________________________
_a true life story_
1⃣➖🔚
NA
*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_
_PEN WRITERS ASSOCIATION_
08034840276
_Only the exqusite and whizkid writers, are opportune to be pen writers_
Sadaukarwa ga: HajiyaZalihat Isma’il (Mamar Ahmad)
_SHIMFIDA_
Da sunan Allah mai rahama mai jinkai, wanda ya saukar wa annabawansa littafai da mu’ujizoji, ya kuma yi umarni da ayi imani da kowanne daga ciki, haka dimbin godiya da yabo na shi ne, kuma ga shi gagara misali wanda ba ya da farko kamar yadda sam ba ya da karshe, tilo ne da ba ya da kishiya haka ko kusa ba ya da tamka, salati na yo ga baban fati wanda shi ne sha-le-le kuma dan gaban goshi, manzon karshe wanda da fararen hannayensa muke kwadayin ya miko muna ruwan alkausara. Na hada da iyalan gidansa da sahabbansa da duk wadanda suka bi tafarkinsu ya zuwa ranar tonon asiri.
Ina mika godiyata ga mahaifiyata wadda banida tamkar ta, da dawainiya da ta sha da ni tun kankanta kawo yanzu, Allah ya biyata da gidan aljanna amin.
Mabiya littafaina kuma masoyana ko da wasa ba zan taba buda feji ba har sai na jinjina maku, na kuma kara mika godiyata gareku, duk da nasan bakina yayi kadan ya isar da sakon soyayyata gareku kamar yadda take tafasa a kogon zuciyata, amma inaso kusan cewa ana tare.
Wannan labarin zai zo ne a takaice, kuma duk abinda ya fito a cikinsa da gaske ne ya faru, a shekarar 2009 lokacin ina karatu a jami’ar USMAN DANFODIO da ke SOKOTO, mukayi wani yajin aiki da a rayuwata bazan taba mantawa ba, domin abin nema ne ya samu, duk da cewa daliban AGRIC a 100 level suna hutawa, mune lokacin ‘yan wahala 200 level na tsani shiga aji daukan darasi, saboda haka da muka tabbatar da cewa yajin aiki ya kankama kuma ba fashi, sai naji zuciyata kamar an zuba mata kankara ne, sai na nufaci hostel dinmu ko da yake squarting nakeyi, a zoo block (zoo4), cikin matsanancin sauri na harhada tufafina a akwatina sai makekiyar jaka da ba komai cikinta sai littafan addini, tun daga manyan littafai har Bible da sun haura goma. Nayi sallama da mutanen dakinmu, idan ba zan manta ba inaga a dakinmu ni na fara ficewa, na iso tashar mota da ke hannun riga da kasuwar garin SOKOTO, ba zaka sha wuya ba wurin neman motar KEBBI kasancewar daga shigowar ka ta kofar da ke kallon yamma wacce sam ba ta da kyaure sai igiyoyi da akayi shamaki da su ta kofofi guda biyu, wadanda masu gadi ke dagawa a duk lokacin da mota za ta shigo, sai in da ake ajiye motocin KEBBI, sai daf da mota bus fara mashin ya ajiye ni, sai gogoriyo da rigangeninyar daukar jakata da akwatina akeyi tsakanin mai lodin motar ARGUNGU da na BIRNIN KEBBI, kasancewar na saba hankalina sai ya koma kan biyan mai mashin, bayan na sallameshi sai na juyo a daidai lokacinda conductor ke tambayata, ina zan je, na sanar da shi cewa BIRNIN KEBBI nayyi, ya mikomin ticket ta dalibai wato saukin kudi, na biya, mutum nake mai kwadayin zama gaban mota saboda gudun takura, kasancewar ko a mota nake karatu ne abinyina (karatun research domin na tsani karatun aji), cike da bakin ciki na fara neman inda zan zauna a layin kujera na biyu, ba tarada na cewa kowa uffan ba na nemi wuri na zauna, a hannun damana wani mutum ne kakkaura baki, ni bansanshi ba amma yadda yake kallona ba shakka ya sanni, domin cikin sakin fuska yake kallona yana neman damar yi mani magana, abin ka da mai daure fuska, ni kuwa sai kokarin bude Bible nakeyi wanda ke hannuna a yayin da dayan yake kan cinyata, wasu samari sai kallona sukeyi cikin shakku, nasan a ransu sai tunanin suke wannan wane iri ne, domin isowata nayi sallama, ga shi a hannuna ina rike da Bible har guda biyu, kusa da mu a layi na bayanmu wata Christian ce baka da ita, sai waya takeyi da wani cikin turanci. A rayuwata a wancen lokacin babu abinda nake nema irin na sami damar firar addini da Christian, saboda haka duk da karatun Bible nakeyi hankalina kacokam yana a kanta, musamman kunnuwana da duk yadda aka furta magana kusa da su daukomin ita sukeyi, a firarta na sami gaba da zanyi matashiya da ita wurin yimata magana.
Ku biyoni cikin littafin domin kuji ya firar tamu ta kasance da ita, duk firar da mukayi da yaren turanci mukayi, amma kasancewar wannan Hausa novel ne zan rubuto komai a yaren Hausa, amma inda zan kawo ayar Bible, da turanci zan kawo, sai nayi tsokaci ko na fassara gaba daya, nayiwa wannan littafin suna da GASKIYA DAYA CE, ina rokon ubangiji da yasa ya amfanar ya kuma sa nayishi ne domin neman lada, idan akwai niyyar riya ko kadan a zuciyata Allah ya kankaremin ita ya mayarmin ita domin neman yaradarsa ya kuma sa nayi tarayya da duk wanda ya karanta domin ya amfana da lada.
Saboda Allah duk wanda yaga gyara ya tuntubeni, galibi duk rubutuna za’a ga lambata, ina rubutawa ne dama domin ayimani gyara ko shawara ko a tsawatamani inda nayi ba daidai ba, kar mu manta duk wanda ya kawo gyara musamman a harkar addini yanada dimbin lada, saboda haka hakkin duk wanda ya karanta ne idan ya ga gyara yayi mani.
_ZAINUDDEEN ZAIN_
A jikina T-shirt ce sky blue mai dogon hannu kasancewar nafison long slipped shirts, sai bakin jeans da nake sanye da shi wamda tsawonsa saura kadan yakai a idon sawu, sai agogon hannu mai kirar gold colour wanda ya kara fidda bakin hannuna, kaina kuwa cike da suma wacce har kalmisa za’a iya yi da ita, idanuwana da basada girma sosai kuwa sai faman kallon littafi suke yi inda kwakwalwata ke kokarin jajibomani hujjojit tana adanawa a asusun zuciyata, dogon hancina kuwa sai zufa nake sharewa da dan sirarin hannuna da ko shi kadai ya isa ya gayamaka labarin tsukakken jikina, a dayan bangaren kuwa sai murmushi nakeyi a raina, ina kokarin sauraro kammala wayar wannan kirista domin na mata tambaya kan gaba da na samu daga firarta. Nayi nisa cikin karanta BOOK OF LEVITICUS SAI naji tayi shu, hakan yasa cikin sauri na kai aya sai na waigo ta.
Siririya ce, itama din dai baka ce kamar ni duk da ta dara ni fari kadan, kyakkyawa ce kuma doguwa amma na fita tsayi, muryarta ‘yar siririya kamar tawu da dalibaina ke yimani sharri wai inada muryar mata, kasancewar na saba yiwa manyan pastors magana har mu zauna mu zanta, ko kadan banji wani shakkun yimata magana ba, idanuwana cikin nata na ce da ita. “naji lokacin da kike waya kin ce Bible maganar Allah ce, ko zaki iya gamsar da ni cewa da gaske maganar Allah ce?” kamar ba zata amsa ba sai ta maidamin kallo duk da ta bayanmu take tana hango Bible da ke hannuna, ta kuma lura mutanen da ke motar ita suke jira ta bada amsar tambayar da nayi mata, kakkauran mutumin nan kuwa sai kara kallona yake yi cikin sakin fuska, sai ta ce “sosai Bible maganar Allah ce” bayan nayi murmushi a daidai lokacin da nake rufe Bible din da ke hannuna na daurashi kan wanda ke kan cinyata, na gyara zama na dan karkata kadan domin naji dadin zantawa da ita, sai nace, “Bible ba gaba dayanshi maganar Allah ba ce, domin akwai magnaganun annabawa a cikinsa, akwai maganganun masana tarihi a ciki, kinga kuwa ba za’a ce maganar Allah ce gaba dayansa ba ba” ta ce, “a a! Duka maganar Allah ce” sai na sake murmushi a karo na biyu na ce “idan har kika gamsar da ni da hujjoji cewa Bible maganar Allah ce, na yi maki alkawari yau dinnan zan koma kirista” cike da mamaki tareda jin dadi ta mayar da hankalinta gaba daya wurina, kasancewar ba wannan ne zantawa ta kan wannan maudu’in na farko ba nasan ba wani abu da za ta daura da shi sai nayi sauri na ce, “tun da kince gaba daya Bible maganar Allah ce ga wannan ki karanta” sai na budo mata SONG OF SOLOMON CHAPTER ONE VERSE TWO :
_BATSA A CIKIN BIBLE_
*your lips cover me with kisses your love is better than wine. There is a fragrance about you, the sound of your name recalls it. No woman could help loving you. Take me with you and we’ll run away be my king and take me to your room. We will be happy together, drink deep, and lose ourselves in love. No wonder all women love you!*.......................... (GOOD NEWS BIBLE (GNB)) da zarar ka kalleta zaka fahimci kalar mamaki da damuwa da ke shimfide kan fadaddar fuskarta, da na fahimci magana take so ta yi sai nayi caraf nace, “kina so ki ce da ni Allah ne ke rera wannan wakar? To da wacce zai je daki ya aikata masha’a? na fada a raiana ina cewa “SUBHANALLAH TA’ALALLLAHU AN ZHALIKA” kafin ta ce komai na kwace Bible din na sake budo wata chapter a wannan karon CHAPTER FOUR daga VERSE ONE *“how beautiful you are, my love! How your eyes shin with love behind your veil. Your hair dances, like a flock of goats bounding down the hills of Gilead. Your teeth are as white as sheep that has just been shorn and washed*…… *your lips are like a scarlet ribbon; how lovely they are when you speak*………… *your breast are like gazelles, twin deer feeding among lilies*. Bayan ta karanta nace “ki karanta CHAPTER FIVE da kyau” CHAPTER FIVE tana magana ne kan har sun kwana tare da safe ta tashi bata ganshi ba, sai nace da ita “wannan aikin ubangiji zai iya aikatashi?” naki bari ta bada amsa na karbe Bible na sake buda wata chapter , a wannan karon CHAPTER EIGHT ……… _then if I met you on the street I could kiss you and no one would mind_……sai nace “don Allah zaki iya ba danki wadannan ayoyi ya karanta?” nan ta fara rabon idanu sai ta fara juya Bible din da na mikamata, budar bakinta sai tace “wannan ba Bible ba ne”, cikin zuciyata na sheke da dariya amma sai na daure a fili domin inaso firar ta daure, sai nace da ita “wannan fa GOOD NEWS BIBLE ne, ga shi a hannunki kuma zaki ce ba Bible ba ne” sai na ce “tau wanne Bible kika aminta da shi”? sai tace “KING JAMES VERSION” sai da nayi murmushi tukun na dauko shi daga kan cinyata, fari tas marfinsa, na budo mata duka chapters din daya-bayan-daya, taga ba bambanci, sai ta fara kame-kame tace, “wannan ai wani namiji ne ke rerowa da waka tareda wata mace” sai nace “amma cewa kikayi da ni gaba daya duk zancen da ke cikin Bible na Allah ne, shiyasa na kawomaki wannan” sai nace idan wannan bai isa ya zama hujja ba, ga wanna:
_TUFKA DA WARWARA A CIKIN BIBLE_
Genesis 6:3 *‘then the Lord said, “I will not allow people to live forever, they are mortal from now on they will not live longer than one hundred and twenty years”* GNB
Genesis 11:16-17 *‘when Eber was 34 years old, he had a son, peleg , after that he lived another 430 years and had another children.* GNB
Sai na ce da ita, “me zaki ce kan wannan”? kafin tayi magana na sake karanto na gaba, a duk lokacin da na karanto nakan bata Bible ta duba ko hakan ne.
Mathew 27:5 *‘judas threw the coins down in the Temple and left: then he went off and hanged himself’*
Acts 1:18 *(with the money that judas got for his evil act he bought a field,where he felt to his death; he burst open and all his bowls split out’*
(judas yana daya daga cikin sahabban annabi isah guda goma sha biyu kamar yadda Allah ya sanar da mu adadinsu a Qur’ani, shi ne wanda ya ha’inci annabi Isah ya mika shi hannun makiya kamar yadda yazo a Bible, amma a musulunce, mutum ne da yayi masifar kama da annabi Isah ta fuskar komai, shiyasa da aka zo shi aka kashe maimakon annabi Isah, a musulunce, amma a Bible ya sami mika annabi Isah aka bashi kudi, abin lura anan shi ne yadda Bible ya kawomuna mutuwarsa ta hanya biyu, dole daya ne daidai, idan kuwa an samu tufka da walwala. Anya maganar ubangiji ce kuwa?)
Haka na kawomata misalai sama da ashirin inda duka cin karo ne da juna a littafinsu mai tsarki, sai nace da ita, “a tunaninki za a iya samun cin karo a maganar ubangiji?”, ta ce “a a!” sai nace “to ya akayi wadannan zantukan suka ci karo da juna? Na kalubalance ki da ki nuna mani ko aya daya da ta ci karo da wata a littafinmu” tayi shiru na wani lokaci, sai tace bayan ta nisa. “ai mu abin da kiristanci ya kunsa shi ne, yin imani da cewa yesu almasihu Allah ne da yazo a sifar mutum ya mutu kan cross saboda zunuban duniya”. Kasancewar na saba arangama da malaman nasara tsofaffi kuma gogaggi, banyi mamaki ba yadda ta sauya zancen da mukeyi daga Bible maganar Allah ce zuwa annabi Isah Allah ne kuma ya mutu saboda zunuban duniya. Sai nayi murmushi na ce, “ai bamu kammala wancen zancen ba ga shi kin dauko wani, amma ba damuwa, duk duniya babu mabiya wani addini da suka darajanta annabi Isah kamar mu musulmi, domin mu kadai ne muka yarda da shi yadda shi karan kansa ya ikiraranta, mu kadai muka yarda cewa ya nuna mu’ujizoji gagararru, muka yarda cewa shi bawan Allah ne, muka yarda da mtuncin mahaifiyarsa, muka yarda an haifeshi ba uba, amma duk da wadannan bamu yi imani cewa shi ubangiji ba ne, domin shi karan kansa yayi inkarin haka a wurare da dama cikin littafinku, a Mathew 21:18 mun karanta yadda ya fito tun da safe yaga wani ice yanaso yaci ‘ya’yan itacen sai ya tararda icen ba ‘ya’ya, sai ya la’anci icen. Abin lura idan shi Allah ne ta yaya zai ji yunwa? A littafin mark 13:32 aka tmbayeshi ya shugaba yaushe ne tashin kiyama, yace ‘wannan ranar ko ni ban sani ba, ba wanda ya sani sai Allah, idan shi Allah ne zai fadi haka? A john 5:30 yace shi fa a karan kansa ba ya iya tabuka komai, wannan Allah ne ba ya iya tabuka komai?” a duk lokacin da na jawo a ya, sai kaga tayi sauri ta buda da Bible da ke hannunta domin ta tabbatar da gaskiyar zancena.
Sai nace “wadannan kadai sun isa su zama hujjoji kan cewa shi ba ubangiji ba ne, amma shi mutum yana bukatar Karin bayani a ko da yaushe, saboda haka zan baki hujjoji da zasu gamsar da ke, nasan kuna kiran annabi isah Allah ne saboda mu’ujizoji da ya nuna da kuma wasu ayoyi da kuke karantawa a cikin littafinku, idan har mu’ujiza ma’auni ce ta Allantaka, ba shakka akwai wadanda suka fi annabi isah cancanta da a kirasu Allah tun kafin ya zo duniya”
_MU’UJIZOJIN ANNABI ISAH_
(a dan bincikena na karamin dalibi, na tattara mu’ujizoji 35 da annabi Isah ya nuna a Bible, amma kasancewar a gurguje ne muke firar da ita, kadan na samu na kawo mata a matsayin hujja)
John 11:38-44 mun karanta yadda annabi Isah ya tayar da Lazarus daga mutuwa
John 2:6-9 mun karanta yadda ya mayar da ruwa giya (abin mamaki)
Mark 6:30-44 mun karanta yadda ya ciyar da mutum dubu biyar da gurasa biyar da kifi daya
Mathew 8:14-17 mun karanta yadda ya warkar da mutane da dama
Mathew 9:27-31 mun karanta yadda ya warkar da makafi.
Sai nace da ita, “mu musulmai munyi imani da duk wadannan mu’ujizojin, kuma mun yarda cewa annabi isah ya aikata su duka, amma ko kusa basu isa su kai shi matsayi na zama Allah ba, saboda shi da kansa ya gayamuna a cikin littafinku cewa ba yin sa ba ne, Mathew 28:18 da John 5:30, haka peter a cinkin acts 2:22 ya tabbatar yin Allah ne ba annabi Isah ne yayi da kansa ba. Me za ki ce gameda wadannan?
_MU’UJIZOJIN WASU ANNABAWA_
Ezekiel 37:1-14 *‘I felt the powerful presence of the loed, and his spirit took me and set me down in a valley where the ground was covered with bones. He led me all round the valley; an I could see that there were very many bones and that they were very dry. He said to me, “mortal man can these bones come back to life?” I replied “sovereign lord, only you can answer that!”. He said prophesy to the bones. Tell these dry bones to listen to the word of the lord. Tell them that I the sovereign lord am saying to them; I am going to put breath into you and bring you back to life, then you will know that I am the lord. So I prophesied as I had been told, while I was speaking, I heard rattling noise and the bones began to join together. While I watched, the bones were covered with sinews and muscles, and then with skin. But there was no breath in the bodies. God said to me “mortal man, prophesy to the wind, tell the wind that the sovereign lord commands it to come from every direction, to breath into these dead bodies and to bring them back to life. So I prophesied as I had been told, breath entered the bodies and they came to life and stood up. There were enough of them to form an army. God said to me “mortal man, the people of Israel are like these bones they said that they are dried up, without any hope and with no future so prophesy to my people Israel that I the sovereign lord I am going to open their graves, I am going to take them out they will know that I am the lord. I will put my breath in them bring them back to life and let them live in their own land. Then they will know that I am the lord I have promised that I will do this and I will, I the lord have spoken.*
Ga wani ya tayar da mutum sama da dubbai daga mutuwa, me yasa ba ku kira shi Allah ba?
1kings 17:21-22 *‘then Elijah stretched himself out on the boy three times and prayed “o Lord my God, restore this child back to life.!” The lord answered Elijah’s prayer; the child started breathing again and revived.*
Ga wani shima ya tayar da yaro daga mutuwa, me yasa kuk fidda shi daga takarar Allantaka?
2kings 4:32-35. Elisha ma ya tayar da yaro daga mutuwa.
A cen gaba a 2kings 13:20-21. Bayan Allah ya karbi rayuwar Elisha, shekaru da dama har ya zama kasusuwa zalla, sai aka zo za’a rufe wani da ya mutu, ashe a kabarin Elisha ne za’a sakashi ba tareda sanin mutane ba, ai ko ana sakashi a ramin yana taba kasusuwan Elisha sai ga shi ya taso daga mutuwa. Me yasa baku kira Elisha Allah ba, ko ba ya da galihu ne?
Exodus 4:1-5 mun karanta yadda sandar Annabi Musa ta zama katon maciji. Idan mu’ujiza ke sa a kira mutum Allah annabi Musa fa?
2kings 6:18 mun karanta yada Elisha ya makantar da wasu mutane.
2kings 6:20 kuma ya bude masu idanuwansu, shi me yasa baku kira shi Allah ba?
Duk a lokacin da na karanto a ka, ita kuma sai tayi kokarin bude Bible da ke hannunta domin ta gasgata ko karyata ni, ni ina karantowa a ka ne, amma daga Good News Bible hardar take, ita kuma kar mai karatu ya manta ta ce da King James Version kadai ta yarda, saboda haka da shi take dubawa, duk da akwai bambancin turanci, amma ma’anar daya ce.
Cikin kariyar jiki, gaba daya idanuwanta sun yi ja, sai ta kalle ni ta ce, “Bible ya gayamuna shi Isah Allah ne kuma ya mutu saboda zunuban duniya ne” bansan yadda zan fassar wannan yanayi da na tsinci kaina a ciki ba, domin duk maganar da nake yi da ita, ina yi ne domin mu cinma wannan gabar. Wato Isah ya mutu kan cross, domin idan zaka iya fayyacewa kirista cewa Isah bai mutu ba a cross ba shakka zai iya barin kiristaanci ya dawo musulunci, sai dai kash a dai dai lokacin ne kuma mota ta tsaya da mu a kan round din Abbasco da ke garin Birnin Kebbi, inda galibi idan ba gareji za ka sauka ba, motocin Boss nan suke ajiye mutane, kamar in yi kuka na fito cikin motar, mu duka aka saukar da kayanmu, muka tari kabu-kabu kowa ya nufi unguwarsu, nayi Badariya ita ko bansan inda ta nufa ba.
*Alhamdulillah.*
Baa shakka musulunci shi ne addinin gaskiya wanda ko kadan babu soki-burutsu a ciki, kun dai ji yadda muka zanta, Bahaushe yace ido kannen kai ne, Allah yayi muna jagora amin.
*ZAINUDDEEN JIBRIL ZAIN*
_DR. ZAIN_