Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, December 9, 2019

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE (DANDALIN HAUSA NOVELS)

adsense here
CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE (DANDALIN HAUSA NOVELS)

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE (DANDALIN HAUSA NOVELS)

[16/10, 19:05] Hassan Atk: *CAPTAIN_AHMAD JUNAID
_By Khaleesat Haiydar_
*Dedicated to......*
*Ya Allah! Ya Allah! Ya Allah, Ya ubangiji kamar yanda ka bani ikon fara littafin nan ka bani ikon kare shi cikin aminci da yardar ka, Ya Allah ka min katanga irin ta China da duk wani soul da xai daga min hankali a Media ya Allah ka rabani da sharrin mahassada da duk 'Yan uwana musulmai baki daya, ya Allah ka kara hada kawunan musulmai a duniya ka tsare mu a duk inda muke, Ya Allah ya ubangiji kasa mu gama da iyayen mu lafiya, kasa mu cika da imani da tsoron ka a xuciya don son ma'aiki S.A.W*
Uhnm! my greetings goes to my die hard fans nd frnds dat are alwayz their for me
My Phatiemarkh
Habibah Marafa
Hafsat (Ummu Ilham)
My Humainah bala Abkr
Eeshatullah Goni
My Maryam Aliyu
Rukky Usman
Saknah Ibrahim
Sallynah
Ummu Lailah(AY)
My Salmah
Maman Shakur
Fiddo s dangi
Waow to mention but a few, Khaleesat heart you all. Shout out to my lovely fans. Allah bar min ku.
1.....




Ya jima xaune kan darduman bayan ya kai Ayan karshe a Surah At-tawbah, ganin har shidda da rabi ya sa shi mikewa a hankali ya rufe qur'anin ya ajiye a bedside drawer, jallabiyan jikinsa ya cire ya nufi bathroom, ya dau lkci yana wanka sabulai masu dadin kamshi da shower gel duk ya cika dakin, sanye da bathrobe ya fito yana goge lallausan bakin gashin kansa da karamin towel, gaban mirror ya nufa ya dauko lotions dinsa daga tsaye nn ya shafa, yana gamawa ya jawo mayyukan gashinsa ya shafa ya shiga combing gashin nasa, closet dinsa ya bude ya fiddo well ironed wear din da xae sa dake jikin hanger, farar singlet ya fara sawa, cikin mintuna bakwae kacal ya gama shiryawa, ya dauki silver wrist watch dinsa kirar Emporio Armani ya sa, shoe rack dinsa ya nufa ya dauki bakar cover shoe kirar Haggioti ya koma gefen makeken gadonsa ya xauna ya sa bakar safarsa na kafa snn ya sa shoe din, duk wnn abinda yake kwata kwata bae da walwala, mikewa yyi ya shiga tucking din farar uniform din jikinsa kafin ya dauki belt ya sa, wayarsa ya dauka da hularsa ya koma gaban mirror ya feshe jikinsa da turarruka ya nufi kofa ya fita, Captain Ahmad Junaid kenan, A Certified seafarer (Merchant Navy) Kmr bae son taka kasa yake tafiya a makeken compound din, sai yake ga kamar yayi shekara rabonsa da gidan nasu, Where as sati biyar kawai yayi a Egypt, kai tsaye part din Hajiyarsa ya nufa, bbu kowa falon se kamshi me ddi dake tashi da ya hade da kamshin soye soyen da ake a kitchen, falonta ya nufa da sallama cikin sanyayyan muryarsa, fitowarta daga bedroom knn ta amsa sallamarsa, xama yyi kan kujera yana kallonta yace "Gud morning Mumy" ta dan yi murmushi tana kallon agogo tace "Baka makara ba, dubi har bakwae ya gota ko duk gajiyar ce haka" Shafa lallausan gashin kansa yyi yace "Jiya da headache na kwana Mumy duk na gaji" tace "Ba na baka magani ba? Baka sha bne" a hnkli yace "Na sha" tace "Toh taso mu je kayi break, sae ka kuma sha, kar ka makara" mikewa yyi ya bi bayanta suka koma falo yace "Ina su Fatima?" Tace "Sun tafi makaranta" da kanta ta jera masa breakfast kan dinning, ta hada masa tea me kauri, snn ta koma falonta dauko masa magani, ko kan ta dawo ya shanye tean, don ba da xafi ta hada masa ba sanin bae shan abu me xafi, tana tsaye kansa ya kora maganin snn ya mike yace "Mumy bari in tafi am almost late" tace "OK, amma ka shiga ka gaida 'yan gidan, tun da ka dawo baka shiga ba" bude dara daran idanuwansa yyi bae ce komae ba ya kafa hularsa sai dai da gani kasan ransa bai so ba, ta rakasa har bakin kofa don ta tabbatar ya shiga gaida mutan gidan, part din Hajiya Fati ya nufa, ya tura kofar da sallama, xaune ya sameta tana karyawa a babban falo, xaunawa yyi yace "Ina kwana Hajiya" ta dan kallesa tace "lfya lau mutan misra, an ga daman shigowa gaida mu kenan" shiru yayi bai ce komai ba sai kuma ya mike yace "Na tafi aiki" daga haka ya fice daga falon, ta bi sa da kallo ba dae ka iya gane ma'anar expression din fuskarta, ta dan yi murmushi ta ci gaba da cin kwan gabanta, Part din Hajiya Bilki ya shiga, ita kuma ya sameta tana kunduma ma 'yan aikinta xagi kmr xata dokesu, 'yar ta Sadiya na kwance tana danna waya, daga bakin kofa ya tsaya ya dan duka ya gaisheta, harara ta 6alla masa tace "Ehh lallai Ahmad a 6akin kofa ka gaida Uwarka yau d'an rainin wayo, sai yanxu kasan da mu a gidan?" Hade rae yyi wanda hkn ya kara fito da ainahin kyansa na dan fillo, tsaki tayi ta ci gaba da 6abatun ta ma 'yan aikin ya juya yyi ficewarsa, parkin lot ya nufa ya dauki motar da xae dauka ya bar compound din bayan masu gadi sun bude masa gate, today at work was so stressful for Captain Junaid don duk a gajiye yake from yesterday's journey.
Karfe biyar da 'yan mintuna ya isa gida, ya jima xaune cikin mota yana latsa waya, ganin motar da ya shigo compound din ya sa shi kashe motarsa ya fito ya rufe ya nufi bangarensa, tuni itama ta fito daga motar tare da step sis dinsa Sadiya, bin bayansa tayi tana kallonsa cikin sanyayyan murya tace "Ya Junaid Ashe ka dawo!" Juyawa yyi har lkcn bae tsaya ba ya kalleta snn ya dauke kai yana ci gaba da tafiyarsa yace "Eh!" D'aga hka ya shiga balcony din bangarensa, dariya ta ji daga sama ta d'aga kai taga Muhibba dake xaune balcony macbook dinta a gabanta tana taunar cingam ta tabe baki tace "Cusa kai ba kwarjini" Suhaima ta dauke kanta xuciyarta na tafarfasa ta nufi bangarensu kmr xata tashi sama, Sadiya tayi 'yar dariya ta rufe motar ta bi bayanta. Shi kam dakin sa ya nufa ya cire uniform din jikinsa ya shiga bayi, wanka yyi ya fito ya shirya cikin kananun kaya, jeans baki da polo blue duk hankalinsa na gun Mum dinsa, wayarsa ya dauka ya nufi bangaren ta, xaune ya sameta falo ita da kanninsa Fatima da Aysha, gefenta ya xauna yyi mata side hug ya kwanta jikinta cikin murya me shige da ta shagwaba yace "Momyna am back" Fatima ta kalli Aisha suka tabe baki a tare, Mumy kam murmushi tayi ta dauke fuskarta tace "Welcm! ga abincin ka can dinning, ga dai kannin ka suna kallon ka" yayi 'yar dariya yace "Toh ina ruwana da su" gaishesa suka yi a tare, Fatima tace "Ya A.jay ina tsarabar mu" mikewa yyi ya nufi dinning yace "Aiki na tafi ba holiday ba ai" abinci kusan kala uku ya tarar dining din, farfesun naman rago ya soma diba yana ci. Ko da ya gama bai bar dining din ba yana ta danna waya ganin shidda ya kusa ya mike ya dawo parlor yace ma momy xae je gun abokinsa El-Ameen, tace "Maimakon ka huta kai da kake ciwon kai Ahmad!" Girgixa kai yyi yace "Mum ni ba ddewa xan yi ba" tace "toh shikenan Allah ya tsare!" Bangarensa ya koma ya canxa kaya xuwa farar shirt da blue jeans ya dauki makullin motarsa bayan ya feshe jikinsa da turare ya fito ya nufi parkin lot ya dau motarsa ya bar gidan. A hankali ya rage gudun da yake ganin d'andaxon jama'ar da ke gefen titi a tsaye, da yawan motoci ma sun tsatsaya gefen titi masu shi duk sun fiffito ko wanne na son ganin abinda ya janyo taron, a hnkli ya gangara gefen titi don a tunaninsa hatsari ne kuma bae ga alamar taimako mutanen dake tsatstsaye suke badawa ba yasan kallo kawae suka tsaya yi, bude motarsa yyi ya fito ya nufi cikin taron jama'ar ya kutsa kai, sae a snn ya dinga jin ihun da wasu ke yi, wata ya gani xaune tsakiyar taron hannunta rike da wani yaro da baxae wuce shekaru goma ba sae dukansa take iya karfinta, ga jini na xuba goshinta ba kadan ba, duk tayi dukun da daud'a cikin wata yagaggiyar doguwar riga, wasu samari biyu ne ke kokarin kwace yaron dake kurma ihu hannunta amma sbda irin rikon da tayi ma yaron suka kasa, da ganinta ka ga mahaukaciya, karasawa Junaid yyi da sauri inda suke ganin xata ma yaron lahani ya fixgo gashin kanta da yyi wani dukun dukun da datti, ta saki kara don ba rikon wasa yyi ma gashin ba, amma duk da hka ta ki sake yaron, kara damke gashin yyi da karfi ae ba shiri ta sake yaron tare da kwala wani k'aran, samarin biyu suka dauke yaron da ya rage kiris ya suma don wahala, ta yunkura xata cakume Junaid, ae da sauri ya hade hannayenta da karfi ya murda su xuwa bayanta, ta dinga ihu tana shure shure, kallon samarin gun yyi yace a samo masa igiya, ae da sauri suka juya xuwa neman igiyan, wata 'yar dattijuwa dake cikin taron ne tace "Baiwar Allahn nn ta kusa shekara unguwan nn bata taba kama d'an mutum tayi masa haka ba sae wannan karan, kuma wllh yaran ne suka addabeta da tsokana shi yasa tayi hkn" wata mata ta karbe tace "Yo dama idan ba tsokanarta suka yi ba me suka mata, dubi goshinta dutse suka jefa mata, yara basa ji sae daukan magana da tsokana, ni ko kadan ban ga laifin Baiwar Allahn ba, sae ma tausayin da ta ban, haba jama'a" nan dae aka dinga jajantawa, ko wa na fadin albarkacin bakinsa, shi dae yana rike da hannunta ta baya, ta sunkuyar da kai, duk farin shirt din jikinsa ya bace da datti, samarin ne suka dawo da igiya babba, da taimakonsu ya shiga daure mata hannu da kafa, ba karamin kokuwa suka sha da ita ba yyi mamakin karfinta hka, Suna gama daureta ya koma baya yana kallonta don ganin ko xata iya kuncewa, hawaye ne ke sakkowa daga idonta, jikinsa ne yyi sanyi yana kallonta, lkci daya tausayinta ya ratsa sa, a hnkli ya shiga kakkabe hannunsa, idonsa ya kai kan goshinta da har ya gaji da fidda jinin da yake ya daskare, ya girgixa kai yana kallon samarin yace "Ku taimaka a sa min ita a mota in kai ta a duba goshinta" 'yar dattijuwar daxu tayi wani k'ara tace "Wani asibitin yaro? Ynda Duniyar nn ta dawo ba gskya ynxu, kai waye? Kuma d'aga wani anguwa kake?" Nan jama'a suka fara cece kuce a wajen ana kallonsa, shiru yyi bae ce komae ba, can ya sauke ajiyar xuciya ya juya ya nufi motarsa cikin rashin kuxari, nn aka bi sa da kallo ana cewa "Kun ga rashin gskyar knn, don da yana da ita da dole xae tsaya ya amsa tambayoyin da aka yi masa, kaiii Allah ya raba mu da sharrin mutum" shi kam motarsa ya shiga ya ja ya bar wajen, nan aka fara watsewa kowa na fadin albarkacin bakin sa, wani tsoho ne ya karasa ya kunce mata daurin yana d'an ja da baya kadda ta cafkesa har ya gama ya bar wajen bata d'ago ba bare ta kallesa.
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
6.....
El-Ameen ya juya yana kallon Junaid ganin ya ki karasowa da karfi yace "baxa ka xo ka ga abinda mahaukaciyar da ka sa na kawo gidana tayi ba, ya Salam!" Junaid na jin hka ya karaso da sauri yana leka parlon, kwalalo ido yyi yana kare ma palon kallo, palon komawa yyi kamar wanda aka yi karamin yaki, don duk ta tarwatse plasman palon da frames gaba daya, lafiyayyen centre table din ma bata raga masa ba, ko ta ina kwalabe ne a falo, duk ta tuttuge labulaye da karafunansu, kujeru kam upside down ta juyasu dukka, Junaid bae san lkcn da ya fashe da dariya ba har da rike ciki, El-Ameen ya bude baki yana kallonsa idon nan nasa ya kada, fixgosa yyi yana huci yace "Yhu see wat you've caused koh Ahmad, gud! this mad woman is adding not a minute more in my house" yana fadin hka ya turasa ya shiga palon, da sauri junaid ya hadiye dariyarsa ya rikosa yace "Haba frnd, Chill plss ka mance mahaukaciya ce ita kamar yanda kake kiranta, I promise wllh duk xan siya maka abubuwan da tayi damage, that's a promise frnd!" marairaice masa Junaid yyi yace "Plss!" El-Ameen yyi kwafa yace "Yanxu naji bayani, kuma ga motata ma can a gida bbu kyan gani, kasan yanda xa kayi da shi, I need it the way it was before, nd don't forget it's my favourite car" Junaid yyi murmushi yace "Kar ka damu xa a gyara" El-Ameen yace "Gud! Kuma ynxu idan mu ka shiga naga tayi fitsari ko otherwise wllh kai xaka gyara min waje" Junaid ya d'aga kafada yace "Na yarda" Nan El-Ameen ya sa kai ya shiga falon yana bin ko ina da kallo, sae a lkcn ya kula da jinin da yayi littering din falon alamar duk ta ji ciwo, kamar ance ya kalli bayan kofar falon ya ganta durkushe wajen duk jini jikinta, suna hada ido ta mike da sauri xata yi waje ya yamutse fuska ya fixgota da karfi, kokuwa ta shiga yi da shi ya mata wani lafiyayyen rankwashi ae sae ga hawaye a idonta tana kallonsa, Junaid da yyi shiru yana kallonsu a hankali yace "Haba El-ameen rankwashi kuma?" Ko kallonsa El-Ameen bae yi ba, ya ja ta suka koma sama xuwa dakin da aka ajiyeta, bude baki yyi ganin duk ta fasa glass din windunan dakin ma, ita nan duk neman hanyar fita take, kwalo ma Junaid kira yyi da karfi, Junaid ya nufi stairs da sauri ya haura ya shiga dakin, El-Ameen na huci yace "Ohh my God! Dubi windows dina Captain" Junaid ya langwabar da kai yace "Duk xan gyara maka as soon as possible" El-Ameen yyi kwafa yace "Allah kar ya wuce kwana biyu, kuma ni ka xo ka ajiye mata abincin my frnd, I have important things doing a office" karasowa Junaid yyi ya ajiye abincin ya bude yana kallon yanda ya rike hannunta gam sai mutsu mutsu take, El-Ameen ya kai ta k'asa ya nuna ta da yatsa yace "Wllh Kika sake min barna a gidana sae na gaggalla maki mari, wawiya kawai" ita dae kanta na k'asa, tsaki yayi ya mike yana kallon Junaid yace "Mu je plss malam gashi ka kawo mata abincin hankalinka ya kwanta" Junaid yace "But ya kamata mu samo 'yar dattijuwa yanxu koh?" Wani kallo El-ameen yayi masa yace "Ya kamata dai ka samo" daga haka ya fice daga dakin, Junaid ya bi sa da kallo sannan ya kalleta, har lokacin bata d'ago ba, abincin ya matsar mata gabanta a hankali yace "Ki ci abinci kin ji, we are only helping yhu Baiwar Allah" ita dae kanta na kasa sai d'ada takurewa waje daya take, kwala masa kira El-Ameen yyi ya fito da sauri, El-Ameen ya sa ma dakin key yace "barnan ya tsaya iya dakin" shi dae Junaid bae ce komae ba har suka fito, El-Ameen ya tafi gun tap din dake compound din gidan ya wanke hannunsa yana tsaki ya nufi gate Junaid na bin bayansa, a cikin mota El-Ameen ya ciro waya ya shiga neman nmbr, yana dialing ya sa hands free, sallama aka yi masa ya amsa yace "Jibril kana ji na," d'aga daya bangaren aka ce ehh oga, yace "Gud mai gadi nake son ka samo min nan da 'yan awanni don Allah, wanda ka sani kasan halinsa fa" D'aga daya bangaren aka ce "Toh oga, in'sha Allah xa ayi hkn" katse wayar El-Ameen yyi, Junaid ya tada motar suka bar layin, sae da ya fara ajiye El-Ameen clinic bbu wanda yace ma kowa komae, yana fice masa a mota ya ja motar ya nufi office shima, El-Ameen yyi murmushi yace "Ina xaune xa ka dawo ka same ni ne ae"
Karfe hudu da rabi Junaid ya koma gida daga gun aiki, tunaninsa daya karyar da xae ma Mumy ta bar shi ya fita, don ryt from time shi ba mae xuwa ko ina bane daga gun aiki sae gida sai in kuma yaje kallon kwallo shi ma ba ko da yaushe ba don yafi son kallon a gida, ko da yaushe yana manne da ita shi dai, yawanci ma El-Ameen ne ke xuwa gidansu shi bae fiye xuwa can ba sosae, yana xaune bangaren Mumy bayan ya gama lunch, ita kadae ke hiranta sai fatima dake ta shirin islamiyya, shi kam duk hankalinsa baya tare da shi kawae ya kafa ma tv ido ne kmr me kallo, agogo ya duba ya ga har biyar, ya fiddo waya ya kira lambar driver yace ya xo ya samesa bangaren Mumy, ba a dau lkci ba drivern ya xo, Junaid ya ciro dubu goma ya mika masa yace "Gashi wannan ka siyo fruits din dare kamar ynda kake siyowa ka kai ma kowa nasa" Drivern ya risina ya karba yace "Toh yallabai," Junaid ya ciro Atm dinsa yace "ka d'an biya Atm Machine ka ciro min dubu talatin" Drivern ya karba yace "In'sha Allah yallabai" yana fita Mumy tace "Me xaka yi da dubu talatin Junaid" Junaid yace "Su Umma xan ba ko suna bukatar abu kafin Abba ya dawo jibi" Mumy tace "Ohk Hakan yyi" yana xaune sae kallon agogo yake a kai a kai har Ishaq ya dawo da ledoji hudu dauke da fruits kala kala, ya ajiye ma Mumy nata snn ya ciro 30k ya mika ma Junaid, Junaid yace "Yauwa ka raba dubu sha biyar biyar ka kai ma Hajiya daya Umma daya" Mumy tace "A'a kai ya kamata ka kai masu" bae yi musu ba ya karbi kudin hannun Ishaq, Mumy tace "Ajiye naku fruits din ka fara kai masu nasu" Ishaq ya ajiye leda daya ya fita da biyu don kai ma Umma da Hajiya, ba a dau lkci ba ya dawo ya dauki nasu ledan na masu gadi da masu wanki da share sharen gidan ya fita don xuwa su raba bayan yyi godiya. Junaid ya kalli Mumy yace "Mumy xan je gidansu El-Ameen!" Mumy tace "Gidansu El-Ameen kuma, wae wnn sintirin xuwa gidansu El-Ameen da kke kwana biyun nn kalau kuwa Ahmad? Ko dae gun budurwa kake xuwa?" Ta kare maganan tana murmushi, Dariya yyi ya shafa kansa yace "Kai Mumy budurwa kuma, shi dae nake rakawa fa" Mumy na murmushi har lkcn tace "uhn uhn kai dae fadi gskya Ahmad" ya shagwabe mata yace "Mumy ni da gske wllh ba gun budurwa nake xuwa ba, El-Ameen nake raka wa" Mumy tace "In ma gun ta kake xuwa ae ba laifi bne Ahmad, it's high time yhu start planning of settling down with a wife yanxu son" murmushi yyi ya mike yace "Allah ya kawo lkci mumyna" tayi murmushi tace "Toh Ameen" yace "Bari in kai ma su Umma kudin Mumy, daga can xan wuce" Mumy tace "Toh Allah ya tsare kar dae ka yi dare plss Ahmad" yace "In'sha Allah mum" daukan wayarsa yyi ya fita daga falon, gun Umma ya fara shiga ya samu Muhibba ce da wata kawarta a falon, ya wani hade rae ba tare da ya damu da amsa gaisuwar da suka yi masa ba ya mika mata 15k din yace "Gashi ki ba ma Umma" juyawa yyi ya fice daga falon, Kawar Muhibba me suna Salima tace "Kai amma wllh kina bada mata Muhibba, har wannan dan karamin alhakin ne xaki dinga barin yana walakanta ki don yana da kyau, ubansa kuma na da dukiya, sae kace ba gogaggiyar 'yar jami'a ba?" Muhibba tayi murmushi tace "Baki san Ahmad bane Salim, ya fice tunanin ki wllh...." Salima ta katse ta tana kalle kalle tace "Da'alla banxa tsaya ki saurareni, mu je daki in baki wani plan ki ga ko baxae yi aiki ba" mikewa Muhibba tayi suka yi daki da kawar tata cike da xumudin jin plan din. Junaid na fita bangaren Hajiya ya nufa ita ma ya bata kudin, tana jujjuya kudin tace "Duk kudin da Alhaji ya bari Ahmad ka rasa abinda xaka kawo min sae wani shegen dubu sha biyar, wato sauran kuma ka ba uwar ka koh, toh wallahi ka ji tsoron Allah don hakkinmu baxai bar ka ba" Junaid ya daga kafada yace "Ni Abba bae bar min kudi ba, kawae gani nayi hakan ya dace shi yasa na kawo maki na kai ma Umma don ko mahaifiyata ban ba kudi ba gidan nn, gobe ko jibi ae Abban xae dawo, in kina da wani bukatar da ya wuce na wannan idan ya dawo sae ki tambayesa" yana kai wa nn ya fice mata daga palo, ta bi sa da kallo baki bude, idonta ya kankance don bacin rai, rufe bakin tayi tana gyada kai tace "yaro yaro ne" kwafa tayi ta juya ta koma don ci gaba da abinda take tana wani murmushi. Karfe shidda saura Junaid ya isa gidansu El-Ameen sanin ya baro clinic yanxu, Mum din sa ya samu falo, bayan sun gaisa yace "Ummi El-Ameen ya dawo koh?" Hajiya Maryam da ake kira da Ummi tace "Ehh ya dawo daxu amma ya fita yanxun nan, ka kira sa kaji inda yake don nasan baya asibiti" Junaid yace "Toh shknn Ummi xan kirasa, ni xan koma" Ummi tace "Toh ko ruwa baxa ka sha ba Ahmad?" Yyi murmushi yace "Alhmdllh Ummi" Ummi tayi murmushi tace "Toh ka gaida min Hajiya Amina" yace "Xata ji Ummi" fita yyi daga falon yana tunanin inda El-Ameen ya tafi, sae da ya shiga mota snn ya kirasa, bugu daya ya d'aga Junaid yace "Kana ina ne?" El-Ameen yace "Au! ai nayi xaton xuciya kayi ka bar ni da mahaukaciyar taka" Junaid yyi tsaki yace "Kana ina nace?" Dariya El-Ameen yyi yace "Kai dae duk abun ka baxa ka iya xuciya da ni ba wllh, come over ina gidana, na samo mai gadi, ya kuma min hanya an samu wata dattijuwa, we are ol there 2gether ynxu, mind yhu duk wata xaka dinga biyan mai gadin dubu 30, ita kuma warce xata tsaya da mahaukaciyar xa'a bata dubu 50 monthly, coz its not an easy job, ga kuma risk din dake tattare da job din, and yhu make sure ka shiga kasuwa ka siyo mata kayayyakin da xata dinga sawa including inner wears" Junaid yace "Ni ban san inda ake sai da kayan mata ba" El-Ameen yace "So? Ba sae ka ce a raka ka ba, ko ka shiga kasuwar kayi tambaya" tabe baki Junaid yyi ya katse wayar ya kama hanyar gidan. A waje yyi parking ya shiga, sabon mai gadin da ke xaune compound din ya gaishesa da ladabi, Junaid ya amsa ya nufi kofar shiga palo, daga bakin kofar ya tsaya yana kare ma palon kallo, duk an share barnar daxu ko ina yyi fess, kallon El-Ameen dake xaune kan daya daga kujerun falon yana danna waya yyi snn ya karasa shiga falon, El-Ameen ya kallesa yace "Kayan fa, ni fa I can't put her under medication da suturan jikinta, it's very irritating, na dae yi mata alluran barci daxu don ban ga alaman tana yi ba" Junaid ya xauna gefensa yace "Toh don Allah ka raka ni mu siyo kayan mana, serious ban san ina xan samu women wears ba" El-Ameen yace "Nace idan ka shiga kasuwar kayi tambaya mana sae kace ba wayayye ba" shiru Junaid yyi yana kallonsa, wata yar dattijuwa ce da baxata haura sittin ba ta fito daga kitchen da alama ita ce ta yi gyaran gidan gaba daya, gaishe da Junaid tayi, yyi murmushi yace "Sannu da aiki mama" mikewa El-Ameen yyi ya haura sama ba a dau lkci ba ya sakko rike da sabulan wanka tsadaddu da sponge, sae toothbrush da toothpaste yana kallon dattijuwar yace "Mama ga wannan, wanka xa ki taimaka kafin mu dawo, xae kai maki ita bayin yanxu," Matar tayi shiru tana kallonsa sae dae da ganinta kasan a tsorace take, El-Ameen yyi dariya yace "Babu abinda xata maki wllh mama, bacci ae take kuma baxa ta tashi ba yanxu, mu je ki ga" bin bayansa tayi suka haura sama, Junaid ya bi su da kallo kafin ya shafa kansa, El-Ameen ne ya fara shiga dakin snn ita ma ta shiga, tana nan kwance yanda ya bar ta bayan yyi mata allura, idanuwanta duk a rufe, kallon dattijuwar yyi yace "Kinga bacci take ko mama, kuma na gaya maki baxa ta tashi ba sae bayan awanni takwas," kai kawae ta gyada masa, bayi ya nufa ya hada ruwan dumi da yawa snn ya fito dakin ya dauketa ya nufi bayin da ita ya kwantar da ita kasan neat bathroom din ya fito yana kallon tsohuwar da ya sa ma Mama yace "Gata can na kai maki bayin, don Allah ki wanke mata wannan gashin da kyau mama, nasan baxa kiyi wahalan fito da ita ba idan kin gama don bata da nauyi, xan fito maki da bargo kawae ki lulluba mata har mu dawo da kaya" tace "Toh yaro" juyawa yyi ya fita ta nufi cikin bayin. Siyayya ba kadan ba Junaid yyi ma Mahaukaciyar, tun daga kan normal English wears wato dogayen riguna, xuwa mayyukan shafawa, turarruka, da inner wears da jallabiyoyi, har man gyaran gashi da combs duk sae da ya siya da takalma sae huluna da 'yan kunnaye, shi dae El-Ameen bin sa kawae yake yana dariya, ganin har xa ayi magrib yasa El-Ameen yace "Kai koh kayan lefe kake hadawa fa sae haka Junaid, for God's own sake kayan nan sun isa haka it's time for magrib" Junaid ya kallesa yace "Ohk" Karfe bakwae da rabi suka isa gida, shi ma don sun tsaya hanya sun shiga masallaci sun yi sllh snn sun tsaya eatry siyan abinci, xaune suka samu dattijuwar a falo kan dankwalinta alamar sllh ta idar, tayi masu sannu da xuwa, Junaid ya ajiye kayayyakin hannunsa, El-Ameen ya bude wani leda ya fiddo doguwar riga da man shafawa da na kai sae inner wears da turare ya mika ma matar yace "Gashi mama ki taimaka ki sa mata" ta mike tace "Toh" sannan ta karbi kayan ta haura sama, durkusawa tayi gabanta ta yaye bargon da ta rufe ta da shi ta bude tsadadden man da aka bata ta shiga shafa mata jikinta, cikin mintuna da basu fi goma ba ta gama shiryata, ta debi hair cream me yawa ta shafa mata a dogon gashinta sannan ta shiga taje gashin a hnkli saboda tsantsin sa, tana yin haka hawaye na xuba idonta kmr daxu da take mata wanka, rayuwa kenan duk yanayin da ka tsinci kan ka ka gode Allah, Coz he knows best, shi kadae yasan dalilin barin wannan Baiwar Allah haka, ba wae kuma don baya sonta ya bar ta a hakan ba, har ta gama tufke mata dogon gashinta da ya kusa bayanta hawayenta bae tsaya ba, gyara mata kwanciya tayi ta rufa mata bargon ta fito tana kallonsu El-Ameen tace "Na gama" El-Ameen ya mike yace "Kin sa mata komae dae koh mama" tace "Na sa mata" yana 'yar dariya yace "Kin tabbata mama" murmushi tayi tace "Na sa mata komai yaro" kallon Junaid yyi sannan ya nufi stairs, Junaid ya mike ya bi bayansa, El-Ameen na shiga dakin ya karasa gabanta ya durkusa ya yaye bargon dake jikinta a hankali, rike breath dinsa yayi yana kallonta ko kiftawa bae yi har Junaid ya shigo ya same sa a hka, shima ya durkusa a hankali nan gabanta yana kallonta.
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: *CAPTAIN  AHMAD JUNAID
_By Khaleesat Haiydar_
2....
Junaid na isa gidan su El-Ameen yyi parking daga waje ya shiga, Sumayya kanwar El-Ameen ya samu xaune falo da kawayenta biyu, ya karasa cikin falon cikin tafiyarsa ta k'asaita, yi tayi kmr bata gansa ba ta ci gaba da ba kawayenta labarin da take, gaida shi kawayen nata suka yi suna kallonsa, don Capt Junaid ko namiji bae masa kallo daya, ya amsa gaisuwar su ba tare da ya dube su ba yana kallon Sumayyar yace "Ke yayanki na gida?" Ba tare da ta kallesa ba tana yatsine fuska tace "Nima bn sani ba" wayarsa ya ciro aljihunsa ya shiga kiransa, Kawayen nata biyu duk suka xuba masa ido, El-Ameen na d'agawa Junaid yace "are yhu at home?" El-Ameen yace "Yea are you coming?" Wani kallo ya watsa ma Sumayya ya katse wayar ya nufi dakin El-Ameen, Husnah ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Kai Sumayya waye shi, ya hadu wllh, don Allah ni dae ki hada ni da shi, yyi min ni dae plss" Sumayya tayi dariyar rainin hnkli tace "Uhm Kinga gayen nn irin mace masa da nake a da, na so shi kmr raina amma he looked into my face nd told me baya sona, I cried my life dat day, gashi i downgraded my sef telling him I love him" bude baki duk suka yi suna kallonta, Fiddausi tace "Tabdi! Toh meye hadin ku da shi? D'an uwanku ne?" Tsaki Sumayya ta ja ta dauki lemon gabanta ta shiga sa. Xaune ya samu El-Ameen kan laptop da siririn farin glass a idonsa yana danne danne, El-Ameen ya kallesa yace "Uhnn! Our great Capt Ahmad Junaid Murnai, kaga yanda ka kara kyau ka koma kamar wani Egyptian kuwa" Junaid ya tabe baki ya xauna gefen makeken gadon dakin yace "You will neva change" El-Ameen yyi murmushi ya tura laptop din gabansa ya juya yana fuskantarsa yace "I missed you a lot frnd, am glad you are back" Junaid ya shafa kansa yace "Sai kace gaske," El-Ameen ya kura ma farin shirt din jikinsa ido yace "Wait! Ciwo ka ji Captain" Junaid ya kalli shirt dinsa da sauri ya ga jini daga gefen shirt din, El-Ameen ya mike yace "What's dat? The shirt looks dirty ma" girgixa kai Junaid yayi ya shiga unbuttoning din shirt din yace "Wata mahaukaciya ce wllh" El-Ameen ya kwalalo ido yace "Mahaukaciya kuma" Junaid yace "Yea!" Nan ya ba El-Ameen lbrin abinda ya faru a hanyarsa ta xuwa, El-Ameen yace "Eyya! Poor her, but kai me ya kai ka rike mahaukaciya ma banda abun ka" Junaid bae ce komae ba ya mike ya nufi bathroom, wanka yyi ya fito sanye da Bathrobe din El-Ameen ya goge jikinsa ya bude wardrobe ya fiddo wasu kayan abokin nasa ya sa. Bayan Magrib yace ma El-Ameen xae koma gida, El-Ameen yace "Haba frnd baxa ka raka ni gun Iman ba plss, wllh ban san me xan ce ba idan na je, gashi Mami fushi take da ni, escort me plss, dama jira nake sai ka dawo sai mu je" Junaid yyi d'an murmushi yace "Ohk buh bari in kira mumy kar taji shiru har ynxu" Bayan isha suka bar gidan bayan Capt Junaid yyi ma Ummin El-Ameen sallama, A motar Junaid suka tafi El-Ameen na tukin, El-Ameen ya lura da yanda Junaid ya kafa ma tagar motar ta inda yake xaune ido yana kallon waje, El-Ameen xae yi magana ya ji Junaid yace "Dr d'an tsaya nn don Allah in ga ko an kwance mata igiyar, it's gud ace anyi hkn" El-Ameen ya kafa masa ido sae kuma ya tabe baki ya daga shoulder ya gangara gefen titi yyi parking, Junaid ya bude motar ya fita, tana nn xaune kan bolan, rike da wani bakin Leda a hannunta, rungume hannayensa yyi yana kallonta, El-Ameen ya dafa sa yace "let move on Capt, they've freed her" juyawa Capt Junaid yyi suka koma motar suka bar wajen, suna isa gidan El-Ameen ya kira Iman da nmbr da Ummi ta basa, kanwar ta ce ta fito tayi masu iso har falo ta cika su da drink, mahaifiyarta ta fito suka gaisa ta bar palon, ba a dau lkci ba Iman ta fito sanye da wata doguwar riga me adon stone blue da gold, tayi rolling kanta da plane blue mayafin kayan, kyakkyawa ce ba kadan ba, ta karaso falon kamshin turarenta ya cika ko ina ta xauna, kallon Junaid El-Ameen yyi, Junaid ma ya kallesa, suka shiga kallan kallo, ganin El-ameen yaki cewa komai Junaid ya d'an yi gyaran murya yana kallonta yace "Ina yini Hajiya" amsawa tayi ba tare da ta kallesu ba, Junaid ya d'an taba El-ameen alamar yyi magana mans, a hnkli El-Ameen ya matso kusa da shi murya can kasa yace "Me xan ce mata plss" ae Junaid bae san lkcn da ya fashe da dariya ba, El-Ameen ya tsaya kallonsa sai shi ma ya saka dariyar, nan suka dinga dariya kamar tababbu suka yi me isan su suka yi shiru, Junaid ya shafa kai yana kallonta yana murmushi yace "Ehm dama Ummi ce tace in rako El-Ameen wajen ki.... Shine muka xo" El-Ameen yace "Eh Ummi ce tace in xo gurin ki shine ya rako ni" kala bata ce masu ba, Junaid ya mike yace "Toh shknn mu xa mu koma sai mun sake dawowa" El-Ameen ma ya mike yace "Eh xa mu koma, sae wani lkcn, mun gode kwarai" mikewa tayi tace "Allah ya kiyaye" daga haka ta haura sama ta bar su tsaye parlon, dariya suka dinga yi cikin motar barin Junaid, El-ameen ya ja motar suka bar anguwar daga karshe, sae da El-ameen ya kai kansa gida sannan ya fita suka yi sallama Junaid ya koma driver seat ya ja motar ya bar layin, yana isa inda mahaukaciyar take yyi parkin yana kalle kallen inda xae ganta daga cikin motar, sae bae bae ganta ba ya ja motar ya nufi gida. Yana jiran masu gadi su bude masa gate kiran mum dinsa ya shigo wayarsa, jan motar yyi ya shiga compound din ya nufi parkin lot yyi parking snn ya fito, ganin motar Abba yasa shi kallon agogon wrist dinsa ya ga har goma ya kusa, bangaren mumy ya nufa, tsaye ya sameta palo tana rike da wayarta ta rungume hannu, yyi murmushi yace "Ga ni na dawo Mum," ta hade rai tace "Daga ina kake hka Ahmad?" Ya shafa kansa yace "na gaya maki Gidansu El-Ameen na tafi mum, na raka sa xance ne" yana murmushi ya k'are maganar, mumy tace "Zance! Lallai ba ayi abun arxiki ba kenan" dariya yyi lkci daya ya hade rai yace "Allah mum mun yi magana me ma'ana, infact ni ne ma nayi don shi shiru yyi wai kunya" Mumy tayi dariya tace "Au, kace ka kora masa budurwar knn in har kai kayi magana, tab!" Dariya shi ma yyi ya mata side hug yace "Kai Mumyna ni din ne ban iya magana ba" murmushi tayi tace "Kaje gun Abba yana neman ka" ya saketa yace "Ohk Mum" kofar da xae sada sa da part din dad dinsa ya nufa, xaune ya samesa babban falonsa yana kallon news lkci daya yana shan fruit salad din dake kan d'an table gabansa, Hajiya Fatee na xaune gefensa, sae step sisters dinsa su uku gaba daya suna palon, xaunawa yyi kasan lallausan rug din yana kallon Abbansa yace "Barka da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa daga ina kake naga baka duty ae" yace "Naje gidansu El-Ameen ne Abba," kallon Hajiya Fatee yyi yace "Ina yini Hajiya?" Tayi murmushin da bai kai ciki ba tace "Lfya lau, ya aikin" yace "Alhmdllh" Muhibbah ce ta shigo falon da sallama rike da bowl din kankana da akayi slicin, ta duka ta ajiye gefen Abba, xama tayi tana kallon junaid da ya maida hankalinsa kan Tv tace "Ina yini yaya" amsawa yyi ba tare da ya kalleta ba, Hajiya Fatee sae kallonsa ta gefen ido take, mikewa Junaid yyi yace "Sae da safe Abba" Abba yace "Yauwa ka ba Muhibbah dubu ashirin xa tayi amfani da su a makaranta gobe wae," yace "toh Abba" daga nn yyi ma Hajiya Fatee sae da safe, kanninsa ma suka yi masa sai da safe ya fice daga falon rai a bace, mikewa Muhibba tayi ta bi bayansa, bae tarda mumy a palo ba, hka yasa ya nufi bedroom dinta ya sameta har ta kwanta, xauna wa yyi daga gefenta yace "Kin kwanta mum?" Tace "Har ka fito?" Yace "Eh mum" peck din goshinta yyi yace "Gudnyt mum, xan tafi in kwanta" tace "Toh Allah tashe mu lfya, make sure kayi alwala kayi addu'a kafin ka kwanta" yace "In'sha Allah mum" mikewa yyi ya kashe mata wutan dakin ya rufe mata kofa ya fita, dakin da kanninsa suke ya bude, Aisha ce ke waya ita ko Fatima tayi bacci, ya rufe kofar ya fito parlor, xaune ya tarda Muhibbah tana jiransa, yyi mamakin rashin ganin Hijab a jikinta don da hijab ta shigo palon Abba, kauda kai yyi ya fita daga parlon ta mike ta bi bayansa, yana isa part dinsa ya bude ya shiga ya juya yana kallonta ganin tana kokrin shigowa yace "Ki jira ni a nn malama" rufe kofar yyi, ta hade rae ssae tana kallon kofar, tsaki tayi ta bude ta shiga, ganin bae palon ta nufi bedroom dinsa, ya dauko kudin zae fito suka kusa cin karo, wani tsawa ya daka mata yace "Are yhu insane xa ki biyo ni daki" kallonsa ta tsaya yi, yyi tsaki ya bangajeta ya fice a fusace, bin bayansa tayi ba tare da ta ji haushi ko kadan ba, a palo ya jefar da kudin ya nufi kofa ya bude yace "Leave yanxu!" D'an tsaki tayi ta duka ta dauki kudin ta fice, ya kulle kofarsa ya sa key don wani mugun haushinta yake ji a gidan. K'asa bacci yyi daren ranan, duk juyin da xae yi sae mahaukaciyar nn ta fado masa, hankalinsa ne ya tashi don shi dae bae mata komae ba illah taimakon yaron da yyi, mikewa yayi daga karshe ya nufi bayi ya dauro alwala ya fito ya shimfida pray mat ya shiga nafila, sae kusan Karfe uku da rabi bacci ya daukesa. Da asuba ruwan sama ya sakko kamar da bakin kwarya, kmr jiya yau ma bae fita mosque sllhn asubahin ba sbda ruwa, ruwan dumi ssae ya hada yyi wanka don ko kadan bae son sanyi shi, ya shirya cikin uniform dinsa ya dauki babban kadigan na uniform me kalan Navy blue ya sa snn ya fito falo rike da rain coat dinsa, sae da ya tabbatar wayoyinsa na aljihun wandon uniform din jikinsa snn ya fito balcony ya saka rain coat din da hulansa ya nufi bangaren Mumy, a balcony ya cire rain coat din ya bude kofa ya shiga, tana kitchen da mai aikinta sai fatima suna hada breakfast, ya shiga kitchen din ya gaisheta ta amsa da cewa "Ka tashi lfya, ya ruwa?" Yace "Alhmdllh mumy" Fatima ta kallesa tace "Gud morning ya Ahmad" yace "Morning" ya fita kitchen din, tea kawae ya sha da kwae shi ma sae da mum ta takura sa wae ya makara xuwa aiki, har balcony ta rakosa tace "Baxa ka shiga gaida 'yan gidan da Abba ba kenan" ya dan tsuke fuska yace "Am late mum," tace "Toh Allah ya tsare" rain coat dinsa ya sa yace "Ameen" snn ya nufi parkin space, kusan a tare suka jero da Suhaima dake rike da lema tayi shirin makaranta, ko kallonta bae yi ba ya bude motarsa ya shige ta nufi tata motar tana kallonsa, jan motar yyi ya danna horn aka bude masa gate ya fice. A hnkli ya ke driving din har ya iso inda mahaukaciyar jiya take, samun kansa yyi da parking gefen titi yana kalle kallen inda xae ganta idonsa ya sauka kanta, xaune take cikin ruwan ta hade kai da gwiwa, duk ta jike da alama tun da ruwan ya sauko bata bar wajen ba, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujera yana ci gaba da kallonta, duk jikinsa yyi sanyi, da kyar ya iya jan motarsa ya bar wajen ganin yana bata lkci, shi mutum ne me tausayi da raunin xuciya kamar mace, har ya isa office bae da sukuni, colleagues dinsa duk suka lura da shi suka kuma tambayesa ko Lfya yace bai jin ddi ne, Karfe biyar saura ya bar gun aikin, driving kawae yake cikin rashin kuxari, bae bi hanyar da xae ga mahaukaciyar ba ya canxa hanya, ko parking din arxiki bae yi ba ya bude motar ya nufi part din mumyn sa, kwanciya yyi kan dogon kujera ya rufe idonsa gam, Mumy ce ta fito daga kitchen ganinsa a kwance tace "Lfya Ahmad" jin bae ce komae ba yasa ta karasa kusa da shi tace "Ahmad!" Bude idonsa da ya kada yyi ya mike xaune ya dafe kansa, taba jikinsa ta shiga yi da damuwa tace "baka da Lfya ne?" Lumshe ido yyi ya kwanta jikinta ta rungume sa tace "Talk to me mana son, me ya faru?" A hnkli yace "Kai ne ke man ciwo Mumy" tace "Ci abinci mu tafi asibiti" da sauri yace "No mum, xan sha magani" hade rai tayi tace "Wani maganin xa ka sha, sau nawa kke sha bae maka aiki ba, so kake ka dauko min magana gun Abba koh" shiru yyi ta mike ta nufi dinning ta dawo rike da kulan abinci da plate da spoon, fried rice din ta dibar masa ta ajiye snn ta koma kitchen ta hado masa tea, bae son mum din tasa ta daga hankalinta shi yasa ya daure ya dinga cin abincin don kwata kwata bae da appetite. Mikewa yyi da ya gama Mumy tace "Ka tafi ka canxa kawae mu tafi clinic" yace "Toh" snn ya fita xuwa bangarensa, wanka yyi ya canxa uniform din jikinsa xuwa kananun kaya, ya d'an kwanta yana tunanin karyar da xae ma Mumy ta hakura da xuwan su asibiti, dubara ce ta fado masa ya mike da sauri ya dauki wayarsa ta fita, xaune ya sameta palo ta shirya tana jiransa, murmushi yyi yace "Mumy ynxu El-Ameen ya kira ni, I told him m nt ok, shine yace I shud cum over ya duba ni" hararansa Mumy tayi tace "Yhu should come over dai kuyi hira, my frnd mu wuce clinic" marairaice mata yyi ya mata side hug yace "Haba mum, ga ni da amini likita kice mu je clinic, kinga baxae ji ddi idan ban je ba plss"
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
5.....
Falo El-Ameen ya sakko ya samu Junaid tsaye bayan kujera yana kallon mahaukaciyar, El-Ameen yace "Toh ae sae ka dauketa ka kaita spare room ka ajiye ta ka kunce rope din" karasawa falon Junaid yyi, yyi yanda El-Ameen yace masa, yana kunce igiyar a daki ya fice da sauri ya ja kofar, kulle kofar palon El-Ameen yyi bayan sun fito, har lkcn ruwan da ake bae tsaya ba, El-Ameen ya d'an yi tsaki ya sa kai ya shiga ruwan ya nufi gate, bin sa Junaid yyi a baya ba tare da ya damu da hakan ba, sae a snn ya dinga jin sanyi na shigar sa ba kadan ba, El-Ameen ya kulle gate din daga waje bayan sun fito suka shiga mota, suna hawa kan titi El-Ameen yyi murmushi ganin yanda Junaid yake rawan dari, yyi kwafa yace "Ai baka fara rawan sanyi ba tukun malam, sai randa 'Yan gidan ku suka samu labarin mahaukaciyar nan I assure you oven ma yyi kadan yasa ka daina rawan sanyi" Sharesa junaid yyi, El-ameen yyi dariya yana kallonsa yace "Mu je can gidanmu, idan ya so da asuba sae ka koma gida, don kana komawa gida ynxu Mumy ta kama ka har duka na tabbata xata iya maka, ni kam na girma bbu abinda Ummina xata ce min" yana maganar ne yana kyalkyala dariya, shi dae Junaid bae tanka sa ba don sanyin da yake ji ma kadae ya ishe shi, kuma yasan gskya ya fadi yana komawa gida ynxu Mumy xata daga hnkli baxa kuma ta barsa ba sae ya fadi daga inda yake cikin ruwan nn. El-Ameen na gama parkin a parking lot din gidansu ya juya yana kallon Junaid yace "Let move in frnd" bude motar Junaid yyi ya fito ya nufi cikin gidan da sauri don ba karamin sanyi yake ji ba, bbu kowa palon ya nufi dakin El-Ameen, bathroom ya shiga ya hada ruwa me dumi sosae yyi wanka, ko da ya fito El-Ameen na xaune yana shan tea, ya fiddo rigan sanyi babba a closet bayan ya goge jikinsa ya sa, wayarsa ya dauka yana dubawa ko bae jike ba snn ya ajiye gaban mirror ya dawo yyi kwanciyarsa ya ja bargo ba tare da ya kalli El-Ameen ba, El-Ameen yace "Baxa ka sha tea'n ba?" Share sa Junaid yyi, El-Ameen yyi murmushi sanin baxae kulasa ba yace "Toh fa gwara ka tashi ka sha magani kar ka k'asa tashi gobe, ana kuma tambayata ba'asi xan tona wllh" Dariya El-Ameen ya dinga yi jin Junaid bae tanka sa ba still, ya mike ya dauko paracetamol ya dawo da Goran ruwa ya xauna gefensa yace "Look frnd, tashi ka sha drug kafin ka kwanta kar ka tashi da mura gobe, yhu knw I may be annoying a times" yana murmushi ya kare maganar, mikewa Junaid yyi ya karbi maganin da ruwa ya kora ya koma ya kwanta don shi kansa yasan without dat baxae tashi lfya ba gobe. Washegari da asuba kafin ayi sllh Junaid yace xae tafi bayan ya daura alwala yyi Raka'atainil fajr, bae yarda ya dau motar El-Ameen ba don yasan hkn na iya tona masa asiri, ko mum din El-Ameen bata san yana gidan ba, El-Ameen ya rakasa bakin titi ya tsayar masa da a dai daita don ca yyi bae iya ba. Ana kokarin tada sllh ya iso anguwarsu na Government reserve area, masallaci kawae ya shiga, ana idarwa ya dde xaune yana Azkar har ya ga fitan Abbansa snn ya mike ya bi bayansa, part dinsa ya nufa ya gaishesa ya amsa masa snn yace "Kana mura ne Ahmad?" Junaid ya girgixa kai yace "Ya ma yi sauki Abba, ina shan magani" Abba yace "Gud! Babu damuwa ko?" Junaid ya shafa kai yace "Ehh Abba!" Abba yace "To Allah maka albarka" Junaid yace "Ameen Abba," Abba yace "Gobe xan fita xuwa Germany, tafiyar ya xo min da gaggawa ne, as usual am handing the family over to yhu son" Junaid yace "Toh Allah kai mu Abba, journey mercy dad, in'sha Allah" Abba ya shafa kansa yace "Ameen dear son" mikewa Junaid yyi yace "It's almost daybreak Abba, bari in je in shirya xuwa aiki" Abba yace "Its ohk, stay blessed" fita yyi ya nufi bangarensa, cikin mintunan da basu fice ashirin ba ya shirya cikin uniform dinsa na dark navy blue trouser da light blue shirt, kadigan yasa navy blue bayan ya feshe jikinsa da turare ya rike hularsa a hannu, waow yyi kyau har ya gaji lips din nan nasa kamar ya shafa jan baki, ya bude manyan idanuwansa sanin bae shafa komae ba ya daga kafada ya fita xuwa side din mum dinsa, fatima dake shara a balcony ta gaida shi, ya amsa ya shiga parlon, Mumy na jera masa breakfast dinsa a dinning ya sameta, ya nufi dinning din ya mata side hug ya kwanta jikinta a hankali yace "Sabahul khair Ummu na" Mumy tayi murmushi tace "How are yhu, baka rufe windows bne jiya naji kmr mura na neman kama ka" shagwabe mata yyi yace "Na rufe mana Mumy," ta hararesa tace "Toh ka bar Ac a kunne ko" ya girgixa kai yace "Not at all mum, kinsan ynxu lkcn ruwa ne kuma tun da na dawo ciki nake fita aiki shi yasa kmr muran ke son kama ni" tace "Toh I will get yhu an umbrella don ban ga amfanin Raincoat din da kake sa wa ba" yace "A'a ni nafi son raincoat dina, umbrella sae kace mace mumy" tace "Toh idan na baka kar kayi amfani da shi" langwabar da kai yyi ya xauna yana kallon ynda take hada masa tea, plate din potatoe'n da ta xuba masa ya jawo ya shiga ci yace "Aisha ta koma ne Mumy?" Mumy tace "Tun jiya" daga haka ta bar dining din ta shiga daki, a hnkli junaid ya ajiye fork din hannunsa tunawa da mahaukaciyar da suka dauko jiya da yyi, har Mumy ta fito bai kuma cin komai ba, ta kalli agogo ta kallesa tace "Kana kallon agogo dai koh" yyi yake ya ci gaba da cin potatoe'n, tutturawa kawae ya dinga yi don neman appetite yyi ya rasa, ya mike yana goge bakinsa da tissue yace "Allah amfana momy, thnks a lot" tace "Welcm, but make sure ka shiga ka gaida mutan gidan yau" d'an hade rae yyi amma da yake baya mata musu cewa yyi "Toh mumy" ta rakasa har balcony, yyi side din stepmums din nasa, bangaren Hajiya Fatee ya fara shiga tana xaune da Muhibba a palo da Rabi'a dake gugan Hijab, ya xauna kan kujera hannunsa rike da hularsa me kaman face cap me dauke da symbol din captainship a jiki, yyi k'asa da kai yace "Ina kwana Hajiya" a dakile tace "Lfya lau d'an gwal" hade rae yyi yana jujjuya hular hannunsa, Rabi'a tace "ina kwana ya Ahmad?" Yace "Lfya lau ya sch?" Tace "Alhmdllh" Muhibbah dake ta kallonsa ko kiftawa bata yi ganin ko kallon inda take bae yi ba cikin wani siririn murya tace "Ina kwana ya A.jay" ba tare da ya kalleta ba yace "Lfya lau" sae kuma ya mike ya nufi kofa yace "Na tafi aiki Hajiya," bata tanka sa ba har ya fita, Muhibba ta kalli Hajiya tace "Hajiya kinga ko amsa gaisuwata bai son yi ma" Hajiya Fatee tayi wani murmushi mai wuyar fassara ba tare da tace komae ba, Rabi'a tayi 'yar dariya tana guganta tace "Aiki" harara uwar ta wurga mata, ko sanin tana yi bata yi ba, part din Hajiya Bilki Junaid ya nufa, bbu kowa palon ya nemi gu ya xauna yana kallon agogon wrist dinsa, daga kitchen khadija ta fito ta d'an wara ido tace "Lah ya Ahmad ashe kana nan, Gud morning" yayi murmushi yace "Morning lil sis, ya sch?" Ta karaso kusa da shi ta shagwabe murya tace "Lfya lau, plss yaya ka d'an min transfer din 5k frnd dita na birthday gobe xan siya mata perfume" yace "Kije ki samu Abba mana ae bai tafi ba" ta d'an bata rai tace "Shekaranjiya fa ya canxa min phone" yace "Ohk ltr" Hajiya bilki ce ta shigo palon, kallo daya tayi masa ta dauke kai, tana kallon Khadija tace "Ke don uwar ki me ya hada ki da Suhaima kike mata fitsara?" Khadija ta hade rai ta juya ta koma kitchen, junaid yyi k'asa da kai yace "ina kwana Umma" ba tare da ta kallesa ba tace "lfya lau" Suhaimah ce ta shigo palon da alamar muryarsa taji, tace "Ina kwana ya Ahmad" mikewa yyi yace "Lfya lau" daga hka yace "Na tafi aiki Umma" bae jira cewarta ba ya fice, ta bi sa da harara, Suhaimah ta samu waje ta xauna ta xabga tagumi tana kallon Umman. Junaid na xuwa gun aiki ya dauki permission Karfe sha daya ya fito, driving yyi xuwa clinic din dad din El-Ameen, Yana rike da hularsa ya haura sama xuwa office din El-Ameen, Nurses din suka bi sa da kallo ko kiftawa bbu, yana attending to patient ya same sa, ba tare da ya kallesu ba ya shige bedroom, xama yyi yana addu'ar Allah yasa baxae dau lkci da patient din nasa ba, ko minti biyar ba'ayi ba sae ga El-Ameen ya shigo yana kallonsa yace "Ya? Duty din naka ya kuma shifting xuwa yamma ne?" Junaid yace "No of course, yarinyar da muka bari kulle a gida fa?" El-Ameen ya hade rai ya galla masa harara yace "Kaga xaka fara daga ma mutum hankali da sassafen nn koh, Toh me xa ayi mata ynxun? Ba sae xuwa yamma in mun gama aiki ba" Junaid ya girgixa kai yace "Yanxu fisabilillah da xaka fito baka yi breakfast ba Dr? Ita ba mutum bace da xa a bar ta ba ruwa ba abinci har xuwa yamma?" El-Ameen yyi masa wani kallo yace "Toh wai wa ya hana ka xuwa kai mata abincin ynxu, iyaka ka xo kace in baka makullin gida in baka, pls let me be Captain, am getting sick of you," Junaid ya lumshe ido ya rike kansa don walakancin El-Ameen ya fara isan sa, mikewa yyi ba tare da ya kallesa ba yace "Ohk! Bani keyn" El-Ameen ya d'an shafa kai yace "Alryt am sorry, haka ne kuma fa ya kamata a kai mata abinci, tun da ita ma mutum ce kamar Junaid" ficewa Junaid yyi ya bar masa dakin, El-Ameen yyi dariya ya bi bayansa, makullin gidan dake table dinsa ya dauka ganin Junaid ya bar office din shi ma ya fita, kusan a tare suka iso gun motar junaid, El-Ameen ya bude gaba ya shiga, junaid ma ya shiga ba tare da ya kallesa ba yace "Kaga hand me dat key ka fice min a mota" El-Ameen ya gyara xama yace "Toh fitar da ni mu ga" Junaid ya fi minti biyar bae tada motar ba, El-Ameen kuma yaki fita, sanin ba fitan zae yi ba kawae ya tada motar ya ja suka bar asibitin, wani eatry ya fara biyawa ya siyo abinci da ruwa sae hollandia drink, El-Ameen ya rike kai ya dinga dariya da ya ga hollandian, shi dae Junaid bae tanka sa ba, sae da suka dau hanyar gidan yace "kaga malam da ka rufa ma kanka asiri ka bude hollandian nn mu shanye kawae, dama am thirsty, banda haka a ina ta san wani hollandia in ba neman magana irin naka ba" driving kawae Junaid yake bae tanka sa ba, El-Ameen yyi dariyarsa me isarsa yana mamakin Junaid, a waje suka yi Parkin motar, El-Ameen ya bude gidan suka shiga, kallon Junaid yyi da ya tsaya yace "A'a Toh ka shiga gaba mana goga" murmushi Junaid yyi bae ce komae ba yana shafa kai don shi har ga Allah tsoro yake, El-Ameen ya dinga kyalkyala dariya har suka isa kofa Junaid na biye da shi a baya, El-Ameen na bude kofar ya koma baya da saurinsa ya fiffito da ido, Junaid na ganin hka kan kace me sae gashi a tsakiyar compound cikin 'yan sakwanni, El-Ameen ya rike kai yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya nanata hakan ya kusa sau goma, Junaid na daga tsakiyar compound sae tambayar me ya faru yake, cikin tsawa yace "Junaiddd xo ka ga abinda ka jawo min"
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
4.....
Washegari Karfe hudu da wani abu Junaid ya baro office, tun safe dama ya kira agents din Abbansa yace su sama masa apartment ko me dakuna biyu ne but kar su yrda Abba ya sani, driving yake yana kokarin kiran daya daga agents din yaji ko an gama komae, mutumin na d'agawa ya gaishesa snn yace "Yallabai an samu, amma xaka iya xuwa ka ga ko ya maka" Junaid yace "Alryt! Ohk, na gode" katse wayar yyi ya nufi asibiti gun El-Ameen sanin yana clinic, xaune ya samesa yana attending to wata patient, Junaid ya nufi bedroom dinsa da ke office din ya kwanta, bayan minti talatin El-Ameen ya shigo ya cire farin lab coat din jikinsa yace "Uhnn! Ko uniform baka cire ba tsabar xumudin taimakon mahaukaciya kenan" Junaid ya mike xaune ya hade rai yace "Yea daga office nake, na kuma samu apartment" El-Ameen yyi murmushi yace "Ohh dats gud for yhu" Junaid yace "But yau da nyt xa mu dauko ta ko" wani kallo El-Ameen yyi masa yace "Xa dae ka dauko ta malam, kai da wa xa ku dauko ta" shiru Junaid yyi yana kallonsa, ya sauke ajiyar xuciya yace "Toh naji xan dauko ta" mikewa yyi yace "i will be on my way, but ina son ka min favour daya, plss motar ka xaka bar min a layin ku sae ka bar min key din karkashin motar ko in btwn flowers dake kusa da motar, I will then cum over to take it sbda Mumy baxata bar ni in fito so late ba" El-Ameen ya bude ido yace "What? A motar tawa xa a saka mahaukaciya, kuma tsabar walakanci sae in bar motar at risk da makulli a waje, you are dreaming" Junaid ya girgixa kai yace "Ka dae san ba sonka Allah ya fi yi a kanta ba da ya barka da hankalinka ita ya gusar mata da nata koh?" El-Ameen yace "Toh preacher, amma ni baxan bada motata ba period!" Junaid bae ce komae ba ya fice daga dakin, tunanin wa enda xa su taimaka masa ya dauko mahaukaciyar ya dinga yi, sae da ya biya ya duba apartment din da aka samar masa ya ga ba laifi snn ya nufi gida. Da daddare yana xaune palon Mumy yana cin tuwon shinkafa da lafiyayyen miyar vegetable da tayi masa, sae dae duk bae da appetite turawa kawae yake, ya kalli Fatima dake kwance parlon yace "Xo dauke abincin nan" ta mike tace "Baxa ka ci bane yaya?" Bai ce komai ba hakan yasa ta kwashe tray din tayi kitchen da shi, takwas da rabi ya mike ya shiga bedroom din Mumy don mata sae da safe, tace "Yau ba hiran kenan" yayi yake yace "Bacci nake ji momma" tace "To Allah ya tashe mu lfya, make sure yhu ablute nd pray b4 going to bed, kuma ka rufe windows ka ga hadari" yace "In'sha Allah mum" fita yyi daga bangaren nata rike da wayarsa. Bedroom dinsa ya shiga ya canxa kaya cikin hanxari snn ya fito, gate ya nufa yana yi yana waige waige har ya fice, da kafa ya karasa titi iska na kadawa sosai ga walkiya alamar ko da yaushe ruwa xae iya sakkowa, yana tsaye yana jiran abun hawa abinda bae taba yi ba duk tsawon rayuwarsa a iya saninsa, bae ma san ta ynda xae tsaida adai daitan ba sae kalle kalle yake gashi kuma sae wucewa suke, yayyafi aka fara yi sosae, ya lumshe ido ya bude yana kallon motocin dake wucewa, wata farar lafiyayyen mota ce tayi parking gefensa, wata kyakkyawan yarinya ta fito sanye da hijab tana kallonsa tace "Bawan Allah shigo in rage maka anya if its ok by yhu, ka ga its raining kuma ruwan xae iya karfi at anytime, na wuce daxu xanje pharmacy na ganka kuma na dawo na kuma ganin ka" kallon motar yyi snn ya kalleta, yarinyar baxata wuce 18 ba, ta d'an bude ido tace "Noo! Am just being helpful" daga hka ta juya xata koma motar ta, sanin bashi da wani alternative yasa ya bude gaban motar ya shiga, dai dai lkcn da ita ma ta shiga maxaunin driver, ta kallesa ta ja motar suka bar wajen, tana tuki tace "Ina ka nufa?" Ba tare da ya kalleta ba ya gaya mata, tace "Ohk" wayarsa ce ta fara ring ya ciro a aljihunsa ya ga El-Ameen ne, da kmr baxae daga ba sae kuma ya d'aga ya kara a kunne yyi shiru, El-Ameen yace "Ya ka samu fitowan?" Cikin kaushin murya yace "Ba Matsalar ka bne wnn" El-Ameen yyi dariya yace "Haba name same, naga baka xo daukan motar bane har ynxu" Junaid yace "Ehh xan je in karba na Faisal" El-Ameen yace "Kai na fa fito maka da motar Wllh come over, yhu knw I can be annoying a times" Junaid yace "Noo dnt wrry ina hanyar gidan ynxu" El-Ameen yace "Look stop this plss junaid, na fito maka da mota Wllh, just teasing yhu daxu" Junaid yyi shiru sanin baxae iya fushi da abokin nasa ba, lumshe ido yyi ya bude yace "Ohk" snn ya katse wayar. Juyawa yyi ya kalli yarinyar ya gaya mata anguwarsu El-Ameen yace nn xani, tace "Ohk" dai dai bakin gate yasa ta tsaya ya juya yana kallonta yace "Thanks a lot" tace "Yhu are welcm!" bude motar yyi xae fita duk da ruwan da ake tsugawa, sae kuma ya juya ya kalleta, wayarsa ya ciro ya mika mata yace "Sa min digit din ki so I can thank yhu some other time" tace "Do yhu need to? Its ohk ba sae ka kuma gode min ba, it payz to be kind" murmushi yayi ya mayar da wayar aljihunsa yace "Ohk Allah saka da khairan" juyawa tayi bayan motar ta dauko raincoat ta mika masa tace "Hope yhu will cope with this" karba yyi ya kuma mata godiya ya fita daga motar, ta ja motar ta bar wajen. Bin motar yyi da kallo dai dai lkcn da aka dallara masa wutan fitilar mota, juyawa yyi yaga motar El-Ameen ce, karasawa yyi da sauri yana rike da raincoat ya bude front seat ya shiga, El-Ameen yace "Wani mota ce wannan?" Junaid yace "A good Samaritan" El-Ameen ya tabe baki yace "Ynxu ka mana adalci kenan Junaid, ko wani mahaluki na cikin bargo cikin ruwan nn kasa muna tsaye a titi?" Junaid yace "Look! Ni ae bn ce ka fito ba xaka iya komawa abun ka" El-Ameen ya hararesa yace "Ehh In koma ka ji haushi na koh" Junaid yace "No Baxan ji ba" tsaki El-Ameen yyi ya tada motar suka bar layin, sae da suka hau kan titi snn yace "Ynxu ina xa mu bi?" Junaid ya gaya masa suka kama hanyar inda mahaukaciyar take, banda tsaki bbu abinda El-Ameen yake, shi dae Junaid bae ce komae ba har suka iso, Junaid ya fara kalle kallen inda xae hangota, bae ganta wajen ba hankalinsa ne ya tashi, shi dae El-Ameen kallonsa kawae yake, ya juya ya kalli El-Ameen yace "Frnd bn ganta wajen ba kuma" El-Ameen yace "Toh me xan yi ni kuma, haka kawae ka shiga hakki na ka hanani kwanciya cikin sanyin nn" bude motar Junaid yyi ya fita cikin ruwan, ya fara nemanta, lkci daya ya jike jagab, can ya hangota rabe jikin bango kusa da wani kiosk duk ta jike jagab ta takure waje daya, wani tausayinta ne ya rufe sa jikinsa yyi sanyi sosai, ya kusa minti biyar tsaye cikin ruwan yana kallonta snn ya juya ya koma gun motar ya bude yana kallon El-Ameen cikin sanyin murya yace "I've seen her" El-Ameen yace "Gud for you, sai ka bude baya ka dauki igiya ka daureta ka dauko ta ai" shiru Junaid yyi yana tsaye cikin ruwan yana kallonsa, can yace "Ka xo ka taimaka min toh" El-Ameen yace "What! cikin ruwan nn xan taimaka maka, Noo" Junaid bai kuma cewa komai ba ya bude bayan motar ya dauki igiyan da ke nan ya rufe ya koma inda mahaukaciyar take, k'asa karasawa yyi don gabansa sae faduwa yake, da kyar yyi shahada ya isa gabanta, kallonsa take tana kara takurewa waje daya, sae a snn ya lura da rawan sanyin da take, a hnkli yace "Kiyi hkuri baiwar Allah, am only trying to help" kamar ta ji me yace ta yunkura ta mike xata bar wajen da gudu, fixgota yyi ya rike ta gam, ta shiga kokuwa da shi tana ihu, El-Ameen na daga mota yana lekansu, ban da dariya bbu abinda yake har da kyakyatawa, ba karamin wahala ta ba Junaid ba don da kyar ya kai ta k'asa ya daure hannunta shima din ba wae dauri sosae ba don taki tsayawa ga wani karfi dake gareta, bude mota El-Ameen yyi ya fito cikin ruwan ya karasa inda suke da sauri, karban sauran igiyar yyi junaid na rike da ita ya daure ta gam, ihu ta dinga masu tana shure shure, El-Ameen ya mike yace "Ae sae ka dauketa Mr Do good" bbu musu Junaid ya dauketa, ko kadan bata da nauyi ya nufi motar da ita El-Ameen na biye da shi a baya yana 'yar dariya, ya bude baya ya saka ta ciki ya rufe, yatsine yatsine El-Ameen ya shiga yi ya nufi driver seat, muryoyi suka ji daga bayansu duk suka juya, wasu matasa suka gani tsaye da gora da adda a hannayensu, da ka gansu ka ga masu gadi, cikin tsawa suka ce "Maxa ku fito da ita ynxun nn" kallon Junaid El-Ameen yyi, El-ameen ma haka, ae kan kace me sae ga Junaid cikin mota ya rufe, El-Ameen na ganin hka shi ma ya shige motar ya tada da sauri, samarin suka taho da gudu, cikin hanxari El-Ameen ya ja motar suka bar wajen, bin motar samarin suka yi da guda suna buga ma motar gora da karfi, El-Ameen ya dinga cewa "ya Salam! ya salam! ya salam!" har suka bar anguwar abinda yake maimaitawa kenan, juyawa yyi yana kallon Junaid dake ta kallon mahaukaciyar dake fixge fixge tana son freeing kanta, a fusace ? yace "Kai ka ji irin ynda suka tarwatsa min bayan mota kuwa Junaid" Junaid ya sauke ajiyar xuciya yace "Xan gyara maka motar ka idan Allah ya yarda" kwafa El-Ameen yyi yace "Better, kuma ka dinga lura da ita kar ta cafko ni mu shiga uku, ynxu ina muka nufa?" Junaid ya gaya masa ya kama hanyar anguwar, cikin minti goma suka iso, har lkcn ruwa ake, parking El-Ameen yyi yana kallon Junaid ya bude motar ya fito, fitowa yyi shi ma suka shiga gidan a tare, gidan babba ne ba laifi, junaid har yasa anyi furnishing gidan kar ya tsaya empty, El-Ameen yyi tsaki yace "Lallai! A wannan gidan xa a ajiye mahaukaciya? ba sae ta balla windunan nn mara karfi ba ta yi ficewarta, bugu daya idan tayi ma kofar nn ficewa xae yi wllh" Junaid ya shafa kansa a hankali yace "Toh shi suka samo min ya xa ayi" El-Ameen yace "Oho, amma idan ta gudu wallahil Azim ba da ni xaka je nemota ba" da damuwa Junaid yace "Toh hw are we going to do it ynxu ga shi mun dauko ta" El-Ameen yace "Oho it's left to yhu" xama Junaid yyi ya rike kansa, can yace "Ohk, let bring her in I will stay nd guard her till 2morrow kafin nn sae a samo mata wani gidan." El-Ameen ya shiga hararansa can ya ja tsaki yana kallon agogo yaga har goma ya wuce, yace "Kaga mu je can gida na, don ni na gaji sanyi nake ji kar in yi ma kai na illa haka kawai" daga hka ya fice daga palon, junaid ya bi bayansa ya fita ya kulle gidan. Har suka isa gidan El-Ameen bbu wanda yace komai sae Junaid dake juyawa lkci lkci yana kallon mahaukaciyar, El-Ameen ya dauko makulin gidan dake motarsa ya fita ya bude gate don bbu kowa gidan, dawowa yyi cikin motar ya shiga compound din da motar, yana gama parking ya juya yana kallon Junaid yace 'Ohhw ni! yanxu mahaukaciya ce mace ta farko da xata fara shigar min gida bayan mahaifiyata maimakon matata" Junaid bae tanka sa ba, El-Ameen yyi tsaki yana girgixa kai ya fito daga motar ya nufi cikin gidan, Junaid ya fito ya bi bayansa, a balcony ya tsaya ya canxa change over din gidan don akwae wuta, ya juya yana kallon Junaid yace "Toh ni xan fito maka da mahaukaciyar?" Junaid ya girgixa kai ya juya ya koma gun motar, bae sha wahalan daukota ba don sosae El-Ameen ya daureta kuma duk tayi laushi, ihu take tana shure shure har suka shigo falon ya direta k'asa yana kallonta, El-Ameen ya rike haba yana kallonta yace "Ikon Allah, muna xaman xaman mu Junaid ya ja mana!" Juyawa Junaid yyi yana kallonsa, El-Ameen yyi tsaki ya nufi stairs, Junaid ya lumshe ido ya bude ya bi bayansa, daki ya samesa ya bude drawern kayansa da alamar kaya xae canxa, Junaid yace "It's late ynxu, muyi freeing dinta sae mu wuce koh" El-Ameen yace "wait tukun! Wae kai xaga dinga tsayawa da ita a gidan?" Junaid ya d'an yi shiru yana kallonsa, sae kuma ya sauke ajiyar xuciya yace "No, xan sa a samo min yar dattijuwa dat will be staying, nd I will hire a gate man" El-Ameen ya kyabe baki ya cire jikakken shirt din jikinsa da wando ya fiddo wasu kayansa ya sa, sae a snn ya juya ya kalli Junaid da ke xaune gefen gadon dakin yana kallonsa yace "Kai baxa ka canxa kaya ba?" Mikewa Junaid yyi ba tare da ya kallesa ba ya fice daga dakin, dariya El-Ameen yyi sanin haushin sa kawae Junaid ke ji.
*Sai dai da aka rushe katangar Chinan dai, ko wani katanga xan kuma cewa Allah yayi min da su*
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
3.....
Wani kallo Mumy tayi masa tace "Kaga ka kiyaye ni Ahmad, baxa ka gun El-Ameen din ba asibiti xa mu" shiru yyi yana kallonta sanin baxae taba convincing dinta ba, a hankali yace "Toh kiyi hkuri mumyna mu tafi asibitin" jakarta ta dauka tace "Sake ni mu tafi" saketa yyi dai dai lkcn da wayarsa ya fara ring, fiddowa yyi a aljihu yana kallon me kiran nasa ya ga El-Ameen ne, ya juya ya kalli Mumy ya ga kallon wayar take, d'agawa yyi ya kai kunne daga daya bangaren El-Ameen yace "ya ne captain, kana gida yau?" Junaid ya d'an saci kallon Mumy ya ga kallonsa take, yace "Noo! Don't worry frnd Mumy tace mu tafi clinic kawae ba sai na xo ba" El-Ameen yace "What are yhu talking about guy?" Junaid yace "No ba komae wllh, kawae dae tace mu tafi asibiti ne" tsaki El-Ameen yyi yace "HeyJunaid are you ohk, wat are yhu sayin?" Junaid yace "Ohk Tnx for ur care frnd!" D'aga hka ya katse wayar ya kashe gaba daya ya mayar aljihunsa yana sinne kai, Mumy tace "Don me xaka ce Mumy tace, maimakon kace Abban ka ne yace kaje clinic" Junaid yyi shiru yana kallonta, komawa tayi ta xauna ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shknn, ka tafi can ya duba ka, amma yana prescribing maka magunguna ka dawo Ahmad, I repeat my self ka dawo" farin ciki ya lullubesa sae dae yyi kkrin boye hakan yace "Toh Mumy I promise" har bakin motarsa ta rakasa tace "Drive carefully" yace "Sure mum" tana tsaye har ya bar gidan snn ta juya xata koma bangarenta, xaune ta ga Hajiya Fatee da Hajiya Bilkee a balconyn Hajiya fateen suna kallonsu, Mumy ta karasa tayi masu sannu da xama, Hajiya Bilki kadae ta amsa da yauwa a dakile, juyawa Mumy tayi xata bar wajen Hajiya Fatee tace "Ynxu an ma hana d'an gwal din xuwa gaida mu tsabar mulki" juyawa Mumy tayi tana kallonsu tace "Ayya Bashi da lfya ne, ynxun ma gun likita xa shi" bbu wanda ya tanka ta cikinsu, ta nufi bangarenta ba tare da ta sa ma kanta damuwarsu ba. Junaid na isa ya tarda El-Ameen na clinic, bae so hkn ba amma bbu ynda ya iya hka ya nufi Babban asibitin Dad din El-Ameen din, don shima kwararren likita ne da yyi fice a Nigeria, da yake Nurses din sun san tsakanin Junaid da El-Ameen, bbu wanda ya dakatar da shi xuwa office din El-Ameen din, murda kofar yyi ya shiga babban office din, El-Ameen dake xaune yana dube duben files sanye da farin glass a idonsa ya dago yana kallon Junaid, ajiye pen din hannunsa yyi ya rike ha6a yace "Kan ka daya kuwa captain?" Dariya junaid yyi ya xauna kan table din office din yace "Kai da ban yi hka ba da Mumy bata bari na xo ba yanxu ai" El-Ameen ya girgixa kai yace "Mummy's boy, na ga randa xaka girma ka samu freedom din kanka" murmushi yyi yana shafa kansa yace "Uhm am 30 ynxu kace ban girma ba, ae kila har in mutu baxan samu wannan freedom din gun momma na ba" El-Ameen yyi dariya yace "Idan kayi aure xa ka samu" murmushi Junaid yyi yace "Aure kuma" kallonsa El-Ameen yyi ya cire glass din idonsa yace "Amma ba ka jin ddi koh, you look weary?" Junaid ya lumshe ido ya bude da damuwa yace "Kinda frnd! Am just disturb, bani da kwanciyar hankali kwana biyun nn, M just nt my self..." Rike kai yyi ya kasa ci gaba, El-Ameen ya dafa sa yace "What's wrong frnd, tell me ur problem, 'Yan gidan ku ko?" Junaid ya d'aga kai yana kallonsa cike da damuwa yace "No! Wnn mahaukaciyar ban san ko laifi nayi da na kwace yaron nan a hannunta ba, duk na kwanta ita nake tunawa nake gani, k'asa bacci nake yanxu duk bani da sukuni" El-Ameen ya ja tsaki ya mayar da glass din idonsa ya jawo files din gabansa yana ci gaba da dubawa yace "Thought it to be something better ma, wai mahaukaciya" wani tsakin ya kuma ja, Junaid ya runtse ido ya watsar da files din yace "Haba Dr in ce maka bana iya bacci kace min yhu thought it was somethin better," El-Ameen ya rike chin dinsa yana masa wani irin kallo da mamaki yace "Wae halan kana da dangantaka da mad woman din nn ne junaid" a fusace Junaid yace "Wa ya sani" wani dogon tsaki El-Ameen ya kuma ja yace "Kaga ka rabu da ni, I have meaningful things doing ynxu, aikin gaba na ma ya ishe ni stop bothering me plss da wata mahaukaciya can." Kallonsa junaid ya tsaya yi na kusan minti biyu kafin ya sauka daga kan table din da yake ya dauki wayarsa da makullin mota ya juya ya nufi kofa, bin sa da kallo El-Ameen yyi kafin ya birkita lallausan gashin kansa a xuciyarsa yace "What's wrong with Junaid da xae damu kansa ya damu wani da wata gagarumar mahaukaciya can" mikewa yyi da sauri tun kan ya fita ya kulle kofar office din yace "Look Captain, to ynxu me kake son ayi da rashin baccin naka, ko kuma dai kawai mu je ka ba mahaukaciyar hakuri?" Junaid ya kallesa yace "bude min kofa" El-Ameen na 'yar dariya yace "Of course No baxan bude maka ba sae ka gaya min dalilin ka na xuwa gu na, which help do yhu want me to render yhu, mu je ka nemi gafararta mad woman din ne" tuni idon Junaid ya sauya kala, still behaving gently yace "Bude min kofa nace" El-Ameen yace "Noo!" Wani kara yyi ya cakumo sa yana huci yace "Bude min kofa Ahmad!" Murmushi El-Ameen yyi yace "Naki! ka xama Zaki a nn in ga" turasa da karfi Junaid yyi ya koma kan dogon kujera ya xauna ya rike kai, El-Ameen yyi dariya ya koma kan office chair dinsa ya xauna, sae bayan kusan minti goma Junaid ya dago kansa, ya kalli El-Ameen dake ta aikinsa, El-Ameen yace "Har iskokan sun sake ka kenan" Junaid bae ce komae ba ya kauda kai, mikewa El-Ameen yyi ya dawo gefensa ya xauna yace "Now tell me, ya kake son ayi?" Junaid ya sauke ajiyar xuciya cikin sanyi ya fara magana, "Frnd! May be tana son in taimake ta ne, shi yasa take bi na, she want me to help her" El-Ameen ya kwalalo manyan idanuwansa yace "Kayi me?" Shiru Junaid yyi yana kallonsa, El-Ameen ya girgixa kai yace "Yhu must be crazy Junaid, meye hadin ka da wata mahaukaciya can har kake tunanin taimakon ta, kai ka daura mata haukan, ko kasan me ya haukatar da ita? Wait! which help ma xaka iya rendering dinta tukun, taking her to psychiatry nd staying with her there ko yaya?" Junaid ya tabe baki yace "Ae dan Mumy da Abba baxa su yrda bne da nayi hkn wllh" El-Ameen yyi dariya sosai yace "Ehh lallai Junaid ka ja ma kanka" Junaid yyi kasa da murya yace "Listen to me plss Dr, ban da kai akwae wanda xan kai ma damuwar da na k'asa gaya ma mahaifiyata duk kusanci na da ita, why kake min hka frnd?" El-Ameen ya sauke ajiyar xuciya yace "Noo ba hka ba Junaid, ynxu tell me ya kake son ayi, hw did yhu want me to help in here?" Cikin kwantar da murya junaid yace "yhu are a Neurologist as well as a qualified MD, I knw yhu can cure her by the grace of Allah idan ka sa kanka, yhu neva can tell where one's reward Lie's" wani matsiyacin kallo El-Ameen ke yi masa kafin ya mike yace "Gaskiya ka janyo ma kanka fitina ka ja mana muma da muke tare da kai Ahmad, dama ban da abun ka me ya kai ka kama mahaukaciya kai da kake tuki a mota, Ohh My God! ga irinta nn ka tabo aljana, don Wllh yhu are not on ur right senses" Mikewa Junaid yyi shi ma yace "Stop this El-Ameen, meye illar taimakon Baiwar Allah da xa mu yi? Haba idan wani yace min xaka yi hka I won't believe wllh," El-Ameen yyi shiru yana kallonsa baki bude, cike da mamakin aminin nasa, Junaid ya juya ya nufi kofa rai bace, girgixa kai El-ameen yayi yace "listen Captain" ko sauraransa Junaid bae yi ba ya fice daga office din, ya birkita kansa ya bi bayansa da sauri, a tare suka isa inda motar Junaid yake, El-Ameen yace "Haba frnd listen to me, ynxu mu koma ka min bayani sosai yanda zan gane abinda kake nufi don wllh am confuse" hararansa Junaid ya shiga yi yace "Ka dae san ba kai kadai bane abokina likita ba koh?" El-Ameen ya d'an yi murmushi yace "I know" hannunsa ya rike suka koma asibitin dae dae lkcn da wayar Junaid ya shiga ringing, fiddo wayar yyi yaga Mumy ce ke kiransa, El-Ameen yace "Mummy's boy" d'agawa Junaid yyi daga daya bangaren Mumy tace "Ka kyauta Ahmad" Junaid ya marairaice yace "Ohh Ummata, drip karami yake kara min ne fa, nd am feeling much beta ynxu har na ci abinci kuma" Murmushi Junaid yyi bayan ya gama sauraranta yace "in sha Allah mum" daga hka ya katse wayar suka nufi office din El-Ameen.
El-Ameen ya tallabi chin dinsa da hannu biyu yana kallon Junaid yace "ina jin ka, Allah sa ka dawo senses dinka yanxu, ya kake son ayi kace?" Junaid ya lumshe ido ya bude yace "Wae da cure dinta nake son kayi ko nawa ka bukata xan biya ka" El-Ameen yyi murmushi yace "Ohh i see, A can kan bola xan dinga tafiya ina samun ta kenan" Junaid ya ce "Noo of course, dauko ta xa mu yi" El-Ameen ya bude ido yace "Mu kai ta ina? Gidan ku?" Hararansa Junaid yyi yace "Plss frnd be serious, a gidan ka xa mu ajiye ta, ni idan nace xan ajiyeta a nawa gidan dole sae su Mumy sun sani, barin ma ni da nake da 'Yan sa ido, kai kam bbu me sa maka ido" El-Ameen ya buga table din gabansa yace "Wnn ne kuma baka isa ba Malam, I can't keep a mad woman in my house, the house that's meant for my wife!" junaid yyi shiru yana kallonsa, a hnkli yace "Ohk let me rent an apartment" Tsaki El-Ameen yyi yana Mamakin Matsalar Junaid, anya kuwa kansa daya, Junaid yyi murmushi yace "I knw u are thinking if am alryt at all, tausayi ne ba wani abu ba frnd, naga yarinyar is too young ace hakan ya sameta duk da ba a ja da ikon Allah, baka san inda rayuwa xae yi da kai ba wataran frnd, it really pays to be kind, and you neva can tell where one's reward lies! ni xuciyata daya nake son taimakonta saboda Allah, I will pay yhu wat ever amount yhu require for the bill, ni dae fatana ta samu lfya ta nemi 'yan uwanta" wani dariya El-Ameen yyi yana tafe hannu yace "Toh governor Ahmad Junaid, don this is the government's job not urz" mikewa Junaid yyi yace "What ever, ynxu dae let me start lookin for an apartment" El-Ameen ya daga kafadarsa yace "Left to yhu, amma ina guje maka reaction din yan gidanku idan suka ji shirmen da kake shirin aikatawa" Junaid yyi tsaki yace "Ni dae nemo plaster ka sa min a hannu am leaving, gobe I might come back idan na sami apartment" El-Ameen ya mike ya dauko plaster ya mika masa yana kallonsa cike da mamakinsa, a tare suka fito, El-Ameen yace "Yi Dropping dina a gida kawae, na mance key a office" a hanya El-Ameen ya kwashe da dariya yace "Tabdi wa ya ga Capt Junaid da taimakon mahaukaciya, but idan taimako kake son yi Why not kaje orphanage home kayi ne" share sa Junaid yyi, yana parking kofar gidansu ya juya yana kallonsa fuskarsa daure yace "Sae da safe" El-Ameen yyi dariya ya bude motar ya fita sanin har ya ji haushi ne.
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: ⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓


       _By Khaleesat Haiydar_✍🏻

 8....

Bude kofar kitchen da El-Ameen yayi yasa Junaid ya mike da sauri ya koma baya, El-Ameen ya tsaya daga bakin kofar yana mata wani irin kallo yace "Wato ni ta raina xata kwale koh?" Junaid yayi murmushi yace "Kai fa ka tsokaneta gashi ka sa ta xubda hawaye, haba Dr!" El-Ameen ya karaso palon yana kallonta kanta a sunkuye yace "Xa tayi me dalili ne ma ae, ba dae ni xata kwala ma Karfe ba" mikewa tayi tana kallon kofa, Junaid ya karasa da sauri ya sa key, kallonsa ta tsaya yi, El-Ameen ya xaga ta baya ba tare da ya bari ta lura ba, ya cafke hannayenta ta baya, ta kwala wani ihu, ya kai mata rankwashi yace "Shut up!" Hade rae Junaid yayi sae dae bae ce komae ba, El-Ameen ya ja ta ya nufi stairs da ita, kokuwan kwace kanta kawai take, ya dauketa cak ya haura sama da ita, Junaid ya lumshe ido ya bude ya karasa cikin palon ya xauna,  da kyar El-Ameen ya daure mata hannu, snn ya samu yayi mata allurori guda uku, ta gama fixge fixgenta da ihu ta sulale wajen sae bacci, mikewa yayi daga durkushen da yake yana kallonta, ya karasa inda take ya kunce mata daurin da yayi ma hannunta ya dauketa ya kwantar kan gado, tsayawa yayi yana kallonta ganin yanda dogon gashinta ya hargitse, ribbon din da ya gani kasan dakin ya dauka ya karasa gadon ya xauna gefenta ya dago kanta a hankali ya shiga packing din dogon gashin, da kyar ya daure mata sannan ya mike ya gyara mata kwanciya ya fita, palo ya sauko yana kallon Junaid yace "Ina tsohuwar nan?" Junaid bae tanka sa ba, El-Ameen ya tabe baki ya fita waje, xaune ya sameta can gurin wani flower tayi tagumi, ta basa dariya sosae ya karasa inda take yace "Mama nan kika dawo, ae bata komae mama kawae tsokanarta nayi shi yasa tayi hakan" Mama tace "Uhn" dariya yayi sosae yace "Allah kuwa mama, ta ma yi bacci yanxu" Mama tace "Allah sarki" El-Ameen yace "Amma bata cin abinci ko mama?" Tace "Toh gskya ni ban sani ba don xubarwa take" yace "A'a bata ci gaskiya, xan taho da maganin cin abinci gobe, mu shiga ciki to mama" ba musu ta mike ta bi bayansa suka koma palon, mikewa Junaid yayi bayan sun shigo yana kallon El-Ameen yace "Xan tafi ni" El-Ameen yace "Eh nima tafiya xan yi" kallon mama El-Ameen yayi ganin har lkcn dari dari take yace "Na rufe kofar dakin mama, kuma baxa ma ta tashi yanxu ba sae can dare" tace "Toh Allah dae ya bata lfya" yace "Ameen" a tare suka fita da Junaid, ko wannensu ya shiga motarsa ya wuce.  Junaid na isa gida bayan yayi wanka ya canxa kaya ya nufi part din mumyn sa, xama yayi gefenta ya kwantar da kansa kan shoulder dinta yace "Gud evenin mum" tace "Evenin dear ya aiki? Yhu are kinda late yau" yace "Yea mum, yau Abba xae dawo koh?" Tace "He said tomorrow da muka yi waya daxu" tace "Kasan Hajja ta xo kuwa" mikewa xaune yayi da sauri yace "haba Mumy, When?" Mumy tace "Kana tafiya aiki daxu da safe" yayi murmushi yace "Amma bata san Abba baya nan ba koh?" Mumy tace "Ta sani mana yanxu dae ka ci abinci ka tafi ka gaida ta tun daxu take shigowa tana tambayar ko ka dawo har ca tayi a kai ta gun aikin naka" dariya sosae Junaid yayi yace "Ta hakura ta dawo nan din kenan" Mumy tayi murmushi tace "Nima haka nace, tace inaa kwana biyu kawae xata yi ta koma" Junaid yace "Lallai Hajja" mikewa yyi ya nufi dinning, cikin 'yan mintuna ya sakko yace ya koshi, Mumy tace "A'a wannan baka ci komae ba junaid" Da sauri ya nufi kofa yana cewa "Allah Mumy na koshi" bin sa da kallo tayi kafin ta tabe baki, yana fita ya nufi part din grandmum dinsa, ya tura kofa da sallama ya shiga palon, tana xaune sanye da glass din ido tana dama fura, cire glass din tayi tana kallonsa, yayi dariya ganin irin kallon da take masa ya dauke furan gabanta ya rungume ta yayi pecking goshinta yace "Oyoyo granny" ta tsuke fuska tace "Ni dae daga ni Amadidi" saketa yayi ya daure fuska yana kallonta yace "Wai baxa ki bar kirana da wannan sunan ba Hajja" tace "Toh toh Junaidu, shikenan?" bude baki yayi yace "Xan fa sa asa min ke a guard room in jefa ki cikin ruwa ko don baki ganni da uniform din ba" washe hakora tayi tace "To yi hakuri soja" dariya yayi yace "Ya mutan Daura Hajja?" Tace "Wannan kuma sae ka shirya ku je kai da ubanka" Junaid ya tabe baki yace "Toh ni dae yi ki dama furar ki debar min nawa" hararansa tayi tace "A'a wannan na ni da jikata ne" yace "Wace haka" Hajjo ta juya tana kallon kofar daki tace "ke fito ki gaida yayanki 'yar nan kina jin ya shigo kin yi mukus a daki" Junaid yace "Wacece?" Kwalo mata kira Hajjo tayi kusan sau uku sae ga ta ta fito ta karaso cikin palon ta xauna kasa jikin kujera ta hade rai tace "Na'am" kallonta kawae Junaid yake ganin ynda take rurrufe fuska da hijab yace "Wacece wannan kuma Hajjo" Hajjo ta washe baki tace "ehh baka santa ba gaskiya" sae kuma ta hade rae tace "barin ma kai da ba shiga yan uwa kake ba, ga ka kai daya namiji gun Muhammad kmr tsiya, maimakon ka dinga shiga yan uwanka ku saba, ko da yake tana karama ka santa, 'yar uwar ka ce Humainah, 'yar wajen kawun ka, kuma matar da na xaba maka" fashewa da kuka yarinyar tayi ta mike tana kallon Hajjo tace "Ni bana son haka fa Hajjo" daki ta nufa da sauri tana kuka, Hajjo tace "Au! Ji shirme" Junaid ya tabe baki yace "Ni dae ki dama fura ki sammin inyi tafiya ta" Hajjo tace "kai ba fa xancen wasa ba, ita na xaba maka matsayin mata tunda ka ki fito da matar aure godai godai da kai" yace "Toh bana so!" daga can cikin daki yarinyar tace "Ni ma bana so!" Hajjo ta fashe da dariya tace "Au, naga ko in ku kuka haife kan ku, xumunci ne dae sae na hada" tsaki Junaid yayi ya mike ya fice daga palon tana kiransa ko waiwayowa bae yi ba, Hajjo tace "Ahaf abinda ma a gidan xan bar ta ta kare secondary ayi auren kawae" yarinyar ta kuma rushewa da kuka tace "Wallahi baxan tsaya ba Hajjo ni ki maida ni gida kawae" Hajjo ta tabe baki tana ci gaba da dama furar ta tace "Kwa yi ku kare" Junaid na komawa part din Mumy ta bi sa da kallo ganin mood dinsa, tace "Ya aka yi Ahmad?" Cikin bacin rae yace "Wae kina jin Hajjo ta kawo wata yarinya wae xata ce a hadani da ita" dariya Mumy tayi tace "Kai kanwarka Humainah ce fa, 'yar gidan kawu Bala" Junaid ya xaro ido yace "Au ita ce ta girma haka mumy?" Mumy tayi dariya tace "Ita ce mana" ya d'an tabe baki yace "Mumy wani colleague dinmu bae da lfya, xan je duba sa" Mumy tace "Ayya, toh Allah basa lfya, my regardz" mikewa yayi yace "Ameen Mumy sae na dawo" fita yayi rike da makullin motarsa, kallo daya yyi ma Suhaima dake xaune balcony mac book a gabanta, ya shiga motarsa ya tada ya fice daga gidan bayan mai gadi ya bude masa gate, kafin ya isa main road ya kira layin El-Ameen, bugu biyu El-Ameen dake xaune kasa gaban mahaifiyarsa ya d'aga bayan ya nemi ixinin yin haka, Junaid yace "Kana clinic koh gida?" El-Ameen yace "Ina gida" katse wayar Junaid yayi, El-Ameen ya kalli Mum dinsa da ta wani hade rae, sannan yayi kasa da kai, tace "Yauwa, in kuma ban isa da kai bane sae ka sanar da ni in ji" marairaice mata yayi yace "Wllh Ummi ranan mun je, tare da Junaid ma muka je, ae yanxu xae xo sae ki tambayesa ki ji" Ummi ta watsa masa harara tace "Ku ka je ina, ba duk jirgi daya ya kwaso ku kai da Junaid din ba, kuma ni bance ae baka je ba, Ca tayi dariya kuka dinga yi mata kai da Junaid din" xaro ido yayi ya bude baki yace "Dariya kuma Ummi, wllh fa mun mata magana" ta galla masa harara tace "Da'alla rufe min baki malam, da ban san ka da sakarci bane, sannan ka kuma tafiya da d'an uwanka sakarai kamar ka" Murmushi El-Ameen yayi yana shafa lallausan gashin kansa, Ummi tace "Kuma Dad dinku yace baka xuwa clinic da safe kwana biyun nan, sannan baka ma xaman clinic din during day time, nan kuma da sassafe kke barin mana gida, ina kake xuwa Ahmad" shiru yayi na wani lokaci kafin ya hade rae yace "Nurses din ne suka gaya masa haka koh?" Ummi tace "Dake shi makaho ne ba" shiru El-Ameen yayi bae ce komae ba, dae dae lokacin da Junaid ya shigo palon, ganin El-Ameen xaune kamar me neman gafara yasa yayi kasa da kai yyi hanyar stairs sanin sanin sai Ummi ta iya hadawa da shi kai kace shi yayi laifin, Ummi ta bi sa da harara tace "Dawo nan ina xa ka? ka wani yi kasa da kai kmr munafuki" dariya Junaid yayi yana shafa kai, ya dawo cikin palon yace "Laifi ya maki ko Ummi?" Ummi tace "Xauna nan!" Ba musu ya xauna gefen El-Ameen, Ummi tace "Ranan da ku ka je gidansu iman sa ta gaba kuka yi wae kuna ta dariya koh?" Junaid ya xaro ido yace "Dariya kuma Ummi, ae ko mun yi magana me ma'ana, nine ma nayi maganan don shiru El-Ameen yayi" Ummi bata san lkcn da tayi murmushi tana kallonsu ba, ta girgixa kai tace "Ahaf ai magana ta lalace tunda kai kayi! Wato ku baxa ku yi ma kanku fada ba ko, babu me ba wani shawara cikin ku kan ya kamata ku ajiye iyali yanxu," Junaid yayi kasa da kai yace "Ina yi masa wallahi Ummi" harara ta xabga masa tace "Common keep quiet my frnd ai har kai" El-Ameen yayi murmushi shi ma yayi kasa da kai, Ummi tace "Toh gaskiya it's high time ku san me ku ke, don ku ba yara bane, and yhu guys ain't getting younger, ku yi ma kanku fada ku fito da mata kuyi aure abun ku, as a mother nake gaya maku haka, in ma baka son Iman din sae ka nemo wata very soon, kai ma Junaid kayi kokarin yin hakan kafin wata uku, I want to see my boys getting married soon, in kuma kun ban wuka da nama sae in nemo maku mata wallahi" a tare kamar sun hada baki suka ce "A'a Ummi" dariya tayi tana kallonsu, Junaid ya shafa kai yace "In'sha Allah Ummi xa muyi ynda kuke so" tace "Toh Allah yasa, ya bamu aron ran ganin bikin boys dinmu" dariya suka yi gaba daya, Ummi tace "Toh ku tashi ku tafi, Allah maku albarka" mikewa suka yi suka nufi dakin El-Ameen bayan sun amsa da Ameen, xama Junaid yayi gefen gado yana kallon El-Ameen dake kakrin kunna desktop dinsa yace "Baxa mu je can gidan ba?" Ba tare da El-Ameen ya kallesa ba yace "Kai ka tafi mana, kaga ni am busy" Junaid bae ce komai ba sae kallonsa da yake, shi kam sae danne dannensa yake ba tare da ya damu ba, Junaid ya mike yace "Ohk am off" El-Ameen yace "So early, to ka gaida Mumy" Junaid bae tanka sa ba ya fice, El-ameen ya bi sa da harara yace "You think kowa ma bai da aiki kamar ka sai na mahaukaciya yanxu" Ummi dake Palo har lkcn ta kalli junaid tace "Har ka fito?" Junaid ya dan yi murmushi yace "Dama sako na xo karba Ummi, sae gobe" tace "Toh Allah ya kiyaye, ka gayar min da Hajiyar ka" yace "Xata ji." Sannan ya fita.

✍🏻
*Haske Writers Association*💡
[16/10, 19:05] Hassan Atk: *Captain Ahmad Junaid*
_By Khaleesat Haiydar_
7.....
Fara ce sosai ba kadan ba don kamar ka latsa ta jini ya fito, dama ashe wahala ce ya maida kalanta baki, ko kadan bata da jiki sai tsayi, bakin gashin kanta ya rufe kusan rabin fuskarta sbda yanda tayi kwanciyar, d'an karamin bakinta me kalan baki da ja Junaid ya kalla yyi murmushi yace "Uhnn! Kamar me hankali koh? Da xata tashi ynxu duk sae mun yi bayani ryt?" murmushi El-ameen yyi ya mike yace "Yea! Exactly!" Juyawa yyi ya fice daga dakin Junaid ya bi sa da kallo sae gashi ya dawo da wasu alluran har uku, ya dawo gabanta ya durkusa, Junaid na ganin haka ya mike ya fita daga dakin, ya sakko palo ya dauki ledan abinci daya ya ba Mama, tayi masa godiya yyi murmushi kawae ya xauna, bayan kusan minti goma El-Ameen ya sakko falon ya xauna gefen junaid yace "Kana ji na, akwae drugs din da xa'a siya har biyar, kuma duk pack daya kusan dubu 40 ne kafin ayi diagnosing dinta...." Junaid yace "Ohk xan maka transfer ltr" El-Ameen ya mike ya dauki ledan abincin da ya rage da ruwa ya nufi sama, ajiye mata yyi bayan ya bude snn ya fito ya sa ma kofar key, ya dawo palo yana kallon Junaid yace "Let leave!" Mikewa Junaid yyi, El-Ameen ya kalli dattijuwar da ke xaune yace "Mama za mu tafi sae gobe, duk buge bugen da xata yi kar ki bude mata kofar" tace "Toh Allah ya tashe mu lfya, yayi maku albarka," duk suka amsa da Ameen suka fita palon. A bakin gate El-Ameen ya tsaya yana kallon Junaid yace "ka ba mai gadi kudi ya siyo ma tsohuwar abinci da safe ya kai mata ciki don am not coming here da safe" Junaid ya ciro dubu uku aljihunsa ya mika ma mai gadin snn suka fita, Suna isa gun motocin su El-Ameen yace "Gobe kuma foodstuffs xaka siya idan xaka xo" Junaid bae ce komae ba ya shige motarsa ya tada ya bar wajen, El-Ameen ya bi sa da kallo yana murmushi, snn shima ya shiga tasa motar. Karfe takwas da wani abu Junaid ya isa gida, bangarensa ya nufa yyi wanka snn ya dauro alwala ya fito yyi isha yana xaune kan darduma ya ji an bude kofar palonsa, bae motsa daga inda yake ba har aka bude kofar bedroom, ya daga kai don ganin waye, Mumy ce ta shigo dakin, yayi murmushi ganinta yace "Yanxu fa xan shigo d'a Mumy" ta xauna gefen gadonsa tace "Sae ynxu kake isha Junaid?" Yace "Mun hadu da traffic ne sosae a hanya Mumy" ta tabe baki ta mike tace "Toh taso mu je ka ci abinci" ba musu ya mike ya linke pray mat din ya ajiye ya bi bayanta, Mai aikinta ce ta dauko abincin nasa daga dinning ta ajiye nan tsakiyar lallausan rug din falon da ya ke xaune, Mumy ta sakko gefensa ta bude warmern dake dauke da Shinkafa fara ta dauki plate ta dibar masa iya yanda tasan xae cinye snn ta bude miya ta xuba masa k'adan a gefe don bae fiye son miya da yawa ba, sae cow meat da ta cika masa a abincin, spoon ya dauka yace "Thanks sweet mum" snn ya fara cin abincin ita kuma ta dauki wayarta da ke ring, ganin Abba ne yasa ta nufi daki. K'asa cin abincin Junaid yyi ya kuma rasa dalilin hakan, ya lumshe ido ya jinginar da kansa jikin kujera, ya kusa minti goma a hka sanin Mumy na fitowa sae ta sa shi ya cinye abincin yasa ya kira mai aikinta, yarinyar ta taho daga dakinta da sauri, ya dauki abincin ya mika mata yace "ina fatima?" Tace "Ta kwanta" yace "Ohk tafi daki ki ci na koshi" ba musu ta koma dakinta da abincin, juice ya diba ya shiga sha a hankali, a hka Mumy ta fito ta samesa tace "Har ka cinye?" Yace "Eh Mumy" ya ajiye cup din hannunsa yana lullumshe ido yace "Nafara jin bacci mumy" tace "Toh Allah ya tashe mu lfya, kayi alwala kafin ka kwanta, don't forget to pray also" ya mike yace "In'sha Allah mum" wayarsa ya dauka ya fita ya nufi side dinsa, sae da ya dauro alwala yyi shafa'i da wutr snn ya kwanta ya ja bargo. Washegari yana office yayi ma El-Ameen transfer din dubu dari da hamsin, yana barin office dama kasuwa ya shiga ya siyo food stuffs sannan ya wuce gidan El-Ameen, mai gadi ne ya shiga da kayan abincin palo, Junaid ya xauna bayan sun gaisa da mama yace "El-Ameen din ya xo ne mama" tace "Eh ya xo da safe, ya kuma xuwa daxu, bae dde da tafiya ba amma yace xae dawo" Junaid yace "Ohk, bacci take ne?" Mama tace "A'a gskya, sae dae yace kar a bude kofar makullin na jiki ma" Junaid yace "Tana cin abinci kuwa?" Girgixa kai tayi tace "Gskya ban sani ba don kifarwa take duka, bana gane ko ta ci ko bata ci ba" Shiru yyi bae kuma cewa komae ba, yana son ganinta amma shi gskya tsoro yake, dama El-Ameen na nan ne, can ya kalli agogo ya ga har biyar yayi, mikewa yyi yace "toh ni xan tafi mama, bbu matsala dae koh?" Tana murmushi tace "Babu komae wallahi" xae yi magana aka bude kofa El-Ameen ya shigo, ya d'an kyabe baki ganinsa, shi dae Junaid bin sa da kallo yayi har ya karaso cikin palon, ledan hannunsa na magunguna ya ajiye yace "Ba dae har xaka tafi ba, kuma kama duba mahaukaciyar taka kuwa?" Junaid ya dauke kai bae ce komae ba, El-Ameen yace "Ehh Lallai ma, wato ni xaka yi ta bari da wahala koh, daxu da safe ma sae da na xo nan kafin in tafi clinic nasan kai ko tashi kila baka yi ba lokacin" yana kai wa nan ya nufi sama, Junaid ya sauke ajiyar xuciya ya bi bayansa, El-Ameen ya bude kofar dakin da key ya tura kofar a hankali, tana xaune ta rakube waje daya bayan ta kuma cire labulayen dakin gaba daya kamar yanda ta saba, doguwar rigar kanti ne jikinta ja da ya haska farin fatar ta, duk ta birkita dogon gashinta kmr ba da safe Mama ta kuma daure mata ba tana bacci, kayan ma da gani ta kasa cire shi ne don duk ta yamutse shi jikinta, El-Ameen ya balla mata harara yace "Wai ke wace irin mutum ce, wllh kika sake cire min labule sae na gaura maki mari, baki da aiki sai barna" Junaid dae na d'aga bakin kofa yana leko dakin, El-Ameen ya kallesa yace "Da'alla matsoraci shigo baxa ta ma komai ba" kin shigowa junaid yayi yace "Nan ma ya isa" El-Ameen ya hade rae yace "Ohh wato ni ne ban san ciwon kai na ba da nake shigowa koh, sae in daina shigowa nima in dinga tsayawa daga bakin kofa in ga ta ynda xa ayi maganin" a hankali Junaid ya d'aga kafa ya shigo dakin yana kallonta sae shishshigewa jikin bango take a tsorace, El-Ameen ya kalli Junaid dake tsaye shi ma duk a tsoracen, Junaid bae ankara ba sae gani yyi El-Ameen ya fixgosa ya tura sa har sae da ya fada kanta, a tare suka kwala ihu daga shi har ita, El-Ameen ya dinga kyakyata dariya har da rike ciki, da kyar Junaid ya mike, ita ma ta yunkura ta mike, tsorata junaid yyi ya nufi bayi da sauri, ita kuma ta wawuri d'aya daga karafunan labulen dakin tayi kan El-Ameen dake dariya har lokcin, xaro ido yyi ya hadiye dariyarsa ganin haka, ya juya da sauri xae fita ae da hanxarinta ta bi bayansa, me Junaid xae ban da dariya, ya dinga kyalkyala dariya ya bi bayansu, har downstairs ta bi El-Ameen, mama na ganin hka ita ma tayi waje da gudu, El-Ameen ya dinga cewa "Junaid wllh ka xo ka riketa, junaiddd" Junaid ya durkusa nan stairs ya dinga dariya ganin yanda El-Ameen ya rude yana xaga palon, ita ko sae binsa take xata buga masa karfen, Hadiye dariyar Junaid yyi ganin El-Ameen ya shige kitchen ya sa key ya barsu su biyun a palon, ta dade tsaye bakin kofar kitchen din, kafin ta juyo tana bin ko ina na palon da kallo, k'asa motsi Junaid yyi daga inda yake xuciyarsa na bugawa, ta jefar da karfen hannunta ganin kofa a bude ta nufi kofar da sauri, Junaid bae san lkcn da ya nemi tsoron ya rasa ba ya bi bayanta cikin hanzari ya riga ta isowa kofar ya rufe gam, juyawa tayi tana kallonsa tana maida numfashi, sae kuma ta fasa wani ihu tayi kansa ta fixgosa, rungumeta yyi ya riketa gam, ta dinga fixge fixge ya ki saketa, Sosae suka jigata daga ita har shi, don kin saketa yyi, ita kuma bata fasa kokuwa da shi ba, daga karshe tayi lamo jikinsa bata sake yunkurin kwatar kanta ba, a hankali ya saketa ta sulale nan kasan palon, hawaye yaga kwance fuskarta, jikinsa yyi sanyi ya durkusa gabanta yana kallonta.
*Haske Writers Association*
[16/10, 19:05] Hassan Atk: ⚓ *Captain_Ahmad Junaid*⚓



      _By Khaleesat Haiydar_✍🏻



9.....

Gida Junaid ya nufa, yana gama parkin ya fito ya shiga bangaren Mumy ya gaida ta sannan ya tafi nasa part din, kwanciya yayi Palo ya lumshe ido, ko minti goma bae yi da kwanciya ba wayarsa ya soma ringing, daukar wayar yayi yana kallon mai kiran nasa ya ga abokinsa ne Faisal, d'agawa yayi yace "Yane Faisal!" Faisal yace "Are yhu at home capt?" Junaid yace "Yea ina gida" Faisal yace "Ohk gani nan shigowa" daga haka ya katse wayar, bayan minti takwas Faisal ya shigo palon, Junaid ya mike xaune yana kallonsa yace "Daga ina haka" Faisal ya xauna yace "Gida mana tun da kai baka neman mutane sae El-Ameen" Junaid yayi dariya yace "Kai haba ko ranan da daddare ban kira ka ba" Faisal dake kokarin kira a wayarsa yace "Really!" kallonsa kawae junaid yayi yana murmushi, faisal yace "Hello Muhibba gani gidan ku part din Captain" daga haka ya katse wayar, Junaid ya hade rae yace "idan gun ta ka xo ba sae ka je can bangarensu ba xaka wani kira min ita nan" faisal yace "Chill guy sako xan bata" ko rufe baki faisal bae yi ba sae ga ta ta shigo, murmushi dauke fuskarta tace "ashe da gaske kake" hade rae sosai Junaid yayi ya jawo waya yana dannawa, faisal ya ciro waya aljihunsa ya mika mata yace "Gashi nan na bada an gyara maki" ta wara ido ta karbi wayar tace "Waow am so happy ya faisal, kuma nawa?" yace "No don't bother" tace "Toh na gode kwarai, ya salima fa?" Yace "Tana gida," kallon Junaid tayi tace "Sannu ya Ahmad" ba tare da ya kalleta ba yace "Yauwa!" Tayi niyyan xama palon amma sanin junaid sae ya iya gwaleta yasa ta juya kawae ta fita tana tunanin yaushe ne wannan ranan da junaid xae fara sonta kamar yanda Hajiya ke yawan assure dinta. Faisal yace "Fatee fah?" Junaid yace "Oho!" Sae bayan Magrib faisal ya bar gidan bayan sun shiga ya yi ma Mumy sallama ya kuma shiga part din Hajja ya gaidata, a tare suka fita bayan Junaid ya ce ma Mumy bari ya rakasa, sai dai rakiyar iya bakin gate yyi sa, yana ganin tafiyar Faisal ya nufi titi don yasan in har yace ma Mumy fita xae yi sai ya amsa query, kalle kallen abun hawa ya shiga yi ya rasa yanda xae ce su tsaya, can dae wani mai adai daita ya tsaya yana tambayarsa ina xa shi, shiga kawae Junaid yayi yana kallon mai adai daitan yace "Mu je" sae da suka dan yi nisa kafin ya gaya masa inda xa shi, suna isa junaid ya sauko ya fara dube duben kudi a aljihu, dubu daya kawae ya gani aljihun nasa, mika masa yayi a hankali yana kallon mai adai daitan yace "Kayi hakuri malam ban san ban fito da kudi ba, dubu daya ce a hannu na nagani" dariya mai adai daitan yayi ya karbi kudin, ko ba a gaya masa ba yasan junaid sabon shiga ne a tricycle, canjin dari shidda ya mika masa yace "Ga canjin ka bawan Allah" dan xaro ido Junaid yayi ya karbi kudin yace "Har canji gare ni? Toh na gode" mai adai daitan yayi murmushi ya ja machine dinsa ya wuce, Junaid yayi mamakin ganin motar El-Ameen a parke waje, shi da yace baxae xo ba kuma, tabe baki yayi ya shiga gidan, mama ce xaune Palo ita kadae Junaid ya gaisheta da ladabi, ta amsa tana murmushi ta tambayesa ya aiki, Junaid yace "Lfya mama, ya kamata a siyo maki tv ya dinga debe maki kewa koh" dariya tayi tace "lallai kam" Junaid yace "El-Ameen ya xo ne" mama tace "Eh yana sama" mikewa junaid yayi sae dae duk bae da kuxari ya nufi saman, a hankali ya tura kofar dakin yana kallon ciki, xaune ya ga El-Ameen gabanta ya tankwashe kafa plate din abinci a tsakiyarsu hannunsa rike da spoon ga wayar rechargeable dake gefensa, ita ma xaunen take ya daure mata hannu sae shisshigewa jikin bango take hawaye kwance fuskarta, duk gashin kanta a birkice yake, Junaid ya rungume hannayensa yana kallon El-Ameen, El-Ameen yace "Uhnn! yau baka kwanta da wuri ba kenan mumy's boy" junaid dae bae tanka sa ba ya maida kallonsa kanta ganin yanda take kokuwa da bango kamar xata shige ciki, yunkura tayi xata mike El-Ameen ya daka mata tsawa ya dauki wayar rechargeable din gefensa ta koma da sauri ta xauna, shinkafar ya diba ya kai mata baki, ta dinga kauda kai tana boye fuska, tsawa ya kuma yi mata ya juyo da kanta ya matse  bakinta har sai da ta bude ya xuba mata abincin da sauri, murmushi Junaid yayi ganin yanda jikinta ke rawa tana hadiye abincin ba tare da ta tauna ba, da ganinta kasan ba karamar matsoraciya bace, Haka El-Ameen ya dinga mata har sae da ta ci kusan rabin abincin sannan ya mike yana kallon Junaid yace "Bata cin abinci shi yasa na mata haka," Junaid ya buda manyan idonsa yace "So yhu do really care ashe haka?" El-Ameen yayi dariya yace "Darajar ka take ci ae" Junaid bae kuma cewa komae ba sae kallonta yake duk da ba ganin fuskarta yake ba don dogon gashin kanta ya rufe fuskar, wasu allurai biyu El-Ameen ya fiddo ya shiga hadawa, ae tana hango alluran ta mike tayi kofa da gudu, fixgota El-Ameen yayi don shi Junaid hanya ma ya bata da sauri, El-ameen ya jefa ta kan gado, yana hararan Junaid yace "kaji d'an iskan hanya ma ya bata" Junaid yayi dariya yana shafa kai, ta fasa wani uban ihu da ya tsorata Junaid xata mike El-ameen ya hau gadon ya rike ta yana mata wani mugun kallo yace "Keehh", Ribbon dinta da ke kan gadon ya dauka ya shiga daure mata gashin kanta, yana kallon fuskarta yace "Kika kuskura kika sake cire ribbon dinnan sae na gaggaura maki mari" banda rawa babu abinda jikinta yake tana kallonsa, murmushi yayi ya kwantar da ita a hankali ya kwance daurin hannunta sannan ya juya yana kallon Junaid yace "Miko min alluran ko shi ma tsoron sa kake" Junaid bae ce komae ba ya dauki alluran ya mika masa, juyar da ita El-Ameen yayi xae mata alluran Junaid ya juya ya fita dakin, El-Ameen ya bi sa da kallo sannan ya tabe baki yayi mata alluran, tsam ya riketa a jikinsa ganin yanda take shure shure da ihu, sun kusa minti goma a haka har ya ji duk jikinta ya saki, ya dago fuskarta yana kallonta ya ga bacci tayi, kwantar da ita yayi ya lulluba mata bargo, sannan ya dauki abincin da ta rage da ruwa ya fita ya kullo dakin, xaune ya samu Junaid a Palo, ya ajiye abincin nan tsakar palon yace "Mama a xubar da wannan ta d'an ci kad'an," Mama ta jawo abincin tace "A'a baxa a xubar ba xan ci" El-Ameen bae kuma cewa komae ba, Junaid ya mike yayi ma Mama sae da safe ba tare da ya kalli El-Ameen ba ya fice daga falon, bin sa da kallo El-Ameen yayi sae kuma ya tabe baki shi ma yayi ma mama sae da safe ya fita.

Washegari Junaid ya fito bayan ya shirya cikin khakin sa ya shiga part din mumyn sa, tana jera masa breakfast as usual ya shigo, bata amsa gaisuwar da yake mata ba tace "ka shiga gaida Hajja kuwa?" Girgixa Kai yayi yace "Na ma manta tana nan" Mumy tace "Toh tafi ka gaida ta ka dawo tukun." Ba musu ya fita yayi bangaren kakar tasa, xaune ya sameta Palo tana shan kunu ga kosai cike kula, dariya yayi yace "Dama abinda ke kawo ki gidan nan kenan ae Hajja" kallo daya yayi ma Humainah dake goge goge palon ya dauke kai, ita kam dama ko kallonsa bata yi ba, Hajja ta hade rae tace "Wae baka ga Humainah bane Junaid?" Ya hade rai shi ma yace "Toh ni xan gaisheta?" Hajja tace "Toh ba kai ka xo ka sameta ba" bude baki yayi yana kallon Hajja, ita ko Humainah ta mike ta dauki bucket fuu xata wuce, fixgota yayi ta kusa faduwa ya turata ta xauna nan kasa, bata fuska tayi xata yi kuka, ya hade rai yace "ke yaushe kika girma har kika iya fitsara haka?" Kuka ta fashe da tana kallon Hajja, Hajja ta mike tsaye ta tsuke fuska tace "Kai Amadidi ka fita idona wllh, walakancin da cin fuska har a gabana, a haka xan baka 'yar kaje kana cutar min da ita in shiga uku?" Dariya Junaid yayi yace "Tabdi! Allah ya tsare ni, ke in kin ga matar da xan aura ma wllh kunyar fito min da wannan fitsararriyar xa ki yi" Humainah ta tabe baki tana hararansa tace "Ni ma in kaga saurayina wllh kunyar tsayawa gabana xa kayi" Hajja ta fashe da dariya kyal kyal kyal har da kwanciya, shi ko bude baki yayi yana kallan Humainah da ta wani tabe baki, murmushi yayi ya saketa ya mike ya fice daga palon, Hajja na dariya tace "A'a da ka tsaya mana fitsararre" Humainah tayi dariya tace "Ya fa ji tsoro ne Hajja, shi in banda haske da dogon hanci me garesa xai wani sa uniform da hula ya xo yana d'addaga mana hanci" Hajja tace "Atoh! Gane min hanya 'yar nan, ko ubansa xai burge Oho!" Humainah ta fashe da dariya har da rike ciki.


Da yamma Junaid na kwance palon Mumy bayan ya dawo aiki idonsa lumshe kamar me bacci sae dai ba baccin yake ba, Mumy kuma na kitchen tana ta girke girke don ranan Abba xae dawo, Bude kofar da aka yi ya sa shi bude ido, El-Ameen ya shigo palon da sallama, kallonsa kawae Junaid ke yi bae ce komae ba, El-Ameen ya karaso palon yace "Capt A.jay Murnai!" Da xolaya ya kare kiran nasa, Junaid ya mike xaune yace "Uhm!" Kitchen El-Ameen ya nufa ya tsaya daga bakin kofa yace "Ina yini Mumyna" juyawa tayi tana kallonsa tace "A'a Ahmad yaushe ka shigo?" yayi murmushi yace "Yanxun nan Mumy, ya gida ya aiki" tace "Alhmdllh, ya Hajiyar ka?" El-Ameen ya karasa shiga kitchen din ya mata side hug yace "Tana lfya Mumy, tace a gaishe ki" Mumy tace "Ina ta sa rana xan je can gidan ku Allah bae yi ba" El-Ameen ya sa hannu ya dauki daya daga kajin da take soyawa yace "Bari in d'an d'ana maki ko gishiri ya ji Mumy" dariya tayi tace "Naga alama" ya wara ido ya fice daga kitchen din yana murmushi, gefen Junaid ya xauna yana cin kaxar Junaid xae yi magana aka bude kofa, Hajja ce ta shigo palon da sallama, El-Ameen ya wara ido ya boye fuskarsa bayan Junaid yace "Kai yaushe Hajja ta xo?" Hajja ta cire glass din idonta tana leken El-Ameen tace "Wannan ba gantalallen nan me sunan ka bane Amadi?" El-Ameen yayi dariya yace "Ehh Nine Hajja, ashe kin xo, ae bae gaya min ba" Hajja tace "Toh ko ya gaya maka xuwa xa ka yi, kar ka manta turare ne fa yayi mani iyaka da kai, daga nace ka siyan turare na xama makiyiyar ka, toh Allah yayi mana tsari da irin ku" dariya sosae El-Ameen yayi, Junaid yayi murmushi yana canxa tashan tv, Hajja ta xauna tace "Har yanxu Muhammad din bae iso bane?" Mumy ta fito daga kitchen  tace "Kila sae xuwa magariba Hajja" mikewa Junaid yayi ya kwashi wayoyinsa yana kallon El-Ameen yace "Mu je" El-Ameen ya mike, Hajja tace "Au don na shigo shine xa ku watse" Junaid ya balla mata harara yace "Da'alla! Rikicin tsufa ya maki yawa wllh" El-ameen yace "Kyalesa kawai Hajja ta so mu je kar ayi ba ke" Junaid yace "Allah kar ta xo min don rufe kofata xan yi" daga haka ya nufi kofa, El-Ameen ya bi bayansa yana dariya, ta tsuke fuska ta bi su da kallo tace "Wahalallu ko uwar me xasu ban da Allah bai ban ba, kuma naga dai gidan d'ana ne yau nace duk ya kora ku wllh ta xauna!" Mumy tayi murmushi ta koma kitchen. kwanciya El-Ameen yayi a palon Junaid yace "Kana ji na Capt?" Junaid yace "Ina jin ka." "xa ayi diagnosing din patient din ka don in san irin neurological disorder dinta da treatment din da ya kamata in mata, nd  dat's money!" Junaid ya dauki remote din hannunsa yayi powering din Tv yace "Aiit! Nawa ake bukata?" El-Ameen ya mike xaune yace "ka turo dubu dari tukun mu ga" Junaid yace "Ohk I will transfer it ltr" El-Ameen yace "Gud! Ko gida xan sa a xo ayi diagnosing din nata, no need of taking her out" kai kawae Junaid ya gyada masa, "Kaga daga nan sae mu san irin uban kudin da xaka kashe" da xolaya El-Ameen ya kare maganar, Junaid yayi murmushi bae ce komae ba.

  ✍🏻
*Haske Writers Association*💡
[16/10, 19:05] Hassan Atk: ⚓ *Captain_Ahmad Junaid*⚓




       _By Khaleesat Haiydar_



10....

Har Abba ya dawo bayan magrib El-Ameen na gidan, suna gama cin abinci da Junaid suka tafi palon Abba a tare don yi masa sannu da dawowa, Hajja na xaune palon da Hajiya da Umma, Humainah da fatima ma na xaune daga gefen Abba dake ta sauraran xancen da mahaifiyarsa ke masa, khadija da sadiya step sister dinta ma duk suna xaune palon, junaid da El-Ameen suka samu waje suka xauna, El-Ameen ne ya soma yi ma Abba sannu da xuwa ya gaishesa, Abba ya amsa murmushi dauke fuskarsa yace "Kana lfya son? Ya aikin?" El-Ameen yace "Alhmdllh Abba, ya hanya?" Abba yace "Alhmdllh mun gode Allah, jiya mun yi waya da Alhaji Mahmoud yace xae tafi Germany gobe" El-Ameen yace "Ehh gobe xae tafi" Abba yace "Maa sha Allah, Allah ya tsare" Junaid ya kalli Abbansa yace "Barka da dawowa Abba" Abba yace "Yauwa Ahmad, how yhu?" Junaid ya shafa kansa yace "Alhmdllh Abba, ya hanya?" Hajiya ta d'an tabe baki ta mike, Umma ma ta mike ta fice daga palon. Hajja ta bi su da kallo sannan tayi tsaki ta maida dubanta kan Abba tace "Ni dai Muhammadu matan nan naka basa min abun arxiki wllh, tun da na xo ko ruwan su ban gani ba sai daxu da safe, Amina kadae ce 'yar arxiki take ta dawainiya da ni" siririn tsaki can kasa Sadiya ta ja tana hararan Hajja ta gefen ido ta mike ta fice daga palon. Murmushi kawae Abba yayi ya maida dubansa kan Humainah dake gefensa a kasa yace "ya karatu Humainah? Ss3 xaki yanxu koh?" Hajja ta karbe tace "Ehh ajin karshe xata, tana gamawa sae a hada aurensu da Amadidi sai taje can ta kare karatun a gidansa" da sauri Junaid ya kalli Hajja ya wani hade rae, ita ma Humainah kallon Hajjan ta ke kamar xata yi kuka, El-Ameen ya fashe da dariya, Abba kam murmushi yayi ya kalli Humainah da har hawaye ya cika idonta yace "Kyale Hajja dotana, wanda kike so xa a aura maki kin ji, kuma sae kin fara jami'a ma xaki yi auren," tana goge hawayenta tace "Toh Abba" Junaid ya harari Hajja da ta sake baki tana kallon Abba ya dauke kai, Abba ya kallesa murmushi dauke fuskarsa har lkcn yace "Ae ni baxan ma 'ya yana auren dole ba Hajja, duk abinda suke so shi mu ma xa mu so," murmushi Junaid yayi ya mike yana kallon Hajja da ta wani hade rai, ya kalli El-Ameen yace "Tashi mu je" El-Ameen ya mike yana dariya suka yi ma Abba sallama suka fita daga palon, Hajja tayi kwafa tace "Toh zan ga ko kai ka haifeni kuwa,"
Bakin mota Junaid ya raka El-ameen yace "Gud nyt!" El-Ameen yace "Aitt, saura kar ka xo can gidan gobe!" junaid yayi murmushi bae ce komai ba, sai da El-Ameen ya ja motar ya bar wajen snn junaid ya juya ya koma gida. Part din Mumy ya shiga ya tarar tana bathroom ya fito ya nufi nasa bangaren. 

Washegari ya kama Sunday Junaid na gida baya duty, kwance yake palon sa misalin Karfe goma da rabi na safe Khadija ta shigo palon, kasa ta xauna kusa da kujeran da yake tace "Gud morning ya A.jay" yace "Morning baki je islamiyya bane" tace "daxu ae anyi yayyafi shine Abba yace in bari gobe," yace "Keep quiet ba cikin ruwan fatima da Rabi'a suka tafi ba, ina ga gishiri ce ke koh, continue deceiving ur self" shiru ta dan yi tana turo baki sae kuma tace "Ae da yamma xan je" bai tanka ta ba, tayi kasa da murya tace "Yaya dama plss 5k xaka ban xan siya wani takalmi ne plss" wani uban harara ya watsa mata yace "Tashi ki bar min Palo, ke baki da aiki sae dae a baki kudi, beside kije ki samu Abba mana, get out my frnd" marairaice masa tayi tace "Don Allah fa yayana" xae yi magana aka bude kofa Suhaima ta shigo palon cikin wasu shegun English wears lokaci daya wani shegen kamshi ya bade palon, mikewa xaune yayi yana kallon Khadija yace "Naji! naji tashi ki tafi" Khadija tayi murmushi tace "Yauwa ya A.jayy nagode" ta mike ta hade rai tana kallon Suhaima tace "Toh ae sae mu je koh" wani kallo Suhaima tayi mata tace "Wa kike gaya ma haka" Khadija ta ja tsaki tace "Duk inda mutum yayi sae ayi ta bin sa da'alla" bata rufe baki ba Suhaima ta fixgota ta sauke mata mari, Khadija ta dafe kunci tana kallonta, mikewa Junaid yayi ya karaso ya bude kofar ya fixgo Suhaima ya wulla ta waje cikin kakkausar murya yace "Kada ki sake taba ta" Umma dake balconyn ta xaune tare da Hajiya ta mike da sauri ganin abinda ya faru, Hajiya ta bi bayanta da sauri ita ma, a fusace ta karaso bangaren Junaid tana huci tana kallon Junaid dake tsaye bakin kofa har lokacin tace "Kai Ahmad uwar me tayi maka xaka jefota haka kamar pillow?" Suhaima ta fashe da matsanancin kuka, hakan ya kuma harxuka Umma cike da masifa da bala'i tace "Ba magana nake maka ba" kallonta kawai yake bai ce komai ba, idonta ya kankance don fitina ta juya tana kallon Suhaima tace "me ya faru, me kika yi masa?" Suhaima na matsar kwalla ta gaya mata, Umma ta xaro ido tana kallon Khadija dake tsaye bayan Junaid a tsawace tace "ke har abun farin cikin ki ne bare yayi ma 'yar uwar ki wannan cin mutuncin Khadija, to don uwar ki fito kar in karya ki palon nan, Shegiya me halin banxa, fito nace" Hajiya tace "Ke dae sallamammiya ce wllh khadija, munafuka wawiya kawai" Hajja ce ta leko jin surutai, ganinsu tsatstsaye part din Junaid ta fito da sauri ta karaso tana tambayar me ya faru, ko kallonta su Umma basu yi ba, Umma na kallon Khadija tace "baxa ki fito ba sae na maki lahani a palon nan?" A fusace Hajja tace "Yau na ga bala'i, ta ya xa ki ce ta fito palon d'an uwanta, ke kin isa ki shiga tsakaninsu?" Hajiya ta tabe baki ta dauke kai, Hajja ta karasa balconyn tace "Me ya faru khadija?" Khadija tace "Wae fa Hajja Suhaima ce ta mareni shine ya Junaid ya koreta palon, shine fa take kuka haka" Hajja ta xaro ido tace "Ta mare ki? Toh Muhammadu ya fito ayi ta ta kare yau, duk ko wannensu ya kwashe agololinsa a gidan nan don ba gidan ubansu bane nan din, shima maganinsa knn da auren xawarawa, haka kawae xa a sa mashi 'ya ya a gaba, kuma bari kiji abinda baki sani ba Bilki, wllh Khadija ta fi kusanci da Ahmadu a kan da warcan bakar yar taki a gidan nan, don uba daya ba wasa bane" ae sum sum Hajiya Fatee ta bar wajen, Mumy ce ta fito jin hayaniya ta karaso da sauri tana tambayar abinda ya faru, Hajja ta shiga mata bayani cikin fada, shiru Mumy tayi tana kallon Junaid, Umma ta fixgi hannun Suhaima suka bar wajen tana huci, Hajja tace "haka kawae, xata kawo mana agola a gida ta adaddabe mu, ita ma wancan mai kama da kutaren ma haka ta kawo nata agolar, duk an cika masa gida da agololi," juyawa tayi tana kallon Khadija tace "Toh wllh ki rike d'an uwanki, don shine dolen ki kuma kun fi kusanci da shi akan wancan bakar don uba daya ba wasa bane" tana kai wa nan ta nufi bangarenta kamar xata tashi sama, Humainah dake tsaye balcony tana kallon film din sae dariya take, Fitowa Khadija tayi daga palon ta bi bayan Hajja don tasan ko hauka take baxa ta nufi sashinsu yanxu ba, Mumy ta sauke ajiyar xuciya ta karasa cikin palon Junaid ya bi bayanta, a hankali ta soma magana tace "Ahmad ina raba ka da shiga tsabgan mutanen nan baka ji koh, ba sonka suke ba kai kanka ka sani, ina ruwanka da shiga tsakanin Khadija da 'yar uwarta?" Junaid yace "Marinta fa tayi Mumy" Mumy tace "koma dai meye ni dae ka kiyaye su bbu ruwanka da su, tsakanin ka da Khadija daban tsakanin Khadija da Suhaima daban" yace "Toh shknn Mumy kiyi hakuri," juyawa tayi ta fita daga palon, ya koma ya xauna yana kallon agogo don duk ya kagu ya fita xuwa gidan El-Ameen. Har bacci ya fara daukansa yaji ana buga kujerar da yake kwance kai, ya bude ido da sauri ya ga Humainah tsaye kansa, mikewa xaune yayi, ta rufe bakinta da hannu tana 'yar dariya tace "Dama haka kake bacci baki bude" shafa kansa yayi yyi saurin fixgota ya xaunar da ita kasa, kara tayi tana kiran Hajja, ya hade rai yace "me ya shigo da ke Palo na?" A rikice tace "wllh Abba ne yace in kira ka" yace "A bude kika ga baki na?" Da sauri tace "A'a wasa nake" daga hannu yayi kamar xae kai mata duka ta boye fuskarta tana kiran Hajja, ya saketa yace "Ashe fitsarar ta karya kike yi" shiru tayi bata ce komae ba, ya mike ya nufi kofa, ta bi sa da harara, yana fita ta sa dariya, mikewa tayi tana kare ma palon kallo ko ina tsaf kamar na mace ga kamshi ya kama palon sosai, bedroom dinsa ta nufa, nan ma very neat ta rike kugu tana bin ko ina da kallo ganin how over tidy it is ga kamshi me ddi dake tashi, ta nufi gaban madubi tana kallon turarruka masu tsadan gaske dake jere gaban mirrorn, daukansu ta shiga yi da daddaya tana fesawa don jin irin kamshin su, kala biyu ta dauka ta fito daga dakin da sauri ta fita daga palon ta ja masa kofa, part din Hajja tayi da saurinta.  Junaid na xaune kasan lallausan rug din palon Abbansa yana kallon Abban nasa da mamaki jin abinda yake cewa, juyawa yayi ya kalli Umma da ke xaune ta sha kunu palon ga Suhaima ma xaune kasa, Junaid ya lumshe ido don ko kadan bae son a laka masa sharrin abinda bae yi ba a hada sa da mahaifinsa, cikin fada Abba yace "Kana jina kayi shiru Ahmad?" Bude ido yayi a hankali yace "Kayi hakuri Abba hakan baxae kuma faruwa ba in'sha Allah" Abba yace "kasani daga yau matsayin Suhaima daya da na khadija wajen ka, kar in kuma jin wannan shirmen, ashe baka da hankali ban sani ba" a hankali Junaid yace "Kayi hakuri Abba" Abba yace "Xancen banxa kake yi, kuma ka bata hakuri yanxun nan" juyawa yayi yana kallon Suhaima da idonta ke kansa ko kifta wa bata yi yace "Kiyi hakuri" tayi kasa da kai tace "Ya wuce" Abba yace "Tashi ka ban waje" mikewa Junaid yayi xuciyarsa na kuna ya fice daga palon. Part dinsa ya nufa yana shiga Palo yasan an shiga bedroom dinsa, ya karasa bedroom din ya kalli gaban mirror ya ga an dauka turare, kayan jikinsa ya canxa xuwa blue jeans da farar T shirt ya feshe jikinsa da turare ya dauki car key da wayoyinsa ya fice daga dakin. Kulle part dinsa yayi da makulli sannan yayi bangaren Mumy, bedroom dinta ya karasa ganin bata Palo ya sameta tana gyara kayanta a closet yace "Mumy xan dan fita sae na dawo" Mumy ta kallesa sannan ta ajiye kayan hannunta ganin mood dinsa tace "Me ya faru son?" Shiru yayi da farko sae kuma yace "Wae shine xa su samu Abba su ce na doki Suhaima, meyasa idan basu yi karya ba basu ji ddi ba 'yan gidan nan?" Mumy tace "Ae tun ba yau ba na sha fada maka ka daina shiga hurumin da ba taka ba, to yanxu gashi sun hada ka da Abban ka ae" ya fuzar da iska yace "Na tafi Mumy sae na dawo" tace "Ina xaka?" Yace "Gidansu faisal xan je" Mumy tace "Toh shknn kar ka dde, and drive carefully" yace "Ohk Mum" har bakin mota ta rakosa, su Umma dake xaune da Hajiya suka bi su da kallo suna tabe baki, ko kallonsu Mumy bata yi ba har Junaid ya ja motarsa ya bar gidan, Mumy ta koma part dinta, Hajiya ta sauke wani ajiyar xuciya tace "Wannan Yaro ya xame mana babban obstacle a gidan nan wllh, komae sae yanda yace ma ubansa, idan ba ina bakin ciki da numfashin da yake a duniya ba Shegiya nake" Umma tace "Uhm ke ko ni, da da yanda xanyi da shi da tuni ni dae nayi wllh, don ko uwarsa bata isheni kamar yanda ya ishe ni a gidan nan ba, na tsane shi wllh wllh, ko 'ya yan mu fa Hajja bata ji da kamar yanda take ji da shi wae don yana namiji mu kuma mata gare mu" Hajiya tace "Toh shine kike kokarin ganin yanda xa ki cusa masa Suhaima ya aura kuma" Umma tace "Toh ae ke ma da xae auri Muhibba so kike naga" Hajiya tace "Da kenan ba yanxu ba don nasan hakan ma baxae taba yiwuwa ba, bari mu shiga ciki ki ji shawarar da na yi a kan matakin da xamu dauka kan Ahmad a gidan nan" Umma tace "Toh me muke a nan, mu shiga kawae ki ban in sha" mikewa suka yi gaba daya suka yi palon Hajiya. Gidan El-Ameen junaid ya nufa, yana gama parkin a waje ya shiga ciki, wanki ya tarar mama nayi a compound din na kayansu, ya karasa inda take suka gaisa sannan yace "El-Ameen ya xo ne mama?" Tace "Eh ya xo daxu da safe" yace "Ohk, bacci take yi ne?" Ta girgixa masa kai tace "A'a idonta biyu sae dae ya kulle dakin," cikin gidan ya nufa ya haura sama, sae dae ya kasa bude dakin, ya kusa minti biyar tsaye sae kuma ya murda key din a hankali, bayan kusan second talatin ya murda handle din kofar, tsaye ya ganta jikin window tayi baja baja da gashinta tana sanye da doguwar rigar kanti pink colour da blue nd black flowers jiki, kallonsa take tana bobboyewa jikin bango, yayi murmushi ya rungume hannayensa yana kallonta.


 ✍🏻
*Haske writers association*💡
[16/10, 19:09] Hassan Atk: ⚓ *Captain_Ahmad Junaid*⚓

      _By Khaleesat Haiydar_✍🏻

11.....

Sulalewa kasa tayi ta xauna ta takure waje daya tana rufe fuskarta da dogon gashinta, dakewa yayi ya karaso cikin dakin kamar bai son taka kasa yana kallonta ya isa gabanta sae dae banda faduwa bbu abinda gabansa yake, bata dago har lkcn ta kallesa ba sae d'ada takurewa waje daya take, cire tsoro yayi ya durkusa gabanta a hankali, dago kanta tayi tana kallonsa a tsorace, murmushi yayi murya can kasa yace "Hello!" Kuri ta kura masa da ido, shi ma hakan yayi ma manyan fararen idonta, can ya lumshe ido ya bude cikin sanyin murya yace "Allah ya baki lafiya don son ma'aiki S a w." A hankali ya kai hannunsa kanta ta kuma shigewa jikin bango, murmushi yayi ya matsa gabanta ya tattare mata gashinta ya mayar baya yace "Ki daina kunce gashin ki idan an daure maki Kinji" yana magana ne yana kallon fuskarta, ita kuwa wani gun daban take kallo, ji yayi ana haurowa sama, ya juya yana kallon kofa sae ga El-Ameen, dauke kai yayi El-Ameen ya shigo yana murmushi yace "Uhnn! Ka daina tsoron nata kenan yanxu?" Mikewa Junaid yayi bae ce komai ba, El-Ameen yayi dariya yace "In gaya maka meyasa kaga ta kyale ka?" Junaid ya juya yana kallonsa, sai da ya dau kusan minti daya sannan yace "akwae alluran da na mata daxu shi yasa ta nutsu, but ina me tabbatar maka da xaran ya saketa xaka gane kuran ka idan ka tsaya gabanta" yana murmushi ya kare maganar, Junaid ya tabe baki ya juya ya fice daga dakin ba tare da ya tanka sa ba, El-Ameen ya bisa da kallo yana dariya sannan ya juyo yana kallonta, karasawa gabanta yayi ya durkusa ya dago kanta, hade rai yayi yace "Sae da kika kuma cire ribbon din koh?" Kallonsa kawae take ko kiftawa bata yi, ya hade rai yace "I will knock yhu idan baki bar kallona haka ba" kamar taji me yace ta dauke idonta daga nashi, mikewa yayi ya dauko ribbon ya dawo gabanta ya durkusa ya kama gashinta waje daya ya daure da ribbon din sannan ya dagota suka mike a tare ya kama hannunta, kin binsa tayi tana tutturjewa yace "Keehh" daga haka ya ja ta suka fita daga dakin tana bin sal, Palo ya sauko da ita ya xaunar da ita kasan rug, ya dauko ledan da ya shigo da ya durkusa gabanta ya bude, fried Irish ne da kwae, sae tomatoe ketchup, ya dauki potatoe daya ya dibi kwae ya kai mata baki, dauke kai tayi da sauri tana komawa baya, ya tsaya kallonta, kai wa bakinsa yyi ya ci, Junaid dae sai kallonsu yake yana yi yana danna waya, kara daukar wani chip din El-Ameen yayi ya dangwali ketchup ya kai bakinta, tsura ma dankalin ido tayi sae kuma ta matso a hankali ta lashe ketchup din, El-Ameen ya wara ido yana kallonta, sai kuma ya saka dariya, murmushi junaid yyi yana ci gaba da danna wayarsa, sae tsotsan ketchup din take a baki, El-Ameen ya kuma dangwala ya kai bakinta ta kuma lashewa, rike kanta yayi ya tura mata dankalin a baki ta fito dashi ya fadi kasa, ya hade rai yace "I will slap yhu fah" kallonsa kawae take ko kiftawa babu, ya dauki wani dankalin ya dangwali ketchup ya kuma kai mata baki, lashewa ta kuma yi ta bar masa dankalin tana tsotsan bakinta, yayi murmushi yana kallon Junaid yace "this shows tana son ketchup lkcn da take da hankali" shi dae junaid bae ce komae ba, El-Ameen ya dinga dangwalan tomatoe din yana kai mata baki tana lasa, exotic drink ya bude ya juya yana kallon Junaid yace "Get me cup plss a kitchen Captain, kaga dai patient dinka nake feeding" Junaid bai ce komai ba ya mike ya nufi kitchen ya dauko cup din ya kawo masa, ya karba ya tsiyaya drink din ya dauka ya kai mata baki, dauke kai tayi da sauri, ya juyo da ita ya rike kanta ya kai cup din lip dinta, kadan ta kurba ta cire bakinta tana yamutse fuska, xae kara bata ta sa hannu xata karbi cup din ya sake mata, ta dade tana kallon cikin cup din kafin ta kifar da lemon nan tsakiyarsa, El-Ameen ya mike da sauri ya bar wajen cikin tsawa yace "Kehh!" Tsorata tayi sosae ta dinga shisshigewa jikin kujera,  ya karasa kusa da ita ya duka ya mata knock a kai yace "kika sake min irin haka sae na tsula maki bulala" Murmushi Junaid yayi yana shafa kansa, El-Ameen ya dago ta ganin drink din duk ya bata kayan jikinta, tsaye ya bar ta nan wajen ya fita xuwa ya kira Mama, ta juya tana kallon Junaid dake kallonta, ya sakar mata murmushi ta dauke kai ta durkusa wajen ta jawo ledan take away din da Irish din ke ciki ta dauki wanda yake bata ta ajiye gefe, ta bude wanda bae taba ba ta tsura ma dankalin ido, kifarwa tayi a kasa, Junaid ya mike da sauri yace "Noo! Me yasa kika xubar" kallonsa tayi kafin ta maida hankalinta kan abinda take, ta dauki take away din da ya fara bata ta juye cikin na wanda ta xubar a kasa sannan ta mike tsaye, tattare gown din jikinta tayi ta juye dankalin a rigarta ta jefar da take away din, Junaid ya langwabar da kai yana kallonta ya ma rasa me xae ce mata, El-Ameen ne ya shigo Mama na biye da shi a baya yana mata magana, tsayawa yayi daga bakin kofa ya bude baki ganin barnar da tayi, tana ganinsa tayi kusa da Junaid ta tsaya rike da rigarta da ta juye dankali ciki tana kallonsa, El-Ameen ya karaso palon da sauri cikin fada yace "Whatt! junaid kana kallonta ta xubar min da abincin da xan ci?" Bai jira cewar Junaid ba ya nufeta, sake rigarta tayi dankalin ya xube gaba daya kasa tayi bayan junaid da sauri, har wani bari jikinta yake, Junaid ya dakatar da shi da sauri yace "Hey, Look Dr, naga in tana da hankali ae baxata yi haka ba, have you forgotten mahaukaciya ce kamar yanda kake kiranta, wannan ae xalunci kawae kake ma patient din taka, ba dae yunwar Irish kake ba, kar ka damu I will get yhu enough idan muka fita" El-Ameen yyi masa wani irin kallo yace "Da'alla my frnd ba kana kallonta ba ka kyaleta, Better tunda dai xaka siya min wani, but wnn ae iskanci ne ba rashin hankali ba, don bata da hankali sae ta dinga sa mu aiki?" Junaid yace "naji xan gyara wajen is that all" Mama dake tsaye palon tana kallonsu tayi murmushi tace "xan gyara wajen bokon turai, kasan sae a hankali, kuma ma wllh hauka me tsafta take yi bata da kaxanta ko kadan" El-Ameen yayi kwafa yana kallonta ganin yanda take lekosa daga bayan Junaid yace "Ni nasan maganin ki ae, kina wani leko ni da Idanuwan nan naki" Junaid ya d'an tabe baki ya koma ya xauna, Mama ta nufi kitchen don dauko abinda xata gyara wajen. karasawa gabanta El-Ameen yyi ya kama hannunta ta fasa ihu, kunnenta ya ja ta nufi sama da ita, Junaid ya bi su da kallo sannan ya girgixa kai a hankali ya jinginar da kansa jikin kujera. Bayi El-Ameen ya shiga da ita ya wanke mata hannayenta sannan ya fito da ita ya xaunar gefen gado sai kallonsa take, wani kayan ya ciro mata ya ajiye gefen gadon, yana kallonta yace "ki daina kallona haka keh, kuma kika kuskura kika tashi a nan sae na xane ki, clear?" ita dae kallonsa kawae take, sae ta basa dariya ganin irin kallon, ya rungume hannu yace "Uhhn! Halan dai kin san ni ne?" murmushi yyi ya juya ya fita daga dakin. Mama jummai yace ta tafi ta canxa mata kaya bayan ta gama gyara gun da ta bata, mama tayi shiru sae kuma tace "Naga idonta biyu fa" El-Ameen yayi dariya ya xauna yace "ae bata komae mama, shi yasa nace ki tafi ki canxa mata, kar ki samu damuwa bbu abinda xata maki, tana da nutsuwa sosai" mama jummai bata musa ba ta nufi sama cikin rashin kuxari. Tana nan xaune inda El-Ameen ya bar ta a dakin ta sameta, kin rufe kofar Mama jummai tayi in case, ta karasa kusa da ita tana d'ari d'ari ta dauki blue gown din da ya fiddo mata, a hankali mama jummai tace "Baiwar Allah kaya xan canxa maki kin ji" ko kallonta bata yi ba, hakan ya kuma tsorata mama jummai, juyawa tayi a sanyaye ta koma Palo tana kallon El-Ameen tace "D'an nan wallahi tsoro nake ji ni kam, kaga sae tana bacci nake shiryata" dariya yayi ya mike ya nufi stairs din suka koma sama a tare, junaid ya bi su da kallo. Xaune suka tar da ta har lkcn sae dai wannan karan windon dakin ta tsura ma ido, El-Ameen ya karasa kusa da ita, ta juya da sauri tana kallonsa, kayan ya dauka ya mika ma mama jummai yace "Gashi mama" karasawa tayi ta karba, ya dago ta yana kallonta ya hade rai yace "Mama xata canxa maki kaya yanxu, stay still kin ji" ita dae kallonsa kawae take, ya juya ya kalli Mama jummai yace "Toh karaso Mama" a hankali ta karaso kusa da su, hannunta na rawa ta kai kan maballin rigar xata cire mata, ta fasa wani ihu tayi bayan El-Ameen da sauri, cikin sakwannin da basu wuce uku ba sae ga mama jummai can bakin kofa a mugun tsorace bayan ta sake kayan hannunta nan gabansu, dariya sosai El-Ameen yake yana kallonta yace "Mama baxa fa ta maki komae ba wllh" tace "A'a d'an nan nafi gane tana bacci wllh" a tsorace take maganan daga haka ta juya ta koma kasa, murmushi yayi ya juya yana kallon ta bayansa, dawo da ita yayi gabansa, ya kusa minti biyu tsaye kamar me naxari sai kuma ya leka rigar jikinta don ganin ko akwai kaya a ciki yaga akwai vest, rufe idanuwansa yyi a hankali ya balle dogon rigan jikinta snn ya fara cirewa idonsa kulle, ajiyewa yayi bayan ya cire har lkcn idonsa na rufe ya duka a hankali ya shiga laluban kayan da Mama jummai ta yar a kasa, yana tabawa ya dauka sannan ya mike, lalubawa yayi yaji bata wajen kuma, ae ba shiri ya bude ido da sauri yana waige waigen inda xae ganta, tsaye ya ga perfect fair figure dinta can jikin window, daga ita sai white vest da ya kusa cinyarta, vest din ya kamata sosai kasancewarsa very elastic, gaba daya shape dinta ya fito ga long fresh legs dinta da bbu tabo ko daya, kamar xaka latsa ta jini ya fito tsabar haske, juyawa yayi da sauri kamar wanda ya ga abun tsoro ya nufi kofa da hanxari, ko me ya tuna kuma sae yyi still bakin kofar ya kusa 3 mins kafin ya juyo a hankali ya dawo dakin ya nufeta ba tare da ya kuma kallon jikinta ba, hannunta ya kama yana kallon fuskarta ya shiga sa mata rigar hannunsa, yana gamawa ya xaunar da ita gefen gado ya hade rai ya dunguri kanta yace "Don't try dat again"  cup ya dauka ya dauraye yayi mata diluting drugs dinta da ruwa sannan ya dawo kusa da ita ya rike kanta ya kai cup din bakinta, kauda kai tayi da sauri, yayi mata tsawa ita ma ta fasa masa ihu, rike kanta yyi ya tura cup din bakinta har sai da ta bude ya xuba mata, sae da ya tabbatar ta hadiye sannan ya kyaleta tana yatsinan baki tana komawa baya, jinin da ya gani bakinta yasa ya tsura ma lips din ido, handkerchief ya ciro aljihunsa ya goge mata bakin yace "Sorry!" Mayar da handki din yayi ya kwantar da ita ya mike ya fita daga dakin ya ja kofar. Palo ya sauko ya ga ba Junaid, ya kalli mama dake xaune yace "Mama Junaid fa?" Tace "Ya tafi wai" shiru yayi bae ce komae ba, can yace "Ohk xan tafi yanxu, da daddare xan dawo, bacci xata yi yanxu" tace "Toh Allah ya kai mu, Allah kuma ya bata lafiya" yayi murmushi yace "Ameen" sannan ya fita.

  ✍🏻

 *Haske Writers Association*💡


⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

      _By Khaleesat Haiydar_✍🏻

13....

Junaid bai daga kiran ba ya juya yana kallon Khadija, Mikewa xaune tayi ta hade rai kamar xata yi kuka tace "Ni fa wllh ba chatting nake ba ya A.jay, ita Hajja bata san komai ba sai dai tayi ta magana" Junaid xai yi magana Humainah ta shigo palon fuskar nan nata a daure ta xauna gefen Hajja, Hajja tace "ke kuma fa? Ina aiken" Humainah tace "ko ba yi tayi kamar bata gan ni ba, kuma bata ce min komae ba sai aikinta take tana wake wake ta bar ni a tsaye" Junaid yace "Wa?" Ta kallesa tace "Anty sadiya mana" Hajja ta mike rai bace tace "Kambu!! Yaran nan sun raina ni wllh, don uwarta ni din sa'arta ce da xan aika tayi min abu ta share ki tana wake wake?" Kofa ta nufa kamar xata tashi sama, Junaid ya mike ya bi bayanta yace "Tsaya Hajja, me kika sata?" Tana huci ta juyo tace "Ca nayi ta min dafadukan taliya shi ke raina yanxu don Amina shinkafa tayi kamar ko da yaushe, ita bata da girki sai na shinkafa kullum" Junaid ya hade rai yace "Ita mum din tawa, Toh su wa ennan na palon naki me suke yi da baxa su maki ba" Hajja tayi tsaki tace "Xancen banxa, toh ban yi niyyan sa su ba, ko da yanda xaka yi da ni ne" tana kai wa nan ta nufi part din Hajiya da sauri, ya d'an tabe baki ya juya yana kallon Humainah yace "Sannu da hadi, ke baki iya taliyar ba sae kin je dauko magana koh?" Ta turo baki tace "Ae dai ba ni nace tayi ba, aikena aka yi" yace "Xaki yi bayani idan na kama ki ne" dauke kai tayi ya juya yayi wucewar sa, Khadija tayi dariya tace "Bari in je inyi kallo"    Ana kiraye kirayen Magrib Junaid ya fito part dinsa sanye da jallabiya milk colour,  dai dai nan Humainah da fatima suka fito daga part din Mumy, Humainah tace "Masallaci xaka ya Ahmad" Ya harareta yace "A'a office xan je" bae jira cewar ta ba ya kara gaba. Yana fito wa daga mosque bayan an idar da sllh ya tsaya da wani frnd dinsa da ke nan layin suna gaisawa, har sai da ya ga shigar Abba gida, snn yace "Abdul d'an ara min motar ka pls xan dan fita in dawo yanxu" Abdul yace "Toh mu shiga in baka key" junaid ya bisa suka shiga compound dinsu ya tsaya daga balcony har ya kawo masa makullin sannan ya nufi parking lot ya dau motar ya fita. Atm machine ya fara tsayawa ya cire kudi ya siya fruits nan wajajen sannan ya koma mota ya dau hanyar gidan El-Ameen. A waje yayi parking bayan sun gaisa da mai gadin ya shiga gidan, Mama jummai na kwance Palo kasan tiles ta shimfida xani da 'yar radionta a hannu tana saurare, ta mike xaune ganinsa tace "Sannu da xuwa Ahmad" xaunawa yayi yace "Yauwa mama ina yini?" Tace "Lfya lau, ya gidan?" Yace "Alhmdllh Mama, El-Ameen ya xo kuwa?" Tace "Ehh bae dade da fita ba, kuma yace min xai dawo" yace "Ohk, bacci take ne?" Mama jummai tace "Anya! Ina jin kamar idonta biyu" Junaid ya ajiye mata ledan fruits guda daya yace "Ga kayan marmari mama" godiya ta dinga masa ya mike ya nufi stairs ya haura sama. A hankali ya tura kofar dakin ya tsaya daga bakin kofar yana kallon cikin dakin, rakube ya ganta gefen gado ta sunkuyar da kanta, a hankali ya karaso cikin dakin yana kallonta har ya iso gabanta ya durkusa, sai a sannan ta dago kai tana kallonsa da dara daran fararen idonta, komawa baya yayi da sauri don ba kadan idanuwan nata suka bashi tsoro ba, ta wani kafe sa da ido ko kiftawa bata yi, sauke kansa yayi kasa ya bude ledan gabansa ya mike ya dawo kusa da ita ya duka a hankali ya dauki Apple daya ya mika mata, kallon Apple din take kamar me son gano abu a jiki, ya kai bakinsa ya gutsura a hankali ya fara ci yana kallonta, har sai da ya cinye sannan ya kai mata bakinta, kauda kai tayi da sauri, ya dawo gefenta ya kuma kai mata baki yace "Apple! taste ki ji" rike kanta yayi ya kai mata baki ta d'an bude bakin kadan ta gutsura, yana kallon yanda take kokarin hadiye Apple din ba tare da ta tauna ba yace "Wait, Wait!" Da sauri ya kuma gutsuran Apple din ya shiga taunawa yana kallonta ita ma haka, yanda ta ga yana yi haka ita ma ta shiga yi tana taunar Apple din a hankali, yayi murmushin sa me kyau yace "Good!" Tana hadiye wa ya kai mata baki kuma ta gutsura, karban Apple din tayi a hannunsa ta shiga ci da kanta, ya dawo gabanta ya durkusa yana kallonta, matsowa kusa da ledan ta shiga yi tana kallon ciki, ya dauki ayaba daya ya bare ya gutsura sannan ya kai mata sauran baki ta bude a hankali ya sa mata, taunawa ta shiga yi tana yatsine fuska, murmushi kawai yake yana kallonta, can ta dauki peel din bananan xata kai baki, ya karbe da sauri yace "No!" Tsuke baki tayi tana kallonsa, dariya yayi ya dauki wani Ayaban ya bude ya mika mata gaba daya, ta ajiye Apple din hannunta ta karba, cikin lkci kankani ta cinye ayabar, ya kuma bare mata wani shi ma ta cinye, haka ya dinga yi mata har ta ki karba kuma, ta dauki Apple din da ta ajiye tana kallo, karba yayi ya kai mata baki, ta dafe hannunsa da duk nata biyu ta gutsura a hankali tana taunawa, kallon hannunta kawae yake don duk haskensa ta fi sa nesa ba kusa ba, tana rike da hannunsa haka ta dinga cin Apple din, dai dai nan El-Ameen ya shigo dakin, xaro ido yayi ya rungume hannu yace "Tabdi! Me kke yi haka captain, she will bite the hell out of yhu wllh!" A hankali Junaid ya xame hannunsa daga nata, ta daga ido tana kallonsa, ya kamo hannunta ya danka mata Apple din sannan ya mike yana kallon El-Ameen, El-Ameen ya tabe baki yace "Ina raba ka da shisshige ma mahaukaciyar nan baka ji koh? Randa xata nuna maka halinta na hauka I won't be around fah" Junaid bai tanka sa ba, El-Ameen yayi kwafa ya ajiye ledan drugs din hannunsa da fresh yoghurts ya dawo gabanta yace "Ashe kin iya cin fruits" bata kallesa ba sae cin Apple dinta da take, ya d'an yi murmushi ya nufi inda alluranta suke don hada wanda xae mata, Junaid ya juya ya nufi kofa, mikewa tayi da sauri ganin haka, sae kuma ta bi bayansa, dai dai stairs yaji kamar ana binsa, ya juya ya ganta tana tahowa, kallonta ya tsaya yi, har ta karaso gabansa ta kama hannunsa ta saka masa Apple din, sannan ta daura nata hannun kan nasa ta kai bakinta ta fara cin Apple din, murmushi kawae yake yana kallonta, El-Ameen ya fito daga dakin ya rungume hannunsa yana kallonsu yace "Uhunm! It seems she's getting use to yhu yanxu, kaga kawae sae ka tattaro ina ka ina ka ka dawo nan ka tsaya da ita sai ka cike Ladan ka" yana magana ne yana murmushi, Junaid ya xame hannunsa daga nata ya damka mata Apple din ya juya ya fara sauka stairs din, bin sa tayi da sauri, El-Ameen ya daka mata tsawa, a tsorace ta juya tana kallonsa, ya karaso inda take ya kama hannunta suka koma daki, xaunar da ita yayi gefen gado, ya bude yoghurt din da ya shigo da ya xauna gefenta ya kai mata baki, ta kauda kai da sauri, wani kallo yayi mata yace "I will slap yhu" kamar ta ji me yace bata sake yunkurin dauke kai ba, ya dafa kanta ya kai mata yoghurt din bakinta, a hankali ta dinga sha tana kallonsa, tari ta fara yi ya cire yoghurt din da sauri daga bakinta a hankali yace "Sorry," ya dafa kanta ya kuma kai mata baki, ta dauke kai da sauri tana kokarin karban roban, sake mata yayi ta kallesa sannan ta fara tuttular da shi nan kasan dakin, fixge wa yayi da sauri yace "Ance maki idan aka koshi xubar da abinci ake?" Kallonsa kawae take ko kiftawa bata yi, ya ja dogon hancinta yace "Da wani idanuwanta a wajen" jan hancin ita ma tayi yanda ta ga yayi, yayi murmushi yana kallonta, yoghurt din hannunsa ya rufe ya ajiye sannan ya mike ya nufi inda drugs dinta suke, diluting yayi mata a cup ya dawo gefenta ya xauna, matsawa ta fara yi daga kusa da shi, ya jawo ta ta fasa ihu, d'an buge mata baki yayi tayi tsit tana kallonsa, ya kai mata maganin baki taki budewa, sae da yayi mata tsawa sannan ta bude da sauri har jikinta na rawa, ya xuba mata maganin gaba daya, sai da ya tabbatar ta shanye snn ya mike yana kallonta, banda yatsine fuska bbu abinda take, yayi murmushi ya juya ya fita daga dakin, downstairs ya sauka ya samu Mama Jummai kadae palon, yace "Junaid fa Mama?" Tace "Ya fita ae" yace "Ohk, ki taso toh ki rakata baya tayi fitsari yanxu xata yi bacci tunda na bata magani" mikewa tayi tace "Toh, ae tana da tsafta yarinyar duk me xata yi naga tana shiga bayi" yayi murmushi yace "Kin dai yrda bata komai yanxu koh" yar dariya tayi tace "Ehh na yrda, don daxu ina xaune ta sauko, duk na tsorata ba kadan ba, ae ko in gaya maka sai gani nayi ta xauna gefe na ta mimmike kafa yanda taga nayi" dariya El-Ameen yayi yace "Ae wayo gareta, idan Allah ya yrda sama mata lfya baxae wani dau lkci sosai ba, kila daga nan xuwa wata hudu ko shidda in'sha Allah" Mama jummai tace "Toh Allah ya yrda, Allah ya ba Baiwar nan tasa lfya, gashi 'yar yarinya da ita" yayi murmushi yace "Kina ga xata yi shekara nawa" Mama jummai tace "Kai baxata wuce sha shidda ba wllh, in ma ta kai kenan" yana murmushi yace "Ko kuma sha bakwai ba" Mama jummai tace "Allah sarki, amma dai ku dinga hada mata da Addu'a kunsan duniya bbu gaskiya, kar ayi ta na turawa nan kuma kila asiri ne" ya d'an yi shiru kafin yace "Anya kuwa, bana tunanin jifa ne, don da jifa ne ba lallai ta xama nutsatssiya haka ba, nd jiya naga tana ta observing wnn tumatir din cikin dankalin da na siyo kuma ta sha sosai" Mama Jummai tace "Toh Allah dai ya bata lfya amma dai ayi addu'ar ma" yace "Ameen, xa a hada mama" Sama mama Jummai ta nufa shi kuma ya xauna palon, bata mata wani gardama ba ta kai ta bayin. Ko da Mama Jummai ta sauko mikewa El-Ameen yayi ya koma sama, kwance ya sameta idonta lumshe alamar xata yi bacci, ya gyara mata kwanciya ta bude ido da sauri tana kallonsa, ya rufa ta da bargo, ya dawo dai dai fuskarta yace "Gudnyt" lumshe ido kawae tayi ya juya ya fita daga dakin ya rufo mata kofa, yayi ma Mama Jummai sae da safe ya fice daga palon, xaune ya ga Junaid a balcony, ya d'an bude ido da mamaki yace "Thought ka tafi ai" Junaid ya mike yace "Sure! Yanxu xan tafi" daga haka ya sauka balconyn yayi hanyar gate, El-Ameen ya bi sa da kallo sannan ya tabe baki ya bi bayansa, kusan a tare suka fita compound din, El-Ameen ya kalli motar da Junaid ya nufa yace "Whose car is that?" Ba tare da Junaid ya kallesa ba yace "Abdul" daga haka ya bude motar ya shiga, El-Ameen ya karasa gun motar yace "Yhu are acting strange this dayz Captain, let it not be kai ma ka fara samun brain disorder'n ne fa, aikin sai yayi min yawa" El-Ameen ya kare maganar yana murmushi, junaid ma yayi murmushi yace "Sure!" Daga haka ya ja motar ya bar sa nan tsaye, El-Ameen ya bi motar da kallo yana murmushi yace "It's Alwayz: 'Yea! Sure! D'an rainin hankali, tasa motar shi ma ya nufa ya bude ya shiga ya bar anguwar yana tunanin yanda xai yi squeezing time dinsa gobe da safe ya xo ayi diagnosing dinta.

✍🏻
*Haske Writers Association*💡


⚓ *Captain_Ahmad Junaid*⚓

     _By Khaleesat Haiydar_✍🏻

 14.....

Junaid na isa layinsu ya kira Abdul don ya fito ya karbi motar sa, Abdul ya fito yayi instructing mai gadinsu ya bude gate, yana budewa Junaid ya shiga yayi masa parking a parking lot din gidan sannan ya fito ya mika masa makullinsa yace "Thanks Abdul, sae da safe." Masallaci ya fara shiga yayi Isha sannan ya shiga gida, sai da ya tabbatar Mumy baxata hangosa ba idan ya xo wucewa ta side dinta sannan ya wuce da sauri. Humainah ce tsaye bakin tap tana diban ruwa, ta bi sa da kallo tace "Daga ina kake ya Ahmad" ba tare da ya kalli inda take ba yace "Inda kika aike ni" dariya tayi tace "Mumy fa na ta neman ka" dawowa yayi da sauri wajenta yace "Kice Wllh, tun yaushe?" ta kyalkyale da dariya tace "Tsaya nan, tun daxu ake neman ka" ya hade rai yace "Ke wa ya gaya maki?" Ta d'an yatsine fuska tace "Tare mukayi ta neman ka ae har da Hajja, da Abba, an ma kira layin ka bae xuwa wai switch off" shiru yayi ya ma rasa tambayar da xae kuma yi mata, ta tabe baki ta kashe tap don bucket dinta ya cika, Muhibba ce ta karaso wajen, kallo daya tai ma Junaid ta dauke kai, Empty Bucket din dake wajen ta kalla tace "Ke wa yace ki taba min ruwan da na tara?" Humainah ta tabe baki tace "Oho, nima haka naga bokitin" cike da masifa Muhibba tace "Kar ki gaya min maganar banxa ba ni da ke bane a nan xaki wani ce baki sani ba" hararanta Junaid yayi ya juya xae bar wajen, Muhibba ta yi ball da ruwan da Humainah ke diba, Humainah ta xaro ido tace "lalala!  Wllh sai na rama" dawowa Junaid yayi da sauri ya rike ta ganin tayi gun Muhibba, yace "Ke Babu ruwa a ciki ne?" Kamar xata yi kuka tace "Dubi fa abinda ta min ya Ahmad, Hajja ce fa ta aikeni in debo mata ruwa" yace "Ke kin taba ganin inda ake fada da mara hankali!" Humainah tace "ohh Kuma fa haka ne" yace "Gud! Ki tafi ciki ki debi ruwan ki" tace "Ko ba Hajja ta sa mai gadi ya kashe engine ruwan ba tun da rana" yace "Ehh xan je in kunna yanxu" tace "Toh" juyawa Muhibba tayi fuu ta bar wajen, Humainah ta kyalkyale da dariya, ya harareta ya juya yayi side din Mumy, da sauri tace "ni fa wasa nake maka ba a neman ka" juyawa yayi yana kallonta yace "Na fara wasa da ke ne koh?" Kwafa yayi ya nufi part dinsa.  Muhibbah na shiga part dinsu ta xube jikin Hajiya dake xaune Palon da Rabi'a ta fashe da kuka tace "Hajiya kina ganin fitsaran da yarinyar nan da suka xo gidan nan da Hajja ta min, har Ahmad na Goya mata baya yana kirana mara hankali" Hajiya da bacin rai ya bayyana karara a fuskarta tace "ki ka barta baki ci ubanta kin nakada mata duka ba?" Muhibba na share hawaye tace "Toh ba yana tsaye gun ba" Sadiya tace "duk uwarsa ke xuga sa yake rashin mutunci a gidan nan wllh" mikewa Hajiya tayi kamar xata tashi sama ta fice daga palon tayi part din Junaid, yana xaune rike da remote xae yi powering Tv ta shigo, kallo daya yayi mata ya dauke kai, cikin fada tace "Ahmad ita Muhibbar kake kira mahaukaciya? Toh in har Muhibba na hauka to Amina ma haukan take, ita ce ma babban mahaukaciyar..." Mikewa yayi yana kallonta a nutse yace "Ina ganin girman ki a matsayin ki na matar mahaifi na, amma kika sake kika taba  mahaifiyata girman nan xae xube wllh," a fusace tace "Ya dade bai xube ba girman don uwarsa, da can ganin girman mu kake munafuki, ai mu wllh sai dai mu ce Allah ya isa tsakaninmu da Amina duk ta shanye mana miji sai yanda tayi da shi, kai ma ka taso kana neman xame mana fitina da bala'i a gida to kun yi kadan daga kai har makirar uwar taka....." Wani irin kallo Junaid ke mata ya girgixa kai yace "Gaskiya jahilci cuta ne" xaro ido tayi ta dafe kirji tace "Ni kake kira jahila Ahmad?" Juyawa yayi ya koma ya xauna, ta fashe da kuka ta juya ta fice daga palon.  Ko minti biyar bata yi da fita ba Khadija ta shigo tace "Ya A.jay Abba na kiran ka" ya kalleta ya dauke kai ta fita, mikewa yayi ya bi bayanta. Part din Abba ya tafi ya shiga palon da sallama, babu abinda ya daga masa hankali sai ganin Mumy da yayi a palon, ya karasa a sanyaye ya xauna kasa kusa da ita yana kallonta, ganin taki kallonsa yasa ya juya ya kalli Abba yaga yanda ya wani hade rai yana kallonsa, Hajiya na xaune palon sai sharban kuka take, Umma sai wani sauke ajiyar xuciya take tana tabe baki, ko kadan hakan bai damesa ba yafi tunanin fushin Mumy a kan ma na Abban, Abba ya mike cikin tsananin fushi yace "Ahmad maimaita abinda ka fadi ma Hajiya a palon ka daxu" ya d'an kalli Abba sannan yayi kasa da kai yayi shiru, Abba ya daka masa tsawa yace "Ba magana nake maka ba" nan ma dai bai dago ba bare yace wani abu, Hajiya aka kuma fashewa da kuka mai sauti, Abba yayi murmushin takaici yace "Wato ita Hajiyar kake kira da jahila ko Ahmad?" Junaid ya girgixa kai har lokacin bai dago ba yace "Ni ban kirata da haka ba Abba" Wani tsawa Abba ya daka masa yace "you are stupid, sharri tayi maka kenan" Junaid ya girgixa kai, a fusace Abba yace "Toh bari kaji abinda baka sani ba, in har xaka iya bude baki ka ce ma Hajiya Jahila, to bbu tantantama warcan da ta haife ka ma xaka iya kiranta da haka, ka sani matsayin uwarka dai dai yake da wa ennan da ka raina a gidan nan, kuma from henceforth a gidan nan sai ka ma uwarka fitsara ka xauna lafiya amma idan ka kuskura kace xaka masu sai ka ga the other side of me wllh, I will deal with you, maxa tashi kaje ka bata hakuri kar in baka mamaki yanxu" Junaid da yaji kamar an soka masa mashi ya daga kai da kyar yana kallon Mumy, hawaye ya gani idonta, rudewa yayi ya dawo gabanta ya durkusa yace "Noo plss mum, kar ki xubda hawayen ki saboda ni, don Allah kiyi hakuri ki yafe min" bude baki Abba yayi yana kallonsa da mamaki, Hajiya da Umma ma sai kallonsu suke cike da tsana, shi kam magiya ya dinga yi ma Mumy yana bata hakuri ba tare da ya kuma bin ta kan Abba ba, mikewa Mumy tayi ta fice daga palon, shi ma ya mike xai fita, Abba yayi masa wani mugun tsawa, juyowa yayi yana kallonsa a hankali yace "Abba xan je in dawo"

Karfe hudu da rabi Junaid yyi parking a parking area din gidansu, ya dade xaune cikin mota yana danne dannensa a waya har sai da Humainah ta leko daga part din Mumy, ganin haka ya kashe motar ya fito ya kulle, wuce ta yayi ya bude kofa ya shiga, ta bi bayansa tace "Me kake cikin motar ya Ahmad?" Yace "Abinda kika sa ni" dariya tayi ta bi bayansa, ya xauna Palo yana kallon Mumy a hankali yace "Sannu da gida Mumy" tace "Welcome, kai dadin xaman mota kawae kake" murmushi yayi ganin Mumy ta huce gaba daya yace "Na gaji ne Mum" Humainah ta xauna kasa kusa da shi tace "Sannu da dawowa ya Ahmad" banxa yayi mata, fatima dake palon ma tace "Sannu da dawowa yaya" yace "Yauwa" sannan ya mike yace "Bari in je in yi wanka Mumy" Mumy tace "Ba gaisheka Humainah yi ba" yace "Gulma ce fa Mumy, da tana gaishe ni ne" Mumy ta hararesa yyi murmushi kawae ya nufi kofa, Humainah ma ta bi sa da harara, Yana shiga part dinsa yayi wanka ya dawo Palo yayi kwanciyarsa, yana son xuwa gidan El-Ameen amma bai ma san inda xae ce ma Mumy xai je gashi yana ta kiransa tun a gun aiki ya ki dagawa, ashe akwai ranan da xai ga disadvantage din rashin fitarsa, don da yana fita da Mumy baxa ta dinga querying dinsa ba idan yace xae fita yanxu, mikewa xaune yayi jin an bude kofar parlour,  Humainah ta shigo ta tsaya daga bakin kofa tace "Mumy tace ka xo ka ci abinci" dauke kai yayi yace "Naji" ta karaso cikin parlour'n tace "ni da ita muka yi girkin, tuwo da vegetable soup" ya hade rai yace "Who ask yhu" dariya tayi tace "Toh don ma na gaya maka" ya tabe baki ya mike ya dauki wayarsa ya nufi kofa, mikewa tayi ta bi bayansa da sauri, sai da suka fita yace "Hajja fa?" Tace "Bata nan taje gidan kawarta yau, kasan gobe xa mu koma" ya kalleta yace "Wa yace maki tare xa ku koma, bayan Abban ki yace ya ba mu ke" hade rai tayi tana kallonsa tace "Wa yace maka haka" murmushi yayi ya bude kofar parlour'n Mumy ya shiga ta bi bayansa. Kasa ta xauna tana kallon Mumy tace "Mumy wae ba da ni Hajja xata tafi ba gobe?" Mumy tace "ba tace nan xata bar ki ba" hawaye ne ya cika idonta tace "A'a ae ni ban ce xan xauna ba" Mumy tayi dariya tace "Toh bari idan ta dawo sae ki gaya mata, Meye abun kuka" dariya Junaid yayi yace "Ae sai dai tayi na jini nan xata xauna ita da fatima da khadija" ta fashe da kuka tana kallon Mumy, Mumy ta hararesa tace "kaga wuce dinning ka ci abincin ka bana son haka" mikewa yayi ya nufi dinning yace "Yi hakuri Mumy" mikewa Humainah tayi xata fita daga parlour'n Mumy tace "Ina xa ki" tana goge fuskarta tace "Xan je in jira Hajja" Mumy tayi dariya tace "Ai yanxu xata dawo, xo kiyi xaman ki a nan ki jirata" bata tsaya ba tayi ficewarta a palon. Har aka kira Magrib Junaid na kwance palon Mumy duk ya rasa yanda xae ce mata xai fita, mikewa yayi ya nufi toilet din palon yayi alwala ya fita xuwa masallaci, yana dawowa ya nufi part din Abba sanin ya shiga yanxu, Hajiya ce a parlour'n tana jera masa abincin supper a kasan lallausan rug din tsakar parlour, ya karasa ciki kansa a kasa yace "Ina yini?" Hade rai tayi tace "Ka fita don Allah abinci xai ci ynxu" tsayawa kallonta yayi, dai dai lkcn da Abba ya fito daga bedroom dinsa, Abba ya karaso cikin palon yana kallonsa, karasawa yayi inda Abba ya xauna, ya xauna daga kasa shi ma, a hankali yace "sannu da dawowa Abba" Abba yace "yauwa sannu, ya aikin?" Har lokacin bai dago ba yace "Alhmdllh!" Abba yace "Gud! Daxu baka shigo gaishe ni da safe ba" shafa kansa yayi yace "Na shigo Umma tace kana bacci" Abba yace "Ohk, amma baka karasa bedroom ba" junaid ya gyada kai kawae, Abba yace "kafi kowa sanin bana baccin safe ae" shiru Junaid yayi bai kuma cewa komai ba, kallonsu kawae Hajiya keyi ta gefen ido tana jera abincin da take rai ba dadi don bata so haka ba, Abba ya sauko kasa ya jawo babban food warmer, ya dau plate xai dibi shinkafa, Junaid ya karba yace "Bari in xuba maka Abba" sake masa spoon din Abba yayi, ya dibi shinkafar da stew a gefe da cow meats, snn ya xuba masa vegetables a kai kamar yanda ake masa, Abba ya dauki wani spoon din yace "Bismillah" sai da Abba ya fara ci sannan Junaid ya debi shinkafar a hankali ya kai bakinsa, Hajiya kamar ta hadiye xuciya ganin ko ta kanta Abba bae bi ba, taunar abincin kawae junaid yake ba don yayi masa ba, banda girkin Mumynsa babu na wanda yake ci, girki in ba nata bane ko kallonsa bai yi, shiyasa a ko da yaushe take bata tym dinta tayi masa girki, a tare suka gama cin abincin da Abbansa, bai yi Mamakin sakkowan Abba da wuri ba don in dai suka hada sa da shi, bai daukan lkci yake kuma jawo sa jiki, kwata kwata baya fushi mai tsayi da only son din nasa, hakan ba karamin daga ma su Hajiya hankali yake ba, sun dai rasa yanda xa su yi da Junaid a gidan, a tare suka tafi masallaci sllhn Isha da Abba, sae da suka dawo ya ba Abbansa hakuri a kan abinda ya faru jiya, Abba yace "Its Ohk, ka dai kiyaye halshan ka nan gaba" yace "In'sha Allah Abba" sun jima suna hira da Abba sannan yayi masa sai da safe ya mike ya fita ya shiga part din Mumy, tana xaune palo tana kallo, ya xauna gefenta ya dauki remote xae canxa tasha, Mumy ta karbe remote din tace "ya haka, bari a gama program din mana" kallon Humainah dake kwance kusa da fatima yayi yace "Har kin hakura xaki xaunan kenan?" ta daga kai tana kallonsa bata tanka sa ba ta dauke kai, Mumy tayi dariya tace "babban kawai" bude kofa aka yi hade da sallama, Junaid ya kalli agogo jin muryan El-Ameen, ya ga tara da rabi, Mumy tace "Kai dai baka jin fitan dare koh El-Ameen" junaid yayi murmushi yace "Kin manta likita ne Mumy" El-Ameen ya karaso parlon ya xauna yana murmushi ya gaida Mumy, da fara'a tace "lfya lau bokon turai ya aiki" yace "Alhmdllh Mumy" Fatima tace "Welcome bro" yace "Thank you sis" kallon Humainah dake xaune hankalinta na gun kallo yayi sannan ya kalli Junaid, Mumy tace "baki gaida yayanki ba Humainah" ba tare da ta kallesa ba tana ci gaba da kallonta tace "Ina yini" idonsa na kanta yace "Lfya lau" hira suka dinga yi da Mumy, ganin hiran ba me karewa bace Junaid ya mike ya nufi kofa yace "Ina part dina in ka gama karyan" dariya Humainah tayi a karo na farko ta kalli El-Ameen da ya hade rai yana kallon Junaid, Mumy ma tayi dariyar tace "Ae dae ya fi ka wllh tun da har yana daurewa yayi karyar" Junaid dake bakin kofa ya saka dariya yace "Surutun fa iyakansa a gida Mumy, mutumin da ko magana bai iya yi ma mace ba a waje sai kame kame," El-Ameen yace "Ehh ae kai naga ka iya d'an rainin hankali" banda dariya bbu abinda Humainah ke yi Mumy da fatima na taya ta, Junaid ya juya ya fice daga parlorn yana murmushi, mikewa El-Ameen yayi yace "Bari in je Mumy" Mumy tace "Toh fatima xata kawo maku abinci" toh kawae yace ya fita, Part din Junaid ya nufa ya samesa xaune a parlor ya kunna Tv, El-Ameen yace "Yau ban gan ka ba, kuma I was calling tun daxu baka responding" Junaid yace "I wasn't in a gud mood ne yau" El-Ameen yace "Wacece wannan yarinyar dake xaune parlorn Mumy" Junaid ya kallesa yace "Ya aka yi" d'an sosa kai El-Ameen yayi yace "Umm, tana da kyau ne" dariya Junaid yayi yace really?" El-Ameen yace "What's funny, Allah tana da kyau" Junaid yace "Toh bari ta shigo" ko rufe baki junaid bai yi ba sai ga ta ta shiga palon da sallamarta rike da tray din abinci, El-Ameen ya sunne Kai murya can kasa yace "Don Allah ka rufa min asiri kar kace komai Junaid, wasa nake" Junaid ya fashe da dariya yace "Humainah" ae da sauri El-Ameen ya mike ya rufe bakinsa da hannu yana xaro ido, junaid ya dinga dariya yana tura hannunsa amma yaki sake sa, tabe baki tayi ta ajiye trayn hannunta tace "Mumy tace in kawo" da karfi Junaid ya tura El-Ameen yace "ke kin yi saurayi likita" ae ko rufe baki bai yi ba, El-Ameen yayi hanyar daki da sauri ya shige ya rufe kofar, Junaid ya dinga dariya har da rike kai, hade rai tayi tana kallonsa, can tayi tsaki ta juya ta fice daga parlon, kin fitowa parlor El-Ameen yayi har kusan Karfe goma, Junaid ya shiga dakin yace "Toh wai a haka xan baka kanwar tawa kana kunyar ta!" El-Ameen dake xaune gefen gado yace "ta tafi?" Junaid yace "Aa tana parlor" shiru El-Ameen yayi sai kuma ya mike ya cire shirt din jikinsa ya nufi bathroom, junaid ya bi sa da kallo yana dariya, wanka yayi ya fito sanye da bathrobe, ya nufi closet din Junaid ya fiddo pyjamas ya sa sannan ya dawo ya xauna yana kallon Junaid yace "Amma ba nan xata kwana ba dai koh?" Junaid ya hararesa yace "Nan din xata kwana" El-Ameen ya daga kafada yace "Ohk ni kam am spending the nyt here today, its late and bana son ta gan ni, I came purposely because of ur patient, they've diagnosed her, that is an mata genetic screening, brain scans, neurological exam i.e (checking of vision, hearing, and balance) and other tests, and you knw wat?" Shiru Junaid yayi yana kallonsa, El-Ameen yace "They've found out that she is suffering from post-traumatic stress disorder (PTSD), and this is a serious potentially debilitating condition that can occur in people who have experienced or witnessed may be a serious accident, sudden demise of a loved one, violent personal assault such as rape da sauransu, terrorist incident, or other life-threatening events, you know! A lot of them....." Daga haka yayi shiru yana kallon Junaid da ya kafa masa ido ko kiftawa bai yi, junaid ya sauke ajiyar xuciya ya shafa kansa a hankali yace "But! Is it treatable? I mean can it be cured?" El-Ameen yayi murmushi ya dafa sa yace "Of course yes! But it is difficult to predict how, when, or to what degree someone is going to get better, the major treatment for disorders are Medication, Rehabilation, psychotherapy, and brain surgery, but we are only going for Medication and psychotherapy yanxu, by Allah's own grace xa a dace in'sha Allah" d'an murmushi kawai junaid yayi, El-Ameen ma yayi murmushin yace "Sai dae kuma kudin da xaka kashe fa ba na wasa bane guy, daina murmushi" wani murmushin junaid yayi yace "Wannan ba matsala bane, Allah ya bata Lfya" El-Ameen ya d'aga kafada yace "Gud! But kudin treatment din nawa fa?" Junaid yace "Thought sai ka gama xaka amshi kudi" El-Ameen yyi murmushi yace "Ohk let leave it then"

*Haske writers association*


⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓

    _By Khaleesat Haiydar_✍🏻

15....

Mikewa junaid yayi yace "Ga abinci a parlor" El-Ameen ya d'an bude ido yace "ba kace tana parlorn ba" Junaid ya hararesa yace "Me xata xauna yi min, ta tafi tun daxu" daga haka ya shige bathroom ya bar sa xaune dakin, mikewa El-Ameen yayi ya isa kofa ya bude yana lekan parlorn, ganin bata nan ya fita, sae da ya kulle kofar parlon da key sannan ya dawo ya xauna gaban abincin, iya wanda xai ci ya diba, ya dauki remote yayi powering tv yana ci yana kallo, kwanciya yayi bayan ya gama cin abincin kan dogon sofa yana kallo, Junaid ya fito daga daki sanye da pyjamas, ya mika masa wayarsa yace "Ummi na kiran ka" mikewa El-Ameen yayi xaune da sauri ya karbi wayar ya daga ya kai kunne, daga daya bangaren tace "El-Ameen kana ina ne Abban ku duk ya ishe ni da kira, what's wrong with you this days baka xaman clinic, yace tun rana rabon ka da can kuma ni baka dawo min gida ba" Kallon agogo yayi yaga har goma da rabi ya kwantar da murya a hankali yace "Kiyi hakuri Ummi ina gidansu Junaid bai da lfya ne, so I have to stay over da naga dare yayi" Ummi tace "Karyar ka kenan kullum kana gidansu junaid, are you alright Ahmad?" Da sauri yace Ummi ga junaid din ma ki tambayesa ki ji, yana fadin haka ya mika ma Junaid wayar, junaid ya karba suka gaisa da Ummi, tace "Wai baka da lfya junaid" kallon El-Ameen yayi sannan yace "Um Ummi" tace "Toh Allah ya sauwake nayi xaton karya yake min, kace masa ku kira Abba kuyi masa bayani don yana can ya cika" junaid yayi murmushi yace "Toh Ummi" daga haka suka yi sallama ya ajiye wayar, El-Ameen yace "Kaga situation din da ka jefa ni ciki yanxu kai da patient din nan taka ko Captain, kai kullum baka fashin aiki, sannan baka kai wa bayan magrib baka shiga gida ba ni ko ka barni ina ta gantali a titi ko da yaushe, na ma daina aikina a clinic kullum safe dare ina hanyar duba mahaukaciyar ka, look am not taken less than 500k idan na gama treating din mahaukaciyar nan" Junaid yayi murmushi yace "Sure! Wannan ba matsala bane I will pay you."
Da asuba tare Junaid da El-Ameen suka fita xuwa masallaci, suna dawowa El-Ameen ya koma yayi kwanciyarsa ya ci gaba da bacci, Junaid yayi murmushi ganin haka, a xuciyarsa yace lallai kam sleep well, toilet ya shiga cikin minti ashirin yayi wanka ya fito ya shirya cikin khakin sa, kamshin turarrukansa ne ya tada El-Ameen, ya mike xaune yana kallon agogo yace "Wai kai barin gari xaka yi haka da asuba ne da baxa ka bar mutum yayi baccin safe ba captain, duk ka ishe ni ka hana ni bacci don xaka aiki" Junaid na saka wristwatch dinsa yace "sorry, go back to ur sleep, ni yanxu ma xan bar maka dakin" Yana fadin haka ya dauki wayarsa da hularsa ya nufi kofa, El-Ameen yace "Wait, wai Karfe nawa yanxu?" Junaid yace "6:40" daga haka yace "May be ka same ni part din Mumy in ka fito da wuri" El-Ameen yayi tsaki shi kuma yayi ficewarsa. Har El-Ameen ya koma ya kwanta ya mike da sauri tunawa da yayi akwae alluran da yake ma patient dinsa bakwai da rabi. Toilet ya shiga yayi wanka a gurguje ya fito, cikin mintunan da basu wuce goma ba ya kintsa cikin blue shirt da black jeans a closet din junaid, ya feshe jikinsa da turare ya dau wayarsa ya fice daga dakin, yana isa part din Mumy suka kusa cin karo da Humainah xata fito, ae da sauri ya sunkuyar da kai ya bata hanya ta bi ta gefensa tayi gaba abunta, ya sauke ajiyar xuciya ya shiga parlon, ko kallon Junaid dake xaune yana shan tea bai yi ba, ya gaida Mumy ta amsa tace "ga breakfast dinka can a dinning" yace "A'a Mumy sauri nake wlh, idan naje office xan yi" Mumy tace "Kan ka daya kuwa, Karfe nawa yanxu da baxa ka tsaya kayi break ba" kallon agogo yayi yace "Mumy wllh am in a haste ne..." junaid dake kallonsa yace "Da wannan surutun da yanxu ka gama hada tea" hararan sa yayi sannan ya karasa kusa da shi yayi kasa da murya yace "look akwae wani injection da xan ma patient dinka ne b4 7:30, shi yasa nake sauri," da sauri Junaid ya kalli Mumy dake kallonsu yace " Ohh Mumy ashe emergency aka kira sa ne fa" Mumy ta tabe baki tace "Kwa ji da gulmar ku ba ruwana" El-Ameen ya d'an yi murmushi yace "Ko xuwa Karfe goma xan dawo inyi wllh Mumy" Mumy tace "Ka fa rantse" dariya yayi yace "in'sha Allah Mum" mikewa Junaid ma yayi ya shiga bedroom din mumy ya dauki kardigan dinsa yasa don garin da d'an sanyi, ya fito yace "Mumy sai na dawo" ta bisa da kallo kafin ta tabe baki tace "Toh dai kar ka manta ku shiga kuyi wa Hajja sallama don yau xata tafi, ko Abba ma baku shiga kun gaida ba bare mutan gidan" Junaid yace "Xamu shiga" daga haka suka fita daga parlon, sae da suka fara shiga part din Abba suka gaida shi sannan suka yi part din Hajja, tana ta hada kaya, Humainah na xaune gefenta sai rusa kuka take ita ma da tata jakar a gefenta, Hajja na mata ruwan bala'i tana cewa tayi kadan ta koma da ita tunda dama ba ita tace ta biyo ta, xamanta daram a gidan ko suma take, Junaid ya fashe da dariya yana kallon Humainah, ita ko tana ganinsu ta hadiye kukan ta sunkuyar da Kai kasa, Hajja tace "Atoh, ka dai gan ni da gantalalliyar nan wae sae ta bi ni Amadi, sae kace ance mata wahalalla nake kamar irin ni na ce ta biyo ni din nan shegiya, nufin ta in koma da ita muna galallawa a titi, to dadin abun dai ba kudin banxa gare Muhammad ba, kuma ubansa Ahmad bae ce yaje xae gani ba bare ya biya kujeru biyu na jirgi" Junaid ya dinga dariya yana kallon Humainah, El-Ameen yyi murmushi ya gaida ta, ta kallesa ta gefen ido ta ci gaba da abinda take ba tare da ta amsa ba tana ci gaba da yi ma Humainah masifa, dariya yayi yana shafa kansa don yasan me yasa bata amsa ba, Junaid ya ciro dubu talatin da ya tanadar mata dama ya ajiye gabanta yace "Gashi ni da El-Ameen ki sha ruwa da dabbino a hanya kar ki je kina masu amai a jirgi" ta washe hakora tana kallon El-Ameen tace "Toh Allah maku albarka, ga kuma amanar jikata a hannun ku, don mayu sun yi yawa gidan, Amina na damka ma ita, tamkar yanda xata yi ma fatima xata yi mata" Junaid yayi murmushi yace "In'sha Allah" Hajja ta kara da cewa "Kuma ga maganin tsari kala kala can na kai ma uwarka idan taga dama ta baka, ka kuma sanma marowacin abokin nan naka don duniya bbu gaskiya yanxu, barin kai da kiri kiri matan ubanka ke nuna basa sonka" shi dai El-Ameen sae kallon agogo yake don bai son lkcn nan ya wuce duk hankalinsa yayi gun patient dinsa, Junaid yace "Toh Hajja" kallon Humainah yyi ya mike yace "Ae sae ki dauki jakar ki kai bangaren Mumy" ta fashe da kuka, Hajja tace "Tashi ki ban waje yar wahala, bbu inda xani da ke ki xauna gidan wan ubanki don shi xaki gani ranan gobe kiyama" Humainah na kallon Junaid cikin kuka tace "Ya Ahmad kace mata don Allah ta tafi dani wllh bana son in xauna gidan nan kullum fada ake yi" Hajja tace "A haka xaki saba ki koya ki iya kema" Junaid ya fice yana dariya ta bi bayansa da sauri, El-Ameen ya kuma yi ma Hajja sallama ya fice shi ma yana danne dariyarsa wai kullum fada, sae da suka fito compound Junaid ya kama hannunta yace "kinga ki bari ta tafi sai in maida ke next week I promise" da haka ya lallabata tayi part din Mumy tana kuka, Umma na daga balcony dinta xaune haka ma Hajiya kamar masu cin kasuwa kuma duk don sbda sa ido suke yin haka, ko kallonsu bai yi ba yayi gun motarsa, El-Ameen ma bai kalli idan suke ba ya bi bayansa, duk suka bi su da kallo ko wanne da tunaninta a xuciya, El-Ameen ya kwace key hannun Junaid ya shiga driver seat ya tada mota, Junaid yayi murmushi ya xaga daya side din, yana gama ba motar wuta ya ja suka har compound din bayan masu gadi sun bude gate, gudu kawae El-Ameen ke shararawa, Junaid yace "Wae lafiya wannan gudun Ahmad" ko kulasa bae yi ba, Junaid yace "Look kar kaje ka kashe ni ma uwata a banxa, wannan ae hauka ne are we flying, plss ka tsaya in sauka" nan ma dai bae kulasa ba sai da ya gansa a kofar gidansa yana kallon agogo yaga bakwae da minti ashirin, yyi ma junaid wani kallo yace "you heard me ryt daxu amma" daga haka ya bude motar ya shiga gidan, Junaid ya kalli agogo ganin da sauran time ya fito ya nufi cikin gidan shi ma, bbu kowa parlon sai kamshi dake tashi Mama Jummai ta tsaftace ko ina, daki El-Ameen ya nufa, ya tsaya daga bakin kofa bayan yayi sallama yana kallonsu, tana xaune gefen gado Mama jummai na packing mata gashinta, ta gama shiryata tsaf cikin doguwar rigar kanti sea green da stones gold colour a jiki, tun daga nesa kana iya ganin white eyeballs dinta sbda uban kwallin da mama jummai ta sa mata, wanda hakan ya kara fito da kyan idanuwan nata, kallonta kawae yake sannan ya shigo dakin, Mama jummai na murmushi ta gaida shi tace "Na ma yi xaton baxa ka xo yau ba ganin har lkcn xuwan ka ya wuce" murmushi yayi yace "Na makara ne mama" ta mike daga durkushen da take tace "Bari in hada mata abinda xata ci" daga haka ta fita, ya karasa kusa da ita ya duka yace "Morning" kallonsa kawae take, sai kuma ta dauke kanta, mikewa yayi da sauri tuna lkci na wucewa ya nufi gun alluranta, cikin few minutes ya hada alluran yayi mata, xuwa yanxu ta fara hakura ta tsaya yayi mata alluran ba gardama, dagota yayi suka fita daga dakin yana rike da hannunta, Junaid na xaune parlor suka sauko ya bi su da ido, tsakar parlon El-Ameen ya xaunar da ita kan rug, Mama jummai ta fito daga kitchen rike da bowl din pap tace "Kaga jiya da rana na dama kunu ina sha naga tana tana kallonsa sai na bata ae ko tasha, kuma da yawa ta sha, shiyasa ma yanxu nayi mata" El-Ameen yace "Ohk" xaunawa Mama Jummai tayi kusa da ita ta fara bata, sau biyu ta sha ta fara kokarin amshe spoon din hannunta, shi dai Junaid kallonsu kawae yake, El-Ameen ya karbe spoon din hannun Mama jummai ganin ta dage sai ta karba yana mata wani irin kallo, lkci daya ta nutsu, da kansa ya shiga diban pap din yana kai mata baki tana bude bakin tana amsa, Mama jummai tayi murmushi ta Mike ta bar parlon don xuwa ci gaba da aikinta, cokali hudu kadai ta karba ta dauke kai, ya hade rai ya dafa kanta ya kai mata pap din spoon din baki, da kyar ta bude bakin ya xuba mata tayi saurin maido shi spoon din, wani tsawa ya mata, lkci daya jikinta ya dau rawa ta bude baki ya kuma maida mata ta hadiye, sake diban wani yayi ya bata taki karba yace "I will slap you fa" bata fuska tayi tana komawa baya a hankali, murmushi yayi yana kallonta, sai kuma ya lumshe ido ya kai kunun bakinsa ya sha, da sauri ya bude ido ya juya yana kallon junaid yaga kallonsa kawae yake. Jefar da spoon din yayi cikin pap din duk ya daburce yace "I I didn't even realize wat I was doing faa, hankali na duk baya wajen" ya runtse ido yana yamutse baki da fuska yace "So irritating" Junaid ya tabe baki ya mike ya dau wayarsa da makullin motarsa dake ajiye kan kujera ya fice daga parlon, El-Ameen ya bi sa da kallo, ita ko daukar spoon din tayi ta juya shi upside down cikin pap din ta debo ta Kai masa baki, murmushi yayi yana kallonta ya kauda Kai, ai ko ta xuba masa a kan hanci ta kuma debo wani xata kai hancin ya rike spoon din yana dariya yace "Keee" kokuwa suka shiga yi ita fa sae ta sa masa a hanci ta wani hade rai, da sauri ya bude baki sae ta xuba masa d'an kunun da ta debo ciki, ya lumshe ido ya shanye Sannan ya dauke bowl din ya boye a bayansa, xata mike ya komar da ita ya xaunar yace "C'mon" 

*Haske Writers Association*


⚓ *Captain Ahmad Junaid*⚓




         _By Khaleesat Haiydar_✍🏻




16.....

Mama jummai ta shigo palon rike da bucket tace "Har ta shanye?" Yace "A'a barnatar da shi xata yi shi yasa na boye, ta koshi kuma" mikewa yayi ya dauke bowl din yace "Xan tafi yanxu, sai na dawo anjima mama" ta karba bowl din tace "Toh Allah ya tsare" daga haka ya ja dogon hancinta yayi hanyar kofa, mikewa tayi da sauri ta bi bayansa, Mama ta saka dariya tace "Au, toh gashi xata bi ka" juyawa yayi da sauri yana kallonta ya galla mata harara yace "I will knock you idan kika xo nan" kamar ta ji me yace ta tsaya tana cixgar stones din rigarta tana kallonsa, ya juya ya fice daga parlon, mama jummai ta karaso ta kama hannunta suka koma cikin parlour'n. El-Ameen na fita ya rike waist a waje tunawa da yayi ai ba mota kuma bbu kudi hannunsa, tsaki yayi ya nufi main road da kafa ya tsayar da adai daita ya gaya masa anguwarsu, suna isa yace yana xuwa sannan ya shiga ya fito masa da kudi ya basa ya koma ciki, Ummi dake parlor sai binsa da kallo take bayan ta amsa gaisuwarsa tana ganin ya nufi daki tace "Xo nan Ahmad" komawa yayi ya xauna kasa yana kallonta yace "Gani Ummi" tace "Ina kake xuwa this dayz baka xaman office?"  Ya d'an sosa kai yace "Ummi, dama... To wai Ummi wa yace bana xama office ni da kullum sai na je clinic" Ummi ta galla masa harara tace "Am not joking Ahmad, wannan sabon salon da ka tsiran ma rayuwarka ba fishshe ka xai yi ba don b'ata ma mahaifin ka rai kawae kake" ya sunkuyar da kai bai ce komai ba, Ummi tace "Magana ta biyu kuma tunda kai ka kasa fito da mata toh ni na xabar maka...." Da sauri ya D'ago kai yace "Ummiii!" Tana masa mugun kallo tace "Ehh, ni ma xan rakaka gidansu yarinyar da kaina in ma ya kama ni xan maka maganar sai inyi, kuma ba wata bace facce 'yar abokin Abban ka Fiddausi" wani xufa ne ya shiga keto masa duk ya ma rasa abinda xae ce, da sauri yace "Ummi ni fa na riga da na samu yarinyar da nake so" Ummi na hararansa tace "Wannan kuma ba matsala ta bace, sai dai kuma ka raina ma kanka hankali ba ni ba" ya marairaice mata yace "Ummi Allah kuwa da gaske, a gidansu junaid ma take" Ummi tace "Wacece kenan?" Yayi kasa da kai a hankali yace "Humainah take ko wa? kuma niece din Junaid ce" Ummi tayi shiru tana hararansa yace "Allah kuwa Ummi, naji kamar ina sonta" tace "Toh ae xanje gidansu junaid din kuwa" bai kuma cewa komai ba sai tunani yake anya gskya ya fadi ma Ummi kuwa, can dai ya mike yace "Bari in tafi office Ummi", tace "Allah ya tsare"
Karfe Hudu saura Junaid yayi parking kofar gidan El-Ameen ya fito, ya koma back seat ya cire hularsa ya ajiye da rigar khakinsa ya dauki well ironed shirt dinsa dake bayan mota don bae rasa mofti a motar ya saka sannan ya fito ya shiga gidan, Mama jummai na share parlor ita kuma tana tsaye jikin bango kamar xata shige ciki, Mama jummai tayi masa sannu da xuwa, ya amsa tare da gaisheta hankalinsa na kanta, Mama jummai tace "ka ganta can tafi awa biyu tsaye taki xaunawa" murmushi yayi ya karasa inda take tsaye, ya kama hannunta suka dawo parlorn ya xaunar da ita, ya rike chin dinsa da duk hannunsa biyu yana kallonta ita ma kallon nasa take, fine beard din da ya xagaye bakinsa ta kai hannunta ta taba, yayi murmushi ya kama hannun cikin nasa yana kallon manyan fararen eyeballs dinta cikin sanyin murya yace "I will call you Jasmine! Do you like dat?" Kwace hannunta tayi daga nasa, ya tsura mata ido, bude kofar parlor aka yi El-Ameen ya shigo, ae tana ganinsa ta mike da sauri ta nufesa ta isa gabansa ta tsaya, Junaid ya bi ta da kallo, El-Ameen ya ja hancinta ya bude hannayensa yace "toh dai bbu abinda na siyo maki" kallon junaid yayi yace "The great Capt Ahmad Junaid ashe kana nan" mikewa junaid yayi yace "Sure!" Daga haka ya nufi kofa, El-Ameen yace "ba dai har xaka tafi ba" junaid yace "Yea daga office nake" daga haka ya fice daga parlorn, bin sa da wani irin kallo El-Ameen yayi kafin ya fita yayi saurin cewa "Hey a minute" junaid ya tsaya sannan ya juya yana kallonsa, El-ameen yace "gaskiya ya kamata ka shiga kasuwa ko kuma ka bada kudi a shiga a sama mana TV a gidan nan, ko ka mance yanda muka yi da kai?" Junaid yace "I will transfer the money later sae ka samu me siyo maka TVn" yana gama fadin haka ya fice daga palon, El-ameen ya d'aga kafada ya kama hannunta suka koma parlor.

As usual ya dade xaune mota bayan yayi parking a lot din gidansu kuma har lkcn bae kashe mota ba yana danne dannensa a waya, Khadija ce ta fito daga part dinsu ta karaso gun motar ta bude tace "ina yini yaya A.jay" ya kalleta yace "Lafiya lau" ta d'an marairaice masa tace "yaya yau ciwo ciki na ke min wllh" tabe baki yayi ya ci gaba da danna wayarsa, ta dan shagwabe masa tace "Yaya ka d'an ban kudi in siya magani mana, Umma ta ki bani" dubu daya ya xaro aljihunsa ya mika mata cike da murna tayi masa godiya ta kara gaba, shigowar motar Suhaima yasa shi kashe motarsa ya fito ya rufe ya fara tafiya, Hajiya ce suka fito daga part din Umma da wata mata alamar rakiya xa su mata, duk suka bisa da kallo, ba tare da ya kallesu ba ya gaida su don dama sai lokacin da yayi suit dinsa yake gaishesu, matar ce kadai ta amsa shi, bae damu da haka ba yayi part din Mumy, Matar da ta bisa da kallo ta maido da dubanta gun su Umma murya can kasa tace "Shine yaron hala?" Cike da tsanarsa Hajiya tace "Ehh wllh" matar tayi wani murmushi murya can kasa tace "Duk ku kwantar da hankalin ku, ku bar min komai a hannu na baxan baku kunya ba" babu wanda yace komai cikinsu suka rakata har waje gun motar ta. Junaid na shiga parlon Mumy ya tarda Humainah kwance da ganinta kasan ba kuka kadan tayi ba, dariya ya saka yace "ohh shikenan an bar mana ita" mikewa tayi xaune idon ta ya cicciko ta kwalo ma Mumy kira, Mumy ta fito daga daki tace "be careful Mr" dariya yayi yana shafa kai yace "Ya hakuri Mumy, ina yini" ta karaso parlorn tace "Nayi xaton ae baxa ka kashe motar ka shigo gida ba" yyi murmushi yace "Ac fa nake sha Mumy" ta tabe baki tace "Haka ne, ga abincin ka can" kujera ta xauna tana kallon Humainah tace "Kema kije ki dau naku abincin ke da fatee, ko baki hakura ba har yanxu" bata ce komai ba tayi kasa da kai, Junaid ya mike yace "Xan dawo Mumy bari inyi wanka" tace "Ohk," bin sa da kallo tayi sae da ya kai bakin kofa tace "Canxa kaya kayi office" murmushi kawae yayi ya fita. Wanka yayi ya kuma canxa kayan jikinsa yyi kwanciyarsa parlor don bai jin yunwa, ya kusa awa daya kwance Humainah ta shigo parlorn rike da tray dauke da abincinsa, ta karaso ta ajiye masa, ya mike xaune cike da xolaya yace "Shikenan fatima ta huta an kawo mana maid kyauta" mikewa tayi a fusace xata fita ya rikota yana dariya yace "Ke dalla wasa nake maki" ta fixge hannunta tace "Bana son wasan" ya daga kafada yace "Ni kuma sai nayi din" wani kallo ta shiga yi masa fuska daure, ya hade rai yace "Toh in kince a biya ki kudin aikin ba sai a biya ki ba ma" hawaye ya cika idonta ta juya xata fita aka bude kofa El-Ameen ya shigo da sallama, da sauri ta kuma juyawa tana kallon Junaid da ya bude ido ganin El-Ameen da ya kasa Karasowa cikin parlorn, Junaid ya mike yana dariya yace "C'mon ka karaso frnd" El-Ameen yace "Um ban gaida Mumy ba am coming" da sauri junaid ya karasa ya rufe kofar da key ya cire sannan yace "ba ta kofarta ka wuce ba kafin ka karaso nan"  El-Ameen ya ma rasa me xai ce masa, dawowa cikin parlorn junaid yayi ya xauna yana kallon Humainah yace "Toh ae sai ki goge hawayen yanxu tunda ga shi ya xo koh, duk kin isheni kin daga min hankali ina El-Ameen toh ga ki ga shi" Humainah tayi wani kara ta durkushe wajen ta shiga kai masa duka tana cewa "ni bana son haka ya Ahmad, bana so" El-Ameen yayi murmushi ya nufi daki, da sauri Junaid ya mike ya rigasa shigewa dakin ya saka key daga ciki yace "Ji min munafukai" gajiya yayi da tsayuwa ya dawo parlorn, can nesa da ita ya xauna yace "Ina yini" ta d'an kallesa ta hade rai tace "Lfya lau" bai kuma cewa komae ba ya dau remote yayi powering Tv, sun kusa minti talatin parlorn bai ce mata ba bata ce masa ba, kamar wanda ya tuna abu ya mike da sauri yana kallon agogo ya nufi dakin junaid ya kwankwasa yace "Look captain akwae drugs din da xanje in ba patient dinka open the door plss ka bude kofar parlor am leaving" junaid dake kwance ya fara bacci ya mike jin abinda El-Ameen yace ya bude kofar, El-Ameen yace "D'an rainin wayo bacci ma kake koh" fitowa junaid yayi suka dawo parlor a tare, kallon Humainah yayi yana murmushi yace "Har kun gama xancen kanwata" ta hararesa ta dauke kai, shi kam El-Ameen har ya kai kofa, Junaid yace "toh dai ki ajiye abinda ya baki idan na dawo mu raba, kuma ki d'an gyara min bedroom saura ki min satan turare ki ga ko ba na saurayin ki xan je in sace ba" yana fadin haka yyi kofa ya bude ya fice yana dariya, El-Ameen ma ya fita, Part din Mumy suka shiga El-Ameen ya gaida ta, Junaid yace "Xan d'an rakasa indawo yanxu Mumy" Mumy tace "Toh sai ka dawo" daga haka suka fice da El-Ameen. suna isa El-Ameen yace "Baka yi min transfer din kudin Television din ba fa, if you provoke me xan fa je in siya da kudina" Junaid yace "I forgot xan yi" fitowa suka yi daga motar suka shiga gidan, Mama jummai na xaune parlor ta daura kanta kan cinyarta idonta rufe, El-Ameen yace "dama tana bacci ba da daddare ba" Mama jummai tace "Ina jin bata jin dadi ne yau, sau biyu tana amai ga jikinta da dumi, ita da ko xama bata yi da rana bare ta kwanta" El-Ameen ya karasa ya durkusa gabansu ya d'ago kanta ta bude ido tana kallonsa, ya gyara mata gashinta a hankali yace "Malaria... I guess" xaunawa Junaid yayi shi dai bae ce komai ba, El-Ameen ya d'agota ya xaunar da ita kan kujera yace "Sorry...." Ya kalli Junaid yace "Ka bada kudi in tafi in siyo mata drugs da injections" kallonsa kawai Junaid yake bai ce komai ba, El-ameen ya kalli mama sannan ya kallesa ya juya xuwa harshen turanci yace "It's not a matter of looking at me dat way captain, don't forget she's ur patient, ur mind agreed to the terms nd condition of helping her, nd I guess before u jumped into the conclusion of doing dat, you already know...." Katse sa junaid yayi yana masa wani kallo yace "did you hear me complain?" El-ameen yayi dariya yace "Not dat I don't have the money to assist you but...." Tsaki Junaid ya ja yace "Enough plss, I don't even need ur goddam help," El-ameen yayi murmushi yace "Ni kuwa kake bukatar taimakona, cos lokacina da na ware for her is far far better then dat money you are spending, anyway! 20k will do for the test nd everything" Atm junaid ya ciro ya mika masa ya karba, ya mike ya haura sama syringe ya dauko a daki da plastic tube na drip ya dawo parlon, da kyar ta bari ya debi jininta don sae da Mama jummai ta riketa, ya mike yace "Bari in je in dawo yanxu, Mama ki d'an bata kunu ko kadan ne ta sha" Mama tace "Toh" sannan ya fita daga parlorn, xamowa tayi daga jikin mama ta kwanta kasan tiles, mama ta d'agota tace "Sannun Kinji Baiwar Allah, Allah ya sauwake maki" kara ta saki alamar bata son tashi a kasan, Mama ta kyaleta ta tafi kitchen, mikewa Junaid yayi ya isa gabanta ya durkusa, kallonsa kawae take kafin ta kauda kanta, ya d'agota a hankali yace "Sorry Jasmine, get well soon" mikewa tayi ta kwace hannunta a nasa ta fara tafiya, ya bi ta da kallo ganin yanda take tafiya, can jikin bango taje ta tsaya, ya mike ya koma kujera ya xauna, har mama ta fito kitchen rike da pap bata bar jikin bangon ba, Mama ta ajiye bowl din hannunta ta karasa ta kamo hannunta, da kyar ta biyota suka dawo parlor ta xaunar da ita ta shiga bata kunun amma taki sha, da ta takurata mikewa tayi ta dawo kusa da junaid ta xauna gefen shi ta jingina jikinsa ta rufe ido gam, duk tayi wani laushi da ganinta kasan bata da lafiya, shi kam kallonta kawae yake wani tausayinta ya dinga ji, ya ji dama ciwon ya dawo jikinsa, ya rungumota jikinsa a hankali yace "Sorry My Jasmine" mikewa mama tayi ta mika masa kunun tace "Toh ka bata Junaid kila ta karba ko kadan ne" yyi murmushi ya karba ya janyeta daga jikinsa ta bude ido tana kallonsa, ya debi kunun kadan ya kai mata baki, ta kauda kai da sauri, rasa yanda xae yi ya bata yayi, kawae ya ajiye, ita ko ta sauka kasa ta kwanta, bayan minti goma El-Ameen ya shigo parlorn, ya ajiye ledan hannunsa ya d'agota yana kallon junaid yace "Ta sha kunun" girgixa masa kai kawai yayi, El-Ameen ya jawo bowl din kunun ya debo ya kai mata baki, ta kauda kae da sauri, ya hade rai yace "I will knock you, c'mon bude baki" kara ta saki ya xuba mata kunun a baki ta xubar da sauri, ya daka mata tsawa, nan da nan jikinta ya dau rawa ya debi wani ya bude bakin ya xuba mata, da kyar ta hadiye hawaye na sakkowa idonta, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido, haka El-Ameen ya dinga bata tana karba da kyar har tayi four spoon sannan ya ajiye, ya fara hada drip da xai sa mata da alluran da xai mata, ita ko kwanciya tayi kan tiles ta rufe ido, yana gama hada alluran ya D'ago ta ta bude ido, gown din jikinta ya d'aga don a lap xae mata alluran, kallon junaid yayi yaga idonsa na kansu, da sauri junaid ya kauda kai, El-Ameen ya kwantar da ita yayi mata alluran, tun bai gama ba ta fara kokarin mikewa, duk jikinta yayi xafi ba kadan ba, ya maidata ya kwantar har ya gama sannan ya dagota yace "Sorry" komawa baya kawae take hawaye na xuba idonta, El-Ameen ya d'an yi murmushi don hawayen shaidar wataran xata dawo me hankali ne sai dai fatansa daya kar tayi loosing memory dinta, kusa da junaid ta koma ta xauna gefensa ta daura kanta a kafarsa ta rufe ido, yana son ya lallasheta duk da yasan ba gane nufinsa xata yi ba amma bae son yin hakan gaban El-Ameen ya ya kafa masu ido, hakan yasa ko kallonta bai yi ba, El-Ameen yayi murmushi ya mike ya nufi kitchen don dauko cup yyi mata diluting drugs ya bata ta sha, Junaid ya kai fuskarsa dai dai nata a hankali yace "Sorry Jasmine...." Ta bude idonta da suka sauya launi tana kallonsa, da sauri ya D'ago jin fitowar El-Ameen, ko kallonsu bai yi ba yi diluting drugs din da ruwa ya dawo kusa da su ya xauna ya dagota yace "Tashi ki sha magani" kara ta saki ta boye fuskarta jikin junaid tana shishshige masa kamar xata shiga jikinsa, El-Ameen ya mata wani tsawa, jikinta na rawa ta rike Junaid tana ihu, janyeta El-Ameen yayi ya hade rai yace "Keehh" cup din ya kai bakinta ta ki budewa, ya mata wani rankwashi ta kwala ihu, da sauri ya jawota ya juye maganin bakinta ya rufe hancinta, sae da ya tabbatar ta shanye su gaba daya sannan ya cire hannunsa hancinta, lkci daya duk ta amayo maganin jikinsu gaba daya su ukun, daga nan ta dinga amai gashi bata ci komai ba, El-Ameen ya mata wani tsawan da ya rikitata ta fasa ihu xata mike ya fixgota da karfi ta fado kansa ya rungumeta tsam jikinsa, sunkuyar da kai junaid yayi jin wani abu da bae taba ji ba a xuciyarsa a lkcn, a hankali ya shiga cire shirt din jikinsa da ya baci da amai, Mama jummai dake tsaye daga bakin kofa cike da tausayinta taji kamar tayi mata hawaye duk ita ma jikinta yayi sanyi, mikewa junaid yayi har lkcn bae kallesu ba ya haura sama, El-Ameen ya bi sa da kallo, a hankali ya d'ago kanta jin ta sakar masa jiki gaba daya ya ga bacci tayi, kamar me rada yace "Jewel!" A hankali ta bude ido tana kallonsa.

 ✍🏻
*Haske Writers Association*💡



CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE (DANDALIN HAUSA NOVELS)

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *