Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Wednesday, 17 June 2020

HALEEMATU-SADEEYA COMPLETE HAUSA NOVEL

adsense here
HALEEMATU-SADEEYA COMPLETE HAUSA NOVEL
[3/11, 10:58] Lovely Sis: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
*HALEEMATU SADEEYA*
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž


     

 
CLASSIC WRITERS ASSOCIATIONπŸ’…(C.W.A)


Written by:Maryam Muhammad Hassan.

*DEDICATED TO MY FANS*πŸ’‹

Page 1--5
*BISMILLAHI RAHMANIN RAHEEM.*
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI,WANDA YA BANI DAMAN RUBUTA WANNAN LITTAFI MAI SUNA HALEEMATU SADEEYA. ALLAH YASA INDA NA FARA DA SUNAN ALLAH IN GAMA SHI DA YARDAR ALLAH.*


ALHAMDULLILAH ALLAH NA GODEMA DA KABANI DAMAN GAMA LITTAFI NA MAI SUNA *MARYAMA*NAGODE SOSAI DA SUPPORT DA KUKE BANI MASOYA NA.


*BAN MANTA DAKUBA*
MUM MU'AXXAM
MAMAN SAHAL
AYSHA
MASHAKURA DIYAR BABA.

Da sauran Wanda ban ambata ba.Ana mugun tare🀝


*S*anye take da hijabi dogo har kasa ruwan bula(blue) hannun ta rike da Qur'ani da alama makaranta xataje.

Ni Baibey cute nace saina bita har India xata.

Daidai wani gate din makaranta ta shiga.
Ina d'aga ido naga anyi rubutu da manyan baki *MARKAZUL IHSAN*(METRO POLITAN SCHOOL).

Budurwan nan wance baxata wuce shekara goma shabiyar ba a duniya tayi sallama"Assalamu alaikum"da muryan ta mai dadin saurara.
Mai gadin makaranta ya amsa mata yana"Ah *HALEEMATU SADEEYA* har kin karaso kenan"
Wanda aka kira da HALEEMATU SADEEYA tayi yar murmushi tace"eh baba wlhy yauma ina ganin na makara har shabiyu da rabi ya gota"
Tayi maganan tana kallon agogon dake makale a jikin bangon.
"Ina wuni baba"
Cewar HALEEMATU SADEEYA.
Mai gadi ya amsa da fara'ar sa yana cewa"lafiya lau yar albarka.Allah yayi miki albarka ya baki abinda kike nema duniya da lahira".

"Ameen thuma ameen baba nagode"
Cewar HALEEMATU SADEEYA datake kokarin shiga haraban makaranta.

Duk malamin data hadu dashi sai sun gaisa.
Koda ta haura sama inda ajin ta yake ta nufa da isarta ta tadda angama shara ana shirin xuwa massalaci domin yin sallah.(dokar makaranta duk wani dalibi a makaranta xaiyi sallah axahar)
Itama kara haurawa tayi dan xuwa massalaci............
Bayan an idar da sallah ne akayi azkar sannan daya daga cikin malamai ya tashi yayi fakadaurwa,kuma ya dauki attendance wanda sukayi sallah a makaranta.

HALEEMATU SADEEYA naga tana saukowa daga stairs, wani aji direct ta nufa Wanda ke kallon sama.Ina daga idona naga ansa primary six(aji shida).

Tana shiga tabi kowa wurin xaman shi sukayi musabaha sannan ta kuma wurin ta.
Ba'afi minti biyar ba wani malami ya shigo,yan aji suka tashi suka gaishe sa.
Ya amsa da fara'a a fuskan shi.

Nan ya umurce su"ku fara muraja'a kafin lokacin 'kari yayi".
Suka fara a tare abin burgewa.

Karfe 2:00pm dai-dai yace xasu fara 'Karin Al Qur'ani.

Malamin sau biyu ya biya musu,suka iya.
Bayan ya gama shafi d'aya yace"duk Wanda keda hadda xai iya xuwa".

HALEEMATU SADEEYA ta fara mi'kewa  ta hau tafiyan ta cikin nutsuwa da kamala har ta isa inda ake bayar da hadda.

Malamin ya umurce ta"HALEEMATU xauna ga wuri nan."
Ya fada cikin sanyin murya.

Tunda HALEEMATU SADEEYA ta fara karatu aji yayi tsit kaman ba mutane sbd 'kira'arta kaman na sudais.......


Sosai malamin ya yaba mata,sannan yace"HALEEMATU dauko littafin hadda ki inyi miki sign."

Haka taje ta dauko yayi mata,ta kuma wajan xaman ta danyin tilawar wasu littafai kafin saura Wanda xasu bada su gama...........

Karfe 3:00 aka fita break dan cin abinci, HALEEMATU SADEEYA na aji naga wata matashiyar budurwa ta shigo da sallaman ta.Wanda baxata wuce sa'ar HALEEMATU SADEEYA ba.

Wurin HALEEMATU SADEEYA ta nufa sukayi musabaha.
HALEEMATU SADEEYA"Dan Allah bangane kiba?"

Murmushi ya bayyana a fuskan matashiyar budurwan.
"Nidai sunana Hauwa'u Usman, anan makarantar nake kullum ina ganin ki kina burgeni,ban dade da shigo wa makarantanan ba amma dabi'un ki sun muna kinada mutumci."
Ta karasa maganan tana murmushi.

HALEEMATU SADEEYA tayi murmushi Wanda ya kara bayyana kyaun ta.
"Nagode ni kuma sunana HALEEMATU SADEEYA MUHAMMAD."

Hauwa'u tayi murmushi tace"ni ina ajin Malam bashir ne aji hudu.kinga inda bangane ba saiki dunga koyamin."
Tayi maganan cikin xolaya.

HALEEMATU SADEEYA ta dauko food flask din abinci dataxo dashi "Bismillah kawata"

Hauwa'u "Alhamdullilah kawata"
HALEEMATU SADEEYA ta hade rai tace" karki manta hadisin annabi Muhammad (S.A.W) yace babu kyau maida hannun kyauta baya,Dan haka bai kamata kice min Alhamdullilah ba."

Hauwa'u tace"uhmmm kawata kenan."

Nanta bude jallof din shinkafa ne  yaji kayan kamshi..........

Saimun hadu a next page.

CLASSIC WRITERS ASSOCIATION(C.W.A)πŸ’…Dan~buxu😍😍😘
08064481429
For comments & correction.
[3/11, 10:58] Lovely Sis: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
*HALEEMATU SADEEYA*
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž*CLASSIC WRITERS ASSOCIATION*πŸ’…
*C.W.A*
Written by:Maryam Muhammad Hassan.


*DEDICATED THIS PAGE TO AYSHA YAR ADUWA*πŸ’‹
*NAGODE DA ADDU'AN KI ALLAH YA BARMU TARE*🀝


Page11--15*A*mmih tace"SADEEYA ki tashi kije kiyi hadda"
Tayi maganan tana kokarin tashi.

Haleematu tace"toh ammih na"
Ta miki tana cewa"baba,ammih saida safe"

Ammih tace"toh Allah ya tashe mu lafiya,kiyi alwala kafin ki kwanta".


Haleematu ta tashi tayi hanyan wani madai_daici daki.
Dakin fes-fes sai kamshi yakeyi.
Katiface da labule saidan drawer a gefe.
Bayin dakin ta shiga tayi alwala tayi sallah sannan ta dauko Qur'ani ta fara karatun ta maidadin sauraro..
.....

Sai karfe goma ta rufe Qur'ani ta hau katifan ta,ta kwanta tayi addu'a kwanciya ta rufe idonta.

*ASUBA TA GARI HALEEMATU SADEEYA*******
*WACECE HALEEMATU SADEEYA*


HALEEMATU SADEEYA Muhammad sunan ta amma mutane sunfi kiranta da SADEEYA.
Alhaji Muhammad Hassan Dan asalin nijar ne buxu ne,irin yan agadaz ne,yana xuwa Nigeria ne yin business har Allah ya hada shi da Hauwa'u(Ammih) har suka yi aure ya dawo Kaduna da xama.
A xaman su,sun Dade basu samu haihuwa ba kwatsam Allah yaba Hauwa'u ciki.
Murna wurin Alhaji ba'a magana.Tattali Hauwa'u take sha kaman yarinya haka ta kuma.
Haka suke rayuwan su har Allah ya sauki Hauwa'u lafiya ta samu santaleluwar b budurwa. Ranan suna yarinya tace sunan mahaifiyar Alhaji Muhammad wato HALEEMATU SADEEYA.
Tunda ga HALEEMATU SADEEYA ko batan wata Hauwa'u bata sakeyi ba.

Haleematu sadeeya farace sosai daka ganta kaga buxuwa,ga gashi har gadon baya.
Masha Allah duk abinda mace kiso xance HALEEMATU duk tasamu.

Wannan kenan.
*CIGABAN LABARI*

Washe gari  haleematu da asuba ta tashi tayi sallah sannan ta dauko Qur'ani ta fara muraja'an hadda datayi jiya.

Saida rana ta fito sannan ta sallama,ta tashi ta fito tsakar gida ta hau aikin gida.


Tana gamawa ta kuma dakin ta.Wanka ta shiga.
Bayan ta fito ne ta shirya cikin doguwar riga mai adon stones ajiki.
Simple makeup tayi amma tayi kyau sosai.


Tana gamawa ta fito ta yadda Ammih da Baba suna 'karyawa,itama kitchen din ta nufa ta debo abin 'karinta ,ta shiga dakin iyayen ta.

Ta durkosa har kasa"Baba ina kwana,an tashi lafiya?"

"Lafiya lau yar albarka".
Cewar baba.

Haleematu ta kara cewa" Ammih na ina kwana,an tashi lafiya?"

"Lafiya  lau Yar Akbar's,kin tashi lafiya"
Cewar ammih.

Haleematu tace"lfy lau ammih na".

Allah yayi miki albarka ya albarkaci rayuwan ki".

Cewar Baba da Ammih a tare.

Haleematu ta amsa da"Ameen iyayena,ina alfahari daku"

Sunji dadin xanjen yarsu.Haleematu ta tashi ta kuma dakinta Dan karya wa.

Bayan ta gama ta fito ta wanke kayan da suka bata sannan ta kuma dakin ta.Karfe goma ta fito Dan daura abinci  sbd xataje islamiyah karfe shabiyu da rabi......


Tana gama abuncin ta sakeyin wanka ta shirya xuwa islamiyya.
Uniform dinta tasa farar riga sai Wanda navy blue,dankwali fari sai hijabinta har kasa shima blue,sai safan hannu data kafa baki.


Tana fitowa ta shiga     tayima ammih sallama sannan ta fito Dan tafiya.
Already tasan baba ya fita.

Tana isa makaranta dai-dai lokacin da motan su Hauwa'u suka iso.

Hauwa'u na hango ta,ta fara kwalla mata kira saboda tanaso su shiga tare.


Yah Abdulfata ne yace"haba lil sis meyasa xaki dunga kiranta ta haka."

Hauwa'u tace"Haba bro sbd ta jirani ne."
Ta fada cikin shagwaba.

haleematu na karasowa wurin Motan suka gaisa da yah Abdulfata.

Yah Abdulfata yace"haleematu kinga kima kawar ki fada ta daina kiran sunan mutane anyhow."
Yayi maganan yana kallon Hauwa'u data  marairaice fuska kaman xatayi kuka.

Haleematu tayi murmushi tace"toh yaya insha Allah xata gyara yauma kuskure tayi."

Yah Abdulfata "auu shikenan wato kuskure tayi."

HALEEMATU tace"aa"

Yah Abdulfata yace"Gud dayafi,nixan tafi sai an tashi."

Hauwa'u da HALEEMATU sukace"Allah ya kaimu lafiya"

Yah Abdulfata ya amsa"ameen"

Yasama motan shi key...........Saimun hadu a next page.

*Yawan comments yawan posting*

Dan~buxu😍😍😘
08064481429
For comment &correction.
[3/11, 10:58] Lovely Sis: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
*HALEEMATU SADEEYA*
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
CLASSIC WRITERS ASSOCIATION(C.W.A)πŸ’…Written by:Maryam Muhammad Hassan.


Page6--10


*N*an suka fara cin abinci har suka gama.

Hauwa'u ta dauko Qur'anin ta.
Tace"Dan Allah biyamin nan inaso gobe in bada hadda".

HALEEMATU SADEEYA ta amsa ta fara koya mata har saida ta iya.


Karfe 3:30pm aka kuma aji domin cigaba da karatu.


Malamin su HALEEMATU SADEEYA ya kira register sannan ya cigaba da biya musu karatu har lokacin sallah yayi.

Hauwa'u ce ta fara xuwa ajin HALEEMATU SADEEYA tare suka fita danyin alwala sannan suka dawo.

A wajan sallah aka fara muraja'a(dokar makaranta kenan in anxo sallah la'asir kafin lokaci ya karasa sai anyi tilawa).............

Ana idar da sallah malamin d'axu ya mike ya kira sunayen attendance wanda sukaxo da wuri,suka tafi Dan cigaba da karatun su.Karfe 6:00pm aka tashi daga makaranta.

Haleematu na gani tana tafiya cikin sanyi harta karaso kofar fita.Tayima mai gadi sallama,tana fito wa ta tadda hauwa'u tana jiranta.


Hauwa'u tace"kawa ke nake jira mutafi mu sauke ki a gida tunda ni anxo dauka na."

HALEEMATU SADEEYA tayi murmushi tace" 'kawa ae gidan mu ba nisa da kafa nake xuwa dakin barshi kawai karku kai magriba a hanya."
Ta karasa maganan tana murmushi.

Hauwa'u tace"toh shikenan kawa ga yaya na ku gaisa dashi.sai ki bimu inga gidan Ku."

HALEEMATU SADEEYA tace"uhmm to bakomai muje."


Suna karasowa gaban motan.

Hauwa'u tace"yah Abdulfata ga new friend dina."

Wanda aka kira da yah Abdulfata ya jiyo fuskan shi da fara'a yace"tohhh lil sis har kinyi kawa"


HALEEMATU SADEEYA tana gefe tana kallon su.
Saida hauwa'u tace"kawata ga yaya na."


HALEEMATU SADEEYA ta gaishe shi.

Ya amsa mata da murmushi sannan yace"ya sunan ki kawar lil sis dina".
Yayi maganan cikin sanyin murya irin tasa.

Haleematu tace"sunana HALEEMATU SADEEYA MUHAMMAD."

Yah Abdulfata yace"wow nyc name."

HALEEMATU SADEEYA tayi murmushi tace"thanks you"

Nan yah Abdulfata yace"SADEEYA ki shigo mu ajiye ki a gida."

HALEEMATU saida ta kalla hauwa'u alaman tayi hakuri.
Amma hauwa'u itama ta nuna alamun saita shiga.

Haka ta shiga ba don ranta.

HALEEMATU SADEEYA na kwatance har suka iso wani madai_daicin gida na rufin asiri.

Haleematu ta fito tace "Hauwa'u ga inda nake rayuwa nida iyayena.
" Ga chan babana Ku fito Ku gaisa."

Tayi maganan tana muna wani dattijo mutum fari sol kaman haleematu.

Hauwa'u tace"toh kawata."
HALEEMATU SADEEYA tace"bari inyi muku iso daga gareshi".


Nan HALEEMATU ta karasa wurin Baban ta Wanda ya ke xaune yana kallon Wanda suka sauke diyar sa daga mota.

Tana karasowa tace"barka da yamma baba"

Ya amsa mata"yar albarka suwaye wanchan na cikin mota?".

Haleematu tayi murmushi.
"Baba wata kawata ce da yayan ta yaxo daukan ta shine tace tanaso taga gidan mu kuma su gaisa dakai da ammih".


Baba yace" maraba lale,yi musu iso".

Nan haleematu taje ta sanar da su hauwa'u.
Tare suka iso suka gaisa sannan hauwa'u tace"bro Dan Allah kaban minti biyu inje in gaida mamanta".

Yah Abdulfata yace"toh karki dade  kinsan mom xata neme mu".

Da sallama suka shiga Maman haleematu tana xaune da alama bata Dade da gama aiki ba ta xauna hutawa.

Haleematu tace"Ammih ga kawata daga makaranta sunan ta Hauwa'u. "

Ammih tayi Yar daria tace"sannu hauwa'u ya mutan gidan?"

Hauwa'u ta gaishe ta.Suka fito Dan tafiya.

Haleematu har bakin mota ta rakata sukayi sallama ta kuma xata shiga Dan anfara kirayen sallah.

Baba ne ya tsayar da ita yace"haleematu inason magana dake in na shigo gidan."

Ba gardama "toh baba Allah ya shigo dakai Lfy".

Bayan sallah isha'i baba ya shigo gidan a parlor ya xauna.
Ammih ta kawo mai abinci sukaci sannan yace" HALEEMATU SADEEYA".

Haleematu ta amsa"naam baba".

Baba yace"HALEEMATU HALEEMATU"

Haleematu ta amsa"naam baba"

Baba yace"haleematu inaso kijini da kunnen basira,hakika nasan ki nasan halin ki,kuma nasan baxaki  abokan banxa ba amma duniyar nan ba'a yadda da mutum dan *MUGU BAIDA KAMA*bare kice xa'a ganesu,Dan haka haleematu ki nutsu kisan da Wanda xakiyi kawance".

Haleematu tace"insha Allah baba xan kiyaye xan dunga lura insha Allah".

Baba yace"yauwa yar albarka,Allah yayi miki albarka".

Haleematu tace"ameen ameen babana nagode Allah ya saka da alkhairi".

CLASSIC WRITER ASSOCIATIONπŸ’…(C.W.A)
Saimun hadu a next page.
Dan~buxu😍😍😘
08064481429
For comments & correction.
[3/11, 10:58] Lovely Sis: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
*HALEEMATU SADEEYA*
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
*CLASSIC WRITERS ASSOCIATION*(C.W.A)πŸ’…

Written by:Maryam Muhammad Hassan.

Page16--20*Fans dina kuyi hakuri wlhy uxuri ne ya hanani yin typing kwana biyu amma Dan Allah kuyi hakuri.Masu kirana da bina PC da masu yimin SMS duk nagode da kulawan ku*


*Ina mai mika sakon ta'aziya ga AYSHA ALI GARKUWA Allah yayi ma hamma umar Rahma yasa ya huta😭😭😭😭*

*Dedicated this page to*

*Ameerah Muhammad Hassan❤(babban yaya)*
*Khadija Muhammad Hassan😍*
*Aysha Muhammad HassanπŸ’‹*
*Muhammad Muhammad HassanπŸ’–(khalifa na soyayyar ka ta daban ce a xuciya na)*

Tare suka shiga makaranta, HALEEMATU tayi ajinta haka ma Hauwa'u.

Kasancewar yau bata makara ba yasa ta fara karanta littafai kafin lokacin sallah ya karasa............

Bayan an idar ne aka dauki attendance,sannan dalibai suka tafi aji.

Malamai kuma suka tsaya Dan akwai maganan da xasu tattauna.Mudir ne bude taron da addu'a sannan ya fara magana kaman haka"bawani abu bane yasa na taraku a nan ba  akan maganan musabaqa da xa'ayi na kasarmu ne,inaso a samu dalibai masu kokari da hazaka a cikin makaranta nan  Dan muna so mu dauki na d'aya,sai muyi fatan Allah ya bamu sa'a".

Gaba daya malaman suka amsa da "Ameen".


Mudir yace" Akwai mai magana?"

Malam Nuhu(malamin HALEEMATU SADEEYA) yace"in baxaka damu ba mudir inada wata daliba a ajina gaskia na yaba da hankalin ta ga shi tanada kokari."

Mudir yace "toh munaji wacece ita?"

Malam Nuhu yace"bawata bace kasan ta *HALEEMATU SADEEYA MUHAMMAD*"

Mudir najin sunan ya gane dan yasanta kuma ya yaba da hankali ta.

Duka malaman suka yi na'am da xancen Malam Nuhu Dan duk wani malami ya santa kuma sun yaba da hankali ta.

Haka aka yanke shawara HALEEMATU tana daya daga cikin Wanda xasuyi musabaqa.

Taro ya tashi kowani malami yayi ajinshi domin lokacin 'kari ya gabato.


Malam nuhu na shiga aji ya fara biya musu karatu kaman yadda ya Saba.

Yana gamawa ya tambayi Wanda xai bada hadda.

Yauma HALEEMATU SADEEYA ta fara badawa,ta kuma wajan xamanta ta xauna har lokacin break yayi yan aji suka fita.

Yauma kaman kullum Hauwa'u ce tazo ajin HALEEMATU.
Sukayi fira kaman Wanda suka dade.

Bayan an kuma ne aka cigaba da karatu har aka fita sallah.


A wajan sallah bayan an idar mudir ya tashi yayi wa'azi sannan yayi sanarwa akan musabaqa da xa'ayi.
Duka daliban suna fatan a dauke su.

Bayan an gama sanarwa ne  aka duba wanda sukaxo da cikaken kayan makaranta.
Wanda basu saba aka basu aiki suyi.

Wanda kuma sukasa suka tafi aji.......................

Bayan an tashi gida ne Malam Nuhu yace"HALEEMATU ki tsaya wurin office din mudir inkin fita."

HALEEMATU ta amsa "toh Malam."

Haka aka yi tana fita ta tsaya wajan office din mudir.

Ba tafi minti biyu ba saiga Hauwa'u itama taxo.


HALEEMATU tace"Ah Hauwa'u may kike yi anan?"

Hauwa'u tace"wallahi Malam Bash ne yace inxo in jirashi".


Haleematu tace" lahhh nima Malam Nuhu ne yace in jirashi anan."

Suna cikin magana saiga wani Dan aji biyar wato Mukhtar Mahmud.
Cikin ladabi suka gaisa shima yace malamin su ne yace ya jirashi.

Basufi minti goma ba saiga  malaman duka suka shiga office din,su HALEEMATU suka Mara musu baya.

Mudir ne ya fara magana"Alhamdullilah mun godema Allah daya bamu daman xama anan wurin,bawani abu yasa aka kira Ku ba saboda ilimi da haxa kar Ku da kuke dashi,kuma badan kunfi sauran ba A'a saboda munfi yarda da kune."

Tunda ya fara magana wajan yayi shiru Dan basusan may yake nufi ba.

Mudir ya cigaba"Ku ukun nan xakuji kuyi muraja'a saboda akwai musabaqa da xa'ayi Wanda na fada daxun a wajan sallah. Kuma nace axo da kune saboda Ku dage kuyi iya kokarin ku."

Ya karasa maganan yana kallon daliban.


Mudir ya kara magana"malamai ajinku xasu ba kowa iya hizbi da xaiyi.Allah ya bamu sa'a."

Duk Kansu suka amsa da "Ameen".
Sannan suka tashi da tashi Dan tafiya gida.

Suna fitowa bakin gate sukayi ma mai gadi  sannan suka karasa fita.

Suna fita suka tadda yah Abdulfata yana jiran su.

Da fara'ar su suka karasa suka gaishe shi.

Yau duk yadda Hauwa'u tayi akan sutafi tare amma sam HALEEMATU ta'ki yarda.
Haka suka tafi ba tare da haleematu ba.
Yah Abdulfata ma baiji dadi ba Dan HALEEMATU na burge shi.
Haleematu na isa gida ta sanar da iyayen ta.

Sosai sunyi farin ciki kuma sukayi mata fatan alkhari.

Haleematu taji dadin yadda iyayen ta ke kula da ita.

(Iyaye na gari kenan Allah ya karemu na iyayen mu ya saka muku da mafi fincin alkhari)

Hauwa'u tun a mota ya fadama yah Abdulfata.
Sosai ya tayata murna.

Suna isa gida ta sanar da mum dinta saboda dad dinta yana abroad.*WACECE HAUWA'U?*Toh masu karatu Ku biyuni Dan jin wacece Hauwa'u.
Saimun hadu a next page.

*Yawan comments Yawan posting*


Dan~buxu😍😍😘
08064481429
For comments and correction.
M.Hassan ce mai kaunar ku❤
[3/11, 10:58] Lovely Sis: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
*HALEEMATU SADEEYA*
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽWritten by:Maryam Muhammad Hassan.


Page21--25*This page is oll urs my sister my friend my mentor Fatima Muhammad (Ummancy)πŸ˜πŸ˜πŸ˜˜πŸ’–**WACECE HAUWA'U*

Hauwa'u Usman ne cikaken sunan ta.
Alhaji Usman yusha'u Dan asalin garin gombe ne.
Alhaji Usman ne kadai danshi a duniya.
Mahaifin shi bawani mai kudi bane amma yanada na rufin asiri.
Da kyar Usman ya gama secondary school dinshi tun daga nan ya tsaya da karatun shi ya kuma Sana'a Dan yasamu ya cigaba da karatun shi.
Alhaji Usman mai rike amana ne shiyasa ya fita xakka a wajan ogan su.
Cikin ikon Allah ogan sa ya sama mishi university a nan gombe ya cigaba da karatu shi inda ya karanci business adminstration.

Bayan wata biyar da gamawan shi Allah yayi ma ogan shi rasuwa.
Sosai mutane gombe sunji rasuwan bawan Allah nan.

Haka Rayuwa ta cigaba da tafiya sannu a hankali har Allah ya ba Alhaji Usman aiki a Kaduna karkashen ma'ikatan NOCACO.

Allah ya budamai sosai, yana tafiye² har Allah ya hadashi da hajiya Bilkisu sukayi aure.

Bayan auran su da shekara daya Allah yayima iyayen shi rasuwa.
Haka Rayuwa ta cigaba harya gama ginin shi a Kaduna ya dawo da xama inda yayima danjin shi alkwarin xai dunga kawo musu xiyara.Ranar da xai tafi sunyi kukan rabuwa sosai.


Bayan dawowan su ne Allah ya azurta su da danshi na farko wato Abdulfata.

Saida Abdulfata ya shekara shida sannan Allah ya azurta su da y'a mace taci sunan Maman Alhaji Usman amma yana kiranta da Jidda.


Hauwa'u chocolate colour ce,ita ba ba'ka ba kuma fara sosai ba.Tanada hanci ga idanu ga diri.

Wannan kenan.


*CIGABAN LABARI*


Yauma kaman kullum HALEEMATU ta tashi tayi aikin da xatayi ta kuma dakin ta danyin muraja'a.

Kasan cewar yau Monday, kuma haleematu ta gama secondary school dinta amma ba halin karasa wa.
Haka ta kuma dakin ta sbd tayi muraja'a har karfe sha biyu sannan ta fito Dan daura abuncin rana saboda karfe biyu da rabi yau xata tafi makaranta.

Tana fito wa kitchen ta nufa ta tadda Ammih na kokarin daurawa.

Haleematu tace"Haba Ammih na gani a gida kuma kina kokarin daura girki,meye amfani na?"

Ta karasa maganan kaman xatayi kuka.

Ammih tace"Toh ae naga kina karatu ne shiyasa nace bari in tayaki."

HALEEMATU tace"Toh yanxu na fito kije ki huta."

Ammih tace"Toh Yar albarka Allah yayi miki albarka ya baki Wanda xasu yi miki biyayya."

Ta karasa maganan tana murmushi, sannan ta fita daga kitchen din tana kara godema Allah daya bata HALEEMATU SADEEYA a matsayin y'a.


Haka HALEEMATU ta cigaba da aikin ta harta gama dafa musu shinkafa da miya Wanda yaji naman kasuwa.

Haleematu na gamawa ta shiga dakinta.
Wanka ta karayi(kunsan HALEEMATU SADEEYA akwai tsafta sosai)

Bayan tayi wanka ne ta dauro alwalan ta.

Tana fito wa ana kirayen sallah, tana gama shirya wa tayi sallah ta dade tana addu'oin kafin ta sallame ta linke abin sallah ta fito.
Kai tsaye kitchen ta nufa  ta dauki babban faranti ta xuba musu abinci sannan ta fito ta nufi dakin Ammih.

Tana shiga ta tadda Ammih akan sallaya da alama ta idar ta sallah.
Ajiyewa tayi tare da bin addu'a da takeyi.
Tare suka shafa addu'a.

Nan suka xauna sunaci suna fira irin ta uwa da yarta.

Suna gamawa ta dauki farantin taje ta wanke sannan ta fito daga kitchen ta kuma wajan Ammih ta.

Nan suka fara hira har saida biyu tayi sannan HALEEMATU ta tashi Dan shirya wa xuwa islamiyya.


Bayan ta gama shirinta ta fito tayima Ammih sallama sannan ta fita.......................

Tana isa ta gaida baba mai gadi kamar kullum ya amsa da fara'ar sa yana samata albarka.


Direct aji ta nufa ba Wanda yaxo Dan haka ajinsu Hauwa'u ta nufa,nanma ba Wanda yaxo haka ta fito Dan kumawa aji.
Kicibus tayi da hauwa'u xata shiga aji.

Hauwa'u tace"Ahh kawata sai yanxu?"

Haleematu ta harare ta"ke xancewa sai yanxu tunda daga ajinku nake ba kuwa."

Hauwa'u tace"wlhy naje wajan Malam Abubakar ne dan jimin hadda na."

HALEEMATU tace"kaii nima bari naje ."

Hauwa'u tace"toh kiyi sauri Dan naji yana cewa xai fita."

Haleematu tace"toh sai anjima,mu hadu a wajan assembly. "

Haka suka rabu kowa yayi tafiyan shi.


*Ban manta dakuba:*

*Mum mu'axxam*
*Maman sahal*
*Maman muwadda*
*Khadija katuru*
*Aysha Yar aduwa*
*Ramlat*
*Ameena*
*Xainab*
*Aysha*
*My Maryam*


Masoya na kunada yawa inxan kiraku page daya yayi min kadanπŸ˜ƒπŸ˜ƒ.
Saidai ince Allah ya barmu tare 🀝.
I heart u ollπŸ’‹Sai mun hadu a next page.Dan~buxu
08064481429
For comments and correction.

M.Hassan ce mai kaunar ku❤
[3/11, 10:59] Lovely Sis: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
*HALEEMATU SADEEYA*
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž*CLASSIC WRITERS ASSOCIATIONπŸ’…*
Written by:Maryam Muhammad Hassan.


Page 26--30*Dedicated to Zahra Muhammad Mahmud(Surbajo)*


*H*alematu na xuwa ta tadda Malam Abubakar na shirin fita amma ganinta yasa ya fasa.
Da sallama ta karasa shiga,ta gaishe shi sannan ta xauna ta fara bada haddan cikin muryan ta mai dadin sauraro.

Tana iddar wa saiga Mukhtar shima yaxo,haka Malam Abubakar ya fasa fitan ya tsaya jima Mukhtar.

Biyu da minti hamsim aka fita assembly, kowani dalibi ya hallara a wajan.


HALEEMATU ce  ta fita ta bude da addu'a sannan tayi karatu Al Qur'ani mai girma.
Tana gamawa aka danyi fakadarwa sannan dalibai suka tafi ajinsu dan karatu.

*Akwana atashi*
Yau ake musabaqa Inda manyan malamai da mutane suka hallara a filin musabaqa domin sauraru.

*HALEEMATU SADEEYA MUHAMMAD* aka fara kira.

Haleematu cikin sanyin hali da nutsuwa ta fara tafiya harya isa kan munbari(stage).

Nan mai jan karatu ya fara jamata.
Cikin ikon Allah duk inda yaja mata sai tayi.
Iyayen HALEEMATU harda hawayen jin dadi saida sukayi.

A na biyu aka kira Hauwa'u Usman, itama duk inda aka kira saita yi.

Abin ya burje jama'an wajan bama kaman yah Abdulfata.

Karshe duk Wanda yaxo wurin sai yaji HALEEMATU da Hauwa'u sun burgesu.

Haka akayi taro kuwa ya watse.

Inda anan iyayen HALEEMATU da Hauwa'u suka hadu sunyi murna matuqa.
*Bayan sati biyu*

Bayan sati biyu da musabaqa aka fito da sakamako.
Cikin ikon Allah *MARKAZUL IHSAN*ce ta daya,inda aka kira daliban kuwa yasamu kyaututuka bama kaman HALEEMATU saboda itace taxo na daya.

Acikin kyautukan ne tasamu laptop, waya da littafan karatu da Qur'ani guda biyu.
Sosai taji dadi kuma ta godema Allah.
Haka Rayuwa take tafiya cikin jin dadi.
Haleematu da Hauwa'u shakuwa ta kara shiga tsakanin su har mutane ke kiransu da *leemahauwa* koh *hauwaleema*.


A bangaren yah Abdulfata kuma kullum da soyayyar haleematu yake kwana yake tashi.Amma ya kasa bayyana mata.

Yau ta kasance Al hamis ba islamiyya, HALEEMATU bata tashi da wuriba sai wajan karfe Tara,lokacin har Ammih ta gama had'a Karin safe ansamata a food flask.Da salati ta tashi,kai tsaye toilet ta shiga tayi wanka,sannan ta fito a shirya cikin Riga da skirt na atamfa.

Sosai dinkin ya mata kyau haka ta tofke kanta Wanda aka yimata kitson buxaye ta daura Dan kwalinta ta fito dan 'karyawa.

Bayan ta gama tayi aikacen ta,ta kuma daki.


Harta kwanta saita tuna wayan da aka bata,sai taji tana sha'awar dubawa.
Mikewa tayi ta dauko ta kunna.

Tana kunnawa taga sakon ni na shigowa.Abin yabata mamaki ita dai tasan yau ta fara kunnata toh waye keda number ta?

A abinda ta ganin shiya kara bata mamaki amma ta barma xucia ta.


Haka HALEEMATU ta cigaba da samun  messages na soyayya.
Wani xubin tayi reply koh tayi banxa dashi.

Sannu a hankali taji son bawan Allah na shiga xuciya ta.Har addu'a takeyi Allah ya bayanna mata masoyin ta.

(Abinda masu karatu basu saniba shine yah Abdulfata ne ya ba mudir din makarantan waya a sama HALEEMATU cikin gifts dinta a matsayin kyautan shi)

*Bayan shekara biyu*

Abubuwa da dama sun faru.
Hauwa'u ta gama secondary school dinta.
A wannan shekaran ne HALEEMATU da Hauwa'u xasuyi sauka Al Qur'ani mai girma.
Sakamakon anyima Hauwa'u double promotion saboda kokarin ta.


Shirye-shirye sukeyi a kowani bangaren.


Yah Abdulfata har yanxu ya kasa gayama HALEEMATU abinda  ke xuciya shi.
Amma suna waya da ita,ta dayan sim card dinshi Wanda kuwa ya sanshi dashi.

Haleematu ta dauka duk shakuwace amma a bangaren ogan ba haka bane.
Yau saura sari gida saukan su HALEEMATU.

A makaranta aka kirasu,dalibai goma sha biyar.

Kowani malami  yayi musu nasiha mai shiga rai............... ..............Yau take ranar alfahari ga daliban.

A haraban makaranta ba masaka tsinke mutane su hallara sosai a wurin harda dangi da abokan arxiki ba Wanda bai xuba.

Anyi programs dinda aka shirya Masha Allah.


Haka akayi faru aka gama inda dalibai suka amsa kyaututuka.

A ranar ne yah Abdulfata ya ba HALEEMATU wani kyauta Wanda ba Wanda yasan maye a ciki.

*TOH MASU KARATU MAY YAH ABDULFATA YA BAMA HALEEMATU SADEEYA*
KU BIYONI DAN JIN LABARI.


Sai mun hadu a next page.Dan~buxu😍😍😘
08064481429
For comments and correction.


M.Hassan ce mai kaunar ku❤
[3/11, 10:59] Lovely Sis: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
*HALEEMATU SADEEYA*
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽCLASSIC WRITERS ASSOCIATIONπŸ’…
Written by:Maryam Muhammad Hassan.


Page31--35
Haleematu bata bude kyautan ba sai washegari bayan an watse.
Tana budewa Qur'ani ne aciki guda biyu sai wata Yar takkada datake ciki.

A hankali haleematu ta fara bude wa harta bude gaba daya.

*"Assalamu alaikum, dafatan kina lafiya?Ina tayaki murnan kammala saukar Al Qur'ani mai girma da kikayi.Kuma a wannan ranan nakeso in fada miki abinda ke xucia na, kuma ina fatan xaki amshe ni hannu biyu.HALEEMATU duk wani sa'ko da kike gani nine nan nake miki ta private number na Wanda har mommy bata sanni dashi ba.*
*HALEEMATU tun ranar Dana fara ganinki naji na kaimu da sonki Wanda nakeji inbake baxan iya Rayuwa ba amma ban gayamiki ba,ina jiran irin wannan ranar farin ciki ne Dan in fallasa miki.Dafatan xaki amshi soyayyata.*
*Daga mosoyin ki Abdulfata Usman"*
HALEEMATU na gama karantawa saita tsinci kanta cikin farin ciki da annashuwa Wanda ta rasa dalilin shigan ta.

Nan ta dauki Al Qur'ani ta ajiye su inda take ajewa.

 Haka ta tashi ta shiga wanka cikin farin ciki.


Tana fitowa wayanta ya fara ringing tana duba wa taga *Yah Abdulfata* murmushi tayi sannan ta d'aga.

Kusan minti goma ba Wanda yayi magana a cikin su.

Yah Abdulfata ne yayi karfin halin cewa"Assalamu alaikum ".

Haleematu ta amsa cikin farin ciki amma bata bari ya gane ba.

Yah Abdulfata yace" Nasan yanxu kin sami sakona?"

HALEEMATU tace"eh na gani".
Ta fada cikin kunya kaman yana ganinta.

Yah Abdulfata yace "toh yanxu may kika yanke?"

Haleematu shiru tayi Dan batasan may xata cemai ba.

Jin shirun ne yasa ya fahimce ta amince.
Nan yaji dadi ya ziyarci xuciyan shi.


Yah Abdulfata yace "ke nake sauraro princesses."

HALEEMATU cikin kunya kaman yana gabanta tace"Allah ya barmu tare."
Tana gama fadin haka ta kashe wayan gaba daya.

Yah Abdulfata ya kara kira yaji switch off. Murmushi yayi Dan yasan kunyace tasa ta kashe wayan.


Wanka kawai yayi ya shirya cikin Riga da wando sunyi matukar yimasa kyau.

Fitowa yayi parlour ya tadda mommy, daddy da Hauwa'u.

Hauwa'u tace"Ahh bro yana ganka sai murmushi yakeyi kaman anyi ma albishir da aljannah."
Ta fada cikin zolaya.

Mommy ta amsa xancen da cewa"Auta kema kya fada dai."

Daddy yace"Ahh yan sa ido Ku barmin yarona."

Yah Abdulfata yace "Uhmm daddy rabu dasu ni yanxu wajan  matata xanje."

Carab Hauwa'u tace"Dan Allah bro inxo in rakaka?"

Mommy tace"Dalla rabu dashi sau nawa yake cemin xai kawomin siruka amma har yanxu shiru nake ji."
Ta fada tana kallon yah Abdulfata din.

Yah Abdulfata yace"Allah mommy yau da gaske nake."

Mommy da daddy sukace"Allah yasa da gaske ne."

Murmushi yah Abdulfata yayi sannan yayi hanyan fita.

Har xai fita hauwa'u ta kara tambayan shi.

Yah Abdulfata yace "A'a banaso ki barshi."
Ya fada yana kallon agogon dake hannun shi.

Hauwa'u tace"Haba Don Allah bro inaso in riga mommy da daddy ganin aunty na".
Tayi maganan kaman xatayi kuka.

Yah Abdulfata ganin xatayi kuma ne yasa yace ta taso su tafi.

Da murna Hauwa'u ta tashi ta dauko gyalen ta.

Tana fitowa tayima mommy da daddy sallama suka fita.

A parking lot ya tsaya.

Yah Abdulfata yace "lil sis amma fa akwai sharadi."

Hauwa'u tace"inaji bro."

Yah Abdulfata yace"Duk abinda kika ganin kiyimin shiru inba haka ba baxan kara fita dake ba,kinji ni koh?"

Hauwa'u ta ce"eh bro naji kuma insha Allah xan kiyaye."

Yace"Gud."
Cewar yah Abdulfata yana shiga driver sit.

Hauwa'u ma xagayawa tayi ta shiga.


Hauwa'u tana ganin anyi hanyan gidan su HALEEMATU.

Cikin murna tace"Br..."

Sai kuma tayi shiru sakamakon kallon daya watsa mata.


Har suka iso itadai Hauwa'u sai kallo kawai. Tana tunanin toh may ya kawo bro gidan HALEEMATU?


Ni M.Hassan nace kedai yi kallon ikon Allah.Bata gama tsinkewa ba saida taga yayan na ta ya dauki wayan shi ya kira HALEEMATU.

Still a kashe wayan.

Kallon shi ya kuma kan Hauwa'u yace"ki kira Ammih kice mata munxo."


HALEEMATU shirya wa tayi ta fito tsakar  gida.

Sai mun hadu a next page.
Dan~buxu😍😍😘
08064481429
For comments and correction.


M.Hassan ce mai kaunar ku❤
[3/11, 10:59] Lovely Sis: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
*HALEEMATU SADEEYA*
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
CLASSIC WRITERS ASSOCIATIONπŸ’…

Written by
              Maryam Muhammad Hassan.
*This page is oll urs my friend my sister AYSHA AL HASSAN*
Much luv to u dear😘Page41--45


Washegari HALEEMATU ta Riga yah Abdulfata tashi,da kyar ta shiga toilet ta kasa jikin ta tayi wanka ta dauro alwala
Koda ta fito bataga yah Abdulfata ba ya fita xuwa massalaci.
Sallah ta tayar tana idar wa ta fara karatun Qur'ani kaman yadda ta saba,har saida yah Abdulfata ya shigo ya sameta tare suka shafa addu'a.

Haleematu ta sun kuyar da kai ta gaishe sa.

Murmushi yayi yace"morning morning my princess."

HALEEMATU tayi murmushi ta mike ta mayar da Qur'ani ta linke pray mat din.

Karfe goma aka fara yimusu knocking din kofar parlour.

Yah Abdulfata ne ya bude,driver mommy ya gani tsaye da basket na abinci.
Gaisawa sukayi sannan yace"Hajiya ce tace in kawo muku breakfast."
Cewar Basiru(Driver mommy).

Yah Abdulfata amsa yayi tare da yin godiya.

Parlour ya dawo,HALEEMATU ta amsa ta jera a dinning.
Bayan ta gama ne ta kuma dakin ta wanka ta sakeyi ta shirya cikin Riga da skirt na atamfa,simple makeup tayi amma tayi kyau.

Lokacin da yah Abdulfata ya ganta koh kwakwaran motsi ya kasa ya tafi duniyan tunani.

Harta karaso bai sani ba saida ta hura masa iska sannan ya dawo hayyacin shi.

Yah Abdulfata yace "My princess you look so gorgeous."

Fari da ido HALEEMATU tayi Wanda ya kusa xautar da yah Abdulfata tace"Tnx you my Prince, food is ready."

Yah Abdulfata yace"OK Princess."

Haka suka nufi dinning area sunaci yah Abdulfata na Satan kallon HALEEMATU.
Suna gamawa HALEEMATU ta kashe kayan taje kitchen saida ta wankesu sannan ta fito.

A parlour ta tadda yah Abdulfata na kallon wani film da akeyi a MBC Bollywood na Annuskha sharma.
Kusa dashi ta xauna suna kallon dan itama tanason actress din.


Saida aka kira sallah sannan suka miki yah Abdulfata ya nufi massalaci ,ita kuma HALEEMATU ta nufi dakin ta Dan yin sallah.

Haleematu na idar wa taji ana bude gate, mikewa tayi ta leka ta window dakinta Dan ganin su waye.

Tana ganin motan tasan na Hauwa'u ne.
Da sauri ta dauko kasa ta nufi kofan parlour.
Suna ganin juna hugging kaman Wanda suka shekara basuga juna ba.
Haleematu bata kula da abokin yah Abdulfata ba saida suka shiga parlour, anan ne ta ganshi sai kunyan shi ta kamata.

Nan suka gaisa dashi, saiga yah Abdulfata ya dawo.

Hauwa'u da mustapha suka hau tsokanan su.


Haleematu taja Hauwa'u suka tafi daki suka bar Mustapha da Yah Abdulfata.


Saida aka kira la'asir sannan suka nufi massalaci.

Bayan sun dawo basu Dade ba sukaji motoci na shigowa.

Kannan Ammih da baba ne sukaxo ganin gida sai mabaruka data rakusu.

Haleematu taji dadin ganin su sosai.

Sunga gida sai Sam barka ake Mata.

Da xasu tafi sosai sunyi mata nasiha akan xamanta kewar aure.

Haleematu harda kukan ta.

Haka suka tafi suka bar yah Abdulfata, Mustapha,HALEEMATU da kuma Hauwa'u.

Karfe shida mommy ta aiko musu da abinci.

Hauwa'u da HALEEMATU suka shirya a dinning saida akayi sallah sannan sukayi dinner suka tafi.Aka bar HALEEMATU da yah Abdulfata.********
*Bayan wata biyu*


HALEEMATU na hango kwance a kan yah Abdulfata sai shagwaba take zubamai shima yana biye Mata.


Saida na kara kunne sosai sannan na ji abinda take fada.

"Dan Allah Prince yau muje kaga fah mun dade,inaso inga Ammih da baba."

Cewar HALEEMATU tana kara narkewa a jikin shi.

Yah Abdulfata yace"Haba princess na ki bari gobe muje kinga bamu fada musu ba."

Ya fadi maganan yana kwaikwayan muryan ta.

Haleematu tayi murmushi tace" toh bari inje inyi girki."
Tayi maganan tana kokarin mikewa..............
Sai mun hadu a next page.

Dan~buxu
08064481429
For comments and correction.M.Hassan ce mai kaunar ku❤
[3/11, 10:59] Lovely Sis: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
*HALEEMATU SADEEYA*
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž

CLASSIC WRITERS ASSOCIATIONπŸ’…
Written by
                  Maryam Muhammad Hassan.


*Masoya na nagode da addu'a ku.Alhamdullilah na gama exams dina lafiya sai fatan Allah yasa result yayi kyau*
*Masu kirana nagode da kulawan ku nasan kauna ce ta kawo hakan*
Ina yinku totallyπŸ’‹

Dedicated this page to my forever and ever friends:
*Xainab farouk*
*Amina Muhammad Auwal*
*Nafisa Aliyu*
*Ramlat Ishaq Al-Madany*
I will really miss you galsPage 36--40
Tana tsakar gida taji wayan ta na ringing, shiga tayi tana dubawa taga yah Abdulfata.

Murmushi tayi sannan ta dauka"Assalamu alaikum."

Yah Abdulfata yace"Wa'alaiki salam SADEEYA ta."

Murmushi HALEEMATU tayi Wanda har saida yah Abdulfata yaji.

Yah Abdulfata yace "toh gani a kofar gidan mu."

A razane HALEEMATU tace"wani gidan?"

Yah Abdulfata yace "wani gidan garemu Wanda ya wuce gidan baba."

HALEEMATU tace"kaida waye?"

Yah Abdulfata yace "nida lil sis dina koh akwai magana ne."

HALEEMATU tace"A'ah Ku shigo."

Ita dai Hauwa'u har yanxu bata yadda da abinda xuciyan ta ke fada mata ba.

Daga haka suka shiga gidan.

Gaba daya HALEEMATU ta daburce Dan ba karamin kunyan taji ba.

Hauwa'u kam yanxu ta gano bakin zaren ta dunga tsokanan su.

Sudai sai murmushi sukeyi har bayan la'asir suna gidan suna hira.

Bayan sun tafine.HALEEMATU ta shiga dakin Ammih ta sameta tayi mata bayanin komai.
Nan Ammih tayi musu addu'a sannan haleematu ta fita Dan daura abincin dare.

Ana kiraye-kirayen sallah ta kammala girkin.
Kai tsaye dakinta ta tafi tayi wanka ta dauro alwalanta.

Shiryawa tayi cikin kayan bacci sannan ta dauko xani ta daura tayi sallah.

Tana idar wa ta fara muraja'a kaman yadda ta saba.A kwana a tashi ba wuya Hauwa'u ta kammla karatun ta na secondary school tana neman admission.

Yah Abdulfata da HALEEMATU SADEEYA soyayya sukeyi ba kama hannun Yaro.

Lokacin da xancen yake wurin parent din yah Abdulfata sosai sunyi farin ciki bama kaman mommy dan ta yarda da tabi'un HALEEMATU SADEEYA.

Hauwa'u kuma yanxu matar yaya take cema HALEEMATU.

Xaman lafiya da yardar juna sukeyi a tsakanin family biyu.
*BAYAN SHEKARA DAYA*

Abubuwa da dama sun faru har bikin yah Abdulfata da HALEEMATU ansa,Wata mai xuwa.

Sosai ake shirye shirye mommy ta dau nauyin kayan kitchen.
Baba yaji dadi sosai sai sama yah Abdulfata albarka yakeyi.

Yarinyan kanwar baba ne taxo daga agadaz,sa'ar HALEEMATU ne tun suna kanana rabon da su hadu.Hakan yasa tace tanaso taga HALEEMATU SADEEYA.

Shakuwa ta shiga tsakanin Mabaruka(yarinyan kanwar baba) da HALEEMATU.

Yah Abdulfata kam gyara gidan shi yakeyi sosai.A kwana atashi ba wuya wurin Allah yau saura sati guda bikin yah Abdulfata da HALEEMATU.

Dangi sun cika gidajen Masha Allah.

Baba yayi ma HALEEMATU kayan dakin ta dai-dai gwargwado.

Yah Abdulfata kam ba yadda baiyi da HALEEMATU ba akan ta yarda suyi dinner amma Sam taqi yarda haka ya hakura badan yaso hakan ba.

Hauwa'u kam xansu masu karatu suga Inda take farin ciki.


Yau ta kama jumm'a kuma yayi dai-dai  da ranar daurin auren
*HALEEMATU SADEEYA MUHAMMAD*
           DA
*ABDULFATA USMAN.*

Daurin auren daya hallaci manyan mutane da abokan arziki,Ku ina na waiga jama'a ake gani suna taya ango murna.

Hauwa'u ce ta kira mai kwalliya ta tsara ma HALEEMATU SADEEYA sannan ta shirya cikin material mai kyau mai tsada kalar light brown, veil ma haka sai agogo black.
Masha Allah masu karatu alkalami da Allo  baxai dauki irin kyan da HALEEMATU tayi ba.Na Baku dama Ku tsara da kanku.

Hauwa'u ma akayi mata kwalliya gaskiya itama ba karya tayi kyau sosai baxaka iya banbace ta da amarya ba.

Bayan sallah la'asir ne akayi walima Wanda hauwa'u ce ta dau nayin yin hakan.

A wajan walima malama Fatima tayi wa'azi sosai akan xaman takewar aure da nasiha.

Haka taro ya tashi karfe shida

Bayan anyi sallah magrib motan kai amarya taxo da kyar aka raba HALEEMATU da Ammih sosai suke kukan rabuwa.
Haka aka dau amarya sai gidanta dake unguwan rimi.Fadin haduwan gidan bata lokacin amma babban gidane ciki yake da shuke-shuke da kayan alatu na xamani.
Masu karatu ku kiyasta kawai.

Yan kai amarya suka watse kuwa sai barka yake mata.
Hauwa'u ce kawai ta tsaya jiran ango.
Basu Dade ba saiga ango da abokinsa Al-Mustapha.

Ango ya biya kudin siyan baki sannan Hauwa'u da mustapha suka tafi.Yah Abdulfata har parking lot ya rakasu.

Yana dawowa ya tadda HALEEMATU ta shiga toilet
Murmushi yayi ya fita ya nufi wani corridor Wanda xai sadashi da dakin shi.

Yana shiga toilet ya nufa yayi wanka ya dauro alwala ya fito ya shirya cikin short nicker da jallabiya  ya feshe jikin shi da   ruka.

Dakin HALEEMATU ya nufa ya tadda tana jiran shi.

Sallah ya jasu bayan sun idar ne ya fito parlour ya shiga kitchen.
Plate da cup ya dauko sannan ya kara fitowa ya dauki Leda.

Fresh milk da chicken ne a ciki xubawa yayi a plate yayi ya fara ba HALEEMATU, tanaci tanajin kunya.
Saida ya tabbatar ya koshi sannan ya faraci har ya kammala.
Ya dauki plate da cup din ya kai kitchen sannan ya dawo ya dauki raguwan fresh milk din ya sa a fridge.

Yana dawowa ya tadda ita xaune inda ya barta.

Brush biyu da maclean ya dauko ya samata a brush shima yasa.
Tare sukayi brush suka fito.

Yah Abdulfata ya kuma dakin shi yasa kayan bacci.

HALEEMATU ma yana fita ta mike ta bude wardrobe din dake dakin ta hau dube-duben inda kayanta suke,har yah Abdulfata ya shigo ya sameta tana DUBA wa.

Tambayan ta yayi"Habibty  na may kike dubawa ne haka?"

HALEEMATU kasa bashi amsa tayi sbd in romantic voice yayi maganan.

Kara sowa yayi ya rungume ta yace"yau rowan Cweet voice xakiyi min."

Da kyar ta iya bude baki tace"A'ah kayana nake Nema."

Murmushi yah Abdulfata yayi yace"Kayan ki na dakina  bari in dauko miki."
Ya karasa magana tare da tafiya.

Dakin shi yanufa doguwar Riga ya dauko mata sannan ya dawo ya bata.
Tsaya wa tayi tana kallon shi.

Murmushi yayi ya fita Dan ya fahimce may take nufi.

Shiryawa tayi ta kalli kanta a mirror taga ko cinya rigar bata kawo mata ba.
Hijabi tasa sannan ta kashe wuta ta kwanta.

Yah Abdulfata saida ya tabbatar ta gama sannan ya shiga.

Murmushi yayi ya kwanta gefen ta yayi musu addu'a kwanciya ya jawo bargo ya rufe su.........................

*ASUBA TA GARI HALEEMATU SADEEYA DA ANGONTA ABDULFATA*
Sai mun hadu a next page.Dan~buxu😍😍😘
08064481429
For comments and correction.

M.Hassan ce mai kaunar ku❤
[3/11, 10:59] Lovely Sis: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
*HALEEMATU SADEEYA*
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽCLASSIC WRITERS ASSOCIATIONπŸ’…
Written by
             Maryam Muhammad Hassan.

Page 46--50*Na sadaukar da page dinnan gaba dayan shi ga MUSAN JUNAH O.H.W.*

*MASOYA NA INA BARA'R ADDU'A KU YAYATA DA KANINA BASUDA LAFIYAπŸ™*


Yah Abdulfata ya jawota yace "Haba princess na inaso in ganki a kusa dani ina kallon abubuwa na muje muyi girkin tare."

HALEEMATU ta sunkuya dai² kunnen shi tayi mai magana Wanda komin kwa² na injiyo na kasa.
Sai murmushi naga yah Abdulfata keyi.

Tare suka shiga kitchen din duk inda HALEEMATU tayi yah Abdulfata na biye da ita kaman tsohon maye har suka gama girkin suka jera a dinning.

Duk kansu daki suka tafi dan yin wanka.

Kusan atare suka gama shirin suka fito.
Dinning suka tafi yah Abdulfata na ba HALEEMATU a baki,itama tana bashi haka har suka gama suka nufi garden din gidan domin shakatawa.

Wurine mai ciki da flowers da kujeru na shan iska ga kuma play group a gefe sai swimming pool.

Had kusan magrib suna wajan sannan suka nufi part dinsu.

Kitchen suka nufa yanxuma tare sukayi girkin.

A bangaren Hauwa'u tun ranar da suka hadu da Mustapha suka kulla soyayya mai tsafta tsakanin su.

Kullum cikin waya sukeyi da HALEEMATU.
Hauwa'u na bata labarin Mustapha.


Lokacin da xancen yaje kunnen yah Abdulfata yaji  dadi sosai,Dan burinshi kenan.
Duk wata mace xataso Mustapha ya xama mijinta.
Washe gari lahadi,Haleematu ta shirya cikin Riga da xani na atamfa Dan yau shine farko da xata fita tunda tayi aure.

Yah Abdulfata na fitowa cikin shirinsa shima.

Breakfast sukayi sannan suka fita.Saida suka tsaya a boutique yayi soyayya sannan suka kaman banyan gidan su HALEEMATU.

Sosai Ammih taji dadi ganin yarta tilo a duniya batada matsala a gidan mijinta.


Sai karfe biyu suka bar gidan.HALEEMATU harda kwanllan ta.


A mota yah Abdulfata sai tsokanan ta yakeyi.

Direct gidan mommy suka nufa.
Mommy bakinta har kunne in~law dinta taxo.

Bayan sun gaisa HALEEMATU ta haurawa sama ta yi ta tadda Hauwa'u na waya.

Hauwa'u na ganin ta batasan lokacin data sake wayan ba.
Hugging juna sukayi tightly.

Bayan sun xauna Hauwa'u ta fara bata lavarin Mustapha har take gaya mata xai aiko parents dinshi.

Duk maganan da sukeyi a kunnen Mustapha saboda ta manta bata kashe wayan ba.

Sosai yaji dadj yadda Hauwa'u ke yaban shi a bayan idonshi.

Saida yaji tace"Bari in jirashi Ku gaisa."
Sannan yayi hanging wayan.

Hauwa'u wayan ta ta dauka Wanda tun xuwan HALEEMATU ta yarda ita.

Bugu biyu Mustapha ya dauka.
Nan Hauwa'u tacemai xasu gaisa da haleematu.

Gaisawa sukayi da HALEEMATU sannan ta ba Hauwa'u.

Suna cikin waya suka tsinkayo muryan mommy na cewa"Ku baxaku fito ba kun shige daki kaman sabon amare."

Hauwa'u tace"gamunan xuwa mommy."

Sallama sukayi da Mustapha tare da alkwarin xai kirata daddare.

Nan suka fita suka xauna a parlour suna ta hira kaman ba sirikai ba.

Saida sukayi dinner sannan suka fito Dan tafiya.

Mommy ta hadama haleematu su turare da humra da saura kayan ado.

Haka suka kama hanya sai gida.
Washe gari tunda asuba  haleematu ta tashi tayi wanka tayi sallah ta shirya sannan ta fito kitchen ta nufa Dan daura ma mijinta breakfast.

Karfe bakwai yah Abdulfata ya fito cikin shirin sa na xuwa aiki.

Breakfast yayi sannan yace"princess na xan tafi."

HALEEMATU tace"Allah ya karemin mijina ya dawo Sakai lafiya,duk wani sharri dake kan hanya Allah ya nusantar dakai dashi da kuma duk wani Dan uwana musulmi,duk wani alkhari dake cikin wannan rana ya hadaka dashi,ya Allah ka karemun mijina a hanyan xuwan shi da dawowan shi."
Ta karasa maganan tana karasowa kusa dashi peck tayimai a forehead dinshi.

Yah Abdulfata yace "Ameen Allah ya biyaki matata ya baki yara Masu yi miki biyayya kaman yadda kike mana."

HALEEMATU ta sunkuyar da kai tace"Allah ya bamu masu albarka."....................


Saimun hadu a next page.Dan~buxu😍😍😘
08064481429
For comments and correction.


M.Hassan ce mai kaunar ku❤
[3/11, 10:59] Lovely Sis: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
*HALEEMATU SADEEYA*
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž

Written by
              Maryam Muhammad Hassan.

Page 51--55This page is oll urs my fans,I love u from d button of my heartπŸ’œ


Dedicated to:
*Khadeeijerh Hamxer*
*Mrs Aminu*
*Fatima BB(TB)*
*Fatima isgogo*
*Ayshat Hassan*
*Fatmalili*
*Maman salamatu*
*Maman Afnan*
*Rashidat Abdullahi*
*Fateemah Yusuf (yusteemah)*
*Fatima uba Akawu(ummu arif)*
*Khadija uba Akawu(Mrs bash gaya)*
*Fateemah xahra umar*
*Maman sahal*
*Maman Afnan*
*Xarah umar*
*Maryam Abubakar*
*mum nauwara*
*Samira Abdou*
*Amina Dkoli magami*
*Fatima idris saulawa*
*Nafeesah Sabi'u(precious)*
*Aisha t hamxa warrah*
*Mmn imam*
*Khadija Muhammad Hassan*
*Aysha Muhammad Hassan*
*Amira Muhammad Hassan*
*Ramlat Ishaq Al-Madany*
*Xainab farouk*
*Amina Muhammad Auwal*
*Ummulkhari Usman*
*Zakiyyah Muhammad*
*Yusra Ibrahim*
*Rahma musa*
*Fatima Nura*
*Nana Firdausi Abdulsalam*
*Hafsat sani Suleiman*
*Sa'adatu Musa yero*
*Nabila M Rabi'u*Washhh hannuna ya gaji,kunada yawa baxan iya rubuta sunan Ku ba kuyi hakuri  kuna raina.
*Ni M.Hassan ina alfahari daku masoyana😘*
Yah Abdulfata yace"Ameen princess dina."

Haka HALEEMATU ta rakasa har parking lot kaman yadda ta saba kullum.

Bayan ta dawo ne ta gyara ko ina sannan ta kuma ta kwanta.


Sai karfe goma ta tashi,wanka ta karayi ta shirya ta fito yin breakfast.

Bayan ta gama ta dawo parlour ta dauki phone dinta ta kira Ammih sun dade suna waya har baba saida suka gaisa daga bisani suka katse wayan badan sun gaji ba.

Tana katsewa kira na shigowa tanajin ringing tone din tasan waye Saboda nashi daban ne na *Oh my durling I love you.*

Murmushi tayi saida hakoran ta suka fito sannan ta dauka.
Sun Dade suna waya har tayi girkin rana,daga bisani HALEEMATU tayi mai sallama.

Yah Abdulfata sai karfe hudu ya taso daga aiki saida ya biya ta supermarket yayima princess dinshi soyayya kafin ya kama banyan xuwa gida.

Yana isa ya tadda princess dinshi na jiran shi a parlour.

Tana ganin shi ta mike tayi hugging dinshi tare da amsan briefcase dinshi.

Sannu da xuwa tayi mai sannan suka nufi dakin shi.
Haleematu ta shiga toilet ta hadamai ruwan wanka.
Duk yadda yayi taxo tayi mai amma Sam taqi yarda ita kunya haka ya hakura ya shiga shi kad'ai.

Bayan ya fito ya tadda haleematu ta fito da farar jallabiya.

Godia yayima Allah sannan ya shirya ya sauko kasa.

A kitchen ya tadda haleematu na aiki,nan ya shiga tayata har suka gama suka jera a dinning.

Kowa dakin shi ya nufa dan an fara kiran sallah magrib.

Yah Abdulfata alwala yayi sannan ya fito ya tafi massalaci.

Haleematu kuwa tana shiga wanka ta farayi ta dauro alwala sannan ta fito.

Shirya wa tayi cikin dogowar riga mai hannun shimi ta feshe jikin ta da humra kala kala mai dadin kamshi.
Sallah tayi bayan ta idar ne ta fara karatun Qur'ani har aka kira sallah isha'i sannan ta gabatar da sallah.

Simple makeup tayi, ta kara feshe jikin ta da turarun ka da humra.

Fitowan ta yayi dai dai da shogowan yah Abdulfata.

Tun abakin kofan parlour kamshi ya dake hancin sa lumshe ido yayi tare da karasowa cikin parlour.

Rungume ta yayi ya hau kissing dinta haleematu bata hanashi ba saida taga yana Neman wuce gona sannan ta xame ta barshi.

Dinning ta nufa yah Abdulfata da kyar ya daga kafan shi ya karasa dinning din.

Haleematu da manta ta dunga bashi a baki a haka suka gama cika cikin su.

Parlour suka dawo suna hira har karfe goma sannan suka nufi daki Dan kwanciya.*BAYAN WATA BIYAR*

HALEEMATU yau tunda ta tashi batajin dadin jikin ta sai kasala kafin wani lokacin zazzabi mai xafi ya rufe ta.

Hankali yah Abdulfata ba karamin tashi yayi ba  daukan ta yayi xuwa Asibitin *VICAS HOSPITAL.*

Bayan likita ya gama gwaje gwajan sa ya fito ya tambaya waya kawo HALEEMATU SADEEYA Muhammad?.

Da sauri yah Abdulfata ya mike.

"Follow me."
Cewar likita.

Yah Abdulfata binshi yayi a baya har office din, Saida suka xauna sannan likita ya cire glass dinshi ya dube yah Abdulfata yace"congratulations sir your wife is pregnant."

Yah Abdulfata saboda tsananin murna har sijjada yayi na godema Allah.

Bayan wasu awwani likita ya sallame su tare da basu magunguna da xata dunga sha.

Yah Abdulfata godiya yayi sannan suka kama hanya.
A hanya yah Abdulfata sai tsokanan HALEEMATU yakeyi"Ahh princess kin kusa xama mother nikuma Father. "

Ita dai haleematu ba baka sai kunne.

Duk abinda ya gani a hanya naci saiya siya cewar shi kar abar mai Yaro/yarinya da yunwa a haka suka iso gida.

Haka suke Rayuwa cikin happy.

Duk wani aiki na gida yah Abdulfata ya hana HALEEMATU in yana gida shi yakeyi Hauwa'u na taya sh,da yake Hauwa'u ta dawo gidan da xama.
*BAYAN SATI BIYU*

Yau tunda HALEEMATU ta tashi gabanta keta faduwa ta rasa dalili.
Gaba daya hankali kowa ba'a kwance yake ba,sai addu'a sukeyi.

Wurin karfe daya wayan HALEEMATU ta fara ringing, Hauwa'u CE ta daga saboda HALEEMATU batada kuxarin dauka barinma dataga bakowar number.

Sallama Hauwa'u tayi.
A dayan bangaren naji wata muryan ta amsa sallama tareda cewa"Dan Allah da HALEEMATU Muhammad nake magana? "

Hauwa'u tace"Eh da ita kake magana wani abu ne?"

A dayan bangaren akace"Toh Dan Allah muna so mu ganki a kawo bustop akwai wata magana mai muhimmaci,inaso kixo da wani naki."
Hauwa'u ta amsa da"Toh ganinan xuwa."

HALEEMATU ta kalleta a sanyaye tace"Waye?"

Hauwa'u tace"Ba'a fadamin ba amma ance muje kawo bustop,bari mu kira yah Abdulfata mu fada mai."
Hauwa'u ta karasa maganan tana dialing number yah Abdulfata.

A bangaren yah Abdulfata shima ya kasa taboka komai baijin dadin jikin shi, yana cikin tunani yaji wayan shi na ringing dauka yayi Dan ganin Hauwa'u ke kiran shi.

"Yah Abdulfata yanxu aka kira mu a kawo bustop ana Neman HALEEMATU."
Cewar Hauwa'u kenan.

Yah Abdulfata yace"Waye?Kuma lafiya yake Neman ta."
Ya fada cikin damuwa.

Hauwa'u tace"Bansani ba wlhy."

Yah Abdulfata yace"OK Ku  jirani ganinan xuwa."
Ya katse wayan.

Wajan ogan shi ya dauki excuse sannan ya kama hanya xuwa gida.

Yana isa ya tadda Hauwa'u da HALEEMATU na jiran shi.

A hanya gaban HALEEMATU sai faduwa yakeyi sai kuma hawaye.

Haka suka isa wurin Hauwa'u na bata baki.

Hankalin HALEEMATU ne ya tashi ganin wajan ciki da Al Ummah.

Suna karasa HALEEMATU tayi arba da gawan...................

Saimun hadu a next page.

Dan~buxu😍😍😘
08064481429
For comments and correction.


M.Hassan ce mai kaunar ku❤
[3/11, 10:59] Lovely Sis: πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž
*HALEEMATU SADEEYA*
πŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’ŽπŸ’Ž


Written by
             Maryam Muhammad Hassan.


Page 56--60πŸ”šπŸ”š*Shafin nan gaba dayan shi sadaukar wa ne ga Baba Garba mahaifi na gari Allah yayima Rahma Allah ya ka huta Allah ya albarka yaran daka bari lallai yau mutuwar ka tadawo mana sabuwa Allah yayi ma rahma😭😭😭*

Ina Neman addu'a ga yayan mahaifi na.Suna karasowa  HALEEMATU tayi arba da gawan mahaifin ta kwance akan titi.
"INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN."
Abinda HALEEMATU ta fada kenan ta xube a wajan sumammiya.

Yah Abdulfata ma kawai na maxa yayi amma mutuwan ta ingixa shi sosai.

Hauwa'u ma tuni hawaye ya gama bata mata fuska tsayuwa ta gagareta.

Yah Abdulfata ya kira Mustapha ya fadamai inda suke.

Ba dadewa Mustapha ya karaso cikin tashin hankali Dan mutuwan ta in gixa shi shima.

Mustapha ya dauki gawan bayan yan sanda sunxo ya nufi gidan HALEEMATU da gawan.

Yah Abdulfata kuma  asibiti ya nufa da HALEEMATU emergency aka dauke ta.

Da kyar likituci suka samu numfashin HALEEMATU ya dawo dai dai amma bata farka ba.
Dakin Hutu aka tafi da hutu.

Ammih itama saida ta suma yadda taga mijinta.

Haleematu kwanan ta bakwai a asibiti sannan aka sallame ta.

Ammih kuma kullum cikin kuka take duk ta rame kaman ba Ammih ba.

Abokin marigayi ne yaxo bayan ya kara yimusu ta'axiyya sannan yace"kafin in fara yimuku bayani inaso kusani kowani mai tabbas mamaci ne Allah yasan munason Muhammad amma yafimu sonshi yanxu addu'a yake nema a wajan mu ba hawaye ba."
Ya karasa maganan yana kallon Ammih da HALEEMATU.

Ya nisa yace"A ranar  Monday daya gabata sha takwas ga watan September 2017,An samu hadarin mota a dai-dai gad'ar kawo anyi lodin xuwa rigacikum,har Allah ya dauki ran mutane uku a take kafin a kaisu asibiti toh Allah yayi mahaifin ki yana ciki yanxu addu'a Ku yake bukata kawai."

Ya karasa maganan yana hawaye.

A parlour ba abinda kakeji sai kukan Ammih da HALEEMATU.

Yah Abdulfata da kanwar Ammih keta basu baki.Haka Rayuwa ta juyawa HALEEMATU ba mahaifin kullum cikin yimasa addu'a takeyi.

Duk yadda yah Abdulfata yasu HALEEMATU ta dawo yadda take a baya amma abun ya gagara.

Ammih kusan kullum saitayi kukan rashin mijinta a haka har Mabaruka ta dawo gidan da xama.


*BAYAN WATA SHIDA*


Watan haihuwan HALEEMATU ya tsaya,
Kullum yan uwa cikin fargaba sukeyi.

Ammih tana ba HALEEMATU addu'oi da xata dunga sha.

Yah Abdulfata kam duk wani shiri na haihuwa ya gama rana kawai yake jira Allah ya kaimu.

*****
Yau HALEEMATU tunda ta tashi da ciwon Mara ta tashi amma sai daurewa takeyi.

Yah Abdulfata ne ya lura da yadda take yace"princess may ke damunki?"
Cewar yah Abdulfata cikin damuwa.

Haleematu daurewa tayi tace"Bakomai."

Yah Abdulfata ya kalleta yace"Baki taba min karya ba yau kar kiyi naga alaman bakida lfy kuma kina fadamin ba komai."

Murmushin karfin hali tayi sannan tace"Haba Prince yi hakuri banajin dadi ne."

Yah Abdulfata yace"Muje asibiti mana tun kafin ciwon yayi tsanani."

Ba musu HALEEMATU ta mike Dan dauko hijabi amma saidai ta kasa durkushe wa tayi wajan.

Hankali yah Abdulfata ne ya tashi ganin halin da HALEEMATU ke ciki.

Kwasawa yayi da gudu ya nufi dakin ta ya dauko mata hijabi ya dawo downstairs.

Ku tsaya wa baiyi ba ya dauke ta da gudu ya nufi parking space.
Da sauri mai gadi ya bude yah Abdulfata ya kwasa da gudu.

A hanya HALEEMATU tasha sannu yafi a kirga.
Kafin su isa ta galabaita.

Suna isa aka cemusu haihuwa ne,
Labour room aka shiga da ita.

Nan yah Abdulfata ya kira mommy ya shaida mata sannan ya kira Ammih.

Ba'afi minti arba'in ba saiga mommy da Hauwa'u.

Yah Abdulfata ya kasa tsaye ya kasa  tsaye ya kasa xaune sai zirga xirga yakeyi a kofan labour room.

Mommy ce ta bada Hauwa'u key din mota Dan taje gida dauko kayan amfani.


Alhamdullilah Allah ya sauke *HALEEMATU SADEEYA* cikin koshin lafiya ta samu santalelan yaronta Tubarkallah sak marigayi ba abinda ya bari wajan kakan sa.

Yah Abdulfata kam mouth har ear bakin shi ya kasa rufuwa Dan murna.

Aka kira Ammih da yan uwa aka sanar dasu.
Nan yan uwa suka cika asibiti amma banda Ammih saboda kunya.
Sai Mabaruka ta aika ta gano mata lafiyan jaririn da uwar jaririn.


Sai bayan la'asir aka sallame su.
Ba yadda mommy batayi ba akan HALEEMATU ta dawo gida amma yah Abdulfata yasama idonshi tuka yace ba Wanda ya isa ya tafi mai da mata.

Koda aka kira Ammih aka fada mata cewa tayi a kyaleshi xa'a samu mai kula da ita.


Haka gida ya cika Dan ganin baby.

Yah Abdulfata har hutu ya dauka a office Dan ya dunga kula da babyn shi.


Ranar suna ya xagayo,India akayi taro na gani na fada.
Yaro yaci sunan kakansa  Muhammad amma ana kiransa da Farhan.

*BAYAN KWANZA ARBA'IN*HALEEMATU da Farhan sunyi kyau sunyi kiba,da yake Farhan mai garin jiki ne.
Inka ganshi xakace yafi kwana arba'in.

Yau Saturday HALEEMATU, yah Abdulfata da Farhan na ganin cikin shirin su na fita.

Yah Abdulfata rike da Farhan ita kuma HALEEMATU ta dauko waya xatayi musu selfie,kai masha Allah sunyi kyau.

Gidan Ammih suka fara xuwa sannan gidan mommy.

Haka suka xagaya gidan yan uwa.

Ammih na son yaron saboda ba abinda ya bari na marigayi komai nashine.
*BAYAN WATA UKU*

Bikin Hauwa'u ya matso shirye shirye akeyi bana wasa ba.

Haleematu, mommy da Farhan su kaje Italy dan siyo mata daki dana kitchen.

Farhan ya kara girma yayi wayo yana Dan mikewa tsaye.


Yah Abdulfata suma shirye shirye sukeyi shine aminin ango kuma yayan amarya.

Itama Hauwa'u cewa tayi baxa'a nuna karya ba,walima kawai haleematu tayi organizing.


Dangin ango sun kawo akwatina dozen,sun samata kaya masu tsada da kyau masha Allah.
Yan uwa sai xuwa ganin akwati sukeyi.

Bayan an gama gani aka dauka aka kai gidan HALEEMATU.

Yau take daurin auren masoya wato *HAUWA'U USMAN*
                 DA
*AL-MUSTAPHA TAHEER*
Manyan mutane da dubban jama'a sun shaida daurin auren.

Sai fatan Allah ya basu xaman lfy.


Karfe biyu aka fara walima inda malama Sa'adatu musa tayi nasiha akan xamantakewar aure a wannan xamani.Karfe bakwai motan amarya taxo aka dauki amarya xuwa gidan ta dake unguwan rimi kusada na yah Abdulfata.
Gida dayane ya shiga tsakanin su.

Tsarowan gidan ba'a  fadi sai wanda yaje ya gani amma fa bai kai na yah Abdulfata ba.


*BAYAN SHEKARA BIYU*

HALEEMATU na ganin xaune da katon cikin ta tana magana"Prince wai ina Farhan yake tun daxu ban ganshi ba."

Yah Abdulfata yace"May be ya fita xuwa garden. "

HALEEMATU tace"muje nima inaso inyi exercise."

Yah Abdulfata ya taso ya hau shafa cikin yace"Princess kodai yan  biyu ne naga suna takuramin ke."
Ya fada magana cikin xolaya.


Duka HALEEMATU takai masa ya kauce yana dariya.

A garden suka sami Farhan yana wasa.

Yana ganin su ya taho da gudu"Oyoyo mami na."
Cikin maganan sa Wanda bata fitowa sosai.

Murmushi sukayi yah Abdulfata yace"yau munyi fada da mami boy. "

Farhan sakin HALEEMATU yayi ya nufi yah Abdulfata da sauri yana cewa"torry Dada."

Duk Kansu dariya suka shiga yimai irin yadda yayi magana shi a dole ya girma ya iya turanci.


Haka suke Rayuwa cikin jin dadi da annashuwa.

Hauwa'u ta haifi yarta budurwa kyakyawa mai suna Ummul khairi amma ana kiran ta ibteesam.


Haleematu ya haifi yarta itama kyakyawa sak yah Abdulfata kaman an tsaga kara.
Taci sunan mommy wato Bilkisu suna kiranta da banafsha.

Farhan ya girma yayi wayo harya shiga makaranta.

Mabaruka ma tayi aure da wani soja Aminu har Allah ya axurta su da diya mace mai suna farida.

A bangaren Ammih kuma ta karayin aure da Dan uwan mommy Alhaji Ibrahim matar shi Allah yayi mata rasuwa ya barshi da yarinya daya Khadija.


Family din Rayuwa sukeyi cikin happy da yarda juna.
*ALHAMDULLILAH*
Anan na kawo karshen wannan littafi mai suna  *HALEEMATU SADEEYA*
Kuskuren danayi Allah ya yafemin.

Sai mun hadu a sabon littafi na mai xuwa very soon.
*BILKISU(MAI GADON ZINARI.)*


Fans dina godiya nakeyi da support da kuke bani,da kuma kauna ta😍😘i love you more.


Jinjinar ban girma ga *HALEEMATU SADEEYA FANS*


GAISUWAR GIRMA GAREKU NA DABAN CE:
*Queen Ayusha ilias*
*MUM SAHAL*
*MUM MUAXXAM*
*MUM MUWADDA*
*Aysha Al Hassan*
*FATIMA MUHAMMAD UMMANCY*
*HALEEMA MUHAMMAD LEEMA*
GAISUWA TA GAREKU;
*HALEEMATU SADEEYA FANS😘*
*MARYAM (M) HASSAN NOVELS*
*MUSAN JUNAH O.H.W*
*QUEEN AYUSH ILIAS&HAWWA SALEH*
*MUM MUAXXAM FANS*
*Ummancy😘NOVELS*
*TIMES WRITERS*
*WRITERS ONLY*
*SURBAJO NOVELS*
*MUHAMMAD HASSAN FAMILY*
*NOVELS UPDATES*
*HAUSA NOVELS*DUK WANDA BAN AMBATA BA KUYI HAKURI KUMA RAINA,ANA MUGUN TARE.
I HEART YOU ALL.


*M.HASSAN CE MAI KAUNAR KU,MAI SON GANIN FARIN CIKIN KU A KODA YAUSHE.INA ALFAHARI DAKU MASOYANAπŸ’‹*
Dan ~buxu
08064481429
For comments and correction.

M.Hassan CE mai kaunar Ku❤

adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.

MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Be With Me Technology

Guide Tricks Blog

Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technology, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *