Shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wato Hausa Novels Blog a kyauta wanda muke kawo muku littatafai daga marubuta daban daban. dandalin hausa novels | dandalin hausa novels| hausa novels facebook | completed hausa novels on wattpad| hausa novels wattpad | hausa novels pdf | hausa novels world | hausa novels documents | dandalin littafin hausa | duniyar hausa novels | dandalin littafan hausa | home of hausa novels facebook | hausa novels world | littafin hausa zalla

Saturday, 5 December 2020

TAKARI COMPLETE HAUSA NOVEL

adsense here
TAKARI COMPLETE HAUSA NOVEL

 [10/3, 14:27] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈  

   👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣

                  1⃣

👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣👣

                  BY

    

          🐎  ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

          🐎  HUGUMA  WRITERS🐎

Kir, kir kir kir kir, 

 fanfom bohle kakeji, Yara ne da matan aure keta diban ruwa a bakin bohol kamar yadda akasaba akowani kauye. 

   Yarinyace yar shekara goma sha daya ke saman karfen tana buga ruwan yan uwanta biyu sunata faman tarawa suna kwashewa gefe. Dahaka har suka gama ciki duk wani kaya da suka zo dashi gurin.

     Wani dan gidan laka suke shiga da ruwan duk rigan jikin su yajike kunsan duk ruwan yana komawa cikin roban da suke daukan ruwan.

  Randa ne irinta laka suke  zuba ruwan aciki duk bakin randan ya fashe , harda faci akaimay da siminti . akwai shukan Iccen shuwaka a,tsaye gefen randan ruwan .

  Inna yar kulu tafito daga cikin dakin lakan da saboda tsufa har ya dan duka kamar zai zube, amma haka yar kulu ke rayuwa acikin dakin tare da yan marayun diyan ta su hudu hafsat fatima mariya sai Abdul wanda suke ce ma datti saboda sunan mahaifin babansu ne akasa ma yaron.

   Kai amma yau hafsi kunyi saurin samun ruwa akan lokaci, hmmm inna aikin san wanan aikin yar gidan kice , fadima . Wlh layin su kuburah taci, tace atabau mun riga su bada ashirin din mu dole aka kyale mu, muka diba aida layi ko kusa damu baizoba. Fadima ce ta fado cikin gidan dawani katon bahon ruwa akanta tana haki ataimaka asauke ta. 


   Inna yar kulu na fada tasauketa, ; haba fadima wanan bahon yafi karfin ki wlh , ai wanan sai ya buda maki gaba ,

bahon waki,ka dauko ne ? Wlh na Asiya ce na dauko ka kafin diba yazo garesu, Don Allah yar nan kibar daukan roba mai girma kada ciwo yakamaki banda kudin kaiki ko wurin mai agangama balle asibitin gari 

   Dagudu ta koma donta maida roban da ta dauko na ruwa.

  Inna tagama kwasan tuwo taba kowa nashi uku kwanon su guda datti nashi daban sai inna ita kadai tsugunne abakin murhu bisa wani dan guntun kujeran katako , tanayi tana kara masu miya a tasu kwanon.

    Duk talauci da maraicin su yar kulu da yaranta baisa tai masu sakaci da karatun addini ba dana zamani haka suke zuwa karatusu ,babu mai taimaka masu sai Allah sai yar sanar, saida kamun koko da inna takeyi haikan garin ansanta da wanan sanar basai yaranta sunje yawon talla,ba.

      Yau ba akaratun boko sungama aikinsu tunda safe suna sauri sutafi makarantar islamiyar su don malam bugunsu yakeyi idan an makara.

    Gefen hayar su ta islamiya su kaga wasu mata su uku a tsaye suna gaisawa , cikin ladabi su hafsat suka gaida matan , suka tafi.

  Kai wanan matar akwai karfin hali ,wlh inji Ramatu daya daga cikin matan da ke tsaye agefen haya wakenan? inji ; Gajiye , yar kulu mana matan marigayi sani mai shago ai yaran tane  nan suka wuce mu taki bari kowa yadaukar mata ko guda ne,Wai a cewar ta itace zata tarbiyar da diyanta don haka ko aure taki yi waisai yaran sun girma , sunyi aure da farko har andauki yar babban amma saboda nacin yar kulu kan wai sai yarinya tayi ilimi dole akadawo mata da yar ta , yanzu duk dangin  ta sun kyaleta da abinta dama mijin ba,asan asalinshi ba, Itace uwa itace uba.

        

       Yar kulu tana da tauhidi azuciyar ta yarda da Allah da kuma duk wani kaddaran da yasamay ta , hakan yasa batasa wa,ranta wani kwadayin duniya ba ita dai akullun taga Allah yabasu abinda zasu ci su sha basai ta tara wani abin duniya ba.

     Kwadayinta su samu dan ilimin zaman duniya data lahira, koda sunyi aurene su iya karanta ko yar wasika ce   

      Saidai mutanen kauyen suna dauka wani girman kaine irin nata , ita wacece da zata hana yaranta talla. 

              GAJIYE takasa zama ta kasa tsaye yanzu yar kulun da tasani itace da wa"yan nan yaran haka jari gida ba,asan yadda za,a sarrafa suba tawani nacewa wai ita yara na karatu ba,talle wata sana,a kwarara. 

   Aiko gobe dole in koma kano wurin hajiya in ji yara yan shekara nawa take bukata idan naga da  irin su acikin yaran yar kulu tau nikan abin yazo min da sauki wlh basai na shiga yawon bida ba ga abu a gida,,,,,,   ,,,,,, ,,,,  


  🐎 ZEE  MAKAWA 🐎

       🐎HUGUMA🐎 🐎WRITERS🐎

[10/3, 14:35] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                     2⃣ 

            👣👣👣👣👣 

              👣👣👣👣👣

                           BY 

       🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWa🐎

     🐎.   HUGUMA WRITERS 🐎


    KANO KANO,,,,  KANO koda maikazo an fika,,, hmmm inji kanawa .

   Gajiye ce zaune saman tabarma an aje mata kwalban coca cola mai sanyi ga shinkafa da miyar naman shanu tanaci, ,,,,,,,

    Hajiya mai sharwali nazaune agefenta suna hira ,Gajiye kinsan wancan karon ba abin kware, kika kawo min ba shiyasa banison kara harka dake ,,,,,,,,,

   Hmmm hajiya kenan aikinsan wanan karon akasi akasamu insha Allah wanan karon 

  ,a samu matsalaba.

            Hajiya mai Sharwali wata matace mai zaman kanta a garin kano , tana harko ki kalakala na bidan kudi, 

       Cikin irin hakane suka hadu da gajiye a,motar haya, tasamo yan mata guda biyu daga jahar katsina. Gajiye ce ke cewa hajiya wa"yanan yaranki ne kuwa sai take fada mata ai , aikatau tadauko su daga kano . Nan ta dinga ba Gajiye labarin yadda harka tasu take da irin kason da ake ba duk wata dillaliya, hajiya tace saidai wanan karon ita ba dillancin zatayi ba daukan kanta ne zatayi don ita ma zata fara nata harka ce.

        Sun, kulla harka da gajiye har ta ke kawowa hajiya maisharwali yan mata daga sashe sokoto.

     Tunda gajiye tadawo gida take tunanen hanyar da zata fara bullo ma al,amarin.

     Saboda tasan idan har taci nasaran daukan wa,"yanan yaran na yar kulu lalai zata caba so sai 

      Don ita a,nata haukan duk yaran biyu masu wayo zata kwashe ma yar kulu, taje taci riban duniya dasu. Sam bata damu da halin da yar kulu zata iya shiga ba.


   Yar kulu na,ta,tsan kamun kokon ta taji sallama ta ansa ,,,,, Saidai bata gane , kowace bakurwar ba , don yar birnice , "tashigo ba irin matar kauyen ,  su na majidadi

bane ; wanan "tawaye dayawa  

    Bayan sun gaisa Gajiye tace nasan diyar kulu bata gane ni ba ko? 

 Gaskiya ban gane kiba inji Inna ,,,,,, nice Gajiye  diyar dada makwabtar ku na kusa da massalancin sarki, a,a,a,aikuwa nagane yanzu kice min abokiyar fada ta itace kuwa.

     Nan aka shiga hiran yaushe rabo tsakani,,,  inda Gajiye ta labta karyan ai aure takeyi a kano harda yaranta, biyar, tazo ganin gida, Ida takawo tsaraba taba inna , su sabulun waka dana wanki sai manshafawa da su turare da turmin zani guda,,,,,,, da kyat inna ta karbi kayan bayan  Gajiye ta nuna bacin ranta . jiki a sanyaye Inna ta karbi kayan tare da godiya .


  Sanu sanu shakuwa mai karfi yashiga tsakanin inna da Gajiye don tace ma inna yar kulu sati biyu zatayi ta koma .

    Ko yaushe inna tai abinci zata ba hafsat ta kaiwa  Gajiye nata , har sati biyu ,yacika ta koma ,Inda ta fito. 

  Tare da tunanen yadda zata shawo kan yar kulu nan gaba.

     Inna yar kulu , nata kokarin kula da iyalenta tarbiyan su da duk wani kulawa da yadace uwa taiwa danta. 

       Su ko mutanen gari gani sukeyi girman kaine kawai yasa yar kulu sa "ya" yanta yin karatun boko ba talla, sai bakar wahala take yi a,kansu.

     Hafsat ta dan girma don duk wani kiran diya mace ya bai,yana mata, 

  Hafsat bata da hayaniya  sosai,  ita farace irin farin yaran fulanin kauye na a,sali batada jiki sai gashin kai ja . Idan tana tafiya kamar ta kalle .

  Fadima bata kai hafsat fari,ba amma tadan fi hafsat jiki kadan tanada round face , fadima bata magana amma akwai ta da zafin nama tafi hafsat kuzari sosai , ita,ko mariya da datti zubinsu guda.

   Mahaifin su yarasu tun da aka haifi datti da wata biyu , yayi hatsarin mota a hanyar shita zuwa cikin    garin sokoto sarin kayan tiredan shi. 

  Tun alokacin rayuwa ta canza ma iyalin marigayi malam Adamu mai tireda danshi, mutumin kirki wanda yasan darajan iyalin shi.

      Yazo kauyen dogon daji  daga yola ya biyo wani dan uwanshi da suke sanar fata tare daga karshe sai Allah yai zaman shi nan kauyen dogon daji ta cikin jahar sokoto .

     Allah ya hadashi da inna sukayi aure shine dalilin zaman shi nan kauyen har Allah ya karbi ranshi.

 

     🐎ZEE MAKAWA🐎

   🐎 HUGUMA 🐎🐎WRITERS🐎

[10/3, 14:39] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈KANO TO JIDDA✈✈✈

        👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                       3⃣

            👣👣👣👣👣

                          BY

        🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA WRITERS🐎


        

        Bayan sati uku Gajiye tadawo kauyen dogon daji da sunan tazo bukin wata diyar yar uwanta, 

    Gidan bukin yacika gwargwadon yadda ake buki a kauye ,

   Tuwo ne na shinkafa sai miyar alaihu da kulili , shimata da yara keta kwasa suna ci. Su Gajiye sune kirjin buki manyan yan birni zaune take ta hakince a saman tabarman roba

   Akawo mata wanan akawo mata wancan ,,,, Saidai ita duk hankalinta baya guri kofa take kallo taga shigowar yar kulu.

    Sai bayan sallah la,asar inna yar kulu ta iso gidan bukin abisa gaiyatar da Gajiye tai mata jiya da dare bayan ta iso harda ankon taimasu , su uku nafitar buki.

        Jamma,a da dama wurin bukin suna mamakin zuwan yar kulu wurin wanan buki saboda ita ko haihuwa kayi da dare take zuwa taimaka barka,. Idan kuma aurene za,tazo taima Allah sa albarka ta,tafi. 

        Yau, sai gashi tazo harda anko kayan da Gajiye taimasu. koda yake mutane sun san akwai zumunci da zaman  makwabtaka atsakanin su tun asali.

       Anci ansha a,wuri tuwo da zobo mai zafi ko sanyi babu amma haka a,ke ta wasoso

     Inna na gefe guda saman tabarma duk a takure take saboda bata saba shiga jamma,a ba haka.

       Uhmmmm wai inna "yan mata ne inji Gajiye, tana tambayar yar kulu ?

    Aiko suna gida lafiya lau kina dai min rowan yaran nan, yar kulu 

   A,a,a habadai Gajiye in,banda abin,ki aike uwarsu ce ta yaya zan maki rowar su ,,,,,,

  Haba ai,sai Gajiye ta, gyara zama saboda tarkon ta yafara kama wa,

  Ainaga ko wurin bukin baki bari sunzo ba yar kulu, ai,kamata yayi a, ce suna nan tunda gani a gari.   Cikin kunya da kamala inna ke magana aikinsan basu da lokaci irin haka tunda suka dawo diban ruwa suka wuce islamiya sai gab da magriba suke dawowa,,,,,

  Kinga ko basu da lokacin zuwa nan gurin amma insha Allah kafin kitafi zanturo maki su, su gaisheki,,,,,,,,,

     Hira sosai mata ke,tayi wurin kamar yadda Gajiye da inna da wasu mata ke gefe guda suna tasu hiran.

    Acikin hiran ne Gajiye kece ma inna akwai diyar mijinta zata haihu insha Allah inta haihu zuwa sabon wata zata zo ta,tafi da su hafsat suje mata buki,,,,,,,,,

    Dam,,,,,,, gaban yar kulu ya fadi aje birni da yaranta ina sam baizai sabu ba,,,, ko a mafarki ma balle ai in yaranta sunje birni to kafansu kafanta ,,,,,, saboda birni ai a can yara ke lalacewa ,,,,,,, 

       Gajiye nata magana amma sam inna bataji ba tana can tana tunane a zuciyan ta.

     Hmmm komai wayyon ki sainaci kudin diyar ki inji Gajiye acikin zuciyar ta don ta kulla inna tai nisa da tunane kuma fuskan ta ya nuna bata amince ba,,,,,,

   Bayan taro yawatse Gajiye taba inna kayan buki wadatacce wai takaima yaranta

   Ramatu, Gajiye ta bida don ta taimaka mata da batun yaran agurin innna.

   Bayan buki da kwana daya Ramatu ta shigo gidan inna ,

      kai kai kai maraba da Ramatu ke ce , yau agidan namu, 

    Nice yar kulu hanya ce tabiyo dani nace bari nashigo in maki yaya gajiyar buki .,,,,,,  

     Aiko nagode wlh 

   Bayan sun zauna andan yi hira ,Can Ramatu  ta kawo zancen zuwa birnin yaran inna.

      Aiko yar kulu kiji 

dadi wlh, Gajiye yar birni zata dauki diyanki zuwa birni da ma ace nice aida yanzu nafara kuri agari ,,,,   

  Take innna ta canza fuska aiko Ramatu tashiga aiki zuga ,,,,,,,,,,,,


      🐎ZEEE MAKAWA🐎

  🐎HUGUMA WRITERS🐎


[10/3, 16:22] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                       4⃣

                        BY 

   🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA WRITERS🐎

    


      Zaune yar kulu take suna cin abinci da yaranta.,,,,,  Yau ma kamar kullun nasiha take masu akan zaman duniya.

        A duk yanayin da suka tsinci kansu su dinga hakkuri da duniya don duk abinda kai hakkuri zakaci riban agaba,,,, Fadima ta dago kai ta kalli mahaifiyar tasu tace inna koda an zallunce mu kina nupin kada mu rama sai muyi hakkuri,,, 

   Kware kuwa inji inna ko baki son Allah ya rama, maki, ne da zaki rama da kan ki ????.

  A,hankali tadago ta,kalli inna tace,Inaso tafadi a sanyaye.

   Murmushi inna tayi ta kauda kai so da kauna da tausayi yaran nata yakara shiga zuciyar ta, Tundai fadima wace tafaye zafin acikin su,,,,,

       Daidai wanan lokacin itama Gajiye tana cikin mawuyacin halin da matsinancin tunane a kano,,,, tana tunane hanyar da zata bullo ma inna ,,,, Don tasha Alwashin wanan karon intazo dongon daji da yaran inna zata dawo kano. 

     Saboda lokacinda sukayi alkawari da  hajiya mai sharwali ya kusa cika. 

    Muskudawa tayi tare da gyara zama dan taji dadin tunanen. Ahaka har barci ya kwasheta bata gama tunanen taba.

      Kwana biyu tana shirye_shirye 

Komawa, dogon daji, har barci take rasawa don tsantsar tunanen yadda zata riski yar kulu.


          Dogon Daji


         Karfe uku na rana tasauka garin, don ,haka gidan, Ramatu tanufa kafin taje gidan su, don jin yadda abubuwa ke tafiya ta fannin, Ramatu.

     Saida safe Gajiye tai sallama gidan inna,,,,, inna nadaga cikin daki tana sallah walha  tadanyi gyaran murya, alamun sallah a ke yi. 

   Cak taja ta tsaya kamar mara gaskiya a,tsakar gida,,,, tana dan waige ,waige har idonta yakai ga dan guntun kujerar innna dake gefen daki jingine... Tsab tabi gidan da ido tana kallo tana wani yatsune fuska azuciyar ta tana fadin ,,,, kai dadina da kauye kenan wlh,.

    Komai nasu na tsafta ne ji randan ruwanta duk da sun tsufa amma an wani lulube shi da wani marfi mai fadi gidan gashi na lakane amma jiko ina tsab,, 

   In a gida nake aiko tashi banyi ba yanzu balle har inyi gyaran wuri.

  Motsin dataji shi yasata dagowa da sauri takai diban ta akofar dakin .

    Hakan yai daidai da fitowar inna a,daki a,a,a lalai marhabin mutanen birni ne yau a garin namu . 

   Cikin sakin fuska da murmushi suka gaisa cikin natsuwa.

    Inna ta koma daki tashinfida tabarma mai haske tace bisimillahgag shigo daga ciki,,, batare da bata lokaci,ba Gajiye ta shiga suka kara gaisawa abisa al,ada irinta bahaushe idan kai bako gaisuwa kusan biyu akeyi,,,,, 

      Hira sosai sukeyi na yanayin lokaci,,,,,,, A cikin hiran tasa Gajiye ta sako zancan daukan yara.  

      Saida inna tanisa sanan tace, a gaskiya Gajiye bawai bani son yaran nan su, gusa, kusa dani bane,aa,Kinsan amana suke gare ni Allah yai ma mahaifin su rasuwa, batare da nasan asalin gidan su ba,. saidai zuciyata tana fada min cewa insha Allahu zasuga danginsu koda kuwa bani raye ne. 

     Saboda hakane yasa nake kokarin ganin nabasu ingattancen rayuwa,.

  Saida gajiye ta gyara zama tace inbada abinki yar kulu ai zuwa kawai zamuyi sudanga inda nake kwana biyu indawo dasu. 

  Kinga aiko watan wata rana su zasu kai kansu inda nake don zumunci ko?  

    Shiru inna, ta karayi tana nazari maganar gajiye acikin ranta. 

    Gajiye kibari sainayi shawara da yaya na malam sale duk abinda yace zakiji kafin ki wuce.     Nakuma gode da kulawar ki,,,,,,

        Malam sale yayane ga inna, "Saboda haka kamar yadda inna tace haka tayi tasamu malam sale ta fada mai duk yadda sukayi da Gajiye shiru malam sale yayi yana nazarin maganar da yar kulu tazo masa dashi .

  Can ya nisa yace tau yar kulu mutum yazu ba abin yarda bane ,  Saidai kuma ita  Gajiye din ai ina ganin ta gida ce koma dai maiye aibazata wuce nan ba.

     Cikin murya mai rauni Inna tace tau yaya duk abinda kace insha Allah haka za,ayi.

   Malam sani ya lura inna batason tafiyan kokadan,,, Sai yace kiyi hakuri diyar kulu addu,a zamu Allah yakai su lfy yadawo muna dasu lfy tace ameen  

   Inna tace zata koma sukayi sallama ,Sai dai shi malam sani yasan cewa inna bata amince da wanan tafiyar ba,,,,, tausayi Gajiye da bata taba haihuwaba yakeyi kuma gashi har ta taya diyan " yar uwan shi idan har bai bada baki ba Gajiye bazataji dadi ba,,,

       Dasanyi gwiwa inna ta dawo gida .

     


   🐎ZEEE MAKAWA🐎

   🐎HUGUMA WRITERS🐎

[10/3, 16:28] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                       5⃣

                         BY

  🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA WRITERS🐎     Inna yar kulu zaune a dakinta cikin dare bayan ta idar da sallah dare kamar yadda tasaba, Tana kai kukanta ga Allah akan Allah yasa wanan tafiyan da za,ayi yazama mata alheri, 

    Allah kuma tsare mata yaranta aduk inda suka shiga.

   Duk wanan addu,an da takeyi a cinkin zuciyar ta takeyin shi, ,,

   Shin wai ma wazata tura wanan tafiyan cikin hafsat da fadima .

    Duk iya tunanen ta takasa tantance wacce zata bari a,tafi da ita,,,,,,,,

      Washegari karfe takwas na safe sai ga Gajiye acinkin shirinta na,tafiya,,, A,zuciyanta tana fadin ai,tunda malam sale ya yarda bazan kara kwana ko guda ba kada in,zo in samu matsalar tafiya,,, Don ita ga haukanta duk yaran biyu zata tafi dasu saboda samun banza.

     Da sallama tashigo yar kulu ta, tare ta da mutunci, Saidai acan cikin zuciyar ta addu,atakeyi ,,,,,, 

  Bayan sun gaisa cikin gimama juna,,,,, Sai yar Gajiye tace tau ina fatan yaran sun shirya ko ?

  Innna dake shirin mikewa ta dauko mata koko tadakata tace yaran kuma ,"eh mana inji Gajiye bada hafsat da fadima zamu ba ,,,,,,,, habadai Gajiye idan na,bakisu dukka nidawa zan zauna au baga Maryam da DATTIJO ba,,,,, a,a gaskiya hakan bazai yiba , ai,ko mutun gudan dazan baki kawai dai don kece an riga anzama daya

      Duk da ran Gajiye ya baci amma sai tadake tanuna ai ba komai ko hakan ma ai, ta gode tunda an,yaba da ita har anbata,,,,,,,,  Saidai acikin zuciyar ta fada takeyi,,,, yo ga matsiyaciya nizaki kulla ma tsiya inga samu inga rashi haba wanan wata irin shu,umar mace, ce

   Muskudawa tayi tare da gyara zama dan taji dawa zata tafi,,,

   Juyowa inna tayi daidai lokacin tai ajiyan zuciya gami da cewa,,,,,,, Ban riga na gama shawaran ko dawa zaki tafi ba tukun ,,,, au mutafi da hafsat ma tunda itace babba.

     A,aa gaskiya hakan zaiyi wuya donkin ga itace maidan wayo daga cikin su. Kinga ko zaiyi wuya inbari tayi nisa dani . Duk da yake fadima itace kusan ke taimakawa hasfsat din, kinsan abu ga tallakka ai sai a hankali.

    Acikin zuciyar gajiye tace duk kigama tsiyar ki sai naci riba dake,,,  

  Inna abu yasha mata kai tara wace zata tura birni,,,,,,,,Caraf fadima da ke da saurin wayo da fahinta tace inna nizani abar hafsat dasu maryam 

 Aiko inna taji dadin hakan don dama tana shakar zuwan hafsat, Saboda shiru shirunta yai yawa za,a iya cuta mata batare da ta dauki wani mataki ba.

    Fadima duk da yarinyace amma ta gane cewa inna batason zuwar hafsat din don ko cikin dare , da ta, farka taji inna na,maganar ,,,,,,,

  Duk zancen da inna tayi cikin dare fadima naji ,,, A ,hakanan ta kwanta zuciyar ta fam da tunane tana fadin,,,,, Kiyi hakkuri inna tunda kin riga kinyi alkawari ,, nayi alkawarin ni fadima nizanje koda kuwa zuwan nada illar kamar yadda zuciyar ki ke fada maki ,,,, kuma gashi kinyi alkawari baki son fasawa,,,, kada Gajiye taga rashin cika alkawarin ki.

     Kuka inna tasaka tana fadin Allah yaimaki,albarka fadima ,,,saboda ta fahinci fadima tagane manufar ta.

Kiyi hakkuri zan maki addua ,,, Sanan kuma ina son jan hankalinki duk da nasan tarbiyan da nayi maku, amma dai inason kisan yanzu birni zaki ba kauye ba ,,,,Don Allah ki kula ki kauda kai ga abin duniya ba ruwanki da abin mutane kiyi abinda yakaiki watau zumunci ki kulada rayuwar kamar kina a gabana,,,Don Allah ki kiyaye ki kare mutuncin ki,,, Sannan nasan ki da rawan kai to ki rage don Allah,,,, Allah yayi maki albarka yakare minke daga duk wani abinki ya azurta min ku da ilimi mai amfani ,,, Zancigaba da yi maki adduan alheri har randa akadawo min dake ,, Allah ya kaiku lfy

   Da kyar ta kai maganar ta da kuka a fuskanta.

    Gajiye ta mike tsaye tana fadin haba yar kulu sai kace wani guri zata haka.,,,,, aiki kwatar da hankalinki fadima gida zata.

     Hmmm Gajiye aikin san danyau saida fada ,,, tau hakane kuma 

  Gajiye tace ina kayanta akadauko wasu yan tsumakara da duk basufi huduba acikin wata tsohuwar leda bage baka aka bata   

   Kuka fadima keyi ta kankamay yan uwanta tana kuka kamar bazasu kara haduwa ba,,,Gajiye tace haba fadima ki yi hakkuri daina kuka ba wai dadewa zakiyi ba ai idan zan dawo tare zamu dawo, ba wai an rabu ne gaba daya ba . Wanan kuka haka ai sai yasaki ciwon kai.

    Gurin inna takoma ta kara riketa tana fadin inna ki yafe min dan Allah ,,,, ita ma inna fadi takeyi cikin kuka baki man komai ba fadima Allah ya kai ku lfy.

    A waje suka tarar da,su Ramatu da wasu yan uwan gajiye suna jiran fitowar su,

  Haba shiru haka inji Ramatu ai mundauka kun fasa zuwa yaune,,,, 

  A,a ,a haba dai mun dai tsaya adan kintsa ne kinsan rabuwar da da mahaifi da wuya tun dai irin wanan da ba,a taba zuwa ko ina ba.

     A haka suka samu motar da zata kaisu sokoto nan bakin hanya ,,, Ana daga masu hannnu fadima ma tana daga masu hannu tana kuka har saida ta daina ganin su,,,,,,,,,,,


     🐎ZEEE MAKAWA🐎

    🐎HUGUMA WRITERS🐎

[10/3, 16:34] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

       👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                      6⃣

                       BY

     🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA WRITERS🐎


       Girmamawa Gareku masoyana👏👏,👏

    ANTY Mariya SB

                 Hafsat yusuf 

                Safiya mai Huguna

Fatima Garba Teema luv

    Maman Rufaida 

      Maman Ihsan

       Anty Amal. 

       Nagode maku sosai,,,,

            (  FARKO )


   Allah sarki  ,,,, Yau litani itace rana ta farko da ni fadima nafara fita nabar kauyen mu dogon daji dake cikin jahar sokoto ,,,itace kuma rana tafarko da na fara shiga mota.

    Tun ina kuka har nadaina gabana ko yanata faduwa ina ta rintse idona ,,,,,, anawa haukan wai,na ga itace na ta gudu .

  Ba ai wani dadewaba muka shigo garin sokoto .

    Muna isa tasha muka samu motar kano saura mutum uku, Gajiye ta biya kudin mutun uku din wai batason a matseta a mota.

   Tun a sokoto nafara ganin canjin fuska a wurin Gajiye. Cikin hali irin na yaro nadan sa guiwar hannuna bisa ciyar ta haba aikawai naji ta fisgar min da hannu ta hankadeni gefe guda . tace kada ki kawo min sakarcin nan irin wanda uwar ku ta koya maku,,,, 

     A, hankali nadaga idona na kalleta idona tab da hawaye,,

   Wani irin a jiyar zuciya nayi na maida fuskata hanyan titi,,,,,,, Ga fitsari ya cika min mara amma tsoron Gajiye ya hanani magana saida naga fitsari na batun balla min mara nasa , ihu cikin kuka nace wayyo Allah fitsari nake ji 

   Driver yataka burki da sauri yana fadin subahanallah shine baki magana,,,,,, Gajiye takai min rankwashi akai tace ja,ira fita da sauri kada ki min ajikina. kafin in tsuguna har yafara fita ko.

    Karfe uku da rabi muka shiga KANO, zokaga kallo wurin yar kauye in waiga nan in waiga nan .  muka sauka a saman hanya Gajiye takara tsaida wata a daidaita sahu sukayi jinga akaita Tarauni. 

      Mun isa tarauni cikin dan kan kanin lokaci, Gajiye ta biya mai adaidaita sahu kudin shi yatafi 

    Wani gida muka dosa gidan akusan tsakiyar layin gidan yake, saidai yanayin wurin yaimin kama da kasuwa a gurin saboda yawaan mutane da kuma abin hawa. 

    Gidan yana darumfa ga katuwar baranda an shimfida  tabarmar roba babba ga benci kuma an jera su kala kala 

    Muka  zagaya ta baya naga wasu yaran mata suna ta gaida Gajiye,,,,,,  HAJIYA tana ciki ne inji gajiye tana tambayar "yan mata wata gutuwa tace mata eh tana ciki,,,, Dakata nan kijirani inji Gajiye . 

    Daya daga cikin yan matan tace Allah sarki Yumma dibi wanan yar yarinyar don daukar alhaki wai itama ankawota aikatau ko bauta,,,,,,, Yarinya da uwar ki tasani da bata barki kinzo ba . 

     Duk da yarinya nake saida cikina yabada kara naji wata iri don, Kande mai aya tagarin mu tana muna hiran yadda turawa suka dinga bautar da mutane da yadda shehu yazo ya dinga yaki da kafirai,,,,,, wanan zancen na kande na tuna.

    Wata murya ta katse min tunane na tace Sukaina ance kiba wanan bakuwar yarinyar abinci taci inji hajiya

   Saida nagama cin shinkafa da miya sai wani ganye da aka zuba sama,,,, bantaba cin ganyen ba sai na yayeshi gefe naci shinkafar kawai mai shegen dadi da nama guda uku aciki, aka kawo min ruwa masu sanyi nasha nayi hamdala.

       Ina gamawa na mike naje gurin wacce akace tabani abinci nakai mata kwano takarba tana fadin kin koshi ko nace mata eh,,,,, saidai don Allah inason inyi sallah ne .

    Tadafa min kai tace Allah sarki zoto in gwada maki wuri, wani dan daki takaini ansa wata tsohuwar kwali agefe tace min yi nan, muma anan , muke dan labewa muyi,,,,, dam sallah kuma ake labewa ayi nafadi haka a zuciya ta.

   Ina cikin sallah naji ana fadin hajiya tace wai a,shigo da bakuwar yarinyar da tazo yanzu 

    Akace mata ina sallah takoma tafada masu,,,

     Bayan na idar wanan Sukainar tace min inzo muje gurin hajiya,,,,Da sallamata na shiga su,biyu ke cinkin dakin maikama da shago, GAjiye tana zaune samar tabarma, itako, hajiya mai sharwali na saman wata kujerar roba fara.

     Cikin gimamawa naje har gabanta na rusuna nace ina wuni hajiya takarba min ba yabo ba fallasawa, najuya na gaida gajiye itama,,,,Ido matar ta kuramin ina nan a tsugune har nadan wani lokaci,,, ina ganin matar nazari takeyi akaina.Dakin yai shiri nawani dan lokaci, kaina yana kasa duke, naji    muryan matar tana fadin a,gaskiya Gajiye don dai kin fada min matsalar ki data uwar yarinyar gane da bazan dauki karaman yarinya irin wanan ba .

   Ai wanan wahalar rainonta kawai mutun zaiyi Ita, ko Gajiye tana fadin ayi hakkuri hajiya , ataimaka muna.

    A,zuciyata  nace taimako kuma ashe dama inna sayar dani ta hada baki da Gajiye suyi shine ban sani ba ,,,,,, Allah sarki inna har talaucin da ake kira muna yakai hakan,,,,,, wasu kwalla masu zafi suka sulalo min ga fuskata na share hawayena na dan, gyara tsugunawa na,sake cewa, Allah nagode ma da ba hafsat tazo ba don ita bata kaini lfy ba ance tana da shawara ajikinta kuma inda tazo ya saurayinta I,Lu  zaiyi yadda suke son juna,,, kusan mu kauye da yarinya takai shekara goma zancen aure yafara ke nan duk wani abu na mata zata fara iyawa....

    Ina cikin tunane naji hajiya nacewa to amma gaskiya bazan baki kudin taba duka sai naga yadda yanayinta yake . Ai ba matsala inji Gajiye nasan insha Allahu zakiyi alfahari da ita.

   HAJIYA taba Gajiye kudina ina kallo tanata washe baki har kune ita kakanta ya yanke saka.

   Hajiya ta waigo tana fadin maye sunanta ne Gajiye ta ansa da fadin FATIMA saidai mu can kauye muna ce mata FADIMA ai, to shike nan sunar yayi kinsan mu nan muna canza ma mutun suna saboda bat,da, kama,,,, 

  Da Gajiye zata tafi tajawoni gefe taja min kune tana fadin to fadima ki kula da duk wani aiki da a,kasaki  kuma banda kwadai don nasan kinga abinda baki saba gani ba don Allah ki kula sosai 

   Wanan kudin kuma zan je dogon daji in kaiwa mahaifiyarki su tasan abinda zatayi dasu,,,, (kaji makirci) irin ta tsofin kilaki,,,

   Har ta fara tafiya cikin muryan kuka nace Inna nan zaki barni tace, "eh fadima  amma zan rika zowa ina dibaki ke kuma dan abinda kika tara saiki bani inkaiwa maman ki.

   Wasu hawaye masu zafi da kunar rai suka kara sulalowa a idona nace to kigaida su hafsat,,,,,,,


   🐎ZEEE MAKAWA🐎

  🐎HUGUMA WRITES🐎

[10/3, 16:40] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                      7⃣

                       BY 

     🐎ZAINAB MAKAWA🐎

  🐎HUGUMA WRITERS🐎

     

     Akullun ina gode maku yan Huguma groups gaba daya da kuma TEEMA Luv Hausa Novels

      Anty mariya sb 

      Anty hafsat yusuf Ali

  Godiya dubu dubu gare ku.

   


    Tun wucewar Gajiye sai nasamu wuri gindin wata bishiya na zauna nayi ta gumi,,,,,

     Ina kallon yan matan dake ta ai yu kan su babu mai kula wata daga cikin su, Wacce naga tana karban kudi kuma nake ganin itace babban su, naga ta biyo ni tace zo kira cin abinci, don idan muntafi gida sai da safe zamu sake cin wani

    Ido na fitar waje, nida inna ta saba aje muna fura da koko duk wanda yadawo ko yashigo yadiba yadda yake so yasha har dare watabi kuma da dare taimuna tuwon mu mai dadi muci.

       Yau nice wai sai gobe zan karya Allah sarki rayuwa.

              Sai misalin takwas nadare muka rufe shago , ina rugumay da dan kulin kayana cikin leda ta baka,,,, naga wani mai adaidaita sahu yazo muka lodu ciki mu biyar , 

   Tafiya maidan nisa yayi damu sai gamu wani dan gida karmi baida get amma ginane kamar ginan mutun daya,,,,,, Falo sai dakuna guda biyu agefe da makewayi a bayasa andanyi makewayin kwano dan karami ashe inda muke kewaya wane , shi wancan naciki na hajiyace ita kadai.

    Muna shiga dakin naga sun,jawo wata tsohuwar tabarman roba sun shinfida 

    Kowa nata wasoson wurin kwanci saboda sunga bakuwa suna ganin ai wurin bai isar mu . Daya  daga cikin su ko ince wacee dazu tace nakara cin abinci tace, min ,zo nan ki kwanta wurina ni sai in kwanta kasa,,,,,,,,, Naga taciro wani tsohon zanin ta, tashinfida akasa ta jawo ghana most go din ta, ta aje allamar filo ke nan, koda na kalli sauran naga suma duk sunyi irin yadda tayi.

     Nima hakan nayi nadan aza ledar kayana na kwanta

  Sai,naga wasun su, sun tashi suna wankin yan kayan su watau ke nan basu da time din wankin kayan su sai cikin dare suke wanki in,sun dawo sai su shanya kafin gari ya waye ya bushe,,,,,,,,,,

   Rugaiyya ta dan juya tace min maiyye sunar ki kaunata, ? nace mata fadima .

        Allah sarki tace daga ina aka dau koki nace dogon daji ,tace ina ne kuma hakana nace mata can can ,,,,,,,

     Tace to ki kula da aikin da,duk a,kasaki kinji ,,,,,,, Nace to 

  Saita nuna min sauran tace wacan itace Yumma wacan Mari wacan Sukaina nikuma Rugaiyya kinji kuma kowa kice mata anty nace to,,,,,,, 

     Karfe hudu na asuba ina cikin barci na mai dadi naji ankai min duka a baya ana fadin tashi dan Allah kinji mu kwashe shinfida,,,,,, Tunda an fada maki barci kikazo yi, aida ki zauna gida kita barci, amma tunda uwar ki nason kudi ai barci baiga idonki ba yarinya.

      Anty Sukaina ce ke fadin hakana , Rugaiyya tace haba dai Sukaina yakamata ki tausaya wa wanan yarinyar dan Allah bai kamata mu matsa mata , ba,ai,,,,,,

      Mari, dake gefe tana gyara kunshin kayanta tace ai bidan kudi tazo yi kamar mu,,,,

   Yumma tace ai maganar Rugaiyya gaskiya ne idan munyi tunane kamata yayi muso junan kamar yan uwa ba wai mudinga cuta wa junan mu ba,,,,, mutaru mu rufawa juna asiri .

       Saboda wanan yarinyar tayi karama da yawa gaskiya ,rashin taudasayine kawai irin na mutane da kwadanyi iyayye kuma ,,,,,

      Nidai ina jinsu ina kallon kowa da irin halinta.


     Cikin duhun nan sukayi sharan gida suka goge , wasun su ,suka debo ruwa a famfo suka cika wani katon roban ruwa,,,,,

     Kafin karfe shidda yayi har an wanke wake ankai nika,,,  

   Mai adaidaita sahun jiya, yazo yadauki Yumma da mari da markaden wake da su, mai ,yatafi ,dasu 

  Sukuma sauran naga sun hura wuta a wajen gidan mu suka fara suya,,,,, 

   Duk wanan abin nadauka hajiya bata a gida sai misalin karfe takwas ,,,Rugaiya tashiga gida ta bata ruwan wanka tafito tsab da ita 

, aka zo a kadauketa zuwa shago.

      Koda tara na safiya yayi duk mun hada komai cikin gida, muka rufe gida, muma mukatafi shago rayuwar ke nan  


    🐎ZEEE MAKAWA 🐎

        🐎 HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 16:43] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈ 

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                     8⃣

                      BY

    🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA WRITERS🐎


        Godiya ga masoyana yan uwa na 

         Mariya SB

      Hafsat Yusuf da maman Rufaida

 Ummi Rabiu da maimuna Adam duk a huguma group
    Tundaga wanan rana rayuwar ta fara canza min, nasan mayye duniya, Ruyuwa ce ta bauta ko , ko tarashin galihu,,, gamunan dai haka gari zaiwaye muna dare ya riske mu a wahalce,,,,,,,,,,, 

     

        Gari yawaye rana ya hudu daga gabas alokacin muna suyan kosai a acikin uguwar mu kafin mutafi shago,,,, 

    Ni aiki na shine a zuba min kosai da yawa a far roba indaga bin gidajen masu kudi in sun fito da safe suna saya suna sadaka,,,,,, 

     Abayana almajirai ke bina wa yanda ke karban sadaka ,,, idan nai sa,a za,a iya saye robar kosan gaba daya alokaci  guda ,,aba ma almajirai sadaka .

    Bakaramin cigaba hajiya tasamu ba ganin irin ribar da take samu damu yasa ta kara yawan kosai da muke sayarwa har da gudun mawar koko a wurin mu,,, kawai mutun yazo ya,saya koko da kanci inda kana son sikari mu zubama,,,       Da rana zuwa goma mun isa shago don fara abincin rana. Wanan yazama ka,ida dole goma taimuna a,shago, duk da aikin mu yafi yawa kuma munfi kawo kudi masu yawa,,,

      A gaskiya ina jin dadin zama da sababin yayyen da nasamu suna kula dani sosai saboda ko aiki sukaga zaimin yawa zasu taimaka min dashi

    Duk da dai aikina bawani mai yawa bane sosai,,,,,,, Idan an,ci, abinci nice zandauko kwanoni in hada su gurin wanke wake muna da almajirai masu wanke muna,, Sukuma abasu abincin da akaci aka raga suci

      Wata rana natafi dauko kwanon da akaci abinci a tsallaken shagon mu ,,,,,,, abinka da yar kauye ban kulaba ashe akwai mota tafe kawai jinayi wata wuta ta,gitta min tun lokacin bansan inda nake ba,,,,,, 

    Muryam mutane nadiga ji sama sama akaina wasu na fadin ai,tana motsi ku,taimaka akaita asibiti,,


       Bankara sanin indanake ba,,,, ita hajiya mai shar wali ana fada mata ta mike da sauri tai waje ,,Tana fadin kada ku bari yagudu ku kama min kowaye,

   Tana wani fiszege fiszege irin abin nan na yan duniyan mata


    A she driven wani alhaji ne ya dauko yara zuwa gida daga makaranta ,,, 

     Asibiti aka, kai fadima ,Likita ya,dibata ga babu kariya saidai inda tadan ji ciwo.

    Likita ce za,a bani gado aga yadda jikin zaidan kasance tukun,,, 

   Hajiya kan kakanta ta yanke saka,, saboda mai motar da aka bugeni shi yadauki dawainiyar zamana asibiti 

    Abubuwan marmari da su kayan tea haka aka jibga muna su ga kudi wurin dubu hamsi yace a,yi duk lalurar da za,ai min inbasu isaba a tambaye shi,,,,


 

       Tun daga wanan ranan da na kwanta ciwo bana iya cin komai daga kwanciya sai kwanciya , itako hajiya duk abinda aka kawo daga gidan Alhajin cinyewa takeyi.

   Har kusan kwana goma ina cikin wanan halin, 

    Tunanen gida da kewan yan uwa na yadawo min sabo acikin zuciyata ,,,, Saidai kaga hawaye na zuba min a ido idan antambayeni ko maye sai ince ba komai ,,,

    Naramay na yankwamay duk nasake sai yar wuyan da na danyi saboda rama.

  Duk kudin da hajiya tasamu gurin Alhaji ssboda ni baisa tabar min fada ba wai lalaci ne kawai don ina mata bakin cikin dan cikin kosan da take samu ,,,,,,

    

       Rugaiyya sukan ce min inyi hakkuri hakana hajiya take ko kana ciwo bata tausayi ka, ita dai kaji sauki ka,bido mata kudi kawai,,,

   Sannu a hankali na fara samun sauki ina danjin kwarin jikina,, 

   Nikan zauna a daki ni,kadai inyi ta kuka saboda a, tunane na da sanin inna ta nake cikin wanan halin.

     Abayana naji ana ce min kiyi hakkuri fadima addu,a kadai zamuyi har Allah ya kawo muna saukin wanan rayuwar,,, Don Allah bai manta da mu ba yana sane da halin da, muke ciki watara sai lbr in munyi hakkuri 

  Tashi ki share hawayenki ki saki jiki ki koma kamar kowa kada ki sake saka kanki cikin wata sabuwar ukuba kinji

   Rugaiyya ce ke min wanan maganar 

   Nace mata to, nabita da kallo har ta shiga cikin gida fito da kayan suyan kosai, 

     Murmushi nayi azuciyata naji tausanyin kan mu sosai naji kuma ina kaunar Rugaiyya har cikin zuciyata. 

     Saboda tun farkon zuwana tana nuna min kauna, tankar ni yar uwartace tajini.Wanan ciwon danayi yasa hajiya sanin dadina sosai tagane inada rana sosai a,gurinta .

     Saboda yawan kudin da take samu aduk safe, yanzu ya rage yawa sosai,,,,  

      

      A haka na daure nakarasa jin sauki a bakin shagon mu don tun ban iyawa ina bin bango har na daure na zama normal . Naci gaba da harkoki na kamar kowa,,,,,,,      🐎    ZEEE MAKAWA🐎      HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 16:52] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

       👣👣👣👣👣

        👣👣👣👣👣

                       9⃣

                        BY

  🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

   🐎HUGUMA WRITERS🐎

        

        HUGUMA GROUP 

         ALLAH YA DAUKAKA 


Almost true life story   Hankalin inna  ya tashi kware ganin, yanzu kusan wata uku ke nan Gajiye batazo garin su ba kuma babu lbr ta

   Inna tai sallama gidan, Ramatu suka gaisa cikin mutunci , sai shiru yabiyo baya har wani dan lokaci


Inna,ce ta kauda shirun tace, shin wai Ramatu ya lbr Gajiye ne naji shiru tunda suka tafi , har yau bajin ko sakon gaisuwar su ba.


    Ramatu sai da hanjin cikinta yakada itama don da farko batayi tunanen hakaba ,,,, saidaga baya da ta fada ma mijinta yadda akayi har Gajiye tawuce da fadima sai ya hauta da fada,,,,,,,,

    Yace ashe dama da hadin bakinta aka cuci inna yar kulu, 

      Gashi gari yadauka saboda kwadai tabari Gajiye tawuce mata da diya birni, Ashe cutar ta akayi,

    Yace ma Ramatu tazauna da shirin duk randa asirinsu yatonu yar kulu taso diyar ta wlh shi ba,dashi cikin wanan rikicin ba.

     Tun lokacin hakalin Ramatu yake a tashe tana tunane ranan da yar kulu zata tambayi diyar ta.  Ramatu tai shiru kamhar ruwa ya cinye ta, nadan wani lokaci 

      Sai can ta nisa tace ,,, A,gaskiya yar kulu banda lbr Gajiye ,

   Asalima dai wlh ban san garin da take zaune ba,,, saida naji kamar an ce kano take zuwa sarin kaya daga sokoto.


       Inna da ke zaune saitaji wani jiri yana kwasan ta , Allah ya taimaka a zaune take da a tsaye ne da tafadi.

       Cikin karfi hali inna tace ban fahice kiba fa Ramatu?. 

    Gaskiya maganar,ke nan yar kulu, 

  Gajiye ban iyace maki ga,garin,da take.

    Nima yadda take zuwa ganin gida hakane yasa muka dan shaku,,, amma da tunda tai aure birni bawai nasan ina take da zama bane balle insan lbr ta.

     

    Habadai Ramatu zancan kikeyi kawai,, kizo har gidana kusan sau biyu akan inbari Gajiye ta, tafi min da diya taga inda take amma sai kice min wai yau aike bakisan Gajiye ba haba dai,,,,

   


   Tun inna da Ramatu suna rikici su biyu har takai makwabta sun fara shigowa saboda gane ma idon su.

    Daga gidan Ramatu, gidan yayanta malam sale tanupa 

    Batare da bata lokaciba ta zayyana masa yadda sukayi da Ramatu.

   Shiru yayi cikin tashi hankali yanisa yace 

   Hakika yar kulu harda laifina ,,,,,,,,Don kamata yayi dakika kawo min shawara  in tsaya in bincika kafin in yanke hukunci

 

 Cikin kuka inna tace ita,kan  kaiconta da har takasa rikon yar mareniyar Allah da tabari har Gajiye ta cuce ta.

     Tacigaba da fadin gajiye kin cuce ni da har kika yaudare ni nabaki yar diyata da sunan sati uku yau gashi har wata hudu ke nan,,,,

   

Malam sale yatafi gidan maigari yakai karan maganan,,,, kowa yayi mamakin wanan maganar

      Maigari yace to ai shi anfada mashi cewa yar kulu ta tura diyar ta birni wurin neman kudi.

   Bawai yadda malam sale ya fada mashi ba,,,,

  

   Ramatu da inna duk suna zaune a zauren mai gari kaida ganin inna kasan tana cikin tashin hankali so sai 

    Bayan mai gari yayi gyaran murya wurin yayi tsit,,, sai yafara da addu,a tare da neman tsarin shedan. 

    Yar kulu muna son jin bayanin tafiyar diyar ki daga bakin ki, duk da yayan ki malam sale yazo yai muna bayani. Sai dai muna son ji daga gare ki.

   

   Inna takawo bayanin tun farkon haduwar su da Gajiye da kuma Ramatu ,har yadda akayi ta wuce mata da diya da irin zargin da gari ake mata 

   Takare bayanin ta cikin kuka tana fadin ko yan uwana ban yarda na basu rikon diyana ba saboda gudun zuciya ,,,, 

    An bukaci Ramatu tayi bayanin abinda tasani , Ita ma Ramatu bata boye komai ba duk yadda sukayi da Gajiye saida tafada a zauren maigari.

   

Zauren yai shiru kowa da abinda yake sakawa azuciyar shi. Maigari yai gyaran murya yace,,, Dake yar kulu da Ramatu duk Gajiye tai maku wayyo ta gwada maku wayewa,, amma ai gajiye mutumiyar banza ce.


  Yanzu addu,a zamuyi ma yarinya Allah ya tsare muna ita duk inda take Allah kuma yadawo muna da ita gida lfy.

   Zan tura abinciko min duk inda Gajiye  take cikin kasar nan anemo muna ita tazo tai muna bayani da kanta.

     Maigari yakara ba inna yar kulu hakuri yace ta kwantar da hankalinta Allah zai dawo mata da diyar ta lfy. 

      Yace kuma wanan yazama maku darasi arayuwan ku,,,,,,, Don yanzu ba,a yarda da mutun koda ko kasan shi ba,aba mutum amma kai tsaye haka,,,,,,,


🐎ZEEE  MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 16:55] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈. 

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                      🔟

                      BY

  🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA WRITERS🐎

     

Almost true life story


 Hafsta Yusuf Ali 

      Mariya SB

        Fatima Garba Teema luv 

     Fadila Lamido novels

      Musha karatu group novel 

     Maman Fati group novel  

   Duk ina ma wanda ke cikin wa "yan nan,groups din fatan, Alheri Allah sada mu da alherin da ke cikin wanan wata mai albarka👏👏👏👏👏👏

Zaune muke  a bakin  shagon mu, anyi, ruwan sama,an,dauke , Kasan cewar lokacin ruwan sama, ne babu wani kasuwa da muke samu yanzu sosai.  Saidai manejin kasuwa .


   To amma fa hajiya ce  maiganin hakan ,,,,,, mudai mun,san ana samu. Ciniki daidai gwargwado 

    Wata yar doguwar rigace ajikina dinkin yai min yawa rigar Mari ce da tagaji da ja tayar shine Rugaiyya ta ce indauka in wanke indinga sawa .

   Tun lokacin da nazo hajiya bata taba yimin dinki ba,,,, yan kayana duk sun kode sunzama ragga,, 

  Amma wai haka take ce muna wai mu kaza mai ne, 

    Ko sabulun wanki a sace muke saye mudan wake kayan mu 

           

   Wani lokaci kuma masu sayen abincin mu sukan dan yi muna alheri jefi jefi,

     Sai dai Rugaiyya ta ja min kunne cewa kada indinga wasa da maza,,,,, kuma ka in,yarda in naje gurin tallan kosai kada in shiga cikin gida in tsaya daga waje

        Aiko alheri akai muna hajiya muke ba wai acewar ta tana tara muna ne idan zamu gida saita hada muna da kudin aikin mu.

        Zaman danayi jira nakeyi agama gyara kayan miya inkai wurin markade. 

     Bayan angama gyarawa nace ma  Sukaina tabani kudin nika , saitace ai atabau tabani kudi tundazu 

   Wasa wasa muka fara wanan rikicin har gurin hajiya muka tafi,,, 

   Sukaina tace ai tun kafin ta wanke tabani kudi

   Hajiya tasa aka cajeni kaf ba,aga komai ba aguri na

   Amma sai hajiya tashiga zagina tana fada inda take shiga banan take fita ba,,,, wai ai dama halina baida kyau shiyasa uwata ta kawo ni yawon duniya  tun ina,,,,, yar karama dani , wai, min shegiya mai shegen ido kakafe,da fari kamar gonar madara gakinan kaman akalla ki kulun kina cimin abinci a,banza baki auki 


Yau duk inda kika kaimin kudina wlh sai kin tono minsu angaya maki barikin banza nafito yi ,

  Ta, daka min tsawa saida na firgita  Munafuka ina magana kin kafeni da shegun idanun nan naki, fita kiban wuri,,,,,

     Sim sim na fita ina sharban kuka,,,,, hakana na dauki nikar nadoshi manika ina hawaye.


  Matar dake muna nika ba ba,haushiya bace bayerabiya .ce,,,,, Cikin hausan yarbawa take min magana

    Yaron hajiya maynene ya , samay,ka,ka nayi kuka yau, na fada mata duk yadda akayi ,,, tace wlh don dai nice kawai zatayi kuma na bata tausayi amma, in,don hajiyace bazatayi ba, don hajiya bakyau,,,,,

   Bayan nadawo daga nikan sai hajiya tace wai wa,ya,bani kudi nabiya kudin nikan,,, nace mata kyauta a,kaimun nikan .

   Aiko hajiya tace karya nakeyi kudinta ne dama naso in mata sata ne,,, Ta samayni taimin dukan tsiya har saida bakina ya kun bura  

     Saida yamma muna tatara kaya,muna kaiwa a cikin shago sai ga kudin da Sukaina tace tabani  angani kasan wani roba ta aje ashe ,,,,,,,, 

   Rugaiyya ranta ya baci ta,fisge kudin taje ta nuna ma hajiya ,,,

    Borin kunya hajiya ta kamayi tana fadin shegu da ban yi mata haka ba da shikenan ashani abanza,,,,,,,,,,

      Kafin safe bakina ya kumbura sindib saikace an aza min dutse akai nake jinsa, hakan yasa nake jin zazabi yana son kamani

     Rugaiyya ce, takama kula dani, taña dan gasa min wurin da ruwa mai dan dumi, tasayo min kwayoyi ta ba ni tace in,hadiye .

    Hakana wuni ranan ina dan jin zazabi ajiki na.

      Saida hakan bai hani zuwa tallan safe da nasaba yi ba na kosai,,,,,,

     Aikin shago ne kawai yan uwana suka taimaka min yi 


     A haka rayuwar tamu tadinga tafiya yau dadi gobe zafi. 

  Girma kuma na zo mun a hankali , duk bautan da mukeyi bai sa Hajiya ta dan tausaya muna ba sai dai kulun cikin kara sabon sana,a mukeyi

   Ita dai tayi kudi by all means ,,,,,,

      Idan naga yara za su makaranta sai intajin wani iri a,zuciya,ta. Sai dai duk da haka dan karatun da ke a kaina bai fita ba dan ina iya karanta wasikar hausa tsaf kuma zan iya ta turanci ita,ma saidai aimin dan gyara kadan


Na riga na hakkura da duk wani halin da zan tsinci kaina banda wata matsala yanzu a,rayuwana sai dai kawai na bidan ma hajiya kudi,

    Gwargwado yanzu hajiya ta wadata damu har takan dan yaba mu,

  Wani lokaci har da kyauta takan dan bamu kamar dari biyu biyu ko kuma ta siyo muna dan abin marmari mu ci

  Wanan kuma yasamu asaline tun ranar da wata kawarta tazo shagon mu taba mu kyauta da zata tafi,,,, 

  Tun agabanta  muka fara ba hajiya kudin, sai bakuwar tace aa ,habadai mai sharwali kibar masu abinsu mana wanan ai kyauta nabasu..

   Mudai muka fita waje muka bar su a cikin suna magana,,, 

 To tun tafiyar bakuwar komai ya canza.

    Abakin Sukaina mukeji wai ashe bakuwar taima hajiya wa,azi tace mata amana fa muke a,gurinta


Shine dalilin ganin canji da muka gani ga hajiya,,,,,,,

    

🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎.   HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 17:05] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

       👣👣👣👣👣

        👣👣👣👣👣

                    1⃣1⃣

                     BY 

    🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

 🐎HUGUMA WRITERS🐎


 Godiya ga masoyiya kuma anty na HAFSAT YUSUF ALI 

     

Almost true life story

  Hajiya mai sharwali ta bunkasa sosai yanzu kusan duk maison cin abincin kware shagonta zai zo ,,,,,,,

    Abincin mu gaskiya yana da dadi sosai , saboda duk wani kayan hadi muna zubawa acikin aikin mu.

    Mukuma muna tsayawa tsakani da Allah muyi mata aiki babu kissa ko cutar wa,

    Yumma da Rugaiyya sun sha fada min cewa hajiya itace , gatan mu a garin kano .

 Saboda zamanta mukeyi nan, ba zaman wani ko wata ba.

   Wanan maganan nasu yakara min kwarin gwiwa wajen yadda da hajiyan mu kamar yadda muke kiranta,,,

     Karfe shadayan rana, idan kazo shagon mu zaka samu mun gama dafa abinci kala kala,

   Mundan gyara jikin mu don kada masu sayen abincin mu suga kazantar mu,,,,,,,

   


   Yau ma kamar kullun mun gama aiki muna zaune muna jiran masaya, abincin,mu su,zo 

    Wata ma,aikata dake kusa damu nan cikin tarauni suke ,,,,,,, Suke zuwa sayen abincin indan sun tashi break, fast.

      Daidai lokacin da suke zuwa cin abincin bamu da lokaci kan mu,saboda aiki kayi yawa kowa da abinda zai, ce a,kawo mai, yaci,,,,,,,,

     

   Daidai wanan lokacin da ko hajiya bata da lokacin kanta,,,,, Wata hadadiyar mota mai ruwan kalar kakin soja tazo ta faka bakin shagon mu.

    Hankalin kowa dake wurin ya kai ga wanan motar kusan , minti goma ba,a bude motar ba.

    Koda,kofar,motar ta bude, Karfar wata mace ce tafara fitowa da shi tawaje amma bata fito da jikinta ba,,, 

    Gashi kusan duk wanda ke wurin hankalin shi naga wacce zatafito cikin motar,,,,,

  

   Wata matace baka yar doguwa kyakyawa girma yadan fara kamata kadan, ita ta,fito daga cikin motar mayafin ta a kafada sai dan jakar fos data rika a,hannunta,,,,,

    Hajiya na gani matar ta mike tsaye tana fadin a,a,a ,,,,,,

   Wanake gani kamar zinaro ,matar tai,wani far da ido taware hannaye tana fadin nice mai sharwali,,,,,,  

    Suka rugumay junnan su cikin farin ciki da an,nashuwa,,, 

    Nan hajiya ta umurce mu da mukawo wa bakuwa abinci, tana fa mubarshi,, amma hajiya na fadin mu kawo duk abinda ke gare ,,,,,  

     Mari tace tirkashi ,yau kan munyi bakuwa mai muhinmanci kenan ,tunda har hajiya tace mukawo duk abincin da muka girka kalala wa bakuwar.

   

  Koda nashigo da turen ferfesun kayan ciki dana kifi danye nasamu hajiya da bakuwar ta sun baje ana yaushe rabo,,,,,,

   Bakuwar ta cire gyalenta tanawani juyawa agaban hajiya ,, hajiya nafadin wai Zinaro kece haka don Allah

   Zinaro tace yo mai yai min tsinanen zafi mai sharwali ,,,,, mayye duniya ,

  Wai yaushe kika zo kasan madai,,,,, 

     Bakuwar tace aini ma abinda yabani mamaki kenan mai sharwali naga,kusan kowa da akai zamar harka a saudiya amma ke bangan kiba . sai na tambaya akace min aikina nan gidin murhu kina halaka kanki,,,, 

 Shin may ku,kazo yi ne a,kasar ?

   A,a buki mukazo mana kinsan Alhajiji yai aure wancan satin,,, 

    Waye kuma Alhajiji Zinaro, ta kalli hajiya galala tace kina ko kasan ga mai sharwali

   Au tana gyara kafadan riganta, 

  Tace shugaban yan daudu mana nakasa kinsan yayi aure daga saudiya shine mukazo kawo amarya,,,,,

   Hajiya ta girgiza kai cikin daurewan kwakwalwa tace gaskiya ban san shiba.

     Tace anya kuwa a garin nan ma kike kuwa ,,,, sarkin yan daudun nakasa zakice baki sani ba ,,,,

    Hajiya tace yo nazama kifin rijiya yanzu ai

   Bani zuwa ko ina daga wanan runfar sai gida aikin kenan.


     Yo kin zo kano kin boye ana can a,nata harka a saudiya 

     Kai habadai yo aike ma dai kinga a,lama aiko   

     Eh aiko nagani.

  Haba dai don Allah kizo kawai acigaba da harka dake, har wa"yanda basu kai ki ba sun take balle ke.

     

   Haka muka dinga shigowa muna, mata sannu da zuwa ,muna fita .

     Ke sharwali duk ke keda wanan harkan haka?

   Harka kuma ina? Gasu nan mana,wa yan nan zukazukan yan matan haka ,, yo aike kice min kin take 

     Kika tafi dasu saudiya ai nabaki watan ni kadan kin take kenan har abada,,,,

     

     A haka bakuwa Zinaro ta dinga zuga hajiya tana cusa mata ra,ayin fita da mu zuwa saudiya bidan kudi🐎ZEEE MAKAWA🐎

  🐎HUGUMA WRITERS🐎

[10/3, 18:54] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                      1⃣2⃣

                         BY

 🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA WRITERS🐎

  Hajiyan mu takasa yin barcin kirki yau,,,, hiransu da hajiya Zinaro ke dawo mata a, rai.

    Sai juyi take tayi tana jin muryan zinaro na fadin in kika tafi dasu saudiya aikin take,,,,,,  

     Nan da nan shedan ya rinjaye ta ,taji kawai zuwa saudiyan take da bukatar yi.

 Ta,manta duk wanan baiwar na samu da Allah ubangiji yai mata nasa nan kano.

 Kafin asamu mai,sa,ar kasuwa inda ake samun, ciniki  irin nata sai an tona.

    Allah Allah gari ya waye takeyi , don taje gidan Zinaro .

   

Kwatancen da Zinaro taimata na masaukin su shi tabi, batasha wani wuya ba wurin gane gidan

 Cikin kankani lokaci ta isa dawanau inda gidan da zinaro take a,karshe wani layi. 

  Gidan ginan jan bulo ne sai kato,kofar baki karfe da ke manne da ginar,,, 

  Koda hajiya tai sallama wani dan saurayi fari dogo , yazo ya bude mata kofar ta shiga .


   Ginan gidan gaskiya ba laifi komai ya hadu daidai da zamani ,,,,,, kujeru ne manya manya sai, kayan kallo dana kida saiti masu kyau.

   Ga dinning table agefe guda,,,, sai wata kofa da zata sada ka da kitchen , shima kitchen din ya hadu sosai komai na bukatar zamani akwai a cikin kitchen din.

   Wasu samari guda uku tagani acikin falon  gidan suna game kowanin su dagashi sai wandon tree quater, da yar singilati.

     Sukayi ma hajiya sannu da zuwa ,,,,, guda daga cikin su ya , shiga ciki fada ma zinaro bayan kamar minti biyar yafito.

    Yace ance tashigo daga cikin uwar dakin.

  

   Hajiya Zinaro zaune a gaban mirrow tana shafa mai dagani daga wanka tafito.

  A ,a mai sharwali kece tafe da safen nan 

   Hajiya na washe baki tace wlh nice zinaro.

   Tun shekaran jiya da kika tafi kin barni da tunane kala kala azuciyata. 

   Shine nace bari inzo don bansan lokacin da zaki koma ba.

   Zinaro ta lakato mai da yatsanta tana shafa ma kafarta tace,,,, "eh gaskiya zan wani dadewa ba zan koma kinsan yanzu ba wani harka sosai a cikin makka kamu sukeyi don haka a jidda ko Riyadh, 

     Sunta dan jefa hiran wa yanda sukayi zama dasu alokacin da suka fara zuwa aikin TAKARI  na farko,,,, 

   Zinaro na bata lbr ai wasu sun dawo gida wasu kuma suna can wasu kuma sun rasu dadewa.

    Cikin samarin dake zaune falo guda ya shigo yana fadin hajiya yau sai mun sayo kayan miya agidan nan don wanda yarage baida yawa kuma sun fara lalacewa.

    Tace kadauki ga kudi can kaje ka sayo abinda duk yadace asaya.

   Bayan fitar saurayin hajiya tace wa " yanan yaran "yan uwanki ne ko 

    Dariya sosai hajiya tayi tace yan uwana na,bariki ba ,Da su nazo daga can  

    Saurayi nane da abokan shi,,, saurayi fa kikace to may ye aciki don nace saurayi nane. 

   Hajiya takura mata ido har dan wani lokaci tace kai haba Zinaro,,,wa " yanan yan yaran zakice wai samarin ki yo ai wanan, ma mun kusa haihuwar su, Idan ma bariki kike so ai sai ki samu daidai dake amma ba wa yan nan yara ba

  Wani irin dariya zinaro ta kyalkyale dashi na shakiyan ci gami da aje roban man da take shafi gefe guda tana rufewa,,

   Ta ce lalai mai sharwali baki akasan don ina ganin ma ko a kanon kauye kike. Ai wa yan nan yaran sufi manya dadin sha,ani don su idan kika basu kudi kadan sai su biya maki bukatar ki fiye da yadda kike tsamani,,, kallonta kawai mai sharwali ke yi,,,,,,,,

    Ta shashantar da maganar ita dai hajiya duk al,ajabi ya kamata, mamaki takeyi da wanan irin hali na su zinaro,,, 

   Saida tagama shirin ta tsab suka fito falon inda zinaro ke ma hajiya tayin samarin ko akwai wanda yai mata taja guda

   Ai barikin nawa baikai can ba Zinaro inji hajiya 

 Taufa ashe har yanzu da sauranki maisharwali. Don ko kinga su nan ba karamin riba naci dasu ba zuwan mu wanan bukin,,,,,,   Zama akayi sosai da hajiya da zinaro taba hajiya shawarwarin abin da yakamata a,yi saboda tafiyar su saudiya.

    Komai an,kan,mala game da tafiya duk wani hanya da za,a bi an yi,,,

    Hajiya taba da kudade masu yawa saboda komai yatafi daidai

   Aiko kafin hajiya zinaro tabar kasan komai ya zama daidai,,,,,,,,,

  

  Lokacin tafiya kawai za,ajira yayi abar kasan zuwa sabuwar duniya


🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA WRITERS🐎

[10/3, 19:02] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

       👣👣👣👣👣

       👣👣👣👣👣 

                    1⃣3⃣

                       BY 

  🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

 🐎HUGUMA WRITERS🐎


Ina  duk masoya novel dina fatan alheri , nagode kware da kulawan ku yan uwa 


 Anty Mariya SB Allah ya baki lfy 
Tunda hajiya ta dawo daga gidan zinaro mukaga canji sosai a wurin ta,  Sai fa,ra,a takeyi da kowa

 Mudai namu idanu kawai tunda babu daman mu tambaye ta,,,,,,,

     Ai yukan mu kawai mukeyi kamar yadda ya kamata ,,,,, saidai mun ga hajiya kamar tana cinikin gidanta da shagon ta dawasu...

   

Mukan ba matsalar mu bace iyaka naji Sukaina yar sa ido na fadin kila hajiya zata maidamu gidajen mu don tana gani zata koma makkah da zama ne.

 Jin haka yasa na fara murnan zan koma gida very soon, 

Zanje inga hafsat dina da dattijo dan kani na ,,,,, har nace sai in saya masu bread da lemo in kai masu ,,,, haka nadinga sake sake a zuciyata,,, 

     

  Wasu mutane sukazo su biyu wurin hajiyan mu sun dade da ita cikin shago,,,,, 

   Hajiya takira Yumma tace taje tafada muna kowa ya gyara jikin shi da,kyau za ,a dauki photo ne. Aiko muka shiga murna za muyi photo.

    Ta,ba mu, wasu kaya  masu kyau doga yen riguna tace kowa yasa,a photo dashi,

 muna ta murna zamuyi photo ban kwana da juna tunda ance hajiya zata bar kasa ne.

    Sam bamu kawo cewa damu za,a tafi ba,,,,,


      Bayan mai photo yadauke mu ya wuce da kwana biyu hajiya ta turo wata mace tazo tai muna kitso da kunshi masu kyau

  Munata murna muka fito shar da mu kamar wasu yan birni,,,,

    Tundaga ranan da akai muna kitso bamu kara zuwa shago ba kuma ,,,,, 

   Kayan dadi muke ci a gida babu wani tsangwama da ake muna yanzu,,,,

     

Bayan kaman kwana hudu tsakani cikin dare muna hira a falon gidan mu

    Sai hajiya ta fito ta zauna a gefen mu duk mukayi shiru,,,, 

    Waya take yi alokacin amma saboda ladabi sai duk mukayi tsit wurin.

  Tana gama wayan takai dibanta gare mu ,,,,,,, lokacin tai wani dan gyaran murya sai duk muka kara maida hankalin mu gareta.

    

   Tace duk ina son ku bani hankalin nan ku saurare ni da kyau ,

    Mukayi shiru cikin ladabi, tafara magana, 

   Tace dukan ku, ku ,biyar, zamu bar kasan nan zuwa kasar makka gobe da asuba insha Allah 

   Nasaida gida na da wasu yan abubuwa nawa, saboda tafiyar mu,,, nasan cewa baza mu dade ba shiyasa ban fada ma kowa cikin yan uwan kuba saboda dazaran angama aikin hajji zamu dawo nan kano muci gaba da sana,ar mu,,,,,,

   Naga ,su Sukaina duk suna ta,murna sai Antyna Rugaiya ce naga bata wani murna sosai kamar sauran. 

    Naga kowa ya shiga hada kayan shi,,, sai hajiya ta shigo dakin na mu da kanta,,,,,, Tace muna ba wasu kaya masu yawa zaku dauka ba kada ya wuce kala biyu kubar sauran idan mun dawo sai kuyi amfani dashi,,,,,

      A , haka muka dan tsinci dan abinda muke so mukabar saura da niyar in mun,dawo mu kwashi abin mu zuwa gida,,,,,,,


     Tunda asuba masu adaidaita suka zo suka kwashe mu zuwa filin jirgi 

   Hajiyar mu ce da wasu suke ta zirga zirga a wurin mudai muna gefe guda, muna jiran ,,, Yadda za,ayi damu 

  Barci nake ji inna hamma Rugaiyya ta ce in kwanta ajikinta kafin , hajiya  mu,tazo daukan mu,,,

    Ina cikin barci naji ana tashins natashi firgigit dani naga an bamu wasu kumshi kaya ance kowa ga nashi ,,,

   Wai goro ne a ciki dasu kayan miya irin namu na nan kasar ,,, wasu kuma wai turamay zani ne a cikin kunshin da sukayan amfanin mata,,,


Barcin da bankara yi ba ke nan duk inda zamu don a auna mun je an muna komai da ya kamata ,,,,, Kuma cikin ikon Allah kowan mu ta samu tafiya saboda an hada mu da wasu mutane can da ban waidasu zamu.

   

   Allah mai ikon shi yau ni FATIMA Mohammed Sani ,ce acikin jirgin sama zuwa makka ,,, wai a sanadin yar ga aiki yau kuma suna zai koma TAKARI,,,,,,,,
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

  HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 19:06] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                  1⃣4⃣

                     BY

  🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎 

   


    

Yan uwa musulumai na, duniya ina muna murna da sallah Allah ya kara ma musulunci daraja da dauka 

   Allah ya rupa ma kowa asiri Ubangiji kataimaki dukkan al,umman musulmai ameen👏👏


            (Dogon Daji)


   

  A gaskiya kamar yadda mai gari yayi alkawarin cewa zai taima ,haka din ne kuwa don ya taimaka sosai wlh wurin neman Gajiye,,, 

  Yakuma fadi a masallacin jumma,a ataimaka ayiwa fadima addu,an Allah yadawo muna da ita lfy,


 Aiko mutanen kauyen mu su kasa Gajiye gaba da tsina da Allah waddai da ita.

 Wasu sukace ai tayima inna maganine kafin tadaukeni wasukuma suna fadin ai kwadai ne yakai inna badani ,,,,  wani gefen kuma sunce ai anfada masu an,sayar dani ne wurin yan yankan kai don Gajiye har tayi arziki a birni ko.


 Wanan maganganu sune suke kara tayar ma inna da hankali sosai ,,,, duk tabi ta ramay bata cikin hayacinta so sai yanzu,,

  Yayana hafsat ma da ta,fita sai ta dawo gida da kukan ta,saboda gorin da ake mata acikin gari.

    Inna kullun tana kai kukanta ga Allah ,, Allah ya tsare mata fadima,tar

duk inda take,,, tana kuma tuba da cin amanan mareniya da tayi

   

  Ana cikin haka kawai saiga Gajiye wani mutumin kauyen mu ya gani a Abuja a kasuwan wuse,,,,,,,,

   Bata ganshiba yayi ta binta har yaga gidan da take ya tambaya ko nan take akace mashi eh lalai a nan take zaune tana haya,,,

    Ya aika gida cewa yaga Gajiye har ma gidan da take zaune ya bincika anfada mashi,,,

  Cikin kwana biyu mutanen dogon daji suka zo wurin wanan mutumin


    Da taimakon jami,an tsaro aka kamata ,,, tana ta fada tana fadin ita mai tayi daza,a zo har nan inda take zaune ai mata cin zarafi irin haka suka ce ai kawai tazo gida mai gari ne ke bidan ta.

     Koda aka isa dogon daji da ita tana wani,wuri wuri da ido har aka kira inna yar kulu tazo kofar maigari,,,,,, 


Maigari yayi gyaran murya ya bude taro da addua , da kuma yima mutanen shi ,nasiha na su ji tsoron Allah aduk lamarin su na duniya,,,,,  su sa Allah agaba saboda zafin ne ma baya kawo samu,,,,,,


Bayan dogon jawabin mai gari yayi ,,,,, Sai duk jikin Gajiye yai sanyi. 

     Gaba daya an daureta da jijiyoyin jikin ta,,,,, Ko magana ta kasa yi sai gyara zama take yi.

    Duk da sanyi da a,keyi ita zufa take yi kawai. Kafin mai gari yayi bayanin shi sai tace,,, A gaskiya mai gari nasan na cuci yar kulu, 

    Nai mata wayo na dauki yar diyar ta da sunan zuwa ganin gida wurina.

   Gaskiyan al,amarin dai shine nakai yariyar kano wurin aiki ne ba wai sayar da ita nayi ba.

  Wurin wata amiyata na,kaita ai,katau, a kano.

   Kuma gaskiya anbani kudin aikinta na shekara na,cinye saboda hakane ma yasa ban dawo gida ba don gudun kada mu hadu da yar kulu .

    Ta nakai nan duk sai wurin yadauki salati,,,,,,

    Wasu ,suna tama Gajiye tir da Allah waddai da halin kwadai irin nata.

        Saida mai gari yayi da gaske yasamu wurin yai shiru,,,,,,,,,

    Aka natsu maigari yace ko Gajiye zata kai su malam sale da wasu mutum biyu inda Fadima take su dauko ta tace "eh zatakai su insha Allah

   Saida gaskiya bata da kudin da zata biya hajiya mai,sharwali,

     Maigari yace kada ta da,mu, shi,zai  biya hajiya kudinta,,,, 

   Aka shirya yadda tafiyan zai kasance idan an,tashi.

    Daga karshe  Gajiye ta roki gafara inna yar kulu tana hawaye, tana rokon gafara,,,,,


 Maigari ya hada masu tafiya zuwa kano wajen dauko fadima,,,

   Tun karfe shidda na safe suka bar garin dogon daji zuwa kano,,,,,,,

    Sun isa kano da karfe biyun rana ,,,,, saida sukaje sukaci abinci tukun kafin su wuce shagon hajiya,,,,,,

   Koda sukaje shagon hajiya  sai Gajiye taga wurin duk ya canza mata ,,,

    Ta,isa wurin wata mace fara kakaura da tagani tana gyara wuta tai mata sallama 

   Matar ta ansa mata cikin hausanta da ala,mar harshen yare,,,, 

 Bayan sun , gaisa da matar, take tambayar hajiya mai,sharwali, mai wanan shagon 

    Sai matar tace gaskiya bata santa ba ma don ita sayen shagon tayi wurin dillalai,.

     Aiko Gajiye ta daura hannu akai tafara kurma ihu tana fadin ta shiga uku ita Gajiye haihuwar mutum biyu ,,,,, 

   Ina mai sharwali  ta, tafi da diyar mutane,,, ita dai wanan matar tace wlh bata sani ba don ita daga lagos tazo kano ta sai shago ita yar ghanace,,,,,

   Gajiye sai ihu take kurmawa mutane nata kallonta ,,,,,,, a, haka mutane suka taru aka zagaye su don jin ba,asi.

   


       Wakilin sarki yace aidama munsan karya kikeyi mutumiyar banza kawai kinzo ki sayar da yarinya kin gudu ki ce wai anan kika kawo ta,,,,  Gajiye sai sharban kuka takeyi tana bidan agaji


    Ana cikin haka saiga wani dan tsoho yazo yatambayi ba,asin abin da yafaru akagayamai komai yai shiru nawani dan lokaci.


     Can yace gaskiya indai matar da yasani ne tana saida abinci a wanan shagon tasai da shago ta wuce saudiya dayaranta duka.

   Yau kusan kwana uku ke,nan da tafiyanta. Kuma shago da gidan ta dashi akayi ciki su duk ta sayar tabar kasan,,,,,,,,,,,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 19:11] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                  1⃣5⃣

                     BY 

    🐎ZAINAB IDIRS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎       Hafsat Yusuf

         MSS ILLYAS

         Nerbilar

       Mariya SB

     Fatima Garba

  Ina maku godiyan kulawa da ni da kuke na gode fatan alheri gare ku ko yaushe,,,,,,,,,

                           

Almost true life story
   

 (Labarin Fadima Takari)    Mun isa filin jirgin jidda lfy ,  muka bi layin bincike akai muna screening na shiga kasar da niyar zamu yi sati biyu muna ibada,,,,,,

    Muna fitowa wajen sai, ga hajiya zinaro tare da wani bakin mutum sun zo daukar .

  Tun a mota aka fara hiran harka zai yi kyau tunda babu wanda yasamu matsala daga cikin mu,,,,,,


  Wani gida aka kai mu mukan sai kallo mukeyi munga larabawa da kuma yanayjn kasar tasu

    Mundan zauna baifi minti goma ba aka dan bamu abinci bawai don mun koshi ba,,,,,, Rugaiyya ce tace min in,tashi  muyi ramuwar sallah da bamuyi ba,,,,,

    

    Muna cikin sallah sai ga hajiya Zinaro da wani sun shigo suna fadi, oya oya kowa takawo bizan ta za,a aje mata kafin mu koma don kada ya bace a hannu mu,

     Jiki na rawa muka mika ma hajiya zinaro,,, sai kawai ta dawo ta gaban mu tace,,,,,

       Ina son kowa ya saurare ni da kyau, tanu muna biza din tace kunga wanan , mukace eh tace to idan ba dashi ba bu batun komawa gida Nigeria sam,,,,

     Saboda haka mun karbe na kowa cen ku ne sai kowan ku ya kawo muna kudin da muka biya masa aka hada wanan biza din kuma ya ba da ribi a sama,,,,,

  Sanan zamu ba mutum abinshi ya koma gida ,,,,,, 


   Wani irin ihu naji Yumma tayi cikin kuka tana fadin don Allah hajiya kuyi hakuri ku maida mu gida don Allah kada ku bar mu anan 

   Ke rupe muna baki kinji inji katon mutumin da suke tare da Zinaro yace ma Yumma,,,,,,

 Sauran ma kuka naga suna yi nidai ina tsaye ina kallon su ido wuri, wuri dani

    

      Daga nan aka kwashe mu lokacin dare ya fara zuwa wani wuri madan nisa saman wani dutse gidan yake dan karami daganin ginan kasan na da ne,,,, kuma na tallakawa ne ,,,,   muna fita motan hajiya Zinaro ta karbi kayan su goron da muka zo da shi tace ma hajiya sai ta dawo zataji yadda za,ayi,,,,,,,,,


     Tunda hajiya Zinaro ta aje mu bata leko mu ba , ga yunwa ga matsi ya ishe mu,,,,,,

   Hajiyan mu ta dan shiga damuwa rashin ganin dawo wan Zinaro,

   Wacce ta tafi da dan kudin da hajiya ta kulla zamu je mu ja jari da shi,,,, 

    Wata makwabciyar gidan da muke Laila yar katsina itace ta dan tai maka muna da abin da zamu ci,,,,,,

    Data,ga la,lai zinaro ba zata dawo ba kuma da alama ta yaudari hajiyan mu ne,,,,,, Sai hajiya Lai,la bata nuna ma hajiya ai yaudaran ta akayi ba sai ta ba hajiya shawaran mai zai hana mu fara bidan kudi tunda muna da yawa ,,,,,,,

     Shawaran matar hajiyan mu ta dauka,,, mata ita taima hajiya hanyoyi kakala don mu fara sana,a a jidda,,,,,

 

      Aiki aka samo muna a gida jen larabawa don mu samu abin kula da kan mu,,,,

     Gidan wasu turawa nasamu aka kaini inda zan dinga kula ma matar da yaron ta na goye gaskiya na ji dadin aiki a gidan saboda da turanci muke magana 

   Ita kuma antyna Rugaiyya goge goge a ka samo mata a wani ma,aikata,,,,, saidai Hajiya Laila tace aikin ba mai dadewa bane zamu bari mu koma Riyahd ne,,, saboda can anfi samun kudi,,,,,


    Uwar dakina Rita ba laifi gaskiya iyakata daukan yaro in,dan mashi wasa sai ku ma da dare indan nane dinshi ta tafi gida ne nake aikin

 Amma ina samun kulawa sosai daga wurin Ritan,,,,,

    Ina yarinta sosai alokacin don haka ban damu da komai na duniya ba,,,,, 

  A lokacin da zamu fara aiki an muna huduba cewa ba ga albashi kawai zamu dogara ba,,,, zamu dan rika hadawa da , dabara samun kudi bawai muce sai abinda aka bamu ba,,,,, 

 

    Yan uwana kowa na na,shi aikin daidai sun fara sabawa da aikin bidan kudi,,,, 

    Ranan lahadi da mutanen gidan mu zasu je wurin ibadan su sai suka sauke ni gida wurin hajiya kafin su dawo,,,,

     Nasamu hajiyan mu bata jin dadin jikinta dan abinda aka bani in kawo mata ,,,,,,,, Da kyat ta iya dagawa donta gani ko may ye acikin katon ledar da nashigo dashi,,,, 

   Duk hajiya sai naga tabani tausayi sosai ,,, amai tafara yi can kuma sai gudawa,,,,,

    Nakama ta na kaita ban daki na gyara mata jiki,,, tea mai kauri na hada mata daga cikin kayan tea da aka bani inzo dashi daga gidan aikina,,,

   Hajiya bata dade da kwantawa ba sai barci yadauke ta,,,

    Natashi nadan gyara mata dan tsukaken dakin namu,,,, daidai naga ma gyara Rugaiyya tadawo daga wurin aikinta,,,

     Munyi murnan ganin junan mu sosai da Rugaiyya ta rungumay ni tana hawaye,,,

   Sai nasa hannu na nashare mata nace kai anty kibar kuka mana ,,, tace Fadima aidole inyi kuka tunda bansan ranan da zamu bar wanan kasar zuwa gida ba,,, nace mata ai babu komai

     Mundan jima muna hira tana tanbayana lbr inda nake aiki daku ma yadda nake zama dasu,,,,,

     Tace fadima don Allah duk ritsi kada ki yarda ki zubar da mutum cinki na diya mace,,,,,, ki kama darajan kanki don Allah 

  har zuwa lokacin da Allah zai kawo muna mafita nace to,,,,,

   Iyayen gida na suka dawo suka,zo suka daukeni muka koma gida,,,

      

    Kamar yadda akace aikin wata biyu zuwa uku zamuyi haka din ne kuwa 

     Saidai ni abin yayi min daidai don dai uwayen dakina ma sungama contract din su zasu koma garin su,,,, 

Kayan afani masu yawa nasamu wurin su

   Nakawo ma hajiya ta sayar muka hada yan kudin mu muka kulla sai birnin Riyadh,,,,,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎

 🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 19:15] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

       👣👣👣👣👣

       👣👣👣👣👣

                1⃣6⃣ 

                  BY 

    


 🐎ZAINAB IDIRIS MAKAWA🐎

 🐎HUGUMA GROUP🐎


Muna godiya ga ubangijib mu sarki Allah da ya nuna muna wanan lokaci mai albarka , Allah ya bamu damana mai albarka ,,,,,,,, 

    Jinjina gareku yan huguma group , musan man Anty hasfsat yusuf da anty mariya sb sai mai group din safiya Abdullahi huguma ,,, 


Almost true life story,,,,,,,
      GARIN RIYADH 


  

Garine mai cike da jama,a kala kala ,,, saboda kasan cewar garin itace babban birnin kasar saudiya,,,,,,

    Bamu sha wani wahala ba sam wajen samun aiki gaskiya,,,, da taimakon hjy laila muka samu wuraren ai yukan mu still wani gidan raino aka kara kai,ni.

     Wanan karon wani katon  gida aka kaini mai kyau ga shuke shuke iri iri a gidan . Muna shiga gidan  naga tunda nake bantaba ganin gida irin wanan ba. Cikin gidan wani  swimming pool ne,ga ruwa yana ga ruwa yana bulbulowa ta cikin wasu duwatsu,suna ba wa grass carpet ruwa da fulawowi , Abin takar a film nake kallo ba ido biyu ba ,don dai ni bantaba ganin irin haka ba arayuwa ta,,,,,,,

    Ina ta murna a rayuwata zan ji dadi ashe ba gidan da muke nupin zuwa bane muka shiga,,,,,

    Bayan hjy tayi sallama wani dan matashi mutum  yafito ,,,,,

    Cikin harshen larabci yake tambayam mu wa,muke bida ne tace gidan Al, shahideen bin Utuman mukazo 

   Sai yace mata ai ba nan bane sai ta kara gida na gaba,,,,,  

     Kusan gidan iri daya ne amma dai akwai bambanci a,gina gidan iri daya,ne dan bambancin kadan ne,,,,,


     Muna shiga cikin gidan muka iske wata, balarabiyan mata, a,kata faren falonta na alfarma tana kallon talabijin tashar tashar makka ce daidai lokacin da suke sallar azahar .

   Matar ba wata babba ce ita ma tana saye da dogon riga sai wani dan karamin hijab akanta,,,carbi rike a hannun ta guda tana ja a,hankali cikin natsuwa,,,,,,

    Ta ansa muna sallamarmu cikin fara,a daidai lokacin kuma ta mike tazo da fara,ar ta tare mu,,,,, 

    Suka rungumay juna ita da hjy Laila ta sunbanci gefen kumatun hjy Laila,,,,,,,  ni, dai ina gefe ina kallon ikon Allah , wai ashe gaisuwa ce hakanan ,,, sai kuma naji sun buge da yaren larabci,,,,,

    Ina dan gefe tsaye naga hjy Laila tana magana tana  nuna ni,  da alamar magana ta akeyi,,,, dariya naga sun sa har fararen hakorar matar ya dan baiya na waje,,,,

    Hannu matar ta mika min alamar inzo gurida a

  Nazo tai min yadda suka gaisa da hjy ,,, sai ta dan lakaci kumatuna tai wani magana cikin larabci. 

    Tajawo hannu na ta zaunar dani kusa da ita,,, maganar cikin larabci take fadin wai gaskiya tana so ,na , saidai nayi karama da aiki,,,,, amma idan zan iya yimata rainon yarinyarta zata daukeni,,,,,,

      Tana shafar kaina tana magana cikin mutunci da girmawa,,,

    Sukayi cinikin aikina da hjy Laila,,,,, 

    Mama Nailabin ta shiga daki ta dauko kudi masu yawa, wanda ni alokacin bansan adadin su ba taba hjy Laila wai kudin aikina ne


     Hjy Laila takira ni gefe tace min to ita zata wuce don Allah in kula da aikina kada in, bari a samu matsala ko kadan daga fanni na don maman, Nailabin tana da kirki so sai,,,

    Tunda,ga wanan ranan aikina yafara  a gidan Al,shahideen bin Utuman ,,,, 

   Ni duk wanan abin da akeyi hankalina ya,na can a wancan gidan da muka fara shiga na farko ina son in koma wurin ruwan nan da naga yana fita acikin duwatsun nan dake malala a green carpets ,,,,, 

    

   Daki guda aka bani ni kadai dakin babu dai ne babu acikin shi don dai wasu abin ma dai ni ban taba gani ba koda nai zama wurin madam Rita a,jidda muna kallon film din su, na, turawa ,amma banga irin haduwa haka ba,,,,

    Maman Nailabin mace ce mai yawan ibada ga natsuwa da kuma sanin darajan mutum,,,,

   Ita,ma a,nata bangaren tana jin dadin yadda nake kula mata da yar ta so, sai ,musan man, goyata, da nakeyi anytime,,,

   Abinda ban sani ba ashe akwai camera a,dakin na suna kallon duk wani abu da zan ma yar su,,, kusan kwana bakwai ana daukar irin kulan da nake wa Nailabin,,,,,,, abin ya basu mamaki don idan tana kuka nai lalashinta batayi shiru ba nima kukan nakeyi,,,,, acikin kukan kuma zan jawo yarinyar inta lalashin ta,,,,,,, sai mun gaji muyi shiru,,,,don kan mu,.

   Barci kuma kusan a jikina takeyin shi ko a goye ko abisa cikina.

   Jindadin hakan yasa baban Nailabin ya sayo min kayan sawa iri,iri ,,,,,, idan ka gani baza ka ce fadimar kauye bace

    Saboda son da nakewa Nailabin da kula da ita tsakani da Allah yasa 

   Iyayen ta sukayi shawar taimaka min ,,,,,makarantar da ke unguwar su suka sani makarantace ta "ya" yan masu kudin kasar sai wani da wani ke makarantar,,,,komai dakwalarcin ka dole kasan abu kafin wata biyu,,, Ranan alhamis da jumma,a ba mu zuwa .

    Amma lahadi da asabar har da yamma muke zuwa ,,,, 

   Hakan yasa suka dauki wata yar aikin don kula da Nailabin ,,,, ita wanan matar balarabiya ce yar uwan,,su.

 

    Tunda natafi gidan aiki na ban, karajin labarin yan uwan tafiya na ba.

   Karatu da rainon Nailabin kawai nasa a gabana .

    Duk lokacin da zan wuce makaranta sai na laika wanan gidan na kusa da mu indinga kallon yadda ruwa ke fito wa cikin dutse yana zuba a kasa.,,,,,,,, 

  Cikin haka wata rana, na leka naga ba kowa a wajen gidan ,,,,,,, Cikin sanda na lalaba har naje inda ruwan yake fitowa nadinga tara hannu na ruwan yana zubu min,,,,,,,🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 19:37] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈ 

        👣👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                  1⃣7⃣

                     BY

   

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


    Jinjina gare ku yan uwa na na huguma group novel da fatima luv group  novel, da fadila group novel, musha karatu group, maman fati group novel,,,,,, nagode maku kware wlh Allah bar zumunci,,,👏👏👏👏👏


Almost true life story,,,Sam ban jikaran bude kofan da akayi ba daga cikin gidan

     Wani balarabe ne abayana cikin jallabiya fara sai kan shi saye da jan kafiya,,,, Da alama fada yake min

   Bayanshi wani farin mutum ne saye cikin kananen kaya ,,,,, wandon jens sai wata bakar riga tie shet mai guntun hannu,,, hannu shi na rike da waya yanayi,,,,, 

   Cikin fushi, na farkon yai niyar jawoni baya ,,,, amma sai wanan wanda nake gani da alma shine oga,,, Ya daga mai hannu cikin wata murya da banji ba yace ya kyale ni kawai,,,,,,,

   Baiko kara waigowa ba ya nupi wata bakar mota da ban ko kula da tana cikin gidan ba ma sai yanzu ,,,,,,  cigaba nakara yi da wasa da ruwana duk na jika jiki na dashi

    Saida nagaji nafito don kai na badon wani ya hanani ba ,,,, ,  Koda nafito ido yai wani ja alamar nasha wasa da ruwa.


     Wanan balaraben na farko na,gani tsaye yana jiran in fito ya rufe kofan da na sata nashigo ta ciki,,,,,

     Harda bye, bye na mai da zan wuce duk na jika kayana sai digan ruwa sukeyi.

  Sadaf sadaf nake shiga gidan mu don kada agani cikin kaya jikake,,,,,

    Jinayi anja min kune ta baya kawai saina sake jakata ta makaranta ta fadi kasa,,

   Jikina yadauki bari ,,,,,,,,

      Muryan shi kawai naji nagane baban Nailabin ce ke magana yakama yi min fada ina naje tundazu antashi daga makaranta amma ni ban dawo ba,,,  gashi hankalin su ya tashi sosai 

   Ina dan magana cikin rashin gaskiya nace motar ruwace taimin bari akai ,,,,,, 

    Baice min komai ba kunsan su larabawa basuyi ma diyan su fada irin namu nan Nigeria

    Maman Nailabin tazo da sauri ta jani zuwa bandaki ta sake min ruwan dumi tace in sauri in watsa in fito,

Kada sanyi ya kamani, don su tsoron mura sukeyi sosai don bai raga masu. 


    Tun wanan ranan in,zandawo sai nadan tura kofar gidan inji ko zanyi sa,a injita ,a,bude,,,,,

   Yau ma ina turawa naji a,na min hon din mota abaya na koda na waiga saina tabas gidan za,a shiga nadan,  Rakube jikin bango gidan har aka bude get motan tashiga,,,,

     Nima nadan sudada nashiga ciki kafin arufe get din bayan motar na labe har, na cikin motar yafito,,, nadauka mai shi ya  shige ciki ne sai nafito daga inda nake labe na nufi gurin ruwan dutse nafara tara hannu na ke nan naji ance ke baki gudun cuta yakamaki ne wai,,,,

     Firgita nayi dajin maganar shi ina shirin gudu na hadu da gudan mutumin ta bayana.

    Yace min in fita cikin tsawa suku, suku nafita ina dan waigen bayana kamar wace za,abiyo baya,,, da guda na karasa waje

   Ina jin sun rufe get din su garam da karfi nikuma na aza da sauri nashige gidan mu

 

     Ina shiga gida nadinga jin hayaniya da kuka abinda bantaba jiba muryan mace na kuka tunda nazo kasar,, shi,naji yau a,gidan mu,,,

    Matar da ke kula da Nailabin ce ,nagani tsugune tana kuka sai wasu maza guda biyu da alamar jami,an tsaro ne su,,,,,

    Maman Nailabin nata sharbar kuka ita kuma ,Nailabin din tana hannun wasu masu fararen kaya

 karar mota naji ta asibiti anzo kofar mu,,, saida naga anfita da Nailabin kamar matatta a hannu ,ai bansan lokacin da na fara kurma ihu ba ina fadin nashiga uku da larabci ina tambayan may yasamu yar kaunata,,,,

    Muna kallo aka wuce da ita zuwa asibiti cikin motar mu, muma muka bisu a baya,,,,,

    Muna shiga asibitin ko fita ba muyi ba akace mu juya zuwa gida ai Nailabin tarasu,,,,,,,

    Munyi kuka sosai hankalina ya,tashi da mutuwar wanan yarinyar sosai don wlh duk da nasan ina son yara ,,, to itakan Nailabin nata daban ne don cikin yan watanin da nayi dasu mun shaku sosai da ita,,,,,,

    Bayan sati biyu da mutuwar Nailabin tunda safe maman Nailabin tace in shirya muje

   Wani wuri mukazo ba mutane da yawa agurin amma akwai jami,an tsaro sosai,,,,

   Sai naga anfito da wata mata ansa mata wani bakin buhu an rufe mata fuska dashi,,,,,

   Aka tsugunar da ita ana bude mata fuska sai naga ashe matar nan ce mai raino ,,,,, tana ta fadi da larabci wai ba itace ta kashe ta ba,,,,

    Kukanasa nima wi,wi nari,rike maman Nailabin duk na shishige mata ajiki ina,noke kaina ajikin ta,,,,,,,

   Muna ji muna gani akasare mata kai,,,,,,

 

  Tun lokacin a tsorace nake a gidan nan,,,,,, sai daga baya nake ji ashe mai, rainon Nailabin itace ta wurgo ta daga saman gado sai akayi sa,an wuyan ta ya kare ,,,

    Ita kuma bata san akwai camera ba,a dakin. Nima sai a lokacin nasan cewa akwai camera a duk gidan,,,,

 Ansa muna cassette din mun kalla naga baban Nailabin yana kuka da hawayen shi,,,,

    Sai sun baka tausayi wlh,,,,

   

   Ni abinda ban sani ba ashe su maman Nailabin ba mutanen kasar saudiya bane,,,

    Mutanen kasar Egypt ne su aiki ya,kawo su saudiya kawai ,,,

    Uguwar , da nake uguwace ,ta ,engineers din matatar mai ta kasan saudiya . duk wanda kagani aunguwar mu kusan a matar mai yake ,,,,, sai babban kusan kasar ke wurin...

     Bayan yan kwanaki, sai baban Nailabin ya shigo gida ina dakina ya kirani nazo nadan zauna .

    Yace min Fatima zamu koma kasar mu don ban iya kara zama wanan kasar ,idan na zauna zandinga tuna Nailabin dina ne ko yaushe.

  Kuka nasa sosai ina fadin zanbisu.

    Dakyat ya bani hakkuri ya lalashe ni nai shiru, yadauko takardu yabani yace min wanan shedar gama makarantar da nayi ne yakarbo min ,,,yace in ina da sha,awar karawa gaba ina iya zuwa.

      Yakawo kudi masu yawa yabani yace inkai ma hajiyan mu 

Ina kuka sunayi suka maidani har gidan hjy Laila,,,,,,,

   Rabuwana da su maman Nailabin ke nan, mutanen kirki da bazan taba mantawa dasu ba arayuwata saboda sun tai maka min da abubuwa da dama ,a rayuwata ga ilimi nasamu ga kuma waye ,,,,  

   


Hakana nadawo gidan da hajiyan mu ta kama da zama ,,,,

     hajiyan mu tayi murna sosai da abin arzikin da nadawo dashi har da albarka ta dinga samin

     Tana cewa da a,ce duk kan mu zamu samu irin abinda nake samu ne ai da mun koma gida ba da dadewa ba,,,,,,,

.


 🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 19:44] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                     1⃣8⃣

                        BY

 🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


Fatan Alheri gare ku yan uwana kuma abokai da kuma masoya wanan novel din nawa


Almost true life story        GARIN MAKKA  Ba mufi wata biyu ba muka bar garin Riyadh muka zo garin makka saboda lokacin zuwa umarah ya kusa kuma baza,a wani dadewa ba za,afara aikin hajji,,,,,

      Hjy Laila ta taimaka ma hajiyan mu muka samu wurin zama a garin makka can saman wani dutse ne ta bayan gari,,,,

     Akwai kau,yuka da dama a bayan dutsen akasarin mu yan zuwa cirani nan muke zama a gefen gari.

        Munyi sa,an samun wurin zama maidan kyau sai,dai matsalar hawan saman dutsen da ba mu sababa

    Hjy Laila taba da shawaran mu dan fara saida abinci kafin baki su kara cika gari don Umurah sau kadan afara,  ,,,,,

   Masa ,muke sayarwa da shinkafa kaza,da miya sai shinkafa da wake da maidayaji da salad,,,,

   Wani lokaci harda fura muke sayarwa

    Wasu samari majiya karfi hajiyan mu ta dauka aiki suke sauko muna da kayan abincin mun kasa don gaskiya bamu iya saukowa dashi mu,,,,,


    Allah naba,mu,sa,an sayar da abincin mu don gaskiya ba laifi mutane, suna yabawa, da aikin mu.

     Idan mun saida  abincin mu da wuri sai kuma mu canza kama, zuwa wurin bara kafin agama abincin marance,,,,,

    Mune kanani muke zuwa yin bara sukuma antyna Rugaiyya suna zuwa su saro gumama su dinga sayar wa a saman gefen titi ,,,,Saidai da anji jiniyar jami,an tsaro dagudu za a sheka abar kayan don da sunkama mutun to babu sauki wulakanci zasuyi ma mutun su kuma kaika duk kasan da suka ga,dama suyar da kai

     Wanan maganar da aka fada muna tun zuwan mu aka koya muna gudu,,,,,

     Mukuma masu bara za,a samu nama danye fresh mai kyau, shiza a,daura ma,mutun agefen kafa ko hannu, da ka kalla saudaya baka kara waigawa ka diba,saidai ka bada sadaka ka wuce

    Za,a daure ma mutum kafa ko hannu idan kani sai ya baka tausayi kamar kayi kuka,,,,,zaka, ga kamar dungu ne kawai mutun haka aka haife shi,,,,


   Wani kuma za,aba mutum keken guragu ka, nade cikin ke kamar mai shan inna kana dan wani nokewa kamar gaske,,,,

  Duk wanan salon baran na, iya su kamar nadade cikin harkan.

   

    Musalin karfe shadaya na rana ,,,Daidai in da motoci ke cunkoso dayawa ,,, wutan titi yanuna masu alamar su tsaya tukun,

      Nazo da muryana kamar ta rarara ina fadi cikin harshe larabci 

    Ina fadi a,taimaka min da abinda zan kai ummeena asibiti

   Wata mota na,nufa mai glass karara ana ganin wanda ke bayan motar zaune yayi irin kwanciyar bayan motar nan,,,,,, Fari dogo kan shi, sai shining yakeyi da ka diba kasan akwai jindadi wurin wanan mutum din,,,,,  


 Hankalinshi,   Yana ga   laptop din shi yana ta dikilanta dagani, hankalishi yadauku sosai,,,,, ,,  Jin murya na,da yayi ta i,she da kuwa, yadan, dago kashi don yaga mai wanan muryan rarara ,,, 

    Ya dago a hankali yakai diban shi inda nake tsaye ,,, yakau da kai,, sai,kuma naga ya waigo ni da sauri

    Daidai lokacin wutan ba da hannu na titi yanuna kore ,, alamar a,wuce anbada hanya ,,,,

   Daidai lokaci ya dauko kudi masu yawa cikin wata jaka agefen shi,,,yamiko min na karba ina ta godiyan jin dadi.

   Motar ta wuce nakai dibana ga kudin saida na fidda ido na don ganin yawan kudin da ke hannu na.

     Cikin Aljihun, rigata mai zip, da hajiya tai muna, na kulle, ina murna wanan rana mai albarka 

   Motar ta,dan wuce green light din kadan saina bayan yace ma driver ya,ga kamar ya gane wanan yarinyar kuwa  saidai ya manta inda yasanta,,,,,,,,,

    Sai driver yace  bai kalleta ba don haushi taba shi saboda nasan baka son hayaniya baka kaunar masu wanan dabi,ar baran musan man ma bakar fata

,,,,,

   Bayan mundawo wurin sa,na,ar mun ta marance, Mungama saida komai namu zamu tafi gida

   Saina jawo antyna Rugaiyya, gefe na nuna mata kudin da na samu yau,  Ido ta zaro waje

    Ina kika samu wanan kudin fadima na fada mata ,yadda akayi tai shiru nawani dan lokaci.

     Sai,tace min mutafi gida to.

     

     Koda muka isa gurin hajiya itama saida tayi mamakin wanan kudin masu yawa ,,, ta,dinga samin albarka tana ta washe baki,,,,

      

Antyna Rugaiyya nasamu waje, zaune gefenta nima nazo na zauna ashe, kuka,takeyi a wajen  bansani ba saida na yi mata magana sai naji tai min shiru nakai dibana ga fuskanta sai naga hawaye,,, 

   Rugumay ta nayi ina kuka nace mata may yasa may ki yar uwata ,,, kuka yakara kubce mata,,,, 

   Tace fadima baki ganewa ne ke,,,,yanzu don Allah haka zamuyi ta bautawa hajiya bazata maida mu gida ba,,, idan har tace sai mun biyata kudin jirginta ai ina gani dai yanzu ta samu ko

    Amma wanan ai bauta mukeyi mata cin amanar yai yawa,,  

   Nadafata nace aikin san tun agida aka bata mu ,,  muyi mata bauta ko ,,, saboda haka sai muyi hakuri har ranan da Allah zai kawo muna mafita,,,, Dan Allah ki daina wanan kukan hakana pls,,,,,,,,,,
🐎ZEEE  MAKAWA 🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 19:49] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                 1⃣9⃣    

                    BY

 🐎ZAINAB IDRIS MAKWA🐎


   Gaskiya muna saki a wanan zamanin da wasu abu biyu da manzon Allah Annabin Rahama yai kwadai ta  muna yinsu zai kaimu Aljanna barin su zai iya kai mu wuta. Hakin,makwabtaka da Zumunci ,,,,,  Allah ubangiji yabamu ikon kula da makwabtan mu da kuma yin zumuci da yan uwan mu Ameeen👏👏👏👏


Yan uwana yan Huguma group ina maku godiya kulun tare da sauran yan wani group da ban fadi sunan su ba,,,,,,


Almost true life story
   Ni fadima na iya bidan kudi kala,kala kamar yadda kusan kudi baya isan TAKARI , Duk wani sallon bara da sana,a an koya min na iya gani yar shekara sha uku zuwa sha hudu,,,,,

    Amma hajiyan mu tana alfahari da ni sosai wlh saidai bata fadi a,gabana acewanta idan ta yabani a,gabana zan yi sanyi indaina samo mata kudi,,,,,  Watan   Azumi ya kama ibada akeyi yanzu sosai yan kasar mu ta Nigeria dama wasu sauran kasa she ,sun cika garin makka da kewayen ta sosai,,,,, 

    Munji dadin wanan cikar don kasuwar mu ta budu so sai

     Muma muna kokari wurin zuwa ibada,,, Rugaiyya tabamu shawaran kulun kafin, mu fara sana,a mu ,ko,karta mu ,shiga cikin Masijid muyi , Dawafi 


    Yauma kamar kulun misalin karfe sha dayan rana nakusa cikin dandazo jama,a ina Dawafi,,, kafin in fita in fara bara don bamu abinci saida Yamma muke yi,,,,,

   Dandazon yan Serbia sokayo kaina duk sun matse ni banko iya nunfashi saboda kowa nason ya kai bakin kofar shan madara,,,,,

  Ji kawai nayi an,dagoni Cak daga cikin rutsun da aka matseni,  An ajeni gefe guda,

     Saida na maida nunfashi na daidai naga wani mutum dogo, fari, kyakyawa gabana yana min fada ,cikin harshen larabci muryan shi kamar yana lalashina amma daga yanayin fuskan shi fada yakeyi min,,,,

Ke wata irin yarinyace wai kina ganin taron yan Serbia kowa na kaucewa ke bakijin tsoron su ,zo su, tatakaki, su wuce ,,,,

   Nidai tunda nasamu na tsira ban ko tsaya nai mai godiya ba na wuce abina ,,,,,,,,,

   

    Bayan kwana biyu da yin wanan rutsun cikin haram da nayi fitar kutsu ,,,, 

    Dadai da angama sallah azahar lokacin baran mu yayi ke,nan .

   Saidai ni nakan canza hanya ne bani zama guri daya,,, idan nai kwana daya ko biyu sai in can wata kofar in kuma canza sallon barana

    

Yau ma kamar kullun sabuwar kofa na sake ina zaune kamar wata mara hannu ina bara sai naga anzo daidai kwanon bara na , an ,aje, min kudi sabbi fill acikin kwano ,,,,

    Koda na daga kai inyi godiya sai naga mai,shi har ya wuce ko,,,,, bayan maishi, kawai nagani amma cikin daga murya nake mai godiya,,,,,

     Kudine masu yawa nagani ,Aiko baran da na bari ke nan ranan ban kara zama ba.


   Kwana uku tsakani kuma na canza wata kofa don zan canza kama ,,,,, 

   Kofar da ake shiga da gawa don ayi mata sallah  itace na zauna na kawo wani nama na aza akafa na sai kuda ke bi,,,,

   Duk da nasan ba kowa ke bi ta wanan hanyar ba sai lima,mai da wasu manyan malamai da mutanen masu son yawan ibada su ke yawan bi wanan hanyan sai ko idan andauko gawa ,,,,,

   Idan mun zauna muna yawan samun sadaka daga yan uwan mamata,,,, bakowani mai bara ke yawan zaman nan ba don wasu tsoro suke ji,,,,,,,

 

Muna zaune tare da yan tsirarun almajiran da ke waje jama,a nata bautar Allah aiko sai a,kace ga gawa nan za,a shigo dasu na wasu mutanen da sukayi hatsari ,,,,,

    Cikin Almajiran mu Atika da take zaune kamar gurguwa aiko sai ta manta yadda ta nade kamar musaka,,,, dadai taji ana fadin tarik tarik tarik aiko saita mike tsaye tana shirin gudu,,,

   Wata mata, dake gefenta zaune tare da mijin ta tanuna ma mijinta Atika,,, tai, mai bayani cewa itace fa, zaune kamar gurguwa, dazu,,, saiko ya mike, yadanko wuyan Atika ta baya, nan suka fara rikici, tana fadin yasake ta tun suna yi su biyu har takai  sunfara ji

Jama,an da ke,wurin ko sukayo kanta wasu na duka wasu na fadin akaita wurin jami,an tsaro,,,,, muna zauna saiga wata da gudu take fada muna ai ankama Atika,,, nan tashiga yi muna bayani ,,,, kafin kace kwabo yan bara sun shiga watsewa saida wanda ke da nakasar gaskiya,,,,,,


   Maimakon in gudu sai kawai na nufi gurin da aka kewaye atika ana duka tanata tsala ihu,

    Wani balarabe ya rike mata wuyan riga ta baya,,,, 

    Duk tausayinta ya kamani,,,,

    Sai kawai nai kukan kura nafada cikin taron nadauko naman da nasa akafa kamar gyambo na jefa ma taron aiko sai aka watse da gudu ,,, daidai lokacin jami,an tsaro suka iso suma saiko naja hannu Atika muka ar,ta da gudu nace mata mu raba hanya,,,  

   Ina cikin gudu na ji an,fisgoni anzaunar dani bisa wani abin sallah har jamian tsaro sukazo suka wuce mu kaina na duke,,,,,,,

   Saida naga lalai sunyi nisa sai nayi niyar mikewa in gudu

   Muryan wanda ya jawoni ranan daga cikin taron Serbia wa naji,,,, yana fadin ki tsaya nan har sugama bincke ,,,, duk wanan maganan baiko waigo inda nake ba,,,,,

   Ana tada sallah la,asar namike nabi jam,i akayi sallah tare dani ,,, koda naga an,kusa sallamewa sai na sulale a hankali batare da sanin wanda ya taimakeni ba,,,,

     Kafin ace haka har lbr yakarade yan bara cewa ankama Atika Ankama Atika,,,,

 Koda nadawo gida ban fada ma kowa ga abinda ya faruba yau,,,,,

  Cikin dare na fara barci kawai naji ana tashina ,,,, nikuma lokacin ina jindadin barci na don dan lokacin da muke samu  muyi barci kadan ne ba muda time,,,,,

   Jin murya hajiyan mu danayi shiyasani mikewa dasauri ,,,barci na ya watsake kamar bani ba.

  Waje ta fito dani sai naga wasu mutane su uku tsaye maza biyu da mace guda,,,

  Hajy tace masu itace wanan  ko sukace eh itace🐎ZEEE MAKAWA 🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 19:57] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

      👣👣👣👣👣

       👣👣👣👣👣

               2⃣0⃣

                  BY

 🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎 

🐎HUGUMA GROUP & KAINUWA  WRITERS GROUP🐎Yan uwa musulumai muso wa "yan uwan mu abinda muke so wa kan mu,,,,,, 


Almost true life story

 Ido na kara ra budewa inga ko suwaye ke bidana cikin wanan daren

    Gaskiya ban san su ba  kuma ban taba ganin su ba ma,

    Babu abinda ya fado min a raina sai abinda ya faru dazu a wurin bara

 Aiko sai naji gabana yai wani dam,,,,,,

    Muryan daya daga cikin mutanen ya katse min tuna ne na, ,,,,

     Yace fadima munzo ne muyi maki godiya ,bisa ga irin taimakon da kikayi wa yar uwa guda dazu,,,,, 

    Agaskiya ba kowane zaiyi irin wanan taimakon ba ,,, kuma inba don ke ba agaskiya yau Atika da dubun ta ya cika gaskiya,,,,

 Ni,ko sai wiki wiki nake yi a gefen su ,Don gaskiya banso hajiya tasan wanan zancen ba don zata iya duka na,,,,,

   Sukayi wa hajiya godiya suks wuce abinsu

 


     Tab suna wucewa aiko hajiya ta ja min kune tana fadin ashe baki da hankali ki,kaje ceton wata maimakon ki gudu shine ke wai gaki uwar tausayi ,,,,, 

   Aida ankamaki da kin raina ma kanki wayo , idan halinki ne gobe ki koma 

    Duk fadan da takeyi kaina yana kasa ban daga kai na ko kalli inda take ba,,, fada iya fada dai nasha shi wurin hajiyan mu ranan,,,,,

    Lokaci ya ja yan umarah sukazo suka rage yawa bakamar lokacin azumi ba.


      Yanzu mun fi bada karfi da  ,"yan buga buga,sayar da kaya da abinci , dakuma yan aikin da,ba,arawa,,,,,, kafin  lokacin aikin hajji yayi.

 

Ni,kan dan kewaya gida je muna dan yin aikatau saidai ni gaskiya ban faye son wanan ,irin aikin ba nafison bara da talla yafi mun,,,,,


   Ko da muka dawo gida daga wurin bidan kudi ,, yau nasamu hajiyan mu da wasu mata a gidan mu,,, 

   Saboda haka ban tsaya inji ko suwaye ba,,, sai nadan fita waje,,,,

   Wai ashe wasu matane yan kun,giya sunzo gurin hajiya ne suji idan zata shiga a,dashe ,,,, saboda tana da yara aiki gwargawado ,,,,,

   Ma,ana akwai kudi sosai a wurinta 

    Inaji dasu Yumma da anty Rugaiyya suka dawo hajiya na basu shawaran cewa zata fara zuba adashe indan ankwashe mata sai mu dawo gida Nigeria dazama kwatakwata don ita ,ta fara gajiya da zaman TAKARI

   Rugaiyya bata yarda da wanan shawaran na hajiya ba saboda tasan halin matan TAKARI basu da tabbas,,,

    Kowa na iya cutan dan uwan shi,,,,

      


   Bayan kowa yayi barci sai Rugaiyya ta tadani ,taimin alamar mufita waje,,,,,

   Bayan munje waje shine take fada min shawaran da hajiya ta fada masu ,, duk da yarinya nake sai kawai naji ban yarda ba,,,


 To amma may ye abin yi kafin dai mu tashi muka tsaida shawar guda,,,

    Abinda hjy zinaro taima hajiyan mu ban manta da shi ba don har gobe yana cikin zuciyar hajiya , Kuma Zinaro itace sillan zowan mu wanan kasar,,,,

  Amma daga karshe yaudaran hajiya tayi ba ko lbr ta.Yanzu duk wani abinda muka samu zamu raba biyu muba hajiya rabi, saura kuma mu boye abin mu ba wanda yasani

    Saboda muma munyi wayo mukuma dan san mutane kadan

   Duk da hajiya bata barin mu muna shiga mutane sosai kulun fada take muna.


    A, cikin irin wanan yanayin narashin nayi muka samu gyaran wani shago,, kamar yadda kuka sani cewa, indan lokacin aikin hajji ya gabato jama,a daga kowani ,yanki , na, kasan suna shigowa gari don saida kayan ,

    Saboda baki mahajjata masu zuwa aikin hajji

   Irin hakan yana kawo muna samun kudi sosai ,,, akan, dauke, mu aikin gyaran shago sauran wuraren masana antu,,, akasari su sai wanan lokacin suke bude shago.

   Idan mahajjata suka wuce baza,akara budewa ba sai kuma wata shekara tadawo,, Za,a bude ta,,,,,,


      Mun samu wanan aikin a,wani babban shagon saida kayan sawa na zamani , na maza da mata da yara moderate masu kyau ,,,  

     Sai kuma gefe guda kayan gyaran daki ne kala,kala irin na matan zamani gudan gefen shagon kuma kayan kitchen ne na zamani masu kyau iri, iri ,,, shagon karshe na kayan turare ne kala kala masu kamshi  sosai.

 Wata hajiya tasamo muna wanan aikin gyaran wurin, 

    Munyi aiki sosai mun gaji yauce rana ta karshe da zamu gama aikin mu ,, 

   Kuma za,a sallamay mu mutafi,,,

      Ina cikin shagon kayan sawa ina dan gyaran wani wuri,,, 

   Dai dai,ta inda nake tsaye naga wallet din wani mutun yafadi ,kasa amma banga fuskan mai shi ba,,, ina dai iya hango kafar shi,,,,,,,

   Da sauri na sauko daga inda nake nazo nadauki wallet din bandai bude ba inga ko may, ye a ciki ba,

    Cikin sauri sauri nake ta diban kafar mutane ko zanga takalman mai wallet din ban gani ba,,,,

    Gabda zai zauna cikin mota ni kuma na sheko da dan gudu ina bidan mai wanan wallet din sai nayi arba dashi zai shiga mota,,,

   Cikin sauri na nufe shi ina daga mai hannu ,alamar su tsaya,,,

    Koda ya waigo sai yaga aidashi nake magana,,,  sai yadan tsaya yajirani,,, Yana mamakin ganin wanan yarinyar kuma a shagunar shi,,,, 

    Mika mai wallet din nayi kawai na juya batare da na tsaya ko yin wani bayani ba,,,,

   Mamaki yakama shi, yasan dai ko babu kudi acikin akwai kusan riyar dubu dari ga kuma American dollars gefe guda aje ,,,,,,, gashi kuma na kawo mai abinshi babu wata alamar da ta nuna antaba komai acikin wallet din,,,,

   Cikin mamaki yake binta da kallo yana fadin anya kuwa wanan yarinyar ba aljanna bace kowa ,,, 

   Ko ina sai na ganta kuma bidan kudi zanga tana bida yau kuma gashi Allah ya bata kudin amma sai ta dawo min da su,,,,,

 Kuma batare da ta tsaya ko in bata wani abuba daga ciki,,,

    Yakoma don ya ganta ,,, saidai ansamu akasin hakan maimakon takoma cikin shagon ashe bata shiga ciki ba,,

    Wucewa tayi zuwa wani shago dake gefen su sayen kayan sanyi don su sha,,,,,

   Ko ina andiba ba,a,ganta ba babu ko almarta acikin shagon,,,,,

    Azuciyan mutane wurin sai suka kama mamaki anya kuwa mutunce ma yagani kuwa kodai ya dan shiga tunane har yaga kamar hakan,,,

    Kusan zai wuce yaji Rugaiyya na fadin ina fadima ,, ina fadima tazo su tafi gida,,,,

    Ahakan yabar wurin saidai yana kiyastawa azuciyan shi wata,rana zaiganta ai,,,


Yana barin gurin tadawo da kayan sha niki,niki acikin leda,,

   Suka dan samu wuri gefen da babu kowa suka sha

   Dazasu wuce mai kula da shagon yai masu godiya yabasu kudin da oganshi yabayar araba masu,,,,,

    Kudine masu yawan gaske saboda jindadin yadda sukayi decoreting din wajen yayi kyau sosai .

   Shiyasa aka basu kudi masu yawa don yabawa da aikin nasu.

  Cikin murna da farin ciki suka wuce gida,,,,

    A hanyane fadima ke fada masu aita sinci wallet din wani mutum amma dai tayi sa,a taga mai shi har tabashi abinshi.

   Sukaina ta dafe kai don takaici tace fadima ki mayar mai fa?

   Ashe har yanzu baki da wayo ke, kudin da muke bida kamar mutashi sama Allah ya ba ki shine zaki mayar ma mai shi,,,,,

    Rugaiyya dake gefe zaune tace au dake ce ashe bazaki mayar mai da kudin shiba kenan,,,,

    Gaskiya fadima bata,kyauta ba inji mari aida bataso inta da ta kawo muna mu muraba,

   Hmmm inji Yumma aiko an baku baku zaku kashe su ba hajiyace zata kwashe su duk inda kuka aje su,,,,,  shin wai kunsan duk lokacin da muka fita sai hajiya ta caje kayan mu.

    Ni ma,ranan da nabar zabirata agida nakoma indauko shine nasamay ta tana ta cajin kayan mu

   Naikamar bangane,ta,ba nadauko abina nafito,,,  

   Hmmmm ai intasan wata batasan wata ba,,, kawai sai anwayi gari ta bide mu bata gan mu ba,,, don daini nakusa gudu daga wurinta ,,,bintu tace zatai min hanya mutafi kasar yamal mu zauna can,,,,,

"Ke,Mari kada kifara hakan wlh kibari kawai mu koma gida yadda muka zo,,,

  Insha Allahu bamu dawama cikin wanan ukubar dole watarana gida zamu.

     Haka sukai ta shawara a tsakanin su har suka isa gida,,,,,
🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 20:41] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

       👣👣👣👣👣

       👣👣👣👣👣

                2⃣1⃣

                   BY


🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

 

   Yan uwa mu kyautatawa yan uwa musulumi ako yashe ladan ka yana ga Allah


Kainuwa group novel da Baiwa group novel ina kara mika godiya na gare ku tare da masayana kuma yan uwana na huguma group,,,,,,,

  Almost true life story,,,,    

 (   Lokacin   Aikin Hajji  )    Wanan lokacin gaskiya muna jin dadi sosai don lokaci ne na harko ki kala,kala 

   Muna kuma ji tankar agida muke,,, duk lokacin danaga yan Nigeria musaman mata jinakeyi kamar kada na bar su su tafi.

    Zandinga kyautata masu ta hanyoyi daban daban 

   Ko abincine zamu sayar masu shi da araha, ne saboda son su da mukeyi tankar a,gida muke.


     Yau ma kamar kulun muna suyar dankalin turawa da kwai da safe tun karfe biyar muke fara aikin mu saboda yawan masaya da muke da su masu son abasu dankalin da kwai,,,

   Saidai duk da yawan da akaiyi, muna ,,,,munayi muna, kallon hanya kada yan bagaladi su zo su riske mu agurin,,,,

   Don basu da tausayi ko kadan da sunzo kumune kawai bayan sun facalar da kayan suyar tamu sai kuma su yi cikin mu da duka da taki kamar jakkai,,,,,

   Shiyasa da mungansu zamu sheka mushige cikin Alhazai mu boye,,, saidai wani lokaci zamu hadu da wasu marasa imani su nuna mu akwashe mu zuwa kasar mu,,,

 Azubar da mutum wulakance babu ko kudin mota balle sutura ,,, duk abinda kasamu acan zakabar shi,,

  Wasu su wawashe ganimar su.

    

      Rana yai zafi mutane yawanci sun shige cikin masallaci sun labe,  

    Nafito da kayan sayar wan da su hajiyan mu suka sai dila na gumama ,suka raba kayane masu kyau ne sai nadan fito dashi nakai bakin titi indan sayar 

    Gaskiya ba laifi na sayar da kayan duk an rufe ni a,na saye muna da yawa a,gurin masu kaya jama,a sun taru,,,,


   Sai kawai naji ance Lah Fadima da sauri na waiga don inga kowaye kekirana hakanan,,,

    Juyawan da zanyi sai naga malam jibo makwabcin gidan kawu sale, gida biyu ne a tsakanin mu da shi a dogon daji.

 Aiko da murna ta ina dan ihun jin dadin ganin shi danayi abin kamar amafarki,

    Muka dan gaisa dashi natan baye shi lbrn kowa nagida,,,,,  Na, tambaye shi masaukinsu yai min kwatance nace mai zan zo Insha Allah,,,,

  Yau kowa yagan,ni cikin farinciki nake,,, saboda jinakeyi kamar a gida nake,,, 

    Ko antyna Rugaiyya ban fada mawa ba naita boyon maganar azuciyata, 

   Tundaga ranan da na gane masaukin malam jibo nadinga da wainiya da shi so sai,,,, nakawo kaya masu yawa da kudin da muke boyewa nida Rugaiyya na,bashi nace ya kaiwa inna da yan uwana,,,,


    Munyi da malam jibo zaizo yaga gidan mu,,,,,, har na shirya don in,zo in kai,shi sai nayi wani tunane kawai sai nafasa.

  Tundaga ranan na canza wurin zama ban yarda mu hadu dashi kokadan,,,, 

    Saidai ni ina ganin ko,yaushe da alamar ni yake bida da ido.


     Mun samu kudin saida abinci sosai dana gumama 

     Malam jibo ya shiga damuwar rashin gani na don shi yaso gaskiya yaga gidan mu da kuma hajiya don yaji ta bakinta yadda akayi tazo dani nan batare da sanin iyayye na ba

    Saidai kassh hakan bai samu ba dole yasamu wuri ya dunkule sakon dana bashi zuwa gida.


      Har yanzu ina yawan zuwa wurin dawafi in nafito bara sai nagama dawafi sai in samu wuri inda ba hayaniya inyi shirin barana ,,,,, batare da wani yagan ni ba.

  

           Mukan bi har cikin gidajen Alhazai mata da dare koda safiya mukai masu tallan haja masu kyau da amfani 

    Saboda hajiya Laila tasan duk wani abinda mahajjata ke bukata ,,, itace ke taimakon hajiyar mu da shawaran abinda zamu dinga sayar wa

   Saboda samun kasuwa .

   Matsalar mu guda hajiyan mu bata da godiyan Allah duk abinda ka iya samowa bata yabawa saidai ta kushe.

      Yau mana,kamarr, kulun nayi ciniki ga kuma kayan gumama na sayar nakumayi bara ajihuna fam da kudi nakawo mata 

     Gashi kuma ina jin ciwon kai tun daren jiya ,saboda rashin barcin da ban samu nadan yi ba, don, ina tunane gida ,,,,

   Tun da naga malam jibo gida yadawo min sabo azuciyata

    Ina ba hajiya kudi nafada mata kaina yana,min ciwo sai kawai tace min wai ,,,, in koma kafin sallah magriba inyi baran maran ce,,,, 

     Bance mata komai ba nafito inajin , wasu hawaye masu zafi na bin fuska suna sauka kasa.

    Ga kuma ciwon kan nawa kamar ana karamin shine,,,,

   Nazo gefen Haram na samu guri nadan zauna sai  she,shekar kuka nayi ,,,, Don gaskiya ban iya kara yin wani bara yan  ciwon kan yana damuna sosai,,,,,,,,,

   Ina cikin wanan halin kaina a,duke sai kawai naga an miko min handcarchef,,,,,,Fari mai shegen kanshin irin turaren nan ta kasan larabawan tsakiya,,,,,,


  🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 20:45] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARU✈✈✈

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                   2⃣2⃣

                       BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAW🐎

🐎HUGUMA GROUP 🐎


    Rikon Amana wani abu ne mai nauyi a,rayuwa, indan bazaka iya ba kada ka dauka domin saba ma rikon amana yana iya jefa bawa acikin bala,i

   Allah ubangiji yabamu ikon rikon amanan dake kawunan mu👏👏👏👏A kulun ina maku fatan alheri a rayuwa yan Huguma group ,Kainuwa group, Maman  Fati , Baiwa group, Fatima luv group, tare da sauran yan uwa masoya wanan novel din nagode nagode nagode👏👏👏👏Almost true life storyBatare da na,kalli wanda yabani ba sai kawai na rike handcarchef din na goge fuskata da ke hawaye,,, amma hannu na guda yana rike da kaina da ke min wani irin ciwo,,,,,,,

      Na share dan gutun majinan da yaleko min ta hanci mai, kama da ruwa,,,, sai na mayar ma mai shi da abinshi,,,

    Cikin larabci yake tamabayata mai yasamay ni ,sai na nuna mai kaina 

     Baikara yimin magana sai kawai naga ya mike yace min intaso muje, yaimin alama da hannu in,biyo shi, 

Sai na tashi nabi bishi,, batare da nayi wani tunane ba,,,

    Wayan shi yaciro naga yana magana ,,,,, kafin mintina kadan saiga wata mota mai kama da kifi a  tsaya,agaban mu, tana tsayawa, aka bude bayanta yai min alamar inshiga na fada ciki.

    Ina shiga wani irin sanyin A, C da kamshi yadake ni sai kawai naji yanayin yai min dadi na fara lunshe idanu na a, hankali, 

   Wai, ashe daga haka na suma ban sani ba,,,,

     Hankalin wanan mutum yatashi kware da yaga na rankwafo mai da zamana acikin mota ba,a,fi ko minti biyu da fara tafiya ba,,,, 

      Cikin daka tsawa yake ma driver magana yayi sauri su, isa, asibiti dani,,,,

    Cikin yan mintina suka iso asibinti 

    Yakira wani abonkishi likita yai mai bayanin gashi damara lfy bakin asibi aka turo wasu masu daukan mutum suka daukeni sai ciki.

  Nadauki dan lokaci ban farfado ba ,,,, da taimakon Allah nadanyi atishawa mai karfi kowa yayo kaina,,,,

   Bayan "yan aune ,aune da akaimin sai aka gane cewa ina fama steeretret

ne ban da hutu ko kadan aiki yaimin yawa ina bukatar hutawa kadan

     Aluran barci akai min daga nan bansan inda nake ba kuma,,, saida komai ya kam,mala likitan yaja hannu shi suka fito waje,, 

     Ahamed ina kasamo wanan yariyan ,,,, likitan ya kashe shi da ido,,,,

    Shiru yai mai ya busar da iska ,,, kawai ta baki sai hannu da ya dunkule ,kamar mai shirin nashin wani

     Dr Umar banda lokacin baka ansa yanzu kaiwai dai served her life pls.

    Ido yabi Ahamed din dashi yana ta tunane azuciyar shi ,,,,,,

    Don dai a iya sanin da yai mai baida kowa anan shikadai ke zaune wanan kasar, kuma ba wai wani mai shiga harkan jama,a bane balle ace, 

      Dokan mu bamu wuce karfe goma na dare a waje yau gashi har kusan sha biyu babu alamar fadima ,,,,,

     Tun abin baidamu hjy ba har ta tashi , tana fada ta tada sauran tace masu ,,, su tashi gaskiya yau ba lafiya ,,, fadima tabace don ,sometimes nakan riga kowa dawowa gida kuma ina fin su samun kudi don zafin namana, 

    Rugaiyya dama idon ta biyu ne batayi barci ba tana ta tunanen ida natafi,,,,

Tuncikin dare ake bidana ba,aganin niba har gari yawaye babu lbr na .

    Hakalin hajiya ya kara tashi sosai ,,,, 

   Duk inda akasan muna zuwa anje babu fadima

    Kuma ba wanda yace ai yagan,ni

    Hajiya tana kuka tace aiko tashiga uku in wani abu yasamu diyar mutane,,,, may zatace a,gida .

  Ko banza bada sanin kowa nawa ta zo dani saudiya ba, gashi kuma laifin nata ya karu na bace.

    

     Tunda nafara barci wanan mutumin bai tafi ba yana gurina yaje yadawo hankali tashe,,,,

     Azuciyan shi yana fadin ai dole hakan ya samay ta ,,,, don wanan yariyan batada hutu son kudinta yai mata yawa.

    Shin wai ma ita wacece ma dai da take wanan irin bat da kama kala,kala gani yar karama dani ,,,,,,

    Washe gari musalin shadayan rana likita yace asamo min abinci in,ci

     Mutum yafita sai gashi da abin lafiyaye cikin take away da abinsha yakawo min.

    Baifi rabin a,wa ba da shigowa na farka zubur dani.

    Yunkurin mikewa nayi sai naji nurse na fadin kin tashi na kada mata kai alamar "eh .

    Natambayi nurse din ko a ina nake sai,tace min asibiti, zubur nayi na mike zaune, 

     Waya kawo ni saita nuna min wanda ke tsaye bakin kofa hannu acikin aljihu, gudan hannu shi waya yakeyi, baka ma sanin akwai mutum yana waya a dakin.

     Nai kokarin dagowa zaune sai naji na kasa nakara yun kurawa intashi ,,, ya nufo gadon danake yana fadin ina zaki haka,,,.

    Nikuma inace ma nurse karfe nawa tace min shabiyu saura na rana 

   Subahanallah nace na, mike da karfi zaune ,,, duk sukayo kaina har shi mutumin da ke tsayen suna kokarin kamani 

    Ina zaki yace min ina fadi da karfi banyi sallah ba , har rana tayi hakan 

    Nurse din tace ai inbari tukun indaji karfin jikina sai intashi inyi saboda nakai a,wa bakwai ina barcin hutu ko fiye,,,,

    Ko saurarenta banyi ba na sauka saman gadon zata tare ni sai mutumin ya daga mata hannu alamar ta rabu dani kawai,, intashi da taimakon nurse din nasamu natashi ta kai makewayi ,,, takunna min ruwa masu dumi nayi wanka nayi alwala na nafito,,,,,,

    Yana tsaye gefe yana kallon yadda nake sallah atsanake kamar ba yar karamar yarinya ba,,,, cikin fidda ka,idodin sallah nakeyi har nasamu na gama.

     Azuciyan shi sai mamaki yakeyi wai ita wace wanan yariyan haka ,,, wani fuska gani saliha wani fuska kuma macuciya,,,,,,,yana cikin tunanen yaji motsin Nurse tadawo,,,,  

   Nadan jima ina addu,a wurin ina idar wa yajawo ledan abincin ya aje min gabana yace min inci in nagama zai zo in mai kwatancen gidan mu sai ya je yafadi ina nan asibiti.

   Saida naci abincina nakoshi sosai nai kat,,,,,Nurse tabani magani na da likita yarubuta akasawo nasha  natashi a hankali nakoma bisa gado na kwanta nai kamar ina barci sai nurse din tadan fita.

     Inajin tafita na bude ido na namike zubur a hankali na leka naga babu kowa sai na gyara rolling din gyalena da kyau nakama hanya,,, har nadanyi nisa sai nadawo nadauki ledar magani na da sauran abincina nafita cikin sanda 

          Allah yataimakeni nasamu nabar asibitin batare da kowa yaga fitana ba. 

   Duk da ina jin dan jiki cikin sauri nasamu har nakai bakin titi natare taxi na shiga saida mukadan yi nisa na tuna aibanda ko sisi a hannu na ce ma mai taxi yadakata nai matuwa zan sauka yanata fada nasauka nasan dai ko banza nayi nisa da asibitin 

    🐎 ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/3, 20:46] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈ TAKARI✈✈✈

          👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                 2⃣3⃣

                    BY 

🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


  Yan uwa musulumai muyi hattara da zamani komai na iya faru daga wayewar zamani musan,man (Zina) mu, nisan ci zina akwai ta zuciya ,akwai ta ido akwai ta tafiya, da sauran su ,,,,,,

     Allah kaba ikon nisantar ta Ameeen 👏👏👏👏👏👏👏👏


 Group din kainuwa da group din maman fati ina muku fatan alheri ko yaushe,,,,,, Huguma group Allah yasa,alheriAlmost true life storyIna zuwa layin mu na ga yan uguwar mu na ta kallo na .

     Wasu kuma mamaki ne karara a, fuskan su , 

   Nai sallama na shiga cikin gidan mu.

    Hajiya ta mike ta rungumay ni tana hawaye ,,,, tana, fadin ina kika shiga fadima,,, tun jiya ake bidan ki.

    Ban bata ansa nasamu wuri na zauna gefe, saboda rashin karfin  jikin da ban banji  sosai ajikina.


    Ledan magani na natura mata agabanta don ta gani,,,, ta,kara zaro ido waje tana tambayana mai yasamay ni.

    Nakwashe lbrn abinda nasani nafada mata,,,dakuma gudun danayi daga asibitin .       Saida nayi kwana biyu banjin karfin jikina sosai ,Ita,ko hajiya sai korafi take min wai naki murmurewa in koma wurin bara.


    Yanzu kan nadan ji sauki nida kaina na shirya fita yau,

    A,hankali nake tafiya har na iso kofar masallaci dai dai kofar shiga Bin dawood nasamu gefe na zauna na hada kaina da gwaiwa na .

     Yakamata ace nasaba da wanan kamshin turaren Al, madinal nuriya, .

       Cikin sauri nadago kaina ,saboda nasan kamshin turaren wanan mutumin da ya taimakeni ne har kusan sau biyu.

     Mukayi ido biyu dashi  abinki da mara gaskiya, saina dukar da kaina kasa, Nadan gyara zama na kadan gefe na ya shimfida salayar shi,

    Batare da ya fuskance ni ba yace min ya jikin na ansa da 

Alhamdullah baikara ce min komai ba sai yaci gaba da lazimin shi baiko kara kallon inda nake ba,,,

    An idar da sallah azahar ina son in je gurin barana .

  Kamar yasan abinda nake sakawa a,zuciyata sai naga,ya mike tsaye ,, ya,miko min kudi masu yawa yace inkai gida basai nayi bara ba yau .

     Hawaye kawai ke zuba min a idona ko godiya na kasa yi mai ,,,

    Hakana na dan lalaba nakai ma hajiya kudin tana ta washe baki tana fadin koke fa, da kina nan kwance da wazai bamu wanan kudin masu yawa haka,

     Nidai bansan komai gamay da wanan mutumin ba amma haka yadinga taimaka min da kudin bara har naji saukin jikina.

    Itako hajiya bata taba tambayana ina nake samo eanan kudin sabbi fil dasu ba ka kamshin turaren shi dake man,ne makudin

  Rugaiyya ce ta lura da hakan saboda idan na raba biyu zan bata wanda muke boyewa kulun ranan ina bata sai tace min Fadima ,,,, 

  Nace na, am wake baki wanan kudin masu yawa haka kulun,,,

     Shiru nayi nadan wani lokaci,,,,ina wasa da yan yatsun hannu na,

    Takara maimaita tambayar ta 

    Cikin tsanaki na warware mata tun lokacin da na fara ganin shi amasallaci har zuwa yau,,,,

    Tanisa a, hankali tace kuma bai fada maki koshi waye ba, nace mata a,a 

    Shiru takarayi tana nazarin maganata,,,,,

    Kidai bi a hankali kiji don mutum abin tsoro ,,,

    Inda nadanji sanyin maganar taki dakikace yakaiki , asibiti kuma ya ce ki gwada mai gidan ku

    Kada kiyarda wani yasan gidan ku fadima, saboda hajiya kin ji.


   Tunda naga naji sauki sai ban kara barin mun hadu da wanan bawan Allah ba,,, 

   Na canza gurin yin harkokina,

    Sai inje in saro kaya irin su jakkuna takalma da dai sauran kayan da nasan mata na bukata indinga bi masaukin Alhazai ina sayar wa ina samun riba masu yawa.

    Hajiyan mu sai tana rena kudin da nake kawo mata wai sunyi kadan ita tafi gane ma indinga fita bara,,,

   Yafi kawo mata kudi da yawa,

   Da,taga naki zuwa baran ranan da nakawo mata kudin cikina sai ta watsa min su afuska ta dinga surfa min zagi wai ina mata bakin ciki yanzu,

    Don karta sa,mu karuwa dani tun tana zagi har ta hau,fada da duka na 

   Saida na,jibgu sosai wurin hajiya san nan nasamu maceta aka, kwace,ni kacal a, hannuta.

   Duk wanan dukan baisa na koma wurin da zanga bawan Allah nan mai taimako na ba.

    

      Sannu sannu mahajjata suka watse kowa ya koma kasar shi akabar mu mu yan labe muna ta labe laben mu don kada akama mu.

    Don da ankama kasai yadda hali tayi da mutum

     Irin wanan lokacin ba komai muke samu ba so sai 

     Don haka mazan mu da matan mu yan takaru, sai mu dinga bin gidaje mu aikin , ana biyan mu kudi,

   

   Muma dai irin hakan ne ta kasan ce damu,,,

    Wani Alhaji aminin hajiyan mu ne ,ina, ganin,shi,yana yawan zuwa wurinta anytime,,,

     Shi yataimaka mata yasamo muna guraren da zamu dan dinga neman kudi don kada a zauna hakana.

   Duk da aikin da muke dan yi muna zuwa bara dan lokaci lokaci, saboda kasan cewar kasar makka kullun cikin yawan baki take baka gane dare da rana anytime akwai jama,a agarin.


     Abinda bamu sani ba nid antyna Rugaiyya shine Sukaina ta gane inda muke boye kudin mu ,,,,, sai kawai muga kudi yana rage yawa .

    Nidai tunda naga kudi na rage yawa nadauka antyna ce ke dauka tana wanu lalurar ta da shi 

     Ita kuma da taga haka sai ta dauka ai nice ke dibar kudin, saidai, da ta,ga da gaske ana zarar kudin so sai ,,,,,,

    Tace min Fadima may kike saye da kudaine haka, 

   Cikin mamaki nace kudi wasu kudi kuma tace wanda muke tarawa mana,,

    Ni tunda nake ban taba daukar ko kwandala ba acikin su,,,,   

 Yo nima may zan saye da kudi ,,,,, kaya dai tun wanda baban Nailabin sukayi min sunake ta sawa ajiki na har yanzu.

   

   Nanda nan naga ta shiga cikin wani hali takai zaune tana fadin mun shiga uku ,,,,,,,,,

     Akwai wace ce tagane inda muke aje kudin mu har take diba.

   Nadauka ko kece ai saida naga abin yai yawa shiyasa natanbaye ki yau.

    Nima nadauka kece ke anfani dasu ai,,,, yo wani amfani kudin da saura kadan mu hada kudin komawa gida mu huta da wanan bakar wahalan,,,,,

  

Cikin bacin rai tace aikuwa zangane ko wace take muna wanan sherin.

    Tundaga ranan muka canza gurin boye kudin mu,,, amma muna dan aje saura a,gurin.

   Antyna ta kula kulun zamu fita Sukaina ce ke zama ta bayan fitar mu,

       Yau bayan duk mun fita sai akabarta abaya tana fadin wai sai ta dan gama abinda zatayi zata fito,

    Har Yumma da mari suna mata ba,an wai tadai saba da zaman na baya yanzu,,,

   Bayan fitar mu da yan mintoci sai kawai tanufi wurin da antyna take boye kudin can bayan fridge din mu kasan wani tsohon basket da muke tara tsofafin kayan mu ciki,,,,

   Ta bude raggan da muke kule kudin ke nan Rugaiyya tashigo dakin sukayi arba da juna,,,

   Ragan da sauran dan kunshin kudin ta karba a hannu ta ta juya tana fadin mun barki da Allah muguwa,,,,,,

   Cikin daga murya tana borin kunya take fadin ,,, eh andauka din aike ma sata kike wa hajiya shiyasa nima nake dauka,,,,,

    Ashe wai saurayi tayi dan bagaladi shi take bawa kudin so sai,,,,

  Shikuma sai yaudar ta yake yi yana karban mata kudi yana lalata da ita,,,,,

   Wai ba zai bari akamata ba,,,,,🐎 ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP 🐎

[10/3, 20:51] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                   2⃣4⃣

                     BY

 🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎 Allah ubangiji bai yo mu daidai ba, indan harka ga wanda yafika to kaima kafi wani, 

 Don  haka yan, uwa, kai ma wanda yafika fatan alheri , karkayi masa hassada, kai kuma Allah zai maka sakaiyan na Alheri,,,,,,,


HUGUMA GROUP ina jin, jina maku tare da KAINUWA GROUP,,,, MAMAN FATI GROUP Allah yakara dauka nagode nagode,,,,,,,


 Almost true life story,,,,           (NIGERIA)

         DOGON DAJI


  Ranan da malam jibo yadawo ranan ya kai sakona gidan mu da

 kanshi,,,,,,,,,


     Inna tana zaune bakin murhu tana hada miyar marance sai taji a,na kwada sallama kofar gida,,,,,, 

   Yaranta duk suntafi makarantan islamiya ,.

    Takoma daki tajawo hijab din ta tayafa,,, zuwa ganin wanda ke mata sallama kofar gida,,,

   Takusa kawai kofar yai daidai da yaran sun dawo daga makaranta,,,, 

    Su sukafara gaisawa da shi, suna fadin Alhaji ho Alhaji ho ,Yaushe ankadawo yace yau munka sauka,,,,

   Sai ga inna ,,,,,, Alhaji jibo kaina tafe lalai da dawon ku,,,,

  Banyan sundan gaisa inna tana gefe guda,tsugune tana sauraren abinda yakawo shi gidan ta ya,u,,,,  

   Ya tura mata sakon gabanta yace yar kulu tace na,am, Ya,sake cewa, Fadima ta tacce inkawo maki wanga sako ,,,,,,,,

    Zubur inna ta mike don kaduwa jin sunan fadima da taji anyi,,,, yaciga ba da fadin awo, ita,taban wanan sakon tacce inkawo maki inda kike

   Kuma tana gaishe ku,,,,

Aiko  motsi bata iya yiba daga inda take,,,, 

   Hasfsat ta tace kaga fadima shin kaka,fadi ,,, yaca, A,woo  da ijjiyan ga na,u, naganeta,

  Aiko inna,sai kuka ita dayara tana fadin wayyo ita Allah fadimarta wayyo fadimata,,,, 


    Fadima don Allah kiyafan ni nakai ga haka,,,, malam jibo dake gefe rakube shima hawayen yake gogewa,,,,

    Yai gyaran murya tun jama,a basu taru yace ke hafsi shiga da kayanga ciki tukub na,,,,

  Shiganta keda wuya sai ga jama,a sun fara taru gidan jin kukan yar kulu da yaranta

   Shin wai mi ka faruwa, na, nanga? 

   Fadimata yaggani makka ,, makkafa ? A,woo ita,ta kuwa naggani da ijjiyaga nau,

   Nan yashiga basu lbr yadda suka hadu da fadima dakuma irin tai makon da tayi mai har da sayayan tsaraban da ta tayashi yasaye.

   Abuguda ya boye bai fadi ba gudun datayi na kaishi masauki, ta,,,

  Kowa yana ta al ajabin wanan maganar ta malam jibo watau fadima na nan da ranta a,makka zaune daram,,,

    Kuma hannu mutanen kirki masu mutunci,,,

    Yayi hakan ne don cire zargin yarinya kamila mai kirki fadima a,zukatan mutane ,,,

   Saida komai ya lafa an watse kowa ya koma gidan shi yana fadin albarkacin bakin,shi 

   

    Cikin dare inna ta tada hafsat ta bude masu sakon da fadima ta aiko dashi,,, sugani.

   Dogayen riguna ne da zanin gado cottoning masu kyau kala biyu sai kudi wanda ya kai kimani kudin Nigeria dubu dari,,,,

     Aiko hankali inna yakara tsshi sam bata yarda da maganar malam jibo ba.

    Tunda safe tadauki kayan taje gidan yayanta malam sale ta kai mai ,,  shima yana gani yaji tsoro ,,,, Anya kuwa yarinya karama kamar fadima zata bada wanan sakon akawo mata gida,,,

    Sana,ar may takeyi can da har ta samun wanan kaya haka masu kyau da tsada,,

  Ya tashi yaje gurin 

 malam jibo dakan, shi ,nan malam jibo yakara yi mai bayani daladala har ya fahinta,,

  Malam jibo yakara yiwa kawu godiyan irin dawainiyar da nayi masa acan,,, 


    Duk da malam sale yakwantar wa inna da hankali yaba kowa sakon shi,yan uwana sunata murna da sakon da na aiko masu dashi,,,, 

    Amma ita inna ji takeyi kamar tayi ihu taganta makka,,,,

 Magana ya kama yawo agari malam jibo yaga Fadima a,makka tare da matar da Gajiye ta sayar mawa ita,,,

   Har zuwa akeyi ganin sakon da fadima ta aiko da shi anata mamaki,,,,

   Bayan kwana biyu inna tadauki kudin takai wa malam sale tace yayi abinda yadace da kudin

     Shiko, sai yace tacire masu yawa asai kiwo da su saura ta sai abinci suci ita da yarant,,,

   Har inna taso taki wanan shawaran malam ya dan lalabata ,har yashawo kanta tayarda ,,, yace kowa da hanyar da Allah yai mai na arzikin shi killa arzikn fadima da, su yana can ne shiyasa yakai fadima har can inda kowa nata bai taba zuwa ba gashi kuma malam jibo yace tana zaune da mutanen kirki.

   

   Da haka inna tadan sake jikinta taba kowani yaro kayanshi tace yasa

    Zanin gado kuma za,a ,aje ma Hafsat na aure ,,dama aurenta ya kusa,


   Tun lokacin inna yar kulu ta kara maida hankali ga addu,a tana neman Allah yakara kare mata tar diyar ta Fadima,,,,,,,,,,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎

 🐎HUGUMA NOVEL🐎

[10/3, 21:02] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                 2⃣5⃣

                    B Y

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎Daure ka/ki biyayya ga iyayenka domin watarana ,kaima mahaifine/mahaifiya Godiya nake,wa,antyna Hafsata yusuf da anty mariya sb, Anty safiya mai huguma,  da babban marubuciyar littafin Dan maliki ,,,,,,,,


   Almost true life story,,,,,


               AHAMED


Wanene Ahamed wai,,,,,


            "hmmm ,,,,,,

 

Ahamed wani bawan Allah ne dan shekara talatin da haihuwu, fari ne irin farin da bazaka iya gane cewa ba,aciki , jinsin larabawa bakake yake ba, Saboda sajewan da jikin shi yayi danasu.

    Dan Nigeria ne,da ke zaune a babban birnin Riyadh ta kasar makka,,,

   

      Karatu mahaifin shi yakaishi yi can ,,Daga nan wani kamfani tatar mai ta kasar saudiya ta dauke shi aki saboda kwazon shi da zama gwani, afanin, gyara gyaran. Kayan nauran mai wanan fannin. 

  Engineering ne a maikatar  da yake aiki,kwanzon ,shi, da zama gwani, yasa suka ki barin ya bar kasan,,, anturashi sauran kasashen duniya, yaje yakaro ilimi sosai,,,,,

   Sauran referners na kasan saudiya masu zaman kansu suna hayanyan shi ,,  Don gyara masu na,urar su, idan sun samu matsala aiki,,,

   Don ,haka kudi,na shigo mai ta kowace hanya time to time, kamar ruwa,

    Ahamad mutum ne shiru ,shiru wanda bai son magana kuma shi baison hayaniy akusa dashi 

Mutum ne,wanda bai wasa da ibadan shi ko kadan, duk abinda yakeyi lokacin sallah bai wuce shi,,, ,,,  hakan yasa ko da yaushe zaka samay shi a masallaci yana ibada,,,,,

   Saikuma, ranakun aiki ba kullun ne zaka ganshi ba . 

      Yanada sha,awan business sosai don hakane ma yabude wasu sha guna masu kyau da kaya masu ma,ana acikin garin Riyadh da kuma garin makka,,, shagunonin suna tashe sosai saboda kayane irin nazamani zaka gani acikin su,,,,,,,

       Idan lokacin aikin hajji yayi hutu yake dauka ta musam man danyin ibada .

   Baya kaunar irin da bi,ar da yaga matan Nigeria suna yi acan don haka shi ko sadaka baya ba irin su,,, don yasan kwadai ne kawai yakaisu bawai rashi ba.

  

    Ahamed haifafen garin maduguri ne,,,, mahaifi sh,i shine, Zannah garin maduguri,,,

     

     Tun yana jariri maihafan shi suka rabu,,,  hakan yasamo, a,saline, tunda daga komawa gida shan ruwan zafi da mahafiyar shi tayi,,

      Yan uwanta suka rike ta, a gida suka ce bazata dawo ba ,

     Dama ba wani dadi auren yayi,ba,  aure ne,na,gidan ,aure na danki yan uwa suka hada ,, tare da sa hannu mahafiyar mahafin shi watau Zannah lawal,,,,,,,,, 

   Mahaifin shi a Landon yazauna inda ya auro hajiya mama, a,can suka hadu da ita kaunar wani abokin shine da sukai karatu Can, 

Ganin kirkin dakega zannah lawal yasa yasa yayan Amina ya hadusu aure dayake shi mutum ne mai hakuri saiko ya amince da tayin abokin nashi,, 

      A,kano aka daura aure aka kai mashi ita can inda yake aiki london,,,

    Saida hjy mama ta haifi diya uku duk maza sanan ,,,,   suka dawo Nigeria da zama,,,,,, irin dabi,un ta yasa mahafiyar ,Alhaji lawal Zannah tace dole ne ya bidi yar gida ya aura.

    Saboda gashi da abin hannushi amma badama yan uwan shi suzo gidan shi,,, sai ace aibasu fadi cewa zasu zo aranan  ba, 

   Dole mutum ya hakkura ya koma inda yafito, ko kuma yuwa takar mutum.

   Ire iren wanan halin yasa maifiyar shi ta je can kauye cikin dangi tasamo mai mata yar asali da mutunci.

    Tunda aka kawo,ya ghana gidan zanna ta koma kamar boyi boyinsu  itace mai masu aikin komai agidan.

  Wani fitina ma wai,sai dare yayi karfe tara zatayi masu pepper soup na kifi, ko kaji ,ko kayan ciki,,,

   Ahaka ,yaghana tai ta bauta agidan bawani jindadin aure da tasani.

  


   Da rabon cikin Ahamed yazo, lokacin hjy mama ta tafi garin kano ganin gida ,shi ne, rabon Ahamed,, yaratsa tsakanin su,,,


 Aiko tunda mama tadawo taga alamar ciki ga yaghana ,,,,,,, aiko ina wuta tasakata,,, 

    Fitinar ma sai ya,kara karuwa fiyeda na da,,, ga lalurar ciki ga wahalar aikin gida

    Taramay taiwani fayau, da ita, 

    Da haihuwar yazo mata tsohuwar dakemasu aike da,sharar gida itace ta kama mata ta haihu ta haifi danta mai kama da uban shi sak,,,

     Saidai shi yaron yafi uban haske da kuma hanci,,, na uwar yadebo,,,

   Har kwana biyu ba,a fada ma  maigidan,Yaghana ta haifu ba , bakula kuma ba abinci mai dadi irin da yakamata aba mai haihuwa, da ita da dan jaririn ta duk suna cikin wahala,,,,, 

    Saida tsohuwar nan mai shara, taga diyar mutane na shirin mutuwa , sai ta saci jiki tafita taje tafada ma wasu dangin su, a,cikin gari,,,,,,

    Sukuma suka aika ma mahafiyar zannah lawal dontazo ta ceci diyar mutane 

Tsohuwar batayi sanyi da gwaiba ba,,, tai masu dirar safiya agidan,,,,,

  Yayi mamakin ganin su da safe haka,, har mama ta fara fadin,,,

   Tau mu bamu san zaku zo ba gashi bamuyi abinci karin kumalo da kuba, 

   Tsohuwar tadaga mata hannu tace aje abincin ki ,, ina yariyar mu,da ta haihu,

 A,lokacin zannah yafito da ido waje yace yaghana ta haihu ne ,,, takama wani inda inda tana cewa dama naso in surprise dinkane ,,,, 

    Ranan yadan yi ta maza yadaka mata tsawa yace Amina ashe baki da imani ne haka ban sani ba

    Yi min shiru inji mahaifiyar shi ai,duk abinda takeyi da saninka don kai ka daure mata ,,,

    Fito min da yarinya na gida ne gashinan mubar maki ki jika kisha babu dan uwan lawal da zai kara zuwa nan muddin ina raye,,,,

    Wani daki da akayi acan bayan dakunan ,su aciki yaghana ke jego, acewar mama wai kada tabata cikin gida da karni.

     


    Tunda tsohuwa tazo ta,tafi da yaghana garin su bai samu zuwa gida diban su ba,,,, da ranan suna ya zagayo yan uwan lawal,su,kasa ma yaron sunan mahafin lawal,,,,, watau Ahamad


     Saida suka kai kusan sati uku agida, lawal mahaifin Ahamad,yazo masu da kaya niki niki dana uwa dana yaro,,,

    Tsohuwa taita masifa tace yatafi da kayan shi ita kudin shi baida may su ba ,,,,  

    Dama ta yi wanan hadin ne don kada zumuncin shi dana,"yan,uwan shi ya lalace,, nan gaba yasa ta aura mai diyar kaunar ta,,,,

    Saboda idan akawai yar uwanshi agidan, aidole dangi suzo gidan ganin ta koda mama bata so,,,,,,

      Sai gashi ashe shi mijin hajiyace sosai bata sani ba,

  Sani Allah sani Annabi ya tara ma tsohuwa jama,a aka bata hakkuri tayarda zata karbi kayan da yazo masu dashi,,,, amma batun komawa sai  yaghana ta huta tukun ita da yaronta,,,,


    Yau zaizo gobe zai zo shiru, kake ji,,  koda yazo kuma har ya koma baiyi maganar komawan su ba,,,, ganin haka wani yayan yaghana yabishi har can birni yakarbo mata takardan saki

    Ya fada mai cewa da ma don zumunci su da tsohuwa suka bashi yagana don tsohuwa da uwar su aba,guda suke,,, 

  Kuma koda uwar su tarasu tsohuwa ce ta koma tankar uwar su itace ke masu komai da yakamata uwa tayi wadanta

    Yace to kagani babu yadda za ayi taso abu wurin mu mu hana mata .

   Mungode ma Allah tunda munyi mata biyyaya munbaka kaunar mu ,

Amma kai, ka kasa mata biyayya ka rike muna kauna amana,,,,,,,, 

   Tunda dan uwanshi ke magana yasada kan,shi akasa baidago ba har yakai karshen maganan shi.Tabbas yasan gaskiya ne yakasa yi ma mahafiyar shi biyayya akan wanan auren ,, wai kuma badon baison yaghana bane ,aa yana son ta amma yarasa dalilin rashin kulatan da baiyi.


🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎[10/4, 07:53] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                   2⃣6⃣

                       BY


🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎 Dan uw/ "Yar uwa , Daure ka/ki rike sallah akan lokaci domin zata sama, hasken a,fuska sanan , Watara zata taya ka kwanciyar kabari ,,,,,,,,,,,,,


 Anty safiya mai huguma Anty hafsat yusuf da anty mariya sb kulun fatan alheri na gare ku bai karewa , Allah yasa mu dace da rahamar sa,,,,,,,👏👏👏👏👏👏Almost true life story,,,,,,.
  Tun lokacin da aka yaye Ahamed sai rikon shi ya koma hannu tsohuwa watau kakan shi,,, 

    Ita kuma mahaifiyar shi yaghana tai wani aure nan kauyen su ta auri wani malamin arabiya mai karantar da yaran garin,,, hankalinta kwance,,,

    Tunda hajiya mama ta lura da cewa Alhaji lawal yana yawan zuwa kauye kai ziyara,wurin " yan uwan shi,,,,, hakan yasa,ta  yin tunane,yan zu saboda Dan shi, yake yawan zuwa kauyen,,,, kuma yana kai mai abin arziki har yan uwa suna samu suna  amfana da Alhaji lawal din,,  jifa,,,,,, Ta mance cewa uwar shi ma tana kauyen zaune

        Aiko sai ta tadda fitina wai ai ita,ce ya,dace, tarike Ahamed a hannunta ba wai akashi kauye ba,,,, kulun cikin cewa takeyi yanzu , shi wanan yaron a kauye zai tashi ga yan uwan,shi a birni  kada yazo sufishi wayewa,,, tana wani tausa murya,,,,,,

   Da, irin wanan dadin bakin har taciyo kan Alhaji lawal,,,

    Watarana bayan yaje kauyen sai ya fito da zancen tafiya da Ahamad birni,,,,

    Nanda nan tsohuwa ta haushi da fada tace babu mairabata da Ahamad ,,,tunda gurin  macuciyar matar sa,ce zai kai shi,

    Ko uwar yaron yaya takare balle dan karamin yaro irin haka,,,

    Hakana yakoma batare da yadauko shi ba,,,,

    Ta naganin ya, dawo batare da yaron ba ai,sai takara haukacewa, 

   Dataga dagaske baza taci nasarar dauko yaron wurin tsohuwa ba sai ta caza sallon takon ta,,,,

   Tafara aika masu da abin arziki akai ma yaron,

    kusan anshi baibar kowa ba , sai mutane suka dauka aita canza halinta ne,,,

    Bayan kwana biyu sai tadauki yaran ta, taturasu hutu kauye ,,,  aiko abinka da yaro nan da nan suka saba da yan uwan,shi, sabo sosai sukayi

    Da za su dawo hutu mahaifin su Alhaji lawal yazo daukan su ,.

   Sai Ahamad yasa kukan cewa zai bisu birni,,, tsohuwa ta hana ,,,,,

    Saida yan uwan lawal suka sa masu baki akan cewa zai je yasa shi makarantar boko ce irin na yan birni don kada yan uwa suzo su fi shi nan gaba.

    Da wanan dabaran Ahamad ya dawo birni da zama amma da sharadin cewa zai dinga zuwa hutu kauye.

    


   Tun da suka iso mama taga da Ahamed ne sai taji kamar ancire mata kaya,,,,

     Da daki guda ta ajeshi da yaranta ,karamin dan ta Suraj yana fitsarin kwance sai tace ai ,Ahamad ne yayi shi ,,, sai taita dukan shi,,, 

     Karshe ma dakin uwar shi inda suke aje shirgin kayan su can tasa aka maida yaron shi daya yake kwana,,,,

    Duk wanan abin Alhaji lawal bai sani ba,,, 

    Saidai yakan lura dacewar yaron baya walwala sosai cikin yan uwa,

    Sai yadauka ai rashin sabone,


    Makarantar da su salis da suraj suke zuwa ta diyan masu hannu da shunine na garin ,,,, can aka fara sa Ahamad .

   Amma da ga karshe saida mama tayi makar kashiyan da aka maida Ahamad wani dan karamin makaranta na kudi nan kusa dasu,,,,

   

      Inda yan uwanshi sukaje karatu shima can yaje karatun shi na secondary FGC minna anan sukayi karatun su har suka kare, 

    Yaran mama suna gaba da Ahamad su tasa Alhaji lawal yakaisu karatu kasar turawa , A,cewan mama can anfi karatu da sanin aiki,,,

    Batasan ta bata tarbiyan yaranta bane ,,, don tunda sukaje sai babban yafara bin kungiyar mawaka suna waka da rawa a clubs  maidan dama daman shine umar nabiyun dan mama shi yana karatu amma yana da shan giya sosai, Suraj kuma wasan kwallon dawaki yakeyi can babu zancen karatu

    Lokacin da Ahamad yagama karatu za,a turashi waje sai mama tai,ta shige da fice wai sai abarshi nan gida don kada su watse babu kowa agida,

   Da har  Alhajin,ya yarda da hakan sai kuma abokin shi kuma aminin shi yayan mama yabashi shawar yaturashi saudiya ya yi karatu can

   Ai ko mama ina wuta tasaka wanta aciki tana fadin da ma bai son ta shiyasa zaice afita da Ahamad waje,,,

    Tun lokacin suka fara samun matsala da yayan nata ,,,,  

    Saboda matar yayan nata tafada mai yadda Amina tamaida Alhaji lawal da yan uwanshi,,,, yai mata nasiha taki bari 

  

Kafin Ahamad yawuce saida yazo,Auno kauyen mahaifinshi don ya sallami tsohuwa da mahaifiyar shi,

     Babu wani sabo tsakanin Ahamad da mahaifiyar shi ,,, ko yaje garin Auno baya yawan zuwa gurinta ,

   Saboda saidai suyi ta zama a daki ba mai madan uwa magana sai yagaji yayi mata sallama ya wuce.

    Dama yanzu da ta haifi yara mata uku bayan shi agidan malam ,,, dasu yake dan hira har yagane halin da suke ciki

     Da zai wuce abin da da mahaifi sai yaghana taji ba dadi aranta

   Dole tafidda kunya taima mijin ta malam magana akan atai maka wa Ahamad da addu,a,,,,,

   Wani ruwan rubutu yabashi sai kuma nafil filin da ya rubuta mai yace ya fakeyin su koyaushe,,,,,


 

   Ahamad na,a shekara farko ,a karatun shi,akaba Alhaji lawal Zannah borno 

   Lokacin kuma ya aje aikin gwaunati yakama harka sana,oi,,,,,,🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 08:00] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

          👣👣👣👣👣  

            👣👣👣👣👣    

                      2⃣7⃣   

                       BY 

  🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA

🐎HUGUMA GROUP🐎   Nasan cewa mutuwa na jirana, kowani lokaci,,,, Don haka sainake ta tanadin guzuri,,,,, Na,kware don shirin gamuwa da Ubangijina Allah subbahanahu, wata,ala,,,,,

    Ya Allah kasa muyi kyakyawan karshe,,,,,, Gaisuwa da jinjina ga masoyan TAKARI nagode da nuna min kulawan ku ,,, ina kara gode ma yan huguma group novel and conversation da suka kara min kwari gwiwa inci gaba da rubutuna nagode nagode

   


Almost true life story,,,,,,Ina zaune bakin masaukin mu saiga hjy Laila tazo da murna na ,natashi natare ta,, saboda takoma muna kamar yar uwan uwa,,,

    Muna ganinsu kamar sune yan uwan da muke dasu acan,,,,

   Cikin harshen larabci take min magana tana tambaya na ina hjy take ,,,,

    Cikin rashin damur ansan da zan bata nace ai sun fita da Alhaji Ali dan takari,,,, 

   Sai naga tafidda ido waje,, tace watau ,Maisharwali bata rabu da wanan macucin ba ko,,,,

   Duk nasihan da naimata nata ja baya dasu macutane , amma taki,,

    Ba magana ta bace don haka sai natashi naje na bude fringed nadauko mata lemon kwanko mai sanyi nakawo mata dan abin taunawa na aje mat,,,,,

   Takama samin albarka tanata yabawa da irin halin mu na hakkuri da hajiyan mu.

   

   Ba,ai wani dadewa ba sai ga hajiyan mu ta dawo ita da Ali dan takari ya sauke ta a mota suna wani irin dariya kamar wasu matasan zamani.

   Ta labulen window falon mu muke hangen su,,,, wani irin tsaki hjy Laila taja ,,,,, har saida na waigo ta,,,

   Tace kaiyya Allah waddain naka ya lalace.

  Fita nayi waje naje naje, nakarbo ma hajiya hand bag dinta,,


   A,a,a Lailas ke ce yau a gidan lale marhabi da ke,, tana kwabe bakaken kayan jikinta ,,

    Saida tacire nasaman tazauna da atamfa yar Nigeria ajikinta,,

  Itama ruwan sha da lemo nakawo mata ,,,

   Tace a,a barshi kawai fadima akoshe nake sosai,

   Saida hjy Laila ta kare shan lemon ta tukun sanan suka fara gaisawa na yaushe rabo kusan wata uku ke nan.

   Nidai nafita waje don nakarasa aikin dake gabana,,, amma ina iya jiyo maganar su ta waje.


   Yanzu mai sharwali duk nasihar da nai maki na ki rabuda Ali takari ,, baki dauka ba ashe,,

   Wlh ina jimaki abinda zaije yadawo nan gaba,,

   Ali takari ba mutumin kirki bane ,, hakana ya yaudari wata aminiyar kawata,,,

   Haba haba hakadai kike gani,, amma ai bazan yarda har hakan ya faru ba kawai dai wani dan business ne ya hadamu,,,,

   Tunda hjy laila ta fuskanci hajiyan mu bata son maganar sai tace Allah ya sauwaka.

 

   Daman nazone infada maki ansamu wurin aiki da yaranan zasu fara, aiki,ba wani dogo bane kafin lokaci yayi.

      

   Akwai aikin girki akawi na gogegoge, akwai naba filawa ruwa, 

   Kinga saiki san yadda zaki rabasu don kece ke zama da su,,,,, kinsan inda yadace kowa taje,,,

     Godiya hajiyan mu tayi mata sosai ,,, kuma ta nuna jindadinta da taimakon da hjy laila tai mata,, 

  Tace zata dawo bayan kwana biyu ta kai kowa gidan aikinta,,,,

 

     Ranar  litani tun tara na safe hjy laila tazo,,,

   Rugaiyya zata dinga girki a gidan wasu larabawa ne, 

    Yumma zata dinga gogegogen wani gidan masu kudi sai sukaina da zata, dinga kula da yara wata mata, mari zata aiki awani restaurant ne,,, nice ban samu wuri ba tukun ,,,,,,

    Ankai kuwa gidan aikin shi yafara aiki sosai don ba wasa acikin harkan bautane kawai tsantsarta ake yi,,,,

   Wai bidan kudi a wahalce za ,a wuni wahal ce za, a kwana,,, ba hutu ko kadan,,,


    Sai bayan kusan sati uku aka,samo,min gidan aiki wani gida ne ,, zan dinga zuwa ina ba flowers ruwa sau biyu a yini sai kuma in watsa ma tsuntsayen da ake kiwo abinci time to time,,,,

    Gaskiya naji dadin wanan aikin so sai duk da ba wani aikine mai yawa ba amman akwai albashi mai yawa sosai,,,,


     Tunda safe zanzo Sai in ba Flowers ruwa zuwa takwas in an gyara ma tsuntsaye  wuri in yini ina watsa masu abinci suna ci,,, da yamma kuma in kara ba Flowers ruwa 

    Sai in tafi gida sai kuma gobe,,,,,

   

    Ba,ni,kadai ce mai aiki agidan ba akwai maza biyu sai wata yar dattijiwar mata,,, 

    Ana, bamu abincin ci sosai kuma yinshi akeyi kamar irin namu na gida, Nigeria,

     Don haka nake dan tsayawa in ci abinci na sosai ,,,, Don duk dadewan da nayi a saudiya ban saba da abincin su ba,,,

    Warin tafarnuwa da sauran kayan hadin su yakan damay ni sometimes, saboda hakan nafi son inci shin kafa kaza kawai.


    Tunda na fara aiki a wanan gidan ban taba zagayawa ko ina ba daidai inda aka ajeni aiki dai gurin nake zama inyi aiyukana ,,, har da marance sai in tafi,,,,

   Tsuntsaye ne masu tsada ake kiwo agidan, wani gefe har da dawakai da rukuma suma ana kiwon su agidan,,,

    Aikin mu kawai mukeyi babu ruwan wani da wani balle ko wani magana ya hada mu.      Abinda na dan lura da shi, shine masu gidan basu nan don dai mutoci ne kawai a parke , wurin haraban aje su,,,

     Amma fa , kulun gidan kwal yake yana kyali kamar akwai mutum,a cikin shi ,. 

 

 Duk sakon da nake bugawa zuwa wurin aiki na, yau akwai babbanci sosai,

   Abinda na,lura dashi yau da nazo aiki na naga flowers anbasu ruwa suna ta diga dis, dis,,,,, Sai na,wuce wurin tsuntsaye don in basu abincin su, wanda gayanan birjit buhu, buhu,,, 

    Can sai natarar da tsuntsaye suna hira alamar a koshe suke,, kunsan tsuntsu da tsaba, nawatsa masu naga kamar, zasuci ,

    Sai suka taba kadan sukabar gurin,,,,,


   Jikina sai yai,sanyi  nan,danan nadauka ai an,kore ni aiki kawai saboda , gazawana,,,

    Sai,naganin agaban hajiyan mu tana ta duka na, 

    

   Hani,niyar dawakai da aka fito da su yadawo dani cikin hankalina,   

    Duk dawakan afito dasu waje sunata harbin iska,,,,,,, Daga inda nake tsaye ina iya hango,gun,gun wasu larabawa sun kewaye dawakan anata yaba su,,,,

 

     Mai kula da, su yana hidimar su yaje yadawo,,,,, gashi ba ruwan kowa da wani cikin mu,, kowa aikin gaban shi yakeyi,,,,


    Sai dibara ya fado min inje gurin dattijiwan nan mai abinci in tambaye ta ko may ke faruwa ,agidan,,,,

     Kitchen na nufa wurinta, tana tsaye ta motsa abinci nai mata sallama ,,,,,

    Cikin tsoro tawaigo ni tace cikin sauri may kike so may yakawo  ki nan ,,, tajero min tambayar lokaci guda,,,,,

   Ta, hada hannayenta biyu wuri guda tace dan Allah inkoma bakin aikina kada inja muna matsala nida ita,,, banzo wurinta ba da masu gidan basu nan sai yau danaga suna nan, har da dan turani takeyi don inbar mata guri,,,,


     Gwiwa ba karfi na,bar gurin nakoma sashen da nake aiki,  na,,,, 

    Bayan mun gama cin abinci, sai kawai akabamu odar mutafi gida aikin yau yakare,,,

    A , hanya inda zan jira mota naga anata wucewa da dawakai da rakuma,,, acikin motoci,,,

   Wasu kuma akasa ake tafiya dasu,,,


   A motar da natare nake jin wai yau za,ayi wasan dawakai da rakuma har da giwaye,,,,

     Ko wani fani da nasu sashe daman al,adan larabawa ne aduk shekara ana wanan wasan tseren dabbobin sosai,,,,

    

    Maimakon in,tafi gida na wuce wurin bara 

    Inna gefe ina bara sai naga wata balarabiya tanama wani mutumi tsamay,,,, 

    Allah yakai idona , nagani, A hankali naje kusa da ita nai mata maganar inbata bari ba wlh yanzu za,a sare mata hannu agurin nan,,,,,

   Taso ta dan turza saina nuna mata wanda taiwa tsamay a,aljihu yanzu ,,,

   kuya ya,kamata agurin tai min godiyar rashin tona ta da banyi ba,,,,

  Hakalina yanaga kallon yan wasu kauye da sukayo ado dawakai inata masu guda,,,

     Saina kamar cikin kunena anafadin mubar bara ne kuma mun koma sata,,,

   Ban waiga ba amma kamshin turaren shi yasa nagane kowaye,,,, cikin rashin wai,gawa in dibe shi nace la,la,la bani fatan inkai ga hakan,,,

    Itama warning nake mata ai.

   Koda na waiga yabar gurin kamar walkiya,,,,


   

🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 08:07] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                     2⃣8⃣

                         BY

🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


Nasan cewa rabona ba wanda zai same shi, saboda Allahu subbahanahu wata,ala nikadai ya,ba rabona dai dai abin da zai bani, shiyasa hakalina ko yaushe a kwance yake, saidai ina tunanen nima may zanyi in nuna godiya na ga Allah,,,,,,,,


Anty mariya SB da sister hafsat yusuf, sister Aishert da miss illayas tare da duk wata wacce take kaunar novel dina duk ina maku fatan alheri arayuwan ku,,,,,


Almost true life story,,,,,,,
Nadawo gida ina murnan nadawo da yan canji kudin da nasamo wurin baran da nayi,,,

   Hajiyan mu ce na iske tare da wasu mutane ana rike ta tana wani hauka kamar sabuwar mahaukaciya,,,,

    Hakalina sai ya tashi sosai, duk da ban fahinci halin da take ciki ba,, amma naji tana fadin Ali takari ni zaka cuta har cikin gidana,,,,,

   Azuciyana nace taufa yau may kuma ya hada hajiya da Ali takari,,,

   Hankalina yai mugun tashi sosai wlh saboda yadda hajiya ke kuka kamar karamar yarinya.

    Dabara ya fado min azuciya ta ,,,,, saboda nikadai ce a gida sauran yan uwana duk suna gurin aikin su,,,nima sa,a akaci nadawo yau da wuri,,,,

    Wayan hajiya Laila nakira, nakuma ci sa,a tana cikin garin makka ranan sun shigo yin wani hidimar gaban su,, don abin ba hutu,,,

    Agurguje nai,mata bayanin hajiyan mu ba lafiya kuma bansan ko may yafaru da ita ba,,,

   Na boye mata abinda naji ,saboda maganar ranan nan danaji sunayi kan Ali takari ,,don kada taki zuwa,,,

   Kusan awa daya da rabi sai gata lokacin ma yan uwana sun fara dawo wa daga gurin aikin su,,,

   Hmmm wai kusan wahalal da mukeyi kulun ,aboye muke gudun kada akama mu,,,

Wahalce mutun zaitafi haka kuma zaidawo,,,


     Hjy Laila na iso wana naji hajiya ta kara rusa sabon kuka wiwiwi ,,, tana fadin Ali yace ni shida Zinaru ,,, sunci amanata wlh,,, 

    Duk abinda natara ya,wa,washe wai zamuyi business daga nan zuwa Dubai da Nigeria,,, ashe cuta,ta zaiyi ,,, gashi yanzu ya gudu min da komai 

   Hatta albashin yaran nan dakika karbo yana gurin shi dasu ya wuce, don rashin tausayi komai bai barmu da shi ba,,,,

    Ihu muka shiga kurmawa muma saboda yaudaran yai yawa sosai.

   Zinaro taci nata yanzu kuma Ali dan takari yaci nashi,,,,


    TAKARI  TAKARI inji hajiya Laila ai inbaka iya duniya ba baka zuwa nan yin takari, saboda duk wanda kikaga yabar kasan shi na haihuwa yazo nan bidan kudi ,,, to takowace hanya zai iya bidan su dan kar ya koma gida ba komai,,,,


   Daga karshe dai tasamu taciwo kan hajiya tadan lafa kukanta tace kuma zatayi karashi ga shugaban nin su,,, idan yana ganin ya ci bulus ne to karya yakeyi wanan karon saidai in yabar kasan saudiya,,,,,


    Tundaga wanan lokacin muka samu kan mu cikin wani mawuyacin hali,,,

    Bamu da komai na anfani Ali ya wawashe mu kaf ,yayi tafiyar shi abin shi,,, 

   Idan mutum yaje gurin aiki dan abincin da yaci sai mu rago ma hajiya mukawo mata,itama taci

   Gashi yanzu ba lokacin azumi bane ko aikin hajji balle mu samu aikin yi,,,


     Da, taimakon hjy Laila mutumiyar kirki muka dan samu dan abincin ci muka aje agida muna maneji dashi.

  

     Tun wanan lokacin hajiyan mu ta dan fara ciwo kadan kadan gashi bata da kudin zuwa asibiti a auna ta,,,,,

   San,nu sannu ciwo nata mata karfi ajikinta,,

    Sai gashi harta kai wasu daga cikin mu yanzu basajin tsoron hajiya sam,,, sai abinda sukaga dama sukeyi kawai,,,

   Tunda naga ciwon yana batun kada hajiya takaik kwance sosai ,,,,, batare da sanin antyna Rugaiyya ba na debi kudin mu da muke tarawa nakai hajiya asibiti,,, Aka auna ta akace tana dauke da cutar hawan jini,,,,


    Nasayo mata magani da dan abincin da yadace muka dawo gida yinin ranar banje gurin aikina ba, inata hidima da hajiyan mu,,,,,, 

   Duk wanan abin da nake mata sai ido take bina dashi saboda bata da bakin magana amma ina ganin hawaye masu zafi na yawan fitowa a idonta,


    Washe gari koda naje gurin aikina sai na iske ashe masu gidan suna gari tun jiya wai,,, 

      Ance idan nazo inzo in,karbi sauran kudin ranakun danayi aiki in wuce,,,,,, 

    Wani falo ne akace min in shiga ina jefa kafana wani sanyi da kamshi kamar kamfanin gidan turaren Al,Rahaf nashiga ,,,

    Sanyin A,C da kuma TV bango suna ta aikin su,,,, acikin falon ,,, duk yadda zanyi lbrn falon ban iya fadin ,,abinda ke cikin shi duka,,,

   Zaune may shi yake ya ba kofar baya ,amma kan shi na duke yana latsar laptop din dake gaban shi,,,, dagani hankalinshi na kan abinda yake browsing,,, 

    Duk karan da tv keyi ana ta wasan tseren rakumma sai ihu ke tashi,,,,

   Nima da na shigo hankalina yana ga TV ina kallon wani dan yalalon balarabe yana kokarin wuce sauran samar rakumin shi,,,

   Aiko bansan lokacin da nakama tafen hannu naba ina fadin yisauri yisauri,,, 

    Cikin sauri ya waigo tareda mike wa tsaye lokaci guda ido waje yana nuna ni,,, 

   Niko a lokacin ina kokarin kara tafa hannu na saboda murnan star dina zai ci,,,

   Hannu da ban tafa ba kenan ,, Saboda gani Ahamad tsaye agabana wanda ayanzu duk inda naganshi zan iya she,dashi,,,,

   Nakama ja baya a,hankali a,hankali har kusa kai karshen kofan cikin tsawa yace min may yakawo gidan shi,,,

  Gidan shi na nuna gidan da yatsa nace la,la,la ainan gidan aikina ne ni,,,

   Al,mustapha Al,mustapha ,,,, cikin sauri may shi yashigo falon mai kama da fadar wata masarauta,,,, 

   Ni Ahamad yanuna ma mai sunan Al,mustapha,,

    Yanatanbayar shi may kawo ni gidan shi har aka bani pass na shigo mai falo,,,

    Yace mai ai nice wacce ke kula da tsuntsayen gida da banzo aikiba jiya 

   Yakara nuna ni yace ita wanan din 

   Hannu ya nuna min alamar inbar falon,,,

   gudu gudu na fita cikin falon sim,sim dani.


    Ina zaune in jiran aban kudi na in wuce sai naga Ahamad yafito cikin shiga ta matasan larabawan zamani ,,,, Sai, kam,shi ke tashi,,,ya zo ya wuce tagaba,na batare da ko ya kalli da nake ba

    Wurin harabar aje motocin gidan ya nufi wata mai kama da kifi kusan ko yaushe nazo gidan nakan ta kallon motocin ,,,,saboda suna burgeni,

   Kamar walkiya ya harba motar shi yabar haraban gidan ,, nabi shi da ido kawai ,,,,,ina fadi a,cikin zuciyata dama nice awanan motar

     Naji ace min intashi incigaba da aikina anfasa sallamata,,,🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 08:20] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                 2⃣9⃣

                     BY

  

   

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


 

  Duk wanda baiji tsoron Allah ba to tabbas zai ji tsoron abinda Allah ya halitta,,,,,

    Allah bamu ikon bauta mashi da tsarkaken zuciya,,,,,, Ina godiya gadukkan masoyana na Allah barmu tare cikin mutunci da kaunar junan mu,,,


  Almost true life story,,,,,, Nishi takeyi guda guda daga kwance ,,, yayin da kowar mu ke sauri fita zuwa wurin aikin shi,,,

    Har na shirya zan fita sai na tuna cewa hajiya bata karya ba tun jiya ina ganin bataci komai ba,,,

    Dole na kwabe rolling dina nacire  bakaken kayan da na sa,a,saman na zauna dagani sai wani dan wando jeans sky colour da riga fara,mai dan hannu iya gwiwar hannu.

    Wanka na fara yi mata sai kuma na gyara gurin kwanciyar ta dafa mata abinci mara nauyi ,,,


  Nidake fita da shidda na safe sai gani yau har kusan goma na safe ,,, koda na iso na samu an min duk aikina ,,,

   Al,mustapha yace may yasa yanzu nake makara ne,,, nafada mai ummi na ce bata da lfy ,,, ina dan kula da ita ne kafin inzo amma zan gyara,,,,

    Tunda naga cewa zan samu matsala a wurin aikina sai nake tashi tun karfe hudu na asuba in yi duk wani abinda ya dace ,,, saboda gudun makara,

  Tun lokacin ban kara ganin Ahamad ba ,,, koda yake ma ko tazo ba sani zamuyi ba tunda ina can gurin abokan hirana tsuntsaye yini nakeyi ina masu watsin abinci,,,

     


      Yau ko da nadawo gida na samu Rugaiyya ta dawo take fada min cewa gidan da take aiki sundawo daga tafiyar da sukayi,,,,

     Nan muka hadu tare da ita muka gyara hajiyan mu ,, nadan fito da ita kofar gidan mu don ta dan kara warware wa,,,

  Da alamar taji dadin hakan don yau harda yar hira munyi da ita,, awajen 

    Matsala guda ce take min complain kafarta takeji yana mata nauyi sosai,,,

 Tundaga rana nake dan yawatawa da ita acikin uguwar mu duk da yake saman dutse muke,,,
Kofar kitchen din su yake kallo daga bakin kofar shiga falon su,,, duk wani motsi da takeyi idon shi na a,kanta wanan abin ya fara isan ta gaskiya ibadon wanan aikin yazama kamar na dole ba da tabar masu gidan su,,,

    Duk lokacin da maigidan yake a gida matsalar da take fuskanta kenan ,,

    Idan sun hada ido wani lokaci har lasan lebon shi yakeyi kamar maye,,,

    Azuciyar ta tace ka boye matar ka ko kuda baya ganin ta amma ni ka hanani shakat da wanan mugun kallon 

    


    Cikin dare suna kwance da matar shi tace mashi maigida nasan duk halin da kake ciki da yar aikin mu ,,, babu matsala zan kawo maka ita har nan gidan tadawo da ,kai na,,,, ni nasan kufi sha,awan wa,"yan nan matan fiye da mu matan ku,,,

   

    Tundaga wanan ranan matar ta fara rarashin anty na Rugaiyya tana wani haba haba da ita,

    Abinci lafiyaye ake bata tana ci sai kuma sutura masu dan kyau da aka sayo mata,


    Tundaga ranan da aka sai mata wa,yan nakayan sawar masu kyau antyna tafara shiga damuwa saboda tana yawan tsorata da mugun kallon da maigidan ke mata yana shafar gemay shi yana lunshe ido,,,,,

   Tundaga ranan  tadawo  gida cikin damuwa,,, tana shigowa ta jefo min ledar kayan da aka sai mata ajiki tana kokarin cire yar bakar rigar da muke sawa sama,,, Don wanan kowa yasan al,adan larabawa ne, bayan sungama kwaliyan ciki dole akwai bakar riga da hijjab ko gyale da zaka rufe fuskan ka dashi takalmi kuma mun fi sa flat cover,,,, 

    To muma TAKARI ,, haka mu tamu shigar saidai lokacin umurah da aikin hajji wasu sukan dan yi dressing din kasar su,,,,

   Ledar nabida kallo ina fadin may ke cikin wanan ledar yar uwa, nakai dibana zuwa gareta don jin ansa,, yo kibude mana ki gani,,  kayane masu kyau dogayen riguna da yan kayan unders aciki rigunan kala hudune,,,

     Daga ina daga uwar daki na matar hamza Abdallah,, 

   Nakalla nakara juya kayan nace gaskiya suna da kyau, halan sun samu wani alheri ne haka,, ta waigo tadan debeni dadai lokacin tana cire kayan kan,ta,,, azuciyar ta, tace ansa may zan baki maryam da sauranki nasan bazaki fahince ni ba,,,

   Kawai sai ta wuce dakin hajiya don ta gaida ita,,,,

    Tanunawa hajiya kayan ,takuma bata dan abin sa ma bakin da tazo mata dashi,,,

Dakin nashigo na zauna gefen gadon hajiya nace mata,,,,,

     Gaskiya hajiya yakamata ki fara fita hakana koda Haram ne ki dan dinga zuwa kina dawafi , zaifi maki wanan zaman , agida kulun .

     Zama wuri guda zai ta kara maki bakin cikine arayuwar don babu ranar da wanan damur zata barki in bakibar tuna wa ba,,,,

    Rugaiyya tace ai na fada mata ba yau ba saboda naga tadan ji saukin jikin nata ai

     Saida hajiya ta gyara zaman ta kadan tace insha Allah zan gwada zuwa ,,, kuma nagode maku sosai da kulawar da kuke bani ,,,, ayadda na dinga cuta maku amma sam baku gujeni,,, sai ma kara shigata jiki da ku,keyi,,,,

     Amma sai gashi Sukaina da mari sun fi karfina don suna ganin banda komai yanzu,,,,

    Takare maganar ta ta tana share kwalla,

   Dama tunda bata da lafiya nadawo dakinta da kwana saboda dare,,,

    

      Ankara min yawan aikin gidan yanzu saboda mai kula da goge,goge baida lafiya kwana biyu baya zuwa,, ,,,,,,  Bance komai ba 

     Tunda safe nake zuwa inyi aikina kafin wani lokaci sai wanan tangamay,may falon yakoma sai kyali yake yi kawai,,,

     Gyaran mace da na miji ba daya ba,,,,don komai na falon sai nai mai tas ,,,,

    Koda Ahamad yazo daga Riyadh inda yafi zama saida yayi mamaki yadda yaga canji a,falon mustapha yai mai bayanin cewa wanan yariyar mai ba flowers ruwa ke gyarawa saboda mai kula da gurin baida lafiya ,,,,,

    Shiru yayi acikin zuciyar shi yana nazarin rayuwa irin na fadima,,, da kwazo , yarinya karama amma ace duk abinda za,a samu kudi akansa zata iya,,,

   Gaskiya yana son jin labarin wanan yarinyar dakuma sunar ta da inda tafito,,,,,,

     Sabod tsoro lamarin ta yake bashi,, ace duk inda yaje sai yagan ta,,,,,

     Almustapha yadawo dashi daga wanan tunanen yana fadin amma kayi hakkuri nima nasan bazata iya ba don dai kada abar gurin hakane yasa nace ta dinga taimakawa,,, amma daga yau,,,,, Hannu yadaga mai alamar yadakata,,, hakana, yace wurin yayi kyau fiye da da kuma ko da mutun uku akace sunyi wanan aikin zanji mamaki balle wanan yar ficikan yarinyar,,,

    Ina gurin Flowers ina basu ruwa yafito cikin wani bakin jallabiya, mai laushi, yana shaning, Sai kamshin turare shi Al, madinal ,noor 

    Jin kamshim kawai nayi nasan cewa shine yafito,,, ,,,,Waya yake yi azahiri amma ni yake kallo cikin zuciyar shi yana fadin wanan yarinyar bata gajiya ne da aiki,,,,,,,, Saida yagama wayan shi atsaye,,,

    Al,mustapha yakira yanuna mashini ,yace aiki nawa nakeyi gidan 

 nan, yafada mai duka,,,

    Saida yadan nisa yace ,, haba Al,mustapha, aikin ai yai ma mutum yawa ,, katausaya mata mana,,,

    Yadan sosa kanshi, yace za,a gyara insha Allah,,,,

Duk abinda suke fadi inajin su,,, 

    Amma ban waiga na kalli inda suke ba don ma kada in gaishe shi,,,🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 08:21] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                   3⃣0⃣

                     B Y

 🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎  Duk Abinda bawa yatarar akabarin sa na alkhairi ko na sherri to, Tabbas shi ya aikata abinshi, domin Allah subahanahu wata,ala ba,azzalumi bane baya zalunci acikin mulkinsa,

       Ubangiji mu sarki Allah mu na rokon ka kabamu ikon aikata alheri arayuwar mu👏👏👏👏    Ina jinjina maku yan TEEMA Luv group novel, Yan HUGUMA group, gaskiya banda bakin gode maku saidai in maku fatan alheri arayuwar ku ako yaushe, Duk masu kaunar TAKARI   novel ina maku fatan alheri Allah yai muna Rahama acikin rahamar sa,,,,👏👏👏


Almost true life story

Yana tafiya a saman titin 57 up zuwa kwanar , massfala junction, Yafito,ne  da,niyar zuwa, wasu,shagunar su na, saida kayan sawa,, na maza, saboda,lokacin da ake odar sabin kaya kafin mahajjata su zo ya kusa, za,diba kayan da suka dan dade sai ayi gwanjon su akawo wasu sabi lates,,,,,

    Wayar dake mane cikin aljihun shi tayi yar tsuwa ,

   Duk da sautin ki,ra,ar ,wasu yan yaran rabawa dake tashi cikin sauti mai dadi a,motar tashi bai hana shi jin wanan tsuwar ta wayan shi ba,,,

   Rage gudun da yakeyi da motar shi yayi  don diba mai kiran nashi ,, idan ba mai muhinmanci bane ya aje har ya sauka,,,

    Ganin sunan da ke a screen din wayan yayi barobaro ABBANA. Jikina rawa yadan samu gefen titi ya perker motar shi gefe guda, fuskanshi manne da yar guntuwar murmushi wanda sai kila bayan wata yake irinta,,

    Saida yabari kiran ya tsinke tukun don haka al,adasa take indai kirace daga Nigeria bai,dauka saidai shi yakira ka saboda yawan cajin kudin da akeyi ma mai shi,

    Cinkin sallama yafara magana sai mahaifin nashi ya ansa mai asanyaye shi don duk kusan halin mahaifin nashi ya dauka,,,

   Haba babana wai fushine kakeyi damu ko kuwa dai rashin kulawa da mune yasa yanzu ko yar wayan ma da kake bugowa don muji lafiyar ka, ka daina sam,,,

    Murmushi yayi mai tsada har uban na jinshi tacikin wayar,,,,Cikin muryan tashi mai kama da baya son magana sai dole,,, la,la,la, Abbana, haram,,haram ,,,,,

    A,kawai dan business din danakeyi a Dubai ne yanzu wanda yadan dauke min hankali da komai,, kwanan bana cikin lokacina ko kadan wlh,,, amma ina mai roko da ayafe min dan Allah ,,, naso in,zo but time ne banda sosai yanzu insha Allah nan badadewa ba zan shigo Nigeria ,,,,

    Uban yace a,a kayi zaman ka mu ai zamu zo don mu gan ka, dama na bugone infada ma cewa zamu zo umurah nida maman ku don adiba muna lafiyanta,

   Yadan yi murmushi yana susan kanshi kamar agaban uban yake yace, amma kilama zan riga ku zuwa, 

   Shima uban dariya yakarayi,, yakauda zancen yana fada mai cewa harda tsohuwa yake son su zo don taga dan lelenta, saboda tana damun su da zancen shi,,,

   Yace ashe inada babban bakuwa kenan dole in samu lokacin in ma wanan zuwan shiri na musan man,,,

    Sundan yi hirar lokaci da kuma yan uwa,,,,, sosai 

    Sukayi sallama uban yana ta farin ciki da jin dadin dan nashi ,,,Saboda hankalinshi, uwa,uba ga ilimin addini ,kusan duk abinda zakuyi dashi cikin ladabi da kuma tarbiya irin na larabawan asali zai ma,,,,

    Lunshe ido uban yayi yana tuna su salis da ya kai turai karatu ,koshida yazauna turai har ya haifesu can baijin turancin tsiyar da suke mai inyana waya dasu,,,

      Garashi ladabi ko waye suna kokarin bashi hannu su gaisaa ba kunya sam ga al,amarinsu,,, 

    Sabanin Ahamada da duk zaman ku bakajin yai turanci saidai laranci, cikin tsanaki,,,
     Shiko Ahamad karasawa yayi shagon nasu, yadan didiba abinda yakamata ayi wa shagon nashi,,,

     Yadawo gida cike da tunanen zuwan mahaifan nashi,, 

    Bazuwan kowa yafi mai dadiba kamar na yar tsohowar nan babarbara mai yawan fitina,,,

    Annurin fuskan shi ta dan sauya lokacin da yatuna cewa bada mahaifiyar shi ba cikin masu zuwa gurin shi,,,

   Rashin mahafiyar shi tare dasu yana yawan kona mai zuciyar shi in,yatuna.. Duk wanan daular da suke samu agidan su bada ita ake ci ba,,,,,, Duk da yana kokarin tura mata da abin anfanin rayuwa yadda yakamata saboda tun yana yaro ,yana jin tsohuwa na yawan yi mai addu,an Allah yasa yasamu ya kula da mahaifiyar shi da yan uwan su,,,,,,,

    Saidai abinda ke dan yi mai sanyi ya lura dacewa inda take aure yanzu tana cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya,, kuma mijin nata yana nuna mai karanci sosai kamar shi ya haifeshi ,,,

   malam na yawan lurar dashi addini tun yana karami inyaje hutu kauyen,,,

   Shiyasa har gobe yana ganin mutuncin shi don yarike mai uwa amana.

   Da wanan tunanen shiga falon shi ,,, ya wurga da key din motar shi a bisa kujer da ke gefen shi,,,,

   Kujera mafi kusa dashi ya zauna gami da dafe kanshi, da hannun shi guda,,,

   Hjy mama hjya mama , hmm,,,, 

    Ya lunshe idanun shi yabi lafiyan kure da yake zaune ya jiginu da yan shi yana murmushi mai nuna bakin ciki a fuskan mutun.

    Shi duk labarin da aka fada mai nazaman maman shi da ita bai kona mashi zuciya kamar yadda tadinga gwada mai rashin kauna kirikiri ba boyo ko kadan, 

   Idan har wasu na iya boye mugun halisu ita sam bata iya boye nata,, akan shi,,,,

     Duk abin da baban shi zai mai na alheri saida in bata sani ba za,ayi shi inko tasani yaza ma tarihi,,,

    Koda kuwa za,ayiwa yan uwanshi ne idan anzo gare shi sai salo ya canza ,,,,,

    Falon yabida kallo nadan wani lokaci yanisa saboda yasan cewa tunda yatare wanan gidan nashi mama bata shigo saudiya ba,,

    Tun yana zama a Riyadh ne kawai ta sangidan shi amma sai da ta nuna hassadanta cewa, ina yasamu wanan kudin haka.

     Waiko dai uban shine ke turo mashi da kudi aboye,,,

    Inba haka ba ya zaifi yan uwanshi samu wuri haka,

    Cikin fushi tabar kasan , 

     Ashe lokacin da taje turai ziyaran yaranta ta dauka sunfi Ahamad jin dadi ne da samu wuri,.

    Donshi baya magana kuma baya nuna cewa shidin wani abu ne can

    Har aikin da yakeyi baban baifada mata ba saida tazo tagani da idon ta,,,

     Amma duk da hakan bata gamsu da cewa komai na Ahamad din ne ba 

    Gani takeyi ai na company da yake aiki ne aka bashi ya zauna,,,,,

     

   

   🐎ZEEE MAKAWA🐎

     🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 13:32] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                   3⃣1⃣

                     BY

 🐎ZAINAB MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


 GiBA wata,kalmace mai saukin fada saida kuma mai nauyi ce wurin fasarar ta Allah ya haramta, zina, sata, shangiya, da kakausar harshe ,,,,saikuma gashi duk GIBA tafisu karfin haramtawa, ,

    Allah zai iya yafe ma bawa tsakanin shida bawan amma banda tsakani bawa da bawa,

   Yan uwa munisan ci Giba atsakanin mu 

    Yi,da junan mu shiyafi komai faruwa yanzu,,,,GIBA watau Gulma,,,,Gaisuwa da fatan alheri dukkan masoya TAKARI NOVEL ,,,,,,, Antys din huguma ga jinjinan ku nan na girma akoda yaushe,,, 


  Almost true life story,,,,,
    Girki ta hada masu lifiyaye irin ta kasar su ,, ta shirya masu akan dining table ,,,,

   Akawai dakin da aka tanadar masu don hutu agidan ,can takoma don ta dan huta bayanta kintsa jikinta tsab da sungama takwashe kayan tawanke sai kuma gobe indan Allah yakaimu basu kara cin wani abinci mai nauyi kuma,,,,,

     Yau ma hakan ne ,, kiranta akayi a intercoms din gidan don kowani daki mai aiki akwai shi, agidan.

   Cikin sauri tagyara rolling din kanta ta isa falon ,,Zau,ne suke saman kujerun dake kewaye da dining table din,,,

    Cikin gimamawa ta gaisu tana dan dukawa na ban girma ga shugaban ka,,,

   Idon shi kur akanta ko  kifta su baiyi ,,shi akulun wanan yarinyar kara sha,awa ta yakeji a ran sa, ,,,,,,

     Sai wani lunshe ido yakeyi kamar may maye,,


   Matar tace ma anty na ta kwashe kayan abincin sungama zasu fita amma don Allah tadan  jira su har su dawo kafinta wuce ,

    Rugaiyya ta ansa cikin gimamawa, 

   

   Har wani lokaci basu dawo gida ba sai zuwa dare lokacin badamar tabi hanya zuwa gida yan bagaladi na hanya,,,

     Cikin damuwa da fargaban iri iri zuciyar ta yake,, don tasan cewa hankalin yan uwanta zai tashi sosai don duk inda mutum ya dole yadawo kafin dare yayi,,,

   Matar ce tai mata bayanin cewa tayi hakkuri ta kwana da safe zata kira Albani din ta taimata bayanin cewa tana tare da su,,, 

   Saboda dole ne duk wanda ya kawo ma ka mai, aiki ka dauki lanbar wayan ,Albani din shi ,,,,

    

  Cikin rashin jindadi ta isa dakin da take hutu aciki idan tazo gurin aikin.

     Uwar dakin nata ce tashigo dakin cikin fara,r ta da sakin fuska,             Ma,isha bata da jiki sosai gajera ce maidan tsawon fuska,,, takai kimanin shekara talatin da wani abu da haihuwa,,

    

   Cup take rike dashi a, hannu ta wanda ke cike da madarar shanu mai kyau mai kauri ta asali ,ko kallon cup din kayi kasan madarar yadauki sanyi,, so sai,,

    Gefen gadon da Rugaiyya ke sama ta zauna wanda ita kuma Rugaiyyan ke kokarin tashi ta zauna saboda girnamawan, shigowar uwar dakin nata dakinta,,,,,

     Ta mika mata cup din tana fadin tasha madarar don zaimata amfani sosai,,,,,  kallon madar Rugaiyya keyi kamar batasan ko maye madara ba da mamaki,

  Mika mata cup din tayi gami darike mata hannu guda tana murmushi, tace madarace mukasha ,shine nakawo maki naki don nasan kina gidan yau kinzama bakuwata,,, takarbi cup din tana godiya.

   Saida ta tabbatar tasha sai tamike tana ce mata tasake jikinta mana ainan ma gidane ko bata saba da su bane har yanzu,,,

 Dan murmushi tayi cikin girmamawa tana fadin ai ba ko mai tunda za,a fadama Albani din ta, cewa tana nan saboda dare yayi mata yau,,,,,,,

      

      Shiko maigidan yana can saman bene, daidai wani dan dake saman harabar gidan nashi yakasa tsaye yakasa zaune, yaje yadawo yana mazurai, da ido yana lunshe su yana shafar gemun shi,,,,

    Ahaka matar tacin masa tsaye yana yawo tsakiyan haraban su yana dunkular hannun shi,,,

    Tabayan shi ,Ma,isha ta rugumo , shi,.

   Yai wani ajiyan zuciya a hankali, 

    Yajuyo da Ma,isha ahankali ta gaban shi suna fuskantan junan su,,,

   Itace ta fara magana ,, tace nasan ganin da kaima wanan yariyar a yau ,shiyakara saka cikin wanan yanayin maigida,,,

     Yace wani abu nake tunane kawai ba wanan ba,,

 Jan hannu shi tayi suka koma ta cikin bedroom dinsu,,

    Tace mai magida na riga na gama shirya  komai ko ,,,yadan yi murmushi ya rungumota,

Tace nan,da dan anjima kadan kana iya zuwa gareta ,,, kalassss,,,

    Ta juya tana shirin kwanciya ,,, 

   

  Amma cikin zuciyar ta tana fadin ita tasan cewa baza ta iya gamsar da maigidan nataba in badon haka ba bazata yarda da wanan akidar tashi ba,,,.

    Saidai kasssh duk yadda tayi yafi gane ma bakaken mata don acewar shi sunfi dadi da juriya dasu,

  Yakuma sheda mata kuma itama din tasani kusan gidajen da kaga yariya bakar fata tana aiki to aiki biyu ne da ta lalurar maigida sai kuma ta zahir,,,, amma bakowa keda wanan akidar ba sai wanda zuciyar shi takekeshe,,,  


      Saida yadauki dan lokaci yana gyara jikin shi,,,,yagama duk wani shiryeshirye shi na kwanciya,,, azuciyar shi yana kiyasta yadda zai kasance da Rugaiyya yau,,, yana fatar tafi waccan da tatafi dadin harka saboda ko banza Rugaiyya tafi, wacan kurciya,, 

 Saida kuma yakan tuna irin dadi damore rayuwa dayayi da,zakkiya yar, kasar, niger,,,, yaji dadin zamanta dasu sosai, ita,din ma,tasamu alheri awajen shi dakuma matar shi,,, idan ko Rugaiyya haka take zai kasan ce mai farin ciki 

Don haka dole yasan irin yada zai kyautata mata da kuma irin kyautar da zai mata,,, dan yajar ra,ayinta,,,

   

   Rugaiyya tagama shirinta tsab ta kwanta,,

  tare da addu,oin neman tsari daga Allah kamar yadda ta saba,,

    Saidai duk, jikinta bata jin karfin shi ,sam tunda tasha madaran da ma,isha ta bata jitakeyi kamar duk gabobin jikinta basu aiki,,,,,,

  Tana kwanci Barci mai karfi,ya dauketa, daga kwancinta,,,

   

    Tafe yake a hankali yake tafiya, cikin dogon baradan dake gidan inda dakunonin yan aikin gidan yake a jere ,,, kusan duk basu yan aikin basu ciki, kasancewar dare ne mafi yawan su sun tafi gida basu kwana agidan ,,,

    Kofar dakin yatura a hankali yai ,sa,a kofar a  bude take,batare da yasha wani wahala ba,,,,, 

    Tsayawa yayi yana kare,mata, kallon irin halittan da Allah yai mata gaskiya ba laifi yasan zai more rayuwar sa anan,

   Cikin barcin da takeyi mai nauyi take jin ana shafarta,, a,hankali ta gyara kwanciyar ta don ta dauka ko duk dadin barcine a gidan masu kudi,, 

     Shiko gogan yaji dadin hakan don yadauka ko shi ta gyara mawa yan kayar fulanin ta sunyi ciciko sunyi tsaye,,

  Nandanan yashiga su ya,,,,,,,,,

   Shafarta yakeyi gami da tsotson wasu sasan jikinta,,,

   Ahankali ta bude idon ta dake tap da barci mai nauyi,,,

 Duk da barcin da ke idon ta bai hanata zabura ba da kokarin mike wa, zaune, cikin tsoro,,,,,,

   Shiko gogan sai ce mata yakeyi cool dawn cool dawn , ,,,,,,

   Data ga zaicigaba saita kama ture shi tana fadi ,,,.la,la la, zina haramu,,,

     Kiss yakara kokarin kai mata,,,,

    Aiko tasa hannun ta da karfi da ja gemen shi iya karfin ta saida yayi wata yar kara, na wahala ido waje, ,,,,,

    Allah yabata sa,a ta jawo Cup din da aka bata tasha madara shi,,,,ta buga  mai a fuska jin zafin da yayi yakai mata mari yakai mata wawan mari, cikin fushi

,,,,,,yasa hannun shi guda ya rike mata wuya, gudan hannun, yana shafar fuskan shi inda yaji kamar sanyi ashe jini ne,

    Ta kara kai mai cizo a wuyar hannun shi guda,baisan sanda zafi ya sa yasake ,ta ba,

  Dakarfi ta ture shi gefe tasamu ta sauko sama gadon ,tasa hannu taja rigarta da ta cire gefe 

,, Sa,arta guda yamanta da yashigo hankalinshi yadauke da ganinta da yayi kwance bai rufe kofa ba,,,


    Da guda tafita hanyar zuwa get din gidan duk suna a rufe ,, 

    Dabara yafado mata tashige parking area na gidan tashige karkashin wata mota landrover,,, talafe tana maida nunfashi ahankali kamar za,aganta takeji ita,,,

 

  Yadafe fuskanshi da hannu guda don jinin dake zuba mashi dakin matar shi yanufa don yasan ba inda zatabi tafita gidan da daren nan ,,,,,

  Matarshi naganin shi tataso da saurinta tana tamabayar shi ko may yafaru haka,,, jayeta yayi gefe yana fadin kinsan cewa wanan yarinyar ba irin wacan da kika samo min bace kika,kaini ta jimin ciwo

 Sai nasa andaure min ita sai an fitar da ita kasan nan,,,

    Hakana yaita fadar shi ita kuma tana gyara mai gurin da jinin ke zuba ga zafin cizon da akai mai,,,

gurin yai ja jarir,,,


     Shike ta fada yana ce ma masu gadi su diba ko ina , nagidan akamo mai ita,

   Duk sun diba har gurin motocin da data,ke kwance tana jin su sai addu,a takeyi abakin ta,,,,

   

Kiran sallah akeyi ko ina taji lokacin da yake fadin kada a bude kofar gidan har sai sun dawo sallah asuba,,

    Ita kuma lokacin tana daidai bayan dakin maigadi,,,

   Allah yabata sa,a maigadin yashiga daki dauko abu,,, aiko ta lalaba tafice dagudun tabar gidan ,,,,

  Gudu taitayi tana waigen bayanta ko ana binta abaya, ,har Allah yasa tasamu mota masu zuwa dawo sallah asuba tabiyo,,

   

   Yadda naga dare haka naga rana don ina cikin mugun damuwar rashin dawowar yar uwata kuma masoyiyata maikaunata da alheri,,,,

   Don dai ni nasan cewa ba gudu tayi ba akwaidai wani dalili mai karfi sosai,,,

   Gari yafara yin dan haske mutane sun fara zirgazirga nafito wajen gidan mu natsaya batare da kowa yasani ba,,,

       Sai ko ga Rugaiyya nagani cikin tashin hankali  da firgita janta nayi gefe nace ta nuna babu komai har kowa yafita don ba wanda yasan batadawo gida ba,,,

   

Hankalina atashe nabata ruwa tai wanka muka shirya kamar kullun, mukafita gidan ,,, 

  Saida mukai nisa da uguwar mu sanan muka rike, junan mu mukaita kuka, 

    Saida mukayi mai isar mu ba mai bamu hakkuri sai Allah,

 Nice nadanyi karfin hali na fara magana cikin sheshekar kuka, ahankali nake tambayar ta may yafaru da ita,,,,,,,,

   Kara rugumay ni tayi takara rusa sabon kuka dakyat na samu tadan tsagaita kukanta,,

   Sannu ahankali ta warware min komai tun farkon yadda al,amarin yafaru da ita , dakuma yadda tasamu ta tsira

   Mun aje cewa koda hajiya tace ta koma gidan aiki bazata koma ba wanga karon,,,,

  Haka muka dunguma dani da ita muka tafi gidan aikina a,ranan
🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 13:37] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                3⃣2⃣

                   BY

🐎  ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎   

🐎HUGUMA GROUP🐎Almost true life story,,,,,


   Imani acikin zuciya take ba,a zahiri ba , Allah yana amfani da aiyukan mune, na zuciya,bana zahiri ba Allah yakara muna imani 👏👏👏👏👏 , Ameen,,,,,,,,Tunda safe muke barin gida zuwa gurin aiki na ,ba mu dawowa sai da dare ,,, 

    Don muna gudun kada azo a,kama Rugaiyya ,,, kamar yadda mugun yai ikirari, cewa zai sa afitar da ita acikin kasar da karfin tsiya,,,

    Koda mukadawo Yumma ke tambayar mu ina Rugaiyya ta,tafi yan gidan aikinta sunzo har sau biyu bidan ta,,,,

 Cemata,nayi ta kyale su don ta,canza wani guri aiki ko,,,

    

    Tun lokacin bamu kara jin komai ba tun muna dari dari ha muka gaji muka sake jikin mu,,,

    Saidai hajiya bata san cewa bata zuwa aiki ba,, abin da muke gudu shine kada lokacin kawo kudi yayi bamu kawo mata ba,,,

  Duk zuwan da mukeyi da Rugaiyya masu gidan basu sani ba dayake gefen mu daban ne,,

   Shiyasa har muka dan  dauki lokaci, agidan ba wanda yasani,,


    Shirin zuwar yan Nigeria umurah akeyi, su hjy mama,

  Sai gyaran gidan ake tayi sosai tundaga fentin gidan har furnitures ancanza sabo sai kuma kayan electronic sabbi nayayi lates,

    Gidan yakara wani haske fayau kamar ancan wani fasalin gina ne,,,

   

Al,Mustapha yake fada ma wanan yar dattijiwan mai aiki suna son karin yan aiki mutum biyu ,,,,,, mata biyu mata maza kuma uku,

   Daidai lokacin na shigo kitchen din don dawo da kayan abincin na,,,

   Saida nabari yafita nadawo gurin matar nai mata ,,,

   hannu na bibiyu nake rokon ta don Allah ta taimaka ta daukar min Rugaiyya daga cikin ma,aikatar,,,

   Shiru tayi tana nazarin maganata, 

  Can tace inzo mata da ita gobe tagani ko zata iya,,,

  Nace mata aitana nan gidan tare muke zuwa,,,,nan nabata labarin abinda yafaru da Rugaiyyan agidan aikinta

   Gaskiya matar ta tausaya muna sosai tai muna alkawarin zata gwada aikin ta tagani ko ta iya,,,


      Washegari kuwa ta,fara gwada aikin Rugaiyya ,tagani ko zata ,iya,,,

   Abinci muka hada mata maidadi kusan kala uku tare da abin sha,,, mafi saukin hadawa,,,

  

 Kofar,  Get din gidan aka wagalle, motoci ne guda uku suka shigo gidan maigidan ne  wanda yai tafiya zuwa kasar Dubai tare da baki ,,,,

     Yaje wani aikine na gagawa a kamfanin wani mai kudi a,Dubai .

    Inda yai masu gyaran wata na,urar,

 Tatan mai da kusan mutun uku ana,daukowa don su gyara hakan baiyi ba,,,

  Shima shiganshi tabiyu ke nan ,ana biyun Allah yabashi sa,ar gyarasu,,

   Wanan gyaran ta sa yasamu alheri sosai ,,, 

    Don har gurin Abu Abdullah ,   aka kaishi don su gana,,

 Abu Abdullah wani matashin dan kasuwa ne akasar Dubai, mai tsananin arziki da dukiya akasar ta Dubai,,Arzkinshi bana haye bane na gadane,,,,, ,

  Duk,wanda yagan shi,, dole maishi yasamu alheri sosai arayuwa,,,, Don mutun ne wanda shi kanshi bai san yawar arzikin shi ba,

    Shiyasa duk mutumin da ya yimai abin farin ciki arayuwa shi,har yaji dadi,

  shikuma zai jika maishi da daula daida gwargwado,,,,

     Saiga Ahamad yaci sa,ar wanan daular shima,,,, 

   Don dama Abu, Abdallah,yayi bakin cikin rashin aikin na,urar da Ahamad ya gyara mai,  kasancewar kafin a,yarda mashi ya mallakesu saida yasha wuya  sosai don an nuna mai hassada so sai, tun mahaifin shi nada rai suke wanan project din,,,,,,

    Yana murnan sunshigo hannu sai kuma gashi,sun,ki aiki yadda yakamata,,,, ,,,,,,,

    Angwada engineers har biyu kafin,Ahmad,abin sunki aiki ,,,,,

    Wani abokin karatun Ahmad da a,ka,kira dan paris tare sukayi karatu da yaje karo ilimi, a,kasar paris,,,

Abokin shiya, ce akira Ahamad dake saudiya agani,,, yasan dawuya in bai iya gyara su,, ,,,,,

   Cikin ikon Allah sai gashi ko ya tayar dasu duka,,, ukun yanzu ba su da wata matsala,,,

  Jindadin hakan yasa,

    Aka shirya yar karamar walima don farin cikin wanan nasarar da akasamu,,,,

  Wurin walimar ya hadu da  abokai kala kala, harda baban manajan companonin, Abu Abdullah, agurin.

   Bayan waliman shima yagaiyace shi zuwa gidan shi shan green tea,,,,,,

    Nan ne suka kulla,business dashi,,,

   Yakumayi ma Ahmad alkawrin za su shi cikin harkan kasuwancin su sosai,,,

    To shine yadawo gida yau tare da abokan shi yan Nigeria da suke can saudiya tare,,, 

    Su sukaje airport su ka taroshi saboda murnan alherin da yasamo,,,,     Kusan su biyar ne suka shiga tangamaymay falon nashi cikin raha da farin ciki kowa na fadin albarkacin bakin shi,,,,

   Al Mustapha ne keta dawainiya dasu,,, 

   Daya daga cikin su yace aishi yunwa yake don tun safe baiyi break fast ba ma,,

    Abinci yace akawo masu suci,,, 

   Cikin sauri Almustapha ya shiga gurin yar dadtijiwar matar mai abinci yana fada mata baki na bukatar abinci,,,

    Gabanta ne ya fadi don dai yau ba itace ta girka abincin ba mune akaiwa gwaji aiki yau,

    Bataboye mai ba tafada mai aiko yabita, da fada, har yana ikirarin cewa har ita sai ya kora aikin nan,,idan har ansamu matsala,,,,,

    

     Abinci suke ci suna hirar su, na duniya,,, daya daga cikin sune ya tsiyaya hadin sobo da mukayi na ainihi,,, yasha,,,

    Dago kai yayi yana tambayar Ahmad inna yasamo mai ,mai  aiki kamar agida Nigeria ,, aishi rabon da yaci abinci irin tamu ta Nigeria har ya manta wlh,,,,

    Shima gudan dake gefe yace kai wlh ka rigani magana ne umar,,,

  Wanan abincin yasa na tuna da gida sosai yau,,

    Almustapha dake gefe yana jiran ayi mai complain yai wani irin ajiyar zuciya gami da hamdala, saboda sam baison abinda zai bata wa maigidan nashi rai,,,

       Don Ahmad mutum ne mai yawan hakkuri duk abinda kaji yai magana to abin akwai matsala akai,, don haka yake taka tsantsan dashi,,,


    Muko muna can matan nan tasamu gaba tana tamuna fada wai naja mata hasarar gurin aiki mafi daraja da ta,taba samu arayuwar ta,,, fada take yi kamar zata doke mu,,, mun dukar da kai kasa Rugaiyya tana ta bata hakkuri,,


  Cikin girmamawa da kula ya bakowaninsu kyautar da saida suka girgiza da shi ganin ,,,,, kudin daya basu mai yawa haka ko bakin godiya basu samu ba,,,

   Yace umar mayye amfanin mutum yasamu bai kyautatawa natare dashi ba,,, 

    Nasamu amfani sosai a, wanan tafiyar kaga kuma da muke tare aidole in taimake ku,,,

    Baysn sun wuce Ahmad yakira Almustapha ,,,

    Duke yake yana serching wani sabon engine a,cikin computer shi,,, kanshi na duke ,,,,,

    Yace Almustapha wayai muna abinci yau agidan nan ,,,,, shiru mustapha yayi kashi na duke akasa,, dama yasan dole atuhu mayshi da wanan laifin maigirma, dan ba kowani abinci oga ke ci ba ,.ko ita wanan matar saida yagwada ta kafin adauketa,,

    Idon shi yadago yakai diban shi ga almustapha,,, bakaji bane yakara tambayar shi,,,

   Cikin in,iniya yace mai dama dama ,,yau wanan matar bata da lafiya ne shine ,,, shine nasa wanan yariyar mai ba Flowers ruwa, ta yimuna,,,,

    What ya,mike tsaye,, gami da ture computer shi gefe guda,, 

    Yace kana nufin wanan yar yarinyar tai wanan abincin yace mai na,am,itace maigida,,,,,,,,

   Kai yakama girgizawa yaje yadawo,atsakiyar falon,

   Azuciyar shi yana tunanen anya fadima mutunce, kuwa,,, yarinya kamar wata Aljanna gaskiya lamarinta akwai bincike don dai she is to young da wa, yanan abin da takeyi gaskiya,,,

Don dai ko agida Nigeria,kamar wanan yarinyar bata isa tayi wanan girkin haka,ba,,,

    Yajuyo inda mustapha yake tsaye yace tana ina,,,,,

   Sim sim na shigo falon hade da sallamata sai faduwar da gabana ya,keyi, don dama jira kawai nakeyi akirani ,asallameni,,daga aikin gidan,,,,, ko dayake nasan cewa mun yi aiki yadda yakamata don ni banga abin laifi aciki ba,,,

  Amma sai naga almustapha da wanan matar duk sun tsorata, nima shiyasa hankalina ya daga 

Don ina gudun inyi sanadin barin aikinta,,,,

   Gyafe guda,nadan rakube a falon,kamar zan shige a,kasa, don ladabi,,,

    Saudaya yadan daga ido ya kalleni yakauda kai,, azuciyan shi ya jita kamar wata ta kirki wani lokaci kuma ta iya shedan ci,,,,

   Cikin kakausar murya yace min,, Keda wa kuka hada abincin gidan nan ,,, nikan nace masa Rugaiyya ce,

  Da sauri ya kalli inda almustpha yake tsaye kamar mai rokon gafara,,,,,,, 

   Dukan su shida almustapha,,sukace Rugaiyya nace eh,,,,,

    Nai masu bayanita kamar yadda naiwa matar nan,,,

   Ita ma,Rugaiyyar,kiranta akayi har matan nan mai abinci,,,,,,, saida yadan yi nazarin mu sanan yafara magana cikin muryan shi mai taush,,,,,

    Yai muna godiyan aikin da mukayi masa na,yau tunda, har bakin shi sun yaba, da aikin mu,,,,,,

    Sai kuma yabar zancen yafara wani

     Ida yace muna mahaifan shi zasuzo daga Nigeria yana son don Allah mu basu kulawa ta musan man dakuma girmamawa, duk wani bukatar su da dawainiyar su mu taimaka masa dashi don shi ba mai zama bane,,,,,,,

    Yakawo kyauta da yawa ba duk, wanda ke gidan, 

   Kyautar ta girgiza duk wani saboda kusan albashin mutum kashi biyu ,,,,,

   yaba kowa agidan yace alherin da yasamo gurin tafiyar dayine, shi ne muma yabamu,mulasa musa mai albarka arayuwar,,shi,,,,,,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎

  🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 13:43] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈. 

         👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                 3⃣3⃣ 

                     BY

 🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

 🐎HUGUMA GROUP🐎


    Duniya saida kudi Lahira kuma saida hali na alheri,, Allah yasa mu dace,,,

   

 Gaisuwa da Jinjina ga Yan Huguma group tare da sauran masoyana na takari novel,,,

 

  Almost true life story,,,,,   Jirgin air max ta sauke bakin Nigeria tun karfe hudun asubahi,,

   Sannu a hankali mutocin da suka ,, kwaso su daga airport suke tafiya dawo,wa gida,

  Daga gurin taron bakin Nigeria, motoci ukune jere na farko driver ke janye da wasu  maza su biyu,,, Saita biyun Ahmad ke jan motar,babanshi ne da hjy mama sai tsohuwa,aciki,,,,motar ta uku kuma Wasu yan matane su biyu sai driver, da,ke jan su,,,,,

   Mu,na, gidan  dama tunda safe duk wanin abinda yakamata muyi don taron bakin, munyi,,, saboda tunda muka zo bamu zauna ba , Don saboda aiki da yai muna yawa, 

  ,,,Aikin yau, ba kadan bane  don yawa gare shi sosai,

   abincine da abinsha kala kala muka hada,irin ta taron baki na musan man,,,,,

    

   Cike da doki nake son sai naga wa,"yan nan bakin da kowa ke ta rawar kafa saboda da zuwan su har mai gidan, namu,da muke ma aiki, 

    Wanda ko kallo mutum bai ishe shi ba da wuya kaji yana magana dawani agidan inyazo dan dama dama Almustapha ko kuma bawani dogon magana bane,,,,,,,

  Duk girman gidan nan saida, hayaniyar isowar bakin,mu duk ya ruda gidan da murna da kuma dararakun su, irin na yaushe rabo,,,,,

   Suna shigowa muka dinga kaimasu gaisuwa ,,, suna ansa muna da larabci don ina ganin basu ga almar mun iya hausa ba saboda yanayin shigar,mu,,,,

  Wata yar tsohuwa daga cikin su tafi dauke min hankali saboda yadda naga kowa na haba,haba da ita ,,,,

   Almustapha yasa aka kwashe masu kayan su zuwa cikin dakunar gidan


    Abinci muka gabatar masu dashi suna gamawa,sai wurin kwana,muka kai kowan su yaga inda zai sauka,, agidan mu mata mu muka taimaka wa su matan zuwa masaukin su,,,,,,,

   Duk wanan dawainiyar da mukeyi, da baki maigidan yana zaune a gaban wani desktop din shi dake falon kamar bashi keda bakin ba,,, yana kallon movement din kowa har mu yan aiki ,, amma azahiri zakadauka aiki yakeyi daga zaunen,,,,

    Ba abinda da yafi bani sha,awa kamar yar tsohuwar da aka so da ita ,, wace zata iya kai shekara kusan,,, tamanin da hayi ,aduniyar kila, 

   Duk abinda takeyi hankalina yana gurin ta duk wani motsin da zatayi sha,awa yake bani wlh,,, gata da fada irin na tsofi,,,, 

    Zuwa nayi nakira Rugaiyya don tazo, ita,ma taga yar tsohuwar mai ko,kari, kamila mai yawan ibada,, ,,,,,

    Muka  dan labe gefen labule muna lekenta 

   Zaune take a dakin da akai mata masauki agidan da ,alama tasbihi takeyi a zaunen don bakinta nata motsi ga tasbaha a hannu ta,,,,

   muna nan labe bayan dan labulen da muke leken ta,,,Dan hira mukeyi,,,. muna dariya a hankali komai nata yana burgeni 

   Nace dama ace wanan  tsohuwar kakatace,,,wlh Rugaiyya da naji dadi so sai naso ace nima ina da yan uwa haka har da kaka,,,, da kullun ina tare da abina ina bata kulawa,,,


    

    Koda ban waiga ba,naji kamshin turaren shi ya bure muna hancin mun hakan ya nuna muna cewa maigidan ya gurin,da muke labe,,,,,,

    Da sauri na sake labulen da na dan hankade muna leke.

  Nayo baya daniyar gudu sai kawai na,ji na yi karo da kafa, shi,,,

  Ahankali, nadago kaina nakai dibana gare shi,,, fuskan shi a daure murtun,,, 

    Muka dan zagaya ta bayan shu muka wuce sim sim da mu,,,

   A,she duk abin da muke fadi yana tsaye bayan mu hannayen shi cikin aljuhun wandon shi,,, ido ya zubu muna, har muka bace mai,,,,,,


   Bayan su yabi da kallon mamaki ,, azuciyar shi yace may wa,"yan nan yaran ke nufi ,,,,

    Suna nufin basu da kowa ko may ,, lalai sai na samu time inji labarin su,,, yadan leka don yaga may muke kallo wurin tsohuwa,, yaga ai zaune take tana ibada,,,

    Murmushi yayi yace mai ran karfe ke nan hajiya tsohuwa ,,,,

    Ba ita ba ba mai iyawa da hjy mama,,

    Don yasan ko wanan zuwan da akayi da ita don shine tazo,,

   Tunda Abba bai fada mai da ita za,azo bada fari,,,,


    Saboda aiki yau mun makara sosai bamuje gida da wuri ba,,,

   Almustapha yasa  driver ya kai mu gida , don dare yayi. Ana iya kama mu,,,

   

    A , hankali muka shiga gidan namu gami da sallama, 

   Mun iske kowa na harkan gaban shi , takalmana tomy na cire na wurgat gefen da muke aje takalmi, 

    Sai niliyata danake warware a hankali, don indan ji iska ajikina , dagani sai yar wando da riga da suka dan matse min jiki kamar wata diyar larabawa kaina dana kule da ribon shima na dan walwale shi don in samu saida agida,,,,

   Nakai kallona ga sukaina ina tambayar ta hajiya fa,,

    Tace min ita ma bata ganta ba tunda tadawo, ido waje nake kallon Sukaina Don ai wanan rashin imani ne,,,,, aiko banza hajiyace silar zuwan mu nan,,,

   Inga mutunci aidole mu mutun ta,ta,,,,,


   Daki na fada da sauri na,,,

   Kwance  na samu,hajiya  jiki ba kwari 

    Cikin tashin hankali nake tambayar ta ko tasha maganin ta,,, ban tsaya jin ansar taba nafita waje da sauri na,,,

     Tea na hada mata mai kauri sai ruwan dumi da na jona mata tai,wanka nabata maganin ta, sha,,,,,


    Tunda safe kuma na tashi na kara hada mata abin kari , nabata maganin ta,sha,,

    Nacewa Rugaiyya ta tafi,ni bazanje ba ,yau,,,,,

    Hajiya ce tace min in tafi ai taji sauki yau sosai,,,

   Hakana natafi badon raina yaso ba, don gaskiya naso in kula da hajiyan mu sosai,,,saboda tausayi take bani don ni har a raina kamar inna nake daukar ta,,,

  

     Muna isa tun da safen nan muka hada masu abin karyawa ,,,kamar irin na mutanen Nigeria mu,,,

    Bayan komai ya kam,mala mun jera masu a, dining table ,,,

   Daya daga cikin yan matan nan tafito tace muna, wai baza ta iya cin abincin mu ba, wai akwai warin tafarnuwa aciki da yawa,,,

     Duk da nasan cewa bamu sa tafarnuwa ba acikin girkin mu,,,

    Saboda wanan dattijuwar  matar da muke aiki tafada muna yan Nigeria basu son tafarnuwa don haka kada muyi masu girki da shi,,,

    Jiki ba kwari muka kwashi kayan da niyar mukara zuwa mu dafa wani,,,


   Muryan maigidan mukaji abayan mu ya na fada, muna cikin larabci mu ,maida komai inda yake mu wuce kuma kada mu dafa abinci rana dasu,,, 

   Zasu tafi haram masijid yin dawafi daga can zai su wuce asibiti da hjy mama,,,

    Yana ma matar da muke aiki tare bayani,,,


    Ya juya wurin yarinyar da yakira da mairo, idan abincin baiyi maki ba kina iya shiga kitchen ki dafa abinda kike so,,,

    Aikin dafa abinci sau biyu kawai nai alkawari dasu , ba,kowani lokaci suka ga dama suke aikin ,ba

    Amma in,kinga zaki iya biyan su hakin aikin da zasuyi maki sai su je suyi maki, wani irin wanda kike ra,ayi ko yafada cikin nuna serious,,,,,alamar ba wasa ga zancen shi,,, 

    Tsohuwan nan ce abaya shi,ta karbe zancen da cewa ai basu san darajan mutum ba su ,

    Sun dauka kowa za,su iya takawa don su na da kudin hakan ,,,

   Saboda irin rashin tarbiyan da ba,a , nuna masuba, agidan su,,,

   Kasan cewa agida yan aikin su kamar bayin su suke,,,

    Sabanin nan da komai  a,ka,ida akeyin shi,,,,


      Daidai lokacin na iso bakin taburin cin abincin ina kokarin taimaka ma tsohuwar don ta zauna,,,

    Plate nadauko mata ,sai kuma tambayar ta da nakeyi cikin hausa may za,a zuba mata,,,

   Kallon gefen da Ahmad yake tayi, tace mai,, kai nifa banjin larabcin da wanan yariyar ke min,,,

     Tsohuwa ai hausa take maki ita madin, inji Ahmad,,,

  Cewa tayi may zakici azuba maki,,,,

   Murmushi nadan yi kadan har fararen hakorana suka dan baiyana waje,,,bayan na zuba mata sai na bar dinning area din don in,cigaba da aikina dama don in,danji dumin tsohuwar naje kusa da ita,,, kalon mamaki yabini da shi ,,,,

    Ina wucewa naji tana fadin ita wanan min ma yar aiki ce hakan ,,,

    Bai bata ansa ba sai mairo ce tace ai tunda kika ganta tana aiki nan kema kin san yar aiki ce

    Wata kila anan aka haifeta , ma,,


    Dakin yar tsohuwar nan nashiga na gyara mata komai tsab kamar ba,a bata ba,,,

    Na kun na kayan kamshi ko ina gidan yadauki kamshi na musan man,,,

    Sai sanyin AC da ya karade ko ina na gidan,,,


     Ahmad ne yafito daki cikin shirin shi nafita, jallabiya yasa fara tas ma laushi da sulbi kan shi da yar karamar hula fara sol itama, sajen shi ya kwanta lub a fuskan shi kamar shiyayi kansa,,,


   Hannu shi rike da dan makulli motar shi,,,,

    A tsakiyar falon ya tsaya yana ba Almustapha umurnin kula da komai yadda ya kamata,,,

    Mahaifin shine suka fito tare da hajiya mama,, suma a cikin shirin su ,,,

    Tana wani yatsine yatsinen fuskanta kamar wacce gidan bai mata ba,,,

    Azuciyar ta kuwa sai mamaki takeyi da irin canjin da tagani ga Ahmad ,,, budi da arziki yataso ma yaro kamar shi yafi kowa iya karatu,,,

   Tasan duk yadda Alhaji yai mata rantsuwar cewa baida masaniyar komai gamay da,sana,ar da Ahmad din keyi,,,

      Ba wai ta yarda bane jira take yi kawai da su koma gida dole asan yadda za,ayi gaskiya,


     Tsohuwa ake jira tafito su tafi tace ita atabau baza taje ko ina ba ,, 

     Su tafi kawai don ita tagaji sai gobe zata fita,

     Haka suka tafi batare da ita ba,,,,

    Hakalin maigidan bai kwanta ba da barinta da akayi gida ,,, yasan dai da wata a zuciyar tsohuwa,,,,

    

     Suna wucewa nice tafarko dana fara zuwa wurinta ,,,

     Ina dan tambayar ta a hankali take bani ansa nace mata Nigeria akwai nisa ko tace min eh ,,,

   Kina son zuwa ne da sauri na bata ansa da eh

   Dariya tayi kawai don ita tana dauka ni haihuwar can ne,, bansan  Nigeria ba,,,

    Kafarta da naga tana dan shafawa almar ciwo nace mata ina zuwa ,,,,   

    Fita nayi zuwa zuwa wurin mama,mai aiki don naga tana yawan,shafa magani ciwon kafa akafar ta dana tanbaye ta sai tace min man zaki ne da na jimina take shafawa akafar,,

   Shina karbo nazo na shafa ma wanan tsohuwar nadinga yi mata masaj din kafar a,hankali ,,,,

 Kafin wani lokaci har barci mai nauyi yadauke ta ,narage mata karfin A,C ,,,naja kofa ,ahankali nafita,

    Saida tai barcin ta sosai ta tashi na hada mata ruwa maizafi tayi wanka tana fitowa nakawo mata abincin ta har daki ,,,,,,, 

    Miyar kaza da dankalin turawa sai su kabej da saurasu yanuna sosai dai yadda zata iya ci fresh milk a cup amma ba mai sanyi ba kware,,,

    Taji dadin wanan kulan da nai mata aranan so sai,,,

    Ahmad basu dawo gida ba saida  takwas na dare,,,,

     Alokacin kuma hankalina yakoma ga hajiya ina son in koma in diba jikin ta inji inda sauki,,,

   Gashi masu gidan basu dawo ba, kuma ban iya wu,cewa inbar tsohuwa ita kadai 

   Don jinta nakeyi kamar mun saba dadewa,,,

    Ita ko sai kallo na takeyi ina bata mamaki ,, azuciyar ta tace wanan yarinyar karama tasan yin komai ,,,

    Ga wa,"yan nan manyan yan matan da mama ta dauko ko ruwan shayi basu iya dafawa ba, injita,,, gashi kuma don samun wuri irin na mama ta nace sai anzo da su umurah ,,

Duk da tagane wayon zuwan da kayi dasu don Ahmad din,tane sabod,,,,,, ,   


🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 14:06] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈ 

        👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                   3⃣5⃣

                      BY

  

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


Recite Hassbunallahu wani,imal wakeel 450 every morning if possible pls,,,,,


    Soyayyata gare ku bai karewa yan uwa,,, Hannah Rabiu ,Maman xarah ,Ayheert, Precious Hindu, Miss Ayush, Maman Mu,Allim, Maijiddah Harazami, Anty Aynah ,Salamatu sale maina,  sai su big antys Anty mariya sb Anty Hafsat Yusuf,Anty Safiyà Abdullahi, da Maman Fareeda,,, all in Huguma groups novels fatan alheri gare ku kullun,,,,

 

Almost true life story,,,,
    Saida nagama da lalurar hajiyan mu tukun sanan na shirya zuwa gidan aiki,na cikin sauri da fargaba,,,,,, 

    Cikin sauri nake tafiya don nasan cewa yau kan na,makara  

   Almustapha mugu, yana iya korata ko yai min wani sabon wulakanci don naga almar baida imani sam,,,,, kawai dai nasan nikan yau, saidai, gyaran Allah kawai,,,,,

 Ahankali na tura get din don kada aji karar shigowo na,

     Ina bude get din gidan saina ga masu gidan a atsaye ana masu loading kayan su,

   Daidai wurin da ake parking motocin gidan,,,


    Karan bude get din danayi ,shiya yasa duk wanda ke wurin hankalishi, juyuwo, 

Lokaci guda kusan kowa ya kallo kofan shigowar, don aga ko waye mai shigowar,,,,

 Daga inda nake tsaye    A,laman gaisuwa nai masu daga nesa kadan,,,,,

   Sai naga Alhaji lawal zanna,ya kirani da hannu alamar inzo inda suke,,, ,,,

   A,hankali natako  Na,isa gurin , cikin ladabi,,,na kara gaishe su,

   Nuna min hjy tsohuwa yayi da hannu , yana min alamar intafi gurin ta,,,,,

    gurinata naje batare da nasan inda zamu ba,,

   Naga, kawai aka  bude min kofar mota da alamar inshiga babu wani mussu ko tsoro azuciya na,,,,,,,

    Nashiga,, saida na zauna da kyau na lura ashe, bani kadai ce za,a da ni ba har da 

   Rugaiyya na acikin motar da mama mai abinci, kai kusan duk kan gidan sai mutane kadan aka bari ,,  ,,,

    

   Tafiya mukayi mai nisa sosai don ni azatona wani unguwa zamu,, sai kawai naga anata tafiya kawai mai nisa,,,,


Motar mu bai tsaya ko inna ba, sai birnin madina, akofar, wani gida hadade wanda in nace in tsaya fadin kyaun gidan da fasalin shi zanci lokaci,,,

    Kayan aka,dinga shiga da shi cikin gidan da muka zo,,

    Sai a,wanan lokacin natuna cewa tafiya mukayi fa ke nan kuma gashi ban fada ma hajiyan mu ba, wacce na bari cikin wani hali,,,,,

     Shiru nayi nadan lokaci nashiga damuwa har ban inya boye damuwar dana shiga,,,,,

    Jinayi an,dafani ta bayan kafada na,

   Ta jiyo dani a,hankali muna fuskantar juna,,,

    Rugaiyya ce,, tace nasan cewa kin shiga damuwa ne saboda rashin fada ma hajiyan mu da bamuyi zamu zo tafiya ba ko, 

  Na kada mata kai alamar eh,

   Kuma gata bata da lafiya,,, nasake ce mata eh

    Hannuna yana rike da nata take min wanan maganar, 

    Zan yi magana tadaga min hannuwan ta ,alamar inyi shiru,,

    Shirun nayi don bin umarnin ta, amma na bita da ido,,,

   Taci gaba da maganar ta, fadima ni maigidan mu ,

     sharif Ahmad yaiwa maganar tafiyan mu jiya,, zuwa nan garin madina inda na nuna mai cewa ai hajiya ta amince sosai da maganar har tana mai godiya,,,, 

    Ido waje nake kallon ta don mamaki, 

    Wanan karon nai magana nace ,,,

    Amma kinsan hajiya na bukatar mu don bata da lafiya, ko,,

    Tace mukuma zuwan munan yafi muna komai dadi fadima,,,,

   Ki kula fadima da yau,

    Tunda mukazo wanan kasar duk yawon da akeyi damu kin taba ganin ko jin ance muzo birnin madina inda Manzon Rahama yake, muyi ziyara,,

    Na girgiza kai a,hankali alamar aa, 

   tace to wanan damace Allah yabamu don muzo mu ziyarci ma,aiki Allah,mai rahama maijinkai,

    Jin hakan danayi munzo garin da Annabi yake sai naji zuciyana tayi min dadi sosai ,na manta da komai dakowa,

    sai ma naga may muke jira bamuje munyi ziyara ba,, tun yanzu,,,,,,,

     A,gidan, inda aka sauke mu

   Dakin mu guda ,da hajiya tsohuwa da mama mai aiki kamar yadda hajiya tsohuwar ta bukata ai mata , ,ta fison a,hadata damu don zata samu abokan hira,


     Saida mukayi wanka muka ci abinci, da aka shirya, muna kafin mu iso, garin,

   Don mun iske wani mai aiki agidan amma na miji ne,

    mushirya tsab saidai kayan da nazo dasu sune nakara sawa ajikina kasan cewa ban zo da kaya ba,,

    Rugaiyya ta jefo min wani dogon riga baki mai wasu ratsin duwatsu blue a hannun, shi sai dan gyalen da zan yane fuska na,,,

     Dayake mun san yadda ake shirin kafin kace haka mun fito tsab, da,mu,

   zakace ko mune ma diyan masu kudin,

    Ai muna fita falo mairo na ganin mu tace itama sai munyi mata dressing kamar irin ta mu ,,

   Hakan mukayi mata ita da yar uwar ta jamila,

    Tare muka fita zuwa masallacin Annabin Rahama, gaba dayan mu,, gidan,,

     Sai hjy mama dake gefe tana sham kamshin ta

 kamar,yadda takeyi kulun, 

Idan, ka kalli fuskanta babu dadin gani ,, bata dariya ko kadan ,

   Gata bakace wulk da ita dogowa karfafa, ga izza da tsiwa, da isa kamar wata yar masarautar kano,,

      Ashe haushin hjy tsohuwa hjy, mama,keyi,

    Don  tace sai anzo da "yan akin gidan makka , madina 

, Don may hjy zata dinga jawo yan aiki a jikin ta suna shiga mutane haka,,kamar yan gida,,,,,

  Ita sam bata yarda da wanan akidar ba ,,,


     Massalaci muka nufa gaba dayan mu gidan,

      sai dai duk wanan abin banga shariffudeen Ahmad  cikin mu ba, Almustapha, ne kawai cikin mu watau  ,,,Ahmad, baizo ba,,,

     Acikin masallaci, annabin rahama mukayi sallah la,asar tare da dandazon jama,an, dake cikin masallacin 

   Mutum zai dauka cewa ko lokacin aikin hajjine yayi,ne wanan irin cikan da akayi 

    Kai ubangiji Allah mun gode ma da kayi mu musulumai har muka samu wanan falalan nazuwa ziyarar manzon rahama,,,,,

   A haka Muma  mu,kabi sahun jama,a akayi sallah  jam,i, da mu,,,

     Muna idar da sallah a,cikin jam,i muka tashi in group zuwa wurin ziyaran ma,aikin Allah S,A,W,

    Munga jama,a ranan nan kamar duk birnin madina akatara acikin wurin,,,

     Duk wanan cikan da ritsin wurin ina makale da hannun hajiya tsohuwa gam a hannu na,,

    Abinda ya fado min a rai shine hiran hajiya laila da hajiyan mu a makkah,,

    Lokacin da ta dawo wani ziyara datazo madina suna hira ni kuma ina dakin ina jin su,,,

   Wanan hiran nasu yazo min acikin zuciyana kamar yanzu akayi shi,,

    Musalin da tayi nadinga bi saiko gashi cikin sauki mun iso gab da kofar shiga Rauda,,,,

     Da sallama muka shiga ciki ,,,, Wani irin sanyi kamshi da ni,imar da bamu taba jiba arayuwa shi muka ji agurin,,,

    Mukayi sallah nafila raka,a biyu  dai saitin green carpet  din da ke seti da kabarin annabin mu,, muka kara gode ma Allah da Annabin shi,,,

   Mundan jima muna addu,a ,mun gaida masoya kuma sahabban annabi da suke wurin tare,,,

   A hankali naja hannu hajiya tsohuwa don mubar wurin kafin yan bagaladi suce muna exist,,,, exist exist muka fita ta wani kofa mafi kusa,,,,,,


    Wanan tafiyan yasa nasamu sausauci sosai gurin hajiya mama,,,

   Don dai tasan cewa mu yan gari ne sosai,,

     A,haka muka dinga ziyarar duk wanu guri da yadace mutafi na tarihi ,,,

    Duk inda zamu ina tare da hjy tsohuwa nazama kamar nice idonta,,

   Mun saba dasu mairo sosai don muna kaisu sayayya kayan English wear masu kyau,,

    Mukan fita tare muyi ta daukan photo tare dasu,,

   Alhaji lawal zannah yabamu kudi tare da su mairo da jamila ,kowa yaje yasai abinda yake so kafin mu koma makkah,,

    Cikin dare Sheriff din mu ya sauka birnin madina daga Riyadh,, ashe yaje wani aikine can company nisu na Riyadh,,

    Yau kuma yabiyo jirgi don akwai likitan da zasu gana dashi da Alhajin su gobe da safe,,,

    Zuwa jibi mu koma makkah,,,,

   

     Wani shago muka shiga mukayi sayayya sosai don su kusan komai a madina suka siya wai ance masu yafi kaya Qualities 

    Hjy tsohuwa ma na sai mata kaya sosai a wanan shagon 

    Dazamu fita muka sai kayan motsa baki da na shaye shayen gwangwani.

    Adakin mu mukayi bajabaja da kaya zaki kala kala saura nasawa hajiya mu cikin kayan ta nace takai tsaraba gida.

    

   Saida muka gama komai su har sunyi wanka sun kwanta natashi ina gyaran wurin da muka bata da ciye,ciyen da mukayi,, marana naji yadaure min 

    Da kyat na iya,daga kafa ta daga inda nake tsaye,,,

   Sainaji yadan lafa min,,

    Nacigaba da aikin da nakeyi,,,

   Ciwon sai gaba gaba nakejin yana min,,,

    Barci yadan daukeni aiko nafarka gigice ina wani irin kugi da nishi mai karfi,,,,

   Cikin barci hjy da Rugaiyya suka farka a razane,,,

    Amai nakama shegawa ga mara na ya daure tam,,,,

    Kawai ban san lokacin da nafara mulmula akasa ba kamar macijiya,

     Ga amai ina yi,,,,

      Rugaiyya tasa ihu saboda rudewa, da firgita don duk iya zaman mu tare ban taba irin wanan ciwon ba,,,

  Abinda zan iya tuna wa shine hjy ke tambayana may yasa mayni,,

    I,hun da sukeyi yasa kowa fitowa acikin firgice,,

     Suna tambayar su make faruwa,

    Mairo ce ke fadin wanan yar karamar yar aikin nan ce zata mutu,,,

     Daidai lokacin sheriff din mu Ahmad yafito dakin shi cikin jallabiya mai ruwan milk mai budaden hannnu kamar banga,,,

     Cikin sauri yafada dakin shida mustapha da kowa yafito dakin shi kusan lokaci guda

     Hjy mama tana zuwa taga halinda nake ciki sai ta fara fada wai ai ga irinta nan anjawo wa mutane magana,

    Inyanzu na mutu a hannusu dole hukuma ta kamasu ta tuhumay su,,

    Zataci gaba Alhaji lawal zannah yadaga mata hannu yace mata is ok pls,

   Kibar mu muji da abinda yafaru, inke bakisan kaddaraba mu munsani ,,

     Idan Allah yace a hannun mu zata mutu ba makawa sai ta mutu agurin mu,,,

   Kingaki yadda da kaddara shine cikar imani,

     Fatan mu Allah yabata lafiya, dole tai shiru badon taso ba,,,

 Sheriff din mu,   Yana diban yanayin da nake ciki yazaro wayan shi yakira wani likitan ma,aikatan,su, yai mai bayani,, likitan yace azo dani asibitin kawai, don zaifi,,,,,,,,,

 Almustapha dayaji karshen wayan ya yunkura zai daukeni 

    Wani tsawa Sheriff Ahmad yabugamai cikin kaukausar murya,,

    Saida kowa dake falon yakallo shi cikin firgici,,,

    Hannu laulausar rigan dake jikinshi ya gyara wuri guda,,,

    Dauka daya yai min sai gani kamar 4month baby a hannu shi,

   Cikin sauri yake tafiya abayan mota yasani,

     Shike jan motar yanayi yana waigen bayan shi ,don yaga yanayin da nake ciki,,,,

 Sultan Abdullarahaman, specialist hospital ya nufa dani,,,,

Muna zuwa    Wani kati yaciro cikin aljihun shi yamika ma wani balarabe da ke gaban wata computer,,,

 Saida yasa katin yadago ido yakalli Ahmad da,kyau sai kira cikin asibitin akazo da keken daukar mara lafiya aka daukeni zuwa ciki sai wani irin kugi nake yi,,,, 

     Likitoci uku ke kaina duk abinda yakamata suyi min suyi,

    Sundauki dan lokaci sanan suka fito,,,,,,,

     Babban likitan yakira  Sheriff Ahmad zuwa office din shi don jin bayanin matsalata,

     Rugaiyya tana bayan shi hankali tashe,,

    Bayan yan rubutun da yayi sai yakalli Ahmad yace,

        Bawani matsala bane mai yawa,mungane cewa period ne zata,fara shi yazo mata ahaka,

    Kuma gaskiya irin hakan zai iya, jawo mata matsala nan gaba,,,,,

   Amma yanzu mun bata magani zamu barta nan

    har nan da kwana uku muga yadda maganin zaiyi mata aiki idan munga bai karbeta ba sai mu canza mata wani,maganin

         Tana yawan shan zaki wanda haka shima yabada gudun mawa wurin blocking din hanyar da jini zai fito mata,,,

   🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 14:12] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                  3⃣6⃣

                     BY

   🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎  Wadatar zuciya ya tabbata ga mutumin da akulun yake gode ma Allah akan kowacce baiwar da Allah yayi masa komai kankantarta ,kuma baya kai karan ubangiji Allah a, wurin wani halittansa.

   


Happy new year 1st muharram 1439AH

O ALLAH!

   Make it easy for us to utilise the year better than the last for achieving everlasting blessing in JANNAH Allahuma Ameen👏👏👏


Almost true life story


Saida likitocin suka gama yi min komai yadda ya kamata,, suka kaini dakin da za,a kwatar dani kamar yada sukayi bayani,,

    Kwance nake ina barci acikin   kwancir hankali,      

Ba kamar dazun da nake ta kugi ba,

     Sheriff din mu, Ahmad ne dakin sai Rugaiyya dake gefe guda tsaye cikin takura da tashin hankali, ,,

     Tana tunanen zuwan da mukayi batare da sanin hajiyan mu ba,,,,,

Jin muryan sheriff Ahmad, datayi yadawo da ita cikin hankalinta,,

    Batare da ya kalleta ba yace,

   Ina iyayen wanan yarinyar suke,,,

   Jin wanan tanbayan yasa Rugaiyya yin hawaye,

    Gefen navain dinta tasa tana goge hawayen da ke bin, fuskanta ,a hankali,

   Jin shurun da yayi yasa shi dan waigota a hankali don yaga ko tana jin tambayar da yai mata,,,,,

    Ga mamakin shi sai yaga hawaye take gogewa, ma,ana tambayar yai mata ciwo ke nan,,,

  Dakin yai niyar bari, don yana ganin bata da niyar  bashi ansa

    Yana batun barin dakin don jin shirun yai yawa,

    Sai yaji muryanta tana cewa iyayen mu suna Nigeria,,

    Nigeria ya kara nanata sunan,,

   Wayazo daku nan,kasan sanan may yakawo ku,,, to,,

  Rugaiyya bata boye,mai komai ba tabashi labarin tunzowan mu gurin hajiya

  Har zowan damu, saudiya ,duk ta, bashi labarin mu, tun farkon har zuwa lokacin da muka fara aiki a gidan shi,,,,,

    Shirun dataji yayi shiyasa ta dan daga kanta kadan ta dube shi,

    Sai taga tunane yakeyi shima din,,,

   Abinda yafado mai arai tunda ta fara bashi labari shine irin son kudin da mutanen yazu keda shi wanda har zaisa asake yarinya kamar wanan har wata kasar 

     Wai zuwa neman kudi diya mace ai ba abin yin sakaci bane,atarbiyanta,

    Yatuna lokacin da yazo karatu farko akasar saudiya akayi case da wasu mutanen kasar Cameron,,,

    Inda wani yazo da yara maza matasa yasa aka sare ma wasun su hannu,saboda su dinga bara suna samo mashi kudi,,,

    Wanda yin hakan ba bisa ka,ida ba guda daga cikin yaran yasamu matsala har takai ga ankai shi asibiti.

    Nan akaita bincike har aka gano gaskiyar maganar,,,

   Tun wanan lokacin yatsani duk wani mai irin wanan halin na bauta,,da yara kanani,,,

   Wanda akasari mutanen mu bakaken fata ke wanan dabi ar,

    Sam bai son yaga irin wa,yan nan masu wulakanta kasu da sunan neman kudi,,,

   koda a,hanyane don abin kunyane ace mu mukafi kowa wulakantar da kai akasa mai tsarki,,,

   Zuciyan shi namai kuna yabar asibitin don zuwa gida saboda gari ya soma wayewa sosai,,

   Gashi kuma zai kai Alhajin shi ganin likitan shi dake nan zaune cikin birnin madinan, wanda saboda ganin likitan yazo garin dama dashi da hjy mama,,,,,


   Saboda samun saukin dana danyi ban farka ba daga barcin,, barcinake yi hankali kwance, sai Rugaiyya dake gefe guda zaune,

     Tunda na kwanta barci ban farka ba har kusan  awa bakwai , ina ta barcin saboda irin alluran da akaimin don in huta,

    Sheriff din mu zuwan shi biyu ban farka ba,,,,

 

     Sanu a,hankali, nadan motsa kadan ,,

   a,hankali nakara,motsawa,duk jikina ban jin karfin sa,saboda yai min wani, nauyi,,nakara gyara kwanci na,,,,,

    Saidai idona arufe yake har lokacin,,,,,

    Muryan Rugaiyya naji tana min sannu da jiki tana dan gyara min kwanciyar danayi,,,,,

    

   A, hankali na bude idona , naga  Rugaiyya zaune a,saman wani kujeran roba blue, kalar na asibiti,, saina gane cewa a asibiti nake

    Kaina,na,dan gyara a,hankali, don inji dadin kwanci,,

   Hakan yabani damar yiwa dakin danake ciki kwance, kallon tsab,,,,,

    Turo kofan da akayi ne a hankali  muka,kai kallon mu ga kofar dakin gaba dayan mu don muga mai shigowa,dakin,,

    Subiyo ne suka shigo  dakin  sheriff din mu Ahmad, da almustapha,,,


    Hannu mustapha yana rike da kayan abinci, yazo gab da gadon da nake kwance ya aje kayan abincin saman wani dan drower dake gefen gadon majinyata,,, 

     Ina ganin almustapha sai na kauda kaina gefe guda batare da na kalli gefen, inda yake tsaye ba,, 

   Saboda ban manta da zafin marin da yai min ba a makkah, daga taimako sai mari,,,,

    shikuma sheriffudeen din mu,ya riko ledoji farare masu tambarin asibiti, guda uku a hannun shi,,,,,

   Magani ne acikin guda,

   Guda kuma kadan pad ne har laida hudu,,cikin ledar gudan,,,

    Sai su underwears quality masu kyau, 

   Ajewa yayi gefen inda  Rugayyai take,yana mata bayanin batare da ya kalli gefen da nake ba,,,,,

  Almustapha yabar dakin don ya lura ina fushi, dashi har yanzu gudun kada Sheriff din, mu yaji cewa ya mare ni shine yafita,,,,,

   Batare da ya kalle inda nake ba yacewa wa Rugaiyya ta ,tadani  zaune takaini bayi  ta,gyara min jikina takuma koya min yadda a,keyi idan ana period,,,,  

    Saboda ya fahinci ban san komai ba gamay da al,adan dana fara yi,,,,,,

     Saita bani  abinci inci indan nagama nurse  zata zo tabani magani,na insha,,,,

   Bai tsaya ba shima yafita dakin ,,,,, yana fita sai Rugaiyya ta kira suna na muna fuskantan July na,,,

   Nan dai, Rugaiyya ta koya min yadda zan gyara jikina dakuma abinda duk yakamata inyi in mace,na period,,,,

     Sai a lokacin na fahinci halin da nake ciki 

    Wani irin kunya da nauyi yakamani sosai saboda zuciya ta ta raya min kowa agidan yasan abinda nake ciki kenan,,

     Nazauna bakin gadon da nake naci gaba da tunane watau ashe irin abinda su sukaina da mari kai har ma da antyna Rugaiyya sukeyi kenan nake cewa suna sakaci da ibadan su,,,

     Yau nima gashi yazo gareni 

   Kunya ne yakamani so sai don duk gidan kowa yana min kallon nasan wani abu ke nan,,,

    Ban san lokacin da wani hawaye masu zafi suka sulalo a fuska na ba,,

     Natuna da inna na da yan uwa na,,, a wanan lokacin ,

   Azuciyana nace idan Allah yayi komawa wata gida inna taga ina wanan abin nasan tabas zata zargeni dayin wani mugun abinda ba daidai ba,,,,

    Wanda ninasan cewa ina iya kokarina wajen kula da mutuncina da inna tace min inkula dashi lokacin da zanbar gida,,,,, 

   Acikin tunanen naje bayi nayi duk yadda tace min inyi nagama nadawo,,,

     Muryan Rugaiyya naji tana cewa kici abinci fadima za,abaki maganin ki kisha,,

   Dataga kuka nakeyi shine tashiga rarashina tana fada min cewa ai bakomai bane duk macen da takai lokacin yi batayi ba to tabbas wanan mace bata da lafiya ne,,,

    Hakadai taita kwantar min da hankali har nadan sake jikina na dan ci abinci,,,,

    Tundaga wanan lokacin banyarda mu hada ido da sheriff din mu Ahmad sam don wani irin nauyin shi da kunya  nake ji,,saboda yasan lalurar da nake ciki,,,,

    Abinda ban sani ba ashe ba wanda yasan ko may yasamay ni,agidan 

    Don yasan cewa wanan wani sirine mai nauyi ba,abinda kowa zai sani bane,,,,

   Daya koma gida kuma ce masu yayi ai zaki nasha da yawa shiya ja min ciwon ciki,,

   Hjy tsohuwa ta nuna mairo da ido tace wanan ja,irar yarinyar tasa su shan shi jiya saida nai masu magana akan kada su sha tarin alawal danaga sun sayo

  Amma basu ji ba, saida suka sha abin su,,

   Yanzu gashi kin jawa yarinya wahala,, saboda ke kin saba da sha tun a,gida

   Mairo tashi , tashige daki tana magana ciki,ciki hjy tace ja,ira fito waje mana ki fada inkin isa,,,,

    Hjy mama da takaici duk ya ci ta azuciyan ta,,,ko magana bata samu yi, ba don dama bataso azo da hjy tsohuwa ba wanan tafiyan 

    Ta,sone su zo su, kadai da ita da Alhaji da yan matan da take riko, kawai 

    Saiga hjy tsohuwa ta tubure masu akan sai tazo ta ga dan lelenta Ahmad,,,

  Kuma duk ta gane nufin hjyn waidon kada suzo su cinye ma Ahmad kudin shi,,,

   Tunda anki bari mamanshi tazo da yan uwan shi, shine kulun korafin hjy tsohuwa,,

,,,,,

     Nasamu sauki sosai don inka ganni bazakace nice mai rashin kafiyan ba,,

    Saboda duk yadda ake kula da mutum nasamu kula daga wayan nan mutanen kirkin masu arziki da sanin ya kamata,,,

    Sun maidani tankar yar uwan su ta jini,,,,,,

      Ashe bell din company da sherrifudeen din mu ke aiki su ne zasu biya duk kudin da aka caje ni a asibitin,,,,,,

   Lokacin da za sallamana yayi ,

    Aka sallamay ni nadawo gida,,, 

    Hatta Alhaji lawal zannah yayi farin ciki da dawowana, saboda ya nuna muna farin cikin shi fili da dawo na,,,,,

  Hajiya tsohuwa taimin fadan cewa in kula da lafiyan jikina in,daina shan zaki tunda gashi saboda zakin da mukasha har saida nayi ciwon ciki kamar zan rasa raina,,

    Acikin zuciyar mu nida Rugaiyya muka gane cewa sheriff din mu bai fada masu ko may yasamay ni ba har nai ciwo, watau ya boye min sirina,,,,,,

    Gefen dayake na,kalla nakoyi sa,a muka hada ido dashi cikin kunya da alamar ko in kula anashi bangaren kowan mu ya,kauda idon shi ga,dan uwa,,,,

     Washe gari da safe jinin ya tsaya min banga komai,tun da,daren har zuwa, da safe yau,,,,,

    Nasamu Rugaiyya a kitchen tana aikin abin karyawan mu na,fada mata, 

   Tadan yi murmushi ta dafani tace kwana uku ke nan zaki dinga yi fadima, 

    Aiko kinyi sa,a,,,,

    Taimin bayanin yadda zan tsarkake kaina bayan nagama jini,,
  Mun shirya komai duk kayan mu anyi parking,

    zamu koma makka zuwa marance yau insha Allah

   Dama rashin lafiya na yasa suka kai har wanan lokacin,basu koma ba,,,,,

     Hjy tsohuwa tace min sai na kaita tayi ziyarar ban kwana a Rauda,,

   Cikin shirin mu nida ita muka fito don mu samu motar da zata kai mu massalacin,,,,,

      Akofar gidan namu muka hadu da sheriff din mu Ahmad ,

     Da baban shi Alhaji lawal da hjy mama,

   Ido suka bimu dashi almar tanbaya ina zamu a fuskan su,,tunda sun san cewa yau za,a wuce,,

   Hjy tafada masu zan kaita ziyara ne kafin mutafi tana son tayi ziyarar bankwana a Rauda,

    Wani irin mugun kallo sheriff din mu yai min saida na tsargu da wanan kallon

   Kayan dake hannushi yamiko min alamar in kai mai ciki,gida,,

   Lokacin da nazo ansan kayan sai ya sausauta, muryan shi,,

    Yake ce min cikin larabci nida banda tsarki shiga massalaci shine zan bi hjy zuwa massalaci, 

    Saida naji kamar in,dauke wuta saboda kunya,,,

    Akunyace idona akasa nace mai nayi tsarki yau insha Allah don har nayi sallah asubah,,,

   Cikin rashin yadda yasa yashiga ciki don ya tambayi Rugaiyya,,,,,

🐎 ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 14:14] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                 3⃣7⃣

                    BY

🐎ZAINAB IDRIS

 MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎 Cikakkiyar nutsuwa da wadatar Ruhi ya tabbata ga mutumin da tunanen laifukansa ya hana shi hangen laifin wani,,,,,   Masoya na asali ko yaushe Maman Nasiba, Mamam Ayman, Sahura Ismaeel ,Anty Batu,ul, sister ,Zainab Ibrahim ,Maman yahy musa ,Anty Hadiza, Ibrahim, maman Rufaida,Anty mariya sb da Anty hafsat yusuf

   Fatan Alheri gare ku da karewa lfy da duniya,,, tare da duk sauran yan huguma group👏👏👏👏Almost true life storAllah yadawo da mu makkah lafiya,  sai dai tafiyan  marance, mukaiyi sai,cikin dare muka iso garin lokacin duhu yayi sosai,

    Saboda tafiyan na marance ne kuma ba gudu  mu,kekayi,ba, tafiya ce ta hankali kwance,,,,

     Saboda haka agidan sheriff din mu muka sauka da muka iso, dole, a nan zamu  kwana da su,,,, 

    Sam ban so hakan ba na so a,ce muntafi gidan kodan inga hajiyan mu,, wace na bari ba lafiya,,,

    Dakin hjy tsohuwa muka kwana kamar yadda ta bukata,

     ,tsohuwa mai albarka ga sanin darajan dan adam,,,


    Mun samu gidan na sheriff din mu, ba laifi an gyara ko ina, tsab,

     duk da munyi tafiyan kwana biyu,,,

   amma wa yanda akabari gadin gidan sunyi kokarin ,sosai komai neat muka samay shi kamar akwai mutane,,,

     Don haka bamu sha wani wahala ba gurin gyarawa gidan da muka iso,,,,,

 Yau,   Saura kwana uku bakin mu, su koma gida, Nigeria, shiri kawai suke tayi, kowa ana mai parking din kayan shi,,,

    Tun da muka,iso na so mutafi gida a wanan lokaci, don ina ganin mun shigo garin makka sai naji ina son mutafi ,,

 saboda hankalina yana wurin hajiyan mu,

   Amma   Hakan bai samu ba don shirin tafiyan da ake tayi,,na bakin mu , 

    Wanda agaskiya banso rabuwa da su ba musan man hjy tsohuwa,,,,

    Ga jamila da mairo sun sani gaba sai na kaisu shagon,, Top ten sun sawo kaya let's one,,

      Dole a haka nadaure na raka su,shagon Top ten din  ,,dake kan hanya sharmansoor,, naso ace natafi gida tunda safe wlh,,

   Muna shiga shagon naga duk sun rude sun ma rasa wanda zasu zaba ,aciki,

    Magana nayi da walk services na shagon nace yanuna muna inda zamu zabi kaya na kware , 

    Sunyi sayayya so sai agurin 

   Kudin da tso huwa tabani in kara mata kaya itama na sawo mata abubuwa masu kyau da ma,ana,,,,

   Saida kusan duk sayayyan ta na yan mata ne ita ma,,, sai kuma jallabiyan maza masu kyau da sayo mata,,,

    Muka koso kayan mu niki niki muka dawo gida dashi,,,

    Ko ,da muka dawo,gida, duk yadda naso nabar gidan kafin dare yayi hakan bai samu ba gareni

      Don,hjy tsohuwa tace sai nakaita tayi dawafin ban kwana, a Ka,aba,,,,,

   Sai dare muka dawo kuma cikin daren nan nabiyo hanya ni,kadai saboda Rugaiyya tace baza tabi hanya ba cikin dare don kada,,,yan, bagaladi su,kamata,

  Mutane jefi, jina   ne a unguwar tamu,, 

    Duk da mutane sun fara shigewa gida saboda dare daya dan soma yi,, 

    Hakan bai hana wasu makwabtan mu su gane ni ba,,,

    Wata makwabciyar mu ne anace da ita,lamilami ta fara ganina, tace min fadima ce nace eh,,,

   Yo ance muna kun gudu kunbar hajjiya mana,, 

   Ban,bata ansa ba nawuce cikin gidan mu kai,tsaye,,,,

    Su ,Sukaina ne zaune suna dan ciye ciyen su sai Yumma da ke wanki a gefen famfo,

     Ido suka bini dashi suna mamaki ina nafito cikin wanan daren , haka, 

   Don kusan sati kenan ana cigiyar mu agari,

   Don, inda duk san,sanin takari yake, anbada cigiyar mu,,,,, saboda suna zaton mun gudune munbar hjy wanda yin haka yana jawo takari irin mu,kanana matsala,

   Don da mutun ya gudu yabar uban gidan shi gara yan bagaladi su kama ka,,,

  Ana cikin kururuwan mun gudu nida Rugaiyya 

    Sai gani nadawo gida hankali kwance abina, batare da alamar wani tashin hankali ba,,,

   Ban tsaya ta kansu ba don nagane nufin su,

    dakin hajiyan mu na fada kai tsaye,,

    Kwance take cikin wani irin mugun yanayi wanda ko kai  waye dole ta baka tausayi,,,,

   bata iya dagawa daga kwance, da take,,

    A,firgice nanufi inda  take kwance, na rugumay ta, ina kuka

     Ina,cewa hajiya may yasa may ki haka kika zama haka cikin lokaci guda,,,

  Ina mai,daga muryana, Cikin kukan nake cewa duk a rasa wanda zai kaiki asibiti sai abarki haka,,,,

     Yumma ce ta fado dakin tana cewa fadima ai na sayo mata yan kwayo yi na sha kuma ina bata abinci,

  Ko yumma bata fadi ba,

     Dama nasan cewa ita kadai ce zata iya dan kula da hajiya, cikin su,,,,

    Dan sauran hajiya bata da wani daraja a idon su yanzu ,

    Saboda sun girma kuma idon su ya bude,

      Su anasu wautan suna ganin cewa hakan da sukeyi ma hajiyan  shine daidai saboda ai itace tafara cutar mu tun a gida,, Nigeria,,,,,,,

    Sun kasa yarda da kaddara cewa Allah yariga yanufi sai mun zo,, munyi wanan bautar koda da kafane sai munzo kasar saudiya munyi takari,tunda hakan na cikin destiny din mu,,,,,

      Na juya wurin yumma nace taci abinci kuwa tace min tunda rana ba kuma ba sosai ba,,,,

     Dama kudin da Alhaji lawal zannah yabamu a madina don muyi sayayya muma,,

    yana ajikina don haka fita nayi zuwa,

    wani shago can kasan mu inda ake saida kayan gasawa iri iri na ci da sha,,,

    Naje nadan siyo mata dan abinda nasan zata iya ci,,

    A cikin daren na gyarata tsab  tare da taimakon yumma, ,don su sauran ko kallo ban ishe su ba,

    nabata abinci taci tasha maganin da yumma ta sayo mata,,,,,

     Tana kwance    Gefen kafar ta nazo nadan zauna ,ina kokarin bude inda nasa kudi don in kidaya su.

   kudin wanda,ke cikin jikina ko zasu i,she mu zuwa asibiti gobe,,,

    Yumma kuma tana gefe tana, cin sauran abincin da hajiya ta rage,,

     Muryan hajiya naji kasa kasa tana cewa ina muka je kwana biyu bamu gida ina Rugaiyya,

    Ban boye mata ba nace mata madina mukaje ziyara tare da iyalin Sheriff din mu, da suka zo daga Nigeria,,,,,,

  Shiru tayi tunda  Maganar dama na dole ne

     daga hakan bata kara cewa komai ba,

Saidai ajiyar zuciyan danaji tayi ,ahankali, ta gyara kwancinta

     Dama tun da nake kirga kudin da ke ajikina dan zamu tafi asibiti da su da safe ,naga mari da sukaina suna min wani kallo, kasa kasa suna magana,,

     Nasan cewa suna iya sace kudin in, nai barci,,

   Aiko haka din ne, ina cikin barci, gefen hajiya kwance dama na faki idon su na canza ma kudin wuri,,

    Cikin barci naji ana lalabata caraf na rike mata hannu nace lafiya,mari ce

   Saicewa tayi wai tana bidan wani abune data aje daidai inda nake kwance,

   Duk da nagane nufinta sai,kawai, na,gyara mata don ta diba  abin,

    nikuma daga haka barcin da ban koma ba ke nan,,,

    Tashinayi na fara gyara muna gida da duk wani abu da yakamata muyi, amma suka yi don son kai,,,


     Tunda safe muka ziyarci asibiti da ni da hajiyan ,mu 

    Allah ya taimake ni muka ga likita da wuri saboda mun fito da wuri daga gida,,,,

     Bayan yan aune aunen da a,kayi wa hajiya aka gane cewa jininta ya hau sosai ,   kuma tana sakaci da shan maganin da likita ya dorata akai

  Don haka tana bukatar aimata wasu allurori har da karin ruwa, aciki,,,  

   Tafiya nake yi, a,hankali,

       Yan kudin da nazo dasu asibiti nake ta kirgawa saboda ina ganin cewa baza su ishe mu abinda ake bukatar yi ma hajiya, ba,,,

     Jinayi nayi karo da mutun agabana har yan kudi nawa suka zube kasa,

    Banko kalli wanda yasa nazubar da kudin kasa ba ,hankalina ya ga kudin magani,, kada iska yajamin su su rage yawa,,

    Duka wa mai shi yayi yana tayani kwashe kudin ,,,,,,

     Saida ya miko min kudin  na karshe ne da,yataya ni kwasa,,

     ,Sainaji kamshin turaren Sheriff din mu Ahmad,

     Da sauri kuma cikin mamaki hankalina, yadawo,nakai dibana gare shi, 

   Shidine kuwa ,shikuma daidai ,

   Lokacin yana mikewa tsaye daga tsugun nin da yayi don kwashe min kudin,,,,,

    Hjy tsohuwa tana a bayan shi tsaye da a,lamar bata jin dadin jikin ta,, ita ma,,

      Batare da yakalleni ba ya ja hannu hjy don suwuce zuwa wurin likita,,

     Sai alokacin hajiya ta ganni don dama batasan cewa nice ba,

    Tanbayana takeyi cikin mamaki ko ya akayi na biyo su asibitin tunda safe, wa ya fada min suna asibiti,, 

    Shiko sheriff din mu azuciyar shi cewa  yakeyi,

     wanan yar wahalan kuma ko may yakawo ta nan tunda safe yarinya kamar aljanna duk inda kabi zaka ganta,

     Can kuma yatuna kodai jinin nawa bai tsaya bane, shine nazo ganin likita,,,

    Muryana dayaji cikin hausana da ba daidai ba Ina fadawa hjy tsohuwa cewa nakawo hjy ta asibiti ne,,, saboda nadawo na samayta bata da lafiya sosai,,,  

     Saboda girmamawa da nuna kulawa sai naji bazan iya wucewa inbar su shida hjy tsohuwa ba

     Kodan irin so da kaunar da yar tsohuwar ke gwada min,,,

 kawai sai na  tsinci kaina da,bin,su abaya har zuwa office din likitan da zasu,,gani,

     Bayan anyi ma hajiya booking din likitan da zata gani, ,,, 

     An,yi komai  har a lokacin muna tare dasu sam na ma mance cewa da hajiyan mu muke, a,asibitin,,,

    Takardan maganin dake hannu ya buka ta ,,,

    Na bashi  yakarba yadan diba kadan 

Sai naga yawuce inda ake saida magani kai tsaye, batare da yai min magana ba,,,

   Maganin yasiyo min harda ledar ruwan da za,akara ma hajiyan mu,,

    Inda take ya buka  nakai shi,

   hajiya na zaune gefe ta wani, makure gefe, duk ta mokade kamar ba itace hajiya mai sharwali ba,,

  Koda mukaje,  Kallon banza naga  yai mata,

  Wanda saida na tsargu, sosai da irin kallon

     duk da tana cikin ciwo baisa ya tausaya mata ba,  saboda irin mugun halinta na cutar da kananin yara,da tayi batare da sanin iyayen su ba,,,

   Sai kawai naji banji dadin yadda naga yana kallon  hajiya ba, 

    Saboda aiko da nake tallaka kuma ,yar aiki shi ai, yakamata a mutunta min yan uwana nima,,, ,,,

    Sam ni bansan cewa Rugaiyya ta fada mai abinda ke tsakanin mu da hajiya ba.

    Tun,a madina

   Ko yanzu yasan cewa nice zan walaha shiyasa ya taimaka mata,,,

    Allah yataimake ni hajiyan mu tadan warwale sosai don duk ledojin ruwan da akasiya ta zuke su ajikinta

     Sai bayan kwana biyu aka sallah may mu daga asibitin 

    Taji sauki sosai wlh,,,

    Kusan kwana biyar nayi banje aiki ba, ina fama da hajiyan mu,,,

    Yau danaga taji sauki sosai nace mata ta kula da jiknta zanje wurin aiki don kada in yi laifi da yawa,,

      Gashi nadauki lokaci ban je ba ban kuma dauki permission ba,,,

   

        Saida na tunkari gidan sanan natuna cewa hajiya tsohuws sun wuce kila, 

      Gashi bamu samu yin bankwana cikin dadi ba ,

   Ina can asibiti da hajiyan mu

    

Ashe basu samu wucewa ba a lokacin don jikin hajiyan da likitan ta ya dan tsay da su,

      Ina shiga nanufi inda Rugaiyya na take aiki ,saboda mun kwana biyu bamu haduwa , ko ,agida  sau guda tasamu lokaci taje asibiti diba hajiya,,,

      Abincin da tagama nataya ta dauka zuwa babban falo don mu jera,

a saman table,

     Amma azuciya na ina mamakin yawan abincin da ta dafa, 

    Sam ban kawo cewa bakin mu suna nan ba,,

    Ina shiga falo naga su, mairo da jamila suna game tunda safe haka,

    Dakin hajiya tsofuwa na nufa don ina kewanta dama sosai 

     Dan shakuwar da mukayi kwana biyun nan yai yawa,,,

     Sheriff din mu ne zaune dakin tare da ita sai,dai fuskan shi da alamar ba, sauki amaganar da sukeyi,, da hajiyan fuskokin su a daure yake,,,

  Cikin sauri na juya zan koma waje,,,,,,,     


🐎 ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 14:14] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                    3⃣8⃣

                       BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

 


  Murna farin ciki da annashuwa, sun tabbata ga  duk wani mutumin kirkin da  tunanen, Hisabi ya hana shi tara dukiya ta hanyar haramu,,,,


   Gaisuwa da jinjina gaduk wanda ya fahinci ma,anar wanan littafin


   Almost true life story   Gefen hajiya tsohuwa nadan rusuna nagaishe ta cikin ladabi da biyayya,

    Zandaga in wuce take tambayana jikin hajiyar mu, inda take ce min taso zuwa ta dibata ,

    Saidai itama din likita yace tadan samu hutu wuri guda shiyasa bata zo ba,,,

     Sheriff din mu dake zaune gefe ya mike a  lokacin zai bar dakin

     Barin zancen namu tayi taci gaba da magana dashi ,

   Tace kadaiji abinda na fada maka, 

   Ka maida hankali kaje Nigeria ka diba ma haifiyar ka da yan uwan ka ,zama anan kashare kowa ba zai maka ba,

    Kasan cewa itama uwar ka tana da hakki akanka don tana bukatar ganin ka ,

Saidai don bata magana ne amma nasan cewa azuciyar ta bata jin dadi

    Sanan batun wa yan nan yan matan sam ban yarda da inkara hada zuri,a da yan uwan Amina ba 

    Yadda mahaifinka yake tauye haka akeso kaima a,tauye min ka ,

    Shiyasa ina jin cewa za,a kawo su nan don kazabi guda daga cikin su nace dani za,ayi wanan tafiyan sai naga yadda za,ai wanan hadin auren in ina da rai,,,,, 

    Kanshi yadan sosa kadan ya jingina jikin shi da bangon dakin hannayen shi na zube a aljihu kamar yadda yake yi,

     Yace haba hjy na fada maki ki kwantar da hankalin ki wanan abin ba zai yiyu ba sam nariga na fada ma ,Abba da kuma ita maman 

    Idan ma hadin zumunci suke so aiga su Suraj can da salis sun gimay ni kuma yan uwan su ne akai masu su su aura mana

     Hajiya tsohuwa da alama zancen yadan yi mata dadin ji,

    Don murmushi nagani a fuskanta,

  Daidai zai fita yace ma hjy Dama ina son in zo Nigeria saboda ummina, da yan uwa ,

Sai kuma malam mijin ummi ina son ganinshi sosai,,,

     To dadai yafi maka walhi 

   Inji hajiya tsohuwa ke fadin hakana

    Har yasa kafa guda zai bude labulen kofar takara ce mai , akula da kyautawa duk wanda ke da bukata in har da halin kyautatawan,, Saboda kyautata zumunci wani abu muhinmin a wurin Allah,,,

   Nasan kana yi ya kokarinka da yin aike,  to ka kara ka dinga kai kafar ka don yafi lada,,

    Kadinga ziyar da kula da lafiyan maihafiyar ka  da yan uwan ta,, 

    Sai kuma maihaifin ka wanda a,halin yanzu na bukatar ku, kaga yan uwan ka ba wanda yasan alkiblan su kuma uwar su bata son sam ayi zancen su ko kadan,,,

      Tana kara ce mai mahaifinka Amadu maihafinka

    Saboda yana bukatar kulawa da komai nashi yanzu,

     Wanan matar tashi sam ban yarda da ita ba,ko a,da, balle yanzu,,,,,

      

        Bayan fitar shi dakin  sai dan shiru yabiyo dakin nadan wani lokaci,

    Fadima nace na,am hajiya tace nagode maki kware Allah yai maki albarka,

     Kikara kula da kanki kinji saboda rayuwar wanan zamanin dace ne,,

    Kuskure kadan zai iya jefa rayuwanka cikin wani hali,,

     Hawaye nabin fuskana nace mata nagode,

     Takara cewa zan yiwa Amadu magana akan ku ku duk kanku,

    Saboda naji dadin zama da kowan ku,,,


     Washegari munaji muna gani su hajiya tsohuwa sukai muna na, baki,

    Sallama akeyi cikin bacin rai don anso rabuwa ba,

    Sunji dadin mu muma munji dadin su,

     Motocin su da yan rakiyan su yatashi zuwa birnin jidda don ta nan zasu tashi,,,,

    

       Tunda suka wuce sai nakoma wata iri banda kuzarin yin koma zuciyana baimin dadi ko kadan,

    Yadda nake aiki da yanzu na rage yi sosai,,

   Nafi yawan zama wurin tsuntayen gidan ,

     Sheriff din mu yanzu bai zama garin  sam saboda yana yawan busy 

    Tsakanin Saudiya da Dubai zuwa Nigeria,

    Akwai wani business da suka hada da Abu Abbdullah company da ke Dubai ,w

     Wanda shi sherrif din mu shine zai kula da wanan business din ta kasa shen biyu, idan har hakan yasa mu,,,

      Mukan ana mu bangaren rashin zaman shi bai damay nu ba sabodo muna samun kulawa sosai ,a,gidan,

    wanda takai yanzu har Yumma itama anan take aiki 

     Ana bamu abuwan bukata sosai bamu cikin wahala ko kadan bakamar da ba,, da muke yawon bara da kuma aiki gidaje da kamfanoni,mutane

    Kudin aiki mu kuma zar albarka,

     

      Hajiyan mu tana samun kulawa sosai daga gare mu yanzu,

    Ina yawan kaita ganin likitan ta cikin lokaci,

     Hjy laila kuma tana iya nata kokarin ita ma

     Yanzu mun kai kusan shekara biyar ko shidda a makka,

    Mun san ko ina agarin

  Indan ma gida zamu koma inajin da akwai kudin komawar mu,

    Saidai yin fasport din ne matsala gare mu,,

    Don shuganbani mu na takari suna da wani kungiya ta musan man wanda duk kusan wani movement din dan takari yana idon su,,,,

    Indai ba kama mutum akayi ba to basu yarda mutum ya bar kasan haka na kai tsaye,     Sauri nakeyi in isa gidan aikin namu saboda yau nadan tsaya gyara muna gida,

     Koda na isa nassmu kusan duk ma,aikatan gidan a kofar babban falon gidan ana masu jawabi,

   Sheriff din mu yazo ke nan yana gari,

    Ahankali na samu guri na tsaya don sauraren jawabin nashi,

    Daidai inda yake cewa lokacin zuwan mahajjata ya kusa yana son kafin lokacin  mun bar wanan gidan zuwa sabon gidan shi,

    Ida yake so akaro mai ma,aikata wa yanda zasu rika dafa abincin karama ana kaiwa kowani san sani na mahajjata,

    Yace wanan aikin kuma sabon Company su ne zata dauki nauyin yin hakan,,,,,

     Daka karshe yace muna zuwa karshen wanan watan kuma zamuyi sabuwar uwar daki ,wata,u ma,ana zaiyi aure zuwa nanda wasu yan kwanaki,

     Saidai duk a wurin nafi kowa farin ciki da wanan zancen danaji,

   Nan  danan na  natuna da maganar su da hajiya tsohuwa, na ranan,, 

   Bayan mun watse ana ta kus kus din batun auren sherriff din na mu

     Nidai nasan cewa koma wace,ce matar zatayi halin kware tunda sherriffudeen din mu shima yana da hali maikyau har yan uwan shi,,,

    

     Shirye shiryen aiyukan da za,ayi na Karama aketayi kusan duk abinda za,a bukata an tanada ko

  Kayan aiki ne irin  na,zamani kala,kala aka kawo,

    Ranan da wa,"yan da zasu diban aikin sukazo daga Dubai sai, yakasance sheriff din mu baya gari amma dai yana hanyar shi ta shigowa makkah daga Riyadh

    Baturen na masu  turanci duk sai akayi shiru don basu fahince shi, gashi Almustapha bai gida yadan fita,

     Nazo wucewa sai naga ana wanan draman natsaya ina kallon su

    Allah yasa nadan fahinci abinda baturen ke nufi,

    Da dan saurina na,isa,gurin na fara ba shi ansa a,hankali tambaya yake yi cewa nan ne gidan sheriff din mu, ko sai kuma yace sunyi waya yace mai yazo, nan  ya,jirashi yana kan hanyar shi ta zuwa makkah,

    Na,kaishi karamin falon danaga ana sauke baki, aciki musan man maza na bashi abinsha da dai duk taron da za,ayi wa bako,

     Har na juya zan wuce baturen yace min ni sister din mr LAWAL ne nace mai a,a ni maide ce mai aikin gida,

   Baiyar da ba don dariya yayi min kawai

   A,bangaren sheriff din mu kuwa yana can yanata kiran layin Almustapha amma bai dauka ba, saboda yabar wayan shi agida yadan je yadawo bazai dade ba,

    Ranshi duk a bace sanin cewa ba, wanda zai tari wanan bakon don bakon baijin larabci,,,,,,

     Sai dukan sitayarin motar shi yakeyi yana fadin Subbahanallah, saboda gani yakeyi indan tun zuwan mr Williams baisamu taro mai kyau ba ai zai iyacewa akwai matsala ga aikin,,,

    Bansan cewa mr Williams yana bayana ba lokacin da nafita zuwa wurin tsuntsaye na don in basu abinci karo na biyu,,,,,

     Jinshi kawai nayi yana wasa da Akun da ke cikin wani kejin golden ,

    Dariya yabani nan muka dinga shiriritan turanci da shi saboda ni nadauka bai gane may nake nufi ba,

    Amma na,ta,karkare sai watsa wanakeyi duk yadda na samu ashe kusan duk daidai nakeyi,

    Mu cikin dariya da mr Williams da ke kyokoyon Aku, kuturu, 

     Saiga Sheriff din mu gabana hannan shi sada kamat kulun a, aljihu 

    Musa,bi,a sukayi da mr Williams din suna dan dariya, 

   Inda yake bashi hakkurin dan matsalar delay din da akasa mu,

    Yace mai no no ai yasa mu taro mai kyau daga little sister yana nuna ni,

      Nikuma a lokacin ina dan gyara wurin da abincin tsuntaye yadan zube a kasa,

    Wani kallo yaimin da bansan kowace iri bace,

   Amma dai nasan cewa kallon nada wani ma,ana

   

  Tun lokacin in mr William  yazo to sai ya zagaya inda nake gurin tsuntaye na,,,

    Mundayi hira sosai don yana son yadda nake turanci  na yana sashi dariya,,

    

     Duk wani aune aune dazasu yi don gane inda zasu aje ma,adanan su, sunyi kuma anci nasara sosai,

   Dadina da ubangidan mu  watau sheriff din da ya samu alheri duk wanda ke tare dashi zai samu 

    Don haka mun samu kyauta so sai daga gareshi,.

  Saboda nasaran da suka samu wajen kafa company Abu Abdallah a saudiya,, da Nigeria,,

    Lokacin da mr Williams zai tafi saida yasa akakirani nadan yi mai turancina  nakuma kaishi wajen 'Aku suka dan yi hira dashi,, 

   Sheriff din mu da su Almustapha suna tsaye suna kallon shirmay mu,

   Da zai tafi yarike hannun sherrif din mu, yana masa magana gamaydani,


     Tun lokacin da mr Williams ya wuce da yan kwanaki shima, Sheriff din mu yayi tafiya zuwa Nigeria,

    Almustaphane ke fada wa mama mai abinci cewa sherrif yatafi wurin iyayen shi,

    Amma ba zai dade ba zai dawo don ankusa fara azumi,

    Yanzu da wuri nake wucewa gida saboda aiki yadan yi sauki yanzu,,

     Hajiyan mu tana kula da shan maganin ta yanzu sosai ina yawan kaita ganin likita time to time,

    


    Jirgin mangal air line yasauke bakin saudiya a Nigeria cikin su harda sheriff din mu ,

    A kano suka sauka saida ya kwana a wani hotel dake kusa da airport din,

    Tunda safe ya dauki drop sai Maiduguri ,  saida ya kusa kaiwa state din yai ma  wani,cousin brother din shi waya wanda ake kira da bashir, 

   Shida bashir suna, shiri sosai, duk da bashir din yadan girmay shi kadan amma nasu yazo daya sosai

    Kauyen hajiya tsohuwa ya wuce direct inda mahaifiyar shi take zaune tana aure, da yaranta,,,

    Bashir ne yazo yatare shi saboda zuwan bazata da yayi masu,

   Hjy taji dadin zuwan Ahmad duk ta rude ta rasa inda zata sa,shi 

     Saboda farin ciki ganishi da tayi,

   Lokacin da ya isa dare ya somayi don haka hutawa yayi kadan yadan ci dan abincin da hjy ta gabatar mai

   Wurin malam yatafi mijin mahafiyar shi, a cikin daren nan

 Don dama bashir ya sanar da malam din zuwan Ahmad din,,,,

    Bayan gaisuwa da yaushe rabo sai dan shiru ya biyo baya,,,

    Malam ne yadan yi gyaran murya yafara magana,

    Yace kamar yadda suke kiran shi Alhaji karami kwana da yawo 

   Murmushi yayi yace kuyi hakkuri malam abubuwan ne suka dan yi min yawa acan,

    haba Alhj karami ai ko,bakazo don kowa ba kazo don nan yar tsohuwar da kullun zancan ta bai wuce naka,

   Ayi hakkuri malam za,a dinga kulawa insha Allah,,


     Sheriff din mu ya fiddo da kudi masu yawa daga Aljihun shi ya dan kidaya yace ma malam wanan kudin malam don Allah ina so abaiwa bayin Allah suyiman saukar  Al,kur,ani maigirma da kuma sadaka ga mabukata dafatan Allah ya biya muna bukatun mu na Alheri,

   Muna son zamu yi wani company na global da zamu kawo daga kasar Arabs country ,wanda in hakan yai muna dadi zamu kawo wasu company na abincin kasa shen waje,,,,

    Sai kuma wanan abama duk wani dan uwan su, Yabi yasa min albarka,

    Yabi kaunar shi dake bi mai wacce malam ya haifa tare da Yaghana, mahaifiyar Ahmad,,

  Malam yai shiru nadan wani lokaci ,, yana kallon kudin 

    Can yace Alhaji Amadu,

 Ahmad yace na,am malam aikin may kakeyi a can har kasamu wanan kudin haka

    Duk da nasan cewa kaidin  yaro mai hali nagari tun kana karami amma saboda canji lokaci da yanayi nasan dan Adam na iya canza wa,,

   Ina fatan rade radin da matar mahaifinka keyi na cewa kana sa,na,ar saida miyagun koyoyi a kasa mai tsarki har ka tara dukiya mai yawa,

    Wanda jin hakan da mahaifiyar ka tayi har yasa tadan shiga cikin wani yanayi ita da hajiya tsohuwa

   Gabanshi ne yabada wani irin dam,

   Har yadinga jin wani irin jiri na shirin kwasan shi, Allah ya taimaka, zaune yake 

   Tunda Ahmad ya dukar da kai bai iya dagawa ba saboda bakin cikin irin kazafin da hjy mama tai mai,

   Bashir ne yaiwa malam bayani duk irin cigaban da yake samu acan da kuma wanan na yanzu da suke shirin yi a wanan kasar,,

  Dayake malam mutune mai wayeyen kai nanda nan yafahita yagane cewa sherin da hassadan kishirya uwace kawai,

   Duk da,dama riga  yasani don tun lokacin da matarshi  yaghana watau maihaiyar Ahmad taji wanan labarin daga bakin, matar, yayan nata,

    Wanda ke fada mata abinda hjy mama ke fadawa yan uwan mijinta da sukaje taron su da ,dawo wa umurah,

 Malam najin wanan zancen ya tashi cikin dare yai nafila 

   Har kusan sati guda yana nafila Alheri kawai yake gani gamay da Ahmad din 

   Tun lokacin zuciyar shi ta tabbatar mai da kuma amincewa da Ahmad din

     Ko wanan maganar yayi shine kawai don Ahmad din yakara gyara halinshi sama da na da,,,

    Bayan malam yakara mai nasiha da kuma jan kunen shi gamay da duniya dakuma mutanen duniya,,,

   Cikin gida akai mai iso gurin mahaifiyar shi,

   Bayan sun gaisa shiru yadan biyo baya kamar yadda suka saba tun yana karami bata iya sake jiki tayi wani dogon zance da shi,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 14:22] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                    3⃣9⃣

                     BY 

     🐎ZAINAB  MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎 Ya, zo sunnah ta ma,aikin Allah SAW cewa ka,nemi Gafaran dan Uwanka a Karshen ko Wacce Shekara, ina neman Gafaran Ki idan na Bata Miki ina Sane ko bana Sane ni na Yafe Maki in har kin Saba min,,,,


Anty Amal Anty safiya Anty mariya Anty billy galadanci, maman rufaida maman fareeda maman ikram sadiya maijjidda harazami Rahma  Anty Batu,ulu Duk ina maku fatan alheri tare da fatan gamawa lafiya da diniya,,,
  Almost true life story    Daga kai yayi a,hankali ya dan kalli mahaifyar tashi ,

   Sai kuma ya juya a,hankali ya dan kalli dakin da suke ciki, 

   Inda ya dan yi tunanen cewa a,nan take rayuwar ta, a cikin wanan dakn haka,

  ita da "ya," yan ta, yatuna irin gidajen da shi yake dasu yanzun haka a,saudiya,

    Tausayinta ne,yakama shi,  Don yasan cewa daidai da rana daya bata taba ronko shi komai ba na rayuwa,

 Sanan  gan shi ita da, shi i yasan cewa basu wani, morewa rayuwar su, nazaman da  da,mahaifiya ba sam,,,,,

    Saboda irin rayuwar da yatashi a ciki batare da mahaifiya shi,ba 

  Dan dama dama yadan samu kulawar , kaka, kadan.

    Yasan cewa Allah ne ke tare dashi kawai,ga al,amarin shi,,, ,, 


    Shirun ne yadanyi yawa ,adakin , sai yadan kau da shiru ,yake tambayar ta sister's din shi,

 Yaganah tadan gyara daurin lafayan ta ,

  A inda take zaune gefen gadon ta, a,takure cikin shigar, lafayan da ta nade duk jikinta da shi,

   Dakin sai kamshin turare ke tashi irin na yan maidugurin asali,,

     Indan ka ganta,A cikin kamala take maganar ta, tana bashi ansar cewa suna makaranta kwana amma, shekarar karshe suke, yanzu

   Nan da sati guda zasu kam,mala karatun su gaba daya, insha Allah,

Azuciyar shi Yayi mamakin  ace har yaran sun kam,mala karatun su bai sani ba,,,

   Lalai maganar hjy tsuhuwa ne yana sakaci da al,amarin mahaifiyar shi, sosai,,,,

  Wacce kamata yayi ace tana cikin hutu, yanzu saboda yakai lokacin da za,ace ta huta, da komai

       Saidai ina, duk lokacin da yaso yayi mata wani abu na musan man sai yaji kamar andaure shi,, ba zai iya yi mata komai ba in yai niya,,

   Kuma yasan cewa yana turo ,ma mahaifin shi da kudi masu yawa koda yaushe ,

  Wanda ya ci ace mahaifin nashi, yanzun haka angyara mata muhallinta, da su,

   Sai gashi yazo yasamay ta a cikin irin wanan yanayin na jiya wayau,

    Babu wani almar tanajin dadi a,rayuwanta sam,,,

   Shiru yadan kara ratsa dakin ,,,,

   Wanan karon yaghana ce ta danyi kokarin yin magana da dan nata,

   Nasiha tadanyi mai gamay da zaman duniya

    Sai kuma maganar aje iyali ,da take tambayar shi, cewa ance mahaifin shi zai hada shi aure da yar abokin shi ko,

   Inda taimai nasihan a kan rikon amana, da gaskiya da, kuma kula da hakin aure,

   Namu har kulun shine mudinga maka addu,an fatan Allah tare da gamawa da duniya lafiya,,,,,


    Tabbas yaji dadin wa, "yan nan magan ganun sosai, musan man kamar yadda take tasai mai albarka, abinda bai taba jiba,,,,,,

   Don tunda yake da, ita basu taba dadewa irin na yau ba suna magana, ko hira,

   Lalai yana da sa,a sosai a wanan tafiyan nashi,, insha Allah tunda yau harda albarka yasamu gurin ta,,,,,,

      Daga karshe ya ciro kudi masu yawa ya aje mata agaban ta,

   gabanta ne ya fadi don tunda take bata taba ganin kudi masu yawa ba haka, 

    Yadago kai da niyar yai mata bayani akan kudin,

   Kaifin yai wani magana yaghana tace a,a, yaro bani bukatar kudi daga gare malam da hjy tsohuwa ba su rage ni da komai ba a,rayuwa na,

    gashi kaima din kana aiko muna da sako lokaci lokaci ta wurin hajiya tsohuwa

  Kabar kudin ka wai don akwai hidi momi agabanka da zakayi,,,

  Ya, Cewa wanan kudin ina so ki samu wani sana,a kifara yi dashi,,,  

             wanda kudin zasu dinga shigo maki kafin in aiko maku dashi,,,,

    Sai kuma wurin su yabi kaunar shi da aka fara yiwa aure, ita ma,ina so adan taimaka mata da wani abinyi,, 

     Sanan bashir zaizo da masu aikin gina ina so ai maku gyaran wanan gidan ya koma irin na zamani,,

   Duk da bata son su hada ido da dan nata,       don yawan kunyan shi da take ji yasa ko daga kai batayi idan yana gabanta,,,

   Amma yau,saida ta daga idon ta da sauri takaleshi

   Tace a,a gyaran wanan gidan ba karamin aiki bane ,

malam kuma yana yawan gyara muna shi lokaci lokaci kawai ka barshi mungode,,, 

  Baice mata komai ba yai mata sallama zuciyan cike da tunane iri iri

   Watau tsohuwa tana taimaka wa manshi da sunan shi,,,

   Bai san ya zai gode ma wanan boyar Allah ba mai kaunar shi a,kullun,,,,,

    Da zai tafi yakona gurin malam,sukayi sallama 

   Inda malam ya kara dan tatanawa dashi,akan aikin da zai turo aimasu da kuma zancen yan kanan shi da zasu kare karatun secondary bana,,,,,,

    Suma yana son ya taimaka masu,,,,,

   Don suci gaba da karatu,,,,


   Gidan tsohuwa ya koma ya kwana cikin dakin shi na yarinta dake gidan,,, wanda bata yarda ta sa kowa acikin shi ba,

   Dakin fes dashi kamar akwai wanda ke kwana aciki, don yawan gyaran da take sa ana ma dakin,,,,

   Washe gari  Saida ya karya kumallo da safe ya kuma, dan gana da wasu daga cikin yan uwan shi ,

    Inda yai masu dan alheri so sai, yakuma, yi masu, bayani irin aikin da yake a,can kasar saudiya dakuma irin aiki dake gaban shi yanzu,

      wanda zasuyi yanzu anan kasar ta Nigeria

   Ya,yi masu wanan dan bayanin ne

  Don kawai yadan wanke zargi da shankun sa da suke yi 

    tunda hjy mama tasa zargin shi, azukatan yan uwan nashi,. ,,,,,,,,

   Sun ko gansu kuma sunyi aman na,dashi

    Inda har,wani kanin mahafin shi kecewa

    munyarda da zancenka Alhaji karami , tunda dayawan mun je mungani kuma mutanen mu in suntafi sunaganin ka ,har yau bamuji komai na assha daga gareka ba ,

   Shiyasa koda tazo tai, taimuna wanan mugun tabon azuciyan mu, bamu dauka don ba mu yarda da ita ba sam 

    Don mu kowani ne yazo ya fadi wanan zancen baza mu yarda ba balle ita din

 Ai,    In,ma sherine kusan kanta taimawa don diyanta tunda suka tafi turai ba wanda yazo kasan nan ko sau daya suna can suna holewar su, 

   Itace mai binsu idan tana bukatar ganin su,, sai ta fake da cewa taje ziyaran sune,,don karatu yai masu yawa,,,,,,

   Kuma labari ya samay mu cewa shashanci suke koyo a turai din,,

   Da haka ya rabu da su sunata zowa suna mai sannu da zuwa da kuma godiya akan kulawar da yanuna masu cewa shidin nasu ne don bai ki su ba,,,,,

   Da murna da farin ciki ya nufi garin Maiduguri,,  

       Don yagana da mahaifin shi kafin ya wuce zuwa Abuja  inda zasu ga wasu kusoshin gwaunati kasar ta nigeria don su fara kaddamar da shirin su,,,

    Na kafa company global da sauran masana,antu,,, acikin kasa,,,

    Mr Williams zaizo, Nigeria inda za su hadu shi Abujan su gudanar da,komai,,,,,

   Yasamu Alhaji lawal zannah a katafaren gidan shi da ya gina a G R A uguwar da mafi yawan mazauna wurin tsofafin masu mulki kasane da manyan attajirai sune mazauna wanan uguwar,

    Mahaifin nashi yayi murnan zuwan shi so sai ,

   Don dai dan nashi ya cika mai alkawain ya nuna mai cewa shi dan halas ne

    Don yazo akan kiran shi dayayi kuma yaimai alkawarin zuwa gashi kuma yazo din,,,

     Ga uwar gaiyar wanu,irin kallon da taron da yasamu gurin ta,, hmmm,hjy mama saidai kawai ayi shiru dama yasaba dà irin hakan daga gareta,,,,

   Bawani sabon abu bane hakan da tayi mai don inda sabo yasiya da halinta,,,,,

    Amma ita in,taje gurinshi ji irin taron da yake mata kamar itace mahaifiyar shi,    Ankawo mai abinci inda ya nuna ma mahaifinshi cewa akoshe ya ke,

   Murmushi dattijon yayi kadan ,daidai lokacin da yake zama a daya daga cikin kujerun dake wurin da aka tana da don cin abincin,, 

    Yace ma dan nashi, babana baka iya cin abincin mu ne yanzun nan ko kuwa, a koshe ka,ke,

    duk da yagane cewa dan nashu, baison cin abincin hjy mamane kawai saboda hajiya tsohuwa ta hane shi tun yana yaro,,,,,

    Ada bai dauki maganar dagaske ba amma da yafara girma yana wayau, sai yake fahintar cewa

    lalai mama zata iya cutar dashi ,

    don tana iya masa komai don ta salwantar da shi aduniyar nan 

   don haka yake taka tsantsan da al,amarin ta,,


    Don yakauda zargi ga zuciyar mahaifin nashi sai yadan isa bisa tebur din cin abincin ya dan zuba fruit, salad kadan yana sha ahankali,

    Alhaji yadan yi murmushi irinta manya ya kalli dan nashi 

    yace mai babana kayi imani da Allah azuciyar ka

   cewa ba Amina ba duk wani mahaluki na duniya bazai iya cutar da kai ba insha Allah,,,,,

    Duk da asiri taci annabawa Allah balle mu,

  Kaidin mutum ne mai kula da yawan ibada da tsare dokokin Allah,

   Yadda yakamata ,,,,, kuma nasan cewa duk wani kariya tsuhuwa ta tanadar maka dasu tun kana karamin yaro har izuwa yanzu,,,

   San nan ina sane da duk wani gudun mawar da mijin mahaifyar ka ke yima,

   Nikaina ina da wata yar alaka da shi wanda bakowane yasani ba kasancewar shi  malam din mutum nei mai gaskiya da rikon amana,

    Kuma inajin dadin yadda ka dauki malam din tamkar mahafin ka,,,,

   Kakula ka kuma kara kula sosai da al,amura, su

   Kaga yan uwanka da ke turai sam ban gane ma komai ba gamay da karatun da sukaje yi a can turai din

   banda dan banzan kudin da nake ta tura masu,

   Inbadon Allah yayini nai  karfin arziki ba da yanzu na durkushe kasa warwaras,

   Kuma mahaifiyar su bata son sam ayi mata zancen su,, ido nasa masu ita da su

   Yakare maganar nashi yana hade wani irin malolon bakin ciki,, da ya tokaro mai a makogwaron shi,,,

   Duk sai dan yaji badadi azuciyar shi,

   Ada yadauka cewa uban bai damu da rayuwar shi ba sam,

   Amma yanzu sai yake fahintan cewa ashe duk wani motsin shi mahaifin nashi yasa ni halarci ne kawai yake nuna rashin ko in kula gaban hjy,mama,,,

    Muryan Abba ta dan dawo dashi seti,

    Yace gamay da yarinyar da nai ma magana badiyar kowa bace illa diyar Alhaji abokina kuma amina,

   Wanda ya nuna min cewa yana son hada zuri,a da daya daga cikin yara na da nashi,

   Hakan yasa naga ba wanda yadace da wanan hadin sai kai,

   Don duk cikin ku ba wanda zan iya tunkara kai tsaye da wanan zancen sai kai 

   Duk da kaima din bawai zan tursasa ka akan dole sai kayi bane ,aa kawi in kaga zaka iya sai kaje kuga juna da yarinyar intayi maka shi ke nan

   Ahmad yadan dukar da kanshi kasa yace a,a Abba basai naje ba idan yariyanyar tayimaka is ok banda matsalar koma ni

   Da mamaki mahaifin ke kallin shi wanda bai,taba zaton abin zaizo mai, cikin sauki haka ba

   Hakika babana kadai halas ne tabbas nasan ka gado halarci gurin iyayen mu sosai

   Don bakowani yaron wanan zamanin bane za,ayi juyashi cikin saukin kai haka ba

   Tundai yadda kake jin kanka acikin lokacin ka, hakan ga, ga,kudi ga ilimin kowani iri katara,,

   Nandai yabar komai wurin Alhajin nashi, akan yayi duk yadda yakamata don shi baida lokaci wada tace na kanshi yanzu,,,

   

    Abuja yawuce  ranan inda yabi jirgin da yatashi marance zuwa birnin taraiyan,

   Saboda mr William's jirginsu zai yi saukan asuba ne,,

  

   Komai ya kan kama a can birnin taraiyan inda shugaban ni sukayi farin ciki da wanan masana,antar da za,a kafa acikin kasa don cigaban kasa da al,ummanta,,

    Kwanasu uku suka juya zuwa Dubai don kai takardun rije,jeniyar da akayi da Nigeria,

  Al,amarin auren shi kuwa Alhaji da bashir tare da sauran yan uwa suka gudanar da komai kamar yadda addini da al,ada suka tanada,,,

    Anje kano wurin iyayen amarya anyi komai cikin tsari,

   Ansa lokacin daurin aure nan da sati uku masu zuwa 

   Don mahaifin nata yace yafi son taje can tayi azumi agidan mijinta,,,,

    Duk wanan zancen hjy mama bata da labari saida aka tsaida komai na buki sanan yayan nata ta bugo mata,

   Ga hauka irin nata aiko saita hau fada tana cewa an munafunce ta,

   Ai diyar yayanta mace wace ta ke tayar wa taso hada auren ta dashi amma shine yayan nasu zai masu wanan cin layin

   Hauka iri iri da zagi anjishi gurin hajiya mama,

    inda take cewa ita ba ruwanta da wanan auren cin amana da yayan nasu yayi,,

   Komai cikin mutunci aka,yishi tare da yan uwa da abokan arziki 

   Inda ango nacan Dubai yana yin sha,anin gaban shi,

   Bashir ne yake gudanar da komai da yakamata ango yayi

   Hjy tsohuwa tayi bakin ciki sosai da akace yar uwan hjy mamace Ahmad ya aura kuma tayi fada har tagaji inda akaita bata hakkuri,

   Daga karshe tayi waya da Ahmad din yakwantar mata da hankali har ta dan huce, 

  Amma badon ta so ba yaghana dai batace komai ba ga al,amarin .

   


 A saudiya kuma muna can abin mu munata harkokin gaban mu don ba wani aiki mai yawa da muke yi kamar da

   Don tunda muka samu wanan  aiki da hajiya laila tai muna hanya aikin gidan sheriff din mu

    Agaskiya mun  rage wahala so sai bakamar daba don yanzu ko abinci bai muna wuya

   yanzu duk yan gidan mu sun,dawo da aikin su nan gidan 

    saboda aikin da za,ayi na abincin azumi dana lokacin aikin hajji , watau abincin Karama,,

     A, yau muke sa ran dawowar sherrif din mu daga dogon tafiyan dayi nakusan wata guda, zuwa gida Nigeria da kuma kasashen larabawa ta tsakiya,,

   Munyi aiki sosai saboda dawo wan nashi,,,,,,

   , aikin kamar su ,,gyaran gida zuwa yin abinci mai kyau da kula da dabbobin gidan, saboda kada sheriff yace mun barsu da yunwa 

  Wanda agaskiya da yana nan da bai nan duk gudane muna kula da komai tamkar yana gari,,,

   Don shi kuma ,akidar shi da ya iso daga tafiya in yayi, gurin dabbobin shi zai fara zuwa yadan diba lafiyan su sai dan yi wasa da su kadan  san nan  ya shige gida,,bai kara fitowa indan ya shige,,

     Yau ma hakance ta kasance ina wurin da nake kiwon tsuntayen

   Jiminan da ake kiwo a,gidan tana miko min wuya ta ina tsokanar ta ina ta dariya dagani sai tsutsayen a wurin,,,

  Dariya na nake tayi hankali kwance don ganin tana son ta tsakwace min hannu niko ina cirewa cikin sauri,,,,

   Kamshi yan company al,rahab naji  duk ya cika min hanci na 

   Ko ban waigaba nasan Sheriff ne tsaye a wurin,

  Don ni Har yanzu nauyin shi nake ji sosai tun lokacin da yasan cewa na fara period, ban son in,ganshi,,,

   A,hankali yataka har zuwa inda kejin Akun shi yake,,

     Sannu da zuwa nadan yi mashi sama sama lokacin yana magana da Akun na,shi,,,

  Saina dan saci kallonshi naga yadan ramay har da baki yadanyi, kadan 

  Ganin bankalin shi naga tsuntsun yasa nadan juya ahankali don in,tafi,

    Zan wuce shi naji muryan shi yana ce min ya jikin hajiyan mu,

     saida nai mamakin jin wanan tanbayar daga bakin sheriff din na mu daidai wanan lokacin, dayake tare da gajiyan tafiya,,,

   Nace mai taji sauki 

      Yace min,  ,I hope tana ganin likitanta har yanzu nace mai 

   eh, kawai

   Cikin gudu gudu nabar wanjen,

   Don kada yakarayi min wani tambaya kuma,,,

    Yagane ni sarai kunya shi nake ji 

    amma dai shi ina ruwan shi tunda yasan cewa mace nake

     kuma ai dole inyi wanan abin,,,

   

Bayan yadawo da kwana biyu mukayi baki daga Nigerian 

   Sai murna nakeyi da rawar kafa ganin ga mutanen Nigeria sun zo

   Don ji nakeyi kamar zasu bani labarin inna na,,,,,

    Sunkai su goma maza da matan su 

  duk da mu bamu fahinci komai ba saidai munga ana ta gyara wuri 

    kamar irin dakunan dake rufe ba kowa acikin sh, kuma ba ko,,yaushe ake bude su ba,,

   Sai gashi Yau ,duk an bude su ana ta gyara ana sa wasu kaya kamar na kwalliyan mata aciki, su,,,

   Nidai ban fahinci komai ba 

   Sai kusan yamma zamu tafi gidane mama may abinci take ce muna wai muzo da wuri gobe saboda munga anyi baki yan kawo amaryan sherrif din mu daga Nigeria,,,,

   Amarya na kara maimata maganar na ta,,,,,,,,

   

🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 14:25] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                 4⃣0⃣

                    BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎      Murna da annashuwa sun tabbata ga mutunin da tunanen hisabin Allah ya hanashi tara dukiyan ta hanyar haramu,,,,


  Yan Huguma groups da Teema luv group maman fati group, mama nawal group Allah ya kara dauka yasa mugama da duniya lfy,,,


Almost true life story,,,,


  Ta ce min eh

    ai sheriff din mu yayi aure ,itace aka kawo shiyasa muka ga jama,a sun zo daga Nigeria,,,

  A gaskiya munyi murna sosai dajin cewa sheriff din mu yayi aure

     Farin ciki fal azuciyan mu saboda munyi sabuwar uwan daki,

   Duk da ba musan halin taba mun dai yi murna da hakan,,

    Ranan cikin farin ciki muka bar gidan muna jin dadi

    Muna zuwa gida labarin da mukaje ma hajiya dashi kenan yau 

   Duk da bamu san ko wace ce, amaryan ba daga cikin bakin da,su kazo,,,,,    

   Saida  muka gama komai muna zaune sai Rugaiyya ke min ita gaskiya bata ga alaman amarya daga cikin bakin da suka zo ba ,,,

     Saboda may kikace haka inji yumma 

   Naga duk kamar ba yara bane kuma babu wace tadan nuna alamar lulubi ko wani dan jin kunya kunya, hakan ga kamar yadda amare ke yi,,

    Ina gefe ina gyarawa hajiyan mu kayan wanki da nayi mata tun daren jiya 

    Yau da safe ban samu gogewa ba,

   Hiran su yasa nadan shiga tunane cewa aiko koni din banga alamar wata yar gaye ko amarya wani sign na amarya ba cikin bakin,,,,

    Sukaina ce tace ita,ko gani takeyi kamar wanan bakar mai dan rawan kan nan itace amaryan 

  Don taji lokacin da take cewa don may za,a ajeta dakin kasa 

   Ita tafi son sama tare da na sheriff,

    Sai wata mata daga cikinsu tace ai tunda nan yabaki sai kiyi hakkuri dashi hakana

   Taji ana cewa Nafisa don Allah kibi wanan mutumin asan nu kin daifi kowa sanin yadda akai wanan auren ,,,,,

   Ki diba fa shekara nawa kina zama agida kuma kiji yadda kaunar mahaifinki tanuna hassadan ta da auren naki

   Yanzu duk wani jidakai ko wani girmankai da iya boko irin naku yakare

   Indan har kina son wanan daulan yafita hannuki kina ji kina gani to bissimillah ki ga ki ga ,,,, 

   Bata karasa maganar ba taga ina falon ina hada masu abinci sai tai shiru

   Banji karashen maganar tasu ba inji Sukaina,,,,

    Cabdijam inji Anty Rugaiyya 

   inko har wanan din itace matar gaskiya wata killa ba shi yabide ta kamshi ba,,,

    Duk hiran da suke yi ina jinsu sai nazarin maganar nakeyi

   Karshe na nisa nace koma dai may,ye aishi ya, auro abinshi mukan namu aiki mu bar masu guri,,,

    Can cikin dare mun fara barci sai kawai muka dinga jin ihu har na tashin hankali,

   Nai zubur zan tashi infita sai hajiyan mu tace min walahi duk nafita dani za,a hada 

   Tace min Askarawa ne da yanbagaladi suka kawo samamay yau shiyan mu,,

   Wata kila watace suka gani suka biyo ta har nan don suka ma

   Jin haka duk mukasha jinin jikin mu don tsoro, daidai kofar mu suka tsaya suna ta buga ma wa, yanda suka kama tsawa,

   Muna labe munyi shiru kamar ruwa yaci mu ba wanda yayi ko dan guntun motsi cikin mu

   Hakan da suka ji tsit yabasu damar wuce don suna zaton ba takari acikin gidan ,,,,,

   Don da datakari da masu shi sunji tsoro sun fito dagudu, suna batun tserewa,

   Amma jin shirun dasukayi unguwar tamu yayi,

    yasa suke zaton sauran gidajen duk na,larabawa ne kawai,ba wani sauran takari wajen,,,,

  Munajin tashin motocin su muka firfito, daga inda muka boye,saida wasun mu suka kewaya don tsoro,,

    Nice, ta,farkon fitowa wajen gidan mu

   don muga kowace ce aka kama daga cikin ,

  Duk da gari bai karkare waye ba,

  Amma mun,gane cewa lawisa ce aka kama

    kuma ita lawisa din nan tanada diya biyu,mace da namiji,,,,,da ta samu dawani balarabe

    yaran kuma sun biyo balaraben sosai,,,,,

   Ashe koda aka kamata bada yaranta ba saboda ganin da sukayi yaran farare ne,,,

      Haka muka karasa wanan daren cikin fargaba da tashin hankali,,

   Dasafe kafin in,wuce naje gidan su lawisa na diba yaran nata,,

    Aiko nasamay su zaune yaran suyi kuka sun gaji 

    sun hada kansu wuri guda sunyi tagumi zaban tausayi

   Jawo su nayi zuwa wurin hajiyan mu

    Aiko hajiya naganin mu tamike tsaye 

  tana,cewa, fadima kina da hankali kuwa 

    Kowa baije yadauko ma kanshi wahala ba ke zaki je ki dauko muna

    muna fama da kan mu ,muma tamu ta,ishe mu ,,,,

   Shiru nayi saida nabari tagama magana nace haba hajiya wa yan nan yaran fa suna bukatar taimako a yanzu,

   Sanan kituna wasila fa tana iya kokarinta da mu,

   Idan baki da lafiya muna gurin aiki takan zo tana diba muna ke,,,

     Sauran yan uwana da basu fita ba sukayo kaina ca,,,, 

   Kamar zasu cinyeni dan ya,,

    Yaran na takure gefe guda sundan rgumay hannun su ,sun wani man,ne majunan su ,zaban tausayi

   Jawo su nayi nai masu wanka cikin sauri nadauko abinda zan karya kumallona da shi nabasu, 

    Har dan abinda zasuci darana saida na hada masu,shi ,sanan nafita zuwa wurin 


    Nikaina nasan cewa yau,na makara sosai, 

  Ina fita taxi,  Kai tsaye na fito na mika ma mai taxi kudin shi ,

   Duk da naga Almustapha a,kofar shiga gidan namu, kauda kaina nayi gefe kamar ban ganshi ba,

   Don shima yasan cewa bazan gaishe shi ba,

    Fada yafara yi min baiko kai aya biyu bu nadaga mai hannu alamar ya isheni hakana,

   Cikin mamaki yake kallo na yana kuma yaba karfin hali irin nawa ,

   Har shine zan daga wa hannu,

   To yau kowaye min tsaye sai nabar gidan nan ,haka yake fadi azuciyar shi,,,

    Na ci gaba da magana ina cewa shike nan don muna aiki bamu da incin kanmu ko wani lokaci na kan mu,

   Ai yakamata a,dinga muna uzuri aduk lokacin da aka ga mundanyi wani abu bawai adauki matakin da babu dalili ba

    Da in tsaya kana mari na ko zagina duk lokacin da kaga,,,,

    Ban samu karasawa ba naga Sheriff's atsaye gaban mu yana muna wani irin kalon mamaki,

   Mari mari fa,, Almustapha ,Subahanalla subahanallah ka doki mace macen ma,,,,,

   Sai ya kasa karasa wa, naga kawai ya dunkule,  hannunshi ya dan daki gudan da shi yana fadin subahanallah,,,

       Nikan nasa kai na wuce cikin gidan ina jin yana cewa yaushe kai wanan aikin bansani 

    Ko kana dukan mace ita wanan din may zaka daka acikin ta,,,

   Wuce wa yayi ciki gidan  ran,shi bace dagani kasan yayi mugun, hasale ,yabar almustapha a wurin bakin get din, cikin damuwa,,,,,

   Don ko yaga fushi yau karara a,idon sheriff din,,nashi wanda rabon shi da yaga wanan fushin yadade,,,,

    

   Ban tsaya yin komai ba gurin tsuntaye nafara zuwa sudake da rai na basu abincin su,,

   Don kusan kowani tsuntsu da kalar abincin shi,

   Ruwa kuma akwai wanda nake sama ,magani acikin nasu, ruwan shan da samun kuzari da lafiya,,,,,

    Danaga komai ya kam,mala sai na bar gurin aikin zuwa cikin gida don inyi aikina,,,

    Daidai gurin da dawakai da dabbobin gidan suke yake tsaye ya rike ciyawa a hannun shi yana ba wani dan farin doki karami,,

   Ke yace min cikin tsawa saida naji tsoro wanan kiran,

     Ya,akayi mustapha ya mare ki yaushe ya,mare kuma a ina,,

    Wani tambaya zan ansa daga cikin ukun,,,

   Duk da ina jin kunyan shi yau sam banji ba

  Saboda dama tun da daren jiyan  abinda akayi wa lawisa a,kasan ya tayar min da hankali sosai ,

    saboda naga bamu da wani gata ko daraja a, wanan kasan.

   Batare da na bashi ansa ba sai na fashe da kuka mai kuna zuciya

    Yana ganin na fara kuka sai ya rintse idanun shi don bacin rai jiyakeyi kamar a watsa ma garwashin wuta ajikin shi,,,,

     In akwai abinda ya tsana yaga mace cikin yanayin kuka ko ban tausayi,

    Ganin idona rintse yasa shi ya sulale yagudu yabar wurin don bai iya daurewa yana jin wanan sautin wanan kukan a rashi ,,,,,,, 

      Ni ko,kukan da , samun yin ,shi ,shiya dan sa  naji wani dan sanyi  azuciya na

    Koda nagama kukan na dan kai dibana inda nagan shi tsaye sai naga wayyau, ba kowa wurin,

   Haka na wuce nabar wurin jiki ba wani kwari don jinakeyi kaman ban iya tafiya,,  

  Ashe da sheriffudeen din mu yabar inda nake tsaye komawa yayi sama yana tunane azuciyan shi,,

   May yasa almustapha zai dauki hukunci mai tsanani akaina,haka har da mari mari fa,,,,,,,,

   Wurin nabari zuwa ciki don inyi aikina,

   Ina shiga cikin gidan sam na manta cewa akwai bakin, agidan mutanen Nigeria dasu kazo jiya,,, saboda tashin hankalin da nake ciki,

Wa,daga cikin bakin,suna  falon gidan zaune su,nata har kokin su,

  Sai narasa ta ina zan soma aiki na ma , tsayi nayi wuri guda,,,

   Don ku san ko, ina akwai mutane a falon,,,,,


      Ina nan a tsaye tsakiyan falon sai naga wata yar dattijiwan takari bakuwace daga cikin mu, ta zo inda nake tana min murmushi ,,,,,

 Cikin girmamawa take magana da harshen

    larabci takecewa tundazu take jiran shigowa na  ,,

  tai min sannu da zuwa,

   Tace min itace mai kula da aikin goge goge yanzun agidan

  Da duk wani aikin da ya kushi cikin gida,

   

Mamaki ne ya kamani don naga aiko jiya nice nayi wanan aikin,kafin muje gida,,,

   Sai,gashi jiya zuwa yau da safe wai an canza wata mai yi,,,

  Kenan an,dakatar dani daga aikn ake nufi ko,,,


   Daidai zan fita inbar falon naji mama mai abinci nace min inzo indiba ko abincin da suka dafa yayi ,,, kalonta nayi itama cikin mamakin

   Don suna son su ba mutane abin kari,,,

   Nuna kaina nayi ina waigen gefe da gefe na ina, nufin ni takewa magana kuwa,,

  , tace min eh,,, dani take

   Ba mussu nabi bayanta zuwa inda naga tabi, kitchen ta nufa,

   Abinci ne na alfarma aka hada masu kyau da dadin gani,sai kamshin dadi ke tashi,,

   Tana kokarin bude min kulolin abinci nace mata la,la,la ta bari don Allah komai ya yi,

   Mama mai abinci tace min in bari ,in,diba in gani, in, akwai wanda bai yi ba sai su sake,dafa,wani,,,,,, 

   Nace mata yayi haba mama, yau kika fara wanan aikin,

  Ta danyi murshi kawai na nuna kula da girmamawa

    Niko duk mamaki ya cika zuciyana ga dinbin tanbaya min fal a,rai,,,,

    Bayan anjera komai wurin very neat, ,

   Rugaiyya tace min inje in fada ma mutanen gidan cewa table is ready,,,

    Bayan mun fita Rugaiyya ke min bayanin cewa yanzu aikina shine kula da duk wani al,amarina aikin cikin gidan, nan nice da alhakin kuwa, dashi,,,,

   Don Almustapha ancanza mai wuri zuwa can company

  

    Nace ma Rugaiyya yanzu duk yawan mu sai nida nake yar karamar ku za aba wanan aikin

   Wanan aikin aida mama mai abinci yadace bani ba


🐎ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎🐎

[10/4, 14:26] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

          👣👣👣👣👣

            👣👣👣👣👣

                    4⃣1⃣

                       BY 

🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎   A, kulun muna gode ma Allah Subbahanahu Wata,ala daya Halice mu a matsayin musulumai,

   Ya Allah muna kara gode maka da ka bakayi mu kafirai ba,

   Allah yakara ma musulunci daraja da daukaka 👏👏👏


 Allah ya kara rufa ma duk al,uman musulumi na duniya asiri


   Almost true life story


    Maimakon in yi farin ciki da cigaban da nasamu ,

   Nikan hankalina yana gurin irin wulakancin da akeyi wa yan takari,,

  Ga lawisa ta wuce tabar yaran ta acikin duniya, batare da sanin makomar su ba,,

  Shin wai may yasa ake zuwa wanan aikin mai wahalar tsiya ,

   Wahalar da ba riba ko kadan sai in Allah yataimaki mutum,, yatar fa wa garin mutum nono to shine zai tsira da dan wani abu,,,

   Duk abinda aka girka a,gidan ranan , saida na sdibar wa,su hajiyan mu da yaran nan, na lawisa,

   Tun lokacin tashi baiyi ba nabar gidan aikin na mu,

 Sauri nakeyi zuwa gida don inkai ma hajiya abinci suci,

   Natafi da niyar gobe insha Allah zan daure in ma sheriff din mu magana ina son ataimaka mu,na indinga zuwa gida da wuri don indan kula da hajiyan mu da yaran lawisa,,, ,,,,,

   Cikin sauri sauri na isa gidan tun ban shigaba nake jin dan she,shekar kukan yar macen yarinyar,

  Wacce ban ko san sunan ta ba ma 

  Da, sauri na karasa shiga ciki don jin ko maya sami yaran

   Hajiya na zaune gefe tai tagumi, sukuma yaran sun dan tsuguna daga bakin kofa shigowa cikin gida,,,

    Banko kalli hajiya mu ba wacce ta nuna mamakin ganina nadawo yanzu 

   Tun lokacin dawowar mu baiyi ba,

    Yaran nake tambaya hankali tashe komay yasamay su suke kuka

   Ganin danayi basu da niyar yin magana,,,

 yasa na wuce ciki kawai tubewa nayi ,nacire dogon rigar da nasa sama,

   Nakoma dagani sai wata yar doguwar riga  English wear kalar sky colour ,wace duk ta man ne min jikina rigar irin na yan Brazil's din nan ce 

   Sai kaina da na daure dawani ribon mai kama da gashin mussa, kalar fari kwal

   wani dogon yan kune fari ne a,kune na, takalman kafana dama munfi sa cover shoes, don , muji dadin gudu idan an biyo mu,,

   Plates najawo guda uku na fara zuba ma hajiyan mu abincin ta kala kala ,nakai mata 

    Nadibar ma wanan yaron nashi saida na cika mai plate , nabashi tare da abin sha,

    Na hada muna nida wanan yar yarinyar a plate guda,

   Cikin lalashi da hikima nasamu yaran suka ci abinci , 

    Har suka dan sake jikin su dani, inda nake tambayar su sunan su,

   Namijin yace min sunan shi umar macen kuma Aisha,,,,,

   Saida naga hankalinsu ya kwanta sanan natashi na gyara wurin da mukaci abincin mu tsab ,,

   Umar da Aisha,naja zuwa gidan su, don indan diba cikin kayan su koza a,samu wani abinda zai masu amfani ,

   Muna fita naga yan kabilar larabawan dake gurin suna ta kallon mu,

    Duk da sun tausaya ma yaran amma basu iya yin komai, gamay da uwar tasu,

    Wani halarci da suke muna shine, indai kana zama a unguwar su baza su taba tona bakar fata ba in har yan  bagaladi sunkawo samamay shiyan,,,,

   Acikin gidan na lawisa naga wasu hotuna da takardun ta sai yan tsun makaran kayan ta dana yara,,,

   Nadan tsinto masu masu dan kyau daga cikin kayan,,

   Muka fito gidan,,,,,

 Nasamu su Rugaiyya sun,dawo gida ko,  takara zo muna da wani abinci wanda zamuci da dare,

    Au ke fadima har yanzu yaran nan natare da ke,

   Ashe shiyasa yau kika bar wurin aiki da wuri ,

  don ki dawo wurin yaran na,ko, fadima baki da tsoro ko,,

    Aiko kin dauko muna wani sabon magana wlh, bamu iya da kan muba shine kuma zaki jajibo muna wani sabon taulali,,,

   Saida na bari ta gama maganar ta , 

   Sanan nace yanzu idan mu bamu taimaki yaran nan ba wazai taimaka masu bayan mu, awanan uguwar

   Kutuna cewa muda lawisa duk guda ne tun da itama takari ce,kamar mu 

   dakuma irin taimakon da tai muna lokacin da mukazo nan gurin,, bamusan kowa ba,,

    Hajiya ce ta katse min zance na da cewa ai sai kisan yadda zakiyi dasu,

  Don nidai ba ruwa na gaskiya, 

   mukan mu , ba musan yadda zamu kasan ce ba,, da tamu rayuwar ba balle

   Allah zai dibe mu nidasu insha Allah na katse zancen kowa,,,  

    daga  haka ban kara ce ma,kowa, komai ba

    na,tashi nafara tanadar wa yaran da inda zasu rika kwaci,

     Ina gamawa na wanke masu yan kayansu da zasu sa, gobe, don duk kayan nasu na da dauda,,,,

    

    Washegari saida naga na tanadar masu da komai sanan na bar gidan zuwa aiki,,,, zuciya na nata min sake,saken yadda zan ma Sheriffudeen din,mu bayanin akan taimakom da nake so ai min, don in samu kula da yaran nan,,,,,,

 Ina shiga gidan Kai tsaye gun tsuntsaye na,na nufa ,,,

   Don ina ba,su abincin, su, 

Saboda sune ban son makara zuwa wurin aikin, saboda sam ban son barinsu da yunwa,,

   Gashi kuma mun saba da juna,,,

  Amma ina zuwa wurin naga wani dan saurayin bakar fata bakon fuska, ne, agidan, yana watsa masu abincin su,,, 

   Tsaye nayi nisa da shi,kadan da inda yake ina kalonshi cikin mamaki,

    Daidai lokacin naji karan bude kofar baya nadan waiga inga kowaye ke fitowa,,,

           Sheriff din mune tare da wata bakar mata matar bata da wani tsayi gajera ce mara jiki,

      Duk da ta lailaye jikinta da lafaya mai ruwan yellow sai dan adon duwatsu churculate colour dake jikin lafayan

Ina iya hango gabanta kamar ba komai, hannunta zanen kumshi ne irin namu na yan Nigeria,, yayi baki wulk

    Takalmin ta ma charculet ne amma mai dan tsinin duduge, wanda nake ganin takalmin ya taimaka mata wurin karin tsayin ta 

     Sai wani kamshin turare kamar na turara garwashi da takeyi mai dan dadi wanda ban iya fassara kamshin shi,,, abindai siri ne kawai,,,

     Gefe guda nadan ja na tsaya, don in basu hanya su wuce 

    tare da masu barka da safiya,

    Batare da ya kalleni ba  ya ansa min a dakile

   Wani irin kallo yaimin mai alamar, may nake yi anan ,,, kaina aduke nayi cikin gidan takofar da suka fito,,,,,,, 

   Idon shi naga dan takarin nan mai ba tsuntsaye abinci,

   Wanda baiko kula da inda nake ba, ma tunda na zo

   Saida yaga shigewana yadawo da idon shi kan hanya,,,

   Ita wanan din wace,ce ita habibi,

   Matar ke tambaya ,batare da yabata ansa ba ya wuce yabar ta, tabishi da dan saurin ta,,,


     Yau kida na shiga cikin gidan banga bakin mu ba 

Sai gidan ya koma shiru ba kamar kwana biyu da akai yawa ba,

     sai mu kadai ne ke ta zirga zirgan mu a cikin gidan,,,

    Daidai lokacin da aka gama, hada komai na abin karin safen su bisa, dinning table din, ,,,

    Lokacin su ma suka shigo cikin falon kai tsaye inda table din yake ke suka nufa,,,

Maigidan ne a gaba, matar na binshi

   Yaja kujera guda ya zauna,,, don suci abinci

       Inda yake zaune naje kusa kadan dashi,,,

    Ina gyara wasu cups da suka danyi nisa kadan da shi,,,

    gyara cups din na keyi ashe kamshin turaren zam,zam lau,, da,na dan murza a jikina yana tashi ban sani ba,,

   Jin kamshin yayi har cikin zuciyar shi,,,, idon shi  lunshe kadan,,, yabude su a,hankali

 Jin yake  Duk kamshin ya wani  sukur,kuta shi wanda hakan ba halin shi bane,,,,,,, cikin dibara ya kauda kanshi gefe guda,

   Yace min cikin larabci in barshi kawai zasu iya hada abincin, ai 

   Saidai indan ba ka saurara da kyau,ba bazaka ce anyi magana a,wurin ba,,, saboda tausa muryan dayayi


   Ina kallo yadda matar ta cika plate fam da abinci,,, wai ita zataci,,,,

     Cikin gidan nashiga don in di ba ko an,gyara masu, dakunan su  duk na gidan ,,,,

     Aiko kafin in,sauko kasa matar har ta cinye kusan rabin abincin plate din da ta zuba,,

   Idona na fitar waje don mamakin ta

    kallon abinda nake kallo sheriff din mu ke yi,, shima

  Bin inda idona yai saiti yayi,,, aiko sai yaga plate din matar  nake kallon ido waje don mamaki,

      Kara diban abinda nake mamakin yayi,

   Ai, shima da ya lura ta cinye wanan tulin abincin saida mamaki ya kamashi,,,,,,

   Tana gani na tace min inzo in zuba mata juice a cup,

    Hannu yadaga mata alamar a,a,

   Yace mata she is not a Made,,

    Cikin larabci yace min in bar wurin,

  Tana son tambayan shi to amma ba fuskan hakan,,,

  

Duk Jina yau nakeyi , kawai ba wani kuzari ,ajikina,don, yau ban yi, wani motsa jiki ba ,

   Saboda aikin komai banyi ba agidan , don akwai masuyin komai da nakeyi a,da,,,,


     Almustapha ne mukayi kicibis da shi daidai fita wurin kofar shigowa falon , gefen shi nabi,

   Zan wuce shi ba tare da na gaishe shiba ,

   Yace min tun jiya yake bida na don yai min wani dan bayani gamay da aikina, da zan rika yi yanzu,,,,

  Amma saidai ya tambaya ance mai natafi gida da wuri jiya,,

    Kuma yaga, ai, lokacin tafiyan mu baiyi,  alokacin, da ya tambaya

   Ko kallon shi banyi ba nace mai

    Sai acire kudin da na wuce kafin lokacin tashi nayai a,cikin albashi na ko,

   Don abinda naje yi gida yana da muhinmanci gareni sosai,,,,,,

 Duk abinda mukeyi da ansan da nake ba shi idon sheriff din mu na kan mu saidai baijin maganar mu sosai saboda yar tazaran dake tsakanin mu da su,

   Amma dai ya fahinci ba jittuwa a,tsakanin mu,,

  Shiku Almustapha galala, ya saki baki yana kallon inda nabi da ido,

    don kuwa nagama bashi mamaki,

    Yana kuma tunanin waidama haka nake banda kunya ashe,

   Kokuwa, yanzune nakoya a sanadin marin da yai min,

    Don a,iya sanin shi da ni, ina da tarbiya da kuma girmama naga ba, dani,

 

     Karar wayan sheriff din mu da yadau ruri yadawo dashi cikin hankalin,shi,, 

   A,hankali ya mike daga kujerar darnnig din batare da ya ko kalli inda matar take ba ya,

  Yajowo cout din shi ya,aza saman farar rigan dake jikin shi ,yanufi hanyar fita falon ,

    Cikin yanayin yin waya, yana wayan yana tafiya zuwa wurin da aka Parker motar da zai shiga yau,

     Almustapha na bayan shi rike da yar briefcase din shi baka wace ke dauke da takardunshi da laptop din shi,

    Kaman ance min in,fito daga cikin wani kofar da zai sadaka da garden din gidan , 

   don indiba aikin da akayi yau wurin,

   aiko na,hango,shi zai fitan ,,,,,

   Da sauri na karaso inda suke dai, lokacin ya bude motar zaishiga,,,,,

   Ina dan maida nunfashin 

  saurin da nayi nakara so wurin motar,

   Yana gani na ,naji yana sallama da wanda yake wayar dashi,

   Juyo wa yayi cikin mamaki yana kallona, da mamaki,

   Cikin ladabi nake cemai taimakona na nake son yayi don Allah

    Sai ya gyara tsayuwar shi da kyau don ya saurare ni

   Nace mai don Allah alfarma nake nema don indinga tashi aiki da wuri saboda ina,da yaran da nake kulawa dasu da kuma hajiyan mu,

   Cikin mamakina da ganin iya karfin halina, na tun karar shi, danayi kai tsaye babu shakka komai yake mamaki na,,,

   Nace koda za,a rage min yawan albashi nane zan yarda indai za,abarni in tafi da wuri,,,,

      Kallon mustapha yayi da ,alamar su tafi kawai,

Ya shige mota batare da ya bani ansaba ,,

    Sukabarni tsaye kimkam,,,motar nabida kallo,

   Koda na waigo don in koma cikin gida sai kawai naga matar danake zato itace amaryan sheriff din mu duk da basu dace ace miji da mata bace,,

    Tsaye tana min wanu irin kallo,

    Batare da na damu da kallon taba nazo shigewa cikin gida,

   Tsawa ta daka min cikin turanci take min magana,  

 Sai nikuma nakama yi da larabci ina fadin ni,banda lokacin sauraren ki je ga mijin ki can kamar yadda akewa wanda baijin yare,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎

[10/4, 14:27] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

          👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                   4⃣2⃣

                      BY

  🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎


 Idan bawa yana sallah ba wani hijabi tsakanin shi da Allah indan har ya kyau,tata sallah shi, don haka yan uwa mudinga tsananta addu,oin alokacin da muke sallah domin biyan bukatan mu,,,,


     Almost true life story,,,,,,


 

  Shike jan motar Almustapha yana gefen shi zaune sun fito ne da niyar zuwa diba shagunan saida kayan su don ana son ayi gwanjon su , 

   Za,a,shigo da wasu, sabin yayi ,

   duk shekara kusan haka shagunonin keyi a kasan  saudiyan,

    Ayi canjin kayan shago zuwa sabbi, da ake yayi,

   Dai inda go slow ya danyi yawa suka dan rage saurin da sukeyi,

    Sheriff Ahmad ya,kauda shirun da ke cikin motar, 

   Batare da ya kalli mustaphan ba yace mai 

   Ya akayi har ka mari wanan yarinyar ,

   Riban may zaka samu da ka doke,

   Shinka san cewa darajanka da kiman ka sun rage agareta da ma wasun ta,,

   Cikin rudu almustapha wanda ranshi ke jagule dama ,

   Yace kuskure ne wlh akasamu , bada niya namare ta ba,a sali, ma dai kawai hakan na tsinci kaina da ai,katawa 

   Wanda danasani ne ke min gizo ko yaushe zamu hadu da yarinyan nan

     Ganin motocin da suka rage yawa yasa shima kutsawa ta cikin su yadauki hanyar zuwa maicizo, don tanan zasu fara,,

    Mace  wani halittace, maidaraja da tausayi, da kuma,,, daukakawa ,saboda muna da uwaye mata muna da kane mata watakila ma watarana zamu haifi diya macen,

    Kaga komai ilimin mace ko mai waye  wanta sai ta bidi taimakon namiji,,,,,

    Nitun ina karami ina jin tausayin tsohuwa saboda ban iya manta wahalar da ta sha dani,

   Kayi kokari ka gyara tsakanin ka da wanan yarinyar ina ga zaifi,ma sauki,,,

    

     Kulun ina kokarin kare aikina kuma ina komawa diba yara da hajiya cikin lokaci,

    Abinci kuma ba ,a hana min diban yadda nakeso inkai masu, abinda banyi shine dibar abincin da ba,adafa ba,,,

    

   Kowa yasan yadda garin makka ake kwantsama rana kamar kace wayyo Allah 

   Yau rana a,keyi sosai don haka mutane sun samu wuri sundan lalabe  

   Duk da zafin ranan da akeyi bai hana masu niyar fita wurin ibada yi ibadarsu ba,,,

   Saboda kowa yasan cewa kulun cikin baki garin yake masu zuwa ziyara,

   Da wuya ai ruwan saman da yakai sau biyar a shekara cikin makka,,,

    Zafin ranan yai yawa da alamar yau akwai rabon ruwar sama ke nan agarin,,,,,

   Iska ce a,kafara masu kaya nata har,harada kayan su ,don kada ruwan ya samay su,,,

  Daidai wànan lokacin muma muna saman titin,57up ,,

   Almustapha ne ke jan mu yau sai nida ke gefen, driver 

   Amaryan sheriffudeen din, mu tana baya zaune tana ta latsan wayan da,ke hannun ta,

   Yau,ce ranan farko da muka fara fita da ita,

   Itamadin inga fitar ta kenan na farko,

   Taso fita ita daya amma sheriff yace baiyar da ba dole duk inda zata saidani,

   Wanan dokan yai mata zafi sosai,

  Don agabana akai case din ,

  Tafito cikin shirinta tasa wasu kananan kaya tana tako daidai , 

   Shikuma yana zaune falo gaban laptop din shi wanda zance shine abokin hiran shi koyau she, 

   Daga waya sai laptop zaka ganshi da su yana latsawa,

    Karan takalmanta dayaji yasa shi dan dago kan shi a,hankali ya kalli inda take saukowa a,step din,

   Kan shi  ya kawar daga, kallonta ,, sai kuma ya cigaba da abin da yakeyi, batare da ya,waigo ta, ba,,

   Ita ko azatonta ta burgeshi ne hakan da take yi,,,

    Saida ya bari ta karaso kusa da shi cikin rausaya da rangwada irin na yan bariki,,

    Habibi na shirya fa, zantafi,

   Batare da ya kalli gefen da take tsaye ba yace mata,

   Ina fa tace mai wurin gyaran kan da nace ma da kuma , yin wasu yan sayaya,

    Still kanshi na ,a duke yace a,hakan ko kuwa da sauran shirinki ,

   Tadan dibi shigan da tayi yace ,ahakali taga ai,baida wani illa, yar dogon riga ce sai dan gyalen da ta yane kanta dashi,

   Batare da yakaleta ba yace,,kitunafa nan saudiya ne ba turai ba,

    Ko ba komai kina gaban tushen musuluncin ki,

   Duk da nasan ba,arasa masu irin al,adan ki amma nidai ba,agida na ba gaskiya,,

   Kamar yada , dama  na  fada maki sharudan zamanki a gidan nan,,

   Gaskiya bazan iya lamuntar wanan irin shigar ba,

  Sanan ki sani fita daga yau ,bake da driver zaku din ga fita  ba dolene, kifita, ke da wanan yarinyar mai kula da duk har kokin gidan nan,

 Zamanto duk inda zaki tasani kuma kuje tare da ita, 

    Saboda haka na,dauketa wanan aikin

   Ita wanan yarinyar wace wai da za,adinga hadani da ita,,,

   Alamar oho yanuna mata da hannun shi saidai hankalinshi naga laptop dinshi kamar bada  ita yake zancen ba

    Yadan dago kai yace mata, idan kuma kin ga hakan nada matsala,  zaki iya fita ,din fine,,,

    Fuskanta ya nuna alamar bacin rai karara, ,azuciyan ta ji takeyi kamar tace ta fasa,,,

    saidai kuma har in ta fasa din kanta da yadamayta da kaikayin rashin wankewa ya,zatayi,,,

   Dole jiki ba kwari ta zauna ga dayan kujeran dake falon tana cewa, 

   Ina yarinyar da zamu tafi,

   Waya yadauka daniyar akirani sai ya hangoni kusa da su ,nida mai goge gogen falon ina nuna mata, wani aikin da baiyi kyau ba,

   Dayake akwai dan nisa a tsakanin mu dasu, sai yai min alamar inzo da hannu ,nai kamar ban ganshi ba sai matar da muke tare ce ke fada min ana magana dani,,,

  Cikin ladabi na isa gurin da suke,,, batare da yakalleni ba yake min bayani  zamu fita tare da matar shine ,zan kaita wurin gyaran kai .

    Cikin ladabu na ansa tare da dan kallon gefen da take ,

   Ko kallon arziki ban samu ba,

   Muje kawai nace mata,

Kanshi yadan dago dan

bini da kallon mamaki

    don baiga ko na dan shiga ciki ba, don indan gyara yadda yaga wasu mata na yawan yi,idan zasu fita,,,,,,,

    Tun fitar mu ko kallo na batayi ba, balle muko danyi wani maganar arziki, da ita,

     Almustapha ke tanbaya ina zai kaimu,

  Atakaice na bashi ansa nace mai nabililabilah,

   Batare da na kali inda yake ba

   Nikaina ansar bata bani ma,ana ba,akune na ba,sam daurewa kawai nayi nafada mai,

   Don ban son yiwa nagabana rashin mutunci sam,, 

  Amma hakan dai naga damar fada don in fanshe haushi na,,,

 Kanshi kawai ya girgiza cikin wayancewa,gamida basar da disgashin da nayi,

     Shiya  dan daure yace min wani road zamu nakara fada mai a tsiwan ce, 

   Gaskiya wurin ba laifi don wani kilantacen wurine wanda matane kawai ke zuwa wurin manya da yara,

   mun samu mata da dan dama suna jiran layi,

   Kasan cewan mun dan san juna da wasu daga cikin yaran aiki yasa na danyi muna hanya wata dabata fito aikin ba ta gyara mata kan,

    Aka wanke mata,kafan ta, da gyaran kunbar hannayen ta,

   Muja futo zuwa wani dan babban shago tasai wasu yan kayayaki bukatar ta,

  Kadan,Pad kawai nadauka a shagon kasan cewa lokacin period dina ya kusa zowa,

   

       To a,hanyar mu ta dawowa gidane wanan hadarin yatare mu,

 Sararin samaniya nakare wa kallo yadda lokaci guda yanayi ya canza gari yayi duhu,

   Almustapha jan motar shi yakeyi hankali kwance abinshi,,,

   A,hankali na mayarda diba na kan matar sheriff ta gefen idona,  dai lokacin tai magana tun fitar mu, dani tace Allah ya taimake mu  wanan yariyar tasan, wasu, tana magana da almustapha

  Tana dan kara leka window motar tace haka ake iska agarin nan,

   Kafin ta rufe baki wata irin iska kamar guguwa ce ta taso tuni wuri ya turnike da kura, 

   Cikin sauri duk muka daga glass din motar don kurar ya mamaye ko ina,,

  A, hankali Almustapne,,, yake tuka motar don ko ganin hanya ba,ayi sosai,


  Matar sherriff duk ta tsorata tace don Allah mudan tsaya har kuran ya lafa, mukara sa gida don gaskiya tana ganin tafiyar mu a haka hatsari ne

    Ganin da nayi zai tsaya yasa nai mai magana cikin larabci, 

   Nace mai yasan sheriff yace kada mudade ko ,kuma gashu mun kusa kawo wa gida,

   Umurnina yabi ya ja motar ahankali,, har muka isa gida lafiya,,,

   Daidai isar mu gidan wata iska mai karfi ta kara gwaucewa da ruwa mai karfi yabiyo iskan,

    Hakana balle murfin motar nafuto cikin sauri zuwa cikin gida,

   Iska na kwasar kayan mu duk tsirangalin kafar mu yana baiyana asarari saboda kada kayan mu da iska keyi,

   Atare muka fada falon gidan nida matar sheriff wace ban san ma tana bayana ba,,,

  Don nadauka zata zauna amotane har ruwan ya lafa,

   Wata ajiyar zuciya na saukar yayin da naji rufewar kofar falon,

   Sheriff ne tsaye a tsakiyan falon yana muna wani irin mugun kallo,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎

[10/4, 14:28] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

       👣👣👣👣👣

        👣👣👣👣👣

                4⃣3⃣

                   BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

   


Al most true life story,,,    Fuska a a daure yake kallon mu, cikin tsawa tsawa yake magana ,

    Ku wasu irin mara hankaline kuna ganin yadda gari ya canza kala ,

   Yanayin da kowa ke gudun shiga cikin sa saboda kariyan lafiyan mutum,

   Shine ku ka biyo cikin shi  haka don rashin sanin ciwon kai,

   Cikin hausa yake fadan duk da hausan ba wai nuna tayi masa ba,

   Sau,biyo muna hada ido dashi lokacin da yake ta faman fadan,,.

    Ina noke kaina a,kasa kamar badani yakeyi ba,

  Duk da Cikin fada yake magana sai naga kamar lalashin mu yakeyi ba fada bane yakeyi,

    Sulalewa nayi zuwa cikin gida don rigar da ke jikina ya fara jikewa ,don haka sanyi ya fara bimin jiki ko,,

   Ido yabini da shi yana mamakin irin girman da ya hango nadan kara yanzu, kafin mu shigo,

   Ashe tunda yaga hadari yakasa zaune ya kasa tsaye, hankali a tashe, don baisan halin da muke ciki ba, 

  Saidai yayi amanan cewa baza mu biyo wanan iskan ba,

    Saman dakin shi ya tsaya, dai inda zai iya hango ta,waje yana yi yana dan leken hanya,

   Aiko sai gamu cikin wanan uban iskan mun doso gida,,

   Mamaki ne ya kamashi haikan ta yadda muka iya kasadan biyo hanyan hakana ba wani fargaba ko tashin hankali

    Har fitowan mu yana kallon mu da yadda iska ke kwasan mu kafin mu shigo gidan

   Cikin sauri yarigamu isowa falon bayan yariga ya kare muna kallon mamaki ko rashin hankali,

   Itama wucewa tayi batare da tabashi hakkuri ba, don gani take gaskiya ya fara takura mata,,


    Dakin da aka tanadar min na gidan nashiga , don indan gyara jikina,

   Ina shiga batare da bata, lokaci ba, don dama duk nayi futub da kura gashi kuma na jika kaya na sama,

   Cire bakan rigan da nasa sama na yi 

Nakoma dagani sai dan wandon jens dark blue,  na mata wata yar karaman riga pink mai guntun hannu ke jikina,, 

   Sai ribon mai kalar baki dana dan daure kaina dashi,

   Nasamu wuri gefen gadon dake dakin na dan baza bakar rigan nawa don yadan bushe kafin in wuce,,

 zaune nake ina kokarin cire takalman da ke kafa na,  ahankali ya turo kofan hannu shi rike da tawul fari,

   Ban san lokacin da na mike tsaye ba ina wage wage ko zan dan samu abinda na rufa ma jikina, alokacin ba komai adakin don ban barin kayana agidan kamar yadda sauran ma,aikata keyi,

     Towel din ya jefo min tunda ya gane nufi na ,,

   Shiko aganin shi baiga wani abin da har zan boye ajikina ba ,

  Yar ficir dani kamar mage,

   Juyawa yayi yabar dakin cikin sauri,

 Shi dai tausayi wanan yariyar ke bashi a,rayuwan shi don koda baiji tarihina ba yakan tausaya min duk lokacin da muka hadu,

   A dakin ta  yasame ta tana kara gyara kwaliyar da akai mata a wurin akafar

   Cikin dan dakikan lokaci ya kalle gyaran kan nata ya kauda idonshi tamkar baigani ba,,

   Tasowa tayi tana wani rangwada ita adole tayi kwaliya ma miji,,

  Tana batun rungumay shi yace cikin dakiyar fuska maynene haka pls,

   Bana son irin wanan shashancin pls,

    Sha shanci fa kace ,kana ,a matsayin mijina zakace min sha,shanci,

   Nifa Ahmad bangane may kake nufi ba dani yau kusan satina uku kenan agidan nan 

   Amma ba wani nuna cewa ni matar kace, balle ,,,

 Bata karasa maganar ta ba daidai lokacin nai sallama dakin dauke da cup din ruwan shayi mai tururi ,

   Dai lokacin kuma wani sabon ruwa yakara gwaucewa kamar da bakin kwarya,,,

   Shayin na gabatar mata ,wanda nasamu gundun mawar harara, 

  Bisa tebur din dake dakin na aje mata nafito abina,,,,

  Dakina nakoma don naga yau abin ba dama,

   Wajen window dakin na zuge glass din nadan tsaya, ina kallon ruwan 

   Wata zuciya kuma tana tuna min hajiyan mu dasu Aisha da umar ko yaya suke yau cikin wanan yanayin,sanyin

   Danagaji da kallon ruwan baidauke ba sai kawai na kara cire rigana na fada bisa gadon mai wani katon bargo da laushi, nace barina dan huta kafin  ruwan yadauke in,tafi gida,,,,

    Har gari yai duhu ruwa ake ta tsulawa bakama hannun yaro,

    Niko kwance nayi barci mai nauyi ne yai awon gaba dani,

     inata barci abina don jin dadin wanan yanayin danayi,

   Nadunkule wuri daya na,hada hannaye da kafana wuri daya na nadae, kamar wata yar mage,,,,

   Kusan sau biyu ya shigowa dakin don ya ta dani daga barci,

   Amma yana samuna dunkule ina ta sharar barci na, daganin yanayin da nake barcin yai min dadi,

   Yasan cewa ko kadan bani da lokacin hutu balle har na barci don hakane ma koda yaga magrib ya kusa daidai lokacin da aka hana barcin marance yayi ,,

   Sai yai niyar zuwa yata dani, saboda bai yarda wani ya shigo mai cikin gida har inda nake 

  Don ni dakina ya ta ciki ne inda kusan inda nasu yake,

   Sabanin nasu rugaiyya dake can ta baya kadan inda hanyar kitchen yake,

   Sanin da yayi cewa ina gidan yasa shi, zuwa kirana don in, tashi ,,,

  Ganin ina ta barcin ne har yanzu yasa shi juyawa ya koma, yata tausaya min cikin zuciyar shi,

    Shidai baisan dalili ba kawai yarinyar tana bashi tausayi so sai wlh,,,,,


    Arazane na mike akan gadon gami da salati , nazaune atsakiyan gadon kafana lankwashe cikin na juna,,

   Nadan lunshe idona kadan don barcin bai sakeni ba,,,,

   Azatona magaruba bai mayi ba tukun, yanayin dai garin ne haka, nadan kara lumshe idona daga zaune,

   Idona yana rufen naji kamshin turaren shariff  din wanda yakara dawo wa daniyar yatasheni daga barcin,,,

   Jinkamshi yasani saurin bude idona saidai banyi sa,a ba yariga ya wuce ko tunda ya leko tagan ni a zaune,,,,.

    Kallo nakaiwa agogon bangon dakin zubar na sauko kasa don ina gizo,,, idona ke min ba wai takwas saura nadare,,,, agogon ya nuna,

    Bayi, nafada nadauro alwala na gabatar da sallah a gagauce,,,,

   Ina idar wa natashi na nufi hanyar cikin gida don indiba abinda gidan keciki ,,,,,,

    Don koni dan karen yunwa nake ji don harda kugi cikina keyi,

    Ina tafe duk su hajiya nake tunane ko yaya suke can ko may zasu ci tunda ba girki takeyi ba,,,

     A dining nasamay sherriff din zaune yana cin abincin shi daya,,,

   Haka kawai ganin shi yasa kirjina bugawa don na tuna da fadan da yai muna dazu,

    Yanzu gashi don jin dadi da samun,wuri na zo nayi kwance inata sharar baci kamar wace Abadan bata da aikin yi,,

    Cikin girmamawa na gaishe shi,,,, 

   Amma maimakon ya ansa min sai dago wanan yadaurarren idanun nashi ya watso min, wanda kulun yakale ni dasu  ban iya gane komai acikin su,

   Shima tambayana yayi kinci abinci kine,

    Batare dana bashi ansa ba

    nace madan bata fito bane, sai kawai na nufi hanyar zuwa dakin ta, nashiga da sallamata,

   Zaune take cikin wata yar rigar barci wanda yake dan iya nuna surar ta waje,

   Dan damtsen hannuta yadan wani murde kamar na matashi kato,,,

    Kanta duk da an gyara shi wai yau yawani yi tsirma tsirma dashi dayake guntun gashi gareta,

    Waya takeyi, har na juya kamar in wuce sai na hago cup din dana kawo mata shayi dazu saina nufi inda yake indauko,

     Jin maganar da tajeyi awayan yasani  faduwan gaba duk na,riki ,

   Saida nayu kokarin saita kaina, don kada tasan cewa ina jin hausa,, don ita duk dauka takeyi, banjin hausa ko dan turanci sai larabci kawai 

     Abinda naji tana fadi shiya tayar min da hankali sosai hankali,sosai 

    Cikin rashin damuwa da inajinta tacigaba da fadin, 

    Wlh duk da auren dukiya nai mai salwa yanzu ina son Ahmad,

   Kafin in fara yaudarshi sai na dan more rayuwata dashi,

   Hmmm zancan kawai hjy ke yi, kina tsan manin cewa zai ta bani kudine a haukace,

   Ganin da tayi nadauki cup din kamar zan fita taimin alama da hannu cewa wai in dakata har ta gama wayan,,,

    Cigaba tayi da maganar ta, Salwa don dai baki ganshi bane shiyasa kike cewa hakan

    Yo nima dana fara ganin shi ai,saida na manta da plans din mu,

    Takare karshen zance da cewa ai dole inbi a,hankali don in Daddy yagane plan din hjy duk mun mutu Salwa,,,

    To sai kin kirani din,,, takashe wayan tana kallon inda nake tsaye 

   Niko alokacin duk nagama rudewa kokarin saita kana kawai nayi,,,

    Yadda naga ta dan zuba min ido yasa nadan tsargu,

   Saidai kuma naji tayi dan tsaki tace, waima ko taya zan ma wanan mara hausan magana fahince ni,,,,,,

     A,lamatai min kawo mata abin sha jiki ba kwari nabar daki nata,,,

    Hankalina a,tashe anya kuwa ba munafuntar Sheriff wanan matar keyi ba, au har ma shakukeyi inji wata zuciya tace min hakana keda yanzu kikaji komai ,

   agaban ki fa akai maganar komai kina ji ba labari aka baki ba ji kijayi,,,

   To inko hakane gaskiya akwai aiki ja agabana 

  Wurin wasu kujeru dake tsakiyan coredon gidan na isa na zauna gami da buga tagumi,  don dai inji dadin tunane, don gaskiya dole in taimaka ma Sheriff nima saboda shima yataimaka min a rayuwat, lokaci da dama,

   Minti goma tsakani na tashi na shiga dakin 

   Wanan karon bisa gado take kwance tayi daidai da ita saman gado da alama akai abinda take tunane,

   Dakatawa na danyi na kare mata kallon tsab sai naji wani tsanar ta  ya shiga zuciyana,

      A sanyaye na karasa gareta na aje mata dan tiren da na hado mata abin shan sama wani dan stol .

   Juya nafito dakin nabar mata cike da tsanar ta,a raina,

   Tausayin Sheriff din naji ya kaman,,,

    a gaskiya dole ne indan taimaka mashi batare da sanin saba,

   Ajiyan zuciya nasaukar daidai lokacin da nagama tunane mafita,,,


    Dole wanan ranan agidan muka kwana, saboda dare yayi ba damar mu fita waje,,,

     Tunda safe dana tashi bayan mun kanmala komai, 

   Naje gun mama mai abinci na fada mata cewa, zanje gida indiba yaran nan biyu,

   Batare da nafada makowa ba na gidan n sulale naitafiya na,

    

  Motar shi yadauka don zai je yadan zagayo wurin aikin su dake cikin gari ,,,,

    Har yadan fara tafiya sai ya lura da wani leda a,gefen kujera, daukowa yayi yadiba sai ya mayar inda yaga ledar, aje,

  Har  Saida yaje yadawo inda zashi ne yadauko ledan ya shiga dashi cikin gida,

     Dakin shi yashiga da ledar ya aje, batare da yayi cigiyar mai ledar ba,

   Falo yadawo don yadan huta, saidai yana zama sai yaga ai kamar yadda yabar falon dazu da safe haka yakara samun shi,,,

   Wayan intercom yadauka yana son kirana 

    Yayi kira kusan sau uku amma ban,dauka

   A fusace ya fito falon yana kokarin yaga ankira ni, saidai an fada mai fita zuwa gida amma nace bazan da de ba zan dawo, yan zun nan,,

   Ranshi bace yakira almustapha yai mai kaca kaca kan sakaci da aikin da nakeyi,..

     

  Agidan mu kuwa gaskiya nasamu hajiya ta kula da yaran don ta basu abinci kuma tai masu wanka,

    Suna gani na suka yo kaina da murna suna nuna farin cikin su na gani na da,sukayi,,,,,,,,, 

   Jawo su nayi a jikina ina farin ciki da ganin su,

    Saida muka gama yar hiran mu naje gurin hajiya muja gaisa na fada mata cewa ruwan samane ya hanamu dawo jiya,

   Tace min ai,gara da muka tsaya can don da munce zamu biyo hanya za,a iya kama mu a,lokacin,

   Nadan kai wani lokaci a gidan tare da hajiya da yaran inda na dan kara gyara wuri,

   San nan mukayi sallama na koma  cikin sauri don sai yanzu nafarga d lokacin da muke ciki,

   Tabas nasan cewa na bata lokaci sosai a gida tare dasu hajiya,

   

      Ina shiga gida tun abakin get aka fara fada min cewa Sheriff yana bida na,

   Babu fargaban komai atare dani nasa kai cikin gidan don ansa kiran Sheriff

    Da salamana na shiga falon, zaune yake cikin shigar cort da wando irin ta maza, saidai ya cire cort din ya sagale ta gefen kujera,, daga shi sai wata farar riga yar ciki mai dogon hannu,

   Tare yake da wani bakon mutun sun zuba tulin takardu suna diba,

    Ganin yana aiki kuma ba shi kadai bane agurin yasa nai shirin juyawa don in,bar wurin,,,,

    Ke yace min cikin daga murya saidana dan ja baya kadan 

   Ina kikaje lokacin aiki , kin ko san ka,idar aikin da kikeyi kuwa,

    Kaina yana kasa bandaga ba balle in kalle shi,

    Wakike son yabar aikin shi yakama maki naki aikin dibà nan ki gani yadan sa yatsan shi yagoga dan  teburin glass din,

    Tare da nuno min ya tsan wai indiba ingani ido nadan daga nakali abinda yake gwada min 

    Saidai ni,banga ko mai ba,

  Amma shi cewa yayi wai aiga datti nan ko ina a falon ,

    Falon nakara bida ido don indiba kozanga dattin da yake nuna min banga komai ba,

    Shiru kawai nayi ina sauraron shi,har yakare, kuma daga yau in har zaki iya aiki da mu to dole komai naki yadawo nan gidan, har kwanan ki,,,

    Saidai kalman shi ta karshe ce ta razana ni har na fidda idona waje,

   Waje don kidima,

Idan  har bazaki iya ba ga hanya nan ki tafi, sai in,dauki wata,

    Kawai ya juya yaci gaba da abinda yakeyi batare da yakara kulani ba,

    Nadan dan yi,jim nadan wani lokaci don mamaki  kalaman shi da yai min cikin kakausar murya 

   Cikin yar muryana mara sauti nace mai,amma kasan cewa inada tsohuwar da bata da lafiya dakuma yara,,,,,

   Zancigaba yadaga min hannu batare da ya juyo yakaleni ba idonshi naga aikin da yakeyi 

   Yace hakan naga dama kuma ban shirya jin ko wani irin korafi ba a yanzu

   Idan zaki iya kije kiyi inko bazakiyi ba,

    Yahada hannayen shi wuri guda alamar ma,assalam 

   Falin nabari cikin sanyin gwiwa don na ma rasa ta, ina zan fara,

  Kitchen na nufa nakira antyna Rugaiyya na fada mata duk yadda mukayi yau da sheriff din,

   Flower da zata kwaba tayi ambuss da shi don abincin dinner ta dauka a wani dan silver ,

   Tana fadin fadima inbanda abinki aikema kinsan aikin ki aikine mai daraja ,ba aikine na wasa ba,

   Don kinsan duk wani kulawa na mutanen gidan nan yana akanki ne

   Wanda ko da acikin dare ne bukatar hakan yataso dole ne ki yi aikin ki,,,

    To idan baki nan waye zai masu fadima,

  Kinsan cewa wanan aikin da muke yi a gidan nan yafi duk aikin da mukayi a wanan gari sauki,ga kuma kudi masu albarka da ake bamu 

  Koda kin fadawa hajiya bazata yarda ki bar wanan aikin ba sam,

   Don haka tun wuri ki wa kanki fada ki zauna gurin aikin ki

    Zanyi magana ta daga min hannun da take kwaba flower dashi tace min ya isa, 

   Ina dai yaran da kika jajibo wa kanki wahala kike tuna ne ko,

   Kaina kada mata alaman eh, tace min to ai mu ,muna gida zan dan dinga kula maki dasu gwargwado,

  

  Hakan ne dalilin dawo wana ,da zama gidan aikinawa,

     Don ko hajiya da naje gida na fada mata ansar guda ce in koma can kawai din,


   Yau kusan satina guda agidan ban zuwa ko ina kulun ina cikin gida , bawani kwareren aiki amma wai aiki nakeyi a,hakan,

     Yau da marance kamar kulun mun gama komai mun hada aikin mu na yau

    Na shirya cikin wasu doga yen riga mai dan kalar rainbow,

   Ina dakina ina kallo wani tashn da ake yin wani gasan talent na larabawa,

   Sai naji kamar  marana yadan murda min aikuwa sai gaba na ya fadi don in har ban manta ba yau nake expecting din period dina,

    Gashi kuma banda magani anan yana gida na bari,

 Kadanda  nasawo ranan da muka fita da a,maryan sheriff ya fado min arai,

   Ban gama tunanen da nakeyi ba naji wayan dakina nakirana,,,

   Alamar ana bukatana acikin gida,

    Zaune suke a haraban gidan shida wasu baki suna tataunawa, 

    Kayan jika makoshi suka bukata, 

   Lafiya  lau nakawo masu, na juya nabar wurin nabasu baya kadan aiko sai na kasa cira kafana,

   Dukawa nayi wurin nadafe cikina,

   Marana kamar zai fashe nake ji na,

     Bango na dan fara bi don insamu inkai dakina,

 Aiko na kasa, idona ya kade yayi ja,

   Cup da magani naga an miko min,,,,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎

[10/4, 14:30] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                    4⃣4⃣

                       BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

 

Matan huguma group Allah ya kara daukaka, 

    Allah ya shirya muna zurian mu ,yasa mugama da duniya lfy,,,,,,


Almost true life story
   Ban san lokacin da na karbi maganin natura baki ba  duk da ban gane kalar magani ba kowane,irine nidai muradina insha magani,,,

   Cikin rawar hannu na karbi cup din na,sha ruwan kadan,

Ina hade, Ruwan da magani    Nakara dunkulewa wurin, saboda wani irin azaban ciwo da naji,,,,,

    Duk da ina jin kamshin perfume din shi ya,na  tashi yana shiga min cikin kai,,

   yau ciwo ya hana ni yin re,acting din komai,

    Kamar kar maganin da ruwa su shiga cikina aiko sai na kara dunkulewa saboda wani irin azaban ciwo dake damuna,

  Cup din na sha ruwan yana rike  hannun shi , ya wurgat da cup din gefe guda,

   Dafa min kafada yayi yace min in dan tashi in shiga ta cikin gida,,,

   Ai,kafin ince zan tashi wani irin amai ne ya zo min nai kokarin indan kauce da kaina,gefe, kadan don kada aman ya taba shi,,,,

  Amma, ina kafin in haka aman yazubo ko,,,,,

  Duk na,wanke mai jiki da shi,,,,

    Sannu kawai yake ce min, cikin nuna rashin da muwa,

  Ina samun yin aman sai nakama wani irin zufa, kamar nasha ruwan masu mugun zafi,

   Idona yadan kama rufewa a hankali, ahankali har ya rufe lub,

    Nai lu, zan fadi kasa yai kokarin yasa hannu shi guda ya tallaboni dashi,  

    Almustapha yakira da sauri ta cikin wayar shi,,, ya fada mai ya zo da sauri ga in da yake,

    Almustaph yana zuwa yaga irin yanayin da nake ciki, shima sai hankalin shi ya tashi,,,

    yace ma Almustapha ya dan rike ni su kaini daki, na,,,,,

    Har mustapha yakai hannu zai rike ni ,

Komai Sheriff yatuna sai kuma

   Yace mai  dakata ,kada ya tabani,

   Cak yadaga ni sama kamar wata baby yai cikin gida dani mustapha na ce mai ba asibiti zasu dani ba,

   Bai saurare shi ba cikin gidan yayi dani,,,

   Anty nafisa na zaune tana waya saman wasu fararen kujeru, ta hango shi dauke dani ga mustapha yana binshi a,baya cikin tashin hankali,,,,,,,

   dakina suka kaini,direct

   Ya shimfidar dani saman gado,

   Ganin ina zufa yasa suka kuna min AC, a,dakin,

   Barci ne mai karfi yadaukeni cikin dan kakanin lokaci  ,kamar yadda dama maganin ke min aiki da nasha,

   Indai har nasamu nai amai to zan yi dan barci indan na farka sai inji ciwon yadan lafa min,,,

  Kofan dakin yajawo ahankali, yarufe min,,,

   Sai a lokacin hankalin shi yakai ga rigar shi dana sharara mai,amai akai,

   Cikn sauri batare da yace ma Almustapha komai ba,ya nufi hanyar shiga  shiyan da dakunan  su yake,,,

   Almustapha da aka bari tsaye da mamaki yakalli kofan dakin da nake kwance yakuma kalli hanyar da sheriff yabi,,,

   Zuciyan shi cike da wasiwasin akan rashin lafiyar nawa,cikin dan kan kanin lokaci haka,

   Anty Nafisa ce tsaye a falo cikin mamaki da  kuma son sanin may ke faruwa, ne haka, har mijin nata tadau koni, ajikin shi,

    Jikin da take muradin tabawa koda yantsan shine bata samu ba yau ga common yar aiki, cikin shi dumu dumu,

     Wuce ta, ya,yi fu,u yahaura sama abinshi,            Inda dakin shi yake, batare da yako kali inda take ba,,,,,,

   Bin,shi tayi da kallo har ya bace mata, daidai lokacin da mustapha ya fito shima daga inda nake,,,,

   Mustaphane,, yagaishe ta cikin girma,mawa zaidan wuce ,,take tambayar shi may ke faruwa ne,

   Yace mata banda lafiya ne shine suka taimaka min ,,zuwa daki,

   Baki ta tabe nuna ko in kula,,,

    Yana shiga dakin shi ya wurgat da rigan tun a kofa, 

    In akwai abinda yaki jini arayuwan shi ne yaga ,amai ,,,  

   Idan yaga amai bai iyan komai ko abinci bazai iya ci ba a ranan ,,,,,,

    yau gashi , an mai amai a jiki, amma yadaure dashi a hakanan

   Subbahanallah, rin,tse idon shi ,yayi tare da sake shower akanshi, ruwa nata zuba mai,,,

   Yafi kusan minti  goma a haka yadauki sabulu da soso duk ya goge jikin shi dashi, don ji yakeyi kamar aman ya mane mai a fatan jikin shi,,,

   Yadauki lokaci da dama acikin bayin san nan yafito, 

   Ya dan gyara jikin shi jallabiya kawai yasa don lokacin sallah magrib ya kusa,,, saboda har in yana gari duk sallah da zaiyi cikin jan,i ne,,,,,

    Koda yafito zuwa masallaci Nafisa tana zaune, falo ta kure karar tv tashan yan rawan kasar turawa, keta ,tashi,, kamar gidan yan rawan disco,,,,,,

   Mamaki yakamashi fal a zuciyar shi,,,,,, don shi tunda yake gidan baitaba sanin ma akwai wanan tashan ba a,talabijin din,

   Batare da yai mata magana ba yadauki remote din dake saman dan karamin tebur din yarage karan tv,

    Yasa kai yafita zuwa masallacin unguwar inda Shek Abdullaraham bin, Inus,, keba da salla, wanda duk ke wanan uguwar yana jin dadin limancin wanan bawan Allah,,,

    

  Barcin da baifi awa biyu ba da,dan wani kai,,,, nayi, nafarka,

   Zubur na mike,daga barcin, inda naji marana yai min karfi kamar na hade dutse,, 

    Ko kari nayi natashi,Wanka nashiga nayi,

     nafito bakin mirror naje nadan dubi kaina naga nawani ramay kamar wace tayi wani dogon jinya 

    Sallah na fara gabatar wa ina zaune ina addu,a abinda yafaru dani dazu yafado min a rai,

    Cikin mamaki nadan motsa kadan lalai ba shakka sheriff udeen din, mune yabani magani na,

    To a ina yasamay shi sai kuma natuna ai shine ma yakaini asibiti a birnin   madina kuma yai min komai,a lokacin  har naji saukin jikina

   Oho,,, ,, hmmm watau wanan mutumin ,Don tsananin kulawar shi bai manta da lokacin yin period dina ba,ke nan yake nufi ko may

   Wa,iyazu billah,, ashe duk wani motsi nawa yana kula dashi kenan,,

  Da wanan tuna nen natashi zuwa cikin gida don in gabatar masu da dinner dinsu,

   Saboda har yanzu ina dan jin jikina marana ban iya tafiya sosai,

   Amma ya zan iya hada ido da sheriff din namu,,

   Ko da naje falon kowa na  falon zaune cikin dabara nake komai, na hada ma anty nafisa nata, nazo gefen da yake don in hada mai sai yace min yau bazai ci abinci ba in bashi juice kawai sai tea da zai sha  anjima, kawai,,,

    Tsayin da nadan yi don in saurari bayanin shi, yasa marana ya kara kullewa wuri guda sai wani irin azaba ciwo ke kokarin taso min,

   Cikin hikima nadan yi dabaran barin wurin,

   Muryan shi naji tun ban wuce ba yana cewa idan nasan cewa banda lafiyane inje inkwanta mana

   kada in jawa kaina matsala tunda ba kullun ne mutun zaiyi lafiya ba,

  Inkuma har ciwon ya matsa min ne inje inga likita ko za,a san may ke damuna,,,

   Wayancewa nayi na,ce mai kainane kemin ciwo kawai, zai fada min zuwa anjima

   Dadabara naja kafana zuwa cikin dakina,, yabini da kallon tausayi

Ina shiga dakin na haye gado na ,

   Na dunkule wuri guda kamar yar mage duk kafana nashige dashi cikin jikin na nade wuri daya,

    Saida nadan samu barci kadan a,hakan bandade ba na farka don ina son in dan fita, in karsa aikina 

    Ina zuwa   Falon shiru yayi bakajin motsin komai sai karar naurorin dake aiki a falon,

   Kayan tea da yace zai sha na hado mai acikin wani dan karamin ture,

   Nakai bisa tebur din cin abincin su na aje,

   Saida na kusa gama abinda nakeyi a bisa tebur din,

   Na,hango shi zaune can wani dan corner da aka kebe afalon , bakowa ke zuwa wurin ba ,sai shi,

   Don koda nazo gidan nafara aiki saida almustapha, yai warning dina kan zuwa wanan gurin,

   Glass ne aka kewaye wurin dashi sai wasu kujerun masu taushi da tulin takardu, akwai alkur,ani mai girma da sauran litatafan addini ciki, sai computers iri iri,

  Nikan shiga sau daya a sati don gyara wurin,

    Ashe shi tun dazu ya gurin yana tura sako a computer wa mr William,

  Koda zai fito saida suka kwashi artabu da nafisa kancewa, gaskiya ita bata yarda duk dare a ce mutun sai ya fita,,,,

    Ba wani kulawa tsakann miji da mata hankade ta yayi gefe yafito abin shi yabarta tana mita,,,,,

    Ita abinda bata sani ba shine bata cikin rayuwar shi sam don jinta yake yi kamar ba mace ba,

   Shi duk da bai taba taraiyya da wata mace ba a,duniya sai ita,

  Yansan labarin mata yakaranta komai a cikin wani, littafin 

   Mai suna, Surar ya mace na wani shahararen balarabe   marubucin addini, musulunci, wanda ya, wallafa duk yanayin kowace irin mace,

   Ita ko nafisa tadauka bai fahinci komai gamay da ita,ba 

   Tunda tanaganin tasha gyara wurin mamanta kafin tazo duk wani sadda baru da kayan mata an hada ta dashi,

   Shiko anashi ban garen 

 Biyayya kawai yake wa tsohon shi kanta saboda ya fuskanci cewa baban nashi nason wanan hadin auren,,,,

     

      Daga inda nake tsaye na hage shi, zaune yamaida hankali ga abinda yakeyi,kuma hankalin shi a kwance yake aikin 

 , bai,man san cewa, ina cikin falon ba alokacin,,,

   Hankalin shi duk ya,naga computer shi,

   sai yaji a,jikin kin shi cewa bashi kadai ke a falon ba

   Da akwai alaman mutun a falon, baigama tune ba,

    yaji motsi a bayan shi lokacin yasan cewa na shigo falon,

   Daidai lokacin da nake aje cup din da zai sha tean cikin dan karamin tiren da na hada mai kayan tea din ciki,

   Naje in juyo haka sainaga mutun gaba na tsaye, 

   saida nadan firgita, saboda tsoro, nadan waiga inda yake zaune naga tabas shi din ne a gaban nawa,

   Kalo guda nai mai na,kauda ido na gare shi, saboda rigar barcin dayasa cotton ce tana nuna mai surar jikin shi waje,

   Muryan shi naji yana fadin keda baki da lafiya may yasa kika fito yin aiki idan natashi shan tea din ai zan kira nafisa ta hada min,

  Ki koma kawai ki,bar shi  koni da kaina zan hada,,, ,          ba musu na juya don dama daurewa nake duk banjin dadi sam,

     Nafara tafiya naji muryan shi yana cewa kin ko ci abinci

 kai na kada mai alamar a,a 

   Batare da yakara magana ba naga yafara hada kayan tea din da na aje mai asaman tebur, din ,,,,,, tea mai kauri ya hada min ya miko min yace inje insha

   Ya miko mi magani, yace   Kuma in,tabbatar da nasha shi yanzu kafin in kwanta,nasamuace tare da godiya,,,

    Nabar falon a duduke zuwa dakina,

   Tausayina yakara kamashi, don harga Allah yana tausaya wa wanan yar yarinyar da aka sako ma,duniya ta yi rainon ta,,  

   Tunda nasha tea din da maganin da aka bani sai naji marana, da ya kulle min tam yadan sake sosai har nadan ji saukin ciwon 

 wani barci mai karfi ya kwashe ni, a hakan ,,

    Bani na farka daga barcin, ba sai daidai lokacin da ake ta kokarin kiran sallah asuba, 

  Dama daidai wanan lokacin nake tashi, koda agida nake don fara ayukan mu,  yau da kullun,,,,

    Jina nayi cikin yanayin   bako tare dani watau period yazo min, hakan  yasani ni kara yin lankwas bisa gadon,

   Da kyat nasamu natashi zaune na rarafa zuwa bayi don in,tsab tace jikina,

   Bayan nafito sai na tuna cewa aiko nasiyo kadan pad ranan nan da mukafita da anty nafisa

   Shinake ta nema cikin dakin tunda nasan cewa ban je dashi gidan hajiya ba,

   Turo kofan akayi duk da ina cikin wata duguwar rigan da zura bayan fito wana wanakan,

   Saida naji kunyan ganina hakan da yayi ba wani saya jiki,.

    Yajikin yace min nace mai da sauki  ledar dake hannun shi ya,miko min, yace min ina wanan ne kike bida,

  Ledar pad dina dana sayo da muka fita nida  NAFISA 

   Juyawa yayi yana ce min indinga kula da rayuwata tunda ni kadai nasan irin wahalar da nake sha,

   Wayyo Allah kamar in shige cikin kasa don kunya kila yafi minti goma da fita ban iya daga ko kai ba balle in cire kafana, 

    Saida naji alamar bakona zai iya zubowa anytime nai saurin kai ma ledar kalo,

    Tabas ledan kadan pad din da na siyo ne, ranan,

   Haka nadaure na dan shiya jikina tsab cikin nasa wando da rigar jeans don gudun wahala,

     Abokiyar aikina ce ta shigo dakina da ture a hannun ta ,

   Kayan tea ne acikin shi sai sauran abin karin kumalo 

   Nai,mata godiya tace min sheriff ne yace akawo min nan kuma insha magani na,

      Daga haka bata kara cewa komai ba ta wuce abinta,

   Tundaga wanan ranan ban kara yarda mu hadu da sheriff ba ko a cikin gida 

   Saima muka fara wasan yar boya da shi yana sane da nufi sarai amma yakamar bai gane ba,,,

   Yai tafiya zuwa Riyadh don dama yafi zama can din saboda aikin shi akusan can yafi yawa 

   Yanzu daine ma da su,ke kokarin bude wanan mai,ai,katar ta Abu Abdallah, 

   Shiyasa yake dan yawan zama cikin garin makka so sai,

     Duk kwanakin da yayi bai gari cikin dadi da walwala nayi su, ban shakar komai,

   Daga anty Nafisa kawai nake dan samun takura wani lokaci, don tana da yawan sa aiki,

   Amma dai ba laifi ina ina jurewa da takurar ta, 

  

     Yau aiki yai muna yawa don saida muka gama abincin dinner sai anty nafisa tace muna wai bata son wanan saidai muyi mata wani mara nau,yi taci,

   Don haka dole muka koma girka wani 

    duk da marance yayi muna, amma bai hana mu yin sauri ba,

    Mun,gama komai muna jerawa a table ,ina dan wake ,wake na na larabci ,

    Sai kawai hancina ya sanar min da akwai mutum abayana don fitinanen kamshin turaren sa, da ya gauraye falon,

    Waigawa nayi kadan don in,tabbatar ko da shi din ne,

   Don koda bai nan gidan namu baidaina kamshin sa ba tankar yana gari,

    Ina waigowa naganshi tsaye yana kokarin karba waya hannu shi rike da briefcases din shi,

   Wayan yake karbawa amma hannkalishi naga reni ,,,, ganin hakan danayi yasa nataka a hankali har zuwa inda yake nakarbi dan briefcase din nashi cikin ladabi ina mai sannu da zuwa,

    Koda nabada baya ido yabini da shi yana mamakin yadda yaga nakara girma cikin dan lokaci guda,

    Dai lokacin yakare wayan shi yana kokarin sa wayar a aljihu yadaga kai gefe anty Nafisa ce tsaye tana kallon shi,, cikin mamaki,,,,


[10/4, 14:31] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

       👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

               4⃣5⃣

                  BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎  Almost true life story    Koda suka hada ido da Nafisa sai ya wayan ce zance saboda gudun zargi,

    Yace mata kidiba fa karamar yarinya tafiki hankalin , 

   Ke ko gaisuwa baki iyawa mitun ,

   Tace au to anan zan gaishe ka a gaban yan aiki,

    Bai ce mata komai ba ya haura sama, abinshi,,

    Yau kusan kwana biyu da dawowan Sheriff Ahmad daga Riyadh,

    Babu zaman gida yanzu sam gare,sh,

   Don tunda yadawo aiki sukeyi tukuru, don kusan komai na kamfanin su ya gama haduwa ko,

   Yana zaune a office din shi,sai ga abokin shi Yusuf da suke zama tare a kasar saudiya tun zuwan shi kasar suka hade da yusuf din 

    Shima karatu yazo yi daga kasar ghana,

  Halinsu yazo daya shine suka kulla abota, 

   Allah kadai yasan sirin su,

 Shi ya aika ma Yusuf din yazo yaga sabon ma,aikatar da suka hada, wanda tallafin ABU Abdallah ya taimaka masu komai ya hadu,

   Inda shi Ahmad din ne zai kula da duk wani aiyuka na kasa shen, biyu saudiya da Nigeria,,, 

    Yusuf yanu farin cikin shi sosai yayi mai addua da fatan alheri a rayuwan , 

   Office din suka koma bayan sundan gama zagayawa cikin company.

   Zaune yake saman kujera irin da ake samu a kowani kayataccen office,

   Hannu yasa ya zuge nicktie din wuyar shi gadan,

   Yadauki daya daga cikin lemon gwangwanin da aka aje, masu, agaban su,,

   Saida ya dan zuki lemon yakai diban shi ga Yusuf wanda ke kokarin diban dabino a cikin wani dan plate,

     Yusuf din ne ke fadin bamuzo dai munga madam ba har yanzu,

   Ina fatan bakayi fushi ba damu,

   Don dama mun yi magana da sauran Friend's cewa zamu hadu karshen wata mu kawo maku ziyara,

   Saida yadan juya kujera tukun sanan yace ai ba wani matsala,,,

   Kafin Yusuf yaci gaba da maganar shi, sai shi  Ahmad din ya tare shi da wani zance,

   Wai ya batun form din danayi ma gana ne, 

    Duk da Yusuf yagane abokin nashi bai son zan cen da sukeyi ne  shiyasa ya basar da ita,,

   Yace mai Af, kaga ko na manta dasu cikin mota, na fa

   An samo form din har ma guda uku, don dama biyun da kai requesting suna bukata sai nayi sa a aka bani uku,

   Idan mun fita sai inbaka su,

   Sunda jima suna hira gamay da wuraren aikin su, dakuma kasa shen su,

    Yusuf din yai haraman komawa don a madina yake zama shi, 

   Tun bayan gama karatun su nan yasamu nashi aikin a wani makaranta,, yana koyar wa,zaman shi sai yafi karfi a madinan,

     Sun mike lokaci guda sun musabi,a Yusuf din ke ma Ahmad magana akan yayi kokari ya rike amana 

   Don sanin halin shi dayayi kan ko bai son abu zai iya hakuri yayi abin,

  Don haka ma yasan cewa ko wanan auren na abokin nashi ba,ra,yin shi bane ,

  Don tunda suke baitaba jin yai mai zancen wata mace ba saida zancen 

  Tsohuwa dana mahaifiyar shi,

   Sai ko kwanaki da yai mai zancen yana son form din makarantar su don ya siyawa sister dinshi,,,

   Kafin su rabu saida suka dan tatauna so sai kan zancen,,,,

   

    Yau a gajiye yadawo gida, dom haka yana dan bukatar hutu kadan,

   Wanka yayi kafin lokacin sallah yayi ya wuce masallaci bai dawo wa sai an idar da sallah isha,i,

 Acikin shigar jalla biya fara kal, mai yar guntun hannu yake,

    Zaune yake saman kujerar yadan kishin gida kadan kafanshi mike a saman  wani dan stol dake gaban kujerar, ,,

    Hannu shi guda ya sa ya dafe  kan shi, kamar wanda kan shi ke mai ciwo,,,,

    Nasan cewa idan yana cikin wanan irin yanayin bai son damuwa sam

   Saboda nataba, yi mai katsaladan watara naganshi zaune irin,hakana nadinga buruntu da kayan da nake jerawa a dinning har cup ya fado ya fashe,

   Aiko ya mike tsaye ba shiri, naji ya ce Ya, Subahanallah,,

    Kofa yanu min da in fita falon , 

   Nikuma ina kokarin nuna mai cewa zan kwashe glass din da yafashe, ne

    Wani uban tsawa yadaka min ban san lokacin da bar falon ba, don tsoro,

   Ina zan yarda wanan katon yamake ni,

   Saida nabari yafita nadawo na kwashe glass din ina yi ina waigen hanyar shigowa,

   Shiyasa yau dana ganshi a hakan nake taka tsantsan da aikina,

   Hankalina na ga abinda nakeyi sai kawai , ban san cewa anty NAFISA ta shigo falon ba,

   Jin  muryan shi kawai nayi cikin wata irin tsawa yake magana Idon shi ya yi ja alokacin ,,,

   Yace Nafisat nafada maki tun jiya Umurni na baki ba wai uzuri na ce ki kawo mini ba ina fatan kin gane,

   Yadda yai maganar shi ya ba kowa dake falon a,lokacin, tabbacin ba alamar wasa acikin zancen nashi,

   Da sauri ta juya rai bace ta shige dakin ta yabita da harara,

  Muda ke tsaye a gefe wani irin mugun kallo ya watso muna,

   Yamike yabar falon cikin bacin rai shima,

    Nikan ko a jikina don nasan wanan  fadan manya ne, kuma mata da miji,

    Dakinta na shiga don in gabatar mata da abincin su na dare,

    Waya nasamay ta tana yi cikin fada, take magana

   Yanzu ummi kamana zaice wai tunda zai yi baki dole sai naje kitchen da kaina na shirya masu wani abincin alfarma, irin ta mu ta gargajiya, wai yan aikin shi basu iyaba

   Yo ni ina zan iya girki ko na mutun biyu bale na mutun fiye da ashirin,,,

  Gaskiya saidai yaji kunya amma na fada mai cewa bazan yi komai bani,

   A bangare wace take cewa ummi hakuri naji tana bata , tana cewa abinda zaki samu lada kuma zai jidadi kila ya baki kudi masu yawa a sanadin hakan,,,

   Duk hakkurin da ake bata bata yarda ba sam dom tace ita bata da matsala akan kudi dashi don ko ma may tace tana so zai siya mata, ne,,,

    

   Niko tunda naji wanan hirar ta nafisa sai na dan shiga halin damuwa don nasan cewa koma su waye zasu zo suna da matukar mahin,manci a gareshi,

   Don haka na kudiri aniyar zan fidda shi wanan kun yan isha Allah,

   To saidai matsalar ban san wani rana bane bakin zasu zo muna,

   Almustapha ne yafado min a rai,

     Nasamay shi yana shirin fita,

   Da dan saurin nakarasa inda yake, shiko yana gani na sai yadan dakata min,

   Bayan nagaishe shi ne nake tambayar shi don Allah ko yasan ranan da bakin Sheriff zasu zo,

  Yace min aibanda gobe ne zasu zo abokan sheriff ne da da matan su, da suke zaune nan kasar saudiya sune zasu zo ziyar shi don suga amaryan shi,,,,,,,

     Naidai nasamu almustapha yai min bayanin komai a cikin hikima,

   Najidadin jin wanan bayani sosai duk da bayanin yazo min a kuraren lokaci,

  Banshiga cikin gida ba direct wurin su Rugaiyya na nufa,

   Naimata bayanin komai acikin tsanaki ba mu bata lokaci ba maka kama shirye,shiyen kayan da za mu bukata wurin aiyukan,

   Tun wanan, lokacin ban samun zama gida ina nan ,ina can, sai zirga zirgan nakeyi kawai,,,

 

   Duk da ya lura da cewa ba wani shiri da nafisan kewa bakin nashi , hakan baisa yadauki wani mataki ba,

   Ido kawai yasa mata don yaga gudun ta,

 Azuciyan shi kuma,yasan abinda ya kulla zai matan nadaukan fansa,

    A,na mu bangaren bayanin da mustapha yai min na taron abokin shi guda da sukaje wani dan kasar mali 

   Shi mukayi amfani da shi muka dan can za namu salon,,,,,

   Washegari, tunda safe muka  tashi masu gyaran gida nayi masu yin girki suna yi,

   Nai decoration din wani fili dake cikin gidan da duk wani abu da ba hause ke gyara gida dashi,

    Hjy laila ce ta taimaka muna da duk wani abinda zamu bukata,

   A fanin abinci munyi masa, da miya tuwon shinkafa da miyar ganye,   tuwon alkama da miyar kubewa,danye, danbun shinkafa yaji carvege,  sai pepper soup nakifi da na kayan cikin rago,

    Sai fura da nono mai kauri wanda yasha sanyin fridge,

  Ga kunun tsamiya da sugari, har da shimkafa da wake da salad,

    Komai an shirya gwanin sha,wa, Idan kagani sai ka dauka ko agida Nigeria ake wani buki ,,,,,,


      Tunda ya iso haraban gidan yaga canji sosai har takai idon shi ya hango mai haraban da muka gyara inda za a ci abincin

   Batare da ya nufi gurin da aikai decorating din, ba ya wuce cikin gida direct 

   Ya mai jin dadin hakan da yagani 

Itako tana zaune falo tasa wani material, ja,dinkin shi yadan matse mata jiki,

   Ta bayan ta yazo yadan rugumay ta kadan saboda farin cikin abinda yaga tayi don sai yau yadan fara cire shakkun ta da yake,

     Godiya da taji yana mata yasa tatsaya sororo tana, kallon shi cikin mamaki,

  Kafin yai wani magana itace tafara magana,

   Tace ban fahince ka ba fa habibi, 

   Murshi yadan yi yajawo zuwa cikin jikin shi yana fadin wanan surprise din haka,

   Tace na may ke nan fa, na taron bakin da kikai muna,

     Tadan daga hannu ta alamar aa bata da masaniya ita,

    Cikin mamaki ya ke kallon ta  takara cewa wlh ban san may kake magana ba aikai 

   Ture ta yayi daga jikin shi rai bace,

   Idan bake bace towa yayi wanan aikin ,cikin ikon Allah dai dai lokacin na shigo falon cikin shigar irin ta hausawa 

   Atamfa ce zani da riga koriya da dan ratsin flawer yello cikin jikin atamfar dinkinta yadan matse min jikina dan dagwas,,, sai gyale dana dan yafa yellow akai na

 Da kagan ni,  Duk alamar girma ya dan bayana min, dan kuguna yadan ciko cif cif ,kirjina yadan kunburo alamar dai nadan kosa  komai na girma ya baiyana sosai ,ajikina,

   Ban ko kula da su ba ina  kokarin nuna wani dan center carpet da za,a dauka zuwa waje

   Kallo duk suka bini dashi na mamaki,

   Sai a lokacin nagan su tsatsaye,,,

   Batare da wani damuwa ba nadan gaishe su cikin girmawa,

   Nacigaba da abin da nake yi abina,

  Da mamaki yabar wurin zuwa sama inda dakin shi yake,

   Yau gezena,shadda yasa mai ruwan chuculate,, dinkin tazarce ne ,,,sai hula yar zanna bukar yar asali da yakafa akan shi ,,,,agogon company rolex yasa a hannu shi takalma bakake, suna wani irin kashe ido,

    Yusuf ne yabugo mai waya cewa gasu nan sun iso ,

    Cikin fara,a nake taron bakin zuwa cikin katafaren falon mu, daguda guda sukai ta iso wa gidan har suka gama zuwa, 

   Saura mutum guda ya rage baizo ba, wanda naji suna cewa Ali baba ,, wai ai baida iyali anytime zai iya iso, daga yamal,,,

    Agaskiya duk wanda yazo wanan yar walimar taron amaryam Sheriff din mu ya yaba da irin tarbon da akai mai sosai,

   Zirga zirga nake tayi cikin jama, don gabatar masu da abin tabawa ,,

  Gefen mata daban na maza daban amma duk da haka ana iya ganin juna don duk guri gudane,

     Wata yar matashir mata fara yar kabilar  yarbawa ce, da baby ta, ina ganin haihuwar fari ce mata,

   Yaron yanata kuka tunda sukazo, tayi lalashi yaron yaki yin shiru,

   Kusan kowa a wurin ya tausaya ma yaron yadda yake ta faman tsala ihu,

   Zuwa nayi na karbe yaron a hannu ta nawuce cikin gida dashi, da ita,

    Ruwa nasa masu zafi nai ma yaron wanka wurin cire pampers naga a she kashi yaron yayi,,,

    Naimai wanka na gyarashi tsab tabani wani kaya na saka mai,

  Lokacin da muka fito wajen taron, mu tararda har an fara cin abinci kowa sai yabawa yake yi da irin girkin da akayi, 

  Nafisa tana gefe fuskata babu ko alamar fara,a 

   Tun matan abokai na janta da yar hira har suka gaji su ka kyaleta,,

   Tana ta wani matse fuska kamar mai jin warin mutane,

   Muna ji suna hiranta kasa kasa suna cewa wanan ai ta tsofe ma Ahmad 

   Wata kuna tace yo ai auren zumunci ne inbashi ina zaikai wanan ai gwago ce,,,

     Gyalen da nasa yana da sulbi sosai, gashi kuma ban iya yafa gyale ba dama sai dai inyi rolling din kaina kawai, gyalen yanata sabule min,

   Ga kuma yaro a hannu na, duk na tsawala ina kokarin mika yaron wurin uwar shi sai gyalen ya karkare faduwa kasa,

   Subbahanallah aiko idon maza caaaaa akaina cikin sauri na jawo gyalen na mayar akaina, daidai lokacin naga sheriff din mu yai min wani irin kallon banza 

   Wanda banji dadin hakan ba, 

   Duk sai naji na tsargu wlh,

  Don ni ban san may nayi ba,

  Daga inda yake yaga nadan shiga damuwa sai yadan yafito ni da hannu, Sukaina ce ke fada min yana kirana,

  Cikin ladabi na isa inda suke zaune shi da su Yusuf,

    Fura yace min in debo masu a cups, 

   Nakai masu furan sai santi sukeyi,,

   Ga al,adan su duk wanda zai tafi sai ya aje wani kyauta mai muhinmanci arayuwar ma,auratan wasu na bada kudi masu yawa, suce aba ma amarya wahalar girkin ta,

  To muma dai haka din ne don wani katon tire aka dinga zuba duk wani gift da aka samu a wurin

   A gaskiya ba laifi don dai an samu alheri so sai,,,

  Muna kallo bakin mu suka dinga barin mu da guda daguda har suka watse suka bar mu mukadai agidan,

   Saida na ga duk mun gyara ko ina agidan sanan nasamu natsuwa, 

   Kayan gift din na hada wuri guda na nufi cikin gida da su wurin anty nafisa,

 A  Falo na samay shi zaune yana waya daganin shi yana cikin nishadi yau

   yana ganin zan  wuce da kayan gift din,inkai ma,anty nafisa,, dakinta sai yadakatar dani da hannu 

   naja nayi tsaye cak wuri guda,,,

  Ina sauraron shi inji mai zai ce min,

   Yana gama wayan ya dakai diban shi gare ni

   yace min in,bude komai yagani a gaban shi na ,aje kayan  

   nan na duka nadinga cire kayan guda gudu ina  kuma karanta mashi,sunan wanda yaba da gift din

   Abin mamaki ina kai ga na karshe sai naji yace min, duk gift din kayan sawan in dauka,

   Kudi kuma in dauka in raba ma duk wanda mukayi hidimar dashi,,,

  Saura in,dauka,cikin mamaki nadago kaina don jin zancen shi,,,

   Zan yi magana ya dago min hannu yace min ya isa

     Jiki ba kwari na tashi don in wuce,

   Sainaji yace min yagode da fitar dashi kunyan da nayi,,

    Ina dan murmushin jin dadi ban san cewa  anty nafisa tana bayana tsaye ba tun lokacin da na fara nuna mai  kayan,

   Gani ta dayi tayi murtuk da fuska yasani dan ja tsaye ,

   Kauce mata nayi nadan bi ta gefen ta nawuce abina da kayan

    Muryan ta naji tana magana cikin tsawa take cewa wanan ai wulakanci  ne,

 tayaya zai dauki kayan yaba yar aiki

 Acikin azama naji yace mata wace,ce yar aiki,

   Nida take gani zaman kaunar shi da suke ciki daya yake dauka, ba matsayin yar aiki nake ba.

  Yace ko kin taba ganin yar aiki tafidda shugabanta kunya kar yadda taga nayi a yau din

   Yace ko kintaba yakara tambayar ta cikin tsawa,,

   Nidai na wuce abina nabarsu nan yana ta gagasa mata maganganu masu zafi,

    Bayan na aje kayan dakina gurin Rugaiyya na tafi,

   Na bata labarin yadda duk mukayi da Sheriff din kan gift din su,,

   Ta dafa min kafada tace fadima halinki ne na alheri ya ja maki,

   Duniya ance indan baka da kudin da zaka taimaka wa mai kudi to kataimaka mai da karfinka,

   Kinga kinfitar shi kunya , 

  yin hakan yasa shi jin dadin alherin da kika mai a yau ko mai yai maki kin can can ci hakan ne fadima,

   Tana fadi tana har hada kayan ta don zuwa gida na mika mata kudin duka nace mata ta aje cikin wanda muke tarawa,,

   Ashe duk kudin na a cikin jikin ta nan take boyewa gudun kada a sace muna,

   Saida ta hada komai tadauki jakar ta da dan abincin da zata kaiwa su hajiya da su Umar,

   Kawai sai naji banji dadin da zata wuce ba jinayi dama muntafi tare don ina kewan su hajiya, ina son ganin su ina son in kwanta tare da su muyi ta waka da labari har barci yadauke mu kamar yadda mukeyi kullun,

    Ina kallo ta wuce ni raina yai min baki,kirin 
  Rugaiyya har ta kai kusa da gida ashe bata sani ba yan bagaladi suna biye da ita, 

   Tundaga unguwar su sheriff din mu  suke biye da ita tunda sun san cewa duk bakin da akayi sun koma garu wan da suka fito, su,,,

   Bata ankara ba kawai taji sun kewaye ta sun mata circle, ba ta da daman gudu,,,,,,,,,,🐎 ZEEE MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

[10/4, 14:31] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                 4⃣6⃣

                    BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA 🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


Allah ka tai Maki Musulumi Duk Inda yake,,,, ,Ya Allah Karufa ma Kullumin musulumi na Duniya Asiri Ameen


    Anty Halima Garko 


Almust true life story,,


   

  Wa,iyazu billah abinda kawai take fadi kenan idon ta a rintse ,

   Inbanda Allah ba wani abinda take iya fadi,

   Basu yi wani dogon bincke ba suka gane cewa takaru ce ita bata da takardan zama yar kasa,

  Rugaiyya bata basu wani wahala ba don haka bata wani sha wuya ba, wurin su,

   A, haka suka tafi da ita zuwa inda ake tara kamamun irin su,,,

   Duk wanan abinda yafaru a idon wani makwabcin mu ne, yana ganin an wuce da ita ,

   Da saurin shi ya isa gidan hajiyan mu yana sheda mata duk abinda yafaru,

   Sun yi kuka sunyi bakin ciki sosai wlh,

    

    Ina can dakina jiki ba kwari tunda anty na ta,tafi har na kwanta sai naji bana jin barci , duk da gajiyan dake jikina,

    Don haka sau,kowa nayi daga kan gadon na zauna kasa,

   Kanya gift din da aka bani na jawo ina fitar wa guda guda ina kalon su,

    Duk kusan dogayen riguna ne har guda hudu nace a raina sai muraba nida Rugaiyya na

    Sai  kuma dikin shadda redmaid masu kya kusan guda uku suma nazabi guda nace biyu in bata tasa don tana son irin wanan kayan tun muna kano,,,

    wani kwali da najawo waya ce mobile cellular mai shegen kyau, cikin kwalinta tare da tarkacen ta,,, 

   Aiko ina ganin wayan ban san lokacin da na ture komai na hau murna ba,

   Koda banda wanda zan kira na dade ina sha,awar waya kodai photo na kalla kuma inyi game,

    Jona ta nayi a wuta don ta samu caji,

   Ganin wanan wayan yasa nakasa karasa kallon kayan da nakeyi,,

    Nakoma saman gado na kwanta ina jiran wayan tayi caji,

   Maganar da naji sheriff nayi da matar shi yafado min a rai na,

    Allah sarki sheriff ai nice ka taimaka don ban manta irin taimakon da yaitamin can baya kafin ma inzo gidan shi,,,

     Juyawa nakarayi ina Allah Allah gari yawaye in nuna ma Rugaiyya wayata,

   Da haka barci barawo ya dauke ni,

   Firgice natashi duk jikina yajike da zufa,

   A c na kalla naga yana aiki, har nadan gyara kwanci sai mafarkin da nayi ya fado min a rai,

   Gabana ne ya fadi dammmm,,,

   Tiryan tiyar na fara tuna abinda nagani a mafalkin nawa,

   Rugaiyya ce ke shiga cikin wani abu mai matakala kamar gidan sama tana murmushi tana min bye,bye,

   Zubur na mike don wani zafi naji tundaga kafana har cikin kaina,

   Bayi na fada nai wanka cikin daren nan nadauro al,wala nazu nayi nafila raka,a hudu,

  Nan wurin na zauna har akai asuba 

   sam jikina bana jin dadin shi wlh,

   Barci ya kara kwashe nan gurin da nai sallah asuba,,,

    Wanan karon Aisha yar karama nagani ta kankamay ni ajikin ta,,, tana kuka,

   Zubur natashi sai naga ashe har hasken rana yafito yau ban fita ba,

   Cikin sauri nadan gyara jikina kodan make-up din danakan yi yau ban tsays yi ba,,,

   Kitchen nanufa direct ina shiga sai naga yau mama mai abinci ce ita kadai tana aikin breakfasts taya ta nayi muna sauri don kada sheriff din mu yafito bamu gama aikin mu ba,,

   Tun ina hakkuri har nakai ga magana nace ma mama yau babu wace tazo daga gidan hajiya wai ko lafiya

   Ba,afi minti uku ba sai ga su sun shigo , daganin su  suna cikin tashin hankali,

    Ban kula sai cewa nayi aikin da muka sha jiya duk ya sa mu gajiya,

    Nadauki kayan break din nafara kaiwa falo aiko na iske sheriff na saukowa daidai lokacin muka gaisa da shi sama,sama nakoma don in dauko sauran kayan

   Abinda kune na yaji Sukaina na fadawa mama mai abinci yasani yanka wani irin ihu, daga inda nake,

  Duk suka razana don basu san cewa har nadawo ba,

   Yake jiki nayi nafadi ina ihu mai kunar zuciya,

   Duk wanda ke gidan sauri take yi ya iso inda ihun nawa yafito,

   Kusan ta,tare suka iso gurin,

  Duk kan mu kuka muke yi har mama mai abinci,

   Cikin tsawa Sheriff din ke tambayar mu abinda ya faru,

  Sukaina ce tai karfin halin fada mai abinda yafaru da Rugaiyya jiya bayan tabar nan gida a hanyar ta na zuwa gida,,,

    Shima ya shiga tashin hankali sosai wlh don baiji dadin ace ta sanadiyar shi hakan yafaru ba,

   Inda na rakube jikin wani standing fridge ina kuka ya kalla,

   Ya kau da kai don jin tausayi saboda ya tuna da labarin da Anty nawa taimai a madina lokacin da banda lafiya,

    Nafisa duk da bata jin larabci tasan cewa wani abu munmuna ne yasamu Rugaiyyan,

    Barin kitchen din yayi zuwa falo inda Nafisa itama ta rufa mai baya,

   Da ya juyo ya ganta ya dakata, har ta iso yace mata, ke baki da tausayi ne abin kuka yasamay su , amatsayinki na mace yar uwan su baki tsayawa ki basu hakkuri,

   Sai cewa tayi yo ni maizan masu tunda basa jin hausa basa jin turanci,

   Ta kaici yakama shi yama rasa may zai ce mata, yaji sanyi,

   Ga sautin kukana yana ji har inda yake tsaye, yana tayar mai da hankali,,,

  

  Muryan mama mai abinci ne naji tana cewa inda za,aga cikin shugaban nin mu na takari ai masu magana wata kila akwai yadda za,ayi sufitar da ita,

   Jin hakan yasa hajiya laila ta fado min a rai,

 Batare da bata lokaci ba na koma daki na na shirya cikin bakaken kaya irin namu nadauko takalmana Tommy nasa nadan gyara fuskana kadan jakata nadauka,

   Nafita cikin sauri taxi natare nace akaini Masfala, by pass,,,

  Tafiyan minti kusan hamsi yakai mu maspalan naba mai taxi kudi 

    Gidan hjy laila na nufa kai tsaye  nasa may ta tana shirin fita, wai zata SHARMANSOOR gidan wata aminiyar ta batada lafiya,

   Kallo daya taimin tasan ba lafiya,

   Cikin tashin hankali take tambayana may yafaru,

  Ina kuka nafada mata abinda duk yafaru da Rugaiyyan

   Itama hankalinta yatashi sosai wlh,

   Tashi mukayi zuwa gidan wani  Alhj Aliyu bandi shugaban matasa na wanan erea din

    Bayan bayani da mukai mai ne ya nisa yafara fadin akwai kudi ko da zasu bi sugani ko za,aiya fitar dasu,

  Nace ma hjy laila duk kudin namu na wurin Rugaiyya dashi ta wuce,

  Kassh yace yawani dafe kan shi, yace ashe ba zancen bi kenan

  Kusan wuri uku mukaje amma zancen shine akwai kudi,

   Daga karshe dayake hjy laila bata iya cin amana ba sai tace min in kyale su mudawo gida,

  Gidan ta muka koma tai ta min nasiha ta kwantar minda hankali,

  Muna nan zaune kafin in tafi mukaji ana sallama da hjy laila mun dauka ma ko maganar Rugaiyya ce aka samu wani labari

    Da saurin mu muka fito shugaban matasan takari na uguwar da mukafara zuwa wurin shine yazo,

   Yan dan wani sosa kai yana gyara yar falmaran da ya aza saman nalabiyan,

   Hajiya tace mai Alhj bandy lafiya dai ko sai yace a,a dama nazo inji cewa ita wanan din a ina take da zama,

    Kai haji bandy walahi kafita idona,

 Kaida keda mata uku a ina zaka sa wanan din 

  Haba hjy kada muyi haka dake fa tace mai har hiya da haka ma sai muyi,

   Inajin haka na banka mai wata irin hara na wuce cikin gidan hajiya,

   Ban wani dade ba nai sallama da hajiya laila mata mai mutunci da karan ci 

   Taimin alkawarin zata zo gidan hajiyan mu don jin bayanin may ake ciki.

 

   Koda na isa gidan hajiyan mu a tsorace na samay su ita da umar da Aisha,

  Suna gani na duk sukayo kaina suna kuka, 

  Tausayin su ne ya kamani har cikin raina tundai hajiya kuka takeyi kamar wace akaiwa mutuwa mai karfi,

   Saida naga maran ce yayi nace zan koma gida saboda yanayin hanya,nai ma hjy alkawrin zandawo badadewa ba,,,,,,,,,

  Ashe can gida kuma hankalisu duk ya tashi saboda rashin gani na da basuyi ba, din fita nayi batare da na fada ma kowa ba,

   Ina shigowa gida nagan su hankali a tashe duk sunyi tsaye cirko cirko a wajen gidan 

  Fadawa nayi a jikin Yumma ina kuka mai kona zuciya cikin sauti mai ban tausayu

  Dafani naji anyi a hankali nadan waiga sai naga sheriff din mu tsaye bayana handkerchief ya miko cikin dakiyar murya yace min kukan ya isa 

   A hankali nadan tsagaita kukan nawa, Almustapha yace ma abude masu yumma dakin ma,aikatn dake ta baya su zauna ciki kafin ansan abin yi,

   Ina ji haka cikin kuka nace hjy da su Umar fa,

 Wurin wa za abarsu,

   Da Yumma suka tafi dashi hargidan namu sun samu har sun rufe gida ta kwan kwasa musu dakyat suga bude masu bayan muryan ta da sukaji 

   komi da muke bukata yumma ta ta dauko muna 

  bawani abinda zai iya nuna shedar cewa mun yi zama, agida koda anzo bincike,,

    Sam bansan cewa anje dauko hajiya ba dasu umar,

   Gani Aisha kawai nayi ta rugumay ni tabaya,

   Wani irin dadi naji dana gansu tare da mu,

   Ashe ko mungode Allah mun gode ma sheriff din mu, 

   Don cikin dare yan samay suka kawo muna farmaki don suna zaton cewa ba rugaiyya bace kawai a shiyan,

   Koda suka shiga gidan namu ba kowa sai yan tarkacen mu na aiki,

  Basu gane komai sukatafi don sun san cewa ko sun tanbayi mutanen uguwar ba su gane komai,


   Tunda akasa su,a ajirgi kasar, Niger jirginya je ya sauke, 

   Dayake ita tana da kudi tab ga jikin ta sai bata samu matsala ba sosai,

    Motar zuwa Nigeria ta shi ga sai kano,

   Da wayon ta tabar gida don haka bata sha wani wahala ba wurin gane gidan su,,

  Mahaifiyar ta na daka a soron gidan su taji sallama 

  Tana waigawa sai taga wata yar gayu kamar  Rukaiya amma dai wanan din tana da haske 

   Zuwa tayi da gudu ta rugumay mahaifiyar nata tana fadin 

   Ashe da rabon zan kara ganin ku ,

   Nan ,da nan gida yacika da jama,a yan zuwa gani bakuwar makka,.

   Kamar yadda takari kan dawo aimasu rade radin sun je yawon duniya ne hakane yafaru ga Rukaiya 

   Zancen ya bazu dan kauyen nasu Rukaiya tadawo daga yawon takari da tabi wata hajiya mai kudi saudiya,

   Tadawo bata da komai, sai hakorin makka da tasa a bakinta,

  Ita dai komai batace ba don yanzu ba lokacin bayani bane,

   Saida komai ya lafa bayan kwana biyu cikin dare ta zauna da yan uwanta tai masu bayanin irin rayuwan da tayi a makka, 

   Tabasu labarin abinda hajiya tai muna da kuma yadda ta baro mu can,,,

   

   Sai bayan komai ya lafa matane tasamu wani malami tace ya raba muna kudin tsakani da Allah yadda baza ta cuta min ba.

   Bayan an raba kudin sai tafara business da nata,

   Saboda a lokacin duk matasan garin su maza, ba wanda ya nuna yason ta don gani sukeyi karuwan ci ne taje yi can,,,

   Sai wani dan uwantane mai mata guda ace wa dashi hamza shine ma yadan nuna yana ra,ayinta,

   Bata kulashi ba don tasan cewa baza tai zaman lafiya da matar shi ba don haka share kowa tayi,

  Takama sana,ar ta haikam, taje kano tasaro kaya kala,kala zo kauyen su ta,saida,,,,,

  Cikin hakane ta hadu wani dan kasuwa a kano wanda ya yaba da hankalin ta yanuna yana son ta da aure,

  Ko shi Harunan da yazo neman aurenta saida aka ja shi gefe aka fada mai yakosan ta taba zuwa yawon duniya har kasar saudiya,

   Duk da hankali shi yatashi sosai da jin wanan maganar sai yadan dake yana son ya kara gwada hankalin ta yagani,

   Kamar ta sani bayan ya koma gida suna waya shine ta dan bashi labarin rayuwanta kadan,

  Saida ya nisa tukun sanan yace mata ai an fada mashi akauyen su da sukazo,

  Saidai shi yabari ne dama yaji daga bakin ta kozata fada mai,

   Idan har bata fada mai ba to tabbas gaskiyan mutanen kauyen ne yawon baza ta,tafi,

  Saigashi kin fada min da kanki,

   Rukaiya nayarda dake dari bisa dari don bakowace mace ce ba zata iya fadin gaskiya haka,


    Kafin ayi bukine ta shirya tafiya zuwa sokoto,

   Kamar yada akai mata kwatancen garin mu,

  Da yake tafiyan safiya tayi sai ta isa sokoto da dan wuri wuri marance bai riga yayi ba sosai

   Motar da zai kai ta dogon daji tayi shata ,

   Ana batun kiran sallah magriba ta isa garin dogon dajin

  Tambayan gidan inna yar kulu tayi batare da bata lokaci ba aka nuna ma driver gida ,

   Har kofan gidan namu ya kaita

   Yafido mata da kayan ta, taciro kudi tabashi tana godiya

   Wasu yaran makwabtar mune da ke wasa saman yashin da aka tare gefen gida makwabcin mu,

   Sutakira sukazo suka kwashe mata kayan ta zuwa cikin gida,

     Ina dake alwala taga yara nata shigowa da kaya niki niki akai,

  Sai kawai ta dakatar da alwalan tana kallon ikon Allah 

   Saboda dai yar matashirya matan da ke bin yaran inna bata taba ganin ta ba,

   Asalima dai ba yar gari bace, ita daganin ta

    Sundan gaisa sama sama sai anty tace abata buta taje tayi alwala

   Ba musu inna ta bata butan  itama,,,

   Tabar man kaba kato inna ta shimfida masu a waje don suyi sallah

   Bayan sun gama ne sun gaisai sai shiru ya biyo baya,

   Anty ce ke tanbayar Hafsat da datti kanin mu 

   Mamaki inna tayi da jin bakuwar birni har tasan sunan yaranta

   Can dai inna ta daure tace ban fa waye kiba yar nan,

   Rugaiyya tai murmushu tace daga wurin fadiman ki nake,

 Wacce ke saudiya zaune

   Cikin kidima inna ta kara matsowa kusa da Rugaiyya tana rike ta tana fadin ina fadima,

 Allah kada ka kasheni sai ga fadima na roketa gafara,

    Rugaiyya ta kwashe duk labari na da ta sani ba inna har zuwa ranan da aka kamata,

   Saida inna ta nisa san nan tai ajiyar zuciya mai karfi 

Sai kuka shaaaaaaaaa

     

      Nandai suka kusan kwana suna labari kamar sun san juna dadewa,

   Tunda safe tadauko kudina taba inna mu ,.

   Sam inna tace bata karba takoma dashi can biirni taita juyawa,

   Saida kyat akasamu ina tadan dauki dubu dari uku kawai daga ciki,

   Anyi ta zuwa gani  bakuwar inna,,

 Dakuma son jin wai fadima na makka,,,,,,,  

🐎ZEEE MAKAWA🐎


✈✈✈TAKARI✈✈✈ 

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                4⃣7⃣

                   BY

  

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎


  Son duniya bala,i ce don babu komai acikin duniya fa,ce rudin shedan, 

    Kusani cewa duniya saida kudi, lahira ko sai da hali mai kyau,,,  


     Almost true life story,,,,


Zaune nake saman gado na cikin wasu rigar barci light pink, wando da riga,

    Nadan sa ma kaina wani hula mai hooking din kan mutum,,,, baka jin komai sai karan A, c dake ta faman aiki,

   Kusan irin zafin da ake yi a wanan kasan,

   Shiyasa idan kana tafiya zaka ga tankin ruwan sanyi masu kudi sun aje gefen gidajen as a sadakatujar, sai dai mutun ya tsiyaya yasha ya wuce,,,

  Shiyasa koda yaushe,AC kune yake muna,,,

  Aisha ce a tsakiyar kafafuna tai barci sai dan buga mata kai da nake yi don ta samu tayi barci da kyau kamar yadda uwaye kewa diyan su,,,

  Wasu hawaye masu zafi ke tsiyayo wa daga ido na, babu kakauci,

    Kallon yariyar nake yi wace tausayin mu ya ke kara sa hawayena zubu min, 

    Yanzu a haka zamuyi ta zama ba wani galihu atare da mu 

   Kulun gamunan kamar wasu marasa gaskiya, ashe mu,

    Kamshin da naji yasa nasan kowaye a dakin nawa,

   Kallon agogon da ke dakin nawa nayi goma da rabi na dare yanzu,

   Sheriff nace cikin siririyar murya, gyara kan Aisha nakeyi don in tashi ,

  Hannu yadaga min alamar in zauna inda nake,

   Ina zaune shima yasamu gefen guda abakin gadon yazauna,

    Batare da ya kalleni ba yake magana,

    Bazaki daina wanan kukan haka ba ko,,,,, ko so kikeyi ki shiga cikin wata matsala, wanda zai saki cikin wani hali,

    Yakamata yanzu ki bidi mafitar da zai fishe ki,ne baki zauna kina wanan kukan ba,

   Dan sheshekan kukan nake yi kadan kadan 

    Muryan shi nakara ji yana cewa kin taba yin karatu ne kai na kada mai alamar eh

     Nafada mai ko aji nawa nake agida kafin gajiye ta zo dani kano,

   Sai kuma  karatun da na a Riyadh wanda baban Nailabin yasa ni,,,

    Ina takardun naki, suke, nace mai suna nan 

   Ya mike yana fadin da safe ki kawo min indiba, ingani,

    Ki kwanta hakana ki daina wanan kukan zan san yadda za,ayi ku koma gida duk kan ku Insha Allah,

    Banko yi mai godiya ba yafita gami da jamin kofar daki na,

    Koba komai naji dan sanyin wanan maganar tashi sosai 

   Don ko waye ke cikin wani hali yana son maidan bashi magana,

    Don haka gyara ma Aisha kwanci nayi najawo bargo muka shige ciki,

   Ba da wani dadewa ba barci yadau ke ni tare da dokin gobe yayi,,

     

    Washe gari ban fito ba saida nayiwa Aisha wanka muka gyara jikin mu,

   Nida ita gurin da hjy mu take muka nufa don mu gaishe ta kafin in fara aikina,

    Umar na dakin tare da hajiyan mu, nan nakaishi ya kwanta don kar mu barta ita daya,

   Saboda yaron nada kwazo yana kuka da hajiya,

   Wanka nasa shi yayi bayan na gyara masu daki yadda yakamata,

    

   Saida nadiba komai na abincin gidan da aka dafa,kamar yadda ya kamata sannan nakai saman tebur din su,

  Nashirya komai neat ,bandade ba naji fitowar su,

   Nafisat na bin shi a baya tana cewa gaskiya ita ba tagane ba duk inda zata sai ace dole saita fita da wanan yariyar

   May ake nufi da ita ne  ko yana nufin wanan yarinyar ta fita wayewa ne,

   Sai alokacin ya juya yadan dube ta cikin takaici,

   Ya kuma juya ,yacigaba da tafiya zuwa dinning table , yaja kujera yazauna,

    Saida nagama hada mai abinda yake son ci ina kokarin wucewa,,,

  Yace min in shirya zamu fita da nafisat unguwa cikin ladabi na ansa mai da toh,,,,

   Har na juya zan wuce sai yace min,,, ina takarda da yace in bashi, cikin sauri naje nadauko mai nakawo mashi

   Batare da ya duba ba yasa cikin briefcase din shi  yarufe,

    Wani wawan harara nafisat ta watso min daga inda take tsaye,,,

   Niko, ko in,kula nai mata,,,,

    Dakina na nufa na dan kara gyara jikina sama,sama,

   Natura Aisha wurin su hajiyar mu har in dawo

   Duk cikin sauri sauri nake,komai don kada in sa nafisa jirana har inyi laifi,

    Aiko ina zuwa a mota nasamu, su ita da driver zaune suna jira na 

   Ina ganin su sai nadan ji shock kadan amma sai na dake ban nuna ba,

    Zaune take tana dakilan wayan ta ko kallo ban ishe taba tayi wani kicin kicin da fuskanta,

   Nadan masu sallama nagaishe ta,

   A wulakance,ta ansa min gaisuwar nawa, gami da watsa min harara,

   Tace min sai ki shigo mutafi tun dazu muna jiran ki,

  Sai lokacin da kika ga dama zaki fito,

   Ke wanan yariyan na lura da ke tunda kin samu shiga gurin maigidan shine,

  Kike kokarin hada kanki da ni wlh ni maganin ku zan yi,, yar kauye kawai matsiyaciyar banza

    Sai na gwada maki cewa tsintacciyar mage bata zama mage,, 

    Naikamar banjita ba,ban masan dani ta ke

 zancen ba ,,,,

   Ina ganin haka na bude gaban mota nashiga abina nai ko in kula da ita,

    Saina kama magana da larabci da driver ina ce mai ina zamu ne,

    Yace bata fada mai ba shima, kawai sai muka sa kai muna ta tafiya,

    Haka muka hau titi babu wanda ke maganar cikin mota,

   Har mukayi dan nisa da gida 

    Danaji shirun yai yawa a motar, sai kawai na jawo wayana dake cikin jakata na fara, game,,

    Aiko tana kyala ido taga wayana da nake game da ita,

     Ji kawai nayi ta wauto wayar daga hannu na tajuya tajuya sai naji tayi tsuki kawai ta wurga min saman cinya na,

     Mashal plaza muka je cen kusa da top ten plaza,

    Kayan make-up tadan saye da sauran kayan bukatun mata,

    Muna futowa muka shiga cikin top ten ,

    Anan naga kayan yara masu saukin kudi sai na dan sai ma Umar da Aisha 

    Saboda duk kayan su mubar su can gidan mu,

Kuma badamar wani yaje ya kwaso masu,,,,

    Ina kallon anty  Nafisa na saurin zuwa biyan kudi don kada ta hada danawa,

     Dariya tabani kawai don inda sabo nasaba da halinta, don komai nata ba mai ci agidan nan,,,,,          nidai na biya kudina cikin chiefest price, saida nayi mamaki, jin kudin cikin sauki haka,na,,,

     

     Bayan mundawo, gidane tawuceni fuuuu zuwa cikin gida, kayan nakwaso zuwa dakin ta,

   Koda nashiga nata  nasamayta har ta dan kwanta saman gado, tana waya,

      Daidai lokacin tana fadin wlh duk tsiyar da zamuyi salwa saidai muyi 

     Mutun ace bai san darajan  mace ba shi nashi kawai zuwa aikini kodyau,she ,,ni gaskiya ban iyawa,

    Saida kawai ace wai yar aiki ce zata raka mutun don kitifi,

   Kayan da ta sawo nake gyarawa asaman dressing mirror dinta 

    Amma azahiri ita nake sauraro ba wai aikin nake yiba,

     Yaushe ne zaki ba da sakon a kawo don in fara barbada wa dan banza,.

    Wani iri naji lalai wanan matar batada dama aiko zamu kwasa da ita ke nan,

    Muryanta naji ta cigaba da fadin ai ina nan ina kokarin binciken inda takardun suke fara daukowa

   Kalonta nayi cikin sauri wanda ita din ma,kallo na tayi batare da zargin ko naji may take cewa ba,

    Tai min nuni da hannu cewa in wuce,

    Daki na nakoma cikin yanayin damuwa, don nasan cewa akwai aiki ja agabana,

    

    Tundaga wanan ranan nafar sa ido ga al,amuran nafisa sosai,

    Tundai ma danaga wata bakuwa tazo wurita daga Nigeria 

    Wai umurah matar tazo shine aka bata sako takawo wa nafisan,

   Aiko zargina yazama gaskiya don wasu magunguna ne kuli kuli a,kabata

 Bayan kwana kamar uku, da kawo sakon   Allah yabani sa,a ta tafi ganin masaukin bakuwar 

    Anso zuwa dani sai na kwanta nace banda lafiya,

   Suna wucewa na kwashi sakon maganin sai masfala gidan hajiya laila,

   Duk wanda muka bude an rubuta bayan nin shi da yadda zatayi amfani da shi,,,

    Hjyan ce tai min dabara tasamo kayan mata masu kyau muka sa mata cikin kowani leda, ,,,ba wanda bamu canza ba 

   Nadawo gida na mayar mata da abinta inda taje,

    Naci gabada harko kina,

   Ina kallon ta lokacinda take barbada mai wanda akace ta sa mai ga abincin shi,

    Dariya yakamani nagudu zuwa dakina naci dariya na can kamar in nutse,

      Washe gari koda nashiga in gyara mata daki na isketa tayi daidai sanan gado tana wani lagabewa,

     Aikinta takeyi waya, tana fada ma salwa cewa kwanan nan batasan may yasamu Sheriff ba don bai ko tausaya mata, 

    Dariyan keta yakamani 

 Nace lalai hjy laila takai tsuhuwar bariki,

    

      Yanzu hankalin mu kwance gaskiya don mun rage wani fargaba kasan cewar muna da mafaka mai muhinmanci,

   Baza,a taba zargin muna da halaka da takari ba in mun fita don duk inda zamu da motane ba wani labe labe ko bin lungu lungu, gudun kada akama mu,

     Yauma nafito ne don in sayi kayan abincin mu da yadan kare,

     Ina cikin wani shago sainaji hayaniyar mutane a kofar shagon,

   Da sauri na biya kudina nafito bakin shagon da ,

    Wasu takarine askarawa suka biyo su uku gudan wai tana suyan dankalin turawa sukuma saura su tsaye abakin titi suna saida gumama da rana,

   Suna ihu suna bidan agaji amma ba wanda ko yakalli inda suke,

   Inaji yar matashirya wace muna iya yin wari da ita tana fadin cewa uwar da ubanta duk suna gari ita ba takari bace,

   Cikin dakiyar zuciya ganin kowa yaki ceton ta naje gurin nace masu ai,yakamata suyi mata uzuri tunda sunji abinda tace

   Jinda sukayi larabcina tsab bakamar na yan koyo ba yasa sukadan saurareni,

    Suka kalli yanayina sai sukaga banda alamar shigan banza 

    Nan shugaban nasu yace min intanbayeta ina iyayenta, 

   Karya nai masu nace iyayen ta suna nan harda kakaninta ma nabasu wrong address ,

 Wanan yariyar tasamu tasha da kyat wurinsu nima dim gabana sai faduwa yakeyi,,,,,

   

🐎ZEEE MAKAWA🐎


✈✈✈TAKARI✈✈✈ 

        👣👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                 4⃣8⃣

                    BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

  

 Almost true life story   Saida naga cewa mun daina ganin yan bagaladin mun masu nisa sosai

   Daidai,Lokocin na danyi ajiyar zuciya, nakalli yariyar da muka kwato daga, hannu yan bagaladin,,,,,

    Wace sai dan she shekar kuka takeyi tana, ajiyar zuciya kai da kai tanayi, tana dan share hawaye, a fuskanta,,,

   Dafata nayi ina  Tabayarta  ko daga wani unguwa take

   sai da ta dan share hawayen da ya dan silalo mata,

    lokacin take ce mun ai daga wani dan kauye dake kusa da gari, take shigowo ,

    Kauyen baida nisa da cikin gari can tsakan wasu duwatsu yake, larabawan daji ke zama agarin

  Inda Mafi yawan yantakaru sun fi labewa a kauyu, ka mafi kusa da garin makka, don gudun kora,,,

    Gida nazo da ita, nadan  bata abinci ta ci ta, huta,  amma duk a firgice take saboda tayi fitar kutsun yau,

     saida naga hankalinta ya dan kwanta,san nasa a,kaita har inda zata samu motar da zai kaita kauyen na,su,

   Tawuce tana ta zabga , muna godiya tana sharan fuska,,,,

  Muna tsatsaye a waje duk jikin mu yai sanyi 

  Don muma mun san cewa bamu wuce hakan ba,,,

   Duk sai ta bamu tausayi wlh,,,, wasun mu harda kuka,


    Washegari dayake ranan weekend ne  saboda su kasar saudiya,Alhamis da jumma,a, ce weekend nasu,,,,

Don haka nasan cewa mai gidan yana gari don duk sallar jumma,a a garin makka yake yin ta,

   Hakane ma yasa yafizama a garin  fiye da ko ina, don yana yawan yin dawafi duk ranan jumma,

  Shiyasa mukatashi dawuri don muyi aiyukan mu saboda tun karfe goma yake wucewa masajid 

   Saboda koea yassn cewa idan kakai shadayan rana da wuya kasamu cikin masallacin saidai kasamu gefen masallacin ta waje koshi a mamatse,,

  Don haka, Tunda safe natashi don mu yi aikin mu cikin lokaci kafin ya fita,

  Nasan cewa yana dakin motsa jiki don halinshi hakan da yadawo daga sallah asuba indan sungama karatun Al,kur,ani maigirma,

     sai ya sauya kayan shi zuwa na games wear,,,

    Idan nasan yana dakin yin exercise ka,ida ne dole inkai mai cup da goran ruwa mara sanyi guda sai kuma milk mai sanyi ,sanyi guda,

   A gefen wani dan standing table dake gefe tsaye nake aje mai,

   Duk da nasan cewa bai shan koda rabin kofin milk din saidai  hakan bai hana kulun in aje mai ,milk din ba, amma,na ruwa sha, kan  shanyewa yakeyi kafin yafito,,,,

   

  Yauma haka dine ya kasance,,, ,yana tsaye yanata tafiyan daba iyaka bisa exercise machine,din shi,,

   A hankali na shigo dakin hannu nadauke da tire din drinks,

    tunda nashigo nagan shi saye da dogon wando irinta maza masu exercise, da bakar singilati, sai  yar karamar tawul da ya, rataya saman wuyan shi,,,

     A hankali na isa saman dan tebur din na  aje mai  dan ture din da na hado mai drinks din ciki,

   Na juya don in fita dakin,

  Karar waya shi da yaji,,,yasa shi dan tsagaita tafiyan da ba tsayi din, dayakeyi,,,

   Da hannu ya nuna min gefen da wayar ke yar  tsuwa,,,

   Nagane nufin shi indauko mai ita yake nufi,

  Wayoyi ne kusan guda uku a wajen, ashe,,,

   Ita mai tsuwar ita ce nadauko mai, ashe wanyan mutanen  Nigeria ce, sunan yan uwan shi ne kawai aciki sai abokai shi, yan kasar Nigeria,

   Malam baba naga an rubuta baro,baro, a fuskan wayan

    Ina mika mai wayan yadiba  yaga kowa ne ke kiran shi yanzu cikin wanan lokacin daga nigeria 

   don yasan cewa ana batun sallah asubu ne yanzu haka a Nigeria 

   Tunda munan a,lokacin karfe bakwai darabi nasafe, ne

   Wanda yayi,  daidai da karfe hudu darabi na asuba, a Nigeria,

   Yana ganin sunan malam saida yaji gaban shi yafadi,  don yasan cewa ba kiran lafiya bace

  Don iyakar malam din yakira shi da misalin karfe biyun rana na nageria lokacin muku ma ana batun yin sallah la,asar

 Daidai lokacin danaga yadaga wayar

 Nikuma ina shirin barin dakin  sai naji yana fadin Innallahi, 

   Da karfi na waigo don nasan cewa wanan kalman ba karamar kalama bace ,sai idan tashi hankali yasamu bawan Allah,

    Ganin ina kallon shi cikin tashin hankali yasa shi dan controlling din kan,shi,,,

    Jinayi yana fadin tun,yaushe ne ciwon yafara mata haka malam,

   Sainaji ya ce dan Allah malam akaita asibitin Maiduguri zai ma Abba waya kafin ku zo, asan abinyi,

   Karshe dai yace ma malam din insha Allah gashi nan zuwa, shima,

   Batare da yadauki ruwan da na aje mai,ba yasauko daga machine din,yanufi hanyar fita, dakin yana fadin ,

   Kiramin Almustapha, da sauri,,, pls

    Bayan shi nabi cikin sauri don zuwa kiran almustaphan, din


   Kafin wani dan lokaci komai na tafiyan shi,an kan mala mai, anshirya komai  zuwa Nigeria

   Su Almustaphane suka kaishi jidda don booking din  jirgin su kayi tun kafin su iso ,jidda wasu ne sukayi mai hanyar komai, don sun saba dashi,tun baro Nigeria dayayi zuwa nan

    Suna isa sunyi sa,a dama an mai booking din jirgi

   kusan daidai time din da jirgin zai tashi su, suka iso wurin

 

    Mudai mun san cewa ba tafiyar lafiya sheriff, yayi wanan tafiyan ba

 don ni agabana akai mai waya din, akan mara lafiyan da yatafi,

   Amma sai gashi ga mamakin mu,

   munga matar gidan sai busha shanta takeyi,ba abinda yadamayta,ita

   Don har wata kawa tasamu wai ita yar lici,,,, wata fara duk man bilicin ya bata mata fuska kamar kuturuwa, 

   Tana magana tana kashe ido tan turo baki, wai ita yar takari,,

     Saboda yanzu kusan sau biyu kenan ina ganin Yar lici agidan namu,

Wace hararane kawai ke rabani da ita, idan tagan ni,

    Don ina ganin ta sai naji kawai batai min ba don wata irin gogagiyace da ganin ta,,,

   Tunda sherrif din mu ya wuce zuwa nigeria 

   suke zama a falo suna ta sa kade kade da raye raye dasu, wake,waken su ,na bin rawar,

 Mu ko, Sai, Abinci da muke ta aikin dafawa, kala kala,

   Don basu koshi sam sanan

  Ga wani irin shewa da sukeyi kamar an gafarta masu, zunuban su

    Yau duk nagaji da aikin da mu kasha saidai kuma idan na tuna cewa sheriff din mu yayi tafiya cikin tashin hankali sai inji duk zuciya na ta min,suya,,,

    Duk da bansan koma may ye matsalar ba, ,hakan baisa nadaina jin bacin rai ba,don nasan ba ta kyauta wa mijin nata ba

,Don inga mutunci ai duk abinda yasamay shi ai yasamayta, itama,,,,

  Amma sai ga amatsayin matar shi tana, ta holewar ta, ba abinda yadamay ta ita,,,,,

    Duk gidan kowa sai mamakin ta yakeyi, don dama da ganinta kaga tantiriya,

   

    Tafiyan shi da kwana biyu ina zaune dakina ina gyara ma Aisha kai sai naji wayan intercoms na dakina ya na ruri da alamar ana bida na afalon, gidan,

   Batare da bata lokaciba na isa falon, cikin sauri,

  Almustapha ne nagani tsaye yana jirana da waya a hannun shi 

  ,ina isowa yamiko min wayar, dake a hannun nashi,wace dama a kune take nikawai ake jira inzo in ansa,,,

   Nakara wayan a kune na ina mai sallama,

  Muryan sheriffudeen din muna ji cikin muyar mara sauti daji zuciyan shi badai

  yana mai kara yi min sallama shima,

   Nakarba da wa,alaikumu salam,

   Yace min don Allah yana son in taimaka mai in gyara mai wasu dakuna daga cikin gidan

    wasu dakuna ne ke cikin gidan da baki ke sauka wanda ke kusa da shiyan nafisa,

  Sai kuma yacigaba da fadin,

   Kuma in yi kokari don Allah, in,bidi abincin da masu ciwon sugar ke ci in,tanadar mai su agidan kafin ya iso,,,

 Cikin siririyar muryan da take dauke da kama da kasala,

   Yace ina ji na ce eh ina madaga mai kai kamar yana gani na,,,, yace min

   Idan har ina bukatar kudi in tamabayi Almustapha zai bani,

  Sai dan shiru ya biyo baya,saina ji yana magana,,

  Yace yaji ance nafisat bata gida kuma ko jiya yakira an fada mai cewa tafita,

   Saina ce mai nayi ai badadewa zatayi ba yanzu zata dawo,,,,

    Cikin tsawa yake fadin kira na ukune fa yai mata yanzu 

Yakare da fadin ina fatan kin fahinci duk abinda nace ai,min ,,,  

    Cikin sanyin murya nace mai to insha Allah za,a yi,

  Daga karshe kuma nai masu fatan iso wa lafiya, tare da

    fatan Allah yaba mara lafiya, lafiya ya ansa da fadin ameen ya gode,, yakashe wayan,,,

   Almustapha na mika ma wayan sai yake ce min sheriff yace ya bani wasu kudade dazanyi amfani da su,,,,

    Kudin da yabani sai naga suyi mugun yawa don haka,saina, nadauki dai wanda zai i,she ni 

   na mayar mai da saura,,, 

  Mamaki yakamashi saidai baice min komai ba ya juya kawai ya wuce, abin shi,

  Nikuma nakoma cikin gida ina tunanen maganar da muka yi da sheriff din,   

    Ashe mahaifiyar Sheriff ce bata da lafiya ciwon sugar ya kamata,

   Shine ta rikice masu, acikin dare har hankalin malam mijin ta yatashi,

   Don yadda ciwon yabugeta sun dauka ko bazatayi ba

   Shine malam din yakira sheriff din a rikice yana fada mai abinda yasamay ta,

   Asibitin FMC Maiduguri aka fara ajeta kafin  sheriff ya iso, daga saudiya,,

   Mahaifin shi Alhj lawal zannah shi yadauki dawai niyar duk wani abinda akai mata a asibitin 

   Ya basu kulawa sosai yadda duk yakamata, yanu cewa ita din kaunar shi ce ta ji,

   Isowar sheriff din mu keda wuya yaga halin da mahafiyar nashi keci yasa duk hankalin shi yatashi sosai

    yasa akai mata biza ita da malam mijinta 

  Da,kuma yan kan,nen shi mutum, biyu zuwa saudiya 

   don mahaifiyar nashi,tazo saudiya adiba lafiyar jikinta da kyau aji komay ye matsalar da ke damunta,

    Shine ya dinga bugo ma nafisa waya don ya fada mata abinda yake so ai masu kafin ya su iso, da bakin nashi,

    Ita kuma bata gida yanata bugowa anace mai tafita,

 Ranshi ya baci sosai yana mamakin ina taje haka cikin garin da bata san kowa ba,

   Duk taka tsantsan dayakeyi a,kanta baihana  ta yin abin da ranta ke so ba,

   Don a bincikin da yasa bashir ya yi a kanta ya,fada maicewa tana shan drugs, tun a makarantar da tayi a kasar waje,,,

  Baida yadda zaiyi ne  saboda umurnin mahaifin shi yake bi, shiyasa ya aureta har ya zauna da ita dole,

    Ashe shine dalilin da yasa bai yarda ta fita ita kadai sai tare da ni,

  Wanan maganar Sirun sune shiyasa baifito fili yace ga abinda yake so indinga kula mashi da ita ba,

    Sai dai yasan cewa ga wayo da irin hankalina zan iya kula da duk wani movement nata,

   Ita wanan kawar nata da samu salwa ce ta sa a,hadasu asaudiyan don matar ta iya harka so sai,

    Zata dinga samo mata kowani irin abu take bukata ,,,   

    

🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                4⃣9⃣

                   BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎   Almost true life story


    Duk wani shiri da yakamata muyi mun kammala shi ko zuwan bakin namu kawai muke jira isowar su

   Sai misalin magrib suka iso garin kasan cewar ba su sauka da wuri ba,

   Mun, masu taro na mutunci yadda yakama ta, mu nu,na namu kulawan gare su so sai,,,

   Don duk kusan wanda ke gidan a lokacin mun fito waje don taron su,

   Jinda kowa yayi cewa mahaifiyar cikon sheriff ce bata da lafiya za,azo da ita,

    Suna fitowa a mota nariga nasan cewa motar da almustapha ke ja itace za,a sata aciki don haka gurin motar na nufa,

   Dan jin kadan ba,a bude motar ba, hakan yasa muma mukayi tsatsaye cirko cirko a wajen,

  Gaban motar nanufa don inga ko may yasa mustaphan bai bude kofar ba,

   Ina zuwa gurin na rike hannu motar kenan sai naga an bude gefen driver,

  Maimakon inga mustapha ke jan motar sai naga Sheriff din mune yajawo motar dakanshi,

   Jayewa nayi kadan don in bashi wuri ya fito, ina mai sannu da zuwa,

   Yana mai ansa kuma hankalin shi naga ya bude gambon kofar motar tabaya da ke ta daidai saitin wurin zaman driver,

   Wata yar matace wace bazan iya cewa taikai dadtijiwa ba take kokarin ta,fito daga cikin motar,

   Gurin na isa da sauri na don in taimaka mata wanda hakan yai daidai da shima sheriff ya miko hannu shi don ya taimaka mata,

   Batare da na damu da inbarshi ya taimaka mata ba nai azamar riko mata kafadar ta ta baya kandan 

   Sainaji tadan yi wani irin ajiyar zuciya, kadan tare da fadin Alhamdullahi ala kulli halin,

   Ina rike da gefen kafadar , ta har zuwa dakin da sheriff yace mu gyara masu,

   Wanda yafi dan girma da kayan alatu acikin shi, na nufa da ita 

   Sai sannu kowa ke mata,

  Shiko sheriff tunda yaga nazo kamata sai yabar min ita don yasan cewa zan iya,, 

   Kuma ganin dayayi a hankali nake takawa da ita yasa hankalin shi ya kwanta,

   Amma yana bin mu abaya a hankali shima,

     Kujeran dake dakin na zaunar da ita sama a hankali,,

   Sai a lokacin da naga ta zauna sanan ido yakai ga sauran abokan tafiyar na su,

   Wani dan dattijo ne baki dogo aje dan gemu mai rabi fari da baki yarata wani dan jan kyale a wuyan shi

   Dagani koba fada maka ba kasan cewa shiga ce irin ta shehunan mu na Nigeria,

   Bayanshi kuma wani matashi shine, baki cikin shigar wandon jeans dawata riga baka anyi rubutu da wani abu kamar gold cikin manya haruffa,

   An rubuta  we are d leaders of tomorrow,,,,

     sai wata yarinya wace zan iya cewa chuculate colour ce ita,

    Tasa wani buje da rigar  na less, ta sa hijab baki saman kanta, tana rike da jaka, baka again,

     Ganin mara lafiyan ta zauna duk suna kanta suna mata sannu yasa ni fita dakin don in gabatar masu da dan abin sha kafin su zo cin abincin su,,

   Daidai zan fita yar bakuwar budurwan tace min dan Allah ina son in dan kewaya pls

   Saida nadan saurara da kyau nagane hausan nata,

   Bayin da ke manne cikin dakin na nuna mata,

    Koda nafito daga bayin don in fita zuwa, dauko masu drinks sai na samu,

   Sheriff din mu ne, rusune gwaiwa bibiyu, akasa, gefen kan mahaifiyar tashi saitin kanta yana mata magana cikin tausayawa,

     Shikuma dattijon ya saman kujera kusa da kafafun ta,

   Drinks nakawo musu cikin tire, na aje masu a saman stol 

  Duk da cikin dare suka iso hakan bai hanani gabatar masu da abincin lafiyyae da muka hada masu 

    Tun misalin karfe biyar na marance, mukayi masu komai 

    Har ita mara lafiyan nida kaina na hada mata abincin ta,

   Agabanta na hada mata abincin nata, wakene sai ganyen lansir da kore da nadan hada mata dashi naimata shi ruwa ruwa sai kaza danai mata gyara nadaban yadda nasan cewa zata dan iya ci,,

    Alhamdullahi do gaskiya ta dan ci abincin sosai 

   Sunyi mamaki don sunce rabon da taci abinci maidan waya haka yadade,

   Natsiyaya mata ruwan Apple da carrot, wanda na markada wuri daya sanan nadan tace mata shi,

    Duk iyalin nata nagefe suna kallpn yadda nake fanam dawai niya da ita,

   Cikin larabci sheriff yace min in kai wayan sauran dakunan su shi malam zaizauna da mama a wanan dakin ne nasan da toh,

  Lokacin shima yafito daga dakin suma bakin ni suka biyo bayan yai masu bayanin cewa zan kaisu dakin cikin harshen Kanuri,,,,,

   A falo sukayi kicibis da Nafisat wace dawo wanta ke nan daga wurin da taje,

   Idonta yayi jawur kamar garwashi, sai wani dan rausayawa takeyi indan ba ka gane ba zakace she is normal,

    Kallon mamaki yake mata don da jiyakeyi bawai ya gaskanta bane,

   Don shi mutun ne mai afani da badili ba zahiri ba,

   Zuwa tayi ta batun rugumay shi tana fadin habibi ,,

   Yaushe ka iso,

  Ai baka fada min cewa kana hanya ba,

   Yanzunan nadan fita,

  Jakar ta na hannuta da ke batun faduwa na karban mata zuwa daki,

   Nadan yi saurin ce ma, sheriff din mu,wani daki zan kai wanan bakon saurayin,

   Sai nuna min yayi da hannu batare da yayi magana ba,

   Yandan bita gefenta yawuce zuwa sama, ranshi a bace,

   Dakin da ke kusa da nawa nakai yar budurwan sai saurayin dake can hanayar fita daga falon,gidan,,

    Na nu makowan su inda zai dinga yin komai agidan,


      Daki ya shiga jikin shi a san yaye saboda tsanan bacin ran da yashiga donganin yadda nafisa ta koma,

   Gashi inba idon shi ke mai gizo, ba yaga har rama tayi gashi ta danyi duhu ,ta yi baki ,,

     Itace ta shigo dakin nashi cikin irin dauriya nan

na yan kwaya,

    Tana fadin ya hanya ya mutanen, takama nuna sama da yatsan ta maganar nata yaki fito wa, 

   Toilet ya fada yabarta nan tana shirmay ta,

   Alwala yadauro daniyar zuwa masallaci 

  Kwance yasamay ta saman gadon shi tana ta nasarin barcin ta hankalinta kwance,

  Tsaki yaja cikin takaici, yafita yabar mata dakin,bata masan inda take ba,

     

      Kafin in kwanta barci  danaga shehi a falo tare da sheriff din mu,

    Sai na koma wurin, 

Ummi, na is,kete kwance tadan dun kule waje guda,

   A C dake aiki naje direct nadan rage ma karfi,aiki,

   Dago kai tayi tana min godiya, 

   Tambayar ta nayi ko akwai abinda take so kafin mu kwanta

  Duk da tace a,a saida na koma naje na hada mata kayan tea na aje masu adakin sa masu kayan kamshi a dakin sai ruwan wanka da na hada mata,,

   sanan nai masu saida safe nafito,

   Ina fitowa muka hadu da sheriff a kofan dakin zai shiga shima yai masu saida safe,

   Nadan rusunna na gaishe shi, hannu kawai yadan daga min kamar kulun, batare da ya ansa da baki ba,

   Yana shiga yaga yadda na kara gyara masu ko ina ga kuma kayan tea da na hada masu saman wani dan stol

   Dadi yaji so sai cikin zuciyar shi  don baiyi tsan manin hakan ba sam,

   Sai gashi yar karama dani nayi abinda yadace ace matar gidan ce tayi shi,

     Washe gari sheriff yana dawo daga gurin sallah dakin da su yaghana suke ya nufa ya diba lafiyar ta, Alhamdullahi jikin yadan yi mata sauki sosai,

  hakan ya da yagani yasa shi dan kwantar da hankalin shi,

    Inda yace masu zai je ya shirya dom su je asibiti da wuri,

     Muma,dai Washegari tunda safe muka tashi tunda munsan cewa munada baki agidan hakan yasamu hi samakon yin aiyukan mu,

   Koda sheriff ya fito ya iske ko ina nagidan fes har abin karin kumallo mun hada ko,

   Batare da bata lokaci ba shima ya ci nashi sama sama don hankali shi wurin kai Ummi asibiti,

    Sam ban kawo cew dani za,a asibitin ba ,

   Allah yatai make ni muna gama aiki na fada wanka nafito tsaf dani cikin shirgar dogurwar riga yau ja ce ajikina ba baka ba,

   Tsaye nake inadan gyara wurin da na gama hada tea a kitchen ina son in kaiwa hajiyar mu,

    Muryan mustapha naji yana cewa sheriff yana magana dani a falo,

   Koda nafito na iske kusan kowa a tsaye har da yaghana da bata da lafiya,

   Tsoro nadan ji don nadauka ko nayi laifi ne, kallo na yayi yana fadin mutafi ko,

   Batare da nasan inda zamu ba nagyara dan daurin rolling dim kaina, narufe ko ina inda nasan cewa gashin kaina zai iya fitowa,

  Nadan kali mahaifiyar nashi naganta cikin shiga na kamala,

    Lafaya tasa duk ta rufe jikinta tsab baka ganin ko ina nata sai tafin kafarta dana hannu,kawai,,

    Shima mijin nata yana saye da jallabiya fara kal da alamar yau yafara sata,

    Sheriff din mu yadan kali dan saurayin yace mai Salim ka tsaya gida har mu dawo, tukun,,,

   Ke kuma Amal da wanan ya nunani da hannu ku kama ummi kuzo muje,,,

   Mota muka shiga sheriff da shehi ke gaban motar saini da yaghana da Amal ke bayan motar inda mukasa yaghanar tsakiyar mu,

   A hankali yake tukin motar yana yi yana dan waigo mahaifiyar tashi don yaga yanayin ta,

   Saida gaskiya ni kallon yana yawan damuna don duk ya waigo kafin ya kai indon shi ga ummi kamar yadda naji yakira yaghana din,

   Sai idon mu ya hadu, sainake dan shiga tsarguwa saboda nice a gefen da ge facing din shi,

    Dana hakan na yawa sai na maida idona gefen titi ina kallon jama,a daketa wulgawa da shaguno nin da suka cika kowani titi, nagarin makkah,

   Sultan Abdulraham specialist hospital muka tsaya bakin get inda muka karbi pass din mu yasa kai ya shige cikin katon haraban asibitin,

   Wuri yasa mu ya perker motar Amal ce tadan rikawa ummin hannu aiko tace don Allah ki sake min wanan duk tafiku iya lalabani,

   Kallona sheriff yayi yana min magana kadan kadan indan rike ummin  a hankali pls, na ansa mai da toh,,,

    Har office din da zamu zauna ganin likita nakaita na zaunar da ita, 

    Ruwa tace muna tana so, don haka da sauri na nafita can wani shago bakin get na siyo muna ruwa roba biyu guda na zam,zam baida sanyi guda kuma mai sanyi na riko muna, shi,

    Na iske sheriff tare da ita ina zuwa na balle bakin roban ruwan nayi bissimillah nabata tasha,

  Bamuyi wani dadewa ba aka,kiramu kunsan su bakamar kasar Nigeria bace 

    likitoci ne na kowani fanni birjit sun fi ashirin ako wani fanni aiki ne kawai ba 

    Shehi da sheriff suka shiga da ummi sai aka bar mu nida Amala, zaune,

   A, lokacin Amal tadan kaleni tace mim ita sunan ta Amla,

    Saida nadan yi takaitacen murmushi san nan nace mata fadima,

   Nakauda fuska na daa gare ta, batare da na kara mata magan ba,

   Sundan jima kadan sai gasuvsun fito da ita saman wani dan keken asibiti mai kama dana guragu,

   Wani dan matashin balarabe mai karfi yana tura kekenn

  Mikewa mukayi tsaye lokaci guda cikin fargaba,

  Da larabci sheriff ke min bayanin cewa zaije yadawo don za,akwantar da ummi ne sai an gano ko maye matsalar ta tukun,

  Cikin rashin jin dadi maganar muka bi bayan su har zuwa dakin da za,a ajeta,

   Dakine lafiyaye mai kyau komai akwai adakin kamar mutun yana gida,

  A gaskiya ummi ta sha awo sosai don tun da aka kaita dakin muke ganin likita kala kala 

   Wanan group din suzo sutafi wasu su zo,,,

    Nida sheriff ne masu zirga zirga don wani lokaci kafin yadawo anbada wani test din dole nice zanje in yi kafin yadawo,

   Don haka duk mungaji,amma sam ban yarda na nuna cewa nagaji ba,

   Abin mamaki har muna batun tafiya gbaigana u labarin matar sheriff a asibitin,

  Har Amal ta kai ga tambayar shi ko lafiya bata gan, ta ba,,,

   Ce ma Amal yayi bata jin dadi ne,

  Sai a wanan lokacin natuna cewa banci komai ba fa yau, cikina ya soma ruri ,.

   Ban ko gama wana tunanen ba wana na yai dan tsuwa alamar kira ya shigo min,,

   Cikin dan sauri nadauki wayar da na aje gefena ina dan diba lambar,

    Nakara wayan akune na ina mai ansa sallama,

    Idanuna su kai kan sheriff, yakafe ni da ido da alamar yana son yasan wanene yakira ni awaya,

    Jin da yayi ina kwatancen inda dakin da muke yasa shi barin kallo na,


  ZEEE MAKAWA24/10/2017, 1:50:11 PM: Maman Safwan: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                   5⃣0⃣

                      BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

 

Almost true life story,,,


    Allah ya karama Annabi darajja da sahabban sa,,, 

 Jumma,atu mubarak yan uwa musulumai,,,

    

    Almustaphane tare da bakon saurayin nan mai suna  Salim suna dauke da kwandon abinci, da abinsha, a hannayen su,

     Nina karbi basket din hannu almustapha, nakai inda zan aje na aje,,,

    Ahankali nadawo inda nake tsaye, nadan tsaya muna kallon ledar ruwan da ake kara, wa Ummi,

   Almustapha gefen da nake yazo ya tsaya gab dani, ,,,

   Shima kallon ruwan da ake kara wa Ummin yake yi cikin tausayawa,

   Dan juyowa yayi daidai saitina ya ce min Aisha na can yau tana fitina wai sai ankawo ta gurina,

    Murmushi nayi nace mai tunda tazo aibantaba dadewa waje hakaba, batare dani ba

   Yace yau kan Yumma tasha rigima sosai

   Ina dan murmushi don tuna Aisha da irin rigimar ta,

    Ina,dan juyo sai ko muka yi ido hudu da Sheriff din mu,

   Dake tsaye daidai saitin inda muke, 

    Hannu shi cikin aljihu yadan jingina da gina kadan,

   Ashe idon shi na inda muke muna magana da mustaphan

 Wani irin harara   Ya watsa min,

  Tare da wani irin mugun kallo na zaki gane kuren ki,

   ,bansan lokacin da na sada kaina kasa ba,

   Don kallon ya firgita ni sosai,

     Tunda ni bansan abinda nayi mai ba, yai min wanan kallon na kishi ga hankalin ki, da ni,

   Shiko Almustapha sai kara fada min yadda Aisha ke fitinar yakeyi,,,

  Duk nadan daga kaina sai mun hada ido dashi daga inda yake tsaye suna magana da shehi,

  Ganin da tayi mustaphan ba daina yimin kus,kus din da mukeyi zai yiba saboda bai lura da sheriff din ba da kallon da yake muna,

Don baya yaba ma sheriff din,,,,

 Daurewa kawai nakeyi ina yar dariya kasa kasa,

   Muryan , sherrif naji gab da mu yana ce min naje muci abinci da Amal a waje

   Kafin in yi wani yunkurin tashi wurin saina ji muryan shehi yana cewa kamar ruwan baya tafiya ko,

   Da sauri ya juya zuwa inda ummi take kwance don ganin robar kara ruwan

   Sai kawai naji duk banjin dadi saina dan shiga halin damuwa, 

   Saboda ban iya fassara laifin da nayi ake min wanan kalon warning din,,

 Abinda ya kawar minda damur dana dan shiga shine,

  Farkawan da Ummi tayi daga barcin da takeyi sanadiyar dan taba mata hannu da akayi,

   yasa nadan saki jikina da sauri na naje gurin ta ka,fin kowa ya isa ciki

     Sauri ina mata sannu da jikinta, Ruwa tace zata sha saina dan daga kaina nakali inda yake ina fada ma sheriff din  bukatar ta wanda dama idon shi naga mahaifiyar nashi,

    Shima gurin gadon ya iso, yadan duka daidai saitin kan ta yace mata tayi hakkuri, Ruwa ake kara mata tabari indan ruwan ya kare sai abata, tasha ruwan shan,,,

  Cikin sanyin gwiwa ya  Mike ya na tafiya yana ce min cikin larabci koda ruwan yakare kada in bata ruwan tasha don akwai tests din da za,azo aimata dan anjima kadan,

    Barcin ne yakara daukanta mai nauyi duk ina tsaye, akanta sai likitocine keta zuwa da dawo kanta, suna aune aune don su gane ko may ye matsalar ta 

     Amal tana gefe zaune ita da salim cikin damuwa ganin irin wahalar da mahaifiyar nasu keyi,,, 

    Muna nan zaune mukaji takon takalma tun daga nisa kwas kwas sai duk hankalin mu yakai ga kofar shigowar don gani ko waye,

  A,she  Nafisa ce tashigo asibitin da marance lip,,,, cikin shigar wando da riga irin na yan Pakistan, take,

    Ta yafa mayafin kayan ta rufe kanta da shi,,,

   Tana shigowa ko wani gaisuwar kirki bata yi wa koda shehi datagai dattijo ba cikin mu balle su Amal dake tsaye gefe

  Direct wurin gadon da ummi take kwance ta nufa, 

   Tadan dibata tana tabe baki kamar mai jin wani, bashi ,bashi

 Ta dan jin tsaye,muma ba wanda yako kulata,

      Ko minti goma batayi ba da zuwa tace zata wuce,,,

   Har takai kofa tajuyo tana min tabayar ina habibi cikin turan ci,,,

    Da larabci nace mata yana can gurin ansan result din test din da akayi, wa ummi,

   Yafuto ni tayi da hannu alamar in kai ta inda yake,

  Ba musu na dan gyara na nufi hanyar zuwa lab, da ita,

    Dan tafiya mukayi maidan nisa sanan muka isa gurin, da yake,

  Zaune yake saman kujerun da aka tanadawa mutane,

   Saidai kan shi yana duke, ba wai kalon jama,a yakeyi ba,

   Dagani jira yakeyi yaji an kira shi, kawai,

    Muryana da yaji cikin lokacin da bai yi tsamani ji, ba yasa shi dagawa da sauri, 

   Yana dagowa saida idon shi yabani tsoro

   Saboda Idon shi yayi jajir kamar wanda yai kuka,

  Nikan nasan cewa ma kukan yayi ,don ko dazu dana kai mai wani takarda da aka bamu na iske shi zaune cikin mota shidaya yana kuka,

   Ganina dayayi yasa shi yadan wayance, don kada in san cewa kuka yakeyi,,

   Tausayi yabani saboda mahaifiya ai ba wasa bace,

  Don gani nima kusan kulun da tunane inna nake wace nake ganin kamar ban kara ganin ta a duniyar nan,

  Gashi tunda naga makwabcin mu ban kara ganin wani dan garin mu ba, 

   Balle ma yanzu da ban bara ban talan gumama atiti kida alhazai sun zo balle inga idon sani,,,,


   Yana dagowa kan shi yagan mu tare da nafisa aiko sai naga yakara tamke fuskan shi tam 

    Kamar wanda aka  aiko mai da mugun labari,,,

   Ita sam bata damu ba sai wani dan kokarin shige mai da take batun yi,,,

    Nikan wucewa nayi don nakoma dakin da ummi ke kwance,

   Don kada su bidi wani abu ban kusa,


   Gida zamu koma don saboda asibiti majinyata basu kwana  aciki,saidai mai jiya kawai da nurse's,

    Saidai gaskiya shi shehi yace sam bazai koma ba zai tsaya asibitin, tare da ummi ne,,

  Saida Sheriff  yadan yi shige da fita aka bar shehin ya kwana, agurin nata,

  

     Mu hudu ne a cikin motar a hanyar mu ta komawa gida 

   Sheriff ke jan motar  duk da dare yayi sosai,amma baka gane wa saboda hasken da garin keda shi ko ina,

   Zakaga duk hasken fitilo ne ya haske ko ina a garin jama,a kuma basu daukewa har galin Allah yawaye,

   A hankali yake jan motar bakajin komai sai sanyin A C kawai dake ta aiki amotar , kirar Jeep baka, wulk,

   Murya a raunane yadan juya gefen da salim yake ya na magana, dashi,,,

 Yace,  yanzu salim kun san cewa ummi batada lafiya kuka barta har ciwo yacita haka ba wanda ya kirani a waya, ya fada min,

   Yanzu saboda Allah kunyi min adalci ke nan,

   May ye amfanin samun da nayi a,duniya,

  Har, da za,ace wai mahafiyata tana dauke da ciwon yunwa ulcer da hawan jini har yai mata mugun kamu, haka ban sani ba,

   Amal ce ta katse mai maganar shi tace wlh yayan mu  Kada kaga laifin mu

    koda mun ce zamu fada ma sai ummi tace batayafe mu fada ma ba,

   Wai kada mutayar ma da hankali, tunda kana iya kokarinka akan mu bai kamata mu dinga sama wasu wahala ba hakana,,

  Wai zai zama kamar rokon ka muka yi ,

   Salim ya karbe zancen da cewa ai ni koda yaushe nikan ce ma ummi  sai na fada ma,        tunda mutane zasu ga kamar cewa ka kasa kula da lalurar mu ne bawai daga  ummin  bane,,,

   Ya ci gaba da fadin,,

     Aiko wanan kiran da Shehi yai ma bada son ranta bane saida yaga ta rikice shine  yadaga waya yakiraka,

   Tsuki yayi yana mai kada kan shi cikin bacin rai,

    ,azuciyar shi kuma, yana tunane kawaici irin na mahaifiyar na,shi har yai yawa, watan ita dai haka Allah yai mata rayuwar ta cikin sanyin hali,

   Hmmm Allah guda gari bambam ,,,,,Wai hausa ne sukeyi haka wanda sai da kyat nagane may suke cewa,

   Get muka shiga ,muna paker motar mu mukafito,

   batare da Amal ta tsaya ba tai niyar wucewa cikin gida abinta don duk a,gajiye take,

   Niko lokacin na dauko basket din da aka kai muna abinci da rana ga flasks din ruwan tea da nake kokarin dauka wa cikin motar da hannu na guda,,,

   Wani wawan tsawa ya,daka mata ta,tsaya wuri guda cak,

   Tare da yi mata masifa, wanda ita dai duk iya saninta dashi baitaba yi mata hakan ba,, 

  Kayan dake hannu na yace mata ta tayani kwasa zuwa ciki,

   Flasks din ta karba a hannu na ba shiri, jiki a sanyaye,

   Shi kuma salim ya kwaso sauran kayan da muka kwaso daga asibitin,yashiga dasu,

   Bin mu yayi da ido yana tausaya min irin wahalar da nasha yau,

  Shin wai ita wanan yarinyar haka zuciyan ta yake ne,

    Don dai gaskiya inbadon yasan ni tun ban karasa kai haka ba da sai yace kila don asani nakeyi wani abu,

    Amma shi duk abinda zanyi sai yaga na tsakani da Allah ne babu kissa aciki,

   Tsaki yaja lokacin da yake kokarin rufe motar,

  Da ya tuna da Nafisa,

  Wace ta nuna mai halin ko in kula, ga mahaifiyar shi,

  Shi yarasa ita kowace irin mutunce mara tunane da lissafi,

   Ace ankawo mahaifiyar shi asibiti daga Nigeria

  Amma wai har ta biyo shi asibiti tana request din kudi a wurin shi,,,

   Ita bata da aiki sai dai yawan tambayar shi kudi da bukata

  Kuma sai yau yakara sanin halinta sosai don,ganin halin ko in kula da ta nuna mai akan ciwon mahaifiyar shi,,,

   Da wanan tunanen ya shiga cikin gidan,,,,  


   Satin mu biyu muna cikin wanan sintirin zuwa asibiti da gida,

   Inda ummi ke jiyan jikinta,

   Saidai gaskiya ba laifi jikin nata yayi sauki sosai 

  Don yanzu har ummi na iya tashi mudan yawata cikin asibitin da ita,

   Shakuwa sosai ya shiga tsakani na da Amal da Salim, 

   Saboda yawan zaman da mukeyi wuri guda, da su,

   Sai ya kasan ce kamar mun san junan mu da ma ,har ina jin dadin su fiye da zaman da muka danyi da su jamila da mairo da suka zo kwanaki

   Duk da nasan cewa Amal ta girmay ni sosai amma hakan bai hanamu zama guri guda ba da ita,

   Muna mu,amula kamar kawaye,

    Har tafiya Sheriff din mu yayi zuwa Riyadh yin wani aiki na musan man da yataso mai shi da mustapha suka tafi,

   Nice yabarwa kula da duk wani lalura na asibitin 

    Har zuwa lokacin da suka dawo daga tafiyan 

   Tafiyan da kusan itace tafiyan da ta zama makowa nagidan alheri nan gaba,

   Don ko Sheriff din mu yasamu cigaba sosai don yanzu ya samu sa hannu a kusan mafi yawan company tatar man fetur ta kasa,saudiya,

   Saboda kasan cewar shi kwararen engineering da suka sani 

   Saboda suna ganin cewa zai iya barin kasan any time daga yanzu saboda hada hannu da suka ga yayi da company Abu Abdallah dake Dubai,

    Cikin dare ya iso  garin don haka direct asibiti suka nufa,

Suna iso wa lokacin su Amal na waje suna shan iska,   

 Nikuma ina tsaye kanta ina kokarin hada mata ruwan shayi,

  Jin anyi yasa na waiga inga ko waye don nadauka ko Amal ce

  Sheriff ne sai su almustapha dake binshi abaya,

    Gurin mahaifiyar nashi ya nufa direct tana zaune saman gadon asibitin jikin ta yanuna alamar tasa mu lafiya sosai,

    Mun mai sannu da zuwa inda yake ansa muna cikin muryan shi maikama da yanajin kasala ko yaushe,,,

     Da kyat yake magana mai karfi don in kaji muryan sheriff to ta baci,rai ya gani tare da mutun ,,,

    Waje nafita batare da sanin kowa ba don in dan basu wuri su dan zanta, shi da yan uwan shi don kusan nice kwai bare,,a cikin su,,,

  A samane dakin da aka kwantar da ummi yake, don haka waje nafito, nadan tsaya,,,

  Daga sama inda nake tsaye ina kallon ina iya hangen katon agogon nan dake mane a kofar shiga masallacin ka,aba,

   Wanda duk inda kake cikin garin makkah za ka iya ganin shi 

   mutanen dake shige da fice cikin kofar asibitin, nake dan kallo jefi jefi,

   A zuciya na kuma ina, Tausayin yadda naga sheriff ya,damu da mahaifiyar shi ne yakamani,

   Don nasan cewa idan yai wanan irin tafiyan yadawo bai fita ko ina har wajen kwana biyu,

   Yana gida yana hutawa saboda gajiya 

    Saidai in rana,kun ya dace da jumma,a a ne acikin ,, shi,,,, Amma yau sai gashi direct asibitin yanufa don gani mahaifiyar shi,,,,

  Ya shiga yaga  ni ,Yana,Ganin jikin ummin yayi sauki sosai yasa shi fitowa daniyar komawa gida, don yadan huta ma ranshi kadan,, 

   Turus yayi daga bakin kofar dakin lokacin da fito, 

  Don, yaga fadima tsaye wace hankalinta na ga kallon waje saidai kuma hawaye take gogewa a fuskanta

  Wace ita kadai ce tsaye a wajen,,

   A,hankali yatako zuwa kusa da inda take yadafa karfen dake gaban su, yace mata lafiya,

   Kaduwa tayi duk jikinta sai yakama rawa saboda jin muryan da tayi na bazata, alokacin,

   Kara tambayar ta yayi ko may take ma kuka hakana,

   Cikin daburcewa tace mai ba,kuka takeyi ba abune ya fada mata a idon ta,

   Bawai ya yarda da ansar data bashi bane kawai ya barta ne don yasan bazai samu ansa ba, a lokacin,


   Nafisa ce zaune a falo tana waya ga Tufan da Anabi, aje agabanta sai madarar  kwali wanda kwalin yasha rabar sanyin, friged ,da ke aje gefe guda tare da cup,

   Waya take yi a,binta hankali  kwance tana yi tana tsunkar Anabi din tana kadawa baki,

   Sautin kidan  yan kasar sudan ya tashi a cikin tv, dake man ne a falon, a hankali,

    Kafarta guda saman dan stol din tangaran da ke falon

    Har ya shigo falon yakare mata kallon Allah waddai,ya hau sama bata  ankara da shi ba,

   Sai gab da zai shiga dakin shi taga wulgawan shi,

    

Cikin sauri ta tashi ta rufa mai baya ,

   Tana shiga ta iske yana na balle butur din rigarshi yana son shiga wanka,

   Ta bayan shi tazo ta rugumay shi tana sun,sunar shi,

    Batare da yace mata komai ba yadan juya ta kadan ya wuce zuwa bayi,

   Ido tabishi dashi tare da mamakin wai shi wani irin mutum ne haka,

   Sam mace bata agaban shi, 

Kwanan shi kusan uku baya gari yanzu kuma da yadawo gashi ya nuna mata bata a gaban shi,

    Zaunawa tayi tana jiran shi ya fito daga bayin,

  Daure da rigar wanka yafito ajikin shi ga mamakin shi sai yaga Nafisa kwance rub da ciki, saman gadon shi tana dan daga kafar ta da ta mayar baya, a hankali sai hannuta da take, lalatsa wayanta, dagani abinda takeyi a wayan yadauke mata hankali sosai,

   Wardrop ya nufa ya ciro wata jallabiya mai ruwan A,she,colour yasa 

   daidai yana zura rigar ta taso daniyar rugumar shi ,,

   Dakatar da ita yayi cikin tsawa, yakama hanyar fita dakin,

   Binshi tayi abaya tana fadin walahi ita tagaji da wanan halin ,

  May wai yake nufi da ita ne ma, da zai dinga mata wanan wulakancin ita yau tana bukatar shi,,,,,

Daidai lokacin mukayi,   Ido hudu  dashi kuma a,daidai lokacin da take wanan furucin nata,

   Ji yayi kamar ya nutse a kasa don kunya, 

   Saidai kuma ya basar da zancen nats kamar ma bada shi takeyi ba,,,

   Ita ko bata daina ba sai kara ci gaba da fadin kalmar da bata dace ba da takeyi,,,

   Takardan da muka dawo dashi wanda zai je yayi filling, gobe akan gwajin da za,ai wa ummi na karshe,,,,

    Na mika mai gami da juyawa da sauri, don ganin irin halin da na riske su ,.

  Dakatar dani yayi don jin bayanin abinda takardan ya kunsa,,,

   Batare da bata lokaci ba nai mai bayanin takardan a gurguje don jin irin hucin da Nafisat ke yi a bayana kamar wata zakanya,

    Da sauri sauri na,sauko saman step din don ji nake kamar zata biyo ni a bayana,,,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎

24/10/2017, 1:50:13 PM: Maman Safwan: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

          👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                    5⃣1⃣

                       BY


🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

 🐎HUGUMA GROUP🐎

 

   Almost true life story,


   Tun karfebakwai na,safe muke asibiti don yaune gwajin karshe da za,ayi wa ummi,

  Kuma ance ya kasance muna wurin kafin a shiga da ita

   Saboda zasu fitar da result din abin da yake damun ta 

   sosai, hankalin mu yatashi jin cewa ya kasance suna gurin ,

   Anshiga da ita wani dan daki da zasu sa mutun cikin einjin don awo,

   Muna waje tsa tsaye dukan mu cikin da muwa saboda bamusan ko wani irin saka mako zamu samu ba,

    Shehi da sherif din mu sai addu,a suke yi daga inda suke tsatsaye,

   Ina gefe tsaye bakin kofa, sai Amal da ke daidai inda nake tsaye ta dan zauna Salim kuma ya na daga waje zaune,,cikin zulumi,,

     Jin karan bude kofar da akayi ne yasa hankalin mu duk koma gurin, da aka bude kofan

  Wani, Dan likitan balaraben yafito yana mai cire kayan da yayi aikin da shi 

    Ummi ce aka garo ta kamar matatta, babu ko alamar ta na motsi ko kadan,,,,,,,

   Aiko muna ganin haka muka bi bayan su da sauri, , cikin tashin hankali

    Kwance take saman gado asibtin inda nunfashin ta ke tafiya a hankali 

   Wanda zaka gane hakane a jikin dan abin nuna nufashin dake mane kusa bango, gefen kanta,

    Dakin yayi tsit ,ba wani mai kwakwaran motsi cikin, sai karan fanka dake tashi da sauran na,urorin

    Waje na sulale ba wanda yasani nakoma narike karfen da ke saiti da dakin mu,

   Bansan lokacin da na fara hawaye ba,daga haka har nadinga kuka wiwi ni kadai a waje,,,

      Bakomai yasani kuka ba sai ganin halin da ummi ke ciki duk da gatan da aka  mata,,

   Sai kawai tunanen Inna da ke yawan damuna kwanan nan, yadawo min sabo

   Ganin da nayi zuri,an  ummi,duk sun kewaye ta cikin damuwa da tashi hankali,

 To inda Inna na ce yaya zatayi,

  Sai tuna ne ko cikin wani hali take ciki yanzu haka,

  Idan ma tana cikin damuwa ne ba wanda, ko wani rashi lafiya saidai hafsat tayi ta kokari,

 Ita daya batare da ni ba,

  Kenan ni bazan samu ladan da "ya" ya ke samu wurin iyayen su ba

   Hakan ke sa duk naga babba ina kokarin tausaya mai,

   Don nasan cewa nima inna na tana can tana bukatar taimako 

   don hafsat ba,zata iya ba ita kadai,


   Kuka ne ya zo min wi,wi babu kakautawa,

     Jin kukan da sukayi yasa su duk fitowa inda nake gaba dayan su,

   Duk sun kidime, don basu san,komay yasamay ni ba haka,na ba yanzu yanzu

   gashi nice mai kokari wanjen kula da ummi 

   Amma yau na gaza sai kuka nake yi masu duk hankalin su sai ya tashi,

   Shehi ne yazo kusa dani ya na tambayana cikin larabci ko may yasamay ni ko banda lafiyane inyi magana mana  ko zasu fahince ni,,,,

   Sheriff yana daga baya tsaye ido kawai ya kafa min yana sauraren sautin kukana kamar wanda ake watsa ma ruwan zafi a zuciyar shi,

    Ganin da yayi dattijon da su salim su dan riko min hannu,

   Yasa shi yin magana daga inda yake 

   Muryan shi sukaji yana fadin baba kyale ta,

   Gida take tunane babu abinda yasamay ta 

  Da sauri nadaga ido na dasuka yi jajir,saboda kuka, ina kallon shi cikin mamaki yadda san abinda yasani kuka,

    Takowa yayi a hankali har zuwa inda nake, duke 

Ya dan dagoni tsaye da hannu bibiyu, sai ya rugumay ni ajikin shi yana dan buga min baya yana cewa ,

  Hayya hayya,  alamar ya isa niko sai na kara nokewa sosai a cikin jikin nashi,

   Nakara aza kuka sosai, duk hankalin su sai yakara tashi,,,

   Abinda yasani dan tsagaita kukan jin karan yar da jakar hannu Nafisa da tayi abayan mu,, wanda 

  Kusan kowa ya juya don gani ko may ye yafadi hakana a lokaci guda,

   Banda ni da kaina ke ajikin sheriff din mu wanda nake ji tankar yayana na ji daya

  Wanda tun zowa na garin makkah yake taimako  na da alheru

   Wanda a,halin yanzu shine yazamo min jigon rayuwata tamkar uwana da ubana nake jin shi

   Tunda har a sanadina ya iya daukan dawai niyar mu gaba dayan mu nida yan uwan tafiya na batare da gazawan hakan ba,

   Wanda ko sau daya bai taba nuna muna kyama kamar yadda sauran masu kudi kewa yan aiki,ba

  Muryan ta ya dawo da hankalin kowa daga kallon jakar da tayar akasa,

  Ahmad gaskiya ban fahinci may kake nufi da wanan yar ficiciyar yarinyar ba wace na tabbatar da ko da haila bata fara ba

   Balle, nasa cewa koda hannu ta karike ba wani abinda zai kara ka dashi na jin dadi,

   Jayeni yayi a jikin shi a hankali ya dan jingina ni ajikin Amal,

   Tako daya yakai gare ta yace,

    Ke Nafisa Allah waddan hali irin naki hali irin na rashin imani da rashin tausayi,.

   Shin ma dai kina cikin hankalin ki kuwa kodai yau din ma kiyi shaye shayen naki ne, daki ka saba,

   Kalman shaye sheye da ya furta shiyasa ta kaduwa so sai,,,

  Don bata taba tsan mani yasan tana shan drugs ba,

   Saita wayance zancen da cewa ni ban san ko ta ina 

   Ka,hada alaka da wanan yar munafukan yarinya ba mai shegen iya yi,

  Yarinya kamar manyya ta wani kafe ka da idon ta kamar gonar madara,

  Walahi nayi hating din wanan yariyar a rayuwa na,,,,


   Shehi ne dake shiru tunda tafar surfa min zagi imani duk ya kashe shi yana tsaye sai mamaki ta yake yi

 Kowata irin mata Allah ya Ahmad haka da ita, wace bata ko san maye aure ba balle dalilin yin auren, ,

  Dama shi yana ganin ta yasan cewa bata da tarbiya,

  Ba,irin matar da yaso Ahmad da ita ba ke nan,,,

   Sai ga shi yau tanu  ita din kowace,ce wurin yi ma yaron kirki kamar Ahmad

   zancen na  haushin wai har kazafi take kokarin yiwa Ahmad din 

   da cewa wanan yar karamar yarinya kirki mailadabi, 

 Don haka shehi din yace mata

Yo, wanan din ai tana bukatar kulawa ne bawai ita din, ta kula da mutun ba, kamar 

Yadda yaga ita ce wai mai kula da su

  Wa na min din aiba wace za ai wa sheri bace irin wanan domin kwazon ta yayi yawa ga kowa,

   Batare da shehi yakai karshen maganar shi ba ta juya tana kuka batare da ta shiga gurin ummin da sai taga dama take zuwa gaishe ta ba,

    Koshi sai idan hjyn ta tai mata fada a waya take dan zo,wa

   Duk zanan mu asibiti zuwan ta na uku ke nan,yau din da tazo,

   Shiko sheriff, baiko damu da tafiyar ta ba idon shi na akaina ganin da yayi Amal na min dan magana kasa kasa ina daga kaina,

    Cikin dakin da ummi take kwance muka shiga nida Amal 

   Ido yabimu da shi har muka shige,

   Duk ranshi bai mai dadi,ba, ga matsalar kukan da nake ta faman yi ga kuma, sherin da nafisa taimai gaban yan uwan shi,,,,,,

  .Koba,a fada ba yasan kukana bai wuce dayan biyu ,ba,

   Ko kukan zaman mun a haka kamar bayi ko kuma na tuna yan uwa na gida

     Tunda bazaice don ganim yanayin jikin ummi danagani yau nake wanan kukan ba,

 Ai inda sabo na saba daganin ummi din a haka    

     Saida ya lura yaga nadaina kukan, nadan sake jikina kadan

   Salim ya karbo muna shayi,

 muna zaune muna sha. Coffee din nida Salim da Amal,

    Sukan sha abinsu ,sukeyi sosai saidai  ni gaskiya shan bugi nake yi wanawa ,

   don cup din da dan storot din da ake tsotson coffee din kawai na rike inayi kamar mai sha,

Sai kuma can nai shiru, ina tuna ne,

             Mu ukune zaune  saman kujerun dake fuskantar dakin da ummi ke ciki,  Tsakiyan su nake zaune nai shiru, da cup din coffee din ahannu na,

    Ido ya zura min daga inda yake zaune,sai a lokacin ya lura da cewa na ramay nayi baki,

   Gaban shi ne yafadi dam,

   Yace kar dai a ce aikin da nakeyi ne yai min yawa haka ,har na dan ramay batare da yasani ba,

   Aiko dai kada ya shiga hakkin yar mutane, da yawafa,

   Yasan cewa dama nayi yar karama da wanan irin dawainiyar da nake yi,

   Kwazo kawai irin nawa kesa ana sani wani abinda ya kamata babba yayi,

   Tashi nayi don injefa cups din kwalin da muka sha coffee din a dustbin 

   Lokacin yakara ganin yar raman da nayi ba kadan bace,

   Saidai kawai nadan kara girma ne ta kasa na,kadan saboda nadan buda alamar girma, ya fara baiyana min,

   amma zuwa sama na duk na dan ramay sai dai na dan kara tsayi sosai,,

   Shehi ne yakatse mashi tunanen shi da cewa, Wanan matar takakuwa diyar cikin aminin mahaifin naka ne,

    Murmushi yadan yi natakai ci dai dai lokacin da yake kauda idon shi akaina lokacin ina kokarin zama inda natashi,

    Yace ma Shehi a gaskiya baba ni bansan komai gamay da gidan Alhajin kano ba don ni dai nasan cewa tun ina yaro saudaya ma nataba zuwa gidan lokacin da zamu koma hutu, suraj yace ma driver ya bida mu ta kano din,

  Kuma muna komawa gida hjy mama ta haushi da fada don may sukaje dani har aka ba mu kyauta iri daya dana,su,

   Tun wanan lokacin naji duk wani dangi na hjy ma ma yafita min arai, na,,,

    Abba na ne yai wanan hadi nikuma na wakilta bashir na mu na wurin kawu sale da ya gabatar da komai kamar yadda Abba ke so ayi,,

   Nadauka cewa Abba zai yi min zaben alheri ni ba wai irin wanan zaben na danasani ba,

   Kuma duk abinda take min bazan iya fada ma Abbana ba don nasan cewa zai iya shiga wani hali idan yaji,,,,

    Haka na wuni arana cikin rashin walwal, duk tunanen yan uwana ya addabe ni ya hanani shakat,,

   Bayan mundawo gida duk wanda yagani aranan yasan ban cikin hayacina da akwai abin dake damuna,,,

   Ina saye da rigar barci ajikina doguwar riga ce pink sai hula fara da rufe kaina na kawo zani nadaura saman rigar,

  Har nadan kwanta sai na tashi saboda da muka dawo,,

   Kowa yaci abinci amma ni na kasa cin komai don haka kitchen na nufa don in dauko madara in dan sha,

   Har na dauko sai naji wani sabon kuka yazo min har yafi nadazu,

   Ashe Amal na biye dani zuwa kitchen din, ganin da tayi ina kukan 

    Hakalinta ya tsahi ta je da sauri takira, sheriff wanda ke zaune yana latsan laptop din shi a falo,

   Cikin sauri ya taso ya biyo ta har kitchen din inda nake durkushe da kwalin madara a hannu,

   Jinayi yana ce min, Ta,al ya ukhti, Ana asfan,,

   A hankali nadan daga kaina sai nagan su a tsaye bisa kaina,

  Namike da sauri, nafada masu ajiki shida Amal ina mai kara sautin kukan nawa,

 Har daki na yakaini saman gado inda Amal ta dan tsiyaya, min milk din a cup ta miko min,

   Ba musu nakarba saboda irin kallon da yake min,,,saida nasha kusa rabin cup din namika mata ta karba ta juya don ta mayar da cup din da sauran milk din

   A gefen gadon yake zaune shi ma ya hada hunnu shi biyu wuri guda ya dun kule, su,

   Nan yake ce min natuna da inna ne ko,   

 Don   ganin da nayi ma ummin su ko ba musu na kada mai kai alamar eh,

    Yace min in yi hakkuri bada dadewa ba zan tafi gida insha Allah

   Dago kai nayi da sauri na kalle shi don in gaskanta maganar nashi,

   Muna hada ido dashi yadaga min kai alamar eh, 

   Gaskiya da na,hango a idon shi yasa na gaskanta zancen nashi,,

   Amal dake tsaye kofa tadan kara sa shigowa daga ciki, dakin 

   Ai Amal bata ko zauna ba aka turo kofan cikin fushi 

    Idon mu duk kofan yake kallo don mamakin ko waye ya turo kofa haka,

   Nafisa ce a fusace daganin ta kasan tana cikin fushi saida ta kare muna kallon rainin wayo gaba dayan, mu, duk ka ukun sanan ta juya tana 

    Kallon banza Sheriff din yabita da shi batare da yai wani magana ba yatashi gami da ce muna saida safe,

   

     Yanafita Amal da rakashi da kallo tace wanan shegiyar sai nayi maganin ta don naga bata da mutunci sam wlh,

   Ranan nan mu uku, muka  kwana mun sa  Aisha tsakiyar mu,

  Washe gari da ciwon kai na tashi sosai saboda kukan da nasha yin nin jiya din,

    Nice kullun mai kokarin tashi don inga an yi duk wani aiki da yakamata ayi da safen,

    Jinda kowa yayi shiru yau gidan ba motsi na ba a,lamana sam 

    Yasa wasu daga cikin yan gidan namu fito,

  Ciki harda Amal da Salim ,

   Don Amal tun asuba ta koma dakinta ta kara gyara kwanciyar ta,

    A falo Salim ya tsaya ganin cewa rana yadan yi saboda zuwan mu asibiti wurin ummi, gashi almost to time,

    Amal ce takware  da nake ciki yadda ta gani cikin bargon yadan bata tsoro,

    Kwance nake ina rawan sanyi, ga wahaye tab ga ido na 

   Aisha na gefe na zaune tana kallo na ina jin lokacin da ta tashi tana ta dan jijigani cikin bargon

   Tana cikin hakane sai ga  Amal Allah ya kawo muna don ban iya dagawa sam wlh,,

     Da sauri taje ta kira Sheriff  wanda suka hadu yana shirin saukowa  kasa ,, Dakin da nake suka nufa duk kan su hankali ta she,

   Yana kallo na a yasan cewa har da fever ya kamani,

    Ina nan dunkule sai kuma naji amai na shirin kamani,,

   Da sauri suka taimaka min zuwa wurin mota, sai makyarkytan sanyi nakeyi,

   Ina dunkulewa,wuri guda

  Muna isa asibiti aka wurin doctor kamal abokin shi ya kai mu,

   Ina ji lokacin da sheriff ke ma doctor bayanin komai tamkar nice ke bayani,

   Bayan an rubuta magani ya kasan ce har da allura za ai min guda,

   Aiko nan muka kwashe ta da nurse din don naki bari taimin Allura sam 

    Sheriff yasa Amal ta rike ni gam ina ta tsala ihu ina fadin Anna tazza habb

   Suna waje suna ji na dagashi har Salim din murmushi suke yi suna min dariya,

   Ina fitowa ina dan share hawaye na,muka hada ido da Salim da shi ,sai duk suka kwashe da dariya,

    Hararan Salim din nadan yi tare da turo baki alamar jin haushin su,,,

Gida aka dawo dani saboda yau badamar zuwa asibitin da ummi ta ke nima ina fama da kaina,,,,

   Barci mai nauyi ya dau ke ni bani na farka ba sai daidai lokacin sallah azahar 

   Duk da nauyin da jikina yai min bai hana ni tashi zuwa don inyi sallah ba

   Abinda nagani yasani mamaki so sai don koda ake ma doctor bayanin abin da yasamay ni ban.   dago cewa sing of period sheriff ke bayani ba don yanzu nadan rage yawan ciwon mara kadan bakamar da ba,

  Don duk wani abu mai zaki na rage shan shi yanzu saboda irin wahalan da nakeyi,

       Jiki ba kwari nadawo nakara nadewa saman gado, ,,,,,   

   

     Allah ya sa na dan ji saukin jiki na so sai har ina dan yin aiyukana na cikin gida

   Yau ne muke sa ranan za,a sallamo ummi daga asibiti

   Saboda samun saukin da tayi sosai jikin ta ya komal normal tasa mu lafiya,

   Duk wanda ke gidan yazo taron ummi da dawo, anayi mata barka da arziki ,,,,,

     Zaune kowa yake a falon anata nuna farin ciki muko sai zirga zirgan hada masu abincin lunching mukeyi don bayan  azahar ne suka dawo gidan

   Nafisa ce zance kusan karshen zuwa tariyan ummin wace tafito cikin kasaita da isa,

      Batare da ko wani dar ba tasamu daya daga cikin kujerun ta zauna,

   Sanan takewa ummin gaisuwa,

 Daga haka mikewa kaiwai t ta koma dakin ta tana tafiya tana wani juya kwan kwaso, ta da karfin dole,

      Ido kowa dake falon yabita da shi da mamaki irin hali ta na ko in kula da takewa ummi

   Mudai ba musan cewa ita din yar uwar hjy mama bace balle mu fasara zance da wani manufa

    Iya kadai muna ganin rashin tarbiyanta da kuma nuna wulakanci ga kowa,

       Muryan Amal ce ke fadin dama hjy tsohuwa ta fadi gashi ko ya bayyana

   Jinin su hjy mams ba jinin alheri bane tasan cewa wahala kawai aka hada yayan su dashi,,

      A cewar ta wanan aida ta samu wuri da tafi hjy mama iya sheri,

   Dadin abin yayan su ne bai bata wuri ba,,,

   Ummi ce ta kwabe Amal din da fadin ta dai sa ido ga abinda bai shafe ta ba,

    Sheriff na jin duk abinda Amal ke fadi dakuma kwabeta da ummi tayi baice komai,

  


🐎ZEEE MAKAWA🐎

24/10/2017, 1:50:14 PM: Maman Safwan: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                 5⃣2⃣

                   BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎


Almost true life story 🎁 *NASIBI* *WRITERS ASOCIATION*🎁

      

            N 🎁 W 🎁 A


  Dawowan Ummi gida da kwana biyu muka lunch zuwa sabongidan gaba daya gidan har hjy mu,

   Saidai gaskiya  wanan gidan yafi karfin wan,can tsoho gidan sosai gida wanda bazan tsaya maku bayanin shi ba, don girman shi,

   Haka kuma naji yana waya akan wani gida daya saye a Abuja Nigeria inda naji yana cewa zaizo yagani kwanan nan,

    Allah ya nufa da ummi za ai wanan shagalin komawar,

   A ciki muka fara azumin watan Ramadan company su yafara aiki sosai a kasar wanda Allah ya basu nasaran samun kwastamas ta ko ina afadin kasar

    Abinci sosai ake yi  na bada karama wata katuwar mota ce ake wa loading abincin buda baki mai dadi, akai bakin haram aje anabadawa hade da abin sha ruwa da lemon kwanko da dabino,

    

   Wani irin shakuwa da aminci mukeyi tsakanin nida Amal da salim,

   Kusan ko yaushe idan ba aiki nakeyi ba zaka samay mu tare,

   Muna hira ina koya mata larabci ko kuma muna karatun novel na hausa da tazo da shi,

   Ummi na jin dadin zama dani kamar yadda nake nin dadin zama dasu.

    Shehi yaso ya koma gida amma Sheriff ya hana acewan sheriff din ya tsaya yayi umurah tukun sanan ya tafi,

   Inda ya aika wa sauran iyalan she da abin azumi batare da sanin shehi din ba,

   Bashir yaba yakai masu duk yan uwa nagari Auno din sun samu wanan kyautar daga dansu jikan su  Ahmad,wanda suke kira da baba karami,

    Sai bayan kwana biyu iyalan malam Shehi,suka kira Shehi din  a waya suna mai godyan kudin da yaturo masu,

  Cikin mamaki shehin yace masu gaskiya bashi bane,

   Saida uwargidan shehi tace bashir ne yakawo masu shine Shehi yagane cewa Ahmad ne ya masu aike,

   Da safe Sheriff zaiyi tafiya zuwa yamal ,

  Da sallama yashiga bangare da su ummi suke inda ya samay su zaune suna lazimi , 

    Ya gaishe su cikin girmamawa da ladabi, ya juya gurin ummi yana tambayar ta lafiyan jikin ta,

    Muryan shehi ce ta katse mai maganar da yakeyi da ummi din

   Dai lokacin nagama hadawa ummi abincin da zatayi break tasha maganin ta,

  Kasancewa rashin lafiyan ta baibari tayi azumi,

   Likitoci sun hanna ta yin azumi saboda ulcer fa yai mata yawa, da ita da hjy mu ce basu azumi tare nake shiga kitchen in hada masu abinci. 

   Shehin yace hakika Ahmad kakai yadda ake duk wani mumini yakai ,

Musan man wurin kyautata wa yan uwa,

   Kayi koyi da yadda hadisin mazon rahama yazo muna,

  Akan idan zamu yi alheri muyi shi batare da hannu hagun mu yasan hannun daman mu yabayar da alheri ba,

  Banda abinda zance sai dai in kara gode ma bisa ga alherin da kaiwa iyali har mada yan uwana,

   Hakika da kai da mahaifiyar ka ku alheri ne gare ni,

   Fatana gare  ka shine Allah yabaka zuri,a masu albarka wa yanda zasu gado halin ka, 

   Saidai gaskiya wani hanzari ba gudu ba shine,

   Sai shehi din yadan yi shiru kadan kamar kalman da taye son furtawa tana da nauyi,

   Lokacin kuma nagama hada ma ummi abinci a gabanta,

   Namike da niyar barin dakin sai naji muryan ummi nace min dan tsaya in bude mata drink din dana aje mata,

   Kallona sheriff din yayi shima ahankali yakali kwankon lemon da ke gaban ummi,

   Shehi yacigaba da fadin gaskiya kana bukatar kara iyali Ahmad,

  Ahmad din da kanshi ke duke saida yadan daga yakali shehi din,

   Shehi yakada mai kai alamar kware kuwa, saboda nan gaba akwai matsala inhar bakayi hakan ba,

   Kai baba shehi kenan wanan din ma yayana iya da ita balle inkara jajibo wa kaina wani ma tsala,

  Murmushi shehi din yakara yi yace zakayi ne Ahamad ko ba shiri idan har lokacin karawan yayi,

   Da haka sukayi sallama yatafi yamal diba wani company tatar mai mallakin gwaunatin kasar saudiya da ya samu matsala ya tsaya 

  Zaije yada da sauran abokan aikin shi su tafi,

    

    Muna ganin Sheriff yai tafiya ,muka yi shawaran zuwa zaga gari,

 Nida su Amal naima driver da nake fita dashi sayayya magana akan zai kai mu unguwa, washe gari,

   Sai da zamu fita nake fada wa ummi cewa zamu dan fita don suga gari,

  Tace muna kada mu dade saboda ba sanin garin mukayi ba, 

   Dariya kawai nayi don nasan guri guda gudane ban sani ba,indai har idon garine,

   Don ba inda bamuje yawon bara ba, a garin,

  Cikin shirin mu ta alfar ma muka fito inda koni shigar tawa tabani sha,awa sosai,

    Wata doguwar rigace ta larabawan Jordan nasa,ban taba sa waba,,, Rigar nafisa ce dayaje Dubai kwanaki yasayo mata ,

   Tun nan inda yaba ta tajefo min tace batasa irin shi ita,

  Itama  Amal shigarta yai mata kyau sosai 

   Mun hade da Salim a gurin mota, har mun zauna driver zai tada mota sai ga nafisa da saurinta,

  Wai mu fito zata fitane itama,

   Nidai ina baya ina jin su har ina shirin balle murfin mota in fita Amal ta hana ni

   Salim dake ta gaban mota ne yace mata sai kiyi hakkuri idan mun dawo kyatafi,

   Yace ma driver ya mota mu wuce muna jinta tana ta haushi kamar wata tababiya 

   Har mukabar gidan suna mata dariya kamar mahaukaciya,

  

    Munje gurare da dama agarin na nuna masu gurare tarihi sosai,

   Sai kuma wasu shagunan kaya da muka ziyar ta, da gurare saida kayan abin motsa baki,.

    Amal duk ta rude sosai  dagani wani katon shago na saida kayan sawa na mata da yara,

   Saida naga tagama rudewa ina mata dariya, daga karshe nake fada masu cewa ai shagon Sheriff ne ,.

    Na nuna masu wani na saida kayan maza dasu carpet din sallah iri iri 

   Baki suka sake suna mamaki har cikin mota suna kara tambayana nace masu wlh nashi ne,

   Wasu manyan motoci da sukayo loading mutane wanda da,alama baki isowar su kenan motar naga tana ta kallo har tana waige,

  Nace mata ai indai wanan garin ne kada kiyi mamaki darin su sushigo kamar haka,

   Nace mata gari ne da zaki ga taron bil,adam kamar duk duniya aka tara tundai ranan jumma, ranan da duk yan kauye da kewaye sun shigo ga baki sai kiga garin yazama kamar ba ko isakan shaka,,

   Duk da dare yayi saida nakai su wasu shaguna dake cikin kasa inda shagunane sunfi guda dari akarkashi kasa akajera su birjit,

    Shagon saida zinare dayafi kowani girma wurin nakaita,

   Saida Amal tace min don Allaj fadima mu fita haka sanyin wurin nan ma yai min yawa ga girman wanan shago kada yasani mafarki pls,

   

     Har muka isa gida tana santin shagunar da duk mukaje,

    A bakin get mukayi tozali da sheriff wanda yafito da niyar zuwa masallaci sallah cikin jallabiya baka , mai dogon hannu kan shi da "yar fula karama fara, sai Almustapha dake gefen shi shima cikin farar jallabiya,

   Tunda na hangoshi sai naji gabana yafadi don musan cewa bayau ne zai dawo ba, sai zuwa jibi,

    Kamar munafukai muka fito motar muna dan nonokewa , 

   Duk da yagane nufin mu bai ce muna kowulakan ,

    Salim ya kalla yace mai ya harama zuwa sallah kafin ata da jam,i,

   Muna shiga gida har mun manta da zancen nafisa ashe ita tana nan tana ta hauka tun wucewar mu,

   Akan dole sai an dauki mataki akan mu tunda munyi mata wulakan

   Masifa take tayi  yasa ginan gida jen su ba irin namu na Nigeria bane,

   Balle wani yaji yadda take masifa ,saboda su ba halin su bane,

   Ina dakina bayan mun idar da duk sallolin mu  sai natashi ,ina cire kayan da sa ajikina ji kawai nayi ambankado min kofa da karfi 

  Najuyo don ganin kowaye yai min wanan irin shigar daki,

   Allah yasa ban cire riga ba nadai cire dan kwali da su yan kunneya na,

   Nafisace tsaye tana wani irin haki  gyalenta a hannu ta rike shi don masifa,

    Tana batun finciko ni taji anjata baya da karfi ko da ta waiga saitaga sheriff ne ,wanda dawo wanshi kenan daga masallaci , zai shigo yaga wulgawanta ,zuwa sashen mu,

    Sanin halinta dayayi yasa shi biyo ta yaga ina zata,

  Ganin da yayi dakina ta dosa yasa shi biyo ta har ciki, ganin yaje yeta yasa tafara 

   Ai ko  sai  tahaudura min ashar ,bakar Ashar,

  Takara yo wa kaina gadan gadan, hakan yasa na boye bayan sheriff din wanda bakin ciki ya hashi yin ko yin magana

   Ganin da yayi  cewa bazata fita dakin ba shikuma mutum ne wanda baison fitina 

   Hannu na yaja zuwa waje, muka barta can dakin,

  Aiko saita sa kuka wi wi, wai ya wulakanta ta saboda yar aiki,

 


     Tundaga ranan sheriff ya hanani duk wani aiki da yashafe fan,nin nafisa tunda tace sai ta halakani,

   Hakuri Shehi yaba shi so sai tare kara mai karfin gwaiwa, akan ya jure,

   Wanan fitinar da NAFISA tayi yasa muka sake jiki ga fadan da muke tsan mani gurin she,

    

    Koda yaushe Amal tana bani labarin Nigeria dakuma labarin yan makaran tar su da sukayi karatu tare,

   Ina jin dadi wanan labari sosai ,

   Idan tana bani sai in yi kwance in yi shiru ina saurare ta gama yanzu da banda wani aiki sosai a gida sai aikin ummi,

   Can mukan zauna muyi ta hirar mu,

   Har kusan lokacin shan ruwa sanan indan fito inyi aikina,

   Aikin yanzu baida wani yawa kamar da iyakata kula da masu ayukan gidan,

   Saikuma in dan zagaya inga abinda yadace ayi ma ma,aikata,


      Azumi na Ashirin baba Shehi yai haramar komawa gida don sallah wurin sauran iyalin shi,

   Shirye shiye sosai a,kayi mai ,

  Ummi tatura mu munje munyi wa yan uwarta sayyaya sosai 

  Jin da nayi ance hjy tsohuwa guri guda take da su, baba shehi yasa naje nasiyo mata maganin ciwon kafa da kuma magani ciwon ido,

   Naba baba shehi yakai mata cikon kayan da na hada naga Amal ta jefa wasika tace akaiwa hjy tsohuwa,

   Ana gobe malam zai wuce nashiga dakin su inkai wa ummi fruit sald kafin ta kwanta 

   Sai na iske malam she da yaran shi Amal da Salim, yana basu wani dan abu suna lasawa,

   Har na juya zan fita yace min yaki "yata sai na dawo nasamu gefe nadan tsuguna daidai saitin da Amal take yace min indawo

    Ni abinda tabasu yadibo ya bani in lasa,

   Na lasa yace min in miko mai hannuwa na na mika mai yakama hannu na dama ya murza min wani abu fari kamar takarda sai naga abin yashige min a jiki,

  Inata juya hannu ko zan gashi banga abinba yabi lafiyan jiki,

   Karshe yace min intashi in tafi Allah ya tsare masu mu mukace Ameen gabadayan mu,

     Washegari malam shehi yawuce yabar mu da kewan shi sosai,

   Dattijo mai dadin sha anni, dakuma fadin gaskiya,

   

      Saura kwana biyar sallah da dare har na kwanta sheriff yace  akirani a falo nasa may shi yace min gobe in shirya in raka Amal madina kuma ga goben zamu dawo,

   Sanin da nayi tsakanin Makkah da madina akwai nisa sosai yasa nadaga kai na kalle shi sai yace inda bamu gama bada wuri zamu iya kwana har jibi in sun gama mudawo,

   San mako mukayi tunda safe muka kana hanyar madina,

    Amal ta dauka ai ba wani tafiya bane mai nisa sai taga har ana batun marance bamu isa ba, nan ta waigo inda nake ta kallon dogon dajin da ma,aiki manzon Allah SAW sukayi tafiya hijira saman rakumai daga makkah zuwa madina,

   Gaskiya mu munzo cikin musulunci mai dadi dibafa a mota muke ta tafiya haka amma bamu kai ba,,,,,

    Amal ce ke ce min fadima har yanzu nace mata saura kadan insha Allah,,,,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎

24/10/2017, 1:50:16 PM: Maman Safwan: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

          👣👣👣👣👣

            👣👣👣👣👣

                     5⃣3⃣

                        BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP ND NASIBI GROUP🐎

    🎁  *NASIBI WRITERS ASSOCIATION* 🎁

           🎁N🎁W🎁A


Ku _yi Afuwa arayuwan ku

Kuyi sasauci ,arayuwa,ku

Ku yawaita murmushi da godiya ga dan uwan,

   Sadaka na kariya sosai ga bawa ranan tsayuwa jiran hisabi,

   Allah yasa mudace,


  Yan huguma group ban taba mantawa da ku ban manta alherin ku gare ni,

Nagode Nagode Nagode


Almost true life story,,,   Gab da sallah la,asar muka shiga garin na madina garin da duk duniya babu inda takaita gaskiya da son jama,a garin mutanen kirki ga mutunci, garin da ba ruwan ko da sa ido ko hassada ga dan uwa,

    

    Cikim larabci nai ma driver mu yusuf magana nace ya wuce damu direct mai kai gaisuwa mu kuma kwaso lada tunda

  Mun makara nasan cewa baza su samu yin abinda yakawo su ba yau sai gobe, 

   Don haka goben ba,la,lai bane musa mu zuwa da wuri kafin mu wuce,

   Saboda nasan cewa madina bakamar garin makkah bace gari da komai acikin natsuwa akeyin shi,

    Al,umman garin madina daban suke da sauran mutanen garuruwan su maci kusa,

   Karfe goma anrufe massalaci Annabin rahama ba,a bari kowa ya kwana acikin shi,

  Bakamar masallacin makkah bane da wasu ma anan masaukin su yake,

   Nan suke kwana suke komai,

   Iyaka sai in anzo shara su dan kwashe kayan su su a,gyara wuri sai su dawi

   A gaskiya koda banda wayo nasan cewa kasar saudiya kasa ce mai albarka da hakkuri da jama,a,

  Duk yadda mutum yake suna hakkuri da shi indai har ibada kaje yi,

  Ba irim mu takari masu zuwa da wani manufa ba na dan ban don tara dukiyar duniya,

    

      Saida muka kusa isa kusa da massalacin na juya nai ma su Amal da Salim bayanin abin da nagaya wa driver ,

    Suma suka ce gaskiyane, nai ma Yusuf driver magana don Allah yayi kokari yakai Salim wurin ziyara manzon rahama idan an, sallamay sallah nafada mai duk yadda zai yi,

   Cikin dauki Salim ya bar mu ya matsu su shige,

    Saboda gajiyar da muke da shi,

   Bayi muka fara shiga muka dan gyara jikin sanan muka dauro Alwala muka fito,

   Duk da wurin ya cika tab da jama,a tun awajen baisa mun tsaya wajen ba ciki na rikewa Amal hannu muka kutsa Allah ya taimake mu muka samu wuri kusa da wasu yan tsufi mutum biyu mata, mutanen Indonesia

   Muna zama yar tsuhuwar guda ta gyara muna wuri muka zauna gab da su jiran afara sallah gudan ce ta miko muna hannuta guda da baida tasbaha muyi mu,sabi,a da ita, 

   Bayan an salamay tsuhuwar guda tace muna mudan taimaka masu suna son suyi ziyara kada a matse su a gurin,

   Tare muka jera da su har cikin Rauda, kusatawa naitayi cikin jama,a har bisa green carpet din nan da akace shine saitin kabarin Annabi yake,

    Dole nice na tsaya masu suka samu sukayi sallah raka,a biyu sukayi gaisuwa ga maikin Allah tare da sahabban shi guda biyu da aka rufe su kusa da kusa,

    Sanan na samu nima nabi ayarin wasu yan Syrian nayi nawa raka,a biyun na addu,a 

   Batare da bata lokaci ba na jawo yan tsuffin nan da Amal mukayi Exist kafin akore mu,

    Anan muka sha ruwa mukayi buda baki dayake watan azumi ne bamuyi wahalan sayen abinci ba ga karama nan kalakala ana bi layi layi ana ajewa sadaka saboda Allah da Annabi batare da kasan kowa yakawo ba,,,

      Sai bayan sallah isha,i  muka, bar masallaci zuwa masaukin mu,

     Dayake nasan gidan sai nai gaba wurin nuna masu, kowani sashi,

     Kafin mu kwanta muna dan hira mu a falon gidan wayata na gefe wacce bata da wani amfani inba game ba dom nasan cewa banda labar kowa da zakira,

   Shine samu yafi iyawa, gadai waya dankareriya amma ba lambar kira saidai gamen da sauran abubuwa,

   Cikin ikon Allah wai yau wayan itace tayi kara alamar ana kirana,

   Salim ne  yace kirana akeyi nace mai, a,a bakira bane,

   Yace to may nace mai oho, 

  Wayanta kara yin ruri alamar kira nabiyu ya kara shigowa kuma,

  Shi yai min received ya kara min a kune na,

   Abin mamaki wai muryan Sheriff din mu naji radam awayan nawa yana sallama,

  Saida nadan daga wayar nakalla cikin mamaki sanan nakara sawa a,kune na,

   Jinayi yana ce min ya muka isa nace mai lafiya,

  Kafin yai wani magana namika ma Amal,

    Saina koma gefe ina mamaki, don ance kira saida sim to aini ko sim din bansa ba balle insa kudi,

    Abinda yafado min arai shine kafin mu bar makkah a daren jiya su sheriff da Salim suna zaune nazo wucewa Salim ke cewa sai faman rike waya nakeyi kamar wace za,akira 

  Yace min inbashi wayan ya gani na mika mai naga yafara game sai nawuce na barshi da ita, kawai 

   Sai zuwa zan kwanta nazo nasamu wayan an aje min samar wani dan tabur dake gefen kujerar zaman Sheriff inda yake yawan zama ya bude system din shi,

     Anan nasamay ta aje nadauka ina gode ma Allah nafisa bata gani ba, aida yau narasa wayan ke nan,,,,,

    Ban kai karshen tunanen ba naji muryam Salim nace gashi zan bata, 

    Dama da larabci yake min magana ni dashi dinma yacigaba dayi min ko yanzu,

    Yafada min cewa kada mu makara gobe zuwa wurin da zasu don Allah inyi sakko in kai su na ansa da fadin na,am insha Allah,, da haka yakashe wayar yana mai min godiya

    Wayar nabida kallo kamar yau na fara rikata mamaki fal a,zuciyana,

      Amal tace min aiko tunda yawa na da sim zata kira wasu kawayen ta da sukayi karatu a FGC bauchi tare , saboda ta fada masu cewa itakan tana saudiya,

   Ganin mamaki a fuskana Salim yace min halan bansan cewa ansa min sim bane , yace min jiya Yayansu yasa min sim sabo yakuma yi loading din kudi saidai baisan ko nawa bane a ciki,

   Bamu dade ba muka kwanta saboda musamu zuwa inda zamu da wuri da safe,

    

      Karfe takwas na safe yai muna a office din mutumin inda ya kaimu wani guri da za,ai muna interview,

    Nikan yar rakiyace don haka binsu kawai nakeyi hankalina kwance sabanin su danaga duk sun shiga damuwa, sosai

    Kwantar wa Amal da hankali kawai nakeyi,,har nasamu naga tadan shiga natsuwa,

   Lokacin da aka kira su sai na zauna ban tashi na bisu ba,

  Mutum ya waigo yace min in yasauri mana intaso  kada muyi delay 

   Na dan waiga gefena inga kodawa yake magana sai naga tabas dani yake saina ce Ana, yace min Na,am

    Da mamaki natashi na gyara nabisu baya tare muka shi mu uku,

   Abu na farko da na lura dashi shine sun fara diba shigar mune, sai kuma natsu,

     Bawani dongon tambaya sukai muna ba sundai tatace takardun dake gaban su cewa mudin ne bawasu bane,

  Don haka suka ce muna mufito waje,

   Mamaki min fal a zuciyata don ban san ko may ke faruwa ba,

    Mutumin da yai muna jagora ne yake ce muna gaskiya munyi sa,a sosai saboda shigar da mukayi ya nuna masu cewa muna da kamala kuma sun auna tarbiyan mu sunga ba mu da matsala shiya sa muka samu saukin interview din,

   Amal ce ta kallo ni don ina ganin ta tuna da yadda mukayi jafin mubar gida dazu 

   Don wani dogon riga tadauko English wear zata sa na ce ma, la,la,la,

   Kada tasahi nazaba mata wani dogon jallabiya baki maidan adon duwatsu bakake naba ,sai ta kama ce min ita gaskiya bata iya wanan shigar tamu kulun mutun ko yayi kwaliya mai kyau sai yadauko wani bakin riga cen ya aza sama,

   Ban kulataba na gyara mata rolling dinta baka ganin komai nata sai dan fuskanta kadan duk da bataso bataki tanawa ba,

   Munfito falo naga Salim da wandon jeans da riga yar karama duk ta matse mai damtse hannunbshi surar jikin shi yafito,

   Shima magana nai mai yai kamar zai make ni da dan filon dake kan kujerar falon sai nadan kauce ina dariya 

    Amal tace mai nima kaga yadda tasani shiga kamar wata yar shi,a can

    Zuwa yayi yasako jallabiyar shi fara, tare da yar fullashi fara,

   Yafito nace mai to ko kai fa, ya zakazo wa mutane haka kamar mai zuwa wasan wrestling,

   Dariya mukasa muka sa gaba dayan mu, sai muka, fita zuwa wurin mota,

   Hannu na Amal tarike gam batare da taimin magana ba,

    Har muka gama komai tana rike da hannu na cikin nata,

   Saida muka shiga  mota don dama mun fitogaba dayane da niyar komawa gida,

     Amal take ce min kai Fadima anya kuwa, ke ba,, sai kuma tai shiru, 

bataci gaba da magana ba,

    Wata ce tai yar tsuwa alamar kira yashigu, nadauka tare da yin sallama cikin tatausar murya ya ansa yana ce min 

    Yacigaba da cewa shukuran shukuran ya ukhtin Ana asfan,

   Murmushi nayi kadan har fararen hakora na suka dan baiyana afili,

  Ashe sautin murmushi har inda yake yaji shi, alamar naji dadin yabon da yai min,

       Kafin yafadi wata magana sai na mika ma Amal wayan ,jinayi tana cewa yayan mu nice 

    Dariyan danaji tana yi yasa nadan waiga gefenta sai naji tace walahi yayan mu Fadima Allah bata wayo itace fa tasa mu wanan shigar har ina fada da ita,

   Salim harda maketa yatashi yi don tace baza mu fita dashi hakana,

    Salim din ya karbe wayan hannun ta shima yashiga hira da dan uwan nashi,

     Akarshe yadan ihu da murna najin dadi yana fadin an aikawa wa yayan mi cewa duk andauke mu a makarantar 

 Murna mukasa a cikin motar Allah yasa Yusuf gwanine da saidai yadda hali yayi, kawai,

     Bayan mundan tsagaita murnan Amal ke ce min wai yaya nasan cewa suna considering da shigar mutun ,

    Saina bata labarin lokacin da baban Nailabin zai sani karatu yadda mukayi a makarantar, dasu wurin ganin shigar da wasu sukayi,,


      Mun isa gida lafiya cikin murna dafarin ciki dakin ummi muka wuce direct, 

     Yadda nags sun rugumay ta nima kusan hakan naje na rugumay ta tajowo ni sosai cikin jikinta, 

   Bansan lokacin da na fara hawaye ba, ummi tace a,a,a tajeye Amal takara jawoni sosai cikin jikinta tana share min hawaye tace asha fadima godiyan da zakiyi wa Allah ke na ta dagoni tana mai girgiza kanta tace min inyi sadaka in nafila ingode ma Allah shine abin yi ba wai kuka ba,

     A gasikiya ni dai bansan may zance wa wayan nan mutane ba don godiyar da baki bai yi sai dai shukuran,

     Saboda irin halarcin da suke gwada min yai yawa walahi banda wani matsala yanxu sam

     Matsalata gudane itace Nafisat wace kusan kowa agidan taza mai ciwon ido,

   Har maigidan takai mai ko ina, arayuwa bin umurni mahaifi ne kawai yasa shi yin hakuri,

     Dana tashi gurin hajiyar mu na nufa naje naimata bayanin komai da akeci,

   Taimurna so tayi farin ciki dajin bayani da nai mata inda tayi min addu tare da kara roko na gafaran abinda taimin can baya,

   Har kullun ce mata nakeyi ni batai min komai ba don komay yafaru da mutun tab batacen al,amari ne,

    Tun ran gina tun ran zane duk abinda zai samayka saifa yafaru,

   Don haka zuwa na gurinta da kuma zuwa na makkah koba ta dalilin taba saina zo

    

       Sheriff din mu bai gida yatafi Riyadh gurin aiki don haka koda muka dawo mun samu baya gari,

    Don  haka hankalin mu kwance, muke komai kasan cewa gidan mu na yanzu babba shiyasa badole bane wani yaga wani inba da wani dalili ba,

    Nafisat zan iya cewa rabon da naganta tun ranan da ta,tashi shaka na aka ceceni gurin ta,

   Yanzu wanan kawar data samu itace tadauko mata yar aiki wace itace ke mata komai,

   Mudakeyi da duk andakatar da mu, ko sai dai muyi aikin mu na tsakar gida zuwa fannin sheriff 

   Komai na sheriff nice mai kula da su duk da kasan cewar shi ba mai zama gida bane ,,,

    Anytime yana gurin aiki,n shi, shida Mustapha,

  Yau na zo zan wuce ta ban garen dakin nafisat  aiko sai naji muryan su kasakasa ita da yar lici 

   Waya na dan na record 

Daidai lokacin tana cewa, gaskiya yar lici, malam garin nan aikisu baici don daini gaskiya banga wani canji ga Ahmad ba yace sai na kori wanan yarinyar ajiki na aiko zaiyi amma gashi bata tare dani har yanzu nakasa samun kan Ahmad din

  Kada kidanu uwar daki komai zaizo daidai insha Allah kinsan cewa,

   Yanzu watan azumi ne basu faye yin irin miyagun asiran nan badon iskokai andaure,su

    Ko shekaran jiya dazai wuce na yi,nayi dashi yaban wasu yan kudade amma sam yaki,

     Sai ce min yayi kyautar shi sai yaga dama kuma ko yayi niya idan mutum yatambaye shi shi bai badawa kuma,

       Dama yau nazo in fada maki cewa akwai wani malami dan kasar ghana da yazo gurin shi zamu kafin ya koma,

     Don insha Allah wanan karon sai mun gwada mai mun fishi sani duk wani takon shi,

   Har zan wuche saina da tsaya nakara saurarawa, jinayi nafisa tayi dan tsaki tace wlh indan yafi karfi na sai kawai insa akashe min  shi har shegeyar uwar tashi kawai ingaba da komai nawa,

    Sainaji sun tafa,

    Kafana naji baiko iya dauka na don tsoro, dabayabaya nabar gurin nakoma dakina

    Aiko atake zazzabi ya sauka min

    Gazafin ciwo ga tunane ya isheni, azuciyana

   A kan gado na zube sanan na lumshe idona bugawar zuciyata kawai nake sauraro yadda yake kara karuwa,

   Meye abin yi? Tambayar da nayiwa kaina ke nan

   Cikin wani hanzari na mike nafada bayi don inyi alwala sai kawai naga bani da tsarki, ,,,

   Adadafe ranan naje kitchen haka na daure nadafa masu hjy da ummi abinci har dani,

    Adakin na koma don in nazauna dakina tunane zai min yawa nikadai,

  Acan naita fama da ciwon mara na ana min sannu,

    Dana danji sauki saina debi abinci don in,dan ci 

   Nafara ci nakai cibiyu nabiyu kena sai mukayi arba da 

   Sheriff wanda ke tsaye bakin kofa yana kokarin dauko wayan shi, dake tsuwa aljihun shi,

   Cibin na mayar don kunyar danaji yakamani,,yai min wani irin kallo na C U, Salim dake bayan shi ne ke fadi kai amma fadima,


_ 🐎ZEEE MAKAWA🐎

24/10/2017, 1:50:21 PM: Maman Safwan: ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                  5⃣5⃣

                    BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎


🐎HUGUMA GROUP🐎

🎁NASIBI WRITERS ASSOCIATION🎁

🎁N🎁W🎁A


   Almost true life story


A kofar gidan da maman umar tai kwatancen take muka tsaya gidane mai hawa goma sha biyu gidane wanda yan umarah ko aikin hajji ke zama aciki shi,,,

    kimanin dakuna ,dari da hamsim ke cikin gidan ,

    Nice nafita zuwa wajen yan matan takarin da naga suna saida abincin a kofar gidan,

     Na,tambaye su ko bakin da suka sauka da ga Nigeria suna ciki,

   Ko sun tafi, tunda anyi sallah ba za su tsaya ba wuce zasufara yi,

   Tunda nasan cewa tashigo kasan ne amatsayin wacce tazo yin umurah,

   Kuma nasan muddin bata samay muba zata iya zaman boyo bazata koma ba sai taga yaranta,

   Nuna min wata mata da ke xaune ta ba mu baya, tana saida wasu kayan tarkace akofan masaukin  da mukazo sukayi,,,

   Matar tana da dan tazar damu kadan don haka ba lalaine taji maganar muba daga nisa,

   Na,isa gurin da take zaune ta kasa kayan su takalma da rigunar barci sai su hijab,

  Duk wanan abin su Almustapha da Salim na cikin mota suna kallon na 

  Sallama nai wa matar ta waigo a hankali daidai lokacin tana ciniki da wani mutum mai son sayen hijjab agurin ta

    Fadimar mama Sharwali,

   Tamike tsaye,cikin sauri ta dafe kirjin ta tana dan kokarin waigen bayana kazata ga garan,

   Cikin kidima da rudewa take ce min Umar da Aisha fadima suna ina don Allah,

   Dama nasan cewa zasu samu taimako daga gurin ku insha Allah ,,,,

    Sai kuma ta fashe da kuka, mai tsuma rai, ,,, ganin da nayi tana shirin tara muna mutane,

   Yasa ni jawo hannu ta muka nufi, motar da mukazo da ita,

   Muna bayan motar  nida ita take ce min tunda aka kamata da kwana biyar aka wuce da ita kasar ghana can jirgi ya zube su,

   Allah yasa tana da dan kudi ajikin ta shine tasamu tazo gida dashi, katsina,

   Tana fadin wanan maganan sai zuciyana tatuno min da Rugaiyya na,

   Nace ko tayi sa,a tasamu jirgin yan Nigeria  ankaita gida,

   Sai natuna cewa koma ina aka kaita insha Allah tana da wada,tacen kudi wanda zasu kaita, gida,,,,

   Motar muna tsayawa umar ne yafara taron mu, ya inda flower's suke yana wasa 

   Tsaye yayi cikin mamamki yana kallon uwar don gani yakeyi kamar idon shi na gizo ne, 

   Zuwa yayi ya rungumay ta, tam yana cewa ummi ke ce ko kuwa ummi may yasa kika gudu kikabar mu ,

   Tun yana surutu yana sambatu, har yagaji yai shiru yana sha shekar kuka,

   Aisha kan fafir kin zuwa tayi wurin mahaifiyar nasu ba yadda ban yi da ita ba amma sam taki, 

 tace ita,sam bata zuwa, gurin uwar,,,,

   Saida Sheriff yadawo nagabatar mai da ita tare da yaran nata 

 Inda nake zaune itama yarinyar anan take zaune duk falon yayi tsit kamar ba, kowa ciki,


   Saida yandayi gyaran murya san nan ya fara magana, bayan sallama yai ma Allah godiya da ya nufe mu da ganin wanan ranan, mai albarka da anfani 

   Saida yai ma kowa dake wurin nasiha so sai mai kashe ma bawa jiki da kara imani a zuciyar mutum,,

   Sanan yajuya inda duk muke zaune har ummi da su Yumma da hajiyan mu, 

     Yafara da tambayar ta yace itace ta haifi yaran kokuwa tace mai itace,

   Yace to yanzu zata bar kasa saudiya da su ne ko kuwa zata kara zama acikin kasar ne kaman da,

   Amatsayin yar takari, Saida tashere wani gumi da ya keto mata, tunkun sanan ta dan daga kai ta kalleshi, 

   Hannu bi,biyu ta daga tacewa don Allah yatai make ta ya ce,ci rayuwan su,

   Idan tace zata koma bata da kudin jirkin daukar yaran,

    Kuma idan taje dasu Nigeria za,ace yaran basu da uba ,

   Nasan cewa ganin da naimata ta,tana kuka zai iya sani kukan nima, 

  Don haka dagawa na tsab rike da hannun Aisha muka shige ciki,

   Ina tashi yabi inda nabi da kallo yasan abinda zanje yi ,, watau kuka ke nan,

    Yace mata tadaina kuka zai taimaka yaba su sana,ar yi wanda zasu dan samu,

   Amma fa su sanda cewa nada wani dan lokaci insha Allah zai taimaka masu kowa ya koma gida,

   Kafin yabar kasan, kowan su yayi murna akayi godiya ,

  Bayan an watse ummi tadinga samai albarka tana mai godiya,

   Ina ciki ina kallon Aisha cikin tausayi don nasan cewa tabbas za,a raba mune da ita ne yau

    Shiru shiru ina ciki ina jiran azo ace min in kawo Aisha zasu tafi sai naji shiru, 

  Jin shirun yai min yawa saina dan gyara mata kwaciyan ta a hankali na fito waje,

   A hankali nake saukowa daga step din  dagani na kasan banda wani  kuzari ajikina,

   Shiru naji wurin yayi ba motsin kowa, a wurin cikin mamaki nakarasa saukowa ,

    Ganin ba kowa yasa wuce wa dakin ummi,

  Don in gani ko may ke faruwa nida nabar falo tab da mutane , dazu sai gashi cikin yan mintina nafito banga kowa ba,,,

     Ummi ce kawai adaki daganin ta ta idar da sallah nafila ne don dai lokacin sallah da sauran tsamu

   Gefen kujerar dake dakin ta na,dan samu gefen hannun kujerar na zauna,

   Inajiran ta shafa addu,an da na samay ta, tanayi,

   Ina dan wasa da yatsun hannu na ina lankwasa su,suna ba dan kara wani dawani  dan sauti,

    Muryam Sheriff ne naji yai sallama dakin, zubur nayi na gyara zamana ,tukun a tsorace nadan waiwaya kofar shigowa dakin na ummi,

    Barka da rana, nace mai cikin sanyayan murya,,, 

   Saida ya dan kalli gefen da nake  zaune sai ya kauda kanshi

    Wani, irin dan guntun murmushi ya makale, agefen fuskanshi , yace yawa,

Sai  Yace min nazo ne in ma ummi ruwan hawayen da nafi kowa iya zubar wa, itama tagani ko,

  Sigar da yai maganar sai yasa nadan sake jiki ga tsoratar danakeyi mai

  Tun jiya ban son mu hadu dashi,

  A hankali yatako yazo ya shiga dakin,,

   Ta inda nake zaune dole zai wuce tagabana, yana sanye da farar T shirt an rubuta agaban rigan iam proud to b a Muslim, da jan kala, sai dogon wandon chunus da yasa mai kyau kalar ruwan toka,, Wani farin agogo ya makala na kamfanin D&G wato, Dolece & Gabbana, sai wasu fararen takalma masu daukan ido ruffafu, dasu, amma a kofa yacire takalman,

   Yazo tagabana yawuce hancina kamar cikin kwalban turare na nutsa shi,

   Don kamshi shikam sheriff  Allah yabashi son kamshi sosai don har abin ya bi mai jiki,

  Don ko wuri ya zauna yatashi kamshin bai barin wurin,  

     Danaga ya shigo saina dan mike da niyar in fita waje,

    Cikin saurin yace min in zauna abina ba zama zaiyi ba  sako ne yazo fada mata,

   Kaita dago a hankali tana kalllon shi, saiyake ce mata Abban shi yai mai waya zasu iso nan da gobe insha Allah,

    Adduan tadan katse cikin lokaci guda , tace sai in koma wancan gidan naka ke nan ko har subar gari,

   Dan murmushi yayi wanda yakara mai kyaun fuska,

   Yace koda sunkai su dari ne insha Allah inada inda zan aje su ummi, basai kin bar gidan ki ba,, 

   Idan baki so su ganki ne ,har su koma babu wanda zai ganki,daga cikin su,, 

    Tace aishi zannah dan uwa  hauwa nane ka ga bazan ce ban kin ganin shi mu gaisa amma sheri irin na hjy mama nake ma gudu,

   Saboda gwanace ta kware wurin kulla sheri

 Nidai Inajin su nai tsit kamar ruwa ya cine,

Don nauyin da nake ji,  

   a  dakin sai nakoma takure cikin su gashi ina son fita tun farko ya hanani,

    Ya ce ummi ki kwantar da hankalin ki don mama a halin yanzu kinfi karfin duk wani sheri da zata iya yi maki yazama tarihi insha Allah

   Ummi tace ai inaga halin nasu a jini yake don kusan itama wanan yarinyar ta wurinka ba inda tarage halin Aminar

   Saidai kawai muce Allah ya gyara tunda kun riga kun gaurayu da su ko,

   Yace amin a sanyaye ya dan satan kallon na inda nake zaune,, 

  Duk hiran da suke yi shida ummi kaina yana kasa ban daga ba don duk a tsawale nake, cikin su

   Saboda ba maganar da za,ayi agabana bane,,,,,  

     Sai alokacin ma natuna da nafisa don tun wurin cin abincin sallah jiya ban kara ganin ta ba

   Dakina na koma batare da na tambayi ummi maganar mahaifiyar su umar ba,

    Amal ce ta fado min a raina don nasan cewa zanji komai da yafaru a wurinta, gamay da maman su umar din,,

   Tana zaune saman gadon ta duk tai dadaya da kayan ta wai ta fara shirin tafiya makaranta ne, inji ta dariya nai mata nace ai akwai sauran time,

   Da sallama  na karasa  shiga dakin nata, tana duke tana ta faman gyaran takardun ta,

   Wani littafi mai hoton wasu ma,aurata nagani a gefen ta sai na jawo nadan fara diban hoton dake jikin bangon 

   Nace mata gaskiya sunyi kyau sosai wallahi, 

   ✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                  5⃣5⃣

                    BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎


🐎HUGUMA GROUP🐎

🎁NASIBI WRITERS ASSOCIATION🎁

🎁N🎁W🎁A


   Almost true life story


A kofar gidan da maman umar tai kwatancen take muka tsaya gidane mai hawa goma sha biyu gidane wanda yan umarah ko aikin hajji ke zama aciki shi,,,

    kimanin dakuna ,dari da hamsim ke cikin gidan ,

    Nice nafita zuwa wajen yan matan takarin da naga suna saida abincin a kofar gidan,

     Na,tambaye su ko bakin da suka sauka da ga Nigeria suna ciki,

   Ko sun tafi, tunda anyi sallah ba za su tsaya ba wuce zasufara yi,

   Tunda nasan cewa tashigo kasan ne amatsayin wacce tazo yin umurah,

   Kuma nasan muddin bata samay muba zata iya zaman boyo bazata koma ba sai taga yaranta,

   Nuna min wata mata da ke xaune ta ba mu baya, tana saida wasu kayan tarkace akofan masaukin  da mukazo sukayi,,,

   Matar tana da dan tazar damu kadan don haka ba lalaine taji maganar muba daga nisa,

   Na,isa gurin da take zaune ta kasa kayan su takalma da rigunar barci sai su hijab,

  Duk wanan abin su Almustapha da Salim na cikin mota suna kallon na 

  Sallama nai wa matar ta waigo a hankali daidai lokacin tana ciniki da wani mutum mai son sayen hijjab agurin ta

    Fadimar mama Sharwali,

   Tamike tsaye,cikin sauri ta dafe kirjin ta tana dan kokarin waigen bayana kazata ga garan,

   Cikin kidima da rudewa take ce min Umar da Aisha fadima suna ina don Allah,

   Dama nasan cewa zasu samu taimako daga gurin ku insha Allah ,,,,

    Sai kuma ta fashe da kuka, mai tsuma rai, ,,, ganin da nayi tana shirin tara muna mutane,

   Yasa ni jawo hannu ta muka nufi, motar da mukazo da ita,

   Muna bayan motar  nida ita take ce min tunda aka kamata da kwana biyar aka wuce da ita kasar ghana can jirgi ya zube su,

   Allah yasa tana da dan kudi ajikin ta shine tasamu tazo gida dashi, katsina,

   Tana fadin wanan maganan sai zuciyana tatuno min da Rugaiyya na,

   Nace ko tayi sa,a tasamu jirgin yan Nigeria  ankaita gida,

   Sai natuna cewa koma ina aka kaita insha Allah tana da wada,tacen kudi wanda zasu kaita, gida,,,,

   Motar muna tsayawa umar ne yafara taron mu, ya inda flower's suke yana wasa 

   Tsaye yayi cikin mamamki yana kallon uwar don gani yakeyi kamar idon shi na gizo ne, 

   Zuwa yayi ya rungumay ta, tam yana cewa ummi ke ce ko kuwa ummi may yasa kika gudu kikabar mu ,

   Tun yana surutu yana sambatu, har yagaji yai shiru yana sha shekar kuka,

   Aisha kan fafir kin zuwa tayi wurin mahaifiyar nasu ba yadda ban yi da ita ba amma sam taki, 

 tace ita,sam bata zuwa, gurin uwar,,,,

   Saida Sheriff yadawo nagabatar mai da ita tare da yaran nata 

 Inda nake zaune itama yarinyar anan take zaune duk falon yayi tsit kamar ba, kowa ciki,


   Saida yandayi gyaran murya san nan ya fara magana, bayan sallama yai ma Allah godiya da ya nufe mu da ganin wanan ranan, mai albarka da anfani 

   Saida yai ma kowa dake wurin nasiha so sai mai kashe ma bawa jiki da kara imani a zuciyar mutum,,

   Sanan yajuya inda duk muke zaune har ummi da su Yumma da hajiyan mu, 

     Yafara da tambayar ta yace itace ta haifi yaran kokuwa tace mai itace,

   Yace to yanzu zata bar kasa saudiya da su ne ko kuwa zata kara zama acikin kasar ne kaman da,

   Amatsayin yar takari, Saida tashere wani gumi da ya keto mata, tunkun sanan ta dan daga kai ta kalleshi, 

   Hannu bi,biyu ta daga tacewa don Allah yatai make ta ya ce,ci rayuwan su,

   Idan tace zata koma bata da kudin jirkin daukar yaran,

    Kuma idan taje dasu Nigeria za,ace yaran basu da uba ,

   Nasan cewa ganin da naimata ta,tana kuka zai iya sani kukan nima, 

  Don haka dagawa na tsab rike da hannun Aisha muka shige ciki,

   Ina tashi yabi inda nabi da kallo yasan abinda zanje yi ,, watau kuka ke nan,

    Yace mata tadaina kuka zai taimaka yaba su sana,ar yi wanda zasu dan samu,

   Amma fa su sanda cewa nada wani dan lokaci insha Allah zai taimaka masu kowa ya koma gida,

   Kafin yabar kasan, kowan su yayi murna akayi godiya ,

  Bayan an watse ummi tadinga samai albarka tana mai godiya,

   Ina ciki ina kallon Aisha cikin tausayi don nasan cewa tabbas za,a raba mune da ita ne yau

    Shiru shiru ina ciki ina jiran azo ace min in kawo Aisha zasu tafi sai naji shiru, 

  Jin shirun yai min yawa saina dan gyara mata kwaciyan ta a hankali na fito waje,

   A hankali nake saukowa daga step din  dagani na kasan banda wani  kuzari ajikina,

   Shiru naji wurin yayi ba motsin kowa, a wurin cikin mamaki nakarasa saukowa ,

    Ganin ba kowa yasa wuce wa dakin ummi,

  Don in gani ko may ke faruwa nida nabar falo tab da mutane , dazu sai gashi cikin yan mintina nafito banga kowa ba,,,

     Ummi ce kawai adaki daganin ta ta idar da sallah nafila ne don dai lokacin sallah da sauran tsamu

   Gefen kujerar dake dakin ta na,dan samu gefen hannun kujerar na zauna,

   Inajiran ta shafa addu,an da na samay ta, tanayi,

   Ina dan wasa da yatsun hannu na ina lankwasa su,suna ba dan kara wani dawani  dan sauti,

    Muryam Sheriff ne naji yai sallama dakin, zubur nayi na gyara zamana ,tukun a tsorace nadan waiwaya kofar shigowa dakin na ummi,

    Barka da rana, nace mai cikin sanyayan murya,,, 

   Saida ya dan kalli gefen da nake  zaune sai ya kauda kanshi

    Wani, irin dan guntun murmushi ya makale, agefen fuskanshi , yace yawa,

Sai  Yace min nazo ne in ma ummi ruwan hawayen da nafi kowa iya zubar wa, itama tagani ko,

  Sigar da yai maganar sai yasa nadan sake jiki ga tsoratar danakeyi mai

  Tun jiya ban son mu hadu dashi,

  A hankali yatako yazo ya shiga dakin,,

   Ta inda nake zaune dole zai wuce tagabana, yana sanye da farar T shirt an rubuta agaban rigan iam proud to b a Muslim, da jan kala, sai dogon wandon chunus da yasa mai kyau kalar ruwan toka,, Wani farin agogo ya makala na kamfanin D&G wato, Dolece & Gabbana, sai wasu fararen takalma masu daukan ido ruffafu, dasu, amma a kofa yacire takalman,

   Yazo tagabana yawuce hancina kamar cikin kwalban turare na nutsa shi,

   Don kamshi shikam sheriff  Allah yabashi son kamshi sosai don har abin ya bi mai jiki,

  Don ko wuri ya zauna yatashi kamshin bai barin wurin,  

     Danaga ya shigo saina dan mike da niyar in fita waje,

    Cikin saurin yace min in zauna abina ba zama zaiyi ba  sako ne yazo fada mata,

   Kaita dago a hankali tana kalllon shi, saiyake ce mata Abban shi yai mai waya zasu iso nan da gobe insha Allah,

    Adduan tadan katse cikin lokaci guda , tace sai in koma wancan gidan naka ke nan ko har subar gari,

   Dan murmushi yayi wanda yakara mai kyaun fuska,

   Yace koda sunkai su dari ne insha Allah inada inda zan aje su ummi, basai kin bar gidan ki ba,, 

   Idan baki so su ganki ne ,har su koma babu wanda zai ganki,daga cikin su,, 

    Tace aishi zannah dan uwa  hauwa nane ka ga bazan ce ban kin ganin shi mu gaisa amma sheri irin na hjy mama nake ma gudu,

   Saboda gwanace ta kware wurin kulla sheri

 Nidai Inajin su nai tsit kamar ruwa ya cine,

Don nauyin da nake ji,  

   a  dakin sai nakoma takure cikin su gashi ina son fita tun farko ya hanani,

    Ya ce ummi ki kwantar da hankalin ki don mama a halin yanzu kinfi karfin duk wani sheri da zata iya yi maki yazama tarihi insha Allah

   Ummi tace ai inaga halin nasu a jini yake don kusan itama wanan yarinyar ta wurinka ba inda tarage halin Aminar

   Saidai kawai muce Allah ya gyara tunda kun riga kun gaurayu da su ko,

   Yace amin a sanyaye ya dan satan kallon na inda nake zaune,, 

  Duk hiran da suke yi shida ummi kaina yana kasa ban daga ba don duk a tsawale nake, cikin su

   Saboda ba maganar da za,ayi agabana bane,,,,,  

     Sai alokacin ma natuna da nafisa don tun wurin cin abincin sallah jiya ban kara ganin ta ba

   Dakina na koma batare da na tambayi ummi maganar mahaifiyar su umar ba,

    Amal ce ta fado min a raina don nasan cewa zanji komai da yafaru a wurinta, gamay da maman su umar din,,

   Tana zaune saman gadon ta duk tai dadaya da kayan ta wai ta fara shirin tafiya makaranta ne, inji ta dariya nai mata nace ai akwai sauran time,

   Da sallama  na karasa  shiga dakin nata, tana duke tana ta faman gyaran takardun ta,

   Wani littafi mai hoton wasu ma,aurata nagani a gefen ta sai na jawo nadan fara diban hoton dake jikin bangon 

   Nace mata gaskiya sunyi kyau sosai wallahi, 

   Sai tadan,diba tace ai yan uwan mu ne wanan bashir kenan dan yayan ummin mune, ita kuma matar yar uwan su ummi ce ta haifeta,

   Cikin littafin na bude na fara karatu, sai naga sunaye ne mutane da lambobin su birjit,

   Batare da ta waigo ba Amal ta,ke ce min sunayen abokaina ne da mukayi karatu da su a bauchi,

    Ina ta karantawa tana dan yi min bayanin wasu masu mahin manci, daga cikisu,

   Har nakai ga wata Khadijat Abdullahi dogon daji,

   Zubur na mike don jin sunan dogon dajin dayi,

   Nace mata ita tasan dogon dajin ne bata waigo ba tace min a,a ita kawai a school suka hadu da ita Khadijat din amma yar kano ce,

      Nace Anty,Amal tace ummm dataji kiran ba na wasa bane sai ta dan waigo ni,

   Nace dongon daji fa sunan garin mu ke nan,wata wata kila, ita Khadijat din yar garin muce,

  Don Allah ki taimaka min ki buga mata waya muji ko Allah yasa yar garin namu ne, ita din ne,

   Nakara cewa don Allah Anty Amal ki taimaka min kikiramin ita,

  Batare da ta waigo tace min to naji, amma sai kin kwashe min wa,yan,nan takardun kin mayar,

  Babata lokaci natashi na kwashe duk kayan da ra baza saman gadon 

  Har abinda batace ba saida nayi mata adakin

   Ya,mutsa fuska tayi tana fadin, ke nifa Khadijat ba wai muna wani shiri da ita bace,

   Ko wanan lanbar ma ina karba ne tana gurin kada taji daban shiyasa nace abata,

   Nakara cewa haba Amal tace o Amal ko nace anty Amal,

  Tace min in kawo wayana takira ta,

   Aikafin takira layin Khadijat din saida takira kusan mutum uku kafin takira tana fada masu cewa tana kasar saudiya,

    Saida taga dama don kanta tai dialing din noban khadijat din

   Yako shiga amma har wayan ya katse ba a dauka ba,

  Kusan kira biyu mukayi ba,a daukan wayan,

   Dole muka kyale amma raina a bace,

      Washe gari tunda safeg

        Ina saye da yar doguwar rigar danayi sallah da ita ajikina ban riga na shiga wanka ba tukun,,,,

    kirana aka yi ta intercoms din daki na

   Cikin sauri sauri na sauko batare da na canza kaya ba,

   Ina zuwa nadinga jin wani iri kugi da huci a saman ,dakuna kamar wani irin halitta ne yashigo muna,

   Kusan duk kowa yana tsaye ina zuwa sai nake tambaya ko may ke faruwa haka na ne,

   Almustapha ne yace min in shiga dakin matar sheriff ne sautin ke fitowa gashi kuma Sheriff bai gida yatafi wurin judging tunda safe,

  Ba bata lokaci na fada dakin, Nafisat ce kwance cikin wani irin hali ga.  kwalaben sirup nan kusan kala biyar tayar a kasa gefen gadon ta,

   Ina shiga na tallabo ta aiko sai kokarin sakewa takeyi kamar mara rai,

    Saketa nayi da sauri na fito dakin nata cikin tashin hannankali,

    Nace ma almustafa yasa adauko min zuma da madara da sauri,

   Ana kawowa nayi dibara nabude bakinta na tura mata kusan cokali biyu na zuma,

   Aiko yana shiga cikin ta tai wani irin yunkurin amai, saida kowa ya watse don sun dauka ko ta shake ni ne,

   Sheriff ne tsaye da kayan games ajikin shi yana mamakin ihun da yake ji tun shigowar shi get,

   Sai gashi kuma yaga kowa na batun gudu,

   Cikin tashin hankali mustapha ke mai bayanin abinda ke faruwa,

   Dasauri ya haura sama dakin nata koda ya shigo tana kwance sharbat da ita saman jikina,

   Ga wani irin amai da take kwarawa,

  Maman su Umar na tsaye daga kofa rike da goran zuma da na madara,

     Cikin tashin hankali yake kallon ta yana tambayar may yasa may ta haka,

   Ban kai ga bashi ansaba idon shi ya kai ga kwalaben kayan mayen da ke zube kasa gefen gadon ta,

   Cikim tashin hankali ya fidda idon shi waje don mamakin 

    Wani aman ta kara zubowa mai wari,

   Sainace wa maman Umar ta miko min goran madaran da ke hannu ta shima cikin hikima na dura mata shi Allah ya ban sa a,a ta sha sosai,

   Sai wani irin amai ya zubu mata, sai kawai jikin ta ya sake ta 

     Duk sheriff ya rude yama rasa may zaiyi,

  Ganin da yayi mata haka yasa yace mu kamota muje asibiti,

   Nace mai idan mun kaita asibiti haka za,a tuhumay ka sosai kai ma,

   Yagane may nake nufi shi yasa shi yin shiru don hukumar kasan saudiya indan sun fara binciken lamari sai sun gano harda abin da ba suyi niya bincike ba sai sun gano shi, ga mutum

      Nafada mai cewa zata samu sauki sosai,insha Allah idan ta farfado saboda naga irin haka a makwabciyar gidan su hajiya laila ,

   Dakin na gyara mata tasa sai abin kamshin daki da nasa don dakin ya rage warin da yakeyi, 

   Abinci naje kitchen nadafa mata maidan nauyi saboda nassn cewa tana fafadowa zata bidi abinci ne taci,

   Sheriff duk mamakin wanan yarinyar ya kama shi ,, yace,kai yarinya karama da shegen wayo da dabara haka, 

     Ummi tashiga cikin wani irim yanayi na,damuwa,

    Tayaya har Alhji zanna ya bari danshi ta auri wanan yarinyar da bata da tarbiya ko kadan,

    Ita dai tasan cewa duk da Alhj zanna mutun ne shiru shiru,

     To amma bai yadda da aikin assha a gidan shi 

  To ta yaya zai ma Ahamad wanan hadin haka,,

   Sai misalin karfe ukun rana nafisat ta farka daga barci tana mai dan bude idon ta da yai mata nauyi sosai,

   A hankali ta bude su gabadaya idon ta ya sauka kaina ina tsaye gefe guda,

    Ina kallon ta,ta kara lunshi idon nata tayi kamar zata tasahi amma ta kasa, yun komai,,,, 

        Matsowa nayi kusa da ita ina mata sannu,

   Ta yunkura ta tshi saikawai taji ai bata iyawa sam 

   Nagane nufin ta sai naje kusa da ita nadan tallafa ta ta bayan ta sai tayi kokarin hanani amma ganin da tayi bafa zata iya ba

   Saita hakkuri da intaimaka mata din,

 Saina kara riko saita dan dago daga kwance, nataimaka mata muka sa,uko daga saman gadon 

   Munkai tsakar dakJain's ga sheriff fuskan shi murtuk kamar bai taba yin dariya ba

     Wani wa,wan kallo yai muna, nikan sai na noke kaina

   Da taimako na nasamu taci abinci sosai tako shi,

   Ganin da nayi sheriff yadawo dakin yasa ni fita waje 

   Sai a lokacin nasamu nadan gyara jikina tsab nafito shar dani,

   Noban wayan yar dogon daji ya fado min a rai na tashi nadauki waya zuwa dakin Amal

   Ina shiga tace min gaskiya fadima bansan cewa baki da zuciya ba sai yau wlh,

   Nagane nufin, ta don haka, Kafin taci gaba sai nace mata kowa yataimaki wani Allah na taimakon shi, saboda Allah nayi saboda kuma Sheriff wanda hakan ba karamin rufin asirin shi bane

     Cikin jin haushina takara kiran labar wayan amma sai bai shiga ba,

     Haka na hakkura nakoma dakin nafisa nasamu ta kara yin barci 

   Dakina nadawo daniyar indan kwanta kafin anjima kadan

   Barci mai nauyi yadauke ni sai gab da sallah magrib na farka

   Nayi barcin kusan awa hudu,

     Sallah nagabatar cikin sauri, sai nayo waje domin yuwa nake ji banci komai tunda safe dana danci kwai kadan ,,,

   Saboda ina fara ci natuna da aman da nafisat tayi sai na kasa ci,

    Ina fitowa falo saiko mukayi arba da hjy tsohuwa da Abba, sai 

   Da ihu naje nafada mata ajikin ta ina murna na manta da duk wa yanda ke falon zaune

   Saida na natsu san nan naga wayanda suke tare, cikin ladabi nagaida kowan su nai masu sannu da zuwa

   Abinci naga batar masu sai kuma masaukin da aka kai kowan su,

  Fafir hajiya tsohuwa tace ita sai dakin ummi zata sauka ko kuma na Amal,,,,  

🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                   5⃣6⃣

                      BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎🎁NASIBI WRITERS associations

🎁

 🎁N🎁W🎁W

  

   Almost true life story,,,


 Washegari natashi tunda safe na hada masu break fast, yadda yaka mata tare da taimakon su yumma,

   Saida kowa ya kamala,break din ya  sanan aka dawo falo aka zau zauna,

   Ina tsaye ina hada kayan da suka gama cin abinci da su sai naji Allah Alhaji lawa zanna yana cewa a kamalo mai kowa da yakamata a kira mai agidan,

    Falon yai tsit kowa na jiran ana sauraren abinda za a ce masu,

   Wani takarada Abban yafitar daga cikin aljihun jallabiyar shi,

   Sai da,ya fara bude taro da addu,a tukun sannan ya, kallo kowa dake falon,

   Hjy tsohuwa tana zaune kusa da ummi,

  Salim da Amal su gefe guda suma zaune, 

   Sai Sheriff da nafisat dake zaune kusan wuri guda 

  Duk da ba karfin jikinta take ji ba daurewa kawai tayi tadan fito tana yatsinar fuska,

    

  Alhaji zanna yace ubana mun zo ne wannan kasar don mu tatance wani takarda sako da aka tura wa hajiya acinkin kayan da aka kai mata sako daga nan,

   Sai lokacin Sheriff ya dan daga kanshi yadan kali Abban da ke magana ,mamaki yakeyi don bai san kowa yaba da sako zuwa wurin hjy ba,

    Jin falon yai shiru yasa Abban yace ma hajiya tsohuwa ,

   Hajiya wane ya aika maki da sako,

   Sai tace wanan yariyar mai kula da ku, tana dan waige ,waige ko zata gan ni,

    Cikin mamaki sherrif yace fadima 

  Ta kware itace,

  Ta aiko min da sakon wani magani dana taba saye na ciwon kafa da kuma na idanu,

  Acikin sakon ta jefa wanan takardan

  Ta nuna takardan da bakin ta daidai inda Abba ya aje takardan

    Sheriff yace mai takarda ya kumsa Abba,

  Sai Abban yace yanzu kuwa zaka ji,

  Don inba zuwa nayi da hjy taga lafiyan ka kuma taji zancen daga bakin ka,ba ,ba,zata taba yarda cewa lafiya kake ba,

     Saboda Abba yasan cewa kazafi akai wa nafisa a takarda don ba halinta ba ne

   Asani shi diyan Aminin shi suna da tarbiya sosai,

  Salim akasa yaje yakirani,

   Lokacin ina nagama wanka ina gyara jikina kafin hjy tsohuwa tafito inda sukeyin mitin,

    A cikin sauri da kuma shakku na isa falon gidan 

  Inda suke zazaune ana jiran in, iso,

   Gefen kujera nasamu nadan labe cikin ladabi nakara gaida su,

   Alh zanna ya kalle ni azuciyar shi yace kai mutun abin tsoro ne,

  Ji wannan yariyar da ko yaushe nake ganin kirkin ta wai itace yau take wanan kullin sherin don kawai ta raba ma yara hannkula, su,

   Ina gama gaishe su sai Abba yace min fadima "nace na,am Abba

  Yace, ke ,ce kika aikawa hjy da sako nace eh yace harda takarda aciki 

   sai nayi dan shiru ina tunane. takardan may ke nan kuma,

     Yace ke ce sai nace eh cikin rudewa, 

   Abba yace Alhamdullahi,

  Yace Ahmad wani irin zama kakeyi da matar ka har yakai wanan yariyar taima hjy sako akan azo a ceci rayuwan ka kafin , nafisa ta halaka ka,

  Zubur na mike ina nuna kai na nace la,la,la haram, haram bani bace, 

   Bantaba rubuta wasika ga kowaba zuwa Nigeria,

  Tsawa Abban yadan daka min, yace bayan mun tambaye ki kin ce muna kece ki, aika,

    Ina kuka wi,wi, ina sharban majina,

   A hankali sheriff yadan daga yakalle ni cikin tausayi,

   Saboda yasan cewa koda nice ma din ai ba karya nayi ba saidai kassh,

   May yasa fadiman tai mai haka, saboda yasan cewa ko shi yakai karan nafisa gurin Abba abinda zai faru ke nan

   Abba baison ace ga laifin ta sam,

   Shiyasa yake hakkuri da komai taimai ,

    Saidai fa gefe guda na zuciyar shi tana ce mai bani ce nayi wasikan ba , akwai dai, gaskiya,

    Nafisa ce cikin karfin hali tana magana tace Abba bansan ko mai nayi wa wanan yariyar ba,

  Ta hana ni shakat agidan mijina,

 Idan nai magana yace min ita din amana take gareshi,

   Hjy tsohuwa tace ke rufe muna baki zuriar yan sheri aiba don Allah kuka mamaye min jini na ba,

  Ta Allah ba taku ba,

    Abba na jin hajiyan shi sai yadan yi murmushi don yasan cewa bakin jinin Amina ce yashafi duk danginta,

    Jin kukan danakeyi yai yawa yasa sherrif dinmu yin maga a wurin,

   Yace, Abba ina takardan Abba yadauko takardan ya nuna mai yace gashi nan, daga nesa inda yake zaune,

   Yace bani son kaga abinda aka rubuta don sheri ba kyau,

    Saboda ni nasan cewa ko yaushe ne ma waya kana fada min lafiya lau kuke da matar ka,

    Tashi yayi har inda Abba yake yace rubutun zan gani kawai bawai zan karanta bane,

   Dan dagowa da takardan yai mai kadan,

  Da sauri ya waiga gefen da Salim da Amal ke zaune yace cikin ku wake da wanan handwriting din,

  Salim yadan waiga gefen da Amal take zaune yana dan kallonta cikin mamaki,

   Yace mata ko ke ce tadan girgiza kanta cikin alamar, rashin gaskiya, tace ,a,a

   Kawai dai sheri ne ni nasan ba gaskiya bane,

   Tausayi naba Salim ganin irin kukan da nakeyi ga kuma Abba nata min fada ina kuka cikin gumza,,

    Amal ce ta rubuta ni nace ta rubuta mu aika wa hjy tsohuwa da shi ko zata zo ta ceci yayan mu daga bala,in da nafisa ke son jefashi cikin wanan kasar,

   Kowa waigawa yayi inda salim din ke magana,

  Har zaici gaba sai kawai yaji saukar mari a kumatun shi, sheriff ne yai mai wanan marin masu kyau,

    Sheriff yace shine tundazu ana magana kai shiru ka share mutane ,kasa anata cin zarafi yar mutane,

   Abba ya daga hannu shi ma sheriff yace kyale shi,

     Ai nasan cewa zasu iya tunda uban su ne yakawo wanan takardan,

   Inda yayi halin dattako aida bai bari takardan yakai hannu hajiya ba,

  Ita kuma hjy tsohuwa ta cabe zan cen da fadin Shehi baida laifi don ko bayan nasa an karanta min takardan 

   Saida na kirashi don inji daga bakin shi sai naga ai baima san komai gamay da sakon ba,

 

    Duk bayanin da sukeyi baisa nadan tsagaita kukan da nakeyi ba,

   Sheriff yai min magana da larabci wai inyi hakkuri inyi shiru,

   Mai hakkuri bai iya fushi ba dama, ummi ce tafito falon cikin kamala,

   Don ko ina na jin ta arufe yake lif baka iya ganin komai nata saboda wani zunbudede hijjab da tasa,

   Fuskan ta na saye da wani farin medical glass da man mai

   Idan zatayi karatu nake ganin tana sa shi,

   Guda guda take take takawa a tsakiyan falon,

   Guri ta samu gefe guda ta zauna a hankali,

   Shiru tadan yi yayin da duk falon kowa yai shiru, saboda mamakin fitowar ta,

    A hankali ta dago kanta tace, yaya lawal nadauka ko da kowa zai ce Shehi bai kyauta ba don naji kana cewa ubansu ne yakai sakon tundaga nan har nigeria 


Ke nan da sanin shi yakai sakon takardan da yara suka aika ma Umma dashi ki,

   Ta dan girgiza kai tace Allahu akbar, tace

   Ina zaton kai mai kareshi ne don kusan kafi kowa sanin kowaye shehi din,

   Kamar yadada shi wanan din  ta nuna sheriff da kai ,

  Ke kokarin rufe zancen don gudun bacin ranka ina haka shima shehin ke yi, don gudun barna goma, tsakanin kaida aminin ka,

   Inda yai niyar fadin abin da zaman nasu ke ciki da ya fada ma tun yana nan kasan,

   Saboda kasan halin da ka jefa dan ka aciki, 

   In badon Allah ya taimake shi ya hada shi da zama da mutanen kirki ba da yanzu labari yacin maka,

   Ido ware bashi kowama don ba mai tsanmanin ummi zata iya wanan maganar mai tsawo haka kuma akan Ahmad,

   Matar da tana iya yini batai maganar dayafi goma ba,

   Nunani tayi da baki tace inta wanan yar marainiyar Allah bata can, canci haka ba daga gare ku gaskiya,

  Kudiba fa duk guda nawa take da har za,ace komai itace mai gudanar wa nagidan nan

   Aida ganin haka kunsan cewa baiwace kawai daga Allah,

   Tamike tsaye tana cewa naso ace ajiya ka iso wanan garin kila da ka koma yau din

   Inda nake tsugune nasha kuka tazo, tadan dagani,

   Tanafadin Kada Alhakin wanan yarinyar ya kama ku wlh,

   Ka binciki taka diyar mugun halinta kafin ka tuhumi diyar mutane,

   Tajani zuwa dakinta ina kuka, wi, wi 

   Yaune rana na biyu danayi danasanin zama gidan sheriff din mu

   Ido yabi  mu dashi yana mai tausaya wa yarinyar sosai,

  Salim ne ya walwale masu komai gamayda irin zaman da akeyi da nafisat tunzo wansu,

   Irin abinda suka gani dakuma recoding din da wani yayi awaya sukaji har zuwa irin abinda yafaru jiya agidan,

   Shiru falon yayi don saurare Salim da kuma jimamen halin nafisat da basuyi tsanmani ba, daga duk wani da ,da yafito gidan mahaifin nata,

   Alhj zanna yace azuciyar shi lalai yanzu ba wani fa,ida ga mutum ya kai yaro shi  karatu nisa da gida, 

  Musam man kasar turai inda yara ke koyo mugum tar biya

  Mai makon yaro ya koyo karatu sai kum yaro ya koma kiyon bakar dabi,a,,,

  Niko muna shiga daki da  ummi tadauko min lemon gwangwani mai sanyi tabani kai na girgiza alamar ban sha,

   Maimakon insha din sai kukan dana kara sautin shi sosai,

   Ido ummi tasa min kawai don tasan abinda akai min akwai cin zuciya sosai,

    Afalo kuma hjy tsohuwa ce ta sa masu fitinar lalai sai nafisat tabar gidan nan

   Inba haka ba ita zata wuce da shi don kada nafisa ta jawo masu kashe mutm akashe mata shi abanza,

   Salim yace aida za ta iya da baki zo kin samay shi. 

   Don ko abinda akayi jiya ya i,she shi shiga wani hali,

   Tana jin haka ta mike takama jan hannun Ahmad wai subar falon 

   Dariya kowa yasa afalon don sun san cewa a rude take,

  Alhj zanna ne yaiwa Ahmad alamar yabita kawai don shi zafi sauki,,

   Dama yana bidan hanyar fita ne daga falon tun lokacin da ummi ta wuce da fadima hankalinshi ya ke tashi kamar ya,bisu duk kansu biyun 

   Saboda bai taba ganin ummi cikin bacin rai ba irin haka

  Ga kuma yar mutane akan gaskiyan ,ta an musguna mata rayuwar ta ga banxa yau 

    Yana zuwa dakin ya iske ni jikin ummi nasa kaina saman ciyan ta ina ta rusa kuka mai tsuma zuciya,

    Tsayawa yayi daga kofan dakin yana jin sautin kukan kamar digon garwashi ake watsa mai ajikin shi,,

  Idon shi a lunshe suke ya nadan kada kafan shi gudu, a,hankali a hankali

  Hajiya tsohuwa ce tafado dakin tana cewa nidama nasan cewa haka zai kasan ce don duk zurian su Amina babu na albarka ciki

    Ganin da tayi ina kuka yasa ta tsaida fadan nata, ta samu guri tazauna tace min inyi hakkuri ai gaskiya tayi halinta, ko

   

    Hakana na wuni a,ranan ba wani walwala tare da ni dakin su ummi nakoma can kuryan gado na dunkule wuri guda tunane kala kala nayi shi aranan,

   A gaskiya inda nasan yadda zanyi in koma gida wurin inna na danayi nakoma wurinta don in huta da gorin duniya kala,kala da nake sha 

    Saboda dai nisan cewa ina iya kokari naga cewa komai nawan nan gidan yana tafiya daidai

    Amma sai gashi yau wai ni ake zargi da kokarin wargaza zaman lafiya atsakanin ,masu gidan, 

   Hawaye ne yakama dan silaluwa daga idona yana gangarowa a,fuska,

   Tissue aka miko min ki bandaga kaiba nasan cewa sheriff ne, batare da ya ko kalin ind nake ba yake magana,.

    Kiyi hakkuri ni nafi kowa  sanin an maki abinda bai dace ba ayau, 

   Saboda anzarge ki akan abinda baki aikata, ba,

  Saida kisani cewa shi mai gaskiya yana tare da Allah koyaushe,

  Saboda haka ina son kitashi kije kiyi aikin ki kamar yadda kika saba kamar  kullun,

   Idonshi dana kalla naga ai ba wasa kokadan aciki yasani shirin mikewa zuwa waje,

   Ummi ce ta fito daga bayi da alwalar ta ganin da taimai gani nikuma ina shirin tashi,

   Yasa take kallonshi cikin mamaki, da tuhuma,

  Kafin tayi magana shi yarigata,Ce mata yayi aiki yake son nai mai 

   Tace mai ya ina sauran ma,aikatan gidan suke da ba,zaa iya sa wani aikin ba sai ni,

  Zaiyi magana tadan daga mai hannu alamar ba wasa acikin maganar ta,

  Fita yayi yabarni dole, adakin ummi din ,


     Nafisace tare da wan mahafinta da Alhj zanna da sukazo daga Nigeria,

   Yace agaskiya nafisa kin ba mu mamaki wai ace acikin zuriar Alh har akasamu mace mai wanan dabi,ar

   Inbadon Allah ya taimaka ya hada ki da yaro mai kirki dan arziki wanda yasan ya kamata,

   Aida agida nigeria ki kai wanan abin dayanzu mutunci da martaban gidan ku ya zube ko, ga idon jama,

     Yanzu kinga babu yadda za,ayi dole mu koma dake gurin iyayen ki kamar yada hjy tsohuwa ta bukata,

  Kinga idan kwai sauran zama a tsakanin ku sai ki dawo,

   Wani irin kuka nafisat tasa tana cewa ai mata hakkuri bazata kara yin 

  Ko wani irin abuba maka mancin irin wanda tayi tace rudin shedan ne,

   Saidai kiyi hakuri ki rungumi kaddara don kinji ma kun nuwar ki abinda tsohuwa tafadi


     Mu muna shirin wuce wa madina wurin  karatu duk wani shiri munyi, tare da taimakon sherff din mu

   Inda yai muna sayaya tafiya madina,, karatu sosai 

   Tundaga kayan sawa har abin da ake so muzo dashi daga makarantar duk yai muna tanadi,

   Ba abin da ya rage,

  Kuma yai muna albishir din cewa da maman su umar zamu tafi itace xata dinga yi muna aikin a binci da gyaran gida 

 Su kuma mutanen Nigeria suya ta kokarin shirya nasu kayan don komawa gida, da mugun labari,

  Babu yadda nafisat batayi ba don Sheriff yabari ta fita amma fafir yaki yarda,

   Ganin da tayi bazai bari ba yasata cewa nice zan raketa 

  Bada son raina ba dole nashirya muka fita tare da ita,

  Wani lungu mai yawan takari, kuma gasunan birjit kamar a kasar Nigeria ko wani kasa

    Gidan su yar lici  ne ashe mukazo 

   A,mota tabar ni tace min in,zauna injira tawai,

  Wanigida nan kusa dasu yar lici suka do nan suka nufa, 

   Wani dan yakwamamen saurayi yafito 

   Daga nesa ina iya hangen duk abinda sukeyi 

       Ko ban rantse ba ina iya ganin wani abu ya basu cikin laida fara haka irin laidar company 

  Cikin dibara takada abin a jakar  ta, tadan gyara kamar ba abinda faru.  

      Saida nabari mun dawo gida tadan fita sai naje nakwashe duk maganin 

    Aiko tunda ta diba taga bakomai inda ta boye sai,duk ta rude 

   Bakunya tana fadin wai an mata sata 

  Amma takasa fadin abinda aka sace matan,

🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                5⃣7⃣

                   BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUM GROUP🐎

🎁NASIBI WRITERS ASSOCIATION🎁

🎁N🎁W🎁A


   Almost true life story,,,


  Labarin da naji natafiyan nafisat yatayar min da hankali sosai agigice natafi side dinta,

   Da sallama na ,nashiga dakin nata,

   Kwance take saman gado ta dunkule waje guda da ka ganta kasan cewa tana cikin damuwa sosai,

   Kallo daya nai mata sai naji wani irin tausayin ta yakamani,

   Jin datayi alamar anshigo dakin nata shiyasa ta dan gyara kwanciyar ta kadan, tadawo da kallon ta sai tin kofar shigowa dakin,

   A hankali nadan karasa har bakin gadon nata,

  Kusan wani dan lokaci ba wanda yace kala tsakanin nida ita,

  Gefen gadon inda kafarta yake, nai saurin isa gurin,

   Maimakon inyi magana sai kawai nadan fara kuka mai tsima rai,

   Shiru tayi nadan wani lokaci tana jina,

   Saida ta daure sanan ta iya ce mim kin ji cewa zanbar gari ko,

  Nadan gyada kaina alamar eh,

   Tace min hakika fadima ke yarinya ce karama wacce tasan ya kamata a rayuwa,

   Ta dan dago daga kwacen idon ta sun gada sun yi ja jajir, dagani tayi kuka sosai,

   Sai jiya nagane cewa kina kauna na fadima, nakuma gane cewa duk abinda kikeyi ba don kowa kikeyi ba sai don Allah,

   Nayi nadama da danasanin kuntata makin da naitayi, abaya wanda dana sani in rugumay ki,takar yar uwata saboda irin yadda kika rikeni,

   Tsayin wani dan lokaci babj wanda ya,iya cewa kala acikin mu,

   Ahankali na dan iya bude bakina nace don Allah idan har na saba maki kiyafe min don Allah

   Tashi tayi ta zauna da kyau tace da sauri haba fadima duk iya zaman da nayi daku nice mai yawan saba maki,

   Saboda rudin shedan da mugan kawaye, 

   Duk kokarin da zakiyi kifitar dani kunya kin yishi fadima don gudun kar zamana da mijina ya baci kinyi iya kokarin ki wajen gyara min zama,

  Don ko jiya ina sane da cewa kece kika dauke abin da yar lici ta bani 

   Wanda in badon kin dauke a,yadda nake ji ajiyan wlh da nasha mai isata saidai su Abba su ganewa idon su irin abinda nake yi,

   Kinga duk da Ahmad yasan abinda nakeyi da kuma irin plan din da muke shiryawa akanshi baisa ya canza min ba ko ya nuna min cewa, yagane komai,

   Duk sai jiya wurin bayanin da salim yayi yass nagane cewa kece kika taimaka ma rayuwa na sosai,

   Wanda in badon ke ba da ban san ya zata kasan ce dani ba awanan kasar,

  Masu daukan doka a hannu ba sai ta baci ba 

    Tausayin tane yakara kamani so sai bansan lokacin da na rike taba ina kuka, ajikinta,

   Ina fadin kada kitafi don Allah kiyi hakkuri ki zauna tare da mu,

  Itama din kuka takeyi na nadama sosai da danasani

   Mundan kai wani lokaci a hakan ba mai ba wani hakuri a dakin sai itace ma tai karfin halin cewa don Allah intaya ta rokon Allah akan irin rayuwar da take ciki,

    Sai a lokacin nakula da cewa nafisa bata jin dadin jikinta har yanzu karfin haline kawai takeyi,

   Abinda tayi yanzu yayi matukar bani mamaki saboda sai nake gani kamar a mafarki nake ba wai nafisan da nasani bace har take cewa in yafe mata ,,

   Kai duniya abin tsoro ne gaskiya,

  Idan bakabi duniya a sannu ba saidai tagama dakai karaf daya badai kai ka gama da ita, ba,,,,

    Muna a haka ban mu fargaba sai jin muryan sheriff mukayi ya bakin kofa, a,storace muka waiga duk kan mu,,

    Inda yake tsaye, fuska a daure, Gabana saida yafadi don tsoro,

   Takowa yayi zuwa cikin dakin yanawa nafisa wani irin kallon kyama, Nima dai kallon nashi nakeyi  da kumburarun idan nu na da su ka sha kuka acikin kwana kin nan,, 

  Tabayana yayi yana fadin may kukeyi anan dakin , wurin wanan mara,imani,

    Kafin in bashi ansar tambayar da yai min sai nima na wurga mai tawa tambayan

   Nace mai Sheriff din mu don,Allah kazama mai yafiya da uzuri ga duk wanda Allah ya hada ka zama dashi,

   Kayi hakkuri kayafe mata kada ka bari ta wuce a,haka cikin wanan yanayin da take ciki

   Dan dariyar yake yayi tukun ya juwa zuwa kofan dakin da ya shigo yana cewa  

   Da kin fara bani ansar dana tambaye ki kafin ki ce zaki min halin yan adam,

  Bayan shi nabi da sauri don naga cewa yana shirin barin dakin,

  Amma sai bancin masa ba don ya bi hanyar fita wajen gidan ne,

    Daki na koma don in yi nazarin abin yi don gaskiya ban son tafiyar nafisat sam wlh,

  Ina shiga dakin Amal ce kwance a saman gado na , tadauki wayana tana dakila,

   Tana ganin na shigo dakin tajamin wani irin uban tsaki,

   Tadan kalleni ta tabe bakinta idonta na saman wayan dake hannu ta, ta min ,

    Wai ke fadima wata irin yarinya ce wai da bata da zuciya haka,

    Wanan matar da har kike wani shishigin zata tafi, kinsan komai akanta,

    Sanan saboda tsabar kiyayyan da take maki har iki,rari tayi da cewa sai ta halakaki, agaban kowa,

   Kuma taso taiwa yayan mu sheri da kazafi duk akanki,,

 Wai shine rashin zuciya kalar taki har kina kokarin tayar ma kanki da hankali,

   Akan hukuncin da magabata suka yanke, ke  ina ruwan ki da maganar manya da har zaki sa kanki aciki,

   Jin da nayi tace maganar manya sai jikina yai sanyi lankwas saboda nassn cewa gaskiya Amal ta fada min bawai ba,

    Kan gadon nakaraso na zauna jiki ba kwari ajikin gadon nadan jingina, gami da yin tagumi da hannu na guda,

   Ido tazuba min da alamar mamaki take kallo na

   Cikin tausayawa nake magana, nace haba dai Amal da ba,a yafe ma mutum aida Allah ya shudemu ko kamar mutanen farko,

    Saboda irin aiyukan zunubi da sabon Allah da dan Adam ke aikatawa akulun,

   Zancen Amal takawar tana fadin ke fadima waiko ma kin shirya kayan tafiyar ki kuwa,

   Sai a lokacin nadan yi murmushin karfin hali nace har may zan shirya Amal

   Hararana tayi tace min ina kayan da yayanmu yasaya muna badasu zaki ba 

   Sanan kinsan cewa dasu Aisha da Umar zamu tunda da maman su za,a tafi,

   Sai alokacin nadanji wani dan shakat azuciya na jin ance aida su Umar zamu tafi 

   

   Washegari muna kofan gida duk kanmu gaba dayan mu su nafisa da Abba da wani dan uwar su nafisa wanda ya wakilci,, mahaifinta sai hajiya tsohuwa ,

   Nafisa tafito cikin shigar kayan indiya wando da riga sai gyalen da ta dan rufe kanta da shi ,

   Kallo daya zakai mata tabaka tausayi saboda koba komai taga samu taga rashi,

   Saboda samun miji gare ta irin sheriff din mu ba wasane ba gareta, saidai dayake, ,, ba,adai fidda tsanmani kawai,

  Ni, a haukana ganin nakeyi, Duk wanda ke wurin ya,na tausayin nafisat,ne,,

   Ashe ni ban sani ba kowa dake wurin, murna yakeyi da tafiyan ta don duk ta ishe su agidan basu da yadda za,suyi ne kawai

   Kuma shi sheriff ba mai daukar magana bane da yakori kusan kowa na gidan,

     Ina hada ido da ita sai naji wasu yan kwalla nabakin ciki na batun sulalo min,

   Amal ta kula da hakan sai ta dafa min kafada tace min hjy tsohuwa na magana dani,

  Muna kallo suka wuce agaban mu ba mu da yadda zamu yi da ita,


     Mumadai gadan gadan shirin tafiya mukeyi zuwa madina inda zamu fara wani sabon rayuwa,

  Gaskiya sheriffudeen Ahmad yai muna na mijin kokari sosai 

  Don ni azatona wanan gidan nashi da nasani,na ma,aikatar su dake madina zamu zauna

   Ashe abin ba hakana ba hakana yake ba,, 

  Don gata ne na sosai akai muna wani dankareren gida mai kyau aka sai muna a tsakiyar gari anan zamu zauna ,

   Gidan baida nisa sosai da makarantar mu, da kuma masallacin haram,

   Zamu iya yin karatun mu ,zamu ,kuma samu yin ibadar mu a sau,kake ,

   A gaban ummi muke ana gobe zamu bar garin tana muna fada kamar yadda duk wata uwa ta kware zata iya yiwa danta fada,

  Tai muna nasiha sosai da ja muna hankalin kanmu guji don abin duniya wanda hakan shi yafi yawa ga alumma yanzu , 

   daga karshe tai muna nasiha akan kuka da ibadar mu fiye da komai na duniya,

  Sai fatan alheri da taimu dakuma muriki junan mu cikin amana da fahintar juna,,,

   Shiru mukayi dakin saboda nasihar nata duk ya kashe muna jikin mu, sosai wlh,

   

  A hankali yake saukowa daga matakal jirgin idon shi mane da wani dan farin tabarau wanda yadan kara ma fuskan shi kyau 

   Fari dogo kyakywa dashi matashi ne maiji da lokaci da ganin shi,

   Shigar shi kawai ta isa taba mutun ansan hakan. 

  Kallon garin yake yi a tsanake yana anyana cewa lalai tsarin garin tayi mai daidai,

    Hotel din filin jirgin yadan kama don yadan huta gaji kafin ya kira dan uwan nashi dayai ma tafiyar bazata,

    Saida yadan huta sanan ya kira da uwan nashi don ya sanar mai cewa yana kasar tasu pa


    Saidai fa ni gaskiya jama,a tun lokacin da nasamu admition dina har zuwa yau ban yi wa sherrif din mu godiya ba 

   Don haka yau na kudiri aniyar sai nayi mai godiya kafin mu wuce gobe, insha Allah,

   Falo shi yake zaune bayan yagama cin abinci , duk da ba wani abincin, mai yawa yake ci ba so, sai,

  Hankalishi yana ga  kalon wasan polo, da akeyi a,tv falon, shi din

   Da sallama na na,isa gurin da yake zaune na gaishe shi cikin ladabi da biyayya,,,

   Dan juyowa yayi cike da mamakin gani na a wanan lokacin ,

      sai kuma ya kauda kai shi zuwa ga kallon tv da yake yi,, 

    Sai dai ina ganin shi,,gaskiya naga ya ramay min sosai ya kuma yi dan baki,

   Kai,na na kasa nace nadan gaishe shi,,ahankali batare da naji ko ya ansa min ba

   Nace mai nazo ne in mai godiya bisa ga irin kokarin da yai muna nida yan uwana,

  Har zanci gaba da magana dana fara 

  sai wayanshi tai yar tsuwa,

 Hannu ya mika tare, da Dauka wayar yana dan yi yana waigen tv ,

  sallama yai ma wanda yakirashi cikin murmushi,

   Bayan sun gaisa da maishi naji yace what a surprise, kake shirin yimin Suraj,

   Waida gaske kakeyi kana cikin saudiya, shine koka fada min cewa zaka shigo insan irin taron da zan ma,ka,

   Ai yana fadin haka sai ya mike bai kara bin ta kaina na ba naji yana kiran mustapha tawaya suzo suje, wurin dauko suraj da yashigo gari,

    Bayan sheriff din na,mu nabi da kallo daga inda nake tsugune, ina mai mamakin kowaye wanan da yabugo wanan wayan,, 

   Komadai waye yanada muhinmanci sosai ga sheriff din mu,

   Tunda daga bugo wayan bakon  ya mike tsaye cikin murna da farin cikin zuwa taron shi,   

   A tsaye suka samay shi daidai inda yai masu kwatancen cewa yake,

  Tundaga motar da yaga anzo taron shi da ita ya ce a ranshi kalai maganar mama yana da kamshin gaskiya,

 Cikin farin ciki da so da kauna suka runguma junar 

   Wani irin dadi Ahmad din ke ji azuviyar shi ganin yau dsn uwsn shi yakawo mai ziyar a inda yake

   Ai Suraj bai rude ba sai da yaga irin gidan da suka tunkara wanda ake nufin cewa , wai Ahmad ne, ya mallaka, shi,

   Wani irin dan huci yayi mai fidda iskan zafi abaki saida kusan kowa na motar yaji shi,

   Sai yadan basar da cewa duk gajiya ce saboda yafito nisa,

   Sai cikin dare suka karaso gidan don haka ni koda suka isa har na kwanta barci, abina,

   Saboda ina tashi da wuri yin aiki safe, shiyasa na saba da kwanci da wuri,

    Wani bangare guda na gidan aka ware mai inda akaimai masauki ke nan,

   Maman su umar ce ta gabatar masu da abinci

   Kasancewar tana da kula da aikinta ga tsabta ga iya girki kamar na wani gidan saida abinci,

   

     Na shirya komai nawa har na Aisha sai dan abin da ba, arasa ba kawai nabari adakin namu,

    Da safe ma saida na hada ma sheriff komai yadda nasaba sanan na wuce don inyi wanka in shirya,

   Dogom riga na sa yau pink kalar ta amshe ni sosai, ajikina,

  Ina kokarim daura dan kwalina naji intercoms din dakina yai kara alamar kira daga falo,

   Cikin sauri nafito dan in ansa kiran oga na sheriffudeen Ahmad,

   Zaune suke su biyo a dining table din suna kokarin fara bude abincin

   Saida nagan su su biyu sanan natuna cewa ai yana da bako 

   Gashi kuma abincin shi, shi kadai na aje agurin table din,

    Cikin ladabi na iso tare da sallama na,

  Sheriff din wanda kanshi ke din ban kasa yadago daniyar yimin bayanin in karo masu plates da spoon,

   Sai idon shi ya caraf ga irin kwaliyar da nayi yau din,

   Cikin mamaki da kuma shauki yake min maganar cikin harshen larabci,

   Yace min bansan yai bako bane nakawo mai abinci kamar shi kadai,

   Nace ma la, agaskiya ban sani ba saidai ina mai neman afuwan gare,.  

    Saida ya dan lunshe idon shi kadan yace min ba matsala ina iya zuwa in karo masu ,

   Shi ko bakon jin muryan dayayi kamar s,na busa sarewa yasa shi dan waigowa,

   Sai yaga wata yar sabuwa mata shiyar budurwa ce ke tsaye a bayan shi tana wanan zazakar muryan,

   Ganin da yayi suraj yadan bini da kallo yasa shi ce min inbar shi kawai zasu yi manage da wanan na gaban su,

    Ban karasa fita ba itama Amal tashi dining erea, din cikin shiga ta kamala,

    Azuciyar suraj yace kai Ahmad din  ya hada kyawawan yan mata haka may su keyi agidan ne wai,

  Jindayayi Amal na magana cikin harshen kanuri yasa shi budar baki da mamaki yana kallonta, sai ya hango dan kama da tayi da mahaifiyar Ahmad yagana,

   To ita kuma waccan ta farkon fa ,hakan yai daidai da kara waigawa dayayi yana kallon hayar kofan da nab 

   Sheriff ya kula da shi sarai shiyasa ya canza shawara koda zu,

   Saima ya tuna cewa ai yau zasu wuce madina abinsu,

   Don haka sai yai bar wanan zancan zucin da yake, 

   Suka hauhirar yaushe rabo 

  Suna gamawa sukaje gurin ummi don ya gashe ta   

  Ummi tayi farin cikin zuwa ziyarar dan uwan shi dayayu, tundaga kasar turai har nan 

   Bai ai,wani dadewa ba salim ,yasa kowan mu fitowa da kayan shi don Aloda a motar da zamuyi tafiyar da ita,

    Wata yar far mota ce ake ta loader kayan mu a cikin, wace da alama da ita zamuyi tafiyar,

   Kowan mu yafito cikin, shiri  shi, gun ,hajiyar mu na nufa don mu bankwana da ita,

    Allah yagani banso wucewa inbarta ba saiga shi itace ma ta kara min kwarin gwiwa akan in tafi in yo karatuna watara zai amfane ni ne,

   

    Ganin da suraj yayi munfito ana muna rakiya yasa shi tambayar ko ina zamu haka na

   Atakaice yabashi ansa da fadin madina,

   Yakara tambayar shi may yasa bazami bi jirgi ba 

   Yace mai ai jirgi bai shigowa garin makka, sai  dai sauran garuruwan dake gefen makka,

   Wata tambayar yakara watso mai saboda may jirgi bai zuwa,

   Dan murmushi sheriff yai mai yabashi ansa atakaice da cewa Ka,abah,,,

   Ganin da sheriff yayi muna kokarin shiga motar yasa shi saurin karaso wa wurin mu duk da Almustapha ya yi a ranging din mu yadda yakamta, amma saida yasa aka maida umar wurin salim dake gabar motar tare da yusuf driver,,,,

    Daidai motar zata tashi kowa na daga muna hannu mukayi ido biyu da ni da sheriff wanda naga bakin shi na motsi yana fadar wata kalma da ban gane ba,,,

 Da sauri na kauda idona cikin nashi wanda hakan yadan sashi wata makalalan dariya,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈TAKARI✈✈✈

          👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                  5⃣8⃣

                     BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


🎁NASIBI WRITERS ASSOCIATION🎁

🎁N🎁W🎁A


  Almost true life story,,,,,,


  Haka motar mu ta harba saman titin hanyar garin madina,

   Tafiyane mai tsawo a gaban mu, saboda ba wani gari maidan girma da mutum zai gani ko ya ce zai dan yada zango,

   Gidan larabawan kauye ne jefi jefi a cikin dajin,

   Danjin wanda babu yalwan manyan itatuwa sai dai tsaunika madai daita da zakai ta gani,

    Mun dan yi nisa sosai dagarin makkah duk zukatan mu badadi sam

   Ina tunanen hajiyar mu ne koda yake nasan cewa Yumma zata kula da ita sosai 

   Muryam salim naji yana cewa wai shi wanan ta ina yafito yazo muna nan ne,

    Amal da tadan kai kwance daga bayan motar,  ta  dan jingina  jikin ta a sit din motar

   Tace yazo gurin dan uwan shi ne mana, tunda kasan dole suyi zumunci tsakanin su,

   Salim yace nikan duk ban yarda da yaran mama wlh don suna iya yin komai ga yayan mu,

    Ina jinsu sai alokacin nadan yi magana nace ma su au

   Wanadin dan uwan Sheriff ne, aiko naga kamar suna da dan kama da junan su,

    Saidai sheriff yadan fishi tsayi da fari ko,

   Salim ya ce kai basu da wani kama a ko kadan, ai shi Yayan mu duk kawu ya kwaso,

   Suko sun biyo mahaifiyar su ce inaga tundai yanayin jikin su yanada kama,

   Haka sukayi ta zancen su muba jin su har suka gaji sukayi shiru, don kan su,,,

   Bayan isan mu ne mukasan cewa an canza muna gida,

  Ida muke zaton zamu zauna ashe ba a nan bane,

   Munyi farin ciki sosai na ganin irin gidan da aka kama muna,

   Afalo muka zube gaba dayan mu, 

   Salim ne yace bari ya, tashi yadan zagaya gidan, don yaga dakin da zai dauka,

       Kafin yatashi ne Yusuf driver ke mai bayanin akan dakunan,

   Yace sheriff yai mai bayanin inda dakin kowan nen mu yake,

    Dani da Amal dakin mu kusa da na juna ne, sai maman su umar dake can ta bayan mu kadan kusa da kitchen,

   Salim da Yusuf driver  mu nasu bangaren daban  mai kama da namu side      din 

    Suna ta farkon shigowa cikin gidan ne su,

    Komaimirrow  agidan ba wanin abinda zamu ce mun bukata na zamani,

   Maman Umar bata da sanyin jiki muna zuwa bata bi ta gajiyan da muke dashi ba 

   Kitchen ta fada ta dafa muna abinci mai saukin sarafawa,

   Daga nan kowan mu ya fada dakin shi don gyara inda zamu zauna, 

  Dakin bai bukatar wani gyara komai neat ne, akwai gado da mirrow sai wardrobe , sai tv da dan karamin fridge, dake dauke da kayan sanyi,

   

    Washe gari tunda safe muka shirya saboda yaune, zamu fara shiga lectures,

   Makarantar babba ce ita jami a mafi girma agarin madina,

   Bamu samu wani matsalaba wurin gudanar da komai,

   

    Ahakana mika dinga karatun ba kama hannun yaro,

   Muna samun kula sosai ga sauran yan uwan mu dalibai don ganin da suke muna cikin shigar mutunci koyaushe,

    Sannu sannu na fara fice a department din mu kowa yasan da ni,, koya malami yakoyar dani insha Allah zan hadace shi akaina,

    Wanan kokarin yasa nadan fara fice sosai ga kawaye na,

   Mun hadu da yan Nigeria can da dama , suma sunzo karatune kawai,

   Akwai wata Salimat yar kano damukr yawan hadewa wurin karatun mu da ita,

   Saidai ayadda na fahinta ita matar aure ce,  don ba yarinya bace,

   Dafarko salimat bata kulani amma ganin da tayi inada kwazo sosai yasa ta dan sake jiki dani,

  Hakan yasamo asaline watarana da akai muna test bata zo ba sai na kokarta nai mata,

  Kafin in mata saida nasha wuya aranan don da kyat nasamu information nata,

   Bata shigo school ba sai bayan kwana biyu ,Ashe bata da lafiya newai kuma tarasa wanda zata aiko,

   Abin mamaki saida akazo rabon test din sai taga ai har da ita kuma abu guda muka samu,

   Ina can gefe ban ko kali gefen da take ba na,

   Ina karatuna sai ganin ta nayi gaba ta dafa fan table din dake gabana tana mai yi min sallama, 

   Ahankali nadago kai na kalle ta ina mai ansa mata sallamata 

  Sai take ce min tazo ne taimin godiya don tasan cewa duk wanda ke wanan ajin na computer science ba wanda zai iya taimaka mata bayan ni,

   Naso in boye mata cewa bani bace nai mata amma ina sai tace min,

    Ba yauba ina lura dake kina da hakkuri da sanin yakamata,

   Nimatar aure ce mijina ya hanani hulda dakowa don gudun gurbatar tarbiya,

   Shiyasa kikaga ban kula kowa acinkin wanan department din na mu 

   Don gudun saba ma Kama train da tadauka kafin tazo, amma inyi hakkuri zatayi wa mijin ta bayani komai gamay dani

   Tundaga wanan lokacin muka yi sabo da salimat sosai,

   Inda nagane cewa ita kadai ke zaune a gidan ta, karatu yakawo ta madina ,

   Mijin ta yana Nigeria da zama,,salimat tana da kishiya a Nigeria wace nake gani kamar yar kasuwa ce tana kano to Dubai,

    Nafahinci hakane indan suna waya da mijin in ta tambaye shi yara da maman su sai yace ai ta tafi dubai. Koyace ai tadawo rana kaza,

   

    Karatun da mukeyi bai hana mu yin ibadar mu ba, don kusan kulun muna zuwa sallah a haram , saidai ba kowani lokaci ba,

   Amma sallar ranan jumma,a bata wuce mu sam,

   Saboda itace ranan weekend muna zama tun safe har dare acan 

    Ranan alhamis mukan taya maman umar gyaran gida da sauran aiki  gida da ya kamata

  Idan mundawo wani lokaci mukan dan zauna da maman Umar mudanyi hira kokuma in koya ma su Umar da Aisha karatu,,,

   Kusan watan mu guda a madina, Sheriff din mu yazo ziyar mu, tare da ummi da hajiyan mu, 

    Munji dadin wanan ziyar so sai don ji mukayi kamar mun kai shekara bamu gansuba,

   Koda suka iso bani gida mun fita dani da Aisha, munje wurin gyaran kai ,

    Wurin baida wani nisa da gidan mu sosai don haka da kafa muka tako dazamu dawo,

   Waje nasamu sheriff shida,Almustapha, yana waya a,lokacin,

   Tunda na bude gida zan shigo idon shi ke akaina, nima ganin da nai masu na bazata yasani mamaki,

   Cikin fara,a na isa gurin su ina masu sannu da zuwa,

  Kamar yadda yake ansa min a dakile yau din ma hakane,

  Cikin zuciyar shi kuma sai mamaki yakeyi, may yarinyar ga ke ci haka tawai wanan girman cikin lokaci guda,

   Anyako madai tana karatun kuwa kodai jin dadinta kawai takeyi abinta sai kuma wata zuciya tace mata a,a ina bayazatayi hakana ba don yasan ni da kokari sosai,

   Balle ma yasancewa ina son karatu sosai arayuwa na,

  Muryan mustapha ce takatse mai tunanen shi inda mustaphan ke ce min ina mukafito haka,

    Nikuma ina washe bakin murnan ganin shi,nace mai ai,nafito can  wurin gyaran kaine, nida Aishan

    Azuciyar shi yace badai tsafta ba kan wanan yarinyar akawai kulada kai,

   Ciko na shiga inda yabi bayana da kallo da sauri ya kauda kanshi don gudun yin sabo,

   Saboda wani irin mugun girma yaga nayi mai lokaci guda, saida gaban shi yafadi,

Inashiga cikin gida, kuma nai arba da ummi da hajiyar mu zaune a falon mu,

   Da dan ihu na, naRugumay su ina murna,na daidai lokacin shima sheriff ya shigo cikin gidan 

   Saida nagama murna na san nan natuna cewa, aiba abasu komai ba na dan motsa baki,

   Da sauri na shiga na hado masu kayan sanyi a ture tare da dan fruit ,

   Ummi tace aidama nace diyata bata gidan ne tunda naga ko ruwan sha ba,abamu ba balle,

  Ina dariya ina tsiyaya mata a cup nace mata murnan ganin ku ne ya hanna ta baku ai,

    Sheriff na zaune yayi kicin,kicin da fuskan shi,na iso da cup da lemon zan zuba mai,

   Agaban shi na dan tsugun na gab dashi sai kamshin, turaren na da ke hawa mai kai,

   Yana min wani irin kallon mamaki a fakaice,

   Bayan nadan tsiyaya mai ne nadan dago kaina a hankali nace mai ga lemu na yasha

   Hannu yadaga min kawai alarmar godiya,

   Natashi a hannakali cikin tafiyar da ni ban masan cewa ina yin irinta ba, nabar gurinshi 

    wurin mustapha nanupa don shima in tsiyaya mai,

  Ban karasa kawai wurin mustaphan ba naji karan cup din da na zuba ma sheriff lemo ya fadi,

   Cikin sauri na aje cup da gwangwanin lemo agaban mustapha na juyo wurin  sheriff da sauri,

   Lemon ya zube a kasa har yadan taba mai rigan shi kadan,

    Ruwan da ke gefe na bude nadan zuba mai daidai inda lemon yataba mai riga,

   Cikin rudewa na cire gyalen da na yane fusaka na dashi na fara goge mai wurin,

   Kaina da akai ma gyara sai kamshi ke tashi ya dan tsira ma ido

   Yana kallon yadda gashina ya kwanta lub bakikirin da shi,

    Ga kamshin mangashin dana turare na ya rude wurin ,,,

   Idonshi yadan rintse kadan gabanshi nata faduwa,

  Don shifa gani yake wanan kamar ba fadimar yar takarin da ya sani bace,

   Saboda canzawan nawa yayi yawa cikin dan lokaci guda haka,

  Idonshi yadan kara lumshewa yana mai dan maida nufashi, a hankaki ta yadda ba mai iya ganewa,

  Cikin kidima naje da sauri nadauko moper na goge kasan , Sai faman yi mai sannu nakeyi,.

    Saida na gama gogewa san nan hankalina yadawao daidai

     Ko da na daga kai in kara yi mai sannu sai naga idon shi a lunshi sainadauka ko ranshi ne ya baci ,

    Cikin sanyin murya nace mai dan Allah yayi hakkuri ba san zai zube mai ajiki ba ,,

  Idon shi yabude wanda naga kwayar idon shi yai ma jajir ,saida naji tsoro,.

    Hannu yadaga min alamari is ok,

   

     Bayan fitar su sheriff ne muka zauna muna ba ummi da hjy labarin makarantar mu 

    Nafada mata yadda ake karatu a wurin da kuma salimat da na hadu da ita,

  Wacce yanzu nake jinta tankar wata yar uwan na najikina,

     Nan sukayi muna weekend saida sheriff da mustapha ba anan suka sauka ba su,

   Washe gari sheriff yace min zaiyi baki,

    Mudanyi mashi abincin da zasuci don wani meeting zasuyi 

   Shago mafi kusa natafi ta sayo duk wani abin bukarar da zamuyi amfani da shi,

    Don mu a shago ake saida kayan abinci a can ba wai a kasuwa ba, 

   Abinci kala kusan biyar muka hada masu nida maman su Umar,

   Saida muja gyara falon yayi neat sai kamshi ke tashi ko ina, da sanyin A C

   A,babban dinning table muka hada masu  wurin yayi kamar za ai wani dan kwara,kwaran walima,

   Su hudune suka shigo dai almustapha da ke tare da sheriff ko yaushe, suka zama su biyar,

    Sun gaida ummi da hjy cikin ladabi da girmamawa,

   Bayan dan hiran lafiyar jikin ta da sukai mata wanda duk kusan bayanin hajiyar mu ne ma mai basu ansa, don ita ummi bata magana,

    Nice shigo falon cikin wata doguwar riga ja, wacce a hannu ta kawai da kasar rigan keda ado,

   Saida na gashe su tunkun sanan na juya wurin da sheriff yake nai mai bayanin abinci is  ready

    Wani irin kallo yai min wanda ban iya fadan dalilin hakan,

   Ina cikin damuwan naji muryan wanidaga cikin bakin yana fadin masha Allah,

   Ahmad kai keda kauna haka akasan nan kuma ban sani ba

   Sai naji sheriff dake kokarin jawo plate agaban shi yace to aikaga yanzu ka sani ko,

   Batare da jin kunyar kowa ba a wurin shi mutumin ke ce min 

   Sunan shi Ali Baba don Allah yana son in soshi, dama yadade ya son mata mai irin duk siffan dake gare ni bai samu ba,

   Ashe ma wanan mugun yana da ita a gida yabarni kulun ina cigiyar yar matashiya, mai,,,,,,,,

   Sheriff dakatar dashi da fadin Aliyu is enough don Allah kazo gaban yar yarinya kana faman zuba shirmay kamar wani karamin yaro,

   Wanda aka kirada Aliyu yace to be Frank ba wasa a zance Ahmad naga sister ka kuma ina so 

   Idan har ba zaka taimaka min ba nida kaina zan bidi so a wurinta gakuma ummi a gari,

   Bai kakarasa yasake ce mai ban fa son shirmay wanda ke karatu zaka zo ka damay ta, ka koya mata shirmay,

   Aliyun yana dariya yace o shirmay ko zaka gani in shir may zan koya mata

   Sai ya sauko daga kujerar da yake zaune yadan tsuguna kasa yai kasakasa da muryan shi yace ma sheriff ina wuni yaya,

   Gabadaya falon suka sa mai dariya banda sheriff da ya dan tsuke fuskan shi,

    Yace ma Aliyu dan iska wanan ta wuce yaudar ka ka koma can wurin yan duniya irin ka kuyi tayin duniyar cinku,

   Yace Iam telling you wanan karon wlh ba wasa acikin magana na Ahmad,

  Nidai ina gama zuba masu abinci na wuce ciki abina batare da nasan ya suka karasa ba,

   Ina shiga dakin kiran wayan salimat ya na shigowa mani,

   Nadauka tare da yi mata sheri ina cewa anty amaryan ke nan,

   Tanbayana tayi bata gan mu ba masallaci wanan weekend din,

   Sai ina fada mata cewa wlh su ummi ne da hjy sukazo muna weekend harda yayan mu

   Fada takama min tace lalai fadima baki da kirki yanzu har su ummi su zo arasa wanda zaikirani yafada min cikin ku

  Hakuri na bata nafada mata cewa suna nan ai tukun don sheriff na wani dan aiki ne,

  Taimin alkawalin zata zo zuwa marance insha Allah,

   Ina jin hayaniyar su sheriff har suka gama suka fita,

   Inda Aliyu ke ce mai yakirani muyi sallama dan Allah ko kallon shi baiyi ba don takaici,,

    Sai kuma gani nafito zanje gurin maman Umar dake aiki a baya,

  Duk da sheriff yasan cikin rashin sani nafito amma saida yaji haushina sosai,

   Aliyu na mai dariya yace brother in-law kaga ikon Allah ko ga ta tafito da kanta,.

   Banko waige su balle insan sunayi wurin da zani nasa kai, har zan shige sai naji shi yana cewa yar uwa dan tsaya min inzo pls 

   Waigawa nayi kowani angul banga kowa da yake ma magana ba sai ni don haka sai na dan dakata mai, 

   Ya tako cikin tafiya gayu har inda nake tsayee,

   Yace shi sunan shi Aliyu baba dan kasar Nigeria ne shi mutumin katsina ne aiki yazo yi a wanan kasar daga Nigeria,

   Kuma baida mata amma ya gane ni yana so na kuma yai ms sheriff bayani komai,

  Mamaki yakamani kamar ni yar aiki wanan dan gayun zaice yanaso 

   Sai nadan leka don inga  ko da mai ganin mu 

  Aiko sheriff ne tsaye cikin wani irin mugun kallon da yake min ina nai abinda ba daidai ba.

   Dayagane cewa na ga sheriff ins jin tsoro sai yace min ba matsala zaidawo ya gan ni amma may ye suna na

   Cikin sauri zan wuce nace mai fadima,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA


✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                  5⃣9⃣

                     BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


Almost true life story


   Cikin hikima da dabara Aliyu baba yafara koya min So,

  Saboda bayan tafiyan su sherrif yakawo muna ziyara alokacin ni bani gida ina school 

   Noban wayata yace salim ya bashi zai kirani yaji ko banda bukatar komai,

   Salim bai fada min ba lokacin da na dawo har kusan kwana biyu,

  Misalin tara na dare naga komai da nakeyi nasamu guri nadan zauna indayi nazarin wani takardan da muke da test akanshi cikin sati mai zuwa,

    Wayana naji yana kara, cikin mamaki nadauka don nasan cewa ba, a kirana a wsnan lokacin,

    Bakon noba ne nagani mai kiran don dai dama daga Salimat ne sai Sheriff din mu ko shi ba koyaushe yake kirana ba,

    Sai kusan karshen wata zai kiramu yaji ko muna da bukatar wani abu,,,,

   Cikin girmamawa nayi sallaman, , adayan bangare naji an,ansa min tare da yar sautin murmushi,

   Bayan haka sai dan shiru ya biyo baya,

   Can naji maishi na fadin fadima baki gaidani ko,

   Ya salam nace don jin sunana da mai shi yakira, balle ko ince ai wrong noba ne,

   Yakara ce min hakana sai nace mai ina wuni to yace min lfy, yatambayeni ya karatu nace mai Alhamdullah,

   Ya ce min kin san kodawa kike waya kuwa, nace mai a,a sai yace min

  Ina waya ne da Ali baba abokin Sheriff Ahmad,

   Dam gabana ya fadi don natuna cewa sheriff yai muna fada sosai akan duk wace take kula maza zai dakatar da karatun ta yai mata aure,

  Tuna hakan da nayi yasa nafara bashi hakkuri kamar wace tayi wani laifi

  Nace mai don Allah yayi hakuri kada ya kara kirana don in yabari akaji za,afadama sheriff,

  Dariya nabashi yace min to wazaiji aishiyasa ma yakirani yanzu don yasan cewa ina daki na ni kadai,

   Hakana yaita min dadin baki irin na maza, ina jin shi duk na matsu takashe wayan saboda sai ina ganin kamar za,azo akamani ina wayan,

  To tundaga ranan yake kirana duk dare da sunan wai mu gaisa,

  Da haka da haka yaita cusa kanshi gareni, tun ina iya boyewa har na fara rashin boyewa ko gaban waye ma zai iya kirana kima musha hiran mu,

   Yanzu hankalina ya kasu gida biyu ga karatu ga soyayya, Ali baba akaina kuma duk biyun ina kokarin kulawa da su,

   

   Yanzu karatu mu ya fara nisa sosai don gaskiya bamu da lokaci irin da,

  Gashi kuma tunda mukazo bamu taba zuwa hutu makkah ba 

   Ko anyi hutu a madina muke tsaya abin mu muyi hutun mu Bamu zuwa ko ina,

   Salim ne yatafi makka bayan mun samu wani dan gutun hutu,

   Bayan yadawo ne yake sheda muna cewa ai sheriff yai aure a dubai wata yar Nigeria ce amma acan take zama wai yar kasuwa ce,

  Nayi murna so sai da jin cewa sheriff yayi wani aure, 

   Nace ma salim ya labarin nafisat sai yake ce min ai tana Nigeria amma ance wai basu rabuba don Abba ya hana sheriff ya bata takarda,

  Kawai sainaji dadi wlh har cikin raina don ban son rabuwar su da nafisat sam,

  Amal kuwa saida ta gama jin labarin da salim ke min sai, tayi dan guntun tsaki tace wanan ai auren shirmay ne

   Kaji ance mata yar kasuwa aikai kasan babu wani abin kwarai aciki sai barikan ci kawai,

  Duk da sheriff yake dan uwanta ne amma, Sai naji haushi kalman nata

   Naga cewa ai yin auren yafi mai daraja da zama hakana ba mata,

   

     Yau dagani har Amal da mama su Umar agidan maman salimat mukayi ni don tayata aikin taron mijinta da zai kawo mata ziyara daga nageria

   Saida mukaga komai yayi tsab mukayi mata sallama muka bar 

   Lokacin da muka iso namu gidan sai muka tarar da baki 

  Sheriff ne tare da wata mata fara sol da ita,  saida bata da tsayi don ina iya cewa gajera ce,

   Da murnan mu muka tare shi, wanda yaji dadin hakan har cikin ranshi,

   Nice ma na kula da matar wace ke zaune gefe tana wani shan kamshi,

   Nagaisheta nai mata sannu da zuwa, a yatsine ta ansa min, 

  Azuciya na nace taupa abin jiya yadawo ke nan,

  Amal ma a gadarance tace mata sannu, 

  Wanda hakan ya nuna sheriff baiji dadin hakan ba shima,

  Maman Umar takawo masu dan abin sha tana tambayar su komay za,a dafa masu,

  Da hannu ta nuna adauke abin shan kamar wace aka aje ma kashi agabanta tace ita bazataci komai, ba sai sunje hotel,

  A hankali na duka zaukwashe kayan sai sheriff yai min ahannu alamar indakata da shi,

   A hankali yazuba lemon  stwberry, a cup din wanda yai sanyi sosai sanan ya jawo wani dan gutun snack ya na ci,

   Bansan lokacin da nai ajiyan zuciya ba wacce har takai mai akunen shi

  Da sauri yadan kalloni yana mamakin ajiyar zuciyar nawa,

  Wanda dama mamakin yadda yaga nakoma yakeyi , don a kulun yagani sai yaga na kara wani irin girma,

   Hira sukeyi da salim inda na dan tashi a hankali na koma kan kujerar dake falon gefe guda na zauna

   Saidai daga inda suke muna jin hirar komai, niko irin kallon da matar ke min ne yasani komawa gefe na zauna,

   Don ina zaton ta san cewa ni yar aiki ce kuma gani ina watayawa kamar kowa,

   Wayana ne yadauki tsuwa alamar kira ya shigo ,

  Duk wanda ke falon saida yadan kalleni alkarayi ,,,,

  Dan basarwa nayi har kiran ya katse, ido sheriff yadan zubo min ganin kiran ya katse ne yasa shi dan kauda kai

  Kiran nawa aka karayi cikin rashin damuwa nadauki kiran  tare da dan yin murmushi a fuska na

   Bandamu da barin wurin ba don nasan babu mai jina a inda nake kuma nai tsabar keantar da muryana bamai jin abinda zan fada,

  Bayan mun gaisai sanan na tambaye shi ya aiki, yace ba wani nadai gane inbani nakiraki ba watau ke baki iya kirana fadima,

  A hankali nace natuba zan fara kiran,

   Abin mamaki dariya naji ya kwashe dashi, sai nadan yi murmushi  nima daga inda nake,

  Sai yafara magana da dan saurisauri yake ce min jirgi zai shiga shine ya bugo min don muyi sallama zaije wani akine a paris,

  Sau biyu muna hada ido da sherrif  yayin da nake wayan, sai nadauke kaina daga gefen su nacigaba da wayana ,,

   A hankali naimai fatan alheri tare da Allah tasa

 adawo lafiya ina mai yin murmushi cikin kashe murya na,,,

   Daidai lokacin da nakashe wayan nawa ne muka ido hudu da sheriff din mu wanda yazubo min idon shi da suka dan sauya daga fara,a zuwa fushi, 

   Sai naga ashe kusan kowa dake falon ni yake kallo ban sani ba

   Mikewa nayi abina nawuce wurin maman Umar a kitchen,

  Tundaga wanan lokacin sai hiran nasu yadan rage karfi sosai,

  Nasamu ta hada masu abincin labawa mai saikin dahuwa ga dadi,

   Najera a tire nadauko nakai masu har gaban su na aje,

   Ina cewa ga abinci nan nasan zaku iya cin shi don ba mai nauyi ne ba,

   Sai alokacin yadan sake fuska kadan yai ma matar da ko sunan ta bai gabatar muna ba balle yace muna ai matar shi ce,

   Abincin suke ci hankali kwance har da ita matar sai salim da ke taya su cin abincin,

   Amal tace wai yaya bakuwa ce kayi don bamu santa ba, kuma na ganku atare, 

   Yanajin dadin zama da kan nen shi sosai don yana son su saboda sune mafi kusanci da shi fiye da kowa,

    Murmushi yayi kadan ya kalli salim tace baka fada mata tayi sabon anty bace,

   Saida Amal ta dan kalli matar tace to, nida ke gefe ina kokarin jona tv na juyo da sauri ina fadin masha Allah,

    Gaskiya munyi farin ciki kuma muna mata sannu da zuwa da fatan zaki kula muna da dan uwa fiye da komai a rayuwan ki,

   Koba komai tadanji dadin hakan don tasan nafi Amal dama tunda har nai mata fatan alheri,

    Sundan kai wani lokaci a tare da mu anata hira tsakanin shi da yan uwan shi,

   Inda aziza ta fahinci cewa yana son yan uwan shi sosai saboda bataga abinda yake ba muhin manci ba kamar su,

   Don ta kula ko awaya yake magana dasu zaidade suna hira yana nuna jindadin shi,

    Saidai tasan cewa bata sami karbuwa ga Amal ba sam

   Shakata guda ne ni saboda tace niba yar uwsn shi bace ta jini amma yada yake kula dani yana daure mata kai so sai,

   Wayana yakara tsuwar kira again, 

  Wanan karon salimat ce ke kirana tana fada min mijin ta ya iso ko 

   Bansan lokacin da nadayi dan ihu murna ba nace mata tai mashi sannu da zuwa ,

   Nan nake fada mata nace mata ai yayan mu yazo da amaryan shi mai kyau da ita,

   Wanan magana yaiwa Aziza da sherrif dadi don na fahinci cewa yana son aziza sosai,

   Nikuma duk abinda yake so ina son shi don yawan kaunar da ya nuna min tun farko,

   Da murna nake fada ma Amal sakon salimat Amal din tayi dan dariya tace ashe yau anty amarya ce,

   Basu wani dadewa ba sukai muna sallama zuwa masaukin su,

    

    Acikin barci naji tsuwar waya na kamar kada in tashi sai dai nadaure na ansa kiran ,

  Amma abin mamaki mai kiran ya boye nobar shi,

   A cikin harshen turanci mai shi ke min magana,

  Dafarko yace min sorry da damuna da yayi ina barci na,,

   Sai na ce ba komai amma dan Allah dawa nake magana ne,

   Shiru ne yadan biyo baya, jin danayi ba ansa yasa nace ma maikiran kada ya kara kirana ni matar aure ce ,

  Idan yakara zan fada ma mijina,

  Dan murmushi yayi yace good ina iya infada ma mijin nawa, 

   Ganin da nayi zai jani da dogon zance yasani kashe wayar gami da tsaki, nagyara kwancina,

   

      Anashi bangaren jinda yayi nace zan fada ma mijina yasa shi dagaba   yace kai wanan yarinyar,

   Tashi yayi tsab yakoma cikin bedroom inda Aziza ke kwance tana jiran shigowar shi,

   Ce mata yayi baki yi barci bane, saitace mai a,a,

    Yana shirin kwancine ta jeho mai tambaya ,, dayasa shi yin tsit,

    Tace mai wai Ahmad ya kuke da wanan yariyar fadima ne,

   Batare da shakkunta ba ko jin wani dar yace mata yar uwatace itama,

  Tace mai maman ku guda ne da ita din ma,

  Atakaice yace mata aa, yar uwata ce kawai,

  Saida tanisa sai ta dan juyo setin shi tace mai ke nan akwai aure a tsakanin ko ko,

  Cikin firgita da jin kalminta yasa shi saurin waigo ta da karfi yace baki da hankali, aziza,

   Sister dinace fa sai tace and so what,

  Kallonta yakama yi a kufule,

 Ita ko kodar bataji ba, irin halin nan na kasaitatun mata,

   Daga haka baikara cemata komai ba ya kwanta zuciyar fam da wasiwasin,

     Tunda safe muka hada masu break fast din su tsab ,

    Amal takira shi tace mai ko salim ya kawo masu abincin su inda suke ne sai yace mai aa kawai sujirashi gayan zuwa suci tare,

   Kowa ya zauna a table din don cin abincin sai ni kadaice ban zo ba,

  Salim yace yafada min suna jirana,,,, 

  Salim na fada min duk saina rude don gaskiya ban taba cin abinci agaban shi ba,

   Table din nazo na zauna kowa na cin abinci niko sai wasa da cibi dake hannu kawai nakeyi,

  Aziza ta kalli sheriff takali fadima tace man kici abinci mana yar uwa

    Dan murmushi nayi nadan dibi ruwan chayi dake gaba nadan kurba kadan sai naji gaskiya ban iya sake jikina a gaban shi hakan,inci abinci,,,

  Tana kallon shi taga ya ture kayan abinci ya mike ya ce mata zai je yadawo ta zauna nan ta jirashi zai je yadawo,

   Ido tabishi da shi don mamaki tabas akwai wani dan feeling da sheriff ke boye wanan yariyar amma koma dai maye zata bincika,, 

   Ga mamakin ta sai kuma taga yanafita nafara cin abincina nomal kaman bani bace nakasa ci dazun,,,, 🐎ZEEE MAKAWA

✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

               6⃣0⃣

                  BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

 

Ya Allah ka azurta muna dukkan Aluman Mususllumi da lafiya, arziki ilimi mai amfani a rayuwar duniya da lahira,

   Jinjina da fatan alheri gare ku masoya na asali yan huguma groups gabadayan ku ina kara maku fatan alheri, 

   Banta mantawa da ku yan uwa na asali ,Anty,Hafsat yusuf, Anty,Mariya SB, Mama farida ,Anty Safiya mai huguma, Maman Rufaida, daduk wani wanda ya cancanci in rubuta sunan shi ban rubuta ba, nagode, nagode, nagode maku kwarai da karfin gwiwar da kuka bani, tun farko har yau gani ga shafi na sitin daidai cikin hikimar ubangiji,,,,,👏👏👏👏👏


Almost true life story ,,,,


    Aziza ce a masaukin su dake cikin masurin hotel din nan mai suna, Al,ni,imati

    Waya takeyi cikin kasaita da nuna isa ita wata kawar da taje Turkey sarin kayan furniture's

    Ai kawai kibari hindu, duk maganin su zanyi har shi din,

   Ai tunda nasamu har ya shigo hannu to shi sunan shi sorry don nan da wani dan lokaci sai yadda na juya shi,

   Ke dai kibi sannu aziza don kinsan cewa in badon taimakon Abu sultan ba da babu yadda zai amince ya aure ki haka,

   Kidibi tun lokacin da kike binshi amma ko kallo baki ishe shiba,

   Saukin ki guda da Abu sultan ya shirya muna wanan plans din cewa ke, marainiyace kuma ga mijinki ya mutu kina son miji mai mutunci wanda keda tsoron Allah da kuma kauda kai ga abin duniya ,,,

    Shewa suka danyi ta cikin wayar tace mugu wai shi nan ustaza kada

   Komai wayon shi sai naci kudin nan,

    Gabadaya sai na mallake komai nashi sannan in barshi a tutar ba bu,

      Wani dan guntun shewa suka kara yi, tace nasan ki mutumiyar baki da wasa ga duk wani abinda kike so,,

  To su yan uwan fa ya zaki dasu, 

   Tace kai haba Hindu saikace kin mata da kowa cece aziza kuwa,

   Motsin da taji kamar ana murda kofan dakin su za,a shigo shine ya hana takara sa zancen tace ma kawar nata Hindu sai wani lokaci ma karasa,

    Mao kula da sashen sune yadau kowa sherrif kayan da yasayo a reception room, 

    Tana kwance tui da ita samar gado daga ita sai wani dan towel da ba ko rufe mata habar kataran ta guda ba,

   Yana gani yadan kauda kai gefe, kadan 

   Duk da take matar shi ce ta sunna bai son irin halayyanta saman don ita nata matsalar bata da kamun kai ko kadan,

   Abinda yafara notice ke nan irin tantiran matan nan ne ita 

   Sai bayan Abu sultan yasa shi ya fada tarkon su ne yake dan gane wasu daga cikin halaiyanta, da basuyi mai ba,

    Abu guda ne tana kula da duk wani bukata nashi sai kuma yana ganin tana kula da duk dokan da yasa mata,.

       Saida ya gama kintsa jikin shi sai ya koma saman kujeran dake fuskantar gadon ya zauna ya jawo system din shi suna fuskantar juna,

   Yana cikin aiki take, ce  mai amma gaskiya na yaba da halin wa yan nan kanen naka wlh,

   Dan murmushi yayi na jin dadi har cikin zuciyar shi,

    Tace saidai ita Amal akwaita da dan jan aji ba kamar Fadima take ba don duk kusan hiran mu da fadima mukayi shi ,

    Ai halinsu ba guda bane su nada banbanci so sai,

    Da irin wanan kissan tai ta jan shi hira akan mu shi ko duk sai yaji dadi a ranshi cewa matat shi na son yan uwan shi,

   Kenan baza,a samu matsalar komai ba daga gurin ta akan su,,,,


      Tafe nake acikin sauri amma tunane ya,addabeni sosai ,agogon hannu na na duba da sauri sai kuma ,nakai kallo na ga katon agogon dake makale bakin shiga department din mu,

  Tabbas ya nayi latti har ankusa rufe shiga class din don ka,idace hakan,,,

    Sauri na kara na isa class din dai lokacin da malamin shima zai shiga,

   Guri na samu nazauna gami da yin tagumi, don dai gaskiya komai ban fahita ba daga lecture din na yau,

   Gashi kuma salimat bata shigo ba yau kasancewa mijin ta yazo ganinta

    Ana tashi ban tsaya jiran komai ba kamar yadda mukan dan saba yi indan muntashi sai mundan tsaya mun fahintar da junan mu tukun 

   Yau taxi na tare zuwa gida don ban son in wahal da yusuf yazo ya kaini kuma ace yadawo daukan su salim,

    Ina sauka nadauko kudi zan mika wa mai taxi mukayi arba da sheriff wanda motar su ke shigowa kwanar gidan mu a hankali,

    Yana baya zaune shida aziza, tun cikin motar yai min wani mugun kallo,

   Zan shige gida cikin tsawa ya kira suna na cak na ja natsaya wuri guda,

    Ina kikafito cikin rawar murya nace mai school yace ina yusuf yake da baije yadauko ni ba har na shigo taxi

    A,hankali nadago idona da sukayi dan ja kadan nace mai ban son ya wahala ne ni banda lafiya ne shiyasa yau nadawo nabar su Amal, sai anjima Yusuf zaije yadauko su,,  

     Bina yayi da kallo kawai yace matar nashi tafito motar tashiga ciki yana zuwa, 

   Duk da ranta ya baci amma sai ta dake ta nuna aiba komai, ta bini muka shiga cikin, gidan tare,

   Daki nafada nadan rage nauyin kayan jikina,

    Nafito dagani sai wani dogon wandon da riga mai yar guntun hannu, dai dai iya damtsen hannu na, kaina nasa mai hula baka,

    Inda take zaune tana waya duk kamshin ta ya karade falon namu kamar ba mace ba,

   Abin sha na hado mata cikin tire na aje mata agabanta, najuya nabada baya

    Ido  ta bi bayana dashi har nakai saman kujera na zauna kafa na guda nadan taushe guda yana kasa,

   Acikin ziciyar ta tace kai wanan yarinyar Allah yayi halittan shi wallahi jita kamar ita tayi kanta yar karama da ita amma komai nata acan acan gwanin ban shawa, wlh,

   Wanan dai nasan cewa na isa haihuwar ta da ace ban bar kauye ba,aure akai min da wuri da gaskiya zan iya haihuwar ta,

   TV na kuna mata tasha ralabawa suna wani film na ban dariya aciki,

   Ganin da nayi ta gama wayan yasa nace mata ga abin sha nan tasha kafin agama abinci,

  Dan murmushi tai min kadan tace ai a koshe nake kedai saidai ko zuwa anjima,

  Ban kwashe kayan ba sai na barshi agabanta, namaida hankalina gun TV,

   Da na kula wasan bai mata dadi ba sai nafara bata labarin wasan a hankali, ina dan mata bayani,

   Amma kaina yana saman kujerar da nake zaune,

   Hausana dariya yake bata don ji takeyi kamar larbci nake yi ba hausa ba,

  Tace min nako taba zuwa Nigeria, kafin in bata ansa sai aka turo kofar falon tare da sallama, shi,

   Naji kunyar yada yazo yasamay ni ba wani kayan kirki ajikina wlh,

   Don inda nasan cewa zai dawo ne da ban fito hakana ba, falon ganin da nayi dagani sai itane yasa ni fitowa a hakan

   Almustapha zai shigo dauke da ledar sai yai sauri yatare shi ya karbi ledan da ke hannun shi yace ya koma wancan bangaren su salim ya jira shi,, 

   Saida yai kamar zai dan da ki aziza da ledar dake hannun shi, cikin tsigar wasa sai ta dan noke cikin kujera,

   Ganin suna dan wasa da junan su yasa nai niyar barin falon,

   Da hannu ya nuna min inzauna, sai na koma na zauna saman kujeran din 

Magani ya bare a hannu shi sai yadan kalli inda aziza take yace mata tazuba min drinks a cup,

   Daman wanda nakawo mata yana nan ban dauke ba,

   Tadan tsiyaya min ta miko mashi tana wani dan murmushin kissa,

   Maganin da nake sha ne na hana ni ciwon mara yasawo min ashe,

     Cikin mamaki na karba dole na wasta abakina yamiko min ruwan juice din yace in hade da shi,

   Sai ya miko min leda mai dauki da pada har kusan sunki uku,

   Duk kunya ya kamani narasa inda zan sa kaina don nauyi,

    Duk abinda ke faruwa aziza na kallonmu cikin mamaki don dai bataji nace mai ga abinda ke damu na, ba cewa kawai nayi banda lafiya shine ya juya yaje yasayo min wanan kayan

  Saida yaga nadan sha maganin san nan yatashi yakoma inda aziza take zaune yadan zauna gab da ita yana mata magana kasakasa murmushi kawai naga tayi mai ,

   Yamike tsaye yana fadin sai sun dawo kenan acikin hausar shi da ba ta kware ba,irin hausan kanuri, 

    Idona a,TV yake amma zuciyana na wurin balaguro 

   Sai mamaki nakeyi ashe sheriff ya iya soye wa,

   Ita wanan da alamar tafi nafisa farin jini gurin sheriff don nafisa ko kwatan kwacin haka bata samu ba,

   Muna hada ido da ita sai muka sakarwa juna da murmushi,

   Tace min amma dai yayanki na son ki da yawa gashi har yasan time din period dinki,

  Ban bata ansa ba saidai dariyan da nayi kawai,

   Anan inda nake  mai nauyi yadauke ni saboda haka maganim ke min,

   Sheriff yadawo ya samay ni kwance a kan kujera nadunkule wuri guda ina barci na hankali kwance ita ko aziza tana charting da Hindu tana nuna mata irin kayan da tayi oda akasar Turkey,

    Kallon tausayi yai min ji yayi kamar ya dauke ni yakaini saman gado daki na, don yasan cewa idan na tashi jikina zai min ciwo a haka,,,,

    Maman Umar yakira yace tazo ta tadani zuwa daki in kwanta,

   Wayana yadan yi tsuwa kafin in farka daga barcin  a,hankali yadauki wayan yayi hanyar waje da ita hankalin aziza bai kai gareshi ba tana can tana hira da hindu,

  Kallo sunan mai kiran wayan yayi sai yaga narubu, Al noor, baro,baro

   Ya maimaita sunan a hankali alnoor,,,,,,,,

    Ya danna pick kafin wayan takara katsewa yasa, a kunen shi ba tare da yace hlo ba,

   Muryan Ali baba yaji yana cewa sweet sahiba, mun gama meeting din ga shinan zan taso yanzu jirgin mu zai tashi,

  Jiyayi kamar ya wurgata da wayan kasa ta raratse a kasa don ta kaici, 

   Watau ashe koda ya hanani kula da Ali baba, saida na kulashi,

  Kai amma Ali baba yakai katon shege ji yayi kamar afili yake ya shake shi don takaici,

   Nan da nan barebarin suka hau,

   Jin shirun da Alin yayi yasa yake cewa hlo hlo,

   Muryan sheriff da tai kama da  ta zaki yace kai dan iska na fada ma cewa kafita hanyar wanan yarinyar tun farko to tana da aure a kanta 

  Inba hakaba zan iya halaka ka wlh ,,,,yana mai kashedi cikin kakausar murya,

   Alin baba ya kalli wayar tamkar sheriff yake kallo a filin yace lalai ashe za,a ji mu da kai ke na Ahmad lawan zanna ai ban taba son abu inyi saurin jayewa ba da sauri,,,,

    Abincin da bai ciba ke nan ranan saboda bacin rai,

   Yasa noban na Alin a block,,

    Kamar kada yaba ni wayana yakeji saidai kuma yace bari kawai ya mayar min dashi, tunda yayi blocking line din,,

   Ai zai kama ni nan gaba indai ban daina ba ,

   Abinda bai sani ba duk layin na Alin gudu uku ina dasu, a wayana,,

    Amal tadawo cikin fushi don na bar school batare da najirata ba kuma Yusuf yace bashi ya dauko ni zuwa gida ba yau,,,,,

    Maman Umar ne ke fada mata cewa banda lafiya ne shiyasa nadawo da wuri yau,

    Sheriff na can saman kujerar dinning yana magana da Mr William, a video call,

     Wurinshi tawuce direct kamar bata ga aziza ba,,,

    Yayanmu sannu da aiki a hankali yadago yace, mata baiji ta gaida aziza ba,,

   Cikin dan turo baki tace nafa gaisheta bata dai karba min bane,

     Murmushi kawai aziza tayi mai nuna da magana gaba,

    Saida suka ci abinci su ka huta tukun duk lokacin sheriff' yana gidan mu yana ta aikin wasu takardun masu yawa,

   A hankali yake tambayar Amal da salim dake gefen shi,cikin yaren kanuri,

   Batare da yadago kan shi ba yace mata tun yaushe nafara waya da Alin baba,

   Gaban Amal yafadi dajin wanan tambayan don batai zaton jin haka gare shi ba

  Cikin dan rashin gaskiya take gaya mai cewa gsakiya bata sani,

   Abinda yakeyi ya wane ya dan kura ma Amal din ido, nawa nidan lokaci can yace mata, wayan da yabugo mata yau har yana cewa agaida ke ba gaskiya bane ko,

    A,hankali tacd gaskiya koni tai min fada nadai ki saurarenta ne kawai,

  Amma ayi hakkuri bazan kara ba,

    Kafin yai wani magana su Umar ne da Aisha suka dawo daga school cikin uniform din su, 

   Jallabiya ce fara sol na maza sai na mata bakar jallabiya don duk kusan haka uniform din yaran kasar yake,

   Direct gurin sheriff suka nufa sukayi mubayi,a dashi cikin murna da dokin ganin shi,

  Sheriff yana son yaran sosa, haka kawai yaji yana son su,

   Duk yagan su sai yaji kamar ace shine mahaifin, shi,

    Wasa yadan yi dasu kafin su shige ciki cikin nuna kulawa,

   Tunda muka zo yasa Yusuf yasa wata makarantar dake acikin unguwar mu,

   Hakan da yakeyi da yaran yasa ni da uwar su muke kara mutunta Sheriff din namu,

  Don yana da kokarin kula da duk wani wanda ke kar kashin shi,

   Salimata ne tazo da mijinta don ya ganmu yayi muna godiyar dawai niyar da mukeyi da ita don duk wani kula juna da mukeyi tafada mai,

   Kuma ya yaba da hankalin mu so sai tun bai ganmu

    Nan suka zauna falo da sheriff suka danyi hiran gida Nigeria 

   Sai marance lis na farka daga barcin ganin da naima salimat ne yasa ni dan mamaki har kasa irin gaisuwar mu na yan Nigeria nai mai saida kamar yadda kowa ke fadi wai ban iya hausaba,

    Muna ta hira sai naga kamar Aziza a matse take da zama agurin tana ta ya mutse fuska kamar mai jin warin mutane 

   Nace mata koza ta dan shiga daga ciki ta huta ne 

   A,a tace min kawai don duk ta matsu su wuce ashe tundazu take mai test a waya akan su tashi su tafi tana son taje tayi wanka,

   Sai yafita batunta kamar baiji ta ba,

   Sunyi musayar noba da mijin salimat sheriff yai mai alkawarin in ya shigo Nigeria zai ne may shi insha Allah,,,,

     Da haka sukayi sallama damu suka nufi  masaukin su, don duk aziza tagwada mai tagaji sosai 

   Ashe duk hiran da akeyi sheriff yana nan yana ta harara na ne kawai ya ma rasa ta inda zai bullo min akan zancen,

    Sai bayan wucewan su ne ce Umar yadauko min wayana in diba, 

  Kusan 4miss call nagani da layin etisalt din Ali baba 

   Nai mamaki da bai kirani da layin da ya saba kirana dashi ba,

  Kiranshi nayi sai yace min in bari yakirani 

  Yace tundazu yake kirana don sundan sauka wata kaaane adan huta amma insha Allah yakusa tasowa,

   Har zan kashe waya sai naji muryan shi yana ce min fadima Ahmad yana gidan ku har yanzu ko ya wuce ,

  Damamakin yadda yasan cewa Ahmad na garin yasa nace yafita sun tafi inda su ka sauka,

    Cikin sanyin murya yace min ya akayi yadauki wayan ki,

  Da mamaki nace yadauki wayana fa,aini ga wayana a hannu na,,

    Dan murmushi yayi har inaji tawayan yace min suyi waya dashi dazu tawayana 

  Indai bari inyazo zaimin bayanin komai,

 Mukayi sallama yakashe wayan,.

   Aiba shiri na ce ma Amal taji wai sherrif ya dauki wayana yau har sunyi magana ,,

  Cikinbko in kula tace min may yasa na aje wan inda zaigani

     Nafada mata yadda mukayi tun dawo wana gida har yadda,

  Nayi barci nabar wayan, nawa a falo, inda yagani yadauka

    

   Amasaukin su duk abin duniya ya ishe shi taya har Alin baba ya samu karbuwa a wurina 

    Saboda iya sanin da yai min ni mace ce msi kamun kai da sanin mutuncina na "ya mace

  Saikuma gashi Alin na so ya cutar da ni ,

  Baikai karshen tunanen shi ba wayan shi taikara, Abba ne yakira shi,

  A sanyaye cike da  girmama wa ya gaishe da Abban daga can dayan sashen Abban yace mai ya aiki ta jama,a

   Ya ce to babana ina nan dai ina ma tuni akan matar ka kayi hakkuri kazo kadauki abin ka 

   Tunda tagyara halinta yanzu duk wanan mugun rayuwan ta daina su,

   Shiru Ahmad din yayi yana  sauraren shi,,,  shi

  Cikin hikima da iya kwanrar murya yaje fada ma Abban shi cewa yayi aure a dubai,

  Abban yai dan shiru nawani dan lokaci,

  Can yace ma sherrif din babana kai aure batare da sanin mu ba,

   Yace Abba kayi hakuri auren ne yazo min abazata wlh,

  Shiru Abban yayi tare da cewa to Allah yasanya alheri ya ansa ahankali da cewa Ameen,

     Can Abba yace to ya makomar ita nafisat din yake yanzu,

  Dan shiru yayi tukun sai yace yana nan Abba,

   Zanzo insa agyara mata gida a Abuja ta zauna can, don yanzu kusan aikina zai dan koma can Nigeria ne,

  Sukayi sallama da Abban da shi,

 Abban yai dan shiru yana kallon wayan yana mai tausaya ma dan nashi saboda irin sanyin zuciyar shi,,,,   


🐎ZEEE MAKAWA🐎

✈✈✈TAKARI✈✈✈

          👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                  6⃣1⃣

                    BY 

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

     AMINCI WRITERS ASSOCIATION

🎁NASIBI WRITERS ASSOCIATION🎁

🎁N🎁W🎁A


  Almost true life story

 

Aiki sosai so sheriff sukayi a garin don company su da Abu Abdallah ya yi girma sosai kusan duk manyan biranen kasan na saudiya sun kafa ma,aikatar su,

   Sai bayan kwana biyu Alin yazu gurina lokacin sheriff ya wuce washegari ke nan,

   Nai mai komai nataron bako nida Amal yai muna tsara masu kyau kayan sawa ne irin na matan kasar Paris,

   Sai wasu set din sarka da dan kune masu tsada gaske,

   A falon mu na sauke shi, inda ya samu tarbo na mutunci daga gurin maman Umar,

    Duk kunya ya lunlube ni don tunda nake bantaba tsaya da saurayi ba da sunan soyayya,

   Yausai gashi wai nice akazo wa hira ,

   Cikin dakiya da daurewan zuciya nake duk na wani daburce,,,

   Daguda guda kowa ya watse falon aka barni da gani sai, Alin kawai,

   Shiru yadan biyu baya kadan. Kaina yana akan wayana ina dan daddanawa,

   Jin shirun da nayi yasa nadan dago kai inga komai yakeyi,,,

   Ido muka hada dashi, ashe zaune yake yakura min ido kawai yana kare min kallo,

   Acikin zuciyar shi yana yaba min komai nawa yayi mai yadda yake burin ya mallaki mace,

   Dadin dadawa gashi ni yar karama ce sosai , don yanzu haka ban fi sha bakwai ba , yake gani,

    Kunya ne ya kamani ganin irin kallon da yake min

   Tambayana yayi yace min ya yaga na yi shiru, irin taron da zan mai kenan 

   Duk zumudin zuwa yaganenin da yake yi,

   Da sauri nadan dago kaina nadan kalleshi sai kuma na kawar zuciya na fal da mamakin shi amma sai na dake na ce mai

   Cikin murya mai jan ra,ayi da daukan hankali wanda ni kai naban san ina yi ba,

    Nace wani kuma irin taro kake bukata wanda yafi wanan din da nai maka,

    Matsawa yayi zuwa dayan kujeran da ke fuskanta na yace,

   Yace min look fadima ina son kisan cewa aure nake son yi da ke 

   Very soon ba dadewa ba so ina son ki fadamin gaskiyan zuciyan ki 

   Don kisan yanzu ni bazance na tsaya wani wasan soyayya ba,

  Indan kin amince min zan ga Ahmad yakaink gurin iyayyennki don in gabatar da kaina garesu

   Yakarashe zancen yana mai komawa saman kushin din, yadan jingina bayan shi da makarin kujerar

    Yakura min ido alamar yana jiran asa ta,

  Jin shirun da nayi yasa shi kara ce min,

   Ke nake sauraro don banson zuwa wurin Ahmada batare da naji wani kwakwaran magana daga gare ki ba

    Ke nake sauraro fa na tsinkayi muryan shi cikin kun,nuwa na, 

   Bansan lokacin da nadan dan,dago kaina ba muka hada ido sai na sakar mai dan guntun murmushi,

   Ok kina nufin kice min kin amince min ke nan ko

    A hankali nadan daga mashi kai alamar eh,

   Cike da mamakin wanan saurin amince mashu danayi yake yi

    Don bai dauka abin zai zo mai da suki irin haka ba

   Ajiyan zuciya yayi yadan tsinki Anebi da maman Umar ta aje mai acikin plate din dake gabashi tab da kayan fruits,.   

     Yana taunan Anebin din yake ce min ya akayi ranan na aje wayana har Ahmad ya dauka 

  Murmushi kawai nayi batare da na bashi ansa ba na ce,

    A hankali nace mai lokacin banda lafiya ne, acikin mamaki yake ce min har ciwo nayi shine ban fada mai ba,

    Haka mukai ta dan hira jefi jefi dashi cikin rashin walwala,

   Sai marance lis yai muna sallama zai tafi kuma yace muna ba kwana zaiyi,

   Har bakin motar da yazo da ita na rakashi, 

  Cikin kulawa da kuma kewar juna muke sallama hannu na yana irike da Aisha,

   Wace keta dan kokarin in saketa taje tadan yi wasa,

   Muryan Alin ce ke ce min Can I trust You fadima,,,sai na kada mai kai ahankali. 

   Yace duk ritsi da zamu shiga da Ahmada kada kice mai kin jaye zancan auren mu nida ke a nan gaba ,

   Pls sai ya hada hannu shi guri guda duk ka biyu yai min alamar rokon Abu,, 

   Yashiga motar shi yana daga min hannu ciki shaukin so da kauna mukayi sallama da junan mu,,,,

   Saida motar shi ta ba ce min da gani san nan nadanyi ajiyar zuciya na koma cikin gida,

  

      Ina shiga gida na iske Amal tsaye da wayana a hannunta 

   Fuskanta kawai na kalla nasan cewa akwai magana ,

   Inda take tsaye na nufa cikin damuwa nake tambayar ta ko lafiya naganta haka,

  Batai min magana ba saida ta zauna saman kujera ta miko min wayana a hanmukeq,

   Nakarba ina ma wayan kallon mamaki, sai kace zan fahinci wani abu acikin wayan,

   Wuri na samu nima na zauna gefen ta kadan don nasan cewa da magana a irin yanayin da naga Amal ciki ,

    Fuska a daure batare da ta kallo ni ba tace yayan mu ne ya bugo waya kisan idan ya bugo sai ya tambayi kowa abashi su gaisa nace mata eh hakanane 

   Yatambaye ni ina kike nace mai kina barci sai yace min ba gaskiya bane,

   Don bai taba ganin kinyi barci by this hours ba,,,

   Sai ce min yayi kina waje tare da Alin ko , shirunayi kafin in bashi ansa har ya katse wayar ko,,,

   Wani dan dum naji sai kuma akarshe nace to ma maye na boyo aciki tunda ai dole yasani

    Sai kuma na tuna irin warning din da yai muna kafin muzo karatu,

   Nace to in har yafitar dani ai Alin zai iya karasa biya min kudin karatun har in karasa abina

   Amal ido ta kura min tana kallo na ina cikin nazarin abinyi,

  Sai tace min gaskiya fadima yadda kika bari har son Alin ya shige ki baki kyauta ba,

  Tunda kinsan cewa yayan mu yai muna nasihan akan kada mu yarda mu kula kowa har sai mun gama karatun mu,,

  Tunda ta fara magana bakinta na tsura ma ido har ta kare zancen nata,

   Gani irin kallon da nake mata yasa tagane cewa nayi nisa ko cikin wanan tarkon da na fada,

   Tace nidai shawarar da zan baki shine a matsayina na yar uwanki kuma mafi kusa dake shine 

   Kibi a,hankali tunda har kikaga yayan mu ya nuna bai ra,ayin hakan, to ki daina 

    Saboda shi namiji ne kuna shi ke tare dasu shiyasan halin su,

   Don dai kinga bazai cutar da mu ba,

   Tagumi nayi da hannaye na ina kallonta,

   Itakuma sai taci gaba da fadin namiji abin tsoro ne, 

  Kibi a hankali don yanzu muke idan lokaci yayi sai muyi abin mu, 

  Magana kawai takeyi nikuma jinta kawai nakeyi don nayi nisa ko,

   Ta lura da ni sai ba wai na yarda da shawaranta bane,

   Don haka tashi kawai tayi tai shigewar ta tabar min falon,

   Hakan da tai min sai naji banji dadi ba,

   Hutu mukeyi dama ba wani karatu mai dan yawa agaban nima shigewa nayi abina,

   Tunjiya nake cikin rashin walwala saboda maganganun da mukayi da Amal,,,,

 Maganar tasani cikin damuwa don dai gaskiya ina son Alin 

   Amma kuma maganar sheriff tayi min tasiri azuciya na

   Saboda irin taimakon da yadinga min ba cutar wa a rayuwa saidai shukuran tsakani na dasu,

    Shin idan har naki bin maganar wanda yake kamar uba gare ni ai nayi butulci mai karfi ,

    Tsuwar da wayana keyi  yasani dan farfadowa daga cikin tunanen da nakeyi  

    Sai gabana ya dan fadi don nasan cewa sherrif ne ke kirana tunda tunjiya bamu gaisa ba 

    Wanda akullun dole yagaisa da kowan mu,

   Saboda yaji lafiyan mu Sunan Salimat ce nagani ta ke kirana, 

    Saida nadanyi sanyayan ajiyar zuciya danaga itace,

   Ina dauka tacs min mufito mutafi masallaci don mu samu jam,in jumma yau,

   Cikin sauri natashi na shirya don sam na manta cewa zamu iya makara idan mun wuce shadayan rana bamu fita ba,

    Bandau wani lokaci ba ina shiri nafito abina tsab dakin Amal na nufa itama acikin shirin ta nasamay ta duk da tun jiya  sama sama muke da ita,

  Saboda maganganun da mukayi da ita din,

    Ganin datai min yasa tamike don tasan inda zamu,

   Da kafa muke rafiya zuwa sallah jumma,a kudi nadauka da zamu fita,

   Duk da saurin da mukayi mun iske har ta wajen haraban duk jama,ane zazaune suna jiran lokaci,

  Har  Ciki muka kusa muka samu wurin zama,

   Saida naga mundan zauna nafito waje saboda na tabbatar da mun samu gurin zama ko,

   Wurin saida alkama natafi na saye mai yawa, da hannu na naita watsa ma tanatabaru cikin masallaci wanan alkaman sadaka, akan ina bidan sauki ga al,amarina,,,

    Saida nagama watsa masu san nan na nufi hanyar toilet naje nadauro wani sabon alwala nadawo inda mukasamu guri na zauna,

  Har Umar da Aisha muke tafiya masallacin don haka da dan kulan abincin su muke zuwa don sai dare muke barin masallacin,

    Har aka idar da sallah akayi na la,asar muna nan zaune,

    Kafin ai sallah magrib muka tafi ziyaran rauda, muna dawowa muka fito wajen harabar masallacin don idan an idar da sallah mu samu hanyar fita dmukeyi 

   Muna nan zaune aka fara bude lemar haraban masallacin suka fara ma haraban feshin ruwan almuski da sanyi na,un,,,

   Muna na har aka tashi saida mukaga Salimat ta shiga gidan ta sannan muka kama hanyar namu gidan,

   Gab da zamu shiga kwanar layin gidajen mu ne kiran wayan sheriff yashigo min ,

   Namika ma Amal wayar ta karba tare da yin sallama nan ya sheda mata cewa zai dawo saudiya gobe insha Allah muma yanason mu hadu a garin makka agoben tunda hutu mukeyi

  Duk da ina son zuwa makka yau sai naji,

   Sam sai banji dadin hakan ba araina saboda ina gudun haduwar mu da Sheriff din mu,

     

    Tunda safe mukabar garin madina zuwa makka, 

   Kallon dajin kawai nakeyi wanda har kullun ina naga nisan tafiyan da mukeyi a mota, sai in kara jinjina ma Annabin rahama tare da masoyin shi Abubakar,

    Da su arakumi sukayi hijara daga makka zuwa madina,

   Amal ke ce min idan mun isa muje muyi  umurah, kafin mu isa gida 

   Tunda sheriff yace daga Malishiya zai zo goben,

   Kinga kafin ya iso mun sauke nauyin ko,

   Kai kawai na daga mata don nasan cewa wanan tafiyan kusan don nice za,ayi shi,,,

   Muna shiga gari muka wuce mukayi umurah duk kan mu,

   

    Yau shekara daya dawata tara ke nan rabonmu da garin makka,

   Kallon ko ina na garin nakeyi  cikin jin dadi da tuna wasu abubuwan da suka faru da ni lokacin ina yar karama da nazo garin,,,,

   Lunshe idona nayi ina tuna Rugaiyya ta yar uwata masoyiyata mai kaunana tsakani da Allah

   Hawaye naji masu zafi sundan sulalo min a fuska na daga cikin idona,

   A hankali na goge su sai kawai naji raina yawani yi min bakikirin wlh, 

   Nanda nan kewar Rugaiyya yadawo min sabo fill a zuciya,

   Ko saudaya banta tunanen cewa wai Kudina yana gurin Rugaiyya ba,

   Iyakadai ina mata fatan Allah yasa tasamu ta tsira da kudin ba,a karbe mata ba,,,

    Gidan na Sheriff yana nan tsab kamar yadda muka wuce muka barshi 

    Saidai tun shigar mu naga wasu yan bakin fuska agidan ba wa yanda nasa ba ne ada,

   Ina murna yau zanga yumma da su Sukaina da Mari,

   Hjy ma fushi zandanyi da ita tunda sau guda taje tadiba ni ,

   Amma duk dadewan nan ko waya babu 

   Troller's din mu aka kai muna cikin gida  har da su maman Umar da mukazo wace muke jin dadin zama da ita sosai ,

   Matace mai sanin yakamata kuma batayarda ta saba ma ko gudan mu,

   Idan kuma taga zamuyi abinda ba daidai ba batayarda muyi shi,

   

     Dakina na fada tunda mukazo nashige abina nafada bayi nai wanka nadauro alwala,

   Bayan na sallamay sallah na nadan zaina gurin ina dan tunane,

   Daga nan natashi don inje ingaida hajiyan mu da su yumma, tunda nazo basu zo suntare ni ba,

   A hankali na ke tafiya cikin wani dogon riga mai kama da silk ina tafiya yana shaking,

   Ina zuwa sashen dakunar su sai nai turus, wuri guda ganin dakunan nasu duk arurufe suke, ba alamar akwai mutane aciki,

   Da saurina karasa har kofan dakunan nasu sai ga ,alamar andade ba,a cikin daku nan don duk wurin yayi dan datti da yanan gizo 

   Hakan bai isheni shedaba saida nadan tura kofan inji ko abude suke,

   Gabana yaba da dam dam dam,

  Cikin wani irin sauri nake tafiya kamar zan tashi sama, don sauri,

   Tunane nakeyi azuciya ina hajiyan mu da su yumma, ina yan uwana, ina gatana ,

   A falo mukayi kicibis da sheriff shida Salim ganin da yai min cikin tashin hankali kuma yasan daga inda nafito,

   Cikin daga muryan da bantaba yi ba agabanshi yau nai magana da larabci mutanen akbass nake magana cikin sauri sauri nace ina hajiyana da yan uwana suke,

    Ido ya kura min kamar wanda ba zaiyi min magana ba, 

   Sa can yai magana cikin murya mai taushi fa natsuwa yake ce min 

   Shine gaisuwar da zan mai kokuwa shine karatun da nakoyo,

  Sai alokacin nadan sami nadan yi kokarin natsa kaina guri guda,

   Nagane cewa ban ma gaisai dashi ba, sam na ma kasa ganin cewa yanzu ya iso gidan daga tafiyan da yace yayi,,

    Dakin shi ya haura sama batare da yakara yin wani magana ba,

    Wurin Amal natafi tana zaune tana gyara kayanta, cikin jakar hannunta,

   Ina shiga na fada jikin ta ina wani irin kuka mai gumza,

   Duk hankalin Amal din sai yatashi, saboda ganin irin kukan da nakeyi 

  Da kyat tasamu tadan lalashe ni nadan tsagaita kukan nawa,

   A natse take tambayana komay ke faruwa  nakwashe abinda nagani gurin dakunan nasu nafada mata,

   Karazancen da cewa kodai yan bagaladi sunzo sun kama su ne ba,afadamin ba,

   Sai kuma nakara shige mata cikin jikinta ina wani irin kuka mai tsuma rai da zuciyan bawa,

  Har maman su Umar saida ta iso dakin don jin ko mai ke faru ne haka,

   Amal tadan dago min kai tace indan saurareta inji dan Allah,

   Jin danayi tace dan Allah yasa nadan tsagaitata kukan nawa,

    Ina saurarenta, tace min fadima kinsan dai duk inda suke yayan mu yasani ko , kai nadan kada alamar eh,

    Tace kuma dai kinsan bazai bari ai masu wulakanci ba ko,

  Kallonta nakeyi ina naxarin zancenta a hankali,

   Ganin da tayi nadan tsagaita kukan yasa ta fara share min hawayena  da hannun ta a hankali,

   Bata barni ba saida taga nasamu dan natsuwa, tukun sanan tayarda naje daki na 

   Ranan ko abinci banci ba hakana nasamu guri nadan kwanta don indan samu natsuwa,

    Tunda na kwanta ban tashi ba sai cikin dare, nafarka, natashi, nadauro alwala, nazo nayi nafila raka,a hudu kamar kulun 

   Saida gari ya waye san nan na tashi a hankali naje na gyara jikina tsab nafito cikin shigar wasu jajayen, da dan ratsinyau

ki,baki kayan yan na mutanen  Japanese ne mata, rigan yanada dan budewa a kasan shi sai dan guntun hannu daidai, gwiwar hannu,

   Bakin gyale nasamu nadan daure kaina dashi,

 A hankali na ke tafiya kamar banson taka kasa, fito wa nayi zuwa falon gidan 

    Don indan samu abinda zan danci saboda tun jiya ban ci komai ba, yunwa nake ji yau

   Zaune suke shida Salim a dinning table din suna cin abinci su hankalo kwance,

   Ganin da nayi masu shi yasa nai niyar komawa daki sai kuma wata zuciya tace min ban gaida sheriff ba,


     Takawa nayi har inda yake nadan karasa cikin ladabi na gaishe shi nai mai yaya hanya,

  Salim yai min tayin abinci, yace min ya dauka ko nima barcin nakeyi don baiji motsina ba,

    Batare da nace mai komai ba nawuce kawai zuwa cikin kitchen inda na saba diban abincin mu,

   Saboda gaskiya ban iya zama inci abinci agaban sheriff din mu, yana kallo nha

   Har nakai kofar shiga side din da zai sada ni da kitchen din sai naji  muryam sheriff, cikin  harshen larabci yana ce min inzo, a hankali nadawo har inda suke kujera dake gefen Salim ya gwada min in zauna sama,

  Sai naji wani dummm narasa yadda zanyi sai naga ya mike yabar gurin yana waya, 

   Nawaiga a hankali sai naga yabar falon gaba daya, hakan yasa naji dadin zama nazauna naci abinci na hankali kwance,

   Saidai zuciya cikie take fam da tunanen inda yan uwana sukaje,

   Batare da sani wani 

  Ina tashi wurin maman Umar na nufa don inji komay mafitar zancen,,,

    Itama dai hakkuri tabani tace min in bari zata bincika min a hankali, 

   Amma dai duk ida suke shariff yasani ai 

   Kusan kwdayataso baice min komai ba nikuma cikin damuwa nake sosai

   Ranan da muka cika kwana biyu ne ina zaune a daki na ina nazarin a kan wani sabon computer da yafito sai naji anturo kofar dakin na a hankali,

   Nadauko ko Aisha ce sai dai kamshin turaren da ya ruda min hanci yafada min kowaye

   Cikin shigar kananin kaya yake yau kayan sunyi mugun karban jikin shi,,

    In ganin shi sai nayi niyar saukowa daga saman gadon , 

   Hannu yadaga min a hankali yai min nuni da inzauna inda nake,

   Gefen mirrow dakin yaje yadan tsaya yajingina jikin shi da mirrow

   Hannu shi cikin aljihun  Kafan shi na harde cikin guda,

   Ido yadan zuba min kusan na minti biyu sai yakira suna na ahankali, nakarba,

   Ina mai dan dago kaina shima ahankali nadan kalle gefen da yake sai na sauke idon nawa

   Yace min wani irin tambaya kikai min shekaran jiya, 

   Shiru nayi ba ansa yakara ce min haka yakamata kiyi tambaya,

   Ko kinga cewa hjy zata bace a gida nane,

   Karshe yace hjy da sauran yaranta sun koma gida Nigeria, dammm dammm gaba na ya harba 

   Wanan karon kallon shi nakeyi cikin ido sosai saidai na kasa dole na sauke kwayar idona da yacika fam da hawaye,

   Na maimata maganar nace sun koma Nigeria,

  Yaushe, kuma ta yaya san nan nifa , 

  Ni may yasa suka wuce suka barni, sai kawai nasa kuka mai bala,in tsuma zuciya, 

   Ganin da yayi nafara kukan yasa shi fita dakin cikin sauri, duk da yaso  son   yai min bayani komai amma ina bai iya tsaya yanajin kukan mace a gaban shi hakana,, 

   Nai kukana har saida nagaji banda wani bayani dole na hakkura na maida lamari na ga Allah,

    Sati biyu zamu yi a makka don haka muna garin sheriff ya wuce zuwa  Nigeria wurin wani aiki dayataso mai akan sabon kamfanin su,

     Don haka mu kadai yabari a gidan,,

   Ganin da nayi bai gari yasa na shirya zuwa masfala wurin hajiya laila, don inji bayanin abinda ke faruwa tunda na fuskanci sheriff baida niyar fada min komai,,,

   Ina zuwa sai nai rashin sa,a ance hjy laila ta koma birnin Riyadh da zama 

   Haka nadawo gida hankalina tashe, banda wani sukuni ko  kuzari tare da ni ko kadan

   Maman su umar ne nasamu take dan kwantar min da hankali yanzu, 

   Saiko Amal wace take iya kokarinta wurin kula da al,amarina ,

   

        Saidaga baya na fahinci cewa aziza ba ,a garin  take da zama ba ashe wai a Dubai take zama don a can take sana,a har tagamu da sherrif din mu awajen wani taron yan kasuwan kasashen afirika da akayi,

    Tun lokacin ta lake mai so sai, da taga gurinta ya cika, 

    Tana son sheriff don yayi mata kuma tana ra,ayin kudin shi ,,,

    Wanan zuwan da yayi Nigeria har da batun dawowa da nafisat gidan shi yakai shi,

    Nafisat zata zauna a Abujane tunda yanzu zaidinga zuwa aiki can sosai,

    Ita kuma aziza zata dinga zuwa nan saudiya ko kuma shi yaje can inda take,

   Ya iske kaunar shi yayan su Amal ta hai ko suna ba,ayi ba 

   Yai mata sha,uku na arziki ita da mijinta har su shehi da sauran yan uwa sunji dadin wanan zuwan nashi so sai,

    Kamar yadda maman su Umar tai min alkawarin bincken labarin su hjy mu haka din ne ko 

   Saida ta binciko mai tazo min da labarin yadda maganar yake cewa hjy da su yumma sunkoma gida ne da taimakon Sheriff saboda gwaunatin saudiya tasa anata binciko mata duk inda takari suke zaune akasan 

    Hakan da yagani ne yasa yai masu bizan komawa gida suka koma tare da su yumma,

   Saidai akwai sauran bayanin da batai min ba tadan boye min su,

   Jin hakan da nayi yasa nadan ji sanyi azuciya na sosai ,,,,,    


🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                  6⃣2⃣

                     BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


   Almost true life story,,,,,


    Har muka kare hutun mu a makka Sheriff bai dawo ba daga tafiyan da yayi, don yace daga Nigeria zai biya kasar Italy 

    Mundawo madina lfy, munci gabada gudanar da karatun mu lafiya,

   Bamu da wani matsalar rayuwa yanzu don koda yaushe sheriff yana turo muna da kudi

   Duk da babu abinda muka rasa na rayuwa amma sai ya aiko muna da kudin nan,

   Salimat tasamu ciki mai wahal da ita sosai, don kusan duk abinda taci sai ta amayar da shi,

   Don haka yanzu kusan karatun mutum biyu nake yi , inyi nata inyi nawa,

   Saboda gaskiya ba yabon kai ba wlh ina da gwargwadon kokarina sosai,

  Shiyasa koda nake hada aiki na da na Salimat ba wai wani mugun wuya nake sha sosai ba,

   Dagani har Amal muna iya kokarin mu wurin kula da ita saboda inkaga yadda ta koma sai ta baka tausayi sosai,

   Ganin irin wahalar da take sha ne kuma gata gidan ita kadai ne aciki yasa mijin ta yabugo min waya cewa don Allah yana son mu taimaka mai salimat tadan dawo wurin mu ta zauna har taji dan sauki,

  

    Saboda nasan cewa nima laba ni akayi sai ban boye mai gaskiya ba nace zan bugawa  sheriff yawa in fada mai idan ya amince zan fada mai saita dawo gidan  namu,,,

   Sai da nafara yiwa Amal bayanin komai inda ita ma tace gaskiya Salimat tana bukatar taimako don ita kadaice a gidan batare da kowa take zama ba,

    Tace min inwa sheriff magana ko zai yarda, 

   Saida dare bayan na gama komai kuma na tabbatar cewa shima yanzu duk inda yake ya dan natsu ,

   Watakila yana sama computer shima, 

   Sainai dialing din noban shi,

   Zaune yake shida aziza a falon su na garin Riyadh, tayi dan filo da cinyan shi ,

   Shiko yana aikin latsan  system din shi, wayar shi tadan yi kara kadan 

    Bai dauka ba saida kiran ya kusa tsinkewa dakanshi,

   Sanan yadiba yaga kowaye,

   Sunan fadima dayagani shi yabashi mamaki ,

   Saida yakara maimaita sunan san nan ya ansa sallama da nai mai cike da mamaki yake don dai gaskiya bantaba kiran shi a waya ba saidai shi din yakiramu yaji lafyan mu,

   Saida na gama gashe shi sai kuma nadan shiru, jin shirun da nayi ne yasa shi yadan daga wayar nashi yadiba kona kashe ne sai yaga ina online,

   Hlo yace na ansa mai da naam yace min lafiya dai ko,

  Cikin inda inda nafara mai bayanin salimat da kuma abinda yasa nakirashi, 

    Saida yagama jin bayani na san nan yace min fadima na ansa da naam 

   Yace kina ganin dauko da zakuyi ku aje agida bai zama maku matsala nan gaba kadan 

   A hankali na ansa mai da cewa a,a dan murmushi kawai naji yayi,

   Yace min idan har kunga cewa hakan bazai shafi lafiyan karatun kuba ai is ok, 

  Nakasa boye farin cikina saida ya gane daga inda yake don na manta cewa ban kashe waya ba yaji sanda nake ihun murna ina fada wa Amal cewa ya yarda 

   Murmushi yadan yi wanda har saida aziza ta dan dago kanta takaleshi,

  Bayan ta maida kanta kan ciyan yashine take tambayan shi ko may yafaru, 

   A,takaice yabata ansa yace mata shida su fadima ne ke waya kawai daga nan bai kara ce mata komai ba,

  Yacigaba da aikin shi na tura sakon ni dayakeyi, amma zuciyan shi fam da tunanen son baby a ranshi, gashi da mata amma ba wace keda alamar haihuwa acikin su,

   Ganin da yaiwa babyn sister shi daya je Nigeria ne tun lokacin yaji yafara son haihuwa don duk wanda  ya ganshi sai ace aida shi baby ke kama wai kamar su guda lokacin yana karami 

   Don haka sai yaji yana son yaron aranshi sosai,

  Kafin yadawo duk wani abin jin dadi na jarirai saida yasawa yaron,

  Sai kuma yanzu maganar cikin Salinat da nai mai yasa shi cikin wani tunane mai dan zurfi,

   

   Aziza yace cikin dan kasalalen murya ta ansa da umm sweet sahibi,

   Yace mata when are u ready for our babies,

   Wani dan shock taji wanda saida kyat ta iya saita kanta kafin tadan dariya 

   Tawani shake murya tace tun yanzu sweet sahibi,

   Saiyadan dagota yace da sai yaushe kike shiri ke,

   Tadan kashe mai idlafiya nan da two years coming ko,

   Yace mata u are out of ur sense,

   Niko yau ki shirya kikarbi dan Riyadh basai ma gobe ba,

  Dariya suka sa gaba dayan su, saida suka dan tsakaita dariyan ne yasa ke ce mata gaskiya ina bukatar haihuwa, very soon 

   Aranan wanan maganan aziza ta kwanada shi azuciyar ta washe gari maganar na cinta sai taji sheriff dake kokarin daura tie din shi awuya yana ce mata ihope kin karbi ajiyan baby ko,

    Murmushin dole ta sake don maganar baby nan yana tayar mata da hankali sosai walahi 

  Ya manna mata kiss a goshi yafita yana mai mata sallama,

  Bayanshi tabida kallo bayan wucewar shi,

   Wayan ta ta jawo dake gefen filo aje,takira layin Hindu  ,

    kira guda Hindu ta dauki yawan tana dariya,

  Jin muryan Aziza cikin tashin hankali ne yasa tagane cewa ba lafiya

   Tambayan Azizan tayi komay ke faruwa ne haka,taji ta badadi tunda safe haka,

   Aziza tace bari Hindu Ahmad nason ya dauko min wani sabon bala,ai ne wai shi haihuwa yake so,

   Dariya Hindu tasa mata mai cin zuciya , saida tayi mai isar ta tace

   Aziza yar lashi, yo ke da mai kike nufi, 

   Ko kin manta cewa matashi kika aura, 

   Ai hakan nacikin ilar auren shi da na hango maki,

   Shiyasa naso kiyi hakkuri da yan tsofin Alhazan da muke bi don su ba batun haihuwa gare su saidai life 

   Don sun riga sunyowa bariki shiri kafin su shigo sun aje dukiya sun kuma tara iyali,

 Amma ke kudi da kyawon shi da kurciya suka debe ki,

   Yo aiko shi in baice yana son haihuwa ba yan uwan shi na son suga zuriar shi 

    Nidan Allah kin isheni da zance Hindu kiranki nayi inji may abin yi yanzu,

    To ki saurara da kyau don wanan maganar ba tawaya bace kibari har mu hadu sai musan abin yi,

    Ahaka suka rabu hindu na ta kwantar mata da hankali cewa ta kwantar da hankalinta komai zai zo mata da sauki insha Allah,


        Mu uku muka tafi gidan su salimat da salim da maman umar mun samayta tana jin jikin ta sosai yau, 

   Kayan sawan ta kawai muka dan diba sai wasu tan abin bukatu na mata da na tataro matasu cikin jakka hannunta,

   Salim ya jawo mu zuwa gida da ita, ahankali yake tafiya da ita duk kyawon da hanyoyin keda baisa salim yin gudu ba saboda tausayin irin halin da yaga Salimat 

   A dakina mukayi mata masauki ,tundaga wanan lokacin maman umar ke kokarin kulada salimat

   Don itace tasan yadda harkan ciki yake duk abinda salimat tace zataci shi za muyi mata, 

   

     Hjy mama tare da yayan ta akasar Spain taje ganin likintan ta da ke diba mata kafa ,

   Zaune suke duk kan su saman kujerun da ke falon tana ta faman surfa masu masifa,

   Akan may har suka bari Ahmad yafi tara abin duniya akansu ita bataga amfanin karatunsu a turai ba gashi duk wani dan dukiyan ta turo masu shi, 

   Suraj ne ya katse ta dacewa, haba mama arziki fa na Allah ne duk yadda mukaso yin shi idan Allah bai nufa ba baza muyi shiba sai lokaci yayi,

   Imun shiru tace mai acikin daka tsawa kai ai kafi kowa bani mamaki har nan fa muka shirya dakai zakaje ka dibo muna wani irin sana,a yakeyi haka, har yai wanan mahaukacin kudin dan karamin yaro dashi,

   Duk kun girmay shi fa amma jiku dan Allah bawani wanda zaitada wani, da cikin ku,

    Suraj yace duk iya binciken da zanyu wlh nayi anaje amma banga wani abin tir da yakeyi ba,

     In mabaki sani ba kisani mama  don yanzune kudin shi zasu kara habbaka saboda ya hada hannun jari da Abu Abdallah na Dubai wanda ake gani kamar yafi kowa yawan dukiya a kasar ta Dubai da kewayenta 

   Salis wani irin dogon tdaki yaja yace niki duniya zai tara ba abinda zai damay ni

   Koma dai may ye ai nasan cewa dan uwa na ne shi,

   So ni banga abinda zaisa hankalinki yana tashi haka ba wlh,

   Yasa hannun shi a aljihun shi yadauko karan sigarin shi ya kuna yakashe guntun asha nar,

    Saida yadan busar da hayakin yace mata shi yatafi kuma daga yau kada akara kiranshi akan maganar Ahmad,

   Yabuga kofa yafita abinshi, yawuce zuwa club,

  Rai bace tabishi da kallon mamaki tajuyo wurin sauran saitaga su,ma suna kokarin wucewa ne,

  Aikawai saitasa masu kuka wiwi,

   Suraj ne yje yadan tsunguna gabanta yakama hannayenta biyu wuri guda yace mama kibi sannu 

   Zamu san abin yi nazuwa dan wani lokaci

  Kidaina tayar da hankalin ki haka kinsan kinada hawan jini fa,


    Balaifi yanzu na sake jikina sosai nadaina dar,dar din da nakeyi akan maganar Alin kulun kamar kara girma nakeyi,

   Don yanzu na zama babban mace nayi wani irin hip, irin na mata masu cikakkiyar kira,

   Fatan na yayi man wani dan lub lub tamkar irin na larabawan Pakistan 

   Kyau na da kamala na sun baiyyana sosai, dakaganin ni saikayi sha,awar kakara kallo na,

   Ko tafiyana yasake yanzu ga suturu na alfarma ana sayo mun duk kasar da sheriff yaje aiki zai kwaso muna kayan da matan kasan kesawa na alfarma,

   Amal takan min sheri tace wai fadima may sirin wanan canjin naki ne, sainake ce mata ai itace za,a tambaya 

  Saboda ni gani nakeyi tafini haduwa sosai,,,,itama din tasan cewa nafita haduwa shiyasa bata yarda, idan nace nafita haduwa,

 Salimat tadan ji sauki yanzu mukan fita jefi,jefi zuwa makaranta tare da ita, saidai ba kulun ba

   Yau ma hakane munyi jiran salim ya zo da mota yadauke, mu a school jin shi shiru da mukayi yasa muka dan fara ta,takowa da kafa, 

   Dan dogon tsaki Amal taja tace ban san may yasa Salim yake muna haka ba yanzu,

   Ni gaskiya da ace mata suna jan mota a kasan nan walahi da sai ince yayan mu yasaya muna wata motar 

   Mufita harkan jiran salim ko yau saiya gama bata muna lokaci, tadan kara jan guntu tsuki,

     Dariya maganar ta tabani nace aiko Salim yana iya kokarin shi damu yaudai ne akadan samu akasi,

   Sanan kuma kinsan cewa babu yadda za,ayi yan saudiya su yarda da tukin motar mata akasar su,

   Saboda tunkin motar mace yana cikin gurbatar tarbiyan diya mace,

   Kinga ashe su ko bazasu taba yarda abada wanan dokar akasar su,

   Duk wani abinda zai kawo masu lalacewan matasa da gurbatar addini bazasu taba yarda dashi ba,

    Ba muyi wani dan nisa da makarantar ba sosai sai mukaga an park muna wata mota fara sol da ita har farin ta yana cin ido, 

   Duk inda mota takai da kyau wanan motar takai can,

   Amal ce gefen da motar tadan tsaya sai salimat na tsakiyan mu nice agefen karashe,

   Nacikin motar yadan zuke glass din motar baki balarabe ne daganin shi matashine saidai ba yaro bane kwarai,, salama yafara muna,

  Da larabci yake magana yace muna may yasa muke tafiya cikin rana haka,

   Muzo mu shiga ya sauke mu gida, mufada mai inda zamu

    Sukan duk sai naga alamar tsoro a fuskan su saboda gani sukeyi zai cuta muna na

   Kallo guda nai mai daga yanayin shigar shi har maganan shi sai nagane cewa saboda Allah ne zai taimaka muna,

   Amal na bude ma gaban motan nida salimat muka shiga baya,

   Basuyi min wani mussu ba duk muka shige ina mai kwatance kawai sai ya gane layin mu ,

  Tundaga nan bai kara ko kallon gefen mu ba,

   Muna shiru mukayi cikin natsuwa har muka isa gidan mu,

   Naimai godiya nafito har zan shige sai yake ce min dan Allah mukama mutuncin mu badadi agan mu asaman hanya haka muna tafiya da kafa,

  Godiya nakarayi mai muka shige abin mu cikin gida,

  A falo sukai min ca waidaga ganin mutun sai kawai insa su fada motar shi, ni bani ganin komotar shi abin kallo ne, 

  Daga yau idan zan shigane inshiga ni daya,

   Dariya duk suka bani don sai yanzu nagane nufin su,

   Saida na samu wuri nadan zauna sanan nadan kalli Amal nace mata

   Kinsan abinda yasa ya taimake mu tace a,a nace mata saboda tafiyan da mukeyi dakafa maza na ganin mu wanda hakan baidace ba ,

   Wani wanda baida tsoron Allah zai iya shiga wani hali mara kyau idan yagan mu da kafa,

  Mace abu ce maidaraja da kima ba abin wasa bace,

  Saida na kalle shi tsab nagane cewa ba bu yaudara kishin addini ne kawai yasa yataimaka muna,

   Sai alokacin naji sundayi ajiyar zuciya nace mata ai tana ganin shi tasan cewa badan karamin gida ba ne

  Tsatsan addin ne kawai azuciyar shi,

   Tundaga wanan rana bamu kara yarda mun tako da kafa ba,

  Tafiyan mu da kafa shine zuwa masallaci kawai,

   Salimat cikin ta yanata kara girma saidai tadan rage yawan alolayin ciki yanzu 

    Kwadai kawai take so na abu mai sanyi, koda yaushe,

  Zaune take ta ta faman shan ice cream roba roba ta aje agabanta,

   Dakatar da karatun da nakeyi nayi na tsaya kallon ta,

   Ina mamaki yadda take shan ice cream haka a yini batare da yafita ranta ba,

   Dan cikin nata yadan taso sama Allah ya taimake ta rigunan,ta kusan duk dogaye ne in bashi ba daduk basu daukanta,

   Maman Umar ta kawo mata wani dan ruwan shayi mai suna azahab lai, green tea ne kusan matan larabawa idan suna da ciki shi suke yawan sha, don yana rage ma mace yawan zaki da sanyi 

   Yanasa baby kuzari tun a cikin ciki, sai ciki yakai kaman wata biyar ko shidda ake shan wanan ganyen shayin,

   Kusan duk wani green tea yana ma mace mai ciki wanan taimakon,

    Zama tayi da cup din tea din a hannun ta don ta tabbatar da cewa tasha tea din 

   Saboda ralura cewa bata son shan shayin saidai ice cream kawai komai dare zata fito falo ta zauna tasha sanan ta kwanta,

   Robobin ice cream din na,kwashe gefe guda na ce mata sai tagama shan ruwan shayin sanan inbata abinta, 

   Tadan jingina da bango tace min baki ganewa ne Fadima, 

   Bawai bani son shayin bane walahi wani irin suya nake jin zuciyana yake min shiyasa kikaga ina son insha ice cream din koda yaushe,

 Amal tafado dakin ta iske muna wanan rikicin da Salimat,

   Tace ma salimat gaskiya tasan cewa mu nan duk bamu san komai gamay da ciki ba,

   Amma tunda maman Umar ta ce mata tadinga sha zai taimaka mata dan Allah tafake da shan shi kada azo asamu wani matsala, nan gaba,

  Salimat tasa hannu ta karbi cup din shayin ta kurbe shi gaba daya,

   Daga inda nake zaune naga tana ya mutsa fuska sai tabani dariya 

   Duka takai min tace min ai ita ma watarana zata ramane,

  Kafin inbata ansa sai wayana yashiga ruri alamar kira ya shigo min 

    Alin babba ne, tashi nayi niyar yi inda fita daga waje don kada su damay ni da hayaniya

   Amal ce tadan harare ni cimin wasa tace min wazan gudu mawa cikin su, 

    Dadariya nabar dakin falo na koma muna waya inata dan dariya na,

   Sam banji alamar mutun ba saidai kaiwa kamshin da ya mamaye min hanci na tako ina 

   Ahankali na bude idona sai ko nai arba da sheriff tare da salim tsaye a tsakitan falon namu,,,,,,  

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈TAKARI✈✈✈

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

               6⃣3⃣

                 BY 

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

               &

 AMINCI WRITERS ASSOCIATION GROUP


Almost true life story

 

     Hannu shi ya miko min alamar in,bashi waya na, 

  Wani iri naji a,raina don da kamar kada in bashi sai wata zuciya tace min kada shedan ya rude ki,

   Mika mai wayan kurun duk abinda zaiyi ki gani kiji yafi ki,mai taurin kai don sheriff yafi karfin haka gare ki,

   Cikin sanyin jiki na mika mai wayan jiki ba kwari nayi niyar tashi inbar wurin 

   Alamar inzauna inda nake yai min shima gefe guda yasamu ya zauna ran shi bace,

   Kashe wayan yayi yadibi noban wanda nake magana dashi , 

  Idon shi ya nuna mai cewa Alin ne, zuciyar shi ji yayi kamar Alin na kusa yau yagane kuren shi,,,

    Cikin wata irin murya yace fatima, may yasa wai bazaki min kyakkyawan fahinta ba,

   Wallahi da za ace min kece ke wanan halin batare da nagani da ido na ba bazan taba yarda ba, 

   Kifahince ni fatima bada wani manufa nakafa maku wanan dokar ba sai don kwakwarar hujan dake gare ni akan ku,

   Duk kan ku kuna da tabaibayi akan ku wanda yin hakan agare ku babban ilace agareku ,kuna da bambanci mai yawa da da, da yanzu, try to understand me,

   Mace mai shekaru irin naku suna bukatar kulawa da sa,ido akan duk wani motsi nasu, don gudun fada ma halaka,,,

  Wanan da bi,ar bataku bace, na san koke ba lafin ki bane nasan kowaye Alin nakuma san sherin shi, fiye da kowa,

   So don haka ina rokonki fatima daga yau kada kikara barin sherin Alin yayi tasiri azuciyar ki , wanda yin tasirin zai iya ilatar maki da rayuwan ki , agaba,

    Kaina dukar ina kallon kasan falon sai kawai na ji kunyar kaina da kaina, da har na bari shedan da Alin yayi  nasara akaina kan kin umurni da kuma dokan da sheriff yasa muna, tun farko,

   Saidai kuma naji sam yananu baya zargina, don haka zargin da naje tunanen yake min yawanke araina tas

   Tabbas sheriff da zuciya daya yadaukeni har cikin ran,shi 

  Don gashi ya fada min gaskiya kamar yadda zan iya fada ma Amal ,

  Yakuma rikeni kamar yadda yake rikon ita Amal din,

   Ina fatan zaki fahinci kalamai na da kyakkyawan manufa fatima,,

  Cikin sauri na gyada mai kai na alamar eh nafahinta din,

   Idona da yacika taf da hawaye dama jira kawai sukeyi su zubo suka samu hanyar silalowa, daga idon zuwa saman fuska na,

   Da kyat nadan iya bude bakina nace ma,sheriff dan Allah yayi hakkuri insha Allah ban kara tsallake dokan shi,

   Murmushi yayi mainu alamar dacin rai, yadan gyara zaman shi yace nasan ki fatima nasan halikin wanan aikin bayinki bane aikin Alin ne  kuma zanyi maganin shi don yasan halina fiye da kowa 


     Nuna min hanya yayi alamar ina iya tafiya, 

   Dan dar dar nayi nayi narashin sanin abinyi tukun 

   Kara dagowa ina mai bashi hakkuri,

  Kan sa ya dan rausaya gefe yace pls u can go, ki kula da kanki daga yau, 

   A sanyaye ganin idon shi na akai na yau ko kauda su bai yi kamar da, nadan juya a hankali nabar falon,

   Ido yabini dashi zuciyar shi cike da mamakin yadda halittana ya koma cikin dan kankanin lokaci,

   Juyowa yayi inda salim ke zaune yana kallo da sauraren mu,

   Yai wani irin sanyayan ajiyat zuciya, gami da kutawa 

   Yace Alin Alin hmm hmm, zamu hadu, dakai,

   Ina shiga daki nafada saman gado ina wani irin kuka mai tsuma zuciya,

   Salimat bata hanani ba saida taga nayi kuka mai i,sata tukun don kaina nadan tsaigaita,

   Ruwa ta miko min tace insha, ba musu nakarba nadan kurba na mayar mata da cup din,,,

   Nakara matse waje guda zuciya tab da takaici da danasanin yarda da naiwa Alin har yai galaba da soyayyar shi akaina,

   Gashi cikin ruwan sanyi sheriff ya walwale min manufar wanda ni nakas fahintar shi tun farko,

   Nadan kara hadiyar zuciya na takaici na ce araina sheriff zai min daukar maiyawan son maza ce ni, kila,

   Sainaji wani irin mugun kunya da nauyi yakamani,

   Salimat ce ta dafani shiru tadan yi nawani lokaci tana mai kura min ido,,

    Suna,na takira a hankali 

   Na ce mata na,am a hanakali 

   Ido ta kura min tana nazarina ,

   Ta ce min fadima kiyi hakkuri ki daina wanan kukan haka pls 

   Sai tai shiru bata kara cewa komai ba kamar mai tunanen wanin wani abu,

   Can sai tace min naganki da sheriff a falo dazu, kuma nasan wanan kukan yana da nasaba da ganin da nai maku din dake dashi da salim,

  Kifada min ko may ke faruwa da ke haka,

   Wani irin nauyi naji azuciya na da kunya, sai na janye hannunta daga dafa nin da tayi,,,

   Karo na biyu ta koma kirana tace min kina jina 

Kar ki boye min komi ki daukeni tankar yar uwar ki fadima,,,

   Wani sanyi naji a raina, naga ai maganar ta gaskiya ce, komai na son abokin shawara,

   Dakyat nai shiru na labarta mata komai tundaga farko har karshe dakuma irin taimakon da sheriff yai min a rayuwata,

  Bakina ta kurawa ido tunda nafara mata bayani

   Cike da mamaki take jin cewa ni ba yar uwa su Amal bace 

   Asali ma dai ni yar takari ce ba wata ba,

  Cikin mamaki take kallo na tana nu,nani,tace min fadima ke takari ce takari fa,

   Tai wani dan ajiyan zuciya tace min gaskiya ki gode ma Allah don kin shigo takari da kafar dama,

  Don kisan cewa babu wani abu cikin takari banda kaddarar rayuwa kala kala, 

   Don takari da kyata yake sha in har yasamu komawa gida da lafiyan shi yagode ma Allah,

   Ke gashi Allah ya hada ki da dan albarka kin samu har zaki hada digree din ki asanadiyar takari,

   Tace zan baki shawara kamar yada duk wani dan uwa zaiba nashi shawara,

   Agaskiya baki kyauta ba fadima yadda kikayin nan da ace shi ba mai sanyin halin bane zai iya daukan mataki akan ki, tunda ga kaunar shi ma tayi kokarin kiyaye dokan daya sa maku

   Kiyi kokari duk wani doka dakuma abinda zai cutar da shi ko ke  ,ki kare shi daga gareshi,

   Takara dan dafa min kafadana tace min kikula fadima duk dokar dayasa maku ki kiyaye shi pls, babu cutarwa acikin shi insha Allah,,,

  Tagumi nayi da hannayena ina kallon ta

    Ina kuka nace mata insha Allah zan kiyaye daga yau,

  Tace min to ki daina wanan kukan hakana kisake jikin ki,

   Asake nace mata to yanzu yazanyi in ba sheriff hakuri 

  Tai dan murmushi tace ai yana da saukin kai sosai don da wani ne da abin bai kyau,

   Tace min ki kwatar da hankalinki text zakiyi mai kiba shi hakuri,

   Sai kuma kiyi kokari kisan yadda zaki nuna mai agaban shi cewa ke din diyace kin rabu da Alin din har abada,

   Tadanyi murmushi tace kinga hakan zaisa yasan cewa shi din ya isa dake, kuma ke mai bin umur ni ne,

  A sanyaye nace mata nagode kwarai da kulawar ta,

   Tace min ai itace da min godiya ba ni ba,

     Tunda nashiga ban fito ba dama, 

   Nadan gyara cikin wata yar riga da ta matse min jiki tam, nadauko wayana da niyar zuwa falo indan samu wani abu, in ci,

     Sam basan cewa yau sheriff a gidan mu ya sauka ba ganin cewa wancan karon ba,a nan ya sauka ba,

   Ina shiga falon wayana yana tsuwar kira ya shigo ko bandiba ba nassn cewa bakowa bane sai Alin ne

  Shine din kuwa, da sallama ta karba wayan Sheriff dake zaune agaban computer shi yai shiru yana sauraren ta da kuma mamakin abinda yakawo ta falo cikin daren nan,

   Gurin fridge yaga ta nufa tabude tadauko lemun gwaba da corns acikin leda kujera da ke kusa da ita ta zauna,

   Tana shan lemun tana waya sai yagane cewa yunwa yafito da ita yanzu,

   Muryan ta yaji tana cewa adake nan yanzu nafada maka cewa banda lokacin wanan agaba na, 

  Sai yaji tadanyi shiru tana sauraren maganar da ake fada mata, tana kurban lemun da ke hannunta tana jefa corn din guda guda a bakinta,

     Tace aiko mada sheriff din ne yace min in rabu da kai yayi gaskiya tunda ya isa akai na, 

   Zai iya sani zai kuma iya hana ni, duk lokacin da yaga dama,

  Balle kawai zato kakeyi, sheriff baiko da labarin ina tare da kai, yanzu,

    Kawai ra,ayi nane in maida hankalina a karatuna indaina bata lokacina 

  Don ni ba yanzu zanyi aure ba  ,,,

    Haka mukayi ta musayar magana daga karshe nai warning din shi cikin kakkausar murya akan daga yau kada ya kara kirana pls,,

   Idan kuma yakara zan fada ma sherrif don yadaukan min mataki akanshi,

    Murmushin takaici naji tayi yace ai baku isa ba daga ke har Ahmad din, 

  Nace mai Allah yafika Alin duk yadda kaso ka cutar da ni Allah bai yarda na,kashe wayan ina ta fada kamar yana a fili inda nake,,,,

    Sheriff yasan cewa ban gashi ba har nagama natashi zuwa cikin daki abina,

  Cikin tausayin hali irin nawa yabini da ido har na shige part din mu,

   

  Cikin dare nai mai text nabashi hakuri nakumayi mai alkawarin cewa bazan kara yin abinda baiso ba insha Allah,


     Hindu na zaune tana fuskantar aziza wacce du ta dan ta da hankalinta,

   Cikin tausa murya tace ma aziza gaskiya kamata yayi kisan yadda kikayi dabaran janshi kuje wurin likinta da yasan kan ciki sosai 

   Tunda naga ke kina ra,ayin hakan,

  Hindu gaskiya ban son inyi loosing din Ahmad a rayuwa na don naga alamar in banyi da gaske ba wanan maganar na iya kawo muna matsala arayuwar mu, nan gaba,

   Aziza na fada maki cewa ki kwantar da hankalinki tunda har kina son mijinki zan yi iya kokari na inga cewa kin mallaki baby, tare da shi,

   Sundan dade suna ta tattaunawa akan yadda zasu shawo kan sheriff zuwa wurin wani likita a kasar indiya, wanda zai diba su da ita dashi,

   

     Bayan kamar sati yai mata waya cewa zai je Nigeria gurin Nafisat, 

   In akwai abinda taki jini shine taji cewa wai ita aziza tana da kishiya, 

   Don ita arayuwa bata kaunar kishiya sam koshi don son da take mai ne yasa har ta amince 

  Kuma ganin da tayi cewa shi ba mazauni guri daya bane,

  Yadda sukayi da aziza haka sukayi da Nafisat akan haihuwa, itama din tadan shiga cikin rudu, 

   Don ta tabbatar da cewa sai Allah in mahaifar ta na iya daukan ciki saboda yawan kwayoyin da tasha tun tana yar secondary tafara harkan shan kwaya,

   Wanda ansha warning din ta cewa zai iya mata illa amatsayin ta na mace,

    Don haka maganar ya tayar mata da hankali, 

  Tunda safe ta ziyar ci wani likitansu inda yaba ta appointment cewa taje tadawo aimata gwajin agani ko zata iya daukan ciki,


     Saura kusan shekara guda yarage min inkare karatuna, don haka ba bu kama hannu yaro, babban burina shine nagama da sakamako mai kyau 

   Danagama in wuce Nigeria wurin yan uwana da iyayye na ,

   Don babu ranan da ban tunawa da inna a cikin rayuwata,

   Karatun sai yazamamin biyu saboda salimat cikin ta ya tsufa sosai yai mata wani irin girma kamar cikin ta gwaye,

  Duk zaman da takeyi agidan mu bata taba haduwa da sheriff ba sai yau , koda ya iso itace zaune dirsha afalon mu duk da sanyin A C dake ta aiki a falon ita sai zufa takeyi,

    Duk kan mu munfito muna mai sannu da zuwa yazauna yana kokarin cire sock din dake kafar shi, 

  Drinks nahado mai a ture na zo na aje mai gap da shi,

     Wani irin kamshi da sanyin A C suka hade suka canja launin shakar mutum 

  Yadda naji nashi kamshin shima haka yaji nawa kamshin cikin kasala ya dan kara dukowa yadauki cup da niyar zai zuba ma kanshi sai hannu mu suka hade wuri guda da sauri naga yaje hannu shi yana fadin 

   Subbahanallah, cikin lunshe idon shi duk wanda ke falon saida yadan waigo mu,

   Na tsiyaya mai ahankali yakarba tare da fadin Shukuran,,,

    Sock din kafan shi da yacire don ya dan sha iska na duka gefe ina tsincewa, mangashin da nai gyaran kaina na dashi ya kara shaka,

   Tun lokacin yadan ritse idon shi cup din drink rike a hannun shi,

   Salimat ce tayi kokarin tashi daga inda take zaune sai ta kasa dariyan da yaji na Amal yasashi dan bude idon shi daga zurfin tunanen da yashiga,

   Abu kamar wasa sai salimat takasa cire kafar ta ga sheriff a falon duk mun rasa dabaran da zamuyi don ta samu ta tashi don tashi da kyat takeyi,

     Dan tabur din da ke gaban sheriff nainiyar indan tura dakafa idan yaga haka zai maida hankalinshi ga tebur din har salimat tasamu ta daga don naga kunya take ji, 

    Sainai rashin sa,a nafada dani da tebur din duk saman jikin sheriff wanda ke zaune yana waya,

   Ji kawai yayi nafado mai a jikin shi babu shiri gaba daya na,

   Wani irin yarrrrrr  gaba dayan mu muka, naso in mike sai dan kune na ya lake mai a aljihun rigar cort din shi tagaba,

  Duk kamshi kaina yana shaka a hanncin shi,

    Wanan karon bai samu kiran subbahanallah din ba 

   Rikeni ya dan yi gam ajikin shi yadda har muna iya jin hucin junan mu, yasa hannu shi guda yazagaye ni dashi, a hankali ya cire dan kunin a jikin rigan shi,,,

Duk wanan abin rabin    Idon shi a lunshe yake,

    Salimat har tasamu tadaga ,

    ni ba,a sake ni ba,

   Sai can yadan sakeni a hankali yace min are u, ok, 

   Kai kawai na iya kada mai tare da mikewa tsaye cikin sauri,

      hannun shi na rike da ni har saida yaga na mike da kyau , ya sake ni a hankali,

   Sai yace min b/careful

        Daga haka sai, yamike zubur yadauki wayan shi dake saman hannun kujera yayi hanyar waje,

  Alokacin ita kuma, Amal tasa min wani irin mugun dariya tace min daga zuwa taimakon salimat gashi nan natashi jin ciwo,

   Inbadon a jikin yayan su nafada ba da  tabur din yajin man ciwo abanza,,,

  Duk maganan da takeyi ban fahintan ta saboda wani abu da na,ke jin yana , min yawo ahankali cikin jikina har kwakwalwana ,

   Abinda bantaba sanin ana,jin shi a rayuwa ba yau shi ne naji ga jikin  sheriff din,

   Har takaraci dariyan ta tagama ban ce mata uffan ba 

Saboda weak din da jikina yai min,

   

   Yanafita waje cikin mota yashiga da niyar ya bar gidan ko yasamu dan relief a zuciyan shi,

   Don tunda yake bai taba jin irin wanan yanayi ba,

  Don dai da shi yadauka cewa duk mata iri daya ne ba banbanci,

   Ama yau yafara shedawa cewa akwai banbanci sosai a tsakanin mata,

  Shi bai tada motar ba kuma shi bai fito ba,

   Ahaka salim yazo yasa may shi zuwan salim din ne har yadan yi kokarin saita kanshi,

   Suka fita cikin gari da salim din, dole badon yaso ba yau salim din ne mai jansu a mota,

   Don shi jin shi yakeyi kamar duk an zare mai lakkan jikin shi gabadaya

   Barci daine barawo har ya iya dauka na don da na rintse idon abinda yafaru nida sheriff nake gani, 

    Duk na rasa sukuni sai juyi nakeyi kamar wacce, ake muntsula, ajiki

   Da haka har barci ya sace ni cikin wanan yanayin, 

    Washegari tunda safe natashi nafada kitchen don in hadawa sheriff abin karin kumallo don idan yana garin ko in munje hutu makkah nice mai yi mai duk wani hidimar da ta shafe shi,

   Don kowani yayi mai yakama korafi ke nan kamar zai tashi sama, 

   Amal bata so sam tasa hannu ga duk wani abinda yashafi aikin sheriff din,

    Don gudun korafin shi,

Nasan cewa yanayin aikin su na madina tunda safe suke fita su dawo zuwa karfe dayan rana,

    Shiyasa nake tashi da wuri in mai break fast,

  Ina gamawa na fada dakin mu don indan watsa ruwa a jikina,

    Salimat ce na iske cikin wani irin yanayi, naban tausayi,

    Gurin da take na nufa cikin sarsarfa,  tana kasa kusa da hanyar shiga bayin mu

 Ta dan zauna tayi dai,dai da ita tana maida nunfashi guda guda,

   Dasuri nakarasa gurin ta ina mata sannu,

   Kai kawai tadan daga min alamar ansawa ta na cizon  bakin ta da kyat sai gumi dake ta zubu mata kamar an,tsa mata ruwa,

   Duk sai na firgice na duka saitin ta ina mata sannu,

  Tace min cikin karfin hali fadima kila haihuwa zan yi,

   Ido waje nace mata what cikin karfin hali ta daga min kai,

   Nace to barin kira maman umar tazo muje asibiti ko,

    Har nakai kofa sai naji tayi wani irin nishi gami da salati mai karfi,

   Aida sauri nayo kanta ina fadin sannu salimat

  Wanan karon bata karba min ba ido kawai ta zuba min duk sun firfito waje,

   Sai naga tafar wani irin nishi makarfi

   Da sauri na rungumay ta ina kokarin daga ta sai naji duk taimin wani irin nauyi, kamar ba salimat ba,

   Kafin in kifta ido har ta sullubo yar baby ta tana fama calara ihu irin na jarirai,

    Wani irin mugun tsoro naji yakamani, don bans an abinda zan iya taimaka mata dashi ba,

   Idonta a lunshe tana hamdala tace min fadima kira maman umar da sauri tazo

   Aiko aguje na kwasa da gudu na manta sam banda wani rigan kirki ajiki, 

  Sai falo ina ihun kiran maman umar,

  Suna falo suna break sukaji ihu na kowa sai ya watso min ido don jin komai yafaru hankalinsu tashe,

 Da sauri maman umar tafito kitchen din cikin rikecewa,

  Mu kaci karo a kofar kitchen din da ita, 

  Ina haki  nace salimat ta haihu,

    Duk a rude suka tashi tsaye cikin mamaki suna kallo na,

  Maman umar da sauri ta shiga dakinta ashe ita dama da shirinta take,

    Muka bita diiiii abaya sai dai wanan karon akofa na tsaya munajin baby nata  tsala ihu duk ta karade gidan ,

   Sai da tagama gyara su sanan ta miko muna yar baby fara sol da ita kamar uwarta, an nade ta cikin farin shawul,

   Amal akafara ba sai ta wuce direct inda Sheriff yake tsaye nisa da mu cikin damuwa,

   Saida yakare mata kallo ban sha,awa sanan ya kalli gefen da nake tsaye yace min indauko mai dabino da ruwan zam,zam cikin sauri natafi na debo mai su nakawo mai

  Na iske yanawa baby kiran sallah da yagama yakarbi dabino yadan tauna yasa mata abaki,

 Yakama dan lasa mata ruwan zam zam din,

  Saida yagama yadago kai mukayi arba dom dama duk mun kewaye shi,

Da sauri na dukar da kaina kasa

      🐎ZEEE MAKAWA🐎

,✈✈✈TAKARI✈✈✈ 

        👣👣👣👣👣

         👣👣👣👣👣

                    6⃣4⃣

                      BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

  🐎 HUGUMA GROUP🐎


   Almost true life story,


    Saida komai ya lafa, ne kowa ya dan natsu guri guda, 

 Maman Umar tagama gyara komai sai ,Sheriff din ya shigo dakin don yaiwa salima sannu da kuma barka da arziki,

   Ina kitchen naje hada mata abincin da zata dan ci , abinci mara nauyi nai mata,

   Sam basan cewa ya shigo dakin ba don da banshiga ba alokacin,

   Salimat nagani na ta ce min sannu fadima da kokari,

   Nagode kware da hidimo min ki,,

   Gare ni Ubangiji Allah ya baki miji na gari,

   A kunyace na ansa mata da amin aiba komai,

   Sai alokacin nagan shi tare da su Amal da Salim suna ma baby wasa,

  Amal tace aidole ki godewa Fadima salimat, tunda itace yau nurse mai karban haihuwa 

   Cikin mamaki Sheriff yace, what fatima, yana mai dan nuna ni da yatsa yace 

   Yace interesting nd welldon,

  Ke yar karama da ke har kin iya karban haihu kuma agida,

   Dan murmushi nayi gami da sadda kaina kasa,,,

   Amal tace ai fadima tayi kokari don daini gaskiya bazan iya ba,

   

     Sheriff yace gaskiya dole a,tafi asibiti da baby da uwar don adiba lafiyan su

   Yadan kalli gefen da salimat ke zaune tana wani irin zufa yace mata kin san kunyi kasada kware don haihuwa ya tatare da matsala acikin shi

   A sanyaye tace wallahi sheriff a bazata abin yazo min don ban dauka cewa haihuwa bane,

   Allah yasa fadima tazo itace ta taimake ni,


     Acikon mota sheriff zaikai mu asibiti tare da Salimat da baby ta,

   Amal ta mika min baby tace in zauna da ita agaban mota itada Salimat su shiga baya,

    Ahankali yake tuki motar sai kira,an dake tashi nawani dan saurayin matashin balarabe,

   Baby tai dan wani hirgita kadan tare da ajiyan zuciya madan sauti,

   Cikin sauri sheriff yadan duko inda nake zaune da ita ,yadan kware showul din yana diban fuskan babyn 

   Wace ke ta sharan barci abinta,

   Amal na kallon mu daga bayan mota da suke zaune, daidai lokacin ta dauke mu hoto a hanka, batare da sani na ba

    Saida muka je aka diba lafiyan jariri da na uwa aka tab, batar da duk suna lafiya,

   Sheriff ne da kan shi yabuga ma mijin salimat waya yasheda mai cewa salimat ta haihu,

    Sunyi mamaki sosai don duk dauka akeyi ba month din haihuwanta ba ke nan,

  Ba karamin kokari sheriff yayi ba saikace shi akaiwa wanan haihuwan 

  Satin ta biyu a saudiya mijinta yazo yadauketa zuwa Nigeria ,

   Yai muna godiya sosai kafin su wuce , duk bamuso su tafi da baby Asma,u, ba wai sunan mahaifiyar mijin ta ke nan,,,

   

      Karatun mu mukaci gaba dayi duk da bawai dogon lokaci yarage muna ba,

 Saidai karatun namu sam bai hanamu yin ibadan mu ba,

   Ko yaushe muna zuwa muyi sallah idan an idar da sallah mushiga muyi ziyara 

   Mufito wani lokaci kuma salim ne zai kwashe mu ga mota yakai mu baki,ya muyi ziyaran kaburbukan bayin Allah da sukayi sha hada,

   Ina son zuwa ziyara a bakiya don ko ba komai zakaji wani karin imani nashigan ka,

   Don zaka dinga gani kamar ace sahaban manzon Allah SAW dake kwace cikin wanan makabartan zasu tashi ka gansu, 

   Sai mutun yaji indan ana bada tarihin su kamar ace shima a wanan lokacin aka halicce shi yazaman to a cikin su,

   Gurine da akayiwa security ankewaye shi da waya saidai ka tsaya ko kuma idan zaka iya hawa dutse ka,hau kaje kai masu addu,

   Salim yana yawan sha,awar zuwa ziyara a bakiya, don kusan duk ranan alhamis sai yakaimu ziyara munyi masu addu,a tare yiwa kan mu ,muma fatan cikawa da kyau da imanin ubangijin mu,

 

  Za,zaune muke duk kan mu cikin falon muna hira, kamar yadda muka saba yi indan weekend  ne zama mukeyi inda mun dawo daga masallaci ayita hiran rayuwa

  Yau,ma hakan ce ta kasan, da mu,

  Amal ce zane a tsakiya ta magana wayanta yana a hannun ta tana dube dube,

  Photo na dake cikin wayan ,sai idon ta yakai ga wanda tai muna ni da sheriff da baby Asma,u, wace muke ce ma husna,

    Saida tadan tsaya taima hoton kallon tsab sanan take gwada muna,photo,

   Mamaki yakamani kware daganin picture don basan lokacin da ta dauka, ba,

  Idan ka gan mu a cikin photo zaka zaci cewa ko wasu ma,aurata ne nida shi,,,, 

   Salim yace kai dama ace wanan baby na yayan mu aida basan irin farin cikin da zaiyi, ba,

    Kusan koyaushe sai  yai min korafi akan yana son haihuwa , yana son yasamu baby shima,

  Ace ai wanan baby shi don yace hjy tsohuwa tana yawan yimai korafi indan sun hadu,

  Amal tace banga wace ke shirin haihuwa ba cikin wa yan nan yan gayun mata nashi,

   Tace du matan nashi ni gaskiya basuyi min ba babu wace ta dace dashi acikin su,

    Sai lokacin nasa masu baki a,zancen su, da sukeyi 

   Nace ,a a Amal ai aure mukaddari ne matan mutun kabarinsa,

   Aiko duk matan nashi suna son shi kuma idan lokacin haihuwan su yayi ai zasu haihu komai fa dan lokaci ne,

   Daga haka ban kacewa ufan ba, daga zancen nasu,

   Wanan zancen yasa naji duk tausayin sheriff yakamani nai alkawri araina insha Allah zan sa shi a,addu,a ta, koyaushe,

   

     Aziza ce zaune duk ta rikita mai lissafin shi adole sai sunje  sunga likita a kasar Germany, yadibata

  Saida yagama jin korafinta yadan yi murmushi yace aziza mubar ma Allah zabin sa idan lokaci yayi sai yaba mu bawai sai munje muna ta nuna rashin tawakkalin mu akai ba,

  Allah da yayi mu bai manta da muba,

   Ganin da yayi shima dai din yana son yaga baby shi a duniya yasa har ya amince mata

    Bayan aune aunen da sukayi likita yatabbatar masu cewa lafiya lau, maigidan yake kuma ita ma din zata iya samun ciki saida akwai wani abokin shi dan kasar indiya yafishi  kwarewa ta wanan fan,ni sosai,

   Don haka yace suna iya zuwa su ziyarce shi,

   Bayadda aziza batayi da sheriff ba amma yace shi tunda lafiya lau yake bai zuwa ko ina,

  Itada hindu sukaje gani doctor Khan a indiya din bayan duk wani awo da zai mata yayi ya,kam,malla ne yake sheda mata cewa, agaskiya mahaifarta bazata iya daukar ciki ba da kanta saidai inda zata yarda ai mata artificial insemination, to ko shi din sai kila ne cikin zai iya tsaya mata,

  Haka suka dawo gida cikin tashin hankali ,don tasan cewa idan ko har baza ta haihu ba , ba makawa sai sheriff ya kara wani aure tunda nafisat itama har yanzu gata can shiru ba wani labarin ciki,

   In akwai abinda bata kauna shine taga Ahmad dinta, da wata mace koda ko abokiyar aikinsa ce,

  A ranan tashi yi mai mita ke nan , shi mamaki ma take bashi, saboda irin mugun kishin ta,

   Tun ajirgi take ta rusawa hindu kuka, hindu tai rarashin kawar nata har tagaji,

   Jiki ba kwari tadawo mai a Dubai suka hadu yana ganin ta tagane cewa batai nasaran tafiyan ta ba ,

   Shima dai din cikin zuciyar shi baiji dadi ba, 

   Saida dare bayan sun gama komai sun kwatane take mai bayanin  da likita yai mata, saida ta boye mai cewa ance ko artficial insemination din bazai zama dole ya tsaya mata ba,

   Tana kai karshen zance yamike har zaune daga kwancen

    Yana fadin tir Subbahanallah wa,iyazu billahi 

   Ai wanan rashin imani ne da kuma aikin jahilci, taya za ace mutum bai imani da Allah ,

  Idon shi yai ja sosai don irin masifan da yake ta balballa mata,

   Yakawo mata aya da ku hadisai masu kashe jiki,, yai mata,

    Rai bace sukayi barci a wanan ranan batare da kowa ya kara cewa tak ba,

   Tunda safe ya shirya tafiya a ranan saboda bacin rai yabaro Dubai din zuwa saudiya,

   Satin shi guda ta wuce Nigeria saboda wayan da akai mai cewa hjy tsohuwa ba lafiya sosai,


  Yana zuwa yaga irin yanayin da take ciki yasa adauko ta zuwa asibitin Abuja,

   Cikin ikon Allah hjya tadan samu sauki,don tasamu kulawa sosai, 

   Acan Abujan ma bai tsira daga fitinar nafisat ba don ita ma din so takeyi suje suyi gwajin haihuwa ita dashi don aji ko may ye matsalar,

   Shi mutun ne mai kokarin fitar wa natare dashi da hakkin zaman tare,

   Don haka baki zuwa ba bayan da likta yai ma su shiya tayar wa nafisat da hankali,

  Inada yace masu mahaifar ta ya samu matsala drug's din da take sha yasa ba zai taba iya daukan ciki ba,

   Cikin takaici suka iso gida ga kukan  da nafisat ta i she, shi da shi 

   Suna shiga gida tazauna tai tagumi hannu bibiyu ta ta zub da hawayen bakin ciki,

   Tunda ya ajeta ya fita bai dawo gidan ba sai cikin dare yadawo,

  Zuciyan shi duk ta jagule mai,

   Duk kan su, su,biyu kusan case din su guda ne, ba zasu iya daukar ciki dan dama azizan da yake tana kan tracings na doctor ne tukun,

  Yana sa ran cewa zata iya samun ciki indan har Allah yakawo,

      Hakuri nafisat ta kama bashi akan don Allah yayi hakkuri kada ya bari iyayyen ta suji wanan zan ce, 

  Bai samu ce mata komai ba saboda bacin rai,

   Tunda safe yaje gidan Bashir don yagaida hjy tsohuwa don tace sam bata zuwa gidan nafisat ta zauna

   Saboda hakane aka kaita gidan bashir din don ta zauna can

   Bayan sun gaisa ne da hjy sai ga ya shigo dakin dauke da,yar diyar  shi tana wasa da fuskan baban nata,

   Sheriff Ahmad ya mika hannu don yadauke sai taki, zuwa, ta kara rungumay mahaifin nata,

  Bashir yadan hada kai da fuskan yar yarinyar yace, baki zuwa daddy ya,dauke ki ko,

  Dariya yar diyar tayi na kuyya,

   Hjy dake kwance gefe tace, yanzu Alhaji karami ba zan ga zuriar ka ba , sai bayan na mutu,

  Sai tadan kama kuka kamar wace akai ma wani abu,

   Dakyat suka samu suka lalabata shi da bashir, har tai shiru yai mata alkawarin cewa,

   Insha Allahu zata gani bama zata mutu ba sai ta yi ta goya mai zuri,an shi,

   Dahaka tadanji sanyi ,sanyi tai shiru tana fadin Allah yasa Allah yasa,


      Amal ce ke son muje makkah mudan yi hutu can ni na rasa may yasa yanzu Amal ke son muje makka hutu,

   Badon naso ba nashirya muka tafi, muka rufe gida sai makkah 

  Cikin dare muka isa garin don haka kowa dakin shi ya nufa saboda gajiya ga dogon tafiyan da mukasha,

    Dasafe natashi da dan ciwon kai don haka ban fito ba barci nakoma yi,

   Sai da rana yayi so sai na samu kan nawa yadan dai,na min ciwo,

  Nafito cikin wani buje da riga yar rigar ta matse min jiki duk suran jikina yafito da kyau,

   Sai bujen rigar da yani bude kamar dawisu daga kasa, shi gyalen jayan ne nadan yi rolling akaina, sai takalmana plat shoes da nasa akafa na,

    Abinci na yana a cikin cooler saman tebur saboda dama nasan cewa any time natashi zan iske abin karin nawa da zafin shi,

  Sam na manta cewa yau weekend ne Sheriff nagida  yau baya fita ko ina sai massalaci kawai zai,sa,shi fita gidan,

    Na zauna kenan zan fara cin abinci Salim yafito yace  min yajikin nawa 

  Saida naja kujera na zauna tukun nace mai naji sauki dama gajiyan jiya ne kawai  yan sa min ciwon kai,

   Har zai fita nace mai dan Allah ina son in nagama yaikaini kundifal zan je in dan siyo wasu yan kaya ne da na manta bandauko ba,

   Salim yace min zasu fitane da mustapha yanzu,

   Cikin rashin damu nace mai ba matsala zan tafi da taxi idan na kare ai,

   Ina ganawa na gyara jiki na tsab ba inda zaka iyagani surar jikina a waje don na rufe shi lif,

   Taxi natare da niyar in shiga zuwa kundifal sayen kayan kwaliya irin na mata ,

  Har zan bude motar naji maganar Sheriff a bayana yana cewa

  Cikin dakarkiyar fuska yake ce min ina zan je batare da izini ba duk sai na dan dabur ce,

   Don nasan cewa ina fita ko ina ai batare da fada ma kowa cewa ga inda zani ba,

  Balle ma ni yar takari ba lasi,. 

   Aiko ina zan iya kutsawa dan nema kudi cikin gari batare da wani shamaki ba,

    Wata zuciya tace min kidibi kan ki a,yada kika koma yanzu, ba da bane 

  Kina da ban banci sosai da da din,,,

     Naba mai taxi hakkuri yatafi najuya da niyar komawa cikin gida 

   Sai dai ina ina kaiwa tsakiyan compound din gidan naga yafito da wata, 

  Landrover jeep let's one ban ma ko taba sanin yana da ita sai yau nagan shi da ita,

   Bude min gidan gaba yayi ta gefen shi na zauna,.

   Nasan cewa mawuyacin abune sheriff ya ja mota da kanshi saidai aja shi,

   Ina zama ya sa lock yakule ko ina , wani irin sanyi da kamshi motar keyi,

  Batare da ya kalle ni ba yace min ina zan tafi ne ma wai,

  Cikin murya kasa, kasa nace mai ka Kundifal plaza zani,

   A hankali yake tukin motar cikin gwanewa kira,ar sudes na tashi a hankali don kusan ko yaushe kira,ar shi yake sawa a motar shi,

    Natakure wuri guda cikin rashin wal,wala, saboda bawai nasba dashi bane har yanzu,

  Dan dama dama idan su Amal da salim na kusa nikan dan sake jikina kadan in suna hira insa baki,

   Tambayar bazata naji yai min saura wata nawa mu kare school, cikin dan in,da,inda nace ina ganin kamar takwas yarage muna nace mai,,,

   Yace o iam not even sure gani kawai nakeyi ko,

  Abinda yasa ni dan yi murmushi ke nan yau a gaban shi ,

   Nace takwas din daine kawai,

  Zaiyi wani magana wayan shi tayi tsuwa alamar kira yashigo mai,

   Nikan sai na maida hankalina saman titi ina ta kallon manyan gine ginen da ake tayi acikin gari ina mamaki irin cigaban da kullun aje samu agarin,

   Agaskiya gwaunatin saudiya na kokarin wurin kula da jin dadin al,uman kasan don komai na,zamani su na kokarin su yi shi akasan daidai yadda bai saba ma shari,a ba,

  Mun kusa kawai wane hankalina yakai ga wata yarinyar takari yar baka da ita tana tallan kaya a saman hanya duk tayi zufa saboda rana gata kuma a tsorace take don tana yi tana waige waigen yan bagaladi,

  Tausayi yarinyar tabani don da gani yar sabon shigane,

   Wani irin ajiyan zuciya nayi wanda har  ya dan baiyyana afili,

   Shima yana lura da hankalina yana gurin yarinyar da nagani yasan cewa dole in tuna wani abu dama,

   A hankali na furta Alhamdullah, wanda ban tsan mani zai kai a kunen shi ba saboda dan rage karan kiran da ya yi lokacin da zai fara waya,

  Kallona naga yayi cikin sauri yana mai dan  lunshe ido yana sallama da mai wayan

   Wanda nake kyautata zaton aziza ce don naji yana cewa saita zo din, 


     A cikin shago sashen saida kayan mata naje nadan zabo abinda nake bukata,

   Sheriff ne na hango can  layin saida kayan mata expensive one yanata dibawa yana zabe, 

   Tsayawa nayi ina kallon shi da mamaki a raina nace ashe dama shima zaizo sayayyane, a gurin,,,

   Kallin shi kawai nakeyi da naga yayi layin saida gold ina binshi a baya ahankali ,

   Wasu yan kune da sarka masu kyau Dubai naga yadauka, yamika mamai binshi abaya asa a gram,

    Saida yagama ya,hada kudin dana wanda nadan zaba, ya biya, aka kai muna kayan har cikin mota,

   Bayan mun shiga mota ne nafara yi mai godiyan kayan da ya biya min

   Hannanu shi yadaga tare da rike min yan yatsuna da nake kokarin yi mai godiya yana ce min la,la,la,

   Basai nai mai godiyaba yace duk abinda yai min kamar yaiwa kanshi ne don na can can ci hakan agare shi,

   So daga yau duk abinda yai min baya son in kara yi mai godiya ko kadan,

   Yana mai kallon gefena yace nagane ko nadan gyada kai a hankali alamar eh,

  Inba mafarki nayi ba to tabbas yadan murza min karshen yatsa na abinda yasani cikin dan rudani kadan ,

   Koda muka isa gida na dan tsaya na kwashe mai kayan da nasawo na hada da nawa,, 

   ban kawo  ko mai a raina ba 

   Zan shiga ke nan naga motar Almustapha da salim a,she har da Amal suka fita ban sani ba,

   Gani da kaya niki,niki a hannu na 

   Mun rigasu shiga ciki sai nawuce daniyar in kaimai kayan part din shi tsayawa yayi yana kallo na da mamaki yace min ina zan kai kayan 

  Tsaye nayi sororo nadan kali kayan shima na kale shi sai yace in tafi dasu duk nawa ne,

   Cikin mamaki ido bude nake kallin shi,

   Jin tafiyan su Amal dayayi shigowa yasa shi shigewa part din shi nan nadan tsaya sororo da mamaki 

  Wai yau ni fadima yar takari keda wanan kayan alfarman dana ga ansiya a,kundifal,

  Jiki ba kwari na wuce dasu dakina kafin su Amal, su shigo ciki,

  

    Sai cikin dare na bude kayan nadiba gaskiya saida gabana ya fadi sosai gani irin kayan da sheriffudeen din mu Ahmad ya saya min,

  Dan kit din gold din na bude inata shafan set din a hankali,

  Tex nagani ya shigo min a wayana, 

  Kaman kada in karanta sai na bude short note ne kamar haka 

   Wear d blue dress tomorrow morning ,,,

   Da sauri nakai kallona ga blue dresses din dake gabana, nadan daga shi wani dogon rigane mai shegen kyau na yan lebon, ka taushi ga santsi, 

   Dogo ne har kasa da wani irin aiki a gaban rigar da fararen duwatsu, sai dan gyalen shi da ribon dake makale a jikin shi,


🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈

           👣👣👣👣👣

            👣👣👣👣👣

                  6⃣5⃣

                     BY

🐎 ZAINAB IDRIS MAKAW🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


  Almost true life story,


      Bakaramin mamaki text din yabani ba saidai ban gama mamaki ba naji anturo min kofar dakina,

   Firgigit nayi natura kayan gefen gadona na zauna kamar ba komai nakeyi ba,

    Amal ce tashigo dakin da murmushin ta zo har inda nake tadan zauna bakin gado tace min,

   Ashe baki barci ba nace mata eh, saita ke ce min yanzu yayan mu ke fada min cewa wai gobe akwai inda zamu da karfe, hudun marance,

   Sainake cewa ko kin sani shine yace min yafada maki ai kin san da zancen 

   Mamaki yakamani tunda nasan cewa bai fada min komai ba,

   Iyaka ce min yayi insa blue din kaya gobe kuma bai fada min komai, ba ai,,,

   Washegari sai ban fito ba har wani lokaci ina daki ina karatu abina kusan ba wani abin da zan bukata wanda babu shi,

   Aisha ce tazo min dakin da kukan ta wai umar ya dake ta,

   Dole natashi nafita daga buyar da nakeyi yau, agidan don kusan ince 

   Yau ba wanda zaice yagani acikin gidan sai maman umar da taji shiru tabiyo ni dakina da abinci na tace min inci

    Ta hanyar baya nabi don kada su gan ni cikin rashin sa,a sai gashi na hade da salim 

   Murmushi yaimin kadan yace wai fadima maye sirin ne kulun fa sai kara girma kikeyi da kyau,

   Salim baka gajiya da zolaya kai ni yau ko mirrow ban diba ba bale in gyara fuska na,

   Kafin inkai wurin Umar din saigashi yasamay mu inda muke tsaye da salim,

     Nadan mai fada akan ya daina saurin dukan mutun ,

  Idan yasaba ba zai ji dadi ba nan gaba in ya girma,

   Nan na fara ba salim labarin marin da Almustapha yai min lokacin da na raki hajiya tsohuwa dawafi,

   Salim yadinga yi min dariya kamar a lokacin abin yafaru, 

   Nima dai dariyan na kama nacigaba da fada mai yadda nadinga ji kamar in rama marina in gudu alokacin

   Salim yana nunani yana dariya yace fadima an fada min cewa bakyaji kina karama sosai,

   Dariya muka karasawa gabadayan mu nayo baya da niyar in dan waiga gefen tsuntaye na ingani sai naci karo da 

  Sheriff tsaye cikin wasu yan kananin kaya sunyi matukar daukan shi kamar shi yayi kan shi,

    Fuskan shi atamke babu alamar dariya cikin dan dukawa nayi cikin ladabi na gaishe shi,

   Batare da ya ansa ba yake ce ma salim  yabi yo shi sutafi,

   Saida naga sun bace min azuciya na ce bahagon mutun ba,a gane gabas dinka sai kaso,

   A falo nukayi kicibis da Amal tace min kin gama kwanciyar dakin kin fito ne,

   Murmushi kawai nai mata don nasan komay zance mata bazata yarda ba sam 

   Ita madai din shi tabi ni dashi tana tafiya tace min fadima karfe uku da rabi zan shigo wurin ki mu gyara jikin mu don tafiya zuwa wajen walimar da za,ayi na yan African Youth Found mazauna saudiya saboda tallafawa yan uwa musulumi kasa shen,baka ken fata ,

   Nace mata to a zahiri 

  Amma cikin zuciya sai cewa nayi wanan ba wurin zuwan yar takari ba ce saidai ku masu hali,

  Bama zan koyi rigimar cewa zan tafi ba tunda ko mai gidan bai sheda min ba,

  Kuma na hadu dashi dazu bai ce min komai ba kenan wanan fitar bai shafe ni ba,

  Saidai in ita Amal din keson ta kasa dani,

   

    Hakalina naga littafin da nake karatu na course dina danakeyi,

   Hankalina yatafi sosai ga abinda nake nazari akai,

  Amal tashigi dakin da yar fara,ar ta ganin da tai min zaune ko niyar tashi don in shirya banda,

   Zama tayi gefen gadon da mamakinta ta fisge littafin a hannu na,

   Wani irin ajiyar zuciya na sake nadago kaina nazuba mata idona cikin nata,

   Lokaci guda na karanto bacin rai a kwayar idon nata,

    Muryan ta naji tana cewa lalai ma fadima baki da dama,

   Yanzu duk tuna makin danayi cewa zamu fita yau kuma fitan mai muhin manci ne sosai bai sai kin maida hankali ba don mushirya da wuri shine zaki zo ki kama karatun ki,. 

   To san nu alhudahuda sarkin karatu,

  Na, uhum Amal ba hakana bane gaskiya naga cewa sheriff baice dani za,a wanan gurin ba kamar kece kawai ke kokarin zuwa dani,

   Dariya tadanyi min mai dan shewa tace o watau ni daban ce da ke yau ko,

   Saboda yayanmu bai fada maki cewa, dake za,a ba da bakin shi shine rashin daukar maganar tawa da gaskiya ko,

  Murmushi nayi nace a,a wlh ba hakana bane,,

   Ta,tare nida cewa hakanane mana,

   Jiya da yafada maki cewa zaku fita da bakin shi aikin shirya kun fita mu biyu, ko,

Jin na kaina nayi nace haba Amal ko jiyan ai a hanya ne tafiyan ya hadamu,

  Tana mikewa tsaye tana cewa ki dai tashi da iya salon takon  ki ki shir kin ji don ba,zaki samu bata lokaciba

   Dama tun safe nagane nufin ki kina wani noke ma wanan tafiyan don baki son zuwa,

    Gaskiya ba hakana bane kawai dai bani ,,,,

   Hannu tadaga min tace min kin makaro yarinya zuwa ba fashi don sai kin je shi,

  Fita tayi tabarni da tunane fam azuciya saboda irin canjin yanayi dana nake gani iri ga sheriff din mu

   Nifa yar takari ce wana wuri kuma wurine na bada donations ga kungiya to ni mai zai kai wurin,

   Wurin da yan kasan Africa daban daban musulumai ke haduwa don tallafawa al,umomin su,

    Har na kwanta da niyar ban zuwa sai kuma hudubar salimat yafado min arai nakuma tuna da irin hararcin da sheriff ke min tun haduwa na dashi koma bai ce inje tunda yar uwan shi ce tabukaci inje aidole in tafi,

   Wanka nafada yi bayan nafito nadade gaban  dressing mirrow, gashi na nafara gyarawa bayan na gama sai na fara gyaran fuska na

   Ina gama gyaran fuska sai text din nan na jiya yafado min a raina,

   Kayan nadauko nasa  nadaura dan ribon din kayan na kama kaina dashi,

   Nida kaina nakarewa kaina kallo a,mirrow saina ga ashe rigar tsakiyar ta a matse take ta ciki tasama andan buda ta

    Ajiyar zuciya na saukar a hanakali ina kallon kaina wainice fadima inna yar kulu na koma haka yau,

  Najawo kit din sarka da aka siya min jiya jiya na daura ma wuyana nasa dan kunen 

   Wohoho sai kin gani da kanki zaki karasa bayanin yarda na koma,

    Daidai lokacin naji anturo kofan dakin nawa, ko ban diba ba nasan cewa Amal ce 

   Sainace mata Amal kidiba kigani yarda nakoma yau ni fadima yar takari diyar inna yar kulu yar mutan dogon daji, nice,,,,

   Bankarasa zancen bada naji shirun yai yawa sai na waiga inga may yasa tai shiru bata ansa min ba,

   Sheriff ne tsaye ya zuba min ido cikin shigar wasu kayan Indians Pakistani, farare sol kayan wando da riga kayan sun karbi jikin shi sosai 

   Takowa yayi a hankali cikin tafiyan shi na kasaita, irin na matasa masu tashen nairai,

   Yatako har inda nake tsaye gaban mirrow,

   Gyalen kayan yadauko ya mika min yai min alamar in yafa ma kaina batare da yai min magana ba ya juya yafita yana mai kallon agogon hannun shi da yadaura,

   Ina gama shiri a bakin kofa nasamay duk cikin shigata alfarma, irin ta musulumai,

   Motocin ne guda uku a jere waje kowani yakai akirashu mota,

   Dan jin nayi tsaye don basan ko wace zamu shigaba nida Amal,

   Salim ne yai min magana kasa kasa yace min waccan farar itace zan shiga, 

   Ga mamakina sai naga Amal ta nufi gudan motar wadda naga mustapha ya shiga bayan ta itama dai din bayan motar tashiga,

   Nadan waiga na kusan nikadai ce a,tsaye wurin don salim har yafara tafiya zuwa motar da zai shiga tare da wani mutun bakon fuska da nagani,

   Banda zabi motar da salim yagwada min inshiga itace din na nufa,

  Ina isa kusa da motar da driver motar ke rike da gambun motar yana jiran karaso wana,

 Ga mamakin da zan gani ciki sheriffudeen din mu ne Ahmad zaune a bayan motar yana waya,

   Kamar in,koma baya don fargaba,

  Sai kuma, nadaure nai dan kokarin shiga na zauna ahankali,

  Batare da na waiga gefen da yake zaune ba na takure gefe guda kamar ankai buzuwa yaye,

  Yana gama wayan dan kallo ni a hankali yace ko sanyin A C yaimin yawa ne na takure wuri guda, 

    Nadan kada kaina alamar a,a 

   Bai ce min komai ba kuma yadan tatara  hankalin shi ga titi ya na kallon hakali kwace,

 Mun iso gurin wani babban dakin taro ne da ake kira da King Fahad central, holl, 

A cikin larabci akai rubutun,

   Nan muka dosa don ni  nasan gurin mu kanzo bara ko goge goge, indan anawani occasion, a lokacin da nake takari

   Motoci ne birjit agurin ga security nan kala kala, sai mutun yaji tsoro indan bai saba ba saboda irin tsaron da akasa agurin,

  Ko ina hasken fitilo ne keta wal,wal,wal suna haska mutane, dake guri kala kala,

   Koda mu muka fito daga motar zuwa cikin dakin taron,

Akwai dan tafiya maidan nisa kafin mu shiga cikin dakin taron,,

    Tafiya muke yi a jere da juna batare da dayan mu ya yi magana ba, muna gab, da shiga dakin  taron naji sheriff din mu ya riko min hannu na, yarike cikin nashi sai sanan yadan rada min akune ne ya ce min

    Kinyi kyau sosai, fatima,

  Sai naji, nakasa controlling kaina   

   Kamar a mafarki naji zancen nashi ji nayi kamar in nutse acikin kasa saboda kunya,

  Ban tanka ba daidai lokacin kuma ,muka kutsa kai cikin dakin taron wanda ke cike da yan uwa musulumai bakaken fata, na kasa kasa

   Shigar mu keda wuya a ka fara taken kasar saudiya, tare da daga tutar su mai photon dabino da takkuba,

  Bayan angama malamai kala kala suka dinga jero addu,oin su tare da yin nasiha, akan cigaban addini, musulunci,

   Abinda na lura dashi agurin shine duk wanda keda mata ko miji gefen su daban tare da tawagansu, 

  Wanda kuma basu zo da matan su ba suna gefe guda na maza gefe guda namata,

   Saida aka nuna muna inda gurin zaman mu yake ne nagane cewa ashe su mustpha na bayan mu cikin tawagar company Abu Abdallah wanda sheriff ne ke jagoranta su,

   A gaskiya tsaya infadi irin kyaun da mukayi aguri bata lokacine,

 Yan jarida ne kawai keta faman daukan photo kala kala a,gurin

   Zaune nake kusa gab da sheriff din mu idan ka gamu zaka dauka ko wata mata da miji ne sabon aure saboda yarinta na ya baiyana sosai , daka diba kasan cewa Allah yayi hadin shi agurin ,,,,,

   Koma mai nawa baka iya gani sai dan round din fuska na kawai ya dan baiyyana afili,,,,

    Kowa nata harkan gaban shi sai donations ake ta bayar wa kala kala, 

   Yawancin duk wanda ke gurin zaka ga yana magana da abokin tafiyar shi,

   Banda ni dake zaune gefen sheriff ina ta faman, dan wasa da wayana dake a hannu na,

    Banyi aune naji ana kiran sunan sheriff da tawagan shi sufito suba tasu gudunmawar,

  Hannu yamika min nagane nufin shi nima sai na miko mai yadan makale hannun nawa cikin kafadar shi muka mike atare, lokaci guda,

   Kyauta sheriff ya gabatar irin ta alfarma  da bajinta da kuma kulawa da addini, 

    Inda jama,a keta sa masu albarka dashi da kamfanin su,,,

  Andayi hira dashi har ake tambayan shi sunan amaryan nashi  nadauka zai ce aziza ko nafisat,,,

    Sai kawai naji ya fadi suna na full da mamaki nadan kalleshi cikin dabara, sai yadan kashe min ido guda 

   Duk wani irin kunya da nauyi ya kamani agurin, duk wani motsinawa yana akan idon sheriff tunda naje gurin banyi magana da kowa ba,

  Yana rike da hannu na duk gaisawar da yakeyi da jama,a

    Jinayi ana dan tafawa a hankali abayan mu, batare da na diba ba kowaye ba tun da ba wai sanin su nayi ba,

  Na ance kai amma ko gaskiya kun dace da hakan aida kace min in bar maka ita din takace bana kowa ba,

  Gabana yaba dam don ko ban waigaba nasan cewa wanan muryan  Ali baba, ne  

   Alin ya zagayo da kyau ta gaban mu yasa hannu cikin aljihun shi yana muna wani irin mugun kallo,

   Doctor kamal abokin sherrif na gurin bai gane may Alin ya ke nufi ba sai ya ce 

    Walahi nayi farin ciki da wanan auren na Ahmad fiye da kowani auren da yayi abayan 

   Don wanan itace daidai da aure ka

   Alin da ke gefe yace o ko asai akace yayi kwace ga wani don kawai tazama mallakin shi,

   Sai lokacin sheriff yace ma Alin kai dama dan akuya ne acikin mu karasa wacce zaka bida sai wacce keda aure akanta,

   Murmushi Alin yayi yace wacce da aka kwace ake shirin aure ko,

   Zaici ga ba da magana security din company su sheriff sukazo suka dan jaye Alin din gefe 

   Inda muka ratsa tagaban shi tare da sauran tawagar mu muka wuce shi cikin mamaki,

  Almustapha,ne yai,  mai dan bayani a takaice sai yabimu da wani irin kallon mamaki har muka bace mai da gani,

  Danaga mun fito daga dakin taron nadauka zai sake min hannu nane sai naji yadan kara rike min su tsam,

  Ahaka har muka shiga mota, ranshi a bace akan abinda Alin yai mai ne,

  Tafiya motar keyi sit ba wanda ke magana daga cikin mu,

    Can naji sheriff yakara kamo yan yatsun hannu na ya dan matsa su a hankali,

   Sai nai kokari jaye su,saboda nasan cewa ba abu mai kyau ba ne hakan haramun ne,,,

   Amma ga mamakina sai naji ya rike su gam yadan  daga kai ya kalle a hankali, 

  Cikin wata irin murya mai kasala yace min, haram haram kada ki haramta min abinda Allah ya hallata min pls,

   Haka na kyale shi yai ta yadda yake so da yan yatsun nawa,

   Mun kusa shiga kwanar unguwar mu naji rikon da yai min har yafi na dazu,

   Duk jiki sai naji ba karfi, daga rikon hannu sai naji, ya kwantar dani a saman kirjin shi ya rike ni gam kamar zai maida ni acikin zuciyar nashi,

   Inajin yadda zuciyar nashi ke bugawa sai wani irin tsoro da fargaba ya kamani,

  Ga driver nata tuki mota amma sai,nake ganin cewa kamar a tsaye yake wuri guda ba tafiya yakeyi ba,

   Duk na storace na shiga wani yanayi nadaban wanda ban taba shiga ba,

   Saida motar ta tsaya naji yai wani irin ajiyan zuciya madan sauti,

  Sai a lokacin nasamu ya sake ni a hankali,

  Inajin yasake ni, ban ko tsaya jiran wani abuba na balle gabun motar

    Dai dai lokacin naji muryan shi cikin kasala yana ce min Shukuran shukuran nafita da sauri,

   Bina yayi da kallo har na bace mai da gani sai yakoma yadan jingina bayan shi da sit din motar ya lunshe idon shi

   Sai yaji yadan tabo wani abu daidai inda nayashi ashe wayanane nabari saboda sauri,

   Daidai lokacin da zai dauki wayan nawa ne yaji massage ya shigo mai atashi wayan

   Batare da ya diba ba ya shiga cikin gida 

   Dakin shi yawuce harda wayan nawa, 

   Saida ya kan,mala komai yafito falo dauke da wayoyin mu a hannu shi,

   Alokacin ne yabude wayan shi don ganin sakon nidake gare shi,

   A sako na hudu ne yaga wani sako da Amal ce ta turo mai shi,

  Yabude don yaga kowani irin sako ne taturo mai,

   Photo mu da ta daukeni ni,dashi da baby asama,u, lokacin da aka haifeta zamukaita asibiti,

   Saida ya gyara zaman shi da kyau don photo ba karami burgeshi yayi ba,

   Waya na ya dauka daniyar yakaimi abina, 

   Da sallama ya,shigo dakin kwance nake rub da ciki tunda muka dawo inata gaman fidda hawayen takaici da bakin ciki may yasa sheriff yai min hakana vc.   

   Sai kuma naji muryan shi adakin dai dai wanan lokacin zubur nai niyar mikewa daga kwan ciyar da nayi,

 Zama yayi gefena tayadda babu dama in tashi zaune 

   A hankali yace min may yasa nake kuka don ya taba ni ko kuwa don ban so,

   Ya cigaba da fadin in yi hakkuri komai naga yayi da sannu zan gane manufar shi, 

  Sai dan mike tsaye tare da aje min wayana gefen bedside,

   Yace inkula da kai pls saida safe,

  Duk kan mu wanan daren ba wanda yai barci a cikin dadi don kowa da abinda yake tunawa,

   Ba komai sheriff ke tuna ne ba sai wanan photo da Amal ta turo mai photo da yasa duk hankali shi yau yakara tashi,

   Ba abinda yake bukata da muradi arayuwan shi yanzu kamar a ce matar shi tasamu ciki,

   Niko ina can ina cewa wai ko sheriff na cikin hankalin shi saboda duk iya sani nada shi ban taba ganin shi ko jin yayi wani harkan banza agabana ba 

  Sai yau ko yau din ma yana kirarin cewa wai kada in damu ,

   Hmm aiko dole ne indamu da haka naita sakawa ina warwalewa, nikaida sai Aisha dake gefena kwance tana barcin ta hankali kwance sai naji dama ace nice ke barci haka hankali kwance,,,

    

    Washegari muka wayi gari da babban bakuwa, Aziza ce tazo daga Dubai don ita yanzu can tafi zama, da tana zuwa Nigeria kaida kai amma yanzu ta daina,

   Zuwan ta yasa nadan saki jikina kadan wai ni ina gudun tagane abin da yafaru ni da mijinta,.

    Sai har yanzu ban iya hada idona sam da sheriff saboda wani irin mugun kunyar shi da nauyin shi nake ji sosai walahi 

    Da ina da dama dana koma madina in karasa hutuna acan don zaifi min

   Shiko ina lura da shi da munda hada ido ko nai wani dan motsi sai yadan wani lunshi idon shi,

   Don hakane ma na koma daki abina ban kara fitowa ba,

   Photo da Amal ta turo mai ne ya dauka yake nunawa Aziza yana mata bayani akan photo,

   Saida ta kalli photo tsab sai wani tunane da tadade tanayi ba mafita yafado mata a rai 

   Cikin wani irin yanayi ta dan gyara zaman ta don taji dadin yin nazari akai


🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈

          👣👣👣👣👣

            👣👣👣👣👣

                    6⃣6⃣

                      *BY*     

🐎 *ZAINAB *IDRIS**MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP 🐎


   Almost true life story,,,,


     Tabbas wanan yarinya yakamata ta taimaka mata, badon komai sai don hakan zaifi mata sauki da rufin asiri,

   Ganin da tayi cewa sheriff din mu yayi barci mai nauyi yasa fito daga dakin 

   A cikin duhu take tafiya saboda kashe duk wani haske dake falon da akayi 

   Saboda koyi da,sunnan maikin manzo sallalahu alaihim wasallam,

     Sai yanzu nake jin yuwa na dan damu , dama bani abu bane abinci drink's ne nake yawan sha, da corns,

   Don haka na tashi nafito falon gidan don inda samu abinda zan agaza wakaina, dashi,

   Dayake ahankali nake tafiya na sai naji kamar ana magana kasa kasa acikin falon don haka sai nadan rage tafiya na don jin kowaye, cikin wanan uban dare,

   Ga mamaki na sai naji muryan mace kuma da harshen hausa take magana,

   Kara matsawa nayi daidai gurin da sautin ke futowa,

   Aziza gabana yaba da dam,

  May takeyi haka acikin dare koma dai may ye sirine bata son kowa yaji ta,

  Har zan juya sai wata zicuya tace min indan dakata inji ko da kadan ne,

   Murya kasa,kasa take cewa Hindu na fada maki cewa bazan samu matsalaba ga wanan yarinyar insha Allah zata yi yadda nake so,

   Hindu tace Aziza wanan maganar ba karamar magana bace fa, maganace da ke bukatar siri acikin ta,

   Kinga ko gara mufita waje can mu samo wacce zata yi muna aikin mu cikin rufin asiri batare da kowa yasanaikin

 Sai, Muba ta kudi mu sallame ta tayi gaba in bukata ya biya,

    Azizs tace hindu wanan yarinyar itace zata iya zama dai,dai da nufin mu, baki ganewa ne shiyasa,

   Hindu, tace kidai bari mu, mukara dibawa ko zamu samu wacce ta dace da aikin

    Haka sukai ta sakawa suna walwalewa a tsakanin su,,

   Ina labe ina jin su duk jikina yai sanyi kamar in zunduma ihu,

    Ban gushe daga inda nake labe ba naji motsin Aziza alamar tagama waya zata dawo, dakin su,

  Shan jinin jikina nayi na lafe a bango, saida tazo dai kusa da inda nake labe sai kawai taja ta tsaya dai gurin,

  Gabana yafadi dam don a,zatona tagan ni ne har na rufe ido na ,nasadakat kawai ta gani,

   Shirun da naji yasa nadan diba sai naga a she, wayan take kashe,

  Saida naji takon, kafarta ta wuce har ta haura sama dakin su ta rufe,

  Nai ajiyan zuciya, da sanda na la,laba nadauki lemu na koma daki na hankalina a tashe,

  Juyi nake tayi barci ya ki dauka na, sai,  Tunane kawai nake saboda bansan kowa ni irin shiri ba ne zasu ai,watar, hakana,

   Hakana na kwana da wanan tunane cikin zuciya na sai sake sake nake tayi har gari yawaye,

  Tsakani na da sheriff tunda wanan abin yafaru tsakanin mu bamu kara haduwa ba,

  Sai na bari rana yayi nasan cewa yafita zan dan fito waje,

   Yau nasan cewa yatafi ma,ia,katar su ta Riyadh aiki, 

  Don yaune ranan zuwan shi can Riyadh din sai ya kwana biyu ko uku zai dawo garin makkah,

     Wando da riga nasa wandon jeans baki ,mai kafar pencil sai yar wata riga da nasa wanda tsawon, rigan yatsaya min iya gwiuwa na, hannu shi ma hakana ya tsaya min,

   Bakin gyale na daura a kaina, sai fuskana da ban mai wani makeup ba,,,

   A hankali na,tako zuwa falon gidan Salim na samu zaune, yana kallon wani shirin na Arabs got talents, 

   Sai Amal dake gefe tana waya cikin kashe murya kamar wacce batason aji may take fada,

    Gefen salim na zauna don muyi kallon tare, ban  wani dade da zama ba, wayana yadinga tsuwar alamar kira in agaza  mai,

  Salimat ce takirani dan ihun murna nayi don jin dadin jin ta, danayi

   Dauki wayan ina fadin maman As,mau nayi fushi gaskiya,

   Tace ,a,a haba dai fadima idan kinyi fushi dani ai ko na shige su,

   Nace kawai kin wuce, abinki ko ki tuna da mutane 

   Tace fadima kin san matsalar Nigeria har kauye saida naje gashe su, wani guri babu ko services da zan kira ki,

   Yanzu ma mun dawo kano ne shine,nace barin kira ki mu gaisa kiji motsin diyar ki,

   Munyi hira sosai har ina ce mata gaskiya na matsu ta dawo walahi ina kewan ta so sai,

   Amal da tagama waya ta zagayo ta baya na ta fisge wayan ta shiga yiwa salimat ,sheri 

   Karshe  dai taba mu hakkuri tace muna zata dawo bada dadewa ba Insha Allah,

   Saida muka natsu daga dariyan salimat da muke yi ne,

   Sai Amal ta jefo min tambaya wai fadima lafiya bakya fitowa waje duk kwana nan,

   Salim dayaji tambayar Amal sai na ji yana dan gyaran murya kamar wani mai shirin yin magana,

  Gaba dayan mu mukai diban mu gare shi, don ji ko ganin may zai ce,

   Dariya yakama yi yana ce muna ya mukr kallon shi haka, 

  Amal tace fadi dai muji may zaka ce, kada kabari a ciki ya kashe ka, kai daya,

  Sam ban gane mai yake nufi ba sai naji Amal nace kai dai kace ba ni nace,

   Aji shi a bakin ka ba ruwana,

  Kafin wani da cikin su yakara fadin watakalma Aziza ce tafi to daga sashen su cikin shirin fita, 

  Daya daga cikin wasu saitin kujerun da ke can gefen mu ta zauna a saman guda, 

   Waya takeyi tana wani murmushi tana gyara rigar da tasa da kyau,

   Duk hankalin mu ya gurin kallon TV da salim keyi,

  Amma dai gaskiya muna kallon ta ta wutsiyar idon mu, 

  Tundai ni da na ke fargaban shirin da naga tana kokarin aiwatar wa, a boye,

   Muryan ta na tsinkaya cikin murmushi take magana daidai lokacin ta taso daga inda take zaune zuwa gurin da muke,

  Cikin murmushi take cewa fadima unguwa za mu tafi yanzu , Ahmad yace kece zaki rakani ko tana fadi tana wani kashe ido irin na yan duniya,

   Gaba na yadan fadi don jin abinda tace 

  Sai kawai na tuna da abinda naji tana fadi a waya,

   Ganin da tayi kamar ina  dan tuna ne yasa tace min ko baki son fitar ne yau, ai sai in fasa har zuwa gobe

  Sai mu fita ko, takalleni tana wani kashe murya 

  Saida nadan yi ajiyan zuciya saina ce da sauri, haba, haba,

  Ai kawai muje barin dan sa asshifal dina a sama kawai,

   Nakoma daki nadauko wata sabuwar Asshifal, baka mai kyau na za saman jikina nada nan nagyara daurin dake kaina ya koma rolling sai na aza dan gyalen wanan Asshifal din saman rolling din kana gani na kasan nayo shigar mutanen musuluman kasar, Sydney 

   Ina fitowa falon inda take jira na muka hada ido da Amal saita sakar min wani irin uban harara,

  Cikin larabci tace min indai bi a hankali da wanan

  Murmushi kawai nadan yi mata don kada aziza ta gane cewa da ita mukeyi,

  Yusuf driver ne zai ja mu, muna shiga mota sai tace min ince mai kada yai tuki sosai yabi da ita a hankali pls,.

  Haka ko yakama tuka motar a hankali yake tukin ,

   Naima yusuf magana nace yasa muna ki,ra,an Shuriem don ina son kira,ar shi sosai,.  

   Idanuna nadan lunshe ina sauraren kira,ar ina kuma bin shi a hankali, sai ina tuna ne a gaskiya ba abinda yakai alkur,ani dadin sauraro,

   Muryan Aziza naji tana cemin acikin hausa shagon, saida kayan masu kyau zamu fara zuwa idan mun gama sai mu tafi wurin gyaran jiki ,,

  Sabon shagon da aka bude a cikin Bin,Daewood na kai ta sainaga duk ta rude saboda kyau wurin 

   Komai akwai acikin shi shagone tundaga sama har kasa sai inda idon ka ya tsaya, da gani,

  Ganin cewa danayi gamu cikin massalacin Ka,aba ai yakamata mudan yi koda nafilla raka,a biyu ne kafin mu wuce,

  Nace mata idan mun gama sai mu tafi muyi sallah da dawafi, ko

  Saida ta dafani tana murmushi tace min idan munce mu tsaya yin dawafi ai zamu makara da zuwa gurin gyaran jikin mu ko,

   Sororo nayi saboda mamakin ta, ga wasu can nason suzo kota halin ka,ka 

   Allah bai basu ikon zuwa ba, ita gata tasamu har tana barin damar ta a banza,

   Haka nabi  bayan ta da mamaki fam a cikin zuciya naita

    Saidai ina ta jiran inji ko zanga wani abin da yashafi maganar da naji tanayi a waya ranan

   Sai banji komai ba shiru,,

  Hakan yasani nadan sake jikina da ita

  Munashiga shagon kayan kyalkaylin mata, sai, tafara jidan kaya masu kyau 

  Masu kuma tsada hatta su undies sai da muja jido su kamar hauka,

  Har zan shiga wani shagon saida kayan kamshi sai ta kirani,

    Da sauri nadawo wata riga ce mai masifar kyau irin tamu matasa yan mata,

   Kala kala different design masu kyau, kowani da gyale ko wani abayan hada shi mai kama da alkyabba,

    Cikin sha,awa tadinga gyada kai, tana, yaba kyawon kayan tana cewa wanan kan sai ku yan mata, fadima,

   Ina kallonta takwashi kusan guda biyar kala kala,

   Ina tsaye gefe ta biya kudin kayan ,mamaki kawai nakeyi irin yawan kudin da naji an ambata akan kudin da mukayi sayayya haka,

   Saina tuna cewa ai ita,

 matar sheriff ce fa ita dole in ganta da kudi hakana,

  Muryan ta naji tana cewa Sannu fadima na gajiyar da ke yai ko,

   Na gode kware ki ji bayau ba ina son fitowa inda zaga gari rashin samun abokin tafiya ne yasa ban fito,

   Saida Ahmad yace min in je dake ai kin san ko ina a garin ke,

  Tace sai kuma ban samu fuska agurin kuba kin san dangin miji tundai Amal na fuskanci bata ra,ayina takare maganan cikin muryan tausayi

   Nace a,a haba dai aiko muna son ki sosai kedin ai matar,yayan mu ne kin ga ko dole mu soki, 

   Tunda muna son shi, aidole muso duk abinda yake so ko,

   Cikin nishadi tace min kai amma kuwa yau naji dadin zancen ki walahi 

   Ban san cewa haka zan samayki ba ai da tun tuni mun dade da shakuwa a tsakanin mu,

  Rashin ganin fuskan da banyi ba ne agurin ku yasa ko zama ban son yi wurin Ahmad,

  Bansan lokacinda da wata yar dariya ta subce min ba nace kai haba hjy saboda mu zaki ki zuwa gurin mijin ki. 

   Muda ba ma,a garin muke ba, saida irin haka in munzo kawai, sha mudan wuce, abin mu,,,

  Tsayawa tayi tana min wani kallo cikin mamaki tace hai fadima,

   Fadima kema kinsan cewa gurin ki kawai nake dan samun sauki acikin ku muryan ta yai wani rau, rau kamar zatayi kuka,

   Ban iya cewa komai ba don tabani tausayi harga Allah,

   Haka muka karasa har inda muka aje motar mu a bakin tin da ke gefen haramm,

  Daga nan muka wuce wurin gyaran jiki,

   Ga mamaki na nadauka ko itace kawai za ai mawa sagashi dani da ita duk an muna

  Nakoma kamar wata yar bakaken indiya komai na sur mace da nake da shi yakara fitowa tsab ajikina,

  Tun a mota Aziza ke yaba irin kyaun da nayi sai murmushi nakeyi kawai don nasan cewa ba karya tayi ba ,,

   Saida muka kusa shiga unguwar mu ne take ce min duk fa ke na siyo ma wayan nan rigunan ,

  Cikin mamaki na,kalleta nace ,a,a aikin san cewa bani kadai bace sai dai ni da Amal ,

  Sai ga tadan bata rai kadan can kuma tadan sake ranta tace kece kika rakoni kuma kedai na siyawa ,

  Ba matsala zan raba da ni da ita kin ga tasamu albarkaci na aiko,

   Har muka kara gida tana min hiran jin dadin da tayi na ganin nasake jiki da, ita,

   Ko ba a fada ba nasan cewa Sheriff din mu yadawa daga tafiyan da yayi taniyar yin kwana biyu a babban headquarter kasar saudiya watau Riyadh,

   Da mamaki nakai kallona ga motar shi da naga yana yawan shigarta,

    Kamar Aziza ta gane  mamakin da nakeyi azuciya sai tace ashe har sun iso don dama yau ba zai kwana a can ba don suna da wani meeting da ma,aikatar su gobe, Insha Allah,,

   A falo muka samay su duk kan su har almustapha sun baza wasu takardu a gaban su suna dibawa,

   Sallaman da mukayi ne yasa kowa dagowa kai don yaga ko suwa ye,

   Dammm gaban shi yafadi saboda ganin da yayi ko yaushe kara canzawa kawai nake yi,

  Cikin kwarewa da shagwaba take mai magana, har ka iso Sweet habibi,

   Kai kawai ya kada mata alamar eh , ga kaya ahannu mu niki  niki ta,isa inda yake tadan man na mai kiss a tsakiyan goshin shi,

   Sai ta,Zube saman kujerar dake gefen ta tana cewa wassh Allah na duk nagaji wallahi,

   Aikin da sukeyi yadan aje gefe guda yadan kalle ta yace,

  U are to lazy, wanan dan fitan da kikayi kike cewa wai, kin gaji,

   Suna juna wani irin kallo cikin shaukin so,,

   Kayan nazo gaban ta na zube gefen kujera datake zaune,

   Kai yadago A,hankali ya bini da kallo sai kuma yawani lunshe idon shi a hankali kamar maijin barci , 

   Kamshin turarain da yaji ina yi duk yakara rikida shi,

   Kamar mai rada yace mata wai har ina kukaje ne haka yau kuka kwaso wanan kayan mai yawa,

  Ke kaya basa isan ki dai ko nuna ni tayi da hannu ta guda tana cewa yau ai duk kusan sayayyan ga mai su can,

  Muna hada ido da Amal takara sakar min wata uwar harara da yafi nadazu,,,

   Ida nake tsaye ina,sha wata uwar harara daga Amal yadan kalla lokacin kuma hararan da Amal take min yabani dariya,

    Sai yayi sa,a ina dariya a lokacin, Abinda yadade baigani ba ke nan tun ina yar karama a Riyadh lokacin da nake shiga cikin ruwa ina wasa agidan shi,

  Murmushi ne ya subce mai ba shiri saboda tunawa da yayi da wanan lokacin 

  Saboda yaga yadda nake wasa daruwa har dawo yakeyi ya tsaya ta glass din falon shi yana kallo na ,,

  Saboda haka kawai yaji in burge shi dan banda tsoro ko fargaba kai tsaye nake abina,,,

   Aziza ce tace min inzo in kwashi kayans intafi dasu,

   Tazabe duk wanin abinda take bukata daga ciki tabar min sauran tarkacen da rigunonin,

   Da alama sheriff yaji dadin hakan da tayi har cikin rashi yace mata

   Kai amma dai wanan fitar dama na tane ko ,

   Tadan rausaya kanta tace aikasan dole in saya mata tunda har ta bata lokacinta ta rakani batare da nuna gazawanta ,,,

   Ina kwasan kayan gurin Amal na nufa direct dasu nara dai dai nace mata ta  zabi duk wanda take so tabar min kashi guda,. 

   Dariyan yake tayi ko shi  don yayanta ya gurin ne don kada yace wani abu da bata karbi kayan ba,

  Amal tace a,a ki bari kawai in dauki wanan,

  Wani dan  rigar barci kawai ta dauka,

   Tundaga wanan ranan wani irin shakuwa da amin taka ya shiga tsakani na da Aziza ,,

   Amal tai min fada taimin nasiha tace inyi hankali da ita don yar duniya ce,

  Badan Allah take so na ba ita tana ga da wani manufa take jana ,a jikin ta,

  Sai naga cewa kawai, kamar dai don basu ra,ayinta ne kawai,


  Yau shiru tunda safe banga Aziza ba a waje  ganin da nayi cewa anytime tafito sai ta nemay inda nake ,

  Yasa da banganta a waje ba na hausama zuwa dakin su,

   Kwance take rub da ciki nai sallama a hankali ta ansa min ,

  Tajuyo daga rub da cikin da tayi kwancen, sai naga fuskan ta ya kunbura idon ta da almar tayi kuka ma,i,shin ta,

   Subbahanallah nace da sauri na isa gurinta ina mai kokarin dafa ta,

  Nace cikin rawar murya hjy mai yasa may ki ,ko baki da lafiya ne,

  Duk lokaci guda na sako mata wanan tambayar a jere da juna

  Girgiza min kai tayi kamar karamar yarinya,

  Ta, bude baki da kyat tace min babu ko daya 

Fadima

  Matsalata tafi karfin fahintar ki kona fada maki bazaki gane ba saboda,

   Ke yarinyace, shiru nayi kamar ina na,zari, can nace to amma anty aiko banza gane ba ai zan yi kila taimaka maki ta wani hanya ko,

  Saida tadan shere wani hawaye dake shirin fito mata daga cikin idonta, ta hade miyau da karfi sanan ta mike da ga zauna 

    Hannaye na takama duka biyu ta hada wuri guda tace Fadima inda zaki fahince ni da kin san cewa muna cikin tashin hankali dagani har Ahmad saboda matsalar da ta samay mu,

   Sai duk naji na matsu da insan kowata irin matsala ce haka wadda har yasa wanan jarumar matar kuka haka ,

   Dan Allah hjy ki daure ki fada min koma maye ko zan san abin yi pls,

   Fadima muna cikin matsala rashin haihuwa nida Ahmad munje asibiti likita yace bazan iya daukan ciki ba,

   Sai kuma tasa kuka wi,wi,

  Sai naji duk hankalina yatashi,, saboda wanan maganar ba karama bace ga duk wani mahulukin da yasan ciwon kanshi,

   Tana shere hawaye taci gaba da fadin ,sai wanan test din da mukayi na karshe likita yace muna inda zan samo wata wacce zata taimaka min asa mata cikin ma,ana ai mata dashen cikin

   Idan ya fara girma sai amayar min da abina yace yana ganin haka zai sa in samu baby,

  Kinga kuma shi Ahmad baya ganin laifin kanshi sai nawa kinji halinda naje ciki fadima, tanayi tana kallon fuskana don taga irin re,action din da zan nuna,

   Fuskana fal da tausayin su ban san lokacin da nafara kuka ba ,wi,wi, nima don ba karamar magana bace wanan,

  Mutun kamar sheriff ace ba zai haihu ba, treble,,

    Muryanta naji tana cewa amma fa kada ki fada ma kowa wanan sirinane da mijina na fada maki,

  Saboda yarda da nai miki yasa har na fada maki sirina,

   Hmmm hmmm

  Wani sabon kuka nasa mai tsuma rai an muka rugumay juna mukai ta kuka har saida muka gaji,

  Nakoma dakina fam da tunane da tausayin su,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈

           👣👣👣👣👣

            👣👣👣👣👣

                    6⃣7⃣

                      BY

🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


  Almost true life story,,,,,


    Cikin dare na kasa yin barci mai nauyi saboda yawan tunanen da ke ta addabata,

  Juyi kawai nake yi ina faman ajiyan zuciya  da dan guntun tsaki,

   A, gaskiya na tausaya ma sheriff din mu so sai yanzu ace duk tausayin shi da mutuncin shi bazai haihu ba,

  Ashe haka wasu Allah ke halittan su, batare da haihuwa both miji da mata,,

   Saboda ni nadauka cewa mutun guda akan ce baya haihuwa mijin ko matar,

   Amma su sai,gashi wai duk kan su case din su gudane,

   Babu mai karfin haihu daga cikin su,

  Dan sanyin da naji shine cewar da tayi idan an yi dashen cikin za su iya haihuwa insha Allah,

  Kwancin bai min hakan yaban damar mike na shiga bathroom na dauro alwala na fara nafila ina fadin bukata na, a wurin Allah,

   Nafilan nan da nadan samu na gabatar yasani jin sanyi a zuciyana ,

   Har na dan samu barci maidan nauyi yadauke ni zuwa asuba ,

  Hakan ne ma yasani makara da sallah asuba,

Saida gari yadan yi haske nafar ka zubur da salatina a baki,

   Saidai duk jikina ba karfi hakana naje nadauro alwala,

   Ina zaune inda na sallamay sallah asuba ina ta kwarara ma sheriff da iyalin shi addu,a,

   Shawar da na yanke tun cikin dare shi na yi niyar aiwatar wa,

   Amal na dakinta kwance nafito nace mata zan je masjidul nana Aisha ,,

   Da mamaki ta kalleni daga kwancen da take tace min tunda safe haka,

   Murmushi nadan yi mata, nasamu gefen gadon ta, na zauna ina gyara belt din takalma na,.

   Ido takura min har na kare daura belt din sai tace min may ke damun ki fadima,

  Cikin dan basarwa nace mata kamar ya fa,

  Hmmm kawai tace min,

   Sai kuma tace bana son ki sa kanki acikin fitinar da ba zai amfane kiba, wlh

   Saida na mike tsaye da kyau nace mata ba wani fitinar da nasa kaina, aciki Amal kece dai ke hasashen hakan,

   Amma for me ba komai ina fadin haka na sa kai nabar dakin 

  Zuwa masjidul bai dauki wani lokaci saboda sanin hanyoyin da na yi acikin sauki,

    Ina isa nai addu,a na dauro niyar umrah nadinga addu,a da larabci, da hausa kai har mada turanci duk na hada ,

   Saida na gama dawa,fi, nadawo daidai saitin indararon nan naita zuba addu,a 

   Saikuma na koma daidai kofar dakin naba mukamin ibrahim baya, nadinga kwararo addu,a agurin,

   Dalilin dayasa nai haka gurin hjy Laila nataba ji suna hira da hajiyar mu cewa indan mutum yana neman haihuwa koda dan uwan shi ne keson haihuwa,

  Sai yaje yayi dawafi, ga bakwan karshe saika dada addu,a agurin indararo saboda anasa rai cewa guri ne da duk abinda ka roki ubangiji agurin zai ansa ma insha Allah,

   Indan ka gama sai ka dawo daidai saitin kofar shiga shi ai,nihin dakin ka,aban ka tsaya tsakiya, inda hali ka dauki ruwan zam,zam kayi wanan dawafin da shi,

   Karoki Ubangiji Allah bukatar ka insha Allah Allah zai karba ma mutun,

  Wanan ruwan zam,zam din sai kaba wa wace ko wanda ke da lalurar haihuwa ko wani ciwo yasha ya shafa tare da bissimillaj,

  Sanin danayi cewa Aziza bazata sha ruwan ba kila ko nakai mata yasa ban dauki ruwan nayi mata dawafin da shi ba,

   Saidai addu,an da na tsaya tsakanin mukamin Ibrahima da kofar dakin ka,aba nayi na Allah yataimaka ya bawa sheriff din mu haihuwa mai albarka a rayuwan shi,

   Tare da kwararo wa sauran al,umman musulumi a ddu,a,

   Daga karshe na tsaya daga can gefen yamma kadan nadibi ruwan zam,zam nasha sai nayi nafila raka,a biyu 

   Nagode ma ubangijina subbahanahu wata ,ala,

  Dana gama nadade gurin zaune na zubawa dakin ido sai naji wasu hawaye masu dumi suna zubowa daga ido na,

   Nadade a hakan sannan natashi nasamu guri na zauna a gefe guda,

  Ranan anan nai sallolina har i,sha,i ina gurin,

  Sai da dare na zo hanya don in tare taxi zuwa gida sai na dinga jin hayaniya,

  Ko ban waiga ba nasan cewa yan bagaladine ke kokarin kama wasu daga cikin yan yawon takari,

   Hakane ne kuwa don dai daga inda nake inajin muryan su sunacewa Nigeria,

  Duk da hayaniyar da akeyi agurin bai hanai jin kuru,ruwar matar da aka kama ba

   Azuciya na ,na,ce ya Allah yasa mutanen mu su daina wanan kazamin da bi,ar , tazuwa yawon takaru ba lasisi shiga kasar,

   Idan ma mutum na so za,s iya bashi, lasisi idan har yabi ta hanyar daya dace,

   Saida na ji cewa ni a halin yanzu zan iya zuwa ko ina saboda ina da kardan zama akasar ,,

   Wanda bakowa ne yai min wanan hanyar ba sai sheriff Ahmad Lawal Zanna,

   Zuciyata jinta nakeyi tai min shakat kamar an cire min wani nauyi acikin ta, 

   Haka na dunfari gida cikin wal,wala da sakin fuska ba wani damuwa atataredani,

    

    Har kusan karfe shida sheriff baigan ni ba kuma baiga, na fito waje ba koda ko falon gidan ne,

    Duk iya kannewar da zaiyi yayi har dai yakai ga tambayar Amal cewa yau bai gana fito ba koda sau dayane waje, ko lafiya nake,

    Sai wannan lokacin Amal ke mai bayanin cewa tunda safe natafi masjidul

  Kuma dama nace zan dan dade yau ban dawo ba,

   Don haka lokacin da na iso gida suna zaune shida Aziza saman dinning table suna cin abin dinner,

    A hankali nayi sallama cikin katafaren falon gidan namu wanda ba lalai bane wanda ke ciki yaji muryan mutun da ga kofar shiga,

  Ganin da nayi masu zaune su biyu suna cin abinci yasa nayi niyar wucewa batare da na gaishe suba,

  Aziza ce tafara gani ,wanda a zahiri ba haka abin yake ba, sheriff yarigata gani na sai yai wani irin sanyayan ajiyar zuciya,,,

   yadai daure ne yai kamar bai gan ni ba , don alokacin inda ban dawo ba da saura kiris yaja almustapha suje bida na,

  Aziza ce ke min fadima yau ina kika shigane haka tunda safe naje dakinki yafi sau biyu ban ganki ba,

   Naso mudan fita zuwa  cikin gari kadan,

  Saina dan yi mata murmushi yake kawai badon komai ba sai wanda ke gefenta dake min wani kallo 

  Da ban iya cewa ga irin shi ko ma,anar shi,

    Bangaren da nake tsaye yadan kalla yace min ina tafi ,

   A marairaice kamar mai shirin kuka nace mai masjid natafi,

   Yar karaman harara yasakar min  yana kada spoon a plate yace, 

   Oho ashe yanzu duk inda kiga dama saiki sa kai kawai ki tafi batare da sanin kowa ba,

   Nankan shiru nayi masa don banda ansan da zance duk da dai na fada ma Amal cewa zan fita,

   Yace je ki duk abin da kiga yafi maki je ki yi tunda ba ki under control din kowa,

   Jiki ba kwari batare da kuma na iya cewa yayi hakkuri ba na shige ciki, abina,

   Tunda dai nasan cewa ba wani mugu wuri naje ba,

 Ina shiga daki,na  Ko Nanfal dina ban cire ba,Amal tashigo dakin tana cewa

   Gaskiya yau fadima baki kyauta tun safe fa kika fita duk da nasan cewa ga inda kika tafi ai bai kamata ki kai har dare haka ba,

  Don nagajarce zancen ko zan samu saukin bacin ran da naji nace,

   Amma dai Amal na fada maki ai kafin in fita ko,

   Kafin Amal tace wani abu sai naji murywn sheriff yana cewa 

  Don kin fada ma Amal ni kin fada min ne ko,ko zaman Amal ki keyi a nan,

  Kaina yana kasa don ganin da nai wa sheriff tsaye a tsakiyar dakina

  Yacigaba da fadin idan wani abin yaje yasa may ki can fa ya kike son muyi

   Ace tun safe mutum yabar gida sai yanzu yana mai diban agogon hannun shi,

   Acikin sanyin murya nace mai dan Allah kayi hakkuri bazan sake irin haka ba insha Allah,

  Ido yadan kura min nadan wani lokaci kamar mai nazari na tukun sai kuma ya juya yabar dakin batare da yakara magana ba,

   Dagani har Amal wani irin ajiyan zuciya mukayi na fargaba,

   Amal takai zaune saman gadona tace min gaskiya Fadima yau kin batawa yayan mu rai sosai wlh,

   Yayi fadan fitar ki ke kadai batare da kowa ba yace wai laifina ne da nabari kika fita kedaya ban hanaki ba,

  Murmushi nayi nakai zaune ina cewa haba dai sakace wata bakuwar gari ,

 Bace wa zan yi halan,

   Kada dai ki kara irin wanan halin pls,

  Kofar dakin aka turo maman Umar ne dauke da abinci kala kala cikin wani dan keken tura abinci zuwa dakuna,

   Cikin mamaki naje cewa may yasa takawo min abinci har daki aida tabari infita waje in diba ko,

   Dukawa tayi tafara zuba abincin tace min sheriff yace mata ta tabbatar da naci abinci kafin in kwanta,

   Amal dake zaune gefe na tadan tabe baki tace kaji yar gatan yaya ko har da abincin ma sai yasa a,yi gadinki har ki ci ko,

     Maman Umar tace ai hakan yana da kyau don kinsan cewa fadima ai zaman amana take gare shi kin ga ai dole ya kulata,

  Taciki abinci kala kala aplate tamiko min daga inda nake zaune a bakin gado na,

   Kawai don tace min ance mata sai naci shiyasa nadan tsakuri abincin kadan,

   Nace mata na koshi saidai fruit salad din duk munsha har Amal din,

    

     Nasan cewa yanzu sheriff yana falon shi yana tura sakonne a system din shi,

   Duk dare sai yayi wanan aiki in da duk yake  

  Hakan yabani damar fitowa don in kara bashi hakkuri kamar yadda Amal da maman Umar suka ce min

   Dogon rigace ajiki tunda nafito wanka na sauya ta,

    Sai plat shoe's ne akafa na shi ma baki mai photo yar kwakwa karama kamar buzubuzu haka,

    Ganawa wautar na manta cewa da ba yanzu bane don haka ko mayafi ban dauka ba , tunda naga cewa ai a cikin gida ne kuma sheriff ne fa wanda yasan ni tun ina yar karamana,

    A hankali na tako har inda yake zaune saidai ba sakon yake turawa ba shiru yayi yarike gefen habar shi da hannu guda da alamar tunane yake yi,

   Jin motsin da yayi a bayan shi yasa yadago a hankali yadubi gurin da yaji motsin,

   Sai mukayi idi biyu dashi, amma sai naga kwayar idon shi ya kada yayi ja sosa,

 Da sauri batare da tunanen komai ba nace subbahanallah ,

  Barci kakeji ne, nasa mu kaina da tambaryan shi,

   Shiru nadan wani lokaci bai ansa min ba,  

   Saidai yadan girgiza min kai kawai,

  Ikon Allah saikuma nakara cewa kana ciwon kai naga idon ka ja,

  Murmushi yau sherie din yai min da alamar tambayar nawa ya bashi dariya 

   Yana mai kura min ido shi ja da suka rine yace, min,

   Bawa ni ciwon kai illa keda keson ki tarwatsa min kwakawalwata, fadima har ke zaki fita kibar gida tun safe har dare baki dawo ba,

    Cikin sauri nakai durkushe a kasa nace mai kayafe min dan Allah insha Allah bazan sake ba,

  Da wata dakusarshiyar murya ya ansa min yace gaskiya baki kyauta min ba fadima,

   Kaman zan yi kuka nakara cewa ya yi hakuri pls,

    Kafin yai wani mafana sai mukaji muryan Aziza abayan mu tana cewa haba dai habibi,

   Ai tunda har ta bada hakkuri takamata ka yafe mata hakana pls,

   Tazo inda nake tsugune tadan dagoni tace mai haba dai ai koda laifin da tayi yafi haka yakamata kayi hakuri ,,

    Kujeran dake gefen shi ta zainar da ni tana mai dan jan shi da hira irin ta masoya duk da na lura bai son ansa mata sai dai yace eh, ki uhum atakaice,

     Saidai takan dan jefani cikin hiran nasu jefi jefi,

   Hira sukeyi abin su, cikin kwanciyar hankali, a,takure nake a cikin su kamar wace a ka tsure,

   Amal ce tafi daukan cup a kitchen tagan ni zaune acimin su,

 Daman hanyar gudu nake bida,

    Aiko ina ganin ta na mike ina mai yi masu saida safe ,

   Aziza ce ke ce min kin gudu ke nan fadima baza ki zauna muyi fira ba ke nan,

    Kada ki manta cewa gobe tunda safe nake son mi fita,

    Kafin ta kai karshen zancen yatare da fadi ba inda zan fita kuma, tunda nafita yau,

   Da mamaki take kallon shi tace mai ai guri. Gyaran kai kawai zamu tafi 

    Nidai ban san ya suka karasa ba na wuce nabar su, abina,

  Washe gari ina son indan motsa jikina sai na fada kitchen wurin masu aiki tare mukai aikin da su 

   Najera komai a dinning table din  falon ,kamar yadda nassba yi da kafin intafi school,

   Lokacin da sheriff yadawo gida shida almustapha, direct sashen shi yanufa 

  Saida yan gyara jikin shi yarage yawan jayan dake jikin nadhi bayan ya watsa ruwa, 

   Sai yafito ,wurin abinci ya nufa don shi  baya cin abin a waje ko ya ya kyau abu yake sai dai wanda aka girka agidan shi,

       Don haka da yadawo yai wanka yadan kintsa kafin yai komai sai ya fara cin abinci tukun

   Zaune suke da Aziza sai salim da ke tare dasu Amal tunda aziza tazo takaurace ma yawan zama falon sam,

   Acewar ta wai aziza batai mata ma,

   Wai ruwan yan duniya ke ga aziza, 

  Don hakane ma bata son irin yadda taga inayi da aziza din,

   Cibin farko da yakai bakin shi sai ya tsaya cak ,

   Duk wanda ke table din sai ya bishi da kallon mamaki komai yasa ya dakatar da cin abincin ,

   Fadima ya furta a hankali Aziza ta ce fadima ya ce na,am sai tadan fara waigawa kozatagan ni afalon, 

   Ga mamakinta batagan ni saitace mai yafaru da ira,

  Cikin murmushi yace mata ya akagi tashi kitchen  ai muna girki,

  Aziza tace kamar ya don ban fahinta ba sai yace mata, wana girkin nata ne,

   Har suka kare cin abincin tana mamakin shi,

    Wani irin shakuwane a tsakanin mu haka ace har da girki in nayi zai gane,

  Dan murmushi tayi maikama da na mugunta,

  Batayarda ba sai da taje kitchen din ta tambaya suka ce mata tabbas nice nayi girkin

  Dakina ke ina kokarin jona waya a cikin chaji naci kam shin turan sheriff a dakina ko ban diba din ba shi,

  Ya saye da jallabiya mai ruwa assh colour, 

     A bakin kofar dakin ya tsaya yana karewa dakin kallo kamar yau ya fara shigo,

   Tambaya ya jefo min da ga inda nake tsaye,

  Ya akayi nai,cooking yau agidan nan,

  Cikin mamaki na dan kallo shi nace mai cinkin han kali 

   Kawai dai nayi ra,ayin yin hakane, 

   Saida yadan dade tsaye yana min wani irin kallo mai kama da kallon sha,awa, sai nai sauri nadan waiga in ko may yake kallo a jimina hakana,

   Hakan da yagani sai yai saiuri ya juya yabar dakin,

  Mamaki wanan sauyin na sheriff nake ji saidai gaskiya ban wo komai araina ba,

   Sai kawai na shere zan ce,,,naci gaba da aikina

    Waje muke kusan duk kn mu gidan muna shan iska ne saboda mudan shakata,


 Salim na badminton shida sheriff a gefen can nisa da mu, kadan,

   Wayan aziza yai kara dai dai lokacin da Amal ke shirin tashi zuwa cikin  gida tadauko drink da ma nice zan tafi sai Amal tace min wai in bari ta,tafi don zata danyi wani abu acimi dama,

   Hinduce mai kiran saina dan tashi cikin dabara nabar gurin don kada in takura masu,

   Bayan sungaisa take tambayar ta ko tagama plans din datakeyi sai tace mata tana dai gab da gamawa,

   Sundanyi hira kadan takashe eayan lokacin da taga Amal tafito daga cikin gida da tuen kayan drinks ,

    Amal naganin ta kashe waya tace azuciyar wanan akwai kakar mata ganin da taimin zuwa yasa tajadhe eayan sherin da takeyi,

   Fuska a sake take min zancen wai kawar tace bata da lafiya a dubai tana son kafin mu koma indan tafi in rakata indawo 

   Don yanzu idan tace ita kadai zata sheriff ba zai yarda ba,

  Amal ta kalleni don ta ji mai zan ce sai taga na shiru bance komai ba, har muka tashi, dagurin shan iskan,

    Adaki kamar Amal zataciyeni danya, saboda bacin ran da tanuna min,

   Saida nabari ta gaba,

Cikin ruwan sanyi nace mata,

  Amal nidake ba daya muke a gidan nan ba kituna cewa fa niyar aiki ce bai wata shakikiyar maigidan nake ba, kamar ki taimakone kawai Allah yaza mai yai min harkikaga ina zama ahaka daku,,

   Shiru tayi tana nazarin magana na nace kin san cewa aziza mata sheriff ce kina ganin cewa zata sani abu  ko tasao in mata abu in ce a,a,

    Saboda haka kin ga dole in mata biyayya ke kina da damar dazakiyi mata komai don ke yar uwan mijintane,,Sabanin ni 

    Duk da haka kibi a hankali don wana yar duniya ce sosai,

   Koda Aziza ta fada ma sheriff cewa tare zamu tafi, saida yai dan mamakin hakan 

   Irin shakuwar da yaga mun yi abin na dan bashi  mamaki arayuwan shi,

 

     An muna shirin komai na zuwa dubai nida Aziza Amal jitakwyi kamar ta kamani tai min dan karen duka,

  Rabona da shiga jirgi tun lokacin da muka shigo kasar saidiya da yan uwa na sai gashi yau kwasan  tafiya yakamani,

       Hjy hindu wata iri garmakekiyar mace ce ga tsawo ga kiba, muryan ta irin dan shakakken nan ne,

   Ana ta kain i gurare ina ta dauka photo kusan duk inda naje,

  Saidai guri wani likta da ta, ce min in rakata,,

 Likitan indiya ne yanata turanci kusan maganar shi sai naji kamar ai yashe fe ni sosai

   Ama da muka fito sai take ce min doctor yace dazata samu yar matashi kama zai san dabar da yayi yataimaka masu 

   Saikawai tasa min kuka acikin motar wai ita yan inda zata samu wace zata taimaka mata ai mata dashen shi take naima,

     Ita bakomai ba sheirriff take tausayi,

  Har muka kawo gida ina tunane mai zurfi araina 

   Nace idan ban yarda bafa watace can za,a dauko ta taimaka watakila ba mai halin kware bace tazo ta haifa ai bala,i,

   Tana falon zaune na samay ta zaune a hankali nakira sunan ta nace mata hjy insha Allah ni zan yarda  intaimaka maki ai min wanan dashen

      Jawoni tayi ajikinta tana murna da magana na da na fada mata harda kukan  taba fayce majina

      Sai godiya take zaga min wai ta gode da rufin asirin da zan mata,


🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈

        👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                  6⃣8⃣    

                     BY   

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎  

🐎  HUGUMA GROUP🐎


    Almost true life story,,


     Saida ta tabbatar da cewa komai ya kanmala ga duk wani shiri da suke aiwatar wa,

   Acikin shewa suke ta hiran su tafawa kamar ea yanda akaiwa bushar da gafara,

   Saida Hindu tadan kurbi drink din dake gaba tukun sanan ta aje cup din saman table ,

    Takalli Aziza wace take kokarin zuba nata drink din a cup ,

    Tace mata wlh Aziza ban ta dauka wanan maganar, zai zo muna a cikin sauki haka, ba,,,,

    Itama din kurban drink tayi tana lunshe idon ta a hankali,

   Saida ta kara kurbawa sanan ta,aje cup din gefe,

   Tace hindu Allah kawai yatai make akan wanan yariyan don kinga bawai kwadai bane ko ko ne man guri ,a,a 

   Hakatake, kwai wai ita sarkin tausayi, da wauta, idan ba tsabar wawanci ba da rashin wayo 

   Ko a ina ta bajin cewa, an ana dashen ciki idan ya kosa acire amayar inda akeso,

   Aikawai dana samu anyi mata wanan dashe gaskiya, ninafi kowa sa,a da murna arayuwana, 

    Sai kuma idan lokacin da take tsamani, za,a cire mata, cikin zuwa nawa yayi sai kuma in samu sabon dabara in bullo mata da shi ,,

   Sukayi wani irin shewa suka taba a tsakanin su, don murna da farin ciki

   Taci gaba da cewa kima da zaran ta haihu karbe dana zan yi batare bat lokaci 

   Nasan cewa kuma dole dai yaro yai bearing din sunan uban shi da nawa,,,

  Hindu ta dan gyara zaman ta kadan tace, aina san cewa zaki iya yin koda fiye da hakane, mutumiyar 

   Tamika mata hannu suka tafa cikin shewa,


    Doctor kamal ne zaune a office din shi da cikin asibitin sarki fahad,,,

   Asibitin da  ke a kan shifidaden titin, khalifas road's

   Kujerar dayake sama tana dan juya shi a hankali, 

   Cikin dariya yake maganar shi a gaskiya Ahmad kana bani mamaki ace mutum ya zauna ya hali irin wanan kamar ba namiji ba

   Shiko dai kana tsoron matan kane baka son ransu ya baci kake wanan rufa rufan da baida anfani,

    Kadiba fa yau shekara kusan uku kenan da yin wanan auren naka, 

   In a lokacin kana ganin cewa yarinyar nan she is young yanzu fa da takai mallakin hannakilin ka,.

   Sheriff dake kokarin mike wa da ga kujerar da yake zaune 

   Yake ce ma doctor kamal ni bansan ko may yasa kake yawan damuwa da wanan zancen ba,

   Ina son kasan cewa ni ba saboda komai har na yarda a wanan lokacin aka daura wanan auren ba sai kawai don in tsirar da mutunci su daga wulakancin da ake shirin masu,

    Saboda hakan kawai zan yi in masu gata su koma gida acikin mutunci,

    Hmmm nifa tun wancan lokacin bawai nayarda da manufar ka bane,

    Ai ba kai kadaine namiji da zai iya taimakawa ba ko,

   Ina ga takaru nan yan uwasu da suke aure saboda kawai su zauna akasar sudan yi yadda suke so indan sun tashi tafiya sukashe auren kowa ya kama gaban sa,

   Wasu kuma shikenan har abada su zauna atare,

   To ni na fadama cewa don in tallafa wa wanan yarinyar yasa har na amince,

   Doctor kamal din shima mike wa yayi daga kan kujera suna fuskantar juna su,

   Cikin kashe ido yace ma sheriff Ahmad yan zufa ,

  Duk a cikin taimakon ne hakan kamar yadda nagan ku a,wurin taron African youth development found,,

   Baiyi mai magana ba har yakai bakin kofar fita office din sanan yadan waigo yana kallon doctor yana gyara kwalar riganshi,

   Yace ban san abinda yasa kake sa kan ka ga abin da bai shafeka ba yan zu kamal,

   Yabuga kofar daidai lokacin da doctor ke cewa zan zo har  gida mu karasa zancen,yafadi yana dariya,,,,

    Yana fitowa Yusuf ya bude mai mota ya shiga, suka fara hanya,

   Yace ma Yusuf suwuce zuwa gida kawai, saida motar tazaunu a saman titin ne yakai kallon  shi ga dogon agogon da yake tsaye a tsakiyar gari,

   Wanda duk inda kake cikin garin makka zaka iya hango shi a tsaye,

   Sai kuma ya dan lunshe idon shi a hankali gami da yin sanya,yaar ajiyar zuciya,

   Tinyar tinyar abin yafara dawo mashi a rai kamar yanzu aka yi zan cen

   A lokacin da matsi ya kai matsi ga duk wata takari dake zama a cikin kasar saudiya batare da lasisi ba,

   Hjy Lailai  ce tare da wani takaru na miji  sukayi mai sallama a kofar gidan shi,

  Cikin mamaki yake kallon su don yasan cewa baida wani halaka da su to may yakawo su gidan shi,

   Bayan sun gaisa ne shiru yadan biyo baya sai shine yake ce masu ko daga ina suke,

   Hjy ce ta tayi karfin halin fara magana don daga cikin su,

   Ta ce mai sun zo gurin shi naiman taimako akan yaran takarin da ke  aiki, agidan shi,

   Shiru yayi kadan yana dan sauranta

   Tace mai ansa mu wanda yaje yafada yan bagaladi cewa suna nan gidan shi,

   Shine sukazo neman taimako akan cewa suna son ya taimaka ya rufa masu asiri don idan aka gane cewa su takari ne da gaskiya za,a iya yi masu mugun wulakanci don hakane ma tazo tare da wanan Alhj tanuna wanda suke tare,

  Inda shikuma yadan gyara tsayin shi ya shiga yiwa sheriff bayani yadda abin yake cewa komai zai iya faru dasu, 

   A ,kakauce yace to may ye mafita aciki sai Alhj yace zaiyi kokari ya samo wanda za,a daura wa aure da mutun gudan su idan yaso koda za,azo sai a nuna wanan takardan kan cewa yan uwar  su ne sukazo daga kasar su yin umrah bawai zama sukeyi ba,

    Magana dai takai har Alhj na batun dukawa kasa akan sheriff yarufa masu asiri ya yarda akawo wani na miji adaura aure,

   Sunbar wurin shi da niyar cewa zasu dawo tare da mijin bizan da zasu dauko ne,

   Shine Almustapha yakara yi mai bayanin yadda abin yake sai yaga rashin dacewar hakan ,,,

   Sai tunanen shi da na hjy laila yazo daya don hakane ya yarda akan cewa za,a daura mai aure da Fadima saboda yasan cewa yar karamace ni daga cikin mu 

  In yaso idan yagama shirin yarda zai taimaka ya maida mu gida Nigeria gaba dayan mu sai ya maishe mu,

  Saikuma ya hasale min auren shi tunda dama, ba wai da sani na bane,

   A massalaci aka daura auren bayan sallah jumma,

  cikin din bin al umman musulumi da suka halarci sallah jumma,a na ranan,

    Alhj umar mai takari sarkin takarin tsakiya da Shehi mijin mahaifiyar sheriff, sune  suka zama uban amarya,

   Inda Su doctor kamal su ka tsaya a bangaren ango,

   Murmushi yakarayi saboda tuna abinda yafaru bayan dawowar su, daga wurin daurin auren,

    Inda abokan shi suka sa shi agaba akan su na son su san kowacece wanan Amaryan,

   Sai ce masu yayi su bari idan lokaci yayi na su sani zasu sani,,,

   Auren yaba duk wani abokin Ahmad mamaki saboda basu da masaniyar hakan don sun san cewa bai ko zancen aure da su, 

   Sai mamaki sukeyi ko wace,ce amaryan da basu san labarinta ba,

  Kudin sadakin da a kabayar a masallaci Alhj umar sarkin takari ya kawo ma sheriff yace yarike a hannu shi asamu abinda akayi ma amarya na samun karuwa, cigaban ta,

   Sai yaba Shehi mijin mahaifiyar shi bayan yai mai bayani duk yadda maganar yake,. 

   Don adinga juyawa kudin kafin in girma ko in wuce Nigeria,

   Saidai shi a lokacin har ga Allah taimakon mu yayi don gudun wulakanci,

   Saidaga bayan auren ne aka gane ko waye kewa yan takari wanan sherin wurin hukumomin kasar na saudiya 

   Inda shima akasamu wasu suka tona mai asiri, akan harkan saida kwayoyi, dayakeyi,,,

   Duk da auren na sheriff da fadima yana nan daran. 

   Sarkin takari yace abar shi saboda gaba zai mata amfani tunda tana cikin kasar har yanzu,,,

   Saidai yanzu ne kuma gaskiya, yake dan ji wani abu agamay da fadimar wace ada banda tausayi ba abinda yarinyar ke bashi,,,

   A hankali yai ajiyar zuciya don yasan cewa duk wanan abin fadimar bata da labari

   Saboda kafin ta dawo yasamu damar daukan nauyin hajiya mai sharwali tare da sauran yaranta zuwa gida Nigeria tare da guzuri mai tsoka wanda zasu iya tallafawa kan su idan sun koma gida Nigeria

   Wanan abin yai ma su dadi so sai inda hajiya ta roke shi alfarman rike mata amanan fadima yarinya mai kirki da mutunci,

  Saboda tayi dana sanin zuwa yawon takarin da tayi don abin bai amfana ta da komai,

   Yanzun haka yazo ganin doctor kamal kam yawan damuwar dake damun shi,

   Inda doctor yagano abin dake damun sheriff har ya sako mai zancen auren shi,,,


     Jirgin safiya muka biyo zuwa saudiya a,Riyadh muka sauka sai muka karasa garin makka kafin ayi sallah azuhur duk muna cikin garin makkah,

  Dakina na wuce don indan huta saidai kuma zuciya na fam yake da zunlumi da tunanen abinda ke gabana,

 Gashi kuma maganar siri ne ba bu damar in fada ma wani,

   Duk da basan ko ya maganar dashen ciki yake ba nasan cewa abune mai girma,

   Saidai inda nake jin saukin al,amarin shine kawai in ance indan yafara girma za,a cire ne amayar mata da abinta a cikin cikin ta

   Wanan abin zan yi shine kawai don sheriff din mu mutun mai mutunci da sanin yakamata,

   Koma maye ai dolene in sadakar da rayuwa na agare shi don in,taimaka mai kamar yadda shima din yataimaki rayuwa na ta fan,ni daban daban,

   Tunda muka dawo daga wanan tafiyan Amal tagane cewa ina cikin damuwa, sosai tunda ba haka tasan nake ba,

   Tunda ta tambaye ni nace mata ba komai tun lokacin tasan cewa bazata gane komai ba kawai ido tasa min,,,

    Ita ko Aziza ba abinda ya damay sai farinciki kawai takeyi da an,nashuwar ta,

    Aziza taima sheriff bayani cewa likitan ta yace nanda dn wani lokaci yanason ta koma tare dashi don zai dan gwada wani fasaha akasu tayadda ciki zai zauna mata,

   Cikkn rashin yarda da maganar ta yace Aziza na fada maki cewa bani bukatar wanan plan din naki pls,

   Nabarwa Allah al,amari na idan Allah yatashi bani haihuwa basai natafi wata uwar duniya ne ma har inda nake zaibani

   Kisani cewa rabon mutun bai wuce shi, idan kikayi imani da tawakkali sai ubangiji maji rokon bawan shine sai ya karba muna addu,an mu,,,

   Kuka tasa mai , maitsuma rai yadda yakasa daurewa har yabar mata dakin 

  Yafito waje,

   Ga mamakin shi sai ga alamar innuwar mutun a cikin duhun daren,

    A hankali yanufi gurin da ganin kowaye wajen zaune,,, fadima  ce zaune cikin wanan duhun ta hada kafa da gwaiwa da alamar akwai abinda ke damun ta, 

   A hankali ya furta sunan ta cikin mamaki, 

   Sai na dago kaina nimadai din cikin mamakin may yafito da shi cikin wanan lokacin haka,

   Tambaya yawatso min a gagauce, lafiya, may kikeyi haka anan cikin wanan lokacin,

   Bakomai na iya furtawa, cikin dan karamin,sautin,

  Gefen guda yasamu yadan zauna gab da inda nake, 

   Yadan kura min ido na dan wani lokaci,,

   Can yace fadima har yanzu kina akan tunanen yan uwanki ne da suka tafi, kokuwa da akwai wani abinda ke damun ki ne azuciyan ki,,

   Maimakon  inyi magana sai kawai nadan girgiza mai kai alamar a,a,.

   Kamar mai rada ya ce fadima baki da wanda yafini duk cikin fadin kasar nan,

   Amma ace kina cikin wani hali nadamuwa wanda har zai hanaki sukuni da samun barcin  

  Duk ki fada min to waye kike da shi bayan ni da zaki fadamawa,

   Ban kara cewa komai ba kawai dai sai nai shiru saboda nasan cewa duk tsananin tambaya bazan taba fada mai komay ke damuna ba,

  Saboda alkawarin da na dauka na boye wanan babban sirin ga kowa,

   Sai bayan raina, ba mai jin cewa ai nice nataimakawa sheriff, 

  Shima dai din shirun yayi har takai kamar babu kowa agurin saboda shirun da ya ratsa gurin,

    Duk sai yaji ba dadi acikkn zuciyar shi, saboda yasan cewa lalai akwai abinda ke damun wanan yarinyar sai zurfin ciki irin nata bai bari ta fadi, komadai may ye zai kokari yasa mata ido sosai ,a,al,amuranta 

   Wata ajiyar zuciya ya sauke da karfi gamida fesar da wata iska irin ta dan relief din nan,

 Yakara daga ido ya kalle ta sai wani irin tausayinta ya kamashi yasan cewa tana kokari dole ta shiga cikin irin wanan yanayin,

   Narashin kowa nata kusa da ita hatta wace takawo ta kasar ta wuce tabarta,

    A,hankali ya dan matso gab da inda nake zaune dan kalleni cikin tausayi,

    Ya sa hannun shi yakamo hannu na yadan matse cikin nashi,

   A raunane yace min kiyi hakkuri fadima da zanran kin gama karatun ki nida kaina zai kai har gaban iyayenki insha Allah,

   Yakara matse hannu na acikin nashi yace min tashi kije ki kwanta ki dan huta zan san abinda zan yi ,

   Kala ban ce ba na mike da niyar in wuce saidai kuma hannu na na rike a cikin nashi,

   Shima dai din tasowa yayi a hankali ya zo gab dani yadan matse ni a kirji shi tayadda har ina iya jin yadda zuciyar shi ke bugawa,

     Cikin sauri nayi kokarin kwace kaina daga jikin nashi, amma ina yarike ni gam,

   Saida yai ra,ayim kanshi nasamu yasake ni

   Tunda yasaakeni ban ko kara waigawa ba nai ciki da sauri, ina maida nunfashina ahankali,

  Nadade barci bai dauke ni ba tu nen sabon salon da sheriff ya bullo min da shi nason ko yaushe ya hada jikina da nashi nakeyi,

 

   Hakana nakwana cikin wanan damuwar gari nawaye nasamu maman Umar wace yanzu take min kamar yar uwata jini,

    Data saura min cikin fadin saudiya saiko salimat da ke tare dani,

   Ban inya boye mata komai ba tana wankin kayan su umar a laundry saida ta matse kayan takuma gama jin bayani na 

   Saita zauna a dayan kujeran da nake zaune gefe ta dan kamo hannu na ta kalli kwayar idona tace min

   Fadima kin dai fi kowa sanin cewa sheriff ba mutumin banza bane balle mu tuhumay shi  

   Don idan sani ne na dokokin Allah ke ma kinsan cewa yasan komai fiye da sanin mu,

   Don haka wani zargi bai ko taso ba a tsakanin ku,

  Tace kawai ni abinda na fahinta yana maki hakane don daukar ki dayayi kanar yar kaunar shi,

  Kinko ga dole ne ki dinga gani irin haka ,saboda haka kada ko kisa wani zargi a tsakanin ku dashi,,,.

   Wanan maganar na maman Umar yasa nadan ji sanyi araina nafitar da duk wani zargin sabon canjin da nagani ga sheriff din,

    Hutun mu ya kusa karewa ga kuma shirin tafiyan da Aziza keyi dani zuwa gurin dashen cikin da za ai min na aje mata baby ta da zanyi,

    Nasan cewa dole Ina kallo Amal da salim za su  wuce madina don cigaba da karatun mu wanda daga wanan hutun insha Allah mun gama karatun mu ke nan,

   Saura kamar sati biyu mu koma wurin doctor aziza a kasar indiya su Amal suka koma madina 

  Wanda sam sheriff baiso ace sun tafi sun barni ba saboda da yasan cewa yanzune zamu karatun mu na karshe,

   Amal sun wuce da kwana biyu Hindu ta bugowa Aziza waya cewa su hadu Nigeria  saboda wasu kaya da sukayo oda akasar chaina ance jirgi ya nutse dawa su don haka dole ne suje su ganewa idon su abinda ke faruwa,

   Bada son ranta tabar kasar saudiya zuwa Nigeria da niyar bazata dade ba saboda tafiyan da zamuyi,,,

    Tun da marancen ranan nake jin jikina bana jin dadin shi sam ga kuma gidan duk kusan kowa ya watse gidan yai min girma,

   Don hakane saina dan koma dakina na kwanta daniyar kila indan nasamu barci na tashi zandan ji damar jikin nawa,

   Mun muna mafarkin danayi yssa na farka inata zufa a goshina, duk da na farka daga barcin ina iya tuna mafarkin

   Maciji nagani a cikin daki na  yavkokarin shige min ajikina, 

   Naje in gudu sai kuma na kara gani gida ya nufoni gadan gadan ya shige min a jiki,

   Innalillahi kawai nake iya furtawa a bakina ban iya koda daga hannu na don jiki na duk naji ba karfi,

   Daidai lokacin naji takon kafar sheriff zuwa dakina,

  Don nasan cewa in bashi ba wanda ya isa yatako har inda nake,

   Da sallama ya shigo dakin saidai a kwance yagan ni da alamar ba lafiya tare dani ,

  Da sauri yakaraso inda nake kwance ya na tambayar ko may yasamay ni ,

  Baki na bude da niyar in mai magana sai naji ban iyawa,

    Sai hawaye da suka dan biyo kumci na 

   Tabayana yakeyi arude baki da lafiya ne na kada mai kai almar ,a,a 

    Sai ya lura cewa na dafe kaina

   Yakoma da sauri yadoko man magani yabani,na samu nasha 

        A hankali ya hawo gadon yadan rugumoni ajikin shi yana min addu,a sai nayi wani irin ajiyar zuciya ,

   Na lunshe idona ina ji ina shakar kamshin turaen shi tun ina danjin karan A C har barci yadaukeni 

  Tundaga lokacin ban kara sanin inda nake ba,

   Dasafe koda natashi sai kawai nakamajin jikina ba karfi ko ina nawa ciwo yake mun,

   Na koma ko tashi da kyat nake iyawa don nauyin da nakeji ajikina,

    Acikin wanan halin har azizata dawo tasa may ni a hakan ,

   Saboda son ranta duk da taga banda lafiya saida ta tafi da ni wanan tafiyar hakana,

   Sau kin abin tare da sheriff muka tafi yana ta faman nan nan da ni,

   Ranan da mukaje washe gari duk muna office din likita  da su inda lita naga yakaini su wani daki su biyu,

   Bayan sunfitone aziza tace ma liktia ya dibani banda lafiya,

   Saita ja sheriffs da hira akan harkan maikatar su,

   Ina shiga likita yace in kwanta  awin farko naji yace in tashi da sauri gabana ya fadi,

   Sainaji yace min infita kawai basai yadibani ba zai dai  bani magani,

    Shiko sheriff tunda na shiga hankalinshi na gurin mu yanayi yana kallon hanyar office din doctor saigani nafito,

   Tana gani na fito ta mike tsaye,,,,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈

          👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                   6⃣9⃣

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎  Almost true life story


A hankali nafito da ga dakin likitan jiki ba kwari, Aziza tana ganina ta taso  cikin sauri ta tare ni ta na fadin sannu fadima ya jikin naki,

   Sheriff na tsaye gefe guda ya tsura min ido babu ko kiftawa, hannayen shi zube a cikin aljihun ,shiru yayi kawai yana kallon mu,

   Wani dan takarda da doctor yace zai bani na magani , shine doctor yasa akawo muna don aje asiya maganin

    Sheriff ne yakamata yatafi amma sai aziza ta caraf ta karbe takarda tace in zauna taje tadawo tana mai kashe min ido alamar kada in fada ma sheriff komai 

   Mamaki tabashi na rawan kan da yaga tana yi da ni,

   Kofar dakin likitan ya duba inda sunan shi da phone number doctor ke rubuce,

   Ya kwashe a wayan shi,

 Saida yagama ruburun shi kaina na duke kasa alamar dai bana jin dadi ajikina, sam yasa na bashi tausayi,

     Ya dan matso kadan kusa dani yace min mai ke da mun ke ne fatima,

   Nai narai narai da idona wanda ya nuna alamar hawaye aciki nace mai nima ban sani ba fa

   Aziza ta dawo dauke da ledar magani a hannu ta, tun anan cikin asibitin ta balla min tace min Insha,

  Kwanan mu biyu a indiya muka dawo straight zuwa saudiya,

    Hankalina gurin karatuna don haka ban ko huta ba na kama ha yar madina tare da Yusuf driver,

   Saidai kafin in wuce Aziza taja min kunne sosai akan in bi a hankali dan Allah kada in yi garaje,

  Kamar ince mata nifa likita bai min komai ba dan injin kawai yadora min a mara yace min sauka in fita,

   Saidai kuma ina tunanen cewa kodai haka din ne dashen cikin da tace za,ai min,

    Tunda nadawo Amal take ganin kamar na canza mata, sosai don ta lura da cewa ban son yawan magana kamar da

   Sai kuma nida ke yawan cewa muji masallaci yanzu sam ban zuwa saidai in kwanta in ta barci, kawai,

  Salimat tadawo da yar diyar tayi wayo sosai yanzu tazama big girl,,

   Karatu nakeyi mai wahala yanzu sosai don dai duk inda na zauna sai kawai inta zuba gyangyadi,

  Banda wani aiki sai barci,

   Zaune muke falo muna hira da Salimat da ta kawo muna yini yau agidan mu kasan cewa yau ba karatu,

   Duk irin abinda muka aje na ciye ciye a falon fruit kawai nadan dauka na sha,

    Hira muke yi duk kan mu amma ni sai jefi jefi nake basu ansa daga inda nake zaune nadan dunkule wuri guda,

   Salim yafito da shigar yan RACE don yana yawan zuwa wurin wasan race,

   Gab da inda nake dun kule yazo ya dan zauna,

  Wani irin kamshin turen dayasa yadaki hannci na,

   Sai naji wani irin  a,mai, yazo min a gigice natashi da sauri na

  Wani irin kallo duk kan su suka bini dashi, sai kuma suka kalli junan su cikin mamaki ,,,

Ina shiga, dakin na nufi toilet nafara sharara amai saida nayi kamar zan amaye hanji na duk ka,

 Amal ce tsaye bayana ta kura min idon mai nuna kallon mamaki,

   Gado na fada nadan kwanta don inda huta saboda jikina duk yasake min,

    Tunda muka dawo saudiya sheriff ke kula da yadda aziza ke wani farin ciki tana nadewa wuri guda,

  Hakan yasa ya maida hankalin shi sosai gurin ta don yana son ya fahinci ko may ke faruwa da i ta hakana,

    Saidai bai fahinci komai daga gareta ba,,amma hakan baisa ya daina sa mata ido ba,

   Tare suke shi, da Aziza a cikin motar shi ke tukawa yau ba driver ba zai kaita wani shagon saida kayan shafa,

   Saboda yasan cewa shagon na matane, yasa yacewa Aziza ta shiga ta fito 

  Aziza ta dauki yar poss din ta data sa kudi a ciki tabar babban jakar nata acikin mota saboda nauyi, ciki harda wayan ta,

   Tana shiga sai ya dan gyara zaman shi a kujerar ta, a hankali,

   Wani dan farin takarda yaga zai fito daga cikin jakar nata,

   Sai yai zaton cewa kila wurin sauri ne ta jawo takardan gashi har zai fadi kasa,

  Abinda yagani shiyasa shi gyara zama cikin firgita, takarda ne risit, na Artificial Insemination pregnant, mai dauke da sunan hajiya dakuma wata,

   Yarinya yar kimanin shekara sha takwas da haihuwa,

   Date ya diba sai gaban shi ya fadi, ras, saboda daidai ne da kwanan watan da Aziza tace tace mai likita yace ya na bukatar suje tare da shi a gwada sperm din su agani ko zai iya produced din baby acikin sauki,

  Tabbas kuma sunje din har an debi sperm din nasu shida ita, an je gwadawa,

  Fatima what ya mike zaune da inda yake zaune ya bude ganbun motar shi cikin tashin hankali,

   A haukace yake kamar ya cin ma Aziza ciki ya shaketa, don ya matsu ta fito yaji may yasa akai artificial insemination don ya hana ya fada mata yace bai so don shi ba jahili bane,

  Kuma wace ce akai ma dashen don risit yanuna cewa ba, Azizar bace,,

    FATIMA zuciyan shi takara nanatawa sai yace ina yasan fadima da kaifin hankali da sanin ya kamata,

    Kafin yai wani abu sai yaji karar wayan Aziza da tabari acikin jakarta yana ruri,

  Kamar ya share sai kawai yasa hannu ya dauko wayar yadan na daukar kira batare da yai magana ba

   Yaji murya Hindu ta,na fadin Aziza kina ko kula da time din komawar ku asibiti da yariyar nan don a binciki ko cikin na cikin koshin lafiya,

   Bai karasa jin zancen ba ya kashe wayan cikin tashin hankali,

   Idon shi ya kade ya komar kamar garwa shi, wuta, don bacin rai,

   Aziza ce ya hango tafe tana tafiyan ta na kasaita ta nufo motar su,

   Kafin ta iso yayi kokarin gyara motion din shi saboda dan nazarin da yayi akan maganar,

    Bayan an gama sa mata kayanta a,buth din motar su tashigo motar tana fadin wassh Allah na duk na gaji tana mai kokarin dauko jakarta tana sa poss din ta ciki,

   Fuskan shi ta dan kalla sai taga duk yanayin shi yacan za,

   A hankali takara diban shi tace mai may yafaru taga duk ya can za lokaci guda,

   Saida yasa hannu ya ahafa sumar kan shi yadan lashi busashen laben shi da yake ji kamar ba miyau,a bakin shi,

   Yadan ce mata may kika gani halan tace haba dai sweet habibi, ai ba haka na barka ba

   Dan murmushin yake yayi yace mata, kawai waya nayi da masu sauke muna injin din da mukayo oda yau wai kuma sun fasa sai nan da sati biyu killa,

  Taidan dariya maikama da fito tace to ai ka huta, kai kenan kullun cikin aiki baka da hutu,

   Har suka isa gida ita kadai ce keta zuban ta, bai ce mata komai 

   Sai tunane yakeyi yadda zai bullo mata idan ya kare binciken shi,

    Tsaye yake da waya a hannu shi,yan saye da farar jallabi mai dan yagwai a gabn rigar anyi kamar anyi saka ajikin shi,

   Noban Salim yake kira don ya fara tambayar shi,

  Bayan salim din yadauki waya sun gaisa ne,

   Ya danyi shiru jin kadan can yace ma Salim duk lafiya kuke ko Salim ya ansa da eh,

   Yace, kowa na zuwa makaranta kamar yadda yadace ko suka ce mai eh,

   Can yace to ita Fatima fa lafiya take, yakara ansa mai da eh Salim din  yadan daga wayan yakamar yayan nashi yana ganin shi,

   Sai kuma yakara maida wayan a kunnen shi ,,yacigaba da sauraren dan uwan nashi,,,,,,

    Kashe wayan yayi cikin damuwa yasa hannayen shi biyu ya tokare su ga karfen da ke kofar su,

   Yai shiru, tare da yin tunane kala kala azuciyar shi,

   

     Duk irin abin cin da salimat tasan cewa ina yawan ci su tagabatar min a gabana

  Kassh amma yau kamar ta aje min guba nake ganin abincin,

   Zargin salimat yafito daidai lokacin da na toshe baki har hanci na saboda wani amai da nake ji, yana taso min,

   Sai bayan nagama aman nadawo falon ta, na zauna hankali,

   Salimat ce naji ta dafamin kafada, ahankali nadago idona na kalle ta,,

   Saida, ta zana kusa dani har takai muna iya jin hucin juna tace min fadima may yasa may ki,

   Da sauri nadago nace mata may kika gani halan Salimat,

  Nadan gyara daurin dake kaina kadan nace  mata kawai ina ganin cikina yai min dadti ne kawai,

   Ido ta kura min tace look fadima kisani cewa ba wai daukar wasa nai maki ba jinki nakeyi tamkar yar uwata taji kaunata wacce muka fito ciki daya da ita,

   A hankali nadan dago kaina kalli Salimat sai kuma na dukar da kaina kasa,

   Tabbas nasan cewa ban jin dadi jikina duk kwanakin nan, ba abinda ke min dadi gashi sam bana son jin koda kamshin ture na hatta sabulu wanka idan naji kamshin shi zuciyana duk sai ya tashi,

 Indinga jin amai na taso min 

   Wanan karon hannu na biyu duk ta hada wuri guda tadan kara matsowa gab dani ta kalleni da kya sai naga wasu hawaye suna fitowa daga cikin idon ta zuwa kumcin ta,,,

   Kai muka hada wuri guda nida ita mukayi kuka mai isar mu saida muka gaji,

   Can tai karfin hali tace fadima wayai maki wanan abin

   Waya cuci rayuwan ki haka

  Ya akayi ki ka aikata zina,

  Kalman da tasa na zina ciki shiyasani kallonta da sauri ina ce mata la,la,la tunda nake ban taba sha,awar zina ba balle har in aikata ta,ta,,,,,

  Ta kalleni da kyau tace min waiyai min ciki toh

   Dukar dakai na nayi don bansan ta inda zan fara mata bayani ba,

   Kawai sai na dake mata akan lafiyata kalau, kawai dai banajin dadi ne,

   Ido kawai tasa min bawai ta yarda da maganar da nai mata ba,

  

     Zaune nake saman gadona ba abinda ke fitamin sai hawaye,

   Ina tsoro da fargaban maganar Salimat, tunda ta fara ganewa kada Amal ma da muke tare ta gane,

   Allah Allah nakeyi har Aziza ta cire cikin ta kada wanda yagane cewa ina da ciki,

   Don gudun zargi irin wanda Anty Salimat tafara min,

   Nasan cewa ana iya jefe ni idan har hukuma taji,

   Sheriff mutun ne mai yawan ibada nasan cewa sam bazai lamince min ba,

    Ihun da naji Amal tayi ne daga dakin ta yadan katse min tunanen da na zurfafa ciki,,,

   Da murnan ta iso har inda nake kwance ina kokarin tashi,

   Fada min tayi saman jiki na da karfi saida naji wani irin abu cikin karfin hali da daurewa na dan mike ina mata dariyan yake

    Tana murna ta na fadin Ummi nan acikin saudiya , tadan kara fadowa saman jiki na sai naga ta mike da sauri ta hadiye murnan data,keyi,

   Ta dan kalle ne cikin firgici tace min fadima jikin ki da mugun zafi 

   Baki da lafiyane haka sai nadan wayan ce zancen kawai,

    Lafiyata kalau may kikaji halan

   Wani kallo ta watso min gami da dan taba gefen wuya na,

   Kafin tai magana sai nace mata yaushe ummi ta iso tace wai yau takai kusan sati uku ai

     sundai ki fada muna ne don kada muce zamuzo,

   Nima na nuna farin ciki na sosai da zuwan ummin,

   Don haka washegari muka shiga shirye shiryen taron Ummi da zata zo ganin mu daga makkah,

   Duk abincin da a ka dafa komai na kasa ci daga ciki sai

   "Ya,yan itace kawai nake sha kamar hauka, abinda takeyi tabari da sauri ta nufi hanyar kitchen hankali ta tashe ga abinda take hasa she

    Kirana tayi daga kitchen din tace min inzo in kama mata aiki,

    Ina shiga warin man da take suyar rotinar ya nashi hanci ai sai naci kamar in kurma ihu,

   Kofar baya na nufa ina shirin kakarin amai,

   Cikin sa,a aman bai zoba na, taso da kyat da niyar in koma ciki 

    Maman Umar din ce dai na ci karo da ita tsaye da cibin tsamar rotinar a hannun ta tana min wani irin kallon tuhuma, 

   Nai kamar ban gane nufinta ba nai niyar shigewa na ciki in barta,

   Tareni tayi tana ce min, may take shirin gani a tare da ni haka,

   Duk yadda naso in noke mata saida ta tsaidani amma fir nace mata Iam, ok

   Sai kusan Yamma lis bakin mu suka iso saboda nisan da ke a garin wanan karo harda sister din su Amal wacce ke aure da yaronta aka zo,

   Zokaga irin murna da farin cikin da muke yi a ranan,

   

    Sheriffudeen Ahmad shine yashigo karshe daga cikin su ,

   Daidai lokacin nafito daki da murna na nafada bisa jikin Ummi,

   Nalafe nadan wani lokaci batare da nai magana ba,

   Itace ta dagoni a hankali tana min kallon mamaki tace fadima ke ce haka, 

   Sai na kara noke kaina ajikin ta ina dan dariya,

   Sheriff na tsaye ya kura min ido gaban shi na faduwa saboda irin masifafen canjin dayaga nayi na lokaci guda,

   Nai wani irin fari ko ina nawa ya ciko cif,cif kamar wata katuwar budurwa,

 Gashin jikina yayi kwance lub, lub fatana yakara wani shiki da haske,

   Jinda nayi su Amal na mai sannu da zuwa yasa nadan daga daga jikin UMMI na nufi gurin shi don in gashe shi,

   Yana tsaye cikin shigar turawa yasa suit a jikin shi,

  Har na isa gab da inda yake idon shi na akaina, yana min wani kallo cikin sha,awa,

    A,hankali nai mai sannu da zuwa kamar yarda muka saba idan yazo,

   Yadago yakalleni idon shi yayi wani jajir kasala ta sauko masa da kuma wata irin sha,awa,

  Tana fisgan shi,,

   Gabada ya lokaci guda duk ya birkice, wuri guda,

   A sanyaye ya ansa min da cewa ya nake,

  Nace mai lafiya lau,

    Amal tace wai lafiya lau ko jiya da dare jikinta kamar garwashin wuta, yake don zafi,

   Muryan bakuwar da suke tare ne da su  tace wanan ce fadimar,

   Amal tadan jawo ni tace itace fa kedai anty falmata,

   Mai suna falnatan tace masha Allah sam barka,

   Nadan murmushi yake na ce mata barka da han ya anty cikin ladabi da girmamawa

    Hannu ta miko min alamar inzo gurin ta natako a hankali na zauna gefen ta inda ta nuna min,

   Mukayi gaisuwa na musabi,a

   Saida sukayi sallah har mu sannan muka zo falo gabadayan mu gidan don cin abinci dinner da aka shirya ma zuwan su

    Su salim da Amal sai washe baki sukeyi,

   Dan yaron Anty falmata na karba ina mai wasa UMMI tace min in aje shi kawai inzo muci abinci, 

   Kamar in ce bazan ciba sai dai nadaure natafi don kada UMMI taga banyi mata biyaya ba,

   Sheriff dake zaune gefe da tasbaha a hannu shi guda, 

  Yanajiran azuba mai nashi sai dai duk idon shi na ga duk wani motsi nawa a fakaice,,,,

    Wani irin shauki so da kaunar fadima kawai ke fisgan shi, 

  Ji yayi kawai yana son ya kasan ce tare da ita,

    Bude abinci da maman Umar tayi don ta fara zubawa mutane yai daidai da shakar kamshin abincin da nayi,

   Har ina ture Amal gurin tashi da sauri na toshe bakina da hannu guda na shige daki,

   Duk suka bini da kallo gabadayan su,

   Amal ce tace bansan wanan sabon salo da fadima ta dauko ba walahi duk aka bude abinci ko ta shaki warin turare sai ta ce wai ita mai, ta fadi karshe da alamar nuna ko oho,ho,

   Ba sheriff ba hatta UMMI saida taji wani irin shock din zancen na Amal wacce ita bata kosan tanayi ba,

  Ture kujerar dake gabanshi yayi ya nufi dakin nawa,

   Ina ciki duke a bakin toilet inata kakarin amai 

     Ina,gamawa, sai nadago daniyar in ja kafa na zuwa kan gado na

   sai na ji na kasa kuma ga sheriff a,tsaye gaba na ya kura min ido kur cikin tuhuma,

    Ganin shi danayi tsayen cikin kallon tuhuman da yake min shine,

   Yasa na, dan ja kafana nadafa bango don kiris ya rage min in fadi a yadda nake ji,

   Hannu ya mika min alamar in miko nawa dole na mika mai hannu yakamani a hankali har ya kaini saman gado 

   Yazaunar dani ko yanzu ido yakara kura min, a hankali na sada kaina kasa 

   Don ban iya jure wanan kallon,

  Muryan shi naji yana fadin may ke damun ki fatima,

   Bakomai na ce mai haiyya ,,,

  Kai kawai yakada yakoma falo zuciyar shi na ta mai wani irin tuhuma, akai na,

   Lokacin da yashiga falon duk ido suka sa mai don jin ko ya mukayi,

   Banda UMMI daketa cin abincin ta, mama umar ce ta yan ko min fruit a plate ta nufo daki na dashi 

   Sai Amal tace shine kawai abincinta yanzu nayi fada amma bataji sai ,,, bata karasa ba ya daka mata wani irin tsawa saida ta firgita don tsoro,

   Ita batasan cewa maganar shi jinta yakeyi kamar zubar ruwan zafi a zuciyar shi,

   Ummi tace Amal kin faye surutu da yawa kiyi mata fatan Allah bata lafiya kawai ba wanan surutun naki ba,

   Sheriff baici abincin ba tashi yayi ya fita kawai duk suka bishi da kallo 

    

     Ina kwance ba barci nakeyi ba idona biyu hannu na rike da handout ina kokarin dubawa amma tunane ya hana ni shakat,

 Sheriff na dakin nawa cikin wata jallabiya baka yasa yar fulla fara daidai tsakiyar kai,

   A hankali nadago idona na bishi da kallo har ya zauna, kusa dani 

   Minti kusan biyu da zaman shi duk munyi tsit dakin yace Fatima na ansa a tausashe da na,am,

   Yace min tun yau she ne rabona da inyi period, dina, 

   Sai a lokacin na tuna da zancen period din da nakai wani lokaci ban gane shi ba, fa,

  Kuma batare da na damu ba na share zancen kawai, abina

  Ganin da yayi cewa bazan asa mai ba yasa shi mikewa yabar dakin cikin tashin hankali,

   Washegari kowa kokarin cin break fast niko yayan itace ne a gabana inata masu shan hauka,

  Ummi ce ta min Fadima koba kyson cin abinci ki daure kici hakana kinji ko zaki amayar ba duka zaki fitar ba dole a samu wanda yadan tsaya maki a ciki 

   Don kinga bake kadai bace yanzu, 

  Maganar bai wani bamu mamaki ba tun da bawai mungane ko may take nufi bane,

   Sheriff ne cikin kamar hasala yace min in shirya ya kaini asibiti kawai,

    Batare da wani bata lokaci ba na mike zuwa shiryawa,

  Ina fitowa naji muryan anty falmata na cewa   UMMI sun dace a gaskiya da yaya wannan itace daidai da shi walahi, 

    Yariyar ta burgeni sosai walahi,,

   

    Cikin shakku da fargaba nai wanan tafiyan zuwa asibiti ina ta rokon Allah yasa kada aga komai a tare dani,,,


    Likita ya auna ni yadda ya kamata inda yace, ma sheriffudeen Ahmad matarka nada ciki na wata uku kwance a maranta, kuma munyi bincike abinda ke ciki lafiya lau yake,,,,

    Wani irin dam dam naji azuciya na sai naji kamar in kurma ihu don fargaba da rasahin sani mako mata ga sheriff a halin da muke ciki,,,

    Sai yanzu nake nadama da danasai ciwo ne na rashin shawar da banyi da kowa ba har haka yasa may ni 

   Nasan cewa konayi rantsuwa yafi dubu ba mai yarda da cewa ba zina nayi ba,

 Aziza Aziza may yasa zaki min haka na pls, keda kika ce da zan ran ciki yadan tsaya zakizo a cire maki abinki amayar maki shine zaki min haka Y pls, Y,

   Wani irin kuka mai tsuma zuciya nakeyi a can ciki ciki don tsananin nadamar da ya lulubeni,

   Motar naji anyi parking da karfi har saida na dan razana,

  Nadogo kaina a hankali na kalli inda muke don ni azatona mun kawo gida ne,

  Gefen maikatar su ne ya parker motar hakana,

    Yafidda wayan shi da sauri naga ya bidan wata nonba hankalina duk ya tashi don na dauka hukuma zaikira

   Can kuma naga ya tsaya yajowa ni takarda a  cikin yar briefcase din shi, yadiba wani rubutu,

   Sainaji yadan yi ajiyar zuciya kadan

    Kaina yana kife inata aikin kukan da yasa may ni,

  Kiran mai shi yayi naji yana cewa, doctor, Khan,

    Sai yadan zagaya bayan mota don suyi magana,

  Bayan sun gaisa ne da doctor yake mai bayanin ko shiwaye,

  Nandai yadinga jefo ma doctor tambaya akan artificial insemination din  da matar shi tazo da yariya don ai mata ko yayi a lokacin,,,

   Doctor kan yace mai no, no,no d girl is already have two, week's pregnant b4,

     

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈TAKARI✈✈✈

         👣👣👣👣👣

          👣👣👣👣👣

                  7⃣0⃣

                     BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA

🐎HUGUMA GROUP🐎


 Almost true life story,,,,


 Motar yashigo tare da mai da  kofar motar da karfi,,,

   Saida nadan firgita, don tsoro, hakan bai hana ni cigaba da she,shekar kukan da nakeyi ba,

   Shiru ya yi kawai ya dan kura min ido don takaicin wanan kukan da nakeyi yake ji ji yakeyi kamar ,,

   Make ni saidai kuma da yai dan tunane sai kawai ya dan murmusa kamar bashi bane ke cikin bacin rai yan mintitika da suka wuce,

   Jin hannun shi nayi ya dafani a hankali, tare da anbatar suna ,

   Batare da na dago kai ba kuma ban iya ansa wa ba saidai na dan tsagaita kukan nawa kadan,,,

  Wani irin ajiyar zuciya mai nauyi ya yi tun kun kafin  ya fara zance shi,

     Yadan dago min kai a hankali  da niyar mu yi ido biyu dashi, 

     Amma sa na saurin kwantar da fuska saboda ban iya jure jimirin kallon shi ido da ido hakana,

   Sai yadan yi murmushi kadan ,

   A, hankali naji shi kamar may rada yace min nawa Aziza ta saye ki har kika amince da zuwa ai maki, dashen ciki ajinki ki,

   Jin nayi shiru kamar ruwa ya ci ne saboda ba kara min mamaki nayi ba jin cewa yasan da zancen dashen ciki a jikina,

   Wanan karon cikin daga murya, yake maganar shi,,,

  Ina hankalinki yatafi, ina wayonda nasan ki dashi, ina amfani ilimin da kike yi yake, 

   Ashe ke zaman da kikayi da su hjy as a takari bai sa kin san halin dan adan ba, har yanzu,

   Yadan tsagaita fadan yai shiru yana maida nun fashi guda guda kamar wanda zai make ni,,

   Yace ki godewa Ubagiji Allah da wanan abin bai zama tabbatace da kin san kowa ye dan adam,

   Nadago fuskana, cikin sauri jin danayi yana cewa wai dashen bai faru ba ,

   Bayan yanzu likita ya yagama fada muna cewan ina da cikin wata uku a jikina,

   Kamar yagane mamakin da nakeyi sai yace na,am kina da ciki a halin yanzu amma bana dashe ba, ciiii

   Saina kasa daurewa inji abinda zai ce gaba nace,

   Amma duk halin da nashiga ciki sheriff saboda kaine 

   Don ka na sadakat da rayuwa har akai min wanan dashen don farincikin ka,

  Kataimakeni da yawa arayuwa wanda narasa may zanyi in saka ma dashi 

   Saiga Aziza ta samayni da bukatar intaimaka mata ai maku dashen ciki ajikina idan ya isa cirewa sai acire amayar ta da abinta a jikin ta,

   Yan security da suka ga motar mu tadan dade tsaye gefe ne suka dan iso gare mu suna tanbayar mu ko lafiya ,

   Sheriff yace lafiya shida matar shice,

   Batare da yakara magana ba yaja motar zuwa gidan su na ainihi da nasa wanda mukafara zuwa garin madina muka sauka aciki dasu hjy tsohuwa,

   Cikin gidan ya umurce ni da shiga ba tare da yin musu ba na bishi a baya,

  Falon gidan muka zauna, 

   Yace in fada mai gaskiyar yadda mukayi da Aziza tun farko,

   Batare da naso ba kuma banda yadda zanyi dole yasa na kwashe duk irin magan ganun da muka yi da Aziza har da likitan su nafada mai,,,.,

    Dan teburin katakon dake gefen shi yabuga da karfi yace,

   Aziza y pls y may yasa kikai kokarin rushe min farin ciki na,

   Yamike tsaye yana cewa, Ya Allah, Subbahanal, Wallhamdullah Allahu, Akbar,

    Kuka naci gaba dashi cikin sauti mai kashe zuciyar mutun dake sauraren kukan,,

   Ji nayi ya zogab dani ta yarda har zan iya jin nun fashin shi yace min,

   In dakatar da wanan kukan da baida wani amfani gareni,

   Cikin kukan nace ya barni inyi kuka don abin kuka yasamay ni ni fadima may zan je gida in cewa mahaifiyata da yan uwana,

   Yau nice dauke da ciki cikin da ba uban shi, atare da ni,

   Shiiii naji yace min kamar yadda ake tsaida yaro idan yana kuka,


   Cikin san yayyan murya yace min fadima cikin jikin ki ni ne uban shi,

  Ni nai maki ciki da kaina kika samu wanan ciki, najikin ki batare da an maki wani dashe ijin ba,

   Asali ma banda labarin plan din ku da Azaiza koda hakan ya faru,.

   Zubur na mike tsaye da ga zaunen da nake cikin mamaki nace 

   Nace sheriff kada ka zolaye ni pls

  Bantaba jin kayi wani abinda ba daidai ba a rayuwar zaman da nayi tare da kai,

   Balle har ta kai ga kayi wa kanka sherin yin Zina da ni fadima har takai ina dauke da dan shegen ka,,

  Banko karasa zancen ba yayo cikina cikin zafi,zafi yana fadin kada ki sheganta min baby na fatima,

   Dan cikin ki dan Sunna ne kamar yadda kowa wani dan sunna ya ke tin kaho da ubanshi ni ma haka cikin dake,jikin ki ya, ke tin kaho dani Ahmad lawal a matsayin uban shi,, na sunna,

   Da mamaki nadago saboda gani nakeyi son haihuwa yasa shi wanan haukar, da ikirari,

  Anya kuwa sheriff ne ke wanan zance, ina yawan alherin shi da addinin shi ya tafi,

    Kamar ya gane may nake nufi, ko tunane araina,

   Sai naji shi ya rungumay ni cikin jikin shi,

   Magana yake min kamar rada, rada kamar kuma akwai, wani kusa da mu wanda,zaiji may zaice min,

   Yace min Fatima ki kwantar da hankalinki, ki saurare ni da kyau , kiji bayanin da zan maki,

   Ina rugumay a cikin jikin shi naji shi yana fadin 

  Ina son ki yafe min akan maganar da zan fada maki, 

   Yau shekara uku da wasu yan watan ni ke nan da aure na da ke fadima, 

   Dasauri na dan jaye jikina daga jikin shi ina mai kallon mara hankali ko kuma wani zautace,

    Ya ce min yes abinda kikaji haka yake,

    Tun zuwan ku nan madina bada wani dadewa ba wanan abin yafaru,

  Shehi shine hjyn ki tasa  ya wakilci auren ki, dani tare da wani dan takari na tare da su,

   Ni na hanna afada maki a wanan lokacin saboda a lokacin nadauka auren rufin asiri ne kawai mukayi,

   Nikuma, ina son ko ba komai ki samu ilimi daidai gwargwado, yadda zaki amfanana nan gaba,

   Sai dai ba a dauki wani lokaci mai tsawo ba naji kawai ina bukatar wanan auren namu yaza mai daurewa har abada,,,

  Na,kara daga kai na kalle shi, cikin mamaki,

    Yadaga min kai tare da kafadan shi yace yes, I mean it,

   Aure na da ke mutu ka raba ba wai na jeka na yi ka ba ne,,,Auren nadan wani lokaci kadan, a, a kireke a ranki cewa nida ke sai mutuwa,

   Idona tab da hawaye, nace Sheriff yace min shiiiiii yasa dan yatsan shi ga baki alamar in yi shiru,

    Tun da farko Fatima ban yarda cewa ina son ki ba nadai san cewa duk wani lamari naki tausayi yake bani,,,

   Amma sai ga shi cikin ikon Allah naji na fara son ki, 

  Ban gama tabbatar da  cewa ina sonko da gaske ba sai, 

   Sai lokacin da na sanki diya mace na dan dani zumar ki, nakuma gane baiwa da ni,imar da Allah yai maki, duk baki a cikin hankalinki,

   A lokacin na tabbatar wa kaina ko zan rasa raina ba zan taba rabuwa da ke ba,

   Ya nuna min cikina da hannun shi yace min ni nayi abina da kaina batare da taimakon wani likitaba,

   Kara dagowa nayi nakalle shi again,,

   Lokacin da baki da lafiya a makkah da Aziza tasamu urgent call daga Nigeria nadago da sauri na ina mamaki 

    Baki da lafiya aranan kina, ciwon ki na mara da kikeyi lokacin da kika gama period dinki,


   Sai na dukar da idon kasa, wani irin kunya  naji, alokacin,, sai,

   Abinda ya faru ya fara dawo min dan tunawa tiryan tiryan a lokacin,

   Dana farka bayan nasha maganin da sheriff ya bani barci mai nauyi yadauke ga kuma tsoron mafarkin macijin da nayi sai kuma gidan da ba kowa a,lokacin mun rage yaw,

   Ina farkawa  Sheriff nagani akaina cikin damuwa a fuskan shi ina tashi yai ajiyar zuciya , 

   Shi ya taimaka min zuwa bayi har nakai kofan shiga bayin yace min idan nashiga tunda nayi mafarkin maciji in,yi wankan tsarki kafin in fito,

  Sai na waigo da mamaki ina dan tunanen saboda mafarki da na yi,zanyi wanka,

   Kawai dai sai na shege abina batare da wani kwankwanto,ba,

   A bayi kuma ruwa zafi nafara anfani dashi, sai,daga baya nasa masu  dumin da yace min indan shiga shiyasa har na dan ji saukin zafin da nake ji ,

      Nadade acikin ruwa zafi na,gasa jiki dasu, hakan yasa har nadan iya,  inya tafiya kadan da na fito , dana fito duk zafin da nake ji dazu ya rage min,,,,

   Bayan nayi sallah ne, nakoma na kwanta tare da shan maganin da sheriff yakarabani a lokacin,,,,

    Tunanen da yaga ina yi yasa shi yin shiru yana kare min kallo cikin tausayi,

  Ina kai karshen tunanen nadago kaina da sauri muka hada ido sai ya kada min kai alamar eh haka zancen yake ai,

    Durkusawa nayi kasa nakara rushewa da wani sabon kuka wi,wi,

  Shiko, sheriff, Ido kawai yasa min nayi kuka mai isa na batare da yalalashe ni ba,,,

    

    Fadima wanan kukan da kike yi yafi maki dadi ga wanda Aziza taso jefa ki aciki,

   Nadago kai nakalle shi may ye babbacin hakan da wanda taso sani ciki,

    Aini gare ni duk dayane, basu da bambanci agurina ,

   

   A cikin zuciyar shi , wani iri yake ji gamay da fatiman , saboda duk ta birkice mai a lokaci guda,

   Sai lumshe ido yakeyi, tuna ne kala kala, na shiga zuciyarsa, 

  Idon shin kan a kyakkyawar matar tashi,

   wace yake ji tankar ya hadeye ta don so, a yan zu

   Sai fadi yake cikin zuciyar shi yana cewa, Allah nagodema da kabani wanan yarinyar  a matsayin mata ta,

   kuma uwar "yaya na, anan gaba tabbas wanan yarinyar kyautace daga ubangijin shi,,

   Duk da girman shi da kuma kudin shi da ikon shi, sai ga sheriff tsugune a gaban yar karamar yarinya fadima

   Yadan riko hannu ta ya hade cikin nashi yace mata, 

   Fatima kiyi hakkuri ki rugumi kaddaran da Allah ya kawo muna ,ba don mun yi mai laifin komai ba,a,a hakan dai yaga daman bamu namu rabon,,,,

   Cikin rashin fahinta, na kara kallon shi, inda yaci gaba da maganar shi,

   Saidai ina son ki san cewa ni agare ni cikin yai min daidai, kuma yazo min a lokacin da nake bukatar shi,

  Don Allah kadai yasan dalilin dayasa wanan cikin yasamu a wurin ki ba,a wurin ta ba can daban ,,,,

  Don haka ni bawa ne mai rungumar kaddara, a,duk ta yanda kaddara ,yazo min,,,,

   

      Ya mike tsaye yana  cewa idan kin gama kukan ki sai ki share hawayen ki, 

   Mutafi in kuma anan kike son mu kwana har ki huce U are welcome,

   Da sauri na mike tsaye don gani nakeyi kamar zai kara tursasa ni ne kuma,

   Yadan yi murmushin ganin irin mikewar da nayi cikin sauri don yasan cewa aikin gama ya,gama ko,

  Ina batun fita daga falon yace min dakata a inda kike tukun, cak na ja, na, tsaya guri guda don bin umurnin shi,

   Yai dan taki kamar biyu ya iso inda nake yace min,

  Wanan zancen ban son kowa yaji ina son ki barni da Aziza tukun ,,,

    Kai kawai na gyada mai alamar naji,,

    Ji nayi yadan rungumu ni zuwa, jikin shi, a,hankali naji yakai hannun shi saman marana yana dan shafawa a hankali,

   Jin danayi bazan iya jure hakan ba don yau saina ga yakoma min kamar ba sheriffudeen Ahmad din da nasani ba,

    Zukewa nayi na silalo kasa na zamay jikina daga nashi a hankali,

  Yadan kalli inda nake tsaye ina maida numfashi na guda guda,

  Saida ya lashi laben shi  yadan shafa kan shi kadan yai murmushi, kawai,,, 

   A, Lokacin karfe kusan daya na rana, don haka muka wuce gida 

  A mota kowa da abinda yake kullawa azuciyar shi, 

  Nidai kamar a mafarki nake jin zancen cikin nan  nawa,

   Wai yau ni fadima diyar inna yar kulu ce, ke dauke da cikin wani na miji batare da sanin mahaifiyata ba,

  Ni dawani irin ido zan kalli inna na,

  May yasa hjy ta wuce tabar ni a saudiya 

  Data tafi dani da hakan bai faru ba ,

  Ya Allah ni kuma irin tawa kaddaran rayuwan ke nan,

  Abinda muke ji ko gani yana faruwa, yan takaru sun koma gida da goyo ko ciki shi yafaru akaina,,,

   Gab da zamu shiga kwanar unguwar mu ke nan, nake wanan zamcen zuccin 

  Ganin da yayi nafara shirin sulalo da wasu hawayen yace min 

  Idan har ina son Amal su gane irin halin da nake ciki ne to sai in matsa inta kuka,

   Dole nadan goge hawayen dake shirin fito min cikin kunar zuci

   A hankali nafito daga cikin motar yana tsaye gefe guda yana min wani irin kallon tausayi,

   Shikam shi gaskiya duk da ya son haihuwa baiso hakan ta kasance dani ba a lokaci guda sai kuma yai istigifar cikin sauri don yasan cewa ba ai ma Allah shishigi,

    Har na shige ciki yana tsaye yana kare min kallo cikin tausayi,

   Ummi ce nasamu a falo zaune tana kallon yadda ake ta kiran sallah a garin madina da kewaye cikin tv,

   Da murna ta tare tai min alamar inzo inda take, in zauna,

  Ina zamake nan take ce min ina mijin nawa yake ne yatafi dani ya barsu da tunanen ko lafiya tun dazu,

  Da mamaki nake kallon UMMI watau duk sun san da cewa ni matar sheriff ne dama 

   Amma ba wanda yataba fada min

   Anty falmata ce takawo min fruit cikin plate ta zauna kusa dani tace ce min in sha kozan dan ji karfi jikina tunda bana son komai,

   Sheriff yashigo UMMI ce ke rambayar shi cewa ko mun ga liktata sai yake cewa daga can muke ai,

   Ya zauna da niyar cin abinci sai wayar shi tai kara,

  Aziza ya furta a sanyaye yadan daga kai yaga irin re,action din da zan nuna,

    Niko da sauri nadago kaina muka hada ido nai saurin kawar wa gefe,

  Aziza ke sheda mai cewa zata iso saudiya tana son zuwa ta ziyar ci, su fadima ta dan dade bata gan su ba,

   Sai yake ce mata hakan nada kyau ai shima suna  gurin mu sun zu da su UMMI ziyar mu,

  Cikin yawan take ce ma yaka ganar min fadimar pls,

   A, fadima tai wani girma tayi kyau da ita ai,

   Tai murmushin mugunta har yana jinta,

   Yadan daga wayan yakalla kamar itace yake kallo a fili,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈

          👣👣👣👣👣

            👣👣👣👣👣

                   7⃣1⃣

                     BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎

  Almost  true life story,,,,,


 Su biyu ne, zaune a bayan motar ita Hindu wacce ta dade rabon da tashigo kasar saudiya 

  Tafi zama can Dubai suyi harkokin su ,saboda can ne world businesses center,

   A hankali hindu tai ajiyan zuciya tace kina kokari Aziza nasan cewa in ba don wanan habibin naki ba da babu abinda zaisa ki irin wanan tafiyar haka mai nisa,

   Saida tadan yatsine baki kadan sannan tare bari kedai a,gaskiya koni wani lokaci ina yawan mamakin kaina,

  Duk nabi na su,su ce akan wanan bawan Allah,

  Idan wani yace min zan iya tsaya in bata lokacina ga wani da namiji irin haka, ada wlh zance karyane,

   Hira ce sosai sukai tayi tsakanin su gamay da auren Ahmad da Aziza tayi,

   Sai gab da sallah magrib suka iso madina daga birnin Riyadh,

   Cikin farin ciki kowa ke taron su, ana masu sannu da zuwa, 

   A hankali na, sauko daga saman gadona da Amal ta ce min ai sun iso,

   Na, dan gyara rolling din kai, rigar da nasa rashin sani yasa ni sashi don ban zaci cewa yana nuna cikin nawa ba,.

   Saboda yadan matse ni kadan  kasancewar yanzu duk wani sura nawa yafito ,

  Irin yadda mai sabon shigar ciki kanyi kyau, tana,haske haka na koma,

  Falon nashigo cikin natsuwa, nake tafiya, sallaman da nayi a falon shi ya maida hankalisu gare ni,

   Duk kan su sunga baiyanar cikina adai,dai wanan lokacin,

  Aziza tamike tsaye don mamaki ta tako har inda nake ta riko min hannu,

   Sam takasa boye farincikin da take ciki, ta ma manta cewa abin siri ne,

   Sai tafara dan ta,taba min jiki cikin mamaki, tana ce wa iye fadima wanan kyawo haka

   Gaskiya abin yayi kyau sosai,

   Shigowar Sheriff kenan cikin falon don shima yadade baya gida tunda safe yafita sai yanzu yadawo,

  Amal da ke gefe tai wani dan guntun tsaki wanda yasa kowa ya kallota,

   Sheriff shigowa dakin idon shi akaina ya sauka, 

  Sai kuma ya kula da irin rikon da Aziza tai min,

    Cikin hikima naga ya dauke mata hankali don ta sake,

  Juyawa tayi wurin shi babu ko kunyar UMMI da ke falon tawani kama sunbantarshi,

  Ina ganin haka najuya don in koma dakina sai UMMI tace min 

   Fadima zo nan ki zauna mana karki koma daki ki kwanta ,

  Badon naso zaman falon ba na koma kusa da ummi na zauna,

   Saida komai yadan lafa ne, kowa na sa harkan gaban shi 

  Aziza tazo har dakina ita da Hindu, suna shigowa 

  Aziza da sauri ta karaso har inda nake, ta janyo ni zuwa jikinta ta rungume tace fadima,

    Kingama min komai aruyuwana tunda kin sama min abin faricikina da kuma alfahari,

   Kin gusar min da duk wani bakin ciki da tashin hankalin da dagin miji zasu iya kumsa min nan gaba ,,

   Saikuma ta juya inda Hindu take tsaye tana fuskantar ta, tace,

   Hindu Duk wani barazan nan da zai taso nan gaba ina mai tabbatar maki cewa zan iya jurewa intun kareshi ga ko waye,

   Saboda abinda nake nema nasa mu ko,

  Suka dan tafa gami dayin dan shewa,,

   Ashe duk wanan zancen da Aziza keyi a idon sheriff din mune bata sani ba,,

   Maganar ta doke har cikin ranshi,

   Jiyayi kamar yai magana a wanan lokacin, 

   Saidai kawai yadake yace bari yaga iya gudun su tukun,

   Ina tsaye daga inda nake idona ya ci,ciko da kwalla, mamaki su da kuma tausayin kaina ya kama,ni,

  Lalai mutum ba kyau wallahi ji yadda Aziza taita lalashi na akan in taimaka mata amma tun yanzu har ta fara ikirarin cewa zata iya fuskantar kowa akan wanan case din, 

   Hmmm mutum,

  Saida suka gama shewan su ta waigo taganshi tsaye, a kofar daki ya zubo mata ido,kawai, sai basar da ita ya nuna mata cewa baiji komai da take fadi  ba,

  Cikin halin ko in kula yake ce masu may kuka samu haka kukasa fadima a gaba kuna murna,

   Sai taji kamar ta fada mai komai a wanan lokacin don duk abinda zaiyi ayita 

   Sai kuma ta tuna cewa ai a kasar saidiya suke, 

   Yanzu ana iya sa ajefe su ko a rataye su bari kawai idan ta koma ta sanar dashi ko da tawaye ne,

   Yafi,mata alheri lokacin cikin ya kara girma sosai ta yadda baza,a iya zubar, wa ba,, idan har an gane plan din ta,

   

   Suna fita dakin na durkushe inda nake tsaye na fara wani irin kuka mai tsuma zuciya ni kadai a daki babu mai lalashina,

   Ji nayi andafa nadago kaina a hankali don inga ko waye,

   Maman Umar ce ta shigo dakin 

   Ta tasheni a hankali ta jamin hannu zuwa bakin gado ta, zaunar da ni,

 Ita ma din dai samun wuri tayi gefen gado ta zauna a hankali, 

  Tace min fadima duk da kina boye min matsalar da ki,ke ciki,

    A, gaskiya ni bazan iya sa ido ingan ki a cikin wanan hali ba,

   Kifada min may ke faruwa ne don in san ta inda zamu bullowa lamarin,

   Saidai kafin kice min komai yanzu haka salimat tana hanyan zuwa 

   Idan tazo dole ne muji abinda ke faruwa dake,

   Salimat ce tashigo don yiwa UMMI sannu da zuwa acewar ta,

   Wanda ko azahiri ba haka zancen yake ba, maman umar ce ta bukaci da tazo,

   Ganin da nai mata acikin shirinta yasa nagane cewa anan zata kwana ke nan,

   Batai min magana ba a lokacin munyi hira sosai da su Amal har wani lokaci,

  Mu kayi, shirin barci, sai a lokacin maman umar tashigo dakin itama,

   Saboda mun san cewa a lokacin kowa na gidan yai barci,

   Salimat ce ta fara matsamin akan lalai sai na fada masu halin da nake ciki 

  Saboda banda wanda ya wuce su a halin yanzu,

  Dafarko na rasa taya,ya zan fada masu cewa wai, ni fadima ina dauke da cikin da ban tantace kowaye uban shi ba har yanzu,

  Shin cikin dashe ne ko kuwa cikin sheriff ne, da yake ikirarin shi uban ciki,

  Kaina na sada kasa saboda na rasa ta hanyar da zan fara zancen nawa,

  Sai da takara kwantar min da hankalina ne 

   Na labarta masu komai tunda ga farkon zancen da aziza ta yaudare ni har zuwa dashen cikin ta kaini aimin,,

   Da kuma abinda sheriff yafada min da mukaje asibiti,

  Lokacin ne na fashe da wani irin kuka na ban tausayi,

  Suma dai din kukan sukeyi, 

  Cikin kukan ne nake cewa may zance wa mahaifiya idan Allah yayi komawa na gida,

  Nakara sa wani kukan kuma, 

   Maman Umar ce ta dan dakatar da mu daga sharban hawayen da mukeyi,

  Tace min fadima ba karya sheriff yafada ba,nikaina nasan cewa kina da auren shi, akanki da dadewa 

  Da sauri nadago kaina ina kallon ta cikin mamaki,

  Saboda haka maganar shi abin dubawa ne ,

   Sanin halin sheriff da mukayi shi zai sa mu kara gaskanta da maganar shi,,

    Saida salimat tadan dade tana nazari sai take cewa,

  Inko hakane gaskiya Fadima kin yi sa,a arayuwar ki 

  Saboda kowace mace na kokarin ace ta mallaki miji irin Sheriff Ahmad,

  Mutum mai tausayi da sanin addinishi ga taimakon na kasa da shi,

  Kawai yanzu sai mu jira kamar yadda kikace yace zai dauki mataki akan aziza macuciya,

  Wacce taso ta yaudari yar marainiyar Allah, saboda son kai da iya ha,incin tallakawa, ko na kasa gare su,

   Haka Salimat da maman Umar sukaita lalashi na har saida suka ga nadan samu na tsuwa,

  Salimat ta roke ni akan in kwantar wa kaina da hankali in ba sheriff hadin kai ta yadda zai samu yaci nasara akan azizan,

  Naji dadi kasan cewa tare da su yau don ko ba komai na samu, dan natsu ga irin nauyin da zuciya na yai min duk cikin kwana kin nan

  Ranan haka muka kwana muna hiran mu suna kara bani shawara akan in daure da kaddaran da yasamay ni,

   Sai kusan asuba muka dan samu muka dan ritsa idon mu, bada wani dade wa ba muka ji kiran sallah ya karade ko ina,

  Da safe saida salimat ta daidaici kowa na falo wurin yin break fast tasa na yin kwaliya cikin wani super wax mai ruwan green da dan adon flower yellow,

  Cikin kayan sallah da ummi ke aiko muna dasune daga Nigeria ,

   Dinkin ya matse ni cib,cib duk da ban iya daura dan kwalin atamfaba yau nadan kokarta, na dana wa kaina,

   Kurciya na fito da kyau duk wanda ya kalle ni yasan cewa sweet seventeen ce ni,

   Duk da ban son kamshi saida salimat tasa na daure nadan murza,

  Tare muka fito falon da ita ina dauke da baby As,ma,u, a hannu na,

   Fitowar namu yasa kowa kallon kofar dakin namu,

  Tunda na tunkaro kofar idon sheriff ke akaina, itako Aziza tana min wani kallon jin dadi da farnciki hakarta ya fara cin ma ruwa,

  Mai makon mu zauna asaman dinning table din sai muka zarce inda ummi take zaune saman wani carpet,

   Aziza tace wa maman Umar ta dibar muna abinci ta kai muna,

   Ina kallon miji da matar cikin su na rasa wanda yafi jin dadi gani na ahakan, yau,

   Amal ce ta ce kai fadima waiko kece kuwa kodai gizo idona ke yi min

  Salim yace gaskiya fadima nima dai ban fahinci ko may sirin ba fa,

   Wani iri naji azuciya na saidai kawai nadan basar da zancen da yin murmushi kawai,

  A, gaskiya babu yadda za,ayi in iya cin abincin nan da maman Umar ta aje min,

  Spoon din nadauka, narike kawai na, kama wasa dashi, ,,

   Ummuce tace min inci koda kadan ne,. 

  Duk yadda naso in daure inci nakasa,

   Ikon Allah to may kike so kici yanzu ko haka kike son ki zauna da yunwa aciki,

   Saida nadan marairaice murya nace UMMI ice cream zan sha,

  Nan kowa yasa ko min ido, da caaaa akaina, 

   Saida naji wani dan nauyi, 

  Kafin ummi tai magana sheriff ya riga kowa yace baki da tausayi ne fatima,

  Ki tausaya wakanki mana, tunda safen nan abu mai sanyi haka,

   Hindu tai shiru cikin zuciyar ta tana tunane kodai sheriff yasani ne,

   Amma ai da yasani da yai magana indai wanan mai kawo wa mutun Allah kusa ne,

   Aziza ta ce ,a,a ha kawai idan ra,ayinta kenan dan Allah kubarta ta sha abinta ai ra,ayi ko,,.

    Fruits maman umar takawo min cike da plate, ta aje min aiki na fara sha kamar hauka dama wani irin yunwa nakeji, sosai,

   Plate din da nasha fruit na dauka da niyar zuwa kitchen in kaiwa maman Umar,

  Daidai dan dogon corridor da zai kaika kitchen din naji an jawo ni da karfi,

   Nadauka faduwa zanyi a lokacin sai naji na fada ajikin mutun,

  Kamshin turaren shi yasa nagane sheriff ne,

 Tsintar kaina nayi da kara noke kaina sama kirjin shi 

   Saboda dadin kamshin turaren shi dana shaka,

  Da mamaki yakara matse ni cikin jikin shi, maimakon in zuke saina dan kara shigewa,

  Hindu ce tagan mu acikin wanan yanayin, ta  window dakin da take ciki,

  Kara ware idon ta  tayi don ta kara gaskanta idon ta ,

   Tabbas nice da Ahmad zuwa tayi don takira Aziza tazo ta ganewa idonta, 

   Abinda tagani, don bazata iya fada mata da baki ba ,

   Saboda irin son da Aziza takeyiwa Ahmad, idan batagani da idon taba bazata gaskanta taba,,

   Daukana yayi cak daga wurin zuwa ta cikin garaje din motar ta inda ba mai iya ganin mu,

  Saida na shaki mai isata na dan jaye jikina da sauri,

  Sai a lokacin naji wani irin mugun kunya har ban iya daga idona don kunya,

   Cikin dan kashe murya yace min fadima don Allah ki daina shan kayan sanyi pls kada ku samu matsala, keda baby na,

   Sai alokacin na tuna rashin kunyar danayi yanzu,

  Cikin kunya nadaga mai kai alamar naji,

  Hindu na tajan hannun aziza zuwa wurin window suna laikawa tana fadin kidiba kiga ikon Allah da kanki,,,

   Bakowa wurin wayau sai dogon corridor kawai suke hange,

  Wai Hindu may kika gani ne haka ke jana, kamar wata rakuma,

  Hmmm ba zaki gane ba idan nafada maki, tunda baki gani ba balle ki gaskanta, da idon ki,,

   Fadamin may kika gani ne wai tadan gyara tace Ahmad dinki da wanan yarinya mai kayan cikin ki ya rungumay ta

   Dariya tasa mata tace af ai saikiyi indai Ahmad ne haka yake ji da yan uwan shi , 

   Aishiyasa kikaga na daure ina son in kamo shi da kyau, 

  Kallon mamaki Hindu kemata na rashin gane gaskiyan da tagani,

    

     Har na kama hanya da niyar wucewa zuwa cikin gida, 

  Yace fatima na tsaya cak gobe zamu ganin likita 

   Don haka kada ki manta pls,

  Nakada mai kai nawuce ciki 

  Dariya nake bashi yanzu sosai rashin yin maganar da ban so na kara komawa yar karamar yarinya sosai,

    Doctor yakira suka shirya abinda in munzo goben za afada,

  Doctor ya dinga mai dariya cikin zolaya yana fadin zai fada man gaskiya ne kawai, idan munzo

    Washegari cikin dakewa yace Fadim ki shiya in maida ke asibiti likita yakarasa diba ki,

  Likita ya kara dibani ya dan yi rubutu a wani dan pepper 

   Sanan ya fuskance mu yace a gaskiya Ahmad baby baida isasar kuzari saboda rashi kulashi da bakuyi,

   Ban fahinta ba inji sheriff yace ma doctor 

   Doctor yace ma sheriff baka yawan yin sex da madan don haka baby baida wani kuzari aciki,

  Hakan ma na iya sa abincikin cikin ya zo da matsala,

   Harda dan zaburan mamaki sheriff yayi,

   Sai yadan kalloni don yaga ya zanyi 

  Likita ya ce katabbatar da daga yau kafara aiwata da komai yadda yafara,

  Wani irin kunya ne ya lulubeni a wurin kamar in nutse,

   Wai nice ake cewa inyi taraiya da Sheriffudeen Ahmad a matsayin mata da miji,

   Haba haba tayaya hakan zai faru kuwa,

  Har muka fito ba wanda ya iya magana daga cikin mu,

  Maimakon mutafi gida sai naga sheriff ya dauke har zuwa wani lafiyayyen gida yashiga har ciki da motar shi,

  Ganin danayi haka nadan kalleshi da mamaki 

  Batare da yakalleni ba yabani ansa yace taimakona zakiyi fatima kada baby na yashiga cikin wani hali pls,

   Ina ji inagani sheriff ya rabani da kayan dake jikina a hankali, , yana mai bani hakkuri da kuma kara yi min dadin baki,

   Haka sheriff ya shiga aiwatar da aikin sa lokacin da idona yake a rintse saboda ba zan iya hada ido da sheriff ba ayau,

    Sai lokacin da komai ya lafa, yaga damar hakkura da kanshi, badon ya gajiba,

   Yadan kamo habar na yana kokarin mu hada ido dashi duk da kukan da nakd kunzawa,

  Yadan rugumay ni saman kirjin shi,yana shafa min kaina a hankali yana bani hakkuri,,,

  Shirun da yaga nadan yi yasa yadan kura min ido yana lunshewa, sai tunane kala kala yake idon shi kyan akaina, yana gode ma Allah da yabashi wanan yarinyar mai tarin baiwa da ni,ima

  Hakan yasa yatuna da ranan da ya fara kusantar ta duk da ba ta cikin hayacin ta amma ya rude balle yau da take kusan idon ta biyu,,,

   Hawaye masu zafi suka dinga zobu min duk wani farinciki da fatan da nakewa rayuwa na ya rushe a yanzu a dalilin wanan cikin najikina,

🐎ZEEE.  MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈

           👣👣👣👣👣

            👣👣👣👣👣

                   7⃣2⃣

                     BY 

🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎 Almost true life story,,,


    Ina kwance na kasa koda dan motsawa daga inda nake 

   Nasan cewa tawa takare kenan tunda har haka yafaru da ni 

   Tare da kuma mutumin da nake ganin mutuncin shi fiye da kowa aduniya,

   May zance ma duniya, may zan fadawa inna na, tare da sauran yan uwa na,

  Jin da nayi yadan rugumoni ta baya shi yakara sani wasu irin hawaye masu dumi,

  Suna silalo wa daga idona 

  Zuciyana tana min wani irin radadi da soya,

   Lunshe idon shi yayi yana tunane kala kala na shiga zuciyar shi  idon shi kan  yar kyakyawan matar shi,,,

  Murmushi jindadi yayi ya kara mirginowa dai inda nake kwance,


   Ban ankaraba naji shi yana shafar min mara ahankali dai inda "da ke kwanci, acikin ciki,

  A lokacin naji yayi wani irin ajiyar zuciya mai sanyi,

  Kada ki fushi ko kuma zargin Ahmda da baburuwan shi da yin ikon Allah,

   Fadima na ji yana fadin  ada can babu wata kalman So ko Kauna a tsakani na, da ke,,

   Saidai tarin tausayi da dakuma taimakawa irin ta tsakani musulumi da dan uwan shi musulumi,

  Sai kuma kyautatawa irin ta anfito jinsi daya,

  Koda na aure ki kisan cewa ba na aureki bane 

   Koda na aureki bawai na aureki bane da niyar mu zauna irin haka na mata da miji ko abokin rayuwa, aa nadan wani lokacine kawai har in dan yi maku shiri kukoma gida,

   Sannu a hankali idanuna suka fara hasko min wasu abubuwa daga gareki,

   Tun ban yarda cewa ina sonki ba fatima sai gashi lokaci, guda idanuna na bukatar suyi ta kallon ki, 

   Kunnuwa na suna son suyitajin muryan ki, , haka har komai nawa yakoma kaunarki da taisayin ki kawai, ke min yawa azuciya,

  Ban kara tabbatar da hakan ba sai lokacin da kuka zo hutun da ya wuce a makkah,

   Tun wanan lokacin naji sha,awarki na yawan damu,

  Hakan yasa na kasa samun sukuni har Allah ya nufeni da saniki a matsayin diya mace wacce ni ne mutum na farko da na fara kusantarki a rayuwan ki,

   Sai lokacin da na dadani zumar ki nagane yadda kike ,

   Na tabbatarwa kaina kozan rasa banzan iya rabuwa dake ba farima,

   Akanki na gane cewa mata suna suka tara, saboda ada duk bugu guda nakewa mata,

  Ashe abin ba hakana yake ba, da, akwai banbanci sosai a tsakani,

   Duk cikin matana kece mace ta farko da na fara huda mata budurcin ta,

   Alhalin duk auren yan mata kuke a wuri na ,,,,,

  Yadan kara matseni a jikin shi kadan yace 

    Yai kamar yana shakan kamshin  gashi,kaina,

  Yace, Fatima kin taimaki rayuwana da abubuwa da dama kusan ince kin sadaukar da duk wani lokacin ki a kaina,

  Duk wani abinda zai tai maki rayuwa na kin yi min su tun kina yar karamar ki,

   Yakara jan suna na a hankali yayi wani dogon ajiyar zuciya  

   yace Fatima don Allah ki kasance a tare da ni ki taimaka min kibar wanan baby dake jikin ki yasa mu walwala ,

  Saboda ki haifo min shi cikin koshin lafiya,

    Yace har in zaki min haka to kisan da cewa kin gama min komai da nake fata arayuwa,

   Mamaki maganganun dayake suka bani har saida nadan yi ajiyar zuciya,

  Sheriff da nasani mai mata irin Nafisat da Aziza yan gayu shine ke wani zuzutani agaba haka,

   Yakara fadin fadima ki fahince ni pls da sannu zaki gane ko waye Ahmad, 

   Haka dai yai ta lalabani har saida yaga nadan samu natsu 

   Sannan  yakyale ni saida naga fitowar shi daga bayin,

   Ko yagane cewa ina jin kunyar shine, yasa yadan fita ta falo kaman mai yin waya,

   Na dan lalaba na mike, nafada bayin ,

   Ruwa masu zafi nasamu ya ciki min a bath, nashige ciki a hankali, ina wanka wasu hawaye masu zafi su ka dinga zubo ,

   Wani irin bakin ciki da tausayin kaina nake ji,,,

  Ina fitowa na kimtsa jikina tsab kafin ya shigo,

   Yadawo dakin cikin shirin shi tsab kamar ba shi ba,

   Kallo guda yai mata sai ta bashi tausayi yadda yaga tadan takure gefe,

   Yarinyar da ada yake dauka yar karamar yarinya yana raina mata wayo,,

  Yau itace wace ta kawar mai da duk wani, kwadayin daya dade, yanayi ga diya mace,,,

   Dan gefe na yazo yadan zauna,kusa dani, yace min kin shirya muje ko ,

   Yanayin muryana na dole yaba mutum tausayi, nace mai eh,

   Yakara tambayana ko akawo min abinci inci na kada mai kai kawai nayi,

   Ya ja wani dogon numfashi yace to tashi muje ko,

   A, hakali na mike saidai yanayin tafiya na yadan canza sosai  

    Ya dan tsaya daga baya yana kallon yadda nake takawa cikin dabara, yadan girgiza kan shi kawai,

   Azuciyar shi yace yarinyar na bukatar kulawa gakiya dole ne yadauki mataki da wuri,

   

   A falon gida muka samu kowa zaune wasu na hira wasu na kallon tv ,

  Sai ummi ce zaune da casbaha a hannun ta, tana ja,

   Shigowar mu yasa Aziza shiga cikin wani guntun tunane 

  Shin tare muka fita da sheriff ko kuwa ya akayi muka hadu,

   Abin mamaki sai naga yarikide min kamar da kamar bashi bane yaga min wa yan, nan kalaman dan lokaci kadan da suka wuce,

  Anty falmata ce ke min sannu da jiki, dakuma tambayana ko zan ci wani abu,

   Kifin inyi magana muryan Amal ne take cewa ai don taga kowa na damuwa da ciwon ta ne shiyasa taje kara narkewa mutane,

  Abarni kawai idan naji yunwa nida kaina ai zan bidi hanyar abinci,

  Ummi tace mata amma Amal baki da tausayi yarinya tana fama da lalura irin haka har zakina ce a kyale ta,

  Dan murmushin yake nai ma Amal kawai azuciya na kuma ina cewa  ummi ta kyaleta tana da gaskiyar ta sanin da tai min bana yan zuba,,,

     Maman umar takawo min fruit's masu dan sanyi da kuma lemon kwanko,

   Nadanci kadan sai kuma yau naji kawai ban ra,ayin ko fruit din 

   Wani irin amai ne yataso min narike bakina da hannu guda  da sauri nature kayan plate din gefe na fada daki, na,

   Aziza ce ta tashi da sauri tabi bayana don ita azaton ta ina shirin zubar da cikin ne,

   Nafito daga bandaki ke nan tafado min cikkn daki a hasale,

  Cikin tashin hankali take maganar ta, fadima may kikaje kikayiwa dana,

  May aka baki ki kasha kike wanan aman haka,.

   Don  lafiya kalau kibar gidan nan koda natashi akace min kin tafi asibiti, wai,

  Tana batun kara matsowa kusa dani , ni,ko ina tsaye ina kallon ta cikin mamaki,

   Muryan Sheriff ne mukaji ta bayan mu yana cewa,

   Aziza cikin ki ko nawa da mamaki ta waiga inda yake tsaye tana mai kallon mamaki,

  Cikin rashi, facinta, ta ke mai, kallon shi wani iri,

   Ya buga mata tsawa yace may kike zaton zatayiwa cikin da ke da uban shi,

  Cikon da baida uba wanda ba,a yarda dashi shine ake ma yunkurin halakawa akoda yaushe,

  Yanuna ni amma ba irin wanan mai uban ba, kuma uban mutum mai tsoron Allah irina ba,

  Macuci wanda zai cutawa rayuwar yariyar da bataci ba batasha ba,

   Ya karaso inda nake tsaye ya kama min hannu a hankali yace min in zauna,

   Za taimagana yakara daga mata hannu yace may zaki fada min 

  Aziza shin mugun kudurin da ki kayi niyar yi, da yar mutane ko kuwa nida kike,so ki kulin ,sheri kikeso yi min bayani,,,

    Dan murmushi tayi irin na yan duniyar mata, 

  Ta tako har inda yake tsaye,

  Itama wani irin harara ta dankara mai tace kana nufin ka gane nufina akan wanan cikin da nasa ai mata dashe ko may,

   Ya buga mata tsawa yace ke dan Allah yimin shiru, 

  In ba haka ba yanzu in kira maki hukuma atafi da ke,

   Aiko kamar ya tunzura ta, ,, matstawa tayi har gaban shi ta rike kugun ta da kyau,

  Tace har yanzu ban fahinci irin butulcin da kake shirin yi min ba,

  O saboda rashi tausayi Ahmad shine zaka ce wai yanzu kai ne uban wanan cikin 

  Saida ya dan murmusa kadan yace mata, 

 Aziza kin so ki cuce Allah bai yarda ba kamar kuma yadda kikaso ki cuta wa mata, ta fatima da mugun nufin ki na kudirin sai kon haihu ko ta halin kaka,

   Ai idar har kina son haihuwa da kin haihu da kanki 

   Kiga alokacin zan san cewa ki na kaina na


 Cikin nuna alamar bata fahince shi ba take maganan ta still,

  Tace au kana nufin kun hada baki ne da fadima ku cuce ni,

  Tobari kuji,

   Sperm dinka da nawa likiti yai amfani dashi yasa ma fadima 

   Kaga kenan abinda ke cikkn cikin fadima nawane nida kai ,,

   Ita nata wahalar kawai shine tai min rainon ciki idan ta haife in karbi baby na nagama da ita,

  Idan kuma har kana da ja ga wana maganaa shirye nake da muje wurin duk wani hukuma ta duniya don ai muna sheri,

  Saida sheriff yadan kallo inda nake zaune lokacin da tai kalamin ta na karshe,

   Kafin wanin su yai wani zance muryan UMMI ce ke tambayar may ke faruwa ne haka,

   Shiru duk kan mu ukun mukayi a lokacin,

  Mamata dan kalli gefen da yake tace mai matar ka bata da lafiya kazo kuma kuna daga mata hankali haja a gabanta,

 

    Cikin mamaki take kallon ummi ta nuna inda nake da yar yatsarta tace

   Fadima ce matar Ahmad kuma,. 

   Saita bushe da wani irin dariya tana tafa hannayen ta,

   Tace mamaki  yau kuma kulin sheri ne haka wai don aimin dabaran rabani da abinda na kwallafawa rai,

   To karyan ku don baku isa ba wlh,

 Ganin da yayi idonta ya rufe zataima harda ummi rashin mutunci yasa shi cewa cikin tsawa get, out my friend,

   Ai baka isa ba Ahmad sai naji matsayin da kuke son ku sa cikina aciki tukun,

   Ummi da bata fahinci zancen ba sai take cewa Alhamdullah mata biyu da ciki lokaci guda,

   Aziza takara kawai ummi kallo tace wai nida wace matar tasa,

   Wanan karon falmata ce a kofa jin da sukayi fitinar yana kara yawa suka taso gaba dayan su zuwa dakin ,

  Tace kina nufin kice baki san cewa fadima matar shi bace tobarima kiji don inaga ita din ta rigaki auren shi, tana mai nuna inda nake zaune,,,

  Tawani kyalkyale da dariya kamar wata tababa, 

  Tace yau naji na gani,

 Hindu ce tayi kokari ta kusa kai cikin dakin taja hannun Aziza tana fadin ki kwantar da hankalinki Aziza muji bayanin su,,,

   Hindu wa yan nan mutanen suna son su raina min wayo,

   Kiji fa wai cikin da nasha wuya kafin samun shi ,shine yau suke son su cuta min akan shi,

   Yai dan murmushi yace mata Hindu ki barta har in bata yarda ba sai mu koma gurin likita taji da kunnen ta ko,

  Cikin fushi ta fita dakin Hindu ta mara mata baya,

  Adakin su take ta zirga zirga taje tadawo,

  Hindu tace saida na fada maki cewa  karki yarda kiyi wanan plan din da wanan yarinyar kika ce min ai baza a samu matsala komai ba ke kinyarda da ita to yanzu gashi irin abinda ta jawo maki,

  Kidiba irin wahalar da mukasha, da irin kudin da muka kashe akai,

  Hanna tadaga wa hindun tana hade wasu miyau masu daci tace,

  Bar wanan zancen Hindu aiba zaiko sabu ba wai bindiga a ruwa,

   Ni za,ai wa wanan drama din,

  

   Da sauri ta jawo jakarta  ta lalibo wayarta, 

   Number doctor Khan takira bayan sun gaisa take sheda mai cewa tana son su zo wurin check up da da wanan yarinyar , 

  Doctor Khan yai dan shiru nawani lokaci, can yace mata, 

  Ai bai ma wanan yariyar komai ba saboda yarinyar nada ciki already a lokacin,

   Hakan yasa baisa mata komai ba don babu zancen yin artificial insemination, ga wanda ke da ciki,

  Yakare zancen da cewa ta diba prescription din da yabata tagani zata ga komai ai a rubuce,

  Da sauri ta jawo jakar da tasa takardun a ciki diban farko ya nuna mata cewa ba ai min wanan dashen ba,

  Ta wurgar da wayan don ta daina jin zan cen doctor Khan wanda kamar ruwan zafi yake kwararo mata a kune,

   Sai a lokacin take tuna nen cewa kudin da ta tura mai na aikin tabbas bai cire ba har tanawa Hindu complain din haka,

    Aiko nan da nan idonta yakoma kamar garwashin wuta,

  Sun wani kade sunyi jajir

   Yau ita Aziza za aiwa rainin wayo haka,

  Ita Ahmad zai wa cin amana haka,

  Tare da yar yarinyar da take ma daukar yar ficiciya,

  Wasu irin hawayen bakin ciki suka ahiga zubo mata, daga idon ta,

  Tarike kan ta da hannu biyu,tana fadi sharaf saman gadon ta,

  Tashiga rusa kuka kamar wata yar karamar yarinya,

   Ita Aziza za aiwa rainin hankali irin wanan babu abinda zata sa agabanta wanda bata samay shi ba,

   Babu wani wanda zai mata wanan rainin hankalin ta kyale shi,

   Kowaye dole ne saita dauki fansa akan wanan cin fuskan da ake shirin yi mata,

  Hindu ce takara kwantar mata da hankali akan cewa ta bari,a bisu a hankalin har ta dau fansa  a,kan duk wani cin amanar da Sheriff yai mata,,,,Dan Allah kuyi hakkuri saida na gama typing tun a,round six saboda yau weekend ne ashe banyi storing ba sai ya goge kuma wlh nagaji da typing,

   Pls kuyi min afuwan 👏👏👏👏👏

   

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈

          👣👣👣👣👣👣

            👣👣👣👣👣👣

                       7⃣3⃣

                           BY

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎


   Almost true life story,,,


    Ina daki takure wuri guda, sai tunanen abinda Aziza tace min yanzu keta min yawo a hankali,

  Watau Allah ne ya rufa min asiri da ya kawo min sanadin wanan cikin, najiki,

  Da Allah kawai yasan irin bakin ciki da tashin hankalinnda zan shiga, akan wanan cikin ukubar da ta , tashi sani,,

   Salimat da Amal suka shigo dakin a tare, yadda salimat tagan ni zaune, cikin damuwa,,

  Amal ce tazo,Gefena ta zauna muna dan fuskantar junan mu nida ita,

  Naji muryan ta na fadin Fadima a gaskiya kin bani mamaki kwarai,

   Yanzu ace har kin yi wanan plan din keda Aziza muna tare wai ban sani ba fadima,

  Tana kada kafa tana magana cikin fushi, ,

  Takara waigowa takale ni tace min fadima na fada maki cewa Aziza ba mutumiyar arziki ba ce,

   Ki ka ki yarda da duk wani shawaran da nake baki akanta,

  Ki ga mace haka ai kema kinsan cewa ba tsarar yin ki bace,

   Salimat tace Amal ke nan, ai ke ayadda ki,ka gane kowaye Aziza Fadima bazata gane hakan ba ,

  Don tazo mata da fuskan musulunci ne saboda fadima ce tie get din ta dama,

  Kawai kirabu da mutun macuci,

  Yanzun dai ai Allah yafita yakuma fi sherinta,

  Ina jin su amma har suka kare maganan da zasu yi ban iya daga kai na kalli inda Amal take ba,

   Saboda kunya dakuma wani irin nauyinta da nake ji,

  Don nasan cewa tanzu tasan cewa sheriff yai min ciki

  To a yaushe ,kuma a ina, ?

   Sai kawai na ji wani irin hawayen bakin ciki na silalowa da ga idona,

  Subbahanallahi fadima na hanaki wanan kukan baida amfani wlh kisan cewa bake kadai ba ce yanzu,

   Amal ta dafani tace min haba matar yayan mu 

  May kuma zai saki kuka  matas sai nakara jin wani zafi,

  Da bacin rai kamar in ta dukan ta, nake ji,

   Salimat ta kawar da zancen da Amal ke ta tsokanata, 

   Ta ce min waiko fadima kina karatu kin san fa mun kusa fara exam ,

   Sai a lokacin na tuna da zancen wani karatu can don, har na man da zancen karatun naga abinda yafi karatu fitina,,,

   Saida Amal ta dan fita dakin Salimat tasamu tadan matso kusa dani kadan tace min,

   Bana son wanan kukan dakike yi fadima watau baki rugumi kaddara ba ko ,

  Mutum zai iya yiwa kasan abinda Allah bai tashi yi mai ba,,,

   Nadan girgiza mata kai, kadan tace, kinga dai yawan bacin randa kikeyi zai iya jawo maki wata lalura,

  Ki daina haka na ,ki godewa irin baiwar da Allah yai maki,

  Haka taita min kalamai masu dadi har hankali yadan kwanta nai mata Alkawarin insha Allah zan daina,,,

    Naji tai shiru nadan wani lokaci, can tace min 

  Fadima ina son ki yarda da mijiki don gudun shiga hakkin aure ,

   Ada rashin sani ne yanzu ko kin san komai sai ki dauki damaran kyautatawa a tsakanin ku,

  Saboda gujewa wa fushin ubagiji ki, 

Da ma duk wanda yakama, hanyar Aljanna zaita haduwa da abubuwa, masu wuya wanda zuciyar mutun bataso

   Haka na wanda yakama hanyar wuta shima zaita haduwa da abubuwa da zuciyar shi ke so,

  Shiyasa aka ce daga cikin hakkuri, da ake son mutum yayi cikin rayuwan sa 

  Harda hakkurin biyayya ga Allah da manzonsa, da kuma,hakurin yarda da kaddara kowace iri ce dan gujewa sabon Allah,,,

  Ki daure ki ja mijin ki a,jiki shike karasa shakuwa da yarda ta kara dauruwa a tsakanin ma,aurata,

   Kisa ni cewa duk kan ku uku matan shine, kowa ce da ga cikin ku da halinta zai zauna da ita,

  Don haka kada ki bari abarki abaya,

  Idan baki zama ta farko ba kada ki bari ki zama takarshe a gurin shi,,,

   Shiru nayi ina ta ina jin wani kuna a zuciya na,,

 Ina kuma,sauraren ta har ta kare ta mike tana fadin cewa gobe in shirya zamu tafi ziyara don in kai wanan cikin gurin ziyara,

  Hakan yasa nadan murmusa don ni kaina nasan cewa na dade rabona da zuwa ziyara,

   

    Duk ilahirin gida jen shi yasa ansa mai CCTV a boye batare da sanin kowa, ba,

   Saboda tsaro da gudun wani abinda za a iya kara kullawa,

   Maganar Salimt ne keta min yawo a kwakwal wa na,cewa in bi mijina to ta yaya, hakan zai faru,,,


     Washe gari da safe na fito falo ko zan dan wal,wale kafin mutafi ziyara rauda, anjima,

   Aziza da Hindu sun sa sheriff tsakiya kamar ba bu abinda ya faru ,jiya tsakanin su,

  Azuciya na ,nace tabbas salima kin yi gaskiya zama saida gwanan cewa,

   Ummi ce ta fara hangoni ta ce min a fatima kin tashi ko zo ki zauna nan ki karya kinji,,

    Sai nadan waiga inda suke zaune don gaishe  su ,,,

   Muna hada ido da Azizat tai min wani irin wawan, harara 

   Sai na dan dukar da kaina don a gaskiya ban iya mata rashin mutunci ko kadan,

   Sheriff yace min inzo in zauna gefen su sai nadan marairaice murya na nace mai gurin UMMI zan zauna nagode,

    Sautin murmushin shi na ji itama azizan shi tawaiga don ganun abinda yakewa murmushin,

  Nice yabi da ido har na zauna, kusa da inda ummi ta mayar kamar dakinta gefe guda daga cikin falon,

   Wai don ta jaye mai hankali shi daga gare ni sai ta dauko jam tana shafa mai a bread din shi tana wani , kokarin matse jikin ta da nshi,

   Tamiko mai yace a,a barshi kawai na koshi zan je in sha fruit,  da mai cikin can,,,

  Itama yunkuri tayi ta mike tsaye tana fadin barin riga ka kagin ka isa, nima in taya ku,,

   A hankali ya lunshe idon shi yai dan takaittacen murmushi,

   saboda yasan cewa Aziza nada wani manufa azuciyar ta gamay da ni,

   wanda ba zai taba yarda hakan ya faru da, ita insha Allah,

  Dar dar nake da ita ta zauna tana wani nan ,nan da ni,

   Sai kawai naji fruit din sun fita min a rai sam,

  Ganin da yayi ta takura min har ban iya shan fruit din yasa ,

   Shi mikewa yana cewa zai je ya dawo, yanzun nan,

   Yana fita tabini da wani mugun kallo wanda bani ba har ummi saida ta tsargu da ita, 

   Suka tashi suka bar falin zuwa cikin dakin su da suka sauka,

   Suna shiga Hindu tayi shewa tace mutumiyar kin yi wlh kinga gun ma da kika daure kika nuna afili cewa ba komai,

   Kinga yanzu sai mu fara shirin yadda za mu bullo wa lamarin,

    Tun bayan faruwan wan rikicin sai yau na kira sheriff a wayana wayanda bansan inda ma na jefata ba, da,,,,

   Kiran farko yadauka yana mai cewa Assalamu aikum,

  Cikin siri,riyar murya na ansa mai sai kuma na kasa mai magana

   Nai shiru kawai ina kalon kasan daki,

  Muryan shi naji yana cewa fatima kiyi magana mana,

  A hankali na ke ce mai zamu tafi Rauda ni da salimat , anjima kadan,

   Shiru yayi  can yace aida ni yakamata mu tafi  bada salimat ba don muje mu gaida fiyayyen halitta tare da Sahabban shi, ko,

  Amma tunda da salimat zaku tafi sai kun dawo saboda ni har na riga kuzuwa don yan zun haka daga can nake dawo,

  Dàn Allah ku kula da kan ku saboda irin yawan da akeyi wurin ,

   A hankali na ce mai to,

   

       Tare muke da Salimat harda Ummi da falmata duk sun biyo mu,

  Bayan munyi sallah muka isa cikin rauda don ziyara,

  Nidake kokarin wajen tare wa, mutane fili don suyi nafila, raka,a biyu,,

   Sai gashi yau na kasa dole nice aka tarewa gaba da baya har na samu na,idar da sallah na dade zaune gurin ina rokon Allah mafita akan lalura, ta tare da naiman kariya, daga duk wani sheri,

  Ummi da falmata suna kallon yadda nake komai nawa acikin tsanaki da kwanciyar hankali,

   Hakan yasa su kara godewa Allah da ya Ahmad irin matar da suka dade suna mai sha,awan yi,,,

   Muryan falmata ne yakatse ni lokacin da nake tsaye ina ma manzo na salati,

    Tana fadin kiyi adduan Allah bayas da masu albarka, dayawa,

  Maganarta yasa ni dan yin murmushi kadan, kunya yakamani na dan dukar da kaina kawai,,,

   Motar salim ce  muka shiga, ina baya tare da anty Falmat da Salimat ummi ce gaba tare da Salim

    Munje har bakiya aranan, 

  Muna kan hanyar mutadawo wane Sheriff yakira layi na,

   Yace min ina fatan kun kama hanyar dawo wa yanzu saboda baby na kada ya wahala,

   Kin san Allah ya sauwakawa mace mai ciki kaifin ibada,

  Cikin jin kunya don banson zance yai nisa don gani nakeyi su falmata da salimat na jin mu ,

 Na ansa mai a hankali da fadin eh,,

  Mundawo gida lafiya bawa ni damu atare dani ko kasala kamar yadda nasaba ji ajikina duk kwanan kin nan,

   Duk wanda yagan,ni yasan cewa ina cikin walwala yau din,


   Abin mamaki yau harda dan abinci da ummi tasani gaba saina ci nadan tsankwara kadan,

  Batare da nayi amai ba,,ni kaina nayi murnan hakan 

  Don har nake cewa salimat yau banyi amai ba,

   Haka mukai ta zama gidan mu tab da baki kala kala,

   Kowa ta shi irin lalurar da ya kawo shi

Irin Aziza da zaman hada plan kawai sukeyi a madina,

   Saidai tayi rashin sa,a saboda ta manta cewa a babban birnin da isalama take ne duk cikin duniya,

   Annabi yace idan duniya ta kusa kare har addini zai kasu kashi kashi, kuma duk islam ne 

   To idan har ana son a gane alkibila ta gaskiya aje garin Madina,

  Har duniya ta tashi garin Madina suna akan sunna ce ta gaskiya,

   Baza su taba canza alkibil da manzo ya dora su akai ba,,,,

  Don haka addini ce sahihiya a madinan kusan duk bukata ta alheri ta wanzuwa ga bawa, amma banda na sheri,,,

   Duk yadda taso ta fara aiwatar da niyar ta takasa dole suka shirya tafiya komawa Dubai har suje su kara hada sabon plan in yaso sai su dawo da shirin su,,,

    Washe gari tunda safe suka shirya da niyar bin nirgi daga madina,zuwa Dubai,

   Ina tsaye a dakina ina shirin fita zuwa school yau,

  Aziza ta turomin kofar daki ,

  Jin yadda aka turo kofan yasa na kalli hanyar shigowa da sauri, don inga kowani mara hankali zai min haka,

   Ganin yanayin da takene ba cikin kwanciyar hankalin ta take ba yasa ni nadaure na gaishe ta, acikin sakin fuska,

   Hannu ta daga min alamar inyi shiru,

   Tadanzo gabana tazagaya harta bayana ta na kare min kallo 

   Ina tsaye cikin doguwar riga mai yar guntunwar hannu, baka tadan matse ta tsakiya, sakuma kasar rigar tadan bude kamar rigar indaya 

   Flower farin zare ne akai yi mata a tsatsaye nikaina nasan cewa rigar tai min kyau so sai,

    Saida takare min kalli da kyau tadawo ta gabana ta tsaya gab da ni har muna iya jin nunfashin junar mu,

  Ta nunani da dan yatsan ta tace fadima ina mai tausaya ki da kika yaudari Aziza a rayuwan ki,

  Aziza ba a cutar ta a kwashe lafiya, kisani cewa 

  Ahmad nawa ne kaida bada kowace mace ba haka kuma wanan dan dake a cikin cikin ki nawane har abada ,,

  Wani karfin hali naji yazo min da tace hakana,

  Nadan kali inda take tsaye tana wani dan buga kafa nai dan murmushi irin mai ba mutun haushi

    Nace mata, tunda har Ahmad din da kike gadaran cewa naki ne ke kadai bada kowace mace,ba

  Gashi yau yadawo ga yar karamar yarinya har yakai ga mata abin dake kikadade kina bida da kudin ki da ilimin ki,

    Taiwani kukan kura kamar zata shake ni, ashe Hindu nata wajen kofa tana kallon masu shigowa da fice agidan,

  Ta rike mata hannu ta baya tana fadin ki,kan mantacewa agarin da shariar musulunci tafi karfi muke aziza,

  Takai kusan minti biyu tsaye tana min wani irin mugun kallo na tsana 

  Ina tsaye kyam ina kallonta babu kowani tsoro,

   Ganin kallon bai da alamar karewa yasa nadan geza da gefenta nayi tafiyana zuwa wurin mirroww na din in daura dan kwalina,

  Saboda time na kure min na zuwa school,

  Tai wani irin kutawa Hindu najan ta suka fita dakin suna fadin cewa zamu hade dake yarinya very soon,

  Saida suka fita nabi suda kallo kuma ina mamakin kaina wai yau nice na iya tsayawa  gaba da gaba ina bawa aziza ansa 

  Duk da nasan cewa bata da gaskiya amma nasan cewa hakan bsidace ba tunda ita ba warin yina bace,.

  Kafin indaura Naifal dina Yashigo dakin rike da yar briefcase din shi, da alamar cikin sairi yake,,

   Saida yai min wani kallo na sha,awa tukun sanan yace min ya muka kwana,

  Ina tsaye nadan jingina da mirirrow kaina yana kasa,

  Nace mai Alhamdullah,

 Masha Allah yace, yakaraso ya man namin kiss a tsakitar goshina,

   Kunyan haka da yake min nake ji sosai

  Muryan shi naji yana cewa ina son in je in sauke su Aziza airport yanzu, 

  Yana fadi yana kallon agogon hannunshi,

   Yadan kallo ni yace min kada ki damu kanki da duk wani barazanan da aziza zataimaki 

   Ashirye nake da daukar mataki a kanta,

  Har zai fita sai na tsinci kaina ina may mai fatan alheri da adawo lafiya,

 Saida yadan waigoni don mamaki,,,,,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈

           👣👣👣👣👣

             👣👣👣👣👣

                     7⃣4⃣

                       BY 

🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎  Almost true life Story,,,


   Tun tafiyar su Aziza sai gidan namu yakoma normal kamar yadda muke ada can babu wani haya niya,

  Daga can sheriff ya bugo muna waya cewa yatafi Riyadh ba zai samu dawo wa ba.

   Hakan yakara dan sani na sake jikina kadan don in samu time din yin karatuna,

  saidai kusan ko yaushe ina daki na kwance ko ina karatu,

   A yau mun tashi da wuri saboda zamu dan yi test,

   Saboda haka a tsatsaye muka shirya don saurin da mukeyi,,

   Muna shirin fitane Ummi ta tsaida ni akan cewa bazan fita gida batare da na yi break fast ba,,,

  Gudun kar wani abu yaje yasa may ni acan daga salim har Amal dariya suka kamayi,

   Ummi ta ce ai bani kadai ba waidon ina da ciki tace, a,a duk musulumi ba,a so yabar gidan shi batare da yasamu dan wani abu yasa a baki ba koda one spoon na koko kona tea, ne

   Saboda yin hakan ya a tare wa bawa, kaddara, so sai,

  Tace amma ku yanzu saboda ilimin zamani duk kun can za akidar alherin da aka dora mu akai

   A hankali na koma na dan hada ruwan coffee kawai batare da nazuba  wani abu ba na 

   Nasamu guri nadan zauna nasha,

   Ina tunanen irin alherin da Ummi da yaranta ke min akoda yaushe, abin baiko lissafuwa, 

   Muryan Salim ce ta katse, min yar tuna nen da nashiga,

  Yana cemin idan nagama inyi sauri mutafi in ko zan zauna ne inkara narkewa 

  Shikan zai tafi ne,

  Murmushi na saki gami da mikewa tsaye ina ma su Ummi sallama,

    Allah sarki rayuwa haka abubuwa sukai ta dan faru acikin yan kwanakin nan ,

  Wuni mukeyi yanzu zungur a makaranta saboda muna gab da fara exam 

    Hakalina a kwance yake don har naka dan manta da lalurar dake tare da ni,

   Abinda ke a gabana kawai shine exam da nasawa rai kamar may 

   Burina kawai inga na gama wanan karatun,da nakeyi ko zan san ida na dosa da tushi,

   

   Yau ni kadai ce na na dawo, gida , saboda na rigasu fitowa 

  Sai kawai naji bazan iya tsayawa in jira su ba, natari taxi yakawo ni har kofar gida,,

   A kusa da kofar gidan mu kadan naga wasu matasa biyu suna gyaran motar su, 

  Da alamar lalace masu tayi kila,

  A hankali na wuce su zuwa ciji batare da na kula su ba,

   Ina shiga ciki naji cikin,

  Gidan namu shiru kamar ba kowa aciki, nadiba inda ummi ke yawan zama a falo, bata gurin itama,

  Ina mamakin ko ina suka tafine sai na ji muryan su ta bayan gida don haka sai ban tsaya bin ta nasu ba,

   Daki na nufa nasamu guri na kwanta, don indan, hutu ,Agajiye nake so sosai,,

    Barci mai nauyi yai a,won gaba da ni, so sai,

A, cikin barcin nake jin kamar ina shakewa numfashina yana dan sizing a hankali,

  Allah yatai makeni nadan bude idona, a hankali,

   Wani dan kya mushashen bakin  balarabe nagani rike da wata farar takarda a hanni shi,,,

  Ganin da yaimin na farka yasa shi kokarin jada baya a hankali,

  Ina son in yi ihu amma nakasa ko da dan motsawa, daga kwancen da nake,

    Allah yaban iko nadan yi ihu da karfi har mama Umar dake kitchen saida tajini tare da su ummi mama umar na kawowa suna cin karo da wanan mutumin 

   Ya,bita tagar dake facing din baya yadira waje,,

   I,hun danayi yasa kowa saurin zowa inda nake, a lokacin ne kuma idona yake rufewa a hankali,

   Cikin rudani da tashin hakali kowa dake gidan yake 

   Shigowar Salim yasa su dan natsuwa nan maman umar tai mai bayani ihu na kawai sukaji,

  Saidai lokacin da zata shigo ta hadu wani dan saurayin bakin balarabe yana kokarin fita ta window tagar dake kusa da dakina,

   Salim bai jira komai ba yakira yayansu ya fada mai abinda ke faruwa a hankali, 

  Alokacin yana can U S A suna kokakarin kara hafbaka company nonin su ,

   Asibiti aka kaini direct har lokacin ban ko da iya dan motsawa ,

   Likitoci sunyi iya kokarin su don gane may ke faruwa da ni,

  Tun karfe ukun rana da abin yafaru ba agane komai basai kusan shabiyu dare aka gane cewa a shaka min wani powder wanda zai gusar min da hankali har na kwana kusan uku ko biyu,

   Daga U,S,A ,sheriff yataso ranan duk da uban aikin dake gaban shi,

    Sai asuba ya iso garin madina, ,a masallacin dake kusa da asibiti yai sallah asuba sanan yakaraso cikin asibitin,

  Kwance na ke sharkaf dani sai ta nunfashin da nakeyi ta na,urar taimakawa mutun ne za,a gane cewa ina da sauran rayuwa ajikina,

  Duk wanda ke gurin a cikin tashin hankali yake, saboda irin yanayin da nake a ciki,

  Sheriff kawai akayarda ma yashiga inda nake saboda tsaron guri ba,a yarda kowa ya shiga sai wanda ya ke,zama dolen ka, miji ko mata sai kuma mahifan mutun,

  Yana shiga yadan ja ya tsa daga kofa yana min wani irin kallon tausayi,

   A, hankali yatako jiki ba kwari har zuwa bakin gadon da nake kwance,

Durkusawa yayi gab dani yana kare min kallo, sai kace bani bace fadimar da yasa ni cikin dan lokaci guda duk na zabge


   Hannu na yarike a hankali ya dan duka agefen gado yana min kallo acikin tausayi,

    Zuciyar shi duk ta cunkushe da bakin ciki da bacin rai ga wani radadi da zogi da yake masa yawo a zuciyar shi,

  Yadan daga kai ya kalli gefen da nake kwance tausayi na yakara kamashi sosai,

   Da sauri ya mike daga bakin gadon kamar wanda aka mintsira, yasoma zagayen dakin yakasa zaune ya kasa tsaye,

  Duk da sanyin A, C dake dakin bai hana shi karyo da wani irin zufa ba, alokacin,

  Wanene wanan mutumin da ake tunanen cewa ya shiga mai gida,

   May yake bida a gurina, ko kuma waya turo shi, yazo yai min hakan

   Juyawa yayi a hankali yana kallon yadda nake fitar da numfashi a hankali,

   Sai kara jin tausayi na yana shigar shi,

  Yadan lunshe ido yana tuna yanayin da yasan ni da shi tunfarko, ganin da yai min,

   Son wasa da ruwa, murmushi dayawan yin kwazon aiki, sai yar tsiwa ,ga hangen nesa, surutu idan tasan mutum, saikuma iya yin fushi, uwa uba kykkyawan zuciyar da Allah yabata saboda bata rikon mutum duk laifin da ka iya yi mata,

    Ya furta a hankali fatima ke ba kowa ce amma kuma kina da komai da kowa ke so,a tare da ke,

   Halaiyarki kadai ya ishi ni abin alfahari,

   Zama dake yasa ina iya zama da yan uwa na akoda yaushe,

    Fatima bazan iya jure rashin mace irinki ba, aduk lokacin da na kalleki, yana wanke min duk wani damuwa da maraicin rashin saboda iyayyena da ban yi ba abaya,

   Saboda ita gata mace kuma yar karama amma ta dangana ta jure da rashin ganin yan uwanta da batayi ba,,,

  

    Cikin ikon Allah da tai makon Likitoci suka samu da kyat Allah ya basu sa,a nadan farfado,

   Daga dogon sumar dole da ,aka sani,

  Sheriff ne tsaye yana fuskantar inda nake kwance sai likitocin da suka dan zagaye ni ,,,

   Abuna farko da akafara yi shi ne diba, lafiyan baby da ke a jikina,

  Sun tabbatar da lafiya kalau baby yake saidai weak din da abin cikin, cikin nawa yayi, kawai,

   Wani irin yunwa na farfado dashi, wanda har jikina rawa yake yi,

   Duk wanda ke kusa saida yai mamakin irin abincin da naci, yau,

  Nida kowa yasan cewa bani cin abinci sai gashi nakusa share plate guda ina gamawa na kara kwantawa, sai barci,

   Haka sheriff yakwana kusan a zaune ranan don da na motsa abinci zanci,

  Sai yakasan ce duk wani motsi nawa idonunshi na akaina musanman rana yana tare da ni,,

    Sai bayan kwana biyu na san cewa a,asibiti nake kwance,

   Nayi mamakin hakan kware da gaske don ban san ko mai yakawo ni ba,

   Sai lokacin da askarawan saudiya suka shigo gurina don suyi min dan bincike,

   Abinda nasani kawai na iya fada masu,

   Suka rubuta tare da shaida wa sheriff cewa an kusa cin nasarar gane ko waye wanan mutumin,

    Saida jikina yai min karfi sosai aka sallamo ni daga asibiti,

   Bayan sun tabatar da cewa lfy ta kalau, har baby nawa,

   Saibayan kamar sati guda aka gaiyaci Sheriff a office din bincike sun gane cewa yaron da yai yunkurin shaka min wanan powder daga Yamal yake,

    Kuma bincike ya nuna cewa sun dade suna bibiya na ,

   Sai a wanan ranan Allah yaso basu sa,a,

  Sheriff najin cewa daga Yamal suke sai, ya mike tsaye yana fadin Alin Alin 

  Bayan an gane cewa Ali baba ne yaturo su kuma daga shi har su , sun bar kasan tun wani dan lokaci 

  zuwa kasar turawa inda Alin din ke aiki yanzu,

    Wanan abin yaiwa Sheriff ciwo so sai saida kuma yasan cewa komai dadin dadewa zasu kara hadewa da Alin din insha Allah,

   Kowa yaji mamakin cewa wai Alin ne yaturo atafi dani a cewar shi wai dole ne sheriff yai min na aure shi,,,

   

    Kulawa ta musan man nake samu so saidaga sheriff tare da sauran yan uwan shi,

   A haka na fara rubuta jerabawa na karatune sosai babu kama hannun yaro,babban burina shine in sama sakw na results mai kyau dan in amfana da abina nsn gaba,

   Kusan ko yaushe, ina samun sakon cards da kuma gaisuwa da fatan alheri daga Sheriff,

    Saida mukayi first exam din mu sheriff ya ce ma ummi yana son ya kaini kasashen waje s diba lafiyar jikina dakyau da na baby shi,

   Jin haka yasa sam bakawo komai ba a,raina jin danayi cewa zamu tafi ganin likitane,

   Amma sai nake cewa Salimat yanzu duk irin kokarin da likitocin saudiya sukayi akaina za,ace kuma sai ankaini wani guri,

   Nace mata nidai gaskiya nafi gamsuwa da aikin su tunda su, yan uwa nane musulumai 

  Wa yan can ko kafirai ne wa yanda ba sa kaunar  cigaban musulumai sam,

    Salimat tace ai saikiyi shin dake da baby da baby duk mallakan shi ne kuma kudin shine zai kashe bana ki ba iyakar ki, zama ajirgi yar uwa,

  Dole haka na Salimat ta shirya min kayana a yar karamar kit muka tashi zuwa Riyadh da marance saboda tafiyan dare zamuyi zuwa kasar paris ,,

   Tun a madina da mukayi sallama da su salim da sukayo muna rakiya,

   Nafara ganin canji ga sheriff,

  Sai a wanan tafiyar nasan cewa ashe dama ban san kowaye sheriff Ahmad lawal ba,

   Saboda ya canza min ga sheriff din da nasani ya koma ma min wani can da ban,

   Wata irin mahaukaciyar soyayya yake nuna min wanda bantaba sanin cewa akwai shi ba har za,a iya yiwa mace shi ba,

    Tunda muka kasance a guri guda koyaushe kusan sheriff ya man,ne a jikina

   A marci kawai yake ta faman kwasa abinshi, al,amarin yaki barinsa balle, yaji na gundure shi,

   Sai kuma wani sabon shagwaba yazo min wanda ni sam ban ma san cewa ina yi ba sai fama langabewa nakeyi

  Wanda iyakar gaskiyana ke nan saboda ban saba irin haka tare da namiji ba,

   Sheriff yakoma min kanar wani wawa saboda yawan like min dayake har takai yadan daina fita wurin harkokin sa sosai, koda yaushe yana like da ni 

    Saida fadima taga abin banawasa bane ya sa taimai maganar abinda yakawo ta 

  Murmushi ya yi yajanyo ta zuwa jikin shi yace mata haba Fatima aikwai wani likitan da yafi iya,awone a yanzu,

    Kiya addu,a kawai Allah ya sauke ki lafiya ki haiho mi baby mai kama da ke ,

   Kunya ta kamata, ta kwantas da kanta sosai a kirjin shi,

  Cike da shagwaba  tace to amma aini ce min kayi zan zo a kara diba lafiyata ne so sai,

  Ya ce in bada ke Fatima kina ganin cewa akwai wanda zai auna ki da kyau bayan ni,

   Ya dan kara janyo ta kadan yace kidan kara daurewa nan da wani sati zamu koma gida insha Allah,

   Danbuga kafar ta takamayi alamar ita bata yarda ba wayo kawai yake mata,

  Yadan lunshe ido yace fadima bakya jin dadin kasan cewa atare da ni ne koko ya, ya ne a,

    Tace ni kawai dai gida nake son komawa gurin su Amal,

   Yasan cewa ba laifinta bane, don bawai ta saba dashi bane irin haka yasan cewa dama sai a hankali,

   Saboda duk yadda yaso ta cire kunyan shi fadimar ta kasa hakan,

  Satin su biyu cif a paris suka wuce kasar italy  daga italy suka wuce dubai,

   A ranan fadima ta godewa Allah da yai mata wanan baiwar da daukaka a,rayuwan ta,

  Ina rungumay a jikin shi ,don haka yake min duk inda zamu indan har tare zamu fita,

   Ajikin shi zan man,ne har inda zamu ba zai sake ni ba,

    Wasu makullaiya ya miko min yace min makullaiyan moticin kune wanan keda su,

  Nafisata saboda nasan cewa saudiya basa barin mata su tuka mota yasa za a wuce maki da shi Nigeria 

  Idan kintafi can zaki dinga amfani da ita,

  Murna zanyi ko farin ciki, sai kawai naji baki na yana zuba godiya,

  Yace mu a,a ni ban son godiya kinfi kowa sani, 

   So nake kawai ki so fiye da komai da kike so aduniya sai kuma sai zuria masu albarka da zaki dinga bullo min,

  Daga karshe in kasance  namijin dayafi kowa dace da gyaran wurin gado,

  Murmushi  na danyi nace mai insha Allah zan kwatanta,.

   Murshi yayi kawai a ran shi yace badai wayau ba Fatima,

  Sosai wanan karon ya matse ya ce min Fatima banda wani guri yanzu a rayuwana da ya wuce in samu zuri,a masu albarka indan kikai min haka nagode Fatima,,,

   Wanan maganar da yayi ta karshe yasa yabani tausayi sosai ban san lokacin da na shige cikin jikin shi ba sosai,

   Ji nayi ya nemo bakina ya man,ne da nashi, wuri daya, can wata duniyar na tsinci kaina irin duniyar mai nuna kalar kore shar,

  Wanda kesa ka manta da kowa da komai naka,

    Fatima sai godiya take ga Allah ubangiji subahanahu wata,ala da wanan baiwar da yai mata lokaci guda,

   Matsalarta guda yanzu shine mahaifiyar ta da yan uwanta su ne matsalar dake da mun ta,

   Idan ta tuna kowani irin hali suke ciki yanzu sai hankalinta yatashi so sai,

   Don haka ko yau da ta tuno da su sai ta tsinci kanta da rashin walwala.

   Da jin komai na duniyar yafita mata a rai gaba daya,

   Lokacin Sheriff da yafita zuwa maikatar su na Abu Abdallah ya shigo masaukin nasu,

   Hannun shi rike da yar briefcase din shi dake dauke da laptop dinshi da sauran takardun su,.

    Ganin da yai mata cikin irin wanan yanayin yasa ya nufe ta da sauri yana mai aje yar case din shi saman kujera,

   A gabanta ya durkusa ya dan kamo hannun ta ya ce may yafaru ne fatima,

   May ye matalar ki fada min pls,

  Duk sai tambayar yakara ruda ta, nan da nan idon ta ya dan ciciko da hawaye,

  Sai hankalin Sheriff yakara tashi,

  Yace haba fatima kada kimin haka pls ki fada min damuwar har in akwai 

   Farin cikin ki shine nawa fatima, don ke ce kusan duk wani kwanciyar hankalina,

   A hankali nadan zamay daga rikin da yai min na ce,

  Ina tuna maifiyatace da yan uwa na, saboda ban san irin halin da suke ciki ba acan,

   Ba karamin dukar zuciyar shi wanan zancen yayi ba saboda yasan cewa gaskiya fatima ke yi,

   Shi yakamata ya fara tuna wa da hakan tun kafin ta fara magana

  Amma sai abubuwa suka sha mai kai har ya shafa da zan cen,

   Ki kwantar da hankalinki Fatima idan har Allah ya sauke ki lafiya dole muje su gan ki da akwai shirin da nakeyi gamay da hakan,

   Hakadai yai ta mata dadin baki har ta hakkura tadan kara sake jikinta shiko yai ta kwasar garan shi,

   

      Ba karamin sayayya Sheriff yai min ba din kayane irin na matan manya na alfarma ya saya min

   Suturu ne masu tsadan gaske ya saya min, irin kayan matan larabawa tsakiya ma su tsadan gaske,

   Wasun su suna hade da alkyaba mai hade da hula,

    Sai dogayen riguna different design masu kyau da daukar ido kowani da abin lailayan jikin shi,.su takalma da jakkuna kala kala,

  Ita da kanta tace mai kayan sun isa haka,

   Saboda cika mata ido da sukayi, ga kayan baby unicef da ya saya suma masu tsadan gaske,

   Murmushi yayi da tace mai kayan sun isa hakana yace fatima shigar ki ta alfarma cikin suturu ne mutunci na banda wani buri arayuwa na banda in kyautatawa iyalina da yan uwana,,,,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈

            👣👣👣👣👣

            👣👣👣👣👣

                   7⃣5⃣

                      BY

🐎 *ZAINAB* *IDRIS* *MAKAWA* 🐎

🐎 *HUGUMA* *GROUP* 🐎


    Almost true life story,,,,,


 Jirgin da zai sauka birnin madina, ran daren Laraba muka shigo,

   Salim ne yazo taron mu shida wasu mutum biyu, cikin farin ciki da kwanciyar hankali muka sauko 

  Kallo guda zakaiwa sheriff kasan cewa ya samu lafiya fiya da ,da ya wani murje yadan kara kaurin jiki kadan gawa wani haske da yakara,

    Muna hada ido da salim naga yai min wani kallon mamaki, yana murmushi,

  Mungama clearing na komi ,muka fito cikin air port din ,motoci ukune muka jera zuwa gida,

  Katuwar pickup din dake bayan mu an lodo mata kaya saida ta shake fam,

   Muna tafe salim nata zolaya na yanata mamakin irin kyaun da nakara cikin dan lokaci guda,

  Ina jin duk abinda yake fadin saidai ban iya ansa mai alokacin saboda duk a gajiye nake 

  Ga wani irin barci da nake duk ya kara saukar min da kasala ajikina,

     Maimakon mu tafi gidan mu inda muke sai naga mun yi parking a wani kyakyawan gida mai kyau da kuma girma sosai,

   Sai alokacin Sheriff dake gefe na zaune yadan waigo yana kallona 

   Ya dan duko kadan daidai saitin kunne na yace min welcome to your new house, fatima,

  Da sauri na mayar da dibana akan gida cike da tunane iri,iri,

  Dan kallon shi nayi da mamaki sai kawai yadan daga min kai kadan alamar eh,

  Cak naji nunfashi na kamar ya tsaya min saboda mamakin, jin wai wanan gidan gidan da zan zauna ne,,

  A,zuciyana nace ni fadima diyar inna yar kulu ce zata shiga cikin wanan katafaren gidan mai kyau,

    Ginan gidan yakai gina a gaskiya kowa yasan yadda gidajen saudiya suke da kyau da tsari kamar ba hannu yai aikin ba,,

    A hankali na fito motar sheriff yafito inda nake a ya dan rika min hannu cikin kulawa da so da kauna,

   Mukashiga cikin gidan gami da sallaman mu,

  Kallon mamaki kawai nake bin gidan da shi, saboda irin tsaruwar da gidan yayi,

   Motsi da naji alamar akwai mutum a gidan ya sani daga kai da sauri nakai kallona ta gefen da naji motsin,

   Don in ga ko waye, hakan yai dai da lokacin da mama Umar ke kokarin bude falon gidan don mu shiga,

   Mukayi ido biyu da sauri na ja hannu daga jikin sheriff na nufe ta da murna na,

   Muka rungumay juna cikin murna da son junan mu,

  Kafin in mata wani magana saiga salimat rugumay da As,mau tana muna lalai mar ha bbin,

   Bansan lokacin da na sake maman Umar ba na nufe ta, na rugumay su,

  Gyaran muryan da sheriff yayi ne yasa muka dan waiga ya tsaye inda na barshi hannu shi a cikin aljihun shi 

   Yana muna kallon cikin nuna alamar in bi a hankali pls,

 Sukuma su Salimat cak suka tsaya gaba dayan su suna min wani kallon cikin mamaki,. 

   Murmushi na sake masu, gami da karasa ga kujerun da ke falon nadan zauna,

   Ganin kallon yai yawa yasa na dan kalli kaina ina mamakin ko may sukaga na canza ajikina suke min wanan kallon,

    Cikin natsuwa na dan kalle su nace anty Salimat, wai may nayi ne kuke min wanan kallon haka,

  Kafin su bani ansa Amal ta fado falin da kusan gudu,gudu,sauri,sauri,

   Tana zuwa ta fada min ta rungumoni ajikin ta, muka dan kankame junan mu cikin murna da an nashuwa da jin dadi,

    Sai a lokacin naga UMMI tsaye, a bayan Amal, tana muna murmushi,

   Tana fadin, a a tafiyan cikin, dare haka, aiko saidai jirgi kam,

   Tsam,tsam na isa gareta saboda kunyar ta da nake ji na dan rugumay ta, 

  Haka aka hau murna da farin cikin dawo war mu lafiya,

   Ganin da Ummi tai min na a gajiye nake yasa ta cewa ya kamata mudan huta kafin a kira sallah,

   Kowa yace gaskiya kam,

  Wata sabuwa wani kato bedroom mai dauke kayan alatu iri, iri Amal ta kai ni,

   Mamaki duk ya cika ni jin cewa wai shine daki na,

  Cikin mamaki da kuma nuna hankali nake karewa dakin kallo,

  Fitar Amal ya bani damar cire kayan da ke a jikina a, hankali don duk a gajiye nake a lokacin,

   Sheriff ya shigo dakin a lokacin shima a gajiyen yake saboda dan bata lokacin da jirgin mu yayi a Dubai kafin ya taso,

   Ta bayana yadan zo yana kokarin tayani cire rigar,

  Saida yaga ya cire saura yar breezeir kawai da dan bujen ciki yasa ya dan kyale ni, rigar barcin da nagani a saman gado nadauka, na sa ajikina,

 Sai a lokacin na fahinci cewa ashe wai daki guda zamu zauna da ni da sheriff ,

  Tirka shi, ga ummi ga su salim da Amal zan zauna da shi daki guda 

  Gaskiya da sake bazan iya ba sam 

   Yagane mai nake nufi sarai, saidai bai nuna min yagane ba, wanka yaje yayi yana fitowa ina zaune bakin gado har yanzu sai ce mun  yayi bangaji ba ke nan tun da ban kwanta ba ko,

   Nadai san cewa bazan yi wanka ba a cikin daren nan ba, ko,

  Saida na dan bata rai nace, ni gaskiya dakin Amal zan koma,

   Kafin in wani maga sai kawai naji ya kwantar dani ta baya a hankali,

   Bada son raina ba dole na hakkura hakana na kwanta tare da shi daki daya,

   Duk da gajiyan da muka kwaso hakan bai hana mu farkawa da wiri ba don yin sallah a suba ,

   Sai dai ina idar,wa na kara kwantawa kuma ,sai wani barci mai nauyi yakara daukana,

   Yuwa kawai ya sani farkawa, da ga barcin,

   Wanka nayi nafito cikin shigar wata doguwar riga irin ta matan Brazil,

   Rigar light blue ne, har kasa take saidai hannuwan ta shara shara ne haka bubude, cotton ne sosai sai wani sulbi da yauki takeyi, nasa yar gyalenta na daure kaina,

   Saida naci abinci so sai na koshi a lokacin ne, nake tambayar anty falmata,,

   Amal ke sheda min cewa ta koma gida tun bayan wucewar mu da kwana uku,

   Gaskiya banji dadi da ta wuce bani a gari ba don, 

   Salimat da ke gefe take ce min fadima waiko kinga yadda kikawani kara girma ga fari dakikayi,

  Kinyi wani kyau sai kace irin matan nan da muke gani a TV ko muji rabarin su,

   Murshi kawai nai mata nace aike dama kullun haka kike cewa idan kin kwana biyu baki gan ni ba,

   Tace gaskiya wanan daban yake, ba kamar na kullunba Allah sai kace an maki wani famfon girma,

   Duk muka dara gaba dayan mu dake a cikin falon 


   Mun dawo bamu wani dade ba sheriff yakoma harko kin sa,

   Sosai yanzu arzikin sa ke ta bunkasa kamar  daga sama,

  Ikon Allah ke nan, don har yan uwan haihuwan shi su suraj yana kokarin taimaka masu 

  Duk da hassada da bakin cikin da hjy mama ke nuna mai hakan bai hana shi sasu cikin harko kin shi ba,

   Don suma din sungane gaskiya tunda wayayyu ne ba su bari hjy mama ta ruda su ba,,

   Mahaifin su yaji dadin wanan abin da Ahmad yayi wa yan uwan shi ya sha albarka so sai da fatan alheri ga tsohon,

   Hankali na a kwace na ci gaba da harkokina sosai saura yan kwanaki mu gama karatun mu,

   Gashi da mun gama zasu tafi Nigeria don daurin auren Amal da Almustapha da za,ayi a can mahaifar su, Amal din,

    Ranan da na samu wanan labarin gaskiya nayi farin ciki sosai saboda nasan cewa Almustapha mutumin kirki ne ,

  Kuma gaskiya sheriff yayi dibaiya so sai wuri bashi yar uwan haihuwar da ya aura,

   Almustapha mutumin kasar Sudan ce , gurin aikin su guda da sheriff yana zama a matsayin yaron sheriff ne,

   Hakan sai wani shakuwa da yarda yashiga a tsakanin su, 

  Har abin yazama masu kamar zumunta,, mai karfi a tsakanin su,,,

  She nice ban sani Amal sun dade suna soyayya da almustapha ,

  Wani irin rana ake fatsamawa agarin kowa kagani yadan samu wuri yadan boye ma wanan zafin ranan,

   Don haka nima ina fitowa daga exam nakira driver mu na ce yazo yakai ni gida,

   Don haka, a cikin wanan ranan  nadawo daga makaranta a gajiye nake saboda nauyin da cikina yafara yi min ga kuma zafin ranan da akeyi, yau din

   Ina shiga gida dakina na fada da niyar in tube kayanan jikina inda watsa ruwa ,

  Aziza ce kwance a she me,me tayi da daya a saman gadona tana waya abinta hankalin ta kwan ce

   Da yar mamaki makale a fuskana, na tsaya sororo tsaye ina kallon ta,

  Allah yabani ikon karanto mata addu,oin kariya daga duk wani sherin dake tare da ita,

 Cikin daurewa nai mata sannu da zuwa 

  Hannu kawai ta daga min batare da ta ansa min ba,,

  Ganin danayi wulakanci take son tai min kawai yasana juya daniyar in fita waje, sai ce min tayi daga yau kada inyi gigin cewa zan tako mata daki,

   Da kyar na iya lalubo na tsuwata wuri guda nace mata dan Allah tayi hakkuri bansan cewa tana ciki ba,

   A hankali nadawo baya ina mai rufo mata kofar dakin,

  Duk gajiyar da na debo da zafin da nake ji sai na bide su na rasa, alokaci guda,

   Wani  irin duhu da na tashin hankali nake gani don gani aziza ba alheri bane gareni,

    A hankali nake tafiya cikin yar doguwar corridor da ke sada mutun da daku nonin gidan

   Zuciya tab da tausayin kaina saboda dama nasan ko mijin suwa na aura,

   Daga Aziza har nafisat na san su nasan halin su, 

   Jikina gabada daya yayi san yi na rasa ma wani guri zan dosa a lokacin,

  Maman Umar ce ta fado min a rai gurinta na nufa kitchen,

   Itama din tana gani na ta taso cikin sauri ta tare ni, tace min cikin larabci kada in nuna ma Aziza nadamu da zaman ta a dakina ko kadan tace min ta gyara min daki guda dake gudan bangaren mu,

   Murmshin karfin hali nayi mata nace mata aiba komai rayuwace duk hakan,

   Maman umar ce ta jagorance ni zuwa dayan dakin kusan komai na dakin iri dayane da wanda nake a ciki,

  Saidai dan banbanci kadan dakuma irin kayan bukatu da yasa min ciki,

   Ko wanka da nake ma sauri banyi ba na fada saman gado na kwanta a hankali,

   Ashe tun fita har dawowan mu da maman Umar Aziza ta labe tana kallon mu,

  Tai wani dariyar mugunta ta koma cikin dakin tana karewa dakin kallo saboda irin tsaruwan da dakin yayi,

   Tai mamakin yadda sheriff ya haukace akan yar karamar yarinya alokaci guda,

   Mai wanan yar kwailar yarinyar keda shi wanda ita bata dashi har yake rawan kai akanta,

   Zanyi maganin ta in har don wanan cikin yake wanan rawan kai haka zata barar da cikkn kowa ya huta,

   Don ta riga tasha alwashin cewa bata barin garin nan sai taga cewa ta halaka cikin dake jikin na ni, fadima,

   Idan yaso tasan kuma yadda zata raba wanan aure da yake ikirarin cewa ya dade da,aure bada sanin ta ba,

  

   Niko tunda naga aziza tazo sai nake tsoron cin komai na gidan duk da maman Umar na iya kokarinta wurin ganin cewa

  Tana kula da duk wani tako da kuma kulli da Aziza keyi, akaina,

    

   Gurin Salimat nake yawan zuwa inci abinci kafin in dawo gida, ko kuma kafin in tafi school sai in biya incika cikina fam, in wuce,

   Sannu a hankali maman Umar ta san kwaso min wasu kayan bukata na tadawo min da su cikin dakin da nake zaune, a yanzu,

   Ganinda Aziza tayi cewa duk wani kullin da takeyi bai ci yasa ta sake min fuska faran faran,

   Duk da yarinya nake hakan baisa na yarda da shimfidar fuskan sherin da take, kulla min ba,

   Satin Aziza guda a gidan ,duk su Ummi har Amal  ba su san cewa ba,a dakina nake zama ba,

   Kuma gashi kusan ko,yaushe muna tare da Amal amma ban taba fada masu cewa ai Aziza adakina take ba,

   Sai a yau da Amal tazo gurina ansan hand dryer dina saboda nata yadan samu matsala,

   Da yar sallamata tafada dakin kamar yadda mukeyi a kullun,

   Ganin mutum tayi saman kadon tim kamar antara kayan wanki, wuri guda,

  Duk da tasan cewa ciki ke gareni amma dai ban kai ko kwatan haka tari ba,

   Da mamaki ta isa har bakin gadon tana kare ma aziza kallo cikin tsana da kiyayya, take mata kallon raini,

   Takara juyawa takalli dakin tsab taga cewa ba wani alamar da ya nuna cewa na kwana acikin dakin,

  Cikin sauri tafito waje zuwa wurin Ummi don ta fada mata cewa bata ganni ba a daki na sai dai aziza dake kwance,

    Maman Umar da ta dauko min abin breakfast wanda ta kasa ta tsare a kitchen din ko gusawa bata yarda tayi ba saida ta gama min komai tadauko zuwa dakin da nake ciki,

   Ina zaune dagani sai yar doguwar rigar barci har kasa mai yar kuntun hannan shimi,gefen rigar ta kasa andan tsa, tsaga ta, kaina babu dan kwali,

  Kusan atare suka shigo dakin ina zaune a gaban mirrow da waya a hannu na,

   Cikin mamaki da masifa Amal take min wani irin kallo ,

  A hankali maman umar ta aje min abincin a saman wani dan stol ta na kokarin gyara dakin ,

   Amal tace min cikin fada fadima ban gane ba shin da yardan ki Aziza ta zauna maki a daki ko kuwa ,

  Saboda may zaki dawo wanan dakin ki zauna kibar mata dakin ki, 

  Murmushi nai mata na jawo dan teburin abincin a gabana wanda, nadade banci abincin gidan ba,,

   Kafin in bata ansa maman Umar ta kwashe yadda akayi tun ranan da Aziza ta iso muna school ummi tace a kaita dakin da sheriff yace a dinga aje baki nagida,

  Amma sai tace ita ina ne dakin Sheriff maman umar tace mata ai daki guda muke 

   Sai tace to ita a nan zata sauka,inda sheriff yake, da tace mata to ni fa sai cewa tayi wai in koma dakin baki

   Dakin sheriff nata ne ita dashi fadima bata kai matsayin da zata zauna inda taje zama ba,

 

      Da sauri Amal ta juya cikin fushi tabar dakin nawa, A dakin Ummi ta samay ta rai a bace take mayar ma ummi da komai dake faruwa agidan 

  Hakalin UMMI yatashi matuka don sam bata zaci hakan ba daga Azizan,

  Ina kwance a daki kasan cewa yau ban shiga school, yasa da nagama abin da nakeyi sai na koma na kwanta , saboda in samu indan huta,

   Jin sallaman Ummi na daga sama a cikin dakina nayi mamaki kware har na nuna mata hakan a fuskana,

   Mikewa nayi zaune daga kwanciyar da nayi, ina mai gaida Ummi, dake kokarin zama saman yar kujerar da aka a je a cikin dakin

    Shiru yadan biyo bayan zaman nata,

   Can takira sunana a hankali tace may yasa kibar ma Aziza dakin ki 

   Alhalin kisan cewa wana dakin shine dakin ki na halal malal,

 Saboda ko wanan gidan saboda ke ce yasa aka gyara shi,

   Idan har ba zata zauna inda yace na baki ba da ai sai ta koma inda tafito 

  Don ni ba ga abinda yakawo ta wanan garin ba tun da Alhajin karami baya kasar, ban san zaman may take anan ba,

   Saida na barin ummi ta kare zancen ta  duk kai na yana a kasa,

   Can nadago kaina ido na sunyi raw ,raw alamar kuka ,

  Nace , La, ummi ai ba komai anan din ma inda nake babu wani matsala gaskiya,

  Ummi kinsan cewa ita ce, matar sheriff, itace ta can can ci zama a wanan dakin bani ba,

  Ummi kinsan cewa aurena da Sheriff kawai nufi na ubangiji amma ai ni ban kai matsayin auren shi ba,

   Ummi tace min assha, fadima aure ai baida wani can,can ta ko sa,ayi,

  Abune mukaddari daga Allah, 

   Idan har kikace haka to gaskiya baki godewa Allah da ni,imomin da yai maki ba,

   Nace a hankali na gode mana Ummi, baga shi ko ina godiya akai ba,

   Dan murmushi na manya mai nuna cewa yaro dai yaro ne tai min,

   Tace fadima wa,yan nan kishi yoyin naki da kike gani basu san Allah, don basa aiki da maganar Allah,

  In bashi ba gaskiya da batayi wanan abin kunyar da tayi ba 

   Donko kowa yasan cewa ai ba dakinta bane dakin ko,

   Son zuciyane kawai irin na marasa tsoron Allah, wa yanda basa tsoron gamuwar su da Allah

   Aida tana da imani da ta tausaya maki acikin wanan halin da ki ke ciki haka,

   Amal ko tana waje sai faman kiran layin dan uwan su takeyi bata samu ba,

   Sai a na karshe ne tasamu layin nashi ya shiga,

  Bayan sun gaisa ne take tambayar shi ko yasan cewa aziza tana saudiya kusan sati guda,

   Yadda yai ihu mamaki saida Amal taji shi,

   Yace nafada mata cewa ina na turkey muna kokarin muga cewa duk kayan mu ansa a conterner neno anturo muna dasu gaba daya,

   Maimakon Amal taji yai magana sai taji kawai ya ma kashe layin nashi gabadaya,

 Dif kake ji,

   Wani haushe yakamata tadan kali wayar tai tsaki, 

  Tace in fa yayan mu yasan cewa bazai iya daukar wanan amanar ba gwara kawai saki diyar mutane 

   Don kada su taru shida matan shi su cuta min, tunda duk sun fini wayo da sani ta duniya,

    Azizs na daki abinta hankali ta akwance sai waya takeyi ta yarda zata samu ta samu, sa,ata taci 

   Nasarar lalata min cikina ko ta halin kaka, sai taga bayan cikin nan,


🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈

            👣👣👣👣👣

             👣👣👣👣👣

                      7⃣7⃣

                        B Y   

🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎   Almost true life story,,,


 Assalamu Alaikum yan uwa musulumai,

   Dan Allah a tsakanin marubuta da makaranta yakamata asamu kyakyawan facin ta,

  Bawai challenge's ya shigo ciki ba, idan har marubuci tayi wani abin da yadan kauce wa addini ko tarbiyan mu yakamata akirata in prevent aimata gyara ,

   Babu wanda yawuce gyara aduniya, tundai na fannin addin mu,

  Yima marubuci cin fuska a bainin jama,a baida amfani wlh,

  Wanan rubutun da kuja ga munayi abune mukaddari daga Allah, akwai masu so soyi amma Allah bai basu ikon yi ba,

  Bakaramin wahala ke cikin rubutun novel ba yan uwa,

  Yakamata duk yadda marubuciya tai novel din ta a gode mata, indan har da gyara akira mutun a gefe not in public aimai gyara,

  Pls mukuma marubutan Allah yakara bamu hakkuri a tsakanin mu mukara daurewa da makarantar , duk abinda kayi ba aima korafi akai ba, wanan abin baida ma,ana ne ,,,,,

   Idan nafadi ba daidai ba ina mai rokon gafaran ku yan uwana,👏👏👏👏
    


 Kitchen din shiru yake babu kowa acikin shi sakamakon kashe na,urar da zata sada ma kitchen din da ruwa,

   Hakan yasa ma,aikatan fita waje don ganin ko may ye matsallar ,

   Maman Umar abin ya bata mamaki kasancewa ko a daren jiya itace tayi aikin karshe a kitchen din kuma ruwan yana zuwa normal,

   A hankali ta fito daga dakinta tana tafiya cikin sanda har ta shiga kitchen din,

  Saida ta leka ta tabbatar da ba kowa a waje lokacin ta ciro wani dan koya daga cikin gefen breast din ta ta jefa a cikin flower sinasir da maman Umar ta kwaba ,

   Tafito da sauri tana dan waige waige, bayanta,

  Tana shiga dakin ta tashige bayi ta wanke hannuwan ta tsab, takoma saman godon ta kamar wacce bata tashi daga barci ba,

   Bayan angyara matsalar ruwan maman Umar ta dawo taci gaba da aikin ta,

 Tanagamawa ta jera komai a carpet saura kuma masu ci a table aka kai masu nasu, saman tebur,,

   Saida kowa kusan ya hallara a falon wurin karin kumallon safe,

   Kusan nice ta karshen zama a falon saidai ba a saman kujera na nufa ba,

  Wurin Ummi na nufa don a saman carpet, take zama ,

   A hankali na dan durkusa gami da kara gaida Ummi karo na biyu,

   Saida na sawa plate dina komai da nake sha,awa, nadan tsiyaya ruwan sha, a cup na aje a gefe na,

    Nai bissimillah nadauka zankai wa bakina,

   Aziza dake zaune daga gefen mu ta kura min ido, Allah Allah take yi in kai a bakina,

  Daidai lokacin da zan kai a bakina sai wayana dake gefe yadauki ruri 

  Mayar da sanasir din nayi cikin plate na, nai saurin daukar wayan , diba massage din,

   Ganin nobar Amal, da nayi yasa ni saurin ta shi kusa da Ummi , 

   Kada kici abincin nan fadima ,

   Kuma in kin karanta kada ki dago kai ki debe ni pls,

    Gashi dai nagama karantawa amma sai na kasa daga kaina sama, 

   Wani irin mugun tsoro ne yakamani saboda nasan cewa Amal bata maganan banza 

   Maimaikon in juya sai na mike kawai daga, gurin da niyar tashi ,

   Muryan Ummi ce na ji tace min fadima da wo mana kici abincin cikin sanyin murya nake ce mata,

   Ummi zan dauko ma salimat takarda ne a daki, yanzu zan dawo, sai kuma wani dabara yafado min nace ma ummi bari ma dai intafi da abincin daki na kawai sai inci a can,

  Wani wawan ajiyar zuciya Aziza tayi,jinda tayi cewa zantafi dakina in ci,

   Mutun biyu ne Allah yanufa suci sanasir din, dayake suna da rabon wahala,,

  Da Salim sai Ummi duk yadda Amal taso ta hana Ummu ci acikin hikima hakan baiyi, ba,

  Ciwon ciki ne mai karfi ya turnike su sai ,

  Tun ana abu wasa wasa har takai ga anyi rushing din su asibiti,

   Nan likita yai masu dan bayani akan cewa akwai abinda sukaci Allah nai yatai make su sun kawo su asibiti da wuri,

  Yace amma inda mace mai cikine taci gaskiya da abin yafi nan worse,

   Jin hakan yasa hankali kowa tashi kowa da abinda yake tunane acikin zuciyar shi gamay da abinda likita yace,

  Kwanan su biyu , a asibitin aka sallamo su zuwa gida,

  Har a lokacin Amal batace min komai gamay da text din da tayo min ba,

   Hakan dai danaga irin wahalar da su ummi suka sha yasani shan jinin jiki na sosai,

  Sai yakasan ce duk gidan hankali na a tashe yake so sai,

  Gurin Salimat na tafi da kukana nafada mata duk yadda mu kayi da Amal,

  Itama dai shawara tabani sosai akan yadda zan zauna da kowa agidan 

  Tace min akwai abinda Amal take zargi a gamay da ni,

  Hakan yasa tunda ga wanan ranan Salimat ce ke kawo min abinci a boye ko kuma intafi gidan ta ince a can,

   Yau bazan tafi school ba don haka na koma nadan kwanta don in huta,

   A can cikin barci na rika jin kamar ana tabani sama sama,

   Sai kuma na dinga jin kamar ana kiran suna na a hankali,

   Cikin karfin hali na bude idanu na a hankali, tayadda ba kowa zai iya gane cewa na bude ido na ba,

 Aziza ce tsaye da wani abu kamar jan kyale a hannun ta,

   Can kasan gadona naga ta duka ta aje kyalen a hankali kuma ta taso ,

   Ta kama hanyar kofar dakin fita zuwa waje,

  Ido kawai nabita dashi a hankali har ta kure min 

   Bakina duk adduan da na sani na tsari saida nayi shi a lokacin wani ba ni ko karasa shi nake daukar wani,

  Sai da na tabatar ta wuce tundazu sai na sauko da bissimillah tare da naiman tsari ga Allah ,

  Ta gefe gudan nabi ban yarda na bi ta inda nagantaba tsaye,

 Bayi na fada da wayana nakira Salimat na sheda mata abinda nagani,

   Ba,adauki wani lokaci ba ta shigo gidan da shirinta,

  Ita da Amal ne suka dauke wanan jan kyalen suka samo wani jan kyale na rigar Amal irinshi suka aje mata agurin,

    Mamaki duk ya kashe mu, Salimat ce tafara magana daga cikin mu,

  Tace wai may yasa wanan matar batada imanine haka,

   Mundade muna shawara a tsakanin mu so sai,

A ranan ga dare ya raba amma sam babu alamar barci a ido na,

  Duk da nasan cewa sun fitar da mugun abin a dakina 

  Tunane nayi ko may yasa sheriff yin tafiya tun ranan da yadawo batare da yadauki ma aziza wani mataki ba  ,

    Ajiyar zuciya na saukar cikin tausayawa kaina ina tuna nen wanan sabon rayuwa da na tsinci kaina a cikin sa,

    Gaba sai bugawa yakeyi saboda alamar gitawa da naga anayi ta dan hasken da ke hasko min ta jikin window daki na,

   Na rintse idona ina ci gaba da addua acikin raina,

   Saboda na sadakar da raina cewa nawaya kare kawai a wanan ranan,

   Can kuma sai naji shiru nadaina jin motsin komai kuma naga a daina wanan gittawan da ake ta min,

    Duk da nasan cewa na rufe dakina yau da makulli, amma hakan bai hanani jin tsoro ba,

  A haka barci barawo yazo yadan yi awon gaba dani,

   Sai da asuba nafarka cikin dan firgita don ji nayi kamar za a shigo min ,

  Saida na kwanatar da hankalina sannan na gane cewa ai ba komai har yanzu,

    Saida na tabbatar da cewa gari ya waye kuma tabbasa kowa yadan fara fitowa waje 

   Natashi naje nai wanka nafito kenan ina shiri naji alamar ana buga min kofan daki da karfi kamar za,a tsaga shi biyu,

   Na nufi kofan pa gigice nabude a hankali, hannu na guda yana rike da dan towel din da nake tsane jiki na da shi,,

   Ga mamakina Aziza ce tsaye tana ganin na bude daki naga tai wani irin shock na nuna alamar mamaki,

   Kallonta nakeyi sosai babu kaukautawa,na zuba mata ido, nima,

   Ganin da nayi cewa , kallon nata bana girma da arziki bane,

    Kallon tababiya naimata  na kallo ta wani irin shekeke, 

   Na juyawa nayi da zumar in koma cikin dakina,

  Sai naji ta turo kofar ita ma da karfi kamar zata bangaje ni,

   Turus na tsaya gami da rasa na yi hannuna, yana rawa, ina kallon ta don inga abida zatayi,

    Cikin tsayin wani lokaci shiru ya biyo baya sai dai na kula da ita kamar tana kokarin kallona tana na,zarin wani abu,

  Nadai daure da nagaji da kallon kallon da mukeyi na ce mata lafiya dai ko hjy,

    Cikin dakewa ta ce min da akayi may fa,

   Cikin rawar murya nace mata, naga kamar kina bukatar wani abune a nan,

   Ta buga min wata uwar harara ta kuta saida gabana yai mugun faduwa da ga ni irin yadda tai min,,

     Tawani irin juya da karfi kamar mai fada da iska tawuce, 

   Nanta bar ni tsaye da mamakinta,

   Gakuma wani irin tsoro da firgicinta da ya kamani 

   Don nasan cewa a yadda taimin yanzunan zata iya aiwatar da komai akaina,

   Inda tawuce tabarni nan nake tsugune amma tsabar fargaba abinda take shirin yi min yasa ni zarya a corridor

   Ina ta tunanen mai yasa Aziza take farautana haka saboda kawai na auri mijin ta ne ko ko may,

    Da sauri namike na isa inda wayana yake jone a caji na ciro cikin sauri na kira layin ,

  Sheriff tsayin wani lokaci naji shiru, sai can daga bisani naji computer tana gaya min wayar a kashe take,,

   A rude na nemi layin Amal, itama hakan ne ta kashe wayar ta,

   Sai dabaran kiran Salimat yazo min,

  Ina samun ta ta dauka,nan na shiga, fada ma Salimat cewa tazo ba lafiya,

   Hankalina a tashe nake maganar , hakan yasa tace min gata tafe,

  Kafintazo saita bugowa maman Umar waya tasheda mata cewa tazo dakina da sauri ta diba mata halin da nake ciki,

    Maman Umar tasamay ni na dan rakube a bakin gado ina kuka,

   Ban boyewa maman Umar komai ba tun abinda Aziza tai min safiyan jiya,

    Har zuwa cikin dare dakuma yadda mukayi yanzu da ita,

    Salimat tafado dakin a rude nafada mata duk yadda na kwana a dakin da kuma abinda mukayi da ita yanzu

   Saida ta nisa sosai can tace min shawar guda zan baki fadima,

  Tace min ina passport dina nafada mata cewa yana nan,

   Ita ta shirya min duk yadda komai zai kasance gare ni,

   Tasa maman Umar ta kwaso min duk wani abin bukatana adakin dakuma wasu kudi masu yawa da naita boyon su da dadewa,

   Salimat ta kwashe kayan zuwa gidan ta batare da sanin kowa ba,

  Ta yadda ko CCTV  ba za a gane cewa kaya ta dauka ba,

    Duk wani motsin da za a yi a wanan yini a tsorace muke nida su salimat da maman umar don ko ruwan gidan nadaina sha yanzu,

   Azizako sai fita takeyi tana dawo tare da wata yar doguwar takari fara wace tayi bleaching duk ta kode,

   Ranan dole tare muka kwana da maman Umar adaki daya,

   Washegari tun da safe nai shirin zuwa makaranta, saboda kasancewar itace ranan da zan rubuta jerabawar karshe,

    Ina kallon Ummi cikin tausayawa saboda har yanzu jikinta baida wani karfi sosai,

   Amal tana ta jana da hira saidai sama sama naje dan ansa mata,

  Can dai tace min wai may yasamay ni ne yau taga duk bani cikin hayacina sosai,

   Nadan kakaro murmushin dole nace haba Amal yaune fa zan gama exam dina aiko kinga dole in dan damu,

   Dazamu tafi naba maman umar takarda nace taba sheriff idan yadawo kasan ,

   Ina gama exam ko min ti biyu bamu karaba muka dauki shatan taxi nida salimat sai jedda,

    Ina rugumay da Aisha wace mamata ta ce min in wuce da ita duk inda zani tabar min ita,

   Batare da bata lokaci ba akai muna screening duk na  ka gu inga mun shiga jirgi 

   Ina jin anfara kiran yan jirgin mu sai kuma kuma al,amarin ya juye min duk naji ba dadi, a raina, 

   Saboda nasan cewa Ummi bazata ji dadin abinda nayi ba, 

  To amma yaya zanyi dole ne in tserar da rayuwana ,

   Karfe tara na dare jirgin mu yatashi daga jidda zuwa Nigeria,,,,,,


🐎ZEEE MAKAWA🐎[11/5, 5:57 PM] ‪+234 816 741 8349‬: ✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈

           👣👣👣👣👣

           👣👣👣👣👣

                   7⃣6⃣

                     BY

🐎 *ZAINAB*IDRIS *MAKAWA*

🐎 *HUGUMA* *GROUP*🐎   Almost true life story,,,,Jirgi dare ya biyo zuwa saudiya, A, Riyadh ya sauka ,

  Daga Riyadh, shiga mota sai madina,

   A madina safiya tai ma shi,,a cikin gidan mu,,

   Mudai mun tashi munga bako don mun san cewa saura kusan sati guda ko kwana goma yadawo,

    Tsaye nake bakin dressing mirrow dina ina dan gyaran jikina saboda ina son inyi samako zuwa wurin salimat inci abinci,.  Don yau natashi ina jin yunwa sosai,

    A, hankali yaturo kofar dakin cort din shi na sagale a kafadan shi, hanaye shi zube a cikin aljihuwaye shi,. 

   Waigowa nayi don inga kowaye yashigo min daki a lokacin,

  Kafin ma in karasa juyawa hanncina ya isar min da sakon sheriff ne,

Mamakin gani shi na yi a wanan lokacin da safe haka, 

  Don nasan cewa badai ta madina yai landing ba don da Salim ya tafi dauko shi,komai dare

    A hankali yatako har inda nake tsaye yazo ya rugumay ni ta baya, 

   Yana kokarin juyo dani don in yi facing din shi da kyau,

   Cikin yar siririyar murya nace mai sannu da zuwa ya hanya a lokaci guda,

  Dan murshi yayi  dai, dai lokacin da ya man na bakin shi cikin nawa yana fadi a hankali wani zan ansa maki cikin gaisuwar,

   ,Alokacin kuma maman Umar ta turo dakin don ta kawo min abin breat fast,

   Takoma da baya cikin sauri tana fadin muyi hakkuri batasan cewa yana a ciki ba, 

   Asalima dai batasan yadawo ba, daga tafiyan , ganin ta baisa ya sake ni ba niko duk nauyi da kunya ya rufe ni,

   Ta koma da baya baya, tana mai bada hakkuri tajawo kofar dakin,

   A lokacin yakara dan matse ni cikin jikin shi sosai, ya dan sun sunan kamshina yana wani lunshe ido,

  Amma sai na dan jaye jikina dagana nashi a hannkali, cikin hikima

 Sai yadan tsaya tsaye sororo yana kallo na,

  Najuya da niyar indan gusa daga gare shi kadan,

   Sainaji ya riko min hannu na ta yadda bazan iya juya wa ba da kyau,

   Kokari yayi mu hada ido amma sai na kasa saboda gaskiya bazan iya ba don har yanzu mugun nauyi da kun yar sheriff nake ji,

    Murmushi yayi yadan kalleni cikin tausayi yace min,

    Fatima bakiyi murnan dawo wana bane,

  Nadan dago da sauri na kalle shi nace saboda may,

   Sai yaji kawai na bashi tausayi, don ko ba komai yasan cewa ina bukatar kulawa so sai a yanzu, da cikina yafara girma sosai

   Kuma gashi wana yar ballija,un ta zo ta takuramin,

   Sai a lokacin yakare wa dakin da nake ciki kallon a hankali,

   Sai yaji wani mugun tausayina yakara shigarshi,

   A lokaci guda yaji sam bai kyauta min ba ,

   Saiya dan tsaya jin yana dan tunane da nazari,

   Yarasa abinda zaice min sai ya sakar min hannu, a hankali,

  Wanan lokacin ne rana na farko da yaji yaji kunya na da nauyi na sosai, aran shi

   Ada kam baidauki wai don ya aureni zai sa yaji wani abuba akaina, ba

   Sai gashi yar karamar yarinyar da yake ji yake kuma gani kamar bata da wayyo , tana batun wuce wa da lissafin shi,

   Yau yana jin kunyarta da nauyin ta, sosai 

    Don yasan cewa an raina mata hankali da yawa kuma baisa tace zata dauki mataki ba, akai,

    Ko ta kirashi ta fada mai abinda ke faruwa, ko da a waya ne,

    Kenan ta bar mai hukunci a hannun shi, sai yaji wani iri a ranshi yace kada Allah ya kamani da laifin hakkin wanan yariyar fa,,

   Bakin mirrow yasa mu yadan zauna kadan, yana facing di na,

   Cikin son mu hada ido yake har yanzu , duk na gane nufin shi sai naki daga kaina

   Niko  sai kokarin gyara Nafal dina kawai, nakeyi batare da na kalle shi ba,

 Sai lokacin  Yace min fatima lafiya kika dawo wanan dakin da zama,

   Cikin mamaki na dago kaina a hannkali na dan kalle shi don tambayar ta zama ta rainin wayo ko hankali,, nake gani,

   Yakara nanata tambayar sai na dan dago kadan cikin sanyin murya nace mai ba komai,

   Yanayin muryan danayi dole taba mutum tausayi so sai ,,,

   Sai yace to may yasa ki ka dawo nan din kuma,

  Can fa yafi maki nan, don kinga nan ba wani abin da akasa  sosai don jin dadin ki,

   Shiru nayi, saikuma na ga kamar ai baisan cewa Aziza tana gidan ba shiyasa,

   Yake min mugun  tambayar nan, da nake jinta har cikin raina,,,       

  Ji nayi ya kara riko min hannu karo na biyu,

   Yace min ko dakin bai maki bane,,,

  Sai nai rau,rau da ido na kamar mai shirin kuka nace 

  Matar ka fa ke ciki wancan dakin , tayaya zan zauna a ciki tare da ita bayan tace wanan dakin baidace dani ba 

   Saboda dakin kune kaida ita, 

    Asalima ita sam bata yarda da cewa ka aure ni ba don bata da wanan tabbacin,

   Cikin hasala gami da mikewa ya ce may yasa baki kirani kin fada min cewa Aziza tana gari ba don in dawo ,, cikin lokaci,

  Kinsan fa cewa Aziza zata iya maki komai don ba tausayi ke gare ta ba,

    Nace banyi zaton cewa zata iya kai har war haka agarin nan ba don baka nan,

   Shiyasa ban kiraka ba saboda nadauka cewa zata tafine bayan kwana biyu,

   Yaja dogon nun fashi yana kokari cire nicktie din dake a wuyan shi,

   Sai a lokacin nadan  daga kai na kalleshi nace mai, ai ba komai tunda ita bakuwa ce idan ta gama abinda takeyi, tafiya zatayi,

  Wanan kalami da nayi yafi komai nauyi a tare da shi,har wani dan gumi ya ke keto masa ya rasa abinda zai ce min,

  Yai dan tagumi ya kura min ido yana nazarin wasu abubuwa, da ga zuciya na

   A hankali na ce mai don Allah kayi hakkuri, ina son in karasa shiryawa don zan fita school ne,,

   Sheriff yace haba Fatima wanan hakkurin da kike bani yana kara min kunya da nauyin ki, 

  Ki daina bani hakkuri dan Allah,ke ce yadace in baiwa hakkuri da zalluntar da Aziza tai maki,

  Ke da dakin ki da komai na sirin ki a ciki tasa kikafita kikabar mata daki 

  Kikadawo nan ki zauna saikace wata bakuwa ko wace batada iko da gidan ta,

   Wanan gidan naki ne don ki na saya don farin cikin ki da na yan uwana,

   Ita na ta gidan na Dubai da Abuja don tace bata iya zama a saudiya saboda zafi da kuma yanayin garin da bai mataba,

   Niko kinga zamana anan yake saboda anan Allah ya tsagamin arzikina,

  Kinga ko dole in gyarawa iyalina inda zamu zauna cikin don rayuwa tare da yan uwana,

   Dan murmushi nayi mai,irin mai, nuna alamar bakin ciki azuciyar mutum,

   Nace bam cancanci kabani hakkuri ba sheriff saboda ko da can nasan wanan rayuwar zai biyo baya daga matan ka,

   Babu wacce ban san abinda zata iya ba da wanda baza suyi ba,

   Don haka don nadawo nan ai ba wani abu bane saboda duk cikin gida gudane kuma dan bambancin dakin kadan ne kawai,

  Saboda haka duk wani cin fuska da aziza ko nafisat za suyi min zan hakkura dashi matsayin ba rayuwata ko lafiyata zasu yi kokarin tabawa ba,

   Da sauri ya rufe min baki yana fadin ki daina fadin haka Fatima ,

  Ya dade rugumay da ni a jikin shi yana dan shafa min baya kamar wacce tai kuka ake lalashi,ta,,

   Sai kuma ya sake ni da sauri naga ya wurga da tie din shi saman gado, yafita waje da sauri,

  Ina ganin fitar shi nai sauri na suri yar jakata na fita cikin sauri nabar gidan,


   A kwance take abinta saman gado tayi wani shamay shamay da ita tana ta kwasan barcin ta a hankalin,ta kwance,

    Daskarewa yayi wuri guda yana mata kallon takaici da tsana,

  Mace kamarta ace,bata ina kwanciyan cikin kimtsi ba, ko na tsuwa, 

  Wanan ai sha shan ci ne,

   Kwace take tana saye da yar doguwar, riga, kusan duk rabin cinyarta a waje yake, tim,,

  Saida ya gyara tsayi   yadan lalubo natsuwar shi saboda takaici da haushin ta da yake ji,a lokacin,

   Gurin gado ya nufa rai a bace, don yasan cewa ko sallah batayi ba a lokacin,

   Labule dakin yadan daga sai hasken rana yadan baiyana,

   Dan bubuga mata kafa yayi tai wani irin mika, tadan bude ido da niyar yiwa mai shi masifa,

  Sai sukayi ido biyu da sheriff, dake tsaye fuska tamau, a gaban ta,

   Harara ya dankara mata yace mata kinyi sallama dai kuwa,

  Takara yin mika tace yanzu nake batun tashi in yi fa,

   Yakara tsayawa saitin kanta yace may kike yi a dakin Fatima kuma,, cikin wani irin dakiya  yai mata magana,,

  Ban fahince kaba Ahmad ,

  A ina kake son in sauka dama 

   Cikin mamaki yace mata duk gidan nan ba wani daki ne sai wanan da Fatima take aciki,

    Daga kwance tai wani gyara kwanciyar ta tace ina, wanan shine dakin ka,

  Kuma aciki na sauka,

   Shout up my friend, baki da ko kunya da zaki fadi wanan maganar,

 Itama dai wani mikewa tayi zaune, tace,

   Ta dankara mai wata muguwar harara, tace ban fahici hausar ka ba ada amma yanzu nagane nufin ka sosai 

  To bari kaji, niba wulakantancciya ba ce, balle ka wulakantani ka kaini masaukin baki kace in sauka a ciki,

   Ya buga mata tsawa da bai taba mata irin shi ba sai yau yace, 

  Ke dan Allah ki yi min shiru, in ba haka ba, yanzu ki san ko waye Ahmad,

   Tayi murmushi ta mike tsaye daga zaunen da take, 

  Tazo gaban shi, gab da shi ta tsaye da kyau a gaban shi tace , au tau, 

  Ashe da ban san kowaye Ahmad ba zaune nake da kai kawai,

   Tayi wani irin murmushi mai nuna takaici,

  Ai,Saika gwada min ko kai waye yau in gani tunda na shiga dakin yar kwailar matarka saboda ita saika dake ni ko,,,

  Tana wani jijiga jiki da kafa,

   Kafini sanin ko wacece Aziza,kuma kasan kadan daga cikin aiki  iskancina ya damay naku ya shanye,

   Ahmad ni bani kwadayin dukiyar ka kai kawai nake so,

  Wani malalacin kallo yai mata a lokacin da tace ita bata da mu da dukiyan shi,

   Batasan cewa CCTV ya tona mata asiri ba ko,

   Taci gaba da fadin akan wanan yar kwailar baka isa ka wulakantani ba,don kaga ina sonka har za kai min wulakanci a kan wata,mace,

   Yau ran yan maza ya baci so sai, gashi ba halin shi bane bugun mace ko zagi,

    Kafin yadauki wani mataki maman Umar tashigo daki don dafa mata ruwan zafi 

   Ganin da tayi Aziza natawa sheriff masifa kamar zata dake shi, ta juyo zuwa gurin su da sauri 

  Kafin tai magana sai ya juya yabar dakin rai a bace,

   Dakin da nake  yakoma yana shiga ya iske har na wuce ko,

   Ya samuri ya dade a tsaye yadan dafa bango, ya na ta tunane,

   Idanu shi sun juye sun yi ja jarir tunda yake baitaba tozarta irin yau ba,

  Wai matar da yake aure ce hakana kamar zata dake shi,

   Inda ace shi mai dukar mace ce bugu daya zaimata sai an zuba mata ruwa,,,

    Itako Aziza yana fita dakin  idon ta yakade, yai jawur, ta dinga tuna ko ita wace da har za,ai mata wulakanci akan fadima,

    May fadima ke nufi da itane a rayuwa yadda take son Ahmàd ace yau, shida kan shi har zai mata wulakanci akan yar aikin matar shi,

   Wasu hawaye suka zubu mata na bakin ciki ta fada saman kado ta shiga rusa wani irin kuka,

  Saida ta gaji ta mike don kanta, tace fadima sai na ga bayan ki kafin in bar kasan nan,

   Gobe bazaki kara tsaya min agaba ba,,,

  

   Gidane ginan laka irin na kauye duk da gidan tsohon gidane bazaka gane ba saboda sabon yaben da akaiwa gina ga sabon jinka asa asaman rufin dakin ya koma kamar sabo,

   Ta kofar dakin ayin mai sabon shafe irin na kauye laka laka,siminti ,siminti,

   Darni gidan na subur karan dawa ne akayi amfani da shi,

   Ga icen zogala da na durumi  an zagaye darnin gidan da su gefe tulun na ruwa ne da babban randar ruwa suma sabbi fil da su,

   Daga can gefe han yar zuwa yauce (makewayi) turke ne na raguna manya manya sai wani fasashe rada inda ake zuba ma dabbobin abinci,,

   Ga kaji nan sunkai goma irin na gargajiya suna ta kiwo atsakar gidan,

   Tafito dakin da tana gyara daurin zanin ta da ke kokarin banyewa irin daurin zanin yan kauye da ake tankwahewa gefe guda,

  Hannu guda na dauke wani dan karamin kwarya,

   Cikin kwaryan gumba ne wanda zata dama kunu dashi don karin kumallin su na safe,

   Inna yar Kulu ke nan mahaifiyar Fadima,da ke zaune a garin dogon daji mai rijiyar biri,zam,zam dake acikin jahar sokoto,

   Duk da mutanen kauyen nawa inna yar kulu kallo wata wacce ta ke cikin wani irin daula ,

   Ga kiwon tumakai da akuyoyi da takeyi, ga kuma shanu har biyu da ta turke gefe guda,

   Duk cikin kudin da Ruggaiya ta kawo masu ne, duk da inna taki karban kudin duka a hannunta,

   Bakin murhu ta zauna tana dan gyara iccen da ke kama da kara sai tarin hayaki da ya bude gidan dashi wanda har makwabta a na iya hagen shi,

  Alamar cewa ke nan ta hura wuta a gidan ta kasan cewa bakowani gida ake dama kunu ko yin wani abin kari ba,da safe,

  Saidai fura da za,a aje a cikin wata r langa ko kwarya ko fanteka, 

  Wanda aka dama tun jiya ko kuma an kirba shi tunjiya, yayi tsami har yagaji, 

   Shiza asama ruwa a motsa kowa yazo yadinga diba, a yar korya ko roba ana sha,kamar yadda kowa yasan kowani kauyen hausa sukeyi,

   Abinci sai ranan jumma,a ake dan yin tuwon shikafa ko na dawa, yara su dinga murna suna fadawa junan su cewa yau jumma,a 

   Kowani gida za,ai girki tuwo da miyar yakuwa da alaihu, da kabewa,

   Wasu kuma tuwon kullun dawa da miyar danyar kubewa ,,ko kuka, fara fat da ita,

   Hakan yasa suke ganin cewa inna ita tanajin dadin ta sosai don tun filazan ita gidanta tana dafawa yaranta abinci ko ba dadi sai sunyi shi sau ukun nan,,,

   Gidan inna ko yaushe tsab yake da shara, duk da kiwon da takeyi bai hanna ka gane cewa tayi shara, a rana,

  Saida ta gama dama kunun ta sa ma mariya kira wacce ke daki tana shirin zuwa makaranta boko ita da dan autar inna Abdul wanda suke cewa datti,

   Mariya tafi cikin kayan makarantan ta tazo inda inna ke dan motsa mata koko a cikin wata yar roba mai fadi,

   Inna tace mata ta koma daki ta dauko sukari a cikin leda wanda suka siyo jiya ya rage,

   Alokacin Datti ya shigo gida da yar leda baka a hanun shi wanda ya sayo kosai da shi,

   Ya mika wa inna laidar tadan jawo wani dan plate din silver ta kasa masu kosan kashi uku ,kowa guda guda,

   Saida Datti ya fara shan kokon ne yace inna ai na manta ban hwda maki ba,

  Kai wai wani irin yarona haka duk sanda kattaho cin abinci sai kayi dumi, (magana)

  Waga dabiar banzata koda yaushe ina hwda maka, 

   Ko ni,an inna ki kasani ko wani sabon batu na yyajiya shina shika son shi,hwda muna,

  Ke,ke ke banison shegantaka kejiya,

    Mariya dake gefe takalli Abdul tace tadan tausa murya don kada inna taji su tace, 

   Shin minana kaka son cewa Adullahi,

  Ke ko ni an bashi tun da wanda abin yya shahwa tace in bari to ni mi nika hwdi kuma,

  Inna dake jin su ta waigo takawai mariya rankwashe akai tace 

   Kai waga diya anyi yariyar kawai, 

   Shin kuna sauri kutaizuwa makarantaga ko ko sai kun yi abinda mallam yattabi jikin ku,

   Abdull daya tashi yana sa takalmin shi na roba na makaranta saida yakai kusan fita bakin gida ya waigo inda inna ke tsaye ta sance kullin kudin da tayi a gefen zanin ta,wanda zata mariya kudin kashi, haka yara ke kiran irin wanan kudin safen da uwaye ke basu dan sayen dan wani abu,

  Ya waigo cikin dan daga murya don inna taji maganan,

  Yace mariya ke,

 Macen nata wadda akacewa ta sace fadima ita ta naggani jiya ana taratara da inta anka hiddo ta cikin mota wai bata da lahiya ,

  Tasamu mutuwar jiki,na shina za,ashiga da ita cikin gidan su dan isah yyacce wallahi tallahi shikam sam bagidane  ba tunda yawon dandi ttahito ,

  Wassani ko mugunyar ciwona, takkwaso ta taho ta watsa musu duk su mace har ita,

   Inna da mariya da ke tsaye suna sauraron shi duk sun maida hankali gare shi,

  Cikin karaji inna yar kullu tace , shin wata macce na kaka nuhi,

  Badai Gajiye ba ta gidan su Dan isah 

   Ya awo ita ta mana naka nuhi,

  Ko yanzu da natai z duduwa mai kosai maganan na nijjiya suna yi ita da tunba,

  Salati inna yar kulu tasa sai da duk yaran suka kallo inda take tana ta rafka salati,

  Shinka wa hwda maka wagga mugunyar magana,

 Nihw da ijjiyana naggani inda muka warigi dadare nan na motat tatsaya aka tambaye mu gidan su dan isah,

   To, to to kutai zuwa inda zakuna dawagga bakar labari dakkatare mu da shi tunda wagga farar sahiyan,

  Bayan hita yaran sai duk maganar da Abdull yafadi ya dami inna acikin zuciyar ta duk sai taji bata da sukuni, 

   Tana gama duk wani dan aiki dake gabanta tashiga daki tadauko hijabin ta tasa tasa ma kofar dakinta kwado padlock,,, kamar yadda takeyi idan zata fita  ,,

   Gidan su yar Ammo mai masa tafara shiga don jin ko maganar gaskiya na ttajiya,

  Aiko tana shiga, cikin gidan su yar Ammo ko gaisauwa bata barin sunyi tace 

  Tace aho yar kulu, agaishiki,

  Inata ingwaiya,

 Kun kwan lahiya,

  Kedai wagga an ko gaisuwa ban bari munkayi ba,

  Shin nicce ko ke jiya 

Minana, inji ina,

  Batunga da anka hwdi mana Ganiye ta tazaka naniyagga da cutar kabari kusa, 

  Ke ga dadi yayi kai ke nan,

  Ta ballo goro da tadauko daga cikin radan ruwan ta ta balla ta miko wa inna dan guntun balli,

  Inna ta ce a,a ha, aini yanzu sam banicin gora, wadda nicci shi hakana zaita wahalsam,

  Shina, sa, dai nibari kedai,

To yanzu a,a ankaciki da ita shi,

 Kedai bari yar kulu am,

Ance saida maigari yakkiranwo dan isa da kainai yamai hwada 

  Yanzudai can dakin da suka aje tumakainai da can na yaggyara mata,

  Jin haka sai tausayin Gajiye ya kama inna tun bata ganta ba,

 Ita da su Yar Ammo suka tahi gaida Gajiye inda suka hadu da wasu mata, yan gulma sunyo turuwa sun gano gajiye zasu fito daga cikin gidan,

  Suna gani inna sai suka kama magana cimin tausayi 

  Allah sarki ke gani ba dakanta ttataho gaisheta,

  In, nita wallai banzuwa gaida wagga bakan mace 

   Wadda taimin sanadin batan "yata ta salwanta cikin duniya,

  Sherin tana kacin ta,

Inna dai tabi ta gefen su ta raba ta wuce batare da ta tsaya sunyi wani dogon gaisuwa ba,

   Cikin gidan kuma suka iske wasu tsatsaye gefe ana ta maida fadi,

  A ho yar kulu inji wata bakar mata yar likutitiya da ita,

  Kema ketaho nan niya inda Gajiye kiga wadda Allah yai maisheta,

  Jin yar kulun da Gajiye tayi an ambata daga cikin dakin da take kwance cikin ban tausayi, yasa ta dan yin yunkurin dagowa da sauri,

   Nan take mata suka sa ihu suna shirin watsewa da gudu, don tsoro ,,

  Inna ce tai karfin halin shiga don ta leka taga Gajiye saita ganta kwance cikin, kazanta duk ta bata jikin ta, salati ina tayi tadibi wanan matar tace mata,

   Habadai inno a,a kuka barin maralahiya cikin wanga kazanta haka,

 Ke yar kulu waka zuwa kusa da ita yakwaso wakainai cutar zamani,,

   Cikin karfin hali innata ce abata baho ,

  Inno ta ce a,a walla wakabada baho nai a halaka mai,

   Dan haka inna ta koma gida dasauri ta dauko bahon ta sabo da hafsi ta aiko mata, dashi lokacin da ta haihu ba goyo,

  Wanka inna tai mata ta gyara dakin tas tasa turaren wuta na tsuke sai dakin yadan canza kamshi,

  Saida ta gama mata komai saita bata dan sauran kunun da suka sha dazu ita da yara,

   Hakan da inna taiwa Gajiye sai kawai ta kama zubda hawaye tana cewa inna ta yafe mata dan Allah, 

  Dan tasan cewa ta cuce su ita da diyarta,

   Dan isah ne ya shigo gida cikin sauri lokacin da yan gulma suka fada mai cewa inna taiwa Gajiye wanka,

  Can yadan tsaya ta kofa ya ce ,

  Shim ina yar kulu inata ce gani nan ,

  Yace mikkai ki wanga kasada, innatace tamay fa dan isah,

  Wankafa ankace kin mawagga muguyar bakuwa da tazzaka da cutan zamani,

   Ganiye na kuka tana fadin ita ba cutan zamani ke jikinta ba,

   Hawan jini ne yakamata,

 Yace kaji yan nema bakar mugguya, aniyar ki ta biki,

  Lokacin da kike, Gajiyen ki wakika kulawa cikin mu,

   Yanzu da ciwi yakam maki shinakin kasan kina da yan uwa nananga ko,

   Innata ko ni am dan isa karaga mata ko taji dan dama dama,

  Shin dawane zataji,wagga tsiyaye dakaka mata ai shizaisa takara kawai kwance,

     

     Hakana inna tadauki dauniyar Gajiye har abincin ta,

  Anna cikin haka watarana Allah yakawo Ruggaiya taxo ganin inna ita da mijinta suka zo ma inna da kayan masarufi kamar yadda takeyi bayan duk wata uku uku saitazo ganinsu takawo masu kayan amfani ,

  Inna ta ba Ruggaiya labarin gajiye sai Ruggaiya tace kai inna kusan dai duk halinki ashe fadima ta kwasa ke nan,

   Inna tace to maye duniya ai mutum bai wuce gaddaranshi,

  Allah ya nufi Gajiye ce sanadiyar rabani da yar diyata

   Amma ko kusa ban rike taba don nasan cewa komai mukaddarine,

 Rugaiyya ta taimaka ita da mijin ta don akai Gajiye asibitin sokoto dan agane ko may matsalar ta,🐎ZEEE MAKAWA🐎

[11/5, 5:58 PM] ‪+234 816 741 8349‬: ✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈

            👣👣👣👣👣

             👣👣👣👣👣

                      7⃣7⃣

                        B Y   

🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎

🐎HUGUMA GROUP🐎   Almost true life story,,,


 Assalamu Alaikum yan uwa musulumai,

   Dan Allah a tsakanin marubuta da makaranta yakamata asamu kyakyawan facin ta,

  Bawai challenge's ya shigo ciki ba, idan har marubuci tayi wani abin da yadan kauce wa addini ko tarbiyan mu yakamata akirata in prevent aimata gyara ,

   Babu wanda yawuce gyara aduniya, tundai na fannin addin mu,

  Yima marubuci cin fuska a bainin jama,a baida amfani wlh,

  Wanan rubutun da kuja ga munayi abune mukaddari daga Allah, akwai masu so soyi amma Allah bai basu ikon yi ba,

  Bakaramin wahala ke cikin rubutun novel ba yan uwa,

  Yakamata duk yadda marubuciya tai novel din ta a gode mata, indan har da gyara akira mutun a gefe not in public aimai gyara,

  Pls mukuma marubutan Allah yakara bamu hakkuri a tsakanin mu mukara daurewa da makarantar , duk abinda kayi ba aima korafi akai ba, wanan abin baida ma,ana ne ,,,,,

   Idan nafadi ba daidai ba ina mai rokon gafaran ku yan uwana,👏👏👏👏
    


 Kitchen din shiru yake babu kowa acikin shi sakamakon kashe na,urar da zata sada ma kitchen din da ruwa,

   Hakan yasa ma,aikatan fita waje don ganin ko may ye matsallar ,

   Maman Umar abin ya bata mamaki kasancewa ko a daren jiya itace tayi aikin karshe a kitchen din kuma ruwan yana zuwa normal,

   A hankali ta fito daga dakinta tana tafiya cikin sanda har ta shiga kitchen din,

  Saida ta leka ta tabbatar da ba kowa a waje lokacin ta ciro wani dan koya daga cikin gefen breast din ta ta jefa a cikin flower sinasir da maman Umar ta kwaba ,

   Tafito da sauri tana dan waige waige, bayanta,

  Tana shiga dakin ta tashige bayi ta wanke hannuwan ta tsab, takoma saman godon ta kamar wacce bata tashi daga barci ba,

   Bayan angyara matsalar ruwan maman Umar ta dawo taci gaba da aikin ta,

 Tanagamawa ta jera komai a carpet saura kuma masu ci a table aka kai masu nasu, saman tebur,,

   Saida kowa kusan ya hallara a falon wurin karin kumallon safe,

   Kusan nice ta karshen zama a falon saidai ba a saman kujera na nufa ba,

  Wurin Ummi na nufa don a saman carpet, take zama ,

   A hankali na dan durkusa gami da kara gaida Ummi karo na biyu,

   Saida na sawa plate dina komai da nake sha,awa, nadan tsiyaya ruwan sha, a cup na aje a gefe na,

    Nai bissimillah nadauka zankai wa bakina,

   Aziza dake zaune daga gefen mu ta kura min ido, Allah Allah take yi in kai a bakina,

  Daidai lokacin da zan kai a bakina sai wayana dake gefe yadauki ruri 

  Mayar da sanasir din nayi cikin plate na, nai saurin daukar wayan , diba massage din,

   Ganin nobar Amal, da nayi yasa ni saurin ta shi kusa da Ummi , 

   Kada kici abincin nan fadima ,

   Kuma in kin karanta kada ki dago kai ki debe ni pls,

    Gashi dai nagama karantawa amma sai na kasa daga kaina sama, 

   Wani irin mugun tsoro ne yakamani saboda nasan cewa Amal bata maganan banza 

   Maimaikon in juya sai na mike kawai daga, gurin da niyar tashi ,

   Muryan Ummi ce na ji tace min fadima da wo mana kici abincin cikin sanyin murya nake ce mata,

   Ummi zan dauko ma salimat takarda ne a daki, yanzu zan dawo, sai kuma wani dabara yafado min nace ma ummi bari ma dai intafi da abincin daki na kawai sai inci a can,

  Wani wawan ajiyar zuciya Aziza tayi,jinda tayi cewa zantafi dakina in ci,

   Mutun biyu ne Allah yanufa suci sanasir din, dayake suna da rabon wahala,,

  Da Salim sai Ummi duk yadda Amal taso ta hana Ummu ci acikin hikima hakan baiyi, ba,

  Ciwon ciki ne mai karfi ya turnike su sai ,

  Tun ana abu wasa wasa har takai ga anyi rushing din su asibiti,

   Nan likita yai masu dan bayani akan cewa akwai abinda sukaci Allah nai yatai make su sun kawo su asibiti da wuri,

  Yace amma inda mace mai cikine taci gaskiya da abin yafi nan worse,

   Jin hakan yasa hankali kowa tashi kowa da abinda yake tunane acikin zuciyar shi gamay da abinda likita yace,

  Kwanan su biyu , a asibitin aka sallamo su zuwa gida,

  Har a lokacin Amal batace min komai gamay da text din da tayo min ba,

   Hakan dai danaga irin wahalar da su ummi suka sha yasani shan jinin jiki na sosai,

  Sai yakasan ce duk gidan hankali na a tashe yake so sai,

  Gurin Salimat na tafi da kukana nafada mata duk yadda mu kayi da Amal,

  Itama dai shawara tabani sosai akan yadda zan zauna da kowa agidan 

  Tace min akwai abinda Amal take zargi a gamay da ni,

  Hakan yasa tunda ga wanan ranan Salimat ce ke kawo min abinci a boye ko kuma intafi gidan ta ince a can,

   Yau bazan tafi school ba don haka na koma nadan kwanta don in huta,

   A can cikin barci na rika jin kamar ana tabani sama sama,

   Sai kuma na dinga jin kamar ana kiran suna na a hankali,

   Cikin karfin hali na bude idanu na a hankali, tayadda ba kowa zai iya gane cewa na bude ido na ba,

 Aziza ce tsaye da wani abu kamar jan kyale a hannun ta,

   Can kasan gadona naga ta duka ta aje kyalen a hankali kuma ta taso ,

   Ta kama hanyar kofar dakin fita zuwa waje,

  Ido kawai nabita dashi a hankali har ta kure min 

   Bakina duk adduan da na sani na tsari saida nayi shi a lokacin wani ba ni ko karasa shi nake daukar wani,

  Sai da na tabatar ta wuce tundazu sai na sauko da bissimillah tare da naiman tsari ga Allah ,

  Ta gefe gudan nabi ban yarda na bi ta inda nagantaba tsaye,

 Bayi na fada da wayana nakira Salimat na sheda mata abinda nagani,

   Ba,adauki wani lokaci ba ta shigo gidan da shirinta,

  Ita da Amal ne suka dauke wanan jan kyalen suka samo wani jan kyale na rigar Amal irinshi suka aje mata agurin,

    Mamaki duk ya kashe mu, Salimat ce tafara magana daga cikin mu,

  Tace wai may yasa wanan matar batada imanine haka,

   Mundade muna shawara a tsakanin mu so sai,

A ranan ga dare ya raba amma sam babu alamar barci a ido na,

  Duk da nasan cewa sun fitar da mugun abin a dakina 

  Tunane nayi ko may yasa sheriff yin tafiya tun ranan da yadawo batare da yadauki ma aziza wani mataki ba  ,

    Ajiyar zuciya na saukar cikin tausayawa kaina ina tuna nen wanan sabon rayuwa da na tsinci kaina a cikin sa,

    Gaba sai bugawa yakeyi saboda alamar gitawa da naga anayi ta dan hasken da ke hasko min ta jikin window daki na,

   Na rintse idona ina ci gaba da addua acikin raina,

   Saboda na sadakar da raina cewa nawaya kare kawai a wanan ranan,

   Can kuma sai naji shiru nadaina jin motsin komai kuma naga a daina wanan gittawan da ake ta min,

    Duk da nasan cewa na rufe dakina yau da makulli, amma hakan bai hanani jin tsoro ba,

  A haka barci barawo yazo yadan yi awon gaba dani,

   Sai da asuba nafarka cikin dan firgita don ji nayi kamar za a shigo min ,

  Saida na kwanatar da hankalina sannan na gane cewa ai ba komai har yanzu,

    Saida na tabbatar da cewa gari ya waye kuma tabbasa kowa yadan fara fitowa waje 

   Natashi naje nai wanka nafito kenan ina shiri naji alamar ana buga min kofan daki da karfi kamar za,a tsaga shi biyu,

   Na nufi kofan pa gigice nabude a hankali, hannu na guda yana rike da dan towel din da nake tsane jiki na da shi,,

   Ga mamakina Aziza ce tsaye tana ganin na bude daki naga tai wani irin shock na nuna alamar mamaki,

   Kallonta nakeyi sosai babu kaukautawa,na zuba mata ido, nima,

   Ganin da nayi cewa , kallon nata bana girma da arziki bane,

    Kallon tababiya naimata  na kallo ta wani irin shekeke, 

   Na juyawa nayi da zumar in koma cikin dakina,

  Sai naji ta turo kofar ita ma da karfi kamar zata bangaje ni,

   Turus na tsaya gami da rasa na yi hannuna, yana rawa, ina kallon ta don inga abida zatayi,

    Cikin tsayin wani lokaci shiru ya biyo baya sai dai na kula da ita kamar tana kokarin kallona tana na,zarin wani abu,

  Nadai daure da nagaji da kallon kallon da mukeyi na ce mata lafiya dai ko hjy,

    Cikin dakewa ta ce min da akayi may fa,

   Cikin rawar murya nace mata, naga kamar kina bukatar wani abune a nan,

   Ta buga min wata uwar harara ta kuta saida gabana yai mugun faduwa da ga ni irin yadda tai min,,

     Tawani irin juya da karfi kamar mai fada da iska tawuce, 

   Nanta bar ni tsaye da mamakint