Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Monday, September 7, 2020

RASHIN RABO COMPLETE HAUSA NOVEL

adsense here
RASHIN RABO COMPLETE HAUSA NOVEL 

Copied By

HAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT) 

(ADMIN OF ADMINS)

        (admin 

   Hayat hausa novels

Hausa novels and fashion

Cool novel, makeup and kitchen1⃣

Cool novel, makeup and kitchen2⃣

                   AND 

Cool novel, makeup and kitchen3⃣) 

      WHATSAPP NO:


*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻


💦💦💦💦

*RASHIN RABO*

💦💦💦💦


*R🅰SHIN R🅰BO*


*MEELAT MUSA*


*Domin samun littattafanmu sai ku nemu a shafinmu na facebook*


*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP*


*AMEENAT XEEYAN ina maki fatan alkairi kuma ina maki sannu da zuwa, matashi ta sauka da kwari,,,,, Allah yasa an dawo a sa,a ubangiji ya ƙara lafiya da nisan kwana,,,,,,,*


*1-3*


***


*D*a gudu ya shigo cikin gidan yana ɗaga hannuwansa ta cikin babbar riga, har tuntuɓe yakeyi sai ihu yake babu ko salati,,,,,,,,,,


Barka barka Allah ya kawo gwamna, yauni arxiki ya sauka gidana,,,,,,,,,, ya ƙara maganar da tafa hannuwansa yana riƙe haɓarsa,,,,,,


A bakin ƙofar ɗaki wata tsohuwa ta tareshi tare da cewa isiman, kasancewar bata iya faɗar usman ba,,,,, kayi haƙuri an sauka lafiya amma abinda aka samu baizo da rai ba,,,,,,


Wanda aka kira da usman ya fashe da kuka tare da faɗuwa ƙasa yana birgima kamar ƙaramin yaro,,,, wayyo Allahna yanxun cikin nan tun yana kwana ɗaya akasa na fara siyo tsire ina siyo kaji banci ba ban sha ba, ban  siyi gona ba,,,,


Haka ban sayi rago dan turka ba, kullum ban bacci ina addu,a gwanna yaxo kuma gwamna yaxo sai akashe shi?"" ya ƙara fashewa da kuka tare da turjewa ƙasa yana maganganu marasa kyau,,,,,


Tsohuwar dake tsaye a bakin ƙofa tace kai isiman bafa gwamna bane, cikin kuka yace shugaban ƙasa ne?" tace ta mace ce,,,,, tsaki yayi sannan ya miƙe tsaye yana kakkaɓe jikinshi tare da sauke ajiyar zuciya,,,,,, na gode daba gwamna ne ya mutu ba, yana maganar ne cikin shashsheka,,,,,,


Yaci gaba da cewa shegiya gara data mutu, ina amfanin haihuwar mace?""" banda tazo ta cinye tattalin arxikin gida mi takeyi?""  ku miƙo Lbanza aje a jefar, a daidai lokacin da yake ƙoƙarin shiga cikin ɗakin,,,,,,,


Ita kuma durƙushe take tana kuka dan baƙin ciki rashin abinda ta haifa daya koma, usman ya tsaya a gabanta tare da cewa shegiya ragguwar banza duk ƙaton cikon nan ashe ba arxiki ne kika ɗura  a ciki ba tsiyace,,,,,


To bari kiji goben nan saina kaiki asibiti likita ya ɗaure bakin mahaifar inga ta ina zaki sake ɗaukar cikin bare ki cinye man kuɗi da cin malaƙi ƙarshe kizo ki haifo man babba asara,,,,, adaidai lokacin daya kai mata kwanya saman kanta,


Dukawa yayi ya ɗauki gawar ɗiyar yana cewa wallahi ko likafani bazan siya maki ba, shegiya kinyi ma kanki sassauci da kika mutu da nine zan shaƙeki harsai naji bakya nunfashi,,,,,


Tsohuwar tace haba isiman wannan wace irin magana ce?""" tsaki yayi sannan ya kalleta yace rufe man baki, kema saboda san abun duniya ai da kika tashi ni kika haifo ba mace ba,,,,,,,


Kuma wannan ɗiyar a bola zan yadota ba ubanda zai kaita maƙabarta,,,,, cikin ɗan gyashi da tsufa tsohuwar ta bishi yana cewa don Allah isiman ka tsaya, ko inda take bai kallaba kuma bai saurareta ba, ya fice da gawar jaririyar yana ci gaba da zungurawa uwar jaririyar zagi,,,,,,,


Da sauri tsohuwar ta koma ɗaki tare da cewa halima kiyi haƙuri Allah yana sane dake, ki daina biyewa da abinda yayi maki , kuma ɗiya Allah zai sake baki wani rabon indai muna da rayuwa,,,,,,,


cikin kuka tace to inna, amma ai yace zai kaini a ɗaure man bakin mahaifa,, kuma kinsan ina san samun "ya"ya,,, inna tace Allah zai baki masu amfani insha Allah, 


haka inna tayi ta magana mai daɗi cikin sigar rarrashi tana bawa halima haƙuri, ita kuma halima tana gamsuwa da bayanin inna,,,,,,,


usman kuwa yana fita sai ɗaga jaririyar yake yana cewa Allah ya isa tsakani na dake, a daidai lokacin da yake zama saman wani dakali, ya ajiye jaririyar a ƙasa, yana latsa cikinta yana ƙara fashewa da kuka,,,,,,


yace kai marigaya ban yafe miki ba,,,,,, tsire na, bashi na ciwo wurin sa,idu mai nama,,,, madara ta wurin ɗan kawo mai shago na sato ta, dan a baki kisha kiji daɗi,,,,, 


wake da shinkafa inaji ina kallo uwarki ta cinye kasonta ta dosa da nawa saida ta cinyeshi kakaf, irin tattalin arxikina da kika ƙaras bansan iyakarshi ba,,,,,


amma tunda kin mutu kin huta,,,, zanje bakin juji in yarda ke,,,, ya dafe kanshi da hannu biyu yana ƙara ɓarkewa da wani irin kuka yana maimata ban yafe maki ba wallahi,,,,,,


Kuma duk abinda uwarki taci nawa saita biyani,,,,, a daidai lokacin daya ƙara latsa cikin jaririyar yana cewa shegiya baƙar banza ko ɗan kyau ɗinma bakiyi ba,,,,,, wayyo Allahna,,,,,,


Wani mutum ne tsaye a kanshi, yana cewa haba usman waikai dan Allah yaushe zaka daina wannan halin naka?""" usman yace in daina?"" lallai malam nuhu baka ƙaunata,,,,, cikin ɗaga murya usman yace komai na gidan ta cinye fa,,,,,, ya sake maimaita maganar,,,,,


malam nuhu duƙawa yayi ya ɗauki gawar ɗiyar ya nufi gidanshi da ita, usman baibishi ba, a gidan malam nuhu acan akayiwa marigayiya jaririya sutura aka kaita makwancinta ,



***


*T*un asubar farko usman yake tsakar gidan yana ɗaga murya tare da cewa duk shegiyar matar data san ina aurenta ta fitooooooooo,


babu ɓata lokacin mata suka ringa bulbulowa daga cikin ɗakunan su,,, suna zuwa gaban usman suna durƙusawa cikin girmamawa tare da tsoro,,,,,,


Matanshi huɗu da suka gurfana a gabanshi usman yace to kunsan abinda yasa na tara ku anan ne?""" sukace A, a gaba ɗayansu,,,, 


usman yace to zankai halima asibiti a cire mahaifarta saboda ta haifo man mace a cikin gida,,,, dan haka duk wanda take gurin haifar mace saita kiyaye,,,,,,


cikin kuka halima tace kayi haƙuri don Allah ka sake bani koral idan na sake haifar mace a gidan nan, ka sakeni na yadda,,,,,,,,, 


wata irin dariya usman ya kece da ita tare da cewa kunfaji abinda tace?"" kun yadda?""" sukace E , yace halima tace in saketa idan ta sake haifar mace,,,, cikin kuka halima tace Eh,,, usman yace to kowa ta tashi tata ta fishsheta,,,,


gaba ɗaya suka tashi kowa ta koma ɗakinta,,,,,,,,,,,


***


*B*ayan wasu watanni, usman ya ɗuro wuta wa iyalinsa, cewa ya yaji shiru har yanxun baiji an fara amai a gidan ba,,,,,


Wata matarsa suwaiba, "yar duniyace ta bugawa a jarida,,,, tace mai gida nidai ina maka albishiri tare da sanar dakai cewa ina ɗauke da cikin shugaban ƙasa,,,, cikin jin daɗi usman yace kin tabbata?""" suwaiba tace ta tabbata, usman yace yawwa,,,,,,


Tou pha gaba ɗaya usman ya maida kulawarsa akan suwaiba, duk inda yaje ya dawo yana ɗakinta wannan ciki ana ririta shi,  duk daren duniya sai an yanka kaza suwaiba taci,,,,,, to usman baisan suwaiba bata ɗauke da cikin uwar kowa ba,,,, 


Koda watanni suka ci gaba da shuɗewa ganin asirinta zai tonu tace ma usman zataje ganin gida,,,, usman bai yadda ba, amma saboda kwarewa da bariki irinta suwaiba, saida ta labbaci usman ta tafi...........


bayan tafiyar suwaiba, wata matarsa zulai ta aihu, ta samu ɗa namiji, amma baizo da rai ba,,,,, usman yayi kuka sosai dan haka ya saki zulai tare da cewa lallai itace ta shaƙe minister ya mutu,,,, bazaiyi ta asara ba,,,,,,,


bayan tafiyar zulai da wasu watanni Allah ya sauki ɗayar matarsa binta ta samu ɗiya mace amma bata zo da rai ba,,,,,,,,,



usman yayi hauƙa sosai sannan ya lallaɓa ya saki binta, kuma yace ta ɗauki gawar ɗiyarta ta tafi ta bar mashi gida,,,,,,,,,,,,,


ana cikin haka kuma Allah ya sake bawa halima ciki, wannan ƙaron usman baiyi wani rawar kai ba,,,,


koda halima ta tashi aihuwa mace ta sake aihuwa , tana durƙushe idonta na zubar hawaye, zufa sai keto mata takeyi tana kuka sosai,,,, 


Usman ne ya shigo ɗakin yana ta balbala bala,i sai bori yake kamar zai kashe halima,,,,, inna ta gaji da abinda yakeyi dan haka ta tafi ta kira malam nuhu,,, kafin malam nuhu yaxo Allah yayi wa halima rasuwa,,,,,,, amma ko a jikin usman sai ya koma masifa lallai bazai zauna da ɗiya mace ba a gidanshi, haƙiƙa saida asan gidan ubanda za,a kaita,,,,,


malam nuhu ya zaunar da usman yayi masa nasiha, tare da faɗakar dashi su zuri,a duk wanda Allah ya baka ka ansa hannu biybiyu kayi addu,a tare da fatan Allah ya shirya,,,,,,,


yace mashi wani yana can yana neman Allah ya bashi amma bai samu ba, malam nuhu yace kai kuma usman tunda Allah ya baka kayi haƙuri, dan Allah ya baka mace ya baka namijin kuma duk basu rayuwa ba, dan haka kayi haƙuri ka anshi wannan jaririya da Allah yasa mahaifiyarta ta rigamu gidan gaskiya,,,,


Usman yace to wallahi ko ta zauna a gidan nan babu ruwana da ita, babu abinci na babu sutura ta kuma wallahi bazan sanya mata suna ba,,,,,,,,


malam nuhu yace ba komai ni zanyi mata huɗuba, malam nuhu ya kalli inda jaririya take ta zabga kuka karmar zata suƙe,,,,,


Inna ta matsa kusa da jariryar ta ɗauketa tana rurruguta, ta rasa abinda zata bata tasha, haka aka shirya halima aka kaita makwancinta na gaskiya kamar yadda addini ya tanadassssss,,,,,,


Jarirya ranar haka ta kwana tana kuka amma usman ya hana a bata komai saboda bala,i irin nasa,,,,, jaririya ita kaɗai a ɗakin mahaifiyarta, kuma usman ya kama ƙofa ya kulle, yayi tafiyarsa da makulli, inna tazo ta zauna gaban ɗakin itama sai kuka takeyi kamar yanda jariryar takeyin kuka,,,,,,


Inna ta rasa wanda zai tayata bada haƙuri usman ya buɗe ɗiyar nan babu wanda ke akwai a gidan dan halin usman yasa ko "yan zaman gaisuwa babu,,,,


Haka ɗiyar tayi ta tsula kuka har gari ya waye, inna itama tana nan zaune tana kuka a ƙofar ɗaki,,,,,


Saida hantsi ya fito sannan usman ya dawo, ya buɗe ɗakin bayan ya shiga ya ɗauko ɗiyar da hannu ɗaya sannan yazo ya wurgota da hannu ɗaya wurin inna,,,,,,


aiko ɗiya ta ƙara ƙanƙarewa da kuka, inna ta ɗauki ɗiyar tayi ɗaki da ita,,,,, inna tana zuwa ɗaki ta shirya ta ɗauki ɗiya sukayi asibiti, a can aka rubuto ma inna madarar da zata riƙa bawa jaririya,,,,,,


haka inna ta dawo gida ta siyar da awakinta ta siyi madara,,,, to innace taci gaba da kula da jaririya wanda taci suna da safina,,,,,,,,,,


Bayan wasu watanni suwaiba ta dawo da yaronta namiji wanda yakai shekara ukku, amma saboda idon usman ya rufe bai tsaya bincike ba, sai murna yake yana cewa gwamna yaxo, to haka aketa kiran usman da baban gwamna,,,,,,,,,,


***


*B*ayan shekara goma, ɗakin suwaiba ne ta kunna waƙar barmani coge, a gabanta kuma yaronta ne, take ma shirin makaranta, tana bin waƙar tana cewa yaro kayi kyau da kakin soja""" sama ruwa ƙasa ruwa, ahayye sama ruwa ƙasa kuɗi,,, tana ma yaron shirin makaranta,,


to bayan ta gama shirya fahat ta miƙe tare da kama hannunshi suka fito tsakar gida inda mai kaishi makaranta yake zaman jiranshi,,,,,


bayan takai fahat ta dawo, tazo ta canja waƙa, kai kukama sana,a mata,,,, kukama sana,a mata macen da bata sana,a aurace,,,,,, dake da babu?"""" ta ɗaga muryarta tana kiran safina, dan haka babanta yake kiranta, wai da ita da babu,,, 



inna dake kwance bata da lafiya, ta kalli inda safina take amma ta kasa magana, safina dake zaune a gefen inna tana ta kuka dan jikin inna yayi tsanani sosai,,,,,,, taji suwaiba tana ƙara cewa dake da babu,,,


Da sauri safina ta miƙe tare da cewa iye,,,,,,,,, ta fita daga ɗakin da gudu,,,,, bayan taje ɗakin suwaiba ta durƙusa ƙasa tare da cewa gani umma,,,,,,,,,, suwaiba ta taso daga inda take zaune tazo gaban safina,,,,,,



kunne safina suwaiba ta kama ta murɗe ta murza cikin sigar cuta sannan tace ni nake kiranki zakice Eye?""" cikin kuka safina tace kiyi haƙuri na,am,,,, 


suwaiba tace shegiya marar *RABO* ɗauki kayana kije dana fahat ki wanke su,,,,, cikin kuka safina tace umma inna zan bawa abinci,,,,,,, suwaiba cikin tsawa suwaiba tace wallahi ƙaryane, wacaccan matacciyar tsohuwar bazaki bata abinci ba,,,, abincin uwaki,,,,,,


da Allah malama ɗauki ki fita,,,, safina ta miƙe jiki a sanyaye ta kwashe kayan ta fita daga ɗakin................

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻


💦💦💦💦

*RASHIN RABO*

💦💦💦💦


*R🅰SHIN R🅰BO*


*MEELAT MUSA*


*Domin samun littattafanmu sai nememu a shafinmu na facebook*


*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP*


*4-6*


***


*T*ana fita ta ajiye kayan ta nufi ɗakin inna,,, tana shiga da sauri ta ƙarasa don inna tana ƙoƙarin faɗowa daga saman katifar da take kwance,,,,,,


Tana matsawa, ta hau saman katifar ta riƙe hannun inna tana cewa matso kada ki faɗi ƙasa, dan bata da ƙarfin da zata jata saman katifar sosai,,,,,,


Cikin kuka da rawar murya irin ta majiyyaci yana jin jiki, inna tace sahina mutuwa zanyi,,,,, cikin far gaba da tsoro safina ta fara kuka tana cewa ki rufa man asiri kada ki mutu ki barni, ta ƙarasa maganar tare da ɓarkewa da wani irin kuka mai kama zuciya,,,,


Inna ta juyo da kanta a hankali ta kalli safina sannan tace kira man suwaiba,,,,,


Da sauri safina ta miƙe ta nufi ɗakin suwaiba, tana cewa umma inna tna kiranki,,,,, suwaiba dake kwance saman kujera kamar an ajiye asara, tayi wani shirgingim, ta tashi tana cewa ,


Kai waccan tsohuwa da jarabar tsiya take ko uwarmi zan bata ne?"" tsaki tayi sannan tace da Allah wuce kije kiman abinda na saka ki, idan kika sake komawa ɗakin saina tsiyaye maki idanuwa,,,,,,


Safina tace to, sannan ta fita daga ɗakin,,,, tana fita ta nufi inda ta ajiye kayan wanki ta fara,,,,,,,,


Duk kancareriyar ranar data kancare duk mutmin daya san ciwon jikinshi yana ɗaki ko wata lafiyyar inuwa yana sararawa, amma ita safina saboda rashin gata tana cikin ranar duƙe tana wanki,,,,,


Sai zufa takeyi ga wasu haweyen wahala da suke ta kwararowa daga cikin idonta,,,,,,


Babu ko sallama kuma babu yanayi na tausayi ya shigo cikin gidan, jin shigowarshi yasa ta miƙe da sauri tana goge zufar goshinta tare da goge hawayen idonta,,,, tace baba sannu da zuwa,,,,,,


Ɗaure fuska yayi sosai sannan yace dake da babu wai banace kada ki sake man magana ba?"" a daidai lokacin daya matso kusa da ita,,,,,,


Yaci gaba da cewa na la,aneki kuma sai kin lalace, yanda uwarki ta dasa man baƙin ciki ta sulale lahira ta barki sai kin zamar mata bala,in da zai hanata kwanciyar kabari,,,,,,


Baki safina ta saki tana kallon baba, yace kallarni da kyau usman ne baban gwamna, 


Murmushi safina tayi sannan ta duka taci gaba da wankinta,,,,,, shi kuma ya wuce ciki famkam fankam,


Bayan safina ta gama wankin ko matse kayan bata iyayi saboda sunfi ƙarfinta haka taje tahau saman turmi taci gaba da shanya kayan,,


Suwaiba data fito tsakar gidan cikin tsawa da magana mai firgitarwa tace lallai yarinyar nan ke tsinanniyar yarinya ne, dan uban uwarki nine zakiyi wankin kaya haka?"""


Cikin girmamawa safina tace umma , ai sun fita,,,, cikin zafin rai suwaiba ta iso wurinta taci gaba da gaggaura mata mari,,, baba daga ɗaki ya leƙo yana cewa ƙara mata ƙafirar Allah da haihuwarta tsinanniyar yarinyar nan wallahi gara a bani buhun masara,,,,,


saida suwaiba tayiwa safina lilisi sannan ta barta , safina tana duƙe wurin tana kuka mai tada hankali, ita kuma suwaiba kicin ta shiga ta ɗauko abinci sannan ta nufi ƙofar ɗakin inna,,,,,,


daga bakin ƙofa ta duƙa ta gyargyara mata abinci tare da cewa uwar miji mai tsawon kwana, kina mutuwa wannan ɗakin za,a rusa shi ayi gini mai kyau wa gwamna ana ciki  zaiyi rayuwa mai daɗi,,,,,


Yana zama gwamna zamu tafi gidan gwamnati, lokacin ke kuma ƙasa ta gama haɗiyeki ta mayar dake ƙasa, ta ƙarasa maganar tare da sheƙewa da dariya tare da tafa hannunta taci gaba da cewa,,,,


A lokacin da jiniya za,a riƙa yawo damu a gari munajin daɗi ina cikin mota ina cin kaji,,,,, baba daga ɗaki baba yace kwarai kuwa muje makka, gwamna ya gina mana gida mai bene,,,, suwaiba ta sake bushewa da dariya, haka dai tayi ta tsiyaya rashin mutunci baba yana kama mata,,,,,,


bayan ta gama ta tafi, safina ta tashi a gajiye ta nufi ɗakin inna,,,, inda suwaiba ta ajiye abincin ta ɗauka sannan ta matsa kusa da katifar inna,,,,, tana goge mata hawayen idonta,,,,,


bayan ta gama ta buɗe abincin ta fara bawa inna dake kwance,,,, dan bata iya tashi kuma safina bata iya tashinta zaune, dan haka daga kwance take bata abincin,,,,,,


saida safina ta tabbatar inna ta ƙoshi sannan ta goge mata bakinta ta bata ruwa tasha,,,,, sauran abincin ta ɗauka ta fito waje, dan ita dama tunin duniya babu kasonta a gidan,,,,,,,


tana fitowa a ƙofar ɗaki ta zauna saman kuɗinka, ta buɗe abincin ta fara ciki,,,,, baba da yake fitowa daga ɗaki, yaga safina tana cin abinci ya zaro idonshi tare da ɗaure fuska tamau kamar amerika ta kawo mashi yaƙi yayo kan safina,,,,,,,,


kafin ya iso da sauri ta tattara abinci ta kwashe ta tura shi duka cikin bakinta,,,,, tana zaro idanuwa saboda yanda abincin yake wucewa a maƙoshinta cikin wahala da taƙura,,,,,


yana isowa kusa da ita ya duƙar da kanta, yayi tayi mata ƙulli yana cewa amayo man abinci dan uwarki,,,,, safina kuma sak sauri takeyi ta haɗiya dan azabar yunwa dake damunta,,,,,,,


haka baba yaci gaba da dukanta yana takata yana talbinta,,,, hankalinshi bai kwanta ba, saida safina tayi gyatsa abincin ya fara dawowa ta amayeshi kaff sannan ya kwaso ƙasa ya zubawa aman yana cewa shegiya, sai yunwa ta kashe ki na huta,,,,,,,,


durƙusawa yayi kusa da safina sannan ya riƙo gashin kanta ya gaggaura mata mari sannan yace da kinsan yanda bana ƙaunar haihuwar ɗiya mace ba, da bakiyi gigin zuwa a matsayin ɗiyata ba,


Cikin yanayin wahaltuwa safina ta ɗago kanta tana kallon baba, hawaye suka ci gaba da kwararowa daga idonta, duk da ƙarancin shekarun safina tasan babanta baya da adalci,,,,


baba yace bari kallona shegiya , wallahi dake da babu ban kaunarki, bansanki saboda bana san ɗiya mace kwata kwata,,,,,, safina har yanxun kallon baba takeyi hawaye naci gaba da kwararowa daga idonta,,,,,,,


baba yaci gaba da cewa nan in baki abinci , inyi maki ɗinki in ƙare duk wahalata a kanki, kuma ki tashi aure inyi maki kayan ɗaki?"" ke kuma baki zuwa nemo ko sisi,,,,, tsaki yayi sannan ya miƙe tsaye tare da ƙara kaiwa safina harbi,,,,,,,


a daidai lokacin da fahat ya shigo gidan,,,,,,, da gudu baba ya ruga yana cewa oyoyo gwamna,,,,, ya rungumeshi , fahat yana ta dariya,,,,,


baba yace gwamna, sannu ɗana , maza kaje ka cire kayan nan muje in siyo maka abun daɗi, wata shegiya kuma saida yunwa ta kasheta,,,,,,, murmushi safina tayi daga inda take zaune , sannan ta goge hawayen da yake zubowa daga idonta,,,,,,,,,


haka baba yaja fahat suka tafi ɗaki, bayan wani lokaci suka fito,,,,, a gaban safina baba ya duƙa yace hau bayana ɗana,,,, fahat ya haye saman bayan baba ya goyeshi suka fita daga gidan,,,,,,,,,,,,,,,,,


Safina da gudu ta tashi ta shige ɗakin inna tana zuwa ta faɗi ƙasa tana kuka,,,,,,, inna dake kwance tayi amai a wurin jikinta sai ƙarma yake ,,,,,, safina ta fara turje turje tana cewa inna miyasa ni  mamana ta haifeni ta mace?""""


tunda tasan baba yafi san namiji miyasa bata haifeni namiji ba?""" taci gaba da kuka mai taɓa zuciya,,,,,,, daga ɗaki suwaiba ta fito tana guɗa ayyuri yuriiiiiiii,,,,,, ta tafa hannunta sannan tace da gwamna zakiyi takara ne?"""" yarinya gwamna yayi gaba saidai kibi ta bayanmu,,,,,,,,,,


safina taci gaba da kuka, suwaiba tayi ta hayaƙata, abinka da yarinta safina sai kuka takeyi tana faɗuwa ƙasa,,,, haka tayi ta kuka har baba ya dawo,,,,,,,


tana jin shigowar baba ta fito da gudu,,,,,,, sabon keke baba ya siyo ma fahat , fahat yahau sama baba yana turashi suna ma safina gwalo,,,, niko nace anyi ƙaton banza,,,,,,


Da sauri safina ta koma ɗaki,,,, baba yace yawwa ɗana bari inje in siyo maka ɗiyar roba,,,,,, wai saboda safina tana san ɗiyar roba shine bazai siya mata ba, amma dan ya ƙona ran safina zaije ya siyo wa fahat,,,,,


Safina ta ƙara fitowa daga ɗaki tace baba nima don Allah ka siyo man,,,,,,, baba yace Allah ya sawaƙe, ɗana kaɗai zan siyama wa, fahat yabi bayan baba yana rawa yana tsalle,,,,, baba ya rungume fahat yana sunbatarshi,,,,, baba yace yi mata Eho ɗana ,,,,,,,,


Fahat ya kalli safina, yayi murmushi , sannan ya kalli baba yace baba basai anyi mata ba,,,,, baba yace idan bakayi mata ba bazanje dakai ba,,,,,,,


Kuka fahat ya farayi,,,,, da sauri baba ya kama hannun fahat yana cewa muje dan bayasan kuka fahat,,,, haka suka sake fita baba yana riritashi,,,,,,,,,,


ita kuma safina ɗaki ta koma ta gogewa amai da inna tayi,,,,,,,,,,,,,,,



***


*I*nna yau jikinta yayi tsanani sosai, sai fizge fizge takeyi,,,, safina taga abin yafi ƙarfinta, don haka tazo tace wa suwaiba, umma inna bata lafiya,,,,,,,,,


suwaiba tace waccan matacciyar tsohuwa ta isheni muje inga uwarmi takeso,,, safina tayo gaba suwaiba ta biyota,,,,,,,, a ɗakin suka samu malam nuhu,,,,


suna shiga ɗakin ga baba a gefe ga suwaiba ga malam nuhu ga safina,,,,,, cikin yanayi jigatuwa inna ta fara magana cikin rawar murya,,,,


Tace suwaiba, abinda nakeso dake sahina ki adanata ki daina biyewa isiman , kina wulaƙanta ta, inna ta lumfasa, sannan taci gaba da cewa shi yaro duk abinda kayi masa bazai manta dakai ba,


Yarinyarnan bata da mahaifiya tunda ta rasu idan kikayi mata riƙon adalci idan tsufanki yazo bazata barki ki wulaƙanta ba, zata adanaki ta tattalaki ta mayar dake "yar gatar tsohuwa,,,,,,


saida inna ta sake sararawa sannan taci gaba da cewa, shi isiman abinda na fahimta jahilce ne yake damunsa , dan wulaƙanfa waninka *RASHIN RABO* ne,,,,,,,


tunda nake ban taɓa ganin ubanda baya ƙaunar jininsa ba kamar isiman,,,,, inna tayi tari ƙuhul ƙuhul sannan taci gaba da cewa, suwaiba sahina ɗiyar mijinki ce , na baki amanarta, idan kika riƙeta kin samu ɗiya idan kuma kika wulaƙanta ta haƙiƙa kema kinyi dibgegen *RASHIN RABO*


tsaki usman yayi sannan yace da Allah suwaiba rabu da ita,,,,, tunda kike a duniya kin taɓajin mace gwamna?"" ko kin taɓajin mace shugabar ƙasa?"" to ko kansila kayan banza babu mace,,,,,, tashi mu tafi ta wani zaunar damu tana raina mana hankali,,,,,,,,


Suwaiba ta miƙe tsaye ta kama hannun gwamna, shima usman tashi yayi suka fita suka bar ɗakin,,,,,,,,,


Ɗaki ya rage daga malam nuhu sai inna sai safina,,,,,  inna tana ta magana amma kwata kwata maganar bata fita, saidai bakinta da yake motsi,,,,,,,



malam nuhu yace safina, ibo ruwa, maza maza, saboda malam nuhu ya kula inna tana cikin yanayin halin gangarawa,,,,,,,,


safina tana fita, inna tace ta fara salati,,,,, da sauri malam nuhu ya matsa kusa da inna, yana tayata salatin har rai yayi halinsa,,,,,,,,


Ita kuma safina da gudu ta shigo ɗakin da ƙofin ruwa a hannunta, amma tana shigowa taga malam nuhu yaja zani ya lulluɓe inna, tace malam miye?""" yace kiyi haƙuri safina,,,,,,


Kofin hannunta ta saki ya faɗi ƙasa, sannan tace inna tayi bacci ne?""" """"""

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻


💦💦💦💦

*RASHIN RABO*

💦💦💦💦


*R🅰SHIN R🅰BO*


*MEELAT MUSA*


*Domin samun ƙayataccin littattafanmu sai ku taremu a shafinmu na facebook*👇🏻


*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP*


*7-9*


***


*S*hiru yayi baiyi magana ba, safina cikin kuka ta matsa kusa da inda inna take kwance malam nuhu ya sauketa daga saman katifar tana ƙasa ya lulluɓeta da zani,,,,


Durƙusa tayi kusa da gawar inna sannan ta yaye zanin da aka lulluɓeta dashi tace inna tashi ki koma saman katifa,,


Malam nuhu ya kalli safina cikin yanayin tausayawa, sannan ya matsa inda take durƙushe ya kamota ya miƙar da ita tsaye,,, sannan yace kiyi haƙuri inna ta rasu,,,,,,,,,,


Cikin rawar baki safina tace inna ta rasu,?"" a daidai lokacin da idonta yake kawo hawaye,,, malam nuhu yace Eh kiyi haƙuri kinji?"" dan wannan mutuwar ke kaɗai akayi ma ita,,,, ai safina bata tsaya jin ƙarashen maganar malam ba, ta saki wata irin ƙara mai tada hankali  tare da sulalewa ƙasa somammiya,,, da sauri malam nuhu ya fita daga ɗakin tare da kiran usman usman,,,,,,,,


Daga ɗaki yake cewa ya akayi ne malam?"" cikin damuwa malam yace ka fito inna ta rasu,,,, subahanallah inji usman sannan yaci gaba da cewa baiwar Allah tsohuwa an isko sheraka, runfa ta gaji da shirgi ta rushe, a daidai lokacin da yake fitowa daga ɗakin gaba ɗaya,,,,,,


Usman yana fitowa yace to malam nuhu ka zama sheda basai sauran "yan uwa sunxo ba kace baka san wannan wasiyyar ba, a gabanka kafin inna ta karci ƙasa haka tace wannan gidan ya zama nawa?""


Malam nuhu ya kalli usman sannan yace a ina akayi haka?"" usman yace a ɗakin tsohuwa, malam nuhu yace ni ya akayi banji ba?"" usman yace oho maka bansan ina hankalin naka ya tafi ba,,,,,,


Malam nuhu yace ƙaryane, usman yace kaine kake ƙarya babban munafiki mai hassada kuma wannan gidan babu maishi saini baban gwamna, ni nake da *RABO* a gidan nan, yana maganar yana buga ƙafarshi ƙasa, tare da tada jijiyoyin wuya,,,,,,


Malam nuhu ya kalli usman ya girgiza kanshi , cikin jimamin hali irin nasa, gaba ɗaya yabi ya birkice saboda tsabagen san abun duniya, duniya ta rufe mashi ido ba mutuwar mahaifiyarshi ke gabanshi ba, wai ta gida yake,,,,,,


Usman yace duk munafincin da zaka ƙulla a ranka wannan gidan nawa ne, babu maishi saini,,, yana maganar ne yana bubbuga ƙafarsa ƙasa,,,,


malam nuhu yace to , yanxun ba wannan ba, kira "yan uwanka ka sanar dasu rasuwar mahaifiyarku,


Tsaki usman yayi sannan ya fiddo wayarshi, ya fara kiran dangin shi, duk wanda ya ɗauki waya sai usman ya fashe da kuka, yana shashshekar kuka tare da phayce majina,,,,


haka yayi ta faɗar rasuwa, bayan ya gama ya shiga ɗakin inna, malam nuhu yabi bayanshi,,,, suna shiga baba yace itama wannan ta mutu ne?"" malam nuhu yace A, a, baba yace ta mutu itama, malam nuhu yace gatanan tana lunfashi suma tayi,,


baba yace ubanda yasa ta suma shi zaisa a haɗa da ita akaita kabari,,, malam nuhu yace wai miye yake damun kanka ne?""" da sauri usman yace baka san abinda yake damuna ba?"""  malam nuhu yace Eh, baba cikin zaro idanuwa yace kuɗi , ya ƙara zaro idonshi sannan yace kuɗi  sune matsalata,,,,,, 


tsaki malam nuhu yayi tare da cewa Allah ya tsaremu da baƙin hali irin naka, daga haka malam nuhu ya fita ya samo ruwa, ya fara yayyafawa safina,,,,,,


Bayan ta farfaɗo malam nuhu yace tashi kije waje, safina ta miƙe jiki a sanyaye sai taɓe baki takeyi tana ci gaba da kuka,,,,,


To haka mutane dai sukayi ta taruwa a hankali, duk "ya"yan inna sun hallara, "ya"yanta maza ne dukansu su ukku, kuma dukansu Allah yayi masu rufin asiri ya basu arxiki sai baba dake cikin talauci da baƙin hali,,,,


Haka akayi sutura wa inna, kamar yanda addini ya tanada, lokacin da aka fito da gawar inna danyi mata sallah akaita makwanci, safina da gudu taje ta riƙe mankarar , cikin kuka mai taɓa zuciya tace , tace haba inna, mi nayi maki zaki tafi ki barni?"""


kiyi haƙuri ki tashi don Allah, idan kika barni bansan ya zanyi ba?" babu mai sona saike, ki tausaya ma rayuwata innata ki dawo,,,,,,,,,,,,, ta sake fashewa da kuka,,,,,,,


Cikin zafin rai baba ya matso ya fizgeta da ƙarfi ya wurgar da ita gefe ɗaya, sannan yace sannu uwar shishigi toko mu data haifa munyi haƙuri bareke karere kayan banza, to dan uwarki idan kika sake riƙe mankararnan saina sa an tafi dake an haɗa da innar an rufe inga tsabar kauna,,,,,,


yayan baba, Abubakar yace haba usman miye haka?""" baba yace kainaci uwarka , ina ruwanka da rayuwata, ko kaga nayi maka magana tunda kazo?"""


tsaki Abubakar yayi amma baice komai ba,,,,,, inda safina take zaune ya kalla tana riƙe da hannunta da alama wurgawar da baba yayi mata taji ciwo,,,, tsaki yayi sannan ya fita daga gidan,,,,


Haka akaje aka kai inna makwancinta, aka dawo, akaci gaba da zaman gaisuwa, amma safina tana cikin damuwa ga rashin inna ga kuma wahala da takeji na hannunta da yakeyi mata ciwo,,,,


Bayan anyin addu,ar bakwai, kowa ya kama gabanshi,,,,, gida ya rage daga fahat sai suwaiba sai baba sai safina,,,,,,,


safina ce kaɗai kwance a saman tantagaryar sumintin ɗakin inna, tana ta juyi ga azabar ciwo wanda bata iya ɗaga ko hannunta , kuma hannun yayi kumbiri sosai, ga azabar yunwa da takeji,


baba ne ya shiga ɗakin , tare da cewa tashi, cikin tsawa ya sake cewa tashi dan uwarki ki fitar man daga ɗaki,,,,,, a galabaice safina ta ɗago kanta ta kalli baba, cikin kuka tace baba don Allah ka taimakeni ka barni in zauna, anan, don Allah kasa a bani abinci yunwa nakeji,,,,,,,,,,,


Durƙusawa yayi kusa da safina, sannan ya riƙo gashin kanta ya ɗago mata fuska, yace dake da babu, kin cika taurin rai, kinga inna ta sare taga tafiyar mai nisa ce,  saboda azaba ta buɗa, tana can cikin ƙasa tana sararawa, toke zaman mi kike a duniya??"""""


Hawaye yaci gaba da ambali a fuskar safina, ta sake kallon babanta sosai,,,, tasa hannunta ta goge hawayen idonta, cikin rawar murya tace baba, waimi nayi maka?"""


zaro ido baba yayi sannan yace bama kisan abinda kikai man ba ko?"""" cikin kuka safina tace don Allah baba idan wani abu nayi maka ka faɗa man nifa ɗiyarka ce,,,,,,,


kasheta da mari baba yayi , da sauri ta duƙar da kanta ƙasa tana ɓarkewa da kuka saboda azabar marin, baba yace dan uwarki kin taɓa jin inda namiji ya haifi mace?"",,,,,, safina tayi shiru, riƙota yayi da niyar ɗaga ta,,,,, hannunta mai ciwo daya riƙe yasa ta saki wata irin ƙara, harsai da tayi fitsari saboda azaba,


Baba yace kam kam kam, jijjjigata yayi sannan ya wurgota tsakar gida, yana cewa ni zakiyi ma fitsari, toyau saina cire wannan shegen hannun,,,,,, safina ta tashi zaune dakel , tana wani irin nishi , tace kayi haƙuri na fito daga ɗakin,,,,,,,,,


Kayanta baba ya fara watsowa daga cikin ɗakin, saida ya watsosu duka sannan ya rufe ɗakin,,,,, yana kakkaɓe hannunshi yana cewa sai a tafi abarman gida,,,,,,,,,


safina tace baba idan na tafi ina zanje?"" watsa hannuwa baba yayi sannan yace kije can dangin uwarki, fahat ne ya shigo gidan yana cewa lafiya?""",,,,,,,,,


Baba yace gwamna nace ta tafi tabarman gidana,,,,, fahat yace haba baba, kayi haƙuri,,,,,, baba yace kai ba haƙuri a lamarin zama da ɗiya mace,,,,


fahat yace to idan bazaka zauna da mace ba, nima zan haɗa kayana inbita,,,, da sauri baba yace ina zakaje ?"" yace ita ina zataje?"",,,, baba yace duniya zata shiga daga can saita halaka kowa ma ya huta,,, fahat yace nima can duniyar zanje,,,,


baba yace A, a, muna tare , fahat yace to itama muna tare da ita,,,, inda safina take zaune baba ya kalla sannan yace shegiya,,,, yaja fahat suka wuce daga wurin,,,,,,,,,,,,


Safina tana nan zaune tana kuka har hadari ya taso, duk ruwan da akayi akan safina ya ƙare saboda bata iya tashi, banda rawar sanyi babu abinda safina takeyi, ga kayanta duk sun jiƙe, wanda baba ya watso mata daga ɗakin inna,,,,,,


tana wurin kwance tana kuka, babane ya fito, safina tabishi da kallo amma ta kasa magana,,, harya fita daga gidan,,,,,,


jan jikinta tayi ta koma zaure,,,,, anan ta samu ta raɓe taci gaba da kuka, bayan baba ya dawo zai shiga ciki tace baba don Allah ka taimaka man hannuna ka bani kuɗi inje ayi man gyara,,,,,


Ko inda take baba bai kalla ba, ya wuce ciki famkam famkam, a gajiye safina ta miƙe cikin wahaltuwa, tayi gidan malam nuhu...................


bayan taje, a ƙofar gida ta samu malam nuhu, suka gaisa, tace malam hannuna yana man ciwo ne, malam yace miya sameki ne?"" safina tace nima bansan abinda ya sami hannun ba,,,,,


Malam yace muga hannun, safina ta matsa kusa dashi tana tallabe hannun, malam nuhu kasancewa mai ɗauri ne, haka ya duba hannun safina yayi mata kamu,,,,, ihu takeyi sosai saboda ciwon ya daɗe sosai,,,, saida yayi mata kamu sannan ya ɗaure hannun,,,,,,,


cikin gidanshi ya shiga ya kawo mata abinci taci, sannan yace to taje gida maza maza ta cire kayan jikinta, godiya safina tayi sannan ta tashi ta taho gida,,,,,,,,



safina haka taci gaba da jinyar hannunta, lokaci lokaci tana zuwa wurin malam nuhu yana mata gyara,,, ,har ta samu sauƙi sosai,,,,,


Zaune take a zaure tana gyara kayanta tana sawa a cikin kwali, bayan ta gama ta kwanta ta ɗora kanta saman kwalin tana tunanin rayuwa,,,,,,,


suwaibace ta shigo cikin zauren , tare da wasu matsa tana cewa yawwa anan zaku saka man tukwanen , sai a rataye man tattabaruna, inda safina take zaune takai mata halbi tare da cewa matsa daga nan jaka, tattabaruna za,a saka man anan,


Murmushi safina tayi sannan ta tashi ta ɗauki kwalin kayanta tayi cikin gida,,,,,,,, haka aka ɗaura tukwane a sama aka rataya ma suwaiba tattabarunta,,,,,,,,


To haka rayuwar safina taci gaba da tafiya, bata da wurin kwanciya ita da gidan ubanta, idan ruwan dare akeyi haka zata raɓa a zaure cikin tattabaru da kwalin kayanta tayi kwanciyarta, idan kuma ba,ai ruwa tana tsakar gida,,,,,,,,


shi kuma baba sai wani gyaran ɗaki akeyi waishi zaiyi sabuwar amarya, hmmm suwaiba ko sai bala,i takeyi tare da hanama gidan zaman lafiya,,,,,,,,,,,

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻


💦💦💦💦

*RASHIN RABO*

💦💦💦💦


*R🅰SHIN R🅰BO*


*MEELAT MUSA*


*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP a shafinmu na facebook zaku nemu dan samun littattafanmu*


*Dedicated REAL MAI DAMBU*



*10-12*


***


*D*a sauri suwaiba ta fito daga cikin ɗaki tana masifa tana zage zage, inda safina take tsugunne tayi kanta tayi ta dukanta summun buƙumun , babu ji babu gani,,,,,,,,


Cikin kuka safina tace umma mi nayi?"" suwaiba tace ubanki yaja maki, da zaiyo man kishiya,,,,,, inci uwarki inci uwarshi sannan kishiryar taxo itama inci ubanta,,,,,,,,


Saida suwaiba tayi dukawa safina sosai, sannan ta koma ɗaki tana zage zage, bayan suwaiba ta koma ɗaki safina ta ɗauki kwalin kayanta tayi cikin barandar tsakar gida,


tana zuwa zama tayi sannan ta riƙe idonta da yake mata zafi wurin dukanta suwaiba taji mata ciwo,,,, kwanciya tayi ta ɗora kanta saman kwalin kayanta amma har yanxun hannunta yana riƙe da idonta,,,,,


Kuka takeyi daga kwance sosai,,,,, amma babu sauti sai hawaye da suke kwararowa daga cikin idonta,,,,,,,,,,,,,,,,,,,


Baba ne ya shigo cikin gidan yana riƙe da hannun fahat,,,, daga kwance safina ta ɗaga muryarta tare da cewa baba sannu da zuwa,,,, bai kalli inda safina take ba suka shige cikin ɗaki,,,,,,,,


Da safe safina sai kuka takeyi saboda azabar ciwon ido,,,, tana nan baba ya fito, ta gaishe shi bai ansa ba, yayi gaba yaci gaba da tafiyarshi, bayanshi safina tabi tana kuka sosai,,,,,,


Tace baba don Allah ka siyo man maganin ciwon ido, cikin zafin rai baba ya juyo sannan yace bazan siya ba, nawa uwarki ta bani tace in kula dake bayan bata da lumfashi?""",,,,,


safina tayi shiru, baba yace to wuce kiba mutane wuri,,,,, cikin sanyi da kalar tausayi safina tace baba ka  taimaka man kada idona yazo ya daina gani,,,


Baba baiyi magana ba, fahat ya iso wurin tare da cewa baba ka bani kuɗi,,,, babu tambaya ba komai dafa kanshi baba yayi sannan yasa hannunshi a aljihu ya ciro kuɗi ya bashi,,,,,,


Yana bashi fahat yayi gaba, baba ya kalli safina sannan yace Allah yasa idanuwan naki su tsiyaye, ki makance ki kurumce sannan kuma ki haɗu da cutar hauka,,,, safina batayi magana ba ta juya tayi cikin gida,


Tsaki baba yayi sannan shima ya juya yayi tafiyarsa, saida rana tayi sosai sannan safina ta tashi ta lallaɓa tayi gidan malam nuhu, bayan taje ta faɗa mashi tana ciwon ido,,,,,,


shima baya da kuɗi don haka wani farin kwalli ya bata yace tayi amfani dashi, duk dare zata riƙa shafawa, safina ta ansa tayi godiya sannan tayo gida,,,,,,,,,


Safina duk dare tana shafa kwallin da malam nuhu ya bata, kuma idonta yana mata sauƙi sosai, 


yau gidan nasu safina ya kacame sosai, dan suwaiba banda tsine tsine babu abinda takeyi, saboda yaune ranar da amaryar baba zata tare, danginta cike da gida suna mata jeren kayan ɗaki,,,,,


To suma dai "yan masifa ne, dan duk wanda suwaiba ta zaga ko ɓatanci akan su basa haƙuri ramawa sukeyi, to suwaiba taga inda aka fita tsantsan iskanci don haka ta shafa ma kanta lafiya ta koma ɗaki ta zauna,,,,,


haka suka gama jerensu tsaff, kuma basu tafiya sai an kawo amarya,,,,,,,,,,,,


da daddare aka kawo amarya, banda guɗa da sheganta babu abinda sukeyi, sai habaici da suke zungurwa suwaiba, suwaiba kuwa taga inda aka fita tantagaryar iskanci don haka ta koma ɗaki tayi muƙus,,,,,,


haka ƙawayen amarya suka gaji da iskancinsu, sannan sukayi bankwana wa amarya raliya suka tafi,,,,,,,,,,,,,,,


Bayan tafiyar ƙawayen amarya suwaiba ta fito, tunda taga babu kowa a gidan daga ita sai raliya, don haka ta fito dan taci mata bira,uba, saboda haka ɗakin raliya suwaiba tayiwa tsinke,,,,,,,,,,,


tana zuwa, babu ko sallama tace ke jaka ubanmi ya kawoki gidana?"""",,,,,,, raliya tayi shiru, suwaiba tace to fita kibi wa,anda suka kawoki tun kafin in kware maki fatar jiki saboda azaba,,,,,,,,,,


Wata irin guɗa raliya tayi sannan ta dunƙula wani luƙeƙen zagi ta zungurawa uwar suwaiba, sannan tace ke jaka, ka dabba ke karuwa, ke ɗiyar gidan talakawa, kama kanki dan raliya tafiki bala,i, raliya taci gaba da cewa kinji ana faɗin renon cikin ƙasa??""""""",,,,,,,


Raliya ta nuna kanta sannan tace to nice nan,,,,,,, duk duniya irin raliya ɗayace, danni cikin kabari aka haifeni,,,, nonon gawa nasha na girma, cikin kabari nayi rayuwa, shi yasa na tashi rabi mutum rabi ifiritu, lunfasawa raliya tayi sannan taci gaba da cewa,,,,,,,


Idan nayi maki duka ɗaya yau za,ayi jana,izar ki in ɗaukeki saman kafaɗata in kaiki har kabari,,,, dan haka fice man a ɗaki,,,,,,,,


Tsaki suwaiba tayi sannan tace duk wannan haukar taki batasa inji tsoronki, ko daga lahira kika dawo, sai kin fitar man a gidan miji,,,,,,,,,


saukowa raliya tayi daga saman gado sannan tazo kusa da suwaiba ta tsaya, tace uwarmi kike da suna ma?""" raliya ta tambayi suwaiba,,,,,, suwaiba tace uwarki nake da suna,,,,, raliya tace to bara kiji, tun kina gani ki fita kafin insa rashin imani in tsiyaye maki idanuwa babu tausayi,,,


Tsaki suwaiba tayi sannan  takaiwa raliya wani irin duka,,,,,,, cikin ɓacin rai raliya ta tattara suwaiba ta wurgata tsakar gida, sanna ta fita,,,, inda suwaiba take kwance tana nishi,,,, raliya ta nufa, saman ƙafarta raliya ta ɗora kafarta, sannan tace ya kikaji "yar rali?"",,,,,,,,,,


suwaiba tayi shiru, raliya tace zancen banza , kawai,,,, tsaki tayi sannan ta koma ɗaki,,,,,,,,,


Saida suwaiba ta gaji da nishinta sannan ta miƙe tayi inda safina take,,,,,, tana zuwa takai mata wani irin halbi tare da cewa dariyar uwarmi kike?"""",,,,, wata irin ƙara safina ta saki saboda zafin harbin,,,,,, raliya daga ɗaki tayo waje tana cewa uwarmi tayi maki ne?""",,,,, taci gaba da cewa ni na dakeki a wurina zaki rama ba wurin yarinya ba,


tsaki suwaiba tayi sannan ta nufi ɗakinta, ita kuma raliya tace zo nan ,, safina ta miƙe tayi wurin raliya, cikin tausayawa tace sannu kin daina jin zafin?""",,,,, 


cikin kuka safina tace mata E, raliya tace ya sunan ki?""",,,, safina cikin muryar kuka tace safina,,,,, raliya tace sapna kenan suna ƙawata,,,,,,,


Ke kuma ina mamanki?"",,,, safina cikin maganar kuka da rawar murya tace ni banda mama, durƙusawa raliya tayi cikin tausayawa sannan tace ba gani ba, tana maganar tana murmushi tace ai nine mamarki,,,,, jawo safina jikinta tayi sannan ta rungumeta sosai, tanajin ƙaunarta a ranta,,,,,,,, 


itama safina rungume raliya tayi sosai,,,, raliya ce tace amma miyasa bakya wanka ne?"",,,,, safina tace ummana kinji inayin wari ne?"",,, raliya tace A, a ƙamshi kikeyi, ta ƙarasa maganar tana murmushi,,,,,


safina tace ummana idan kinyi abinci ki bani inci yunwa nakeji, cikina yana man zafi , raliya tace aiko yanxun nan mamanki zata baki abinci ina ne kicin?""",,, kallon raliya safina tayi sannan tace ai idan kinje umma zatayi duka ma dukanmu,


raliya tace babu mai iya dukana kinji, muje "yata,,, kama hannun safina tayi sukayi kicin,,,, raliya tana zuwa ta fara bubbuɗa kwanuka har ta samu abinci, 


Ɗaukowa tayi suka fito ɗakinta taja safina suka tafi, bayan sun shiga ta ajiye mata abinci tace ta zauna taci,,,, zama safina tayi tana zama ta fara cin abincin wani irin ci take mashi, bata taunawa haɗiyewa kawai takeyi,,,,,,,


raliya tace kici a hankali, babu wanda zai ansa maki kinji, magana safina tayi irin akwai abu a bakinta, tace idan baba yazo shine zai kwace ya zubar,,,,,,, tana maganar ne tana zaro idanuwa ta saboda yanda abincin yake kartar maƙoshinta yana wucewa kamar tana haɗiye bala,i,


tsaki raliya tayi sannan tayi tagumi tana kallon safina, haƙiƙa wasu matan basu da adalci dan taƙamar babu maman yarinyar a gida, sai a kunna mata azaba da ƙangin rayuwa?"",,,,,,


tana tunani taji safina tace ummana na cinye,,,, raliya tace tashi muje inyi maki wanka,,,,,,, da sauri safina ta fara cire kayan jikinta, dan rabonta da wanka bata san adadin kwanakin ba,,,,


a daren saida raliya tayi wanka wa safina, gal, sannan tace ina kayanki?""",,,,, safina tace suna zaure , raliya tace zaure kuma?""",,,, kai safina ta ɗaga mata alamar, Eh, raliya da kanta taje ta ɗauko kayan safina bayan ta zo ɗaki ta buɗe kayan taga babu kayan sawa kwata kwata, dan kayane tun na jarinta,,,


Bata da yadda zatayi dole ta mayar da kayan ta rufe,,,, a kayanta ta ɗauko zani ta bawa safina ta ɗaura sannan tace ta hau saman gado ta kwanta,,,,,, safina ta kama gado taye tayi kwanciyarta,,,,,,,,,



lokacin da baba ya dawo ya shiga ɗakin amarya cikin jin daɗi da nishaɗi, dan baba ba ƙaramar ƙauna yakewa raliya ba,,,,


bayan ya shiga ya zauna, raliya tayi mashi sannu da zuwa,,, ya ansa cikin kulawa,,,, inda safina take kwance ya kalla, sannan yace waccan ɗiyar waye ya kawota nan?""",,,,,,, raliya tace uwarta ,,,,, baba yace waye uwar tata ne?""",,,,,,,, raliya tace nice,,,,,,,,,


baba yace haba "yar rali, gaskiya fitar da ita daga ɗakin nan,,,,, "yar rali tace miyasa zata fita?""" baba yace saboda bana ƙaunarta, raliya tace miyasa baka santa?"""",,,,,,,


baba yace saboda ɗiya mace ce ita,,,,,, raliya tace ita ɗiya mace ba,a santa ne?""",,,,,, yace nine bana san ɗiya mace,,,, raliya tace ko akwai dalili?""""",,,,,,,,,,


baba yace basai kinji ba amma gaskiya fitar da ita , raliya tace bazan fitar ba, gaskiya duk da baka faɗa man dalilinka ba, amma ina horonka da kaji tsoron Allah, su "ya"ya amana ne a wurin iyayensu, ka sani su "ya"ya haihuwarsu kake amma baka san waye zaiji ƙanka ba,,,,,


na roƙeka kabarmin sapna a hannuna idan baka santa ni ina santa albarkacin soyayyar da nake maka,,,,,tsaki baba yayi sannan yace nifa bazaki gane ba,,,, raliya tace nima bazaka gane nawa manufar ba,,,,,,


yayin da sheɗan yake ingizaka zuwa ga wata hanya wanda bata da kyau kai bazaka gane rashin rabo ne, sai tsufanka yaxo,,,, to da kuɗi da "ya"ya ba,ayi masu wuguwar riƙo, zaka mutu kuma zaka iske Allah duk abinda kayi akan iyalinka da ahalinka sai ubangiji ya tambayeka,,,, kaji tsoron Allah kada ka wulaƙanta abinda Allah ya baka,,,,,,,,,


kada ka manta wani da kuɗinsa yana neman Allah ya bashi ɗan ko ɗiyar bai samu ba,,,,, kana iya faɗar dalilin da ubangiji ya hanashi?""",,,,, kaida Allah ya baka faɗaman nawa ka bashi ya baka kyautar sapna?""",,,, tsaki usman yayi sannan yace ta tashi muje,,,,,,,,,,,,,,,,


yaci gaba da cewa ni bana san wannan maganar taki irinta malamai,,,,,, murmushi raliya tayi sannan ta miƙe tabi bayan usman suka nufi ɗakinshi,,,,,,,,,,

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻


💦💦💦💦

*RASHIN RABO* 

💦💦💦💦


*R🅰SHIN R🅰BO*


*MEELAT MUSA*


*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP a shafinmu na facebook domin samun littattafanmu*


***


*13-15*


*T*un asalitin farko raliya ta fito daga ɗakin baba tazo ta tashi safina tayi sallah, 


Safina tashi tayi ta sauko daga saman gado, taje tayo alwalla, taxo ta dungura sallah tunda bata san yadda ake sallah ba,


Safina tana nan zaune idan tayi sallah, raliya ta shigo ɗakin tana cewa tashi ki shirya kada ki makara ga fahat ce harya shirya,,,,,,,,,,,


Safina tace ina zani ummana?""", raliya tace makaranta mana a daidai lokacin da take zama gefen gado,,,,,,,,


Safina tace ai bana zuwa makaranta,,, raliya tace miyasa?""",,,,,, duƙar da kanta safina tayi wasu hawaye suka gangaro daga kwarin idonta, raliya tace bakiji ina magana ne?""""",,


Cikin kuka ba tare da  safina ta ɗago kanta ba tace bana makaranta, kuma nace baba ya sani amma yace bazai sakani ba, ta lumfasa sannan taci gaba da cewa, yace karatun ɗiya mace baida wata amfani amma ɗa namiji shi ake ginawa yayi ilimi saboda zama gwamna,,,,


Raliya tace wannan wane irin zance banza ne?"" adaidai lokacin data miƙe tsaye,,,, hannun safina ta kama tajata suka fita daga ɗakin,,,,,


Ɗakin baba tayiwa tsinke, har yanxun tana riƙe da hannun safina, suna shiga ɗakin baba suwaiba tana zaune,,,, sallama raliya tayi sannan tace mai gida,,,,,,,,,


Ɗago kai baba yayi yana kallon raliya ba tare da yayi magana ba, raliya tace akai yarinyar nan makaranta,,, tsaki suwaiba tayi sannan tace sannu gwana, shi uban yarinyar baya harkarta saike?"",,,,,,,


Shin waike jira ma, kike wani rawar kai, waye yace maki ana nuna gwaninta akan ɗiyar kishiya?"""",,,, haka zaki ginata ki dage akan a bata ilimi ki kyautata mata, amma idan ta girma ta girgije kece zata fara ciwa kanbura,uba,,,,,,,


Inda suwaiba take zaune raliya ta kalla sannan tace da Allah malama dakata badake nake ba,,, da uban yarinyar nan nake magana ta nuna safina da hannunta, sannan taci gaba da cewa ni don Allah nakeyi banyi dan safina ta girma ta zama mai kuɗi ko wani abu ba ta kyautata man,,, A, a, nayine saboda Allah dan nima bansan yanda tawa rayuwar da bayana zata kasance ba,,,,,


Dan uwar yarinya ta mutu shine sai ace bata da sauran galihu da "yan ci a gidan ubanta?""",, ke kina da tabbas taki rayuwar zata ɗore dake da ɗanki?""",,,,, ciwo ko mutuwa suna iya kamaki, baki so a auro wata taxo ta kyautata maki ta kyautatawa rayuwar ɗanki?"""",,,


suwaiba tace aini ba mutuwa ba ciwo a tsarin rayuwata kuma makaranta baza kaita ba, idan dai ina lunfashi a doron duniya, raliya tace aisai Allah ya kasheki idan har zaki zama fitina a rayuwar wani,,,, da sauri suwaiba ta miƙe sannan tace baƙin bakinki ya faɗa maki ɗiyar matsiyaciya,,,,,,


Raliya tace ai kinsan ni ba ɗiyar matsiyata bace, amma abinda zan faɗa maki ki fita daga rayuwata idan ba haka ba, wallahi zan maki dukan rabani da yaro,,,,,,,,,,


Baba yace ke "yar rali?"" kallon inda baba yake tayi amma batayi magana ba,,,,, baba yace wai duk saboda dake da babu ake ta tada jijiyar wuya ne?""",,,,,, raliya ta riƙe ƙugu sannan tace Eh, kuma da dole asata makaranta,,,,,,


baba yace to wallahi bazan sakata ba, kuma idan har baki daina haɗa rayuwata data yarinyar nan ba, haƙiƙa zaman lafiya zai ƙare tsakanin ni dake,


raliya tace uban waye ce dama a zauna lafiya?"" naci uwar zaman lafiyar kuma naci uwar duk wanda yake so a zauna lafiya, kuma da babbar bala,i sai ansata idan ba haka ba, nima zaman lafiya ya ƙare a gidan nan,,,,,,


Taci gaba da cewa kai kasan wace ce "yar rali,,,, ta nuna inda suwaiba take sannan tace wallahi ke kuma kiyi kuka da kanki,,,,,, tsaki tayi sannan  taja hannun safina raliya ta goge hawayen da suka zubo daga idonta,,,, har zata fita daga ɗakin ta juyo ta kalli suwaiba sannan tace nayi imani da ɗiyarkice wallahi duk bala,in da za,ayi sai kin sama mata ilimi,,,, kiji tsoron Allah kuma kiji tsoron haɗuwarki dashi dan baki da imani,,,,,,,,,


dariya suwaiba tayi sannan tace, an faɗa maki ni kaɗai zan haɗu da Allah?""",,,,, duk ga arna nan, ga barayi nan, ga masu fashi da makami?"",,, gamasu yankar kai?"",,,, to juyo mani zaman wanda suka shuɗe,,,, inasu abu jahil?""" ina su fir,auna?"",,,, kai wai a tsaya jiran suwaiba?"",,,,, 


raliya tace ake jahila ce, kuma irinku basa ganewa, jan hannun safina tayi suka fita daga ɗakin,,,,,,, tsaki suwaiba tayi sannan tace wallahi matarnan tafa zo da rainin hankali, kaima ka saki banza kawai ni banga amfanin zama da macen da bata bin ra,ayina ba,,,,,,,,,,,,,


baba yace ke kada ki sake cewa in saki "yar rali,,, kin manta labarinta?"",,,,, ai ita idan ta auri namiji aurenta baya sakuwa dan haka kima daina cewa in saketa,,,, tsaki suwaiba tayi sannan tace ita ɗin banza da baza a saketa ba, shiru baba yayi bai sake magana ba, sai suwaiba tayi ta tsegumi da mita,,,,,,,,


raliya tana zuwa ɗaki tayi ta rarrashin safina , tana kwantar mata da hankalinta, daga baya ta kira wata ƙawarta tace don Allah cikin kayan yaranta na sawa ta sammata ko kala ukku ne,,,,, tace insha Allah zata bada a kawo mata,,,,,,,


To haka dai rayuwar raliya da safina baba da suwaiba da fahat taci gaba tafiya, don kullum "yar rali da gejeren wandonta daga ciki saboda ɓacin rana, kuma sai anyi danben masifa take samawa safina abinci, dan ba suwaiba ba har baba idan yazo ya sami safina tana ci abinci sai yacicci ubanta sannan ya anshe abinci,,,,,,,,,


Ƙawar raliya ta kawo kayan sawa wa safina, masu yawa,,,,, dan haka raliya tana sa safina wanka ta goge bakinta, kuma ta nuna mata yanda akeyin wanki,,,,,,, saboda rayuwa, kuma tana koya mata karantu ga abinda ta sani,,,,,,,


kwanci tashi babu wuya a wurin ubangiji fahat ya kamla karatun secondary  ɗinshi kuma baba ya ɗaure masa gindi dan kasar waje baba ya fitar da fahat danyin karatunsa na degree, 


Shi kuma baba yanxun Allah ya buɗa masa ya samu kuɗi ba laifi dan haka yana ginin gida, kuma ya jaddawa raliya lallai bazai koma sabon gida da safina ba, raliya kuma tace saidai idan bata lumfashi amma haƙiƙa sai ta tafi da ɗiyarta,,,,,


Baba yace to kije da ita ɗin in gani, dan kan wannan yarinyar ina sakinki,,,,, dariya raliya tayi tare da tafa hannunta tayi guɗa a daidai lokacin da take kai hannunta saman hancinta ta riƙe, tace ƙarya ne, ai aurenmu auren zobone, babu saki babu yaji kuma babu kishiya har abada,,,,,,,


baba yace to mu xuba , dan tuni na ɓalle dan banzan zoɓen,,,,, raliya tace idan kaji wahala da kanka zakaje wurin walda a nane maka shi,,,,,,,, shiru baba yayi yana ci gaba da kallon raliya dan "yar masifar ƙarshen duniyace,,,,,,


Suna haka da baba raliya taji safina tana wani irin ihu kamar za,a fitar da ranta,,,,, da gudu ta tashi ta nufi ɗakinta dan ganin kukanmi safina takeyi,,,,


lokacin da raliya taje safina har ta faɗo daga saman gado jikinta ya jiƙe da wata irin zufa, ga hawaye dake kwararo mata daga cikin ido babu ƙaƙƙautawa,,,,, cikin rawar jiki raliya tace lafiya sapna?"" a daidai lokacin da take ƙoƙarin tsugunniya kusa da ita,,,, ita kuma sapna tuni ta mike tana ƙoƙari zubawa da gudu,,,,,,


Kafin raliya ta riƙe sapna tuni tayi tsakar gida,,,,, da gudu raliya ta fito daga ɗaki tayi kan safina, jikin safina sai kyarma yakeyi tana kuka tana cewa kada kaman haka mana, da gudu raliya ta isa wurin ta riƙe sapna da ƙarfin tsiya sannan ta jijjagata tace wai miye?""""",,,,,,,


sai yanxun safina ta buɗe idonta, tare da sauke ajiyar zuciya ta rungume raliya tace ummana, raliya tace miye?""",,,,,, cikin kuka safina taja hannun raliya sukayi ɗaki,,,,,,,,


Bayan sunje ɗaki raliya ta zaunar da safina a gefen gado sannan ta jawota jikinta, cikin damuwa raliya tace miye kike kuka?""",,,,,,, sai yanxun safina ta dawo cikin hayyacinta,,,, haƙiƙa wannan maganar bata faɗuwa yama zatayi ta faɗawa umma wannan maganar don Allah?""",,,,,


Raliya tace kinyi shiru,,,,, ajiyar zuciya safina tayi sannan tace ummana gani nayi kura ta biyoni zata cinyeni,,,, tayi ma raliya ƙarya,,,, dariya raliya tayi sannan tace to kuma kike cewa kada yayi maki haka?""",,,,, murmushi safina tayi a daidai lokacin data goge hawayen idon ta sannan tace,,,,


wani ne ya saki kurar yace ta cinyeni, kuma ya rufe fuskarshi,,,,, shafa kanta raliya tayi sannan tace ki riƙa addu,a idan zaki kwanta bacci kinji ko?""",,,, safina tace to,,, raliya tace kwanta, kwanciya safina tayi sannan raliya ta miƙe tabar ɗakin,,,,,,


tana fita safina ta sauke wata muguwar ajiyar zuciya, hannu ta miƙa ta jawo pillow ta mitse a ƙirjinta sosai sannan ta kwanta saman hannun damarta, ta ƙara matse pillown sosai, lumshe idanuwanta tayi tare da sakin murmushi sannan ta fara ayyano abunda ta gani a bacci,,,,,,,,,


Murmushi ta sakeyi sannan tace a bayyane miyasa baza ka buɗe fuskarka in ganka sosai ba?,,,, gyara kwanciyarta tayi fuskarta na kallon rufin ɗakin ummanta amma har yanxun idonta rufe yake,,,,,,, kuma fuskarta na ɗauke da murmushi har yanxun, 


Ɗaga ƙafafuwanta tayi sama tare da cewa yeeccch tare da rumtse hannuwanta duka biyun,  sakin pilown tayi sannan tashi tsaye saman gado tayi yar rawa, sannan ta sake kwanciya ta kifa fuskatarta saman filow tace ina sanka,,,, dariya tayi ta rufe idonta da hannunta kamar tana ganinshi,,,,,,,,


ajiyar zuciya tayi sannan tace amma kada ka sake taɓamin jiki,,,, juye juye tayi tayi saman gado har bacci yayi gaba da ita,,,,,,


Zaune take a gefen wani rafi a ƙasa ta zauna ta miƙe ƙafafuwanta ta ɗora ƙafa ɗaya saman ɗaya, tana wasa da ƙasa da hannun damarta kanta na duƙe,,,,,,,


tun daga nesa tajiyo ƙamshin turarensa, da sauri ta ɗago kanta yauma haka yawansu yake sunfi su ishirin dukansu ƙatti ne sosai kuma girman nasu mai firgitarwa, sannan dukansu fuskarsu rufe, 


da sauri ta miƙe tsaye, tare da cewa sannu da zuwa,,,,,, ajiye mashi kujera akayi ya zauna sannan ya ɗauki ƙafa ɗaya ya ɗora saman ɗaya,,,,,,, ita kuma matsawa tayi gabanshi sannan ta tsuguna, shi kuma juyawa yayi bayanshi sannan yace ku kamota,,,,, da sauri ta miƙe ta zungura da gudun tsiya,,,,,,, shi kuma ɗaga murya yayi sannan yace ku kamota kada ku bari ta gudu,,,, safina gudu take na tashin hankali sosai take gudu ba tare da wasa ba,,,, suma biye suke da ita sosai,,,,,, juyin da zatayi taji ta buge da bango,,, dan haka za sauri tace innalillahi wa,inna ilaihir raji,un, a daidai lokacin data buɗe idanuwanta,,,,,,,, sauka tayi daga saman gadon sannan ta haska fitila taga 2:37am,,,,,,,


jiki a sanyaye safina ta koma saman gado ta kwanta ba tare da ta kashe fitilar ba,,,,, saboda tana ganin kamar dan babu fitila take mafarkin nan,,,,,,, 


kuka safina ta farayi, a bayyane tace towai mi nayi maka ne?"""",,,,,, miyasa ma zaka kamani?""",,,, kuma ka saba zuwa kai ɗaya miyasa yau kazo kai da yawa??"""",,,, tashi tayi zaune a saman gadon pillow ta jawo sannan ta ɗora saman ciyarta ta ɗora hannunta saman filon tayi tagumi, saida tasha "yan hawayenta sannan ta goge su gashin kanta daya warware ta tattara ta ɗaure, amma ta kasa komawa bacci,,,,,,,,


safina tana nan zaune har asuba tayi ta tashi taje tayo alwalla, tazo tayi sallah, tana zaune saman abin sallah tajiyo muryar raliya da baba suna faɗa, baba yana cewa wallahi saita bar min gida idan kuma ba haka ba, wallahi saina sakeki,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻


💦💦💦💦

*RASHIN RABO*

💦💦💦💦


*R🅰SHIN R🅰BO*


*MEELAT MUSA*


*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP zaku nema a shafinmu na facebook domin samun litattafanmu masu ƙayatar daku*


*Kai kai kayyyyyyy, hmmmm, abin mamakiyos wai makaho da tuƙin mota duk dai wanda yahau ai yasan ina zai sauka,,,,,, daga tace itace REAL MAI DAMBU, kowama ya zama real mai dambu, to real dai ɗayace, ita kaɗaice daga ita babu wata, itace dai REAL MAI DAMBU ɗin marubuciyar shahararrin luttattafan nan wanda suka haɗa da YARO MA NAMIJI, marubuciyar KISHIYATA JAHADI NA, marubuciyar WANI AL,AMARIN, saboda daɗin sunanki har naga real mai ɗan wake, da real mai shinkafa, nidai tawa gwanar kowa yasan REAL MAI DANBU ce, haka ma rundunar AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION suma sunce sai MAI DAMBO real mai dambu tamuce damu da ɗaukacin masoyanmu,,,,,,,,,,*


*Baiwar Allah ASMEENAT XEEYAN ina maki sannu da jiki kuma ina addu,a Allah ya yaye maki damuwarki kuma ubangiji ya baki lafiya dake da dukkan marasa lafiya na gida dana asibiti, mu kuma da muke da lafiya ubangiji ya ƙarama darajar manzan Allah S. A. W 🙏🏻*


***


*16-18*


*C*ikin sauri sapna ta miƙe tsaye tare da cire hijabin jikinta,,,,,,,,


Ƙara matsawa tayi a bakin ƙofar ɗakin ummanta dan taji lallai abinda baba yake faɗa da gaskiya ne?""",,,,,,,,


Cikin muryar kuka da sigar lallashi tajiyo muryar ummanta tana cewa haba mai gida?""",,,,,,, saboda tsabagen rashin adalci zakace zaka sakeni?""" daga na faɗa maka gaskiya?,,,,,,,,,,, to miye laifina a ciki?"""",,,,,


Cikin masifa da rashin wadataccen ilimi baba yace saboda ban ƙaunarta, kuma yau zan nuna rashin ƙaunar da nake mata ra,ayil ani kowa da kowa ya gani,,,,,, a zuciye ya fito daga ɗakin raliya tana biye bayanshi tana kuka mai tada hankali,,,,,,,


Wata irin walƙiya akayi tare da cida mai tada hankali ruguguuuuuuuu,,,,,,, kasancewar garin na damina ne,,,,


Zugwi zugwiii baba ya nufi inda galanɗin fetir yake ya ɗauko, da sauri ya nufi kicin zuzuuuiii, yana zuwa ya ɗauko ashana,,,,,,, idanuwa raliya ta zaro tare da cewa mi kake ƙoƙarin aikatawa haka ne?""",,


baba yace yau ɗin nan saina cinta mata wuta ta mutu kowa ya huta,,,,,, sapna dake tsaye bakin ƙofa da sauri ta fito daga ɗaki,, a daidai lokacin da raliya ta riƙe baba tana cewa ka rufa man asiri kar ka ƙona ta,,,,,,,,


a fusace baba ya juyo ya kalli raliya sannan yace idan kika sake bani haƙuri a bakin aurenki,,,,,,, da sauri sapna ta isa kusa da raliya sannan ta daɗe mata baki, dan raliya tana ƙoƙarin yin magana,,,,,,,,,,


cikin kuka sapna tace ummana dan ƙaunar da kike man da tausayin da kike man kada kiyi magana wannan shine zai nuna man kaunar da kike man gaskiya ce,,,,,,,,,,,,,


Kallon sapna raliya tayi cikin kuka amma batace komai ba,,,,, murmushi sapna tayi sannan ta riƙe hannun raliya tace kinyi man alƙawari ko ummana?"",,, ta ƙarasa maganar tana buɗe idanuwanta tare da ɗaga duka girarenta,,,,,,,,,, kai kawai raliya ta ɗaga alamar Eh,,,, sapna zatayi magana taji anyi mata wanka da fetir,,,,,,,,,,,,,


a gigice sapna ta tunkuɗa raliya gaba ta faɗi ƙasa, difff,,, sannan tace ummana kiyi man alƙawari kada kiyi magana ki cika man farin cikina, kuma ki riƙe alƙawari in tafi lahira da kwanciyar hankalin nabar igiyar aure akanki, sapna ta ƙarasa maganar hawaye na kwararowa daga idon,,,,,


Ita kuwa raliya batama san abinda sapna take cewa dan tun ingijewar da sapna tayi mata ta faɗi ƙasa somammiya,,, baba matsawa yayi kusa da sapna sosai sannan ya ɗaga galanɗin fetir ɗin yaci gaba da zazzaga mata shi,,,,, tsayuwa tayi tana kallonshi,,, hawaye na zuba da idonta,,,,,,,, amma kwata kwata baba baiji tausayin sapna ba,,,,,, ya fara ƙoƙarin kyarta ashana,,,,,,,,,,


cikin rawar baki sapna tace haƙiƙa ko a film ban taɓa ganin mahaifin daya nunu ƙiyayya wa abinda ya haifa ba saikai,,,,,,,, alfarma ɗaya zan roƙe kada ka kasheni kabarmin rayuwata, saboda tana da amfani a gareka, idan baka buƙatata a yanxun akwai ranar da zaka buƙaceni,,,,,,,,,,,,,,,,,,


baba yace ai sai kinyi rayuwa zaki ce haka ko?"",,,,,, rayuwarki bata da wani amfani a wurina da al,umma baki ɗaya,,,,, sapna tace haƙiƙa ina da amfani a wurinka amma bazaka gane hakan ba sai bayan bana lumfashi,,,, tsaki baba yayi a daidai lokacin daya ƙyarta ashana ya wurgawa sapna,,,,, da gudu tayi waje tana kuka,,,,,,,,,,,,,,,,


hadarin daya riƙe ruwa yaci gaba da ambaliyar ruwa kamar da bakin kwarya..........,,,,,,,,,,


ɗaki baba ya nufa, ba tare daya kalli inda raliya take kwance ba, kuma ba tare da imani ko tausayi ba,,,,,,,,


Sapna gudu take da wuta a jikinta tana ihu, tana neman taimako,,,, wani mutum ya hangota yana cewa ke yarinya lafiya?""",,, amma sam sapna bata saurarenshi da gudu ta isa bakin wata rijiya ta faɗa ciki tunjummmmmmm,,,,,,,,,,,,


Mutum a gigice ya fara salati tare cewa yekuwa jama,a a kawo ɗauki, ku taimaka kuyi ceton raiiiiiiiii,,,,,, cikin kiɗimewa yake maganar kamar babarshice aka jefa a rijiya,,,,,,


babu ɓata lokaci jama,a suka fara taru duk da ruwan saman da akeyi bai hana mutane bulbulowa daga cikin gidajensu ba,,,,,,,


haka aka taru kan bawan Allahn nan ana tambayarsa lafiya, ya kasa magana saidai yace  nuna rijiya ,,, wani mutum ya riƙeshi sosai sannan ya jijjigashi yace lafiya?"" ka tara mutane a cikin ruwa wai miye yake damuwa ne?"""",,,, a sanyaye yace ta faɗa rijiya,,,,,,,, wace ce?"" ya tambaya cikin zaguwa ,,,,,


yace watace tana ci da wuta sosai,,,, da sauri mutane sukayi wurin rijiyar,,,,, suna zuwa kowa ya dafa rijiya ya leƙa, bayan sun leka kuma gaba dayansu suka ɗago kansu suka maida dubansu ga wanda yace sapna tana cikin rijiya,,,,,, wani ne yace ku taimaka ku fito da ita don ceton rayuwarta,,, anan aka samu wani jarumin namiji ya nannaɗe ƙafar wando ya surmiya cikin rijiya dan ceto ran sapna,,,,,


Saida ya daɗe sosai a cikin rijiya sannan ya fito da sapna goye a bayanshi,,,,,,,, yana fitowa da sapna mutane sukace ayi asibiti da ita mana,,,,, babu ɓata lokaci cikin mutanen wani ya koma gidanshi da saurinshi ya ɗauko motar, haka aka ɗauki sapna akayi asibiti da ita,,,, Allah sarki niko nace irin Allah basa ƙarewa,,,,,,,,


ruwan sama saida ya daki "yar rali sosai sannan ta miƙe jiki a sanyaye tana ci gaba da kuka,,,,,, jikinta jiƙe da ruwa sosai sannan ta nufi ɗakinta tana wata irin tafiya kamar "yar kaciya,,,,,,,,,,


tana shiga ɗaki a bakin ƙofar ɗakinta ta durƙushe tana wani irin kuka mai kama zuciya,,,,,,,,,,,, saidai ta ɗora hannunta saman kanta tayi kuka sosai sannan ta ɗukar da kanta ƙasa saman sumintin tsakar ɗakinta ta ƙara fashewa da kuka,,,,,,


Saida "yar rali tayi kuka sosai sannan ta tashi ta cire kayan jikinta ta canja wasu, zama tayi a gefen gado, inda kayan sapna suke taje ta ɗauko saida ta ɗaga su, ta kalla, ta mayar ta ajiye,,,,,, murmushi tayi a daidai lokacin data tuno sapna, lokacin data fara sa kayan, ta tuno murmushi sapna datace , ummana ya kika ganni?""",,,,,,, raliya tace kinyi kyau "yata,,,,,,, sapna tace Allah yasa kiyi kuɗi sosai kiman kaya masu kyau a daina bani kwance,,,,,,,,,


rungume kayan raliya tayi sosai sannan ta saki wata irin ƙara tare da durƙusawa ƙasa tana ƙara ɓarkewa da kuka sosai,,,,, suwaiba daga ɗakinta tajiyo kukan raliya don haka tashi tayi tayo ɗakin "yar rali,,,,,,,,,,,


suwaiba tana zuwa a bakin ƙofa ta tsaya ta yaye labilen ɗakin raliya sannan tace da Allah kiyi ma mutane shiru sai ki zauna kiyi ta mana jiniya kamar wata motar "ya"yan kwane kwane?"",,,,,,,  cikin ɓacin rai raliya ta tsagaita kukanta tare da ɗago kanta da idanuwanta da sukayi wani irin mugun jaaaaa,,,,,,,,,,


miƙewa tsaye tayi cikin ɓacin rai sannan ta matso kusa da suwaiba, nunata tayi da ɗan yatsa sannan tace ke yarinya fita idona idan ba haka ba zanmaki bugun leƙa lahira,,,,,,


dariya suwaiba tayi sannan tace kada ki kaini lahira ita dai ɗiyar da kike taƙama takice tuni baban gwamna ya cinna banza wuta ta babbakr ƙaffff ruwan sama ya tafi da garin tokar tokar ja,ira ,,, huwwww tayi ma raliya gwalo sannan ta saki labilen tayi ɗakinta cikin sauri,,,,,,,,


Raliya komawa tayi saman gado ta zauna jugum, tana nazarin mutuwar sapna,,,,,,,,,,


Suna isa asibiti babu ɓata lokaci aka anshi sapna, cikin ikon Allah aka fara bata taimako sosai,,,,,, inda taɗanyi ƙuna daga gefen cikinta sai cinyarta , haka likitoci suka haɗu kanta sosai dan ceto rayuwarta,


saida aka latse cikinta ta amaye ruwan data kwankwaɗa a cikin rijiya tayi ta bubulosu kamar tsaka na aman wuta,,,,,,,


Inda ta ƙone aka kwashe wurin sannan akayi mata diresin, likitan yace a canja mata kaya sannan ya fita daga ɗakin,,,,,,, mutumin daya kawo sapna shine ya koma gida ya ɗauka kayan matarshi ya kawo aka sa mata,,,,,


Haka akaci gaba da kula da sapna a asibiti, kwananta biyu amma har yanxun bata farfaɗo ba, saida ƙarin ruwa ake jona mata, da wannan ya ƙare ya jona wannan kamar an tara jarka a bakin fanfo,,,,,


Bawan Allah da sapna bata sani ba nima bansanshi ba, shine yake ta ɗawaini da ita, a asibiti, kuma komai shine yake biya dan kula da lafiyarta,,,,, niko nace irin Allah basa ƙarewa,,,,,,,


haka sapna taci gaba da jinya a asibiti har Allah ya bata lafiya ta warware sosai,,,,, ganin ta samu sauƙi sosai kuma likita ya tabbatar bata da sauran wata matsala ko damuwa, don haka aka rubuta sallama wa sapna,,,,,,,,,


mutumin daya kawota asibiti yace to an sallameki, Allah ya ƙara sauƙi kinji,,,,, murmushi sapna tayi sannan tace ngd sosai,,,,, shima fatan alkairi yayi mata, sannan yayi gaba,,,,,,,, binshi da kallo sapna tayi harya ɓace ta daina ganinshi murmushi tayi sannan tace Allah sarki kaji daɗinka kai namiji , nima da na sakance namiji da ina can gaban mahaifina,,,,,,, murmushi ta sakeyi da gefen bakinta sannan ta duƙa ta ɗauki ledar daya ajiye mata ta fara tafiya,,,,,,,,


saida ta fita daga asibiti baki ɗaya sannan tayi tsaye a bakin get ɗin asibiti, saidai ta kalli gabas ta kalli yamma ta kalli kudu ta kalli arewa,,,,,,, ajiye ledar hannunta tayi a gabanta sannan ta riƙe ƙugunta, kanta ta ɗaga tana kallon sararin samani tare da cewa ina mafita?""""""""""""""

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻


💦💦💦💦

*RASHIN RABO*

💦💦💦💦


*R🅰SHIN R🅰BO*


*MEELAT MUSA*


*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP zaku nema a shafinmu na facebook domin samun littattafanmu*


*21-23*


***


*A* firgice sapna ta ɗago fuskarta tana kallonshi,,, sake kecewa yayi da dariya mai taɓa kwokwon kai, dasa firgici a daidai lokacin da yake girgiza jikin sa, naman jikinshi yana motsawa kamar wani ɗan matashin zaki,,,,,,,,,


Da sauri sapna ta rufe idanuwanta, dan gaba ɗaya tsoro ya kamata, dan tunda take a duniya bata taɓa ganin murɗeɗan ƙato kamar wannan ba,,,,,,,, shi kuwa sai nishi yake kamar wata mai naƙuda yana wani lashe laɓɓansa kamar wani tsohon maye,,,,,,


cikin isa, ya fara tattaki yana matsawa kusa da sapna,,,,,, cikin rawar baki ba tare data buɗe idanuwanta ba, tace yayana don girman Allah kada ka wulaƙanta man rayuwa,,,, a daidai lokacin da hawaye ya kwararo daga cikin idonta,,,,, shi kuma a daidai nan ya iso kusa da ita,,,,,,,,,,,,,


dariya yayi sannan ya juya yana kallon sauran dakarenshi,,, yace kunji fa, wai kada a wulaƙanta mata rayuwa,,,, dariya yayi sosai sannan yace ai kin gama wulaƙancewa tunda kika zo hannuna anan zan zaunar dake, babu ke babu wani sauran jin daɗi, zan mayar dake karuwata makwancina a jikinki kawai zan riƙa hutawa, idan na gama in albureshi ki tafi lahira,,,,,,hhhhhhh ya sake sheƙewa da dariya,,,,,,,


ajiyar zuciya sapna tayi sannan ta buɗe idanuwanta, cikin dakiya tace wai mi nayi maku?""" kuma a bisa wane dalili kuka kawoni nan?""" tun jiya kuke gana man azaba, miye laifina?""",,,,,,,,,


bakiyi laifin komai ba,,,,, jin daɗi da morewa yasa muka kawoki, a daidai lokacin daya kai hannunshi daidai gaban rigar sapna yaja ya yageta ƙiyyyyyyyyy,,,,,,,,, saida ya dire rigar dukanta, brezia kaɗaice a jikinta sai zaninta,,,,


da sauri sapna ta rufe idonta, saboda kunya, kuma gashi an ɗaure hannunta bata da damar riƙe gabanta da hannu saboda ɗaurin da akayi mata,,,,,, su kuma ɗiyan asarar sai suka sheƙe da dariya, hhhhhhhhhhhh,,,,,, sunayin dariyar suna jinjina dariyar tare da tafa hannuwansu,,,,,,,,,


ƙara matsawa yayi kusa da sapna, sannan ya riƙo gashin kanta ya ɗago mata fuska tana kallonshi,, yace "yan mata ya kikaji ne?"",,,, uhum?"",,,, kema kinji wani abu a wannan yanayin ko?"",,,,,, 


Kallonshi sapna tayi sosai,,,, amma batayi magana ba,,,, shima kallonta yayi sannan yayi dariya,,, juyawa yayi yaci gaba da tafiya sannan yace kuyi taci mata uwa har yanxun bata canja ba,,,,, da sauri sukayi kan sapna sukaci gaba da dukanta,,,,,,


saida ya tabbatar sapna taci gidansu sosai sannan yace ku barta haka,,,,, dakatawa sukayi shi kuma yace ke kin shirya zama karuwar *GIDI*?"""",,,,,,,


kai kawai sapna ta ɗaga saboda tsananin azaba,,,,  gyara zamanshi saman kujerar da yake zaune akai,,,,, yayi sannan ya kece da dariya tare da ɗaga ƙafarshi daya yana dariya irinta "yan duniya,,,,,,,,


ku kunceta , da sauri aka kunce sapna,,, saboda wahala ana kwanceta faɗuwa ƙasa tayi, ta kwanta,,,, su kuma gaba ɗayansu fita sukayi daga ɗakin,,,,,,,,


Raliya kaɗai take rarrashin baba, tana bashi haƙuri tare da faɗa mashi kalamai masu kwantar da hankali,,, ita kuwa suwaiba tsaki tayi sannan ta juya tayi ɗakinta,,,,,,,,,


Kama baba raliya tayi ya miƙe sannan sukayi ɗaki tana bashi haƙuri,,,, bayan sunje ɗaki ta zaunar dashi a gefen gado, kallon raliya yayi sannan yace Allah yayi maki albarka raliya tace ameen a daidai lokacin da take zama kusa da baba,,,,, riƙe hannunta baba yayi sannan yace kije ki gama abinda kike zan baki wani labari,,,, murmushi raliya tayi sannan ta miƙe tabar ɗakin,,,,,,


ganin babu kowa a ɗakin,,, yasa sapna ta miƙe a hankali banda hajijiya babu abinda take gani ga kuma azabar yunwa dake caccakar mata hanji,,,, ganin zata ba kanta wahala wurin tashi zaune, dole ta haƙura ta koma ta kwanta,,,, wani irin wahalallen bacci yayi gaba da ita,,,,,,


Yanayin wurin yayi kyau sosai saboda ruwan da akayi aka ɗauke,, ita kuma tsugunne take tana wasa da ƙasa kamar yanda ta saba,,,, tun daga nesa ta hangoshi yana tahowa,,,,,,


tafiya cikin aji da nuna jarumta, sai yanga yake dan gayu,,,, da sauri ta miƙe tayi wurinshi da gudu,,, tana zuwa kusa ɗashi taja burki, tana sauke nunfashi a hankali saboda ɗan gudun da tayi,,,,


yauma fuskarshi rufe take, kamar yanda ya saba zuwa mata a bacci,,, kusa dashi ta matsa sosai sannan tace sunanka,,,,, baiyi magana ba,,,, tace to buɗe fuskarka mana,,,, bai buɗe ba kuma baiyi magana ba,,,,, ajiyar zuciya tayi sannan tace gaskiya ina cikin damuwa,, baiyi magana ba, ya juya yaci gaba da tafiya, tayi tsaye a wurin tana kallonshi harya ɓace,,,,,,,, Ƙoƙarin binshi takeyi amma abin ya faskara taji kamar an riƙeta a wurin ne, dole ta haƙura tayi tsaye a wurin,,,,,,,,


Da sauri sapna ta buɗe idonta,,, tana sauke ajiyar zuciya,  kalle kalle ta farayi, ganin wasu na bacci wasu kuma duk suna cikin yanayin maye,,, yasa ta miƙewa a hankali, bango ta farabi saɗaf saɗaf ta fara tafiya,,,,,,, cikin yanayin maye gidi yace ina zakije ne?""",,,,,,,,, itama cikin irin maganar yan maye tace zanje bayi ne,,,,, gidi yace kada kije dawo nan,,, sapna bata tsaya ƙara bashi bayani ba tayi gaba da gudu,,,,,,


wani irin ihu gidi yayi sannan ya yada kwalbar giyar dake hannunshi yana cewa ku tashi ƙattin banza ta guduuuuuuuuu,,,


kamar anyi masu usir haka suka miƙe gaba ɗayansu , suka nufi hanyar fita,,,, da gudu suka fice daga gidan,,,,,,


gudun babbar bala,i sapna takeyi tana jan zaninta sama ta ɗora a ƙirjinta,,, gudu takeyi sosai, ba tare data san inda take saka ƙafarta ba,,,,, a ɓarke suke biye da ita sosai, tare dayi mata barazanar harbi amma sam bata saurarensu,,,,


da gudu motar tasha gaban sapna,,, wata irin tirjiya sapna tayi tana waiwayen bayanta, har yanxun suna biye da ita da gudu sosai, ahhhhhh, tace tare da sauke ajiyar zuciya sosai sannan ta maida dubanta ga motar,,,,,,,


juya sitiyarin motarshi yayi sannan ya fara tafiya da motar yana zageye sapna,, itama juye juye ta farayi tare da bin motar da kallo,,, saida ya gama zagayeta sannan ya tsaye,,,,


juya kan motar yayi ta inda suke tahowa sannan yasa full light na motarshi,,, suna tahowa da gudu ganin haske sosai ya kashe masu idanuwa yasa su dakatawa,,,, saboda kwata kwata basa ganin gabansu,,,


Sapna kallon masu binta tayi sannan tayi sauri ta maida dubanta ga mai motar, sake kallon kanta tayi daga ita sai ɗauren ƙirji ga kuma gashin kanta gaba ɗaya ya war ware ya zubo saman gadon bayanta, ƙafafuwanta ta kalla babu ko takalma,,,,, ajiyar zuciya tayi sannan ta sake maida dubanta ga masu binta,,,, sannan kuma ta sake kallon inda motar take,,,, 


da sauri tayi wurin motar har yanxun yana cikin mota bai buɗe ba, kuma bai fito ba, da gudu sapna ta zagaya ta buɗe motar ta shiga,,, har yanxun baiyi magana ba, jan motar kawai yayi suka ɓace daga wurin kamar walƙiya,


Su kuma suna ganin tafiyar motar da sauri gidi yace kuje kuje kujeeeeeeee ya ƙarasa maganarne da kakkausar murya ne,,, da sauri suka fara haska fitila suka ci gaba da gudu dan kamo sapna,,,, tsaki gidi yayi sannan ya duba agogon wayarsa yaga 4:59am,, tsaki yayi sannan yace idan na kama shegiyar yarinyar nan haƙiƙa saina kacaccala ma banza rayuwa,,,,,, niko nace kana da aiki gidi,,,,,


Saida yayi tafiya mai nisa sannan ya taka wani irin  burki ƙiyyyyy,,,, da sauri sapna ta kalleshi, tana jiran abinda zaice amma baiyi magana ba,,,,,, ƙura masa ido tayi sai kallonsa takeyi kamar jariri sabuwar aihuwa, baiyi magana ba har yanxun, dakewa tayi sannan tace fita zanyi ne?""",,,,, kai kawai ya ɗaga mata alamar Eh,,, gyara zamanta tayi sosai a cikin motar sannan tace wallahi bazan fita ba, ina tare dakai, saidai idan mu fita gaba ɗayanmu,,,,,,,,


kunna fitilar motarshi yayi sannan ya cire gilas ɗin idonshi, gaban sapna ya faɗi dasss dasss, da sauri ta sauke ajiyar zuciya sannan tayi magana cikin sanyi tare da sigar lallashi , tace ayyyyy idan ka matsa ma in sauƙa nama gode ai ka cecini daga hannun azzaliman can, amma kayi haƙuri kaje dani kafin zuwa gari ya waye zan tafi insha Allah,,,,, maida gilas ɗin idonshi yayi ba tare da yayi magana ba, sannan ya kashe fitilar yaja motar suka tafi,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,


tafiya yake summun buƙumum, gaban sapna sai faɗuwa yakeyi kuma yaƙi yayi magana ma, idan tayi magana ma bayayin magana sai yayi shiru,,,,,, bawan Allah wai kai kurma ne?""",,,, sapna ta tambayeshi,,, baiyi magana ba,,, taɓe baki tayi sannan tace kaji dashi, juyawa tayi tana kallon baya, rigar sanyi ta gani ajiye, juyawa tayi sosai sannan ta ɗauko rigar ta sanya a jikinta,,, kallonta yayi amma baiyi magana ba,,,, har suka isa inda zaije,,,,,,,


suna zuwa bayan yayi parking sannan ya kashe motarshi ya fita, da sauri ta fita, itama,,,, ta rufe motar, remote ɗin motarshi ya latsa tayi tsuuuu alamar ta rufu,,,,,


Tafiya yaci gaba da yi,,, da sauri tabishi da gudu, suna shiga ya tsaya bakin ƙofar wani ɗaki ya buɗe, shiga yayi itama da sauri ta shiga,,,,, suna shiga shine ya dawo ya rufe ƙofar ɗakin da makulli,,, zaro idanuwa sapna tayi sannan tace kai malam miye zaka wani kullemu da makulli kuma?"" tayi maganar ne cikin tsiwa da nuna isa kamar wani gidansu,,,,


baiyi magana ba, matsawa yayi kusa da wata plastic chair akwai wani ƙaramin benci a gaban kujerar, sannan ya cire jaket ɗin jikinshi ya rataya saman bayan kujerar sannan ya cire glass ɗin idonshi, ya ɗora saman bencin,,,,, daga shi sai t-shirt, baƙa da dogon wando baƙi,,, jiki a sanyaye ya zauna saman kujerar sannan ya jingina bayanshi da kujerar, kanshi yana kallon ƙasa,,,,


ita kuma tashi tayi ta matsa kusa dashi riƙe ƙudunta tayi sannan tace malam a ina zan kwanta ne?""",,,,,, kallonta yayi amma baiyi magana ba,,, fuskar nan tashi ba wasa kamar america ta kawo ma nigeria hari,,,,,,


da sauri ta juya tabi wata ƙofa da gudu ba tare data san ko ina ne ba,,,, tana shiga taga lafiyayyen gado yasha gyara,,,murmushi tayi sannan taja da baya ta ruga da gudu ta soke saman gadon, tana hayewa tayi dariya, sannan tajawo pillow ta ɗora kanta taci gaba da bacci,,,,,,,,,,,,,,


Saida rana tayi sosai sannan sapna, ta farka , salati tayi tare da kallon agogon dake maƙale jikin  bangon ɗakin, da sauri ta sauko daga saman gadon ganin wannan lokacin, 7:39am,,, da sauri ta fito saboda babu toilet a ɗakin,,,, tana fitowa ta nufi wata ƙofa dan ta tabbatar nan ne toilet ɗin bayan ta shiga alwalla tayo ta fito, sannan ta koma ɗaki tayi sallah, bayan ta gama ta fito farlo, dinning area ta nufa dan a wurin ta ganshi yana ajiye wani ɗan ƙaramin akwati a wurin,,,,,,


tana zuwa taja kujera ta zauna tare da cewa barka da safiya,,,, baiyi magana ba, ya sauka daga wurin ya nufi kicin,,,, yana tafiya, ita kuma ta jawo kwatin ta buɗe,,,, zaro idanuwa tayi tare dayin salati dan ganin bindugu a ciki,,,,,,,  


Wata "yar ƙaramar bindiga ta ɗauka tana jujjuyawa tare da cewa saina iya harbawa idan na iya, inje in kashe babana kowa ya huta,,,,,, shi kuma a daidai lokacin ya iso wurin da flet a hannunshi da sauri ya ajiye flet ɗin sannan ya kwace bindigar hannunta, ita kuma taci gaba da cewa kai ɗan fashi da makamine ko ba haka ba?""",,,,, to ina so ka bani horo akan wannan harkar,


zama yayi a daidai lokacin daya jawo akwatin sannan ya rufeshi, ya ɗora ƙaramar bindiga akai da bulet sannan ya tura akwatin gabanta, yace gashi, wannan shine gudamawa ta a gareki,,, ɗauki ɗauki ki tafi,,,,,,,,,,,, cikin tsoro ta fara ɗaga hannuwanta tare dayin magana cikin dariya, tace  a,a, a,a, ai banji wani iri ba,,,,, ai duk sana,a sana,a ce, ga malamin asibiti ga lawyer ga "yan sanda, ga malamin makaranta, suma ai duk aiki sukeyi,,,,,, kai kuma aikinka tare mutane a hanya ka kwace masu kuɗi,,,, ta ƙarasa maganar tana dariya,,,,,


da ɗan yatsa ya nunata sannan yace to kada kiyi amfani da kwalwarki ki faɗa abinda bai dace akaina ba, ya ƙarasa maganar cikin ɗaga murya,,,,,,,,, tura mata flet ɗin yayi gabanta sosai tare da tura mata biredi yace ɗauki kici maza ki kama gabanki,,,,,,,,,


tace to amma..........,,,, hannunshi ya ɗaga mata alamar tayi mashi shiru,,,,, rufe bakinta tayi ta haryar cusa mashi biredi,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻


💦💦💦💦

*RASHIN RABO*

💦💦💦💦


*R🅰SHIN R🅰BO*


*MEELAT MUSA*


*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP zaku nema a shafinmu na facebook don samun ƙayatattacin littattafanmu* 


*19-20*


***


*H*awaye masu zafi sosai suka kwararo daga cikin idon sapna,,,,,,,,,,,,,,,,,


Sauke kanta tayi tana kallon ƙasa, innalillahi wa,inna ilaihir raji"un tace , sannan ta miƙa hannunta ta ɗauki ledar data ajiye a gabanta ta ɗauka, matsawa tayi wurin wata bishiyar bedi ta tsugunna tana ci gaba da kuka,, sai shashsheka takeyi, tana goge hawaye da gefen hijabinta,,,,,,,


Sapna ta daɗe wurin tana zaune, tun tana tsugunne har ta cire takalminta ta zauna a sama,,,,,


Wani irin tagumi ta zagba  kamar wanda taga mutuwa a gabanta, wata irin gajiyayyar ajiyar zuciya ta sauke sannan ta buɗe ledar gabanta,,,,, kayane na sakawa aciki,


Bayan ta gama duddubawa, ta kama bakin ledar ta ɗaure, miƙewa tsaye tayi ta ɗauki ledar ta sannan tace haƙiƙa gabas manema lada,


Don haka gabas na dosa ubangiji ka sadamu da alkairin dake cikin gabas,,,,, abin hawa ta tare bayan tayi ciniki dashi ta faɗa mashi inda zai kaita,,,,,


Shiga tayi sannan suka tafi, tafiya mai nisa sosai sukayi har suka shiga cikin unguwar , mai nepep nan yayi inji sapna ta faɗa,,,,, parking yayi sapna ta buɗe ledar ta fiddo kuɗin napep ta bashi sannan ta fice,,,,,,,


Gidan tayiwa tsinke, gabanta sai dukan talatin da biyu yakeyi,,,, har ta isa bakin get ɗin gidan,,,,


Tun a bakin get mai gadi ya tare ta, tare da cewa ja baya malama,,,,,, cikin yanayin a tausaya mata tace miyasa zanja baya?""""" sapna ta tambaya, mai gadi yace saboda nan ba gidan ubanki bane,,,,,,,


Idanuwa sapna ta zaro tare da dafa ƙirjinta, tace ni kake cewa nan ba gidan ubana bane?""",,,,,, yace nace, danma kina ke, aida uban nakine sai na wanwakawa ma banza mari nacicci ubansa sannan in faɗa mashi,,, amma maza ki ɓace anan tun kina iya tafiya da ƙafafuwanki,,,,,,,


Sapna batayi magana ba,,,,,,, ƙarar horn dataji yasa  ta maƙale kalama da take son fesewa mai gadi masu zafi, dole tasa ta adana kalaman da suka taho a harshenta, don haka tayi shiru ta juya tare da bin motar da kallo,


kusa da sapna yayi parking, sannan ya sauke galshin motarshi, tabarau ɗin idonshi ya cire hannunshi na dama yana riƙe da sitiyarin motarshi,,, da sauri sapna ta rungume ledar hannunta sannan ta tsugana cikin girmamawa tace baba sannu da war haka,,,,


kallonta yayi ƙasa da sama sannan yace miye ya kawoki gidana?"",,,, da sauri sapna tace baba ka taimaka man ka ajiyeni a gidanka ka barni in zauna dakai na wani lokaci, murmushi yayi sannan yace wato uban naki ya kasa shi yasa ya turoki don ganin bayana kamar yanda ya faɗa?"""


cikin rawar baki sapna tace baba kayi haƙuri shi ba babana bane, a suna kawai yake baba amma a zahirance bai tabbata mahaifi ba,,,,,


Wani wulaƙantaccen kallo yayi ma sapna sannan yace yanxun ya kikeso ayi?"" ya ƙarasa maganar tare da ƙanƙance idanuwanshi, da sauri sapna ta gyara durƙushin da tayi ta ƙara rungume ledar hannunta sannan tace ka taimakeni ka raɓani a iyalinka rayuwa tayi mani ƙunci,,,,,,


Baba yace to jirani inzo inyi maki maganin ƙuncin rayuwa,,,,, buɗe mashi get akayi ya shige ciki da sauri,,, sapna tana nan tsugunne a wurin tana jiran fitowar baba,,,,,,


wani mutum yaxo kusa da sapna sannan yace yarinya in baki shawara ?"",,,,, kai kawai sapna ta ɗaga mashi alamar Eh, yace to na rantse maki da Allah ki tashi ki gudu wallahi kar ki bari alhaji abu ya dawo ya sameki anan, 


Kallonshi sapna tayi sannan tace miyasa kace haka?"",,,,, yace gabar dake tsakanin mahaifinki dashi zata shafeki, dan haka hanzarta don tsira da rayuwarki,,,,,,


sapna jiki a sanyaye ta miƙe, dakel take ɗaga ƙafarta saboda wata irin azabtacciyar yunwa dake gurgurar mata "yan hanji,,,,, ta matse "yar ledarta taci gaba da tafiya,,,


Sapna bata daɗe da tafiya ba, Alhaji Abubakar ya fito daga cikin gidanshi da gudu da wata "yar ƙaramar bindiga a hannunshi yana wani irin huci kamar kura ta kama mutun ya kufce,,,,,


cikin tsananin ɓacin rai baba yace ina take lbanzar?"",,, mai gadi yace ai ta gudu ranka ya daɗe,,,, tsaki yayi sannan yace ai dana alburusheta banza ta huta da ƙuncin rayuwar,,,,,


Alhaji Abubakar yaci gaba da cewa waini za,a cuta yana maganar ne yana nuna kanshi da hannunshi,, yaci gaba da cewa a faɗa man nine baba, lunfasawa yyi sannan yaci gaba da cewa kaji mayaudariyar yarinya,,,, riƙe haɓarsa yayi sannan yaci gaba da cewa bayan nan wurin usman yaxo ya gama tsiyaye man jalop ɗin rashin mutunci, bama da miya yayi ba, komai ya afka a tukunya,,,,,


Tsaki yayi sannan yace  da na kashe banzar yarinyar nan lallai usman daka ɗanɗani gubu da ɗacin mutuwar ɗiya, sakaran banza da baka gode kyautar Allah, niko nace daka kashe mashi ita ai daya huta,,,,,,


saida ya gama ɓaɓatunshi ya gama rarara ɗinshi sannan ya nufi cikin gida yana ƙara zungurawa uwar sapna zagi,,,,,,,,


Tafiya sapna take sosai, ba tare data san ina zataje ba, tsayuwa tayi a gefen titi sannan tayi tagumi daga tsayen,,,,, a bayyane tace haƙiƙa ya kamata insan abinda yasa baba ya tsani aihuwar ɗiya mace??,,,,,, amma kafin in san haka ina ya kamata in nufa?""",,,,, hawaye ya kawo a kwarin idanuwanta taɓe bakinta sapna tayi sannan tace ga duniyarma yanxun kowa baya yadda da kowa saboda halin rayiwar yanda ya koma,,, shin ina dangin mahaifiyata?""" a daidai lokacin da hawayen suka kwararo daga cikin kwarin idonta,,,,,,,,


Tsuguniya sapna tayi sannan ta duƙar da kanta tana kallon ƙasa ci gaba da kuka tayi,, sannan ta sake cewa dan mahaifiyata ba raye shi yasa na zama abin gudu ga kowa?""",,,,,,, ku kuma dangin mamana miye aibuna a wurinku?"" nayi imani da mamana tana raye haƙiƙa da kun riƙa zuwa wurinta, har ku ganni,,,,, wata rana zaku buƙaci inje wurinku da yini ko da hutu,,,,,,,,


Goge hawayen fuskarta tayi sannan taci gaba da cewa, miyasa bakwa adalci wa rayuwar marayu?"",,,, haka zaku barni inyi ta balbaɗewa a titi?"",,,,, ina zan tunkara suji damuwata?"" waye zai riƙeni da gaskiya?"",,,, bakwa gudun abinda zai sami rayuwata?"",,,,, kowa baya tunanin rayuwar tawa saboda shi ya tattala nashi zuriar a gida?"" waishin miye ma aibun ɗiya mace?"""""""


sapna bata ƙarasa maganarta ba, taji wani yana cewa yawwa ga munafuskar nan ku afkawa wa banzar,,,,,, da sauri ta ƙara rungume ledar hannunta ta taƙa ƙafafuwanta alamar so take ta samu sa,a ta zungura da gudu,,,,


juye juye ta farayi tana kallon yawansu, wasu da bindigu a hannunsu wasu kuma da irin kulkin "yan sanda a hannunsu, masu kulkin sai ɗaga shi suke a hankali suna dukan hannun haggunsu dashi, suna ɗan zageye zageye, wani irin kallo sukeyi wa sapna, wanda ya ɗaga mata hankali gashi kuma sun zageyeta babu damar ta fece, murmushin ƙarfin hali sapna tayi cikin rawar jiki tayi sanyayar magana , tace yayuna mi nayi maku?""",,,,,, a daidai lokacin data yaga ƙafarta sosai ta ibi fili,,,,,,,,,,,,


Ɗaya daga cikinsu yace idan kika gudu wallahi saina harɓe ki,,,, tsayuwa ƙam sapna tayi tareda ɗauke lunfashinta gaba ɗaya, juyowa tayi ta fuskancesu a yanayin damuwa,,,,,, amma batayi magana ba,,,,, mutumin ne yace ku kawota muje,,,,, kamar jira sukeyi yayi magana gaba ɗayansu sukayi kan sapna, zasu riƙota,,, da sauri ta yada ledar hannunta tare da ɗaga masu dukan hannayenta tana cewa ku saurara ina zaku kaini ne?"""",,, cikin maganar daba wani yace kaji "yar rainin hankali waimu zata tambaya abinda tayi,,,,,,


rirriƙe sapna sukayi sosai,,, ita kuma ta fara kicinayar anshe kanta,, amma sunfita ƙarfi bata da yanda zatayi saboda haka suka jata ƙiyyyyy suka nufi wurin motar, suna zuwa suka sanƙamata a mota, gaba ɗayansu suka shiga babu ɓata lokaci sukaja motarsu suka ɓace daga wurin ko ƙurar motarsu baka gani,,,,,,,,,


Cikin masifa ya shigo cikin gidan, jikinshi har ɓari yake saboda tsabagen bala,i, lallai da mutum yana mutuwa so biyu haƙiƙa saina ƙashe yarinyar nan sau dubuuuuuh yayi maganar ne cikin kakkausar murya, tare da buga ƙafarsa ƙasa,,,, 


Da sauri raliya ta fito daga ɗaki,, tana cewa ya akayi ne?""",,,, bakin baba ya fara kyarma zufa tana zubowa mashi daga jikinshi, kumatun fuskarshi sai ƙarma suke dan bala,i kamar zai kama da wuta,,,,,


cikin ƙunar rai baba yace waini shegiyar yarinyar nan zata tonawa asiri?"",,,, waiiiiii kamarni?"" ya nuna kanshi da hannunshi yace waini dake da babu zataje gidan Abubakarrrrrr,,, ya ƙarasa maganar tare da jinjina kanshi sannan yaci gaba da cewa ta durƙusa ƙasa tana cewa waiya taimaka mata,,,, a daidai lokacin da hawaye ya kwararo daga cikin idon baba,,,,,,


Cikin maganar kuka baba yaci gaba da cewa yarinyar nan bata da hankali,,,, waye yace mata ana bawa a bokin gaba amanar rayuwa?""",,,,,, wani irin kuka baba ya saki yace haƙiƙa ban taɓa ƙunci irin na yau ba,,,,,,,,, yaci gaba da cewa nan Abubakar da kanshi yazo yayi ta man dariya na haifi ɗiya mace, yace babu ni babu arxiki har a nannaɗe duniya ya dulmiyar dani cikin halaka yasa na tsunduma cikin tsananin san abun duniya, saboda su duk sunfini arxiki kuma a cikinsu babu mai ɗiya mace duk "ya"ya mata suka aifa,,,,,,,,  nazo na tara matana nace masu su rufa man asiri su haifar ɗiya maza, saboda Abubakar yace ɗiya mace lalurace,,,,,,,


Zama baba yayi a ƙasa ya saki wata irin ƙara, wanda yasa suwaiba fitowa daga ɗaki da gudu,,,,, zufa taci gaba da ambaliya daga jikin baba banda kyarma jikin baba babu abinda yakeyi,,,,,, raliya cikin damuwa ta matsa kusa da baba ta tsigunna, baba yasa bayan hannunshi ya goge hawayen fuskarshi sannan yaci gaba da cewa,,,,,,,


haka sukaci gaba da nuna man cewa inyi la,akari da inna tunda take aihu bata taɓa aihuwar ɗiya ta mace ba,,, gashi duk maza ta zazzago kuma kowa yana da kuɗi,, baba ya kalli raliya sannan ya riƙe hannunta yace "yar rali banma san ta ina zan fara ba?"",, haƙiƙa "yan uwana sun cuci rayuwata, nima na cuci kaina,,, banma san ta ina zan fara ba,,,,,,  dan sunce man duka rayuwata akan ɗiya mata zata ƙare,,,,,


jiya naga amfanin "ya"ya mata tun rayuwa batayi nisa ba,,,, ni kuma na ƙori dake da babu na babbaka mata wuta, dan ta mutu amma Allah bai kasheta ba tunda Abubakar yace taje gidanshi, yana faɗa man yana man dariya wai taje a ƙarƙashin ƙafafuwanshi tana neman taimako,,,, da sauri baba ya miƙe tsaye yace waini Abubakar zaice ya tattaka ɗiyata,, baba yana taka ƙasa da ƙafarshi yana murmurzawa yanda Abubakar ya nuna mashi,,,,,


durƙushe baba yayi ƙasa saman guyawunshi sannan ya runtse hannu wanshi, yace banma san ina zan ganki ba, da ƙarfi yayi magana yana cewa ina kikeeeeeeeeeeeeeeeeee???????"""",,,,


suna zuwa ɗaure Sapna sukayi da wasu irin sarƙoƙi wanda basa ɓallewa duk tsananin azaba, da bokitan ruwan sanyi aka kawo da ƙanƙaru a ciki, haka akayi ta kwararawa sapna, gaba ɗaya jikinta yabi ya sandare tana jinshi kamar ba,a jikinta yake ba,,,,,,


A wahalce sapna ta buɗe idonta cikin galabaita ga hannunta sai ciwo suke mata yanda aka ɗagasu sama da yanayin ɗaurin da akayi masu,,,,,,,,,


Wani azzalimi ne ya matso kusa da ita,,, gashin kanta ya damƙo cikin sigar cuta, ya ɗaga mata fuska tana fuskatarshi sannan ya kasheta da mari, a galabaici sapna tace ka daina dukana hakanan, ku barni in huta don Allah ta ƙarasa maganar hawaye na gangarowa daga cikin kwarin idanuwanta,,,,,,,


sakin kanta yayi , kan nata ya fara lilo dan yanayin riƙon da yayi mata da kuma yanayin yanda ya saketa,,,,, sannan yace kallaemu nan adaidai lokacin da yake cire rigar jikinshi, yana dariyar mugunta,,,,,,


yace kin ganmu dukanmun nan?""",,,, yanxun zamuci uwarki sannan dukanmu yawanmu ɗaya bayan ɗaya sai munyi fyaɗeeeeee wai ke,,,,,,,,,,,,,,,,

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻


💦💦💦💦

*RASHIN RABO*

💦💦💦💦


*R🅰SHIN R🅰BO*


*MEELAT MUSA* 


*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP zaku nema a shafinmu na facebook domin samun ƙayataccin littattafanmu*


*27-29*


***


*J*uyawa yayi ya koma inda yake aikinshi yaci gaba da harkar gabanshi,, 


Miƙewa sapna tayi ta matsa kusa dashi tare da riƙe cikinta, sannan tace yunwa nakeji fa, ka bani abinci inci, kasan mutane sunajin yunwa a hanasu abinci wannan ai ɗaukar alhakine,,,,,,,,,,


Kallonta yayi, amma baiyi magana ba,,,, murmushi sapna tayi tare yin magana cikin dariya, tace to ai babu komai ma, bama sai naci ba azumi ma nakeyi, ta ƙarasa maganar tana murmushi,,, tare da riƙe cikinta da hannunta, don azababbiyar yunwa takeji sosai, bai sake kallonta ba, kuma baiyi magana ba,,,, yaci gaba da aikin dashen shuka ɗinshi,,,  jiki a sanyaye ta wuce daga wurin, saida ta matsa sosai sannan tayi tsaye,


Kallonshi tayi tare da yin magana a hankali mutum bai ajiye komai ba sai baƙin rai da zuciya, tsaki tayi sannan ta zauna,,,,,, shi kuma bai sake kallon inda take ba,,,,,,,,,


Tana zama tayi tagumi wasu hawayen ɓacin rai suka zubo mata daga idonta,,,,, ajiyar zujiya tayi da sauri saboda wani abu dataji yana ƙoƙarin ɓare mata maƙoshi, a ranta tace baba, baba, baba,,,,,,, haƙiƙa baka cancanci zama mahaifi ba,,,, nayi imani da mamata ce duk abinda zanyi mata bazata iya rabuwa dani ba,,,, tana tare dani tana kula da rayuwata, idan banyi daidai ba ta gyara man, tana kula da wanda nake tare dasu idan basu cancanta da rayuwata ba ta rabani dasu dan gyara man tarbiyya,,,,, amma kai ka koroni daga gidanka ma kwata kwata,,, duk inda nayi bina akeyi a kasheni,,,,, wannan da nake zama dashi shi kuma ko waye shi?"""Oho tace a bayyane tare da taɓe bakinta,,,,,,,,,,,,


Juyowa yayi ya kalleta,,, amma baiyi magana ba, sannan kuma ya juya ya nufi toilet, saida yaje ya wanke hannunshi sannan ya dawo ya nufi kicin, saida ya daɗe sosai sannan ya fito da flet a hannunshi, a gabanta ya ajiye ba tare da yayi magana ba,,,, da sauri taja flet ɗin gabanta tare da cewa nagode ɗan uwa,,,,,, baiyi magana ba, ita kuma ɗaukar abinci tayi ta juya taci gaba daci,,,,,,,,,,,,


saida ta gama cin abinci sannan tace na gama,,, koya man yanda ake harbi da bindiga,,,, a zuciye ya juyo tare yin magana cikin tsawa yace ke an faɗa maki ɗaukar bindiga wasa ne?""",,,,,,,,, inda ya ajiye akwatin bindigun yaje ya ɗauko sannan yaxo ya ajiye a gabanta,,,, tare da cewa to wannan hatsari ne idan kuma kin matsa sai kin ɗauka hannunki yana iya gundilewa,,,,,,,


tsaki tayi tare da ɗaukar "yar ƙaramar bindiga, shi kuma yabita da kallo saida ta matsa kusa da window sannan ta fara harbi ta ta tata ta tata, sannan ta juyo ta taho kamar wata jarumar gaske,,,,,, saida ta matso kusa dashi sosai sannan ta nunashi da bindi tare da cewa ya kaji?""",,,,, baiyi magana ba, ya anshi bindigar ya mayar da ita a cikin akwatin sannan ya ɗauka ya mayar dashi inda yake ajiyewa,,,, murmushi tayi tare da tashi ta nufi ɗaki ta kwanta,,,,, tana kwanciya tayi dariya tare da cewa wata rana da bindugunka zan harbeka in ɗauka inyi tafiya,,,, umm tace tare da gyara kwanciyarta ta fara bacci,,,,,,,,,


Sallamar malam nuhu yasa raliya fitowa daga ɗaki da sauri tare da cewa baba ka dawo ne?""",,,,,,, malam nuhu yace Eh,,,, raliya tace ya akayine?""",,,,,,,, a daidai lokacin data koma ɗaki take ɗauko tabarma,,,,,,,,


shinfiɗawa tayi tare da cewa zauna,,, bisimillah yayi tare da zama saman tabarmar, kallon raliya yayi sannan yace usman yaje wurin, wato ɗayan yayan baba,,,,, kuma duk munyi magana da Abubakar amma yace lallai ko zai bayar dashi sai an bada miliyan biyar,,,,,, idan kuwa ba haka ba, kada ya ƙara ganin ƙeyar kowa a wurin,,,,, raliya tace ita dama hukuma haka take ne?""",,,,,, murmushi malam nuhu yayi tare da cewa Abubakar dai, shi yana so sai yaga usman cikin ƙunci ne, da ƙuna,,,,,,


Raliya tace to babu damuwa, bari a kira fahat a sanar dashi,,, da gudu suwaiba ta fito daga ɗaki tare da cewa kam balasti, babu ubanda zai kira man ɗa dan kutumar uban maiso ya kirashi a wayar,,,,, raliya tace to duk miye yayi zafi haka?"",,,,,


Ai naga babanshi ne kuma dama an fanin aihuwar kenan idan kana cikin damuwa ɗanka ya fitar dakai,,,, tsaki suwaiba tayi sannan tace idan aka kirashi sainaci uwarki,,,,,,, raliya tace indai ci uwarki, rufe gida zanyi in zane maki jiki,,,,,,,


malam nuhu yace rabu da ita, taso muje,,,, a daidai lokacin da malam nuhu ya miƙe tsaye, nannaɗe tabarmar raliya tayi sannan ta shiga ɗaki,,,, hijabinta ta ɗauko sannan ta fito taja ƙofar ɗakinta,, tabi bayan malam nuhu suka fita daga gidan,,,,,,


Suna fita gidan malam nuhu suka nufa, bayan sunje suka gaisa da mai ɗakin malam nuhu, tabarma tasa masu suka zauna,,,, raliya, tace wai su waye usman?"" kai kuma wayensu ne?""",,,,, murmushi malam nuhu yayi tare da cewa ni aminin mahifinsu ne,,,, sanna ya ɗora ,,,,,,,,


Malam tanimu, da hadiza sune iyayen , su Abubakar da umar da usman,,,, kuma tun daga su basu sake aihuwa ba,,, malam tanimu yana san "ya"yanshi sosai kuma yana nuna masu kulawa sosai yanda ya kamata,,,,,,


haka suka taso cikin jin daɗi da kaunar juna,,, babu abinda suka nema suka rasa,,,,,, inna wato mahaifiyarsu ta kasance tana san usman sosai, saboda tana kawaicine akan Abubakar kasancewar shine babba ɗa,,,, wanda dama wannan aƙida ce ta fulanin asali,,, kuma haka take nuna kawaici akan umar, amma tana san usman sosai,,,,,,,


Idan yace anyi mashi abu haƙiƙa inna ta kama faɗa kenan, tana binbini, idan kuma yasu yasu sukayi faɗa to haƙiƙa inna saita fasa ma mutun fata saboda usman,,,,, 


haka a gaban su Abubakar da umar inna bata ɓoye soyayyar usman wannan abun yana masu ciwo,,,,, ganin wannan halin da inna takeyi malam tanimu yayi mata faɗa tare da cewa ta riƙa ɓoye soyayyar usman a cikin "yan uwanshi saboda kada ta jefa ƙiyayya a cikinsu,,,,


amma sam inna ta murje idonta taci gaba da abinda taga dama,,,,,,,, wannan dalili yasa su Abubakar suka fara jin haushin usman, saboda idan yayi masu abu a matsayinsu na yayunshi inna saita murje idonta ta bawa usman gaskiya su kuma suce ƙarayane,,,,,


idan inna ta tashi addu,a haka zata dage tana cewa Allah kasa usman ɗina yayi kuɗi yakaini makka, idan su Abubakar sukace sufa?"",,,, sai inna tace ɗan autana dai,,,,,,,,,


haka ko makaranta zasu tafi inna tabi usman tare da mashi addu,a shi shi ɗaya, idan kuma suka dawo usman zai rugo inna ta rungume usman tana mashi sannu da zuwa,,,,,,,


Haka rayuwa taci gaba da tafiya har suka girma Abubakar yayi aure, umar shima yayi aure,,,, amma har girmansu inna bata daina wannan halin nuna banbanci ba, anan cikin rayuwa Allah yayi wa malam tanimu rasuwa ba tare da jinya ba,,,, wannan mutuwa ta taɓawa inna da ahalinta zuciya sosai,,,,,


haka akashe koke koke,,,, akayi zaman gaisuwa kamar yanda dai akeyi a  addinance, koda aka zo wurin rabo gado inna ta murje idonta fesss tace wannan gida babu maishi sai isiman,,,,, wannan abu ya ɓata masu rai,,,, dan haka sukaje sukayi magana wa malam nuhu amma sam inna tace babu wannan mai gida saishi,,, kafin rasuwar malam yace a bawa auta gidan,,,,,,


haka suka haƙura, amma suna da baƙin cikin wannan gadon gida,,, ana haka usman yayi aure, kuma ya tare da matarshi a gidan gadonsu,,,,,,,,,


shi kuma Abubakar tunda yayi aure Allah ya azurtashi da aihuwa "ya"ya maza, kuma ga aiki ya samu kuma ya shiga aikin police da sa,a dan tashin farko matakin A S P , ya fito,,,,,,,


Cikin ikon Allah ubangiji yasa ma nemanshi albarka,,,,,, amma usman har yanxun bai samu aiki ba,,,,, yana nan gida zaune, babu aikin fari bare na baƙi,,,  wannan abun yayi ma Abubakar daɗi sosai,,, danshi dama umar babu abinda ya dameshi,,,,,


ana cikin hakan matar usman ta aihu, Allah ya albarkace ta da ɗiya mace,,, usman yayi murna sosai, yaji daɗi kamar mi,,,,,, lokacin da Abubakar yazo barka, bayan yayi barka yace ma usman zo muje waje,,,,,,,,,


haka usman ya tashi yabi bayan ɗan uwanshi,,,, suna fita suka zauna a saman dakalin ƙofar gidansu,,,, sannan Abubakar ya kece da wata irin dariya,,,,,, usman ya kalli Abubakar tare da cewa lafiya?""",,,,,, Abubakar ya dafa kafaɗar usman sannan yace bawan Allah wallahi har ka bani tausayi, sannan ya ƙara sheƙewa da dariya,,,,,,,,,,


usman yace wai miye ka kirani anan sai dariya kake man, Abubakar yace to ai kaine ɗin dole in fara dariya sannan , wai inna tana maka fatan kayi arziƙi,, kaga bakayi ba, nine nayi arxiki, ga kuɗi ga mulki,,,, yayi dariya sosai, sannan yaɗan kai duka a kafaɗar usman sannan yaci gaba da cewa,,,,,,,


kuma saboda baka da sa,a kaga kana tashi aihuwa sai aka fara maka da ɗiya mace,,, niko ina tashi aka fara bani da mazaje,,,,,,, kaga ɗiya mace bata da wani amfani,,, kana cikin talauci kaga babu wani mai kuɗi da zaizo ya aureta,,,,,,,,,


Bata zuwa nema bare tayi wani ƙoƙarin taɓuka wani abu, idan ta tashi aure kaine zakayi mata kayan ɗaki, shi ko namiji shine zaije ya nema da kanshi,,,,,, kuma su maza ba,a sakinsu saida su mata a sakesu a gidan aure,,,, kaga zata dawo gidanka kaga wahala bata ƙare maka ba,,,, haka dai yayi ta cusa ma usman baƙin ciki,,,,,,,,


shi kuma yahau ya zauna,,,, Abubakar na tafiya Usman ya koma gida, yaci gaba da balbala bala,i baisan ɗiya mace sai namiji,,,, wannan dalili ne yasa bayasan aihuwa "ya"ya mata,,,,,,,, to yarinya ma ashe bamai rayuwa bace,,,,,,,


shi kuma Abubakar saboda banbancin da inna take nunawa shine dalilin da yasa ya tsani usman wannan abunne ya jefe ƙiyayya a tsakaninsu,,,,,,,,,,,


raliya tace to Allah dai ya kyauta,,,, malam nuhu yace ameen, malam nuhu yace kinga dai dole cikin "ya"yanka akwai wanda kafi so, amma ya kamata ka riƙa boye wani abun saboda haifar da zaman lafiya, a cikin ahalika, yaci gaba da cewa kuma na tabbata dan yaga iyakar usman zaice a bashi miliyan biyar,,,,,, raliya tace ba komai Allah baizai hana yanda za,ayi ba,,,,,


haka dai sukaci gaba da tisa zance daga baya kuma raliya ta tashi ta tafi gida,,,,,,,,,,,,


Tunda safe bayan sapna tayi sallahr asuba, ta fito farlo,,,,, bayan ta zauna tayi mashi zuru tana kalloshi,,,,, baima san tanayi ba, danshi abinda ya dameshi shine damuwarshi,,,,,,, sapna bata daɗe da zama ba,,,,,, sukaji jiniyar motocin "yan sanda,,, da sauri ya miƙe ya leƙa ta windowa bayan ya tabbatar dasu ne,,,,, da sauri ya dawo ya nufi wurin ƙofar yana kullewa da sauri,,,,,


Bayan ya kulle ya dawo da sauri, ya fara haɗa "yan kayanshi,,, miƙewa sapna tayi tare da cewa miye?"" ina kuma zakaje?"",,, baiyi mata magana ba, yaci gaba da haɗa kayansa, yana gama haɗa komai nasa,,, ya ɗauki wani gwangwani yana fesawa jikin labileyen ɗakin yana gamawa yaje inda sapna take tsaye hannunta yaja, sannan ya  kunna layter ya wurga gaba ɗaya ɗakin ya kama da wuta,,,,,


Su kuma suka fita ta ƙofar baya,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻


💦💦💦💦

*RASHIN RABO*

💦💦💦💦


*R🅰SHIN R🅰BO*


*MEELAT MUSA*


*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP zaku nema a shafinmu na facebook domin samun ƙayataccin littattafanmu*


*Don Allah ku daina riƙeni, Asmeenat Xeeyan ki sakeni,,,, gafara rukky haƙiƙa bazan tsaya ba, sai nakai bauchi,, koda mota ko babu yau a ƙafafuwana zanje garin bauchi haƙiƙa garin masoyi baya nisa,,,, dolene jameela musa tayi tirjiya inja da baya in babbaka da gudun babbar biredi da boter in isko REAL MAI DANBU,,, mace mai mutunci da kara, sai kace a garin katsina taso, domin katsina akwai kunya da nuna kara,,,, ashe suma "yan bauchi haka suke?""",,,,, haƙiƙa mai dambu ngd sosai da ƙaunarki a gareni ina sanki, ina ƙaunarki , ina alfahiri dake, Allah ubangiji yabar min real mai dambu,,,, kayana bisa kai haƙiƙa sai nazo garin bauchi gari na kara da mutunci,,,, garin da aka san darajar baƙo,,,, gani nan zuwa tare dani da ɗaukacin AMEENCI WRITER'S ASSOCITION,,,, damu da masoyanmu muke cewa sai MAI DAMBU , tamu ce, tasu ce, taku ce, tawa ce, mai dambu ta kowace, Ummu Farhana ma tace ke tatace,,,, kowa yace sai mai dambu, katsinawan dikko ɗakin kara suma sunce sai mai DAMBU, Alkairin Allah ya isoki har garin bauchi, ubangiji yasa ki kamla queen meelat lafiya Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana,,, meelat musa kecewa ki sarara abinki ki hutawa tawa, kiyi ƙarko tare da yin shekaru irin na DABINO,,,,,,,,,,,*


*30-32*


***


*C*ikin kuka sapna take cewa ina kuma zaka kaini?"" ina zakaje dani ne?"",,,, ina magana baza ka bani amsa ba?"",,, tayi ta jero tambayarne ba tare data bari taji abinda yace ba,,,,,,,


Shi kuma Alhaji Abubakar suna isowa wurin yaga motar imam malik haka ya tabbatar masa lallai yana gida,,, don haka da sauri yace ku shiga ku shiga muje yaci gaba da cewa kuyi kamar kuna da jini a jikinku mana,,,, ya ƙarasa maganar ne cikin ɗaga murya tare da nuna tsananin ɓacin ransa,,,,,,,


Da gudu "yan sanda sukayi ciki,,,, ganin hayaƙi yana fitowa daga cikin gidan ne,,,, yasa Alhaji Abu tashin hankali tare da cewa ku ɓalle ƙofar ɗakin mana,,,,, yayi maganar cikin ƙaraji,,, tare da fashewa da kuka cikin kukan ne yake cewa imam malik Allah yasa ba wannan baƙar zuciyar taka tasa ka babbakawa kanka wuta ba,,,,,


Sapna sai sake tambayrshi takeyi wai ina zakaje haka ne?""",,, tana maganar ne tare da goge hawayen idonta,,,,,,


Jan hannunta kawai yakeyi amma har yanxun bai kalleta ba,,,, bare ya faɗa mata dalilinshi na tahowa da ita ba,,,,, tafiya sukeyi sosai ,, ita kuma cikin kuka taci gaba da cewa,,,,,,


Mai zai hana ka faɗaman miyasa muka bar can?"",,,,taci gaba da cewa ina ta maka tambaya amma kayi shiru, mi zai hana ka faɗaman miyasa mukabar can??"""  tana maganarne tare da nuna bayanta da hannu,,, taci gaba da cewa kanaji ba, amma ka wani basar dani kamar ba kaine nake magana ba,,,,,, ta ƙarasa maganar ne tare da fashewa da kuka,,,,,,,


Tsayuwa imam malik yayi , don haka itama ja tayi ta tsaya,,,,, cikin izza da isa yace,,,, babana ne yaxo , kuma nine yake na bake ba,,, na kuɓutar dakene kada ya sameki,, dan yana samunki a wurin zaiyi wata fahimta wadda ba haka bane,,,, lumfasawa yayi sannan yaci gaba da cewa, kuma nayi imani yana kamaki haƙiƙa ƙaryarki ta ƙare,,, ya ƙarasa maganar  tare da ciza haƙoransa,,,,,,yana buɗe leɓansa duk jijiyoyin kansa sun tashi,, idanuwansa sunyi kalar bada tsoro,,,,, sannan yaci gaba da cewa kinga yanxun na kuɓutar dake dan haka sai ki yanke ina zakije?""",,,, ya ƙarasa maganar tare da ɗaure fuskarsa sosai,,,,,,,


da sauri sapna ta kauda kanta gefe guda, saboda tsoro, hannunta tasa ta goge hawayen idonta sannan tace to amma nikam ina zanje?"",,,,,, cikin fushi da ɗaga murya yace ki zaɓi inda zakije don kema ki ceci rayuwarki, dan ni bazanci gaba da zama dake ba,,,, ya ƙarasa maganar tare da nuna kanshi da hannunshi,,,,,


cikin kuka sapna tace kaga,,, nifa banda wani wurin da zanje na yadda cewa tarayya dakai shine tsirana magana ta gaskiya, ta ƙarasa maganar tana goge hawayen idonta,,,,,, tare da jan majina kamar ƙaramar yarinya,,,,,


Tun kafin ta ƙarasa maganar imam malik yayi tafiyarsa,, tsayuwa tayi wurin tun tana hangensa har ta daina ganinsa,,,, murmushin ƙarfin hali tayi da gefen bakinta sannan tace a bayyane saina isko wallahi bazan bari ka barni ba,,,, goge hawayen idonta tayi da bayan hannunta sannan tabi bayan imam malik da gudun tsiya,,,,,,,,,,,,,,


Jin maganar fahat yasa raliya fitowa daga ɗakinta cikin sauri tare da cewa gwamna kaine haka da zuwan bazata?"",,,, tana maganarne cikin nuna farin cikinta,,,,, ko inda take bai kallaba ya wuce zuwa ɗakin uwarsa,,,,,,


murmushi raliya tayi tare da taɓe bakinta sannan tace kaji dashi,,, shi kuwa fahat yana shiga ɗakin suwaiba, bayan sun gaisa ne,,, ta kwashe komai ta faɗa mashi,,,,, ajiyar zuciya fahat yayi sannan yace to umma yanxun miye mafita?""",,,,,,


Gyara zaman ta, tayi sannan tace abinda dai zan faɗa maka shine,,, kada ka kuskura ko zai mutu ka bayar da kuɗinka na faɗa maka,,,,, fahat yace umma miyasa?"",,,, cikin wulaƙanci umma tace kai arrr can sakaran banza, ka adana kuɗinka kaima kayi wani uziri dasu,,,, ka samu ka kammala karatunka sai ka samu abinyi,,,,,,


Taci gaba da cewa shi kaga tashi dai tazo ƙarshe, yanxun zai koma sabon gidan kuma anzo an damƙeshi, za,a bayar da wannan zunzurutun kuɗin,,, ka faɗa man ta ina zai sami wasu yaci gaba da kula da iliminka?""",,,, fahat yayi shiru, suwaiba taci gaba da cewa to ko za,a mutu kada ka kuskura ka bayar da kwandalar ka na faɗa maka,,,,, cikin fahimta yace to,,, haka taci gaba da ɗurawa fahat baƙaƙen ɗabi,a shi kuma yaci gaba da ansar saƙon suwaiba,,,,,,,,,,,, niko nace kaji butulci,,


Alhaji Abu saida aka buɗe ɗakin amma bai fahimci komai ba, dan komai na ɗakin ya babbake da wuta,,, tun a wurin yake kuka tare da bin duk wani abu daya gani yayi kama da mutun yana ɗagawa,,,,,,, yana cikin hakane wayarshi ta fara tsuwwa,,,, bayan ya ɗaukane sannan yace imam malik?"",,,, to gamu nan zuwa,,, da sauri yace "yan sanda su biyoshi,,,, babu ɓata lokaci suka bar wurin,,,,,,,,


Sapna kuwa bin bayan imam malik take da gudun tashin hankali, sai kuka takeyi kamar zata sheƙe, tana bayanshi harya isa wata hotel ta shiga da gudu sannan ta riƙe mashi hannu tana ci gaba da kuka,, da sauri ya juyo, ganin sapna yasa gabanshi faɗuwa,,,,, kallonta yayi sannan yace ya akayi ne?""",,,


Kamar jira sapna takeyi yayi mata magana , ta ƙara fashewa da kuka sosai,,,, sannan tace don Allah kada ka kwana dani a hotel,,, ɗaure fuskarshi yayi sosai sannan yace to nace zan kwana dake ne?""",,,,, cikin kuka ta ƙara matsawa kusa da imam malik, riƙe hannushi da hannuwanta biyu tayi sannan tace ka rufa man asiri don girman Allah in kwana dakai zuwa da safe tana maganar ne tana nunawa da hannunta, taci gaba da cewa insha da safe zansan mafita,,,,,,,


tsaki imam malik yayi sannan ya juya da sauri sapna tabi bayanshi har suka fita daga hotel ɗin,,,, tafiya suke sosai,,, sapna sai surutu takeyi ma imam malik shi kuma ko ansa baya bata ita kuma ko irin ɗan jan ajin nan batayi ,,,,, niko nace waya ga ba saban ba?""",,,, saida ya gaji da surunta ta sannan yaja yayi tsaye,,,, itama ya tayi ta tsaya,,,,,,,,


cikin fushi ya juyo sannan ya kalli sapna, yace ke da Allah kiyi man shiru bana san surutu,,,,, tun ɗaxu kike man rarara haba ,,, murmushi sapna tayi ba tare da ta sake cewa komai ba,,,,,,,, ci gaba yayi da tafiya don haka itama taci gaba da bin bayanshi,,,,,,,,,,


Tafiya sukayi mai nisa sannan ya tsaya wurin wata super market, yace ma sapna ki jirani anan ina zuwa,,,, kai kawai ta ɗaga mashi, shi kuma ya shige ba tare daya tsaya yaji komi zatace ba,,,,,,


Yana shiga suka gaisa da abokinshi sannan yace mashi gida mai kyau nake so zan siya, ko za,a samu ne?"",,, abokinshi yace haba "yar laɓai da kanka siyen gida kuma?"",,,, imam malik baiyi magana ba, yana kalloshi dai kawai,,,, shine yaci gaba da cewa to gidanjenka fa?"",,,,, imam malik baiyi magana ba,,, har yanxun dai ya kafeshi da idanuwa yana kallonshi sosai,,,, abokin nashi ne yace to bari ina da gida mana sai ka zauna a ciki duk da dai bakace man komai ba,,,,,,,,,, kai kawai imam malik ya ɗaga mashi alamar gamsuwa,,,,


makullin gidan ya ɗauko ya bashi, sannan suka fita da imam malik tare, suna fitowa ba tare daya kalli inda sapna take ba yace kina iya tahowa,,,, da sauri sapna tabi bayansu,,,,,, saida sukayi tafiya mai nisa sannan sukaje gidan,,,,,,,,


a ƙofar gidan ne yayi ma imam malik sallama, ya juya,,,, imam malik ya buɗe gidan ya shiga, itama da sauri ta shige,,,, tare da kulle ƙofar, tunda suka shiga gidan sapna taci gaba da zazzaga surutu,,,,,,,,


Ta fara cewa kai kaga gida?""" irin wannan gidan sak nake gani a markina,,,, ga farlo mai kyau bugu da ƙari ma mu biyu zamu riƙa zama a cikin gidan nan,,,,, shi kuma shige shige ya riƙayi yana leƙa gidan,,,,,,,


Itama binshi tayi suka shige toilet a tare,,, sannan tace ga kuma ban ɗaki yalwantace, baiyi magana dubawa yayi sannan ya kalleta,,,, murmushi tayi da sauri sannan tace to miye ma damuwar?"" da ban ɗaki yalwatacce da ƙanƙantar ai duk amfaninsu ɗaya,,,, fita yayi ba tare da ya sake kallonta ba,,,,, itama da sauri tabi bayanshi suka nufi bedroom,,,,,,


suna shiga ta kalleshi tayi dariya sannan tace O nan ne ɗakin bacci,,, amma gado ɗayane tak a ciki, taci gaba da cewa to nice zan riƙa kwana anan, to kai ina zaka riƙa kwana ne?""",,, kafin ta fito ya fice daga ɗakin tare da jan ƙofar,,,,, ita kuma da sauri ta taho dan haka ta buge da ƙofar,,,,,,,,,,


Tsaki tayi sannan ta buɗe kofar ta fita,,,, tana ci gaba da cewa bara in nuna maka inda zaka riƙe kwana acan zaka kwana, tana nuna wurin da hannunta,,,,, sannan taci gaba da cewa ni kaɗai zan riƙa kwana a saman gado,,,,,,,,,,,,,


juyowa yayi ya kalleta sannan yace ni banda buƙatar gado domin inyi bacci, dariya tayi sannan tace to sai kayi ka kwana a kan kujera, wallahi wancan karon naji mamaki daka kwana akan kujera duk yanda akayi kayi wani darasi akai ko ba haka ba?""",,,,,,,,,


Bindiga ya fiddo daga cikin aljihunshi, sannan ya ɗaga ta saitinta yace jekiyi bacci,,,,, da sauri tace to to bari ɗagawa kada a samu matsala ka bindige man ƙwalwa,,,,,, ai dama bacci nakeji sosai,,, saida safe asuba ta gari,,,, ta ruga da gudu ta shige ɗaki,,,,,,,


saida taje ta kwanta, sannan tace hamago kawai to waishi yanajin shi waye?""" tsaki tayi sannan tace zan fashe maka kaine idan bakayi hankali ba,,,,,,, ummm tace tare da rufe idanuwanta,,,,,,,,,

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻


💦💦💦💦

*RASHIN RABO*

💦💦💦💦


*R🅰SHIN R🅰BO*


*MEELAT MUSA*


*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP zaku nema a shafinmu na facebook domin samun ƙayataccin littatafanmu*


*33-35*


***


*D*a sauri ta buɗe idonta,,,,,,, kamar wanda aka kaɗawa ƙararrawa,,, zama tayi sosai saman gadon, ko tunanin mi tayi Oho tashi tayi ta fito farlo,,,,,,,,,,,,


Tana fitowa inda imam malik yake zaune taje tayi tsaye tare da riƙe ƙugunta,,,,,,,,, sannan tace wai kai kanajin kai waye ne iye?"" kawai ina cewa ka faɗa man sunan ka baza ka faɗa ba?"",,,,,,,


Zama tayi ƙasa, tare da naɗe ƙafafuwanta,,, sannan ta ɗaga kanta tana kallon fuskarshi,,,, murmushi tayi sannan tace wai don Allah ya kake ji idan ka kwana akan kujera?""taci gaba da cewa, sai ka wani haye abinka kamar wata mage?"",,,,, to wai shi baban naka waye shi?"" kayi wani abu a gida shi yasa ka gudu?""",,,,, dariya ta sakeyi sannan taci gaba da cewa dama baban ya kama yayi maka duka,,, da ganin ka taurin kai gareka,,,,,,,


Kallonta yayi , da sauri tace ah ai bawai ina nufin yayi maka duka ba,,, kawai dai ina so inga yanda zakayi ta zaro idon nan naka ne idan ya kama ka,,, naga yanxun bamu haɗu dashi ba, amma duk ka wani bi ka tsorata,,,,,, taci gaba da cewa nifa nan daka ganni bana jin wani tsoro,,,,,,,, ƙara ɗaure fuska imam malik yayi sosai sannan yace to tunda bakyajin tsoro tashi ki fitar min daga gida,,,,,,,,,,


Hannuwanta ta fara ɗagawa da sauri tana cewa haba kaiko?""kai baka san wasa ba?,,,, idan na tafi a tsohon daren nan ina zanje?"",,,, hawayen idonta suka gangaro saman kumatunta,,,,,, don haka maganarta ta koma cikin kuka,,,, tare da cewa don Allah ka rufa man asiri, kaman alfarma ka barni in zauna dakai don Allah, ta ƙarasa maganar ne tare da haɗa hannayenta, biyu alamar tuba,,,,,,,,,


Tsawa yayi mata tare da cewa ki saurari abinda zan faɗa maki, da sauri ta gyara zaman ta tare da cewa tom,,,,,, yace idan har kina so ki kasance tare dani, tou fa lallai dole sai kinbi tsarirrika na,,,, da sauri ta sake cewa tom, a daidai lokacin da hawaye suka ƙara kwararowa daga cikin idonta,,,,, imam malik yaci gaba da cewa, kawai zakiyi man magana ne idan ya zama dole,,,, sapna ta sake cewa tom,,,,, yace idan nace kiyi abu kiyi kawai bana buƙatar kiyi anfani da naki tunanin , ta sake cewa tom, yace kuma ki daina cewa tom akan komai , ta sake cewa tom a daidai lokacin da take goge hawayen idonta,,,,,,,


Ba tare daya kalli inda take ba yace maza kije ki kwanta,,,,, miƙewa tayi ta tafi,,, shi kuma tsaki yayi sannan ya ciro wayarshi daga aljihunshi,,,,,, sapna tana zuwa ta kwanta,,,, amma ta kasa bacci,,,,,,,,,,


Da safe sapna bata fito ba, sai wurin 7:29am, tahowa tayi tana miƙa tare da yage bakinta tana hamma,,,,,, kallon inda imam malik yake tayi, yana excercise,,, ya ɗora ƙafafuwansa saman kujera, hannuwansa a ƙasa ya dafa ƙasa, fuskarshi tana kallon ƙasa,,,, yana sama yana ƙasa,,,, press up,,, wucewa tayi wurin derning taja kujera ta zauna,,,,,,, tagumi tayi tana kallonshi,,,, a ranta tace wai ko wahala bayaji,,,,,, tana nan zaune tana tunani har ya gama,,,, wurin firij ya nufa,,,,,,,


Kwalin madara ya ɗauko hollandia, da glass cop, sannan yayo inda take zaune shima kujera yaja ya zauna, kallonshi tayi tare da gyara bakinta da sauri tace ina kwana,,,,, da kanshi ya amsa gaisuwar,,,,,, zuba madarar yayi sannan ya miƙa mata,,,,, kallon kofin tayi sannan ta kalleshi,,, shi kuma hankalinshi yana kan wayarshi, sai latse latse yakeyi,,,,,,


a ranta tace kam lallai ma wannan mutumin ɗan rainin hankali ne,,,, yana nufin wannan "yar abar zanyi kalaci dashi ne?""",,,,,,  kallonshi tayi shima ita ya kalla tare da taɓe bakinshi, girarshi ya ɗaga tare da cewa yadai?"",,,,,,,,,,


Cikin tsiwa tace wai wannan ɗan madarar zansha?"",,,, mi zata man?"" kawai kaman wayau ina can ina bacci komai da komai ka tattara ka cinye nine zansha madara sai kace wata mage?""",,,,,,,,,, tsaki imam malik yayi a daidai lokacin daya kai hannunshi zai jawo kofin da sauri sapna ta ɗauka ta shanye!"""",,,,,,,


Miƙewa yayi tare da ɗaukar kwalin madarar da kofin,,, miƙewa tayi itama ta bishi taci gaba da zazzaga surutu,,,,,,,,, juyowa yayi ya kalleta, da sauri tace yi haƙuri,,,,,


kamar dai yanda kace saiya zama dole zamuyi magana kawai duk lokacin dakaji magana na tayi yawa kawai kayi man alama, taci gaba da cewa taya zansan maganata tayi yawa?""" ta ƙara tausasa muryarta sannan taci gaba da cewa, bayan bakaman wata alama da zan gane ba?"""",,,,


imam malik bai sake saurarenta ba,,,, ya shige ciki,,,,, itama komawa tayi ta zauna,,, ya daɗe sannan ya fito cikin shiga mai kyau,,, da sauri sapna ta miƙe tsaye,,,, tare cewa ina kuma zakaje?""" baiyi mata magana ba, ya raɓa ta ya fita daga ɗakin,,,,,, taɓe baki tayi a daidai lokacin da take zama saman kujera, tsaki ta sakeyi sannan tace kila dan yana da kyau yake wulaƙanci,,,,,,


Raliya ce zaune a farlon Alhaji Abu tana bashi haƙuri akan ya taimaka ya saki mai gidanta,,,,, amma yace idan ya sake ganin ƙafarta a gidanshi lallai zai haɗa da ita  da usman ɗin dukansu ya rufesu banzaye kawai dasu,,,,


cikin kuka raliya tace waikai wace irin zuciya gareka ne?"",,,, dariya yayi sosai sannan yace irin ta uwarki ce,,,,, banzaye dake da mijin naki shashashu kawai masu talauci,,,,,, murmushin takaici raliya tayi sannan tace ai talauci Allah yake ɗorawa bawansa,,,, kuma kai da kke ganin mai arxiki ne mi kayi ma Allah ya baka kuɗin?""",,,,,,


Alhaji Abu yace idan na fahimceki kema kina man hassada ba?""",,,,,, to mijinki ma yayi ya gama, gaya can zai ƙare rayuwarsa a gidan kurkuku,,,,, tsaki raliya  tayi sannan tace wani ya kashe?"" ai ina tunanin sai ka kashe wani ko ka haura katangar gidan wani za,a maka ɗaurin mutuwa,,,, Alhaji Abu yace can maki dai a daidai lokacin daya miƙe yabar farlon,,,,,,


haka raliya taci gaba da kukanta mai isarta,,, sannan ta miƙe ta fito jiki a saɓule,,, cikin gidanshi ta shiga wurin matarsa bayan sun gaisa raliya ta kora mata jawabin komai,,,,,,,,,


ajiyar zuciya tayi tare da cewa ai abun nasu dai sai addu,a amma haka halin Alhaji yake,,, kuma waye ma yace saboda usman ne imam malik yabar gida ne?"" halin babanshi ya koreshi,,,,,,


Saboda Alhaji duniya ya bata gaba ba baya ya bata ba,,,, daga ya faɗa masa gaskiya ne shine abin ya zama masifa,,,,,, taci gaba da cewa kiyi haƙuri insha Allah komai zai zama daidai,,,,,,,,,


Haka taci gaba da bawa raliya haƙuri tana kwantar mata da hankali, a cikin bata haƙurin ne take cewa irin wannan abunne yasa ɗanshi yyi nisa dashi kwata kwata,,,,,,,,


wai wani mutum ne yayi sata a gidan wani mai kuɗi, aka kamashi aka kaishi wurin "yan sanda, amma wai saboda san duniya na Alhaji sai mutumin ya bashi miliyan biyu tare da cewa ya ƙaryata zancen yayi sata,,,,, haka kuwa akayi,,, to wannan abunne yasa imam malik yayi masa nuni da bbu kyau,,,,,,,


shine yayi ta masifa, tare da cewa ya bar masa gidansa, dan shine ya haifishi ba imam malik bane ba ya haifeshi,,,,, to na tambaya ance man kusan sati biyu baije wurin aiki ba,,,,, yanxun hankalinsa ya tashi amma ya jawo abun ya haɗashi da usman,,,,,,


Amma kiyi haƙuri insha Allah idan na samu imam zanyi magana dashi,,,,, ajiyar zuciya raliya tayi sannan tayi godiya ta tafi,,,,,,,,,


lokacin da raliya ta iso ƙofar gida mutane ta gani cirko cirko a ƙofar gidan,,,, tamabayar ba,asi tayi da abinda ya tara su a wurin, ashe wai suwaiba ce ta siyar da gidan da sabon gidan da baba ya gama ginawa, 


wani irin dunƙulelen zagi raliya ta ciko bakinta da shi sannan taci gaba da zuzzungurawa uwar suwaiba,,, tare da cewa kawo kuɗin nan dan du.......bata ƙarasa ba, malam nuhu ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu,,,,,,, raliya sakin suwaiba tayi sannan malam nuhu ya matso kusa dasu sosai yace ke suwaiba kawo kuɗin nan, yaci gaba da cewa yama zakiyi haka?"" ki ɗauki gidan mutum kawai ki maka a kasuwa saboda wane dalili?""",,,, cikin masifa suwaiba tace gadon ɗana na fitar,,,,


Malam nuhu yace ai inace shi gado sai mutum ya mutu ko?""",,, suwaiba tace to bazan bayarba saidai a mutu ta tari lumfashin malam nuhu ba tare data barshi ya gama faɗar abinda yayi niyya ba,,,,,,,,,,, raliya ta kama suwaiba da kokowa,,,, fahat ya iso wurin tare da zare belt ɗin ƙugunshi yana cewa sakar min uwa tun kafin in lalata miki fata,,,,,, malam nuhu yace kai matar babanka zaka daka ne?""",,,,,


kallonshi fahat yayi sannan yace har kaima ɗin sai inci uwarka wallahi,,,,, idanuwa malam nuhu ya zaro tare da cewa ni fahat?"" ya nuna kanshi da hannu,,, fahat yace to dama akwai wani bayan ka?"",,,,, ajiyar zuciya malam nuhu yayi tare da cewa Allah ya sawaƙe,,,,,,, tsaki fahat yayi sannan yace umma muje,,,,,,


Sun juya har sun fara tafiya, malam nuhu yace kai fahat wallahi kaji tsoron Allah,,, mahaifinka wane irin gata ne bai nuna maka ba?"" amma yau shi yana cikin matsala da ƙunci na rayuwa ana neman yanda za,a fito dashi amma shine zaka kwashe dukiyarshi kace uwarka tazo ku tafi?"""",,,,,,


juyowa fahat yayi sannan yace uwarka ce na tafi da ita?""" baki malam nuhu ya saki tare da cewa Allah ya baka haƙuri,,,,,,,, fahat dafa kafaɗar suwaiba yayi sukayi tafiyarsu,,,,,,,


juyowar da raliya zatayi har an gama watso mata kayan ɗakinta a ƙofar gida an rufe gidan,,,,,, wani irin ihu raliya tayi tare da cewa kaiiiiiiiiiiiiiiiii, bazan yarda ba,,,,, sai kunci uwarku idan mai gida ya dawo,,,, ta sake fashewa da wani irin kuka mai jijjiga jiki,,,,,,,,,, haka malam nuhu yayi ta bata haƙuri , sannan yasa aka kwashe kayan nata suka nufi gidanshi,,,,,,,,,,,,,


Har dare yayi sosai imam malik bai dawo gidan ba,,,, hankalin sapna ya tashi sosai, gashi tun madarar daya bata tasha da safe har yanxun bata sake cin komai ba, haka ta gaji da jiransa taje ta kwanta tayi bacci,,,,,,,


Shi kuma bai dawo gida ba, sai wurin 12:09pm, haka ya shigo gidan a gajiye,,, da ledar kayan daya siyowa sapna,,,, bayan ya shiga, ya ajiye kayan sannan ya cire suite ɗin jikinshi ya ajiye, saman kujera ya zauna, yana ƙoƙarin kwanciya yaji kukan sapna,,,,,,,,,,,


yiiiiiiiii yiiiiiiii yiiiiiiiii, uhummm uhummm wayyo Allahna,,,,, mutuwa zanyi,,,,,,,, tashi tayi ta sauka daga saman gadon tare da fitowa farlo tana ci gaba da kuka,,,,,,,,,,, ta ɗora hannunta a saman idonta, tana ƙara kukan sosai har wata jiniya takeyi,,,,,, tana fitowa tayo inda yake zaune,,,,, ko kallon inda take baiyi ba,,,, ita kuma tana zuwa tace yunwa nakeji,,,,,,,,


ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa da sakata, tana ɗan turo bakinta,,,, tsaki yayi sannan yace to idan kinajin yunwa sai akayi me?""",,,,,, cikin hayani tace saika bani abinci inci,,,,,, kwanciya yayi a daidai lokacin da yake cewa idan kuma ban baki abinci ba sai miye zai faru?"""",,,,,,, dira ƙafarta ƙasa tayi sannan tace sai inyi tafiyata,,,,,,, yace dama wani yace dole sai kin zauna ne?""" a daidai lokacin da yake rufe idonshi tare da ɗora hannunshi saman goshi,,,,,,,,,,,,,

⚜ *BRELIANT WRITER"S ASSO* 🖊


*RASHIN RABO*


*MEELAT MUSA* 


*39-41*


***


*S*apna saida tasha kukanta ta gaji sannan ta tashi dan girka abincin da zasu ci,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,


Raliya ce,,, zaune a gaban malam nuhu tana cewa baba yanxun an samu dubu talatin da biyar, kallonta malam nuhu yayi sannan yace to Allah yasa a samu cikon tace amin,,,, niko nace lallai kuna da aiki a gabanku, mai neman 5million kuna maganar 35k?""",,,,,


Suwaiba kuwa tana can ta ɓalle bishasharta, tana jin daɗin duniyarta, kuma malam nuhu yaxo yayi juyin duniya ta rufa asiri tama bada kuɗin baba wanda ta siyar masa da gidaje amma tace bata san zancen ba,,,,,, don haka suka haƙura suka zubawa sarautar Allah ido,,,,,,,,,,


Sapna tana zaune a farlo tana jiran dawowar imam malik, tunani daban daban a cikin zuciyarta,,,, tana nan tana nazarin rayuwa taji shigowar shi,,,,,


Da sauri ta miƙe tayi wurinshi, amma batayi magana ba,,,, shi kuma raɓa ta yayi ya wuce derning area ya nufa, yana zuwa yaja kujera ya zauna,,,, cikin natsuwa sapna tayi wurinshi,,, tana zuwa kusa dashi tace kayi haƙuri, tayi maganar ne cikin sanyi, tare da langaɓe kanta tayi kalar ban tausayi,,,,, imam malik yayi kamar baiji ta ba,,,,,,,,,,


Ƙara gyara tsayuwarta tayi tare da ƙintsa bakinta,,,,, ta ƙara marairaice murya kamar mai shirinyin kuka tace, nasa maka abinci , gashi anan, ta nuna wurin da hannunta, sannan taci gaba da cewa kuma yau ban ƙona abincin ba, ko inda take bai kalla ba,,, murmushi tayi tare da ɗan ɗaga muryarta kaɗan tace,,,,,


Shima dankalin yau ban ƙonashi ba, hada doya na dafa maka, kuma na gasa maka ita da kyau,,,, ta ƙara maganar tana ƙara faɗaɗa murmushinta,,,,, idanuwanta a kanshi taci gaba da cewa kuma nima banci komai ba, a harzuƙe ya miƙe tare da ɗaga murya yace sai inyi me kenan?"" Eye?"" da sauri sapna taja baya tare da juyawa ta ruga ɗaki da gudu, tana zuwa saman gado ta faɗa tare da ƙara rushewa da kuka sosai,,,,,,, shi kuma komawa yayi ya zauna, 


Yana nan wurin zaune, har yayi ɗan baccinsa ya farka, amma bai dainajin kukan sapna ba,,, miƙewa yayi ya nufi toilet, bai wani daɗe ba ya fito,,,,,,,,


Inda sapna ta ajiye abincin yaje ya ɗauka filet ya zuwa dan kali ya nufi ɗakinta,,,, yana shiga ya kunna fitilar ɗakin haske ya bayyana cikin ɗakin,, da sauri ta kalli bakin ƙofa, ganin imam malik tsaye da filet yasa ta tashi da sauri, ta zauna,,,,,


Shiga yayi, a bakin gado ya zauna, da sauri sapna ta nannaɗe ƙafafuwanta tare da jawo filo ta ɗora a saman ƙafarta, shi kuma kallonta yayi sannan ya ɗauki dankali ɗaya , da sauri sapna ta gyara bakinta, tana ƙara masawa kusa dashi sosai,,,,, bakinta ya nufa da dankali da sauri ta ƙara yage bakin kamar mage taga ɓera,,,,,,


Da sauri ya janye hannunshi ya nufi bakinshi da dankalin ya cinye,,,,, miƙewa tsaye yayi yana dariya, da kallo sapna ta bishi itama dariyar takeyi, dan tunda ta haɗu da imam malik ko murmushi bata taɓa ganin yayi ba, haka yaci gaba da dariya sosai, har jikinshi yana jijjigawa,,,,,,, itama dariya takeyi sosai,,,,,,,,, a hankali ya fara haɗe ransa har fuskarshi ta koma kamar wanda bai taɓa sanin miye dariya ba,,,,,, taɓe baki sapna tayi itama ta gyara bakinta,,, cikin sansanyar murya, tace,,,,


 miyasa ka daina dariya ne?"" yi dariya, tana yi tana kaɗa kanta, alamar yayi, taci gaba da cewa dariya tana maka kyau, don Allah kayi , yi mana,,,,,, kallonta yayi sannan ya ajiye filet ɗin yabar ɗakin,,,,,, yana fita sapna tayi murmushi tare da kwanciya, ta miƙe ƙafafuwanta, tare da buɗe hannuwanta, fuskarta tana kallon silin ɗin ɗakin,,,,,, taci gaba da tunanin imam malik, dariyar sa taci gaba da dawo mata a zuciyarta, har tayi bacci,,,,,


Raliya ce a gidan su imam malik, sai haɗa hajiyarsu take da Allah tasa baki Alhaji ya sake mai gida,,,,,, hajiya tace kiyi haƙuri wallahi nayi maganar nayi magiyar nayi juyin duniyar nan amma yaƙi saurarana,,,,, amma nayi maki alƙawari idan har imam malik yazo wallahi sai usman ya fito, taci gaba da cewa kiyi haƙuri ki koma gida, ki daina wannan ziyar ki kwantar da hankali,,,,,,,, haka dai tayi ta bawa raliya haƙuri, raliya tayi godiya sannan tayi ma hajiya sallama ta tafi gida,,,,,,,,,,,


Zaune yake yana karatun alkur,ani, ita kuma fitowa tayi daga ɗaki tare da cewa don Allah muje yanxun nan zan dawo wani abu kawai zan siyo sai mu dawo ,,,,,,, baiyi magana ba yaci gaba da karatunshi,,,,,,


sapna wuri ta samu ta zauna,,, har imam malik ya gama, ya rufe alkur'ani yaje ya mayar dashi inda yake ajiyewa sannan yace muje,,,,, da sauri ta miƙe tabi bayanshi,,,,,,,,


Tafiya sukeyi a ƙasa amma babu wani wanda yake magana wa ɗan uwansa,,,,, har suka isa bakin wata super market, imam malik yace jirani anan ina ina zuwa,,,, yana faɗin haka yayi ciki,,,,,,


sapna tana nan tsaye harta gaji da tsayuwa ta ɗan leƙa, tana ganin imam malik ta ɗaga masa hannu, kallonta imam malik yayi tare dayin murmushi kaɗan, itama murmushin tayi tare da matsawa daga wurin,,,,,,


tana nan wurin tsaye , wani mutum yazo kusa da ita, yace don Allah malama kina da waya ne?"",,, sapna batayi magana ba, ta girgiza kanta alamar A,a dariya yayi tare da cewa duk kyawunki?"" yanda kike ɗin nan baki da waya?,,, yanda yayi abin ya bata dariya, don haka gaba ɗayansu sukayi ta dariya sosai,, daga ciki ya hangosu don haka ya fito,, rai a ɓace ya iso wurin ba tare sa yayi magana ba, yace ja hannun sapna, saida suka matsa sannan yace,,,,,


Cikin hayani da ɗaga murya yace shin banyi maki kashedi ba?""",,, kallonsa sapna tayi sannan itama tayi magana cikin ɗaga murya tace towai miye matsalar ka?"" kawai fa cewa yayi ina da waya?""",,,,,


Nuna ta yayi da yatsansa tare da cewa daga yau kuma bana san jin gatsala daga gareki, idan kuma kikaci gaba dayin haka toufa bazanci gaba da zama dake ba, cikin sanyin jiki tace tom, yace zanje in dawo nan da minti biyar kada ki sake ki motsa daga nan, tace tom,,, tsaki yayi sannan ya juya ya koma ciki,,,,,,,,,


Bayan ya gama abinda yake ya fito,,,, hankalinsa ya tashi ganin baiga sapna,,  da sauri ya fara tambayar mutane wata yarinya mai kaza mai kalar kaza da kaza basu ganta ba?"",,,,,, kowa yace bai gani ba, haka imam malik yayi ta neman sapna, hankalinshi ya tashi sosai, duk inda yaga mace sai yaje ya dubata,,,,,,, har yamma lisss imam bai koma gida ba, neman sapna yake yi,,,,,


Saida yayi magrib da isha'i sannan ya haƙura ya tafi gida,,,,, yana zuwa ya kulle ƙofa ya shiga cikin gida jiki a saɓule,,,, bayan ya shiga farlo, har zai zauna yajiyota tana "yar waƙa,,,,, da sauri ya nufi ɗakin,,,,, yana zuwa ya ganta kwance ,,,,,, ita kuma ko inda yake bata kalla ba, ta kuma kame bakinta tayi shiru tare da ɗaure fuskarta tamau,,,,, kamar mai shirin kai hari,,,


Kallonta yayi sannan yace ke wai mina faɗa mike ne?"",,,, yaci gaba da cewa ba nace  karki bar wurin nan ba?"" miyasa kika bar can?""" Iye?"" cikin ɗaga murya yace bakyaji na ina magana ne?"",,,, kin ɗauka ni shashasha ne?"" ba inda banje ba ina ta nemanki"""


ganin sapna bata da niyar magana yasa ya fita yabar ɗakin,,, yana fita kicin yaje ya ɗauko madarar sa, da kofi , ya dawo farlo,,,,, zama yayi tare da buɗe madarar ya zuba a kofi, ya ɗaga zaisha yaga sapna tsaye a gabanshi sai faman gyara riga takeyi,,,,,,,,


Ɗaure fuska yayi tare da ɗaga kofin yakai bakishi, murmushi sapna tayi sannan tace ina sanka,,,,,,, da sauri imam malik ya feso madarar daya kai bakinshi dan kalamin da sapna ta faɗa ya hana madarar shiga cikin maƙoshinshi bare ta samu damar isa ga "yan hanjin sa,,,,,, yana gama watso da madarar ya riƙe bakinshi tare da kallon sapna,,,,,,,,, itama shi take kallo tare da ƙara gyara tsayuwarta,,,,,,


taci gaba da cewa gaskiya nake gaya maka, na faɗa sanka, da gaske, wani irin kallo imam malik yayi mata mai haɗe da harara, ita kuma taci gaba da cewa da fari zuciyata ce ta sanar min,, shine nima yanxun nace bara in sanar dakai,,,,,,


Yace ke, tare da yi mata wani irin kallo,,,, yace da alamu kanki ya kwance, murmushi sapna tayi tare da cewa ko kusa wallahi amma tabbas wani abu yana faru dani, komi ba yanda ya saba faruwa ba, idan kai nisa dani sai inji ina so ka dawo, idan kuma kana kusa dani sai kawai inji cikina yana man wani iri,,, ta ƙara murmushi tare da nuna mashi cikin tana yawo da hannunta saman ciki, taci gaba da cewa kawai dan daɗi,,,, 


kawai nayi tunani akai cikin natsuwa, nayi ta nunani harsai da kwakwalwata ta daina tunani ma gaba ɗaya, a wannan lokacin ne zuciyata ta gaya man kawai sanka takeyi,,,, kuma sannan kaima kana sona,,,,,, yace ke kinga, da sauri itama tace kaga, tare da matsawa kusa dashi sosai kamar zata shige cikin cikinshi, sannan ta sassauta muryarta, tare da cewa ni ba shashasha bace, miyasa ka gwada kishinka akaina lokacin da kaga ina magana da wani?"",,, kuma lokacin daka fito baka sameni ba miyasa baka taho gida ba?"",,,, amma sai ka tafi nema na""",,,,, kuma lokacin da kake nema na baka sameni ba miyasa hankalinka ya tashi?"",,,, miyasa kake ta ƙoƙarin nema na?"",,,,,  baka so kaga ina magana da wani, riƙe ƙugunta tayi tare da ƙara tausasa muryarta tace idan kuma bama tare hankalinka ya tashi,,,,,,,


dariya tayi sanna ta ɗan ja baya kaɗan, ta ƙara ƙasa da muryarta sosai, sannan tace idan ba so bane haka miye?"",,,,,, imam malik yace kar kiman shirme anan, tace ba shirme bane , bakai kace man in karɓi rayuwa duk yanda ta bani ba?"",,,,, to rayuwa ta bani kai, kuma tafiyar da nayi ai ba fita nayi daga rayuwarka ba, naje na siyo maka wata kyauta ne, in kawo maka?"" ta yage baki tana dariya,,,,, baiyi magana ba, dan haka ta juya da gudu tayi ɗaki,,,,,,,,,,,,,,,

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻


💦💦💦💦

*RASHIN RABO*

💦💦💦💦


*R🅰SHIN R🅰BO*


*MEELAT MUSA*


*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP zaku nema a shafinmu na facebook domin samun littattafanmu*


*36-38*


***


*Ƙ*ara matsawa sapna tayi kusa dashi sosai sannan tace zanfa tafiii,,,,,,,,, tayi maganar cikin jan faɗa ne,,,,, shiru yayi kamar baiji abinda tace ba,,,,,,,


Tafiya ta farayi tana cewa rigar sanyin ka fa?"" ko ka barmin ne?"" taci gaba da cewa kada in tafi kuma kayi kuka,,,,,,, kace dama ban tafar maka da kayarka ba,,,,,, ganin baiyi magana ba, yasa ta dawo ta sake matsawa kusa dashi tace kai wallahi yunwa nakeji sosai,,,,,,,,,


Taci gaba da cewa kace baka san surutu wai magana na yayi yawa kuma idan nayi magana kaɗan baka fahimta ta, ta ƙarasa maganar ne cikin yanayi damuwa,,,,,, ba tare daya buɗe idonshi ba yace to a ina za,a samu abinci a tsohon daren nan,,,, riƙe cikinta tayi tare da cewa ka taimaka man wallahi zan iya mutuwa,,,,


Tsaki yayi sannan yace akwai madara kije kisha,,,, a zuciye ta tashi tana cewa komai madara madara,,,,, ni anan zan zauna inyi ta shan madara sai kace wata jaririya?""",,,,,,, buɗe idonshi yayi ya sauke su a kanta,,,,,,, murmushi tayi sannan tayi magana a nutse tace ai idan ka matsa zansha madarar kawai dama nafi san madarar ma,,,,,,, juyawa tayi , ta nufi firij ta ɗauka madarar tasha sannan ta wuce ciki ba tare da ta sake cewa komai ba, tana shiga ɗaki ta kwanta, sai tsaki takeyi,,,,,,,


Da safe sapna, lokacin data fito imam malik harya kusa fita daga cikin farlon,,, da sauri tace kai ji mana,,,,,,, tsayawa yayi ba tare daya juyo ba,,,,, tafiya tayi taje tasha gaban shi tare da cewa ina kuma zakaje?"",,, baiyi magana ba,,, taci gaba da cewa to ai yanxun sai muje kasuwa mu siyo kayan abinci,,,,,,,,,


Bayan kasan babu komai a gidan nan kuma shine zaka wani saka kai ka fice?""",,,,, to muje zan faɗa duk abinda muke buƙata a gidan a siyo, ni banyi karatun boko ba ai dana tsara dukan jaddawalin a takarda,,,,,


Muje zan faɗi komai nasan abinda muke buƙata, kayan kicin da kuma kayan abinci,,,, cike da izza yayi magana cewa kije kiyi sayayyarki ni yanxun fita zanyi,,,,,, cikin faɗa ta ɗaga murya tare da cewa ai haka babu adalci bari in faɗa maka kaima fa zaune kake a cikin gidan nan, ta nuna gidan da hannunta,  cire glass ɗin idonshi yayi da sauri tace iye,,,, cikin sanyi murya tayi magana ,,,


Idan ka matsa sai inje niɗayanma, kawai dai banda gogewa ne, akan sayayya, biredi kwai madara wannan suna da sauƙi, amma magana ta gaskiya ka kawoni gida wanda babu komai a ciki, taya za,ayi ƙaramar yarinya kamarni, wacce bata da ƙarfi zata kinkimi duk wa'annan abubuwan?"" tana maganarne cikin sigar lallashi, ta ƙarasa maganar da cewa yi magana, tanayin maganar tana ɗaga kanta kamar wata ƙadangare tare  taci gaba da cewa cene wani abu mana, yi magana,,,, maida glass ɗinshi yayi a idonshi sannan yace kije ga leda acan ya nuna da hannunshi, akwai hijabi a ciki ɗauko kizo muje,,,,,,,


da gudu ta isa wurin ta buɗe tana ɗaukar hijabi ya saka kusa dashi taje tayi tsaye sai murmushi takeyi tace na saka,,,,, ba tare daya kalleta ba yace muje, shine yayi gaba ita kuma tabi bayanshi,,,,,,,,,


A wurin siyayyar da sukaje duk abinda sapna tace shi za,ayi siya imam malik saida yabi ta da ido,,,,, haka tayi ta jibgar kaya,,, shidai kallonta kawai yakeyi,,, saida ta gama sannan tace an gama ɗan uwa,,,, kallonta yayi sannan yace haka ya maki?"",,,,, tace Eyy yace kin tabbata?"" tace Eyyy, yace to da kyau,,, kuɗi da yawa imam malik ya biya, sannan suka tattaro sukayo gida,,,,,,


haka suka shigo gidan sapna tana gaba da kaya a hannunta shima yana bayanta da kaya,,, da ƙafarta ta harba ƙofar ɗakin ya buɗe ta shiga,,, tana cewa ka kira mai gyaran wuta zai gyara mana fanka famfunan ban ɗaki basa kawo ruwa, towai duk ma waye zaiyi wannan aikin ne?""" ni wallahi har kaina ma ya fara ciwo, gaskiya saidai a raba aikin nan,,, ni zan gyara kicin kai kuma kaje ka gyara farlo ka wanke toilet da gyaran bedroom,,,,,,


lallaɓawa imam malik yayi ya ajiye kayan sannan ya juya da sauri ya fice daga farlon,,,,, ita kuma zama tayi tana ci gaba da cewa wai baka ji ina magane?""" adaidai lokacin data juyo,, tsaki tayi tare da cewa ya ɓace abinsa,,,, tsaki tayi ta tashi taci gaba da aiki bbu ji bbu gani,,,,,


Suwaiba da fahat kuwa gida sukaje suka siya mai kyau, sannan ta tattala wani abun ta bawa fahat dan komawa makaranta,,,,,,,,,


raliya kuwa zaman ta a gidan malam nuhu lafiya qalau amma duk tabi ta fige ta lalace ta fita hayyacinta kwata kwata,,,, kullum tana zarya gidan Alhaji Abu, tun yana zaginta har ya gaji ya daina,,,,, amma har yanxun babu wanda yasan ina usman yake,,,, kuma babu wanda ya gansa,,,,,,,


Sapna kuwa bayan ta gama gyara gidan nan, tayi abinci, wanka taje tayi sannan tasa kayan da imam malik ya kawo mata, ta kame saman kujera tana jiran dawowarshi,,,,,,


tana nan zaune farlo ta fara ɗan gyangyaɗi taji shigowarsa don haka da sauri ta miƙe tayi wurinsa,,,,,,, tana cewa yawwa ka dawo?""" da kyau!"""  tana maganar ne tana ƙara faɗaɗa murmushinta,,,,,,


Taci gaba da cewa kawai ka tafi ka barni nayi ta fama da aiki, ni kaɗai,, kallonta yayi sannan yace to duk waye yasaki wannan aikin ne?"",,  cikin faɗa kamar zata kai mashi duka tace haka ma zakace?""" to idan ban gyara ba ka faɗa man a ina zaka zauna kaci abinci ne?""ɗaure fuska yayi, ita kuma dariya tayi tare da cewa ka gane?""" yau ɗin nan na girka maka abinci ga ɗumi ga daɗi a shirye yake , kaje kayi wanka ina jiranka a tebirin cin abinci,,, juyawa yayi ya tafi ba tare da yayi mata magana ba,,,, taɓe baki tayi tare da cewa bazai canja ba,,,,,,


tana nan zaune ya fito daga toilet da towel a hannunsa yana goge hannunshi dashi,,,, ita kuma tana zaune wurin derning ɗin sai ɗan gunguni takeyi,,,, bayan yazo ya zauna tayi murmushi tare da cewa yau gaba ɗaya zuciyata na saka a cikin girkin nan,,,, miƙewa tsaye tayi taci gaba da cewa idan kaci tou pha lallai saika tanɗe hannu tana maganar ne cikin sakata dan sangarci,, shidai binta yayi da kallo danshi ba mutum bane mai magana kuma haka bayasan surutu sosai,,,,,,,,


Ita kuma ta dage taci gaba da cewa yau idan kaci abincin nan tou pha lallai sai kayi santi,, a daidai lokacin data fara buɗe abincin, shinkaface ta dafa amma gaba ɗaya duk ta babbake, zuba mashi tayi tare da taɓe bakinta tace kayi haƙuri shinkafar ta ɗan ƙone ne,,,,,,,,,


Baiyi magana ba,,,, rufe shinkafar tayi tare da cewa to kaci dankali mana, ai dankali yana da daɗi,,, a daidai lokacin data fara zuba mashi,,, ƙyafta ido ta farayi tana cewa kayi haƙuri wallahi shima dai dankalin yaɗan samu ƙonewa , kallonshi tayi shima ita yake kallo,,,,,,  


Cikin tsoro tace kayi haƙuri don Allah wallahi sabon kaskone shi yasa aka samu matsala, amma kaci bbu wani damuwa nima naci kuma akwai daɗi, ta ƙarasa maganar tana mashi murmushi,,,,,,,


Tsaki yayi sannan yaja flet ɗin a gabanshi ya fara cin dankalin,,,,kana ganin yanda yake ci kasan dole tasa saboda kwata kwata bbu daɗi , kuma baiyi ba ma,,,,, a hankali ta zauna tayi tagumi tare da zubawa imam malik idanuwa,,,,,,, tausayinshi ya kamata ta fara hawaye dan lallai tasan tayi mashi ɓarnar abinci amma yayi haƙuri, da babanta ne da yana nan ya fara ɓaɓatu, amma shi yayi haƙuri ko babu daɗi ɗin baice komai ba,,, kuma yaci dan taji daɗi,,,,, tashi tayi ta barshi a wurin tare da cewa idan ka gama ka wanke kwanukan danni nayi nawa aikin da rana,,,,,,


tana shiga ɗaki ta haye gado tayi kwanciyarta,,,, shi kuma ganin ta tashi yasa ya nufi toilet yayi ta kwarara amai,,,,, saida ya gama sannan ya wanke bakinshi ya yazo ya kwanta a wahalce,,,,,, danshi ba ma,aboci cin wani abinci mai nauhi bane,,,, dan daga madara hollandia sai lipton zaiyi wahala yaci abinci mai nauhi sosai,, dan baida lafiyayar ciki,,,,,,


Tunda safe sapna ta fito, tayi "yan aikace aikacenta,,, bayan ta gama ta gayara duk inda ya kamata, 


shi kuma fitowa yayi da sauri ya fito cikin shiga mai kyau da kama hankali,,,, sauri yake sosai dan akwai idan zaije anyi masa waya,,,, inda ya ajiye bindungunshi ya nufa ya ɗauka, amma sai yaga wurin wayam,,,,,


gabanshi ne ya faɗi sosai,,, da sauri ya ƙara ɗagawa amma fa lallai babu, da sauri ya juya zuwa bedroom ɗin sapna, amma sai ya jiyota a toilet tana waƙa,,,,, dan haka da saurin shi ya nufi toilet ɗin tare da cewa kinga binduguna?"" yana maganar ne cikin nuna tsananin damuwar sa,, dariya tayi sannan tayi magana cikin shagwaɓa tace bindugunka?"" gasu nan ina wanke , taci gaba da cewa naga sunyi datti ne, da alama kayi shekaru masu yawa baka wanke su ba ko?""" da sauri ya shiga cikin toilet ɗin cikin hayani da magana mai tada hankali dasa furgici sosai yace baki da hankali ne?"""" yaci gaba da cewa baki san akwai banbanci tsakanin bindigogi da kaya ba?"" yana maganar ne yana nuna ta da ya tsanashi gaba ɗaya imam malik ya fita hayyacinsa,,,, idanuwanshi sun rikiɗa sun koma zuwa launin ja,,,,, 


Ganin yanda yayi yasa sapna miƙewa da sauri ta fara ja da baya tana kuka,,,,,,, cikin kuka tace miyasa kake fushi haka sosai?"",,, tana maganarne tare da ƙara kuka mai tsanani,,,


Ƙara ɗaga murya imam malik yayi cikin tsananin ɓacin rai yace kin lalata man bindugogi, kusa da ita ya matsa sosai lokaci guda jikin sapna ya fara kyarma,,,,, shi kuma cikin nuna tsananin ɓacin rai yace shin ban faɗa maki cewa ba, abinda nace kiyi shine zakiyi?"" bawai kiyi amfani da kwalwarki ba, yana maganar yana nunata da yatsanshi yana cije haƙoranshi tare da ɗage laɓɓansa,,,, da sauro sapna ta ƙara ja baya, shima matsawa yayi kusa da ita sosai sannan ya fizgota ya ɗaga hannunshi ya kwarara mata mari,,, wani irin ihu ta saki tare da dire dire saboda marin ɗan sanda akwai zafi,,,,,, ba irin na baba bane,,,,,,,,,


Ya ɗaga hannunshi ya ƙara marinta kuma ko miye ya tuna ??"""" Oho dunƙule hannunsa yayi tare da kaiwa ƙofar toilet duka, da sauri ya fita yabar farlon,,,, ita kuwa sapna kuka taci gaba da yi,,,,,, tare da kuɗirin fasa mashi kai da bindiga idan ya dawo,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

⚜ *BRILLIANT WRITER'S ASSO* 🖊


*Je suis fier BRILLIANT WRITER'S ASSO Nous aimons nos fans où qu'ils soient Adorons tous fans* ❤


*RASHIN RABO*


*MEELAT MUSA*


*42-44*


***


*T*sayuwa imam malik yayi yana jiran fitowar sapna,,,, da gudu ta fito daga ɗaki ta ɓoye hannuwanta a baya, sai yashe baki takeyi tana dariya,,,,,,,,,,


Kallonta kawai yakeyi amma baiyi magana ba kuma baya murmushi,,, saida tazo gabanshi ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya,,,,, cikin shashsheka irin ta wanda yayi ɗan gudu tace ɗan uwa tayi maganar cikin sakinta baki ɗaya ne, sannan tayi ajiyar zuciya, tace in baka ne?"",,,,,  tayi maganar tare da ɗaga kanta alamar tambaya,,,,,,?


Ɗaga mata kai kawai yayi alamar Eh,,, da sauri ta fiddo hannuwan gabanshi tare da cewa kaga wannan rigar wallahi zata maka kyau, ta ƙarasa maganar tare da ɗaga mashi gira ɗaya tana murmushi,,,,


Baiyi magana ba ya ansa,,, ɗaga rigar yayi ya kalleta sosai sannan ya kalli sapna, murmushi tayi tana ƙara matsawa kusa dashi tana cewa ka saka mana, saka zata maka kyau,,,,,,,,,,,,,, tsaki yayi tare da ɗora rigar saman kujera yace ke bana so, lokaci ɗaya ta ɗauke dariyarta, tare da ƙimtsa bakinta,, ɗaukar rigar tayi ta riƙe a hannunta sannan tace miyasa baka so?""",,,, baiyi magana ba, ya koma ya zauna, madararshi ya ɗauka yaci gaba da sha,,,,,,,,


Murmushin ƙarfin hali sapna tayi sannan tace to babu damuwa,,,, na gode sosai,,,,, ɗaki ta nufa da rigar a hannunta, tana zuwa a bakin gado ta zauna tare da yin tagumi, a zuciyarta tace lallai safeena kinyi hauka, waye yace maki ana faɗawa namiji ana sansa?""",,,,, haƙiƙa kinyi yarinta sosai,,,, wata zuciyar tace kije kice mashi bakya sanshi,,,,, tashi maza kije safeena danma kada yayi tunanin wani abu,,,,, wani irin kuka ya kwacewa sapna da sauri ta rufe bakinta tare da silalewa saman gado ta kwanta,,,,, tanajin wani iri a zuciyarta,,,,, haka tayi ta kukanta har bacci ya ɗauketa,,,,,,,


Yana gama shan madararshi tashi yayi ya nufi toilet, alwallah yayi yazo yaci gaba da sallah,,,,,,,,,,,,,,,


Alhaji don girman Allah kayi haƙuri kayi ma zumunci ka saki ɗan uwanka,,,, kasa shi cikin bala"i, ka hana mashi zaman lafiya dashi da ahalinsa, wannan ɗaukar alhakine,,,, kayi haƙuri ka barshi don Allah,,,,,, ina tsoron maka alhaki ne da kuma faɗawa a cikin fushin ubangiji saboda girma da daraja da yake a cikin zumici, ka rasa wanda zaka ƙuntatama sai ɗan uwanka uwa ɗaya uba ɗaya, wannan wane iri ci baya ne?"""",,,,,,,  gashi yanxun matarshi ta tattara mashi dukan gidaje ta siyar, ɗiyarsa ta tafi duniya, ɗansa dayake taƙama dashi ya juya mashi baya, kayi haƙuri ka sakeshi don Allah ko zai samu natsuwa,,,,,,,,


Wani irin wulaƙantaccen kallo Alhaji Abu yayi mata tare da cewa daga yau idan kika sake sako ma mutane wannan sakaran bakin naki zaki fuskanci fushi na,,,, a sanyaye tace Allah ya baka haƙuri,,,, yaci gaba da cewa kuma na rantse da Allah idan imam malik bai dawo gida ba, to ki tabbatar kema zaman gidan nan ya ƙare a wurinki,,, saboda na lura duk kece munafikar , murmushi tayi tare da cewa ka kirashi mana ai kana da numbershi, daga haka bata sake magana ba ta fice daga ɗakin,,,,,


Da sauri ta fito daga cikin ɗaki riƙe da rigar data siyo mashi a hannuta,,, inda yake kwance taje wurin taga bacci yakeyi, da sauri ta duƙa kusa dashi tana kallonshi,,,,,,, hannunta, ta sa daidai idonshi tana ɗan yawo dashi don ta tabbatar bacci yakeyi,,,,, taga baiyi motsi ba,,,, da sauri ta miƙe ta nufi hanyar fita,,, harta taɓa ƙofa taji yace ina zakije ?""""",,,,,,,,,,,,, juyowa tayi tana kallon cikin farlon inda yake kwance ta kalla amma da mamaki taga bacci yakeyi,,,,, tana tunani taji yace bakiji ina magana ne?"",,,,,, ina zakije ne?"",,,,, cikin tsiwa tace zan tafi kawai,,,, murmushi yayi sannan yace kada ki tafi dawo, sapna tace bazan dawo ba, a daidai lokacin data buɗe ƙofar ta fice,,,, da sauri, shima da sauri ya sauka daga saman kujera, yabi bayan sapna da gudu,,,,,,,


Itama ɓarke tayo cikin gida, tana ihu,, da imam malik taci karo,,,, a firgice ta kalli imam malik tana kuka,, riƙeta yayi shima ita yake kallo, tare da tambayarta miye?""" jin muryar Alhaji Abu yayi yace ubanka ne,,,,,,, idanuwa imam malik ya zaro tare da mamakin ya akayi yazo nan,,,,,, dakewa yayi tare da cewa dady miye?"",,, ita kuwa sapna jikinta banda kyarma babu abinda yake yi, sai kuka takeyi,,,,,,,,,,, da hannun damarshi yaja sapna jikinshi ya riƙeta sosai tare da cewa waye ya dakeki?""",,,,,


Cikin ɓacin rai Alhaji Abu yace imam malik ka bani mamaki kuma kaji kunya kaci baya kayi asara,,, shashasha sakaran banza da saboda wannan jakar yarinyar kazo ka tare a gidan aboki?""",,,, kallarta mi gareta, mata masu aji da kamun kai duk baka gansu ba sai wannan ?""" ya nuna sapna da hannunshi,,,,,, tare da ci gaba da cewa duk ta gama balbaɗewa a titi da sauri imam malik ya runtse idanuwanshi tare da kauda kanshi daga kallon dady,,,,,, dady yaci gaba da cewa saida maza sukayi gwanjonta da yake kai mahaucine zaka shigo da ita cikin rayuwarka?"""",,,,,,,


A hankali imam malik ya buɗe idonshi ya kalli dady,,,,, saida yayi kusan minti biyar yana kallonshi,,,, shima dady kallon imam malik yakeyi, cikin sanyi yace dady ina kasanta ne?""" imam malik ne yake tambayawa dadyn sa,,,,,, cikin hayani dady yace kaima kasanta dan uwarka,,,, imam malik ya kalli da sapna dake kwance saman jikinshi ta rufe idanuwanta sai hawaye ki zubowa,,,,,, sannan ya kalli dady, yace wallahi bansanta ba,,,,,,, dady yace ɗiyar usman ce,,,,, imam malik yace waye shi?""",,,, danshi bai wani san usman ba,,,,,,, dady yace wannan wanda banso,,,, imam malik yace kaima kasanshi dady aini ban san kowa ba,,,,,,


dady yace to bana santa jiya dakel nayi bacci saboda tsananin tashin hankali ance man kana tare da ita,,,, imam malik ya kalli dady tare da taɓe baki yace to dady ni ina ruwana da ita?"",,, babu wani abu kawai tana yin bacci a ɗaki, ni kuma ina kwanciya a saman kujera ba wani komai akeyi ba,,,,, dady yace ai kai sakaraine,,,, murmushi imam malik yayi tare da janye sapna daga jikinshi,,,,, dady yace kuma duk abinda kakeyi yau kaje office sannan wannan yarinyar ta kama gabanta,,,,,,,,


kallonta imam malik yayi sannan yace toke kinji wai dady yace ki tafi,,,,,,, dady yace saima ka faɗa mata?"" ai tajini dan uwarta,,, ya daddanna mata zagi,,, imam malik yace bana san kana zagi kuma bana san kana mata magana mai muni,,,, waishin jira ma dady ita kuma mi tayi maka ne?""",,,,,


babu abinda taman bansan ta ne kawai saboda bana san ubanta,,,,,,,, imam malik yace ashe ko babu komawa gida?"",,,, dady yace miyasa?"" imam malik yace dan gaskiya bazan tafi in barta ba,, kawai zanje Office anjima, amma bazan dawo gida ba, dady yace saboda mi?"",,,, inda sapna take tsaye ya kalla tare da cewa saboda '"safeenah'" dady yace safina ɗin uwarka ce?"",,, mu ba barinmu kayi a gida yazo nan ba?"",,,, saida nasha wahala sannan na sameka, to barima kaji in faɗa maka wannan yarinyar dole saika barta tunda ba tare aka haifeku ba,,,,,,,


Juyawa imam malik yayi tare da jan hannun sapna suka koma ciki,,, binsu dady yayi shima ya shiga ciki, tare da ci gaba da faɗa,,,, har yanzun imam malik yana riƙe da hannun sapna,,, sai janta yake yana matsawa yana haɗa kayanshi da hannu ɗaya,,,,,,,,,


Dady yace ina zakaje ne?"",,,, imam malik baiyi magana ba, yaci gaba da haɗa kayanshi,, yana gamawa ya ɗauki kayanshi tare da jan hannun sapna zai fita dady ya riƙeshi,,,, yace ina zakaje ne?"",,,, kallon dady yayi sannan yace gidansu zamu koma,,, dady yace ban gane ba,,, imam malik bai sake magana ba, yaja sapna suka fice, cikin tashin hankali dady yabishi yana kiran sunan shi dan dady bai haɗa imam malik da kowa ba,,,,


yana fita ya riƙe imam malik, sannan yace jira, tsayuwa yayi, dady yace naji ba komai ku tafi gida,,, murmushi imam malik yayi , amma baiyi magana ba, yaja sapna suka fita daga gidan,,,, suna fita dady yace kaci uwaka, ka kaita gidan nawa ni kuma zan kaita can inda na kulle ubanta,


Hh dady baisan imam malik yafi shi sheganta ba, suna fita, suka hau napep, sapna sai kuka takeyi, shidai bai iya bada haƙuri ba don haka ya basar da lamarinta,,, kuka takeyi sosai,, amma imam malik bai sake kallonta ba,,,,, har suka isa inda zasu je, bayan sun sauka napep ne, suka fita, imam malik ya kalli sapna yace da Allah kiyi ma mutane shiru ni wallahi bana san kuka,,,,,


Tsaki yayi tare da fiddo wayarsa daga aljihunshi ya fara latsawa tare da karata a kunnenshi, yawwa ina ƙofar gidanka, okey, munajiranka, bayan ya gama wayar ya mayar aljihunsa, ya kalli sapna yace kada kije ko ina, ki zaki zauna a gidan nan wurin matar abokina zanje office idan na gama abinda nake zan dawo anjima kinji?"",,,, sapna tace Ey, imam malik yace nadai faɗa maki, wallahi wannan karon idan kikaman yarinta, to ɗinki, sapna tace tom,,,


suna nan tsaye yana ƙara jawa sapna kunne har abokin nasa ya fito, bayan sun gaisa ne imam malik yace gata nan, ko dady yace maka tana nan kace A, a, idan ance taxo kada ka bari tazo sai ka ganni da idonka sannan ,, yace to ranka ya daɗe, imam malik yace amma fa idan ka bari ta tafi tou fa gaskiya akwai matsala,,, yace insha Allah baza a samu matsala ba,,,, kallon sapna yayi sannan yace saina dawo,,, batayi magana ba, imam malik ya juya yayi tafiyarshi,,,,


bayan sun shiga cikin gidan matar Aliyu tayi ma sapna tarba mai kyau, ta kawo mata abin kalaci , amma sapna bataci komai ba,,,, haka hadiza tayi juyin duniya amma sapna taki yadda taci komai,,, haka ta haƙura ta kwashe komai nata tayi waje dashi,,,,,,


Imam malik yana tafi gidansu yaje, a gaggauce yayi wanka ya shirya cikin uniform ɗinshi, yayi matuƙaryin kyau sosai dan karuwun jiki imam malik yake dashi duk abinda ya saka sai ya mashi kyau,, yana fitowa motarshi ya ɗauka ya nufi Office,,,,,,,,


Alhaji Abu ne yake waya da gidi, cewa safeena fa tana gidanshi, don haka yanxun ya samu ya tura imam malik office suje su kama banza suje su jefar da ita, gidi yace "yar laiɓai ka rufa man asiri kasan halin imam malik,tunda ya shigo ciki nidai wannan aikin gaskiya bazan iya ba,,,, Alhaji Abu yace zan baka kuɗi masu yawa, ku kamata dan ku fitar man ita daga cikin rayuwar ɗana,,,, koma kashe banza kukayi nifa banajin komai,,,,, gidi yace gaskiya nida bazan iya ba,,,,,, yana faɗin haka ya kashe wayarshi tare da mitar cewa haka kawai kaje ka kaimu ka baro, shima uban nata sakinshi zanyi dan ɗiyar tana faɗawa imam lallai kashin kowa ya bushe,,,,,,,


yana tashi daga Office yayo gidan Aliyu tun kafin ya iso yayi waya cewa safeena ta fito,,,, Aliyu yace to ,,,, bayan imam malik ya iso ne, ya ɗauki sapna a motar ,,,,,,


Bayan sun fara tafiya ta fara kuka wai ita yunwa takeji, ko jiya da daddare bataci abinci ba,,,,, da wutsiyar idonshi ya kalleta amma baiyi magana ba,,,,, ita kuma taci gaba da surutu kamar radio taji sabon batiri,,,,,,


Haka tayi ta surutu, wani yayi murmushi wani kuma ya basar,,,,, tace nifa abinci zanci,,, yace babu abinci fa sai madara idan zakisha,,,,,, shiru tayi bata sake magana ba,,,,,,


Saida yayi tafiya sosai sannan ya tsaya wurin wani siyar da abinci,,,, yasa aka kawo mata abincin sannan suka tafi, a mota take cin abinci tana ci gaba da surutu,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,


⚜ *B. W. A* 🖊

⚜ *BRILLIANT WRITER'S ASSO* 🖊


*Je suis fier BRILLIANT WRITER'S WRITER'S ASSO Nous aimons nos fans où qu'ils soient Adorons tous fans* ❤


*RASHIN RABO* 


*MEELAT MUSA*


*Gaba dai gaba dai real mai dambuuuuuuuuuuu,,,,,, haƙiƙa taken naki daban ne, babbar yarinya anbuga dake anbarki,,, kina ƙamshi muna binki da humra, wayace dake bake ba, kinyi zarra haƙiƙa naki salon dabanne, kandami babbar ludde, rumfa inuwar makaranta { readers } keɗin ta dabance mai dambu ko rabo ake ke kaɗai ke cika baki,,, haƙiƙa BRILLIANT WRITER'S ASSOCIATION suna alfahari dake,,,, ga jinjininar ban girma, saƙon gaisuwa da fatan alkairi,,, zan isar da saƙonsu*


Asmeenat Xeeyan { Asmee }

Rukayya Hassan Othman { rukky }

Fatima Abubakar A first

Ummu Farhana,


*Mai dambu Surayya ma tace a gaisheki,,,,,,, saƙon gaisuwa ne, daga taskar tsakar gidan brilliant association, ki huta abinki kai ki sarara REAL MAI DANBU, ni Jameela Musa { meelat Musa } nake cewa kiji daɗinki abunki, ki huta tawa,* 👍🏻


*45-47*


***


*T*saki imam malik yayi sannan yace don Allah kiyi mana shiru nikam wallahi bana san surutu, waike bakinki baya maki ciwo ne?"",,,,,, murmushi sapna tayi sannan tace abinda yasa kaga banajin ciwon baki ko?"" to saboda shekaruna har yanxun basu wuce na shan madara ba,,,,,,


Nine kike ma baƙar magana?"",,,,, dan nace bana san surutu kike cewa shekarunki basu wuce nashan madara ba?"",,,,, da sauri yayi farkin a gefen titi tare da cewa fitar man a mota,,,,, cikin sanyin magana sapna tace haba ɗan sanda miye yayi zafi haka don Allah kayi haƙuri kaji insha Allah bazan sake ba,,,, ɗaga murya yayi sosai tare da cewa nace ki fitaaaaa,,,,,, cikin kuka sapna haɗa hannuwanta biyu tare da cewa don Allah ɗan uwa kayi haƙuri wallahi na daina,,,,


Sassauta murya yayi tare da cewa baza ki fita ba?"",,,,, sapna tace kayi haƙuri ni banma wani ga laifinka ba dan kasha madara, kayi haƙuri maganar dai ta riga data fito bata komawa amma insha Allah hakan bazai sake faruwa ba, nayi maka alƙawari,,,,,, imam malik yace saifa kin fita na faɗa maki, kuka ta ƙarayi da yawa da yawa tare da cewa don Allah kayi haƙuri wallahi ina tare dakai, kaji tausayin maraini mana?"",,, idan ka ajiyeni ina zanje yanxun?""",,,,,,


So kake inyi ta balbaɗewa a titi, yunwa ta kamani?"",,, babu ma wani wanda zaiji tausayina ya bani abinci,,?"",,, to kayi haƙuri ka sama miji kawai inyi aure kaga sai ka huta ma,,, ta ƙarasa maganar tana murmushi,,,, goge hawayen idonta tayi tare da cewa muje kawai,,,,,,


Ba tare daya sake magana ba, yaja motar sukaci gaba da tafiya,,,, kallonshi sapna tayi tana dariya,,, tace ashe kaima ka fara jin yanda nake ji ko?"",,, amma kamar nafika jin wani iri sosai,,,, gashi kaima baka iya rabuwa dani,,,, tana maganar tana murmushi,,, shidai bai sake magana ba har suka isa inda zasu je,,,,,


a mota ya barta ya fita saida ya gama abinda yake sannan ya dawo tare da cewa yanxun gidanmu zamuje,,,,,,, 😳 gidanku?"" inji sapna ta ta faɗa,,,, cikin kuka da tsoro tace don Allah kayi haƙuri kada kaje dani ajiyeni anan , murmushi imam malik yayi sannan yace bazan ajiyeki ba, dan nima yanxun bana san inyi nisa dake,,,, sapna tace haba da Allah wannan ai wasan ɗauke lunfashi ne,,, kallonta imam malik yayi tare da cewa gidanmu ne wasan ɗauke lufashi?"",,,, sapna tace nidai gaskiya bana zuwa,,,,, 


gudu yake falfalawa da mota sosai, amma sapna ƙoƙarin buɗe motar take ta dire,,,, shi kuma ko inda take bai sake kallo ba dan ya dannawa moter lock ne,,, sapna kuka takeyi sosai, har suka isa gidansu imam malik, ba ta daina kuka ba, sai zufa takeyi, tana ƙara bawa imam malik haƙuri,,,,,,, bayan yayi farking ne ya kalli sapna tare da cewa ashe duk ƙarya ne kike cewa bakya iya yin rayuwa bada imam malik ba, goge hawaye tayi tare da jan majina tace, nidai bazan zauna anan gidan ba,,,,,


murmushi yayi tare da direwa daga cikin mota,,, da sauri ta buɗe ta fita, da gudu ta isa kusa da imam malik tayi tsaye tana ci gaba  da kuka,,, murmushi ya sake yi tare da cewa dandan dandandannnn,,,,, yau wata yarinya zata kwana gidansu, tafa hannu yayi tare da cewa muje, muje ciki yarinya,,,, gaba yayi yana tafiya, da gudu sapna tabi imam malik tana cewa wai ɗan uwa miye haka don Allah?"",,,,


Firgicewa tayi ganin Alhaji Abu yana fitowa daga wata hanya,,,, a ɗan hanzarce imam malik ya bashi hanya, tare da jan hannun sapna zasu wuce,,,,,,, Alhaji Abu yace lallai baka da kunya,,,,, nine zaka kawo mace a gida na?"",,,, imam malik yace a cikin kaso na zata zauna,,, daga haka bai sake magana ba yaja sapna sukayi ciki, Alhaji Abu yayi tsaye yana faɗa tare da cewa kason uwaka,, to wannan yarinyar bata zama gidan anan na faɗa maka,,,, kai innalillahi wannan wane irin masifa ne wai?"",,,,,,, tsaki yayi sannan ya wuce,,,,,,,,,,


Suna shiga part ɗin imam malik suka nufa,,,  waya yayi aka kawo abinci sapna taci, bayan ta gama ne ya ɗauko wata leda ya bata tare da cewa uniform ne a ciki , kije a wurin momyna zaki riƙa kwana kuma tunda safe zan ajiye ki makaranta sannan in wuce office,,,, magana na ƙarshe bana san surutu na faɗa maki idan naji kina magana a gidan nan tou pa lallai zaki kama gabanki,,,,, duk wanda yayi maki magana daga Eh sai A, a, kinji na faɗa miki ko?"",,,, ya ƙarasa maganar ne cikin kakkausar murya,,,,, cikin tsoro baki na kyarma tace Eh,,,, saida yasha madara sannan yace ma sapna suje,,,,,


A farlon momy suka zauna, imam malik yace momy gata nan,,,, momy tace to Allah ya kauda fitina, imam malik yace bbu wata fitina, idan ma yayi magana kawai kice ya sameni,,, kuma na rantse da Allah babu inda zataje anan gidan zata zauna wallahi,,,,,, yana faɗin haka ya miƙe yayi waje,,,, bayan ya fita momy ta kalli sapna sannan tace wuce ciki ki kwanta,,,, tashi tayi ta shige ciki,,,, a gefen gado ta zauna,,,,,, tayi jugum,,,,, saida ta gama tunani tunaninta ta kwanta bacci,,,,,,


Tunda safe momy ta tashi sapna tayi sallah, bayan ta gama sallah ne, momy tace taje ta gaishe da Alhaji, sapna tace A, a, momy tace miyasa ?"" sapna tayi shiru dan tasan yace daga Eh sai A, a, shine magana, sapna ta sake cewa A, a, momy tace kiyi magana mana, sapna ta ƙara cewa A, a, shiru momy tayi itama ba sake magana ba,,,,


Raliyace ta fito da gudu daga ɗaki tare da cewa baba ya akayi ne?""",,,,,, malam nuhu yace ga usman can a ƙofar gidanshi yana cewa gidanshi ne waye yace ba nashi bane?""",,,,,,, raliya da gudu ta wuce malam nuhu tayi waje,,,,,,,


tun daga nesa ta hango usman ta tabbatar lallai shine,,,, da gudu ta isa wurin tare da rungumeshi tana kuka mai kama zuciya, riƙeta usman yayi tare da cewa miye kike kuka ne?"",,,,,, cikin kuka raliya tace wannan gidan yanxun ba namu bane,,,,, usman yace kamar ya ba namu bane?"",,,,,, , raliya ta kwashe komai ta faɗawa usman ajiyar xuciya yayi tare da murmushin ɓacin rai,,,,, yace innalillahi wa'inna ilaihir raji"un, a hankali ya dafa bango tare da sulalewa ƙasa saboda wata irin hajijiya dayaji tana nema kwaɗashi da ƙasa,,,,,,,,,,,,,, a daidai lokacin da malam nuhu ya iso wurin ya kama hannun usman suka nufi gidanshi,,,,,,,


Bayan sunje ne malan nuhu yayi ma usman nasiha, tare da nuna mashi yin haƙuri da ƙaddara mai kyau ko mara kyau,,,,, amma har yanxun ya kasa magana banda kuka babu abinda yakeyii,,,,,,,,,


Shirye sapna ta fito cikin uniform ɗinta sunyi mata kyau sosai,,, riga da sket ne, sket ɗin wurin guiwa ya tsaya mata sai "yar ƙaramin hijabi, da safarta tayi kyau sosai,,, ta fito farlo, momy tace kinga takalminne?"",,,, sapna tace Eh , momy tace toki saka mana yana jiranki,,, sapna tace A, a, momy tace A, a, mi?"",,,, sapna tayi shiru dan ita baza ta saka ba, sai taje ƙofar ɗaki,,,, kuma baza ta iya yin wannan dogon jawabin ba,,,, momy tace ki saka nace,,, da sauri ta saka takalmin sannan ta fita daga farlo ba tare da tace ma momy sai ta dawo ba,,,,,,,,


tana fita ta nufi part ɗin imam malik bata isa ba taci karo dashi ya fito yana sauri,,, ba tare da yayi mata magana ba, yayi gaba yaci gaba da tafiya,,,, ajiyar zuciya sapna tayi tare da bin bayanshi,,,, a ƙofar farlon dady ya tsaya saida sapna ta iso sannan yace shiga muje,,,, kallonshi sapna tayi da alamar tuhuma, da kanshi ya nuna mata suje,,,, itace a gaba, imam malik yana bin bayanta,,,,,,,,,


Suna shiga yace mata maza kije kiyi break , tsayuwa tayi tana kallonshi,,,, kusa da ita yaje yaja hannunta suka nufi darning area, yaja kujera ya zauna, itama yace ta zauna zama tayi ba tare da tayi magana ba,,,,, da kanshi ya haɗa mata kalaci yace tayi sauri,,,, ta gama sun makara a daidai lokacin da yake duba agogon hannunshi,,,,,,,


dady ne ya fito daga ciki,,, shima inda suke zaune yazo ya zauna danyin break dan duka gidan kowa da kowa a nan farlon akecin abinci,,,,, bayan dady ya zauna, imam malik ya gaisheshi, ya ansa itama sapna gaishe da dady tayi ya ansa,,,,, kallon imam malik sapna tayi tare da cewa na ƙoshi tayi maganar ne cikin kalar tausayi,,,,, imam malik yace baki ƙoshi ba,,,, idanuwanta suka kawo hawaye tace Allah na ƙoshi,,, ita kuma ganin dady yasa taji duk ta takura,,, miƙewa yayi tare da cewa muje,,,,, 


Imam malik ya miƙe suka fara tafiya, dady ne yace kuzo nan,,,, juyawa sukayi dukansu suka koma inda dady yake,,,,, dady yace waye zai kaita makarantar ne?"",,, imam malik yace nine,,, dady yace waye zai riƙa ɗaukota ne?"",,, imam malik ya sake cewa nine,,,, dady ya kalli safina sannan yace to Allah ya bada sa,a imam malik ne yace amin tare da cewa muje, yayi gaba sapna tabi bayanshi,,,


A motar sapna sai faɗa takeyi wai imam malik yasa tayi shiru batayin magana, yama za,ayi a hanata magana ita da bakinta, wannan ai ɗaukar alhakine,,, shidai baice mata komai ba, har suka isa makaranta sapna surutu takeyi babu kwama babu aya, babu waƙafi babu linfasawa, shi mamaki ma yakeyi mutun yayi surutu ko ciwon kai bata ji,,,,,


a motar imam malik yabarta saida ya gama abinda yakeyi sannan ya fito ya tafi da sapna ciki, amma yaso a ajiye ta ko prmry 4 amma prmry 3 aka ajiyeta, ita kuma sai cewa takeyi ya za,ayi da girmanta a ajiyeta cikin "yan yara, ai wannan ma kawai dan asa yara su raina mutane ne kawai, sapna taci gaba da cewa ai ita ina ma laifin ace tana s s 1 yanzun,,,, shidai imam malik, tafiyarsa yayi,,,, bayan ya tafi ne aka bawa sapna aji,,,,,,,,,


Usman saida yasha kuka sosai sannan yasa aka kira mashi suwaiba,,,,, bayan tazo ne, ya kalleta sannan yace suwaiba mi nayi maki haka ne?"",,,, da zaki ɗaukar man gidaje ki sayar?"",,,, a ina kike so nayi rayuwa ne?"",,, duk halakcin da nayi maki haka zaki saka man ne?"",,,,, maza kirawo man gwamna,,,,,,, 


tsaki suwaiba tayi tare da cewa wane gwamna kuma?"",,, usman yace guda nawa kika sani ne?"",,,,, miƙewa suwaiba tayi tsaye tare da cewa babanshi ya anshi ɗanshi,,,,,,,,,,,,,


Malam nuhu yace ban gane ba?"",,,, suwaiba tace ai fahat ba ɗanka bane,,,, babanshi yace yana buƙatar ɗanshi a kusa dashi dan haka yazo sun tafi dashi,,,,, wani irin ihu Usman yayi tare da cewa kaiiiiiiiiiiiiiiiiiiii,,,,,,,,,, yana ƙoƙarin miƙewa tsaye ya faɗi ƙasa somamme,,,,,


da malam nuhu da raliya sukayi kanshi,,,, suwaiba kuwa da gudu ta fita, dillalai ta samu sukaje suka sayi gidanta,,, dan haka bayan sun siya suka bata kuɗinta ta ɗaure abunta ta fara haɗa kayanta dan barin garin,,,,,,,,,


Bayan an tashi su sapna imam malik yazo ya ɗauketa, har sukaje office din imam malik sapna batayi magana ba,,haushi takeji an ajiyeta prmry 3,,,, shima bai mata magana , ba,,, yadai yi waya gida an kawo mata abinci, sai ya tashi Office zasu tafi gida tare,,,,,,,,,,,,,

⚜ *BRILLIANT WRITER'S ASSO* 🖊


*Je suis fier BRILLIANT WRITER'S ASSO Nous aimons nos fans où qu'ils soent Adorons tous fans* ❤


*RASHIN RABO*


*MEELAT MUSA*


*48-50*


***


*B*aba sai wani irin gurnani yake yi,,,, idanuwanshi na tsiyayar da hawayen baƙin ciki,,, a hankali ya buɗe idanuwanshi ya kalli raliya tare da cewa "yar rali sake kira man suwaiba,,,,,


Tsaki "yar rali tayi tare da cewa da Allah ka kyaleta saura kuma a kirawota tazo ta sake ɓata maka rai ne?"",,,,, baba yace inaso inji abinda ta faɗa gaskiya?"",,, malam nuhu yace yama za,ayi ace haka?"",,,, duk duniya ai kowa yasan gwamna ɗanka ne,,,,, wani ajalalliyan murmushi baba yayi sannan yace barta ma kawai,,


A gajiye baba ya miƙe ba tare da yayi magana da kowa ba, yayi ƙofar gida,, wani yaro ya samu ya tambayeshi gidan suwaiba, yaron ya nuna mashi,,,, godiya baba yayi sannan yayi ma gidan tsinke,,,,,,,


Sapna sai gyan gyaɗi takeyi saman kujera a office ɗin imam malik,,, miƙewa yayi tare da ɗaukar wayarshi, inda sapna take zaune yaje  yace taso mu tafi inkaiki gida, turo baki tayi da zatayi magana kuma sai ta fasa,,,,


Tashi tayi tabi bayan shi,,,, har sunje wurin motar zasu shiga, yace ma sapna shiga ina zuwa nayi mantuwa,,,, buɗe motar tayi ta shiga shi kuma ya koma office,,,,,, bayan ya ɗauko abinda zai ɗauka ya dawo motar ya shiga yaja suka bar wirin,,,,,,


Saida sukayi tafiya mai nisa sannan imam malik ya ɗauki wata hanyar daban,,,, tafiya mai nisa yayi sosai yaci gaba da shiga cikin daji, da sauri sapna ta kalleshi tana cewa ina zaka kaini kuma?"",,,,,, baiyi magana ba,,,,,, yaci gaba da tafiya, wayarshi datayi ƙara ya ɗauka tare da cewa dady na kusa isowa,,,,,,,,,


Kuka sapna ta farayi tare da cewa kada ka kaini don Allah, wallahi yau zanyi tafiyana kayi haƙuri,,,,, taɓe baki imam malik yayi ba tare da yace komai ba,,,,


Bayan sun isa ne,,,,, imam malik yayi farkin tare da cema sapna muje,,,,, saukowa tayi daga motar ta juya ta kalli bayanta,,,, wanda lallai idan akace mata ta fita,,, kafin ta shanye wannan hanyar lallai an kira sallah magrif,,,,, juyowa tayi ta sake kallon imma malik,,, zatayi magana, ya ɗora hannunshi a saman bakinshi tare da cewa shittttttt,,,,,,, idanuwan imam malik ta kalla,,,, sai taga sunyi wani iri,,,,,,,,,,


Kusa da sapna imam malik ya matsa sannan yace safeena kina so na koba haka ba?"",,,,,, kai kawai sapna ta ɗaga alamar Eh, yace to ki riƙe magana ɗaya idan mun shiga,,,, daga Eh sai A, a, daga haka bance ki sake cewa komai ba kinji ko?""",,,, sapna tace tom,,,, imam malik ne yayi gaba sapna tabi bayanshi,,,,,,,,,,,


Suwaiba ina fahat yake yanxun?"",,,, baba ne yake magana wa suwaiba,,,,, kallonshi tayi ƙasa da sama sannan tace bansani ba,, murmushin taƙaici baba yayi sannan yace nine kike cewa baki sani ba?"""",,,,,


Tace, naje nace ta faɗa,,,, ni wallahi sai yanxun ma nakejin takaicin aurenka,,, ƙwallan matsiyaci irinka miye abin zama tare dakai?"",,,,, ga ɗan uwanka can yana tashe a garin nan babu wanda baisan da zaman Alhaji Abu tanimu ba,,,,, ga ɗansa imam malik sadiq kowa ya sansu uba da ɗa "yan sanda, "yan sanda na kirki ba ƙanana ba, kaiko babu komai sai fatara da tsabar babu,,,,,,,,, kai gaskiya wasu mazan haka nan suka rako gwarazan maza duniya, mazan kirki suna can sun hunce kuɗi kawaiiiiiiiiiiiiiiiiii,,,,, kaiko saboda kai sokone, zaman jiran kake ka haifi maza su nemo maka,,,,,, to yau uban namiji yace nashi ɗan yake so a bashi abun sa, ai kasan hannun wani baya ibar ma wani miya, idonka ya rufe da duniya ɗiyar ɗaya daka aifa san duniya tasa ka salwantar da ita,,,, kaico da halin ka har a badan duniya , gaskiya baka da *RABO* 


Suwaiba taci gaba da cewa kaga yanxun babu kare bin damo,,, kawai bani takardar sakina na,,,,, idan kuma ba haka ba, wallahi insa sara,,,,,, dan kai duk duniya ban taɓa ganin mutum marar *RABO* ba irin ka,,,, kai gaskiya tirr tittitirtirrrrrr da halinka,, 


Wani irin jijjigaggen murmushi baba yayi mai kama da kukan mutuwa,,,, sannan yace lallai nikam ina rabo,,,,, dani dake, babu wanda yayi *RASHIN RABO* irin ki,,,,,, domin da kin riƙe safeena da mutunci haƙiƙa da kinci sa'a tunda bata da uwa ta taso cikin maraici da ƙunci rayuwa, kuma turbar dana saka kaina,,,, tunda ke mace ne, kuma ke kina aurena, wani abun da kin nuna man idan nayi wani bazanyi wani ba,,, amma saboda tsabar rashin imani, kika barni na azabtar da yarinya da bata da gata,,,, wai dan ta kasance ɗiya mace,,, kuma nayi imani da mahifiyarta na raye idan nayi wani wani bazai yuwu ba,,,,,


banji baƙin cikin yima gwamna abinda nayi mashi ba,,,,, wannan ba komai bane,,,, amma ɗiyar dana aifa a cikina na gana azaba salosalo a gareta,,, na nuna mata tsana, ta taso cikin wahala da azaba na rayuwa,,, kika kawo wani daban kika ce wai shine ɗana,,,,, hmmmm baba ya ƙarasa maganar yana ɗiga hawayensa ƙasa,,,, tare da dafe daidai saitin zuciyarshi da hannunshi na dama,,,,,,


sannan yaci gaba da cewa bari tun yanxun kiji babban *RASHIN RABO* da kikayi,,,,,,,,, murmushi yayi sannan yace ina kuɗin da kika siyar da gidan nan ne?""",,,, da sauri suwaiba ta lalabu cikin kwagirin data ɗaura a ƙugunta,,,, jin babu shi yasa ta ɗago da sauri tana kallon baba,,,,,,, shi kuma murmushi yayi tare da cewa ya kika fara jin wasan ne?"",,,,  suwaiba tayi shiru,,,, gyara tsayuwa baba yayi tare da cewa sauran kuɗin da kika siye "yan kunne gold ko kinsan ina "yan kunnen suke ne?""",,,,,, da gudu suwaiba ta faɗa ɗaki dan ɗanko "yan kunne inda ta ajiye nan ma bbu komai,,,,,,,


Baba ya sake kecewa da wata irin dariya,,,,, lokaci guda kuma ya ɗaure fuskarsa,,,,, kallon suwaiba yayi sannan yace kinji nawa salon?"",,,,,, yanxun muka fara,,,,,, saina sake dawowa zakiji abinda yasa na kiraki da baki da rabo,,,,,, yana faɗin haka ya fice daga gidan,,,,,,, silalewa suwaiba tayi ƙasa tare da yin zama irin nacin tuwo,,,,, tana nazari,,,,,,,,, miye nayi na rashin rabo?"",,, sannan ina kuɗina ina kuma "yan kunne na?""""",,, wani irin ihu tayi tare da cewa ƙaryaaaaaneeeeeeeeeee,


Wata irin jiniyace ta karaɗe kakaff anguwar ji kake wawawaaaaaaa,,,, wuwuwuwuuu,,, ƙuyƙyyyyy,,, tsitsitsiiiiiii,,,,,,,, ga wasu irin sodoji masu firgitarwa,,,,, kowa ka gani babu wasa a idonshi, sun wani ƙame da bindigoginsu jira kawai suke suga kallon banza su fara aman harsashe,,,,


Haka motocin sukaci gaba da wucewa fiyuuu fiyuuu, motoci ne sunfi  talatin,,,,,, duk yawan motocin nan a ƙofar gidan malam nuhu sukayi parking,,,,,, haka sodoji sukaci gaba da dirowa kamar tsuntsaye, bayan sun gama saukowa ne,,, kai tsaye gidan malam nuhu suka nufa,


basu daɗe da shiga ba,,,, suka fito da malam nuhu a cimimiye,,,, sun wani dunƙuleshi kamar ramar datasha ruwan zafi,,,,,, suna fitowa a motar suka jefer dashi tare da cewa ina Usman?"""",,,,,, ciki rawar baki malam nuhu yace gaya can yana tahowa,,,,,,,, kafin baba ya iso sun isa wurin da yake tahowa shima sun duƙule banza, sun jefa shi a motar,,,,  raliya data rugo da gudu, tana kuka itama aka taɗa da ita aka cusa ta a mota,,,,,,,, babban cikinsu ne ya kalli usman tare da cewa ina halima?"""",,,,,, idanuwa baba ya zaro tare da dafa ƙirji, sannan yace ta rasu,,,,,,,


Ta ra,,,,,,, me?""""",,, cikin tsoro baba yace ta rasu amma don Allah kuyi haƙuri,,,,, wata irin tsawa aka dakawa baba,,,,,, tare da cewa idan kaje ka basu bayani,,,,,,, kaje ka gudo da ita ka kawo a nan ko?""",,,,,, muje mu tafi,,,, yau kaji a jikinka,,,,,,,  raliya cikin tsoro ta kalli baba tare da cewa su waye su?"",,,,, murmushin tashin hankali baba yayi tare da cewa daga gidan kakannin safeena ne,,,,, a daidai lokacin da motocin suka fara tafiya,,,,, da gudun tashin hankali suka fice daga cikin anguwarrr,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,su baba ana bayan mota sai raba idanuwa ake kamar karyar da'aka kwashewa "ya"ya,,,,,,,


Imam malik yace yawwa muje,,,, shine a gaba sapna tana bin bayanshi,,,,,, suna shiga cikin wurin,,,, wani irin ihu sapna tayi dan ganin gidi a wurin,,,, ɗan uwaaaaaaa,,,,, ta faɗa cikin ƙaraji tare da durƙushewa wurin tana kuka,,,, sai ɗaga hannunta take alamar kada ya isa ya dawo,,,,,,,,


Juyowa yayi ya dawo inda take ya durƙusa kusa da ita,,,,, sannan yace ya haka kuma?"",,,,, sapna tayi shiru sai hawaye yake zuba daga idonta,,,, murmushi imam malik yayi tare da miƙa mata hannunshi yana cewa ki kasance dani,,,,,, insha Allah ni bazan bar rayuwarki ta salwanta ba,,,,,


idan har kina tare dani,,,,,,, ya nuna kanshi sannan yace taso,,,, muje, inji kiran sai mu tafi,,,,,,, cikin magana ƙasa ƙasa, sapna tace wancan makashi ne,,,, ta nuna inda gidi yake zaune,,,,, juyawa imam malik yayi ya kalli gidi sannan ya juyo ya kalli sapna murmushi yayi sannan  yace ƙaryene,,,, bazai maki komai ba,,,, ni nafi ƙarfinsa taso kuma ki gani,,,,,, kamata yayi ya miƙar da ita tsaye,,, bayan ta miƙe ya saki hannunta,,,, yace muje,,, jerawa sukayi ita dashi suka isa inda su dady suke zaune,,,,,,,,


Suna isa wurin, dady ya kalli imam malik ƙasa da sama sannan yace,:• imam inaji dai nine ubanka ko?""",,,,, murmushi imam malik yayi amma baice komai ba,,,,,,, ya zurawa dady ido yana kallonshi kamar ango da aka kawai sabuwar amarya,,,,,,,


Dady yaci gaba da cewa ai dama nasan baza kayi magana ba,,, amma abinda nake so dakai shine,,,,, kasan dai nina na haifeka,,,,, kuma na reneka,,, tun kana ƙarami na kula da tarbiyyarka,,,,, ci da sha na nemo da ƙarfi na baka kaci dan kaji daɗi, ,,,, na gina maka rayuwarka ta hanyar baka ilimin addini dana zamani,,,, bayan ka gama karatu nine na samar maka aiki,,,, dan ci gaban rayuwarka,,,,,,,,


bansan nayi wauta da hauka ba sai yau,,,,, da kaje ka jawo ɗiyar maƙiyina zatazo ta cinye man tattalin arxikin gida,,,,,, shi ya koreta ne saboda bata da wani amfani a wurinshi,,,, amma kai saboda kai yaro ne,,, mahaukaci bakasan inda kanka yake maka ciwo ba, shine zakaje ka jajibo man ita ka kawota cikin ahalina,,,, ya karasa maganar cikin ɗaga murya sosai,,,,,,, tare da nuna sapna,,,,,, sannan yaci gaba da cewa,,,,,,


Ilimi dai nasan bazai kwatu ba,,,,,, tunda ya riga ya zauna a cikin kwalwarka,,,, arxiki kuma na Allah ne ko?"",,,, haka yake kaima jiya haka ka faɗa man ko ?""",,, da gira imam malik ya bawa dady ansa,,,,,


murmushi dady yayi tare da ajiye wata takarda a saman wani ƙaramin benci da yake gaban imam malik, sannan ya ciro bero daga gaban aljihunshi ya ɗora saman takardar, gyara zama dady yayi a saman kujerar da yake zaune,,, sannan yace ai nine na baka aiki ko?""",,,,,,, taɓe baki imam malik yayi tare ɗaga kanshi a hankali yana jinjinawa alamar Eh,,,,,


Dariya dady yayi tare da cewa yau saika zaɓa, aikinka ko safeena?""""",,,,,,,, murmushi imam malik yayi tare da cewa da duk saboda haka ne kake ta wani yawo da hankali?"",, imam malik yace to  na ajiye aikinka na zaɓi safeena,,,,, a daidai lokacin daya ɗauki bero ya saka hannu,,,,,,,


Cikin ɗaga murya dady yace amma kai dabba ne,,,,, bansan kai jaki bane sai yau,,,,,,, ƙanƙance iduwa imam malik yayi tare da cewa sanin nine dabba ko jaki , duk basai kaji ba,,,, bayan hakan miye kuma kake so nayi?""",,,,,,


dady yace sai ka cire mana uniform tunda ba uwarka ta ɗinka su ba,,,,,,, murmushi imam malik yayi tare da cire hular kanshi,,,,,, hawayene ya kwanta a cikin kwayar idonshi,,,, lallai yana san aikinshi,,,, tun yana ƙarami yake san zama ɗan sanda,,,,, idan dady ya dawo daga office yana ɗaukar hularshi yasa, tun yana ƙarami ya rayu da san zama ɗan sanda, a zuciyarshi,,,,,,,,,, Haka komai ya fara dawo mashi a idonshi,,,,,


ganin yana hawaye dady yace ajiye, ajiye mana sakaran banza,,,,,,, shashasha,,, da sauri sapna ta matsa kusa dashi tana ɗaga hannuwanta A, a, A, a, ɗan uwa kada ka ajiye aikinka ka zaɓeni kayi haƙuri wallahi zan tafi yanzun nan nayi alƙawari zan fita daga rayuwarka,,,,,,


Wani irin kallo yayi mata tare da cewa waye yace kiyi magana ne?""",,,, sapna tace gaskiya nake faɗa maka wallahi kada ka ajiye aikinka,,,,, dariya dady yayi tare da cewa miye na faɗa maka?"",,,, ai dama nace maka ba dan Allah take sanka ba,,,,,, kana gani taga zaka ajiye aiki tana neman sulalewa wai zata fita daga rayuwarka,,,,,,,


Sapna tace A, a, ba haka bane, ina sansa kuma bbu ruwana da aikinsa ko rashin aikin nasa,,,,, dady yace to ai sai ya ajiye aikinki ya biki mu gani,,,,, a daidai lokacin da imam malik ya ɗora hularsa a kan tebirin,,,,,,,


ya ciro "yar ƙaramar bindiga a cikin inda "yan sanda suke ajiye bindiga, tare da cire bulet ya ajiye a saman ɗan ƙaramin bencin,,,,,, sannan ya kalli dady yace sai miye?"",,, dady yace sauran kayan zaka bani,,,,, imam malik yace zan kawo maka,,,,,,,,


Ba tare daya sake magana ba yaja hannun sapna suka bar wurin,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

⚜ *BRILLIANT WRITER'S ASSO* 🖊


*Je suis fier BRILLIANT WRITER'S ASSO Nous aimons nos fans où qu'ils soent Adorons tous fans* ❤


*RASHIN RABO* 


*JAMEELA MUSA*


*51-53*


***


*S*una fita dady ya kalli gidi tare da cewa kabi man yaron nan safsaf ka ɗauke man motar banza,,,, sai kinga da wacce zai riƙa bada faɗi,,,


Gidi yace tuba nake wannan aikin yafi ƙarfi na gaskiya,,,, dady yace to bbu damuwa ni zansan abinyi a hannuna,,,,, gidi ya rusuna tare da cewa hakan shine mafita,,,,,,,,,,,,


Kuka takeyi a cikin motar tare da cewa nifa banga amfanin abinda kayi ba?"",,,, haka kawai ka tanƙwarewa kanka rayuwa saboda gina rayuwata?"",,, tanayin maganar ne cikin kuka da nuna rashin jin daɗin abinda imam malik yayi,,,,,, murmushi yakeyi ba tare daya ce mata komai ba,,,,,,,,,,,,


Taci gaba da cewa nifa yanxun ya zamuyi?"",,, bayan kasan ina so inji daɗin rayuwa ta,,, kawai ka wani kama kaje ka ajiye aiki?"",,,,,, yanxun waye zai riƙa siya maka madara?"" nima waye zai biya man kuɗin makaranta na?"",,, kuma idan ina san abu waye zai siya man?""",,,,, imam malik yace Oho maki?"" ba kince kina san imam malik ba?"",,, kawai sai muje muyi aurenmu , muyi zamanmu a gida kawai basai munci abinci ba,,,,,,,


Cikin tsiwa sapna tace wallahi bazai yuwu ba,,, ana rayuwa babu abinci?"",,,, kowa sai yaci abinci yake girma,,  kawai ni saika molaƙe man rayuwa,, bana ci bana sha?"" towai jirama a gidan naka kake wani cewa kayi aure dani don Allah faɗa man zan zauna babu abinci ne?"",,, yace ƙwarai ma kuwa,,, ba gani ba?""" sapna tace kaine abinci kenan?"" yace Eh mana ninan kaɗai na isa in ƙosar dake, kedai kawai muyi auren,,,,,,


Sapna tace nikam gaskiya bazan iya ba,,, infito a wahala kuma in ƙara faɗama wahala?"",,,, ni kenan rayuwata a cikin yunwa da babu zata ƙare?"",,,, imam malik yace mafita kuma ta rage gareki,,,,,,,,,, daga haka bai sake magana ba,,,,,,


Sapna sai masifa takeyi ita fa bata auren shi tunda bashi da abinda zai riƙeta,,, yanxun ko ɗan dankalin ma bazai ƙara siya mata ba,,, kuɗin da kake dashi ma ai idan munaci zai ƙare,,, tunda ba wasu ake nemowa ba,, kallonta yayi tare da cewa wallahi ƙaryane sai anyi auren tunda tun farko kince kina so na,,,,, kuma kada ki samu damuwa komai kike so nayi maki alƙawari shi zan baki,,,, bazan barki da yunwa ba,,,, kuma zakiji daɗi a gidana,,,,,,,


Cikin ɗaga murya sapna tace a hakan zanji daɗi?"",,,, to naji zanji daɗi yanxun bara in gani idan da gaske kake,,,, maza muje can ta nuna da hannu,,, tare da cewa waccan ƙatuwar, ƙatuwar kazar, waccan nake so ka siya man,,,,, murmushi yayi sannan yace to,,,,,,


Parking yayi sannan ya fita,,,,,, kazar ya siyo mata ya kawo mata,,, yana fara tafiya tace wayyo ba kaza ba,,, yought nake so,,,, yace shima za'a siya miki,,,,, bayan ya siya mata ,,, tace wayyo ɗan uwa kanaji fa nace maka balango nake so,,,, yace to,,, balangun ya siya mata,,,, sapna tayi tsaki tare da cewa kana da matsala ɗan uwa nafa ce maka hada tsire,,,, imam malik yace shima zan siya maki,,,,,,,,,


Haka sapna tayi ta gyargyara imam malik,,,, wancan take so bata san wancan,,,, shi kuma ya biye mata,,,, yace kinga zan iya dake ko?"",,, sapna tace a hakan siyan ɗan abu kaɗan kaɗan?"",,,,,  yace mai yawanma zan siya,,,,, haka dai sukayi tayi har suka iso gidansu imam malik,,,,,,,


Bayan sunzo ne,,, yace taje ta cire uniform tayi wanka,,,, kuma kada ta fito saida safe idan Allah ya kaimu,,, tace to waye zai kaini makaranta goben?"",,, yace nine zan kaiki,,,,, tace to,,, wucewa tayi ta nufi ciki shima nashi part in ya nufa,,,,,,,


Tunda dady ya dawo sallah asuba yake faɗa duk wanda yake cikin gidan babu wanda bayajinsa,,,,, faɗa yake yana ƙarawa, ɗakin momy ya nufa yana cewa babu wanda ya ɗaurewa yaron nan ƙugu yake iskanci sai ita,,,,,, cikin girmamawa momy tace kuma ni miye laifina?""",,,,,,, dady yace koma miye lafinki bai dameni ba,,,, imam malik yazo ya bani mota ta,,, kuma yau ɗin nan saiya barmin gida, wato saboda tsabar ya mayar dani wata fira girke nine zai raina hankali har haka?""",,, momy tace to ai bakaine ka siya masa motar ba,,,,, dady ya daki ƙirjinsa tare da cewa ai nina na samar masa aikin daya siya dan haka yau ɗin nan duk ubanda ya tsaya masa zai bani duk wani abu daya sani nine nayi masa hanya ya sameshi,,,,,,,,


momy tace bakaine kayi masa hanya ba Allah ne yayi masa kuma ya buɗa masa ya samu,,, dan haka bazai bayar ba,,,,,, dady yace to ki hana in gani,,,, kuma saiya barmin gida dan uwarki,,,,,, idanuwa momy ta zaro tare da dafa ƙirjinta tace ni kake zagi haka?""",,,, dady yace na zageki kuma an ƙara cewa uwarki,,,,,,,,,,,,, idan kin isa saiki rama mu gani,,,,, murmushi momy tayi tare da cewa nikam nasan abinda nakeyi,,,,,, dady yace Oho nine jahili idan na fahimci abinda kike magana ko?""",,,,,,,, momy bata sake magana ba, tayi ciki,,,,,,,


Tsaki dady yayi tare da fita daga ɗakin momy,,,, kai tsaye wurin imam malik ya nufa,,,,,, yana zuwa babu ko sallama, imam malik shi kuma yana zaune yana karatun Qur"ani ,,,, dady yace imamu,,,,,, kallonshi yayi amma baiyi magana ba,,,, dady yaci gaba da cewa duk wani abunda ka sani nine nayi maka silar samunsa yau ɗin nan komai da komai nawa ka tabbatar ka ajiye manshi,,,,,, tunda wancan yarinyar ka zafa,,,, kaje can ubanta ya baka duk abinda kake ganin bana baka,,,,


sannan kuma tunda kace ita kake so gobe idan Allah ya kaimu zan ɗaura maka aure da ita saiku tafi ku barmin gida,,,,,, kaje dan uwarka kaga idan auren cine,,,, dan duk ahalin usman farar ƙafa garesu,,, shima bai tashi talaucewa da tsiyacewa ba saida ya haifi waccan balbaɗaɗɗiyar yarinyar,,, kaima ban tashi saka ajiye mana aiki ba saida kace zaka aure ta,,, to zan aura maka ita zakiji abinda nake gudar maka dan rigar sawa ma sai "yan uwanka sun saka su cire su baka kwance,,,,,


Murmushi imam malik yayi tare da cewa Allah ya sawaƙe,,,,, dady yace babu abinda Allah zai sawaƙe maka daga cikin duk wani bala"i da zai sameka matsawar kana tare da yarinyar nan,,,,, aure dai ko?"",,,, kaje ka aureta,,,, Allah ya bada sa'a, yana faɗin haka ya fice daga ɗakin imam malik yabi bayan dady da kallo tare da cewa Allah ya sawaƙe man duk mugun alkaba'in dake fatar man,,,,,,


Su baba kuwa bayan sun isa a garin Abuja a gidan kakannin Sapna,,,,, masauki mai kyau aka basu,,, babu abinda aka ragesu dashi naci da sha haka kuma ɓangaren abubuwan more rayuwa,,,,, bayan sunci sunsha sunji daɗinsu,,, kakan sapna yasa aka kawosu farlonshi,,


Bayan an kaisu suna nan sunyi wani cicciro kai cicciro kai, sai ciccira idanuwa suke kamar sabbin munafukai,,,,, kakan sapna kyakkyawan tsohone,,,, kana ganinsa kasan ɗan gatan tsohone,,, babu wani abu daya rage masa najin daɗin duniya saida fatan samun ƙarshen makoma,,,, Allah yasa mu cika da imani ubangiji ya bamu sa'ar tafiya,,, Allah ka nufemu da aikata alkairi dan samun rahama da kyakkywan makoma,, ameen,,,,,,


kallansu yayi tare da cire tabarau ɗin idonsa,,,, sannan yayi magana cikin dattako , da yanayin manyanta,,,, yace malam nuhu ku zauna,,,,, jiki na rawa malam nuhu ya kalli su baba da raliya yace masu mu zauna,,,,,,,


gaba ɗayansu zubewa sunkayi a ƙasa,,,, tare da miƙa gaisuwa wurin tsoho,,,,,, bayan gaishe gaishe ne, kaka yace malam nuhu ina halima?""",,,, da sauri malam nuhu ya kalli inda baba yake zaune , sannan ya maida dubansa wurin kaka tare da yace wallahi Allah yayi ma halima rasuwa,,,, kaka yace amma hakan kunyi man adalici kenan?"",,,,, kowa yayi shiru,,, kaka yaci gaba da cewa nan kazo girma da arxiki ka nemawa yaron nan ɗiyata,,,,, ya nuna inda baba yake zaune,,,,, sannan yaci gaba da cewa nace bana bashi ɗiyata amma ka kafe kaida fata nace maka bama bashi auren ɗiyata,,,,,,,,


ka tambayeni dalili,,,, nace maka kawai ni yaron baiyi mani ba,,,,,kuma na raina tarbiyarsa, amma saida ka kai ruwa rana nace maka bana bashi,,, kaje kuma ka samu ɗiyata ka hure mata kunnuwa,,,,, tunda tana da wanda zata aura,,,, a lokacin,,,, tace man duk duniya bata san kowa san wannan ɗan banzan lalaccen yaron,,,, ya nuna usman,,,,,


Kuma yanda kayi nasara akan halima haka kayi nasara akan uwarta,,,,, wannan dalilin yasa nayi fushi da ita, kuma nace idan ta aureshi tazo wurina ba tare dana nemeta ba ban yafe mata ba,,,, kuma nace duk wanda yaje wurinta shima ban yafe mashi ba,,,,, ashe ɗan iskan yaron nan daya tafi da ɗiyata gana mata azaba yayi tayi,,,, baba zaiyi magana kaka yace idan kace man tuffff saina sa an kware man fatar jikinki saboda azaba,,, shiru baba yayi tare da ɗauke lunfashinsa ƙam,,,,,


haka kaka yayi ta faɗa,,, kamar zai daki baba,,, cikin kuka kaka yace gaskiya ka munafinceni,,, amma na yafe maka dan duk abinda mutum yayi kansa yayi ma,,,,, amma kasan hakan akwai ɗaukar alhaki,, ace ɗiyata ta rasu baka faɗa man ba,,,,,,,


baba cikin girmamawa yace kayi haƙuri don Allah wallahi banyi haka dan wata manufa ba,,, kuma ya riga daya faru kayi hakuri don Allah baba,,,,,,, kaka yace shikenan ,,,, ina zuri'ar halima?""""",,, gaban babane yayi mummunar faɗuwa, tashin hankali wai ance da shege ina ubanshi!""""""""


Raliya ce tace sunan ta safeena,,,, kuma taje gidanmu hutu ne,,,, kallon ta kaka yayi tare da cewa ke kuma wace ce?""",,,, malam nuhu yace ita matar usman ce,,,, kaka yace to yayi kyau,,,, ita safeena ɗin yaushe zata zo nan?"",,,,, domin akwai saƙon da kakarta ta bayar a bata kafin rasuwarta,,,,,,,


tace idan an samu halima a bata idan ba'a samu halima ba to lallai a bawa ahalinta,,,,,, baba yace saƙon miye ne?"",,,,,,, kaka yace sai kunxo da aita sannan zan bata hannuna da nata,,,,,, idan tace a baka tunda kaine mahaifinta zan baka idan kuma mijinta tace a bashi shine zan bawa,,,,,,,,


cikin zumuɗi da ƙagara baba yace ai bata da aure,,, dan haka ko tazo nine zatace a bawa,,, kaka miye saƙon ne?""""""",,,,,,, kaka yace to nidai sai tazo dan haka kuje kuxo da ita,,,,,,,,,


baba yaji baƙin ciki sosai dan yaso a faɗa mashi ko miye idan na danfarewa ya matse abinsa,,,,,,,,


da suka tashi tafiya talatin da tara na arxiki kaka yayi masu,,, haka ya haɗasu ya zane su da bulalar kuɗi,,, aka barsu baba da jinya,,, mota biyu masu kyau kaka ya bawa baba,,,, baba yayi ta godiya,,,, tare masa alƙawalin kawo masa sapna,,,,,,,,,,

⚜ *BRILLIANT WRITER'S ASSO* 🖊


*Je suis fier BRILLIANT WRITER'S ASSO Nous aimons nos fans oú qu'ils soent Adorons tous fans* ❤


*RASHIN RABO*


*MEELAT MUSA*


*Hmmm haba keko hajiyata mi nayi maki?"",, ni bana faɗa kuma banajin haushin kowa,,, haka bana riƙe wani azuciyana,,, mi nayi maki zakiyita zungurawa uwata zagi saboda Real Mai dambu?,,,, waini kike zagi🤔 kam,,🤔 ke?"" kinko san meelat musa?"" to ki kiyayeni, dan haka saurareni da kyau kiji,,, daga yau sai yau, idan har kika sake zagarmin mamana kema saina zagi uwarki,,, ni babu wani ruwana da rayuwar kowa,,, harkar gabana nakeyi,, kuma ƙauna dani da REAL MAI DAMBU tarayya kuma babu rabuwa insha Allah,,, Amana takai maki mai dambu jinjinar ban girma,, saƙon gaisuwa daga hannun meelat musa,,,, zaman lafiya jin daɗi kwanciyar hankali farin ciki su daddanneki,,, alkairin Allah ya iskoki har cikin bargon baccinki,,,,, zuciyar meelat musa tana hannunki mai dambu tawa,,, Allah ya barmu tare, gaba dai gaba dai, haƙiƙa kamar yanda kika ce JAMEELA TAWA CE,,, lallai ni taki ce, kuma kema tawace real mai dambu tawace*🥗


*57-59*


***


*S*apna tana shiga a farlo ta yada zango,, hijabin jikinta ta cire tare da faɗawa saman kujera ta kwanta,,,, bata wani daɗe da kwanciya ba bacci yayi gaba da ita,,,,


"yar rali wai yanxun ina kike ganin za'a gano safeena tawa?"",,,, baba ne yake tambayar raliya,, raliya tace kawai cigiya za'a bayar,,, dan kaji dai kaka yace ƙarshen watan nan lallai safeena yazo,,,,


Baba yace kada ki samu damuwa,,,, zamu ganta,, nasan na kusa kuɗancewa,, dariya baba yayi tare da kwanciya ya ɗaga ƙafafuwansa sama yana farin ciki,,,, cikin jin daɗi yace "yar rali zamuje makka,, muji daɗinmu Allah dai ya bayyana man ɗiyata,,,,,,, dariya raliya tayi sannan tace,,,,,


Wallahi baka da kunya,,,, kallonta baba yayi tare da cewa rashin kunyar mi nayi?"",,,,,, raliya tace ka manta nan kake cewa da ita da babu?"",,,, sai kuma yanxun dan kaji za'a bata kuɗi kake cewa safeena,,, safeenar ma wai taka,,,,


Cikin hasala baba yace da Allah rufe man baki,, safeenar taki ce ba tawa ba?"",,,, bawar Allah ina san safeenata,,, Allah ya bayyana manke yarinya mai biyayya,,, kai wallahi yarinyar nan tana da haƙuri,,,,,, bazan manta ba "yar rali ina san safeena itama tana so na,,, kullum idan na dawo sai taman sannu da zuwa,,, kuma nasan idan ta dawo komai zata mallaka man ,, saboda ɗa da mahaifi sai Allah,,,, tsaki raliya tayi sannan tace ai saita baka,,,,,,, shiko baba sai jin daɗi yake kaka zai masu wankan talauci,,,,,,


Suwaiba dakel ta samu taja jikinta ta matsa ta ɗauki wayarta,,, wata aminiyarta ta kirawo tace mata don Allah tazo cikin sauri ta taimaketa takaita asibiti kafin ta mutu,,,,, babu wani ɓata lokaci tazo ta tafi da suwaiba asibiti dan cetonta rayuwarta,,,,


Bawan Allah imam malik dakel ya samu ya ƙullu sch uniform ɗin sapna, yayo gida a gajiye,,,,, lokacin daya zo ya samu sapna tana bacci dan haka bai tasheta ba,,,, ya ajiye kayan ya fita,,,,,


Saida ya fito waje sannan yayi tsaye,,, danshi baima san a ina zai samowa sapna abinda zataci ba,,,, laluba aljihunan sa yayi kaf babu ko sisi,,,, ajiyar zuciya yayi tare da cewa lallai yarinyar nan ta tashi babu abinda zataci fa akwai matsala,,,,


Murmushi yayi sannan ya sake dawowa cikin gidan,,,, yana shiga farlo zama yayi ya zabga tagumi,,,,, jijiyoyin kansa gaba ɗaya suka fito farr hawaye ya zubo a idon imam malik,,,,, innaliillahi wa"inna ilaihir raji'un ya faɗa a bayyane,,,, jin muryarsa sapna ta buɗe idonta da sauri,, tare da saukowa tana cewa ɗan uwa miye?""",,,,,


Kusa dashi ta matsa tana ƙara tambayarsa abinda yake damunsa,,,,, murmushin ƙarfin hali yayi irin wanda ke nuna kana da damuwa dake gurgurar maka zuciya,,, idanuwansa da sukayi ja sosai kamar garwashin wutar ƙira,,,


Hannunsa yasa ya jawo sapna jikinshi,,, rungumeta yayi sosai, har tana jiyo buguwar zuciyarsa,,, haɓarsa ya ɗora saman tsakiyar kanta,,, sannan ya sauke ajiyar zuciya sosai,,, wanda hakan da yayi yasa ma sapna jin wani irin baƙon al'amari,,,,, ƙara lafewa tayi jikinsa kamar zata koma cikin zuciyarshi,,,


A hankali imam malik yayi magana cewa kina jin yunwa?"",,, turo baki sapna tayi tare da cewa saima ka tambayeni inajin yunwa ko bana ji?"",,,, miƙewa tayi daga jikinshi taci gaba da zazzaga tsiwa,,, ai kamata yayi ina tashi kawai inga ka shirya man abinci a tebirin cin abin,,, yanxun babu ma abinda zanci kenan ko?"",,, to yayi maka kyau,,,,,, tsaki tayi tare da koma saman kujera ta zauna,,,


wani irin kallon yayi mata sannan yace bari kiji in faɗa maki,,,, akwai banbanci tsakanin da, da kuma yanxun, ni mijinkine kuma bana san rashin kunya,,,, ki kama kanki,, idan ba haka ba zakici na jaki a gidan nan,,,,,,,,


tsaki sapna ta sakeyi amma batayi magana ba,,, imam malik yace kuma duk matar da takeyi ma mijinta tsaki zunibi takeyi,,, wallahi ki daina ,,, danni bana so,,,, idan kuma baki daina ba,,, zanyi maganinki,,, murguɗa baki sapna tayi tare da cewa aisai kayi man na jaki ɗin in gani,,,, ɗan gajeren tsaki yayi sannan ya miƙe yayo inda sapna take zaune,,,,,


da sauri ta miƙe dan tunaninta dukanta zaiyi,,, riƙo hannunta imam malik yayi sannan suka zauna a tare saman kujera,,,,, lumshe idanuwanshi yayi sannan ya buɗesu a hankali ya sauke su akan sapna,,, murmushi yayi sannan yace ke nifa banwani san a ina zan sama maki abinda zaki ci?""",,,, idanuwa sapna ta zaro sannan tace miyasa?""",,,,,


ƙara matsawa yayi kusa da sapna sosai sannan ya ɗora kanshi saman kafaɗarta ya riƙe hannunta cikin nashi yana ɗan murzashi a hankali sannan yayi magana a sanyaye ,,,,,, safeena nidai tunda nake a rayuwa wallahi ban wani san wahalar rayuwa ba,,, tunda na tashi a rayuwa ban taɓa ganin babu ba kullum akwai nake gani, kuma ban taɓa nema na rasa ba,,,,, ni wallahi duk wani iri nakeji safeena ni bamma san a ina zan samu kici ba, ni banajin kaina ke nakeji,,,,, kiyi haƙuri insha Allah zaki sameni mai faranta maki rai kuma zakiji daɗin zama dani,,,, sannan kuma nayi maki alƙawari zan maye maki gurbin mama da baba,,,, ki yadda dani kinji sapna?""",,,,,,,,


Cikin kuka sapna tace wane jin daɗi zaka bani bayan zaka bari yunwa ta kasheni?"",,,,,, cikin damuwa imam malik yace bazaki mutu ba yanxun insha Allah sai imam malik ya jiyar dake daɗin insha Allah kuma saina saki farin ciki,,,,,, 


sapna tace ni farin ciki ɗaya nake so ka bani,,, kawai ka bani inci mai kyau insha mai kyau, ta ƙarasa maganar tana murmushi tare da kallon cikin kwayar idon imam malik,,,, shima murmushi yayi tare da cewa kuma imam malik zai baki kyakkyawan masauki,,,, sapna tace Eye?"",,, yace Eyyy,,, murmushi sapna tayi,, shi kuma yaci gaba da cewa,,,,,


Ki kwantar da hankalinki don Allah,,, sannan kuma ki daina gaya man maganar da zata sa inji wani iri ,,, ki jiyar dani magana mai daɗi da kwantar da hankali daga gareki kinji?"",,,, murmushi sapna tayi tare da cewa insha Allah,,,,,


Kuɗin hannuta ta bawa imam malik ,,,, murmushi yayi tare da ɗora hannunshi saman nata,,, alamar baza karɓa ba,,,, ya ƙara da cewa kuma idan na samu wasu kuɗin zan ƙara maki,,,,,, juyin duniya tayi amma bai karɓa ba,,,, fita yayi wayarshi ya siyar sannan ya siyo mata ɗan abinda zata buƙata na wani lokaci, shima ya siyo madararshi sannan yayo gida,,,,


To haka dai rayuwar sapna da imam malik taci gaba da tafiya,,,, shidai yana lallaɓata amma ita idan har ta nema ta rasa tou pha lallai a gidan babu zaman lafiya,,, idan dai kaji sapna tana ɗaga murya ta duba bata samu abinda take so ba,,, to ganin haka ma yasa imam malik daya ga wani ya kusa ƙarewa kafin tayi magana zaije ya siya ya ajiye mata,,,,,,


Hankalin baba yakai maɗigar tashi dan rashin ganin sapna, duk inda yasan zaiga sapna babu inda baije ya nemata ya rasa,,,, kuma yana nemanta sosai har yanxun bai haƙura ba,,,,,,


Suwaiba kuwa bayan ta samu sauƙi, tasa layar ɓata,,,, ma"ana ta gudu abinta,,,,, shi kuma fahat yaje ya samu baba ya bashi haƙuri,,,, dan yasan babane kaɗai zai gano masa suwaiba ita kuma ta haɗashi da iyayenshi,,,, dan haka baba da fahat aka koma sabon gida,,,,,,,,


Sapna da imam malik zaune a tsakar gida suna wanki kayan sawarsu,,,, imam duk yabi ya jiƙe jikinshi sharaf da ruwa,,,,  kana ganin yanda yake wanki kasan bai iya ba,,, amma saboda fitar sapna tace  dole sai sunyi tare,,,,, da wutisyar idonshi yake kallon sapna,,,, amma idan ka gani zaka ɗauka hankalinsa yana cikin bokatin wanki ne,,,,,


cikin damuwa yace sapna nifa na gaji da wankin nan ,,,,, wallahi hannuna ciwo yakeyi man,,,, sapna tace to ai sai ka tashi kayi shanya,,, cikin sanyi yace to,,,, miƙewa yayi ya fara shanya kayan,,,,, ita kuma tana ɗaurayewa,,,,,,


Suna wankinsu suna fira,,,,, sallamar dady ta dawo da hankalisu suka zubawa ƙofar gidan ido lokacin da dady yake shigowa,,, cikin tausayawa dady ya kalli imam malik, sannan kuma ya kalli sapna,,,


Da sauri sapna ta gaishe da dady,, ya amsa,,, imam malik ma rusunawa yayi ya gaisheshi,, dady ya ansa,,, sapna ce tace dady ka shiga mana,,,,, dady yace to,,, itace tayi gaba dady yana bin bayanta,,,  bayan sun shiga dady ya zauna,,,,,,


Sapna taje ta kawo mashi ruwa da lemo,,,, godiya dady yayi ,,, imam malik ne ya shigo farlon,,,  ya wuce ciki ya sako kaya sannan ya fito parlon shima ya samu kujera ya kame,,,,,,,,,,


Bayan dady yasha ruwan ne, ita kuma sapna tana kicin dan samo ma dady ɗan abinda zai taɓa,,,, dady ne ya kalli imam malik yaga duk ya rame yayi wani iri dai,,,,,, cikin rashin jin daɗi ya gyara zamanshi tare da cewa imam miye yake damunka ne?""",,,,,,,


murmushi yayi tare da taɓe bakinsa sannan yace dady mi ka gani ne?"",,,,,,, dady yace kayi rashin lafiya ne?"",,,, girgiza kai yayi alamar A, A, dady ya gyara zama tare da cewa gobe kaje office,,,, a daidai lokacin da sapna ta fito daga kicin riƙe da flet a hannunta,,,,,,,


Imam malik yace A, a, a daidai lokacin da sapna ta durƙusa gaban baba ta ajiye flet ɗin,,, imam malik yace gaskiya dady ni na gama aikin police gaskiya,,,,, dady yace miyasa ?"" gyara zama imam yayi sannan yaci gaba da cewa haka nan bana so kawai ,,,,, sapna ta kalli imam malik da niyar yin magana ya harareta,,,, dole tayi shiru,,,,


Dady yace ni zakayi ma zuciya?"",,,,,, taɓe baki imam malik yayi sannan yace babu wani zuciya kawai dai bana so,,,, dady yace to yayi maka kyau,,,, makullin motarshi ya ciro ya wurga mashi tare da cewa gashi nan ga motar nan a waje,,,, imam malik yace wallahi bama buƙatar motar ko mashin mun gode,,,,,, 


Yana faɗin haka ya miƙe yabar farlon,,,, bayan ya fita ne,,, dady ya ciro kuɗi masu yawan gaske ya ajiye a saman kujera,,,,, miƙewa yayi ya fita shima ba tare daya sake magana ba,,,,,,, bayan ya fita ne,,, yasa yara sukayi ta shigowa da kayan abinci ko madarar imam malik da yake amfani da ita dady ya sauke mashi mai yawa babu adadi,,,,,,,


Dady kuwa a ƙofar gida ya samu imamu yayi masa tatass, sannan kuma yace ya koma aiki,,, imam malik yace dady bana so ina jayayya nidai gaskiya bana so kawai,,,, dady yace to mi zakayi ne?"",,,, yace akwai zan samu wani aiki insha Allah,,,,, dady yace to Allah ya bada sa'a,,,,, imam malik yace amin,,,,,,,


Bayan dady ya tafi imam malik ya dawo gida,,,, lokacin ita kuma safina ta fito daga wanka,,,, da sauri ya matsa kusa da ita yana cewa bazan yadda ba,,,, kawai daga na fita sai kiwani je ki kama ki wani yi wanka?"", yana maganar ne yana mata wani irin kallo mai shiga cikin ɓargon jikin masoya,,,,,, murtuke fuska sapna tayi tare da cewa naje nayi wanka,,, taɓe baki imam malik yayi tare cewa ni kike cewa kinje kinyi?"",,,, ke bakijin magana dai ko?"",,,,,,,,


sapna tace yanxun don Allah ance kaje aiki sai kace baza kaje ba,,, imam malik yace bazaki gane ba,,, aike yarinya ce,,, adaidai lokacin da yake janta suna komawa cikin toilet ɗin,,,,,,


Wanka yayi itama ya ƙara wankota fess kamar haƙorin makka a bakin mai tsafta,,, wato kunsan shi haƙorin makka idan yasha wanki ƙyalli yake yana walƙiya,, to haka ya wanko safna sai walkiya takeyi, yana rungume da ita a gefenshi,,, bansan abinda sukema dariya ba,,, saidai ta kalleshi tayi murmushi,,,,, ɗaki suka shige,,, shine yaɗan murza mata mai sama sama,, shima yaɗan murza kaɗan,, sannan ya zura jallabiya ya tafi masallaci dan gabatar da sallah magrib,,,,


Imam malik bai shigo gida ba, saida yayi sallah isha'i, sannan ya taho gida,, cikin farin ciki,,,,,, yana shigowa farlo kicin ya shige,,, madararshi ya ɗauko da glasscup ya nufi ɗakin sapna,,,,


"Yar rali! "yar rali!! "yar rali!!!,,,,, baba ne yake ta kwaɗawa raliya kira,,, da gudu ta fito dan jin dalilin daya sa baba yake mata wannan firgitaccen kira mai kama da akawo mana ɗauki jama'a,,,, cikin damuwa baba yace wallahi anyo waya daga Abuja kakan safina bashi da lafiya,,,,yana maganar yana zaro idanuwa kamar mazuru yaga mage,,,, wai duk abinda mukeyi gobe goben nan muje da safina,,, dan yana san ya bata saƙo, ajiyar zuciya baba yayi sannan yace nifa kada tsohon nan ya buɗa bai bawa yarinyar nan saƙonta ba,,, ya kika gani?""" raliya tace gaskiya ne,,,,, 


baba yace to ba komai yau ɗin nan zanje wurin Abubakar ince ya rufa man asiri ya nuna man hanyar da safeena tabi daya koreta daga gidanshi,,,,, raliya tace to babu damuwa,,,, baba ya fita ya fige motarshi ya nufi gidan Abubakar,,,,,,,,,, wato dadyn su imam malik,,,,,,,,


Lokacin daya shiga ɗakin sapna tana kwance saman gado hannuta saman cikinta,,,,, kinyi sallah isha'ine?"" imam yake tambayar sapna,,, a daidai lokacin da yake zama a gefen gado,,,, jan jikinta tayi ta matsa kusa dashi ta ɗora kanta saman cinyarshi ta kwantar da kan nata sannan tace mashi Eh,,,,


shafa gashin kanta yayi sannan ya zuba madararshi ya fara sha,,,, ɗago kai tayi tana kallon imam ,, gira ya ɗaga mata tare da kashe mata ido ɗaya,, da sauri ta maida kanta ta kwanta danjin datayi kamar jinin jikinta ya ƙare,,,, murmushi yayi a daidai lokacin daya ajiye kofin,,, kama kan sapna yayi ya juyota tana kallonshi wani irin gajiyayyen kallo yake sauke mata tare cewa yarinya zakisha ne?"",,,,, murmushi sapna tayi tace A, a,,, yace babu wani kisha kawai daɗi,,,,, yaɗan yi ɗah, ɗah, ɗahɗahɗahɗah yayi da harshensa alamar akwai daɗi,,,, yanda yayi abunne yasa sapna taji jikinta ya mutu,,,,,, a hankali ta maida kanta ta kwanta,,


murmushi yayi sannan ya ɗauki madarar yaci gaba da sha,,,,, ƙara kallonshi sapna tayi murmushi yayi sannan yace kina sha gaskiya tashi kisha,,, tashi tayi zaune saman gadon,,,, matsowa yayi da ita kusa dashi sosai sannan ya matsa da kanshi kusa da fuskarta,,, haɓarta ya kama ya ɗago suka haɗa ido,,,, murmushi yayi a daidai lokacin daya kai bakinshi daidai saman lips ɗinta,,,,,,,,


Duk jijiyoyin jikinta suka ansa,,,,, da gudu suka fara tafiya dan kai saƙonni ga saura gaɓoɓin jikinta duk wani ɓargo na jikinta dan suma suji yanda sapna takeji,,,, ƙara riƙe kanta yayi da hannuwanshi bibbiyu sannan ya haɗa bakinshi dana nata,,,, a hankali ya riƙa ɗura mata madarar bakinshi,,,, lokaci guda jikin sapna ya ɗauri rawa,,,,,,,, dan bata taɓajin irin wannan taken ba,,, shi kuma bai saketa ba,,,, yaci gaba da jagwalgwala ta,,,, ganin karatun nasu ya girmi rubutu na,,,,, nabi bayan baba,,,,,,,


Kai shiga gidan nan kace ana sallama da mai gidan,,,, baba ne yake tura yaro ya kira mashi dady,, yaron yaxo zai wuce mai gadi yace koma, koma dan bindin uwarka,,,, yaron yayo baya da sauri,,,,,, baba yace kai ya akayi ne?"",,,, mai gadi yace bazaije ba kuma idan ya sake zuwa anan saina sare wa banza ƙafa,,,,,


A zuciye baba yayi wurin yana zuwa yaci gaba da dukan mai gadin babu ji babu gani,,, dan baba gani yake kamar mai gadin nan zai hana mashi samun saƙon hannu kaka, danji yake kafin goben kaka zai mutu ne,,,,,, dady ihun mai gadi yaji dan haka cikin sauri yayo waje da gudu da bindiga a hannunshi,,,, ganin baba yasa dady ƙaraso da sauri tare da cewa kai usman miye haka ne?"",,,,,,,


baba sakin mai gadi yayi tare da halbinshi da ƙafarshi,,, sannan yayi kan dady tare da cewa don Allah ina safeena,,,,, kai tsaya dady yace tana gidanta,,,, baba yace ina ne gidanta?""",,,, dady yace gidan aurenta mana,,,, wani luƙeƙen zagi baba ya ciko bakinshi dashi sannan ya ɗirkawa uwar dady,,,,, baki dady ya rike tare da cewa ni kake zagi haka?"",,,, baba yace ba kai nake zagi ba,,,,, uwar wanda ya auri safina,,,, dady yace ai imam malik ne,,,,, kaiiiiiiiiiiiii,,,,,,, baba ya faɗa cikin ƙaraji da rawar baki sannan yace kutumar ubanka,,, wane ɗan matsiyaciya ne ya haɗa auren ɗiyara da matsiyancin ɗanka?""",,,,


Dariya dady yayi sosai sannan yace kaje ka sami imam ka tambayeshi,,,,,, baba yayi kan dady ya shaƙe mashi wuya,,, yana kuka,,,, cikin kukan yake cewa sai an sakar man "yata,,,, ƙara kecewa da dariya dady yayai sannan yace ai ba nine mijinta ba,,,, imam malik yana can ,,, dady yayi mashi kwatancen gidan tare da cewa kaje kaga idan zaka iya dan nima nayi na haƙura,,,,,, amma kila kai a dace,,,,,


ai baba bai bari dady yakai ƙarshe ba,,,, ya juya ya jige motarshi yaja yayi gaba,,,,,,, yana tafiya dady yace banza shashasha,,,,, imam malik yafi ka taurin kai,,,, Allah yasa saiya gama zane maka fata banza sannan yasan ko wayen sapna ne kai,,, dady ya gyara ƙwalar rigarshi tare da cewa shima ɗayan sakaran da baya da waya,,,,,,,


Kai lallai sapna taci gidansu yau dai imam malik ya kashe bakin tsiwa,,, ƙiri ƙiri sapna ta kasa ta haɗa ido dashi,,,, shiko yau yana cikin farin ciki,,,, sapna jiki a kunyace aka wani ja jiki aka nufi toilet,,,, shima binta yayi sukayo wanka,


bayan sun dawo ɗaki ne,,,, ya cire bedsheet ɗin ya canja wani,,,, ita kuma sapna ta saka kayanta hayewa tayi saman gado taci gaba da baccinta abinta,,,, shi kuma jallabiyarshi ya zura ya ɗauka zanin gado ya nufi toilet,,,,,,,,,,,


Wanke zanin gadon yayi, bayan ya gama ya fito waje don shanya zanin ne yaji ana buga ƙofa kamar za'a ɓalleta,,,, saida ya gama shanyawa yaje bakin ƙofar ba tare daya cewa waye ba ya buɗe ƙofar,,,,,,dan yaga waye yake ma ƙofar gidan sa wannan dukan na rainin hankali?"" bayan ya buɗe ne, yaga baba, dan haka daga baba har imam malik kallon juna sukeyi,,,,,,,,,,, kowa yi ma kowa kallon kallo yakeyi,,,

⚜ *BRILLIANT WRITER'S ASSO* 🖊


*Je suis fier BRILLIANT WRITER'S ASSOCIATION Nous aimons nos fans oú qu'ils soent Adorons tous fans* ❤


*RASHIN RABO*


*MEELAT MUSA*


*60-62*


***


*I*mam malik ne ya fara magana cewa yadai?"""" baba yace ina neman gidan safeena ne,, gyara tsayuwa imam malik yayi tare da shafa ƙeyarshi amma baiyi magana ba,,,,


Baba yace ko bakaji na ne?"",,, imam maik yace inajin ka,, amma kafin injika kai waye ɗin sapeena?"",,,, baba ya daki ƙirjinsa tare da cewa ninan ubanta ne,,, ni haifi abata,,, imam malik yace ai duk wanda ya haifi ɗiya mace ko namiji suna gida sun adanasu kuma suna basu tarbiyya daidai gwargwado,,,,


Baba yace kai kar kayi man rashin kunya, ni ko ubanka nafi ƙarfinsa bare kai kayan banza,,, murmushi imam malik yayi sannan yace kaida babana daban abinda ya shafini dakai daban,, kana tambayar safeena nace maka ba'anan take ba,,,,, baba yace to bani hanya,,,,,,


Imam malik yace kaje ina ne?"",,,,,baba yace idan na sake magana saina kasheka da mari wallahi,,,, kaga man shegen yaro,,, ɗaure fuska imam malik yayi sannan yace wallahi kaci albarkacin safeena,,, danni ba'a marina,,, kuma ba'a faɗa za'a mareni dan haka kiyaye harshenka saboda gaba,,,,,


Yanda imam malik yayi abun ne,,, yasa baba jin faɗuwar gaba,,,, imam malik yaci gaba da cewa kafin ka shiga gidana saika faɗa man miyasa kake neman safeena?"",,, bayan kaine ka koreta daga gidanka,, kuma ka kunna mata wuta,,, ai ba'anan ya kamata ka nemeta maƙabarta ya kamata ka fara tafi dan kai mata ziyara,,,,,


Cikin sanyi baba yace itace tace maka na ƙonata da wuta?"",,, imam malik yace ko ɗaya ni banma taɓa magana da ita ba'a abinda ya rabota da gidansu ba,,, nine nayi bincike na gano hakan,,, kuma ina santa tana so na dan haka mukayi aure,, baba idan kayi gigin faɗar cewa zaka raba auren,,,,,,,,  ya nuna baba da yatsa hawayen idonshi suka fara ambaliya yace akwai fa matsala,, ya ƙarasa maganar yana taɓe bakinsa,,,,,,


Baba bin imam malik yayi da kallo a daidai lokacin da imam malik yake cewa shiga muje,, yana nuna mashi da hannu,,, baba jiki a saɓule yabi bayan imam malik zuguzugu,,, suka shiga a farlo suka zauna,, imam malik ya kawo mashi ruwa da lemo,, sannan ya zauna suka gaisa,,,, 


imam malik ne yace ya'a akayi ne baba?"",,, baba yace ina safeena take ne?"",,,, miƙewa imam malik yayi ba tare da yayi magana ba, ya nufi ɗakinta,,,,, safeena kuwa da tun dataji ana buga gida ta farka daga bacci,,, jin maganar baba a farlo yasa ta sakin fitsarin tsaye,,, imam yana shiga ɗakin da gudu tazo wurinshi tana kuka,,,,,,


Cikin damuwa yace na siyo maki mana,,, a kicin na ajiye in ɗauko miki ne?"",,,, girgiza kai sapna tayi ,,, tare da cewa bashi nake so ba,,, riƙeta imam malik yayi a jikinshi sannan yace miye?"",,,, cikin kuka ta nuna mashi ƙasa,,, kalla yayi yaga ruwa a kwance,,,, yace kene kika zubar?"",,,, girgiza kai tayi alamar A, a, yace nine?"" ya nuna kanshi,,, tace ni nayi fitsari,,, idanuwa imam malik ya zaro yace fitsari kuma?"" safeena?,,,,,,,


miyasa sai kiyi fitsari anan bazakije toilet ba?",,,, murguɗa baki tayi tare da cewa wallahi maganar baba naji na tsorata,,, yace miyasa zakiji tsoro?",,, keda zakiyi farin ciki baba yazo sai kiyi damuwa?"",,,, ki canja kaya ki samemu a farlo,,,,,


Zai fita ta riƙo shi da sauri,,, cikin kuka tace ka jirani kada ka tafi,,,, ni yanxun zan canja da sauri,,,, goge wurin ɗan uwa kada yace zai shigo ya gani,,, zama yayi a gefen gado yana cewa gaskiya na gaji tun safiya kike sani ai a gidan anan sai kace wani yaronki,,,,


sapna tace haba kaiko goge mana,,, na yafe maka bama zan anshi kuɗin break ba gobe,,, murmushi yayi sannan ya miƙe ya nufi toilet,,, ruwa da towel ya ɗauko yazo ya gyara wurin,,, tana gama saka kayan shi kuma ya gama,,,, kusa dashi ta matso tare da riƙe ƙugunta, kai baka san wasa ba,,,, bani kuɗin break ɗina,,,,


yace bazan bada ba,,, safeena tace gaskiya sai ka bani,,, yace wanda yasa kika ce inyi maki aiki,,,, kullum sai kisa inyi maki abu kice bazaki ansa ba,,, kullum saikin ansa,,, ƙarashigewa jikinshi tayi tana cewa kafa bani abuna,,,, murmushi yayi yasa hannunshi a aljihun jallabiyarshi ya ciro kuɗin ya bata,,, yana cewa kuma Allah goben bazan raka ki sch ba,,, tace naji nasan hanya zanje dakai na,,,,, yace kuma ko an tashi Allah bazanje ba, tace naji,,,,, kuma insha Allah bazan dafa maki abinci ba,,, zaki dawo kiyi abinki,,,,, murmushi sapna tayi sannan ta maida mashi kuɗin a aljihushi,,,, dariya yayi sannan ya fita itama bin bayanshi tayi,,,,,,


Aikin sapna kenan,,, sai tace yayi sharar farlo ya cire cikin kuɗin break ɗinta,,,, yayi mata wankin uniform,,, zata biyashi,,, bani abinci a baki zan biyaka,,, yiman kaza kaza,,, wai tunda baya da aikinyi ita ta daukeshi aiki,,, haka take gyargyarashi,,,, amma sai yayi haƙuri,,, wani lokacin ma idan yace bazaje rakata sch ba,,, ko yanajin bacci da sauransu sai tace rakani zan biya ka,,, kuma fa bata bashi,,,,, shima kuma dama badan ta bashi yake mata ba,,,,, kawai dai sapna tana bashi tausayi,,,,,,


suna shigowa farlo a inda imam malik ya zauna a wurin sapna ta zauna ta wani shishshige mashi kamar zata koma cikin cikinsa, baba ne yace safeena "yata dawo nan mana,,,, murmushi sapna tayi tare da girgiza kanta alamar A, a, yayi yayi ta dawo amma sapna taƙiya,,, imam malik yace tashi kije kusa da baba mana,,, sapna tace A, a, kusa dakai,,,, shima haƙura yayi bai sake cewa ta tashi ba,,,


baba yace safeenata,,, ya gida?"",,,, idanuwa sapna ta zaro tare da cewa safeenarka?"",,,, a ranta tayi maganar,,,,, amma a fili sai tayi murmushin yaƙe tare da cewa baba inayini,,,, baba ya ansa,,, shiru na wani lokaci amma baba ya rasa ta ina zai ɓullowa lamarin,,, dan haka kawai sai yace dare yayi da safe zai dawo,,,, miƙewa baba yayi don haka kowa yabi bayanshi danyi mashi rakiya,,,,


Da safe sapna tayi shirinta cikin schuniform nata,,, ta tashi imam dake bacci yace ta tafi anjima zaizo,,,, sapna tace sai an tashi zakazo?"",,,, cikin muryar bacci yace ummm,,,, tace to na tafi,, yace Allah ya bada sa'a a daidai lokacin daya ƙara lulluɓewa da bargo yana cewa kija gidan idan kin fita sai nazo,,, tace to,, 


Raliya ki tashi muje mu ɗauki safeena mu wuce Abujar don Allah idan munje kinyi mata bayani da kanki kila tafi saurarenki,,, danni wallahi wani iri nakeji idan na ganta,,, duk sai inji kunya ta kamani wallahi,,,,, raliya tace nikam gaskiya bazanje ba, ɗiyarka ce,,, kuma nayi imani zata saurareka,,, duk yanda baba yayi su tafi da raliya amma taƙi,,,, dole ya haƙura ya wuce gidan imam malik,,,,


Fahat kuwa yana ganin fitar baba ya sulale ya shige ɗakinsa,,,,, makullin motarsa ya ɗauka,,, da wasu kuɗaɗe daya samu da kayan baba da takalma duk ya tattara yaje ya jibga a motar yabar gidan,,,,,


Saida yasha baccin sa mai isarsa sannan ya tashi,,,,, toilet ya shiga ya wanke bakinsa sannan ya shiga kicin,,,, dankalin da safeena taci ta rage ya ɗanci yasha madara,,,, sannan yazo ya fara gyara gida ko ina da ko ina,,,ya gyara ya goge fesss kamar mace tayi macen ma wanda tasan sirrin gyaran gida, dan haka sukeyi,,, ranar makaranta shine yakeyin komai ya dafa mata abinci,,,,, ita kuma ranar da babu makaranta takeyin komai da komai,,, wanki kuma suyi a tare,,,,,


Saida ya gama sannan yayi wanka,,,, ganin lokaci ya tafi sosai yasa shi ƙara hanzari ya shirya a gaggauce,,, bayan ya gama da sauri ya fita dan sapna ta kusa dawo yaje su taho tare,,,,, yana fita a ƙofar gida suka haɗu da baba,,,,,, amma sai imam malik yayi kamar bai ganshi ba ya wuce,,,,, baba ne yace imam ,,, amma saiya basar yaci gaba da tafiyarshi,,,,,


Da sauri baba yabi bayanshi tare da riƙoshi,,,, a sikwane imam malik ya juyo tare dayi ma baba kyakkyawan kallo hannunshi yasa a daidai inda baba ya riƙe shi ya cire hannun daga wurin tare da cewa ni ba'a dafani,,, ya akayi ne?"",,,,,,,, baba yace ina safeena take ne?"",,,, imam malik yace safeena safeena safeena komai safeena haba wai mi zata baka ne?"",,, baba yace kakanta yake nemanta shine zamu tafi yanxun dan baya lafiya kuma baya cikin halin iya magana saboda ciwon nasa yayi tsanani,,,,,


ita idan taje mi zata bashi ne?"",, inji imam malik,,, cikin damuwa baba yace kayi haƙuri yana san ganinta ne,,,, imam malik yace bazata je ba,,,, dan nine nake iko da ita,,, kuma nace bazataje ba,,,,, cikin ɓacin rai baba yace sai inci uwarka kuma in ɗauka ɗiyata inyi tafiyata,,,, murmushi imam malik yayi da gefen bakinsa tare da cewa ba'a man hayani saman kai,,,, yayin da kake man ihu a kai a lokacin izzata take tashi bana so inyi maka abinda zakaji babu daɗi,,,,, safeena bata zuwa,,,,,, yana faɗin haka yayi gaba da ɗan sauri dan yasan idan har aka tashi baije ba,,,, tayi ta mita har gari ya waye,,,,dan ko bacci tayi ta farka sai tace baije ya ɗaukota ba saboda baya santa,,,,,, bafa a mashin ba kuma ba'a motar ba,,,, yaje su taho ƙasa saboda rashin aikinyi irin nashi shima,,,,,


Tun daga nesa ya hangota ta taho sai fushi takeyi,,,, da sauri ya isa wurinta ya anshi schbag inta tare da mata sannu,,,,,  tace wallahi nasha baza kazo ba har nayi zuciya,,,, yace Allah ya baki haƙuri nima bacci nayi sosai banma daɗe da tashi ba,,,,, to mika girma man ne?"",,,, yace ai dana tsaya girki kuma da bazanzo ba,,, cikin faɗa ta fara yarfa hannuwa tare da cewa ai wannan babu adalci tunda safe danayi kalaci ni banma wani sake cin komai ba,,, amma saboda baka kauna na haka zan koma sai kuma nayi zaman jira kaman wani girki,,, amma ai ka iya buɗe frig kasha madara,,,, yace ni wallahi inama da inda zanje banda lokacin maki girki ,,,,  kuma babu abinda zan siya maki dan bani da kuɗi,,,, kuturmar,,,,, tace bata ƙarasa ba imam malik ya kasheta da mari,,,,,, yana nuna kanshi nine zaki zaga?"",,,, cikin kuka tace bafa zaginka zanyi ba,,,, kawai zance kutumar dumma du ne,,, tsaki yayi tare da wurga mata jakar yace kinja ma kanki,,


Duƙawa tayi ta ɗauka jakar tana goge hawayen idonta,, cikin kuka tace kayi haƙuri,,,, tsaki yayi tare da cewa babu abinda yake damunki sai rashin ilimin addini,,, baki san kalmar da zaki faɗawa miji mai laushi ba,,, kullum kinajin ke daidai kike dani,,,,, to bari kiji in faɗa maki ni nine na ajiyeki,,, kuma ya zamar maki dole kiyi biyayya mani dan na gaji da iskanci wallahi duk maganar data zo bakinki sai ki faɗa man saboda rashin kunya,,,, ina iya bakin ƙoƙarina bakya gani wannan ai hauka ne,,,,,,, karatu kanki farau,,,,,


wasu ma haka suke zuwa makarantar basu ci komai ba,,, kuma su dawo basu samu ba,,, saboda basu dashi,,, su mutuwa sukayi?"",,,, to daga yau kin daina makarantar sai ki zauna a gidan kiji idan zaman gidan daɗi ne,,,, tunda karantu ya zama hauka,,, kullum kina ƙara girma da shekaru amma hauka cikin kanki tana ƙara ƙarawu,,, tsaki yayi tare da fiddo makullin gidan ya wurga mata yayi gaba,,,,,


cikin kuka ta duƙa ta ɗauki makulin,,,, sannan tabi bayanshi da sauri tana bashi haƙuri,,, har suka iso gida baiyi mata magana ba,,, a ƙofar gida suka sami baba, dan a tunanin imam malik baba ya tafi tun ɗazu,, safeena ta gaisheshi,,,,, ya ansa,,,


sannan yaci gaba da kora mata jawabi,,, da faɗa mata rashin lafiyar kakanta,,,, baba yaci gaba da cewa kuma yace duk abinda ake yau muje,,, kallon imam malik safeena tayi shi kuma hankalinsa yana kan wayarshi,,, amma duk abinda suke cewa yana jinsu,,, kusa dashi ta matsa cikin tsoro sannan tace kaji zanbi dady muje,,,,, banza yayi kamar baiji abinda tace ba,,,


hannunta ta ɗora saman wayar tare da ƙara maimaita mashi zanje,,, ta saman idonshi ya kalleta sannan yace bazakije ba,,,,,,, jiki a saɓule ta juya wurin baba tace baba yace bazanje ba,,,, cikin hayani baba yace wannan wane irin iskanci ne?"",,,,,,, taɓe baki imam malik yayi tare da cewa ke yarinya buɗe mana gida,,,,,,,,  baba yace anƙi a buɗe banzan gida,,, ni zaka faɗawa kana da gida,,, gidan banza gidan wofinka,,,,, murmushi imam malik yayi a daidai lokacin da safeena ta buɗe gidan,,,,,


Jan hannunta yayi suna ƙoƙarin antayawa cikin gidan baba ya riƙe hannu safeena,,,, shima imam malik riƙe yake da hannun nata,,, baba yace kaga man ɗan iskan yaro da wani banzan gashin kanka kamar ganyen bishiyar darbejiya,,, kallonshi imam malik yayi amma baiyi magana ba,,,, baba yace kayi haƙuri don girman Allah ka barta muje tare da ita,,


Ka tausaya ma rayuwarta,,, tunda bata san mahaifiyarta ba ka barta taje ta gana da kakanta kafin shima ya buɗe,,, imam malik yace to sai Allah ya kaimu zan kawota da kaina abujar idan mun shigo zamu nema ka,,,,,,  baba yace ka taimaka muje yau don Allah, imam malik yace wallahi baza muje yau ba,,,,,, baba yace to goben ƙarfe nawa?"",,,,, imam malik yace zamu faɗa maka ,,,,, baba yace to zan jira goben sai mu tafi tare,,,,, 


imam malik yace to bbu damuwa,,, sallama baba yayi masu ya tafi,,,, sapna tana so tayi magana da imam malik amma taga yau kanshi hayaƙi rashin mutunci yakeyi dole ta haƙura ta kame bakinta,,,,,,


Suna shiga ciki sapna wanka taje tayi,,, saida ta shirya sannan ta fito farlo,,, imam malik yana zaune yana kallon boll,, kusa dashi taje ta zauna,,, amma batayi magana ba,,,,, ganin ta zauna kusa dashi yasa ya miƙe ya fice daga farlon gaba ɗaya ma yabar gidan,


Abin baƙin ciki yayi mata amma saita barshi kawai,,,,, babu abinda ta tsinan a gidan tana nan zaune saida a kira sallah ta tashi tayi,,,, har daren sosai imam malik bai dawo ba,,,,, haka nan ta haƙura taje ta kwanta amma bataci komai ba,,,,,,,


Shi kuma lokacin daya dawo gida,,,, sapna tayi bacci dan haka a farlo yayi kwanciyarsa saman kujera,,, bacci bai daɗe da ɗaukarsa ba,,, jayi kukanta,,,,, yiyiyiyiiii tana yi tana jan majina,,,,,, tayi zaune saman gado sai wani firfira idanuwa takeyi kamar bata da gaskiya, tashi yayi ya nufi ɗakin,,,,,, tana ganinshi tayi shiru,,,,, tsaki yayi sannan yace ya akayi ne?"",,,,, cikin kuka tace sanyi nakeji,,, shiga yayi ɗakin ya kwantar da ita sannan ya lulluɓeta da bargo,,,,, hannunshi ta riƙe,,,,,  tare da cewa nagode,,,,, baiyi magana ba ya fice a ɗakin,,,


bai daɗe da fita ba kuma ta tashi zaune taci gaba da kuka,,,,, daga inda yake zaune yace wannan wane irin abune zaki hanani inyi bacci ne?"",,,, cikin kuka tace ɗan uwa wallahi yunwa nakeji,,,, bakaji yanda cikina yake man ba,,, agogon farlon ya kalla yaga 12:35am yace to a ina za'a samu wani abinci a daren nan ne,,, fitowa tayi daga ɗakin tazo kusa dashi ta zauna tana kuka,,,,,, 


tsaki yayi ya kwanta,,,, itama saman jikinshi ta kwanta , tare da cewa ina kaje wai?""",,, yace zance naje,,,,, da zatayi zagi amma sai ta tuna ɗaxu ya mareta saboda zage zagen da takeyi,,,,, cikin kuka tace miyasa kake zuwa zance ne?"",,,,,, ba gani ba,,,,, tayi murmushi cikin kuka,,, yanda tayi abun ne ta bashi tausayi,,,,,, lumshe idanuwanshi yayi sannan ya buɗe su sukayi mata wani iri,,, cikin sigar lallashi tace haba ɗan uwa don Allah nidai ina kaje?""",,,,,,, yace kina ganin kamar ina wasa ne?"",,,, to neman aure naje,,,,, gyara bakinta tayi tare da cewa Allah yasa a kasaka,,,, murmushi yayi amma baiyi magana ba,,,,,,


tashi tayi ta nufi ɗaki tana kuka,,,, ƙara gyara kwanciyarshi yayi yaci gaba da baccinshi abinshi,,,,,,,, itama haka tasha koke kokenta ta gaji tayi bacci,,,,,

⚜ *BRILLIANT WRITER'S ASSO* 🖊


*Je suis fier BRILLIANT WRITER'S ASSOCIATION nos fans où qu'ils soent Adorons tous fans* ❤


*RASHIN RABO*


Jameela Musa


*Kalli masoyiyata,,, kina raina kullum kullum, ina sanki da yawa da yawa,,, ina kaunar ki daɓa daɓa,, kuma ina ƙara dirzazo saƙon gaisuwa ta a gareki aminiyar arxiki,,, Real mai dambu 🥗 ina tare dake kuma inajinki har cikin babban birni zuciyata* ❤


*63➖65*


***


*L*okacin da baba ya koma gida ya samu labari fahat ya kwamashe mashi dukiya da sauran tattalin arxiki saida yayi zawo saboda tsabagen san abun duniya,,,,


Baima san a ina zai samu fahat ba,,, dan gaba ɗaya ya daina zama sai idan yana san kuɗi yake zuwa ya kwashe ya gudu abunshi,,,,


Haka baba yayi ta neman wayar gwamna amma maganar ɗayace suke sake maimaitawa a kashe,,,, haka ya gaji da gwadawa ya kwanta bacci dan tafiya babban birni abuja da safe,,, yana gudun kada ya makara,,,,


Da safe baba shirinshi yayi daga masallaci sallah asuba,, gidan su sapna ya wuto,,, danji yakeyi kamar yayi tsunstu ya ganshi a abuja,,,


Yana isowa ya fara dukan ƙofar gidansu kamar an aiko shi da saƙo,,, imam malik daya dawo daga masallaci yana ƙoƙarin kwanciya yaji dukan gida kamar da gayya,,,, ya kwalawa sapna kira,,,,


A tsiwace ta fito tazo gabanshi tayi mashi tsaye ƙerere kamar arne ya fito wanka,,, kallonta yayi sama da ƙasa sannan yayi murmushi,,,, tare da faɗin Allah ya shirya man ke inji daɗi,,,, ina kwana,,, tsaki tayi sannan tace dan ka gaisheni dama kake man wannan kiran don Allah?"" tana maganar tana ɓata fuskarta kamar taga kashi,,,


Murmushi imam malik ya sakeyi tare da cewa muje inga waye?"",,, zama sapna tayi tana faɗin ni gaskiya bana zuwa tsoro nakeji,,, miƙewa yayi ba tare daya sake magana ba,,,, yayi waje,,,,


Bayan yaje ya buɗe yaga baba ne,,,, tsaki yayi a ranshi tare da faɗin kai wannan ɗan tsoho da fitina yake,,, baba ne yace ashe ma baku shirya ba?"",,,,, imam malik yace ina jirane a kawo mani motar,,,, baba yace wace irin motar ne?"",,,, yace motar da zamuyi tafiya da ita ne,,,, baba yace baga tawa ba?""",,,,,


Taɓe baki imam malik yayi tare da cewa A, a kawai zamuje a tamu kaima kaje a taka,,,, sapna jin imam malik bai dawo ba,,, yasata miƙewa tayi waje,,, da sauri ta iso wurin tana cewa ɗan uwa miye?""",,,,, baba yace uwaki ce,,,,,,


Sapna zatayi magana imam malik yajata sukayi cikin gida,,,, suna shiga parlour yace maza kije kiyi wanka,,, da sauri ta shige ciki,,, shi kuma ya shiga kicin dan samar mata abinda zatayi break,,,


Tana gama wanka ta fito da sauri ta sameshi kicin,,,, yace ya akayi ne?"",,,, yanda ta shigo kicin ɗin a firgice yasa gabanshi ya faɗi,,,, da sauri ya juyo ya riƙeta a jikinshi yana cewa miye?"",,,,, ƙara shigewa jikinshi tayi tana kuka,,,,, cikin damuwa yace wai miye?""",,,,,,,,,,


Cikin shashshekar kuka sapna tace,,, baba ne,,,, yace mi baban yayi?"",,,,,, kamo fuskarshi tayi ganin haka yasa ya duƙo saboda yafi ta tsayi,, daidai kunnensa tayi magana ƙasaƙasa tace baba zaisa ɓarayi su kashe ka,,,,, cikin nuna rashi tsoro yace waye ya faɗa maki haka ne?"",,,,,,


Tace yanxun yake waya,,, tsaki imam malik yayi sannan yace yanxun kin gama wanka ne?"",,,, yayi haka dan kauda maganar dan ya lura sapna tana cikin tashin hankali sosai,,, tace Eh,,, yace ɗauko dankalin ki na gama,,, sapna tace ban iyawa,,,,,,


Ba tare daya sake magana ba ya ɗauki flet ɗin yaja hannunta suka fita kicin ɗin,,,, saida suka shiga ɗaki yace ta zauna,,, zama tayi,, ya ajiye flet ɗin a gabanta,, shi kuma ya fita,,,, bansan abinda yayi ba,,, amma naga yana waya bayan ya gama ya wuce kicin, ɗauko kwalin madara yayi ya fito,,, yana shigowa farlo yaga baba zaune saman kujera ,,, ba tare daya kalli inda yake ba ya wuce ciki,,,,,,


yana shiga ya ajiye madarar,,,, ya shige toilet,,, wanka yayi bayan ya gama ya fito,,, har lokacin sapna tana zaune bataci komai ba,,, kofi ya ɗauka ya haɗa mata tea yace yi sauri kisha,,,,, kayan da zata saka ya fiddo mata,,,, sai kallon imam malik takeyi tana kuka,,,, shi kuma lokaci lokaci yana kallonta yayi mata murmushi,,,,,,


Dan ita sapna bata ma san komai ba,,, ashe idan taji dalilin da yasa baba yake zumuɗin tafiyarsu da batace zataje ba,,, dariya yayi a bayyane dan bata san wace ce raliya a wurin baba,,,, sapna cikin kuka ta kalli imam malik tare da cewa miye?"",,,,,,,,, murmushi yayi tare da cewa ba komai,,,,, itama murmushi tayi,,,,,,


ganin bata da niyar yin kalanci yasa ya matsa kusa da ita,,,, zama yayi tare da fara bata a baki,,, tanaci tana kuka, saida ya tabbatar ta ƙoshi ya tashi yasa kayanshi,,, itama kayanta tasa,,, wani irin kallo yake mata wanda ita kanta bata san ko miye ba,,,,


Saida ya gama komai sannan ya ɗauki wayarshi da kwalin madararshi yaja hannun sapna suka fito farlo,,, ba tare da yayi magana da baba yajata sukayi waje,,,,


ganin sun fita yasa shima ya tashi yabi bayansu ,,,, yana fitowa har imam malik ya shiga mota itama sapna tana cikin motar,,,, baba yace wannan wane irin iskanci ne?"",,,,, kafi ƙarfin kaman magana ne?"",,,, murmushi imam malik yayi tare da cewa ai ka matsa aje ko?"" to muje yau gaskiya zatayi halinta insha Allah,,,,


Baba yace naci uwar gaskiyar,,, murmushi imam malik yayi a daidai lokacin daya ɓalle marfin madarar shi ya ɗaga yana tsiyayawa a bakinshi yana sha yana dariya,,,, jawo sapna jikishin yayi ya kafa mata kwalin a bakinta,,,, tace banasha ,,, murmushi yayi ya riƙe kanta sosai yaci gaba da bulbula mata a baki tare da zare mata ido yace sha,,,,,


Cikin tsoro taci gaba da shan madarar ƙwat ƙwat,,, tana sha,,,, saida ya tabbatar ta shanye duka sannan ya lashe bakinta,,, yana murmushi,, baba yace kai ɗan iska ne ko?"",,,, dariya imam malik yayi sosai har haƙoransa suka fito,,, da hannu damarshi ya riƙe sapna a jikinshi sosai sannan ya tada motar,,,, yana cewa saika taho,,,,,


da sauri baba ya fita,,, yaja motarshi,,, lokacin imam malik yayi nisa sosai,, suna tafiya har yanxun babu wanda yayi magana,,, sai imam malik da yake yawan waya,,,,, lokaci lokaci kuma ya kalli sapna yayi murmushi,,,,, ita ko ta kasa gane miyasa yake mata haka,,, kuma da tazo zatayi magana sai kawai yace yi haƙuri,,,, ya hanata magana,,, har suka kai abuja imam malik yana rungume da sapna a jikinshi,,,,


baba dake bin bayansu ganin sunyi ma unguwar kakansu sapna tsinke ya fara al'ajabi,,, bai gama tunanin lamarin imam malik ba saida yaga yayi ma gidan tsinke,,,,, baba ya fara horn biyyyyyyitttt,,,, imam malik ya kalleshi ta cikin madubi yayi murmushi,,,,,


Imam malik yana isowa bakin get ɗin gidan yayi horn,,,,,, da sauri aka buɗe mashi get ya shige,,,,, yana shiga baba ya shiga shima,,,, parking yayi a wurin da aka tanada don ajiye motoci,,,,, sannan ya fito,,,,,, inda sapna take ya zagaya ya buɗe ya fiddota,,,,,,,, yana riƙe da sapna har yanxun da hannu ɗaya,, bayan motarshi ya buɗe sannan ya fiddo wata rober maltina,, ya miƙa mata tare da cewa sha muje,,,, shi kuma a daidai lokacin da yake zare safar hannunsa,,,,


yana kallon baba yana dariya,,, sapna tana fara sha ta miƙa ma imam malik tare da cewa anshi bana sha babu daɗi,,,, ansa yayi ba tare daya kalleta ba yashanye,,, ya wurgar da robar,,,, yaja hannunta sukayi ciki,,,, baba yabi bayansa yana cewa waikai uwar waye  ya sanka a gidan nan ne?"",,,,,,,


sapna ta kalli imam malik tana kuka tace bakaji babana yana magana ne?"",,,, zaro mata idanuwa yayi tare cewa idan kika sake kallona saina kwakwale maki idanuwa,,,,, sapna taja tayi tsaye,,,, tana juyawa tana kallon baba,,, sai kuma ta kalli imam malik,,,,, murmushi yayi tare da cewa tsoro kike ji?""",,,,,,, 


murmushi yayi tare da cewa yi haƙuri na bari wasa nake maki,,,, wani za'a kwalkwalewa idanuwa,,,, a daidai lokacin da baba ya iso wurin,,,, ya ɗaga hannu da niyar marin imam malik,,,,,,, wani irin kallon imam malik yayi mashi tare da nunashi da hannu amma baiyi magana ba,,,,


Baba yace safeena zo,,,, imam malik yace idan ka sake kiran sunanta saina yanke maka harshe,,, tsohon banza marar mutunci marar adalci marar rabo,,,, wani irin mari sapna takaiwa imam malik tare da cewa kai ashe baka da mutunci babana kakace tsohon banza?"",,,,  wani irin mari imam malik yakai wa sapna har saida ta ɗauke wuta,,,,, ya ƙara fizgota ya sake gagara mata ya dirzazashi mata marin, wani gagararren mari,,, sannan ya matse mata kai da bango yace baki san arxiki ba,,, banda ni yanxun da kina lahira,,,, ina kyautata maki baki gani,,, har nine zaki mara?"",,,, to bari inji in faɗa maki ni mace ko kallon banza bata isa tayi man ba,,,, amma tunda kika mareni yau basai gobe saina datse maki hannu,,,,,


Da sauri sapna ta kalli hannunta,,, a daidai lokacin da raliya ta fito tana cewa waye ya taɓa sapnar kuma?"",,,, baba ya saki baki tare da cewa "yar rali mi kika zoyi anan gidan kuma?""",,,, murmushi tayi tare da juyi,,,,, tace zakasha ruwan sanyi ne?""",,,,,,,, tana maganar tana ɗaga mashi gira,,,,,,


Kallon imam malik tayi tare da cewa kai kuma miyasa ka daketa ne?"",,,, tana maganar tana shegantaka,,,,, baba bai gama tsinke lamarin sa ba,,, saida yaga malam nuhu ya bayyana,,,,,, ƙanƙance idanuwa baba yayi tare da cewa malam nuhu,,, ya akayi ?"",,,, dadyn su sadiq da umar ƙanin dady,,,,,, dady ne yace ma imam malik miyasa ka daketa ne?"",,,, cikin ɓacin rai imam malik yace dady wallahi yarinyar nan ta raina man wayau,,,,, dady yace amma mi na faɗa game da ita ne?"",,,, cikin tsananin ɓacin rai imam malik yace dady marina tayi fa,,, a daidai lokacin da hawaye ya zobo mashi daga idonshi,,,,,,


ita dai sapna binsu tayi da kallo dady ne ya ja hannun ta,,, raliya tace swry sapna na,,,,, dady ya kalli imam malik tare dace mashi ya za'ayi yanxun?"",,,, inda sapna take ya kalla ya harareta tare da cewa mu shiga ciki,,


sapna kwacewa tayi daga hannun dady ta koma wurin imam malik dan bata yadda da kowa ba har yanxun,,,,, tana zuwa kusa dashi ta kalleshi tana kuka,,,,,, kallonta yayi cikin tausaya mata sannan ya jawota jikinshi suka shiga ciki,,,,,,,


suna shiga cikin farlon taron mutane babu adadi,,,, sodoji ne masu sa firgici,,,, kowa ya samu wuri ya zauna,,, baba ma ya samu wuri ya zauna,,, sapna tana kusa da imam malik ta shige mashi kamar zata koma cikin cikinshi,,, wurin yayi shiru,,, difff kamar babu mutane a ciki,,,,, 


Daga ciki tsohon ya fito cikin isa, kana ganinshi kaga tsohon daraja ma'abuci addini,,, zama yayi saman kujera,,,, sannan ya kalli imam malik yace imamu zo nan,,,,,, miƙewa imam malik yayi tare da kama sapna ya miƙar da ita suka matsa kusa dashi,,,,


kaka wannan itace sapeenah,,,, murmushi yayi tare da cewa alhamdulillah,,,, raliya zo nan,,,, "yar rali ta matsa kusa dashi tana kuka,,,, gyara tabarau ɗin idonshi yayi sannan yace don Allah ku saurara mani,,,,, kusa dashi raliya ta matsa ta ɗora kanta saman ƙafarshi tana kuka,,,,, jawo sapna tayi kusa da kaka ta dora mata kanta a saman cinyarshi kamar yanda tayi,,,, hannunshi ya ɗora saman kansu dukansu yana shafawa,,,,,,


Imam malik ya kalli sapna yayi murmushi a daidai lokacin daya ke goge hawayen idonshi,,,,, baba yace malam nuhu wai ya akayi haka ne?""",,,, gyaran murya kaka yayi tare da cewa imamu muna saurarenka,,,,,,


murmushi raliya tayi tare da ɗago kanta,,,, tace ai ba imam malik zaku tambaya ba,,, ni zaka tambaya,,, gyara zaman ta tayi tare da cewa kowa ya saura ,,,,,, ,,,,,,  



Dady ne ya kalli imam malik tare da cewa imam  ka taho da kaset ɗin ne?"",,,,,,, yace Eh dady,,,,,,,,,


Kaka yace yawwa kunna mana mu gani,,,,,,, imam malik ne ya miƙe,,, ya matsa kusa da tvstand yaɗan duƙa daidai dvd ya soka kaset ɗin,,,,, yayin da hankalin kowa na farlon ya koma wurin,,,,,,,,,



Maman sapna ta bayyana ne a jikin hoton kallo ya fara kamar haka,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,

⚜ *BRILLIANT WRITER'S ASSO* 🖊


*Je suis fier BRILLIANT WRITER'S Nos fans où qu'ils soent Adorons tous fans*  ❤


*RASHIN RABO* 


*MEELAT MUSA*


*63➖65*


***


*S*ai kuma hoton raliya,,,,, raliyace take kuka sosai kamar zata mutu saboda kuka,,,, maman sapna ce take goge hawayen idon ta sannan tana bawa raliya haƙuri,,,,


Cikin kuka raliya ta riƙe hannun maman sapna tana cewa ki rufa man asiri yaya don Allah ki riƙe man abinda yake cikin cikina idan Allah ya saukeni lafiya,,,,,


Cikin kuka maman sapna tace Hafsat miyasa?""",,,,, cikin kuka raliya tace yanxun zan faɗa maki dalili,,,,, sunan raliya hafsa,,, data auri baba ta mayar da raliya,,,,


Hafsat,,, wato yar rali,,,, tace kinga mai gida baya lafiya,,, wato mijinta,,, kuma kowa yasa ido akan cikina,,,, kowa nemana yake ya kasheni,,, saboda shi bai taɓa aihuwa ba,,,, kuma kowa tarin dukiyar daya tara yake mawa,,, sai akaina Allah ya bashi rabo,,,, kuma nayi shawara dashi yace in gudu inje in ɓoye,,,, idan Allah ya saukeni lafiya in bada ɗan ko ɗiyar a boyeman har ya samu sauƙi,,,,


Yaya ki taimaka man don girman Allah idan na aihu sai ki ajiye man abunda na samu,,,,, cikin kuka wanda ake ganin itace maman sapna ta fashe da kuka tare cewa nikam hafsat kin sani a tsaka mai wuya,,,, ki rufa man asiri,,, amma idan namiji kika samu zan riƙe maki idan ta mace ce gaskiya bazan riƙe ba,,, saboda baya san "ya"ya mata,,,,,


Kinga kwanan nan na haifi "ya mace amma bata zo da rai ba,,,, bakiga yanda yayi ba,,,, cikin kuka raliya tace ki rufa man asiri,,, ranar naka sai naka,,, ranar dole ma sai naka,,,, cikin kuka tace to Allah yasa namiji zaki haifa,,,,,


Amma idan rayuwa ta kasance akaina fa?"",,, ma'ana na mutu,,,, murmushi raliya tayi tare da cewa,, bama zaki mutu ba insha Allah,,,, wannan hoton da nasa ake mana,,, saboda rayuwa,,, idan nice na mutu wannan ne shedar da zaki nunawa baban abinda zan haifa,,, kuma kema dan idan gaba mijinki bai yadda ba wannan hoton shine shedar da zan nuna ma kowa ya gani,,,,


Murmushi marigaya wato maman sapna ta da,,, tayi,,, raliya tace to,, muje wurin wata ƙawata,,, ita zata sa maki abunda za'a gani kamar ciki,,,, 


Hoto ya ɗauke,,, ma'ana ya ƙare,,, malam nuhu ya ɗora,,,,, kamar haka,,, bayan ita Allah ya jiƙanta tazo ta sameni tayi man bayani tare da roƙona alfarma in rufa mata asiri,,, inbar "yar uwata ta zauna a gidana,,,,, kuma tayi man bayani na gamsu sosai,,,,,


Gamai ɗakina nan ,,, kallo ya koma wurin matar malam nuhu,,,, tace haka akayi ,,,  daren data fara jin nakuda ta faɗa man,,,, dagani har mai gida mun shiga damuwa dan yanda zamu shiga gidan usman mukai mashi wannan abinda za'a haifa,,,,


mai gida,, wato malam nuhu shine yaja shi sukayi tafiya,,,,, ni kuma ina tare da ita,,,, tana aihuwa,,, na nannaɗe jariri da kuma uwa,,, kuma nasa tsumma na kwashe jinin kaff, na goya safeena gata nan muka tafi,,,,,


lokacin dana je ita tsohuwa wato inna tana bayi,,, na shiga da sauri na ajiye uwa a ƙasa,, nakuma zuba jinin Akuyar da malam ya yanka,, ya tara a bokati,,, ina ajiye safeena nafita,,, nan nabar ita halima tana kuka,,, wato maman sapna data rasu,,,,


Cikin tashin hankali baba ya miƙe tsaye tare da cewa ƙarya ne,,, ƙarya ne dan uwarka ,, baban sapna na gaskiya yace idan ka sake magana a wurin nan saina harbeka da bindiga,,,,, dan naji duk irin azabar daka ganawa ɗiyata,,,, kwana a zaure,, konata da wuta,,, ka barmin ɗiya ta balbaɗe ta shiga, duniya,,,, idan har ɗiyarka ta gaskiya ce zaka mata haka?"",,,,


Lokacin da labarin haihu ya sameka,,,, sai kayi ta murna gwamna yaxo,,, shida ka kyautata ma,,, bayajin ƙanƙa,,, da kuɗi da "ya"ya ba'ayi masu muguwar riƙo,,, yau daka kyautatawa safeena haƙiƙa dasai kaji daɗi,,, amma da yake babu rabo,,, dan rayuwa baka san mai cetonka ba,,,,


Raliya tace ni kuma lokacin da malam nuhu ya faɗa man halin da safeenata take ciki,,, hankalina ya tashi sosai,,,, dole nasa mijina ya sakeni,,, kuma shine yayi man hanya na aureka,,, nasha idan an maka nasiha zakaji ashe har a ranka baka ƙaunar safeena,,,,,,


lokacin daka watsa mata fetir da ashana,,, hankalina ya tashi tun anan zaka gane safeena ɗiyata ce,,,, saboda yanda na shiga cikin bala'i da ruɗanin duniya,,,,, ninan da kaina naje nace ma Alhaji Abu nasan sapna zata zo wurinshi idan tazo ya ƙoreta,,,,,,, kuma nace ya tsanan ta,, kada ya bari ta zauna tare dashi, dan yanda usman ya ƙonata nasan idan yasan tana wurinshi zai iya sawa aka kashe man ita gaba,,,,,


Lokacin da gidi ya ɗauki sapna shi kuma sai ya nuna zai wulaƙanta man rayuwar ɗiya,,, dan na lura shima munafiki ne,,,, nice nan nasa Alhaji Abu yasa imam malik ya ɗauki sapna,,, nace su gudu,,,, 


Daya ɗauki sapna kuma nace ma Alhaji Abu ya kama usman ya rufeshi yace ya gudar mashi da ɗa,,, kamar yanda yake faɗa saiya ga bayanshi,,,, haka muka tsara nace ma Alhaji Abu yaman wulaƙanci sosai ,,, kuma kada ya nuna yasanni,,, 


Haka nayi ta zurubtu a gidan una neman a bani mijina,,, kuma komai da malam nuhu muka shirya shi,,,, kuma "yar uwata babu abinda ya kasheta illa tashin hankali da masifar da zata fuskanta,,,,,,,


Babanmu yayi fushi da ita sosai,,, saboda ya hanata auren usman dan tun farko bai yadda da ɗabi'unsa ba,,,, amma ta kafe kai da fata saida ta aureshi,,, shine ya hana mu zuwa wurinta,,, kuma yace kada tazo mashi gida,,,, da matsala ta taso man nice na nemi inda take naje,,,, na nemi alfarma,,,,,


Kuma da baiwar Allah sai rigamu gidan gaskiya,,,, "yar tsohuwa ta ɗauki sapna,,, tayi ta wahala da ita,,,, tsagaitawa raliya tayi sannan ta mayar da dubanta wurin tsohon mijinta tace mai gida,,, ga ɗiyarka,,, sapna tashi kije wurin babanki,,,,


wani irin ihu baba yayi tare tashi yaje ya shaƙe wuyan malam nuhu,,, baban sapna ne yasa sodojin da suke wurin suka kamashi,,,, raliya ta miƙe tsaye tare da dakatar dasu,,, sannan tace nice nan kuma nayi ma mijina waya nace na gaji da zaman gidan ka wahala,, ya turo sodoji suxo su tafi damu ayi komai dan a wuce wurin,,,  kaji dalilin zuwanmu abuja,,,,,, a wancan lokacin,,, nace ma kaka yace an bayar da saƙo sai safeena tazo za'a bada,,,,


Kai kuma da yake alashe money ne,,, cikin daƙiƙan lokutta kaje ka samota,,, dariya tayi sosai sannan taci gaba da cewa,,,  idan zaka tuna lokacin da kake cewa safeena taka,,, ai na faɗa maka magana ganewa ke bakayi ba,,,,,,,,


Shi kuma imam malik abinda yasa nace ma Alhaji Abu ayi masu aure tare saboda imam yace man sapna ta faɗa da bakinta tana sanshi,,,, kuma ni nace ma Alhaji Abu shi kuma ya gwada man imam malik ta hanyar sashi ya ajiye aiki,, dan shima inga idan da gaske yana santa,,, dariya tayi sosai sannan tace bawan Allah kuma sai ya yadda shima,,,,


Kallon baba sapna tayi sannan tace baban sapna ga sirikinkan nan fa,,,,, nidai yanxun usman kafin ka tafi gaskiya ka sawwaƙe man aurenka na gaji,,,


Wani irin ihu baba yayi tare da sulalewa ƙasa somamme,,, baban sapna yace a fitar dashi,,,, haka akaja shi akayi waje,,,,,


Hafsat wato raliya ta matsa kusa da sapna,,, ta kamota,,, ta matsa da ita kusa da babanta,,,, inda imam malik yake zaune ya kalla sannan yace zonan siriki na,,,, imam malik ya tashi ya matsa,,, dadyn sapna ya haɗasu ya rungumesu sosai,,, yana godiya ga Allah,,,,,


Kakane yace kuma wannan abun bazai hana inyi maki hukuncin da nayi niyya ba,,, murmushi hafsat tayi tare da cewa ba komai baba nidai tunda "yata ta dawo alhamdulillah,,,,, malam nuhu yace wai ita hafsat miya sa usman bai santa bane?"",,,, kaka yace ai lokacin tana oxfort ne,,,


Amma yana da labarinta,,, shi yasa taje mashi as raliya,,, ita dai halima haka Allah ya ƙaddara mata,,, baƙin cikin namiji yakaita lahira, tunda babu yanda banyi da ita kada ta aureshi ba,,,, amma haka Allah ya tsara,,,,,


Bayan an gama dadyn imam malik yace zai tafi,,, kaka yaso su kwana amma suka ce tafiya zasuyi,,,, dadyn sapna kuɗin zunzurutunsu naira miliyan 50,, ya bawa dadyn imam malik, da kuma umar ƙaninshi,,,, sannan sukayi godiya sosai suka tafi,,,


dadyn sapna kuwa sai waya yakeyi ma danginsa Allah ya dawo da sapna,,, daman tun kafin zuwanta ya faɗa masu,,,,, dadyne yace ma hafsat zamu tafi da sapna,,, tace wallahi babu wanda zai tafiyar mata da ɗiya,,, duk wanda zai ganta yazo nan ya ganta,,,, haka ya matsa taƙi yadda dole ya haƙura,,,,,


malam nuhu ne yace Alhaji ni kuma gaskiya kada usman yayi man wani abu,,, murmushi yayi tare da cewa bazai maka ba,, insha Allah dan horon da zan mashi yafi gaban ya sake mugun hali,,,,,, shima malam nuhu da mai ɗakinsa haka dadyn sapna yayi masu harsahin kuɗi,,,, wanda saida malam nuhu ya kusa zaucewa,,,,,


Dadyn sapna saida ya shafa kan sapna sannan yaja hannun imam malik suka fita tare,,, raliya tasa aka ɗauki su malam nuhu dan mayar dasu gida,,,,,,


bayan kowa ya tafi farlo ya rage daga sapna sai hafsat wato raliya,,,,,,  sai kaka faɗa yayi tama hafsat sosai,,, hafsat dai bata sake magana ba,,,, sai kuka takeyi sosai,,,,,,


Kaka yace wannan ai ganganci ne,,,, yanxun banda wannan shedar waye zai yadda ?"" ga yarinya harta kai shekara shashidda,,,,, wannan sakaci ne babba,,,, kuma banda iskanci kika sa mijinki ya sakeki saboda kawai kije wurin ɗiyarki?"",,,,,,


Haka dai yayi ta faɗa amma hafsa tayi shiru,,,,, faɗa yake sosai cikin kuka tace to ai da yadda baban sapna nayi hakan,,, kikayi hakan banza?"",,,, gata bata mutu ba,,, kuma da kin barta a wurinki ma babu abinda zai sameta,,,,,,,


Hafsat tace lokacin nan fa da yayi haɗarin nan baya iya tashi kuma baya iya komai,,,,, ai shine ma yace man in gudar mashi da abinda yake cikin cikina,,,, dan yana ganin yanda ake so a salwantar masa dashi,,,,, kaka yace wallahi kin bani haushi,,,,,, tsaki yayi sannan yace ma sapna taje tayi sallah taci abinci ta kwanta bacci,,,,,


Hafsa ta tashi taja hannu "yar ɗiyarta suka tafi ciki,,,,, kaka yabi su da kallo,,,, dan lallai uwa uwace,,,,,, suna shiga ciki hafsa ta zaunar da sapna a bakin gado,,,,, tana ƙara rungume ɗiyarta tana kuka sosai,,, ita dai sapna batayi magana ba,,, haka hafsat tasha kukanta ta gaji,,,,


sannan tace ma sapna taje tayi wanka ga kayana ta saka,,, miƙewa tayi ta shige toilet ba tare da ta sake magana ba,,,,,,,,



lokacin da usman ya farfaɗo,,, wani irin ihu yayi ,,,,,, tsaff abinda yayi ma sapna ya fara dawo mashi sabo,,,, idan yayi mata abu yana ɗaukar fahat yana ririta shi,,,,, ya siyo mashi wancan ya bashi wancan,, ya gina mashi rayuwarshi ya ilimantar dashi,,,,


Ya sangartashi shi,,,, ya wulaƙanta sapna ya fifita fahat akan sapna,,, yau gashi ɗan yayanshi ya mashi rashin kunya,, amma sapna ta mareshi kuma mijinta ne,,,,,, duk wulaƙanci da yayi ma sapna amma tana hana a mashi rashin mutunci,,,,,,


amma fahat kullum cikin sace mashi kuɗi yakeyi,,,, yana mashi rashin mutunci,,,, 


Lallai dana sani da banyi ma sapna haka ba,,,, dana riƙeta da mutunci da lumana,,, lallai da tana kallona a matsayin uba,, abinda nayi mata lallai shine zai nuna mata lallai ba nine babanba,,,,, nayi mata horon yunwa na hana ta taci abincin gidana,, wani irin ihu baba yayi tare da cewa lallai wannan shi ake kira *RASHIN RABO* 


ni bana san "ya"ya mata,,, an bani namiji shima ba nawa ba,,,, ɗiya macen ma ba tawa ba,,, lallai,,,, goge hawaye idonshi yayi tare da cewa kuma raliya tace saina saketa,,,,,, ga kuma wani babban *RASHIN RABO* dama na sani da raliya tace in saka sapna makaranta dama na sakata,,,,, wayyo Allahna na shiga ukku,,,,,,


haƙiƙa sapna na azabtar da ita,,, na horata da nau'in azabobi iri iri,,, taya ma za'ayi ko nace nine babanta ta yadda?"",,,, wani irin ihu yayi tare da cewa wai wannan wane irin *RASHIN RABO* neeeeeeeee!!!


sapna tana fitowa daga wanka,,, hafsat tace mata maza ki shirya mijinki yace yau zaku tafi,,,, sapna tace ummana miya sa bazan kwana ba?"",,,,, tace sapna yace zakije sch gobe,,,, kiyi haƙuri ku tafi kawai,,,, ba dan sapna taso ba ta shirya,,, kayan da ummanta ta bata ta saka,,,,,,


tare suka fito farlo,,, imam malik da Abbanta suna nan zaune,,, kusa da imam malik taje ta zauna,,, bai kalleta ba,,, tace ɗan uwa wai miyasa baza mu kwana ba?"",,,,, shiru yayi kamar baiji abinda tace ba,,,,,,


Kallon Abbanta tayi sannan tace Abba miyasa baza mu kwana ba?"",,, murmushi yayi tare da cewa kiyi haƙuri kuje mijinki yace baza ku kwana ba,,, zai kawo ki ranar juma'a,,,, ummana wai?"",,,, murmushi tayi sannan ta kalli imam malik tace imamu ko ka barta ta kwana don Allah?"",,,, murmushi yayi sannan ya shafa kanshi,,, Abba yayi murmushi tare da cewa barsu kawai suje,,,,


Umma taso sapna ta kwana amma imam malik yace A, a, haka ta haƙura,,, da suka tashi tafiya,,,, Abban sapna kuɗi dai ya bawa imam malik cikin wani ɗan ƙaramin akwati,,, Abba yace sauran bayani sai sun dawo juma'ar,,,,, 


Umma tanaji tana gani imam malik ya ɗauki sapna suka tafi,,,, saida motarsu tabar gidan sannan suka koma,,,


bayan sun koma farlo Abban sapna yayi ma kaka sai anjima,,, sannan ya fito, sodoji suka rufe masa baya har wurin motarsa aka buɗe ya shige,,,, sannan motaci masu yawan gaske suka rufa mashi ba,, haka suka fice daga gidan,,,,


Gida ya rage daga hafsat sai kaka sai kuma masu gadi,,, sai karnuka da suke kuka,,,,,

⚜ *BRILLIANT WRITER'S ASSO* 🖊



*RASHIN RABO*



*MEELAT MUSA*


*69➖🔚


***


*H*mm bawan Allah baba yasha tashin hankali sosai,, dole tasa shi yaje ya nemi suwaiba,, dan fahat ya ƙarar dashi dukanshi,,, baya da komai,,, shi fahat ma ƙoƙarinsa ya siyar da gidanshi yake yi,,,


Wannan dalilin ne yasa baba ya nemi suwaiba ya haɗa ta da fahat,,,, lokacin da fahat yaga suwaiba duka dai zagi tasha shi kamar bala'i,,,, haka ya tisa ƙeyarshi ta gaba ta kaishi wurin wanda ta satoshi,,,,


Itama waccan ɗin saida fahat yayi mata shegen duka,, sannan suka ɗunguma zuwa gidan iyayenshi,,, bayan sunje suka shiga sashen uwar gidan wanda itace ta sace fahat ita kuma jin baƙin cikin an haifi ɗa namiji wannan dalilin yasa ta saceshi da sunan a kasheshi,,, wadda ta bawa suwaiba fahat,,, ce tayi mata bayan suwaiba shine dalilin ba'a kashe fahat ba aka bawa suwaiba shi,,,,


Ihun da matar babansu fahat keyi yasa duk wanda yake gidan saida ya fito,,, dan fahat duka yake mata bana wasa ba,, bayan kowa ya haɗune,,, suwaiba ta fara bayani sannan ƙawarta,, sai ita matar babansu,,, babansu fahat yayi kuka sosai daga baya kuma ya godewa Allah daya nuna mashi ɗanshi,,,


Shima fahat yaji daɗi ganin gidansu gidan "yam gayu ne,,, haka suwaiba aka tashi sumi sumi aka tafi,,,,, suka bar fahat a gidansu,,,,


Haka shekaru sukaci gaba da tafiya,, imam malik ya zama kicima yayi kuɗi na tashin hankali,, ita kuma sapna an gama secondrysch,,, dan haka an dawo gida,, sai nunawa juna so akeyi,,,


Bayan gama secondrysch inta da sheƙara ɗaya Allah ya sauki sapna lafiya,, ta samu yaronta,,, kai anfa cashe sosai,, Abba yayi hauƙa da kuɗi sosai,, dadynsu imam malik shima haka ya haukace yayi ta ɓarnar naira,,, shima giwar ba'a barshi a baya ba,,, ranar suna aka sakawa yaro suna muhammad,,,


Shi kuma baba ya samu "yar matarshi yayi aurenshi,,, suna zaune lafiya qalau,, ita kuma suwaiba ya saketa,,, dan cewa yayi da tana da halin kirki da bata bari yayi ma sapna azaba ba,,, lokacin da baba ya saki suwaiba itama tayi kuka na tashin hankali tare da cewa itama tayi *RASHIN RABO* data riƙe sapna da amana,, da sapna ta taimaketa,, yanxun ma ganin sapna wahala yakeyi,,, dan zuwa gidansu ba zuwan yara bane,,,,


Haka rayuwa taci gaba da tafiya,,,, lokaci lokaci sapna tana zuwa kaduna ta duba baba tayi mashi Alkairi sosai,, haka kuma take leƙa malam nuhu,,, shima tana mashi kirki sosai,,,,


Sapna fa yanxun anyi ilimi ansan darajar miji,, kuma tasan maganar da ake faɗawa tasan wanda ba'a faɗa mashi,,, imam malik yana jin sapna sosai har cikin ransa,,,,,


Wai baku cewa ina umma ne?"",, hafsat ko ince maku "yar rali,,,, ita kuma an maidai aurenta da baban sapna,, dan haka duniya tayi masu daɗi,,,, 


Shekarar muhammad 3 sapna ta ƙara haihuwar ɗanta,,, kai shima dai an molaƙe sosai,, yaron yaci  sunan baban sapna,, wato Aliyu,,, kada kuce man usman fa,,, danshi uban riƙone marar adalci,,, suna kiran yaron da Aslam,,


Bayan shekaru da dama,,, burin sapna ya cika na zama cikakkiyar likita,, dan haka bawai kuɗi takeyi ma aiki ba,, tanayi ne dan taimakon al'umma,,, domin duk abinda zataje ta nema akwai daɓa daɓanshi a gidan aurenta da kuma gidan iyayenta,,,,


Saƙon da kaka yake cewa za'a bawa sapna sai yanxun ya bata shi,,, wanda ta haifi ummanta ce ta bayar da zunzunrutun kuɗi masu yawan da kwakwalwa bata ɗauakr lissafin,,,,


Sapna tana taimakon mutane sosai,,, jin irin kuɗin tashin hankalin da sapna tayi yasa suwaiba ta nemo ta,, taje gidanta,,,


daga farko hanata shiga akayi,, dakel ta samu aka barta,,, lokacin da sapna taga suwaiba bata ganeta ba,, saida ta bata bayani,,, sapna ta tausawa suwaiba sosai kuma haka tayi mata bulala da kuɗin da sukata ta kasa magana,,,


haka ta tafi tana jinyar zuciyarta dan sauran kaɗan ta buga,,,,, data koma gida tayi kuka kamar ranta zai fita,, tace data sani ta riƙe sapa da amana ,, amma ta kyautatawa fahat gashi idanma taje gidansu saida yasa masu gadi suyi mata Eyho,,,, suwaiba tayi kuka tare da danasanin wannan jibgegen *RASHIN RABO* data tayi,,,,,,,,


bayan shekara goma,, sapna tana da yaranta biyar huɗu maza mace ɗaya,,, kuma tace ita ta tsaya da aihu daga haka,,, yaran fa suna ganin gata sosai,,, dan duk imam malik yace basu karatu nigeria,,,,,



To haka dai rayuwa take ubangiji yasa mu cikin masu *RABO* Allah ya rabamu da *RASHIN RABO* duniya da lahira,,,,,, Ameeeeeeeeeeeeeeeeeeeen



*Alhamdulillah*


*Alhamdulillah*


*Alhamdulillah*


*Jameela Musa*


*Meelat Musa*


sai kuma mun sake haɗuwa 🙌🏻


🔚

          🔚


🔚


Copied By

HAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT) 

(ADMIN OF ADMINS)

        (admin 

   Hayat hausa novels


adsense 2 here
Share:

Burodin ayaba

Barkanmu da ganin wata mai girma tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin burodin ayaba. Za a iya gwada wa a lokacin yin buda baki ko kuma don yi wa bakin da aka gayyato shan ruwa. Kamar yadda muka yi muku alkawari , za mu cigaba da kawo muku nau’ukan girke-girke daban-daban.

Abubuwan da za a bukata:
•Fulawa
• kwai
• Suga
•‘Baking powder’
•Ayaba
•Madara
•Bata
Hadi:
A samu ayaba biyu a kwabasu da cokali mai yatsu, sannan a zuba fulawa a kwano sannan a zuba ‘baking powder’ da suga da madara sannan a kwaba. Bayan haka, a zuba bata kamar cokali biyu sannan a kwaba sosai. Sannan a fasa kwai biyu da wannan kwababben ayabar a cikin fulawar da aka yi masa hadin suga da sauransu. Sai a gauraya don su kwabu. Sannan sai a dauko na’urar gasa burodi a zuba sannan a saka a gidan gasa burodi. Bayan mintuna arba’in da biyar, sai a cire.
Za’a iya cin wannan hadin burodin da shayi bayan an sha ruwa. Kuma za a iya aika wa makwabta domin su dandana sabon salon burodi. A sha ruwa lafiya.


MAJNOON hausa love novels


Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune, Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage, Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake...... Read more

Mutane uku ne a duniya

1. Wasu kamar guba ne gudunsu akeyi. 2. Wasu kamar magani suke, ba a nemansu sai ta baci. 3. Wasu kuma kamar abinci suke, akullum dole a nemesu. Ya kai dan uwa mai daraja, kayi kokari ka zama cikin wadanda akullum ake nemansu saboda amfaninsu. Allah yasa muna cikin wadanda ake nema akoda yaushe, Albarkar Annabi {S.A.W}

Talla a Gidan novels


Litattafan da Muka Kawo Muku

Tunatarwa

ANNABI (SAW) yana cewa:

Idan lokacin (Kiyaamah) yakusa, ayyukan (Alkhairi) zasuyi karanci, ROWA zata YAWAITA, FITINTINU zasu YAWAITA, haka kuma Alharju zai YAWAITA. Sai sahabbai (RA) sukace Menene Alharju? Sai Annabi (SAW) yace: Kashe-kashe. (Bukhari ya ruwaito a 6552). Ya Allah ka Kare mana IMANINMU, ka kubutar damu daga fitintinun zamani.
Kasa mucika da imani.

Kada ka rama cuta ga wanda ya cuceka!

kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka kai kayi hakuri zaka samu abu biyu sakamakon hakan *na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. *Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.

Visitors

Translate

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Contact Form

Name

Email *

Message *