JASE[3/2, 5:44 PM] Daxling🌹: ⚔🦃 JASEENA🦃⚔ 2016
🐚Na Jeeddah jao🏵🐚
1⃣⏯5⃣
Gudu yake
kan wani farin doki mai kyaun gaske da ka ganshi kasan a rude yake ,wata mata
ce a bayanshi ta 'kank'ame shi sai zare ido take yi yayinda shi kuma sai 'kara
gudu yake ,da an hau tudu ko tsauni sai matar ta sa 'kara ta rike ciki da hannu
daya, da 'kyar ya samu wani kogon dutse ya shige ga dukkan alamu Matar na'kuda
take yi domin dauke take da juna , 'karar dawakai da yaji sun tukaro inda kogon
yake yasa ya toshe wa Matar baki da hannun shi ganin tana kuka duk jikinta yana
b'ari ,mutanen suka gama dube -duben da zasuyi sai wani daga ciki yace
"sun yi nisa sosai!! Mu koma kawai ,a lab'en da suke babu wanda ya motsa
har mutanen suka tafi sannan ya cire hannun shi daga bakin Matar da tuni
na'kuda ya zo mata gadan-gadan, Allah cikin ikonsa ya jiyo 'karan ruwa daga
d'ayan 'bangaren kogon ya mayafin ta ya nufi hanyar da gudu ,kafin ya dawo ma
har ta haifu Yar cikin Jini Kwance a 'kasa itama uwar haka ,ruwan da ke jikin
tsumman ya d'an matsa a fuskar ta ta dan farfado ,shi da kanshi ya gyara
yarinyar ya mik'a mata. Murmushi take yi tana hamdala amma hawaye ne zafafa ke
bin kuncin ta ,ta sumbaci yarinyar sannan ta rufe idonta hannunta ta sa ta damk'e
hannun mutumin wanda da ka ganshi kaga sadauki, tana salati rai yai halinsa.
🦂wani
'kara mutumin ya saka wanda duk kogon sai da ya d'auka, ya kifa kai a cikin
matar yana ta rusa kuka mai ban tausayi ,idanuwan shi suka rine kamar garwashi
ya mik'e tsaye ya d'aga jinjirar sama cikin murya mai firgitarwa yace"
masarautar KALAHARI !!! Sai na mayar muku jin dad'i da walwala !! Na lashi
takobi!! da ikon Allah sai JASEENA ta
zamo ciwon ido ga azzalumi JALALUD-DEEN!!!!
🐚 🐚🦂🦂🦂🦂🦂🦂🦂🦂🐚🐚
Asalin labarin
Masarautar
Kalahari babbar masarauta ce wanda ake sakota a matsayi na farko cikin jerin
masarautu, mai kuma cike da tarihi, mayak'a da kuma kayan ma'adanai na 'kasa
kamar su lu'ulu'u , gwala-gwalai da sauransu. Sarki Hameed shine ke mulkin
Wannan masarauta, mutum ne jarumi ,mai tausayin talakawa gashi da kwarjini.
Hameed shine d'a na biyu kuma na k'arshe
gun mahaifin su ,ma'ana yana da wa mai suna JALALUD-DEEN ,wanda ya kasance baya
son talakawa kuma shi duk abunda zai yi in dai don ya musguna ma talaka ne toh
ya fi burgeshi, son zuciya gareshi , hakan ne yasa da aka tashi bada sarautar
sai dattijawan gari suka zabi a bawa Yerima Hameed kasantuwar d'abiun sun daban
ne kwata kwata JALALUD-DEEN bai chanchanta ya mulki Kalahari ba, a fuska
JALALUD-DEEN ya nuna babu wani abu amma dai na ciki na ciki !!domin zuciyar sa
tafarfasa takeyi kuma a nan ne ya k'udiri niyyar ganin bayan Hameed !!!
Jeeddah jao🏵
[3/3, 7:07 AM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵 Jeeddah ja'o🏵🐚
6⃣⏭1⃣0⃣
Bayan an na'da Yerima Hameed a matsayin sarkin Kalahari sai
Jalalud-deen ya fuskanci cewa matar sarki Hameed Sarauniya JASEENA tana dauke
da juna biyu hakan ya tunzirashi ya kasa zaune ya kasa tsaye ko baccin kirki
bayayi tsabar Kishi domin gani yake yi in har Hameed ya samu magaji to tabbas
babu makawa ko 'kamshin sarautar ma zai daina ji............
🏵cikin
Sarauniya Jaseena yana wata tara ,haihuwa ko yau ko gobe ,tana zaune cikin
dakinta mai cike da kayan ado da k'yal-k'yali sarki Hameed ya shigo ,mutum ne
mai tsayin gaske ga haske kyakkyawa ne wanda ba sai na tsaya misalta shi ba
haka ma Jaseena kasantuwar a kasar masar ya auro ta , zama yayi kusa da ita
yana zolayan ta suna ta hira ,basu ankara ba sukaji 'kara a waje ,a tare suka
mik'e cikin firgici Jaseena ta rike Hameed ta 'boye ta bayan shi jiki na rawa
yayin da shi kuma ya zare takobin shi 🗡ya rik'e yana dube-dube don yaga
ko waye zai shigo Kwatsam sukaji an banke k'ofa kamar daga sama mutanen suka yo
kansu nan suka kaure da fad'a ,gashi mutanen fuskar su a rufe da kyar ya iya
fisge mayafin d'aya daga cikin su ,abun da ya gani ya matuk'ar girgiza shi !!!
Amintaccen shi na fada ne Zakar da wasu wanda ya tabbata fadawan shi ne ,da
yaga sarkin yawa ya fi sarkin k'arfi kaway ya figo Jaseena suka fita yayinda
mutanen suka bi bayansu ganin Jaseena ta gaza yasa ya kwantar ta bayan wani
k'aton tukunya yace yana zuwa ,cikin sand'a yake tafiya har ya isa gurin da
dawakai suke ,fito kawai yayi wani kyakkyawan ingarma ya nufoshi fari ne fes
,ya shafa kan Dokin sannan ya haura shima ya nufi inda ya bar Jaseena,ya sameta
yanda ya barta cikin ciwon na'kuda ,take ya umarci dokin da ya kwanta ,hakan
yayi ma Jaseena daidai yanda zata samu sauk'in daidaitawa a saman dokin ,kafin
su ankara sukaji harbi kibiyar ta chaki Jaseena ta gefen ciki ganin sun kusa
far musu yasa ya fita a d'ari da dokin suma suka hau dawakai suka bi bayan su
har suka samu suka shiga Wannan kogon dutsen........
🦃🦃🦃🦃🦃 JASEENA. 🦃🦃🦃🦃🦃
Hameed ya
d'auki gawar Jaseena ya fito bakin kogon ya tsaya , kasantuwar bai taho da
komai ba daga shi sai takobin shi haka ya dinga tono da Wannan takobi har rana
ta fito yayi gumi ba na wasa ba hannuwan sa duk sun salube sun ya'yyanke har
saida ya gama tono ya sallace ce sannan ya binne ya d'au takobin ya koma cikin
kogon ya zauna ya k'urawa jaririyar ido ,tsananin tausayin ta ya kama shi
kasantuwar ta zo duniya ne lokacin da uwarta take gangaren barin duniya ,gashi
shi bashi da abincin da zai ciyar da ita gata kuma abar tausayi kasancewar ta
bak'uwa a duniya ,ya d'aga hannayen sa biyu yace " ya Allah ga baiwar ka
ta zo duniya lokacin da zalunci ya mamaye al'umma Kowa burinshi yaga shine a
gaba ,Allah na rok'eka ka raya ta kan tafarki madaidaiciya kuma ka bata ikon
kare hak'k'kin duk wani wanda aka zalunta a gaban idon ta ,ya Allah ka kareta
da ikon kariyar ka!!!
🏵 Kukan Jaseena(sunan mahaifiyar ta ya maida
mata) ne ya katse shi ya je da sauri ya
dauketa ya rasa ta inda zai fara domin kuka take na fitar hankali ,kamar ance
d'aga kanka sama kawai ya hango wani haske ya hasko cikin kogon kuma ba daga
asalin k'ofar da ya shiga ba ne, ya mik'e ya nufi gurin dokin shi ma ya bishi
kasantuwar kogon makeken gaske ne .....,
Abunda idon shi
ya gane mishi yasa ya zaro idanuwa ya d'aga hannu yana godiya ga Allah
.,........,🦃
Jeeddah jao🏵
[3/3, 11:10 AM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔
🐚🏵Jeddah ja'o🏵🐚
1⃣1⃣⏭1⃣5⃣
Wata
sabuwar duniya ce domin kogon nan zagaye yake da wani dutse wanda tsakiyar
Wannan dutse ya kai girman rabin masarautar Kalahari gashi kuma jeji ne sosai
mai yawan duhuwa ,kayan itatuwa kuwa babu kalar da babu ga ruwa yana gudana
daga saman dutse tsuntsaye sai shawagi suke a gurin ,🕊🕊 , 'kara
da yaji ta wani 6angaren ya tabbatar masa akwai namun daji ciki kuma masu cike
da had'ari🐅
🦃ya ja
dokin sa har inda ruwan yake hannun shi d'aya kuma rik'e da Jaseena. Ruwa ne
mai kyaun gaske ,yanda yake gudana ma abin kallo ne a nan ya dauraye jikin
Jaseena dokin shi ma ya sha..nan ne fa Hameed ya fara sabuwar rayuwa daga shi
sai dokin shi Zabil da kuma Jaseena wanda mahaifin ta ya maida ruwan kwakwa
abincin ta, shi kuma yakan kama kifi ya busar don ya samu abin ci ,ko kuma
y'ay'an itatuwa..haka suka yi ta rayuwa a jejin...........🦁
🦂bayan
shekaru goma sha shida(16 yrs ltr)🦂
Zaune yake a fadar
sa, su waziri sai zuba fadanci ake , wasu maza wad'anda da ka gansu kasan cewa
magidanta ne sanye cikin kayan da basu fi a k'ira su da tsumma ba suka shigo fada gami da zube wa
'kasa suna kwasar gaisuwa duk jikin su sai 6ari yake yi d'aya daga cikin su
yace " Allah ya baka nasara sarki !!! Mun kawo k'arar Yerima !! Ya
takurawa y'ay'an mu ko diban ruwa basa iya fita saboda da ya gansu sai ya fasa
tulun,shine muk.............kafin ya
k'arasa yaji sauk'ar mari Tas!!!! Hakan yasa ya mik'e a firgice yaji an sake
kwarfe shi ta k'afa take ya zube 'kasa warwas !! Sarki ya ja tsaki Mtsew!! Yace
" ni zaku dubi tsabar idona Ku zo min da zancen banza Wai kun kawo karar
Yerima? Toh baku isa bah !! Wato har an fara sa mishi ido kenan ? Ina so ku
sani ,Rizwan Jini ne na sarauta yana da ikon taka duk wanda ya so kuma babu mai
tanka masa " ya dubi sarkin yak'i yace " me kuke jira ne Amjad?!!!
Aje a rufe min su a kurkuku da kuma horo mai tsananani!! Da sauri sarkin yak'i
Amjad ya kama hannayen su ta baya ya tisa 'keyar su suka bar fada yayinda
Jalalud-deen ya koma kan kujerar sa yana maida numfashi kamar wani damisa 🐅
Sarkin
yak'i Amjad yana fita da su yayi hanyar kurkuku dasu ,murya 'kasa- 'kasa yace
sai dai ku yi hakuri da irin Wannan zalunci da ake muku ni na tabbatar cewa
akwai ranar da zata zo idon Jalalud-deen sai ya raina fata kuma sai ya zama
wulak'antace a idon jama'a!! Yayi d'an murmushin takaici dai dai lokacin sun
iso mashigar kurkukun ya wuce chan ciki da su ,sun dad'e suna tafiya kafin su
iso d'akin da za'a sa su ,ganin masu gadin na kallon sa ya sa ya hakad'a su
ciki a fusace ,gami da rufo k'ofar ya juya idonsa cike da k'walla ya fice Daga
kurkukun.....
🗡🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🗡
Gudu take a kan
dokin sanye da bak'in dogon wando mai fad'in gaske ta sama , ta 'kasa kuma a
tsuke,rigar jikinta na cikin dogon hannu ne da shi kuma sak'awa akayi da auduga
na saman kuma da fata akayi shi bak'in mayafi ne rataye a kanta wanda har ya
zagaye fuskar kamar wanda tasa nik'ab baka ganin komai sai girar ta ,idon ta da
kuma saman zirin karan hancinta , takalmin k'afarta ma na fata ne ,ta rataya
wata y'ar jaka a jikinta sai wani dan biri da ke zaune a kafad'ar ta yana ta
fama da ayaba🐒.....
" Hyaaaa!!!" Ta fada gami da bugan dokin
ta baya ,yayin da shi kuma ya kara gudu. Sun dad'e suna tafiya kafin su isa
mashigar garin tana isa ta sauk'a daga saman dokin ta kama linzamin suka ci
gaba da tafiya basu zame ko ina ba sai kasuwar garin nan ta wuce gun wani mai
saida ganyeyaki na magani ta mik'a masa jakar , ya karba ya Ciro kad'an daga
ciki ya shinshina sannan yayi murmushi ,yace " yayi kyau Jaseena !! Wannan
na'a na'a mai kyau ne !! Ya sa hannu
cikin aljihun shi ya Ciro sulalla ya muk'a mata ta kar6a ta juya abunta ba tare
da ta ce k'ala ba ........
Cikin kasuwar
ta sake kutsa kai tana ganin yanda Kowa ke gudanar da alamuran sa cikin
kwanciyar hankali ,kai tsaye ta nufi gun mai shinkafa ,ya auna mata ta kar6a
kawai ta jiyo hayaniya bata ankara ba ta hango dawakai kusan biyar sun dumfaro
inda suke ,da wasu matasa a kai sai 6arna suke ,guda daya daga cikin su ya sha
ado da kaya irin na alfarma shi ya fi Kowa ma ta'adi a cikin su suna ta buge
mutane ,suna zubar musu da kayayyaki ,ta gefen Jaseena suka wuce gami da banke
wata mata mai juna ta fad'i 'kasa kayan
marmari da ta siyo ma duk suka zube ,a fusace Jaseena ta dubi mai shinkafan
tace "Wannan kuma su waye haka
kamar mahaukata ??!!! Mai shinkafa ya zaro ido yace ki rufa ma kanki asiri
baiwar Allah!! Wannan shine Rizwan d'an sarki Jalalud-deen !! Ta juya ta sake
kallon hanyar da suka wuce tana wani irin murmushi na k'eta " a ranta tace
lallai yau kakarta ta yanke sak'a!!! Mai shinkafa ya ce " amma baiwar
Allah kina garin nan kice baki san Yerima Rizwan ba? Murmushi kawai tayi ta
d'auki shinkafan ta sa a Jakarta ta juya ba tare da ta kalle shi ba balle ma ta
bashi amsa ,ta nufi gun matar da ta fad'i kasa wanda duk an zagaye ta ana kallo
kuma babu wanda ya ma je kusa da ita don
ya taimake ta................🦃
Jeeddah ja'o🏵
[3/3, 10:16 PM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔
🐚🏵jeeddah ja'o🏵🐚
1⃣6⃣⏭2⃣0⃣
Kutsawa tayi
cikin taron mutanen da k'arfin hali ta samu ta shige inda matar take ta d'aga
ta tana yi mata Sannu yayinda sauran mutanen suka watse daga gurin Kowa ya fara
tattare 6arnar da akayi masa amma da ka gansu kasan a tsorace suke duk da
Jaseena ta fuskanci hakan bai sa ta ko girgiza ba ta d'aura matar kan dokin ta
sannan ta ja akalar dokin suna tafiya matar na mata kwatance har ta kaita gidan
ta, ta kuma taimaka mata har cikin gida ,wanda ba girma gareshi ba amma sai
tsafta ,wani gadon kara ne gefe guda ta hango ta ja matar har gurin ta zaunar
da ita sannan ta tashi ta nufi d'ayan 6angaren gidan don nema wa matar ruwa,
akayi sa'a ta samu ta d'ebo mata....
Bayan ta
tabbatar matar ta samu nutsuwa sai ta tashi zata fice ,hannun ta matar ta rik'e
ta ce " nagode baiwar Allah !! Amma yaya sunan ki ? Ta juyo da murmushi
tace " "Jaseena " matar ta d'an jinjina kai ta ce " amma ke
bakya tsoro labari yaje kunnen Yerima Rizwan cewa kin taimaka wa wanda ya
wulak'anta? Zai ce kin raina mar hankali ,sannan ya sa a miki horo mai tsanani
,kuma gashi ke yarinya ce bai kamata kina k'arama ki jefa kanki cikin had'ari
ba !!! Murmushi kawai Jaseena ta sake yi tace " Kar ki damu umma !! Ni ma
ba kanwar lasa bace !!!in yana ji da sarauta nima ina ji da ita !!🗡 ke
dai ki kula da kanki kuma ki daina fita ke kad'ai domin hakan ba k'aramin
had'ari bane" tana kai Wannan ta juya ta fice gamida rufo k'ofar gidan
,matar ta bita da kallo ,a ranta tace " yau naga mace mai kamar maza!!
Yanzu har a masarautar Kalahari akwai macen da zata iya tsallake dokar Yerima
?? Ta girgiza kai ta koma ta kwanta.
🐚 kasuwar ta
k'ara komawa ta gama saye-sayen da zatayi sannan ta juya ta bar garin , da
la'asar ta isa kogon su ta shige ta nufi inda tasan kullum mahaifan ta yake
motsa jiki da yamma ,wani d'an fili ne ya zagaye da itatuwa a nan ya ke koyawa Jaseena
dabarun yak'i ,da gudu ta nufi inda yake ta zari wani sanda suka fara fad'a
cikin raha har suka gaji suka bari.
🔥wuta
suka hura tana taya shi gasa kifi sai zuba take yi don duk abunda ya faru a
Kalahari sai da ta zayyano masa shi dai bai ce 'kala ba ya ci gaba da gasa
kifin ,ganin ba sauraron maganar ta yake ba ta mik'e ta nufi wata duhuwa mai
siriryar hanya ,gaba kad'an ruwa ne ke sauk'a ta saman dutse birin ta wanda
take k'ira da suna Zainu yana nan kan kafad'ar ta yayinda take Kutsawa cikin
duhuwar 🌳 kukan damisa ta jiyo hakan ya sa ta wata Yar siriryar dariya
ta kama wata reshe kamar biri tana lek'o inda taji kukan ,domin takan ji kukan
ne tun tana Yar yarinya amma bata tab'a yin gaba da Wannan gurin ba kasantuwar
daga Wannan dutsen mai ruwa babu wani guri a gaba balle ta ce ko daga chan ta
jiyo k'arar........
🦃
yau de ba Jaseena bace zata fita ,mahaifin ta Hameed ne zai fita duk da ranta
bai so ba amma tasan bata isa hana shi fitan ba ,kamar kullum ya debi ganyeyaki
a jaka ya ja Zabil suka fice .....tana cikin wasa da zainu su kama Wannan
reshen su saki wancan Kwatsam ta sake jin Wannan kuka na damisa ,ai kuwa nan ta
k'udiri niyyar sai ta gano duk inda Wannan 'kara ke fitowa !!! Diro wa tayi
daga saman bishiyan tabi hanyar da ta jiyo karan kamar kullum de bakin dutse
take riskar kanta amma yau tace bazata juya ba sai taga menene a bayan ruwan da
yake zuba kuma zata nemo inda Wannan damisa take 🐅
Hawa tayi kan
dutsen duk ruwa yana ta jik'a ta a hankali ta mika k'afan ta gaba taji dai ya
zauna ai kuwa sai ta kutsa kai ,zainu kuwa tun da yaga ta shiga ruwa ya koma
gefe yana kallon ta itama bata biya ta kanshi ba tai shigewarta..............🦃
Wata Yar siriryar
hanya ce a ciki sai duhun tsiya amma don rigima ta shige sai tafiya take ,har
tayi tsakiya ta juya tana kallon hanyar da ta baro ,sai kuma ta tabe baki ta ci
gaba da lulawa...............🦂
Jeeddah jao🏵
[3/4, 7:41 AM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵Jeeddah ja'o🏵🐚
2⃣1⃣⏭2⃣5⃣
Ta kai
ak'alla minti talatin tana tafiya wani wajen ma sai ta sunkuya don ta wuce amma
bata fasa ba har sai da takai wata Yar k'aramar k'ofa wanda aka toshe bakin da
Yar ciyawa tasa hannu ta ture ciyawar dayake rana ta kusa faduwa Hasken wanda
yay ja ya dalle mata ido sai kakkarewa take da hannun ta ,cikin dabara ta fito
daga ramin dutsen ta tsaya ta jikin dutsen tana bawa idonta abinci domin banda
dajin da yake gurin tana hango wani gini mai tsayin gaske ga kyau ,da gani
kasan masarauta ce amma gaba yake da dajin shima ta hango shi ne don tana saman
dutsen ne ta hango amma akwai wata siriryar hanya da ta bi gurin. Daji ne mai
kyau don har yafi na inda suke kyau, da gudu ta juya tana dariya ta koma kogon
bata yi wata wata ba sai gida Zainu na ganin ta yai tsalle ya koma kafad'ar ta
yay zaman shi ita kuwa ganin yadda tayi datti yasa yasa ta nufi inda take wanka gefen Wannan
ruwan tai ta wanke jikin ta tana wasa da ruwa ,k'iran da babanta yay mata ne
yasa ta fita da sauri ta nufi inda taji Muryan shi ,fuska a turnuk'e yace
"ina kika je?!!!" Nan ta fara kame kame ya juya ya barta gurin bai
kuma cewa qala ba....
Cikin sand'a ta
nufi d'akin ta, gami da turo k'ofar shi kuwa Hameed sai da ya gama kaifa
takobin shi sannan ya wuce d'aki. Cikin dare ya kasa bacci domin jikinshi na
bashi akwai abunda zai faru ,duk zuciyar shi sai bugawa take ya rasa dalilin
faruwar hakan ,ya d'auki takobin shi ya nufi d'akin Jaseena wanda itama ba
baccin take ba ,tana ganin shi ta tashi ta zauna tace " baba na mai ya
sameka? Yaya na ganka cikin daren nan? Murmushi yayi sannan ya kama hannun ta
ya d'aura takobin ta daga kai tana dubanshi bai daina murmushi ba har
Lokacin yace " Jaseena !! Ko ma me
zai faru yau d'in nan ka........... Kafin ya k'arasa yaji motsi a waje tuni ya
ce Jaseena ta fita ta bayan d'akin amma ta ture Wai itama zata iya fad'a ai
kuma bazata tafi ta bar shi ba ,ya gaura mata mari wanda tsabar ta rikice sai
da taga wuta🔥 ya ce " nace ki tafi !!! Cikin kuka ta zari jakar ta
na fata ta rataya zainu na biye da ita ta fice ta kofar bayan shi kuma ya fita
don ya duba me ke wakana. Sauk'ar itace yaji a kansa wanda hakan yasa shi k'ara
da zubewa a 'kasa sumamme , duk abun nan da ya faru a idon Jaseena ne domin
la6e wa tayi tana ganin duk abunda ke faruwa duk mutanen ta ga fuskokin su
kasancewar Hasken farin wata duk ya mamaye gurin suka jashi suka tafi da shi
,nan ta zube tana wassu zafafan hawaye na takaici, a ranta tace " toh ya
akayi suka gano inda baba ya 6oye? 🗡......,
🐚🕸🕸🕸🕸🕸 🕸🕸🕸🕸🕸🐚
Kafin kace wani
abu har gari ya waye Jaseena na idar da sallah tana goge takobin da Hameed ya
bata kawai taji takun mutane ,cikin sauri ta haye wata bishiya cikin duhuwa
zainu ma ya bita , a hankali suke magana tana jin su ,"sarki yace a duba
ko akwai Dan sa ko kuma d'iya domin da ciki a jikin matar sa ya baro Kalahari
!! Jin haka yasa Jaseena ta diro ta yi hanyan Wannan kogon wanda ke bayan ruwa
mai zuba ta shige Wannan ramin Wannan karon har da zainu a tare da ita tana dirowa
ta d'auki Yar ciyawar ta maida shi gurbin da yake ta fara tafiya tana bin
Wannan hanyar da ta gani sai kalle kalle take yi zainu kuwa an samu bishiyoyi
ya hau wancan ya kama wancan. Har lokacin bata daina kuka ba ,don tsoro take yi
Kar a kashe mahaifin ta.. Gurnani ta jiyo ta gefen hanyar kamar na zaki ai kuwa
Kwatsam yayi tsalle ya tare gabanta 🦁 ta tsaya chak a gurin ta zubawa
sarautar Allah ido , bata ankara ba taga wani kyakkyawan sadauki a gabanta ya
tsugunna yana shafa kan zakin ,damtsen shi ma. Kad'ai abin kallo ne shi kanshi
kamar zakin yake ga gashi har Ka fad'a wata Yar farmalam ce a jikin shi wanda
gabanta a bud'e take ya rataya kwari da baka a bayanshi takalmin 'kafar shi
kuwa na fata ne , ya mik'e yana kallon Jaseena sannan ya k'arasa kusa da ita
,hawayen da ya gani a fuskar ta yasa ta bashi tausayi saidai ba tare da yace
komai ba ya ciro k'ullin gurasa a jakar shi ya bata ,kamar yasan tana jin
yunwa. Da sauri ta wafce ta nemi guri ta nad'e k'afa ta fara ci ,chan sai ta
tuna da mahaifin ta, hawaye na zubo mata sai chusa gurasar take yi tsabar ta
zuciya ,har ya shak'e ta ta fara tari kamar dama jira yake , matashin ya ciro
wata Yar gora na fata ya mik'a mata ta
kar6a sai bayan ta d'an nutsu sannan ta dubeshi tace " nagode !!👏🏽
murmushi kawai yayi ya yi mata nuni da hannu
ma'ana ta tashi su tafi , nan ne ta gane cewa baya magana kuma ba kurma
bane yana ji sarai amma baya iya magana ,saidai akwai kyau kamar balarabe , ta
tashi ta bi bayanshi suka ci gaba da tafiya har suka k'ure Wannan dajin ,abin
da ya bata mamaki shine wani tafkeken kogi ne a gurin saidai daga bakin ruwan
ma kafi ganin masarautar ,jirgin ruwa suka shiga mai tuk'in yan ta fama da
tuk'in shi kuwa sai wasa da ruwan yake yi.....,.......🦃
Jeeddah ja'o🏵
[3/17, 11:35 PM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵jeeddah ja'o🏵🐚
2⃣6⃣⏭3⃣0⃣
Isarsu masarautar
,bai zame da su ko ina ba sai cikin hanyar fada ,yana gaba tana biye da shi
cikin ranta tace " yanzu har akwai masarautar da bawa zai dinga kutsa kai
cikin fada ba tare da izini ba? " bud'ewar wata k'atuwar k'ofa ne ya katse
ta daga tunanin da take yi ,kai ya kutsa ba tare da fadawan sun Hane shi ba har
ya k'arasa ya nemi guri ya zauna ........🦃
Zubewa tayi
itama tana kwasar gaisuwa kamar yadda yayi sannan ta gyara zama. Wani bak'in
mutum ne wanda fuskar shi ba wani almuru don ko murmushi da yake yi kamar dole
aka sa shi yake yi . " yarima har an dawo ne!!? " tambayar da sarkin
yay masa kenan ,yayin da shi kuma saurayin ya gyad'a masa kai ,nan yaci gaba da
yi masa kwatance da hannu irin na kurame ita dai Jaseena ta zuba musu ido cike
da mamaki da kuma tambaya dake cikin zuciyar ta " me yasa Yerima guda babu
ko hadimai balle shiga ta alfarma?! " don ita da tayi zaton bawa ne😄
gashi kuma kyakkyawan gaske amma mahaifin sai bak'i da muni 😂 ,ta d'an
jinjina kai tace " hala mahaifiyarsa ya biyo"
Maganar sarkin
ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga " Yaya sunan ki baiwar
Allah? " shine abunda yayi karo da kunnen ta. A d'an rusune tace
"Jaseena". Sarkin ya d'an yi murmushi yace " daga yau na baki
masauk'i cikin masarauta ta domin Yerima Haidar ya sanar da ni cewa 6ata kikayi
,toh nan ya zama miki gida kina da iko ki shiga duk inda kike buk'ata a
masarautar nan ! Tai ma sarki godiya sannan Haidar ya ja ta suka fice daga
fadar ya mik'e da ita har wani hanya
daban wanda ta yi nisa sosai da fada ga k'ofofi kala kala masu kyau da kwalliya
ga fitilu masu haske abin ba'a cewa komai .....
Wani d'aki ya
nuna mata ta sa hannu ta bud'e ta shiga da murmushin ta zainu na biye da ita
,shima murmushi yayi sannan ya juya ya fice daga wajen yayinda ta bishi da
kallo kamar Yar k'auye.
🐚🐚🐚🏵 🏵🐚🐚🐚
Yau kwanan
Jaseena uku a Wannan gari wanda ko ita kanta bata san sunan garin ba ,Haidar
kuwa kusan kullum da safe sai ya lek'o don ya duba lafiyar ta ,haka take wuni
ita kad'ai sai zainu yana d'ebe mata kewa kasantuwar Haidar bai cika dawowa da
wuri ba in ya dawo ma sai gari ya waye yake duba su...." Yau kam sai na
fita na zaga gari!!" Cewar Jaseena kenan tana ta faman gyara zaman dogon
rigar da ta saka ,sai duba kanta take ta madubi don bata saba saka irin kayan
nan ba ,ita kanta ya mata kyau ,sannan ta dauki mayafin wanda da shi da kwalin
tata duk d'aya ta yafa a kanta ta nannand'e ta fice zainu na binta a baya kamar
yadda ya saba , tana tafiya tana faman tattare riga don yadda yake Jan 'kasa a
haka har ta bar fada ,tana ta kalle kalle ta tsaya can ,ta ta6a wancan , tana
cikin haka har tayi nisa da masarautar a can nesa ta hango wasu mata guda uku
kowacce da tulu sun sha ado sai ture -turen juna suke a kan hanya suna ta
raha......
Cikin sauri
Jaseena ta k'arasa inda suke ,tana iskesu ta sa hannu ta ta6a kafad'ar daya
daga cikin su duk suka juyo suka k'urawa Jaseena ido sai kuma suka bushe da
dariya suna nuna ta da yatsa 👉🏾 hakan yay matuk'ar bawa Jaseena
haushi ta yamutsa fuska tace " toh me nayi kuke min dariya !!😠. A
tare suka tsare kamar da gaske sannan suka sake bushe wa da dariya ,wata Yar
siririya sosai tace " ke kuma Wacece haka !? Ko rigar ma bata iya sak'awa
ba Yar k'auye kawai!! Suka juya suka ci gaba da tafiya yayinda ita kuma Jaseena
ta tsaya Kallonsu har suka shige ta daina hango su ma...............🦃
🏵Jeeddah ja'o🏵
[3/18, 9:58 AM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵jeeddah ja'o🏵🐚
3⃣1⃣⏭3⃣5⃣
Duk Wannan abun
da ya faru Haidar na tsaye yana kallon ta ,shi ma kanshi ta bashi dariya kawai
ya tsare ne,kwata - kwata rigar baibai ta saka shi bayan haka kuma gaba a baya
,duk da hakan da tayi yay matuk'ar yi mata kyau amma ba daidai bane shi yasa
matan ke mata dariya....
🎗Nan ta nemi k'ark'ashin wata y'ar bishiya ta zauna
tana ta 6ata rai harda d'an hawayen ta ,tace " ai yanzu da baba ne bazai
min dariya ba cewa zai yi yayi min kyau !! Toh ma miye laifin kayan nan tunda
dai ba tsiraici na bari a fili ba!!!Mtsew!!!" Take ta zabura ta mik'e
tace" Baba!!!"
🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸
Kwance yake cikin
wani matsatsen d'aki mai duhun gaske duk ruwan datti ta nan yake biyo wa ,ya
tashi ya mik'e tsaye sai kai kawo yake a d'akin yana cizon le6e ,duk tunanin
shi ya koma kan y'ar sa Jaseena addua kawai yake yi Allah ya sa Kar su gano ta
,Allah yasa basu kamata ba duk da yasan k'arfin damtse na y'arsa da kuma wayo
irin nata. " HAMEED!!! K'iran da waziri Zakar yayi masa kenan , hakan ya
sa shi juyawa cikin sauri fuskar shi a d'aure. " kamar yadda muka kamoka
kamun wulak'anci haka zamu kamo d'iyar ka da kake tak'ama mai k'arfi ce mu
wulak'anta ku a bainar jama'a !!! Hhahhah !!!!! " Zakar kenan yayi Wannan
magana ,bai ankara ba yaji an shak'e wuyan shi har saida idanuwan shi suka fito
kwala kwala ,ya kasa magana. Hameed kenan !! Yana cikin kurkuku ma amma k'arfi
na nan !!💪🏼. Wasu masu gadin gurin su biyu ne suka tunkari inda
suke da 'kyar suka cire waziri daga rik'on da Hameed yay masa sukayi waje da
shi ,yayinda shi kuwa gogan ya koma ya zauna yana maida numfashi 😤.............
👑.
👑
A tsayen da take
tana tuna halin da mahaifin ta zai shiga a Kalahari taji durowar abu ta bayanta tuni ta zari wata
y'ar wuk'ar ta ta juya zata kai hari ,hannu ya sa ya tare ,wuk'ar ta yanke shi
a hannu. Tana juyawa taga ashe Haidar ne 🙄ta zare ido,a rikice ta cire
gyalen da ta rufe
kanta ta raba gida biyu ta d'aure masa yankan da tayi sai
bashi hak'uri take yi ,ga dukkan alamu bai ji zafin ciwon ba sai murmushi yake
mata ,jiki a sanyaye ta nemi guri gefen bishiyar ta raka6e tana y'ar hawaye....
Wata murya mai
dad'in gaske da ratsa zuciyar duk wani mai sauraro taji yace " Jaseena!!
Ai barin kashi a ciki baya maganin yunwa ,inaga lokaci yayi da zaki sanar da ni
matsalar ki wata'kila na nema miki mafita ko in taimaka miki!! Kinga dukkan mu
nan ko wanne yanada matsalolin da yake neman mafita amma 6oye su bazai amfane
my da komai ba har lokaci ya k'ure mana !! A firgice ta juya tana neman inda
akayi maganar amma ta rasa domin ta lura babu Kowa a gurin sai Haidar da har
Lokacin murmushi kawai yake yi rik'e da hannun shi yana kallon ta da kuma
mamakin yadda ta rikice tana neman wanda yayi magana.........
Ta dawo gaban
Haidar tana kallon cikin idon shi tace " bakaji wani yayi magana ba ? Baka
ga wanda yayi ba?" Murmushi ya sake yi sannan yace " ni nayi miki
magana Jaseena !!" Nan ta tabbatar tabbas shi ne yayi magana ,kafin ta ce
komai ganin yadda ta saki baki kamar wawuya yasa ya fisge hannun ta yabi wata
hanya da ita sai cikin wani daji dake gefe da gurin ,kan wani gungume ya nuna
mata ta zauna ,yace " eh nine nayi magana ! Kuma ke kad'ai ne kika san
hakan ko sarki bai sani ba ,kuma ina so ki rik'e shi a zuciyar ki ,duk Lokacin
da kike buk'ata muyi hira to kizo nan amma Kar ki kuskura wani yasan ina magana
!" Kai kawai ta girgiza mishi cike da mamaki har lokacin ta kasa nutsuwa...,..........🦃
🏵Jeeddah ja'o🏵
[3/19, 12:16 PM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵jeeddah ja'o🏵🐚
3⃣6⃣⏭4⃣0⃣
"Dama
kana magana ne?" Shine tambayar da ta fara fita daga bakin Jaseena. Haidar
yayi wata Kyakkyawar dariya yace ,ina magana amma banda iyayena babu wani
mahalukin da yasan hakan ko sarki Hasheem da kika gani bai sani ba ,duk da
shine silar dawowa ta hakan !! Duk Wannan maganganu da yake yi babu abunda
Jaseena ta fahimta duk ya dagula mata tunani , Ta mik'e tace in na fahimce ka
,kana so ka ce min kai ba d'an Wannan sarkin bane ? Kuma akwai abunda kake 6oye
masa a matsayin sa na wanda ya yi rainon ka?
Wata dariya ya
saki mai ban mamaki yace " Jaseena duniyar tamu zagaye take da azzalumai
masu bak'ak'en zuciya da son abun duniya !! Zan baki labari na da kuma dalilin
da yasa na zama haka ,amma kafin na baki labari ina so ki min alk'awari babu
wanda zai san ina magana a cikin masarautar nan ko da wasa ne! " Jaseena
ta furzar da iska daga bakinta tace " inshaa Allah bazan bari Kowa ya san
da Wannan zancen ba !! Sirrin ka zan killace shi kuma na bashi mazauni na
musamman a zuciya ta !!" Murmushi yayi yace na gode !! Amma yanzu muje in
nuna miki gari ,gobe zan sanar da ke tarihi na in Allah ya yarda " Jaseena
ta d'an 6ata rai tace" me yasa bazaka fad'a min yau ba? " murmushi
kawai yayi yace " muje " ya tashi ya mik'e ita ma tabi bayan shi har
ta sa k'afa zata tafi sai tace " kai ka je !! Ni zan gyara riga na, ba
tare da ya tanka ba yayi tafiyarshi ita kuma ta juya rigan ta gyara tsaf sannan
ta fito daga duhuwar da take ...
Tsaye ta same
shi a gefen Wannan bishiyar yana jiranta " na gama mu tafi" shine
maganar da ta ratsa kunnen sa ,ya juyo ya k'ura mata ido kamar ya had'iye yace
" muje" ya fara tafiya ta bi bayanshi sai fama da doguwar rigar
takeyi duk ta mata nauyi ta tattare rigar har guwiwa hakan yasa ta bata sauri sai ta d'an ruga ma take iske
Haidar duk da ya ga yadda take fama da rigar wanda hakan ya bashi dariya matuk'a
amma ya kafse kamar bai san ma tana yi ba .
⚜kasuwar garin ya fara kai ta
,sai kalle kalle take yi ,Kwatsam ya bi da ita layin sayar da tsuntsaye ,su
Jaseena an samu abun yi ,nan ta dinga bin keji keji tana ta dariya kamar pagal
(mahaukaciya) shi dai haka yake a tsare sai tafiyar shi yake in taga yayi nisa
sai ta sa gudu ta taro shi ,ga shegen surutu kamar aku ta sha gaban shi yana
tafiya ita kuma tana tafiya da baya baya ," kai nace ka d'an tsaya mana
sai sauri kake yi ko baka ji na ne!! ? A garin ja da baya ta banke wata budurwa
ta d'ebo kwai a kwando ta fad'i k'asa kwayayen suka fashe ,a gurin ta daskare
ta kasa magana ,budurwar ta mik'e tana karkad'e jikinta yayinda Jaseena ta
sunkuya tana kwashe mata wayanda basu fashe ba sai hak'uri take bata. Murmushi
yarinyar tayi tace " babu komai !! Ba kece wadda muka gani dazu zamuje
deban ruwa ba?" Jaseena ta d'an d'aga kai alamar tunani tace "🤔
" Eh nice !! Ina sauran guda biyun suke?" Yarinyar tayi murmushi tace
suna can gida ni sunana Jauda , ke kuma fa?" Ni kuma Jaseena! Shine amsan
da Jaseena ta bata .
Ta juya sai dube
dube take yi bata ga Haidar ba murya can
k'asa tace "toh shi Wannan ina ya tafi ne?!" Murmushi Jauda tayi tace " tun yaushe ya
tafi!! Kizo mana mu tafi tare zamu nuna miki cikin gari ni da yan uwa na
!" Da 'kyar Jaseena ta yarda ta bi ta suka tafi.............
🏵Jeeddah ja'o🏵
[3/21, 9:24 AM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵Jeeddah ja'o🏵🐚
4⃣1⃣⏭4⃣5⃣
Suna tafiya tana
mata hira har suka isa wani babban gida ,ginin mai tsayi ne sosai ga kyau kuma
tare suka shiga kai tsaye hanyar d'akin girke -girke suka nufa yarinyar ta
ajiye kwandon kwai din ,a d'ayan 6angaren kitchen din kuma wayannan yan matan
nan ne da suka mata dariya tare da Jauda suna tsaye sun zuba musu ido ,d'ayar
tace " ke!! Benaxir fa ta dawo !!! Kika shigo da Wannan bakya tunanin zata
iya 6ata miki rai in ta ganta ko??!" Murmushi Jauda tayi sannan tace
" babu komai Aisha ai zamu fita ta baya in Mun gama aiki !!" Aisha de
bata sake tanka mata ba ,Jaseena tace " Wacece Benaxir har kuke tsoron ta
haka ? D'ayar da tun farko bata tanka mata ba tace " Wannan bai shafe ki
ba !!😏" a tare Jauda da Aisha suka daka mata tsawa gami da k'iran
sunan ta Meenah!!! Wai ke me yasa bakya son mutane ne kin cika bak'in hali !!?
" Aisha ce ta k'arasa maganar......
Jaseena tayi
murmushi tace " ni zan koma ,nagode da kyautata wa da kuka yi min "
Aisha tace don Allah ki tsaya mana yanzu zamu gama aiki mu tafi fada ,yau akwai
tseren doki a fada kuma Kowa zai halarci gurin domin fidda gwani a wajen sarrafa
doki ,kuma fa har akwai fad'a da zaki ,kowacce shekara yarima Haidar ke gaba a
duk fannin.!! Kinsan yarima Haidar da son mutane ! Ai shine ma sadaukin Wannan
masarauta Kowa yana karrama shi ,ba kamar mahaifin shi sarki Hasheem ba ,bai
d'auke shi a kan komai ba ,Kinsan Haidar abokin mu ne tun muna k'anana tare
muka taso har yanzun nan da kika gani ,ko lokacin da muka miki dariya a hanya
ma ai shi ya hana mu in ba haka ba da abun ya fi haka ,ko wacce a cikin mu na
da labari mai ban tausayi tun yarintar mu kuma labari mai ban tausayi amma da
Sannu zaki san komai amma kafin nan ko zaki iya bamu labarin rayuwar ki da
yadda akayi kika tsinci kanki cikin Wannan masarauta ta Ramali?? "
Nan Jaseena ta
kwashe duk labarin rayuwar ta ta fad'a musu har yadda akayi ta fito daga dutsen
da had'uwar ta da shi Haidar ,duk sun tausaya mata matuk'a , Jauda ta mik'e
tsaye tace " toh ai duk labarin d'aya ne duk fa akan mulki aka k'ask'anta
mu kawai don an fi k'arfin magabatan mu toh yanzu zama zamuyi a dinga cin kashi
a kan mu ne??!! Aisha ta mik'e tace " inaaaa!! A'a Sam bazai yiwu ba dole
mu kwace hak'k'kin mu da kan mu mu tashi muyi yak'i mu k'watar ma kammu
y'anci!!! " Jauda ta sa hannu tace " wa yake tare da ni??" Duk
suka d'aura hannayen su a kan nata gami da cewa "ni!!" Duk suka maida
dubansu ga Meenah da ko motsawa bata yi ba ,ganin duk sun sa mata ido itama ta
d'aura nata hannun" Jaseena ta rasa Wannan wane irin hali ne Meenah take
da shi kwata kwata batada fara'a a fuskar ta. A tare suka watsa hannayen sama
kowannen su yana murmushi irin na masu k'arfi a jika 💪🏼
💞🏵 Jaseena. 🏵💞
Guri ne
babba na gaske amma mutane duk sun cika gurin an zagaye makeken filin wanda Hasken farin wata ya cika
shi fal! Gurin da mutanen suke hawa hawa ne ga fitilu nan ta ko ina sun haska
benen dake sama sosai shine inda sarki Hasheem ke zaune shi da wata Kyakkyawar
mata tasha ado na zinare ,gefe d'aya kuma sarakuna ne da matan su wayanda suka
zo suma da y'an wasan su ma'ana sadaukai na k'asar su don suma su fafata a
cikin gasar ,akwai gefen sarki Hasheem wanda duk cikin guraren ya fi ko ina
k'ayatuwa ,wani sarki ne bashi da haske sosai amma da ka ganshi kasan ya dama
ya shanye a sarauta ,gefen shi wani kyakkyawan saurayi ne ya sha ado gwanin
sha'awa fuskar shi babu almuru ga dukkan alamu d'an sarkin ne ,ga kuma wani ta
bayansu a tsaye da alama sarkin yak'in su ne don sanye yake cikin kayan yak'i
saidai ya manyanta sosai don dattijo ne....
Toh masu ku
biyo ni a episode na gaba don jin wainar da zata toyu a Wannan fili na gasa
,ina godiya masu karatu love you all!!💞
🏵Jeeddah ja'o🏵
[3/23, 9:15 AM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵jeeddah
ja'o🏵🐚
4⃣6⃣⏭5⃣0⃣
Haidar ne a kan
doki suna Jere shi da wasu ,yayan sarakuna ,Jaseena da ke zaune a bene na farko
kuma na k'asa ita da su Jauda kawai ta mik'e ba shiri ,su Aisha ma suka mike
suna tambayar ta ko meyasa ta zabura haka? Fuskar ta babu almuru tace "
tabbas na san wancan !! Shine Rizwan d'an sarki Jalalud-deen !!! Me kuma yake
yi anan ? Duk yadda akayi sarki Jalalud-deen ma yana nan !!" Aisha tace
" kice ba mu muka je neman su ba su da kansu sun kawo 'kafar su inda ya
dace!!" Duk suka bushe da dariya ,chan kuma sai Jaseena tace " toh
amma ai in an gama gasar yau gobe zasu tafi ko ?" A tsare Meenah tace
" sati biyu ake yi ana wasannin lallai muna da dama " duk suka
jinjina kai ,yayin da Jaseena tayi murmushi cikin ranta tace " lallai
Wannan Meenah d'in y'ar ganin dama ne !!.
Tun da aka fara
tseren dawakai Haidar ne ke Jan ragamar Kwatsam sai dokin shi tayi wani irin
'kara ta tik'a shi da k'asa ta yi gaba ,yarima Rizwan wa wuce shi yana masa
wata muguwar dariya gami da cewa "Wannan karon kam baka isa ba!!! "
dokin Haidar da ya fita a guje ya zagayo ta inda su Jaseena ke zaune kawai se
ta mik'e tayi tsalle ta fad'a kan dokin " Hyaaaa!!! " ta sa gudu
,ganin yadda ta kusa cimma Rizwan yasa sarki Jalalud-deen ya mik'e tsaye yana
zare idanuwa.
Gudu suke daf
da daf da ita yayinda Rizwan ya kasa mai da hankalin shi kan tseren ,abunka da
mayen mata ,ya tsura mata ido ita kuwa ta sakar masa da wata hadaddiyar
murmushi wanda ya sa sai da ya kusa tsaya wa. Sai da ta tabbatar ya gama
rud'ewa kawai taja linzamin dokin ta kara gudu har ta tsallake Jan layin da aka
zana ,ta zo na d'aya ,bak'in ciki ya sa Rizwan ya gagara k'arasawa yayin da
idon Jalalud-deen suka rine tsabar haushi ace duk shirin da suka yi na ganin
sun ci amma hakan bai yiwu ba?
Mutanen gari aka
hau ihu ana Jaseena! Jaseena !! Jaseena!!! ,Wannan sunan da aka kira yasa sarki
Jalalud-deen d'agowa cikin sauri yana kallon Jaseena !tabbas babu maraba
tsakanin ta da mahaifiyar ta ,saidai a tunanin shi wata'kila idon shi ne ke
mishi gizo sai yayi tsaki ya juya ya bar wajen ,yayinda Rizwan da sarkin yak'i
Amjad suke taka mishi baya.
🏵Jeeddah ja'o🏵
[3/24, 7:40 PM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔
🐚🏵Jeeddah ja'o🏵🐚
5⃣1⃣⏭5⃣5⃣
Haidar kuwa
murmushi kawai yayi ya nufo inda take ,kanshi a k'asa yace " nagode
jarumar mata!!! " Wannan sanyin Muryar tashi ta sa Jaseena lumshe idanuwa
tana murmushi ba tare da ta tanka masa ba,shi ma yadda yayi maganar ba wanda
zai gane magana yake yi ..
🐚. Gurin duk an watse Kowa ya koma gida, daga
Aisha ,Jauda, Jaseena sai Meenah da Haidar, suna ta hirar su cikin nishad'i
Meenah ce kad'ai kamar bata gurin. Jauda tace "Jaseena mu zamu tafi dare
na yi sosai Kar Benaxir ta rufe k'ofa Kinsan ba mutunci gareta ba! Nan suka yi
sallama suka bar ta da Haidar. Ganin sun share mintina babu wanda ya tanka wa
wani yasa Jaseena ta mik'e tana kad'e rigar ta tace " sai da safe yarima
,idon shi cikin nata yayi mata wani murmushi ba tare da ya tanka ba ,ganin
shiru yasa ta juya zata tafi.......
Mahaifina sarki
Mahmoud shine mai mulkin Wannan masarautar mutum ne wanda bai yadda ya ci ya
sha ba tare da ya tabbatar jama'ar k'asar nan sun wadatu ba kullum burin shi
yaga na gefen shi cikin walwala koda shi zai rasa ,hakan ne yasa ya fita daban
da sauran yan uwan shi wanda kuma sun kasance ba uwa d'aya suke ba domin shi
d'aya mahaifiyar shi ta Haifa kuma halin shi ma babu mai irin sa kasantuwar
,kakan mu mata biyu gareshi.....
Da sauri Jaseena
ta juyo ta dawo inda yake ta nemi guri ta zauna don ta jiye wa kunnen ta
....... Yerima Haidar yaci gaba da cewa
" duk mahaifina ne babba a ciki domin mahaifiyar sa itace ta fari daga
baya ne zaliha (ta biyun ) ta haifi maza
biyu Hasheem ,Hayatud-deen ,da kuma mace d'aya Saleemah. Duk cikin su ukun
Saleemah kad'ai ke son baba na don sun shaqu sosai hakan ne yasa tun tana y'ar
shekara goma ,mahaifiyar ta Zaliha ta bada ita aure a wani masarauta Wai shi Kalahari aka daura
mata aure da d'an sarkin garin yarima Jalalud-deen , wanda hakan yasa bata
'kara zuwa ko da ziyara nan masarautar ba,Domin shine hud'ubar da mahaifiyar
tata tayi mata.
Jin haka yasa
Jaseena ta mik'e a razane ta ce " Kalahari?? Jalalud-deen?!! " shima
Haidar ya mik'e yace "eh! Kin san su ne? Nan ta kwashe labarin rayuwar ta
ta fada masa yayinda ya cika da mamaki " haka Allah yake abin shi!! Shine
abunda Haidar ya iya cewa kenan ,ya dubi Jaseena yace "Kin ga yanzu dare
yayi ,ki je ki kwanta ki huta gobe in shaa Allah zan sanar da ke dukkan labari
na. A nan suka rabu da alkawarin zai sanar da Jaseena komai game da shi
washegari.................
🏵Jeeddah ja'o🏵
[3/25, 12:20 PM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔
🐚🏵Jeeddah ja'o🏵🐚
5⃣6⃣⏭6⃣0⃣
Tafiya take
tana ta fama da y'ar doguwar rigar ta ,tazo wucewa ta gurin fada kenan taji
kamar maganar mutane,ta d'an lek'a daya daga cikin tagogin fadar don taga su
waye a fadar cikin Wannan dare. Tana lek'a wa idanuwan ta suka yi karo da sarki
Jalalud-deen da kuma sarki Hasheem suna tsaye ,koda ta kasa kunne don tajiye
wa kunnen ta abunda suke shiryawa......
" Ai
Wannan ba komai bane ni a gurina domin a kan sarauta babu abunda bazan aikata
ba !!! Ko yarima Haidar da ka gani ban barshi a Wannan masarautar ba saida na
tabbatar cewa yana da nak'asa sannan kuma ban daukeshi a kan karon komai ba !!!
Duk da ma de Y'ata Meenah bata k'auna ta Sam !! Amma Wannan karagar mulkin da
ita ya dace ba Haidar ba!!!" Sarki Hasheem ne yayi Wannan maganar
hannunshi rik'e da kofin zinare. Sarki Jalalud-deen ya mik'e yayi wata y'ar
muguwar dariya yace " lallai abokina baka da wayo !! Ai sai da wuta ake shan
Zuma!!!domin dan hakin da ka raina shi zai tsone maka ido ,yaran yanzu da ka
gani ,zamani ya chanja domin babu wata dabara da basu sani ba ,bar ganin shi da
nakasa ,kaga fa yadda ya mamaye zukatan al'umma ! Abun yi kawai shi ne ka kawar
da shi kwata kwata domin in baya nan tare da kai babu yadda za'ayi Meenah ta
'ki kar6ar mulkin Ramali ,ka duba fa ka gani ,mace ce mai kwarjini ga jarumta
bai kamaceta bama a ce Wai ta bar daular dake cikin wannan masarautar! Ni ina
da shawara ,me zai hana a had'a su aure da d'an wajena Rizwan? Kaga zasu yi
mulkin Ramali cikin kwanciyar hankali ,kasan ko d'ana Rizwan bashi da masaniya
akan abubuwan da nayita tufkawa a masarautar Kalahari , don na lura yan da son
gaskiya shi yasa na ci gaba da 6ata shi da sakalci don in har ya gano ni ba mai
gaskiya bane ,Rizwan zai iya juya min baya kasan duk da ba Saleemah bace ta
haife shi amma goyon ta ne shi yasa nayi duk yadda zan yi su daina ganawa da
juna kullum!!" Duk suka bushe da dariya Hasheem yace " baka da dama
abokina!! Shikenan! Na amince da shawarar ka!! .....
Jaseena ta
toshe baki da hannayen ta ,ganin fitowa zasuyi yasa ta ruga a guje ,bata ankara
ba taji an fizgo hannun ta cikin wani d'aki an rufe k'ofar ,zata yi magana yasa
hannu ya toshe bakin ta yace , "ki nutsu" tana juyawa tayi ido hud'u
da Rizwan😳 tace " kai!!!
Sake min hannu na !!! " ta fisge hannunta daga rik'on da yayi mata ,ta
bud'e baki zata 'kara wata maganar ya ce " naji duk abubuwan da suke
shiryawa !! Kamar yadda kema kika ji su ' da na zaci ni ne asalin wanda ya
cancanci sarautar k'asar Kalahari ashe ba sarauta ta bace ta wani ne ! Duk
rashin mutunci da cin amanar da nake wa mutane ashe de duk a banza ne , duk
kuri da gadara da mulki ashe ba ta mahaifina bane !!! Kaicho na wlhy nayi
nadamar samun irin wannan uban ,wanda kawai son zuciya ya saka a gaba ,kuma
yanzu na tabbatar ba sona yake ba don yana turanine cikin halaka !! Wani hawaye
ne ya biyo kumatun Jaseena tace " hakane yaya Rizwan amma ai babu komai
akwai Allah!! Tana kai wannan ta fice tana goge hawaye ,tabar Rizwan yana
tunanin dalilin k'iran shi da tayi da yaya Rizwan ; cikin ranshi kuwa sai
tambayar kan shi yake ,dama akwai ranar da zata zo har zai zubar da kwalla da
kuma jin tsananin tsanar mahaifin shi?
Da sassafe
Jaseena ta shirya cikin irin shigar da ta saba ,ta fice don gari ko gama wayewa
bai yi ba ,bata zame ko ina ba sai inda sukayi alk'awari zasu na had'uwa ita da
Haidar ,amma abun da ya d'aure mata kai shine tun da taje tana masa magana ko
kallon inda take bai yi ba ballantana ya amsa mata ,da gani kasan ranshi a 6ace
ne. A fusace ya tashi zai bar gurin ta sha gabanshi da gudu tace " Wai ni
laifin me nai maka ne!?tun d'azu ina maka magana ka min shiru kamar da gunki
nake magana alhali na tabbata kana ji na "! Bai saurareta ba ya bi ta
gefenta zai wuce ta sake tare shi ,cikin tsawa yace ME KIKE YI JIYA A DAKIN
RIZWAN!!! " shiru tayi tana kallon shi ido da ido ta ce " me kake
nufi Haidar ? Me kuma zanyi a d'akin Rizwan ,chan ta juyo tace ,yaya Haidar !!
Yaushe muka fara haka da kai? Me yasa bazaka fad'a min ba? Me yasa kake boye
min ? " Haidar yayi sauri ya tari bakin ta yace " Jaseena ban fahimce
ki ba " tayi murmushi wanda yasa hawayen da ke idanuwan ta suka zubo ba
shiri tace " ka kasa fadamin kana sona ko" ka kasa kuma bawa zuciyar
ka hak'uri har ta fara zuga ka,ka fara zargin abin da kake k'auna kuma sannan
ka kasa daurewa! " Haidar ya juyo yana kallon cikin idonta" yayinda
ta juya zata bar gurin. Haidar yace " na soki Jaseena kuma har abada zan
soki " ya durk'usa k'asa yace " kiyi hak'uri ya ke Kyakkyawa ! Ki
taimaka min da zuciyar ki domin tawa ta riga ta kufce min ! Ban kuma san yaushe
zata dawo gareni ba don ta fita farautar abunda tafi mata komai soyuwa
ne!"
🏵 Jeeddah ja'o🏵
[3/25, 10:45 PM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵Jeeddah ja'o🏵🐚
6⃣1⃣⏭6⃣5⃣
Jaseena ta
juyo idanuwan ta duk sun yi ja ,tace "Na baka !! Na baka ya Haidar!! Ka
kula da ita domin taka ta riga ta iso inda zata tsaya da farautar kuma bani da
tabbacin zata koma gareka !!" Haidar ya mik'e yace " nagode kyakkyawa
!! Jaseena tayi murmushi tace " akwai maganar da nake son sanar da kai ne
" Haidar yace" ki fad'a mana ko ma menene. Ta kwashe duk abubuwan da
ya faru a daren jiya ta sanar da shi har abunda yasa ta shiga d'akin Rizwan.
Haidar ya sake bata hakuri ,sannan ta gyara zama ta ce " baka k'arasa min
labarin ka ba" ya d'an yi murmushi sannan ya ci gaba........
🕸🐚🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🕸🐚🕸
A lokacin ina da
shekaru goma sha shida ne ,k' anin babana wato Hasheem ya bi rud'in uwarsa na
cewa Kar ya kuskura ya bar babana da rai don in har ya tsufa a kan karagar
mulki nine zan gaje shi na zama sarki , don shi a cewar shi ni ba komai bane in
ya kawar da mahaifina, da duk wani mai ji dani, kasantuwar kullum da safe muna
fita daji ni da kakana yana nuna min nau'in ganyayyaki da amfanin su ,hakan
yasa ya shirya mana gadar zare.
Mun yi Nisan kiwo
nida kaka har bayan la'asar sannan muka iso gida ,muna shiga wasu mutane a kan
dawakai su kuma suna fita ,ga gari duk ya turnuk'e da hayak'i ko da muka
k'arasa cikin fada nan muka tarar da gawawwakin iyayena da kuma na k'annen k'
anin Hasheem Hayatud-deen , Hasheem ya kwanta a kansu sai kukan munafurci yake
yi kamar da gaske ,a nan ne zuciyar kakana ya buga take rai yayi halinsa ,
bayan kwana uku da faruwar hakan ,kawu Hasheem ya na'da kanshi a matsayin
sarkin Ramali ,duk dattijawan da basuyi Na'am da hukuncin da ya yanke ba sai ya
sa aka kwashe su aka kai su masarautar Kalahari aka rufe ana basu horo mai
tsanani ,daga cikin wadannan dattijawan sun had'a da mahaifan Aisha da kuma
Jauda ,kamar yadda na fad'a miki Meenah itace d'iyar kawu Hasheem amma tun tana
y'ar shekaru tara ne abun ya faru don duk sa'anni suke da Aisha da Jauda kinga
kuma k'awaye ne hakan yasa ta baro fada ta
zab'i zaman bauta a gidan Benaxir har ta girma ta kawo lokacin nan da kike
gani....
Ni kuwa tun
lokacin da abun ya faru na daina magana da Kowa da na gano hakan kawu Hasheem
ya ke so sai na nuna mishi ma kwata kwata bana magana na daina yi ko da da wasa
,a haka shi da mabiya bayansa suka zata na riga na zama miskini. Kin ji yadda
rayuwa ta ta kasance kullum cikin k'ask'anci amma ko a jikina domin na san dole
ne wata rana sai gaskiya tayi halinta!!" Amma tunda haka abun yake toh mu
zamu fara wargaza mishi rayuwar sa" Jaseena ta goge d'an hawayen fuskar ta
sannan tace " lallai ka shiga k'uncin rayuwa Haidar !! A nan ne Jaseena ta
kwashe labarin ta ta bashi ta kuma sanar da shi ko wanene sarki Jalalud-deen.
Sun dad'e suna shan hirar su ,kafin nan suka nufi gidan Benaxir don yin magana
da su Jauda..........
🏵Jeeddah ja'o🏵
[3/27, 11:25 AM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵Jeeddah ja'o🏵🐚
6⃣6⃣⏭7⃣0⃣
Sarkin yak'i
Amjad ne zaune a gefen sarki Hameed hannun shi rik'e da na Hameed. Na ganta!
Naga y'ar ka Jaseena ,tana cikin k'oshin lafiya ,kuma ga dukkan alamu tana
cikin shiri,Hameed ya mik'e yana murmushi yace " nasan ban haifi
lalatacciya ba!! Kuma nasan dama tana nan tafe , amma ya maganan mayak'an da na
ce ka tara ? Amjad yace ,komai an kammala shi kuma yanzu haka suna chan a kogon
tare da y'an fursunan k'asar Ramali! Da sarki Hasheem ya sa Jalalud-deen ya
d'aure shekaru kusan goma sha da suka wuce " Hameed yayi murmushi yace
" da kyau sarkin yak'i!!! Aikin ka yana kyau ,Allah ya mana jagora!!
Sarkin yak'i yace "Ameen"sannan ya mik'e ya fita.........
Yau tun da
safen nan Jaseena take motsa jiki tun bayan sun dawo daga gurin su Jauda Zabil
kuwa ya samu Haidar ba kasafai yake waiwayar inda Jaseena take bama don in zai
fita daji tare suke tafiya. Saidai yau Haidar bai je ko ina ba yana tare da
k'anwar sa Meenah a cikin makeken lambun dake wannan masarautar suna ta hirar
su duk da ma dai itama maganar kurmancin yake mata amma ta saba don ko ubanta
Hasheem bai iya magana dashi sosai ba. A nan ya sanar da ita cewa yana soyayya
da Jaseena, murmushi kawai tayi. Haka sukayi ta hira har kusan azahar, sannan
ya tafi domin gudanar da ibada yayinda itama Meenah ta juya tabar wajen ,zata
koma gidan Benaxir.
🏵🐚🏵🐚🏵🐚.
Jaseena🐚🏵🐚🏵🐚🏵
Yau kwana na
uku kenan ana ta bidirin gasa, Sam Sam Rizwan abun ma bai dameshi ba balle ma
ya shiga ,hasalima cewa yayi babanshi ya chanja wanda zai yi wasan shi bazai
iya ba ,babu yadda aka iya haka aka chanja shi da wani k'ak'k'arfa daga cikin
mayak'an Kalahari. Jaseena kuwa tun ranar farkon nan bata sake shiga filin ba
kullum tana daga chan baya ita da su Aisha amma fa ta lura cewa sarki
Jalalud-deen hankalin shi bai kwanta da ita ba. Washegari da safe ta shira
cikin dogon bujen wandonta bak'i da wata riga fara sannan ta rataya takobin ta
da y'ar jakar ta ta fice daga fada ,fuskarta a rufe ta bar idanuwan ta a waje
kamar wanda ta saka niqab , tafiya take cikin sauri kamar zata tashi sama, duk
saurin ta sarki Hasheem yana tsaye ta
sama a d'akin shi daga tagar d'akin yana kallon duk abunda ke faruwa
,tana fita Rizwan ma ya bi bayanta, ganin haka ne yasa sarki Hasheem shima ya
rufa wani k'aton mayafi don Kar Fadawa su ganshi su ce zasu rakashi ya fice
daga fada suna tafiya yana binsu duk yana jin abunda suke fad'a har suka shiga
Inda Haidar yace za suna had'uwa ,ya lab'e bayan wani dan ice yana sauraron duk
abunda suke fad'a.....
🏵Jeeddah ja'o🏵 BACCI😴😴😜
[3/30, 9:17 AM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵Jeeddah ja'o🏵🐚
7⃣1⃣⏭7⃣5⃣
Haidar, Jaseena,
Aisha, Jauda, Meenah, da Rizwan!!!! Duk na ji abubuwan da suke shiryawa !!! Don
haka dole ne mu kawar da su tun kafin su cimma burinsu🙄. Sarki
Jalalud-deen ya mik'e tsaye ya rasa me zai ce saboda ko kad'an baya son dansa
ya shiga wannan alamari amma tunda ya nuna taurin kan shi a fili toh lallai ba
makawa sai an hukunta shi.
Haidar yana sane
da cewa sarki Hasheem yana wannan gurin shi yasa ko 'kala bai ce ba a gurin
,sannan kuma yasa Jauda tayi karya akan shirye shiryen da sukayi ,sun yi akan
sai an gama gasa zasu far musu amma ashe shirin Sam ba haka yake ba !!! Cikin
dare k'afa duk ya d'auke suka shirya duk irin yadda Jaseena take shiganta ,suka
shigo fada ,Jaseena akwai ilimin duk wani abu da ya shafi yayan itatuwa da ganyayyaki
saboda haka ta shiga d'akin da sarki Hasheem yake ta zauna bakin makeken
gadonsa tana wani muguwar dariya 🤓ta fito da had'in maganin da tayi
sannan ta debi kad'an ta watsa a fuskar
shi a take ya farka gami da yin wani atishawa ya sulale ya koma kan filow ,nan
ta d'aure shi ga igiya tam sannan tayi fito a hankali ,Haidar ya shigo shi da
Rizwan suka ciccibeshi suka yi waje. Haka ne ya faru da sarki Jalalud-deen ma
,suna fita basu zame ko ina ba se cikin wani tangamemen daki mai kama da keji
suka tura su ciki ba komai bane ke gadin wajen illa damisa guda uku manya manya
🐅
Da dariya
suka fito su Jauda suka d'aga Jaseena sama yayinda Haidar da Rizwan ke ta musu
dariya, suka koma cikin gari ,kasantuwar inda suka je da nisa ,sai kusan asubah
suka iso cikin Ramali ,wannan kurkukun kuma shine asalin kurkukun masarautar
Ramali kafin sarki Hasheem ya hau mulki. Isarsu cikin gari basu zame ko ina ba
sai fada ,Haidar yasa a tara masa duk jama'ar wannan masarautar su hallara a
cikin fada ,kafin awa d'aya duk Kowa ya samu isowa ,Haidar yayi murmushi ya
gyara murya sannan ya fara da cewa:
Al'ummar
Ramali !!! Akwai wani d'an karamin labari da zan baku labari ne na mikiya kuma
ina kyautata zaton daga jin wannan labarin zaku fahimci Inda na dosa!!" Cike
da mamakin jin magana da sukaji yarima Haidar yayi suka amsa da " muna
sauraron ka yarima!"
🏵Jeeddah ja'o🏵
[4/3, 10:43 PM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵Jeeddah ja'o🏵🐚
7⃣6⃣⏭8⃣0⃣
Ita mikiya wata
tsuntsuwa ce wadda zata iya rayuwa har tsawan shekaru saba'in, amma domin kaiwa
wannan Shekarun ,dole sai ta d'auki tsatsauran matakai,domin lokacin da takai
shekaru arba'in dogin faracinan ta zasu zama basu da karfin neman ko kuma
chafke abunda zasu samu a matsayin abinci,wannan dogon bakin ta mai kaifin zai
kwanta (lank'washe ) fukafukan zasu zama tsofaffi, masu kauri kuma ga nauyi ,
wannan fukafukan masu kauri da nauyi ,zasu zama kamar a k'irjin shi suke hakan
zai basu wuya wajen tashi sararin samaniya daga nan ne mikiya zata zama bata da
wani zabi wanda ya wuce guda biyu kachal ✌🏾
ko ta MUTU ko kuma ta rayu cikin salo mai wuya na neman SAUYI! Hakan yana
bukatar mikiyar ta tashi ne sama ta hau kan tsauni ,ta zauna cikin gidanta
(nest) sannan sai Yayita buga wannan tsohon bakin nashi jikin dutse har sai ya
fincike shi , sannan wannan mikiyar zata bari har sai sabon ya fito sannan sai
ta fincike tsofaffin faracinan ta da shi ,lokacin kuma da wadannan faracinan
suka fito ,sai ta fara fiffige tsofaffin fukafukan nata da shi wannan shine
chanji da yafi ciwo zafi!! Toh daga nan ne wannan mikiyar take sake daukan
sabuwar rayuwa ta sake yin wasu shekaru talatin din a gaba! ME YASA AKE
buk'atar CHANJI??? Saboda a rayu kuma ayi zamantakewa!! Muma dole mu bi hanyar
SAUYI!!! Amma ba kamar mikiya ba ,Muma dole mu sauya munanan d'abiun mu zuwa
kyawawa da kuma abubuwan da muka aikata marasa kyau zuwa masu kyau ,mu zama
masu koyi da abunda addini ya zo mana da shi!!
Saboda haka
domin daukar hanya zuwa wannan SAUYI sai ku watsar da wadancan d'abiun domin
samun sababbi ,duniyar da fadi take amma mu bita a Sannu! Ku bude ajiyayyan
k'wak'walwar ku don ku Adana wannan ko zaku tashi da sabuwar rayuwa irin ta
mikiya!!!........
Kowa yayi shiru
jiki a sanyaye ,fadar tayi dub kamar babu wata halitta a cikinta , wasu na
hawaye amma hawaye ne na farin ciki cewa yau gaskiya ta dawo masarautar Ramali!
Wani dattijo ya mik'e yace " wannan haka yake yarima Haidar! Muna tare da
kai ! Dattijawan gari suka na'da Haidar a matsayin sarkin Ramali , ganin yadda
komai yazowa Haidar cikin sauk'i yasa Rizwan ya mak'ale mishi yace shi zai raka
shi masarautar Kalahari don ya nemi gafarar mutane wata'kila in yasa baki za'a
yafe masa shashanci da yayi ta aikata musu ba dare ba rana,nan suka sake sabon
shiri dukan su tare da wasu mayak'a guda ashirin suka d'au hanyar
Kalahari............
🏵Jeeddah ja'o🏵
[4/7, 6:04 AM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵Jeeddah ja'o🏵🐚
8⃣1⃣⏭8⃣5⃣
Kasantuwar ba
hanyar da su Jalalud-deen suke bi don shiga k'asar Ramali zasu bi ba ko dawakai
basu d'auka ba cikin sauki suka bi ta inda Jaseena ta fito suka shiga wannan
ramin ruwan har ta kaisu ga asalin cikin kogon ,bayan sun gama dirko wa daga
wannan dutsen ne suka tsaya karkade jiki su Jauda se kalle kalle ake yi basu
ankara ba suka ga sojojin yak'i sun zagaye su kowanne hannu rik'e da mashi
,gashi kuma abun da ya basu mamaki duk babu saurayi cikin su don duk sun
manyanta da gani kasan sun yi zamani, Jauda ce ta fara jefar da jakar da ta
rik'e tana motsar k'walla " baba!!! Abunda ta iya furta wa kenan ta nufi
gurin d'aya daga cikin wad'anda suka zagaye su ta rungume tana kuka Aisha ma ta
nufi gurin wani da ke tsaye yana kallonta sai hawaye ,Jaseena da ke kallon su
tuni itama ta fara k'wallar saboda ta tuna nata mahaifin da bata ma san wanne
hali yake ciki ba , Muryar sarki Haidar ne ya dawo da ita daga duniyar tunani,
tana juyawa taga gurin babu Kowa daga shi sai ita ta fara juye juye fuskar ta
cike da alamar tambaya?? Kafin ta furta komai Haidar yace " ya ke
ma'abociyar kyau da farin hali, kada ki damu Mun basu dama ne su gana da iyayen
su domin kuwa sun yi kewar juna " Murmushi Jaseena tayi sannan ta fara
share hawayen da ke gangaro wa daga idanuwan ta ,Haidar ya matso kusa da ita
yace " ya isa haka Kar ki sake yi min asarar hawaye ! Kuma baba yana cikin
k'oshin lafiya" Jaseena ta d'ago manyan idanuwan ta tace " don Allah
muje in ga baba na ,don hankali na bazai kwanta ba in ban sa shi a ido ba tana
fad'in hakan hannunta guda kuma ta chafke wuyar rigar shi ,inda ta shak'e ya kalla
sannan yayi Yar murmushi cikin murya irin na zolaya yace " irin wannan
chafka haka ,duk kin yamutsa min riga! Lallai kina so na sa a kulle min ke a
kurkuku yanzungaske.😜 " Hakan yayi matuk'ar bata dariya yadda ya
ta6e fuska kamar da gaske. Ya ce Haba!! Ko ke fa ? Amma matar sarki guda gashi
kuma jarumar mata amma tana hawaye kamar raguwa?" Dariya ta bushe da shi
tace " Aa ba wani nan ! Cewa zakayi jarumar mata da maza 😝 ai
mazan ma saidai in basu nemi in sambad'e su
ba 💪🏼". Dariya sosai ta bawa Sarki Haidar har ya
shagala ya nemi gurin zama yana kallonta, ita ko sai fama take da y'ay'an
innibi🍇 ,yana kallon yadda karamin bakinta ke motsawa cikin nutsuwa ta
lumshe idanuwa sai faman tauna take, yayi murmushi ya mik'e ya d'auki wani dan
karamin dutse ya wulla mata ya samu damtsen ta ,tuni hankalin ta ya dawo daga
duniyar da ta lula tace " ya dai?*
ya had'e rai yace " kin barni babu hira sai faman tauna kike yi !!
Ni na fa gaji ma kuzo mu tafi inda zamu je kafin dare yayi mana" chan sai
suka lura ko ina yayi shiru cikin kogon
Cikin sand'a yake
tafiya tana biye da shi ,haka suka gama dube duben su basuga Kowa ba a cikin
kogon ,Jaseena tace " toh ina suka tafi ne?" Haidar ya yi shiru na
yan mintina sai yace" duk yadda akayi sun nufi Kalahari ne zo mu tafi!!
" ko da suka fito bakin kogon suka tsaya suna tunanin yadda za'a yi su
tafi Kalahari babu doki kuma gashi da nisa suna so su tadda su Jauda. Har ta
hak'ura ta jingina da jikin kogon kawai suka jiyo sautin doki ,tana juyowa ta
hango zainu shi kad'ai ya dumfaro su ta juya ta dubi Haidar tace baba ne ya
turo shi , na tabbata sun isa Kalahari!! "
🏵 Jeeddah ja'o🏵
[4/7, 9:36 PM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵Jeedah ja'o🏵🐚
8⃣6⃣⏭9⃣0⃣
Isarsu Kalahari
basu zame ko ina ba sai cikin fada kamar wanda ake jiran isowar su mutane aka
fara bude hanya don su samu su wuce ,Jaseena kam da ta hango baban ta taga
yadda suke tafiya a hankali a saman dokin ,yasa ta dirko daga kan dokin ta
ruga. Rungume mahaifin nata tayi tana kuka ,ya d'ago ta yana faman share mata
hawaye ,zata yi magana kenan suka ji Hameed ya ja wani irin numfashi kamar an
shak'e shi ,idon shi na hawaye ,tace " baba!! Me ya sameka baba??"
Kallo na biyu da zata masa ne ta ga abunda ya matuk'ar tada mata hankali ,mashi
ne a wuyan shi ga kuma Jini yana malala kamar ruwa ,a take ta kurma ihu ta zube
a k'asa jiki na b'ari ,da gudu Haidar ya iso inda suke ya rike Hameed yana
hawaye , abunda ya iya furtawa shine " ga Y'ata nan Amana ,Kar ku cutar da
ita marainiya ce don Allah!! " ya dan saki wani 'kara gami da Kalmar
shahada take ya mace a gurin ,wani irin ihu Jaseena tayi ta sulale daga zaunen
da take ta fad'i sumammiya Haidar ya dubi su Jauda da ke faman zubar da k'walla
yace " ku kai Jaseena ciki ku tabbatar ta samu kulawa don Allah ! Suka yi
kamar yadda ya umarce su.
Haidar yace
sojojin yak'i su shiga su nemo koma waye yayi wannan Harbin a kawo masa shi.
Ana cikin wannan alamari ne wani soja ya zo da gudu wujiga wujiga duk jikinshi
yanka ,sai haki yake yana kiran sarki Haidar. Fadawa suka tare gurin shigowar
amma ya umarce su da su barshi ya karaso domin daga ganin shi kasan akwai wata
matsalar da ke tafe da shi. Kafin mutumin ya fara magana ,Haidar ya juya ya
dubi su Rizwan yace " a shirya gawar baba mu sallace shi Mu kaishi makwancin
shi na gaskiya," sannan ya juyo ya dubi mutumin yace " bawan Allah me
ya faru da kai haka? Wa ya aikata maka wannan taaddancin kuma daga ina kake?
Cikin rawar jiki
mutumin yace " Allah ya baka nasara daga Ramali nake ...." Ko da
Haidar yaji an ambaci Ramali yasan tabbas babu lafiya gashi sarki Hameed ya
rasu ,ga Jaseena Kwance babu maraba da matacciya dole su Jauda su kasance tare
da ita , toh me ma yake faruwa ne haka?" Tambayar da yayi wa kanshi kenan
gaba daya ya kasa tunanin abu daya, ya tura wasu Fadawa tare da mutumin su
bashi taimakon gaggawa kuma a kula da shi".......
Ana shirin
sallatar Hameed ne Jaseena ta farka ,bata bi ta kan su Jauda ba ta furma a guje
ko mayafi babu duk gashi a barbaje gashi duk ta zabga gumi gashin ya mammanne mata
a fuska bata zame ko ina ba sai gaban gawar mahaifin ta cikin yanayi na tausayi
,bakinta karkarwa kamar mai jin sanyi , ta d'aga hannun ta mai karkarwa kamar
zata yaye masa fuska sai kuma ta fasa ta dunkule hannun cikin kuka tace "
baba !! Ka tashi don Allah kar ka tafi !!! Abunda ta yi ta maimaita wa kenan
hakan ya sake tada wa Haidar hankali don a tunanin su ta zauce ne ,yadda take
yi din abin tsoro da kuma tausayi. " Meenah ku koma da ita ciki don Allah
" shima yana kokarin danne kukan da ya so kufce mishi.
Bayan sun dawo
daga janaiza Haidar bai zame ko ina ba sai cikin fada don ya nemi dakin da
Jaseena ke Kwance ,ko da ya iso gurin shi da Rizwan basuga Kowa a d'akin ba
,babu Jauda ,Jaseena Aisha da kuma Meenah. Haidar ya fito a fusace ya dubi
bafaden da ke bakin k'ofar yace " ina suka tafi kuma ?" Bafaden yace
ranka shi dad'e sun fita su hud'u amma fa naji kamar suna maganar Ramali ban
sani ba ko Chan suka nufa....... Bai ma saurari k'arshen zancen ba ya juya suka
nufi hanyar fita...................🦃
🏵Jeeddah ja'o🏵
[4/8, 8:19 AM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵Jeeddah ja'o🏵🐚
9⃣1⃣⏭9⃣5⃣
Gudu suke kamar
zasu tashi sama ,Jaseena ce kan gaba sai faman k'walla take yi zuciyar ta na ta
tafarfasa har suka isa masarautar Ramali ,shigan su ke da wuya suka ji ana ta
rufe kofofin gurin wasu sojoji suka zagaye su kamar masu kama barayi ,babu
wanda ya motsa a cikin su tabbas Jaseena ta lura cewa duk sojojin da ke zagaye
da su kibiyar da ke kwari da bakan su iri d'aya ne da wanda aka harbi mahaifin
ta ,ta tabbatar cewa wannan aikin Jalalud-deen ne ba Kowa ba ,abunda ya sake
kulle musu kai shine yaya akayi suka fito daga wannan kurkukun? Jauda ma abunda
take ta sak'a wa kenan.........
Ko da Haidar
ya fito waje ,yasa an tara mishi jama'ar garin manya da k'anana da kuma gagga
gaggan sojojin yak'i wadanda ake ji da su suma sun hallara nan ne Yerima Rizwan
ya rok'eksu yafiya kuma ya sanar da su cewa zai yi koyi ne da irin halin kawun
shi marigayi sarki Hameed ya kuma yi rantsuwa da hakan ,Kowa ya ji dad'in
wannan alamari saboda haka dattawan garin basuyi wata wata ba suka na'da shi
sarkin Kalahari ,bai hau kan karagar mulki ba yace har sai yaje an yak'i
azzaluman da suka kashe sarki Hameed kuma in har bai dawo da rai ba ,toh ya bawa
Meenah wannan gadon mulkin domin ita tafi chanchanta ,amma idan har komai ya
tafi daidai toh za'a hada masarautar Ramali da Kalahari su zama masarauta d'aya
a k'ark'ashin mulkin sarakuna biyu wato sarki Haidar na Ramali da kuma sarki
Rizwan na Kalahari ⚔
Jaseena bata
wani tsaya 6ata lokaci ba ta zare takobin ta ta diro kasa suka fara fada su
Jauda ma suka biye mata gurin ya kaure bakajin 'karar komai sai na had'uwar
karafuna kafin kace wani abu sun gama da sojojin suka tsaya a gurin sai haki
kamar zakanya Jaseena ke yi ta mayar da takobin cikin rigar shi ,d'aga kanta da
zata yi kawai ta hango munafukan guda biyu ,sarki Jalalud-deen rik'e da kan
d'aya daga cikin damusar da ke gadin kurkukun ya d'aga sama yana kyalkyata
dariya daga chan saman benen da yake yace " me ya farune GIMBIYA JASEENA!?
Ina fata ba karaya kika yi ba don in hakane wasan Sam bazai yi dadi ba ! In kin
isa yadda na saka tsaro dinnan ki karaso kiga me zai faru! Amma ko da yake ina
so inyi magana da ke ,kuma ke kadai don haka ke kadai nake so ki zo ki sameni
babu makami kuma !!! Ya sake burgewa da wata muguwar dariyar. Jaseena da
idanuwan ta sun kad'a sun yi jajir ta kau da kanta daga duban da take masa tace
KAI !!!! MATSORACI!!! KAI NE KAKE TUNANIN TAKOBI KO BAKA SHINE ASALIN MAKAMI
,AMMA ASALIN MAKAMI A ZUCIYA YAKE!!!!"
Ta zubar da makaman zata tafi su Jauda suka sha gabanta Aisha tace
" Jaseena ba zamu barki ki shiga ke kadai gurin wad'annan azzaluman ba
gaskiya" Jaseena tayi murmushi tace Haba Aisha ,ai koda kashe ni zasuyi
inshaa Allah zan shiga kuma zan d'auki fansa!!😡 ta wafce hannun ta tayi
ciki duk fadawan suka bita da kallo 🙄
Shiganta kenan
su Haidar suka iso gurin ,garin ma shiru kamar babu Kowa , a nan ya iske su
Jauda cikin matsananciyar damuwa , suka sanar dashi duk abunda ke faruwa
hankalinshi ya tashi Rizwan yace " yanzu meye abun yi ??¿
Jaseena kuwa da
ta shiga kai tsaye fada ta nufa shiganta kenan taji an rufe k'ofa ta juya da
sauri don taga wanene daga cikin su, Muryar shi ne ya fara ratsa kunnuwan ta
tabbas sarkin yak'i Amjad ne😳 ta waro ido waje tace " kai ! Dama
Kaine?!! Me kake yi a nan kuma?!!" Ya matso kusa da ita ya makureta a
bango kamar me neman kasheta ,sai taji yana mik'a mata abu a hannun ta ,tayi
amfani da tunanin ta taji ashe karamar wuk'a ce
tayi wata k'aramar dariya yace " godiya nake" shi kuma ya
hankad'a ta gefe ta zube a 'kasa su Jalalud-deen kuma basu san wainar da suka
toya ba sai wani dariyar keta sukeyi. Jalalud-deen ya karaso inda take rik'e da
irin kibiyar da aka harbi Hameed yace " ban sani ba Jaseena ! Ko tayaya
zan fara gamawa da ke ! Ko in sambad'e ki da wannan takobin ne kokuma wannan
kibiyar wadda itace silar barin ubanki da uwarki duniya?? Ko kuma............
Kafin ya karasa ta buga masa wannan y'ar wuk'ar a daidai mak'ogoro kamar me
bud'e madarar peak 😜 tuni ya durkusa kan gwiwar shi ,Jini na malala
kamar ruwa, ta zare wuk'ar tace ,ba sai ka za6a ba 😏 take ya fadi 'kasa
ya gama shure shuren sa har ya margaya (Hmmmm duniya kenan budurwar wawa akan
son abin duniya har ka kai kanka ga halaka!!) Ta juya ta dubi sarkin yak'i
tace" ina Hasheem? " ya nuna mata k'ofar fita yace " ya fice tun
tuni! Mu bishi!!!!! Jaseena tayi wata muguwar dariya tace Kar ka damu ,yayi
gudun gara ne ya tadda zago don nasan yanzu haka jikina yana bani ZAKI
NAH!(Haidar) ya riga ya iso 👣
Suka dunguma
sukayi waje suma, ko da suka fita basu tarar da Hasheem a raye ba amma kuma
kamar mutuwar kasko sukayi da Jauda😭 da gudu Jaseena ta yo kan Jauda da
ke Kwance a gurin matacciya ta rungume ta ,kuka takeyi duk ta susuce su Meenah
ma na durk'ushe a gaban su suna kukan. Haka ranar Jaseena ta kwana tana kukan
zuci wanda yafi kuka ciwo😭...............
🏵Jeeddah ja'o🏵
[4/8, 10:20 AM] Daxling🌹: ⚔🦃JASEENA🦃⚔ 2016
🐚🏵Jeeddah ja'o🏵🐚
9⃣6⃣⏭1⃣0⃣0⃣
BAYAN SHEKARA
D'AYA
Zaune yake kan
kujerar mulkin sa yana magana da waziri Jabeer ,sarki Haidar ne cikin kaya na
alfarma na sarauta sai hira sukeyi wanda har masu gadin ma suna saka baki , ana
ta raha, chan waziri yace " Allah ya baka nasara zan iya yafiya
yanzu?" Haidar yayi murmushi yace me zai hana ? Ko so kake kayi tafiyar
dare baka ga yamma ta kawo kai ba ? Waziri Jabeer yayi murmushi ya mik'e ya
nufi hanyar fita.
Dank'o ne a
hannun ta irin na Harbin tsuntsaye ta saita shi a kan kujerar ta sake masa daya
a hannun shi ,ko girgiza bai yi ba ya basar ,har tayi sau uku ,sannan ya juya
don ganin me aikata masa hakan. Had'a idon da zasuyi kuwa ta zaro manya manyan
idanuwanta da suka sha ado da kwalli😳 sannan ta tattare doguwar rigarta
ta ruga a guje ta fice zuwa lambu , murmushi kawai yayi ya mik'e ya kwashi
duwatsun da ta jefo mar ya fice ,bai ma san inda ta nufa ba shidai kawai yana
ta kallon yadda mutane Kowa ke gudanar da alamuran shi cikin lumana wasu yara
kyawawa sun kai biyar suka rugo da gudu suka rungume shi suna dariya ,sai d'aga
su sama yake yi yana musu wasa wata tazo wucewa dauke da kwando cike mak'il da
kayan marmari ya tsayar da ita ta kawo ma yaran ,sai tace " Allah shi
taimake ka Sarauniya JASEENA ke da buk'atar su " murmushi yayi yace "
ki basu sai a kai mata wasu , tana ina ne itan?" Matar tace tana cikin
lambu " gami da mik'a masa kwandon ta wuce. Shi kuwa ya durk'usa gaban
yaran ya ajiye musu kwandon yace " bismillah! " kowannen su ya d'eba shima
suna ta Saka mishi a baki sai da yaga sai loda mar suke ya mik'e da sauri yace
" Yauwa maza ku cinye kafin na dawo ya wuce ya barsu suna ta fama ,ba ma
mutane ba har dabbobi ma sun san akwai y'anci a Ramali😊.
Lek'o ta yayi
suna had'a ido ta ruga da gudu ya bi bayan ta sai fama take da doguwar riga
hakan yasa ya cimmata ,ya d'aga dutsen data wurga masa kamar zai rama sai yaji
daga waje wani mayak'i yace " Allah ya baka nasara sarkin Kalahari Rizwan
ne tafe da Sarauniya Meenah!!!! Jin hakan yasa ya sauk'e hannun shi yace ,a
shirya tarbar su ,kuma a sanar da sarkin gida " mayak'in yace toh ranka
shi dad'e! " sarki Haidar ya maida dubanshi ga Jaseena yace ,kin taki sa'a
yau da sai na rama jifan da kika min!!" Ta rungume shi tana ta dariya tace
" kai dai kace kaji tsoro Kar na fille maka kai yanzun nan 😝
" ya bushe da wata irin dariya yace " ni din ? Toh ko za'a gwada
karfi ne?" Ai ko bamu gwada ba kasan na fika k'arfi 💪🏼"
ya sake bushewa da dariya yace " karfin cin tuwo ba! Yanzu ma naga an taho
da k'aton kwando cike mak'il da kayan marmari Wai naki ne 😜 " Tuni
ta had'e rai tace " toh ai kasan ba ni kadai bace shi yasa 😒
" " Ohhhhh na gane !!! Kar kiyi ma d'ana sharri ,ke kad'ai kike cin
kayanki ☺" ta bugi kirjin shi da
hannun ta tace " zan rama ai!!!"
Ya kama hannunta suka fita suna tafe yana tsokanan ta...........
Haka dai
rayuwar su ta kasance cikin farin ciki da kaunar juna ,ga gaskiya da rikon
Amana ,sukan ziyarci junansu daga su har su Rizwan ,Aisha ta auri abokin Rizwan
ne majeed aka kuma suka zauna a gidan
Benaxir don yanzu kam bata nan dama ba gidan ta bane mallakin su Aisha ne
,majeed kuwa likita ne don babu wani magani da bai san amfanin shi da kuma
yadda ake hadawa ba!! Saboda haka wannan babban gida ake kiranshi da gidan
majeed likita!
Akwana a tashi
yaran Jaseena biyu ,na farkon sunan mahaifin ta ne wato HAMEED na biyun kuma
mace ce mai sunan JAUDA yara ne kyawawan
gaske son Kowa !
Bangaren Meenah
kuwa danta daya mai sunan mahaifin Haidar wato MAHMOUD! Aisha kuwa mace ta Haifa sunan ta Sameerah
sunan kanwar majeed da ita ,gaba daya suna cikin farin ciki ,nutsuwa da
kwanciyar hankali ,zalunci ya kau!!!!
🙏🏽ALHAMDULILLAH🙏🏽
Godiya ta tabbata
ga ubangiji Allah mai Kowa mai komai wanda ya kawo ni har izuwa wannan ranar da
na kammala wannan takardan nawa mai suna JASEENA !!
Dama ance in kaki
sharar masallaci zakayi ta kasuwa ,kuma abunda kashuka shi zaka girbe , masu
iya magana sunce RABON KWAD'O BAYA HAWA SAMA!!!
Duk abunda Allah ya kaddara zaka samu tabbas babu makawa sai
ka same shi ,amma in kasa son zuciya toh
lallai zai zamto sanadiyyar zubar ruwan idanuwa a gareka 😭 Allah kasa
mu dace AMEEN
ALL CREDITS GOES TO
MY BESTIES
- Rukayya Abdullahi Kakumi (Rukey kaxs)
- Aishat Muhammad (maman abd Shakur)
- Sufeeyah abdoul
- mah Nancy trbl
-my 'kawas Zeetu and Zainab Ahmad.....
And Ameener esmael(
maman Ilham)
GODIYA TA
MUSAMMAN
AJAJIGEEE GROUP
ZINARE BOOKS
SADAU GROUP OF WRITERS !!!
AND OTHER MEMBERS OF JEEDDAH JAO 📚NOVELSTOPIA🏵ENA