[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
*_My beloved onece, with the grace of GOD the owner of everything. Am back with a new writting true live story novel which is, SANADIN SOCIAL MEDIA i was been parmited by the person the story, all rights reserved. Nopart of this publication may be reproduced, distributed, or transmitted in any form or by any means, including photocopying, recording or other electronic or mechanical methods, without the prior written permission of the publisher, except in the case of brief quotations embodied in critical reviews and certain other noncommercial uses permitted by copyright law._*
25/06/2018
*Da sunan Allah mai rahma maijinƙai*
1.
Banda sautin kiɗa babu abinda yake tashi a gidan, ƙattin sifiku ne suke ta aman waƙoƙi na turanci su kaɗai babu mai basu haƙuri, dum dum dummm, haka sautin kiɗan yake fita sai kayi da gaske zakaji abinda ake faɗa a cikin waƙar dan kiɗan ma baya bari kaji!
Waƙoƙi ne babu adadi a ciki domin wannan tana ƙarewa wata ce zata shigo, ta baya baya ta fito daga cikin toilet!
Da wani ɗan tsangalallen towel a jikinta wanda baima san akwai guiwa a jikinta ba bare ma a saka ran zai kawo mata iya guiwa,
"""Gaban towel ɗin a buɗe yake ta riƙe shi da duka hannuwanta biyu wanda idan wani ya shiga ta gabanta babu abinda zai hana shi ganin duk wasu halittu na jikinta!
Rawarta take ci gaba dayi tana tahowa ta baya baya dan ida shigowa cikin ɗakin gaba ɗaya saidai tayi ɗan tsallenta ta yarfa kanta gefe, duk inda tayi da kanta haka gashin kanta yake yin tsalle ya koma wurin ya maƙale sakamakon jiƙa gashin kanta da tayi wurin wanka!
Kana ganinta dai tana cikin farin ciki, tsalle tayi tare da direwa saman gado ta haye, saida ta daka wani uban tsalle sannan tayi ƙundunbala ta miƙe tare da cewa wuhuuu wuuuu, sake miƙewa tayi tsaye taci gaba da rawa a saman gadon!
Ƙittt aka kashe waƙar dake tashi a cikin ɗakin, da sauri ta juyo dan ganin ko waye, a shagwaɓe ta sauko daga saman gado tana magana cikin sakata kana ganinta kaga sangartacciya!
Yiiiii momy ni kunna min abuna kawai kin wani kama kin kashemin abu, ta ƙarasa maganar tana shigewa cikin jikin mom,
Haba doughter na, hakan bai kyautu ba, kin tashi bacci babu sallah babu salati sai ki fara da kunna waƙe waƙe? Bazaki kiyi sallah ki godewa ubangiji daya baki aron lafiya da lumfashi ba? Yau wasu suna can sun tashi da baƙin ciki,
Domin yayin da kike farin ciki yayin wani yake cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, yayin da kike damuwa a lokacin wani yake cikin farin ciki, yanxun haka wani yana can kwance a gadon asibiti baya iya ci baya iya sha, numfashin kirki ma baya iyawa sai an taimaka masa da oxgyn,
""Kuma duk da a cikin yanayi da yake bai hanashi bautar Allah ba, amma ke Allah ya baki lafiya kinƙi ki gode masa sai sakarci da shashanci, ɗan gajeran tsaki tayi a daidai lokacin da take fita daga jikin momynta tana cewa suma marasa lafiyan sun samu sauƙi, a daidai lokacin data matsa ta kunna waƙarta taci gaba da rawa!
Da sauri momy ta sake kashe waƙar taci gaba da yiwa Rabi"a nasiha, turo baki tayi tare dayi ma momy wani irin kallo sannan tace idan kika sake kashe min waƙa kinja ma kanki yau ko abinci bazanci ba, niko nace kada Allah yasa kici ai cikinki ne,
Allah ya shirya momy ta faɗa tare da fita daga ɗakin taja ƙofar, ita kuma rabi"atu taci gaba da iya shegenta,
Saida tasha rawarta ta gaji sannan kuma ta sake nufa hanyar toilet tana mai ci gaba da rawarta, babu ko addu"a ta kusa kai ta shige cikin toilet ba tare data rufe ƙofar ba, da gudu ta isa ciki tana zuwa ta soke cikin kwamin wanka tana ci gaba da waƙe waƙenta,
Tana wanka tana waƙa, idan taji baitin da yayi mata daɗi kuma ta miƙe ta ɗan danse, ta daɗe tana iskancinta a toilet sannan ta fito da sauri, tana fitowa idonta ya sauka akan agogo, ɗan zaro ido tayi sosai sannan ta matsa jikin wadrof da sauri ta fara zaliƙo kayan da zata saka,
Murmushi tayi dan ganin kayan data ɗauko, ajiye kayan tayi a gefen gado danji wayarta na neman ɗauki, da sauri ta matsa inda ta'ajiye wayar ta ɗauka, ganin mai kiranta yasa ta shafa wayar cikin sauri tare da karata a kunnenta, gani nan zuwa haka kawai ta faɗa ba tare da ɗayan ɓangaren anyi magana ba ta kashe wayarta,
A gaggauce ta matsa jikin madubi ta fara shiri, cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala, turaruka ta shiga bulbulawa a jikinta babuji babu gani kamar a bata haƙuri,
Ajiyar zuciya tayi kamar wadda tayi wasan dambe sannan ta ajiye turaren, murmushi tayi a lokacin da hoton fuskarta ya bayyana a cikin madubi, tace uhum sisin mom, ta ƙarasa maganar tana kashe ido ɗaya,
Juyowa tayi kamar mai shirin fareti taje gaban gado, kayanta ta ɗauka ta fara sakawa, ƙananan kayane riga da wando, wanda sun matse ta sosai dan idan tayi ƙwaƙwƙwaran numfashi zasu iya yagewa, bayan ta gama sakawa ta tattara gashin kanta ta ɗaureshi tsakiyar kanta amma saida gashin kanta ya sauko saman gadon bayanta, jikin madubi ta matsa ta ƙara gyara fuskarta bayan ta gama ta ɗauki wayarta jakar da maƙullin motar ta babu ko ɗan kwali ko hula ko wani ƙaramin mayafi a kanta tayi gaba!
Cikin ƙwarƙwasa da ƙwalisa takeyin takonta har ta isa farlo, hy mom ta faɗa tare da ɗaga mata hannu a daidai lokacin da take ƙoƙarin fita daga cikin farlon,
Zo nan, zo zo zo, momy take faɗa babu ƙaƙƙwautawa, amma sai tace zauna ki jirani sai na dawo, da sauri momy ta tashi tabi bayanta tana kiran Rabi"atu bakyaji ina miki magana ne?
Dariya tayi tare da jice leɓonta na ƙasa tana mai ƙara sauri a cikin tafiyarta harta isa bakin get, ta fara kwalawa malam sani mai gadi kira, da gudu yazo ta gabanta, daka masa tsawa tayi tare da cewa ba nan nace kazo min ba zaka wani zo gabana kamin ƙiƙam kamar arne ya fito daga wanka ƙofa zaka buɗe min kabarni ina ta faman ɗaga murya na har na fara jin ciwon haƙarƙari ta ƙarasa maganar cikin yanayin gajiya!
A guje ya juya yaje buɗe mata ƙofa a daidai lokacin da ita kuma ta shige motar ta bata wuta bun bun bunn, a hankali ta fara tafiya, tana ƙoƙarin fita momy ta iso tana magana, dariya rabi"atu tayi sannan ta ɗauki wani irin dakeken gilashi ta danƙarashi a fuskarta, kallon mom tayi sannan tayi murmushi tana mai girgiza kanta alamar rawa tana mai bin waƙar data kunna cikin motar ta, ganin momy ta kusa zuwa kusa da ita yasa,
A hankali ta ɗage gilashin motarta taci gaba tafiya, kallo momy ta bita dashi dan tama rasa abin cewa, ita kuwa rabi"a, a guje tabar gidan wata "yar guntuwar ƙura tayi mata rakiya,
Innalillahi wa"inna ilaihir raji"un mom ta faɗa tare da gyara ɗaurin zaninta ta juya dan komawa cikin gida ranta a jagule kamar zatayi kuka dan baƙin ciki,
Ita kuwa hankalinta kwance gudunta take ta falfalawa a titi dan bata da lokacin kaucewa kowa idan dai ka ganta kaine zaka tsere dan bawa lafiyar jikinka kariya,
Bata zame ko ina ba sai a ƙofar gidansu ƙawarta Aisha, tana zuwa ta samu wuri tayi parking in motarta, baban Aisha ta gani dashi da wani abokinsa zaune suna fira,
A hankali ta buɗe moter ta fito tana mai gyara zaman ƙaton gilashin daya cinye rabin fuskarta dan girman sa, saida taje kusa da inda baban Aisha suke zaune shida abokinsa ta durƙusa har ƙasa ta gaishe su cikin girmamawa, gaba ɗayansu suka amsa cikin sakin fuska sannan ta miƙe tayi ciki,
Abokin baban Aisha ne ya kalli babansu Aisha yace ina kasan wannan arniyar mai ɗa"a da tarbiyya? Murmushi yayi sannan yace ba kafira bace musulma ce, 😳 musulma? Musulma da irin wannan shigar kamar ɗiyar arna? Murmushi baban Aisha yayi sannan yace kaidai bisu da addu"ar shiriy.............
"""Bai gama rufe bakinsa ba, Aisha da Rabi"atu suka fito, Aisha ko inda babanta yake bata kalla ba, ta nufi wurin moter rabi"a, kallo suka bisu dashi domin a ganinsu ma shigar da rabi"atu tayi yafi na Aisha mutunci domin ita Aisha tafi feƙewa idanuwanta sun gama buɗewa da bariki, dan Aisha barikakkace ajin farko, dan kanta yafi ƙwallon kwakwa fashewa idan an ƙwaɗashi da ƙasa,
Wata irin rigace a jikinta wanda ita da babu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, ga wani ɗan ɓingilin skert da ta saka kuma anyi mishi wani irin tsaga wanda idan ka duƙa zaka iya ganin kalar pant in data saka,
Kallo ɗaya zakayi wa Aisha kasan tatatciyar "yar bariki ce kuma ta gama gogewa da barikanci, fatar jikinnan tata kuwa tasha mai harta ƙoƙe, wani uban gammon attach ne akanta an nannaɗe mata gashin kanta kaf anyi mata kitso irin na "yan duniya, an wani sake kitson a baya har ga ɗuwawunta, nonuwunta kuwa sunsha powder wanda take ƙara musu girma sunyi ɓulu ɓulu dasu kamar zasu fasa riga su fito,
Daƙel take ɗaga idanuwanta ta kalli mutane saboda tsantsagwaron iskanci dake cikin ƙoƙon kanta, a haka suka buɗe moter suka shige, rabi"a taja suka bar ƙofar gidan...........
Suna fara tafiya Aisha tawani ɗan kishingiɗa kusa da rabi"a tare da nuna mata wayarta, da alama wani abu take nuna mata, murmushi sukayi a lokaci ɗaya yayin da rabi"a ta daki sitiyarin motarta da alama abunda ta gani ya mata daɗi,
Wani sakaran kallo Aisha tayiwa rabi"a tare da cewa aike wata dusar gero ce, hajiyata nace miki ki ajiye ƙauyanci mu shiga gari tare dake amma kin wani tsaya kina abu irin na ƙauyawan daji,!
Ke wallahi bari kiji ko a ƙauye yanzu kai a waye yake, ɗan taɓe bakinta tayi sannan taci gaba da cewa ke ko a ƙauyenma "yan tallar fura fura suma biyawa suke ana matse su dan kowa ya gane duniya gari ya waye, dan wayiwar gari bacci ya ƙare tashi kuma ba babba ba yaro,
Dan haka yarinya ki tashi ayi dake tun kafin duhun sallar kwanciya bacci ya riske ki, { isha"i } take nufi,
Ajiyar zuciya Rabi"a tayi tare da cewa ke nifa gaskiya tsoro nakeji nan da kika ganni, dan duk ƙananan kayan nan da na saka kece ma kika koyamin, shima gidanmu faɗa ake min inaga kuma na sako kaina harkar da kike nufi? A gaskiya inajin tsoron hayewa mazan zamani,
Dariya Aisha tayi tare da cewa kai amma kin zama banza da kikejin tsoron maza, ɗan gajaren murmushi tayi tare da sassauta muryarta tayi ƙasa sosai kamar tanayiwa Rabi"atu raɗa taci gaba da cewa aike banza ce, keda ya kamata maza suji tsoronki sai ki lalace wai kinajin tsoron maza? Mi garesu wanda yake firgita ki?
Murmushi rabi"a tayi tare dayin parking a gefen titi ta kalli Aisha tace wallahi maza basu da kunya kwata kwata, haka fa daga haɗuwata da wani shi gurinsa ma kawai yakai hannunsa ya taɓa min ƙirjina, ta faɗi maganar cikin jin kunyar Aisha, wani kallon "yan duniya Aisha tayi ma rabi"a sannan tace kinji banza daga gani? Gani fa ba ci ba? Kawai taɓawa zaiyi fa ya bar miki abuki, to miye a ciki?
Rabi"a tayi shiru, Aisha tace kai kedai wurin nan anyi dabbal arab, to bari kiji yarinya zamani ya riga daya canja, mazan yanzun gogaggin mata suke so, dan namiji ma yana zuwa wurinki yaga ke wata ƙullun koko ce ya gama dake dan babu mai san kidahumar mace, maza fa basa san banzayen mata, dan suna fara zuwa wurinki sukaga ke ruwan kogi ce saisu barki, a nan za'a barki ki jibgare dan baki shigo a cikin duniyar wayayyun mata ba!
Dan haka idanma kina gyarawa tun wuri ki gyara idan kuwa bazaki gyara ba lallai gab muke da raba jaha, ajiyeni gaba kaɗan dan zanga wani alhaji na, yau kam banda lokacin zuwa club domin ina da baƙo na musamman!
Ba tare da rabi"a tace komai ba taja mota ta fara tafiya, ita kuma Aisha taci gaba da cewa banda ma kike baƙauya ai maza alama ake musu idan ma basuyi niyar yin wani abu ba sai suyi, daga mutum ma ya ɗan nemi yakai hannunsa ga nononki sai shiga damuwa? Tou bari ma kiji yarinya ƙarewar wannan da aka miki, ni idan ma naga mutum baƙon abunne babu abinda ya dameni saima inyi masa wawan zama banajin komai, kinga kuwa mutum yana ganin talabijin kuwa aisai gyara zama yasha kallo,
Murmushi tayi tare da kallon rabi"atu tace ana gwada miki zuma kina hayewa iccen maɗaci, yauwa dakata nan zaki ajiyeni kije gida kiyi nazari mu haɗu a club gobe idan Allah ya kaimu sai anjima, ta faɗi maganar ne gaba ɗaya babu ƙwama babu filistof, ta buɗe motar tayi waje abun......
Kallo Rabi"a tabi Aisha dashi harta shige wani gida, ajiyar zuciya tayi tare da tattaro hankalin ta dawo dashi ga moter, jiki a sanyaye ta fara jan motar dan ita yau taso suje club dan aɗan rakashe amma da alama Aisha ta ɗauki zafi sosai, jiki babu ƙwari taja moter ta kama hanyar gidansu......................
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
26/06/2018
2.
Jiki babu ƙwari taja moter ta ta kama hanyar gidansu...................
Tuƙi takeyi cikin natsuwa amma bayan daƙiƙun lokutta kuma takanyi murmushi wanda ita kaɗai tasan dalilinta nayin haka!
Kallon kanta tayi sosai a madubin mota ta lumshe idanuwanta a hankali zuwa wani lokaci kuma ta buɗe su gaba ɗaya sharrrrrr!
Fuuuuu ta ƙara fizgar motarta sosai ta kama hanyar gidansu babu ɓata lokaci, bata wani ɗauki lokaci mai tsayi ba ta isa ƙofar gidansu!
Biyyyy ta ɗanne horn, malam sani yazo da gudunsa ya buɗe mata ƙofa ta sulala da hancin motarta cikin gidansu, wurin da aka tana da dan ajiye motoci itama taje ta jera ta ta........,
Bayan tayi farkin bata fito ba tana zaune a cikin moter, tana ƙididdege yawan motocin da suke a wurin taga kamar sun ƙara yawa,
Ɗan yatsina fuskarta tayi sannan ta buɗe motarta ta ziro ƙafarta ɗaya amma bata fito ba!
Daga ina kike? Haka taji an faɗa, ɗan taɓe baki tayi ba tare da tace komai ba, kuma bata kalli mai maganar ba, bakiji ina magana ko saina farfarasa miki baki? Ya sake maimatawa,
Ɗan suke bakinta tayi tare da ƙara sautin kiɗanta tana rawa da jikinta alamar waƙar da takeji tana shiga cikin jikinta sosai!
Tsoki yayi tare da fizgota daga cikin moter da ƙarfi har tana neman faɗuwa ƙasa, murmushi tayi data samu riƙe kanta bata kai ƙasa ba, har yanxun batayi magana ba sai ƙoƙarin komawa moter da tayi zamanta taci gaba da rawarta da kanta!
Ci gaba yayi da faɗa amma saita basar kamar bata san yanayi ba, wani irin halbi yakai da ƙafarsa murmushi rabi"a tayi tare da janye ƙafarta da sauri bai sameta ba, ɗan ƙaramin yaƙe tayi wanda ba duka haƙoranta suka bayyana ba sannan ta ɗaga duka girarenta taci gaba da rawa da kanta tana mai cije leɓonta na ƙasa ,
Ke ni kika ɗauka sakarai ko? Ina miki magana kin mayar dani wani shashasha ko? Hannunta tasa ta ɗauko wani choculet ta buɗe shi ta saka a bakinta sannan ta kashe waƙar dake tashi a cikin moter tace swry yaya me kake cewa? Ɗan taɓe bakinta tayi tana mai ci gaba da cewa ai kaine naga kazo da hauka shi yasa na barka, amma tunda ka nemi sulhu faɗa min cikin ladabi ina jinka,
Dun ƙule hannunsa yayi da niyar kai mata duka, da sauri ta riƙe hannunsa tare da fitowa daga cikin moter ta rufe har yanxun hannun yaya yana riƙe a hannunta, ɗaure fuska tayi ba alamar wasa a yanda ta nuna, cire gilashin idonta tayi sannan tace wannan shine na farko kuma ya zama na ƙarshe idan ka sake nuna min hannunka da sunan faɗa ko duka saina ƙaryashi, hmmmmm ta saki hannun da ƙarfi ta juya ta fara tafiya,
Saida tayi "yar tafiya sannan ta mayar da gilashin idonta tana mai ci gaba da waƙar data kashe daga cikin motarta , jahdu teyry nazarr, waƙar film in darr, kallo yaya Ahmad ya bita dashi yayi daskare a wurin kamar tulun daya lalace,
A gadarance ta shiga cikin farlon babu sallama kuma duk wanda yake a farlo batayi ma kowa magana ba ta wuce ciki abunta tana mai ci gaba da waƙarta, kowa ya bita da kallo amma an kasa mai cewa wani abu,
Tana shiga ɗakinta tarkace hannunta ta ajiye sannan ta nufi toilet dan watsa ma jikinta ruwa, bayan ta fito bata tsaya shafa mai ko wani abu ba, ta ɗauki wata "yar ɓingilar riga ta saka iyakarta guiwa, wayarta ta ɗauka ta kunna waƙa sannan ta saka earpies a kunnenta ta nufi farlo tana mai jin daɗi,
Kallo tabi kowa na farlon sannan ta wuce dirning area tana zuwa babu ɓata lokaci taja kujera ta zauna, abinci ta zuba taci harta gama batayi ma kowa magana ba, kuma batajin firarsu domin ta daɗe kunnenta da earpies,
Bayan ta gama ta miƙe ta fara tafiya, saida tazo kusa da mom tace saida safenku, ba tare dataji abinda sukace ba tayi gaba abunta, tana wucewa yaya Ahmad yace momy ki barni nayi ma yarinyar dukan rabani da yaro,
Murmushi Yaya Abdul yayi tare da cewa inajin akwai tsutsar dake mata yawo a kanta, Yaya fadeel yace babu wani tsutsa tsagwaron iskanci ne kawai amma ku bari nasan maganinta,
Itadai momy cewa tayi Allah ya shirya tare da miƙewa tabar farlo, su kuma nan suka zauna suna neman mafita akan rabi"atu, sun daɗe suna ƙullawa suna kwancewa daga baya kuma kowa ya tashi ya kama gabansa,
Da safe kuwa koda rabi"a ta tashi kamar dai yanda ta saba da wake waƙenta ta farka, haka ta ƙure volume duk inda kake a cikin gidan nan babu inda kiɗan nan baya kaiwa!
Wayarta ta ɗauka ta ƙira Aisha, babu wani ɓata lokaci Aisha ta ɗauka, gaisawa sukayi bayan gaisuwa Rabi"atu tace yau zamuje club ne? Shiru na wani lokaci sannan Aisha tace E amma wace shawara kika yanke?
Har yanzu banyi nazari akai ba, ta faɗa a taƙaice, Aisha tace ashe ko babu zuwa club, dan bazan iya tafiya dake ba a food flaks, ni kuma ina cikin flet, Rabi"atu tace tou aini ba abinci bace bare a sakani a food flaks, Aisha tace ai kuwa kema ce abinci kuma abinci da kowa yafi buƙata a duniya abincin a kuler yana rufe waye zai saka rai? Amma idan a buɗe yake kowa idan ya gani sai miyansa ya biya,
"Yan mata ya kika ce? Aisha ta tambaya! Cikin tsananin ɓacin rai da fushi Rabi"a tace dan taƙamar zamuje club dake shine sai kiyi tamin maganar banza da wofi? Idan kina zuwa muje idan bazakije ba an faɗa miki bansan hanya bane? Mtswwwwwwww tayi tare kashe wayarta,
Ajiyar zuciya Aisha tayi tare da cije leɓonta na ƙasa ta jinjina kanta alamar tana da banban aiki a gabanta, murmushin ƙeta tayi tare faɗa a bayyane cewa fushi ba naki bane Aisha, ƙanƙance idanuwanta tayi tare dayin murmushi da gefen bakinta sannan tabi wayar Rabi"a da kira,
Lokacin da ƙiran Aisha ya shigo a cikin wayar Rabi"a basarwa tayi kamar bata gani ba, haka Aisha taci gaba da ƙiranta amma babu ƙira ɗaya da Rabi"a ta ɗauka, daga baya ma da taga ƙiran yayi yawa sai ta kashe wayarta gaba ɗaya,
"""Lokacin da Aisha taji wayar Rabi"a a kashe hankalinta ya tashi, dan haka da sauri ta miƙe tsaye tana cewa shirin zaune yafi na tsaye bara in iskoki har gidan naku!,
A gaggauce taje tayi wanka, bayan ta fito gaban mudibi ta zame, anan tayi tsaye zuciyarta cike da mugunta ita kaɗai tasan abinda take kullawa, murmushi tayi sannan ta fara shafe shafe,
Bayan ta gama shafa, ta ɗauki wasu sheɗanun kaya ta saka riga da wando, wandon ya matse mata cinyoyi sosai, rigar ta kuwa shara shara har cibiyarta kana gani, ƙirjinta kuwa banda ta saka vra da babu abinda zai hana shima a ganshi, amma duk da haka zaka iya ganin abunda idanuwanka suka gani!
Warware atach in kanta tayi ta gyara ma kitson zama yanda take san ganinsa a kanta, ɗan juyi tayi tare da juyo ƙugunta ta ganshi a cikin mudubi, ƙara gara ƙijinta tayi sannan ta ɗan turo shi tayi wani iskanci, juyowa tayi tazo inda takalmanta suke ta ɗuka tana sakawa,
Wani irin tsini takalman suke dashi, danni kam gaskiya bana iya sakawa dan ina tsoron kada in faɗi, bayan ta gama saka takalmin ta ɗauki jakarta tayo waje, tana fitowa mamanta tace kai amma gaskiya kinyi kyau sosai Aishatu, ngd mama ta faɗa a daidai lokacin da take fita daga tsakar gidan,
Tafiya takeyi kamar mai tafiya saman wuta sai wannan irin yatsina takeyi kamar tanajin warin mutane, a haka harta isa bakin titi ta samu abun hawa ta faɗa masa inda zai kaita,
Ita kuwa Rabi"a bayan ta kashe wayarta toilet ta nufa, brush tayi tare da ɗaurayo fuskarta sannan ta fito da towel a hannunta tana goge fuskarta, a gefen gado ta yada towel in tayo farlo dan taji an fara mata flashing a cikin cikinta,
Babu kowa a farlon itama bata damu da hakan ba, tasan kuma yau monday dan haka mom ta tafi Office, zama tayi break babu ɓata lokaci ta gama, tana ƙoƙarin tashi a wurin Aisha ta shigo,.........
Kallo ɗaya Rabi"atu tayi mata ta ɗauke kanta, amma da yake Aisha "yar duniyace saita basar bata nuna damuwa ko wani abu ba, ta fara cewa, haba keko? Duka miyayi zafi? Daga magana sai fushi? Tuba nake ranki ya daɗe nasan ma nayi baban kuskure shine kika ga na taho da kaina dan neman afuwa a daidai lokacin data zube saman guiyawunta tana mai kama kunnuwanta alamar tuba,
Ita dai Rabi"a da yake ba mai yawan magana bace kuma bata san tayi magana mai yawa a wannan lokacin, dan haka saita nuna Aisha ta tashi kawai ya, bayan Aisha ta miƙe, Rabi"a tace ki kiyaye gaba dan bana san cece kuce! An gama gimbiyar mata,
Wucewa Rabi"a tayi ta nufi ciki, dan haka itama Aisha sai tabi bayanta, suna zuwa ɗaki Aisha dan neman shiga akamar kwaɗo yaga ruwa, ta fara ɗan gyagygyara ɗakin duk da ba wani datti yake dashi ba, kakkaɓe can goge can gyara can, ita kuma Rabi"a ta wani kashe saman gado kamar mai jego na jiran na aski ranar suna,
Bayan ta gama ta dawo kusa da Rabi"a ta zauna, zata fara wani maganganun banzarta Rabi"a ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hanni, babu ɓata lokaci Aisha ta gimtse bakinta, Rabi"a tace kije gidan zanzo, to baza muje club inba yau? Shiru tayi na wani lokaci sannan tace ummm kije kawai sai Allah ya kaimu gobe dan yau banji zan iya fita!
Murmushi Aisha tayi tare da miƙewa ta ɗauki jakarta tana mai cewa na barki lafiya Allah ya huci zuciyar manya! Kallo Rabi"a tabita dashi ita kuma tana ta kirara Rabi"a harta fita daga ɗakin amma Rabi"a batace komai ba!,
Haka Aisha ta fita tana maijin baƙin cikin rashin zuwan Rabi"a club dan taso suje su wulaƙance, amma babu damuwa da sannu haƙarta zata cimma ruwa, idan dai da rayuwa itama Rabi"atu zata koma KARUWA kamar ta, da sannu zata gogar da ita, dan bazai yuwu suna ƙawayen juna ba ita ta lalace ta zama ƙwartuwar ƙarfi da yaji amma ace ita Rabi"atu bata karuwanci, ƙaryane................... Ta faɗa da ƙarfi tare da dunƙule hannunta ta kaiwa bango duka, tana mai cewa,
Da sannu zan warware duk wata tarbiyyar ki, sannan kuma da sannu zan ganar dake ta hanyar nuna miki hotunan banza, da sannu zaki nemi maza ta hanyar jin maganganun ɓatsa, da kanki zaki kai kanki wurin maza, sanna kuma da kanki zaki basu abinda kike ɓoyewa,
Dariya Aisha tayi sosai tare da cewa yarinya zaki faɗo tarko......., tana faɗin haka tayi gaba abinta zuciyarta cike da farin cikin ta kusa samun mafita,,,,,
Yinin ranar Rabi"a bata je ko ina ba, tana gida kuma a ɗakinta kwanciyarta, waƙoƙi ne iri iri daga wannan ta ƙare wannan zata shigo,
Momy koda ta dawo daga office jin waƙoƙi ya tabbatar mata doughter tana nan bata je ko ina ba, wani farin ciki taji ya maƙalƙale mata zuciya, a ranta kuwa tana mai cewa doughter ta fara yin hankali, murmushi tayi tare da cewa ubangiji ya shirya minke,
Koda daddare bata fito cin abinci ba domin batajin yunwa, dan haka wanka tayi ta saka kayan bacci tayi kwanciyarta, ita kuma momy saida ta gama cin abincinta, sannan ta nufi ɗakin Rabi"a, ganin tana bacci yasa ta kashe socket dan waƙoƙin su dakata suma suji kunnuwansu,
Bayan ta kashe ne ta matsa kusa da Rabi"a ta kalleta na wani lokaci sannan ta fara motsa bakinta da alama addu"a takeyi, bayan ta gama ta tofa ta shafe mata jikinta, sannan taja bargo ta lulluɓeta tare da cewa kiyi bacci cikin natsuwa da yardar Allah,
Tana faɗin haka ta duƙa ta sunbaci goshinta { kiss } sannan ta fita daga ɗakin taja mata ƙofar, itama ɗakinta ta nufa dan shirin kwanciya bacci, saida ta gama abinda takeyi tsaf tana kwanciya ta jawo wayarta dan kiran mijinta suma suɗan shana,...
Yau kam tun asubar farko Rabi"atu ta tashi daga bacci sakamakon tayi baccin dare jiya da wuri, tana saukowa daga saman gado da sana"ar tata ta fara, innalillahi wa"inna ilaihir raji"un momy ta faɗa tare da ɗaga kanta ta kalli agogon dake maƙale jikin bangon ɗakinta taga duka duka 4:58am, a hankali momy ta sauko daga saman gado ta nufi toilet tayo alwallah,
Tana fitowa tayo waje dan zuwa ɗakin Rabi"atu, a farlo suka haɗu da Ahmad ya taho da zafinsa, ganin sa yasa momy ta koma ɗakinta dan gabatar da sallah asuba!,
A zuciye ya nufi ɗakin, ita kuma tana kwance cikin bargo tana jin nishaɗi dan waƙoƙi suna sakata farin ciki mai daɗi, shiru taji sauti ya daina tashi, dan haka ba tare data buɗe kanta daga cikin bargon ba, tace waye wanda ya gaji da duniya?......................
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMAN DEE*
27/06/2018
3.
Dan haka ba tare data buɗe kanta daga cikin bargon ba, tace waye wanda ya gaji da duniya?..................
Shiru Yaya Ahmad yayi ba tare daya bata amsa ba, jin anyi shiru yasa taci gaba da cewa ko waye nan bayaji ina magana? Idan fa na fito jiki zaiyi ma ko waye babu daɗi, maza maza kunnamin waƙana ka kama gabanka tun kana gane hanyar fita basai ka nemo ɗan jagora ba! Ta ƙarasa maganar cikin ɗaga murya mai amon harruffa babu adadi,
Murmushi yaya Ahmad yayi tare da gyara tsayuwanshi ya jingina jikinsa da bango ya rungume duka hannayensa a ƙirjinsa yana kallon inda take kwance,
Rabi'atu jin shirun tayi yawa yasa ta yage bargonta da sauri cikin ɓacin rai ta diro daga saman gadon gaba ɗayanta tayo kansa, har yanzun yana tsaye kamar yanda yayi tun a farko yana ma rabi'a wani irin kallon mai nuni da bata da hankali,
Wani irin kallo tayi masa mai nuni da zaka gane kurenka! Murmushi Yaya Ahmad yayi tare da gyara tsayuwarsa, yace kiji tsoron Allah ki gyara rayuwarki saboda mutuwa zata iya riskarki a duk lokacin da baki tunani, ajiyar zuciya yayi sannan yaci gaba da cewa!
Kiyi ƙoƙarin gyarawa, sannan kuma kiyi rayuwa mai kyau domin tsira ranar gobe ƙiyama, idan baki fita daga harkar dujalanci ba da shiga ta baɗala da kika koyawa kanki wanda wannan ba tarbiyyar gidan nan bane, sannan kuma a al'adance bai dace ba, idan kuwa akayi magana a addinance kinsan yin hakan haramun ne!
Allahu akbar! Haka rabi"atu ta faɗa tare da cewa yaushe ka zama malami ka fara wa'azi ban sani ba? Ai da nasan zaka zama mai wa'azi da faɗin gaskiya da bansha wahalar zuwa islamiya na sauke Al'qur'ani ba, da banbawa ƙwalwata wahala ba wurin koyo hadissai da kuma ɓata lokaci wurin sanin mai kyau ko kishiyarsa, Yaya duk abinda zaka faɗamin na riga dana sani,
Kai sai ƙwalwarka tayi tunani sannan zuciyarka ta yanke hukunci sai bakinka ya faɗa, niko ni naje na karanta na gani, kaje kayi abinda kake ganin shine mafita a gareni kaima kayi naka, murmushi yaya Ahmad yayi sannan ya juya dan fita daga ɗakin!
Ganin zai fita yasa Rabi"atu tace yawwa ji nan, tsayawa yayi ba tare daya juyo ba yace uhum! Taci gaba da cewa sai magana na gaba dana manta ban faɗa maka ba ahine ku soke lissafi na daga cikin "ya"yan nan gidan tunda ku kuna da kamun kai ni kuma banda shi, kowa ya fita daga harkata, ɗan gajeran tsaki tayi sannan tace sai kuyi ta sani yawan magana har kaina ma ya fara ciwo, ta ƙarasa maganar cikin sassanyar murya mai kama da zatayi kuka,
Murmushi Yaya Ahmad yayi ba tare daya ce komai ba yayi gaba, ita kuma ta kunna waƙar Aashiqui_2_tum_hi_ho_ft_arijit_singh, haka taci gaba da caskaɗewa abunda,
Momy bayan ta gama shirinta na tafiya Office ɗakin rabi"a taje, har a lokacin rabi"atu rawa takeyi, ko wahala ma bataji, murmushi momy tayi tare da cewa doughter zan wuce office, da hannu tayi mata alama da ta dawo lafiya!
Allah ya shirya momy ta faɗa tare da fita daga ɗakin ranta a jagwale dan ita kullum addu"arta bai wuce taga shiriyar rabi"atu ba, ga ilimin addini bare ta ƙira abun da jahilci, a bayyane tace ubangiji ya baki ikonyin amfani da iliminki domin gyara rayuwarki,
Zuciyar momy cike da tunani barkatai harta fito farfajiyar gidan, malam sani ne yazo ya gaisheta amma saita ɗaga masa hannu dan batajin zata iya magana a wannan lokaci, dan zuciya tayi mata ƙunci a haka ta shiga motarta ta ja amma hankalinta kwata kwata baya jikinta,
Ita kuwa Rabi"atu fitar momy ta wuce toilet tayo wanka, shiri ta shiga yi mai ɗaukar hankalin wanda ya ganta, ta wani ɗame, ta zuge ta dunƙule, ta caskaɗe san ranta, makullin motarta kawai ta ɗauka sai wayarta dan yau abun bamai jaka bane, haka ta fito tana wani irin tafiya mai ɗaukar hankali sai wani ƙwanbarewa takeyi kai ka rantse da Allah bata san wani abu ba waishi yaren hausa, bare kayi tunanin tana da Ezif 60 akanta gadai ilimin amma ba'a aiki dashi,!
Duka yayunta suna farlon dan haka tana hangosu ta haɗe rai danma kada su kawo mata raini ta fara rairo "yar guntuwar waƙar turanci yanda sautin waƙar yake fita yana nuni da duk nafi ƙarfinku!
Tana ƙoƙarin fita daga farlo gaba ɗayansu suka rufa mata, ɗam suka dawo da ita cikin farlon sukaci gaba da caskaɗata saida sukayi mata lullusar fitar hayyaci sannan suka jata zuwa ɗakinta, wurgata sukayi sannan suka rufe ƙofar ɗakin da makulli ta waje,
Ina Rabi"atu bata san inda kanta yake ba, nan suka barta a some, sannan suka koma farlo suka ci gaba da ƙullawa yanda zasu gyara mata rayuwarta, sun daɗe sannan daga baya kowa ya kama gabansa,
""Aisha kuwa jin Rabi"atu shiru bata zo ba yasa ta fara ƙiran wayarta, wayar Rabi"a kuwa tana hannun yaya Fadeel, shi kuma jin waya ta fara ringing yasa ya cirota daga aljihun wandonsa dan ganin mai ƙira, *FRIEND* ya gani dan shine sunan da Rabi"a ta faɗawa Aisha kenan a waya!
Haka wayar ta gaji da ihunta bai ɗauka ba, Aisha jin ba'a da niyar ɗaukar wayar yasa ta haƙura ta daina ƙira, amma tayi shiri dan zuwa wurin Rabi"atu dan ita a tunaninta Rabi bata daina fushi ba,
Haka tayi shirinta dan zuwa gidansu rabi"atu, koda Aisha tazo gidan haka su Yaya Abdul sukaci uwarta sosai tare da faɗa mata idan suka sake ganinta tare da "yar uwarsu sai sun lalata mata faɗa, Yaya Ahamd yace ke kallarni,
Cikin rashin jin daɗi ta juya ta kalli inda Yaya Ahmad yake zaune a saman but in moter, robar ruwansa ya ɗauka sannan ya diro yayo tattaki zuwa kusa da Aisha, banda tunƙwal tunƙwalƙwal babu abinda gabanta yakeyi,
Wani irin wulaƙantaccen kallo yayi mata wanda yasata saurin sauke kanta kasa, idan kika sake ɗauke idonki a kaina ban gama faɗar abinda zance ba zaki bar gidan nan cikin ɗimuwa! Jin maganar Ahmad yasa jikin Aisha ya fara ƙyarma dan tasan baida mutunci kona miyan bacci,
Dan haka ta ɗaga kanta a hankali ta kalli Ahmad tana mai zubar da hawaye dan tsoron kada ya wulaƙanta ta, watakan kece Friend ko? Kece kika shigo rayuwar ƙanwata dan ki gurɓata ta kamar naki rayuwan? Shiru Aisha tayi dan bata san abun cewa ba, hannunsa yakai daidai ƙugunsa yana ƙoƙarin ciro belt in da yake ɗaure a jikinsa,
Fadeel ne ya matso kusa dashi da sauri yace A, a yana mai riƙe hannunsa, yaci gaba da cewa barta taji da dakon najasar jikinta, keeeee ya faɗa yana mai kallon kwayar idonta, idan na sake ganinki a gidan nan saina ƙwaƙwule miki idanuwa babu tausayawa kama gabanki ballagaza,
Abdul daga inda yake tsaye yace yawwa tunda de ke "yar iskace to kiyi ma ƙafafuwanki gargaɗi idan na sake ganinsu a gidan nan saina gunɗule miki su, duk garin nan babu wanda baisan iskancinki ba, kin lalace kike a burinki wasu su lalace suma,
Yaya Ahmad yace fice a wurin nan dan kutumar ubanki, ya faɗi maganar cikin ɗaga murya sosai, da gudun bala"i Aisha ta fice daga gidan tana maijin baƙin cikin maganganun Abdul a zuciyarta, saida tayi tafiya sosai sannan ta tsaya a ƙofar wani gida ta goge hawayen idon ta sannan tace!
Tace Abdul nice "yar iska ko? Murmushi tayi tare da jinjina kanta, nice aka sanni a garin nan saboda iskanci na ko? Hmmm da sannu zan nuna maka ni dakakkar "yar iskace zan nuna maka ni "yar barikin cikin birni ce, saina lalata maka rayuwa kaima da sannu zan lalata ka, in kuma riƙeka gam a hannuna harsai ka dirkakamin ciki a ranar za"a gane ɗan iska tsakanin ni dakai, tsalle tayi tare da cewa dani dakai mun fara wasan!
Koda momy ta dawo daga Office taje ta taɓa ƙofar Rabi"atu taji a rufe kuma babu waƙoƙi haka ya tabbatar mata da bata nan, dan haka momy abinci taje taci sannan ta shige ɗaki dan ta kwaso gaji sosai tunda idan ta tafi office tun 06:30am bata dawo sai 06pm take dawowa gida!
Tunda Rabi"atu ta tafi duniyar suma bata farfaɗo ba sai 03:22am da kuka ta farfaɗo dan duk jikinta yayi mata tsami saboda su yaya ko ina suka doddoke daƙel ta tashi tana mai tsiyayar da hawayen wahala, a wahalce taja jikinta ta matsa jikin madubi,
Wani irin ihu tayi ganin yanda halittar fuskarta ta canja lokaci ɗaya, an wani murguɗe mata fuska an jirge mata baki ya koma gefe ɗaya, wani irin takaici ya kamata, cikin fushi ta nufo haryar fitowa amma tana taɓa ƙofa taji ta rufe rufff jin ƙofa a rufe yasa Rabi"atu tayi haƙuri tayi tsaye a wurin satata kamar macen data kada miji,
Ganin bata da mafita ta haƙura ta koma ta kwanta tana jiran safiya ta gama wayewa,...................
Koda safe data gama bacci har yanxun ƙofa a rufe take, agogo ta kalla 09:45am haka ya tabbatar mata da momy ta tafi aiki, dan haka bata wani ji damuwa ba ta kwantar da hankalinta ta shiga tayi wanka, saida ta gama wankanta cikin kwanciyar hankali sannan ta fara ƙoƙarin ganin ta zare glasis ɗin jikin window ɗin toilet,
Tana zarewa tana magana ƙasa ƙasa cewa wai kamarni nan za'a rufewa ƙofa dan anga banda maƙullin a hannuna ko? Hmmm tou yau ko za"a mutu gaba ɗayan gidan nan sai naje club mai sha'awar zuwa birnin lahira ya matso kusa dani duk wanda ya taɓani sai na turashi E zuwa duniyar mutuwa...........
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukar gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
29/06/2018
4.
Saida ta sauke glasis in jikin window toilet tsaff sannan tayi dariya ganin hanyar da zatabi ta wuce ta buɗe,
Jiki na kyarma tabi ta window ta fita, tana ganin ta fice a hankali ta dawo cikin toilet in cike da farin ciki tayi wani irin tsalle tare da dunƙule duka hannayenta tace yeccccccccch,
Da gudu ta fito daga toilet tana rawa tare da raira "yan guntuwar waƙa tanajin daɗi sosai a cikin ranta, tana fitowa jikinta har tsumi yake dan wannan farin cikin lallai ta danganawa ranta dole sai taji waƙa,
Dan haka ta kunna waƙar dake ɗauke a bakinta, tanayi tana rawa tare da tsantsarawa jikinta ado, bayan ta gama shafa ta ɗauki kayanta ta zuge kamar yanda ta saba ɗaukar ado!
Bayan ta gama ta ɗauki duk wani abinda tasan zata buƙata, stool ta ɗauka ta nufi toilet dashi,
Glasis in data kwanto daga jikin window ta jera su akai, sannan tabi ta window ta fice, tana fita ta samu wata kujera ta taka ta kaso glass in ta fara jerasu kamar yanda suke a farko,
Tana gamawa ta kama hanyar fita kanta tsaye takeyin tafiyarta ba tare da jin shakku tsoro ko fargaba,
Harta fita daga gidan babu wanda ta gani ko ya ganta dan bada moter ta fita ba, bata san inda makullin yake ba tun dukan da aka mata a safiyar jiya, babu waya ba makullin moter,
Tana fita napep ta tare sai gidansu Aisha, a ƙofar gidan taga mutane suna fitowa, bata wani ji damuwa ba ta nufi hanyar shiga gidan gadan gadan........
Da sallama ta shiga cikin gidan, Aisha dake daga cikin ɗaki taji sallama Rabi"atu ta fito da gudu tare da rungume ta, a hankali ta ɗago dan kallon idon rabi,a amma sai tayi tozali da fuskar Rabi"atu duk an kwamtseta
Haɗari kikayi? Ta faɗi maganar cikin nuna damuwa, murmushi rabi tayi tare da cewa miya faru naga gidanku mutane suna fita? Ta tambayeta ba tare data bata amsar tambayar da Aisha ta mata ba!
Murmushi Aisha tayi tare da cewa wai tsohon gidanmu ne aka ɗan gogeshi da moter, subahanallah Rabi"a ta faɗa cikin nuna damuwa da tashin hankali yana ina ta faɗa a ruɗe?
Aisha tace ummm tare dayin ɗan gajeran tsaki cewa tou yana can ɗaki aka ajiyeshi shima tsoho ya cika taurin rai ya buɗa kawai ya wani tsaya kwakwar tsiya ni banma ga bura'ubar dazai tsinta a duniyar nan ba danni dai wallahi kona samu kuɗina bazanyi wani wahala dashi ba nima takaina nakeyi in samu in tara kuɗin da za"asha lemo da shinkafa dan bazai yiwu ba in tara mutane wurin zaman gaisuwa ayi ta ɗirkaka musu tuwo kamar tumakai ba!
Da sauri Rabi"a ta zare glashin idonta tabi Aisha da wani irin wulaƙantaccen kallo mai nuni da kin halaka,
Ɗan taɓe baki Aisha tayi tare da ci gaba da cewa kinji wani iri ko? Ta ƙarasa maganar tana mai ɗagawa Rabi"a gira ɗaya, har yanzun Rabi"a, kallon Aisha takeyi kallon mai nuni da Aisha ta samu warwarewar tunani,
Aisha taci gaba da cewa ni babban baƙin cikina ma gidan nan sai yaci buhun siminti huɗu, to ko sayen yashi maginin ma cewa saidai a ajiyemin tifa ɗaya, ni banma san bokitin fenti ya tashi ba, kuma lallai gidan nan zai iya haɗiye bokati biyar a tunani na haka na ƙiyasta,
Muje na ganshi inji rabi,atu Aisha tace yana can ɗakin gaba danni haushi ma yake bani, ɗan gajeran murmushi rabi"a tayi sannan tayi gaba zuwa ɗakin da tsohon yake kwance
Da sallama ta shiga, tsohon yana kwance cikin mawuyacin hali dan haka baisan zuwa Rabi"atu ba bare ya ansa sallamarta, itace ta durƙusa a gabansa ta kama hannayensa duka biyun tare da cewa sannu baba, idan bango yayi magana to baba yace yawwa,
Tana nan durƙushe tana ƙara tausaya mishi taji muryan Aisha tana kiranta, dan haka ta tashi ta fito, Aisha tace muje fa kinga wuri yana ƙurewa! Rabi"atu tace haba ina kuma zamuje? Bayan baba baida lafiya?
Hannun Rabi"atu taja tare da cewa muje kinji manta dashi danshi tashi ta ƙare mudai mu maida hankali muyi abinda yake gabanmu, tana riƙe da hannu Rabi"atu tana janta kamar makauniya,
Haka ta jawota har suka fito waje, ina moterki? Ta tambayeta, banzo da moter ba ta faɗa mata a taƙaice, okey a hanzarce ta tare napep ta faɗa mishi inda zai kaisu babu ciniki suka ɗunguma suka burma kansu sai club.......
Aisha ta sallami mai napep suke shige ciki, babban wurine anyi mishi ado da fitilu masu ruwan blue da red glovs in juyawa sukeyi sai kuma su lumshe sannan su saki amma duk iya kwalailaitar ka bazaka iya gane mutumin da yake a kusa dakai ba,
Saidai idan mutum yayi magana ka ɗauki muryar sa, kiɗa yake tashi a wurin sosai, a gefe ɗaya kuma wurine da alama dai kayan malaƙuta ne aka ajiye babu abinda babu a wurin idan dai na harkar shana ko tamnawa yayin da wasu suke shan giya wasu lemo kowa dai abinda ransa yake muradi shi yake basa!
Rabi"a kuwa an samu yanda ake so dan jin sauti kiɗa takeyi har cikin babban birnin ruhunta, Aisha tana "yar rawarta dai irin wanda ma"abota zuwa club sukeyi tace ma Rabi"a kidai kula da kyau domin a wurin nan ba kowa yakeyin rawa da kansa ba kema zaki samu aboki dan haka kada fa ki yaba mana kinji ƙawata,
Murmushi Rabi"atu tayi ba tare da tacewa Aysha komai ba itama ta fara rawa kamar yanda taga kowa yanayi a wurin dan rawar club ba ɗaya bane da "yan rawar gaɗa ba,
A gidan su Rabi"a saida aka ƙira sallah insha'i sannan yaya Fadeel ya nufi ɗakin Rabi"a dan kai mata abinci, da sallama ya shiga ɗakin, amma yaga babu rabi"atu dan haka zama yayi a gefen gado a tunaninsa tana toilet,
Shiru shiru babu alamar Rabi"atu a cikin toilet dan yakai 55minitus amma babu alamar ta a toilet dan baiji motsin ruwa ba kuma baiji alamar dai kwata kwata tana nan!
Dan haka ya tashi ya nufi toilet babu Rabi"a faɗuwar gaba yaji dan haka ya shiga duddubawa da sauri ko ina ya duba a ɗakin babu ita, haka ya fita yaci gaba da dubawa amma babu alamarta ko ɓarɓashinta a gidan,
Ganin babu ita yasa ya kira Ahmad ya sheda mishi amma basu faɗawa momy ba dan tana ɗakinta tana hutawa,
Rabi"a kuwa tana club har 12:45am sai yanzun ta fara tunanin gida, gashi bata zo da moter ba, kuma ga dare yayi babu abin hawa, dan haka tace ma Aysha tasa akaita gida kafin a ankara bata nan ai bata masan dare yayi haka ba ita ina zata saka kanta saukinta ma ɗaya dady baya nan!
Aysha tace ke haba miye duk na tada hankali? Kibi sannu mana bara insa a kaiki, Rabi"atu tace tou, da ɗan sauri Aisha ta juya taje ta faɗawa wani jijjigegen ɗan duniya ya mayar da Rabi"atu gida,
Dan dama tunda suka zo yayi mata maganar Rabi"atu amma sai ta faɗa mishi cewa ita Rabi"a fa tsami ce dan ita bahagguwa ce, amma yace yaji ya gani zai ɗorata a hanya,
Haka ta mishi magana zai tafi da Rabi"a yace ta taho dan dama haka yake so yana ganin dama ce ta samu a gareshi gara yayi amfani da damar shi tun kafin ta suɓuce mishi, da sauri Aysha ta koma taje ta taho da Rabi"atu suna zuwa wurin moter, tace a sauka lafiya a daidai lokacin da take buɗewa rabi"atu gaban moter,
Rabi"a tace ba dake zamu tafi ba? Murmushi Aisha tayi tare da cewa mu muna nan kinsan 12 marecen kura ta ƙarasa maganar tana mai kashewa Rabi'atu ido ɗaya, taci gaba da cewa a sauka lafiya ƙawata a daidai lokacin data rufewa Rabi"a ƙofa ta zagaya wurin kamal cewa to ni na gama saita maka komai dan haka kai kuma kayi ƙoƙarin ganin kahau hanya daidai,
Dariya kamal yayi dan ya gane hausar Aisha, ita kuwa Rabi"atu bata gane karatun ba dan haka kamal yace kada ki damu kinsan doki ne ake nuna mishi hanya ya riƙe dan kana bin hanya dashi sau ɗaya sai ka bashi sirdi zai kaika inda kake so saidai idan wurin zuwa ka canja zaiyi ɗimuwa,
Amma ya kika lura da jaki? Yayi murmushi sannan yaci gaba da cewa yafa san hanya amma sai an haɗa da duka, ƙyaƙyaƙyaƙyaaaaaaa yayi dariyar mugunta tare da jan moter buuuuuuuu ya kwashi hanya...........
Suna tafiya a wurin Aysha ta sheƙe da dariya sosai tare da taɓa duka hannayenta, tace shege kamal wallahi saddajjen ɗan iska ne lallai yau yarinya ƙaryarki ta ƙare banza doluwa dake ina nema miki jin daɗi kina amma kina zuƙewa, ɗaga muryarta tayi sosai kamar kamal zaiji ta tace, kamahlllll............Asha shagali lafiya...............................
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Kulli nafsin za"ikatl maut......., innalillihi wa"inna ilaihir raji"un, ina miƙa saƙon ta'aziyyata a gareki NUSAIBAH UTHMAN, Allah ya jiƙan baba ubangiji yasa ya huta, Allah yakai rahma kabarinsa, ubangiji ya baku haƙurin rashin sa Allah ya albarkaci abinda ya bari, ubangiji ya jiƙan wanda suka rigamu gidan gaskiya, mu kuma Allah ya kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo*
*FATIMA MUHAMMED Allah ya raya baby yasa cikon addini ne, Allah ya baki lafiyar shayarwar dashi am3n*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
01/07/2018
5.
Kamahlllll...............Asha shagali lafiya..............
Da "yar rawarta ta juya tana takawa irin rawar "yan duniyar nan kamar kwarto ya samu matar matacce, haka taci gaba da iskancin rawarta harta koma cikin club ranta fayau kamar ta kashe kishiya!
Rabi"atu kuwa a gaban mota sai ciccira idanuwa takeyi kamar tayi sata a gaban sarki!
Kallo ɗaya kamal yayi mata ya ɗan gauda kansa domin shi ɗin jugunan ɗan bariki, kuma ya iya yiwa mace hajiji harsai ya kwaɗata ƙasa,
Ita kuwa abinka da ba saban ba sai irin kakkame jikinta takeyi kamar dai ɗan kauye ya shiga jirgi,
Hajiyata yadai? Duk kin wani kama ko ina kin tsutsuke sai kace zan wani ciccinyeki ya ƙarasa maganar yana mai matsawa kusa da fuskar Rabi"a yaɗan buɗe bakinsa,
Tsarrrr taji a jikinta duk tsikar jikinta ta mimmiƙe, murmushi yayi tare da ɗan ɗora harshensa a leɓonsa na ƙasa yaɗan riƙeshi da haƙoransa yana mai kashe mata ido ɗaya,
Murmushi rabi"atu tayi a ranta, amma a fuskarta murtuke take kamar hadarin tsakar dare, mayaudarin murmushi kamal yayi tare da miƙa hannunsa ya taɓo hannun rabi"a,
Ɗaga idonta tayi ta kalleshi cikin yanayin fushi amma sai ya basar cewa swry! Hannuta riƙe a hannunsa yaci gaba da driving ba tare da wanin su ya sake cewa komai ba har suka iso ƙofar gidansu,
"""Ajiyar zuciya kamal ya sauke mai bin ɓargon jikin wanda yaji, a kasalance ya kwantar da jikinsa a site in moter ya lafe kamar ƙadangare yahau bango mai manja, amma har zuwa wannan lokaci hannun rabu"atu yana a cikin nasa!
Ƙoƙarin buɗa motar rabi"atu ta farayi, amma sai taji ta a lock, kallon kamal tayi tare da cewa buɗemin mana, murmushi yayi mai sauti sannan yace duk wahalar nan da nasha nufikinki a haka zaki barni?
To na gode rabi"atu ta faɗa a taƙaice, murmushi kamal yayi sannan yace ai ba haka a keyin godiya ba, ɗaure fuska tayi sannan tace kowa na duniya yasan abinda kalmar na gode take nuf.....
Bata gama rufe bakinta ba taji kamal yaɗan rungumo ta jikinsa a daidai kunnenta yayi mata raɗa wanda bazan iya jiyo abinda yace mata ba, bayan ya ɗago ne ya kalli cikin kwayar idonta tare da sauke kwakwkwaran ajiyar zuciya wanda haka yayi sanadiyar mutuwar jikin rabi"a ji tayi kamar an zare mata lakkar jikinta,
Buɗe mata murfin motar yayi yana murmushi tare da cewa to ki huta gajiya kinji zuciyata ya ƙarasa magana yana mai dafa ƙirjinsa, jiki a sanyaye Rabi"atu ta fita ta fara tafiya cikin rashin ƙwarin jiki,
Murmushi kamal yayi ganin yanda Rabi"atu take tafiya, dariya yayi sosai tare dakai dukawa sitiyarin motarsa yabar ƙofar gidan zuciyarsa na masa saƙe saƙe sosai akan Rabi"atu dan ya lura ita lusara ce!
Jiki babu ƙwari Rabi"atu ta isa ƙofar gidansu, a gajiye takai hannunta ta taɓa ƙofar amma sai tajita rufe ruff, ƙara turawa tayi taji da gaske rufe take sosai, cikin tashin hankali ta ɗago da kanta ta kalli agogon dake ɗaure a tsintaiyar hannunta 3:02am,
Ɗan zaro ido tayi da sauri ta juya ta nufi ta bayan gidansu, daidai saitin BQ ɗin gidansu ta tsaya da akwai wani babbar kwata ne a wurin an giggita rodiner amma sunɗanyi wara wara dan haka cikin rawar jiki ta fara turniƙa kanta, ganin bazata wuce ba yasa ta ɗauko wani ƙaton dutsi ta fara duka summun buƙmun!
Sai 03:55am ta samu ta buɗe hanyar data iya wucewa, da sauri ta ajiye dutsen a can gefe sannan tabi ta wurin ta shige cikin gida, tana shiga wani samu wani katako ta rufe wurin ta danne da babban dutse,
Da gudu take wucewa ciki, har ta isa ta bayan toilet in ɗakinta, cikin rawar jiki ta fara zare glasis ɗin addu"arta ɗaya kada momy ta ganta a wannan daren yama zata faɗa mata? Daga ina zatace ta dawo? Duk wanda ya ganta a wannan lokacin lallai babu abinda zai hana baza ace mata "yar iska ba!
A haka tayi ta tunani harta gama zarewa, bayan ta gama da sauri tayi ƙundun bala cikin toilet ɗin, murmushi Yaya Ahmad yayi jin shigowar Rabi"atu a daidai lokacin daya ɗaga kansa ya kalli agogon dake maƙale a jikin bangon ɗakin 04:05am, jinjina kansa yayi alamar zata ci ubanta,
Tana shigowa ta maida glassan yanda suke, sannan ta cire kayan jikinta ta fara wanka, Yaya Ahmad yace lallai yariyar nan kinfa zo da rainin hankali,
Banjam banjam tayi wankanta tana gamawa ta ɗauki towel ta ɗaura ta nufo cikin ɗaki sannu da zuwa haka Yaya Ahmad ya faɗa, ɗan yatsina fuska Rabi"atu tayi tare da wucewa kamar bata ganshi ba,
Jikin wedrof ta tsaya, zuwa wani lokaci ta fiddo da kayan baccinta ta koma toilet ta saka sannan tazo ta baza towel in a jikin ƙofar toilet in ta ja ta rufe,
Tana ƙoƙarin hawa saman gado Yaya Ahmad ya sauko inda Rabi"atu take kwance ya kamo ƙafafuwan ta ya jawota ƙiyyyy hakan da yayi ne yayi sanadiyar faɗowarta ƙasa feff, wani irin ihu ta saki sakamakon buguwar da tayi sosai,
Innalillahi wa"inna ilaihir raji"un momy ta faɗa dan jiyo ihun rabi"atu da tayi a cikin bacci, kafin ta gama buɗe idonta taji kukan ya ƙaru sosai dan yafi na farko jin hakan da saurin ta, ta sauko daga saman gado tayo ɗakin dan ganin ko lafiya............................
Ihu take sosai dan tun tana ƙoƙarin rama duka wurin Yaya Ahmad har ƙarfinta ya ƙare saboda duka yake mata bana wasa ba ko ina na jikinta zane sa yake kuma shigar sauri yake ma fatar ta, dan kafin ta sosai wani wurin belt inshi ya sake shigewa wani sashen,
Momy tayi iya bakin ƙoƙarinta ta karɓi Rabi"atu amma ta kasa, dan haka a ruɗe ta fito tana cewa a kawo mata ɗauki Ahmad zaiyi kisan kai saboda shi zuciya yake dashi kuma bai iya ɓacin rai ba dan in yana cikin fushi saidai a mutu, wannan dalili yasa hankalin momy yafi jirgin sama tashi, dan dukanshi yana yi yana dirdira mata ne, cikin tashin hankali momy jikinta har kyarma yake take kiran sunan fadeel......................
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on*
*Wattpad @ meelatmusa*
*Instagram @ meelat_musa*
*Tafasar tukunya bata rage gefe, sai hali yayi daidai akanyi abota, in Allah yaƙi addu"ar biri sai ya mutu a gonar arne,*
*Gaisuwa a gareku HAƊIN KAI GROUP*
*HABIBA IDRIS* _{ Hubbeey }_
*REAL SMASHER*
*MAIMOUNATH O.G*
*HALIMATU SADIYA MUHAMMED* _{ Leema }_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
*Ubangiji ya ƙara haɗin kai da zaman lafiya Am3n*
*Ina miki sannu da jiki SURAYYAHMS Allah ya baki lafiya, ubangiji yasa kaffara ne!*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
04/07/2018
6.
Jikinta har kyarma yake take kiran sunan fadeel,
Daidai zata fita daga cikin farlon suka haɗu gaba ɗaya har karo suke kaiwa juna saboda babu wanda yasan da zuwan kowa!
Lafiya momy? Abdul ne ya tambayeta, cikin in ina bakin momy har ƙyarma yake tace Ah...Ah..Ahma....Ahmad ne zai kashe min ɗiya, gaba ɗayansu sukayi tsoki a lokaci ɗaya tare da sauke ajiyan zuciya suka ce momy mu mumma ɗauka wani abu ne suka faɗa a tare, juyawa sukayi suka bar wurin...,
Wannan wane irin iskanci ne haka? Ina faɗa muku Ahmad yana dukan doughter amma zaku kama gabanku? Saboda ba ɗiyarku bace ko? Ba tare da sun juyo ba sukace ai momy muma idan muka je ƙara mata zamuyi Allah ma yasa ta mutu kema ki huta da ciwon zuciya,
Ni kuke haɗa ma baki kuna bani amsa a tare ko? Babu wanda ya ƙara magana suka wuce abunsu, ganin basu da niyar zuwa yasa momy gyara ɗaurin zaninta tare da komawa ɗakin Rabi"atu cikin kiɗimammen tunani,
Shiko Ahmad riƙeshi momy takeyi amma sai kara kai zamiya yake ya tirje saitin haƙoran Rabi"atu saida yayi mata lullusar fitar hayaci dan bai samu natsuwa ba saida yaga Rabi"atu ta sulale ƙasa ta daina motsi sannan hankalinsa ya kwanta,
Gyara hannun rigarsa yayi sannan ya nufi toilet, alwalla yayo dan gabatar da sallah asubu tunda lokaci yayi, yana fitowa ko inda momy take bai kalla ba ya fice a ɗakin,
Momy durƙushewa tayi a wurin tana kuka tare da kamo Rabi"atu ta ɗorata saman jikinta ta riƙe daidai kanta ta riƙe tana kuka sosai har jijjiga jikinta takeyi saboda yawan kukan,
Ganin kukan baya fishsheta ta sauke Rabi"atu daga jikinta da sauri ta fita a ɗakin, a falor taga Ahmad zaune akan abin sallah ko kallon momy baiyi ba itama bata kalleshi ba saima haushin sa da takeji kamar tayi mishi duka tunda har yayi dukawa rabi"atu,
Tana shiga ɗakinta da sauri ya tashi ya nufi ɗakin Rabi"atu, ɗaukarta yayi yaje ya kaita can wani ɗaki ya ɓoyeta sannan ya dawo ya zauna a inda yake zaune a farko dan yasan buri momy ta kaita asibiti ne,
Bai daɗe da zama ba momy ta fito daga ɗakinta da alama itama saida tayi sallah ta canja kayan jikinta, da saurin ta, ta wuce shi ta nufi ɗakin Rabi"atu amma ga mamaki babu ita babu dalilinta,
Dubawa momy tayi ko ina babu ita, cikin rashin natsuwa tayo farlo tace Ahmad ina kuma ka kaita? Wake nan? Ya tambaya tace ban sani ba, ɗan taɓe baki Ahmad yayi ba tare daya ce komai ba, momy tace dan ubanka bakaji ina magana ba?
Ɗan ɗaga idonsa yayi ya kalli momy ba tare da yace mata umm umm ba, ganin zai raina mata hankali yasa cikin fushi momy ta ɗaga hannunta tayi ta kwararawa Ahmad mari tako ina ba tare data sassauta masa ba,
Saida tayi masa mari sosai sannan ta rufeshi da duka, saida ta gaji sannan takai masa harbi tare da cewa ina ka kaimin ɗiyata? Tayi maganar ne cikin kakkausar murya kamar zata faɗi ƙasa saboda ɓacin rai,
Murmushin ƙarfin hali Ahmad yayi tare da kallon momy baice ƙala ba, cikin hasala momy tace na rantse da Allah idan ka bari na sake magana zakaga yanda zanyi dakai a gidan nan,
Jin hayaniyar tayi yawa yasa su fadeel shigowa suna bawa momy haƙuri kuma a tare sukayi maganar cewa haba mom tun safe sai faɗa kikeyi wai miye yake faruwa a gid...........dakatar dasu tayi ta hanyar ɗaga musu hannu,
Ku barni idan ma mutuwa zanyi in mutu saboda duk a cikinku babu wanda yasan darajar "ya"ya zaku kamamin yarinya ku kasheta,,,,,,, da Abdul da Fadeel suka ce kashewa kuma momy? Suka faɗa a tare suna masu riƙe haɓarsu alamar mamaki,
Saida ta mari fadeel sannan tace Ey mutuwa dan uwarka, Allah ya baki haƙuri momy ya faɗa a taƙaice yana mai kallon Ahmad yace kai kuma bross daga hukunci sai kisa? Yayi maganar ne yana kashewa Ahmad ido ɗaya,
Hannunsa Abdul yaja cewa baka nan akayi muje ka barsu daga momy sai Ahmad murmushi sukayi wa juna sannan suka bar farlo, ina ka kaimin "ya? Har yanzun yaƙi magana kuma tasan halinsa bazaiyi ba, dan haka tace kada ka ajiyemin kanta da ƙafafuwanta,
Tana faɗin haka ta shige ciki zuciyarta na mata ƙuna, bata daɗe ba ta fito cikin shirinta na tafiya Office ko inda Ahmad yake bata sake kallo ba ta fice abinda,
Saida suka tabbatar momy ta tafi sannan suka haɗu a farlo dukansu suna dariya, Fadeel yace kawai sai momy tayi ta dukanka, babu wanda yayi ma magana a cikinsu amma yana kallonsu tare dayin ɗan gajeran murmushi da gefen bakinsa,
Abdul yace a ina ka ajiyeta yau kowa a gidan nan sai ya ƙare ƙarfinsa a kanta, jinjina kansa yayi alamar su barta, miƙewa yayi dan bacci ne bai fita a idon sa ba, ganin Ahmad ya tafi yasa suma suka bi bayansa!
A Office kuwa momy sai fyacewa takeyi tare da goge hawaye da tissue, Ƙawarta dake zaune da kusa da ita wanda tunda momy ta shigo Office tasan tana cikin damuwa,
Dan idan taga momy cikin damuwa tasan akan Rabi"atu ne, cikin tausayawa ta gyara zamanta tare da cewa kiyi haƙuri ki daina ajiye damuwa a ranki,
Saida momy ta ƙara goge hawayen idonta sannan tace duka yayi mata na zalinci, shashshekar kuka tayi sannan taci gaba da cewa nace su daina dukanta subita da addu"a, amma na lura su dukansu basu ƙi ta mutu ba, murmushi hajiya zaleefa tayi sannan tace...
Kiyi haƙuri baza ta mutu ba, kuma duk abinda sukeyi sunayi ne dan ganin sun ceto rayuwarta ne daga wani mawuyacin hali, dan ita yarinya ce dole saida kwatanci da nuniya, dan tana da ƙaranci shekaru zata ga duk abinda tayi shine daidai to dole sai ana taro ana nuna mata rashin fa"idar abun har ta gane halin da take harin zuwa ba mai kyau bane, duk abinda kika gani namiji yayi magana a kansa koya tsawata yasan ba abu bane mai kyau, am amma abinda nake so dake kiyi haƙuri kisa musu ido, ki barsu su hukanta ta daidai yanda suke ganin shine mafita ke kuma sai ki bita da addu"a,
Dan idan yaro yana wazgewa ba"a tarosa akwai matsala nuniya da kwatanci shine namu shiriya kuma daga Allah ne, kowa yana san nasa ya hukunta sa dan idan har Rabi"atu ta gyaru sai kinfi kowa farin ciki da jin daɗi a rayuwarki, idan ta lalace kuka naki ne, su basu da damuwa kuma maza ne ba mata ba, dan sai kiga idan ma sukayi aurensu basu harkarta dan yau duk duniya babu wanda yake san mutumin banza sai kai da Allah ya ƙaddara maka, dan haka ki cire hannunki a kanta ki barsu suyi mata hukunci tun kafin kowa ya kama gabansa,
Ajiyar zuciya momy tayi tare da furta innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, amma kinsan Ahmad shi idan yanayin duka sai yaji kamar zai matar da mutun, hajiya zaleefa tace Allah ya shirya mana zuri"a, momy tace am3n,
Haka hajiya zaleefa tayi ta bawa momy haƙuri akan ta rage san Rabi"atu a ranta kuma ta rage shagwaɓa ta, bawai ta daina kwata kwata ba, A, a, ta dai riƙayi tana tsare gida dan duk yanda kakeji da yaro bazai hana kayi hukunci akansa ba idan yayi abinda za"a tsawata masa,
Koda momy ta dawo daga Office bata bi takan su Abdul ba, kuma koda sukayi mata sannu da zuwa babu wanda tace yawwa duk ta basar dasu,
Sai 01:32am Ahmad ya tabbar kowa na gidan yayi bacci sannan ya nufi BQ babu wanda ya kawo a ransa a can ya ajiyeta, kofin koko ne a hannunsa ya huce kuma ma duk yayi tsami saboda tun safe ya bada aka samo mishi shi dan wannan hukuncin nasa ne shi ɗaya baya neman kowa ya shiga a ciki,
Saida ya tsaya jikin ƙofar sannan ya ciro mukullin daga cikin aljihun wandonsa ya buɗe ƙofar ɗakin ya shiga wayarsa ya ciro ya haska Rabi"atu zaune kanta ko kallabi babu gashin kan nan nata duk ta haukatashi kamar tayi ɗan ƙaramin hauka,
Fuskarta ta koma kamar an aro mata ita, gaba ɗaya dai ta koma kamar ba ita ba har yanzun kuka takeyi fuskarta kuma duk jini ne, wani ya bushe wani kuma ɗanyene dan akwai jini kwance a gefen bakinta,
Barka da sararawa a duniyar sama ya faɗa tare da shafa gefen sajensa, da sauri Rabi"atu ta miƙe tana neman bugeshi ta wuce, dan tun data farfaɗo take neman yanda zata fita amma ta kasa kuma BQ insu tayi nisa sosai da inda part insu yake kuma koma tayi kuka babu mai jinta kuma babu kowa a wurin...
Ina zakije? Ya faɗa fuskarsa a murtuke, cikin kuka tace ni yaya ka daina min wannan abun tunda nace ka fita a hanyata ka fita idan baka fita ba zakaga yanda zan maka,
Ɗan guntun murmushi yayi da gefen bakinsa tare da ajiye mata kofin kokon a gaban yace ga taimako daga wurina hannunsa a saman ƙirjinsa yana nuna kansa ya ƙarasa maganar tare da taɓe bakinsa ya ɗan jinjina kansa, sannan ya juya, da gudu ta biyo sa, da sauri ya juyo tare da ɗaga kafarsa ya halbata ta koma ciki tana kuka ya rufe ɗakin yayi fitowarsa,.......
Wani irin ihu Rabi"atu tayi tare da tafiya wurin kofin koko ta buɗe shi tunda ta buɗe shi wani irin tsami ya daki hancinta kamar zatayi amai,,,, ga wata fitanninyar yunwa da takeji ga duk jikinta ciwo yake mata ƙara kallon koko tayi daga tsaye sannan ta fashe da wani sabon kuka mai kama da ana fitar da aljannu a jikin bil'adama,.......
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on*
*Wattpad @ meelatmusa*
*Instagram @ meelat_musa*
*Idan angulu ta biya buƙata zabuwa ta tafi da zanenta! dan komai wayan Amarya sai ansha manta, wasu kuwa ganin baƙin hadari yasa su wanka da kashi domin shidai karambani tsalle ɗaya kake ya jefaka rijiya amma sai kayi dubu baka fita ba, dan duk wanda Allah ya bawa haƙuri yafi a zageshi shegun gari an iso kare yaga kura, da alkairi kishiya ta hau kura, gudu da waiwaiye shi yake jawo mugun zato........*
*Gaisuwata a gareku!*
*HASSAN ATK*
*YAYA HAYAT BABA ZUBAIRU* _{ Admin of Admins }_
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
06/07/2018
7.
Kuka mai kama da ana fitar da aljannu a jikin bil'adama,......
Wani irin wulaƙantaccen kallo Rabi"atu ta sakeyi ma kokon, ɗan gajeran murmushi tayi tare da yin magana a bayyane cewa wai kamar ni nan za"a bawa tsari? Tsari fa? Abinci dadbobi ta ƙarasa maganar da kakkausar murya,
Ɗan gajeran tsoki tayi tare dayin short da kofin koko cikin tsananin ɓacin rai, saida kofin kokon yayi sama sosai sannan ya dawo ƙasa feff, rumtse hannayenta tayi tare da ɗaga kanta sama ta cije bakinta sannan ta rumtse duka hannayenta jikinta har kyarma yake kamar an kada ɗan wasan dambe tace kayyyyyyyyyyyyy ta faɗa cikin ƙaraji tare da daka tsalle a saman kofin ya tar watse gaba ɗaya,
Bana shan koko bana sha, ni za"a bawa koko sai kace Akuya? Shashshekar kuka tayi sannan taci gaba da cewa Akuyar ma wandda bata da "yan ci, kuka sosai sannan taci gaba da cewa shikenan nima na zama Akuya tunda har an fara bani abincin dabbobi wayyo Allahna............
Haka Rabi"atu ta ɗora hannayenta duka biyun a ka taci gaba da kuka a cikin daren nan babu ji babu gani,
Shi kuwa Ahmad ɗakinsu ya nufa yayi kwanciyar sa hankalinsa kwance kamar ya hau jirgi mai ya ƙare,
Da safe dukansu suna zaune dirning suna break momy ta fito, da shirinta na tafi aiki, dukansu gaisheta sukayi amma babu wanda tayi ma magana tayi gaban abunta,
Abdul ne ya tashi da sauri yasha gabanta lokacin har tana ƙoƙarin fita daga cikin farlon,
Kama kunnuwan sa yayi alamar neman yafiya sannan ya fara cewa,
Kiyi haƙuri momy ki gafarce mu dukanmu baki ɗayanmu, ya ƙarasa maganar ya nuna inda sauran "yan uwansa suke zaune,
Kiyi mana afuwa fushinki barazana ne a rayuwarmu, ki yafe mana gaba ɗayanmu, nuna kansa yayi tare da ci gaba da cewa ni yau zan wuce insha Allah, ki manta fushin da kikeyi dani a zuciyarki,
***
Hajiya Fatima itace mahaifiyar su Rabu"atu kuma mata ɗaya a wurin mahaifin su wato Alhaji Sulaiman Muhammad,
Aurene na zumunchi aka masu dan ƙara yaɗa zaman lafiya a cikin ahalinsu,
Wanda wannan abu ya zamar musu kamar ibada, dan yarinya tana fara tasowa za"ace an bawa ɗan gidan wane ita,
Familynsu babban family ne daya tara manyan mutane wanda suka haɗa da "yan kasuwa da manyan ƙusoshi a cikin gwamnati dan kisan boko sunfi yawa a cikin familyn,
Duk wanda ya taso a al'adar su dole sai kayi auren zuminci a matarka ta farko sannan idan zaka ƙara aurenka sai kayi daga baya amma a dole "yar uwa zaka aura a farko,
Basa jira sai yarinya tana so ko bata so, sannan kuma basa jiran shi yaro yana so ko baya so, haka suka taso da wannan aƙida tun iyaye da kakanni,
Itama haka ta kasance ga momy wato momyn su Rabi"atu, dan ita har akayi aurenta da dady bata wani zance dashi amma tasan sa kasancewar sunayin taro na "yan uwa a duk ƙarshen shekara { family meeting, } taron da suke kira da na ƙarawa juna sani,
Haka aka wanke momy itama aka mata auren zuminci da ɗan yayan babanta, kuma tunda aka kawota a gidan mijinta tayi haƙuri tayi zamanta har itama Allah ya haɗa ta da nata zuri"ar,
Tana da yaranta huɗu, Abdul shine babba, sunan sa Abdulrahman, sai Ahmad, sannan fadeel wanda yaci sunan kakansu rabi"atu wato Muhammad amma suke kiransa da fadeel, sai shugabar gayya wato Rabi"atul Adawiyya!
Haka suka taso cikin kulawa da jin daɗi kuma haka iyayensu wato momy da dady sukayi tsaye wurin bawa yaransu tarbiyya, kuma suka gina su da ilimin addini dana zamani, dan duk a cikinsu kowa yana haddar Al'Qur'an a cikin kansa,
Dan haka kuma duka yaransu sun tashi a cikin tarbiyya da nutsuwa
itama haka Rabi"atu ta taso cikin tarbiyyya da natsuwa, dan ita ma irin mutanen nan ne wanda basa san yawan surutu tare kuma da ƙyanƙyamin ƙawaye dan ita ba ko wace bolar ƙawa take abota da ita ba,
Rabi"atu ta haɗu da Aisha ne tun a primary sch, Aisha irin ƙawayen nan ne masu shegen shishshigin tsiya, ga ƙwaƙwa wanda ana yarfar dasu suna liƙewa kuma basa jin kora kamar ƙuda ya kama bangon sukari,
Dan gidansu basu da wani ƙarfi itama makarantar kuɗin da taje yayan mamanta ne ya sakata da yake a wurinsa ta tashi, tunda shima yaransa makarantar kuɗi suke karatu,
Ganin Aisha ta samu warwarewar tarbiya yasa ya tattarata ya mayar da ita wurin uwarta dan idan tayi abu ya hukunta ta sai ace yayi zalinci tunda ba ɗiyarsa bace,
Shigarta jikin Rabi"atu yasa tayi nasara wurin tarwatsewar tarbiyarta kamar yanda taga ta koma, haka tayi ƙoƙari ta mayar da Rabi"atu, kuma Aisha tayi nasara wurin ganin duk ta rugeje ginin da iyayen Rabi"atu sukayi mata na tarbiyya tun tana ƙarama haka Aisha tayi yaƙi sosai ta ɓatawa Rabi"atu hali,
Amma Allah bai bata damar koya mata irin harkarta ba ta banza wato zinace zinace, amma duk wannan hali najin waƙe waƙe raina kowa yawon zuwa club saka ƙana nan kaya duk itace munafika ta ɓatawa ɗiyar mutane tarbiya lokaci ɗaya,
Momy tana aiki banki ne, dady kuma contractor, Yaya Abdul Business man, yana zaune a cairo, Ahmad doctor ne yana zama a saudiyya a can yake aikinsa, sai fadeel yana jordan shima banker ne shine ya gado maman sa,
Allah ya kawo su duk suka haɗu a lokaci ɗaya, suka ga "yar uwarsu ta canja hali wannan dalilin yasa suke ƙoƙarin gyarata kafin kowa ya koma,
***
Momy kinyi shiru Abdul yake mata magana, tsoki tayi tare da ƙoƙarin bi ta gefen sa zata fice abinta, don girman Allah momy kiyi haƙuri kada na tafi kina fushi dani,
Cikin faɗa tace ai dama da kuka zo banyi farin ciki da zuwanku ba dukanku, ta nunasu da ɗan yatsa wanda ake nuni dashi, sannan taci gaba da cewa dan tunda kuka zo a gidan nan nake cikin ɓacin rai, nake cikin kunci, tunda kuka zo kuka kora farin ciki waje kuka saka yarinya cikin kunci da damuwa ku haka nayi muku ne? Kun kama yarinya kun takura mata a cikinku akwai ubanda ya haifar min itane? Ko kunfi ni santa ne? Ko kunfi ni so ta zama ta gari ne?
Dan haka idan kun sani ku sani, idan baku sani ba a yau zaku sani, idan ma kun sani ku ƙara sani,duk nafi santa akanku, kuma kowa haka yayi rayuwarsa cikin jin daɗi ban takura masa ba, miye aibu dan yarinya ta saka irin kayan da take so? Miye aibu dan tana fita taje wurin da tasan zatayi nishaɗi? Uban waye bayajin waƙoƙi a cikin ku?
Saboda haka dole dole yarinyata tayi abinda ranta yake so, tunda duka da takura bazai sa ta shiryu ba, dan da duka yana sa mutum ya zama na kirki da duk wanda ya fito daga gidan yari to lallai daya zama limamin masallanci unguwarsu,
Sa ido ai baiyi ba, kawai aje a sakawa yarinya ciwon zuciya? Shi yasa bature duk abinda ɗansa zaiyi yake barinsa yayi abunsa amma an wani taso kowa Rabi"atu kaza kaza kaza,......... To kuje kuyi hukunci naku wannan tawa ce a barni in hukunta abata dakaina tunda ni kaɗai na haifota ba wani ya tayani ba,
Tana faɗin haka tayi gaba abunta, Abdul yabi bayanta yana ci gaba da cewa momy kada kiyi koyi da yahudawa sufa halakakki ne, a zuciye ta juyo cewa dan uwarka inda kake ƙoƙarin ka koma ai nice na nunawa ubanka ya barka ka zama bayahuden harni zaka gayawa kar na biyewa yahudawa? 😠
Wa"azin da kake nema kamin nice na dage kai da ƙafafuwa nake ɗaukarku a motar da sanyi da zafi da ruwa nakai ku makarantar, tunda shi dadyn naku idan ya tafi sai ya daɗe bai dawo ba, yauni har zaka faɗawa Allah yace Annabi yace? Tou idan ka sake shiga hanyata tunda na fita naku saina bi takanka da motar na wuce idiot mtswww.........
Tana faɗin haka tayi gaba abunta, dole Abdul yayi haƙuri yana kallo har momy tabar gidan, da sauri ya dawo ciki har yanzun Ahmad yana zaune a dirning yana shashshafa wayarsa,
Kai ka fito mata da ɗiyarta tun kafin rayuka sufi haka ɓaci, Abdul ne yake ma Ahmad magana, amma ko inda yake Ahmad bai kalla ba,
Bakaji ina maka magana ne? Yayi maganar cikin ɗaga murya da harzaƙa, Ahmad yayi mishi shiru, idan na sake magana saina fashe maka baki, amma idan bango yayi magana Ahmad yayi wa Abdul magana.......
Ƙwalar rigarsa ya kama tare da cewa kai har ka isa ina maka magana kamin banza? Wani irin kallo Ahmad yayi masa tare da cewa sakeni, bazan saki ba sai kaci uwani sannan zan saki,
Ni bazan zage ka ba, amma ina maka gargaɗi da ka sakarmin wuyana tun kafin iyi fushi, kayi uwar fushi idan ka tashi, fiddo mata da ɗiyarta tunda ba kaine ka haifar mata ba dan baza ka jamin ta haɗa dani ba, zanyi tafiya in tafi tana fushi dani,
Kaine Ahmad ko nine? Nine nayi duka kuma nake hukunci dan haka babu abinda ya dameka sakarmin wuyana idan ta dawo zan faɗa mata nine nake hukunci kayi tafiyarka abinka, bazan tafi ba saika fito da ita,
Kai,,,,,, ji nan sakarmin wuya kafin raina ya ɓaci, marinsa Abdul yayi tare da ja masa hanci cewa na ɓata ran ya ƙara kai masa mari yana cewa da hypor zaka wanke sa ko da klin...............
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on*
*Wattpad @ meelatmusa*
*Instagram @ meelat_musa*
*Idan lokaci ya iske man shanu ko an a zashi a wuta baya ƙamshi,* 😊
*Asma"u Zayyana, { Asmee } ina gaisuwa ta musamman a gareki, domin keɗin ta dabance a cikin babban birni zuciyata*
*Asan mutum asan cinikin sa inya bari a san ya fasa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
08/07/2018
8.
Da hypo zaka wanke ran naka koda klin? Abdul ya sake tambayar Ahmad, na dai faɗa maka, ka dai daina dukana dan haƙuri na gab yake da ƙarewa, Ahmad ya faɗa, ya mutu ma dan uban haƙuri, inji Abdul,
A daidai lokacin daya sake kai masa duka a hanci, Ahmad bai gama jin zafi ba Abdul ya sake sokewa da hannunsa a saman bakinsa,
Lafiyayyen duka ɗaya yai masa bakinsa ya fashe, da sauri Ahmad yakai hannun sa daidai inda yake jin zafi ya shafa,
Jini ya gani a lokacin daya dawo da hannun nasa dan gani lemar daya taɓo a gefen bakin sa,
Kai kai kaiii, ni ka fasawa baki? Yayi tambayar ne cikin nuna tsananin ɓacin ransa, ganin Abdul baiyi magana ba yasa shi sake cewa, nace ni ka fasawa baki na?
Dunƙule hannunsa yayi tare da kaiwa Abdul duka cewa nine ka fasawa baki,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,??????,,,, cikin fushi, dukan da Ahmad ya kaiwa Abdul yasa suka cakume faɗa babu ji babu gani, faɗa sukeyi kowa yana cakuwa kuma kowa yana dakuwa daidai irin dukan daya haɗeye,
Amma idan Ahmad yakai nasa dukan yana tambaya wa Abdul nine ka daka harka fitar wa da jini? Fadeel yayi ya raba faɗa amma abu ya faskara, dan shi faɗan Ahmad baya rabuwa saidai idan bai fara ba,
Haka suka ɗauki lokaci mai tsawo suna caskaɗewa dan tun Abdul yana faɗa yanajin daɗin dukan da yakewa Ahmad har ya fara gajiya dan yaga Ahmad ɗin yaƙi yayi laushi dan gani yakeyi kamar anayi masa wahayin ƙarfi ne a duk bayan daƙiƙa ɗaya,
Ganin abun nasu bamai ƙarewa bane fadeel ya fara kiran wayan momy, su kuwa sai canja wurin dambe sukeyi kamar "yan dambe,
Momy lokacin data ga wayan fadeel ƙin ɗauka tayi, ya ƙirata babu adadi amma bata ɗauka ba, ganin taƙi ɗauka yasa shi tura mata saƙo cewa, ana faɗa Yaya Abdul da Yaya Ahmad,
_So kashe kansu_
Shine amsar da momy ta bawa fadeel, kuka fadeel ya farayi tare da nufa inda suke kaiwa juna duka, cikin kuka yace Yaya Abdul don Allah kai kayi haƙuri tunda kaine babba ya ƙarasa maganar yana mai kai hannunsa jikinsa dan ƙoƙarin rabasu,
Cikin muryar wanda yasha dambe ya gaji yace barsa fadeel bara na koyawa yaron nan hankali, murmushi Ahmad yayi tare da cewa kai fadeel matsa a wurin nan kada in ɓata maka jiki da jini,
Fadeel ganin Ahmad yayi magana yasa ya matsa kusa dashi yace don Allah yaya kayi haƙuri kaima don Allah ku daina, koni da Rabi"atu yanxun bama wannan abun saiku manya,
Sai yanzun Ahmad ya tuna ma bai kai mata kalacin safe ba, dan haka ya yarfe Abdul daga jikinsa cewa zaka sake shigo harkata,
Cikin shashshekar gajiya Abdul yace Allah dai ya rufa maka asiri an bani haƙuri wallahi yau da sai kayi jinya banza sakarai, Ahmad bai sake magana ba ya fice daga cikin farlon,
Shima Abdul fita yayi ya wuce dan fara shiri saboda yayi alƙawari zai tafiyarsa shi gidanma ya bashi haushi gaba ɗaya dan yayi alƙawari da zuciyarsa idan ya tafi bazai dawo ba sai yayi shekaru masu yawa kafin ya dawo!
Ahmad saida yayi wanka sannan ya koma kicin ya ɗafa indimie, ya ɗauka nufi BQ dan kaiwa Rabi"atu abinci,
Da sallama ya shiga cikin ɗakin sannan ya mayar da ƙofar ya rufe, a gabanta ya ɗuka ya ajiye plet in indomie sannan ya ɗago jin gina yayi da bango ya rungume hannayensa a ƙirjinsa yabi ɗakin da kallo inda ta watsa kofin kokon ya kalla sannan ya jinjina kansa!,
A gadarance yayi magana cewa ashema kina da sauran abinda zaki ci na kawo miki wani? A daidai lokacin daya duka zai ɗauki plet in, cikin shashshekar kuka tace nifa banda wani komai tun jiya nakejin yunwa banci abinci ba yunwa ta hanani bacci, ta ƙarasa maganar tare da sakin kuka mai ƙarfi,
Daukar plet in yayi ya riƙe a hannunsa sannan yace ƙarya ne, da yunwa ya hanaki bacci ai da baki zubar da kokon nan ba, dan haka sai kin kinbi duk inda kika zubar da kokon nan duka kin lashe min shi sannan ni kuma zan baki indomie kici,
Cikin kuka tace Yaya ai bansan a lokacin zanji yunwa ba, O dama kana zubar da abinda baka so ne a bola? A, a, Yaya ba haka ba, ni bana shan koko ne, idan bakya so kuma waye yace zubarwa akeyi? Ai banda wanda zan bawa kuma nima banda wanda zanci, ai da sai kiyi haƙuri kawai kisha dan ba daɗi gidan naƙoshi ta kwana,
Juyawa yayi tare da ci gaba da cewa wannan kokon da kika zubar zai kaiki har wayewar wata safiyar, da haka nake cewa mu kwana lafiya, yana faɗin haka yayi gaba abunsa da indomie n sa, jin yana rufe ƙofar da makulli ya tabbatarwa Rabi"atu tafiyarsa zaiyi bata gama tunaninta ba taji ya fice,
Wayyo Yaya don Allah ka dawo wallahi mutuwa zanyi zanfa iya mutuwa a ko wane lokaci saboda yunwa,,,,,, durƙushewa tayi a ƙasa tana ci gaba da kuka mai ƙarfi,
Ahmad kuwa kicin ya koma ya ajiye indomien sannan ya koma bakin get a saman bayan motar sa ya zauna yana waya sai wani ɗaɗɗaga hanci yake yana shaƙar iska yana basarwa, bai daɗe da zama ba Abdul ya fito da shirin sa, fadeel yana biye bayansa da wata "yar ƙaramar jaka,
Ahmad taso ni zan wuce, tou pha Yaya wucewa da wuri haka? Baza ka bari sai dady ya dawo ba? Cikin satin nan zai dawo kayi haƙuri mana, dafa Ahmad Abdul yayi sannan yace A, a, ɗan gajeran murmushi Abdul yayi tare da ɗan kaiwa Ahmad duka ɗan kaɗan a ƙafaɗarsa, ba tare daya sake cewa komai ba ya juya ya nufi wurin motar sa!
Binsa baya Ahmad yayi amma baice komai ba, suna tsaye a wurin har driver yaja suka wuce a wurin kowa yana ɗagawa juna hannu ,
Fadeel ne ya fara wuce yana kuka, dan idan suka rabu da juna sukan ɗauki sheƙaru kafin su sake haɗuwa, ɗan gajeran tsaki Ahmad yayi tare da cewa shasha ka fara wannan koke koken banza harsai ka ɓatamin rai jaki kawai mtsww,
Fadeel wucewa yayi abunsa ba tare da yace ma Ahmad umm umm ba, koda momy ta dawo ta samu labarin tafiyan Abdul itama dai taji wani iri dan haka taji gidan duk ya mata wani haggunce,
A ɓangaren Rabi"a kuwa tasha kukanta har ta godewa Allah, kuma tayi alƙawarin idan har Ahmad yazo buɗeta gobe saita cicci ubansa ta fice,
Miƙewa tayi ta leƙa ta window ganin duhu sosai ya tabbatar mata an tafi salasu nan dare, ajiyar zuciya tayi jiki a saɓule ta dawo ta a kwanta ƙasa kamar an shanya garin kwakwaki,
Ƙurawa silin ɗin ɗakin ido tayi tare da fara ayyanowa da bata kasance a tsare ba da yanxun tana can tana hidimomin, dan haka tunaninta ya fara!
Culub cike yake da mutane, yayin da masu shawuwa suke ƙwalewa abunsu, a gafe kuma ga "yan mata da maza suna ɗan murjewa abunsu, a gefe kuma ga kiɗa yana tashi da waƙar da tafi ƙauna a duniya, ita kuma gata nan ta shigo cikin club ɗin ta matse da ƙananan kayanta tayi kyau ga gashin nan nata ta gyare shi, Aisha ta taho da gudu ta tareta tare dace haba friend ina kika shige kwana biyu? Kuma kona kiraki a waya ma a kashe,
Ya kika koma gida ranar nan da fatan dai ba"a miki faɗa ba, murmushi tayi tare da cewa uhum babu wani komai, ina kamal? Aisha tace kamal lafiya qalau, amma miye yaji miki ciwo a fuskarki? Tana ƙoƙarin kai hannunta ta taɓa ciwon,
Wai Allahna kada ki taɓamin, Rabi"atu ta faɗa a firgice tare da dawowa daga sakaran tunanin data tafi, hannunta takai ta taɓa inda ta tabbatar akwai ciwo a fuskarta, ɗan gajeran murmushi tayi a bayyane tace lallai ina da babban aiki a gabana dan idan aka ganni da wannan tambarin to lallai fa babu girma amma ya zama lallai sai na fita a wurin nan kota halin ƙaƙa,
Dafe cikinta tayi wanda taji "yan hanjinta na barazanar fitowa saboda yunwa, haka tayi ta murƙushe murƙushenta amma bacci yaƙi zuwa dan yunwa ta hanata rumtse idanuwanta,
Saida gari ya waye tangara gam Rabi"atu ta shiga toilet in da take bala"in jin ƙyanƙyaminsa, kallon window tayi taga bata da mafita fa, dan lallai da irin windows in toilet nasu bane dan da irinsu ne da tuni ta face abinta,
Haka dai ta haƙura tayo alwallah ta fito a ƙyanƙyame tare da ɗaɗɗaga hannuwanta tana sinsina jikinta sai ƙara duƙawa takeyi tana sinsina wasu wurare na jikinta dan jinta takeyi kamar tana ɗan bashi bashi,
Hannuwanta ta ɗora a saman hancinta ta rufe hancin da bakinta taɗan hura iska bakinta, ɗan gajeran tsoki tayi tare da cewa yau kwana biyu kenan ban wanke bakina ba, Allah ma ya sawaƙe min bai fara wari ba!,
Zuwa tayi ta zauna tana jiran zuwa Ahmad yazo kawo mata abinda zatayi break dan ta ɗaukarwa ranta yau saidai komai zai faru ya faru saita fita daga wurin nan,
Zaune suke dukansu a gaban momy, fadeel da Ahmad, gyara zaman ɗan ƙaramnin gilashin dake zaune a fuskarta tayi sannan tayi gyaran murya Ehem Ehem,
Momy barka da safiya, fadeel ya faɗa cikin ladabi, lafiya qalau ta faɗa tare ɗaga hannunta, momy ina kwana Ahmad ya faɗa ba tare daya bari ta faɗi abinda take san faɗa ba,
Lafiya qalau, bata sarara ba taci gaba da cewa Ahmad tsanani bazai shiryar da Rabi"atu ba saboda gashi daka fara kulleta a ɗakinta kana kallo ta toilet ta fice abinta,
Data dawo kuma ta samu an rufe gida saita koma ta baya ta ƙara fasa wuri ta shigo, ka faɗa min idan da masu binta a baya, bata bawa ɓarayi lasisin shigo mana a gida ba?,
Ahmad yayi shiru, momy taci gaba da cewa to abinda nake so dakai ka dawo da ita gida kila a can ma daka rufeta kila tana ficewa abunta baka sani ba, ka barta ta dawo ta fita abunta a gaban idonku kuma ta dawo,
Idan kuka ga ta daɗe kuce idan ta tafi ta daina daɗewa, a hankali zaku kwatanta mata kaji? Naji momy, to ina ka kaita ne? Kiyi haƙuri momy nayi alƙawari sai harsai dady ya dawo zan fito da ita,
Cikin fushi momy tace dan kaga ina lallashin ka? Ni zaka faɗawa sai dadynku ya dawo? Eh momy idan ya dawo zan faɗa masa cewa Rabi"atu ta canja hali dan haka yasan mafita akanta dan idan ma aure zai mata yayi mata tun wuri kowa ma ya huta,
Zaro idanuwa momy tayi sosai kamar wanda ta haɗiye kwaɗo ya tsaya mata a maƙoshi, tace kai kayi hauka ne? Wannan "yar jaririyar yarinyar za"ama aure? Amma lallai yau nasan ka samu warwarewar tunani,
Momy ai tunda mazan take so gara ki aurar da ita tun kafin taje ta jajibo mana abin..... wasu irin lafiyayyun marika fau fau fau fau fau, momy tayi ta saukewa Ahmad a jere ba tare data lunfasa ba, saida ta tabbatar ya maru sannan tace ka gyara kalamanka akanta na faɗa maka,
Ya buɗa baki da niyar zai ƙara cewa wani abu, da sauri ta matsa jikin scokert ta ciro hiter tayi kwaɗa masa a kai.......
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
10/07/2018
9.
Jikin scokert ta ciro hiter tayi ta kwaɗa masa a kai..... Shi kuma yana durƙushe a gabanta kansa yana kallon ƙasa bai kalli momy ba bare ma yayi yunƙurin tashi dan tsirar da lafiyarsa,
Momy don Allah kiyi haƙuri fadeel ya faɗi haka tare da miƙewa da sauri ya riƙewa momy hannunta da take dukan wa Ahmad dashi,
Wani irin firgitaccen mari momy ta kwakwkwaɗawa fadeel tare da cewa idan ka sake riƙeni saina ɓata maka rai sakemin hannu dan uwarku,
Momy kiyi haƙuri don Allah ki daina dukansa, naje na dake sa saima na haɗa dakai duk naci muku zaka san raina ya ɓaci, ɗan gajeran murmushi fadeel yayi sannan yace momy karfa ki manta yanzun nan kika gama faɗa cewa tsanani da duka baya sawa mutum yayi abinda bai saka kansa ba, sannan kuma baya shiryarwa,
Tou momy dukan yaya bashi ne zaisa ya fito da Rabi"atu ba, kiyi haƙuri shima ki lallaɓa shi, wani irin kallo momy tayi wa fadeel tare da cewa ni zan lallaɓa sa fadeel? Dani dashi waye ya kamata ya lallaɓa wani? Zan lallaɓasa amma sai inya faɗa min nina aifesa ko kuwa shine uwana?
Murmushi Ahmad yayi da gefen bakinsa ba tare daya kalli kowa a cikinsu ba, yace kai fadeel gafara daga nan, fadeel zaiyi magana Ahmad ya daka masa wata irin tsawa wanda tasa "yan hanji kaɗawa,
Ga fara a wurin tun kafin in taso, da sauri fadeel ya saki hannun momy ya matsa a gefe, jan guyawunsa Ahmad yayi yaja jikinsa zuwa daf da momy, sannan ya ɗora duka hannayensa a saman ƙafarta cikin ladabi ya fara magana cewa,
Momy kiyi haƙuri insha Allah zan fitar da hannuna akan Rabi"atu idan har hakan zaisa kiyi farin ciki,
Sannan kuma zan daina hukunci akanta idan har kikace min ba kece kika aifeni ba tou zanyi haƙuri da hakan in daina hukunta miki ɗiyarki zan barta da "yan uwanta ni kuma in kama gabana danni idanuwana basa iya ɗaukar abinda takeyi ba tare dana tsawata mata ba, idan kuma har kece uwa a garemu dukanmu dani da Rabi"atu tou kibarta dani, dan muɗin mune jigo ga rayuwarta bata da kamarmu,
Tou bani bace uwarka bani na aifeka ba shikenan kake so kaji ko? Tou na faɗa maka sai kuma miye? A hankali Ahmad ya ɗago da kansa ya ɗaga idanuwansa dakel ya kalli momy,
Kallarni da kyau idan bakaji abinda na faɗa ba, cewa nayi bani bace uwarka bani na aifeka ba,
Kuma maza ka ɗauke idanuwanka a kaina idan baka daina kallona ba saina ƙwaƙwule maka idanuwa munafikin Allah tashi ka ɓacemin a wurin, kuma zuwa anjima idan banga Rabi"atu ba saina maka wulaƙanci daya fi wannan dan banga amfanin ɗan daya raina manya ba,
Jiki a saɓule Ahmad ya miƙe ya fice a ɗakin, fadeel ganin Ahmad ya fita yasa ya kalli momy, kallo ɗaya yayi mata tare da girgiza kansa cewa nima yau zan wuce, cikin tsananin ɓacin rai tace kaima idan ka tafi ka nemi taka uwar munafikin da wani shegen kanka kamar na sadaka,
Cikin sauri fadeel ya fice, yana zuwa ɗakinsa wanka yayi babu ɓata lokaci yayi shirinsa duk wani ɗan abunda yasan zai ɓuƙata ya tattara ko ta wurin Ahmad bai biya ba saƙo kawai ya tura masa cewa Yaya ni na wuce sai mun sake haɗuwa,
Ahmad baiji shigiwar saƙon ba kwata kwata dan yayi nisa a cikin tunani, maganar momy kawai take masa yawo a cikin dodon kunnuwansa, ji yakeyi kamar yanzun momy take faɗar maganar,
_Kallarni da kyau idan bakaji abinda na faɗa ba, cewa nayi bani bace uwarka bani na aifeka ba,_
_Bani bace uwarka bani na aifeka ba,_
_Bani na aifeka ba,_
_Bani na aifeka ba,_
_Bani na aifeka ba.................._
Da sauri ya daɗe kunnuwansa da duka hannayensa, yana cewa A, a, A, a, momy A, a,,,,,,,,,,,,,,,, cikin sauri ya janye hannunsa dan famo wani ƙaton malulu da momy tayi masa wurin jibga masa hiter a ka wanda ya fama ta sanadiyar cewa A, a, momy,
Cikin ɓacin rai Ahmad Yace kece kike cewa ke ba mamana bane? Kawai saboda ki bawa sheɗan goyon baya yayi tasiri wurin rushewar tarbayya da kika daɗe kina aza tubalin ginawa ɗiyarki, son da kike wa yarinya ya rufe miki idanuwa bakyaji bakya gani, ƙaunar Rabi"atu ta makantar miki da zuciya, san kai da biyewa huɗubar sheɗan ta dagular miki da tunani wannan ba rayuwa bace momy, ya ƙarasa maganar tare da sakin wani irin wahalallen kuka,
Haka yaci kukansa kamar ƙaramin yaro daga baya bacci yayi gaba dashi, dan yau kam yama manta da zance wata Rabi"a bare ma yakai mata abinci,
Bai farka ba sai bayan azahar ya tashi da wani irin matsanancin ciwon kai, dan haka a daddafe yayi wanka yasha magani sannan yayi sallahr azahar a inda yayi sallah anan ya kwanta yaci gaba da baccin wahala,
Ca Rabi"atu kuwa yunwa ta ladaftar da ita, tana ta azumin dole wanda bata san matsayin sa ba, kuka kuwa tayi harta tsinewa kanta data jawo aka tsareta kamar wata tsinanniya, amma a gefen zuciyarta tana roƙon Allah ya fitarta da ita wallahi ko Ahmad zai mutu sai taci gaba da zuwa club babu wanda ya isa ya takura mata, idan shi ta ƙamarsa zuciya haƙiƙa ni kangarace haka ta faɗa a bayyane,
11:30pm, Ahmad ya tuna da Rabi"atu, salati yayi cikin tashin hankali ya miƙe da gudu ya nufi BQ gabansa nata faɗuwa Addu"arsa ɗaya Allah yasa Rabi"atu bata mutu ba,,,,,
Wata irin tirjiya yayi daya tsaya a ƙofar ɗakin, cikin rawar jiki ya saka hannunsa a aljihunsa ya fito da makullin ɗakin ya buɗe, ajiyar zuciya yayi daya ga Rabi"atu zaune ta ƙurawa ƙofar ɗaki ido ƙuri kamar mage ta ɗanawa ɓera tarko,
Ajiyar zuciya yayi a kasalance tare da jingina jikin ƙofar bai shiga ba, cikin wahalalliyar murya yace ke zo nan......,
Banza tayi dashi kamar bataji abinda yace ba, jin rabi"atu batayi magana ba yasa ya ɗago kansa ya kalleta yace bakyaji na ina magana, har yanzun idanuwanta a ƙure suke ƙam a kansa amma taƙi motsasu kamar wanda ya mutu ba"a shafawa idanuwansa ruwa ba,
Da sauri ya shiga cikin ɗakin ya durƙusa a gabanta hannunsa yasa daidai saitin idanuwanta yana giggitawa amma da yake Rabi"atu shaƙiyyace taƙi ta ƙabta, dogon kallon Ahmad yayi mata tare dayin murmushi kansa a ƙasa hannunsa na dama ya dafe ƙasa dashi,
Da sauri Rabi"a takai masa halbi saida ya faɗi ƙasa, ta tashi cikin kwarin guiwa ta tsallekeshi da gudu, cikin zafin nama Ahmad ya miƙe yabi bayanta da gudu a lokacin harta fita daga cikin BQ ɗin, part insu tayi ma tsinke tana kiran sunan momy,
Tsalle takeyi tana tsallake duk wasu "yan ƙanana filawowi ta gefe takeyi dan kasawa Ahmad hankali, fasa nufa part in nasu tayi taci gaba da wana Ahmad kamar damisa ta kama mutun ya fece,
Murmushi Ahmad yayi tare da ɗan shafa sajen sa, lokaci guda kuma ya ɗan ɗaure fuskarsa yana kallon Rabi"atu dake faman gudu kamar ta samu taɓin Ƙwanya,
""Saida ya kalleta na wasu daƙiƙa komi yasa yayi haka Oho? Murmushi yayi da gefe bakinsa sannan ya zagaya ta gefenta tana ƙoƙarin ƙara tsallakewa ya taɗo mata ƙafa ta faɗi ƙasa jigif, janta yaci gaba dayi tana ihu, tare da dafa hannuwanta ƙasa saboda zafin gurzar da yake mata dan idan zuciyarsa ta kangare shi bayajin tausayi amma yana da laushi kafin ransa ya ɓaci,
Kukan biyu ya komawa Rabi"atu domin tasan yau ƙaryarta ta ƙare dan abun biyu zai koma, dan abinda yasa tayi masa haka bata nufi wurin momy kai tsaye ba dan ta ɓatawa Ahmad rai, ashe yafita mugunta,
Ɗaki ya mayar da ita saida yacicci ubanta da belt sannan ya rufe ɗakin ya barta kwance a ƙasa tana kuka zuciyarta cike da baƙin ciki, ta daɗe tana nan kwance tana kuka har Ahmad ya dawo ya buɗe ƙofar, a bakin ƙofar ya gyargyara mata abinci yaja ƙofar ya rufe yai wucewarsa abunsa,
Kwana masu ɗan yawa Rabi"atu tana ta ansar hukunci a wurin Yaya Ahmad gaba ɗaya Rabi"atu ta fige ta lalace tayi baƙiƙƙirin ta jeme ta molaƙe ta soye kamar anyi gobara a samanta,
Momy kuwa kullum saitayi wa Ahmad rashin mutunci amma saidai ya bata haƙuri,
Tsaye yake a jikin window yana hango Rabi"atu dake zaune tana kuka, cikin murya irin ta wanda yasha kuka harya godewa Allah tace Yaya kamin alƙawari don Allah ka kaini ɗakina inyi wanka don girman Allah ka tausayamin nayi maka alƙawari inayin wanka shikenan zan dawo har zuwa ranar da zakayi haƙuri, murmushi Ahmad yayi sannan yace..........
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Ganin gida kesa kare ya zagi kura amma ba daji ba, mun ƙoshi da nama warinsa mukeji, ana zaman ƙarya bamaguje yazo gari ya iske babu masussuka dan muguwar miya bata ƙarewa a tukunya, ba"a cewa maci wake yasha ruwa,*
*Fataken dare basa bacci, Allah ya ƙarawa kogi ruwa kududdufi ya samu, kowa yaci ladan sarki ya masa yaƙi, jinjina a gareki FADILA LAMEEDO ja muje Meelat Musa tana biye dake gaisuwa ta ga Ashmar da zakiyya*
*NA'IKKE: Abokin kirki yafi mugun ɗan uwa, duhun damisa maganin mai kwaɗayi, kuwwa da kuwwa bata korar buzu, tsoro na daji kunya na gida, dan ansan da wuyan biri ake ɗaure sa a ƙugu, ni JAMILA MUSA nake tunkuɗo saƙon gaisuwa ta zuwa a gareki, fatan alkairi nake mana da addu"a ubangiji yasa albarka a cikin ABOTAR MU*
*Jama"a ku tayani jaje wai mai Dambu tawa take cewa kowa ya fita yayi katin zaɓe, can kuma sai naji wata tace mata Allah yasa nan gaba karki ce A. P. C, towai tambaya shin siyasa ta fara ko kuwa ya abun yake?*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
11/07/2018
10.
Murmushi Ahmad yayi sanna yace kiyi wankanki anan mana? Faɗamin ruwane babu ko sabulu? Ya ƙarasa maganar yana mata kallon ukku saura kwata,
Kallon kanta tayi daga sama har ƙasa sannan tace koda akwai nan ne bana buƙatar yin wanka sai ɗakina,
Gyara tsayuwarsa yayi sannan yace kenan idan aka miki aure kin gama wanka? Eh kullum gida zanzo in abuna,
Da kyau haka Ahmad ya faɗa tare da shafa sumar kansa sannan yaci gaba da cewa, zan fitar dake kiyi wanka amma bisa sharaɗi 1 ya nuna mata da hannunsa tare da ɗan taɓe bakinsa ya tambayeta da kansa zaki iya?
Kawai sai in ansa sharaɗin da ba,a faɗamin ba? Saurin me kikeyi ne to? Baga ni gaki ba? Ya nuna ta sannan ya nuna kansa, ya ƙarasa maganar yana ɗaga duka girarensa,
Tsoki tayi tare da cuno bakinta sannan ta gyara zamanta cewa inajinka, murmushi yayi sannan ya tura hannunsa ta jikin window n ya shiga ciki, taso kizo nan,
Babu gadma ta taso tazo kusa da window ta tsaya, kallonta Ahmad yayi sannan yace ki ɗora hannunki akan hannuna ki ɗauki alƙawari yanzun zan faɗa miki burina, zaki iya? Idan kuma kinsan bazaki iya ba kada ki ɗauka danni idan mutum ya ƙaryamin alƙawari kinsan azaba nake masa mai tsanani, shin zaki iya ne?
Da sauri ta janye hannunta tare da runtse idanuwanta ta fara dogon tunani, kallo kawai ya bita dashi yana jiran yaji abinda zatace, wata zuciyar tace ki yadda banza yayin da wata take gargaɗinta da ta kikayi kanta Ahmad baya ɗaukar raini,
Ki yadda banza ɗan dukan da za"a miki ai zai huci, ke nan zaki zauna ayi ta dukanki kamar wata jaka? Tou miye ya dakeki kawai ki rama, yanzun zaman "yan ci akayi Rabi"atu zaki bari a wani rufe ki sai kace lokacin mallakar bayi, lallaɓashi ya fitar dake idan kika fita zamu samu mafita, zuciyarta ce ta kasu kashi da dama take ta maganganu kamar anan cin kasuwa a cikinta,
Jin gardamar tayi yawa yasa Rabi"atu ta dakawa zuciyar tsawa a bayyane tace saurara ya isa haka nan, cikin dakiya ta kalli Ahmad sannan tace yaya miye sharaɗin naka?,
Bai bata amsa ba ya zagayo ya buɗe ɗakin ya shiga, sannan yace mata sharaɗi na ɗaya ne, zan fitar dake gaba ɗaya a dakin nan amma wallahi duk ranar dana kamaki kin fita ko kina dawowa ko wani abu wanda baimin daɗin ba wallahi sai maki dukan dasai an ƙara lumfashi kin yadda? Cikin rawar jiki tace Eh, wuce ki fice,
Da sauri zata fita yace yawwa, magana ta gaba idan na tashi hukuntaki ba"a gidan nan zan ajiyeki ba wallahi tafiya zanyi dake saikin raina kanki, cikin zaguwa ta jinjina kanta alamar gamsuwa da gudu tabar BQ ɗin Ahmad yabi bayanta da kallo ta window,
Saida ta kusa shiga part insu sannan ta fara kuka wayyo Allahna na shiga ukku, da gudu ta isa ɗakinta tana kuka dan tasan idan ta nufi ɗakin momy ma bata nan tana Office,
Babu ɓata lokaci tayi wanka, da gudu ta nufi kicin jikinta har rawa yakeyi saboda yunwa, abinci mai sauƙi dahuwa ta girka, tun kafin ta fito farlo ta fara cin abincin,
Ahmad yana zaune yana kallonta da gefen idonsa, kusa dashi ta zauna tace yaya bisimillah, alhamdulillah ya faɗa a taƙaice, tsakiyarsu ta ajiye abincin sannan tace don Allah muci tare kaji,,,,,
Kallon cikin kwayar idonta yayi na tsawon wasu lokutta sannan ya kalli abincin, murmushi Rabi"atu tayi sannan tace muci ko yayana,? Jinjina kansa yayi sannan ya ɗauki cokalin ya fara ci,
Zuciyar kowa da abunda take saƙawa, "yar fira Rabi"atu ta fara jansa da ita tun yana basarwa harya fara biyewa, wani yayi dariya wani kuma yace hmmm, ko kuma yayi ko da kyau,
Bayan sun gama cin abincin ne ta ɗauke flet ɗin ta nufi kicin, zuciyarta cike da tunanin yanda zatayi taima Ahmad wayau ya bata wayarta,
Shi kuma tana tashi shima miƙewa yayi yabar farlon, ita kuma daga kicin ɗakinta ta nufa ta fara haɗa dabarar da zatayi idan zata fita anjima zuwa club,
Haka ta yini tana kullawa tare da warwarewa har momy ta dawo daga Office, a farlo ta samu Rabi"atu zaune cikin farin ciki momy tayo wurin Rabi"atu kusa da ita ta zauna ta fara cewa ɗan iska ashe yaci uwarsa shi yasa ya dawo dake,
Murmushin yaƙe Rabi"atu tayi wa momy tare da ce mata sannu da zuwa, momy ta ansa cikin farin ciki, tana mai rumgume ɗiyarta a jikinta hada hawayen murna momy, ita dai Rabi"atu ta ciki na ciki a dole takeyin magana dan momy ta katse mata tunaninta kada dabararta ta gudu ma,
Ganin ƙaunar bazata ƙare ba yasa Rabu"atu ta fita daga jikin momy tana cewa nidai na shige momy, momy bata so Rabi"atu ta tashi ba dan ita dai duk cikin "ya"yan ta dabance kodan ita ɗaya ce mace a wurinta Oho? Tana nan zaune har Rabi"atu ta shige,
Itama momy ɗakinta ta nufa dan tayi wanka ta huta, Rabi"atu zaune a ɗakinta ta kalli agogo, murmushi tayi sannan ta miƙe ta nufi ɗakin momy wanda tasan irin wannan lokacin tana wanka,
Da sanɗo ta shiga ɗakin, wayarta ta ɗauka ta fito da saurinta, da sauri taje kicin tana zuwa ta saka lambar Aysha ta fara kira, babu ɓata lokaci Aysha ta ɗauka,
Friend Rabi"atu ta faɗa a lokacin da taji Aysha ta ɗauki waya, jin muryar Rabi"atu yasa Aysha tace Ah ƙawata gaba ɗaya kin wani ɓoye kin cushe a gida sai kace matar matacce, ke aiko matar wanda ya mutu yanzun an daina takaba gayu akeyi a fita neman wani kana gama idda a ɗaura maka aure,
Cikin rashin gaskiya Rabi"atu tace jira bamu da isashshen lokaci, a gaggauce ta bawa Aysha labarin tun daga ranar da suka rabu har zuwa yanzun, ajiyar zuciya Aysha tayi sannan tace barshi dan idan yasan wata baisan wata, yau kamal yana birthday inshi kuma ya kamata kije masa gaskiya,
Rabi"atu tace bana faɗa miki halin da ake ciki ba? Wannan ba damuwa bane idan zakije kawai faɗamin ni zan baki mafita, zanje, tou ki jirani a bayan gidanku ta wurin da kike shiga tunda ba waya a hannunki ki riƙe lokaci da kinga 12am tayi in sameki a wurin da shirinki, to babu damuwa sai najiki Rabi"atu ta faɗa tare da kashe wayar ta goge lambar taje ta mayar da momy wayarta ta fito da saurinta ta koma ɗakinta,
12:00am dam agogon ɗakin Rabi"atu ta buga, Rabi"atu kuwa tsaye a jikin madubi ta zuge yanda tunanin mai tunani baya ɗauka, after dress ta ɗora a sama sannan ta fice ta ƙofa,
Kamar yanda Aysha ta faɗawa Rabi"atu a wurin ta sameta, Aisha durƙushe a wurin da yake wurin lungune har sai a kashe mutum wani baizo wucewa ba, wani ƙallene Aysha ta miƙawa Rabi"atu tare da cewa maza kije ki shaƙawa banza kizo mu wuce,
Taya zan shaƙa mishi har bai ganni ba? Kawo kunnenki kiji, matsawa Rabi"atu tayi Aysha tayi mata magana wanda babu wanda yaji abinda suke cewa, da sauri Rabi"atu ta miƙe bayan Aysha ta gama mata raɗa,
Ɗakin Ahmad ta nufa da saurinta kamar ana tunkuɗata, knock ta farayi Ahmad yana zaune saman abin sallah yana karatun Al" Qur"ani mai girma, jin baza a daina dukan ƙofar ba yasa ya tashi dan ganin ko waye,
Rabi"atu ya gani tsaye a ƙofar ɗaki, da sauri ya juya ya kalli agogon dake maƙale a jikin bangon ɗakinsa, sannan ya dawo da kallonsa wurin rabi"atu yace lafiya?,
Murmushi tayi tare da wucewa cikin ɗakin bata tsaya farlo ba ta wuce bedroom, ganin ta wuce yasa Ahmad yabi bayanta yana tambayarta abinda aka mata, zaune ya sameta a gefen gado dan haka shima zama yayi kusa da ita cikin damuwa yace miye?
Shashshekar kuka yaji tanayi dan haka da sauri ya ɗagota yana cewa wai miye ne? Yaya bana jin daɗi ne, miya sameki? Ya tambayeta fuska a haɗe, kowa idonsa a cikin na ɗan uwansa, murmushi Rabi"atu tayi a hankali ta ɗago hannunta data riƙe ɗan ƙyallen ta shafa masa a fuska, suuuuu...Ahmad ya tafi ya kwanta saman gado,
Tsalle Rabi"a tayi tare da gyarawa Ahmad kwanciyarsa ta lulluɓe sa da bargo ta kashe hasken ɗakin, tana ƙoƙarin fita ta dawo da sauri ta kunna fitila yaye bargon tayi fuskarsa ta bayyana sannan tace munafi mari nawa ma kayimin? Ta ɗaga kanta a lamar nazari, yawwa na tuna mari ukku tayiwa Ahmad sannan ta tofa miyau a fuska tayi waje da gudu abunta,
Aysha na ganinta tayi dariyar sun samu nasara, Rabi"atu ta fice suka shige cikin motar saurayin Aysha suka nufi inda Kamal ya tanada ayi shagali dan a tayashi murnar zagayowar shekarsa............
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*IYA KUƊIN KA, lallai IYA KUƊIN KA hausawa kuwa suka ƙarawa maganar da cewa IYA KUƊIN KA IYA SHAGALIN KA, ni kuma nace iya karatun ka iya buguwar zuciyarka, nikam dai kin baddalamin tunani gaskiya, amma masu iya magana nacewa, sannu bata hana zuwa, mutane kuwa suka ƙare da saidai a daɗe ba"aje ba, gaskiya na jinjina miki bisa namijin ƙoƙarin da kikeyi a cikin wannan littafin naki mai taken IYA KUƊIN KA, kindai san ƙorafina akanki leema basai na faɗa kowa yaji ba*
*BAKIN GANGA, lallai sai BAKIN GANGA masu karatu karku bari na baku labarin littafin nan, domin fasaha da tsantsar basira marubuciyar tayi amfani da ita, har yanzun baku makara ba domin sabon fitowa ne yana tafiya daidai da zamani dan marubuciyar KUNYANGAR QUNCHI itace dai ta dawo da sabon salon nata mai taken BAKIN GANGA nemi naki dan kallon cakwakiya*
*SO MAKAMIN CUTA, wayyo Allah ni kuma sai ya kama mani zuciyata, Allah ya ƙara basira da hazaƙa nima ina biye dake*
*NI YA NA"EEM NAKE SO, nima dai nace sai yaya na"eem*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
13/07/2018
11.
Banda dariya babu abinda sukeyi a cikin motar saidai su haɗa hannu a kashe taf,
Sun Ibi lokaci sosai suna tafiya a motar kafin su isa wurin partyn kamal,
Lokacin da suka isa wuri ya cika ya batse gam da jigajigan "yan duniya, amma wai baza a fara partyn ba sai 1:30am,
Ga wani irin kiɗa da yake tashi dan har cikin zuciyarka kana jin kiɗan, dan duk inda kakai da iya saka idonka ko bindiddiƙi bazaka ga sifikun ba, dan haka suka cewa kiɗan daga cikin bango yake fitowa,
Idan kuwa mutum yana kusa dakai ya kama kunnenka yayi maka raɗa tou duk iya lafiyar kunnenka bakajin abinda yake faɗa saboda yanda kiɗan yake fita,
Maza da mata an zuge kowa ka gani ya ansa sunan sa ka kirasa da sheɗan dan sune magoya bayansa da duk wani abu na halaka sun bawa sheɗan gudamawa,
Rabi"atu a gafen Aysha tana ta ƙara kallon yanda mutanen duniya suka goge abunsu, lallai ya zama dole itama fa ta ƙara zage ɗamtse dan lallai ji take an barta a baya,
Haka ta buɗe idanuwanta taci gaba da kallon "yan mata da suka ƙwace, Aysha ce taja hannunta suka fita waje danyin magana,
Rabi"atu ga kayan da zamuyi amfani nan dasu ta nuna mata, cikin rashin fahimta Rabi"atu tace miyasa baza mu tsaya da namu ba?
A, a, Rabi"a wannan sune kowa yake sakawa baki lura ba? Dan haka muma mu saka kinaji gashi can an fara magana cewa kamal yana iso wa,
Ansar kayan rabi"atu tayi a lokacin har Aysha ta cire rigar jikinta ta saka riga mai ɗauke da sunan kamal a baya, ɗan bingilin wando ne, wanda ko rabin cinya bai kawo ba,
Kallon shigar Rabi"atu tayi sosai tare da cewa Aysha gaskiya nidai bazan saka ba, cikin lallashi Aysha tace haba friend ai kamal bazaiji daɗi ba, kawai kiyi haƙuri ki saka dare ne fa babu wani wanda zai ganmu yi sauri ki saka mu shige,
Saida Rabi"atu tayi jim na wasu lokutta sannan dai ta basar ta saka kayan, woo Aysha ta faɗa, taci gaba da cewa yarinya kinfa ci taro, da kin tsaya da wannan ƙauyawan kayan ai da taro yaci mu ta ƙarasa maganar tana dariya,
Tafawa sukayi sannan suka rankata zuwa ciki, kamal yayi farin cikin ganin Rabi"atu sosai ga wasu dirarrin "yan tashan mata wanda sunci uwar bilicin harda ubansa ga wani atach irin na ɗiyan arna a saman kansu, sune tsaye a gefen kamal sai wani kwartanci sukeyi, kallo ɗaya zakayi wa kamal kasan ya gama karatun iskanci dan matan sai wani lillinda kamal sukeyi suna liliyashi shi kuma sai wani kashe ido yake yana lashe baki kamar wani tsohon maye,
Ɗan kashewa Aysha ido ɗaya yayi wanda ita ta gane abinda yake nufi, dan haka taja Rabi"atu suka matsa zuwa inda kamal yake zaune,
Barka da zuwa sarauniyar zuciyata, haka kamal ya faɗa yayin dasu Rabi"atu suka zo inda yake zaune yana nuna mata wurin zama a saman cinyarsa,
Murmushi Rabi"atu tayi tare da girgiza kanta alamar A, a, murmushi kamal yayi sannan ya miƙe tsaye tare da ɗan rungume rabi"atu a gefensa,
Ganin Rabi"atu a gefen kamal yasa wuri ya cuɗe da hayani, yayin da kiɗa ya daina tashi MC ya fara bayani cewa wannan ƙayataccen taro anyi sa ne domin taya mai girma kamal murnar zagayowar shekarar aihuwar sa, sannan kuma yana sanar da maza da mata cewa a yauɗin nan ne zai saka zobe a hannun sabuwar rayuwa wato Rabi"atu don Allah jama"a ku taɓawa masoya guda biyu, tafi rafraf gaba ɗaya aka ɗauka a wurin,
Ihu da sowa ya hana ma kaji abinda MC yake faɗa yayin da wasu kejin kamar su rabawa Rabi"atu kanta da gangar jikinta, ɗan kwabar zobe kamal ya fita a cikin aljihunsa ya kama hannun Rabi"atu ya danƙara mata zoben alƙawari, yayin da ihun yaci gaba da ƙaruwa wanda yafi na farko,
A wurin yanka cake ma hannun kamal a ƙasa na rabi"atu a sama aka yanka cake Rabi"atu ta iba ta bawa kamal a bakinsa tare dayi masa murnar zagayowar ranar aihuwarsa, sannan ta cusa sauran a bakinta a daidai lokacin da kiɗa ya ci gaba da tashi a wurin babuji ba babu gani,
Haka a kaci gaba da ranƙwashewa yayin da wasu sukaci gaba da antayawa cikinsu giya dan duk kayan mayen da ka sani kuma kake nema akwaisu a wurin, hakan take ga Aysha itama tasha ta kwale abunta,
Kana mata magana zatayi kamar ta faɗo maka sannan tayi magana cikin maye cewa sun gode sun gode, Rabi"atu kuwa tunda wuri ya cakume kamal yaja hannunta suka silale a wurin,
Cikin tashin hankali Rabi"atu takeyi wa kamal magana cewa itafa kayanta data cire bata gansu ba, cikin magana mai kashe jiki kamal yace mata me zakiyi dasu ne? No ba komai ina so kawai in canja ne dan bansan lokacin da zan shiga gida ba, yaya yace idan na fita sai yayi min dukan da za"a ƙaramin lumfashi, idan kuma ya ganni da wannan kayan kila zai kasheni ne,
Murmushi kamal yayi tare da jawo Rabi"atu a hankali zuwa cikin jikinsa, hannunsa saman gashin kanta kallonta yayi ido cikin ido sannan yace kada ki wani damu, a kullum ki zama mai dakakkiyar zuciya kada ki bari wani ɗan ƙaramin ƙwaro ya firgitaki, karki manta matsoraci baya zama gwani, a haka zamuyi soyayyar?
A, a, wannan bai shafi soyayyarmu ba, ɗan ƙara fizgota yayi sosai cikin yanayin tsoro a jikinsa saida fuskar kowa tazo kusa data kowa sannan kamal yace *TSORO* murmushi rabi"atu tayi tare da sauke ajiyar zuciya ta kwanta jikin kamal sosai dan jikinta ya gama rasuwa,
Murmushin mugunta kamal yayi tare da ɗagata daga jikinsa dan yaga a sauƙaƙe zai kamo Rabi"atu, saida ya zaunar da ita a mazauninta yace muje in ajiyeki gida an fara kiran sallahn asuba,
Murmushi kamal yayi sannan ya fara tafiya har suka iso ƙofar gidansu Rabi"atu babu wanda ya sake magana, godiya tayiwa kamal bayan sun tsaya sannan ta fita,
Kamal yana kallonta har tasha kwanar gidansu tunda bata ƙofa take shiga ba, da sauri ta duƙa ta kurɗa ta inda take shiga, da sauri ta shige sannan ta danne wurin da katakon da take rufewa tayi ciki da gudu ba tare da wani ko wata ya ganta ba!.....
Da saurinta ta isa ɗakinta wanka tayi tare da ɗauro alwallah tazo ta haye saman abun sallah,
Tayi raka"atanil fijir sannan tayi sallah asuba saida tayi karatun Qur"ani sannan ta kwanta,
Kwanciyarta ke da wuya ta lumfeshe idanuwanta danyin bacci amma bacci yace baisan idanuwan Rabi"atu ba, abubuwan da suka faru a wurin bithday ya fara karakaina a cikin ƙoƙon kanta idanuwanta kuwa data rumtse kamal ne tsaye ɗauke da kyakkyawan murmushi a fuskar sa yana miƙo mata hannu.........,
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on Instagram @ meelat_musa*
*Ba sauran kwarewa bayan ka riga ka zamo maƙura, ita jallabiya Allah wa'alamu ce ƙawar social media dan babu basarake babu talaka sannan kuma babu mai kuɗi dan kowa hawa yake yi, tou itama jallabiya haka take sanyata babu gamai kuɗi babu ga basarake babu ga talaka wannan magana tawa jawabi ne amma sai mai cikakken hankali da zai gane inda zance nawa ya dosa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
17/07/2018
13.
Lokacin da zai saketa a hukuncin farko, tafiya yakeyi babu ji babu gani,
Saida yayi tafiya mai nisa sannan ya tsaya ba tare daya fito ba ya ɗauki wayarsa ya fara kiran fahad,
Babu daɗewa ya ɗauka Ahmad yayi masa sannu, murmushi mara sauti fahad yayi tare da cewa kana ta ina ne yanzun?
Na kusa ƙarasawa tsayawa nayi Ahmad ya faɗa, fahad yace tou ka sauka lafiya sai na taho, yayi babu damuwa Ahmad ya faɗa tare da ajiye wayarsa yaci gaba da tafiya,
Saida yayi tafiya kamar zaije wulƙihu a ƙofar wani katafaren gida ya tsaya sannan yayi horn, babu wani ɓata lokaci mai gadi ya yaye masa get in shi kuma ya silala da motar sa cikin farin ciki zaici uwar Rabi"a babu shakku,
Bayan yayi parking ne ya fito daga cikin motar, saitin da Rabi"atu take zaune ya buɗe ya fito da ita bawai fitowa ta ahankali ba fizgota yayi cikin matsanancin ɓacin rai,
Janta yakeyi yana tafiya da ita kamar ɗan jagora yanajin haushin makohon da yake masa jagora,
Har ya isa inda zai ajiyeta, tashin hankali bayyane a fuskarta har zufa takeyi kwalkwal tayi da idanuwa ta fara kuka dan ji takeyi kawai ta isko lokaci,
Zama Ahmad yayi saman kujera ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya taɓe bakin sa yayi tare da yatsina fuska sannan yace barkanmu da sake saduwa a cikin wannan gwabzawa karo na biyu,
Ɗan gajiyayyen murmushi Rabi"atu tayi tare da zama saman karfet tace haba dai kaima dai yaya miye abun wani gwabzawa? Kawai dai kace zaka hukuntani, tou kuma miye laifi a ciki dan Yaya ya hukunta ƙanwarsa? Ai wannan ƙauna ce mai girma, bazan maka gardama ba na kaita basai na bawa shari'a wahala ba!
Kallo Ahmad yabita dashi ba tare daya ce mata komai ba, rashin gaskiya yasa ta taci gaba da cewa uhum Yaya ke nan wai wai wai waiii gwabzawa karo na biyu, murmushi tayi tare da ci gaba da cewa wallahi sai naga abun kamar a film irin ector ya kama boss zaici ubanshi, ɗan yarfa duka hannayenta tayi sannan tace tou shikenan naji kaine ector nine boss kasheni kawai wasan yazo ƙarshe,
Ai basai kince nacicci ubanki ba, yanzu kuwa zan cika alƙawarin dana ɗauka, miƙewa tsaye yayi tare da riƙo abinda zaiyi hukunci dashi, danuwa Rabi"atu ta zaro sosai kamar taga mutuwa dan ganin abinda Ahmad ya ɗauko zai daketa dashi, da sauri ta miƙe tare da furta,
"""La""ilaha i"llallahu muhammadur rasulillah, S. A. W, kuka ta farayi tare daja da baya tana mai nanata innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, shima binta yakeyi, ganin yana biyota yasa ta fara gudu a cikin makeken farlon tare da faɗin momyna kizo ki ceceni, idan kuma sai bayan na mutu kika zo na yafe miki momy idan kin samu wata ɗiyar ki saka mata irin sunan na kuma ki riƙa bata labarina da rashin jin da nakeyi kuma kice nabar wasiyya cewa kada ta sake tayo irin halina dan makasanta suna tare da ita,
Ƙyaleta Ahmad yayi duk sai data gama guje gujenta sannan ta dawo kusa da inda yake tsaye da sauri ta ɗurƙusa ta kama ƙafafuwansa tana neman gafara, cikin kuka tare da shan majina tace kayi haƙuri shashshekar kuka sannan taci gaba da cewa idanma azumin kakeji saida ta ƙara shan majina sannan ta ɗago ta riƙe daidai guyawunsa taci gaba da cewa ai saima inyi maka azumin,
Waiwaye waiwaye takeyi tana ci gaba da cewa ɗan uwa rabin jiki ɗan uwana nakaina wayyo Allahna ina ƙaunarka ina sanka a daidai lokacin da samu nasarar riƙo wata rober yaji { tashshi } dake bayanta tana mai ci gaba da cewa,
Ubangiji yasa kayi hannun riga da baƙin ciki ɗan uwana ina sanka a daidai lokacin data miƙe ta sheƙawa Ahmad yajin nan a fuska, banda salati babu abinda Ahmad keyi,
Wata irin dariya Rabi"atu ta sheƙe da ita tare da tafa duka hannayenta zama tayi saman kujerar ta ɗora ƙafarta ɗaya saman ɗaya sannan ta gyara hannun rigarta duk da cewa hannun bai kawo inda take zato ba, dariya takeyi sosai tare da cewa an faɗa maka ni sa"ar wasan yaro ce? Ya kaji nawa salon a cikin wannan tsohon daren?
Taɓe baki tayi sannan ta fara kwaikwayon maganar Ahmad, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan gwabzawa karo na biyu, ɗan gajeran tsoki tayi sannan taci gaba da cewa to an haɗu ka kasa gwabza uwar komai, yau nice zan rufe a gidan nan yau zaka fara ansar sakamako daidai da irin iskanci da aikatamin a baya, faɗamin irin nau"in abincin da baka so? Hahhhhhhh ta kece da dariya,
Yau wani yaro zaici gidansu, Ahmad kuwa banda ihu da kuka babu abinda yakeyi lallai yau zaici uwar Rabi"atu harsai ta raina kanta, muryar rabi"atu yaji tana cewa da Allah rufe mana baki sai wani yagewa kakeyi wayyo wayyo tana kwaikwayon yanda yakeyin kukan,
Ɗifff Ahmad ya ɗauke lumfashin sa dan ya gama tsorata da Rabi"atu idonsa a rufe baisan abinda zata masa ba yanzun, ina mukulin daka rufe mu yake? Ta tambaye sa, zo na raɗa miki inda na ajiye shi,
Da yake akwai sauran yarinta sai ta nufi inda Ahmad yake tsaye, ram ya riƙeta ya fara ci mata yanda ya kamata dayaji idansa ya masa zafi adadin dukan da zai kawaiwa Rabi"atu saidai ya dunƙule hannunsa ya soke a awazu, { haƙarƙari } saida taci ubanta sosai yayi mata jagaja sannan ya barta,
Janta yayi ƙasa har wannan lokacin idonsa a rufe yake, saida yakaita wani ɗaki ya wurgata sannan ya rufe ɗakin,
*** ***
Saida Rabi"atu tayi wata biyu curr Ahmad yana gagara mata azaba, momy kuwa halin Ahmad bata san irin sa ba addu"a kawai takeyi ubangiji ya shirya Rabi"atu ta huta da horon wahala,
Kamal kuwa ya shiga ya fita rashin Rabi"atu a kusa dashi yana masa ciwo, kuma Aisha ta faɗa masa cewa Rabi"atu bata da waya, kuma ya siye waya sabul dal tecno K A 7, ya bawa Aysha ta bawa Rabi"atu amma ganin Rabi"atu yayi wahala a wurinta bama ganin nata ba labarinta kwata kwata babu dan ta zabga uwar hijabinta da niƙaf taje gidansu babu ita babu dalilinta,
A ɓangaren Rabi"atu kuwa ta anshi horo daidai da abinda take aikatawa a wurin Ahmad tacicci ubanta yanda ya kamata, tayi baƙiƙƙirin ta rame ta koma wata sokuwa dan azaba mai tsanani Ahmad yakewa Rabi"atu dan a ganinsa ta hanyar wannan horon zata samu natsuwa,
Yau shida fahat suka shigo tana kwance kamar gawa dan Ahmad yace ƙoshi ne yake sakata iskanci shi yasa baya bata wadataccen abinci, hankalin fahad ya tashi yanda yaga Rabi"atu ta koma saida yayi kuka saboda tausayinta gata ta koma kamar an tsafata sai wani wuƙil wuƙil takeyi da idanuwa kamar mage ta faɗa tarko,
Cikin kuka fahat yace Ahmad don girman Allah ka cire yarinyar nan daga cikin wannan akubar, a hankali Rabi"atu ta ɗago kanta da idanuwanta da suka ƙara fitowa ta kallesu, Ahmad yace wannan yarinyar fa munafika ce babu abinda taji daga cikin abinda na mata ina saketa anjima zata fice daga gida,
Fahat yace to ko dai tana da iska ne? Ahmad yace koda iska akwai iskanci, fahat yace A, a, kusa ayi mata ruƙiyya akwai wani malami da na sani mai fitar da aljannu bara zan kawoshi a jaraba sa"a mu gani,
Bayan kwana biyu Fahat yazo da malamin ruƙiyya, Ahmad ya fito da Rabi"atu aka miƙeta a saman tabarma aka fara karatu..............Gadai yanda Rabi"atu take cewa idan taji an taɓo aya mai zafi,
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
20/07/2018
14.
Gadai yanda Rabi"atu take cewa idan taji an taɓo aya mai zafi, saidai ta sulale ƙasa tayi ta muɗiɗɗika kamar an watsawa maciji ruwan zafi,
Cikin murya dai ta irin wanda ake fitarwa aljannu ta fara cewa, a saurara a saurara tana ɗaga hannunta alamar a jira,
Da sauri Ahmad ya matso sosai kusa da alaramma yace malam ci gaba kada ka sake ka saurara don Allah, baiwar Allah ashe aljannu ne suka shigar mata a jiki suke ta fitar da ita baiwar Allah,
Ɗan buɗe idanuwa Rabi"atu tayi tare dayin hamdala a ranta jin Ahmad ya yadda tana da aljanu dan haka tace kowa ya cire hularsa idan ba haka ba aradu cikin rawanin alaramma zan shige..........
A lokaci ɗaya gaba ɗayansu kowa ya cire rawanin sa ya ajiye ƙasa, saida tayi wani irin gurnani sannan taci gaba da cewa su waye cuke tukanmu? Ta ƙarasa maganar tana kallon inda Ahmad yake zaune,
Kallonta Ahmad yayi sannan yace nine nan kuma ko yanzun ma idan baku fita ba wallahi saina zane ku! Murguɗa baki Rabi"atu tayi sannan tace ai ce ka fugemu a banza cunda zamewa daga jikinta zamuyi kayi ta dukan ƙanwarka mu ina yuwanmu?, ta ƙarasa maganar tana hararar Ahmad!
Kai haka dai aka yini ana abu ɗaya Rabi"atu tana iskanci san ranta, kuma tayi alƙawari idan ba"a barta take zuwa inda ranta yake so ba, tou lallai zata ɗauki Rabi"atu ta tafi da ita bayan duniya.....,
Abun yayi wa Ahmad ciwo dan duk Rabi"atu ta gajiyar dasu tashi yayi ya ɗauki wata zabgegiyar dorina yaci gaba da dukan Rabi"atu babu ji babu gani a zuwan aljana yake duka,
Rabi"atu jin zata mutu yasa tace zamu tafi zan fita, Ahmad bai saurara ba, jin azaba tayi yawa yasa ta faɗi ƙasa tare dayin wata irin jiniya irin dai yanda aljannu sukeyi idan zasu fita daga jikin bil adama,
Ajiyar zuciya Ahmad yayi cikin yanayin gajiya yace shegu kai ai da idan zaku yini Ahmad yana kwana ba tare daya gajiya ba....,
Jan Rabi"atu yayi zuwa cikin ɗakin da yake ajiyeta, bayan ya shigar da ita ya kulle ƙofar ɗakin, gaba ɗayansu suka fita daga gidan......
***
***
Bayan sati biyu,
Tunda safe momy ta tashi dan tunda tayi sallah asuba bata koma bacci ba! Sai gyare gyare takeyi, saidai ta kakkaɓe can ta goge can, saida ta ɗauki awanni masu yawa tana gyare gyare ba tare data zauna ba!
Bayan ta hattama ta nufi kicin anan fa ta zuge dan yiwa mai gidanta dake shirin dawowa yau ƙayataccin girke girke, wanda zaci yasan ya dawo gida....,
Abinci iri iri momy ta girka, bayan ta gama ta jujjuye ta fara ɗaukowa haka tayi ta jidowa daga kicin tana zuwa farlo haka tayi ta jera jibga jibgan food flarks a saman diarning table,
Bayan ta gama ta koma ta gyara kicin inta, bayan ta gama ta nufi ɗakinta danyin wanka, tana fitowa babu ɓata lokaci ta zuge cikin shiga mai tsabta dan momyn "yar gayun ƙarshen zamani,
Ƙamshi ta ƙara sakarwa gidanta gaba ɗaya gida ya ɗauki ƙamshi sosai, saida ta tabbatar komai ya zama daidai sannan ta ɗauki wayarta dan kiran dady ta mishi ya hanya,
"yar firansu dai ta masoya sukayi bayan dady ya ɗauki waya, daga baya kuma dady ya tabbatarwa momy gab yake da gida idan Allah ya yadda, fatan alkairi ta ƙara masa daga baya sukayi sallama,
Ahmad zaune yake a saman bayan motar sa, yaɗan kwanta ya ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya waya yakeyi cikin jin daɗi da kwanciyar hankali, ƙarar buɗe get dayaji yasashi tashi a hankali dan ganin mai shigowa,
Ina zuwa zan kiraki anjima ya faɗa tare da kashe wayar, cikin sauri ya diro daga saman motar mamaki bayyane a fuskarsa dady? Haka ya faɗa a bayyane tare da cewa amma kuma munyi waya dashi ɗazu amma miyasa baka faɗamin zaka dawo ba?
Bai gama tunani ba yaga fitowar dady daga cikin motar da sauri yayi wurinsa tare da ɗan rungumesa irin dai yanda "yan gayu keyi idan sunga mahaifansu bayan sun daɗe basu haɗu ba,
Cikin farin ciki dady yace doctor a basu magani, murmushi Ahmad yayi tare da cewa barka da dawowa dady ya ɗan duƙa tare da shafa kansa cikin girmamawa, dafashi dady yayi suka suka nufi ciki suna fira,
A farlo suka samu momy zaune, itama cikin farin ciki ta tashi tayi wurin mijinta tare da mishi barka da dawowa, cikin jin daɗi ya amsa gaba ɗaya suka ida shiga cikin farlon sukayi wa kansu masauki,
Fira sukeyi sosai cikin farin ciki, can kuma dady ya juya ya kalli momy yace ina Auta ne? Kallon Ahamd momy tayi ba tare da tace komai ba, shima dady kallon Ahmad yayi sannan ya sake kallon momy banda faɗuwa babu abinda gaban dady keyi addu"arshi ɗaya kada ace wani abu ya tsami ɗiyarsa daya ɗauki san duniya ya ɗora mata,
Ajiyar zuciya Ahmad yayi sannan yace dady tana nan lafiya qalau, cikin rashin fahimta dady yace ban gane ba! Sassauta murya yayi sannan yace dady ka kwantar da hankalinka zan maka bayani, cikin faɗa sosai dady yace bazan kwantar da hankalin ba, abun rashin gaskiya sai wani kame kame kowa yakeyi, ku faɗamin ina doughter?
Ƙara langaɓe kai Ahmad yayi sannan yace dady ka huta sannan in maka bayani, ni babu wani abu da zanyi a cikin natsuwa ko kwanciyar hankali a yanzun harsai naji cikakken bayani akan Rabi"atu cewa dady,
Ahmad zai sake magana dady ya dakatar dashi tare da cewa ina Rabi"atu ne? Dady bara naje na taho da ita, dan dady yana san yaransa sosai kuma yana da kyakkyawan shaƙuwa dasu yana jansu sosai a cikin sa, amma baya da wasa idan mutum yayi sakarci ko shirme,
Da sauri Ahmad ya miƙe yabar farlon yana gunguni wanda ni kaina banajin abinda yake cewa bare kuma dady da momy, bayan Ahmad ne dady ya tashi momy tabi bayansa..................!
Babu daɗewa suka fito a tare uhum abundai ba bayani, domin dai ehem ehemm, haka suka jero suna fira har zuwa tebirin cin abinci, anan momy ta fara gabatar da abinci wa dady,
Yana ci suna fira yana ɗan bata labarai itama tana mishi fira cikin jin daɗi da shauƙin so da ƙauna suke fira amma sam momy batayi wa dady zance abinda Ahmad yayiwa Rabi"atu ba dan tasan mijin nata baya da wasa saboda baya san wani abu na rashin fahimta yana shiga tsakanin yaransa shi a ganinsa rashin jituwa ko cuta babba yanayi wa ƙarami a ganin sa hakan kan jefa gaba tsakanin juna!
Fitar Ahmad kuwa ɗakinsa ya wuce saida ya tabbatar ya tattara duk wani abu da yake da buƙata ya ɗirka a motar sannan ya sake komawa ɗakinsa yayi wanka ya shirya, a gagauce ya fito ya shige motarsa sai inda ya ajiye Rabi"atu,
Yana zuwa babu ɓata lokaci ya cirota janta yakeyi babu magana saida ya kaita motar sannan ya kulle da makulli danshi yayi alƙawari da Rabi"atu zai tafi sai tayi hankali ya dawo da ita!,
Tafiya Ahmad yake bata wasa ba, hankali Rabi"atu ya tashi sosai ganin Ahmad ya ibi hanya ɗoɗar dan ya ficewa daga cikin garin kaduna ya doshi hanyar abuja babu tsatsatawa gudu yakeyi bana wasa ba!
Yaya ina kuma zamuje? Rabi"atu ta tambayeshi cikin daƙilalliyar murya mai nuni da tasha wuya harta gode Allah, ba tare daya juyowa ba yace tafiya zanyi dake kila zaman nigeria yasa kika koma mahaukaci idan munje can zaki gane ni ne ubanki......,,,
A, a, Yaya don Allah kada muyi haka dakai, ai mumma yi hakan idan kina gaya min ciwo ni kuma saina faɗa miki mutuwa, ƙarya ne wallahi ƙaryar banza haka Rabi"atu ta faɗa tare da fara buga hannunta a jikin glashin motar tana ƙoƙarin fita,
Ke kina da hankali kuwa Ahmad ya faɗa tare da juyawa ya kalli inda take ta dukan glashi da hannuta babu tausayawa jini duk a hannunta saboda duk hannunta ya fashe saka makon dukan da take kaiwa glashin,
Da sauri ya juya ya kalli gabanshi danji motar ta sauka a titi, yana ƙoƙarin saita motar amma Rabi"atu saida ta sauke glashin nan tass kafin Ahmad ya tsaya, yana tsayawa kafin ya fito tafi ta ƙofar motar ta fice fuuu kamar walƙiya,
Tana direwa ta sheƙaƙa da gudu, Ahmad ya fito shima ya bita da gudun tsiya, wata ƙatuwar motar ta taho irin mai ɗauko kayan nan Rabi"atu na ganinta ta ƙara ƙaimi wurin gudu Ahmad ma gudunsa ya fiddo na baɗi da shakarar basasa!
Gudu suke a saman titi kamar masu gasar tsare, hankalin Ahmad a tashe kada Rabi"atu ta koma gida ya ƙarawa kansa laifi a wurin dady domin yayi da dady zai kawo masa Rabi"atu sai kuma yaji labarin yace zai tafi da ita?
Wani irin tsalle Rabi"atu tayi ta kama wannan ƙatuwar motar ta haye sama, tashin hankali Ahmad ya faɗa a bayyane ganin Rabi"atu ta haye saman motar, tsaye tayi tare da goge zufar goshinta ta riƙe ƙugunta gwalo tayi wa Ahmad tare da cewa ina gayyatarka partyn da zanyi jibi idan Allah ya kaimu party ne daya amsa sunansa dan ƙawayena ne zasu tayani murna na samun "yancin kai za"a raƙashe a cakule sosai sai kazo...........Amma fa idan zaka zo tsarin partyn namu maza zasu saka jar riga da baƙin wando sai hular peniscap itama red, mata kuma zasu saka jan sikarta da yallow riga atattach shine kallabin kowa ina maka fatan alkairi sai kazo........
Har yanzun Ahmad gudu yake yana bin motar, banda dariya babu abinda Rabi"atu takeyi harda riƙe cikinta, dakatawa tayi da dariyar cikin sakata ta tara hannayenta alamar ya taho tana mai cewa wayyo yaya ƙaro gudu sosai rugu da gudu mun kusa tserewa pha, dariya ta sakeyi sosai hada kwaikwayon yanda Ahmad yake gudu, dariya ta sakeyi tare da zama, harta zauna kuma ta miƙe tsaye tare da cewa yawwa Yaya na manta idan zaka zo da budurwarka don Allah ka tabbatar ta iya rawa, kuma kada ka sake ka kawoma jiƙaƙƙiya kaga jibine dan haka ka fara koya mata rawa tun daga yau, bye....😜
Saida tayi rawa sannan ta zauna tana mai farin ciki, Ahmad ganin ya kasa kamo motar yasawa ransa salama, cikin tashin hankali ya juya da gudu dan komawa wurin motar sa, babu ɓata lokaci yaja ya nufi babban birnin abuja...........
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Assalamu Alaikum, barkanmu da wannan lokaci ina muku fatan alkairi mabiya littafin SANADIN SOCIAL MEDIA, ƙorafe ƙorafenku ina ganinsu kuma inajinsu, yayin da wasu suke cewa don Allah kar na bari Kamal yayi nasarar raba Rabi"atu da budurcinta, wasu kuma suna cewa ta cika taurin kan tsiya yayin da wasu kuma suke cewa bata da kunya da sauransu kowa dai da abinda yake faɗa, to duk naji kuma na gani na gode sosai da shawararku a gareni, amma kuyi haƙuri kada ku manta tun kafin na fara rubuta littafin nan na faɗa muku cewa labarin nan da zan rubuta da gaske ne ya faru sannan kuma da sanin mijin Rabi"atu da yardarsa nake rubuta wannan labari, dan haka ina baku haƙuri duk wanda yaga ban masa yanda yake so ba to don Allah yayi haƙuri wannan labari ba nawa bane kuma ba ƙirƙirarsa nayi ba haka labarin yake kuma haka nake tafiya dashi, da fatan kun gane abinda nake nufi, daga ƙarshe kuma nake cewa ku huta lafiya na gode taku mai ƙaunar farin cikin ku, JAMILA MUSA ngd da yawa ku sarara abunku tare dayin ƙarko ina muku fatan kuyi shekaru irin na dabino*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
15/07/2018
12.
Yana miƙo mata hannu...............murmushi tayi tare da miƙa hannunta itama, ganin ta kama iska ya tabbatar mata da tunani takeyi, ajiyar zuciya tayi tare da gyara kwanciyarta ta rufe idanuwanta cincin ƙarfinta dan ba idonta haƙƙinsa,
Ƙarfe 09:09am Ahmad ya fara motsi addu'ar tashi daga bacci ne ɗauke a bakinsa, tare da yin miƙa sosai,
A hankali ya fara buɗe idonsa wanda yayi masa nauhi kamar an ɗora masa dutsin dala a sama, marmara idanuwan sa ya farayi cikin yanayi na wanda yasha bacci har ya godewa Allah,
Hasken ranar dake hasko masa kwayar idonsa ya tabbatar masa da lallai yayi ranar bacci, a ɗan firgice ya buɗe idanuwan sa gaba ɗaya tare da sauke su saman agogon dake maƙale a jikin bangon ɗakin sa,
Innalillahi wa"inna ilaihir raji"un ya faɗa tare da dafe kansa da duka hannayen sa, lumshe idanuwan sa ya sakeyi cikin yanayin tunani, ya daɗe a cikin wannan yanayi, murmushi yayi dan lallai duk abinda ya faru a daren jiya tsakanin sa da Rabi"atu kaf ya tunosa a cikin kwalwar kansa,
A gajiye ya ziro ƙafafuwan sa daga saman gadon sa ya nufi toilet a wahalce, saida ya watsa ruwa sannan ya ɗoro alwalla dan gabatar da sallah asuba data wuce sa,
Bayan ya gama abinda yakeyi ya nufi ciki amma a ransa yayi alƙawarin bazai wa Rabi"atu magana ba kuma bazai nuna mata yasan abinda ya faru ba amma sai ta gane shi yafita iskanci,
Ɗakin momy ya nufa kasancewar yau ba ranar aiki bane ya shiga dan ya su gaisa, kwance ya sameta tana waya da da dady wanda ya ɗaga ranar zuwan sa, gefen gadon ya zauna yana jiran su kammala!
Ganin wayar ba mai ƙarewa bane yasa ya ɗan kwanta, amma sai yaji yanzun ma suka fara, labaransu kawai sukeyi shima yana bata suna dai yin wayar ne cikin jin daɗi da farin ciki,
Ganin haka yasa ya haƙura ya fito dan yin kalaci, bayan ya gama break yana zaune a wurin yana chat har zuwa 12:00pm yana a wurin zaune,
A gajiye ta fito daga ɗaki tana miƙa sai hamma takeyi saboda gaji kuma batayi wani wadataccen bacci ba, saida ta ƙara miƙewa sosai sannan tace Yaya harka tashi?
Murmushi yayi a zuciyarsa yace shegiyar yarinya wato tasan ta shaƙamin koken harma wani tambayata takeyi wai yaya harka tashi, kallonta yayi a bayyane yace na tashi kema kin tashi kenan ko? Eh yaya a daidai lokacin da take zama,
Kyakyawan kallon Ahmad yayi mata sannan yace gaskiya yau kinyi bacci da yawa, bata kaida bashi amsa ba momy ta fito, itama zama tayi gaba ɗaya suka gaisheta ta amsa cikin jin daɗi,
Fira sukeyi cikin jin daɗi da kwanciyar hankali zuciyar momy fal da farin ciki yaranta sun haɗa kansu yanzu babu wani faɗa tsakanin Rabi"atu da Ahmad shima kuma ya daina takura mata,
Sun daɗe suna fira daga baya kowa ya tashi ya nufi ɗakinsa dan gabatar da sallah azahar,
*** ***
Rabi"atu durƙushe a wurin data saba jiran zuwa Aysha tana jiran isowarta ta bata abinda zata shaƙawa Ahmad su kuma su kama gabansu,
Duk abinda takeyi Ahmad yana kallonta ya ɓoye a cikin flowars, saidai tayi tsoki ta kalli agogon hannunta, zuwa wani ɗan lokaci mai tsayi yaji tsayuwar motar dan haka ya ƙara gyara tsayuwar sa don kallon ikon Allah,
Aysha ta duƙo ta miƙawa Rabi"atu gyalle kamar jiya, tayi magana wanda dani da Ahmad duk bamuji abinda suke cewa ba, da sauri ta miƙe a wurin tayo cikin gida,
Murmushi Ahmad yayi tare da bin bayanta da kallo harta ɓace, Murmushin mugunta yayi wanda a ransa har ya tausayawa Rabi"atu,
Da gudunta ta shiga ɗakin Ahmad cikin sauri ta kunna fitilar ɗakin ki, a yanda idonta ya bata Ahmad kwance ne a saman gado kuma bazata bawa ranta wani ne bashi ba, dan haka da sauri ta yaye bargon sa ba tare data kalli fuskar ko waye ba ta shaƙa masa ƙyallen yauma saida takai masa harbi tare da cewa ɗan iska,
Da gudu ta fita a ɗakin harta iso ta inda zata fita gudu takeyi, Ahmad yana tsaye yana kallonta har yaga ta fice wuƙil kamar ƙyabtawar walƙiya,
Saida yaji tashi motar su sannan ya koma ta hanya ya fita da sauri, a inda ya ajiye motar sa yaje ya shiga yaja dan bin bayan su Rabi"atu,
Yauma saida suka sha dariyarsu san ransu sannan Aysha ta fara nunawa Rabi"atu wayarta, wai ta kalli ikon Allah wani chart ita bata ma sansa ba sai jiya takejin labarin sa a wurin birthday in kamal, kallon wayar Rabi"atu tayi sosai tare da karanta sunan abinda aka rubuta a jikin Application in *WECHAT* taga an rubuta ,
Kallon Aisha Rabi"atu tayi sannan tace ni banma taɓa jin labarin sa ba kwata kwata, Aysha tace ay yanzun kinji friend ni abinma ya burgeni kema ki sake waya dan muma muyi kunɗin bala mu faɗa ko muma an dama damu a duniyar *SOCIAL MEDIA* karki yarda ayi babu ke ƙawata,
Murmushi Rabi"atu tayi tare da gyara zamanta tace to shi kuma ya akeyin sa? Ko shima kamar whatsapp ne? Eh amma kuma tsarin nasu ba ɗaya bane domin shi wannan shake shake akeyi sai ayi conecting inki da wani daban wanda baki sani ba,
Ansar wayar Rabi"atu tayi taci gaba da dandannawa tana kallon chat in abun ya matuƙar burgeta sosai dan haka tayi gudurin neman waya, da tunani iri iri a zuciyar Rabi"atu har suka isa club,
Ahmad ganin sunyi parking yasa shima ya ajiye tasa motar a can nesa dasu sosai ya sauka ya fara tattaki dan bin bayansu,
Tun kafin ka matse da wurin kakejin kiɗa na tashi na tashin hankali, ga "yan mata kowa da irin tasa shigar wata ma idan ka kalleta so ɗaya baka marmarin ƙara kallonta dan da ita da wanda yake tsira basu da banbanci, shigar Aysha ya kalla itama nata yayi muni sosai amma yaga na Rabi"atu da sauƙin kallon,
Haka yabi bayansu a hankali har suka shiga gaba ɗayansu, haka ya tsaya ya ƙarewa wurin kallo ga mutane suna wuce abunsu, amma duk macen da zata shiga tana laƙafe a jikin namiji wani namijin ma mata biyu zai rurrungomo a jikinsa ya wuce dan haɗama,
Jinjina kai Ahmad yayi alamar tausayawa rayuwar da yaran nan suka cakuma kansu a cikinta, wanda bata da hanya sai sunje sun kwasowa kansu hayaniyar duniya sannan a koma gida a bar iyaye da wahala,
A hankali ya fara tafiya dan shiga ciki, kowa cashewa yakeyi san ransa Aysha ya hango da wasu gardawa majiya ƙarfi su biyu sun sakata a tsakiya sai wani lallasheta sukeyi yayi da wani kuma yake ta tattaɓa wasu sassa na jikinta ita kuma sai wani mimmiƙewa takeyi shegiya kamar damisa takai wa mutum zamiya,
Da sauri Ahmad ya ɗauke idonsa gefe tare da furta A'uzubillahi minashshaiɗanir raji"un, innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, hazbinallahu wani'imal wakil, Astagafurullah, yayin da idonsa ya sauka akan Rabi"atu ita kuma tana ta rawa abunta kamar wata maciya,
A zuciyarsa yace na shiga 3 ni Ahmad itama Rabi"atu haka zatayi ta rawa har wani ya ganota ya ɗaukota itama a mata yanda akewa Aisha? Da saurin ya goge hawayen idonsa ganin Rabi"atu tana tahowa wurin sa, waye ya nuna mata shi? Tambayar da yayiwa kansa kenan amma kafin ya samu amsa Rabi"atu ta iso wurin cikin dabarbarcewar tunani, tace Yaya ashe kaima kana ɗan leƙo?............ Ashe kaima kana san casu amma idan na kunna waƙa a gida sai kayi ta faɗa kana dukana kace kana san zuwa club amma kake ta wani ba kanka wahala? Ai da sai kawai ka bari mu riƙa zuwa tare muna koma tare abun ko ya ka gan....
Bata gama rufe bakinta ba Ahmad ya ƙwaɗa mata wani irin firgitaccen mari mutanen da suka gani Ahmad ya daki Rabi"atu gaba ɗaya sukayo ca kansa da niyar suyi masa duka dan kamal ya gama gabatar musu da Rabi"atu tare faɗa musu matsayinta a wurinsa saboda haka suna bata tsaro yanda ya kamata,
Cikin tsananin ɓacin rai Ahmad ya ɗaga hannunsa na haggu tare da daka tsawa cewa kaiiii kansa na duƙe a ƙasa hawaye yana ɗiga na baƙin ciki, gaba ɗaya suka dakata,
Ita kuma Rabi"atu taci gaba da cewa to kaima dai yaya miye abun duka a ciki? Kawai kazo na zo to miye? Sai kawai kayi abinda ya kawoka ka wani manta da gidanmu ɗaya kowa yayi abinda yakeso sa ma"ana tasa ta fishsheshi amma hada mari hak........
Ai bata gama rufe bakinta ba dan Ahmad gani yake ma ta raina masa hankali waishi ne take cewa kowa yayi abinda ya kawo sa, ɗaga ta yayi ya rabata da ƙasa ƙoliƙoli yayi da ita tare da dakata da ƙasa,
Gaba ɗaya sautin kiɗan dake tashi ya tsaya cak a wurin, yaran kamal kuwa sukayi kan Ahmad suka rufasa da duka tako ina, wata irin jirgiza Ahmad yayi tare da ɓarar dasu yaci gaba da dukan duk wanda ya riƙe saida Ahmad yayi musu kacha kacha ya barsu a cikin jini sannan yaja Rabi"atu ya fice a cikin club ɗin,
Aysha kuwa banda kuka babu abinda takeyi dan ta gwada layin kamal yafi a irga amma bata tafiya, hankalinta a tashe duk ta kiɗeme dan lallai idan bai fitar da Rabi"atu daga hannun Ahmad ba zata shiga matsananciyar wahala,
A bayan motar ya wurga banza sannan ya rufe, zagayawa yayi ya shiga mazaunin driver sannan ya ciro wayarsa, mai gadin gidansu ya kira bayan ya ɗauka yace yaje ɗakinsa zaiga Fahad abokinsa kwance a gado akwai zuma a saman sitebed ya lasa masa a bakinsa idan ya farfaɗo to ya faɗa masa cewa ya kirasa, an gama ranka ya daɗe ya faɗa sannan Ahmad ya kashe wayarsa,
Juyawa yayi ya kalli Rabi"atu wanda gaba ɗaya komai nata ya tsaya cak ya daina aiki, saboda ta tafi ɗimuwar rabin awa, batajin komai a cikin kunnenta sai kukan gyare idanuwanta kuwa basa ganar mata komai sai walƙiya, tsoki Ahmad sannan yaja motar sa tare gudurin jinyata Rabi"atu kamar yanda yayi mata alƙawari a lokacin da zai saketa a hukunci farko,
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
20/07/2018
15.
Nufi babban birnin abuja..........
Rabi"atu kuwa zaune a cikin motar ta ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya sai shaƙar iska takeyi dan yau jinta takeyi kamar ammata gafara,
Ɗan gajeran tsoki tayi sannan ta ɗora hannunta saman wani kwali tare da tashi zaune ta buɗe kwalin, murmushi tayi ganin abinda yake a cikin kwalin,
Ayaba ce irin manyan nan masu kyau, dan haka cikin farin ciki ta buɗe kwalin ta faraci abunta hankali a kwance,
Tana ci tana tillar da ɓawon ayabar a saman titi, cak taji motar ta tsaya dan haka bata wani ji damuwa ba taci gaba da cin ayabarta dan yunwa takeji kamar zata mutu,
Yaron motar ne ya fara fitowa daga cikin motar da sauri ya taho dan haka yana taka ɓawon ayaba ya tafi suu...... Salati ya farayi tare da kiran Ogansa!
Da sauri ya fito daga cikin motar dan ganin me yasa yake kiransa dan sudai tsayawa sukayi shi yaron motar zaiyi fitsari,
"""Kafin ya iso wurinsa shima yaji ya taka wani abu ya tafi dashi, cikin zafin nama ya dire daga saman abinda yaji ya ɗauke sa, juyawa yayi dan ganin ko miye a daidai lokacin da Rabi"atu ta sake tillo wani ɓawon ayabar,
Salati suka farayi gaba ɗayansu dan a tunaninsu aljani a cikin motar tunda sudai sun san basu taho da kowa ba kuma basu tsaya ko ina ba sai yanzun!
Dan haka cikin dakiya yaje ya kama motar ya hau saman bodynta, Rabi"atu ya gani zaune tayi irin zaman sarakuna saicin ayaba takeyi, gashin kanta kuma ya rufe mata fuska baya ganin fuskarta saidai hannunta dake shiga cikin gashin dan tura ayaba a cikin bakinta,
Cikin tsoro da fargaba yace baiwar Allah mutum ko anjan? Ba tare data ɗago ko tace wani abu ba, tace anzo kaduna ne? A, a, zamu dai shiga nan da minti 20 idan Allah ya yadda,
Da hannunta ta masa alama da ya tafi kawai, babu musu ko gaddama ya sauka, a lokacin har yaron nasa yayo fistari ya dawo haka suka shiga motar yaja zuciyoyinsu da tunani barkatai,
Suna shigowa kaduna yace hajiya anzo, yawwa sannu driver, a daidai lokacin da take ƙoƙarin tashi, saida ta sauko daga motar sannan ta zagaya wurinsa tace na gode fa, banda Allah ya kawo man kai lallai da ina can ina ansar horo,
Yaƙe yayi wanda yafi kuka ciwo 😬, murmushi Rabi"atu tayi tare da cewa kayi haƙuri na ci muku ayaba don Allah wallahi ba laifina bane laifin "yan hanjina ne, dan ji nayi zasu tsinke saboda yunwa fatan ka yafe min ko? Jinjina kai yayi tare da cewa na yafe miki dan ya ƙagara ta tafi shi tsoronta ma yakeji,
Yawwa sauka lafiya na gode, sai anjima🙌🏻 tana faɗar haka ta juya ta tsallaka titi cikin sauri, abun hawa ta tare amma ba gidansu ta nufa ba gidansu Aisha ta wuce,
Suna tsayawa ƙofar gidan su Aysha ita kuma tana fitowa tare da wasu ƙawayenta murzajjin karuwa wanda ko a karuwanci sun ansa sunansu na karuwa, dan ko iskanci ya gansu saiya sara musu saboda "yan iska ne ajin farko,
Fitowa Rabi"atu tayi, cikin mamaki Aysha ta kalli Rabi"atu dan ita a farko ma bata ganeta ba! Saidai tayi mata kallon ƙurillah sannan ta gane ashe ƙawarta,
Cikin kuka Aysha ta rungume Rabi"atu tare da cewa friend kece haka? Murmushin takaici Rabi"atu tayi tare da cewa sallami mutumin can ya tafi, Aysha ta kalli ɗaya daga cikin abokananta tace sallami yaron can ki samemu cikin gida,
Jan hannun Rabi"atu tayi suka shige gida zuciyarta cike da damuwa iri iri, da sallama suka shiga babu kowa a tsakar gidan amma dai gidan ya ɗan canja saboda yasha gyara sosai kuma a ɗakinsu Aysha shima an gyareshi yanda ya kamata komai yaji sai san barka,
A saman kujera 2siater suka zauna, Aysha tace ƙawata ya na ganki haka? Uhum Rabi"atu ta faɗa ba tare da tace komai ba, dan ita tana kishin kanta da "yan gidansu,
Ganin Rabi"atu baza tace komai ba yasa Aysha tace bazaki tambayeni meya faru ba bayan bakya nan? Ba tare da Rabi"atu ta kalleta ba tace bana san jin komai fatan na sameku lafiya?
A daidai lokacin da mamansu Aysha ta shigo da wani uban gammonta a saman kai, Rabi"atu ta faɗa cikin mamaki! Murmushi Rabi"atu tayi tare da cewa barka da yini mama, barka dai ya kike? Lafiya qalau, ai nasha faɗa kukayi da Aysha da banganki wurin zaman gaisuwa ba!
Cikin rashin fahimta tace waye kuma ya rasu mama? Babanku mana, idanuwa Rabi"atu ta zaro tare da miƙewa tsaye cikin tashin hankali dan ita a tunaninta babansu daya aifeta take magana, tace mama yaushe? Ta faɗa tare da dafe ƙirji hawaye ya wanke fuskarta sosai,
Wata biyu da sati ukku da kwana biyar yau, dan tundai wannan bankar da aka mishi bai ƙara lafiya ba har Allah ya anshi rayuwarsa, basarwa Rabi"atu tayi dan ta gane yanzun inda mutuwar ta nufa sai tace wayyo Allahna ubangiji ya jiƙansa mama Allah yasa ya huta ubangiji ya kyautata namu ƙarshen idan ajalinmu yazo,
Gaba ɗaya suka amsa da amin, fita mama tayi daga ɗakin bayan Rabi"atu ta gama mata ta'aziyya, bayan ta fita suka ɗora nasu zancen duniyan,
Sai bayan sallah isha"i Rabi"atu ta tafi bayan ta shaidawa Aysha akwai party a gidansu jibi idan Allah ya kaimu tana so a tayata murnar samun "yancin kai, ita kuwa Aysha ta bawa Rabi"atu wayar da kamal ya siya mata tare da sabon layin waya kuma akwai numbers a ciki,
Lokacin da Rabi"atu ta shigo gida bata samu kowa ba, dan haka itama bata bi takan kowa ba ta shige ɗakinta abinta,
Tana shiga ɗaki wani ɗan guntun towel ta ɗauko tare da fara goge kayan sautinta duk da ba wani datti ne dasu ba dan kullum momy sai ta saka an gyara ɗakin kuma an balbaza mishi ƙamshi saboda tasan ɗiyar ta ta, ma'abociyar tsafta da gayu ce!
Tana gama gogewa ta saka wani faifayen sidi mai ɗauke da waƙoƙin india amma waƙoƙin cikin film in ajnabee ne duka a cikin cd flet in, waƙoƙi suna fara tashi saida Rabi"atu ta ɗan taka sannan ta nufi toilet danyin wanka,
Ta daɗe sosai a toilet sannan ta fito, saida ta gabatar da sallah magrif da isha'i sannan ta ɗan shafa mai sama sama, ta ɗan murza powder kayan bacci ta saka sannan ta haye saman gado tare da rungumo wayarta dan kiran sweety kamal,
Haka tayi ta kiran wayar amma a kashe dan haka ta haƙura ta daina kiransa, number Aysha ta fara kira bayan ta ɗauka suka ƙara gaisawa Rabi"atu ta ƙara jaddada mata jibi akwai party a nan gidansu fa kada ta manta,
Sannan kuma tana so tayo mata gayyar wayayyin yara kada ta sake ta kawo mata jiƙaƙƙi tafi san wanda suka kwace suka iya tsalle sosai, Aysha ta tabbatar wa Rabi"atu bata damuwa, sun daɗe suna waya daga ƙarshe Rabi"atu tace kuma tana so idan tazo a buɗe mata wechat, face book, instagram, whatsapp, da dai sauran duk chat mai amfani,
Aysha tace babu damuwa, haka sukayi sallama tare da ajiye magana zasu haɗu jibi a gidansu dan tayata murnar ansar "yancin kai, ganin bacci yana neman ɗaukarta yasa ta sauka dan kashe waƙar data kunna tayi bacci saboda gajiya sosai a jikinta, a hankali tazo ta haye saman gado ta lulluɓe dan bawa ido nasa haƙƙin!
Da safe kuwa koda tayi sallah asuba bacci ta koma bata farka ba sai 09:31am, a hankali ta sauka daga gado ta fara da ibadar ta ta, sannan ta wuce toilet,
Momy da dady suna zaune a farlo dan tun jiya suke kiran wayar Ahmad amma a kashe ake ce musu, kuma sunyi yawon neman Rabi"atu har sun gaji amma yanzun kuma ga sauti yana fitowa daga ɗakinta abun sunji shi yayi musu wani iri,
A tare suka tashi suka nufi ɗakin Rabi"atu suga abinda yake faruwa, da sallama suka shiga a tare, cikin farin ciki Rabi"atu tace dady.......ai tun kafin ya ansa ta fara rattafa masa irin yanda Ahmad yacicci ubanta tare da faɗa masa yanda ta dawo gida ba tare data tsahirta ba!
Duk alamar da momy takewa Rabi"atu tayi shiru saida takai aya sannan ta ƙarasa da cewa sai hararata momy keyi wai karna faɗa maka, murmushi dady yayi danshi gani yake yarinta ce kawai yake damun "yarsa,
Cikin sigar lallashi yace doughter idan mutum yayi tafiya ko? Kin daɗe baki ganshi ba, idan ya dawo bazaki faɗa masa wani yayi miki abinda bakiji daɗi ba ko kuma ki kawo ƙara, sai kin fara da sannu da zuwa fatan alkairi wa mutum, idan kika tabbatar mutum ya samu natsuwa sai ki faɗa masa abinda aka miki daga nan shi kuma sai yayi hukunci ina fatan kin gane?
Kusa da dady ta matsa sannan tace to sannu da zuwa kuma dady wallahi yajijji min ciwo ta nuna masa hannuta data fasa glass dashi kallon hannun dady yayi sannan ya kalli momy yace ta kaita asibiti dan hannun yaɗan kumbura ne,
Kuma dady zanyi party gobe in Allah ya yadda zan tara ƙawayene su tayani murna dadyna ya dawo lafiya, murmushi dady yayi tare da dafa kan Rabi"atu yace Allah yayi miki albarka doughter, kuma Allah yasa muna da rayuwa goben, amin ta amsa, dady yace kuje tou,
Fita dady da momy sukayi daga ɗakin tare da cewa kiyi sauri ki fito, suna fita Rabi"atu tayi tsalle ta dire saman gado tana dariya wai dady bai gane partyn ansar "yancin kai zatayi ba, yayin data lallaɓa ta ɗora abun da za"a tayata murnar dawowar babanta lafiya,
Da sauri ta shirya cikin dai shigar data saba, ta kalmi mai tsinin tsini ta saka aka wani dan ɗauki sidebag aka ɗan raɓa, kwas kwas ta fito, a farlo ta samu dady da momy suna zaune, da zasu tafi dady ya shedawa momy duk abinda Rabi"atu zatayi amfani dashi gobe a tabbatar an tanadar mata,
Momy ta ansa da insha Allah sannan suka fice, dady kuma ya koma ɗakinsa dan ƙara hutar da gajiya, a motar kuwa momy ke tuƙin Rabi"atu ana gefe an wani kame suka nufi asibiti,
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*HAƊIN KAI GROUP*
💝💝💝
💝💝
💝 *MEELAT TAMU*
💝💝💝
💝💝
💝
Daga alƙalamin *AUNTY MAIMOUNATH O. G*
_{ "Yar mutan kazay }_
*Macen birjimi babu mai ganin mafakarki, tangal tangal tafiyar mulki duhun kabari sa nadama MAIMOUNATH yar mutan kazay, ke sammu ba'a miki sammu dan iccen sammun dashi kike asawaki, teku uwar arziƙi kowa ya raɓeki sai ya ƙwasa, asara sai mai kaya talaka saidai jaje, gamsheƙa fitarki sai rana rana, munjira kin wuce kamun yaro ko babba yana shakka, idan ka raina "yar wuƙa ka haɗiyeta, jingim bakin aiki mill dubu iyakar tafiya, gefe kike duk girman mutum saiya duƙa, kowa yaso rawa ya koyawa ɗansa kiɗa ne, idan kaji a zuba miya cinikin tuwo ya ƙare, zama da mai turare yafi zama da maƙeri, komai yayi yawa yayi gimsa amma banda lafiya, haƙiƙa meelat taki ce, tasu ce, taku ce, kuma nawa ne, meelat tana tare daku!*
*MAIMOUNATH O. G*
*SMASHER*
*HUBBEEY*
&
*MEELAT TAKU*
*HAƊIN KAI GROUP KE MUKU FATAN ALKAIRI NI MEELAT MUSA NAKE CEWA KUSHA KARATU LAFIYA, MEELAT TAMU YANA NAN HANNUNKU!*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
24/07/2018
17.
_Ya sunan ki ne?_
_Daga wace ƙasa kike?_
Wannan shine saƙon da abokinta ya tura mata a karo na biyu bayan tace masa hi, shima yayi mata dan ita sauka tayi saboda bacci shi kuma yaci gaba da ɗirkako wa Rabi"atu tambaya kamar anje da makoho london, dan shidai ba idanuwa ba kuma ba ɗan gari ba amma duk inda aka gitta sai yace nan ina ne muka zo?
Murmushi Rabi"atu tayi, tare da ajiye wayar a gefe ba tare da ta bawa mai tambaya amsa ba!
Baccinta taci gaba dayi dan tana so ta ƙara hutawa sosai tunda Aysha ta gaya mata akwai babban tsalle yau a club,
Saida tasha baccinta ta gaji ta farka dan kanta, ruwa ta watsa bayan ta gama ta shirya, fita tayi farlo dan gabatar da karin safe!
Da sauri ta kalli agogon jikin wayarta tare da kallon momy dake zaune a gefen dady, ba tare data tsaya ba tana tafiya take cewa momy yau lafiya baki je Office ba? Har rana yayi?
Ajiyar zuciya momy tayi sannan tace lafiya qalau dadynku zai tafi ne, na bari ya tafi sannan na fita gaba ɗaya, Allah sarki dady har ka gama ganinmu? Ta faɗa a daidai lokacin da take zama a kujera,
Ey doughter, tou dady kayiwa yaya magana ya faɗa maka inda ya Ejiye wayana da key in motar na? Ban kirasa ba dady ya faɗa a taƙaice, haba dady ya za"ayi duk inda zan tafi sai ina tafiya a napep? Sai kace gidanmu ba"a so na? Wannan fa abun da yaya yayi dady kaine ka kyale sa hakan ai ɗaukar haƙƙi ne,
Cikin lallashi dady yace swry doughter, itama cikin kuka tace dady wane swry? Kawai kayi masa magana ya bani abuna, tou zan masa shikenan ko? Shiru rabi"atu tayi ba tare da ta sake cewa komai ba ta miƙe a wurin tama fasa break in,
Daga dady har momy babu wanda ya sake mata magana! Sun ɗan daɗe a farlon suna fira sannan dady ya wuce ɗakinsa dan fara shirin tafiyar sa itama momy tabi bayan mijinta dan taimaka masa,
Cike da sakata tattare da sangarta Rabi"atu ta shiga ɗakinta, jigif ta faɗa saman gado tana kuka wai ita a dole ba"a mata adalci ba, saida tasha kukanta sannan ta ɗauki wayarta ta koma online!
A lokacin har abokinta ya sake turo mata da wani saƙon ne!
_Kinyi shiru baki ce komai ba_
Saida ta goge hawayen idonta sannan ta fara rubuta masa kamar haka!
_Suna na Rabi"atu,_
_Kuma ni "yar nigeria ce_
_Ina zama da iyayena, muna zaune ne a garin kaduna!_
_Bayan wannan kuma sai me kake san sani daga gareni!?_
Bayan ya gani ya rubuto mata kamar haka!
_Yayi, kina da aure ne?_
_Ka cika tambaya!_
_Kiyi haƙuri, to faɗamin kina da aure ko kuwa?_
_Ni "yar yarinya ce_
_Tou turo min hotonki na gani mana_
Shigowar momy yasa bata bashi amsa ba! Kallo ɗaya Rabi"atu tayi wa momy ta maida hankalinta a wayarta, momy tace taso dadynku zai tafi,
Kamar jira takeyi momy tayi magana ta ajiye wayarta tare da fashewa da kuka wai ita lallai acewa dady Allah ya kiyaye tunda ya daina santa, yana gani anci zalinta amma bazaiyi wa yaya Ahmad magana ba!
Cikin rarrashi momy tace haba doughter hakan babu kyau, mai fushi da iyaye bazai samu rahmar Allah ba, su iyaye ba"a zuciya dasu taso , taso kinji "yar auta ta?
Daƙel momy ta lallaɓa Rabi"atu suka fita, ta rakata taje tayiwa dady ban kwana, kuɗin daya saba basu duk tafiyar da zaiyi yana basu kuɗi masu yawan gaske haka ya bawa Rabi"atu , nidai dady ka bar kuɗinka kawai motar na nake so a bani don Allah dady ta ƙarasa maganar cikin sakata,
Lallashinta dady yayi tare da mata alƙawari ko baya nan idan yayi magana da Ahmad zaisa momy ta bata makullin, kallon momy Rabi"atu tayi sannan tace au dama yana hannunki momy kika ɓoyemin? Ni baya wani hannuna ka faɗa mata mana dadynsu,
A, a, baya hannunta ina nufi idan ya faɗamin a ina ya ajiye sai na faɗa mata ta ɗauko miki, daɗi taji sosai, dan haka da ita akayiwa dady rakiya harya tafi, itama momy ta shiga motarta taja dan tafiya Office ita kuma Rabi"atu ta dawo ciki,
Wayarta ta ɗauka ta koma online dan bawa sabon aboki amsa, abinda ta fara ce masa shine,
_Yi haƙuri na barka nayi wani abu ne!_
_Ba komai, kin gama ko?_
_Ey_
_Kace na turo maka hotona ko?_
_Eh haka nace ba_
_Hmm kawai saina tura maka hotona bayan bansan waye kai ba?_
_Ni na faɗa maka suna na kai baka faɗamin naka ba tou,_
_Murmushi yayi sannan yace_
_Ni suna na JISHAD_
_Tou kaima wane gari kake?_
_Kerala_
_Ina ne kerala kuma?_
_Hahaha, ni india nake_
_kerala shine garina_
_Kamar ke ai kina nigeria, amma a kadun kike to nima haka kin gane?_
_Na gane yayi,_
_To turomin hoton naki_
_zan turo_
Daga haka bata sake cewa komai ba,
Haka kwanaki sukaci gaba da tafiya, amma a halin Rabi"atu babu abinda ta bari zuwa club dan yanzun ta gyare har sai safiya take dawowa, kuma har yanzun ba"a bata makullin motar ba, kullum idan tayi wa dady magana sai yace bai samu wayar Ahmad ba!
A ɓangaren *JISHAD* suna gaisawa lokaci lokaci da Rabi"atu amma har yanzun bata tura masa hotonta ba,
Yau ma suna fira da jishad, yace mata!
_Ki bani hotonki na gani mana_
_Kai nifa bana hoto_
_Murmushi yayi sannan yace, ni dani kika ce na tura miki nawa da na tura miki, dan ina so muyi abota mai kyau_
_Turo mu gani,_
_Hotonsa ya tura mata_
Da sauri Rabi"atu ta tashi zaune tare da riƙe zaninta da tayi ɗaurin ƙirji, sosai ta kalli hoton jishad sannan ta koma ta kwanta ta rubuta masa kamar haka...,
_Ni hotonka fa nace ka turo min ba hoton wani ba!_
_Ai nine na turo miki_
_Dan haka ki turomin naki kema na gani!_
_Gaskiya bazan tura maka hotona ba tunda kaima kaƙi ka tura min naka_
Juyin duniya jishad yayi amma Rabi"atu taƙi ta tura masa hoto, haƙura yayi ya barta!
Yau tun 09:22pm tabar gida, a club suka haɗu da Aysha can aka daddale sosai sai rabin dare Rabi"atu ta dawo gida, a gajiye ta shigo dan haka yau ko ɗan wanka data sabayi batayi ba, kayan jikinta da takalminta kasa cirewa tayi ta haye saman gado sai bacci!
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
22/07/2018
16.
Saida suka gama da asibiti sannan suka shiga kasuwa dan siyo abubuwan da Rabi"atu zatayi amfani dashi a wurin party gobe,
Siyayya sosai suka jibgo sannan suka nufo gida a gajiye, Rabi"atu bata wani tsaya taya momy cire kaya a cikin motar ba ta wuce abunta,
Mai gadi ne da mai kula da tsirran dake gidan suka kwashi kayan suka kaiwa momy ciki, ita kuwa Rabi"atu ɗakinta ta wuce wanka tayi ta fito taci abinci sannan ta koma ɗakinta taci gaba da gwada number kamal,
Ganin ta kasa samunsa yasa ta ƙara fawwala wa ranta tare da bawa zuciyarta haƙuri kamal yayi mata nisa dan haka ta haƙura,
Yinin ranar haka ta yini cikin rashin jin daɗi har dare yayi tana cikin tunani, yau kam abinda ya hana ta zuwa club bawai ganin dady ba A, a, kawai dai saboda tana hidima ne gobe,
Haka ta kwana tana tunani duk lokacin data farka cikin dare saita gwada layin kamal amma dai yaren iri ɗaya ne tun shekaran jiya ake faɗa mata shi dan haka ta haƙura,
Da safe tunda tayi sallah asuba bata koma bacci ba, wayar Aysha ta kira ita har lokacin tana club bata koma gida ba!
Bayan ta ɗauka suka gaisa sannan Rabi"atu tace mata don Allah ki shigo da wuri saboda shirye shirye, Aysha tace insha Allah ina club ban koma gida ba amma insha Allah daga nan zan wuto gidanku, Rabi"atu tace tou sai kinzo, Aysha tace to, sallama sukayi kowa ya ijiye wayarsa,
Dakel ta koma bacci bayan sun gama waya da Aysha, sai 12:30pm ta farka, da addu"ar tashi daga bacci ɗauke a bakinta, agogon dake maƙale a jikin bangon ɗakinta ta kalla sannan ta sauko daga saman gado a hankali ta nufi toilet,
Ruwa ta watso sannan ta fito, tana fitowa wayarta ta ɗauka dan kiran Aysha amma sai taga miss call inta yakai 11 dan haka ta fara kiranta cikin sauri dan da zata kwanta bacci silent ta saka wayar dan ta samu bacci mai inganci,
Saida kiran ya kusa tsinkewa Aysha ta ɗauka cikin faɗa Rabi"atu tace haba banda iskanci wai sai ayita ƙiran mutum baya ɗaukar waya, cikin sanyi Aysha tace kiyi haƙuri na kirane baki ɗauka ba, kuma abinda ya hanani zuwa gidanku kai tsaye yayunki sunce idan suka sake gani na sai sunmin duka Yaya Ahmad kuma cewa yayi saiya ƙarya min ƙafa ta baya!
Tsoki Rabi"atu tayi sannan tace tou do Allah ni kiyi sauri kizo, Aysha tace tou gani nan zuwa da yarda Allah, kashe wayar Rabi"atu tayi tare da ajiyewa a gefen gado sannan ta fita danyi kalaci, dady yana zaune a farlo yana karatun jarida momy kuwa ta tafi Office, dan haka gaishe da dady tayi sannan ta wuce diarning area dan gabatar da karin safe,
A gaggauce tayi kalaci ta tashi a wurin dan gaba ɗaya jikinta tsimi yakeyi ta ƙagara ayi shagalin nan dan ta tabbatarwa da ƙawayenta ta samu "yancin kai dan yanzun idan ta tafi Club sai safe zata riƙa dawowa kuma tasan ko banza dole sai yaya Ahmad ya faɗawa dady a ina ya ajiye mata key in motar ta, tasan zata ƙaro sabon wulaƙanci sheganta ka kuwa yanzun zasu fara sabuwa domin yanzun zata fara chat zata shiga network idanuwanta zasu ƙara buɗewa,
Tana cikin wannan nazarin taji sallamar Aysha daga cikin ɗaki ta amsa tare da cewa shigo mana, Aysha da zugar wasu ƙawayenta ƙyanƙyasar bariki sun kwace sosai ido ya buɗe jiki ya nuna cikin tako irin na "yan duniya suka nufi ɗakin Rabi"atu,
Da sallama ɗauke a bakin Aysha, Aysha ta fara shiga su kuma suna bayanta, a yatsine Rabi"atu ta ibesu sheƙeƙe tare da taɓe baki sannan tace sannunku? Yawwa suka amsa, kallon Aysha tayi sannan ta ɗauke kanta ta fita daga ɗakin, dukansu jikinsu yayi sanyi Aysha kuwa gabanta ya fara faɗuwa dan haka tabi bayan Rabi"atu da sauri dan tasan tana iya yaba mata a gaban ƙawayenta,
Da gudu ta isko Rabi"atu tana ƙoƙarin fita daga cikin farlon ta riƙeta ta baya cikin lallashi da tausassar murya tace Friend don girman Allah ki rufamin asiri, cikin rashin fahimta Rabi"atu tace meye kuma? Cikin rawar murya Aysha tace naga munzo dani da ƙawayena amma kin wani yi wani iri, ɗan gajeran tsoki Rabi"atu tayi sannan tace to so kike na goya ki dake da abokan naki ne?
A, a, Rabi"atu ba haka nake nufi ba, kawai ki ɗan saki ranki ki zauna muyi fira a ɗanyi labarin duniya, wani irin kallo Rabi"atu tayiwa Aysha sannan tace saurara kiji, ni nine ƙawarki umm? Sannan su kuma abokanki ne? Ina fatan kina ganewa dan haka ke kaɗai na sani kece ƙawata kuma idan zanyi firan ma dake zanyi bare banda lokacin wani labari ina da abunyi, tana kaiwa nan tayi gaba abunta,
Da sauri Aysha ta ƙara shan gabanta tace don girman Allah Rabi"atu ki rufa min asiri kizo mu koma dan darajar iyayenki, kinga daga nan ma idan bazakiyi firan ba su sunayi ni kuma ina buɗe miki wechat in koya kika gani ne? Ɗan gajeren murmushi Rabi"atu tayi sannan tace tou babu damuwa jeki ina zuwa nan da minti 2 ta nuna mata sannan tayi gaba, ajiyar zuciya Aysha tayi sannan ta koma ciki jiki babu ƙwari,
Rabi"atu ta daɗe sosai a ɗakin Ahmad sannan ta koma ɗakinta dan wayarta taje nema kuma ta duba sosai amma bata samu ba! Da sallama Rabi"atu ta shiga da ajinta dan ba sakara bace, Aysha tace yawwa taho nan friend wucewa tayi daidai inda Aysha ta nuna mata ta zauna,
Friend kinga ƙawayena, murmushi Rabi"atu tayi ba tare data kallesu ba hankalinta yana kan wayarta tace sannunku ƙawayenta yawwa suka amsa cikin rashin aji,
Wayarta Aysha ta ansa ta tura mata Whatsapp, Face book, Instagram & Wechat aka buɗe su dukansu sannan Aysha ta ɗanyiwa Rabi"atu bayan yanda Wechat yake dan tasan sauran chat in Wechat shine baƙo a wurinta dan haka tayi mata bayani yanda yake,
Bayan an gama gwada mata yanda wechat yake suka tashi dan fara shire shirensu na partyn ansar "yancin kai! Saida suka tabbatar sun gama komai sannan Rabi"atu ta shiga wanka bayan ta fito Aysha tace mata ga mai kwalliya tazo da ita kuma ta biyata kuɗin Rabi"atu tace nawa ne kuɗin? Mai kwalliyar tace 20k ne kuma ta bani,
Kwalliya mai aji akayiwa Rabi"atu babu hauka a cikin kwalliyar babu kyauyanci kwalliyace mai natsuwa kana ganin kwaliyar kasan wayayyiya ce tayi kwaliyar dan itama yarinya tana da ilimin kwalliya sosai akanta haka ta fente Rabi"atu sosai kuma ta fentu aradu,
Haka akaci gaba da yiwa kowa kwalliya bayan an gama yiwa Rabi"atu ta shige cikin shigarta dai kamar yanda ta saba kayane ƙanaƙan tasa masu kyau da ɗaukar hankalin duk wanda ya gani, haka sukaci gaba da shirinsu mutanen da Aysha tayo gayya kuwa suna shigowa wasu su biyu wasu kuma su ukku ya danganta dai, a ƙofar gidansu Rabi"atu kuwa an tara motoci sosai kamar ana taron ɗaurin aure,
Masu dj da Aysha ta ɗauko sune suka gyara wurin suka ƙawata shi abun burgewa da sha'awa, basu fara gudanar da shagalin bikin ansar "yancin kai ba sai 09:02pm, kuma koda momy ta dawo batayi musu magana ba fatan alkairi tayi musu, wuri ya cika da "yan mata da zawarawa matan aure wanda suka raina mazajensu duk sun halakta mata fa sun taru sosai kamar zasuyi ihu a wurin dan Aysha tace gidan masu kuɗine za'aci asha a raƙashe,
Bayan an buɗe taro da addu"a aka shedawa jama'a dalilin da yasa aka tarasu a wurin nan dan taya "yar uwarsu Rabi"atu murnar ansar "yan cin kai, Aysha ta anshi abin magana itama tayi ta ta maganar mai iskarta sannan Rabi"atu ta ansa tayiwa kowa da kowa fatan alkairi tare da musu godiya da suka halakci wannan babban taro nata ta gode sosai sannan tana addu"a yanda kowa yazo lafiya Allah yasa ya koma gida lafiya sannan kuma Allah yasa taro ya tashi lafiya,
Bayan Rabi"atu ta gama jawabi aka saki kiɗa, kai ko ina Rabi"atu ta samu kuɗi? Itama Aysha a ina ta samo nata? An cashe sosai Rabi"atu tayi ɓarin kuɗi kamar bata san darajarsu, haƙiƙa Aysha batayi ƙarya ba, domin anci ansha kuma duk wanda yazo wurin wannan partyn abinda Rabi"atu ta bada tukwuici "yar ƙaramar waya baby nokia duk wanda yazo wurin wannan party abinda aka bashi kenan,
Naman kaza da lemuna abinci fa ya wadata sosai can naga mai dambu da leema suna ƙoƙowar naman kaza sai naji Asmee tace musu kuyi sannu abinda duk mutun ɗaya rabin kaza aka saka mishi, nidai lallaɓawa nayi nace saura inga kun cinye aci a rage saboda harkar girma, maryam hassan tace meelat nidai duka zan cinye nace aiko wannan abun kunya ba dani ba, wurin Rabi"atu na matsa nayi mata murnar nima aka bani "yar wayata na raɓa abuna cikin jaka na dafe jikkata na tattara kan "yan BRILLIANT nace ku kuyi gaba saina taho,
Saida na tabbatar sun tafi sannan na dawo naci gaba da kallo, sai 12:30am sannan wuri ya rage sosai dan dady yace ayi haƙuri a tashi haka nan, Aysha gidansu Rabi"atu ta kwana saura kuwa kowa ya kama gabanshi yana san barka domin taro yayi daɗi,
Aysha bacci takeyi sosai saboda gajiya dan a daren jiya club ta kwana, kuma da safe batayi bacci ba, ita kuwa Rabi"atu bayan tayi wanka ta saka kayan baccinta ta haye saman gado,
Wayarta ta ɗauka ta shiga wechat, nan ta fara yi yanda aka nuna mata shake sheke tayi cikin hukuncin ubangiji akayi conecting inta da wani ba"indiye....
_Hi_
tayi masa, shima yace mata
_Hi_
Daga haka bata sake cewa komai ba ta sauka tare da ijiye wayarta a gefe dan bacci takeji sosai a idonta,
Tunda aka fara kiran assalatu ta tashi tayi nafiloli har aka kira sallah asuba tayi sallah amma Aysha ko motsi batayi ba! Dan haka Rabu"atu ta fara tashinta tayi sallah amma Aysha tace ummm ummm Rabi"atu tace ke da Allah ki tashi kiyi sallah malama kinji,
Bana sallah Aysha ta faɗa Rabi"atu tace ƙarya kikeyi wallahi tashi sai kinyita, Aysha tace a ban sallah zanyi sallah? Ey tashi karki raina min hankali yau nawa ga wata ne? Ɗan gajeran tsoki Rabi"atu tayi sannan taci gaba da cewa wai ni zaki faɗawa bakya sallah? Tashi tashi kinji, ba'a san ranta ba ta tashi ta sauka ta nufi toilet cikin ƙunar rai dan ta tsani tana bacci a tashe harma a wani ce tayi sallah saboda Rabi"atu ta raina mata hankali,
Watsawa idonta ruwa tayi ta yayyafawa ƙafafuwanta ta fito, a dungure tayi sallah tana gamawa tace nidai tafiya zanyi, Rabi"atu tace sauka lafiya idan kin fita kija min ƙofar, tana miƙewa wayarta kaɗai ta ɗauka ta fice daga ɗakinki tare dajan ƙofar kamar yanda Rabi"atu ta umarceta,
Aysha na fita Rabi"atu tayi tsoki tare da cewa jaka, wayarta ta ɗauka ta haye a network, tana shiga saƙon mutumin jiya ta gani dan haka ta fara karantawa kamar haka..........
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Gaisuwa gareki* 👇🏻
*FADILA LAMIƊO*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
25/07/2018
18.
Bata daɗe da fara bacci ba wayarta ta fara kururuwa, cikin bacci taji wayarta tana ta ringing amma saboda tsabar gajiya ta kasa motsawa,
Haka wayarta tayi ta ringing amma Rabi"atu gajiya ta hanata ta tashi taga mai kiranta, data gaji da jin kukan wayar a kusa da ita dan taji yana neman hanata tayi bacci, a kasalance ta lalabuto tare da kashe wayar taci gaba da baccinta,
Da safe kuwa bata farka ba sai 08:31am salati tayi da sauri tare da sauƙa daga saman gadon, dan ita tunda take ko wane irin gajiya ne tanayin ƙoƙari tayi sallah asuba a cikin lokaci,
Toilet ta shiga da sauri tayo alwallah ta fito dan gabatar da sallah da batayi a cikin lokaci ba!
Bayan ta gama sallah toilet ta koma tayo wanka, saida ta shirya sannan ta fita palo danyin kalaci,
Ita ɗaya zaune a dirning area wayarta a hannunta tana shafawa kalaci takeyi amma gaba ɗaya hankalinta yafi tafiya a kan wayarta,
Tsoki tayi mai sauti tare da ɗaukar kofin dake ɗauke da ruwan tea takai bakinta! Saida ta ɗan jashi kaɗan sannan ta ajiye a bayyene tace kaiji mutum zai rainawa mutane hankali!
Ina wani ruwansa da inda naje jiya bana online? Saida ta ƙara yin tsoki tare da tura dankali a cikin bakinta sannan tace to baka san ni ko gidanmu babu wani wanda yake cewa ina naje ina zanje ba?
Ƙara kallon wayar tayi tare da ci gaba da karanta saƙon da jishad ya turo mata",,
_Kina gani ina miki magana amma kikayi shiru_
_Kai na gani kuma ai kaima kasan na gani, kai nifa ba yarinya bace da zaka wani sakani a gaba kana cewa jiya ina naje baka san ba"amin tambayar "yan yara ba?_
Murmushi yayi mai aji, sannan ya rubuta mata!
_Allah ya baki haƙuri_
_Kaima Allah ya baka, ina dai faɗa maka abinda bana so ne a rayuwata, abota kawai sai kayi ta shiga wani hurami daban,_
_Kiyi haƙuri_
_Idan na faɗa maka inda naje me zakayi ma?_
_Babu abinda zanyi sannan babu abinda zanji,_
_Ina so ne kawai naji dan inji idan kuma kuna irin al'adunmu ne!_
Gyara zama Rabi"atu tayi sannan ta ajiye wayar a gefenta taci gaba da kalancinta,
Saida ta gama abinda takeyi tsaf sannan ta koma ɗakinta, saida ta kunna waƙa sannan ta kwanta saman gado,
Number da akayi ta kiranta da ita a daren jiya taci gaba da nema amma babu a kashe, nazari Rabi"atu ta fara waye ya ƙirata da wannan number ne?
Haka ta gaji da gwadawa sannan ta haƙura,
A lokacin kuwa saƙon jishad ya taru sosai dan haka ta fara ƙoƙarin karantawa, dan itafa tsoro ma takeji kada ya shanye mata jini tunda yace shi ba'a nigeria yake ba, sannan kuma bata san da gaske yake ba ko kuwa me yake nufi tunda bata shiga zuciyarsa ba!
_Rabi"atu nifa bana so ina magana da mutum yana tafiya,_
_Idan zakije wani abu ki faɗamin sai idan na yanda sannan ki tafi_
Kutumelesi, Rabi"atu ta faɗa tare da riƙe haɓarta alamar mamaki, sannan taci gaba da cewa kaiji mutum,
Ashema saida izininki sai kace wani babana, to ko Yaya Ahmad ma bai isa yamin wannan rainin hankali ba bare kai wani tushad, kallon wayar tayi tare da ƙara duba sunan swry ashe jishad ne sunanka!
Ci gaba tayi da bin saƙon daya rubuta mata tana karantawa cike da mamaki dan gaba ɗaya komai ta lura kawai izini yake bata bawai shawara ba, dan a yanda ta lura kawai tsaye yakeyin abunsa,
_Ki turo min hotonki yanzun nan!_
_Kuma miya hanaki bakiyi fira dani ba jiya?_
Wata zuciya tace mata tura masa don Allah yaci abinda zaici da hoton! Sannan kawai ki faɗa masa club kika je tunda ai ba saninki yayi ba haɗuwa ne kawai na SOCIAL MEDIA baku ƙasa ɗaya baku gari ɗaya tou miye?
Hotunanta tayi ta tura masa ba tare data gaji ba, ta tura masa hotuna masu yawan gaske ita a tunaninta zaice ta barshi haka, shi kuma baiyi magana ba,
Itama ganin baiyi magana ba yasa bata dakata ba! Saida taga tazo maƙura dan kanta sannan ta sanya stop,
_Kai ya baka gani ba?_
_Murmushi jishad yayi tare da cewa na gani_
Rainin hankali ni zaicewa ya gani bazaice nayi kyau ba?
Shiru yayi daga wannan lokacin bai sake cewa Rabi"atu ummm ummmm ba, wannan abu kuwa ya kasheta, ya za'ayi ta tura hotunan ta ƙaranci sunkai 50 amma ya raina mata hankali babu godiya bare yabawa da irin dress nata,
Tun daga wannan ranar saida aka share kusan wata ɗaya jishad bai sake magana da Rabi"atu ba, ita kuma aji ya hanata ta masa magana, shima kuma yanaji da nasa ajin,
Amma ita a ganinta ko tayi masa wani laifi ne? Amma dai taji babu daɗi a ranta, ya kamata dai yau su gaisa,
Tana wannan tunani taji wayarta na kuka, da sauri ta duba dan ganin mai kiranta, wannan number ne da aka kirata da ita kwanaki a cikin dare, da sauri ta ɗauka amma me? Tana ɗauka kafin ayi magana a tsinke kiran,
Da sauri tabi kiran amma sai aka ce mata kashe take, can matsalar mai kiran ta faɗa a bayyane, tare da shiga wechat inta ta fara rubutawa jishad saƙo kamar haka!
_Barka da rana_
Shiru yayi bayan yaga saƙon bai bata amsa ba!
bataji haushi ba ta sake rubuta masa kamar haka,
_Ya kake?_
Shiru babu amsa,
_Ya india?_
no answer,
Tunani ta farayi me yayi zafi haka? Gashi yana online amma sai tayi masa magana yayi shiru baya amsawa?
Kai ka sani nima bazan sake neman ka ba!
Haka suka ƙara kwashe satittika masu yawa basuyi magana ba, amma hankalin Rabi"atu idan yayi dubu ya tashi ita babban tashin hankalinta shine, hotunanta data tura masa ko ba komai tana san tasan matsayarsu a wurin jishad,
Dan da daɗi kayi abu a yaba ka, kayi gayu ace kayi kyau, idan kayi abu na gwaninta shima a yaba ka, idan na gwazo ne a yaba da ƙokarinka, idan kayi hoto ka tura shima ya kamata ace kayi kyau,
Amma shi jishad babu babu, tayi kyau bata yi ba bata sani ba? Ta burge bata burge ba, kai lallai akwai damuwa,
Ganin kwanaki suna ƙara shuɗewa yasa Rabi'atu ta ƙara damuwa ta rasa abinda ya faru, da irin wannan shirun ai gara kasan abinda kayi dan ko gaba zakayi da mutum kasan abinda ya haɗaku,
Lallai nice na fara neman sa dan haka kuma zan ƙara neman sa a karo na biyu na basa haƙuri sannan kuma na lallaɓa shi ya goge hotuna na daga cikin wayarsa, idan ya goge nima saina gogesa daga rayuwata,
Saida taci abincin rana sannan ta kunna dater ta dan ganin jishad ta tambayi dalilinsa na ɗauke mata wuta,
Gadai yanda tambayoyin da Rabi"atu ta fara rubutawa jishad kamar haka!
_Jishad ina maka fatan alkairi,_
_Ya kake ya kowa da kowa?_
_Kar kace banda zuciya nima fa na iya zuciya_
_Ka maido min hotuna na dana turo maka, na fasa tura maka_
_Wai kai waye ma? Lallai akwai alamar tambaya a cikin lamarinka,.mtswww_
Murmushi jishad yayi bayan yaga saƙon ƙawarsa, sannan ya shiga gallery insa yayo marking duka hotunan Rabi"atu sannan ya tura mata........,,,,,
Har a ranta bataji daɗin haka ba, amma sai ta dake tare da cewa sai ya biyata ɓata lokacin da tayi dashi tana magana,
_Itama maganar zan biyaki ne?_
_Ey biyani ɓata lokacin da nayi ina magana dakai,_
_Zan biyaki, amma sai kin faɗamin ke musulma ce?_
Tashin hankali?
_Kai ban tambayeka kai musulmi bane sai kai kace min musulma ce?_
dan taji haushin wannan tambayar, jishad yace,
_Ni musulmi,_
_Kamar yanda kake musulmi haka nima musulma ne_
_Musulma da irin wannan shigar?_
_Kai baka ga yanda kukeyi taku shigar ba!_
_Karki haɗa kanki da abinda wani yakeyi_
_Wannan dalilin yasa tun farko na faɗa maka cewa ka daina wuce da yawa ka tsaya matsayinka na abokin SOCIAL MEDIA_
_Lallai idan har abota ta zama abota haƙiƙa aboki yakan gyara kuskure da abokinsa yake aikatawa wanda baida kyau_
_Lallai idan har ni abokinki ne, tou ya zama lallai idan nayi abu wanda baida kyau ki gyaramin,_
_Idan har kina so muyi abota mai tsafta mai ɗorewa wanda nake fatan har zuminci ya haɗamu lallai sai kin ɗaukeni ɗan uwa_
_Sake kallon hotunan da kika turo min da kyau, baki sanni ba ban sanki ba, nace ki bani hotonki na gani, ji irin hotunan da kika turo min_
_Tou miye a cikin hotunan?_
_Zaki iya fita da irin wannan shigar?_
_To miye a ciki? Duk yawancin hotunan a club na ɗauka, kuma ai kuna zuwa club,_
_Nace miki ki daina kallon abinda wani yakeyi kice irinsa zakiyi, kina mace kuma musulma kina fita a haka_
_Almar'atu, kulliha auratin, ma'adal wajahi, au kaffaihi, au rijilaini_
_Lallai ina mamaki da kika ce min ke musuma ce!_
_Kuma na karyataki, duba tulin attach in dake bisa kanki, kalli fa, kalli kalli haba, haba haba........._
_Wai kuma a haka har kike zuwa club sai kace bakya kishin addini_
_Mtswww haba ina ma amfani? Mtswwwwwww..........._
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
26/07/2018
19.
Shiru Rabi"atu tayi tare ƙurawa wayarta ido tana kallon chat in mamaki ne kwance a fuskarta, tama rasa abin cewa dan gani takeyi ma jishad ya rainata, duk wanda ya ganta dai yasan ita musulma ce,
Kuma a cikin arna babu suna Rabi"atu bata taɓa ji ba amma wai kamar ita da iliminta da addi"ninta jishad yake cewa wai yayi mamaki da nace masa ni musulma ne, ai duk wanda ya ganni yasan ina da banbanci da ɗiyan arna,
Hawaye taji ya ziraro mata daga cikin kwayar idonta, haƙiƙa duk wayewar da bata musulinci ba lallai ta zama daƙiƙanci, lallai wayewar zamani halaka ce!
Tana bahausa cikakkar bahausa, iyayen ta musulmai ta tashi a cikin addinin musulinci kuma shi ya reneta iyayenta suka ginata da ilimin addini tun tana ƙarama har girmanta wai yau ita ba'indiye zaice mata bai yadda musulma bace,
Sauka tayi daga online jiki a sanyaye ta ajiye wayarta a gefe, tunani ta shiga yi har na tsawon wasu lokutta, murmushi tayi tare dayin magana a bayyane cewa aidai tsoron Allah a zuciya yake can kai ta matsewa nidai Allah ya sani musulma ce tunda ma ina sallahta abuna,
Fara kwaikwayon maganar jishad tayi kamar a gabanta yayi magana bayan fa cht sukayi, saida ta yatsina fuska tare da ɓata bakinta kamar tasha wani abu waishi ba daɗi....,
Lallai nasha mamaki da kika ce min ke musulma ce! Kuma na ƙaryataki, dubi tulin attach in dake bisa kanki, kalli fa, kalli kalli haba, haba haba........
Miƙewa tayi tare da cewa ɗan rainin hankali, da gunguni ta shega toilet har tayo wanka ta fito mita takeyi tare da tisa zancen kamar wanda aka cinyewa haƙƙin gado ta,
Agogo ta kalla tare da maida hankali wurin shiri, tanayi tana cewa ai suma indiawan ai munsan komai suma suna saka gashin doki ba munsan duk karyar banza bace har man bilicin suke shafawa,
Haka kawai haɗuwar SOCIAL MEDIA ka nemi ka wani mayar dani ƙaramar yarinya, bama sai na sake chat ɗin dakai ba zaka sake raina ni?
Bayan ta gama shafa jikin wadrof ta matsa ta fara duba kaya, murmushi tayi tare da zaro wasu matsaccu, fitinannu, sheɗanu, halakakkun ɓadda tunanin mai shirin sakawa,
Haka ta zuge abunta, tare da sakin gashin kanta a jikin madubi ta matsa cewa wai wannan gashin ne na attach? Baka san gashi na bane ba,
Wayarta ta ɗauka tare da ficewa daga cikin ɗakin da sauri, aikin dai ɗaya ne fa, dan tsayawa in faɗa muku cinye feji ne, sai 12:39am ta dawo gida, yau kam babu wata gajiya a jikinta ko bacci a cikin idanuwanta,
Wanka kawai tayi ta shirya cikin kayan bacci, sannan ta fita daga ɗakinta dan yunwa takeji tana kartar mata hanji, kicin ta nufa ta dafa indomie bayan ta gama ta zuwa a flet, ɗakinta ta koma taci tare da korewa da ruwan lemu mai sanyi!
Tana zaune a ƙasa saman kafet ta miƙe kafafuwanta ta ɗan ɗora hannunta a gefen gadonta, wayarta ce riƙe a hannunta da mata riƙon mutunci da hannu biyu,
Murmushi tayi a lokacin data ga saƙon jishad, buɗewa tayi ta fara karantawa kamar haka,
_Har yanzu bakiyi bacci ba?_
_Kaima miyasa bakayi ba?_
_Ni ina wani abu ne!_
_Aini ma wani abun na gama yi yanzun_
_To miye ya hanaki kiyi bacci, ƙarfe nawa yanzu?_
_01:32am_
_baki da lafiya ne?_
_Lafiyana qalau banma daɗe da dawo daga club ba_
_😳 club kuma?_
_To kanajin mamaki ne?_
_A, a, ban wani ji mamaki ba, kiyi bacci haka nan tou,_
_Ai banajin bacci,_
_Sai me kike ji?_
_Fira,_
_Yayi kyau,_
_Na tambayeka?_
_Ina jinki!_
Sai kuma tayi shiru, jishad ya sake cewa faɗi ina saurarenki mana, shiru Rabi"atu tayi dan itama bata san dalilin da yasa tace zata tambaye sa ba, kuma koma tambayar me zata mishi ne Oho!
Sauka tayi daga online, tare da dafe kanta wai miyasa ma nace zan tambaye sa? Tou mema zance masa? Mtsww nama zama banza, wai ya akayi ma ban fita harkarsa ba?
Hmmm lallai ya zama dole gobe na faɗa masa bana yin abotar dan da gani wannan mutumin sai yayi shishshigi komai nasiha komai wa'azi ko an faɗa masa nima ban iya ba,
Ummm tayi tare da kwanciya saman gado ta lumshe idanuwanta sai nayi maganinka, gyara kwanciyarta tayi tare jan bargo ta lulluɓe sai bacci!
Kwanaki sun shuɗe sosai tsakanin Rabi"atu da jishad ba tare da sunyi chat ba, dan yanzun ma bata da lokacin yin wani chat kwata kwata hidimomi sun mata yawa,
Dan kullum Aysha akwai sabon salon da take kawo burin ta ɓarna badai gyara ba, basu da aiki sai zuwa party, idan kuwa ɗaya daga cikin ƙawayenta ko waya ta canja sai sunyi party dan basu da magaya,
Rabi"atu zaune a gaban momy tana kuka wai ita a rufa mata asiri a bata motar ta, ya za'ayi tana tsallenta ace kullum zata ƙare raɓe a motar ƙawayenta? Momy tace haba daughter ba dadynku yace sai sunyi magana da Ahmad ba?
Cikin kuka tace wane magana, kullum zasuyi magana amma basu yi, yau watan dady nawa da tafiya har ya fara maganar zaizo amma an wani manta da anyi maganar ansar motar tou lallai idan dai baza a bani motar na ba saidai a siya min wata, tana kaiwa nan ta tashi da gudu ta wuce ɗakinta tana kuka,
Momy tabi bayan Rabi"atu da kallo a zuciyarta tace ubangiji ya shiryar dake, da gudu ta isa ɗakinta tare da faɗawa saman gado tana kuka, ta daɗe a cikin wannan yanayin sannan ta nufi toilet, fuskarta ta wanko ta dawo ta zauna a gefen gado tare da rungume kanta da duka hannayenta biyu dan taji yana mata barazar ɓarewa,
A hankali ta juya ta ɗauki wayarta dake ringing, sunan Aysha ya bayyana a jikin screen in wayarta a hankali ta kara wayar a kunnenta bayan ta ɗauki kiran,
Ba tare da ta bari Rabi"atu tayi magana ba, ta fara cewa friend kinsan wannan ƙawar tawa? Zainab ɗin nan? Tou wani Alhaji ta samu ya siya mata wata irin jibgegiyar motar yarinya hau online na tura miki hoton ki gani,
Ba tare da Rabi"atu tace komai ba ta kashe wayar tare da hayewa online dan ganin motar da aka siya wa zainab dan ita tama raina yarinyar wata ƙazama da ita sakara wanda ko riga bata iya sakawa ba!
Lallai motar tayi kyau ubangiji yasa alkairi Rabi"atu ta rubuta tare da turawa Aysha a lokacin da taga motar da aka turo mata, bayan Aysha ta gani itama ta rubuta cewa kizo muje ɗani,
Murmushi Rabi"atu tayi a bayyane tace kaji Aysha da wani kidahumanci Allah na tuba ni motar wace iri ce ban hau ba? Tun ina cikin cikin uwata ake hawa motar dani, tunda nazo duniya nake hawa motar har nima nakai minzalin da aka siya min tawa, duk motocin gidan nan saina je an ɗanani a motar sai kace wata sakara, nima na tuƙa kuma na tuƙa wasu,
Amma saita rubutawa Aysha kuje zan hau wata rana yau banajin daɗi kuma banajin zan iya fitowa, Aysha tace tou Allah ya baki lafiya sai na shigo, yayi rabi"atu ta faɗa,
A wechat kuwa saƙonni sosai jishad ya tura mata, yana ta faɗa mata cewa baiji daɗi ba kwana da yawa da bata nan, ya saba suna gaisawa kullum amma ya rasata kwana da yawa, Allah dai yasa lafiya?
Murmushin ƙarfin hali Rabi"atu tayi tare da cewa bawan Allah, goge hawayen da suka ƙara ɗigo mata daga cikin idonta tayi sannan ta fara rubutawa kamar haka!
_Ina nan babu inda naje kawai abubuwa ne yayi yawa_
_Uhum to ya kike ya jin daɗinki?_
_Lafiya qalau, fatan kaima kana lafiya?_
_Da dai sauƙi!_
_Kaima baka jin daɗin ne?_
_Ey mana,_
_Meya sameka ne?_
_Ciwon tunani_
_Ya kuma ciwon tunani?_
_Ey haka ne sunan cutar da ta sameni,_
_Tou kasha magani mana,_
_Ai nama samu sauƙi tunda naji ki,_
_Tou Allah ya ƙara sawaƙe,_
_Amin,_
Daga haka babu wanda ya sake magana,
Washe gari kuwa Rabi"atu ta kasa kalaci saboda tsabar baƙin cikin rashin motar, koda tayi wanka komawa tayi ta kwanta,
Wayarta ta ɗauka danyi chat taga ko ta samu sauƙi, bayan tahau online, itace ta farawa jishad,
_Hello_
_Hi_
_Ya kake?_
_Lafiya qalau, ke fa?_
_Bana lafiya_
_Subahanalla, miya sameki?.........._ 😭
_Mutuwa zanyi_
😳 _Wayyo Allahna na shiga 3 🙆🏻♂ mutuwa kuma?_
_A, a, don Allah ki rufa min asiri kada ki mutu dan kina mutuwa nima mutuwa zanyi Rabi"atu............._😭
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
28/07/2018
21.
Kiran wayar Rabi'atu ya farayi amma saidai ta ƙari ihunta ta tsinke, haka yayi ta kiranta ba tare da ya gaji ba ko yaji wani abu a ransa ba,
Ya kirata yafi sau babu adadi sannan ya haƙura, ita kuwa Rabi'atu tunda jishad yace ta bashi minti biyu zai ɗanyi wani abu tana ganin minti biyun ta cika ta ajiye wayarta tayi tafiyarta club,
Dan tace ai saida waya a hannunta dama zaiyi mata wani lissafin rainin hankali, suna can an raƙashe kamar dai kullum dan yau kam bata dawo gida ba sai da aka fara kiraye kirayen sallah asuba!
A gajiye ta dawo gida mai gadi ya buɗe mata ta shige, dan dama shine yake buɗe mata duk daren da zatayi tana dawowa idan tayi knock zai fito ya buɗe,
Dawowan Ahmad yasa ta fara bi ta baya dan tasan tana kwankwasawa yaji zai fito, tou tunda bayanan yanzun shine take fitarta hankali kwance,
""A gajiye ta shige ciki, tana shiga ta fara cire kayan jikinta ta ɗaura towel, gefen gado ta zauna tare da kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta!
Magana tayi a bayyane cewa lallai bara nayi sallah kafin na kwanta ta ƙarasa maganar tare dayin hamma dan baccine sosai a idonta,
Miƙewa tayi ta nufi toilet tare dayin hamma wata nabin wata, wanka tayi tare da ɗoro alwallah, tana fitowa ta zura wasu riga da wando marasa nauhi,
Sharceciyar hijabi ta zura tare da shinfiɗa abin sallah ta fara nafila kafin a kira sallah tayi, bayan tayi sallah asuba saida tayi karatun alkur,ani mai girma sannan tayi addu'o'i bayan ta gama ta miƙe,
Wurin wayarta taje ta ɗauka tare da dubawa taga tulin missculatay ba tare data dubasu ba ta kashe wayar gaba ɗaya, kwanciyarta tayi ta fara bacci dan yau ji takeyi tana iya kai sallah isha'i a haka,
A ɓangaren jishad kuwa bayan yayi ta ƙiran Rabi"atu bata ɗauka ba haƙura yayi yahau online babu ita ta ɓace kwata kwata, dan haka ya danganawa ransa da salama yayi abinda zaiyi ya manta da wannan lamarin,
Rabi"atu kuwa ansha bacci dan bata farka ba sai bayan azahar, tana tashi alwallah ta farayi ta gabatar da sallah azahar sannan ta fita dan yunwa takeji sosai,
Babu komai a gidan kowa yaci ya lashe a wanke komai an gyara gidan, kicin ma haka ta sameshi komai a wanke a gyara a goge tsaftsaf, mai aikinsu tasa ta sama mata ɗan abinda zataci idan ta gama ta kawo mata ɗakinta,
Juyawa tayi ta koma ɗaki waƙa ta kunna sannan ta nufi toilet, ta daɗe sosai sannan ta fito a daidai lokacin da lami ta shigo ɗauke da abinda ta kawowa Rabi'a ta Ejiye mata a gabanta, sannu Rabi'atu ta faɗa, yawwa lami ta amsa sannan ta fita tare da jan ƙofar ɗakin,!
Gyara zama tayi tare dayin bismillah ta fara cin abinda lami ta kawo mata, bayan ta gama ta ɗauki wayarta ta fito palo, kunna wayarta tayi ta Ejiye a saman kujera sannan ta fita daga palon,
Saida ta gama zagaye zagayenta sannan ta dawo ta ɗauki wayarta tare da zama, miss calls in ta duba amma ga mamakinta kaff jishad ya tara mata su! Allah sarki bawan Allah kaima nayi ta jiranka baka kira ba bayan kasan bana da wani isashsen lokaci,
Amma tunda haka ya faru kayi haƙuri du Allah ta faɗi hakan kamar jishad inne a tsaye a gabanta, daterta ta buɗe saƙonni suka fara shigowa amma hankalinta yafi tafiya taga na jishad saƙon ta fara dubawa kamar haka!
_Ki zama mai riƙe alƙawari da martaba abota duk runtsi duk wuya karki manta da alƙawali!_
_Basai na tambayeki dalilin da yasa baki ɗauka wayana ba wallahi naji a jikina kin fita ne_
_Miyasa ne Rabi'atu? Bayan nace miki ki jirani zanzo zanyi magana dake amma kawai kika wani kama kikayi ficewarki abinki_
_Hmm ni ban isa ba kenan? Ince ga abinda nake so kema wanda kike so shi zakiyi tou yayi ba komai ngd,_
_Kayi haƙuri, kaine fa kacemin minti biyu kuma naga har minti biyu tayi naji shiru_
_Amma ya mukayi dake? Nace miki karki kuskura ki tashi a wurin da kike zama, amma sai kika nunamin ban isa dake ba da kika tashi gaba ɗaya ma sai kika bar gidan!_
_Tou kayi haƙuri kaji,?_
_To babu damuwa nayi, ya kike ya gajiyar club?_
_Lafiya qalau, kaima kana lafiya ko?_
_Lafiya qalau nake,_
_Tou faɗamin abinda kace zaka faɗamin jiya_
_Zan faɗa miki amma saida daddare_
_Miyasa saida daddare?_
_Lokacin nake da lokaci_
_Me kakeyi yanzun?_
_Ina Office kiyi haƙuri kinji ko? Ina aiki yanzun zamuyi magana anjima_
_To Allah ya taimaka,_
_Amin ngd bye 💋_
Murmushi Rabi'atu tayi tare da cewa Allah ya kaimu anjimar naji abinda zaka ce,..........
Kuyi haƙuri da wannan don Allah wallahi abubuwa ne da yawa sunka shamin kai,
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMAN DEE*
26/07/2018
20.
Wani irin wulaƙantaccen murmushi Rabi"atu tayi tare da ɗaga idonta ta kalli sama, ajiyar zuciya tayi, sannan ta goge ɗan guntun ɗigon hawayen da yake mata ƙaiƙayi a saman fuska,
Kaji wani ƙarfin hali? Kaida baka taɓa gani na ba? Bamu taɓa waya ba, daga chat sai chat, kuma mu a ɗaukar lokaci mai tsawo bamuyi magana dakai ba, amma har kake ikirarin rakani zuwa lahira,
Allah sarki, tou bara naji dalilin da zaisa zaka mutu kaima idan har mutuwata tazo, saida ta ƙara goge hawaye sannan ta fara rubuta masa kamar haka,
_Miyasa kace zaka mutu idan har na mutu?_
_Saboda abota, kinsan ni ina girmama aboki_
_Daga abota kawai idan na mutu sai ka kaima ka fece lahira?_
_Lallai haka ne, kin yadda dani?_
_Eh_
_To idan har kin yadda da jishad kuma kina martaba abota idan har kina yin abota dani idan har kin yadda da ni abokinki ne, to ki faɗamin abinda yasa kika ce mutuwa zakiyi, daga lokacin da kika ambanci mutuwa har zuwa yanzun idanuwana da zuciyata sun kasa samun natsuwa, faɗamin don girman Allah miye yasa kika ce haka? Ko nine bakya so ina matsa miki ne?_
_A, a, ni baka matsa min ba,_
_To faɗamin miye kinji?_
_Motar ta!_
_Murmushi jishad yayi sannan yace me motar tayi ne?_
_Yayana ya kwace min key in motar ta ne_
_Tou sai me ya faru kuma?_
_Shine basu dawo min da makullin ba, kuma nayi wa dady magana har yanzun bai sake min magana ba, kuma idan na kira dady ya daina ɗauka, kuma nayi ma momy magana itama bata ce min komai ba!_
_Iyya swry,_
_Ke yanzu saboda motar kike cewa zaki mutu?_,
_Eh_
_To kiyi haƙuri kada ki mutu don Allah, jishad yana tare dake kinji ko?_
_Bani number da zan sameki zan kiraki yanzu!._
_08034528........,_
_Kada kiyi nisa da waya zan ƙiraki anjima kaɗan_
_Ohk_
Bayan ta gama chat da jishad ta rufe dater ta, tunanin maganar jishad takeyi wai zai mutu idan ta mutu, wai don Allah ki rufa min asiri kada ki mutu,
Murmushi Rabi"atu tayi tare da gyara kwanciyarta tana nazarin maganar jishad lallai indiawa sunsan darajar aboki kuma suna da riƙon amana,
Haka tayi ta tunani barkatai gaba ɗaya ta hana zuciyarta sikuni, tana cikin wannan tunanin ne wayarta ta fara ringing, da sauri ta lalubota, ganin number waje yasa ta tabbatarwa ranta jishad ne,
Ɗauka tayi tare cewa hello? Ajiyar zuciyar jishad yayi lokacin da yaji maganar Rabi"atu ta daki dodon kunnensa, ita kuma gaba ɗaya kalasa taji ta lulluɓeta saka makon jin jishad ya sauke ajiyar zuciya!
Shiru sukayi gaba ɗayansu na wani lokaci, sannan jishad yace ya kike ne? Wani iri taji a jikinta, dan haka itama ta ɗan daure tace lafiya qalau, me kikeyi ne yanzun?
Banayin komai kawai ina ɗaki ina hutawa ne, murmushi mai sauti jishad yayi tare da cewa da kyau da kyau, kina tare da momy ne? A, a, na barta a palo ɗazu ina ɗakina ni,
Mi yasa haka? Kawai na ɓata da ita ne, kai? 😳 ɓatawa kuma? Ey mana tunda bazata sa Yaya ya bani makullin motar na ba, jishad yace A, a, baza'ayi haka ba waye yace miki ana ɓatawa da iyaye ne? Aisu ba"a fushi dasu kuma ba'a zuciya iyaye idan sun maka abu ko kaji daɗi ko bakaji ba su sun zama lallai haƙuri akeyi dasu,
Idan suka ɓata maka rai haƙuri kakeyi idan suka maka abun farin ciki ko kai bai zama najin daɗi a wurinka ba, idan harsu dai sunyi dan kaji daɗi ka nuna ya maka daɗi, dan haka maza maza kije ki bawa momy haƙuri kinji ko ƙawata?
Ta ya zan fara bata haƙuri? Ni bazan wani bata ba, a ɓatamin rai kuma nine ma zance ayi haƙuri? Aini sukayi wa laifi sune zasu bani haƙuri, murmushi yayi mara sauti tare da cewa kiyi haƙuri kije ki bawa momy haƙuri idan har kina san albarka a cikin abotarmu,
Aini gaskiya ban iya bada haƙuri ba, nine zan koya miki kada ki kashemin waya harsai naji momy tayi magana, tashi kije da sauri idan kina wurinta kice min gaki kinje,
Kamar baza ta tashi ba jishad yaci gaba da magana cewa ta tashi ita bata san wata rana tace yayi wani abu idan yayi zataji daɗi ai amfanin abota kenan ka nemi alfarma a wurin abokinka yayi maka wannan shine ake kira abota na gaskiya, tashi yau ina so ki nuna min cewa abota na dake abotace mai ƙarfi wanda ko bayan bana nan nayi imani zaki riƙe alƙawari tashi muje,
Miƙewa tayi jiki a saɓule ta fita daga ɗakinta, kai tsaye ɗakin momy ta nufa saida ta shiga sannan ta cewa jishad ta shiga, me takeyi momy? Batayin komai tana tsaye ne a jikin mirrow, to matsa kusa da ita, matsawa Rabi"atu tayi sannan tace na matsa,
Duƙa ki riƙe duka ƙafafuwanta da dukan hannayenki, yanda yace tayi haka tayi, sannan tace nayi, idonki ya kalli saman ƙafafuwanta, hawaye suka ɗigo daga cikin idon Rabi"atu suka sauka a saman ƙafar momy, jishad yace tou kice momy don girman Allah kiyi haƙuri nayi miki laifi kuma nasan ban kyauta ba insha Allah bazan sake ba!
Cikin kuka Rabi"atu ta fara yin yanda jishad yace mata, duƙawa momy tayi tare da ɗago Rabi"atu ta rumgumeta a jikinta tace doughter? Ai kinsan bana fushi dake ni nayi haƙuri bana fushi dake kuma kema kin sani, jishad yana jin momy ta fara magana ya tsinke wayarsa,
Cikin kuka tace insha Allah momy na daina, momy tace tou babu komai kije kici abinci, tou saida ta ƙara rungumar momy sannan ta fita daga cikin ɗakin,
Da daddare kuwa ta ɗauki wankanta ta fito cikin shiga ta ficewa zuwa club, kiran wayar jishad ya shigo a cikin wayarta, ɗauka tayi tare da fitowa daga cikin ɗakin da sauri a palo ta sami momy hannu ta ɗaga mata tare da cewa saina dawo momy,
Tana ƙoƙarin fita daga cikin palon taji jishad yana cewa ina zakije ne? Club zanje, shine bazaki faɗamin ba? Murmushi tayi sannan tace to kayi haƙuri zanje club, gaskiya yau bazakije ko ina ba ina san zanyi magana dake,
Kaiko kayi haƙuri mana saina dawo mayi magana daga baya, cikin sigar shagwaɓa yayi magana cewa kiyi haƙuri ki dawo, ya ƙarasa maganar yana mai ɗan janta, yanda yayi maganar ne yasa Rabi"atu tayi tsaye, umhumm banji kin juya ba, muje, muje mujeee mu koma ɗaki, babu musu ta juya ta koma ciki,
Momy dai taga ta dawo bata san abinda ya dawo da ita ba dan haka bata tambayeta ba, Rabi"atu ta wuce ciki, ƙarar rufe ƙofa jishad yaji haka ya tabbatar masa da ta dawo ciki, yawwwwwwa, ya faɗa tare dajan ta sai kace an danneshi, yanda ya fidda sautin yasa Rabi"atu taji tsikar jikinta gaba ɗaya ta motsu, sassauta muryarsa yayi sannan yace zauna a gefe gado ki jirani zanyi wanka,
Karki sake ki tashi saina fito, amma idan kin gaji da zama na yadda ki kwanta amma bance ki kwanta a saman pillow ba! Sumbatar wayar yayi tare da kashe ta, hakan da yayi Rabi"atu taji kamar a jikinta yayi kiss ɗin, a hankali ta kwantar da jikin a saman gado,
Jishad kuwa yana gama waya da Rabi"atu yana miƙewa wayarsa ta fara ringing, murmushi yayi da gefen bakinsa ganin mai kiransa, a bayyane yace, RESMIN,
Shafa lallausan gashin kansa yayi tare da ɗaukar wayar, yana ɗauka ta fashe da wani irin kuka cikin kuka ta fara cewa wai me nayi maka? Kana canjawa na lura kana rage soyayyana a zuciyarka me nene yake faruwa?
Idan ina ƙiranka a waya sai kaga dama kake ɗauka, yauma sa'a nayi, ta ƙarasa maganar tare da ɓarkewa da wani irin kuka mai kama zuciya, dole tasa jishad ya koma ya zauna tare da cewa kiyi haƙuri aikine yasha min kai da yawa da yawa da wane zanji ne? Kinsan kina raina ni da zan zama mijinki tou miye kuma abun tashin hankali bayan kinsan jisahd yana sanki sosai,
A da kake nawa banda yanzu, kiyi haƙuri kada kice haka nayi miki alƙawari insha Allah zan gyara, lalaɓa resmin yayi tare da ƙara nuna mata girman soyayyarta dake a ransa saida ya tabbatar da ta samu natsuwa sannan ya barta tare da cika mata ranta da farin ciki yabar zuciyarta da dakon kalaman daya ɗora mata!
Tsoki yayi sannan ya Ejiye wayarsa Allah yasa Rabi"atu batayi bacci ba ya faɗa a bayyane, dan wayar ta ɗaukesa lokaci mai nisa ne, a gaggauce yayi wanka yana fitowa ya shirya tare da shiga ɓarin ruwan turare a jikinsa dan jishad ɗan gayu ne ajin farko,
Agogo dake maƙale a ƙaton ɗakinsa ya kalla sannan ya matsa jikin gado da sauri tare da ɗaukar wayarsa!
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*YAYANA NE*
*BY : ANFA*
*_Uhum lallai zamu ga wasar kura gardawa sun ƙoshi da gumba, Allah yasa ki kammala lafiya my fa'iz, amma gaskiya basma sai yaya bilal ya koya mata wayau, dan na lura wayau yayi mata ƙaranci, ina biye dake dani da RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE_*
*sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
29/07/2018
22.
A hankali ta koma ta kwantar da jikinta saman gado, murmushi tayi tare da sauke ajiyar zuciya!
Lumshe idanuwanta tayi a hankali dan bacci takeji sosai,
Babu wani daɗewa bacci mai nauhi ya ɗauketa, cikin natsuwa da alamun kwanciyar hankali a tattare da ita dan tun daga yanayin baccin nata zaka gane babu wani abunda yake damunta a rayuwa,
Bacci yayi mata nisa sosai taji ihun wayarta, ba tare data buɗe idonta ba ta miƙa hannunta ta lalubo wayarta ta shafa idan zata ɗauka sannan ta karata a kunnenta,
Hello, ta faɗa cikin muryar bacci, baby barka da sararawa! Ya faɗa cikin daƙilalliyar murya mai kashe garkuwar jikin mai saurare,
Waye? Kamaladdeen ne, murmushi Rabi"atu tayi tare da gyara kwanciyarta ta ja bargo ta lulluɓe jikinta sosai sannan tace ka ɓoye abunka kawai,
Wayarka ma idan an kira ba'a samu nace ko lafiya dai ko? Uhum yace irin mai fitar da sautin nan wanda yake daɗewa yana yawo a cikin jiki kamar yanda jinin jiki yake guda a cikin jijiyo!
Harma kina da bakin magana? Abinda ke tsoronma mutane kikeyi, umm umm ba haka bane ko a club inma bana ganin ka ai, kene baki so gani na ba, inasan ganinka mana, tou ki faɗawa Aysha ta kawoki inda nake,
Tou babu damuwa sai kajini na gode sosai, yayi ki sarara ruhina, murmushi tayi tare da tsinke wayar ba tare da ta sake cewa komai ba,
Ɗan gajeran tsoki tayi tare da fita daga cikin bargon ta nufi toilet cikin ɓacin rai dan bata so ta farka a daidai wannan lokaci ba tanajin daɗin baccinta kawai ya wani tasheta ba tare da wani dalili ba mtswwww,
Wanko fuskarta tayi sannan ta fito, jikin sockert ta matsa ta kunna lokaci guda kiɗa ya fara tashi a cikin ɗakin, gyara labulayen ɗakinta tayi sannan ta tafi a hankali ta haye saman gado ta kwanta,
Da daddare kuwa saida ta dawo daga club wurin ƙarfe 1:59am ta shigo gida, tana shigowa wayar jishad na shigowa,
Ɗauka tayi bayan sun gaisa yace mata ta hawo online, cikin sakata tace yanzun nan fa na dawo gida ko ɗaki ban shiga ba, gaskiya na gaji bacci zanyi, kaima wai duk yinin ranar nan da nake da lokaci ba zakayi magana ba sai tsakar daren nan haka, tou ni gaskiya baccina zanyi,
Ajiyar zuciya jishad yayi sannan yace tou haka kike so ko? Eyyy ta faɗa cike da tsiwa tou babu damuwa kije kiyi bacci muje na rakaki ɗakin, tou ai sai mu tafi, ci gaba tayi da tafiya tana tafiya yana mata sannu, harta isa ɗaki,
Tou saida safe ta faɗa, shi kuma yace tou kiyi bacci cikin jin daɗi da kwanciyar hankali, muah 💋 yayi mata wanda taji sautin har cikin zuciyarta,
Washe gari da sanyin safe Aysha tayi mata waya zata je Abuja wurin ƙawarta nan da take bata labari wanda suka haɗu *SANADIN SOCIAL MEDIA* da ita, cikin faɗa Rabi'atu tace waike bazaki rabu da wannan yarinyar ba? Ta ɓata miki rayuwa ta gurɓata ki kuma baza ki rabu da ita ba har yanzun?
Uhum to miye kuma na tada jijiyar goshi? Da ban haɗu da ita ba har na waye idanuwa na su buɗe har nasan club kema na jaki nakai ki? Rabi"atu tace ke dakata kada kimin rashin kunya kinji? Ni zaki faɗawa idanuwanki sun buɗe,
Buɗewar idanuwankin banza, a ina kikaje ina aka sanki wa kika gani da idanuwan banzar naki har kike wannan zance sun buɗe mtsww banza daƙiƙiya ƙazamiya ma irinki, ɓurum Rabi"atu ta kashe wayarta,
Lallai yarinya nice kike cema ƙazamiya? Aysha take faɗa bayan taji Rabi"atu ta kashe wayarta wallahi bazan sake biya miki zuwa club ba sai kin gane kuranki,
Tsoki Rabi"atu tayi tare da cewa can keta matse mawa, jaka ni babu ma wani in ƙara ruwa dake kuma club ai nasan hanya tunda kema ba gidan babanki bane,
Kwanciya tayi tare da yin tsoki ta haye duniyar online, gadai yanda firar tasu ta fara ita da friend *JISHAD*
_Hy_
_Murmushi_
_Ya kuma murmushi?_
_Murmushi_
_Wai miye haka kuma_
_Murmushi_
_Haba kayi magana mana sai wani murmushi kake yi!_
_Murmushi_
_To ai sai kaje kayi tayin murmushin ni wallahi harma ka bani haushi_
_Sai anjima_
_Hahahahhh 😜_
😭
_Swry_
_Bara na baki labarina cikakkiyar abokiya_
_To inajinka_ 👂🏻
_Rabi"atu kamar dai yanda na faɗa miki suna na jishad to lallal wannan shine ai nahin suna na!_
👂🏻
_Suna na jishad muh'd kt kerala, mu ukku a wurin iyayenmu kuma dukanmu maza ne a gidanmu ba'a taɓa aihuwar mace ba,_
_Jamnash, jey sai ni, shi jey yana da mata ɗaya sunanta babi, mu "yan yaran malayalam ne, banda aure amma ina da wanda take so na!_
_Ya kuma baka da aure amma kana da wanda take sanka?_
_Eh, akwai ɗiyar abokin babana da take so na, amma fa ni ba wani cancan nake santa ba dan kwata kwata babu wani sha'awar aure a rayuwata,_
_Amma ni ina da wani hali a rayuwata bana san ɓatawa kowa rai ina ƙoƙarin ganin na kare haƙƙin duk wani wanda yake ƙoƙarin kare nawa, wannan dalilin yasa na amince da resmin_
_Da farko ƙanwa na ɗauketa kasancewa yanda abota da shaƙuwa na babana da babanta yake inajin resmin kamar a ciki ɗaya muka fita,_
_Bayan girma kuma resmin ta ɗaura min raki na abota, na barta a matsayin ƙawata munayin abota, amma sai iyaye suka lura kamar soyayya ne, wannan dalilin yasa babana yace na auri resmin, ni kuma na ansa dan ganin farin cikin iyaye,_
_Tou pha, dama dai kuna jin soyayyar junanku a zukata ko ba haka ba?_
_Uhum Rabi"atu kenan ta ya ake gane hakan?_
_Ta ya za'ayi nasan haka? Tunda ni ba ma'abociya soyayya bace? Hasali ma gaskiya bana tare da masu soyayya bare na fahimci yanda sukeji, kaini gaskiya rashin aikin yi na ɗauki masu soyayya, kamarni kaga idan dare yayi bana nan idan kuma na dawo da safe banda lokacin kowa sai idanuwana_
_Murmushi_
_Baya yuwu wa domin ita soyayya wani halittacen abune da Allah ya halittashi a cikin zukanta bayi, uwa da ɗa, miji da mata, saurayi da budurwa, ƙawa da abokiya, a cikin so shima so ɗin ya kasu kashi da dama,_
_Gashi nan dai yana rayuwa kuma yana tafiya daya samu wurin da yayi masa sai kawai ya fake_
_Ke ya kikeji don Allah a kan so?_
_Ni gaskiya bana wani jin komai,_
_Tou yayi manta da wannan maganar, kina karatune?_
_A, a_
_Matakin karatunki fa?_
_Secondry school,_
_Mi yasa baki ci gaba da karatu ba?_
_Ina hutawa ne,_
_Wane irin hutu kuma?_
_Kawai dai banda lokacin karatune!_
_Kiyi haƙuri ya kamata ki koma makaranta_
_Muyi magana anjima zanyi wani abu yanzun plz_
Kafin ta bashi amsa tuni ya dire daga online, dan haka batace komai ba itama ta sauka,
Saƙon Aysha ta gani yana shigowa dan haka ta fara karantawa kamar haka..............,
[13/08, 20:02] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
30/07/2018
23.
Rabi"atu mi yayi zafi haka kamar dai kina jirana? Daga magana sai zagi? Kifa duba abun duka bai kai haka ba amma kin zafafa idan dai har tayi miki zafi tou kiyi haƙuri Allah ya huci zuciyarki,
Tsoki tayi bayan ta gama karantawa tace ba zafi tamin ba tasafa nayi kuma rabuwa da ƙawar SOCIAL MEDIA karki rabu can matsalarku daƙiƙai masha "yan iska ma irin ku,
Koda ta gama karantawa bata bawa Aysha ansa ba dan bata da lokacinta, ajiye wayarta tayi ta shiga sabgogin gabanta,
***
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya tsakanin Rabi"atu da jishad shaƙuwa sosai ta shiga tsakaninsu wanda duk wannan tarayyar suna ganinta a matsayin abota ce,
Zama da jishad yasa Rabi"atu ta fara iya ɗabi"u da kuma al"adu irin na indiawa domin shaƙuwa bata wasa sukayi da jishad ba, wanda babu mai iya kai wani lokaci ba tare da yayi magana da ɗan uwansa ta chat ko waya,
Maganar club kuma yana ƙoƙari wurin ganin ya hanata zuwa amma abin ya shiga jikinta sosai dan jishad ya lura abin dai sai a hankali zata rabu dashi amma badai rabuwa ta lokaci ɗaya ba!
A ɓangaren momy ta lura Rabi"atu ta rage rawar kai gaskiya kuma taji daɗin haka sosai tana ta ƙara addu"a sosai wannan abun farin ciki har Ahmad ta faɗawa,
Aysha kuwa tayi iya iyawarta su shirya da Rabi"atu amma ina Rabi"atu ta nuna mata ita jar wuyace, dan tama manta da lamarin wata Aysha banza,
Ko a club suka haɗu haka Aysha zatayi ta binta amma Rabi"atu ko kulata batayi dan gaba ɗaya ma haushin Aysha takeji,
Ko dady da yazo yaga Rabi"atu ta fara hankali shima yaji daɗi yayi farin ciki sosai yana ƙara addu"a sosai Allah ya shirya,
Zaune take a palo saman kujera wayarta maƙale a kunnenta tana cewa, don Allah nidai ka barni na fita wayyo Allahna, ta ƙarasa maganar cikin sigar sagwaɓa sosai,
Murmushi jishad yayi sannan yace nifa nace bazaki fita ba idan kuma fitar zakiyi tou mu gani, saida tayi "yar ƙaramar jiniya sannan tace nidai gaskiya saina je,
Rabi"atu ni kike cewa sai kinje? Eyyy ta faɗa tare da murguɗa bakinta kamar jishad yana kallonta, ni ko? Eyy nace sai naje, tou babu damuwa Allah ya baki haƙuri a sauka lafiya idan kin dawo kimin magana, ba tare data bashi amsa ba ta kashe wayarta,
Shirinta tayi, tayi ficewarta daga gida saida tasha casunta mai isarta sannan ta dawo gida, bata kira jishad ba kuma batayi chat dashi ba, shima ido ya sa mata bai kirata ba kuma koda yaga tana online baiyi mata magana ba!
Haka suka share kusan wata ɗaya babu wanda yayi ma wani magana, itace ta gaji da gabar tayi masa magana a chat,
_Assalamu alaikum_
_Wassalamu alaikum_
_Ya kake?_
_Shiru_
_Friend ya kake?_
_Shiru_
_Ya resmin?_
_Shiru_
Tayi magana takai goma amma idan jishad ya gani saiya basar gashi fa ya gani amma baya bata amsa,
Wannan abun yayi ma Rabi"atu baƙin ciki dan haka tayi wani irin ihu tare da kwaɗa wayarta a ƙasa, ta fara kuka sosai wanda ihunta yasa momy fitowa daga ɗakinta da gudu,
Amma tana taɓa ƙofar ɗakin tajita rufe ruff, ga Rabi"atu a ciki sai kuka takeyi kamar ranta zai fita,
Dukan ƙofar ɗakin ta farayi tare da cewa daughter buɗe mana, wai miye haka ne Eye? Buɗe buɗe kinji auta, ta ƙarasa maganar cikin sigar rarrashi!
Ina Rabi"atu kuka takeyi babu ji babu gani, dan ta tsani a rayuwarta tayi magana ayi mata shiru, momy tana nan tsaye taji ƙarar fashewar abubuwa masu glass duk wani abu daya danganci hannu zai iya fasawa Rabi"atu saida ta ɓarar dashi a ɗakin nan,
Sannan ta koma gefe ɗaya ta zauna tana mai ci gaba da kuka a hankali mai kama zuciya, momy ta rasa yanda zatayi dole ta haƙura ta koma ɗakinta,
Har gari ya kusa wayewa Rabi"atu bata daina kuka ba kuma bataci abinci ba, ita ta kasa ganewa miye ma take wani tada hankalinta akan jishad ɗin banza? Wata zuciya ta gargaɗeta da ta daina cewa na banza,
Ganin ta kasa samun sassauci yasa ta haƙura ta tashi tana laye kamar sabuwar "yar maye ta tafi tangal tangal gaban wayarta ta durƙusa ta ɗauki wayarta data tsastsage ta ɗauka a hankali ta koma saman gado ta zauna saida ta goge hawayen idonta sannan ta fara ƙiran wayar jishad,
Haka tayi ta kira amma jishad bai ɗauka ba, ta koma chat ta tura masa saƙo yafi a irga amma babu amsa, haƙura tayi ta barshi,
Bayan wasu kwanaki masu dama duk wanda yaga Rabi"atu yasan tana cikin damuwa dan gaba ɗaya ta canja launi, ta rame tayi duhu, bata cin wani abinci kullum tana ɗaki a kulle kamar matar mamaci, duk mai imani idan yaga Rabi"atu sai ta bashi tausayi,
Kullum tana ƙoƙarin kira amma jishad baya ɗauka, momy tayi rarrashin duniya amma ta gaji ta haƙura, yau kam tana ƙoƙarin rubuta masa saƙo,
_Friend don Allah me nayi maka?_
_Kayi haƙuri don Allah, kada ka manta kace na zama mai martaba abota, na zama mai riƙe alƙawari kuma ban saɓa alƙawari ba mi yasa kai ka karya?_
_Shiru_
_Tou babu damuwa, nidai na baka haƙuri kayi haƙuri ka yafe min, nasan nice ta farko dana fara tura maka da saƙon gaisuwa, ina neman yafiyarka ka yafemin....._
_Shiru_
_Daga ƙarshe ina maka fatan alkairi ka dawwama cikin farin ciki da nishaɗi, na barka lafiya......_
Typing... jishad ya fara wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyar Rabi"atu lallai da tasan abinda ake cewa so haƙiƙa da tace son jishad takeyi amma ita a ganinta babu wani soyayya ko ɗaya kawai dai sabo ne da tayi dashi wanda dama ko mutuwa sabo ne akema kuka,
Ta kasa ɗauke idonta a wayar tana jiran saƙon jishad ya shigo,........
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*_Real SMASHER kina bani dariya sosai wallahi Allah yabar mutum da masoyinsa haƙiƙa ina sanki ina matuƙar ƙaunarki har cikin raina, Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana, ubangiji ya barni dake yasa albarka a cikin tarayyarmu!_*
*_Bana gajiya da gaisheki FADEELA LAMEEƊO kina cikin raina kullum kullum ina tunaninki so adadin bugawar zuciyata!_*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
31/07/2018
24.
_Yawwa ngd sosai ki huta_
_Jishad miye haka wai?_
_Wani abu ya faru ne?_
_Ko ɗaya me kika gani ne?_
_Naga idan na ƙiraka baka karɓa kirana ina tunani ko na maka laifi ne?_
_Kinyi laifi ne ke a ganinki?_
_Taya za'ayi na sani tunda bana ganinka? Abinda ka rubutamin dashi zanyi amfani ka daina irin haka babu kyau_
_Aini banga wani mara kyau da nayi ba!_
_A iya sani na mun rabu dakai zamuyi magana idan na dawo, bayan haka bansan komai da ya sake faruwa ba,_
_Tou ai kinga ba laifina bane naki ne,_
_Tou kayi haƙuri don girman Allah_
_Babu damuwa nayi ya wuce, ya kike?_
_Lafiya qalau, naji wani iri da bana tare dakai gaskiya kai abokine mai kirki jishad_
_Babu damuwa kema abokiya mai nagarta ce Rabi"atu,_
_Naji daɗi fa da muka shirya yau zanji daɗi nayi bacci mai tattare da natsuwa kada ka sake ɓatawa dani kaji my friend?_
_Nayi miki alƙawali_ 🤝🏻
_Tou bara nayi wanka zanci abinci yau ina cikin farin ciki,!_
_Murmushi,_
Cikin farin ciki ta miƙe ta nufi toilet babu wani bata wani ɓata lokaci ba ta fito ta zuge cikin shigarta dai data saba, saida ta gama shirinta tsaff sannan ta kira jishad ta shaida masa zata fita anguwa,
Bayan jishad ya ɗauka ta gaisheshi ya ansa cikin sakin jiki, Rabi"atu tace zanje kasuwa fa, murmushi jishad yayi sannan yace ke da waye zakije?
Nida kaina, umm yayi kyau tou ɗaukar min hoton kanki yanzun nan ki tura min kafin ki fita, tou Rabi"atu ta faɗa tare da cewa bara na tura maka yayi ina jiranki,
Bayan ta gama wayar ta fito palo da sauri lami mai aikinsu ta fara kwaɗawa ƙira, da gudunta ta taho tana cewa hajiya gani, murmushi Rabi"atu tayi sannan tace yawwa du Allah maza kimin hotuna suyi kyau sosai, hajiya yau bakya ɗaukar solfie in ne?
Ba buƙatar solfie kedai kawai maza maza kimin karna ɓata lokaci, ansar wayar lami tayi Rabi"atu ta fara jirgewa ana ɗaukarta hotuna, saida ta mata da ɗan yawa sannan ta bawa Rabi"atu wayar da sauri Rabi"atu ta koma ɗaki ta fara tace hotunan masu kyau sosai sune ta turawa jishad,
Gaskiya ban yadda ki fita haka ba, jishad ya faɗa a lokacin da yaga hotunan da Rabi"atu ta tura masa,
_Saboda me?_
_Ai wannan ba wani abu bane,_
_Lallai wannan shine ma komai, dan haka idan har kina san fita sai kin saka hijabi_
_😳 hijabi kuma?_
_Hahaha haba dai sai kace dai wata daƙiƙiya zan saka hijabi? Ai sai kyauyawa suke saka hijabi mu anan idan kaga mace da hijabi to gaskiya bata waye ba! Yoni aka ganni da hijabi yanzu ai dariya ma za'ayi min,_
_Gardama baya cikin tsarin abota, bin umarni shine yake ƙarawa abota martaba a zukanta mutane biyu yayin da abotarsu take ƙara martaba a idanuwansu koda kuwa basa ganin juna!_
_Amma aini bana cewa kayi kuma bana cewa ka bari hasali ma ni babu wani ruwana da damuwarka!_
_Swry,_
_Nidai nace ki saka hijabi idan kuma ban isa ba banda mutunci a zuciyarki yanzun nan ina so ki nuna cewa kai jishad baka is aba! Shikenan sai nayi haƙuri_
_Ni bance baka isa ba!_
_To nunamin na isa minti 3 na baki zan kiraki a imo vidio yanzun nan naga idan kin saka hijabi, karki manta 3minutes kaɗai kinji babbar ƙawata!_
Bata bashi ansa ba ta miƙe tana kuka, da gudu ta fita daga ɗakinta tayi ɗakin momy duk wanda yake cikin gidan nan yanajin kuka Rabi"atu harta ɗauko wata ƙatuwar hijabi mai hannu a ɗakin momy ta fito har yanzun kuka takeyi,
Jikin madubi ta tsaya ta saka hijabin tana mai goge hawayen idonta da tissue banda ajiyar zuciya babu abinda kake ji yana tashi a cikin ɗakin,
Kallon agogo tayi taga har minti 5 dan haka da sauri ta matsa ta ɗauki wayarta, a daidai lokacin da kiran jishad ya shigo, goge hawayenta tayi sosai dan bata so ya gane tayi kuka,
Wani irin kallo yayi mata wanda yasata taji kamar bata da gangar jiki bayan ta ɗauki ƙiran, murmushi jishad yayi sannan yace dan Allah ya kika ganki? Eum?
Shiru tayi tare da sadda kanta ƙasa tana mai ƙara ɓata fuskarta murmushi jishad yayi tare da gyara zamansa sannan yace kallarni yayi maganar tare da ƙura ma daidai saitin fuskarta ido,
A hankali Rabi"atu ta ɗaga kanta ta kalli jishad wani irin gajiyayyen murmushi yayi tare da ɗan lumshe idanuwansa, kallonsa Rabi"atu tayi tare da ƙara sadda kanta ƙasa,
Yi murmushi mana, jishad ya faɗa yana mai ci gaba da cewa nifa idan kina wani ɗaɗɗaurewa gabana faɗuwa yakeyi, ya ƙarasa maganar tare da kashe mata ido ɗaya na haggu,
Murmushin ƙarfin hali Rabi"atu tayi ba dan ranta yaso, ɗan sakin baki kaɗan jishad yayi kamar mai nazarin wani abu sannan yaɗanja leɓonsa na ƙasa ya riƙeshi da haƙoransa yace ki dawo lafiya Allah ya tsare, yana faɗin haka ya Ejiye waya ba tare da ya jira abinda Rabi"atu zatace ba!
Jiki a sanyaye Rabi"atu ta miƙe tayi tunanin cire hijabin tunda ta gama waya dashi amma sai take ganin tana cire hijabin kamar jishad yana kallonta haka ta haƙura ta fito palo amma a ranta tanajin ƙuna mai yawan gaske, wai kamar ita zata fita da hijabi yau itama za,a ganta daƙiƙiya kamar yanda take kallon mutane, dan ita a rayuwarta duk mai saka hijabi daƙiƙi wawa baƙauye ta ɗaukeshi saida ta ƙara share hawayen idonta sannan tace nima yau haka kowa zai kalleni, da wannan tunanin takai kasuwa ta daɗe sosai a kasuwa kuma ta samu duk abinda taje nema dan bata dawo gida ba sai da aka fara kiraye kirayen sallah magrif,
A palo ta samu momy zaune momy ganin Rabi"atu da hijabi yasa ta kasa kai cokalin data ciko da haɗɗen abincin da take ma cin yunwa, sallama Rabi"atu tayi tare da cewa momy sannu da zuwa, kai kawai momy ta jinjina dan ta kasa magana, itama Rabi"atu daga haka bata sake cewa komai ba ta wuce momy ta juya kanta tana kallon Rabi"atu har ta shige ɗakinta,
Allahu akbar momy ta faɗa tare da cire gilashin dake maƙale a saman kyakkyawan fuskarta, Ejiye cokalin abinci tayi tare da miƙewa tsaye tabi bayan Rabi"atu,
A daidai lokacin da Rabi"atu ta fito daga toilet ga dukkan alamu alwalla tayo, momy tace *RABI"ATU?* sunan da Rabi"atu bata taɓa jin momy ta ƙirata dashi ba, ita sunan data sani a bakin momy daga doughter sai auta idan kuma momy tanajin nishaɗi zatace autaress,
Na"am momy, zama momy tayi a hankali a gafen gado sannan tace waye ya sakaki saka hijabi? *JISHAD* ta faɗa a takaice tare da hayewa saman abin sallah dan an fara sallah,
Jishad momy ta maimata tare da miƙewa tsaye tabar ɗakin, tou waye jishad ɗin? Waye shi a ina doughter tasan jishad? Ina suka haɗu? Wane yare ne sunan jishad? Tambayoyi barkatai momy tayi wa kanta wanda ta rasa mai ansa mata su,
Bayan wasu kwanaki faɗa sosai tsakanin Rabi"atu da jishad amma shi bai biye mata ba, saidai taci zungureren rubutu ta tura mishi idan ya gani ya karanta saidai yace Allah ya sawaƙe, wannan abu ba ƙaramin kunna Rabi"atu yayi ba, wai kuma duka saboda yace ta daina zuwa club take ta masifa ita fa babu wanda ya isa ya takura mata a rayuwarta waye shi me yake taƙama dashi da har zai maida ta ƙarƙashin ikonsa? Ganin abun yayi zafi sosai yasa jishad ya fara!
_Allah ya baki haƙuri, ubangiji ya huci zuciyarki_
_Koma kada ta huce ko ta tsaya da zafinta ina dai faɗa maka kai baka isa ka hanani nayi abinda raina yake so ba,_
_Tou naji, kuma niɗin banza, Allah ya baki haƙuri na bari, kije club abinki Allahma yasa ki dawo lafiya kinji ƙawar jishad_
_Ai koma baka ce na dawo lafiya ba lafiya qalau zan dawo,_
_Ni na isa ma,_
Bata sake bashi ansa ba ta miƙe ta fara shirinta, saida ta gama tsaf ta saka kayanta ta bulbule turare a jikinta sosai sannan ta fito, har ta kusa fita daga palo taja tayi tsaye,
_Babu gardama fushi ko ɗaukar zafi a cikin zuciyoyin abokanai gudu biyu, gardama da yawan faɗa yakan ruguza abota sannan kuma ya hanata tayi tasiri, rashin cika alƙawari yakan lalata alƙawarin abokai guda biyu ba tare da abota tayi tsawo ba, ki zama mai riƙe alkawali nayi miki alƙawari ina tare dake babbar abokiya!_
Ajiyar zuciya Rabi"atu tayi bayan ta tuno maganar jishad da sauri ta koma ɗaki ta ɗauki hijabi ta saka, hotuna tayi sannan ta turawa jishad, a ƙasan hoton ta rubuta,
_Haƙiƙa aboki na gari ba abun wulaƙantawa bane komai faɗa aboki ya zama mai riƙe alƙawari tunda baka san ina fita babu hijabi gani nan na saka!_
Tana gamawa ta ajiye wayar tayi tafiyarta,
Lallai zuwa club da hijabi kuma? ,,,,,,🤔
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
01/08/2018
25.
Murmushi jishad yayi a lokacin da yaga saƙon Rabi"atu, kallon hotunan ya ƙarayi sosai sannan ya rubuta ya tura mata kamar haka!
_Ina alfahari dake sosai kuma ina miki fatan alkairi, ki dawwama a cikin farin ciki har ƙarshen numfashinki_
_Albarka ta biki darajar martaba abota da kare haƙƙin abota dan gudun lalacewar zuminci, ngd sosai Allah ya dawo min dake lafiya ayi rawa mai yawa a club_
Bayan tayi parking ta fita ta tasar ma ƙofar da zata sadata da cikin club ɗin haiƙan tana ƙoƙarin shiga taji an take mata hijabi ta baya,
Taja taja dan tafiya amma taji riƙe take gam, dan haka a zuciye ta juya dan ganin waye wannan wanda ya raina mata hankali haka?
Wani lafiyayyen ƙato ne ta gani, ga Aysha da ƙawayenta "yan duniya a gefe suna kallon Rabi"a suna dariya irin dariyar rainin hankalin nan maidai cin rai,
Aysha ce ta fara tahowa wurin Rabi"atu bayan ta gama dariyarta, wannan abu yayi wa Rabi"atu baƙin ciki dan haka Aysha tana matsowa kusa da ita Rabi"atu babu wani ɓata lokaci ta ɗaga hannunta tare da sheƙaƙawa Aysha mari harsai da Aysha ta faɗi ƙasa,
Duk wata ƙawar data biyo Aysha tayo kan Rabi"atu, cike da masifa Rabi"atu tace kai ku dakata, duk wanda tsotsayi yasa ta shigo cikin faɗan nan haƙiƙa tana yankawa kanta tikitin zuwa lahira ne, dan kunsan masu iya magana nacewa duk faɗan da babu ruwanka daɗin kallo gareshi,
Idan kuma kaga faɗan da yafi ƙarfinka to maza ka mayar dashi wasa dukanku a cikinku kowa da Aysha ya sanni dan haka wallahi duk yarinyar da tayi gigin taɓani dukanku babu wanda ban sani ba nasan gidajen iyayenku wallahi saina sa an ɗauremin yarinya an ɗaure uwarta,
Wanda ya take mata hijabi ta juya ta kalla sannan tace kai kuma ya akayi ne? Saida ya sake shaƙa abun mayensa sannan yayi magana cikin maye yace kamal yace ki cire hijabinki karki kuskura ki shiga club da wannan hijabin tunda ba gidan wa'azi bane nan ina fatan kin gane karatun,
A daidai lokacin da Aysha ta taso tayo wurin Rabi"atu tace ni kika mara ko? Ɗan gajeran tsoki Rabi"atu tayi dan ita a ganinta ma ta tsaya bawa Aysha amsa gani takeyi ɓata lokaci ne!
Dan haka ta mayar da dubanta wurin wanda yake mata magana sannan ta kalli hijabin jikinta, tana ƙoƙarin cire hijabin taji gabanta yayi mummunan faɗuwa,
_Ki zama mai riƙe alƙawari ki daina ganin bama zaune a ƙasa ɗaya dake, shi alƙawari girma gareshi idan har kika ɗaukeshi tsakaninki da mutum zaman lafiyarki ki riƙeshi idan kuwa ba haka ba sakayya tana biyowa baya!_
Yanzun idan ban cire hijabi ba bazan shiga ba? Sosai ma kuwa faɗamin tunda kike a duniya kin taɓajin labari wata taje club da hijabi?
Gaskiya bazan cire ba domin ita hijabi mutunci ce sutura ce ga duk mutum mai kishin kansa, haƙiƙa saina shiga cikin club ɗin nan saina ga ubanda ya isa ya hanani idan gidan baban mutumne,
Wata irin dariya yayi sosai tare da cinnawa tabar hannunsa wuta har yanzun cikin maye yake magana, saida ya ƙara "yar gajeriyar dariya sannan yace yo Rabi"atu wane mutunci gareki kuma kishin kanki ai kinbar gini tun ranar zane, a club ɗin nan kinzo daga ke sai gajeran wando rigar da kika saka ko cibiyarki bata rufe ba, mu munfa san komai munsan tal munsan sal tou me kuma za'a ɓoyewa masai dan babu abunda bai gani ba!
Wannan hausa Rabi"atu bata ganeta ba, dan haka tace can matsalarka taja hijabinta da ƙarfi tayi cikin club da saurinta, dashi da Aysha da zugar ƙawayenta suka goya mata baya zuwa ciki,
Duk masifar da akeyi ma Rabi"atu tazo club da hijabi bai sa ta fito ba, kowa sai cewa yakeyi tazo ta ɓatawa yaransu tarbiyya duk masifar nan Rabi"atu bata fito ba wanda take da lokaci ta bada amsa wanda bata dashi ta basar da ko waye,
Kamal kuwa da yake kallon Rabi"atu murmushi yayi dan shidai haka nan Allah ya sani yana san Rabi"atu kuma yanajinta har cikin ranshi dan komai nata da takeyi shidai burgeshi yakeyi, addu"arsa ɗaya Allah yasa ya mallaki Rabi"atu a rayuwarsa, da wannan tunanin ya juya ya wuce ciki,
12:37am tabar club a gajiye Aysha tabi bayanta a zuciyarta tana mai jin baƙin ciki wai Rabi"atu zata dawo mata da aiki baya tana ƙoƙarin taga ta ƙara lalacewa amma shine yau zata zo da wata hijabi a jikinta lallai ya zamar mata dole sai ta tashi haiƙan dan wallahi yanda ta lalace tayi alƙawarin sai Rabi"atu tayi haka koda so ɗaya ne tana san taga an keta mutunci Rabi"atu,
Da gudu ta isa wurin motar ganin Rabi"atu ta shiga motar tana ƙoƙarin rufewa Aysha ta riƙe murfin motar da sauri ta durƙusa ƙasa tare da riƙe ƙafar Rabi"atu ta ɗora fuskarta a sama ta fara kuka, cikin kukan tace Rabi"atu ki rufa min asiri don girman Allah kiyi haƙuri wallahi bazan sake ba kiyi haƙuri dan mutunci iyayenki a zuciyarki,
Rabi"atu zame ƙafarta tayi, da sauri Aysha ta ƙara rungumo ƙafar taci gaba da kuka mai kana zuciya tana bawa Rabi"atu haƙuri, jin hawayen Aysha a ƙafarta yasa taji jikinta yayi sanyi dan haka tace to babu damuwa nayi jeki ina sauri ne bacci nakeji kije,
Miƙewa Aysha tayi tare da kakkaɓe jikinta tana cewa na gode sosai Allah ya kyauta gaba, ba tare da Rabi"a tace komai ba taja motarta tayi tafiyarta,
Dariya Aysha tayi tare da cewa har kin bani tausayi yarinya zaki san dani kike magana sai na zamar dake abun tausayi sai kinyi ta bina fiye da yanda nake binki saina miki mummuman hukunci wanda zaisa kiyi jiyya biyu!
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya kullum shaƙuwa tsakanin jishad da Rabi"atu ƙara wuce matsayin abota takeyi amma ita Rabi"atu bata ma san wani so ba kawai dai tana ɗauka abotace dan bata taɓa so ba kuma bata zauna da wanda ya taɓa soyayya ba sudai abinda sukafi sani kawai shine suyi wanka su tafi club shine aikinsu,
Dan ita dai bata karance karance ko na littatfai ballanta taji yanda ake kwatanta girman so da matsayinsa a zukatan masoya guda biyu ba, kuma bata taɓa haɗuwa da wanda ya faɗa matsalar soyayya ba, tadai san ana zuwa club ne ayi rawa "yan iska kuma sunayin iskancisu mashaya kuma sunayin shaye shayensu barayi kuma suna sacewa ne idan suka ga anyi wa abu ajiyar banza!,
Jishad kuma yayi ƙoƙari wurin ganin ya mayar da Rabi"atu ta koma makaranta dan yana ganin hada rashin aikinyi yasa take wannan zuwa club ɗin banza,
Aiki biyu ya haɗewa Rabi"atu yanzun ga magana da jishad a chat ga karatu yanda Rabi"atu ta canja lokaci ɗaya yasa momy tayi ta bincike da bin ƙwabƙwab har ta gano waye jishad itace ta labarta wa kowa na gidan ta kuma shaida musu yanzun ma Rabi"atu tana karatunta a online, online university,
A ɓangaren Aysha kuwa ta shiga tashin hankali tare da ƙara ɗaura ɗamara dan wani lokaci Rabi"atu takanyi kwana biyu bataje club ba, kuma idan ta tashi zuwa zata shata shareriyar hijabinta yanzun ma abunda ta gane harda niƙaf take sakawa, wannan abun yana ma Aysha ciwo sosai jishad yana ƙoƙarin gyara ita kuma tana ƙoƙari wurin ganin tana warwarewa!
Da sauri ta fito daga toilet dan Aysha tace mata yau zata zo su tafi club dan haka tana sauri wurin ganin ta shirya, tana cikin shirin ne jishad ya kirata, da sauri ta matsa wurin wayarta ta ɗauka tare da karata a kunnenta ta maƙaleta da kafaɗarta,
Me kikeyi ne yanzu? Bana komai, murmushi mai sauti yayi sannan yace ni kuma naji a jikina kamar kinyi wanka ne ina zakije? Idanuwa Rabi"atu ta zaro tare da kallon jikinta, ajiyar zuciya jishad yayi sannan yace mi yasa kikeyin mamaki?
Wai ke me kika ɗauki jishad ne? Shiru Rabi"atu tayi jishad yace ki gama kwalliyar ki kwanta kiyi bacci ko kofar ɗaki bance ki fita ba aikin bacci kawai na sakaki kuma kada ki sake ki tashi saina tasheki na faɗa miki, yana faɗin haka ya kashe wayarsa,
Rabi"atu ajiye shafa man tayi jiki na rawa ta haye saman gado tana hawaye dan ji take kamar jishad yana kallonta ne, daga gefenta taga jishad tsaye wato yana mata gizau, ɗan buɗe idonsa yayi tare da cewa maza ki lulluɓe, innalillahi wa"inna ilaihir raji"un Rabi"atu ta faɗa tare da rufe idonta tana mai motsa bakinta cikin ƙyarma alamar addu"a hannunta ta miƙa taja bargo ta lulluɓe dukanta,
A hankali ta buɗe idonta da sauri ta maidashi ta sake runtsewa tana mai fitar da sautin kukanta, ji tayi kamar jishad yace tayi masa shiru da sauri ta haɗe kukan bata sake ko motsin kirki ba sai bacci,
Ita kuwa Aysha sai ƙarfe 09:23pm ta shigo gidansu Rabi"atu,
Lallai zamuyi kallon wasan kura gardawa sun ƙoshi da gumba, tsaya muga maganar wa Rabi"atu zata bi? Zatabi Aysha ko kuwa jishad zata bi maganar sa ne?
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*_Assalamu Alaikum, zuwa gareku ma'abota karanta littafin SANADIN SOCIAL MEDIA, ina miƙo saƙon gaisuwa ta zuwa gareku kuma ina muku fatan alkairi a duk inda kuke a faɗin duniyar nan,_*
*_Ke kin tambaya ita tayi su sunyi, kinsan kanki tunda har nayi magana dake a farkon labarina nace kar a kuskura ayi me yasa kikayi? Nace a kiyaye me yasa baki kiyaye ba? Wannan labarin da nake rubutawa ba ƙirƙirarren labari ne ba labari ne da ya faru da gaske saboda haka na roƙeki da Allah ki daina danni bana san tashin hankali haka kuma bana san inyi ta abu na ƙaranta amma idan kika kiyaye sai a zauna lafiya gaba ɗaya, na faɗa cewa na roƙa alfarma ne akan wanda abun ya faru dasu nake rubuta wannan littafin ne domin fatakar al'umma banyi danke ba, banyi da ita ba haka kuma banyi dan su ba, kiyayewa na biyu kenan na faɗa karki bari raina ya ɓaci dan zan gwada miki baki da wayau, idan kunne yaji tou fa lallai ganganr jiki ya tsira!_*
*_Ku kuma masu cewa wai wannan hoton JISHAD ne shine da kansa kunce min ɗan wasan film in india ne, tou shi baya film doctor ne a dubai yake aiki,! Hoton dai ɗaya ne shine, shine, shine da kansa JISHAD MUH'D KT_*
*_Gaisuwa da jinjinar ban girma a gareki,! NUSAIBA IBRAHIM USMAN ZANGO, star nucee 360, jamila musa tana gaisheki, na gode sosai da kulawarki a gareni,!_*
02/08/2018
26.
Tun daga palo Aysha take ta fama kwarara sallama, amma babu mai jinta bare ta saka ran za'a ansa mata sallamar, domin dai lami bata nan momy kuwa tana wanka ita kuma Rabi"atu an sata baccin dole!
Jin shiru yasa tayi wa ɗakin Rabi"atu tsinke, da sallama ta shiga ta ƙara nanatawa Assalamu alaikum ta sake faɗa har kusan sau 4 , ganin Rabi"atu batayi ko motsin ba yasa ta matsa bakin gadon tana kiran friend,
Tashin Rabi"atu ta fara yi a firgice ta farka tana mai faɗar innalillahi wa'inna ilaihir raji"un, dan ta kwanta da bacci da tsoro,
Aysha tace lafiya kike? Girgiza kanta tayi alamar ba komai da sauri ta rufe idonta tare da komawa ta kwanta,
Aysha ta sake ɗagota tana mai ƙara tambayarta abinda ya faru take cikin tsoro haka? Ƙara rumtse idanuwanta tayi sosai ba tare da ta sake cewa Aysha komai ba, addu"arta ma ɗaya Allah yasa jishad baiga ta tashi ba dan tasan tayi laifi tunda yace kada ta tashi tayi bacci harsai ya tasheta,
Cikin nuna damuwa Aysha ta sake cewa don Allah wai miye? Ai Rabi"atu kasa magana tayi dan ita a tunaninta idan tayi magana jishad zaiji a jikinsa tayi, dan haka ta basar da Aysha,
Haka Aysha ta ƙari zamanta maganar duniya tayiwa Rabi"atu amma ko ɗaya Rabi"atu bata ansa mata ba!
Dan haka Aysha ta haƙura tayi tafiyarta tare da jin baƙin ciki sosai a zuciyarta wai ita Rabi"atu zata wulaƙanta lallai akwai matsala sai Rabi"atu ta gane bata da wayau dan zatayi maganinta sai ta gane koko ruwa ne!
Sai gab da asuba jishad yayi waya dan tada Rabi"atu, saida ya ƙirata kusan sau 5 sannan ta farka da sauri ta miƙa hannunta saman bedsite ta jawo wayarta,
Herlo ta faɗa cikin muryar bacci, a lokacin data kara wayar a kunnenta bayan ta ɗauka, swry jishad ya faɗa tare da ci gaba da cewa kiyi haƙuri don Allah wallahi abubuwa ne suka sha min kai da yawa sai yanzun na gama abinda nake fatan dai kinji daɗin bacci?
Alhamdulillah ta faɗa daga haka bata sake magana ba! Jin an ɗauki lokaci bata sake cewa komai ba jishad yace zamuyi chat ko? Shiru tayi bata bashi amsa ba, murmushi yayi wanda bai wuce saman lips inshi ba ya sake cewa ina magana pa,
Eh, yaww.............a, cikin murya mai saukar da kasala ya faɗa, murmushi Rabi"atu tayi sannan tace bara nayi sallah zuwa anjima, ohk tom idan kin gama ki faɗamin kinji ko?, to babu damuwa sai kaji , aha nima sai naji..........k....i ya faɗa a shagwaɓe,
Murmushi Rabi"atu tayi bayan ta gama waya da jishad a gajiye ta sauka daga saman gado ta nufi toilet,!
Da mamaki jishad ya juyo resmin ya gani bayansa tsaye cikin yanayin ɓacin rai da nuna fushi sai nishi takeyi kamar ta kada zaki, murmushi yayi tare da yin tattaki zuwa inda take tsaye, jawota yayi zuwa cikin jikinshi ya rungumeta sosai sannan ya sassauta muryarsa cikin sigar rarrashi yace miye?
Kwantar da kanta tayi saman ƙirjinsa cikin kuka tace wace ce kakeyin waya da ita? Murmushi jishad yayi tare da sakin resmin daga jikinsa hannunta yaja zuwa saman kujera ya zaunar da ita sannan ya tsuguna a gabanta hannuwansa a saman jikinta ya ɗora yana kallon cikin kwayar idonta miye ya sake tambayarta a karo na biyu,
Miƙewa yayi tsaye ya matsa shima ya zauna saman kujera daga ɗan nesa da ita sannan yace to ina ruwanki da wanda nake waya ne? Sai ki sakani a gaba kina min tambaya, miƙewa tayi cikin fushi tana mai sakin kukanta sosai tayi hanyar fita,
Cikin tashin hankali jishad yabi bayanta tana ƙoƙarin sauka daga saman benen da zai sada ta da palon gidansu yasha gabanta da sauri ya riƙeta dan yasan tana zuwa tana kuka yaja ma kansa faɗa dan abbunsu baya san ganin ɓacin ran resmin,
Riƙota yayi ya jata suka koma ɗakinshi, cikin rarrashi ya fara cewa haba resmin miye haka? Nifa bana san haka kin sani, to miye ma abun fushi? Cewa nayi bazan faɗa miki waye ba?
Tsugunawa yayi a gabanta ya fara goge mata hawayen idonta sannan yace idan kina so na faɗa miki to kiyi murmushi, ɗan yaƙe tayi murmushi jishad yayi da gefen bakinsa sannan yace gaskiya wannan baimin ba sai kin canja, dariya tayi sosai sannan ya riƙeta a jikinsa yace Rabi"atu ne,
Wane shi? Ta tambayi jishad? Ɗan taɓe bakinsa yayi sannan yace wani ne baki sansa ba, a ina yake ne? Yana kaduna ne, ina ne kaduna? Yace sunan garinsu kenan, bata kawo ranta komai ba dan ita Rabi"atu namiji ta mayar dashi!
Saida ya tabbatar ya saka resmin farin ciki sannan ya lallaɓa ta ta tafi dan hankalinsa da tunaninsa gaba ɗaya ya tafi wurin Rabi"atu, tana fita yayi ajiyar zuciya tare da dannawa ƙofarsa key!,
Wayarsa ya ɗauka tare da hayewa saman gado dan fara chat da Rabi"atu,
Kuyi haƙuri da wannan plz,
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
03/08/2018
27.
Jikin Rabi"atu har kyarma yakeyi wurin ɗaukar wayar jishad, bayan ta shafata ta karata a kunnenta amma batace komai ba!
Tou ya aikai ne? Jishad ya tambayi Rabi"atu, ɗan turo baki tayi kamar tana gaban jishad sannan tayi harara,
Duk da jishad bai ganta ba murmushi yayi dan tunda yaji tayi shiru yasan ɗaya daga ciki tanayi zuciyane dan aɗan zaman sa da Rabi"atu ya fahimceta tana da saurin girmama abu tana da fushi sosai kuma tana riƙe gaba abinda ya fahimta a iya karatun da yayi mata kenan,
Tou hajiyata chat zamuyi ko waya wane kika zaɓa? Duk wanda ka zaɓa shi za'ayi, ohk tom hawo online in baki labari! Tom ta faɗa tare da kashe wayarta!
Saida ta canja kaya sannan ta koma saman gado ta kwanta tare da kunna dater inta, gadai yanda firan tasu,
_Hey 🙋🏻♂_
_Sannu da zuwa_
_Yawwa ya kike ya jin daɗinki?_
_Alhamdulillah_
_Ya momy?_
_Ta tafi Office!_
_Yayi Allah ya tsare!_
_Am3n_
_Am Rabi"atu tambayarki zanyi_
_Ina jinka_
_Yaushe ne ranar aurenki?_
_😳 Aure kuma? "yar cakukula dani za"a ma aure? Haba Allah ya sawaƙe aini wallahi ban isa aure ba!_
_Uhum kece "yar cakukular?_
_Eh mana idan ka manta ni a hoto ko na tashi tsaye na sake ɗaukar maka kaina ka gani?_
_Haba ni wallahi ma akamin aure yanzun ai nasan mutuwa zanyi tunda har yanzu jikina baiyi ƙwari ba! 😢_
_No basai kin sake ɗaukarmin ba_
_To amma kina da saurayi ko shima A, a?_
_Haba Allah ya sawaƙe min inyi saurayi saidai kace wata "yar iska?_
_Gaskiya kuma wallahi keba "yar iska bace!_
_Tou miyasa kikeyin aboki da namiji?_
_Ai "yan iska ne?_
_😳 kenan nima ɗan iska ne?_
_Nifa ba kai nake cewa ba, wasu mazan nake nufi, kayi haƙuri!_
_Tou nayi, amma ni na isa aure?_
_Kam wallahi ka isa ma har kayi yawa,_
_Ya ake gane namiji yayi yawa don Allah?_
_Kaini babu ruwana sai anjima_
_Hahaha don Allah faɗamin ya akayi nayi yawa faɗamin don Allah!_
Sauka Rabi"atu tayi ba tare da ta bawa Jishad amsa ba, dariya jishad yayi sosai tare da miƙewa tsaye yana miƙa, hamma yayi tare da sauke duka hannayensa cikin sauri dan Rabi"atu ta bashi dariya wai ya isa aure har yayi yawa,
Jigun Rabi"atu tayi ta tallabe fuskarta da duka hannayenta biyu ta faɗa kogin duniyar tunani, ko tunanin me takeyi Oho......
***
Bayan wasu kwanaki,
Da gudu Rabi"atu ta fito daga cikin toilet inda wayarta take ringing taje ta ɗauka cike da masifa ta fara magana! Ba tare da ta bari wanda ya ƙirata wayar ya fara cewa wani abu ba,
Babu abinda zaka cemin ina ganin canji tuni ba tun yau ba, dama ance mata sunfi maza riƙon alƙawali duk irin yanayin da nake a rayuwa ban taɓa mantawa dakai ba babu second ɗaya da zai zagaya a harya dawo a jikin agogo ba tare dana tuna dakai ba, ina tunaninka fiye da yanda nake tunanin asarar lumfashin da yake fita daga jikina,
Sassauta muryarta tayi ƙasa ƙasa sosai sannan tace jishad me nayi maka kwana da yawa baka ɗaukar wayana ne Eye? Ta ƙarasa maganar cikin yanayi na tausayi!
Kiyi haƙur.........da Allah rufe min baki ba tare da ta barshi ya faɗi abinda zai faɗa ba, cikin rarrashi jishad yace tou ai kece kika ce na faɗa miki abinda yasa banayi waya dake ko? Bana so banaji kuma ka goge number na daga cikin wayarka komai nawa ka goge a zuciyarka ma ka gogeni nima daga yau na manta dakai!
Kashe wayar tayi tare da rushewa da kuka, banda faɗuwa babu abinda gaban jishad yakeyi danshi a rayuwa ya tsani kansa da yayi laifi wa wani mutum to bare kuma Rabi"atu, cikin tashin hankali ya sake ƙiran wayarta, tana shiga tayi rejecting tare da kashe wayarta gaba ɗaya,
Innalillahi wa"inna ilaihir raji"un jishad ya faɗa lokaci guda yaji jiri yana neman kwaɗashi da ƙasa, gaba ɗaya idanuwansa ma basa gani wani duhu mai tada hankali yake gani a gabansa, addu"arsa ɗaya ma Allah yasa kada Rabi"atu ta canja layi tunda tace kowa ya goge kowa daga cikin zuciyarsa kai amma yarinyar nan mahaukaciya ce da gaske bata san so ba, tou ko Rabi"atu ta fara jin soyayyasa ne a zuciyarta?
Kai A, a, da tana so na bazata faɗi haka ba kai yarinyar nan kanta yana rawa, a hankali ya dafe kansa tare da sa ɗayan hannunsa ya fara laluben hanya,
Riƙeshi yaji anyi ta baya kuma an kwantar da kai saman bayansa, yanajin magana amma baya iya gane ko muryar waye, hannunsa yasa ya jawota ta zagayo gabansa murmushi resmin tayi tare da ƙara rungume jishad sosai cikin damuwa shima yaɗan riƙeta dan itama wata burkutacciya ce,
Kazo muje shan coffie, A, a, jishad yace tare da ƙoƙarin cire resmin daga jikinsa amma ta wani naniƙe ta manne sai kace an zubawa leda wuta, cireta yayi da ƙarfin tsiya daga jikinshi ya wuce ciki a wahale ya faɗa saman gado,
Da gudu tabi bayansa tana kuka saman jikinsa ta kwanta tare da ƙara fashewa da kuka sosai cikin kuka take cewa duk ƙawayenta suna fita da masu sansu amma ita banda ita dama ai tasan ba santa yakeyi ba shi yasa kullum idan tayi masa magana zaice A, a,
Gyara kwanciya jishad yayi sannan yaja resmin zuwa saman ƙirjinsa hannunsa a saman lallausan gashin kanta yace yi haƙuri banda lafiya, ɗagowa tayi ta kalli jishad ido cikin ido sannan tace meya sameka ?
Kamar ya faɗa mata Rabi"atu ta ɓata dashi dan yana cikin damuwa ganin hawaye nabin gefen idon jishad yasa resmin tashi zaune da sauri cikin ruɗewa tace ina yake maka ciwo ne, daidai zuciyarsa ya nuna mata tare da cewa nan ne!
Tou ai gani nazo ko? Nice a zuciyar kuma gani a gabanka miye wani damuwa taso muje....ta kama hannunsa alamar ya taso, cikin tsawa yace bazanje ba haba,,,, ga dugu resmin ta sauƙa daga saman gadon tana goge hawaye, tausayi ta bashi dan haka yace resmin, tsayawa tayi ba tare data juyo ba,
Sauka yayi daga saman gadon bayan ya miƙe tsaye ne ya gyara zaman necktail insa hannunsa yasa ya gyara gashin kansa har lokacin resmin tana tsaye still kuka takeyi,
Murmushi jishad yayi a daidai lokacin da ya tsaya gaban resmin, gajiyayen kallo ya sauke mata wanda yasa taji ƙafafuwanta basa iya ɗaukarta da sauri ta riƙe jishad tana mai sauke ajiyar zuciya, riƙeta yayi a gefen damarsa sannan suka fara tafiya a ransa kuwa ji yake dama Rabi"atu ce,
Dakel yake driving dan gaba ɗaya hankalinsa yana kaduna shi babbar matsalar data fi damunsa Rabi"atu tace kowa ya goge kowa daga cikin zuciyarsa wannan abu shine abinda yafi ɗagawa jishad hankali, ɗan gajeran tsoki yayi a bayyane yace wallahi yarinyar nan mahaukaciya ce ƙwafa yayi tare da taka burki dan resmin tace ya tsaya!
Saida resmin ta gama abinda takeyi sannan suka tafi sunɗanyi yawo sosai saida ya tabbatar yasa farin ciki da natsuwa a zuciyar resmin sannan ya mayar da ita gidansu, saida ta sunbaci goshin jishad ta wuce murmushin ƙarfin hali jishad yayi sannan yaja motarsa a gajiye ya wuce gida dan samun mafita,
Bayan kwana biyu momy ce ta shigo ɗakin Rabi"atu dan bata san abinda yake faru da ɗiyarta ba, ita dai kullum kawai zatayi tafiyarta Office kuma lokacin da zata dawo a gajiye take dawo bata da buƙatar komai sai hutawa,
Tana shigowa tajiyo Rabi"atu a toilet tana ta kwarara amai da sauri ta shiga toilet in tare da tambayar lafiya? Amma sai ƙara yunƙurin amai taƙeyi babu abinda yake fitowa sai irin wannan aman da hausawa kece ma aman kumallo wanda mutum bayayinsa sai idan baici abinci ba!
Doughter lafiyarki kuwa? Cikin kuka ta riƙe momy tare da cewa jishad ne, mi yayi miki jishad in ne? Momy jishad, cike da tashin hankali momy ta ƙara tambayar Rabi"atu miye jishad yayi miki wai?
Shine shine shine......... Tou naji kiyi wanka ki sameni ɗakina kuma kizo min da wayarki, tou kawai ta faɗa momy ta fita daga ɗakin ta nufi ɗakinta,
Babu wani daɗewa Rabi"atu tayi wanka, bata shafa ko mai ba ta zura kayanta wayarta ta ɗauka ta nufi ɗakin momy, da sallama ta shiga momy na zaune a gefen gado amsawa tayi Rabi"atu ta shiga cikin ɗakin,
Wuri momy ta nunawa Rabi"atu ta zauna, tashi momy tayi taje ta haɗo mata lafiyayen tea ta ciko a wani ƙaton kofi gaban Rabi"atu ta tsaya dashi sannan tace maza shanye sannan ki bani labari!
Kwanciya Rabi"atu tayi tare da cewa na ƙoshi, tasan halin Rabi"atu da kafiya dan haka ta ajiye tace kirawo min jishad in, momy ni nayi faɗa dashi mun ɓata kuma nace kowa ya manta da kowa,
Tou ni bani numbershi na ƙirashi babu gadma ta fara karantawa momy number jishad bayan ta gama momy ta fara kiransa, babu wani ɓata lokaci ya ɗauka suka gaisa da momy ta faɗa mishi ita maman Rabi"atu ce, ajiyar zuciya jishad yayi tare da cewa ina Rabiatu?
Tana nan lafiya qalau, wannan abu yabawa jishad haushi wato lafiyarta qalau, Eh lallai wannan ko shaƙuwa bata sani ba bare kuma tasan *SO* momy ta katse masa tunaninsa ta hanyar cewa fatan kana lafiya? Lafiya qalau ina Rabi"atu take?
Gata nan, momy bata waya, miƙawa Rabi"atu waya tayi cike da zumuɗi ta fara magana dan tanajin babu daɗi kwana biyu da basu tare, mantawa yayi da sunyi wani abu ya basar ya buɗe sabon pegi ya rufe wancan dan babu fa"ida taɓo abunda ya wuce nanata zance shikesa a ƙara cakumewa da dambe, ƙawata ya kike? Lafiya qalau ya kaduna?
Alhamdulillah, ya club ya karatu? Komai alhamdulillah, yau zamuyi chat ko? Eyyy ta faɗa tou babu damuwa muyi magana anjima ina Office kinji ko? Tou babu damuwa na gode yawwa sai anjima ki huta lafiya, na gode sosai a gaishe min da kowa hada resmin tou babu damuwa zataji,
Wani irin ihu tayi bayan ta kashe wayar tare da ɗaukar wannan tea in da momy ta Ejiye tunda ta kafa kanta a kofi saida ya ƙare ta sauke kofin ihuuuuuuuuuuuuuu wuuuuuuu tayi tsalle ta haye saman gado ta haye tare da ɗaga kanta sama ta buɗe duka hannayenta tana mai farin ciki, momy yau ina cikin farin ciki inajin nishaɗi sosai na shiga sabuwar rayuwa sabon da sabon farin ciki,
Murmushi momy tayi tare da cewa lallai nima ina cikin farin ciki doughter ta samu masoyi, sauko da kanta tayi ƙasa ta durƙusa kusa da momy ta riƙeta sannan tace ko ɗaya babu wani so kawai dai naji daɗi ne,
Momy tace ai idan ka ɓata da mutum ka shirya dashi idan har kaji farin ciki wannan shine *SO* saukowa tayi daga saman gado tare da cewa haba babu wani nan Allah ya sawaƙe min nayi soyayya sai kace wata sakara saina ƙara girma tana faɗin haka tayi waje, da gudu ta isa ɗakinta tana zuwa ta kunna waƙa taci gaba da caskaɗewa har ta ƙagara dare yayi tayi chat da jishad🤸🏻♀ yau zataji daɗi zatayi bacci cikin farin ciki 🧖🏻♀,
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
04/08/2818
28.
Saida ta gama caskaɗewar ta sannan kuma ta koma palo dan yau jinta takeyi kamar wata sabuwa,
Yinin ranar haka Rabi"atu ta yini cikin farin ciki, dan yau ji tayi ma dare yayi mata nisa bata palo bata ɗakinta bata ɗakin momy sai zagaye gidan takeyi tana jin kyakkyawan nishaɗi!
Ana kiran sallah magrib saida ta dafe cikinta ɗif da abinci sannan ta wuce ɗakinta, ruwa ta watso tare da ɗoro alwallah tana fitowa ta zura doguwar riga ta atamfa,
Hijabi ta zura tare da shinfiɗa abin sallah ta fara sallah! Saida tayi sallah isha"i shafa"i da wutiri ta tashi wurin,
Cire hijabinta tayi ta ninke ta ɗauke abin sallah cike da zumuɗi ta haye saman gado ta buɗe dater ta,
Jishad itace ta fara tura masa saƙon gaisuwa, bayan ya gani shiru yayi, Rabi"atu shiru shiru har wani lokaci jishad bai ansa ba, dan haka ta sake tura masa nan ma shiru,
Shima babu amsa kuma yaga saƙon, kasa haƙuri tayi ta fara ƙiran wayarsa, userbusy tun 08:38pm take kiran jishad har 09:58pm busy wannan abu ya hayaƙa Rabi"atu sosai bata sanma da waye yakeyin wayar ba!
Haka tayi ta kiran jishad harta gaji tayi zuciya, ya za"ayi yace mata zasuyi chat amma kuma ya kama wata wayar rainin hankali, ji tayi gaba ɗaya gidan yayi mata ƙunci dan haka ta fara tunanin zuwa club amma kuma sai wata zuciyar tace da kije ai gara kiyi bacci tunda idan ya gama abinda yakeyi zai tashe ki,
""Da wannan tunanin tayi bacci, amma koda safe data tashi babu miss call in jishad a wayarta, ta koma online shima babu reply na saƙon data tura masa,
Bata sake masa magana ba ta saka masa idanuwa dan taga iya gudun ruwansa, haka aka sharari kusan sati ukku babu jishad babu labarinsa gashi tana ganinsa online amma baya mata magana, wani maƙoƙo taji yazo ya tare mata maƙoshi har ta rasa ta ina yawun bakinta zai wuce, haƙura tayi ta rubuta,
_Mtswwwwww_
❤ _Kai amma na gode 💋_
_Mtswwww_
_Na gode sosai babbar ƙawata_
Tunani Rabi"atu ta fara to kodai jishad baisan tsoki ba? Wata zuciyar tace mata ya sani faɗa masa tsoki kike masa, gaskiya bai sani ba, tunda har wani cewa yakeyi ya gode,
Kiyi ta rubuta masa shi da kansa sai ya gane abinda kike nufi, A, a ba haka za"ayi ba daina saka tsoki, haka dai tayi ta tunani tare dayin gardama da zuciyarta daga baya kuma taci gaba da typing...
_Kai miyasa kwana biyu ka manta dani ne?_
_Kinji babu daɗi ne?_
_A, a, ni banji wani babu daɗi ba kawai tambaya nayi,_
_Hahaha, to ko kina so na ne?_
_Tirrr Allah ya sawaƙe inso ka_
_Murmushi, to wa kike so?_
_Ni wani nake so daban_
_Kai amma nayi miki murna Allah yasa alkairi, insha Allah kika tashi aure zanzo har nigeria saboda ke_
_Nima nayi maka alƙawali zanzo har india ranar aurenka_
_Kuma kamar kinsan na kusa yin aure_
Saida Rabi"atu ta ɗauke lumfashi, wani irin tashin hankali taji yana dirkokoni a cikin zuciyarta, shi kuma jishad yaci gaba da cewa,
_Gobe ma ake nikka ina!_
_Shiru_
_Wallahi shi yasa na zama busy_
_Shiru_
_Kuma ga resmin tun kwana da yawa tana nan gidanmu_
_Banda lokacin kaina kinsan Resmin kishi gareta ko namiji nakeyin waya dashi zata zo ta zauna a kusa dani ne, chat ma haka nakeyi tana jikina tana kallon komai shi yasa kika ga na ɗan manta dake wannan kwanakin_
Wani irin ihu rabi"atu tayi ganin jishad yana typing da sauri ta miƙe tsaye tare dayin wani irin wurgi da wayarta, innalillahi wa"inna ilaihir raji"un,
Goge hawayen idonta tayi tare da komawa a hankali ta zauna, wai ita jishad yake faɗa mata wata tana kwanciya a jikinsa, wato saboda resmin ya ɗan manta dani wannan kwanakin, jinjina kanta tayi lallai jishad ya raina mata hankali matuƙa!
Lallai idan na tsaya yana ci gaba da turomin irin wannan shirmen nasa zuciyata zaiyita karta ba tare da nasan dalili ba!
Wurin wayarta ta nufa danjin tana ringing, niko nace wannan waya da taurin kai kike, tana tsugunne a gaban wayar tana kallo jishad ne yake kiranta amma tana tsugunne taƙi ɗauka hawaye kawai ke zirga zirga a kumatunta,
Haka jishad yayi ta kiran wayar amma Rabi"atu bata ɗauka ba, shi kuma ya ɗauki alƙawari da zuciyarsa ko zai mutu yau bazai daina ƙiran Rabi ba harsai ta ɗauka dan yaji yanayin data shiga,
Ganin abun bana saiti bane yasa Rabi"atu ƙarfin hali ta ɗauki wayar cikin kuka tace hello, cikin rarrashi jishad yace to miye kuma muna chat kin wani shareni? Idan ke nayi ma saikiyi ta cewa nayi shiru miye abun fushi kuma a ciki? Ai ba soyayya mukeyi ba ko?
Cikin shashshekar kuka tace Ey, jishad yace to ko kin fara so nane baki sani ba? Kinga kishi fa yana ɗaya daga cikin alamomin so, ko kema kin faɗo baki sani ba? Faɗamin inji? Cikin kuka tace Allah ya sawaƙe ni wallahi babu wani san da nake maka,
Ƙaryane gashi nan kinayin kuka dan nace miki zanyi aure, to ina ruwana da aurenka auranka banza! Murmushi jishad yayi tare da cewa gaskiya ne auren banza ni kuma naki bana banza bane a wurina, ni ina sanki kuma ina san duk abinda kike so a rayuwa ni banji baƙin ciki ba kince min kina da wanda kike so ba amma shine ni harda wani cewa matatar banza, zansa resmin ta ramanin yarinya,
Cikin masifa tace kaje ka sakata ko ance maka inajin tsoro ne, dariya jishad yayi sosai sannan yace ki riƙe waya resmin tana zuwa,
Maganar resmin Rabi"atu ta jiyo cikin waya tana cewa kai da waye kakeyin waya? Kallonta jishad yayi amma baice mata komai ba yadai tsareta da idanuwansa masu firgita mata,
Uhum? Ka tsaya kana kallona kawo wayar na gani mana, murmushi jishad yayi tare da saka wayarsa a aljihun wando shi ya rungume resmin ta baya ya ɗora kansa a saman kafaɗarta hannunsa yana saman cikinta kinci a abinci baki jirani ba ko? Cewa nayi naga wayarka, murmushi yayi sannan yace tou ai na gama wayar ne baki gani ba, tou waye kayi waya dashi? Wani abokina ne yace zaizo gobe wurin saka ranar aurenmu shine nake magana dashi,!
Tou kawo na gani, haba haba muje, ya saketa daga jikinsa yana jan hannunta suka fita, bayan sun fita ya ciro wayarsa daga cikin aljihu dan bawa Rabi"atu haƙuri ga mamakinsa yaga ta tsinke kiran,
Lallai akwai matsala, resmin ki jirani ina zuwa na manta wani abu a ciki, yana faɗin haka yayi ciki da gudu, tsoki resmin tayi itama tare da bin bayansa cikin salon kwarewa,
Tun kafin ya ida isa ɗakinsa ya fara kiran Rabi"atu, itama cikin ɓacin rai ta ɗauki wayar tare da cewa baka da gaskiya miyasa data tambayeka baza kace mata nice ba, wato kanajin tsoro ko?
Ba tsoro bane, ni banajin tsoro ko fargaba kawai de ke nakejin tsoro baki so na, da kince kina sona kuma zaki yadda ki aureni babu wani abinda zan boye tunda ba zunubi bane, kuma ba haramci bane dan na aureki, sassauta muryarsa yayi ƙasa ƙasa yace ki yadda dani Rabi"atu ni gaskiya bazan ɓoye miki komai ba ina sanki wallahi so mai girma wanda bazan iya kwatanta girmansa a cikin zuciyata ba, ki amince dani nayi miki alƙawarin aurenki idan har ina nunfashi,.ya kika c...........
Ihu Resmin yasa ya juyo da gudu ta fita tana ihu wanda sanadin ihun ya fito da kowa na gidan kafin jishad ya fito daga cikin ɗaki tuni gidan gaba ɗaya sun taru a palo ana tambayar resmin abinda ya faru?
Banda faɗuwa babu abinda gaban jishad keyi, cikin tashin hankali ya iso yalwataccen ƙaton palon gidansu tun kafin ya sauko daga saman benen palonsu yaga kowa na masa kallon hadarin kaji,
Wurin resmin yana nufa ya riƙeta a jikinsa tare da tambayarta lafiya? Kwace jikinta tayi daga jikinsa tayi wurin ummu maman jishad, ta shige jikinta tana kuka mai kama zuciya!
Cikin damuwa yace resmin meye ne? Cikin kuka resmin tace ummu kalleshi yana wani nuna baimasan abinda ya faru ba! Abbu ne yayi gyaran murya tare da cewa duba jishad ni kake so ka watsawa ƙasa a ido ko? Tou wallahi auren resmin babu fashi tun kafin na haifeka muke zumincinmu zuwanka bazaisa ka lalata zumincin dake tsaƙaninmu ba,
Jishad zaiyi magana abbu ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu yana mai ci gaba da cewa kake mata alƙwalin aure to ka rubuta ka ajiye babu kai babu auren kowa bayan resmin kana cutar kanka ne tunda kasan mace ɗaya kaɗai zaka aura a duniya kana yaudarar zuciyarka ne kuma akanka zata ƙare, yana faɗin haka ya juya gaba ɗaya kowa yabi bayan abbu jishad kaɗai aka bari tsaye a cikin palon,
Gyara bakinsa yayi tare da sauke ajiyar zuciya, a hankali ya juya ya koma ciki saida ya watsa ruwa saboda tirin zafin dake fita daga cikin jikinsa, bayan ya fito ya shirya ya ci gaba da kiran wayar Rabi"atu, a kashe yajita,
Tunanin sa kiran wayar momy tunda yana da numberta dan ta kirasa kwanaki, amma haƙura yayi ya barta dan baisan irin al"adarsu ba sudai a nasu al"adar dan mai san ɗiyarka ya ƙira wayarka yace a haɗasu suyi magana ba damuwa bane,
Yau farin ciki baibar gidansu jishad sunyi wadataccen bacci ba, tunda safe banda fushe fushe babu abinda yake tashi kamar dai yanda sukeyi a al'adance dangi na kusa dana nisa wanda suka samu halattar nikka na jishad sunzo akasha shagalin saka ranar aurensa da resmin,
Haka aka tsaida kwanakin aure, farin ciki a wurin resmin babu ya kamarta, amma banda jishad kuma kowa yasan yana cikin damuwa haka dai aka sha shagali kowa ya kama gabansa suna masu addu"a Allah ya nuna musu lokaci lafiya.....,
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki*
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
04/08/2018
29.
Jishad kuwa ya gwada kiran Rabi"atu amma karatun ɗaya waya a rufe, baida yanda zaiyi dole yasawa ransa sawaba,
Rabi"atu kuwa damuwa kullum sai abinda yayi gaba dan gaba ɗaya ta canja layi kan wayarta dan tun ranar da jishad yaƙi faɗawa resmin ko wace ce ita abun ya babba mata rai,
Yanzun kam babu wani maganar zuwa club ta maida hankalinta ga karatunta duk wani abu na shirme ta tattarashi ta zubar,
Bata da wata damuwa, damuwa ɗaya wanda tafi damunta yanzun banda tunanin jishad kuma ta goge numbobinsa kuma bata riƙesu a kanta ba kuma ta duba a wayar momy babu sai yanzun ta gane lallai ta jibga baban kuskure!
Gaba ɗaga Rabi"atu jinta takeyi kamar matacciya, dan ta tabbatar yanzun gangar jikinta da ruhinta basu da wani amfani, mutuwa itace kawai tafi cancanta da rayuwarta,
Lallai idan de wannan shi ake kira so haƙiƙa baiyi ba, baya da wata rana da zuciya zata so mutumin da bata taɓa gani ba, mutumin da yayi nisa sosai taɓa daidai zuciyarta tayi tare da cewa gaskiya bakiyi ma kanki adalci ba,
Kin cuci kanki kuma kin tashi aiki domin gab kike da tarwatse wa, ban baki haƙuri wallahi kuma bana rarrashinki kece kika jawo ma kanki saboda tsabagen san kai irin naki,
Rushewa tayi da wani irin gigitaccen kuka cikin muryar kuka tace miyasa da jishad ya tambayeki kina sansa kika ce A, a? Gashi yanzun ya tafi baya sake dawowa har abadan duniya,
Sassauta muryarta tayi sannan tace kuma kika yaudari kanki kika goge hotunan shi, da sauri ta miƙe tsaye dan jin wani abu yana biyu daga cikin maƙoshinta wanda bata san ko miye ba!
Layi ta fara yi kamar wanda tasha kwaya tayi tatul da layi ta fito taga ɗakinta tana tallabe da ƙirjinta ɗayan hannunta kuma tana dafe bango, cikin murya kamar ta "yan maye ta fara cewa ai laifinki ne ya tafi yayi miki bye bye kila sai kin mutu zaizo gaisuwa,
Momy ta ɗaga muryarta tana ƙira, cikin wata irin murya mai tada hankali, momy dake sallah taji faɗuwar gaba dan jin muryar da Rabi"atu ta kirata dashi,
A wahalce ta zauna saman step na ƙarshe wanda tana sauko ƙafarta ta shigo palo, sabbatu tayi tayi wanda ni bana iya ganesu bare na rubuta muku su,
Momy na sallame sallah ta fito da sauri rabi"atu ta gani zaune sai amai takeyi, subahanallah ke kuma taki lalurar da amaye amaye take zuwa?
Kafin ta ƙarasa kusa da ita tuni ta tafi luuuuu,,, cikin tashin hankali da ɗimaucewa ta ƙarasa wurin da sauri, riƙeta momy tayi ta fara jijjigata lafiya doughter?
Ke lafiyarki ? Doughter miye haka ne? Ai doughter bata san momy nayi ba, cikin birkicewa momy ta sauke Rabi"atu ta nufi ɗakinta cikin sauri
Tana shiga wayarta ta ɗauka ta fara ƙiran dady babu wani ɓata lokaci ya ɗauka ko gaisuwa babu momy ta fara rattafa masa halin da Rabi"atu take ciki, faɗa dady ya farayi sosai tare da cewa yarinya tana cikin matsananci hali baza ki kaita asibiti ba sai ki tsaya kirana?
Maza a kaita asibiti mana, da sauri momy ta ajiye waya ta fito tana kwalawa lami mai aiki kira, da taimakon Allah suka saka Rabi"atu motar momy taja suka tafi asibiti Allah yakaisu lafiya dan momy bata gani haka nan kawai take tuƙin,
A asibiti taimakon gaggawa aka bawa Rabi"atu dan ceto lumfashinta da yake ta faman kai kawo, bayan komai ya lafa momy ta tambayi likita me yake damun ɗiyarta ne?
Likita yace su sameshi Office, bayan sunje Office wurin zama ya nuna mata ta zauna, bayan "yan rubuce rubucen na ma aikantan jinya sukeyi shima yayi nashi a saman takarda gyara zaman gilashin idonshi yayi sannan yace hajiya kwantar da hankalinki,
Da ido momy ta tsareshi, shi kuma yaci gaba da cewa ba wata damuwa bace ɗan tunane tunane take sakawa ranta idan ta daina zata zauna lafiya idan kuma bata daina ba zata iya jefa kanta a matsala Allah ya kyauta,
Amin momy ta faɗa, doctor ya bama momy wata "yar takarda yace magunguna ne a nemo su, ansa momy tayi ta fita ba tare da tace dashi komai ba, dan ta lura ɗan iska malamin jinya ne komai tsaye yake faɗa a mutu ko rayuwa,
Tana fita ta bawa lami kuɗi da takardar tace ta samo wannan maganin, ansa tayi cikin girmamawa ta tafi, ita kuma momy ta koma ɗakin da aka kwantar da Rabi"atu,
A takaice dai kwanan rabi"a biyu a asibiti aka sallamesu tare da bawa momy shawarwari dan ganin Rabi"atu ta kaucewa faɗawa matsala,
Ahmad kuwa ya kira momy an haɗashi da Rabi"atu yayi mata tatas yace tunda yake a duniya bai taɓa ganin mahaukaci irinta ba, soyayyar ƙarya soyayyar SOCIAL MEDIA, idan ma banta take daƙiƙiya uban waye yake soyayya da mutumin da bai sani ba,
Cikin sanyi tace Yaya nifa ba soyayya nake dashi ba, kawai ina tunanin sa, Ahmad yace banza wannan ai shine so, an faɗa miki indiayawa suna auren wanda ba yarensu ba? Mahaukaci ya rainaki yana can ya manta da lamarinki, saboda daƙiƙanci kina ganin ita wannan sakarar ƙawar taki { Aysha }
*SANADIN SOCIAL MEDIA* ta samu ƙawa ta lalata mata rayuwa ta gurɓata mata tarbiyyar da iyayenta suka bata, har tayi nasara wurin ɓata taki tarbiyar,
Ke kuma naki lissafin soyayya saboda doɗewar basira, goge hawayen idonta tayi sannan tace yaya ai well come back in layika na zanyi nasan zai kirani, kinji wani jakkancin kuma ana faɗa miki rashin fa"idar abun kina nema ƙara mayar da kanki ruwa, ƙasa ƙasa yayi da murya sannan yace yarinya kiyi haƙuri ki goge wannan ɗan iskan a ranki kiyi addu"a ubangiji ya baki miji na gari,
Nidai wallahi bazan yi haƙuri, ke Rabi"atu saurara a faɗa miki ko a bari duniya ta faɗa miki? Ki manta da wannan jishad in ƙarya kindai ji na faɗa miki,
Tsoki Rabi"atu tayi tare da kashe wayar, miƙawa momy wayarta tayi tace wallahi saina yi well come back layikana nasan wata rana jishad zai nemeni, ita dai momy bata ce komai ba ta fice daga ɗakin,
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya kwanci tashi asarar mai rai kullum Rabi"atu babu tunani saina jishad ta shige ɗaki ta rufe tayi ta kuka abinci ma wahalar ci yake mata ga ɗaya tabi ta kakkaɓe tayi duhu,
Momy tayi rarrashi da ban magana har ta gaji ta fita harkarta, ita kaɗai take rayuwarta tare da tunanin jishad duk daren duniya idan zatayi bacci,
A ɓangaren jishad kuwa kullum da tunanin Rabi"atu maƙale a zuciyarsa idan bai manta lissafin ba yau kusan 7mouths rabonshi da ita, lallai ya zamar masa dole ya nemo Rabi"atu dan tayi masa alƙawarin zuwa bikinsa kuma gashi lokaci ya ƙarato,
Lallai yayi alƙawari yau ko zai mutu sai ya kira wayar momy, danshi tun lokacin da yake kiran Rabi"atu baya samu yama daina tunanin kiran wayarta kwata kwata amma a daren yau saiya raya zuciyarsa da jin muryar Rabi"atu, addu"arsa ɗaya kada Rabi"atu ta ɗaukesa mai ƙarya,
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
05/08/2018
30.
Rabi"atu kulle a ɗaki banda kuka babu abinda takeyi, tun safiya an ajiye mata abinci bata ci ba, saidai lami ta ɗauke wani flet in ta ajiye wani amma yanda ta Ejiye haka take ɗaukar kayarta,
Yaya Ahmad ya ƙirata ya mata nasiha yayi rarrashi amma Rabi"atu tace idan dai akan jishad ne yama daina wahalar da bakinsa wurin rarrashi dan bazatayi haƙuri dashi wallahi,
Shima fadeel ya ƙirata babban yaya ma ya kira amma duk a banza dama dai Ahmad ne yafi shiga rayuwarta danshi ya tsani yaga tana cikin damuwa ko murguɗaɗɗiyar hanya yanzun zai tashi hankali,
Kuma koda tayi well come back babu kiran jishad saida na kamal shima data ɗauka taji shine tsoki tayi ta kashe wayarta, ya kirata ya tura saƙo amma bata bi ta kanshi ba!
Zaman gidan yayi mata ƙunci dan duk lokacin da ta shiga ɗaki a daidai irin lokuttan da take chat ko waya da jishad ji takeyi kamar zuciyarta zata fito daga cikin gurbin da take!
Kusan kwana biyar jishad yana kiran wayar momy amma a kashe yakejinta, shima dai addu"a ɗaya Allah yasa momy batayi fushi ta canja layika ba!
Rabi"atu tana kwance a saman gado tana baccin wahala dan gaskiya wannan bacci baza"a kirashi da baccin jin daɗi ba! Aradu na wahala,
Aysha tsaye akanta tana kallonta cikin tausayawa ko ba komai gaskiya Rabi"atu ta canja ta kakkaɓe kaf tayi duhu,
Jiki a sanyaye Aysha ta zauna gefen Rabi"atu ta fara tashinta, idanuwanta ta fara buɗe a hankali ta sauke idanuwanta a kan Aysha, murmushin ƙarfin hali tayi tare da cewa yaushe kika zo ne?
Cikin ladabi Aysha tace shigowata kenan kuma gidan babu kowa na haɗu da lami a waje tace min zataje kasuwa ne, Friend mi ya sameki ne? Ta ƙarasa maganar tana mai ɗiga hawaye daga cikin kwarin idanuwanta,
Murmushin ƙarfin hali Rabi"atu tayi itama tare da goge hawayen da suka ƙwararo daga cikin idanuwanta dan wannan aiki shikenan ɗaya idan dai idanuwanta biyu,
Gyara zama Rabi"atu tayi tare da rushewa da wani irin gigitaccen kuka, cikin tashin hankali itama Aysha ta fara kuka ba tare da sanin dalilin da yasa Rabi"atu ke kuka ba!
Saida Aysha tasha kukanta ta gaji sannan tayi shiru dan ita Rabi"atu bata san kuka yana da wahala ba, dan ita a halin yanzun dariya tafi mata wahala tafi jin daɗin kuka 100% akan dariya,
Toilet Aysha ta shiga ta wanko fuskarta sannan ta dawo dab da Rabi"atu ta zauna cikin sigar rarrashi tace miye wai kike ma kuka? Cikin kuka Rabi"atu tace *_SOYAYYA CE_* zaro idanuwa Aysha tayi sosai tare da cewa waye ya baki ita?
*_JISHAD_* a ina ya ganki? Bai ganni ba, a ina kika sanshi? *SANADIN SOCIAL MEDIA* shiɗin waye shi? Kamar yanda na faɗa miki daga haka bansan komai a game dashi ba!
Mi yaja miki? Waye yakai ki? Mi yasa ki yadda da ɓoyayyan masoyi? Kila ma kina iya ganin ƙarya ne babu wani jishad wani can daban ya samu numberki dan ya latsaki,
Wata irin shaƙara Rabi"atu tayi wa Aysha tare da ci gaba da ƙuma mata kanta babu ji babu gani kai mata tunkuri takeyi kamar dai yanda raguna sukeyin faɗa, Aysha cewa takeyi mi nayi miki kuma? Au baki ma san laifinki ba ko?
Wani irin kukan kura Aysha tayi ta kwace kanta dan ganin jini yana fita daga hancinta, da gudu ta fita daga gidan gaba ɗaya ko takalma bata tsaya ɗauka ba, tana fita Rabi"atu tace tsinanniya mai baƙin baki wai ni zatace wa babu jishad a duniya ai da kin tsaya da yau sai nayi rinciff da uwar iskanci,
Naga ubanda zai ƙara cewa babu jishad a duniya yaga yanda zan nannaɗawa uwarsa sirdi in hau saman banza inyi ta sukuwa bisa tsinan, waini zai azo a kafa min baki a ɗaukeni a tafi dani talla a duniya na samu saurayi *SANADIN SOCIAL MEDIA* na susuce akansa, tsoki tayi a daidai lokacin da ta shiga toilet tana ci gaba da cewa da wane zanji mtswwww,
Haka rayuwar kunci taci gaba da faru a wurin Rabi"atu kullum babu lafiya hawayen idonta harsun ƙare zuciyarta harta bushe saboda masifar tunani dan yanzun idan aka bata abun zane saita zana jishad dan kullum tana ganinsa a ƙoƙon kanta dan a idonta bata ganin komai saishi, yawan tunaninsa yasa ta koma kamar wata zararra,
Momy a Office aiki yasha mata kai ga damuwa tayi mata bake bake a ranta tunanin zuci ya dameta banda tunanin Rabi"atu babu abinda takeyi dan yau taji wani irin labari daya ɗaga mata hankali taji labarin wata yarinya data haɗu da wani balarabe shima dai through social media wai ya aureta saida ya mayar da ita zawara yayi mata saki ukku kuma babu wanda yasanshi dan aurenma ba'a tare ba anan gida nigeria akayi komai da ance za,ayi party wai aka fasa, niko nace wane irin party tunda abinda za"ayi partyn danshi yasanshi,
To ina ga Dougter? Ita data mutu kan jishad? Yanzun idan haka yayi mata wane hali ɗiyarta zata faɗa? Innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, momy ta ambata a daidai lokacin da tunaninta ya dawa dan jin wayarta na kuka,!
Juyawa tayi ta kalli inda wayar take, zare ta tayi daga jikin sockert in data maƙala chargy sannan ta ɗauki wayar tare da karata a kunnenta!
Sallama tayi kamar yanda ta saba a duk lokacin da aka ƙirata, ansa sallamar yayi tare da ci gaba da miƙo gaisuwa wurin momy, ya kuma bata sani shine jishad idan babu damuwa don Allah ta haɗashi da Rabi"atu, momy tace tou pha lallai kam ina Office yanzun amma insha Allah na koma zan haɗaku ɗan gajeran tsoki momy tayi tare da cewa ka kira wayarta mana!
Momy kwana biyu ina kira ai babu, A, a, ka kirata yanzun zaka samu insha Allah, godiya jishad yayi tare da yima momy sai anjima da addu"u"o i sannan ya kashe wayarsa,
Yana kashe kiran momy ya fara ɗanawa number rabi"atu kira, babu wani ɓata lokaci kibiyar network tayo kaduna, Rabi"atu na kwance a ƙasa saman kafet taji wayarta na ringing bata tashi ba kuma batayi niyar ɗauka ba dan a tunaninta kamal ne!
Haka jishad yaci gaba da kiran wayar ba tare da ya gajiya ba dan yau duk duniya baya da natsuwa sai ya kashe wannan ƙishirwar tasa ta hanyar jin muryar Rabi"atu!
Ganin an ɗauki tsawon lokaci ana abu ɗaya yasa Rabi"atu tashi cike da masifa ta nufi wurin wayar ta ɗauka ba tare da duba number ko suna ba, wai kai da Allah baka ƙyaleni? Ni wallahi bana san mayata haba mtswww,
Allah ya baki haƙuri ai ban ɗauka har yanzun kinayin fushi dani ba, da sauri ta sauke wayar daga saman kunnenta sannan ta duba number taga ba number kamal bane, mayar da wayar tayi saman kunnenta sannan ta fashe da kuka mai kama zuciya!
Shiru jishad yayi shidai baice tayi shiru ba kuma bai bata haƙuri ba sannan kuma bai kashe wayar ba, kuka tayi tayi shi kuma ya saka wayar a speaker ya ajiye a gefensa yaci gaba da aikinsa,
Saida Rabi"atu ta gaji da kukanta sannan tace hello, inajinki, jishad ya faɗa, ashe kanajina kayi min shiru, tou na sani ko sha"awar kuka kike yi ne? Ai bari nayi ki gama naki uzirin sannan kiyi nawa, danshi duk lokacin daya samu matsala da Rabi"atu ko sun ɗauki wani lokaci basuyi magana ba baya cewa anyi kaza da kaza kawai da ranar yake amfani,
Majina taja sannan tace shine ka daina kirana ko? Yanzun kece kika kirani ne? Tou miyasa ka manta dani tsawon wattanni da dama, saboda baki san amfanin so ba amma ga dukkan alama zuciyarki ta baki labari to duk ma ba wannan ba ya kike ya jin daɗi ya mantawa da jishad?
Ni na ɓata dakai, aini bana ɓatawa da mace dan ita rauni gareta itace zata jawo faɗa da kanta amma idan ka biye mata daga baya sai tayi da nasani, kinga kuwa tunda nine babbanki dole kiyi haƙuri dani, ya karatu?
Shiru tayi, shi kuma yaci gaba da cewa ina maganar alƙawalinmu? Kince zaki zo ranar aurena, da gaske zaki zo? Saida ta ƙara goge hawayenta sannan tace Eh zanzo tou kindai gani lokaci yayi ko? Na sani kinmin alƙawali zaki zo? Murmushi tayi sannan tace na maka alƙawali idan aka hanaki fa? Duk da hakana nan zanzo,
Tou babu damuwa muyi magana anjima kinji ko? Tou na gode nima na gode, tana gab da ajiye waya yace yau bazaki gaishe da resmin ba? Murmuguɗa baki tayi kamar tana ganinsa sannan ta kashe wayarta,
Murmushi jishad yayi lallai Rabi"atu ta ladabtu amma yanzun ƙyaryane Rabi"atu tace bata san sa! Miƙewa yayi cikin farin ciki tare da dafa table in gabansa ɗan taɓe bakinsa yayi tare da ɗaga duka kafaɗunsa alamar ko Oho ko miyasa yayi haka nima dai bansani ba!
Tou haka dai rayuwa taci gaba da tafiya kwanaki suna tafiya dan bikin jishad yazo kuma Rabi"atu ta miƙe ƙayar baya zarr tace sai taje india, dady da momy hankalinsu ya tashi sosai kuma sunce Rabi"atu bata zuwa amma Rabi"atu tace ko za"a sake maimaita yaƙin badar sai taje, dan haka ta shiga cuku cukun yin viser tafiya bama ta sauraren kowa,
Lallashin duniya dady yayi amma Rabi"atu tace wallahi abu ɗaya zai hanata zuwa india shine mutuwa amma madamar tana lumfashi sai taje india wallahi yama za"ayi kamarta da girmanta tayi ƙarya, sudaiyi haƙuri tunda kawai zataje gaskiya sai taje,
Momy tayi juyin duniyar nan tare da faɗawa Rabi"atu labarai masu tada hankali game da india amma wallahi Rabi"atu tace saidai idan taje ta mutu, Ahmad yayi masifa yayi lallashi amma daga baya Rabi"atu daina ɗaukar wayarsa tayi daga ƙarshe ma a black list ta sakashi,
Aysha kuwa taji labarin Rabi"atu zataje india amma batace mata Allah ya kiyaye ba kuma bata bata haƙuri ba bare ta kirata dan ita yanzun tsoro Rabi"atu take bata, amma ta yaba haukan Rabi"atu fiye da nata haukan, kawai *SANADIN SOCIAL MEDIA* ta wanke ƙafafuwa ta tafi india saboda hauka?
Bakaje ba ma sun tsafeka ina ga ka isko su gidansu? Ita kuwa Rabi"atu shirye shiryenta takeyi hankalinta kwance tare dajin shauƙi zata haɗu da babban abokinta dan jishad yace itace babba abokiyar ango, wannan matsayi da jishad ya bawa Rabi"atu ya bala"in burgeta, shirinta takeyi cike da kwarin guiwa da jishad yake ɗirkaka mata!
Lallai nikam nace anya naje india? Amma dai kila nayi ƙoƙari idan dai har *RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE* zataje nima naje, dani da ɗaukanci marubutan dake cikin nagartacciyar ƙungiya wato *BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION* masu zuwa ku faɗa da wuri dan shirin tafiya kunsan bizar india wahalar samu take!............
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
06/08/2018
31.
Uhum a ɓangaren jishad kuwa yabi rankataf dangi "yan uwa da abonkan arziƙi zuwan babban abokiyar ango a gari mai girma da karamci wato india,
Jishad ya ƙara da cewa Rabi"atu masoyiya ce ta haƙiƙa wanda taci a yaba mata da irin namijin ƙoƙarin da zatayi dan zuwa wurinsa saboda tayasa murnar aurensa,
Yace kuma Rabi"atu tana girmama shi sannan kuma tana martaba sa, haka kuma tana girmama ƙasar india ne saboda shi,
Faɗa abbu yayi masa sosai tare da masa gargaɗi cewa lallai wurin yayima yayimansa zai ɗauko kansa masifa, lallai idan ya ɗauko Rabi"atu wallahi saidai ta ƙare kansa badai su ba
Jishad yace Abbu ita iyayenta basu gujemu ba? Tsoro ko fargaba suka sake ɗiyarsu ta taho india domin mu? Wannan fa abun dubawa ne kuma ya kamata ayi ƙoƙari kowa na gidan nan ya nunawa Rabi"atu karamci domin itama tana ɗaga daga cikin ahalinmu nan da kwanaki kaɗan itama zata zama surukar gidan nan!
Wani irin tarwatsetsen mari Abbu ya saukewa jishad tare da masa gargaɗi lallai idan har ya sake gigin kwatanta baƙar fata da sunan surukar gidansu haƙiƙa saiya gundulewa jishad harshe,
Jishad dafe inda Abbu ya gagara masa mari yayi, sannan ya kalli Ummunsa sannan yace wallahi sai tazo sai ta zo kuma inga yanda za"ayi a mayar da ita nigeria, sai tazo anyi bikin shikenan ma sai amin auren dole? Nifa ma resmin ɗinnan kowa yasan bana santa ina biyayya ne kawai daga tana yaya dani shikenan dan hauka saita juya soyayya?
Yanda fa resmin takeji baƙin ciki a ranta idan taji ko ta ganni ina magana da mace ita Rabi"atu tafi tajin baƙin ciki mai ƙuna a ranta, sakin inda aka maresa yayi sannan yaci gaba da cewa kallon banza harara ko hantara duk wanda yayi ma Rabi"atu wallahi sai yabita nigeria ya koma can da zama,
Yana faɗin haka ya juya ya fara tafiya yana cewa ni tunda nake a rayuwa ma ban taɓa ganin namijin da ake ƙoƙarin yima auren dole ba saini, harma nayi biyayyar kuma ni baza"abi abinda nawa zuciyar yake so ba? Hmmm Allah ya kawomin ke ƙasar india da alkairi,
Kuka resmin ta farayi danjin maganganun jishad Abbau ne yace saurara saurara "yata daina kuka ki barni dashi, cikin kuka resmin tace ina da kyawuna fari dogon hanci ga yalwataccen gashin kai bugu da ƙari a tara mata dubu samun kamar resmin aikine ya samu ya sameni a sauƙaƙe yake wani cika bakin baya so na,
Bayan yasan yanda maza suke wahala na sauraresu amma banda lokacin kowa ina laifin wanda yace yana sanka? Abbu yace karki damu resmin ki barni dashi ya ƙarasa maganar yana mai gogewa resmin hawayen idonta,
Jishad kuwa shigarsa ɗakinsa wanka yayi ya zuge cikin shiga mai kyau da tsari wanda take nuni dashi cikakken ɗan gayu ne ajin farko da ƙarshe uwa uba kana kallonsa kasan cikakken ɗan bokona idanuwan sa sun buɗe sosai yana da aji daidai na misali kuma yana da wadatar wayewa bawai irin "yan jagaliyar india ba,
Haka ya fito yazo ya wucesu zaune a palo suna ta ƙullawa da warwarewa Abbu kuwa sai ƙara nanatawa yake baiyi ma iyayensa gardama ba bai haifi ɗan da zai tsallake maganarsa ba, kuma yake ma maganar auren dole ai nima auren dolen akamin da uwarsa amma gamu nan bulumbuƙui dan haka ya ƙara jaddawa resmin ta saka ranta a inuwa anayin auren zai manta da lamarin wata Rabi"atun banza can,
Murmuahin farin ciki resmin tayi Abbu da Ummu da sauran "yan uwan jishad suka ci gaba da bata ƙwarin guiwa suna masu ƙara jaddada mata shirme ne maganar Rabi"atu babu baƙar fatar da zai yadda da wannan shirmen na ya aura ɗiyarsa wa ba"india ko kuma ya barta tazo daga nigeria zuwa india,
Shiri fa sosai Rabi"atu takeyi babu wasa, kokonto ko fargaba babu ɗaya a zuciyarta haiƙan take gyara duk wani abu wanda tasan zaisa jishad yaji babu daɗi ko kuma danginsa suyi mata kallo hadarin kaji ƙoƙarin gyara ɓaraka takeyi dan saka farin ciki a cikin zuciyar jishad,
Suturu masu tsada da kyau Rabi"atu ta ɗinka dan zuwa india dasu ta ɗinka kaya sunkai kala 15 jikkuna takalma da gyaluluwa da sabbin hijabobi da baƙaƙen riguna masu fitinan nan kyau, a ɓangaren sarƙa da "yan kunne "yan hannu da zobe duk dai abinda tasan zai ƙarawa tafiyarta armashi aradu saida tayi,
Takuma ibi ƙana nan kayanta masu kyau amma ta ɗauki after dressis guda 3 wai zata riƙawa jishad gayu dasu idan taje, hardai gyara jikin Rabi"atu tayi wannan tafiya fa momy da dady sun kashi nera dan kuɗi ne dama an tarasu gasu nan addu"a kawai akeyi Allah ya kawo abinda zaici su na alkairi,
Tunda sunyi juyin duniya Rabi"atu kada taje tace ko za"a maimaita yaƙin biyapara zango na biyu a kanta sai taje, dan haka suka sakawa ransu salama tare da mata addu"ar dawowa lafiya!
Duk kayan data jida momy tace ta ragesu dan kwana ukku ta bata amma sai Rabi"atu tace lallai momy kinsan ko tafiyar awa nawa ce daga nigeria zuwa india? Yaushe naje yaushe na huta yaushe na dawo? Momy tace faɗamin nisan tunda ke zaki ni banje ba, Rabi"atu tace koma dai miye idan har kika ga banyi wata 4 ba tou lallai jishad ne yace in dawo,
Shiru momy tayi tabi rabi"atu da kallo, ganin kallon yayi yawa yasa Rabi"atu tace nasan fargabarki wai kar in mutu ko na halaka ko? Wallahi lafiya qalau zan dawo cikin aminci da yardar Allah, gaban momy taje ta duƙa ta riƙe dukan hannayenta sannan tace nayi miki alƙawari zan dawo a duk lokacin da kika ce momy, ta ƙarasa maganar tana mai kallon cikin kwayar idon mahaifiyarta,
Cikin damuwa momy tace babu komai doughter ki dawo duk lokacin da jishad yace, saboda na lura yafini matsayi a wurinki, kin fifitashi akaina, ina faɗa miki kina gyara min zance, idan yace ki zauna can gaba ɗaya kenan zama zakiyi tunda ni dadynku da "yan uwanki bamu da sauran amfani ko kuma baki da buƙatarmu tunda kin samu jishad,
Dariya tayi tare da jijjiga hannun momy tace momy momy haba waya isa kuma? Ina tare da uwata maganin kukana tafiyarma idan kikace a fasa aisai a barta dan a zauna lafiya, murmushi momy tayi tare da cewa tou ki barta ɗin mu gani, dariya Rabi"atu tayi sannan tace kedai mubar wannan maganar zan tafi wankin kai saina dawo,
Hijabinta ta zura tare da ɗaukar makullin motar momy tayi gaba, momy tabi bayanta da kallo tare da ɗurara mata addu"a,
An wanko kai fa ya wanku kuma anyi masa gyara yanda ya kamata bata saka attach ba saboda tana da wadataccen gashin kai sosai dama iskanci ne da gyara club martabarsa yasa Aysha tasa Rabi"atu take daƙon gashin doki akanta,
Ƙafafuwanta da hannayenta kuwa sunsha zanen kunshin zamani mai kyau da daɗin kallo karfa ku ɗauka wasar aljanu akayi mata a ƙafarta? A, a, kunshi mai aji wanda ko resmin ta ganta saita ƙyasa,
Haka ta dawo gida cike da farin ciki, dan jinta takeyi gobe tayi mata nisa, a daren Ahmad ya kira momy ya buɗe wuta harshen sa har hucin zafi yakeyi saboda bala"i,
Wai ya za"ayi tabar Rabi"atu ta tafi india, aishi wallahi ya ɗauka zancen banza ne ya rantse da Allah da ya dawo yaga ubanda ya isa yabarta zuwa wurin wani banza can daban, wannan ai haukane baligar ɗiyarta zata bari ta tafi india wurin wani ƙaton banza can daban? Kila ma babu wani auren da zaiyi akwai iskanci ne su kuma sun saketa saka saka zata taka jirgi daga nan har india sai kace bata a kowa,
Tsoki momy tayi tare da kashe wayar dan ita ɓata mata rai ma yakeyi, tana cikin wata damuwar zai ƙara ɗura mata wata, Rabi"atu dake gefen momy ta kece da dariya tace hukuncin ki yamani daɗi dama kin zagi ɗan iska, fara gwaigwayon maganar Ahmad tayi saida ta gaji sannan tace sakarai da wata maganarsa can akamar mace takai masa shaƙa!
Momy dai bata sake magana ba, dan haka Rabi"atu ta tashi ta koma ɗakinta, tana zuwa wayarta ta ɗauka ta ƙira jishad, suka sha fira cikin jin daɗi ya faɗa mata cewa gobe suna tare yana faɗa mata irin yanda zaiji daɗi idan ya ganta, sun dai daɗe suna fira tare da nunawa juna muhimmanci junansu, amma wannan aiki duk na jishad ne domin ita dai Rabi"atu babu abinda ya dameta burinta kawai ta ganta india taga jishad ido da ido masu cewa ƙarya ne babu jishad ta ƙaryata su,!
Sun daɗe suna fira daga baya sukayi sallama da juna, bayan sun gama wayar ne ta kwanta zumuɗi ma ya hanata tayi wani wadataccen bacci, asubar farko ta farka ta sheƙaƙawa jikinta wanka, ta ɗanyi shafa sama sama, bayan ta gama ta gabatar da sallah asuba dan lokaci yayi, tana gamawa tayi addu"a sosai saida tayi karatun alƙur"ani mai girma tare dayin shahararin addu"o"i Allah ya sauketa india lafiya,
Baƙar riga ta saka mai kyau da tsada na fitar tunanin mai karatu, gyale kuma ta ɗan yanashi ta sagalashi yayi kyau sosai kamar dai yanda meelat musa takeyi nata idan ta saka baƙar riga, kai masu karatu tsayawa faɗa muku irin kyawun da Rabi"atu tayi aradu rubutun ya zuƙen chajin waya!
Takalma ta saka masu kyau wanda suka dace da rigar jikinta "yar ƙaramar sidebag ta kawo ta kafa, ɗan madaidaicin glashi ta saka mai kyau wanda ya dace da kyakkyawar fuskarta kuma yayi kyauɓda shigar da tayi, kallo ɗaya zakayi wa Rabi"atu kasan tayi kyau kuma "yar gayun sabon zamani ce, saboda Rabi"atu tasan mustahabben ɗaukar wanka tasan sunnonin tasan wajibinsu kuma tasan farillan gayu, kuma tasan duk abinda yake warwaresu,
Cikin takon manyan mata ta fito, ta nufi ɗakin momy wanda tuni itama ta gama shirinta dan itace zata kai Rabi"atu abuja, lami itace ta fito da kayan Rabi"atu aka jibgasu a motar bayan an gama shirya komai momy ta shiga mazauni driver lami tayi musu fatan alkairi momy taja suka ibi hanya dan zuwa binnin tarayya,
Suni sa Abuja lafiya cikin yaddar Allah, momy tana nan bata tafi ba har aka gama komai da komai tayi ƙarfin hali wurin ƙara yiwa Rabi"atu nasiha sosai, tare da mata fatan alkairi, 10:00am jirginsu Rabi"atu ya ɗaga dan zuwa india,
Bayan sun tashi momy ta kira wayar jishad ta sheda masa Rabi"atu sun taso yanzun nan, godiya yayi ma momy tare da addu"a Allah yasa su iso lafiya, bayan momy ta gama waya da jishad taja jikinta cikin damuwa ta koma motarta taja dan komawa kaduna garin gwamna,
Taf lallai kam nima dai bara nayi ƙoƙarin samun chargy kafin jirginsu Rabi"atu ya gama shawagi a saman sararin samani nima na harba india dan tsinto labari!
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
ni matsalata ɗaya kar naje india na kasa cin abincisu shine kaɗai damuwana, dan gaskiya bana wasa da cikina kece sheda dan an baje a babban palonki, kindai san gejin meelat musa, 😜 tunda nayi babbar loma a gabanki kin gani, Asmeenat zeeyan, REAL MAI DAMBU da leema surayyahms da maryamu tare da sweety ummuherrny aradu duk baku gani ba! 🙇🏻♀
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE* naje bacci 🧖🏻♀ idan kun isa india ki sanar dani 🤓
*JAMILA MUSA* 🤸🏻♀🤸🏻♀ zataje indiyasco!
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*_Assalamu Alaikum! Fatan kowanku kuna lafiya mabiya littafinfi sanadins social media? Ina muku fatan alkairi, don Allah akwai wata baiwar Allah da mukayi magana da ita, inajin ku biyu ne nayi muku alƙawari nace zan neme ku daga baya saboda aiki yamin yawa tou ban ajiye numbers inku ba, whatsapp ina ya lalace a taƙaice dai idan Allah yasa kunga saƙona tunda kuma kunsan kanku tou kumin magana sai muyi magana na gode sosai!_*
*_HARSASHEN SO ina baku haƙuri naji na kwana biyu kuyi haƙuri ku daina min bahagguwar fahimta, baza ku gane yanda abun yake ba, amma insha Allah a satin nan zaku ci gaba da jina insha Allah ngode sosai ku sarara_*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
07/08/2018
32.
Banda shawagi babu abinda jirginsu Rabi"atu yakeyi a saman sararin samana!
Rabi"atu kuwa zuciyarta fes abunta yau zata haɗu gata ga jishad,
Tunani barkatai a cikin kanta da kuma zuciyarta, ko a mafarki batayi tunanin zata taɓa zuwa india ba, amma yau cikin hukuncin Allah gata zataje india *SANADIN SOCIAL MEDIA*
Zataje zuwa na farko kuma mutumin da bata sani ba bata taɓa gani ba, amma tayi amanna dashi kuma tanaji a jikinta jishad alkairi ne a gareta kuma babu cutarwa ko zalinci!
Tunani sosai takeyi sai taji jikinta yayi mata sanyi gaba ɗaya taji tausayin kanta dana iyayenta, ajiyar zuciya tayi tare dayin magana a bayyane cewa!
Allah kasa "yan uwan jishad su amsheni da karamci ubangiji kasa suji daɗin gani na kuma suyi alfahari dani su ƙaunace ni sosai kwatankwacin son da jishad yake min, Allah ka hanasu ƙyama ta, su soni sosai kamar dama sun sanni,
Da wannan tunanin bacci ya ɗauke Rabi"atu dan a daren jiya batayi wani wadataccen bacci ba saboda zumuɗi,
A ɓangaren momy kuma ta koma gida lafiya cike da tunanin ɗiyarta ta kuma bita da addu"a tare da mata fatan alkairi, tana shiga garin kaduna Office ta wuce kawai,
Jishad kuwa tunda momy ta masa waya cewa Rabi"atu ta taso ya kasa samun natsuwa yana cikin farin ciki yau zaiga jishad 2 dan ko a wayarsa jishad ya rubuta mata a jikin numberta,
A cikin jirgi! Jirginsu Rabi"atu saida ya kwashe awowi 2 da wasu mintina sannan ya dira a filin jirgin dubai dan sauke wasu fasinjoji, anan su Rabi"atu suka ɗan huta duk mai wani ɗan uzirinsa yayi,
Saida sukayi awa ɗaya a dubai sannan jirginsu ya ɗaga dan zuwa babban birnin india,
Jishad kuwa da tunda momy ta faɗa masa yake ta faman duba agogo sai kace wanda aka shiga da matarsa titiyar gaggauwa, sai safa da marwa yakeyi a cikin ƙaton ɗakinsa sai yakai bango sannan ya dawo yana ta fama irga awanni danji yakeyi kamar ya zama tsuntsu yaje ya ɗaukota,
Saida lokaci yakai masa yanda yake so sannan ya shiga wanka, wanka yayi ya ƙara gurjewa ya durje sannan ya goge jikinsa da ruwan wanka mai shegen ƙamshi,
Saida ya tabbatar ya wanku jikinsa har wani santsi santsi wankuwa yakeki kamar jariri kwana biyu da aihuwa, da ɗan gajeran towel ya fito a hannunsa yana goge jikinsa cikin farin ciki! Amma fa ya ɗaura wani a ƙugunsa 😳, yawwa ai shine dan karkuce bance ba,
Resmin ce ta shigo da gudu cikin farin ciki da wani abu a hannunta can dai irin na indiawa wata cimarsu ce nifa bansan sunan abunba, amma ku tambayi *RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE* gaskiya ita ta sani saboda ita taje india nikam banje ba, dan gaskiya da naje saina rubuta muku littafin nan da yaren indianci,
Tana neman shigewa jikinsa yaja baya tare da faɗa mata ta dakata, kila dan karta goga masa datti ko? Ja tayi ta tsaya tare da bin kyakkyawan surarar jikinsa da kallo, kallonta yayi yaga hankalinta baya wurinsa dan haka ya maida dubansa ga inda take kallo a jikinsa, murmushi yayi da gefen bakinsa sannan yayi mata taƙaitaccen kallo sannan ya miƙa hannunsa inda rigarsa take ya ɗauka ya saka,
Ke juya zan saka kaya, haka ya faɗa ba tare daya sake kallon inda take ba, juyawa tayi cikin fushi tayi waje gaba ɗaya, ɗan gajeran tsoki yayi tare da cewa matsalarki!
Tana fita ya cire rigar ya fara bin duk wasu gaɓoɓi na jikinsa yana jikasu da ruwan turare, sannan yaɗan murza wani haɗaɗɗan mai irin nasu na "yan gayu, gyara fuskarsa yayi sosai sannan ya saka kayanshi,
Ci gaba yayi da wanka da turare ƙamshi mai daɗi ya fara tashi a ɗakin kundai san indiyawa "yan gayu ne, to shima dai jishad ɗan gaye ne ajin farko, saida ya tabbatar ya ɗaurayu ya wanku ya pinfu sannan yasa hannunsa ya shafa kyakkyawar sumar kansa sa wadda yasan tana ɗaga daga cikin abinda ke ɗaukar hankalin "yan mata sannan kuma ya tabbatar tana ƙarawa kyakkyawar fuskarsa kyau, kallon kansa yayi sosai a madubi ya sauke wa kansa kyakkyawan murmushi wanda ba Rabi"atu ba shi kanshi yaji ya birge kanshi,
Cikin takon isa saman tsadajjin takalmansa ya farayi har ya fito palo, ko inda resmin take bai kalla ba kuma baiyi ma kowa magana ba dan tunda ya faɗa Rabi"atu zata zo sukeyin fushi shima bata su yake ba farin cikinsa kawai yake jiran zuwanta dan ko ba komai yau zai kwana a cikin farin ciki gashi ga Rabi"atu,
Motarsa ya shiga yaja ya tafiya, tafiya mai ɗan nisa yayi sannan ya isa tashar jirgin ƙasa! Wuri ya samu yayi parking in motarsa sannan ya fita tare da kulleta dan bata tsaro,
Da sauri ya shiga cikin jirgin dan an fara sanar da matafiya jirgin zai tashi, ajiyar zuciya yayi a daidai lokacin daya zauna kansa jingine da kujerar cikin jirgin idanuwansa a lumshe, saida jirgin ya fara tafiya sannan ya duƙo da kansa tare da duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, jinjina kansa yayi cikin farin ciki,
07:30 daidai jirgin su Rabi"atu ya dira a babban filin jirgin delhi, faɗuwar gaba Rabi"atu taji sosai wani irin tsoro da fargaba ya kamata gaba ɗaya ta rikice danjin ance anso delhi air port, ganin mutane suna ta fita yasa Rabi"atu ta fara ƙoƙarin sauka tare da "yar jakar kayanta,
Wani irin baƙon yanayi Rabi"atu taji gaba ɗaya wata irin natsuwa ta musamman ta dirar mata cikin jikinta ta kama kanta dan ta gane akwai babban banci tsakanin nigeria da india dan idan batayi hankali ba yanzun nan ta zama tarihi a doron ƙasa,
Cikin natsuwa ta fara tafiya hannunta janye da akwatin kayanta, wayarta ta cire bayan ta kunnata ta fara kiran wayar jishad, yana ɗauka sannu da zuwa ya farayi mata, ai Rabi"atu tanajin muryar jishad ta fashe da kuka, kukan farin ciki ne? Na damuwa ne? Tsoro ne? Ko kuwa na miye Oho? Danni *RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE* batamin bayani ba!
Murmushi jishad yayi tare da kashe wayarsa dan yana gab da Rabi"atun ne, abinda yasa ya kashe wayarsa dan wannan rarrashin yafi ƙarfin ta waya!
Ai wannan kashe waya da jishad yayi yasa Rabi"atu taji wani zawo zawo yana neman fitowa dan tsoro kardai jishad bazai zo ba? Niko nace da kinci gidanku, texi na tsayawa jishad ya fita da sauri dan sunyi dashi zai mayar dashi ne a tashar jirgin ƙasa,
Tunda ya hango Rabi"atu yakejin kamar ya zama magana ɗiso ya zuƙo ta zuwa cikin jikinsa, wayarsa keta ringing ko mai kiransa bai duba ba barema yasa ran zai ansa kiran, cikin farin ciki ya isa gaban Rabi"atu yana ƙoƙarin jawota jikinsa ta juya bayanta,
Zagayawa yayi ta gabanta tare da ɗan ɓata fuska yace miye? Kuka yaga Rabi"atu tanayi fuskarta kaca kaca da hawaye baiyi mata magana ba, a daidai lokacin da mai taxi ya ɗauki akwatin Rabi"atu yaje ya saka a but,
Hannunta jishad yaja suka nufi inda motar take, saida ta fara shigar da ita sannan shima ya shiga, driver yaja suka tafi, suna fara tafiya jishad ya jawota cikin jikinshi yace miye? Bakya san gani na ne? Girgiza kanta tayi alamar A, a,!
Murmushi yayi dan ya lura tana cikin yanayi na tsoro, ɗagota yayi sukayin kallon ido cikin ido yace tsoro kikeji ne? Murmushi tayi ba tare da tace komai ba, sosai jishad ya kalleta sannan yace ki yadda dani babu wani abinda zai faru wanda baza kiji daɗi ba kinji ko? Tom ta amsa, yaci gaba da cewa nayi miki alƙawari ya miƙa mata hannunsa itama da saka nata a cikin nasa,
Glass ɗin idonta ya ɗaga zuwa can saman goshinta bafa a goshin ba, dan ya hau saman gashin kanta, rumgumeta jishad ya ƙarayi sosai yana maijin wani irin baƙon al"amari wanda bayajinsa idan yana riƙe da resmin!
A haka suka isa tashar jirgin ƙasa, mai motar ya saka musu kayansu a cikin jirgi bayan jishad ya sallameshi, bayan jirgi ya gama ɗaukar fasinjojin da zai ɗauka ya fara tafiya,
Shi kuwa jishad sai faman sannu yake ma Rabi"atu sai kace tazo a ƙafarta, kuma idan yayi mata magana batayin magana irin dai yanayi na baƙunta kawai take nunawa bawai rashin waye ba! Ni kuma gaskiya nafi ganin abu da gajiya,
Jishad shima shiru yayi tunda idan yayi magana baida mai tayashi, dole tasa ya sawa bakinsa linzami! Har suka iso, da kanshi ya ɗauki akwatin kayanta ɗayan hannunsa kuma yana riƙe da ita har wurin motarsa!
Sake hannunta yayi sannan ya buɗe but in motar ya saka kayanta hannunta yaja bayan ya rufe, gaban motar ya buɗe ya shigar da ita sannan ya rufe ya zagaya yaja suka nufi *NIRMALAYAM HOTEL* dan acan zata zauna tunda gidanusu basa maraba da zuwanta shi kuma baya so a ɓata mata!
Tafiya mai nisa sukayi sannan suka isa, bayan yayi parking yace ma Rabi"atu muje, fita tayi babu wani ɓata lokaci ta zagayo inda yake fitowa, bayan ya fito daga motar ya duƙa dan ɗaukar wasu "yan takardu, bayan kwaso su ya rufe motar yace ma Rabi"atu mu tafi, a jere suke suna tafiya amma bai riƙe mata hannunta ba,
Har suka shiga cikin hotel in, ɗakin daya kama ya wuce da ita kai tsaye, bayan sunzo bakin ƙofar ɗakinne yasa hannunsa yasa a aljihu ya ciro mukulin ya buɗe da sallama ya shiga shine a gaba Rabi"atu tana bin bayansa! Ki cire key in ki rufe ta ciki idan kin shigo ya faɗa mata tare da wucewa saman kujera ya ajiye kayan dake hannunsa,
Yanda jishad yace tayi haka tayi, bayan ta shiga ne tayi ma kanta masauki a saman kujera inda jishad ya Ejiye takardun daya shigo dasu shi kuma ya wuce ciki yana gyara lalabulayen jikin window,
Da farin cikinsa ya fito yana mai cire agogon hannunsa yace sannu a a daidai lokacin da ya ajiye agogon a saman center table hannunsa yasa a cikin aljihunsa ya fito da duk wani abu dake ciki, sannan ya zauna kusa da Rabi"atu daidai ƙugunta ya riƙo da duka hannayensa guda biyu, sannan ya ɗora fuskarsa daidai ƙirjinta yana mai sauke ajiyar zuciya!
Uhum ai su Rabi"atu kasa motsi akayi, jin bata motsa ba yasa jishad ya ɗago kansa ya kalleta yace mene ne wai? Sai kiyi tayi kamar wata baki sanni ba, ummm yace alamar tambaya tare da ɗaga kansa, murmushin ƙarfin hali tayi still bata ce masa ummm ummm ba!
Cire glass ɗinta yayi da agogon hannunta duk ya Ejiye a inda ya Ejiye nasa gyalen rigarta ya cire mata sannan ya fara ƙoƙarin cire mata rigar jikinta, idanuwa ta zaro tare da cewa miye haka kuma? Ɗan taɓe bakinsa yayi tare da cewa babu komai wai zan taimaka miki kiyi wanka ne saboda gajiya ko zaki samu sauƙi,
Ni bana san haka, murmushi yayi mai kyau tare da cewa kada kiji komai na yadda da kaina babu wani abinda zai faru amma kafin nan bara na ƙira momy nace mata kin sauka lafiya,
Tou ai na ƙirata saida na fara ƙiranta sannan na ƙiraka, babu damuwa nima zan faɗa mata kinzo lafiya a daidai lokacin daya kara wayarsa a kunne, bayan momy ta ɗauka suka gaisa yayi mata godiya sosai tare da sheda mata Rabi"atu tazo lafiya ya gode sosai, sannan kuma ya haɗasu sukayi magana, bayan sun gama wayar ne ya kama hannunta tare da miƙar da ita tsaye ya riƙeta a jikinsa da hannu biyu sannan yace kiyi wankan yanzun ina dawowa,
Cikin sanyi tace ina zakaje? Tou zan fara kawo miki kayanki sai inje in kawo miki abinci, A, a, nidai tsoro nakeji, babu wani abunda zai sameki insha Allah ina dawowa yanzun, shi burinshi yaje ya ansa wayar gidansu, amma Rabi"atu ta kafe kai da fata bazai tafi ba, haƙura yayi suka fita tare ya ɗauko mata kayanta sannan suka dawo, jishad yace taje tayi wanka ko har toilet in ya rakata ne? A, a, ta faɗa sannan tace ya rufe idonshi zata cire kayanta,
"yar gajerar dariya jishad yayi tare da cewa tou pha Allah ya kawoni, kallon Rabi"atu yayi sannan yace to ni ina wani ruwana kinga ki cire kawai babu wani kallonki da zanyi wallahi na faɗa miki babu abinda zai faru tsakanina dake, haba fr.......iend ya faɗi maganar kamar yana luguda ta, ya ƙarasa faɗarta cikin wata irin murya wanda yasa Rabi"atu saurin zama,
Murmushi jishad yayi ba tare da ce komai ba, ya tashi wayarsa kadai ya ɗauka ya wuce ciki! A saman gado ya kwanta ya fara kiran Abbu daya matsa masa da kira tun ɗazu,
Ita kuma Rabi"atu gaba ɗaya ta shiga toilet a tsorace ta farayin wanka sai nishin wahala takeyi dan duk ta daddaɓawa idonta sabulu da tana wanke fuskarta tanayi tana buɗewa wai kada jishad ya leƙota!
Saboda tana cikin tsoro ji tayi kamar ana tahowa dan haka da sauri ta yayimi towel ta ɗaura, jikinta duk kumfa sannan ta leƙo taga jishad ma baya nan! Ajiyar zuciya tayi sannan ta koma ta gama wankanta ta fito,
A saman kujera ta ɗauki gyalen rigarta ta yafa sannan ta wuce ciki inda kayanta suke, wayarsa ce a hannunsa yana chat amma gaba ɗaya hankalinsa yana kan Rabi"atu da yake ɗan duniya ne sai ya nuna ba ita yake kallo ba amma gaba ɗaya attension nashi yana kanta ta wutsiyar idonsa yake kallonta amma a zahirance kuma ka kalla typing yake ki a jikin wayar,
Tunda daga ƙasan "yan yatsun ƙafafuwanta ya ɗauko kallonshi bai wani daɗe ba ya ɗaga idonsa zuwa daidai kwabrinta, yayi minti biyu yana kallonsu sannan ya ƙara ɗagawa sama zuwa guyawunta, ɗan cije leɓonsa na ƙasa yayi a daidai lokacin da jikinsa ya fara ɗaukar chargy, ajiyar zuciya ya sauke tare da kai idonsa daidai kirjinta,.......jin zuciyarsa na neman kwacewa yasa shi ya fara jan a"uziyya dan neman tsari daga kaidin sheɗan ya ɗauke idonsa daga kallonta gaba daya ya tattara hankalinsa wurin wayarsa dan yau ya rantse da rayuwarsa tare da Rabi"atu zai kwana a ɗaki ɗaya kuma a saman gado ɗaya!
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE* to ke kinji pa!
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
08/08/2018
33.
Cikin yanayin gajiya jishad ya kalli Rabi"a murya a wahalce yace Friend zo kiji! Yana mai miƙa hannunsa alamar ta taho,
Ɗan turo baki tayi sannan tace to ka fita in saka kayana mana! Murmushi jishad yayi tare da rufe idanuwansa cikin sarƙaƙƙiyar murya yace amana na kulle idona saka kinji idan kina so na ki saka a gabana plzzzz,
Buɗe akwatin ta tayi ta ɗauki kayanta fuuu zata fita, idanuwansa a rufe yace kada ki fita kiyi haƙuri ki dawo ki dawo don Allah,
A hankali ya juya bayansa wannan dalilin yasa Rabi"atu ta saka kayanta, bayan ta gama ta faɗawa jishad ta gama a daidai lokacin da take ajiye towel a gefen gado,
Ajiyar zuciya jishad yayi tare da juyowa ya sauko daga saman gadon, gyara zaman belt in ƙugunsa yayi tare da gyara zaman necktail insa hannunsa yasa saman kansa ya ƙara tada sumar kanshi sannan ya kalli Rabi"atu tare da kashe mata ido ɗaya!
Murmushi tayi tare da kallonsa sosai, shi kuma ɗaukar towel in yayi tare da cewa zo muje, yana faɗin haka yayi gaba Rabi"atu tabi bayansa da after dress a hannunta tana ƙoƙarin sakawa saboda ƙananan kaya ne ta saka,
A saman ƙyauren ƙofar toilet ya sagala towel in sannan ya taya Rabi"atu saka rigar, bayan ya taimaka mata ta sakane ya tallabo fuskarta da tafikan hannuwansa yana kallonta, kinyi kyau sosai ƙawana,
Murmushi Rabi"atu tayi tare da lumshe idanuwanta tace na gode, saida ya rungumeta sosai a jikinsa sannan yayi magana da yarensu wanda daga Rabi"atu harni bamu san abinda yace ba,
A gajiye ya saketa tare da jan hannunta suka fita, ko a moter yana driving Rabi"atu na kwance a jikin jishad, tafiya mai nisa sosai yakaisu wani lafiyayen wurin cin abinci yasa aka gabatar da abinci wa Rabi"atu shine ya bata a baki harta ƙoshi shidai baici abinci ba shayi kawai yasha suka wuce,
A gajiye suka koma masaukinsu domin Rabi"atu tana cike da gajiya sosai, suna shiga tun a palo jishad ya ɓalle mata after dress inta, yaja hannunta sukayi ciki!
A gefen gado ya zaunar da ita, sannan ya fara ƙoƙarin cire kayan jikinsa, idanuwa Rabi"atu ta zaro sosai tare da kauda kanta gefe ɗaya dan taga jishad ya koma daga shi sai gajeran wando,
Fita yayi tare da ɗaukar wayarsa ya koma palo, banda faɗa babu abinda Abbu yake ma jishad yace duk abinda yakeyi wallahi kada ya ƙara 20minutes baya gida tou kawai yace tare da kashe wayarsa gaba ɗaya!
Bayan ya gama wayar ya Ejiye ta a gefe ya miƙe ya nufi toilet wanka yayi sannan ya fito, wayarsa ya ɗauka ya wuce wurin Rabi"atu, ita kuma harta fara bacci,
Tashinta yayi tare da cewa ta cire wannan kayan na jikinta, batayi magana ba ta tashi cikin yanayin gajiya ta canja kaya zuwa kayan bacci ta kwanta,
Shima hawa yayi saman gado yana mai kallon fuskar Rabi"atu, da sauri taja baya, jawota yayi sosai harsai data shiga jikinshi, cikin wata irin ruɗaɗɗiyar murya yace ki kwanta ya ƙarasa maganar yana mai rufe idanuwansa a hankali!
Kuka ta farayi tace ita dai ya sake ta, ba tare daya buɗe idonsa ba yace haba keko ƙawar ango miye haka? A daidai lokacin daya buɗe idonshi ya sauke kallonshi daidai ƙirjinta, murmushi yayi da gefen bakinsa idanuwansa ƙam a saman ƙirjinta yana kallon dukiyar fulaninta yace kwanta kwanta kwanta........, kwanta.......... Da sauri sauri ya faɗa!
Da sauri ta kwanta dan yanda jishad yayi maganar taji tsoro, riƙe hannunta ɗaya yayi a cikin nasa, hannunsa ya miƙa ta baya ya jawo pillow ya saka a tsakiyarsu yace to rufe idonki bacci babu ɓata lokaci maza maza, ya faɗa yana mai ɗaure fuskarsa,
Ɓata fuska tayi kamar zatayi kuka cikin tsoro ta ƙara kallon jishad jikinta har ƙyarma yakeyi, cikin sanyin murya tace nidai mu tafi gidanku, murmushi yayi tare da janye pillon ya jawota sosai a jikinshi, daidai saitin kunnenta yayi mata magana a hankali wanda yasa Rabi"atu jin wani ɓakon yanayi,
Jishad kuwa ɗago kansa yayi ya kalli Rabi"atu sannan yace kin yadda? Kainta kawai ta ɗaga masa alamar Eh, y.......a.......w........w......a ngode, yafaɗa tare da sauke ajiyar zuciya,
Maida pillon yayi yanda yake sannan ya sake riƙe hannunta yaja bargo ya lullɓesu, babu wani ɓata lokaci bacci ya ɗauki Rabi"atu ta lula duniyar jin daɗi!
Aiki sabo wannan dare jishad ya kasa bacci ya tsare Rabi"atu da kallo zuciyarsa tana zarga masa abubuwa da dama amma bazai iya cin amanar ƙawar ango ba, rumtse idanuwansa yayi da ƙarfin tsiya dole tasa bacci ya shiga dan saka idanuwan jishad bacci!
Tunda suka kwanta babu wanda ya sake motsin kirki har gari ya waye tangaram gam, saida jishad yayi wanka tare da ɗoro alwalla sannan ya tashi Rabi"atu,
Cike da mamaki take kallon jishad dan ita jin abun takeyi kamar a mafarki, miye ? Ya tambayeta, yi tayi kamar zatayi kuka amma batayi magana ba! Jishad yace ki tashi kiyi wanka gida zamu tafi ko yau a gidanmu zaki kwana ne? Eh tace masa jishad yace to kiyi sauri kiyi sallah ni bansan ya akayi ma na makaraba yau wallahi,
Da sauri ta sauka daga saman gado shi kuma abin sallah ya shinfiɗa ya fara sallah, ita kuma kayanta ta cire ta ɗaura towel inda jishad ya ajiye ta nufi toilet, lokacin data fito wanka har jishad ya shiya kayansa na jiya ya maida ya fita palo,
Momy ya fara kira bayan ya zauna, ya sheda mata sun tashi lafiya, taji daɗi sosai tace ina doughter yace tana wanka idan ta gama zata kirata, godiya momy tayiwa jishad tare da addu"a Allah ya tsare ya amsa da amin,
Rabi"atu kuwa sallah ta farayi sannan tayi shafa ba wani hauka tayi ba, sama sama tayi kwalliya dan Rabi"atu tana da kyau sosai a nan ƙasarmu ta hausawa amma a india zasu ganta mummuna, shidai jishad a haka yake san ƙawarsa,
Ɓaƙar riga ta saka tayi matukar karɓuwa a jikinta, turare taɗan watsa sannan ta ɗauki wayarta ta fito, na gama ta faɗa, yanda tayi maganar ne yasa jishad yabi ɗan kyakkyawan bakinta da kallo yana murmushi mai burgewa,
Tom muje, suka fita, amma a ransa bakin Rabi"atu ya burgeshi kuma wallahi daga gani zaiyi daɗin sha, uhum yayi tare da juyowa ya sake kallonta a gefen damarsa ya ɗan riƙota tare da ɗan ɗora hannunsa na haggu a saman bakinta yace bakinki yana da kyau!
Ɗan ɗaga idonta tayi ta kalli jishad shima kallonta yayi sannan yace shima idon yamin kya..... Wani abokinsa ne yayi masa magana shine ya hana ya ida faɗar abinda zaice, bayan sun gaisa da jishad ya miƙawa Rabi"atu hannu yayi alamar su gaisa itama, kallon jishad tayi mai nuni da tambaya, nuni yayi mata da babu damuwa miƙa masa hannu tayi suka gaisa kamar dai yanda sukeyi a al"adarsu,
Riƙe hannun Rabi"atu yayi ram a hannunsa tare da kallon jishad wannan fa? Ya tambayi jishad, jishad yace to saki hannunta sai na faɗa maka ko? Sakin hannun Rabi"atu yayi sannan ya tattara hankalinsa wurin jishad yana jira yaji ƙarin bayani,
Jishad yace ƙawata ce tazo ne wurin bikina daga nigeria, da kyau ya faɗa tare da ƙara kallon Rabi"atu, kallonshi jishad yayi sannan yace yayi maka haka ko? Kanshi ya jinjina alamar gamsu, jishad kuma yaja Rabi"atu sukayi gaba,
A motar suna tafiya duk inda suka wuce jishad yana nunawa Rabi"atu tare da mata bayani sosai takejin nishaɗi har suka isa gidansu jishad, bayan yayi parking yace ta jirashi yana zuwa,
Bin gidansu jishad tayi da kallo lallai su jishad masu kuɗi ne, gidane ya tsaru ya haɗu sosai tsari irin na "yan gayu, tana cikin wannan tunanin ta hango jishad ya taho,
Da sauri ta kama kanta ta daina wani juye juye ta daina kalle kalle, amma taga yanayin jishad ya canja ba kamar lokacin da sukazo daga farko ba,
Buɗe motar yayi ya shiga ya zauna, kwantar da kansa yayi a jikin Rabi"atu yana mai shafo fuskarta, cikin lallashi yace friend kinajina ko? Eh inajinka, yawwa ki kwantar da hankali kada ki wani damu kuma karkiji tsoro ko kinji Abbu da Ummu suna faɗa kinji ko? Cikin sanyi tace tou,
Kallonta jishad yayi tare da gyara kwanciyarsa saman jikinta yana kallon cikin idonta yace idan Resmin ta miki wani abu ko? Tou kada kice mata komai ki barni nine zanyi maganin ta kinji? Tou tace,
Tausayi Rabi"atu ta bashi sosai amma sai ya dake yace to muje kinji, a hankali ta fita shima fita yayi daga motar saida ya ƙara lallashinta sannan yayi gaba tabi bayansa,
Saida suka shiga ciki Rabi"atu ta ƙara tsinkewa da lamarin su jishad gaskiya daga ganin wannan katafaren gida an tara kuɗi na tashin hankali a ciki, kowa yayi cirko cirko ana jiran aga Rabi"atu dan jishad yana wasata sosai,
Bara nayi na *RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE* Kowa yana tsammani zaiga fara kyakkyawa, sai suka ga "yar bilaki! 😜 duƙawa jishad yayi ya gaishe da Abbu itama Rabi"atu tayi yanda taga yayi haka yayi ma ummu itama tayi kamar yanda take gani jishad yanayi,
Cikin yarensu Abbu yace wannan mara kyau ɗin itace abokiyarka? Saboda ita kake rufe ido kana wulaƙanci wa resmin? Zaiyi magana Abbu ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu sannan yaci gaba da cewa yana daga cikin tsarinmu tun kakanni rashin wulaƙanta baƙo amma banda haka yau dasai kaga yanda zanyi da wannan yarinya a gaban idonka,
Duk da Rabi"atu batajin abinda Abbu yake cewa amma ta fahimci faɗa yakeyi, kallon jishad tayi murmushin ƙarfin hali ya sakar mata tare da jan hannunta ya wuce da ita zuwa ɗakinsa,
Abbu yaci gaba da cewa wannan gado bazamu yarda shi ba, al"adar gidanmu tana nan na shiya tserar da ita dan haka a kyautatawa baƙo kamar yanda tarihin gidan nan ya nuna, babu ɓata lokaci aka fara gabatar da abinci iri iri a saman tebirin cin abinci,
Rabi"atu kuwa kuka takeyi dan ita bata so taga ta dalilinta jishad ya samu matsala da ahalinsa, yayi rarrashin duniya amma Rabi"atu sai kuka takeyi tare da fitar da zufar wahala sai shashsheka takeyi tana ƙarawa,
Bai ƙara mata magana ya koma ya rufe ɗakin da key, wanka ya shiga dan canja kayan jikinshi harya fito ya shirya Rabi"atu bata daina kuka ba, kusa da ita ya zauna ya jawota jikinshi cikin yanayin damuwa yace wai miye? Kiyi shiru bakyajin wahalar kuka ma? Kinga ke baƙuwa tace ko? Aidai ni banyi miki komai ba, tou kiyi haƙuri bayan Abbu babu wanda ya isa ya keta ki ban rama miki ba, ai kinga ummu batace komai ba? Ɗaga kanta tayi alamar Eh jishad yace to kiyi haƙuri tashi muje muyi kalaci,
Cikin muryar kuka tace na ƙoshi, ta ƙarasa maganar tana shashsheka, miƙewa jishad yayi ya fita, a ɗan ƙaramin kofi ya zubo mata tea a ciki har a lokacin Abbu bai daina faɗa ba, jishad baice masa ummm ummmm ba ya wuce,
Bayan ya kai mata tea ɗin da kanshi ya bata tana sha yana cewa swry, hannunta a saman nashi hannun ta tayashi riƙe kofin jikinta sai kyarma yakeyi saboda tsoron abinda zai biyo baya, jishad kuwa ji yakeyi shima kamar yayi kuka saboda Rabi"atu ya tausaya mata sosai gaskiya ta baro ƙasarta tazo tashi dan farin cikinshi amma ana neman a ɗaga mata hankali a ɓata mata rai babu dalili,
Saida ya sumbaci daidai bakinta bayan ta gama shan tea in, fita yayi da kofin tare da zubo mata gurasa da miyan ganye duk lokacin da Abbu yaga jishad sai ya ƙara zafafawa, wai jishad ya rainashi da yace kada a saki a kawo masa baƙar fata a gidanshi saida jishad ya kawo dan ya nuna shi ya raina mutane,
Shidai baiyi masa magana ba ya wuce ciki, ƙara ma Rabi"atu lodi yayi sosai sannan ya koma ya zubo mata wani ɗan lemu tasha, saida ya tabbatar ta ƙoshi duk da dai wannan ba wani abinci bane a ganinta tunda su ba irin wannan cimar sukeyi ba kuma duk da haka dai ita Rabi"atu bata da wani cin abinci sosai gaskiya,
Shima ɗan kaɗan kaɗan yaci sannan ya koma ɗakinshi, rufe ƙofa yayi sannan ya wuce ciki, saman gado ya kwanta tare da nunawa Rabi"atu daidai ƙirjinsa wai tazo ta kwanta, babu musu ta hau saman gado ta matsa kusa da jishad ta kwanta kamar yanda ya nuna mata tayi,
Tashi ki cire wannan rigar tana kartar min jiki, tashi tayi ta durƙusa saman gado ta cire rigar jikinta sannan ta koma ta kwanta a jikinsa, hannunsa yasa cikin lallausar gashin kanta yana ɗan yamutsawa a hankali, yanda yake mata yasa ta yin baccin dole,
Saida ya tabbatar tayi bacci sannan ya sauketa daga jikinsa ya tashi ya ɗauko laptop insa ya ci gaba da danne dannensa, bai daɗe da farawa ba ya jiyo hayaniyar resmin dan haka da sauri ya miƙe ya fito dan baiso Rabi"atu ta tashi bare har taji abinda zai faɗa mata rai,
A ƙofar ɗakinsa suka haɗu shi yana fitowa ita kuma tana neman shiga a hankali ya jawo ƙofar ɗakin tare da ɗaure fuska sosai, da hannunsa ya nuna mata alamar tambaye cewa miye? Zatayi magana ya sassauta murya cewa muje palon ƙasa ,
Cike da masifa tace ita babu wani palon da zataje yau saiya fito da Rabi"atu saita kasheta, idanuwa jishad ya zaro tare da cewa kashewa? Eh Eh Eh Ehhhhhhh, ta ƙarasa maganar tare da riƙe ƙugunta da dukan hannayeta biyu,
Murmushi jishad yayi sannan yace to me tayi miki zaki kasheta ne? Saboda tana soyayya dakai, kuma kasan ina kishinka, baki da hankali banda toshewar basira bana faɗa miki abokiyar ango ce ba? Kima daina wannan maganar dan zaki jawa kanki, baiwar Allah ta taso daga wata ƙasa tazo dan tayaki murna zakiyi aure, amma saiki rasa abinda zaki saka mata sai rashin mutunci? Da har inayin soyayya da ita zata zo bikinki? Kije kiyi nazari,
Tsoki yayi ya juya dan komawa ciki yana ƙoƙarin rufe ƙofa, resmin ta fara magana cikin kuka tace nima shigowa zanyi, ba tare da yayi mata magana ba ya wuce ciki itama ta shiga!
Da gudu yaga Rabi"atu tayo wurinsa ta riƙeshi tana kuka, itafa ba bawai tsoro takeji ba A, a, ka tadda mutum har ƙasarsu gidansu cikin danginsu kai ɗaya tsinken raginka kayi fitana dashi baya yuwuwa yanzun nan kaci na jaki harka rasa hanyar dawowa nigeria, dan Rabi"atu tsaf zata zanewa resmin fata amma idan ta daketa ko Abbu yaci uwata ga duk "yan uwan jishad dama babu wani wanda ya damu da ita jishad kaɗai ne yake hauka a kanta,
Cikin damuwa jishad yace miyasa bakiyi bacci ba? Tana goge hawayen idonta tace nayi tama tada hankali gaba ɗaya ta kori natsuwa daga cikin jikinta, yana riƙe da ita harya matsa gefen gado zama yayi sannan ya zaunar da ita saman cinyarsa yace saurara nace miki bana so kina wannan tashin hankalin ko? Cikin kuka tace Eh jishad yace to kwanta kiyi bacci ki saka a ranki kina gidanku kinji ko? Kwantar da kanta tayi saman kafaɗarsa cikin yanayin tsoro tace nidai mu tafi,
Cikin rarrashi jishad yace kiyi haƙuri bara muci abincin anjima sai mu tafi kinga idan muka koma mun huta fita ko? Tou tace, jishad yace tou kwanta a hankali yana mai kwantar da ita saman gado,
Miƙewa yayi tsaye bayan ya kwantar da ita, kallon resmin yayi wanda kishi yasa duk ta canja kamannu cikin yarensu yake mata magana, amma shima dai da alama faɗa yakeyi, itama masifar takeyi amma a zahirance jishad yafita zafi da kuma ɗaukar zafin,
Rabi"atu tana kwance sai zaro idanuwa take kamar dambu ya shaƙe tsohowa, ita bata san taga jishad yanayin faɗa dan wasu idan suka ɗauki zafi suna saukewa ne akan kowa, idan kuwa har jihsad yayi mata haka da bata san yanda zata ƙare ba a india,
Jishad, Rabi"atu ta kira sunanshi, ba tare daya juyo ba yace ya akayi ne? Dan Allah nidai zan tafi a daidai lokacin data sauko daga saman gado ta ɗauki rigarta ta fara sawa, jishad yace kina gane hanya ne? Rabi"atu tace Eh jishad yace to a sauka lafiya saina taho!
Cikin damuwa ta ɗauki takalminta ta koma gefen gado ta zauna tana sakawa saboda maɗauri garesu, cikin bala"i resmin tayi wurin Rabi"atu tana zuwa babu wata wata ta shaƙeta sosai harsai da idanuwanta suka firfito taci gaba da dukan Rabi"atu ta ko ina, jin alamun kamar ana kai duka yasa jishad juyowa cikin sauri dan hankalinsa yana ga laptop insa kuma ya basu bayane baisan abinda suke ciki ba tunda shidai dama da magana yake amfani wata yaba resmin ansa wata kuma yana basarwa, cikin tashin hankali ya ida juyowa dukanshi dan ganin resmin saman ruwan cikin Rabi"atu tana ta dukanta tare dayin sukuwa saman ta kamar ta hau doki!
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
08/08/2018
34.
Cikin tashin hankali jishad ya matsa wurin yana ƙoƙarin cire resmin daga jikin Rabi"atu, daƙel yake janta dan yana ɓamɓarota take ƙara kwacewa tana komawa saman jikin Rabi"atu!
Ƙara fizgota yayi da hannu ɗaya da ƙarfin jarumta, wani irin ihu resmin tayi tare da kaiwa Rabi"atu halbi cikin kuka tace ma jishad saina kasheta wallahi,
Idanuwa jishad ya zaro kafin yayi magana ta ƙara komawa tana dukan Rabi"atu ciki zafin rai da tsananin ɓacin rai jishad ya fizgota tare da zazzabga mata mari, da sauri ta tattara gashin kanta tare da ɗaga idon ta kalli jishad ɓarkewa tayi da kuka mai tada hankali tace ni ka mara saboda mace?
Da gudu Rabi"atu ta taso ta ɓoye a bayan jishad tana kuka, hannunsa yasa a bayan sa ya jawo Rabi"atu rungumeta yayi sosai a jikinsa cikin birkitacciyar murya yace kiyi haƙuri,
Resmin ta sake maimata tambayarta nika mara saboda mace ko? Eyy na mareki naje na mareki ko zaki rama ne? Da gudu Resmin ta fita tana ihu kamar mahaukaciya,
Ƙara riƙe Rabi"atu yayi sosai a jikinsa yana ƙoƙarin haɗa bakinsa da nata Resmin ta shigo da gudu da wuƙa a hannunta, da sauri jishad ya ɗago tare da maida Rabi"atu bayanshi da sauri, ita kuma a daidai lokacin data caka wuƙar a tsautsayi ta yanki hannun jishad,
Murmushi jishad yayi tare da kallon inda resmin ta yankeshi sannan ya ɗaga idonshi ya kalleta, amma baice mata komai ba dan yasan kishine kawai yake damunta,
Jan hannun Rabi"atu yayi tare da ɗaukar mata rigarta suka fara tafiya Rabi"atu duk tabi ta daddafe jishad tana ƙoƙarin runtumawa da gudu jishad ya riƙeta sosai,
Resmin kuma biyo bayansu tayi tana ta hauka a cikin yarensu wanda Rabi"atu bataji amma shi jishad yasan abinda take cewa "yar gajeriyar dariya yayi a daidai lokacin daya tsaya daidai tebirin cin abincisu ya ɗauki wata "yar madaidaiciyar food plaks,
Suka fita a palon duk maganar da Abbu yakeyi jishad bai saurara ba, dan a gaskiya iyakar rashin kyautawa ba"a kyautawa Rabi"atu ba ai ba"a rayuwa haka,
Saida ya saka kular a baya sannan ya sakawa Rabi"atu rigarta ya sakata a motar sannan shima ya zagaya ya shiga yaja suka fita a gidan zuciyoyin kowa a kuncice,
Da hannu ɗaya ya riƙe sitiyarin motar ɗayan hannun kuma yana rumgume da Rabi"atu dake ta faman shashshekar kuka shidai jishad bai iya bada haƙuri ba dan wani irin hali yake dashi wanda shima kanshi da kanshi yana shan wahalar kansa,
Har suka koma masauki babu wanda yayi magana, suna shiga da gudu Rabi"atu ta wuce ciki ta fara tattara kayanta, jishad daya shiga daga baya yaga Rabi"atu tana ta faman parking da sauri ya isa wurinta ya riƙeta ta baya yace miye haka?
Cikin kuka Rabi"atu ta juyo tace nidai tafiya zanyi bana iyawa, murmushi jishad yayi cikin sigar zaulaya yace haba keko ƙawar ango da wuri haka? Ya ƙarasa maganar yana mai ɗan ɗaga girarsa,
Sassauta muryarsa yayi sannan yace ai baza mu sake ma komawa ba anan zanyi zamana dake babu ruwana da aurensu nidai ke nake so zaki aureni don Allah? Ya ƙarasa maganar tare da ɗan riƙo daidai ƙugunta ya ɗan fizgota sosai a jikinsa ita kuma hannuwanta a saman kirjinsa yanda yayi mata abun yasata saurin lumshe idonta a hankali,
Murmushi jishad yayi tare da ɗan buɗe idanuwansa sannan yaɗan lumshesu yaɗan ƙara mayar dasu havcorent sannan yaɗan ƙara riƙeta ya ƙarasa shegantakar tasa da murmushi,
Dariya Rabi"atu tayi sosai dan yanda jishad yayi ya burgeta tabi idanuwashi da kallo ba tare data ƙyafta idonta ba har na tsawon wani lokaci, zaunar da ita yayi a gefen gado shi kuma ya durƙusa a gabanta yace don Allah ki soni friend resmin ta koma kawar ango ke ki zama mata ta don Allah ki aureni kinji Rabi"atu,
A jiyar zuciya Rabi"atu tayi tare da kwancya saman gadon kanta yana kallon sama ta ɗaga hannuwanta alamar miƙa tashi jishad yayi ya ɗan kwanta saman ta kaɗan, tureshi ta farayi, girgiza kansa yayi alamar ta daina, nidai ka sauka mana miye haka? Bazan sauka ba da jiya da yau duk kema a cikin jikina kikayi bacci nima ramawa zanyi,
Nidai bana so gaskiya, tou shikenan yi haƙuri sauka yayi tare da duƙawa ya ɗora duka hannayensa a saman cinyarta ya saki ƙarfinsa sosai saida jikinta yayi ƙara ƙasss, cikin shagaɓa tace wayyo,,,, dariya yayi sannan yace ramawa nayi, da sauri ta tashi tace aiko bazan yadda ba tunda ni ban maka haka ba, ta ƙarasa maganar tana mai ɓata fuska kamar zatayi kuka, dariya jishad yayi tare da ɗaukar makullin motarsa da sauri yayi mata gwalo 😜 yana cewa kiyi wanka kafin na dawo!
Da sauri tabi bayanshi lokacin harya fara sauka daga saman benen yanda yake tafiya yasa ta tsaya tana kallonsa ya iya tafiya sosai irin ta maza masu aji, da sauri ta koma ciki tana leƙen jishad ta window harya shiga motar ya tafi saida ya ɓace sannan ta koma ta kwanta tare da tunanin jishad,
Marin da yayi na resmin yayi mata daɗi sosai da sauri ta tashi tare dayin "yar rawar farin ciki lallai jishad yana da kyau kuma gashi yana saka mutun a cikin nishaɗi idan yana fushi lallai duk macen data auri jishad a matsayin mijinta taji daɗi gashi ɗan gayu wayayye kuma kisan boko,
_Kiyi wanka kafin na dawo!_
Da sauri ta tashi ta nufi toilet tayi wanka babu wani daɗewa ta fito, tayi shafa, riga da sket ta saka na atamfa masu kyau kuma sunyi mata kyau sosai gaskiya ta tattare gashin kanta ta ɗaureshi, bayan ta gama ta haye gado tayi kwanciyar ruf da ciki kanta saman pillow ta ɗorashi fuskarta tana kallon ƙasa rufe idanuwanta tayi tunanin jishad kawai,
Jishad kuwa ya daɗe bai dawo ba, dan daga asibiti yaɗan wuce wani wuri ne, saida marece ya dawo a gajiye da wasu manyan ledoji a hannunsa, ita kuma Rabi"atu tana toilet, a palo ya zauna saman kujera 3siater yaɗan jirge tare da sassauta zaman necktail insa yaɗan buɗe gaban rigarsa amma hankalisa yana kan ƙofar toilet jiran fitowar Rabi"atu yakeyi,
Fitowa tayi daga toilet in da wayarta a hannunta ta kunna waƙa kallo jishad yabita dashi amma baiyi magana, murmushi tayi tare da ɗan taka rawa mai kyau ɗan duƙawa tayi irin wannan rawar da hausawa ke cewa tambola yanda tayi rawar yayi ma jishad kyau sosai murmushi yayi kaɗan tare da ƙara tsareta da idanuwansa yana kallon ƙugunta saida ya kalleta na wasu lokutta sanna yaɗan kwantar da kansa a saman ƙafaɗarsa ta haggu yana ƙara kallon Rabi"atu,
Waƙar hausa ce tasa shi bansan abinda ake cewa ba tunda ba hausa yakeji ba, ajiyar zuciya yayi tare da jingina bayansa da kujerar ganin Rabi"atu ta shige ciki, ƙara sauke ajiyar zuciya yayi tare da shafa kansa, tashi yayi ya shiga toilet in, alwalla yayi ya fita dan zuwa masallaci,
Bai dawo ba sai bayan sallah isha"i, ita kuma Rabi"atu tunda tayi magrib taci abinci bayan tayi sallah isha"i kuma ta kwanta dan bacci takeji sosai tunda resmin tayi sukuwa a saman ruwan cikinta,
Koda ya dawo Rabi"atu tayi bacci bai tasheta ba a bayanta ya kwanta tare da riƙeta a jikinsa, ƙafarsa ɗaya yaɗan ɗorata a jikinta, wayarsa ya ɗauka ya kira momy suka gaisa yace suna lafiya saida safe yayi mata sannan ya fara chat,
Haka Rayuwar Rabi"atu tayi ta kasancewa tare da jishad shaƙuwa mai ƙarfi ta ƙara ƙulluwa sosai a tsakaninsu dan tunda aka fara hidimar bikin jishad baije ba kuma bai aika ba, wayoyinsa gaba ɗaya ya kashesu, hankalin Abbu idan yayi dubu ya tashi kowa na gidan yana cikin damuwa domin babu wanda yasan inda jishad yake,
Gashi gobe ɗaurin aure resmin kuwa tafi kowa masifa da shiga tashin hankali kamar zata mutu, dan tunda sukayi faɗa da Rabi"atu jishad bai sake komawa gidan ba, kuma duk inda yasan wani daya sansa zai ganshi yaƙi yadda yabi ta wurin kuma babu wanda yasan yana nan hotel danshi yama manta da wata resmin ɗin banza can,
Kullum yana nan naniƙe da Rabi"atu suyi bacci tare suci tare susha tare, amma babu wani iskanci da sukayi kuma basa wanka tare, amma idan zasu yi bacci yana riƙe da ita a jikinsa, tun Rabi"atu bata so harta haƙura dan taga babu damuwa, shidai jishad ba ɗan iska bane, kuma zai ɗauketa yakaita yawo su dawo cikin farin ciki,
Zaune yake saman kujera ya ɗora ƙafafuwansa a saman center table hannunsa na haggu akan kujera hannun damarsa riƙe da wayarsa da airpies kunnesa hankalinsa yana kan wayar sosai da alama abunda yake kallo yana da mahimmanci a wurinsa,
Ji yayi kamar kukan Rabi"atu ƙasa ƙasa, ɗan ɗaga idonsa yayi ya kalli gefen damarsa da haggunsa ba tare daya jujjuya ba, amma kuma bai sake jin kukan ba, ci gaba yayi da abinda yakeyi sai kuma yaji tanayin kukan, Rabi"atu miye? Ya tambaya ba tare daya ganta ba, cikin kuka tayi magana amma bayajin abinda take cewa,
Zoki nan ki faɗamin banajinki, cikin kuka ta fara tahowa tana magana cire airpies in yayi ya kalleta yace wai miye ne? Da sauri taje kusa dashi ta shige jikinsa wai gida take tunawa, murmushi jishad yayi amma bai mata magana ba yaci gaba da kallon wayarsa,
Ci gaba tayi da kukan jishad yayi kamar bayajinta, shidai Allah ya sani bai iya lallashin kowa ba, dan yana ganin kamar tanajin daɗin kukan ne shi yasa ma baice tayi haƙuri ba, tunda yasan babu abinda yayi mata,
Riƙo fuskar jishad tayi, kallonta yayi ido cikin ido tace ni gidanmu, wani irin kallo yayi mata wanda yasa taji fitsari zai zubo mata, da sauri ta ɗauke idonta, gyara zaman sa yayi sannan yace inzo mu kwanta ne? Daga kanta tayi ba tare da tayi magana ba kuma bata ɗago ba, jishad yace to shikenan ɗaukarni kikaini saman gado,
Da sauri da ɗago ta kalleshi, ""gira ya ɗaga mata tare da kashe mata ido ɗaya, cikin shagwaɓa tace nidai gaskiya bana iyawa, kina iyawa mana ɗaukarni , kuka ta farayi, tashi yayi zaune sosai yace ni idan kina min kuka nasan maganinki tunda nace bana san kuka,
Da sauri ta ɗauke lumfashi, ajiye wayarsa yayi sannan ya miƙe tsaye wayoyinsa ya ɗauka yasa a aljihun wandonsa kallon Rabi"atu yayi tare da dukawa kusa da ita yace ni in ɗaukeki? Kai ta ɗaga masa alamar Eh, tou shikenan rufe idonki, a hankali ta lumshe idanuwanta, murmushi jishad yayi tare da dafa kujera da duka hannayensa ya matsar da fuskarsa kusa da fuskar Rabi"atu,
Da sauri ta buɗe idonta, kallonta jishad yayi da idonsa ya nuna mata ta rufe, da sauri ta sake rufewa kada ki buɗe saina kaiki ɗaki, tou tace, riƙe wuyana to, hannuwanta ta ɗaga ta riƙo wuyansa, tou matso da bakinki kusa da nawa, Eye? Tace""" jishad yace Eyyy, matsawa tayi har yanzun idonta a rufe, tou buɗe bakinki, buɗewa tayi, kinaji ko? Da kanta ta bashi amsa, to ɗaga harshenki sama, ɗagawa tayi tou koma ki jingina da kujerar yi tayi kamar yanda yace, jishad ya matsa kusa da ita sosai sannan ya saka harshensa a cikin bakinta gigicewa Rabi"atu tayi, A, a, zauna fa nace, jishad ya faɗi haka, wayyo Allahna Rabi"atu ta faɗa, tsoki jishad yayi sannan yace,
Buɗe idonki, da sauri ta buɗe tana kallon jishad yace miye na kuka tou? Kanta da girza alamar babu komai, ɗaure fuskarsa yayi sannan yace rufe idonki nace, da sauri ta sake rufewa, ɗora ƙafarsa yayi saman kujera sannan ya riƙe kanta da hannunwasa biyu,
Cikin kuka Rabi"atu tace wani iri yakemin fa, tou faɗamin yanda kikeji, ni bazan iya ba, ashe kuwa zamu kwana a haka, don Allah kayi haƙuri, shiru yayi yaci gaba dayi mata wani irin salo a cikin bakinta gaba ɗaya Rabi"atu ta fitittike ta gigice duk ta ruɗe,
Jin jikinta yana ƙyarma yasa shi cewa buɗe idonki, da sauri ta buɗe tana mai matse hawaye, murmushi jishad yayi tare da mata wani irin kallo irin na wayayyin maza da suka san kansu, kina so na?................... Eh ina sanka,..................Zaki aureni?..................Nidai, kedai me? Faɗamin zaki auri jishad a daidai lokacin daya ɗauketa suka nufi ciki, Eye zaki auri jishad?
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*_Assalamu Alaikum masoyana! Ina baku haƙuri naji na shiru jiya, kuyi haƙuri don Allah wasu "yan hidimomi ne suka riƙeni, ngode sosai ina muku fatan alkairi tare da addu"a Allah yasa muyi juma"a cikin farin ciki._*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
10/08/2018
35
Wutsilniya ta farayi kamar kifi ya faɗi a ƙasa ana ƙoƙarin kama sa, tsayawa jishad yayi da tafiyar tare da kallonta yace wai miye kikeyin abu don Allah kamar wata ƙaramar yarinya?
Shiru tayi, sauketa yayi tare da cewa sauka tunda baki so ai kin huta! Yana faɗi haka ya juya ya koma baya, toilet ya shige ya watso ruwa, yana fitowa ciki ya koma rai a haɗe ya ɗauko kayan da zai saka ya koma palo ya saka bayan ya gama ya haye saman kujera yayi kwanciyarsa,
Tunda Rabi"atu taga yanayin jishad yanda ya shigo hankalinta ya tashi, a hankali taja bargo ta lulluɓe addu"a ɗauke a bakinta, ita taga ta kanta shima jishad yanayin fushi,
Wani irin wahalallen bacci ya ɗauketa, babu abinda kakeji sai ajiyar zuciya, dan ita dai zuwa india bai mata daɗi ba,
Jishad kuwa saida ya tabbatar bacci ya ɗauki Rabi"atu sannan ya koma ciki, kusa da ita ya kwanta kamar dai yanda ya saba tunda tazo, a hankali ya jawota jikinsa dan gudun kada ya tasheta,
Jin lokaci lokaci tana fitar da ajiyar zuciya yasashi juyota yana kallonta da gaske bacci takeyi, tashin ta jishad yayi, da sauri ta buɗe idonta cikin damuwa, tashi ki cire wannan kayan ki saka kayan bacci,
Dakel ta haɗiya yawun bakinta tare da sauka a hankali daga saman gado, ta ɗauki kayanta zata fita, ""cikin faɗa jishad yace ina zakije ne wai? Cikin in ina tace palo zanje na saka,
Da tsawa yace mata bansan shirmen banza ki saka kizo ki kwanta nace, komai palo komai toilet mtswww tare da juyawa yace Allah yasa ki fitan kiga yanda zan dakaki a wurin nan,
A siƙwane ta koma ta saka kayan danshi jishad ya bata baya ba inda take yake kallo ba! A kunyace baiwar Allah taje ta hau saman gado a raɓe ta kwanta kamar wanda akayiwa iyaka da hawa gadon,
Ba tare daya kalleta ba yace dawo nan kusa dani, jan jikinta tayi ta matsa kusa dashi saboda wata irin munafikar kunya takeji haka nan taji tanajin kunyar jishad a daren nan,
Bayan ta kwanta kusa dashi yace tayi addu"a, addu"ar bacci tayi bayan ta shafe duka jikinta yace ta matso ta riƙeshi, kuka ta farayi tana ƙoƙarin buɗe baki dan tayi magana jishad ya watsa mata wata irin harara, wanda tasa ta riƙeshi da sauri ta cusa fuskarta a cikin ƙirjinsa ta fara bacci,
Saida tayi bacci sannan shima yayi bacci tunda suka kwanta basu sake motsawa ba saida asuba!
Saida yayi alwalla sannan ya tashi Rabi"atu, shi kuma masallaci ya wuce dan ya samu jam"i, bayan jishad ya tafi itama ta nufi toilet danyo alwallah,
A gidansu jishad tun a daren jiya ake neman jishad babu shi babu labarinsa, resmin kuwa ta wasa wuƙaƙenta sosai idonta idon Rabi"atu saita aika ta lahira, amma duk tashin hankalin da resmin take ciki batakai Abbu ba domin dai yace jishad yana so yasa yaji kunya a idon iyayen resmin,
Abbu yaji baƙin ciki harya rasa inda zai saka ranshi yaji sauƙi, kuma duk wayoyin jishad a kashe suke wannan abu shine ya ƙara ɗaga hankalin Abbu,
Jishad kuwa daga masallaci dawowa yayi, dan har Rabi"atu itama tayi sallah ta koma bacci, palo ya kwanta shima babu wani daɗewa bacci ya ɗaukeshi,
A gidansu jishad duk wanda ka gani tsakanin ahalin ango da ahalin amarya babu kwanciyar hankali a fuskokinsu, kowa yana tattare da damuwa, Baban resmin ya samu Abbun su jishad yace masa idan wannan abu baya yuwuwa tou a faɗa masa zai tafi da ɗiyarsa tun kafin abun yazo ya zama ya lalata abota,
Kafin Abbu yayi magana resmin tayi ɓingilim tace kayi haƙuri Baba, yana dawowa yanzun nan, Abbu yace kayi haƙuri yanzun wani abokinsa yace min ya ganshi a *NIRMALAYAM HOTEL* yanzu zamuje wurin insha Allah!
A cikin nuna damuwa Baba Resmin ya jinjina kansa tare da masu addu"a samun nasara,
Sukam masoyan haɗuwar media bayan sun gama baccin safensu wanka kowa ya shiga da guda gudansu, bayan sun gama wanka jishad ya zuge cikin shiga ta ƙananun kaya masu burgewa na ƙasarsu,
Yayin da Rabi"a ta zuge cikin riga da skart na atamfa masu shegen kyau made in nigeria, tafa bi jikinta tsaf da kayan ado masu ɗaukar hankali dan fita zasuyi dan zagawa a cikin gari,
Shirin sauri sukeyi dan jishad ya ƙosa su bar wurin yana da abinda yakeso yayi idan sun dawo, gashi ko kalaci basuyi ba, da sauri Rabi"atu ta fito tayi kyau sosai ɗan madaidaicin gyale ta yafa ta kawo glass mai kyau wanda yayi matuƙar dacewa da fuskarta ta kafa,
Kallo ɗaya jishad yayi mata yace maza kije ki cire wannan kayan, cikin rashin fahimta Rabi"atu tace tou miye matsalar kuma? Ko suna da matsala ko babu ni gaskiya baza ki fita da wannan kayan ba!
Cike da shagwaɓa Rabi"atu tayo inda jishad yake zaune ta faɗa jikinshi sannan tayi magana cike da sakata, ni gaskiya kabarmin haka nafi so haka nidai, kallon rainin hankali jishad yayi mata sannan yace yaushe kika raina ni? Har ina faɗa kina cewa ke ba haka kike so ba? Ko dan kinga ina kwana gado ɗaya dake ne?
Yana magana yana kallon ɗan kyakkyawan bakinta, ɗan turo bakin tayi cike da tsiwa tace nidai gaskiya nafi san wannan kayan, cire glass ɗin fuskarta yayi sannan yace kallarni ni nake cewa kiyi kina cewa A, a,
Ɗan gajeran tsoki tayi wanda yinsa yasa tunanin jishad tsayawa cak, murmushi yayi da gefen bakinsa sannan ya jawo Rabi"atu daf da fuskarsa daidai saitin bakinta yayi magana wanda banji ba!
Murmushi Rabi"atu tayi tare da ɗan ƙara tsuke bakinta, yanda tayi yayi ma jishad kyau dan haka ya ƙara jawo Rabi"atu sosai tare dakai bakinsa daidai bakinta dan yanajin natsuwa sosai idan ya haɗa bakinsa dana Rabi"atu,
Turo ƙofar da akayi da karfi yasa jishad ɗagowa cikin fushi dan ganin wane ɗan rainin hankali ne haka? Abbu ya gani da sauran mutanen da bazan iya tsaya faɗa muku su ba!
Ajiyar zuciya yayi tare da jingina bayansa da gujera, sauke Rabi"atu yayi daga jikinsa, yace wato da na dawo sallah ban kulle ƙofa ba!
Cikin tsoro Rabi"atu ta ƙara komawa ta ƙadaddabe jishad, dan yanda taga mutanen cikin fushi hankalinta ya tashi, ƙara cireta daga jikinsa yayi amma sai ta maƙale kamar ƙaguwa ta liƙe a jikin mutum,
Cikin sanyin murya jishad yace zauna in tashi saiki riƙeni ban iya miƙewa tsaye dake, wayyo Allah tace ganin Abbu yana shigowa ciki, ƙara ƙaƙume jishad tayi tare da sakin muryarta gaba ɗaya ta saki wani irin ihu..........
Cikin fushi jishad yace wai miye haka? Cikin kuka tace fitar dani waje tsoro nakeji, a daidai lokacin da Abbu ya iso wurin ya fizgo Rabi"atu da ƙarfin tsiya da sauri ta kwace ta ƙara koma jikin jishad a lokacin ya miƙe tsaye,
Cikin kuka ta riƙe fuskar jishad da hannunta biyu zaro idanuwanta tayi hawaye nabin fuskarta tace jishad nidai tafiya zanyi yau zan tafi kayi haƙuri,
Murmushi yayi tare da riƙe Rabi"atu sosai a jikinshi yace babu inda zaki kwantar da hankali, ƙara fizgota Abbu yayi sosai tare da ɗaga hannunsa zai kwarara mata mari da sauri jishad ya kareta marin ya sauka a fuskarsa harsai da jini ya fita a gefen bakinsa,
Abbu nayi alƙawari harta koma gida babu abinda zai sameta, miye laifin Rabi"atu? ina laifin wanda yace yana san naka? Miye laifinta? Tun kafin na santa nasan resmin kuma na faɗa cewa bana santa ni bana san aurenta, idan zaka aura min aure a yau saida ka aura min da Rabi"atu,
Cikin fushi Abbu ya rufe jishad ya duka, da gudu Rabi"atu ta riƙe Abbu tana cewa ba jishad ne ya dace ayi duka ba itace za"a daka, saboda iyayenta sunce kada tazo ta shirya tazo dama duk wanda ya tsallake maganar yana tattare da nadama, haɗa hannayenta tayi duka biyun tace na roƙeka kayi haƙuri zan fita daga rayuwarku in Allah ya yadda, ka daina dukanshi banajin daɗi, ta ƙarasa maganar tamai rushe wa da wani irin kuka mai tada hankalin mai saurare,
Da sauri jishad ya riƙeta yace ke babu wani fita rayuwarmu, miyasa zakiyi ƙarya bayan na hanaki ƙarya? Faɗa masa cewa bazaki tafi ba kina nan saikin aureni, ki faɗa duniya taji wanda ya sani ya ƙara sani wanda bai sani ba a yau ya sani, wallahi na rantse da wanda ya busa min lumfashi saina aureki,
Kallon Abbu yayi sannan yace wallahi ku daina wahalar da kanku sannan kuma kowa ya koyawa zuciyarsa san Rabi"atu, gata nan shigowa cikinku insha Allah,
Muje a ɗaura aure da resmin ita da kanta zata saki kanta bani ba, yana faɗin haka yaja hannun Rabi"atu su Abbu suka rufo masa baya, ko motar banda faɗa babu abinda yakewa Rabi"atu sai faɗa yakeyi kada ta kuskura ma ta ƙara cewa zata fita daga rayuwarshi idan da tsautsayi sai ayi gaban masu baƙin baki sunce amin pha,
Idan har na fita rayuwarki saikinfi kowa shiga matsala na faɗa miki, dan tuni ba tun yau ba nasan kina so na kuma nima ina sanki so mai inganci wanda babu wacce zan iyama irin shi wallahi, ita kuma resmin zata gane bata da wayau idan ina wasa da ita!
Har suka isa wurin da za"a ɗaura auren jishad bai daina faɗa ba, tsayuwar motar jishad yasa kowa ya dawo da kallonsa duk wanda yake wurin saida ya miƙe tsaye dan ganin ikon Allah,
Cike da izza jishad ya fito, zagayawa yayi ya fito da Rabi"atu saida ya ƙara goge mata hawayen idonta ya gyara mata fuskarta sannan yaja hannunta suka fara tafiya, mutane kuwa sai darewa sukeyi dan basu hanya su wuce, nan "yan ƙana nan maganganu suka fara tashi wanda bazan iya fassara muku su ba, dan dagani har Rabi"atu bamajin wannan yaren saidai Jishad kuma shima bai kulasu ba,
Da sauri resmin ta taso tayo wurin jishad ta rungumeshi tana kuka magana takeyi cikin yarensu, tare da ɗaga hannun haggunsa ta shiga jikinsa ya riƙeta tana ɓarin haggu Rabi"atu tana ɓarin damarsa, kowa a cikinsu kuka yakeyin amma banda jishad,
A haka suka isa wurin da malamin da zai ɗaura musu aure, a gefensa ya zaunar da Rabi"atu resmin na gefe, sannan aka fara gabatar da hidimar ɗaurin aure,
Abbu da Baban resmin suka matso a wurin sosai, yayin da malami ya fara tambayar jishad yana san resmin kamar dai yanda sukeyi a al"adarsu, ya amsa musu, itama resmin aka tambayeta ta amsa, sadaki gwalagwalai masu yawan gaske a cikin wani ɗan ƙaramin akwati aka bayar wanda shine matsayin sadaki!
Aka ɗaura auren resmin da jishad, ana gama ɗaurin aure aka nemi ango da ƙawar ango aka rasa, dan jishad tuni ya ɓace ya tafi yakai Rabi"atu tayi break,
Su Abbu kuwa su kaɗai suka ida hidimar bikinsu aka kai resmin ɓanɓareren gidan da jishad ya ɓamɓara a cikin garinsu, gida ne na gani na faɗa, gidan "yan gayu mai kyau da tsari na fitowa a cikin shirin film ɗin indiawa dan gaskiya iyakar tsaruwa gidan ya tsaru, resmin kuwa tayi farin ciki sosai yau gata a gidan babban masoyinta jishad, jinta takeyi wata ta dabance a rayu,
A ɓangaren jishad kuwa hankalinsa kwance gashi ga Rabi"atu shima haka yake jin duniya kamar alewa bisa tsinke, yayi da aka bawa yaro ita yana cikin farin ciki amma tana ƙarewa zai shiga taitayinsa,
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya dan Rabi"atu ta datse wata biyu ciff a india kuma bata ma marmarin komawa dan zamanta da jishad yana mata daɗi inama su dawwama a haka?
Amarya resmin kuwa tunda aka ɗaura aure jishad baije gidan ba, babu abinda ya dameshi da ita dan saida ya faɗa bayayi Abbu yace sai yayi tou shidai gaskiya bayajin zai iya wata rayuwa irin ta ma"aurata da ita,
Momy kuwa ta tashi hankali Rabi"atu ta dawo amma tace ita bazata koma ba, dan haka tayi ma jishad magana cewa yayi haƙuri Rabi"atu ta dawo haka nan don Allah kuma yayi mata alƙawari insha Allah a cikin watan nan zata dawo,
Amma saida aka shanyeshi babu labari, hankalin momy ya tashi sosai ta shiga damuwa dan gani takeyi Rabi"atu bazata dawo ba, shi yasa ta matsa ta kafe kaida fata, babu dare babu rana kira takeyi tana cewa jishad ya rufa mata asiri har an fara surutu a familynsu ta tura baligar ɗiya ta tafi india babu dangin uwa babu na uba,
Badan jishad yaso ba, ya fara shirye shiryen komawar Rabi"atu nigeria, hidima yakeyi ta tashin hankali kuɗaɗe kuwa ya ɓatar baisan iyaka ba wurin ganin yasa farin ciki a zuciyar Rabi"atu danshi da san samunsa ne ya nannaɗe india ma yabawa Rabi"atu gaba ɗaya ta tafi da ita,
Ana gobe zata tafi yakaita gidansu dan suyi bankwana dasu Abbu!,
kuyi haƙuri da wannan do Allah, ngode sosai💋
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
10/08/2018
36.
Allah sarki shima Abbu baiji daɗi ba da Rabi"atu zata tafi, yayi mata fatan alkairi tare da binta da manyan addu"o'i sannan suka haɗa mata 99 ta arziƙi,
Da jishad ya ɗauki Rabi"atu zasu tafi Abbu da ummu da sauran "yan uwan jishad saida suka ɗan matse hawaye,
Jishad yayi farin ciki sosai da gaya gidansu sunji baƙin cikin rabuwa da Rabi"atu haka ya tabbatar masa lallai wata rana zasu karyo harsu amince da aurensu,
Gidanshi ya kaita tayi sallama da resmin wanda tunda aka ɗaura aurenshi da ita sai yau jishad ya taka gidan, resmin ko zuciya batayi ba tana ganinshi ta ruga da gudu ta maƙalƙaleshi tana mai farin ciki sosai,
Bayan an natsu ne jishad ya faɗa wa resmin cewa Rabi"atu zata tafi, amma ko in kula kuma bata ce mata umm umm ba, dan ta tsani Rabi"atu kuma haushinta takeji,
Dan ita a tunanin resmin Rabi"atu ta hana jishad zuwa daɗi ma takeji zata tafi su baza sabuwar rayuwa irin ta ko wasu ma'aurata,
Basu wani daɗe a gidan jishad ba suka koma masauki ko wannensu a gajiye yake, dan haka jishad shine ya farayin wanka, bayan ya fito Rabi"atu ta shiga shi kuma fita yayi dan zuwa masallaci yin sallah magrib,
Rabi"atu tana fitowa itama sallah tayi saida ta gama sallah sannan ta ɗan murza mai kaɗan dan fatarta ta miƙe, bayan ta gama ta zauna a gefen gado rai a cakuɗe dan Allah ya sani tana mai baƙin cikin rabuwa da jishad,
Tana nan zaune tana ta tunanin da babu mafita har lokacin sallah isha"i yayi ta tashi tayi sallah, bayan ta gama ta saka kayan baccinta ta haye gado tayi kwanciyarta,
Jishad kuwa bai dawo ba, sai 12:04am ya shigo a lokacin Rabi"atu ta manta da tayi bacci, yana shigowa ya kulle ƙofar, cikin damuwa ya shige ciki daya tuno gobe kamar yanzun baya tare da Rabi"atu sai yaji kamar zai haɗiya rai ya mutu,
Bakin gado ya matsa ya jawo ƙafafuwan Rabi"atu har daidai inda yake tsaye, sannan ya kwanta saman jikinta, da sauri ta buɗe idonta ta kalli jishad, murmushi jishad yayi tare da cewa haba ƙawar ango har kina iya bacci a wannan dare mai tattare da fargaba?
Taɓe baki tayi tare da kallon cikin kwayar idon jishad amma batayi magana ba, sauka yayi daga saman jikinta ya ɗorata saman jikinshi yana cewa ya kikeji zamu rabu don Allah,
Ita dai Rabi"atu shiru tayi dan bata san *SO* ba sai akan jishad, kuma bata wani iya kalaman soyayya ba, dan haka ta kasa cewa komai sai kallonshi takeyi kamar yaron daya ɓata ya gane uwarshi,
Shima kallonta yakeyi dan yama rasa ta ina zai fara faɗawa Rabi"atu irin matsayinta da kuma girman son da yakeyi mata a zuciyarsa, yanda yakejin baƙin cikin rabuwa da ita a yau yana ji ina ma babu haramci ko zunubi akan abunda yake san ya akaita,
Yana jin ciwo sosai yana jin damuwa wanda ta addabi ruhinsa da gangar jikinsa, yana so ya dasa wani babban al'amari wanda zai ƙulla babbar alaƙa da Rabi"atu ya girmamashi wanda zaisa bazata rabu dashi ba har numfashin sa na ƙarshe,
Da sauri ya rufe idanuwansa kamar wani abu ya faɗa mishi a ido, sauka Rabi"atu tayi taje tayi fitsari ta wanko fuskarta da bakinta ta fito, firij ta buɗe ta ɗaka ruwa tasha,
Bayan ta gama shan ruwan ta ƙara komawa toilet, kiran sunanta jishad ya farayi babu ƙaƙƙautawa, daga toilet in take ansawa amma shi bayajinta, dan haka ya taso ya biyo ta palon,
Ganin bata nan yasa shi shiga toilet in gaba ɗaya, da sauri Rabi"atu ta juyo lafiya? Ta tambayeshi? Tunda ba wani abu takeyi ba alwallah takeyi, amma gabanta ya faɗi a ranta tace to da wanka takeyi haka jishad zai leƙota,
Da sauri ya isa inda Rabi"atu take kamar mage taga ɓera haka jishad yakai fizga wurin Rabi"atu yayi mata wani irin firgitaccen riƙo wanda hakan yasa mata jin mutuwar jiki, cikin dasashshiyar murya tace menene?
Sunanta ya kira cikin matacciyar murya yace kizo muyi bankwana mana ya faɗi maganar kamar zaiyi kuka, murmushi Rabi"atu tayi tare da cewa tou wane irin bankwana kuma yanzun da daddare haka?
Tou ai yanzun ne yafi daɗi zo muje kiga yanda akeyi, yau zan nuna miki yanda masoya sukejin baƙin ciki idan zasu rabu da abinda suke matuƙar ƙauna ya ƙarasa maganar yana mai jawota su tafi,
Kulle famfon tayi jishad yajata cikin rawar jiki wanda da Rabi"atu na ganewa da ta gane jishad baya cikin hayyacinsa amma ita bata kawo komai a ranta ba!
Saman gado ya kwantar da ita tare da miƙe mata ƙafafuwanta dukan su, yace ki tsaya haka kinji? Ya ƙarasa maganar yana mai sassauta kallon idonsa ɗaya,
Tou tace, yace buɗe hannunki, murmushi tayi tare da ware duka hannayenta, juyata yayi ta kallo inda yake tsaye a gefen gado, kallonta yayi sosai sannan yace ya kika ganni? Lafiya qalau na ganka, jinjina kansa yayi alamar gamsu, suite insa ya cire sannan yace kinji wani abu yanzun?
Banji komai ba, yayi kyau, idan nahau gado a wannan yanayin ya zakiji? Bazanji komai ba! Tou idan kuma na riƙeki a yanayin da kike me zakiji? Nifa babu wani abinda zanji, idan kika tafi gida ya zakiji idan bana nan?
Murmushi yayi a daidai lokacin daya fara hawan gado, jin baɗuwar gaba Rabi"atu tayi, ja da baya ta farayi, harararta jishad yayi tare da cewa me nace miki daga farko, shiru tayi bata ce komai ba, cikin wata irin murya yace faɗamin so nawa zaki riƙa tunani idan kika tafi? Ɗago hannunta tayi da niyar ta nuna masa,
Miya sami bakin ne? A daidai lokacin daya kwanta saman jikinta kamar yanda ya kwantar da ita yasa ko wane hannu a nasa hannun nata, daidai wuyanta ya fara fitar da wani irin numfashi wanda yasa Rabi"atu lumshe idonta, uhmmm faɗamin so nawa zaki riƙa tunani ne? So biyu, da yaushe da yaushe?
Da safe da rana! Ni gaskiya yamin kaɗan, a daidai lokacin daya haɗa bakinsa da nata, bayan wani lokaci kuma ya ɗago faɗamin inji so nawa zakiyi tunanin jishad? So nawa kake so nayi?
A, a, ke zaki faɗa da bakinki, nidai ban sani ba! Baki sani ba? Eh, tou yayi, yadai lura Rabi"atu tana da kidahumanci kuma bazata gane yaren nasa ba, dan haka ajiyar zuciya yayi cikin sacewar guiwa ya sauka daga saman jikinta, baya ya bata ya rufe idanuwansa cikin ƙuna,
Yaso ace Rabi"atu ta yadda ta tayashi ya samu natsuwa dan idan ta tafi yana cikin kuncin rai, wata zuciyar tace masa ga resmin, Allah ya sawaƙe ya faɗa a bayyane,
Ita kuwa Rabi"atu hankalinta kwance bata san abinda jishad yake nufi ba, dan haka ita daya ƙyaleta ma daɗi taji abunta taci gaba da baccinta,
A idanuwan jishad kuwa bacci babu, har gari ya waye idonsa biyu, yama rasa taya zai kwatanta baƙin cikin daya keji, ita kuwa Rabi"atu tunda safe tayi wanka ta shirya dan jirginsu 11 zai tashi,
Gaba ɗaya jishad ya fita hayyacinsa ji yakeyi kamar yabi Rabi"atu su tafi, ita bata ma da wata damuwa abinda ya lura, hankalinta a kwance danshi tun shekaran jiya yayi bankwana da abinci amma ita haɗiya kawai takeyi kamar kabari,
Tunda ƙarfe 8 tayi faɗuwar gaban jishad ya ƙara ƙaruwa, yana kallon Rabi"atu tana ta hidindum ta saidai yabita da ido, saida ta gama abinda takeyi sannan tace masa na gama ka tashi mu tafi fa, tou zan tashi, nidai ka tashi mu tafi don Allah, tou Rabi"atu ki jira, nidai gaskiya ka tashi haka nan sai wani naji naji kake cewa su kakeyi momy tace ni laifi na ne?
Sai in faɗa mata laifina ne ai, riƙe gudu tayi sannan tace nidai mubaryin haka dakai don Allah, jawota yayi jikinsa sannan yace idan nace bazaki tafi ba ya zakiyi? Sai inyi haƙuri in zauna, tou kiyi haƙuri muyi zamanmu anan zamu daina zama hotel ma daga yau nayi miki alƙawari, nidai kayi haƙuri zan sake dawowa, yaushe zaki dawo? Sai resmin ta aihu, ai bata aihuwa,
Bata da lafiya ne? Nine dai banda lafiya, tou idan baka da lafiya miye ya shafi ciwonka da aihuwarta ne? Mace ɗaya na tsara a tsarin rayuwar aure da ita, idan ta mutu har abadan duniya bazan sake aure ba, idan kuma tana da rayuwa babu ni babu ƙara aure har a busa ƙaho, saboda haka ɗaya nakeso, ɗaya zanyi da ita, da ita zanyi, ita zataji, kuma ita zata aifa,
Me zataji ita ɗayar? Kanki ɗanye ne har yanzu bai gama nuna ba shi yasa bakya gane karatun, tashi muje, tashi rabi"atu tayi da tunanin maganar jishad,
Wai _Ɗaya nakeso, ɗaya zanyi da ita, ita zataji, kuma ita zata aifa,_
Oho can shi ya sani, komai jishad ya tattara an jibga su a motar, haka suka kama hanya dan tafiya tashar jirgin ƙasa, tafiya sukeyi amma jishad baƙin ciki yakeji dakel yake tuƙa motar,
Har suka isa ya kasa magana, ko jirgin ƙasa ma baiyi magana da Rabi"atu ba damuwa duk ta tattare ta toshe masa zuciya, a taxi ma haka ce ta kasance tsakaninsu har suka isa, komai an jibga a cikin jirgi, kuɗin da suka gigita Rabi"atu jishad ya bata wanda ko za"a kashe ta batasan yawansu ko iyakarsu ba, aradu tsoro ya hanata ansa kuka tayi ta mishi tana haɗashi da Allah ita dai bata so, hhhhh niko wallahi dani aka bawa saina ansa, 😜
Jishad baida yanda zaiyi dole ya haƙura dan yaga zuciyar Rabi"atu gab take da bugawa, kai wohoho sunsuna dai Rabi"atu tashata kiss kuwa da yana fitowa da yayiwa Rabi"ati tsiro,
Lokacin da jirginsu ya ɗaga dan zuwa nigeria mutuwa kaɗai jishad baiyi ba, da ciwon zuciya ya koma gida, masassara tayi masa lulluɓe!
Momy kuwa tunda jirginsu Rabi"atu ya taso take cikin farin ciki tare da musu addu"a saukowa lafiya, momy da kanta ta gyara ɗakin Rabi"atu ta wanke toilet ko ina da ko ina itace ta goge fes tabi ɗakin da kayan ƙamshi ta feshe tsaff ɗakin yayi ta ƙamshi kamar teƙun turare ya ɓallo,
Komai daya dace momy tayi, ganin lokaci ya kusan ƙurewa ta tafi Abuja dan ɗauko sweety Rabi"atu abokiyar ango, kafin taje har sun sauka, ita kuma uwar rashin haƙuri ta fara dokawa momy waya, tace ta kusa isowa da yardar Allah!
Wayar jishad ta kira dan faɗa masa ta sauka lafiya amma a kashe take, babu wani daɗewa momy ta iso Rabi"atu ta rungumeta tana mai farin ciki, bayan sun kwashe kayansu suka kama hanyar kaduna,
Tun a motar Rabiatu ta ɓalle fira, momy har tayi mamakin Rabi"atu wanda ko magana bata sha mata kai ba! Surutu tun daga Abuja har garin Kaduna, tayi farin cikin dawowa gida lafiya, anci ansha anyi firar yaushe gamo, tsarabar da Rabi"atu ta dawo da ita aka fara buɗewa momy tayi mamaki sosai gaskiya da irin wannan ɓarnar kuɗi da jishad yayi kamar baisan martabar tattalin arixiƙi ba!
Wani ɗan akwati mai ɗauke da gold wanda momy ta buɗe nan kallonsu ya tsaya shine abunda Abbu ya bawa Rabi"atu lallai momy ta yaba da mutunci da kuma karamci irin nasu jishad, bayan momy tayi ma komai filla filla ta gani ta tattara komai ta mayar, ita kuwa Rabi"atu ɗakinta ta tafi dan hutawa, dan bacci takeji ga kuma gajiya sosai,
Baya da ƙura, tunda Rabi"atu ta dawo bata samu wayar jishad ba, hankalinta idan yayi dubu ya tashi da guda guda, yanzun kusan wata huɗu ɗa dawowarta amma babu labarin jishad bare ahalinsa,
Dan tunda Rabi"atu ta taho jishad yasha rashin lafiya sosai, wanda haka yayi sanadiyar canjin wurin aiki, aka dawo dashi nan gida kerala, resmin kuwa babu haƙuri ƙiri ƙiri take faɗa jishad baya bata haƙƙin aurenta kuma shi jishad yace bayayi mace ɗaya zaiyi da ita haka yake kuma ya tsara a cikin jaddawalin rayuwarsa,
Dole tasa iyayi suka raba auren ba tare da ɓacewar zuminci ba, amma resmin tana mutuwar san jishad kamar ta kashe kanta, bayan raba aure da wasu wattanni yayi maganar Rabi"atu amma sam Abbu yace bazai aureta ba tunda shima baibi zaɓinsa ba saidai ya mutu babu aure,
Duk inda jishad yasan Abbu yana ganin girmansu yakai ƙara amma fur Abbu yace saidai jishad ya mutu babu aure, wannan abu ya ɗaga masa hankali, dan haka ya fara faɗawa mutane cewa zai koma nigeria wurin Rabi"atu saidai a nemesa a rasa kuma wallahi idan ya tafi baya dawowa,
Abbu yana ɗauka wasane ya fara ganin ƙaramar magana ta fara zana babba, dan wallahi jishad da gaskiyarsa shirin tafiya yakeyi, wannan dalilin yasa Abbu yasa aka tsare jishad a wani sirrintaccen wuri na daban, amma jishad saida ya fita,
Ranar daya dawo gida Ranar ya faɗawa Rabi"atu yana zuwa nigeria a cikin satin nan, farin ciki wurin Rabi"atu kamar tabi takan jariri ta wuce, ta faɗawa momy itama tayi farin ciki sosai shima dady an faɗa masa, su yayama duk sunji amma Yaya Ahmad hankali yaƙi kwanciya dan haka a ranar da jishad zai sauka nigeria shima a ranar zaizo, dan ganin jishad kuma yaci masa mutunci ya rabashi da "yar uwarsa,
Abbu ya lallashi jishad cewa ya manta da Rabi"atu duk ɗiyar wanda yakeso ko waye babanta a india zai aura masa amma ya manta da zancen baƙar fata, jishad yace alƙawari nayi da zuciyata kuma dole saina bata abinda take muraɗi, babu macen da zata cika wannan burin sai ita saboda da ita aka tsara rayuwar,
Ummun jishad tafi kowa shiga damuwa dan dai tasan idan jishad yace zaiyi sai yayi idan baya yi baya yi kaifi ɗaya ne shi kuma a magana baya juyawa ko za"a mutu, dan haka ta shiga bawa Abbu haƙuri yayi haƙuri kawai yabar jishad ɗin ya auri Rabi"atu amma sam Abbu yace yafi jishad taurin kai,
Lokacin tafiyar jishad yayi kamar yanda ya tsara, magana ta balbaɗe kaf ahalinsu jishad zashi nigeria wurin baƙar fata, kuma idan yaje yace baya dawowa, wannan abu ya ɗaga hankali a cikin ahalinsu, Abbu dai ganin jishad lallai babu fashi tafiya sai yayita yasa shi zama da jishad dan su samu mafita, bara muji wane hukunci Abbu zaiyi!?
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*_RAMLAT ABDULRAHMAN { real mai dambu }_*
*_&_*
*_JAMILA MUSA { meelat }_*
_Meelat Musa_
*_Ke na gani, na gani!_*
_Mai dambu_
*_A ina kika gani, kika gani?_*
_Meelat Musa_
*_Yanzu yanzu zani baki labari, inna kulle idona,_*
_Mai dambu_
*_Uhmn_*
_Meelat Musa_
*_Ko na buɗe ido na!_*
_Real mai dambu_
*_hmm uhmm, na baki zo ki anshi dukan soyayya!_*
_Meelat Musa_
*_Hmmm haɗuwarmu nidake silarta soyayyace, na daɗe ina nema na samo burinki, wanda yaso in a kaso shi yai babbar nasara ce, tunda kin so ni da gaske nima bani barinki,_*
_Meelat Musa_
*_Ngde miki zuciyata kinmin adalci, da kika sani na yadda naso mai inganci, so guda ɗaya wanda babu haɗi kuma ga "yan ci, na tabbata gamon da nai da alkairi!_*
*_Ina miki fatan alkairi Mai dambu Allah yasa albarka a cikin tarayyarmu, wato kin burgeni ne, kaff social media akace waye ƙawarki wanda kikeji da ita budar bakinki kawai sai kikace Jamila Musa, haka ya tabbatar min da ina da matsayi na daban a zuciyarki, ina ƙaunarki! JAMILA MUSA na godiya_* ❤💋
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
11/08/2018
37.
Abbu ya daɗe yana kallon jishad sannan yace jishad mi yasa kake so ka koyi halin da ba naka ba?
Shiru jishad yayi baice masa komai ba, Abbu yace tou kayi haƙuri da yarinyar nan kaji ko?, ɗan gajeran murmushi jishad yayi tare da ɗagowa ya kalli Abbu amma baice komai ba!
Murmushi Abbu yayi tare da cewa kayi haƙuri ko jishad? Ya ƙarasa maganar yana mai dafa kan jishad, murmushin ƙarfin hali jishad yayi tare da cewa bakina ya haƙura, amma bara a tambayeta ita idan ta yadda!
Abbu yace wace ce zaka tambaya? Jishad yace ita mana, Abbu yace bata da suna ne? Dariya jishad yayi sosai kamar zararre yace wai zuciyata mana, Abbu yace kai dakata bana san shirmen banza,
Ɗan lumshe idanuwa jishad yayi tare dakai hannunsa wurin zuciyarsa yace kina ji na? Bayan wani lokaci yaci gaba da cewa saƙo daga Abbu fatan zaki karɓa? Shiru ya sakeyi na wani lokaci sannan yaci gaba da cewa ai nasan kinji komai amma kiyi haƙuri dan tayani cika umarni mahaifina mana!
Da sauri ya ɗago kansa idanuwa ya zaro sosai tare da kallon Abbu yace wallahi tace bazata yadda ba! Yaci gaba da cewa Abbu ka rufamin asiri ka barni ka barni don ƙaunar da kake ma ummuna, kayi haƙuri ka bar zuciyata da abinda take so,
Da sauri Abbu ya miƙe tsaye shi kuma jishad durƙusawa yayi tare da riƙe daidai guyawun Abbu ya kwantar da kansa yana cewa kayi haƙuri wallahi idan ma na tafi bana dawowa shi kenan ranka bazai sake ɓaci ba, Rabi"atu tayi min alƙawarin zamu zauna a gidansu nidai ka barni kafin na mutu na roƙe ka Abbu, ya ƙarasa maganar hawaye yana fita daga idonsa,
Murmushin takaici Abbu yayi sannan yace wa Ummu wai kinji wai zai mutu, ka mutum mana ance maka zamu fasa rayuwa ne idan baka numfashi, kanayi muma munayi dani dakai zanga fasashshe, yana faɗin haka ya cire jishad daga jikinsa ya wuce,
Da sauri jishad ya miƙe ya nufi inda ummu take tsaye, rumgumeta yayi yana cewa ummu kema baki san abinda nake so? Itama zaɓewa tayi tabi bayan mijinta,
Dariya jishad yayi tare da goge hawayen idonsa ya gudu ɗakinsa, fara haɗa kayansa yayi dan tafiya wurin Rabi"atu, bayan ya gama komai ya dukawa Rabi"atu waya, bayan ta ɗauka yace mata zai bar gida daga yau cikin satin nan insha Allah zanzo, ihu Rabi"atu tayi wanda ya ƙara saka jishad farin ciki tare da kwarin guiwa,
Rabi"atu tace nima a ɗakina zaka riƙa kwana ko? Murmushi jishad yayi sannan yace sosai ma, amma idan zan dawo zaki bini mu taho tare ko? Rabi"atu tace wallahi zan bika mu tafi, tou babu damuwa sai nazo in Allah ya yadda, tsuwa Rabi"atu ta ƙarayi wanda tasa jishad kashe waya da sauri,
Da gudu ta fito daga ɗaki sai hauka takeyi kuma momy bata nan, dan haka ta rasa wanda zata faɗawa ya tayata murna, kiran wayar jishad ta ƙarayi ta ƙara sheda masa tana farin ciki da zuwansa pha,
Ita tayi kiɗin ta tayi rawarta danshi jishad yanzun baya cikin natsuwa Rabi"atu kawai..........bayan ta kashe waya jishad ya fara fitar da kayanshi yana jibgawa a motar, wannan abu ya ɗagawa Abbu hankali sosai, dan haka ya fara bawa jishad haƙuri akan ya haƙura su tafi tare baya so yaje nigeria shi ɗaya ya ɓata,
Jishad yace idan ka shirya ka taho daga baya, Abbu ya ɗaga hankali sosai dan gani yakeyi idan jishad ya tafi baya ƙara dawowa har abadan duniya, dan haka ya bashi haƙuri akan wani satin zasu tafi kuma zai nema masa auren Rabi"atu ya aurota su dawo india gaba ɗaya,
Wannan abu kuwa yayi farin ciki wa jishad dan haka ya haƙura amma bai faɗawa Rabi"atu zaizo shida Abbu ba dan kada ƙarshe azo basu zo tare ba yayi ƙarya shi kuma abinda ya tsana kenan!
Zuwan jishad yasa dady dawowa Yaya Ahmad da Yaya Fadeel da Yaya Abdul duk sun dawo gaba ɗaya gida ya cakuɗe Ahmad kaɗai yake masifa wai garin yaye yayenta zata je ta yayi bo musu masifa, dan har Rabi"atu taje india Momy bata yadda ta faɗawa "ya"yan ta ba, amma shi dady ya sani saboda da izininsu taje,
Shiri sosai akeyi a gidansu Rabi"atu dan zuwan jishad momy tana so tayi wa jishad karamci kamar yanda ya karrama masu doughter da taje, dan har yanzun jishad bai faɗa da Abbu zasu zo ba,
Ana gobe zasu zo ne, ya sanar da Rabi"atu su huɗu zasu zo, Abbu sai yayan jishad jamnash sai Babansu Resmin, saishi jishad babbar gayya, Rabi"atu tayi murna sosai kuma ta faɗawa momy su 4 zasu zo,
Su, su momy a tunaninsu ziyara ce kawai su kuma gaba ɗaya suka taho dan neman auren Rabi"atu, su nema a basu a ɗaura su tafi da ita,
Hidima sosai a gidansu Rabi"atu wanda duk lokacin data wuce sai Ahmad ya harareta ita dai saidai tayi masa murmushi dan ita bata tare da fushi ko ɓacin rai,
Su Rabi"atu ansha gyaran kai anyi ƙunshi kayan na musamman masu kyau da burgewa ta ɗinka dan tararar jishad shida a halinsu, kallo ɗaya zakayi ma Rabi"atu ta burgeka domin dai babu laifi tana da kyau daidai misali tana diri mai ɗaukar hankali tana da ƙaton gudu wanda yake sa maza fita daga hayyacinsu, tana da idanuwa masu ban sha"awa da burgewa tana da zara zaran gashin ido haka tana da girare masu kyau wanda kamar an musu jagira, saidai kash Rabi"atu tana da duhu, amma ba baƙiƙƙirin ba, wankan tarwaɗa ce, { coculet colour }
Kowa ka gani a cikin farin ciki yake banda Ahmad da yake ganin Rabi"atu ta ɗaɗɗako musu matsala ta tinkaro su da mutu gaba ɗaya, momy dai bata faɗawa kowa ba zuwan jishad ba haka dady bai faɗawa kowa ba, sunyi abun ne a assirce dan basu san surutu,
Yau tunda safe gidansu Rabu"atu a rikice yake bakajin komai sai kiɗe kiɗe da Rabi"atu ta addabi gidan dashi wanda take ganinsa da sunan farin ciki, tunda su jishad suka taso itama ta fara shirin tarbarshi,
Tsaye take a gaban madubi sai nunawa takeyi irin rungumar da zata mishi, da yanda zatayi magana saida tayi ta canja, kallo da yanda zatayi magana da yanda zatayi tafiya komai takeyi tana ba kanta da kanta marki,
Haka ta gaji da nunawa ta tafi ɗakin momy acan tayi wanka wai ta wanke toilet inta da kanta bazata shiga ta ɓata ba jishad shine zai fara shiga yayi wanka idan yazo,
Tunda aka gama sallah isha"i Abdul da fadeel suka addabi Rabi"atu ta fito su tafi kada su sauka suyi ta jiransu, danshi dai Ahmad yace baya zuwa dan haka da Fadeel da Abdul da Rabi"atu sune zasu ɗauko su,
Rabi"atu sai rawar kai takeyi, motoci ukku suka tafi dasu, driver da Rabi"atu dan tace bata shiga da jishad a motar su fadeel , Abdul a tashi shi ɗaya haka Fadeel motoci ukku na alfarma suka nufi Abuja,
09:30pm jirginsu jishad ya sauka a filin jirgin Abuja, wanda yayi daidai da zuwansu Rabi"atu, Allah sarki jishad wani farin ciki yaji yayi masa lulluɓe a zuciyarsa tunda yake a duniya bai taɓa tunanin zuwa nigeria ba, amma gashi a cikinta Allah ya ƙaddara zaizo amma ta *SANADIN SOCIAL MEDIA* lallai yana alfari da *SOCIAL MEDIA* domin da babu ita da har abada bazai haɗuwa da Rabi"atu ba, shi gani yayi ma saboda haɗuwarshi da Rabi"atu aka ƙirƙiri wechat a duniya,
Juyawa yayi yana ƙarewa filin jirgin kallo a bayyane yace ikon Allah, Allah ɗaya gari banban, juyowa yayi dan fara tafiya, da gudu Rabi"atu ta ƙadaddaɓe jishad wanda wannan abuɓ ya zama baƙon lamari wurin Fadeel da Abdul ganin abun sukayi wani a haggunce, wannan wane irin hauka ne?
Murmushi jishad yayi tare da riƙe Rabi"atu shima a jikinsa yana mai jin farin ciki mara musultuwa, tou fa tun a wurin Rabi"atu ta fara nunawa jishad kunshinta ta buɗe kanta tana nuna mishi dariya yayi tare da cewa kinyi kyau sosai,
Fadeel ne ya iso wurin tare da cewa ke wannan wane irin hauka ne kikeyi? Murmuɗa ɗan ficicin bakinta tayi ba tare da tayi magana ba, jishad kuwa abun nema ya samu bin bakin yayi da kallo tare da ƙalƙalewa da dariya,
Hannunta yaja suka isa wurinsu Abbu tayi musu sannu da zuwa Abbu yaji daɗin ganin Rabi"atu haka nan yaji farin ciki, saida yasa mata albarka tare da addu"oi masu daɗi, shima Baban Resmin haka jamnash,
Motar Abdul suka shiga su ukkun, a motar fadeel kuwa kayan da suka zo dasu aka jibga daga but har bayan a site in motar har gaba site in da babu kowa amma saida aka cika wasu a motar su Rabi"atu wasu ma a cikin motar Abdul aka jibga su kaya fa sukazo dasu marasa musultuwa tunda sudai aure suke so a basu na Rabi"atu,
Haka suka ɗauki hanya dan dawowa kaduna cike da farin ciki Rabi"atu da Jishad suna baya, tayi wani shame shame a jikinsa sai labari take bashi wani yayi dariya wani yayi shiru danshi ba mutum bane mai yawan san hayani itama Rabi"atun haka take amma dai tana so ta nunawa jishad taji daɗin zuwansa,
Cike da farin ciki suka iso gida, tara dai ta mutunci iya bakin gwargwado an sauki iyayen jishad da mutunci, tunda shide jishad tunda suka shigo Rabi"atu tajashi zuwa ɗakinta kuma ta kulle ƙofa tama hanshi yaci abinci su gaisa da dady da momy,
Dady ne yayi mata waya ta bari jishad yazo su gaisa dare yanayi suje su huta, amma sai Rabi"atu tace ita dai jishad a ɗakinta zai kwana, tashin hankali idanuwa dady ya zaro tare da fita daga cikin mutane yace doughter me kikeyi haka ne? Kin taɓa ganin inda baligai mace da namiji suka keɓe har suke kwana a tare, cike da sakata tace dady ai da naje ma india tare muke kwana, innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, dady ya faɗa tare da nufa ɗakin Rabi"atu cikin faɗuwar gaba,
Dukan ƙofar ɗakin dady ya farayi amma sai Rabi"atu tace ma jishad ya manta dasu, murmushi jishad yayi tare da sauke Rabi"atu daga jikinshi yaje ya buɗe ƙofar ba tare daya ce mata komai ba, dady ya gani dan haka yaɗan raɓe dan bashi hanya ya shigo, cikin yarenmu na hausa dady ya fara ma Rabi"atu faɗa amma bai riƙa ɗaga murya ba yanda jishad zai gane yanayin faɗa ba, saida ya gama sannan yaja hannun jishad cewa yazo suje, itama tashi tayi tabi bayansu tana magana amma babu wanda ya saurara mata,
Bayan sunci sunsha aka ɗan gaisa sama sama kasan cewar dare yaɗanyi sosai, momy ma tazo suka gaisa, sannan dady yace da Ahmad ya kaisu masauki, gidansu Rabi"atu ƙaton gidan ne sosai, akwai ɗakuna wadatacce, palo bedrom & toilet, ko wane yana ɗauke da gadon bacci da kujeru masu kyau a palo, Abbau ɗakinsa daban Baban Resmin ma, shima Jamnash nashi daban sai Jishad wanda Rabi"atu ta kafe kanta ƙasa tace wallahi tare zasu kwana,
Ahmad yace ke, ke "yar iska ce? Cike da masifa ko a mutu ko a rayu Rabi"atu tace ita "yar iska ce, Ahmad yace to zanyi maganin iskanci wuce dan ubanki kije ki kwanta, riƙe jishad tayi ta fara kuka ita wallahi bata yadda tare zasu kwana babu wanda ya isa ra rabasu ta gani,
Momy ta fara mata faɗa, amma sai Rabi"atu tace kedai momy babu ruwanki nan da naje india tare mukeyin bacci abun shi yayanshi baice ɗan iska bane sai kawai Yaya Ahmad yace min "yar iska ?
Dady yace doughter mu anan al'adarmu ba haka take ba, kiyi haƙuri a gida ɗaya zaku kwana da safe zaku sake haɗuwa haka zakuyi ta haɗuwa har ranar da zai tafi, dady kaidai don Allah kuyi haƙuri wannan abunfa babu kyau shiga haƙƙin wani, kuje kawai kuyi baccinku na yafe muku,
Dady da momy tafiya sukayi Ahmad kuwa Rabi"atu tace udan bai wuce ba wallahi zatasa jishad ya ɓarar masa da haƙoran gaba, amma sai Ahmad yace saidai su kwana ɗaki ɗaya hada shi,
Cikin rarrashi Rabi"atu tace Yaya kaidai kayi haƙuri na rabaka da harkata idan ba haka ba zakaji babu daɗi, Ahmad yace yaji, haka dai sukayi ta cacar baki daga baya dai ya haƙura dan shi a ganinsa babu mai laifi sai su dady da suka ma tura Rabi"atu taje india, ba dole zatace ɗaki ɗaya zata kwana da jishad ba tunda ya gama waste mata rayuwa,
Ɗakin Rabi"atu suka koma, jishad shidai baisan abinda ya faru ba tunda ba"a faɗa cikin yaren da zai fahimta ba, wanka yayi ya shirya sannan ya hau gado ya kwanta dan gajiya ce kecin ƙasusuwanshi take ta daddaƙarshi,
Bayan ya kwanta ya jawo Rabi"atu jikinsa kamar yanda ya saba idan zasuyi bacci a india, itama riƙeshi tayi cikin farin ciki suka fara bacci,
Koda asuba Rabi"atu da kanta ta raka jishad har masallaci, saida aka gama sallah sannan suka dawo tare, dady dasu Yaya Abdul sunga ikon Allah, haka suka dawo suka koma ɗaki suka koma bacci,
Sai 12 suka fito Jishad cikin shiga mai kyau sai yanzun kowa na gidan ya ƙara masa kallo gaskiya jishad yana da kyau kuma yana da shiga rai, Rabi"atu ta rakashi suka gaisa da momy da dady har wurin su Yaya Ahmad, da zasu fita ne Ahmad yace suzo su zauna suyi break anan dan jishad ya burgeshi gaskiya,
Anan sukayi kalaci su fadeel suna ɗan janshi da fira a bisa dogon nazari da karatun da sukayi ma jishad gaskiya yana da kirki, sun lura bashi da wata matsala dan haka bayan sun gama duk abinda sukeyi suka fita dan zagawa da jishad amma Rabi"atu tana jikinsa ita batajin komai dan zamanta dashi yasa ɗabi"unsu ya zauna mata a jiki, batajin kunyar kowa ta rungume ta kuma sun banta,
Kwanan su biyu da zuwa su Abbu da Baban Resmin suka faɗawa Dady abinda ya kawosu, wato neman auren Rabi"atu kuma suna so a ɗaura aure su tafi da ita, tou shidai dady abinda yace Allah yasa haka shine alkairi, itama momy haka ta faɗa, Ahmad yafi kowa farin ciki ai gara ayi mata auren wannan zaƙewa haka tayi yawa,
Dady kuwa ya faɗawa "yan uwansa suma dai fatan alkairi sukayi domin su wannan bawai wani abun mamaki bane ko aji wani iri haka, dan sunsan anayin irin wannan auren amma nasu Rabi"atu ya basu mamaki ace *SANADIN SOCIAL MEDIA* ta haɗu da jishad amma wannan ba abun mamaki bane dan al"amarin Allah yafi gaban nan!
Maganar auren Rabi"atu dai ta balbaɗe duk inda aka san suna da dalilin sani, dan haka an shiga hidima sosai babu ji babu gani dan ma Abbu yace jibi zasu tafi, farin ciki a wurin jishad yafi kowa,
Maganar auren Rabi"atu takai kunne Aysha taji baƙin ciki iyakar baƙin ciki Rabi"atu zatayi aure, kuma wai ta rasa ina zata samu miji wai ta *SANADIN SOCIAL MEDIA* baƙin ciki ya hanata zuwa itama Rabi"atu bata faɗa mata ba, Aysha tayi kuka taso ace ita ta samu irin wannan sa"ar amma ita sai ta haɗu da musiba da taɓarɓarewar tarbiya da ta haɗu da tata ƙawar a *SANADIN SOCIAL MEDIA* ta gurɓata mata rayuwa ita ta ɓata ta Rabi"atu,
Lallai *SOCIAL MEDIA* yana gyara tarbiya kuma yana ɓatawa, na ɓata tarbiyyar Rabi"atu amma ta shiryu a *SANADIN SOCIAL MEDIA* ni kuma da tawa tarbiyyar *SANADIN SOCIAL MEDIA* an warwaremin ita, wani irin kuka ta saki mai kama zuciya cikin kuka tace ance an barni da zinace zinace shaye shaye sace sace lallai kina tare da wahala Aysha, hannunta biyu ta ɗaga tare da cewa Allah ka kawo min mai shiryani ta *SANADIN SOCIAL MEDIA* Rabi"atu dai ta tsira an barni da kukan baƙin ciki,
Ranar Juma"a aka ɗaura auren Rabi"atu da angonta *_JISHAD MUH"D KT_* akan sadaki budu ɗari, sai ɗan ƙaramin akwati mai ɗauke da gwala gwalai wanda kyauta ne ga Abbu, an ɗaura aure cikin farin ciki Rabi"atu tabar tarihi a cikin danginsu,
Duk da ba wani shagali akayi ba amma mutane sun sheda su jishad manyan mutane ne, kuma masu kuɗi sun sheda ko a india su ɗin na daban ne, domin sunyi aman kuɗi sun kashesu sun lalata nera wallahi kamar basu san matsayin kuɗi ba,
Washe gari kuma tunda asuba suka fara shirin tafiya dan jirgin 9 zasu bi, kuka wurin momy kamar hawayenta zasu ƙare, dady ma dai duk da yana namiji saida ya matse, Yaya Ahmad yayi kuka sosai kuma ya faɗawa Rabi"atu zaizo in Allah ya yadda,
Rabi"atu kuwa ta kira Aysha tayi mata bankwana tare da neman yafiyarta, haka ma tayi ma kamal waya ta faɗa mishi tayi aure, kamal yayi kuka kamar zai haukace, Rabi"atu ta kashe wayarta abunta,
Jishad ne ya shigo ɗakin tare da ɗaukar wata "yar ƙaramar jaka, harya kusa fita ya juyo ya kalli Rabi"atu yace me kikeyi ne wai? Taso mu tafi mana,
Jiki a sanyaye Rabi"atu ta miƙe tazo wurin jishad kallonta yayi sannan yace meye ne? Hawaye ya gani sunabin fuskarta, cikin damuwa ya rataya jakar a kafaɗarshi sannan ya riƙeta a jikinshi cikin rarrashi yace baki da lafiya ne?
Cikin kuka Rabi"atu tace lafiyata qalau, jishad yace to miye kikeyin kuka? Babu komai, murmushi yayi ma Rabi"atu tare da juyawa ya ƙarayi ma ɗakin kallo sannan yace ɗakinki ya baki tausayi zaki tafi ki barshi ne ko miye? Shiru tayi,
Jishad yaci gaba da cewa nayi miki alƙawari zan saka farin ciki mai ɗorewa a zuciyarki, zan zama miki komai da komai, zan zama dady da momy Yaya Ahmad da Yaya Fadeel da Yaya Abdul zan zama Aysha zan saka farin ciki a rayuwarki nayi alƙawari bazaki shiga damuwa ba ko kunci, na rantse da Allah bazan barki kiyi kuka ba, zakiji daɗin zama dani fiye da tunaninki ban aureki ba dan ƙiyayya so yasa na aureki kuma shi zanci gaba da nunamiki har ƙarshen nunfashina, ki daina kuka zan baki duk wata kulawa kinji ko?
Ita dai batace komai ba, murmushi jishad yayi cikin sigar zolaya yace to kiyi ma ɗakin bye bye ya ɗaga hannunta alamar bye, murmushi tayi dan yanda yayi abu ya bata dariya,
Fadeel ne ya iso yana cewa kowa ya shiga motar ku kaɗai ake jira, kamar ba tare zaku tafi ba? Kallonshi jishad yayi sannan yace wai ɗakinmu muke ma bankwana, kuma kada a fitar mana da komai abar mana abunmu haka harsai jikikon gidan nan sunzo,
Dariya fadeel yayi tare da kallon Rabi"atu data narke jikin Jishad sosai tausayinta yaji ya kamashi dan haka yace kuzo muje don Allah, hannunta jishad yaja suka fito,
Momy kuwa sai kuka takeyi tana goge hawaye dady dai bai bata haƙuri ba dan shima zuciyarsa kamar zata fito daga mazauninta, da su dady aka tafi dan rakiyar Rabi"atu,
Har suka isa Abuja momy kuka takeyi, babu wasu kaya da suka tafi dasu dan Abbu yace komai kada Rabi"atu ta ɗauka dan haka daga ita sai jakarta,
Ban kwana aka ƙarayi sannan su Rabi"atu suka wuce dan shiga jirgi, momy kukanta ƙara ƙaruwa yayi sosai bata ma san abun ba mafarki bane saida jirginsu ya ɗaga dan zuwa india, kuka ya kwacewa momy sosai tabi jirginsu da kallo harya ɓace, momy da massara ta dawo gida,
Gaba ɗaya gidan ya mata babu daɗi ji takeyi ina ma dady zai yadda suma su koma india wurin Rabi"atu,
Jirginsu Rabi"atu kuwa yana can cikin sararin samani yana tafiya zuwa india dan sauke masoyan dake ɗauke da farin ciki a cikin zukatansu,
[13/08, 20:03] +234 701 612 8778: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
💝 *SANADIN SOCIAL MEDIA* 💝
*Written by*
*JAMILA MUSA* _{ meelat }_
*Follow me on wattpad @ meelatmusa*
*_Habiba Idris Hubbeey ina tayaki murnar zagayowan shekaran aihuwar, Allah ya albarkaci rayuwanki ubangiji ya ƙaro shekaru masu albarka Am3n._*
*Sadaukarwa gareki* 👇🏻
*RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE*
12/08/2018
38.
🔚
Cikin ikon Allah su Rabi"atu sun sauka india lafiya, kai tsaye gidan Abbu suka nufa gaba ɗayansu,
Ummu tayi murna tayi farin ciki sosai tare da taya jishad murnar samun Rabi"atu a matsayin matar aure, dan ita dama babu ruwanta Abbu ne ya hau kuma ya sauko tare da musu fatan alkairi dan Allah ya ƙaddara Rabi"atu matar jishad ce, wannan aure ikon Allah ne ace mutum yana nigeria wannan yana india amma da Allah ya kawo silar haɗuwa sai Allah ya kowa haɗuwarsu ta *SANADIN SOCIAL MEDIA*
Bayan anci ansha Abbu da Ummu sukayi nasiha wa jishad sosai tare da ƙara nuna masa ya zama mai riƙon amana ga Rabi"atu ya dubi girman Allah ya kulata sosai saboda ya ɗaukota daga cikin ahalinta ya kawota wani wuri daban bata san kowa da kowa ba saishi, bata da wasu dangin sai nashi ya zamar mata farin ciki mai farin ciki a rayuwarta! Tunda har ta tsallako ahalinta ta biyoshi lallai ta cika mai ƙaunarsa,
Abbu ya ƙara da cewa ya kula da kyau karya kuskura Rabi"atu tayi damuwa kada tayi tunani ya zama haske a gareta ya zama farin ciki, karya bari taji ƙunci kuma kada ya kuskura ya bari tayi baƙin cikin rabuwarta da iyayenta,
Nasiha sosai Abbu yayi wa jishad, sannan itama Rabi"atu Abbu yayi mata bayan ya gama yayi musu addu"ar zaman lafiya tare da samun zuri"a masu albarka!
Bayan Abbu da Ummu sun gama nasiha jishad ya ɗauki amarya Rabi"atu dan zuwa gidanshi,
A motar Rabi"atu duk wani iri takeji ta kasa wani sakewa, sai yanzun takeji wata irin nadama a rayuwarta, tunani takeyi ta tashi tun tana ƙarama harta girma tana tare da momy, bata taɓa tafiyar kwana ba sai haɗuwarta da jishad ko club ta tafi tayi ƙoƙarin duk runtsi tsakar dare ta dawo gida,
Amma yanxun ta rabu da Momy har abadan duniya saidai ta zagata da sunan ziyara, Allahu akbar wata irin rayuwa daban kowa da yanda Allah ya tsara masa rayuwarsa,
An aifeta a cikin "yan uwanta ta taso a cikinsu ta rayu a cikinsu amma yau wani daban yazo ya tafi da ita cikin wasu ahali daban wanda bata taɓa tunanin rayuwa dasu ba!
Tunani dai iri iri takeyi har suka isa gidan jishad, sai yau ta ƙara ganin kyawun gidan ko dan ya zama mallakinta ne Oho!
Tana riƙe a jikin jishad suka shiga ciki, har suka isa ɗakin baccin ɗakinta tana riƙe a jikin jishad, gefen gado suka zauna a tare, kallonta jishad yayi tare da cewa sannu da gajiya,
Murmushi Rabi"atu tayi tare da ɗan kwanciya a jikin jishad cikin yanayin gajiya, kallo jishad ya bita dashi amma baice komai ba, ɗan lumshe ido ta farayi alamar zatayi bacci!
Ɗagata jishad yayi daga jikinsa, miƙewa yayi tare da cewa tashi muje muyi wanka bacci nakeji sosai na gaji wallahi!
Komawa tayi ta kwanta tare da cewa waye zai farayi a cikinmu? Tsohon zance jishad ya faɗa, tare zamuyi, idanuwa Rabi"atu ta zaro tare da ɗago kanta da sauri ta kalli jishad, ɗaga mata gira yayi tare da kashe mata ido ɗaya, ya duƙa tare da fara ƙoƙarin cire mata kayan jikinta,
Haba miye haka wai? Wannan ai rashin kunya ce saika cire min kaya ance maka ni "yar iska ce? Dariya jishad yayi sannan yace Oho maki dai, yaci gaba da cire mata kayan,
Kuka Rabi"atu ta farayi tana cewa ni wallahi ba "yar iska bace, babu wanda ya taɓa ciremin kaya ni ban taɓa zama gaban wani ƙato babu kaya ba, a lokacin har jishad ya cire mata riga ya ɓalle mata bra,
Wani irin kukan kura Rabi"atu tayi tare da rirriƙe jishad da hannu bibbiyu ta darkaka masa cizo, da sauri ya saketa cikin tashin hankali dan ya cizu, da gudu ta shige toilet tana kuka,
Da sauri jishad ya kalli inda Rabi"atu ta cije shi, hannunsa yakai daidai wurin tare da shafawa wurin, murmushin baƙin ciki yayi wai yau shine Rabi"atu ta ciza saboda ya cire kayan jikinta kawai? Lallai idan nayi babban aiki kuma fa? Kai ina da aiki a gabana,
Fita yayi daga ɗakinta ya nufi ɗakinsa, yana zuwa wanka yayi ya saka kayan bacci yayi kwanciyarsa,
Rabi"atu kuwa saida ta tabbatar babu jishad a ɗakinta ta fito jikinta sai ƙyarma yakeyi, da gudu taje ta kulle ƙofa, wayarta ta ɗauka ta fara kiran momy,
Goge hawayen fuskarta tayi da bayan hannunta bayan momy ta ɗauki waya, cikin rawar murya tace momy wallahi banasan jishad ashe ɗan iska ne? Hada cire min kaya yana kallon jikina, ta ƙarasa maganar tana mai ɓarkewa da kuka sosai,
Momy da tayi nisa cikin bacci ta buɗe idonta sosai tare da kallon gaban wayarta sannan ta sake mayarwa a kunne tace doughter wannan wane irin zancen banza ne? Cikin faɗa momy ta faɗa,
Cikin kuka Rabi"atu tace momy wallahi babu wanda ya taɓamin irin iskancin da jishad yamin tunda kika aifeni nazo duniya, ashe ɗan iska ne, ni wallahi waccan zuwan da nayi wallahi baimin irin wannan abunba amma wallahi gobe saina kai ƙararsa gidansu gobe idan Allah ya kaimu,
Cikin faɗa sosai momy tace wallahi idan naji kinje gidansu kin faɗi wannan maganar ban yafe miki ba, kuma saidai ki nemi wata uwa badai ni ba banza daƙiƙiya wanda iliminki bai miki rana ba, kina da ilimin addini mai zurfi amma har ki kirani ki faɗamin wannan maganar,
Ina jishad ɗin yake ne? Cikin shashshekar kuka tace ya fita, momy tace ubangiji yana fushi da duk matar da ta saka mijinta a cikin fushi dan haka kima nemi yafiyarsa tun wuri, tana faɗin haka ta kashe wayarta,
Wani irin ihu Rabi"atu tayi tare da dirjewa ƙasa tayi zaman cin ɗan wake, wai momy dake mata faɗa ta kiyayi iskanci yau harta faɗa mata jishad ya cire mata kaya amma wai kuma ita zata ma faɗa,
Tsoki momy tayi tare da gyara kwanciyarta tace stupid girl, dady dake zaune saman abin sallah ya kalli momy amma baice mata komai ba,
Wannan dare Rabi"atu ta kasa bacci sai kuka takeyi, data kalli ƙirjinta ta tuno jishad ya kalla ya taɓa sai taji kamar zata mutu, haka tai ta koke kokenta har bacci ya ɗauketa,
Koda safe jishad baibi takan Rabi"atu ba ya shiga huɗɗoɗin gabansa, itama da safe wanka tayi ta saka kaya masu burgewa, har rana ta ɗaga tana ɗaki kulle tun tana zama na marmari harta fara gajiyawa dan yunwa ta fara cin hanjinta,
Fita tayi ta fara neman inda madafar abinci yake, amma harta gama dube dubenta ta dawo bata gani ba, domin dai gida ita dai wani iri yake mata idan tabi ta wata hanya ta dawo sai taga ta sake dawowa palo, wannan abu ya ɗaure mata kai gata ta kasa gane ɗakinta inda ta kwana jiya,
Haka tayi ta safa wal marwa daga baya ta bada ci ta zauna palo tana jiran dawowan jishad dan ita tsoron ma gidan takeji kada ta sake fita wani hanyar ta fita wani wuri daban inda bai ganota, haka ta yini zugum babu ci babu sha ta rasa inda zata saka ranta har magrib jishad bai dawo ba, ga kuma tabar wayarta a ɗaki,
Tayi kuka tayi majina har kanta yayi ciwo, dan jishad bai dawo ba sai bayan isha"i, kuma shi a ransa ya bayar zatayi girki ne, tunda komai a gidan akwai, abinda kuma yasa baisa a kawo mata abinci ba daga gidansu koshi ya kawo mata saboda ta kulle ƙofar da zai fita ma ƙofa a kulle ya gani haka ya tabbatarsa masa da bata fitowa,
Tunda jishad ya shigo take harararsa, ɗan taɓe baki yayi ba tare da yace mata komai ba ya wuce, da sauri ta tashi tabi bayansa har zuwa ɗakinshi, zama tayi a gefen gado tana tambayarsa ina ne ɗakinta? Nima ban sani ba adaidai lokacin da zai shiga toilet ya faɗa mata haka,
Itama toilet in ta bishi danshi a lokacin harya fara wanka ita kuma wani fitsarin wahala ne ya ɗaure mata mara, tana shiga taga jishad yana wanka da sauri ta rufe idonta tare da cewa to rufe jikinka ni fitsari zanyi ni bansan kanayin wanka ba na shigo kuma fitsarin ya kamani a daidai lokacin da take ɗaga zanin jikinta,
Kallon rainin hankali jishad yabi Rabi"atu dashi sannan yace lallai kin rainani harkin faɗamin, kamarni inayin wanka zaki faɗo toilet bayan kin gama kalleni tsaf zaki faɗamin cewa in rufe jikina? Kayi haƙuri don Allah a daidai lokacin data fara fitsari,
Wallahi banyin haƙuri saina rama, jiya daga cire miki kaya har cizo na kikayi ko an faɗa miki cewa ni banda haƙora ne? Ɗan haɗa haƙoransa yayi sukayi ƙara, sannan yace kuma kikayi kuka ko? Kika gudu toilet kika kulle ƙofa, an faɗa miki bana kishin jikina ne?
Kayi haƙuri a daidai lokacin data fara maida pernt inta, wani irin kallo jishad yayi mata tare da cewa koma ki cire kayanki kada ki fita, ni babu wanda ya isa yasa na cire kayana tunda ni ba "yar iska bace ba, ni ɗan iska? Ni bance maka ɗan iska ba, tou kada ki bari raina ya ɓaci ki cire kayanki kizo ki cuɗani sannan nima na rama kallon da kikamin kuma nima in miki wanka,
Nidai A, a, jishad yace shima A, a, kuka ta farayi, shima yanda takeyi ya farayi, idan tayi tari shima zaiyi, idan ta canja launin kuka shima haka yakeyi duk yanda tayi haka yake kwaikwayonta, cikin kuka da siririyar muryarta tace yunwa nakeji, jishad yace nima yunwa nakeji, yanda yayi abun yasa ta goge hawayenta tana kallonshi, ɗan buɗe idanuwansa yayi sosai tare da cewa hajiya yada kallo haka kuma? Ko kin manta inda muke ne?
Da sauri ta rufe idonta tace nifa so ɗaya na kalle ka, ai nima so ɗayan zan kalleki saukinma baki taɓani ba, matsawa yayi ya jawota ya surmiyata a cikin varf wutsilni ta farayi yace saurara, a hankali ya fara cire mata kayan jikinta ita kuma tana kuka wiwi, 🤸🏻♀ haka dai akayi wanka cikin manya manyan huɗɗoɗi amma har yanzun ba"a buɗe hanya ba,
Dukansu a wahalce suka fito daga toilet jishad yana rungume da Rabi"atu a jikinsa kamar wata "yar jaririya sabuwar aihu, haka ya bajeta saman gado kamar an shanya masara ko motsin kirki bata iyayi,
Ganin manya manya saƙonni da jishad ya fara ɗirkakawa jirkin Rabi"atu yasa na rufe wannan pegin! Dan komai dai ya faru, amma bazan tona sirrrin ma"auratan nan ba,
*** *** ***
Abubuwa da dama sun faru bayan tsayin wasu shekaru da suka gabata, zaman lafiya sosai tsakanin jishad da Rabi"atu kowa yana ƙoƙarin nuna abokin rayuwarsa kulawa ta musamman,
Momy tazo india dan ganin inda ɗiyar take aure kuma taji daɗin ganin Rabi"atu sosai dan gaba ɗaya ta murje ta mulmule tayi gwanin burgewa, taji daɗi sosai wallahi,
Yaya Ahmad ma yazo shida yaya Fadeel, suma sunyi murnar ganin "yanda "yar uwarsu takejin daɗi a gidan mijinta domin jishad yana kula Rabi"atu fiye da tunanin abinda marubuta suke rubuta soyayyar cikin littafi,
Dady shima yaje dashi da Yaya Abdul sukaje, a lokacin ana ta shire shiren bikin Yaya Ahmad da Yaya Abdul,
Kuma Rabi"atu taje bikin ita da jishad sati biyu sukayi suka dawo saboda jishad ya samu canjin wurin aiki ne zuwa Dubai!
Aysha tayi aure ta auri kamalladdeen, Rabi"atu bata zo ba, amma tayi mata waya tayi musu Allah yasa alƙairi sai kuɗi masu yawan gaske ta bata gudamawa momy takai musu, gaba ɗaya hankalinsu ya tashi ganin yawan kuɗaɗen da Rabi"atu ta aiko dasu, tou ai dama haka tare take dan abun duniya mandiri ne idan ka buga saika bawa ɗan uwa shima ya buga,
Resmin dai har yanzun taƙi haƙura da jishad, amma shi jishad ya ɗauke "yar matarsa dai sun sake sheƙa suna dubak hankalinsu kwance, arziƙi sai abinda yaci uban na da!
Zaman lafiya sukeyi sosai domin dai Allah ya albarkaci wannan aure nasu da zuri"a masu albarka Rabi"atu tana da yara 3 maza 2 mace ɗaya,
*Faruk*
*Sadiq*
*Aisha*
Ita Aisha suna ce mata Kohinoor { special diamond }
Gaskiya Rabi"atu ta dace kuma tana zaman lafiya da mijinta da "yan uwansa gaba ɗaya, kuma lokaci lokaci suna zusa nigeria sosai,
*_Alhamdulillah ngode ma Allah da ya bani ikon kawo ƙarshen labarin nan lafiya, kurakuran da nayi ciki Allah ya yafe mana baki ɗayanmu, ubangiji ya bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali ya ƙara kauna tsakaninmu da mazajenmu!_*
*_Ina godiya sosai ga RABI"ATU AMINU MAMMAN DEE, sannan kuma ina miƙa saƙon gaisuwa ta da jinjina ga kwarzon namiji kuma jajirtacce wato JISHAD MUH"D KT, Allah ya ƙara kauna tsakaninka da Rabi"atu, kuma ina ƙara godiya sosai_* 👏🏻
*_Mabiya littafin SANADIN SOCIAL MEDIA ngode sosai da kuka kasance dani, mu kasance daku a sabon littafina wanda ya daɗe da fita mai suna HARSASHEN SO_*
Jamila Musa meelat ina muku fatan alkairi 🤝🏻