Edited by
ASMART🌸🌸
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg1⃣
KATSINA
Duk wanda ya san Jami'ar Umaru Musa Yaradua dake garin
Katsina yasan wajen gari take, a k'alla ba a kasara ba tafiyar minti arba'in da
biyar (45) ne zuwa cikin gari.
Daliban aji d'aya,
na (Department of MicroBiology) ne suka fito a gajiye daga aji misalin karfe
shidda da minti biyar (6:05) na yamma kasancewar sunyi lectures 4-6.
Mimi tayi
wujiga-wujiga don tsabar gajiya, ta kalli kawayenta biyu tace
"Wayyo Allah!
da alamun zamu kwana a Hostel yau, ji yanda garin ya hade rai, ko dai ruwa
zaayi?"
Usheey cikin damuwa
tace "kai! dole captain ya nema mana sauki gun lecturer nan, a yi
rescheduling lectures din, ko wednessdays ne da safe, don bala'i 4-6 ran
saturday?"
Dayar me sanye da
nikaf tace
"Don Allah ku
mu daga kafa, kar su cike bus din, kun dai san mazan nan ba hakuri zasu yi ba,
balle yanda suka ga hadarin nan kowa so yake ya tafi gida." Miemee tace
"nikam i dont have dat strength."
Usheey tace
"aikam tafiyarmu zamu yi mu bar ki, suka cigaba da tafiya.
Mai sanye da nikaf din tace "laahhh! kun gani ko,
school bus2 sun tafi." Miemee tace "wallahi kina da damuwa, mu kadai
ki ka ga bus din ta bari?"
Mai nikaf din ta
dauke kai don tasan da ta sake bude baki tana iya fashewa da kuka. Usheey tace
"Ai ke Mimi ko
karfe nawa zamu kai na san ko a jikin ki."
Daga nan ba wacce ta
kara magana, ko da suka karasa Student center duhu ya fara yi, kuma matan da ke
gurin daidaiku ne, wasu an basu lift. Miemee tace "ko mu zauna a kujerun
SUG kafin bus ta dawo?"a Usheey tace "chap sabod gamu gantaIallu
ko?"
Dayar tace "to
ya zamu yi? ko mu karasa gate kila mu
samu ko commercial a chan?"
Mimi tace "chap
wallahi bazan iya tafiyar minti ashirin ba."
Usheey tace "toh
bari mu barki nan."
Tafiya su ka fara yi miemee tace "bala'i wlh ba za ku
barni nan ba, ta bi bayan su da sauri. Tafiya su ke yi suna fira jefi-jefi,
dare kam har ya fara yi ga hadari ya kara haduwa, Agogon wayar ta karfe7 saura
minti 15, Idon mai nikaf ya ciko da hawaye, tsiraran motoci suke wucewa, miemee
tace "wlh a ruwa muke, dama mu samu lift. Usheey tace "eh wlh".
Ba su rufe baki ba sai ga wata bakar mota mai bakin gilashi
ta danno a guje, har ta dan gifta su, sai kuma motar ta fara dawo da baya da
baya. Miemee tayi saurin gyara zaman rigarta, tace "yauwa ai nasan na
annabi ba sa karewa, ga lift nan na zuwa" usheey tace "Barkan mu
Allah ya takaita mana wahala ba sai mun je gate ba" me nikaf cike da
mamakin kawayenta tace "yanzu motar nan mai tint zaku shiga? Kuna jin
sauti na tashi kamar ba dare ba?" Usheey da miemee suka buga tsaki a tare,
Usheey tace "kinga dai Besty idan muka bar motar nan ta tafi, ba mu san
lokacin tafiyar mu gida ba, daga cikin makaranta ta fito balle mu ce sace mu za
ayi, " Miemee cikeda takaici tace "Abu mai sauki, idan ba ta shiga
sai mu yi tafiyar mu mu barta nan" kafin tace wani abu motar nan ta iso ta
tsaya daidai su.
Ido suka zuba ma bak'in windon motar, a hankali glass din ke
sauka, idanuwan 'yan matan nan 3 tsam cikin halittun da ke zaune gaban sits din
motar, Su biyu ne, daya na zaune sit din direba, dayan kuma na zaune a kujera
me zaman banza, da alamu abokai ne, Mimi da fara'arta tace "sannun ku fa,
please, cikin gari kukayi"? Me tuk'in motar ya dan yatsina fuska, a
tak'aice yace "Eh" dayan ko kallon su beyi ba, ba tare da bata lokaci
ba mimi ta sa hannu ta bude baya, zata shiga kenan me tukin motar yace "ba
dai da Ninja din chann za a shigar min mota ba?" Mimi ta kalleshi da
mamaki, tace "ninja kuma"? Yace ehmana wanchan me Nikab din, Ushee a
hankali tace Seebi daga nikab dinki, wacce aka kira da Seebi ta kalli Ushee
cike da takaici tace bazan daga ba, ba zan kuma cire ba, sai a sannan Abokin ya
juyo don kallon mai nikab, itama ta dago kai kenan suka hada ido, sun dauki
kusan seconds goma suna kallon-kallo, yayi saurin dauke kai, ya maida kallon
shi ga Abokin shi, murya kasa-kasa kamar bai son magana"yace Maalesh
donAllah mu tafi" wanda aka kira da Maalesh ya kalli miemee yace
"Malama kulle min kofa ko?" Miemee za ta yi mar magiya kan yayi
hakuri mai nikaf tayi saurin kulle kofar, Maalesh ya ja motar sa a sittin ya
bar gurin.
Mimi cike da fada
tace "Haba SEEBI menene haka?" kin wargaza mana damar da mu.ka samu
na tafia gida, Ushee tace aa fa mimi, shima ya sa wulakanci a alamarin shi,
menene abun ce mata Ninja? kuma har sai ta cire nikab zai taimaka ya dauke mu?
Mai nikab din tace "Dama chan basuyi niyyar daukar mu
ba". Ushee tace Seebi kin lura da na gaban motar? Side view din shi kadai
nagani, amma nagane Azababben guy ne ko kallo fa ba mu ishe shi ba, Uhm kadai
Seebi tace a yayin da ta tuno kallon-kallon da suka yi da shi, Miemee cike da
masifa tace tunda dai sun tafi ai shikenan, Seebi ta mana Bukulu, kila da ko
numbern mu sun amsa, Usheey ta ce ke kuma matsalarki kenan sun amsa number?
Harararta mimi tayi Seebi me nikab ta sa daria don ta saba ganin haka gun
kawayen ta biyu, yanzu ba wannan ba burin ta a yanzu be wuce ta bude ido ta
ganta a gida ba.
_Bibilicious Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg2⃣
Haka suka cigaba da tafiya har suka fita gate, suka tsallaka
titi, a lokacin kuwa dare yayi don bakwai ta gota. Zuciyoyin su ya fara karaya,
tsoro da fargaba ya mamaye su, barin ma mai nikab din da ta fara hawaye a cikin
nikabin ta.
Sunyi nesa da gate Ushee tace "idan ba so kuke mu
karasa cikin Gari a kafa ba ku tsaya mu
samu mota ko daga cikin wadannan masu wucewa ne" Miemee please ki taran
mana lift, Miemee ta tabe baki, tace "ba zan tsaida ba" donAllah mana
miemee inji Mai nikab, in tsaida ki k'i shiga? Da sauri ta zame nikabin
fuskarta, tace "kinga na cire gabaki daya" Miemee tayi murmushi tace
"eh lallai dagaske kike" ta dan matsa bakin titi ta sa hannu, motoci
goma suka wuce da karfi ba tare da sun
tsaya ba, Mimi tace ba fa zasu tsaya ba, ni na gaji. Ushee tace "Dont give
up" Miemee ta wurga mata harara tace malamai kuzo ku sa hannu kila mu samu
wani ya tsaya. Ushee tayi daria ta matso kusa da mimi suka sa hannu.
Daga nesa suka hango wata Jan Mota ya doso da full light
dinsa, suka dage wurin daga hannu yanda za a gansu daga nesa, Motar ta cigaba
da dosu har ta gifta su, Ushee da karfi tace "kaii yau mun shiga 3"
Seebi da ke gefe hawaye kadai ke zuba daga idanuwanta.
Horn suka ji ga baki dayan su ka kallo inda suka ji horn
din,Miemee tace "lahh ga wata BMW
na na zuwa da baya da baya, mai jan motar nan ne ya dawo, ushee tace muyi sauri
mu karasa gunshi kafin ya chanza ra'ayinshi, sauri-sauri suka nufe me motar
nan.
Mimi ce gaba suna biye da ita a baya har suka iso inda
mutumin yayi parking motarsa, ta window miemee tace Assalamu Alaikum, mutumin
ya sauke glass din motar sa, hade da amsa sallamar Mimi, Waiyo Allah! Mimi bude baki tayi tana kallon
mai motar, don ya hadu iya haduwa kamar shi yayi kanshi. Ganin kallon da Mimi
ke mishi ne ya sa shi cewa "Cikin Gari zaku?" Ushee da ta lura
kwatakwata hankalin kawarta mimi be jikinta ya sa ta matso kusa, itama kusan
abun da ya faru da Mimi ya kusan faruwa da ita, amma ta dake tace ina wuni?
Cikin gari zamuje, donAllah ko zaka rage mana hanya? Yace Bismillah, Ushee tace
Mungode, tayi saurin zunguran Mimi, Mimi ta wayance tare da saurin shiga gaban
motar, Ushee ta bude baya ta shiga tare da kallon kawarta da ke tsaye waje,
tace "Seebi shigo mana" cikin
sanyinta ta shigo da Sallama, ya dan waigo ya amsa sallamarta ya dauke kai,
bayan ya kwashe takardun da ke bayan sit din.
Gaishe shi sukayi duka ya amsa musu, yace Students ne ku,
suka amsa mishi da eh, amma a hostel kuke ko? Ushee tace No day, cike da mamaki
yace Day students kuma?ya akayi kukayi dare haka? Mimi cike da yanga ta bashi
bayanin dalilin su na yin dare, ya jinjina kai, yace ya kamata a san nayi, in
rescheduling lectures din za'ayi tok, idan kuma Buses za a karo don tabbatar da
an kai kowa gida, is very risky a bar dalibi mara abun hawa a nan, balle ku
mata. Allah shi kyauta suka amsa da Amin. Haka ya cigaba da tukin shi, Ba wanda
ya sake magana, ba kajin komai sai karatun Qurani mai Girma kira'ar Sudais.
Dif-dif sukaji,
Alamun shigowar waya, mimi ta lek'a wayar kirar Iphone 6s da ke jone jikin
radion mota (AUX) taga Meema jikin screen din, Mutumin yace ma mimi dan taimaka
ki min swiping, da sauri mimee ta yi yanda yace.
Ba tare da ya kanga wayan a kunnesa ba yace "Hello
Assalam Ailaikum" wata Zazzakar murya su Ushee sukaji ta cikin speakers ba
cewa "Hello Uncle Zaid kanajina?" Yayi murmushi yace "Ohh Meema,
so nawa zan miki maganar amsa sallama? Oh sorry Waalaikum Salam, Uncle Zaid
baka iso bane har yanzu? Meema ina cikin katsina, but sai naje masauki, idan na
huta zuwa anjima ko da safe sai na zo gidan ko? A shagwabe tace "haba mana
Uncle Zaid, You promised to come see us immediately you arrived" Ya sauke
ajiyar zuciya, yace "toh bani 30mins zan karaso InshaAllah" tayi
dariar murna, yay Uncle Zee Thanks, u d best" yace "erhm, Rafeek na gida?" tace
"No be dawo ba ko" ya danyi shiru yace "toh sai na iso"
kafin tace wani abu ya latse wayar.
Ushee ta kalli Seebi, sukayi murmushi, matuk'a wanda aka
kira da Uncle Zaid ya burgesu, daga jin wanda su kayi waya da ita sun san yar
gata ce, don yanda take shagwaba da magana, a hankali ushee ta rada ma Seebi
'kila diyar yayar sa ce' seebi gyada kai tayi.
Zaid ya dago wayarsa, ya dan rage gudu, ya shiga neman layin
nephew dinshi, callertune din yazo karshe ba amsa, ya sake redialling, yanzun
ma kamar ba za'a dauka ba, a ka dauka ba tare da ance komai ba, Zaid yayi
gyaran murya, yace "Rafeek" chan kasa sukaji ance "Barka da
yamma" Zaid yace "lafia lao, Kana ina?" kamar bazai tanka ba,
yace "Gani nan Maalesh zai saukeni gida" yace"Okay toh, ku je ku
min booking Liyafa hotel" Ok kadai yace ya kashe wayar, Zaid ya murmusa a
baiyane yace "Rafeek ikon Allah"..
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg3⃣
Zaid ya kallo Miemee yace"Ina kukayi?" mimi ta yi
far da ido tace"dukkanin mu unguwanni daban muke, ka ajiye mu a National,
sai mu hau keke napep" yace "Junction din bus? No, kubari na sauke ko
wacce a unguwar su" mimi ta yi murmusi mai sauti tace "ji fa nayi ana
jiranka" yace kar ku damu, ya kalli mudubi daidai saitin Seebi, yace Malama
wani unguwa kuke? Seebi baki ya fara rawa ta kasa magana, da sauri ushee tace
mu muna ta Wurin Gidan Masari, Miemee kuma na GRA wurin motel. Zaid ya jinjina
kai yace wace Miemee? Miemee na murmushi tace "nice nan" ya sake
kallon madubi yace kece wa? Ushee tace nice Ushee, wannan kuma Seebi, Zaid yayi
murmushin da ke kara ma fuskar sa annuri, yace "inyee!, sunan yan gayu ne
daku, Miemee, Ushee da Seebi" sukayi daria duka, yace toh bari mu fara
sauke Miemee, ku ta unguwarku nayi.
Da taimakon Miemee na nuna mai hanya Zaid ya iso har kofar
Gidansu, yayi parking, miemee ta sadakar zaid zai tambayi numbern ta, sai
wannan yanga takeyi, amma shiru takeji, a ranta tace kila zai tambayi su Ushee,
ta bude murfin kofar tace "Thanks So much Uncle Zaid" ya yi murmushi
yace bakomai, ta juya ta kalli kawayenta tace "toh kar dai a manta a fito
da wuri gobe don muna da GSP karfe takwas (8:00)" Ushee tace
"InshaAllah" Seebi tace "ki gaida Mummy" Miemee tace
"Zataji, dayanku ya dawo gaba" Ushee ta bude murfin motar ta koma
gaba. Mimi ta daga ma Zaid hannu, Ya ja motar ya bar layin ita kuma ta shige
gida.
Shiru ba wanda ke magana, sai da yazo unguwar yace ta wurin
ina kuke? Ushee tace "ka ajiye mu a wurin Makarantar Salamah" ba
wanda ya sake magana har suka zo daf da makarantar Salamah, yayi parking, Ushee
tace mungode sosai, Seebi ta bude murfin motar, tace"Jazakallahu
khair" Allah ya biyaka yanda ka taimake mu" da sauri ya waigo don
yaji dadin adduar nan, duk da be samu ya ga fuskar yarinyar sosai ba yace
"Amin Nagode" Suka rufe kofar ya ja motar sa yayi cikin unguwan, Ushee tace toh Seebi
sai da safe, Allah ya kaimu Ushee, ko wa tayi hanyar Gidansu.
Sai da tayi tafia sosai kafin ta iso gida, ta na ture kofar
gidan ta ga Nenen ta tsaye, da sauri Nene ta rungumota tare da matse kwalla
tace "Nasiba, ina kika tsaya haka? Duk kin tashi hankali na, ince dai
lafiya ko?" Nasiba ta kalli kakarta cikin tausayawa, tace "Nene kiyi
hakuri, darasi mukayi 4-6, ko da a ka tashi ba mu samu abun hawa da wuri ba,
sai da ma mu ka tako har wajen gate kafin muka samu wani bawan Allah ya kawo mu
har gidansu ushee" Nene tace bakiji yanda na tada hsnkali na ba, don naga
baki taba kai wa haka a makaranta ba, na ci kuka na ni kadai, na fi minti 30
gaban gidan nan, ga shegen unguwar nan, ba wanda zaka aika. Da na hana babanki
ya sai man waya, amma saboda irin haka, dole xai siyo min, Seebi tayi daria
tace bari na shiga ciki in watsa, ko Laasar banyi ba wlh" Nene tace
"yi maza, ga abincin ki chan a madafa" ta amsa tare da shigewa cikin
gidan.
Assalam Alaikum yayi sallama a kofar falon gidan, mamimakon
a amsa mai, sai jin ihu yayi, yayyy!!! Ga Uncle Zee oyoyo, wasu yanmata biyu
suka zo suka rungumeshi, takaici ya cika Zaid, be da yanda zaiyi sai dai
k'irk'iro murmushin dole wanda hausawa ke cema Yak'e kafi kuka ciwo, Babbar ta
ja hannunshi zuwa dinning area, tace "Uncle Zaid, i know u must be
hungry" murmushi yayi yace "Aa meema, ciki na a koshe yake" ta
marairaice tace "donAllah kaci, ni da kaina na girka maka, wallahi na dade
ina yi, please" Ya mata murmushin da ke kashe ta yace "Meema i'm full
wallahi, some other time ko?" be bari tace komai ba ya kalli dayar
budurwar yace "Aneesa Yaya na nan? Tace "eh Uncle Zaid yana
sama" mikewa yayi ya hau sama.
Ya shiga da parlorn yayan sa da Sallama, Yayan ya amsa mishi
cike da farin cikin ganin danuwansa, Barka da Yamma yaya, yayan ya amsa mishi
da "Sannu da zuwa Engr. Zaid Ibrahim Lema, Zaid yayi daria, yace ka fara
ko yaya? Nan suka fara fira irin ta wa da kani cike da aminci da kaunar juna,
suna cikin firan ne Hajia Saude tayi Sallama ta shigo dauke ta tray, tana
kwarkwasa kamar wata yarinya, "Ahh! Zaidu, ka iso kenan? Ya amsa mata ba
yabo ba fallasa, ta dire tray din gabn mijinta ta na tsiyaya mai ruwan zafin
shayi a dan karamin kofi, tace" Kaima
a zuba maka Shayin ko Zaid? Ya mike da sauri yace "aa nagode, bari
inje masauki nagaji" ya kalli yayanshi yace "Yaya bari na tafi zan
shigo da safe in Allah ya yarda", Alhaji Habib Ibrahim Lema yace
"Allah shi huta gajia Zaidu".
A parlorn kasa ya iske meema da alamun jiran shi takeyi,
tana ganinshi ta nufo shi da sauri, Uncle Zee har ka gama da daddy? Yace eh
nagaji ne, zan tafi na kwanta, tace yanzu ba za kaci abun da na girka domin ka
ba ko? Yace "sorry Meema" sai da na ci abinci kafin na karaso. Ba
haka taso ba sai dai ba yanda zatayi da shi tace "toh munje in raka
masaukin naka" yace wa zai dawo dake? Don ni bazan sake fitowa ba sai
gobe, ta mai fari da ido tace"ba sai na kwana chan ba" ya zaro ido,
yace ke bana son shiririta, ta wayance tace "haba, kasan wasa nakeyi"
ya wuceta ta bi bayanshi "mai zan dafa maka da safe?" Yace
"Nothing". Ta juyo a fusace tare da fashewa da kuka haye sama..
Daidai haraban gidan mai gadi ya wangale gate, wata bakar
mota mai bakin gilashi ta shigo, Uncle Zaid ya tsaya kallon motar har tayi
parking, bangaren kujeran direba a ka bude, na cikin ya karaso gun zaid da
sauri yace "Uncle Zaid sannu da zuwa, ya Kaduna? Zaid ya amsa cikin sakin
fuska lafiya lao Mahmud. Dayan ya fito cikin takun kasaita, kamar be son taka
kasa, ya karaso gun da su Zaid ke tsaye, sai da ya zo daf da su, ya tsaya ya
cire baki da kyar yace "ka zo lafiya?" Zaid yayi murmushi yace
"lafiya kalau Rafeek, ya karatu? Maimakon ya amsa shi, hannu ya sa a
aljihu ya zaro makulli ya bashi, yace " room 108, Allah huta gajia" ya
maida duban sa ga abokinshi yace "Night Maalesh" ya juya ya bar Zaid
da Maalesh a gurin. Zaid yayi murmushi ya tsaida shi ta hanyar kiran sunan shi
"Rafeek Lema " Chak ya tsaya.
_Bibilicious
biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg4⃣
Uncle Zaid ya tako har gaban shi ya, yace "kana da
matsalan wani abu? Do u need anything?" girgiza kai rafeek yayi, yace No,
nothing, Zaid yace "nawa aka kama min daki? Rafeek yace "na riga na
bada" kayan abincin ka fada kudi? Rafeek yace "akwai saura"
karatu fa? A takiace yace "Lafiya " Zaid yayi daria yace "baka
tambayi Mami ba" Rafeek ya dago jajjayen idon sa ya kalli kawun shi, Zaid
ya fara daria don ya san ya kure hakurin shi, tunda har ya sa shi magana haka,
yace to "ka tafi ko?" kamar jira yake ya fara tafia part dinshi, Zaid
ya juya gun maalesh, Mahmud ya abokin na ka? Maalesh yace "Uncle Zaid,
akwai improvement, don yanzu yana zuwa lectures, daga chan muke wai yayi
lectures 4-6", Zaid ya kalleshi yace "good, kai yaushe kake gama
service din? Maalesh yace"karshen wata" Zaid yace yayi "kyau
copper, ka kawo min CV dinka kafin na bar katsina" Maalesh yace nagode
Uncle Zaid.
Kamar daga sama yaji muryan Rafeek nace wa "erhm, nace
ba?" Zaid da Maalesh suka kallo shi, Zaid yace "naam, kace
mene?" Rafeek ya danyi guntun tsaki yace " kace ma wannan yarinyar ta
daina shiga harkata, ta daina kula ni" tsaf Zaid ya gane yarinyar da ya ke
magana, amma sai yace "wace yarinya kenan?" Rafeek ya bata rai yace
"Aneesa" Zaid ya dan murmusa, yace "haba Rafeek, ya zaayi ta
daina kula ka? Ai ko ba komai zumunci ya hada ku, ba wani abu bane don ta kula
ka, besides ai kanwar ka ce, duk da ba a saba ganin fuskar shi da murmushi ba,
amma kallo daya zaka mishi yanzu kasan ranshi ya baci, ya daure fuskar nan
tamau, zuciyar sa na tafarfa sa, da karfi yace " she's not my Sister,
she's Nothing like my sister" Maalesh ya tsorata da yanayin abokin sa, don
ya dade be ji ya daga murya haka ba, kuma uncle Zaid ya ke ma ihun nan? Kai
Rafeek be cikin hayyacin sa"
Rafeek ya runtse ido gam, Zaid ko sai daga baya yayi da na
sanin cewa Aneesa kanwar Rafeek ce, tunda ya ga haka, ya san ran shi ya baci,
kwata kwata be son ganin tillon dan yayan shi a damuwa.Rafeek ya bude ido a
hankali ya sauke su fes kan Zaid, dan gajeren tsaki yayi yace "I am
sorry" Zaid yayi murmushi yace "je ka kwanta Rafeek" Maalesh kai
ma ka wuce gida Allah ya bamu Alheri" ya fada motarsa, Maalesh ya shiga
motarshi ya tada, a ka bar rafeek tsaye yana kallonsu, maigadi ya bude gate
Maalesh ya fara fita, daidai Rafeek uncle Zaid ya tsaya, yayi winning glass ya
miko mishi takarddun Kilishi guda 2, yace a hanyar K'ank'ara na siya "
Rafeek ya amsa yayi murmushi da gefen bakin sa, Zaid yace "Baka tambayi
Ayman ba" Rafeek ya dan gajeren murmushi, yace "she's fine, she is
always" Zaid ya jinjina kai yace "Good night Son" Rafeek ya daga
mai hannu ya wuce.
Nasiba, yau ba darasi ne zaki tashi ko sai kin makara? Nene,
na gama makara wallahi, amm dai shiryawa nakeyi, na kusa gamawa, Nene tace"
kin san nafi kowa son karatun nan, so nake naga kin zama dapta" Seebi tayi
daria, tace"Nene Doctor ake cewa, kuma ai Nene ai ba karatun da nakeyi ba
kenan" Nene tace "ke dalla rabani, duk daya ne, tunda ance zaki iya
aikin asibiti da karatun,dama ni buri na in ga yar jikalle na aikin asibiti,
idan naje ba ruwana da bin layi" Nasiba ta fito tana daria, tace "Oh
Nene akwai abin daria, nikam bari in tafi don na san nayi latti." Nene
tace "ga kalacin ki chan, yanzu na siyo miki kosai, ga koko na dama
miki" tace Wallahi na tsaya kalaci latti zanyi, ushee na chan National ta
na jirana, idan naje makaranta zan siya, Nene ba ta ji dadi ba, amma ba yanda
zatayi, ta ciro #200 a hab'ar zaninta tace "gashi kin kara" Nasiba ta
rungume kakarta, tace "nagode Nene sai nadawo" har waje ta rako Seebi
ta na mata addua.
Ya shigo gidan Cikin shiga
k'ananun kaya, yayi kyau matuka, a parlo ya zauna yana neman layin
Rafeek, ringing na 3 ya dauka "Barka da Safiyya" Zaid yace
"Rafeek, ka tashi lafiya?" eh kawai yace, ka tafi school din ne?
Rafeek yace "Eh, ina da lectures ne yanzu" Zaid yaji dadi sosai, yace
"ni gani nan zan wuce Abuja, sai na dawo kaduna, ko na biyo ta makarantar
muyi bankwana?, Rafeek ya girgiza kai yace ba sai kazo ba, Allah ya tsare
hanya, ina gaida Ayman dina" Zaid yace "Ayman dinka zataji, amma ita
kadai? Rafeek yayi saurin cewa "Safe journey" tare da latse wayan.
Aneesa ce ta saukko taga Uncle Zaid zaune, bude murya tayi
tace "Aunty Meema, ga Uncle Zaid" ta karasa gunshi "good Morning
Uncle Zaid, Zaid yayi dan murmushi yace "Aneesa kin tashi lafia? Lafiya
lao Uncle Zaid ba dai yau zaka tafi ba? Yace yanzu kuwa "yaya ya tashi
ko?" Eh ya tashi, Uncle Zaid, ina da matsala" Ya dan kallota na me
fa?, ta gyara Zama "Uncle Zaid, Yaya Rafeek ne, ba ya son in rabe shi,
kullum da ya gannin kamar ya ga mutuwar shi, rannan har mari na yayi don na je
dakin shi" ta karashe maganar ta tana kwalla, Zaid ya sauke numfashi, shi
ma besan ta inda zai bullo ma lamarin Rafeek ba, kullum sai fadin rai, ya kasa
manta abunda ya faru a baya, ya kasa cigaba da rayuwar sa kamar yanda wasu ke
cigaba da rayuwar su idan wata k'addara ta fado musu. Ya daure yace " kiyi
hakuri Anee, kinsan halin Rafeek, Miskili ne, ki daina shige mishi, kar wata rana ya illata ki, ki yi hakuri, ki taya
shi da addua Allah ya shirya shi, da ina da ikon chanza shi da na chanza shi,
amma Addua kadai yake bukata. Da sauri Aneesa tace Uncle Zaid wallahi zan iya
chanza, ina son shi, zan iya zama da shi ta ko wanne hali, ku aura mishi ni, ni
ce ALHERINSA.
_Bibilicious Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg5⃣
Zaid ya yi mamakin maganar Aneesa, banda yarinta ya za'ayi
tace a aura mata Rafeek? Uncle Zaid baka ce komai ba, Aneesa ta katse mishi
tunanin.
Yak'e yayi, yace "banda abunki Aneesa, wa zai ma Rafeek
aure yanzu? Rafeek fa yaro ne, he is just 24" tace "Uncle zai- ya
katseta ta hanyar daga mata hannu yace "please anee, no one is getting
Rafeek married now" tayi raurau da fuska,
tace"Wallahi ina son Rafeek, zan kuma jira shi, zan jure duk wani
wulakancin da zai min.
"Tunda maganan Soyayya akeyi, bari kuji labarin rai
na"
Meema ce ke fadin haka a yayin da ta ke sauko wa daga bene
har ta karaso gaban su, sanye take da shara-sharar rigar baccin da ko guiwar ta
bata rufe ba, Zaid ya dauke duban sa daa kanta, masauki tayi kan kujerar da
yake zaune, fari take mai da ido tace "Uncle Zee, kasan irin son da nake
maka? Ni bansan yanda akayi na fara sonka ba, kuma na sha mafarkin mun yi aure
mun haifi kannen Ayman, Uncle Zaid ka aureni please.
"Ya Salam!" Zaid ya furta a hankali tare da dafe
kanshi, wasu irin mata ne wannan? Masu tallan kan su, Ya cije ya kalli meema da
ke ta wurwulla idanuwa don ta burgeshi, wani takaici ya tokare mai wuya, ya san
Meema na son shi, tun kafin yayi aure, amma ba zai iya auren ta a haka ba, sam
rayuwar su basuyi kama ba.
Alhaji Habib Lema da matarshi Hajiya Saude suka sauko kasa,
da sauri Zaid ya tashi ya nufi gun yayan shi, yace "Barka da safiyya"
Yayan yace "lafiya lao, Engr. Har anyi harramar tafiya?" Zaid yace InshaAllah "ya juya ya kalli
matar yayan sa yace "Madam an tashi lafia?" fuska sake tace
"lafiya lau Uncle" yayan yace "Zaid muje daga waje akwai wata
maganar da nake so muyi, yace "toh yaya" Zaid ya musu Sallama da ga
chan zai wuce, ba haka hajia saude ta so ba, ta so taji maganar da Alhaji zai
gaya ma Zaid, ta so taji me zasu tautauna a kai.
Meema ta kalli yayar ta rai a bace tace na "Nagaji
Sauda, ya za'ayi na dinga mishi tallan kai na ya na ba dani? Nifa na fi karfin
wulakanci da namiji" H.saude ta murmusa, tacd dadi na dake Maryam gajin
hakuri, ai komai sai an bi a sannu a ke dacewa ko? Kiyi laakari da yanda ni na
samu Alhaji, ki kara hakuri komai ya kusa zuwa karshe" Aneesa tace
"Mummy ni kum-- Hajia saude tace
" shhh, Matsalarki Rafeek ko? Nima shine kadai matsala ta, bana jin Zaid,
Rafeek nakeji, amma kar ya damu idan ya sn wata be san wata ba, ku bar komai a
hannuna kunji?" Meema da Aneesa suka chafe hannu cikin murna suna fadin
"sai ke mata daya rak a gidan Habib Lema" ita ko dadi wannan kirarin
ya mata dadi ta haye sama.
A hankali yake
tuk'insa, yana tunanin maganar da yayan sa ya gama mishi yanzu, a kan karatun
Rafeek ne, inda yayan ke cewa "kaga Zaid, ni sai nayi wata da watanni ban
daura Rafeek a idona ba, be yarda mu hada hanya, anya yaron nan be shaye shaye?
Da sauri Zaid ya girgiza kanshi, yace " wallahi Rafeek be shan ko
Sigari"
Yayan yace "Zaid na kasa yarda da hakan shekara ta uku
kenan Rafeek na Spill over a makaranta, last upper year spill over from
nowhere, be gyara ta ba, last year ma be
gyara ba, ina tsoron wannan shekarar abun da ya faru ya sake faruwa don da
alamun abokan banxa yake bi suke bashi wasu k'wayoyin da ke taba mai kwakwalwa,
shisa ya kasa kwantar da hankalinshi yayi karatu" da sauri Zaid ya katse
shi, ta hanyar cewa "aa yaya, ka fadi Alkhairi ko kayi shiru, kowa ya san
Rafeek mai k'okari ne da hazaka, kar ka manta tunda Rafeek ya shiga UMYU shine
over roll dinsu, 4+pointer, komai ya dagule ne sakamakkon k'addara da ta riga
fata, amma InshaAllah komai zai daidaita. Alh. Habib ya jinjina kai yace
"haka ne Allah shi kyauta, amma kasan har yanzu ba ya min magana? Zaid ya
tashi yana daria yace bari na tafi "Yaya sai na dawo karshen Sati"
Alh. Habib yayi daria "wato ba ka son laifin shi
ko?" Toh Allah ya kiyyaye.
Wata tsohuwa ya gani da ga gefe ta na sa mai hannu, yayi
mamaki don ba a titi yake ba, har yanzu be fita daga cikin Unguwar ba, ya dan
gangara ya sauke gilashin motar shi, yace Lafiya Iya? Tsohuwar tace Yauwa bawon
Allah taimaka ka zo ka ka duba min layin wutan chan, k'auri yake yi,nafi minti
30 tsaye ko zan ga wani namijin da zai duba mun, amma tun dazun shiru, Zaid
yayi shiru ya na karantar tsohuwar nan.
Can ya fito ya kulle kofar yace muje nagani, tsohuwar ta ja
shi har cikin madaidaicin gidanta, daidai gurin, fuse din har ya fara spark ,
"SubhanAllah, kinga ya fara kamu da wuta" Zaid ya ga in dai ya bata wani lokaci wires din
wurin za su fara ci, kuma baa san inda wutan zai tsaya ba, yayi jihadin sa
hannun shi ya zaro fuse din ya cillar.
Tsohuwar ta sa ihun murna har da tafin ta, tace "sannu
dan Albarka, Allah ya sa ba abunda ya samu hannuka" Zaid ya dago hannun
shi, Cikin ikon Allah ba abunda ya samu hannun.
Zaid yace "ina zuwa, ya fita" tsohuwar ta bishi da
ido, motarsa ya shige, bayan mintuna kadan sai gashi da mai gyaran wuta, Zaid
ya kalli tsohuwar yace " Toh Iya, ga mai gyara nan, ni zan tafi" baki
bude tsohuwar nan take kallon shi, bawan
Allah tsaya, Zaid ya tsaya, tace Nagode kaji? Allah ya biyaka, Zaid yayi
murmushi. "Amin Nagode Iyah, ni na wuce" tace "donAllah ka
tsaya, na kwadanta maka zogale" yace "wallahi, sauri nake, kaduna zan
tafi yanzu" tace toh dan jirani da sauri ta shige kitchen, sai ga ta da
bakar leda ta mik'a mai, tace gashi ya amsa yana mamakin me ke ciki, tace kayan
miya ne irin su daddawa, kuka, kanwa da su kanumfari" ya ce toh ni iyah--
ta katse shi ta hanyar cewa a kai wa Uwargida, idan babu kuma akai ma
mahaifiya, Zaid ya sake wani murmushi, farat daya yaji son tsohuwar nan har
ranshi, yace "toh nagode Iya" tace bakomai har ya juya tace
"nidai, in kace min iyah, ji na ke kamar ka mayar dani wata tsohuwa, zaid
yayi daria sosai, yace ai tsohuwar ce" tace "kai bawan Allah, ban
wani tsufa ba" yace toh shekarun ki nawa? Tace goma-goma guda shiddada
hudu Zaid(10*6+4) ya bude baki yace lalala 64 fa kenan? eh lallai baki tsufa
ba" a tare sukayi daria. Yace "toh me zan dinga kiran ki dashi ? Tace
"yanda jikoki na ke ce min, NENE"
_Bibilicious
biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS
ASSOCIATION(NWA)
Pg7⃣
"Kinsan jiya sai da nayi mafarkin Azababben Guy din
nan?" Miemee ce ke maganar nan, Ushee da Seebi suka yi daria, Ushee tace
ai ya hadu ne ba karya, Seebi tace ku ma kuka ga fuskar shi, ni jiyan nan ai a
tsoroce nake, Miemee tayi tsaki, "ai wlh kina bada mu, kiyi ta wani nok'e
nok'e kamar wacce tayi karya". Seebi tace banyi karya ba amma ai KUNYA
ADON MACE (Na feedon biebee). Miemee ta kada idanuwa tace "story for the
gods" Ushee tayi daria tace "ya isa, ku tashi muje Library mu fara
Assignment din Wagini, Seebi tace "wallahi yunwa nakeji, daure wa kawai
nayi aka gama first lecture" Ushee tace kinsan dai gobe za'ayi submitting,
kuma gwara mu yi mu dawo before 12 kafin Mr Ola ya shigo, kin dai san rules
dinshi ba a shiga idan ya shiga" Seebi tace "ba zaki gane yunwa Da
nake ji bane, ku je ku mana Assignment din, Miemee tace "aa muje dai tare,
sai mu fito mu ci abincin sha biyu saura minti talatin (11:30) Seebi tace
"i can manage har time din muje".
Tayi Sallama ta shiga Cafteria, tsirarrun mutane suka amsa
ta dinga raba idanuwa, don yau kadai ta zo CAF ita kadai, dalilin hakan kuwa
shine " ba su gama samun Assignments din ba gashi har sha biyu saura minti
sha biyar(11:45), Miemee tace "tunda kin fi mu jin yunwa, kije ki yi
sauri kici abincin, sai mu hade a class
kiyi sauri fa, don muma duk ta kare tafiya zamu yi" Seebi tace Ok, muje ko
Ushee? Miemee tace wlh ba za taje ba, ni kadai za a bari nan? Ki tafi kawai don
you are waiting your time" Seebi ta harari Miemee tace "in kun ga
dama kar kuyi sauri" Suka yi daria duka.
Seebi ta wuce straight wurin reception desk, tace
"Sannu ko" yaron ya amsa da mai "za'a kawo miki?" tace
nikam bani koma meye sauri nikeyi aji zan shiga yanzu" yace"
toh" ya shige ciki da sauri, don sauri ma ta kasa zuwa ta nema gurin
zama. Jim kadan sai gashi ya fito da
tray yace "hajia baki zauna ba?" tace "mik'o min kaji?"
tray din ya bata, FriedRice ne da cowslow sai pure water. Nawa ne kudin? Yace
"Dari Uku (#300)ne" ta ciro ta bashi ta amsa tray din Sai dai me?
Juyawan ta ke da wuya ta ci karo da wani, ba ta san sadda ta
sake tray din abincin ta ba, duk kayan ciki ya zube, ta dago idanuwan ta da
suka kada suka yi ja ta kalli wanda ta buge, shi ko tunani yake wani me kasadan
ne ya zubar mai da abinci a jiki? yana dagowa suka hada ido, tsaf ta gane shi,
shine na gaban motar jiya, haushi ya turnike ta da ta tuna wulakancin da suka
musu na k'in daukar su don tana sanye da nikab.
Rafeek yayi dan guntun tsaki, da zai yi magana sai kuma ya
fasa, ya juya don tafia, Nasiba tayi saurin shan gaban sa ta na huci tare da
rik'e kugu, ranta a bace matuk'a, ga haushin ta zubar da abincinta, ga haushin
yunwa, ga haushin missing lectures din da zata yi, ga haushin bata da wani
kudin siyan abinci. Idonta ya kawo ruwa ba tare da saninta ba hawaye suka fara
zuba daga idanuwan ta. Ido Rafeek ya kura mata, so yake ya tunkude ta yayi
tafiar sa, ba halin shi bane tausayi, be damu da damuwar kowa ba, amma abin
mamaki sai ya tsinci kanshi da ce mata "Me kike so?"
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS
ASSOCIATION(NWA)
Pg6⃣
Zaid ya murmusa yace "toh nene" tace "kai ya
sunan ka"? "Sunana Zaid" tace "Zaidu Bawan Allah" yayu
dariya yace "toh Nene bari dai in wuce kar nayi rana". tace
"Gaskia ne, ince kaduna zaka ko? Ko ka san d'a na? Hafizu Mamman? Fari dan
fulani" Daria sosai Zaid yayi yace
"Nene kaduna babban gari ne, ba yanda zaa yi na san shi" tace
"Allah ka bincika, duk kaduna shi kadai ne" Zaid da ya k'osa ya tafi
yace "Toh Nene", Kudi ya ciro ya ba mai gyara suka kara Sallama.
Har bakin motar shi ta rakashi, tana daga mai hannu tana mai
addu'oin kariya. Ya tada motarshi yayi ribos,ya dau hanyar barin unguwar, Nene
ba ta koma ciki ba har sai da ya kure ganinta kafin ta koma cikin gida,
bini-bini sai ta saki murmushi tana tunanin Zaidu bawan Allah.
Asalin Sunan Nene :Amina amma an fi saninta da Aminene,
'ya'yanta 6, dattijuwa ce me kimanin shekaru 65, Mijinta ya rasu shekaru 20 da
suka wuce ya barta da 'ya'ya 5, a halin
yanzu 2 suke da rai 3 sun rasu. Cikin wanda suke da rai akwai Fatiti, ita ce
diyar Nene ta biyu, tana aure a Jihar Jigawa 'ya'yanta 3, Amina,Umar da
Muhammad.
Muhammad Bishir Sunan autan Nene, yana zaune da matarsa da
'ya'yansa biyu a Malali cikin jihar Kaduna. Nasiba ce ta farko sai kaninta
Anan. Muhammad Yayi aiki a National Trust fund kafin a kulle kamfanin
(Company). A hanlin yanzu ba ya aiki amma yana karban pension duk wata.
Nasiba yar kimanin shekaru Sha tara a duniya(19), ba za a sa
Nasiba a jerin farare ba, haka kuma ba za a sata a jerin bak'ake ba, wankar
tarwada ce, me dara daran idanuwa, idan tayi murmushi kumatun ta sukan lotsa,
bata fiye tsayi ba, kuma tana da dan jiki daidai ita, a takaice Nasiba ta kai
macen da ake kira da masu kyau.
Tayi karatun ta na Nursery, primary harda Secondary a Kaduna
Capital School(KC). Bayan ta gama ne baban ta ya siya mata JAMB, da doki tace
Abba ai Katsina zan sa ko? Ya harare ta cikin wasa yace "kina nan, don ko
Rigachikun ba za ki wuce ba" ta turo baki tare da bubbuga kafa tace nidai
wallahi Abba bana son KASU" tun nursery dina a nan nayi Abba, Shekaru 15
ina karatu a kd, ai change of environment na da dadi, ka ga sai in kular maka
da Mamanka tunda tak'i yarda ta dawo gidan nan da zama"
Umma tace "Eh
kinyi gaskiya Nasiba, Nene na bukatar wani kusa da ita, tunda anyi anyi ta dawo
kaduna ta ki yarda, ya kama ta kije chan kiyi karatun, Mutum ai rahama ne"
Abba ya jinjina kai, yace "ko don Nene zan barki kije Katsina karatu"
tayi ihun murna tace yauwa "Abban mu"
Anan yace Adda Seebi yanzu kina murna zaki tafi ki barni ko?
Sai ya fashe da kuka, da saurin ta rungume tillon kaninta ita ma kukan take yi
tace yi shiru Anan, ai zan dingw dawowa hutu kaji?kuma ga Abban mu ga Ummin mu
ai ka ga ba kai kadai bane ko? Da
kalamai masu dadi ta lallashe shi har yayi bacci, ta dauki form din ta fita don
zuwa dakin ta, ta cika 1st&2nd Choice UMYUK, Microbiology course don school
din basu fara Medicine ba.
Abba ya kalli matarsa yace Ummin yara, gidan nan na
layout(Gidan gadon shi), ina ganin zan tada mutanen ciki Nene ta koma can,
Gidan Kofa Uku ya tsufa,nan aka haifi marigayi Yaya Shehu fa, Umma ta kada kai
tace lallai ya tsufa kam, kinga kuwa sai ta koma gidana na layout din, Ummi
tace "toh Allah ya sa ta yarda, don yanda take son Unguwar nan, raba ta
dashi sai Allah, saboda mutane da Abokan arzikkin ta ya sa ta hana a dauko mata
wacce zasu dinga zama tare saboda kadaici," Abba yace ai Nene in ta kafe
ba me tankwara ta, amma bakomi na san yanda zan bullo wa lamarin" Ummi
tace Gidan fa? Yace "sai in gyara a zuba yan haya ciki"
Cikin Ikon Allah, Watannin da basu rufe 10 ba, Nasiba ta
samu Admission a Jami'ar Umaru Musa, course din da ta zaba suka bata, Gaba ki
dayan su suka zo Katsina don rako Seebi, don daga Registeration ba za ta dawo
Kaduna ba.
Nene tayi murnan dawowan Seebi gunta, don ta na son jikokin
ta sosai, bayan sun huta, Abba ya kebe da mahaifiyar shi, Nene tace "Ya
akayi ne Mahammadu? Cikin ladabi yake maganan, yace " Nene, gidan nan ya
tsufa, katangar kamar zata fado, shine nace ko zaki koma chan gidana na layout,
tayi saurin katse shi "kai tsaya,
ni da gidan nan mutu ka raba, shekaru sama da 30 ina zaune da yan unguwan nan lami
lafia, kawai sai kace na tashi? Too don naki Garin Gwamna (Kaduna) shine kazo
da wannan salon? Toh ba zan tashi ba, ina nan ni da gidan nan mutu ka raba,
idan katangar ya tashi fadowa ya fado kaina, kaga nayi mutuwar shahada
kenan". Abba ya ja numfashi ya san a rina. Ya sadda kansa kasa yace "
Nene, ba wai gaba ki daya za ki koma chan ba, gyara zaayi, idan an gama daga
katangar sai ki dawo, tace kai yaro ni zaka yi wa wayau? Ko da nake kauye ba a
riga na zauna ba, ka fita idona. Abba ya girgiza kansa ya ciro waya ya kira
yayar sa Fatiti, ringing biyu ta dauka, ya mata bayanin kudirinsa kan Nene,
tayi na'am da maganar, ya mik'a mata wayar itama tayi tayi amma Nene tace aa.
Ummi ma ta sa baki, Sai da aka kai ruwa rana kafin ta yarda, tace ni abunda ke
batan rai shine unguwar nan shiru kamar ta mayyu baka ganin kowa awaje don
bakin hali. Daga Abban har Ummin ba su tanka ba don kar ta chanza raayinta. A
ranan Abba ya kira masu mota suka kwashe kayan Nene na bukata suka kai Gidan
layout, A rannan Nene batayi kwanan Kofa Ukku ba".
Abba ke raka Nasiba
Registeration. A gurin reg. Ne ta hadu da Ushee da Miemee. Hussaina Umar(Ushee)
Aisha Saliz (Miemee) kawayen juna ne, tun JS1 suke tare, Ushee da Miemee suna
da kirki sosai, suna son junan su, Miemee ta fiye surutu da kaudi, Ushee kam
akwai jan mutane a jiki.
Wurin signing course form suka hadu, Inda Nasiba ta tambayi
Miemee da ke bayanta a layi Biro, tace "donAllah ara min biro na rubuta
mat.no dina nawa ya tsaya, Miemee da murmushin ta ta ciro ta bata, Miemee na
son kyawawa, tace keme MCB kike? Tace "eh" Sunana Miemee, wannan
kawata ce Ushee" Seebi tayi murmushi ta mika musu hannu sukayi musabaha
tace"its nice meeting u all" nan suka dinke da labari har ya kai su
da exchanging numbers, a nan ne suka gano gidan su Ushee be da nisa da gidan
Nene. Haka Abotar su ta samo Asali.
Wannan Kenan..
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS
ASSOCIATION(NWA)
Pg8⃣
Ta sa bayan hannun ta ta share hawayen ta, tace "ba
kaine ka tsaya a baya na ba na kifar da abinci na, ka juya zaka yi tafian ka,
ba ka ban hakuri ba, gashi yunwa nike ji, abun da ya fi ban haushi shine zanyi
missing lectures dina."
Kallon ta kawai yakeyi, ba wai ya fahimci bayyanan da take
mishi bane, don shi ba ma'abocin sauraron korafe-korafen mutane bane, yana iya
maka laifi ya fi ka zuciya, amma dai ya ji dai tace zatayi missing lectures. Mutane sai kallon
R-lema sukeyi don da wuya kaga yana magana da namiji balle mace, in ka ganshi
cikin CAF to takeaway yazo yi.
Ya kalli mai bada abincin yace sake zubo abincin, ya samu
wuri ya zauna, be kara bi ta kanta ba, tsaye tayi tana murza idanuwa, cleaner
yazo don share gun, chan sai ga shi an kawo wani tray din, kallon ta yayi yace
"zauna" ba musu ta zauna ya tura mata tray din gaban ta, ta kalli
abincin ta kalle shi, tsaki yayi a ranshi, ya miqe ya fita, haka ta gyara zama
taci abincin ta, wannan karon har da Orange juice. Tayi hamdala ta zaro
wayarta, ta ma Ushee text "Lecturer ya fara? Jim kadan sai ga Ushee tayi
reply da "eh ya shiga, kina ina?" ta mayar mata da "ina CAF,
yana bari a shiga? Ushee tayi reply da " wlh bai bari, yanzu ya wulakanta
su Chinyere, kuma ya kulle kofa" Nasiba ta hadiye kukan da ya so zuwa
mata, ta ma Ushee reply da "ni na wuce gida, sai Allah ya kaimu Gobe"
ta mike tare da daukar jakkarta tayi waje.
Ba ta lura dashi ba har ta dan gifta yayi dan tsaki yace
"erhm, nace ba? Ta dan juyo a firgice ganin shi ya sa ta sauke ajiyar
zuciya tace "Wlh har na tsorata, kace mene?" kamar ba zai yi magana
ba don yanda tayi maganar ta tuna mishi d wani abu, chan yace "Meyasa
zakiyi missing lectures?" nan da nan idon ta ya kawo ruwa, tace "nayi
latti, yana daga cikin ka'idojin malamin, na idan ya shiga aji ba wanda ya isa
ya shiga, 12 yake shiga, gashi yanzu 12:19, kaga ko gwara na tafi gida akan
naje ya hanani shiga karshe kuma ya wulakanta ni" Rafeek yace wani mallami
ne wannan? Tace Mr Wagini ne. Yace ina kuke lectures din? Tace "Science
Theatre" a takaice yace "biyo ni" be jira bin ta bakin ta ba
yayi gaba.
Babu yanda zatayi dashi da ya wuce ta bi bayanshi, tafia
yake a nutse kamar be son taka kasa, fuskar nan tamke tamau duk inda suka wuce
ji kake ana "R-Lema" mutane ba su damu da yanda yake basar da su ba
idan sun kira sunan shi, ita ko Seebi ta kasa dauke idanuwan ta daga kallon
shi, karantar shi take yi, komi nashi daban, ba kamar wasu mazan ba, ta
tabbatar da wani ne suka jero haka sai ya isheta da magana, amma shi ko wannan
ko kallo bata ishe shi ba, haka suka iso bakin Lecture hall din, Nasiba ta ja
ta tsaya, tana kallon yan latti nan suna leke ta window, Rafeek ya taka har
gaban kofar ajin da ke kulle ya sa hannu ya kwankwasa.
Daga ciki Mr Wagini ne ke tunanin wani me kasadan ne ya ke
kwankwasa mai, bayan shi da hannun shi ya kulle kofar, rai bace yace da na kusa
da kofar"open the door" da sauri yaron ya je ya cire sakatar kofar ya
bude, idon kowa a kan kofar, so suke su ga mai karfin halin kwankwasa ma Mr.
Wagini.
Shigo wa yayi yana tafian nan nashi,ya na bouncing a
hankali, ba Matan ba harta mazan sai da su kaji ya burge su, kowa ya shiga tofa
albarkacin bakin sa, da yawa za su so Mu'amala ko da ta gaisuwa ce ya hada su
da Rafeek, Miemee tayi saurin tabo Ushee "OMG, ga wani Azababbe nan, ya
tafi da imani na" Ushee tace "ni baki ji nayi shiru ba? Ai ya hadu ne
over, mu dai kalli draman da zasuyi da Wagini".
Har gaban Lecturern yaje, da alamun akwai sanayya tsakanin
su, magana suka danyi kafin Rafeek ya juya ya bar Lecture hall din, Nasiba na
tsaye inda ya barta, ta gaban ta ya wuce ta bishi da kallon mamaki, shi kuma
wannan lafian shi kalau kuwa? Ko be gane ta bane ya wuce ta gaban ta ba tare da
ya kalle ta ba? Ko kuma ya na nufin ta bishi ne? Duk a zuci take zancen nan, ba
ta gama zancen zuci ba taji ana cewa "Mr Wagini yace duk na waje su shigo
aji" da sauri suka fara tururuwar shiga ajin. Wuri ta samu ta zauna ta na
tunanin Wannan Bawan Allah me tarin ban mamaki har a ka gama lectures ba ta
fahimci komai ba.
Kusan kowa zancen gayen da ya shigo aji dazun suke, wasu
suce daga ganin shi dan zafin kai ne, wasu suce ya burgesu, Miemee ta kalli
Seebi tace "kinyi missing, ba ki ga wani Azababben guy da ya shigo ji
dazun ba" Ushee tace ni abun da ya daure min kai shine, yau Mr wagini yayi
abun da be ta bayi ba shine barin late comers su shigo aji, Miemee tace
"kuma fa immediately after fitan wannan ne yace ace su shigo" toh ko
shi ya rok'i alfarmar abar su su shigo? Miemee tace wane shi? Be yi kama da
lecturers ba, yaro ne student kamar mu, da kwai abun da ya kawo shi" kawai
muce yau yan kirkin Mr Wagini suna kanshi" Ushee tace "gaskia
kam" ta zunguro Seebi da kwata-kwata ba ta tare dasu, tafiya kadai takeyi,
Seebi ta dan firgita ta k'akalo murmushi tace "Uhm" cikin zuciyarta
kuma tunani take "Is it possible shi ya roke Mr Wagini akan a barsu su
shiga?" Meyasa fuskar sa fa ba annuri? Meyasa da ya fito ko kallon ta beyi
ba? Meyasa ko sunan ta ya kasa tambaya? Meyasa fuskar sa yake cikin yanayi na
damuwa ko rashin walwala ne bata san ya za ta sa abun ba? Tambayoyi da yawa da
take bukatar amsoshin su. Haka kurum taji tana son sanin Wanene wannan R-Lema?
Nima biebee nace waye Rafeek Habib Lema??
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg🔟
CAIRO INTERNATIONAL AIRPORT
"Assalam Alaikum, that's my seat" ta dago fararren
idanuwan ta ta kalleshi tace "oh sorry" tare da mik'ewa ta rabe ya
shige ciki ya zauna itama ta zauna. Wayar shi ya ciro ya kira Alhaji Tijjani
Salam Baba gani nan cikin jirgi yanzu zamu tashi" dsga bangaren Alh yace
to ya an dace? Habibullah yace "Eh baba, zuwa karshen sati zasu iso"
Alh yace toh MashaAllah, Allah ya kawo ku lafiya Amin"
Sanarwa akayi jirgi zai tashi kowa ya sa seat belt dinsa,
duk suka yi yanda aka umarta, cikin mintuna kalilan jirgi ya fara yunkurin
tashi.
Runste ido ta kusa dashi tayi, da yazo daidai tashi ta yi
saurin dafa Habib tare da ririke mai hannu gam, ba yau ta fara hawan jirgi ba,
amma Duk sanda jirgi yazo tashi haka take tsintar kanta cikin tsananin tsoro.
Sai da Jirgi ya daidai ta a sararin samaniyya ta dawo
hayyacin ta, da sauri ta kalli Habib baki bude, tace "donAllah kayi
hakuri, i'm always like this duk sanda jirgi zai daga" Habib ya kalleta
baki bude, yace "dama kinajin hausa" ta harareshi cikin sigar wasa
tace "wai ma, ga zahiri ka gani"
Habib dai kasa magana
yayi, yana satar kallon ta. Kwata-kwata bata yi kama da bahausa ba, tafi kama
da larabawa, a hankali ya karance ta; Fara ce sol, mai siririyar fuska,
hancinta kamar fensir, tana da dan tsawo, sanye take da bakar Jallabiya ta nade
kanta da bakin gyale, kai duk yadda akayi ta hada iri da Larabawa. Tana sane da
irin satar kallon ta da yake yi, murmushi kadai tayi ba tace komai ba, ta ciro
wani novel daga cikin handbag dinta.
Habi dai ya kasa hakuri sai da ya tanka ta, yace "
Erhm, amma ke ba bahaushiya bace ba ko?" ta dan daga kai sama tarw da
murmushi tace "bahausa ce mana, bakaji hausa na radam ba amma meyasa kace
haka?" yace "anya kuwa ke hausa ce?" kila zama da hausawa ya sa
kika iya hausa, ko kadan bakiyi kama da hausa ba kinfi kama da balarabiya"
dariya takeyi sosai, tace toh Baba na bahaushe ne gaba da baya mama tace yar
kasar lebanon" Habib ya dan tafa hannayen shi biyu, yace "Ahap, ga
magana nan ta fito, kin dai hada jini da Larabawan" dariya tayi, haka suka
cigaba da fira har suka iso Aminu Kano
Airport.
Bayan sun gama Clearance ne suka fito wajen Airport din,
Habibullah yace "nan garin kike?" tace "aa, katsina nake"
Habib ya zare ido yace "Lah,ashe yar garin mu ce" yace toh zaa zo
daukan ki ne? Tace noo ai bama su san yau zan dawo na, i want to make it a
suprise" yace "that's nice, toh muje mu yi shatar motar chan" ya
fada y na nuna motar kwamkwasiya da sukayi layi a chan gefe, tace "kar ka
damu, i can take myself home" ya harareta ba tare da yace mata komai ba ya
ja trollyn ta ya yi gaba, bata da zabin da ya wuce ta bishi a baya tana murmushi.
Kafin ta isa har sun daidaita da da mai motar ya sa akwatin
ta a booth, Habib ya bude mata baya yace "Bismillah", ba gardama ta
shige baya, shi kuma ya bude kofar gaba ya shiga direba ya ja suka dau hanyar
Katsinan Dikko dakin kara.
Karfe 8 suka iso, Yace wani unguwa kikayi tace "GRA
Bayan gidan Govenor", ya juyo da
sauri yana fuskantar ta, yace ai unguwar mu ce, tace wai dagaske? Ya ce eh, to
wani gida kike?" tace gidan Alhaji Tijjani Masanawa ai nan Habib ya
hangame baki Yace u must be kidding me, Gidan Baba na kike? Itama da mamaki
tace "nifa bana son zolaya" yace dagaske ba wasa ba" shine last person
da nayi magana da shi a jirgi, Abokin baba na ne sosai, he's like a 2nd father
to me and my siblings" tace "banyi mamaki ba, its a small world
afterall, yace "haka ne but ya akayi ni ban sanki ba? Tace "da yake a
Cairo nayi College zuwa Masters dina, so ban fiye zama a Nigeria ba, ko na zo
banyin 1month nake koma wa" Habib yayi mamaki matuk'a yace wai ko kece
Aisha?" Tayi murmushi tace ya akayi kasan sunana? Yace ai na kanji baba na
waya dake, na taba tambayan shi wacece suke yawan waya?" Yace "kanwarka
ce Aisha, tana Misra tana karatu" a haka suka iso Gidan Alhaji Tijjani,
wani tangamemen Gida ne, har ciki direba ya shiga dasu.
Habib ya fito ya bude mata ya ciro kayan ta yace"
Shatu, Allah ya huta gajia ko?" sunan da ya kira ta dashi ya bata daria,
tace "wato ba zaka shigo ba? Ko daman labari ne kawai ka keyi?" yayi
darian shima yace mutum da gidansu sai an gayyace shi ciki?" karki damu
inaso naje gida na huta, zuwa da safe zanzo ma gaida Baba " tace to
shikenan, ta shige gida, shikuma ya koma mota suka fita daga gidan.
_Bibilicious Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg1⃣2⃣
Anas ya cigaba da cewa "Ka same su kace su baka hakkin
ka kana da bukatar su, duk yanda zasu so shawo kanka ka fandare musu ka bada ma
idon ka toka, duk inda suka bullo maka to ka bulle musu" Hafiz ya jinina
kai, yace "toh, bari zan gwada bayan bikin Yayan sai na bijiro musu da
bukata ta" Anas yace "bayan biki ai ya gama bushashar sa, yanzu ya
kamata kaje ka sake sa" Haifz ya mike yace "bari inje" Anas yace
Allah bada sa'a kar ka manta, sai ka nada ma idanuwan ka toka".
"Yadai Hafiz?" naga kamar bakinka akwai magana? Ya
akayi ne?" Habib ne ke tambayan Hafiz da tunda ya shigo dakin yake ta
kame-kame. Hafiz yayi ta maza yace
"Yaya, Gado na nake so a bani in rike a hannuna, a bani hakki na"
Habib cike da mamaki yace "Lafiyar ka Hafiz? Bakaji me baba Tijjani yace
ba? Sai kun gama Jamia za'a baku, Hafiz ya fandare ido yace "shidai a
bashi yana da buk'ata"
Habi yace "to shikenan Hafiz zan yi shawara da Baba Tijhani".
Hafiz ya dan yi ysaki yace "Yaya, Gado na ne ko? To
nace abani kayana ban son ajiyar, ina da hankalin da zan rike abu na, banga
dalilin yin shawara ba, tunda dai shi da kanshi ya kira a ka raba Gadon nan,
toh ni dai nace a bani kaso na"
Yanda hafiz yake magana ya ba Habib Mamaki, zuciya taci
Habib ya mike yace biyoni, ko kunya Hafiz be ji ba ya bishi, a waje suka ga
Zaid, da sauri ya taro su yace "lafiya? Yana ga fuskar ku ba walwala?
Habib yace "kaima biyo mu" ya fada motar sa ya bar gidan hanyar Bank yayi. Zaid da Hafiz mota daya suka
shiga, a hanya ne Zaid ke tambayan Hafiz" Bros, wai ya naga yaya haka? Me
ya faru? Hafiz ya dan tabe baki yace" ba fa abin da ya faru, kawai don
nace yaban Gadona a hannuna ba sai ya ajiye min ba, ni zan aje abu na da kaina
shine ka ganshi haka"
Cike da mamaki da takaici Zaid ke kallon shi yace
"Hafiz kasan me kake cewa kuwa? Me zaka yi da Gadon ka haka? Idan wani
bukata ne dakai ka sanar dashi, shi me iya baka ne ba tare da ka taba Gadon ka
ba, Haba danuwa na" da sauri Hafiz ya katse Zaid ta hanyar daga mai hannu
yace "in kai yaro ne, ni ba yaro bane, ina da damar da zance a bani hakki
na, idan kao ba za ka amsa naka ba, to ni zan amsa nawa, so please spare me the
lecture"
Kasa magana Zaid yayi har suka zo Safe din babansu, inda ya
ke ajiye kadarrorin sa, Tuni Habib ya haye sama, suka bi bayanshi, Cikin Lokaci
kalilan ya tattara duka Gadon su, da ma a kashe suke, ya kalle su yace
"tunda, baba ya rasu ban taba daukar ko sisi ba nayi amfani dashi, duk kudin da kuka ga na
taba to kudi na ne, hakkin gurin Aikina ba na Gado ba, to yanzu Hafiz ka bukaci
Hakkin ka, ni Musulmi ne na san hukuncin wanda ya danne ma wani hakki, nikuma
bana daga cikin masu dannewa mutane hakkinsu" ya tura mai wani dan safe
box yace "Wannan Miliyan hamsin da hudu(54) ne, a ciki akwai filaye 3 da
location dinsu, da gidaje 2 a garin Katsina" ya juya ya kalli Zaid yace
kai kuma ga naka hakkin Miliyan hamsin da--" da sauri Zaid ya katse shi ta
hanyar cewa "Haba Yaya? Me zanyi da kudin nan? Ni bank'i a sadakar da su
Allah ya Jikkan su Baba, ba abunda zanyi da su, shi da ya ga zai iya ai
Shikenan ka bashi hakkin sa" a fusace Zaid ya tilla ma Hafiz key din mota
ya juya ya bar gurin rai a bace.
Hafiz ya duka ya dauka key din motar da murmushi a fuskar sa
yace "Nagode Yaya, hakika kai uba ne a gurin mu,tunda har ka san Hakkin
dan Adam baka tauye ni ba, Nagode Allah ya bar Girma" mamaki ya hana Habib
Magana. Hafiz ya dauke Safe din ya fita.
Sai da ya kai Safe din Bankin da Baban su ya bude musu kafin
ya kira Anas a waya, tunda suka hadu da Anas, Anas ke faman kuran ta shi"
The multiple Millionaire, yanzu za a dama da kai, ina dukiyar? Hafiz ya dan
bata rai yace ba ruwanka da inda suke" Anas yayi daria yace to shin kai
filayen nan d gidaje me za kai dasu? Ai kawai kasa su a Kasuwa ka ci kudin su,
in yaso in Ka tashi mallakar Gida sai ka gina Uban uban su".
Da wannan huduba na
Anas Hafiz ya sa gidajen shi da filayenshi kasuwa, a ka siyesu a wulakance ba
tare da sanin kowa ba, Hafiz ya zama wani tauraro cikin abokan shi, yayi ta
musu bushashar kudi.
Baba Tijjani yayi fada sosai da yaji abunda Hafiz yayi, amma
ya fi ba Habib laifi akan biye mishi da yayi, Habib yace "Baba ya zanyi
dashi?, tutiya yakeyi Hakkin shi ne, ba wanda zai danne mishi, baba naga nima
wannan nauyi ne ka sa mun, shiyasa na sauke nauyin, shi Zaid da na mika mai
naahi kin amsa yayi yace ba abunda zai yi dasu, ina ga kar ka daga hankalin ka,
kowa yayi da kyau zai gani. Baba ya jinjina kansa yace "Allah shi
kyauta" Zaid "yace Amin".
Bayan Sati daya
Aka sha bikin Habib Iro Lema da Amaryar sa Aishatu Tijjani
Masanawa bisa sadakin Naira Dubu Dari. Biki ne wanda ya amsa sunan biki, ba a
tsawalla ba, ba ayi karya ba, ko lefe akwati 6 yayi a cewar Baba Tijjani
Albarkar aure akeso.
Ran da akayi dinner Hafiz ya taka rawar gani, don sai da
masu Kida suka san da zaman shi, don
dubu dubu ya dinga likawa, Suko sai kara kudashi suke suna cewa
"kanin ango hafiz mai naira" shi ko kanshi sai kara girma yake yi ya
cigaba da rawar sa yana ruwan liki. Da yawa cikin mata sun kyasa Hafiz don a
cewar sa yaro da kudi sai a bashi ya sha. Habib zaune a high table yana kallon
Hafiz na barin kudi. Hafiz ya koma wani abu daban, kamar ba kanin shi mai kunya
ba, amma ji lokaci daya ya fandare ya zama mara ta ido, ya tuna satin da ya
wuce inda hafiz ya sameshi a parlo yace "Yaya Ya shirye shiryen
biki?" Ba yabo ba fallasa Habib yace "Alhamdulilah Hafiz muna
tayi" Hafiz yace "Allah taimaka, yaya ga gudummuwa ta bikin ka"
ya ciro wani da case, ya bude mishi, sarka da yan kunne ya mika mishi, Habib ya
sa hannu ya amsa, Habib baki bude, yace Hafiz me zan gani haka kamar sarkar
Zinari? Yayi daria yace Zinari ce yaya, a matsayina na kanin ka shine na ga ya
dace na baka gudummuwa, ka hada a lefe" Habib ya bude baki da ya kara
kallon Sarkar, ya tsorata da lamuran Hafiz, yace Hafiz wannan sarkar da kake
gani Jiya da naje Siyayya a Shoprite a Kano na tayata, wallahi exact sarka,
kasan nawa nagani? 450,000. Tsadar ya hanani daukarta amma tayi kyau, naga dai
akwai Zinari a lefen da na sa shisa na barshi, Hafiz meyasa ka kashe makudan
kudi wurin siyan sarkar nan? Hafiz yayi dan daria yace "yaya kenan, toh
kare da kudin sa sai ya sha lahaula" so nake nima na taka rawar gani a bikin
yaya na mai sona, shisa na cire kudi har haka na siya maka, kuma ko da ya fi
haka zan siya, don su san cewa ba Tsiya a dangi Lema, saboda haka yaya
gashi" Habib yace shi sam ba zai amsa ba, Hafiz ya bata rai, yace don ba
maman su daya ba shine ya ke nuna mai wariya, da Zaid ya kawo mishi abu amsa
zaiyi, amanar da baban su ya bashi kenan? Nan da nan Habib ya rude
yace"haba Hafiz ya kake magana irin wannan? kasan da kai da Zaid daya kuke
a wurina" yace toh idan haka ne ka amsa, Habib ya amsa yace toh "Nagode"
Habib ya kai kallonshi kan Zaid da ke zaune a gefe yana
kallon mutane, shi ko dancing floor din be shiga ba, a ranshi yace Allah ya
shirya Hafiz. Haka aka gama taron biki aka kai Amarya Gidan ta da ke Layout.
(Amarya Aisha Allah bada Zaman Lafiya)
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg1⃣4⃣
Hafiz ya yanke hukuncin ziyartar Save din da daddare, haka
ko akayi, dare nayi wurin 8 ya san Yayan su na gida time din, ya wuce straight
Gidan inda Save din yake, da yake an san Hafiz dan Gida ne, kuma ba wanda ya
musu shamaki da shiga gidan ya sa mai Gadi ya wangale kofar Gate din, Hafiz ya
shiga da motar shi, Staright office din ya wuce, ya bude lockcode (LEMA)din ya shiga
hankalinsa kwance.
Wardrobe din ya bude ya ga Save's biyu sai kuma inda aka
cire nashi safe din, Irin Save dinshi mai kama da nashi ya jawo, aka sa enter
password, Hafiz ya hau chanki-chankan(guessing) passwords, ya sa;Lema, be bude
ba, wani tunani yazo mai, ai password din safe dinshi Hafiz Lema ne, kuma Yaya
Habib ne yayi setting dinshi, which means toh wannan Save din can either be
Zaid Lema or Habib Lema, bari ya fara da Zaid, cikin ikon Allah ya na typing
Zaid Lema safe ya bude, wani ihun jin dadi Hafiz ya sake, baiyi wata wata ba ya
kaushi kudin son ranshi, ya kulle yayi
locking ya maida komai yanda yake ya fita.
Bayan kwana 3 Hafiz ya dawo ya kara diban kudin nan, haka
Hafiz ya maida Save din Zaid Bankin kudin shi, da yan bukattunshi ya tashi ko
na abokan shi sai yaje Ma'ajiya(Save) din Zaid ya jida na jida, da abun yayi
kamari sai dai Hafiz ya dauke Save din ya kai gida, cikin Save dinshi ya juye
dukkan dukiyar da muhimmar takarddun daga Save din Zaid. Ya na tunanin ya zaiyi
da Empty Save din Zaid? Ina zai wurgar inda ba zaa gani ba?
Rafeeq da Rafee'ah
sunyi bulbul da su, kowa na sonsu, maman su na ta zuwa Aiki, da su take
tafia tunda tana da mai aiki, Soyayyahr su sai gaba takeyi da Habibinta.
Hold up ne ya tsaida Zaid daidai titin Kofar kaura,kamar
ance waiga gefe, Wani yake hangowa kamar Hafiz da wata babbar mata dake gaban
mota, daga baya kuma Anas ne zaune, Zaid yayi mamaki, to ko dai Mamar Anas ce?
Kai aa, in mamar Anas ce sai dai ta zauna bayan mota ko shi Anas din ya
tuk'ata.Gani yayi matar ta sa hannu ta shafi kumatun Hafiz, cikin Zaid ya
kada, Haka kurum zuciyar Zaid ya ki
aminta da ganin da ya ma su Hafiz, ya bi Bayan su da aka basu hannu.
Be bari sun lura dashi ba, don a hankali yake bin bayan su
har suka zo wani Gida da Hafiz ya siya don holewa da yan matanshi ya shiga yayi
parking, ganin wani mota a bayan su ya sa Maigadi barin gate din bude don a
zaton sa tare suke. Tun da Hafiz yayi parking motar nan suka fara watsewa da
wannan matar cikin mota, Anas kuma na kwankwadan Syrup duk sunyi nisa gun
aikata Sa6o.
Iya karfin shi ya shiga bubbuga gilashin mota, ji kake kwam
kwam!! A firgice suka dago, Hafiz ya tsorata, da sauri ya fito, idanuwan Zaid
suka kada sukayi jaa, da karfi yace "Haba Hafiz, me zan gani haka? Dama
harkar mata kake yi? Ji wannan matar a haife ta haifeka wlh, amma kaji
kunya". Hafiz dai ya kasa magana don kunya ya kama shi kamar kasa ya tsage
ya shige ciki, Anas yayi ta maza yace "Ji mana Zaid" Zaid ya galla
mai harara ya kalli matar da ke tsaye tana gyara tsayuwar rigar ta yace dallah
wuce ki ba wa mutane guri, ko a jikin ta tace "Fizboy my balance"
jiki na rawa ya ciro rafar dubu 1 ya bata ta sa a jiki ta mai blowing kiss,
Zaid ya bita da harara" ya juya a fusace zai bar wurin, da saurin Hafiz ya
rik'e hannunshi, yace "Zaid, i'm terribly sorry, Sharrin shaidan ne, yau
na fara, kuma iyaka ta kenan wallahi, Zaid ka yarda dani" Zaid ya kalle
shi shek'ek'e yace wannan kuma tsakanin ka da Ubangijin ka, shi zaka roka
gafara bani ba" da sauro Hafiz yace" Wallahi na bari, da ma ba halina
bane, kai ka sani, don Allah kar ka gayawa Yaya" Zaid ya kalli Hafiz, ya
ga hawaye kwance cikin idanuwanshi, ya bashi tausayi matuk'a, yace Allah shi
Kyauta ya shige motarshi ya tafi".
Anas yace "Fizboy, Zaid ya ga gurin kwanan ka, yana
kaninka amma ji yanda yake gasa maka magana kamar ka kashe wani, mtsww dole ka
dauki mataki a kanshi" Hafiz yace "barni da dan shegiyar, zanyi
maganin shi nan ba da jimawa ba"..
SATIN DA BAI WUCE BIYU BA.
Hankalin Habib yayi mummunar tashi da ya bude Wardrobe ya ga
ba Save daya, ya duba ya ga Save din Zaid ne babu.
Habib ya kwala wa
Securities kira cikin rudewa, suka zo a gurgurje, yace "Akwai wani baren
da ke shigo gidan nan ne?" Security
yace "ai Oga Gidan nan ba me shigar shi daga kai sai kannenka biyu, a rude
yace yaushe suka zo last? Yace " Oga Zaid yazo jiya, sai bayan Maghrib ya
tafi, Oga Hafiz kuma ya kusa 3weeks rabon shi da nan arean"
Habib ya fita da sauri ya shige motar shi, yayi gidan shi.
Tsaye suke a parlo suna ball shi da Rafeeq, Aisha ta fito
dauke da Warmers ta ajiye kan dinning ta kalle su cikin murmushi, tace Uncle
Zaid da danshi, wallahi ku ka fasa min Showglass sai kun biya ni, in banda
abunku wa ke kwallo cikin parlo? Zaid yace "haba Matas, don dai Showglass?
In mun fasa ni da boy dina muna da kudin sayen miki wani ai--" be rufe
baki ba Habib ya shigo kamar zai tashi sama. Aishatu ta tsorata, Zaid ya dauke
Rafeeq da sauri don kiris ya rage Habib ya ta kashi.
Aishatu ta matso da sauri, Daddyn Rafeeq me ya faru? Lafiya?
Yace "ina lafiya shatu? Banga Save din Zaid ba. Kai zaid ka dauki Save din
ka ne?" cikin rashin fahimtar abunda Yayan sa ke fadi yace "Yaya meye
kuma Save?".
Yaya har sai ka bata bakinka wurin tambayan inda Save din
Zaid yake? Ai shi zai dauki abunshi? Idan ba shi ba wa zai dauka? Duk suka
maida hankalin su ga Hafiz da yake shigowa parlorn, ya cigaba da cewa "
bros, ashe baka gaya mai ka dauko ba?"
Zaid baki ya sake galala yana kallon Hafiz, sai yanzu ya gane me suke nufi.
Ran Habib in yayi dubu ya gama baci, da karfi yace "Zaidu, Ya za ka min
haka? Idan kana da bukkatar Gadonka kamata yayi ka gaya min, ba wai kaje ka
dauka kai tsaye ba, haka kurum ka sa hankali na ya tashi?" Zaid cikin
rawar murya yace "Yaya, Wallahi ban dauka ba, hasalima ban san inda suke
ba" Hafiz yace "Ka fara jokes dinka ko? Jiya jiyan nan kace man kana
da bukatar Gadon ka na baka shawara ka sanar da Yaya" Zaid cikin bacin rai
yace "Kaji tsoron Allah Hafiz, yaushe mukayi haka da kai? Wallahi ban san
inda Save din yake ba Wallahi ban dauka ba" Habib yace "dallah rufe
wa mutane baki, mutumin banza mutumin hofi, karya za a maka?, yace "Yaya wallahi-- tasss kakeji, Habib ya
tsinke Zaid da Mari, ya shiga dukkan shi ba kaukauta wa, ni za ka tada ma hankali?
After all i'm doing for u? Dukkan shi yake ko ta ina, Rafeeq na ta tsala Ihu,
Aishatu ma kukan takeyi, da kyaur ta kwace Zaid hannun Habib ta turashi waje
tace "Ruga daki Zaid". Habib ya zube kan kujera yana maida numfashi,
yau yayi abun da be taba yi ba, bugun kanneshi,.
Ran Aishatu bace, ta daga kai don neman Hafiz, tunani takeyi
ina Hafiz yaje da Habib ya ke dukkan Zaid. Tsaye ta ganshi daga gefe, da alamun
yana gun a lokacin da Habib ya ke ta jibgar Zaid, In dai idanuwanta ba yaudarar
ta suke ba, to murmushi ne kwance kan fuskar Hafiz.
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg1⃣6⃣
A parlor ya iske ta ta ciro Latop dinta ta shiga yanar gizo,
tace "wacce Kasa kake da burin karatu, kumae kake so karanta?" Ya
danyi jim alamun tunanin yace "USA, ina son karantar Engineering".
Murmushi tayi ta fara searching Relevant Schools a USA; tace " zo ka gani Zaid, ga wani Havard
University Cambridge nan" ya matso, details din School da komai ta duba,
tayi naam da makarantar, shima haka ama ba laifi makarantar zaiyi tsada.
Nan da nan ta fara ma
Zaid processing, bayan Sati daya ta tura wani Yaron babansu da Zaid American
Embassy dake Abuja don neman Visa. Komai ya kankama, don saura kwana 2 tafiyar
Zaid Makaranta.
A ranar Habib ya dawo gida Bayan ya sada Hafiz da makaranta,
ya mai Wa'azin da ko kofar kunnen shi be shiga ba, Habib ya tabbatar mai da
cewa duk wata zai dinga jin Alert na shigo mai, Hafiz yayi godia Sosai.
Zaid ya zo mishi sannu da zuwa amma ko tanka shi baiyi ba,
Aisha tace ya yan makaranta? Yace "Hafiz dan Malaysia ana chan bawan
Allah, da zan taho harda kukan shi, ya ban tausayi". Aishatu tace "Allah Sarki, Allah ya bada
Sa"ar karatu" yace Amin.
Tace "Shima Zaid dai ya kusa tafiya" ya dan zaburo,
ina zai tafi?" tace "yo karatu mana a USA, ko nan zai tsaya ya
lallace?" Habib yayi tsaki, yace kinga abunda nake gaya miki ko? Shi ya
dauke dukiyarsa,in ba haka ba, waye zai biya mishi karatu a Havard University?
Aisha tace "nice nan,ni na dauki nauyin shi, zan tsaya mai har sai inda
karfina ya kare" cikin mamaki Habib ya kalleta yace "Ke Aishatu, ina
mai umartan ki da ki janye hannunki kan Zaid, tace ita sam, ita ta sa kanta
Shin ba kai kace ba ruwanka da duk wanda zai taimaki Zaid ba? Kaine dai kwabon
ka ba zaiyi ciiwo ba?Toh ni zanyi sponsoring dinshi, i'll endorse him, Deal
with it Habibullah! Ta fice ta barshi zaune da mamaki.
Kwana biyu ba zaman lafiya tsakanin Habib da Aishatu, Zaid
yayi takaici, don a ganin shi shine sillar faruwan komai, har ya sameta yace
"Aunty, tunda Yaya ya haneki da taimaka min, a bar maganan karatun nan
kawai, Allah ya biyaki". Tace sam Zaid, karatu kamar ka tafi ka gama ne,
i've spent alot on it, ba zan yi hasara ba, so make me proud, kaje kayi karatun
ka, ta mishi yan nasihu da waazi.
WasheGari Zaid ya je Gidan Baba Tijjani ya maj Sallama, Ya
dawo gidan yayan shi ya durfana gaban sa ya na hawaye yace "Yaya ka yafe min, kar kayi fushi
dani, kaine Ubana, kaine Uwata, fushinka kamar na Iyaye ne, Yaya kayi wa Allah
ka samin Albarka a karatun nan da zanyi"
Sosai ya ba Habib hakuri, shi yasan yana son kaninshi, amma
fushi ya rinjaye shi, a ranshi ya sa ya yafe ma Zaid, yace "tashi ka tafi
Zaid, Allah bada saa, a kula, know where you come from".
Rannan tafiar Zaid da
kyar aka banbare Rafeeq jikin shi, kuka yakeyi kamar ana zare mai rai, Ko
Rafee'ah da bata san komai ba sai da tayi kuka, Aunty Aisha ma ta koka.
4Years Later(Bayan Shekaru 4)
Abubuwa da yawa sun faru, cikin shekaru biyar nan, Ciki kuwa harda gama makarantar Hafiz da Zaid, ya
kamata ace Hafiz ya gama ya dawo gida tun last 2years saboda Course duration
dinshi 2and half year ne, amma shashanci da Iskanci ya hanashi dawowa, Hafiz ya
kware a fannin Chacha da harkar cocaine (Gambling) duk Malaysian Gambling
center sun san da zaman Hafiz, duk ya karar da kudin Zaid, kuma kullum shine
tambayan Habib kudi, gashi duk bayan Wata 5 yake zuwa Nigeria, abun ya damu
Habib amma bai yi magana ba.
Hafiz shine drugs, duk wasu kayan maye Habib ba wanda be
sha. Amma abun alajabi shine, hafiz beyi kama da mai shan ko da sigari bane.
Yanzu dai Hafiz ya talauce, baida kudin Chacha, baida kudin Cocaine, ga Bashi
ana binshi na wurin Gambling, wasu thugs ke barazanar daukan rayuwar shi, sunce
ya biya su, yace Yayan shi zai turo,
shiru sukeji don tunda ya ma Habib maganar kudi shiru kakeji, zaman shi
Malaysia baida wani amfani, Returning ticket dinshi yaje yayi renewing don zuwa
Nigeria, Ogan Yan Chacha ya had Hafiz da wani yaron shi don ya bishu Nigeria ya
taho musu da kudin su. Hafiz beyi gardama ba, don shima yana da bukatar kudi,
dole ko yazo Nigeria Alabasshi idan ya kara hada wasu kudadden ya dawo.
Tunda Zaid ya tafi USA ya fara karatun shi cikin kwanciyar
hankali, Kullum suna waya da Aishatu, Rafeeq da Zaid sun yi wani irin Shakuwa
kamar yana Nigeria, da ya dawo school har ya san ya bude datan maman shi ya
shiga Skype don suyi Video Call da Uncle Zaid, Rafee'ah tayi ta kuka kan Hamma
Rafeeq ya bata wayar amma haka zaiyi banza da ita ta yita tsala ihu har sai
Mami tazo ta amshe wayan ta bata ko shi Rafeeq din ya ga daman bata wayan. Duk
wata Aishatu na raba Albashin ta ta tura ma Zaid rabi, Habib kan kira shi su
gaisa, amma bai taba tura mai ko taro sisi ba itama Aisha bata taba tambayn shi
ba. Wata sa'in idan ba a ma Aishatu Albashi ba, ba ta da sukuni, ta dinga zirga
zirga kenan, ina zata samo kudi ta tura ma Zaid? Zaid ko yana fuskantar ta duk
da ba ta fito fili ta gaya mishi damuwar
ta ba ya kan fahimceta. Yace Aunty kar ki dinga damun kanki, zan sanu part time
job a nan ko da Cafe ne, zanyi serving as Waiter. "Waiter? kar ka sake
inji Zaid, kafi karfin nan, kar ka damu, i'll find a way to make money
kaji?" yace "naji Allah rufa asiri" Jin ta kawai yayi, ba zaiyi
kwance tana mishi komai ba, shima zai tashi don taimakon Kanshi.
Tun tafiar Zaid Shekara Biyar kenan be taba dawowa gida ba,
a ganin shi takura ne ga Aishatu ko kudin Jirgi matsala ne, shisa duk yanda taso yazo gida fir sai yaki
yace har sai ya gama toh gashi dai ya gama sai shirin dawowa.
BAYAN DAWOWAR HAFIZ.
Tunda ya dawo ya ke sak'e sak'en inda zai samu kudi, yaje
Warehouse be ga komai ba, da alamu Habib ya chanza ma'ajiya. Tunanin mafita
yakeyi, gashi ba zai iya tambayan Habib kudi ba. Wani tunani ya fado mai, da
sauri yayi murmushi.
Karfe sha dayan dare(11pm), bayan Yara sunyi bacci, Aishatu
ta dauke su ta kai dakin su, ta wuce dakinta ta tsala wankan ta, ta saka night
gown ta fito ta jawo kofar tayi dakin Mijinta Habib, da sallama ta shiga, yace
"Shatou na, har yaran sunyi bacci? Tace eh sunyi, Rafee'ah da rigima wai
sai dai kar hamman ta ya Kwanta a cinyana, Habib yayi daria, yace "ina
ruwan kishiyoyi, yauwa Shatou, dauko bargon dakin ki, jiya naji sanyi wallahi,
tace kamar akwai bargo a nan, yace "eh yayi k'ura, gobe zan bada a
wanke" tace "toh bari naje na dauko" ta juya ta fita a hanzarce.
Hafiz na ganin Shigewar Aishatu dakin Habib yasan ita da
fitowa sai gari ya waye, sadaf-sadaf ya shiga dakinta, drawern madubi ya je ya jawo be ga wani abun
dauka ba, side drawer ya koma ya bude, dubu biyu da dari biyu ya gani (#2200)
ya gani ya zare ya sa a aljihu yace ko sigari na sha. Yana jawo na kasan ya ga
wayam, kamar ance ya ciro dirowar ga baki daya, yana cirowa sai ga wani dan
case a kasa, ya ciro case din hannu na rawa, yana budewa ya ga wata
dankareriyar Saitin Sarka da yankunne, da abun hannu da zobe, tsaf ya gane
sarkar ce da ya siya ma yayan shi a matsayin gudummuwa lokacin bikin Aishatu,
ihun murna ya sake harda yar hamdalan shi, yayi daria yace "wannan shi ake
cema ja ya fado ja ya dauke" yayi sauri maida Drawern ya tura case din
cikin rigar shi ya mik'e don fita. Juya wan da zaiyi wa zai gani? Aishatu ce
tsaye kikam tana kallon ikon Allah hannayen ta kan kirjinta.
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg1⃣7⃣
Iyakar tsorata Hafiz ya tsorata, ga case rike a hannun shi
ba wurin boyo, amma da yake Hafiz namijin duniya ne sai yace "Aunty, ashe
baki kwanta ba" kallon kai dakata ta mishi, tace "meye a
hannunka?" yayi dan murmushi yace "Oh wai wannan? Sarka ne da yan
kunne da na ba Yaya Ajiya kwanaki na dauki kayana" baki bude take kallon
shi, tace "kai Hafiz kaji tsoron Allah, ajiya ka bashi ko kyauta? Ina cewa
kayi ya sa a Lefen sa, shine gudumuwar ka?, kasan daukan abun wani ba tare da
Izini ba Sata ne? Ya kalleta shek'ek'e, yace "Sata? Ta ina ya zama sata? I
bought it da kudina, don na dauki abu na shine sata? Its mine anyways. Tace
" its fine kai ka siya, i knw that, don ya gaya min, Hafiz Ka riga ka
bashi, shi kuma ya bani, ko shi baida iko akan shi, its no longer
yours". Yace "Madam, its mine,
noone can get it from me, not even your husband, saboda haka sai da safen ki,
idan kin isa ki gaya mishi ya zo ya amsar miki". Ya wuce ya barta tsaye.
Aishatu da dafe kai, wai Hafiz ke gasa mata magana haka? Duk
Habib ya ja mata, da be amsa ba tun farko, da wannan ranar ba tazo ba. Tabbas
ta san duk cikin Sark'ok'in ta ba wanda ya kai na Hafiz? to ya za tayi tunda ya
bukaci abin shi? A fili tace "Allah
shi kyauta" Zuciyar ta ta ke waswasin gaya wa Habib? Toh tace mishi me?Ta
haddasa fitina tsakanin su? Balle shi Habib dake matukar son Hafiz, ko Zaid be
so haka.
Kuma bata son wani abu ya kara shiga tsakanin ta Hafiz, don
tsakaninta da Allah tsoron Hafiz takeji, yanayin sa na bata tsoro, a ranta ta
kudiri cewa ba zata gaya ma kowa ba, idan yayi wari sa ji, ta dauki Blanket
dinta ta datso kofar ta, tayi dakin mai gidan ta.
Da Sassafe Hafiz ya je kasuwa don saida Sarkar nan,
kasancewar ta tsaddadiyar sarka tun shekara biyar da suka wuce, da aka auna
Kadan ne babu cikin Miliyan, Naira dubu dari tara da goma(910).
Hafiz ya cire 650 ya ba yan Malaysia ya rike sauran da
niyyar zai je Lagos Gambling kila ya ninka kudinshi so biyar (Allah ya shirya
ka Hafiz.)
Matashi dan kimannin shekaru 22 yayi sallama a kofar parlon
Habib da ke zaune shi da iyalan sa, Habib ya dago kai tare da amsa Sallaman,
kallon shi kawai yake yi yana son tuno fuskar, Aishatu ce ta mike tace
"Zaid?" Rafeeq ya sake Ihu da karfi, da gudu ya nufe shi ya je ya rungume
shi, shi ko Zaid ya daga shi sama yana "Oyoyo my boy" i've missed you
so much, look at you" Rafeeq dan shekara 5 yace "welcome home Uncle
Zaid" yace "Thanks son, ina baby Rafee'ah? Cikin hausan shi da be
fita Rafeeq yace gata chan tana fushi wai ka daukeni" Zaid ya sauke shi
yace "Ohh my baby come here" da gudu ita ma tazo ya dauketa, suka ida
shiga parlorn, Sai da ya durkusa har K'asa ya gaida Aishatu da ke ta faman jera
mishi sannu da zuwa, kafin ya kalli Yayan shi yace "Barka da Rana
Yaya" Habib baki sake kamar soko yake kallon Zaid, kwata kwata ya chanza
kama, kamar wanda aka ma wankan Engine yayi Jazir yayi kyau. Suka gaisa, kafin
kace kwabo Aishatu ta cika shi da abinci.
Kamar daga sama Hafiz ya fado Parlorn, da Zaid ya ci karo,
kamar wanda yayi Gamo da Aljan yayi saurin juya wa, ashe Habib na kallon shi,
yace "Hafiz ina zaka, baka lura da danuwan ka bane? Ba yanda zaiyi dole ya
dawo.
Wani murmushi ne kan fuskar Hafiz mai wuyar fassaruwa, yace
" Hello brother, its good to see you again, welcome home"
Zaid ya hadiye miyau, ya shiga tunanin baya, komai ya dawo
mai sabo, ya sake hade wani bakin miyau, be san murmushin da Hafiz keyi na meye
ba, a ranshi yace Allah ka min tsari daga Sharrin me sharri" a fili kuwa
yace "Thanks, its good to see you too".
A year Later(Bayan Shekara 1)
Zaid ya gama bautar kasar shi a shekarar shi ta 23, Hafiz
kuma a Shekara 24, Zaid Ya zama wani Azabbaben Guy, tun yanzu mata ke kawo
mishi hari, Aishatu ta mishi maganan Masters yace, sai yayi settling. Rafeeq da
Rafee'ah na ta zuwa school, da aji daya Rafeeq ya fi Rafee'ah, Dukkan su Allah
yayi musu Baiwa na Kokari...
"Kutumar Uban chan" Hafiz ya lailayo wata ashar,
wa nake gani kamar Anas? Anas da ya koma wani Giant, Giya ta hura shi yayi
daria yace "ni ne fa" Hafiz ya diro daga kan mota suka rungume juna,
yace ashe "rai kan ga rai"? Rabo na da kai tun kafin in dawo Nigeria,
kuma na yi ta kiran wayan ka baya shiga, gashi bansan gidan ku bare naje(wai
duk abun nan, Hafiz bai san Gidan su Anas ba, What a fool😆). Anas yayi
daria yace " wallahi na koma Porthacourt da zama" chan nake
sana'a" Hafiz yayi shewa "da kyau maza, wannan wace irin sana'a ce da
yayi transforming dinka lokaci guda? Duk ka koma wani Don? Anas yayi darian yan
bariki, yace " abun sirri ne" Hafiz yace haba mutumen, kar ka min
haka, ka fada mim hanyar samu nima in karu, Anas yace "Zaka iya?"
Hafiz yace koma menene zan iya, indai har zan samu kudi" Anas yace "haka ne, kasan sai da kudi
ake neman kudi, akwai kudi gurin ka? Hafiz yace "aa babu, kamar nawa ake
bukata?" Anas "yace half million(#500,000). Hafiz yayi jim, sannan
yace Ba matsala, i'll find a way, like always."
Rana Dubu na Barawo....
Babu inda Yaya Zai ajiye Safe dinshi da wata kadarar sa,
indai ba a bank ba, toh defintely a Office din kusa da dakin Baccin su ne,
tunani Hafiz ke nan, ya zaiyi ya shiga ciki ba tare da kowa ya ganshi ba? Anas
ya kira don shawara, Anas yace "kar ka damu, ina da master key din da zai
iya bude ko wani kofa, kawai dai bari sai daren, sai na zo muyi operation din
tare.
Da daddare misalin 12:30 na dare, Anas da Hafiz basu sha
wahalan shiga Personal Office din Yaya Habib ba. Suka shiga neme nemen, Hafiz
ya jawo wata yar durowa, sai ga wata tamfatsetsiyar Agoggo Swatch ta fado,
murna ya hau yi, Drawer na biyu kuwa wani Safe ne a jikin tare da kwado, Hafiz
yace "Anas look what i've found, it got a small lock" Anas yayi daria
yace "worry not, i gt a small key" ya sa dan karamin key, tsaf kwado
ya bude.
Wurin bude Safe suka ji gam, insert password ya nuna musu,
Hafiz yayi murmushi, yayi typing, *Habib Lema* lock ya ki buduwa, ya yi typing
*Habibullah* incorrect password, yayi tsaki ya yi typing *Habib* a nan warning
alert ya fara, Anas yace "meye matsalar? Dama baka san password din
ba?"
Cikin barci yaji Alert mai karfi, a firgice ya tashi don ya
jima da kwantawa, ya kunna bedside lamp, ya duba gefen shi ya ga Aishatu na
barshi, still Karan na kara yawa, wayar shi ya shiga lalube, don a zaton shi
Alarm ne, duk da beyi tunanin yayi setting Alarm ba, Ya duba ya ga ba wayar
bace, ya dan fara bubbuga Aisha don Karan na kara yawa, ta tashi tana
mutsitsika ido, "yadai Daddyn Rafeeq?" yace tashi"ki kashe Alarm
din nan na wayar ki" cikin mamaki tace "Alarm dai"? Ta kalli
Agogon dakin taga 12:40am, tace kai "Aa, ban sa wani Alarm ba".
Habib ya Sauko daga
kan Gadon, nan yaji karar ta wurin bedside drawer ne, ya dan matsa gurin.
Zuciyar shi ta ayyana mishi *Brief case*Da sauri ya nufa Brief Case dinshi, don
ba tantama *Warning Alert* din Safe din shi ne.
Da sauri ya bude
pincode din ya dauko wani dan karamin Machine kamar dan Ipad, Aishatu da dawo
kusa dashi, Habib ina tunanin ba mu kadai ke gidan nan ba, ka hanzarta kiran
Polisawa, yace Aishatu whoever this is, he's among us, in ba haka ba, wa ya san
ina da office cikin Gida?.
A Zuciyar shi, ya ce Zaid ne, aiko zai dauko mummunar mataki
kan Zaid, yace "ba sai na kira police ba, i can handle this, idan nace
miki Zaid na da Halin banza bazaki yarda ba, bari na nuna miki proof" wasu
danne danne yayi a jikin machine din sai ga Fuskokin Hafiz da Anas sun bayyana,
suna ta fama da saka incorrect Passwords. A hankali Habib ya furta "Hafiz?
No it cant be" Aishatu ko batayi mamaki ba.
"I dont know where the problem is, amma for sure Yaya
sunayen mu yake sa as passwords, misali kaga zaiyi naming password after the
owner, kamar ka ga da na dauki Safe din Zaid, karon farko na saka Zaid lema
Safe ya bude, toh ban san mesa wannan yaki budewa ba, na saka Habib, na sa
Habibullah duk sunki budewa, could it be
possible ya sa Sunan First Son dinshi?" Rafeeq? Yes thats it! We are rich
bro, password din is Rafeeq"
Habib najin Haka ya zabura a guje yace Shikenan Aishatu ya
gano Password din, Da Karfi Habib yace *Hafeeeeeeez*!! Sai da Gidan Ya amsa.
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg1⃣8⃣
Ihun da Habib yayi ne ya tashi Zaid da Mdaga bacci, da sauri
ya fito suka fito daga dakin baccin shi,
yayi cikin Gidan don ya san tabbas ba lafiya.
Hafiz a kidime yace " Akwai Matsala" Anas yace
"mu ware kawai" Hafiz yace "aa its too late, lets just act
smart" daidai nan Habib, Zaid, Aishatu suka shigo dakin.
Zaid ya damke Anas, Habib kuwa bai yi sanya ba ya chakumo
wuyar rigar Hafiz yace "What have you turned yourself to? A monster? A
heartless, selfish person? Me ya sa ka dauke Safe din Zaid? Bayan kowa an bashi
Kason shi? Ka k'ulla mai sharrin shi ya dauka, Wannan wani irin cin Zali
ne?" Zaid ya kalle su cikin rashin fahimta, yace "whoa!, wani Safe aka
dauke nawa? Hafeez cike da borin kunya yace " I dont know what You're
talii about, let me go" Habib ya kai mai nushi a baki, ya ja wuyar Rigar
shi har gaban TV din Office din ya kunna, ya kara jan shi har gaban Safe
din ya saka Password din, Safe ya budu,
dan karamin security camera da ke jone da Safe din Habib ya danna, sai ga
fuskokin Hafiz nan da Anas tunda suka fito da Safe din, duk abubuwan da suka
fada sai da suka gani kuma suka ji kamar a film, Zaid ya dinga maimaita
Inalillahi wa ina ilaihir rajiun, Be son sanda ya sake Anas ba ya nufa Hafiz
cikin zafin nama, Anas na gannin haka ya arta a guje. Zaid na zuwa ya daga
hannu ya faska ma Hafiz mari har kala 2, yace "how dare you Hafiz?"
dama kai ka dauki Akwatin nan kace nine? Ka sa Yaya ya tsane ni? Ka sa ni cikin
Halin Kunci? Hafiz me na maka? Ni da kace ka na son kudin wallahi zan mallaka
maka halak malak, amma sai ka bi ta bayan Gida, Hafiz i wont forgive you "
Hafiz ya fashe da daria cikin borin kunya wacce aka ce da
hauka ake nadeta, yace " *So what? Now that y'll know my deepest secret,
what are you going to do? Ehh? Ya kalli Yayan shi what are u going to do Habib
Lema? Hand me over to the police? Go on you never cared dama, ka kira min
polisawa su tafi da ni, kaga ko ba wani Abu bane don dan kishiya ya tura
kaninsa gidan kaso(jail)*."
Zaid yace "Kar ka damu Hafiz, ai daga nan Police
station kayi, naga you are so eager ka ganka behind bars(bayan kanta.) Hankalin Habib ya tashi ba zai taba tona
asirin Gidansu ba, hada Hafiz da police kamar tona ma marigayi mahaifinsu asiri
ne, Habib ya kalli Zaid yace "Zaid, so kake Hafiz ya biya ka kudi da
kaddarar da ya satan maka?" Zaid yace "ni ba abunda zanyi dasu,
Burina Allah ya ji kan mahaifa na, ya ji kan yanuwa na" Habib yace
"Madallah, let him go" a tare
Zaid da Aishatu sukace "what?" Habib yace Hafiz is our Family, kar mu
tona asirin junan mu, mu taya shi da Adduan shiriya" Zaid be tanka ba ya
bar office din, Aishatu ta bi bayan shi, Habib ya kalli Hafeez cikin sanyin
murya yace"Jeka kwanta its late" Hafiz kunya da tausayi suka lullube
shi, ya sa hannu cikin aljihun shi ya
ciro Agogon Swatch din da ya sata, ya mika ma Habib yace "da a ce baba na
da rai, he'll be very oroud of you Yaya" habib ya sa hannu ya amshi Agogon
ba tare da yace komi ba, shi ko Hafiz ya sauka kasa zuwa dakin shi.
Cikin dare Hafiz ya tattara kayan shi tas, ya ciro wayar shj
ya kira Anas, Anas a tsorace ya dauka yace "hello, matsoraci kana
ina,?" Anas yace kaii kaji yanda hanji na suka kada, na mugun
tsorata?" Hafiz yayi dan tsaki yace "kai ni zo ka dauke ni ina nan
ina jiran ka" Anas yace wa? Ba dai ni ba, bari ma turo maka Escaley
kawai" cikin mintuna kadan Escaley ya kira Hafiz yace mishi yana waje,
Hafiz ya kwashi kayan shi da kyar ya fita waje, Escaley ya taimaka mishi, Mai
gadi na tsaye yana kallon ikon Allah, farar takarda Hafiz ya ciro ya ba mai gadi, yace ya ba Yayan shi ko Zaid
da safe, me gadi yace "Oga Hafiz ina zakaje da daddaren nan, 2 ta kusa
fa" be amsa shi ba ya shige mota Escaley ya ja motar.
Tare suka dawo daga Sallahr Asuba, tun a hanya ba wanda ya
kula wani, Zaid fushi yake da yayan shi kan abun da ya faru da daddare, Habib
kuwa ya san dole ran shi ya baci, don ba a kyauta mai ba da be dauki wani
hukunci kan Hafiz ba, Zaid ba zai gane ba, be san halin mutane ba, ana iya cewa
don Uwar su ba daya da Hafiz bane ya tura shi prison, Amma zai mishi bayani
idan ya sakko. Suna shiga Gidan mai gadi ya ciro takarda ya mik'a ma Ogan shi
Habib yace "inji Hafiz, jiya karfe 2 ya bar gidan nan" hannu na rawa
Habib ya warware takardar, Zaid har yayi gaba ya dawo don yana son jin me Hafiz
ya rubuta a wannan wasikar. A bayyane Habib ya fara karantawa, ga abun da ya
rubuta nan ;
"*I know i'm a disgrace to this family, which is why i
left you, na barku, zan shiga duniya, kar ku neme ni, ku mance kuna da wani
danuwa me suna Hafiz, ba zan bari ku kara gani na ba, ku Shafe Hafiz Lema daga
babin rayyuwan ku, saboda Hafiz Lema doesnt exist, Enjoy your lives without me
brothers"
Ba Habib ba harta Zaid sai da hankalin shi ya tashi,
tsakanin danuwa da danuwa sai Allah, Jini ba wasa bane, nan da nan Zaid ya fara
hawaye, da gudu ya shige daki Habib ya bishi a baya, Zaid ya dauko wayar shi ya
shiga neman layin Hafiz sai da ya mishi missed calls nawa kafin ya dauka, A
dake yace Ya akayi ne Zaid? Zaid na kuka yace DonAllah Hafiz ka dawo, kar ka
barmu, Wallahi na yafe maka, ka dawo, nd i promise we'll be like Nothing wrong
has ever happened, donAllah, i need You. Hafiz ya fashe da dariya, yace
"You dont need me oo, idan na tsaya zan cigaba da yi muku barna ne, gwara
nayi nesa daku, kar ku sha wahalan nema na, don ba za ku taba binciko ni
ba" Zaid ya fashe da kuka, Habib yayi saurin karban wayan, ya kara a
kunnen shi, yace "Hafiz ka saurareni" Hafiz ya katse shi, yace
"Yaya kar ka bata bakin ka, i've decided, be Happy brother kafin yace wani
abi Hafiz ya latse wayar. Habib ya shiga neman layin yaji swtiched off ashe
Hafiz fito da Sim card din yayi ya tauna a bakin shi ya zubar.
_Bayan Shekara Sha Biyar_ *(15 Years Later)*
Gidan Alhaji Habib Lema cike makil da mutane , da Alamu Biki
akeyi, Hajia Aishatu na hango zaune kan Gado cikin wata tanfatsetsiyar Leshi,
kamar yarinya yar shekara 20, sam girma be nuna a jikinta ba, shigowa akeyi ana
mata Barkan an daura aure lafiya, wasu mata suka shigo suna fadin "ina
Uwar Ango take, taje ta fito mana da Amarya?" ta tashi tana daria, tana
fadin "Ni da kaina?" suka ce
" ke fa da kanki Maman Zaid tunda da bakin ki kikace Zaid ba kani bane,
d'a ne" tayi daria ta nufi inda aka tanada domin Amarya da kawayen ta
Amare, ta shiga da Sallama suka amsa tace ince dai kun gama kimtsa min Amarya
ta? Duk sukayi daria, Amarya Safiyya ta sunkuyar da kanta, Aunty Aisha ta
nufeta ta dago kanta, tace "MashaAllah, Safiyyah kinyi kyau, ku muje Filin
Launcheon din, an tattaru Amarya kawai
ake jira"
Ango Engr Zaid Lema Suka shigo filin launcheon da Abokan
shi, İnda aka tana da domin su suka
zauna, Amarya ma aka rakota har gurin
Angon ta, Bayan Aunty Aisha ta bude taro da Addua ta ma manyan Baki sannu da
zuwa ta koma ta zauna kusa da Mijinta Alhaji Habib Lema.
Dj ya kunna kida gida ya kaure da sauti, gudu yake yana
bangaje mutane, babban burin shi ya ganshi a filin rawa, Maalesh na kwala mai
kira kan ya bar gudu ya ki, har hularshi ta fadi, Maalesh yace "ka ga
hular ka ta fadi, ka tsaya ka saka" ina samm bai ji ba. Sanye yake da kaya
komai iri daya Da Ango Zaid wato farin Shadda Kaftan mai Malummalum, yana zuwa
Filin rawan ya wani ci burki, ya fara kallon kowa one by one, ya juya ya kalli
Mamin su ta girgiza mai kai alamun kar yayi,
ya kashe mata ido daya(wink), Abban su kuwa murmushi ya mai, Ya kalli
Uncle Zaid Ango, ya daga mishi gira alamun go ahead haba kamar wanda aka sa ma
battery, ya fara takunshi daidai da sautin kidan, abun be mishi ba har sai da
ya cire Malummalum dinshi ya wulla ma Maalesh ya cigaba da rawan shi yayi gaba
yayi baya. Ango Zaid yace ma amaryar shi "kinga mutumin ki na cizgar rawa
ko?" da yake ba kallo take yi ba kanta a kasa yake tace wanene? Zaid yace
"waye in banda RAFEEQ?"
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg1⃣9⃣
Amarya ta dan daga kai taga tabbas Rafeeq ne ke wannan
chashewar, wuri ya dauu sowa sabida Rafee'ah ta tashi cikin takun ta ta biyo
Rafeeq filin rawa tana mishi like, shi ko sai rawa yakeyi iya karfin shi. Sai
da Zaid ya mishi alamun ya isa kafin ya tsagaita.
MC ya fara gabatar da shirin Biki, Hajia Aishatu ta bude
taro da Addua, Rafeeq ya bada tarihin Ango, biki yayi biki, anci an sha, an
gwangwaje, Rafeeq da Rafee'ah sun taka rawar gani, shima Ango ba a barshi a
baya ba don sai da Rafeeq ya sashi rawan dole, akayi hotuna, sukayi Family
Photo.
Washegari aka daure aure, aka kai Amarya Gidan ta da ke
Kaduna U/rimi, da yake chan Zaid yake aiki. Part daya aka ware ma Rafeeq a
gidan Zaid don Zaid da Rafeeq kamar abokai suke, ba za ka gansu kace Kawu da
dan shi bane.
Rafeeq dan dangi ne,duk inda ya gifta sunan shi kawai zakaji
ana kira, yanuwa da abokan azziki, manya da yara, kowa Rafeeq, tabbas Rafeeq
yana da farinjini, ba don komai ba don shima he's a simple somebody, ba ruwan
shi da zabe, yace ina yi da wannan ba nayi da wannan, aa kowa nashi ne, yana da
son mutane, da son wasa, ya ja wannan tsokana, ya ja wannan tsokana, maza da
mata, bashi da kyamar talaka. Rafeeq fari ne, bai ciki tsawo ba, bai cika
gajerta ba, dan daidai, be da kauri sosai, kyakyawa ne ajin farko, har friends
dinshi na mai kirari da ''all ladies eyes on Rafeeq'' duk budurwa mai ji da
kanta ta na so a ce da ita budurwar R-Lema, saboda ya hadu, Arzikkin baban shi
be sa shi girman kai ba ko kadan, haka fa yake a makaranta, kullum suna
Cafteria shi da Abokin shi Mahmud Maalesh, Maalesh abokin Rafeeq ne tun
Secondary School, Abotan Maalesh da Rafeeq ne ya sa Iyayensu ke zumunci, idan ka
ga Mami da Mummyn Rafeeq zaka zata yanuwan juna ne, Maalesh is his partner in
crime, idan sunyi laifi Uncle Zaid ke hukunta su, don ba sa jin magana, duk
wani party sai sunje sun sha rawa, ba sa shaye-shaye, ba sa bin mata, amma
yanmatan su sunfi 50, don shi Rafeeq kafin yace yana so to an riga cewa ana
sonshi, Irin Matashin nan ne wanda be da wata matsala a rayuwa, kowa na shi ne,
kar kuyi zaton Rafeeq be mayar da hankali a karatunshi, to ba haka bane, Duk
Department din su na BioChemistry, ba kamar Rafeeq, Lecturers kance, "idan
akwai abun da yafi 5point, to tabbas Rafeeq zai buge shi" irin su ne ake
cewa "Always ahead of the Lecturers" saboda kokari, Allah ya ba
Rafeeq k'wak'walwa, both ilimin Addini da na boko, a shekaran shi na 16 ya
sauke AlQurani mai Girma ya kuma shiga Jami'a, Yanzu haka yana da shekaru 20
cifcif kuma bana zai gama Jami'a.
Rafee'ah kuma tana karantar Sociology tana aji 2. Ba su fiye
shiri da Rafeeq ba don ita shiru shiru ce, shi ko yayi ta tsokanan ta, Rafee'ah
kyakyawa ce, bata fiye son magana ba, amma indai Rafeeq na gida dole sai ya
sata magana da yawan surutun shi da tsokanam ta da yake yi, tun bata biye mishi
har ta fara biye mishi, da ya mata take ramawa, idan kuma abun yafi karfinta,
sai taje tana ma Mami kuka, mami kuma ta ma Rafeeq fada, hakan ba zaisa gobe ya
kuma tsokanan ta ba.
Gidan Habib Lema, gida ne da aka ginata cikin So, Aminci da
yardan juna, suna matuqar son junan su, ba su da Matsalan komai, Mami(Hajia
Aisha) ta tsaya tsayin daka wurin tarbiyantar da yaran ta bisa tafarkin Addinin
musulun ci, tun suna yara Uncle Zaid ne Discipline Master, idan sunyi laifi shi
ke hukunta su, Shiyasa Suka tashi da son junan su (Wannan Kenan).
Daga sama Mami taji ana "Assalam Alaikum" ta bude
idanunta a hankali don a gajiye take tun bayan biki, ta dan bude murya ta amsa
sallaman tare da cewa "ku hawo saman please" Suka nufa sama, su biyu
ne, kana ganin su kasan uwa ce da diyarta, diyar ba za wuce shekara 17 ba, a
bakin kofa suka iske Hajia Aisha, tana ganin ta fadada murmushin ta, "Saude
kece anan? Sai da muka gama bikin zakizo?" Saude tace "Ayyah madam,
wallahi naje gida ne, shiyasa banzo biki ba" "bakomai ai, wannan
diyar ki ce? Kafin kace wani abu yarinyar har ta zube kasa tana kwasar gaisuwa,
Mami ta dago ta tana kallon ta, wani irin kama taga yarinyar nayi da Rafee'ah,
tace what's ur name? Yarinya tayi murmushi tace "Sunana Aneesa" Wow
nice name, sannun ku da zuwa, ku shigo" suka shiga ciki, kafin kace meye
wannan Mami ta cika musu gaba da kayen ciye-ciye, suna ci suna fira jefi-jefi,
Saude tace "bakowa a gidan sai ke?" tace "eh wallahi, ni kadai
ce, duk suna kaduna, tunda aka kai Amarya basu dawo ba, Saude tace "Ayyah
Allah basu zaman lafia" tace "Amin"
Saude Secretary din Hajia Aisha Lema ne a Office, watan ta 6
kenan da fara aiki a office din Matar Habib Lema, tana da kwazo wurin aiki,
shiyasa Hajia Aisha ke ji da ita. Six months back ne ta kawo CV dinta da qualification dinta na NCE, office din Madam
Lema.
Wurin interview ne suka bata tabbacin ba sa daukar masu NCE
sai masu Degree, ta dinga kuka wai a taimake ta, mijin ta ya rasu, ya barta da
diya daya, ba halin ciyar da ita suna cikin hali na kuncin rayuwa, yanda take
kuka taba interviewer din tausayi, yaje ya sanar da madam din su, madam ta nemi
ganawa da Saude, ta bata bayani, itama taji tausayin ta, tace "Madam ki
taimake ni, kamar yanda Allah ya taimake ki, you are a mother, kinsan irin son
da uwa ke ma diyarta, Miji na ya rasu ya barni da diya daya, dangin shi sun
kwashe Gadon, ta tsaya a Secondary, ki taimake ni ki bani aiki da zan kula da
diyata" Hajia Aisha ta ja numfashi, sosai Saude ta bata tausayi, tace
"can you be my Secretary?" ai ko nan Saude ta zube ta na godia, tace
tana so ta gode Sosai harda kukan murnan ta" washegari ta fara aiki as Madam's
Secretary, Saude akwai kokarin aiki, da zasu tafi Hajia Aisha ta shiga Dakin
Rafee'ah ta tsinto ma Aneesa kwancen kayan Rafee'ah, ta cika su da abun arziki.
Bayan Wata Daya
Gaba ki daya suke zaune a Babban parlorn Habib Lema, Uncle
Zaid na fira da Uwar dakin shi Mami, Rafee'ah na kusa da Baban ta tana karanta
mishi newspaper, daga gefe kuwa Rafeeq ne ke ba ma Aunty Seema(Matar Zaid
Safiyya, sunzo ne) labarin yanmatan shi na makaranta da na Unguwa, tana ta
daria, da kagan su kasan Happy Family ne wanda basu da damuwan komai da kowa.
Wayan Alhaji Habib Lema yayi ringing, Rafee'ah ta tashi ta dauko mai kan
sidestool, ta amsa ta sa ma babanta a kunne, "*Hello* *Yaya*? Dam gaban
Alhaji Habib ya buga, ya mik'e tsaye cikin kidima, a hankali yace "Hafiz,
kaine? Zaid da Mami suka mik'e tsaye suka nufo Alhaji da jikin shi ke rawa, ya
kasa cewa komai, Zaid ya amsa wayan ya sa handsfree yace "Hello?"
daga dayan bangaren aka ce "Hello Brother" Zaid yace "Hafeeez,
is this you brother, where are you?" karbe wayan akayi daga hannun Hafiz akace
"Hello This is Secret Service Agency Lagos, Hafiz Lema's been Jailed
10years ago, he's completed his Sentence, and is fined 500usd, come to the
Agency for more details". Dif ya kashe wayan.
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣0⃣
"Inalillahi wa ina ilaihir rajiun" duk suke fada,
Alhaji Habib ya zauna ragajab kan kujera ya dafe kanshi da hannuwan shi, tunani
yake me Hafiz yayi haka da aka kulle shi for 10years ba? Zaid yace yaya
"meye abunyi?" Habib ya hadiye miyau yace "Zaid, a siyo ticket
mu wuce Lagos din kawai, Zaid,yace "Yaya ka bari ni zanje Lagos din gobe
da safe" Habib yace shi sam be San wannan ba, tare zasu tafi, nan da nan
Zaid yayi waya Chanchangi Airlines ya siya tickets biyu.
Shiru sukayi kamar anyi mutuwa, Rafee'ah ta yanke shirun
tace "Abba wanene Hafiz?" Abba ya kasa magana sai Uncle Zaid yace
"Yaya na ne, you were too little when he left, i dont think ko Feeq zai
ganeshi" Rafeeq yace "na tunashi but i can't remember anything about
him" Uncle Zaid yace yeah u were all young then" duk sukayi shiru,
kowa da abun da yake sakawa a zuciyar sa, tunanin su daya, me hafix yayi a ka
kulle shi har tsawon shekara 10?.
Lagos
Karfe 9 na safe Uncle Zaid da Alhaji Habib na Secret Service
Agency (SSA), bayan long process aka sa da su da wani Oga, tambayoyi ya musu na
Alakar su da Hafiz, Habib ya bashi amsa da "mu yanuwan sa ne, ni yayan
shi, wannan kuma kanin shi" Ogan ya dauki wasu files guda biyu ya mika ma
Alhaji Habib, ya amsa hannu biyu ya bude, hotuna ne na Hafiz da wasu 6, Zaid ya
gane daya daga cikin su, abokin Hafiz nr wato Anas, a cikin hoton aka ga
Boma-bomai,Bindigogi da wuk'ak'e, cikin su ya juya, Habib ya bude dayan file din, paper ce doguwa, ya shiga karantawa, Hafiz
was an accomplice to Armed Robbers. Hankalin Habib ya tashi, ya fara hawaye,
Zaid ya amsa ya karanta shima, kanshi ya girgiza cike da takaici. Oga yace
"toh sati 2 da suka wuce ne ya cika Shekarun da aka diba mishi, an ki
sakin shi ne sai ya bada 500usd, mun ta tamabyan shi wa zaizo bailing dinshi,
yak'i magana, da ya ga bamu da niyyar sakin shi ne shine ya bada numbern ku, Zaid yace
"yanzu 500usd za a baku sai ku sake shi?" Oga yace "eh"
Zaid ya danyi guntun tsaki ya sa hannu cikin aljihun shi, ya ciro rafar dubu 3
ya dora ma Oga kan table, mutumin yayi murmushi yace "Sir we dont do it
this way, u go to the bank and draft it to our Account" Zaid ya dan daga
murya yace "you should have said that at first, u think we have time for
this? Habib ya kalli Zaid yace "Calm down Engr" Mutumin yace
"unless you'll pay here the change will be mine, you know 500usd is
approximately to N250,000, and this is 300k" Zaid ya mai tsawa yace
"shut the fuckup, take d goddam money and get us our Brother" Mutumin
yayi daria ya mike tare da kallon Alhaji Habib, yace "i see your bro has
guts, i'll get ur brother now" ya fita.
Alhaji Habib yace "Zaid, kayi hakuri, muke nema gurin
su, dole mu kwantar da kan mu" Zaid cikin fushi yace "yaya rabu dasu,
iskanci ne, ji fa yanda yake magana, matsiyaci, kudi ne matsalan shi"
Habib yace "ayi dai hakuri" duk sukayi shiru.
Turo kofa akayi, Habib da Zaid suka mik'e tsaye, idon su kan
kofar shigowa, Ogan ne ya fara shigowa Hafiz a bayan shi, Hafiz yayi bak'ih duk
kyaun nan ya disashe, ga wata uwar k'asumba ya ajiye, duk yayi ba kyan gani,
Rige rigen zuwa gunshi Zaid da yayan shi sukayi, Hafiz ya fashe da kuka, suko
ba su damu da yananyin da yake ba suka rungume shi suna hawayen suma. Da kyar
hafiz yace "ku gafarce ni yanuwa na, na san ban kyauta muku ba"
Alhaji Habib yace "shhh, Hafiz not now, lets get outta here"
Suka nufa hanyar fita, Zaid ya watsa ma Oga harara, shi ko
dariya ya bashi don yaga Zaid ya dauki abun da Zafi, yace ga Kayan shi da aka
amsa kafin a kulle shi, Zaid yace "ka jika ka sha an bar maka" sosai
Officern yayi daria, yace "till we meet again ko" Zaid yace
"ganinka ba Alheri ba, ba Amin ba" ya fita shima.
Drivern Office din Lema textile Company Zaid ya kira, within
some minutes ya hallara Agency din, ba jira suka shiga, Golden Hotels suka
nufa, Hafiz ya shiga dakin shi, yafi 1hour yana wanka, yana fitowa ya ga Wasu
riga da Wando da Zaid ya siyi mishi, ya dauka ya saka yaci abinci yayi Sallah.
Bayan sun huta Driver ya sake zuwa ya dauke su, yayi Airport dasu, don yau suke
son wuce wa. Bayan mintuna kalilan jirgin su ya tashi, Cikin Awa daya suka iso
Kano ta dabo. Kafin suje masauki sai da suka biya Barbers Corner don a ma Hafiz
Aski, Tsaf hafiz ya fito da kyau, don yini dayan da yayi ya fara kyau.
Washegari driver ya dauke su sai Katsina ta dikko dakin kara.
Tana tsaye tsakar
Gida tana jiran isowar su, don tun da suka shigo KT Alhaji ya kirata yace sun
iso, ga su nan karasowa. Rafeeq da Rafee'ah na school, Mota na shigowa Haraban Gidan gaban Hafiz ya
bada Hinqim, komai ya dawo mai sabo, a ranshi yace "it all started
here" Sannu da zuwa Aisha take ta faman yi ma Hafiz, harda hawayenta,
Hafiz duk ya koma wani sukuku, be sakin jikin shi, ta gabatar musu da abinci,
kadan Hafiz yaci, yanda kuka san bak'o sai rab'e rab'e yake tayi. Alhaji Habib
ya lura dashi yace "ka sake jikinka Hafiz dis is your home" Hafiz
yayi murmushin takaici, yace "Yaya, nasan duk kuna da miliyoyin tambayoyin
da kuke so ku min, kuna so kuji yanda na tsinci kaina a kurkuku" Habib ya
katseshi yace " Aa Hafiz, abunda ya wuce ya riga ya wuce, kar a maida
hannun Agogo baya, muyi addua Allah ya tsayar nan kawai" Hafix ya girgiza
kai yace "Aa yaya, dole ku san me ya faru, dole kusan irin rayuwan da nayi
bayan bari na Gida" Zaid yace "Gaskia ne, muna sauraronka" Hafiz
ya fara labarinshi kamar haka:
Shekaru Goma da suka gaba ta(Last 10years)
Muna barin Katsina, Straight
dauki hanyar Porthacourt, ni da Abokaina 2, Anas da Eskaley, mun kwana
mun yini a hanya, har muka isa wani gida, Gidan Thug Gang (Sunfi kama da
kauraye )din su Anas ne Amstrong da
Willy, Kwanan mu 2 a PH Anas suka nuna min wuraren bude idanuwa, kamar Night
Club, Gambling Center, Da Gidajen giya, duk na kware a harkokin nan.
Ba mu rufe Sati 2 ba naji Armstrong na gaya ma Anas su
shirya akwai Operation yau da daddare gidan Commisioner, yace "okay we'll
prepare" nace da Anas wani irin operation ne wannan? Anas yayi daria yace
"my guy, ba zaka gane bane, share kawai" Nace "haba Anas, kar ka
mun haka, ka fada min mana" yace "kagane, Amstrong ce min kawai yayi
zamuje iperation, amma be gaya min takamaimin me zamuyi ba" Nace
"then i will go with u" Anas yayi dariya yace "no u cant, yi
shiru kar ma Armstrong ya jika" ashe Armstrng na jin mu, yace "he's
right you cannot come with us boy" boy ne sunan da Armstrong ke cemin
kenan tun zuwan su PH, a ganinshi ni karamin dan iska ne, cikin fusata nace "i am not a boy"
Armstrong yayi murmushi yace "show
me, today get ready and be prepared" Anas yace "Oga i dont think this
is a good idea" Armstrong yace "its time we train him".
3:00am
Gidan Commisioner of Youths suka kai ma farmaki, duk suka
hade kan mutanen gidan cikin babban parlor harda shi Commisioner din. Hafiz aka
bari a Cikin mota, da bindigar Katako, bayan Armstrong ya buge mai warning, kar
ya bar bakin mota, no matter what, don zasu iya fitowa at anytime, Anas,
Eskaley, da armstrong suka shiga ciki, duk a zaton shi sauran ma bindigar
katakon ne, duk a zaton shi kudi kawai zasu amsa suyi gaba, sai labari ya sha
bambam da yaji karar bindiga, sosai ya tsorata, Be ankara ba yaji Siren din
motocin police, Hafiz ya kidime ya fito daga motan da gudu, charap police suka
kamashi da yake Ajebo ne be iya gudu ba.
Su Eskaley kuwa sai
fafatawa suke da jamian tsaro, suna harbin junan su, nan take a ka harbe su 3,
ko shurawa basuyi ba suka mutu, Iyalan Commisioner kuwa ba wanda ya mutu, sai
dan shi da Anas ya harba a kafada, an garzaya dashi Ambulance.
Abun da ya faru shine, Ashe Akwai diyar Commisioner da take
wayan dare(NightCall) ta bayan dakin ta taji ana cewa "Idan ya kawo
gaddama kawai mu harbesu mu shiga mu nemi golds a dakun nan su, yanzu kawai mu
nemi hanyar shiga cikin gidan" da gudu ta diro a kan gado ta fita da gudu,
straight dakin babanta tayi ta gaya mai Abun da taji, da sauri ya danna waya ya
kira Jami'an tsaro ya sanar da su, suka bashi tabbacin gasu nan zuwa, da sauri
ya nufa dakin matar shi da babban danshi don sanar da su, kafin kace meye
wannan yaji an dora mai bindiga a kai, Anas ne yace "idan ka motsa sai na
tarwatsa kanka" Commisioner ya sandare, Eskaley da Amstrong suka shiga sauran dakuna suka fito da duka
mutanen gidan, suna tambayan kud'adde ne Police sukayi surrounding dinsu duka
har suka kashe su Anas.
Hafiz ya cigaba da cewa" ko bincike ba a tsayayi ba aka
maka ni kotu, kasancewar ni kadai suka kama jikina yayi sanyi, na fada musu
gaskia, na amsa laifi na, Kotu me adalci ta ya yanke min hukuncin 10years a
Jail+ hardships da 500usd Fine, to kunji abunda ya faru dani bayan bari na
Gida. Allah sarki danuwa mai dadi, daga Alhaji Habib da Zaid kuka suke barin ma
Aisha da tun farkon Labarin Hafiz take kuka. Sai da sukayi me isar su duka
kafin Hafiz ya duk'a har k'asa ya nemi gafarar su duka, Habib yace bakomai
Hafiz Allah shi kyauta gaba, Allah ya sa kuma ka koyi darasi, duk wanda ya bar
gida gida ya barshi. Hafiz yace "InshaAllah Yaya, ba za ku sake kamani da
wani laifin ba", yace "toh Allah yasa" ya juya ya kalli Aunty
Aisha yace "Aunty kiyi hakuri da duk abunda na miki, da sauri ta katse shi
tace baka min komai ba, Allah ya yafe mana" Hafiz ya kalli Zaid zai yi
magana, Zaid ya tareshi da murmushi yace "Welcome home Brother".
(Muma munce Welcome Hafiz Lema, Lubie maitafsir tace
"Dont cause any trouble" Aisha Yau kuma tace "Allah ya sa ba
tuban muzuru kayi ba😐", nidai Biebee nace ku biyoni kuji rayuwan
Gidan Lema bayan dawowar Hafiz Lema)
_Bibilicious
Biebee
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣1⃣
Rafee'ah ta shigo parlorn da gudu ta na kukan Shagwaba ta
fada kan baban ta, Abba yace "Rafee'ah baby me ya sameki?" ta turo
baki tace "Abba ba Hamma bane kece min Jaki head" Zaid ya fashe da
daria, yace "kema ki dinga k'ok'ari kamar Feeq dina, kin tsaya kan
makeup" Abba ya harareshi yace Zaid mind your own bussiness" Zaid ya
sa wani darian, Rafee'ah ta kara tunzura, ta sake saka wani kukan, Mami tace
"Yi shiru babyna, ki barni da Rafeeq da Uncle Zaid dinku, zanyi maganin
su, ta mak'e kafada, nidai ba Uncle Zaid dina bane, na Hamma ne"
"Shikenan baki gaida Uncle Hafiz ba, ko ba ki ganshi bane"
Zumbur Rafee'ah ta tashi, ta nufa Uncle Hafiz da ya kura
mata ido, yana murumushi, fadawa kanshi tayi, tace "Welcome Home Uncle
Hafiz, we missed you" ya shafa kanta yace my preety princess, nayi missing
dinku duka, na dawo, ba zan sake nesa da ku ba" ta rungume shi, yace
"ina Hamman naki?" ta turo baki, sai yaje dropping Ya Mahmud a gida,
ke waya dawo dake? Tace shi ne fa, chan baki layi ya sauke ni, harda cemin Jaki
head" Zaid zaiyi daria Rafee'ah tace "ntoorrrh, ai dai Uncle Hafiz
dina ya fika kyau". Duk sukayi daria. Hafiz yace "wani level kike
yanzu?" tace level 2 Sociology" "uhm nice, meye CGPA dinki? Da
murna tace 3.70, tafi Hafiz ya fara, yce "thats my girl, so smart,keep it
up kinji?" Zaid yayi gyaran Murya yace "talking about Smart, kun tuna
min da wani matashi, wanda ko shekaru 20 be cika ba, wanda idan ka ganshi da
malamai zaka zata lecturer ne, hwanda lecturers suke using dinshi to shine,
CGPA dinshi 4.98(is it possible?) wanda ake ma lakabi da 'Face of Science
department' wannan ba kowa bane illa: Rafeeq Habib Lema" Rafeeq da ya
shigo parlorn yanzu yayi bowing yana daria, thanks Uncle, Zaid yace "dont
mention son" Rafee'ah ta tabe baki, Rafeeq yaje ya rungume Hafiz ya mishi
sannu da zuwa, Hafiz yace "me Princess ta maka ka sata kuka?" Rafeeq
yace "pri mene? Princess din daddawa?ai wannan she's no princess, she's
Jaki head, tayi scoring 10/15 a Assingnment" Hafiz ya harareshi, yace
"Wallahi ka fita idona, tayi kokari sosai, dont mind him primcess, kinyi
k'okari kinji" Rafeeq yace Uncle Zaid, gaya musu if an Assignment is to be
marked over 15, what would be R-lema's Score? Zaid ya gyara murya yace 19/15.
Daria suka fashe da, har Hafiz, banda Rafee'ah da tabe baki tace "whatever
", tasan idan ta biye ma Uncle Zaid, da Hamman ta kuka zatayi, haka suke
ganging up a kanta kullum ko Mami ba ta isa ta sa su su daina ba, ta mik'e ta
shiga ciki. Abba da Mami sai daria suke tayi suna kallon draman team Feeq da
team Fee'ah.
Rayuwan jin dadi, So da kaunar Juna akeyi a Gidan Habib
Lema, Zaid ya koma bakin aikin shi, Rafeeq da Rafee'ah suna ta zuwa makaranta,
Hafiz kuwa Mami ta mishi processing aiki a office dinta, yau ta shaida mishi da
Monday zaifara zuwa aiki.
Sallam tayi, Rafeeq da ke zaune a parlorn ya dago ya amsa,
da murmushi a fuskan shi, Sannu da zuwa, Aneesa ta ma kanta mazauni akan
kujera, ta gaida shi tana wulla idanuwa, Rafeeq yace "Ammata ya kike?
Feeyah kike nema? Aneesa tayi fari da ido, "noo Mami nazo gaidawa"
yace "Ayyah, Mami kuwa na Office" tace bakomai ai" nan suka
shiga fira, abunku da masu surutu biyu, sai labari sukeyi ba sa gajia, ya
tambayeta wani school take? tace "zata sake WAEC da JAMB ne, this
year" har indomie suka dafa a kitchen,
cikin lokaci kalilan Aneesa ta kamu da son Rafeeq, ni dai nace indai
Rafeeq ne, zaiyi pieces da zuciyanki.
Aneesa na nan har Maalesh yayi dropping Rafee'ah daga
School, Kallon rashin Sani Rafee'ah ta ma Aneesa. Aneesa na ganinta tace sannu
da zuwa sis" Rafee'ah tace "yauwa sannu" tana kallon ta, don
somehow taga suna kama da Aneesa, Rafeeq yace Aneelurv, bari na miki
introducing wannan, She's Jaki head, Diyar House Help din gidan mu ce"
Rafee'ah ta bata rai tace "Hamma mana, wallahi sai na gaya ka da Uncle
Hafiz" Rafeeq ya dinga daria, Aneesa tace share Yaya Rafeeq, kowa ya san
kin fi karfin diyar house help, muje ciki ki rage kaya" Rafee'ah ta harari
Rafeeq suka yi ciki ita da Aneesa, sai da ya bisu ciki, don idan Rafee'ah na
gida baya barinta, yana son tsokanan ta. Tun daga rannan, Aneesa ta maida Gidan
su Rafeeq gidan zuwanta, tana shishige musu, don Aneesa akwai ta da son 'yayan
masu kudi, ga shi son Rafeeq ya kamata, yana hankalce da ita, bata san Rafeeq
ba irinta yake so ba, a cewar shi son yara yan Secondary School ChildAbuse ne,
kuji dan rainin wayau, ko shi din nawa yake?.
Tazo shiga parlorn, shi kuma ya fito hannun shi dauke da
Plate din abinci, suka ci karo, Shinkafar da ke plate din ta zube, Aneesa tayi
saurin durkusawa tana tattarawa, yace "Oh Sorry, wallahi ban gani ba"
Hafiz ya dago kai don ganin wacece da muryan nan, defintely ba Rafee'ah bace,
Haka kurum sukaji gaban su ya fadi dukkan su, suka kura wa juna ido, k'okari
Hafiz yakeyi ya tuno inda ya san fuskar nan, don defintely ya san wannan
fuskar, amma da yayi la'akari da wannan ba zata wuce shekarun Rafee'ah ba, yace
a ranshi kila kama ne, to da wa? Oho!. Yace "karki damu, zan sa a
share", tace "thanks" yace ke kawar Rafee'ah ce? tace "noo
yaruwata ce" a ranshi yace no wonder suke kama, dama ina tunanin inda na
san fuskar ashe don kamar da sukeyi ne da Rafee'ah nake ganin kamar na santa,
kila dangin Mami Aisha ne. Da haka ya wuce part dinshi ita kuma ta shige cikin
Gidan.
"Attention Everyone, this Is Hafiz Lema, yau zai fara
aiki a wannan Company din,zaiyi Serving as General Manager, ina fatan zaku
bashi hadin kai da goyon baya kamar yanda kuke bani" Director kenan Aisha
Lema ke sanar da Co-workers dinta kan sabon Manager da aka samu, ta nuna ma
Hafiz Office dinshi, ta shige nata. Waya ta kira reception, take tambaya har yanzu
Secretary ba ta zo ba?" aka ce "eh bata zo ba" tace ina ne manta
immediately ta na zuwa" yes madam.
Da sauri ta shigo Office din Madam, tace "Madam kiyi
hakuri, Wallahi-" Hajia Aisha Lema ta katseta ta hanyar daga hannu, tace
"Issokay, dama ince miki anyi sabon GM, kije kiyi filing credentials
dinshi, and kiyi documenting Account
dinshi, and ki bashi Constitution of his Office" Cikin ladabi Secretary
tace "yes Ma" ta amsa files din daga hannun Madam, ta karanta Sunan
da ke jiki 'Hafiz Ibrahim Lema' a tsorace ta dago kai ta kalli Madam dinta,
hajia Aisha na lura da ita tace "yadai, Secretary?" ta k'irk'iro
murmushi tace "bakomai", ko kina mamakin Sunan ne? Ba abun mamaki
bane, Hafiz kanin mijina ne, Yayan Zaid ne, yayi dan tafia ne sai yanzu ya
dawo. Murmushin da be kai zuci Secretary tayi, tace "i'll go ahead"
ta fita, tayi kan desk dinta.
Hannu bibiyu ta dafe kanta, tunani ya cika mata k'wanya,
Hafiz lema ya dawo? Hafiz lema zai bata mata shiri, Hafiz lema zai wargaza mata
duk wani Plan din da zatayi kan Lema Family, kaii ba zata yarda ba, tana da
advantage kan shi, she'll use it against him, zumbur ta mik'e ta harhada files,
tayi Office din GM.
Sai da ta k'wankwas kafin ta shiga da Sallama, a yayin da
Hafiz ke waya da Zaid, be dago yaga ko wacece ba. Wuri ta samu ta zauna tana
karantar Hafiz, Ya Chanza, yayi kyau ya kara haske da sanin da mishi a da.
Hafiz ya katse wayar
ya juyo da kujerar sa, da murmushi ta kalleshi tace "Good Morning
Sir" zumbur Hafiz ya mike cikin firgici ya nuna ta da yatsa yace
"Saudah" tayi murmushi ta mik'e tana fari da ido tace "Don Hafiz
Lema feezoboy, its good to see you again" Hafiz ya dan sausauta murya yace
"Sauda what are you doing here?" ta daga kafada tace "i work
here" yace "Sauda what are you upto?" tace "nothing much, i
just want to give our daughter a proper life?" a rude Hafiz yace
"What?, me kike cewa? Tayi darian 'yan duniya tace " Our love bore
fruit, da ka tafi ka barni, ka barni da cikin diyarka, yanzu kuwa ta zama 'yar
budurwa cos she's 18 now"
Darian takaici Hafiz yayi, yace ke Saudah, na sanki da
duniyanci, i wont let you blackmail me, ko kina so kice min ko a lokacin da
nikadai kike tarayyah, kar kiyi tunanin na manta ko ke wacece, ina sane
dake" tace "nasan zakayi tunanin hakan, amma ina da proof Aneesa
diyarka ce" ta ciro wayarta fa lalubo hoton Aneesa ta mika mai, tace
"gashi duba kagani, duk wanda yaga wannan ya san Jinin Lema ce, don ba ta
da maraba da Rafee'ah Lema. Hafiz cikin rudani ya amsa ya kura wa Hoton Aneesa
ido, ya gane ta, itace ya gani a gidansu kwanakin baya, tabbas wannan gudan
jinin shi ce.
Ya dago kai yace "tasani?" tace "aa bata sani
ba, she believes you are dead" yace "Sauda, gaya min gaskia, what are
u upto? me kike shirin yi?" tace "its simple, So nake Habib Lema ya
aureni, and you going to help me da taimakon ka zan shiga Gidan shi matsayin
matar shi"
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣2⃣
Daria Sosai Hafiz yayi, yace "i know you are stupid,
but bansan stupidity dinki ya shahara har haka ba, kina son Habib Lema ya aure
ki? A mafarki ko? To bari kiji, ko a mafarkin, Habib Lema ya fi karfin ki,
Habib Lema ya miki fintikau, Tsakanin ki da shi nesa nesa" tayi daria ta
mik'e tace "Hafiz, Sai na Auri Habib Lema, i am asking u now nicely to
help me, u know what i am capable of right? Bani da kyau, kuma dole ayi abu
yanda nake so".
Zuciya taci Hafiz ya zo ya makure mata wuya ya buga ta da
bango, k'akarin amai ta fara, tace "Feezo, ka sakeni DonAllah, you are
hurting me" Yace Saudah "
listen to me close, wannan shine warning dina na farko kuma na karshe, Stay
away from my family, Habib be miki komai ba, idan akwai wanda ya miki wani abu,
to nine, ni zaki hukunta, dont let my Family into this, they didnt do anything
wrong, ina rok'on ki Saudah" ya karashe magana yana mai sausata murya,
tare da sakinta.
Ta gyara tsayuwar rigarta, tace "nifa ba wani mugun abu
nace zanyi ba, Allah ne ya jarabbeni da son shi, kamar yanda ya taba jarabbata
da sonka, amma son da na maka, ko rabin wannan be kai ba, ina son Habib Lema,
Ina ganin zan rasa raina idan be aure ni ba, so ka kwantar da hankalin ka,
Aurena kawai nake so yayi, ba wai ina so na tarwatsa muku Family bane, zaka
taimaka min, ko don Diyarka" ta na kai wa nan ta yi hanyar fita, Hafiz ya
dinga kiranta amma bata tsaya ba.ta fice.
Har aka kusa tashi
office Hafiz be samu sukuni ba, tunanin maganganun su da Sauda yayi tayi, Wai
yanzu shi ke da diya? Shegiya? Wacce aka haifa ba ta hanyar aure ba? Ya akayi
haka?.
Shekaru 16 da suka wuce (16 Years Back).
Food is Ready
Restaurant Sabon Gari Kano.
A lokutta da dama idan Hafiz da Anas sunzo yawon banzan su a
Kano, wannan Gidan suke zuwa don cika Cikin su, da rabon kudin da suka ciyo
wurin Gambling(ChaCha). Wuri ne 'wanda yan iska da yan tasha ke cin Abinci,
Shagon Maman Sauda ne, Sauda da kanwarta Maryam suke serving abinci, idon su
bude yake don suna hulda da yan tasha, har Sauda na ba da Jikinta don Kudi, Tun
randa Allah ya fara kawo Hafiz Shagon maman Sauda, Sauda ta kamu da son shi
bilhakki, ta fada ma mamanta, maman ta tace "ke kinga Saude, wannan yaro
akwai kudi jikin shi, ki tatso mana shi kawai, ki bar wani batun soyayyah
kinji? Ta turo baki, tace ni gaskia mama son shi nake, har ina so na aure shi,
Maman tace "aure? Babban magana" a haka Saudah ta kudurta a ranta ko
ta halin k'ak'a sai ta auri Hafiz Lema, don gayen ya hadu ta kowane fanni.
Anas ya Kalli Hafiz yace "Kaga Saudah sai signal take
maka ko? DonAllah ka bata chance, kullum muka zo Kano, bata da wani sukuni, sai
neman attention dinka, kalleta fa She's not bad, da kyanta, da dirin ta, ta
hadu ko ta ina" Hafiz ya buga tsaki yace "na sani mutumin, nifa da
zata zo in huta da ita in biyata da na fi kowa jin dadi, amma ita sam wannan be
gaban ta, wai aure take so muyi, kai har wani abu take so muyi wai shi
Soyayyah" Anas ya tuntsire da daria yace "duk a zatona Sauda ta waye
ashe da sauran ta, wake Soyayyah yanzu? Ai kawai mata yan hutu ne, a huta dasu
a biyasu kowa ya ware, banda jakkan ci har ta na so ta aure ka" "bar
banzar" inji Hafiz.
Karaf kan kunnen Saudah, tazo ta zauna kusa da kujerar
Hafiz, tace "Anything for u" mikewa tayi ta ja hannun shi, shi ko sai
binta yake, wani daki ta ja shi. Anas ko
sai babbake wa yakeyi da daria.
Bayana Wata 3
Kai ya banga gilmawar mutuniyar taka ba, Hafiz yace ga
Maryam chan bari in kirata, "Maryam" tazo tace "sannu, baka ga
Aunty Sauda ba ko?tana Gida Mummy ta rufeta, wai tayi Ciki kuma kaine ka mata
cikin" wani irin Ashar Hafiz ya lailayo, yace "na ma uwar ta ciki? A
gidan uban wa? Da ke da saudan da Uwarku food is ready kun kwashi kan--- Anas
yayi saurin taran numfashin shi, yace "Haba my man, kaga ka fara janyo
hankalin mutanen nan, yanzu za suyi mana caaaa, nan ne Maman Sauda tazo, ta
sassauta murya don bata son mutane su ji su, tace "Hafiz, zo mu shiga daga
ciki, akwai magana" da kyar Anas ya ja Hafiz cikin dakin. Maman Sauda ta
fara magana, tace "Hafiz, dama jira nake kazo kano, don na san zakazo,
Sauda na dauke da ciki wata 3, tace cikin kuma naka ne, Hafiz ya zaburo yace
"bangane ciki na bane? Ni kadai nayi hulda da ita, ni so daya na taba
hurda da ita, so taje ta nemo uban cikin ta ba ni ba" Maman sauda tace
"aa Hafiz, kar kace haka, Allah ya jarabci sauda da son ka, tunda ta fara
ganin ka ta kilace kanta don kai, kuma ta tabbatar min da cewa cikin ka
ne" Hafiz yace ba fa zam yarda ba, yarinya taje tayi ciki zaa ce ni na
mata?" Mamar Sauda tace "to ko zaa bari ta haihun ne, sai aje a gwada
jini?" Anas yace Sam hakan ba zai faru ba, ai abun be kai ga haka ba, kudi
kawai zaa baku ku cire, kai feezo ciro kudi kawai, ka bata ta murje shege, idan
aka bari ta haife cikin Yawah go dey, kasala go burst" Hafiz ya danyi wani
tunani yace nawa zai isa a cire ciki? Mamar Sauda taji maganar kudi, tace 250,000.
Hafiz ba ji komai ba ya rubuta mata Cheque din dubu dari uku. Suka bar gurin,
tunda daga ranar be sake waiwayan Food is Ready Restaraunt ba.
Abunda ya faru bayan nan;
Maman Sauda tayi tayi sauda suje a zubda cikin nan, sauda ta yi k'ememe
tace wallahi ba zaa zubar ba, tana son babyn ta, a cewar ta, da an zubar da
cikin nan duk wani burin ta na auren Hafiz zai ruguje, Abun da zata haifa kadai
ne zai sa Hafiz ya aure ta.
Bayan kankanin Lokaci Maman Sauda ta rasu sakamakon ciwon
cikin da tayi rana daya, ko kwana bakwai baayi ba Sauda ta saida gidan Abinci
suka hada kayan su ita da kanwar ta suka bar garin, suka nufa Wudil wurin
dangin baban su, da suka ganta da ciki sai tace ai tayi aure mijin ya rasu,
dangin sunyi mamakin auren Sauda ba da sanin su ba, amma ba suyi mamaki sosai
ba don sun san cewa uwar su Saudan ba kirki ne da ita ba.
Lokacin haihuwar Sauda nayi ta haifi diyar ta mace, Ba su ko
kara ganin Hafiz ba ko abokin sa Anas, diya dai taci suna Aneesa, haka Aneesa
ta tashi gata nan dai, Sauda ko ba binciken da batayi akan Hafiz ba amma ta
kasa gane komai game dashi, ta sa ba dan Kano bane zuwa yake, amma ta kasa gane
takamaiman garin da yake, haka ta hakura da binciken shi, har ta manta dashi.
Bayan 15 years
Aneesa na da
shekara16 ta gama Secondary Sch din GGS wudil, don ma mamarta na mata jumping,
don Aneesa na da Girman Jiki sosai, idan kaganta zaka zata irin yan matan
Jamian nan ne. Aneesa shagwababiyar yarinya ce, ta samu daurin gindin Mamarta
da Auntyn ta maryam, acce take kira da Aunty Meemah, sai ahunda takeso akeyi,
ta taka duk wanda ya so kawo mata cikas.
Sauda na kitchen taji ana kiran "Habib Ibrahim
Lema" a TV da sauri ta fito ta k'ura ma Tv ido tana kallon wanda aka kira
da COO (Chief Operating Officer) of Lema's Machinery Company. Tsaf ta karance
shi, tabbas wannan jinin Hafiz ne Baban Aneesa, Habib na kama da Hafiz Sosai,
amma yafi Hafiz komai, ta fada a ranta, ta aiyana ma ranta, ta kudurta a ranta,
ta ma kanta alkawarin Auren Habib Ibrahim Lema, ko ta halin k'ak'a don yanzu
tafi karfin Hafiz Lema.
Asuban Fari ta ma Gidan bokan ta na kan tudu Sammako, ta
zaiyane mai bukatun ta, boka yayi daria yace Saude kin debo mai Zafi. Tayi
daria tace "ina sane, shiya sa na zo don ka gaya min koma don Abun ya zo
min da sauki"yace gaskia ne, nan boka ya zaiyane mata komai game da Habib
Lema, da Iyalan sa, Har Hafiz dake lagos kulle sai da aka shaida mata, komai
bokan kan tudu ya gaya mata game da Family din Habib Iro Lema. Tayi daria tace
lokaci yayi da zan tarwatsa Happy Family din nan, tana dawowa Gida ta shirya
yanda zata yi komai tun daga farkon zuwan ta Katsina, ita da diyarta don Meema
na makaranta a nan Wudil, Tana zuwa Katsina ta nufi wurin Aikin Aisha Lema, ta
samu karbuwa gunta kuwa, toh gashi abu zaizo mata da sauki tunda Hafiz ya dawo,
ita da bata sashi cikin list dinta ba, amma tinda har ya dawo, komai zai zo
mata a sauk'ak'e zatayi amfani dashi ta cimma burinta.
Wannan shine Labarin Hafiz da Saudah, da kuma Musababbin
zuwan Sauda Katsina, to ko Allah na bata ikon auren Habib Lema baban Rafeeq?
Nidai nace wane ita tayi kishi da Mameen mu Aisha? Ku biyoni don jin yadda za'a
kaya.
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣4⃣
Zaman Lafiya akeyi a gidan Alhaji Habib Lema, Har yau Amarya Sauda na nan a matsayin Secretary na
Mami Aisha, da Mami tayi maganan a chanza mata wurin aiki tace "aa, ita
dai a barta nan don ta saba, haka mijin su ya barsu don yana jin dadin yanda
matan shi suka hade kansu.
Hafiz ma girma yake basu duka, ba za ka ta bacewa sun san juna shi da Sauda
ba, don da ga gaisuwa ba abunda ke hada su, Aneesa kuwa in kaga tayi wani abu
sai ka rantse da Allah ita ce diyar Habib Lema ba Rafee'ah ba. Rafeeq kuwa be
da matsala, idan ya shigo gidan be da aikin yi sai tsokanan Rafee'ah da Aneesa
fada..
Bayan Wata 2 (Bakin Rana)
Gidan Shiru kamar ba
kowa a ciki, Rafee'ah na Kaduna Gidan Uncle Zaid, taje taya Aunty Safiyya zama
don ta na da juna biyu, kasancewar hutu, Aneesa na BUK wurin Aunty Maryam,
Rafeeq na chan suna flexing da su Maalesh, Hafiz da Alhaji Habib sunje wani
Bussiness trip . Sauda ta kirashi a waya tace " Alhaji ya Lagos? Yace
"Ohh, banso kika kira ba, coz suprise nake so na muku, sai dai kawai ku
ganmu, yanzu ma in less than 2hrs zamu shigo katsina" daria tayi cikin salon yaudara tace
"kace yau da mun sha Suprise" yace "ina Shatou na?" ranta
ya sosu, ta tsani taji yace "Shatou din shi" gashi shi be jin komai
gaban kowa haka yake ce mata, zai sani, itama zata sani, don kawai ta barsu
suyi enjoying time dinsu ne for the main time kafin ta fara operation dinta, ta
daure dai tace "ni dai duk yau ban ganta ba, k'ila ta fita ko kuma tana
daki" yace "to ki dai sanar mata da zuwan mu" ta murguda baki
kamar yana ganinta tace toh sai kun kar'iso."
Dakin Mami Aisha ta shiga da Sallama, tana zaune kan gado
tana latse laptop dinta, ta amsa mata cikin sakin fuska, tace "Sauda kin
tashi lafiya?" "lafiya lao Yaya Aisha" suka yi shiru, har saudah
zata gaya mata dawowan Alhaji sai wata zuciyar tace kar ki gaya mata,
sak'esak'en da ta jima ta nayi ya fado ranta, ta tambayi zuciyar ta "to ko
damar ce ta samu yanzu? Bari inyi amfani da damar nan" ta mik'e da sauri
tace "bari in dan hada mana Sobo" Mami Aisha tace kamar kin san ina
marudin shan Zobon ki. tace "karki damu i wont take long".
Ta shiga dakinta da sauri, tana sak'esak'en abun yi, ta
yanke hukuncin kiran Mak'ale, ringing daya biyu ya daga, cikin muryan yan iska
yace " Hello Matar lema ya akayi ne?" tace "mak'ale kana ina
ne?" yace gani wurin Goruba road" tace "donAllah yi sauri kazo
akwai aiki" yace "to gani nan karisowa" "yauwa idan kazo ka
kirani"
Ta gama hada tsobonta tsaf, ta ciro wani k'ulli daga habar
zaninta, ta ware, magani ne na gari ta zube shi a cikin cup din ta karkada, sai
kuma ta ciro wasu k'wayoyin magani ta zuba
a ciki, ta karkada sosai ta dauka ta nufi dakin Mami Aisha. "Lahh
har kinyi me?" tayi daria tace "har na hada, ai ba wuya" ta dire
mata jug da cup din, Mami tace "nagode sosai" tace "haba ai
bakomi bari inje in daura sanwan rana" ba jira ta tsiyaya sobon a kofi ta
sha, ta kara tsiyaya wa ta shanye, ya cigaba da aikin ta a kan computer. Saude
da ke Labe bakin k'ofa ta daka tsalle ta na murnan ta sha, da sauri ta koma
dakin ta ta kira Mak'ale tace "wai ya? Kana ina? Yace wallahi gani nan
bakin gate dinku yanzu nake shirin kiran ki" tace "toh bari in fito
in shigo da kai" ta yafa mayafi ta fita da kudi a hannu.
"Baba ina kwana?" Sauda ta gaida baba mai gadi,
Cike da faraa da rawan jiki ya amsa da "Mun tashi Lafiya Hajia?" tace
"Alhamdulilah, dama dan Ganyen Latas (lettuce) ke so ka siyo min" yace "toh toh ba
matsala, barin samo yaro ya siyo don ba a bar gate din haka ba ba kowa"
"aa baba kai zaka je ka siyo, sauri nakeyi" tace a dan fusace, ya
danyi shiru sai yace "to, barin in yi sauri in je" nan ta tsaya har
sai data ga ficewan shi, ta lek'a taga yayi nisa. Ta hango motar mak'ale daga
nesa ta kira shi a waya yace "hello baby?" tace ka shigo mak'ale" yace "toh gani nan".
Tare suka shiga cikin gidan,
parlo ta tsayar dashi tace ina zuwa, lek'awa dakin Aishatu tayi taga tayi daidai kan Gado tana sharar bacci.
Murmushi Sauda tayi, ta janyo laptop din tayi shut down, ta maida cikin jakkar
ta ajiye kan side drawer, ta kwashi sobon ta da cup ta fita dashi, ta dawo ta
dinga bubbuga Mami Aisha, amma ko shurawa batayi ba, kamar matatta haka take
kwance. Saude ta danyi ihu taga ko zai tada Aishatu, amma ko ta motsa, Sauda ta
saki murmushi tace things will go as planned.
Bayan Minti Talatin(30 mins Later)
Bakin Gate Hafiz ya dinga Horn, ba alamun Baba mai gadi, to
ko ina yaje? inji Alh Habib, daidai nan Rafeeq ya danno motar shi kwanar Gidan,
ya k'araso, Ganin Motar Uncle Hafiz tsaye ya sa shi fitowa daga nashi motar,
zuwa yayi ya k'wank'was kofar side din Uncle Hafiz, yayi winning "Sannun
ku da zuwa Uncle Hafiz, Daddy Sannu ya hanya? Bamu san yau zaku dawo ba"
Suka amsa mishi gaisuwan su, Uncle Hafiz yace "mu kam Rafeeq bude man gate
dinnan, Bansan inda Baba yaje ba" Rafeeq ya kalli Gate din yace "to
ko ina yaje? Its unlike him" ya karasa tare da shiga gidan don bude Gate,
Uncle Hafiz ya shigo da motar sa, Rafeeq ma yaje ya shigo da tasa. Sauda na jin
dirin motar su ta fara tsalle, ta gyara zaman kan kujera tarw da rafka Uban
tagumi hannu bibbiyu.
A tare su 3 suka shigo parlorn, Alhaji Habib na ba Rafeeq
labarin Bussiness trip din su, suka shiga da Sallama, Ta dago ta amsa a
sanyaye, Sannun ku da zuwa Alhaji, Hafiz sannu" "sannu ya gidan?
Rafeeq yace "Auntyn mu lafia naganki haka?, u look disturbed" tace
"Rafeeq, wallahi Mami ce naji ta shiru, tana daki tun da na tashi, na
kwankwasa na kwankwasa shiru, na zata ma ta fita ne amma baba maigadi ya bani
tabbacin kai kadai ka fita yau" Rafeeq yace "toufa, its unlike her
baccin Safe, This is just 12:30" Sauda tace "nima dai haka nagani"
Hafiz maybe she needed the sleep, shes just sleeping" Alhaji Habib da yaji
Hankalin shi ya ki kwanciya, yace "kaii Rafeeq, je ka tado ta, Azahar ma
ta kusa" Rafeeq ya haye sama, Sauda ta cigaba da cewa "tun dazun da
mukayi waya da kai na lek'a don in gaya mata dawowan kuamma shiru na jita
wallahi".
K'wank'wan "Mami kina ciki?", ya murda k'ofan sai
dai damk'e ya jita, yace "mammy, ki bude Rafeeq ne, ko duk baccin ne haka?
"Mammy mana, ki bude Daddy ya dawo" nan ma shiru, duk ya rude ya shiga k'wankwasa kofar iya
karfin shi.
Alhaji Habib ya dan daga murya yace "Rafeeq Har yanzu
ba ta bude ba?" daga sama Rafeeq yace "Daddy ba ma ta magana, kuma
kofar is Jammed" da Sauri Alhaji Habib ya mik'e ya hau Saman, su Hafiz
suka rufa mai baya. Shima knocking ya fara yana cewa "Shatou na, kina
ciki? Are you okay" Shatou taso ki bude mana k'ofa" Sama sama sukaji
a na magana, da suka kasa kunne sukaji muryan namiji ne na cewa, "Mun
shiga 3, Aisha ki tashi, tashi maigidan ki ya dawo, Haba Aisha duk gajiyan ne,
ai ya kamata ki tashi daga baccin nan haka, ki tashi ki nemo min hanyar
fita"
Rudani da firgici ya ziyarci zuciyar Alhaji Habib, kirjin
shi kamar ya tsago daga rigar shi ya fado don tsoro, hannu ya sa ya toshe bakin
shi don wani kuka da yaji ya zo mai, yana k'okarin lalibo adduar
"Innalillahi wai inna illaihir raji'un"
"Allahumma arjirni fi museebati wa akhlifni khairin
minha.
Hafiz kuwa take Ran shi ya bashi wannan makircin Sauda ne,
ya kai duban shi ga Sauda yana mata kallon tuhuma, da ta lura da kallon da Hafiz
ke mata, ta girgiza kanta alamun ba ruwan ta, tayi saurin kawar da kanta daga
duban shi.
Rafeeq ko da be fahimci komai ba ya cigaba da k'wank'wasa
kofar, "Mami na Open up please, you are making us worried" ji yayi an
taba k'ofar, ya matsa baya yana murmushi ya kalli Daddyn shi, yace "Dad,
she's opening up, she's fine". Bawan da yace da shi komai, sai k'ofar da
suka tsura wa ido.
Mak'ale na cire key ya murda kofar ya danna a guje har yana
buge Alhaji Habib da ke kan hanyar shi, duk suka bishi da ido, Hafiz yayi
yunkurin binshi da gudu Alhaji Habib yayi karfin halin rik'o Hafiz, ya girgiza
mai kai alamun rabu da shi, Rafeeq cike
da alamun tambaya yace "Daddy waye shi?" Alhaji Habib be ce komai ba
face hawayen da ke zuba daga idanun shi, ya matsar da Rafeeq gefe yaym shiga
dakin Aishatu, burin shi ya ga Aisha ta ce mishi "mafarki yake, this is
not true" don so yake ya tashi daga wannan mummunan baccin da yake, Hafiz
ma ya bi bayan shi, sauda ma ta rufa musu baya suka kutsa dakin Mami Aisha.
Rafeeq da shifa
kwatakwata k'wak'walrshi ta dode, be gane komai ya bi su a baya. Hafiz yayi
saurin dauke kanshi daga duban Aisha, Sauda kuwa daura hanayenta tayi guda biyu
a kai, Alhaji Habib ya zame k'asa tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma
rai, Rafeeq da ke tsaye kamar mutum-mutumi (Robot) don duk wasu daurar da ke
aiki a k'wak'walwar shi ta dauke dif, sakamakon abun da ya gani. Mahaifiyar shi
ce Kwance Zindir ba kaya haihuwar Uwarta. Rafeeq da karfi yace
"Mammmmmmmiiiiiiiiiiiiiiiyy" firgigigit Mamy Aisha ta tashi.
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣5⃣
Da karfi Mami Aisha tace "Inalillahi wa ina ilaihir
rajiun, ne zan gani haka?" ta fada tare da neman abun da zata kare jikinta
dashi, da sauri Sauda ta bude Closet
dinta ta ciro mata zani da hijab ta bata, ta amsa da sauri ta suturta jikin ta.
Ta bisu da kallo daya bayan daya, ta fashe da kuka, me ya faru dani? Aljannu
suka shige ni ko? Suka min tunbur? Kumin magana" Sauda ta fara kukan
munafurci tace haba "yaya, ya zaki ce haka? Kwarto fa kika kawo cikin
daki, amma yanzu kina neman cema na ba kisan me kikayi ba? Zurum ta zube a
kasa, don kafafuwan ta sun gaza daukar ta, a ranta tace kwarto? Ta dago taga
yanda Alhaji Habib ke zubar da hawaye da sauri ta rarrafa gurin shi, ta rik'o
hannun shi, Kamar wanda shocking ya taba, yayi saurin janye hannu shi tare da
mik'ewa, ya nuna ta da yatsa yana kuka, "Aisha, kin cuceni, kin haince ni,
kin ci amana ta, was it hard for you to wait for me?" kuka take yi sosai,
ta kasa cewa komai sai girgiza kanta da takeyi, da kyar tace "kayi hakuri
Habibullah" wannan magana da tayi ne ya sa shi tabbatar da zance, shikenan
Aisha ta ci amanar shi, ta kawo kwarto har cikin dakin ta da tsakar rana, ba
tsoron Allah. Da kyar yace "Aisha na sake ki saki daya" ya fice daga
dakin, Sauda ta hau kururuwa ta bishi a baya "haba Alhaji be kamata kayi
haka ba, be kamata ka yanke hukunci kana bacci ba, Alhaji ka maidota yanzu
pls" tsawa ya daka mata yace "Saudat, kina so ki bita kenan? Da sauri
tayi shiru kar daga neman kiba ta nemo rama. Ba ta ji dadin saki dayan da
Alhaji ya mata ba, duk a zaton ta saki 3 zai mata, amna dayan ma ba laifi, zata
tabbatar Aisha ba ta dawo gidan ba har abada.
Hafiz ya kalleta cike
da tausayi tabbas wannan aikin Sauda ne ya rasa me zaice shima ya fita ya rage
daga Rafeeq sai Mami, har yanzu tana nan duk'e inda Habib ya barta, Rafeeq ko
na nan tsaye, ya kasa motsi, abubuwan ke dawo mishi kai, ya kasa yarda da Abun
da idon shi yagani, da ya runtse ido Mami yake gani zindir, Mami ta dago kai a
hankali ta sauke su kan Rafeeq, da jijiyoyin kanshi sun mimike, fuskar nan tayi
Ja, idanuwan sa ma sun kada sunyi jazir, Mami bata damu da halin da take ciki
ba ta mike ta nufo Rafeeq, yanayin da ta ganshi ya firgita ta matuk'a, ba ta
taba ganin Rafeeq a haka ba.
Hannu ta cire zata riko shi don ta zaunar da shi kan gado,
da sauri ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu, yace "dont touch me,
Kar ki taba ni" cike da mamaki ta kalle shi, tsana da kiyayya taga ni
kwance kan fuskar Rafeeq, yace "bana so in sake ganinki" baki na rawa
tace "Rafeeee--q" yace "Wallahi na tsane ki" kafin ya sake
wani magana yaji wani lafiyayyen mari tassss a fuska, hannu ya sa ya dafe
kuncin sa, ya na dagowa ya sake ji a kara sakar mishi da wani marin da ya fi na
dazu, duk a zaton shi mamin sa ce ke marin shi, dagowa yayi don sake yab'a mata
wasu bak'aken maganganu, sai ya ga akasin haka, Hannun Mami ya gani rik'e da
hannun Uncle Zaid da ke niyyar sake marin Rafeeq karo na 3, ta tare shi ta
hanyar rike hannun.
Huci Zaid keyi, ya nuna Rafeeq da hannu "How dare you
Rafeeq?" kasan da wanda kake magana? Rafeeq be bi takan Zaid ba ya kalli
mami ido cikin ido, yace " i wish i had a different mother" ya juya
ya fice. Cikin zafin rai Zaid yace" Rafeeq Habib Lema, come back
here" Mami tayi saurin cewa "Zaid, laifi na ne, na mishi babban
laifi, na ma kowa babban laifi, i dont know what exactly happened but i know i
didnt do what they are accusing me of'' Zaid yace " Mami wai meke faruwa
ne? Na rasa ganewa, tun kafin in shigo katsina na dinga neman layin ki, be
shiga, na shigo gida na ga alamun ba lafiya, don Hafiz na k'asa na kuka, na
tambaye shi me ya faru ya kasa magana, ban bi takan kowa ba na hayo sama gunki,
na iske wannan mugun kalamai da Rafeeq ke fada miki, ina zargin Rafeeq koya
fara Shaye shaye"
Mami na kuka sosai tace "ko daya Zaid, Rafeeq na da
hujjan yin hakan, kaji kaji abunda na sani" "inalillahi wa ina
ilaihir rajiun" inji Zaid, Mami har tayi nadaman gaya ma zaid, a zatonta
shima yarda zaiyi da zargin da ake mata na kawo kwarto cikin gida. Tace Zaid
"Wallahi ban san komai game da
hakan ba, ni dai kaji yanda na tashi na tsinci kaina" Zaid yace "yi
shiru mami kar kiyi zunubi, na san halinki,Wallahi akwai wata k'ulalla, akwai
wata a kasa, tabbas wannan wani irin tuggu ne aka shirya miki, to wa??"
Mami tace "Allahu Aalam, Zaid ka saurareni da kyau, wannan boyayyen
alamari ne da ba wanda yasani sai Allah, Habib ya sake ni, i wont be there to
protect my children, whoever came for me is coming for my kids, is defintely
coming to hunt my Childeren down, sunci nasara a kaina, Zaid kar su ci nasara a
kan 'ya'ya na, Zaid i want u to protect them"
Zaid na kuka yace "Mami yaya ya yi saurin yanke
hukunci, baya cikin hayyacin shi ne sanda ya sakeki, mu bari ya sauko, sai ayi
magana nasan gaskia zata fito, ya maido ki dakin ki. Murmushin takaici tayi,
tace " Zaid kenan, yanzu dai bawanan ba, Rafeeq yayi fushi sosai, fushin
da be taba yin irin shi ba, ina tsoron kar zuciyya ta kai shi yin aikin da na
sani, ina tsoron zuciyar Rafeeq, Zaid ka bishi donAllah, Ka kula min da d'a
na" kamar wanda aka tsunkula ya
tashi zumbur, don ya mance halin da ya ga Rafeeq dazun. Yace "Mami ki
jirani i'll be back and everything is going to be Alright" a hankali tace
"Go Zaid, Go" be sake magana ba ya fice da Sauri. Matakala bibbiyu,
uku uku Zaid ya dinga hadawa ya sauka k'asa, sai dai ga mamakin shi Wangale
yaga gate, ya duba gefe ya ga ba motar Rafeeq da yagani Parke a gefe hankalin
shi ya daga, daidai nan sai ga Baba Maigadi ya shigo gidan da Cefane da Lettuce
din da Sauda ta aike shi a hannu, Zaid yace "baba ina Rafeeq" Baba
yace " Zaid yanzun nan na ga motar shi ta wuce fiyauu, na tsorata da yanda
naga yana tuk'i, da alamu sauri yake" Hankalin Zaid ya tashi, ya na tafiya
ya na magana yace "akwai matsala a gidan nan baba, matsala
babba" Zaid ya fada motar sa ya bi
bayan Rafeeq baba Maigadi ya mishi Allah ya kiyaye.
Zaid na fita itama ta hada kayan ta, kana ganinta kasan
hankalin ta a tashe yake, duk ta dauki abubuwan buk'ata, ta sauko k'asa ta bude
motar ta da ta siya da kudinta ta tura Akwatin ta, da sauri Baba Maigadi ya
nufo gunta, "Hajia Lafia? Tafia zakiyi? Ince dai lafiya fuskar ki tayi
Jaa, kuka kikeyi ne?" da kyar tace mishi "Baba, Habib ya sake
ni" Salati maigadi ya saki, yau mun shiga uku, shi habibun ya sake
ki?" me yayi zafi haka?" Murmushi tayi tace baba barin tafi, don
Allah a kula da su Rafeeq, akwai wata Musiba da ta shigo gidan nan" Baba
da ya fara kwallah yace InshaAllah, Allah shi yaye ya sa ku daidai ta da Alhaji
ya maidoki dakin ki, don Wallahi ba shi kadai yayi rashi ba muma munyi".
Tace nagode ta bude motar ta ta shige ta bar Haraban Gidan Habib Lema.
Gudun da Rafeeq keyi na tashin hankali ne, kamar zai buge
mutane, Allah dai ya cigaba da kare shi, don be ganin gabanshi shi dai yasan
tuk'i yake, ba tare da yasan inda ya dosa ba, Kiran Zaid ya shigo wayar sa,
amma yanda sauran kiran suka shigo suka yanke haka wannan ma ya katse, Zaid ya
damu matuk'a da kyar ya kira Maalesh ya ji in gidan su Rafeeq ya nufo Maalesh
ya bashi tabbacin tun wurin 11 suka rabu. Zaid gudu yake yana duba hagu ko dama
inda zai ga Rafeeq, kawai dai ya yanke hukuncin bin Hanyar Jamia ta wurin Ring
road, speed ya k'ara, ba jimawa kadan Zaid ya hango motar Rafeeq daga chan
nesa, gudu yake kamar dan tseran mota, hamdala Zaid yayi ya k'ara gudun motar
shi, horn yake ta mai amma yak'i tsayawa, ta mudubin motar Rafeeq ya gane motar
Uncle Z, shima ya kara gudun motar shi, Shima Zaid ya kara na shi, Gudun da
sukeyi yafi kama da na masu race, ba me niyyan tsayawa, Burin Zaid ya tarar da
Rafeeq, shi ko be da wani burin da ya wuce ya ta tafia har sai ya manta da wani
damuwar shi.
Zaid ya taka motar nan da karfi, har Allah ya bashi ikon
shan gaban motar Rafeeq, Ran Rafeeq ya baci, niyyan shi ya cigaba da tuk'in har
ya buge motar Zaid, amma zuciyar shi ba zai bari ba, Uncle Zaid ne fa a motar,
mutumin da yake so sosai, ba zai so ya buge shi ba, be da wani zabin da ya wuce
ya tsaya da motar sa.
"Aishatu lafiya? Kinzo kin tasamu gaba kina ta kuka,
wani abun ne ya faru?" Baba Tijjani ne mahaifin Mamin su Rafeeq ne ke mata
tambayar nan, duk ya tsufa sosai, mamar tace "haba mama na, idan wani abu
ya faru ki gaya mana, ba wai ki tasamu da kuka ba" da k'yar ta tsagaita
kukan ta ta labarta musu iyakar abun da tasani, Sallalami da Salati suka fara,
mamarta harda kuka, Baba Tijjani yayi shiru yana nazari, chan yace Aishatu, na
san wa na haifa, na yarda dake, ban haife ki don ki zama ma zinaciya ba, da
mijin ki da 'yaranki, tabbas idan aka duba wannan lamari zaa ga shiri ne a
dunkule sai mai hankali zai gane" Mamar Mami tace "amma shi kuma
habib harda Saki? Baba Tj yace "sharri ne dai don a hadata da mijinta, ni
ban ga laifin Habib ba, don ko ya samu duk wani evidence da ya ke bukata, ko
wani namiji haka zaiyi, amma ina da tabbacin da Habib ya kwantar da hankalin
shi ya duba lamarin nan zai gano gaskia, tashi ki shiga daki Allah shi zai saka
miki" tace baba ina so in bar gidan nan, don na san Zaid ba zai taba bari
na a nan ba, duk yanda zaiyi sai ya maida ni gidan Yayan shi, bana son hakan ya
faru na fiso Habib ya gano gaskia da kanshi kuma ina bukatar lokaci da zan huta
in yi idda na, ina neman izinin ka na barin garin" "Aa Aishatu, ba
zan bari kiyi zaman kanki ba" Mama tace "ta je Malumfashi gurin Inna
mana" Baba Tijjani yace "kina iya zama malumfashi gun kanwara
mamarki?" tace "Eh Baba, idan ka min izini yanzun zan tafi" yayi
shiru yace "Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare ki kula da kanki".
Ganin Rafeew be da niyyar fitowa daga motar shi ne ya sa
Zaid fita da sauri ya nufe shi, har ya tako gaban motar Rafeeq, ya bude gaban
motar, ya sa hannu ya fito da Rafeeq, ya kalle shi, shima ya tsorata da yanayin Rafeeq, fuskar nan ta yi ja, idanuwan
nan sun kada sunyi jazir, ga digon hawaye ko k'wallah, jijiyoyin kanshi sun
mik'e. Zaid ya tausaya ma Rafeeq sosai yace "Rafeeq" Ko kallon shi
Rafeeq beyi ba, Zaid ya kara cewa "Rafeeq kayi hakuri, kayi kuka, cry it
all out, kar ka barshi a ranka, pour your heart out, i know this is hard for
you, let it flow Rafeeq, let it flow"
Da sauri ya rungume
Zaid sosai, sai a sannan ya samu Hawaye suka fito daga idanuwan shi, sai a
sannan ya fara kuka a hankali yace "Uncle Zaid, Help me"
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
*Assalamu Alaikum*
_Da farko zan fara da nuna godiata da jin dadin yadda kuke
biye dani a cikin_ _littafina na *KE ALHERI CE*_
_Nagode sosai Allah ya saka maku da alkhairi yabarmu tare._
_Kamar yarda
korefe korefe sukayi yawa akan page 23 na littafina masu yi a grps da masu
biyoni prvt duk ina son inyi clearing mind dinku daga abinda kuke ganin na
aikata da wasunku suka daukeshi daidai da kuma wadanda suka dauke shi ba daidai
ba. (Yin daidai sai ubangijinmu cos_ _dukkanmu tara muke bamu cika goma ba_)
_Kamar
yadda kuka sani duk wadda tabi littafina daga page one zuwa yanzu tasan inda
littafina ya dosa.. Kamar yarda kuka karanta kuka gani there is darkness in
*Rafeeq's* life wanda yake saka shi yin duk wani abu da wasu dabiu da ba
halinshi bane a da, wanda har na gangaro zuwa page 24 inda kowa ya gane dalilin
shigar *Rafeeq* wannan yanayin da yake na yanzu._
_Kaidi irin na mata(
*Wanda ko shaidan tsoronsu yake*) ya kuma hadu da kaidi na kishiya mara imani
babu abinda baya janyowa.. abinda ya
faru da Mami is well planned by Saude so ko sirikinta ne zai iya ganinta a
yanayin data samu kanta_ _balle kuma dan cikinta sbd dama burinta ta kafa
shaida mai kyau ta ido sbd idan dunia
zata taru tana gaya ma *Rafeeq* abinda_ _mahaifiyarshi tayi bazai taba yarda ba
kamar yarda uncle Zaid da iyayenta basu yarda ba..Saude tayi hakan ne dama don
su gani da idonsu su zama shaidar kansu,wanda hakan ya tabi zuciyar Rafeeq har
ya_ _haddasa mai duhu da bakin cikin da yake kwana yana tashi dashi kullu
yaumun.._ _haka kuma rayuwarshi ta watse ta tarwatse sbd abinda ya gani da
idonshi._
*_Kowacce tayi addua Allah ya rabata da muguwar kishiya sbd
babu abinda basu iya aikatawa tunda babu Allah a cikin al ammuransu._*
_Allah yasa muna fahimta da amfana da darussan rayuwa dake
ciki_
*Biebie* luv u loads💖❣💕
Pg2⃣6⃣
Kuka yakeyi kamar karamin yaro harda majina, Uncle Zaid beyi
yunkurin hanashi ba, sai da yayi ma ishi kafin ya tsagaita da kukan. Uncle Zaid
ya kira Maalesh yace yazo ya iske shi ring road yana jiran shi, kar yazo da
mota, baa fi 15mins ba sai gashi, a rude Maalesh ya fito don be san meke faruwa
ba yace "guy howfa? Kallo isasshe Rafeeq be ma Maalesh ba, Zaid ya mai
alama da yayi shiru. Key din motar shi ya ba Maalesh, ba tare da ya tambayi me
zaiyi da key din ba ya shige motar Uncle Zaid, shikuma zaid ya tura Rafeeq
cikin motar sa, Zaid ya zauna a mazaunin driver ya ja motar ba me cema danuwan
sa k'ala, jefi jefi Rafeeq yake sauke ajiyar zuciya, hanyar gida suka dauka, a
hankali Rafeeq yace "please dont take me home" ba musu Zaid ya chanza
hanya ya nufa gidan su Maalesh, daidai gidan su Maalesh Zaid ya tsaya yin horn,
Rafeeq be jira maigadi yazo ya bude gidan ba ya fita daga motar ya shige
Gidansu Maalesh ya nufi side dinshi.
Zaid ya girgiza kai ya fito, Maalesh ma ya fito, yace Uncle
Zaid me ya faru da Rafeeq ne? Ban taba ganninshi haka ba, da kyar Zaid yace
"he is broken" ya sake bashi key din motar shi, yace "je ka kai
motar Rafeeq gida ka dawo yanzu" Akwai mutane cikin gidan?" Maalesh
yace "aa Mummy taje kaduna, ba kowa" yace key din dakin ka fa?
Maalesh yace "akwai daya gun Rafeeq, amma ga wannan incase ya barshi
gida" Zaid ya amsa ya nufa cikin Tangamemen Gidan su Maalesh.
Be ga Rafeeq ba a kofar dakin, hakan ne ya bashi tabbacin
Rafeeq na ciki, ya murda kofa yaji ta rufe, key din da Maalesh ya bashi ya zaro
ya bude kofar, tare da shiga da Sallama, chan kusurwa ya ga Rafeeq kwance, be
kula shi ba ya shiga toilet yayi Alwala kasancewar lokacin Sallah yayi.
Bayan ya idar da Sallah ya zauna kusa da Rafeeq ya janyo
hannun shi ya hade da nashi, yace Rafeeq ka saurareni, "Mamin ka ba tayi-
da sauri yace kar kayi shaidar zir Uncle Zaid, ni nasan abin da nagani, naga
zahiri ba labari aka ban ba" Zaid yace najih Rafeeq, kaga zahiri ba labari
aka baka ba, amma shin kagan su suna aikata Zina? Mahaifiyar ka ba ta
chanchanci haka daga gareka ba, kar ka mance irin So da K'auna da take maka,
Rafe--" Uncle Zaid ya isheni, Wallahi zan bar maka gidan nan, idan kana
min maganar ta kana sawa ina k'ara tsanar ta" jimm Zaid yayi, sai ya yi
shiru don baiwa Rafeeq Lokaci, ya mik'e yace "bari inje in dawo".
Isketa yayi kitchen tana kokarin dafa ma Alhaji Habib Ruwan
Zafi, Hafiz yace " Sauda, na san kina da hannu akan abun da ya faru da
Aishatu, komai shirin kine ke ki ka k'ulla mata wannan sharrin." tayi
wulwul da ido, tace haba Hafiz, me kake cewa? Rashin imani na be kai nan ba,
muna zaman lafia da ita me zai sa in neme ta da sharri, ni bansan me ka mayar
dani ba, yace "Sauda na san halinki sosai, wallahi nayi bincike nagano
gaskia, to zan tona miki asiri wallahi" Sauda tayi daria tace "Hafiz
kenan, to barin fito maka da real color dina, idan nice me zakayi? Uban me kake
iya yi? Kasan dai halina ko? Ka ka shiga gona ta, idan ka min shishigi zakayi
kuka da kanka, kar ka manta Rayuwarka a tafin hannuna yake. I own u, so
watchit" ta fice ta barshi tsaye.
Bakin gate ya hadu da Maalesh, yace ka kai Motar? "Eh
Uncle Zaid" ok ban key dina ni, Maalesh ya nika mishi, yace "Uncle
Zaid" Zaid yace ina sane da kai Maalesh, nasan there are millions of questions da kake so kayi, ka jirani ina
zuwa, and Rafeeq give him space" Maalesh yace "Sai Ka dawo". Ya
shiga ciki Zaid kuma ya fito.
Da Zaid ya koma gida be ga Mami ba, hankalin shi ya tashi,
ya sauka kasa ya tambayi baba mai gadi yace ko ya ga wucewar ta? Ya bashi
tabbacin ya ga ta fita da kaya, da alamu tafia zatayi, da sauri ya shige mota
ya nufa gidan Baba Tijjani.
A sukwane ya shiga Parlorn, Baba Tj na zaune yana Azkhar,
yace Zaid "lafia ka shigo a haka?" yace "baba ina Mami?"
cikin mamaki yace wace "mamin? "Ina Aunty Aisha mamar Rafeeq?"
Zaid ya dan fada a fusace, Baba Tijjani yace tana gidan ta mana, ce maka tayi
zata zo nan? Baba dagaske ba ta nan? Yace "dama Ina maka karya?"Zaid
yace "aa baba ba haka nake nufi ba, tabar gida ne na zata nan tayo, kuma
wayarta a kashe" yace "aa ba mu ganta ba" Zaid be jira ba ya
fita ba tare da ya basu labarin abun da ya faru ba, a ganin shi abun kunya ne
suji Yayan shi ya sakar musu diya bayan hallacin da Baba Tijjani ya musu.
Mama tace "Alhaji ya ba ka gaya mishi gaskia ba? Yace
kinsan halin Zaid, ba zai barta ba, duk inda take sai yaje ya daukota, abar ta
ta gama iddan ta, she needs time" tace "Hakane"
Hankalin Zaid a tashe Matuk'a, duk inda yasan zai bincike
Mami Aisha yaje be ganta ba, ya kira wayarta yafi a irga a kashe, Zafi biyu, ga
rashin sanin inda take, ga matsalar Rafeeq, a bayyane yace "Allah kayi
mana Agaji" yayi niyyar zuwa gidansu Maalesh don ganin Rafeeq, sai ya fasa
don yasan Rafeeq na bukatar lokaci sai kawai ya wuce gida.
Hafiz ya sake labarta mai abunda ya faru, Zaid yace
"wallahi Hafiz Shiri ne, ban yarda ba, akwai wata manakisa, kuma i promise
i wont rest har sai na gano who is behind this na sada shi da hukuma"
Hafiz ya danyi jim, so yake ya gaya ma Zaid wacce yake zargi, amma sai ya tuna
gargadin da ta mishi dazun, inda take cewa "Hafiz, dont try to bring me
down, if i go down, i'll drag you down with me" miyau ya hadiye yace
"gaskian ka Zaid, its hard to believe, Allah ya baiyanar da Gaskia cikin
sauki" Zaid be ce komai ba saboda yanda Zuciyar sa ke tafasa. Wurin Yayan
shi ya hau a sama, ya ci saa shi kadai ke Parlorn, ya shiga da Sallama, har
yanzu be bar kukan ba, Zaid ya kalli yayan shi cike da Tausayi, yace "Yaya
kaima kuka kakeyi?" Habib Yayi murmushin takaici yace Zaid " kaga
abun da uwar dakin ka ta yi min ko?" Zaid cikin bacin rai yace "yaya
kaima ka yarda? Haba yaya, wai ba ka san wacece Aisha ba? Shekarun ku nawa da
ita? Tun kuruciyart bata kawo gardi gida ba sai yanzu da ta fara tsufa har da
diyanta? Haba Yaya kai haka kake baka bincike? Haka fa kamin a baya, dai daga
baya kazo kana da nasani, you should have give her a time to explain, am sorry
but ka dinga amfani da hankali." Habib yayi shiru yana nazari,
magananganun Zaid sun shige shi, daga kallo daya zaka san cewa jikin shi yayi
sanyi, amma ya kasa cewa komai, Sauda da ke labe a bakin k'ofa ta ja tsaki,
tace wannan Zaid din yana neman bata min shiri, amma da sannu zanyi maganin
shi"
Tana shiga daki ta kira Boka na kan tudu, ta nemi da ya
janye tunanin Aishatu daga kan Habib, Boka yace ba matsala, anyi an gama, tace
"yauwa, saura Maganan k'anin nan nashi, Zaid, Boka yace "uhm uhm
Sauda, kar ki b'allo ma kanki ruwa, ki rabu da wannan, amma shi kina iya hadawa
da kissan ku na mata" tace "to shikenan yanzu dai ka janye min
hankalin Alhajin".
"Rafeeq be kamata ace kana fadan mugun kalamai kan
mahaifiyar ka ba" Maalesh ne ke zancen nan cikin bacin rai, Rafeeq ya
kalleshi galala yace "Maalesh, ka min shiru, idan kuma so kake ka nuna min
nan Gidan ku ne, sai na tafi na bar maka gidanku yanzu, ba wai ce maka akayi na
rasa wurin zuwa bane" Maalesh ya buga tsaki tare da fita ya bar mai dakin
don idan ya biye ma Rafeeq zasuyi ba dadi cikin daren nan.
Bayan Kwana 3
Gari yayi ma Zaid Zafi, ba inda zai saka ranshi yaji dadi,
Gashi ba inda be nemi uwar dakin shi ba labarin ta, Gashi Idan ya ma yayan shi
maganar ta sai ya hau masifa don jiya saura kiris Ya mareshi don yace mishi ya
kamata ya yi bincike don gano gaskia(Bokan kan tudu yayi aiki kenan) Gashi idan
yaje gun Rafeeq don su tautauna kan Mahaifiyar shi sai ya birkice yak'i ko
tari, don Zaid ya fara magana har ya gaji Rafeeq ko k'ala ba zai cemar ba haka
zai bar Gidansu Maalesh ya koma Gun Yayan shi, nan ma ba wani sauki, sannan
kuma ya zagaya duk inda ya san zai ga Mami Aisha amma shiru ba wani dace.
Bayan kwana Uku
Yau Sunday aka kira Zaid a Office, aka ce ya dawo Kaduna
saboda akwai aikin da zaa tura shi Lagos, be da wani zabi da ya wuce ya koma
Kaduna, kafin ya bar Katsina sai da yaje Gidan Baba Tj, ya roke shi da ya gaya
mai gidajen Yanuwan su da ya ke ganin Mami zataje amma fir yak'i gaya mishi,
haka ya bar gidan cikin rashin jin dadi, Gidan su Maalesh ya nufa.
Maalesh ya gani tsakar gida yana Basketball, Maalesh ya
karaso ya gaida shi, Zaid ya amsa mai cikin sakin fuska ya tambaye shi
"Mahmud, ya abokin naka?" Maalesh yace Uncle Zee wlh ba sauki, abun
Rafeeq gaba yake kara yi, tun gaisuwan da naji ya maka jiya da Safe, Wallahi
har yau ban sake jin yace ko a ba, haka zan gama surutai na ko kallo ban ishe
shi ba" Zaid ya jinjina kai, yace Abun Rafeeq sai Addua bari in
ganshi".
Zaid ya Iske Rafeeq Zaune, kallo daya ya mai ya ga rama da
Baki'n da Rafeeq yayi, Zaid ya cire baki ya kira sunan shi cike da tausayawa,
Be amsa ba ya juyo ya kalleshi, idon nan har wayau jajir, Ya tsura ma Zaid ido,
Zaid yace Rafeeq zan tafi Kaduna yanzu, akwai abun daya da nake so kamin please
ba don na isa ba" da Sauri Rafeeq ya tashi yayi hanyar toilet, don baya
son zancen da Uncle Zaid ke son mishi, da sauri Zaid ya dakatar dashi ta hanyar
cewa "Rafeeq ka saurareni, Wallahi ba maganar Mami zan maka ba"
Rafeeq ya dan dakata don shi a zaton shi maganar Mahaifiyar shi zaa mishi. Zaid
ya umurce shi da ya zauna, kamar ba zai zauna ba ya zauna, Zaid yace "Son,
Ina so ka koma Gida, zaman ka a gidan aboki ba zaiyuwu ba, kar ka manta ba
zaman kanka kake ba, kana da mafada, na baka lokaci don ka dawo daidai, amma
abun naka girmama yake, dole ka koma Gida, kaji ko?" Shiru Rafeeq ya
mishi, Zaid yace "Rafeeq Habib Lema, kajih ai?" kamar ba zai tanka ba
ya gyada mai kai alamun yaji, Zaid yayi murmushi yace "thank you, Rafeeq,
zan koma Kaduna yau, there are somethings i need to attend to" Shiru dai
Rafeeq ya mishi be ce komai ba, Zaid ya gaji da zaman shi ya tashi yace
"to Rafeeq ni na wuce" nan ma be ce mai komai ba, Har Zaid ya kai
bakin kofa a hankali Rafeeq yace "Uncle Zaid" da sauri ya juyo yace
"naam Rafeeq, me kake so? You need something?" Rafeeq dai yayi shiru
kamar bashi ya yi magana yanzu ba, ya rasa me zai ce mai, Zaid dai yayi tsaye
yana jiran me zaice mai, amma yaji shiru, da Rafeeq ya rasa me zai ce ma kawun nashi sai ya
taka har gaban sa ya rungume shi, Zaid ko ya rungume shi shima, daidai da
saukan hawayen Rafeeq, Zaid ya dinga lallashin shi, a hankali Rafeeq yace da
Zaid "Please dont tell Rafee'ah..
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣7⃣
Zaid ya dago yace "kar ka damu Rafeeq, Rafee'ah ba za
ta sani ba" gyada kai kawai Rafeeq yayi, Zaid yace "akwai wani abun
kuma? ya sake girgiza kai Alamun Aa, Zaid yace "toh, na tafi" Rafeeq
ya koma kan Gado ya zauna. Zaid ya fice, gun Maalesh ya isa, yace "Mahmud,
ni na wuce Kaduna, sai weekends kuma, Nagode sosai, Yau zai koma gida, ka
cigaba da kula mun da Rafeeq, zan dinga kiranka ina jin yanda yake"
Maalesh yace "Bakomai Uncle Zee, mudai fatan mu Allah ya sa gaskia ta
baiyana, Rafeeq ya dawo normal self dinshi, don nafi kowa Affected da yanda
Rafeeq yake yanzu" Zaid ya jinjina kai ya chanza zancen yace "In bada
na shan Mai?" Maalesh ya sosa kai yana daria, Zaid ya ciro Bandir din dari
200(20000) a Aljihu ya ba Maalesh. Maalesh yayi Godia sosai ya raka Uncle Zaid
har mota kafin ya dawo gun Rafeeq.
Rafeeq ya kalle shi zai yi magana sai kuma ya fasa, ya mik'e
ya zira takalman shi, ya je gaban Tv inda Maalesh ya ajiye Key din mota ya
dauka ya zo ya ba Maalesh, cikin wasa Maalesh yace "kai ni fa ban san
iskanci, kurma ka koma ne?" Rafeeq uban Zuciya ya galla mai wata muguwar
harara ya wurgar da Key din ya fice daga dakin, Maalesh yace "ikon Allah
har yayi fushi? Duk da muke wasa fiye da wannan be ta fushi ba sai yau?"
binshi yayi a guje har ya taddo shi, yace haba "R-Lema, wasa ne fa, Gida
zakaje ko? Muje" Rafeeq dai be ce komai ba ya zagaya ya shige mota.
Gidan su Rafeeq kamar ba mutane, shiru kake ji, Rafeeq ya
fito daga motar Maalesh ya bi Haraban Gidan da kallo, komai ya dawo mai sabo,
yaji ranshi ya kara jagulewa, part dinshi kawai ya nufa ko cikin gidan be kalla
ba, Maalesh yace "R motar Daddy na nan, ba zaka je ka gaida shi ba?"
ko kallo Maalesh be ishe Rafeeq ba ya bude dakin shi ya shige, Maalesh ne ya
shiga cikin gidan, ya iske Daddy da Saude a parlor suna fira, da alamun ba su
da damuwar komai, ya karisa da Sallama, Alhaji Habib ya dago yace "Mahmud
ne?" "eh daddy nine ina kwana?" ya amsa mai cikin sakin fuska,
"Maalesh ya su maman ka?" inji Sauda yace "suna lafia sunce a
gaidaku aunty" A. Habib yace "Mahmud ina abokin ka? Maalesh ya fara
sosa kai, yace "yana daki be dan jin dadi ne" Zumbur ya mik'e yace
"SubhanAllah barin je inga dan Zaid" ya fita Sauda ta rufa mai baya,
duk ranta ba dadi ganin yanda mijinta ya rude don yaji ance Rafeeq be lafia.
Sunfi minti uku suna Sallama ba amsa, a zaton su bacvi yakr
yi, Maalesh ne ya tura kofar suka shige ciki, ga mamakin su zaune yake idon shi
biyu, kallo daya ya musu ya dauke kai, ganin da ya ma Daddyn shi cikin koshin
lafia, be da wata damuwa abun ya bashi haushi, wato be damu da abunda matar shi
tayi ba kenan? Kwafa yayi a ranshi".
Sauda ta dan matso kusa dashi cike da kissa tace
"Rafeeq my boy, are u Alright?" Rafeeq ya kawar da kanshi kamar be
san da wata halitta tsaye a gun ba, muryar ta ya tuna lokacin da take cewa
"Yanzu yaya kwarto kika kawo cikin dakin auren ki?" haka kurum yaji
ya tsane ta, be son ganin su duka har Daddyn shi. Alhaji ya matso yace
"Rafeeq ka min magana, wani abu ke maka ciwo?" da kyar bakin shi ya
motsa yace "donAllah ku fita" don kwata kwata be son ganin su. Ba
Gardama Alhaji Habib yace "muje Sauda he wants to be alone "
Suka fita suka bar mishi dakin har Maalesh. Wayar shi ya
jawo har zai danna kiran Uncle Zaid ya fasa, sai ya tura mishi sakon message
"I'm home" kadai ya tura mai,
lokacin da sak'on ya isa ga Zaid tuk'i yakeyi, ya bude sak'on yayi murmushi
yasan Rafeeq ba zai k'i yin abunda yake so ba, sai ya maida mai Reply da
"Nagode".
Haka Rayuwar Rafeeq ta kasance cikin k'una da dacin rai, duk
ya koma wani iri, ga wata uwar K'asumba ya fara ajiyewa, ba ruwan shi da kowa
da komai, har mahaifinshi don ya zame mishi dole ne yake amsa mai magana shima
maganar bata wuce "a" ko "aa", Alhaji Habib be jin dadin
yanda danshi ke yin dari dari dashi, ya kira kaninshi Zaid ya kaimai kara, Zaid
ko saidai ya bada hak'uri yace a tayashi da addua. Hakan ba zai hanashi gobe ya koma dakin
Rafeeq din ba, tunda shi ba shiga yakeyi ba, sai a kwana a yini Rafeeq be ce
"a" ba, tun Maalesh na damuwa har ya daina damuwa.
Hankalin Maalesh ya tashi da ya tuna Jibi zasu koma
Makaranta, 2nd Semester Level 400 final Semester dinsu kenan a Jami'ah, ga
project ga defence ga wacece, taya Rafeeq zai wuce idan yana haka? Da sauri ya
dialing number Uncle Zaid ringing biyu Zaid ya dauka "Hello Mahmud?"
bayan gaisuwa Maalesh yace "Uncle Zaid Jibi fa muke komawa School, ga shi
shine final semestern mu a makaranta, Dole sai Rafeeq ya kwantar da hankalin
shi yayi focusing kan Semestern nan, shi ke topping din Department dinmu, Uncle
Zaid Wallahi duk Sciences bs kamar Rafeew Lema, lecturers naji da shi, idan ya
sa wasa zaiyi k'asa sosai don abun nashi k'ara girmama yakeyi wallahi, yanzu da
idan nazo tayashi fira ya kan dan kulani, amma yanzu wallahi har inzo in gama
surutu na, in gama zama na in tafi in ya tanka ni, kai da ba ka gurin ka tanka,
Uncle am afraid for him" hankalin Zaid yayi kololuwa gun tashi, burin da
ya jima yana ci kan Rafeeq na son rugujewa, tunda Rafeeq ya shiga nursery yake
adduan Allah ya nuna mai randa zai gama Jami'ah, to ga lokacin yazo daidai da
k'addarar sa, ya zaiyi? Dole Rafeeq ya maida hankali, dole Rafeeq ya dawo
normal self dinshi, Zaid yace "Mahmud kar ka damu, gobe InshaAllah muna
nan dawowa da Rafee'ah tunda hutu ya kare, komai zai daidai ta."
Sun Iso Katsina Lafia, tunda suka shigo Haraban Gidan taji
Gabanta ya fadi, ta kalli Uncle Zaid tace "Uncle Zaid gaba na ke faduwa,
kamar wani abu na shirin faruwa" Zaid yace "kin fara superstitious
beliefs din nan naki ko, ba abunda zai faru kinji Rafee'ah?" tace
"Allah ya sa, i cant wait to see my Mami and my troublesome Hamma
Rafeeq" Damm gabanshi ya fadi, ana wata ga wata sai yanzu ya tuna Rafee'ah
bata san wainar da ake toyawa ba, ba ta san me ya wakana ba tun bayan Zuwan ta
kaduna, ko da ta ishe shi Kan tana kiran wayan Mamin ta a kashe sai yace taje
India Medical Checkup, kuma Dr ya bata rest so ko waya bata amfani da shi, ta
yarda dashi don ta san be mata karya, kafin yace wani abu tuni ta fita daga
motar, ta na kiran "Hamma Rafeeq i'm home" da karfi ta ke maganan,
Gaban Rafeeq ya fadi jin muryar Rafee'ah, be san lokacin da ya shige toilet ba
ya wanke fuskar sa don kar ta ga damuwa itama ta tada nata hankalin.
Cikin gida ta shige ta na fadin wai ya na ji Gidan shiru ne?
Ba kowa ne? Alhaji Habib ya fito yana Oyoyo Baby, hajia Sauda tana biye dashi a
baya, da sauri Rafee'ah taje ta rungume Daddyn ta tana "Daddyna i've
missed u" daga ta yayi sama yana juyi da ita kamar wata baby ita ko tana
ta daria. Ya direta yana "i missed u more my angel" taje ta rungume
Sauda, Sauda na ta murmushin munafurci tana "haba ai gwara da Zaid ya dawo
da ke, tunda ya dauke mana ke gidan ba dadi" ita ko Rafee'ah sai
k'yalk'yala daria take yi, tace ina Aneesa? Sauda tace tana chan BUK wurin
kanwata, zuwa k'arshen wata zasu dawo" Daddy yace ya Safiyya(Matar Zaid)?
Rafee'ah tace "Daddy ta na nan lafia, ta kusa haihuwa ma" Allah ya
raba lafia. "Daddy wai ina Uncle Hafiz da Hamma Rafeeq?" Daddy yace
Uncle dinki na Yobe na aike shi, Rafeeq kuma na Dakin shi. Tace "Ohh yana
jina yayi shiru ya kyale ni ko? Barin je in iske shi" ta sauka k'asa tayi
hanyar dakin Rafeeq.
Tunda daga waje take kiran "Bigbro Rafeeq, wai ba zaka
fito ka ganni ba? ta kutsa kai cikin dakin, turus ta tsaya ganin Rafeeq zaune
kan kujera sanye da Bak'in Gilashi, mamaki ya baiyana fuskarta, da sauri ta je
ta rungume shi, ganin yanda ya mata ne yasa ta dagowa da sauri, "Hamma na,
baka ganni ba? A hankali yace "naganki, Rafee'ah" baka yi murnan gani
na bane? Shiru ya mata, ta dinga mishi tambayoyi be bata amsa ba, Ga mamakin ta
sai ganin hawaye tayi ya gangaro kan kumatun sa, cikin rudewa tayi saurin zare
Gilashin idonshi, tace "mai ke faruwa ne? Baka da Lafia ne?" Daidai
nan Zaid ya fito daga toilet din dakin yace "Rafee'ah, ki rabu dashi, be
da lafia ne, kuka ta fashe da tace be da lafia? Wani irin rashin lafia ne wannan?
Uncle Zaid ko kallona fa beyi ba, Hamma da kullum ya ganni burinshi ya takura
min, ya nemi tsokana na, tunda na tafi Kd be kirani ba, idan na kirashi beya
dauka, and yanzu kuma na dawo irin welcome din da zai min kenan? Ko kallo ban
ishe shi ba? Ina mai magana ko tanka ni beyi ba? Uncle Zaid ko wani abu yace
"na mishi?" da sauri Rafeeq ya rungume kanwarshi ya na kuka itama
tana kuka ama ya kasa ce mata komai, sun ba Zaid tausayi, da sauri ya rabasu
yace "fee'ah tashi ki shiga ciki" ba musu ta fita daga dakin tayi
sama, Zaid ya kalli Rafeeq, yace "if you really dont want her to find out,
then be yourself" yana kaiwa nan ya kabbara Sallah don ya san bazai samu
amsa daga bakin shi ba. Yana idar da Sallah ya kalli Rafeeq yace "muje
cikin Gida" Rafeeq ya dago ido ya kalleshi zaiyi Complain amma maganar ta
mai nauyi, Zaid yace "ina jiranka" yayi gaba ya bar shi Zaune be da
niyyar motsawa".
Aunty Yaushe Mami Zata dawo? Kafin Sauda tayi magana Zaid
dake shigowa Parlorn yace "nace miki sai taji Sauki, Dr ya bata bed rest,
soon zata dawo" ya karashe maganar yana me kallon Sauda yana mata inkiya
da ta goyi bayanshi, sai a yanzu ta gane dalilin da yasa dazun Rafee'ah ba tace
ima mamar ta ba, wato sun boye bata, aiko ba zai sabu ba, sai ta samu hanyar
fallasa mata. Zaid yace "Aunty ina Yaya?" tace "yana nan Office
in kusa da dakin shi" Zaid yace da Rafee'ah "ki shiga ciki ki kwanta
ki huta" ta mik'e ta nufa daki. Sauda tayi Parlorn Alhaji Habib, Zaid ya rufa mata baya.
Yana zaune, Zaid ya gaishe shi, Alhaji Habib yace
"Engineer har an iso? Ya hanya? Ina aka tsaya ne sai dai na ga shigowar
yar gidanka? Zaid yace "Alhamdulilah, Ina Dakin Rafeeq ina Sallah"
Alhaji yace "hmm lamarin Rafeeq sai gaba yake k'arayi, bansan me na mishi
ba" Zaid yace "ba ka mishi komai ba, lokaci kawai yake buk'ata
maganar shi ce ma nake so muyi" kamar an jefo shi ya shigo parlorn, yayi
Sallama amma Zaid kadai ne ya fuskancin Sallama yayi, ya samu wuri ya zauna
kusa da Zaid, Zaid ya tsura mai ido yana mai nuni da ya gaida Mahaifin shi da
Auntyn su, fuska yayi yaki kallon side dinsu. Zaid dai ya san bazai tanka ba ya
juya ga yayan shi yace "Rafeeq dama na kiraka ne nan gaban Ubanka mahaifi,
shawara zamu baka, ba mu da gatan da zamu maka da ya wuce Addua da Shawara, kai
Baligi ne kasan ciwom kanka, kasan abun da yake daidai kasan wanda ba daidai
ba, kasan fari kasan bak'i, Rafeeq Abun da ya faru ina so Ka dauke shi a
matsayin kuskure, Kaddara, ka rungume kaddararka, Kai musulmi ne, ba wai nace
ka yafe ma mahaifiyar ka bane, so nake ka gano gaskia ka gane kurenka dukda ba
laifinka bane, shisa kaga na daina takura maka da maganar ta. Alhaji Habib da
matarshi dai ba su ce komai ba Zaid ya cigaba da cewa " Well this is not
about your mom. Its about you, ina so ka maida hankali ka fara last semester din
nan naka da kyau, yanda kowa ke Alfahari da kai kar ka bamu kunya, kamar yanda
kake yi da, make us proud like always, ka fita da first class dinka that you
truly deserve kajih?" Rafeeq kallon window kawai yakeyi, be tanka Zaid ba.
Don dai ya sa Rafeeq
Farin ciki Zaid yace "kuma zan siya maka mota son ranka, ka fadi wanda
kake so Gobe ka ganshi a gidan nan" nan ma be ce komai ba, Hakan yasa
Alhaji Habib yace "toh nima Uncle din Yara baza a barni a baya ba, nima
ina da kyautar da nakeso in ma Rafeeq" ya mik'e ya fita duk suka bishi da
ido gaban Sauda ya fadi tana ta tunanin meye kyautar da Alhaji zai ma Rafeeq,
Jim kadan sai gashi ya dawo da wasu files ya zauna, yace "Sauda da Zaid
kuyi shaida, Kafin a samo Shaidu,
Companyn Tie and Dye na Sokoto, da Hide and Skin na Keffi na Mallaka ma
Rafeeq, ko na mutu ba su a cikin Gado, kuma da ka gama Service, komai na other
Companies dina zasu dawo k'arkashin ku kai da Rafee'ah, Zaid ya washe Bakih
yace kai MashaAllah, Angode Allah ya k'ara girma" Sauda kuwa Ba tasan
duniyar bakin cikin da ta lula ba, kiris ya rage ta fashe don ta kumbura, ta
kasa boye bakin cikinta da hassadar ta.
Amsa Rafeeq, Alhaji ya miko mishi Files din, Zaid ya mai
Alama da ya amsa, kamar ba zai karba ba ya sa hannu ya amsa a hankali yace
"nagode" Daddy yace tashi kaje ka adana. Kamar jira yake ace yatashi
ya tafi ya mik'e da sauri, Files din ya mik'a ma Zaid, Zaid ya sa hannu ya
amsa, yana bashi ya fita daga Parlorn. Zaid ko Farinciki yake tayi. Sauda kuwa
ta na hada hanya don ta daina gani saboda bakin ciki ta fita.
Daki ta fada ta fashe da wani irin ihun takaici, ta daura
hannu a kai, na shiga uku, Alhaji har ya fara rarraban kamfanonin ka? Be sakani
cikin lissafi, wato daya gama Sabis zai maida komai karkashin sa shi da kanwar
shi, ni kuma da tawa diyar oho, wallahi ba zai sabu ba, sai inga ta inda zai
gama makarantar balle yaje service din har ya zama wani tsiya , ita kuma
Rafee'ah sai ta tsani kanta, don boka na kan tudu zan sa ya Sa Rafeeq ya mata
Fyade, ko kuma ta zama karuwar Yayanta, sai in ga ta inda zasu zama abun
Alfahari ga mutane. Sai kowa ya tsanesu, shima Alhaji ya tsine musu ya koresu
daga gidan shi, su shiga duniya, sai ya rage daga ni Sai diyata sai muci
karenmu ba babbaka ta sa shewa kamar wata zararriya da sauri ta ciro wayarta ta
latso number Boka na kan tudu ta labarta mishi plan dinta. Yace "Saude
wannan magana ba ya waya bace ki zo Gobe kawai sai a duba" tace "to
na kan tudu, ka tsumayi zuwa na gobe, da Asubar fari zan taho".
Bibilicious Biebee
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
*Allah Sarki
Yanuwa da Abokan Arzikki, da Masoya❤
duk na ga sak'onnin Ta'aziyoyin da kuka min, nagode Allah shi karb'a, ya biya
ku, shikuma mamaci Allah ya ji k'anshi (Baba Hashimu) Allah ya gafarta mishi,
Allah kasa ya huta. Da duk Musulman da suka riga mu Gidan Gaskia, mukuma in
tamu tazo, Allah ya sa mucika da kyau da Imani Amin, Nagode Nagode Nagode,
Allah ya barmu tare.👏🏽👏🏽👏🏽.*
Pg3⃣5⃣
Firgici da tsoro suka ziyarci zuciyar
Nasiba, ta fara karkarwa, ta na ja da baya, baki na rawa tace
"Fa+ta-talwa" Rafee'ah ta yi saurin cewa "DonAllah kar ki ji
tsoro, banda niyyar cutar dake, ke musulma ce, kuma kinyi Imani da hakan, karda
ki sa ma ranki ni Fatalwa ce, ni ba Fatalwa bace, da iko da k'uddirar Allah
nazo miki a Mafarki, Mafarki kike yi dani, DonAllah ki kwantar da hankalin ki,
banda niyyar cutar da ke .(Mu sani Ba Fatalwa a musulunci, Wanda ya mutu ya
mutu, ba yanda matacce zaizo cutar da kai, in ka ga Mattace a ido, to gizo yake
maka, ko kuma kayi mai mugun abu kafin ya mutu, ka sa ma ranka ne,shine kake
ganin kamar zaizo maka, amma Tabbas ana mafarki da Matattu, _to Nasiba dai
Mafarki takeyi da Rafee'ah_.)
Nasiba ta sauke numfashi, hankalin ta ya dan kwanta, Sai da
Rafee'ah ta ga Nasiba ta samu natsuwa sai tace "Kamar yanda nace, ina so
kin dan wanene Rafeeq, ina so ki shiga Rayuwar Rafeeq, ina so ki sauya duk wani
abu da ya danganci Rafeeq, ina so ki warware zare da abawan cikin gidan Lema,
akwai abubuwa da yawa da zaki fuskanta, akwai hadari a cikin wannan aikin, amma
ki sa Allah a gabanki, ba zai barki ke kadai ba, sai kin jure kin daure".
"Bazan iya ba, ni ala musuru ce? Da
zan miki duk wadannan abubuwan? Saboda mene zaki dinga bibiyata cikin mafarki
kina sani abubuwa?" inji Nasiba, Rafee'ah ta nuna ta da yatsa, tace saboda
*"KE ALHERI CE"* cikin rashin fahimta Nasiba tace *"NI ALHERI
CE?"* Rafee'ah ta gyada kai tace *"Eh, KE ALHERI CE"* ba za ki
gane ba yanzu, amma a sannu zaki fahimci dalilina na ce miki haka, ta dan
sasautar da murya tace "Nasiba, Rafeeq yaya na ne ina sonshi sosai,
Rayuwar shi na cikin 6ata, ki taimake ni ki min wannan aikin, Allah kadai zai
biya ki" Nasiba tayi shiru tana tunani, tabbas ita shaida ce kan halin Rafeeq
na Shariya, da k'yaliya, itana tana kwadayin jin labarin shi, kuma tasan tabbas
yana cikin damuwa, chan tace "Shikenan, Allah ya mana jagora" dadi ya
lullube Rafee'ah, tace "Nagode Sosai, but one more thing, you must not
tell anyone about your Dreams and your Mission, kar ki gaya ma kowa, komai kusancin ki da mutum, ki
min Alkawari kinji?" Nasiba tace "InshaAllah ba wanda zai sani"
Nagode sosai, ki fara binciken ki da wuri, ba mu da lokaci" Rafee'ah tace
"InshaAllah". Rafee'ah ta mata sallama ta tafi, daidai nan Nasiba ta
sauke ajiyar zuciya me nauyi cikin bacci, gyara kwanciyarta tayi.
_7:50am_
"Nene yi
zaman ki, barin je in siyo k'osan", aa Seebi budurwa dake sai a ga kin
tsaya bakin titi siyan k'osai? Yo meye? Wa ke bina bashi?" ni zanje, ba me
bina bashi" Nene tace "kawai sai a ga yar budurwa kamar ki na bin
layin k'osai?" Nasiba tace "ni kuma gani mara tausayi, kina fama da
Masassara don kar ace gani budurwa, sai in barki kije siyan k'osai, to ba dani
ba, kinga tafiya ta" Nenen tace "ai sai kiyi, tun yaushe zazzabin ya
sauka?" Nasiba ba ta tsaya tanka ta ba ta fita daga dakin, Nene kuwa ta
dan kishingida, ko minti daya baayi ba wayar Nasiba ta hau ruri, Nene ta buga
tsoki " wani dan anacen ne ke kiran waya da fara saffiyan nan? Sun maida
waya Kamar wata Ramadana, haka ta dinga mita har wayar ta tsinke, chan ta hau
ruri, Nene ta mik'e ta zaro wayar k'ark'ashin pillown Nasiba ta latsa tare da
cewa "Hello" "Assalam Alaikum Seebin mu ni da Nene" Nene
tace "Laaah, Zaidu bawan Allah, Kai ne?" yayi murmushi kamar yana
gavanta, yace "Eh Nene, nine, kamar kinsan kiran nan naki ne" tace
"Allah ko? In ka ji kira Samu ne" yayi daria, yace "Addua nake
buk'ata, an tura ni Ingila wani Aiki, kuma zanyi sati 3zuwa wata 1 a chan,
shine muke barar addua" tace ai addua kullum cikin yinta muke, Allah ya
kareka daga masu jan Kunne" yace "su waye masu jan kunne?"
"Tabdijam! Turawa mana" Dariya Zaid yayi sosai, tace "Af! Daria
na baka ko? Ai turawa muggai ne, sai an hadasu da *Li'ilafi kuraysh*"
Sosai Zaid ke dariya, yasan idsn ya biye ma Nene, haka zata dinga sa shi daria
har yayi missing flight dinshi, yace "nikam ina Seebin mu?" Taje siyo
K'osai da burodi" Zaid tayi dan jim, Nene ta fuskanci shirun Xaid, Ehtace "kai ma kagani ai,
gardama tsiya gareta sai da nace mata ta bari in siyo, tace wai aa, wai ban
lafiya ita zata ta siyo" Zaid yace "baki Lafiya Nene? "Zazzabi
ne ya lullube ni jiya da daddare, amma yanzu ta sauka, na ji sauki"
"Nene ko zakije asibiti? "Kai ni rabani, komi Asibiti, to naji sauki"
yace "to shikenan Nene, ni zan tafi, kice da Seebi zan kirata idan na
sauka" Nenen tayi Murmushi tace "to Zaidun Seebi, Allah ya tsare ya
kare ya bada saa" kiris ya rage dadi ya kashe Zaid, yaji dadin wannan
kalami na Nene, yace "Amin Nenen mu".
*Kaskon Mai K'osai*
Lubbatu mai k'osai
(Sorry Lubie😂) ta shahara gun soyen k'osai, ga dadi, ga tsafta, gaban
kaskonta mutane ne sosai suna jira a soya a basu, Nasiba na daga cikin masu
jira, tayi tagumi daga gefe tana tunanin
Mafarkin ta na daren jiya, tana tunannin yanda zata bullo wa lamarin, taya zata
shiga Rayuwan R-Lema ba tare da taimakon kowa ba? Ta ya zata san ko shi waye ba
tare da ta tambayi Zaid ba? Allah ka kaow min Mafita" sama-sama ta ji
firan Lubbatu mai K'osai, da wani dan datijjo, da alamun Customern ta ne inda
datijjon ke cewa "Ni banga k'awar fada ta yau ba, da ta na nan ba zan gaji
da jiran layin nan ba" lubbatu tayi daria, tace " nima bangan ta ba
yau, da ta na nan da ta dinga mitar har
yanzu ba a soya min nau ba?, ko kuma tace ta rigaka zuwa nan" daria yayi
yace "aiko idan zan wuce gida zan biya gidan ta inji ko lafiya yau ba ta
fito siyen k'osai ba" lubbatu mai k'osai tace "anya Maigadin Gidan
Lema ba da Aminene za'ayi ba?" ya fashe da darian jin dadi yace "ai
na fi k'arfinta" Nasiba da ta yi k'ask'e tana jin su, a ranta ta maimaita
"Maigadin Gidan Lema? Isit possible gidan su R-Lema yake Gadi?" Don
tana da tabbacin wuraren nan gidan su R-Lema yake, kuma tabbas maganar Nenen ta
suke yi, Allah sa haka ma, Don ta fara aiwatar da aikinta tun wuri.
Ba jimawa a aka sa ma Baba Maigadi Gidan Lema k'osan shi,
cikin saa a ka zuba ma Nasiba nata, Baba Maigadi yayi Gaba Nasiba tabi bayan
shi, tace "ina kwana baba?" da faraa yace "lafiya lao
Jikata" haka suka cigaba da tafia har Nasiba tazo gida, zata shige kenan
yace "Jikata dan tsaya?" cikin gidan nan zaki shiga?" tayi
murmushi tace "eh, Baba" yace "ko Aminene na ciki? Na jita shiru
yau bata zo siyan k'osai ba" tace "eh ta na nan, bata ji dadi bane
jiya da daddare " yace "Assha! DonAllah kice da ita, Maigadin Lema na
Sallama" bawai don tana da tabbas ba tace "Baba kai Maigadin su
Rafeeq ne?" ya washe baki yace " Yo eh, ai nine Maigadin su, tun
lokacin Iro Kakan Rafeeq kenan" Murmushin Nasara Nasiba tayi, tace "Baba,
barin maka Sallama da Nenen" ta shige gida.
"Nene ana
Sallama da ke?" Nene tace Sallama kuma? Wanene? Seebi cikin sigar zolaya
tace "bazawarin ki" ke zan saba miki, badai Zaidu bane don yanzu ya
kira yace an turashi Ingila aiki zaiyi wata Guda" Haka kurum Nasiba taji ba
dadi, zata yi kewan Zaid, tace "wani Maigadin gidan Lema" murmushi
Nene tayi tace "Danrainin wayau, nasan zuwa yayi jaje na yau be ganin ba a
gurin siyan K'osai" Nasiba tace "Toufa, har kun saba da Shi, ko dai
ko dai?" harara Nene ta jefeta da shi, tace barin je mu gaisa" Nasiba
tayi saurin cewa aa, barin dai ce ya shigo sai ma in shek'a mana koko, Nene ba
ta ce komai ba Nasiba taje ta shigo da Baba Maigadi.
Bayan sun gama kalaci ya musu Sallama, Nasiba tace
"barin raka ka baba" yace to Jikata, ya kalli Nene yace to
"Aminene, Allah ya kara sauk'i, sai na sake zagayowa" cikin wasa tace
" Idan zaa dawo a dawo da karin ciwo, bawai azo a isheni da dimin surutu
ba" Gabaki daya suka sa daria..
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣8⃣
As promised, This page is for you Aunty Baraka❤❤❤
Washegari Alhaji
Habib yace da Sauda zata raka shi Kano, haushi kamar ya kasheta don tayi niyyan
zuwa gun boka na kan tudu yau, haka suka tafi Kano ba don taso ba.
Rafee'ah ta rada
ta inda zata bullo ma Rafeeq, don har yanzu bata san damuwar shi ba, da ta
matsa ma Zaid sai ya gaya mata, sai yace mata "zaifi kyau ki taya shi da
addua, Shi kadai yake bukata, kar ki tsananta Bincike you might end up hurting
yourself" haka Rafee'ah ta cigaba da shishige ma Yayan ta ko zata samu ya
dawo yanda yake a da, amma shiru ba cigaba, haka zata karashe surutun ta ta
barshi, duk yanda yake so ya dan dinga kula Kanwar tasa hakan ya faskara, abun
ya zame mishi jiki, Yanzu magana ya zame mishi wani gagarumin Aiki, da Zaid
kadai zakaji yana magana, shima be wuce ya bishi da kalma biyu ko uku ba, abun
Rafeeq ya wuce Miskilanci, don abun yayi k'amari har ace be iya shiga cikin
Gidansu ya ci Abincin da Matar Uban shi ta dafa, kai ko daki aka biyo shi dashi
be ci haka zai bar musu shi inda suka aje mishi shi, Be cin abincin Gidan su
kwata kwata, sai dai yaje gun me indomie ya sha shayi, da Zaid ya lura da hakan
sai ya siyo mishi Cupcakes,Biscuits Shortbread da Drinks kalakala ya ajiye mai
a daki tunda yana ganin asaran cin Abincin Gidan su..
Da kyar Maalesh
ya sa shi shirin Makaranta, ba don yaso ba, sai dai kawai baya so su tsaya
gardama da Maalesh, ya shirya suka wuce School, tunda suka isa Sciences aka
zagaye motar Maalesh, Maza da Mata kasancewar R-Lema na kowa ne, Maalesh yace
"Guy, dole ka fa sake fuska, mutanen ka na jiran fitowar ka" be kula
Maalesh ba sai ma dauko wani Bakin Gilashi irin no respect din nan ya k'wama a
fuskar shi, ya bude Kofa ya fita, ji kake ana R-Lema, ko kallo basu ishe shi
ba, tafian shi kawai yakeyi, burin shi
ya ganshi a Class, duk suka bishi da kallo suna mamakin wanna Shariya na
R-Lema, sai duk suka maida kallo ga Maalesh, Maalesh ya shiga raba idanu kamar
yayi K'arya, da k'yar yace "kuyi hakuri, R-Lema na da dan damuwa ne, ky
tayashi da Addua". Mutanen kam suka jinjina kai, da alamu kam, don ba haka
suka saba ganin shi ba, shi mutum ne mai son jamaa, da da ne, da ya fito zai
dinga ba mutanen nan hannu suna gaisawa, ya dinga jan tsokanan yan matan nan,
ana wasa ana daria, lallai dole suke tayashi da addua Allah ya yaye mishi
damuwar shi.
Ai ba Daliban ba,
harta Mallamai sun san da Chanjawan R-Lema, yanda kasan hoto haka yake zaune a
aji, ba motsi, ba kamar da ba, kafin Lecturer ya gama tambaya har ya bada amsa,
amma yanzu ko sun tambaye shi shiru zakaji yayi, bawai be gane abun da ake
koyar dashi bane, tsaf yake fahimta kamar kullum, abunda yake ganin asara shine
ya bude baki yayi magana ko ya bada amsa, yana jin kuiwar magana, kwanaki da ya
ba wani Lecturer haushi koran shi yayi a aji, don ya dinga mishi magana jo tak
Rafeeq be ce mar ba, abun ya ba mutumin haushi ya kore shi, sai da Maalesh ya
je ya sanar da Level Coordinator dinsu, kasancewar Coordinator abokin Zaid ne,
Yazo ya bada hakuri, yace yayi hakuri Rafeeq is Mentally Sick, yayi considering
dinshi tunda kowa yasan ba haka yake a da ba. Da haka aka rufe bakin lecturers,
ko sunzo ba sa tambayan Rafeeq don sun san ba tanka su zaiyi ba.
Duk nacin da
Yanmatan Rafeeq keyi don ya kulasu haka suka gaji suka hakura, don ko sun fi
k'uda k'wak'wa iskar da ya debo su Rafeeq be kallo, Cafteria da da ya maida shi
Gidan Uba, a rana sai yaje so nawa, yaje ya siya ma yanmata abinci, yanzu kuwa
ko kallon hanyan beyi, in ka ganshi cikin Makaranta yana aji, da sun gama
lectures be kara ko minti zai bar ajin don be son surutu, Chan bayan Labs inda
ba ka ganin kowa yake zuwa ya zauna shi kadai. Haka Rayuwar shi ta cigaba da
tafia..
Duk Yanda taso ta
kebe ya je gun bokan ta Alhaji Habib ya toshe, be bata damar zuwa ko nan da
chan ba, ko ina zaije da ita yake zuwa, be barin ta ita kadai, ta rasa yanda
zatayi, haka dai ta hakura har suka karaci kwanakin su a garin Kano.
Bayan Sati Uku
Sauda ta kalli
Boka cikin kunan rai tace "ya zaka ce min hakan ba zaiyiwu ba? Meye ba
zaiyiwu ba? Kaine fa kake share min hawaye na, kai ke biya min buk'atu
na"(Waiyazubillah, ya mu Mata, mu kula, mu lura, aikin Boka na tasiri ne
da Yardar Ubangiji, Boka be Isa Ya biya mana Bukattun mu ba. Allah sa mu dace).
Ta yaya zan ce maka ga abun da nake so kace min ba zaiyuwu ba? Kasan taya na
bar Katsina na zo nan? Ni yanda nake so haka zaayi, Kawai Rafeeq nake so ya
fyade kanwarsa". Boka yace "Saude kar fa ki manta, duk aikin da kike
samu muna miki shi yanda kika buk'ace shi, tunda kikaji nace wannan bazaiyuwu
ba toh ki hakura da wannan, amma na riga na biya miki dayan bukatar hana Yaron
Gama Makaranta" Sauda ta katse shi ta hanyar cewa "yo ni raba ni da
wata makaranta, yo ya gama ina ruwana, ni buk'ata ta shine Alhaji ya tsine musu
duka, kai ni ban k'i su mutu ba" Boka yace
"Ke Saude saurareni kiji, jijsan aiki na kamar yankan wuk'a yake,
ba wanda ya kaini aiki me kyau, na hango miki gaba ne, duk wanda zai ce miki ki
bashi kudi ya miki Aiki kan Mijinki akan 'ya'yansa, to nayi imani kudinki kawai
zasu ci, ba wani mugu a doren k'asar nan da zai iya hada Mijinki da Yaransa ba,
wai shin baki san so da ke tsakanin d'a da mahaifi ba? Kar ki ga kinci nasara
kan Matar shi, kice suma zaki ci nasara, Saude shawara zan baki, idan kika
matsa kan hakan, to Asirin ki na Gaf da tonuwa..
Sauda ta k'ule matuka, ta mik'e cike da Masifa, tace"
kai na kan tudu, kar ka cika ni da wannan soki burutsun, ai baka gaya min Imani
ya fara shigan ka ba, idan ka tsufa baka
iya biya min buk'ata ta sai ka sanar dani, bawai ka dinga ce min hakan bazaiyiu
ba? Ba ka k'ara gani na nan, zanje in samo wanda zai iya min abun da nake
so" ba ta jira amsar shi ba ta fice daga Bukkar.
Cikin Kwanaki 20 Saude ta zabure sosai, duk inda ta san zata
samu bokaye ta bi, burinta Rafeeq ya lalata ma Rafee'ah Rayuwa, sun san aikin
da ta ke so a mata ba me yiwuwa bane amma sunk'i gaya mata sai dai su ce mata
taje Gida zata ga aiki da cikawa, haka zata dawo gida tayi ta jiran tsammani,
shiru takeji, sai ma wani Gatan da Alhaji yake k'ara ma yaran sa, haka zata
chanxa wani boka, Bokaye kuwa sai cin kudinta suke yi, da ta gano su dai tayi
watsi da dukkan su ta zauna gaban Madubi ta na kallon kanta tace "Haba
Saude, sai kace ba mace ba, idan Plan A yak'i ci, sai a gwada Plan B, Wato
K'issa" ba Bokan da zai k'ara cin kudina, cikin ruwan Sanyi zanyi maganin
ku Rafeeq da Rafee'ah..
Bayan Wata Daya
Karatu suke kain da nain, Rafeeq ya dage da Project dinshi,
be kula kowa yake abubuwan shi, kwanaki kadan ya rage su fara Final Exams,
Rafee'ah har ta saba da Shariyar Rafeeq, itama tana ta karatun ta cikin
kwanciyar Hankali, Babban Tashin hankalin ta Mamin ta, ta fara gano akwai wata
makarkashiya, duk wanda ta tara da maganar mahaifiyar ta sai yayi shiru, har
takanas taje gidan Kakanin ta don tambayo idan Mahaifiyar ta take, amma bata
samu amsa daya k'wak'wara ba, sai hanya hanya suke mata.
Yau tace InshaAllah dole sai ta gano gaskiar inda Mahaifiyar
ta take, Bayan ta dawo School ta nufa dakin Aunty Saude, ta tura kofar da
Sallama, Sauda daga ciki tana waya da Meema da Aneesa tayi saurin latse wayar
tana addua Allah ya sa Rafee'ah bata ji me take fada ba. Ta amsa mata
sallamarta, "Rafee'ah sannu da zuwa kin dawo?" "eh Aunty ya
Gida?, kina da lokaci? Akwai maganan da nake so muyi" Sauda tace ohh
Rafee'ah, barin yi Sallah sai inzo muyi magana ko? Rafee'ah tace toh, nima
barin shiga in watsa ruwa".
Sai da tayi wanka
tayi Sallah ta fita parlorn k'asa, Saude ta sauko itama, tace "Rafee'ah,
har kin fito? Tace "eh Aunty i'm just eager to talk to you", Saude
tace "tohfa, what's it about?" Rafee'ah ta rik'o hannayen Saude guda
biyu ta zaunar da ita, tace "Aunty, donAllah ina so ki gaya min gaskia,
duk wanda na tambaya baya bani
gamsashiyar Amsa, ki taimaka ki gaya min, ina Mami na take? Na kusa wata
3 daga dawowa na da kaduna, ba labarinta, kar kuna 6oye mun wani abu, please ki
gaya min".
Cike da makirci Sauda ta fashe da kuka, nan da nan Rafee'ah
ta rikice "Aunty me ya sameki? Ko dai Mami na mutuwa tayi?" Saude
cikin kukan munafurci tace" ko daya Rafee'ah, zan gaya miki abunda na sani
game da Mamin ku, amma kar ki ce ma kowa ni na gaya miki don ba sa so ki
sani" Rafee'ah ta gyara zama tace "InshaAllah" Sauda ta kara
sautin kukan ta, tace "Rafee'ah, ashe maminku yar iska ce? Ashe Magajiya
ce uwar karuwai? Kwarto ta kawo cikin dakin auren ta, Kwartu--" bata
k'arashe zancenta ba taji an sauke mata wasu
kyakyawan mari biyu, a zabure ta dafe kuncinta, ta daga idanuwan ta taga
Rafee'ah tsaye tana huci kamar Zakanya, Sauda ta dago a fusace, tace
"Rafee'ah, ni zaki mara? Don na gaya miki gaskia? Don ma ban gaya miki
gaskian lamarin ba? To kwance a ka ganta haihuwar uwarta da gardi" Wasu
Mari ta sake ji an sake mata wasu na bin wasu, Mamaki ya rufe ta, tabbas ba
Rafee'ah ce tayi marin nan ba, kafin ta ankara taji muryan mijinta Alhaji Habib
cikin daga murya yana cewa "Rafeeq, dont, kar ka sake taba ta" Rafeeq
beji ba illa ma dunk'ule hannun da yayi zai kai mata nushi, da murya karkausa
Uncle Zaid ya kira sunan shi "Rafeeeeq".
_Bibilicious
biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg2⃣9⃣
Fasa nushin ta
Rafeeq yayi, ya sauar da hannu yana ajiyar zuciya, Zaid ranshi a bace, be ji
dadin abun da Sauda tace game da Mami ba, k'ila da shi ke kusa da ita da ya
karairayata, Alhaji ne yace cikin
fada"ke ma dai me yasa kika gaya mata? Tun farko Zaid ya nema Alfarma gun
mu yace kar a gaya mata, do u want to break her? Bakiga yanda abun yayi
affecting Rafeeq ba? kinsan zai yi affecting dinta, maybe worse than Rafeeq, u
shouldnt have told her" Sauda ran
ta ya gama baci, amma ganin Mijinta da
Zaid tsaye ya sa ta fara kukan munafurci, tace "Haba Alhaji kasan ba zan
taba yin wani abun da zai cutar da su ba, ina son su kamar ni na haife su,
Rafee'ah ce ta titsitsiyeni da tamabayoyi.
Rafee'ah ta sake
ihu dakata " Daddy, Uncle Zaid,
Hamma, wai me ke faruwa? Bana fahimtar komai, tell me this is not true, ku
fahintar dani, ku ce mun Sharri aka mami na" kuka takeyi sosai, kamar
ranta zai fita, Rafeeq ya rikota, yace "kiyi hakuri Rafeeah, shiyasa tun
farko ban so a sansr dake, coz nasan cewa u'll be broken" ta dan zabura
kadan, ta ma rafeeq wani kallon da be taba ganin ta mai ba, tace "Me kake
so kace? Ka yarda da sharrin da aka ma mami? Ashe wayon banza ne dakai?"
Da sauri ya kalleta don be tabajin irin maganar nan daga bakinta ba, sam be ji
haushin ta ba, yace "Rafee'ah, i saw Mami with my eyes" da sauri tace
"you must be stupid Rafeeq, da ka manta who ur Mother really is, ka manta
the type of woman she is, ka bari anger yayi controlling dinka, look at you
now, you are miserable" Alhaji yace "Rafee'ah, ki kula da yanda kike
ma Yayanki magana, beyi k'arya ba, tabbas abunda sauda ta fada miki gaskia ne,
Zaid ne ya nemi Alfarman a boye miki saboda kina iya shiga wani hali a matsayin
ki na mace, amma tabbas Mamin ku Kwarto ta kawo dakin aurenta, Mamin ku ta dade
tana cin amana ta" tsananin bacin
rai Rafee'ah ta shiga, tace "whoever believe this is a stupid idiot,
wallahi sharria aka mata, makiri ba ta inda be yin makircin shi, ta daga
hannayen ta sama ta cigaba *amma Wallahi Tallahi Billahi*, _da yardan Allah da
izinin Allah_, _Whoever did this to my mum is going to pay for it_, _ba zan taba
hutawa ba har sai na bi mata hakkinta_ *Ya Allah ko yau na fadi na mutu Allah
ka bani hanyar saka wa Uwata*, *Ya Allah ka amshi addua ta ka bani iko Ameen*
Wani irin dumm Sukaji a jikin su gaba ki daya, gaba ki dayan
su suka ji a jikin su wanna addua ta Rafee'ah karb'abba ce, Sauda hankalin ta
ya tashi matuk'a, Zaid da Alhaji Habib bakin su ya mutu murus, Rafee'ah ta juya
da gudu ta haye sama tana kuka, Rafeeq kuwa hankalin shi ya gama tashi, abun da
yake gudu ne ya faru. Zaid yayi saurin bin bayan Rafee'ah.
Sauda ta dafe kanta takaici goma da ashirin, Yaran Mijinta
sun mammareta a gaban mijinta amma ya kasa cewa komai? Nan gaba k'ila belt zasu
sa mata su mata mugun bugu, wai har Rafeeah ta daga hannu ta mareta, Rafeeq ma
haka. Tabdijam aiko sun tsokalo wa kansu tsuliyar dodo, ita kadai tasan abun da
zata musu, ba shegen bokan da zai ci kudinta wanna karon da kanta zatayi
maganin su once and for all, ita kadai ke ta maganar ta.
A.Habib ya shigo dakin matar shi, tana ganin shi ta fara
murmushi, Alhaji ka shigo, yace eh "Saude, hakuri nazo baki kan abunda
yaran su ka miki, basu kyauta ba" sauda a ranta tace "jar uba, wato
ba zai ban hakuri a gabansu ba don kar suce ya musu ba daidai ba shine ya
biyota daki ko? A fili kuwa tace "haba Alhaji, ni ko daya ban rik'e su a
rai na ba, ai da na kowa ne, na mata uzuri, tana cikin tsoro da rudani, amma
wlh Alhaji bakomai" Alhaji har ranshi yaji dadi, yace "shiyasa nake
son ki, nagode Saude."
Bayan Maghrib
Uncle Zaid ya shiga dakin Rafee'ah da Sallama, ciki ciki ta amsa don tana ji
haushin kowa a gidan, Kan side drawer ya zauna yayi yace "Rafee'ah"
ta dan yi shiru kafin tace "kaima ka yarda da k'azafin da akayi ma Mamin
mu?" Zaid yace "ban tab'a yarda ba Rafee'ah, Mami ba haka take ba"
farinciki ya lullube ta, da sauri ta juyo inda Uncle Zaid yake zaune, ta riko
hannuwan shi biyu tace "Uncle Zaid, ka taimake ni mu gano inda Mami take,
Uncle Zaid so nake a wanke ta daga zargin da suke mata duka, har Daddy ya
maidota dakin ta, Uncle Zaid so nake duk wanda yake bayan wannan manakisar ya
wahala, ya wulakanta, Uncle Zaid ka taimake ni" Zaid ya sauke gwaron
numfashi yace" Rafee'ah its not easy as u think, Wallahi ba inda ban neme
Mamin ku ba, a wani zuciyata ta bani she's safe, only if i know where i can
find her, zan fi kowa jin dadi" Rafee'ah tace "Uncle Zaid, dole mu
nemo Mami, Zaid yace "toh Rafee'ah ta yaya?" tace muje mu ga Baba
Alhaji (Baba Tj) na fi zaton yasan inda take" Zaid yace "wallahi nafi
sawu nawa yace shima nemanta yake" Rafee'ah ta mik'e ta zura Hijab dinta
tace "Uncle Zaid, i dont believe baba Alhaji, i have a feeling he's hiding
something". Zaid yace "lets go findout" a tare suka bar Dakin
don zuwa gidan Kakan su Rafeeq.
Rafee'ah ta
durkusa gaban Kakanta, tana kuka kamar ranta zai fita, tace "Baba Alhaji,
mesa ba zaka gaya mana inda Mamin mu take ba? Haka kake so mu cigaba da rayuwar
mu ba Uwa? Kua da ranta? Baka ga yanda Rayuwar Rafeeq ya koma ba? Hankalin Baba
Tj ya tashi, cikin in ina yace " wai waya gaya muku na san inda
take?" Rafee'ah tace kaji tausayin mu ka gaya mana, watanni 4 kenan rabon
mu da mahaifiya, please ka fada mana" Baba Alhaji yayi shiru, yace
"nifa ba zan maida ma Habib Aisha ba, har sai gaskia ta baiyana da kanshi,
sai Habib ya bambance. Sai a sannan Zaid yayi magana yace " Baba ba mu na
nemanta bane don ta koma gidan Yaya ba, ina so na tafi da ita gida na ne, na
san duk inda take kadaici ya ishe ta, amma idan ta zauna gidana time to time
zata dinga ganin su Rafee'ah" Baba Tj yace Aa Zaid, zan dai gaya muku inda
take amma bazai yiwu ka kaita gidan ka ta zauna ba, ai akwai matsi da takura ga
ka da iyali" Zaid yayi saurin cewa "Haba Baba,kar fa ka manta ko bata
auri Yaya Habib na ni me kula da ita ne, ma tsare mutuncin ta, donAllah baba
kar ka hanani" Mama tace "gaskia ne Alhaji, ni na amince ma Zaid, ka
fada musu" Baba Tj yace "Hakane, Aisha na gidan Goggon ta dake
Malumfashi tsawon watannin nan, kuma har ta gama Iddanta" Rafee'ah tayi
saurin rugume kakan ta don murna yace "tafi chan kar ki karya ni".
*KUYI HAKURI, ABUNDA YA SAMU KENAN YAU, BA KUMA NAN NA SO
TSAYAWA BA,WANNAN YA FARU NE SABDA WASU DALILAI. INSHAALLAH GOBE DA SAFE ZAKU
GA CIGABAN 29 ATTACHED TO THIS PAGE, DA NA SO BARI SAI DA SAFE, AMMA DA YAKE
NAYI ALKAWARI SHISA, PLEASE BEAR WITH ME THANKS*
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg3⃣0⃣
Saude ce ta nufa
gun Rafeew ta na kururuwa, tana fadin yau mun bonu "Shima ya mutu"
Zaid dake tsaye tun dazun ya kasa motsi sai hawayen da ke bin kumatunshi, ya
tuna inda Rafee'ah ke rok'on shi ya barta ta bishi Malumfashi, da ya hanata
binshi da duk sai yaji ya tsani kanshi, ya share hawayen shi, ya taka har
toilet din Rafee'ah ya dibo ruwa a cup, yazo ya yayyafa mai, Zumbur Rafeeq ya
tashi, Saude mamaki ya lullubeta, ya akayi Rafeeq ya tashi? Daman be mutu ba?,
Rafeeq ya fashe da kuka, tare da Rungume Zaid, "Uncle Zaid, Rafee'ah ta
tafi ta barni, Rafee'ah ta mutu, she was in my room yesterday, telling me she
loves me, Uncle Zaid why didnt i tell her i love her back? Ina sonta wlh Sosai,
ta dawo, i so much hate myself right now" duka dakin suka fashe da wani
irin kuka mai tsumma Rai. Hafiz ne yayi karfin halin cewa sai ayi Gaggawar
kaita makwancin ta, barin je in sanar a gidan Radio, karfe Goma Za'ayi jana'iza,
Alhaji Habib kamar mace kai kadai ya daga. Zaid yace da Hafiz "donAllah
ayi prolonging dinshi zuwa Azahar" Hafiz yace saboda me? "Ai gwara a
kaita gidanta na gaskia" Zaid yace "ina zuwa" ya fita da Sauri,
be tsaya ko ina ba sai gidan Baba Tj, nan ya shaida musu Mutuwar, yace
"Allahu Akbar" Zaid yace "Baba, so nake ka kira Mami ka gaya
mata, Iliyasu ya dauko ta ita da Safiyya, ba zaa kai Rafee'ah ba sai Mami tazo
ta mata addu'a, Ba musu ya lallubo ta a waya, ta dauka da Sallama, Baba "ina
kwana?" ya amsa, yanda taji muryan shi ta tabbatar ba lafia, gaban ta ya
tsanan ta faduwa don tun ran da Rafee'ah ta tafi taji jikinta yayi sanyi kalau.
Yace "ki shirya ke da Matar Zaid direbanshi zai dauko ku ya kawo ku
Katsina" cikin daburcewa tace Lafiya Baba? Waye be lafia? Mama ce?"
yace aa Mamarki na chan daki kalau take" to baba Gaya min na san tabbas ba
lafia" Yan nasihohi Baba ya fara mata kan daukar K'addara, nan ta dago
mutuwa akayi, cikin rawar murya tace "Baba, Rafeeq ya rasu ko?" yace
"aa, ba Rafeeq bane, Yaruwar sa ce" wasu zafaffen hawaye na tashin
hankali suka soma kwaronyowa daga idaniyarta, a hankali tace
"Rafee'ah" Baba yace "itace, Aishatu" _Inalillahi wa ina
ilaihirrajiun, Allahumma Ajirni fi Musibati wa akhlifni khairin minha_ jikinta
ya fara rawa. Ta zube kan kujera, "hakuri zakiyi Aishatu, yau da safe ta
tashi da Amai" da kyar tace "Baba yanzu Safiyya zata taho, ni ba zan
zo ba, ayi gaggawar kai ta makwancinta, _Ubangiji Allah ya yafe ma Rafee'ah,
Allah ya gafarta mata, Allah ya sa chan ya fiye mata nan, Allah ya sa Aljanna
firdaus ce Makomarta_ *Ameen* dif ta datse wayar.
Zaid yace " Baba, ya tace? Tace a kai Rafee'ah a rufe
ta, ba za tazo ba" Zaid yace "aa Baba, ta zo donAllah, barin sake
kiranta" Baba ya dakatar da shi "Aa Zaid, ka barta, chan din zai fiye
mata kwanciyar Hankali a bata Space, shes a mother". Ba dan Zaid ya so ba
ya rabu da ita. Suka tashi suka tafi Gidan Lema.
Mami ta iske
Safiyya a Daki, tace "Safiyya sai ki shirya ko? Tafiya ta kama ki
katsina" yanda Matar Zaid ta ga Mami ta san ba lafiya duk da ba kuka take
yi ba" tace "Mami Lafiya?" tace "Rafee'ah ce ta Rasu"
Inalillahi wa ina ilaohir rajiun tace ta pashe da kuka" Mami tayi saurin
fita daga dakin. Sai da ta ci kukanta ta gode Allah kafin ta kira Mijinta Zaid,
ya tabbatar mata da Mutuwar yace yanzu ma Wanka zaa mata, karfe Goma zaa yi
Janaizar ta. Ya tambaya "ya Mami?" tace "gata nan dai, Allah ya
dora mata Tauhidi, tayi tawakkali" yace "Allah sarki Mami, to ke ki
lallaba ki shirya, Iliyasu ya kawo ki Allah ya kiyaye hanya tace
"Amin".
Bayan tafiyar
Matar Zaid Mami ta fito Parlor, ta zauna ta shiga tunani, Allahu Akbar daidai
nan Suka rabu Shekaran Jiya, ta tuna Yanda Rafee'ah ke ta nannukarta tun zuwan
su Kaduna, yanda bata yarda tayi nesa da jikinta, ta rungume ta ta kwanta kan
cinyarta, ko toilet zata shiga sai ta rike hannun Mami ta jata har bakin toilet
din ashe duk na bankwana ne? Ta tuna lokacin tafiar ta har ta fita ta dawo da
gudu tace Mami kice Allah ya min Albarka, " tayi daria tace Allah miki
Albarka Rafeeah, Allah baki miji Nagari, wanda zai kula min dake" tayi
daria tace "Ina sonki Sosai Mamina" "nima ina sonki Sosai
Rafeeah ta" muje in rakaki Uncle Zaid dinku na waje yana jira. Nan mami ta
fashe da kuka mai tsumma zuciya. Allah ya gafarta miki Rafee'ah, na yafe miki
duniya wa lahira, Allah ya hada fuskokin mu a Aljannah firdaus..
11:00am.
Rafeeq kwance kan Gadon Asibiti, don a Mak'abarta ya sume
yayin da aka Birne Rafee'ah, daga Gidansu zuwa Makabarta yayi suma kusan kala
5, da ance a maida shi gida sai yace shi be yarda ba dashi zaayi Janaizar
Kanwar shi, kafin a rufeta ya suma, bayan an rufeta ma haka, Maalesh ne yace da
Hafiz, Uncle Hafiz barin kaishi asibiti, ya samu hutu a chan, Hafix yace
"kayi dabara Mahmud".
Haka Rafeeq yayi ta zaman Asibiti har sai da aka gana Zaman
makoki, da ya tashi ya fara sambatu zaa mishi Alluran bacci.
Bayan Kwana 3 Rafeeq zaune cikin dakin shi, Maalesh na gefen
shi, dawowan su kenan daga Asibiti, Maalesh ya k'ura wa Rafeeq ido, kallo daya
zaka mai kaji ya baka tausayi, Mutuwar Rafeeah ya mugun girgiza shi, idan an
lek'o yi mishi gaisuwa har mutum ya zauna ya gama maganar shi Kallo be ishi
Rafeeq ba, Maalesh ne ma dai ke amsa gaisuwar, Bayan an watse Maalesh ke cewa
"kai Rafeeq abun ka fa k'ara gaba yakeyi, muma fa duk mun girgiza da
mutuwar Fee'ah, barin ma gaya maka abunda baka tab'a sani ba, Ina mutuwar Son
Rafee'ah, na sota kamar raina jira nayi lokaci yayi in baiyanar mata da son da
nake mata, nayi dakkon sonta da dadewa, amma ta tafi ta barmu, nayi Alhinin
mutuwart amma Sai naga ba abunda ta fi buk'ata da ya wucei Addua, sai na dau
k'addara ya kasance ko da yaushe ina mata addua, toh idan addua take buk'ata,
har mutane suzo don taya ka Addua ka gaza ce musu Amin? Haka akeyi?" kamar
Rafeeq zai yi magana sai kuma ya fasa, ya mik'e don fita daga dakin, ganin haka
Maalesh yayi saurin mik'ewa yace ba sai ka bar min dakin ba, dakin ka ne, nine
zan fita" ya fice ya bar Rafeeq tsaye, yana so yace mai ya dawo amma ya
kasa.
Meema da Aneesa
kanwar Sauda zaune cikin Parlor, tun randa akayi rasuwar sukazo, Zaid ya shigo
ciki, Aneesa ta mik'e da sauri, tace "Uncle Xaid ina wuni?" ya amsa
da murmushi lafia lao Aneesa, kinsha hutu ya kano?" tace Alhamdulilah, ya
k'arin hakuri? Allah ya jikanta, ya Amsa da "Amin" Aneesa sai zungurin
Auntyn ta Meema take tayi, tun shigowar Zaid parlo ta sandare daga zaune, don
farat daya taji Son Zaid ya mamaye mata Zuciya, Sai da Aneesa ta takata da
karfi kafin ta dawo hayyacin ta, da sauri ta gaida Zaid tare da mai gaisuwa, ya
amsa ta tare da cewa "barin hau sama gun Yaya". Ya haye Sama. Meema
ta kalli Niece dinta tace "Omg, Wallahi naga mijin aure, ina sonshi, kuma
sai na same shi ta halin k'ak'a waye shi? Aneesa tayi daria tace " Kanin
Daddyn su Rafee'ah ne, kuma yana da mata" tace "ba mata ba ko Matan
sa hudu sai ya aureni". Aneesa tace "muje dai ki gaya ma mommy".
Sama Suka hau dakin Sauda, Meema tace da yayarta "Sis,
nayi new catch cikin gidan nan, kuma ance K'anin Mijinki ne, nidai na samu
mijin Aure" Sauda ta zaro ido a ranta tana Allah ya sa ba Hafiz bane,
karaf Aneesa tace "Uncle Zaid ne" Sauda ta sake Ajiyar zuciya tace
"Ke wannan ya miki nisa, yana da mata" Meema tace nidai na samu miji,
sai ki min hanyar samun shi" Saude tace "sai ki ja hankalin shi ta
hanyar Kissa" tace "Ahap sis har sai kince, kar fa ki manta wacece
ni" sukayi shewa tare da chafe wa, Aneesa tace Kinga ni in auri Rafeeq, ke
ki auri Uncle Zaid, mummy na auren Daddy, kinga shikenan duniya zata sanmu as
Rightful Heirs to the Lema's property. Duk sukayi daria, Meema tace "shi
kuma Rafeeq din wayei? Aneesa tace "haba Aunty Meema, so nawa zan gaya
miki Rafeeq dan Mijin mommy ne, kuma love of my life, don shi zan aura "
Saude ta kalli Diyarta Aneesa, ta san yanda take son Rafeeq, kuma ba za taso
yin magana gaban ta ba tace "Aneesa je ki duba yanda Rafeeq yake, m sure
he needs someone to talk to" tace "eh wallahi bari inje" ta fita
da sauri..
Fitowar Hafiz
kenan daga Parlorn Alhaji Habib lema, ganin Zaid ya sa shi fitowa, ya dan basu
guri ne don su tamu tataunawa da Zaid, yazo wuce wa, daidai kofar dakin Sauda
yaji tana cewa;
Saude ta kalli
kanwarta tace "Meema, shi wannan Rafeeq din da kikaji Aneesa na magana dan
Alhaji ne fa, wani irin banza yaro ne me baudaden zuciya, wai shi Aneesa ke so,
kinsan kuwa yaron nan har Marina suka tabayi shi da wanda ta mutu?" Meema
ta zaro ido tace "ke haba?, to ke me kika musu,kar kice min baki masu komi
ba? Tace "trust me, ban musu komai
ba time din, illa kara jan su jiki da nayi, sai
Mak'ale ya kawo mun poison, na zuba musu Abinci, poison din ba me
kashewa nan take bane, slowly ya ke cin yan hanji, a karshe sai mutum ya mutu
don gudun zargi, to too bad Rafee'ah din ce kadai ta mutu da alamu shi be ci
abincin ba, amma bakomai shima ba dadewa Zai bi yaruwar sa". Sowa Meema ta
sake tace " shisa nake sonki, nobody dare mess with us" tashin hankali ya rufe Hafiz, Ya bugo kofar dakin da karfi.
Sauda da Meema suka tashi a firgice.
Suna rok'on Allah
yasa Hafiz be ji su ba, wani irin kallon tsana ya bi Saude da Meema, Yau duk me
zai faru sai dai ya faru wallahi, don he wont let this pass, dole ya tona
asirin Sauda, Meema tayi saurin cewa "Uncle Hafiz ina wuni kwana da
yawa" wani irin mugun kallo ya wurgeta dashi, cikin dacin murya ya fara
magana "Sauda ashe rashin imanin ki yakai haka? Wani irin zuciya ne dake?
Shin baki tsoron Allah? Ba kiji komai ba kika kashe innocent soul kamar
Rafee'ah? Kisa fa Sauda? Toh wallahi asirinki ya gama tonuwa, yau din nan xaki
fuskanci hukuma, Duk duniyancin Sauda yau ta rude, ta shiga rok'on hafiz da ya tsaya
suyi magana, ba abunda yake zato bane, yace "baki da hankali, kina nufin
banji me kuka ce bane? Ko ban fahimci abunda kuka ce bane? Ai duk abunda kuka
fada is straight, ba sai na nema wani bayani ba, abu daya kadai zance miki,
dole a zartar da hukunci kanki. "I wont let you keep hurting innocent
souls, i wont let you keep hurting the people i love" ko ina na jikin
Sauda rawa yake, tace "Hafiz Is not that you are saint or perfect, kar ka
manta kai ka kawo ni matsayin da na ke a yanzu, da taimakon ka na shigo gidan
nan, kuma kar ka manta da diyarka Aneesa, think wisely, tona ni barazana ce ga
ruining reputation dinka, kuma if i go down, you go down with me as well".
Hafiz yayi wani murmushi, yace "Sauda kenan, i dont care, ko me zai faru
ya faru, ni nakawo ki gidan nan right? Kuma nine silan barin ki, its time i do
good thing to the people who did alot for me, i dont care about the
consequences, I am Ready, you cannot use me again". Yana kaiwa nan ya juya
don barin dakin, Sauda da Meema a rude suka bishi a baya suna mai magiya amma
fir ya k'i kula su, Parlorn Alhaji Habib ya shiga, Wayam ya gani, ya lek'a
dakin nan ma baya nan, Sauda ta sauke numfashi, Hafiz ya wurga mata harara ya
ciro wayar shi ya danna ma A.Habib Kira ringing daya ya dauka "Hello Hafiz"
"naam Yaya, kuna ina, ni da na barku parlo kai da Zaid" yace "Eh
wallahi, dama Zaid ne ya buk'aci muje Makarantan su Marigayi mu sanar dasu
Rasuwarta" Hafiz yace "Okay, gani nan zan biyoku Umaru Musa din"
Alhaji Habib yace "lafiya Hafiz?" Hafiz yace "sai dai nazo, yau
ranar tonon Silili ne, there are things
you need to know, yau ZAN FASA KWAI" dif ya kashe wayan, Sauda ta rude
matuka, tana ma Hafiz magiya, we can fix this, feez-boy na tuba kar ka min
haka" ai ko kallo bata ishe shi ba ya fice ya bar dakin.
Hannu ta daura a kai ta saka ihu, "Shikenan tawa ta
sameni, karya ta ta kare asiri na ya tonu"
Meema cikin
tashin hankali, don gani take idan asirin Yayarta ya tonu, bata ba auren Zaid
gashi ita kuma har ga Allah ta sama ranta auren shi, cikin bacin rai tace
"Haba sis, dont easily give up, akwai hanyar hana tsaida Hafiz, tunda
yanzu fita zaiyi, kawai ki kira bad boys dinki kice su tareshi su gama mai
aiki" Sauda cikin doki tace "kutt har na manta da wannan hanyar,
hankalina ne baya jikina, bari nayi hanzarin kiran Mak'ale" da gudu ta
fita tayi dakinta ta dailo numbern Mak'ale. Ringing biyu ya dauka "Hajjaju
mutanen makka" ba ta tsaya sanya ba, tace "Mak'ale kana ina?"
yace "gani ta wurin Fatima Shema Housing Estate" Hamdala tayi tace
yauwa, wani aiki nake so ka min, ga Hafiz nan zuwa Umaru Musa University, so
nake ka tareshi, ka kashe shi, i dont want him to make it to Umyuk"
mak'ale yayi shiru yace "haba hajia, wannan aiki da safiyyan nan? Ba kya
tsoron aka mamu? Gashi mu uku kadai ne, ba sauran mu" tace Mak'ale ka
taimakeni, akwai matsala idan Hafiz ya isa Jamiar nan, zan baka Miliyan
Guda" Shewa Mak'ale yayi yace angama "Hafiz Lema ya zama gawa"
tace "yauwa Mak'ale, zaka gane shi ko?" yayi daria yace "baki da
matsala, har kalar motar shi na sani" ya datse wayar Sauda ta sake Ajiyar
Zuciya tana labarta Meema yanda sukayi da mak'ale.
Tuk'i yakeyi
gaban shi na faduwa, ya sha round din Alkalem University ya dauki hanyar
Institutions Road, ya na duba side mirror daidai FCE yaga kamar ana binshi, ko
da ya duba mirror din sosai ya gane fuskan Mak'ale, shine ya fito daga dakin
Maman su Rafeeq a ranar da suka ganta zindir. Nan jikin shi yayi sanyi, tabbas
Sauda ce ta turo shi ya mishi wani mugun abu, gaban shi ya tsananta faduwa, ya
taka giya ya k'ara gudun motar shi, suma su makale suka kara gudu, Hafiz ya
tsorata matuk'a ya zaro wayar shi yayi dialing numbern Zaid "Hello Hafiz
ka taho?" Hafiz yace "Zaid kazo ka taimake ni, akwai wasu masu
bina" SubhanAllah a ina? Gamu nan mun kusa Batagarawa, sai fafatawa
mukeyi, a guje Zaid ya fito daga office din da suke zaune shi da Alhaji Habib
be tsaya mishi bayani ba ya fita, Alhaji Habib ya mik'e, yana kwalawa Zaid
kira, Zaid be tsaya amsa shi ba. "Hafiz kana jina? "Eh zaid ina
jinka" "yauwa i'm on my way" Zaid incase i dont make it-- Zaid
yayi saurin katse shi Hafiz stop, i wont let anyone hurt you gani nan
zuwa" "Zaid listen to me, ina
so ku yafe min, And you cannot trust Sauda" kafin Zaid ya ce wani abu ji yake
kiiiiiiii Alamun cin birkin mota, da karfi Zaid yace "Hafizzzzzz" sai
ji yayi ance "kai fito daga motar nan" Zaid ya kara gudun da yakeyi har ya kai inda
yayi parking motar shi.
Mak'ale suka ma
Hafiz mugun bugu kafin suka tura shi motar su suka bar gurin.
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg3⃣1⃣
A cikin mota suka
lumama Hafiz Wuk'a, bude k'ofa sukayi suka wurgar dashi suka wuce, nan da nan
mutane Suka taru kan Hafiz, Zaid ya fito daga Jamiar ya dinga kiran layin Hafiz
har ya katse ba a dauka, nan ya ga taron jamaa daga gefe, kamar ya wuce sai
Zuciyar shi ta kwadaita mai da ya tsaya, yayi parking motar yq kutsa cikin
mutanen nan, ganin Hafiz yashe a k'asa jini ya sa shi karasawa da sauri, Yana
kwala mai kira, Ya rungume Hafiz a jiki, sai tari yake tayi, murmushin Karfin
Hali Hafiz ya sake da k'yar yace "Zaid, brother, ina neman yafiyar ku kai
da Yaya akan duk wasu abubuwan da na muku, ku yafe min, ka ce ma Aunty Aisha ta
yafe min itama, na san na mata laifi" Zaid kuka yakyi sosai, yana cewa
"Stay Still Hafiz, i'll bring you to a hospital" Jamaa ku taimaka
mana donAllah, Aiko bayin Allahn gurin Suka ciccibi Hafiz, suka kaishi motar
Zaid, Zaid ya rokesu idan da wanda ya iya tuki ya jasu, wani dan makaranta ya
ansa key din, shi da wani gaba, Zaid rungume da Hafix a Bayan mota, tarin Hafiz
ya tsananta, kafin a kaishi asibiti ya amsa kiran Allah, Zaid ya fashe da wani
irin Kuka, Gida ya bukaci su wuce, Alh Habib yai ta kiran Zaid a waya, da kyar
Zaid ya dauka ya gaya mai halin da ake ciki, nan gaban Alhaji ya yanke ya fadi
kasa Sumamme, don har Ranshi yake son Hafiz, DVC din UMYUK ya shiga rudani, da
sauri ya dauko bottle water ya shafa ma Alhaji Habib, Attishawa yayi da k'arfi
ya farfado, Sallalami ya farayi, yana kuka kamar mace.
Gida DVC ya kawo
shi, a tsakar gida ya ga an shinfide gawar Hafiz, duk yan gidan na nan tsaye,
ya tako har gaban gawan ya bude fuskar Hafiz, gashi nan fuskar tayi fayau,
Waiyo Allah, zo ku ga kuka gun Alhaji Habib, Rafeeq na tsaye yana hawaye,
mutuwar Rafeeah ta dawo mai sabo, ga Uncle Hafiz ya rasu, kwana Goma Tsakaninsu
da Rafeeah, Zaid a zaune kusa da gawan yana kuka, Sauda da ke gefe sai ihu take
tayi, Aneesa da ba wani sabawa sukayi dashi ba taji jikinta yayi sanyi, kuka
take kamar ranta (Mahaifi ba wasa bane) Liman yace "ai sai a gaggauta a
mishi sutura akai shi Makwancinsa" da taimakon Baba Tj da Yan Unguwa aka
yi ma Hafiz wanka a Parlon Gidan, cikin Mintuna da basu wuce 50 ,ba aka kai
Hafiz gidan shi na gaskia.
Alhaji Habib fa ya zare, ko Rasuwan Rafeeah be firgita shi
kamar yanda na Hafiz ya gigita shi ba, duk ya bi ya fita daga hayyacin shi, Ya
fara tambayan kanshi? Why are these happening to him? Da sauri yayi Istighfari
da zuciyar shi ta tunasar dashi kar kayi sabo, kai musulmi ne.
Bayan Sati 1
Anyi Sadakar
Bakwai din Hafiz, Zaid zaune da Habib da DPO din Police suna bincike, don ankai
report cewa Kashe Hafiz akayi, Maganganun da sukayi da Hafiz ranar da ya rasu
Suka dawo ma Alhaji Habib, Alhaji Habib da har yanzu be dawo normal ba yace
"nifa da ya kirani, cemin yayi zai biyo Makarantar su Rafeeq, akwai
Maganar da yake so ya gaya mana, har yana ikirarin Yau zai fasa kwai" Zaid
yace "Jim kadan kuma ya kirani a tsorace yana neman taimako gurina wasu na
binshi a baya, wasu da be san ko su waye ba, ina jinsu lokacin da suka umarce
shi da ya fito daga motar" Officer yayi rubutu ya dago yace ko kun san shi
da abokan gaba ko da wanda kuke zargi? Alhaji Habib yace "babu" Zaid
ya tsaiya tunani, Hafiz yace mai he should'nt trust Sauda, to me tayi? Based on
what? He's not sure, so ba zai zargeta ba, amma mesa Hafiz zaiyi warning
dinshi? He has no clue". Officer ya musu Sallama ya tafi don fara gudanar
da bincike. Zaid kuwa ya kudurta a zai fara binciken shi shi kadai, zai kuma
fara da Sauda.
Bayan Sati 2
Zaid ya kalli
nephew dinshi yace "Rafeeq, saura kwanaki biyar ku fara final exams dinku,
Shin Rafeeq ba zaka ma kanka fada ba? Shi ba zaka fara karatu ba, ina da
labarin ko lectures baka zuwa, duk tests din da akayi bakayi ko daya ba,ina so
kayi karatu ka fita da first class, for how long do u want to live in the past?
Its time you move on, please start studying" shiru ya mai be tanka shi ba,
Zaid yace "Feeq, kana fa jina" kamar ba zai tanka ba yace "I
dont want to, i am not ready" Zaid ya dan sassauta murya yace "Haba
Feeq, ka kwantar da hankalin ka ka koma makaranta, kana da hope, kana da what
it takes to acheive your dreams in life, please Rafeeq buckle up" Zaid fa
ya kai Rafeeq bango, cikin daga murya Rafeeq yace" bana son acheiving
komai, my life is already ruined long time ago, i dont have any hope, i dont
want to live anymore, Rafeeah should be here, i supposed to die, i dont wanna
live, i want to die, meyasa da ta sake ziyartar Family din nan ta dauki uncle
Hafiz? Mesa ba ta daukeni ba, ni ke son mutuwa, mesa da Thugs suka zo kisa suka
kashe uncle Hafiz? Ni ya kamata su kashe ba shi ba, i wish Akwai wanda zai
kasheni, or i wish i could end my life" Zaid ya kashe Rafeeq da Mari, ya
nuna shi da yatsa "I didnt raise you as my child to be a non-believer, Kai
Musulmi ne, You act like one, not one who fight with his Destiny, you are
Rafeeq Habib Lema, kuma Dole ka rungumi kaddararka, Makaranta kuwa sai kayi
shi, i've waited for this for so long" Rafeeq ya k'ek'eshe ido yace
"Wallahi bazan yi karatu ba, i dont want to study, i dont want to, idan
kuma ka matsa mun Zan shiga duniya, you will never ever see me again" Zaid
ya tsorata, yayi saurin Rungume shi, yana kuka, "aa, Rafeeq be kai ga haka
ba, na bar maganan ba zan matsa maka ba, please dont leave me i cant live
without you" Jikin Rafeeq yayi sanyi ganin Uncle Zaid na hawaye a kanshi,
wani irin so Uncle Zaid ke mishi, ya dan dago ya share mai hawaye.
Washegari Zaid ya
je Umaru Musa Yaradua University, Maalesh ya mai jagora gurin HOD dinsu, Zaid
ya gaya musu matsalar Rafeeq, yana so a bashi shawara, Level Coordinator na su
Rafeeq yace "Inaga yayi deferring semester din, har sai ya dawo normal, so
that it wont affect his CGPA" HOD yace "Gaskia, ne, Yayi Deferring
Semester din wato zai Jiginar da Semester din, ba wai yayi spilling bane, only
disadvantage din shine, Mates dinshi zasuyi Graduating shikuma zai dawo"
Zaid yace is better ai hakan, InshaAllah zuwa next year din zai dawo normal
self dinshi sai ya zo ya cigaba daga inda ya tsaya" nan suka tsaida
Magana.
Zaid ya samu Yayan shi ya mai bayanin komai, Yayan yayi naam
da hakan, yace to kai Zaid meye plans dinka kan danka? Ina tsoron Zuciyar
Rafeeq tunda har ya iya ikirarin shiga dunia, kar abokanan shi suyi influencing
dinshi, su koya mai wasu halayar" Zaid yace " nayi tunanin haka,
shisa nace za mu danje hutu da shi, zan dauke shi muje Embassy muyi purchasing
Visa" Alhaji Habib yace "hakan yayi, K'ila ya dan washe ya dawo
daidai". Zaid ya sanar da Rafeeq zasuje dan hutu a kasar waje, ya fadi any
country of his choice, Rafeeq beyi wani murna ba don shi a ganinshi be kamata
ace yana jin dadi ba, be ce komai ba, Zaid yace ko muje Dubai, ko London, ko
Saudi? Rafeeq dai be ce komai ba.
Zaid dai ya yanke hukuncin zuwa Paris Bayan sunje sunyi
Umra, ya gama musu komai, ya dauko Hutun Wata 3 a Gurin Aiki, suka wuce Saudi
Arabia da, sai da sukayi kwana 7 kafin suka wuce Paris.
Watan su Biyu a Paris daga shi sai Zaid a daki daya a Gado
daya, Yanzu Ba yabo ba Fallasa, kadaran-kadahan dai, da kyar ya ke bin Zaid
gurin bude ido, Zaid be da wani burin da ya wuce ya ga ya kyautata ma
Rafeeq,hakan ya sa Rafeeq ya sa Zaid a zuciyar shi sosai, yaji duk duniya be da
wanda yake so sama da Zaid, ya sama mishi gurbi a ranshi, shima ya kudurta a
ranshi InshaAllah zaiyi k'okarin kyautata ma Rafeeq.Haka suka dawo Nigeria.
Nigeria ta na nan
yanda suka barta, ba wani cigaba game da binciken Hafiz, ba wani leads, Alhaji
Habib yace a barsu Allah e Zai isar musu, Mayya kuwa Wato Meema, son Zaid kamar
ya kasheta, ba gun bokan da bataje ba ya karkato da hankalin Zaid gareta amma a
banza, da taga ba sarki sai Allah sai ta fara chusa kanta gunshi, tana nuna
maitar ta fili, tuni Zaid ya dagota, amma shi ya datse ma kanshi, shi Mijin
Mace daya ce wato Safiyya. Zaid ya kasance mai taka tsantsan da Sauda, duk da
be ga wani alamun Sauda na da wani hali ba, amma be cin abincinta be kwana
gidan, dadin shi daya ba ruwan Rafeeq da cikin Gidan, shisa yake siyo mishi
abubuwan bukata na kayan kwali da gwangwani.
Zaid ya koma bakin
aikinshi, Mami ta rok'i Zaid da ya nema mata dan karamin Gida, ba zaiyiwu ta
cigaba da Zama a cikin shi ba, da iyalan shi, wata rana zaa gaji da ita, duk
yanda Zaid yaso tankwara ta ya kasa, be da wani choice da ya wuce nema mata
Gida a Malali, tayi Parking ta koma chan, tana me kewan Safiyya da ta sha kuka
ranar rabuwar su.
Bayan wata 1
Su Maalesh sunyi
Graduating, suna ma jiran ayi posting dinsu Service (Bautar kasa).
Rafeeq ya kira
Zaid a waya, Zaid yayi mamakin ganin kiran wayan shi, da sauri ya amsa, kamar
ba zaiyi magana ba Rafeeq yace "an fara registeration, nayi, idan anzo 2nd
Semester zan koma Makaranta" dadi kamar ya kashe Zaid, ya dinga shima
Rafeeq Albarka, yasan yayi hakan ne don shi, don ya sa shi jin dadi, kuma ya sa
shi din".
A yau Asabar Safiyya
Matar Zaid ta haifi diyarta Mace kyakyawa Kamar Rafee'ah, Jini ba wasa ba,
Murna gun Zaid kamar ya rungume Iska, Ranar Suna aka radawa diya Suna Rafee'ah,
yan Katsina sunzo suna, Sanin zasu zo ya sa Mami tak'i Zuwa sunar tayi zaman ta
Gidanta, Rafeeq ma ya zo, ya dauki diya ya rungume yaji sinta har cikin jinin
jikinshi, dadi biyu, Ga ta jinin mafi soyuwar Halitta Uncle Zaid, ga ta da
Sunar Rafee'ah.
Bayan Yan suna sun
watse Safiyya jini ya barke wa Safiyya, ta fara tsinkau tsinkau,Zaid ya tsorata
matuka ya danna kiran Aunty Aisha, suka dunguma suka kaita Asibiti, Nan dai
Safiyya tace ga garin ku nan. Inalillahi wa ina ilaihir rajiun. Bayyana Rudun
da Zaid ya shiga bata baki ne, kowa ya ji mutuwar Matar Zaid Safiyya, sai dai
mu roki Allah ya sa Aljanna ce makomarta.
Zaid ya Zare kamar
zautattace, don yana kaunar Matarshi fiye da tunani, yana tausayin su shi da
diyar shi Rafee'ah-Ayman, Rafeeq da Baban shi da Maalesh sunzo janaizar, sun
sauka masauki, Meema ji take yau Sallah a gunta don ba karamin farinciki
mutuwar matar Zaid tayi ba.
Kwana 3suka tafi,
banda Rafeeq da yace shi zai tsaya da Zaid don yasan yana bukatar shi, kamar
Lokacin suna, Mami bata bari sun ganta ba, sai Bayan da suka tafi ta dawo gidan
Zaid tana kula da diyar shi.
Rafeeq ya fito daga
mota ya shiga gidan Uncle Zaid, Kai tsaye yayi Parlor, Tsaye ya ga Fuskar da ba
zai taba mancewa ba, Fuskar Mahaifiyar shi, tsaye take rungume da jaririya,
Jikin Rafeeq ya hau kyarma, idon shi ya rufe da sauri ya je ya fizge
Rafeeah-Ayman, daga hannun ta, ya rungume ta, Zaid ya mik'e da sauri yace
"Rafeeq" yace "me wannan Matar takeyi a gidan nan? Har ta ke
taba min k'anwa? Zaid ya sausauta murya yace "Shes been here for a while"
Rafeeq cikin bacin rai yace "and you never bothered to tell me? Zaid
yace" coz u never asked, u never wanted to talk about her" Idan har
kana so ka kara ganin kafana a gidan ka, This woman has to leave, bana so in
sake ganinta, kar kuma ki sake daukar min kanwa don kar ta koyi baki da mugun
halinta" Zaid ya kaura mai Mari, ya nuna shi da yatsa" I wont let you
disrespect your mother" Baby ta fashe da kuka, Rafeeq ya rungumeta, be
damu da marin da ya sha ba yace "yi shiru kinji fee'ah, zan samo miki me
raino, mace mai mutunci ba kamar wasu matan ba" Zaid yayi saurin kwace
diyar shi daga hannun Rafeeq, yace "bata da wata mai raino da ya wuce
Mami, ba ta da Uwa da ta wuce Mami, itace Uwarta, duk me zakayi kayi"
Rafeeq ya kalli Mami da fuskarta yayi jazir saboda kuka yace "Ba zaka sake
gani na a gidan ka ba" ya fita a fusace, Mami ta bishi da gudu tana
"Rafeeq, ko kallonta beyi ba" Zaid ka bishi kar ya dauki hanyar
Katsina yanzu, kar wani abu ya same shi" haka Zaid ya bishi a hanya, ya
dinga lallashi, da yake Rafeeq din be iya fushi da Zaid, nan da nan ya sauko
amma dole ya bar Kaduna a ranar ya wuce Katsina a ganin shi zaman shi be da
amfani.
Bayan Shekara
Daya (A gurguje)
Abubuwa da dama sun
faru a shekarar da ta gabata, Kamar yanda Sauda ta sha k'okarin Kashe Rafeeq ta
hanya da dama bata samu nasara ba, har ta hakura ta barshi na wani lokaci, kila
yayi amfani, Daga abubuwan da suka faru, ciki kuwa har da Spilling din da
Rafeeq yayi a Makaranta, an rasa gane dalilin spilling dinshi, don an binciko
takardun shi an ga Yayi passing, an rasa ta ina aka samu tangardan(Ni dai nace
Boka na kan tudu), Rafeeq kuwa ko a jikin shi, dama da Uncle Zaid ya koma
karatu last year, amma yanzu ko sama zata hade da kasa ba me sashi komawa
School, Su Maalesh sun fata bautar kasa.Zaid yayi Mamaki matuka, dole kenan sai
ya sake dawowa? Matsalar shi daya yanda zaiyi convincing Rafeeq ya sake wasting
shekara daya, Sai da Zaid ya hada da kuka kafin Rafeeq ya amince da zai sake
dawowa, da sharadin idan ya sake failing ba shi ba boko har abada, Zaid yayi
saurin Amincewa da hakan, a ganin shi Wannan karon akwai nasara.
A wannan karon ne Seebin Nene suka Shiga Jamiar Umaru Musa
Yaradua.
*Wacece Alheri?*
Ta yaya ta zama Alheri?
*Shin Sauda zata cigaba da Samun Nasara a duk abunda ta sa
gaba?*
*Rafeeq na tava dawowa daidai kuwa?*
Da tambayoyi da dama da kuke son amsoshin su, ku biyoni
sannu a hankali.
***********
CIGABAN LABARIN.
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg3⃣2⃣
*UMYU Katsina*.
"Nasiba
Muhammad, maabociyan sa nikab, yanzu da hukumar Makaranta tayi hani da sa nikab
sabo da matsalolin tsaro ya zakiyi?" Miemee ce ke maganar nan, ta na yi
tana daria, Ushee tayi saurin shafewa tace "Ahh, k'ila zata daina zuwa
Makaranta, yajin aiki zasuyi ita da yanuwanta Ustazai masu sa Nikab" suka
sake fashewa da daria. Nasiba ta dan harare su, tace ba abun daria bane
"Dollah ku bar dariya, its not like its funny, ni ban ga amfanin hana mu
sa Nikabi ba, idan yan Boko Haram din sun tashi shigowa Makaranta Nikabi zasu
saka?" Miemee ta sake fashewa da wani dariyan tana cewa "Seebi dangin
Shekau" Ushee ta tuntsire da daria, duk suka k'ular da ita, ta san cewa
idan ta biye musu zata iya fashewa da kuka, sai ta tashi ta bar musu Ajin, su
kuma daria taci k'arfin su, sun kasa bin ta.
Tafiya takeyi
tana mita, R-Classes ta nufa, hanyan da tasan ba kowa ta bi, tana ta tafiyar ta
ta na tunanin yanda zata cigaba da zuwa Makaranta ba Nikab taji kamar
K'andagare ya hau ta, wani irin tsalle ta daka sai ta ji ta buge wani abu, a
firgice ta dago, tsoro ya kamata da ta ga R-Lema, yana lulaya goshin shi don
anan ta kaimai karo, ta tattaro nutsuwar ta tace "donAllah kayi hakuri,
K'andagaru suka biyo ni, ban ganka a gabana ba, sannu kaji? rabawa yayi ta
gefenta ya wuce ba tare da yace mata uffan ba, Mamaki ya turnike Nasiba, a
baiyane tace "shi kuma wannan wane iri ne?".
*Malali, Kaduna*.
"Ayman, ga
Daddyn ki" dugul dugul ta tako tana ta washe baki, Zaid ya daga ta ya
wulla ta sama ya chafe, ya rungume ta yana juyi da ita, ita ko sai dariya take
tayi. Mami da ke kallon su tace "ka ga, kar ka sake min d'iya ta
fadi" Zaid yayi daria, yace wane ni
in kada diyar Mami?dariar tayi tace "ashe kana tafe? Ya hanya? Ya yan katsina?
Yace "Alhamdulilah suna ta gaishe ku" tayi dai murmushi don ta san in
banda iyayenta ba wanda zaice a gaida ta, tace "barin dora ma ka abinci,
nasan ka gaji" yace "Wallahi kuwa Mami, Yunwa nikeji banyi breakfast
ba na taho" me kake so kaci? Yace "tuwo miyan kuka" tace
"ahh ba yunwar kakeji ba, tuwo ai zai dauki lokaci" yace
"Wallahi ina jin yunwa, amma ina iya tsayawa har ayi tuwon" tace
"sai dai daddawata ta k'are" ya mike tsaye yace "kar ki damu na
miki tsarabar daddawa da kuka, duk sun bide min mota da wari, Wallahi kiris ya
rage na wurgar dasu, ashe zasu min rana" be jira ta cewarta ba ya fita,
Ayman a hannun shi, har ya bude mota ya dauko ledar k'ullin ya dawo, ya mik'a
mata, ta bubbude tace "Zaid wadannan kayan daga ina? Yace " Wallahi
wata tsohuwa ta bani" Tsohuwa kuma a ina? Yace "a Katsina" tace
Zaid ka santa ne ka amshi wadannan abubuwan? What if shes upto something,
number 1 lesson, u cant trust people?" Yace "Relax, i trust this one,
i trust Nene, yanzu dai ki sa daddawan da yawa, miya ya fi dadi" Mami ta
kwashi ledar ta na mita, tace "yanda na ga dama haka zanyi, in kayi fushi
kayi aure and stop ordering me around" Daria yayi sosai yace "yi
hakuri Mamin mu".
Haka Mami ta gama tuwo miyan Kuka da ya ji busasshen kifi,
Zaid ya ci sosai, yaji dadin Miyar nan, ita ma Mami taji dadin Kukar, daga
jinta sabuwar kuka ce, sai santi suke tayi, Mami ta kwashe kwanukan ta kai
Kitchen shi kuna Zaid yac cigaba da ma Ayman wasa, Yarinya kyakyawa sosai, yar
shekara 1 da yan watanni, idan ka ganta za kayi zaton tayi 3years din nan,
sabida yanda take yar b'ulb'ul da ita, kuma ba wai Nono ta sha ba, bayan
Rasuwar Safiyya Madara ta ke ta sha, NAN kuma aka ci saa ya karbeta, Dangin
Mahaifiyar ta sunso su amshe ta amma Zaid ya hana, yace shima Mamar shi(Mami)
zata riketa, haka suka hakura, Little Rafeeah na zaune tare da Mami a unguwar
Malali, kullum Zaid sai yazo ya duba lafiyar su kafin ya tafi Gidan shi, yana
tausayin Ayman, amma idan ya tuna tana tare da Mami sai hankalin shi ya kwanta
don ya san Ayman ba za tayi maraicin Uwa ba.
*KATSINA*
"Me ya samu
Nasiban Nene na ga ranta a bace haka? ko
shi lapturo(lecturer) din ku ne ya bata miki rai gobe in mishi asubanci inji
dalili?" ba ta san lokacin da ta fashe da daria ba, tace "Nene,
Wallahi Hukumar Makaranta ce wai mu daina sa Nikabi saboda k'asa ba lafia, ana
iya yin Basaja a shiga Makaranta ayi barna" Nene tace "kai sun
kyauta, ba ki san yanda na k'ijinin in ganki da nikabi ba, kamar wacce tayi
k'arya, ke da ba tsiraicin kika fiddo ba, amma duk ki rufe fuskar ki ruf"
Nasiba ta shagwabe fuska tace "Kai Nene, so kike ranar Makaranta ta kodar
dani? Kuma mutane suyi ta kallo na?" Nene tace "ke tafi chan, yo ai
sai ki shafe fuskar ki da hoda, kuma in ta kallo ne ai kin kai a kalleki, yar
jikalle ta jikan Yan Sudan, donAllah ki dinga gyara fuskar ki kamar wannan yar
gayun, Meemo take ko wa?" Nasiba ta fashe da dariya, ta tashi ta yi hanyar
daki tana cewa "Miemee ake cewa ba Meemo ba" Nene tace "ni
rabani da sunan Aljannu, yarinya da sunan ta me dadi Maryam ta koma wata Meemai
ko wace tsiya" ita dai Nasiba daga cikin daki take ta daria, Nene ta
cigaba da Mitar da idan ta fara bata san tsa tsaya ba, "kema Baban ki ya
bata miki suna wai ba a iya kiranki da sunan Yankan ki sai Seebi har ya koya
min nima" a hankali tace "Amma fa sunan fa da dadi, na yan gayu,
Seebi, Seebin Nene" me Nasiba zatayi in ba daria ba. Nene ma ta sa daria
ashe ta na jinta, ta mik'e tana fadin "Uban me ake ma daria cikin
k'urya?".
Maalesh ya fito
daga Motarshi da ya parka ta a haraban Gidan su Rafeeq, Aneesa na ganin shi ta
k'araso da sauri tana yauk'i tana karairaya, Maalesh ya fara mata murmushin da
be kai zuciyar sa ba, " Yaya Maalesh, howfa" yace "Anee baby ya
kike?" Lafiya fa, dama ina so in kara maka tuni kan Yaya Rafeeq, Wallahi
son shi na cinye min yan Hanjina, na rasa me na mishi da ko ganina ba ya son
yi, idan na je gurin shi yanda kasan yaga bak'ar Jab'a, kallon arzik'i baya
min, gashi zuciya ta ta kasa hakura dashi, ya zanyi?" Maalesh da ya k'osa
ta gama maganar ta don warin gashin dokin ta ya cika mai hanci, yace
"karki damu zan mai magana" dadi ya rufeta, kafin tace wani abu
Maalesh yayi gaba.
"Guy
Yane?" Rafeeq ya dago kai ya kalli Maalesh da ya shigo yanzu, da k'yar
yace "Normal" Maalesh yace "ba ka kirani nazo nayi picking dinka
yau ba?" kamar ba zai ce komai ba yace "Da mota naje" "Ohh,
is that so?" nan Maalesh ya shiga bashi labarai, abubuwan da suka faru da
friends din su, har zuwa inda Aneesa ta tare shi, Rafeeq dai be ce komai ba ya
cigaba da latsa wayan shi, Maalesh be damu da shariyan Rafeeq ba don inda sabo
ya saba, wasu lokuttan Maalesh na bashi labarai ne ba don yaji ta bakin Rafeeq
ba, kawai don dai Yayi keeping dinshi Company, kasancewar he's alone, Ba wai
Rafeeq be gane Labaran da Maalesh ke badawa bane, tsaf ya ke fahintar shi, don
wasu lokaci idan Maalesh ya bashi daria ya na dan murmusawa abu kadai ke mai
wuya, Magana. Ya na jin k'yuwan Magana, yana ganin Asaran Yin magana.
"Sis nikam
Nagaji, ya zanyi wai da son Zaid?" Sauda ta kalli kanwar tace "Meema,
dont give up so easily, kafin ki samu abun da kikeso dole ki wahala, kar ki
manta wahalar da na sha kafin na samu kaina a Gidan nan, kar ki damu, ke dai
kawai ki cigaba da jawo hankalin shi" wani Jawo hankali? So nawa kuma? Ai
ni ina ganin idan har na yi Zindir gaban Zaid ba zai ji na burge shi ba"
Sauda tace kar ki damu in ya san wata, be san wata ba".
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
3⃣3⃣
Wannan Pagen Naki ne *Aunty Sady Yar Mutanen Jegal*, Nagode
Da Kaunar da kike nuna min, Allah ya bar Zumunci Amin😘😘.
*UMYU
Katsina*
Kallon wurin da
ta ci karo da R-Lema take tayi da suka zo wucewa ita da su Miemee, kamar ance
ta waiga ta ganshi Zaune kan dakali, ba Waya, ba littafi ba komai da ke taya
shi hira, shi kadai tal, Miemee tace "Lahh, ku kalli Azababben gayen nan
na rannan, Usheey ta kallo shi, Seebi dama shi take kallon, Miemee tace "
Wallahi sai naje mun gaisa" Nasiba tace "Uhm uhm Miemee ina jiye miki
Wulak'anci" Miemee tace "haba Seebi ba kalar mu bane a ke Wulakanta
wa, just watch me" ta gyara zaman rigar ta tana karairaya ta nufi R-Lema.
Kusa dashi ta zauna tana cewa "Sannu fah" kallo daya ya mata ya dauke
kai, Miemee bata damu ba tace na ga kai kadai ke zaune, its seems you are
lonely, shiyasa nace barin zo in taya ka fira. Rafeeq ya tashi tsaye ya bar
mata gurin a ranshi kuwa cewa yayi "wannan ta cika hayaniya" Me
Nasiba da Usheey zasuyi? In banda Daria. Miemee ta k'ulle iyakar k'ullewa, tace
to meye abun daria, cewa yayi yana da lecturers, Nasiba tace "kaii Miemee,
muna fa kallonku, ko A be ce miki ba" Usheey ta kara tuntsirewa da daria,
Miemee da haushi ya kamata ta harare su tace "to sai me?" tayi gaba,
suna daria suna binta a baya don abun ya basu laugh.
*Malali
Kaduna*
"Waalaikum
Salam" Ummi ta amsa Sallamar da taji daga waje tare da fitowa, "Ahhh
Mamin Ayman ce da Ayman? Sannun ku da zuwa" da sauri ta koma ciki ta ciro
tabarma. Mami dake dauke da Ayman a hannu kuwa tana ta murmushi, Ummi ta fito
ta Shimfida tabarma tare da umurtan Mami ta zauna, suka gaisa. Mami tace
"wato Ummin Anan, na ganeki, bakya son shiga gurina ko? Gashi Allah ya
riga da ya hadamu, ko Anan ba kya turomin yazo tayamu fira, ko ba ki san
Hak'k'in Mak'otaka bane? Ummi tayi Murmushi tace " Wallahi ba haka bane,
abubuwan ne sai a hankali, kiyi hakuri zamu dinga shigowa" kafin su k'ara
magana Wayar Ummi dake kan window tayi ringing, Ummi ta mik'e ta dauko wayar, Seebin Nene ta gani a jikin Screen din, ta
dauka da Sallama, daga chan aka amsa, Ummi ina wuni? Ya gida da kowa da kowa?
Lafiya Alhamdulilah, ya karatun ki? Muna tayi Alhamdulilah, toh Allah ya bada
sa'a, ina Anan?yaje Islamia, ina Nenen? gata nan, Nene ta amsa wayar da cewa
"Halo, Dije, ince dai kuna lafiya? "Lafiya lau Nene" Ina
Mahammadu? tace "ya fita" Nene tace "to kice mai jiya kiris ya
rage muyi gobara, wannan abun chanza layi yayi ta k'auri, ni kadai cikin Gida
kamar Mayya, lokacin Nasiba na Makaranta, ina ta bacci kawai naji abu na
k'auri, da kunji sak'on mutuwa ta, ko da ka fito wajei neman taimako sai da na
share kusan minti 30 waje banga ko akuya yazo wucewa ba, sai ga Zaidu bawan
Allah har da mai gyara ya kawon, Na dade ina gaya ma Mahamadu bani son unguwar
nan, ba mutane, wai sai yace "Haka Unguwan yan gayu suke" yo ni ina
ruwana da wata Unguwan Gayu? Yanzu da ba
dan Zaidu bawan Allah ba, da gidan nan ya kone kurmus" Ummi tace
"SubhanAllah, Allah shi kyauta gaba ya kuma kare" Nene ta cigaba da
mitar ta "daidai da burodi idan zaka saya sai ka taka har bakin titi,
k'osai kuwa sai kin ci uwar tafia zaki ga mai k'osai, ni na saba Unguwar mu ta
da, duk lungu da sako akwai mai k'osai, ko tari nayi zaa jini a Mak'ota, nidai
gaskia ba zan iya ba, a maidani cikin Mutane, ba na son Unguwar nan na masu
k'arya". Ummi ta karai da murya tace Nene kiyi hak'uri zan sanar dashi
InshaAllah, za'a samu Mafita". Nene cikin tsegumi tace "Ai gwara a
samu Mafitan, kuma kice--" Nasiba tayi saurin kwace wayar tace
"Laahh, Katin sun K'are" tayi hakan ne don ta san Nenen ta da mita,
idan ta kama zance bata san ta tsaya ba, ko bari batayi sun gaisa da Umminta ba
da kyau, aiko zata sake kiranta da ta k'ebe.
Ummi ta kalli
Mami tace " hakuri Mamin Ayman, ina magana da surukuwa tace, Mami da ta
gama jin Zancen Ummi na waya, kasancewar Wayar China Phone ce. Mami tace "
Bakomai, najita akwai barkwanci, wani gari take ne? Ummi tace tana Katsina,
diyata na chan tare da ita, tana karatu a Jamiar Garin. Mami taji faduwar Gaba
don duk yanda taji an ambaci Katsina sai ta jita wani iri, balle wannan da taji
wani bak'on almari na ziyarta tace "Allahu, Ayman zo mu tafi Gida"
Ayman da ke ta wasa ta gunguro gun Maminta Ummi ta musu Rakiya har bakin kofa.
Bayan Wau 'yan kwanaki.
*Katsina*
Zaid ya shigo
Unguwar su Alhaji Habib Lema da misalin k'arfe 3:30pm, yana tuk'in shi cikin
kwanciyar hankali Daidai Gidan Nene ya tsaya ya parka Motar shi, bari ya shiga
ya gaida Nene, ya fita ya shiga Soron Gidan da Sallama a bakin sa, "Assalam
Alaikum" Wata siririyar murya yaji ta amsa mai Sallamar shi, Hijabi ta
jawo kan igiyar shanya, tana me mamakin yau waye a gidan su? Lek'awa tayi ganin
Zaid tayi tsaye ya, shima kallon ta yakeyi, ji takeyi kamar ta sanshi wani
gurin, shikuma kallo daya ya mata ya gane ta, itace ya taba lift ita da
kawayenta kwanaki, Sansayar Murmushi ya mata yace Seebi? Da sauri tace Ina
wuni? Ya amsa mata, cikin wasa yace
"Me kikeyi a gidan Kakata?" ta zaro ido cikin sanyinta tace
"Nenen ce Kakar ka?" Dariya yayi yace "ehmana" daga ciki
Nene ta fito, Nasiba ke da waye ke ta dumi a waje? Cikin murna tace
"Lahhh, ga Zaidu bawan Allah" da sauri ta rik'o hannun shi har cikin
Gida, tace da Nasiba "ke dauko Tabarma ko darduma" da sauri ta dauko
ta shimfida mai, "Zaidu Sannu da Zuwa, kazo lafiya?" Nasiba dai ta
bisu da kallo, tana ta kallon ikon Allah yanda Zaid da Nene suke ta labartawa,
"Nasiba baki san shi ba ko?" ai Shine Zaidu bawan Allahn da bakina ya
kasa daina ambaton shi, wanda ya taimaka mana randa muka kusa Gobara, Nasiba
tayi murmushi tace "Allah Sarki, Nene ta bani labarin abun da ya faru,
Mungode da taimakon da ka mana, Allah ya saka maka da Alheri" har ranshi
yaji dadin adduarta gareshi, yace ai Seebi mun taba haduwa kece dai ba ki gane
ni ba" tace "ni? A ina?" yace wata rana ba a wuce Sati 2 ba, na
dauko daga wajen Umaru Musa, na a je kawarku wurin Motel, ku biyu kuma kukace
in sauke ku a Salamah, kin tuna? Nasiba ta zaro ido, Tabbas kaine, na tuna,
dama nima ina ta tunanin inda na sanka, nan fira ya barke, idan kaga Nasiba,
Zaid, da Nene na fira sai ka rantse sun dade da sanin juna, Nasibar da ta ke da
wuyar sabo, bata da saurin sabo, sai gashi nan da nan taji ta sake da Zaid,
haka kurum taji Zaid ya samu gurbi babba a zuciyar ta. Sai da Zaid yaci
Burabiskon Da Nene tayi kafin ya musu Sallama ya wuce Gidan Yayan shi.
"Assalam
Alaikum" bakin shi kadai ya kalla ya san ya amsa Sallamar, da ka kalleshi
ka san yaji dadin ganin Zaid, amma ya kasa nunawa, Zaid dai ya Zauna, yace
"R-Lema" da k'yar Rafeeq yace "Sannu da Zuwa?"" yauwa
Rafeeq ya kake? Ya skul? Sai da ya dauke shi Seconds kafin yace
"Alhamdulilah" "Kaci abinci?" kai kawai ya daga mai tare da
nuna mai Ledan take away din da yayi a Crispy. Zaid ya jinjina kai yace
"akwai wata matsala? Ko akwai abunda kake so?" Rafeeq ya girgiza kai
alamun aa, Zaid ya mik'e tare da dafa Rafeeq yace "Good" bari in
k'arasa cikin Gidan isowa ta kenan, Rafeeq bece komai ba, har sai da Zaid ya
kusa barin dakin ya cire baki yace "Ya Rafeeah-Ayman? Zaid ya juyo da
murmushi yace "Shes fine, tana Gaida Yayan ta" Murmushin gefen kumatu
Rafeeq yayi, ya dauke duban shi daga Zaid don kar ya mishi wata magana da zai
bata mai rai (kun dai san Maganar ko? Maganar Mami).
Meema na ganin
Zaid da zuro a guje zata rungume shi, da sauri Zaid ya ja gefe yace lafia?
Cikin kissa tace "Uncle Zee, naji dadin ganin ka ne, nayi ta kiranka ba ka
dauka ba, na Kuma kace mana zaka zo ba, da kyar yace "i was driving"
ya yi saurin hayewa Sama don ya k'i jinin Meema, wani irin warin Man bleaching
da gashin doki takey tayi. Meema taje ta barbade jikin ta da turaren da boka ya
bata, wanda yace "idan har Zaid ya shak'i kamshin, to sai yanda tayi da
shi, Zaid juwa ya shiga ya gauda Yayan shi, Sauda na zaune tace " a kawo
maka abinci?" ya danyi murmushin yak'e yace "aa Nagode" ta kalli
Mijinya cikin Kissa tace "ka ganshi nan Alhaji, ni bansan me na mishi ba
be cin abincina, be taba ci ba, haka zai kamo hanya tunda daga Kaduna, amma ko
ruwan Gidanka be sha" Zaid ya dan wayance yace "Wallahi sai na cika
ciki na kafin nake k'arasowa nan" Alhaji Habib dai ya murmusa yace
"kun fi kusa" yauwa Zaid, ya karatun Rafeeq? Kasan idan be ci Exams
din nan ba Spilling na 3kenan zaiyi ko?Mates dinshi daga masu Service sai masu
Aiki" Zaid yace " Yaya, Rafeeq zaici Exams dinnan da yardan Ubangiji,
this is his last year a School, just have faith" Alhaji Habib yace
"Allah shi yarda" Sauda a ranta tace "sai mu gani" Zaid ya
musu Sallama ya sauko k'asa.
Meema na
ganinshi ta k'araso, Da sauri Zaid ya toshe hancin shi saboda wani irin warin
tashina hankali da ya ziyarcin hancin shi, Meema meye ke wari haka kamar
Jab'a?" tace "Jaba kuma?" Zaid yace "sai anjima idan na
tsaya a nan Kaina zai min ciwo" da sauri ya bar gurin takaici ya hana
Meema bincshi, wai ita ke warin Jab'ar ko turaren? Ta fashe da wani kuka mai
tsuma rai.
*UMYU
KATSINA*
Jugum jugum sukayi
suna neman mafita, Awan su 3 a Library, suna neman yanda zasu yi Solving wannan
Assignment dinsu na Calculus, gashi 5 ta wuce, gashi da Sassafe karfe 8 zaayi
Individual Submission a Office din Course tutor, kuma yace idan suka kwafa na
juna zai gane, Ana tsoron Malamin da Course dinshi kasancewar dangin Maths ne,
ana samun Carry Over da yawa, hankalin daliban da keyi a tashe, ko wannen su ya
dage yana iyakar k'ok'arin shi, gashi 5 har ta wuce, ba yanda Miemee Usheey da
Seebi zasuyi illa su wuce Gida don Maghrib ta k'arato, Miemee tace zata ba
lesson teacher din k'annenta ya mata Solving, Usheey kuma tace " Zata duba
cikin Note book din brother dinta shima yayi Course din lastyear, idan Allah ya
sota ta samu, Nasiba da idon ta ya ciko ruwa ta kasa magana, don bata da wata
mafita, ta tsani CarryOver amma ta sadakas ta fadi course dinnan, dole sai ya
dawo mata Next Year. haka suka wuce Gida.
K'arfe 7 Zaid ya Shigo Gidan, tunda ta gaishe shi bata sake
magana ba ta cigaba da Kallon Takardanta kamar ansa zai fito, Zaid ya zauna
kusa da Nene, yace "yau Seebi boko ake ta sha? Yau ba a ma Nene
Fira?" Nene tace rabu da ita 'yar nema, ka ganta nan tun dazun nake ta
magana ta min banza, tunda ta dawo take ta rubuce rubuce tana yaga takarda, ko
abincin kirki ta kasa ci, shine kagan mu zugum zugum kamar kurma, ina ta Addua
Allah ya kawo mun kai. Yayu daria, yace "Seebi Assignment ne halan?"
tace "Wallahi Uncle Zaid, part of our CA test ne, kuma ban iya ba, tun
dazun nake ta solving amma na kasa, yace "mugani" da sauri ta mik'a
mai ya bude baki "lalala, Calculus, tabdi, ai ko lokacin da mukayi
Calculus da k'yar nayi passing course din yanzu ko ko kasheni zaayi ba zan iya
cewa ga yanda akeyi ba" hawayen da take makalewa suka gangaro, Zaid kadai
ne hope dinta, gashi shima be iya ba, Zaid ya lura da yanayin da ta shiga yace
"yaushe zaayi Submitting? ta fashe da kuka, Zaid ya rude yace " Calm
down ki kin magana" tace "Gobe da Sassafe before 8, kuma individualy
yace don zai gane idan mun kwafa daga junan mu".
Zaid yayi shiru for sometime, wani tunani yazo mai, amma
yana gudun abunda zai faru, amma kuma dole ya taimaki Nasiba don tana bukatar
taimako shikuma yana da halin taimaka mata, ba tare da tunanin me zai faru ba
ya ciro wayar shi ya latso Numbern Rafeeq.
Kamar ba zai daga
wayan ba ya dauka ba tare da cewa komai ba, Zaid yace " Hello Son"
chan k'asa Rafeeq yace "Yeah" yace "kana Ina?" da kyar yace
"gani nan zanje gidan su Maalesh" "donAllah i need your
help" Rafeeq yayi saurin cewa "Menene are you ok?"don yaji Uncle
sounds so serious, Zaid yace "i'm fine, i need you to come back, daidai
kwanar Gida kafin kaje Salamah, Please" be bari yace komai ba ya kashe
wayar shi ya na rok'on Allah ya sa yazo" Nasiba ta tsare shi da idanuwa,
yace "Nephew dina ne, ina ganin Zai iya miki Solving problem dinki"
Dadi ya lullube Nasiba, Mintuna 45 suka shude, ba Rafeeq ba alamun shi, Nasiba
ta damu kwarai, Zaid kuwa ya cire rai da zuwan Rafeeq, don har yace ta miko mai
ya gani yayi trying solving din. Kirrrrrr Wayar Zaid tayi Ringing, da sauri ya
dauka ganin Rafeeq, "Hello" Chan k'asa yace "Nazo kwatacen"
da sauri Zaid ya zura takalma yace gani nan fitowa.
Daga nesa ya ga Rafeeq, da sauri ya k'arasa gunshi,
"Rafeeq thanks for coming" Rafeeq be ce mai komai ba illa binshi da
yayi da ido, alamun ka min bayani, Zaid kuwa yak'i cewa komai don ya san Halin
Rafeeq, yana iya ce mai wata zaiyiwa Assignment yace ba zaiyi ba ko kuma yace
be iya ba k'arshe ya tafi ya barshi, shiyasa Zaid be ce komai anan ba, k'ila
idan a chan ne yaji kunyar Nene da Nasiba ya mata, duk da ya san ranshi sai ya
baci, yace "please ka biyoni, ganin asarar cewa ina zamu?ko me zanyi? Yasa
Rafeeq bin Zaid a baya ba tare da ya ce uffan ba, har Soron Gidan Nene, Zaid
yayi Sallama, cikiciki Rafeeq yayi Sallaman shima Nene ta amsa, Zaid na gaba
Rafeeq na biye dashi kan shi a k'asa, Nasiba na ganin R-Lema tayi Zumbur ta
tashi tsaye, Nene tace "Lahh Zaidu Bawan Allah, wanene wannan me kama da
kai?" kallo ba ta ishe Rafeeq ba, Zaid yace "Rafeeq ba ka gaida Nene
ba" ba tare da ya kalleta ba yace "ina wuni"ciki ciki Nene ta
amsa tana mai wasa, dauke kai yayi ya sauke shi kan Nasiba, kallo daya ya mata
ya dauke kamar be taba ganin me irin halittar ta ba, Rafeeq da ya k'osa yaji me
ye amfanin zuwan shi gidan nan ya kalli Zaid cikin tuhuma, Zaid ya k'i yarda su
hada ido, don yasan shi yake kallo, ba tare da ya kalli Rafeeq ba yace
"Son, Assignment ne ya gaggari Seebi, nima na gwada tawa fasahar na kasa,
nasan you are in good in Calculus, shine nace bari in kiraka ka taimaka mata
DonAllah" Waiyo Allah kuzo ku ga bakinciki kwance kan fuskar Rafeeq ji
yake kamar ya dora hannu a kai ya sa ihu saboda takaici, wai me ya sa Uncle
Zaid ke mishi hakane? Zaid kuwa har yanzun ya ki kallon Rafeeq din balle ya san
halin da yake ciki, "I am sorry" ya furta a hankali don ya san Rafeeq
din shi yake kallo.
(Readers me kuke ganin Rafeeq zaiyi? K'ila tafiar shi zai yi
ba tare da yace musu komai ba, don da Alamu Uncle Zaid ya gama kashe Rafeeq)
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg3⃣4⃣
Kusan Mintinu
Biyu Rafeeq na tsaye, shi be ce komai ba shi be tafi ba, Nasiba ba tayi mamaki
ba, don ta san halin Rafeeq na shariya da k'yaliya, Nene kuwa ido ta sa ma
Rafeeq ta kasa gane me ke shirin faruwa, har Yanzu idon Zaid na kallon Gefe,
Rafeeq da takaici ya gama rufe shi ya hau tunani, tabbas da wani ya mai abunda
Uncle Zaid ya mishi da ba abun da zai hanashi barin gurin, Amma Uncle Zaid ne,
ya fi K'arfin Wulakanci a gunshi, ajiyar zuciya yayi ya mik'a ma Nasiba hannu
kamar me rok'o, Nasiba tace me zan baka? Rafeeq ya dan yi guntun tsaki, Zaid
yayi saurin kallon su yace da Nasiba "bashi question Paper din, da sauri
ya dauko ta bashi, ya amsa ya karanta, a ranshi ya yi tsaki yace Question din
is straight forward, i dont knw why some people are dumb, ba su san komai ba,
ji wannan simple Question din,(ni bibi nace ba kowa bane kamar ka ba dan rainin
wayau) wata zuciyar tace harda Uncle Zaid fa, a ranshi yayi dariya, amma a
baiyane fuskar nan tamk'e tamau.
Kan tabarman ya hau, ya ciro biro cikin wandon shi, ya duk'a
ya fara solving question din, tunda ya fara rubutu be dago ba sai da ya gama,
yana gamawa kuma ya mik'e ya zira takalman shi ya bar Gidan. Zaid ya bishi da
sauri, Nene da Nasiba suka bishi da ido, ita Nene Mamakin Wannan yaron Zaidu
BawanAllah take, a ranta tace ko kurma ne? Nasiba kuwa Mamakin da takeyi yanda
tafi Awa 5 tana kokarin yin wannan Assignment din ta kasa, amma shi cikin
mintinan da basu wuce 7 ya gama komai, lallai ta jinjina mai, shiru-shirun shi
ba a banza ba tunda ya san abunda yakeyi, haka kurum taji Rafeeq ya burgeta, ta
durkusa ta dauki Papern, rubutunshi ta bi fa ido, neatly kamar irin rubutun
Computer, tabi steps din da yabi, taga abun very clear, kawai sai ta tsinci
kanta da Murmushi a hankali ta furta R-Lema. Nene da ta zuba mata ido, tace
"Toooooooh, ke kuma gamo kikayi? Nasiba ta fashe da daria.
Ko da ya fito
har Rafeeq ya kai bakin motar shi, Zaid yace "Rafeeq" chak ya tsaya
ba tare da ya juyo ba, Zaid ya iso har gabanshi yace "ka saurareni, nasan na maka laifi, na
maka karambani, kayi hak'uri" dan guntun tsaki Rafeeq yayi ba dan komai ba
don Zaid zai sa shi magana yace "ka isa da ni ne, bakomai, stop
apologising" ya shige mota ya ja ya bar Zaid tsaye, Zaid kuwa dadi ne ya
lullube shi, lallai Rafeeq is improving, shi a zaton shi fushi zaiyi dashi,
amma Rafeeq ya bashi mamaki kuma yaji dadi, a ranshi yace"Allah ka kawo ma
Rafeeq Sauyi" ya juya ya koma gidan Nene. Ya na shiga Nene ta tare shi da
maganar Rafeeq, "Nace Zaidu Bawan Allah, shi wannan fa?" Zaid yace
"Dan Yaya na ne" Nene tace baya magana ne? Ko kurma ne? Zaid yayi
murmushi yace "yana Magana" Nene tace "to ya na ganshi haka
kamar wani Zararre, ji uban gashin da ya ajiye, ko ni Mace ya fini, shi ko bai
da lafiya ne?" Nasiba ta kasa kunne don jin me Zaid zaice don ta na san
sanni meyasa Rafeeq yake haka, Zaid yace "haka yake, miskili ne" Nene
ta jinjina kai tace "Lallai kam naga Alama, Shekaru na 68 ban taba ganin
Miskili kamar shi ba, ya ci a bashi Sarkin Miskilai" Daria sukayi duka,
Nene tace "Bari in tashi in zubo maka Tuwon Masara miyan kuka da na dafa
maka" Zaid yayi murmushi yace "yauwa Nenen mu ni da seebi
kadai".
_Bayan kwanaki Biyar_.
*UMYU
Katsina*
"Nasiba
Muhammad, MCB 1220" Gabanta ya buga ya fadi a lokacin da Course Tutor ya
sake kiran sunanta a karo na biyu, a hankali Miemee tace "Seebi ke fa ya
ke kira" jikinta ya hau rawa sosai, idonta ya ciciko da hawaye, ai ba inda
zataje, kuce bata zo ba tunda ba sani na yayi ba, cikin karaji lecturer yace
"Where is Nasiba1220?" bata san lokacin da ta mik'e tsaye ba saboda
ya firgita ta sosai, yace "are you Nasiba?" kai ta daga alamun eh,
yace come down here, gabanta ya tsananta faduwa, bata san me tayi ba, k'ila
batayi assignment din ta da kyau ba, jiki na rawa take tafia, all eyes on her,
haka ta daure ta karada gaban stage, karo na farko da ta fara missing Nikabin
ta, ta tsaya gabanshi, ya mika mata Marker bayan Yayi copying Question din da
ya basu, yace "solve this"Nasiba tayi Adduoin ta ta fara rubutu kan
Board, dama tayi mastering Solution din da Rafeeq ya mata, har sai da ta gama
komai, Lecturer ya ciro scripts dinta ya mik'a mata, ta amsa ido ta zaro,
*20/20* tagani murna ya ziyarce ta, yace "give her a round of
applause" Aji ya kaure da tafi raf raf raf. Yace shes the only one that
scored 20/20 apart frm her none of you made it to 15/20, am proud of you"
A hankali tace "thank you sir" ya zaro 2000 a aljihu yace "have
this" da sauri tace "no sir, you dont have to This" ya tsare ta
da idanuwa ta amsa tayi godia, aji suka tafa mata, kamar ance ta lek'a window,
tana lekawa ta ga Rafeeq ya zo wucewa,
ta kalli Lecturerr tace "excuse me please sir" da murmushi yace Goon
my dear, da sauri ta fita daga Ajin, sauri sauri, gudu gudu ta cimma shi don ta
san ko kiranshi tayi ba zai juyo ba ga idon mutane a gurin, sai da tazo gab
dashi ta mai Sallama, kamar ba zai tsaya ba ya tsaya tarw da juyowa, suna hada
ido cikin in ina tace "Erhm, dama ina son yi maka Godia ne, anyi Marking
scripts kuma nikadai naci 20/20" ta karasa tare da mika mai takardan
hannun ta, ido ya tsareta da shi, ba tare da ya kalli papern ba ya juya zaiyi
tafian shi, da sauri tace "Nagode Allah ya saka da Alheri, Allah ya kara
basira" Chak ya tsaya, ita kuma ta juya ta ta fi, da sauri ya juyo amma
har tayi gaba, ya dade rabon da yaji shi cikin Wannan yanayin, a hankali ya
furta *"Me ke faruwa*?"
*MAFARKI*
"Baiwar
Allah", taji wata zazzakar murya tayi kiranta, Nasiba ta juyo ta
kalleta,sanye take da fararan kaya masu alfarma, fuskarta sai kyalli, tace
"donAllah taimako nake so ki min, idan kika taimaka min Allah zai taimake
ki, Nasiba tace wani irin taimako kike so in miki? Tace "wallah, bashi
naci a wani Shago, wata rana na je siyan lemo lacasera, na bada dubu aka ce ba
chanji, in tafi idan na samu na kawo, toh har yau Allah beyi na kai ba, yanzu
kuma nayi nisan da ba zan iya dawowa in ba mai shago hakkinshi ba, ki taimake
ni ki kai mai Nera 120, kinsan Allah na yafe hakkin komai banda hakkin mutim,
Nasiba tace " bakomai, a wani shago ne?" tace " Masanawa
Supermarket,Umaru Musa" toh InshaAllah zan biya miki, to ya sunanki? Don
yanda zanma mai shago bayani" tace karki damu, kedai kawai ki bada da
niyyar ni ki ka biya ma wa, hakan ya wadatas" Nasiba tace "Zanyi
hakan InshaAllah " tace nagode". Nasiba ta muskuta daga baccin da
tayi, don ta jima batayi mafarki ba, ta koma bacci.
Washegari
Tunda tayi Sallahn Asuba ta dinga tunanin Mafarkinta na
jiya, Neneta lura da ita tace "lafiya Seebi?" Nene nayi mafarki da
wata jiya, tana rokona in biya mata bashin lemun da ta siya, ina so in yi yanda
tace" Nene tace "Sannu Sharifiya, wa yace miki Mafarki Gaskia
ne?" nan Nasiba ta shashantar da maganar.
Tun daga ranar Nasiba ta dinga wasu Mafarkai masu tsoro, sai
in dai bata kwanta bacci ba, da ta kwanta sai mafarkai masu ban tsoro, Yau dai ta tsaya tunanin dalilin mafarkanta,
zuciyarta tace k'ila wannan mafarki na da nasaba da k'in biya ma wannan matar
bashinta, tunda rana daya ta fara wannan mafarke mafarken, dole zata je ta biya
mata bashin, ko ta samu kwanciyar hankali ta daina Mafarki.
Yau ta na zuwa
Makaranta ta wuce Masanawa Super Market, ta ciro dari biyu ta mik'a ma me
shago, yace "me zaa baki?" tace bakomai, wata rana kawata ta zo siyan
Lacsera da dubu kace ba chanji, shine ta aiko ni in kawo maka, me shago ya amsa
ya mika mata chanji, tazo juyawa taji ta taka kafar wani, a tsorace ta dago,
ganin Rafeeq ya sa zuciyanta halbawa, be tsaya bin ta kanta ba ya wuce fridge
ya ciro Soy milk, yazo gun biya ya ciro dari 5 ya bashi, be tsaya karban
chanjin shi ba ya bar Shagon. Me shago yayi Murmushi yace "R-Lema
kenan" Nasiba tace "mallam ka san shi ne?" yace ai ba wanda be
san Rafeeq ba" Nasiba ta matso gunshi tace donAllah kasan dalilin da yasa
yake haka? Yace "da Rafeeq na kowa
ne, da da ya shigo zai dinga ja na da surutu, rana daya ya chanza, ba wanda
yasan dalilin chanjin shi, gashi da k'okarin shi, duk Sciences shine over roll,
amma Shekarar shi 6 a jamian nan, mates dinshi duk sun gana services dinsu, ba
wai be da k'okari bane, aa ba wanda yasan dalilin Spilling din da yake
tayi" Nasiba ta jinina kai tace "abun akwai ban mamaki, amma me ya maida
shi hakan? Yace "ba wanda ya sani, iyakar abunda na sani kenan".
Nasiba a ranta taji tana son sanin me ya maida R-Lema haka.
*MAFARKI*
"Ina
Godia da Biyan bashin da kika min, Nagode, don yanzu na samu kwanciyar
hankali" Nasiba tace toh "Alhamdulilah, bakomai" Yauwa kinyi abu
na farko cikin Uku da na keso ki min, abu na biyu da nake so kimin shine; ina
So ki binciki wani Makwabcin ku mai suna Rafeeq Habib Lema, ina so ki san ko
shi waye, sannan kuma ina so ki shiga rayuwar shi" a razane Nasiba tace
what? Kinsan me kike fada ne? Saboda mene zaki ce inyi haka, baiwar Allah don
na taimaka miki dazun ba shi zai saki ki dinga sani abubuwa ba, ba zanyi ba, ba
zan yi ba, mutumin da ko kallon arziki ban ishe shiba, toh ba zanyi yanda kike
so ba, Musulmi na kwarai shine wanda be shiga hakkin da ba nashi ba"
Yarinyar ta kama hannun Nasiba, kamar zatayi kuka, donAllah ki taimakeni, ki
yarda dani" Cikin masifa Nasiba tace "Sabida mene zan yarda dake?
Bansanki ba, bansan komai game dake ba, kinzo kina sani abubuwa? Toh wannan
karon ba zan tainaka miki ba, kizo kiyi abunda kike sani da kanki, duk nisan da
kike kizo ki yi aikin ki da kanki, idan kinso daga yau ki di ga zuwa min da
mummunar siffa, ki hanani bacci, ba zanyi yanda kike si ba" . Yarinyar
tayi dan murmushi, tace "da zan iya da nayi" Nasiba tace" zaki
iya mana tunda kina tunanin ni zan iya" tace ke zaki iya don kina nan
duniya, ni kuma ba zan iya ba, don bana duniya" cikin firgici Nasiba tace
"me kike nufi da hakan?" Yarinyar tace " *My Name was Rafee'ah
Habib Lema, na Rasu Shekara daya da Rabi da suka wuce*".
_Bibilicious Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg3⃣6⃣
A hanya, Nasiba
ta dinga jan shi da fira, da yake Baba Mai gadi saurin sabo ne dashi, nan da
nan yake bata amsar tambayoyin da ta ke mai, Nasiba a ranta tace "Hanya
Mafi saukake da zan san ko kai waye Rafeeq" Baba mai gadi yace "ke
Nasiba, kinga har kin rakoni Gida, na jaki da yawa" tace "lahh har
mun iso? Ya nuna gidan da yatsa, yace "ga gidan nan" gabanta ya yanke
ya fadi, wani irin Tamfatsetsen gida ta gani, gidan ya hadu, a ranta tace
"So this is where you live R-Lema" Baba yace to ki koma gida Nasiba,
sai nazo gobe, ta dan marairaice fuska tace "Baba nasan Nene ta koma bacci, idan ba damuwa in zauna nan in tayaka
fira" bench ya dauko ya ajiye gaban Gidan, ta Zauna, yayi daria yace wani
irin fira zamuyi? tace "labari zaka ban" "wani iri kenan" a
ranta tace "Astagfurullah Zanyi karya" ta sausauta murya tace
"Baba labarin Rafeeq zaka bani, Makarantar mu daya, da ni budurwar shi ce,
yana sona sosai, amma rana daya ya sauya min, ina son shi kamar me, amma sai
naga ya daina kulani, yanzu ko gani na yayi kallo ban ishe shi ba, shine nake
tunanin ko yaudarata dama chan yakeyi?" da sauri ya girgiza kai yace
" kar kice haka, Rana daya Rafeeq ya sauya ma kowa, Rana daya K'addara ta
gifta ma Rafeeq" Nasiba tace Baba
ka ban labari *Wanene Rafeeq* Ajiyar Zuciya yayi, yace Rafeeq D'a ne kamar
kowa, mai fara'a da son Jama'a, kinji kinji................ Tsaf Baba maigadi
ya kwashe ya bata labarin duk abunda ya sani game da Gidan Habib Lema har zuwa
zaman da sukayi yau. Sosai Nasiba ke kuka har da Majina, lokaci daya tausayin
Rafeeq ya lullube ta, Sam bata ga laifin Rafeeq ba, lallai Rafeeq abun tausayi
ne, Lallai Rafeeq na buk'atar taimako.
Baba Maigadi yace
"Nasiba mun dade zaune a nan, ki tashi ki tafi Gida" ajiyar zuciya ta
sauke tace "Baba, Labarin Rafeeq na cike da Abubuwan ban Alajabi da
Mamaki, da tausayi, baba yanda kasan a fim" Baba maigadi yace a takaice ma
kenan, "zato zunubi amma ina Zargin Matar Ubanshi Saude ga duk wani abun
da ke faruwa cikin gidan nan, ban taba dai ce ma kowa komai ba" da sauri
tace "Saboda me kace haka Baba?" "Saboda randa aka ce an kama
Mahaifiyar Rafeeq da kwarto cikin daki, Saude ta fito ta aikeni siyan Gayen
lataz, kafin na dawo har an saketa, tun daga rannan komai ya sauya, Alhaji be
kara maganar da kowa ba, kinga kuwa beyiwu haka, ko yaya ne sai an maida
magana, amma ko maganar ka mishi zai nuna be ma san wacece Aisha ba, kinga ko
anan akwai ayar tambaya, sai maganar Karatun Rafeeq, makarantan ku daya, ke
kinsan irin kokari da fasahar da Allah ya bashi, amma har yau ya kasa gamawa,
abokin shi Maalesh har ya gama bautar k'asa, nan ma akwai ayar tambaya, sai
maganan Rasuwar Rafee'ah, mutuwa dole ce ta na kan kowa, Ana gobe Rafee'ah zata
rasu, ta fito da Cooler abinci ta fito nan tana zolaya ta, tace dani
"Baba, yau da Hammana zan ci abinci" nace kice sanwa kika ma yayanki
tace "Aa, antu saude ta dafa mana" ta shiga ciki, chan sai ta fito,
nace har kun cinye? Tace "be ci ba ya riga da ya siyo nashi, ni kadai
naci, ko na juye maka sauran a plate? Nace "aa Rafee'ah nagode" washe
gari Rafee'ah tace ga garinku nan. Tunda Aisha ta bar Gidan nan, ban kara cin
komai na Gidan ba, don ba bani ake ba, ruwa Saude bata taba miko min ba, Alhaji
be taba cewa don me baa bani abinci ba, shi da ke ganin girma na da darajata,
Zaid kadai ke min ihsani, da idan kinga yanda muke wasa da daria da Rafeeq,
abun ba aa magana, amma yanzu komai ya jagule, ni Wallahi ina Zargin Saude,
hanalina be kwanta da ita ba". Nasiba ta nutsu ta na jin Zancen baba
Maigadi tace "Allah shi saka ma wanda aka zalunta" yace "Amin"
horn akayi da k'arfi, jiki na rawa yace ina zuwa ya shiga gidan da sauri ya
wangale Gate din, Meema ce da Aneesa cikin wata katuwar Mota, Meema ta harari
megadi tace uban me ya hanaka bude gate da wuri? Yace "kiyi hakuri"
tsaki ta buga ta figi motar da Sauri Nasiba ta ja baya don kiris ya rage su bi
ta kanta. Saida ya kulle gate din ya dawo gun Nasiba tace baba su waye wannan?
Yace "Kanwar Saude ce, da diyarta, in sukayi wani abun sai ki rantse su
'yayan alhaji ne, ita Aneesar naji labari har ta koma Aneesa Habib Lema a
Makaranta" Nasiba ta jinjina kai
tace "baba barin wuce" nan sukayi Sallama.
Tun kan hanya Nasiba ta hau tunanin yanda zata fara wannan
Mission dinta har ta je gida tana sak'a da warwara, ta rasa yanda zata yi, amma
abun da ta kudirta a ranta, Zata taimaki Rafeeq, zatayi yanda Rafee'ah ta
bukace ta da tayi, nan Allah ya cire mata duk wani tsoron abun da zai je ya
dawo, ta san its not an easy thing, amma
haka kurum zuciyar ta ta amince da duk halin da zata shiga, zata yi sacrificing
kanta, she's willing to take the risk, bayan jin ta bakin Baba Maigadi, da
hujjojinshi na Zargin Matar Baban su Rafeeq,komai zai zo mata da sauk'i, nan ta
gane ba Rayuwar Rafeeq kadai zata shiga ba, Rayuwar Gidan Lema gaba ki daya
zata shiga "So help me God". To tambayan shine "Ta yaya zan
shiga Rayuwar su Gaba ki daya?" zuciyarta tace "barin jira Rafee'ah a
mafarki".
Da daddare sai juyi take don tayi Mafarki, amma Shiru ba
Rafee'ah, washegari ma kwatakwata batahi mafarkin komai ba, kwana 3 ta jera
tana jira tayi Mafarki da Rafee'ah amma shiru, tace ma kanta " it seems
like i am on my own, Allah ka taimake ni."
*5:50pm*
"Sannu
Nene" Nasiba tace cikin damuwa, tun kwana 2 da suka wuce Nene ke kwance,
ta rasa me ke damunta, ta k'i yarda suje Chemist, kuma ta k'i yarda Nasiba ta
gaya ma Abban ta, Nasiba duk ta shiga wani yanayi, a iya wayon ta, ba ta taba
ganin Nene tayi ko da ciwon Kai ba, cikin rashin kuzari Nene tace "Wai
uban meye zaki tasani gaba ki zabga uban tagumi kina kuka iyi? Ko kinga na mutu
ne? Nasiba tace "Nene nifa ban taba ganin kiyi ciwo ba" Nene tace da
yake ni Waliyya ce sai in k'i ciwo, ko kullum in banda lafiya sai inzo inyi
kwance kamar wata ke a gurin, to Nasiba ko ciwon Ajali ne me zuwa ma mutu farat
daya, to barin bar miki wasiyya" da sauri Nasiba ta tashi ta shiga daki ta
bar Nene kwance tsakar gida, don ta san Nenen k'arfin hali kawai takeyi tana
maganar nan, kuma idan ta biye mata sai ta sa ta kuka don Bakin Nene ba ya
shiru. Nasiba ta rasa yanda zatayi, ba ta san kiran Abban ta don ta san shi da
damuwa, yana iya kamo hanyar Katsina da Marecen nan, ya zatayi? Bata gama
tunanin ba Wayar ta ta hau ruri da sauri ta dauka + ta gani wato lambar waje
ne, ta dauka da Sallama, a dayan bangaren "Waalaikum Salam Seebin mu ni da
Nene, ya kike ya karatu? Tace " Uncle Zaid, Alhamdulilah, ya Aikin? Yace
"Alhamdulilah, ina Nenen?" kamar jira take ta fashe da kuka, lokaci
guda Zaid ya rude, "me ya faru? Me ya same Nene? Wani abin yake faruwa a
katsinar? Ki min magana Nasiba" daga jin muryar shi kasan hankalin shi a
tashe yake" ta dan tsagaita tace "Uncle Zaid, Nene ba ta da Lafiya,
tun kwana 5 da suka wuce, ina tsoron wani abu ya same ta, ban taba ganin ta
haka ba, amma ta k'i yarda muje Asibiti ko nagaya wa baba na" Zaid yayi
dan shiru yace "no wonder, randa na kira naji muryar ta wani iri, ashe ba
lafia, kuma bata gaya min ba" "ai ba zata gaya maka ba, don Nene wata
irin mata ce me Zurfin ciki, nima don ta kai kuri na san cewa bata jin dadi,
har yanzu bakin ta ya ki mutuwa" Zaid yace "ki kwantar da hankalin
ki, ki tashi kuyi shirin Asibiti aje a dibo ta" Nasiba tace Uncle Zaid
" ba zataje ba, Nene is so stubborn" yace "trust me on this ki
kai mata wayan".
Haka ta mik'e ta
kaima Nene Wayar, Nene ta amsa da Sallama, Zaid ya gaida ta, "lahh, Zaidu
bawan Allah, kaine Ya Ingilar?" yace "Alhamdulilah, ashe ba kiji dadi
ba?" saida Nene ta wurga ma Nasiba harara kafin tace "Kai kalau
nake" "Aa Nenen mu, ga muryar ki nan, ni dai ki tashi ki kimtsa gashi
na turo a zo a kaiki Asibiti, donAllah kar kice Aa" ba yanda zatayi tace
"Toh Zaidun Seebi, tunda yanzu maganar ta kadai kake ji" duk sukayi
daria, ta mik'e da k'yar ta shiga bandaki, yace "Nasiba, ku shirya za a zo
a kaiku Asibiti" tace "Uncle Zaid ina iya kaita, ba sai an zo ba"
yace "don't be silly, zan sake kira inji ya jikinta" dif ya katse
wayar. Nasiba tayi murna, tace "Allah Sarkin Uncle Zaid, Our Guardian
Angel."
A karo na 3 Ya
shiga lalluben layin Rafeeq, sai ya kusa shiga sai ya datse kiran, don yana
fargaban abun da zai ce mai, Rafeeq be son irin haka, amma ya zaiyi? He is his
only choice, chan dai yayi shahada ya sake kiran wayar Rafeeq, ringing biyu
Rafeeq ya dauka ya kafa a kunne ba tare da yace komai ba, Zaid yace "hello
son, ya kake?" kamar ba zai yi magana ba yace " Barka da Yamma"
Zaid yace "Kaci abinci?" "Uhm" kadai yace, Zaid yace
"Rafeeq ka tuna Nene? Wacce kama granddaughtern ta Assignment last week?
Kamar ba zai tanka ba yace "yeah" " she's sick wallahi, she's
been sick for days" a ranshi yace to why are u telling me? Allah ya sa ba cewa
zaiyi inje in gaishe ta ba don ba zuwa zanyi ba, shiru be ce komai ba Zaid yace
"Kaji ai?" da kyar yace "Allah ya bata lafia" "Amin,
Rafeeq i want you to do something for me, DonAllah ka dauke ta ka kaisu
Asibiti" cike da mamaki yace "What??" Zaid yayi saurin kwantar
da kai, donAllah they need help, kaisu Asibiti kawai zakayi, this is all i'm
asking for, Please" dif Rafeeq ya kashe wayan, takaici uwa ya kashe shi,
shi be san meyasa Uncle Zaid ke sa shi yawan magana ba, in banda neman Magana
shi zai kaisu Asibiti? Why they need help, shi First Aid box ne? Kai akwai
Sakel, shi be kai kanshi Asibiti ba zai kai wasu? Ga Maalesh baya nan, to ko
dai ya kira musu Ambulance? Amma Uncle Zaid ya fi k'arfin ya sashi abu ya k'i
yi, be da wani Zabin da ya wuce mik'ewa ya shiga mota.
Daga gidan su zuwa
gidan su Nasiba yayi tsaki yafi dubu, gashi yanzu fi Minti 5 yana tunanin yanda
zai shiga gidan, Kamar yayi kuka, Ya ciro wayar shi ya tura ma Zaid text,
"i'm there" don be son mishi magana a halin yanzu, Zaid yayi saurin
kiran Nasiba, yace "ku fito yana waje" ta shaida mai da yanzu zasu
fita. Ya tura ma Rafeeq da cewa "there are coming now, kindly greet the
sick person please, Please Rafeeq, for me" tsaki ya buga Wannan Uncle Zaid
din yana sani abun da ban yi niyya ba, takaici ya hana shi tsayuwa, ya koma
motar shi ya Zauna" ba ayi minti Daya ba Nasiba ta fito rik'e da Nene, ta
waiga ta waiga bata ga kowa ba, daga chan taga wata jan mota mai bakin Gilashi,
da alamu ba kowa ciki, "to ina wanda Zaidun ya aiko?" "inaga bai
karaso ba, mu koma daga ciki" duk wannan lek'e lek'en da sukeyi Rafeeq na
kallon su, ganin zasu koma ciki ya sa shi yin horn, Nasiba ta juya inda taji
horn, ta ga haske a ta cikin motar nan zuciyar ta ya bata, R-Lema ke cikin
motar chan, ta tsinci kanta da murmushi ko ba komai zata samu ta shiga rayuwar
shi, tace "Nene, ga motar chan" "wanchan mota kalar jini, ga
bak'in windo shi kike nufin mu shiga?" cike da takaici tace "toh, ko
Uncle Zaid din ne zai sa a cutar da mu?" da sauri tace "ni ba haka
nace ba muje muje kar ki kaini gaba" su ka karasa har inda yayi parking,
har yanzu be fito ba, Hannu ta sa ta bude k'ofar baya, Nene ta shiga da Sallama
ita ma ta bita ta shiga ta rufo kofar, Nasiba ta kalleshi tace "ina
wuni?" be amsa ba, shi dai ya tsinci kanshi da cewa "Ya jiki? Sannu
da jiki" Nene ce da fara'arta tace "Naji sauki sosai" be sake
magana ba ya ja motar, cikin nutuswa yake tuk'in shi, Nasiba na karantar duk
wani abu da yakeyi, tausayin shi take ji sosai, ba tasan lokacin da hawaye suka
soma zubo mata ba, tayi saurin sharewa don kar Nene ta gani ta tara mata
mutane, be zarce ko ina ba sai Asibitin K-Dara, ya shiga yayi parking, shiru
shiru be ce musu komai ba, Nasiba tace "Nene anzo fito mu shiga"suka
fito, ga mamakin ta shima ya fito yayi gaba hanyar entrance din, suka bishi a
baya, Nene na mata mitar "shi kuma wannan haka yake dunkum?" Seebi
dai bata ce komai ba, Rafeeq ya tsaya ya yanki kati, ba layi, ya kira Dr Daran,
yace "Baba gamu gaban Office dinka" yace to Rafeeq ku shigo, hannu
kawai ya nuna ma Nasiba Office din ya samu guri ya zauna, Nasiba kuwa ta gane
me yake nufi, ta sake rik'e Nene suka shiga cikin office din, yace kune Patient
din Zaid? Nasiba tace "eh" ai ya kirani ya sanar dani zuwanku"
ya shiga yi ma Nene tambayoyi, da gwajegwaje, kusan Minti 45, kafin yace "
Inna Zamu baki daki, Hawan jinin ki ya tashi" Nasiba ta zaro ido tace
"hawan jini Dr?" meyasa ta samu hawan jini? Yace "Ke kuwa ta
tsufa, ai tsufa ce, don ma jikinta me kyau ne kuma tana regulating din shi,amma
still zamu bata gado don kar ta kamu da Diabetes, don na fara ganin Symptoms
din a tare da ita, kar ki daga hankalin ki, yanzu barin na muku processing
gado, Suka fita waje da Dr din, Nasiba ta leleka bata ga Rafeeq ba, a ranta
tace "ya ma yi kokari da ya kawo mu" Dr ya rubuta aka basu Gado, A ka
kaisu har dakin, Nasiba na tunanin yanda zataje Gida kwaso kaya.
Rafeeq ya shiga
Office din Dr, ashe Sallan Maghrib ya je yayi, ya ga basa nan, Dr yace
"nayi admitting din su ne,suna room 12, HBP ne da ita, and a minor Diabetes,
shine muke so ta samu rest, zan kira Zaid in sanar dashi don yace duk me ake
ciki in kira shi, Rafeeq ya danyi gajeren tsaki yace " Me ake so?" Dr
yace wannan taje ta dauko musu kayan bukatar su, don zasu kai 3-5days, payment
kuma zan tura ma Zaid, Rafeeq yace "a ina zaayi?" yace a gun Cashier,
Rafeeq be sake cewa komai ba ya fita, sai da yaje yayi payment kafin ya fita
daga Asibitin, Jifatu yaje, ya siyo kayan Amfani, Su kayan Tea ne, fruits,
karton din Ruwa, Bargo, Sallaya, da duk wani abun da yasan zasu buk'ata, Rafeeq
shine da tsaywa siyan Kaza, ya koma Asibiti, Irin leburori yasa suka kwasan mai
kayan, yayi gaba suna binshi a baya, har gaban dakin room 12, umarni ya musu da
su shiga da kayan, shi kuma ya juya, daidai nan Nasiba tace Nene barin je in
dauko kayan bukatar mu, don ba musan har yaushe zamu tsaya anan ba, Nene tace
"toh akwai kudin Nape hannun
ki?" eh akwai. Tana bude k'ofa ta
gansu tsaitsaye da kaya nik'i nik'i, ta bude baki, sukayi sallama tace wannan
kayan kuma fa daga ina? Suka ce wanchan ne yace mu shigo da su nan, Nasiba ta
lek'a don tava wasu ke nufi, ga mamakin ta Rafeeq ne yana tafia da sauri, da
sauri ta bi bayanshi, gudu gudu amma ta kasa cimma shi, daga nesa take ta kwada
mai kira tana "R-Lema, R-Lema dan tsaya don Allah" shi kuwa yaji
wannan kiran da ake mai, amma be tsaya juyowa balle ya ga ko waye, a tunanin
shi irin mutanen nan ne da suke binshi a school, be juyo ba balle ya tsaya ya
cigaba da tafian shi, ita kuwa bata fasa binshi ba, ba ta fasa kiran shi ba,
bata damu da yanda ake kallon ta ba, "Rafeeq Please tsaya" wani
tunani ya zo mata ta dan daga murya tace *"Hamma Rafeeq"* Chak ya tsaya, gaban shi ya yanke ya fadi,
Muryan K'anwar shi yaji, a hankali ya furta "Rafee'ah?"...
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE 🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
This Page is
for you Hauwa Nayaya❤.
Pg3⃣8⃣
Yana jin shigowar
ta amma be dago kai ya kalleta ba, illa tada motar da yayi ya ja motar suka bar
Asibiti, ba wanda ke cewa danuwan sa k'ala, gaban Seebi sai faduwa yake tayi,
shi kuwa jefi jefi sai taji ya buga tsaki, ko tsakin me yakeyi? oho! Ga mamakin
ta sai gani tayi ya sha kwanar Unguwar su, tayi saurin kallon shi, sam be san
iskar da ya dauko ta ba, don ko ta gefen ido be kalleta ba kuma yasan Shi take
kallo, daidai gidan su Seebi yayi parking, be ce da ita komai ba, har kusan
minti 3, ganin ba zai mata magana bane yasa ta fita daga motar, tana fita kuwa
yaja motar ya tafi, baki hangame ta bi k'urar motar da ido, shi kuma haka yake?
Yanzu da bata dauko jakkar da ta ajiye makullan gida ba ya zatayi? duk yanda take zaton Rafeeq ashe ya wuce nan,
ya wuce tunanin ta, a baiyane tace *"R-Lema, you are full of
wonders"* zata bude gidan kenan ta hango Baba Maigadi, da sauri ta k'arasa
gun shi, da faraa suka gaisa, yace *"Nasiba, Aminene shiru, dazun da naje
siyan k'osai na biyo tanan na ga k'aton kwaddo, shin lafiya?"* Nasiba
cikin damuwa tace *"to da sauk'i dai, jikin ne, amma tana asibiti"*
*"Allah sarki wani Asibiti kenan?"* *"Asibitin Dr Dara"* ya
tabbatar mata da zaizo, sukayi Sallama ta bude gidan ta shiga, sai da ta share
gidan kafin ta shiga tayi wanka, tana fitowa ta shirya, ta dauki litattafai ta
sa cikin jakka, ta ciro waya ta kira Ushee, ringing daya ta ծauka, bayan
gaisuwa Seebi tace *"Ya Karfe nawa zaa fara lectures?"* *"11
ne"* *"Okay to gani nan zuwa, Allah sa in samu Mota a
National"*(School Bus Stop).
Ta fito ta
rufe gidan, ta fara tafia, tsaki tayi don tasan ba zata samu Napep din da zai
kaita National ba sai ta kai bakin Titi, na Nene tace Unguwa kamar Mak'abarta.
Tafia take da sauri, sai ji tayi mota na mata horn, k'in tsayawa tayi sai ma
saurin da ta k'ara, daga cikin motar yayi tsaki ya k'ara gudun motar har ya sha
gaban ta, kallo daya ta ma motar ta shaida me ita, ta tsura ma Bak'in gilashin
windon motar ido kamar tana ganinshi, shima anan ya samu ya k'are mata kallo,
abunda ya kasa ganewa shine, meyasa take rinewa ta koma mai Rafee'ah? Mesa idan
suna tare yake ji kamar yana tare da Rafee'ah? Ya lumshe idonsa a hankali ya
bude, chan kuma ya buga guntun tsaki. Nasiba da ta gaji da tsayuwa a gun, Har
yanzu dai be fito daga motar ba, be sauke windown shi ba, gashi kuma ya tare
mata hanya, to me ya ke nufi ne? Ko yana nufin ta shiga motar? ta yanke
hukuncin shiga motar, ta yi jihadin bude motar ta shiga, dama abunda yake jira
kenan, ya yi ribos ya dau hanya ba tare da yace mata k'ala ba.
Ya duba agogon
hannun shi, yayi guntun tsaki, k'arfe 10 da minti 10, Lectures dinshi 8-10 ne,
ya tabbatar an gama yanzu, ya maida hankalin shi ga tuk'in sa, Nasiba tace a
ranta *"barin ja shi da labari yanda zai sake da ni"* jikin ta na
rawa a hankali tace *"Hamma Rafeeq wani Course Kake?"* shiru kakeji
ba amsa, a zatonta be ji me tace ba ta bude murya ta sake mai tambayar, guntun
tsaki taji yayi irin kin dameni nan, yayi mata banza ya manna mata hauka, Waiyo
Allah, Nasiba duk tabi ta tsani kanta, tana dana sanin mai magana, ji take
kamar tayu kuka, Allah yaso ta ba gaban mutane take ba, da ta gama jin kunya
don wannan ya kai Dizgi, hawayen ds take mak'alewa suka soma gangarowa, da
sauri ta juya tare da share hawayen tana
kallon window inda suke k'etara wurare don Makarantar da nisa haka suka cigaba
da tafiya ba me cena danuwansa komai, a hankali taji yace *"ina
BioChemistry"* da sauri ta juyo ta kalleshi, kamar ba shi yayi magana
yanzu ba, ita har ga Allah ta manta da ta tambaye shi, wato sai da ya ga dama
ya bata amsa ko? Muje zuwa indai zaka dinga amsa min da sauki, a ranta take
waddannan maganganun, tace *"BioChemistry naso a bani,suka ban
MicroBiology, na so yin change of course don course din akwai wahala"*
shiru yayi na wasu mintuna, chan ciki yace
*"You are so lazy, ke komai wahala, i wonder how you passed your
WAEC"* ta juyo ta kalleshi da mamaki, fuskar nan tamk'e, kamar ba shi yayi
magana yanzu ba, ta murmusa a shagwabance tace *"Allah Hamma Rafeeq i'm
not lazy, ka tambayi Nene"* da sauri ya waigo ya kalle ta, har sitiyari na
k'okari kubce mai, tabbas da da mota ko machine a gefensu da ya buge su, Muryar
Rafee'ah sak yaji, ya tsura mata ido, murmushin ta mai kayatarwa take mai,
zaiyi magana kuma ta fasa ya maida hankalin shi kan tuk'i, ta lura da yanayin
da ya shiga, itama ta tsorata hajan yasa ta ja bakin ta tayi shiru, har suka
iso Makarantar be sake cewa 'a' ba, har gaban department dinsu ya kawo ta, yayi
parking, a hankali yace "MicroBiology Is a very good course, dont worry
you will enjoy it with time" da k'yar take magana kamar ance dole sai
yayi, da bata kasa kunnenta sosai ba da bataji me yace ba, don ciki ciki yayi
maganar, murmushi tayi tace *"Nagode Hamma Rafeeq, Allah ya saka da
Alheri"* dif kamar ruwa ya shanye shi duk sanda yaji ta kira sunan shi ya
kan shiga yanayin da besan yanda zai fassara shi ba, ta bude murfin mota tace
*"Hamma Rafeeq na tafi thanks once again"* Waiyo Allah ji yayi kamar
yayi ihu har ta kusa barin motar yace *"nace ba?"* ta gyara zama tace
*"ya kace Hamma Rafeeq?"* dan guntun tsaji yayi yaba takaicin tsaidara
da yayi, amma dole ya kawo karshen abun tunda shike cutuwa ya sake wani tsakin
yace *"Sunana Rafeeq"* murmushi tayi tace *"ai nasani Hamma
Rafeeq"* an kuma, runtse ido yayi ya bude yace *" you dont have to
cal my name, in kuma ya zama dole si kin kira sunana ki kirani da Rafeeq ko
R-Lema not Ham-whatever"* tace *"aa Hamma Rafeeq, ba zaayi haka ba,
kasan dai ka girmeni, kuma ni Ummi ta tace in dinga girmama nagaba da ni, i
cant just call your name without showing some respect, So I chose to Call You
_Hamma Rafeeq_ wato _YayaRafeeq_ kagane?"* Waiyo Allah, ta gama kashe
Rafeeq, ya ma kasa ce mata komai, sai k'ura mata ido da yayi, gabata dayata
rikide t koma Rafee'ah, yanayin maganar ta irin na Rafee'ah, har yanda Rafee'ah
ke turo baki idan tana so ya mata abu wannan ma nayi, kanshi ya dau Zafi,
Nasiba kuwa tsaf ta gano shi, *Hamman* ne beso tace mai, ba yanda zaayi ta
daina kiranshi da hakan don ta gano wannan ne Weakness(Weakpoint) dinshi, da
haka zata sa shi a hanya, bude murfin motar tayi ta wuce ce Department dinsu, tana mamakin k'arfin
halin da tayi, yanda ta cire kunya ta fara mission dinta a yau, ta sara ma
kanta don ta yi namijin k'ok'ari wurin sa Rafeeq magana da yawa haka.
Rafeeq kuwa
kasa motsi yayi ya bita da ido har ta k'ulle ma ganinshi, mamakin kansa yake
yi, wai yau shine da magana da wata mace haka, yau yayi sentence din da ya fi
biyar? Kuma ba da Uncle Zaid ba ko Maalesh? Lallai abun mamaki tsaki yayi yace
ma kansa "I wont let this girl affect me, shes not Rafee'ah, stop getting
into my head" Jiki a sanyaye ya kunna mota ya bar gurin.
*"Allah
sarki ashe Nene bata ji dadi ba? dole kam muje mu dubo ta after School"*
Miemee gayu ke maganar nan, Usheey tace "gaskia kam da mun gama lectures
sai muje mu tari Bus" hankali Seebi be gunsu, tunanin diramar da sukayi dazun
da R-Lema takeyi, lallai ta yi k'ok'ari.
Miemee ta zungure
ta, kina jin mu kuwa? Firgigit ta gyada kai, suna mamakin sabon haliayar Seebi, amma dai ba su ce komai
ba, haka suka cigaba da lectures har karfe 2.
Da sauri suke
tafia amma sun makaro, Buses sun tafi, sai sun jira dawowar su, Usheey, tace da
muyi ta Wannan jiran, gwara mu taka bakin gate mu tare su a chan, kafin suzo
nan duk mazan nan su shige su bar mu, kunga anyi ba'ayi ba" haka suka
dauki hanyar gate suna fira jefijefi, banda Nasiba da ta lula duniyar tunani,
kamar daga sama ta ji horn din motar shi, waswasi take anya kuwa shine? Miemee
kuwa tuni ta fara gyara zaman rigarta, tana fadin "kunga wata Azababben
mota na mana horn?" a tare suka juya ga motar, gaban Nasiba ya fadi ganin
motar Rafeeq, bata son su Miemee su san halin da suke ciki, a dabar ce tace
"kun ga dai kuzo mu wuce" Miemee tsce wlh idan ba ku shiga ni sai na
shiga" Usheey tace "muje Seebi, ba mu san lokacin da za mu bar
Makarantar nan ba, muje kawai" Miemee tace daga ganin wannan gayen Ya
Azabtu, don ba kowa zaki ga an bar shi ya shigo da Tint makaranta ba, Allah
kasa yace ya na sona" Seebi kawai sai taji daria ya zo mata, a ranta tace
"Lallai Miemee, indai Rafeeq ne zaice yana sonki to zaki bushe".
Usheey tace kun ga dai kuzo mu shige kafin ya chanza raayin shi, Miemee ce tayi
gaba suna binta a baya, ta bude k'ofar gaba ta shiga, Seebi tayi murna da hakan
fatan ta daya kar ya nuna ya santa, ita da Usheey suka shiga Baya, Waiyo Allah
Miemee na ganinshi taji wani irin dadi, tana fari tace "Ina wuni"
Usheey ma ta gaida shi, bece komai ba ya kunna motar shi ya bar wurin, suka bar
makarantar suna tafia, Miemee ta sake cewa "sannu fa? Ya School?" nan
ma ba amsa, daga baya Seebi ta rada ma Usheey a kunne kar ki sake magana, ta
dinga zungurar Miemee ta baya don tayi shiru, amma Miemee Zak'al taki yin
shiru, wai kai baka magana ne? K'iiii ya taka burkii, ya gangara k'asan titi
yayi parking, tsaf Seebi ta gane me yake nufi, yana nufin su fitar mai a mota
don Miemee ta dame shi, idan ya bar su a dajin nan ai be kyauta musu ba, Miemee
da fi'ili tace "yadai motar ce ta lalace? A hankali yace "Get
Out" da mamaki Miemee da Usheey sukace "What?" cikin dan daga
murya yace "ku fita nace" a tsorace suka kalle shi, Usheey tace
DonAllah BawanAllah kar ka aje mu nan, kaga nan ba inda zamu samu abun hawa, ka
taimaka ka kai mu ciki gari, be ce komai ba, be kuma tada motar ba.
Ba tayi niyyar
magana ba amma tasan hali nai, ba zai tafi ba har sai sun bar mai motan shi,
daidai yanda zai jita tace "kayi hak'uri Hamma" ta mirror ya kalle
ta, yayi dan guntun tsaki, ya kalli Miemee yace "kina da
hayaniya" da sauri tace "yi
hakuri, ba zan sake magana ba" ta bude murfin motar ta fita ta zagaya gun
da Seebu ke zaune ta bude, "inshort Seebi koma gaba donAllah ke baki da
hayaniya" Daria suka bata su duka, ta bude murfin motar ta fita ta koma
gaba, ta na rufe wa kuwa ya ja motar shi ya bar gun, ba wanda ya sake magana
har suka shigo cikin gari, a Royal Reataurant yayi parking ya fita, suka tsaya
kallon kallo, ko cewa zaiyi su fito, yayi shigewar sa abin shi, Usheey ta
tuntsire da daria Seebi ta taya ta, dariar da suke rik'ewa tun Batagarawa,
Miemee ta hade girar sama da ta k'asa, sai da sukayi mai isar su, Usheey ta
kalli Miemee tace "kina da hayaniya" Seebi ta sa daria, Miemee ta
harare su tace its not funny wallahi, Wannan wani irin Guy ne? Kullum cikin
k'unci, kun ga fuskar shi murtuk'e?amma fa hakan be hana kyawunshi fitowa fili
ba" Seebi ta girgiza kai tace "kina da damuwa" duk suka fashe da
daria, suna ganin ta fito duk suka yi shiru kamar sunga wani dodo, dauke yake
da ledoji a hannu, ya bude motar ya ajiye wurin kafar Seebi, ya ja mota ya
tafi, tafia sukeyi, shi be tambaye su inda zai aje su ba, Miemee ta rada ma
Usheey ince mishi ya aje mu nan? Usheey tace baki daddara ba ko? To ba ruwana,
duk suka ja baki sukayi shiru, mamaki ya cika Usheey da Miemee da suka gansu a
Asibiti, to ko da ma ya san nan zasu zo? To waya gaya mai? Seebi ce ta fara
bude motar kafin su Miemee, duk suka mai Godia, be ce komai ba, sauri sauri
Seebi ta bar gun suna binta a baya, ya juya ya kalli ledar da ta bar mai a mota
ya buga tsaki da k'arfi, ni ta bar ma Abinci?ni me zanyi dashi? Tsaki ya sake
bugawa ya kwashi ledojin zai shiga Asibitin kenan ya ga Baba Maigadi, yayi mamaki
amma be nuna mamakin sa ba, illa dauke kai da yayi dob be san tambayoyi, da sauri Baba maigadi ya karaso yace
"Ahh Rafeeq me kazo yi a Asibiti? Nuna mai ledojin hannun shi kawai yayi,
Au abinci ka kawo wa wasu? Ya gyada kai, yace "Nima wata makwabciyar mu
nazo duba wa" da sauri Rafeeq yace "Nene?" da mamaki yace
"eh ita" ko da yake ba abun mamaki bane tunda Nasiba ta san shi, amma
dai Aminene ta ciri tuta tunda har Rafeeq zai zo dubata harda karin ciwo,
Rafeeq yace "Baba ka kai musu wannan inji Uncle Zaid" "ya dawo
ne?" tsaki Rafeeq yayi yace "baba ka amsa" da sauri ya amsa
Rafeeq yace "daki na sha2" don kar ma ya sake sa shi magana ya juya
ya tafi, shi ko Baba maigadi ya wuce cikin Asibitin.
Miemee da Usheey
suka ma Nene Sallama, Seebi ta fito rakasu, a bakin k'ofa suka hadu da Baba
Maigadi, ta gaida shi, tace "baba barin raka k'awaye na, yauwa 'yar baba
je ki dawo ina nan" sai da ta rakasu bakin gate din Asibitin ta dawo, yana
nan inda ta barshi, yace "ya jikin Aminene? tace "da sauk'i"
yace "gashi inji mutumin ki Rafeeq, wai inji Zaid" ya mik'a mata
ledar, ta bi ledojin da ido, ohh dama na su ne? Lallai Rafeeq a gaishe shi,
tace "Yanzu muka rabu, be ce min namu bane" ai na mayi mamakin ganin
shi anan, bayan abun da ya faru yau da safe a gida" da sauri tace
"Baba Me ya faru yau?" Ya kwashe komai da ya faru tsakanin Rafeeq da
Baban shi da su Aneesa, harda abunda Saude tace da martanin da Aneesa ta mayar,
Nasiba ta tsorata, tace *"Baba kar suyi mishi wani mugun abu, Dole Rafeeq
ya dage da Adduo'i, zan tambayi baba na ya rubuto min adduoin tsari"* Baba
Maigadi yayi murmushi yace "lallai Nasiba, baki san waye Rafeeq ba, Yo
Allah na tuba Sallah kadai Rafeeq keyi don ya zama dole yayi shi, to tsaya
kiji, Rafeeq be Sallah a Massalaci baya jam'i, sai a daki, kuma da ya idar yake
tashi, baya addua a ganin shi be da bukatar wani abu da zai rok'a, be da saurin
jin dadi, shifa yanzu be k'i ace ya mutu ba, a takaice dai Rafeeq baya
Addua" Nasiba ta fashe da wani irin
kukan da bata san lokacin da ta fara shi ba, cikin kuka tace
*"Waiyazubillahi, wani irin Masifa ce wannan? Wane irin mugun hali yake
son jefa kanshi ? In banda abun shi wa ke cire rai daga rahamar Allah? Waye baya da bukkata gun Ubagijin shi?"*
cikin Masifa da dacin rai kamar tana gaban shi tace *"R-Lema kana cikin
6ata Wallahi, kuma ko ka k'i ko ka so sai ka dawo hanya"*
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
This is for you
*Maryam AD Bappa(Umm Eeman)* Thanks for Everything ILY❤❤❤
Pg3⃣9⃣
Nasiba ci
kukan ta ita kadai, ta share hawayenta, ta kimtsa fuskarta gudun kar nene ta
ishe ta da tambayoyi, suka dunguma zuwa dakin tare da Baba mai gadi. Kowa da
abun da yake sak'awa a ransa.
Shigar su dakin yayi daidai da fitowar nene daga bandaki,
inda ta dauro alwala zatayi sallah, Hajjo kuma na zaune kan darduma tana
lazumi.
Nene ta washe baki ganin Baba maigadi suka hau gaisawa, yai
mata ya jiki, Seebi kuwa duk yadda taso
ta boye damuwarta ta kasa, Nene ta dan
gane yar jikallenta na cikin damuwa, ta tambaye ta "ko lafiya?" Seebi
tace "Nene ba komai, gajiya ce kawai amma nasan in na dan huta zan
ware" Nene ta amsa da to Allah huta gajia.
Bayan tafiyar Baba ne suka zauna suka ci abinci su ukun
duka, suna kammalawa Seebi taja gefe ta rusuna tana tunanin ta inda zata fitowa
*R-LEMA* don tabbas rayuwarsa na cikin gagarumin hadari.
Kuma He is proving so difficult to deal with.
Haka ta dinga 'yan tunane tunanen ta, ta sak'a wannan ta
kunce wancan har bacci ya dauketa ba tare da ta samu mafita ba.
Yau Alhamis
kwanan su hudu kenan a Asibiti.
Seebi ta idar da sallar Asubah ta kammala adduoin ta,
littafanta ta janyo ta dan dudduba don tana da lectures 9am kuma Malamin ya iya
test din bazata.
Bayan ta gama revising ne ta rufe ta maida komai cikin
jakarta, ta saka Hijabi kan kayan baccin dake jikinta tare da gyara fuskar ta
sama sama don batayi wanka ba,
tayi wa nene da hajjo sallama ta wuce gida don shirin
Makaranta saboda sauran kayan da ta da ke Asibitin sun yi Datti.
6:50 ta isa
gida, sai da ta share gidan ta ta gyara ko ina kafin ta fada toilet tayi wanka
ta shirya ta, ta fito Gida 7.55am. Sauri take ta isa bakin titi don ta samu
abun hawan da zai kaita National don kar tayi missing Bus.
Kamar kullum,
Tuk'in shi yake cikin qasaita, daga nesa
ya hangota, kamar ita kamar ba ita ba, kai itace, wannan yarinyar ce, a
ransa yace "Wannan kuma me takeyi a nan? (kuji se kace be san nan gidansu
yake ba) guntun tsaki yayi yace "Da naje daukan ta a Asibiti da nayi zuwan
banza kenan" ya sake wani tsakin kamar yana gabanta. Horn taji da karfi,
da sauri ta dode kunnenta tare da juyawa a k'ufule don ganin me neman kashe
mata dodon kunne, ita da ba kan hanya take ba, Idonta ya kai ga Motar Rafeeq,
haka kurum taji dadin ganin shi duk da ta san ba wai kulata zeyi ba, ko ba
komai, ba zatayi latti ba, kuma zata samu daman mishi magana.
Bude motar tayi ta
shiga don tasan ba ce mata zaiyi ta shiga motar ba, cikin wata muryar da bata
san tana da shi ba tace "Ina Kwana Hamma Rafeeq"
Jan motar shi yayi, ya dau hanyar school yayi kamar be jita
ba, har ta cire rai da zai amsata, don sunyi tafiyar kusan 4mins kafin taji
yace *"lafiya"* da mamaki ta
kalleshi, ta ma manta da ta gaishe shi, a ranta tayi dariya tace *"bakasan
waye jikar nene ba sai ka dawo hanya da Yardan Allah"* wani kwarin guiwa
taji, ta gyada kao tace "i can do it" Cikin sigar shagwaba tace
*"Hamma na please..."* sai kuma tayi shiru tare da duban sa.
Wani uban tsaki ya buga da sai da taji tsoro, ya maida
hankalin shi ga tukin sa, don duk yanda ta kirashi da *"Hamma
Rafeeq"* sai numfashin sa ya dauke, balle yanzu da ta zak'e wai
*"Hamman ta"* "wannan yarinyar ta fara koyon surutu, ta fara
zak'ewa"
Kamar ba zai ce komai ba yace " what?" ta ji dadi
tare da samun karfin guiwa, tace dama
zance ko in munje wancan shagon zaka dan tsaya na sai Ziza Milk, don banci
komai ba ina sauri kar nayi latti.
Besan lokacin da
murmushi ya subuce masa ba, cikin sakwan
da be wuce 2 ba ya daure fuska, a ransa yace "what is funny?"
ji yadda take sunne kai kamar mara gaskia, lazy girl she cant even skip
breakfast. Be dai ce da ita komai ba
Daidai wani shago ya tsaya, tayi murmushi tace "yawwa
Hamma na Nagode" Ta dauki jakarta,
tana k'okarin bude kofar taji ya bude tasa kofar ya fita tare da rufowa.
Gyada kai tayi cike da tausaya wa, don shi duk abunda yakeyi bata jin haushin,
illa ma tausayin da yake bata. Be dauki lokaci ba ya dawo da leda kunshe da
soft drink da kuma date bars ya aje mata kan cinya, ta masa godia suka dau
hanya.
Ta bude jakarta don saka ledar a sama ta tsinci muryar sa
*"EAT NOW"* tace " *to Hamma na*. Ta bude tana ci har suka iso
School, har bakin Department dinsu ya
kaita, kimtsa bakin ta tayi masa godia
ta fice. Shikuma ya ja motarsa ya k'ara gaba.
Yana wucewa ta
sauqe wani gauron numfashi tace
"Wai Allah nagode maka da ka sa min dauriya, Allah ka kara shige min gaba
Ameen"
Zaune take gefen
nene tana waya da Uncle Zaid, inda take
sanar dashi cewa Nene ta warke, likita yace zuwa magriba zai Sallamesu.
Uncle zaid yace "Alhamdulillah, Nene ta ji sauk'i, idan anyi sallamar ki
sanar dani" tace "toh"
Ta masa godiya suka yi sallama. Ta miqe ta shirya tace
"Nene zan shiga makaranta bani da lecture, amma ina da Assignment din da
zanyi submitting kafin lokacin sallahr Juma'a, da an gama sallahr Jumaa'h zan
dawo wuraren k'arfe biyu, sai a hada kayan kafin likitan ya zo ya bamu
Sallama".
Murna gun Nene kamar me, tace "wlh dama na gaji da
Asibitin nan, Mutum da lafiyarsa amma an kawo Asibiti an ajiye, amma fa zanyi
kewar 'yar gasasshen Kazar da dunkum ke kawowa" (Dunkum ne sunan da
Nene ta sa ma Rafeeq) ba Seebi ba harta
Hajjo dake gefe sai da ta dara tace" Kai k'awalliya, jika na ne Dunkum?"
Nene tace "yo ehmana, ayi mutum shi he daria, be murmushi be magana? Hajjo
tace "lamarin Rafeeq sai du'ai, haka yake" Nene tace "Shiyasa na
rik'e furfurata, ba ruwana dashi, don in na mai magana ya share ni, ina iya
kulle shi daki karfe ukun dare inci Ubanshi, dan uban mutum" me Hajjo da
Nasiba zasuyi in ba daria ba, Nasiba har da kwallah, Hajjo tace "Lallai Nene Lafiya ta
samu" Nene tace "dama garas nike, uwayen fiili suka daura man zaman
dole a Asibiti, wato Seebi da Zaidu
bawanAllah" Nasiba dai ba ta tanka ba.
Dan zaman da sukayi na kwanaki biyar Hajjo da Nene suka Saba
don Nene akwai surutu da saurin shiga rai, hajjo kuwa akwai barkwanci..
Ku daga daga k'afa
mu isa on time kunga yau Friday, Buses cika zasuyi da wuri. Seebi ce mai maganar nan, Usheey tace
"in ba haka ba sai mun ci uwar trekking kafin mu samu naAllahn da zai bamu
Lift.
Kamar Baki, ga
Buses har uku amma duk a cike mak'il har bakin K'ofa, Seebi ji take kamar tayi
kuka don haushi.
Tasan Nene na chan na zuba idon ganin ta, ita da ce mata 2
zata dawo, gashi har uku.
Miemee ta bada shawarar su fara takawa Ko Allah zaisa su
samu lift ko kuma rage hanya kan Buses su jiyo atleast yafi tsayuwar.
Usheey tace "Miemee don Allah in za a bamu lift yau kar
ki yi over sabi please" Seebi na
gimtse daria tana fuska, Miemee ta daure fuska tace "Munafuka, say your
mind" Seebi tace "Kina da Hayaniya" Miemee tace "Kuna da
damuwaaa" ai kuwa duk suka fashe da daria, Miemee tace Wallahi gayen nan
ya mugun raina ni" sukayi daria suka fara tafia.
Tafia suke
tayi, sun danyi nisa sai ganin motar R-lema sukayi a gaban su, basu tsaya wata
wata ba suka nufe motar, Seebi zata bude kofar baya ta shiga Usheey ta buge
hannun tace "donAllah shiga gaba kar ya chanza raayin shi" Miemee ta
harare su tace dama ce muku akayi zan shiga gaba? Seebi ta shiga gaba duk suka
koma baya, a tare suka gaida shi, kai kawai ya daga musu, ya ja motar shi ya
tafi, ko da suka iso cikin gari ya kalli Ushee ta mirror kamar zai yi magana
sai fasa, tsaf Seebi ta dago shi, so yake yace dasu Usheey ina zai sauke su
amma ya kasa, Seebi tace "DonAllah ta wurin Asibitin Dr Dara kayi?ni nan
zan sauka" Shiru yayi kamar be ji ba, ganin be da niyyar tsaiyawa ya sa
tace "Kana iya ajiye mu anan" kamar jira yake kiiii yaci burki, yayi
parking, Usheey da Miemee suka mai godia ko uffan be ce musu ba, suka bude suka
fita, Seebi zata bude k'ofar kenan ta fita ya sa lock, su Miemee na kullewa ya
ja motar shi yayi gaba" Su Miemee suka bi motar da Ido baki a hangame.
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg4⃣0⃣
A tsorace ta
dan kalleshi, ko bi ta kanta beyi ba ya hau titi kanshi a tsaye, Maimakon suyi
hanyar Asibiti, sai bani tayi ya dauki hanyar
*Sally's Cuisine* ba tace da shi komai ba har ya iso yayi parking, fita
yayi ya shiga, nan ta samu damar amsa Wayar Usheey da tun da suja aje su take
ta faman kiran ta, "Hello Seebi ina zai kaiki?" tayi daria tace
"Asibiti" "haba har hankalin mu ya kwanta" tana ganin ya
fito tayi saurin katse wayar, Hannun shu dauke da ledoji 4 ya aje mata 3, dayan
kuma ya aje a seat din baya yaja mota sukayi Asibiti.
Ko da suka isa
Asibtin, har ta bude murfin mota zata fita, Zuciyar ta ta bata shawara, ko
bazai amsa ba, ki masa godiar dawainiyar da yake tayi daku, Abinci lunch da
dinner baya fashin kawo muku, ga kai ki makaranta da dawo dake duk da ba kullum
ba.
Ta juyo ta gyara zama yanda tana fuskantar sa tace *"Hamma Rafeeq, Yau Dr ke sa ran
Sallamar mu, mun gode kwarai da dawainiyar da kakeyi da mu, Allah ya biya ka,
Allah ya saka da Alheri ya, Allah ya ji kan Magabata, Albarkaci Rayuwar ka,
Allah ya kuma Saka maka duk Zalincin da aka taba maka, wanda ba za ka iya yafe
su ba"* tana kaiwa nan ta fice daga motar, bata tsaya sauraren abun da zai
ce ba, Yanda kuka san Hoto, haka Rafeeq ke zaune a gun, ko yatsar shi ya kasa
dagawa, be san lokacin da ya furta *"Ameen*" ba.
Haka kurum yaji dadin
Adduointa, Shi be san meyasa ba, amma yana jinta a jikin shi, kawai yaji ya
bata babban matsayi a ran shi, jinta kamar FEE'AH.
Da k'yar ya kunna mota, saboda jikin sa ya mace gabaki daya,
ji yayi ya kasa tafiya, guntun tsaki ya sake ya duba Aljihun motar shi ya ciro
paper da biro, rubutu yayi sannan ya fita ya shiga Asibitin, daidai Dakin ya
chokara a jikin kofar yadda in an bude
zaa gani, yayi tafiayar sa.
Seebi na idar da
Sallah ta dauki Abincinta, Su Nene har sun gama da Abincin da Nasiba ta shigo
dashi,nan zaman jiran Sallama sukeyi,
Nasiba tace "bari inje in ga Dr,
k'ila ma ya mance da yace yau zai sallame mu" Nene tace "E
danAllah, na k'agara inga nayi juyi kan Gadon K'arfe na" sukayi daria
duka.
Tana murda kofa
wata kaaramar Takarda ta fado, duk'awa tayi ta dauka, ta na budewa tabi rubutun
da ido, Murmushi tayi a hankali tace "R-Lema" a nutse ta fita daga
dakin ta fara karantawa ga abun da yace
_"Ameen to your Duas. Idan an sallame ku, ga number na
ki min text you DONT have to Call just TEXT"_.
Seebi tayi murmushi
ta sake karantawa, tace *"R-LEMA kenan Allah ka bani ikon taimaka ma
beautiful soul dinnan"*. Tasa kai ta wuce office din Dr. A hanya suka hadu
da Dr da Nurse Sai suka juya suka koma dakin.
Nurse ta gwada Bp
da Temperaturen Nene, komai daidai, Likita yace "Mama, kin ji sauki sosai,
zan sallame ku, Amma donAllah ki rage cin Jan Nama" Nene ta bishi da
kallon kai gaja, tace *"yaro wani Nama ne Ja?"* yace "Naman Sa,
ko na Awaki" Nene ta tuntsire da daria, tace "Su balangu da tsiren da
nake ci kake son hanani ci ko? Yace " Mama saboda Lafiyar ki ne, bawai ina
son hanaki bane" ta tabe baki tace "toh dai bari kaji Ubana *Mamman*
Shanun shi 31, duk bayan wata ake kashe mana daya, ba saidawa ake ba ci mukeyi,
kuma ban taba jin ance wani naman Shanu yasa shi ciwo ko wani abun Allah
sauwak'a ba, toh nidai _Aminene Mamman_ da bakin ciki ya kashe ni gwara Dadi ya
kasheni Ehe" Nasiba tayi saurin cewa "I'm so sorry, She's always like
this, InshaAllah she'll regulte it" Dr yace "Dont worry i have
someone exactly like her at home" Nene ta cika tayi fam tace "Oho
dai, Sai ka sallame mu yau, Ke kuma ni zaki chanzawa ko? To in ma zagina kukai
da Ubanki Mahammadu kuke" Dr ya fashe da Daria yace "yi hakuri Mama
ga takardar sallamar ki" yafi maka don yau ko baka sallameni ba gida zan
kwan" Nasiba ta girgiza kai cike da takaici, Hajjo kuwa sai daria take tayi.
Dr na fita Nene tace " _kinga latso min Zaidu bawan
Allah a waya, ba gardama Seebi tayi yadda nene tace, Yana ganin kiranta ya
yanke ya sake k'ira
Zaid yayi Murna kwarai da jin Sallamar su Nene, kuma ya bata
shawaran bin yanda Likita yace, jin shi kawai Nene tayi don ba ta da Mak'iyi kamar me son rabata
da Nama, nan dai ta hau yi mishi Godia da Adduoi, Ya tsaidata ta hanyar cewa
Haba Nene, Kun wuce nan, babu godia a tsakanin mu. Sukayi Sallama. Bayan Seebi
ta karba wayar ne yace mata zai turo a maida su gida, tace ai "Hamma
Rafeeq yace in gaya mai idan an sallame mu" da Mamaki Zaid yace
"Rafeeq dai?" tace "eh shi" shi da kanshi yace haka?"
tace "eh" "Rafeeq yana zuwa ne?" tace "Duk da ba shigowa
yake ba, amma yana kawo mana Abinci Rana da Dare, sometimes ya na aje ni
makaranta" Allahu Akbar zo ku ga jin dadi gun Zaid, Ashe Rafeeq na da
sauran Mutunci da tausayi a tattare dashi? Be taba ganin Rafeeq ya damu da
lamuran wasu ba kamar su Seebi lallai akwai Improvement, yace da Seebi "to
sai kun koma gida mayi waya" sukayi Sallama. Duk zaton Nasiba da Nene Zaid
ne ya sa Rafeeq dawainiya dasu, duk abunda yake yi saboda Zaid ne, nan suka
gane cewa ashe Rafeeq ne ya sa Kanshi, ba kowa ba. Nan Nasiba ta k'ara samun
wani k'warin guiwar Aiwatar da Kuddirinta.
Seebi ta kwafi numbern da Rafeeq ya
bata, ta masa text din as he demanded. Ga abun da tace;
_"Assalamu alaikum Hamma Rafeeq anyi discharging din
mu, mun shirya, we are good to go"_
Yana wanka yaji wayarsa alamar shigowar sak'o, bayan yayi
Sallah, ne ya daga wayar ya ga message daga new number, ya bude ya karanta, dan guntun tsaki ya ja (Ikon
Allah! sak kace bashi yace ta mai ba).
Key kawai ya dauka ya fice daga gidan sai Asibiti, yana isa
ya mata text "Ku fito".
Seebi na jin shigowar text ta duba taga Shine, ba su wani
dau lokaci ba suka fito harabar Asibitin da kayan su. Inda yake aje Motar shi
sukayi, ta na zuwa ta iske Booth a bude, be fito ba haka Seebi ta shiga saka a
kayan boot sai da ta gama, sannan ta
bude gaba ta shiga ta zauna su nene kuma sun shiga baya.
Sai da suka bar Asibitin, da kyar yace " Ya
Jikin?" Nene ta murmusa a ranta tace Uban Kasaita, a fili kuma tace
"Alhamdulilah, na watsake" kamar ba zai ce wani abu ba yace
"Sannu Fah" tace "yauwa" a hankali tace kamar dangin
Maguzawa wai sannu" Hajjo da Nasiba kadai suka jita, Murmushi kawai
sukayi, tun daga nan ba wamda ya sake magana har sai da suka iso gida, ya juya
ya dan kalli Hajjo yace "Hajjo Mom tace ki k'ara Sati daya sai ki koma
gida" tayi murmushi tace "ba damuwa"
Tare da taimakon
Hajjo suka shiga da kayan su ciki, sai da ya tabbatar sun gama kwashe wa ya
danna horn, ta lek'o ta window, ya mik'a mata manyan ledojin Abinci, yaja motar
sa yayi gidan su Maalesh.
*England*
Zaid ne kwance kan
tafkeken Gadonsa yana waya da Mami, inda aka bashi Ayman ta dinga mai gwaran
cin ta, har sukayi Sallama sannan ya kira Nasiba,
Suk gaisa ya tambayeta ya jikin Nene ta amsa masa da sauk'i.
Suka danyi hira sannan ya gaisa da Nenen itama ya musu
Sallama.
Nan ya hau tunanin wanda zai sa ya musu Grocery shopping, don ya tabbatar suna da
Buk'ata, baya son takura wa Rafeeq, Saboda abunda ya fahinta, Rafeeq has done
more than Enough, kuma baya so ya k'ure shi .
Maalaesh ya fado ransa, Take ya kira wayansa, Ringing biyu
ya dauka "Hello Mahmud" nan take ya gane Uncle Zaid ne, don shi yasan
shi kadai ke kiran shi da sunan shi na Asali, "UncleZee ina wuni"
suka gaisa, yace "Mahmud ina so donAllah ka min Shopping na kayan Abinci,
da kayan buk'ata na Gida, ina so ka kai wani Gida na nan ku sa da gidanku na
Layout(Gidansu Rafeeq yake nufi) Nan ya mishi kwatancen gidan. Malaesh yace
"Angama, anything for you uncle Z" barin je yanzu ma, "barin maka transferring kudin" da
sauri yace "Noo akwai kudi hanuna Uncle Z" "dont be Silly Son,
i'm sending now" Murmushi Maalesh yayi yace "Nagode" suka yi
Sallama, Nan take Zaid ya mai Transfer din 100k.
2:47pm
Seebi na zaune bisa kujera yar tsugune, tana yi wa Nene
tsifa, i Nene da Hajjo na kan tabarmar k'asa, Sallama suka ji, da sauri Seebi
ta zaro Mayafin ta kan Igiyar Shanya, Nene ta daura dankwali tare da Amsa
Sallama, Maaleah yace "donAllah nan
ne Gidan Nene?" da sauri tace Eh Yaro Shigo, nice nan Aminene, yace toh ina zuwa, Yara ya samu ya sa su
kwasan kayan ya ce suka shiga gidan nan, Mamaki ya rufe su Nene, ana haka ne
Maalesh ya bi bayan su ya shigo, yana ganin Hajjo ya bude baki "Laaaah
Hajjo, kece nan?" tace "Maalesh yaushe a gari?" yace "jiya
na shigo, na tambayi Mom kina ina tace ba kya nan" tace aiko dai gani
anan, ya durkusa ya gaida Nene, ta amsa mai cikin Fara'a, yace "kece Nene
daga gani" ta nuna kanta da Yatsa tace "Nice nan Aminene Yar Mamman,
duk duniya ba wata Nene sai ni" ta nuna Nasiba da hannu tace "Nenen
Seebi kake ji" ya juya ga wacce aka cema Seebi, ya ga shi take kallo, tsaf
tagano shi, shine wanda kwanaki da zai basu Lift yace sai ta cire Nikab, kuma
Shine Abokin R-Lema, ta dai maske ta gaishe shi, "Lord have Mercy"
inji Maalesh, tuni Nasiba tayi gaba da Imanin shi, da kyar ya amsa mata fuskar
shi cike da Annashuwa.
"Hajjo tace
Maalesh wannan kayan fa?" yace "Uncle Zaid yace a kawo" Nene ta
chafe "Allah Sarki Zaidu Bawan Allah, Allah shi biyaka ya saka da Alheri,
Malush kaima Nagode maka" Yayi daria yace Nene "Maalesh nake ba
Maalush ba" duk sukayi daria, na da nan Maalesh suka dinke da Nene,
k'wank'waman su iri daya na surutu, sai yi suke tayi yanda kasan sun dade da
sanin juna, dama shi Maalesh saurin Sabo ne dashi, nan Hajjo ta zubo mai
Burabusko ya kwasa kamar ba gobe, sai kallon Nasiba yake tayi, ita kuwa sai
smilling take tayi tana jin diramar su da Nene, har kusan Laasar be da niyyar
tafiya. Wayar sa tayi k'ara, ya ciro daga Aljihu ya duba, ya kalli Hajjo yace
dan gidan ki ne, tayi murmushi tace "Rafeeq Ho" ya dauka "my guy
howfa?" kusan sakwan 3 beyi magana ba chan yace "kana ina? Nazo gida
baka nan" Maalesh yace "Wallahi gani ta wurin gida Uncle Zaid ya
aikoni" tsaki Rafeeq yayi yace "ina jiranka" ya kashe wayar,
Nasiba ta tsura wa wayar Maalesh ido, kamar tana jiran Rafeeq ya fito daga
ciki, Nene tace "Wannan uban Yan k'asaitan ne ko?" Maalesh yayi daria
yace "Nene kinsan Rafeeq ne?" ta ta6e baki tace "ai wannan sai
kun hada mai da tofi" yayi daria yace barin je, sai na dawo ya musu
Sallama ya kalli Nasiba yace "Bye Beautiful" ita kunya ma ya bata ta rufe
fuskar ta da tafin hannayen ta.
Yana shiga
Dakin shi ya ga Rafeeq kwance kan Gado, ya bubbuga mai k'afa, kamar ba zai
tashi ba, ya mike sukayi side hug, Maalesh cike da doki yace "I met
her, Wallahi naganta yau" da k'yar
Rafeeq yace "Who?" Maalesh yace "The love of my life, Seebi,
Uncle Zaid ya aike ni Gidan su yanzu in kai ma Nene sak'o" a dan tsorace
Rafeeq ya kalleshi, kamar zaice wani abu sai ya fasa, be damu da Rashin Ansashi
da Rafeeq yayi ba, Maalesh ya cigaba "Shes beautiful, ai kasanta, ta hadu
ko? Zamu dace? Haka ya ishe Rafeeq da maganar Nasiba, yace " Guy do you
think she'll like me? Wallahi ina sonta, kawai ganinta nayi gefe na kamar an
jefo ta, ina ganin ta naji She's the one, wannan shi ake kira "LOVE AT
FIRST SIGHT" cikin kufula da daga murya Rafeeq yace "Will you Shut
the f**k up?
_Bibilicious Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg4⃣1⃣
Maalesh ya
kalleshi da mamaki yace "Guy, Calm down" Rafeeq yayi guntun tsaki
cikin yanayin shi yace "ban ga dalilin da zai sa ka dinga min maganar wata
yarinya ba, duk ka bi ka ishe ni" Maalesh cikin doki yace "Feeq ba
zaka gane ba, Wallahi ina sonta, sosai fa" kamar ba zai ce komai ba yace
"She's Innocent, dont hurt her" da sauri Maalesh yace "Wallahi i
wont, shes not like the rest of the girls i'm with, Wannan ta dabance, guy bani
shawara ya zanyi?" chan cikin mak'ogaro yace "Tell her"
"bansan mesa ba i lost the courage, ai da tun dazun na gaya mata"
Rafeeq yayi shiru ya cigaba da latsa wayar shi be ce komai ba, Maalesh ya yi
rigingine kan Gado, Rafeeq ya dora wayar shi kan cikin Maalesh, Maalesh ya
tashi da sauri ya dauki wayar Rafeeq ya duba, kan Screen din ya ga Message ya karanta, ya kalli Rafeeq don neman
k'arin bayani, guntun tsaki Rafeeq yayi
yace "The girl's Number" wani irin super Maalesh yayi ya duro,
ya rungume Rafeeq, donAllah numbern ta ne? Kai Nagode Breh, naji dadi Wallahi"
Shi dai be ce dashi komai ba, Maalesh yayi copying number din yayi saving a
wayanshi.
Tana tsakiyar
su Nene suna fira, wayar ta yayi ringing, ko da ta duba New number ne, ta dauka
da Sallama, Muryarta yafi komai dadi inji Maalesh, ya amsa yace "Hello,
Beautiful" wani ajiyar zuciya ta sake ta amsa da Ina wuni don ta san me
muryar, yace "kingane me magana ne? Cikin jin kunya tace "eh" to
waye? ta yi Murmushi tace "Ya Maalesh ne" Waiyo dadi, Ya Maalesh, karo na farko bayan
Rasuwar Rafee'ah yaji an kirashi ta wannan sigar, yace "Seebin Nene, you
are a Blessing, kinji Voice dinki kuwa?" kunya ya bata sai bata amsa shi
ba, yace "are u there? Kinyi shiru?" a hankali tace "i'm
here" "Seebi will you be my friend?" Daria kawai tayi, ya kike
daria? "Ba kya so in zama Abokin ki?
A hankali tace "Aa" yace "Aa mene? Kina so? Will you be
my friend? A hankali tace "yes" Darian jin dadi yayi yace "let
me warn you, my friends usually say i'm a Sweet Soul, abun nufi shine Wata rana
Abokantakar mu na iya rikidewa ya koma Soyayya" Daria kawai tayi, nan suka
sha fira don Maalesh akwai Zance, sun dade suna waya inda ya shaida mata zaizo
Gobe don Jibi zai wuce Kano inda yake Service.
*Washe
Gari*
K'wank'wasa
k'ofar yayi, sai da ya kusa minti 3 kafin yazo ya bude mai, hararar shi Maalesh
yayi ya ra6a ta gefen shi, ya shige cikin Dakin, Da k'yar Rafeeq yace
"Sorry i missed your call" Maalesh yace "and you cant call
back?" Guntun tsaki Rafeeq yayi yace "I said i'm sorry didnt i?"
Maalesh ya k'ulu ya mik'e zai fita da sauri Rafeeq ya rik'o shi, kasa magana
yayi ya girgiza kanshi, Maalesh ya dawo ya zauna, Rafeeq yace "Look,
wannan Aneesar banzan ce take takura min, shisa na kulle k'ofana, coz duk
abunda zan mata bazata yi zuciya ba, so da ka kirani i thought itace shisa ban
dauka ba" Maalesh ya girgiza kai cikin takaici, ya akayi sunana da na ta
yayi kama, har da ka zata itace?" a takaice yace "ban duba wayar
ba" "Oh lord have Mercy" Inji Maalesh da sauri Rafeeq yace
"Kayi kyau Sosai, ina zakaje ne haka?" Don dai ya 6atar da zancen don
yasan Maalesh da mita kamar Nenen Seebi. Murmushi Maalesh ya sake yace zanje
Gidan Nene ne, zanje musu bankwana, Tsaki Rafeeq ya sake "Do you really
have to go there?" Maalesh ya amsa da sauri "Yes My other Half is
there" wani Mugun tsaki Rafeeq ya sake tare da kwanciya kan Gado, Maalesh
ya mik'e yace "Feeq, barin je sai na dawo" da sauri Rafeeq yace
"Wait" da Mamaki Maalesh ya kalleshi, Rafeeq ya dauke ido be so su
hada Ido da Maalesh yace "I'm Bored, i'm coming with you" be jira
cewar Maalesh ba ya fice daga dakin, Maalesh da mamaki ya maimaita "He's
Bored?" Sabon Salo, gemu a kafada, yau Rafeeq yake cewa he's bored, shida
be k'i ya kulle kanshi a daki ba, be komai, lallai kam, toh K'ila ya fara
Chanza halinshi, Allah ya sa don sai nafi kowa Farinciki, ya fita tare da kulle
dakin da Mukulli ya bi bayan Rafeeq.
Bakin Zauren Gidan Maalesh ya doka Sallama "Assalam
Alaikum" daga Ciki Nene ta Amsa, tare da cewa "Bismillan
ku" Maalesh a gaba Rafeeq na bin
shi a baya sai shan k'amshi yake tayi, kamar an ce dole sai ya shiga, ta Window
Nene ta hango su, da sauri ta fito tana tafa hannayen ta, tana fadin "Ga
Maalush ga Maalush" wani Murmushi Rafeeq ya saki ba tare da ya sani ba,
suna hada ido da Nene yayi saurin daure fuska tare da dauke kai, ko meyasa be
so taga Murmushin shi oho,a fili Nene tace "Chan ta Matse maka a matsatsen
wandon ka"Maalesh ya fashe da daria, yace Nene ke dawa?" ya juya ya
kalli Rafeeq da ya hade girar sama da ta kasa, Nene tace ni rabani da wannan
Mara fara'a, Sannun ku da zuwa dai" ta bude baki tace "Seebi, fito da
tabarma, ga Malush da Dunkum" Maalesh dai sai daria yake tayi, Hajjo ta
fito, suka gaisa da Maalesh, tace "Rafeeq" Murmushi kadai ya mata, ya
dauke kai, Nene sai ikon Allah take kallo, a ranta tace "Lallai yaro, kazo
gidana ka dinga sha min kunu? To uban tauri ma yaci ubanshi" ta gyada kai
ta shiga cikin kichin don ita kadai tasan me zata ma Rafeeq, Nasiba taji dadin zuwan su, ta dauko Tabarma
ta fito kanta a k'asa ta shinfida musu, Maalesh ya fara zama sai Rafeeq,
Maalesh ya bita da ido, ta dukursa ta gefen da Rafeeq ke Zaune tace "Ya
Maalesh, Ina Wuni?" Maalesh yace "Lafiya lao Beautiful, ya Jikin
Nene?" "Nene ta ji sauk'i Alhamdulilah" Kafin yace komi wayar
shi ta fara ringing, ya dauka, Nasiba ta kalli Rafeeq, duk da ba ita yake kallo
ba yasan shi take kallo, kamar ance ya kalleta, Idanuwan su suka hadu, ido
cikin ido suke kallon Juna, a sanyayye Nasiba tace "Hamma na Ina
wuni?" tsaki yayi ya dauke kansa, ko a jikinta ta tashi ta koma ciki, da
sauri ya bi bayanta da ido, duk ya ji haushin da be amsa ta ba, tsaki yayi ya
juya ga Maalesh, ashe tuni ya gama wayar, kallon juna sukayi, Nene ta katse
musu hanzari, gaban Maalesh ta ajiye kwano, tace "Maalush dan Albarka, ga
Zogale na kwandon ta maka kaci kai kadai kar ka ba kowa" ta karasa fadin
haka tana kallon Rafeeq ta gefe ido, sosai ta ba Rafeeq daria, kallon Gefen shi
yayi ya dinga Murmushin mara sauti a ranshi yace "Chill Tsohuwa, i cant
eat this Sh*t" Maalesh yace "Kai
Nenen mu kina ji dani fa, duk wannan ni kadai?" Ehmana dole nake ji
da kai, wasu ko kallo basu isheni ba ai" Rafeeq ya kawar da kanshi gefe
don yana gudun kar daria ta kubuce mai, wai don shi tsohuwar nan ke habaice
habaice, lallai tana da damuwa, ta shekara tanayi ko a jikin shi, haka Maalesh
ya zage sai cin Zogale yakeyi, da yake shi yana son abubuwan gargajia, Nene ta
dauko kujerar tsakar gida ta zauna, don ta na ta Rok'on Allah sa Rafeeq ya nuna
yana son ci ta k'are mai tanadi. Ga Mamakin ta har Maalush ya gama Rafeeq be
dago kanshi ba, Rafeeq ya zunguro Maalesh, ya k'agara su tafi, Maalesh yace
"Nene, bari mu tafi, gobe zan koma kano InshaAllah" Nene ta hau
suburbuda mai Adduo'i kala kala, ta kwalawa Seebi kira tace kuzo kuyi bankwana
Gobe zai tafi, ta fito ta raka su har Waje.
"Ya Maalesh a kano kake aiki? Yace aa, Service nakeyi,
befi wata 2 in gama ba, sai in samu aiki sai in fito a sa bikin mu ko? Dariya
tayi sosai tace "you are funny" yace "you think so ko?" ya
kalli Rafeeq yace "Guy, tell her ba wasa nakeyi" tsaki Rafeeq ya buga
tare da bude mota ya shiga, duk ba su damu ba don sun san saran Rafeeq na
tsaki, sai da sukayi Sallama kafin ya Shiga mota suka wuce.
*MAFARKI*
"Assalam
Alaikum Nasiba" Murmushi tayi tace "Sai yau Ko Yaruwa ta
Rafee'ah?" "Afuwan Ukhti, Ya Hakuri da Hidima?" Nasiba tace
"Toh mungode Allah" Rafee'ah ta fara magana cike da natsuwa "Da
farko zan fara da gode miki, kin aiwatar da Aikin Farko da na saka ki, ina me
miki albishir da kin riga da kin shiga Rayuwar Rafeeq, kinyi Namijin k'ok'ari,
ina jinjina miki, abu na gaba shine, kinsan ance duk yanda mutum keso ya ci
Nasara, ya kuma samu Albarka da Ribar Rayuwa, to ya bi Mahaifanshi, Musamman
Mahaifiya, duk yanda kake son samun Nasarar Rayuwa, Idan baka bi Mahaifiyar ka
ba, to ba zaka taba ganin daidai ba, duk me ka taba zai ruguje, kai ko da ka
samu to bazaiyi Albarka ba" Nasiba ta jinjina kai tace "Haka ne"
Rafee'ah ta cigaba "Toh abu na gaba shine, ki daidaita tsakanin Rafeeq da
Mahaifiyar shi, indai kina so Rafeeq ya gama Makaranta wannan Zangon, to dole
sai ya samu Albarkar Uwa, ba wannan ba dai, Duk da yana cikin Duhu, ya nemi
gafarar Uwarsa, don ko yau ya fadi ya mutu sai Allah ya tambaye shi, don be
nema samun Haske ba, ki Daidaita tsakanin su, Nasiba" Nasiba cikin Firgici
tace "Ta ya zanyi haka? Kinfi kowa sannin kafiyar Rafeeq, ina zan nema
Mahaifiyar ku? Ina zan ganta? Ta ina zan fara?" *Ke Alheri Ce* *Ke Alheri
Ce* *Ke Alheri Ce Nasiba Muhammad* bat ta Rafee'ah ta bace, a firgice Nasiba ta
farka daga Baccinta, "ki taimake ni Rafee'ah, atleast give me hint ya
zanyi? duk ta bi ta jike da zufa, Minsharin Hajjo ya tunasar da ita Mafarki ne tayi, da sauri
ta sauka kan Gado ta fita daga Dakin, ta dauro Alwala tazo ta kabbara Sallah,
sai da tayi Raka'ah Shidda kafin ta dukufa da Adduoi, Alkah ya shige mata gaba,
ya kawo mata komai a Sauk'ak'e.
*9:45am*
"Ki tsaya
kiyi Kallaci Seebi" "Aa Nene zanyi a Makaranta, sauri nake kar bus ta
tashi" "to Allah ya taimaka, a gaida miemo gayu" "Zataji
sai na dawo" da sauri ta bar Gidan ta na ciro yar Tecno dinta a jakka ta
latso number Usheey, "Usheey, kin isa National? Akwai Bus? Usheey tace
" Eh Seebi, biyu sun tashi saura daya, kiyi sauri kar ta cika mu
tafi" Seebi kamar tayi kuka, tace Gani nan na kusa bakin Titi, zan samu
Napep" "Okay to sai kinzo" Ji take kamar tayi gudu, don in Last
bus ta wuce bata san yadda zatayi ba.
Kamar a sama ta ga Motar Rafeeq a gabanta, bata san lokacin
da ta sake Murmushin da ke kara ma fuskar ta kyau ba, ba watawata ta zagaya ta
bude K'ofar ta shiga, k'amshin sa ya sa ta lumshe ido, ta bude baki zata gaishe
shi, sai kuma ta tuna wani abu sai ta fasa, har ya ja motar shi shiru shiru
bata gaida shi ba, ya saurara yana jiran ta gaishe shi amma bata ce ko 'a' ba,
a ranshi yace ko lpy? Ta gefen ido ya kalleta sai hura hanci take yi, tana
girgiza kaf'a tana kallon window, yau kuwa meye Haka? Guntun tsaki yayi yace ma kanshi "why do
i even care?" ya dauki hanyar Makaranta, kusan minti 10 ba wanda yace da
danuwan sa k'ala, Nasiba tayi wani shu'umin Murmushi, sun kusa Makaranta daidai
Daji-dajin hanyar, Nasiba ta daddage ta buga tsaki da k'arfi, har cikin kunnen
Rafeeq, da sauri ya dafe kunnensa da hannu daya, be yi magana ba, Tsut ta k'ara
jan wani tsakin da ya fi na farkon k'ara, Haushi ya cika Rafeeq, kamar yayi me,
be dai tanka ta ba, ya tsani Tsaki (kuji mun Rafeeq, wai ya tsani Tsaki) Nasiba
na lura dashi, ta k'ara jan wani dogon tsaki daidai ta taka burkin Motar da
Rafeeq yayi ji kake k'iiiiiiii, Nasiba ta tsorata sosai, ta kalleshi cike da
tsoro, ba tare da ya kalleta ba yace "Get Out" Nasiba ta juya ta kalli
dajin nan ga sanyi, gashi bata tunanin zata samu na Allahn da zai karasar da
ita Makaranta, har zata bashi hak'uri, sai kuma ta fasa, bude k'ofar tayi ta
fita, kamar jira yake ya ja motar shi ya wuce, ya barta nan tsaye, hawaye suka
soma kwaranyowa, tayi dana sani, meyasa take son k'ureshi? Ita dake son fiddo
shi daga yanayin da yake ciki, Meyasa ta k'osa, to gashi ya direta kan hanya,
kuma ba zata iya takawa ba, don tafiar da saura, ta rasa yanda zatayi ta zauna
gefen Titi ta na me rokan Allah ya kawo Bus ta tsaida su ko a tsaye sai ta
tsaya.
"Mtswwww" tsakin da Rafeeq yayi kenan Karo Na 8 bayan ya dire
Nasiba, meyasa zai ajiye ta bakin hanya? Yanzu if shes not careful Mota ya
bugeta fa? Tsaki ya sake yi tare da kallon Mirror dinshi, chan ya hango ta
zaune gefen Titi kamar Almajira, Tsaki ya sake yi yasa trafficator yayi U Turn
ya koma Baya, horn ya mata da sauri ta dago ta sake Murmushi, a ranta tace "Ba zai iya bari na anan
ba" kawar da kanta tayi gefe kamar bata ganshi ba, tsaki yayi da k'arfi,
ya danna mata horn, ko dagowa batayi ba,
takaici kamar me, wai shi yau ake ma haka? Allah Allah take kar yayi
zuciya ya barta nan, amma wani zuciyar ta bata karfin guiwa, Matso da motar
yayi kusa da ita ganin zai take mata k'afa yasa ta tashi ta hau kan dakali, da
k'yar yace "Get In the Car" A takaice tace "No thanks"
tsaki yayi yace " Nace ki shigo ko? So kike kiyi Missing Lectures?" a
tsiwance ta murguda baki tace" What do you care idan nayi missing
lectures? Werent you the one that dropped me here? Ba zan shiga ba" ta sake murguda bakinta, kamar Tv ya ke
kallonta, mamakin ta yake, yaushe ta koyi Rashin kunya? Yaushe ta samu guts din
mai magana haka? Yau Shi R-Lema ake ma haka? Lallai Yarinyar nan bata sanshi
ba, be san me ta taka ba. Abun Mamaki be daddara ba yace "ki shigo motar
nan" ta juya tace "ba fa zan shiga ba nace" kamar zaiyi kuka, besan lokacin da yace
"Will you Please get in the Car now? Please".
_Bibilicious Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
*This is for
y'lls Members of Miemee Bee 👄Novels, You guys are Simply the best, I see lotta _™Nasi-Feeq_ ,
lotta _™Nasi-Zaid_,
too bad no ~™Nasi_Lesh~ ,
lols😂 ILY'lls❤❤❤ Together
we keep it moving💋 *#1love*
Pg4⃣2⃣
"Oh
shit" ya fada da ya tuna abunda yace, yau shine da cewa please? Kuma ba
amfanin shi ba, sai na wanda ya ce ma wa? Lallai in har bata shiga motar nan ba
zai tafi kuwa ya barta, a 6angaren Seebi kuwa, kalmar 'Please' ta maimiata cike
da mamaki, Yau Shi R-,Lema ke cewa please, aah akwai cigaba, akwai nasara, amma
me tasan in ta tsaya jan aji tafia zaiyi ya barta, kuma ba lallai bane ya dawo
a wannan karon, a sakwan da be wuce iku ba Rafeeq yayi shawaran tafia, sakwan
da be wuce biyu Nasiba ta fada motar, be tsaya jira ba ya hau kan titi, ko
kallon shi batayi ba, shima bai kalleta ba, har suka zo Makaranta, ya kawo ta
bakin Department dinsu, ya na parking ta fita tayi banging door shi kanshi ya
firgita, ya bi ta da ido yana mamakin Wannan bak'uwar Halin da shi be san da
ita ba, to ko dai tana da damuwa ne? Saboda ya san ta kullum ta shigo Motar shi
sai ta gaida shi, in ko yayi dropping dinta sai ta zabgo mai addua tana mai
Godia, amma yau ba Sannu bare Nagode. Tsaki ya ja yana fadin "Matsalar ta,
i dont need her thanks, greetings whatsoever" ya ja motarshi yayi gaba.
Zaune take
kan lallausan Rug dake kusurwar dakin ta, jingina tayi kan luntsuma luntsuman
throw pillows da aka wa bangaren ado, Grapes take ci a k'asaita ce, Meema ta
shigo ta zauna kusa da 'yaruwarta, ta daga kai sama tana kallon POP din dakin,
da Walpaper, da wakeken gadon ta, ga madubi shak'e da turarruka masu yawa. Ta
dafata tace "Meema, ji yanda kike kallon dakin kamar yau kika fara shigowa"
Meena tace "Hmm Sis, ina mamaki ne, rayuwa na gudu, a wani lokaci, ko
gidan kanmu ba mu da, ba mu da Sanaar da ta wuce saida Abinci, amma in one
time, God has buttered our Bread" Sauda tayi saurin cewa "You mean My
Bread?" daria sukayi gabaki daya, tace " Tabbas ke mai sa'a ce, don
kuwa duk abunda kika sa a gaba, ba makawa sai kin cimma sa, ga ki da hangen
nesa da kuma hikimar magance Nesa tun kan tazo kusa" Saude tayi wani
shu'umin murmushi, tana jin dadin yadda kanwar ta ke k'oda ta. Meema ta cigaba
da cewa "saidai wannan karon na rigaki hango nesan da zata iya kawo miki
cikas, da sauri ta gyara zamanta tace "yi magana Meema" Meema ta
gyara zama tace " kin taba tunanin yadda Rayuwa zata kasance miki idan
Alhaji Habib yau ya fadi ya Mutu? Tace "Da sauri tace "bangane ba
Meema, yi min bayani dalla dalla"
Ina nufin yau in
Alhaji ya mutu, in banda tumunin takaba ba abun da zaki tsira dashi? Kina da
labarin Yau Alhaji ya mutu tsinke ba za a ba Aneesa ba? Don bata da Gadon shi?
Komai zaa tarkata a ba Rafeeq, be fi a baki kaso daya cikin takwas ba, sauran
kuwa na Rafeeq ne, shi zaa ba komai" tace Meema ina son Habib, ba na ma
tunanin mutuwar sa, kuma ni bazan kashe shi ba sabida Gadon sa be dameni
ba" Meema tace "ai ba ina nufin ki kashe shi bane, ina nufin in ta
Allah ta kasance ya mutu yau, da me zaki tsira, ai bana tunanin zaki tashi da
abun azziki, gashi diyarki bata da gadon sa balle a sa rai zaiyi yawa"
Saude tayi zuruuu tana nazarin Maganganun Meema, tabbas tayi Magana kuma abun a
duba ne "toh Meema yanzu, meye abun yi?" Meema tace kawai sawa zakiyi
ya Mallaka ma Aneesa wasu k'adarorin sa, da dukiya" Saude tayi Murmushi
tace "i know what to do, bari ya dawo daga tafiar nan".
Kwanci ta shi
ba wuya gun Allah, su Seebi Semester ta ha, don yau suka fara hutun
Mid-Semester break, haka kurum taji ita ta na son Zuwa Gida gun Iyayenta. Dama
Safiyyar Yau Hajjo ta koma gida, don Nene tace ta koma bakin aikinta ta ji
sauki, Nasiba ta shiga gun Nene, "Nene barka da hutawa" Tace
"yauwa Seebin Nene" tace "mun dan samu hutun kwana 7, shine nace
mu shirya mu tafi Kaduna mu dan chanza guri" Nene ta yi Kamar bata ji ta
ba, Seebi ta sake maimaita mata, tace" KE nasiba ki fita ido na, shin ni
tsarar kice? Nasiba ta kalli Nene da mamaki, tace me nayi? Nace wani abu da ba
daidai ba? Nene tace ki kalle ni ki ce man in zo muje Kaduna hutu, ni yar
firamare ce? Sai inje in ma Uwaki zaune cikinem gida, yan unguwa su tacewa Uwar
miji ta tare Gidan D'a to ba haka nake ba, in ma Mahammadun ya aiko ki to shima
zan gamu dashi" Nasiba ta kalli ta Nene cike da mamaki, shin me yayi zafi
haka? Girgiza kai tayi tace "Wallahi you are always out of point"
Nene tace "Eh baturen ma yaci kutumar ubanshi, nan gani nan bari"
Nasiba ta shige daki tana mamakin Nene, ita in anyi gabas to yamma zatayi, ta
gurgiza kai ta hau hada kayanta.
WasheGari
Tun da farar
Safiyya Nene ta shiga kasuwar 'yar kutungu, tayo ma su Ummi Siyayya, su garin
Alkama, Sansamin yaji, Kuka, busasshan kubewa, daddawa da dai sauran su. Sauri take ta dawo gida, tana shigowa taga
Nasiba na kalaci, ta sauke ajiyar zuciya, tace lafiya Nene? Nene tace
"Allah Allah nake kar ki tafi, don nasan ki da d'oki, tace "ya zanyi
in tafi ba muyi Sallama ba?" Nene tace "yo nasani? Da kin tafi da sai
kin raina kanki wallahi" tayi daria, "Me zai faru da na tafi"
tace "Wallahi mota zan shiga in biki har kadunan, in lakada miki na jaki,
sannan in juyo in dawowa ta Katsina" me Nasiba zatayi in banda daria,
daria har da hawaye, Nenen ma Dariya tayi.
Tayi shirin
tafiya, Nasiba tace da Nene "kinga ki shirya mu tafi, ya zaayi ki zauna ke
kadai a nan, hajjo ba ta nan, DonAllah Nene nah" Nene tace "Shin in
tambayeki, Shekaru 21 da daya da nayi nikadai cikin gida me ya cinye ni? Me ya
kama ni? Eyi? Nasiba tace " Wanchan Unguwar akwai mutane, kina jin motsin
mutane, wannan fa? Tace "Ke ni rabani, ba fa inda zani, Ina nan kinji
Nenen Seebi? Allah ya kaiki lafiya ya dawo mun dake lafiya" Amin Nene na,
tace to Nene ga wayata nan zan bar miki, sai mu dinga gaisawa muna jin lafiyar
Juna, ba musu ta amsa, sukayi Sallama har tasha Nene ta raka Nasiba gaban ta
suka tashi. Ta musu fatan Allah sauke su Lafiya. Ba ta bar tasha ba sai da ta
ma wani Conduster tatas don yace mata "Hajiya tafia ne?" tace
"aa uwarka ce". Tunda ta fara masifa bata yi shiru ba, wai ya mata
rashin kunya yana mata maganar Yan tasha, Da k'yar wani mutumi ya lallabata ya
Ya fidda ta waje ya sama mata Napep ta wuce Gida.
*Malali Kaduna*
Karfe Hudu saura
minti 10 (3:50pm)Nasiba ta shigo Unguwar su,m, a Lokacin ana ta kiraye kirayen
Sallahr Laasar, da ta hangi Gate din Gidan su taji wani sanyi ya ratsa ta, ta
biya mai Napep kudin shi ta fada gidan, tun daga Gate take kwada Sallama.
Ummin da ta yi
Rakiyya tace "Muryar wa na keji haka kamar Seebin Nene? Bata ankara ba
taji an fado mata a jiki "laah itace ashe", ta rungume diyarta suna
Daria, daga Katsinar? Ina Nenen? " tana chan ta k'i yarda ta biyo ni"
tayi daria tace "ba ki gaida Mamin Ayman ba" tayi daria tace
"sorry ban lura ba" Seebi ta juya ga inda matan da Ummi ta rako ke
tsaye, ga Mamakin ta, matar ita take kallo, ta shagala da kallon ta, Nasiba ta
tsurawa matar ido tana son tuno inda ta san fuskar, ta dai daure tace "
Ina wuni? Shiru, Ummi ta dan dafa Mami tace "Mamin Ayman wannan diya tacw na ce miki tana karatu a Jamiar
Katsina" Firgigi tayi kamar wanda aka tada daga bacci, tace "Allah
Sarki" ta juya ga Seebi tace "Lafiya lau, kin dawo Lafiya?"
"Alhamdulilah" ba ta jira sunce wani abu ba tace "barin koma
gida kafin Ayman ta tashi" to a gaidata inji Ummi, suka juya cikin Gida,
Mami ta tsaya bakin gate ta juyo tana kallon bayan Seebi, a ranta tace
"Allah mai iko, meyasa nake ganinta kanar Rafee'ah?".
Murna gun
Abbi da Anan ba a magana, kamar sun yi shekara basu ga juba ba, nan Nasiba ta
dauki wayar Ummi ta kira Nene, har tayi Ringing ta gama bata dauka ba.
*WasheGari*
Tun da Safe Nasiba
ta shirya Anan, ta raka shi har Makaranta, ta dawo gida ta ciro Garin Alkaman
da Nene ta siyo musu ta tankade shi, Abbi ya fito daga daki, ya ganta sai aiki
tankade takeyi, yayi Murmushi yace "Sarkin aiki, kin fa dawo kenan, to me
za a mana yau?" tayi daria tace "Barka da fitowa Abbi, Alkubus zan
mana" yace "Ahh kice yau zamu kwashi Gara" tayi daria, ta cigaba
da aikinta, ko da Ummi ta fito tace zata sa mata hannu cewa tayi "Ummi ki
bari, aiki na ne" haka ta zage ta kwaba Alkamar nan, ta yi hadin Alkubus,
da kanta ta fita tayo cefane, tazo ta gyara kayan miya da kabewa ta yanka
Alaiyahu, ta hada da kifin gwangwani, sai da Kwabin Alkamar ya tashi kafin ta
zuba a madanbacci, nan da nan gida ya kaure da k'amshi, bayan ta gama ne ta
zuzzuba a Cooler, Ummi tace "Ki saka ma Mamin Ayman, na san zataji dadin
shi" Wannan matar da kika rako jiya? Tace "eh ita, tana da kirki, ba
su dade da dawowa nan Unguwar ba, ta girmeni amma tana mutuntani" Allah
sarki inji "Nasiba" Ummi tace
"kiyi wanka ki mik'a mata, tunda Anan ya tafi Makaranta" Nasiba tace
"toh".
Kwanan shi
biyar be ganta ba, so da dama zai zo bakin k'ofar gidan yaga ko zai ga fitowar
ta amma shiru, ya mata text kala 2 ba reply, wayarta in ya kira har ta gama
ringing baya dauka, a rana sai ya jera tsaki fiye da dari, haka kawai yake jin
kanshi wani wani iri, gashi Maalesh ba ya nan, haka kurum yaji he wants to see
her, zumbur ya tashi daga kan gado, ya zura takalman shi, fita yayi daga gidan
be dauki Mota ba, ya taka har k'ofar gidan Nene, mintin shi sha biyar tsaye
gaban gidan, ya rasa yanda zaiyi, to wai ma ya ganta yace mata me? Tsaki yayi
ya juya, zuciyar shi tace to ko lafia dai? Ko ciwon Nene ya tashi ne shisa ya
daina ganin gilmawarta, ko a Unguwa sometimes ya kan ga wucewarta zuwa shago,
dawowa yayi, ya tura k'ofar gidan, ya shiga Chan k'asan Mak'ogaro yayi Sallama,
Nene na zaune tsakar gida tana gyaran wake ta amsa Sallamar tare da cewa
Bismillah, kamar ya juya da ya ji muryar Nene, amma be san me ke tunzura shi ya
shiga ba, cikin tafiar shi ya ida shiga gidan, Idon Nene a kan shi, a ranta
tace "Yau su Dunkum ne a gidanmu" ba yabo ba fallasa tace k'araso ga
wuri ka zauna, kan kujera ya zauna, chan taji yace "Sannu fa" kallon
shi tayi tace "Ahh! Ai kai ke da Sannu me ciwon baki" be tanka ta ba,
suka zauna jugum ita kuwa ta cigaba da tsintar waken ta, shi ko waige yake ta
inda zai ga ta bullo, amma shiru, ko duniya zata nad'e ba zai iya tambayar Nene
inda take ba" sun kusa minti 30 ba wanda yace ko 'kala, Nene ta yi Kamar
bata san da kowa gun ba, sai 'yan wakokin ta takeyi masu kama da habaici (kuji
min Nene kamar wata yarinya)haka ya k'araci zaman shi ya mike sai da yayi dan
guntun tsaki kana yace "sai anjima" kamar jira take tace "mu
jima da yawa" ya juya ya fita, ta bi bayanshi da gyatsine tace
"Dunkum dangin Tsaka".
"Assalam
Alaikum" ta fada cikin Siririyar muryar ta, Mami na zaune ta yi firgigit
ta tashi don Nasiba ta gani tsaye gabanta da kwano a hannu wasu lokuttan tana
rikidewa ta koma Rafee'ah, da Sauri ta amsa Kwanon Hannunta, ta rungumo tana
shafa fuskar ta tana hawaye, Sandadar Nasiba tayi, ta kasa tabuka komai, chan
Mami ta dawo hayyacin ta, da sauri ta ja baya tare da fadin "I'm so sorry,
kina min kama da diyata, kiyi hakuri" Nasiba ta girgiza kai tace
"lahh bakomai" ta jawo hannun ta ta zaunar da ita, suka gaisa, tace
"Ummi ce tace ako miki" ta bude Coolern tana fadin me muka samu? Ahh
Alkubus? Aikam Nagode sosai" ta dan ballo tasa a baki" gashi kuwa
yayi dadi" Murmushi kawai Nasiba keyi, Ayman ta shigo parlon dauke da Doll
babyn ta a hannu tana tafia dagwas dagwas, da alama tafiar batayi kwari ba,
Nasiba ta tsura wa 'yar diyar ido, har Ayman ta tako kusa da Mami, Mami ta
dagata sama, "Ayman baby na kin tashi? wa ya sauko dake daga kan gado?
Yarinyar dai lafe wa tayi jikin Mami, Nasiba tace "Ayman sunan ta? tace
"eh" Nasiba ta mik'a hannu tace "Zo nan Ayman" ga Mamakin
Mami Ayman ta nufa gun Nasiba, Mami tace lahh kin ciri tuta, k'uiywa ne da ita,
amma tazo gunki, ba ta yarda da kowa, ko gidanku mukaje bata yarda ta sauka
k'asa zata mak'ale a jiki, daga ni sai Baban ta je daukan ta" Nasiba tayi
murmushi tace "haka yara suke ai" Mami tace "to ya karatu? Wane
Course kike?" tace "MicroBiology" "Allah sarki ajinki
nawa?" tace "Aji na Daya" idon Mami ya kawo ruwa, Nasiba ta lura
tace "Mamin Ayman lafiya?" Mami tace "you see, Diyata bata samu
ta gama Makaranta ba, da ajinta biyu zata uku" Nasiba tace "Allah Sarki,
Aure tayi ne?" Mami tayi murmushi ne ciwo, tace ta koma ga Mahalici, shekarar ta
daya da rabi da Rasuwa" Nasiba ta rausayar da kai cike da
tausayawa, tace "Allah Sarki Ubangiji Allah ya mata gafara, ya sa ta huta
Amin" "Amin Nagode, shekarar ki nawa?" tace "19" tace
"ita kuwa tana da Shekaru 20 ta riga mu gidan Gaskia, Shes just like you,
ba wai kuna kama bane, aa, kawai ina ganinta a cikin ki, i see alot of her in
you, shiyasa lokacin dana ganki i was so emotional, ki dinga sata a adduar ki
kinji? Murmushi Nasiba tayi tace " InshaAllah, Ya Sunanta?" Murmushi
Mami tayk tace "Sunanta Rafee'ah" zabura tayi ta zaro ido tace
"Rafee'ah Habib Lema?" da sauri Mami
ta gyada kai hadi da cewa "Eh itace, kinsan ta ne?".
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
*Wannan Page din
nakune Masoya _Nene Mamman(Nenen Seebi)_
Nene loves you all❤*
Pg4⃣3⃣
Nasiba ta fara
sheshek'ar kuka ta nuna Mami da yatsa tace "kece Mamin Rafeeq?" da
Sauri Mami tace "eh nice Nasiba, kin san Rafeeq ne?" Allahi Akbar da
sauri Nasiba ta rungume Mami tana kukan farin ciki, Mami tarasa gane me Nasiba
ke nufi da kukan da takeyi ne, daga bisani ta tsagaita kukan da takeyi, ta
share hawayen ta, Mami ta tsura mata ido, tace "Nasiba me yasa ki kuka?
Shin dama kinsan Rafeeq da Rafee'ah? Ki min magana ծiyata. Wani guntun tunani
tayi ta girgiza kanta da sauri tace "aa ban sansu ba" ta mik'e da
sauri tace "barin je gida Umminmu na Jirana" ba ta jira cewar Mami ba
ta juya zata bar gun, da azama Mami ta rik'o hannun ta tace "Nasiba kar ki
min haka, na san kina b'oye min wani abu, daga yanayin da kike a yanzu nasan
kin san su, dukkansu, sanin da kika musu Sosai ne, ki fada min, Ya Rafeeq yake?
Ba ta bari sun hada ido ba, murya na rawa tace " ni bansan su ba"
haka kurum taji bata yarda da ita ba, akwai abin da ta ke 'boyo, ya zaayi da
farko ta nuna ta sansu har ta na fada mata sunayensu yanzu kuma tace bata san
su ba, ba zaiyiwu ba, yanda Nasiba takeyi ya nuna cewa tasan wani abu game da
Rafeeq.
Ta kamo hannunta tace "Nasiba ke da Anan kadai ne gun
Mahaifanku ko? Toh haka Rafeeq da Rafee'ah, na rasa Rafee'ah, K'addara ta
rabani da Rafeeq, Ina sonsa sosai, ina so in san Halin da yake ciki, tun bayan
tafian Uncle dinshi, bana samun Details yanda ya kamata, Misali Ummin ku ke
cikin situation dina, zaki so ki ganta cikin matsanancin hali?" ta nuna
zuciyar ta da hannu ta cigaba da cewa "You see dis heart of mine? Its
Empty, you have no idea what i've been through, i mean what i am going through,
i've Swallowed alot, ki taimakeni, Help a Helpless Mother please".
Nasiba ta isa gareta ta rungume ta, kuka takeyi sosai, ta
dago ta share hawayen Mami, tace " Mami ki bar kuka, i will tell you
everything i know about Rafeeq, da yanda na sanshi, Komai" jan Mami tayi
har kan kujera, ta dauki Ayman ta sata a baya, da hijabin jikin ta ta goya ta,
ta fara rirriga ta har ta koma bacci, ta kalli Mami tace "ina zaa kaita?
Da hannu Mami ta nuna mata cikin daki, Nasiba ta kai Ayman daki, ta dawo ta
zauna kusa da Mami.
"A Makaranta na
fara ganinshi, shi da abokin shi Maalesh, ina tare da k'awayena muna neman abun
hawan da zai maida mu Cikin
Gari.............................................." tsaf ta kwashe komai
da ya wakana tsakanin ta da Uncle Zaid da Rafeeq ta gaya mata daga ranar da ta
fara ganin su har zuwa rana irin ta yau. Abu daya ta boye mata, Mafarkan da
takeyi da Rafee'ah, bata gaya mata tana mafarki da Rafee'ah ba.
Mami tayi Murmushi tace "Its a Small World afterall, So
kakar kice Nenen da Zaid ke ban labari? Wacce ta bashi kuka da daddawa?"
kai Seebi ta daga, ta riko hannunta tana murzawa tace "Labarin da Maigadin
Lema ya baki, dukda ba ki gaya min me yace miki ba, kin yarda zan iya aikata
abun da ake zargina dashi?"
Murmushi Nasiba tayi tace " Bansani ba, and i wont Judge you, but i know a
responsible Mother wont do that at her Matrimonial Home" Murmushi Mami
tayi tana jin son Nasiba har ranta, irin son da take ma Rafee'ah tace
"kinsan lokacin da na fara ganinki, naji ina sonki, like i told you I see
Rafee'ah in you, Nasiba shin zaki zama diyata? We'll you make me feel like a
Mother again? Kuka Nasiba ta fashe dashi, ta rungume Mami ta na daga mata kai,
tace "Mami nah, you are my Second Mom" kukan farin ciki Mami ta fara
yi "Seebi na, ina sonki kinji?" nima ina sonki Mamina". Daria
sukayi duka.
Nasiba tace
"Ayman fa? Kin sake aure ne? Mami tayi murmushi tace "anya zan sake
Aure kuwa? Bana tunanin zan so wani ծa namiji baya ga Daddyn su Rafee'ah"
da sauri tace "Aa Mamina kar kice haka, ba me cire rai daga rahamar Allah,
kar kiyi Mamaki zaki koma dakin ki, abu ne fa na Allah, bana so kina cewa haka
kinji Mami na" Murmushi Mami tayi ta k'ara jin son Nasiba a ranta, tace
"Rafee'ah-Aymana taci sunan Marigayiya Rafee'ah, Ayman diyar Zaid ce, be
taba gaya miki yana da ծiya ba? tace "aa be fada min ba" Mami tace
"Matar shi ta rasu Shekarar da ta wuce, bayan suna ta Rasu" cike da
tausayawa tace "Allah Sarki, Allah ya gafarta mata, ya sa taci Albarkar
Haihuwa, ita kuma Allah ya rayata" "Ameen Ameen" Mami tace "to kodai Yak'i gaya miki yana
da d'iya ne don kar kice ya miki tsufa, ba kya son tsoho? Cike da kunya da jin
nauyi tace "Lahhh Mami" tayi saurin boye fuskarta jikin Mami don taji
maganar wani iri, ita kuwa Mami sai dariya take mata.
*Katsina*
"Shin
Sallama ake ko fito? (whistle) inji Nene, daga bangaren shi ya buga tsaki da
yaji muryan Nene, ji yayi kamar ya koma, don dai zuciyar shi na tunzura shi
yazo ya ga Seebi da ya juya wlh, don Wulakanci ya daddage yayi Sallama amma sai
tace yana whisir? Wannan tsohuwar na da damuwa, be bi ta kanta ba ya sake
Sallama cikiciki, tace "Shin, an amsa maka ka shigo mana" tsaki yayi
ya nufa cikin gidan, sanye yake da 3quarter, Nene na ganinshi ta chanza fuska
tace "Touuu, nidai ince, nasan za'a rina naji sallama kamar fito, ashe su
dunkum ne dangin tsaka" Ya kalleta sosai yayi kamar be jita ba, tace
"ka tsareni da ido, to ai sai ka zauna ga tayani gulma nan" ya tsaya
yana mata kallon rashin fahimta ta nuna mai kujera tace cewa nayi ga kujera ka
zauna, guntun tsaki yayi ya zauna, yana kallon saitin dakin su, yana jiran yaga
fitowar Seebi, Nene ta zauna kan tabarma kusan minti 15 be ce komai ba, da taga
shirun yayi yawa ta daure tace "ina Malush?" shiru be amsata ba, a
ranta tace ko dai be ji ni bane? Ta bude murya ta sake cewa "Nace ina
Malush?" shiru ya mata, Nene ta bude baki cike da mamaki tana kallon shi,
chan k'asa taji yace "Yana Kano" Lallai kawai tace tana jinjina kai.
Shiru ya sake giftawa har fiye da na dazun, kusan minti 20.
A karo na uku (3)
ya sake jin K'arar waya, tun dazun wayar ke ringing tana katsewa, k'arar wayar
na damunshi, kuma shi yak'i tashi ya tafi, dan guntun tsaki yayi ya kalle ta
yace " Wai ba karar Waya nakeji ba?" Nene ta hau salati, tace
"kai don Manzon Allah? Wai wayace? Yo tun Shekaran jiya nake jin irin
k'arar nan banyi zaton waya bace, wai ashe wayar Nasiba ce" be dai ce da
ita komai ba har wayar ta sake ruri, cigaba da surutu tayi tana bashi labarin
yanda takejin k'arar wayar kullum, ta ma mance rashin jituwar su, yace "ai
sai kije ki dauko ga wayar chan an sake kira" da gudu ta ruga daki, amma
kafin taje ya katse, kan Wardrobe ta ciro wayar, tun randa Nasiba ta bata wayan ta aje a sama ba ta sake
bi ta kan shi ba, ta fito da wayar a hannu ta mika ma Rafeeq "kaga dunkum,
duba min kagani waye? Kamar bazai amsa ba, sai da ya gama kallon wayar a
hannunta kafin ya amsa, ya jujjuya wayar a hannun shi, a ranshi yace
"Tecno, sai k'arar tsiya" ya bude wayar, 34 Missed Calls ya gani,
accordingly ya duba Missed Calls din, Abbina Uncle Zaid, Ummina, Ya-Maalesh
Miemee, Usheey, Hamma na, a ranshi yace Hamman ta? Messages ya duba, Daga na
Uncle Zaid, sai na Maalesh sai wanda ya mata, a sama yaji muryan Nene, inda
take cewa "Shin zaka gaya min wanda ya kira ko sai ka gama latse latsen
wayan, ko no engilish? Guntun tsaki yayi, da kyar yace "wai Abbi"
tace "Mahammadu ne, baban Nasiba latso min shi" a ranshi yace wa ya
tambaye ki? Ya mata dialing numbern, ringing daya suka dauka, cike da doki tace
"Halo, Mahammadu ya kuke? Yanda Nene ke waya zar takaici, kamar bakauyiya,
hakan yasa shi mikewa don tafia, ya kalleta yanda take daria, a hankali yace
"kina da matsala" karaf kan kunnen Nene, tace "da wa kake? Ni ke
da matsala? Matsalar ubanka?" be tsaya bi ta kanta ba ya fice daga gidan,
ta bi bayanshi har zaure, "tsaya mana, rasa kunya beran kitchen, da ba don
ina kunyar Zaidu bawan Allah ba yau da sai na maka mugun duka, in maka
lagalaga, in kuma kai ka Asibiti, yanda kayi jiyyata nima inyi jiyarka dan
banten uba" kwatakwata ta manta da wayar da takeyi. Su har sun gaji da
Magana sun kashe. Ta dawo ciki tana mita, ta kafa waya a kunne, Hello, daidai
nan Seebi ta sake kira da wayar Abbi, a firgice Nene ta cire wayar daga kunne
don k'arar ya cika mata kunne, ta latsa wayar ta kafa a kunne, tace "hallo
Mahammadu" Seebi tace "Nene na nice" cikin masifa Nene tace
"to dan kece sai ki dod'en kunne da kira?" Nasiba ba ta damu ba tace
"ke da wa kike fada, naji kina ma wani masifa?" nene tayi tsaki tace "ni
da wannan dunkum dangin tsakan mana, wai ni zai kalla yace ina da matsala"
Seebi ta gane da Rafeeq take, da Sauri tace "shi yazo?" tace
"tun tafiar ki kullum sai yazo, ya tasani gaba yayi ta kallo kamar Tb,
shine zai ceman wai ina da matsala, ai wallahi da ya tsaya da sai na bubbuge
shi" Nasiba ta shiga tunani a ranta tace "Allah sarki Hamma, ni yake
nema, i made a mistake da ban sanar dashi zanzo Kd ba" Nene tace sai ki
man shiru? Dallah bani Uwar taki mu gaisa" da sauri tace "Ahh Nene ga
Ummin ba sai kin zaga man Uwa ba". Daria Ummi keyi ta amsa wayar suka
gaisa da Nene. Seebi kuwa ta tashi ta fada gidan Mami.
_Malali
Kaduna_
Haka Nasiba zata zauna tayi ta ba Mami labarin Rafeeq, wani
zubin taji tausayin shi wani zubin tayi daria, kamar yanzu Nasiba ta bata
labarin Dramar Nene da Rafeeq, Mami tayi dariya harda k'walla, tace "ai
Nene ce daidai shi" tana burgeni, Seebi tace "ai haka mutane ke cewa,
wai Nene na na burge su, don dai basu zauna da ita bane, da tuni ta gudire su,
Nene is very Annoying Wallahi, don dai kawai tana da ban daria, amma kwana daya
zaki yi da ita duk zakiji ta isheki" Mami tace "ba wani nan, ni dai
ba zata ishe ni ba" Seebi tace "hmm, wallahi Mami ba zaki gane
ba" wayar Mami tayi ringing, Nasiba ta je ta dauko mata kan dining, Zaid
England ne ya fito a Screen, Nasiba tace "Mami ga Uncle Zaid" Mami
tace dauka mu rudar dashi" Seebi ta dauka wayan "Assalam Alaikum
Uncle Zaid" da sauri Zaid ya duba Screen din wayan ya ga dai Mami ya kira,
to ya yake jin muryan Seebin Nene? To ko kiran ya yi roaming ne ya koma numbern
Seebi? Tambayoyi da dama, da k'yar ya Amsa Sallama, yace "Seebin mu nida
Nene" tace "lahh ya akayi ka gane?" "your voice is always
on my head, ba zan taba manta da voice dinki ba" taji kunyar maganar shi
amma sai tace "arent you suprised? Ba number na ka kira ba fa? Zaid ya
tashi zaune yace "Noo way" tace "Yes Way, bari ma ka gani"
ta mik'a ma Mami wayan ta mata alama da bara taje gida ta dawo, Mami ta amsa
tana Daria, yace "Mami how is this possible? You met Nasiba?" tace "Ehmana,
what makes you think i wont find my Sister Inlaw? Or ince daughter na, don
diyata ce, kai ne siriki na" yace "shhh Mami kar ta jiki" tace
"kar ka damu ta je gida, mak'otan mu ne, Yayan Anan" da mamaki yace
"dama Nasiba yayan Anan ce?" tace "iko na Allah" yace to
Mami ya akai kuka saba da juna haka? Mami ta kwashe labarin da Nasiba ta bata
duk da briefly ta bashi, labarin da shi kanshi Zaid be sani ba, ya jinjina kai,
Mami tace "Wallahi Zaid baka ga yanda take son Ayman ba, yanzu haka tana
bayanta ta goya ta" Dadi ya lullube Zaid, duk me son shi, to ya so Diyar
shi, nan ya ba Nasiba wani matsayi a zuciyar shi, Mami tace "Allah ya sa
yanda take son Ayman ta so babanta, ko da yake dan k'anina haծaծծe ne, ba macen
da zata k'i shi" daria Zaid yayi yace "easy dai, sai na dawo zan
sanar da ita _sirrin dake raina_"
tace "sai ka dawo, yanzu sai yaushe?" yace "don sun raina
mu sun k'ara mana additional 2weeks, sai next month in Allah ya yarda" toh
Allah ya yarda, nan sukayi fira sukayi Sallama.
*Katsina*
Nene ina kika shige
ana ta kira? tace kai dai bari, gani ina ta Soya Farar da Anan yace a soya mai
in ka dawo da Seebi in baka ka kaimai" Abbi yace "kema dai Nene, sai
ki biye ma Anan don yace yana son Fara, shi yanzu haka ya mance" tace
"Tiya biyu na siyo mai, baka ga bak'ar wahalar da naci a kasuwa ba, kuma
ina dawowa na gyara ta, yanzu har na soya tiya daya, gani ina soya gudan
tiyar" Abbi yace "Taya b'era b'ari".
Yau be jira amsan Sallamar ta ba ya shigo ciki, sakamakon
wani k'amshin da yaji, ya na tunanin k'amshin meye wannan? Wannan dai ya fi
karfin suyan kaza, tana waya ta ganshi tsaye, tace " yau kuma Sallamar da
akeyi k'asa k'asa baa samu damar yi ba?
Ko muryar ce ta ida daukewa? Ni tashi min akai ga kujera chan" Abii yace
"Nene ke da waye?" tace "ni da Dunkum" "wanene kuma
Dunkum?" tace "ka tambayi Seebi waye Dunkum dangin Tsaka" Inaaaa
Sam Rafeeq be san tana yi ba, hankalin shi na kan Soyayar Farar da ke cikin
gwagwa, ya hadiye wani mugun miyau kamar tsohon maye, rabonshi da Fara shekari
sun fi 10, tun suna zuwa Islamiyya, nan Rafee'ah zata siyo musu, suyi taci, har
Farar dari 2 suke siya, haka kurum yaji yana son cin Farar nan, ko don tuna
baya, yana son cin farar nan for times
sake, kuma dai yana so. Nene ta sauke kaskon ta hadeshi da na gwagwan, tana
dagowa taga idon Rafeeq tsam kan gwagwar Fara wani shu'umin Murmushi tayi, a
ranta tace"Yau ranar Nene ce" Ta dauki soyayyar cinyar farar nan ta
sa a baki, ta wani lumshe ido tace "kaii wannan fara zad dadi, kamar kunne
na ya tsinke" Rafeeq ya sake hadiye miyau, suna hada ido da Nene yayi
saurin shan mur ya dauke kai, a ranta tace "yaro da ni kake zance" ta
shige daki ta zauna tana kallon shi ta windo, a ranshi yace "na san wannan
tsohuwar ba bani Faran nan zatayi ba, kuma gashi raina ya biya, i want, i will
just take it" be tsaya wata wata ba ya durkusa ya dibi guda biyu ya sa a
baki, waiyo dadi, yana kara sa hannu yaji an damk'o bayan rigar sa tace
"Yihuhu Na chafko shi, na chafko b'arawon fara ta" a hankali yace
"Akwai matsala Lord Have Mercy".
_Bibilicious Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg4⃣4⃣
Ya dago fuska
a daure kamar bai taba dariya ba, ya bi hannunta da ido, yanda ta rik'e mishi
bayan riga, a hankali yace da ita "Sakeni" tace "nak'i na sake
ka din, nace nak'i" yace "me na miki da zaki rike min riga?"
"tambaya kakeyi? To Sata kai man, ka satar min Fara" ya sake tamk'e
fuska, wai wani irin Sata?" wanda ka min mana, ai daukan abun da ba naka
ba Sata ne, ni kuma ban baka Fara ta ba ka dauka" ya nuna farar da yatsa
yace "wanchan abun zanci, Allah ya kiyaye in ci k'waro" tace
"Kai Dunkum, ka fita idona, ni da na ganka durkushe, in ba ci min Fara
kakeyi ba meyasa zaka durk'usa a gun? Ruku'u kakeyi?" da k'yar yace
"da ki ka ganni Durkushe k'andagare na ga zai hau, shine na kore shi, dana
sani da na barshi ya hau" tace "Ayiriri nanaye, kai Dunkum ka raina
ma kanka wayau ba ni ba, Shekaru na Goma so Shidda da dori (60+) kasan ko ba
kalar barikin da ban gani ba, tunda ka ci min Fara ta, ina so ka amsa laifin
ka, ka bani hak'uri a wuce wurin" guntun tsaki yayi ya juya zai bar gidan,
da sauri ta jawo rigar shi, tace "Sai fa ka ban hakuri" a k'agauce
yace"Goodness, Wallahi kina da Damuwa, ga ki da Hayaniya" tace
"zaka ga damuwa idan kaji ka a *Jakar Magori*" kallon Rashin Fahimta
ya mata, tace "Too, ba ka san Jakar Magori ba ko? No radio a gida? To
wurin da zan kai Labarin ka ne, k'arfe 11 dare in ka kunna Radio zakaji ance
"Jakaaaar Magori, Dunkum ya Saci Farar Nene a garin Katsina" a ranshi
yace "this Woman is Unbelievable, zata aika" ganin idan ya biye mata
zasu ta Fafatawa ne, gashi kuma yau ta sashi magana fiye da Sentence 10, kanshi
har ya fara ciwo, juyawa yayi zai fita, Nene ta sake Chafko Rigar shi, Tsoki ya
buga da k'arfi yana cewa "wai ke wace iri ce?" "sai fa ka bada
hakuri"
Daidai nan Maalesh ya shigo da Sallama, Nene na ganin shi
tace "Yauwa Maalush, zo kayi Shaida, Dunkum ya min satar Fara"
Maalesh da Murmushi kwance kan fuskar shi yace "Nene, ban gane ba?"
tace ka tambayi "Dunkum ya maka bayani" ya juya ga Rafeeq ya ga irin
rik'on da ta mai kamar wanda ya saci Mota, daria ya kubce mai, yace "Guy
howfa? Looks like you've fall into the Old Woman's trap, what did you do?"
Rafeeq cikin k'uluwa, yace "Tell her to let go" dak'yar Maaldsh ya sa
Nene ta sake Rafeeq, tace " yo Maalush, ci min Fara yayi, kuma ni ban
bashi ba, kuma ya k'i yarda ya ban hakuri, ni ko na kamashi kamar na kama
Aradu" Maalesh ya fashe da Daria, ya juya ya kalli abun da aka kira da
Fara, ya yamutse fuska kamar ya ga kashi, ga kalli Rafeeq da mamakin ta ya ya
ci wanchan abun me kama da kyankyaso, yace "you ate that? Rafeeq yace
"You are crazier than she is, i cant eat that" kamar ta san abunda
yake cewa tayi saurin cewa "Karya yake, a shinshina hannun shi"
Maalesh ya shashantar da maganar ta hanyar tambayar Nasiba tace "ai Nasiba
kwananta 4 Kaduna Jibi zata dawo" "Lord of Mercy" inji Rafeeq,
so All this While Nasiba na Kaduna? Yake bata lokacin shi on this Woman? Yazo
ya sha zaman banza amma bata ce mishi Nasiba ba ta nan ba? (Ka tambayeta ne?)
dogon tsaki yayi ya fincike mukullin hannun Maalesh ya fita, Nene ta bishi tana
dariya tana fadin "Dunkum tsaya kaci Fara, tsaya a k'ulle maka Leda"
daria takeyi sosai, don ta san yau tayi maganin Dunkum, Maalesh yayi Dariya,
yace "ranshi ya baci, barin je" tace ranshi ne ya baci? To ya sa omo
ko kilin ya wanke shi" Maalesh yayi dariya, yace barin je Nene zan dawo
Anjima nima iso wata kenan" tace "Allah huta gajiya" ya fita amma be ga komai ba sai k'urar Motar shi,
Murmushi yayi ya taka zuwa Gidan Lema a k'afa.
Yana shigowa
dakin ya fada Toilet dinsa, Shower ya sakar ma kanshi, tunani kala kala, wai me
ke kaishi gidan Nene ne? Zuciyar shi ta bashi amsa da "Kana kewar wannan
Yarinyar ne" da sauri yace "Noo, ba ita nake missing ba, i only miss
seeing my Sister in her" tsaki yayi yace "stop getting to my head i
dont want" haka ya cigaba da magana shi kadai kamar zararre.
*5:00pm*
Zaman kadaici ya
ishi Nene, ta rasa yanda zatayi, gashi ita ba gwanar shiga Makota ba, don
gidajen makwabtan akwai Karnuka, kuma ai ta k'wank'wasa wa ba a amsa, Wayar
Nasiba ta dauko ta kura wa wayar ido tana jira a kirata, shiru, ta na ta 'yan
latse latsen ta, bata san ma dai abun da takeyi ba, tsaki ta buga "ina
dalilin zaman mutum shi kadai" (Nene ke kika jawo) ta jawo Gyalenta ta
fita waje,tana kallon Unguwar, Mugun tsaki ta buga da ta ga Unguwar Wayam ba ko
dabban da ke wucewa, Kamar a sama taga wata Mota Me kalar bula(blue) ta doso
ta, ai da murna ta fara sa ma Motar
Hannu.
Birki na cikin
motar su ka ja k'ii, don ba su lura da ita ba, a fusace Meema ta fito, Aneesa
ma ta fito, Nene da Murmushin ta tace "Sannunku 'yan jikokina, kuyi
hak'uri na tsaida ku, DonAllah ku dan latso min Zaidu bawan Allah a wayar
nan" ta na me mik'a musu wayar Nasiba, Meema ta kalli wayar cike da tsana
tace "Ke Almajira, in banda
jahilci, ba ki sanmu ba zaki tsaida mu kice mu kira miki wani? Har kina daura
k'azamin hannun ki kan mota ta?" Aneesa tace "Aunty Mee mu tafi don
Allah, irin wannan da su ake conspiring a maka wani mugun abun, its all a
ploy" Ta ja hannun Auntyn ta, suka koma Mota, Meema ta ja motar tare da
bad'e Nene da k'ura, yanda kuka san Hoto haka Nene ta tsaya, wai yau ita a ka
ci ma fuska kuma ba tace komai ba, haushinta daya da ba ta ci uwar babbar su
ba, amma a fili tace "Ubangiji Allah ka sake hadani da su" ta koma
Cikin Gida tana jin haushin kanta.
*Malali
Kaduna*
"Nasiba, kin
taba ganin uwar da tayi fushi da danta? ko tayi fushi dashi na wasu lokaci ne,
ko me ya ke mata ba za ta tab'a fadin Mummuna kalami a kanshi ba, tsakanin d'a
da Mahaifi sai Allah, balle ni da ban taba ganin Laifin Rafeeq ba illa Laifina,
nice na sakashi a halin da yake ciki yanzu". Nasiba ta kamo hannun Mami
tace "karkiyi Blaming kanki, k'addara ce ta riga Fata, nidai DonAllah kice
kawai ki yafe mishi duk da kince be miki komai ba" Mami tayi Murmushi tace
"Toh Nasiba, na Yafe ma Rafeeq Duniya da Lahira, na yafe mishi, Ubangiji
Allah ya sa ya gama da Duniya lafiya, Allah ya bashi saar karatu, Allah ya ma
Rayuwar shi Albarka" da sauri ta Rungume Mami dadi kamar ya kasheta, ita a
ganinta zataji Saukin komai tunda Rafeeq na tare da Adduar Mahaifiya, tace
"Ameen Mami, ki Cigaba da mishi addua kullum, InshaAllah ba zai tab'a
tab'ewa ba" Mami ta tsura wa Nasiba ido cike da k'auna tace "Bless
you Daughter, you have an Amazing Heart, Ke Alheri Ce" Murmushi kawai Nasiba tayi, don bata son
tayi magana Mami ta cigaba da kukan da takeyi, tace "Mami yaushe zakizo
Katsina? Katsina na missing dinki" Murmushi tayi tace "i have no
Bussiness left in katsina, Duk Wata Baba na da Mama na su na zuwa duba ni"
Nasiba ta sigar zolaya tace " are you sure you have no Bussiness in
Katsina? Mahaifarki ce fa, besides, your One and Only Love is there, nasan he
still inside that pure heart of yours" Mami ta daburce tana unconditional
Murmushi, tace "ke Nasiba maganar me kikeyi haka? Shuttup ni ba kowa a
zuciya na, na tsufa" Nasiba tayi dariya tace "Is that so? Then why are
you blushing?" Murmushi Mami tayi tace "How i wish zan sake ganin
Habibullah" "Awwwn Mami ta tuna da tsohuwar Zuma" tace
"Kinsan ana cewa Zaid me kyau ne, Hafiz Me kyau ne, amma Wallahi duk Habib
ya fi su kyau, harta Rafeeq da ke kama dashi be kamo k'afar shi ba" Sosai
Nasiba tayi daria tace "zai k'ara kyau idan kika koma dakin ki" Mami
tace "Hmm nagaji da tsammanin Ranar nan" Nasiba tace "Dont worry
Mami,Akwai Allah, gaskiya zata baiyana, zai gano gaskia da na rashin bincike ne
ya sa shi daukar mataki take yanke, amma kar ki damu, Have faith" Mami
tace "dadi na dake you give me Hope" Sukayi Murmushi, kuma chan sai
Mami ta fara matsar k'wallah, Nasiba tace bari in kira miki Nene ki sha dariya.
*Washegari*
Ina Nasibar ne?
Sai mun rasa Motar K'arfe 10? Ummi tace "wai ta shiga yi ma Mamin Ayman
Sallama yanzu zaka ga ta taho" Abii yace ai gwara tazo mu ta tafiya.
Mami tace "Yanzu ba zaki k'ara mana hutun ba? Kin bari
mun saba sosai sai kice zaki wani koma?" tace "Ayyah Mami, nima na
saba dake Sosai, idan mun tafi ba zamu dade ba zamu dawo, trust me zan
dawo" Mami tace "to shikenan, ga wannan kiyi using as Pocket
Money" "Nooo Mami i cant accept your Money" Mami ta tsura mata
ido, tace "ni na dauke ki ne a matsayin Rafee'ah, and i can do anything
for you, don break my heart" "Mami kudin sunyi yawa ne ki raba
biyu" " Haba Nasiba dubu Goma ne fa, ba yawa, inshort why dont you be
like Rafee'ah? Be like Mami kudin sun min kadan, i need more" daria Nasiba
tayi tace "Okay, I'll accept this Nagode" "Yauwa diyata"
tace "One more thing" ta zaro dan karamin Zoben da ke k'aramin yatsar
ta ta sa ma Nasiba a yatsa tace "this is my love for you" Nasiba ta
bi zoben da kallo, tana so ta tuno inda ta san Zoben, Zoben me kyau ne sosai,
kuma Azurfa. Mami tace "kinsan waya bani Zoben Nan?" ta girgiza kai,
Mami tace "Rafeeq ya bani shi on my 40th Birthday, Daga Dubai ya sa akayi
su Guda 2, ran Birthday na ya sa min a yatsa yace "Mamina, this is my love
for you" ya bani gudan yace in sa mishi a, yace "this is the twin of
your ring, even if we are far from eachother, this Ring is linked to Our
hearts" daria kawai nayi nace dashi"he's Crazy" amna Nasiba
yanzu Rafeeq ya tsane ni, nasan Ya dade da wurgar da Zoben shi" Nasiba
tace "Aa Mami, wallahi be wurgar dashi ba, yana nan a yatsar shi, ni na
san na san Zoben nan a wani wuri, a Yatsar Rafeeq na sanshi" Mami tayi
dariya tace"Nasiba kenan, you want me to feel better, shikenan naji, its
yours now" Nasiba tace "Aa Mami, wannan naki ne, ki ansa" Mami
tace "bansan gardama tashi muje, ni ma zan kai ku tasha, kar ku rasa motan
hawa" suka fita tare, a ranta tace "with this Ring Rafeeq, you'll be
your Mother's Son Again". Da sauka shiga gida ne ta nuna ma Ummi kudin da
Mami ta bata, Ummi ta mata fadan meyasa ta amsa, Mami tace don na ba diyyata
kudi shine nayi laifi? Ko iko zaki nuna min kanta ki nuna min diyarki ce, tace
"laaaah Mamin Ayman be kai nan ba, ai an fi so diyarki taji
tausayinki" Mami tace kya dai ji dashi, gabaki daya sukayi daria.
*4:00pm*
*Layout, Katsina*
"Sannun ku da zuwa, kun sha hanya"
Ya mutan Kaduna? Duk suna lafia, Nene ta gabatar musu da Danwaken da ta musu,
tana basu labarin zaman kadaicin da tayi, Nasiba tace "Oho dai, ke kika
jawo, sai da na ce miki ki taho mu tafi kaduna, ki ka k'i" tace "ke
ni ban son mita ba gashi kin dawo ba? Ko wani abun ya kamani?"
tace"kin daiyi kewa ta" Nene tace ko kadan, ban k'i ki koma ba, ko a
habar zane na" Abbi dai na jin su sai dariya yake musu. Suna cikin cin
danwake sai ga Maalesh da Rafeeq sunyi Sallama, da Sauri Nasiba ta kalli kofar
zaure don jin muryar shi, sanin kanta ne tayi missing din Hamman ta, shima
karaf idonshi kanta wani naunauyar Ajiyar Zuciya yayi, "Finally! shes
back" Maalesh kuwa Murmushi ya bita dashi, Maalesh ya matso ya ba Abbi
hannu, ko be sani ba yasan Baban Nasiba ne, Abbi ya bashi bayan hannu don yana
cin danwake da hannun, Maalesh a ladabce ya gaida shi, Nene kuwa cewa takeyi
Sannu da Zuwa Malush, Nasiba ta tashi da sauri tayi kamar zata shiga kichin,
daidai yanda zaijita tace "He's my Dad, show some Respect" harara ya
bi bayanta dashi, yayi dan guntun gajeren tsaki ya da zata ji shi ita kadai, ya
dan matsa kusa da Abii da k'yar yace dashi "Barka da Yamma" Abii yace
"Muna lafiya?" Ido Cikin Ido suka kalli juna, nan da nan yaga baban
Nasiba ya mai kwarjini, haka kurum ya kasa shiru ya amsa da "Lafiya
k'alau, anzo lafiya?" Abbi yace "Alhamdulilah" Nene tace
"Ahh su Dunkum yau anyi Wayau" Hararar ta yayi ya dauke kai, Abbi na
kallon shi, akwai wani Hikima tattare da yaron, akwai wani abun da ya hango
game da yaron, daga gani Yaron dan Baiwa ne, yanda yake abubuwan shi, yana
kallon yanda Maalesh ke bin Nasiba da ido, amma shi wannan kallo bata ishe shi
ba, haka kurum yaji yana son sanin game da Yaron, bude baki yayi yace
"Seebin Nene, zubo ma bak'i danwake" Maalesh Yace "Aa Baba
mungode bana cin danwake" "Abokin ka fa?" da sauri Nene tace
"Ya k'oshi da dai Fara ne, wannan ko ba a bashi ba zai dauka" duk
suka bita da ido cikin rashin Fahimta, dauke kai Rafeeq yayi, Abii ya k'ara
cewa "a zubo maka Danwaken?"Kamar jira Rafeeq yake yayi saurin hadiye
wani miyau, tun da ya shigo gidan ya ke bin Danwaken plate din Abbi da ido, ya
sha Mai, da kayan hadi, yana iya cewa Danwake ne best food dinshi, rabon shi da
ci tun Mami na nan, kuma gani yake wannan tsohuwar da gayya take abubuwa don ya
nuna ya na son ci ta samu damar Wulakanta shi, girgiza kai kawai yayi alamun
aa, in har yace baya son cin danwaken nan to yayi k'arya, har ranshi ya biya,
kuma besan dalilin da ya sa Nene keyin duk wani abun da yake son ci ba, shi da
abinci be damai ba, tsaki kawai yayi, Duk abunda yakeyi a idon Abbii, ya kalli
Maalesh yace "ya sunanka?" Maalesh cikin ladabi yace "Sunana
Mahmud" Nene tace "laah gaka da suna me dadi amma ka yarda ake ce
maka Malush" daria kawai yayi, Abii ya maida hankalin shi kan Rafeeq da
kwatakwata ya dauke kai, yace "Kai fa ya Sunan ka?" Rafeeq yayi kamar
be ji ba, shi kuma Abii be sake tambayan shi ba, Nasiba kuwa jikin ta ya fara
rawa, bata so Rafeeq yayi banza da mahaifinta, bata so mahaifinta ya tsani Rafeeq
kan halaiyar shi, da Rafeeq yaji shiru, ba a sake tambayan shi ba, ya dago kai
a hankali ya kalli Abii, shima shi din yake kallo, gajeren tsaki yayi a hankali
yace "Sunana Rafeeq" Abii ya jishi sarai, yace "Banji ba"
kamar ba zai tanka ba, amma Abii ya mai girman da ba zai iya share shi ba, ya dan bude murya yace
"Sunana Rafeeq". Abii ya jinjina kai, Rafeeq yayi Zumbur ya mik'e
sabida yana jinshi wani iri gaban Abii, ganin haka Maalesh yace "to Nene
mun gaida ku, bari mu wuce" tace "Toh Malush mungode, su Dunkum a
gaida gida" tuni ya kusa Zaure, Abi ya bude murya yace "Rafeeq"
k'yam ya tsaya ya kasa tafia, da k'yar ya juyo, Abii ya kalli Nasiba yace
"Je ki zubo mishi Danwaken" a hankali Rafeew yace
"Nak'oshi" Abbi yace "Ka tafi dashi anjima sai kaci" dama
tuni Nasiba ta cika Umurnin Mahaifinta, ta kawo ma Rafeeq Coolern, dauke kai
kawai yayi, ganin haka yasa ta ba Maalesh Coolern, Maalesh ya amsa yayi Godia,
ya ja Rafeeq suka bar Gidan. Nene tace "Yau kam me ke damun Dunkum?"
Abii ya zauna yace "Seebin Nene, Wanene wannan? Me kika sani game
dashi?" Gaban Nasiba ya yanke ya fadi, Nene tace " ai wannan shin
d'an Zaidu Bawan Allah da na jima ina baka labari, shi haka yake, wani Dunkum,
ba fara'a, ba ilhamar fuska, yanda kasan takashin shanu, haka fuskar shi take
murtuk'e kullum" Abbi ya jinjina kai, yace "Seebi, bakin ki akwai
Magana, me kikasani game dashi? Ni na hango bak'in duhu tattare dashi"
Nene tayi karaf tace "bawani bak'in duhu, Fadin Rai ne kawai ya mai
yawa" Seebi tace "aa Nene, akwai wani Labarin da ban sanar dake game
da Rafeeq ba, kunji kunji••••••••••.
Tsaf ta kwashe labarin Gidan Lema ta basu, kamar yanda Baba Maigadi ya sanar da
ita, kamar Yanda ta gaya ma Mami, Ta dai b'oye Mafarkin da take da Rafee'ah.
Allahu Akbar inji Nene "Allah Sarki Dunkum, ashe ba yin ka bane, Lallai
akwai B'oyayyen Alamari a tattare da Gidan nan, ni gaskia ina zargin matar
Baban su" "aa Nene kar kiyi saurin zargi" "tace dole iz
zargeta mana Mahamman, ita kadaice zata yi hakan" Abbii yace "kamar
yanda shi da kawun shi suka taimaka miki lokacin da baki da lafiya, InshaAllah
zan taimaka mishi da wasu Adduoi, kuma kafin in bar Katsina zanje gun Abokina
Me *Arriyadh Islamic Medicine* a taimaka mishi da magunguna, har shi mahaifin
shi, in ma akwai Kaidin Mace da yardar Ubangiji komai zai warware cikin iko na
Allah" Nene cikin jin dadi tace "Yauwa dan Mallam Jikan Mallam, da ba
ka shashanatar da kanka kan boko ba, da yanzu ni nasan kai babban Malami ne da
ake tak'ama dashi a k'asa baki daya, yanzu ma na san zakayi k'okarin ka"
Nasiba kuwa bata san kalar Farincikin da zata yi ba, hak'k'un ta yarda da
Mahaifinta, kuma ta na murnan zai taimaka ma Rafeeq, sai dai su Rok'i Allah ya
basu nasara.
_Bibilicious Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Assalam Alaikum,
ina muku fatan Alheri, ina godia da yanda kuke biye dani a wannan labarin, ina
me baku hak'urin rashin ji na da kukeyi kullum, hakan na faruwa ne saboda wasu
'yan dalillai, kuyi min uzuri don zan dinga tsallake kwana daya banyi typing
ba, in kuma an samu yanda nikeso, zaku dinga jina kullum kullum, Nagode Allah
bar zumunci.
Pg4⃣5⃣
Abbii da
Nasiba gaban Mallamin *Arriyadh Islamic Medicine* bayan Abbii ya karanto ma Mallam
Matsalolin Gidan Lema. Mallam Usman ya jinjina kai, yace "Alhamdulilah,
wannan labari da kuka bani akwai 'kulalliya, ko ba sihiri zamu taimaka da
adduoi, balle wannan ma daga ji an san akwai Sihiri, ta iya yiwuwa Shi Alhajin
an sa shi ya mance Uwargidansa, tunda kunce be sake waiwayarta ba, sai kuma shi
Rafeeq baa so ya gama Makaranta tunda ance shekarar sa ta biyu kenan yana
maimaita aji, kuma ba wai don ba ya ganewa ba, kuma ba ya k'aunar uwarsa,
alhalin duk yanda Uwarka take to akwai wannan So da K'auna dake tsakanin su,
toh tabbas akwai Mak'arkashiya a ciki kuma InshaAllah zaa warware komai da
yardan Ubangiji. Abu na farko;
Ina so su sa a ransu cewa duk abunda ya samu bawa to da
yarda da ikon Allah ya same shi. Su kasance masu Adduoi da Tauhid, Zaa musu
magani duka, Shi Alhaji zaa bashi maganin da zai taimake shi ya tuno abubuwan
da suka faru a baya, shi kuma Rafeeq zaa bashi Maganin da zai sa mai dangana a
ranshi, yanda zai yafe ma Mahaifiyar shi, wani Jarka Mallan ya dauko, yace
"Wannan Ruwan Karatun Kurani mai girma da Addu'oin Shifa, Lallai Rafeeq da
Habib su maida shi ruwan Sha din su, in so samu ne ko abinci a dinga dafa musu
da shi, shi zai tsare su daga Sharrin mai Sharri" ya ciro wani robar swan,
yace wannan kuma Man itattuwa ne, Man Habbatussauda, Man Ridi, Man Hulba, Man
Zaitun, Man tafarnuwa, Garin Luban, da Adduoi kama daga AmanarRasulu, Ayatul
kursiyu, da zikirin Safe da Maraice, Wannan na Rafeeq ne, shi ne zai saka mishi
Salama da dangana a rai har yaji cewa yana son sanin abun da ya faru a wannan
bak'in rana. Sai Kuma Saukar Alkurani da zaa musu sai ayi tawassali da Karatun
sai a rok'i Allah ya baiyanar da Gaskia. Amma dole sai sun yarda da hakan,
maana sai sunyi Imani da Allah shi zai firda su daga Abun da ya shige musu
duhu".
Abbii yayi Godia Sosai, yace "InshaAllah zaayi yanda
kace Mallam Usman, Nasiba kina ji ko?" Nasiba da zufa ya gama keto mata,
tana tunanin yanda zaa sa Rafeeq shan wadannan Magungunan. Da sauri ta gyada
kai, tace "Eh Abii, zaayi yanda yace" yace to Madallah. Magungunan
Dubu Sha biyar ne, amma saboda Sanayyar da ke tsakanin Mallam da Abii yace su
bada dubu 10, kafin Abii yace wani abu Nasiba ta zaro kudin da Mami ta bata ta
mika ma Mallam, Abii ya bita da ido, ta shaida mishi "ai kudin da Mamian
Ayman ta bata ne" haka suka dawo gida cikin Keke Napep.
"Tabdijam, ai yanda ka bashi Magungunan nan haka zai
dire maka su don ba sha zaiyi ba Wallahi" cewar Nene bayyan sun bata
labarin abunda ya faru a Islamic center, Nasiba tace "Abii ka kirashi ka
mai Magana k'ilan idan yaji daga bakinka, ya dinga sha" Abbii ya jinjina
kai, yace "Kira min shi a waya" da sauri Nasiba ta amsa wayar Abii ta
sa mai Number Rafeeq tayi dialing, Wayar ta dade tana ringing, har ta gaji da
ringing ta mutu, kallon Abbi tayi tace "be dauka ba" Nene tace
"ina zai dauka yasan zaku sa shi magana, Abii yace "sake kiran
Shi" Nasiba ta sake kira, sai da ya kusan tsinkewa ya daga, dama yana
ganin kiran farkon, ganin be san number ba yaki dagawa sai yanzu, Karawa kawai
yayi a kunne ba tare da yace komai ba "Assalam Alaikum" muryan Abbi
ya ratsa mai kunni, zumbur yayi ya mik'e, sai dai ya kasa amsa Sallamar, Abii
yace "Rafeeq, in ka samu lokaci, kazo gidan Nene yau ina jiranka"
Abbii be jira amsar Rafeeq ba ya kashe wayar, Rafeeq ya tsura wa Wayan Ido
kamar zai ga Abii a hankali yace "Why is he Bossing around?" guntun
tsaki ya koma ya kwanta.
Da kyar ya iya
cewa "Assalam Alaikum" Abbii ya amsa tare da umurtan shi ya shigo, ya
shiga ya zauna kan tabarma, Nene da Nasiba na ciki, basu san shigowar shi ba,
Abbii ya tsura ma Rafeeq ido, guntun tsaki yayi yace "Barka da Yamma"
Abbii yace "lafia lao Rafeeq, ka ci Abinci?" samun kanshi yayi da
girgiza kai alamun "aa" Abbi ya ciri baki ya kira Nasiba "Seebin
Nene, zubo ma Rafeeq Abinci" Nene ta kalleta tace "Dunkum yazo
ne?" Seebi tace "ya zaayi in sani ni da muke nan zaune dake"
Nene ta kai mata duka tace "Tambayar ki nayi ba ce miki nayi ki gayan
magana ba". Rafeeq ya kalli Abii, yana so yace mishi kar a zubo mai abinci
amma ji yayi bakin shi yayi nauyi, ya kasa Magana, shi besan dalilin da yasa
yake jin shi wani iri gaban Baban Yarinyan nan. In ma dai girma ne Daddyn shi
ya girme Abbii Nesa ba kusa ba, guntun tsakin mts yayi, Nene ta zubo mai
Shinkafa da Miya, da lettuce a gefe, tazo ta ajiye mai, karaf idon shi ya kai
ga Zoben yatsan ta, kafin ya samu damar sake ma Zoben kallo ta tashi, tace
"Hamma Ina wuni" bata sa ran ya amsa ta ba ta koma cikin daki, Abbii
yace "Bismillah" ba musu ya ja plate din gaban shi ya fara ci a
hankali, be ci da wani yawa ba ya ture, Abbi bece komai ba yace
"Rafeeq" Kasa amsawa yayi ya dago kai ya kalleshi, Abbii Wani
makaranta kake? A k'agauce yace "Umyu" wani Course?
"BioChem" Abbii yace shekarar ka nawa a School din? Da sauri Rafeeq
ya kalleshi, Abbi ya mishi alamun ina sauraren ka, guntun tsaki yayi yace
"6years" Abbii yace "Spilling kake tayi?" "Uhm"
kawai yace don baban Nasiba ya fara k'ureshi, "Let me help you" a dan
tsawace yace "I dont need your help" Shiru Abbii yayi ya kawar da kai
gefe, ganin be kyautu a ce ya daga ma Babban Mutum murya haka ba yasa shi cewa
"Look i'm sorry, but i dont need your help". Ya mik'e zai tafi, Abbii
beyi yunkurin hanashi ba don yasan dole Rafeeq zaiyi wuyan Sha'ani, amma zai
lallaba shi har ya yarda.
"Dunkum Yazo
daki ya gaida ni, k'afana na ciwo" chak Rafeeq ya tsaya shi beyi gaba ba
shi beyi baya ba. Me wannan tsohuwar ke nufi da shi ne, kamar yayi gaba kuma
sai ya tuna She's Uncle Zaid's Favourite, in har ta kirashi ta gaya mai bata da
Lafiya, to tabbas zai maido shi yace yazo ya dubata ko kuma ya kaita Asibiti,
kuma dole ya buge mata warning, ta daina ce mai Dunkum" Dogon tsaki yayi
ya dawo ya wuce Abbi, ya cire Takalma gaban daki ya shiga ko Sallama, Nasiba na
ganinshi ta mik'e tsaye, bata yi tsammanin zai dawo ba, ko kallo bata ishe shi ba,
ya kalli Nene cikin b'acin rai yace" ki daina ce min Dunkum, ba sunana
kenan ba" Nene tayi daria tace "Au haba? Ashe ba sunanka kenan ba, ai
ni bansani ba, duk zato na sunan ka Dunkum, ya sunanka? Cikin daga murya yace
*"I am Rafeeq Freaking Lema* "get that into your Oldie Skull"
Nasiba cikin rudu tace "Heyy, Watch It" ya juyo ga Nasiba a fusace
yace "Warn your GrandMother She should Stay the Hell away from me, you all
should" ya bar Wurin a fusace be ma lura da Abbii baya nan ba ya fice,
Nene ta bude Murya, "Sunanka Kenan Dunkum dangin tsaka, har sai randa ka
koyi Magana kuma ka bar tsaki, rannan zaka koma sunan yanka ka, amma yanzu dai
muje a Dunkum din" yana jinta amma be tsaya tankata ba, don ya san ya sake
bude baki yana iya fashewa da kuka.
"Nene meyasa
kike ce mai Dunkum? Ki bari donAllah, kinsa shi ya tunzura har yana gaya miki
magana, Gudumuwar da zaki bada wurin ganin Ya warke kenan?" cewar Nasiba,
"Ke dallah rufen baki, kinzo kina min fada kamar Inna Ladingo(Maman Nene)
ni ko zan bada Gudummuwa babba wurin saito Rayuwar Dunkum, Gundunmuwata daya
shine zan taimaka in dinga sa shi yana magana ko ya k'i ko ya so, tun beyi har
yazo ya saba ya dinga magana, kuma wannan shegiyar tsakin, dole sai ya bari, in
yayi tsaki har k'walkwata wallahi, amma dai yanzu ya daina ban haushi tunda na
fahimci cewa ba yin kanshi bane, be 6atan rai, tun asali ma be 6atan rai,
shirun shi da miskilancin shi ne bana so, kuma dole sai ya koyi magana"
Seebi ta kalli Nene ta girgiza kai "to wa ya ce miki ana so ya dinga
magana, miye matsalarki da rashin magana?" "ke tafi chan, ke me kika
sani? Sai ya koyi surutu ko yana so ko be so, wata rana kuma sai ya gode mun
dana bada guddumuwa gun sa shi magana" Daria kawai Nasiba tayi tace "
ta ina bayan kin korashi, bana tunanin ko gidan nan zai sake zuwa" Nenen
tace "Lallai yarinya baki sanni ba, ai ni ba wanda ya isa ya shareni, ko
ka shareni kan ka ka mawa, shiyasa lokacin ina kamar ki banjin komai don
saurayi yace ya fasa, don ba a kwana zai dawo, kar ki damu da sannu Dunkum zai
kawo kanshi" daria Nasiba tayi tace "yo ai ko halinki ya isa ya kori
saurayi, nasan lokacin ki an sha gwagwarmaya da ke" Nene tayi shewa tace
"Kamar kinsani, duk samarina sun sha masifata, Kakan ki kadai ne ya kasa
ya tsare yace sai Aminene" ta girgiza kai tace "Allah ya ji k'anka
Mallam, ka cika masoyi na hak'ik'a" Nasiba tayi daria, Nene ta cigaba da
bata Labarin kalan Soyayyar da sukayi da Kakan Nasiba.
Ashe yana binshi a
baya har ya isa gida, yana jin duk abunda ya faru tsakanin Rafeeq da Nene,
yanda ya fito daga gidan rai a bace ya sa shi binshi a baya har ya banka gate
din gidan su ya shiga a fusace, Baba maigadi ya mik'e yana cewa Rafeeq Lafiya?
Banza yayi da shi yayi hanyar dakin shi, Sallama Abbii ya ma Baba Maigadi, suka
gaisa a mutunce, yace "gun Rafeeq nazo" Baba Maigadi ya kalleshi yace
"Anya zaka so gannin Rafeeq a halin da yakr yanzu? Yanzu ya shigo gida rai
a bace" Abbii yace "ba damuwa, ka min izinin ganinshi" Baba
maigadi yace "Indai nine bakomai, yaro kana min kama da wata Aminiyata
Aminene" Abbii yayi Daria yace "Ni ne Autan ta" Baba Maigadi
yace "Haba biri yayi kama da mutum, kaind Mahaifin Nasiba ko? Ga kama nan
wallah" daria yayi yace "barin ga Rafeeq" ya nuna mishi dakin
Rafeeq da yatsa, kai tsaye Abii ya nufa dakin.
"Assalam Alaikum"
be jira amsar shi ba ya shiga ciki, kwance ya ganshi yayi ruf da ciki, kafar
shi ya dan ja, Zumbur Rafeeq ya tashi tsaye, yana mamakin Abbii, a ranshi yace
wai "me mutumin nan ke nufi da shi?" Abbii ya kalli Rafeeq yace
"Kasan cewa Nene Mahaifiya ta ce? Ita ta haifeni?, ko ya take i cannot
replace her, She's my Mom ba zan lamunce wani ya mata rashin kirki ba, i cant
watch anyone disrespect her, the words you used on her were harsh" shiru
yayi, yana nazarin maganganun Abbii, tabbas be kyauta ba, the woman is soo
annoying, sai dai ya dubi Girman Abbii yace "Kayi hakuri" Abbii yayi
Murmushi yace "Bakomai" na maka Uzuri ai. Rafeeq ya kalleshi, Abbii
ya cigaba da cewa "Kana jin zuciyar ka na maka nauyi, kana jin ka tsani
duniya, wata sa'in ka kan so da ma ka mutu, kana gajia da rayuwa, kana cikin
wani Bak'in duhu, Bacin rai da rashin Dangana ya hanaka neman Haske, abu yayi
k'amari da har Addua baka iya yi don a ganinka baka da wata buk'ata da ya wuce
a ce ka mutu, baka da wata ragowan Jin dadi a Duniya" be bari yace komai
ba ya cigaba da cewa "Rafee'ah, mafi Soyuwar k'anwa a gareka, ka san wani
hali take ciki a yanzu? Ba kasan tana bukatar adduar ka ba? Baka san ba abun da
mamaci ya fi buk'ata da ya wuce addua ba? k'anwarka na bukatar Adduarka, in dai
hakane, to for her sake, you have every reaaon to stay alive, you have to
survive, you have to achieve your Goal in Life, you have to go back to your
normal self, and one day get Married and your kids will pray for your Late
Sister, You have to Fight that Demon in you for your sister" wasu manyan
jijiyoyi suka ma Rafeeq tsaye a kai, so yake yayi kuka amma ya kasa, kukan
yak'i fitowa, shi kanshi yasan cewa yayi sakaci, a hankali yace *"Help Me"*
Alhamdulilah inji Abbii, yace "Help yourself first, How? ina so ka fara
Sallah cikin Jami'i, kai Bawa ne dole ka rok'i Allah haka zaka yi da hannu ka
gaya mishi bukantunka, Akwai wani ruwan adduoi da zaka mai dashi ruwan sha
dinka, ba daci ba bauri ba komai, ruwa ne Kawai ka maidashi ruwan ka, sai abu
na k'arshe akwai Wani Magani da zaka dinga Zuwa Gidan Nene Kana sha Yamma ko
Dare, InshaAllah wannan zasu taimake ka" Rafeeq ya ja gwaron Numfashi,
yace " I will do everything you said, amma i dont have to go to her Place,
zan iya shan Maganin a nan ba sai naje gidan ta ba" Abbii yace "Ina
so ka yarda dani, kayi yanda nace" dan guntun tsaki yayi yace
"Najih" Abbii yace Your Medication Starts today, muje kasha maganin,
sai ka taho da Jarkan Ruwan" be kulashi ba ya tashi ya fita, Abbii ya rufa
mai baya.
_Bibilicious
Biebee_
[2/12, 10:31 AM] 🌸Asmart🌸: 👧🏽KE
ALHERI CE🙇🏼♀
NA
BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
This Page is for
you Mrs Ruff Baby Aisha(Maman Irfaan) ILY❤
Pg4⃣6⃣
Abbii ya shiga
gidan, Rafeeq na biye dashi a baya, Nene ta kallesu zatayi magana Abii ya mata
nuni da tayi shiru. Ya kalli Nasiba yace "Seebi kina iya dauko Jarkan
ruwan nan? Ta daga kai, ba ta jira cewar Abii ba ta shige daki ta kinkinmo
jarkan Ruwan, da kanshi ya dauko Kofi ya bulbulo ya Mik'a ma Rafeeq Cup din,
yamutse fuska yayi ya kurba, jin da yayi ba taste, ya sashi kafa kofin ya
shanye ruwan ciki tass. Ya shiga cikin Dakin, ya dawo da Robar magani na hadin
mai da zuma, Ya nuna ma Rafeeq yace wannan shine dayan Maganin, shine wanda
nake gaya maka za ka dinga sha so daya a rana, kuma shine zaka dinga zuwa wurin
Nene ka dinga sha, Cokali daya ne, ba zaka ji dadin shi ba, amma daurewa zakayi
ka sha" kai kawai Rafeeq ya daga, Spoon Nasiba ta mik'o ma Abbi, ya
tsiyaya maganin cike yayi bakin Rafeeq dashi, Rafeeq ya bude baki Abbii ya juye
mai, wani iri taste mara dadi yaji, tuni yayi yunkurin zubdo shi, amma Abbii ya
sa shi dole ya hadiye, ya sake bulbulo mai ruwa Rafeeq ya shashe bakinshi, Abbi
yace "Sannu, daurewa zaka dinga yi, kasan magani ba dadi, Allah dai yasa a
dace "Zan tafi" inji Rafeeq, Abbii yace "To ka tafi da jarkan
ruwan" Rafeeq ya kalli Jarkan ya ga bazai iya dauka ba har gida, yace
"Zan dawo in dauka" Abbi yace ai ba da duka zaka tafi ba, diba maka
zaayi, idan ka shanye sai ka ka'ara kawowa a dura maka, ko robobin da kake shan
Ruwa, dazun naga kusan guda nawa a Dakinka, yanzu ke Nasiba ki samo roba ki
zuba mai, gobe sai ya kawo Robobin da za a dura mishi a ciki, sai ma ya sa a
fridge in yana bukatar mai sanyi", "sai kuma chan gida ka basu su dinga
maka abinci da ruwan" ganin yanda ya chanza fuska ne yasa Abbi fahimtar be
cin abincin gidan, kuma ya tuna Nasiba tace siyan abinci yakeyi, sai yace
"ko su nan zasu dinga dafa maka abinci? In dai ka samu lokaci ka dinga
lek'owa kaji ko?" kai kawai ya daga.
Nasiba ta dura mai, kamar jira yake tana bashi ya juya, har ya kusa fita
ya juyi ya kalli Nenen da tsura mai ido, ya danyi guntun tsaki yace ma Abbi
"kace mata ba ruwan ta da ni, magani kawai zata dinga bani" Murmushi
kawai Abbi ya mai alamun Yaji, Nene zata yi magana Nasiba tayi saurin toshe
mata baki, duk sukayi daria.
"Nene nasan ba zai jure shan maganin nan ba in yana
wurinshi, shiyasa nace zan bar maganin a gunki, yanda zai dinga zuwa yana sha a
gabanki ya hadiye, amma DonAllah kar ki biye mishi kuyi ta sa'in sa" Nene
ya ta6e baki tace "najih" Abbii yace "Nikam Seebi Rafeeq baya
miki kama da wata?" Murmushi Nasiba tayi tace "Mamin Ayman" Abbi
ya gyara zama yace "ya akayi kikasan ita ke raina?" tace "saboda
da ita su ke kama, Mamin shi ce" Abbi yace "bangane ba" tace
"Maman shi ce Mahaifiya" "Allahu Akbar biri yayi kama da
mutum" inji Abbi nan Nasiba ta shiga basu labarin yanda sukayi da Mami,
duk suka tausaya mata.
*****************
Yau ne tafiyar
Abbi, ya shirya kayanshi sun fito domin rakashi tasha, sai ga Rafeeq ya fito
daga motarshi da Robobi cikr da Leda, ya kalle su one by one, kafin yace "Barka da
Safiyya" amsa wa sukayi, binsu yayi da ido kafin yace "Ruwan zaa
bani" Abbii yace "to ke Nasiba kije ki dura mai ruwan, Nene kuma kiyi
zamanki ba sai kinyi wani rakiya ba" tace "ai wallahi sai na raka
ka" Seebi tayi fuskar tausayi tace "Hamma Rafeeq bari mu raka Abbii
tasha, idan mun dawo sai in dura maka" Rafeew be ce komai ba Abbi yace
"Aa, je ki dura mai, muna jiranki" nan Rafeeq ya gane cewa yau Abbi zai
koma Kaduna, ya kalli Abbi cike da nutsuwa, dan zaman da sukayi tsakanin Jiya
da Yau yaji zuciarshi ta kwanta da shi, be son ya tafi, ina ma ace ya k'ara
kwanaki, yanzu da be zo ba tafiya zaiyi without saying goodbye? a hankali ya
kalli Rafeeah da ke jiran ya miko mata ledar robobin, yace "Wait, we'll
all go" Abbii yace "aa Rafeeq, ka tsaya kayi uzurin ka" Rafeeq
be jira cewar Abbi ba ya taka har gabanshi ya amshi jakkar hannun shi, ya wuce
motar shi ya bude ya saka a booth, hakan ne yasa Abbii Murmushi ya nufa motar
ya zauna gaban mota, su Nene da Nasiba cikin murna suka shiga bayan mota,
Rafeeq ya ja motar yayi Tashar KTSA. Ba me maganar har suka iso Tashar, har
cikin tsar Rafeeq ya shiga da motar sa, bayan da Abbi beyi ba da a sauke shi
nan su juya, amma yak'i, jin ana Fadin Kaduna Kaduna ya sa Rafeeq parking ya
nufa Motar, da Sauri Abbi ya fita ya bi bayanshi, Rafeeq gaban kwandaster
(conductor) yace mai "Nawa?" karen mota yace "1500" Cikin
Aljihu Ya sa Hannun shi, ya zaro 2k Abbii yayi saurin rik'e hannun Rafeeq,
Rafeeq ya kar6e hannun shi cikin nutsuwa tare da girgixa ma Abbi kai ya mik'a
ma Kwanduster din, kamar jiran zuwan Abbi ake, Motar su ta tashi, bayan sun
bishi da adduoin sauka Lafiya, suka koma Mota. Rafeeq ya ja ya bar tasha.
***********
Da dare ya nufa Gidan Nene amsan Magani, Sallama yayi ya
shiga, Nene ke zaune tana jin radio, Nasiba na gefe tana duba Wani Littafi,
tace "Hamma na sannu da zuwa" Kallon Nene yayi instead ya amsa
gaisuwar Seebi yace "Sannu Fa" Nene da yak'en da ya fi kama da kuka
tace "Ahh kai ke da Sannu" be kulata ba ta tashi dauko Magani don ta
zan silar zuwan kenan, Ganin haka Nasiba ta matsa kusa dashi tace "Hamma
ka ci abinci?" kamar ba zai amsa ba yace "i am not hungry" ta
marairaice tace "DonAllah in dafa maka ko Indomie ce?" shiru yayi
kamar be ji ta ba, har ta cire rai zai amsata ta mike don komawa mazaunin ta,
cikiciki taji yace "Ki dafa min" Da sauri ta juyi da murmushi dauke
kan fuskar ta, daure wa yayi kamar ba shi yayi maganar ba, da sauri ta zura
Hijab ta bude jakkar School dinta, yana kallonta, sai da tayi hanyaf fita ta
tsinkayi muryar shi yace "Ina zaki" tace "Shagon Ummu Sudais
zanje in siyo Indomie din" (GWS Ummu Sudais ILY). Guntun tsaki yayi ya
mik'e ya zura takalman shi ya fita daidai ita yace "Ki barshi" tace
"Hamma-" katse ta yayi ta hanyar daga hannu yace nace "ki barshi
ko? Koma ciki" ba musu ta dawo ciki amma ranta ya baci, to meye abun daga
murya? Nene ta fito da Goran Maganin a hannunta tace "Ina Dunkum
din?" Seebi ta ta6e baki tace "ya tafi" Nene ta daga murya tace
"Kika barshi ya fita?" Seebi cike da takaici tace "rike shi
zanyi ince ya dawo? Nene tace "ke tamabyar ki nayi bace miki nayi ki zagar
min uwa ba" Seebi dai ba ta sake magana ba ta shige Daki.
Chan sai ga Rafeeq ya shigo da Carton din Indomie da crates
din k'wai guda biyu, Nasiba na ganin shi tayi saurin tashi ta tarye shi
don ta ga yanda yake tafia kamar zai
kife, tace "Hamma you dont have to do that" hararar ta yayi yace
"jeki dafa min, i am hungry" wani dadi taji ya lullube ta da sauri ta
aje kwalin gaban Nene, Nene ta kalli Rafeeq tace "Sannu fa" wani
murmushi ya kubce mai, wai shi take koyo, wannan tsohuwar is full of wonders.
_Bayan Minti 15_
Gaban shi ta
dire Indomie din da aka dafa da ruwan Magani da fried Egg, kamshin ya cika mai
hanci, tuni ya fara Salivating, Ba wasa ya hau cin indomie din yana jin dadi,
Nene ta ta6e baki tace "kadifiri, a gama jin dadi a zo a kur6i
magani" ai ko yana gama sha, ta zuba magani a cikin spoon tace
"Kar6i" warin maganin ya daki hancin shi, ga shi ya ci k'wai haka
kurum yaji amai ya taso mai, ya fara k'ak'arin amai, ganin yamutse yamutsen
fuskan da yakeyi sai tayi zaton iyarshege ne, da sauri ta toshe hancin shi,
kafin ya ankara ta mai dure, ta juye maganin a bakinshi, ta sa gudan hannubta ta
damk'e bakin Rafeeq, gashi be nunfashi, be da zabin da ya wuce ya hadiye
maganin, sai da yayi sakwan 15 kafin Nene ta sake shi, Nasiba ta kasa ce ma
Nene komai don tasan yau akwai dirama, da gudu ta bulbulo mai ruwan Maganin shi
ta mik'a ma Rafeeq, ba sanya ya kafa kai ya shanye ruwan, ya juyo ya na ma Nene
wani irin kallo. Kunnenta ta kama da hannu biyu tace "Sori Gaye"
Sosai ta bashi daria, kauda kai yayi lokaci daya ya murtuk'e fuska, chan kuma
yace "kina da hayaniya, ki dinga yin abu a hankali" Nasiba ta bude
baki, a zatonta Nene zata balbale shi da masifa, sai ta bata mamaki da cewa
"Naji Dan gaye na, ga Farar ka tun rannan na ajiye maka" ta ciro
Farar a gefen Tabarma da yake dare ne ba wanda ya lura dashi. Murmushi Rafeeq
yayi wanda ya sa fuskar shi kyau Sosai ya sa hannu ya amsa tare da kallon Nene,
Nene ta san me zai ce, a tare sukace "Sannu Fa" Nene da Nasiba suka
sa daria, shi dai Murmushi kawai yayi. Nasiba tace a ranta "Finally these
two are getting along. Lallai magani ya fara aiki so soon"
***********
Bayan Kwanaki
Goma(10days later)
(Kuyi hakuri da page din nan, girman Alkawari ya sa nayi
typing page din, Zan dasa daga nan gobe InshaAllah👻)