Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, December 9, 2019

DA NA KOWA NE COMPLETE HAUSA NOVELS

adsense here
DA NA KOWA NE COMPLETE HAUSA NOVELS

DA NA KOWA NE COMPLETE HAUSA NOVELS

[22/12 7:16 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
D'A NA KOWA NE
      © BY BEBEELO
🌿🌿
         PG (1~5)                   

                 ••••••••••••••

   Kamar wata mahaukaciya take famar tura kod'addun kayanta cikin wani yagaggen bakko, tana tura kayan tana sharar kwalla dake mata ambaliya ta kyakkyawar fuskarta.

Yar dattijuwa ce mai kimanin shekaru hamsin ta shigo dakin nasu wanda bayan tarkace ba abinda ke cikin dakin, tsaye tayi ta kurawa yarinyar ido tana kallonta harta gama tura kayan cikin jakar,



Juyawarda zatayi suka had'a ido da dattijuwar, murmushin karfin hali dattijuwar tayi, sanan ta bude bakinta da kyar tace" 
      Ummi ina zakije?

Wai ke yaushe zaii yarda da kaddara, ashe yanzu zaki iya fushi da kaddarar da Allah ya saukar maki dan ya gwada imaninki?
  Kwalla matar ta share sanan tace"tunda kin nace to wlhy na cire hannuna bazan hanaki tafiya ba,

Saidai inaso ki sani duk inda zakije, sai lokacinda Allah ya kaddari zaki samu mijin aure sanan
Ki same shi idan lokaci baiyi ba nasan ko'ina kk je bazaki sameshi ba, musamman da baki yarda da kaddara ba,
wlhy kin bani mamaki amma kije nidai a matsayina na mahaifiyarki ba da yawuna ba.
tana fadar haka ta fita waje tana rusar kuka, itama Ummi durkushewa tayi tana
kuka, kamar ta fasa tafiyar amma sai ta tuna fa mijin aure take nema.
Take ta shiga tunani ace yau shekara dai dai har talatin takeda amma har yau ba wanda yace yana sonta, sai gori ake mata a kauyensu, sa'aninta har an fara neman yayansu mata.

Da sauri ta mike, tana gyara zaman jakara a kafadarta, ita sam bata damu da talaucinda suke ciki ba kamar rashin aurenda batayi ba, haka ta saba jakarta ta fito.
Tsakar gida ta samu Innar Larai kishiyar babarta, wacce kullum itace gaba gurin yimata gori akan rashin aure,
shewa Innar Larai sanan tace"aa anrasa mashin shini shine aka fito zuwa gantali kuma to Allah ya bada kasuwa.

Kala Ummi batace ba da sauri tabar gidan tana rusar kuka, haha aja dinga nunata tasa ba idan da sabo duk ta fita sai a dinga tsokanarta ana kiranta da uwar yara
da kyar ta samu tabar kauyen  na saran dosa dake cikin garin birinin kebbi, harta iso bakin titi kuka take, anan ta samu motar kebbi ta shiga.
cikin motar ma bayan kuka ba abinda take, tasha suka sauka rikici ya kaure tsakaninta da masu motar kasancewar kudinta basu cika ba, ganin wulakancinda ake mata yasa wata mata da suka sauka tare ta cire kudin ta cika mata.

Godiya Ummi tayi mata nan matar tace ba komai yarinya ai D'A NA KOWA NE.harta tafi Ummi na mata godiya,
Zaune tayi cikin tashar tana rusar kuka har dare bataci komai ba gashi batasan kowa ba kuma batada ko sisi.
A ziciyarta tace kodai na koma gida naci gaba da hadiye bakin cikinda nake cikin shi,
Wata zuciyar tace karki koma gwara nan da can, haka ta yarda da wanan bakar shawarar na karta koma.
har bacci ya fara kwasarta ga yunwa tanaji, haka tayita fama har sawu ya dauke sam takasa bacci akan yunwa, zaune tayi tayi tagumi.
Abu tagani da gudu yayo kanta da karfi ta mike zata gudu, sai taga abin yy cikinta ya rungumeta saboda tsoro kasa ihu ma tayi, zaune ta fadi tana haki,
mutane ta gani da gudu sun biyo sai waige waige suke ga alama wani suka biyo amma kasancer duhu ne basa ganin komai har suka gaji da dube dubensu suka juya da sauri ta duba abinda ke rike da ita,
Dan yaro ne karami da bazai wuce shekara shidda ba, duk ya kamata ya rike sai bari jikin shi keyi.
 Da sauri Ummi ta dago shi tana kallon shi duk da ba ganin shi sosai take ba, bakinta na rawa tace'kai daga ina ka fito cikin wanan daren ina babanka da mamanka?
Yaron cikin muryar kuka,ta yara da basu gwane sosai ba yace"sun kashe mumy sun kashe Dady, sanan sun zubawa Uncle powder a idanu, shine nima zasu kashe ni.

Ido Ummi ta zaro tace"nashiga uku!!!! bakin shi ta rufe tace"kayi shuru kar suji kaji kai ya gyada mata, nan ta saka shi jikinta ta matse, take yy bacci yana maida numfashi, kallon shi take tareda haska mashi fitila, yaro mai kyan gaske, nan ta fahita da wani file dake hannunshi cike da takardu, karba tayi kasancewar batayi karatun boko ba sai yazama bata gane komai ciki ba, kodaddiyar jakarta ta bude ta tura file din, nan ta shiga tunani to waye ya kashe mashi iyaye har yakeso ya kashe shi?
waye Uncle da aka zubawa abu a ido?
Me sukayi masu, ai ita da d'auka D'A NA KOWA NE, dan me to wadanan azzaluman ke nema su cutarda yaro karami haka?

Ku kasance da Bebeelo acikin wanan littafin na D'A NA KOWA NE, dan jin amsar wadanan tambayoyin.
Amma sai bayan Sallah😉


         

Sadaukarwa ga UMMI AISHA
    By Bebeelo😘
[22/12 7:21 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿

D'A NA KOWA NE 👭👭

🌿🌿

       ©BEBEELO  (MUM IMAN)

                    (5~10)
                 ***********


~Ido ta kurawa yaron sai kallonshi take, take taji tausayinshi ya kara shigarta da kaunar yaron, ji take kamar d'anda ta haifa da cikinta.
sunar kanshi ta kama shafa saida ya dan motsa take kuma ya kara cusa kanshi kirjinta yana maida nunfashi alamar gajiya tattare dashi hannunta ta saka ta rungumeshi tana d'an bubbuga bayan shi.
  Bacci mai nauyi ya kwasheta tuni ta manta yunwarda takeji, sai da akayi sallah sanan ta mike bakin wani fanfo taje tayi arwallah tazo tayi sallah saida gari ya fara haske sanan ta tada yaron ta wanke mashi,baki kallonta kawai yake har suka isa inda suka kwana d'ankwalinta ta cire ta goge mashi fuska tayi mashi murmushi shima ya mayar mata kanta ya dafa yace"kene mumyna ynz?cox Mumyna itake min brush early in the mrng, murmushi tayi ta shafi gefen fuskar shi tace"nice mamynka ynz tace mashi haka amma sauran abinda yace sam bataji saboda ya sakko turanci ta lura yaron ko hausa bai k'wareba sosai sai dai turanci a ranta tace akwai aiki kuwa
 ya sunanka?tace mashi
Dariya yy yace" Mukhatar amma Mumyna use to call me sweet boy haka Dadyna kuwa My mukh yake cemin.

   murmushi tayi tace"toni ban iya kiran wad'anan sunan ba zan kiraka da Mukhtar, turo baki yy yace"no ni bana son shi Sweet boy zaki cemin, dariya tayi tace"toni ban iya kiran haka ba dariya yy yace"zan koya maki 
wane class kk a makaranta Mumyna kam tagama makaranta asibiti take zuwa kema kina zuwa asibitin ne?
  Dariya tayi ta mike tsaye ta fahimci surutu ne dashi ga shagwaba ragajabun jakarta taja tace"muje sulut boyi kar mutanen suzo su sameka nan, dariya yy yace'not sulut boyi Mumyna sweet boy ake cewa, itama dariya tayi tace da haka zan koya ai tunda kace dole shi kake so.

   Rungumeta yy yace"I luv you new mum, murmushi kawai ta mashi dan batasan me yace ba hannunshi ta rik'e gam sanan ta d'auki suka d'auki hanya, tafiya kawai take amma sam batasan inda zasu dosa ba ga yunwa taci karfinta, ji tayi yy tsaye cak  juyowa tayi ta ganshi tsaye d'an dukawa tayi gabanshi tace" suwut boyi menene? nan ma saida yy dariya yace"bafa haka ake cwa ba sweet boy da k'yar tace sweet boy to me ya faru, sake shan mur yy yace ni yunwa nakeji Kince kene Mumyna kuma Mumyna after tamun brush yummy breakfast take bani plantain nd fresh milk, batasan me ya ce ba, illah yunwa dayace 
mata yana ji, kallonshi tayi tace ka sani dan zakamin magana ka dinga gayamin da hausa kaji, kai ya gyada mata yace"but sauran ban san sunansu da hausa ba, cikin mamaki tace"wai kai ba baushe bane? kai ya gyada mata yace nima ban sani ba, kai ta gyada tace to gayamin sunan abincinda kk ci da hausa.
   dariya yy yace" da safe Mumyna plantain da madara take bani da rana kuma fried rice da kwai da hollandia take bani da dare kuma kamin na kwanta tuwon semo da hanta, idan zan kwanta madara nake sha, na ranar monday kenan, menene monday kuma? ido ya zaro yace"Mumy bakije makaranta bane ni Mumyna tasan Monday, dariya tayi tace"gayamin banje makaranta ba amma ai zaka koyamin ko ehh yace yana murmushi amma ai kinyi katuwa ni Mumyna ita ke koyamin murmushi tayi tace" toni kai zaka koyamin ko? kai ya gyada yace" ehh
    Gani tayi ya zaro ido.duk ya razana harda yan kwallan shi da sauri tace" menene ?hannunshi ya nuna mata bayanta da sauri ta juya wasu gardawa tagani sun nufo su ba alamar mutunci da saussauci balle rahama a tattare dasu take tagane ko su su waye da sauri taja shi ta aza a kafada ta figi jakarta ta zuba da gudu batama san inda take saka kafarta ba, haka suma mutanen suka rufa masu baya jam'a sai kallonsu ake.nima dai Bebeelo na gudu nayi wanka naje yawon sallah😂.

BY BEBEELO

     HAPPY EID MUBARAK
[22/12 7:23 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
D'A NA KOWA NE 👭
🌿🌿

       © BEBEELO (MUM IMAN)

                 (10~15)
                 ********

~Bata daina gudu ba saida taga takai dai dai gurin wani tafki ana ginar rami ta gurin za'ayi rijiya saidai ginar batayi zurifi sosai ba, tsayawa tayi jikinta sai b'ari yake tana shawarar ko ta fad'a ciki dan tserata'rda rayuwarsu amma kuma a kasan zuciyarta tana tsoro!!!
mukh kuwa tuni ya gama tsorata sai kuka yake kasa ta ajiye shi jikin shi sai b'ari yake ya rik'eta gam, ya runtse idanun shi hannunta narawa ta tab'a shi tace"Mukh zamu shiga nan kaji kar suzo su samemu kar kayi ihu kaji kuma ka daina kuka lar su jiyo mu  kaji.
  kai ya g'yad'a mata alamar tam itama runtse ido tayi ta tallabe shi suka fada ciki ji kake timm!!!
kamar tayi 'ihu saboda fad'awa kan hannunta da tayi amma saita kasa 'ihun, haka ta kama Mukh ta rungumeshi sai maida nin fashi suke su duka.

Har mutanen suka iso sai waige waige suke inda zasu hango su Ummi amma sam sun kasa hango su, guri suka nema suka zauna sai huci suke, d'aya daga cikinsu ne yaja tsuki yace"oga inagafa mu daina wahalarda kanmu saboda wanan yaron kamar aljani yake idan ba haka ba ya za'ayi ace kamar wanan d'an mitsitsin yaron tun jiya mun kasa gamawa dashi.
  Wani 'irin mari yaji akan fuskar shi ji kake tass-tsss!!!
Ogan nasu ne ya mare shi yana hak'i yaci gaba da cewa kai banza ne wawa, kai wanan ma abin kunya ne kake fad'a, shekara d'ai d'ai har ashirin ina wanan sana'ar kuma 'inacin nasara sai wanan jinjirin yaron ne zai hanani sakat, mikewa yy da k'arfi yana juya wuk'ar hannun shi, sanan ya kalle su d'aya bayan d'aya sauran d'uk suna tsoron suce wani abu yanzu su bak'unci lahaira, saboda shima damisa dan Ogan naji dashi ne saboda k'okarin kisa da yakeda, da c'ikinsi ne sukace haka da yanzu sum zama gawa.

   Wata irin dariya Ogan ya fashe da ita sanan ya sake b'ata fuska yace"wanan sakaran lauyan ma mun halaka balle wanan yaron, dan haka ba zamu koma ba sai da gawar wanan yaron, sanan ku sani itama wanan yarinyar da ta tari bala'i da kanta inaso d'uk kuka kamasu ku cire min kanta baki daya saboda ni itace ma yanzu ke batamin rai.Dariya suka saka sanan suka mike nan Damisa yace"angama ya Oga nima inason na kama yarinyar saboda itace ta lalata mana komai, murmushin mugunta Ogan yayi yace"ko kufa aje aci gaba da aiki ni yanzu zan koma naga gawar wancan bazan lauyan dan nasan yanzu ya karasa, dan haka ku tabbata kun zomin da gawar su, saboda naji dad'in bawa Alhaji Muji labarin mai dad'in sauraro.

   Dariya suka shek'e da ita suka hade addunan hannun su ji kake kassss-kasssss, sanan suka mike har sunyi nisa d'aya daga c'ikinsu ya dawo baya dai dai raminda su Ummi suke c'iki, jin motsin mutum yasa Ummi rikic'ewa!!! ta kara matse Mukh cikin jikinta sai bari suke, addu'a iri iri da ta iya take, wata mantawa ma take da karshenta sai ta sake ta kamo wata.wandon shi ya zuge dan yayi fitsari, haka ya dinga kwara'rawa su Ummi fitsari, har ya gama abin shi ya ja wandon shi yayi gaba.Saida Ummi ta kawatanci sun tafi sanan ta d'ago Mukh amma sam baya motsi wani irin ihu ta saka!!!!
 ta shiga ji'jjiga shi amma sam bai motsa ba......
 da saurinta ta figi jakarta ta d'ora wani bolo dake c'ikin ramin ta fara turo Mukh sanan ta fito ta d'ora shi a kafad'a sai gudu take tana kuka saida ta kawo titi ta tsaya d'uk motarda ta samu taro take amma ba wacce ta tsaya wasu ma kallon mahaukaciya ake mata hmmm duniya kenan inji Bebeelo.ta jima gurin tana neman taimako amma ba wanda ya taimaka mata sai wucewa ake tanayi tana ji'jjiga Mukh amma har lokacin bai motsaba, wata mota kirar venz ta wuce Ummi na taron motar ta tsaya, glass d'in motar aka saukar, take k'amshi ya daki hancin Ummi ga wani sanyi mai ratsa jiki kid'a kawai ke tashi a motar, wani k'yakk'yawan saurayine a motar k'asa da sama ya kalli Ummi sanan ya

 yace"Malama lafiya?
    Tana kuka tace mashi"dan Allah ka taimaka min yarona ne ba lafiya inaso na kaishi asibiti dan Allah wlhy banaso ya mutu dan Allah ka dubi girman Allah ka taimakeni.Wani irin tsuki yaja yace"gaskiya nikam bazan iyaba cox yanzu wani party zanje na frend d'ina so bazan rasa shi ba akan d'anki, amma zaki iya tsayuwa anan idan na gama naga da lokaci zan 'iya taimakonki.
   Ido ta zaro tace"haba bawan Allah kai bakada tausayine yanzu da ace d'anka ne ai bazaka barshi cikin wanan halin ba, ai shi D'A NA KOWA NE.

a fusace ya kalleta!!!!!
  sanan yace"ke ni zaki gayawa haka?

 marai'raicewa tayi tace" dan Allah kayi hakuri ka taimaka min, wani wawan tsuki yaja,wani 'irin zarin fitsari yakeji sunayi, ya maida glass din motar shi ya jata da k'arfi, hannun ta d'ora aka!! tana innalillahi wainna'ilairajiun.
   sulalewa tayi ta fad'i k'asa daga ita har Mukh d'in yana saman k'irjinta.Yaga lokacinda ta fadi! sai yaji bazai iya tafiya ba ya barsu sitayirin motar shi ya daka yaci birki yayo baya, da saurin shi ya fito da k'yar ya b'anbare Mukh a hannunta ya fara saka shi gaban mota sanan itama ya d'agata baiyi mamakin rashin nauyinta ba kasancewar ta batada k'iba, bayan mota ya sakata bai zarce ko 'ina ba  dasu sai F.M.C fedaral medical center dake birnin kebbi.

     Cikin tashin hankali Oga  rodu ya fito daga d'akin sai waige waige yake ya bud'e nan ya bude c'an, d'uk gidan ba 'inda bai duba ba amma baiga abinda yake nema ba. Wayar shi ya c'iro ya kira Damisa, cik'in murya mai karfi Oga rodu yace"aiki ya dawo sabo!!!
   A razane Damisa yace"Oga meya faru ne?

 Wanan banzan Barrister.Umar mana, banga gawar shi ba ko 'ina na bincika gidan amma ban ganshi ba.Cikin mamaki!!
 Damisa yace"Oga yafasha alburushi sosai dan haka ka k'ara dubawa bana tunanin zai'iya rai har ya gudu.
   Tsuki Oga rodu yaja ya kashe wayar, sake danna kira yay, bata jima tana ringing ba aka d'aga c'ikin 'isa da mallaka Alhajin ke magana, dafatar har kun binne su?
 dan muma gamu nan mun binne iyayensu har mun dawo.

    Ajiyar zuciya Oga rodu yayi yace" Alaji akwai matsala fa!!!
da sauri Alaji Muji ya mike!! yace"matsala kamar yaya? kar dai ka gaya min baku kashe yaron ba da Barrister?
  "Alaji bamu samu yaron ba har yanzu kasancewar ya samu taimakon wata kafa'ffiyar yarinya, sai wani abin mamaki, kasan d'uk c'ikin yarana ba wanda ya iya harbi kamar Damisa, to shi ya harbi Barrister har sau biyu a kirji bayan mun saka mashi hoda mai lalata ido.Amma kuma kamin muje mu kama yaron daya gudu sai muka tarar ba Barrister ba labarin shi.

 C'ikin razana Alaji Muji yace"a'ikuwa kun kashe maciji ne kunbar wutsiya, saboda barin Barrister da wanan yaron da rayuwa to tonuwar asiri na ne daku baki daya, dan haka ya rage naku kuje kusan d'uk yadda zakuyi ku kashe su, amma wlhy Oga rodu kaban mamaki duk a'iki irin naka amma ace mace ta hanaku a'iwatar'da burinku kai tirrr wlhy!!!

  kashe wayar yayi, wani irin huci Oga rodu yayi yaja wuk'ar shi ya saka a c'ikin bakar safar shi mai warin tsiya. Yanawa kanshi kirari ni Ogar rodu mai zuba aradu akan wanda kwana suka k'are, yazama dole na c'iro kan wana'n shegiyar yarinyar, Barrister kuwa duk in'da ya shiga sai na gano shi yana fad'ar haka yabar gidan.


        BY BEBEELO

SADAUKARWA GA UMMI AISHA
[22/12 7:26 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
D'A NA KOWA NE 👭👭
🌿🌿

    ©BEBEELO (MUM IMAN)

                      (15~20)
                     *********
~Tsaye yake bakin kofar (emergency room),  ya rungume hannuwan shi a kirjin shi, yana juya key din motar shi ta gefe.Imagining kanshi yake kawai na yadda wanan kujakar ta tsaida shi zuwa sabgar shi, yana cikin haka, d'aya daga cikin Nurses dinda suka karbesu ta fito da takarda a hannunta.

      ko ajikin shi harta bashi takardar ya karba da gadara yana kallon takardar, bai fahimce komai ba kasancewar ba duk mutum ke fahintar rubutun likitoci ba, kallon Nurse din yayi sanan yace"

    meye anan?
cox ni ban fahimci wanan rubutun ba.

  juyawa tayi tace" magani ne da ake bukatar ka siyo za'a basu, da kalar abincin da zasu ci
     bata jira me zaice ba ta wuce abinta ganin irin rainin hankalinda yake mata.

    ya jima tsaye yana kallon takardar kamin daga baya ya fita yana jinini, har ya siyo maganin, abincinda akace ya sayi dama fresh milk ne sai costard da fruts.Yana shigowa ya zarce d'akin da suke Nurse din ya sama ya mika mata kayan, zai juya cikin gadara Nurse din tace" Dr. na nemanka a office din shi.

   kafa ya buga a k'asa yace"
ohhhhh my God.......

 i'm tired of this wahala gaskiya, wace riba zanci ga wanan taimakon tunda ba budurwa ba ce da aurenta. A fili yayi maganar har ya wuce yabar Nurse da mamaki.

  Kai tsaye ya wuce Office din Dr. Zaune ya same shi yana dannar laptop dake gaban shi,  Dr.ya d'auki minti goma kamin ya kalli Ammar wanda haushi ya kusa sukewa.

   Hankali Dr. ya tattara ya mayar ga Ammar wanda shima Dr. yake jira, bayan sun gaisa Dr ke tambayar Ammar matsayin shi ga Ummi da d'anta.
  g'yaran murya Ammar yayi yace" ba abinda ya had'ani da ita face taimako.Murmushi Dr. yayi yace" well kayi abinda ya dace saika ida cika ladarka cox suna buk'atar taimako sosai.

  Ajiyar zuciya Ammar yayi yace"

kamar wane irin taimako suke bukata?
g'yaran murya Dr. yayi yace"

  taimako sosai saboda sanadiyar yaron ya tsorata sosai, har yayi sanadin k'wak'walwar shi har ta samu matsala, ga wahala da yunwa da sukaci karfin shi, sai ita kuma uwar wahala, damuwa, da yunwa su suka haifar mata da wanan halin da take ciki.

   Abu na gaba shine duk aka barsu a wanan halin komai zai iya faruwa dasu, so tunda ka dauko taimako saika ida nufinka, kasan kowa ya taimaki wani Allah zai taimaka mashi

 baksan inda suka fito ba,
 bakasan meke damunsu ba,
bakasan halinda zasu shiga ba idan baka taimaka masu ba,
haka zalika bakasan baiwarda suke tare da ita ba.

    ga baki daya jikin Ammar ya mutu da kalaman Dr.
Nisawa yayi yace"bakomai za'a iya masu duk abinda ya dace na d'auki alk'awarin zan biya ko nawa ne.Murmushi Dr. yayi sanan yace"
  Allah ya biyaka abinda ka masu mukuma zamuyi iya kokarinmu ganin sun samu lpy insha'Allahu.Allah yasa inji Ammar sanan ya bawa Dr hannu ya fice daga Office din.

D'akin da suke kwance ya shiga, nan ya samu Ummi ta farka Nurse ta zuba mata fresh milk a glass cup tana sha a hankali, Mukh shima ya farfad'o amma an mashi allurar bacci dan ya samu ya huta.

    Ido suka hada shida Ummi, a hankali ya furta mata
" ya jikin naki?
 itama haka ta bashi amsa a hankali
" da Alhamdulillah.

   shuru ya biyo baya, bayan Nurse tabata magani ta fita, nan Ummi ta samu damar cewa"

  mun gode sosai da taimakonda ka mana nida d'ana Allah ya saka maka da mafifici alkhairi.
   murmushi yayi sanan yace" 
ba komai ku godewa Allah sanan ai shi D'A NA KOWA NE.

   Ba kowa yasan haka ba bawan Allah, dan haka kaidai mungode.
Sunana Ammar!
 ke kumafa da yaronki?

   Nisawa tayi cikin muryarta mai zaki tace"

Ummi!
yarona kuwa
Mukhtar!

   Murmushi yayi yace" wow nice names..
D'agowa yayi ya kalleta, sanadiyar kanta na kasa ya bashi damar kallonta da k'yau, a ranshi yake yaba k'yanta, k'yakk'yawa ce ajin farko fara tass, ga diri idanunta manya ne masu d'aukar hankali, sumar da ke kwance gaban goshinta ya bawa Ammar damar wasi wasin za'ayi gashi a kanta. kan lips d'inta ya dawo masu d'aukar hankali kalar pink bata buk'atar janbaki.

  haka Ammar ya dinga biyarta da kallo har suka had'a ido da saurin shi ya kauda kai itama haka, sum sum ya fara, yace mata zaije gida amma anjima zai dawo, godiya ta kara mashi sanan ya fice cike da tunaninta a ranshi, itakam mikewa tayi take bacci ya kwasheta.


                   *******


A b'angaren su Oga rodu kuwa sai nemansu suke, kuma sunga lokacinda Ammar ya sakasu mota.Haka suka bi bayansu amma kasancewar Ammar d'an race ne sai ya tsere masu, sunyi mamaki sosai irin yadda ya iya sarrafa mota.
   Da haka har suka isa nan suka ga asibiti ne, ya nufa dasu ga shi akwai tsaro sosai a asibitin haka suka juyo cike da takaici amma sun k'udiri bibiyar rayuwar wadanan bayin Allah.

Ayi hakuri da wanda ya samu please nasan yayi kad'an, kutayamu murna mun samu Baby boy yau.

             BY BEBEELO

SADAUKARWA GA UMMI AISHA.
[22/12 7:30 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
D'A NA KOWA NE 👭👭
🌿🌿

   ©BEBEELO  (MUM IMAN)

                 ( 25~30)
                 *********

~ A hankali Ummi ta fara aiki gidansu Ammar, zagi, rank'washi habaici, Kora da hali ba wanda Ummi bata gani gurin Mum,

    amma sai tayi kamar ba da ita take ba saboda tanaso ta zauna gidan dan rufawa kansu asiri.Har lokacin Mukh bai tuna komai saidai Ummi har wanan lokacin ya d'auketa uwa saboda irin kulawarda take bashi, shima sam baya jin dad'i gidan idan ya shak'ata to gurin Ammar sai Inna data maida shi kamar jikanta mugun sonshi take kuma tana kula dashi sosai.

     A kwana a tashi har Ummi tayi wata d'aya gidan, amma ko lek'a bakin gate bata taba ba daga ita har Mukh.Oga rodu kuwa zaman k'ofar gidan ya zame masu kamar ibadah amma sam basu taba ganin Ummi da Mukh ba, kuma sun san suna gidan amma sun d'auki alwashin ci gaba da bibiyarsu har lokacinda zasu same su.

      Yauma ma kamar kullum Ummi ce a babban kitchen d'in gidan tana sarrafa nau'i nau'i na abinci kasancewar lokacin komai ta iya na girki kalar na birni, Inna ce ta shigo d'auke da alayyahu ta kife kan tebur, murmushi Ummi tayi tace" Inna me za'ayi da alayyahu?

    Inna dake k'ok'arin wanke alayyahun tace
" Hajiya tace ayiwa Alhaji miyar hanta da wake, kulle tower Ummi tayi da ta gama had'a miya sanan tace" to bari nayi mana, naga kin fara wankewa.Murmushi Inna tayi sanan cikin farinciki tace
  
" aa"
Ummi;
 ke kenan kullum aiki sai kace agogo, tunfa da safe da kika tashi baki zauna kin huta ba dan haka bari nayi yanzu kinji.

itama Ummi murmushin tayi, sanan ta karbi wuk'ar daga hannun Inna sanan tace

   " Inna;"
matuk'ar ina gidanan to dole ki dinga hutawa, kamata ace ina zaune kina aiki, 
    to meye anfanina a gidan?.

Dan haka karki damu bari nayi kawai ina ai miyar d'aice shikenan sai kuma aikin gobe, murmushi Inna tayi sanan tace
   " Ummi";
Allah Ubangiji ya maki albarka ya d'aukaka rayuwarki, na jima banga mace mai hali irin naki ba Allah ya barmaki yaronki.

Ameen Ummi tace, cikin jin dad'i ta furta, kinga ai gashinan na samu albarkarki, dariya Inna tayi sanan ta juya tace
   " ai albarka kin fara shanta kenan, bari naje natada mai gidana tun d'azu bacci yake, dariya Ummi tayi tace

   " wanan mai gidan anaji dashi, fita Inna tayi tana dariya, tayi d'akinsu ta tada Mukh daketa famar bacci.

                     *********
  A store ya hangota tana famar d'ebo manja, ya jima yana karewa halittar kallo, duk da zami da riga ne a jikinta bai hana dirinta ya fito ba gashi duk da tana wahala ta d'anyi kyau abinta tunda tanaci ta k'oshi. karasowa yayi gurinta batasan da mutum ba ji tayi kawai an shafi bayanta da saurinta ta mik'e tana salati.

    juyowarda tayi suka hada ido da Ammar, mur tasha sanan tace
   " Malam meye haka?

shima fuskewa yayi yace kamar yaya?

   k'ala batace mashi ba ta fito abinta tayi kitchen, shima tsuki yaja yayi d'akin shi, kan lafiyayyen gadon shi ya zube yana maida nunfashi tareda tuno laushi da taushi na bayan Ummi, mirginawa yayi tareda lumshe ido a fili ya furta gaskiya kowa ya samu wanan matar zai more rayuwar shi.

    Baiso maitar sa kwad'aita mashi Ummi ba, cox tana bashi girma shima kuma haka kawai ya tsinci kanshi da shakkunta, amma kuma yanzu sai kara sha'awarta yake, mik'ewa yayi ya dunk'ule hannunshi yakaiwa gado noshi, a ranshi ya furta gaskiya sai nasan yadda zanyi na kore kishin wanan yarinyar mai cike da kayan alalatu na morewa da kore duk wata kishirwar d'a namiji.


                   *********
A hankali Dr: ya cire mashi bandage d'inda ke d'aure da fuskar shi, kasa bud'e idon yayi sai yaje ya bud'e sanan ya kulle su kuma, murmushi Dr: yayi sanan yace mashi

    " Don't be scared Barrister, just open your eyes.

Daurewa yayi ya bude idon, Aminin shi Ahmad yayi tozali dashi, murmushi ya saka mashi sanan yace

"Alhamdulillahi"

    Ahmad najin haka ya taso ya rungume Aminshi sai murna suke, Dr. dake tsaye yace

" dama na gaya maku baisa kun wahala zuwa k'asar waje ba, cox matsalar ba wata babba ba ce, kallon Barr yayi yace

   " Hop komai normal, murmushi yayi yace" Dr. may be ma nafi gani yanzu akan da.Dariya sukayi suduka tareda godewa Allah sanan suka shiga yiwa Dr. godewa.Sallama ya basu sanan suka tattara komai nasu suka kamo hanya.

     Shuru kakeji cikin motar ba mai magana, nisawa Ahmad yayi yace
   " Barrister";
kadaina damun kanka sosai kaga yanzu you need hutawa, cox kaga halinda ka fito ciki.Kallon shi Umar yayi kamin daga baya yayi wani d'an murmushin yake sanan ya furzarda 'iska yace

   " Ahmad;"
bani ba hutawa harsai nasan inda Mukh yake, yazama dole idan yana raye ina raye na nemoshi kuma na kwata mashi hakk'in shi da wanan azzalumin yaci.

    Bance karka nemeshi ba, fad'ar Ahmad kenan,
 but you have to be very careful, very-very careful,
 cox kasan halin Alaji Muji sosai, so kasan plan d'inda zakayi kamin kasan yadda zaka tunk'are shi 
cox idan baka iya kamun barawo ba shi sai ya kamaka.

   Hakane kam inji  Umar ni tuni na kammala plan d'ina, nidai kawai nasan inda Mukh yake shine gabana.
  Allah yasa mudace Allah kuma ya baka sa'a,
 " Ameen Barr yace.

  Yanzu goben zaka isa Delta state, ehh Barr yace
  " Haka nakeso insha'allahu cox Mamina  ta damu k'warai, tace sai na dawo dole, d"an murmushi Ahmad yayi yace 

  " tanada gaskiya dole ta damu, cox katuna kai kad'ai ke gareta lkuma taga ana nema a hallakaka so tanada gaskiya.

   Kala Umar baice ba haka yaja baki yayi shuru sam Ahmad bai damu ba saboda idan da sabo ya saba da aminin nashi bamai son surutu ba ne.


                 ***********
Kicibis tayi taja ta tsaya ganin mutum, sabida batayi tsammanin ganin shi d'akin ba dan bai saba zama ba idan zata gyara, 

da saurinta zata koma ya rikota, sai gata kirjin shi, wanan shine karo na farko d'a da namiji ya tabata tana cikin hankalinta sai taji abin bambaram bam.
   A fusace tace
"Malam miye haka dan Allah?

    wani shu'umin murmushi yayi sanan yace
  "Abinda kika gani mana, cikin karaji tace
" to kasakeni yanzu wallahi kamin na maka ihu, 
dariya yayi  yace
" gidanmu nefa, kuma Ummi idan bakeba nifa na taimakeki a rayuwa, dan haka nima dan Allah ki taimakeni, sau d'aya kawai, na kore kishina akanki.
  A fusace tace
" wallahi ni ba yar' iskace ba dan haka kayi gaggawar k'yaleni na tafi, tun kamin na maka illah.

kawai  jitayi ya sunkuceta ya cilla kan gado, nan hankalinta ya k'ara tashi, tambayar kanta take to me wanan mutumin ke nufi?
 bata ankara ba taji ya hawo gadon yayo cikin ta sai shafarta yake, nan ta shiga  yakushi da cizo ba wanda bata mashi amma yak'i saketa tuni ya zare hajibin jikinta.

   Ganin  yak'i sakinta har yana shirin cire rigarta yasa ta rarumo kwalba kan side drawer ta shiga k'ok'arin rauka mashi, 
sai taji yayi k'ara.....!!!! ya zube jikinta, da k'yara ta ture shi ta rarumi hijabinta tayi waje, nan tayi kicibis da Mum dake tafe da gudu, sanadin ihun Ammar da taji.

   Ganin Ummi a firgice yasa Mum fad'awa d'akin da sauri, leme ta samu Ammar baya motsi, jij'jiga shi ta shigayi amma sam ba alamun rai tattare dashi. Aikuwa salati ta rauka ta fito da gudu tana ihu......

   shikenan ta kashemin d'a!!!
ashe ajalinshi ya yayebo, dama na fad'a wanan yarinyar da ganinta munafukace akwai abinda tayi aka korota.

Ashe makashiya ce.Duk wanan surutun Mum ita kad'ai ke yinshi,
Ummi kuwa fad'awa d'akinsu tayi ta rarumo jakarta da Mukh Inna na tambayarta meya faru,
 amma sam takasa cemata komai gudu kawai take ta jawo hannun Mukh.
    Taci sa'a masu gadin suna sallah, nan ta samu damar barin gidan, koda Mum ta sauko tana a tare Ummi ina tuni Ummi tabar gidan, nan Mum ta zube k'asa tana ihu.

Gudu take kamar ranta zai fita, tuni Mukh ya gaji ta d'auke shi ta d'ora a kafad'a, bata kara rikicewa ba saida taga su Oga rodu a nayanta sun biyarta damasu kullum zaune suke kofar gidan zaman jiranta, ai sai ta karawa kafarta wuta.


    bakin titi, wata babbar mota ta kawo, Ummi na taronta ta tsaya batayi wata wata ba kawai ta fad'a motar, aikuwa tana shiga sai kawai suka zube kamar matattu ita da Mukh, murmushi mutumin yayi yace
   "yau akwai sa'a, daga fitowa, cigaba yayi da tuk'in shi hankalin shi kwance.Wayar shi ya d'aga nan yafara magana, ehh yanzu ina kan hanya zan iso dasu Delta karkaji komai, yau k'ungiya zasu sha jini su k'oshi, dariya ya ke da ita ya katse wayar, sanan yaci gaba da tuk'inshi cikin kwanciyar hankali.


  NOTE:Masu comments akan A RASHIN YAFIYA, ba kullum zan dinga yinshi ba, kwana d'aya d'aya ne shi.D'A NA KOWA NE, shi zan dinga yi kullum da yardar Allah.Bebeelo ke maku fatan a'lkhairi


              BY BEBEELO

SADAUKARWA GA UMMI A'ISHA.
[22/12 7:32 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
D'A NA KOWA NE 👭👭
🌿🌿

        ©BEBEELO (MUM IMAN)

                ( 20~25)
                *********

~ Yana isa gida ya taradda Mum d'in shi a babban falo tana cin d'atun gari da salad yaji kuli kuli da albasa ga kamshin tafarnuwa na tashi.
Zubewa yayi kan kujera dake mamaye da falon da yasha kayan alatu na zamani, 

   washhhhh Allah na!!!!
  
Abinda ya fad'a kenan lokacinda ya zube kan kujerar, a kasale yace" 
Mum sannu da hutawa, kallon shi tayi tayi murmushi tace" 
  yawwa Ammar

Kara nazarinshi tayi tace" inace sai dare zaka dawo, amma na ganka yanzu kuma kamar a gajiye.Yatsine fuska sanan yace" 
   eh;
amma hakan baiyu ba, cox na kad'e wata mata da yaronta yanzu haka suna asibiti.
Yatsina fuska tayi kamin tace" 

hala yar waye ka kade?

   kara nocewa yayi cikin lallausar kujerar yace" 
Mum;
Ba y'ar kowa ba ce hasalima inaga daga k'auye suke, cox suna cikin wahala.
Tsuki taja to shine kake damun kanka ai sai ka biya ayi treating nasu ka dawo amma shine ka wani je ka zauna kana jinyar su mtswwww......

   Dariya yayi yace"
    Mum da talaka ba zama lafiya.

 spoon takai baki sanan tace" kaima ka sani bana shiri da talaka, dan haka kaje kawai labada duk abinda ake bukata karka koma gurinsu dan banaso.

  tam yace sanan ya mike yace" 
  Mum me aka tanada min inajin yunwa?

Dariya tayi tace"
 yaron Mum kenan, ai tuni nasa Inna ta d'ora maka

 tuwon semo,
 miyan danyar kubewa, da ganda.

 dariya yayi yaje ya rungumeta yace thats my lovly Mum, bari naje nayi wanka kenan kamin a karasa.

  AMMAR:
D'a tilo ga Alaji Tijjani babban d'an kasuwa, wanda ya shahara ban garen shigowa da manya manyan motoci kirar zamani.
 matar shi daya Hajiya Saratu, bafulatana nace ta k'asar 
Niger; 
tanada kyau sosai, sabanin mai gidanta, Ammar ga baki d'aya ita ya kwaso gurin k'yau.

   itama yar babban gida ce, tun tasowarta ta tsani talaka, bata sha'ani da talaka ko kadan sai matan masu kudi.
Ammar akwai shi da shgwaba yayi karatun shi a Indunesia, bangaren Electrical enginering.

    yanada wulakanci saidai wani lokaci yanada tausayi, y'anmata kam buhu-buhu haka yakeda su, kuma ba wacce bai zuki ni'imarta ba.
 Ya iya sarrfa mota sosai, saboda zaman shi can k'asar waje yayi race sosai yaci k'y tuttuka sosai, Ammar kenan.


    Satin Su Ummi d'aya sunji sauk'i sosai sunyi garau, har yar kiba Ummi tayi, ita ke kula da Mukh saboda ita taji sauki.Abin tausayi Mukh ya kasa tuna komai kallo kawai yake biyar Ummi dashi itama bai ganeta ba, tayi kuka harta godewa Allah.

   sai tambayar kanta take ya za'ayi tasan yan'uwan Mukh yanzu?
   Dr: ya sallamesu, sai Ammar yayi k'arfin halin kaisu gidansu duk da yasan Mum din shi ta tsani talaka, amma dayake yayi magana da Ummi ta amince akan  dan Allah ko aikine ya samo mata gidansu.

 Cox daya nemi labarinta tagaya mashi cewa mijinta ya rasu, kuma itama iyayenta duk sun rasu, sai y'an uwan mijinta suka cinye dukiyar mijinta suka koresu.

   yaji tausayinta sosai shine ya amince da rok'onta, akan zai lallabi Mum d'inshi ta barta ko aiki tayi gidan.Da haka suka isa gidan, har falon Mum yayi masu iso tana zaune tana kallon tashar larabawa, nan hankalinta yayi kansu.
  
ko shakka batayi ba tasan sune Ammar kebata labari, shiyasa ta gimtse fuska, a ranta take cewa

 to me sukazo yimin a gida?

    aikuwa take Ummi ta shiga taitayinta, sai b'ari jikinta keyi ganin fuskar Mum ba alamum rahama.Guri ya nunawa Ummi ta zauna ta jawo Mukh jikinta ta mak'ale shi tana jira taji yazata kaya dasu.

  Kusa da Mum Ammar yaje ya zauna, sanan yace mata" gafa wad'anda nake gaya maki nan na kad'e ya nuna su Ummi, nan Mum ta kallo su, sai Ummi tad'an rusuna kai ta gaida Mum, da k'yar Mum ta karba mata.Sanan ta juya ga Ammar tace" to me kakawo su suyi?

   marairaicewa yayi yace" 
Mum;

 basuda kowa mijinta ya rasu yan uwanshi sun kwashe komai sun koro su shine nace bari ko aiki ne sai  ki bata tunda naga Inna mai aiki tana bukatat taimako kinga sai su dingayi tare zatafi jin dad'i.

   Harar shi Mum tayi tace" baka isaba, ba aikinda zan d'auketa cikin gidanan. Dan haka tun wuri tasan inda dare ya mata.

    Take wasu k'walla suka zagaye fuskar Ummi, nan Mukh ya kalleta yace" Mumy lafiya kike kuka?
  rungume shi tayi tace" ba komai Mukh idona ke ciwo, Sai lokacin Ummi ta kalli Mum dake binsu da banzan kallo tace"
 Hajiya kidubi girman Allah ba danni ba, kodon wanan karamin yaro ki taimakami, wallahi duk aikinda kika bani inaso, Hajiya shi D'A NA KOWA NE, dan Allah ki taimakemu.

Hararta Mum tayi tace" Allah sikari sarkin zaki, aini basan D'A NA KOWA NE ba sabida ni d'ana kawai na sani dan shi nakecin amfanin shi.

 Dan haka nace bazan taimaka ba kifita tun kamin ranki ya b'aci kibarmin gida na.

    Ammar kamar zaiyi kuka ya dinga lallashin Mum, da k'yar ya shawo kanta, ta yarda, kallon Ummi tayi tace"

 kunci albarkacin d'ana da wallahi ke baki isa ki zaunamin gida ba, sabida daga ganinki ke munafuka ce wama yasan abinda kikayiwa wad'anda suka koroki d'in.
   Saida Mim tacima Ummi mutunci tass sanan ta bata aiki, g'yaran falo da d'akin Ammar, da taya Inna girki, aikuwa Inna taji dadi sosai dan aikin yamata yawa, Ummi sai godiya take amma Mum ko kallonta batayi ba.

   D' akin Inna aka sauke su kasancewar shi babba kuma gado biyu ne cikin shi da wadrobe ga mirrow, sai ban d'aki, nan Ummi ta ajiye yar jakarta da taketa fama dashi tayi zaune tana nazarin wace irin rayuwa kuma zasuyi anan?
 Allah kad'ai ya sani.


       BY BEBEELO

SADAUKARWA GA UMMI A'ISHA.
[22/12 7:33 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
D'A NA KOWA NE 👭👭
🌿🌿

    ©BEBEELO ( MUM IMAN)

                 (30~35)
                **********

~ A hankali ta bud'e indonta wanda ya mata nauyi sosai, dishi- dishi ta fara gani irin na mutum yayi bacci mai nauyi.

     kamin daga baya taji idanun nata garau.Aikuwa da k'arfi ta mik'e tsaye tana salati jikinta sai kak'karyawa yake sakamakon abinda tagani.

    Ba komai ba ne illah mutane ne tarshe maza da mata yara da manya.
 Ko wannensu zaune cikin jajayen kaya sunyi zaune shuru ba mai magana, ko wannensu da uban tambarin lamba a goshin shi.Cikin firgici da tsoro ta ja k'afarta da k'yar, 

wani d'aki ne kusa da d'akinda suke ciki k'ofar tana a kare, a hankali ta taka gurin ta lek'a, da saurinta ta shek'o ta zube k'asa tana k'wallah sai yanzu ta gane inda take. 

  Ba komai ta gabi ba 'illah yadda ake yanka mutane ana kad'awa cikin wani guri yana dad'datsawa, nan ta k'ara bin mutanen d'akin da kallo suma ita suke kallo amma basa magana, da sauri ta isa gurin wata mace mai tshon ciki tana jijjigata tace"

Boyar Allah dan Allah nan inane nan?
 waya kawo ku nan, kuma me kukayi?

shuru bata bata amsa ba, hakan yasa taje gurin ta kusa da ita, tana tambayarta itama shuru ta mata, ai sai Ummi ta fashe da kuka dubanta takai d'ayan gefen take nunfashinta ya nemi d'aukewa, da gudunta ta je gurin ta tallafo shi ta rungume jikinta tana jijjiga shi tare da kiran sunan shi

   " Mukh!!!"," Mukh!!"
dan Allah ka tashi, bud'e idon shi yayi yana ganin itace ya k'ara mannewa jikinta yana k'yarma

   d'agosho tayi tace
   " menene?

Yana k'walla yace 
"Mumy kinyi bacci kin barni inata tada ke, cox mutanen na zaune tsoratani suke banason kallon su, sashi jikinta tayi tana shafar kanshi, addu'a tashiga jerowa tareda tofe masu ajikin su, sanan ta zubarda wasu k'walla masu zafi da wahala.

   A Fili ta furta, wanan shine kalar kaddarada Allah ya rubutomin, kuma nayi imani ya Ubangiji, amma ina rok'onka Allah ka taimaki wanan yaron ba danni ba, ba don halina ba, kai kace duk bawanda ya kiraka da wanan sunan yana mai imani dakai da manzonka Annabinmu, masoyinmu Muhammad (S.A.W), to zaka ce ya rok'a kawai an karba.

   dan haka "YA RABBI, YA RABBI, YA RABBI."
  gani gabanka a matsayina na baiwarka,
 yar bawanka, 
yar baiwarka.

 Ina mai k'ask'antarda kaina, kaji tausayin wanan yaron ka tseratarda shi, saboda yana buk'atar tsawon rayuwa, tana gama fad"ar haka ta fashe da wani irn kuka, amma sam bakinta bai fasa furta addu'a ba.
         

                        ***
    Amma kayi k'ok'ari sosai, jalo. Saboda wanan shekarar kafi kawo harka, dariya Jalo yayi yace
   " kuma ba shan wahala, ina kan hanya kawai sai gasu, dan haka yanzu aje kawai azo dasu bama sai anyi kiyo ba, dan k'oshe suke.
    Haka kam inji sauran yan k'ungiyar su, wani bakin k'ato mummuna aka umarta dayaje yazo dasu Ummi, yana sauri harda tuntube ya je dan zowa dasu.


                        ***
Mutane sai shigowa ake ana karban gaisuwa, kowa yazo ya fita sai Mum ta bashi tausayi saboda ta dawo kaman zautatta, sai sambatu take, Alajin Ammar ma ne ya d'anyi k'arfin hali yana lallashinta.
   Alaji gaskiya wanan yarinyar batayi halacci ba, kuma ya kamata a d'auki mataki, dan tasan ba dan tsana ta kashe ba, d'an mutum ne kuma d'an masu fad'a aji.
Wani raunannen ajiyar zuciya Alajin Ammar yayi bayan nazari da yayi akan maganarda amininshi Alaji Tukar keyi.

   Nisawa yayi sanan ya furta
   " Alaji Tukur ai tuni na kai report a ofishin manyan yan sanda dake garin Abuja, kuma sun tabbata min akan sun ma fara bincike akan wanan case d'in, sanan na gaya masu ko nawa ne zanbiya koda abinda na mallaka ne ga baki d'aya, zan bayar matuk'ar za'a kamata ayimata hukunci dai dai yadda tayi, koda hankalin matata zai kwanta.

Ajiyar zuciya Alaji Tukur yayi
 " to Allah yasa a dace, ku kuma Allah ya baku 'ikon dangana, ku yawaita mashi addu'a kawai.

"Ameen kawai ya fito daga bakin Alajin Ammar saboda Alhini da yakecikin shi na rashin tilon d'an shi Ammar.


                         ***
    Amma wallahi danasan haka zaku min wanan a'ika a'ikar da ba abinda zaisa na sakaku wanan a'ikin,
haba Oga rodu, ko kasan da rayukanmu ne kuke wasa, muddin wanan al'amarin ya fita to asirina da naku yagama tonuwa, kuma kunsan ba k'yalemu za'ayi ba, haba! haba! mstewwwwe!!!!!

  Duk wanan sambatun da Alaji Muji keyi Oga rodu bai tanka ba, saida yagama, lokacinda Alaji Muji ya zube akan kujerar da ke falon shi yana maida nunfashi, sanan Oga rodu ya zaro bindigar shi jikin shi na rawa kamar irin masu dambe nan a filin daga,

     " Alaji na rantse maka da sarkinda ke busan numfashi yanzu ba sanya a wanan lamari, saina kama su su duka na masu eh aha da wanan bindigar!!!!
  Waima dan wulak'anci ni Oga rodu za'a rainawa da hankali Allah dan uwarsu saina hukunta su.
sai lokacin Alaji Muji yayi dariya sanan ya juya kallon shi ga Oga rodu daketa sambatu yace
   "Yawwa mutumina mai zuba rodun alburushi ga mai k'arar'ren kwana.

 Allah yasa yau kwanansu ya ka're hannun shi ya d'ora a wuya yayi murmushin keta, sai kawai ka masu haka, dariya suka bushe da ita, kamin Oga rodu ya kwankwad'i k'wayoyin shi yabar gidan yana mashalo kamar wani sabon kamu.


                      ***
Bama yaron kad'ai ba inaga harke Allah zai k'wata, da sauri ta juyo dan taji mai magana, wani d'an saurayi tagani tsaye bakin kofarda suke ciki, da sauri ta mike tace
" Malam kai kanajin abinda nake fad'a ne," kai ya gyad'a mata alamar ehhh.
   Hannu ta d'aga sama tace

    "Alhamdulliahi Allah na gode maka.

  Bawan Allah meya sa..........

katseta yayi ya jawo hannunta yace
   " Bamuda lokacin magana kizo kawai na fitardaku wanan gidan keda yaronki.Juyowa tayi ta kalli mutanenda ke zaune, sanan ta kalle shi tace

" Bamu kad'ai ke neman taimako ba ga wasu nan, d'an murmushin haushi yayi, sanan yace
   " kedai kizo kawai taimaka masu bayada amfani!!!!

akan me zakace haka?
  dan Allah suma ja taimaka masu.

   Ba zaki gane ba wad'anan da kika gani, anriga angama tsafesu, duk yadda kikayi bazasu d'aga daga inda aka kafesu ba.
 Ke bama zasuyi maki magana ba idan kuwa kin shekara d'ari gurinan kina masu magana, saboda mugun tsafinda aka masu, kema dai dan Allah yasa sunaso suyi amfani daku da wuri ne shiyasa basu maku haka ba, saboda Allah ya k'addari zaku kub'uta.
    Ummi na kuka ta kalli mutanane zaune abinsu sun kafe ido guri d'aya, take taji wani sabon kuka yazo mata, saurin hanata saurayin, yayi yajata suka dinga rusar gudu kamar ransu zai fita.

         
                       ***
   Wayam yaga d'akin basu ba labarin su, da saurin shi ya koma ya gayawa su Alaji Jalo, aikuwa suma da gudunsu suka yi d'akin amma basu Ummi.Da sauri Jalo yace
  " ayi maza a kad'a k'araurawa, abin mamaki mummunan mutumin na zuwa yaga anyi barna ga k'araurawar bata kad'awa, haka ya dawo ya gaya masu, shuru Jalo yayi yace
  " babu shakka wanan gagaren ne da muka kwaso ya fitarda su", dan haka kaje ka shaidawa dakarun gidnana su bazama nemansu duk inda suka shiga, haka kuwa akayi, da saurin su suka fita.

   Duk irin nisanda gidan keda tsakanin shi da gate d'in gidan sai gashi su Ummi sun isa cikin k'ank'anin lokaci da ikon Allah, addu'a kam bata fasa ba, gurinda ake ajiye motoci, yaje ya d'auko d'aya, ya b'allata ha had'a wayoyi, sanan ya samu wani k'aton gatari dan gidan gatari banza yake, yace Ummi ta shiga mota, ta shige itada Mukh ta kankameshi jikinta sai b'ari suke.
    
   A hankali yaje daga bayan mai kula da gate d'in ya mashi rusau da gatarin a kai, saida Ummi ta runtse idonta jini sai b'ass b'ass yake, amma shi ko ajikin shi makulle ya cire jikin mai gadin, ya bud'e wangamemen kwad'on da ke lak'e jikin wangamemen gate d'in da k'yar ya bude shi,danma yana cikakken mai k'arfi ne kamar Dadyn Iman, da bazai iya bud'eshi ba lol.

        Mukh dake jikin Ummi da sauri ya saketa ya fita motar da gudu, tana kiranshi hankalinta tashe,
 dai dai saurayin ya shigo motar, kuma suma mutanen da aka turo sun kusa isowa, Ummi na ihu itama ta fita tabi bayan Mukh dake gudu.

    Duk kiranda saurayin ke mata batako waiwaya ba, Mukh kuwa sai gashi ya d'auko jaka, ya mikawa Ummi girgiza ahi tayi tace
" Mukh akan wanan banzar jakar tawa zaka halakamu, nan saurayin ya samesu da motar suka shiga Ummi na kuka tana juyo bayan su saboda har lokacin mutanen na biye dasu suma cikin motocin su.
   Ta kalli mutumin ta kalli motar mutanen, amma sai taga sun basu tazara sosai, saboda shima ya iya sarrafa mota domin kuwa harma yafi Ammar iya sarrafa mota.

   Ba k'aramar tafiya sukayi ba, sanan suka shigo gari, ganin sun iso gari dole wad'ancan suka koma.
 Hamdala Ummi tayi ta kalli Mukh da yayi bacci kamin ta maida kallonta ga wanan bawan Allah da yayi rawar gani ya Allah ya bashi 'iko ya taimaki rayuwarsu.

     Kallonshi tayi da k'yau, k'yakk"yawa ne na k'arshe, kuma karamin yaro, saboda a yadda ta canko bama zai girmeta ba koda ya girmeta da kad'an ne, amma girman jiki zaisa kace babba ne, saboda irin jikin nan ne na cikakkun maza, masu kirar k'arfi, jikin shi yana kama da d'an wasan dambenan da ake kira Muhammad Ali.

    Nisawa tayi sanan tace
  " Mungode sosai da taimakonda ka mana, bai kalli inda take ba yace
" yiwa kaine ai"

"Amma bawan Allah dan me ka taimakemu?
 kuma kai waye?
 ko kaima tsafin kake, kawai kaji tausayinmu ne?"

   sai lokacin ya kalleta, dan guntun murmushi yayi, sanan yace
"Ni ko a film ban taba ganin yadda ake mafia ba, cox ban taba kallaba.Nima kawoni akayi yadda aka kawo ku, daga taimako dana masu suka kawoni nan, nayi kwana biyu gurin tsaurin kaina da yadda da Ubangijina yasa harna fito yanzu.
Ba irin tsafinda basumin ba amma akan ni kullum shafe nake da addu'a sai yasa tsafinsu ya kasa tasiri akaina, sun so su kasheni ta hanyar takobi, amma k'arfinsu bai kai can ba, saboda nayi koyon sarrafa takobi a k'asar Chaina, a wani makaranta da ake kira kungfu,
kuma sai Allah ya tsareni da tsarewarsa. D'an zamanda nayi yasa na fahimci komai na gidan, na zaga ko'ina gidan duk  da kuwa fad'in shi da kike gani. 

 A  duk lokacinda wani ya nemi ya gudu daga gidan, ko wani babban al'amari ya faru wanan kararurawar da kike gani ita suke kad'awa, take zakiga mazaje sun bayyana, ta kowane sako.

    Shiyasa kikga na cireta, Kema addu'ar da kika fakene yasa ina zagawa sai kawai naji harna iso inda kuke, saboda dama nayi alk'awarin ba zanbar gidan ba saida wasu idan ankawo zan taimakesu mu tsira tare, kinji yadda akayi.

   kai Ummi ta girgiza tace
" lallai kacika jarumi, to amma waima nan inane?
 saboda naga kalar mutanen kamar ba hausawa ba.Murmushi yayi yace
"idan dai kinsan Delta state to nan ne k'asar bata hausawa ba ce, kud'in mota a kalla zaki kashe dubu goma kamin kizo.

  da k'arfi Ummi ta zaburo, tace 
  "na shiga uku ni Ummi yanzu daga shigarmu motarshi har muka zo nan ban sani ba, lalle wanan yakai shaharren matsafi.
Murmushi kawai yayi batare da ya tankata ba.

Shuru ya biyo baya, sai tafiya suke har suka isa wani d'an madaidaicin gida mai k'yau, akwai tsaro sosai a gidan.
 Ummi sai kalle kalle take, fitowa yayi daga motar tana biye dashi, da d'an alamun tsoro a fuskarta tace

" ina ne nan?
fuskarshi ba walwala yace "gidanmu, ne kizo kuhuta kamin kifad'a min adress na gidanki sai na kaiku. idan kuwa kinada wanda kika sani anan garin kina iya tafiya sai anjima. 

Yana fad'ar haka ya shige gate d'in, aikuwa da gudunta tabi bayan shi Mukh na a kafad'arta ta saba shi, sai baccin wahala yake.

 y'ar tafiya mai nisa ce kamin su isa falon gidan, nan Ummi ta samu damar tambayarshi sunanshi, duk da ta fahimci ba mutum ne maison magana ba, amma bata fasa tambayar shi ba
  da k'yar yace mata 
"ki kirani da Barrister kawai.

   To ni Bebeelo kardai Barrister Umar ne😳


            
               BY BEBEELO

SADAUKARWA GA UMMI A'ISHA.
[22/12 7:34 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
D'A NA KOWA NE 👭👭
🌿🌿

       ©BEBEELO

                   (40~45)
                  **********

~ Kai tsaye aka wuce da Ummi babban Offishin y'an sanda dake Abuja, kamin aka kira Alajin Ammar aka shaida mashi an samu cafke Ummi tana nan hannu.Murna kawai suke shida Mum, wacce har lokacin tana cikin alhini.

       Haka shima Barr ya shirya yaje can ofishin, nan aka bashi report akan Ummi kisa tayi, yayi mamaki matuk'a to ya za'ayi ace tayi kisa kai........
ba gaskiya ba ne.Neman ganinta yayi, da k'yar aka bashi minti biyar yayi magana da ita.

 Nan aka umarci azo da Ummi, duk da Barr bai cika kallon Ummi ba bama zaice ga ainihin kamminta ba, amma daya ganta yasan ta fita kammaninta sosai, tasha azaba sosai cikin kwana d'aya.

Su kad'ai ne a d'akin dake d'auke da table sai kujeru guda biyu, tun zaman Ummi kuka take kuma Barr bai hanata ba.
Saida ya kwatanci tana cimasu time gashi ba shi, dole ya daure fuska yace

  " banzo dan ki sakani gaba kina kuka ba, nazo naji wasu bayanai daga bakinki, 
duk gaskiyarki da kika sani ki tabbata kin gayamin, karki yarda ki boye wani abu, ko kiyimin k'arya.
   Saboda gobe za'a shiga court da case dinki.Nisawa Ummi tayi sanan ta sake wani d'an murmushi wanda za'a iya kira dana takaici,

    " ina Mukh d'ina" da Ma;

C'ikin mamaki Barr ya kalleta, sanan ya basar, kanshi kasa yace"

bashi na tambayeki ba, Mukh yana gida gurin Ma; sanan tun jiya yak'i yaci abinci.

 Bayan sunanki ba abinda yake kira, Ma; kanta tak'i walwala, so kinga yaxama dole ki bani had'in kai dan sanin mafita, saboda bana son wani abu yasamu Mukh da mahaifiyata.

     karo na biyu kenan da tayi murmushi, kamin d'an k'aramin bakinta ya furta

" ta yaya zan ce bani na kashe shi ba, sanan a yarda? 

ta fad'i haka tana mai k'urawa
 Barr ido,
   nasan bama za'a taba yarda akan bani na kashe Ammar ba, saboda ni aka kama dumu dumu.
  
Dan haka ka daina wahalda kanka kawai, Mukh kuwa da Ma; ka lallabasu harsu manta dani saboda nasan ni nawa yazo k'arshe za'a kasheni kamar yadda na kashe...!!

     A fusace Barr ya mik'e, saboda tuni Ummi ta suk'a shi, 
a wulak'ance ya kalleta sanan yace
" Good zanyi k'ok'ari su manta dake, dan dama bazanso su zauna da makashiya ba!!

idanunta fal da k"walla ta kalleshi, taji zafin maganar shi sosai, kai ya g'yada mata alamar He mean it,
 girgiza kanta tayi ta mik'e itama sanan ta furta

" Naji ni makashiya ce, kuma dama bance maka ba haka nake ba. sai dai inaso ka sani......Officer ne ya katse su da time is off, 
cikin bak'in ciki Barr ya kama hanyar fita, 
inda shi kuma Officer  ya tasa k'eyar Ummi gaba, dan maidata a cell.

   C'an Barr ya tsinkayo muryar Ummi

" ka taimakamin kaje K'auyen Saran-dosa, ka nemi gidan Malam Bukar 

ka nemi mahaifiyata ka gaya mata halinda nake ciki, 

tazo mu gana kamin na mutu, wanan shi.... 
baiji sauran zancen nata ba saboda an shige da ita.A fusace ya fita ya fad'a motar shi, yana tunanin mafita.
 Shikam wanan wace irin matace?

 da anaso a taimaka mata tana dojewa, to kodai ita d'in ne ta kashe shi....
saurin katse tunanin shi yayi da no it can be possible, ba zata iya kisa ba.

     Kanshi ya d'auki caji sanadiyar hango Alaji Muji da wani d'an sanda sun fito Office d'in commisioner, 
aikuwa da sauri ya noce kanshi ya figi motar shi da sauri ya bar station d'in.


                       ***
"Barrister!!
yanzu yak'i naka ne, 
yazama dole ka taimaki wanan matar, cox kaima ta taimaka maka.
  " tsuki yaja sanan yace bazaka gane ba Ahmad yarinyar akwaita da taurin kai, 
bafa yadda banyi ba naji gaskiyar lamari amma tak'i ta bani had'in kai.

   Nayi amfani da dabara irin tamu, har nake kiranta da makashiya koda zataji haushi ta gayamin, 
amma sam tak'i duk da taji haushi, amma sabida taurin kai tak'i tayimin bayani.

   Murmushi Ahmad yayi sanan yace
" kadai dage tunda har kaga Alaji Muji da Commisioner to kasan akwai wani tuggu da zasu k'ulla....
 kuma inaga basu san kanan ba dan haka ka iya takunka, kasan kuma plan d'inda zakayi.

   Tabbas hakane, yanzu na yanke hukunci zanje can k'auyen su,
 na gayawa mahaifiyar tata.

   sanan plan d'ina shine: sai k'arshen shari'ar zan bayyana a matsayin lauyer mai kareta.
 Saidai kullum zan kasance acikin court d'in kuma ba tare da sun san koni waye ba.

 zanci gaba da bincike na, cox banaso su san inanan a raye.
matsalana d'aya tak!!!

  " meye?
 inji Barr Ahmad

" Mukh da baya cikin hayyacin shi, kasan shi kanshi zai tai maka mana sosai, 
amma yanzu sam baya tuna komai.
    Nisawa Ahmad yayi yace" karka damu akwai wani abokina Dr ne
 na k'wak'walwa zan had'aku dan ayi treating Mukh insha'allahu za'a dace.

   " Tanks Ahmad, ka nuna kai masoyina ne nagode sosai

" yiwa kaine inji Ahmad"

bari na tashi dan zanbi jirgi na isa Birnin kebbi, sallama sukayi sanan kowa ya kama gabanshi.


                       ***
C'ikin nutsuwa kowa ya shigo babban d'akin na shari'a, mutane ne cike tam, kowa ya nutsu ba'a k'ara nutsuwa ba saida A'lk'ali Usman ya shigo Alk'ali mai adalci.
mik'ewa jama'ar d'akin sukayi saida ya zauna sanan kowa ya zauna akayi tsit ana sauraro.

 Daga ciki kuwa harda Barr Umar wanda ya sauya kama, duk nacinka bazakace shine ba, sunan wani film Basaja😂.

      Babban table ne gaban na A'lk'ali wanda yake da kujerun Lauyoyi maza da mata, ko wannensu da littafi da biro gaban shi, 
  suna sanye da suit da bak'ar riga ta lauyoyi akan suit d'in.
   mik'ewa Registara yayi ya fara karanto abinda ke cikin littafin gaban shi.
          
        Lauyoyin suka mik'e d'aya bayan d'aya suna gabatarda kansu ga A'lk'ali.
 Na k'arshen shine Barrister Habib lauyan wad'anda ke k'ara.

A yau 13-2-2015, zamu saurari k'arar  tsakaminAlaji  Tijjani da Ummi.....
 akan kashe tilon d'an shi da Ummi tayi. Har wa yau kuma zamu saurari k'ara tsakanin Alaji Muji da Ummi akan zargin kashe k'anin shi Alaji Mistapha Nera, da kuma matarshi Haji Safiyya, da kuma yi gaba da dukiyar su, tareda halaka tilon d'ansu, Mukhatar.

   Registara na gana fad'ar haka ya zauna, nan A'lk'ali yayi g'yaran murya, sanna yace
" Ina Ummi A'isha?

Ummi dake tsaye y'an sanda biyu na bayanta take gabanta ya shiga dukan uku- uku, 
   "waye Alaji Musthapa kuma da matar shi, da d'ansu?
    Abinda take fad'a ra ranta kenan.
 tareda zubowar k'walla a idonta.

 C'ikin kanta aka kaita tayi tsaye, nan ta d'aga ido ta kalli A'lk'ali shima ita yake kallo, 

yana mamaki ace wanan itace ta aikata duk wad'anan abubuwan, "ba mamaki yace a ranshi, ita shari'a sab'anin hankali ce.

    Wani azababben kuka mai ciwo Ummi ta fashe dashi, wanda duk wanda ke cikin gurin ita yake sauraro.

Cikin kakkaurar murya A"lk'ali yace
" Ummi

ta d'ago kanta tace
" Na'am

cigaba yayi da cewa kin tab'a zuwa kotu?

kai ta girgiza tare da fad'ar
" aa
 wanan shine karo na farko dana taba shigowa ma Birni balle kotu.

Shuru A'lk'ali yayi kamin ya furta
" da kin tab'a zuwa kotu dana hukuntaki!!
saboda d'ora hannu da kikayi akan kanta, dan ba'a dorawa.
 Da sauri Ummi ta d'auke hannunta
   " tuba nake ya mai shari'a, hakan tace sanan,
 taci gaba da k'walla.

  Nan A'lk'ali yace "
"ko ina lauyan wacce ake k'ara?



                  BY BEBEELO

SADAUKARWA GA UMMI A'ISHA.
[22/12 7:35 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
D'A NA KOWA NE 👭👭
🌿🌿

    ©BEBEELO (MUM IMAN)

                (35~40)
              **********

~ "Barrister!!! Barrister!!!!."
       Shine abinda Ummi ke nanatawa a bakinta, kanta ta tambaya to menene ake nufi da Barrister kuma?

baki ta tabe taci gaba da tafiyarta, shima bai waigota ba har suka isa babban falon gidan.Diitijuwar da saurinta ta rungume shi, sam Ummi batayi mamaki ba dan tasaba da ganin wanan tsakanin Mum da Ammar, har abinci Mum ke bawa Ammar a baki.

     Murnar shi kasa b'oyuwa tayi har saida Ummi tayi mamaki, "dama ashe ya iya dariya haka, amma yake wani shan k'amshi, hmmm haka kawai tace a ranta.

       saida suka gama murnar ganin juna sanan matar tayi magana cikin harshen turanci wanda Ummi bata fahimta ba.
   murmushi yayi sanan yaci gaba da magana shima cikin harshen turanci, take matar ta k'araso gurin Ummi ta rungumeta tana dariya.

   Ajiyar zuciya Ummi tayi, itama sai ta maida mata da murmushi, dan taji dad'i da ba 'irin Mum d'in Ammar ce ba.Shidai kallon su kawai yake kamin ya sake magana da mahaifiyar tashi sanan ya bud'e wani d'aki daga cikin d'akunan ya shige.

    Matar Hannun Ummi taja, ta kaita wani d'aki, da hausarta da bata k'ware ba tace

" D'ana yamin bayanin akanki dan haka saiki zauna ki huta idan yaso sai a maidaki gidanki kinji.Tam kawai Ummi tace tareda godiya, sai lokacin matar ta kalli Mukh dake sab'e a kafad'ar Ummi tayi murmushi tace

    " yaronki mai k'yau dashi, itama Ummi murmushi tayi tace
  " kema kinada kyau Mum, wani irin dad'i taji Ummi ta kirata da Mum kasancewar batada d'iya mace a duniya, murmushi tayi tace
  " Nagode daugther na kuhuta kinji bari naje na kawo maku kaya da abinci, tam Ummi tace sanan matar ta fita tana cike da farinciki.Ajiyar zuciya Ummi tayi a filii tace
" inama haka Mum take......
 da munyi zama mai dadi, sai lokacin ta tuno da Ammar, take taji wasu k'walla na mata kwarara, ko ya ake ciki yanzu, itakam bataso Ammar ya mutu ba,
 ko banza ya taimaketa a rayuwa hud'ubar shaid'an ce kawai tayi tasiri akan shi. To ita yanzu ya za'ayi ta shaidawa duniya cewa ba ita ta kashe Ammar ba?

   Tana wanan tunanin matar ta dawo d'auke da tiren abinci, ganin Ummi cikin damuwa harda yan k'walla yasa ta zauna kusa da ita tana tambayarta lafiya?
    da k'yar Ummi ta share k'walla ta k'irk'iri murmushi tace
" ina tunanin ina zamuje ne daga nan.Cike da mamaki matar tace
" kamar yaya?
ina kike auren ne, ina mijinki?

   Labarinda ta bawa Ammar dai shine ta basu, take matar ta shiga tausayinta, mik'ewa tayi tace
   " karki damu gidanan ni kad'aice dama, dan haka na aminta dake,
 na yarda dake kiyi zamanki da d'anki har randa kikaso tafiya.

   Nikuma na maki alk'awari zakiji dad'in zama, kuma zan maki duk abinda uwa kema y'arta keda d'anki ai shi D'A NA KOWA NE. Dan haka ki daina kuka kinji ki saki jikinki.

   k'asa Ummi ta zube tana godiya, "ba komai matar tace,
    saida taga Ummi ta fara cin abinci sanan  ta fita.
A falon ta same shi zaune, nan take bashi labarinda Ummi ta bata, shima yaji tausayinta amma shi ba abiblnda ke gabanshi illah neman Mukh ko ina zai ganshi?


                        ***

    Ya yarda da shawarar mahaifiyar tashi wacce yake kira da:
Ma;
     
Akan za'a samo mai yiwa Ummi lesson, kasancewar batasan komai akan boko ba, sanan shima Mukh za'a saka shi school.
 Wai je kaga murna gurin Ummi kamar zatayi hauka.Komai shiya ma Mukh na school, amma har lokacin bai ganshi ba saidai kida zai shigo Mukh ya juya baya, kozai shige d'aki, so bai taba ganin fuskarshi ba.

                            ***
          Washe garinda Mukh zai fara zuwa school, Barr yayi tafiya zuwa Osun akan wani case, duk da jikin shi ba k'wari, haka ya fice ya tafi.
Shi har lokacin bai saka Ummi da d'anta a ido ba,

     cox ba damuwa dasu yayi ba, koda yanacikin gidan saidai ya shige d'aki yana plan d'in ganin Mukh, da yadda zai bullowa Alaji Muji.

        
                  ***
A kwana a tashi Ummi gidan su Barr har tayi wata uku, sosai takejin turanci, kuma ta fara fahimtar karatunda ake koya mata.
 haka shima Mukh, ga wani gogewa da tayi ta k'ara k'yau abinta, zaman jin dad'i suke 'ita da Mukh a gidan.
 Ma; komai ta samo su take kashewa, ji take sosai da Mukh.

   
                        ***
Ummi na kitchen tana had'a masu pounded yam da egusi soup, 
Ma da Mukh a falo suna honework d'inda aka bashi school. 

Kncoking sukaji, Ummi ce taje ta duba, d'aya daga cikin securities d'in gidan ne, bayan ya gaisa da Ummi ya bata takarda,  yace na Ma; ne.
Ta karba tazo ta mik'awa Ma;
   Cikin mamaki Ma tace
" waya kawo?

Ma; bani kawai wanan yayi bai gayamin waya kawo ba, okay Ma; tace
" jeki kawai, hannunta na rawa ta bud'e, ta soma karantawa da saurinta ta mik'e tana salati!!!

   Aikuwa Ummi data koma kitchen da saurinta ta dawo tana tamabayr Ma lafiya.
    " Na shiga uku Ummi Umar ne yayi had'ari, yanzu haka yana Asibitin abuja!!!

Subahanallahi Ummi tace
"garin yaya?

    " shibne ban saniba inji Ma.

Da sauri Ma tayi d'akinta ta fito kuma,
" Ummi ki shirya Mukh ki had'a mana kaya yanzu zamubi jirgi muje bama zan 'iya tafiyar mota ba, tam Ummi tace
" jikinta ba k'wari ta shirya kayansu dana Ma; aikuwa suka d'auki hanya, Ummi gabanta sai dukan uku- uku!! yake.


                         ***
   Sun iso Abuja lafiya, kuma Alhadulliahi sun samu jikin Barr da sauk'i har yasamu yayi bacci, nan Ma: da Ummi suka shiga godewa Allah.sallar isha'i sukayi kasancewar sai sunan akayi magariba kuma sunyi, sanan suka zauna sunacin abinci suna d'an tab'a hira, Mukh kuwa na kan kujera yana shan icecream.

    icecream d'in hannunshi ya d'iba a spoon ya azawa Umar dake bacci a baki, sai kallon shi yake kamar ya taba ganin shi tun ba yau ba. 

Umar jin sanyi a leb'enshi yasa ya bud'e idon shi tareda motswa, sai tozali yayi da Mukh, aikuwa cikin zafin nama ya mik'e yana fad'ar "Mukhtar!!!

   hakan da yace ya jawo hankalin su Ma; da Ummi, da sauri sukayo nan, Hamdala Barr yayi ya kama Mukh ya rungume yana k'wallah, Mukh ashe dama kanan da rai?
   ashe dama zan sake saka ka a idona, kai Allah na gode maka.

k'wallah Ummi ta fara, wani dad'i taji a ranta, kamin tace
" dama kasanshi ne?

sai lokacin Barr ya kallota, sanan yace, ke zan tambaya ina kika sameshi?
Nan ta kwashe komai ta gaya masu, hamdala Barr ya sakeyi, yace
    " Lallai kin cancanci a yabamaki, a jinjina maki, saboda ke kin nunawa duniya cewa D'A NA KOWA NE.
   mun gode maki sosai Allah ya biyaki,
" duk wanan halin da kika shiga ta sanadin shi ne?
   Ma; ce tayi wanan maganar, kai Ummi ta g'yada mata alamar ehh

  rungumeta Ma; tayi tace 
    "wallahi kincika y'ar halak, lallai sunanki yayi daidai da halinki UMMI A'ISHA, tabbas kin zama UMMI, dan ba kowa za'a samu mai 'irin wanan halin naki ba.

 Amma ba abinda zamuce sai Allah ya biyaki Ummi, tana murmushi tace
  " Ameen Ma;
 nagode Allah da yau na had'u da Uncle Umar, saboda wanan sunan kullum shine abinda ke bakin Mukh, so nasan kai kad'aine zan mika shi hannunka hankalina ya kwanta, kuma gaka Alhamdulillahi.
    Tana share k'wallah taci gaba da cewa dama nayi alk'awarin duk sanda na mik'a Mukh hannun y'an 'uwanshi zan koma gida, to sai gashi yanzu na samu wanan damar, amma ba halin na koma gida, yazama dole naje nakai kaina hannun yan sanda dake nema dan nasan yanzu haka.......!!!

    shuru tayi sanadiyar ganin yan sanda sun shigo ba zato cikin d'akin, hannayensu duk rik'e da bindiga sun saitawa Ummi, shugabansu ne ya furta

" UMMI A'ISHA!!!! your under arrest, komai kasa cewa Ummi tayi, Barr ne yayi k'arfin halin mikewa yace
  " kamar yaya Officer for what?

Ma; kam kuka ta fashe dashi, d'an sanda kuwa yasan Barr farin sani, nan yace
  kana iya sani idan mukaje court,  ya tura k'eyar Ummi gaba, da k'yar Ma ta b'anb'are Mukh daga jikin Ummi yana kuka yana kiran

 Mumyna!!! Mumyna!!!!
        karki tafi ki barni kinji.....!!!

    Runtse ido Ummi tayi, tana wasu k'walla masu zafi, batason kukan Mukh ko d'an.Har suka fito cikin asinitin, mutane sai kallonsu ake.Ummi kuwa ko kallonsu ta kasa k'walla kawai take tana takaici da mamaki wai yau itace haka,  
 Ma;
 ce ta shiga jijjiga Barr, Umar karfa ka bari suje da ita dan Allah, tana wani kuka ma tsuma zuciya, rungumesu yayi itada Mukh, yace

   " Ma; ba abinda zasu mata, yanzu zanje na nemi sallama, gurin Dr, zanje sai inda k'arfina yakare insha'allahu, da haka ya mik'e yayi office d'in Dr.

   Ummi kuwa a mota aka sakata, aka tafi da ita, murmushi kawai take tana tuna kalaman mahaifiyarta na karshe lokaccinda zata fito daga gidansu.

  " Ummi bazan hanaki tafiya ba, amma kisani bada yawuna ba, kuma kisani duk inda kikaje dai randa Allah ya k'addari zaki samu mijin aure, sanan ki samu!!!!!

wani 'irin kuka ta fashe dashi, tasan bakin mahaifiyarta ne Ke bibiyarta........



                BY BEBEELO

SADAUKARWA GA UMMI A'ISHA.
[22/12 7:37 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
D'A NA KOWA NE 👭👭
🌿🌿

    ©BEBEELO  (MUM IMAN)

                   (45-50)
                 **********

~ Shuru kakeji, ba wanda ya tanka.A'lk'ali maida kallonshi yayi ga Ummi wacce ke tsaye hankalinta a tashe, nazarinta yayi kamin daga baya yace

Ummi ko ina lauyer mai kareki?

Bakinta na rawa tace banida shi ya mai shari'a.Maida kallonshi yayi, ga d'unbin lauyoyin sanan yace "
"
ina lauyan masu k'ara?

 mik'ewa Barr Habib yayi, yad'an sunkuyarda kai tareda fad'ar

" gani ya mai sharia.

Hankali A'lk'ali ya tattara ya mayar kan Barr Habib,
ko kanada k'orafi akan wanan zargi da ake ma Ummi.....?

gyaran murya Barr Habib yayi, sanan yaci gaba da cewa, ya mai shari'a, babu shakka ko kokanto Ummi ita ta kashe d'a tilo ga Alaji  Tijjani ta dalilin buga mashi k'walba, wanda shine yayi sanadin rasa ranshi.

   Gaban Ummi sai dukan uku uku yake, kamar zai fito takeji, yan rubuce -rubuce A'lk'ali yayi sanan ya d'ago kanshi yana mai duban Barr Habib.

" Barrister ko zaka iya kawo shaidarka wacce zata tabbatarwa kotu da wanan zancen naka?

  Cikin zumudi Barr Habib yace "kwarai ya mai shari'a, inada k'wak'k'waran  shaida.
Zanso kotu ta bani dama na gabatarda shaidata ta farko.

     " Barrister kotu ta baka dama...

dan rusunawa yayi yace nagode ya mai shari'a, sanan ya karbo abu a leda hannun d'aya daga cikin y'an sandanda ke tsaye gefen shi.

   Budewa yayi ya fitarda k'walbar a leda, kamin ya 'dagata sama yace
" ya mai shari'a wanan itace k"walbarda Ummi tayi amfani da ita gurin bugawa Ammar, 
wanda binciken da likita yayi ya tabbatarda shatar hannun Ummi ce akai.

Nuni A'lk'ali yayiwa Registara daya karbo k'walbar, cikin azama ya mik'e ya karbo ya mik'awa A'lk'ali.
Duba kwalbar A'lk'ali yayi kamin yaci gaba da "yan rubuce rubucen shi, sanan ya bada k'walbar ga Registara.

    "Kotu zataso likitanda yayi bincike akan wanan k'walbar ya halatta a gaban ta.
Mi'kewa Dr Fareed yayi ya isa gaban kotu, ya d'an rusuna kanshi yace 

"gani ya mai sharia....

       g'yara zama A'lk'ali yayi sanan ya dubi Dr Fareed yace
"kaine likitanda yayi bincike akan shatan hannunda ke jikin wanan kwalbar?

   "Ehhh ya mai sharia nine.

" Kotu zataso kayi bayani bisa gaskiyar bincikenda kayi akan wanan k'walbar da kuma shatan hannunda ke kai.

    "Tabbas babu tantama shatan hannun Ummi shine ajikin k'walbar, kuma mun shaida haka saboda munyi bincike har asibiti uku, kuma duk abu d'aya suke nunawa shine shatan hannun Ummi,
takarda ya cire yace
" wanan shine sakamakon bincikenda mukayi komai yana jikin wanan takardar.

Registara ya karbi takardar ya mik'awa A'lk'ali ya kalla, yayi y'an rubuce -rubuce, sanan ya sake mik'awa Registara.

"Dr, zaka iya tafiya inji A'lk'ali,
"Nagode ya mai sharia,inji Dr.

Ko lauyan masu 'kara nada wani abu da zai sake cewa?

mik'ewa Brr Habib yayi yace 
"ehhh ya mai shari'a.

"zanso nayiwa Ummi wasu y'an tambayoyi, kallon shi A'lk'ali yayi tare da fad'ar Kotu ta baka dama

" nagode ya mai shari'a ,yace

zarcewa yayi gurin Ummi wacce bayan zarar ido ba abinda take, kafeta da ido yayi saida ta tsorata, kamin daga baya yace 

"Ummi

Na'am tace jikinta na rawa, ko zaki iya yiwa kotu bayanin meyasa kika kashe Ammar, kuma akan me?

 Jikinta na rawa  haka bakinta tace
" ba....bani ....ba niii, ban.....wallahi.......

    kasa ma maganar tayi ta fashe da kuka, murmushi Barr Habib yayi, sanan ya juya gaban Alkali yaci gaba da cewa

" ya mai shari'a, Ummi itace ta kashe Ammar, kuma tun daga wanan kamekamen zaisa a fuskanci batada gaskiya, Ammar yayi mata halacci sosai amma saita saka mashi da sharri.

  Akan wanan zanso Na kira Mahaifiyar shi mamacin dan ta bama kotu shaida akan haka.
  " kotu ta baka dama, inji Al'k'ali
mahaifiyar Mamacin ta zo gaban kotu...
  
tasowa Mum tayi jikinta sanyaye, ta iso gaban kotu, wani mugun kallo ta aikawa Ummi, take Ummi ta ida rikicewa,

 cigaba Barr Habib yayi da cewa, 
" kece Hajiya Saratu, mahaifiyar marigayi Ammar 

Ehhhh ta furta nice

"Hajiya ko zaki iya gayawa kotu gaskiyarda kika sani akan wanan zargi da kukewa Ummi akan kashe tilon d'anku?

K'walla ta share kamin tace


 Ba zargi bane Barrister, saboda abin ya faru ne ranar talata, 17-12-2014, ina kwance a falona naga shigar Ummi a d'akin Ammar, 
wanda g'yara ne ya kaita. Batafi minti goma da shiga ba na jiyo k'arar Ammar, 
hakan yasa nayi azama na nufin d'akin sai ganin Ummi nayi ta fito d'akin da gudunta duk a rikice.
 Banyi ta kanta ba nayi d'akin sai ganin Ammar nayi sheme k'asa baya nunfashi.
   k'arashe maganar tayi tana kuka, koda aka kaishi asibiti bayada rai kuma likitoci sun tabbata mana abu ne aka buga mashi wanda yayi sanadin lalata k'wak'walwar shi har yazama sanadin rasa rayuwar shi, tun lokacin Ummi ta gudu daga gidan ba ita ba labarinta har wata uku, aka samu cafketa a garin Delta.

" C'igaba Barr Habib yayi da cewa, ko zaki iya gayawa kotu dangantakarki da Ummi?

    "Tab'e baki Mum tayi, banida wani danganta tsakanina da ita, bayan taimakonta danayi.

   Ammar ne ya kawota, shima kad'eta yayi, ya kaita asibiti harta warke dama ba wani rauni taji ba sosai.
Bayan an sallamesu take gaya mashi cewa, mijinta ya rasu yabarta da d'a, kuma yan uwan mijin sun cinye gado sun korota, wanan kenan yasa naji tausayinta na d'auketa a mtsayin y'ar a'iki, cikin kuka Mum taci gaba da cewa

" Amma duk irin wanan taimakon da nawa Ummi baisa tagani ba saida ta kashemin yaro, Allah ya isa tsakanina dake.....

   kasa kuka ma  Ummi tayi lokacin, kuma tana so tayi kukan amma sam k'walla ya kasa fitowa idonta.
  Lallai kuka ma rahama ne,
Nan Akace Mum taje ta zauna.

       kallon Ummi Al'k'ali yayi yace
" ko kinada ja akan shaidarda aka bayar akanki?

   kai ta girgiza tace 
" banida ya mai shari'a.

Kai Barr Umar ya girgiza,  yana d'an guntun murmushi.
Yaji dad'in halarta da yayi, amma ta wani b'angaren Ummi haushi take bashi, na rashin bud'e baki tayi magana.

    Bayan A'lk'ali yayi y'an rubuce rubucen shi, ya 'dago yana mai fuskantar al'ummarda ke cikin kotu, duk sun nutsu suna saurare yace

" Kotu ta saurari shaida akan wanan shari'ar, kuma kotu ta gamsu da shaidar da aka bayar, akhan wacce ake zargi,

 kuma kotu ta gama sauraren wanan karar.
  kamin yanke hukunci kotu ta d'aga wanan shari'ar, har zuwa 20-2-2015,
inda kotu zata saurari k'arar Alaji Muji itama akan Ummi,
 sanan kotu ta bada dama da aci gaba da tsare wacce ake zargi a   cell, kuma ba tare da beli ba.
    Yana kai k'arshe ya buga gudumar shi ya mik'e, kowa kuma ya mike tareda fadar ko........tu!!!!

   wucewa akayi da Ummi, inda shima Barr Umar yayi gidan aminshi Ahmad.
" to yaya shariar?inji Ahmad

Kaidai bari Ahmad, shar'iar akwai k'alubale, amma idan muka shirya mata zamuyi nasara insha'allahu

zan nunawa Alaji Muji kuskuren shi, yayi wauta, dankuwa ya kawo kanshi mahalaka.

"wani abin mamaki Ahmad, kusa da Barr Umar Ahmad ya zauna yace meye?

d'an murmushi Umar yayi yace, wai Alaji Muji Ummi suka d'orawa Laifin kisan Abul Mukh, saboda sunganta batada galihu.

cikin mamaki Ahmad yace
" lallai kuwa Alaji Muji yacika azzalumi, yakuwa kamata yagane kuren shi.

"barni dashi, k'yalci Umar yayi yana murshi, yace

Allah ya kaimu 20 ga wata.... ranar tonon asirin azzalumai, ranarda zan k'watowa Ummi da Mukh y'ancin su insha'allahu.
  
 "Allah ya bada sa'a, inji Ahmad.

  " Ameen Barr yace sanan ya mik'e ya shiga band'aki ya sakewa kanshi shower, amma kuma sai fuskar Ummi ke mashi yawo, baki ya tab'e a ranshi yace
" duk tausayinta ne kesa ina ganin ta a idona.

    Nidai Bebeelo dariya nayi nace ehh mungane irin tausayin😜


               BY BEBEELO



SADAUKARWA GA UMMI A'ISHA.
[22/12 7:37 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
D'A NA KOWA NE
🌿🌿

©BEBEELO

                   (  60~65) 
                   **********

~    Kuka Ummi ta fashe dashi mai tsuma zuciyar mai sauraro, shuru Alkali yayi, shikam tunda yake shari'a ya jima baiga case irin wanan ba, sai can yace Ummi dan me yasa kika yarda da zarginda ake akanki?

    "kallon Alkali tayi ta share k'walla, sanan tace ya mai shari'a, saboda banida wata shaida, nasan Allah ba azzalumin kowa ne ba, matuk'ar inada gaskiya zai bayyana ta, sai gashi, na yarda da Allah nayi imani da shikad'ai ne zai fitardani ba bakina ba.Sanan kuma banason sake kasancewa da rayuwa saboda sunana ya riga ya b'aci, kuma nasan wanan bakin mahaifiyata ne akan rashin biyayya dana mata, nayi dana sani, nayi kuskure akan rashin d'aukar maganar mahaifiyata, ta lularar dani akan kar naje ko'ina da sunan neman mijin aure, amma sam ban saurareta ba, inaga shine Allah ya nunamin kuskurena ya jarabceni ta wanan hanyar, amma nayi farin ciki saboda nasan ubangijina na sona shiyasa ya nuna min kuskurena.

   "inaso nayi amfani da wanan damar na jawo hankalin sauran masu hali irin nawa akan iyayensu suji tsoron Allah sukuma bi magaranr iyayensu saboda sunga yadda nasha azabar rayuwa, wanda dak'yar Allah zai fitarda ni.

      kowa na gurin saida jikin shi ya mutu da zancen Ummi, wasu harda k'walla wasu kuwa kuka harda majina akan tausayi.

  "Nisawa Alkali yayi zaiyi magana, sai ji sukayi ance Mumyna Mukh ne da gudun shi ya shek'a ya rungume Ummi yana kuka itama Ummi kukan take tana shafar sumar kanshi, kamin ta d'ago shi tace My Mukh kagane ni yanzu, kallonta yayi yace

" kece Mumyna na biyu mana, ai naganeki kuma nagane Uncle d'ina danke gaya maki gashinan, yana had'a ido da Damisa ya fad'a jikin Ummi ya boye fuskarshi yana nuna Damisa yace Uncle sune suka kashe Dady nd Mumy suka biyoni nida new Mumy suma ka kashe su, banason ganin su....

  Rungume shi Ummi tayi tace "karka damu Mukh nan gureni da ake k'watarwa da duk mai gaskiya hakk'inshi, jan shi Barr Umar yayi yakai ya zaunar yana lalla bashi.

   G'yaran murya Alkali yayi ya fara karanto abinda ya sake rubutawa.

" Kotu ta saurari wanan k'arar, da kuma shaidu wad'anda kowa ya shaida nan ba kotu kad'ai ba, dan haka kotu ta ganecewa Alaji Muji shine mai hannu akan wanan kisar, dan haka kotu ta yanke mashi hukuncin d'aurin rai da rai, tareda mutanen shi, sanan kuto ta ci Alaji tarar nera dubu d'ari da zai ba Ummi na k'azafi daya mata, har wayau kuto ta umarci Alaji Muji bada tara naira dubu d'ari biyu ga Barr Umar na niyar kashe shi da yayi, tareda horo ma tsanani a gidan kaso.

    Haka zalika kotu taci Malam Yusuf  da Larai tarar Naira dubu d'ari d'ari, akan shaidar k'arya da suka bayar akan Ummi.

sanan kotu ta wanke Ummi tsaf akan zarginda ake mata, kuma ta sallameta, kuma kotu ta bada damar aje a tsige comisioner akawo shi kuto domin yanke 
mashi hukunci, sanan har wayau kotu ta bada dama akan aje a kamo sauran abokan barnar Damisa da mai ainkin gidan Mahaifin Ammar.

      Haka zalika kotu zatayi amfani da wanan damar tayi kira ga yara, akan jin maganar iyayensu,
lallai Allah mad'aukakin sarki  ya fad'a acikin Alqur'ani cewa iyaye a k'yautata masu kada a wulak'antasu,kada a gaya masu wata mummunar magana, saboda yarda Allah na tare da yardar iyaye.

   Bai kamata ace ana wulak'anta iyayeba, saboda bakinsu kamar lalle ne akan y'ay'ansu kamu yake da sauri, inaso y'ay'a su sani cewa duk lokacinda Iyaye sukayi fushi dasu to Allah ma yayi fushi dasu.
 Dan haka mu kula, mu duba, mu g'yara muji tsoron Allah, mubi iyayen mu muji maganarsu akan mu, saboda iyaye ba zasu saka mu akan turba marar amfani ba, dan haka KUKAN KURCIYA JAWABI NE, amma ga mai hankali, yana gama fad'ar haka ya mike tareda buga gudumar kowa ya mike akace ko.....,tu.

     Kama Alaji Muji akayi da sauran aka wuce dasu, inda Ummi take rungume da Mukh, ta fito tareda Barr Umar take yan jarida suka taresu ana masu tambayoyi, da k'yar suka samu sukabar kotun bayan Barr Umar sunyi masabaha da Barr Habib yana mashi murnar cinye shari'ar.


  A mota Barr Ahmad ya d'aukesu sai gidan shi, nan sukaci abinci suka huta suna jiran isowar Ma; wacce ta k'agu taga Ummi da Mukh. Ummi kam zaune tayi komai kasa ci tayi bayan kuka ba abinda take, Mukh mak'ale da ita yana share mata k'walla.
D'akin ya shigo yana mai k'are mata kallo, kamin yace

"bafa zakizo ki sakamu gaba kina mana kuka ba sai kace wacce akama wani abu,
rinannun idanunta ta d'ago ta kalleshi dasu, kala batace mashi, amma a ranta cewa tayi waishi wanan bashida tausayi ne?
 ko me yake tak'ama dashi ne?
 kamar wani babba yazo yana gaya min magana.

   Hannun Mukh yaja yace muje ka rakani nazo da Ma; ta iso kaji, da k'yar Mukh ya bishi, har sunakai bakin k'ofa ya juyo yace
" ki tabbata kin shirya cox da Ma; ta iso zamu wauce can k'auyenku domin hannanta ki ga mahaifiyarki, gobe kankajelinki ya sake fitarda ke neman miji, yana fadar haka ya fita abinshi....

iya suk'uwa Ummi ta suk'u da maganar shi, saita dake kawai, amma ta d'auki alwashin ramawa insha'allahu.





                   BY BEBEELO


SADAUKARWA GA UMMI A'ISHA.
[22/12 7:38 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
D'A NA KOWA NE
🌿🌿

   ©BEBEELO (MUM IMAN)

               (50~55)
               ********

~ Shirinshi yake cikin kwanciyar hankali, ranshi fari tass sai d'an murmushi yake.Karosawa Barr Ahmad yayi hannunshi d'auke da cup, shima murmushin yake, sai da kalli Barr Umar sanan yace

" sai wani farinciki kake yau.

Shima Barr Umar murmushi yayi, yace

ba dole ba, yau k'aryar Alaji Muji zata k'are da yardar Allah, wani file ya d'auko yana nunawa Barr Ahmad yace

" kaga wanan ga baki d'aya bincikena na ciki, sanan ina farin ciki da shaidu da nakeda su sosai, wad'anda zasu tabbatarwa da kotu gaskiyar abinda ke ciki.Murmushi Barr Ahmad yayi yace

" Allah shine abin godiya, kaga ga cofee d:inka saika hanzarta ka isa kuto din.Shima Barr Umar  murmushin yayi ya karbi cup din ya aza a baki, da sauri ya ajiye yana kallon Barr Ahmad, yace

"Haba man so kake na k'ona bakina, ka wani bani abu da zafi, cikin mamaki Barr Ahmad ya kalleshi ya shek'e da dariya yace

"Amma kai kam kacika k'orafi, idan ban bakaba kace kazo gidana na hanaka brekfast, wallahi matarka nada fama.....

tsuki yaja yace....

" kai mata suka dama, ni kam ba mace a tsarina dan banason raini, kawai na zauna mace na maidani kamar wani wawa tabbbb, wanan sai ku
     nan ma dariya Ahmad yayi yace
" muna zaune zanga mace na janka kamar rak'umi wallahi.

" God forbid wallahi, aini ban d'an iska ne ba, yana fad'ar haka ya ajiye cup d'in yace
" ni kaga tafiyana ma, haka yabar Barr Ahmad na k'wasar dariya.



                               ***
     Ya mai shari'a, duk wani shaidu sun tabbata cewa Ummi itace ta kashe, Alaji MustaphaNera da matar shi Hajiya Safiyya.

  Kallon shi Alk'ali yayi yace
" Barrister ko zaka iya bawa kuto k'wakk'warar shaida akan wanan?

     "Tabbas ya mai sharia, ina shaida, 

Ummi ta kasance mace wacce ta jima tana neman Mijin aure, da mamaki Ummi ta kalli Barr wanda a iya rayuwarta bata taba ganin shi ba, amma har yake fallaso tarihinta haka, 
to ina ya sani?

Nan Barr Habib yaci gaba da maganarshi, Hakan bai samu ba, saboda duk sa'ointa sunyi aure har sun haifi yaya, anan haka Mahaifin Ummi Malam Bukar ya rasu, sai Ummi ta samu damar yi, shagalinta a kauyen.Daga baya sai ta tattara ga baki daya tabar kauyen ta shiga duniya, Ummi kusan mamaki ne ya kusa kasheta na Barr irin sharrinds ake mata kiri kiri.

     Ya mai shari'a, Ummi ta had'u da Alaji Mustapha a wani gidan abinci inda ta dinga bibiyarshi akan tana sonshi, amma dayake shi mutum ne na kirki sai ya zama sam bai kulata ba, anan hakane Ummi ta shiga har gidanshi ta kashe shi shida matar shi, sanan ta yaudari Barr Umar wanda kowa yasan shi da aiki tukuru, kuma babban Barrister ne, ta hanyar saka mashi powder mai lalata ido, daga karshe ta harbe shi tayi gaba da dukiyar Alaji Mustapha kasancewar komai nashi na hannun Barrister Umar.

" Ya mai Shari'a Ummi bata tsaya nan ba saida, tayi gaba da d'a tilo ga Alaji Mustapha, wanda har yau ba'asan labarinshi ba.

    gyaran zama A'lk'ali yayi, sanan ya dubi Barr Habib, wanda yagama koro bayani hankalin shi kwance, yace

" Barrister kotu zataso shaida a zahirance, ba ta fatar baki ba.

Murmushi Barrrister Habib yayi yace, ya mai shari'a zanso kotu ta bani dama zan kira shaidata ta farko.

"kai A'lk'ali ya gyada yace
" kutu ta baka dama Barrister.

Mikewa yayi yacewa yan sandan a shigo da ita, dam dam gaban Ummi ya fadi ganin Baba Larai kishayar mahaifiyarta, harta tsaya gaban kotu Ummi na kallon ta tasan Allah kadai za fitarda ita kam....

     Gyaran murya Alkali yayi yace
" kotu zataso tasan sunaki da alkarki da wacce ake zargi.Hanakli kwance tace sunana Larai, ni abokiyar zaman mahaifiyar wacce ake zargi ce....

nazarinta Alkali yayi kamin yace
" kotu zataso ki fadi gaskiya abinda kika sani tsakani da Allah.

gyaran murya Baba Larai tayi sanan ta fara kwararo karya hankalinta kwance, tabbas komai akace zata iya, saboda Ummi ta kasance banba d'add'iyar yarinya, sam bata jin magana ko kadan, sanan tun tana yarinya idan tayi fada 
mazgar yara take sai an kwace su, sanan bakin cikinta ne ya kashe mahaifinta, saboda mugun halinta ya saka ma ta rasa mijin aure har yanzu da takeda shekara talatin da watanni sama.

          kai Alkali ya girgiza yace
"zaki iya tafiya  kotu taji bayanan ki, tana murmushi ta juya caraf suka hada ido da Ummi wacce fuskarta ke dauke da tambaoyi kala kala, sam lokacin zuciyarta tayi bala'in dakewa, tariga ta fawwalawa Allah lamuranta shine zai mata maganin komai.

    Ya, rubuce rubce Alkali yayi kamin yace, ko lauyan masu kara yanada wani shaida na gaba?

"cikin jin dadi da alamar samu, nasara Barr Habib yace ehhh ya mai shari'a, sake fita yayo ya shigo da wani mutum d'an dattijo dashi, nan yaci gaba da cewa ya mai sharia, wanan sunan shi Malam Yusuf, shine mai gadi a gidan Alaji Mustapha wato marigayi.
   kallonshi Barrister yace ko zaka iya gayawa kuto gaskiyar abinda ka sani?

gyaran murya yayi yace
" Da misalin karfe 10 na dare abin ya faru, nayi arwallah dan gabatarda shafa'i da wuturi, sai naji ana k'wank'wasa k'ofa, ban fara sallar ba sai naje na bud'e sai kawai naga mutane maza su uku, da mace daya, d'ayan daga cikin su ya saka wani sanda ya bugeni dashi daga lokacin ban san inda nake ba, saida karar bindiga ya farkarda ni.

ina farkawa sai gasu sun fito da gudu, saina koma nayi kamar na mutu, Mukhatar naga sun biyo da gudu inda wanan matar dake tsaye itace gaba tana a kamashi kar a bari ya gudu, 

     cikin mamaki Alkali yace ka tabbata itace, kara kallonta Malam Yusuf yayi yace
"tabbas wanan itace bazan taba mantawa ba, itace.

kai Alkaki ya girgiza, ya kalli Ummi wacce ke tsaye ta kafe ido yace
" Ummi
a hankali ta juyo ta kalli Alkali, nan yaci gaba da cewa

" kinji tun daga kara ta farko shaidarda aka bayar akanki, kai kawai ta gyada 
ashi, kuma kin yarda ko kinada ja...?

Bakinta na rawa tace banida jaa ya mai shari'a hakane, take duk wanda ke cikin kotun ya shiga jin jina kai ana mamaki, kai Alkali ya girgiza ya fuskanci mutanenda ke gurin ya fara karanto abinda ke cikin takardar shi.

      "Sakamakon shaidu da aka bayyanar a gaban kotu, da kuma ik'irari da wacce akae zargi tayi da bakinta, kotu ta yarda da zarginda ake ma Ummi akan cewa itace ta kashe rayuka guda biyar, wani irin murmushi Alaji Muji yayi najin dadi.

"Sabida haka kotu ta yanke hukunci akan Ummi kamar haka:

Da sauri ya mike yace
" yace inada ja ya mai sharia......

cikin mamaki Alkali ya kalleshi, da mutanenda ke gurin duk shi ake kallo amma sam sun kasa gane waye...

har ya isa gaban kotu, biro Alkali ya kife yace
" bawan Allah kai waye da zaka yiwa kotu katsalandam acikin al'amarinta?

d'an rusunawa Barr Umar yayi yace 
" sunana Barrister Umar!!!
lauya mai kare wacce ake zargi...
   Dam dam gaban Alaji muji yayi, da sauran wad'anda suka san Barr Umar,  shi shi kanshi Alkali yasan da Barr Umar kuma yayi mamaki,  shine zai kare Ummi bayan itace akace ta illata shi,lallai shari'a sabanin hankali.

" kuma nazo ne dan na tabbatarwa da kotu cewa duk shaidarda aka bayar ba gaskiya ba ne.Kai Alkali ya gyda yace
" kotu na saurarenka Barrister Umar.Murmushi yayi ya cire b'adda kama daya masu, aikuwa take aka shiga mamaki, kowa sai fad'ar albarkar bakin shi yake, su Alaji muji kuwa anyi mutuwar tsaye.

Kallon shi Barr Umar yayi, ya dalla mashi murmushi, sanan yaci gaba da magana cikin k'warewa da dabara ta c'ika'kkun lauyoyi.



              BY BEBEELO


SADAUKARWA GA UMMI A'ISHA.
[22/12 7:38 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
D'A NA KOWA NE
🌿🌿

©BEBEELO

                 (55~60)
                 *********

~ Ya mai shari'a Ummi ba itace ta kashe duka wad'anan rayukan ba, rayuwa uku ne aka rasa, amma sam Ummi batada hannu akan kisar....

   cikin mamaki kowa ke kallon Barr Umar, d'an farin glass d'inda ke a fuskar Alkali ya cire ya kife a table din gaban shi, ya kalle Barr Umar cike da mamaki yace

" Barr Umar kotu na buk'atar kayimata cikakken bayani akan wanan sark'akk'iyar.

d'an murmushi  Barr yayi, yace 

" ya mai shari'a nida ake zargin na mutu yanzu nasan kowa yasan gani da raina, kuma za'ayi mamaki ta yaya...

"Ummi batasan wanene Alaji Mustapha ba, hasalima Ummi wanan shine shigowarta na farko  a wanan garin, Ummi itace wacce ta ceci rayuwar Mukhatar d'an mamacinda ake zargin ta kashe, wanda yanzu haka yanan da ranshi, saidai matsalar k'wak'walwa daya samu wanda hakan ya faru ne sanadin azzalumai.

    wani kallo Alkali yabi  Barr dashi, kamin ya furta

"Barrisrer har yau baka warwarewa kuto kalamanka ba...

Tsaye Barr yayi cak gaban Alkali yace

        Ya mai shari'a Alaji Mustapha kamilin mutum ne, mai mutunci da tausayi kowa yasan da haka.Na kasance d'an kabilar Ighbo,  a jahar Delta, amma kuma mun tashi cikin musulunci,
kuma mahaifina ya rasu, daga ni sai mahaifiyata muke rayuwa cikin k'unci, har na kammala karatuna na secondry, amma sam na tsaya da karatun saboda babu kudinda zanci gaba, hakan yasa na dage da sana'ar hannu, har Allah ya hadani da Alaji Mustapha, ta sanadin yada jakar shi da yayi mai d'auke da mak'udan kudi.

    Banyi k'asa a guiwa ba na nemi address din shi na kai mashi, hakan yasa yaji dadi, ya nuna D'A NA KOWA NE,ya taimakeni ta hanyar samamin admission, a Usman D'anfodio dake jahar Sokoto, a bangaren Low.

       Dagewa nayi naci gaba da karatuna, kuma a gidan shi nake yana kula dani kamar d'an cikin shi, haka matar shi na kula dani sosai, ina shekara ta biyu aka haifi Mukhtar, wanda muka shaku dashi sosai, ssboda yaron hannu na ya tashi.
    A shekarana na uku, Alajin ya turani karutu a k'asar Chaina inda na samu kusan shekaru biyar a can, na samu cigaba sosai bayan dawowana, wanda lokacin inada shekaru talatin.

   Nayi case kusan goma wad'anda nine nayi nasara, na tara duk wani abu wanda d'a namiji ke fatan samu,duk ta sanadin Abul Mukh, saidai har lokacin na rasa dame zan sakawa Alaji akan halaccin da yamin, amma sam ban samu ba.Bayan dawowana ne na fuskanci Abul Mukh na cikin wani hali na damuwa, amma sam ya kasa gayawa kowa.

" ya mai shari'a A ranar  Laraba 1-12-2014, ina zaune a office dina, naga kiran shi da misalin tara na dare, ban jinkirta ba nayi azamar isa, a falon shi na same shi cikin damuwa, nan ya gayamin halinda yake ciki akan yayan shi Alaji Muji daya tasa shi gaba akan dukiyar shi, har yana neman halaka shi, shine ya tattara komai ya saka a file da sunan d'an shi tilo Mukhtar, ya damk'amin na rike amana dan gudun bacin rana.

    muna cikin wanan tattaunawar ne mukaji shigowar mutane, kamin nayi wani yunk'uri sun zuba min hoda mai lalata ido, sai karar bindiga naji yana tashi, ana haka ne naji ihun Mukhtar wanda har yazo kusa dani yana tabani, nan namik'a mashi wanan file din nace yabar gidan da sauri, da haka ya bar gidan, sukabishi wanda hakan ya bani dama lalubo wayana na samu na kira abokina Barr Ahmad yazo ya d'aukeni, ya kaini asibiti naci gaba da jinya.

    Fitar Mukh ba wanda yayi tozali dashi, sai Ummi itace ta taimaka mashi, ba irin halinda ba ta shiga ba ta sanadin shi, wanda sakamakon wahala da tsorata da yayai ya saka k'wak'walwar shi ta tabu.

    Saida yakai nan ya dire, take kowa ya maida hankakin shi yana sauraro, har Ummi da batasan da wanan labarin ba,

cigaba Barr Umar yayi da cewa, inada shaida guda biyu zuwa uku da su tabbatarwa da kuto gaskiyar abinda na fad'a.

Da sauri Barr Habib ya mike yace
" ya mai shari'a inaso kuto da tayi gaggawar watsa da wanan cin mutuncin da rainin wayo da Barr Umar ke mata...

   katseshi  Alkali yayi da Barrister Habib k'orafi bai karbu ba, nan ya kalli Barr Umar yace
" kuto tabaka damar gabatarda shaidun naka Barrister Umar.

  Murmushi Barr Umar yayi, yayi godiya, sanan ya mike yacewa yan sanda su shigo da shaidun shi, nan aka shigo da shi, dam dam gaban Alaji Muji ya fadi ganib Damisa d'aya daga cikin yaran Oga rodu, nan Barr yace mashi "ko zaka gayawa kotu sunanka?
cikin dasashiyar murya irin ta wahala yace sunana Damisa

   " menene alak'arka da wancan mutumin, cewa da Alaji Muji?

cikin muryar su irin ta yan ta'adda yace"

 shine wanda ke sakamu muna aikata laifuka, d'an murmushi Barr yayi yace kamar me?

  harar Barr yayi kamin yace kisa da shigo da miyagun makamai, take Alaji muji ya noke kai sai zufa ke karyo mashi, hula ya cire yana fifita.Murmushi yayi Barr yace ko zaka fad'awa kuto me kasani dan gane da mutuwar Alaji da matar shi, da kuma Ammar?

    cikin zafin nama, Barr Habib ya mike yace ya mai shari'a yakamata kuto ta gargadi Barr mai kare wacce ake zargi ya canza salon kalaman shi.

" Mur Alkali yasha yace
" Barr Habib har yanzu k'orafinaka bai k'arbu ba, kallon Barr Umar yayi yace kana iya ci gaba da tambayoyinka akan shi.Murmushi Barr Umar yayi yace na gode ya mai sharia,sanan yaci gaba da tambayar shi.

" Damisa kai muke sauraro inji Alkali.

Tabbas shine ya sakamu mu kashe Alajin da kai da kuma matarshi da d'an shi, saidai su kawai muka samu kashewa, bayan mun d'auka kai ka mutu sai mukabi yaron, inda wanan itace ta taimakama yaron har ya tsira, munyi iya k'okarinmu amma munkasa kashe su, akan wanan yarinyar data taimaka mashi. hakan yasa da mukasan gidanda take sai muka k'ulla da d'aya daga cikin masu aikin gidan yana kawo mana rahoto, nan muka samu labarin yaron gidan Ammar akwai shi da son mata.
 Shine muka samu Apple muka saka mashi k'wayoyi masu tada sha'awa sosai, sanan muka saka mashi guba wacce zatayi kisa ba tareda fitar jini ko kumfa ba, wacce daga k'wak'walwa take shiga ta lalata.

    Haka muka mik'a Apple din ga mai aikin gidan, wanda shine ke sawo fruits din gidan, shine ya saka cikin fruits din Ammar, wanda dayaci zaiji sha'awa sosai kuma bayan minti biyar zuwa goma guban zata kashe shi.Munyi haka ne dan kuwa munsan mafi sauki da Ammar zai samu shine Ummi dake kusa dashi, wacce idan har yaje mata har ya mutu iyayenshi bazasu barta ba, hakan zai saka mu lallabo mu samu Mukh dan zamuce mu yan uwan babanshi ne, kuma zamu d'orawa Ummi kisan Alaji Mustapha Nera, inda bayan haka ne mun sami abinda mukeso ne Barr yayi nasarar cafkeni, shida jami'an tsaro.

   yanakai k'arshe kowa ya saka salati, saida Alkali ya buga yar gudumarshi, sanan kowa yayi tsit.Wucewa akayi da Damisa, sanan Barr Umar ya mika wani disc aka saka, saiga Alaji Muji da Comisioner suna tattaunawa akan makircinda suke k'ullawa.

  saida aka gama kallo, aka kashe, nan Barr Umar yaci gaba da cewa, wanan disc din na sameshi ne ta hanyar d'aya daga cikin yan sanda wanda yake aiki tareda comisioner, shiya saka na'ura a office din comisioner ba tare da ya sani ba, sanan sunyi bincike sunje sun d'auko kishiyar mahaifiyar Ummi wacce kowa yasan Ummi ba kamarta a k'auyensu gurin kamun kai da mutunci, amma suka danne gaskiya suka fadi k'arya.

Da wanan nake rok'on kotu da tayi nazarin akan wadanan azzaluman ta fitar ma masu gaskiya da hakk'insu na gode ya mai sharia.





          BY BEBEELO


SADAUKARWA GA UMMI A'ISHA.
[22/12 7:38 pm] ‪+234 816 559 2090‬: *🌿🌿*
*D'A NA KOWA NE*
*🌿🌿*

   *©BEBEELO*

                 *(65~70)*
                 **********

~ Ummi samun kanta tayi cikin farin ciki daga lokacinda *Ma*ta iso gidan, juna suka rungume suna kuka, kamin daga baya *Ma* ta shiga yiwa Ummi godiya da lallashin tayi hakuri ta manta da komai daya faru ga rayuwarta.

    Bayan sun huta ne suka d'auki hanya kuma zuwa k'auyen su Ummi, tana farin ciki kam saida kuma wani bangare na zuciyarta tana tsoro, yadda zata koma gida, yadda yan k'auyensu zasu karbeta, da kuma yadda mahaifiyarta zata karbeta, take sai jikinta ya mutu.

                             ***
Lafiya suka isa k'auyen, Ummi saita kasa shiga gidansu, tsaye tayi tana kallon mutanen k'auyen wad'an suka bar abinda suke suna kallonta, wasu mata harta katanga ake leke, hmmm gulma ajali.
     *Ma* jawo hannun Ummi tayi tajata zuwa cikin gidan, inda Brr yayi tsaye bakin mota sai kallon banza yake bin Ummi dashi, cikin mota ya koma ya danna kida abinshi a ranshi sai fada yake da Ummi.

   Sallama *Ma* tayi hannunta na rike dana Ummi,  Ma sai dubin gidan take duk da tayi rayuwar talauci amma sam wasu sun fita talaucin, lallai Ummi nacikin wahala kam.Mahaifiyar Ummi ta fito da sauri tana amsa sallama, tsaye tayi cak ganin Ummi.....

itama Ummi ita take kallo kamin daga baya ta fashe da wani irin kuka, Ma ce ta shiga lallashinta, kamin daga baya ta gaisa da Umma, nan Umma ta kirkiro murmushi ta aikawa Ma take tace "
maraba ku shigo mana sannunku da zuwa, bari na dauko maku tabarma.
   Da saurin Umma ta d'auko tabarma ta shimfida, suka zauna ta d'auko d'aya daga cikin kwanonin iya tsufa yayi, amma kuma shine mai dan daman daga cikin kwanukan Umma.Fura ce ta zubo masu taji nono, k'auye kenan komai talaucinka baka rasa shan fura kam.

  Godiya Ma tayi ba wani k'yank'yami ta aza kwanon tana kwankwad'ar furarta, dama Umma gurin tsafta ba'a magana duk da batada arziki, amma tsafta kam sai kace malamar duba gari.

   Ummi lokaci lokaci take satar kallon Umma amma sam ta kasa gane a wane yanayi Umma take ciki.

    D'an murmusawa Ma tayi tace 'wanan furar ta kirbo sai kace kindirmo, har Ummi saida tayi dariya ba Umma kadai ba, nan Ma tace
" Ummi ki kaiwa Umar ragowar kar dadi ya wuce shi nan ma darawa Umma tayi, tace au tareda d'ana kuke aka bar shi a waje, bari na dobo mashi tashi daban mikewa Umma tayi ta samo kofi na silba ta saka mashi, ta dora marfi akai, Ummi da saurinta ta karba tana mai kallon fuskar Umma, amma har lokacin bata gane me Umma ke nufi ba, dan kuwa fara'a ce tsaf a fuskarta.

   Tayi mamakin ganin Ma da Umma sun sake har haka, kamar wad'anda suka san juna, to inama Umma tsan Umar?
ko sanda ta rokeshi ne yazo har ya saba da Ummanta?
  kenan Ummanta tasan halinda takeciki fushine kawai ya hana taje kotu?

da wadanan tunanin kawai harta isa, batamasan takai ba, tsaye tayi bakin k'ofar motar komai ta kasa cewa, yana zaune abinshi cikin mota, ya d'an kwantarda kai ya lumshe ido yana biyar wakarda ke tashi a motar shi, ta justien biebier luv ur self.Yaganta sarai amma saiya share da ita, ta jima tsaye kamin ta dan k'wank'wasa mashi, nan ya dago fuskar shi ya watsa mata harara, batasan sanda ta mayar mashi ba, ta mika mashi kofin furar ba tare da tace komai ba, kin karba yayi ya barta rike da kofin.

    wani irin haushi taji, take ta juya da niyar komawa cikin gida, ji tayi ya riko hanunta, take kofin furar ya masu kaca kaca daga ita har shi. Aikuwa wani irin haushi ya kulle Barr, a fusace yace kin cimma abinda kikeso saiki tafi,

 ko damuwa batayi ba ta furta kai ka jawa kanka so kar kaga laifina, ta juya ta tafi abinta, kamar ya daki kanshi yaji, me ma ya kaishi tabata yanzu ai sai ta mashi wani fassara, shikuma yayi haka ne dan karta koma da furar aga yayi wulakanci, gashi yanajin nauyin Umma, kai kawai ya gyada ya fito motar yayi cikin gidan duk rigar shi ta lalace.

   Tana shiga ta sami su Umma sai fira suke suna dariya, nan ta k'ara mamaki, a ranta tace kai wadanan sun saba ga dukkan alamu ba had'uwar yau ce ba.Ganinta hakanan Ma tace
" meye haka Ummi barin furar kikayi hala?
ehh tace bata rufe baki ba saiga sallamar Barr shima haka kaca kaca, Umma ce tace kardai a jikinka ta bare furar, dan satar kallonta yayi kamin yace ina wuni Umma?
"aa lafiya k"alau lauya, ya dawainiya kuma?
 angode Allah yasaka maka da kahairan, 
" ba komai Umma yiwa kaine, mikewa Umma tayi tace bari a samo maka ruwa ka wanke jikinka tunda ita batada hankali, da sauri Ummi ta mike tace

" bari na bashi, harga ran Ummi taji dadin ganin Ummanta ta kulata, sai taji wani sanyi a ranta.Da saurinta ta debo mashi ruwa suka koma gefe ta mika mashi, wani irin mugun kallo ya mata, kasa kasa dan kada su Umma suji yace, "kece kika bata min kaya so ke zaki zuba ruwan ki wanke, harar shi tayi, a ranta tace jimun wanan k'aramin yaron zai sakani aiki mtswww.

   Batasan tsukin harya fito fili ba, da sauri ya mata wani mugun kallo yace
" never repeat it, na tsani tsuki so karki sake min, harar shi tayi, kamin tace
" kai asuwa da zaka hanani nayi abinda nakeso?

    kallonta kawai yayi baice komai ba, tana zuba mashi ruwan yana wankewa, kallonsu kawai Ma keyi tana d'an murshi, maida dubanta tayi ga Umma tace
" kinga abinda nake gaya maki ko?

Murmushi Umma tayi, tace 
" Hajiya na gaya maki banida matsala kawai a tuntube su aji, Ma murmushi tayi itama tace
" zama su amince insha'allahu.

isowa sukayi gurin, suka zauna, nan Umma ta zubo mashi wani fura, yasha abin shi ba wani kunya, cox shi wayayyen mutum ne.Gyaran murya Ma tayi kamin ta kira Ummi, aikuwa Ummi hankalinta ta tattara ta bawa Ma.

" Ga mahaifiyarki nan, tun zuwanmu na farko da Umar muka nema maki gafara gunta, kuma ta yafe maki, kawai dai tace bazata iya zuwa kotu ne ba, da zaki ganta.Dan haka saiki sake rok'onta gafara.Sai magana ta gaba munyi shawara da ita kan zamu had'aki aure da Umar......!!

   Daga ita har Umar din kallon juna suke, duk hankalin su a tashe, sam Umar baisan da wanan zancen ba."Ku muke saurare inji Ma kun amince.

Umar sam bazai iya tsallake maganar mahaifiyar shi ba, to sai yace 
mata bazaiyi ba?
"aa bazanyi haka ba.
Amma kuma Ummi bata daga cikin tsarin matanda yakeso, shi yafison K'aramar yarinya kamar yadda Ma'aruf ya auri Bintu,
 amma Ummi kam ai ta mashi girma shekarun su d'ayafa haba, dan me Ma tayi mashi haka? hasalima shi haushin Ummi yakeji ya rasa dalili.

    Ummi kuwa wasu k'walla take, duk da sanadin neman aure ya sakata wanan halin, kuma tanaso tayi auren, baisa tayi farinciki da wanan hadin ba. Kallon Ummanta tayi wacce itama Umman kallon Ummi take, a ranta tace
 "duk da banason Barr bazan iya sake bijire Umarnni Ummana ba cox bansan yanzu me zai sake samuna ba.

karo na biyu da Ma ta sake watso masu tambaya, da k'yar Umar yace 
"Ma ba abinda zakice nayi na rasa yinshi, matuk'ar bai kauce hanyar islama ba.Dan haka na amince wanan daice ban sanama ba kila ita bataso kingatana famar kuka. 

Da gayya yace mata haka, itama a suke ta kalle shi, take tace"
au saboda ni ce marar d'a ko, to nima bazan tsallake umarnin iyayena ba kamar yadda kaima bazaka tsallake ba, tana fad'ar haka ta fada jikin Ummanta tana kuka, Ummana na amince nidai kawai ki yafeni, naga jarabar rayuwa, naga k'unci duk a sanadin rashin yimaki biyayya, saboda haka yanzu bazan sake aikata haka a gareki ba, kiyi duk yadda kikaga dama dani kinada iko, a kaina
 bazan bijire maki ba.

  Itama Umma na k'walla, ta rungume Ummi
" Ummi dama banyi maki baki ba wallahi, kuma bana fata naga ranarda bakina zai furta mummunan furuci akanki, jarabawar rayuwace kawai kikagani, dama Allah ya k'addaro haka, dan haka nayafemaki wallahi na yafemaki,kuma naji dadin amincewa da kikayi,Allah yayi maki albarka.Wani irin dadi Ummi taji nan ta k'ara shigewa jikin Umman nata.

      

              *BY BEBEELO*



          *🌿🌿*
*D'A NA KOWA NE*
           *🌿🌿*
           
*©BEBEELO*
                    *75~80*
                    *********
  
Alhamdulillahi Ma tace, yanzu tunda sun aminta, zan koma mu fara shiri, sai a saka rana mungode sosai.Nan su Ma suka dauki hanyar komawa, da niyyar zasu dawo aka, saka rana.A mota har kuka Barr yayiwa Ma amma sam ko kallon shi batayi ba, dayaga abi, da gaske ne dole ya yi shuru.Ummi kuwa sai dadi takeji yau gata ga Ummanta, mai share kukanta.

   Nan take tambayar ina Baba larai, Umma tace tun sanda taje kotu bata sake ganinta ba andaice tunda batada kudin tara, an riketa sai randa ta biya ko aka biya mata, kai kawai Ummi ta girgiza tace
" k'aik'ayi koma kan mashek'iya kenan, Umma basarda maganar tayi.Yan k'auyen take magana ta shiga kunnen kowa Ummi ta dawo, dama sunji labarin komai, haka aka dinga shiga gidansu ana gulma, tabbas sunga alamar Ummi tasha wahala, saboda farar fatarta duk ta dishe, fita suka dingayi ana gulma.

                             ***
kwana uku su Ma suka dawo, da y'an uwan Barr maza, dama Umma ta gayawa dangin mahaifin Ummi, suma sun had'u, aka saka rana wata mai zuwa, da sadakinsu suka zo aka bayar naira dubu talatin, Ummi murnar ganin Mukh yasa ta manta da bakincikin hadata aure da Barr.
   sai mak'ale Mukh take jikinta, lokacin Baba larai ta dawo shima kuma mai gari ya saka baki akanta, nan Barr ya biya kudin, aikuwa sai kame kame take, tuni maganar auren Ummi ta zaga ko'ina na k'auyen, basu gama mamaki ba saida aka kawo lefen Ummi akwati goma sha biyu, ai kamar gidan zai fashe da mutane, Umma harda kukan dadi tayi, 
kwana biyu ta kira k'anwarta dake Sokoto ta hado mata kayan mata ta shiga tsumar y'arta, Ma ma ba bayaba gurin hada Ummi, har mai gyaran jiki ta d'auko ana gyaran Ummi.

     Kaji da k'wai kam ci take harta gaji, aikuwa ta mulle tayi kiba ga wani kyau da tayi,y'an k'auyen sai surutu ake.Ana saura sati biyu bikin Barr yazo, tana kwance d'aki ita da Mukh Umma ta gaya mata Barr na zaure yana jiranta, turo baki tayi kamar wata baby ta saka hijabinta taja hannun Mukh suka fita.

   A zaure ta same shi, yana sanye da kaftani color din black, an mashi kwad'o white, yana sanye da agogonshi mai tsadar gaske, hula kam babu dama bai cika saka hula ba,kaftanin ma sai idan zai shiga inda yake kunya.
Yafito matashin yaron shi ga kyau, sai k'amshi yake zubawa, da k'yar tayi sallama, haka shima dak'yar ya karba ba tareda ya kalleta ba, zama tayi d'an nesa da shi, amma duk da haka yana jiyo k'amshin da take zubawa. Mukh kuwa da saurin shi ya fad'a kanshi yana Uncle oyoyo....

    sai lokacin Barr yayi dariya ya rungume Mukh, kamin yace 
"My boy ya kk?
" lafiya Mukh yace,  Barr yana dariya yace
" nagafa sai k'iba kake k'arawa, me Umma ke baka kanaci haka?

 dariya Mukh yayi yace 
"ba granny ce ke bani kaji da fura ba wai dan nayi kiba tunda nida Mumyna bamuda auki, kamar a buga iska mu karye, ita Mumy ma harda wani abu mai tsami da zaki ake bata, idan nace a bani granny tace aa idan yaro yasha kashi yakeyi.😂

   Ummi kam zare ido tayi, kardai Mukh ya tona mata asiri, yaronan ya rainata, idan yaji kayan mata take sha, akan shi...

    sunan wata kande mai tonon silili😅
          
   Dariyar gaske Barr yayi, sai lokacin ya kalleta, tayi mashi wani irin kyau, ga haske ta k'ara,duk da cikin hijabi take yaga alamar tayi bul bul da ita, saurin d'auke kanshi yayi lokacinda zata d'ago kai itama, nan yaci gaba da hirar shi da Mukh, kamin ya mika mashi k'atuwar leda yace
" oya jeka kawai Granny ta ijeyemaka nacika al'kawari chocolate ne, tsalle Mukh yayi ya kwashi ledar yaje bude d'aya ya kai bakin Ummi yace
" sai Mumyna ta fara ci haka mukeyi, dariya tayi ta gutsura sanan ya shek'a cikin gidan, har ga ga Allah Barr sun burge shi sosai, kamar itace mahaifiyar shi da gaske.

    sun jima ba wanda yayi magana, kamin Barr yace
" shaifa d'an k'auye haka yake baya saurin wayewa mtsww, tsaf ta gane mai yake nufi, kuma da wa yake, amma sai tayi tsit batace komai ba, tsuki ya sake ja karo na biyu yace

" Amma dai kinsan baki d'aya daga cikin matanda nakeso na aura ko?sabida ni nafison mace wayayya, k'aramar yarinya, kuma mai zurfin ilimi.

d'an murmushi tayi kamain tace
" sai gashi kuma a kaina ka k'are, duk irin ilimin naka da haduwarka, dan nice zaka aura dai so sai hak'uri kuma.Sanan nima kaina ina bakin cikin shiga gidan k'aramin yaro irinka

yayi mamaki sosai da tace haka, kallonta yayi itama shi take kallo, d'auke kanshi yayi yace
" zaki gane ne, turo baki kawai tayi harga Allah abin datayi ya bashi sha'awa, amma sai ya fuske, yace" 

Ma ta turoni ne akan kiyi list din abinda kikeso najemata dashi, dan haka saiki yi ki bayar ina mota, yana fad'ar haka ya mike, har yayi nisa ya juyo yace,
" kin san kince kina bakin cikin ki shiga gidan yaro k'arami irina so sai ki shirya zuwa gidan yaro, yana fad'ar haka ya fice, dan guntu, tsuki taja ta mike itama tace"
ai ba k'arya nayi ba kai k'aramin yaro ne.....







              *BY BEBEELO*



~SADAUKARWA~ <GA> *UMMI A'SHA**😘*
[22/12 7:39 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
*D'A NA KOWA NE*
            🌿🌿

      *©BEBEELO*

                 *80~85*
                  ********

~ Tana komawa ciki, ta rubuta yan abubuwanda take bukata ba wani masu yawa ba, ta mikawa Mukh ya kai mashi, lokacin iya sukuwa ya suku yadda ta barshi yana jira.
Sallama yayi da Umma ya fice yana mai nazarin irin zamanda zasuyi shida Ummi.
                    **    **    **
Shagali ya kam kama sosai, gidansu Ummi ba zakace shine ba irin yadda aka gyara ahi,
harda su fenti, yan uwa ancika gidan, da wanda aka gayyata da wanda na baa gayyata ba sunzo dan ganin kwakwaf.
Ma tayi rawar gani sosai har Umar M Shareef ta gayyota domin ya masu waka, tabb je kaga mutane yadda aka taru ranar.
Abinci kala kala da lemu ake fitowa dasu, ga naman kaji dana rago kai harda talotalo.
Ranar daurin aure 12 na rana aka daura auren  *Ummi A'isha*da angonta *Barrister  Umar*Aurenda ya samu hallattar manyan mutane, daga mutanenmu bakar fata har fararen fatar.
Bayan an dawo daga daurin auren, aka shirya amarya cikin code less arsh color sai head dinta red da net dinda ta rufe jikinta shima red, sarkarta ta gold da sauransu, tayi kyau har ta gaji.
Take kaji ana rangada guda, aka kira amarya da ango dan daukar hoto da yan uwa.
Ma itace ta jawo amarya takaita inda angon yake zaune kan wata kayatacciyar kujera, mai ado.
Yasha dinkin kaftani shaddar fara sol taji kwado red, hula da takalma duka red shima.
Fuskar shi ba yabo ba fallasa, zaunarda Ummi akayi take kaga sun haska gurin kamar wasu taurari,
ga kalan kayan nasu, ita kanta Ummi tayi mamakin haka, tasan bazai wuce aikin Ma ba.
Barr sai satar kallon Ummi yake yadda yaga tayi bala'in kyau, bama zakace wai tayi ko shekara ashirin ba balle talatin.
Hannunta yabi da kallo yadda aka tsantsara mata kunshi, mai dauke da baki da ja,
yayi kyau sosai, a ranshi ya fadi haka amma baisan hakan ya fito fili ba, saida tadan saci kallon shi,
ta sake juyawa kai gefe, ba laifi ta fada a ranta,nan mai hoto yace su gyara a dauke su.
Kallon juna sukayi suna dubin to wane gyarawa zasuyi bayan wanan, mai hoton bayarbe ne shi da kanshi yaje kusa dasu ya nuna masu yadda zasuyi.
Kallon juna suka sakeyi, sanan ko wannensu yayi shuru ganin Ma da Umma sun kura masu ido yasa,
Umar yayi karfin halin yanyo ta jikin shi din kamar yadd mai hoton yace suyi.
Aikuwa su duka wani irin shock sukaji, daurewa kawai Barr yayi amma wani irin hali ya shiga haka itama Ummi.
Dariya wayayyun mutanenda ke wurin suka saka inda yan kauyen suka fara suruce suracen babu kunya.
Bayan an gama d'aukarsu su kadai,Mukh ya arto ya fada jikin su ya hade fuskokinsu guri daya har suna juyo nunfashin juna, take k'wak'walwar Barr ta fara dif.dif.
Sumba Mukh ya kaiwa Ummi a kunce, tana dariya aka dauki hoton sunyi masifar kyau kamar su suka haifi yaron.
Bayan an gama Umma tayiwa yarta nasiha mai ratsa zuciya da kukanta shabe shabe,
nan aka wuce da ita dakinta, babu rakiyar ko mutum d'aya dama Ummi batada kawa, sadai taje can zan hadata kwance da Chuchu, ga Meena dan Musa, gasu Benazir, tabb inaga na hadata da Ummu samha, waiiwaihh na manta da Jabo, shawara kuwa sai na hadata da anty Ybk.😘

                      **     **       **
Ankai Ummi dakinta lafiya, a nan Abuja, bayan Ma da mutanenta su, watse ne, Barr Ahmad suna tafe a mota shida Barr Umar, sai surutu Barr Ahmad keyi,
amma Barr ya k'yaleshi.
Dariya Barr Ahmad yayi yace"wanan shan kamshin na meye kuma?
D'an murmusawa Barr yayi yace"bansan meyasa Ma ta auramin wanan bagidajiyar ba wlhy.
A fusace Barr Ahmad ya kalle shi yace"komai dai mecece ita yanzu ta zama matarka,
kuma wlhy ka daina irin haka ba kyau.
Shima a fusace ya kalli Barr Ahmad yace"idan na fada sai ka mutu, nifa bana sonta,
wlhy sanan kaima kasan ba ajina ba ce, nafison karamar yarinya wacce zamu more yarantarmu,
amma wanan me ma zan sama a jikinta, tunda budurcin ma ya zube a hanya mstwwww ya fada,
dai dai sun shigo gidan ya fito.
kallo kawai Barr Ahmad ke binshi dashi, tabbas yasan wani gefen abokin shi nada gaskiya,
cox Ummi sa'arshi ce, irin yadda sukeji kuwa ance idan mace ta jima batayi aure ba,
budurcinta tafiya ya ke😳
da haka shima ya shiga gidan, falo ya sami she ya zube, murmushi yayi yace"ka tashi na kaika har dakin matarka.
Tsuki yaja yace"ban tashi ba ka tafi kawai, badai ka kawoni gida ba?
"saifa ka tashi, ganin ya takura shi yasa ya mike ya shige room din shi yabar Barr Ahmad nan,
shima fusata yayi yabar gidan.Yana shiga yayi wanka ya saka kayan baccin shi,ya zube kan gadon,
yana tunanin irin rayuwarda zasuyi shida Ummi, da haka har bacci yayi gaba da shi.
                        **   **   **
Ummi bata kwanta ba, saida tayi wankanta tayiwa Mukh ta shirya su cikin kayan bacci suna kamshi, ta cika karamin galss cup da fresh milk ta bawa Mukh yasha itama ta cika tasha, sanan ta kashe masu wuta taja masu balnket take bacci ya kwashe su dama sun gaji.

      *Washe gari*
Tunda asuba tayi sallah, ta sake komawa bacci, Mukh kam tashi yayi yana buga game din shi,
Daurewa Barr yayi ya shigo dakin acewar shi saboda Mukh ya shigo,Mukh na ganin shi ya sheka,
ya rungume shi, shima yana shafar kanshi yace"My Mkukh ka tashi lafiy.......bai idar ba sanadiyar abinda ya hango.
Ummi ce tayi dai dai kan gado, da yar karamar rigan baccinta pink, mai shara shara hatta pant din ciki kana hangowa,
gashi zaninda ta dora yayi gefe akan nauyin bacci, wani yawu Barr Umar ya hadiye, kamin ya saita kanshi.
Da saurin shi ya nufi gurin ya d'auki filo yana dukanta dashi, yana fad'a, ke boyar Allah, ai sai ki tashi haka an samu gado mai taushi ko?
haka ya dinga kiranta, a hankali ta bude idonta, ta mike tana mika tareda salati, aikuwa da sauri Barr yabar d'akin,
saboda ashe botirin rigar ya balle, gashi ta buga uban mika,na fulaninta a fili, gasu tsaye cak, tsuki taja ta mike ta shige ban d'aki.
Barr kuwa har wani duhu yake gani kamin ya isa falo ya zube, tabbb meke shirin faruwa dashi? abinda yake tambayr kanshi kenan.
ohh boy Brr na luv ohhhh😉



               **     **     **
Ina farin ciki masoyana, akan irin yadda kuka nuna damuwarku,akan ciwonda nayi.
Nagode maku kuma Addu'arku a gareni ta karbu, cox naji sauki sosai. Allah ya sakamaku da khairan Allah kuma ya barmu tare
*Bebeelonku*😘




~SADAUKARWA~ <GA> *UMMI A'ISHA**😘*
[22/12 7:39 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
         *D'A NA KOWA NE*
                🌿🌿

*©BEBEELO*

                    *85~90*
                     ********

~ Wankanta tayi, kamin tayiwa Mukh, ta nado so a towel ta shirya shi, sanan ta turashi falo itama ta shirya dan idan yanan bazata shirya yadda takeso ba.
Kwalliyarta tayi abinda sam bata saba ba shiyasa ma ko iyawa batayi ba sosai, gani, girar bata jawu ba yasa ta goge ga ba daya, a ranta tace tunda inason wanan kwalliyar ta zamani dole naje na samu *Miemie Bee* ta koya min.
Da haka ta kimtsa ta fito, a falo ya ta sami Mukh da Barr suna buga game sai dariya suke tabbas sun burgeta tsaye tayi tana kallon su kamar ance Brr ya dago aikuwa sai suka hada ido,sam kasa dauke kanshi yayi daga dubanta.
Sanye take cikin riga da wando na pakistan yellow sunyi mata kyau sosai matuka.
Saurin dauje kai tayi tasha murr akan kallon kurullan da yake mata, shima wayancewa yayi, ya dauke kanshi, dan kar ta raina shi, dariya Mukh yayi yace"Uncle Mumyna tayi kyau ko?
Tambayar dariya ta bawa Barr, kuma yaji dadin tambayar, saida ya kalleta kasa da sama, sanan ya kalli Mukh dake jiran amsa yace"Nop gaskiya batayi kyau ba cox dana hangota saida na nemi guduwa powder nata yayi heavy kamar wata sabon kamu.
Rai Mukh ya bata ya tashi kusa dashi yace"nayi fushi Mumyna is the most beutifull Mum in the world.
Ba karamin haushi Ummi taji ba, amma sai ta wayance kawai, cox tasan yimata shine yake kawai nd batayi dan shi ba, so mezaisa ta damu, ai abin haushi ace kayiwa miji kwalliya ya gwaleka shine da cin rai, dan haka murmushi kawai tayi wanda ya dauki hankalin Barr, tace"ina neman kitchen din gidanan zanyi girki.
Kamar bai jita ba, nan Mukh yace"Mumyna muje na kaiki naga Uncle ya hado cuffee dazu, hannunta yaja ya kaita kitchen nan ta shiga hada abinci irin wadanda ta koya gurin Ma, Plantain da kwai tayi cox sune fouvrite na Mukh dinta, sanan ta hada masu ruwan Tea a flaks masu kamshin ginger.
A danny ta shirya komai bata cewa Barr kala ba tayi servin nasu ita da Mukh suka zauna sunaci suna dariya abinsu, lokacinda ya  fito ya hangosu sunyi balin burge shi, Mukh yana zuba mata kwai a baki suna dariya.
Shima zama yayi kamshin da ya bugi hancin shi ne ya saka shi saurin jan food flaks din ya zuba aikuwa ya shiga ci ba batu, yanga, shi sam yama manta kusa da Ummi yake, saida ya koshi ya fice yabar gidan.
Sai kusan bayan isha'i ya dawo, lokacin Mukh yayi bacci, dakin shi ya shige yayi wanka sanan ya fito falo ya kunna TV.
Bayan tayi wanka tana daure da towel d'an karami, tana rike da hand drayer tana busarda kanta.
 taji alamun TV na motsi,ya dawo kenan ta fada, murmushin keta tayi, ta banye towel din ta kara daura shi sama, take manyan cinyoyinta suka bayyana, ta fidda rabin kirjinta, ta bude k'ofar ta fito, a ranta tace"zan numa maka nayi kama da sabon kamu wallahi, ko kallon inda yake zaune batayi ba sai zakudar gaba da baya take, ga gashin kanta daya dan jike da ruwa still  drayer din na hannunta tana busadda kanta, tayi hanyar kitchen.
Mutuwar tsaye Barr yayi baki sake ya bita da kallo, tun cikin kanshi yakejin abu na mashi yawo, bai ankara ba yaji madam tana mashi knocking, da sauri ya hade kafafun shi idon shi sunyi jawur, harta fito hannunta d'aya rike   da fresh milk daya kuma ta rike hand drayer, ta saka cup a hammata tana yan wake wakenta, ta shige d'akinta, tana shiga ta zube tana dariya, kamar ranta zai fita, rigar baccinta ta saka tareda turaruka, tana murmushi tace"zaka san kayi kuskuren gayamin magana Barr.
A brkice yazo bakin kofar nata ya bude, kanshi ya leko tana zaune tana tunke gashi, kanta cox bata iya baccci dashi a hargitse, da k'yar yace"kizo ki tabbata kin kashe komai kitchen dinan naji kamar baki kashe ba, kamar zatayi dariya sai kuma ta fuske tace"Malam nasan aikina dan haka komai na kashe, a dan fusace yace"nima ai nasan aikina shiyasa nace kizo ki k'ara dubawa.
Turo baki tayi bata damu da rigar jikinta ba ta fito ta wuce shi tsaye tayi kitchen sai kunkuni take, bayanta yabi shima yayi kitchen din ya jawo kofa ya kulle.
Harga Allah saida gabanta ya fadi, "meye haka Malam? Murmushi yayi yace"takarata akayi shine zan rama nima,sam bata gane ba, saida tajita a  cikin k'yakk'yawan kirjin shi, take zuciyarta ta shiga bugawa, tsayuwa ma ta gagareta.
Cikin fad'a tace"bafa nason wanan rainin ka sakeni, muryar shi kasa yace"ai kinsan ni yarone ba komai zan iya ba so karki damu, nan ya hade bakin shi da nata.



    *NOTE* Ayi hakuri da wanan pls, jikin ne nawa sai a slow, ina neman addu'arku.


              *BEBEELO*


*SADAUKARWA GA *UMMI A'ISHA*😘
[22/12 7:39 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
       *D'A NA KOWA NE*
                🌿🌿
*©BEBEELO*

                   *90~95*
                     *******

~  Duk yadda taso ta kwace kanta ta kasa, haka ta sakawa sarautar Allah ido.
Shikuwa Barr sam hankalin shi gushe ga baki daya, ya kasa controling kanshi, duk ajin nashi yau ya zube gashi gaban Ummi tun baije koina ba yana sambatu.
jin yana nema ya cire yar rigar jikinta yasa ta buga uban ihu,
wanda ya maida Barr hankakin shi, yana saketa ta bude kofar da sauri ta gudu.
cije lebe yayi a fiki ya furta zamu hadu ne.
D'akinta ta fada ta kulle, kwanciya tayi tana maida nunfashi, sai kuma ta dinga murmushi tana mamaki wai Barr ke mata haka wanda yace ta mashi babba hmmm, namiji kenan.

*Washe gari*

Tana gama sallah ta shiga kitchen tana hada masu abinda zasu karya, Mukh na biye da ita duk inda tayi yana mata surutu, sai dariya take.
Haka ya iso falon yana sanye da suit sai k'amshi yake, kyau kam yasha har ya gaji.
a kofar kitchen din ya sameta, dan murmushi ya sake mata, ita kuwa ko dagi kai batayi ba,
Mukh fadawa jikin shi yayi yana dariya yace"Uncle you look  so muahhh, ya dallah mashi sumbar a kumatun shi.
Shima Barr dariya yayi ya manna mashi kiss a kumatun shi, yace"tanks my luvly son.
Mikewa yayi ya kalleta yace"zanje office sai na dawo, ko kallon shi batayi ba tace"naji,
murmushi kawai yayi, yacewa Mukh my Mukh me zan dawo maka dashi?murmushi Mukh yayi yace"icecream nd chocolate,
shima murmushin yayi mashi yace"angama my mukh sai na dawo, ya fice abin shi.
A mota sai tunani yake, irin hali na Ummi, ita bisa bilhakki, tana nufin bata son shi ya mata yaro hmmm, dariya yayi mai dan sauti, a fili ya furta ina sonki Ummi kuma zan nuna maki ni ba yaro ne ba.
                          **  **   **
Komai ta kammala tayi wankanta, tayiwa Mukh sai famar k'amshi suke, guntun wando ne kawai ta sakawa Mukh sai vest, idon shi radam da kwalli yayiwa farar fuskar shi kyau matuka.
Abinci ta ajiy masu a nan tsakar falon, sunaci a nutse, suna kallon Cartoon.
Sallama yayi ya shigo falon,
da sauri Mukh yaje ya mike ta dalla mashi harara ba shiri ya koma ya zauna.
ganin ya bata rai ta jawo shi jikinta tana lallashi, haba my son kaine ka taka dokana,
bana gaya maka idan kanacin abinci ka daina tashi ba, dagowa yayi yayi murmushi yace"
na manta ne Mumyna i'm sorry, ya fada tareda kama kunnen shi.
Murmushi tayi tace" bakayiwa Mumynka laifi ba, oya cigaba da cin abinci, loma ta debo tura mashi baki suna dariya.
Barr na kallonsu, yara wane irin kaunace tsakanin su, shima murmushin yayi ya kife ledar kusa da ita yayi dakin shi, a ranshi yana yaba irin tarbiyarda take koyawa Mukh.
Saida suka kammala, ta bude ledar gasassun kaji ne guda biyu, sai manya fresh milk guda biyu suma, da icecream sai chocolate.
madarar daya ta cire masu, sai kayan Mukh, da kaza daya, sauran dayar madarar da kaza ta ajiye mashi a danny.
A plet ta saka masu kazar ta dauko masu glass cup sunaci suna dariya abinsu, harya same su.
Zama yayi, saida ya kalleta tukun tayi mashi kyau sosai, riga da zani ne na atamfa ta saka dinkin mai brest cupe yamata kyau sosai,
"ki mayar min da abincin anan tunda baki iya tarban mai gida ba, d'an harar shi tayi a ranta tace"kuduba min wanan dan yaron sai wani sakani aiki yake, mtswww,
bata zaci tsukin nata ya fito ba cox ita a tunaninta a ciki tayi shi, kallonta yayi yadan fuske, kamin yace"akwai ranar kin dillanci, sam ita bata gane inda ya dosa ba, tayi danny din,
ta kwaso abincin Mukh na kan cinyar Barr yanacin naman shi bai masan sunayi ba.
harta ajiye zata juya yace"baki isa ba, kizo ki zubamin, wanan ne kuma.....shuru tayi taki karasawa akan Mukh dake gurin, sai kawai tazo ta zuba mashi, ta koma inda take zaune.
Batafi minti goma ba ta mike, tace da "Mukh muje ka kwanta, baiso ba amma bazai iya mata musu ba, haka ya fice Barr sai kallonta yake.
shirin kwanciya tayi masu, ta kashe fitilar d'akin ta kwanta, can taji wayarta na kara, ganin sunan Ma ya saka ta dauka da sauri tana dariya.
Nan Ma ke tambayarta komai dai lafiya, tace lafiya kalau, yar nasiha Ma tayi mata akan zaman takewar aure, sanan aka bata Mukh suka yita firar su, kamin Ma tayi masu sallama.
Shigowa yayi dakin, lokacin Mukh yayi bacci, tana ganin shi ta hade fuska, saman gadon ya zube ya jawota jikin shi, tana turjewa amma yaki sakinta, sako yake aika mata ta koina, kasa motswa sosai tayi dan kar Mukh ya farka yagansu a haka, hakan ya bawa Barr damar fincike yar rigar baccinta.
Ba k'aramin mamaki yasha ba ganin na fulaninta tsaye cak ba abinda ya tabasu, aikuwa nan ya koma yana wasa dasu, Ummi takusa d'auke wuta, ganin yana shirin aikata mai gaba daya yasa dak'yar ta furta, ka daina banida tsarki.
Gefe Barr ya zube yana maida nunfashi, ranshi duk a bace, sai shi baiso haka ba, mikewa yayi yabar dakin yana kallonta cike da damuwa, yana fita ta zube itama tana maida numfashi, tabb dama haka wanan yaron yake ya iya karuwanci, kodai zamanda yayi.....shuru tayi tabar zancen, a ranta tace"haba Ummi ance ka fadi alkhairi ko kayi shuru.
Haka ta kwanta tana tuna irin zazzafar soyayyarda ya nunamata, take ta samu kanta da farinciki.
Wanka shikam ya shiga yayi, sai tsuki yake bugawa, a fili ya furta lallai dan hakinda ka raina.....
Bashi yayi bacci ba sai gab da asuba, aikuwa har lattin sallah yayi.
                             ***
Kullum yawo da hankaki take mashi ya galabaitu iya galabaituwa, an saka Mukh makaranta har ya fara zuwa, haka Ma ta kawo masu ziyara Ummi sai murna take baki bai rufuwa, ganin su cikin farin ciki ya saka Ma taji dadi sosai.
   D'akinta ya sameta tana sallah, raka'ar karshe saida ta sallame, wani mugun kallo ya wurga mata, duk da ba wani shiri garesu ba, tadanji kunyar k'aryarda take mashi kullum.
kai kawai ya gyada ya fita, jiki ba k'wari ta mike ta shirya masu abinci a tsakiyar falo, saboda itakam ta tsani cin abinci a danny.
Kasa cin komai tayi saita sami kanta da jin nauyin Barr, shikam sai loda abincin shi yake shida Mukh, mikewa ma tayi zata shiga daki, a dunkule ya wurga mata magana, ina fatar dai kin shirya yau kam, dan ba fashi.
Dariya Mukh yayi yace"Uncle ina zakuje hala?
dan murmushi yayi yace"ba inda zamuje dama wani assigment ne zan bata yau dinan, dan haka kayiwa Mumynka addua idan taci kaima zakaji dadi sosai, dan zata samu result mai kyau.
ihu Mukh ya saka yaje ya kama hannun Ummi yace"Mumyna dan Allah kici asigemtn dinan kinji banaso ki fadi kar Uncle ya maki dariya, yace"baki iya komai ba kinji.
Harar Barr tayi wanda dariya ta kule har yana nema ya kware,  tace"ni k'aramin yaro kamar ka, bai isa yabani assigment ba. kabari manya wadanda suka isa su bani amma ba kai ba,sanan ta maida dubanta ga Mukh tace"wai bana hanaka tashi idan kanacin abinci ba so kake muyi fada kenan, opps sorry Mumyna, nidai kici asigemtn din kinji, wucewa tayi ta shige dakinta, sai masifa take, lallai ma wanan ya raina mata da wayo.
Barr kuwa abincin shi kawai yake suburbuda cike da farinciki har ya gama, yabar Mukh nan yana buga game ya shiga yayi wanka, yana dannar laptop din shi yana duba wani case.
Itama wanka ta shiga, koda tazo falo Mukh har yayi bacci nan gurin, ranta bace tace"ji wanan mutumin yau ya hana nayiwa yarona wanka, kuma bai  sha madar shi ba , tsuki taja ta aza Mukh a kafad'anta tayi d'akinta dashi ta shimfide shi, saida ta tofe su da addua'a kamin ta kwanta.
Batayi bacci ba sai tunanin kalaman Barr take, sai kuwa gashi ya shigo d'akin, d'an guntun tsaki taja isowa yayi, ya yaye bargonda take ciki, ya d'auki Mukh a kafad'a, sai lokacin tayi magana da k'arfi, Malam ina zaka kaimun yaro? bai ko kallota ba yayi waje, itama binshi tayi, batama bi ta zaninta ba daga ita sai y'ar rigar bacci iya cinya, gashin kanta yau batama tufke shi ba yana barbaje.
D'akin Mukh taga ya nufa yaje ya shimfede shi, ya kashe mashi wuta ya jawo k'ofar, a bakin k'ofa ta tsaya ta rike k'ugu cike da masifa tace"meye dalilinka nayin hakan? ji tayi kawai an cirata sama, d'akin shi ya nufa da ita, ya sauketa kan gadon, ya tube rigar jikin shi, tareda fad'ar, dama na gayamaki ki shirya yau zan nuna maki aikin yaro.
kanta yayo yana aika mata da sako kala kala, wanda sam k'aramin yaro bazai iya irinshi ba, tam su *Ummi A'isha*, sai munzo jinya da safe😜



     *BEBEELO*


*SADAUKARWA GA UMMI A'ISHA*😘
[22/12 7:39 pm] ‪+234 816 559 2090‬: 🌿🌿
    *D'A NA KOWA NE*
               🌿🌿
*©BEBEELO*

                    *95~100*

~  Ga baki daya duk wani suturar jikinta, yayi fatali da ita.Ummi kam ikon Allah kawai take kallo,
ita sam tama rasa me zatayi, iya kokarinta na ta kwace tayi amma sam ta kasa,ko motsi.
Tana mamakin inda Barr ya iya wadanan abubuwan, jin irin abubuwanda yake mata har,
ya saka jikinta ya mutu.Sam takasa wani yunkuri, saboda duk wani kashin jikinta yamutu.
Take ta samu kanta da jin dadin abinda yake mata.Barr kuwa tuni hankalin shi ya fara,
tafiya ya matsu ya jishi tsumdum.Aikuwa saida ya gama kashe mata jiki da romance,
sanan ya fara karkarin keta abarshi, saida yadda yayi tsammani ba haka ne ba, saboda
gam yaji abarshi kamar wata yar shekara goma.Yayi mamaki matuka, bai sham mamaki ba,
saida yashiga cikin.Ummi kuwa tun tana dauriya da wanan lamarin harta fara kwalla, batayi wani ihu ba,
illah kwalla kawai na zafinda takeji, idanunta ta kulle gama tareda dora hannuwanta biyu,
akan kirjin Barr, ganin abin nashi yayi yawa ya kasa sauraramata yasa tadan fara kuka mai
sauti tana magayi akan ya kyaleta, amma sam saida ta wahala iya wahala.Sanan,
ya sauka kanta, gefenta ya zube, ga kamo hannunta yana murzawa.Daidai fuskarta,
ya matso yana share mata kwallanda take, wani irin kunya ya kamata, dan murmushi yayi,
ya mike yayi ban dadi, saida yayi wanka sanan ya fito zuwa lokacin ya kwatanci ta dan huta.
Hannu ya mika mata, hararshi tayi tace"me kake nufi mtswww, mikewa taje tayi, amma
saita koma zaune.Dariya yayi yace"kinzata aikin yaro saukine dashi, gwara ki bari naje na gasaki.
Kuka ta fashe dashi tace"wallahi zalunci ne kawai kuma sai........rufe mata baki yayi, da nashi.
Daga haka ya dauketa zuwa toilet yana kaita ya saka ta ruwan zafinda ya shirya harar shi tayi ganin zai jaye zanin jikinta,
dariya ya saka yace"Malama boye boye name kuma, akwai wanda ban ganiba ne?
nan ma wata harar ta dalla mashi, dariya yayi ya janye zanan ya fincilar, sanan ya shiga gasata.
saida yabata magani shima da kyar ta karba tasha, take tayi bacci.Ido ya kura mata yana kallonta.
Kyakkyawa ce ta gaske, wani sonta yaji na shigar shi, juyawa yayi yana mamaki, to ya akayi,
ya sameta cikakkiyar budurwa?
da haka dai yayi bacci, koda ya farka bai ganta ba, murmushi yayi ya fada toilet yayi wanka.
A falo ya hangota tana shirya abinci a danny, har tayi wanka abinta, tayiwa Mukh.
Lallai jarumace ya fada a ranshi, wani zuciyar yace mashi kawai tanayi ne, dan karka gano lagonta.
D'an murmushi yayi ya k'araso, da gudu Mukh ya fada jikin shi, yace" Uncle meya sami Mumyna take fushi?
na Tambayeta ka bata asigement din tace na bari kazo na tambayeka,Uncle ka bata din ne?
Saida ya kalleta hararshi take, dariya yayi yaja hannun Mukh suka zauna a kasa, yace"nabata mana tun jiya, but im sorry to said Mumynka bata iya ba, komai bataci ba ciki.
Bata fuska Mukh yayi yace"Uncle may be kabata mai wuya ne, but promise me zaka sake bata wani mai sauki.
Dariya Barr yayi yace"ai zan sake bata din i promise, dariya Mukh yayi ya fada jikin shi.
Tana jinsu tayi banza dasu, abincin ta mayar gabansu, irish ne, sai source na kwai da kidney sai k'amshi yake, ga tea ta hada masu.
Komai kasa ci tayi zaunenta take sai tunani take iri iri, kusa da ita ya matso ya sakayo hanunshi,
ta k'ugunta yace"to ya kikaji asigemtn din yaro?harara ta dalla mashi, kamin tace"Malam bafa nason haka.
Mikewa tayi dak'yar har yanzu zafi takeji tayi dakinta, bai bita ba yayi zamanshi falo shida Mukh,
Mukh yaso ya bita d'akin amma Barr ya hanashi, yanaso yabarta tadan huta cox yasan ta wahala sosai.
                                    ***
Haka rayuwarsu ta kasance, tun bata kula Barr harta zo ta fara kulashi, hakan ya faru ne,
akan irin zazzafar kaunarda yake nunamata.Take itama ta fere tana nuna mashi nata salon.
Aikuwa kullum cikin farin ciki suke gidan, irin sonda Barr ke nuna mata har mamaki take.
      kwance take kan cinyar shi, sai shafar k'atoton cikinta yake, dayan hannunshi yayana rike da apple tana ci
"wai yaushe zamuje K'auye? wallahi na k'osa naje, kagafa kusan wata biyar rabo danaje.
Dan fuskewa yayi yace"kema kinsan kina haka bazan bari kije koina ba, so mubar maganar please.
Shuru tayi tareda sako k'walla, batace komai ba, rungumeta yayi, yace"haba my dear kiduba fa kiga,
taifiya ma da kyar kike, so ya zaayi na barki kina tafiya nesa, dan Allah kiyi hakuri,
duka duka meya rage?
saifa kin gaji da mutane.Yadan kwantar mata da hankali, take taji dadi, nan kuma suka lula wata duniyar.
      "Ma yanzu ne ta haihu ko asibiti bamu dawo ba, sunce saita huta ita da babyn, Dariya ma tayi wanda zai nunamaka tana cike da farinciki.Tace aini yanzu zan kamo hanya,
saika tura a d'auko Ummanta kamin na iso, tam yace"sanan ya kashe wayar.
sati na zagoywa aka rad'awa yarinya suna, Pherty, anyi shagalin biki sosai.
Babyn kullum tana hannun Mukh, sai murna yake, Barr farincikin shi bai misaltuwa.
Pherty nada wata uku, Ummi ta shiga wani makarantar mata, mai hade da boko,da
islamiyya, gwargwado tana fahimta, kuma tana zaune da kowa lafiya.Sun shirya sunje Sarandosa, Umma murna gurinta baa magana,
lallai komai lokaci ne.
yan k'auyen sai biyar Ummi ake, kudi kawai take rabama masu, bata damu da irin abinda
suka mata a baya ba.Koda taje ta iske an sako Rabi yar Baba larai, ga yara biyar, kuma bazata wuce shekara ashirin ba,
hakan yasa ta kawo abinci mai yawa gidan ta basu kudi, kuma ta dauki nauyin makarantar yaran,
ga baki daya.Bayan shekara uku su Mukh an k'ara girma k'yaun shi sai k'ara fita yake ga tarbiya daya samu gurin Ummi,
Barr wani irin kara son Ummi yake, ganin irin sonda takewa Mukh, lallai itace mutum ta biyu,
bayan Daddyn Mukh daya taba ganin, sun nuna cewa *d'a na kowa ne*
Pherty ta shaku da Mukh sosai, bata iya zama bata ganshi ba, shikuwa a schl duk wanda ya tabata zaisha mamaki dan kuwa sai inda k'arfin shi ya k'are, Ummi ta sake haihuwar yaronta Sadiq, zamansu suke cikin jin dadi.
Ranar sunje mall suka hadu da Mum, mahaifiyar Ammar, harda kukanta tana rokon Ummi gafara, yaran Ummi sun bata sha'awa sosai, nan Ummi ta mata alkawarin za'a dinga kaisu week end,
hakan yawa Mum dadi sosai.


*Anan na kawo karshen wanan buk din nawa, dafatar kun samu wani darasi a cikin shi,idan kuwa kun samu darasin zanso naji comment dinku,hakan zai tabbatarmin da sakona ya isa ga makaranta*

*inaso na godewa duk masoyana, ina maku fatan alkhairi*

*Ummi Aisha, wanan buk danki akayi, nakine na mallaka maki halak malak, saboda kauna da mutunci dake tsakaninmu, Allah ya barmu tare*

*Sady jegal na gaidaki, kamar kinfi kowa son wanan buk din, Allah yabarmaki yaranki*

*Zanyi kira ga makaranta, dan Allah idan dai har free kk, lokacinda aka fara buk, dan Allah ka daure ka karanta shi lokacin*
*Saboda rashin yin hakan wahala ne ga marubuci* *sai yayi nisa a dinga maida shi baya*
*zakuga wani lokaci kayi wahala**
*kayi typn may be ka tura page 30 haka, zakaji wata taci ka mata sndn farko,ana samun irin haka*
 *sosai*
*to dama ace ita kadaice zakama sndn farko, to ba haka ba, may be mutum ashirin zasu bika ta prvt suce ka masu sndn, kuma ba guri daya ne suke so ba, wanan zatace 30 takeso, wata 60, kuma idan baka masu sndn ba ya isa ace wance wulak'anci gareta*

*Wanan abin ya jima yana cimin tuwo a k'warya, dan Allah kudinga tausaya mana mu marubata, ba yabon kai ba munafa k'okari, bafa aikin typn ne kawai gabanmu ba, akwai masu karatu, akwai masu kasuwanci, akwa masu kula da gida, miji yara, kunga kuwa dole muji jiki, duk da mu muka saka kanmu, amma ya kamata a mana uzuri, Allah yasa mudace*

*Taku Bebeelo*(Mum iman)

sai kun jini a sabo, buk mai suna *HANNE*
littafine dayazo da sabon sauyi akan rubutun litattafan hausa,wanda ba kasafai aka saba irinshi ba, domin zakuga banbanci rayuwar tauraruwar littafin yazo daban da yadda ake sakawa a sauran littafai, sai kun jini.




*©Bebeelo*

DA NA KOWA NE COMPLETE HAUSA NOVELS

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *