nan dai akayita raha cike da so da qaunar junansu.

Bayan sun kammala cin abinci ne Hajiya Hauwa ta umarci Balkisu da ta nunama Suhailat d'akin da zata kwanta, ae kuwa ba musu taja hannunta anty tashi muje.
    Suhailat dai biye take da ita tamkar rak'umi da akala, gabadaya Balkisu tagama shiga ranta yarinya gata kyakawa tamkar yayanta yarinyar akwai saurin shiga rai.

Bayan sun isa cikin d'akin ne Balkisu tace anty ga d'akin nan kishiga toilet kiwatsa ruwa bari inje inhada miki coffee mai d'umi kisha. Kafin Suhailat tace wani Abu tuni Balkisu tafice. Suhailat murmushi tayi gamida girgiza kanta a hnkli tace Naughty girl. Toilet tafada tayi wnka sannan tafito.

Tana fitowa Balkisu nashiga, batareda tace uffan ba ta ajiye coffee din a gefen gado tafice.
Suhailat tayi murmushi takaici cikin zuciyarta tace "uhmm nimai zanyi da wani coffee ae ynxu buqata ta kawai insha kayan aiki(syrup) in wartsake gajiya mtsww" tanafadin haka tabi lafiyar gado ta kwanta batare da biyan sallolin da suke kanta ba.


Abangaran mahaifan su Hafeez kuwa gabadayansu sunhallara a falo suna tsara yadda birthday din Balkisu da enggd din Hafeez zaikasance.

Hakanan sukayita sharwarinsu har akayi kiran magrib Abba da Hafeez suka nufi masallaci yayin da Balkisu tanufi d'akin Suhailat don ta tasheta Sallah.Momy kam tuni tanufi sasheenta.

Abba da Hafeez kam basu dawo gda ba sai da suka gabatar da sallahn isha'insu. Sannan suka nufi gda, sai da kowa ya hallara sannan sukanufi dining area sukaci abinsu,

gabadayansu ranar raba dare sukayi sunata hirarsu cike da nishad'i, daga bisani ne kowa yanemi makwancensa.®NWA
[11:51AM, 10/15/2016] My Nabss: [5:03AM, 7/14/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode1⃣1⃣

Tunda sanyin asuba masu decoration suka bugama Hajiya Hauwa waya cewa gasunan K'ofan gda batare da b'ata lokaci ba tayi musu Iso, masu decoration nan sukafara aikinsu gda yadauki haske da kyawun gaske. Sai da Hajiya Hauwa ta tabbatar da cewa angama gyara gdan tsaf sannan takoma sashinta, bayan ta idar  da sallah sannan tashiga toilet ta watsa ruwa. Tana idar wa ta zauna gaban dress mirror ta tsara kwalliyarta tamkar wata budurwa.

Sashen Abba tanufa koda shigarta ta tarar yana toilet murmushi kawai tayi,  kai tsaye tanufi wardrop dinsa tafitar masa da wata shadda galila mai matuqar kyau da sheqi, tana gama zab'a mishi sai gashinan ya fito fuskan nan d'auke da murmushi cikin muryan rad'a yace yan matana kinyi kyau, Hajiya Hauwa tayi murmushi Wanda hak'uran makkanta suka bayyaina, cike da zolaya Abba yace "a'a irin wannan kwalliya haka? Ashe kwalliya ake tsaramin shiyasa yau ba'a tashemu zuwa massalaci ba? Hajiya Hauwa tayi yar dariya tace"yau Alhaji na lura yan zolaya ne akanka.

     A'a wanne zolaya ae ba zolaya yau din ne naga kinfi koyaushe kyau, "nagode tace masa yayinda take k'okarin barin d'akin.
Koh da fitarta d'akin Hafeez tanufa shima ta tashesa sannan tanufi d'akin da Suhailat take bayan ta tasheta sannan tawuce d'akin uwar gayyan.

Koh da Hajiya Hauwa tashiga d'akin Balkisu ta tarar da Ita zaune bisa sallayah tana sharar hawaye, cikin tsananin damuwa da tashin hnkli Momynta qarasa kusa gareta a hnkli ta jawota jikinta tace"Balkisu lfy kuwa? Balkisu Wanda kuka yaci k'arfinta ta k'ara rungume momynta tanaci gabada kuka, Hajiya Hauwa batayi yinqurin Hana takukan ba sbd batasan mine dalilin yinsa ba.

Balkisu sai da tayi kuka mai isarta sannan tad'ago tadubi mommynta cikin sark'ewan murya tace Momy Dan Allah kiyafemin dukk laifuffukan danayi miki, da sauri mommy ta tallabo fuskar Balkisu ido cikin ido takalle cike da kulawa tace "haba Balkisu meyaparu haka me akayi miki haka karfa kimanta cewa yau ranarkice yakamata ace yau kinfi kowa farinciki meyaparu dake kike kuka,? Balkisu tadubi mommyn nata fuska araunane tace wlh Momy nikaina narasa dalilin wannan kukan nawa kawai dai yau inajin tamkar wani Abu mummuna zai faru dani, Momy tayi murmushi tace "Balkisu kenan insha Allahu babu abinda zaifaru ki kwantar da hanklinki tashi kije kishiga wanka.
   
    Jiki a sanyaye tace to mommy,ba wani gardama ta tashi tanad'e sallayan da tayi sallah' sannan tashiga toilet don ta watsa ruwa. Hajiya Hauwa kam falo tanufa tana jiran iyalen sufito suga decoration din da akayima falon.


Basu wani jima ba dukkaninsu sukafito tsab cikin shirinsu na alfarma, bayan sunhallara afalon ne Hajiya Hauwa ta lura ba Suhailat cikinsu Dan haka tadubi Balkisu tace"Balkisu jeki kirawomin Suhailat" toh kawai tace Balkisu tamik'e  da nufin taje Hafeez yadakatar da ita yace kiyi zamanki barin je infito da ita.

Hafeez yanatafe yana waya da Rafee'ansa awaya.

Abangaran Suhailat kuwa tun lkcin da Momy ta tasheta taje tayi Sallah bata tashi ba sai ynzu. Shiyasa sai ynxu tafito a wanka tasanya wani Riga da wando mai zubin fakistan kalar lemon green da orange kayansun matuqar amsarta zamatayi akan chair din dake gaban dress mirror tazauna tafara tsarawa kanta kwalliya, bayan tagama tak'urawa kanta ido domin kuwa tasan cewa ita kanta tahadu dan haka cikin zuciyarta tace" Suhailat kiyi matuqar kyau sannan yaune yadace kisanar da Hafeez sirrin zuciyarki da kuma BURINki nason aurenshi dix is d ryt tym da zaki fadamishi" k'wank'wansa k'ofan da akeyine yadawo da ita daga dogon tunaninta. A hnkli tace yes com in! Murd'a k'ofan yayi yashiga gamida sallamarsa, Suhailat ta amsa masa da murmushinta kasancewar ta gane muryanshi cike da zumud'i Suhailat tajuyo damm! Gabanta yafad'i domin Hafeez ba qaramin burgeta yayi ba domin sai a ynxu ne ma tagano aenahin kyawunsa. Akasalance ta gaida Hafeez..Hafeez bai amsa mata ba har sai da yagama waya. Sannan ya maida dubansa ga Suhailat tace a'a Suhai irin wannan kyau haka karfa kihadawa mazan Borno go slow, murmushi Suhailat tayi tace wlh kai dai kafaye zolaya wallahi Hafeez yayi murmushi gamida zuba hannayensa cikin aljihun wndonsa yace kiyi sauri Momy najiranki lkci na qoqarin wuce, Suhailat tad'anyi fari da idanuwanta tace okay badamuwa ganinan zuwa amma kafin nan Hafeez pls inaso infada maka wata muhimmiyar mgn, Hafeez yace olryt ba damuwa amma kibari anjima zamuyi mgnr ynxu inada Wurin zuwa kokin manta nace zanyi suprsn dinki?

Wani irin farinciki ne yakama Suhailat tace olryt badamuwa inajiranka. Okay yace mata adan tak'aice sannan yafice daga d'akin, yana fita falo yasanar dasu gatanan fitowa sannan yace yatafi ya dauko Rafee'at don ta halarci birthday din. Hajiya Hauwa tayi murmushi tace toh Hafeez" plss kada  kaje kayi zamanka kana zuwa kad'aukota kujuyo sbd afara prgrm in dawuri kar mubatawa guest dinmu lkci, "insha allahu Momy ynxu zanje nadawo. Yanafadin haka yafice a falon.

Suhailat ce tafito cikin wani irin taku nata tamkar mai tausayin k'asa haka taqaraso cikin falon sannan tagaida Momy da Abban, Balkisu ce ta taso daga inda take zaune taqarasa wajen Suhailat tazauna sannan tace gud murng my Anty, Suhailat najin dadin yadda Balkisu ke bata kulawa, a hnkli tace billy am fyn ya shirye shiryen birthday? Balkisu tace gashinan munayi kinga yadda mommy tasa aka gyara falon? Suhailat tace nagani wlh falon yyi matuqar kyau. Suhailat tace yauwa baki fadamin ba how old ar u now? Balkisu taji kunyan tambayr Suhailat din, dariya tayi gamida rufe fuskanta tace am 13yrs old today. Suhailat ta tafamata tace very gud billy.

Suna cikin haka sai ga sallamar Hafeez tare da Rafee'at sunshigo, Rafee'at sanye take da hijabinta hakan yyi matuqar fitar da ainahin kyawunta, Hankalin Suhailat gabadaya yagama tashi ganin Hafeez tare da wata kyakyawar yarinya sunjero a tare sunayima junansu murmushi wani irin azababben kishi ne ya turnuk'e Suhailat,

Da shigarsu Rafee'at taduqa har k'asa cike da ladabi ta gaishesu gabadayansu kowa yana farincikin ganin Rafee'at amma banda Suhailat wadda tayi duqu duqu da rai kmar zata fashe sbd tsananin kishi., Suhailat da Rafee'at  suna hada ido rass!! Gaban Rafee'at ya buga wani irin kishi taji marar misaltuwa domin kuwa ta tabbata itace Suhailat din da Hafeez kebata lbri ynxu a hnyarsu ta zuwa.®NWA
[11:51AM, 10/15/2016] My Nabss: [12:49PM, 7/14/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode1⃣2⃣

Wani irin azababben kishi ne ya turnuk'e Suhailat, sanin da tayiwa knta cewa bata da control yasa tayi saurin barin falon tanufi d'akin da yakasance masak'inta, da shigarta ta banko k'ofa da gudu tanufi kan gado tana maida wani irin numfashi mai wahalar fita. Tana cikin wannan halin ne taji ana k'wank'wasa k'ofa shiru tayi batace komai ba Wanda ke k'wank'wasa wan jin ba'a tanka masa ba yayi tunanin koh ba mutum cikin d'akin bude k'ofan yayi a hnkli ya zura kansa gamida cewa Suhailat! Jin muryan Hafeez yasa tayi sauri mik'ewa daga kwance da take"tace na'am, da fara'a kuwa d'auke a fuskarsa yak'arasa ciki yayin da Rafee'at ke biye dashi fuskan nan nata adaure tamau!

Hafeez nashiga ciki yace yauwa Suhai yau zanbaki surprise dinki, dama sonake in nuna miki matar aure na wannan itace zan aura sunanta Rafee'at kuma ayaune insha allahu za'ay enggd dinmu after birthday din Balkisu.

Dam! Gaban Suhailat yabuga hnklinta yatashi wani irin kishi ne ya gama sark'eta take anan tafarajin gari Na yawo da ita dasauri takoma bisa katifa tadafe kanta Wanda ke tsananin sara mata, dasauri Hafeez ya matsa daf da ita yace"Suhailat lafiya kuwa?" Wani irin murmushi ta k'ak'aro tace no bakomai kainane ke d'an saramin, plss inba damuwa inaso zanyi mgn da kai,kai dai.

Rafee'at najin Suhailat tace haka kafin ma Hafeez yace da ita wani abu tuni tabar d'akin zuciyarta kmr zata fito sbd tsananin takaici da kishin Hafeez.

        Rafee'at nafita a d'akin Suhailat tamik'e tsaya idanuwan nan nata gaba daya sun rine zuwa jaa! Cikin tsananin masifa gabadaya idanuwanta sun gama kullewa " tace amma wlhy Hafeez kaci amanata ka yadudareni. Ashe dama kanada wacce kakeso shine baka tab'a bani damar fahimtar haka ba' toh kasani hakan dakayiwa zuciyata ba k'aramar illah kayimata ba domin kuwa sonka yayi min rami mai zurfin gaske acikin zuciyata, Adalilin son da nake makane yasa nabiyoka izuwa garinku ashe bansani ba kai kana da wacce kake so nikuwa koh oho koh?

Tsananin Mamaki ne qarara d'auke a fuskar Hafeez cikin tsanin tashin hnkli yasa hannu yadakatar da Suhailat daga sambatun surutan datakeyi masa' dakata Suhailat plss stop dix jokes of urs irin wannan wasan baidace dake ba Sam domin kuwa ni amatsayin yar'uwata nadaukeki nabaki muhalli irin na Balkisu acikin rayuwata so plss stop dix nonsense!

Ran Suhailat gabadaya yagama b'aci tadubi Hafeez da raunannun idanuwanta tace wlh matsayinka yawuce dukk yadda kake tunani acikin zuciyata ni matsayin mijin Aure nadaukeka kuma dukk wani mahaluk'I danake tare dashi yasan da haka, sai kai kad'aine zakacemin baka lura da irin kulawa da tarairayar da nake baka ba?

Ran Hafeez ma gabadaya yagama b'aci a fusace yace olryt nagode da kulawarki gareni amma kisani Rafee'at itace BURIN HAFEEZ ita kadai nake so ita nakewa soyayya ta asali da ita nakeson kasancewa har k'arshen rayuwata, wani irin abune ya soki zuciyar Suhailat a fusace tace toh shikenan naji yanxu inaso kasanar dani tsakanin RAFEE'AT da SUHAILAT wa kake so??

Wani murmushin takaici Hafeez yayi yanuna Suhailat da d'an yatsa yace what do u mean kina nufin zand'auke kine inbar Rafee'at to bari kiji indai wannan shine tunaninki toh gwnda tunda wuri kicanja shi domin kuwa Rafee'at wani b'angarece ta rayuwata bazantaba iya rabuwa da ita ba koh da kuwa sama da k'asa zata had'e, cike da masifa Suhailat tace ohhh haka ma zakace toh wlh inhar baka zab'eni amatsayin wacce zaka aura ba toh wlh inatabbatar maka dacewa sai ka tafka babbar hasara arayuwarka domin bakasan koh ni wacece ba indai matuqar ina raye wlh babu kai babu auran waccan k'idahumar.

Hafeez murmushi yayi ya dakatar da Suhailat yace dakata mallama inamai gargadinki kadaki k'ara cewa matar aure na k'idahuma, maikike zato dama haka kawai zan aureki banda tabbas din koke wacece Rafee'at kuwa tunbata mallaki hankalin kanta ba Allah yard'auramin sonta so ni inaganin bbu yadda za'ayi Na zab'eki nabar ta kingane ae dan haka ki kwntar da hnklinki ayi taron nan lpy kikoma hannun mahaifanki.
Hafeez nafadin haka yasa kai yafice zuciyarsa gaba daya ajagule.

Yana fita falo yanufa, mommy naganinsa tadubesa da murmushi tace yauwa Hafeez ynxu kuwa nake k'okarin nemanka, kaga tun mutane basu fara taruwa ba inaso kaje oasis bakery ka ansoma Balkisu birthday cake dinta. Hafeez yace toh Momy bari inyi sauri inje indawo, karaff Balkisu tace yaya Hafeez plsss nima zanbika da sauri ma Aysha (ummi) autar Momy tace yaya nima zanbika, a hnkli Hafeez yaduk'a wajan autan Momy yace swry ummi bazan iya zuwa dake ba sauri nakeyi zanje nadawo kinji karki damu zanzo miki da ice-cream, gyada masa kai tayi takoma gurin momynta tahau saman kujera taci gabada wasanta. Balkisu kam binshi tayi abaya cike da zumud'i ta marairaice fuska plsss Yaya znbika wlh baxan dameka da surutu ba. Okay kawai yace da ita har yanufi hanyar fita kuma chan sai yajuyo ya kalli Rafee'at wacce kanta ke k'asa tak'i yarda suhada ido sbd fushi takeyi dashi, a hnkli Hafeez ya kira sunanta Rafee'at d'ago knta tayi a hnkli tadubesa shikuwa Hafeez naganin tadubesa yahada hannayensa alamar neman afuwa sannan yayi mata nuni da inyadawo zaimata bayanin komai, murmushi tayi maisauti sannan ta gyada masa kanta.

Da sauri yabar falon yana murmushi, sunafita yanufi parkn spc yadauki mota suka nufi oasis.z

Abangaran Suhailat kuwa waya tadingayi tana fad'awa frnds dinta cewa Hafeez yaci amanarta ya yaudareta ashe yana da mata baifada mata ba, dukk wnda tak'ira sai dai yabata hkri, ganin haka yasa takira daddynta tafada masa maganganun da sukayi matuk'ar girgiza shi hnlkinsa gabadaya yagama tashi, Suhailat kam nagama fadin sak'onta takashe wayarta, gabadaya lkci daya tazama zautacciya hnklinta yagama fita akanta sbd zafin kishi, hakanan tacire d'an kwalin kanta tanata faman sambatu da neman mafita domin kuwa acewarta da taga auran Hafeez da wata gwnda taga mutuwarta dan haka da sauri tabud'e k'ofa tanufi hnyar kitchn koh da shigarta tadauki sabuwar wuqa sai shek'itakeyi cikin zuciyarta tace koh inbisu falo inkashe kowa da kowa sannan nima inkashe Kaina, har tafara fita a kitchen din kome ta tuna kawai saita koma kitchen din nan tafara mgn cikin sambatu wlh sai dai mumutu gabadayanmu bazai yuwu namutu nikadai ba, surutan da takeyine yajawo hnklin Iya ladi mai aiki wacce take k'okarin wanke babbar tukunya awaje kasancewar tana bakin window din tawaje hakan yabata damar lek'awa bak'uwan nance tagani tana k'okarin bude silinda na gas, ga kuma surutan da wannan baquwar takeyi hakan ya bama iya ladi tsoro dan haka tafara ihun Neman taimako tafadin Hajiya! Alhaji! jama'a yar k'unan bak'in wakece wannan bakuwa da gudu tanufi cikin gda don tasanar dasu ta'addancin da ake shirin aekatawa kasancewar da dan taxara shiyasa take gudu tananeman agaji.

Mommy ce tafara jiyo ihuun neman taimako kmr iya ladi ce a kitchen ae da gudu suna Kalmar salati suka nufi kitchen din gabadayansu, mommy na bud'e k'ofa Suhailat na cinnawa gas din ashana ae kuwa take anan gdan yayi  wata irin girgiza tamkar antada bomb take gdn Yakama da wuta ta ko'ina.

Kafin iya ladi tak'arasa ciki tuni Gas din yatashi take itama tasamu nata domin kuwa girgizan nan yasa tayi wata mummunan faduwa Wanda yayi sanadin sumanta..
Inallilahi wa'inna ilaihiraji'un.......®NWA
[11:52AM, 10/15/2016] My Nabss: [1:08AM, 7/15/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode1⃣3⃣


Cikin tsananin tashin hankali gabad'aya jama'ar unguwar kowa yafito, kowa sai mamakin faruwar wannan al'amari yakeyi, Alhaji shehu makocin su shine yayi tunanin kiran fire servirce(motar yan kwana-kwana) bayan shud'ewar wasu yan mintina kuwa sai ga sunan da gudu sunshigo cikin layin ba su tsaya jinkirin komai ba suka zago babban tiyo dinsu sukafara zuba ruwa tasaman gdan, Dakyar akasamu wutan nan ta mutu bayan yan wasu mintuna kenan wasu maza guda uku ma'aikatan fire service cikin shirinsu na aiki suka tunkari hayakin suka afka cikin gdan.

Koh da shigarsu suntarar da gawawwaki tare waje guda gabadaya sunk'one ta yadda koh fuskokinsu ba'a iya ganewa, haka nan suka dibi gawawwakin bisa abin daukar gawa suka fitar da su izuwa waje, sai da suka gama kwashesu sannan sukashiga bincike acikin gdan. Suna cikin lalubensu ne Allah yasa sukaci karo da iya Ladi wacce ke kwance sumammiya da gudu suka k'arasa wajenta ganin cewa tanada sauran numfashi yasa sukayi saurin dauketa don bata taimakon gaggawa.

Hafeez ne tafe shida Balkisu sai surutu take zuba masa Hafeez yadube Balkisu yace ohh Balkisu ke kam daban kike ina yanxun nan da zamu fito kikamin alqawarin cewa baxaki dameni da surutu ba sai gashi tunba'aje koh inaba kin isheni da surutu ynxun nan sai in ajiyeki anan ki hau mashin, dasauri Balkisu tasa tafin hannu tarufe bakinta tana dariya. Chan kuma Balkisu tajuya bayan mota tazura hannunta a sit din baya tadauko robar ice-cream wanda suka siyoma autar Momy.

Balkisu tace amma gsky Yaya Hafeez nima zansha roba daya, Hafeez girgiza kansa yayi yace ohh gsky babu rabonki anan wannan dukk na aura ne. Balkisu ta turo baki cike da shagwab'a wai ita tayi fushi.

Hafeez dai bai kulata ba domin hnklinsa gabadaya yanaga Rafee'at BURINSA bai wuce ya Isa gda da wuri ba don yasamu damar bawa Rafee'at hkri sannan dole ne yasamar wa Suhailat ticket a yau din nan gobe takoma garinsu da irin wannan tunanin Hafeez yashiga cikin layinsu.

Dan dazon jama'a ne suka k'awanye ko ina na cikin anguwar cike da mamaki Hafeez yadinga horn ana bude masa hanya har ya samu ya isa k'ofar gdansu, inalillahi wa'inna ilaihiraji'un shine kawai abinda Hafeez ya iya furtawa dagudu suka fito atare shida Balkisu suka nufi cikin gda, gawawwaki suka gani jere a kwance anrufe da fararen kyalaye Hafeez ne ya nufi wajen da gudu yanafadim meyafaru ne mekefaruwa haka? gabadaya illahirin jijiyoyin wuyansa dukk sunfito bude gawarwaki yafarayi daya bayan daya Hajiya Hauwa yafara gani gabadaya illahirin kammanunta sunsauya gabadaya tak'one nan Hafeez yashiga girgizata yana fadin plss uwata kitashi dan Allah haka yashiga bude gawawwakin yana sambatu, Balkisu kam Sam tak'i kuka tsayawa tayi kyam waje guda chan kuma tafara tafiya a hnkli ta isa kan gawar autan Momy tabude ta nan Balkisu tashiga jijjigata tanafadin ummi! Autan Momy! Kitashi ga ice-cream nakawo miki plsss kitashi qanwata kitashi!! wlh wasa nake miki bazan sha ice-cream dinki ba. Dasauri ta Isa kan gawan iyayen nata natafara fadin Abba kace ummi ta tashi plss Momy ya kukayi shiru ne kunmanta yau ne birthday na Dan Allah karkumin wannan wasan kutashi mushiga cikin gdanmu Yaya Hafeez kace Umma ta tashi anty Rafee'at ba ynxu kikamin alqawari zaki kaini park ba plss kitashi anty Rafee'at nan tashiga ihuuu tanafadin iyayenta sutashi.

Jama'ar anguwan kowa ya tausaya musu, a hnkli cikin tausayawa Alhaji Shehu yakaraso garesu yana lallashinsu Hafeez Balkisu kuyi hakuri iyayenku kam sun amsa kiran mahaliccinsu

Hafeez da Balkisu atare suka fadi k'asa  summanmu. Yan cikin anguwansu kam wasu sai dasuka zubda kwalla sbd tsananin tausayinsu domin kuwa dukk wani dake cikin anguwar matuqar yasan family din Alhaji Abdullahi Shariff toh tabbas yasan irin wannan family din ake kira Happy family.

Da gaggawa motar ambulance ta kwashesu akayi asibiti dasu don basu taimakon gaggawa, inda kuma Alhaji shehu makocinsu yayi tsaye agaban wannan gawarwaki har sai da ya tabbatar ankaisu makwancinsu, Allahu Akbar.®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: 7/16/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode1⃣4⃣

La'illaha'ilallah muhammadur-rasulullah S.A.W, shine abinda iya ladi tafara furtawa lkcin da tadawo cikin hayyacinta da gudu nurse din dake kusa da ita taje ta kirawo Dr, Dr da xuwansa kuwa nan yashiga yi mata wasu yan gwaje-gwaje yana gamawa ya girgiza kansa nan yajuya ga nurse din dake tsaye yabata umarnin tamiqo masa allura da hanzarinta kuwa ta miqo masa take anan yasakeyi ma iya ladi  wata allurar kankace me tuni bacci yadauketa..


Balkisu tunkafin su isa asibiti tasamu farfad'awo sa6anin Hafeez wandake kwance cikin halin RAYUWA Ko MUTUWA! da isarsu asibitin wasu maza majiya k'arfi suka taimakawa nurses din nan aka daura Hafeez bisa gadon daukar marasa lpy I.c.u suka nufa dashi kai tsaye.
     Abangaran Balkisu kuwa wata nurse ce taxo ta tafi da ita izuwa nurses station(wurin zaman nurses) gabadaya nurses din dake gurin babu abinda sukeyi ma Balkisu face nasiha da ban hkri na rashin da sukayi.

Yan'uwa da abokan arzik'i kuwa gaba d'aya sun sami damar halartan jana'izar su Alhaji Abdullahi kowa sai jimamin wannan rasuwa yakeyi mai cike da abun al'ajabi, hakanan gdansu Rafee'at suma dukk sunjigata da wannan al'amari.

Likitoci da kyar suka samu kan Hafeez domin zuwa yanzu yanayin nasa ana iya cewa alhmdllh, Balkisu kam gabad'aya tazama kurman dole tak'itace da kowa uffan wasu irin hawaye masu k'unci da rad'ad'i kawai ke zuba a kuncinta.

Misalin k'arfe uku da rabi na dare Hafeez ya farfado, a hnkli ya fara bud'e idanunsa tun yanaji suna mishi nauyi har dai yasamu ya bud'esu gabadaya  cikin natsuwa yake kiran sunan mahaifan nasa chan kmr wucewa wasu yan sakwani Hafeez ya miqe zaune cikin tsananin firgici take yaji kansa yafara Sara mishi drip din dake sanye a hannunsa ya fisgeshi sannu a hnkli ya zaro k'afafunsa qasa tamkar d'ankoyan tafiya haka yafara fita a cikin d'akin. Balkisu Na zaune daga bakin k'ofa tarafka uban tagumi sai zubda kwalla takeyi maganar bacci kam babushi gabad'aya bacci ya k'auracewa idanunta.

Tana cikin wannan Halin ne taji andafa kanta tare da kiran sunanta da sauri tad'ago ganin Ya Hafeez ne tsaye akanta tamiqe da sauri ta rungumeshi wani irin sabon kukane ya zo mata Wanda Hafeez shi Sam kukan yak'i zuwar masa, a hnkli yake Shafa kan Balkisu Alaman lallashi
     Suna cikin hakane Dr din dake kula dashi yafito daga office dinsa kenan ya hango patient dinsa tsaye, da sauri yak'arasa gurin yana isa yariqe hannun Hafeez yana k'okarin mai dashi cikin dakin, Dakatar dashi Hafeez yayi cikin wata raunanniyar muryansa yace no Dr karka damu am ok nagode da k'okarinka akaina.
    "A ynxu banida wani BURI illah naga k'anwata cikin walwala, nan ya cigaba da Shafa kan Balkisu yanafadin k'anwata Sam kadaki damu domin natabbata mutuwar mahaifanmu dasa hannu wasu aciki inkuwa har hakan takasance nayi imani da maikowa mai komai saina d'and'ana musu abinda suka aikatawa family na sannan Balkisu.." Bai k'arasa fadin abinda yakeson cewa ba sai ga wata nurse nan da gudunta tak'araso wajen Dr din  tanafadamishi cewa wannan tsohuwar tafarfado amma jikinta ya Matsa sosai.

Cikin nuna tsananin damuwa Dr yadafe goshinsa yana fadin ya salaam, nan ya mai da dubansa ga Hafeez yace I thnk itama she ix part of ur family! Hafeez najin haka yace da Dr din plss suje sugani kowaye ce, Dakyar Hafeez yasamu suka k'arasa d'akin da iya Ladi ke ciki, iya Ladi na nan kwance sai jujjuya kanta takeyi tanata furta Kalmar shahada.

Hafeez naganin Iya Ladi baisan lkcin da ya kwala mata kira da k'arfi ba, a hnkli ta waro idanunta ganin Hafeez tsaye akanta yasa take ta k'ok'arin ganin ta tashi zaune amma Sam hakan yafaskara sbd wata irin hajijiya dake d'awainiya da ita, da sauri Hafeez ya duqa daf da ita. Iya Ladi babu abinda tafara furtawa sai Hafeezu yar k'unan bakin wake ce! Hafeez yayi sururu yana tambayar wacece yar k'unan bakin wake? iya Ladi tace" wannan bak'uwa taka da Kuka zo tare itace tayi sanadiyyar gobarar da tashi dasu Alhaji da Hajiya domin naji lokacin da yarinyar take fadin sai takashe Ku kai da Rafee'atu atunaninta kana cikin gdan shine tabude silindan gas yayi ta linking daga bisani ta kyasta ashana nayi k'okarin gudun Na sanarwa Hajiya abunda ke faruwa amma Allah bai bani iko ba har wannan yarinya tasamu galabar kona gdan, take anan Hafeez yamiqe tsaye yafara ja da baya yanafadin no! no!! no!!! Suhailat karkimin haka kinsalwantar dani Suhailat kin ha'inceni kin durqushemin rayuwa kin kassarani kin maidamu marayu no Suhailat dama abunda kike shirin aikatawa kenan? dana sani daban fita a gdan ba, yana fadin maganar yana jada baya har ya isa jikin bango nan yashiga gwara kansa yanafadin nayi nadamar saninki arayuwata natafka babban kuskuren amincewa wata diya macce bayan Rafee'a  na,Suhailat kinci amanata bazanyafe miki ba! Bazantaba yafemiki ba! Kincuceni kincutar da Balkisu  inallillahi wa'ina ilaihiraji'un, ganin bashida niyyar daina gwara kansa a bango Balkisu tazo da gudu ta rungume shi tanafadin yaya kadaina plss kadainan dakyar da taimakon Dr  suka samu Hafeez yadaina amma sai wani irin numfashi yake fiddawa yanata sambatu, Iya ladi dake kwance tace Dan Allah Hafeezu karka kafadamin cewa su Hajiya da Alhaji sunrasu?. Hafeez ya sadda k'asa yace iya Ladi sai dai mu sami dangana domin kuwa Suhailat ta aikatamin abunda har namutu da tabonshi zankoma ga mahallicina, nayi kuskuren amincewa diya macce a ynxu bayan Balkisu babu wata diya macce da zansake yarda da ita Suhailat kin ha'inceni bazan taba yafemiki ba.

Iya Ladi najin kalaman Hafeez nan take tafahimci cewa su Hajiya Allah yayi musu rasuwa, take anan tafirgice jikinta yaqara tsanantawa babu abinda take furtawa sai neman gafara.

Kafin wayewar gari kuwa iya ladi tace ga garinku(iya Ladi ta amsa kira)  Hafeez da Balkisu nasamun labarin rasuwar iya Ladi take anan sukaje komai yadawo musu sabo.
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [9:00AM, 7/18/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode1⃣5⃣

Tashin hankali wanda ba'a samishi rana, a yaune Alhaji Kabeer musa wato mahaifi ga suhailat yayi dirar mikiya acikin garin borno bai wani sha wahala ba kasancewar Alhaji Kabeer da abokin Hafeez yaxo dashi tundaga taraba state kasancewar abokin Hafeez din yasan gdansu shine musababbin dayasa Alhaji Kabeer ya tisa k'eyarsa agaba.

Da isarsu barno kai tsaye gdansu Hafeez suka nufa, koh da shigarsu Cikin anguwar Ahmed(abokin Hafez)ya nuna masa gdnsu Hafeez kafin ma driva yasamu damar parkin motar  tuni Alhaji Kabeer yabude murfin motar yafito yanufi hanyar gdan da aka nuna masa, mazan dake zazzaune daga gefen gdan yan karban gaisuwa tuni ma'aruf(qanin alhaji abdullahi) yataso daga cikinsu don tsaida wannan mutumin dake k'okarin tunkarar gdan da yakasance a kulle, gashi dai daganin mutumin kasan cewa baicikin natsuwa. dan haka da sauri suka isa kofan gdan atare, ma'aruf nazuwa yafara tambayar wannan mutumin yace" mallan lafiya kuwa? Naga kataho a hargitse kana qoqarin bude wannan gdan gashi dai naganka amma babu alamar dangantaka ko sanayya atattare da kai zan iya sanin ko kai waye"

Cikin zafin rai Alhaji kabeer ya dubesa yace"nikuwa nahada dangantaka da wannan gdan tunda yakasance ya'ta tana hannunku, uncle ma'aruf ya k'ufula sosai ganin cewa wannan mutumin yazo masa da rainin hnkli waye kuma yarsa? Da sauri uncle ma'aruf yasake jefa masa wata tambayar akaro na biyu" waye yarka kuma? amma dai ba'anan gdan ba? Alhaji kaber yace kwarai kuwa a wannan gdan ne koh ba nan bane gdansu Hafeez Abdullahi.

Kamar daga sama sukaji ance eh nan ne, da sauri sukajuya a tare don ganin mai basu amsa.
        Hafeez ne tsaye rungume da hannayensa a kirji, fuskan nan tashi tayi fayauu tsakanin jiya da yau gabadaya Hafeez ya rame ya chanja kammanu' a hnkli yake tafiya kasancewar har ynxu bayajin qarfin jikinsa , qarasawa yayi wajan nasu yanuna daddyn Suhailat yace"koba kafadamin ba nasan cewa kaine mahaifin suhailat ko ba komai ga kammaninku nan yanuna, ka kasance mahaifin mai kisan kai azzaluma..

Da sauri dadyn Suhailat yadakatar dashi tahanyar nunashi da yatsa yace "kai Yaro dakata waya baka ryt din ambatarwa yarinyata wadannan munanan alkaba'in? "maza kaje kafito min da yarinyata" cikin tsananin fushI Hafeez yace tirrr da hali irin na yarka.

Ko dayake dama hausawa sunce juma'ar da zatayi kyau tundaga laraba ake iya ganeta,sannan dukk wata tarbiya tana farawa daga gdane sai dai ga dukkan alamu daga kai har yar'taka wacce kake tutiya da ita Sam babu wannan alamun atattare da ku.

Tuni hawaye masu ciwon gaske sun wanke fuskar Hafeez' Daddyn Suhailat ne yadakatar dashi tahanyar cewa "nace kaje kafito min da diyata ko kai kurmane?" Take anan ran Hafeez ya6aci gabadaya kamanninsa suka sauya, jaa da baya yakamayi cike da masifa yakewa Daddyn Suhailat bayanin dukkan abubuwan da sukafaru ta sanadin yartasa' Daddyn Suhailat najin wannan bayani tuni gume ya wankesa, sbd tabbas yasan yartasa zata iya aikata abunda yafi haka, sannan bashida ryt din da zaixo yatada husuma sbd Suhailat da kanta tafadamishi dukkanin abinda tayi niyyar aikatawa, take anan yaji wata irin nadama marar iyaka, cikin ransa kuwa fadi kawai yakeyi inama lkcin baya xai iya dawowa domin ya gyara kuskuren da ya tafka akan rashin bawa Suhailat ingantaciyyar tarbiya.

Mgnr da Hafeez keyice tadawo da Daddyn Suhailat daga dogon tunanin da yatafi" ae ina mai tabbata maka cewa saina dauki fansar ta'addancin da dabbar diyarka ta aikatamin domin tun sanda wannan al'amarin yafaru nake tunanin tayaya za'ayi naga mahaifin Suhailat domin nadauki tawa fansar dukk da cewa Suhailat tariga da ta mutu toh amma ko ba komai idan nadauki fansar abunda ta aikatamini zansamu sassauci.
      Da sauri kuwa Daddyn Suhailat yad'ago kai gamida cewa fansa Kuma? Wacce irin fansa? Hafeez yayi wani murmushi mai ciwo "yace fansar abinda ta aikatamin domin nayi alwashin sai na salwatar da rayuwar nata iyayen, sai kuma alhmdllh gashinan ka kawomin kanka.

Daddyn Suhailat najin haka ae da sauri yakoma gefen uncle ma'aruf yanafadin Subahanallahi Hafeez kasan abinda kake cewa kuwa? Hafeez ya turbune fuska yace tabbas nikuwa na san abinda nake cewa sai dai natabbata bazaka amincewa hakan ba har sai kaga nadauki mataki.

Uncle Ma'aruf ne ya dakatar da Hafeez daga munannan alqawarinsa, Hafeez kam yayi nisa sai sambatu yake yanafadin sai yakashe mahaifin Suhailat, mazan dake zazzaune cikin rumfa masu amsar gaisuwa sune suka taso Dan ganin abun yaqi qarewa.

Dakyar akasamu Hafeez ya dan sauqo sannan ya umarci Daddyn Suhailat daya bacewa ganinsa tunkafin yakira masa hukuma..sbd baya qaunar ganinsa balle jin sunan diyarsa.

Tuni Alhaji Kabeer yabar cikin garin borno.®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode1⃣6⃣

Alhaji kabeer sbd tsananin rud'ewa bai samu daman komawa da Ahmed ba, anan cikin garin borno ya barsa. Hakan ne yabawa Ahmed din damar zuwa yayi ma abokin nasa ta'azziya da jajen abunda yafaru, daga bisani kuma ya jasa gefe nan ne yayi masa bayanin dalilin zuwansa da yadda akayi yazo sannan Ahmed yad'aura da yimasa bayanin ko wacece Suhailat, kwarai da gaske Hafeez yayi matuqar mamakin jin lbri Suhailat wata irin nadama ce tadinga addabar zuciyar Hafeez take yaji gabadaya dukk yatsani kansa.


*Bayan Wata Daya*
Yan'uwa danginsu Hafeez babu yadda basuyi ba akan suna son tafiya da Balkisu tazauna a hannunsu amma Hafeez ya qeqasa qasa yanuna sam bai amicewa hakan ba, dole suka rabu dashi kowa Yakama gabansa.

Bayan kwana 2 Hafeez yasa aka gyara masa gdansu dake cikin federal lowcost chan suka koma shida Balkisu domin a cewar Hafeez baxai iya sake rayuwa acikin gdan da sukayi rayuwa da mahaifansa ba.

Dama ya lafiyar kura balle kuma anta6ota, wasu irin sabbi halaye Hafeez ya qirqirowa kansa gabadaya yakoma miskilin gaske. Gashi ynxu  kwatakwata Hafeez  baya yadda da kowa sannan idan kaga fara'ar Hafeez ko murmushinsa toh tabbas yana tare da Balkisu ne.


             ***
BURIN HAFEEZ a kullum shine yaga cewa ya bawa Balkisu ingantacciyar rayuwa kamar sauran yara, sannan tuni Hafeez ya qudurta a ransa cewa tunda yarasa Rafee'ansa toh babu shi babu kula wata d'iya macce, wannan  shine yabama Hafeez damar nunawa dukk wata diya macce k'iyayya 6aro-6aro matuqar bai had'a jini dake ba, hakan yasa tsakanin macce da  Hafeez kuwa babu komai sai tsantsar hantara da nuna zafin rai domin acewarsa "dukk halinsu d'aya"

Dukk irin yawan yan matan dake nuna tsantsar soyayyarsu ga Hafeez amma Sam basu fuska balle ya amince dasu, sai dai suyi ta nacinsu su gaji.

     Abangaran Balkisu kuwa bata da wani Buri da yawuce  taga cewa yayan nata ya mance da komai yayi auransa don fuskantar sabuwar rayuwa, amma hakan yafaskara. Gashi Hafeez kullum yana cikin kad'aici da damuwa Wanda hakan yayi sanadiyyar jawo masa hawan jini, tun Balkisu na nuna damuwarta har tasaba da kafiya irin na yayan nata.

 Amma sai dai Zuwa ynxu Balkisu taqudurta a ranta cewa sai ta rusa dukk wani BURI na yayanta akan qin son aure wanda atunanin likitansu ya basu shawaran cewa lallai Hafeez yana buqatar macce wadda zata kula da rayuwarsa sosai.

Wannan shawara ta Dr muh'd ta matuqar tsayawa aran Balkisu domin tasan abune mai wahalar yuwuwa kasancewar Hafeez yatsani macce arayuwarsa, shiyasa dukkanin wani tunaninta yatsaya akan taya za'ayi auran Hafeez yasamu yuwuwa?

Balkisu da kanta tasan cewa Hafeez baida wani BURI da yawuce yabata kyakyawar kulawa, ita kanta tasan hakan nafaranta mata rai dahakan kuma take alfahari dashi domin ya zama tamkar uwa uba a gareta sbd babu abinda tanema tarasa, toh amma sai dai ganin walwala da farincikin yayan nata yafi mata komai arayuwa.

"Dan haka kema Balkisu tunda ynxu kingirma kin mallaki hnklin kanki kinfahimci minene rayuwa yakamata kikawo sauyi da farinciki arayuwar tilon Dan' uwanki"  Balkisu tayi nisa sosai cikin tunanin ta, jitayi anata buga mata k'ofa da sauri tamiqe tanufi k'ofan ta bud'e.

Hafeez ne tsaye yasakar mata murmushi itama murmushintayi masa tace" yayana jiki yayi sauqi kenan?" Kyad'a mata kai yayi yace sosaima naji sauqi, ynxun nan ma Nadawo daga masallaci najiki shiru ne yasa nace bari inzo indubaki.

Balkisu tad'an waro idanu waje tace "Yaya anyi kiran sallah ne? Hafeez yadubeta da mamaki yace "kina nufin bakiji kiran sallah ba? Gashi kuma ga dukkan alamu idanuwanki basuyi kama dana mai bacci ba, aikin me kikeyi haka Wanda ya d'aukemiki hnkli?
   
        Ganin Hafeez yatsureta da tambaya yasa tayi saurin cewa Yaya bakomai kawai Allah baisa naji kiran sallah bane, kafin Hafeez yace wani Abu tuni Balkisu ta tajuya cikin d'aki da sauri tafad'a toilet.

Kasancewar lkci yaqura alwala kawai tayi tafara gabatar da sallah.
   Balkisu tajima zaune bisa sallayah sai jero aduo'i takeyi tanamai roqon Allah yashige mata gaba Ya kuma bata ikon cika alqawarin da tadauka nakawo farinciki a rayuwar d'an uwan nata.


"Cigaban lbrin"

®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [2:40AM, 7/21/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode1⃣7⃣

Haka rayuwa taciga da kasancewa, a kullum Balkisu bata da wani tunanin da yawuce tayadda za'ayi auren yayan nata yakasance? Wacce hanya zatabi? wazata tunkara da matsalarta? Gashi dai Hafeez baya bari takula qawayenta balle tasamu wacce zatayi shawara da ita don nemawa kanta mafita.
      Shiyasa a kowanne dare yakasance  Balkisu bata iya runtsawa, kullum tana mai miqa wuya da neman taimakon ubanji dan haka takai kukanta ga mai kowa mai komai.

       **        **        **
Yau tsawan sati d'aya kenan Balkisu na ziryan zuwa gdansu Meena amma kullum bata samunta,(Burin Balkisu shine taga cewa ta taimaki Meena, amma ga dukkan alamu Meenah a tsorace take da Balkisu shiyasa take gudun dukk wata hnya daxata hadasu.)

Yau yakasance ranar Asbar, Wanda hakan yayi dai dai da Balkisu bata da lectures dan haka tun qarfe bakwai na safe tashirya tsaf kafin Hafeez yafito kasancewar tasan qa'idar sa dukk weekend sai 11 yake fitowa dan haka tayi amfani da wannan damar tafice tanufi gdansu Meena.

Balkisu na isa qofar gdansu Meena hakan yayi dai-dai da fitowar ta daga cikin gdnsu fuskar nan ta ta sha6e-sha6e da hawaye ga hannunta d'auke da bokatin alala, Balkisu naganin haka tayi saurin fitowa daga cikin motarta gami da kiran Meena! Meena da sauri tawaiwayo don ganin mai kiranta, wacce tayi tsammanin kuwa ita tagani dan haka ta tsaya kmr wacce aka shukata.
      Dasauri Balkisu ta rufe motanta ta isa ga Meena cikin muryan jajenta Balkisu tace" haba Meena mai yayi zafi haka a kullum nazo bana tarar dake sai kace wacce keqoqarin cutar dake look Meena yakamata kiyarda dani wlh Burina shine kawai inga cewa nataimaka miki sbd nariga nadauki alqawarin hakan"! Sadda kai qasa Meena tayi sannan ta d'ago takalli Balkisu da wani irin murmushinta mai ciwo, a hnkli Meena taja wani gauran numfashi sannan tace" tabbas baiwar Allah nagode da dukk wani qoqarinki akaina sai dai inaso kisani cewa bana buqatar taimakon kowa, plss naroqeki ki janye qudurinki akaina sbd dukk yadda kikaso haKan baxai faruba sbd wasu dalilai dasu ka kasance sirriina Dan haka na roqeki  plss kiyi nisa daga cikin rayuwata gashi ina matuqar ganin girmanki" dasauri Balkisu ta tari numfashinta tace" plss Meena yakamata ki yarda dani inaso kisanar dani dukkan lbrinki sbd hakan ne kad'a xaibani damar sanin koke wacece da kuma yadda zansamu sauqin taimakawa rayuwarki domin jikina yajima yanabani wani abu daban..

Meena tagoge d'an guntun hawayen dake qoqarin zubo mata batare da takoma kallon Balkisu ba tajuya bayanta gami da cewa"na fad'amiki tun a lkcin baya cewa sanin lbrin rayuwata babu abinda zai qareki dashi nidai shawarata agareki kijanye dukk wani burinki nason taimakawa rayuwata nagode" Meena nafad'in haka tad'aura bokatin alalarta a kai taratsa gefen Balkisu tawuce.

Balkisu tsayawa tayi sororo tana tunanin kafiya da taurin kai irin na Meena, "gashi bansan dalili ba a kullum zuciyata naqara azalzalata akan lallai na taimaki Meena, sai dai kash ga dukkan alamu Meena bazata ta6a bani had'in kai ba.

Nan Balkisu tashiga tunanin taya za'ayi tasan lbrin Meena, gashi dai tasan cewa dukk yadda taso taji  lbrin Meena baxata ta6a fara tunkarar Yagana ba.
     Cikin mota Balkisu tashi tazauna d'aukara kanta tayi bisa sitiyarin motan gabad'aya tunaninta ya kwance babu abinda take tunani face mafitar wanda zata tunkara.

Kmr wucewan wasu yan'mintina Balkisu tad'ago da kanta da sauri wani irin murmushin farinciki tasakar wa kanta da sauri tace yess! Wannan shine kad'ai mafita, wuta tabawa motarta da sauri tafice a layin ta hau titi.
      Baifi tafiyar minti 2 ba tayi parkn motarta gefen hanya da sauri tafito ta tsallaka titin tanufi daya site din.

Wurin Baba mai shayi tanufa, ko da isarta bata iske shi ba wasu yan samari guda hud'u ta iske sunata firar kwallo(ball) da sallama Balkisu ta isa garesu, gabad'aya suka amsa mata, cikin natsuwa Balkisu ta gaishesu bayan sun amsa sannan tace Dan Allah ina Baba maishayi wnda ke sai da shayi wurin nan? Daya daga cikinsu yace Allah sarki baba zakiru mai shayi kike nufi? Ae yau tsawon sati d'aya kenan bai fito gurin sana'a ba sbd ciwon qafa yasashi agaba.
     Balkisu tayi jimm! Tana jinjina al'amarin cikin ranta, chan tace Allah sarki Dan Allah koh zan iya sanin gdnshi?
Wanda keyi mata bayanin yace eh ae bbu nisa. Nan yyi mata kwatance.

Balkisu tayi musu godiya sannan tanufi motarta tajuya zuwa inda akayimata kwatancen, Balkisu batayi mamaki dan ganin cewa layi daya suke da su Meena ba, sai dai Mallan Zakirun gdnsa nafarkon shiga cikin kwanar, wanda sukuma Meena gdnsu nad'anda nisa tsakaninsu.

Gdan da wadannan samarin suka kwantanta mata nan tanufa, shigatayi kaitsaye da sallamarta. Wata mata ta tarar tsakar gdn tana sassaqa wani itace dagani kasan magani ne, da sauri matar tadubi Balkisu cikin nuna rashin sani ta amsa sallamarta sannan tasaki fuskarta gami da cewa "sannu da zuwa baquwa iso daga ciki", Balkisu tayi farinciki da hakan ganin yadda yar dattijuwar matar ta tarbeta.
    Shimfid'amata tarbuma tayi sannan ta umarceta da tazauna, Balkisu nazama tagaida dattijuwar matar cike da ladabi.

Cikin fara'a kuwa ta amsa sannan tace "sai dai bangane fuskar ba?" Balkisu tayi murmushi tace hakane Inna dama nasamu lbrin Baba zakiru bashida lafiya shine nazo naduba jikin nashi, murmushi tayi tace Allah sarki sannunki kinji angode sai dai mallan din baya gda yatafi ganin likitan gargajiya anan wani qauye sai zuwa anjima da yamma zai dawo, Balkisu tagyad'a knta tace toh shknan badamuwa Allah ya bashi Lpy ni zanwuce gobe in Allah yakaimu zandawo. Hakanan tafice a gdn tanufi gda tana mai addu'ar Allah yasa tasamu abinda take nema agarshi.
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [7:04AM, 7/21/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode1⃣8⃣

Washe gari da sassafe Balkisu tafito tsaf cikin shirinta Na baqar doguwar jallabiya da d'an guntun hijabinta pink colour, dukk da cewa batayi wata doguwar kwalliya ba amma tayi matuqar kyau. Falo ta nufa sannan takira Daniel tasanar dashi irin brkfst din da xai had'a wa Hafeez, sannan takoma ta sanar dashi cewa bada ita zai had'a brkfst din ba. Hakanan Balkisu tafice batare da taci komai ba, domin a daren jiya da zarar Balkisu ta rufe idanunta Meena kawai take gani dan haka dakyar taga gari ya waye mata.

Da fitarta kuwa bata nufi ko ina ba sai Bolori anguwansu Meena, "wannan karon Balkisu bata nufi gdnsu Meena ba k'ofar gdan Mallan Zakiru ta tsaya,
      A hnkli tafito daga cikin motarta ta nufi gdn Mallan zakiru, cikin zaurensa ta tarar dashi zaune yanata karatun al-qur'ani, jiki a sanyaye tayi masa sallama. Mallan zakiru na kaiwa qarshen ayaa! Ya tsaida karatunsa gami da amsawa Balkisu sallamarta cikin sakin fuska

Fuskan nan d'auke da fara'a yace baiwar Allah shigo daga ciki, Cike da qarfin gwiwa Balkisu tashiga cikin zauren, tana qoqarin zama a qasa kenan mallan Zakiru yace haba ke kuwa yazaki zauna a qasa da wayonki? Balkisu tayi murmushi tace laaah! Baba wlh bakomai, Mallam Zakiru yace a'a ba'ayi haka ba d'an dakata, nan yashiga kwalama uwar d'akin nasa kira bayan ta amsa yyi mata umarnin takawo tabarma, cikin qanqanin lkci kuwa sai gata tafe da tarbama. Da zuwanta ta shimfid'awa Balkisu tabarma sannan suka gaisa amutunce Wanda bayan sungaisane daga bisani takawo mata ruwa sannan ta tashi takoma daga ciki.

Balkisu taji dadin karamci irin na gdn Mallan Zakiru hakan kuwa yaqara bata qarfin gwiwar tinkararsa da tambayoyin da take qunshe dasu, Dan haka byn ta jajanta mishi ciwon qafansa, yace da sauqi, taqara daurawa dacewa Allah yabashi Lpy yasa kaffarane. ameeeeeeeen yace yanamai yin murmushi

zauren yayi shiru na wasu yan mintoci can Mallan Zakiru yace "ae jiya mai d'akina take sanar dani cewa nayi baquwa tayi tayi mini misalinki amma Sam nakasa ganewa sbd Sam bantaba tsammanin kece ba amma ynxu dana ganki natabbar lkci daya cewa kece kika zo nemana jiya, Balkisu tayi murmushi tace Allah sarki, eh wlh haka ne nice
      Mallan Zakiru yadubi Balkisu da kyau yace Baiwar Allah lafiya kuwa?Balkisu ta gyara zamanta tafuskanceshi dakyau tace tabbas lfy dama naxo inyimaka wata yar tambayane, Mallan Zakiru yajinjina kansa yamaimaita abunda tafada "tambaya"?

Balkisu tagyad'a kai alamar eh, Mallan zakiru yace toh Allah yasa nasani.
     Balkisu tad'an ja numfashi a hnkli sannan tace dafarko dai sunana Balkisu Abdullahi Shariff nazone inaso inyimaka wata yar tambaya akan rayuwar Meena inhar kasani.


Sbd tun ranar da muka hadu da yarinyan nan Allah yasamin tausayinta araina naji zuciyata na azalzalata a ko da yaushe akan nataimaka mata, toh amma sai dai yarinyar kwata kwata taqi amincewa dani balle ta yarda dani na taimaka wa rayuwarta, da ita nake kwana nake wuni araina Dan Allah idan kasan wani abu dangane da rayuwar yarinyan nan toh ina roqonka da kasanar dani, wlhy bani da niyyar cutar da ita hasalima inason taimaka matane.

Mallan zakiru yayi murmushinsa cike da dattijantaka, sannan yace" tabbas yarinya bakiyi kama da miyagun mutune masu cutarwa ba hasalima nasan waye mahaifinki marigayi Alhaji Abdullahi, Balkisu najin haka tayi murmushi farinciki tace eh hakane.

Mallan Zakiru yace tabbas zanfadamiki ko wacece Aminatu, amma da sharad'i guda daya" Balkisu ta dan muskuta kadan tace Baba kafadi kowanne sharad'i ne insha allahu zanbi sharud'anka. Mallan zakiru yace madallah, dama sharadin nawa shine inaso kimin alqawarin cewa dukk wani abu dakikaji dangane da lbrinta hakan bazaisa kijuya mata baya ba??

Balkisu tace insha allahu nayimaka alqawari, Mallan Zakiru ya jinjina kansa sannan yadubi Balkisu......
®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [1:13PM, 7/22/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode1⃣9⃣

Mallan Zakiru yaja dogon numfashi mai cike da alhenin tuna abinda yajima yana damun zuciyarsa, a hnkli ya sake kallon Balkisu sannan yace "Wato mahaifin Aminatu Mallan suleman Wanda akafi sani da Sule, abokina ne shi tun tsawon shekara ashirin da suka gabata. Asalinsu yan Gwaza ne nan cikin jahar borno, Sule yakasance aminina tun awajen sana'armu ta gyaran kekuna da mashin anan babban get na Monday market, Sule nada mata daya Rabi wacce itama yar garinsu ce da aurensu atare muka gansu. Mallan Sule yakasance mutun mai son mutane gashi Allah yadaura masa son yara, sai dai kuma babban abunda ke damunsa shine yadda suka dauki tsawon  shekaru goma sha biyu amma Sam Rabi ko 6atan wata bata ta6ayi ba.

Hakan yasa Sule yayi tunanin qara aure, Rabi kuwa Sam bata tashi hnklinta ba kasancewarta macce mai sanin yakamata Sam batada yawan hayaniya, ana cikin hakane Sule ya auro Yagana, Allah cikin ikonsa Yagana nashiga cikin gdan baifi da wata uku ba sai ga d'an qaramin cikinta ya baiyanna.
        Ana cikin wannan hali sai ga Rabi itama cikin hikima da kyauta ta ubangiji sai gashi itama tasamu nata rabon, wai karkaso kaga farinciki awajan Sule.

Abangaran Yagana kam abun ba haka yake ba, domin babu irin masifar da batayi ba wai Rabi munafukace dama tana haihuwa shine dantaga tasamu ciki wato itama shine takwaso nata sbd gasa.

Haka nan kwanaki sukayi ta shud'ewa yayin da Yagana ke azabtar da Rabi batare  da sanin shi abokin nawa ba,
       Gashi a kullum Yagana nayimata barazanar zata kasheta a dukk lkcin da ta kuskura tasanar da mijinsu irin abubuwan da take mata.

   **
Bayan wata tara Yagana ce tafara haihuwa tasamu d'anta namiji aka sha biki, bayan wata biyu itama Rabi Allah yasauqeta lafia inda itama tasamu diyarta macce wato Ameenatu.

Haka nan sukaci gabada zama na rashin jindadi mussaman ma ita Rabi wacce take hak'uri da hallayar Yagana.

Dukk wani hali na qunci da azabar da Rabi ke sha abokina Sule sam bashi da masaniya akai".
   Ana cikin hakane watarana muna cikin tsaka da aikin kanikan cinmu wani bawan Allah yakawo mana gyaran mota, Wanda mukuma bamu fiye son gyaran motociba sbd bamu kware da gyaranta ba, amma awannan ranar cikin ikon Allah sai wani bawan Allah yakawo mana gyaran motarshi Sule ne yakarba yadan soma gwada gyaranta.

Dakyar Sule ya gano inda matsalar motar take, wato lagireto din motan ne yasamu mtsl dole Sule yaje yanemo "jak" wato abin dake d'aga mota, hakanan yasamu nadan taimaka masa yasa jak din motar tadantashi daga bisani kuma yasamu yashiga karkashin motan, Suleimanu na cikin tsaka da aikinsa wannan motan tayi kuskuran fadamishi a kirji,. 'Mallan zakiru yadan goge hawayen da yaxubo masa sannan ya cigaba da cewa" dasauri ma'aikatan da muke wajan muka kawo mishi taimakon gaggawa nan da nan muka samu muka d'aga motar daga kirjinshi, nan fa muka tari texi domin mukaishi asibiti amma kankace wani Abu rai yayi halinsa Allah yakar6i ran abinsa.

Awannan lkcin Ameena naqarama bata mallaki hanklin kanta ba, ayayin da d'an yagana wato bakura shima yana qarami ga Yagana da tsohon ciki. Haka wannan mummanan al'amari yafaru da mu, domin a gsky a wannan lkcin na jima banji irin mutuwar da tashigeni ba kamar ta Sule Wanda hakan yasa tundaga wannan ranar banqara jin sha'awar wannan sana'a ba wannan shine musabbabin dayasa nakoma sana'ar sai da shayi.

Mallan Zakiru yadan yi shiru cike da jimami yadubi Balkisu yace " Balkisu nayi rashin babban amini. Balkisu ta jinjina kai  gabadaya tausayi yacikata.

Mallan Zakiru yacigaba da mgn, " wato bayan sati biyu da rasuwar Sule sai ga wani sabon tashin hnkli Yagana taxo dashi wai ita a dole sai anraba gado tunda tanada d'a namiji ga kuma wani cikin ae tasan dukiyarta sai tafi yawa, awannan lkcin kuwa Sai da yayan Sule yashiga cikin mgnr.
       Nan ne yake tambayar Rabi ko ta amince araba gadon ynxu ko kuwa sai yaransu sundantaso, nan Rabi ta nuna ita dai abarshi zuwa lkcin da yaran suka mallaki hanklinkansu inyaso a wannan lkcin abawa kowa nasa. Ae fa nan Yagana tayi taya6awa Rabi maganganu marassa dadinji.
Ranar wata alhamis ne muka sami wani mummunan lbri Wanda ya girgiza al'umar dake cikin wannan anguwa tamu.

Domin kuwa Yagana cikin dare ta tashi takashe d'anta da hannunta sannan ta yayyaga rigar jikinta tayiwa kanta wasu tambari naciwuwuka tamkar ansameta an yayyageta da wuqa. Ganin tasamu nasara yasa tanufi d'akin Rabi ta ajiye gawar yaron sannan tafara ihuun neman agaji dasauri mutanen anguwa suka farka, kowa yyi shiru yana sauraren inda wannan ihun kefitowa.

Bayan kowa ya fahimci cewa a gdansu Yagana ne ake wannan ihun hakan yasa jama'ar anguwa kowa yanufi chan dan ganewa idonsa.
   Koh da shigarsu cikin
Gdan gabadaya jikin Yagana a yayyanke da wuqa ga kuma yaro kwance cikin jini, ae dasauri suka shiga don axaton jama'a barayine suka shigar musu. Amma da shigar jama'a cikin d'akin sai ga Rabi da wuqa a hannu dukk tarikice yayinda ita kuma Yanaga ke ta neman ceton jama'a.

Ganin mutane suntaru yasa Yagana tacigaba da kuka tanafadin "shikenan Rabi kincika burinki naganin kin hallaka d'ana sbd kina baqin cikin gadon da wannan yaron zai samu, Hakanan Yagana takawo lbrin qarya tasanar da jama'a cewa Rabi ce takashe mata d'a sannan itama tayi qoqarin kasheta wai sbd gado.

Rabi kam mamakine ya baiyyana qarara a fuskarta, wasu irin hawaye masu ciwo ne suka dinga bin kuncin Rabi tunfaruwar wannan al'amarin kuwa Rabi ko uffan takasa Cewa sai hawayen kawai datake ta xubarwa.... Kafin wayewar gari kuwa yan sanda suka zo sukatafi da Rabi police station Wanda daga baya kuma aka kaita koto bisa hujojin qarya aka kai Rabi gdan yari amatsayin daurin rai da rai.

Haka wannan mgnr takarade cikin anguwa da sauran kewaye, wasu sun yarda jin cewa Rabi tayi kisan kai yayin da wasu kam basu yarda ba, sai dai Wanda sukafi yarda sune sukafi rinjaye. Hakan kuwa yasa mutunen anguwa suke nuna halin kyama da gujewa Aminatu hakan yayima Yagana dadi tasamu yadda take so.

Bayan wasu yan kwanaki da faruwar wannan rikitaccen al'amarin Yagana tahaihu tasami diya macce, dukk da cewa ba haka taso ba.

Dukk wata tsangwama da kyarar da Yagana keyima mahaifiyar Amina shine tadawo dasu kan Amina, inda take gana mata azaba kala kala tun Amina batayi wayo ba har ta girma ta fahimci duniyar datake ciki, sbd mutanen anguwan nan tamu gabadaya suntsaneta suna ganin cewa itama inta girma halin uwarta zatabi na kisan kai

Mallan Zakiru ya fyace majina sannan yashare hawayensa yadubi Balkisu yace " kinsan wani abun mamaki kuwa"? Balkisu ta girgiza kanta tace a'a baba sai kafada.®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode2⃣0⃣

Mallan zakiru yacigaba dacewa "wato yadda naga Aminatu nashan wahala tun tana yar qarama hakan yasa nayi tunanin cewa bari ind'aukota tadawo hannuna da zama, kasancewar nima har wannan tsufan yariskeni mai d'akina bata ta6a haihuwa ba.hakan yasa na shawarci mai d'akina akan mgnr d'auko Aminatu, hakanan itama ta nunajinddinta akan shawaran dana yanke. Shiyasa da wani yammaci nashirya naje gdan, inazuwa gdan natarar da Yagana nadukan Aminatu kmr wadda Allah ya aiko, da sauri na k'waceta daga hannunta bayan haka ban tsaya sauraren komai daga gareta ba nanuna mata cewa inason zantafi gdana da Aminatu takoma chan da zama.
       Kafin ma naqarasa abinda nakeson cewa Yagana tabuga wani uban salati nan tashiga kurma ihuu tanafadin "yau nashiga ukuuu ni Yagana wato Zakiru irin cin amanar da zakayiwa babban amininka kenan? Ana cikin haka sai ga jama'ar cikin unguwa suntaru danjin bahasin ihuun da takeyi, nan fa Yagana tashiga basu lbrin qarya wai zuwa tayi ta iskeni tsakar gda ina qoqarin yiwa Aminatu fyade wa'iyaxubillah"  wato Balkisu tunda nake arayuwata ba'ta6ayimin sharri Wanda ya girgizani ba kmr Wanda Yagana tayimin.

Jama'ar cikin unguwarmu kowa sai alawadai da irin halina yakeyi Wanda yagana ce taqaqaba minshi, wani irin tashin hnkli nashiga marar misaltuwa Dan haka cikin sanyin jiki najuya da nufin natafi gda amma Yagana ta ziga samarin anguwan nan tamu dasu rakani gda da ihuuu! Haka kuwa akayi yara da yan samari suka bini sunatayimin ihuuu wnda hakan yyi sanadiyar nafarajin wani irin hajijiya na yawo dani cikin rashin Sa'a inatafiya qafata ta kufce tafada cikin wani rami dakyar nasamu nacireta gabadaya qafartawa takumbura sbd ramin qarami ne, toh fa tundaga nan ne nahadu da ciwon qafa. Daga rana irin ta wannan lkcin ko gaisuwa bata shiga tsakanina da Aminatu bawai Dan inatsoran Yagana ba a'a sai dai inatsoran sharrin da Yagana zatakoma qaqabamin ko kuma Aminatu.

Tabbas wasu sunfara fahimtar hali irin na Yagana shiyasa dukk rintsi dukk wuyan da Amina Zatasha babu mai kai mata d'auki gudun kar tayiwa mutun sharri domin Yagana tadaurawa mutum sharri ba komai bane agurinta. Shiyasa kowa ke gudun taimakawa Amina.

Ana cikin hakane Yagana tatsiro da sabon iskaci na azabtar da Aminatu, da farko idan ta daura mata talla dukk abinda Aminatu tayo ciniki sai yagana tace bazata sammata kudi ladan guminta ba ko tasiyamata wani Abu sbd Amina hayatakeyi acikin gdanta, hakan yasa dukk randa Amina batayi ciniki ba toh ranar awaje zata kwana sbd batayi ciniki sosai ba balle aciri kudin hayarta.

Dukk irin sanyin da akeyi akan Aminatu yake qarewa, sannan dukk wani aikin gdan itakeyin shi kama daga wanke-wanke shara wankin Yagana da na yarta girki zuwa wasu aike kuma komai nisan waje Aminatu da qafa zataje babu Wanda ya isa yataimaka mata, idan Amina tasamu tayi wad'annan ayyukan shine takesamu taci abinci a dukk lkcin kuma da Aminatu bata samu damar yin d'aya daga cikin ayyukan gdan ba toh awannan ranar batada abincin rana ko nadare koda kuwa rashin lafiya tayi.

Mallan Zakiru nafadin Haka yafashe da kuka, Balkisu ce ma tayi qarfin Halin bashi hkri. Mallan Zakiru yadubi Balkisu yace "wlh Balkisu tunda nake arayuwata bantaba ganin mata marar imani kmr wannan matar ba, yarinya ace ita da gdan ubanta sannan ace wai tana haya sannan abincin da zataci sai tayi aikatau a gdansu, wannan al'amari na matuqar damun zuciyata.

Gashi Aminatu tun da girma yarisketa yan samari sukafara zuwarmata manema auranta amma Yagana sai tayi tsaye tace musu ae yarinyar babu abinda ta iya sai kisa da yawace yawace, hakan yasa dukk samari suka fara gudunta sbd ko ba komai tarihi yanuna cewa mahaifiyar Aminatu na gdan Yari.

Mallan Zakiru yyi murmushi yace kinji wannan shine d'an taqaitaccen tarihin Aminatu iya Wanda nasani, sannnan abinda yasa kikaji dazu na kafa miki sharad'in kada kigujeta shine kar labarin Yagana ya wargazamiki lissafi kema kigujeta kamar saura.
     Balkisu ta share hawayen da yagama wanke mata fuska tace " baba ko kadan babu haka acikin raina dukk da kasancewata yarinya mai qarancin shekaru hakan bazaisa na Gaza tunkarar Yagana ba, domin a ynxu danaji lbrin Meena sai naji gabadaya wutar son taimaka mata nadad'a ruruwa acikin raina.

Baba Sam kada kadamu nayi alqawari insha allahu sai na ku6utar da Meena daga cikin wannan qangin rayuwan sbd a ynxu wani irin Tausayinta ne yaqara tasiri acikin zuciyata. Mallan zakiru yace "nikuwa insha allahu zantsayamiki zankasance dake a dukk lkcin da kika buqaci taimakona sannan zandage dayimiki addu'an samun nasara ba dare ba rana. Balkisu tayi murmushi mai sauti gabadaya farinciki ya lullumeta dajin kalaman mallan zakiru.

Bayan sungama tattaunawarsu Balkisu  tamiqe sannan tadubi Mallan Zakiru tace "toh baba ni zan tafi gda dukk yadda ake ciki insha allahu zanke sanar da kai" nan fa mallan Zakiru yayi tasawa Balkisu albarka.

Hakanan Balkisu tanufi gda zuciyarta acinkushe babu abinda take sai tunanin yadda al'amarin zai kasance mussaman abangaran Yayan nata, dan haka a ynzu a shiryetake da ta tunkaresa da dukkanin buqatunta Dan ganin ta tarwatsa dukk wani BURI Na yayanta Dan kawo canji acikin rayuwarsa.
® NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode2⃣1⃣

Balkisu na isa gda qarfe sha biyu na rana na bugawa dai-dai. dan haka sashenta kawai tanufa kai tsaye, koh da shigarta saman gadonta tahau sharaff! Takwanta gabad'aya dukk ji takeyi tagaji. Chan tayi nisa cikin tunani sai jitayi cikin ta na mataguqi alamar yunwa na nuqurgusarta da sauri ta tashi tafice daga d'akin dinning area tanufa tea tahadawa kanta mai kaur sai soyayyan kwan da tad'iba da plan10 falo takoma taxauna sannan tafara bawa cikinta hakkinsa.

Balkisu Na daf da kammala brkfst dinta  sai ga Hafeez yafito daga cikin d'akinsa sanye da farar jallabiya d'akin Balkisu yayi niyyar zuwa har yanufi hanya kmr ance yajuyo sai hango Balkisu yayi zaune cikin falo, wata irin sassanyar ajiyar zuciya yayi wanda hakan yajawo hnkli Balkisu tajuyo, Hafeez tagani tsaye sakar masa murmushi tayi tana fadin Yaya har kafito?

A hnkli Hafeez yaqarasa cikin falon  tsare Balkisu yayi da idanunsa sannan yace Balkisu inakikaje ne tundazu dana farka nanufi d'akinki amma bakya ciki? Kuma nalura dake acikin kwanakin nan kina yawan fita ina kike zuwa?? Balkisu shiru tayi gabadaya tarasa amsar da zata bashi.
        Ganin bata da niyyar cewa komai yasa Hafeez yanemi waje yazauna qara kallon Balkisu yayi fuskan nan ba alamar wasa yace "ke badake nake mgn bane kinmin shiru?

Balkisu gabanta ne ya shiga dukan tara tara bama uku uku ba sbd kalaman da bakinta ke qoqarin furtawa batasan yadda yayan nata Hafeez zai d'aukesu ba, a hnkli tad'ago kanta tadubi Hafeez da raunatattun idanuwanta cike da faduwar gaba Balkisu tafara mgn cikin sanyin murya
    "Yaya kagafarceni amma yazama dole ne intunkareka da wannan mgnr dukk da bnsan da wacce irin siga zaka kalli batuna ba, Hafeez yayi murmushi gabad'aya jiyayi Kansa yakulle domin kuwa yasan cewa qanwar tasa da wani abu mai muhimmanci take tafe, tunanin haka ne yasa Hafeez yadubi Balkisu cikin sigar lallashi yace oyaa qanwata go on ke nake saurare kifadamin dukkanin damuwarki namiki alqawarin zan magance miki ita matuqar bata fi qarfina ba.

Da sauri Balkisu tace yaya insha allahu baifi qarfinka ba, sannan zanfadamaka damuwata amma matuqar zaka biyamin buqatartawa nikuma nayimaka alqawarin zanyimaka dukkanin  wani Abu dakake so matsawar bai keta addini ba, Hafeez ya jinjina kansa ganin cewa qanwar tasa seriou take mgn yasa yayi saurin cewa OK jst tell namiki alqawarin biyamiki dukk wata buqatarki matuqar bai keta addini ba. Balkisu tayi murmushi tace yayana bai sa6a addini ba asalima addini ya horemu da aikatashi kuma bayan haka idan har ka aikata hakan nikuma xankasance cikin farinciki har abada.
     Jin Balkisu tace haka yasa Hafeez yace "okay sanar dani inajinki matuqar zaisaki farinciki.

Balkisu tace "tunda kamin alqawari zanfadamaka sannan karkayi tunanin in nafadamaka zaka bijirewa buqatartawa, cike da qaguwa Hafeez yace "go on kenake saurare.

Miqewa tsaye Balkisu tayi gamida tad'auke dubanta ga Hafeez a hnkli tace yayana inasone Dan Allah ka janye BURINKA nacewa bazaka tabayin aure ba, sbd ina buqatar ganin wata diya macce a cikin gdan nan matsayin matarka hakan zaisani farinciki matuqa Kuma.....! Kafin Balkisu taqarasa abinda take son fadi tuni Hafeez yataka mata burki ta hanyar daka mata tsawa keeee!! Balkisu rufemin bakinki awajan kinsan mekike fada kuwa? Ina mai gargad'inki dakiyi saurin janye wannan buqatartaki kicanja wata domin ina tabbata miki cewa wannan din bata samu shiga ba.

              Da qarfi Balkisu ta fashe da kuka kmr wacce aka aikowa mutuwa, Hafeez kam gabad'aya jiyayi hanklinsa yatashi domin azahirin gaskiya bayajin zai iya biyama qanwartasa wannan buqatar domin kuwa tsakani na da macce sai idanuwa "cewa Hafeeez" wannan kuka da Balkisu keyi gabadaya yatada hnklin Hafeeez da sauri ya qarasa gareta yace "kiyi shiru plsss bnson kisawa kanki ciwon kai, Balkisu tajanye hannunta daga riqon da Hafeez yayi mata
       Shiru Hafeez yayi ganin qanwartasa fushi take dashi yasa ya sassauto murya a hnkli yace "plsss Balkisu u have to understand cewa bana son aure bana buqatar kasancewa da kowa, nan gaba kad'an aurenki zakiyi  hakan ma kawai ya isheni da zarar kinfara hayayyafa yaranki sun isheni sani farinciki sannan idan kinduba Bal....dasauri Balkisu tadakatar dashi cikin muryan kuka tace yaya wannan ba reason bane sbd kaikanka kasan cewa bani da saurayi hasalima baka bari Na kula kowa toh wakake tunanin zai aure ni har wadannan BURi naka sucika Wanda ka lissafo ynxu?

Da sauri Hafeez yace nima sanin kanki ne cewa banida wacce nakeso waxan aura waxan so? Dasauri Balkisu tace wlh yaya believe me idan nacemaka nasamo maka mata nagartacciya Na yarda da tarbiyyan yarinyar akwai nutsuwa da hnkli attare da ita, dasauri Hafeez  yakauda knsa hace "a ina kikasanta?" Balkisu murmushi tayi gamida cewa tabbas Yaya zaka Santa amma baxan fadama ko ita wacece ba har sai ka amincewa buqatata, Yaya Hafeex karkamanta cewa kaine uwata Kaine ubana Ashe kenan dama akwai watarana da uba zai kasance yabar yarsa cikin maraici da quncin rayuwa?

Jin Balkisu tace haka gabadaya hankli Hafeez yatashi, dasauri ya 6ullo mata ta wata hanya yace "naji I will accept ur condition sai dai Inaso kisani cewa hakan zaifarune idan har yaxamto cewa kema kinsami mijin aure sannan xan amincewa buqatarki"

Dasauri Balkisu tajuyo a firgice tace "Yaya wakake tunanin zai soni har ya aureni?"

Jisukayi anbud'e labulen falo a hnkli yaqarasa ciki hannayensa sanye cikin aljihunsa cikin sassanyar muryansa yace gani.


Muje zuwa donji wanene yashigo musu gda kai tsaye gamida amsa cewa shine zai auri Balkisu.


®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode2⃣2⃣

A tare suka juya gabad'aya, Dr Muh'd suka gani tsaye murmushi ya sakar musu da sauri ya k'arasa ciki yace "am swry ban muku sallama ba afuwan Assalamu alaikum" miqawa Hafeez hannu yayi sukayi musabaha, can kuma falon yayi shiru nad'an wasu daqiqa gabad'ayansu kowa da abunda yake tunani cikin zuciyarsa' Dr Muh'd ne ya katse shiru ta hanyar cewa "tabbas Hafeez najima inason Balkisu a zuciyata sai dai na 6oye ne sbd ganin cewa baka bawa kowanne d'a namiji damar tunkarar taba, a haqiqanin gsky soyayyar da nakeyima Balkisu tawuce dukk inda kake tunani domin soyayyar Balkisu tayi tasiri acikin xuciyata Wanda hakan yasa nakasa ganin kowacce irin macce da daraja a idanuna, sannan a kullum sai nayi niyyar tunkarar ka da zancen amma sai zuciyata ta haneni.

Shiru Hafeez yayi gami da dafe kansa gabad'aya jiyayi hnklinsa ya tashi domin kuwa a ynxu shi Kansa yasan bai da tacewa kasancewar Dr Muh'd abokine ga gareshi yasan koshi shi waye yakuma san halinsa Sannan yasan waye  zuri'arsa.
      Balkisu kam dukk kunya ta isheta gabad'a jitayi kmr qasa tabud'e tashiga.

Dr Muh'd ne yace "abokina idan ka amince min inaso kabani auran Balkisu, Hafeez kam jiyayi kmr ya d'aura hannu aka, da sauri ya qirqiro murmushin dole ya dubi Dr Muh'd cikin sigar zolaya Hafeez yace ashee kai ragon likita ne maitsoran macce? Dr Muh'd yace la! la!! la!! Ae ni ba Balkisu nake tsoro ba yayan Balkisun nake tsoro, gabad'aya dariya sukayi Hafeez yad'an bugi kafad'ar Dr Muh'd yace kai dai bawani.

Dr Muh'd yakoma cewa "nidai babban yaya kai nake saurare kabani Balkisu? Hafeez yad'anyi murmushin yaqe sannan yadubi gefen da Balkisu ke zaune tayi shiru ta duqar da knta tana wasa da yatsun hannunta, sannan yasake maida dubansa ga Dr Muh'd yace "of cox y not da bazan baka ita ba amma nifa karkayi tunanin zanma qanwata dole" bari ynxu intashi inbaKu waje kud'an tattauna idan kunfahimci juna ta amince toh falillahil hamdu inkuwa har bata amince ba toh bana tunanin nima zan amince ko nayimata dole".

Hafeez nafadin haka ya tashi yakoma daga cikin d'akinsa dan basu waje sud'an tattauna

A hnkli Dr Muh'd yatashi daga inda yake yakoma gefen Balkisu cikin tattausar muryansa yad'an duqa  daf da ita yace "toh Balkisu miye ra'ayinki agame da tayina ko ince buqatata? Balkisu kam dukk kunya ta isheta qara duqar da kanta qasa tayi,murya na rawa kmr wacce zatayi kuka tace " a'a ni ina ganin baidace na amsa tayinka ba domin kuwa wani 6angare na sashin zuciyata nasanar dani cewa kawai tausayina ne aranka da kuma son taimakamin ganin cewa Yaya Hafeez yayi aure matuqar nima nayi.

Da sauri Dr Muh'd yace ko kusa Balkisu karki kawo wannan gur6ataccen tunanin cikin zuciyarki, wlh soyayyarki ta gsky ce acikin jini da 6argona yakamata ace tuntunima kinfahimci hakan wlh Balkisu believe me when I said banta6a son wata d'iya macce ba kmr ki ina miki wani irin so Wanda ni kaina yana bani tsoro plss kitaimakawa zuciyata nan yashiga yimata magiya
   Ganin yadda ya marairaice fuska kmr zaiyi kuka yasa Balkisu tace "to shikenan na amince ku gama mgn da yaya Hafeeez tana fadin Haka ta tashi da sauri tashige d'akinta gami da banko k'ofa direct gadonta tafad'a tanajin wani irin nishad'i marar misaltuwa na shigarta.

Abangaran Dr Muh'd kuwa hannu yad'aga sama yana jero adduo'i na farinciki da nuna tsantsar godiyarsa ga ubangiji, yana gama addu'ansa d'akin Hafeez yanufa  yayi knckn Hafeez ya amsa yes shigo jiki narawa Dr Muh'd yashiga cikin d'akin wani irin farinciki da nishad'i yake ji nashigarsa da sauri ya rungumi Hafeez yace " yes abokina adduar danajima inayi yau Allah ya amsamin Balkisu ta amince ynxu amincewarka kawai nake jira.

Murmushi Hafeez yayi cikin zolaya yace congrat namaka murna, ynxu kabari idan muka gama tattaunawa da ita Balkisun zankiraka awaya muqarasar da mgnr, Dasauri Dr Muh'd yace "wacce mgn za'a gama ae ynxu angama komai tunda madam ta yarda ynxu kawai izininka nake nema sbd ina so inturo magabata na, Hafeez kam jiyayi gabansa yafad'i da sauri yace olryt karka damu I will giv u a call let

Cike da zumud'i cikin fara'a Dr Muh'd yabar gdan.

Hafeez kam gabad'aya yashiga damuwa jiyayi wani irin rashin sukuni ya ziyarcesa Dan haka da sauri yanufi d'akin Balkisu dan yanuna mata cewa shikam bai amince da wannan chakwakiyar ba.

®NWA
[11:53AM, 10/15/2016] My Nabss: [3:11AM, 7/27/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode2⃣3⃣

A hanzarce Hafeez yanufi d'akin Balkisu don ya nuna mata rashin aminciwarsa akan wannan tsarin deal din da takawo mai cike da rud'ani, a hnkli ya murza kofar d'akin jin bud'e take yasa yashige d'akin kaitsaye turuss ya tsaya cike da mamakin ganin Balkisu cikin wani yanayin dabai ta6a ganinta ba.
        Balkisu kwance take ta kife cikinta ta yayin da tad'an d'aga kafafunta tana lilasu earpies ne a kunnenta tana merming waqa cike da nishad'i" soyayyaa tayi mamaya tayi charaf ta chafkemin zuciya nasamu saurayi madubin duba inata murna" murmushi Hafeez yayi gabad'aya ji yayi jikinsa yayi sanyi a hnkli yafice daga cikin d'akin batare da tasani ba, falo yakoma yazauna gabad'aya tunanin mafita Hafeez Yake nemawa kansa amma dukk hnyar dayabi sai yaga cewa ya tauye dukk wani farinciki na qanwartasa,  kan Hafeez yagama kulewa gabad'aya jiyayi bashida wata mafita ko dubara domin kuwa BURIN HAFEEZ shine yaga tilon qanwar tasa cikin farinciki dan haka komai xai iyayi dukk runtsi dan ganin ya inganta farincikin Balkisu.

 Take anan Hafeez yakira layin Dr M yasanar dashi cewa yanason ganinshi zuwa gobe, Dr M yayi farinciki dajin wannan kira dan haka addu'a kawai yyi yana maifatan Allah yakaimu goben.

Abangaran Balkisu kam wani irin sabon yanayi taji nashigarta kasancewar dukk wunin ranan nan suna maqale da juna awaya ita da gwarzon likitan nata.

**             **              **
Balkisu ce zaune cikin motarta tana zaman jiran dawowar Meena daga talla kasancewar yau Monday ta je skul shiyasa bata samu damar zuwa wajan Meena da wuri ba sai ynxun.

Balkisu ta6ata kimanin awa biyu zaune cikin mota sai zabga uwar hamma takeyi, agogon dake d'aure bisa tsintsiyar hannunta take dubawa qarfe daya saura a hnkli tasauqe wata irin ajiyar zuciya, kmr ance d'ago kanki ae kuwa chan tahango Meena tafe da bokatin alalarta.

 Dasauri Balkisu taja motarta cikin sauri taqarasa wajan Meena a hnkli tayi parkn motarta daf da Meena,  zuge glass din motar tayi a hnkli cikin rashin karfin gwiwa takira sunan Meena, da sauri Meena tajuyo ganin Balkisu ce mai kiran nata yasa tayi saurin niyyar barin wajan, da sauri kuwa Balkisu tafito amotarta gamida shan gaban Meena cikin raunatacciyar muryanta tace Meena plss ki dakata kisaurareni koh da sau d'ayane daga wannan baxan sake takuramiki ba namiki alqawari, zuwa ynxu gabad'aya Meena tagama tsorata da Balkisu jiki na 6ari Meena tace Dan Allah baiwar Allah ki kyaleni haka naroqeki da sauri Meena ta ratsata gefenta da nufin ta wucewarta, cikin sanyin jiki Balkisu tace "olryt Meena kije karki saurareni amma na tabbata kinfi kowa muradin son ganin mahaifiyarki tafito a gidan kaso, da sauri Meena tajuyo fuskarta d'auke da mamaki qarara.
 
Murmushi Balkisu tayi tace " yes Meena nasan komai a gameda lbrinki babu wani 6oye 6oye ynxu daya rage a tsakaninmu, wlh kiyarda dani banida niyyar cutar dake hasalima nidake nakeson muhad'a kai mutaimaki juna, Meena tamaimaita abinda Balkisu tace mutaimaki juna??

Kmr ya mutaimaki juna? Balkisu tace "kwarai kuwa,kuma hakan nidake gabad'aya zai amfanemu, Murmushi Meena tayi tace " anya kuwa kinyi dogon nazari akan wannan maganar taki? Balkisu tace ae ynxu kece zanbaiwa damar yin tunani akan mgnr danaxo muki da ita.

Meena ta gyara bokatin alalarta ta fuskanci Balkisu tace" okay fadi mgnr naji Allah yasa zan iya" Dafa kafad'arta Balkisu tayi cike da qarfin gwiwa tace no karki damu insha allahu hakan bazai gagareki ba.

Balkisu tadubi Meena tace inba damuwa inason kizo mushiga daga cikin mota ta hakan zaifi sirri, dasauri Meena tad'ago tadubi Balkisu, Balkisu tamaqe kafad'a tace yadai ko dai har ynxu baki gama yarda dani bane? Meena ta girgiza kanta tace a'a ba haka bane mujee.
     Cikin motar Balkisu suka shiga Meena jitayi wani irin sanyi yaratsata a hnkli tadubi Balkisu tace inajinki kiyi sauri kada namakara. Balkisu tadubi Meena sannan tad'auke dubanta daga gareta tafuskanci gabanta, Sannan takira sunan Meena bayan Meena ta amsa sannan tasake cewa kinsan menake so dake? Meena ta girgiza kanta tace a'a sannan Balkisu tajinjina kanta a hnkli tasauke idanunta akan Meena tace "so nake ki auri yayana, da sauri Meena ta gwalo idanu waje gamida dafe kirji tace mekikace?  murmushi Balkisu tayi domin batayi mamakin ganin Meena tayi shock dajin buqatarta ba,  Balkisu tajinjina mata kai tace tabbas abinda kikaji shinafad'a inaso ki auri yayana domin inason ganin sauyi da farinciki a tattare dashi, da zaran kinyimin haka nikuma nayi alqawari konawa ne zankashe domin na d'aukaka qara ganin cewa Mahaifiyarki tafito daga gdan yari, sannan inaso karki manta cewa nasan komai agamedake basai kinyimin wani dogon bayani agameda matar babanki ba namiki alqawarin zanji da komai kedai kawai nabaki nan zuwa gobe kije kiyi tunani

Gobe da yamma zandawo domin naji shawaran dakika yanke. Balkisu nafadin Haka tabudewa Meena qofa cikin sanyin jiki Meena tafice daga motar yayin da Balkisu kuma ta wuce tanufi gda nan tabar Meena tsaye cikin tunani.


Note: akan masu complain cewa banason yin typn da wuri inaja muku rai, wlh sam bahaka bane karku manta fa cewa nabaku uzurina plss kumin afuwa insha allahu zanqoqarta nagode.
®NWA
[11:54AM, 10/15/2016] My Nabss: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode2⃣4⃣

Cikin daren ranar Meena kasa runtsawa tayi, babu abinda take tunawa sai ranar da tafara had'uwa da yayan Balkisu irin yadda yanuna mata kyankyami da tsantsar tsana qarara a fuskarsa, dan haka tasan tabbas a zaman auransu xata cutu sai dai kome xainuna mata xa ta iya shanyewa sbd lura da tayin da bashine da kansa yaxo neman auranta ba hasalima qanwarsa yaturo to komiye dalilinsa nayi haka? Nan fa tafara jeroma kanta tambayoyi wnda ita kanta batada amsarsu.
          A ynxu kam gabad'aya tunanin Meeena yatafi akan yadda rayuwarta zata kasance a hannun wanda bai ko kaunar ganinta gashi kuma a wani 6angare tana buqatar mahaifiyarta kusa da ita, Dan haka ta gama yanke shawaran amincewa auransa don tasamu damar taku6utar da mahaifiyarta daga gdan kaso.

Da wannan shawaran aranta har bacci 6arawon yayi awon gaba da ita.


**                **          **
Washe gari
 kafin kowa ya tashi a gdan Meena tariga kowa tashi kmr yadda tasaba, bayan ta idar da sallah ne tafara ayyukanta kafin qarfe 6 kuwa Meena tagama ayyukan ta tsaf, ruwan sanyinta tad'iba tashiga bayi ta watso ruwa, bayan tafito ne tadauki tallan kunun gyad'anta tanufi chan Bolori primary skull inda chan ne Meena zata had'u da Balkisu.

A bangaran Balkisu kuwa ita ma sauri kawai take tayi sbd bata son ta had'u da Hafeez kasancewar tasan sai yayi ta jero mata tarin tambayoyi akan wacce take son had'ashi aure da ita, gashi ita kuma basu gama mgn da Meena ba Dan haka bata da kwakkwarar amsar da xata bashi, hakan ne ma yasa tayi tunanin tad'aga appointmnt dinsu wnda tace su haduwa da yamma tamai dashi zuwa da safe.

Kafin Hafeez yafito kuwa tuni Balkisu tafice a gdan, Bolori primary skul chan tanufa a niyyarta dama intaje tasa yara sunemo mata Meena tunda dama nan ne wurin sana'arta, Balkisu nashiga skul din ba tawani sha wahalan neman Meena ba hangota tayi zaune ta rafka uban tagumi.

Meena! Meena!! Kmr a mafarki taji ana kwala mata kira dasauri tayi firgigit ta juya, Balkisu tahango zaune cikin motarta dasauri Meena tamiqe tanufi wajanta.
     Murmushi Balkisu ta sakar mata sannan suka gaisa da junansu daga bisani tayi mata ixinin shiga cikin motar, a hnkli Meena tabud'e murfin motar tashiga.

Jan motar tayi cikin nutsuwa suka bar gefen makarantar chan wata anguwa suka nufa, sai da Balkisu ta tabbatar sund'anyi nisa sannan tayi parkin, Da murmushi d'auke a fuskar Balkisu ta dubi Meena tace "toh Meena kmr yadda kikaji nace miki zanxo domin naji shawaran dakika yanke toh gani nan na iso gareki don jin shawarar da kika tsaida shin kin amince kuma kinshiryawa auran yayana??

Meena ta sadda kanta qasa hawayene kawai keta kwaranya cikin sanyin murya tace na amince da auransa matuqar xankasance tare da mahaifiyata. Balkisu tajinjina kai tace dakyau amma kinsan dalilina nason ki auri yayana? Meena ta girgiza kai alamar a'a
     Ajiyar zuciya Balkisu tayi sannan tamaida dubanta ga Meena gabad'aya idanun Balkisu sunrine izuwa ja! Cikin natsuwa takawo lbrin rayuwarsu tasanar da Meena, nan Meena tashiga jinjina al'amarin cikin zuciyarta tana mai tausaya musu sai dai kuma yadda taji lbrin Hafeez ta tabbata cewa kawai tad'auko ma kanta dala ba gammo ne amma kuma inta tuna mahaifiyarta sai taji wani irin kwarin gwiwa na shigarta.

Balkisu tadubi Meena tace tabbas na yaba da kyawawan d'abi'unki da yadda kika iya maida mgn ga masu hali irin na yayana hakan yasa na tabbata cewa zaki iya dawo min da Yayana normal kmr yadda yake a lkcin baya.

Murmushin yaqe Meena tayi sannan tadubi Balkisu tace "Allah dai yabani ikon cikamin alqawarinki sbd naga kinsa hope dinki akaina sosai, Balkisu tad'anyi yar dariya tace "Meena kikwantar da hnklinki kedai kawai kisa aranki daga gobe zuwa jibi muna iya xuwa a kowanne lkci gdnku dan neman auranki sannan inaso kada kifadawa kowa wannan mgnr har sai komai yakankama, cike da jin kunya Meena tace insha allahu.

Meena har tabud'e kofar motan da niyyar tafita Balkisu takira sunanta, cikin natsuwa Meena tajuyo.Balkisu tace " aff namanta intambayeki yau mekike sai dawa ne? Meena tace kunun gyad'a ne.
     Balkisu tad'anyi murmushi kmr yadda hakan yaxama jiki agareta sannan tace" gabad'aya kunun na nawane? Meena tace na d'ari biyar ne  zaro dubu biyu tayi ajakarta tamiqawa Meena sannan tace gashinan kiyi sadaka dashi haka har zuwa gobe kiyi manejin wannan bnfito da kud'i bane.

Da farko Meena tanuna kin amincewarta sai da Balkisu tad'an lallamota sannan tasamu ta ansa.


Direct gdan mallan Zakiru Balkisu tanufa don cika alqawarinta kmr yadda tafada mishi cewa dukk halin da ake ciki agame da Meena xataxo tasanar dashi (mgnr lectures kam yau bbu ita)hakanan ta juya akalar motarta izuwa gdan mallan Zakiru.

®NWA
[1:14PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:37AM, 7/29/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode2⃣5⃣

(Very sorry readers nayi mistake din numbr nasa 23 sau biyu makin nasa 24 nayi mistk ynxu 25 xamu tashi)


Kamar kullum yau ma ya kasance  mallan Zakiru na nan cikin Zaurensa yana bitar karatu alqur'ani, da sallama Balkisu tasa kai cikin zauren tare da neman izinin shiga, cikin nutsuwa Mallan Zakiru yakai qarshen aya sannan ya rufe  qur'anin ya ajiye agefensa, cikin sakin fuska yayi mata Iso
       Mai d'akinsa mallan Zakiru yashiga yakira dan takawo masa taburma, Inna takawo taburman tana qoqarin shimfid'awa Balkisu tayi saurin amsa ta shimfid'a tabarman, bayan ta xauna sannan  suka gaisa sannan Inna, ficewa Inna tayi  tabasu waje kmr yadda tasaba in mallan yayi baqi bata zama.

Balkisu tadubi Mallan Zakiru fuska d'auke da murmushi kai dagani kasan tana cikin farinciki, "tace Baba kmr yadda na sanar dakai cewa dukk yadda ake ciki a game da Meena zansanar maka wato naafad'a mata inasone ta auri yayana ynxun nan muka gama mgnr da ita sannan ta amince zata aureshi nikuma nayi mata alqawarin bayan bikinsu zanfito da mahaifiyarta a gdan yari.

Mallan Zakiru yyi murmushin jindadi yace "Masha allahu' Allah sarki Aminatu allah ya sanya alkhairi, Balkisu ta amsa da ameeen daga bisani Mallan Zakiru yadubi Balkisu fuska d'auke da damuwa yace "amma kmr yaushe ne kike xaton zaku turo magabatan ku don neman auran Aminatu?
      Balkisu tace "toh baba muna so mu tsaida ranan ne tukun, mallan Zakiru yajinjina Kansa sannan yace toh wacce shawara kika yanke agameda tunkarar Yagana don niman auran Aminatu?

Balkisu tace Baba karka damu inaso ne in angama ajiye mgn d'aya zamu turo qanin mafaifinmu sbd in.... kafin Balkisu ta qarasa abinda take son cewa Mallan Zakiru yace "Sam kada kiyi haka sbd dukk cikin garin nan bbu wnda baisan waye mahaifinku ba nikuwa nafi kowa sanin cewa muddin Yagana tagano cewa Aminatu gdan masu hali zatayi aure toh fa baxata amince ba.Sbd dukk wata hanya da tasan zatabi don ganin cewa ta lalata wannan auran toh fa zatayi Kuma babu wnda ya isa yadakatar da ita, Dan haka inaso kibar komai a hannuna sannan kitabbatar da cewa cikin qanqanin lkci zakusa lkcin auran don gujewa fitina.

Balkisu tad'anyi jimm! Sannan tadubi Mallan Zakiru sannan tace amma Baba kana ganin ta wacce hanya zamu bi? Mallan Zakiru yyi murmushi yace zansamo wani daga cikin kauyanmu inyimata nuni da cewa shine Wanda yakeson ya auri Aminatu amma fa dukk wani wakili ko waliyi Na ango zaifito ne daga 6angaranku. Nan Mallan Zakiru ya tsatssara ma Balkisu matakin da zasubi don gujewa sharrin Yagana

Kwarai da gaske Balkisu taji dadin shawarwarinsa ae kuwa nan tayi taxu bawa Mallan zakiru godiya, tana mainuna jindadin taimakonsa gareta.

**      ***       **      ***
Qarfe hud'u Na yamma na bugawa Dr Muh'd na isa gdnsu Balkisu don cika umarnin Hafeez kmr yadda yabuqaci ganinsa.

Hafeez kam yau through out bai ko fita bakin get ba yana nan cikin d'akinsa yana sana'ar tashi wato tunani, kwan kwasa k'ofar dayaji anayine yadawo dashi daga duniyar tunanin da yatafi, a hnkli yamiqe batare da yace komi ba yanufi k'ofar bud'ewa yayi Dr Muh'd ne yagani tsaye cikin dakakkiyar shaddarsa mai kyan gaske sai wani zuba qamshi yakeyi, Hafeez yadubi Dr Muh'd har yaso yabashi dariya sai kuma yabasar hannu yamiqa masa suka gaisa sannan Hafeez yace dashi yaje Falo yad'an jira gashinan zuwa

Dr Muh'd kam cike da zumud'i ya nufi falo yazauna dan jiran Hafeez
      Toilet Hafeez yashiga ya sakarwa kanshi ruwa yajima a haka daga Bisani kuma ya silla wankansa, qananan kaya Hafeez yasaka blue riga da baqin wando dukk da cewa Hafeez baifiye son qananan kaya ba amma yau su yaji yana muradin sawa turare mai dadin gaske ya fesa sannan yafice a d'akin.

Falo ya nufa kaitsaye yana shiga kuwa ya tarar da Dr Muh'd na nan zaune yana jinran fitowarshi, murmushi Hafeez yayi ya girgixa kansa.
      Bayan sund'an tattaba hira sama sama' Hafeez ya dubi Dr Muh'd jiki a sa6ule yace "amm abokina wato dalilin da yasa nace kazo ina neman ka yau shine inason inji daga gareka shin kashirya auran Balkisu? In kashirya wa auran inaso nan zuwa gobe kaje chan sabon fege gdn uncle Ma'aruf kasanar dashi dukkan wani jawabi dakake tafe dashi akan auran Balkisu.

Hafeez nafad'in haka ya sadda kanshi qasa cike da damuwa da qunar zuci, dasauri Dr Muh'd yamatsa kusa dashi a hnkli ya dafasa  yace "tabbas abokina nasan kana cikin damuwa da alhenin rabuwa da tilon qanwarka amma kasani zaman Balkisu a gurina tamkar tana hannunka ne insha allahu nayimaka alqawari baxan ta6a cutar da qanwarka ba, zan riqeta amana tamkar kaine awajan sbd inason Balkisu sosai inayimata so Wanda baxan iyaganin abinda zai cutar da ita ba.
      Da sauri Hafeez yarungume Dr Muh'd yana kukan farinciki sannan yace "nagode maka abokina sannnan inaso kasa aranka cewa Balkisu amanace a hannunka sannan inaso idan zaiyuwu a d'aura auranku cikin wani sati if possible"

Dasauri Balkisu taqaraso cikin falon fuskan nan sha6e sha6e da hawaye cikin muryan kuka tace haba Yaya Hafeez aure na nikad'ai nakeji kana mgn banji kana mgnr naka auran ba, karka manta da alqawarinmu sbd nariga nasamo ma nagartacciyar mata Wanda nake da hope din cewa zata kularmin da yayana yadda yakamata.

Rasss! gaban Hafeez yafad'i, shidai bai San mieyasa Sam baya qaunar yaji anyi mishi mgnr wata d'iya macce ba, balle kuma harta kai ga mgnr aure.

Jiki a sanyaye Hafeeez ya maida dubansa ga Balkisu yace "wai wacece wannan yarinyar dakike son Na aura wacece ita a ina kika santa ya akayi kikasan tana da nagartaccen hali meyasa kike son tilastani nayi aure?' a jere Hafeez ya watsoma Balkisu tambayoyi?"

®NWA
[1:15PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:52AM, 7/30/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode2⃣6⃣

D'ago Jajayen idanunta tayi Wanda suka rine sbd kuka, a hnkli ta sauk'esu akan Hafeez, wani irin kukane ya sake kubce mata Wanda ita kanta batasan dalilin yinsa ba, cikin dishashiyar muryanta tace "Yaya Hafeez karka ta6a tunanin cewa auran wacce nakeson had'aku zai zama cutarwa ko danasani a gareka wlh kayarda dani cewa nafi amincewa auran Meena atattare da kai" Meena!! Hafeez yamaimaita sunan da sauri k'urawa Balkisu idanu yayi gabad'aya sai yaji tabashi tausayi, gashi akan wannan Meenar da ta dage dole ne yaga cewa yadaure ya aurenta mutuqar hakan zai sata farinciki da walwala.

Dasauri ya miqe tsaye daga zaunen da yake jawota yayi jikinsa ya rugumeta nan yashiga bubbuga bayanta cikin sigar lallashi, cikin murya qasa qasa Hafeez yace kwntar da hanklinki Billyn mama na amince zan auri dukk wacce kika kawomin ita matsayin matar aure, amma sai dai I have one request 4 u, k'ura mishi idanu Balkisu tayi alamar shi take saurare dasauri ya janye jikinsa daga nata sannan yaci gaba da mgn "na amince zan auri yarinyar da kikeson kawota cikin rayuwata sbd inada yaqinin cewa bazaki ta6a had'ani da wacce bata dace da rayuwata ba, sai dai kuma inaroqonki plss kada kitilastamin zuwa d'aurin auren sbd hnkli da kwakwalwata bazasu iya jurar ji ko ganin cewa wai yau nike aure ba plss kisamu komawaye ya wakilceni sannan dukk abinda kikaga yadace kawai kiyi nabar miki wuqa da nama" Hafeez nafadin haka yayi sauri yabar falon cike da d'acin rai.

Jikin Balkisu gabad'aya yayi wani irin sanyi, a hnkli Dr Muh'd yaqaraso gareta cikin muryan lallashi mai nuna tsantsan tausayi ga masoyiyar tashi, nan fa ya xage damtse yayi ta tausar zuciyar cikin hikima da kwarewa, sai gashi kuwa cikin qanqanin lkci ta manta da komai.

A Bangaran Hafeez kuwa d'aki yashiga ya kulle kansa ji yayi gabad'aya duniyar tamasa xafi.

**       **       **    **    **
Kmr yadda Mallan Zakiru yayi ma Balkisu alqawari haka kuwa akayi yaje can qauyansu yasamo wani matashin saurayi dake aikin faskare.

Abangaran Dr Muh'd shima yaje yasamu ya gana da qanin mahaifinsu Hafeez, wato uncle Ma'aruf, uncle Ma'aruf kam bayan binciken daya qarayi akan hallayan Dr Muh'd yasamu kyakkyawan yabo hakan yasa ya amince domin yafi kowa farinciki dajin lbrin. Dan haka cikin qanqanin lkci aka sanya lkcin bikin Hafeez da Balkisu
         
                Mallan Zakiru da kansa yaje har wajen Yagana yasanar da ita cewa d'an uwansa ne Wanda yaxo daga qauyansu yaga Meena yakuma nuna cewa yana son auranta, Yagana tayi farin ciki jin ancemata daga noma sai  faskare sune aekinsa koshi faskare da noman aekatau dinsu yakeyi ana biyansa dan haka kenan su Meena za'a sha noma wani irin farin ciki ne ya lullu6eta datagama wannan tunanin, Dan haka batare da 6ata lkci ba tanuna amincewarta.
       Mallan Zakiru yyi matuqar farin ciki da hakan domin kuwa hakarsu daf take da cimma ruwa.

Komai ya kankama yan'uwa da abokan arziqi anfara hallara, gwaggwanin su Balkisu da mamaninta dukk sunzo nan suka fara gyara diyar tasu Balkisu tafito fasss da ita baqaramin kyau tayi ba.
   
     Bangaran Yagana da yarta kuwa kullum basu da aiki sai gori da kyarar Meena wai tarasa Wanda xata jaju6o musu sai d'an kauye kauyan ma futuk nan fa zasu taru suyita dan gware tama kai.Meena kam ko uffan bata cewa dasu domin ita tunaninta a kullum bai wuce yadda zata kasance a wani gda a matsayin matar wani ba,sabuwar rayuwar da zata shiga kullum shike addabar tunaninta.

Plan din Mallan Zakiru da Balkisu komai Na tafiya yadda suke so da taimakon ubangiji.

RANAR DAURIN AURE

Ranar juma'a da misalin qarfe biyu na rana bayan ansauqo a masallaci aka d'aura auran HAFEEZ ABDULLAHI SHARIFF tare da AMINATU SULEIMAN akan sadaki dubu hamsin, inda kuma suka sake garzayawa aka sake d'aura auran BALKISU ABDULLAHI SHARIFF tareda DR.MUHAMMAD SHU'AB GASHU'A an d'aura auransu akan sadaki dubu d'ari.
                  ***
Dubu uku Mallan Zakiru yacira daga cikin sadakin Meena yakaiwa Yagana yace gashinan wannan shine sadakin Aminatu, zokaga farinciki awajan Yagana nan fa ta sokare kud'in a ha6ar zaninta

A cewar Yagana tunda Meena takala futuk ta aura to miye zata siyamata tunda dai d'an kudin da Meena kesamowa yaqare a kudin hayarta dan haka baxata siyamata komai ba.
      Da misalin qarfe hud'u na yamma Mallan Zakiru ya je gurin Yagana wani tsadadden material da sarqa da yan kunne da takalmi da kyale set komai yayi match kayan sun matuqar haduwa, Balkisu ce ta aikomishi tace yabawa Meena idan anzo d'aukar amarya tasanya ajikinta. Hakan yasa Mallan Zakiru yakawo kayan dan ciki alqawarinta.

Yagana naganin kayan dake hannun Mallan Zakiru dukk tabi tawani rud'e, miqa mata kayan yayi yace "Yagana ga wannan kayan daga hannun mijin Aminatu sukafito yace dan Allah atabbatar da tasa wannan kayan zuwa an jima sannan kisanar mata cewa kartabari kokadan kayan sulalace sbd arosu yayi daxarar ta isa gdnshi ciresu xatayi yamaidasu inda ya aro, wata irin dariyar k'eta Yagana tafara dukk farinciki yabi ya lullu6eta.

Hakanan akayi shagalin biki a bangaran Balkisu da Dr dinta, sa6anin Hafeez wnda ya kulle kansa cikin d'aki.

Misalin qarfe tara na dare wasu irin manya manyan motoci tsadaddu ne sukayi fakin a k'ofar gdansu Meena, da sauri wata gwaggonsu Hafeez tashiga gdan Cikin shiga ta kece raini dukk da kasancewar dare ne amma shigar da tayi kallo d'aya zakayimata kasancewa an narka daloli.

Yagana kam tabawa Aminatu kayan tasa baqaramin kyau sukayi mata ba, ganin tayi kyau abinta yasa Yagana dukk haushi ya isheta nan tashiga dangwarar kanta tanayimata gori sai wani kusheta takeyi.
      Ana cikin hakane Gwaggon Hafeez Hajiya Nana tashiga domin tafiya da Meena.

Ae kuwa gabad'aya kan Yagana yad'aure shuru kawai tayi tana kallon ikon Allah azatonta dukk wad'annan manyan matan suma hayarsu akayi, al'amarin bai qara tsinkar da Yagana ba sai da tabisu zuwa waje taga wasu irin dan qara dan qaran motoci Wanda sune suka zo d'aukar amarya Meena. Yagana tanaji tana gani aka sanya Meena cikin mota sakeke tayi da baki cike da mamaki domin ita takasa gane wannan Al'amarin jitayi andafata da sauri ta juya Hajiya Nana ce cikin sigar lallashi take lallama Yagana domin ita a tunaninta Yaganan tana cikin alhenin rabuwa da diyarta ne, nan taciro dubu hamsin tamiqawa Yagana. Cikin mota takoma sukaja take anan sukabar cikin unguwar.

Yagana na ganin haka ko gyale babu a jikinta balle takalmi haka tanufi gdan Mallan Zakiru cike da masifa domin kuwa bakin nan nata taf yake da tambayoyi Wanda babu mai amsamata su sai Mallan zakiru.
®NWA
[1:15PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:47AM, 7/30/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode2⃣7⃣

Jiki Na 6ari haka Yagana ta shiga gdan Mallan Zakiru ko sallama babu ta afka musu cikin gda, dai dai lkcin Mallan Zakiru yafito daga bayi hannunsa riqe da buta yana kiran mai d'akinsa ta kawo mishi abinci, Mallan Zakiru sai ji yayi ance "toh algungumi munafiki azzalumi mai sai da yaran mutane" da sauri Mallan Zakiru yajuyo danganin mai mishi wannan alkaba'iran Yagana yagani tsaye ko mayafi babu balle takalmi ta wani riqe qugu sai huci take kmr zakanya, murmushi Mallan Zakiru yayi domin kuwa bai yi mamakin ganinta ba don yatsammaci haka.

Mallan Zakiru yadubi Yagana yace "toh ynxu kuma Yagana wanne laifi nayi haka da har nacancanci ki biyoni gda da masifa?
       Yagana ta gyara tsayuwa cike da masifa tace "ae kuwa kace dani haka tunda ka gama rainamin hankli wato ashe sai da Meena kayi? Kafadamin suwa kasayarwa da ita a nawa kasaidata? Mallan Zakiru yayi murmushi cike da dattijantaka yace "akan naira dubu uku kacal kuma suma kudin suna hannunki, kinga kenan ashee bani kad'ai naci ribar sai da Aminatu ba.

Nan fa Yagana tabud'e murya tana tadajijiyoyin wuya ita alafurr adawo mata da Meeena, Mallan Zakiru kam yau dukk jiyayi lamarin Yagana ya kai mishi mak'ura wata uwar tsawa yabuga mata wnda tayi sanadiyyar shiga natsuwarta.

Sheqeqe Yagaรฑa tayi tana bin mallan Zakiru da kallo cike da mamaki, Mallan Zakiru yadubi Yagana cikin tsananin fad'a yace "wlh kedai tirrr Allah wadai da hali irin naki Yagana wlh ina mai tabbata miki cewa kiyi gaggawar canja halinki kiji tsoran haduwa da mahallicinki domin kuwa a kodayaushe lkci yana iya kuremiki.
      "Dama mai kika d'auki kanki? Kind'auka cewa ke kadaice kike da kwakwalwa da tunanin yadda zaki cutar da wani toh kisani dama irin wannan lkcin nakejira, najima inatunanin ta yadda za'ayi Na ku6utar da Aminatu daga hannunki sai gashi Allah maji roqon bawansa ya amsamin addu'ata da najima inayi akan yabani ikon da zankubutar da Aminatu sai gashi yakawomin hnya mafi sauqi, kuma bari kiji infad'amiki Aminatu dai na gdanta ma'ana gdan mijinta bakuma zanfadamiki inda take ba balle kije kitada musu qayarbaya sbd jahilci irin naki.

Gwalo idanu waje tayi tadubi mallan Zakiru tace "Zakiru nice jahilar"? Mallan Zakiru yajinjina kansa yace"kwarai kuwa" Nan fa Yagana ranta yaqara 6aci cikin tsananin fada tashiga nunashi da d'an yatsa tace "wlh kajira kaga abinda xai biyo baya wlh dani kake mgn" Mallan Zakiru yace "ae shi sharri kare ne kuma mai shiyake bi insha allahu babu abinda xan gani sai alkhairi, kuma indai aminatu ce tayi aure a babban gda gdan dasuka san darajar mutum, gdan da inhar keda zuri'arki zasuyi shekara goma kuna tara dukiya bafa zaku iya sayen koda karen gdan ba, balle kiyi tunanin zuwansa" Mallan Zakiru nafadin haka Yagana tayi kwaf ta kad'akai tafice a gdan cikin tsananin fuskata.

"Mtsssw aikin banza kawai yarinya kin grma bakisan kingirma ba, baki da wani aiki sai tunanin kanki da ahalinki nawa rayuwar duniyar take da zaki d'auki son duniya kid'aurawa kanki" Inna dai natsaye bata ce komai ba, sai bayan da komai yalafa sannan suka zauna yake bata lbrin dukk abin da yafaru.

Innah taji dad'i sosai da jin wannan lbrin.


**        **      **      **   **   **   **
A bangaran Amarya Balkisu kuwa gabad'aya famlyn ango sun hallara don d'aukar amarya, amma Balkisu tace sam batasa Xancen ba, ita bbu inda zataje har sai ankawo Meena cikin gdan ta sadata da yayanta sannan, babu irin lallashin da basuyi ba amma furrr taqi amincewa a dole suka hkra suka zauna zaman jiran isowar matar Hafeez.

Ba'awani jima ba kuwa sai ga yan d'aukan amarya sun iso, hakanan Hajiya Nana ta lullu6e fuskar Meena akashiga da ita cikin gdan, Bayan sun gama bud'arsu da shewarsu ne Balkisu tazo da kanta taja hannun Meena suka shiga d'akinta don suyi mgn.

Meena kam tun isarsu gdan babu abinda take sai kuka daga ita har Balkisu babu mai ba wani hkri, dakyar Balkisu tasamu tayi controlling din kanta sannan tashiga roqon Meena da ta kular mata da yayanta nan Balkisu tashiga fad'awa Meena abinda Hafeez yafiso da wanda baya so.

Meeena kam sai kuka takeyi kmr ranta zai fita, hakanan Balkisu tagama fad'amata dukk abinda yakamata sannan takama hnya har zata fita sai tajuyo tace "Meena Dan Allah kikasance mai juriya da hkri kmr yadda nasanki sannan ynxu da zarar hidimar bikin nan taqare xancika miki naki alqawarin" tanafadin haka tashare hawayenta tafice a d'akin.

D'akin Hafeez Balkisu tanufa nan ma wani sabon kukan tasha, wannan karon hadda Hafeeez shima yazama tamkar wani qaramin Yaro sai kukan yakeyi, Balkisu ta d'ago da jajayen idanunta tadubi Hafeez tace "plsss yaya ka kula da Meena kmr yadda kake kula dani hakan zaisani farinciki, girgiza mata kai kawai yakeyi batare da yace komai ba.

Dakyar Anty munnawara matar uncle ma'aruf ta 6an6are Balkisu daga jikin Hafeeez, sai kuka sukeyi gabad'ayansu.
      Hakanan Hafeez yanaji yana gani akatafi da Balkisu gdan auranta.

Wani irin k'unci yakamaji Wanda hakan yasa ciwon xuciyarsa ya tashi dakyar yasamu yasha magani ya kwanta.

Meena kuwa Hajiya Nana takaita asalin d'akinta Wanda ya kasance mallakinta, d'akin kam ya matuqar had'uwa da tsari komai tsaf tsaf nacikin d'akin.
      Hakanan kuwa Meena tanemi gado ta kwnta wani irin karkarwan d'ari tashigayi ga knta da yake tsananin sara mata sbd ciwo, nan tadunqule waje d'aya ga wani irin azababben tsoro daya dinga shigarta kmr ta shid'e.
®NWA
[1:15PM, 10/15/2016] My Nabss: [12:57AM, 8/1/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode2⃣8⃣

Dukk addu'ar da tazo bakin Meena ita kawai take karantowa, runtse idanuwan tayi sosai bata ko k'auna bud'esu sbd tsananin tsoro, yayin dashi kuma gogan nata ke d'akinsa kwance yanata sharar bacci sakamakon magungunan daya d'irkawa cikinsa.

A bangaran Meena kam dak'yar tasamu itama baccin yayi awon gaba da ita daf da asuba, dan haka bata wani samu ishashen bacci ba, hakanan ta daure ta nufi toilet alwala tad'auro sannan tazo tagabatar da sallah.

Bayan ta idar da sallah ne tarafka wani uban tagumi cike da damuwa,
           Misalin qarfe takwas na safe Meena ta tashi tanufi falo sbd wata irin yunwa da taji ta gallabeta har wani irin duhu duhu take gani dakyar tasamu tafita koh Allah zaisa ta samu abinda tasawa cikinta.

Koh da fitar Meena Daniel tagani yanata zirga zirga tsakanin kitchn da dinning area, shiru tayi tana binsa da kallo domin ita dai batasan ko waye shi ba.
Meeena na nan tsaye kmr wadda aka shuka, Daniel ne yasake fitowa daga cikin kitchn a karo nabiyu hannunsa dauke da flask din ruwan zafi kmr ance ya waiga sai ganin Madam yayi a tsaye kmr wata marar gaskiya, ae da sauri ya ajiye flask din ya qaraso gareta cike da grmamawa yace gud murng madam, kintashi lpy? Cike da mamaki Meena ta amsa lpy kalw, sannan Daniel yace ni sunana Daniel nine ke kula da store room Na gdan nan da kuma kitch, gyad'a kai kawai Meena tayi hankalinta dukk yana wajen dinning area ita dai burinta tasamu abinda taci.

Ganin hakane yasa Daniel yace am swry 4d disturbn u madam, d food is ready da sauri yaqara kan dinning din nan yafara bud'e mata abubuwan da ya girka kala kala, Meena kam riqe baki tayi cike da mamaki tadubi Daniel tace "Daniel dukk suwaye zasuci wannan abincin? Daniel yace "madam boss ne yace ake girka enough abinci yadda kowa zaici ya qoshi", Cikin zuciyar Meena tace uhumm boss kodai runbu irin wannan almubazzaranshi haka.

Sinasir da miyan allayahu shine kad'a Meena taga zata iyaci Dan haka d'aukan plat kawai tayi Daniel ya taimaka mata tazuba abincin, d'aukan plat dinta tayi ta koma falo domin jitayi bazata iya zaman dinning table dinba, zamatayi sosai tafara bawa cikinta haqqinsa.


Hafeez kam yau baqaramin makara yayi ba wurin tashin sallah sai qarfe bakwai da rabi ya farka a gaggauce yashiga toilet yadauro alwala, yana gama idar da sallah yakoma toilet din yayi wanka yazo yasake shiryawa tsaf abinsa, sai wani sauri yaketayi kmr wanda xaitashi sama yau dai Hafeez ko za6en kayan sawanshi bai tsayayi ba sbd yau bashida niyyar wuni acikin gda balle abokan wasanshi suzo su sami damar takura mishi, Qarfe takwas da rabi nayi Hafeez har yagama shirinsa.

Meena kam har tagama cinyye sinasir dinta, wani qatoton qashi ta tsaya gwaigwaya sai faman ko kuwa takeyi dashi, tana cikin wannan halin ne sai ga Hafeez yafito daga d'akinshi cikin sauri sbd baya so ya hadu da wannan Meenan da Balkisu ta d'aura mishi nauyin da bazai iya cikawa ba.
      Hafeez nafito wa cikin harban falo wata yarinya yagani tayi zaman dirshan tanata faman ko kuwa da qashi, wani irin abune ya tsaya awuyan Hafeez domin shi arayuwansa yatsani yaga anacin abinci da hannu balle kuma ita wannan ga dukkan alamu dambe takeyi da qashi.

A fusace Hafeez yanufi falon yana xuwa yace "ke dabbar ina ce miye hakan? Wacece ke ? Wannan wanne irin qazanta ne?"

Meena kam batayi tsammanin da mutum tsaye kusa da ita ba, tsawa kawai taji andoka mata Wanda ya mugun razana ta har qashin hannunta ya su6uce ya fadi๐Ÿ˜‚ da sauri taduqa tad'auki qashinta tamiqe tsaye gamida juyowa domin Meena kam tuni tagane mekiranta da dabba sunan, shi din ne kuwa tagani tsaye fuskan nan a turbune babu alamar wasa acikinta.

Wani irin shock Hafeez yashiga ganin wannan fitsararriyar yarinyar agabanshi domin kuwa har abada baxai manta wannan face din ba, da saurinshi kuwa ya zaro idanu cike da mamaki yace "ke wat ar u doing here? Meya kawo ki cikin gdana? Meena kam quramishi ido tayi gabanta sai bugun tara-tara yake, nan fa Hafeez yafara kiran Daniel! Daniel!! Daniel!!! da qarfi Hafeez ke kiranshi kmr wanda yaga dodo agabansa. Dagudu Daniel yaqaraso yace "yes boss am here" Hafeez yanuna Meena da hannu yana kallon Daniel yace "Daniel who's dis girl?" Daniel ya yadubi Meena wacce ke tsaye hannu riqe da qaton qashinta wani yawu Daniel had'iye cike da tsoro domin shi baisan wacce irin amsa xaibawa boss din nashi ba, dominshi a tunaninsa koma wacece ai shi zai fisa saninta... Daniel!!! Da qarfi Hafeez ya koma kiransa cikin fushi yace "I'm not tlkn to u"? Who's dix girl? Daniel ya sadda kai qasa yace boss I think she is ur wife, amma nibensashi ba fa.

Meena kam tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, Hafeez yadubi Meena up and dwn yace cabb badai wannan abar itace matata ba? 
     Meeena naganin Hafeez xai wuce gona da iri kawai ta ratsa tagefenshi tawuce kitchn ta ajiye plat din sannan ta wanko hannunta.

Dasauri tanufi d'akinta ta banko kofa, ganin tashiga cikin d'akin nan ya tabbarwa kansa cewa lallai wannan yarinyar itace wadda aka had'ashi da ita? Tabbb juyawa Hafeez yayi izuwa d'akinshi take yaji yafasa fitar da yayi niyyar yi.

Dakinsa shima ya shiga da sauri.

®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:53AM, 8/1/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode2⃣9⃣

Kai da kawowa Hafeez ya dingayi cikin d'akinsa gabad'aya jiyayi Balkisu tagama 6ata mishi rai sbd tarasa wacce zata hadasa dashi sai wannan fitsararriyar yarinyar wata qazama da ita yar qauye.
Wani irin haushin Meena yadinga ji, jiyayi kmr yaje yarufeta da duka.

Abangaran Meena ma haka abun yake d'akinta tashige tana zuwa tafada kan gadonta,nan tafara kuka wani irin haushin Hafeez da tsoransa ne suka tsayamata a cikin xuciyarta lkci d'aya cikin ranta tace "wato dai shi wannan uban masifan bashi da aiki sai cewa mutun dabba qyaattt" Meena tayi kwafa cike da jin haushinsa tace ae kuwa zan nunamaka halin dabbancin.Tun daga wannan ranar Meena ta umarci  Daniel da yake kai mata abinci cikin d'akinta, dan haka yasa ynxu kwata kwata Meena da Hafeez sunbar had'uwa dukk da cewa suna gda daya.


**         **         **       **

BAYAN SATI DAYA.

 Tuni Balkisu tad'auka qarara izuwa babbar kotu dake cikin jaharsu, da taimakon Dr Muh'd Balkisu ke gudanar da komai batare da sanin Meena ba.
       Sai da akayi sati guda currr ana abu d'aya shari'ace aka gudanar inda Mallan Zakiru yazo takanas har kotu shida wasu sauran mutanen cikin anguwarsu, suka bada shaidan cewa lallai Yagana itace ta kashe d'anta.

Sbd irin kudin da Balkisu tanarkawa yan'sanda shiyasa sukaje har gdan Yagana suka suka titsa qeyar ta izuwa police station, nan fa suka shiga yimata horo na azaba kala kala akan lallai ta amsa laifinta na kisa, dakyar Yagana ta amsa laifinta ganin tana shirin shurawa zuwa lahira.

Bayan Yagana ta amsa laifinta ne kotu tayanke mata hukuncin d'aurin rai da rai a gdan yari tare da horo maitsanani kasancewar yadda tayi wasa da hankli hukuma.

Balkisu tayi farinciki da samun nasarar da sukayi, hakanan akafito da baba Rabi dukk ta wani tsufa ta rame ta d'an canja kammanu.

Sunanan tsaye mallan zakiru dasu Balkisu, yansanda sukazo wucewa da Yagana hannuta saqale da ankwa ana qoqarin wucewa da ita gdan yari. Dasauri Mallan zakiru yatsaidasu nan fa yayi tayiwa Yagana tuni akan abubuwan dasuka faru yace" ynxu dai gashinan kinga qarshenki (Allah yashiryi masu halin sonkai irin Na Yagana)

     Baba Rabi kam sai godiya take ta jerowa Balkisu, daga bisani ne  Baba Rabi ta dubi Balkisu tace "baiwar Allah ko zan iya sanin koke wacece"? Balkisu tayi murmushi cike da farinciki tace "baba karki damu zanfad'a miki koni wacece amma da farko inaso ki kwntar da hnklinki kinatsu sbd nima yarkice kmr Meena"

Da sauri baba Rabi tadubi Balkisu tace yan nan kinsan aminatu ne Dan Allah tana ina? Kiwa Allah kifadamin koke wacece INA aminatu Na dan Allah kitaimaka ki kaini gareta, Balkisu tace Baba kwantar da hanklinki ynxuma wajan Meena zankai ki yanzu insha allahu zakiga Meena, wani irin hawayen farinciki ne ya lullu6e Baba Rabi.

Kofar wani katafaran gda Baba Rabi taga anyi parkn, cikin girmamawa Balkisu tace "Baba fito mushiga daga ciki", kurawa Balkisu idanu Baba Rabi tayi tana yimata wani irin kallon tuhuma cikin ranta tace "anya kuwa banyi kuskuren amincewa da wadannan mutanen ba, bansani ba ko masu yanke kan mutane ne" tana cikin wannan tunanin ne taji muryan Balkisu tace "Baba karkiji komai wlh babu abinda zamu miki kizo muje nakaiki wajan Meena" jiki a sanyaye haka nan baba Rabi tarufawa Balkisu baya suka shiga cikin gdan.

"Salamu alaikum! Salamu alaikum!! Anty amarya Meena" cewar Balkisu dai dai lkcin da suke qoqarin shiga falon.

      Meena kam nacikin d'akinta tana d'an wasu gyare-gyaren ta juyo kmr ana sallama, kuma kmr muryan Balkisu tajiyo domin dai ita  tasan cewa bata kai matsayin da Hafeez zai mata sallama ba. Dan haka da sauri ta tashi tafice a d'akin da sauri tanufi falo.

Da gudu Meena ta isa falon don tarbon Balkisu, Tursuuu Meena tayi ta tsaya cike da mamaki galala tayi da baki domin abinda taganewa idonta (tsawan shekara tara da suka shige Meena bazata taba mance wannan nagartacciyar fuskar ba) fashewa tayi da wani irin kuka mai tsanin ban tausayi.


Zaku jini anjima don jin cigaban lbrin, nagode.

®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [9:07AM, 8/2/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode3⃣0⃣

Wani irin farin ciki ne marar misaltuwa ya lullu6e Meena da gudu taqarasa wajan Baba Rabi, rungume junansu sukayi a tare suna ta kuka, Balkisu da Dr Muh'd kam suna daga gefe sai murmushi sukeyi.

Daga Meena har Baba Rabi anrasa mai lallashin wani, kuka sukeyi gwanin ban tausayi, dakyar Baba Rabi ta share hawayenta nan fa tashiga Shafa fuskar Meena ta ko ina sai mamakin girmanta takeyi, yayin da itama Meena sai kallon ta takeyi jiki take kmr ta manne a jikin Baba Rabi.

Bayan sun natsu sun zauna Meena ta umarci Daniel da yakawo musu drinks, cike da bin umarninta yakawo drinks kala kala yadiresu musu shi. Sai da suka d'an samu suka sharuwa sannan Meena tadubi Balkisu tayi ta zabga mata adduo'i nafatan alkhairi tare da yimata godiya, Balkisu sai murmushi takeyi.
      Ana cikin hakane Dr Muh'd yatashi yace "shi zai koma office" nan yayi sallama dasu yafice Balkisu har wurin mota tarakashi daga bisani takoma cikin gdan.

Meena kam ana nan liqe da Baba Rabi dan jitake kmr wani zai k'wace mata ita, Balkisu dai sai dariya take mata.
      Meena tadubi Baba Rabi tace 'Amma' (sunan da Balkisu ke kiran Baba Rabi dashi knan) Baba Rabi tadubi Meena tace "Naam Aminatu" Meena ta shagwa6e fuska tace Amma kintafi kinbarni cikin wahalalliyar rayuwa naga rashin gata naga tozarta naga walaqanci naga.....dasauri Baba Rabi ta toshe mata baki tace "haba Aminatu minene kike fad'a haka yakamata ace kin yarda da k'addara mai kyau ko marar kyau a matsayinki na muslma, sbd wannan halin da muka tsinci kanmu jarabawace ta ubangiji dukk abunda Allah yarubuto cikin k'addararka to tabbas babu makawa sai tasameshi" Dan haka karki wanisa damuwa aranki ko kice zaki dinga tuna baya hakan bashi da kyau, ynxu ita wacce kike son yin mgn akanta ae gashinan taga qarshen sakamakonta.

Balkisu ta jinjina kai tace tabbas Baba wannan haka yake, Baba Rabi ta gyad'a kai tace toh kinga in hakane kuwa bai kamata kidinga tuna abinda yariga yawuce ba, Na ma gode Allah dayasa nasameki da ranki cikin k'oshin lafiya gashi har kinyi aurenki a gdan mijinki kinga wannan ma wata baiwace ta ubangiji Dan haka ki gode masa kiqara gode masa a koda yaushe Allah yana tare da mai gaskiya sannan yana bayan masu hakuri.

Da sauri Meena tafada jikin Baba Rabi taqanqameta tana kuka, cikin zolaya Balkisu tace wlh anty amarya in baki daina wannan kukan naki ba xand'auki Baba mutafiyarmu, dasauri Meena ta dubi Balkisu ta d'an turo baki cikin shagwa6a.

Baba Rabi tanumfasa tace "miye naga kina turo baki ae da gaskiyar Balkisu sbd a yau insha allahu inaso naje garinmu nasadu da dangina. Balkisu ta gyara zamanta ta fuskanci Baba Rabi tace "Baba sai dai fa kiyi hkri koda zakije garinku to ba yau ba sbd muma muna buqatarki kusa da mu, sannan kada kidamu ba'anan zaki zauna ba akwai gdan da muka ajiye miki na mussaman a Famfamari, Riqe ha6a Baba Rabi tayi cikin nuna jindadi da farinciki ta waro idanu tace dukk nikadai? Irin wannan d'awainiyan anya kuwa baiyi yawa ba?

Balkisu tace haba dai Baba wanne irin yawa kuma kema fa tamkar mahaifiya kike agaremu dukk abinda zamu iya yiwa mahaifanmu to zamuyi miki dukk da cewan Mahaifan namu basa raye" Baba Rabi ta goge hawayen dake kwaranyo a mata a fuska, nan tashiga sawa Balkisu albarka gamida yimata ta'azziyar rashin da sukayi.

Babban tashin hnkli Meena tashiga yayin da taga Ammanta na qoqarin fita a cikin gdan, kuka takeyi sosai ita fa lallai sai tabisu. Balkisu tace haba Meena miye hakan? Sai kace wadda Baban guduwa zatayi, kiyi hkri mana tunda Yaya Hafeez baya nan kibari idan yadawo xai kaiki shi da kansa.
nan fa Meena tace batasan zancen ba.
     Dole Balkisu takira Hafeez tasanar dashi cewa tanaso zasu d'an fita wani waje tare da Meena, batare da 6ata lkci ba Hafeez yace Allah kiyaye.

Cike da farinciki Balkisu tad'aukesu a mota suka nufi Famfamari inda gdan Baba Rabi yake,
      Wani d'an matsakacin plat house ne mai kyan gaske, falo daya da d'akuna uku da toilet da kitchn sannan kowanne bed room da toilet dinsa.
  Masha allahu gda yayi kyau da tsari, Baba Rabi dai sai godiya take tana sama Balkisu albarka.

Bayan sun gama gyara ko ina Na gdan Balkisu tace da Meena ta shirya tayi dropn dinta a gda ita zata wuce gdanta tad'aura abinci.

Nan ma dakyar Meena ta yarda suka tafi cike da kewan Ammanta.
     Akan hanyarsu takomawa gda Balkisu tadubi Meena tace "toh anty amarya nacika miki dukkan wani alqawari naki inaso nima kicikamin nawa kikular min da yayana tamkar yadda uwa zata kula da d'anta. Dammm!! Gaban Balkisu ya buga a hnkli ta kalli Balkisu jiki a sanyaye ta gyad'a mata kai gamida cewa insha allahu.

Balkisu tayi murmushinta mai sanyi, dai dai nan suka iso kofan gdan, Meena tayi sallama da Balkisu jiki a sanyaye haka tabud'e get din tashiga, motar Hafeez tagani ajiye wurin parkn motoci wato hakan nanufin yadawo? damm! Taji gabanta yabuga sbd alqawarin da tayiwa Balkisu ne yafad'omata.
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [11:21AM, 8/2/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode3⃣1⃣

A hankali ta murd'a k'ofan falon tashiga ciki, Hafeez tagani tsaye hannunsa d'aya sanye cikin aljihu d'aya kuma yana amsa waya ya juya bayansa, cikin tafiyar sand'a kmr wacce bata da gaskiya Meena ta nufi hanyar d'akinta tana isa bakin k'ofa dai dai nan Hafeez na gama waya.

Wani uban tsawa yadaka mata yace "keee!! Zonan nan" Meena sai da tad'an figirta a hnkli ta juya akalarta izuwa falo, Hafeez ya watsa mata wata uwar harara cike da jin haushinta yace ke gdanku ba manya ne? Kina ganin mutane baxaki gaishesu ba ko ba akoya miki bane?  Meena ta turo baki a hnkli tace INA wuni, mtssw Hafeez yayi tsaki yace " bansani get out wuce kiban waje" Meena ta juya da sauri tashige d'akinta tana gunguni.

A hnkli Hafeeez yace "Mtssw village girl gal kawai"cike dajin haushin ganinta yanufi d'akinsa.

•°          •°         •°        •°
Yau ya kasance weekend Hafeez na nan gda sai wasu aikinsa yakeyi a system insa, zaune yake a falo sanye da farar jallabiya gabad'aya ya maida hnklinsa akan aikinshi.

A bangaran Meena kuwa a kullum bata da wani tunani da yawuce taya zata fara jawo hnklin wannan uban yan girman kan yakarka to izuwa gareta har tasamu tabashi kulawan.
       Cikin tunanin da takeyi ne wata dabara tafad'o mata dasauri ta tashi tanufi falo, dama cikin shirinta take tsaff, cikin natsuwa Meena ke tafiya har ta isa cikin falon Hafeez tagani zaune yanata aiki a hnkli taqarasa gareshi tace "assalamu alaikum" dasauri Hafeez ya d'ago kanshi Dan ganin wacece keyimishi sallama.
      Meena yagani tsaye gabansa sanye da wasu material riga da siket sun matuqar amsar jikinta tayi kyau abunta "koshi Hafeez cikin ransa sai da ya yaba wannan shiga" amma a zahiri sai cewa yayi wa'alaikissalam, nan kuma yatsaya sheqeqe yana kallonta cike da nuna isa yafara kusheta yace ke kuma fa miye hakan zaki zo kitsaya akan mutane?

Dasauri kuwa Meena ta zauna cike da sanyi tace "ina kwana" Hafeez ya amsa ciki ciki yace "lpy" Meena taqara da cewa sannu da aiki Hafeez yad'ago kanshi ya watsa mata wata uwar harara batare da ya amsa mata ba ya maida kanshi sannan yaci gaba da aikinsa, Meena na nan tsugunne Chan tasake cewa "amm kayi brkfst kuwa"? Hafeez yakawo iya wuya wani irin haushi yaji tabasa ina ruwanta da cikinsa, kallonta yakomayi ya watsar da yinta yacigaba da aikinsa.

Meena takawo iya wuya danne zuciyarta kawai takeyi dan haka dasauri ta tashi tabar gurin, d'akin ta takoma cike da jin haushin wannan izza da mulki na Hafeez.

Hafeez na nan zaune Daniel ya had'o kayan brkfst akan tire yanufi d'akin Meena dashi, yana zuwa yafara kwankwasa k'ofar d'akin a hnkli, da sauri Hafeez yajuyo dan ganin mai k'wank'wasa kofan d'akin Meena, Daniel yagani tsaye hannunsa d'auke da abinci da sauri Hafeez ya taso dai dai lkcin Meena tabud'e kofa.
    Wani irin takaici ne ya turnuqe Hafeez "cikin zuciyarsa yace lallema yarinyan nan yaushe ma tawaye da har zata fara bada umarni ana kawo mata abinci?sannan ma tarasa Wanda zata sa ya kaimata abinci sai Daniel da irin wannan shiga nata" Meena ce ta katse masa tunanin da yakeyi, jiyayi tace sannu Daniel har ka kammala Daniel yace "yes madam" hannu tasa zata amshi abincinta Hafeez yadakawa Daniel tsawa yace "oyaa maida abincin nan kitchn" jiki na rawa Daniel yajuya da abincin ixuwa kitchn kmr yadda boss din nasa ya umarce shi.

Juyawa yayi gurin Meena fuskan nan a turbune ya nuna tada hannu yace "ke yar qauye bari kiji kinyi kad'an kidinga bada order a gdan nan wai dan akaimiki abinci daga yau irin rana tayau bana so in qara ganin Daniel kofar d'akinki danufin wai yakai miki abinci kinajina koh? Kije da kanki kid'ibawa kanki inba haka ba kixauna da yunwa" har Hafeez ya juya xai tafi sai kuma yadawo ya dubi Meena duba na walaqanci yace "ke yar qauye inaso daga yau kezakina shiga kitchn da kanki kidafa abinci, take anan kuma yashiga kiran Daniel!

Jiki na rawa Daniel yaqaraso yace "yess oga" Hafeez yadubi Daniel yace as 4rm today inaso karka qara bin umarninta nacewa ka kawo mata abinci' Hafeez yariqe kunnensa yana mainuna alamar warning ga Daniel sannan yace "and then daga ynxu ita zata ke dafa abincinta" Daniel yace okay oga.

Hafeez nafad'in haka yajuya yabar wajan, Meena tsayawa tayi tana binsa da kallo cikin xuciyarta tace "jibeshi da anyi magana yawani cewa mutum d'an kauye qyaatt" juyawa tayi cikin d'akinta tad'auko hijabi tanufi kitchn dan tasamu abinda tasawa cikinta domin kuwa Meena intaji yunwa bata wasa da abinci.

Sumi sumi tanufi kitchn don tad'aura wani abun,...Hafeez na nan zaune ta ratsa ta gefensa tawuce, juyowa yayi yana kallonta tsaki yayi cikin xuciyarsa yace "village gal"

Kitchen Meena tashiga nan tafara laluben abinda zata dafa, tana cikin tsaka da dubawa ne taga hango kwalin indomie da sauri ta janyo kwalin tad'auki indomie biyu nan ta kunna rishow kasancewar bata iya amfani da gas ba.

Take anan Meena tafara dahuwar indomie dinta wnda taji albasa da attaruhu, ae fa nan gda ya kaure da qamshi Hafeez kam mayen indomie take anan yajiyo qamshi na dukan hancinsa wani irin yunwa yaqarajin tashigesa kasancewar dama baiyi brkfst dinsa ba.

®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:00PM, 8/3/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode3⃣2⃣

Dasauri Hafeez yamiqe yanufi kitchen din, dai dai lokacin ne kuma Meena ke qoqarin juye indomie dinta a plat, yawun Hafeez ne yatsinke sai wani had'iyar yawu yake (sbd Hafeez na mutuwar son indomie shiyasa ma kullum gdan baya rabuwa da kwalayen indomie) Cikin natsuwa Meena ta bud'e fridge din dake ajiye cikin kitchen tabud'e tad'auki exotic mai sanyi sannan taduqa tad'auki indomie dinta.

Hafeez bai tsammaci fitowar Meena a lkcin ba jiyayi kawai sunyi karo da juna, dasauri Meena tace "subahanallahi" wani irin takaicine Yakama Hafeez ganin cewa ita kad'ai ta dafawa kanta indomen, duba jikinsa Hafeez yashigayi ko allah zaisa yaga inda ta6ata masa jiki yasauqe haushinsa akanta, amma sai dai anyi Sa'a babu inda jikinsa ya6aci,dan haka dubanta ya shigayi kmr wacce tayi wani abun.

Meena kam tsaye tayi tanabinsa da kallo, Chan Hafeez yaqufula yace "ke yar qauye wannan wacce irin qaxamar dahuwa ce kikayi jibi yadda kikawani zabga tarugu sai kace wata maiyya.

Meena tazaro ido waje tace "nice mayya Kuma?"batare da Hafeez ya kulata ba yace "common get out" Meena taratsa ta gefenshi zata wuce tana gunguni Hafeez yace "magana kike ne?" Meena ta manna masa ta wucewarta, Hafeez yayi tsaki yace qyatt yar qauye kawai sai wani faman big head kike xanyi maganinki very soon. Nan yashiga kwalawa Daniel kira!

 
A bangaran Meena kuwa d'akinta ta wuce kaitsaye dukk haushi ya isheta mgnr Hafeez ce kawai ke mata yawo a kunnenya, kwafa tayi cike dajin haushi tace "tabb wato ni Hafeez zaicewa Maiya? Wlh sai yagane kurensa sai na mai dashi yazama mayen shima in yaso mahad'e muzama mayun mu biyu,..Meena sai faman cin  indomien din ta takeyi wnda taji kayan had'i, tanaci tana masifa ita kid'ai a d'aki.

•°         •°        •°       •°
Washe gari.
Meena tunda safe bayan ta idar da sallah tanufi kitchn dan tasamu abinda tad'aura, mgnr Balkisu ce tafad'o aran Meena lkcin da aka kawota inda Balkisu ke sanar da ita abunda Hafeez yafiso yayi brkfst dashi wato soyayyan kwai da tea, dariyar mugunta Meena tayi, nan tashiga farfasa kwai wnda xatayi amfani dashi ta jajjaga tarugu mai yawa ta yanka albasanta tazuba maggi da kayan kamshi ta zuba cikin kwan ta bubbugashi sosai yabi jikinsa, nan tahau suyan kwan, daga gefe kuma tad'aura ruwan zafin tea dinsa Wanda tazuba lipton da citta suga da kalinfari da barkono sosai, ae fa nan qamshi ya karad'e gdan.

Hafeez sai da ya tabbatar da cewa yayi wanka sannan ya shirya tsaf abinsa cikin shaddarsa sky blue sai hularsa wadda tayi matchn da kayansa, agogon hannunsa yad'auka yasa sannan yafesa turare yanufi hanyar fita, bud'e kofan nan da Hafeez zaiyi yaji kamshin ya doki hancinsa da sauri yaqarasa cikin falon ko da yaduba dinning area yaga anshirya komai tsaf tsaf kmr yadda aka saba, cikin hanzari yanufi dinning table yaxauna tare da duban agogon hannunsa qarfe takwas da rabi yana ganin haka yayi saurin zaro wayanshi dake aljihunsa, wata nmbr yayi dialing cikin natsuwa yake mgn yace "yes mansur am on ma way just giv me 15 to 20 mint a will b thr soon" yana gama wayar ya hau bud'e brkfst din ruwan zafin tea din yafara zubawa kadan cikin cup sannan yadibi kwan nashi cikin plat, wani irin kamshi mai dad'i ne yake ta doke hancinsa.

Sai da ya tabbatar da ruwan xafin yad'an huce dai dai yadda zai iya sha sannan yajawo kusa dashi, plat din kwansa yasa agaba dasauri yadebo mai yawa yaddana a bakinsa yafaraci a hnkli yad'an lumshe ido sai da kwan yakai qarshe Hafeez yaji wani irin azababben zafin barkono ya ziyarci harshensa dasauri yafurzar ya dauki cup din tea dinsa ya kurba ko zaiji d'an ji dama, ae fa nan Hafeez ya miqe tsaye idanunsa sukayi jajir harshensa yadinga fiddowa waje sbd tsabar azaban da yakeji ko mgn yakasa(kasancewar Hafeez bayason abuda yaji SBD ulcer)

Meena dake la6e tana kallonsa sai kwasar dariya take abunta, kara leqawa tayi don taga yadda yake daka tsalle ae kuwa tana sa kai sukayi ido biyu da Hafeez.

NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:10AM, 8/4/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode3⃣3⃣

Hafeez nahad'a ido da Meena yatabbatarwa kansa cewa itace tahad'a masa wannan muguntan, dan haka a fusace yayi kanta sai dai Hafeez baisamu daman qarasawa gareta ba sbd wani irin abu da yatsaya a zuciyansa nan da nan yanemi hnklinsa yarasa jagwaaf yafad'i qasa gamida riqe kirjinsa yanata mutsu-mutsu a kasa. Abu dai kmr wasa wasa tun Meena na yar dariyarta har dai talura cewa Hafeez da gaske yake, ae da gudu Meena taqarasa inda yake kwnce nan tashiga jijjigasa tana kiran sunansa.
      Gabad'aya idanunsa suncanja kala Hafeez yajigata sosai zuciyarsa wani irin suya take masa.

Meena ta lura abin nashi dagaske ne ba wasa dan haka dagudu tashiga kiran Daniel, Daniel yazo da hanzari ganin ogan nasa cikin wani hali hakan yasa yafahimci cewa ulcer dinshi ne yatashi  dagudu Daniel yashiga d'akin Hafeez yad'auko maganinsa nan ya qoqarta yasamu yabashi maganin yasha.

A hnkli Daniel yasamu yad'aga Hafeeez dakyar yataimaka mishi ya kaisa d'akinshi. Hafeez jiyayi tsanar Meena taqaru a xuciyarsa.

A bangaran Meena kuwa jitayi gabad'aya jikinta yayi sanyi, sai ynxu takejin kwata kwata bata kyauta ba nadama tashigayi marar iyaka.


Tunda wannan abu yafaru kuwa Hafeez bai qara bin tankan Meena ba, yar kulatan ma dayakeyi suna rigima kwata kwata ynxu ya daina.
      Mgnr abincinsa kuwa Daniel kedafa mishi kmr kullum.

•        •      •     •     •      •
Meena abin duniya dukk ya isheta Hafeez ko kallon indatake baya son yi jiyayi gabad'aya yatsaneta, shiyasa da zarar gari yawaye yake Allah Allah yafice a gdan.

Yayin da ita kuma Meena ke tunanin hanyoyin da zatabi dan taga cewa ta kyautata masa, Hanyar farko da Meena tafarabi shine da zarar Hafeez yafita zuwa office dinshi a wannan lkcin ne take shiga d'akinsa ta gyara ko ina ta wanke toilet tattara under wears dinsa ta wanke masa, haka kullum Hafeez idan yadawo sai yaga komai Na d'akinsa very neat.

Ana cikin hakane Daniel ya samu Hafeez yasanar dashi cewa yanaso zai zaije enugu can garinsu domin gudanar da bikin kirisimeti, Hafeez yayi mishi izini sannan yad'auki kudi mai tsoka yabawa Daniel.

Lkcin da Daniel zaitafi garinsu har qofan d'akin Meena yaje yayi sallama da ita, nan itama tayi mishi fatan adawo lafiya.

*DA YAMMACI*
A yammacin ranar ne Meena tashiga kitchen tad'aura tuwon semo da miyan d'anya ku6ewa, Meena taxage sosai tadafa abinci mai kyau da tsari dukk dan taburge Hafeez.
     Bayan Meena tagama girkinta ne  takoma d'akinta toilet tashiga ta silla wankanta sannan tafito tashirya tsaf abunta cikin wata jar atamfarta mairatsin ash kala, atamfar taimata kyau sosai, simple mark up tayi sannan tanufi falo taxauna ta kunna Tv.

Horn din motar Hafeez Meena taji, dasauri tamiqe taleqa window' Hafeez din ne kuwa ta hango yayinda yake qoqarin fitowa a mota, dasauri takoma maxauninta.

Murd'a kofan falon yayi yashiga batare da ya lura cewa akwai mutun a falon ba, dasauri Meena ta taso da fara'arta tayi mishi sannu da zuwa batare da Hafeez ya kulata ba tasa hannu tana qoqarin ansar briefcase dinsa, wani irin takaici Hafeez yaji baisan lkcin daya tunkud'e ta ba tafad'i. Hafeez ko ajikinsa haka yatsallaka Meena yawuce.

Dinning area yamaida dubansa yaga cewa tahad'a masa abincin dare tsaki yaja mtssssww stupid, Hafeez nafadin Haka yanufi d'akinsa.

Jikin Meena yayi sanyi sosai a hnkli ta tashi a wurin tashiga d'akinta, saman gadonta tahau tarafka wani uban tagumi nan tashiga yin tunani kala kala akan yadda zatabi da hafeez nan dai tayanke shawaran zata jure komai dan ganin tacikawa Balkisu alqawarinta kmr yadda tacikamata nata.

Magri nayi Hafeez ya d'aura alwalarsa yawucewarsa  masallaci, bayan sun idar da sallah restaurant yanufa kai tsaye yacika tumbinsa, dukk da cewa yasan Meena tayi girki amma Sam baijin iyacin girkinta koda wasa.

__•__•__•__°__°__°__•__•__•
A kullum Meena tana qoqari sosai wajan kula da Hafeez, ta gyara mishi d'aki tasa roomfrshnr ta wanke toilet dinsa tagyara mishi kayansa, sannan tayi mishi girki kullum dukk da cewa Hafeez bayaci amma Meena dai dai da rana d'aya bata fasa abubuwan da takeyi ba, tsawa da gyara turi da masifar Hafeez baya hana Meena ta kyautata masa.


Meena ce zaune a falo tanajiran shigowar Hafeez, sai jin tayi telephone Na qara (wato landline wnda kowa xai iya d'auka, kasancewar Meena batada waya) dasauri  Meena tamiqe ta isa wurin da telephn din ke ajiye tad'aga wayan kmr yadda taga Hafeez nayi, sallama tafarayi sannan suka gaisa
      Take anan Meena tagane muryan Balkisu ne nidai naga Meena sai murmushi takeyi daga bisani kuma naji tace mekikace daqarfi!! ?? Gabadaya naga hankli Meena yatashi dasauri tajefar da wayan tanufi d'akinta.
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [11:47AM, 8/4/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode3⃣4⃣

A rikice naga Meena tafito daga d'akinta sanye da hijab dasauri naga taja kofan d'akin ta rufe sannan tanufi hanyar waje a hanzarce, bakin titi tanufa kai tsaye da alamar tana jiran abin hawane.

Kmr wucewan minti biyar Meena na nan tsaye bata samu abin hawa ba, sai ga Balkisu nan cikin motarta tun kafinma taqarasa tagane cewa Meena ce tsaye bakin titi.
      Dasauri Balkisu tayi parkn din motarta kusa da Meena, zuge glass din motar tayi lkcin ne Meena tafahimci cewa Balkisu ce, ae kuwa da hanzarinta taqarasa cikin motar.

Bayan tashiga cikine Balkisu tafashe da yar dariya tace "a'a Anty amarya inazaki haka badai kice mgnr da mukayi bane dukk tafirgitaki haka ba?" Meena tayi wata irin sassanyar ajiyar zuciya tace  "haba Balkisu mai xai hana hanklina baxai tashi ba karki manta fa cewa basan garinsu mahaifiyata ba ynxu idan ta tafi tabarni batare da nabita naga dangina ba mai kike tunanin xaifaru? Gsky nidai xanbi Amma na xuwa garinsu, Balkisu tadubi Meena da murmushin nan nata tadafa kafad'arta tace "haba kekuwa Anty amarya ae baki bari naqarasa miki abinda nake son cewa ba kawai naga kinkatse call din shiyasa kikaga nafito a hanzarce".

Ynxu koh da ace bin Baba Rabin zakiyi hakanan zakitafi batare da izinin yayana ba ko kuwa hakanan zakije hannu siddan babu kayan sawa balle tsaraba?

Meena ta sadda kanta qasa tace "wlh dukk na rikice ne sbd bana fatan abinda xaisa nasakeyin nisa da mahaifiyata" Balkisu tace "hakane amma ae ba yau bane tafiyan nata sai jibi ne fa Dan haka muje namaidaki gda ki kwantar da hnklinki zanfad'awa Yaya mgnr tafiyan naku amma inaso kema kisameshi dakanki kifad'a masa, toh kawai Meena tace.

Hakanan Balkisu ta mai da Meena gda sai faman zolayanta takeyi.


         **        **        **
Hafeez ne zaune awani tafkeken Restaurant yana cin abincinsa hnkli kwance, daga gefe kuma inda ya ajiye wayansa tashiga ruri! A hnkli Hafeez yajawo wayan 'luvly Sister' sunan da Hafeez yayi saving nmbn Balkisu shine ya baiyanna agaban screen din wayansa da sauri yad'auka gamida sawa a kunnenshi, bayan sun gaisa ne Balkisu ke sanar da Hafeez mgnr tafiyan Meena wnda zasu ita da mahaifiyarta, Hafeez yace "olryt Allah yakaimu lkcin" Balkisu tace ameen nan suka d'an ta6a hiransu daga bisani kowannensu ya ajiye waya.

Abangaran Hafeez kam shiru yayi hakanan kuma sai yakejin kmr babu dadi, can dai kuma ya hori xuciyarsa tama daina damuwa da wannan yar qauyan ae ma inta tafi kahuta, inba ma tsabar rainin wayo ba Balkisu nake aure ko ita ae kamata yayi taxo da kanta taneme ixinina wato tanaji ita watace tafi qarfin takawo kanta knan?, hakanan Hafeez yayi tasaqawa da kuncewa a cikin xuciyarsa. Har dai yagama cin abincinsa sannan yanufi gda.

Yau ma kmr kullum Meena tayi masa  abinci ta ajiye dukk da tasan cewa baci xaiyi ba, haka nan bayan shigowarsa cikin gda har bakin kofa tabisa dan ta tarbeshi amma gayen nata ko kallon inda take baiyi ba, balle yanxu dama cike yake da haushinta akan qin xuwa da batayi da kanta tafara tambayarshi ba.

Inda sabo kam Meena tasaba da irin abubuwan da Hafeez ke mata wanda zuwa ynxu kam har sun fara daina damuwarta.
     
Misalin qarfe tara na dare Meena tashiga bayi tayi wnka sannan tad'airo alwala, kayan bacci tasaka masu sauqin nauyi hakanan tajawo xani tad'aura saman sleepn drss din sannan tasanya hijabinta ta gabatar da nafilfilunta kmr yadda tasaba, bayan ta idar da sallah  ne ta yankewa xuciyarta shawaran cewa gwnda taje a daidai wannan lkcin tasanar da Hafeez mgnr tafiyanta inba haka ba da safe koh da zata tashi olrdy ya fita.

Hakanan ta gama yanke shawaran ta, ta amincewa zuciyarta, Dan haka d'akin Hafeez tanufa kai tsaye a hnkli tashiga knckn kofar,...sai da Hafeez yagama jan ajinsa kasancewar yasan babu wnda xai kwankwasa mishi kofa adaidai wannan lkcin sai Meena shiyasa sai dayagama jan ajinsa sannan yace yes come in!  A hnkli Meena ta murd'a kofan d'akinta shiga.
       Hafeez tagani zaune bakin gado dagashi sai farar vest da boxsas yanata aiki da system inshi, da sallama tashiga cikin d'akin, Hafeez ya amsa mata sallamarta batare da yad'ago ya kalleta ba.

Meena taduqa har qasa ta gaida Hafeez,..Hafeez kuwa ko kallo bata ishesa ba amaimakon ma ya amsa gaisuwansa datayi sai cemata yayi yes inajinki fad'i abunda yakawoki kinga aiki nakeyi.
      Meena ta had'iye wani yawu dakyar yawuce sannan ta sadda kanta qasa sbd jitayi gabad'aya Hafeez yayi mata wani irin kwarjini, cikin nutsuwa Meena tace "dama Amma nane xatayi tafiya xuwa gda shine nake so na bita" Hafeez yace "dakyau yar qauye xa'aje qauye kenan? Meena dai batace masa komai ba sai wasa kawai take da d'an yatsanta.

Wani murmushin takaici Hafeez yayi sannan ya d'auko wata waya LG yamiqa mata yace ga waya nan inkinje kiyi amfani da ita, Meena ta amsa tayi godiya sannan Hafeez yad'auko bandir din kudi yan dari biyar biyar ya watsawa Meena cike da gadara yace gashinan wannan akaiwa tsohuwa nasan zata buqata.

Mgnr Hafeez ta matuqar 6ataran Meena amma sai ta danne xuciyarta miqewa tayi cike da d'acin rai takalli Hafeez ta kalli kud'in har dai Meena tayi niyar sakar mishi mgn sai kuma nan da nan ta taushi zuciyarta, ajiye masa kudinsa tayi a qasa dai dai  qarfarshi taficewarta a d'akin.

Binta Hafeez yayi da kallo cike da mamakinta
®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:27AM, 8/5/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode3⃣5⃣

Balkisu da kanta taje wani babban super market tahad'owa Baba Rabi tsaraba masu kyau na amfani, su sabulun wnka wanki turaren shafawa kwalayen biskuit da dai sauransu, hakanan ta kwasa tayi gdan Baba Rabi dasu ta kai mata. Baba Rabi tayi farinciki sosai da irin yawan hidimar da Balkisu keyi da ita, nan tayi tasawa Balkisu albarka gami da nuna farincikinta.

Washe Gari.

Tunda asuban fari bayan Meena ta idar da sallah batasamu ta kwanta ba sai da ta tabbatar da cewa tayi dukkan wani aikinta kmr yadda tasaba, agogon dake liqe jikin bangon d'akinta ne yabuga qarfe 6:30 a gaggauce Meena tafad'a toilet tayi wanka kasancewar tasa qarfe 7:00 Hafeez ke fita, gashi yau tanason tawuni gdnsu dan tasan irin shirye shiryen da yakamata suyi ita da Ammanta.

Wata dakakiyar shadda lemon green wadda akayiwa aiki dazare orange, riga da siket ne su Meena tad'auko tasa (woww ni kaina munay sai dana yaba wannan shiga) dukk da ba wata kwalliya Meena tayi sosai ba amma tai matuqar kyau, nan tad'auko takalmi orange gyale orange.
      Motsin Hafeez taji yana qoqarin fitowa daga d'akinsa dasauri taduba agogo taga 6:57 a hanzarce ta zura wata qatuwar Hijabi tanufi waje.

Ki6iss sukayi da juna Hafeez ke kokarin fita yayin da Meena tafito a d'akinta dasauri tace Yaya!!

Mamakine qarara ya baiyanna a fuskar Hafeez jin cewa Meena ke kiransa da Yaya dukk da cewa bata fiye kiran sunansa ba, sannan a iyazatonsa yana tunanin tayi fushi da shi sbd abinda yayi mata jiya daddare.

Tsayawa Hafeez yayi batare da ya juyo ba, a hnkli Meena taqarasa kusa dashi tace "ina kwana" Hafeez ya amsa a takaice Lfy, Batare da nuna damuwa ba Meena tace "Dan Allah sonake kamin izini xanje gdnmu nawuni acan sannan inba damuwa inaso ka ajiyeni a gda.
       Hafeez har yayi niyyar cewa wani abu sai kuma yafasa, juyowa yayi yakalleta sama da wasa sannnan yace olryt nabaki nan da minti d'aya inbaki shirya ba xan wucewata.

Ae Hafeez nacewa haka dasauri Meena ta miqe kafinma Hafeez yabar falon tuni tashige d'akinta hijabin dake sanye jikinta tacire tasanya gyalenta sai takalminta da tasa tad'auki wayarta a gaggauce tarufe d'akinta da kofar falo, kasancewar ita da Hafeez kowa nada nashi mukullin.

Hafeez ne zaune cikin motarsa yana jiran fitowan Meena, hango ta yayi tafe sanye da gyale dasauri Hafeez yasake kallonta dakyau wani irin abu yaji ya d'arsu a zuciyarsa wanda shi kansa baisan miye ba wani irin kishi yaji domin kuwa ko da ace maqiyin Meena ne yaganta to tabbas dole ya yaba mata sbd tayi masifar kyau, cikin zuciyar Hafeez yace "lallai yarinyan nan ta rainamin hnkli ba ynxu naganta sanye da hijabi ba? Wato dan zata fita shine hadda wani sa gyale.
      Hafeez naganin Meena taqaraso ya  watsa mata wata uwar harara, wanda hakan yasa Meena tasha jinin jikinta, a qufule Hafeez yace kee wato baki shirya fita zuwa anguwan ba shine kikayi westin tym dina?

Meena tadubi kanta sama da qasa sannan tasake duban Hafeez tace "wlh yaya na shirya" Hafeez yadaure fuska yace kina nufin da gyalen nan zaki fita? Meena tafahimci abinda Hafeez yakeson cewa wato bai da tsarin son iyalinsa su sa gyale, dasauri Meena ta koma cikin gda tasanyo hijabi dukk da cewa hijabin sam baiyi matchn dakayan jikinta ba hakanan tasanya abinta domin ita dai buqatarta kawai ta jita ajikin Ammanta.

Gdan baya Meena ke qoqarin bud'ewa dasauri Hafeez yace ke yar qauye wakike ajiye drivanki look inbaki shirya tafiyan ba nixan wucewata ko ancemiki banda abubuwan yine, jiki a sanyaye Meena tabude gdan gaba taxauna Hafeez yaja motan sukafice a gdan.

Sanin datayi Hafeez baisan gdnsu ba shiyasa tadubeshi cikin sanyin muryanta tace "famfamari zamuje wurin masallacin juma'a, ko uffan Hafeez bai ce mata ba hakanan yaja motarsa yanufi anguwan da tafad'a mishi.
      Sunxo dai dai kofan gdan ne Meena tace sun iso tsayawa yayi a hnkli daga gefen hanya, Meena tasa hannu zata bud'e kofan Hafeez yace "ke tsaya yar kauye karki 6allamin murfin mota, zura hannunsa Hafeez yayi yabud'e mata kofan sannan yace, nabaki nan da awa biyar kikoma gda kinji abinda nace?"

 Ran Meena ya6aci sosai amma talura Hafeex neman rigima yakeyi shiyasa kawai ta gyada masa kanta tafice a motar.

Meena taji dadin kasancewa da Ammanta sosai wnda har hakan yasa tashagala tamance da umarnin Hafeez.

Qarfe 2 dai dai Hafeez yakoma gda amma still Meena bata dawo ba, wani irin haushi Hafeez yaji ganin cewa yadawo gda babu Wanda ta tarbeshi dukk da cewa baya kulata amma yau din sai yaji babu dadi.

Wani irin tunani ne yazowa Hafeez lkci d'aya wanda yad'imautashi, dasauri ya zari car key dinshi yafice a gdan, gdansu Meena yanufa kai tsaye sbd tunawan dayayi cewa matuqar Meena tace zata koma gda tofa motan haya xata hau, tunanin Hakan ne yasa ya gaggauta zuwa yad'auko ta da kansa.

Hafeez na danna kan motarsa cikin kwanar gdansu Meena nan ya hango abinda yad'aga masa hankali.


®NWA
[1:16PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:23AM, 8/5/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode3⃣6⃣

Hafeez Meena ya hango tsaye a kofar gdansu ta tsaida mai adai-daita sai faman murmushi takeyi mishi yayin da suke mgn ita da mai adaidaitan, wani irin kishi Hafeez yaji, nan fa jikinsa yafara kyarma a guje yashiga cikin layin ko gabansa ba ya iya gani mai kyau, Hafeez na pake motanshi kafinma yakasheta a hanzarce yabude murfin motan yafita batare da ya kashe motan ba.

Gadan gadan Hafeez ya nufi kan mai adai daita, mai adai daita na cikin tsaka da ciniki da Meena sai ji kawai yayi anshaqo wuyansa ta baya ana dukansa ta ko ina.
       Dasauri Meena tafasa ihuu! Tana roqon Hafeez da yabar abinda yake yi, Hafeez kam kojin ta bayayi gabad'aya jiyake kmr ya kashe mai adai daitan sbd haushi,. ihuun da Meena takeyi ne yajawo hnklin mazan anguwar dakyar suka samu suka kwaci mai adai daita a hannun Hafeez.

Idanun Hafeez gabad'aya sun rine sunkoma ja sbd tsananin kishi, a tsorace Meena tafara ja dabaya sbd gabad'aya Hafeez tsoro yabata sai wani irin huci yakeyi tamkar zaki cikin dawa, gawata uwar harara dayake jeho mata.
     Da gudu tashiga gdansu dai dai lkcin ne Baba Rabi takejiyo hayaniya daga waje dole tamiqe tanufi hnyar waje don ganin mekefaruwa, Meena ce tashigo gdan da gudunta sai faman waiwayen bayanta takeyi.

Hafeez kam mutanen cikin anguwar sai tambayanshi sukeyi mai wannan bawan Allah yamasa? Kota Kansu Hafeez bai biba yanufi motarshi ya kasheta yarufe sannan yanufi cikin gdansu Meena din.
     Meena rungume Amma tayi dukk tsoro yacikata sai wani faman haki takeyi kmr wacce tayi gudun 3kilomita, Baba Rabi sai faman tambayarta takeyi Aminatu lpy kuwa meyaparu waye ya biyoki? Meena kasa mgn tayi sai faman kallon hanyar shigowa gdan takeyi a tsorace "domin atunani Meena hadda ita Hafeez zai hada"

Hafeez ne yashigo gdan sallamarsa, Baba Rabi ta amsa mishi sallaman yayin da ta kura mishi ido tanajiran yafad'i da wacce yazo domin atunanin Baba Rabi shine Wanda ya biyo Meena,(domin kuwa Baba Rabi ko a hoto bata ta6a ganin Hafeez ba) Hafeez har qasa yaduqa ya gaishe da Baba Rabi, Baba Rabi ta amsa "lafiya kalaw" Lkcin ne Meena tayi wata irin sassanyar ajiyar xuciya sannan tace "Amma wannan shine Hafeez yayan Balkisu" Baba Rabi ta fad'ad'a murmushinta sosai tace "Allah sarki kayi Hkri Sam ban shaida ka ba, nan tayi mishi iso ixuwa cikin gdan, A falo Hafeez yazauna Baba Rabi da kanta takawo mishi abinci tuwon semo da miyar allayahu zallah, drinks takawo mishi da ruwan sanyi.

Baba Rabi da Meena kitchn suka koma suka fara had'awa Hafeez juice din kwakwa, Hafeez kam yunwa yakeji sosai dan haka bude kulan yashigayi tuwon semo yagani anyi malmalanshi ansa leda tsaf sai kuma miyan allayahu wnda taji manja, malmala d'aya Hafeez yad'iba yasa a plat bayan yazuba miyan allayahun nan fa yahauci, kafin Hafeez ya ankare tuni yagama da malmala guda"woww vry nyc Hafeez kawai ke fad'i yana lasan baki๐Ÿ˜‹"

Meena ce tashigo Hannunta d'auke da jug din juice din kwakwan, duqawa tayi tad'auki glass cup a kusa dashi batare da ta kalleshi ba tashiga zuba mishi.
       Kura mata idanu Hafeez yashigayi kmr yajawota kusa dashi haka yakeji, Meena nagama zuba mishi juice din ta tashi tabar falon a hanzarce.

Hafeez jiyayi kmr baxai iya tashi awajan ba sbd wani irin qoshi dayayi, rabonsa da cin abinci kmr haka har yamanta, murmushi kawai Hafeez keyi shi kad'ai yasan abinda yasashi murmushin.
      Meena ce tashigo cikin falon wannan karon ba Hijabi, filas din da Hafeez yagamacin abinci dasu shine Meena tashigo danta kwashesu, Hafeez kam sai binta yake da kallo tamkar wata baquwa, Hafeez kam sai mamakin knsa yakeyi yadda ya lura cewa Meena naqoqarin zautar dashi lkci d'aya   mamakin kansa  yashigayi sosai wnda har Hafeez yakama tantamar anya kuwa shine? (LOL)

sai da Meena ta gama kintsa falon sannan Baba Rabi tashiga falon suka sake gaisawa da Hafeez, Baba Rabi tasake da Hafeez sosai sai jansa take da fira, wanda shikuma Hafeez gabad'aya kunya tagama cikasa kasa sakewa yayi da Baba Rabi, bayan sund'anta6a hira sama sama ne Hafeez yaciro kudi Wanda shi Kansa baisan iyakarsa ba yace wa Baba Rabi gashinan tayi tsaraba, dafarko Baba Rabi qin kar6a tayi tace a'a ae Balkisu tayi musu hidima sosai dan haka baxata kar6i kudinsa ba, gabad'aya Hafeez jiyayi daraja da kimar tsohuwar taqaru a idonsa, dakyar dai Hafeez ya samu ya lallama Baba Rabi ta Amshi kudin,....daga bisani Hafeez yace da ita shi xai wuce gda dama yaxo ne dan yayi mata Allah yakiyaye hanya,  Baba rabi nan tayi tasa mishi albarka tana mai nuna jindadinta sosai.

Hafeez nafitowa Meena tasa Hijabinta tad'auki wayarta sukayi sallama da Amma, a hanzarce tarufawa Hafeez baya a tare suka fice a gdan.

Gaban Meena sai dukan uku uku yakeyi gabad'aya taqisakewa sai faman takure kanta takeyi.


®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [8:50AM, 8/6/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode3⃣7⃣

Daga Hafeez har Meena ba Wanda yace da wani uffan haka har suka isa gda, Hafeez nayi parkn Meena tayi sauri tafice a motan, tsuki Hafeez yayi cike da haushinta, a filin gdan Hafeez yayi parkn din motanshi baiko sami damar sakata ma ajiyarta ba, a hanzarce yarufawa Meena baya.

Meena da sauri tabud'e kofan falon sannan tanufi d'akinta, isar take nan takama kofan da niyyar tabud'e sai jitayi Hafeez yace "kee! Tsaya anan Meena ko waigawa takasa tsaye tayi bakin kofar kmr wadda aka shuka.

Hafeez nazuwa a fusace ya manna Meena ajikin Bango, take mata babban yatsanta yayi naqafa da qarfi Meena tasaki Yar qara, Hafeez yace "aikin banxa ashe kina mgn?, Meena ganin Hafeez ya kura mata ido ko kiftawa baiyi yasa tasadda kanta qasa, Hafeez gyad'a kai yayi yace "dakyau hakan Yatabbatar min da cewa baki da gaskiya sannan inaso kifad'a min uban waye yabaki izinin tare mai adai daita har kitsaya dashi kina masa dariya? Meena wacce sai mutsu mutsu takeyi tanason kwace kanta daga riqon da Hafeez yayi ma hannayenta gashi ya taka mata babban d'anyatsa yaqi sakewa, Meena kamar xatayi kuka tace nifa badariya nake mishi ba, kawai tambayarsa nayi anawa xaikain.....kafin Meena taqarasa abinda take son cewa Hafeez yadaka mata tsawa yace ni ba wannan natambayeki ba cewa nayi meyasa kike masa dariya?
    Meena tayi rau rau da idonu tace Dan Allah yaya kayi hkri baxan sake ba.

Hafeez yace no ba laifinki bane laifina ne sbd kin raina ni ko? Meena ta girgixa kanta tace "a'a

Hafeez yace okay toh yayane? Wato hakan ma yananufin cewa idan kukaje garin naku haka xakiyi behaving? Kina tare masu abin hawa kina musu dariya? Toh bari kiji inkikasa wasa a tafiyan nan wlh sai nace babu inda zaki, sannan sbd tsaban kinrainani wato nabaki awa biyar akanki dawo gda shine kikayi xamanki sbd tsabar kinnrainani ma shine kike ganin kinfi qarfin kid'aga waya ki kirani kice xaki koma gda.

Meena tace "wlh ba haka bane nadauka kana gurin aikin kane shiyasa nayi tunanin komawa da kaina, a firgice Hafeez yaqara matse ta da bango wnda gabad'ayansu sunajin numfashin juna, Hafeez yamatso da kanshi daf da fuskar Meena yace" an gaya miki cewa aiki na yafiki muhimmanci ne ko kuwa bakisan cewaa..shiru Hafeez yayi ya kasa qarasa abinda yake son cewa.

Sake mata hannu yayi sannan yanuna ta da yatsa yace toh bari kiji ban amince ko da kinyi wannan tafiyan ki ke yawaita hawan motan haya ba ko kice xakisawa mutane gyale, can kuma Hafeez ya kufula yace ke daga yau ma nayi canceln sa gyale a gareki, inkinga kinsa gyale toh daga ke sai nine acikin gdan nan kinajina ko?
     Da sauri Meena tace ehh!
      Hafeez ya gyara tsayuwansa ya kalli Meena dakyau sannan yace in kunne yaji jiki yatsara, d'akinshi ya wuce yabar Meena tsaye.

Huuhh!! Shine abinda tace kawai tashiga d'akinta
     A gajiye takwanta bisa gadonta tadafe goshinta, cikin zuciyarta tace "hmmm Yaya kenan dama nakawo haka araina sbd naga take takenka kwana biyun nan sokake ka hanani wannan tafiyan shiyasa kake tsiro da rigima kala kala nikuwa nasan halinka dan haka a ynxu dai baxan biye maka muyi ta rikici ba, balle kasamu galaban hanani yin wannan tafiyan.

Kiraye kirayen sallahn la'asar din da akeyine yasa Meena tayi hanzarin tashi tanufi toilet tad'auro alwala.


Abangaran Hafeez kuwa wani irin abune yatsaya mishi arai nan yafara jerowa kanshi tambayoyi wai mema yasa nadamu da lamarin wannan yar qauyen ne mema zaisa naji kishinta ohh my god kar fa najawa kaina raini agun wannan bakauyiyar yarinyar (nidai Munay dariya nayi, nace araina babu mai amsa maka wannan tambayoyinaka sai munturo maka JUMAYMA Yar bincike ta bincika mana kai LoL)

Hakanan Hafeez yayi ta faman sintiri cikin d'aki shi kad'ai yarasa abunda ke mishi dad'i domin gabad'aya jiyayi bayason abinda zaisa Meena tayi nisa dashi. Tunani barkatai Hafeez yayi tayi har dai shima yajiyo kiran sallahn yatashi yad'auro alwala yanufa masallaci.

      **                    **
Bayan dawowar Hafeez a masallaci haka kawai ya tsinci kansa da son xaman falo, kasancewar Meena nacikin kitchen, shiyasa ya zauna yana kallon dukk wani shiga da ficenta.
     Haka nan Hafeez yayi xaune har Meena tagama kirginta ta jerasu a dinning table ta wucewarta d'akinta domin ta shirya kayan da zata tafiya dasu gobe.


*Washe Gari*
Tunda asubar fari Meena ta tashi kmr yadda tasaba tad'aura abin brkfst ta jerawa Hafeez a dinning area, sannan tashiga toilet ta silla wankanta, tana fitowa tashafa versiline sai powdr Meena bata yarda tayi wata doguwar kwalliya ba domin talura a yan kwanakin nan Hafeez na matuqar nuna kishinsa akanta Wanda ita kuma hakan yan burgeta yana kuma bata tsoro, wata atamfarta tad'auko tasa sannan ta sanya hijabi har gwiwa.

Travelling bag dinta tajawo ixuwa falo, sannan tanufi sashen Hafeez ta kwan kwasa mishi kofa.

      Hafeez nacikin d'akinsa yafito a wanka kenan yaji kmr ana buga kofa, jallabiyansa ya jawo yasaka sannan yaje ya bud'e kofan.

Meena yagani tsaye cikin shirinta na tafiya ga kuma nan jakar kayanta a gefe, haka kawai Hafeez ya tsinci kansa da fad'uwar gaba. Jiki a sanyaye hafeez yadubi Meena yace "har kinfito? Meena tace eh! Ina kwana Hafeez yace lpy Lou.

Mamakine Yakama Meena don yau ko ince ynxu taga wani irin canji atattare da Hafeez komai yakeyi tamkar Wanda bashi da lakka ajiki haka nan ya kama jakar Meena yasa a booth din motarshi.

Har gdan Baba Rabi yakaita, Hafeez yashiga sungaisa da Baba Rabin sannan yamusu Allah kiyaye hnya.
     Bai wani jima ba a gdan yayi sallama da Baba Rabi, Meena har tayi xamanta domin bata da niyyar mishi Rakiya, sai da Baba Rabi ta doka mata harara sannan ta tashi tabi bayansa.Xakujini anjima don jin ci gaban lbrin, ynxu banda caji ne. Tnxs oll๐Ÿ˜˜

®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:06PM, 8/6/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode3⃣8⃣

Wurin Motarsa kai tsaye Hafeez yanufa yayin da Meena tarufa masa baya, bud'e motan yayi ya xauna batare da ya rufe ba, hakan ne yabawa Meena dama bud'e daya site din itama tazauna.
     Wata irin nannauyar ajiyan zuciya Hafeez yayi sannan yamaida dubansa ga Meena yace "idan kukayi tafiyan sai yaushe zaku dawo? Meena wacce ke wasa da gefen hijabinta kai duqe tace naji Amma nacewa sati d'aya xamuyi mudawo, dammm! Gaban Hafeez yafad'i amma sai yayi saurin dakewa yace olryt" shiru sukayi gabad'ansu na d'an wani lkci, can dai Hafeez yace "amm Balkisu takirani ta sanar dani cewa drivan Dr Muh'd ne xaikiku can Gwazan ko? Meena tace eh shine..

Ciro kudi Hafeez yayi sannan yamiqawa Meena yace gashinan susha mai a hanya, kar6a tayi sannan tayi mishi godiya, Hafeez ya maida kallonsa ixuwa wani gefe batare da yakalli Meena ba yace "i hope kinji gargad'in danayi miki cewa banda sa gyale " Meena tace insha allahu zankiyaye hakan.

Murmushin jindadi Hafeez yayi yace "vry gud of u"Meena dai batace komai ba. A dan gaggauce Hafeez yace ni xanwuce kada nayi latti Allah tsare hanya, Hafeez sai tsintar knsa yayi dacewa "ki kula da kanki Meena"

Insha allahu shine abinda Meena tafad'a sannan tafice a motan, sai da Hafeez ya 6acewa ganinta sannan tashiga gda.


Hafeez na isa cikin falo gabad'aya sai yaji dukk gdan yamasa fili babu Meena ba Balkisu, wata irin kewa ce tadinga shigarsa Wanda hakan yasa Hafeez  yanufi dinning area yaxauna kawai sai tsintar kansa yayi yanacin abinda Meena ta girka masa
      Hakanan Hafeez yagama cin ferfesunsa sannan yazuba kunun gyad'a yafara sha yana lumeshi idanu, cikin ransa sai tunani yakeyi haka dama Meena ta iya girki bansani ba Oh my God!! Hafeeez yabud'e cikinsa sosai yakwashi girki.
    Bayan ya kammalane yanufi d'akinsa domin ya shirya zuwa office.


**            **           **
Balkisu da kanta ta tura Habu driva yad'aukisu Meena, hakanan suka kama hanya, cikin ikon Allah sun samu isa garin gwaza lafiya.

Yan'uwa da abokan arziqi kowa yayi farin cikin ganin Baba Rabi, haka nan su Baba Rabi sun sami tarbo mai kyau awajan yan'uwansu (kasancewar iyayen Baba Rabi sunjima da rasu, a hannun kawunta ta taso) Khadija yar gdan kawu Usman tun zuwan Meena gdan nan Allah ya had'a jininsu khadija tayi farin ciki sosai da xuwan Meena(kawu Usman shine kawun Baba Rabi) yaransa guda biyar mata hudu daga ciki dukk sunyi aure sai khadija auta.

Meena ma tajidadin kasancewa da Khadija sosai, gashi sunkasance sa'anin juna, khadija tabawa Meena wata hud'u shiyasa inkagansu atare tamkar wasu twns,
     Tun zuwansu gwaza Meena kullum tana tare da khadija tana d'aukan lesson domin kuwa khadija akwai wayo da son gayu shiyasa kullum Meena na tare da ita tana koyan wasu abubuwan.


Abangaran Hafeez kuwa fushi yake da Meena wanda ita batasan ma yanayi ba,..fushi yakeyi sbd Meena bata kirashi tasanar dashi sun Isa lafiya ba, sai abakin Balkisu yakeji. Kullum Hafeez wayanshi na kusa dashi yana jiran call daga Meena amma shiru kakeji, da xarar Hafeez ji kira yashigo wayansa da hanzari xai jawota yaduba a tunaninsa Meena ce takira, Hafeez nason kiran Meena a koda yaushe amma girman kai yahanashi aikata komai.


*Bayan Sati Daya*
Dakyar Hafeez yaga wucewan sati dayan nan domin kuwa jinsu yake tamkar shekara d'aya wani irin farin ciki Hafeez yake ji idan ya tuna cewa Meena yau zata dawo kmr yadda tafad'a mishi, hakanan Hafeez yatsinci kansa da fita waje yana sadaka sbd farinciki.

A gajiye Hafeez yakoma gda falo ya kwanta domin yahuta, baifi wucewan minti biyu ba yafarajin bacci na fisgarsa, kmr daga sama yaji wayansa Na ringing da farko har ya share har ta tsinke baid'aga ba sai da aka  sake kira a karo na biyu sannan yasa hannunsa ya lalubo wayar d'aukan kiran kawai yayi batare da yaduba sunanan ba.
      Cikin muryan bacci yace "hello" a bangaran Meena tace Assalamu alaikum, lkci d'aya Hafeez ya fahimci mai mgn firgigit ya miqe ya xauna dasauri Hafeez yace Meena kece?

Meena tace eh Yaya nice dama nabugo insanar maka cewa akwai wani biki da zamuyi anan bazan samu damar zuwa yau ba inaso zanqara wani satin sbd in.....kafin Meena taqarasa abinda take son fad'i tuni Hafeez ya katse wayan.

Wani irin numfashi Hafeez keyi cike da tashin hnkli sbd tsabar takaici baisan lkcin da yayi wurgi da wayansa ba yace "ohhh no Meena baki Isa ba I cnt tollrt it any more idan baxaki iya dawowa da kanki ba nizanje nadawo dake, tsawan wannan satin dakikayi bakisan halin damuwar dakikabar ni aciki ba, am vry eager to c ur cute face Meena.

Hafeez nafad'in haka yanufi d'akinsa da sauri car keys dinsa ya Zara yadawo yadauki wayansa afalo ya fice a gdan.

Hafeez na kan hanya yakira Dr Muh'd yace yanaso Dan Allah yabashi aron Habu driva zai rakashi izuwa wani waje, Dr Muh'd yace okay Abokina ba damuwa.

Asibitinsu Dr Muh'd Hafeez yanufa yad'auki Habu driva yace dashi yanaso yarakashi garin da yakaisu Meena a yau din nan. Cike da bin umarninsa Habu driva ya harba motansa izuwa garin gwaza.®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [2:54AM, 8/7/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode3⃣9⃣

Kasancewar Habu driva yasan gdan kawu Usman hakan yasa   suka nufi gdan kai tsaye.

Meena ce zaune tsakar gda ita kadai ta rafka uban tagumi tunani ne sosai aranta addua kawai takeyi kar Allah yasa Yaya Hafeez yace baxa tasamu daman tsayawa bikin nan ba, 
       Meena tayi nisa sosai cikin tunaninta sai jiyayi andafata a hnkli tadago kanta, Khadija tagani tsaye, ae kuwa bashiri tasakar mata murmushi, cike da kulawa Khadija ta duqa daf da Meena tace sister anya lpy kuwa? Wani murmushin yaqe Meena tasakeyi sannan tadubi Khadija tace "sister lpy Lou mekika gani?" Khadija tace a'a naga kinxauna ke kadai kin zuba uban tagumi ko dai kina tunanin Shine? Dasauri Meena tace haba dai khadija wlh ba haka bane kawai nadamune sbd inason natsaya bikin Hamza (hamza qanin Kawu usman ne) Khadija tayi murmushi sannan tadafa kafadan Meena tace "kema bnda abinki banace ki kira mijin naki kisanar masa cewa kina son yabaki damar qara wasu kwanakin ba?.

Meena tashare kwallar dake qoqarin zubo mata tace "wlh sister na jarabba hakan hasalima dana fadamishi bai ce dani qala ba kawai yakashe wayansa.

Khadija tace ohhh wlh kina damuwa da abinda baikamata ace kindamu ba, kikasani ko ntwrk ne ko rashin caji kibari anjima kisake tryn. Murmushin yaqe Meena tayi tace oky.

Khadija tace yauwa kokefa, nan taja hannunta tace tashi ma muje kasuwa daxu Baba yabamu kudin sayen anko yakumacemin haddake dan haka kisaki ranki kitashi mutafi.

Jiki ba kwari hakanan Meena ta tashi tashirya  suka tafi kasuwa.

Su Meena ko minti uku basuyi da tafiya kasuwan ba sai gasu Hafeez sun kunno kai cikin anguwar.
     Dai dai kofar gdan Habu yayi parkn, kafinma yace da Hafeez wani Abu tuni Hafeez din yafahimci cewa nan ne gdan.

Fitowa sukayi daga cikin motan sannan suka sami yaran dake wasa kofan gdan suka aiki daya daga cikinsu akan yaje yace wai ana sallama da Meena

 Yaron kuwa dagudu yashiga cikin gdan kmr yadda aka umarce shi, yana zuwa yace "wai inji wani mutumi awaje yace ana sallama da Meena"

Amma nadaga cikin d'aki tajiyo muryan yaron da sauri tafito waje tace da yaron "waye ke sallama da Meena?" Yaro yace shima baisani ba, Baba Rabi tace da yaron yatsaya nan tashiga ciki tad'auko hijabi tace da yaron suje tagani.

Koda fitar Baba Rabi izuwa waje Hafeez tagani tsaye jingine da mota, dasauri taqara wajansu tana musu sannu da zuwa, Hafeez kam sai waige waige yakeyi inda xai hango Meena.

Baba Rabi tace "sannunku da zuwa Hafeez kai ne tafe? Hafeez yayi murmushin yake yace wlh kuwa Baba nine, Baba Rabi tace toh sannunku da zuwa kushigo daga ciki.

Dakin Kawu Usman Baba Rabi tasauqe su Hafeez, bayan sunqara gaisawane baba Rabi takawo musu ruwan sha.
     Sannan tace da Hafeez yad'an jira kadan Meena sunfita ita da yar'uwarta, shiru Hafeez kawai yayi, tunanin inda Meena taje a wannan yammacin kawai yakeyi.


Abangaran Meena kuwa suna can kasuwa wajen siyan anko, bayan sungama ne Meena tace sister inaso kikaini inda ake siyan gyale da hijabi, haka nan Khadija takaita gurin da tabuqata, Meena tasaima kanta hijab kallan ankon nasi sannan tasaima Khadija Gyale itama kallan ankonsu.
     Haka nan suka gama siyayyansu cike da farinciki suka koma gda.

Mai taxi na ajiye su Meena fitowan nan da zatayi idanuwanta sukayi tozali da motar Hafeez, rass!! Gabanta yafad'i, amma sai tadake domin tana tantama kmr ba motansa bace, hakanan suka kwashi kayansu suka nufi cikin gda.

®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [3:57AM, 8/7/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode4⃣0⃣

Suna shiga cikin gdan da sallamarsu kafin sunemi waje suzauna Baba Rabi tace "kee! Aminatu daga xuwa kasuwa kuje kudawo shknan sai kumaida gari naku kuje kuyi xamanku, Meena tace Amma wlh ba haka bane mund'an tsaya siyan wasu abinne shiyasa mukadan jima.

Baba Rabi tace toh ae kunkyauta sai kitashi kije d'ankin Kawu Usman kinyi baqo, dasauri Meena takalli Baba Rabi tace "Amma baqo kuma"? Baba Rabi eh kawai tacemata tabar wajan.
     Khadija tadubi Meena tace sister tashi kije natabbata babu wani namijin daxaixo yanemiki har ayimishi izinin zuwa d'akin Kawu face mijinki, plss tashi ki kintsa kijeki.

Kafin Meena tace wani Abu Khadija taja hannun Meena izuwa d'akinsu, nan ta tsara mata kwalliya mai kyan gaske Khadija da kanta tabud'e akwatin Meena taza6o mata wasu riga da siket masu kyau tace tasasu. Batare da Meena ta musawa Khadija ba hakanan tadauki kayan tasa, sai da tashirya tsaf sannan tasanya hijab tanufi d'akin kawu usman.

Qamshin turaren Meena ne yadoki hancin Hafeez, dasauri yad'ago kansa Meena yagani tana qoqarin xama bisa kujerar da yake zaune.

Meena wacce gabanta yatsananta Faduwa cikin siririyar muryanta tace sannu da zuwa Yaya ina wuni? Hafeez ya kura mata idanu ko qiftasu bayayi, shiru yayi tamkar baxaice komai ba , can dai yace Meena ba wannan ne yakawoni ba  "Habu driba  kam tun shigowar Meena yabar d'akin" Meena tayi shiru tana sauraren Hafeez taji da wacce yaxo.

Hafeez ya matso daf da Meena yace zuwa nayi domin inaso kimai maitamin abinda kikace lkcin da kika kirani awaya d'axu.
     Shiru Meena tayi takasa cewa komai sai faman wasa takeyi da d'an yatsanta,, Hafeez yaqufula sosai yace ko bakyajina ne nace kimaimaita abinda kikafad'a daxu. Cikin tsananin faduwar gaba tafara mgn tamkar ta mai in'en "tace umh uhm dama cewa nayi inaso kabani dama domin na samu halartan bikin Hamza.

Hafeez yace okey dukk satin da kikayi anan basu isheki bane,? Meena tayi shiru! Hafeez yace kibani amsa mana ko kuma baki san cewa kinbar mijinki shi kad'ai cikin wani hali na kewa ba?
      Kewa?? Shine abinda Meena tamai maita cikin xuciyarta, Hafeez yace toh bari kiji nazo intafi da mamata kuma ayau din nan komin dare xamu bar Gwaza mukoma Maiduguri, Meena tad'ago kai fuska a maraice tace "Dan Allah yaya kayi hkri kabarni ko kwana biyu ne inqara.

Cike dajin haushinta Hafeez yace kinsan Allah bari kiji wlh ko awa d'aya bazan bari kiqara ba, kuma kitashi ynxun nan kije kihado kayanki inajiranki a mota.

Hafeez nafad'in haka yatashi yabar d'akin, a tsakar gda ya tarar dasu Baba Rabi.. nan yaduqa har qasa yayi musu sallama yace "Baba ni zan wuce ynxu" Baba Rabi tace haba Hafeez baka tsoron kuyi dare a hanya, murmushi yayi sannan yace Bakomai insha allahu, nan yayi musu godiya yafice a gdan yakoma cikin motarsa yana zaman jiran fitowan Meena.

Abangaran Meena kuwa dagudu ta tashi takoma d'akinsu Khadija sai faman kuka takeyi, Baba Rabi nazaune cikin d'aki taga wulgawar Meena dasauri ta tashi tabi bayanta.
      Ko dashigarta ta tarar da Meena na kuka tana had'a kayanta, Baba Rabi tadubi Meena tace "ke kuma miye kikewa mutane kuka?" Meena wacce kuka yaci qarfinta tafashe dawani sabon kukan tace " Amma Yayane yace yaxo tafiya dani bayan Kuma nafadamishi cewa muna da biki.

Baba Rabi wani uban tsaki taja tace "mtsww aekin wofi kawai yoo dama inkika zauna bikin kawu Hamza uban mexaki tsinana toh kisani dukk wani abu marar muhimmanci dakike tunani yafi miki bin umarnin mijinki domin kuwa bikin Kawu Hamza kodake ko bake xa'a daurashi dan haka kirufewa mutane baki tun baki tarawa kanki jama'a cikin d'akin nan ba.

Meena kam gabad'aya takawo iya wuya wani irin takaicine ya sarqe ta, dasauri tashirya kayanta tsaf tayi sallama da kowa kafin Khadija tadawo tayi saurin ficewa tabar gdan (khadija na gurin Sa'idu tailor ta kaimusu kayan ankonsu dinki)
    Fushi Meena tayi sosai dan haka tana xuwa tasa kayanta a booth tabud'e gdan baya tazauna.

Hafeez naganin haka yafito daga gaban mota yadawo baya inda Meena ke zaune, kowa na gdan yafito yayi musu Allah kiyaye hanya.

Batare da Bata lkci ba sukabar cikin garin gwaza, suka kama hanyan Maiduguri.

®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [7:59AM, 8/7/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episod4⃣1⃣

Su Hafeez sunyi nisa sosai da tafiyarsu amma da gashi har Meena ba wanda yace da wani uffan! Hafeez nema tunfara tafiyansu yaketa satar kallon Meena sbd kwalliyar dake fuskarta baqaramin kyau yamata ba.

Ajiyar zuciya Hafeez yayi a hankali ya maida bayansa ya kwanta jikin mota sai fama tunani yakeyi a cikin xuciyarsa, "Hafeez ke tambayar kanshi dama akwai watarana da xataxo ni Hafeez zanso wata fiye da Rafee'a ohh gosh! Nan yafara tunanin ya akayima yafara son Meena badly haka"? Hafeez na cikin tunaninsa wayar dake riqe a hannunsa yana jujjuyata nan tafara ringing.

Firgigitt! Hafeez yayi yadawo daga duniyar tunanin da yatafi, cike da kasala Hafeez  yadubi wayan don ganin mai kiransa.

Sunan Dr Muh'd Hafeez yagani ya bayyana akan screen din wayarsa hanxarce yad'uki wayan gamida karawa a kunnesa "hello Abokina Allah yasa bakayi nisa ba wlh Balkisu ce bata lpy tana fama da laulayi tundazu take damuna akan nakiraka nace tabari zuwa an jima idan ta huta amma Sam taqi, a hanzarce Hafeez yace ya salam tana kusa plss bata wayan.

Hafeez na amsan wayan Balkisu tafashe da kuka tanafadin Dan Allah Yaya Hafeez kayafemin mutuwa xanyi wayyoo Allah na bayana xai fashe yaya, gabad'aya Hafeez ya rikice kashe wayan kawai yayi sannan ya umarci Habu driva da yaqara gudu.

Baifi tafiya 3Omint ba su Hafeez sukashiga cikin garin Maiduguri, direct gdan Balkisu suka wuce kmr yadda Hafeez yace. Suna isa cikin gdan da sauri Hafeez yanufi ciki batare da yajira su Meena ba.

Meena kam batasan meke faruwa ba, amma a hanzarce itama tabi bayan Hafeez.
     Hafeez na isa cikin falon yafara kiran Balkisu! Billyn mama!! Shiru yaji dasauri yanufi wani d'aki inda nan ne yake tunani d'akin Balkisu yake.

Kafin Hafeez yaqarasa  d'akin sai ga Dr Muh'd nan yafito daga d'akinshi dasauri yakira sunan Hafeez yace "no abokina gatanan kwance a d'akina nayimata allura ne tayi bacci, fuska d'auke da damuwa Hafeez yace plss mike damun Balkisu Dr Muh'd yana jin nauyin amsa masa tmbyarsa amma babu yadda ya iya domin yaxama dole ya amsa masan.

Jan Hafeez yayi izuwa wani corido sannan Dr Muh'd yadubi Hafeez yace "abokina munsami qaruwa ne Balkisu nad'auke da cikin wata biyu, sai dai da mtsl.
      Dasauri Hafeez yace mtsl Kuma? Mtsl kmr tame kenan, Dr Muh'd yace kasan dai nikadai iyayena suka mallaka arayuwarsu shiyasa tunda girma ya riskeni suka takura akan lallai sai nayi aure domin suma suga jikokinsu suncika gdan nan.

Toh sai dai ba'anan gixo ke saqar ba, Balkisu tasamu ciki sai dai yana masifar azabtar da ita kome taci baya xama acikinta dukk tarame tafita hayyacinta kullum tana cikin ciwo.
     Nikuma tausayinta yajani nayi tunanin zubar da cikin, sai dai kafin na kai ga aikata hakan iyayena sunce muddin nabari cikin dake jikin Balkisu ya zube to basu yafemin ba.

A gsky Hafeez ina cikin damuwa domin ni lfyr Balkisu tafimin komai arayuwata.
    Murmushi Hafeez yayi sannan yashiga kwntarwa Dr Muh'd hankali dukk da kasancewar shima nasa hanklin a tashe yake.

Sai qarfe Tara da rabi Na dare su Hafeez suka bar gdan, suma suka nufi nasu gdan, Meena kam hadda hawayenta ganin yadda Balkisu tarame lkci d'aya gashi har suka bar gdan bata samu ta farfado ba.

Restaurant yafara wucewa dasu don sunci abinci, Amma Hafeez gani yayi maza sunyi yawa agurin cin abincin Dan haka take away kawai yayi musu suka nufi gda kai tsaye....
®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [9:52AM, 8/8/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode4⃣2⃣

Tun sanda Hafeez yaje gwaza yad'auko Meena suka dawo yaga canji a tattare da ita sosai domin gabad'aya ta kauracewa ganinsa dukk abinda tasan zai had'ata hnya da Hafeez Meena tajanye , hakan kuwa baqaramin d'a hanklin Hafeez yayi ba gad'aya yashiga damuwa ga uban taurin kai ko ince girman kai da yahanasa kai kanshi gareta balle yasan halin da take ciki.

Yau ya hakasance weekend, hakan yasa yau Hafeez na gda bai je ko ina ba,..Wanda a bangaran Meena kam hakan bai mata d'adi ba domin tanason fita zuwa d'aura musu abin brkfst gashi kuma Hafeez yayi zamansa a falo.
      Gabad'aya Meena taqagu Hafeez yabar falon Dan tasamu damar wucewa a  hankali Meena taske tabud'e kofan d'akinta taleqa ko Allah zaisa taga Hafeez nan amma sai taga wayam! baya cikin falon, hakan yasa tafito a hanzarce tanufi kitchn.

Dai dai lkcin ne kuma Hafeez yafito daga waje hannunsa d'auke da wasu takaddu daganin alama daga waje yafito dasu, dasauri Meena tashiga kitch abinta. Hafeez kam murmushi yayi gamida girgiza kansa domin yaga lkcin datashige kitchen dasauri,  falo yanufa ya ajiye tarin takaddunsa sannan yanufi kitchen din.

Meena ce tsaye cikin kitchn ta tawani riqe qugu tana tunanin abinda yakamata suyi brkfst dashi.
     A hankali Hafeez yashiga kitchen din batare da sanin Meena ba, Meena kam sai ji kawai tayi an rugumota tabaya tsamm.

A tsorace tad'an juya Hafeez tagani take anan tasauya kamaninta tawani turbune fuska kamar zatayi kuka, a hnkli Hafeez yajuyo ta tafuskance shi sannan ya riqe hannayenta cikin muryan rad'a yake mata mgn "haba Meenata fushi kikeyi da d'an bawan Allah nan? plss kimin afuwa wlh a lkcin jinayi bnda control inba d'aukoki nayi ba u know i really miss u alot Meena ynxu yakama ki juyo ixuwa ga mijinki kimanta da komai kimin afuwa kinji matar da babu irinta."

Hafeez nagama surutunshi Meena tadungujeshi dasauri tabar masa kitchen din, hnklin Hafeez gabad'aya yatashi riqe goshinsa yayi sbd yadda yaji knsa nasara mishi cikin sanyin jiki haka Yaja jiki yanufi hnyar falo.

Kmr daga sama Hafeez yajiyo muryan Balkisu tana kwala mishi kira tunkamin tasamu taqarasa cikin falon.

Dasauri Hafeez yajuya Balkisu yagani da gudunta tanufato shi, a hanzarce Hafeez yaqarasa wajenta yana fad'in ke Billyn mama kanki d'aya kuwa? A cikin wannan yanayin dakike ciki shine kike wa mutane gudu haka? Balkisu ta turo baki cike da shagwa6a tace ni gaskiya yaya cikin nan ya takuramin wlh shikenan ni baxanyi abinda nakeso ba.
       Hafeez yayi murmushi yaja hannunta suka nufi cikin falo, bayan sun zauna ne Hafeez yadubi Balkisu yace "lpy kuwa Balkisu naganki da sassafe?" Balkisu tace lpy law wlh dama My precious ne yayi tafiya takama ynxun nan izuwa wani qauye shine yacemin sai xuwa dare xai dawo dan haka yace  nashirya yayi dropn dina anan domin bai yarda yabarni nikad'ai ba.sannan dama nazo ma da anty amarya wani lbri mai dadi, Hafeez yace "minene yafaru" dasauri Balkisu tamiqe tace yaya inaxuwa. Kafin Hafeez yace wani abu ta tashi da sauri tanufi d'akin Meena

Koh da shigarta ta tarar da Meena kwance tayi rufda ciki, dasauri Balkisu ta qarasa ta kwnta a hnkli cikin sand'a yadda Meena baxataji ba,..Meena kam batamaji shigowarta ba Dan tayi nisa sosai da tunani sai jitayi ana huramata iska a kunne dasauri tarazana tace miye haka ya.....shiru tayi takasa qarasa abinda takeson cewa sbd wacce tagani a gabanta. Dasauri Meena ta tashi zaune tadubi Balkisu cike da zolaya tace "a'a gawa taqi rami kece yau a gdan namu"? Balkisu tahad'e fuska sosai tadubi Meena sannan tace Anty Amarya koda baki cemin komai ba tabbas akwai abinda yake faruwa a gdan nan sbd daga ke har Yaya na lura bakwa cikin walwala, keda mukayi alqawari dake amma sai nazo naga sa6anin haka domin tunshigowata gdan nan idanuna suka ganemin cewa Yayana nacikin matsanancin damuwa wanda cikin alqawarinmu nafad' a miki cewa banaso kibarshi cikin kewa ko damuwa sbd laluran dayake fama dashi.

Wata irin nannauyan ajiyan xuciya Meeena tayi sannan tadubi Balkisu tace "wlh ba haka bane amma kimin afuwa insha allahu zangyara kuskure na".

 Murmushin yake Balkisu tayi sannan tace Allah yasa. Cike da sanyin jiki Meena tace Ameeen!!
     Lkci d'aya kuma Balkisu tasaki jikinta da Meena daga bisani kuma taja hannun ta tace " yauwa Anty amarya taso muje wurin Yaya domin naxo muku da kyakkyawan labari. Meena tadubi Balkisu tace "kyakkyawan lbri kuma?" Balkisu tace sosaima kuwa kedai taso muje.

Meena tace to Balkisu banqi takiba Amma kiyimin afuwa Bari nasamu nad'aura mana abinda mukaci, dasauri Balkisu tace plss kawai kidafa mana indomie muci kinsan Yaya ma naso. toh kawai Meena tace sannan ta tashi tanufi kitchen tad'aura musu indomie da kwai.

Meena sakewa tayi sosai a gaban Balkisu da Hafeez, Hafeez se satar kallonta yakeyi ji yakeyi kmr ba ita ba, sai washe baki yake yana jin wani irin farin ciki na shigarsa.
   
         Bayansu Meena sun kammala cin indomien sune Meena ta gyara falon tsaf sannan tadawo taxauna don suji lbrin da Balkisu tace tazo  musu dashi.


®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [10:56AM, 8/8/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode4⃣3⃣

Balkisu cike da d'aukin son fad'a musu abinda takeson sanar dasu tadubi Hafeez tace "Yaya Allah yasa dai bazaka bamu mtsl ba" Hafeez yadubi Balkisu yace mtsl kuma Billynmama kmr name meyaparu? A hnkli Balkisu tazamo daga kan kujerar da take zaune takoma kusa da Hafeez sannan tace "dama Yaya akan mgnr karatun Meena ne shine nace mai zai hana anema mata admission domin itama tafara zuwa skul.

Dasauri Meena tadubi Balkisu tace haba dai Balkisu kinta6a ganin wacce batayi makarantar gaba da secndry ba kuma ace tashiga jami'a, cikin tsananin damuwa Meena tace kinmanta acikin lbrin dakikace anfad'a hala dai shi wnda ya fad'amiki lbrina bai sanar dake cewa banyi xurfi a karatun boko ba?

Shiya tun farko naso na qarabaki wasu kad'an daga cikin lbri na amma hakan baisamu ba kikace dani basai nayi miki bayanin komai ba kinsan komai a gamedani.
 
      Meena tashare hawayen idonta sannan tacigaba dacewa "dama nasan dole wataran wannan ranar zatazo, sai dai Balkisu ina mai baqincikin Sanar dake cewa karatuna baiyi zurfi ba iyakata primary kuma koshi ta window aji nake d'aukar darasi, hakan shima yaxama bashida wani amfani tunda har naqare la6ela6e na na window ban kar6i sakamakon komi ba.

Sai dai kuma tun tasowa ta ina qarama Allah yasamin son karatun boko shiyaasa nasa naci a lkcin danake la6ewa a window,  nasan abubuwa da dama tunda ina iya karantawa ina Kuma iya rubutawa,
       Sai dai ynxu gsky is too late baxan iya shiga makaranta ba na gwammace inyi  xamana a haka." Meena nafad'in haka tafashe da matsanancin kuka da gudu tabar falon ta nufi d'akinta.


Abangaran Hafeez kam gabad'aya jiyayi kansa a kulle yakasa fahimtar inda mgnr tasu ta dosa, ajiyar zuciya Balkisu tayi sannan tadubi Hafeez tace "yaya nasan xakayi tunanin munbarka a duhu sai dai a yau ina tunanin xan sanar dakai abunda bakasani ba agame da LABARIN RAYUWAR MEENA, dama hausawa sunce ranar wanka ba'a boye cibi.

Batare da 6ata lkci ba Balkisu tashiga zayyanawa Hafeez lbrin Meena, (sai dai Balkisu bata sanar da Hafeez cewa deal suka had'a akan ita da Meena akan zata kula dashi ba sbd Balkisu naganin wannan wani sirri ne a tsakaninsu ta dai sanar dashi cewa sbd kyawawan d'abi untane yasa ta amincewa auransu.)

Hafeez ya matuqar tausayawa Meena lkcin da yakejin lbrinta. Hakan yasa yaketajin wani irin wutar son Meena naqara ruruwa acikin zuciyarsa, sai dai Hafeez yarasa yadda zaiyi da soyayyar Meena wadda ke axabtar dashi.

Hafeez yadubi Balkisu yace ni inaganin wannan mtslr mai sauqi ce, tunda Allah yasa Meenan ta iya karantawa da rubutawa xanyi amfani da wannan damar insata a computer skul yadda xata iya sarrafa harkokin kasuwanci da kanta, sbd nayi tunanin sama mata Sana'a wnda xa'ake kawo mata kaya daga qasashen qitare inaga hakan ma xai taimaka tunda dai BURIN MEENA shine taga cewa ta taimakawa yan'uwanta, nikuwa insha allahu zancika mata wannan damar.

Wani ihuun murna Balkisu tayi tanufi d'akin Meena dagudu dan tafad'a mata wannan kyakkywan albishirin.


๐ŸŒนspecial greatin to ma Jidda Aliyu nagode sosai da kulawa๐Ÿ˜˜


®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [10:43AM, 8/9/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode4⃣4⃣

Meena ce xaune tsakiyar gado ta had'e kai da gwiwa tana tafaman rusar kuka mai cike da qunci,..

 Balkisu kam da d'an gudunta tashiga d'akin Meena fuska d'auke da fara'a tana takiran Meena Anty Amarya! Anty Amarya!! "kina ina?" Turuss Balkisu tayi lkcin da tahango Meena a kan gado har ynxu tana kuka, cike da sanyin jiki Balkisu ta hau gadon gamida jawo Meena ajikinta, cikin sigar lallashi Balkisu tace "haba Anty amarya mine kuma nakuka plss kishare hawayenki wannan bawani abun damuwa bane" dasauri Meena tad'ago rinannun idonta tadubi Balkisu tace "wlh rashin wadataccen ilimin boko ko Na addini wlh cutane kuma abin damuwane karkimanta cewa wataran mu iyayene mexance da yarana a lkcin dasuka zo gareni domin nataimaka musu da home wrk wannan ma wata babbar damuwace, a rayuwata inaso naga cewa nayi zurfi sosai a karatun boko sai dai Allah bai nufi hakan ba kum....dasauri Balkisu ta tari numfashinta Meena tace "shikenan ae kingama mgn tunda kikace Allah ne bai nufi hakan ba, dan haka inaso kisani Anty amarya komai da kikagani yafaru da bawa to dama rubutacce ne cewa sai yafaru dashi, kinga kenan kowacce qaddara da nata salon, sannan kuma kinsan ita qaddara wata jarabawace daga ubanguji Dan haka inaso kimaida komai ba komai ba, kisamu kiyi kokarin cin wannan jarabawan kisa aranki cewa komai muqaddarine daga ubangiji babu Wanda ya isa ya gujema qaddarar sa.

Dan haka ki kwntar da hankli insha allahu BURINki nason taimakawa al'umma yakusa cika domin kuwa Yaya Hafeez da kansa yace xainema miki Sana'a wacce zaki tallafawa kanki ba lallai sai kinyi boko zaki samu aikin yi ba, sbd akwai hanyoyi da dama wnda zakibi ki samu sana'ar yi balle ma ynxu da akasamu hanyoyi mafi sauqi, hakan ne yasa Yaya yace zai saki cmptr skul ta yadda zaki koyi saraffa kasuwanci batare da wani husuma ba.

Wani irin farin ciki ne ya sarqe Meena batasan lkcin da ta rungume Balkisu ba tana dariyar farinciki.
        Balkisu ma dariyan tayi domin shawaran da Hafeez yakawo hakan yamata sbd BURIN Balkisu shine taga Meena cikin farin ciki a ko da yaushe.

**             **              **
Kmr yadda Hafeez yayima Meena alqawarin sata makarantan computer hakan kuwa akayi batare da wani 6ata lkci ba Hafeez yasamar mata gurin da zata fara zuwa, cike da dinbun nasara Meena tafara zuwa comptr centre kuma alhmdllh kasancewar Meena tasa naci akaratun shiyasa abubuwan ke xuwar mata da sauqi.

Dafarko Hafeez ke kaita yana d'aukota, amma daga bisani kuma ya yanke shawaran siyamata motar kanta, wata 206 yasiyamata fara cikin sati guda kuwa Meena tafara kwarewa a koyan tuki wnda Hafeez ne da kanshi yake koyamata dukk weekend,...ganin tafara kwarewa ynxu yada Hafeez yabarta ita dakanta take kai kanta ta tadawo.

Yawan kyautatawan da Hafeez ke wa Meena Hakan yasa ynxu Meena ta d'an saki jiki da Hafeez, dukk wata hidima da takeyimasa ada ynxu tadawo dayimasa shi.

Qarfe tara na safe Meena ke xuwa comptr cntr, shiyasa a kullum idan ta idar da sallahn asuba bata komawa.
      Kmr yadda Meena tasaba zuwa d'akin Hafeez ta gyaramishi haka yau ma a gaggauce tanufi d'akinshi daga ita sai wata farar vest da wndo skin tied kanta daure da ribon tayi kitson shuku ko d'an kwali babu akanta tanufi d'akinshi domin atunaninta yawuce gurin aiki.
      Da sauri ta murd'a kofan dakin tashiga kai tsaye, toilet tafara nufa tashiga ta wanke ko ina fess sannan tasa roomfrshnr toilet din yad'au qamshi, fitowa tayi dasauri dan tagyara mishi nasa d'akin kayanshi dake zube aqaasa ta kwashe tanema musu gurin da ya dace, tana gamawa tanufi gadon Hafeez bargonshi  tafara jawowa da nufin ta linke masa.

Meena najan bargon tahango Hafeez dunqule cikin bargon yanata karkarwan d'ari, dasauri Meena tasaki bargon tahau gadon ta jawoshi  jikinta gabad'aya hnklin Meena yatashi ganin Hafeez cikin matsananin hali.
      Meena kmr zatayi kuka nan tashiga  tambayar Hafeezz, Yaya  Hafeez lpy kuwa Yanaji jikinka da xafi haka meyaparu mike damunka ina ke maka ciwo? Hafeez kam ko idanunsa yakasa budewa sai mgn yakeyi qasa qasa wnda babu mai iya juyo abinda yake fad'i.

Mai dashi tayi ta kwntar aguje tanufi kitchen tasamu roba tadan zuba ruwa mai sanyi tanufi d'akinshi da Sauri tana zuwa tashiga toilet tasamu wani d'an qaramin towel nan tashiga daddana masa towel din ajiki,  a rikice Meena ke tsoma towel din cikin ruwan tana dannawa Hafeez ajiki, hakanan Meena keyi mishi har tasamu zafin jikinsa ya sauqa.

A hankli Hafeez ya bude idonsa yad'aura su akan Meena wani irin abu yaji take anan yaji wani irin qarfi yaxo masa amma sai Hafeez yakoma ya langwa6e da gangan, Meena kuwa dukk ta rikice sai dafa mishi goshinsa take tana cemasa sannu.
     Can dai Meena tamiqe zatafita caraff Hafeez ya riqo hannunta dasauri tace "am swry Yaya ina zuwa", a hanzarce tafice a d'akin tanufi dinning table tea ta had'a masa mai kaurin gaske sannan takaimishi,

       Sarai Hafeez na iya tashi amma sai yaqi tashi yawani langa6e kai. dole meena ta zauna ta d'an jawoshi jikinta ta taimaka mishi yafara sipping tea din.

Meena sai sannu take mishi domin kuwa Hafeez ya bala'in bata tausayi, Hafeez kam kasancewarsa a jikin Meena jinsa yake awata irin duniya hakan yasa yaqara rungumeta tsamm a jikinsa yana shaqar qamshinta, cikin lkci qanqani kuwa Hafeez yafara fita hayyacinsa sai wani sambatu yake mata, Abangaran Meena kam gabad'aya ta tsorata da irin abubuwan da Hafeez kemata nan tafara wuqi wuqi da idanu.®NWA
[1:17PM, 10/15/2016] My Nabss: [1:07AM, 8/12/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode4⃣5⃣

Babu irin abunda yafad'oma Meena a rai kmr yadda kullum Balkisu ke mata tuni akan tacika mata alqawarinta ta nakula da tilon yayanta,...sai dai a ynxu abinda Hafeez ke shirin aikatawa agareta sam bazata iya jurar saba, Hafeez kam qara rungume Meena yayi tsam ajikinsa yayin da ya cigaba da aika mata wasu irin sakwanni masu rikitarwa, Meena kam ta tsorata da al'amarin Hafeez hakan yasa tadingi kiciniyar kwace kanta cikin dabara, sai fad'i take plsss yaya dnt b disturb kabari ind"auko maka maganinka kasha kasha.

Hafeez kam gabad'aya idanuwansa sun rine izuwa jaa, batare da ya kula Meena ba yacigaba da abinda yake shirin aikatawa agareta, a firgice Meena ta tashi tsaye jikinta sai wani irin kyarma yake yi ganin Hafeez Na qoqarin cire mata vest din dake sanye ajikinta.

Hafeez gabad'aya yawani irin jigata sai roqon Meena yake da ta taimaka masa,amma ina Meena ta tsorota sosai sai wani rawar sanyi takeyi, idon Hafeez arufe sai laluben Meena yakeyi yana wani irin nishi, aguje Meena tafice zuwa d'akinta maganin bacci tad'auko ta dirkawa Hafeez, domin  ganin yanayin da Hafeez ke ciki ya bala'in d'aga mata hankali.

Wani irin nannauyan bacci ne yayi awon gaba da Hafeez, a hnkli Meena tarufeshi da bargo tajawo masa kofan d'akin tafice.

D'akinta tanufa tana zuwa bisan gadonta tahau jagwaff sai wani irin mai da numfashi takeyi gabad'aya hankalinta ya tashi.
       Kasancewar Hafeez baijin d'adin jikinsa shine yasa Meena yau bataje comptr training cntr dinta ba zama tayi a gda domin tabashi kulawarta.


Qarfe 12pm dai dai Hafeez yafarka daga nannauyan baccin da ya d'aukesa, ko da ya bud'e idanunsa gabad'aya jin jikinsa yake tamkar anyimishi dukka, a hnkali yatashi yanufi toilet ya watso ruwa sannan yadawo yasanya jallabiyansa yanufi falo jiki ba k'wari.

Meena jintayi zaman d'akin ya isheta hakan yasa tadawo falo ta rafka uban tagumi tana ta faman saqawa da kuncewa domin Burin ta a ynzu shine taga  cewa tacikawa Balkisu alqawarinta kamar yadda itama tacikamata nata alqawarin, ta Kuma kyautata mata fiye da tunaninta, gashi shikansa Hafeez din a kullum BURINsa shine yaga cewa ya kyauta mata ko ta yayane,.. sai dai a yau abinda Hafeez d'in ke shirin aekatawa a gareta a gsky batajin zata iya jurewa.

Hafeez na isa falo ya hango Meena zaune ta rafka uban tagumi, cike da damuwa Hafeez yaqarasa wajenta a hnkli yazauna kusa da ita, amma dukk da haka Meena bata masan yana wurin ba, sai da Hafeez yad'an tafa hannayensa sannan Meena tayi firgigit tadawo daga duniyar tunanin da ta tafi.

Hafeez tagani zaune kusa da ita dasauri tad'an ja da baya gami da qaqaro murmushi tace "a'a Yaya kafito yajikin naka? Mekakeji ynxu? Hafeez kam qurawa Meena ido yayi sbd lura da yayi yadda take mgn tamkar wata firgitaciciya wadda aka tsoratar gabad'aya tawani rud'e.
     A hnkli Hafeez yariqo hannun Meena yayin da ya sake qura mata ido cikin tuhumarta yadubeta face to face yace "Meena meke faruwa ne naganki kmr kina Cikin damuwa ?" Murmushi Meena tayi sannan tace Yaya bakomai am jst woried about ur health, mekake son ci yau indafa maka" Hafeez yawani maqe kafad'a yace "no am oky" Meena tawani turo baki cike da shagwa6a tace "nidai gsky a'a kafad'a min abinda kakeso inkawo ma" Hafeez yadubi Meena da mamaki ganin yadda Meena yau take wani irin bashi kulawa na mussaman, al'amarin kaa ya matuqar d'aure masa kai a hnkli yadubi Meena yasauqe wata nannauyan ajiyan zuciya yace "its okey ki kawomin kunnun gyad'a mai zafi insha. Meena ta d'an saki murmushi tace yauwa Yaya da kuma me? Hafeez yad'an riqe kumatu alamar tunani can kuma yace kidafamin indomie, a hanzarce Meena tamiqe tanufi kitchen dan ta had'omasa abunda yabuqata.

Hafeez na nan zaune yana d'an nazari akan canjin dayagani yau awajen Meena, wayarsa dake gefensa ajiye tafara ringin da sauri ya katse tunanin dayakeyi yamaida dubansa ga wayarsa DANIEL yagani kan screen din wayar tasa kamar yadda ya rubuta, dasauri yad'auki wayar gami da karata a kunne, "hello gud aftrnoon sir" cikin natsuwa Hafeez ya amsa mishi "am fyn Daniel how wz evrtn thr" Daniel yace "fyn sir" shiru Daniel yayi daga bisani kuma yace plss sir ayimin afuwa wasu yan uzuri ne suka riqeni my wyf ba lfy plss inaso akaramin wasu yan kwanaki" Hafeez yad'an muskuta kad'an yace eyyaa swry ya maijikin? Daniel yace dasauqi.

Cikin nuna tausayi a gareshi yace don't wrry kazauna ka kula da matarka sosai harta samu lpy sannan idan lkcin biyanka yayi zantura ma da salary dinka, Daniel yayi tazuba godia har yakashe wayan.

Murmushi Hafeez yayi cikin ransa yace "Daniel kenan ae no more place 4 u in d kitchen, bari kadawo I'll have to look anoda job 4 u"
meena ce tafe d'auke da cup din kunnu da plate na indomie a hnkli ta ajiyesu gaban Hafeez tace "com on Yaya sauqo qasa kaci abinci, ba musu Hafeez yasauqo tura mishi plate din tayi gabansa alamar yafaraci, Hafeez yasauqe dubansa akan plate din ga indomie nata tiririn zafi babu spoon a ciki, dasauri Hafeez ya kalli Meena cikin muryan shagwa6a yace "Mrs Hafeez abdoul pls whr is d spoon, yadda Hafeez yyi mgnr tamkar wani qaramin Yaro abin yaso yabama Meena dariya amma sai tayi saurin guntsewa tace "ae yau ba spoon da hannunka zakaci, dasauri Hafeez ya gwalo idanu waje yace what ar u saying? Meena ta gyad'a kai cike da mugunta tace yes abinda kaji shinace.

Hafeez yagyad'a kai yace olryt feed me wit ur hands in ba haka ba bazanci ba, dasauri Meena tamiqe tace a'a baza'ayi haka ba bari nakawoma spoon dinka Hafeez ya maqe kafad'a yace no nida hannunki nakeso kibani inci, Meena dafarko tad'auki abin wasa sai dataga cewa Hafeez da gaske yake sannan ta zauna daf dashi cike da jin kunya take feeding dinsa shima Hafeez din ba'a barshi a baya ba haka nan suka ciyar da junansu.

Cikin kwanakin nan kuwa wata irin shaquwace mai qarfi tashiga tsakanin Hafeez da Meena, wanda ynxu a tare suke cin abinci suke wasu ayyukan mussaman a qarshen sati kullum suna liqe da juna.
       Yayin da Hafeez yaci alwashin cewa bazai ta6a qara neman Meena da auratayya ba har sai da yardarta da kuma amincewarta, abangaran Meena kuwa ganin Hafeez bai qara tunkararta da abinda ke tsorata taba hakan yasa tasaki jiki dashi sosai.

Kullum suna cikin bawa junansu kulawa ta hanyar kyautatawa junansu, cikin wasu yan kwanaki kuwa daga Hafeez har Meena sunqara kyau da cikar zati sai wani shining suke, lyk zoya nd asad.๐Ÿ˜œ


®NWA
[1:18PM, 10/15/2016] My Nabss: [3:23AM, 8/12/2016] MUNAY✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode4⃣6⃣


*BAYAN SHEKARA DAYA*

Bayan shekara d'aya abubuwa da dama sunfaru ciki kuwa hadda qarin matsayin da Hafeez yasamu wajen aikinsa, sai Meena kuma wacce ta kammala koyan sarrafa comptr tafito da kyakyawan sakamako hakan yasa Hafeez yasama mata sana'ar yi Wanda tasamu dinbun nasararo aciki, wanda hakan ya yakaita ga bud'e wani kantamemen supermarket nakanta har kauyan su Baba Rabi Meena taje tad'ebo maza yan'uwanta marasa sana'ar yi tad'aurasu akan sana'arta, hakan yasa komai na tafiya normal.

Abangaran Balkisu kuwa tahaihu tasami baby gal sunanta Aysha sunan mahaifiyar Dr Muh'd amma suna kiranta walida. Watan walida 7 da haihuwa Balkisu tasake samun wani cikin. Rigimace ta6arke sosai a tsakanin family Dr tare da Balkisu domin kuwa ita tace zubar da cikin zatayi mahaifin Dr ne yace wlh muddin ta kuskura tazubar da cikin nan sai yayi qararta, sanna yace da  ita in har ita batason ya'yan to shikam yanason ganin  jikokinsa ta ko ina wannan shine Burinsa.

Sanda Meena tasamu lbrin samuwar wani ciki ga Balkisu hakan yasa taje har gdan da kanta takwantar wa Balkisu hnkli sannan tad'auko walida da kanta tadawo hannunta, tundaga wannan lkcin nekuma riqon Walida ya dawo hannun Meena.

"
 **        **         **       **
Meena kam ta d'auki son duniya tad'aurashi akan walida kullum tana cikin bata kulawa hakan yasa ynxu ta rage bawa Hafeez kulawa kamar yadda tasaba, madara masu tsadar gaske Meena take bama Walida hakan yasa Walida tayi yar kibarta sai dai yarinyar ta kasance mai qaramin jiki hakan yasa bata samu damar koyan zama da wuri ba.

Hakan yasa Meena da kanta taje wani babban shopn mall tasiyoma Walidanta keken koyan zama dasauran kayan wasa.
      Suna dawowa gda Meena garden dinsu tanufa ta ajiyewa Walida kayan wasa kala kala, a can suke zama suyita wasansu.

Meena na matuqar son Walida, haka awani 6angare na zuciyarta tanajin son Hafeez a xuciyarta sai dai Sam bata yarda da hakan ba, kawai tad'auki hakan a matsayin wata shaquwa da sukayi, kuma alhmdllh a ynxu tacikawa Balkisu alqawarinta na kula da Hafeeez domin shida kansa yana yabamata gamida samata albarka sai dai kuma ta lura da Hafeez acikin yan kwanakin nan kamar baya cikin walwala, amma sbd irin kulawar da take bawa Walida gabad'aya hnklinta ya dauku akansa.


Abangaran Hafeez kam ya kawo iya wuya da al'amari Meena sbd kwata kwata yalura Sam bata tausayinsa bata sonsa.
A lkcin da Hafeez yayi wannan tunanin wata irin zuciya ce tad'e be shi da sauri yabaro office dinshi yanufi gda.

Kmr yadda Hafeez yayi zato haka kuwa yafaru domin yana shiga cikin gdan yahango Meena da Walida a garden sunata wasansu hankli kwance

Wani irin haushi Hafeez yaji a fusace yafito a motarsa yanufi garden din ranshi a 6ace, batare da Hafeez ya kula Meena ba yanufi kan Walida a hnkli ya d'auketa sannan yadubi Meena a diqile yace "ba dai akan Walida ne kika canjamin ba to yau xan kawo qarshen abun domin kuwa ina mai miki albishirin cewa a yau zan maida Walida gdansu, dasauri Meena tamiqe tsaye cike da tashin hankali tabud'e baki zatayi mgn Hafeez yasa ya hannu yadakatar da ita cikin tsananin fusata yace badai baby kikeso ba don't worry zaki samu naki nakanki a yau din nan.

Hafeez nafad'in haka yadauki Walida yanufi wajen motarsa da ita, yayinda Meena tabisa da gudu tanata faman roqonsa akan kada yamai da walida, Hafeez kam koh kulata baiyi ba balle yasauraretq bud'e motarsa yayi yasata ciki sannan ya fice a cikin gdan.
     Durqushewa Meena tayi wajen tana kuka sai faman kiran sunan  Walida takeyi.

Hafeez dafarko niyyarsa ya kai Walida gdnsu amma daga bisani ya canja tunaninsa yanufi gdan Baba Rabi da ita.
      Baba Rabi kam na zaune a falonta tana kallon tashar Arewa24 sai jiyo sallamar Hafeez tayi, dasauri ta tarbeshi da fara'arta kamar yadda tasaba. Hafeez kuwa durqusawa yayi har qasa ya gaisheta sai da suka d'antaba hira  sannan Hafeez yace " dama Baba Meena CE bata d'anjin dadi shine nace bari in d'an kawomiki walida wajenki kafin Allah yasa tad'anji sauqi, Baba Rabi ta washe baki cike da farinciki domin kuwa azatonta itama Aminatunta tasamu rabo.

Baba Rabi tace asssha Allah Sarki Ashe Aminatu bataji dad'i ba to kace ina mata sannu kaji, mumurshi Hafeez yayi sannan yace insha allahu zataji, sannan Baba anjima zankawo madaran Walida da kayan sanya wanta.

Baba Rabi tace to shknan sai kadawo, batare da 6ata lkci ba take anan Hafeez ya juya akalar motarsa izuwa gdansa rai 6ace.


®NWA
[1:18PM, 10/15/2016] My Nabss: [11:26AM, 8/13/2016] Munayshat✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode4⃣7⃣~4⃣8⃣

Kamar yadda Hafeez yabar meena duqe tana kuka haka nan yadawo ya tarar da ita duqe tana tafaman zubda k'walla sai wani kumbure kumbure takeyi, a fusace Hafeez yafito daga motarsa, wajen Meena yanufa yaja hannunta batare da yace mata uffan ba.

Meena sai wani turjewa takeyi, yayin da Hafeez yacigaba da janta batare da ya saurara mata ba. Falo ya direta, gabad'aya jiyayi ransa yagama 6aci cikin tsananin fushi yadubi Meena da jajayen idanunsa yace "abubuwan da kikemin sun isheni Meena matsayin mai kika d'aukeni mutun ko icce? Baki da tausayine a zuciyarki ko kinaso kice dani har yau din nan bakisan mi ake nufi da aure ba, ko cemiki akayi girka abinci da gyaran d'aki shine kawai aure, ko kuwa angayamiki nid'in itace ne toh bari kiji idan har ke babu zuciya a qarqashin kirjinki toh ni inada ita, yanzu kiduba auren mu yana so yacika shekara biyu nan da yan watanni.

shiru Meena tayi sai faman zubda kwalla takeyi tawani zauna kmr mai zaman tahiya. Yayin da Hafeez yacigaba da mgnrsa cikin tsananin fushi yace "Meena inaso kisani son ki da qaunarki sunyimin qaqa gda acikin zuciyata narasa yadda zanyi indai najin sonki sbd tunanin danayi hakan ne kawai zaisa nasamu sassauci a cikin zuciyata, sai dai Meena a kullum baki da wani Buri da yawuce kiga cewa kin quntatawa zuciyata, ashe Kenan irin sakayyar da zakiyima zuciyata Kenan, ko kuwa laifine dan na kyaleki kinayin yadda kikaso ko kuwa laifine dan nasoki. Meena Kin wahalar min da zuciya Meena kin azabtar da ita ta hanyoyi da dama, dama ashe haka so yake inkuwa haka so yake to nayi allah wadai da soyayya, dama ashe mata dukk halinku d'aya a ynxu Meena bakida wani bambanci da Suhailat.

Wani irin Numfashi Hafeez yaja lkcin da ya ambaci sunan Suhailat sai kuma can yadubi Meena fuska araunane yace "bambancinku kad'an ne sbd Meena soyayyarki ta makantar dani banaji bana ganin hanya sonki yahana zuciyata ganin laifinki" Meena idan akwai wani mummunan hali dakika hango atattare dani yasa kike quntatawa zuciyata to inaso kidubi girman Allah kisanar dani namiki alqawari zan gyara.

'
Wani irin iska mad'aci Hafeez ya furzar sannan yyi murmushin qarfin hali yace " any way tunda bakida abincewa toh INA mai farincikin sanar dake Meena a yau din nan zan kawo qarshen dukk wani 6acin rai a gdan nan, tunda na lura cewa babu dashasshiyar zuciya a qirjinki, kawai ina ganin zaifi kyau na sallama miki kikoma gdnku domin kuwa bana ta6a tunanin cewa wataran zaki soni Meena,..Hafeez na fad'in Haka yagoge hawayen dake qoqarin zubo masa sannan yadafe kirjinsa, dakyar yake Jan qafafunsa izuwa d'akinsa' kafin yashiga yajuyo a hnkli yadubi Meena wacce har ynxu tana zaune, murmushin yaqe yayi Wanda yafi kuka ciwo a hnkli yace "tunda narasa iyayena  na rasa farin cikina, narasa maisona da gaskiya (Rafee'a) narasa qannena hakan yasa tundaga wannan lkcin naji dukk wata d'iya macce tafita araina a wannan lkcin ne ni Hafeez nadasawa kaina BURIN kula da Balkisu batare da nayi aure ba sai dai Balkisu tayi kuskuren kawomin ke cikin rayuwata, dafarko nayi zaton tafiyar zatayi dai dai sai dai asheee gur6ataccen tunani zuciyata keyi a koda yaushe na tunanin cewa wataran zaki soni amma ynxu na fahimci cewa al'amarin sam ba haka yake ba, amma inaso kisani Meena cewa kin illatamin zuciya"

Hafeez na fad'in haka ya bud'e kofar d'akinsa yashige, direct briefcase dinsa yanufa ya bud'e jakar da hannu d'aya hannu d'ayan ya dafe kirjinsa dashi sbd wata irin azaba da yakeji a zuciyarsa.

A hnkli ya zaro memo da Biro.

A bangaran Meena kuwa tashin hankli tashiga wanda ba'a samishi rana domin kalaman Hafeez sun d'aga mata hankli sunsata natsawa cikin duniyar danasani da na dama.

Cikin zuciyarta kuwa Kalmar inalillahi wa'ina ilahiraji'un shine kawai abinda take iya fad'i dasauri tamiqe tanufi d'akin Hafeez domin kuwa batasan abinda yake nufi dacewa yau zai kawo qarshen dukk wani 6acin rai ba, rasss!! Gabanta yafad'i lkcin da wani tunani yaxo mata kar dai ace Hafeez sakinta zaiyi, ae da gudu ta tashi tashiga cikin d'akin Hafeez. dai dai lkcin ne Hafeez ya d'aura hannunsa akan takarda hawaye na zubo masa.

Batare da Meena ta jira komai ba ta d'ale saman gado dasauri ta rungumi Hafeez tana wani irin gunjin kuka sai fad'in take plss Yaya kayafemin wlh inasonka ina kaunarka hasalima banta6ajin son d'a namiji ba sai akanka dan Allah karkace xakayimin katanga a tsakanina da kai wlh bazan iya rayuwa babu kai ba.

Inasonka!
Inasonka!!
Inasonka!!!

Dasauri Hafeez ya jefar da biron dake hannunsa ya rungumi Meena sosai a jikinsa shima sai faman nanata irin sonda yake mata yakeyi, kuka sukayi sosai daga bisani kuma suka shiga bawa junansu hakuri.

Hafeez ya dubi Meena da murmushi yad'an lakaci hancinta yace "gsky Meena I can liv wit out u I luv u so much" Meena tad'anyi fari da idanu gamida murmushin jindadi tace nima haka yayana.
Wani dariya farinciki sukayi atare, nan  Hafeez yarungume abarsa sai faman rad'amata kalamai masu tsima zuciya yakeyi, hakanan suka kasance cikin farinciki (nikaina Munay murmushi nayi nace Allah gwadamin auran BABY AMRAH๐Ÿ˜„) ganin da nayi Hafeez na qoqarin zarce gona da iri hakan yasa nayi saurin ficewa daga cikin d'akin narufo musu kofa abinsu.


®NWA
[1:18PM, 10/15/2016] My Nabss: [12:44PM, 8/13/2016] Munayshat✍๐Ÿฝ: ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ
     ✨BURIN HAFEEZ✨
๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

                     By

©MUNAY

®NAGARTA WRITTERS ASSOCIATION.


Episode4⃣9⃣~5⃣0⃣

Last episode.

Bayan shekara goma nasake komawa gdan Hafeez da Meena domin na d'aukowa fans dina rahoto.

Hafeez na hango zaune a falo tare da wasu yara su uku kewaye da dashi,  babban cikinsu ne yake mgn kmr xai yi kuka (yaron baxai wuce kimanin shekara tara ba, sai d'ayar mai bimasa itama baxata wuce shekara bakwai ba, sai kuma wata yar qaramar yarinya da bata wuce shekara d'aya da rabi ba). babban yaron naga ya riqema Hafeez hannunsa yana fad'in plss Daddy katashi muje ka kaimu gdan Amma (grannynsu)

Meena ce tafito daga cikin d'akinta sanye da hijab dasauri tanufo falon babban yaron naji tana kwalawa kira Mu'aisin!! ina mamana da Imrah ne? Wanda aka kira da suna Mu'aisin yace yes mommy gamunan a wajen daddy yaqi kaimu wajan Amma.

Meena tayi wani irin kyau da haske tawani cika ta qara kyau da wayewa, " murmushi Meena tayi tace "wlh Mu'aisin bakwa rabuwa da rigima maimakon ka kama qannenka kuje kuyi home work shine kazo kukasa dadynku agaba kuna damunshi ko?"

Dasauri d'ayar taqaraso gamida riqe hannun Meena tace Momy ae tundazu Yaya Mu'aisin yayi mana home work, mudai kikaimu wajan Amma tayi mana tatsuniya. Girgiza kai Meena tayi gamida yar dariya tace toh shknan Mamana jeki d'auko hijabinki kuzo mutafi gdan Amman, ihuuun murna suka saki a tare da gudu suka shirya suka nufi waje.

Hafeez yadubi Meena da Murmushi d'auke a fukarsa yace "maman 'yan uku naga kina qoqarin barin Imrah dasauri Meena ta gwalo ido waje tace "a'a rufamin asiri ina zan iya tafiya nabar auta na", duqawa tayi tadauki Imrahn gamida kallon Hafeez tace Yaya bari nakai yaran nan gdan Amma nadawo, Hafeez yace "ahh toh kiyi sauri kidawo domin inaso yau kidafamin tuwon dalayi da miyan ku6ewa, Murmushi Meena tayi sannan tafice a falon yayinda Hafeez yabita da kallon farinciki yana qarajin son Meena naratsa ko ina na zuciyarsa a hankali Hafeez yayi ajiyar zuciya afili yace "I Luv u Meena"  murmushi Hafeez yasake sakarwa kansa a karo na biyu yace "BURIN HAFEEZ a ynxu shine nakasance da MEENA a koda yaushe.

Su Meena Na fita gdan Baba Rabi suka nufa kai tsaye,.. "Wadda Baba Rabi a ynxu Meena ta gina mata wani tamfatsetsen gda anan cikin sabon fegi dake cikin garin borno, Da sallama su Mu'asin su shiga cikin gdan, inda na hango Baba Rabi kwnce wata yar mataciyar kyakyawar budurwa tana gyara mata farcen qafa (Baba Rabi ta qara tsufa ga wani irin hutu da jinddi yazauna mata) Mu'aisin nashiga falon naji yakira yarinyar dake gyarawa Baba Rabi farce "anty walida wannan tsohuwar kike gyara mana ne?" Walida tayi murmushi tace Mu'aisin ina ruwanka da ita, Baba Rabi tayi yar dariya cike da dattijantaka  tace "a'a mai gdana Mu'aisin yau kaine a gdan nawa? Dasauri suka qarasa wajenta.

Jin kiran sunan Walida yasa nayi mamakin ganin girmanta,

"sallamu alaikum" Meena tayi sallama lkcin da take qoqarin shiga cikin falon, gabad'ayansu suka amsa "wa'alaikissalam" dagudu walida taje ta tarbi Meena "oyoyoo mommyna" Meena tad'an harareta tace "hmmm walida kinqimu kinqi Balkisu da Abbanki wato gabad'aya kintare kindawo wajan Amma koh? Walida tariqe baki dasauri tace a'a mommy ina nan zuwa a weekend kuma ko jiyama naje gdnmu nawuni. Meena tayi murmushi tace toh shknan yayi kyau ga qannenki nan nakawo muku ku wuni tare anjima daddare daddynsu zaizo yad'aukesu. Bayan sund'anta6a hira kadan Meena tace nizan wuce gda inason naje nayima Yaya Hafeez girki, sallama sukayi sannan tawuce.

Abangaran Balkisu kuwa bayan tahaifi Walida takoma haifan yara uku macce d'aya namiji biyu, wato Fahad da Faruk sai kuma qaramar ummie. Walida kam na wajan Baba Rabi sbd tunsanda Hafeez yakaita bai d'aukotaba Hakan yasa ta taso a hannun Baba Rabi cike da kulawa da kuma bata ingatacciyar tarbiyya, hakan yasa Walida takeji da Baba Rabi sosai aranta.

Abangaran Meena kuma yaranta uku wato Mu'asin shine d'anta nafari mai sunan mahaifin Hafeez sai kuma ta tsakiyar maisunan Baba Rabi wacce Meena ke kira da Mamana, sai auta Imrah mai sunan Balkisu. Yaran suntaso cike da so da qaunar junansu.

           **      **
Meena na isa gda kitchn tawuce direct dominta  d'aurawa Hafeez tuwon dalayinsa kmr yadda yabuqata, sai da Meena ta kammala girkin tsaff sannan tad'auki abincin tanufi d'akin Hafeez dashi, sauqowa qasa Hafeez yayi yafara kwasan girki sai faman santi yake zuba mata kmr yadda yasaba, murmushi kawai Meena keyi cikin zuciyarta tace " _*Da fari NAYI ALKAWARI kan cewa SAI NAGA JIDDA ALIYU   kodan in cika BURIN HAFEEZ sai na fahimci cewa DA KAMAR WUYA tunda har RABI'ATUL ADAWIYYA ta fini wannan burin saina sakar mata ragamar kasancewarta  gimbiya mai babban matsayi amma bawai matsayinta na gimbiya kadai yasa hakan ba sai dan tunasar dani da SA'EEMAH tayi domin zan iya sadaukarmata sadaukar karamcinta koda ita din BAIWA CE*_

(Nikam munay murmushi nayi domin sharhin Meena ya burgeni)

Bayan Hafeez yagama cin tuwon sane yadubi Meena gami da kashe mata ido yace "I Luv u so much my wife" sannan ya manna mata kiss a goshi

Nikam dasauri nabar d'akin, nace araina Allah yabar soyayya HAFEEZ DA HAFEEZA lolz*Tammat bihamdullah* domin anan nake kawo muku qarshen d'an taqaitaccen labarin nan, kuskuren dake ciki Allah ya yafemin ladan dake cikinsa Allah ya sadamu dace baki d'aya.

Nagode sosai masoyana a dukk inda kuke.

*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin gareki *AFRAH* tare da dukkan masoyan MUNAIYSHAT.

*A kullum kuna raina*

My Nana fu'ad and my Namcy ESHA
Rash Kardam
My Nana
Sanah s matazu
Xee Mmn khdy
My Shafa
S.A Azeez
Jidda Aliyu
Rookie bby & illham
Asmee b Aliyu
My nabss

Special thanks goes to
DUNIYAR MAKARANTA
HAUSA NOVEL ONLY
AMRAH ND RABI'AT SK NOVELS
DAGA TASKARMU yan group dina (Luv u so much❤)
MACCEN GABAN GOSHI
ASMEE FANS
LADIES NOVEL WRLD
FOULANI CERDIYA FNS
QURRATUL AYN dcmnt

Dama sauran gwnda ban lissafo ba dukka kuna raina๐Ÿ˜˜

*Ban manta daku ba*
Ummi ck
Queen miemie my douter
Autar hajiya
Foulani
Hajia jamila
Anee
Chuchun gaye
Khadija candy
Mmn meenat
Adda beena
Billy spcial
Jidda Joe
Billy giro
my Futha
Billy Sarki
P.hassy
Asea
My Sadeey splxy
Baby amrah
Amrah nd rabiat
Dasauranku dukka kuna raina

Taku jinjinar tadabance NWA Allah yaqara kaifin baseera

Ina miqa sakon gaisuwa tagareku masoyan burin hafeez nagode sosai da kulawarku gamida lkcinku๐Ÿ˜˜ 
Sai munhadu a sabon buk dina

Taku har a kullum AYSHAT ABUBAKAR SADEEQ GASHUA CITY ๐Ÿ˜€๐Ÿ’ƒ

                          *MUNAY*

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *